Skip to content

Chapter 15

Chapter 77

Babu So Mi Yakawo Kishi Book One Complete Hausa Novel 15,711 words 0 views Progress saved
Download Book

77

........Kaɗan ya rage zuciyar Fadwa yin tsale ta fito, jikinta na rawa tace, “Wlhy ƙaryane, munafukar tsohuwa da bazataga MANZON ALLAH ba”.

  Saukar mari taji lafiyayye daga Mahaifinta. Gwaggo ta jinjina kanta cike da jin daɗi, “Nagode Sadiqu. Ba laifinta bane uwace bata moraba. Yo dama yaushe Halima taga wata tarbiyya balle ta bata. Ai bakai dace da mata ba wlhy”.

  Cikin matuƙar mamaki su Daddy suke kallo da sauraran Gwaggo da alamu suka nuna akwai suɓutar baki a kalamanta. Gwaggo Halima zatai magana Alhaji Sadiq ya dakatar da ita. “Wlhy kikace tak sai kinyi nadama Halima...”

   “Barta tace in ma tanada abin cewar mana. Dan kuwa inada ƙwaƙwaran hujjar ita ta zubar da cikinta da kanta, saboda karya hanata waɗan nan raye-rayeda sukeyi na zamani a wannan abubuwan da kuke kira yanar gizo-gizo ko uwar mima. K Luba kiramin Bibah ta shigo da likitan da ta saka yaymata aikin. Amma kafin sannan fara latso min ita a wayarki su gani”.

   Cikin rawar ɓutiya Hajiya Luba ta latso Fadwa a tiktok ta miƙama Baba Ibrahim dake a tsakkiyar Daddy da Abie, sai Baban Fadwa a gefen Daddy, Abba kuma na gefen Abie. Wani video ne na rashin mutunci da aka ɗauka a ranar kamun Fadwa. Ana gobe ɗaurin aurenta da Shareff kenan. Kayan barcine jikinta riga fingila iyakarta cinyarta amma ta kusa gwiwa, sai gashinta dake a buɗe tama warwaresa akan kafada. A yanda taketa komanta kai tsaye da farko na rawar wata wakar turanci zaka san bata san ana dauka ba. Sai a kusan ƙarshe-karshe take kare jikinta da filo data ɗauka tana masifar miyasa zatai mata video, sai dai anyi cutting sunan wadda ta ambata na mata video ɗin. Bayan shi akwai wasu daban-daban na rashin mutunci, abindama zai baka mamaki kamar an tsinto iya wanda tayi abin ALLAH wadai ɗinne kawai an ɗora a shafin. Hatta wayarsu ta ranar daurin aure da Shareff duk akwai a wajen, duk wani faɗa datai da wani a tiktok ko rawar banza cikin shigar wofi duk sune aka tato aka ɗaura. Harda ma wanda bata kai tiktok ɗin ba

    Komai ya ƙara tsayama Shareff cak, bama shi kaɗaiba hatta sauran jama'ar falon gaba ɗaya. Kafin wani ya samu damar tofa tasa sai ga Bibah da likitan daya zubdama Fadwa ciki. Harga ALLAH tayi matuƙar firgita. Zuciyarta ta dinga tsitstsinkewa lokacin da Gwaggo ke faɗa masa ya faɗi miye alaƙarsa da Fadwa. Kansa tsaye babu fargabar komai saboda an toshe bakinsa da kuɗi ya fara bayani tiryan-tiryan tun zuwan su Fadwa da ƙawayenta Sima da Amal. Baice akwai Bibah da Siyyah ba. Sai yanzu ne Fadwa ta samu damar fashewa da kuka.

   “Wlhy wlhy ba haka akaiba. Bibah kiji tsoron ALLAH, dan kina son auren mijina basai kin ƙullamin sharri ba.....”

   “Sharri kuma. Idan sharri nake miki aiga wayarki a hanunki a amsa a duba agani”.

  Duk da Fadwa tasan duk waɗancan videos ɗin tayisu amma ta goge mafi yawa a ciki saita bada wayar tata, saboda sanin masu dama-damar ne kawai a shafin nata na yanzun. Baba Ibrahim ne ya amshi wayar, sai dai koda aka duba babu wani accaunt akai sai irin wanda Bibah ta nuna.

     “To'ai babu banbanci tsakanin wannan da wanda ke anan ciki”.

  Ba karamin ruɗewa Fadwa tai ba. Harta fisgi wayar a hanun Baba Ibrahim batare da tasan tayi ba. Koda ta duba itama sai taci karo da abinda suke maganarne kawai babuma accaunt ɗinta data sani akan wayarta kwata-kwata. Mamaki da tsoro suka risketa. Takai dubanta ga Bibah sai ta samu tana murmushi, hakan ya bata tabbacin itace tai komai. Wata irin wawuyar mikewa tai ta shaƙi Bibah, nan take kokawa ta kacame Bibah ta fara kakarin mutuwa. Da ƙyar Maheer ya rabasu shi da su Aunty Bintu.

    “Shareff idan baka saki Fadwa ba wlhy wlhy wlhy har abada babu ni babu kai. Yanzu nan ka saketa, dan baka taɓa rayuwa da wadda ta zubar maka ciki ba dan son zuciyarta, sannan ballagaza.”

   Shareff da gaba ɗaya brain da Heartbeat ɗinsa sun tsaya cak daga aiki, ya dago yana kallon Mommy.” “Ba kallona nace kayiba saketa nace, idan kuma bazaka saketaba to wlhy zan......”

   “Haba Nafisa kinada hankali kuwa, ki tsaya abi komai a sannu mana”.

  “Yaya daina wani maganar a sannu, ai tunda Ubansa ya sakeni wlhy shima sai ya saki Fadwa. Dan na tabbatar abinda na aikata bai kama kafar abinda taiba. Itafa ciki ta zubar masa”. Kafin ma Baba Ibrahim yace wani Shareff da dake cikin matsanancin fushi ya furta “Na saketa saki biyu”.

   Tamkar saukar aradu Fadwa taji saukar wannan kalma. Tai baya ta zube ƙasa, ihu take son yi amma ta kasa yi tsabar yanda falon ke juya mata tana ganib bibbiyu, da sauri ta rarrafa gaban Shareff.

   “Soulmate dan girman ALLAH ka saurareni, wlhy ba.....”

  Wani irin hankaɗata yay tai baya ta zube har kanta na buguwa da kujera sai da Abba ya tareta. “Wlhy idan kika sake koda matsoni zan iya shaƙeki ki mutu, ballagaza. ALLAH ya isa ban yafe miki zubarmin da ciki ba, na tsaneki, na tsaneki, bana buƙatar sake ganin mummunar fuskarki a rayuwata har abada. Idan har zaki iya salwantar da ƙyautar da ALLAH ya bamu, abinda ke amsa suna gudan jininki to zaki iya halakani nima, na tabbata zaki iya kasheni saboda cikar burinki. Kin wulaƙanta aure na, kin nunama duniya ke ɗin baki da tarbiya, har wasu banzaye najin wani abu akanki saboda kin nuna musu ke ballagaza ce. Anya Fadwa kinada ilimin addini kuwa? Anya kin san darajar kanki kuwa? Anya kina tuna zaki mutu kuwa?, na godema ALLAH ma da ban haihu da ke ba, dan bana fatan ƴaƴana su taso su kalleki matsayin mahaifiya balle har halayenki su zama naso ga tasu rayuwar. ALLAH ya wadaran mace irinki mai tara ƙawaye da bata da ra'ayin kanta sai nasu, kije ƙawayen naki su cigaba da baki rayuwar da kike buƙata, kije, kije bana son ganinki wlhy”. Idanunsa har tara ƙwalla suke na tsananin ɓacin rai, Shareff nada kishi matuƙa akan duk abinda yakeji ya killace matsayin nashi. Yanzu haka yanajin kamar zuciyarsa zata tsage, babu abinda ke masa amsa kuwwa sai zantukan samarin ɗazun a kanta. Wata muguwar shaƙa ya kai mata jijiyoyin kansa na matuƙar tashi. “Fadwa na tsaneki, bazan yafe miki ba.....” da ƙyar su Abie suka ƙwace Fadwa a hanunsa, sai numfashi take fiddawa da ƙyar na wahala ga Gwaggo Halima na ihu da kururuwar kuka zai kashe mata yarinya. Kansa ya kife a jikin Abie dake kusa da shi, yana mai ƙoƙarin danne hawayensa. Abie ya shiga shafa kan nasa cikin lallashi tausayinsa na ratsashi. Ba Abie kaɗai ba kowama yaji tausayin Shareff ɗin dan abune mai matuƙar ciwo ga duk namijin daya san ciwon kasa. Su kansu sunajin raɗaɗi a zukatansu matsayin iyaye, mahaifinta kam ma ai ya kasa ko motsi dan gaba ɗaya ya tattara laifin a kansa shima, zuciyarsa suka take matuƙa a ƙirjinsa...........”

   *_“Tabbs da ace kayi haƙuri saki bashi bane mafita Yaya MM”._*

  Kusan gaba ɗaya suka waiwaya a inda sautin maganar ta fito. Anaam ce sanye da hijjab har ƙasa. a kallo ɗaya zaka fahimci a barci ta tashi ma. Kuma yanayinta yana nuni da batajin daɗi....

   “Ke kuma a wa, kajimin ƴar iskar yarinya. To ko ubanki Usman da uwarku basu isaba balle ke haihuwar yau”.

   “Badan na isa bane na faɗa Mommy, ba kuma dan iyayena nada wani kusanci da zama masu isa a wannan Family ɗin ba. Sai dan kusan gaskiya ku daina dukan jaki kuna barin taiki (ALLAH yasa na faɗi hausar tawa dai-dai). Tabbas Fadwa bata taɓa ƙaunataba. Kamar yanda Gwaggo Halima bata taɓa ƙaunar iyayena guda uku ba. Haka kema baki taɓa ƙaunarsu ba. Kafin wata rana ina ganin laifinku matuƙa ina kuma jin zafinku mai tsanani, sai dai lokaci ya saukaƙamun hakan sakamakon fahimtar kuma a haka aka raini zukatanku. Zan faɗi gaskiyane a yanzu ma badan ku soni ni da iyayena ba, sai dan ku sani wadda ta raineku ku kanku ba ƙaunarku take ba bawai iyayena ne kawai take ƙi ɗinba. Lallai da sanin Fadwa aka zubar da cikin jikinta, sai dai kuma Gwaggo itace ta tsara komai da taimakon momyn Bibah, su Bibah ƙawayenta su huɗu suka ɗarata a hanya har komai ya faru.....”

   Wani irin harziƙowa Hajiya Luba tayi, amma sai Baba Ibrahim ya dakata mata wata irin razananniyar tsawa. Komawa tai ta zauna daɓar. Anaam tai murmushi mai ciwo da dafe karfen benen takai zaune saboda jiri da take gani. Sai da ta ɗan dafe kanta na wasu sakkani sannan ta ɗago tana ɗan murmushi. “Kuyi haƙuri.” Batare data jira cewar wani ba ta cigaba da faɗin, “Ban faɗa muku wannan maganarba sai dana riƙe hujja, kuma dama irin wannan ranar nake jira dan nasa duk yanda Maman Bibah da Bibah zasuyi da Gwaggo sai sunyi domin Yaya MM ya auri Bibah, kuma Fadwa itace kawai makaminsu da Mommy”. Ta ƙara maganar da miƙa wayarta dan bazata iya tasowa ba saboda jiri. “Gashi komai na'a cikin nan. Ku kira Amrah ma kuji dan tasan abubuwa da yawa itama”.

   Aunty Bintu ce ta amso wayar, ta kaima Baba Ibrahim. Gwaggo ta miƙe a fusace sai dai jikinta rawa yake. Amma sai Gwaggo Halima tasa ƙafa ta taɗota ta koma zaune daɓar har tana sakin ƙarar azaba data ratsa ɗuwawunta. Sosai da mamaki mai cike da ɗunbin razani suka bayyana a fuskokinsu Baba Ibrahim. Dan kuwa dai ga muryar Gwaggo gata Hajiya Luba da Bibah. Su Mommy zasu fara hayaniya Baba Ibrahim ya hanasu, cikin matuƙar razanarwa Baba Ibrahim yace Hajiya Luba ta faɗa kokuma ya ɗauka mataki a kanta. Jikinta tsuma yakeyi, musamman da taga irin mugun kallon da Shareff ke jifanta da dashi, wanda ba ita kaɗai ba, hatta Gwaggo haɗiyar yawu take da ƙyar...

    “Wlhy Yaya mu ba laifinmu bane, kawai dai Bibah ce ke tsananin son Shareff, nayi-nayi Nafi ta fahimci abinda nake buƙata na mu haɗa aurensu taƙi, sai nunawa takeyi da Fadwa za'a haɗa. Har nayi zuciya da hakan sai dai Bibah ta shiga damuwa, shine nazoma Gwaggo da batun ko akwai yanda za'ayi, amma saita nunamin itama bata san zancenba. Ban gajiba muka cigaba da binta har akai auren Fadwa da Shareff, sai lokacinne ta fara saurarena, ta kuma tabbatar min idan har muka taimaka mata cikin Fadwa ya zube zatai duk yanda zatai dan auren Shareff da Bibah ya yuwu”.

   Salati falon ya ɗauka baki ɗaya, yayinda a lokaci guda Gwaggo Halima da Mommy suka kaima Gwaggo shaƙa, da ƙyar aka ɓanɓareta a hanunsu idanunta har sun firfito waje kamar na tsohon kwarto. Nan fa sabuwar hayaniya ta kaure har wani baijin zancen wani, dan Fadwa kam tuni ta turmushe Bibah tana jibga, itama uwarta Hajiya Luba ta turmushe Fadwan. Ƙurace sosai ta tashi a falon, wadda ta saka Anaam ji kamar duniyar na juya mata. Cikin sa'a Shareff ya hangota tana jujjuya kanta. Da sauri ya miƙe yay inda take, cak ya dauketa ya koma saman da ita tana faman jujjuya masa kanta, Mamie da itama ta hangosu tai saurin bin bayansa dan ita kam ma ba komai take fahimtaba a abinda ke faruwa a falon.

