Skip to content

Chapter 8

Book one

Maradams Book One Complete Hausa Novel 4,395 words 0 views Progress saved
Download Book

Free page

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO

bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 8

"Ahankali  take tafiya cikin sand'a  tamkar   wata  'barauniya  yana   hankalce  daita  duk da idanunshi a runtse  suke amman bazaka ta'ba gane hakan ba  sai wanda yayi masa cikakken sani , da d'an sauri   ta nufi  hanyar d'akinsu  tana sauke numfashi  Tare da ajiyar zuciya ,ta cire mayafinta ta wula saman katifa sannan ta samu waje ta zauna tare da rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa zuciyarta a matukar tsorace take  duk da tasan ba wani laifi tayi ba amman tasan tsoronta baya rasa nasaba da muguwar kiyayya da tsana mai tsananin  da ya adam yayi mata  tayi shiru tana sake zurfafa tunaninta sam  bata hango ta inda zata iya amincewa aurensa ba gara kowa yaje ya nemo abokin rayuwarsa a waje
domin rayuwar aure dashi daidai yake da kamuwa da cuttutuka kala dabam dabam ."

       "mr ATA ya cigaba da zama a parlour'n yana karkada kafarsa daya har sanda  hajiya  zulaiheart ta shigo parlour'n fuskarta a sake amman ganin  yanayinsa yasa ta d'an shiga damuwa muryarta a raunane ta soma mgn "Adamcy nah  har ka dawo ? ya had'e rai sosai  tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa  tare da gyada mata Kai kawai batare da yayi magana ba "Lafiya naga duk kayi wani iri ?fuskarshi a murtuke ya soma magana cikin tsananin fushi "wa yace waccen yarinyar tayiwa saurayinta masauki  akan  kujerun zamana ?mami ta numfasa irin nasu na manya kana tace " ban da abunka Adamcy wa zai sa tayi haka ?" ta dai yi haka né dan tayi ra'ayi  tô ma  menene aciki dan ta zauna da bakonta  akan kujerarka kwana nawa ne ma ya saura ?"ni  dai babu ruwana da wani kwana nawa ne   ya saura ni dai banaso  dan  ba ra'ayi bane kawai  raini  ne  idan ba haka ba kujerun da  nake zama akai shine ya zama na zancenta?yayi maganar yana shan kamshi ."

"Kai dai wallahi anyi rigimamme wannan zuciya wannan zuciya !! Allah ya sausauta maka, bakaken magana ya dinga fad'a akan maryam batare da yayi la'akari da matsayinta a gurin mahaifiyarsa ba  mami batace komai ba har sanda ya dasa aya sannan ta kira sunansa a tsanake  "Adam !bai amsa ba illa ya tsura mata kwayar idanunshi dake cike da bakinciki yana kallonta ta sake kiran sunansa "adam ! "a karo na biyu  shiru yayi still yaki amsawa tunda yayi haka tasan bazai amsa ba yasa ta soma magana cikin kaukausan murya "zaka iya yin komai da kake so  amman at least kayi respect din emotion din wani idan kai baka  son maryam ka girmama masu sonta  kuma naji dadi da hakan ya faru domin kasan diyata  ba rasa masoya tayi ba yasa zan  hadaku aure."

wani kallo yayi wa mami yana mai rausayar mata da kwayar idanunshi cikin nata muryarsa can kasa yace  "alright  sweetheart amman da me zai hana ku  bar masa ita  ya aureta dan zata fi bukatarsa   da duk wani abinda kuke bukata daga gurina "tabbas nasa zata samu, zata samu duk wata kulawa a wajen duk wanda ta aura acikin masoyanta domin kuwa suna mata   tru love  most especially lawan kalli kaga irin abubuwan daya zo mata dashi ."ta fad'a dan qara masa haushi dan babu abinda ya tsana sama da wannan arayuwarsa ,ai kuwa tayi nasarar takalosa."

