Chapter 3
Book one
Free page
*AYSHA A BAGUDO*
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page3
......da wani irin sauri mr ATA yayi saurin d'auke kwayar idanunshi akansu yana juya baya tare da jin wani zafi mai tattare da bakin ciki, gabadaya ya rasa me Ke masa dadi arayuwarsa a halin yanzu babu fuskar daya tsani gani kamar fuskarta ."daga Inda maryam take bata sake yunkurin qara taku daya ba ta cigaba da tsayuwa a waje daya qirjinta na bugawa da matsanancin karfin gaske sbd tsananin tsoronsa ."wannan dalili yasa dole shima muhd bello ya tsaya anan suka qarasa maganarsu ta juya da sauri ta koma ciki ranta duk babu dadi kallonta nana hauwa'u tayi tace " ba dai har kin dawo ba ? ta fad'a haka ne sanin da tayi duk lokacin da suka ke'be da ya muhd bello suna daukar lokaci suna tautaunawa dan jininsu ya had'u sosai dashi ."
maryam bata ce mata uffan ba tsabar bakinciki dake kunshe acikin zuciyarta nana hauwa'u ta cigaba da magana tana dubanta a tsanake "halan ya adam na waje ne naga kin shigo fuskarki wani iri ? ta'be lip's dinta tayi tana cewa " ai kema kinsani idan ba ganinsa ba me zai sa fuskata tayi haka ta sauke naunayen ajiyar zuciya " sister na rasa dalilin wannan tsana da ya adam yayi min ,wannan abu na matukar ci min rai ina jin kamar na tattara na bar gidan nan na huta da ganin irin kallon tsanar da yake min kamar ni kadai ce acikin gidan nan ? " tsana kamar ya kashe ni."
"haba haba !! sister dan me zaki fadi haka?" ai ba ke kadai yakewa haka ba , ki daukeni misali ma kawai ya isa ki kwantar da hankalinki , ba ke kadai ya adam yakewa haka ba shifa tsanarsa kowa yake wa "maryam ta sake tabe lip's dinta "kowa yake wa amman wallahi nawa yafi na kowa nifa ko kallona baya qaunar yayi na rasa me na tsare masa arayuwa kamar fa ya kasheni haka nake gani acikin kwayar idanunshi nana hauwa'u tai murmushi kawai "kisan ma abinda ya qara kona min rai ne ?nana hauwa ta girgiza mata kai "alamun a'a " wai yana hangomu nida ya muhd bello mutumin nan ya juya mana baya da sauri kamar yaga wani mugun abu ,wallahi bakiji yadda na muzanta ba gabadaya kasa cigaba da tafiya nayi " nana hauwa'u ta kamota zuwa Kan kujerar da take zaune ta zaunar daita tana murmushi a hankali ta shiga kwantar mata da hankali tana kawo mata misalai iri iri dan bata son abinda zai sa maryam ta bar gidan dan ko babu komai abubuwanta na social media na sakata nishadi shiru kawai maryam tayi tana sauraronta ."
muhd bello ya k'araso Inda Mr ATA yake tsaye ya Kai hannunsa d'aya ya dafa kafad'arsa ya juyo dashi a hankali ya tsura masa idanunshi fuskarsa kwance da murnushi yace "why ATA ? "me yasa kake quntatawa rayuwarka ?"me maryam ta rasa ? "me yasa bazaka bi zabin mahaifiyarka da yan'uwanka ba ? ya lumshe lumtsatsun idanunshi yana furzar da iska me zafi daga bakinsa "kasan komai akaina m.b tun daga farkon rayuwata har zuwa yanzu da nake tsaye a gabanka babu abinda baka sani ba ..."
Na sani ATA ! ya fad'a yana sake matsoshi sosai " Amman at least ka duba lamarin mahaifiyarka da yan'uwanka sun dauki tsawon lokaci da baka dama amman shiru babu wani bayani amman yanzu tunda suna sonka da maryam ka amince masu ka sota ."
shiru mr ATA yayi yana masa wani irin kallon up and down "ka amince masu ka sota " kwalkwa
luwarsa ta maimaita masa abinda ya fad'a yanzu kafin a hankali ya kai hannunsa daidai saitin zuciyarsa da yaji bugawarsa yana qaruwa sakamakon furucin muhd bello ,bai an kara ba yaji sautin muryar muhd bello ya cigaba da magana " itama maryam din bata san da maganar ba a yanayin yadda mami ke maganar zaka fahimci hukuncinta ne ta yanke akanka kuma ina da tabbacin ko tasani bazata ki ba, biyyawa kawai zatayi ta aureka koda ranta bai so "shawarata ka amince da aurenta yarinyar nan tana da natsuwa da hankali sosai bazata baka matsala ba ,sannan tana da ilimi tana da kirki daidai nata uwa Uba jininku daya daita abinda yayi ka shi yayita, shi abinda kake gani acikin rayuwarka ba lallai ya zamo gaskiya ba dan ba kowani mafar......"
"Stop!
"Mb don't don't !! talk anything rubbish okay ya fada a fusace yana sake fuskantarshi sosai ya rungume duka hannuwansa a faffadan qirjinsa ido cikin Ido suke kallon juna tmkr ranar suka fara ganin juna zuciyar mr ATA na wani irin tuttukin bakinciki da zafi muryarsa a zafafe ya cigaba da magana "ko kai ne Allah da zaka fad'a min haka ?" well I don't care about all what you said dan nasan da Allah na dogara ba da kai ba kuma nayi Imani bazai wuftar da lamarina ba zai cika min burina."