   Faɗa sosai ya kaure, duk yanda su Abba sukaso kwantar da abun ya gagara, dan tun anayi a falo har aka koma tsakar gida, kafin kice mi ƴan biki sun fara tururuwar shigowa bama idonsu abinci tunda dama akwai ƙofar dake a tsakanin gidajen wadda basai kaje gate ba. Cirko-cirko mutane sukai sunajin fallasa da tonon asirin da su Mommy sukema juna, yayinda Gwaggo ke neman naɗe tabarmar kunya da hauka. Sai dai fa ganin lamarin yafi ƙarfinta dan hatta Mommy yau la'antarta take ga ƴan biki sai ta nema fita a gidan tana kuka wai su Daddy sun shirya wulaƙantata. Nanfa wasu a munafukai masu son jin ba'asi suka take mata baya, sai dai taƙi sauraren kowa, tana gab da barin layin nasu wani mai mota ya shawo kwana, duk da horn da yakeyi sam Gwaggo daketa faman sambatu da surutai batajisa ba, shi kuma ALLAH ya hanashi damar taka birki, ya kwasheta sama ya direma kasa, yana son riƙe kan motar ina saida taya ɗaya ta dirza ƙafar Gwaggo har ana iya jin karar farfashewar ƙashi. Tun ƙarar azaba ta farko data saki bata sake fahimtar ina take ba ta suma. Dan danan aka rufu kanta, har su Daddy labari yazo musu sun fito, nan fa layin ya cika dankam. Matasa zasu rufu kan mai mota da ƴan biki yazo dauka baba Ibrahim ya dakatar da su. Kamalarsa da dattakon kasancewarsa tsohon arziƙi ya sakasu bin umarni, sai dai an kama Gwaggo da babu alamar numfashi a jikinta an saka a motar mutumin aka nufi asibiti.

    Babu ko tausayi a fuskar Gwaggo Halima, sai ma faffaɗar magana take wai ai ƙarshen Gwaggo kenan. ALLAH ma ya kara sakata a masifa fiye da hakan. Mafi yawan mutane maganganun Gwaggo haliman basu ɓata ransu ba, sai dai duk da mugun halinta baban Fadwa ya kasa haƙuri shima a wajen ya yanke igiyar auren Gwaggo halima biyu. Ai sai lokacin Fadwa da Mommy suka sake tunawa da mutuwar nasu auren fa suma. Nan guri ya kara daukar zafi faɗa ya dawo sabo fil da ƴar koke-koke abin zakkunya da takaici...........✍*_Typing📲_*

*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_78_*

.........Wannan harmutsi da dangin mijin Aysha suka tarar yasa suka dakatar da ɗaukar amarya, acewarsu ai basu san haka uwar amaryar da danginta suke ba. Ƙololuwar tashin hankali Mommy ta sake shiga, har takai ta yanke jiki ta faɗi itama dai sai da aka kaita asibitin. Gwaggo halima dake dariyar mugunta ta tafi gida ranta fes Mommy da Gwaggo a bala'i, sai dai kuma mahaifin Fadwa ya hana mata koda shiga gate, yace Fadwa kaɗai ce ƴarsa, itama zai bata mafakane har tai idda saboda karya salwantar da rayuwarta a cigaba da samun bara gurbi a cikin al'ummar musulmai. Amma ta sani bazata taɓa jin daɗi ko ɗigon farin ciki a gidansa ba. Rikicewa Gwaggo Halima tayi, kamar yanda Fadwa dake kuka rirus dama dan da ƙyar Gwaggo Halima ta jawota suka tahonan saboda ido rufe take neman Shareff amma taƙi ganinsa. Masu aiki yasa suka shigo da ita, Gwaggo Halima kuma ya tabbatarma masu gadi ko hanunta ya taɓa masa gate abakin aikinsu. A karan farko itama ta fara kuka, dan a zatonta koda yay sakin guda biyu zai haƙura ya barta ta cigaba da zama cikin ƴaƴanta har a sasanta. Sanin da yay mata zata iya ƙin nufar gida ya sakashi turata a mota da kansa yaja motar ya maidata gidan su Daddy da tuni ƴan biki sun fara watsewa, ba kowa na ɓangaren Mommy. Na ɓangaren Mom kuwa da dangin su Daddy zama daram wasuma shirin tafiya dinner ɗin Khaleel da amaryarsa suke. Dan su Hajiyar Sudan sun shiryama wannan biki kwarai da gaske....

       Komai ya hargitse, komai ya rikice. Burin Gwaggo na watsa biki wani yankinsa ya tabbata. Domin kuwa akan bigire na duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka ake. Ita dake amsa matsayin suna uwar daba tana can asibiti ƙafa a ragargaje batama san inda kanta yake ba likitoci sun rufu akanta. Manyan dodannin fadarta su Mommy sun masifar tsanarta fiye da rayukansu a yanzu. Dan kuwa Mommyn da kowa kema kallo matsayin ƴarta da zata iya zama magajiya a gareta na kwance bisa gadon asibiti jininta yay ƙololuwar hawa har yana son zarce abinda ba'a fata. Tana da saki guda biyu a kanta, igiya daya ce kacal ta rage mata a yanzu, kuma Daddy ya tabbatar musu daga asibiti su wuce da ita karta sake dawo masa gida. A daren daga gidan angon Aysha takardar saki ta iso a cewar iyayen ango ɗansu bazai rayu da ƴar mace ba. Wannan al'amari yayi matuƙar ƙona zuciyar su Daddy har Abie na tabbatarwa sai ya kaisu kotu, da ƙyar su Abba suka lallashesa. Gwaggo halima data ɗauki Gwaggo tamkar uwarta mahaifiya a yanzu babu wanda tafi tsana a duniya sama da Gwaggo, a sanadinta ɗiyarta mafi soyuwa a gareta ta rasa ciki ta rasa aurenta, ita a karan kanta ta rabu da ƴan uwanta shekara aru-aru a dalilin huɗuba ko muce tarbiyyar Gwaggo. Ta rasa igiyoyin aurenta da ƴaƴanta a cikin abinda bai gaza awa shidda da barinta gidan mijinta cike da fatin ciki ba.
     Yayinda Aysha itama ke can tana rusar kuka tamkar ranta zai fita, dan kuwa ta tabbatar alhakin mahaifiyarta da kakartane ke bibiyar ƙaddararta, a ranar da aka ɗaura mata aure a ranar miji ya saketa ko gidansa ba'a kaita ba. mijin data ɓata tsahon shekaru tana mutuwar so da ƙauna.
         Haka zalika Fadwa celeb.... Wadda ke ganin ko ta tashi a rayuwar da ita a karan kanta bata taɓa gundurartaba balle kallonta a juye. Shareff shine dukkanin farin cikin duniyarta, da sonsa ta rayu da shi ta horu, a rana ɗaya dalilin makircin ƙawayen data ɗauka babu yasu a duniyarta da cigabanta ta rasashi. Auren mahaifiyarta da aka ƙulla tsahon shekara talatin yau ya girgiza shima a dalilin wadda suke kallo gunkiyarsu da bayan horon tarbiyya ga uwarsu suma akan zaren tarbiyyar tata suka horu.....
      Shareff da komai ya ƙwace masa a wannan gaɓar tunaninsa yama rasa ina zai kama ko samun mafaka, sai dai ya jure, ya danne wajen tattare hankalinsa kan matarsa da jikinta yay ruɗewar da daren sai da Dr Jamal yazo ya sanya mata ruwa....,  ya kuma saka Fharhan a daren kaima su Sima, Siyyah, Amal, Bibah ƴan sanda suka cafkesu, tare da doctor ɗin dayay aikin.
    Abba, Daddy, Abie, aunty Mimi. Mamakin Gwaggo da ɗunbin al'ajabinta ya hana zukatansu bugawar gaggawa a ƙirazansu. Sun rasa wane aji  na duniya ya kamata sunan Gwaggo ya fita, dan a iya hasashensu sun gagara kama minene dalilinta na duk aikata waɗannan abubuwan?. Kenan akwai abubuwan da suka shuɗe da yawa a baya dake buƙatar nazari mai faɗi da neman ba'asin dalilin aikatashi ko ganinsa a aikace. Sunyi ta mazan bin su Baba Ibrahim asibiti, inda har dare ya raba suka dawo gida babu wani bayani akan jikin Gwaggon likitoci dai sun rufu a kanta sunata faman kaikawo....

    *_WASHE GARI_*.

           Sai a yau asabar zuri'ar MD Shareff suka sami ganin Gwaggo, sun fara shiga ɗakin da aka kwantar da Mommy itama bisa matsawar Abie suka dubata, inda acan suka sami Shareff da Maheer tare da ita. Basu jimaba suka fito, Mommy da abubuwa da yawa ke cin ranta musamman sakinta da Daddy yayi ta taso ta biyosu, duk yanda su Shareff sukaso dakatar da ita taƙi yarda da hakan. Hankalinsu ya tashi da ganin jikin Gwaggo, dan ƙafarta tayi wani irin mahaukacin kumbura daya ninka jikinta biyu, gashi an yanketa daga gwiwa zuwa ƙasa dan can ɗin yayi ragargajewar da bazai ƙara aiki ba. Sai kananun ciwuka da ba'a rasa ba. Da ƙyar take iya amsa musu, sai dai abin mamaki idonta a soye babu ko alamar hawaye. Bayan sun jajanta da ɗaukar kusan mintuna goma sha biyar a ɗakin sukai haramar tafiya. Muryarta a ɗashe, amma hakan bai hanata fita da kaushi ba ta dakatar da su...
      “Na rikeku na muku gata fiye da uwar data haifeku, amma a dalilin kanƙanin abu kuke nuna alamun juyamin baya Muhammadu. Bazan hanaku ba, sai dai ku sani bazan yafe muku wahalar dana sha a kanku ba”.
      “Bakece zaki ƙi yafe mana ba, mune bazamu taɓa yafe miki ba Hindatu...”
    Muryar Gwaggo Halima ta ratsa kunnuwansu a bazata. Su dukansu suka juya suna kallonta da mamaki, dan kuwa babu lallashin da basu mata ba danta biyosu tace bazata ba. Ta cigaba da takowa firingau-firingau dan a kwana ɗaya duk ta sususce ta fita a hayyacinta tamkar ba halima ƴar gata ba. Ta ƙaraso gaban Gwaggo tana mai share hawayenta. “Hindatu kamar yanda na faɗa mune bazamu yafe mikiba annamimiya azzaluma. Musamman ni nan Halima. Hakama iyayenmu dake kwance a cikin kabari, da sunada damar da zasuyi magana sautin yaje cikin kunnuwanki da sun nanata miki kalmar ALLAH ya isa fiye da sau dubu. Kinga wannan ƙafar taki da aka yanke, ba itace kaɗai ƙarshen azabar da zakisha a duniya ba. Yanzu kika fara gani, bayan ɗanɗanar ɗacin rashin haihuwa na shekaru sama da sittin da kikai a duniya, yanzu zaki cigaba da fuskantar raɗaɗin azaba ne mai muni tsinanniyar tsohuwa mai zubin ƴan wuta.......”
     “Ke ce dai mai zubin ƴan wuta...”
Cewar Mommy a hasale. Dariya Gwaggo Halima ta sanya. “Ke kumafa? Maza je kiji da kanki shasha kawai. Hawan jini da zawarci ma sun ishi rayuwarki ƴar wahala, sannan kema a gurinta baki tsira ba”.
    “Hahaha garama ni, kuma koba komai zuwa yanzu na tabbatar miki Shareff jinina ne tunda gaki a zawarci ƴarki a zawarci. Kuma yanda ya saki Fadwa itama Anaam sai ya saketa dan bazai zauna da zuri'ar waɗanda basu san hallaciba. Ƴar dukiyar da akaga ya tara akemawa to babu mai cinta har kai uban nasa”.
          A karan farko Daddy ya ɗago yana kallon Mommy, amma sai kafin yace wani abu Abba ya cafe murya a kausashe.
     “Mu bamu kasance marasa halacciba Nafisa. Wannan tsohuwar dake da kika rayu a gidanmu matsayin agola kune marasa halacci, kuma dukiya da kike takama Shareff ya tara bara na buɗe muku zancen yau, kaso biyu bisa ukun abinda kuke ganin Shareff ya tara na Usman ne.......”
     “Please Yaya Abubakar ba wannan gaɓar mukeba...”
   Abie yay niyyar katse Abba. Amma sai Abban ya fisge jikinsa. “Barni Usman, gara wannan mahaukaciyar tasan ANNABI ya faku. Duk da ƙulle-ƙulle datai domin ganin ta raba tsakaninku da Usman hakan bai hana ka cigaba da tallafa rayuwarsa ba, har take iƙirari da fariyyar dukiyar ɗanta. ki shiga hankalinki kuma kisan mikikeyi, daga ke har uwar taki, sakamako kuma yanzu kuka fara girba, dan wlhy Gwaggo alhakin iyayenmu kaɗai bazai barki sake jin daɗi ko farin cikin rayuwa ba. Tur da masu irin halinki na annamimanci da hana zaman lafiya a cikin zuri'a. ALLAH zai saka mana matuƙar sakayya a ranar da gaɓoɓi zasuyi magana madadin bakuna”.
      Tuni Mommy da kanta ke bada wani yuuuu na haurawar jininta sama ta dafe gadon da Gwaggo ke kwance. Kallon Shareff take cike da son ƙarin bayani. Lips ɗinta na rawa. Kansa ya jinjina mata tun kafin tace komai. “Mommy abinda Abba ya faɗa shine gaskiyar magana. Dukiyar Abie ce ni nawa basu wice kudin siyan ruwa ba a cikin taron biki”.
      Wata irin ƙara Mommy ta saki da faduwa ƙasa daɓar, Gwaggo ma tuni gadon da take a kai ya fara jijjigar shiga a tashin hankali. A halin da take ciki da dukkan ƙarfin halin nata Shareff ɗin shine kawai gadararta a yanzu, dan ko maganar aikin da ake faɗar za'ai mata na ƙafarta ta gama sawa a ranta ko kowa ya gujeta suna da Shareff ai. Ashe-ashe abinda sukema gadarar ma ba nasu bane. Da tasan haka bazata taɓa yarda taima su Abba hakaba. Da ta cigaba da musu fuskarta ta tun ƙuruciya. Amma yanzu ta tabbatar bakin alƙalami ya rigada ya bushe kuma....
     Cikin ƙanƙanin lokaci duk sukai waje, hatta Shareff da Maheer ji sukai bazasu iya zama ba, dan dama tsananin kunyar su Daddy sukeji saboda abin kunyar da kakarsu ta jima tana tafkawa da mahaifiyarsu duk da kuwa akwai Gwaggo Halima tare da su......