     " He most be a fool  da har yake bayyanawa common mace emotiona dinsa  ta wannan hanyar , Kinsan allah sweetheart  ko mafarkina na hadu daita a zahiri bazan iya mata  irin wannan haukan ba ta zabga masa harara alokacin da yake kokarin yunkura wa  zai mike  ta dakatar dashi "adam !koma  ka zauna ya koma ya  zauna a kufule yana dubanta "kowani dan adam da yadda yake irin tashi soyayyar idan kai abubuwan bai maka ba watakilla su samarinta  ya masu ,dan  kyauta yana da matukar kyau ga masoya domin yana qara damkon soyayya  dan haka kar na sake jin  ka fadi haka ,kai kullum kana yin kuskure amman kai gani kake daidai kake aikatawa ,kowani dan adam yana kuskure amman wannan bana tunanin akwai wani kuskure acikisa sai ma kyautatawa soyayya sam  sam bana jin dadin abinda kakeyi ...."

"to ku aura mata shi dan allah kunga ni  na huta daman ni wallahi bana sonta dan wannan auren babu abinda zai jawo sai damuwa I really has to tell you the truth before everything could mess up ya fad'a a matukar zuciye ."murmushi hjy zulai tayi dan gbdy ta fahimci dan nata haushi yaji koma tace kishi yake yaga maryam da wani ,ta  girgiza kai "ai kasan bana magana biyu tunda muka tsaida  magana  da mahaifinta idan kaga baayi auren nan ba to mutuwa nayi ,idan ba mutuwa nayi ba kuwa na rantse da girman allah  adamcy sai ka aureta kai ko yau na mutu a daura maka aure daita zan bar wannan wasiya  maryam takace ta har abada haka zalika kaima nata né mutuwa ce kawai zata rabaku sannan kai ma muna jiran naka gift din soyayyar tunda ka kamu  idanushi ya ware sosai akanta  yana kallonta a rude tare da furta kalmar "what ?

" your gift !
ta fad'a tana tsare shi da idanunta "Allah ya tsareni da wannan shirmen hau..."shut up Adamcy ai baka da wannan bakin dan ka rigada ka haukace tunda kake son abinda babu shi a duniya kuma lallai ka tabbatar da ka kawo naka gift din soyayya ranka shi dade a matukar zuciye ya juya ,da sauri sauri ya dinga taka step zuciyarsa kamar ta kama da wuta ta sake saida shi "adamcy nah !wannan karon a fusace ya juyo kamar zai yi kuka  yace "what again ?  "kaje kayi wanka ga dinner dinka ya kammala "bana bukata ya fad'a a kufule  ."this is totally nonsense my love ta furta tana sakar masa murmushi dan tasan bancin itace da abinda zai fad'a kenan a fusace ya sake  juyawa  yana girgiza kai ."

Hjy zulai zaune  tana sake duba  kayan da lawan ya kawo  ta kiran maryam ta fito da sauri tana amsawa cike da girmamawa "maza tattara kayanki ki kai daki  shi kuma Lawan din kin fad'a masa an tsaida miki miji dan ya daina wahalar da kanshi ? ta sauke numfashi sannan  ta girgiza mata kai alamun" a'a ! "okay kice masa yazo gobe ina son ganinsa ta gyada mata kai kawai ta tattara kayanta ta shige dakinsu cike da zullumi ta bar Hjy zulai cikin zullumin wannan auren da take kokarin hadawa sam sam
bata jin maryam domin ita din yarinya ce mai tsananin biyayya da hakuri akan komai adam take ji tasan shi tasan halinsa shine matsalarta tunda yace bai só tô har cikin ranshi bai só né sai ta tashi tsaye da rarrashi da addua ,zata bari adduarta yayi karfi da sadaka , sosai tayi zurfi cikin tunani ."

Bayan kamar  wasu mintuna ya fito sanye  da wasu kayan wondo da riga farare sol kana ganin shigar  kasan fita zai yi ,lokacin daya sauko parlour'n babu kowa zuciyarsa nayi masa wani irin zafi kamar zai fito waje ,sai dai ya  kasa fita koina Kmr yadda yayi niyya ya bude bayan motarsa  ya shiga ya zauna yana sake jin bacin rai mara iyaka yana marmarin shan sigari domin shansa na rage masa bacin rai sai dai tunanin illarta yasa baya son yawo daita domin yana bukatar ya bar shanta na har abada ." mr ATA  bai shiga  gidan ba sai karfe shabiyu  na dare yana daf da  wucesu ya haye step  yaji sautin muryar mami  "adamcy  !cak ya tsaya yana ciccin magani "zakazo ne ranka dade koni na taso nazo ?"tayi mgnr cike da tsokana."