"Na sani Allah ba zai wuftar da lamarinka ba amman dole sai kabi umarnin mahaifiyarka tukun allah zai duba lamarinka domin Allah ( swa) yace waqada rabuka alla tahbudu ila iyahu wabil walidaini ihsan sannan manzon allah (saw )sai daya ambaci abi uwa har sau uku kafin uba kaga tunda har kasan allah keyin komai to ya kamata kasa aranka kamar anyi wannan auren an gama da izinin Allah har ma na fara tsinkayo sautin muryoyinku cikin farinciki kai har ma ka durka mata ciki yan shida tana takawa da kyar kana rike da jakarta kana mata sannu ya karasa maganar cike da zolaya yana murnushin mugunta tare da dukan kafad'arsa wanda hakan yasa mr ATA sake d'aure fuskarsa sosai yana zabga masa katuwar harara ."
suna cikin wannan halin hisham dake tsaye gefensu yana waya ya gama ya tura wayarsa cikin aljihunsa ya qaraso yana mikawa muhd bello hannu shima ya mika masa nasa hannun yana cewa tun dazu nake allah allah ka gama wayar kazo mu taru mu taya mami yakin karshe "akan wa kenan ?"akan wannan stupid din d'an nata mana mai shegen taurin kai kamar dutse "nan ya shiga zayyane masa halin da'ake ciki hisham ya gyada kai yana cewa "gsky mami ta yanke hukunci mai kyau sai dai muce allah ya tayaka rikon amanar maryam , dan allah friend ka amince karka zubawa mami kasa a idanunta bugu da kari aure shine cikar kimar mutun duk inda zaka shiga matsawar baka da aure wallahi kimar ka raguwa take , nima nan da kagani kokarin shawo kan nuzla nake kaga idan allah ya taimakeni ta amince kawai sai a hada bikinmu tare." Mr ATA yaja dogon tsaki ya zabga masa harara Kmr kwayar idanunshi zasuyo waje "naga alamar kai ma baka da hankali kamar wannan "ya fada tare da juya yana kiran all you of are very stupid ."
Ahankali mr ATA yake daga kafafunsa batare da ya sake yin wata magana ba dan idan yace zai cigaba da magana sai dai d'ura masu zagi , yana tafiya yana sake jin bacin rai duk wanda ya gansa yasan yana cikin damuwa ,dan haka masu kula da lafiyarsa duk suka shiga hankalinsu kowa na taka tsantsa ,da sauri escort dinsa suka biyosa cikin kamewa da taka tsantsan kiyaye aikinsu , dan duk lokacin da ransa yake a bace yafi dakatar da mutun daga aiki ."
muhd bello ya biyosa suka jero tare zuwa Inda akayi parking din motocinsa escort suna kokarin bude musu murfin mota yayinda hisham ya juya ya nufi gidansu ."mr ATA na qoqrin shiga mota Kira ya shigo wayarsa ya tsaya cak hade da tura hannunsa cikin aljihunsa ya ciro wayar yana dubawa sunan aunty shahida ya gani yana yawo akan screen din wayar ya furzar da iska me zafi sannan ya danna koren maddanin ya manna wayar a kunnensa yayi shiru yana sauraronta "
can bangaren aunty shahida ta fara magana saboda tasan ba magana zai yi ba "kana Ina yanzu ? shiru ya cigaba da yi yana ciza lips dinsa na kasa sai data sake maimatawa sannan ya bude bakinsa da kyar "Ina shirin barin gida yanzu "to karka kuskura ka bar gida batare da kabawa mami hakuri ba "naji zan dawo anjima da daddare dan tayi fushi sosai yanzu yayi maganar yana runtse idanunshi zuciyarsa na suya "no kaje yanzu saboda nasan ranta yayi mugun 'baci shiyasa kaji nace haka Kuma bana son tayi fushi da kai adam kasan mami na matukar hakuri damu most especially kai tana hakuri da kawaici akan komai, wannan ma ka kaita makura ne "to ni yaya kuke son nayi da rayuwata ne ?
"hakuri sannan kabi umarninta ta fada atakaice "shikenan haka ni rayuwata zata qare cikin kunci Kunki ku tsaya ku fahimceni ? "Wani fahimtarka Kuma zamu tsaya yi tunda an baka lokaci Kaki kayi komai akai ?"fatanmu kayiwa mahaifiyarmu biyayya ka rike mana amanar maryam karka cutar daita sannan na tabbatar maka zakaji dadin maryam dan .."Kinga shahida karki dameni da wani amana ko zan ji dadinta kar in cutar daita "yayi saurin katseta ta hanyar fadar haka " kanku kawai kuke dubawa baka duba halin da zan shiga akan auren nan haka kawai zaku cutar dani akan wani auren baza "shahida kai tsaye ko adam ? "ta tambayesa numfashi ya sauke bai ce komai ba " kiran sunana yau babu ladabi ba komai ba ?"share wannan maganar raina ne ya baci zan zo office din na sameki idan na gama da sweetheart mu tautauna wasu abubuwa daya shafeni ,"
"karka sake Adam kazo min da wani tsari ko rashin kunya dan ba zan tsaya naji raayinka ba sannan kasani bazan dauki raini ba ,dan iskanci tun yaushe ake fama da kai ? shekara biyar kenan ana fama da kai ka fito da mata Kaki kullum ka zaunar da mutane kana masu karyar baka samu tru love ba ,haka kawai kanata batawa kanka lokaci abanza,tukun nama kana wannna iskanci na ji da kai da fadin rai yaushe zaka samu tru love ."?" kai wace shegiyar ce ma zata dauki wannan wulakanci da ji da Kan da kake fama dashi ? ai daman karshenka kenan ayi maka auren dole kaje can ka karata kowa ya huta dan .."bai tsaya Jin abinda zata sake cewa ba ya sauke naunayen ajiyar zuciyar yay disconnecting din Kiran Yana adduar samu sausauci daga gurin mahaifiyarsa ."