_________★

     Kwanaki sun cigaba da shuɗawa, ta tabbata dai Gwaggo Halima ta dawo gida da zama, dole ta share sashen Baba Umar da babu wanda yasan a duniyar da yake yanzu ta zauna. Mommy kuma ta koma gidan Baba Ibrahim kamar yanda ya shardanta mata, dan ya hana su Shareff bata wajen zaman da sukai niyya. Yayinda Gwaggo ke cigaba da jiyya mai wahalarwa a asibiti. Dan kuwa babu wani mai jiyyarta sai Nurse's dake kula da ita. Mommy din ma data raina da kanta tace bazata iya jiyyarta ba dan ƙafar tata duk da likitanci na kula da ita wari takeyi matuƙa. Su Daddy basuyi butulci ba tare da su Baba Ibrahim da mahaifin Fadwa ke biyan kuɗin zamanta a asibitin. Hakama Fadwa na gidansu, mahaifinta ya amshe wayarta, ya kuma kwashe dukan ƴan aikin gidan yanzu itace ke komai ga ƙanenta, girki, gyaran gida, ya baza camaras tako ina, inma bataiba ko baya gidan zai gani, hakama waya kota ƴan uwanta ta ɗauka da nufin kiran wani itama tasan sauran. Duk ta fige ta fita a hayyacinta saboda kuka da tsananin ƙulafucin mijinta da takeyi, ga Gwaggo Halima ta mata nisa yanzu, ƙanenta kuwa sai zuba mata rashin kunya sukeyi tunda dama a haka suka taso na ƙasa baya girmama na sama da shi. Satinsa uku a gidan maganar auren Babansu ya tashi da wata hamshaƙiyar mace ƴar boko mai babban mukamin gwamnati a jihar ta kano...........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**_Typing📲_*

*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_79_*

..........Yanda Fadwa ke jigatuwa a gidansu haka Mommy ke jigatuwa a gidan Baba Ibrahim, dan kuwa matansa babu kanwar lasa a ciki. Basa raga mata koda da wasa. Abinci kuwa iya abinda suka bata shine zataci, bata isa cewa tak ba Baba Ibrahim zai silleta tass. Kaf ƴaƴanta an hanasu raɓarta har su Shareff kuwa. Itama duk ta fige ta ruɗe da damuwa mai tsanani, ga rashin aure, ga rashin ƴaƴa, ga dukiyar ɗan da take taƙama dashi ashe ta maƙiyintace. Kai ina itako zata saka kanta taji sanyi wannan rayuwa haka.

       Gwaggo Halima kam ai zamu iya cewa ta susuce a wannan gaɓar. Dan kuwa maganar auren mijin nata ya risketa dan abune da aketa faman watsasa a gidajen talabijin da rediyoyi. Bikine ake shiryawa na hamshaƙai biyu masu daidaiton ƙwarya tabi ƙwarya. Ga rashin ƴayanta tare da ita, dan kuwa itama dai su Abba sun ƙwace wayoyinta, sun kuma kafa mata sharadin inhar tana buƙatar zama da su sai ta nutsu, inba hakaba zata bar musu gida, dan yanda sukayi haƙuri da ita a baya a yanzu kam bazasuyi ba.

     Kwanan su Sima takwas a police station aka shiga kotu, dan duk magiya da roƙo da iyayensu ke ma Shareff ya rantse sai sunyi shari'a. Kasancewar laifinsu a bayyane yake ba'awani wahalar da shari'a ba a zama biyu kacal aka yanke musu hukuncin zama gidan yari na watanni goma shaɗa. Tare da tara mai tsoka. Kafin kace mi media ta ɗauka, babu abinda ke trending kamar labarinsu. Manyan yaran da akeji dasu a tiktok da istagram dama mafi yawan kafafen yanar ta gizo sunsha ɗauri a dalilin shugabarsu. Ga labarin mutuwar auren Fadwa ya zama kamar wani abin izgili a bakunan wanda suke jin haushinta. Sai dai wasu hakan ya sanyaya musu jiki matuka. Dan inhar haka zata kasance ga Fadwa suma ɗin basu tsiraba kenan tunda duk iri aiki guda sukeyi, wasu ma nasu yafi nata muni matuƙa. A take wasu suka fara goge wasu videos na rashin tarbiyya dake a shafukansu, wanda kuwa ke kai musu ji suke yanzu aka fara wasan ma. (Ya rabbi ka shirya mana zuriya damu baki ɗaya😭🙏🏻)

Kwanan Anaam goma sha biyar a gidan Shareff ya dauka matarsa suka koma gidansu, dan ta ɗanji daɗin jikinta. Sai dai an sama mata mai aiki tare kuma da Aysha suka koma can dan itama tana cikin kunci da damuwa abin tausayi, dan ma Anaam ɗin na tsaye a kanta wajen ganin ta sakama ranta salama da daukar komai matsayin jarabawa.. Komawarsu gidansu da sati guda su Abie suka koma, dan Abie yayi iya koƙarinsa na ganin komai ya daidaita amma hakan yaci tura, ya zube kuɗi masu tsoka na kula da Gwaggo a asibiti ya tattara iyalansa da su Aunty Mimi suka koma Malaysia, inda suka bar Anaam na faman kuka sai da Shareff yayta lallashi...

★★★

     Zuwa yanzu abubuwa da yawa sun ɗan lafa ba kamar da ba, Anaam da Shareff sun buɗe sabon babin soyayya mai tsayawa a rai, mantawa suke da kowa da komai suna kallon kansu tamkar su kaɗaine a faɗin duniyar kawai. Tun Aysha da mai aiki najin kunya har da suka saba da gani. Dan kuwa dai tare da Shareff ake rainon cikin Anaam ɗin. Tana da sauƙin laulayi, abinda kawai bata so hayaniya. Inhar waje ya cika hayaniya yanzu zata jangwaɓe babu lafiya. Hakan yasa babu inda take zuwa sai bayan sati uku zuwa huɗu ya kaita can gidansu ta yini. Gaba ɗaya ya tattara lamarin Fadwa ya ajiye a gefe. Ko tunawa da ita ma baya sonyi balle jin sunanta. A dalilin ta yay ma tiktok tsana mai tsanani, dan zuciyarsa na ayyana masa duk wanda ke a wajen mutumin banza ne irinta. (Sai da Shareff da sauran ƴan uwa ba haka bane. A yanda muke kallon tiktok ba hakan bane. Shima dai dandaline tamkar kowane dandali na media. akwai na ƙwarai akwai bara gurbi. Kawai dai a komai bara gurbi sun fi saurin yin shura a idon al'ummarmu ne da yaɗuwa. Kuma ita yanar gizo tamkar kasuwa take, abinda kai niyyar shiga ka saya shine zaka nema kuma ka samu. Dan haka tiktok akwai mutanen kirki a cikinsa masu yaɗa abubuwan alkairi saɓanin tunaninmu na musu kuɗin goro. Fatanmu matan aure irinsu Fadwa da suka tsunduma rayuwarsu a waɗannan hanyoyu ALLAH ya shiryesu. Hakama ƴammatanmu da basuyi aurenba ALLAH ya shiryesu ya basu mazaje na gari, hakama zawarawa da samarinmu baki ɗaya).

     Watanni kusan huɗu da faruwar komai aka sake ɗaura auren Aysha da Dr Jamal, sai dai su Abie basu zoba sun dai saka albarka. Hakama Daddy ya haramtawa dangin Mommy zuwa bikin har ita kanta Mommy din. Tako ci kuka mai zafafa zuciya, har tanajin inama bata biyema Gwaggo ba da ayanzu haka tana nan an dawo da ita gida. Sai dai kasancewar babu inda zata zauna a gidan baba Ibrahim aka haɗasu ɗaki ɗaya da Mommy. Ko kallonta Mommy batayi, balle ta taimaketa koda da bada magani ne. Kullum cikin mata ALLAH ya isa takeyi. Kaf dangi an rasa mai jinyarta, dan kuwa dai ƙafarta da gaske ta ruɓe, a yanzu hakama ana shirin gundile har cinyar data ragene saboda imfection ya shiga.

     Zuwa yanzu cikin Anaam watanni bakwai ne ciff, hakama matar Maheer an gamu, dan shima dai ya kwantar da hankalinsa zuwa yanzu ya rungumi matarsa. Matar Khaleel ma dai nada cikinta ɗan wattani uku. Haka amaren suka cigaba da rainon ciki musamman Anaam dake a gaɓar gangara. Shareff dai na shan shagwaɓa matuƙa. Dan kuwa kun san mutuniyar taku da raki. Ga kuma cikin daya fara tsufa yana yawan sakata a saurin fushi, hatta da mai aikinta taka tsantsan takeyi. kullum cikin rigimar ita a Malaysia zata haihu take. Su Abie da Shareff nata lallashinta, acewarsu suma sun kusa dawowa Nigeria. Haka dai akaita rarrafawa har ALLAH yasa aka shiga watan haihuwa da ƙyar. Dole fa badan yaso ba Anaam ɗin ta koma gaban Mom ta cikagaba da kula da ita ana jiran naƙuda. Shareff ma sai ya haɗa kayansa ya koma can gidan shima. Dan kuwa dai nan ɗin ya masa daɗi shi kaɗai, yana matuƙar jin kewar ƴar darun tasa.
      A daren wani alhamis ta farka da naƙuda mai tsanani, babu shiri suka nufi asibiti a daren. Sai dai fa tun ana jiran haihuwa har al'amarin yaci tura aka yanke shawarar za'a mata cs kamar yanda Dr Bilkisu ta basu shawara, dan ta tabbatar musu jikin Anaam baida ƙwari za'a iya zamun matsala gaskiya. Dole Daddy ne ya saka hannu da Shareff kwata-kwata baya a hayyacinsa. Yana can maƙale da Anaam tana kuka yana rungume da ita. Anyi-anyi ya bar ɗakin haihuwar amma yaƙi, dan shi gani yake daya gusa zai iya rasata.
    Alhamdulillahi zuwa ƙarfe ɗayan rana aka samu nasarar zaro mata ƴar babynta mai kama da ita kamar tayi kaki ta ajiye. Kowa na murnar ɗaukar Baby shi baban baby hankalinsa nakan uwar baby. Dan bai samu nutsuwar ganin ƴar tasa ba sai da aka miƙa Anaam ɗakin hutawa, ya tabbatar ta ambaci sunansa cikin mayen barci sannan ya samu nutsuwa. Cikin ƙanƙanin lokaci hoton babby ya zagaye dangi har ƴan malaysia, zo kaga murna wajen Abie da Mamie tamkar zuyi tsuntsuwa su ganzu a 9ja kawai. Dangi tako ina shigowa suke asibitin, harda dangin Mommy waɗanda ma ba'ai zaton gani ba.
        Shareff dai na nane da natarsa harta farka, ya rungumeta yana mai sanya mata albarka da tarin godiya. Bata da ƙarfin rungumarsa. Amma tana maijin daɗin addu'oin da yaketa zuba mata da albarka. Ya sumbaci lips ɗinta suna mai kallon juna da murmushi. Ƴar babyn ya ɗakko saitin fuskarta yana nuna mata, ta kai hanunta saman kan yarinyar a hankali ta shafa, tare da sumbatar goshinta hawaye na silalo mata. Ita Anaam itace da baby a hannu mallakinta, ita kaɗai iyayenta suka haifa babu wa babu ƙani, yau sai gata da gudan jininta kuma. A hankali ta furta “I love you Yaya MM”. Cak ya tsaya daga sumbatar babyn da yakeyi, ya tsura mata idanunsa da ke nuna tsantsar rauni da jin kalmar a bazata. Tunda suke tare bata taɓa furta masa ba. Kai duk soyayyar da yake ambata yana mata bata taɓa nuna ta damu ba balle ta karɓa masa. Tana dai ƙyautata masa da kuma shagala a tare da shi a duk sanda shi yake jadada tasa soyayyar a gareta harta bada gudunmawar maida murtani....
      “Dan ALLAH ki maimaita Noorie, danna tabbatar ba mafarki nake ba”.
    “Ba mafarki kake ba Yaya MM. kanwarka na tsananin ƙaunarka, kamar yanda ka rayu da sonta haka itama ta girma da soyayyarka, sai dai wani nauyayan dalilai sun matuƙar ɓoye hakan a zahiri. Kai kaɗai zuciyata ta taɓa so Yaya Al-Mustapha, bayan kai kuma bazan taɓa son wani ba, ina fatan na zame maka mata har a gidan aljanna. ALLAH yasa mu mutu tare...”
     Ta ƙare maganar hawaye na ziraro mata. Hanunsa dana baby da batasan sunaiba tanata baircinta ya haɗa waje guda ya share mata hawaye. sannan ya rungumeta yana mai jera mata tari-tarin kwandunan godiya marasa adadi, tare da sake jadada mata ɗunbin ƙaunarta dake ratsa jininsa da ɓarko a kowanne bugawar cikar sautin sakan na agogo, “Na gode da waɗan nan kalami masu tsada tsadar tsada. Kece mace ɗaya tilo dana fara so, bazan taɓa iya jera sonki dana wata ba har abada.”
       A hankali Fadwa dake tsaye bakin ƙofa taja hanun ƙanwarta suka koma da baya. Dama Daddynsu ne yazo da su suyi barka su kuma duba Anaam ɗin. Shi yana can tare da su Daddy a waje akace su su shigo, shine tai gamo da wannan al'amari. Kuka take rurus zuciyarta na mata raɗaɗi da zafi, tasan ko iya haka aka tsaya Anaam tayi winning a kanta. Shareff kuma ya mata nisa, nisan irin wanda sama kema ƙasa. Duk wanda ya ganta dole ya tausaya mata, dan tana a cikin tsananin ciwo na so da har ya haifar mata da ciwo a zuciya. Tana tsananin son Shareff har bata san iyaka ba. A ƙarshe wannan rana sai a asibiti ta kwana magashiyyan.

