Skip to content

Chapter 8

Chapter 64 64

Babu So Mi Yakawo Kishi Book One Complete Hausa Novel 5,422 words 0 views Progress saved
Download Book

........Dariya take tana masa gwallo. Fuska ya

ɓata, da harɗe hannayensa a ƙirji irin yayi
fushin nan. Yanda yay ɗin sai ya saka Anaam
shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin.
“Kai Yaya shagwaɓa kuma?! ALLAH kamafi
ƙyau a haka fuskanka so cute”. Ta ƙare
maganar da kashe masa ido dariyarta mai
ƙaramin sauti na bayyana fararen haƙoranta.
Ta nuna lips ɗinta da kaɗa masa idanunta
dake cikin gilashi.
“Indai lipstick ɗin nan ne Yaya ba shansa
zakai ba garama ka haƙura”.
“Oh oh haba princess kiji tausayina mana”.
Yaya maganar da matsar da fuskarsa gab da
tata.
Baya taja dasa hanunta ta kare bakinta,
“Babu wani princess na daɗin baki fa Yaya,
barima kaga na shanye abuna, idan baka
ganiba ai dole ka haƙura”.
Yana ƙoƙarin riƙota ta tura lips ɗinta cikin
baki da sauri.. Idanunsa ya waro sosai yana
kallonta cikin langaɓe wuya. Ta fito da lips ɗin
tana dariya da masa gwalo. “Sai kaci abinci yanzu babu”.
“Ni ko? Yarinya zan rama ne”.
Dariyarta ta cigaba dayi ƙasa-ƙasa, shiko ya
ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin aincinsa
fuskarsa da ɗan murmushi.
“Nifa yaya karka cinye min abinci na”.
Idanunsa ya ɗago yana kallonta, sai kuma ya

ɗibo abinci ya nufi bakinta, “Ba marowaci bane irinki ai hahh”.
Bakin ta buɗe ba musu ya zuba mata, a
hankali ta shiga taunawa da faɗin, “Nima ai
bana rowa”.
“Kika min yanzun?”.
“Baga abincina kana ci ba”.
Murmushi kawai yayi batare da yace komai
ba. Itama bata sake magana ba, ya cigaba da bata abincin shima yana ci. Suna gab da kammalawa wayarsa tai ring, ɗauka yay ya duba, ganin Khaleel sai kawai ya ɗaga. Bata san mi'akace masa a wayarba, sai gani tai ya miƙe da kama hanunta....
Da mamaki take kallonsa zatai magana ya girgiza mata kansa. Baki ta ɗan tura dan ita dai bata ƙoshi da abincin ba, sai dai babu yanda zatai dole ta bisa. Hango Khaleel jikin wata mota mai ƙyau fara tas jingine ya sata zare hanunta cikin nasa, bai ce komai ba har suka ƙaraso. Ita ta fara gaida Khaleel ɗin, ya amsa mata fuska da murmushi sannan ya maida hankalinsa ga Yayansa. Gaisheshi yay
da girmamawa. Ya amsa masa da kulawa. “Daga ina haka mazan fama?”.
Murmushin Khaleel ya faɗaɗa dan yana son Yayan nasa ya kirasa da sunan nan. Wani ɗan ƙaramin gi! ya ɗakko a gaban motar, ya dubi Anaam dake kallon motar da ita kanta an

naɗeta da zaren gi!. Sai kuma ya sake maida kallonsa ga Share" ɗin da shima dai motar yake kallo. “Saƙone daga Abie. Abawa Granny”.
Idanu ta waro matuƙa da kai hannunta duk biyu saman bakinta, sai kuma ta dubi Share" da shima murmushi ke shimfiɗe akan fuskarsa. Shine ya amsa ya buɗe key na mota ya bayyana. Ai batama san sanda ta rungume Share" da faɗin, “Wayyo Yaya daɗi zai kasheni”.
Rungumeta yay shina da sakin dariya kamar yanda Khaleel shina ke dariyar. Ɗagowa tai ta amsa key ɗin tana kallo, sai kuma ta ɗagasa a saitin fuskar Share" tana kaɗa masa. Murmushi ya sake saki mai faɗi da faɗin, “ALLAH ya sakama Abie da alkairi Congratulations dear”.
Da amin ta amsa, Khaleel ma ya amsa da
kallonta. “Congratulations Granny. Saura
kuma tukuyci na, k ko Yaya wazai bani?”. “Karka damu Yaya Khaleel, saika zaɓa”. Ta
bashi amsa da shigewa motar da Share" ya buɗe mata, daidai nan Fadwa ta fito hakama Aysha. A tare suka ƙaraso wajen, Fadwa da gaba ɗaya ranta ke'a jagule tun maganganun da Share" ya yaɓa mata ta dubi Khaleel fuska a tsuke. Kafinma tai magana ya nuna musu

