Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Laila Majnun Book One Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

yayin da suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . Ya k’ara da cewa, “Ko Luqman, babban malami masani na tabbata ba shi da maganin ciwon so…Idan ma yana da shi ina fata babu wanda ke tsakanina da Laila. Ya waka wadannan baitoci: A Makka na ce da shehin malami, Wai shin wace ke cutar da ni? Shin laifi ta ke yi to a sanar da ni, Shehi ya ce “d’ana bi a hankali, Azaba na nan zuwa can gare ta Na yi farat na ce masa “a’a na yafe, Da azaba ta samu Laila ko a gefe, Ba ni kauna gara ta same ni a lafe, Da na daina sonta a barci ko fake, Gara na mutu da ciwon kaunar ta Sannan ya ce da murya mai raurawa, “Allah ka ba ni Laila!” GO BE ZÀMU DAURAHIKAYAR LAILA MAJNUN...2 Yayin da iyayen Majnun suka ga haka kullum lamarin nasa k’ara lalacewa ya ke yi, sai suka ga babu mafita face su je su nemi auren Laila wurin iyayenta. Wannan shine mataki na k’arshe da suke ganin zai magance matsalar d’ansu. Suka tashi jakadu na musamman zuwa garin su Laila suka bayyana musu irin halin da d’ansu yake ciki game da soyayyar Laila. Sannan jakadun suka nemi aurenta dominsa. Iyayen Laila suka amsa da cewa, “mu a wajenmu abin da Majnun yake yi domin ‘yar mu wulak’anci ne mai girma. Kuma duk da yake mun san cewa Laila tana da ra’ayinsa amma ba zamu iya aurar da ita gare shi ba. A dalilinsa mun cire ta daga makaranta, mu a wajenmu, mahaukaci ne kad’ai zai rik’a irin abinda Majnun ke yi.” Da haka iyayen Majnun suka ji dad'i tunda su a tsammaninsu idan har ya daina shiririta za su amince su aura masa ita. Saboda haka suka shiga tausasarsa suna ba shi shawarar ya nutsu ya daina abubuwan da yake. Majnun ya amince da haka, amma da sharadin za a kaishi ya ga abar k'aunarsa Laila. Suka shirya suka tafi tare da wakilansa zuwa garin su Laila. Aka sauke su a wani babban gida sannan aka kawo musu abinci da abinsha. An kawata wajen da fitilu masu launi iri dabam - dabam. Sannan a kunna turaren wuta ko'ina sai kamshi ke tashi. An jera kasake masu yawa cike da abinci da fulawoyi masu k'ayatarwa. Zuciyar Majnun kuwa ta kasa nutsuwa, ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya tafi ga masoyiyarsa. Bai iya jurewa ba sai ya mik'e a gaban waliyan Laila ya rika safa da marwa yana rera wadannan baitoci: Na yi nisan zango don na gane ki, Ga shi na zo nan ina ta bid'ar ki, Ina kike ina kika shiga ne in ganki, Zuciyata tana ta jidali domin nemanki Ya ki taho abar begena don Allah nunan kanki Jimawa kad'an sai ga karen da Laila ke zuwa da shi makaranta ya shigo gidan. Majnun sai ya ji ya kasa jurewa, ya zabura wajen karen nan ya rungume shi yana sumbatarsa yana cewa, "Na ga rabin Laila saura rabin. Ya karen nan mai baiwa maza je ka ingizo min Laila." Garin wutsulniyar da kare yake yi da k'afafu ya ture farantan abincin, suka bata gaban rigar wani dattijo mai fada aji a dangin Laila. Shi kuwa gogan naka sai ya d'auki wani tsiron fulawa ya mak'alawa karen a wuya yana ce masa, "maza je ka kaiwa Laila ka mik'a min gaisuwata gare ta." Duk jama'ar wurin suka yi tsit suna kallon ikon