jin ta fadi haka ya soma qokarin qarasowa inda take su maryam naganin hk duk suka mike suka kama gabansu  byn sun masa sannu da zuwa bai amsa masu ba ya cigaba da tsayuwa "zauna ta nuna masa wuri kusa daita "laifin me mahaifiyarka tayi maka da ka dauki  fushi mai tsanani daita ?
"what ?!
"Yes fushi kake daita mana tunda gashi kaki cin girkin data sha wahala ta girka maka da kanta sannan ka tsallake ka bar gidan nan  tun 9:00  sai yanzu batare da kai mata sallama da zaka fita ba wanda hakan ba dabiarka bace muddin kana kasar nan duk inda zaka sai ka sanar min  sannan ka dawo km kana kallona zaka wuce baka da niyyar ce min komai ya dan kalleta ta kasan idanunshi yana cewa "Wannan  yake nufi ina fushi dake ? yayi mgnr a shagwabe Kmr zaiyi kuka ?shine mana idan ba fushi kayi ba fad'a min abinda kayi ?shiru yayi kawai dan bai san me zai ce ba dan fushi fushin yayi dan bai ga dalilin da yasa zata dinga tura masa yarinyar da tasan yafi tsana arayuwarsa wanda shi kansa bai san dalili ba ."

maryam ta lallabo ta fito daga dakinsu ta rabe a gefen step "uhm ina sauraronka shiru ne dai ya sake biyowa baya "ina gift din din  soyayyar maryam "? ya zaro ido sosai  yana kallonta  "haba sweetheart wai me yasa kike min haka ne ?"what did I do to you? yayi shiru yana kallonta Kmr zai yi kuka ta sake bude baki zatai magana yayi saurin dakatar daita .
   "Dan girman allah  sweetheart ki daina hadani da yarinyar nan kin ce na aureta naji na amince yanzu kuma zaki sake hadani da wani sabon aiki kina son na mutu ne tun kwanana bai qare ba ?tai mur mushi irin nasu na manya "mafarkinka bai kasheka ba sai mutun a zahiri ne zai kasheka?"

" adamcy wallahi ka canza rayuwa  ina guje maka hakin mata akanka." yay shiru kawai yana kallonta "yanzu sweetheart fatan da kike min kenan ?me nace maka nace ka canza sai kace zaka canza ko ba shikenan ba ,ni ai kasan bazan ta'ba maka mummunar fata ba amman dan allah ka canza kaji masoyi ta riko hannunsa   cikin nata shima ya daura hannunsa akan nata " naji zan canza Kiyi hakuri da duk abubuwan da nake yi wanda bakya jin dadinsa maryam ta kasa kunne sosai ko zataji abinda suke tautaunawa amman babu abinda taji dan can kasa kasa suke mgnr zai mike  Hjy Zulai tace "abinci fa ?akoshe nake "me kaci dan nasan baka cin abinci a waje ? Kawai dai bana felling cin komai  amman da zan samu tea mai dan kauri zan sha ya fad'a a yatsine ta girgiza masa kai alamun taji  tare da kwallawa maryam kira "ya salam! ya furta yana dukar da kanshi kasa dan bai so haka ba sam baya son abinda zai shi kallon fuskarta ".a natse ta qaraso tana cewa "mami gani ."