motar ita da Aysha yana murmushi. “Ƙyautace daga Abie aka kawoma Anaam”.
“Woow!!” Aysha ta faɗa cikin zaro ido da
shafa motar tana kallo, Fadwa kam mutuwar
tsaye tai. Dai-dai nan Share" da Anaam dake
cikin motar suka fito kowanne fuskarsa har
yanzu da murmushi. Khaleel ya miƙa mata
hannu, “Nifa a tafamin tukuycina”. Kafin tace komai Share" dake danna
wayarsa ya miƙa masa, saka details ɗinka”. “Woow da kyau babban yaya da gudu kuwa”. Yanda Yay ɗin ya saka Anaam da Aysha
kwashewa da dariya. Shigar saƙo a wayarsa yasa bai tankasu ba, ya buɗe da sauri, “What!”. Ya faɗa yana ɗago kai da sauri ya kalli Share". “Yaya duk tukuyci?”.
Murmushi Share" yay da kallon Anaam,
“Idan tace a ƙara maka ma sai a ƙara maka
ai”. A salon da yay maganar da ɗage mata gira
ya sakata rufe fuskarta da dukkan tafin
hanunta dan taji kunya. Matsota yay tare da
ranƙwafawa saitin kunenta. “Nima ina jiran
nawa tukuycin yanzun nan, inba hakaba a
gaban Khaleel zanyi.....”
Da sauri ta buɗe idanunta... “Kayi mi?”.
Maimakon amsa sai ya nuna mata lips ɗinsa cikin kashe ido. Sarai tasan zaiyi ɗin, amma sai ta kauda ido da nufin cewa a'a. Akan Fadwa da sam bata san da wanzuwarta a

wajen ba ta saukesu. Sukaima juna kallon ido cikin ido, ita ta fara kauda idonta da sakin wani tattausan murmushi mai ma'anoni da yawa ta maido dubanta ga Share". Murmushi ta sakar masa shima ta ɗan saci kallon Aysha dake a mota hankalinta baya kansu, ta maida ga Khaleel, ganin shi ɗin dai zaiga komai sai ta ɗanyi jimm na tunani. “Yaya Khaleel kalla can”. Ta faɗa da sauri tana mai ɗane Share" a bazata ta manne tausasan lips ɗinta kan nasa lips ɗin.
Numfashinsa neman shiɗewa yay saboda
rashin zaton hakan daga gareta. Baya ta nema
janyewa ya ƙara cafkesu da saka hannu biyu
saman ƙugunta ta zuba masa mintsini a gefen
ciki da janye jikinta kunya kamar ta nutse.. Khaleel daya waiga baiga komai ba ya juyo
da nufin hararar Anaam, ai babu shiri ya sake
maida kansa gefe da sauri yana dafe bakinsa
da sakin siririyar dariya. Aysha da bata san
mike faruwa ba ta fito a motar tana rungume
Anaam da faɗin, “Wayyo blood motar nan ta
haɗu wlhy ALLAH yasa a kashe da kai”. Wani
bahagon tari ya sarƙe Fadwa, cikin sassarfa
kamar zata kife ƙasa dan sauri tabar wajen
hawaye masu azabar zafi na kufce mata. Gaba ɗayansu kallonsu suka maida gareta,
dan sai yanzu ma shi Share" yasan Fadwar

na'a wajen. Cike da son basarwa itakam Anaam ta rungume Ayshar. “Thanks you blood, thanks you”. Shima dai gogan ya basar a binsa kamar komai bai faru ba, ya nunama Khaleel hanya alamar su shiga ciki idonsa akan Anaam. Anyi sa'a itama ta ɗago suka haɗa ido. Baki ta ɗan murguɗa masa. Ya taune lips dinsa da sakin murmushi alamar azakizo hannu. Kafaɗa ta ɗage masa da labe baki irin na i don't care taja hanun Aysha suka koma motar...
Da ƙyar Fadwa ta iya kai kanta sashenta
saboda jiri dake ɗibarta da lulluɓe ganinta
gaba ɗaya. “Subahanalillhi. Hajiya lafiya?”. Mmn Abu ta faɗa da nufo Fadwa da sauri
dake neman zubewa ta tareta. Kuka ta sakar mata kamar wata karamar yarinya, maman Abu duk sai ta rikice. Kamata tai har bedroom. Tana son tambayarta mike faruwa tana jin tsoro, dole ta fito ta barta cikin damuwa. Tadai san labarin kitse baya wuce ƙoƙi dan ta jima da fahimtar Fadwa na cikin jerin mata masu tsananin kishi. Gata da hali irin na ɓoye abu a rai da idan bakai dogon nazari akanta ba saika ɗauka kishiya cutarta take musamman irin Anaam da bata iya ɓoye abinda ke ranta. “ALLAH ya ƙyauta”. Ta faɗa

da komawa kitchen ta cigaba da aikinta.....
Anaam kam da tuni sun koma ciki tana can cikin farin ciki tana waya da Mamie da Abie ta video call. Addu'a take zubama iyayen nata harda hawaye, yayinda suma suke kallonta murmushi shimfiɗe a fuskokinsu da tsananin ƙaunarta da tausayinta harma da alfahari da ita na kai mutuncinta gidan aurenta. Dan aunty mimi ta sanarma Mamie komai, hakama Mamie ta sanarma Abie, shiyyasa ya danƙara mata mota najin alfahari da ita akan riƙe tarbiyyar da sukai mata. Sai dai su kansu sun san sun kaita wani filin gwagwarmayar rayuwane na yankin kaddararta, amma sukanji sassauci da tunawa zumincin ALLAH suke son karfafawa insha ALLAHU sadaukarwarsu bazata taɓa zama a banza da wofi ba..
______________________________
Tafiyar dai Aysha bata yuwu a yau ba, dan tuni Share" ya fice gidan tare da Khaleel yin godiya ga Abie, Anaam kuma sai ta ƙara samun sauƙin jikinta insha ALLAH zai kaita. Sai da suka fara biyawa ta o"ice yin wasu muhimman baƙi, ba wani dogon zama sukai ba sai zuwa monday idan ya dawo aiki.

