Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Arziki Rigar Kaya Book One Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

to, haka ne. Ko da mahaifina ya mutu bai bar mini kome ba sai zabirar aski domin kuwa shi wanzami ne, kamar yadda ka faɗa. Lokacin da nake yaro ana kirana da suna Abu Muhammad Kasala saboda tsabar ragwancina, ga kuma son jiki sai ka ce kyanwa. Saboda kasala idan na kwanta barci a cikin inuwa sai rana ta cim mini, ina ji ina gani, ban tashi ba, kome kuɗar da take yi mini ba ni tashi in shiga inuwa sai fa in wani ya zo ya riƙa ni na tashi. Haka na tashi a sangarce har na kai shekara goma sha biyar, lokacin ne kuma mahaifina ya karɓa kiran Ubangiji. Ya mutu bai bar mini kome ba na dukiya, sai zabirarsa ta aski. Bayan rasuwar mahaifina, sai mahaifiyata ta shiga ɗawainiyar neman aikin da za ta riƙa samo mana abinci, har ta yi gamo da katar ta sami wurin aiki. Sai ya kasance kullum tana zuwa wurin aiki domin samo mana abin kalaci. Ni kuwa kullum ina kwance gida, sai ka ce ruwa, in mimmiƙe abina bisa shinfiɗa ina jiran dawowarta. Idan ma ta dawo ba na iya tashi sai ta kama ni ta zaunar, sai ka ce mara lafiya. Abincin ma sai ta ba ni ga baki sannan zan ci. Ran nan ina kwance bisa shimfiɗa, sai ga mahaifiyata ta shigo inda nake, riƙe da dirhami biyar na azurfa. Ta ce mini, "Ya ɗana, na ji labarin cewa Dattijo Abu Muzaffar zai tafi fatauci Birnin Sin. Tashi mu tafi wurinsa mu ba shi waɗannan kuɗin, idan ya isa Birnin Sin ya sayo maka wata haja da su, wadda idan aka sayar da ita nan za a sami riba, idan zai koma kuma, mu ƙara ba shi wasu kuɗin tare da ribar ya ƙara sayo mana wata hajar. Wa ya sani ko Ubangiji ya yi mana arziki da waɗannan 'yan kuɗin, domin kuwa shi ne mai arzutta wanda ya so ta inda ba ya tsammani." Ni kuwa a lokacin na ji daɗin kwanciyar da na yi, ba na son ko motsa ƙafata saboda ragwanci. Yayin da mahaifiyata ta ga haka sai ta yi fushi, ta ce, "Na rantse da Allah, idan ba ka tashi mun tafi wurinsa ba, ba na koma kawo maka abinci ko nama. Ko ruwa ba zan ƙara kawo maka ba, sai dai yunwa ta kashe ka." Yayin da na ji haka, ya Shugaban Muminai, kuma na tabbata lalle za ta aikata abin da ta faɗa idan ban tashi ba, sai na turɓune fuska, na ce da ita, "To, riƙa ni in tashi." Ta kama hannuna na miƙe zaune. Na yi miƙa tare da hamma, na ce ta ɗauko mini takalmina. Ta tafi ta ɗauko. Na ce ta saka mini su ga ƙafata, ta saka mini. Daga nan sai na ce, to, ta riƙa ni in miƙe tsaye. Ta riƙa ni na miƙe tsaye, har za ta sake ni, na ce ni sai na dogara ga jikinta zan iya tafiya, idan kuwa ba haka ba faɗuwa zan yi. Haka dai ta yarda na jingina ga jikinta, muka tafi ina jan ƙafafu, jallabiyar da na sanya na taɗiye ni, kamar mai koyon tafiya. Ko da muka isa bakin teku, mun tarar da har tawagar fatake sun shirya kayansu cikin jirgin ruwa suna shirin tafiya. Dattijo Abu Muzaffar shi ne shugaban tafiyar. Mutumin kirki ne, ga shi da gaskiya da riƙon amana, sa'annan kuma akwai shi da tausayin talakawa. Muka gaishe shi, sa'annan na ce da shi, "Ya baffana, shin kai ne Abu Muzaffar?" Ya amsa mini, "Ni ne, ya ɗana." Na karɓi dirhaman nan daga hannun mahaifiyata, na miƙa masa na ce, "Karɓi wannan kuɗin, ka sayo mini wata haja daga ƙasar Sin, ko Allah zai ƙaddara in sami riba daga gare ta idan na sayar da ita a nan." Dattijo ya juya wajen fatake ya tambaye su, "Kun san wannan saurayi ne?" Fatake suka amsa, "I, sunansa Abu Muhammad Kasala. Tun da muke ba mu taɓa ganinsa a kan dugadugansa ba, wai kuma har yana tafiya, sai yau. Rabon da mu gan shi ya fito waje ma an daɗe. Kullum yana gida yana sharar barci." Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, in sha Allah. Bukar Mada 03/05/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (3) HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA Dattijo ya juya wajen fatake ya tambaye su, "Kun san wannan saurayi ne?" Fatake suka amsa, "I, sunansa Abu Muhammad Kasala. Tun da muke ba mu taɓa ganinsa a kan dugadugansa ba, wai kuma har yana tafiya, sai yau. Rabon da mu gan shi ya fito waje ma an daɗe. Kullum yana gida yana sharar barci." Daga nan sai ya juyo gare ni ya ce, "Ya ɗana ba ni kuɗin, ina roƙon Allah ya albarkace su a cikin wannan tafiya da za mu yi." Ya karɓi kuɗi daga hannuna. Ni da mahaifiyata kuwa sai muka juya zuwa gida. Dattijo Abu Muzaffar da sauran fatake suka gama shirin da za su yi duka, suka kwance jirgi suka tsunduma cikin teku, suka nufi Birnin Sin. A kwana a tashi har Allah ya saukar da su lafiya. Suka yi ciniki suka gama, suka juyo zuwa gida. Bayan sun yi rabin tafiya sai Abu Muzzafar ya ce, "Af, na kuwa manta da saƙon yaron nan Abu Muhammadu. Babu makawa mu koma zuwa Birnin Sin in sayo masa wata haja da kuɗinsa, wadda zai ci riba da ita idan mun koma gida." Da sauran fatake suka ji haka, kuma suka ga irin nisan da suka yi da Birnin Sin, ga shi kuma har sun fara jin ƙamshin gida. Sai suka yi ta roƙon Dattijo Abu Muzaffar a kan kada su koma da baya. Abu Muzzafar ya ce musu babu dama, lalle sai sun koma. Fatake suka ce idan ya yarda kowane ɗaya daga cikinsu zai ba da ribar abin da za a samu daga dirhamin nan biyar. Dattijo ya yarda da haka. Fatake suka haɗa kuɗi masu yawa suka ba shi, ya tattara su ya ƙulle wuri guda, sa'annan suka ci gaba da tafiya. Suka yi ta tafiya har suka iso ga wani tsibiri, suka tarar da birni babba a cikin wannan tsibiri. Suka ɗaure jirginsu bakin gaɓa, suka shiga cikin birni domin sayen kayan ƙarau na zinariya da azurfa da nau'o'in jauhari. Abu Muzaffar ya ga wani mutum da birai da yawa wurinsa. Ya ga wani tsohon biri a cikin biran nan, gashin jikinsa duk ya fara koɗewa saboda tsufa. Idan sauran biran nan suka ga hankalin mutumin nan mai kula da su ba ya wurinsu, sai su rufar wa tsohon birin nan da bugu da yakushi, har sai mutumin ya juyo gare su ya yi musu tsawa. Idan ya ƙara juyawa wani wurin sai biran nan su sake rufe tsohon birin nan da duka. Yayin da Abu Muzaffar ya ga haka, sai tausayin birin ya kama shi. Ya matsa kusa ga mutumin ya ce, "Ko za ka sayar mini da wannan biri naka?" Mai biri ya ce, "Nawa za ka saya?" Abu Muzaffar ya ce, "Ina da dirhami biyar na wani maraya da ya ba ni sallahu, idan ka sallama mini shi haka na biya." Mutumin ya ce, "Kawo kuɗi. Allah ya sa wannan biri ya amfane ka." Dattijo Abu Muzaffar ya kawo

Table of Contents

Chapters

9 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9