       Washe gari su Mamie suka iso, nan fa sabuwar murna ta tashi, Baby taga ƙauna a wannan ranar dan kamar za'a cinyeta. Har faɗa ake tsakanin Abie da Mamie wajen ɗauka. Da wannan ya amsa sai ɗayan ya kwace, dole dai aka koma ƴar minti bayan minti. Anaam da Shareff nata faman musu dariya. Kwananta biyar a asibitin aka sallamesu suka koma gida. Kai tsaye wajen Mamienta aka wuce da ita. Inda suka samu ana shirya gagarumin bikin suna da yafi na bikin aure. Dan kuwa su Abie sunce anan zasu fanshe.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**_Typing📲_*

*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_80_*

...........Ranar suna yarinya taci suna *_Ai'shatul-Humairah_* ataƙaice anma Mamie takwara dai. Kowa yaji matuƙar daɗin karar da Shareff ya nuna. Shiko yace yayine saboda Mamie uwace a garesa da bazai taɓa mantawaba. Mommy haihuwarsa kawai tayi, amma badan ALLAH yasosa da rahamar komawa hanun Abie da Mamie ba da yanzu bama asan yaya rayuwarsa take ba. Ga kawunsu nan Umar har kowama ya manta da shi a cikin zuri'arau.
      Tabbas burin su Abie ya cika wajen haɗa gagarumin taron suna daya sake tabbatarma da duniya wanene Abie ɗin. Ashe duk wani waiwai da akeji a bayan kan dukiyarsa abin ya zarce hakan. A ranar ya mallaka company ɗin dake hanun Shareff ga Anaam ɗin da Shareff halak malak, sannan ya ajiye wata gagarumar ƙyauta ga jaririya Aysha Humairah data girgiza kowa a wajen taron nan. Dan Mommy gaba ɗaya neman susucewa tayi saboda ta halarta itama bisa jagorancin Baba Ibrahim. Gwaggo Halima kanta a ranar jikinta ya ida yin sanyi da lamarin Abie. Dama gata a firgice da ganin Amaryar Baban Su Fadwa da a yaune suka fara ganin juna. Da kuwa sai dai ta ganta a television. Taci kuka matuƙa kamar yanda Mommy itama taci nata. Fadwa kam dama dai batazo ba. Amma hakan bai hanata gani a wayoyin mutane dama television da aka nunaba har a NTA. Itama dai ranar batai kwanan lafiya ba, dan kyarshe dai sai dama aka bar ƙasar da ita a washe gari saboda ciwonta yay matuƙar tashi fiye da ko yaushe. Hakanne ya sake birkita Gwaggo Halima ta koma kamar ƙaramar mahaukaciya. Abin tausayi abin dariya.
       Amaryar jego da angon jego kam sun sha ƙyau har sun gaji, dan kuwa kallo guda zakai musu kasan naira tayi kuka. Sati biyu dayin suna su Abie suka ɗauke Anaam sai malaysia. Shareff bai soba amma haka ya dake ya daurema ransa. Abinda ya ɗan ƙara sauƙaƙa masa zuciya ganin Mommy ta matuƙar sakkowa a yanzu, sai dai bayajin daɗin zagin da ake mata a dangi game da watsar da Gwaggo dake a cikin mawuyacin hali. Dan anyi aikin ƙafar an guntule, yayinda likitoci suka gano kuma tana ɗauke da kansar jini bayan ciwon zuciya mai tsanani. Kullum cikin kuka take na rashin samun haihuwa, dan kuwa rashin kulawa daga Mommy na matuƙar caccakar ruhinta. Ga ƴan uwa kuwa dama babu ta inda bata zama fitilar sharri data haska kowa ba. dan haka kowa ɗin gudunta yakeyi, tunda ma wadda ta riƙa tamkar ƴarta ta gujeta waye zai tsaya. Su dama ƴaƴan Baba Ibrahim da matansa basu zurfafaba. Iyaka su basu abinci su koma gefe, dan hatta Mommy mai lafiyar ma ba daɗin zaman gidan takeji ba sam. Sai dai babu yanda zatayi tunda nan dinnne kawai da ita ai. Idan tace zata barsa ina zataje. Da kunya dai ta koma gidan ƴaƴa ta zauna. Ita da Gwaggo Halima kam gaba sai abinda yay gaba. To take jerama Gwaggo ma ALLAH ya isa dake matsayin uwa gareta balle bare.

       Watannin Anaam biyu Shareff ya kasa haƙuri yay shiri yabi bayansu. Babu zato ko sanin zuwansa kawai sai gashi, a lokacin Anaam na falo zaune tana shayar da Muhseenah. Haka suke kiran babyn dashi. Mamie na gefenta tana gyara mata dan har yanzu bata iya komai yanda ya kamata ba. Abie na daga tsaye a ƙafar upstairs yana musu dariya dan Anaam ɗin na darune wai ita yarinyar ta cika ci ita kuma ta gaji. Sallamar Shareff ta sakasu kallon ƙofar kusan lokaci ɗaya, sai dai kowanne zuciyarsa taƙi gaskatawa sam. Abie ne yay ta maza yaje ya buɗe ƙofar. Ya waro idanunsa sosai da faɗin, “Son! Kai ne ɗin dai da gaske?”.
    Murmushi Shareff yayi idanunsa a ƙasa, zai rissina domin gaisheshi Abie ya jawosa jikinsa ya rungume. “Ja'iri ka manta gaban Abie ɗinka kake?”.
        Murmushi yayi dajin ƙaunar Abie ɗin matuƙa. Suka ƙarasa cikin falon inda suka iske Mamie riƙe da Baby Muhseenah da Anaam ta manna mata ta gudu sama tun jin Abie ya Ambaci sunan Shareff. Cike da jin nauyi da kunya ya ƙaraso gaban Mamie ya durƙusa. Mamie dake murmushi tace, “Oh oh Babana miye haka. Tashi mana ni bana son wannan sinne sinnen kan, ko baka iyayen damune yanzun ka ɗauka wani babi daban kuma?”.
     Da sauri ya girgiza kansa. Mamie tace, “Ato gara dai ka gyara kafin mu fara fushi da hakan”. Ta kare maganar da miƙa masa Baby. Gani yay ta ƙara masa girma da wayo, wataninta uku kenan a duniya, kamaninta da Anaam ya sake bayyana matuƙa. Abubuwa ƙalilanne nasa ta kwaso. Ya rungumeta a ƙirjinsa yana maijin sonta da ƙaunarta ta musamman, kafin ya kai lips dinsa ya sumbaci goshinta yana mai ambaton , “ALLAH yay miki albarka NoorulAyn”.
     “Amin ya rabbi”. Abie dake ta bayansa batare daya sani ba ya amsa masa. Ji yay duk kunya ta lulluɓe sa. Amma tuni Abie ya kaudata ta hanyar zama kusa da shi. Dai-dai nan Mamie ma ta dawo ɗauke da tray tana murmushi....

     Duk yanda yaso ganin gimbiyar tasa taƙi bashi daman hakan. dan ƙiri-ƙiri taje ɗaki ta ɓoye abinta, har yaci abinci ya gama bata fito ba. Mai aiki ta kammala gyara masa ɗakinsa dake gidan ya shiga domin watsa ruwa ya ɗan huta. Sai dai kuma hakan ya gagara. Wankan kawai ya iya yi ya fito cikin sanɗa. Sai da ya tabbatar su Abie basa a falon yay wuff sama ɗakin Anaam..
        Tana kwance rigingine ta kifa Muhseenah a saman cikinta waya manne a kunnenta, yanda taketa faman murmushi zai baka tabbacin wayar na sakata nishaɗi. Dan ko motsin shigowarsa ma bataji ba. Ɗakin yana a yanda ya sanshi, komai na cikinsa kalar da tafi so da ƙauna. Tsaf cikin ƙamshi. Sai dai an samu ƙarin wasu abubuwa na Muhseenah. A ɗan zabure ta buɗe idanunta dake lumshe jin an ɗaga yarinyar daga jikinta, cikin ido suka kalla juna, ta lumshe nata tare da ƙoƙarin kaudasu gefe tana sallama da Aysha da suke wayar, wadda itama take faman da laulayin ciki a yanzun. Kwance ya kai kusa da ita shima tare da ɗaura Muhseenah a saman cikinsa kamar yanda ya samesu. Tai ƙoƙarin tashi ya jawota jikinsa.
    “Kai Yaya”.
“Shiiii!!. Ni kikema wulaƙanci ko?”.
Baki ta tura gaba, “Ni wulaƙancin mina maka?”.
  “To fushi ne?”.
Tai ƙoƙarin janye jikinta ya hana hakan, sai ta fara masa kukan ƙarya. murmushi yayi da sauke Muhseenah gefe ya rungumeta jikinsa da ƙyau har sai da ta saki ƴar ƙara, kafin ta sami damar cewa wani abu ya manne lips ɗinsu waje guda ta yanda abinda take son faɗa bai sami damar fita ba. Tun tana masa bori harta amsa ɗari bisa ɗari. Sai da suka cakuɗa junansu matuƙa tafiya zatai nisa Baby Muhseenah ta fara kuka. Da ƙyar ya iya raba jikinsu ya ɗauketa. Ya lakace mata hanci da sumbatar goshinta cikin furzar da numfashi. “Mamana am sorry laifin mamanki ne fa”. Yay maganar yana kallon Anaam. Hararsa ta ɗanyi da juya musu baya. Yay murmushi. Itama dai koda ta juya ɗin murmushin takeyi, ƙaunarsa na sake ratsa mata dukkan jijiya da ɓargon jiki. Sai da ya tabbatar Muhseenah ta koma barci sannan ya sake kwantar da ita ya kwanto jikin Anaam da duk tana jinsu, a tare suka saki ajiyar zuciya.
      “Kazo lafiya?”.
   “Baki so sanin hakan ba ai”.
“To amma Yaya zakazo koka sanar min, sai kawai na ganka kamar daga sama?”.
      “Dama idan mutum zaizo gidansu sai ya shelantama duniya zaizo?. Noorie na na kasa haƙurine kewarku ta isheni ALLAH”.
   “Ni ban yarda ba”.
“Sai na nuna a aikace kenan?”.
Da sauri ta zabura dan tasan ina ya dosa. Ya fara dariya yana maidata ya matse. “Kefa na fahimci matsoraciya ce ALLAH”.
   “Ai tsoro halak ne kuwa, ina zan iya da kai da wannan yankan a jikina. Nifa ba ruwana yanzu an daina wannan dani kaje ka dawo da Fad....”
   Ganin fuskarsa ta tsuke lokaci ɗaya ta haɗiye sauran maganar. Ƙoƙarin janye jikinsa yay a nata ta sake lafe masa. “Miye kuma na tsuke fuskar? ALLAH ko ƙyau bakayi”.
     Muryarsa a ɗan tsaurare yana mai kallon tsakiyar ƙwayar idonta. “Idan ina tare dake bana buƙatar maganar wata, inba hakaba zan hukuntaki”.
   “Am sorry sir, baza'a sake ba ok”.
Ta faɗa tana mai sakar masa kiss a ƙirjinsa. Dole ya saki ajiyar zuciya da sake ƙanƙameta tsam dan dauriya kawai yakeyi. Cikin kunnenta ya raɗa mata, “Zaki rakani wani waje?”.
     Itama a hankali tace, “Ina kenan?”.
“Ba'a faɗa ai”.
   “Mu cema su Abie mi?”.
Cikin tsakkiyar ido yake kallonta yana murmushi. “Zaki raka mijinki mana”. Sosai ta waro masa Raunanannun idanunta dake cikin gilashi. “Tab badani ba wannan ta'asar”.
       Murmushi yayi mai bayyana haƙora sosai, “Shikenan sai muyi zamanmu anan ɗakin kawai to”.
   “Kamar ya?”.
“Kamar yanda kikaji mana. Kina nufin zan iya cigaba da haƙurin nesanta kaina da zumata. Ina kewar garden matuƙa autar mata”.
    Sosai maganar ta bata kunya, ta cusa kanta a ƙirjinsa. “Ni dai babu ruwana ALLAH”.
        “Shiyyasa naga kina maƙaleni”.
Turesa ta farayi yana riƙota suna dariya. “Wasa nake Sarauniya. Ai ke Ustazah ce na sani babu ruwanki, Mamana ma fa a ruwan gidanmu kika shata”.
    Dariya takeyi sosai da kai mata ƙananun duka yana ƙoƙarin riƙe hanun shima yana dariya. Haka suka kasance a cikin ɗakin tare cikin farin ciki mara misaltuwa har sai da akai kiran sallar magrib. Koda ya fito suka haɗu da Abie sai yayta sinne kai. Shiko Abie yay tamkar baima fahimcesa ba. Atare sukai dinner cike da farin cikin. Muhseenah na jikin Abie. Anaam da Shareff sai faman zinguran ƙafan juna sukeyi ta ƙasan table. Daga Mamie har Abie na lure da su sai dai babu wanda ya nuna ya gani ɗin har aka kammala. Falo suka dawo aka buɗe sabon babin hira cike da farin ciki irin na kammaluwar family. Anaam ce ta fara guduwa dan ita bata iya doguwar hira ba, Mamie ma ta ɗauka Muhseenah dan tai mata shirin barci tabar Abie da Shareff. Sun ƙara ɗaukar lokaci suna hira kafin su tashi suma.
    Duk yanda yaso yin barci sai ya kasa, haka yayta juye-juye cikin tausayama kansa. Ya kira Anaam kuma bata ɗagaba, yasan tayi barci dan ita kasa ce bata jimirin doguwar hira. Kasa jurewa yay ya miƙe ya fita, gidan shiru alamar kowa yayi barci, ɗakin Anaam ya shige cikin sanɗa. Tuni kuwa tayi barci abinta, bayan ya shafa kan Muhseenah dake barci cikin ɗan gadonta ya haye gadon tare da ɗage lallausan duvet ɗin da take ciki ya shige abinsa. A jikinsa ya nutsata yana mai sauke ajiyar zuciya, itako da bata san yanai ba tuni ta gyara kwanciya da sake shigewa jikinsa. Sake ƙanƙameta yay yana maijin nutsuwa na saukar masa. A ransa kam yana godiya ga UBANGIJI ne daya mallaka masa wannan halittar daya girma da sonta da ƙaunarta mara misali a zuciya da ruhi, yana fatan su tabbata tare har ƙarshen numfashi batare da wani gagarumin saɓani da zai taɓa zuciya ba.........✍

😝ALLAH yasa su Mamie suyi kamu🚴🏼🤣.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*[11/25, 12:21 PM] +234 906 975 1512: *_Typing📲_*

*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_81_*

.........Da asuba yay wuf ya koma nasa ɗakin, lokacin da Abie ya sakko ƙasan har yayi shirin massallaci suka fita tare. Koda suka dawo anan falo suka zauna shi da Abie suna tattauna abinda ya shafi company har gari yay haske.
Mamie na Kitchen tare da mai aiki suna haɗa breakfast Anaam ta fito. Da ga Shareff har Abie kallonta suke da murmushi, ta miƙama Abie Muhseenah da itama akai mata gayu tanata zuba ƙamshi kamar uwar tata.
Abie dake murmushi ya lakace hancin Muhseenah. “To ni dai baza'a ɗauka hankalina da wannan kwalliyar ba. Matata ma ƴar gaye ce”.
Dariya Anaam da Shareff dake satar kallon juna sukayi, kafin Anaam takai zaune tana gaishesu. Ganin mayataccen kallon da Shareff ke binta da shi ƙasa-ƙasa ya sata barin wajen tana ɗan masa hararar wasa. Kitchen ta nufa wajen su Mamie ta cigaba da tayasu itama.