"Dan Allah maryam hadowa wannan sarkin zuciya tea mai kauri "to mami ! ta juya a hankali ta nufi inda kayan tea yake ta hado ta dawo a natse dan tasan halinsa abu kadan Ke hassalashi bare ita data kasance makiyayiyarsa ko batayi kuskure ba zai iya maidashi tashin hankali "mami gashi ,Yauwa maryam sannu da kokari kinji mika masa" tayi Jim tana jin faduwar gaba da tsoron mai tsanani numfashi ta sauke a boye na samun sausauci tunda mami na gurin komai zai zo da sauki bazata bari wani mummunar abu ya same ba ,bazata bari ya tozartata ba no matter how zata tsawatar idan taga zai yi wani abu jiki a sanyaye ta mika masa tana cewa "yaya ga..."Banza yayi tamkar bai ji ba nan kuwa yaji haushi ne yasa bazai karba ba " maza  ka karba ka shanye ka miko min cup still kin karba yayi ko kaukauran motsi dainawa ya yi a zaunen da yake ma idan ka kallesa ma zaka dauka baya numfashi ne "ka kar'ba mana "sweetheart bana sha ya fad'a yana fusrzar da iska mai zafi ran mami ya soso tasan yayi haka ne dan maryam ce ta hada "amamn kace zaka sha "yanzu na fasa babu yadda mami bata yi dashi amamn yaki  ya karba ya shan akarshe ma ya mike ya mata  sallama  ya nufi saman dakinsa bata amsa masa ba tabi bayansa da kallo har ya bacewa ganinta gbdy mami ta rasa meke mata dadi shiru tayi tana jin bacin rai har sai datayi datasanin kiran maryam amamn ita tayi haka ne dan su dinga samun kusanci da juna, ganin yadda mami ta shiga damuwa yasa maryam ta zauna inda ya tashi ta fara shan tea tana cewa "mami tunda baya sha bari ni na sha daman cikina empty ne shiru mami tayi tana kallonta ita dai bata fushi akan komai "mami dan allah karki damu kanki akan dan wananan abun da bai ya kawo ba "dole na damu maryam mutun Kmr mai zuciyar dutse ?dan Allah kar wannan abu ya dameki nima da yayi dani ban damu ba wallahi ahankali ta dinga kwantar wa mami hankali ."

Cike da  natsuwa ya tura kofar dakin ya shiga ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerar cushion dake dakin  dafe da goshinsa yana furta oh my goodness god wai me yasa sweetheart bazata bar zuciyata ta huta da wannan yarinyar ba ?me yasa abubuwa suke faruwa dani ne komai ya zama worst a gareni ?daman har yanzu anayin auren dole ne bare shi daya kasance nmj "me yasa bazaa barshi har zuwa lokacin da yayi raayin ba ?shine tambayoyin da ya dingawa zuciyarsa ya dauki wasu mintuna zaune sannan ya fara cire kayan jikinsa ya shiga bathroom ya watsawa jikinsa ruwa ya fito ya sauya kaya zuwa na bacci ya hau gado ya kwanta shiru yana tunanin wannan auren da mahaifiyarsa ke bukatar yayi bai wani jima ba bacci ya daukesa  hannuwansa duka  a saman  qirjinsa ."

Washegari "10am ya sauko daga bed dinsa yana mika bakinsa dauke da addua kai tsaye bathroom ya shiga yayi refreshing kansa tukuna sannan ya saka wasu hadaddun kaya wando da Riga suit  duk brown colour shiru yayi lokacin dayazo saka takalminsa domin kusan lokuta dayawa adaidai wannan lokacin mami ke shigowa dakin akarshe ita Ke saka masa ya numfasa ya shan iska komai nashi tô mach yayi har glass din dake manne da idanunshi ya kwashe wayoyinsa ya sauko cikin takun isan nan nashi ya soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa tare da jin kai yana neman inda mami take "sweetheart ! ya kira sunanta bai ji ta  amsa ba ita kuwa tajishi Sarai tayi masa banza dan haka ya nufi hanyar kitchen  dan nan yafi tunanin take idanunshi suka sauka akan hjy zulaiheart cikin shiga na alfarma ."
        a natse ya shiga kitchen din inda masu tayata aiki suka soma kokarin gaishesa sai dai babu wacce ya amsawa acikinsu wanda daman idan da sabo sun saba da yanayinsa ,ya qarasa ya tsaya bayan mami ya daura kanshi a kafardarta yana mai lumshe lumtsatsun idanunshi "my sweetheart good morning?

"Morning! ta fad'a atakaice tana hade rai
"Hope you had a great night? bansani ba kamar yayi murmushi amman ya maze yana cewa "sweetheart kamshin girkinki  so nice tare da kai hannu zai bude kular gabanta "don't open! shiru yayi tsaye shi bai ajiye murfin ba  shi bai rufe ba ya sake kokarin budewa "I said don't open "kullum aikin  kenan yabon girki amman ..." bai san sanda ya tamke fuska ba ya katseta da sauri "you're worst sweetheart ! naji muje parlour'n tunda ka hanani magana dan ban san abinda ya shigo da kai kitchen ba sai ka gama batawa mutun rai kazo kana salo" ya sake hade rai  sosai tamkar an aiko masa da sakon mutuwa "me nayi km ?"Bansani ba wallahi adamcy idan baka kiyayeni ba to tayi kwafa kawai bai sake cewa komai ba ya juya ya fita daga kitchen din ransa a matukar bace dan yasan akan abinda yayi jiya ne yasa tayi masa haka dining ya qarasa ya dauki cup din tea dinsa da chocolate cake yaci duk da shi din ba mai son zaki bane sosai bai jima ba mami ta shirya masa breakfast "your breakfast is ready "am okay ya fad'a ransa a hade  sannan  ya mike tsaye tun kafin tace wani abu ya fita zuwa haraban gidan ya nufi motar daya bada umarni yana son shiga Range Rover black color driver yajashi suka fita zuwa babban  office dinsa kai tsaye ."

