Chapter 3
EPISODE 33
Kwance take tana sharar bacci cikin kwanciyar hankali, cikin bacci ta yi kwakkwaran juyi zata gyara kwanciyarta kwatsam tayi arba da fuskar mutun wani irin firgita tayi a haukace ta zabura zata mike da sauri Benazir ta cafko hannun ta ta ruƙe shi gam, suka ƙurawa juna ido batare da ƙyaftawa ba, Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yayi ba, ta rasa gane meyasa cikin ƴan kwanakin nan matarke tsareta da ido kamar zata lashe ta, aranta ta ayyana kodai ta6in hankalin nata ne Ya motsa? Kada fa ta hau ta da bugu tun ba hankaline da ita ba..tuni tasha jinin jikin ta, tana faman haɗiyar yawu kutt murya na rawa ta furta"am..um.. mamana! Tun yaushe kika farka"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda Benazir tayi mata rumfa kamar zata danne ta, babu alamun zata tanka mata tayi shiru tanata kallon ta...babban tashin hankalin unaisah hajiya layla bacci takeyi balle ta kawo mata ɗauki, tuni ido ya raina fata.
"Dan Allah na roƙe ki, ki daina kallona haka, babaynki ce fa, ki na bani tsoro. .." sai da tay wannan maganar, Benazir ta saki murmushin gefen fuska har dimple
dinta ya lotsa...
"Babyna ne"? La66an unaisah na kerma tace"ni ce, dan Allah kada kiyi min komai..." ƴar dariya benazir tayi, wani irin nishadi take ji..
Shafa sumar kanta tayi har wani kyafkyafta idanu take Yi kamar wata mara gaskiya
Unexpected ta ji ta manna mata sumbata kan kuncinta, kafin tayi wani yunkuri ta kara mata wani kan la66anta, runtse idanu tayi kamar zata fasa ihu ta furta"na shiga uku, tawa ta same ni"! dariya benazir tayi kafin ta janye jikinta daga na unaisah ta koma kan gadonta ta kwanta idanunta na fuskantar ceilling..." wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarta da sauri ta cusa kanta jikin pillow,
Satar kallon ta unaisah tayi, ta rasa gane meke damun matar, ta fara tsorata da lamarinta, kwanakin nan ta canza mata, ba kamar farkon da tafara jinyarta ba, ko meyasa❓
Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta sauko daga kan gadon, ta lalla6a cikin sanɗa take tafiya, backpack dinta ta buɗe ta curo wayarta ta nufi toilet ta shige ciki,
Text message ta tura ma daddynta
"Daddy, barka da dare, daddy ni dai nagaji da zaman asibiti, gida nakeso in dawo" tana tura mashi text din jim kaɗan saiga kiran shi, tayi mamaki saboda batasa rai zai bata amsa ba kusan karfe shabiyu na dare, tayi zaton yayi bacci.
Picking call din tayi tare da kara wayar a kunne"My daughter! Me kike yi har yanzu baki kwanta bacci ba? Wani abu ya faru ne"?
Cikin muryar raɗa ta furta"ba abun da ya faru, kawai bana jin dadin yawan kallona da matar takeyi, duk in na farka tsakar dare saina ganta akaina ta tsare ni da idanunta"
Sautin dariyar shi ce ta ratsa kunnanta aiko ta haɗe fuska kamar tana agabanshi tace
"Daddy dariya kake yi min?
"Sorry daughter, maganarki ce ta bani dariya, but ki ƙara hakuri Anila ta fada min next tomorror za'a sallame ta"
Shagwa6e fuska tayi, ko tsoro bata ji ita kadai a toilet
"daddy ina yan uwana? Yau banji muryoyin su ba"
"Suna nan cikin koshin lafiya, basu da wata damuwa"
Shiru sukayi na wani lokaci, zuciyar ta sai azalzalarta takeyi akan ta tambaye shi ina Danish amma ina takasa furtawa...
Kamar taj ya karanci abunda ke zuciyarta sai taji yace"Daughter, labari me dadi, dan uwanki Danish ya fara koyon rubutu da karatu a wurin chief, abun saiya baki mamaki yana da kaifin basira, kamar ke lokacin da kina ƙarama, kwakwalwarsa tana ja, abun burgewa sun shaku sosai da chief in kika gansu kamar ƴan uwan juna, tare sukeyin komai......." batasan ya akai ta tsinci kanta da sakin murmushin gefen fuska ba, har cikin ranta taji dadin jin labarin nan da daddynta ya bata..