Yauma kamar jiya tare sukai breakfast gaba ɗaya, kamar yanda Shareff ya kasa daina satar kallon Anaam haka itama ta kasa daina satar kallon nasa. Yauma dai iyayen nasu na lure da su. Dan haka suna kammalawa sun koma falo Abie ya maida hankalinsa ga Shareff. “Babana akwai aikin da zan turaka Indonesia kuwa, ni naso wucewa a yau sai kuma wata ta tasomin anan ɗin, kaga zuwan naka yamun daɗi ai, dan haka sai ku shirya zuwa dare insha ALLAH zaku wuce na kammala muku komai”.

Gaba ɗaya Shareff ya daburce, dan kuwa abinda zuciyarsa ke raya masa Abie ya gama harbo jirginsa ne. Kafin ya samu damar yin wata magana Abie ya miƙa masa file ɗin hanunsa. “Duk abinda zaka buƙaci sani yana anan. Sai ku fara shiri ni yanzu zanje ana jirana....
Anaam dai kanta a ƙasa dan itama ta tsargu, daga ƙarshe ma tashi tai tabar wajen kawai, tana mai jin cewa Shareff ya gama da ita kawai. (🙄kamar ba haka take so ba dama😆)

★★Kamar yanda Abie ya faɗa a wannan dare suka wuce Indonesia, basai an tona irin farin cikin da suka tsinta kansu ba a ciki game da wannan tafiya, domin kuwa abin yazo musu ne tamkar wani gift da baka san mizaka gani a ciki ba. Ba wani kaya suka ɗiba ba, dan bama su san adadin kwanakin da zasuyi ba. Shareff na ɗauke da Muhseenah a kafaɗa Anaam na gefensa cikin abaya blue datai mata matuƙar ƙyau. Sai ƙaramin trolley da kayan Muhseenah sukafi yawa a ciki a hanunta. Dolene su burgeka domin kuwa sunyi matuƙar dacewa da juna.
Sun sami tarba ta mutuntawa ga wanda Abie ya tura musu, ya kwashesu zuwa masauki na musamman. Gidane madaidaici da komai na more rayuwa akwai a cikinsa. Komai tsaf fiye da yanda suke buƙata, hatta da abincin da zasuci an ajiye. Bayan wanda ya ɗakkosun ya gama nuna musu tsarin gidan yay musu sallama ya wuce. Shareff ya rungumo Anaam yana murmushi. “Yarinyar nan Abie ya riga ya harbo jirginki shiyyasa ya turomu nan”.
“Ya dai harbo jirginka Yaya, zaka ƙala mun ni salihar nan dani”.
Ta faɗa tana mintsininsa da dariya. Dariyar shima yakeyi da kaiwa zaune ya ɗaurata a cinyarsa. “Su saliha anji jiki fa, ALLAH har naji kunya kamar daga nan na gudu da ku Nigeria kawai”.
“Kaga sai Mamie da Abie su ƙara yarda bakajin magana”.
Kai ya dungure mata da faɗin, “Bama ji dai”.
Ta ƙyalƙyale da dariya tana mai ɗanewa saman jikinsa. Shima dariyar yake tayata da sake ƙanƙameta. Da ƙyar ya iya haƙurin sukaci abinci sukai wanka.
Tana zaune tana shayar da Muhseenah ya tasasu gaba yana kallo da murmushi. Birgesa suke matuƙa, ji yake kamar ya haɗasu ya haɗiye kawai ko zaiji sassaucin ɗunbin so da kaunar da yake musu. Ɗagowa Anaam tai cikin ɗan waro ido. “Oga karka saka ta ƙware mana”. Idanun nasa ya kauda yana mai sakin wani tattausan murmushi. Ta zunguresa da ƙafa kaɗan, ya sake ɗagowa yana kallonsu. “ALLAH murmushi namaka masifar ƙyau Yaya MM. Amma baka sonyi”.
Wani murmushin ya sake saki yana mai girgiza kai, ya ɗan juya idanunsa dake kallon tsakkiyar nata cikin wani salo mai nuna tsantsar ƙaunarta dake ransa. “Indai ke kina gani ai ya wadatar basai kowama ya gani ba *_bugun zuciya_*”.
Murmushi ta saki itama da gyara Muhseenah datai barci. Fahimtar bazatace komaiba ya sashi amsar Muhseenah ɗin daga hanunta, shine ya kwantar da ita tare da mata addu'ar barci. Ya ɗago bayan tayi barci dai-dai Anaam na shirin barci, igiyar rigar barcin da take shirin ɗaurewa ya riƙe. Ta kallesa kai a langaɓe tana marmar da idanu. Matsota yake a hanakali yana mai narkar da nasa idanun cikin nata, harya haɗe jikinsu waje guda. A tare suka sauke ajiyar zuciya, cikin salon shagaltar da ita ya zame rigar saman tai ƙasa ta faɗi, zatai magana ya ɗagata cak zuwa kan gadon yana mai manne lips ɗinsu waje guda. Dole ta haɗiye maganar ta amshe mijinta hannu bibbiyu cike da kewa da tsoron abinda zai iya biyo baya ita dake da ƴar laɓuɓuwar yarinya (😂😂kuji gulmammiyar yarinya fa).

Wannan dare ya kasance wani dare ne na musamman a cikin darare masu nisan zango. Dan kuwa Anaam da Shareff sun tabbatar ma juna suna kewar junansu mara iyaka. Muhseenah ce kawai ke taka musu birki idan sukai nisa. Washe gari ma tare suka yini manne da juna sai ƴar ɗiyarsu sanyin idaniyarsu. Babu mai damunsu koda a waya ne. Zuwa dare suka ɗan fita shan coffee.
Sai da suka kwana uku suna hutawarsu ana huɗu Shareff ya samu ganawa da wanda Abie ya turosa wajensa. A ranar suka gama komai da shi, ya kira Abie ya sanar masa an gama komai zasu taho gobe. Sai Abie yace suyi zamansu har sai garin ya ishesu dan kansu. Tabb ba'ace suyiba ma sunyi inaga an basu dama. Lokacine da suka kirashi na gwangwaje juna fiye da wanda suka riska a baya. Dan kuwa sabon babin Honeymoon aka buɗe tsakanin waɗan nan ma'aurata dake jin tamkar su haɗiye juna su huta. Basu da wata damuwa saita bama junansu farin ciki, sai Shareff dakan ɗan taɓa ayyuka ta system ɗinsa a wasu lokutan. Watansu uku cirrr a ƙasar Indonesia kamar wasa, dan da sunce zasu taho sai Abie yace su ƙara dai, sun zagaya wajaje da dama tare da yin hotunan tarihi kala-kala. Zuwa yanzu baby Muhseenah ta ƙara ƙyau da girma. Dan har zama anayi tayi ɓul-ɓul da ita abin sha'awa. Su Abie nata mamaki su kansu. Sati biyu sukai anan Malaysia bayan sun je sunma Aunty Mimi sati guda itama suka nufo Nigeria. Sun bar su Mamie da kewa mara misali, sai dai suma suna shirin zuwa Nigeria ɗin bikin Amrah da Muzzaffar insha ALLAHU. Dan yanzu sun ƙulle abinsu suma tunda Anaam ta kufce masa ya kama Amrah ya riƙe ram.
Tarba suka samu ta musamman ga zuri'arsu. Kowa sai nannan yake da su musamman Muhseenah. Gwaggo Halima ce dai bata zafafa ba, tana daga gefe dan yanzu ta zama sai a hankali, zaman gidan yay masifar isarta, badan bata samun komai ba, sai dan a girman shekarunta ya wuce na zaman gida. Ga mijinta yana ƙoƙarin ɗarewa kujerar mulki dan kowa na hasashen shine zai zama gwamna. A koda yaushe cikin nunasa akeyi shi da amaryarsa ƴar ƙwalisa. Wannan kaɗai ya isa saka zuciyarta a ƙunci, balle ga damuwar Fadwa da maimakon sauƙi kullum a cikin tashin hankali take, zuwa yanzu ita da kanta ta yanke shawarar duƙawa gaban Shareff da Mommy da su Daddy akan su tamaketa Fadwa ta koma ɗakinta koda ita bazata koma nata ba, Fadwa na cikin mawuyacin hali na rashin Shareff, babanta kuma yayi alƙawarin bazai taɓa roƙa ko tilasta Shareff maidataba sai in shine yay ra'ayin hakan a karan kansa. Kasancewar saukar safe sukai zuwa dare suka nufi gidansu daya sha gyara, dama su kawai yake jira da alama. Washe gari sukaje gaida Mommy aka kuma kai mata jikarta dan yanzu Daddy ya basu damar zuwa suga mahaifiyarsu kamar yanda Baban su Fadwa ma ya barsu zuwa ganin Gwaggo halima. Hakan duk ƙoƙarin Abie ne na ganin dai komai ya wuce. Sosai tausayin Mommy ya kama Anaam, dan duk ta zube babu ƙibar nan tata, tayi duhu sosai. A yanda ta tarbesu zai tabbatar maka ba Mommy ɗin da bace ba. Muhseenah kam tasha gata a wajenta har da su goyo. Sun shiga sun duba Gwaggo dake kwance ana faman jiyya. Tayi masifar tsotsewa a kwance, ɗakin da taken ko shiguwa bayayi saboda warin fitsari da takeyi, masu kula da ita dasu Daddy sukasa aka samo suna biyansu shi da su Abie sai sun gadama suke gyarata. Baba Ibrahim ba zama yakeba shiyyasa, matansa kuma basayi basa faɗa masa abinda ke faruwa. Anaam har hawaye tayi kasancewarta mutum mai tausayi, dan duk wanda yaga Gwaggo dolene ya tsarkake sunan ALLAH mai rinjaye akan komai. Sai ya barka yay maka talala kaita aikata tsiyatakun ka a ban ƙasa, randa ya shirya damƙarka kuwa hummm. Ga dai Gwaggo a halin ha'ula na jiyya, da za'a bata zaɓin mutuwa ko rayuwa zata zaɓi mutuwar ko zata huta akan wannan azabar da take a ciki. Sai dai mutuwarma ta zama mai tsada a gareta dan taƙi zuwa kwata-kwata. Kullum cikin hawaye take idan ta tuna irin rayuwar data taka a wannan duniyar, kishi ya rufe mata ido da raɗaɗin rashin samun haihuwa ta cutar da matan mijinta, bata taɓa son su Daddy ba a ranta, kamar yanda uwarsu ma ba sonta tai ba. Kawai dai lumbu-lumbu take mata, dan taso ace ta tarwatsa rayuwar su Daddy ne kamar Umar, yanda itama bata haihu ba su Umma karsu mora nasu ƴaƴan. Tsanar mahaifiyar su Abie kuwa ta ƙara ƙarfine a ranta saboda tausayi da kullum mijinsu ke nunawa a kanta, sai take ganin ai yafi son bebiya ma a kanta, dan bata damu yaso umman su Daddy ba ko karya sotan, ita dai kawai a sota ita ɗaya. Sai dai kuma har yabar duniya da son bebiyan data tsana ɗin ya tafi, shiyyasa tafi tsanar su Abie fiye da su Daddy. Babban burinta tarwatsa family din MD Shareff gaba daya, su dinga tsanar juna da sukar juna ta yanda bazasu taɓa morar kansu ba kamar yanda itama bata mora zama da shi ba tunda bata haihuba a wautarta, sai dai hakan bata kasance ba da yake UBANGIJI shine mai zartar da hukunci akan ƙaddarar kowa. Duk ƙoƙarin ka, duk walarka sai dai kayi a banza a wofi babu abinda ka isa ka saka ko ka hana a karan kanka balle rayuwar waninka. Ba Gwaggo kaɗaiba, duk wanda zai sakama ransa ganin bayan wani, ko taɗe rayuwar wani, ko ruguza nasarar wani, ko baƙanta hasken fuskar wani, to ya tabbata shine zai dawwama cikin rasa waɗan nan abubuwan a cikin nasa rayuwar, dan baka halicci wani ba baka isa zartar da komai a kansa ba sai abinda ya kasance a ƙaddararsa. (ALLAH ka rabamu da mummunar zuciya, ka nisantamu daga son kammu da son ruguza waninmu. Ka hanamu nasarar cutar da kowa koda a lafazin bakine ko kallo da ido. Duk mai burin taɗemu a rayuwa ALLAH ka zame mana garkuwa a tsakaninmu da shi. Ya rabbi ka wajabta tsoranka a zukatanmu da soyayyar ANNABIN mu 🙏🏻😭).

