Chapter 7
Chapter 7
ya daɗe yana neman hanyar da zai sace ta bai samu ba, sai da ya yi amfani da kai ka ɓata sihirin. Amma kada ka damu, za mu taimake ka, ka kashe shi ka kuma taho da matarka, domin alherin da ka aikata wa ɗan uwanmu." Daga nan sai ya ɗaga kansa sama, ya yi wata irin ƙara da kururuwa mai ƙarfi. Yana rufe bakinsa sai ga gungun wasu aljanu sun bayyana a gabansa. Ya tambaye su labarin maridin da ya sace mini mata, sai ɗaya daga cikinsu ya ce, "Na san inda yake, yana can ƙarshen duniya a Birnin Tagulla, birnin da rana ke faɗuwa." Sai aljanin nan na farko ya dube ni ya ce, "Ya Abu Muhammadu, ka tafi tare da wannan aljani, zai ɗauke ka bisa bayansa, ya kai ka har cikin Birnin Tagulla. Zai gaya maka sharuɗɗan da za ka bi duka, ka kashe maridi ka dawo da matarka. Sai dai ka kula, wannan aljani da zai ɗauke ka ba musulmi ba ne, don haka kada ka furta sunan Allah yayin da kake bisa bayansa. Idan kuwa ka ambaci sunan Allah kana bisa gare shi, to, zai jefar da kai ne, wanda hakan zai iya sanadin halakarka." Na ce masa, na ji na yarda. Ya kira ɗaya daga cikin aljanun ya ce masa ya ɗauke ni ga bayansa ya tafi da ni zuwa Birnin Tagulla. Aljani ya matso kusa gare ni, ya duƙa ya ce, "Hau." Na yi tsalle na haye bisa bayansa, ya kaɗa fukafukansa ya tashi da ni sama. Ya yi ta tashi da ni sama har na daina ganin ƙasa, duniyar ta koma mini tamkar hayaƙi. Muka yi kusa ga taurari, na gan su manya-manya tamkar tsaunuka. Na jiyo wasu muryoyi daga sama suna tsarkake sunan Ubangiji, shi kuwa aljanin nan sai ya takale ni da hira domin kada in kira sunan Allah. Muna cikin tashi cikin iska sai na ga wani ɗan ƙaramin aljani cikin tsanwar tufafi, gashin kansa mai tsawo har bisa ga duga-dugan kafafunsa, iska na kwasar shi. Yana riƙe da wani mashi mai tsinin gaske, tsinin mashin kuma yana fitar da wuta. Aljanin nan ya matso kusa ga kunnena, ya ce, "Ya Abu Muhammadu, ka ce babu sarki sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne. Idan ba haka ba zan soke ka da wannan mashi." Yayin da na ji haka, da ma duk na gaji da rashin kiran sunan Allah da ban yi ba, sai na ce, "Na shaida babu sarki sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne." Ina faɗin haka sai aljanin nan mai tsanwar tufafi ya juya wurin aljanin da yake ɗauke da ni ya ce masa, "ka ce babu sarki sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon Allah ne. Idan ba haka ba zan soke ka da wannan mashi." Aljani ya ce, "Faufau!" Nan take aljanin nan ya soke shi da mashi. Aljani ya kama da wuta, ya ƙone ƙurmus, ya zama toka. Ni kuwa na sulmiyo daga bayansa na yiwo ƙasa. Na rufe idanuna ina ta salati, ina kuma jiran in ji yadda ƙasusuwana za su ragwargwaje idan na faɗo ƙasa. Allah da ikonsa sai na faɗa cikin ruwan teku ƙundum, kamar an jefo dutse. Ashe kuma kusa ga wasu masu jirgi su biyar na faɗo. Suna gani na sai suka jawo ni, suka saka ni a cikin jirginsu. Suka tarairaye ni har hankalina ya dawo jikina, sa'annan suka yi ta yi mini magana da wani irin harshe wanda ba na fahimta. Na yi musu alama cewa ba na fahimtar abin da suke cewa. Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, in sha Allah. Bukar Mada 17/05/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (7) HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA Suka yi ta yi mini magana da wani harshe wanda ba na fahimta. Na yi musu alama cewa ba na fahimtar abin da suke cewa. Suka ƙyale ni, muka yi ta tafiya cikin jirgi har kusan ƙarshen rana. Suka jefa komarsu a cikin ruwa suka kamo ƙaton kifi, suka gasa shi, suka ba ni na ci na ƙoshi. Haka muka yi ta tafiya har muka isa birninsu. Suka kai ni ga Sarkinsu, wanda na fahimci yana gane harshena na Larabci. Na sumbaci ƙasa gabansa, na gaishe shi da ladabi. Ya kawo tufafi na alfarma ya ba ni, ya naɗa ni ɗaya daga cikin fadawansa. Na tambayi Sarki sunan wannan birni, ya ce mini sunansa Hannadu, yana daga cikin yankin ƙasar Sin. Ya hada ni da Wazirinsa domin ya nuna mini gari. Muka zagaya da Waziri ko'ina cikin gari, ya gaya mini cewa, al'ummar farko da ta zauna wannan birni ba musulmi ba ne, sun kasance masu bautar wuta, don haka Allah ya yi fushi da su, ya mayar da su duwatsu. Na zauna a wannan birni tsawon wata guda, ban taɓa ganin wani birni mai yawan bishiyoyi da 'ya'yan itace ba kamar wannan birni. Wata rana ina zaune a bakin teku ina shan iska, sai ga wani mutum ya zo wurina bisa ingarman doki. Ya dube ni ya ce, "Ba kai ne Abu Muhammad Kasala ba?" Na amsa masa, "Ni ne." Ya ce, "Kada ka ji tsoro, labarin alherinka ya iske mu." Na tambaye shi, "Wane ne kai?" Ya ce mini, "Ni ɗan uwan farin macijin nan ne da ka taimaka. Da sannu za mu saka maka da alherin da ka aikata mana." Ya cire rigarsa ɗaya ya ba ni, ya ce, "Karɓi wannan riga ka sanya, kada ka ji tsoron kome. Aljanin da ya ƙone tare da kai bawanmu ne. Tashi mu tafi yanzu in kai ka Birnin Tagulla." Na karɓi taguwa na saka, ya aza ni bisa kuturin dokinsa, ya sukwane shi, muka tafi kamar iska. Cikin dan ƙanƙanin lokaci sai na gan mu a cikin rairayin hamada. Aljani ya ja linzamin doki ya tsaya, ya ce mini in sauka. Bayan na sauka sai ya nuna mini wasu tsaunuka guda biyu can daga nesa. Ya ce, "Ka tafi zuwa ga waɗancan tsaunuka, za ka ga hanya a tsakaninsu. Ka shiga ta wannan hanyar za ka hangi Birnin Tagulla a gabanka. Ka jira a wurin, kada ka shiga cikin birnin sai na zo na sanar da kai ƙa'idojin da za ka bi." Na ce, "To." Na kama hanya na nufi tsaunukan nan, na ga hanya ta bi ta tsakaninsu, na bi ta. Ina shigewa ta hanyar sai na hangi katangar birnin wadda aka gina da tagulla. Na je gun katangar na yi ta zagaya ta amma ban ga ƙofar shiga ba. Daga nan sai ga aljanin nan ɗan uwan maciji ya zo wurina, yana riƙe da wata takobi ta zinariya, an zane dukkan jikinta da ɗalamusai. Ya miƙa mini takobi ya ce idan ina rike da ita babu mahaluƙin da zai cuce ni. Ya yi mini fatar samun nasara, sai ya ɓace. Aljanin nan bai daɗe da tafiya ba, sai na riƙa jin hayaniya da hargowa. Ban ankara ba sai na gan ni a tsakiyar wasu aljanu masu ɗan ƙaramin kai kamar ƙodago, da idanunsu a kan kirji. Suka tambaye ni, wanene ni? Na kwashe labarina na gaya musu. Sai suka ce mini, "Yarinyar da kake nema tana cikin wannan birni tare da maridi, amma ba mu san abin da ya yi mata ba. Mu kuma 'yan uwan farin maciji ne,
Table of Contents