"Daddy, na taya shi murna, kuma naji dadi wlh, Allah ne kadai zai iya biyan chief, yayi mana hallacci arayuwar mu, ina jin dadin kyautatawarshi agare mu, Allah yasaka mashi da mafificin Alkhairinsa....." addu'o'i ta cigaba da yi mashi daddynta yana amsa mata da ameen
Kafin daga bisani yace"daughter, ki koma bacci, bana so ki makara sallar asuba, kiyi addu'a kafin ki kwanta sannan ki kula min da kanki"
"Toh daddy, kaima ka kwanta kayi bacci, ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama da juna, kasa motsawa tayi daga cikin toilet din, wani irin yanayi take jin kanta mara misaltuwa, tanaji aranta kamar tayi missing din wani abu da zuciyarta take muradin son gani, ta wani bangaren taji dadin labarin cigaban da danish ya samu sosai har wani dan murmushi ta saki
Lumshe idanu tayi tare da jingina bayanta jikin wall na tsawon mintuna kafin ta juya ta buɗe kofar, cikin sanda take tafiya tana satar kallon gadon benazir, ta lullu6e jikinta da bargo da alama ta koma bacci, hakan ba karamin dadi yayi ma unaisah ba..
Kan gado ta haye ta kwanta tare da jan duvet tayi covering jikin ta wani baccin ne ya kuma daukarta...
_________________________________✍️
*Hajjaty*
Tun da sanyin safiya bugun kofa Ya farkar da ita, tana tsaka da jin dadin baccin ta, da wata irin kasala ta miƙe ta sauko daga kan gadon tayi miƙa haɗi da yin hamma, Ƴar rigar bacci ce a jikin ta, sai da ta fara daukar hula ta lullu6e kanta kafin ta nufi kofar tana tambayar wanene"?
Daga waje tajiyo muryar sofia cikin tashin hankali tace"Aunty ni ce sofia, ki buɗe min kofa" da sauri hajjaty ta buɗe kofar ta leƙa kai tana kallon sofia wadda gaba ɗaya babu kwanciyar hankali atare da ita ..tunkafin taji me zata faɗa mata gabanta ya fara faɗuwa.
"Sofia! Meke faruwa ne? naganki kamar ba lafiya"? Yarfa hannu safiya tayi murya na rawa tace"marwa! Aunty mun shiga uku, kizo kiga abunda ke faru ! Marwa ta kuturce. .." aruɗe hajjaty ta ce"bangane me kike nufi ba? Meya faru da ita? Wata irin kuturta . "? Bata jira hajjaty ta kare maganar ba, taja hannunta da sauri suka nufi dakin marwa dake anan corridor din da ɗakunan house maids din gidan su ke..
Shigarsu ke da wuya hajjaty tayi arba da ƴan aikin gidan gaba dayansu, sun hallara, fuskar kowan nansu sharkaf da hawaye cikin tashin hankali suke sallallami idanunsu akan marwa.
Suna ganin hajjaty suka buɗe mata hanya don taga abun tashin hankalin da suke kallo,
Lokacin da ta sauke idonta kan marwa dake nannaɗe kan katifarta rass taji gabanta yayi mata wani irin mahaukacin bugu na tashin hankali, ta waro idanu waje, agigice ta daura hannayenta biyu saman kanta, ta zabga salati tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'u!!
la66anta na kerma ta furta"Mar..marwa! Meya faru dake? Ya akai kika koma haka? ta faɗa tana kallon yatsun marwa da suka dunkule irin na kutare ga wani ruwa mai yauƙi dake gangarowa ta tsakaninsu,, la66anta sun shafe babu hudar baki kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba, wani irin nishi take saki, idanunta sun kaɗa jawur ga zufa data wanke jikin ta baiwar Allah ita kadai tasan azabar da take ji, sai faman zare na mujiya takeyi jikin ta nata kerma.