Watansu guda da dawowa Anaam ta fara aiki a company, tana manne da mijinta a ko'ina kenan gida da office. Da safe zasu miƙa Muhseenah wajan Mom, idan sun taso su biya su ɗauketa. Aysha da matar Maheer sun haihu kusan lokaci guda, matar Khaleel dama tun suna malaysia ita ta haihu. Ansha shagalin suna yanda ya kamata, zuwa dare taro ya tashi lafiya kowa yana sanya albarka..........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/25, 12:21 PM] +234 906 975 1512: *_Typing📲_*

*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_82_*

.........Ranar wata alhamis dake dai-dai da saura kwana ɗaya cikar shekarar Muhseenah ɗaya a duniya su Abie suka iso Nigeria domin halartar bikin Amrah da angonta Muzzaffar. Anaam tayi farin ciki matuƙa, dan itace taje tarbarsu da Shareff da Muhseenah. Anaam ce ke tuƙi Shareff na kusa da ita Muhseenah a cinyarsa. Sai gwaranci take da tsalle-tsalle a jikinsa ita a dole zatai magana, sai dai kuma babu abinda ta iya sai gunguni irin na alamar yaro mai son surutu. Babu baki amma tayi ƙafa, dan kuwa tana tafiya sai dai bata gama nuna ba. Shareff dake dariyar son tura masa biscuit da take a baki ya lakace mata hanci, “Mamana wai dole sai naci biscuit ɗin nan ne?”.
     Anaam dake ƙoƙarin ɗaukar titin airport tai dariya da ɗan juyowa ta kallesu ta maida kanta. “Kunfi kusa ai,  yanzu da nice da yanzu an fara ƙananun magana, da zaka tsunkule hanun ai data barka ko”.
     “Oh oh Noorie bana son zuga, Maman tawa zan tsunkula. To anƙi”.
   Ya ƙare maganar da sumbatar Muhseenah a goshi, ita dai dariyarta take tana ƙara mamuƙesa dan tsaye take a jikin nasa tsoronta karta faɗi. Anaam data cigaba da tuƙinta batace komai ba ta taɓe baki. Shiko zaunar da Muhseenah yay. “Sweetheart ɗina, idan kinga su Abie ki taka da ƙyau dan tun a airport ɗin nan nake son su san kemafa kin faso munyi ƙafa”.
     Anaam ta kwashe da dariya tana ɗan dukan steering. “Badai girin-girinba ALLAH, kwaje wajen iyayi ku ci da ka”.
       Shareff ya harareta, “Tufff bakinki ya sari kashi”.
Dariyarta ta cigaba dayi ita dai tana ƙoƙarin yin parking. Koda suka fito kai tsaye wajen da zasu tarbesu suka nufa, kowa ya gansu sai sun baka sha'awa su da ƴar ɗiyarsu.
Basufi zaman mintuna goma ba jirgin su Abie ya sauka, suka zuba idon dakon fitowarsu. Shareff na hango su Abie ya sauke Muhseenah, mi Anaam zatai inba dariya ba, ya dalla mata harara da kai mata mintsini ta kauce, su Mamie ɗinta ta nufa ta rungumesu. Abie dake dariya yace, “Oh oh mamana bata girmaba har yanzu dai”. Fuska ta ɓoye tana dariya, dai-dai nan Idon Abie yakai akan su Shareff. Mamie ya zungura itama. A tare suka sanya dariya.
    Mamie tace, “Ayya ana mana yanga da tafiya, to mungani duk da bata nuna ba”.
        Shareff dake ƙarasowa yace, “Haba Mamie karki bamu kunya gaban ƴan adawarmu”. Yay maganar da nuna Anaam. Dariya Abie da Mamie sukeyi, Anaam kuwa ta taɓe baki da faɗin, “Waifa dole da tsiya-tsiya sai an nuna muku sun fara tafiya, bayan basa iya taku goma zai sun faɗi”.
       “Adai ringajin tsoron ALLAH hajjaju” Shareff ya faɗa yana harararta. Nanma dai dariyar sukayi, Abie ya ɗauka Muhseenah yana ɗagata sama, saita sanya masa kuka ita ƙiywa wajen Abbanta zata koma. Ya dungure mata kai, “Haba ƴar daru ni zakima ƙiywa, to garama mu daidaita tun anan dan indai nine kinta ganina kenan daga yau”.
     Mamie dake dariya tace, “Kaima kenan. Balleni kishiya”.
    Cike da farin ciki suka bar airport ɗin, kamar koyaushe sun sami tarba ta mutuntawa gasu Mom. Duk da dama dai Anaam ta shirya musu abinci na musamman a wannan karon da kanta itama. Ranar duk yanda Shareff yaso lallaɓata su koma gida ƙi tayi, dole ya barsu nan ya tafi shi kaɗai ya kwana cike da kewarsu. Dan yasan dai ba sake ganinsu a gidan zaiyi ba sai kuma bayan biki. Hakan yasa shima ya tattaro inasa-inasa washe gari ya dawo nan gida. Sam daga Anaam har Shareff basuyi waniyi niyyar yima Muhseenah birthday ba, amma sai ga bazata gasu Mamie dan da alama da shirinsu sukazo. Anko sha shagali mai ƙayartarwa, aka kuma sha hotuna masha ALLAHU. Ranar sai da Gwaggo Halima tai hawaye, dan haka kawai taji tana taya Fadwa jaje matuƙa. Mommy ma dai ba'a barta a baya ba sai da tazo, tunda tabar gidan wannan ne karo na farko da tazo, duk da kuwa kullum cikin yima Daddy waya take da bashi haƙuri kamar yanda Gwaggo Halima kema Daddyn su Fadwa. Da gaske sunyi laushi kowacce burinta a yanzu ta koma gidan mijinta. Shareff kansa da su Maheer kullum cikin bibiyar iyayen nasu suke, dan suna tausayawa Mommy sosai dake zaune a raɓe duk da baba Ibrahim yaya yake a gareta uwa ɗaya uba ɗaya. itace kuma tace subi umarnibsa na hanawa susai mata gida da yayi, tace zatai haƙuri ta zauna a gidan nasa.
      An shiga hidumar biki, dan dama dai aunty Mimi sun iso tuni suna Abuja ne gidan yayan baban su Amrah ɗin. Suma sai juma'ar da akai birthday ɗin Muhseenah suka ƙaraso kano, sai dai acan gidan mijinta daya siya shima suka yada zango. Sosai biki ke bada citta, su Anaam ƙirjin biki babu zama ko ina sune. Bata da matsala da Muhseenah tana wajen Mamie, dan haka ta sami damar yin komanta hankali kwance har aka kammala biki amarya Amrah ta tare a gidanta da kowa keta sambarka.
      Sai da Shareff yayma Anaam jan ido washe gari ta yarda suka koma gida. Sati biyu da gama hidimar biki akai taron family. Duk wani da ake buƙata ya hallara. Tun rabuwar Fadwa da Shareff sai yau ne suka haɗu da Anaam dama Shareff ɗin kansa, dan ya toshe duk wata hanya da zata iya ganinsa kojin labarinsa. Duk ta rame tayi wani irin sanyi. Anaam tayi kamar bata gantaba tanata ma Muhseenah data maƙale mata wasa, dan kuwa dai yanzu a hanun su Momie take tama yaye kanta, dama Anaam ɗin ta gaji sai hakan yay mata dai-dai. Fadwa ta tsira musu ido hawaye na silalo mata a kumatu, ji take inama Muhseenah tata ce. Hankalinta bai sake tashi ba sai da Shareff ya iso wajen. Yayi wani fresh da shi ga ƙiba da zama alhajin gaske da yayi, sai ƙyalli yake cikin shadda irin ta jikin Anaam ɗin. ko kunya bai jiba ya ƙarasa inda matarsa da ƴarsa suke. Duƙowa yay jikinta yana mai yima Muhseenah wasa tana ɓangale masa baki da miƙa hannu ita a dole ta gane Abbanta.
     Anaam ta kallesa da murmushi. “ALLAH Yaya kai ne ka koyama yarinyarnan ƙiywa ba wani ba. Ita a dole duk inda ta ganka saita ganeka”.
      “Toya son ranki? Jealousy woman”.
Ya faɗa yana mai kashe mata ido ɗaya. Murmushi tai baki a taɓe. “Fess mana, miye abin jealous anan nima nawa na zuwa zan rama”. Shima murmushi yay idonsa akan lipstick ɗin bakinta. Sarai ta ganosa, dan haka ta tura lips ɗin a baki ta shanye tas. Kafin fitowar nan tasu ta saka yafi sau biyar yana tsotsesa, yanzu ma anan gidan ta saka.
    “Kije ke da ALLAH kuma zan rama”.
Ya faɗa cikin langaɓe mata kai. Dariya take gimtsewa ita dai, ya ɗauke Muhseenah suka bar wajen. Da kallo ta bisu cike da so da ƙaunar ƴar da uban.