*******

Yauma kamar jiya  maryam tana zaune akan kujerar mr ATA  tare da  saurayinta abbas ta tsura masa idanunta tana kallonsa tana kallon yadda yake  sauke numfashinsa ,muryarsa cike da kasala ya soma fadin "ina matukar  sonki maryam da'ace mutun ya Kan iya  shiga zuciyar mutun ya gani hakika da kin shiga tawa kinga irin zallar soyayyar da nake miki  amman ni nasan bakya sona maryam  kamar yadda nake miki wahalar da kaina kawai nakeyi ."
     "yaushe na furta maka  bana sonka abbas ?Ko na taba furta maka haka ?ta fad'a tana hade hannuwanta wuri daya tana kallonsa" tabbas da zata tsaida mijin aure cikin masu sonta da aure to data tsaida abbas domin kuwa yafi sauran dama dama kuma ya dan kwanta mata arai "yadda tayi shiru tana kallonsa haka shima yayi shiru yana kallonta yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa akanta "me yasa kayi  tunanin bana sonka abbas ?ta katse shirun dake tsakaninsu ta hanyar fadar haka ."abbas !ta kira sunansa ya tsura mata ido kawai "kamar yadda kake sona nima ina jin wani abu akan..."

"Shiiii !"shima ya katseta "sam ban yarda da abinda zaki fad'a ba maryam zuciyar dake son mutun bata banza dashi dan haka karki fad'a min cewar kina jin wani abu akaina dan bakyasona maryam , ban  ma ta'ba ganin soyayyata acikin kwayar idonki ba sau nawa zan kiraki sai kinga dama Kike dauka ?baki ta'ba tunanin ki kirani a duk tsawon lokacin da muka dauka koda kuwa zan shekara ban kiraki ba  , duk wata alama ta soyayya da mutun maryam bakya nuna min hakan kawai ya ishi ne hujja amman ni nasan tabbas ina sonki dan allah karki boye min abinda Ke ran..."

Wayarsa ta soma ringing wanda sanadiyyar hakan ya katseshi ahankali ya dan zame hannu shi ya ciro ya duba dan zabura yayi ganin mai kiransa maryam ta dago ido tana dubansa ya dauki wayar ,bata ji yace komai ba sai "to gani nan ya riko hannun maryam cikin nashi adaidai lokacin da mr ATA Ke qoqarin qarasowa gurin wanda wannan ne karo na farko da hakan ya faru "ki kulamin da kanki na samu wani kiran gaugawa ne amman zanzo dawo zuwa gobe mu qarasa maganarmu ina sonki mar..."giftawar mr ATA ya katseshi tayi saurin zare hannunta dake cikin nashi jikinta na daukar rawa ,abbas ya dan bi bayan mr ATA  da kallo sannan yayi mata sallama ya wuce ya bar zuciyarta cikin tashin hankali."

jiki a matukar sanyaye ta shige ciki yana zaune akan kujera kusa da mami sai dai kana kallon fuskarsa kasan yanayinsa babu alamun rahma bata tsaya ba ta nufi hanyar dakinsu mr ATA ya dago lumtsatsun idanunshi da suka canza kala wanda suka nuna tsantsar bacin ran da yake ciki ya zubawa mami sannan ya fara magana a natse sai dai mgnr tattare yake da 'bacin rai byn kmr mintuna goma  sai ga maryam tare da nana hauwa'u sun shigo daskarewa tayi agun zuciyarta na rawa ,kamar ta juya saboda rawar da jikinta yake sai Kuma ta sanyawa jikinta jarumta ta cigaba da tsayuwa tana sauraronsu ,
"wallahi da tasan yana parlour'n har lokacin bai tashi ba bazata dawo ba batare da bata lokaci ba ta fahimci maganae da  mami keyi akanta ne ."