ya maida wayar aljihunsa ya koma cikin gidansu a Inda ya bar sweetheart dinsa anan ya isketa zaune gefenta maryam ce ke matsa mata kafafu suna hira cike da tsantsar biyyaya kyakkyawar datjijuwa me tsananin kyau da nagarta da sanin ya kamata da son zaman lafiya da lumana ta d'ago a natse idanunta sanye da farin glass wanda da gani na Kara lafiyar idanu ne ta zuba masa Ido tana mai tsananin qaunar d'anta ."kamshin dadd'adan turarensa (Reed ) mai sanyi da sanyaya zuciya tare da Kashi jiki da sace zuciyar duk wanda sautsayi yasa ya shaka yasa maryam ta fahimci ya sake dawowa falon ,a hankali ta bar abinda take ta dago idanunta dan tabbatarwa kanta shi din ne ko kuwa , ai ganinsa tsaye kikam kamar wani jami'in tsaro ba dan kasuwa ba yasa nan take qirjinta ya shiga dokawar daya Saba a duk sanda zata d'aura idanunta akanshi sannan ta dinga kokuwa da numfashinta kenan har sanda zai bar gurin ."
Ahankali idanunsu ya tsarke cikin juna wani irin kallon banza me hade da harara ya sakar mata babu shiri ta zare hannunta daga kafafun Mami ta mike tayi dakinsu ,Koda ta shiga dakin ma kasa samun natsuwar zuciya tayi ta rasa dalilin da yasa take tsatsanin Jin tsoronsa haka da Jin faduwar gaba akansa sannan ta rasa dalilin dayasa ya tsaneta haka koda bai fada mata ba tasan baya qaunarta dan tana ganin tsanarta acikin kwayar idanunshi ."
bayi ta bud'e ta shiga qirjinta na dokawa ta kulle kanta dan ganinta shine Inda yafi mata saukin zama ta rarrashi zuciyarta shiru tana tunanin ta nesanta kanta dashi zai samammata kwancinyar hankali, sai dai ina hakan ma ba mai yuwa bane domin mami bazata yarda ba wani sabon tashin hankali ya caki zuciyarta nan take faduwar da gabanta ke yi ya qaru ya wuce misali hattar cikinta sai kadawa take tayi Imani a lokacin da tana da ciki tsab zai fice ya barta ."
cike da ladabi da biyayya ya dan saki rashin kadan ya k'araso ya durkusa a gaban mahaifiyarsa kmr zai mata sujjada "Sweetheart! ya kira sunanta bata amsa ba ta cigaba da kallonsa "kiyiwa Allah kiyi hakuri ki bar maganar nan a tsakankanimu karki bayyanata bare kowa ya sani ita kanta yarinyar idan ta sani sannan taji rashin amincewata zataji babu dadi a ranta ," shiru hjy zulaiheart tayi taki cewa uffun har sanda ya dasa Aya " Allah ya huci zuciayrki hjy sweetheart dan nasan zuciyarki na tattare da fushina amman kiyi hakuri ki yafe min abinda nayi " yana gama fadar haka yaja bakinsa ya sake yin shiru yana sauke numfashi ,hjy zulaiheart ta kafeshi da idanunta sosai ta cigaba da kallonsa taso ya fadi fiyye da abinda ya fad'a idan ma da hali yace "ya amince da umarninta amman sai sa'banin haka yake furtawa ,ya tsaya a iya hakuri kawai da kin amincewa ."ta rasa wace irin zuciya ga Adam sam idan ya kafe akan abu ya kafe kenan is very hard ya canza ra'ayinsa wannan halin kawai tafi tsana a rayuwarsa tun yana yaro tayi iyakar kokarinta akan wannan hali abun ya cutura sai dai akan wannan lamarin ta rantse ko zai rasa ransa sai ta canzasa Kuma sai yayi abinda take bukata ..
ya d'auki tsawon minti goma yana durkushe yana bawa mahaifiyarsa hakuri wanda ita ba hakuri tafi bukata daga tillon dan nata ba amincewarsa tafi bukata ,naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfi sannan tace "shikenan komai ya wuce na yafe maka amman ka San da sanin bazan taba janye maganata ba tunda na baka lokaci mai tsawo ka kawo min wacce kake so Kaki kullum da dramar da kake bullowa daita ayi mgn kace tru love kake jira ,dan haka bazan zuba maka Ido ba kayita zama babu iyali ba "Kai yanzu sbd Allah baka jin kunya ?duk sa'aninka sunyi aure har da yayansu abun sha'awa ? amman Kai baka wannan kasar baka wancan kasar , Neman kudi kawai kasa a gaba to meye amfanin kudin da Babu magada ? Kai da mahaifinka bai haifeka ba ka gaji tarin dukiyar daya bari ?yayi shiru yana riko tafukan hannuwanta cikin nashi dan bashi da amsar bata " ni dai gaskiya na gaji da zaman ka haka babu iyali Ina bukatar ganin ya'yanka idan Kuma kafi bukatar sai na mutu kayi auren shikenan sai na hakura na daina maka maganar amman fa kasani muddin nayi shiru yana nufi babu ni babu kai har abada ko mutuwa nayi zan bar wasiha kar abarka ka ta'ba ga....."