Takardar da zai basu suje su duba kafin zaman ya nema ya rasa, cikin ɗan dafe kai ya dubu Khaleel da Fharhan. “Inaga fa nama bar file ɗin nan a gida wlhy, Khaleel saika koma
kenan dan dole ne mu basu suje su duba.” “Okay bara naje ai bawani nisa bane”.
“Okay ba damuwa, kafin ka isa zan kira su
ɗakko maka kawai”.
Kansa ya jinjina masa ya fice. Shi kuma ya
shiga ƙoƙarin kiran layin Fadwa. Harta tsinke ba'a ɗagaba, yay mata uzirin ko bata kusa ya sake kira, amma nan ma dai hakan, ya ƙara kira har sau uku sai aka koma danna masa number busy. Ransa ya sosu matuƙa, dan ya gane tana kan sani. Amma sai ya shanye kodan baƙin dake tare da shi ya maida akalar kiran ga Anaam. Gama wayarta da su Abie kenan kiran nashi ya shigo, bugu biyu ta ɗauka har yanzu muryarta cike da farin ciki tai masa sallama. A hankali ya sauke ajiyar
zuciya, ya amsa mata.
“Har yanzu murnar motar ce?”.
“Humm Yaya bazaka ganeba”.
Murmushi yayi, “Okay idan na dawo ai sai ki
ganar dani, yanzu nidai nutsu na saki aiki”. “Okay” ta faɗa kanta tsaye.
“Ki duba a study table ɗina, akwai wani file green a wajen ki ɗaukama Khaleel zai zo ya amsa yanzun”.

“Tom”.
Ta duba a kurkusa inda yace amma bataga
file ɗin ba, sai dai kuma hankalinta ne kawai
bai kaiba saboda ya dannesa da wani book.
Ta shiga bin komai daki-daki da kallo tana
ɗan ɗagawa harda buɗe drawers ɗin wajen.
Saukar idonta akan wani ɗan akwati ya sata
nutsuwa tana kallonsa, harta maida drawer
ɗin ta rufe sai kuma ta sake buɗewa ta ciro
akwatin. “Uhhm su Alhaji Yaya mm mi kuma
ake ɓoyewa anan? Koma dai miye zuciyata na
son gani”.
Tana ƙoƙarin buɗewa kira ya shigo wayarta,
shine dan haka ta ɗaga. Kafinma yay magana
tace “Yaya ban ganiba fa, inata nema kuma
tun ɗazun”.
“Kamarya? Bayan nasan yana nan akusa-
kusa. Ki ɗan ɗaga kayan wajen Khaleel na waje yana jiranki amfani zanyi da shi”.
“Oh sorry kamarma gashi anan ka ɗaura littafi akai”.
“Ok ki kai masa yana jiranki”.
Koda ta kaima Khaleel littafin sashen ta sake dawowa. Dan zuciyarta naga akwatin nan haka kawai batare data san dalili ba. Kiciniyar buɗewa ta shigayi, da ƙyar ta dace ya buɗu bayan ta haɗa da ƴan dabaru. Da

littafi ta fara cin karo, ta ɗan jujjuyashi tana taɓe baki ta ajiye. Sai envelope brown babba. buɗeta tai ta zaro albom na hotuna mai tudu sosai sai dai bai cika girma ba a tsaho. “Hotunan sirri ne kenan su Yaya aka ɓoy....” ta kasa ƙarasa abinda ta faro. Ko'a magagin barci aka tasheta babu gilashi a idonta aka nuna mata hoton babu gargada zata bada amsar itace. Hotone da taga irinsa yafi guda ashirin a gidansu. Hoton ne da aka ɗauketa a ranar haihuwarta tun a asibiti. Tana rungume a hanun Yaya Share" Abie da aunty Mimi sun sakashi tsakkiya suna leƙenta a hannunsa ya babbake ya hanasu gani. Da sauri ta koma na ƙasa, shi kuma a ranar sunanta ne ita da shi, na gaba itace da shi da Mamie da Abie da aunty Mimi. Ta cigaba da buɗe albom ɗin mamaki fal ranta dan ta kasa fahimtar ma'anarsa. Hotuna na gaba sun kasance a gurare daban-daban. Wani wajen ita kaɗai, wani ita da shi, wani har da su Abie. Ranar birthday ɗinta na cika shekara ɗaya. “Ya ALLAH” ta faɗa tana cigaba da kallonsu daki- daki. Jikinta ya ɗan fara rawa ganin hotunan da har tana a shekarar shiga primary, secondray, kai har jami'a ma akwai, bayan zuwa lokacin Share" baya tare da su. Duk wani hoton birthday ɗinta akwaisa, hakama

hotunan bikin salla kona wani taron makaranta kona islamiyya duk akwai. Hoton ƙarshe da yay matuƙar bata mamaki shine na ranar ɗaurin aurensa da Fadwa, itama kuma ranar nata ɗaurin auren da bata sani ba. Rubutun da yay a jikin hoton ya matuƙar firgitata..........
End of book
Leave a comment
C
Post
omments
No Comments posted yet

Contact Us
Arewa Books Publishers WhatsApp: 09031774742
Email: arewabookspublishers@gmail.com
Navigation
Home About FAQ's
Social
Facebook Instagram
Legal
Privacy Policy Terms of Service

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io[11/16, 2:25 PM] +234 703 462 8375: ........ *_Cikar burina shine ganin irin wannan ranar

tare da ke gimbiyar mata, kece sirrin ruhuna, nima

inajin raɗaɗi fiye da wanda na gani a cikin ƙwayar

idanunki. I'm sorry! ranarki tana zuwa_*.

