Chapter 2
Chapter 2
Masrur jagora har zuwa ɗakin wanka. Masrur ya ga ɗakin wankan da bai taɓa ganin irinsa ba. Bangayen ɗakin da daɓensa duka na duwatsu ne masu darajar gaske, waɗanda aka cakuɗa da zinariya da azurfa. Ruwan wankan kuma an gauraya su da ruwan wardi. Bayi suka himmatu wajen yi wa Masrur da 'yan rakiyarsa hidima yayin da suke wanka. Da suka gama wanka, aka ba su tufafi na alfarma, waɗanda aka yi wa ado da kumfar zinari yayin saƙa su, suka sanya. Bayan Masrur da 'yan rakiyarsa sun kimtsa sai suka nufi inda Abu Muhammad Kasala ke jiransu, suka tarar da shi zaune bisa wani dandamali da aka yi cikin turakarsa. A saman wannan dandamali aka girke wata ƙatuwar kujera mai kama da gado, wadda aka shinfiɗa wa katifu, aka lulluɓe katifun da zannuwan alharini. A saman wannan kujera maigidan yake zaune. Bangon da aka jingina kujerar kuma an lulluɓe shi da labulen hatsaya da alharini da aka saƙa su tare da zinariya, aka kuma lilliƙa masa duwatsun jauharai masu launi daban-daban. Sa'adda Masrur ya shigo cikin turakar, sai Abu Muhammad ya sauko daga kan kujera, ya tarye shi da fara'a, ya sake yi masa maraba. Ya ja shi suka koma kan kujearar suka zauna wuri guda, sauran mutane kuma suka zauna kan kujerin da ke cikin turakar. Daga nan mai gida ya yi umurni da a fito da abinci da abin sha. Nan da nan bayi da kuyangi suka yi ta jido akussan abinci da gorunan abin sha suna girkewa a gaban baƙin nan. Masrur ya saki baki yana tu'ajjibin kyawun akussan da aka kawo musu abinci a ciki, su dai ba daga itace aka sassaƙa su ba, ba kuma da dutse aka yi su ba, to ko da ƙashi aka yi su? Oho. Ya ce a ransa, 'na rantse da Allah ban taɓa ganin akussa masu kyau kamar waɗannan ba, waɗanda babu irinsu ko da a fadar Halifa.' Kowane akushi da irin abincin da ke cikinsa, wani an zuba soyayyen nama, a wani kuma an zuba dafaffe. A wani akushin kuma an zuba farar shinkafa da zuma, wani kuma gurasa ce da miya. Aka dai girke musu abinci iri daban-daban. Suka fara ci suna taɗi, suna annushuwa, ba su farga ba har dare ya ƙwace musu. Da za su koma masauki, Abu Muhammad ya ba kowannensu dinari dubu biyar. Washegari kuma ya ƙara yi musu kamar yadda ya yi musu jiya. Ya tufatar da su tufafi na alfarma, masu launin kore da ruwan zinari. Ya himmatu ga yi musu hidima. Da Masrur ya ga suna shirin shantakewa, sai ya ce wa Abu Muhammad, "ya kamata ka shirya mu tafi, kada Halifa ya ga mun daɗe, ransa ya ɓaci." Abu Muhammad Kasala ya amsa masa da cewa, "ya shugabana, yi haƙuri dai ka jinkirta mini, zuwa gobe na gama duk shirin da nake yi, sai mu tafi." Don haka suka sake kwana ɗaya. Da gari ya waye, Abu Muhammad ya sa bayi suka shirya masa wata alfadararsa da yake hawa. Sirdin da aka ɗaura wa alfadarar da sauran kayan da aka shirya ta da su duka an yi su ne daga zinariya da azurfa da lu'ulu'u, sai ɗaukar ido suke yi cikin rana. Masrur ya dubi alfadarar nan, ya ce cikin ransa, 'zan yi mamaki idan har Halifa bai tuhumi Abu Muhammad yadda ya yi wannan arziki, idan ya je masa da tarin dukiya haka.' Daga nan suka yi sallama da al-Zubaidi, suka fita daga Basara suka fuskanci Bagadaza. A kwana a tashi, ba tare da sun tsaya ko'ina ba, har Allah ya kai su birnin Bagadaza, gidan aminci. Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah. Bukar Mada 29/04/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (2) HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA Daga nan suka yi sallama da al-Zubaidi, suka fita daga Basara suka fuskanci Bagadaza. A kwana a tashi, ba tare da sun tsaya ko'ina ba, har Allah ya kai su birnin Bagadaza, gidan aminci. Suka wuce kai tsaye wurin Halifa. Bayan sun yi gaisuwa, Halifa ya umurci Abu Muhammad da ya zauna. Da ya zauna, sai ya sake gayar da Halifa da kyakkyawan lafazi, sa'annan ya ce, "Ya shugaban muminai, na zo maka da wata 'yar tsaraba, idan ka yarda na kawo ta gabanka yanzu." Halifa ya ba shi dama. Daga nan sai Abu Muhammad ya ɗauko akwati ya buɗe shi, ya fara zaro tsarabar da ya kawo wa Halifa, tsarabar da babu tamkarta. Daga cikin tsarabar akwai wata bishiya da aka yi jikinta da zinariya, rassanta da yaƙutu, ganyayenta da zabarjadi, 'ya'yanta da lu'ulu'u, girman 'ya'yan kamar ƙwayayen tattabara. Halifa ya cika da mamakin ganin wannan itaciya, gayar mamaki. Abu Muhammad ya kuma jawo wani akwati ya buɗe, ya zaro tanti irin wanda ake kafa wa sarakuna idan sun fita shan iska bayan gari, ko idan an tafi farauta ko yaƙi. Shi wannan tanti an yi rufinsa ne da dardumar da aka saƙa daga alharini da jauharai iri daban-daban, aka ƙawata ta da kwalliyar zinariya da yaƙutu da zabarjadi aka kuma yi zanen surorin tsuntsaye da dabbobi iri-iri, na gida da na daji. Sandunan da ake kafa tantin da su kuwa an yi su ne daga ɗanyen itacen turaren sandal ɗan asalin Hindu, waɗanda da zarar an fito da su waje, wuri zai gume da ƙamshi. Halifa ya yi mamki matuƙar mamaki da waɗannan abubuwa da ya gani. Abu Muhammad ya duƙar da kai ya ce, "Ya Sarkin Musulunci, ban kawo maka wannan tsaraba don kwaɗayin wani matsayi da za ka naɗa ni ba, ban kuma kawo maka su ba a matsayin rashawa wai don wani laifi da ba aikata. Na kawo maka su ne domin kuwa babu wanda ya dace da waɗannan kaya sai kai. Ni ba kowa ba ne face talaka daga cikin talakawanka. Kuma idan Halifa ya yarda, zan nuna masa wata baiwa da Allah ya hore mini." Halifa ya ce, "Aikata abin da kake so mu gani." Abu Muhammad ya ce, "To, madalla." Ya dubi wani gini da ke cikin fadar, ya motsa leɓɓansa kamar mai karanta wata addu'a, sai mutane suka ga ginin ya zo gabansa ya rusuna. Abu Muhammad ya sake yin wata ishara, sai ginin ya koma inda yake, ya kuma miƙe kamar yadda yake da fari. Daga nan kuma ya yi wata alama da idanunsa, sai aka ga dogayen akwatuna sun bayyana a cikin fadar. Ya yi musu magana, sai mutane suka ji kukan tsuntsaye na fitowa daga cikin akwatunan. Waɗannan abubuwa sun ƙayatar da Halifa ainun. Ya ce wa Abu Muhammad, "Ya aka yi ka samu duka waɗannan abubuwa? Shin ba kai ne ake kira Kasala ba saboda ragwanci? An fa ce mini mahaifinka wanzami ne, mai yi wa mutane aski a gidan wanka. An kuma ce mini bai bar maka komai ba sa'adda ya mutu." Abu Muhammad ya ce, "Ya Halifa, abin duk da mutane suka faɗa maka game da ni gaskiya ne, amma saurari labarina ka ji. Akwai abin al'ajabi a cikinsa, wanda da za a rubuta shi da tsinin allura bisa ga kusurwar ido da ya zama abin lura ga masu hankali. Ka sani cewa, ya Shugaban Muminai, Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana. Kamar yadda ka ji mutane sun ba ka labarin ƙuruciyata,
Table of Contents