"Dan Allah Dan girman Allah kiyi hakuri Sweetheart ki daina ambato mutuwar Nan ki rufa min asiri idan kika mutu duniyar fa bazata min dadi ba , kece duniyata, ke kike sakani farinciki idan nayi cikakken awa daya banji muryarki ba Ina rasa gane kaina inaga baki duniyar ...?"kiyi hakuri inshallahu zaki ga aurena nida auta kmr yadda kika ga na saura yanuwanmu amman ki dan bani lokaci zan kawo miki wacce nake so nan kusa ,sai byn da yayi maganar ya fahimci maganarsa ta fito ne ba a yadda ya dace ta fito ba dan ta Ina zai fara ...?
"Wannan lokacin ya Kure Maka Adam har abada Babu wani sauran lokaci da zan sake baka kaje ka fara shirin aurenka da maryam kawai , tana gama fadar haka ta kawar da fuskarta gefe dan idan ba haka tayi ba zuciyarta zatayi sanyi akan tillon danta har ta fasa aiwatar da nufinta akanshi tsam ya Mike ya soma kokarin barin falon zuciyarsa na tafarfasa da tuttukin bakinciki dan yasan tunda ta kafe ta nace Babu wani sausauci baya ga amincewa kudirinta ."
Kai tsaye mota ya shiga muhd bello na ganin haka Shima ya shiga bangaren daya shiga ya zauna suka bar gidan har suka hau kan titi nasiha m b ke masa me kwantar da hankalinli da ratsa zuciya sai dai ko Daya Adam bai jin zai iya saduda da auren maryam gabadaya ya maida idanunshi yana kallon motocin dake gudu akan titi yayinda kwakwaluwarsa ke tunanin neman mafuta dan dole yasan abun yi kafin ayi masa auren dole da yarinyar nan "
"Adam ......"!
M.b ya kira sunansa ko gezau bai yi ba bare ya nuna alamun mutun na kusa dashi bai tsaya jiran jin amsarsa sa ko akasin hk ba ya cigaba da magana "ka kasa fahimtata amman kayi hakuri kasanyawa zuciyarka sallama ,na fahimci yadda kake ji amman me kake son nayi daya wuce na tayaka yiwa mahaifiyarka biyayya ? yayi maganar kmr zai yi kuka dan ya tsani yaga damuwar amininnasa ya dafe kanshi da hannunsa daya yana dukar da kanshi tausayinsa ya kama Adam ya furzar da iska me zafi daga bakinsa sannan ya soma magana .
"MB nima ka kasa fahimtata ne amman Ina da ra'ayina akan mace da nake son na ajiye agidna , muddin na auri Maryam ya zama dole na qara aure abinda bazan so faruwarsa kenan ba bama haka ba ni bani da ra'ayin ajiye mace sama da daya a gidana ."to meye dan ka ajiye sama da daya ? ka Kara mana tunda kana da abinda zaka iya rike mata ko sama da goma ne ba biyu ba ."
tsaki Mr ATA yaja a lokacin da direbansa ya karya kwana yana cigaba da tukinsa ,motar tayi shiru can ya sake motsa bakinsa "mb kasan komai akaina sai dai abinda bakasani ba ni bana son auren farar mace, nafi son mace chocolate colour ita ba fara ba ita ba baqa ba sannan mara kiba wace matakin karatunta iya diploma ne sannan doguwa daidai kafad'ana ba guntuwar mace ba "Kai yanzu me zakayi da doguwa har kafad'arka sbd Allah? " yar daidai fara kmr maryam ai ta isheka rayuwa sannan a matsayinka me zaka yi da mai iya karatun diploma ga mai digree har biyu "
"Zanci master's ne ? yayi masa tambayar a matukar fusace "yariyar nan babu abinda ta iya common ruwan zafi sai an daura mata ga balain son social media ,Kai ni duk bama wannan ba na tsani farar mace arayuwata ni dai chocolate itace type dina kasan Allah dana yi rayuwa da farar mace sol irin yarinyar nan gara na mutu ban yi aure ba saboda na tsaneta "subhanallah ATA ka daina fadar haka dan allah , dukkaninsu halittar Allah ne , da baki da fari duk Allah ne ya haliccesu ya tabe baki kawai yana furzar da hucin numfashi mai zafi haka suka cigaba da tafiya m.b na nusarsheshi ."
