Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Jeji Girl Book Two Complete Hausa Novels 1,256 words 0 views Progress saved
Download Book

Abba zamu gaya masa cewar Hafees kana suka mik'e sukabar parlor. Suna fita ummi ma Takoma bedroom d'inta tareda Kiran momma tashaida mata wannan abun Dake faruwa ga mmikinta setaji momma tayi murmushi tace rabbi yakaisu lpy yamardasu lpy Kuma yasa yarinyar tana Raye....cikin mutuwar jiki ummi tace kema kinyadda datafiyar anty Khadija? Murmushi momma tayi tace na yarda mana mize hana Aida yagayamun tin lokacinda suka dawo da washe gari Doli sukoma suzoda,ita domin Banga anfani dawowa subarotaba tin lokacin tinda har sunsan Bata tareda kowa se Allah awurin ai d'a duk d'a ne fateemah naji inaso sutemaki wannan yarinyar har cikin raina kema ki kwantarda hankalinki insha allah ba,adunda ze faru se alkhairi...allah yasa Hakan cewar ummi kana sukayi sallama....fitowa momma tayi parlor inda tabarsu Safah itada zeelha sunacin k'wadon zugale tace ke zeelha zonan na tsefe Miki Kannan tinda anyi k'unshi tin shekaran jiya Amma ankasayin kitso...Baki tatura gaba tana fad'ar momma da zafifa allah ni banasan kitso..aiko se anmiki cewar Marwa Dake fitowa daga kitchen...harararta momma tayi kana takama hannun zeelha suka wuce bedroom d'inta. Wacece zeelha da fadeel? Y'ay'an abokin Abba ne Kuma ammyn su itama kawar ummi ce Hakan yasa suka taso amatsayin abokai tsakanin fadeel dasu IRFAAN Kuma zeelha tana zuwa gidan kowa takeso acikinsu batada shamaki domin abotarsu Takoma kamar zumunta...sa,annan zeelha itace wadda Hafees kesan aura dudda k'ananun shekarunta domin ayanzu take 14 yeas...itako Marwa itace fadeel keso domin itakam babbar budurwace itada Safah tinda sunada 23y Kuma Safah itace wadda yaya Mahmoud ze aura...Kuma Muneer ma abokinsu Shima tinna yarinta tinda tare sukayi school dashi dukkansu Hakan yasa suka kasance su hud'u sa,annin juna Kuma abokai IRFAAN,,,HAFEES,,MUNEER,,,FADEEL...wannan kenan kunji alak'arsu da juna. Sukuwa suna jita suka wuce gidansu fadeel acan suka sheda mishi abunda ke daruwa..ko gama fad'a Hafees beyiba yace wlh dashi za,aje domin duk Wanda wannan yarinyar Tatemaka baranshine domin Badan da itaba dayanzu baya duniya,,Yana gama fad'ar Hakan yasamu ammy shi yaga yamata aiko Bata hanashiba Sema fatan alkhairi datayimusu....basubar gidanba seda sukaci abunci fadeel yahad'a komai nashi daze buk'ata kana sukayiwa ammy sallama sukabar gidan domin gobe samako sukesanyi....suna fita sukawuce gidansu Muneer Amma kamshi sunsha fama Dan seda yaga ransu yab'ace sosai kana ya,aminta zashi Amma daga farko cewa yayi idan anganshi lahira to kaishi akayi..ahakadai suka Sak'o k'yeyarshi gaba bayan sunyi sallama da momyn shi tayi musu addu,a sosai kana suka nufo gidan momma..koda sukaje ya Mahmoud nagidan Kuma duk Abba yayi mishi bayanin abunda za,ayi Hakan yasa Shima yakura amininshi Naseer domin yasamu abokin tafiya acewarshi bazebi tawagar k'anenshiba shikad'aine babba acikinsu. Washe gari dasafe sukashirya tsab domin tafiyar Sam Basu bari y'ammatan gidan sunsan zasu tafiba gudun karsu b'ata musu lokaci da kike kokensu...momma kawai se Abba sukasanda tafiyarsu suka rakosu harbakin motocinda suka shiga tareda yimusu addu,ar fatan nasara bayan ummi tacika musu manyan warmers da breakfast domin basuci komaiba suka fita.. Airport suka nufa suna zuwa girginsu yatashi zuwa garin Lagos acan kuwa suna sauka Dama un reddy anrigada ansanda tafiyarsu a hidikwatarsu IRFAAN din Hakan yasa suka samu jirgin ruwan 🚒 dazasu hau ashirye tareda rakiyar wasu manyan sojoji abokanan su IRFAAN d'in su 5 sukuma gasu su 6 se suka Koma su 11 kenan ahakan jikinsu yacilla aguje acikin ruwan be tsaya dasu ko inaba sebakin inda ya,ajiyesu aranar Dede wurinda suka shiga wannan surmuk'un jejin... dukkansu saukowa sukayi suna k'arewa wannan sunk'uru kallo musamman su ya Mahmoud dabasu tab'a shogowaba..bayan duk sund'auki abin buk'atarsune suka nausa cikin jejin wasu cikin tsoro da fargaba wasu kuwa zuciyarsu abushe irinsu oga IRFAAN kenan..semuce afito lpy Allah yabada sa,a...! Free page yak'are