Ta haɗiye yawu da ƙyar, da sake maimata

karatun kamar mai bita, dan yayisa ne da yaren

maley ta tabbatar batayi kuskuren karantawa ba.

Zaune takai dan ƙafarta ta kasa ɗaukarta. Ta

cigaba da zaro sauran abinda ke cikin akwatin.

Akwai kashi-kashi na ribbons ɗinta, ta gane

hakanne saboda matuƙar son da takema wasu,

wasu kuwa ta gansu a hotunanta dake cikin albom

ɗin can tun tana yarinya. Sai wani ɗan abunta mai

kamar kwalba cikinsa da taurari da wata suna

yawo, a tsakiyarsu da alkur'ani a buɗe, idan bata

manta ba Mamie ce ta bata shi as gi! ɗin kammala

haddar alkur'anin ta, amma saita nemesa ta rasa a

daga baya duk da kuwa a side drawer na gadonta

yake. Har kuka tayi na rashinsa, kai tsaye kuma ta

zargi mai aikinsu ce ta fasa amma ta ɓoye. Mamie

ce ta kashe wutar a lokacin ta sake saya mata wani

sai dai yasha banban da wannan ɗin dan haka

taita mitar batason sa har sai da Abie ya shiga

zancen ya lallasheta. Ashe Yaya MM ne ya sacesa.

Ta cigaba da kallon abubuwa da dama nata, kuma

masu muhimmanci a gareta data nemesu ta rasa a

lokuta mabanbanta, wanda a iya tunaninta ta rasa

mai ɗaukar mata su, duk da har su Amrah yaran
aunty mimi tasha zarga. Book ɗin ta ɗauka saboda

ji a ranta shima ya shafeta. A shafin farko sunanta

ne da rubutu kamar haka.

*_Juwairiyya Anaam! kece matar aurena kuma

uwar ƴaƴana da izinin UBANGIJINA. Ni kaɗai aka

haifawa ke, zan kuma rayune domin ke insha

ALLAHU._*

Ta buɗe shafi na biyu zuciyarta na tsitstsinkewa.

_Da ace wani bawa nada damar tsara labarin

rayuwarsa da wanzuwarsa, zan tsara nawane

kawai domin ke kaɗai a wannan duniyar. Ina

roƙon UBANGIJI ke ɗin karki zama a cikin

ƙaddarar abinda ALLAH bazai mallakamin ba,

zuciyata bazata iya ɗauka ba, ya rabbi ka zama

gatana akowane hali_.

Haka ta cigaba da karanta abubuwa daban￾daban akan rayuwarta da tasa daya dinga

rubutawa tamkar labarin littafi. Mafi ƙololuwar

ruɗa tunaninta da saukar da hawayenta shine a

gaɓar da Mommy ta takura masa auren watanta.

Duk wani tashin hankalinsa ya zanashi da fargabar

karta suɓuce masa. Zuwanta Nigeria da sunan

hidimar ƙasa mafi girman sassauci dajin ƙwarin

gwiwar yin biyayya da cusa son Fadwa a ransa

matsayin sadaukarwa ko UBANGIJI zai masa

tukuyci da samun Anaam. Kukanta ya ƙara ƙarfi

jin cewar ya kwanta jiyyane akan jin za'a aurama

waninsa ita ba shi ba, harda barazanar kamuwa da
ciwon hawan jini daya nema shafar lafiyarsa.

“Innalillahi...” ta shiga ambata da kifewa jikin desk

ɗin nasa ta shiga raira kuka, wani al'amari mai

girma na ratsa dukkan magudana da jijiya ta

jikinta. Sai da tai kuka sosai harta gode ALLAH

kafin ta ƙarasa ganin wasu zane-zane da yayi

wanda duk fuskartace ya zana, kai kace tana

tsayene a gabansa yay zanen. Da kyar ta miƙe ta

tattare komai ta maida masa yanda yake ta maida

a drawer ɗin sannan ta fice jikinta a saɓule.

Aysha dake zaune a falo tana aikin nata na

tiktok data koya gun Fadwa ta bita da kallo. Ganin

zata wuce bedroom batare data tanka mata ba ta

riƙo hanunta da sauri. Juyowa tai tana kallonta,

hawaye masu ɗumi na sauka mata a kumatu, sai

kuma ta rungume Ayshan tana saki wani marayan

kuka da ita kanta bata gama tantance na minene

ba.

Hankalin Aysha ya ƙara tashi, ta ɗagota da sauri.

“Ya ALLAH blood wai miya farune? Yaya ne ya miki

wani abu?”.

Kanta ta girgiza mata.