Allah. Wakilan da suka rako shi suka rasa inda zasu sa kansu domin kunya. Wakilan Laila kuwa suka cika da fushi iyakar fushi. Wani daga cikinsu ya fusata ya ce wa Majnun, "Shin bautar kare ka zo ko kuwa maganar aure?" Kai tsaye Majnun ya kalli mutumin ya ce, "wannan karen a wurina ya fi mutum dubu daraja, domin a jikinsa ina ganin surar masoyiyata wadda k'aunarta ke d'amfare a zuciyata dare da rana." Duk wuri aka d'auki salati. Jama'a suka rik'a zundensa suna cewa ya haukace. Dattijon nan da aka b'atawa riga da abinci ya mik'e a fusace ya fice daga gidan. Duk jama'a ma suka watse. Da wannan jama'a suka rika rantsewa cewa haukan nan dai bai rabu da shi ba, sai ma abin da ya yi gaba. Daga nan iyayen Laila suka fito kai tsaye suka ce ba zasu aurar da 'yar su ga Majnun ba. To daga nan sai duk wani fatan samun nutsuwarsa ya zama sharon gayya, suka hakikance ba za su iya magance masa matsalar ba, don haka suka sa masa albarka suka kyale shi bisa halinsa. Shi kuwa duk inda ya shiga lungu da sak'o sai ya rik'a cigiyar Laila ko sun san inda take da yadda zai sadu da ita. A haka har ya yi kicibis da wani jakada mai aikin raba takardu. Ya tambaye shi labarin Laila. Jakada ya ce masa Laila da iyayenta sun tashi daga garinsu sun koma wani gari mai nisa, daga nan garin zuwa can tafiyar mil dari da ashirin ne. Majnun ya shiga yi masa magiyar yana ba shi sako zuwa gare. Jakada ya amince zai karb'I sak'on takarda kurum babu wani abu. Majnun ya zauna yayi ta rubutun shafuka da yawa, har jakada ya gaji ya ce masa, "wacce irin wasika ce haka?" Majnun ya ce, "wasikar soyayya ce bata da k'arshe." Jakada ya yi dariya da haka sannan ya ce, "to samu waje ka d'iga aya ka bani na tafi." Majnun ya nad'e takardar ya ba shi. Sannan ya nemi ya yi masa rakiya kad'an. Suna tafe Majnun na ba wa jakada labarin abar k'aunarsa Laila shi kuma yana ta mamaki. Sai da suka shafe mil goma Majnun na tafiya a k'asa Jakada na bisa rak'umi. Jakada ya ce masa, "to ka koma haka, ka yi nisa kwarai da gidanku." Majnun ya juyo ya soma tafiya sannan ya juya ya ce da Jakada da babbar murya, "ya kai k'aunataccen abokina! Wallahi na yi mantuwar wani muhimmin sak'o da nake so na rubuta mata!" Jakada ya ce, "to gaskiya ba zan tsaya ba, sai dai ka fad'a min da baki na fad'a mata. Majnun ya kowa ya same shi suka rankaya. Suna tafe yana fad'a masa sak'on har suka share wasu mil goman. Jakada ya ce, "ka koma haka kada a neme ka a gidanku." Ya juyo ya soma tafiya sannan ya waigo ya ce, "wallahi ba domin kada ka ce na matsa maka ba da na k'ara maka wani sak'on. Muhimmi ne kwarai na mance da shi. Jakada ya ce, "to matso ka fad'a min!" Suka sake rankayawa yana ta fad'a masa sak'o. Haka suka yi ta yi har kafin su ankara sai ga shi sun isa garin da Laila take. Jakada yayi mamakin irin wannan soyayya, sannan ya ce da Majnun, "Babu buk'atar kai wa Laila sak'o gare ni domin kuwa ga shi mun zo garin da take." Da jin haka Majnun ya cika da farin ciki da murna. Ya fad'i sumamme don tsananin farin ciki. ZAMUCI GABA INSHA ALLAHU GOBE" Whatsapp only 08071051138^ LAILA

Table of Contents

Chapters

5 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5