cikin sanyi jiki ya mike tsaye ya soma taku da kyar fuskarsa har lokacin a murtuke take  ya jingina jikinsa da bangon parlour'n yayinda idanunshi ke kallon screen din wayarsa "wa yace ki sake zama
min akan kujera da wani gardin banza  har kuna taba juna dan ku din tattun yan iska ne ?tayi tsuru tsuru tana kallonsa  hantar cikinta na kad'awa da jin kalmar daya jefesu dashi "wannan shine first and last karki yarda ki sake zama min akan kujeru dan ba dan ke na tanadaisu ba koni sa'anki ne ?"tayi saurin girgiza masa Kai kamar ta durkusa ta bashi hakuri dan ya bar zuciyarta ta hutu sai ta daure taki aikata hakan "ban tanadi kujeruna dan wata gardiya da garden banza su zauna suyi iskanci akai  ba "adamcy ! no sweetheart bari na fad'a mata taji ko auta tayi min wannan ganganci sai na ballata wallahi bare wannan useless din ya fad'a yana nunata da babban d'an yatsa hannunsa" idan mutun ya sake min ganganci nima zan masa ganganci aikin banza kawai zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata yayinda tuni hawaye ya soma bin kuncinta "yanzu irin mutumin daake son tayi rayuwa ta har abada kenan ? mutumin da  duk duniya babu abinda ya tsana  kamar ita  burinsa bai wuce ya wulakantata ya tozartata ba  lallai duk yadda zata gujewa wannan hadin zatayi koda kuwa zai zama sanadin rasa rayuwarta ne tun yanzu ma ya kamata tasan abun yi bazata iya ba ,zuciyarta bazata iya   daukar wannan wulakancin ba ta bud'e baki  da niyyar kare kanta kar mami ta dauka maganarsa gsky ce taga tuni har ya  wucewarsa yana jan dogon  tsaki ."

idanuwanta suka ciko da hawaye  cikin rawar murya ta soma "ma..mami wallahi abinda ya fad'a ba gsky ba.."kukan da take ya hanata qarasa maganar nana hauwa'u ta matso kusa daita tare da rike kafadunta
"da Allah meye abun kuka bayan kowa ya San halinsa muje please nana hauwa'u ta janyota suka koma cikin d'akinsu tana rarrashinta "Ina ganin lokacin barina gidan nan yayi zan koma Abuja da zama duk sanda yake gidan nan  bana samun sukuni"wallahi babu Inda zaki idan yayi miki ki daina nuna kina jin tsoro dan hkn da kike nunawa  power kike Qara masa idan yayi miki ki rama duka shekara nawa ya bawa mutune duka fa 9 ne ..?" "naunayen ajiyar zuciya ta sauke "bazan iya daukar shawararki ba sister "manta da wannan maganar yanzu dai ya kuka kare da abbas  ?wallahi ya bani tausayi gbdy na kasa fad'a  masa gskiya sbd ina dan jin wani abu akansa "kenan kina son shi  ?
Ta girgiza mata kai alamun a'a "ina jin wani abu akansa baya nufin ina son shi bane "tunda bakya son ya Adam shi me yasa bazaki bashi dama ba ?"

shiru tayi taki cewa komai "heeeee maryam kiyiwa kanki karatun ta natsu yanzu maza wahala suke karki ga wai iyayenmu nada arzki irinmu wahalar auruwa muke amman Kya kare a auren ya Adam din tunda baki da wanda kike so tana gama fad'ar haka ta d'auki wayarta ta shiga yanar gizo "kisa akawo mana abinci yunwa nake ji sosai ,abincin na fita ci wannan mai dacin zuciyar ya bata min rai " da idanu Maryam ta bita tana jinjina Kai ta d'auki waya ta kira layin kitchen ta bada umarni .
ko cikakken minti biyar ba'a yi ba mutun biyu suka shigo cike da girmamawa suka ajiye tiren abinci da lemun irin wanda suke sha suka juya nana hauwa'u ta bud'e kula ta zuba abinci ta soma cin mrym tana dubanta ."kici abinci mana kin tsaya tunani "jiki a sanyaye mrym ta soma tsukura tana ci tana fargaban sake haduwa da ATA  gara tayi ta gudu tun sakon rashin amincewa aurensa ya Isa kunnensa ya sake  damarar cin kaniyarta koma asani ne tsanar ya qaru"?