“To minene? Ko dai maganar aurence dai har

yanzu? Da zaman wannan gidan?. Dan ALLAH ki

kwantar da hankalinki Anaam. Ki saurareni a

wannan gaɓar na buɗe miki kanki ta yanda wlhy

sai Yaya Share" ya dawo tafin hanunki ta hanyarsoyayya da bin dokokin ALLAH. Na fahimci rashin

sanin minene kishi da rayuwar gidan malam

bahaushe ke sakaki tafiya a haguggunce a wannan

gidan har Fadwa ke jan akalarki da makirci. Ki

nutsu ki saurareni Please”.

Bataƙi ta Ayshan ba, suka koma suka zauna cikin

hikima da basirar da ALLAH ya bama Aysha. Da

kasancewar ta tashi a rayuwane ta cikin gidan

yawa dama salon kishin Mommy da Aunty Amarya.

Ga karance-karancen littatafan nan na hausa duk

tana taɓawa ta shiga warware mata abubuwa

masu yawan gaske. Anaam irin mutanen nanne

masu saurin haddace abu idan an faɗa musu,

musamman akan abinda ke wahalar da su, ko

wani abu da basa ƙaunar a kaisu ƙasa. Hakan ya

bata matuƙar gudunmawa wajen fahimtar Aysha

daki-daki babu kuskure. Sosai taji daɗin bayanin

dan haka ta rungume Ayshan.

“Na gode blood, nagode, irin godiyar da babu

alƙalamin dazai iya rubutawa. Sai dai ki sani duk

abinda kikaga inayi a gidan nan kamar mara wayo

ba rashin wayo bane sarai ina lure da komai da

binsa daki-daki, sannan akan sani nake aikatawa

saboda wasu dalilai nawa. Idan banyi hakaba shi

kansa bazan gama fahimtar halayyarsaba balle ita.

Tabbas nasan bazan taɓa iya kaiku wayon zama a

irin rayuwar da kuka tashi ba, sai dai koba komai

ina shigowa cikinku nima ina ganin wasuabubuwan. Daliline ya sakani zaɓar yin duk abinda

nakeyi. Sai dai a yanzu kalar rubutun zai sha

banban da kalar takardar. A yanzu lokacina ne,

kisa a ranki lokacin Juwairiyya Usman MD Share"

zai fara a gidan Al-Mustapha Muhammad MD

Share". Nayi alƙawarin bazanyi abinda zai cutar

da kowa ba, sai dai zan nunama kowa kowacce

mace da ilimin zaman gidan aure UBANGIJI ya

halicceta, kuma ko wacece ita ko'a ina ta tashi zata

rayuwu, ta kuma riƙe kambunta na ɗiya mace. A

kwanakin da nayi biyar a gidan nan, na karanci

abubuwa masu dama a cikinsu, zan kuma fara

sharar fadata da su domin samun damar shimfiɗa

mulkina batare da wani datti ya sha gaban cikar

burina ba”.

“Woow vary interesting my blood. Haka nake

sonki dan ALLAH. Ki haukata mana Yaya Share", ki

kuma dawo mana da Fadwa hanya tabar bin

karatun su Mommy, ta zama mai ra'ayin kanta”.

Anaam ta ƙyalƙyale da dariya, zuciyarta fes

tamkar an sauke mata dukkan wani nauyi da

ƙuncin da takeji a yau a yanzu yanzu. Basai

amfaɗa ba, da ni da mai karatu duk zamu fahimci

hakan nada nasaba da abinda taci karo da shi

wannda a baya bashi take kallo a fuskar Share"

ba. Sun ƙara tattaunawa sosai akan wasu

abubuwan da dama da Aysha kafin ta miƙe ta

koma sashen Share" domin gyarawa bisashawarar Aysha.

Bata jin daɗin jikinta saboda ɗinkin da akai mata

na sakata jinta tamkar a takure, ga tafiyarta har

yanzu bai zama normal ba kamar da. Amma haka

ta jure a daddafe na rashin sabon da wahala ta

gyara ko'ina na sashen nasa, sauƙin ma babu datti

mai yawa. Sai da ta tabbatar ko'ina ya mata da

kamshi sannan ta rufe ta fito. Baki ta saki tana

kallon yanda Aysha ta ƙara gyara sashenta itama.

Ta saki murmushi da harar Ayshan dake tsaye tana

karanta mata taje tayi wanka ta ɗauki ado dan

Yaya Share" na gab da dawowa. Akwai tsoro

tattare da ita na abunda ya faru, amma gargaɗin

likita akan Share" ya bata ƙwarin gwiwar

tabbatarma kanta babu wani abu tunda ko dai

baya cikin hayyacinsa ai baya nema wani abu daga

garetaba zaren ɗinki na a jikinta. Da wannan

tunanin ta faɗa wanka. Koda ta fito tsareta Aysha

tai wai sai ta mata kwalliya. Badan taso ba dole ta

tsaya kuwa Aysha ta zaneta tsaf dasu jaja leɓe da

barbaɗa kumatu na zamani. Turare kuwa har ji

take yana hawa mata kai dan khumras nata sun

sami haɗine na musamman daga hajiyar sudan,

ga kuma *_YERWA INCENSE AND MORE +234 809

521 5215 da miss xoxo tayo mata haɗi da sai ƴar

gata ke samunsa

!