Fashewa hajjaty tayi da kuka, gaba daya sautin koke koken su Ya cika dakin
"Wayyo Allah! Na shkga uku! Dan Allah ku fadamun meya faru da ita? kaina ya kulle nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Jiya jiyan nan mukayi aikin dinner tare da ita lafiya lou muka rabu da ita...taya akai ta samu wannan lalurar ta kuturta? Ina bakinta yake"? Cikin shesshekar kuka tayi maganar
Abla tace"Aunty bamusan meya faru da ita ba, yau da safe mun tashi zamu fara aikin breakfast, mun ga bata fito daga daki ba, shine nace ma sofia taje tayi mata magana kada mu makara, bayan tafiyar sofia har mun fara aiki muka jiyo sautin ƙararta daga dakin marwa shine muka taho da gudu mu duka dan muga mike faruwa a nan muka tarar da marwa cikin wannan halin.. ." ta ƙare maganar tana kuka
Sofia tace"wlh bansan meya faru da ita ba, Nima haka na sameta, ina shigowa dakin na isketa a nannaɗe kan kafita, har ina zolayarta nace mata bana son iya shege kina ji inata ƙwala maki kira kinyi shiru baki ce min komai, wlh aunty dana zo gaban katifar naga hawaye idonta gashi babu hudar baki, yatsun hannunta sun kuturce bansan sa'adda na fasa ihu ba, ni ban ta6a ganin tashin hankali irin wannan ba, Allah daga gani Aljanune suka shafe ta . ..." gaba daya duk sunbi sun ruɗe, hankalin su Ya tashi, jikin hajjaty na 6ari tace"ba kallonta yakamata mu tsaya munayi ba, bari inje in sanar da mutanan gidan..." da sauri ta fuce daga dakin... .
Kafin wani lokaci gaba ɗaya mutanan gidan suka hallara a dakin marwa, da sauri maids din suka basu hanya don su shuga ciki, baba obie ne kan gaba jikin shi sai 6ari yakeyi, Pravin da twins suna abiye da shi, har sunyi shirin zuwa office wannan abun tashin hankalin Ya risƙe su, hada Hajiya saratu ta shigo ta zumbula buba ajikinta, sai faman raba idanu takeyi tun kafin ma taga meya faru da marwan!!
lokacin da sukayi arba da marwa gaba ɗaya hankulansu suka tashi, sunyi matuƙar razana da ganin yadda halittar marwa ta canza, kowa sai tambayar ba'asi yakeyi, Tafa hannu hajiya saratu tayi"La'haula walakuwata illa billahil azim! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni filmusibati.. Gaba ɗaya tabi ta rikice, "Ya akai Haka ta faru? Wata irin lalura ce wannan"? Ta faɗa tana zare na majuya
Masu aikin suka hada bakin wurin fadin wlh bamu sani ba, haka muka same ta,
Idan hankalin su twins yayi dubu toh ya tashi, wani irin ƙyanƙyami da ƙyamar marwa ne Ya kama su, babu wanda Ya lura suka sa6e daga dakin suka yi tafiyar su don bazasu juri ganin tashin hankalin nan ba.
Tsabar tashin hankali da kiɗima Ya hana baba Obie furta kalma, dama da ƴar cazbahar shi a hannu sai faman jan ta yakeyi yana ambaton sunan Allah
Pravin dake a ruƙe da kofa fuskar shi a hautsine Yana ta faman zazzare idanu kamar na kwarton muzuru har wani gumi Ya haɗa muryarsa na rawa yace"yarinyar nan ba ta rasa iskokai akanta, daga gani aikin aljanune, taya za'ace farat ɗaya mutun ya tashi ba baki? yatsu kuma sun kuturce"?
