Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Laila Majnun Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

fat, alamar babu jini. Ya sake keta wani wajen, nan ma babu jinin saboda bai ci abinci ba ballantana a samu abin da ake buk'ata. Da ya ga haka sai ya soka wukar a hamatarsa inda babbar jijiyar jini take, nan jinin ya rika kwarara. Ya tara ya mik'awa kuyangar wadda tuni tsoro da mamaki sun hana ta motsi. Yayin da ta koma gida ta shaida wa Laila irin abin mamakin da ta gani wajen Majnun, sai Laila ta yi ta kuka tana tausaya masa. A cikin gari kuwa, labarin Majnun ya cika gari, sai aka samu wasu shakiyan matasa suka dauko kulake suka nufi inda yake. Tun daga nesa da Jakada ya hango su sai ya hau taguwarsa ya sulale ya bar Majnun yana wake - wakensa yadda ya saba. Matasan na zuwa suka hau bugunsa suna shuri da naushi da yakushi. Suka daure shi da igiya sannan suka tsaya daga nesa suna jifarsa. Da Laila ta ji labari sai ta sheko da gudu ta zo ta kare shi daga bugun mutane, ta rika zaginsu tana korarsu. Shi kuwa duk da yana daure ga bugu da ya sha amma sai ya ji ransa ya yi fari fat da ganin abar begensa ya rika ambaton sunanta yana cewa: Laila, Laila, Laila tawa ce, Domin akanki ne na haukace, Wasu na kallona wai na karkace, To amma fa yau na samu dace, Da ganin haskenki ya masoyiya Iyayen Laila suka turo aka tafi da ita gida tana kuka. Da suka ga lamarin ya wuce saninsu sai suka yi shirin yin balaguro na wani lokacin. Domin a tsammaninsu idan suka tafo suka jima Majnun zai gaji da nemanta har ya saduda ya hakura. Suka shirya kaya suka tafi wani gari da basu ambata ba, gudun kada ya ji ya bi su can. To amma kafin su tashi Laila ta rubuta takarda a boye ta ba wa kuyangarta ta kaiwa Majnun. Ya bude ya karanta cewar Masoyina, bulaguro za mu yi wani gari mai nisa, haduwar mu zata yi wuya anan. Idan zaka iya mu hadu a zangon farko cikin sahara. Yana gama karantawa ya ce da kuyangar, "ki gaishe ta da kyau da kyau, kuma ki fada mata cewar ina nan tafe." Lokacin da su Laila suka sauka a zangon farko ta tafi ita da kuyangarta zuwa inda ta ce masa ya je zata same shi. A tsammaninta bai isa ya zo wurin ba a wannan lokacin, domin su a abin hawa suke, shi kuwa a kasa yake. Tana zuwa ta same shi ya hada kai da gwiwa yana ta kiran sunanta, "Laila! Ya Laila!! Ya Laila!!!" Ta karaso wurinsa tana mai cewa, "Ya Majnunun Soyayya ga Lailarka ta iso!!l duwatsun kusa da na nesa suka dauki muryarta tana amo. Nan da nan ya zabura zuwa gare ta, yana mai cewa, "shin da gaske ne Laila ke ce anan?" Ta amsa "ni ce!" Ya mika mata hannu ta rike sai suka ji kururuwar mahaifanta suna nemanta domin a cigaba da tafiya. Ta juya da hanzari, ya ce, "Haba Laila kada ki tafi ki bar ni da begenki!" Ta ce, "kar ka damu, idan na dawo za mu hadu anan." "Yaushe za ki dawo?" Ya tambaye ta. Ta ce, "ban san lokacin ba, amma da zarar mun taho zan aika maka." Da haka ta tafi ta bar shi anan. Majnun ya ce a ransa, "idan ta dawo wa zata aika ya fada min? A ina dan sakon zai same ni? Kawai bari na zauna anan din har sai ta dawo." Ya share wuri ya zauna ba shi da wani abinci sai ganyen bishiyar da ke wajen yana shan ruwa dake bubbugowa karkashin dutse. A kullum zancensa shine kiran sunan Laila da addu'ar ta dawo ta same shi. A haka har tsiron bishiya ya fito daga 'ya'yan itacen da yake jefarwa, ganyenta ya nannade masa jiki ya zama tamkar bishiyar a jikinsa ta tsiro. A can garin da su iyayen Laila suka je da ita kuwa, sai wani attajiri ya fito yana sonta da aure. Nan take ya bawa iyayen rakumma dari gami da wasu kyautuka masu yawa. Da Laila ta ga alamar laila za a aurar da ita gare shi sai ciwo ya kama ta. Ta yi ta fama, iyayen suka yi nufin komawa gida domin magani alabarshi idan ta warware sai a yi auren. A hanyar su ta dawowa suka sauka a wannan zangon. Duk da tana fama da jinya Laila ta taso zuwa wurin da suka yi alkawari da Majnun. Ta kusa isa kenan ta gamu da wani mutum ya ce mata, "yarinya kada ki je wurin nan da kika nufa. Akwai wata fatalwa mai kamar bishiya da ta bayyana. Kullum tana kiran sunan Laila, Laila." Da ta ji haka sai ta tabbatar Majnun ne bai tafi ba. Ta karasa wurin da gudu. Yana ganinta yayi zumbur ya mike tsaye yana mai farin ciki, yana cewa "Laila kin cika alkawari? Laila ke ce kuwa? Laila za ki aure ni??" Kasancewar ya jima sosai a zaune baya mikewa sai jiri ya debe shi, a lokaci guda kuma zuciyarsa ta buga saboda tsanannin farin ciki. Kansa ya gwaru da dutse ya fadi matacce. Laila na ganin irin wannan sadaukantarwa ta kasa hakurcewa, zuciyarta ta raurawa, kirjinta ya yi matukar kunci. Nan take numfashinta ya dauke ta fadi a wajen matacciya. Bayan wasu lokuta aka iske gawarwakinsu sai aka binne su kusa da kusa. YAU MUNZO KARSHEN WANNAN LABARIN SOYAYYAH" DAYARDAN UBANGIJI. wanda ni yusuf Abdullahi A jibaga nakawo muku" sai xuwa wani lokaci kuma idan nakawo muku wata hikayar. whatsappp 08071051138 This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online

Table of Contents

Chapters

5 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5