Maryam yan'uwa ne da adam, da mahaifin maryam da mahaifiyar adam uwa daya uba daya maryam ce babbar diya agurin iyayenta sai kanwarta Faiza ,islaha manir , Abusufyan , Salman sai auta izzatu wacce suke kira da izza suna zaune a Abuja yayinda adam suka kasance su biyar agurin mahaifiyarsu aunty shahida itace babba Kuma ma'aikaciyar likitanci ce a babban asibitn gwanaty dake jahar lagos a ikeja ,sai aunty khadeja wacce ta kasance maaikaciyar zenith ,sai adam wanda ya kasance dan boko Kuma rikakken dan kasuwar da duniya ke ji dashi,sai aunty zabiba wacce ta kasance lactura ce a lagos state university, sai auta nana hauwa'u wacce tuni itama ta gama karatunta a London tare da maryam akan harkar compurte science , a london akwai tsananin shakuwa atsakanin nana hauwa'u da maryam Hakan yasa sanda suka kare karatu maryam ta kasa zama tare da iyayenta ta dawo suka cigaba da rayuwa gabadaya dangin mahaifiyarsu da mahaifinsa babu baki duk wanda kagani fari ne sol babu mixed ."
Direban mr ATA bai tsaya akoina ba sai a haraban asibinti da aunty shahida ke aiki yana parking ya fito da sauri ya Bude masa murfin mota mr ATA ya yunkura da kyar ya fito yana gyara zaman rigarsa "friend ka bani minti ashiri yanzu zan dawo "na baka awa daya ma har ya juya m.b yace " , dan Allah friend karkayi wata ja inja da aunty kawai kace mata ka amince wani banzar kallo mr ATA ya juyo ya banka masa sannan ya juya cigaba da tafiya ."
m.b yayi murnushi dan daman yasan sai ya samu tsaraban wannan kallon daga gurinsa kai tsaye office dinta ya nufa cikin takun nan nasa mutane sai kallonsa suke saboda hotunansa sun qarade koina na matsayinsa na dan kasuwar da duniya Ke ji dashi wasu kuwa tsananin kamaninsa da yaruwarasa yasa suka dinga kawo masa gaisuwa wasu ya amsa Wasu ya share barin ma idan ya fahimci yanmata ne , ya tsaya a bakin office dinta yayi knowking ta bashi izini ya shiga yana taku da kyar yana furzar da iska ."
ta dago da sauri ta kallesa tana nuna masa gurin zama Dan tasan Halinsa ba karamin aikinsa bane zuciya tasa ya juya ya kama gabansa "zauna na Dan karasa abinda nake zama yayi ya daura kafarsa Daya akan Daya Yana ciza gefen lips dinsa daya zame masa jiki .byn kmr minti biyu ta tsaida abinda take ta sake dagowa ta zuba masa idanunta "Ina sauraronka wani taimako zan maka ?"kisa a fasa auren nan kawai shine babban taimako da zakiyi min ". "me yasa kake kin auren marym? shin kana da wacce kake so ne data fi Maryam komai ?ya gyada mata Kai alamun "eh ! Yana lumshe idanunsa "a Ina take Kuma su waye iyayenta ?wani mataki iyayenta suke dashi a kasar nan ko ....."? Ki tsaya iya haka ma ya isa dan ban San komai daya shafeta ba sbd ban San komai nata ba , Ina take a ina zan ganta duk bansani ba ina dai kan nemanta sai ki tayani da addua Allah yasa na ganta nan kusa kuyi min auren soyayya idan ma soyayyar zanyi kenan ."
"aunty shahida na San idan na fada miki komai zaki fahimceni sbd akwai fahimta a tsakankanimu shiyasa kika ji Ina maganata Kai tsaye dake , a zahirin gsky matar da nake so na aura ni kaina na dade Ina nemanta sai dai har yanzu ban ganta ba ......"nifa ban gane nufinka ba Adam , " I mean matar da nake so ban San Inda take ba ya sake maimaita mata abinda yace "Amman dai ku bani lokaci zan cigaba da nemanta idan na ganta zan kawo muku ita ya karasa maganar tare da fito da pendat din sarka dake makale da wuyansa wanda ke hade da hoton zannen yarinyar ya nuna mata ."
Shiru tayi tana kallonsa da kallon zanen yarinyar kyakkyawa ce chocolate colour " kinganta aunty ita ce rayuwata , ni dai kaina na zanata akanta na koyi Zane , ta miki kyau ko ?yayi mata tmyr yana sakar mata tsadaddaden murmushinsa wanda ba ko yaushe yake yi ba "subhanallah Adam kana hauka ne ko me ?" Taya zaka kamu da soyayyar macen da baka San Inda take ba hasalima baka taba ganinta ba ....?"Haka ne aunty Amman ta shiga zuciyata ta samu kyakkyawa mazauni acikinta shekara goma sha biyar kenan nake nemanta aunty babu Inda ban nemi yarinyar nan ba acikin garin Nan har ma da kasashe da garuruwan da nake zuwa Amman ban sameta ba ,Kai ko me kama daita Bangani ba "shine Kuma Dan hauka ka cigaba da Sonta? "ya lumshe idanunshi tare da cewa "ya zanyi haka tawa qaddarar ta kasance itama ba wai ina sonta bane amman muddin zanyi aure ita zan aura".