Jin wannan maganar Ta pravin Yasa hankalin hajiya saratu yayi mugun tashi, nan fa ido ya raina fata, dama a tsorace take da lamarin, baban tashin hankalinta kada itama abun ya shafeta, tunda kwana nan suna mutunci da marwa saboda aikin leƙen asirin da take yi mata, batare da kowa Ya lura ba, ta lalla6a ta fuce daga dakin marwa, jiki na kerma ta koma bedroom dinta, ta yi shirin zuwa office don ta bar gidan, saboda rashin tausayi maimakon ta tsaya su nema mata mafita tunda dai ita takeyiwa aiki
Baiwar Allah marwa ba halin Yin magana, kukan zuci take mai ɗacin gaske, ga abu tana so ta fada amma takasa sai kallon hajjaty da pravin takeyi hankalin ta yafi kakarta akansu
Dakyar baba obie Ya haɗiye tashin hankalin shi, Ya dubi maids din dake kuka cikin sanyin murya yace"kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, ba kuka yakamata kuyi mata ba, addu'arku take buƙata..." ya fada tare da kallon Hajjaty"ku taimaka ku dauko ta, muje asibiti aduba lafiyarta. " da sauri hajjaty da Abla suka haɗa karfi wurin cuccu6ar marwa suka fito daga dakin sauran masu aikin suka bi bayansu, tunkafin su fito baba obie yayi waya da ɗaya daga cikin jami'an gidan, Aka fiddo da mota mai kama da bus, aciki suka shigar da ita, kowan nan su Ya samu wurin zama, motarsu baba obie da pravin tana abiye da tasu a jere motocin suka fuce kaitsaye suka nufi asibiti💔 tunkafin sukai asibitin marwa take ta kallon hajjaty kamar zata hadiyeta ita kanta hajjatyn dake aruke da ita tayi matuƙar tsorata da kallon da marwa keyi mata ga wani nishi da gurnani da takeyi😢
(Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana❓❗)
__________________________________✍️
A zaune take kan dinning chair, ta sanya abaya dogo ajikinta, table din gabanta cike Yake da kayan breakfast ita kadai ta rage a dining, tana cikin shan tea a cup, ƙamshin turaren dr shureim Ya daki hancin ta, da sauri ta ɗago tare da kallon inda take jiyo sautin tafiyarshi, a tsanake Yake tafiya cikin kamala, Ya sanya shadda a jikin shi ta zauna mashi yayi wani fresh da shi hannun shi ruƙe da car key,
Tunda ta kafe shi da ido sam ta kasa daina kallon shi, saboda yayi mata kyau
Karasowa yayi gaban dining din, fuskarshi dauke da murmushi Ya furta"sanyin idaniya, ina fata kin tashi lafiya"? Farfari tayi mashi da ido hadi da sakar mashi murmushi kafin tace"hubbyna na tashi lafiya, ina fata kaima haka"
Yace Alhamdulillah,
"Yaya shurem, Ka zauna mu yi breakfast, ko ka riga da kaci ne? Yau ni kaɗai na rage a dining, ban iske kowa ba .."
"Bana jin yunwa, Inason zan fita ne" yanayin fuskarta ne Ya canza, kamar zata fashe mashi da kuka tace"dan Allah ya shureim kada ka tafi kabarni agida ni kadai, kaga mommy ta tafi office, daddy da uncle sun je party meeting, kullum sai ni kadai kuke bari agida bana aikin kome" ta faɗa da shagwaba...
Shiru yayi yana tunanin meya kamata yayi? Shi ma baison suna tafiya su barta agida ita kadai baisan ya zaiyi da ita bane tunda bata son zuwa asibiti wurin Benazir, gashi har benazir ta fara tambayar shi ina zeenatu, itama hajiya layla abun ya fara damunta duk in yaje sai tace wai meya hana zeenatu zuwa.
Wata dabarace ta fado mashi aranshi, da sauri ya dubeta ta kura mashi blue eyes dinta masu walwali
"Zaki rakani mu tafi atare inda zanje"?
"Ina zamuje"?
"Wani wuri ne..." shiru tayi jim kafin tace"ni dai saika fadamin ina ne"
"Yawon buɗe Ido" waro ido tayi kafin tace"dagaske"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, da sauri ta mike tana fadin"yaya shureim bari naje na canza kaya"
"Okey, ki same ni a mota, but karfa ki dade" amsa mashi tayi da toh, jikinta na rawa tsabar zumudi ta nufi part dinta
Murmushin gefen fuska shureim ya saki aranshi ya furta"yau zanga meke akanki my zeenati"! Ya faɗa tare da juyawa ya fuce daga falon
After some mins, Yana zaune a driver's seat, Ya dan jingina kanshi jikin headseat, har ya lumshe idanun shi Yaji motsin buɗe car door, A hankali Ya kalli zeenatu dake kokarin shigowa ciki, wani irin sanyayyan kamshin turarentane Ya ratsa hancin sa, kamar wadda zataje gasar miss world, wata hadaddiyar emirati abaya ce ta sanya launin yellow, abunka ga jinsin turai ta fito fara fess rigar tayi mata kyau, ga wani veil da tayo rolling, hannunta ruƙe da wayarta, kafarta kuwa wasu highhills ne masu tsini, harta zauna dr shurem bai daina kallon ta ba...
