Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Laila Majnun Book One Complete Hausa Novel 1,219 words 0 views Progress saved
Download Book

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng HIKAHIKAYAR LAILA DA MAJNUN maimaici ne√ Hikayar Laila da Majnun an ba da ita kimanin shekaru dubu da suka wuce, kuma an bayar da ita ta fuskoki da dama, to amma dukkan fuskokin sun hadu akan ginshiki daya, watau tsarkakkiyar soyayya ce tsakaninsu. Ga irin hikayar da muka rairayo: Wani saurayi mai suna Qays ibn Mulawwah dan kabilar Banu Amar. Qays ya kasance mai fasahaf da basira a makarantarsu, sai dai ya kamu da soyayyar Laila bint Mahdi Ibn Sa’ad an fi kiran ta da Laila Amiriya, a hankali ya rika nuna mata soyayya ta hanyar kulawa da sauran alamu. Duk lokacin da ta makara zuwa makaranta sai hankalinsa ya tashi ya rasa sukuni, gaba daya sai ya zuba wa kofa ido ba ya mayar da hankali ga karatunsa. Wata rana da zuciyarsa ta cika da bege, ya ji kirjinsa kamar ya fashe, bai san lokacin da ya rika rubuta sunan Laila a takardar rubutunsa ba maimakon abin da ake koya musu. Dalibai da suka ga haka sai suka hakikance lallai ya yi nisa wajen kaunar ta. Da haka ita ma Laila ta soma kaunarsa ya zamana duk makarantar an san su a matsayin masoya. Shi Qays kamar tun yana yaro k’arami masu ilmin taurari suka bayyanawa mahaifinsa cewa zai kasance wanda rayuwarsa za ta fada cikin wahala da musiba. Suka kara da cewa idan ba a yi da gaske ba ma zai iya haukacewa. Tun daga wannan lokacin mahaifinsa ke samo masa lak’ani da magunguna da addu’oi. Yayin da ya data sai mahaifinsa ya dauke shi ya kai shi Dimashka karatu inda anan ne ya hadu da Laila. Ita Laila ta kasance ‘yar shugaban kabilar Sharwaris, wadda a da zamanin Jahiliyya ba sa ga maciji da kabilar su Qays. Laila da Qays suka zama tamkar jini daya tsoka daya idan bai ga daya sai ya kama rashin lafiya, amma Qays abin na sa ya fi tsanani, domin kuwa har wakoki yake rubutawa masoyiyarsa yana karanta su a ko’ina. Daya daga wakokin da yayi mata ita ce: Na so ki ya mai kyau dan gaske Wane wata ko tauraro mai haske Kin shiga ruhina kin mammallake In babu ke to ni kuwa na hakkake Ba za ni rayu a duniyar nan ba A makaranta aka rinka gulmar su ana nuna Majnun duk inda ya wuce, sai ya kasance idan ka yi masa abu ka ce masa ya yi hakuri don Laila, shikenan zancen ya wuce. Da dalibai suka gano lagonsa, suka rika dauke masa kayan rubutu suna cewa ya basu domin darajar Laila. Ba musu sai ya ba su. Maubin (malamin) makarantar ya damu kwarai da irin wannan al’amari. Musamman da ya ga Qaysa wanda yanzu sunan ya bace ya koma Majnun Laila (Mahaukacin Laila) ya rubutawa iyayensu takarda yana fadakar da su halin da ‘ya’yansu ke ciki. Iyayen Laila suka cire ta daga makarantar aka kirawo wani kwararren malami yana koya mata karatu a gida. Ciwon so ba shi da magani! Maimakon hakan hakan ya yi magani sai ya dada rikita al’amari. Majnun ya daina karanta komai kullum sai kuka sai waka, duk abin da ya gani sai ya ga yana masa gizo da kamannin Laila. Nan da nan sai ya soma rera wakar so gare ta. Mahaifin Majnun ya zo takanas ya dauke shi zuwa wajen likitoci da ‘yan tsibbu da bokaye da sauran masu da’awar magani duk abin ya zama tamkar wutar kara ana yayyafa mata fetur. Abokai da ‘yan uwa na kusa da na nesa suka zo domin tausasa zuciyar Majnun ya daina tunanin Laila amma duk a banza. Wani daga baffaninsa ya ce masa, “wai kai Qays me ka gani a jikin Laila da ka nace mata haka? Ka zo mu je na nuna maka mata dubu wadanda suka fit a kyau da kyan fasali da asali da mulki da dukiya da sarauta ka zabi wadda ta yi maka.” Majnun ya dube shi ya girgiza kai ya ce, “idanun Majnun Qays ba wanda suke so da gani tamkar Laila.” Ya daga hannu sama ya ce, “Ya Allah! Na san ba ka yi kyakkyawa a duniyar tamkar Laila ba. Na tabbata ita tana daga asalin Hurul Aini da suka zo duniya shan iska. Ya Allah alk’awarinka bay a tashi, na tabbata daga kan Laila ba zaka sake wata kyakkyawa ba. Ya Allah ka ba ni Laila!” Wani daga kabilarsu ya ba shi shawarar ya dauki Majnun zuwa Makka ya yi roko a ka’aba kan Allah ya dauke masa son Laila a zuciyarsa. Amma saboda tsananin soyayya a

Table of Contents

Chapters

5 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5