"ka manta wannan shirmen dan har abada bazaka ganta ba dan dayawa mafarki ba gsky bane "wallahi aunty jikina na bani tana Nan a duniyar Nan shiyasa kika ga bana son na karbi auren yarinyar Nan mrym gbdy aunty shahida ta dauke maganarsa a matsayin shirme ta cigaba da kallonsa kmr wani sauna ,Taya zai ce yayi mafarki da mace Kuma Yana Saka ran tana Nan acikin duniya Kuma zai aureta sai Kuma tayi tunanin ko aljanu sun shafesa ne a take agurin tace "Adam ka sausarareni da kyau mafarki baya zama gsky ..."no aunty wannan zai zama gsky yayi mgr a fusace .... "
jikinta yayi mugun mugun sanyi ta ajiye nata damuwar ta fara lallabashi dan taga alamun idan ta cigaba da mgn komai zai iya faruwa dan ya zurfafa soyayyar yarinyar sosai ya mike tsaye "ki taimakeni ki fahimtar da sweetheart ku tayani da adduar samota "aikuwa zan fada mata, a ranta tace babu adduar da zamu tayaka tunda mun san abinda muke yi har ya bar office din bata dauke idanunta akansa ba ...."
Washegari aunty shahida ta shirya ta samu hjy zulai "ta Koro mata duk halin da adam yake ciki" mu tashi da addua mami saboda Adam yayi nesa cikin wata duniya ,hjy zulai ta gyada Kai cike da matsanacin fargaban tace "Allah kyauta inshallahu zan tashi tsaye da addua da Kuma sadaka lallai da alamun aljana ta auresa idan ba haka ba ga lafiyyayar yarinya me zai Yi da wata a mafarki "shine abinda nayita kokarin na fahimtar dashi yaki yarinyar Nan tunda ta taso bata da matsala ke din mahaifiyarta ce zamu shiga gidansa a duk sanda ranmu yaso, Kuma zamuyi abinda muka ga dama tunda ta muce ita ."
"Allah yasa ya gane alkhairi ake binsa dashi "Ameen aunty shahida ta fada tare yiwa mami sallama har wannan lokacin Babu Wanda ya sanarwa Maryam batun aurenta da adam ana jiran sai ya amince sannan a tunkareta da batun cikin saa da jajicewar mahaifiyarsa da yayarsa mr ATA ya amince a wanni yammaci sun dade a dakin suna tautaunawa ya numfasa idanunshi a runtse ya cigaba da magana "Amman fa duk sanda na samu yarinyar da nake nema zan Kara da daita "ai wannan ba wata damuwa bane inji cewar aunty shahida ta fadi haka ne sbd tasan da wahala ya samu yarinyar mafarkinsa ita kuwa mami shiru tayi tana kallonsa a karshe ta girgiza Kai tana masa addua acikin ranta ."
aunty shahida ta fito daga dakin mami tare da Mr ATA dake faman cika Yana batsewa da cicci magani bai tsaya ba ya nufi kofar fita aunty shahida tace "adam Dan Allah bari na fito ku saukeni a gurin aiki Bai ce mata uffan ba ya wuce sannan ta Kalli Inda maryam dake zaune tare da nana hauwa'u suna kallo da wayar maryam tace "Maza Maryam dauko mayafinki kizo muje kiyi min rakiya zuwa asibiti Nan take ta mike daman a shiryenta take mayafi kawai ta dauka suka fito tare , Kai tsaye Inda motar mr ATA yake suka nufa limoxin ta bude gidan baya ta shiga maryam ma tayi kokarin bude dayan bangare ,aunty shahida tayi saurin cewa "zauna a tsakiya kusa da adam maryam taji maganar wani iri ta dan saci kallon aunty shahida tana mamakin jin furucinta" zauna a tsakiya kusa da adam to me hakan yake nufi?Tana son tai tmby babu hali dan haka jikin a sanyaye ta bude ta shiga ta zauna nesa dashi kamar wata tsuntsuwa ta kame Kanta tana jin mummunar faduwar gaba from no where " .
Direban mr ATA ya ta-da motar suka soma kokarin fitowa daga cikin gidansu "Ina muka nufa ma kika ce ? ita Kuma wannan ina zaki daita nifa bana son kwashe kwashe a motata? asibiti ta bashi amsa duk da tasan yaji abinda tace , bai sake cewa komai ba har suka iso asibiti ,yaki fitowa Yana jiran aunty shahida ta karasa fitowa dan maryam tuni ta fito "adam muje akwai sakon da zan baka yayi shiru yana maimata maganarta yaji Kmr yace ta bawa mrym ta kawo masa Amman Kuma baya son abinda zai hadashi da yarinyar "a hankali ya fito ransa a bace Kai tsaye office dinta suka nufa aunty shahida ta bude office dinta dukkaninsu suka shiga Yayinda mr ATA ya tsaya daga bakin kofa yana jiran ta bashi sakon da tace aunty shahida tace "bismilla mana ranka shi dade mr ATA shigo ka zauna ga guri nan yayi mata wani irin kallo yana bukatar qarin bayani akan abinda ta keyi "ta gyada masa kai "shigo mana ." da kyar mr ATA ya shigo office din ya zauna yana hura hanci sannan itama maryam ta samu guri ta zauna tana satar kallon fuskarsa kwata kwata babu digon annuri ,"
" Maryam tashi ki bude fridge ki dauko masa ruwa dan nasan bai fiyye shan lemo ba ,ta mike a hankali ta karasa ta dauko masa ta ajiye a gabansa ta koma ta zauna gabanta na faduwa "ka bani minti goma kawai zan duba wani fayal ne yanzu zan gama sannan ta soma aiki tsaki yaja a ransa dan dai tana da matsayin aunty shi ce if not bai ga dalilin da zai yita batawa kanshi lokaci ba akaron banza ba ."baka sha ruwan ba ?ta dago ta tambayesa cike da kulawa "no need !ya bata amsa ataikaice
byn kmr minti biyu ta mike ta fita tace "kanina ina zuwa "zuciya ta sake kawo masa wuya sakamakon barinsa da zatai yi shi da wannan guntuwar yarinyar mai siffar aljanu yaja tsaki yana dafe goshinsa da hannunsa ."