Farfari tayi mashi da ido voice dinta da shagwa6a tace"yaya shureim wannan kallon fa" kayataccen murmushi ya sakar mata, tare da kai hannu ya shafa sajen shi, key yai wa motar, ya ɗanyi reverse kafin Ya fara driving slowly Ya nufi katafaren gate din gidan, tunkafin Ya karaso waɗannan Samudawan security office din suka yunkuro kamar zasu rufe motarshi da bugu ba don komai ba sai don saboda Ya dauko zeenatu...
Ba arziki yayi parking motar, ya sauke glass din Yana kallon su
da kakkausar murya daya daga cikin su Yace"da iznin wa zaka fita da ita.. " saboda karfin hali na dr shureim Ya wani hade fuska Yace"daddyn ta ne Ya bani izni" arude zeenatu ta kalle shi wato taji ya shureim yayi karya agabanta
"Amma mu bai fada mana ba"!
"Ku kira shi awaya sai kuji" ya fada yana ƙara tamke fuskar shi
Kiran alhaji musa sukayi wayar tayi ta yin ringing ba'ayi picking ba, dr shureim Allah Allah Yake kada Alhaji musa ya ɗaga, kai hada addu'a yayi a zuciyar shi, cikin sa'a bai ɗaga ba..
Muryar zeenatu na kerma tace"ku kira mommy ku tambayeta, ay itama tasan da zancen fitarmu, daddyne ma yace ya tafi dani..." ba suyi ƙasa a gwiwa ba suka kira hajiya saratu bugu uku kafin suka samu ta ɗaga...
"Ranki ya dade, da izninki dr shueim zai fita da zeenatu"? Kallon juna zeenatu da dr shureim sukayi duk suka sha jinin jikin su, fargabansu kada hajiya sarah ta kwafsa masu
"To amma shi yalla6ai yasan da fitar su?
Hajiya sarah tace"eh ya sani, kawai ku barsu su tafi"..kusan atare dr shueim da zeenatu suka sauke ajiyar zuciya.. munafukan gate officers din ba don sunso ba suka basu hanya, dr shurem Ya ƙara wa motar gudu Ya fuce daga gidan....
Lumshe idanu zeenatu tayi tana dariya tace"ya shureim kasan Allah da ace daddy ya ɗaga kiran nan da sukayi mashi wallahi bazai bari ka fita dani ba, ni narasa gane dalilin dayasa yake kullena kamar wata matar aure..."
"Mommynki ta rufa mana asiri wlh, naji dadi my zeenatu, kinga yanzu zamu sakata mu wala..." yai maganar hankalinsa na akan driving din da yakeyi, A hankali ta daura hannunta saman dayan hannunshi gefe tare da lumshe idanunta, har satar kallon ta sai da yayi kamar wata jinjira komai nata burge shi yakeyi...
________________________________✍️
Gaba ɗayansu sun shirya tsaf, zasu ziyarci gidan uncle abdallah, tun daga kan mami, ummi, zahra, abi, da uncle ɗan iya, kowannansu ya ɗauki wanka na mutunci namu na hausawa, mutun biyu ke babu a cikin su, mahboob wanda tun safe ya tafi kai baby junaid school, har yanzu bai dawo ba..
A tare suka fito daga falon gidan, suka nufi harabar ajiye motocin su,
Mami tace"yau dai Allah Ya nufa zamu cika mata alkawari, baiwar Allah mun saka mata rai, kullum ayta za'aje za'aja amma shiru.." ummi tace"nasan zatayi farin ciki idan taganmu kwanmu da kwarkwatarmu don ma babu junaid, ay da sai tafi jin dadi munzo mata da ɗan jikallan ta..." .murmushi kowannansu Yasaki,
A bakin motocin suka dakata da yin tafiya, suna jiran Aneelerh da zahra su fito,
Abie Yace"wai zaman me sukeyi agidan? Kwalliyar ce har yanzu ba'a gama ba?
Uncle ɗan iya yace"da rabon mu tafi mu barsu agidan sun taho daga baya, dama tafiya indai da mata za'ayi ta to fa sai an 6ata lokaci, su komai nasu da nawa babu karsashi..." ya faɗa yana haɗe fuska....