       Bayan kammala halartar kowa aka buɗe taro da addu'a. Abbah ya fara da nasiha mai ratsa jiki game da muhimmancin da zuminci keda shi a rayuwarmu, tare da son zuciya akan abinda kai baka isa sakawa ko hanawa ba a ƙaddarar waninka ko kai a karan kanka. Ya ɗora da roƙo da fatan su zama 1family, tsintaiya ɗaya maɗauri ɗaya. Tare da illar nunama juna wani abu wai shi ƴan ubanci. Ƴan ubancin nan babu abinda yake zama a family sai kassara rayuka da maidasu koma baya. Duk family ɗin da babu haɗin kai bazasu taɓa zama masu cigaba ba, dan kuwa zasuyita gabane suna taɗo juna akan ƙanƙanin abu. Sannan iyaye mata na Family ɗin su kiyayi kansu wajen tsaurara ƙiyayya tsakaninsu da ƴan uwansu har ƴaƴansu su fahimta hakan kuskure ne. Kowa yay haƙuri da ɗan uwansa yayin daya ɓata masa rai, dan mai haƙuri baya taɓa faɗuwa sai cin nasara a rayuwa. Su Abie sun isa zama manuniya a garesu. Sosai nasihar ta shigi kowa. Sai faman sauke ajiyar zuciyoyi akeyi musamman Gwaggo Halima. Bayan gama jawabin Abba Abie shima ya amsa. Ya ƙara da musu tashi mai ratsa jiki, tare da shawarar sakama yaranmu ido domin sanin abinda suke aikatawa a wayoyinsu. Dan sakacin rashin bibiyar shike saka yaran ɗoruwa a hanya irin wadda Fadwa tabi a baya. A yanzu tangal-tangal din tarbiyyar yaranmu ta riga ta koma ne a tsinin ƙaddarar yanar gizo da wayoyin hanu suka kawo mana, kenan ya dace iyaye su sakama wayoyin hannun ƴaƴansu ido, karkuma suce bazasu basuba dan in kin hanasu zasuje suga ta ƙawaye ko aboki ko saurayi, baki san kuma minene a ciki ba. Sannan tarbiyya babu ruwanta da inda ka taso, a duk duniyar da kake, a kuma kowacce ƙasa idan kaso ɗanka ya zama na ƙwarai zai zama. Bawai dole sai ya shiryuba, a'a ALLAH ne kaɗai mai shiryarwa, suma waɗanda nasu ƴaƴan suka kauce ba'a son ransu bane, karka ga gazawarsu koka aibanta waɗan nan yaran, akwai ƙaddara amma wasu lokutan akwai sakaci sosai na iyaye. Karka matsawa ɗanka, kar kuma ka sakesa da yawa. Dan matsi na saka lalacewa tunda zai koma a tafin hanun neman sharar ƙawaye ko abokai ne, sannan saki gaba ɗaya ma kuskurene, zai koma a tafin hanunun tarbiyyar ƙawaye ko abokai. A wannan zamanin iyaye sun kashi kaso uku ne zuwa huɗu koma nace biyar ko fiye da haka, masu raunin talauci da komai yaron yayi dan an sakar masa komai ne. (Kamar dai su Sima da Amaal) kaso na biyu rashin wayewar kan sanin mi yaran ke aikatawa ma ko ilimin sanin illar wayoyin ko yanar gizo. Kaso na uku ƴan boko wayayyu da komai akai su a wajensu ba komai bane zamanine. Kaso na huɗu masu tsananin tsaurarawa har ƴayan suna fakar ido suna aikata abinda sukema tsaurin. Kaso na biyar ƴan fifita aiki ko kasuwanci fiye da saka ido akan al'amuran ƴaƴansu komai na hanun ƴan aiki kosu yaran a karan kansu. Iyaye mata suna ƙoƙari matuƙa, duk da a wani ɓangaren akwai sakacinsu, sai dai kuma laifin iyaye maza yafi rinjaye. Da yawa ƴaƴa suna matuƙar shakkar iyayensu maza fiye da matan, sannan a wani fanin iyaye mata nada rauni akan ƴaƴa, dan haka idan kana son ingantuwar tarbiyyar ɗanka yanda ya kamata dolene a matsayinka na uba kaima ka tsaya tsayin daka wajen taimakawa uwa mace ku gyara kuma ku tsawatar, sannan ku haɗa da addu'a. A wani fanin Gwaggo halima tayi matuƙar ƙoƙari wajen tarbiyyar su Fadwa, domin kuwa bata barsu kara zube ba akan wasu fanonin, hakan zaisa mai karatu ya fahimci itafa uwa uwace koyaya take tana buƙatar ganin ɗanta a ƙyaƙyƙyawar nasara bawai faɗuwa ba. Su Fadwa na tsoron mahaifinsu, amma maida hankalinsa a kan hidimarsa da siyasarsa yasa bai maida hankali wajen sanin dukkan motsinsu ba, shi dai kawai idan ya samo ya basu sunci sun sha sun samu komai basu da matsala ya gama nashi. Ba mahaifin Fadwa kawai bane a irin wannan halin, mazanmu na yanzu musamman yarena hausa dana sani wannan shine babban rauninsu akan ƴaƴansu gaskiya. Namiji ya fita tun safe sai dare ko yamma zai dawo miki, komai ya sakar miki akan tarbiyyar yara, masu ƙoƙarin ciki sune ke ɗan zama da yaran weekend, wanima da sun raɓesa zai korasu shi an takura masa yana son ya huta, ko wani ya ɓato masa rai a waje ya shigo gidan yayta tambotsai. Komai sai uwa dai, tayaya uwa zata iya da komai? musamman akan yaran yanzu da sai dai addu'a. Abu mafi girma shine maida nauyin gidajenmu a hanun ƴaƴanmu musamman ga iyayenmu talakawa. Taya zakice yarinya budurwa baliga ko bazawara itace zata nema kuɗi ta ɗauka nauyin rayuwar gida? Ko namijine a wannan zamanin dole ka kasance cikin taka tsantsan balle mace, anji neman nakai nada daɗi, amma komi ƴarka zatai tayi a gaban idonka, bisa control naka kona yayunta domin ceto rayuwarta daga faɗawa wata ƙazamar rayuwa. Tabbas wasu iyayen basu san ƴaƴansu na abubuwan nan a media ba, saboda su basu da wayewar kan sanin mima wayoyin suka ƙunsa ko yanar gizo, wasu kuma masu wayewar hakan basu cika zama masu bin ƙwaƙwƙwafin yaran nasu ba. A ganina hakan duk kuskure ne, akwai abinda baida ƙyau ka cika masa bin ƙwaƙwƙwafi kam, akwai kuma wanda saida bin ƙwaƙwƙwafin komai zai tafi dai-dai. Karmu hana yaranmu wayoyi, kar kuma mu barsu da su su zame musu komai. Idan baku da wayewar kai akan waya samu wasu da zasu dinga bibiyar yarinyarki a kowane shafi nata/nashi suna kawo miki rahoto, idan kunada ilimin bibiya a kowanne dare wayar yaranki musamman mata ko matasan samari masu tasowa dan nasan na manyan gwasaken zaiyi wuya ta kwana a hanunki, dan dare shine mafi girman fili dake basu damar aikata komai a yanar gizo. Sannan ki dage da addu'a da yawaita nasiha mai tsoratarwa ga yaran akan irin waɗan nan abubuwan. Mu kammu iyaye mata da muke shiga a irin waɗan nan abubuwan dan ALLAH muyima kammu faɗa mana, kina tunanin zakiyi ƴaƴanki su kasa koyi dake? Shifa hali naso yakeyi, Fadwa ta fara tiktok tun bata da aure, amma saboda ya zame mata jiki har taje gidan aure tanayi a duk yanda taso. Wlhy wlhy maza da yawa na faɗawa a tarkon sha'awa a kalle-kallen videos na yanar gizo da mata ke yaɗawa a duk shigar da suka gadama. Karku manta wanifa abu kaɗan ke tada masa hankali, shiyyasa zinace-zinace sukai yawa yanzu muka rasa gane daga inane, ada yarinya saita ɓalle daga gida ta shiga duniya ake kiranta karuwa, wlhy yanzu a gabanki za'a maida miki yarinya karuwa ko matarka ko ƙanwarka ko yayarka😭, dan wasu matan a dalilin abinda sukeyi wasu mazan ke hillatarsu harsu bata musu rayuwa. Duk yanda mace take tana son a yaba mata, shiyyasa maza mayaudara ke saurin samun galaba akan ɗiya mace saboda su duk hanyar yabo da gwarzantawa sukebi, suna kuma samun abinda suke so su watsar dake su koma gefe suna zagin iyayenki dake kanki matsayin mara tarbiyya. To hakane ke faruwa a duniyar tiktok dama sauran kafafen sada zumunta, waɗan nan masu zugaki a Comments kin haɗu, kin isa, kin kai, wlhy ba ƙaunarki suke ba, dan daza'ace ɗaya daga ciki ya fito ya aureki sai kin nemesu kin rasa sun gudu. Maza dake kawo matansu ana video su wai soyayya ban taɓa ganin waɗanda basu san ciwon kansuba irinsu wlhy, matarka ta aure sirrinka itace kuma abin ado a shafin sada zumunta?, anya wannan soyayya ce kuwa ta gaskiya? Muji tsoron ALLAH, mu dunga tunawa da mutuwa, mu dinga tunawa akwai kwanciyar kabari, akwai hisabi, dubinki sunyi amma basuci ribaba, tayaya ke kike tunanin zaki ribantu?, bazaku gane illar abinda kukeyiba sai kinje gidan aure namiji na miki kallon zargi ko yana bin irin hanyar daya ganoki wajen gani wasu matan duk da yana dake a gidansa. Ki dauka abu mai amfani ki yaɗa sai kici riba, amma mummuna zakiyi bayani idan baki tubaba. Dan Fadwa a novel ta fito shiyyasa wani a cikin hukuncunta yazo a bayyane, amma ke a zahiri kike ALLAH shine zai hukuntaki idan baki tuba kin koma garesaba, ba kuma kisan ta hanyar dazai hukuntakin ba ma. ALLAH ka shiryemu badan halinmu ba.😭🙏🏻

Shima Daddy koda ya amsa maganar dai ɗaya ce akan zuminci da tarbiyyar ƴaƴanmu. Mu daina sakarma abokai ko ƙawaye ƴaƴayenmu hakan kuskurene. Dan zai zama kina tufƙa wasu na warware miki, yanzu lalacewa basai a zahirin rayuwa ba. Daga budurwa har bazawara da saurayi ko magidanci ko matar aure inhar suna biyema ƙawaye ko abokai zama samu rayuwarsa tana tangal-tangal, dan zai koma ne baida ra'ayin kansa sai nasu, hakan kuma babban kuskure ne.........✍

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_**_Typing📲_*

*_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

*_83 End_*

.........Matsalar ba'a raye-raye bane kawai ko abinda bai dace ba ko mara amfani. Akwai canja abokai, dan dole ne yay abokai a wannan yanar gizon, tun ana ƴar nesa da juna har a kai ga haɗuwa, bai san tarbiyyar waɗan can ba ko inda suka fito, sai kiga an koya masa sabuwar ɗabi'ar da baki san yaronki ko yarinya da shi ba. Shaye-shaye ne, maɗigo ne, luwaɗi ne, fashi ne, sata ne, yahoo ne, kai da ire-irensu daban-daban. Wlhy ko a film naga yarinya na shan shisha inajin zafi a zuciyata, dan wata daga wannan abinda ake ɗauka faɗakarwar zataji daɗi ta cigaba, saboda mu a namu wautan ɗaukar shisha muke ba shaye-shaye ba ma. Daga faɗakarwa an koma feɗe tarbiya, an gyara goma biyar bata gyaru ba. Kullum ƴarki abokai da ƙawaye na janta/jansa bin joint-joint, inda anan zata haɗu da wasu masu buɗaɗɗen idon da yafi nata kuma ko yafi nasa. Ya ALLAH, iyaye dan ALLAH mu dake da addu'a. Sannan muma a karan kammu mu gyara halayen da muka san munayi marasa ƙyau. Dan ba media bace bala'i kawai muma a karan kammu bala'in kammu da kammu ne. ALLAH yasa mu dace.

       Ba Fadwa ba kowa ma a falon jikinsa yay sanyi matuƙa, hankalin iyaye da yawa da ba ɗaukar komai suke matsayin komaiba ya tashi matuƙa, dan kamar an farkar da su ne abinda suka kasa hangowa a tsayin hangensu. Fadwa kuka take matuƙa tana mai dana sani da nadama mara misali. Dan kuwa yanar gizo bata bata komai bai sai komawa baya da sakata a gurbin nadama saboda batabi hanyar da zata amfana da ita ba. Inama sauran wanda suke hali irin nata suma zasu farga da wuri kafin su rasa abinda ta rasa koma fiye da ita. Inama zata iya goge abinda ya wuce a zuciya da idanun mutane?. Sai dai kaico, duk da ta daina a yanzu ko waya bata riƙewa haka bai hana videos nata cigaba da yawo ba a media, saboda wasu sun adana a wayoyinsu, kuma suna cigaba da zama illa a garesu tunda suna koyi da su matsayin abin birgewa. Duk wanda ya koya daga gareta kuma ya lalace tanada kamasho na zunibi itama. Kenan ita baɗala koda kayita ka daina sharrinta na biye dakai har bayan ranka, wani lokacin ma har jikokin jikoki? Ya ALLAH ka ganar damu gaskiya tun kafin ta ƙuɓuce mana. Ka shiryar damu tun kafin guri ya ƙure mana, ka ƙuɓutar damu tun kafin ajali ya riskemu. Ka goge laifukamnu tun kafin ƴayanmu da jikoki su riskesu😭🙏🏻.

         Abie ne ya katse tunanin kowa cikin gyaran murya. Hakan yasa kowa maida hankali a garesa. “Babban abinda ya taramu anan shine sake bada haƙuri da roƙo ga iyayenmu, yayunmu, ƴaƴanmu, kuma ƴan uwanmu. Yaya Muhammad, Alhaji Sadiq, Babana Shareff. Musamman abinda ya faru ya rigada ya faru, kuma hukuncinku dai-dai ne dan duk ɗan halak idan an zunguresa ya dace ya nuna yaji zafi kuma ya ɗau mataki.  Sannan wanda yay laifi idan anga nadama a cikin idanunsa da ayyukansa ya kamata ai masa afuwa koda kuwa bazai samu girman daraja irin ta baya ba. Kamar yanda na roƙa a tun sanda kukai sakin nan kuka maidasu bada sanin kowa ba har su a karan kansu dan mu barsu su horu muga kuma idan zasu gane gaskiya, to Alhmdllh sun gane, a tsahon kusan shekara guda. Ina roƙon alfarmar ku maidasu ɗakunansu, ya rage nasu su riƙe igiya ɗaya data rage musu kosu barta itama ta katse a yanzu. Fatanmu zuminci ya cigaba da gyaruwa ba ɓaci ba, sannan dama shi mai laifi ana masa gargaɗi idan yaji to falillahil hamdu, idan ya nuna kunen ƙashi sai a barsa da halinsa ALLAH ya hukuntashi da ikonsa. Halima da Nafisa kunada sauran igiya ɗaya na aure kuma mun roƙa alfarma an maidaku tun kan ku kammala idda, amma bawai hakan na nufin ku cigaba da abinda ranku ke so ba a wannan family, dan a wannan gaɓar mun shirya ɗaukar mataki akan kowacce dazata zame mana iblis wlhy, babu kuma wani cikinmu dazai sake mata alfarma.”
     Sosai Mommy da Gwaggo Halima ke hawayen daɗi, har basu san sun fara zuba godiya da addu'a akan Abie ba. Yay murmushi kawai dan kuwa bai taɓa tunanin ganin irin wannan ranar ba. Hankalinsa ya maida ga Shareff dayay kicin-kicin da rai, sai dai wani sashe na ransa ya masa daɗin maida Mommy, ya kuma sake jin kima da mutuncin Abie a cikin idanunsa da ransa.....
    “Babana”.
Abie ya katse masa tunani.
Ɗagowa yay ya dubesa, sai dai baice komai ba. Abie ya murmusa ganin yanda ya tsuke fuska. “Nasan a gareka abune mai matuƙar wahala iya manta komai, shiyyasa ko a wancan karon ban tunkareka ka maida Fadwa ba, na barka ka huce sosai da sosai kafin muzo a wannan gaɓar. Babu mai tilasta maka a cikinmu, amma zamu roƙeka alfarma. Dan ALLAH ka maida matarka tunda tayi nadama.....”
     Kansa ya shiga girgizawa a hankali. “Abie batai nadama ba, tana muku lumbu-lumbu ne kawai. Koda zan iya maidata domin darajarku bazan taɓa sake sonta ba, bazan taɓa ganinta da mutunci ba, bazan taɓa iya sauke dukkan hakkinta ba. Har yanzu ina ganinta a idona mai ɓakar zuciya, mai mummunan hali, mai karancin tarbiyya, ballagaza da bata san kima da mutuncin kanta ba, Abie mazafa kallonta sukeyi sunaji wani abu a ransu, shin yara matasa nawane da magidanta sukaji hakan? Mutane nawane suka kalleta a hakan? Ta daina amma har yanzu abinda ta shuka na yawo a wayoyin mutane? Bazan iyaba Abie, wlhy ko tunata bana sonyi, bana son ganinta sam......”
     “Karka tsaurara da ƙarfi babana. Nasan akwai ciwo, akwai ɗaci, akwai raɗaɗi. Sai dai muɗin ba masu shiryarwa bane ba. Sannan samun miji na gari na ƙwarai a gareta a yanzu abune mai wahala, duk da nasan wasu zasu iya amfani da nasibin da ALLAH ya bama mahaifinta na suna da dukiya suce zasu aureta, tunda wasu a gurunsu abinda ta aikata ba komai bane a wautarsu, sai dai bai zama lallai su zama na ƙwarai ba......”
     Fadwa dake kuka ta ƙatse Abie ta hanyar rarrafowa gabansa. “Wlhy Abie bazan iya zama da wani namijiba inba shiba. Ina sonsa, kuma ni kaina ina kaico wa rayuwata ta baya. Na ɗauka abinda nake ba komaiba sai nishaɗi kawai, na ɗaukesa matsayin zamanine kawai, na ɗaukesa matsayin lokacina ne kawai. Wasu tsurarun mutane da bazasu amfaneni da komai a duniya da lahiraba kwarzantawarsu a gareni na ingizani inajin babu yani. A tunani na abinda nake ba komai bane tunda ba'a zahiri baneba. Ashe mummunar rayuwace mai wargaza ƙyawawan ayyuka. Ashe ƙofofin matakin zuwa ga zina ce, ashe raguwar darajace a gareni matsayin ɗiya mace, ashe tanadin abin faɗa ne ga ƴaƴana ga ƴan uwana. Ashe makullun rusa dukkan farin cikina ne da rayuwar aurena. Ashe ƙanƙantar da kaina nake tamkar dabbar da bata san inane rufe ko buɗe ba. Kaico na da wannan rayuwa, kaicon duk wata mace mara kamun kai da fahimtar rashin daidai matsayin nishaɗi ko birgewa. Kaicon mace irina dake nuna rashin ingancin tarbiyya da mutuncin iyayenta wa duniya. Nima bazan matsa maka ka maidaniba, amma bazan daina son ka ba, zan mutune da sonka Soulmate, zan amshi wannan hukuncin domin nasan UBANGIJI ne yake horani ta hanyar aza sonka a raina fiye da komai. Na godema ALLAH daya saka maka da mace tagari tun kan kasan niɗin wacece. Na gode ALLAH daya fargar dani illar abinda nakeyi tunkan tsufa da mutuwa su riskeni......”
    Kuka ya sarƙeta, tausayinta ya saka Anaam fara kuka itama. Amma ga Shareff sai ma faman taɓe baki yakeyi alamar ko'a jikinsa. Dan shikam dai har cikin ransa baya fatan sake zama da Fadwan. Sai dai yana mata fatan shiriyar da tace tayi dan shima yana fatan ALLAH ya shirya masa nasa ƴaƴan daya fara haifa da ƙanensa dama duk ƴaƴan musulmi.