Zamansu daga ita sai shi acikin office din baqaramin tashin hankali maryam ta shiga ba ,gbdy duk ta rude sai zufa take fitarwa da zarar tayi kamar zata dago ta kalleshi sai ta kasa dan gbdy ta nemi natsuwarta ta rasa ji take kamar zuciyarta zata buga allah allah take Aunty shahida ta shigo domin bazata iya cigaba da irin wannan zaman ba ,minti biyar kawai Aunty shahida tayi da fita amman ganin take Kmr awa biyar tayi da barin office din ,shi kuwa mr ATA banda tsaki babu abinda yake yana qarawa domin ya fara gajiya da zamansa tare da abinda yafi tsana arayuwarsa ."
Aunty shahida na fita ko cikakken minti goma batai yi ba sai ga nuzla ta shigo office din bakinta dauke da sunan Aunty shahida,turus tayi sakamakon ganin maryam zaune gefe guda kuma mr ATA ne zaune kallon tsoro tayi masa ta dauke kanta tana gaishesa bai amsa mata ba kamar sauran lukuta ta qarasa ta dafa maryam "marsi ina Aunty shahida ."?
"ta dan fita amman tace bazata jima ba ki jirata ,
"okay da ido tayi mata tmby me ya Adam yake yi ? itama da kwayar idanunta ta bata amsa da bata sani ba dan babu damar ayi magana mai sauti kasamcewar sun san baya son hayaniyar komai saurin ciro wayarta tayi ta maida silet ."
sadiya wacce ta kasance me koyon aiki ce a asibiti ta shigo bakinta dauke da sallama "Assalamu alai...... kasa karasa sallamar tayi sakamakon gani mr ATA zaune idanunshi na kallon screen din wayarsa sanye cikin kanan kaya ,gbdy ta rikice akansa madadin ta karasa ta ajiye file din dake hannunta ta kasa ko daga dan yatsan kafarta garin kallonsa ma har file din hannunta ya subuce daga hannunta ya fadi kasa da sauri ta tsugunna ta dauka jikinta na rawa ta karasa ta ajiye fayal din akan table ,tana faman kallonsa sai lokacin ta lura da maryam dake zaune tana kallon yatsun hannunta yayinda nuzla ke tsaye a gefenta "sannuku da hutawa ta furta a hankali ."
maryam ta dago tana murnushi tace "yauwa ya kokari ? alhamdulillah sadear ta bata amsa tana kallon nuzla sannan ta fita tana waiwayen Mr ATA tana yaba kyawunsa acikin ranta shi kuwa Mr ATA ko ajikinsa dan iskar ma data debota bai gani ba idan da sabo ya rigada ya saba da irin kallon da suke masa haka ma kallon da mrym da nuzla Ke masa bai sa ya dago daga duban wayarsa da yake ba .
Nurse sadiya na fita daga office suka ci Karo da husaina itama maakaciya ce "ke lafiyarki kika fito a hargitse Kmr wacce aka koro ?"uhm ke dai bari husseina wani matashi na gani a office din doctor shahida mutumin yayi min kyau matuka ya dauki hankalina wallahi irin mijin da nake nema kenan mijin duniya Mijin novel ya hadu sosai da gani yana da kudi yana da tarin ilimin boko da Arabic uwa Uba kyau "ke sadear raba kanki da wahala, kina diyar talaka dake naci ma da kyar kuke samu kullum Kuna yawo a gidan haya , yayanki ma da kyar yake daukar dawiniyarki Amman kin kashe kanki da mugun buri , ki roki Allah idan yaga dama zai Baki ki Daina zafafa burin akan auren me kudi ."
sadear ta Dan turo mata karamin Bakinta tana yatsina fuskar ,jikin Sadia yayi sanyi sosai husaina taja tsaki ta wuce ta barta Nan tsaye tana maganar a fili ."
Wayar hannunsa da yake ta faman daddanawa ce ta dauki qara ya manna a kunnensa tare da zamowa kad'an daga Kan kujerar da yake zaune yana lumshe idanunshi "na barota a gida ne ,okay suna bukatar new design's da kaya ?shikenan ki bawa kwararrun wadan da suka iya domin bana son a samu matsalar komai aikinsu dan last time sunyi complain okay may be tomorrow yana magana yana lumshe idanuwa yana lasar lip's dinsa na kasa ."
uzla,maryam duk suka zuba masa idanunsu suna kallonsa kowacce da abinda zuciyarta take saqawa jikinsa ya bashi kallonsa suke dan haka ya tsaida lumtsatsun idanunshi akansu yana masu wani irin kaskantacce kallo sannan ya dauke kansa ya cigaba da waya a daidai lokacin da husseina da sadiya suka shigo tare ita kanta husseina ta jinjinawa kyawunsa dan sai da tabawa idanunta abinci suka dauki abinda ya shigo dasu suka juya ."
