Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Arziki Rigar Kaya Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kuɗi ya ba dillalin birai. Bayi suka ja shi, suka kai ga jirgi suka ɗaure. Bayan sun gama sayayyar da za su yi a cikin wannan birni, sai suka kwance jirgi suka ci gaba da tafiya. A kwana a tashi kuma suka kai ga wani tsibirin. Suka ɗaure jirginsu bakin gaɓa suka taka bisa tudu suka tarar da wani ɗan ƙauye. Suka sami mutanen ƙauyen ba su da wata ɗabi'a sai a yi jinga da su, su yi nutso cikin teku su lalubo ma'adinai irinsu zinariya da azurfa da kuma wuri, su ba wanda ya ɗauki ijara tasu. Fataken nan kowa ya ɗauki hayar mutum guda ya biya shi, mutanen suka faɗa cikin teku suka yi ƙasa suna lalube. Yayin da birin nan ya ga haka, sai ya kwance ɗaurin da aka yi masa, ya faɗa cikin ruwa tare da masu laluben ma'adinai. Da Abu Muzaffar ya ga haka sai ya yi salati, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki. Mun rasa wannan biri bisa ga abin da Allah ya ƙaddara na asarar kuɗin wannan yaro." Bayan wani ɗan lokaci kaɗan sai masu nutso suka yiwo sama, sai ga birin nan shi ma ya yiwo sama tare da mutane, hannuwansa cike da ma'adinai ya kawo wa Abu Muzaffar. Dattijo ya cika da mamaki, ya ce, "Haƙiƙa akwai abin al'ajabi tattare da wannan dabba. Daga nan fatake suka hau jirginsu, suka ci gaba da tafiya, har suka iso ga tsibiri na uku. Shi wannan tsibiri ana kiransa da Tsibirin Zannuji. Tsibiri ne na waɗansu baƙaƙen mutane masu cin naman mutum. Yayin da baƙaƙen mutanen nan suka hango jirgin su Abu Muzaffar, sai kowane daya daga cikinsu ya jawo kwale-kwalensa ya nufi jirgin fataken nan yana lasar baki. Kafin fataken nan su farga har baƙaƙen mutanen nan sun zagaye jirginsu, kowane baƙin mutum ya kama rabonsa daga cikin fataken nan, ya ɗaure ya jefa cikin kwale-kwalensa. Suka juya zuwa cikin tsibirin tare da jirgin fataken, suka ɗaure jirgin a bakin gaɓa. Suka tafi da fataken da suka kama gaban Sarkinsu. Nan take Sarki ya sa aka yanka wasu daga cikinsu aka babbaka masa, ya ce a ɗaure saura a kurkuku. Aka tafi da su, cikin tsananin tashin hankali da firgita, aka ɗaure su. Yayin da dare ya yi tsaka, sai birin nan ya tafi wurin Abu Muzaffar ya kwance shi. Da sauran fatake suka ga haka sai suka ce wa Abu Muzaffar, "Ka taimake mu ka kuɓutar da mu daga halaka, ya Abu Muzaffar." Shi kuwa sai ya ce musu, "Ku sani cewa, wannan biri ne ya kuɓutar da ni, da yardar Ubangiji Maɗaukakin Sarki, kuma zan biya shi dinari dubu ladar kuɓutar da ni da ya yi." Sai fatake suka ce, "Mu ma za mu biya shi lada kamar yadda ka biya shi, idan dai har ya kwance mu daga ɗauri." Daga nan sai biri ya kwance su, ɗaya bayan ɗaya. Suka yi sauri suka nufi inda jirginsu yake. Suka tarar ko allura ba a cire ba daga cikin jirgin. Suka shiga suka tuƙa da sauri, suka bar wannan tsibiri. Bayan sun yi nisa da tafiya, sai Abu Muzaffar ya ce da su, "Ya ku fatake, ku cika alkawarinku ga biri." Suka ce, "Mun ji, mun karɓa." Kowa ya jawo jakar kuɗinsa ya ƙirga dinari dubu ya ba Abu Muzaffar. Shi ma ya ƙirga dinari dubu ya haɗa da waɗanda fatake suka ba shi, ya ƙulle su wuri guda. Sai ya kasance an tara wa birin nan kuɗi masu yawan gaske. Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah. Bukar Mada 06/05/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (4) HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA Bayan sun yi nisa da tafiya, sai Abu Muzaffar ya ce da su, "Ya ku fatake, ku cika alkawarinku ga biri." Suka ce, "Mun ji, mun karɓa." Kowa ya jawo jakar kuɗinsa ya ƙirga dinari dubu ya ba Abu Muzaffar. Shi ma ya ƙirga dinari dubu ya haɗa da waɗanda fatake suka ba shi, ya ƙulle su wuri guda. Sai ya kasance an tara wa birin nan kuɗi masu yawan gaske. Suka ci gaba da tafiya, kwanci tashi, har suka isa birnin Basara. 'Yan uwa da abokan arziki suka tare su da murna, suka yi musu barka da zuwa. Abu Muzaffar ya tambayi mutane, "Ina yaron nan Abu Kasala?" Nan take labari ya ishe uwata, ya Shugaban Muminai, ta zo wurina ina barci, ta tayar da ni ta ce, "Tashi ka tafi wurin Abu Muzaffar, na ji an ce jirginsu ya iso, ka ga me ya sayo maka. Wataƙila Allah ya sa ka sami abin kanka daga kuɗin da muka ba shi." Na mutsuttsuke idona ina gunaguni, saboda an tayar da ni daga barci. Sai ba ce wa mahaifiyata, " To, riƙa ni in tashi." Ta kama hannuna na tashi zaune. Na ce ta ɗauko mini takalmina ta sanya mini. Bayan ta sa mini takalmi, na ce ta riƙa ni in miƙe tsaye, kuma ta taimake ni wurin tafiya. Haka dai ta lallaɓa ni, kamar kwai, muka tafi ina jan ƙafafu, riga na taɗiye ni kamar zan faɗi, har muka isa bakin teku, inda fatake suka sauka. Yayin da Dattijo Abu Muzaffar ya gan ni, sai ya tare ni da fara'a yana cewa, "Lale marhabin, barka da zuwa, ya kai wannan yaro, wanda kuɗinsa suka yi sanadin tsirar mu daga halaka, tare da yardar Ubangiji Maɗaukakin Sarki." Ya miƙo mini biri, ya ce, "Tafi da wannan biri wanda na sayo maka idan na gama kimtsawa zan aiko zuwa gare ka." Na ja biri ga hannuna ina gunaguni, ina cewa, "Wallahi ni dai ban ga alfanun wannan biri da Abu Muzaffar ya sayo mini ba. Ta yaya biri zai amfane ni?" Da muka isa gida na ce wa mahaifiyata, "Kin matsa mini da dole sai na yi kasuwanci, kin hana ni more barcina. To, ga hajar da aka sayo mini nan, dube ta ki gani." Na nuna mata biri. Daga nan sai na sami wuri na zauna, zuciyata cike da takaici. Ban daɗe da zama ba sai ga bayin Abu Muzaffar sun shigo inda nake. Suka tambaye ni, "Kai ne Abu Muhammadu Kasala?" Na amsa musu, "I." Daga nan sai ga Abu Muzaffar ya shigo da kansa. Na tashi na kama hannuwansa na sumbaci 'yan yatsunsa. Ya ce mini, "Ya Abu Muhammad, biyo ni zuwa gidana." Na amsa masa, "Na ji, na karɓa." Ya shige gaba na bi shi a baya, har muka isa gidansa. Ya ɗauko dukkan kuɗin nan da ya samu ta sanadin biri, da kuma kayan jauhari da birin nan ya tsamo cikin ruwa, ya ba ni. Ya ce mini, "Karɓi wannan, duka naka ne. Su ne ribar da aka samu daga dirhaminka biyar da ka ba ni." Ya kwashe labarin abin da ya faru yayin tafiyarsu ya gaya mini. Ya ɗauko akwatuna ya sa mini dukkan dukiyata cikinsu ya kulle. Ya kira wasu bayinsa ya ce su ɗaukar mini zuwa gidana. Ya kawo mabuɗan akwatunan ya ba ni. Ya ce, "Tafi da wannan dukiya, dukkanta mallakarka ce." Na tafi da dukiya wurin mahaifiyata na nuna mata. Ta yi matuƙar farin ciki, ta ce, "Ya ɗana, lokaci ya yi da za ka watsar da wannan kasala taka. Ka ga dai yanzu Allah ya arzutaka da

Table of Contents

Chapters

9 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9