Chapter 3
Chapter 60
60
.......Cikin nasa idanun suka shiga, sakamakon kallonta yake shima. A karan farko taji hakan babban abune a gareta kallon tsakkiyar idonsa tai masa koda harara ne. Janyewa tai a kasalance ta maida ga Aysha dake kallonta fuska da damuwa duk da bata san mike damu ƴar uwar tata ba. Dan ita dai tana gida ya kirata a waya wai ta ɗakko kaya kala ɗata ta fito ta samesa an kwantar da Anaam asibiti. Ya kuma mata gargaɗin karta sanarma kowa, Mommy ma tace mata zataje waje Fadwa ne. Hakaɗin tayi shine ta sami damar fitowa dan itama Mommyn na buƙatar aje mata gidan Shareff ɗin duk da tasan ba lallai ta sami abinda take so ga Ayshan ba. Amma tasan ta inda zata dinga binta tana jin koma ai. Amma sai ta kasa kallon aunty Mimi da itama kallonta take duk da bata san mike damunta ba, ya sanar mata dai kawai Anaam babu lafiya, sai dai bai son su Mamie su sani.
Matsowa Aysha tai suka rungume juna, idon Anaam cike da ƙwalla.
“Blood mike damunki?”.
Ɗan satar kallonsa tai shi da aunty mimi, idanunsa ƙyam a kansu, Hawayenta ta share da girgiza mata kai kawai alamar babu komai.
“Blood ba'a zuwa asibiti ai babu komai, dan ALLAH ki faɗamin”.
Katse Ayshan yay da faɗin, “Idan kinji maganin mi haka zai miki?, malama tashi ki bata abinci ban son surutu mara amfani”.
Badan Aysha taso ba dole tai shiru. Aunty Mimi ta ƙaraso ta zauna saman kujera, gaba ɗaya Anaam ta kasa kallonta, idanunta a rissine tace “Ummi good afternoon”.
“How are you feeling?”.
Kasa amsawa tai sai hawaye data matso. Aunty mimi tai murmushi, “Mamana har yanzu baki san kin girma ba, shagwaɓa dai shagwaɓa dai why?” nanma batace komai ba, aunty mimi da zuciyarta ke ɗan hasko mata wani abu ta kalla Shareff, shima kansa yay saurin kaudawa gefe yana shafo bayan ƙeyarsa da hannu. “Humm” tace kawai. Itace ta taimaka mata ta koma saman gadon. Aysha kuma ta fara zuba mata abinci. Takowa yay daga inda yake tsaye ya zauna kusa da ita a gefen gadon. Jitai kamar ta makesa sai dai babu dama. Koda Aysha ta gama zuba abincin shine ya amsa, sake gyara zamansa yay yana fuskantarta da ƙyau, sai dai taƙi yarda koda wasa su haɗa ido.
“Ko zaki sha tea ne kafin kici abincin?”. Ya faɗa idonsa a kanta. Girgiza masa nata kan tayi, murya a shaƙe tace, “Bazanci komai ba na ƙoshi”.
Komai baice mata ba, ya ɗibo abincin zuwa bakinta yana faɗin, “Hahh!”.
Sosai ta ƙwaɓe fuska, ta ɗan ɗago cikin marairaicewa tana kallonsa, sai kuma ta saci kallon gefen aunty mimi. Ganin basu take kallo ba ta ɗanji sassauci kaɗan. Kanta ta girgiza masa “Banajin cin komai ALLAH”.
Ƙasa-ƙasa yace, “Gashi kuma dole sai kin ci! In ba haka ba kuma.....” ya ɗage mata gira ɗaya batare daya ƙarasa faɗaba. Dole badan taso ba ta buɗe bakin ya fara bata abincin da tun a ɗanɗanon farko ta gane girkin Mamienta ne. Kasa ɓoyewa tai.
“Yaya wajen Mamie ka amso min abinci?”.
Kansa ya jinjina mata da kai babban yatsansa ya goge mata mai daya taɓa gefen bakinta. Sai taji kunya ta kamata kasancewar Aunty mimi da Aysha a ɗakin. Shiko babu alamar hakan ya damesa ma ya sake miƙa mata wani daya ɗibo a spoon. A haka Dr Bilkisu ta shigo ta samesu yana bata abincin, a ranta ta ayyana (Maza ga zaƙi ga harbi kenan). A zahiri kam idonta akan Anaam tana murmushi. “Masha ALLAH my patient jiki yayi daɗi”.
