Chapter 1
Chapter 1
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng 1ARZIKI RIGAR ƘAYA (1) HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA Sarkin Bagadaza, kuma Sarkin Musulunci, Halifa Haruna Rashid na zaune kan karagar mulki ya harɗe, fadawa kuwa sun kewaye shi ana tsakiyar fadanci sai ga wani saurayin bawa ya shigo riƙe da wata hula da masu mulki ke sanyawa. Ita wannan hula ana kiran ta kambin sarauta. Wannan kambi da bawa ya shigo da shi an ƙera shi da jan zinari aka yi masa ado da lu'ulu'u da jauhari da dukkan duwatsu masu daraja, amma ba a rufe saman shi ba. Wannan kambi babu tamkarsa a wannan zamani, kambi ne da kuɗi ba zai iya saye ba. Bawa ya faɗi gaban Sarki ya yi gaisuwa, sa'annan ya ce, "ya Sarkin Musulunci, Uwargida Zubaidatu ce ta aiko ni gare ka da wannan kambi da ta sa aka ƙera mata. Ga shi an kammala ƙera shi, ta nemi jauharin da za a liƙe saman shi, ta kasa samun wanda ya yi daidai a cikin taskarta, duk wanda aka gwada sai a ga ya yi ƙarami." Sarki ya dubi barori ya ce a tafi a dubo irin jauharin da Zubaidatu ke buƙata. Barori suka zabura da hanzari suka tafi. Can jimawa sai ga su sun dawo. Suka ce wa Sarki, "Allah ya taimake ka, mun duba taskar Sarki duka, amma ba a samu jauharin da ya yi daidai da wannan hula ba." Halifa ya fusata ya ce, "ta yaya Sarki kamata, wanda ya mallaki sarakunan duniya duka, ɗan ƙanƙanin abu kamar wannan ya gagare ni mallaka. Kaicon ku! Ku tafi cikin kasuwanni, ku binciki dillalai da tajirai da fatake, maza ku nemo wa uwargida abin buƙatarta." Barori suka fantsama cikin kasuwannin Bagadaza suna cigiya, har Allah ya gajishe su ba su samu jauhari mai girman da suke buƙata ba. Suka dawo gaban Sarki suka ce, "ya Sarkin Musulunci, wannan abu ya wuyata ga tajiran wannan birni da fataken da ke shigowa. Amma an ba mu labari cewa, ba za a samu wannan jauhari gun kowa ba, sai wurin wani attajiri ɗaya da ke zaune a birnin Basara mai suna Abu Muhammad Kasala." Yayin da Halifa ya ji wannan zance, sai ya umurci wazirinsa, mai suna Ja'afaru al-Barmaki, da ya rubuta takarda zuwa ga Hakimin Basara, Muhammad al-Zubaidi, ya faɗa masa cewa, maza-maza a zo masa da tajiri Abu Muhammad Kasala zuwa Bagadaza. Nan take Waziri Ja'afaru ya ɗauki takarda da alƙalami ya rubuta saƙon Sarki zuwa ga Hakimin Basara. Ya buga hatimi kan takarda ya naɗe ta, ya danƙa wa Masrur as-Siyafi, babban haunin Sarki. Wanda shi kuma nan take ya yi shiri tare da 'yan rakiya, suka rankaya sai birnin Basara. Hakimin Basara ya tarye su da murna, ya shirya musu gara, suka sharɓa. Bayan sun huta sai Masrur ya ce wa Hakimin Basara, "to, ba fa zama muka zo yi ba." Ya zaro takarda, ya karanta wa Hakimi saƙon Sarkin Musulmi. Hakimin Basara ya ce, "na ji, na karɓa." Nan take ya shirya wata tawaga ya haɗa su da Masrur suka nufi gidan tajiri Abu Muhammad. Da isar su gidan sai suka ƙwanƙwasa ƙofa. Wani bawa ya buɗe ƙyaure ya leƙo. Masrur ya ce masa, "je ka wurin ubangidanka ka faɗa masa cewa, Shugaban Muminai na nemansa zuwa Bagadaza." Bawa ya koma cikin gida. Jim kaɗan sai ga tajiri ya fito. Ko da ya ga Masrur tare da tawagar Hakimin Basara, sai ya faɗi ya yi gaisuwa, sannan ya ce, "na ji, na kuma karɓa kiran Sarkin Musulmi. Amma ba kwa shigo daga ciki ba, ko ɗan ruwa ku kurɓa kafin na kimtsa mu tafi?" Masrur ya ce, "ai ba dama, sata lahira! Halifa na can na jiran mu. Don haka babu buƙatar ɓata lokaci. Maza shirya ka fito mu tafi, kafin ran Halifa ya ɓaci." Tajiri ya ce, "to bari na shiya yanzu mu tafi, amma ku shigo daga ciki ku zauna, kun san an ce shirin zaune ya fi na tsaye. Idan na shirya kuma na samu ɗan guzurin da zan kai wa Halifa, domin zuwa da wuri ya fi zuwa da wuri-wuri." Ya yi ta lallashin su dai, har suka yarda suka shiga cikin gidan. Da kutsa kansu cikin turakar farko ta gidan, sai suka ga an daje duka bangayen nan da labulayyen alharini wanda aka yi wa cin baki da ɗanyen jan zinari, aka ƙawata su da duwatsu masu ƙyalƙali da daukar ido. Abu Muhammad ya umurci ɗaya daga cikin bayinsa da ya kai Masrur bayi, ya yi wanka, ya fitar da ƙurar tafiya daga jikinsa. Bawa ya yi wa
Table of Contents