Chapter 5
Chapter 5
dukiya, yi maza ka tafi kasuwa ka sami rumfa ka fara kasuwanci." Nan take kuwa sai na ji wani sabon karfi a jikina, ragwancina ya tafi, kamar cirar ƙaya. Ashe dai talauci shi ke kawo lalaci da kasala. Na sami rumfa a cikin kasuwa, na shiga saye da sayarwa gadan-gadan. Kullum kuwa idan na buɗe rumfata sai mu zauna wuri guda tare da birin nan. Abin da na ci shi yake ci duka, abin da na sha kuma shi yake sha. Sai dai wani abin mamaki game da birin nan shi ne, kullum da safe ya kan bar ni, ya yi tafiyarsa. Ba ya dawowa wurina sai da tsakar rana, kuma idan ya dawo yakan zo da jaka ɗauke da kuɗi dinari dubu, sai ya ajiye ta kusa gare ni ya zauna. Haka yake yi kullum. Da wannan kuɗi da biri ke kawo mini kullum da kuma ribar da nake samu a rumfata, sai na zama hamshaƙin attajiri. Na mallaki gidaje da yawa, na sayi ganoki da lambuna. Na mallaki bayi da kuyangi, baƙaƙe da farare, masu yawan gaske. Wata rana ina zaune a cikin rumfata tare da biri, sai na ga yana ta waige-waige, kamar mai neman wani abu. Na ce a cikin raina, "Me yake damun wannan dabba yau?" Kamar ya ji abin da na faɗa, sai Allah ya buɗe masa baki, ya yi magana da gwalamniya, kamar yaro mai koyon magana, ya ce, "Ya Abu Muhammad!" Yayin da na ji biri ya yi magana, sai na firgita don tsoro. Sai ya ce mini, "Kada ka ji tsoro, yanzu zan sanar da kai labarina." Ya ci gaba da cewa, "Ka sani, ni maridi ne daga aljanu. Na zo wurinka ne domin in taimake ka, in fitar da kai daga cikin talauci. Yanzu kana ɗaya daga cikin manyan attajiran wannan birni. Lokaci ya yi da za ka saka mini da tawa buƙata zuwa gare ka." Na tambaye shi, "Mecece buƙatarka gare ni?" Ya amsa mini, "Ina so in haɗa ka aure da wata yarinya kyakkyawa, mai hasken fuska kamar wata daren goma sha huɗu." Na dube shi cike da mamaki na ce, "Da yaya za ka haɗa ni aure da wannan yarinya, kuma wacece ita?" Biri ya ce mini, "Gobe ka sanya tufafinka na alfarma, waɗanda suka fi kowaɗanne kyau. Ka hau alfadara wadda aka ɗaura wa shimfiɗa ta zinariya, ka tafi zuwa ga kasuwar 'yan harawa. Ka tambayi rumfar Sharif, idan aka nuna maka shi, ka shiga rumfarsa ka zauna kusa gare shi. Ka ce masa, ka zo neman auren 'yarsa wance. Idan ya ce maka, ba ka da arzikin da za ka auri 'yarsa, ka zaro jakar kudi mai dinari dubu ka ba shi ita. Idan ya buƙaci ƙari, ka ƙara masa. Idan ya kuma buƙatar ƙari, ka ƙara masa. Ina so ka saye shi da kudyi har ya amince da zai aura maka 'yar tasa." Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, in sha Allah. Bukar Mada 06/05/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (5) HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA Biri ya ce mini, "Gobe ka sanya tufafinka na alfarma, waɗanda suka fi kowaɗanne kyau. Ka hau alfadara wadda aka ɗaura wa shimfiɗa ta zinariya, ka tafi zuwa ga kasuwar 'yan harawa. Ka tambayi rumfar Sharif, idan aka nuna maka shi, ka shiga rumfarsa ka zauna kusa gare shi. Ka ce masa, ka zo neman auren 'yarsa wance. Idan ya ce maka, ba ka da arzikin da za ka auri 'yarsa, ka zaro jakar kuɗi mai dinari dubu ka ba shi