Cikowa idanun Anaam sukai da hawaye, ta girguzama Doctor kanta. “Har yanzu inajin ciwo a wajen”.
Idanu ya waro da sauri jin zatai masa fallasa, ya daura yatsansa akan lips ɗinsa alamar tai shiru, ta gefe kuma yana nuna mata aunty Mimi da ido. Sai dai kuma bai san sarai aunty mimin na kallonsu ba ita da doctor. Ta ƙunshe dariya da kyar, Dr Bilkisu dai kasa dannewa tai sai da tayi tata.
“Ayya karki damu insha ALLAHU zai daina, idan na sallameku zan baki dukkan dabarun da zasu taimaka miki har ki dawo normal a cigaba da amarci ko”.
God forbid”.
Ta faɗa a hankali samman lips ɗinta. Da ɗan ɗagowa zata hararesa suka kuwa haɗa ido. Babu shiri ta mayar ta risinar. Har doctor ta gama ƙara duddubata bata sake yarda ta kalla sashen da yake ba dan tuni tace masa ta ƙoshi da abincin. Shima dai kunya ta hanashi sake wani motsi, dan ya san dai aunty mimi ta gama fahimtar komai kuma. Magungunnanta ya bata ta sha kamar yanda Doctor tace. Sai da ya tabbatar komai yayi normal sannan ya mike yana kallon agogon hanunsa.
“Small Mom ni zanje gida nai wanka bara na maidaki, inaga sai zuwa anjima zan dawo. Aysha ki kula da ita idan da buƙatar wani abu sai ki kirani a waya. Bana buƙatar wani yasan da zamanku anan, idan hakan ta faru ranki sai yafi nawa ɓaci”.
Aysha ta amsa masa da to.
“Karka damu Babana jeka kawai harka dawo, bara naga likitar nan. Aunty Mimi ta faɗa kai tsaye tana miƙewa ta fita. (Shike nan na mutu) ya ayyana a ransa da bin aunty Mimin da kallo. Itako Anaam tuni tai kwanciyartama ta juya musu baya. Har tayi zaton ya fice sai ga saukar numfashinsa a cikin kunnenta, da sauri ta juyo dan ta tsorata, hakan ya bawa fuskarsu damar haɗuwa, ƙoƙarin jan tata tai baya ya hana hakan ta hanyar riƙota.
_“Ina alfahari da ke a wannan rana, alfahari irin wanda zuciya bazata iya ƙayyadewa ba, hannu bazai iya zanawa ba, ke ɗin zinariya ce, idan nace zinariya ina tabbatarwa duniya zinariya a tsakkiyar duhuwar jeji, amsar itace, *Haskenki kaɗai za'a iya gani*”._
Daburcewa tai, sakamakon saukar lips ɗinsa akan nata, ta shiga son ture masa fuska, amma yaƙi yarda da hakan har sai da yay yanda yake so da ita. Yana sakinta sashen da Aysha da aunty mimi suke ta fara kalla, sai dai wayam da alama ma duka basa a ɗakin. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke da saurin kauda kanta saboda ido da suka haɗa da shi. Murmushi ya saki mai faɗi da yalwa dan ya fahimci catake su Aysha na a ɗakin.
Sake ranƙwafowa yay kanta har lokacin murmushi shimfiɗe a fuskar tasa. “A ƙara ko? Nima ban ƙoshiba”.
Ture fuskarsa tai da sauri tana jan bedsheet ɗin dake a matsayin bargo ta ƙudundune kanta. Murmushinsa ne ya ƙara faɗaɗa, ya girgiza kansa kawai da juyawa ya fice a ɗakin.
Sallamar Aysha ta sakata sakin ajiyar zuciya, sai da taji ta zauna a kusa da ita sannan ta buɗe kanta. “Da alama dai kin samu sauƙi tunda naga Yaya ya fita yana faman murmushi”.
