Chapter 2
Chapter 2
kamun Kuma yasulale yabar wurin batareda yayiwa fadeel komaiba Koma yakulada akwaishi awurinba.. Shiko IRFAAN tin lokacinda yakulada Babu Hafees awurin hankalinshi yayi matukar tashi Hakan yasa yashiga jejin nemanshi batareda yanemi temakon kowaba gudun karyasake jefa Wani cikin matsala,,,Kuma tin lokacinda yafito nemanshi beganshiba se yawo yakeyi acikin jejin Amma Babu Hafees Babu dalilinshi....yashafe kusan awa 2 Yana nemanshi se can yahangeshi lab'e wurin Wani sansanin kuraye sunfi 100 sun kewaye wurin shiko Hafees na mak'ure Rai ahannun allah domin mistake kad'an zeyi suyi watandarshi....IRFAAN na tsaye cikin kad'uwa da tashin hankali Yana tinanin ta yadda zetinkari way'anda zaratan miyagun dabbobin yatemaki Dan uwanshi...seka wannan damisar ta,iso gunshi tana gurnani tana bud'ar Baki...d'agowa IRFAAN yayi Yana kallanta adake batsoro balle fargaba yanajiran yaga Dame tazo sekawai yaga tazo kusanshi tareda duk'awa kamar yadda yak'umi keyi idan mutun ze haushi alamar ya hau sutafi...cikin mmki yake kallanta...itako Ganin beda niyar hawane yasa tasaka bakinta taja rigarshi..ba yadda zeyi Doli yahau bayanta tareda yimata nunida Hafees..tana d'agowa taganshi inda yake sekawai tajuya ta kalli Yar uwarta dasukazo tare kana sukayi girgiza sukanufi wurin gadan gadan...tindaga nesa kurayen suka hangosu tafe suka fara darewa suna Basu hanya har suka k'arasa Inda Hafees rakub'e. K'ugi yaji akusanshi Hakan yasa yak'ara had'e ranshi domin yarigada ya sada k'at cewa tashi tazo k'arshe...suko tsaye kawai suke suna kallanshi kamun d'aya damisar tayi yadda d'ayar tayiwa IRFAAN Dan Hafees d'in ya hau Shima...amma Ina Sam shi besamma tanayiba...IRFAAN ne yabud'e Baki Dakyar yace bro zumubar wurinnan nine IRFAAN..aitinkamun IRFAAN yarufe Bakinshi yad'ago Amma abunda yagani yak'ara Maida mishi tsoro sabo sedai Kuma Ganin basuyiwa IRFAAN d'in komaiba ba yasa yamayarda tsoronshi yahau Shima kana suka mik'e tareda rugawa aguje yanufi inda wannan budurwar taturosu....! Masha allah 😊 Ina godiya sosai da comment d'inku da Kuma addu,o,inku agareni ubangiji allah yasaka da alkhairi Kuma allah yabar zumunci naji dad'i sosai Kuma nagode I love you so very much all my lovely fans 😚 💃💃💃💃💃💃💃💃 Autar alheri ✍️ 🌳🌴🌳 *JEJI GIRL*🌳🌴🌳 (Yarinyar jeji renon namun dawa 👱♀️🦣🦍🐆🦑) *Labari meban Al ajabi da birgewa (romantic love and sexy story)* Paid Page 25 & 26 ____✅____&&&&&&&&&&& "Tindaga nesa suka hangesu tafe cikin sauri fadeel yamik'e Yana mik'a mata hannu alamar tamik'e itama,,,aiko ba musu tarik'a kana tamik'e tsayen....suko Basu tsaya ko,inaba se agabanta tad'ago tana kallansu fuska amarairaice alamar miyasa zakuyi nisadamu Kuma kunga yadda wurin yake..shiko IRFAAN yana dirowa yarik'a hannun Hafees Yana kallanshi kamun yace wai miyasa kabarmu bro? Yanzuda way'annan miyagun suncutarda kaifa? Yakakeso nayi kenan datawa rayuwar? Yak'arasa zancen kamar zeyi kuka..cikin sauri Hafees yarungumeshi Yana fad'ar I'm sorry my bro Nima bansan ya,akayi nazonanba kawai nagannine anan alokacinda way'annan namun dajin suka fito ni wlh banmasan ya,akayi nakawo wannan wurinba. "Ya,Isa Hakan my brothers kuyi hak'uri yanzudai tinda komai lpy semu Koma karsu yaya Mahmoud suyinemanmu Kuma fadeel yafad'a Yana dafa Hafees d'in...juyawa sukayi suna kallan wannan damusun dakuma wannan budurwar data duk'a tana sunbartasu...kamun suyi magana fadeel yace itace tatura way'annan bayin Allah sunemo Munaku domin muntifo nemankune tajigata baiwar allah gashi ko lpy batada wlh k'arfin Haline kawai takeyi Amma tana kirki sosai dudda zamanta k'aramar yarinya nibanmasan miyasa take zaune ananba...tinda fadeel yafara magana Idon Hafees sukacikada kwallar tausayinta dakuma tausayin kansu..shiko IRFAAN Wani abunne yakeji aranshi Gameda ita shin itad'in wacece irin mutince Hakan? Tafisan farin cikin Wani akan nata dudda batada lpy Amma takasa samun sukuni tahuta sabidasu? Gaskiyar Babu dayace irinsu ba,abun abarsu bane domin sunada matukar anfani acikin Al,imma..nisawa yayi afili yace tabbas kuwa hakanne domin irinta kad'anne aduniya...mikace bro? Cewar fadeel..nothing