ita. Idan ya buƙaci ƙari, ka ƙara masa. Idan ya kuma buƙatar ƙari, ka ƙara masa. Ina so ka saye shi da kuɗi har ya amince da zai aura maka 'yar tasa." Na ce, "Na ji, na karɓa. Gobe kuwa zan aikata kamar yadda ka umurce ni." Washe gari na sanya tufafina na alfarma, na ɗaura wa alfadarata shimfiɗa ta zinariya. Na tafi tare da bayi goma, biyar na yi mini zagi, biyar na dafe da kuturi, har muka isa kasuwar 'yan harawa. Aka nuna mini Sharif yana zaune a cikin rumfarsa. Na sauka daga kan alfadara, na shiga cikin rumfarsa na gaishe shi, sa'annan na zauna kusa gare shi. Ya dube ni ya ce, "Mun yi murna da zuwanka. Ka zo ne domin ƙulla harakar kasuwanci a tsakaninmu?" Na amsa masa, "I, na zo da wata muhimmiyar magana ce zuwa gare ka." Ya tambaye ni, "Wace magana ce wannan?" Na amsa masa, "Na zo neman auren 'yarka ne." Na sunkuyar da kaina kasa, ina jiran in ji abin da zai ce. Ya dube ni da kyau, ya sake dubana, ya ce, "Ba ka da kuɗin da za ka auri 'yata, kuma menene asalinka da darajarka?" Na zaro wata jaka mai ɗauke da dinari dubu na jan zinari, na miƙa masa, na ce, "Waɗannan su ne darajata kuma su ne matsayina, kamar yadda wani mai hikima ya faɗa, 'babban matsayin mutum ga sauran mutane ita ce dukiya.' Ko ba ka ji yadda aka faɗa ba a cikin wannan waƙa: "Mai dirhami biyu shi yake da abin faɗa, Zancen da yas so duk yakan furta a baki nasa. Ka ga an tsare shi ana ta sauraren batu, Shi ko yana ta isa da alfahari da iko nasa. Sani dai saboda kuɗin ake masa fada, Ba don su ba da ka tarar da ana ta ƙyama tasa. Da zai yi ƙarya 'yar kaɗan ko mai yawa, To sai ka ji jama'a suna ta yabo na zance nasa. Amma talaka idan ya furto gaskiya domin a ji, To za su ce ƙarya yake ta faɗa a zance nasa. Ka sani kuɗi ne martaba a idon mutanen zamani, Mai su yakan miƙe ƙafarsa yana ta mulki nasa. Su ke zama harshe ga mai son yin batu, Su ne makamin far ma duk maƙiya a yaƙi nasa." Yayin da ya ji wannan waƙa sai ya duƙar da kansa ƙasa, ya yi jim cikin tunani. Can ya ɗago kansa ya ce mini, "Idan har da gaske kake yi za ka auri 'yata, to, ka ƙaro mini dinari dubu uku." Na ce, "To." Na aiki ɗaya daga cikin bayina cewa ya ruga gida ya ɗauko mini dinari dubu uku. Da bawa ya kawo mini kuɗi, sai na miƙa wa Sharif. Nan take ya tashi, ya kulle rumfarsa. Ya gaya wa abokansa attajirai maganar ɗaurin aurena da 'yarsa, ya kuma gayyace su zuwa gidansa domin su shaidi ɗaurin aurenmu. Ya juyo wurina ya ce mini, in tafi in shirya, nan da kwana goma za a ɗaura aurenmu da 'yarsa. Na koma gida cike da farin ciki. Na gaya wa biri yadda muka yi da uban yarinya. Ya ce mini, "Ka yi daidai." Yayin da lokacin ɗaurin aure ya kusa, sai biri ya ce mini, "Akwai wani abu da nake so ka yi mini, idan ka yi mini wannan abu to zan ba ka dukkan abin da ka bukyata daga gare ni." Na tambaye shi, "Mene ne wannan abu?" Ya ce mini, "A cikin ɗakin da za ka tare da amaryarka, za ka ga ƙofar wani ɗaki a rufe da kwaɗo na tagulla. Ka fakaici idon matarka idan ta yi barci, ka tafi ga wannan ƙofar ɗakin, ka laluba daga ƙasan ƙofar za ka ji mubuɗin kwaɗon, ka
Table of Contents