Bayan kwana biyu
Mr ATA na kwance akan kujera mai zaman mutun uku a parlour'n hjy zulaiheart ta samesa ta zauna a kusa dashi ta soma magana cikin sanyin murya "kana son ginawa kanka rayuwa na gari dole sai kayi hakuri shiyasa kullum nake bukatar naga kayi aure domin ka zama magindaci saboda hakan zai sa ka canza , mata da ya'ya zasu canzaka saboda qaunar dake tsakanin iyaye da yayansu , Adamcy ka canza Sam bana jin dadin yadda kakewa Maryam acikin gidan nan ko babu komai Maryam yar'uwaka ce Kai yanzu kana ganin da wannan zuciyar zaka samu macen da zata iya zama da Kai ?bari kaji Maryam ce kawai zata iya zama da Kai saboda tana da zurfinn hakuri sosai ,zata yi hakuri da halinka da wannan zuciyartaka ko dokin zuciya ka hau nayi Imani zata san yadda zata faranta maka ka sauko , ka tausaya min Adamcy Kai kadai Allah ya bani namiji acikin ya'yana banason na mutu na barka da wannan zuciyar ta k'arasa maganar kmr zatayi kuka yayi saurin ya mike zaune daga kwance da yake ya  kamo hannuwanta cikin nashi "kiyi hakuri sweetheart karki min haka karki zubar da hawayenki akan wannan matsalar shikenan komai ya wuce ai farincikinki shine nawa inshallahu zan canza Kuma zanyi duk abinda kike so ya karasa maganar yana zamewa ya d'aura Kansa akan saman cinyarta .
Sanyayyayen ajiyar zuciya ta sauke na farinciki ta d'aura hannunta akanshi tana shafa sumar kanshi "Allah yayi maka albarka ,Allah yaye maka damuwarka Allah ya sausauta maka zuciyarka
Allah ya baka zuria masu albarka kuma ya nuna min wannan lokacin, nifa a son raina ma mata biyu naso aura maka a rana d'aya, d'aya diyar talaka d'aya diyar shararran hamshakin mai arziki ."

yayi murnushin gefen baki wanda ita kadai Ke iya ganin hakan ya lumshe lumtsatsun idanunshi yana cewa "lallai sweetheart kina ji dani "sosai kuwa Adamcy nah ai shiyasa kake min salo saboda kasan Kaine zuciyata "Nima kece zuciyata rayuwata sanyin idaniyata Ina sonki fiyye da komai  " a hankali suka dinga hira mai kwantar da hankali daga karshe ta d'auke kanshi ta daura masa akan pillow kujera "thank you my sweetheart "you're welcome my happiness ta fad'a tana mikewa ".
Ko cikakken minti ashirin bata yi ba ta had'o masa abincinsa yana ganin dawowarta ya mike
yana murmushi "sannu da hidima dani sweetheart ",yanzu kam sauran kwana nawa na huta ta fad'a ta janyo karamin stood gabansa ta ajiye "bismillah kaci ya narke mata fuska "yau daya kaci da kanka ya lumshe mata  lumtsatsun idanunshi kana ya soma ci a hankali "kalli cin abinci so nice my dear komai naka dabam ne bai ce komai ba ya cigaba da kai abinci bakinsa tayi gyaran murya ya dan kalleta domin jin abinda zatace tayi shiru dan haka ya d'auke kanshi ya sake Kai abinci bakinsa ."baka ga ya kamata ka fara jan yarinyar nan maryam ajikinka ba"? " ka dinga janta kana kiranta hira ta haka ne zaka...."wani irin tsarkewa yayi ya fara tari  babu kaukautawa "sorry !! ta fad'a tana bud'e rabon ruwa .."

Mmn sudais

💗💗💗💗💗💗
    MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

Table of Contents

Chapters

10 chapters
  1. 1 Book one
  2. 2 Book one
  3. 3 Book one
  4. 4 Book one
  5. 5 Book one
  6. 6 Book one
  7. 7 Book one
  8. 8 Book one
  9. 9 Book one
  10. 10 Book one