Ya sake tsaida idanunshi akansu ganin still shi din suke kallo har lokacin Kmr basu san shi ba wani irin taikaci ya kamashi dan baya son yawon kallo arayuwarsa wani abu ya hadiye mai daci a makoshinsa kafin ahankali yaja tsaki yana cigaba da kallonsu yayinda su kuwa a matukar firgice suke kallonsa cikin tsananin tsoro da firgici sam basuyi tsamanin zai sake kamasu suna kallonsa ba irin kallon da yake masu yasa suka sake shiga rudani dan basu san abinda zai biyo bayan kallon da yake masu ba sannan basu abinda zasu fad'a dan kare kansu ba nuzla ta kalli maryam itama ta kalleta gabadaya jikinsu ya kama rawa nuzla tayi saurin durkushewa kasa bisa gwiwowinta dan tasan na lahira zai fisu jin dadi idan bata hanzarta bashi hakuri ba dan taga maryam bata da alamar bada hakuri "ka..! kayi hakuri ya Adam magana yake son yi amma ina jin isa acikin ransa yasa ya gagara furta komai illa kafarsa daya daya shiga jijigawa yana takaici ."
ganin har kusan minti talatin aunty shahida bata dawo ba yasa mr ATA ya Mike a fusace ya tura hannunsa daya cikin aljihunsa ya bar office din dan jikinsa ya fara bashi so take ta hadasu da Maryam ta fayyace mata komai a gabansa,yana fita nuzla ta nufi kofa cikin sand'a itama mrym ta biyo bayanta, nuzla na gama bude kofar turus sukai yi sakamakon ganin sadiya da husseina tsaye rungume da file suna kallon byn mrs ATA suna magana can kasa kasa sakamakon mutanen dake kai kawo " ai wannan ba bakon fuska bane sadiya matashin dan kasuwan nan ne da duniya Ke ji dashi sannan kani ne ga sister shahida yana zuwa lokaci zuwa lokaci ke baki ga kamarsu ba "?lallai kam sai yanzu na ganesa ko dan na rikice ne amman yafi kyau a fili km suna matukar kama sosai da Sister shahida sai dai har ya fita kyau ,wallahi husseina mutumin nan ya shiga raina sosai ban ta'ba ganin halittar daya dauki hankalina ba kamarsa komai nashi irin mafarkina "uhm uhm sadiya na sha gaya miki ki daina irin wannan hange ki tsaya matsayinki kin kasa fahimtata ."kisani babu abinda allah bayayi bansan dalili ba gani daya nayi masa amman na kamu da matsanancin soyayyarsa " wallahi wannan yafi karfinki Ke ko yaronsa yafi karfinki bareshi idan zaki dawo haiyacinki ki dawo taja hannunta sukai wuce sadiya na juya bayanta ."
Naunayen ajiyar zuciya nuzla da maryam suka sauke atare suna dafe qirji "marsi wallahi ba qaramin tsorata nayi ba ,koni kusan nafiki tsorata wallahi kadan ya rage ban saki fitsari ajiki ba qaramin saa muka ci ba da yau mun sha maruka suka kwashe da dariya "kinga bari na wuce bazan iya jiran Aunty shahida ba daman nazo karban test din hjyrmu ne nace nazo mu gaisa kinga wucewata sai mun hadu a gida ta zame hannunta dake cikin na maryam ta wuce tana daga mata hannu , maryam ta koma cikin office zaman jiran Aunty shahida ."
Bai Dade da wucewa ba doctor shahida ta dawo ta ga wayam bashi Babu alamunsa "sarkin zuciya halan ya gaji ya wuce "eh Maryam ta fada muryarta a sanyaye "okay ta shiga tattara kayayyankinta muje kou daman akwai maganar dana so muyi mu uku Amman zanzo gobe inshallahu idan na tashi daga aiki muyi a gida "magana kuma aunty.?"ta tmbyeta a tsaro ce .
"Eh!
" wacce magana ce haka Kuma har da ya adam zaayi ?aunty shahida tace ",magana ce me mahimmam ci , dan girman Allah aunty shahida wallahi bana son duk abinda zai hadani dashi nifa tsoro yake bani culmdown my sister ki cire wannan tsoro ba wani Abu bane face alkhairi shiru mrym tayi tana nazarin maganar aunty da tunanin wacce magana ce wannan da har sai anyita da ya Adam Kuma tace alkhairi ne ...?
suna fitowa haraban asibinti suga direbansa na jiransu "a ruwa Ina mai gidanka ? sai daya rusuna mata sannan yace "ya kira anzo an daukesa da wata motar aunty shahida ta girgiza Kai ta shiga mota ita da maryam inda take fad'a mata zuwan nuzla "Ayya kanwata ai kuwa na gode sosai itama kuwa ina son ganinta nan hankalin maryam ya dan kwanta jin har da nuzla sai dai har sanda a ruwa ya sauke aunty shahida a kofar gidanta zuciyar mrym bata bar Saka da warwara ba Allah Allah take gobe tayi taji ko meye .."
washegari da misalin karfe goma na safe sakon mutuwar sadiya ne ya riski doctor shahida, tayi matukar firgita da Jin wannan mummunar labari saboda cewar da akayi yankar rago akayi mata ta zabura ta mike daga zaunen da take jikinta na rawa ......."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Table of Contents