(Ba dole ya fita yana murmushi ba tunda ya gama yayyagani) a fili kam sai ta taɓe baki da yunƙurawa zata tashi zaune. Taimaka mata Ayshan tayi ta zauna cikin dauriya dan ƙasanta sosai yake mata zafi zamanma dai tayisane irin na kishingiɗa ɗin nan..
Aysha ta sauke ajiyar zuya tana kallonta, “Dan ALLAH ki kwantar da hakainki na tabbatar zaki ji daɗin zama da Yaya Shareff insha ALLAHU Blood. Yanada ƙyawawan halaye da lokaci ne zai tabbatar miki da hakan kamar yanda nasan kema kina da su. Hatta Fadwa bana son ki biye mata dan ita kanta komai na ƙiyayyarki tanayine ba'a kan tunaninta ba, tunanin su Mommy shike sarrafata tun farko, amma wlhy inhar kika jajirce sai kin ƙwace komai kuma a hankali Mommy zata fahimceki halayen banzar da Gwaggo ta ɗorata a kai duk zata ajiyesu kodan son da takema Yaya”.
A karan farko Anaam ta saki murmushi. “Blood wannan ba magana bace ta nan, Please share kawai yanzu dai ya mutanen gidan? Ina kewarsu ALLAH kamar nai tsuntsuwa na ganni ciki”.
“Aiko bazaki ganki ɗin nan ba, dan a gabana su Abba sukace kar Yaya ya kawoki gida sai bikina”.
Sosai ta waro idanu waje, “Bikinki fa? Hum'um ALLAH bazan iya ba. Dana koma aiki monday zaku ganni”.
“Hhhhh ashe Yaya zai ɓalla miki ƙafar baya kuwa”.
(Yanzu ma ai ya ɓalla min) Anaam ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai tayi murmushi kawai....
★★★★
Yanzun ma daya dawo gidan bayan la'asar yaso shareta, sai dai zuciyarsa ta gargaɗesa a kan hakan dan koba komai hakkintane a wuyansa. A falo ya sameta zaune ta ƙurama tv ido. Mmn Abu na daga kitchen tana aiki dafa mata indomie dan duk yau taƙi cin komai sai tea kawai. Sai yanzu da yunwar ta cita ne sosai bayan tayi wanka ta fito falo tasa mmn Abu din ta dafa mata. Kallo ɗaya tai masa ta kauda kanta, sai dai ta amsa masa sallamar da yay ciki-ciki itama akan lips. Motsin mmn Abu a kitchen ya sashi wucewa bedroom.
“Ki sameni a ciki”.
Shiru kamar bazata bisaba, sai raka bayansa da tai da harara ƙasa-ƙasa. Sai da taja kusan mintuna biyu sannan ta miƙe ta bisa. Tsaye ta samesa ya jingina da mirror. Taima fuskarsa kallo ɗaya ta ɗauke kanta da kaiwa zaune bakin gado.
“Ɗazun ina tambayarki mike damunki kin tashi kin barni saboda raini. Ina gargaɗinki da karki tsiro da wata sabuwar ɗabi'ar banza, hakan zai sa mu sami matsala da kowaccenku idan tace zata dinga kawomin raini wlhy”.
Tasan halinsa, dan haka a hankali tace, “Kayi haƙuri”. Batare data ɗago idanunta da suka cika da ƙwalla ba.
Duk girman laifin dakai masa idan ka bashi haƙuri yakan ɗanji sassauci ko yaya. Dan haka ya furzar da huci kawai. Sai kuma ya sake kafeta da idanun nasa. “Kina fushi da ni saboda na fita da ƴar uwarki, maimakon ki fara neman ba'asin mike faruwa kodan jimawar da kikaga munyi a waje batare da mun dawo ba. Sannan yanayin dana fita da ita a gidan nan yana nuna akwai matsala amma duk kika zaɓi ganin baƙina akan bincikawar!”.
Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo mata. Tasa hannu ta sharesu. “Ni baca nai kayi laifi ba, amma ya kamata tunda ina a gidan na sani, a ƙalla dai an nuna inada daraja ko yayane, amma ta gabana ka wucefa Soulmate tamkar baka ganni ba saboda ka ɗauka mace a hanunka....”