_*. Hakama na kanti duk masu

tsadane da ƙamshi na musamman da aka zuba a

lefe. Ƙanan kayan nata taso sakawa, sai dai Ayshata hanata hakan, acewarta kayanmu na gida sunfi

mata ƙyau. Dole badan taso ba ta haƙura ta shirya

cikin skirt da riga na lass daya zauna mata a jiki

tamkar ka saceta ka gudu. Aysha tai mata ɗauri na

zamani daya saka ita kanta kasa rufe baki sai

faman kallon kanta takeyi a mirror da ƙyalla

hotuna da wayarta.....

A gajiye ya iso gidan bayan idar da sallar isha'i. Ya

fiddo ledojin daya shigo da su na fruits kashi biyu.

Sashen Fadwa ya nufa, ya sameta zaune a falo

ƙafa ɗaya kan ɗaya tanata cika da batsewa. Kallo

ɗaya yay mata ya ɗauke kansa dan ko sallamarsa

bata amsa ba. Ledar ya ajiye batare daya ce ko a

ba yay ficewarsa yana ƙwafa. Dan a yanda ta masa

ya bashi tabbacin tana kan sani taƙi ɗauka masa

wayarsa. Sashen Anaam ya nufa da ɗayar ledar

yanata faman furzar da hucin ɓacin rai......

_

# #

Shike nan an shiga tsakaninmu da

Soulmate

$

, dolene mu koma gidan.... Basai na faɗa ba.
[11/16, 2:25 PM] +234 703 462 8375: jimawa, Anaam dafe da kanta dake mata ciwo

saboda kukan da tasha ɗazun, ga jikinta har

yanzu sam baya mata daɗi irin na shiga

sabuwar rayuwar da ba'a saba ba. Aysha ce ta

amsa masa sallamarsa, ya ƙaraso ciki idonsa

akan Anaam. Ya miƙama Aysha dake masa

sannu ledar hanunsa.

“Ita wannan lafiya kuwa?”.

“Kanta ne ke mata ciwo, nayi-nayi tasha

magani kuma taƙi”. Zaune yakai kusa da ita,

ya janye hanunta dake dafe da kanta. Kasa

kallonsa tai, dan haka kawai take jin wani irin

matsanancin kunyarsa. Shiko ya matuƙar

shagala ne a kallon kwalliyar dake zane akan

fuskarta, a kasalance yakai hannunsa kan

haɓarta ya ɗago fuskar da ƙyau, hakan sai ya

tilasta mata ɗago nata idanun dake cike da

ƙwalla ta kallesa. Ba ƙaramin jarumta yay

wajen jawo numfashinsa dake neman

kufcema ƙirjinsa ba, ya matsota jikinsa tare

da ɗaura hanunsa saman goshin nata.

“Wannan idon naki kinyi kuka da shi, ko

muje asibiti ne?”.

Ya faɗa a hankali cikin kunenta. Kanta ta

girgiza masa da ƙara lafewa a jikin nasa har

hakan ya so bashi mamaki. Dan yasan dai

koshi ya ringumeta turesa take kota janye

jikinta, amma yanzu ga saɓanin hakan yanagani, koda yake tunda abin nan ya faru ya

fahimci ta zama wata shiru-shiru, tsiwar taɗan

ragu kaɗan ko likimo ne, mata sunji maza

kenan. Fitowar Aysha ta sakata janye jikinta,

shima sai ya miƙe yana faɗin, “Bara na watsa

ruwa sai a samo miki magani”.

Baki ta ɗan tura masa da kaiwa kwance. “Ni

basai nasha magani ba fa”.

Juyowa yay daga niyyar barin falon da yayi,

“Oh tunda hakane tashi na fasa barinki anan

ɗin”.

Dole badan taso ba ta miƙe, dan ya tsuke

fuska babu alamar wasa, duk da dama dai

tunda ya shigo babu fara'ar tattare da shi.

Aysha da tuni ta koma kitchen yay kira. Fitowa

tai da sauri tana amsawa.

“Gyaramin fruits ɗin nan”.

“To Yaya. Ko'a haɗa salad?”.

“Duk yanda kikai is ok”.

Kanta ta gyaɗa masa, shi kuma ya kama

hanun Anaam suka fice. Ta bisu da kallo

murmushi bayyane akan fuskarta. Tana fatan

ALLAH ya hana su Mommy raba wannan

auren har abada. Dan sun kasance abin

birgewa best couple ever matuƙa”.

Koda suka iso sashen nasa a falon ya zauna,

ya riƙota saman cinyarsa ya zaunar. Yanzun

ma cikin mamaki yaga ta lafe a jikinsa. Ya ɗan

murmusa da shafar fuskarta idonunsa na binfuskarta dake ƙwaɓe alamar rashin jin daɗi

da kallo.

“Kodai har yanzu garden ɗin na zafinne?

Noorie!?”.

Kanta ta sinne a ƙirjinsa da riƙo hanunsa

dake kaiwa jikinta, dan zuwa yanzu ta fahimci

mi yake kira garden ɗin. “Yaya Please ka

daina”.

“No Aunty babu wannan zancen”.

Ya faɗa cikin kwaikwayon muryarta.

Murmushi ya kufce mata tare da ƙara cusa

kan nata cikin jikinsa. Dan yanda yay maganar

ya matuƙar bata dariya. Shima murmushi yay

da kaima wuyanta kisses. Tsoro ne ya kamata,

tai ƙoƙarin jan jikinta baya amma ya hana

hakan.