yafad'a atak'aice kana Yakama hanyar barin wurin. Dukansu sukabi bayanshi harda yarinyar way'annan damisun nabiyeda ita zasu mata rakiya...tafiya sukeyi sosai domin sunbaro wurin danisa itako gashi tagaji matik'a domin zazzafan zazzab'i yataso Mata gashi Kuma bawasu kayan kirki ajikinta rigar IRFAAN ce kawai Kuma dakad'an tawuce gyiwwarta duk tajigata..shiko IRFAAN yanacikin tafiya seya waigo baya kamar kuwa Wanda akacewa juya kaga aiko seyaga tana layi kamar zata fad'i ga mukarabanta sun sakata atsakiya...cikin sauri yadawo bayan kamun yak'araso kawai tayi baya,,,cikin zafin nama yatarota tadawo jikinshi agalabaice Idonta na lumsashewa...su dukkansu juyowa sukayi Ganin yadda IRFAAN yayi sufa bayansu yatarota..hankali tashe suka had'a Baki wurin fad'ar lpy kuwa bro miyasameta? I don't know but maybe malaria ne..innalillahi sukafad'a alokacinda sukaga yadda take rawar d'ari gashi sunasan k'arasawa garesu suna Jin tsoro dumin duk Idon way'annan askarawan yadawo kan IRFAAN dame dokeda ita Amma dai basuyi komaiba,,,ahakan sukaci gabada tafiya harsuka k'arasa wurinsu IRFAAN na d'aukeda ita. Akwance duk suka samu su ya Mahmoud sunyi bacci haik'an...itako gwaggon birin Nan tana ganinsu daukeda ita tak'araso tana tab'ata Ganin yadda take kamar Bata motsi...shiko IRFAAN ajiyeta yayi kana yak'arasa bakin kogon Dake kasan bishiyar ya kwantarda ita bayan a shimd'a rigar fadeel ak'asa..jakar kayansu ya Mahmoud yad'auko yabud'e Yana Neman maganin zazzab'i ko injection yayi mata Amma duka babusu Sena kashe zogi kawai dayayimata anfanidasu...dafe kanshi yayi tareda Dan ciza lips d'inshi Yana tunanin tayaya ne zasu temaka mata Ganin bayada abunda ze iya tinda ba aikinshi bane yasa yamik'e tareda nufar inda suke kwance,,,ya Mahmoud yatada Dakyar,,bayan yatashi becedashi komaiba hannunshi kawai yarik'o sukazo wurinta yanuna mishi ita..Shima bedamuda rashin maganarshiba domin inda sabo yasaba bakomai IRFAAN ke bud'e Baki yayi maganaba sedai idan tab'ace,,,, duk'awa yayi yatab'a jikinta kana ya duddubata kanshi ya girgiza kamin yak'e yace wlh zazzab'i ne kedamunta Kuma wlh bayan wannan ciwon najikinta hadda sanyin wurinnan shine ya haddasa nata wannan zazzafan zazzab'in...ohh my god IRFAAN yafad'a kamun yabud'e Baki ahankali yace to yanzu abata magani mana. "Wanne magani Kuma IRFAAN ai Babu maganin daze saukarda wannan zazzab'in sanyin wlh se d'imin jikin mutin kawai abunda yafi muyi gaggawar barin jejin Nan domin Asama mata lpy...shiru IRFAAN yayi Yana yiwa ya Mahmoud kallan bakada hankali tayaya zamubar jejinnan da,ita ahakan muma fita yaya,,Amma bece komaiba kawai shiga kogon ya Mahmoud yaga yayi kana yacire rigar jikinshi wadda tarage kana yad'aga yacire tata Amma seda yakare ta yadda su yaya Mahmoud bazasuga jikintaba Shima kanshi be kalletaba kawai yayi saurin had'e fatarsu wuri d'aya aiko seda yazabura tareda fisko numfashi dak'arfin gaske Jin Yana barazanar d'aukewa,,, yad'auki kusan minti 5 kamun yasamu ya dedeta nutsuwarshi kana yak'ara sakata jikinshi yarungumeta sosai tareda d'aukar rikunanshi duka yarufesu. "Ido ya Mahmoud yazaro cikin mugun mmki yace IRFAAN kanada hankali kuwa tayaya zakayiwa har mutane Hakan? Shi kasan abunda ka aikata kuwa ko me Hakan kenufi? Kahad'a jiki da yarinya budurwa Kuma dukkanku Babu kaya ajikinku yoshe kakoma Hakan? "Please ya Mahmoud Dan Allah kadena wannan zancen Bafa komai zemataba kawai temakonta zeyi kasan cewa bazeyu afita da,ita daga cikin jejinnan ba muddin tana Hakan domin wlh way'annan dabbobin bazasu bariba kosokakeyi su hallakamu ko mukoma Bata su Abba suka kasawarmu? Hafees yafad'a yanasan fahimtarda ya Mahmoud d'in abunda yasa IRFAAN d'in yayi Hakan....nisawa yayi Yana kallansu nadan Wani lokaci kamun yace wannan Kuma hakane to Amma aiba muharamarshi bace bakuma matarshiba yanayin yadda suka had'a jikifa za,a,iya samun matsala tinda kowannensu akwai jini ajikinshi kumafa haramunne...Dan murmushi fadeel yayi Yana rik'o hannun ya Mahmoud yace wlh kabani dariya ya Mahmoud karka damu Indai IRFAAN Babu abunda zefaru domin manyan baby's ma suna kawo maikansu
Table of Contents