“Macen dana ɗauka matata ce, kinga hakan yana nufin babu haramci a ciki kenan, kema kuma nasha ɗaukar taki ai. Ki tsaya a laifin ba'a faɗa mikiba kawai bawai ɗaukarta ba. Sannan wannan ya zama na farko ya zama na ƙarshe da zanzo ina miki magana koda kuwa laifin na miki ki maimaita irin abinda kikaimin ɗazun, bazan ɗauki wannan salon ba ga kowace”.
Duk da maganganunsa sun ƙona mata zuciya saita jinjina masa kai kawai. Shima bai sake cewa komaiba yay ficewarsa zuwa sashensa. Har yanzu ba'a kwashe kayan abincin safen ba. Dan haka yay kiranta a waya. Tana ɗagawa ya sanar mata tazo ta kwashesu ya yanke wayar.
Wanka yay, koda ya fito sai ya ɗan kwanta duk da barci yake sonyiba yana son hutawa dan shi ɗin kansa jikinsa duk ciwo yake masa. Ga yunwa na cinsa kaɗan-kaɗan dan duk yau bai wani ci abincin kirki ba. Lokacin da sukaje salla da Dr Jamal bayan sun fito massallaci gidan abinci sukaje. Amma sai ya kasa nutsuwar cin komai sai doughnut kawai ya ɗanci da drink. Daga nan ya nufi gidansu sai dai bai shiga wajen su Mommy ba ya shiga nasu Anaam da niyyar ɗakko Amrah ta zauna da ita a asibiti sai ya iske bata nan. Mamie tayi masa tayin abinci amma sai yace ya ƙoshi yana sauri ne, amma baiwar ALLAHr sai gata da shi ta haɗo a basket saboda tasan abincin da yake matuƙar so ne. Harda plate da drink da alama tayi tunanin office zai koma dan yace mata yazo ɗaukar wasu takardune zai koma wajen aiki. A sirrance ya sanarma Aunty Mimi suka fito tare kamar zasu cikin gida, hakan yasa Mamie bata sani ba. Abincinne ya kaima Anaam taci shiko baima cin ba duk da yana so..........✍[11/15, 11:19 AM] Marsy😘: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_61_*
........Aunty mimi ta ɗan jima wajen doctor Bilkisu sannan ta dawo, sai faman murmushi take, a ranta kuwa faɗi take (ƴan banza kukace da bakwa son juna. Yanzu kuma ina ƙiyayyar taje harda ɗinki?). A zahiri kam zama tai tana kallon Anaam daketa faman sinne kai taƙi yarda su haɗa ido sam. “Wai nikam na zama surukarki ne halan Mamana? Tun ɗazu sai wani sissinemin kai kikeyi daga ke har mijin naki wani abu ya faru ne?”.
Dariya Aysha ta sanya. “Ummie surukartace ke mana, ba ɗanki take aure ba”.
Dariya itama Aunty Mimi ta sanya da faɗin, “Bayan haka ma akwai dai wata a ƙasa ma”. Anaam ta ballama Aysha dake ƙara kwashewa da dariya harara. Sai kuma ta koma ta kwanta tare da lulluɓe har kanta tana murmushi.
★Da shirin tafiya massallaci daga can ya wuce asibiti ya fito. Har yayi niyyar ficewarsa sai kuma ya shiga wajen Fadwa. Samunta yay tayi alwala. Yanzu kam ya ɗanga sassauci a fuskarta, sai dai ba'a sake masaba yanda aka saba. (Idan ka biye ta matan nan baka da maraba da ball ɗin ƙwallonsu) ya ayyana a ransa. A fili kam sai ya juya kamar zai koma yana faɗi,
“Zanje masallaci, daga can zan wuce asibiti”.
Muryarta a dasashe batare data kallesaba tace, “Bara nai sallar sai na jiraka nima zanje na dubata”.
Yanji daɗi har cikin ransa. Dan haka yace, “Okay”. yana ficewa. Da kallo ta bisa, ta sauke ajiyar zuciya da taune lips ɗinta ta haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi. Batai niyyar zuwa ba, Mamanta ce ta kirata tace taje, kuma ta saki ranta duk wani fishi da takeyi ta dainashi hakan zai bama shirinsu damar tafiya yanda suke so.