Tofa πŸ€” chakwakiyafa yanzu akasoma shin koya zata kaya tsakanin su IRFAAN da way'annan miyagun dabbobin ahanyarsu tazuwaga wannan yarinyar? Shinko tana Raye ko kuwa ya hannunta ya,isala bayan tafiyarsu? Shin zata yadda tabisu kokuwa bazata yadda ba? To Kuma idanma ta yadda tabisu way'annan sarakunan dawa zasu aminta afitafa ita cikin wannan jejin salon alonne bayan saboda sukayida ita natsawon wannan shekarun? Kokuwa bazasu bariba? Yaya wannan tafiyar zata kasance dasu? Duk kubiyo alk'alamin Autar alheri ✍️ domin Jin amsoshin wannan tambayoyin cikin JEJI GIRL part 2 insha allah. Free page k'are semun had'u a JEJI GIRL part 2 insha allah ga duk mebuk'atar wannan book nera 500 ne kacal πŸ‘Œ ze iya tura kud'inshi a wannan account d'in πŸ‘‰ 2276776261 Sha,awanatu kasim UBA bank....kana kitura shedar biyanki awannan nomber πŸ‘‰ 07037092176 on WhatsApp πŸ™ Dan girman allah karki karanta novel batareda kinbiyaba ko kifitarmun da abuna batareda kinsan wahalar danayi wurinyin abunaba idan Kuma kiyi to keda alla🀷domin duk Wanda yayi nagari Dan Kansa...allah Yana yafe laifi na tsakaninka dashi Amma baya yafe hakkin Wani yakamata kusan wannan. Autar alheri ✍️ 🌳🌴🌳 *JEJI GIRL*🌳🌴🌳 (Yarinyar jeji renon namun dawa πŸ‘±β€β™€οΈπŸ¦£πŸ¦πŸ†πŸ¦‘) *Labari meban Al ajabi da birgewa(romantic love and sexy story)* Paid Page 19 & 20 ____βœ…___&&&&&&&&&&&& "Tafiya sukeyi sosai acikin jeji suna nausawa surk'k'i da tsaunuka...sudaisu Dr Mahmoud beyi kawai suke dasu suna mmkin wannan mugun jejin dasuka shigo Kuma har suka rayu...tafiya sukayi menisan zango Amma sunkasa Gane ainane wannan yarinyar take gabaki d'aya sun jigata domin har dare yafari Amma Basu Gano komaiba domin duk hanyar dasukabi suna tinanin zatakaisu b'angaren tekunda take sesuga abun ba hakabane sun bullo Wani lungun,,,abunda yafara tsoratarda Muneer dasu Dr Mahmoud kenan. Wani lungun suka shiga me duhun gaske Wanda basa iya Ganin ko tafin hannunsu..cikin Dan daga murya ya Mahmoud yace "wai IRFAAN inane kukesan kaimu cikin wannan daular mutuwar? Kamin IRFAAN yabashi amsa dasauri fadeel yace ya Muhammad wlh imagana ahankali karka kira mana ruwa domin aka,id'ar wannan jejin inaga ba,a magana dak'arfi...kamarya ba,a magan...k'asa k'arasa fad'ar abunda yayi niyya yayi sabida motsin takon tafiya dayaji dawurin dulun baka Ganin komai ba,abun sukunna toch d'in wayarsuba yazan mazauna wurin basasan haske...gabaki d'aya tsit sukayi suna saurarar wannan takon domin kowacce dabbar ce keyinshi to tabbas k'ak'k'arfa ce,,,gabaki d'aya sunyi jugun suna jiran abunda ze biyo baya Su maneer kuwa inbanda rawar d'ari Babu abunda yakeyi shida Dr Naseer abokin ya Mahmoud gabaki d'aya sunshiga demuwa wannan shi akekira adakeka ahanaka kuka ga duhu garashin magana gakuma rashin sanin inda zasu nufa... innalillahi wa innalahi Raji un,,,la haula,wak'uwatti illabillah,,a,uzubikalimatillah tamatin minsharri ma khalaqa.. way'annan addu,o,in ne kawai yaya Mahmoud keyi...cikin tashin hankali Kuma babu damar bud'e Baki balle ayi dak'arfi...sund'auki lokaci a wurin kamin sudena Jin wannan motsin d'in yad'auke...nisawa fadeel yayi zeyi magana kenan Dr Naseer da Hafees suka d'aga kafarsu dazimmar tafiya...ai Wani mugun guk'i dasukajine yasakasu d'auke har lumfashinsu sabida razana...Shima fedeel d'ib yayi yafasa cewa komai....k'uginnan kuwa se k'aruwa yakeyi kamar zetada wirin Kuma basusan daga inda yake fitaba ga dukkan alamu ba dabba d'aya ce keyinshiba sunada yawa.......Wani irin mirdawa cikin Dr Naseer yayi cikin tashin hankali yace innalillahi Dr cikena wlh guduwa nakeji yafad'awa Dr Mahmoud akunne...Ido dr Mahmoud yazaro Shima akunnen yace "tab d'ijam to yazamuyi kenan Dr? Ksmun Dr Naseer yak'ara magana sukaji shashekar kuka kamar za,afashe...cikin sauri IRFAAN yasaka hannu yajanyo mesanyin kukan domin yagano kowaye kamin yakamusu bala,I yayi saurin toshe bakinshi Yanayi k'asa da murya ahankali yace mikakeyi hakane Muneer so kakeyi wannan kukan naka ya kashemu kome? Wlh sukaji kukanka to akanka zasu fara koma

Table of Contents

Chapters

8 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8