“Wayyo kaina zai fashe Yaya”.

Dakatawa yay daga ƙoƙarin cusa hanunsa

cikin rigarta. Ya riƙo kannata. “Ayya. Sorry,

sorry”. Sake langaɓewa tai kamar gaske. A

ƙasan ranta kuwa dariyace ke taso mata tana

dannewa. Da gaske kan nata na ciwo, amma

yanda takeyi ɗin yanzu harda pretending. Yin

hakan kuma shine mafita a gareta saboda

ganin yana neman sakin layi, itako a yanzu in

ba giyar wake tasha ba mizai kaita sallama

masa ya kasheta. Ai anyi kenan babu ƙari

tunda abun azaba kawai akesha a ciki. Ita jiya

tunaninta gaba ɗaya akan tayaya wasu matanke iskanci a cikin wannan wahalar? Ko kuwa

su basajin abinda taji da bazata taɓa

mantawaba har duniya ta tashi.

Zaunar da ita yay a kujerar ya shiga bedroom

ɗinsa. Dai-dai nan Fadwa tai sallama. Anaam

tai kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa

ciki-ciki. Sam Fadwa bataji an amsa ba, sai dai

sanin halin mai sashen da kuma halin da suke

ciki na fushi da juna ya sata shigowa a ganinta

kobai amsa ɗin ba zata shigo. Turuss ta ɗanyi

na ganin Anaam, sukaima juna kallon cikin

ido kowacce ta janye da takaicin ƴar uwarta

da tsagwaron kishi.. Basuyima juna magana

ba, Fadwa ta nema waje ta zauna.

Fitowarsa ta saka Fadwa ɗaga kai tana

kallonsa, shima ita ɗin yake kallo da mamaki

a ƙasan zuciya, sai dai a fuska babu ko ɗigon

hakan sai ma janyewa da yay cikin halin ko'in

kula ya nufi Anaam dake kallonsu ta ƙasan

ido. Ita dai bata san sunada wata matsala ba a

gidan. Dan haka bata kawo komai a ranta ba

game da ɗaure-ɗauren fuskar tasu. A hanun

kujerar da take kwance ya zauna,

“Tashi kisha. Kimmaci abinci kuwa?”.

Sai da ta ɗan saci kallon gefen Fadwa sannan

ta ɗan tura baki da narke fuska. “Ni banajin

ci”.

“Uhhm baƙya son ci, yarinyar nan ki ragetaɓaran nan naki, yanzu abincin ma sai kin

nuna masa hali? Yanzu dai kinga ba'a shan

magani sai da abinci, faɗamin mi zaki ci?”.

Kallonsa ta ɗanyi da juya ƙwayoyin

idanunta, sai kuma ta narke fuska da girgiza

kai. “Da gaske bana son ci, barci nakeji kawai”.

“Uhm-uhm fa, bana son zama da yunwa

sam! Ki dai sha ko fruits ɗin can ne idan Aysha

ta kawo. Zakisha ko?”. Ya ƙare maganar da

ranƙwafowa kanta yana sinsinar wuyanta. Ta

gefen ido ta saci kallon Fadwa, sai taga su

take kallo fuskarta ciɗin-ciɗin kamar zata

fashe har wani jajaja takeyi na alamar ɓacin

rai abunka da fari. Murmushi tai mai sanyi

dakai hannu ta shafi fuskar tasa a ranta tana

faɗin (Ashe kin san akwai ciwo ni kike yi masa

kiss a gabana, zan koya miki iya zaman

duniya). Hanunta da take neman janyewa ya

cafke da sauri yana maidashi akan tattausan

gashin kumatun nasa. “Kin yarda zaki sha?”.

“Ni dai ɗan kaɗan”.

Ta faɗa a shagwaɓe.

Da ƙyar ya iya jan numfashi, dan shagwaɓar

tata ba ƙaramin susutashi take ba. “Good

girl”.

Murmushi tayi da janye hanun. Riƙeta yay, ta

marairaice masa. “Nifa fitsari zanyi”.

“Okayy to ana buƙatar abokin rakkiya?”.Ta faɗa da zille masa tana ƴar dariya.

Bedroom ɗinsa ta nufa batare da ko sashen

Fadwa ta kallaba. Tana shiga ta zube a

gadonsa dan babu wani fitsari dama. Kawai

dai taba Fadwa space ne. Domin rama abinda

tai mata bashike nufin bazata mata adalci ba.

Kuma koba komai yanzu kawai ta nuna mata

cewar alwashinta tabbatacce ne akan mantar

da Yaya MM ita in har tana a tare da shi.

Shiko daga can da kallo ya bita har saida ta

shige, a hankali ya haɗiye murmushi kan

fuskarsa. Miƙewa yay kamar zai bar falon.

Tasan idan tai wasa da wannan damar zatafi

haka shan wahala. Kamar yanda Mama

(Gwaggo halima) ta faɗa mata ba haka ake

buƙata ba, taje ta shirya dashi kodan

kasancewar gobe ne zata amshi girki, suna

buƙatar tai aiki da wasu fitinannun maganin

mata da aka kawo dominta tun daga ƙasar

sudan.

“Dan ALLAH kayi haƙuri” ta faɗa da sauri

tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da tun ɗazun

take son su zubo ko zata samu sassauci.