Maimakon yin sallar magrib ya shigo sai da yay isha'i, ya iske ta cikin shiri dan haka basu ɓata lokaci ba suka fito mmn Abu biye da su da abincin da Fadwa ta sakata shiryawa wanda tayine saboda maigidan. Sai dai kuma Gwaggo halima tace mata ta ɗaukesa ta kaima Anaam ɗin, itama kuma sai ta yarda da hakan tunda da wuya yace zaici a yanda yake kan dokin zuciyarnan. Shiru motar babu mai magana har suka fito daga layinsu. Ya harba motar saman babban titi.
Ɗan kallonsa tai ta gefen ido. Har yanzu fuskarsa ciɗin-ciɗin babu alamar fara'a, sai tuƙinsa ma yake tamkar bai san da zamanta a motar ba. Idonta ya ciko da ƙwalla ta maida kanta gefe tana ƙoƙarin haɗiyesu. A wajen masu saida fruits ya tsaya ya sayi laida biyu yasa a baya, ya kuma tsayawa ya sayi gasashen kifi shima ya saka a baya.
“Sorry na saki jira”.
Kanta ta girgiza masa.
“Babu komai”.
Bai sake cewa komai ba ya tada motar sukai gaba.
★Suna kallon film a wayar Aysha suka shigo, Aunty Mimi kuma nakan sallaya tana addu'a dan ta idar da sallar isha'i ne. Sam Anaam bata kawo a ranta ganin Fadwa ba. Sai da Aysha ta ambaci sunata sannan ta ɗago. Kallon juna sukai cikin ido. Kowanne ya janye lokaci guda. Aysha ta sauka a gadon da sauri ganin Shareff na kaiwa zaune kusa da Anaam ɗin yana nunama Fadwa kujera.
“Kun daiyi salla ko? Da kuka zauna kallon film?”.
“Eh Yaya munyi”
Cewar Aysha. Oganniyar kam tayi kicin-kicin da fuska sabida wani takaici taji na ganin Fadwa. A tunaninta kawai ya kwashe sirrinta ya faɗama Fadwar ne....
Murmushi yayi da ɗan leƙa fuskar tata. “Har yanzu fushin ne autar mata?”.
Cin dauriya da son cusama Fadwa baƙin ciki ta saki ɗan murmushi. Cikin disashiyar muryarta da tura baki tace, “Ni nace ina fushi ne dama?”.
“Uhm-uhm fa, bayan ɗazun har ana jeramin ALLAH ya isa da juyamin baya”.
Da sauri ta saci kallon Aunty mimi, sai taga sallama ta sake kabbarawa da alama shafa'i da wutiri zatai, ganin idon Fadwa a kansu sai ta sakeyi murmushi da ɗan kallonsa. Sai dai batace komai ba ta janye dan kallonta yake cikin wani yanayi daya saka tsigar jikinta tashi lokaci guda. Shima murmushi yayi idonsa akanta ko ƙyaftawa bayayi kamar ma ya manta Fadwa na tare da su fa a wajen, ga Aysha kuma da aunty Mimi.
“Kar dai a sani yarda babu komi aje can ana kuka a bayan idona. Dan naga ke kam baki raina abin kuka”.
Cikin ɗan tura baki tace, “Kuka ai rahama ne”.
“ALLAH?”.
Ya faɗa cikin sigar tambaya da ƙoƙarin ɗago fuskarta.
Murmushi tai da ture masa hannu tana kauda fuskarta gefe. Yay ƴar dariya kawai da jinjina kansa.
Fadwa daketa ƙoƙarin danne hawayen da suka ciko mata idanu ta ɗan dubi Anaam. “Ya jiki? ALLAH ya ƙara afuwa”.
Ciki-ciki ta amsa mata, batare data yarda ta kalleta ba. Dai-dai nan Aunty Mimi ta idar da salla, Shareff ya juya yana gaisheta. Amsawa tai da kulawa tare da duban Fadwa data ɗauke kai bata da alamar gaishetan ita. Murmushi kawai aunty Mimi tayi “Fadwa kuna lafiya ko?”.
