Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Arziki Rigar Kaya Book One Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

dauka ka buɗe ƙofar. Idan ka shiga cikin ɗakin za ka ga wani babban akwati na baƙin ƙarfe, wanda ba ya da marufi. Daga cikin akwatin, a kowace kusurwa tasa, za ka ga wani farin ƙyalle abin rubucewa da ɗalamusai. Daga tsakiyar akwatin kuma akwai wani faifai cike da kuɗi. A bisa faifan za ka ga wani farin zakara a ɗaure, da wata baƙar laya a ƙafarsa ta hagu. Daga gefen akwatin kuma za ka ga macizai guda goma sha ɗaya, a ɗaya gefen kuma za ka ga wata wuƙa ta azurfa. To, ka ɗauki wuƙar ka yanke kan zakaran nan da ita, kuma ka yayyanke ƙyallayen nan masu ɗalamusai. Sa'annan ka kifar da akwatin. Daga nan sai ka yi sauri ka koma wurin matarka, ka kwanta. Wannan shi ne abin da nake so kawai ka aikata mini." Na ce masa, zan aikata abin da ya umurce ni da shi. Da ranar daurin aure ta zo, na tafi tare da jama'ata zuwa gidan Sharif. Aka rubuta takardar ɗaurin aurena da yarinya tare da shaidu, aka shafa Fatiha, mutane suka watse. Da dare ya yi na shiga wurin amaryata, na gan ta yarinya ce kyakkyawar gaske wadda harshe ba zai iya bayyana kyawunta ba, nan take kuwa tsananin son ta ya soki zuciyata, ya bi jijiyoyi ya mamaye dukkan jinin jikina. Muka shiga zance da ita har na lura cewa barci ya soma cin ƙarfinta. Sai na tashi a hankali na duba daidai inda biri ya kwatanta mini, sai kuwa na ga ƙofar ɗaki kulle da kwaɗon tagulla. Na laluba daga ƙasan ƙofar na ɗauki mabuɗi na buɗe kwaɗon, na shiga cikin ɗakin. Na ga akwatin nan, na aikata kamar yadda biri ya bayyana mini duka. Ina shirin fitowa daga cikin ɗakin kenan, sai na ga yarinya tsaye a bayana. Yayin da ta ga abin da na aikata, sai ta dafe kai ta fashe da kuka. Na ji tana cewa, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki. Babu shakka yau Maridi zai yi galaba a kaina." Daga nan sai muka riƙa jin wata irin kururuwa mai ban tsoro, da rugugi mai ƙarfin gaske har ƙasan ɗakin da muke ciki na motsawa. Sai ga Maridi ya bayyana a cikin ɗakin, ya suri yarinya ya tashi sama da ita tana kuka. Na yi tsaye kamar mutum-mutumi, ina tunanin abin da ya faru, ina zargin kaina bisa ga abin da na aikata. Ina nan tsaye sai ga Sharif ya shigo ɗakin da nake da sauri, yana kuka yana marin fuskarsa. Ya ce da ni, "Ya Abu Muhammad, me ya sa ka aikata wannan abu? Ka sani na aikata wannan sirri ne domin in tsare 'yata daga wannan mugun Maridi, la'ananne, wanda tun tsawon shekaru shida da suka wuce yake neman hanyar da zai sace ta daga gare ni. Amma bai yi nasara ba sai yau, babu amfanin zamanka cikin wannan gida, ka tafi ka bar mana gida." Na fita cikin daren nan na nufi gidana, ina mai baƙin cikin abin da ya faru. Na nemi birin nan sama da ƙasa, amma ban gan shi ba. Sai na tabbata cewa lalle shi ne Maridin da ya sace mini amarya, watau da ma yaudara ta ya yi domin in ɓata sihirin da ya hana shi sace ta tsawon shekaru. Mai son abinka ya fi ka dabara! Na zauna ina mai matuƙar nadama bisa ga abin da na aikata. Na riƙa marin fuskata don takaici. Haka na kasance har zuwa fitowar alfijir. Wata zuciya ta ce mini, "Menene amfanin zamanka a nan kana marin fuskarka? Tashi ka shiga duniya neman matarka." Na fita daga cikin gidana, da sanyin safiya, na nufi bayan gari, amma ban san inda zan nufa ba. Na fita daga cikin gari, na shiga cikin daji, wanda ya kasance hamada ce, babu komai cikinta, daga rairayi sai rairayi. Na yi ta tafiya cikin rairayin nan har rana ta take ban tsaya ba. Na gaji tiɓis, ga kuma ƙishirwa ta soma koɗa ni, ba alamar ruwa gaba, ba alamarsa baya. Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah. Bukar Mada 13/05/2023 ARZIKI RIGAR ƘAYA (6) HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA Na fita daga cikin gidana, da sanyin safiya, na nufi bayan gari, amma ban san inda zan nufa ba. Na fita daga cikin gari, na shiga cikin daji, wanda ya kasance hamada ce, babu komai cikinta, daga rairayi sai rairayi. Na yi ta tafiya cikin rairayin nan har rana ta take ban tsaya ba. Na gaji tiɓis, ga kuma ƙishirwa ta soma koɗa ni, ba alamar ruwa gaba, ba alamarsa baya. Can da almuru, ina cikin tafiya ina jan ƙafafu, sai na ga waɗansu macizai guda biyu suna faɗa, ɗaya fari, ɗaya kuma rawaya. Sai na ga rawayan yana neman ya halaka farin. Na duƙa na ɗauki wani ƙaton dutse na kwantsama masa shi, nan take ya mutu. Da farin macijin ya ga haka sai ya gudu. Zuwa can sai ga shi ya dawo tare da wasu macizan guda goma, dukkaninsu farare. Suka tafi wurin gawar wancan macijin, rawaya, suka yi mata kaca-kaca, sai kansa kawai suka bari. Daga nan suka koma inda suka fito. Ni kuwa saboda tsananin gajiya, da kuma wahala sai na faɗi durƙushe a kan gwiwowina. Ina nan durƙushe sai na ji wata murya mai daɗi tana waƙa, na waiga ko'ina amma ban ga kowa ba. Muryar ta ci gaba da waƙa tana cewa: "Haka ƙaddarori kan taho gun taliki, Yadda Jallah ya tsaro su ba mai kariya. Allahu Rabbi yakan yi canjin lamari, A cikin daƙiƙa ko a ƙibta idaniya." Yayin da na ji waƙa amma ban ga mai yin ta ba, ya Shugaban Muminai, sai na tsorata matuƙar tsoro. Sai kuma na ji wata muryar daga bayana tana waƙa waɗannan baitoci: "Yi farin ciki ya kai mutum ga agaji, Da ka ɗauki Ƙur'ani yana maka nuniya. Tsoro na shaiɗan ko mutum duka kar ka ji, Domin kana bisa godabenmu na Anbiya." Da na ji wannan waƙa sai na yi ƙarfin hali na ce, "Ina gama ka da Allah, Ubangijin talikai, waye kai?" Daga nan sai na ga mai waƙar ya bayyana a cikin siffar mutum namiji. Ya ce mini, "Kada ka ji tsoro, labarin alherinka ya iske mu. Mu, muna daga cikin aljanun da suka bayar da gaskiya ga addinin Islama. Shin kai kana da wata buƙata da kake so mu biya maka?" Na amsa masa, "Haƙiƙa ina da buƙata. Ina da matuƙar bukatar wani abu, domin kuwa musiba ta afka mini wacce da ɗai irinta ba ta taɓa afka wa wani ɗan Adam ba." Sai na ji ya ce, "Ai kai ne Abu Muhammadu Kasala ko?" Bai jira na ba shi amsa ba, sai ya ci gaba da cewa, "Ya Abu Muhammadu, ni ɗan uwan farin macijin nan ne da ka taimaka, wanda ka kashe wa abokin faɗa. Mu huɗu muke 'yan uwan juna, ubanmu ɗaya uwarmu ɗaya. Dukkaninmu a halin yanzu kana da bashi a kanmu, wanda dole ne mu biya ka shi. Ka sani cewa birin nan da ya yaudare ka, maridi ne daga cikin kafuran aljanu. Ba domin ya yaudare ka ba har ka ɓata sihirin da Sharif ya yi, da babu yadda za a yi ya sace yarinyar nan. Domin

Table of Contents

Chapters

9 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9