Ratseta yay zai wuce tai azamar riƙosa. Bai

juyoba amma ya dakata. Ta share hawayenta

hanunta riƙe da nasa. “Dan ALLAH kayi

haƙuri, nasan nayi kuskure. Amma wlhysharrin shaiɗanne”.

Ransa a ɓace ya dubeta da wani mugun kallo

daya matuƙar neman gigitata. Saurin sakinsa

tai da girgiza masa kai. “Nasan nayi kuskure

amma dan ALLAH kayi haƙuri haka bazata

sake faruwa ba”.

“Tashi kibar min falo”.

“Please Soulmate dan ALLAH”.

Sallamar Aysha ce ta sakashi haɗiye maganar

bakinsa, ya koma ya zauna da amsa mata.

Itama hawayenta ta shiga sharewa idonta na

satar kallon ƙofar bedroom ɗinsa, dan

zuciyarta raya mata take Anaam na wajen

laɓe tana saurarensu. Sosai takejin raɗaɗi da

ɗacin hakan, amma taci alwashi komi zai faru

a yanzu ɗin bashi ne Anaam ɗin zataci itama

zata rama.

Aysha ta dire tray ɗin hanunta a gabansa,

fuskarta da murmushi ta gaida Fadwa da taƙi

kallonta saboda kar Aysha ta fahimci tayi

kuka. Kanta kawai ta jinjina mata. Ayshan

bata damu ba, dan tasan halin Fadwa wani

lokacin itama akwai yarfi. Hankalinta ta

maida akan Share!, “Yaya a zuba?”. Kai ya

girgiza mata alamar a'a, sai kawai tai musu

sallama ta fice a ranta tana ayyana akwai

matsala gaskiya, sai dai rashin ganin Anaam

yasa taji wani iri.

Kusa da shi ta taso ta dawo, “Soulmate......Hannu ya ɗaga mata a fusace. “Fadwa! leave

me alone. Tashi ki fita”.

Idanu ta tsura masa zuciyarta na mata

raɗaɗi, tasan a cikin fushi yake, kuma shi baya

son yanke ma mutum hukunci cikin fushi. Jiki

a saɓule ta tashi ta fice wasu hawaye masu

zafi da jin matuƙar tsanar Anaam na ƙaruwa a

ranta. Dan a ganin duk an mata hakane

saboda Anaam, ta kuma tabbatar ba haka

iyayen Anaam suka bar Share! ɗin ba kamar

yanda Mama ta sanar mata yanzun.

Ya jima zaune a wajen zuciyarsa na masa

raɗaɗi da ƙuna, baya son ɓacin rai da

damuwa, yama rasa ina zai kama da halin

matan nasa. Ya samu ita Anaam ɗin ta sakko

ya fara samun kwanciyar hankali ita kuma

Fadwar na neman rikita masa lissafi. dole ne

ya musu sabon shiri na zama da kowacce da

halinta. Yasan duk abinda Anaam zatai tana

yinsane a karan kanta sannan bata da ɓoye-

ɓoye. Fadwa kam ya fahimci akwai zugar

mutane baibaye da ita, dan tun zuwan Anaam

gidan ya fahimci ta ajiye wasu halayenta na

zahiri ta aro waɗansu daban, idan bai tashi

tsaye a kanta ba zasu iya laɓewa a bayanta su

tarwatsa masa farin cikin gidansa, shi kuma

harga ALLAH yana sonta itama. Ya furzar da

numfashi mai ɗaci, tunawa da Anaam dakecikin bedroom ya sashi miƙewa ya nufi

bedroom ɗin. Da mamaki yake kallonta

kwance a gado har tayi barci, ya tsugunna

saitin fuskarta yana sakin murmushi da kai

hannu ya shafa kanta. “Dama fitsarin ƙarya ne

kenan?”.

Idanu ta buɗe a hankali dan dama barcin

baiyi nisa ba, sai kuma ta maida zata lumshe

da ture masa hannu. Hannun nata ya riƙo

cikin nashi, fuskarsa gab da tata, “Tunda kin

tashi muje kisha fruit ɗin”.

“Ni na ƙoshi barci nakeji Yaya”.

“Ni kuma ban yarda ba idan kika sha sai kiyi

barcin”.

“Uhhum-uhhum”. Ta faɗa tana noƙe

kafaɗarta. Miƙewa yay yana murmushi, ya

ɗagata gaba ɗayanta. Watsal-watsal ta farayi

da ƙafafunta. “Wayyo Yaya! Wayyo Yaya ni ka

saukeni na ƙoshi”.

“Wayyo Aunty! Wayyo aunty ni bazan

saukeki ba sai kinsha”. Ya faɗa dai-dai suna

kaiwa falon.........

End of bookBABU SO

Table of Contents

Chapters

15 chapters
  1. 1 billy *_Typing📲_*
  2. 2 Chapter 58
  3. 3 Chapter 60
  4. 4 Chapter 62
  5. 5 Chapter: 63
  6. 6 Chapter 63
  7. 7 Chapter: 64 Share:
  8. 8 Chapter 64 64
  9. 9 Chapter: 67
  10. 10 Chapter: 68
  11. 11 Chapter 69 69
  12. 12 Chapter: 70 Share:
  13. 13 Chapter 70 70
  14. 14 Chapter: 76
  15. 15 Chapter 77