Yitai kamar bataji ba, Shareff ya kalleta cikin ɓacin rai a ɗan kausashe yace, “Kina cikin hankalinki kuwa? Itace zatama gaisheki?”.
“Nagafa tana salla ne shiyyasa”. Sai ta juya tana gaisheta. Tsaki yaja mai ƙarfi, yayinda Murmushi ya suɓucema aunty mimi ta girgiza kanta kawai tana amsawa.
Aysha kanta sai bataji daɗin yanda Fadwa ɗin tayiba. A ganinta koba komai yaci Fadwa ɗin ta danne ta amsawa Aunty Mimi cikin daɗin rai tunda har ta karya ƴancinta ta fara gaisheta, tunda ita ta kasa banbance dai-dai ta gaisheta matsayin babba gareta kuma ƙanwar mahaifiyarta. Sai dai batace komai ba saboda Yayansu. Shiru ɗakin yayi zuciyar Shareff a ɓace. Amma sai ya danne a bisa uzirin suna asibiti, sai dai yaci alwashin taka mata birki dan bazai ɗauka wannan banzan halin ba.
Fadwan ce ta katse shirun ta hanyar tura musu basket ɗin da ta shigo da shi. “Ga abinci nan ALLAH yasa zaki iya ci, bansan a asibiti kike ba sai yanzu da Soulmate ya faɗa da an miki wanda zai fi dacewa da mara lafiyan ai”.
Banza Anaam tai mata, sai bayan wasu sakanni tace “Ayya” a taƙaice taja bakinta tai shiru.
Matuƙa ran Shareff a ɓace yake dan har fuskarsa ta nuna hakan, amma tsarinsa na ƙin yankema mutum hukunci cikin fushi ya sakashi yin shiru. Aysha ma kai kawai ta girgiza. dan ta fahimci inhar a haka Fadwa tace zata rayu a zaman aure lallai zata wahala. Domin fidda kishin mace ƙuru-ƙuru a ƙasar hausa tamkar gogama kanta baƙin fenti ne ga mijin dama kowa, domin al'ummarmu kanyi hukunci da zahiri ne a kowanne al'amari musamman akan kishin gidan malam bahaushe. Aunty mimi kam murmushi kawai tai ta maida hankalinta ga Aysha.
Anaam dai kwanciyarta tai ta juya musu baya ma, a ranta tana ayyana saita koyama fadwa hankali wlhy, dan abinda taima aunty mimi ya matuƙar sosa mata zuciya. Aunty mimi suna hira ita da Aysha shi yana faman latsa waya fuskarsa a murtuke. Sai ya kasance ita kaɗaice shiru, sai kuma hakan ya sosa mata zuciya har ƙwalla na cika mata ido, kiran wayarta da akai ne ya kawo mata sassauci ta miƙe tabar ɗakin. Anaam ta rakata da harara, amma sai gilashin idonta ya sirrantasu, juya kwanciyarta tai itama zuciyarta na tauna da raɗaɗin abubuwa kala-kala, sai dai taji sassauci a ranta a yanayin da Shareff ɗin ya nuna ɓacin ransa ga Fadwa kan abinda taima aunty mimi, tasan kuma bawai ya barta hakanan ba zasuyi mai dalili idan sun bar asibitin.
Shigowar Dr Jamal ce ta saka fuskar Shareff sassautawa. Ya gaishe da Aunty Mimi da juyawa kan Anaam da tambayarta ya jiki sannan suka gaisa da Fadwa da shigowarta kenan. Aysha ma gaidashi tayi. Jan hanunsa yay suka fita, kusan mintuna goma sha biyar sannan suka dawo. Batare daya zaunaba yacema Fadwa ta tashi su tafi dare nayi.
Fakar idon aunty Mimi yayi ya ranƙwafa kan Anaam ya sakar mata kiss. Zai ƙara na biyu dakai hanunsa saman ƙirjinta tai saurin buge hanun tana waro idanu waje harda ƴar zaburarta. Tsaye ya miƙe yana dariya, sai ko suka haɗa ido da aunty Mimi. Juyawa yay da sauri ya fice yana cigaba da dariyarsa.....
*_WASHE GARI_*.