     Duk fa yanda aka buga Shareff bai yarda da maida Fadwa ba. Dole aka ƙyalesa dan har yanzu yana akan dokin fushi. Haka taro ya tashi su Mommy dai zasu koma ɗakunansu.

..................

     Rayuwa ta cigaba da shuɗawa har ALLAH ya sake bama Anaam ciki, a kuma lokacin su Abie suka dawo Nigeria, dan haka Muhseenah ta koma hanunsu, wani lokacin kuma tana wajen Mommy data dawo tuni, hakama Gwaggo Halima ta koma, sai dai kuma duk da mijinta ya ɗare karagar mulki ta koma ƴar kallo, komai amaryace ke zartarwa itama ake kira first lady. Haka Gwaggo Halima keshan kukanta, ta kuma ɗauka ɗammarar haƙurin zaman ƴaƴanta. Anaam aka cigaba da rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya. Alhmdllhi wannan karon dai da kanta ta haihu ɗan ta namiji mai kama da Shareff, anyi farin ciki matuƙa an kuma sha shagali. Yaro yaci sunan Daddy. Wato Muhammad Ameen. Za'ake kiransa Muhammad ɗinsa. Anaam da Shareff suka cigaba da rainon ɗansu, wani lokaci Muhseenah takanzo tai musu har sati suma duk da dai kullum sai sun ganta idan sunje kai Muhammad gida idan zasu aiki ko sun taso. A haka shima ya girma yakai yaye. A kuma lokacinne ALLAH yayma Gwaggo data koma abin kwatance rasuwa, tanata kururuwa da ihun a kira mata su Daddy, sai dai kafimma suje rai yayi halinsa. Dolene kaga gawar Gwaggo ta baka tsoro, ta mugun komawa ƴar tsurut kamar ba gawar mutum ba. Ƙarshen Gwaggo ya sake sanyaya zukatan su Mommy matuƙa.

      Muhammad nada shekara uku a duniya rabuwar Fadwa da Shareff kuma shekara shida Abie ya sake roƙon Shareff maidata ɗakinta, dan har yanzu ta kasa aure, mazanma da ake tunanin zasuzo kodan alfarmar mahaifinta tamkar ALLAH ya dakatar dasu duk wanda yazo gareta sai da wata manufa amma ba aure ba. Takanci kuka matuƙa idan suna mata izgilanci da abinda ta aikata baya. A wannan karon dai da ƙyar ya amince, sai dai ya sake tabbatar mata bazai taɓa ƙara sonta ba, ba kuma zata samu wani farin ciki daga garesa ba.
     Tana sonsa dan haka ta yarda da hakan da tunanin zata iya haƙuri aka sake ɗaura aure. Sai dai kuma a tarewarta gidan ta tabbatar da abinda ya faɗa ɗin, dan ta kasa gane komai na Shareff, yana sauke mata dukan hakkin da ALLAH ya daura masa na ci da sha da sauran buƙatun rayuwa, amma ko fara'arsa bata gani balle samunsa a gado, kwata-kwata yaƙi kusantarta, babu wata soyayya a tsakaninsu yanzu, komai yana mata alamar tilasne zama da ita ya zame masa dan iyaye. Takanci kuka ta gode ALLAH musamman idan taga yanda suke soyewa da Anaam a gidan kamar suna mantawa da zamanta. Dan ma Anaam ɗin kan noke wani lokacin a gaban idonta. Ga wata irin soyayya da take gani yanama ƴayansa tamkar ya cinyesu. Dan cikin da Anaam ta samu na uku a gidan sai da taji tamkar ta haƙura da auren ma. Gaba ɗaya ya gama lalacewa a kan cikin, koda yaushe yana manne da Anaam ɗinsa da ƴan ƴaƴansa. Ita tsakaninta dashi kawai abinda yake wajibi. Ya hanata riƙe waya kuma sai rakani kashi, itama ya tabbatar mata zai barta da itane domin adalcin kiran iyayenta. Amma kuma kullum cikin bin ƙwafɗin wayar yake. Hakan na damunta, dan a yanzu sam babu wata yarda a tsakaninsu koda ta magana ce. Ko abu ta faɗa masa sai yace sai ya bincika. Tasan alfarmar Abie kawai takeci na zaman gidan. Amma ta rasa Shareff har abada. Ga haihuwa shiru kaleji babu labari har yanzu, koda yake ba'a kusanceka ba ina zaka haihu. Hakan ma na sake tada mata hankali dayin nadama mara misali.
      A yanzu ma kuka take tana kallon Shareff ɗin da su Muhseenah da tazo musu weekend ta window. A tsakar gida suke suna buga ball harda Anaam dake fama da tsohon ciki. A bisa tsautsayi Anaam ɗin ta gurɗe. Gaba ɗaya Shareff ya ruɗe shida yaran duk sukai kanta, jikinsa ya jawota cikin tsananin tashin hankali, itako tana faman riƙe ƙugu da kiran sunansa.
      “Bayana Yaya, cikina, ƙafata ta riƙe, Yaya muje asibiti wayyo Mamie na”.
    Ai babu shiri yay sama da ita yakai mota, dole Fadwan ta fita itama domin taimaka musu. Amma sai yay kamar bai ganta ba har saida Muhseenah tai magana tana kamo hanunta. “Mamah kizo kima Miminmu addu'a Please kinga tana kuka”.
      Cikin ƙarfin hali ta saci kallon Shareff dake ƙoƙarin saka Muhammad a mota. Amma yay kicin-kicin da rai. Muhseenah ta nufesa tana faɗin, “Abbu Please aje da Mama mana ta riƙeta tunda kai zakai tuƙi”.
     Har yayi niyyar ballama yarinyar harara sai kuma ya dake, ya ɗaga mata kai kawai dan yasan fitinar Muhseena ba barinsa zatai ba. Balle gata da shegen wayo, ba kuma ya son ko kaɗan tasan wani abu mara daɗi tsakaninsa da Fadwan. Dan ko Anaam bayayi a gabanta tsakanin shi da itane kawai yake horata. A dalilin Muhseenah suka tafi asibitin tare, suna zuwa babu jimawa ALLAH ya sauki Anaam ɗin lafiya namiji.
    Cikin ƙanlanin lokaci zance ya zagaye dangi. Kowa sai murna da fatan alkairi, dandanna asibiti ya cika da dangi. Sai da aka sallamesu ƙura ta koma can gidan aka cigaba da shagali. Shima dai yaro yaci sunan Abbah ranar suna. Wato Abubakar Sadiq, zasu kirashi da Saddiq ɗin. A wannan sunanma dai Anaam da jariri sunga gata, itako da iyayenta babu abinda zasuce ma ALLAH sai godiya. Dan yanzu dai family ya zama tsintsiya madaurinki ɗaya kowa na hakuri da ƙoƙarin kai zuciya nesa koda rai ya ɓaci.
Bayan suna da wasu kwanaki Fadwa ta zaɓi neman saki ga Shareff bayan tayi shawara da Gwaggo Halima, itama dai jikintane yay sanyi dan tasan dama an takurawa Shareff bisa komawar Fadwa gidansa, yana jin kunyar su Abie ne kawai shiyyasa ya amince. Amma a yanzu tunda ita Fadwan da kanta ta zaɓi haƙura da zaman ALLAH yasa haka shine yafi alkairi a garesu, dan insha ALLAH a yanzu itakam bazata sake bari wani abu ya shiga tsakaninta da ƴan uwanta ba, saboda komai Fadwa ta zama a baya itama ta bada nata gudunmawar wajen karancin bibiyar al'amarinta da tsawatar mata. A yanzu itama ta fahimci zamansu tamkar cutar da juna ne kawai, shi zuciyarsa a ƙuntace da ganinta, ita kuma zuciyarta a ƙuntace da buƙatarsa ta kuma kasa samu. Bai waniyi jayayyaba suka je gaban su Abie da kanta tai musu bayani, duk da sun fahimci hakan shine sauƙi da farin ciki a garesu basuji daɗi ba. Amma sun musu fatan alkairi, Shareff ya rubuta mata sakinta. Tana hawaye ta amsa dan harga ALLAH tana matuƙar sonsa, bakuma zata daina son sa ba har ƙarshen numfashinta. Ta zaɓi yin nesa da shine domin yazama cikin farin ciki, dan ta yarda da gaske baya son ganinta, ya tsaneta a yanzu. Shi kansa dai yaji tausayinta a wannan gaɓar, amma dai haka shine mafi sauƙi a garesu, dan yayi ƙoƙarin manta komai ya amsheta hakan ya gagara, bayajin zai taɓa iya ƙara kusantar Fadwa, badan komai ba sai dan daya tuna maganar samarin nan sai yaji tsananin tsanarta da zafinta, yanada kishi matuƙa akan duk abinda yake nasa, dan haka koya cigaba da zama da ita sai dai yayta cutarta dan yayi alƙawarin bazai sake kusantarta ba. Yana mata fatan alkairi, idan tuba tayi na gaskiya ALLAH ya saka mata da abinda zai zame mata alkairi anan gaba.✍

*_To nima dai bari nace Alhmdllhi, ALLAH ka ƙaramana haƙuri da juriya a duk yanda wasu zasu so ganin fushinmu ko ɓacin rai ko damuwarmu ALLAH ya hana. Ya ƙara mana haƙuri da juriyar ɗaukar komai da zaizo a ƙaddarorinmu, ka hanamu yin kuka da dana sani mara yankewa a rayuwa._*

*_ALHAMDULILLAHI_*
     *_ALHAMDULILLAHI_*.
            *_ALHAMDULILLAHI_*

Godiya ta tabbata ga UBANGIJIN talikai daya bani aron rai da lafiyar rubuta wannan ɗan gajeren labari. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ka amfanar damu a ladar. Kuskuren ciki ALLAH ka yafemin.

     Wanda duk naima ba daidaiba a yayin rubutunsa ya yafemin, abinda yazo ba'a haka kuka so ba kuyi haƙuri a haka labarin yazo. Ina fatan kuyi amfani da amfanin ciki ku watsar da marasa amfani, dan wani abun ana sakashine dan kawai nishaɗi. Yaranmu masu tasowa ba komai najin daɗin rayuwa dake zuwa a novels ake samunsa a zahirin rayuwa ba. Kowanne bawa da ƙadarar da ALLAH ya tsaro a tasa rayuwarsa. Idan kinga saɓanin rayuwarki dana littafi ki ɗauka wancan labarine dan fadakarwa da nishaɗi bawai dan sai kin tabbata ko kin samu irin rayuwar ba.

ALLAHU ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. ALLAH ka yafe mana.😭🙏🏻

Kamar yanda na fada a tiktok akwai mutanen kirki, masu yada alkairi DA yawa, hakama akwai na banza, mun tabo irinsu fadwa ne Dan su san illa na abinda suke aikatawa, muna musu kuma fatan shiriya da gane gaskiya kafin komai ya kure musu fiye DA Fadwa. Kazama mutumin kirki sai addininka DA al'adarka suyi alfahari DA kai. Ka kuma zama cikakke a cikin al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W) ba komai bane nishadi kamar handa muke kallo a rayuwar wasu yan tiktok, wani abun zubda mutunci DA darajane matsayinki na diya mace musulma.

Masoya muna godiya dan bazamu gaji da godiya a gareku ba akoda yaushe. Muna godiya matuƙa da kasancewar ku da zafafa biyar cikin tafiya mai nisan zango. ALLAH yabar zuminci ya kara mana zama lafiya da kaunar kauna. ALLAH ka bamu shugabanni na gari. Wannan zabe dake tunkaromu ALLAH kasa ayi lafiya a gama lafiya. ALLAH ya zaunar damu a gidajenmu lafiya bisa soyayya da kaunar juna tsakaninmu da mazajenmu. ALLAH ka shirya mana yaranmu damu baki ɗaya. Waɗanan fitintunu da wayoyi suka kawo mana da yanar gizo ALLAH ka bamu ikon tsallakesu. Wanda suka afka ciki ALLAHU ka shiryesu ka ganar dasu gaskiya kafin lokaci ya kure musu. 🙏🏻

Fatan alkairi ga kowa da kowa a duk duniyar dankuke. Kaunar kauna irin trillions ɗin nan masoya😍😍😍😍

Taku

Bilyn abdull ce😍🤗👌🏼.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 billy *_Typing📲_*
  2. 2 Chapter 58
  3. 3 Chapter 60
  4. 4 Chapter 62
  5. 5 Chapter: 63
  6. 6 Chapter 63
  7. 7 Chapter: 64 Share:
  8. 8 Chapter 64 64
  9. 9 Chapter: 67
  10. 10 Chapter: 68
  11. 11 Chapter 69 69
  12. 12 Chapter: 70 Share:
  13. 13 Chapter 70 70
  14. 14 Chapter: 76
  15. 15 Chapter 77