Sai wajen takwas yabar gidan zuwa asibiti batare da yabi takan Fadwa ba, tun da suka baro asibiti jiya suke tafka rigima da ita, dan kuwa ya mata tatas akan abinda taima aunty mimi, ya kuma tabbatar mata inhar ta ƙara sai ya mata abinda bata taɓa zato ko tsammani ba daga garesa.
Gargaɗinsa ya sakata kwana kuka, ta kira gwaggo halima kuma ta hanyar wayar mmn Abu data kira wayar cikin masu aikinsu aka haɗata da maman, zayyane mata komai tayi, suka haɗu sukaita zagin su aunty Mimi wai asiri ne ke cin Shareff ɗin. Amma zata ɗauka mataki ta saurareta.
Ya iske Anaam ɗin na toilet tare da Dr Bilkisu tanayi sit bath. Yana iya jin rakin da take zubawa daga nan, ya girgiza kansa kawai da kaiwa zaune a bakin gadon yana murmushi. A haka Aysha ta shigo hanunta ɗauke da flask ɗin tea. Gaisheshi tayi, ya amsa yana kallon flask ɗin.
“Daga ina?”.
“Yaya gidan Dr Bilkisu mukaje amso ruwan zafi anan cikin asibitin”.
Bai sake cewabkomai ba akan hakan. Itama saita ajiye flask ɗin.
“Kunyi barci dai babu wata matsala ko?”.
“Eh Yaya. Ai da yake a magungunan nata kamar akwai masu saka barci harma makara tayi sallar asuba.”
Bai samu damar bata amsa ba suka fito Anaam na tafiya da ƙyar. Suna haɗa ido ta dalla masa harara dan duk wannan dai bala'in shine yaja mata ai. Shi dai kallonta kawai yake murshi na neman suɓuce masa, tana tafiya kamar wata ƴar kaciya. Doctor ce ta katsesa daga kallon nata. Ya ɗauke kai suka gaisa. Baƴani ta ƙara masa na cewar zatama sallamesu amma sai zuwa anjima kaɗan dai haka akwai abinda zata ɗan jira a kawo mata da zata bama Anaam ɗin.
A taƙaice ya mata godiya yana maida hankalinsa ga Anaam daketa faman sauke ajiyar zuciya daga kwancen da take ta juya masa baya. Tai musu sallama ta fice tana faɗama Aysha taba Anaam ɗin abinci amma ta fara da tea mai zafi. Kamar jiya dai koda Aysha ta haɗa abincin shine ya karɓa. Cikin bada umarni yace ta tashi zaune. Taso sharesa, sai dai a yanda yay maganar ya tilastata tashi dole bakinta a sama. Yi yay kamar bai ganta ba. Ya miƙa mata shayin ta amsa kamar zata fasa ihu. Sai da ta gama shanye tea ɗin tas sannan ya miƙa mata abincin, amma sai tace ta ƙoshi. Bai saurareta ba ya fara ɗiba yakai bakinta, ta kalesa kamar zatai kuka.
“Nifa Yaya nace na kos...”.
Ta kasa ƙarasawa saboda kallon daya wulla mata cikin tsakkiyar ido. Idanunta ta lumshe tsigar jikinta na tashi, dole ta buɗe bakin ya zuba mata. A dai-dai nan Dr Jamal ya shigo. Da alama ma shigowarsa asibintin kenan. Sun gaisa ya tambayi mai jiki, bai jimaba ya fita yanama Shareff dariya da shaƙiyanci da ido. Bai dai kulasaba shi dai.
Karfe kusan sha ɗaya aka basu sallama. Zuwa lokacin yaje office ɗin Dr Jamal ya dawo. Aysha ta tattare kayansu shi kuma ya kama Anaam ɗin da taso botsare, sai dai ya hana hakan ta hanyar tabbatar mata zai ɗauketa. Dole ta nutsu tana tura masa baki. Yay murmushi kawai da sumbatar wuyanta. Mintsininsa tai ya dafe wajen yana ɓata fuska shima. Sai ta saki dariya da masa gwalo.........✍
*😝😜Za'a koma filin wasa🚴🏼*
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/15, 11:19 AM] Marsy😘: BABU SO
Table of Contents