Acan cikin gidan kuwa, fitowa zahra tayi ta dauki wankan atampa, an yafa veil a kafada, hannu ruke da jaka, ta ca6a uban ado, dakin aneelerh ta nufa, kafin takaiga kofar dakin sai ga Aneelerh fito cikin sauri, wata hadaddiyar lafaya ta laga a jikin ta,launin orange mai adon stones, ta fito ɗass abunta, itama ta ruko handbag din ta, zahra na ganinta taci burki tana fadin"Aunty aneeleeh! kinga yadda kikai kyau? Meyasa baki fadamin lafaya zaki sanya ba nima ay saina sanya nawa" ta fada tana hade fuska, murmushi Anila tayi"kai zahra ay kin ma fini kyau, kinga su abie suna jiranmu, mu tafi kada mu 6ata masu lokaci" ta fada tare da ruko hannun zahra suka fara tafiya, har sun kusa fita daga falon muryar Ana ta katse masu hanzarin su
"Aunty Anila, Allah ya kiyaye hanya agaishe min da hajiya adama..." dakatawa sukayi da yin tafiyar, a wani irin yanayi Anila ta dubi fuskar Ana wadda ke acan tsaye kofar kitchen jikinta sanye da riga da mini skirt, ta ɗaure kanta da hula sai faman sakar mata murmushi takeyi .
Batasan ya akai ta tsinci kanta da jin faduwar gababa,
"Zahra kunyi kyau sosai, kun burgeni, sai naji dama hada ni zaku tafi" murmushi zahra ta sakar mata"mungode kada ki damu next time idan zamu ƙara zuwa hada ke zamuje, yanzu dai ki koma kitchen, pls kafin mu dawo ki gyara mana bedrooms dinmu sunyi datti..." amsawa tayi da toh, kafin ta sake kallon Anila wadda keta kallon ta ko kyaftawa bata yi murmushi Ana ta sake yi mata
"Aunty anila, adawo lafiya.."
Dakyar ta jinjina mata kai, cikin sanyin murya ta furta"Ana ba lallai mu dawo da wuri ba! Ki kula da gidan, sai anjima" awani slow ta kau da idonta daga na Ana, taja hannun Zahra suka fuce daga gidan...
Ana tana a kitchen tana goge gogen floor da wiper ta jiyo tashin motocin su,
*AGIDAN UNCLE ABDALLA"
Hajiya Adama Yau ba zama, tunda Anila ta sanar da ita zancen zuwan su, ta fara yan gyare gyaren gida, ganin tana ta wahala ita kadai ga girkin da zata yi masu ko farawa batayi ba, hakan yasa Uncle abdalla Ya dauko mata hayar house help wata bayerabiya kakkarfa, atare da ita suka fara girkin cikin kankanin lokaci suka kammala shi, hajiya adama har mamakin matar takeyi kamar inji bata gajiya da aiki, tana da kwazo da ƙwarewa ta bangaren aikace aikacen gida, kafin wani lokaci sun kammala tsaftace gidan..
da sauri hajiya adama ta shiga toilet, tayo wanka, ta fara shirya kanta,wani tsadadden leshi ta sanya a jikinta, ta kashe daurin dankwali, ta zauna kan mirror chair tana ƙarasa yin make up ɗin ta...
Sallamar uncle abdalla ce ta katse ta,
"Har yanzu ba su iso ba"? ta cikin mirror ta kalle shi suit ne a jikin shi..
"Nima naji shiru, amma ina ji araina sun kusa karasowa,
"Kodai basu gane gidan bane"?
"Bana tunanin hakan, ay na tura mata address din gidan tun jiya, bari na kira Anila naji.." ta fada tare da miƙewa ta nufi wayarta dake ajiye kan mattress, kafin ta ɗauko kiran waya ya shigo da sauri ta duba sunan mai kiran nata, murmushi tayi tare da kallon uncle abdalla"Anila ce ke kira" picking call din tayi ta kara wayar a kunne
"Anila kun taho ne"?
On the other hand anila tace"Eh, dama na kirane in fada maki mun kusa shugowa unguwan naku" wani irin farin cikine ya lullu6eta"Allah ya kawo ku lafiya" bayan ta katse kiran ta kalli uncle abdallah"tace min sun kusa isowa, yakamata muje mu taro su"
Murmushi uncle abdalla yayi"naga kina ta zumudin zuwan su, idan ma don saboda junaid ne kwara ki fidda rai, yau ranar school ne, ba lallai su zo da shi ba" daure mashi fuska tayi"ko baka fada ba, na sani, farin cikin dakaga inayi badan komai ba sai don saboda za'a kawo min ziyara gidana, kasan ba wani ke gareni a garin nan ba..." tay maganar tare da daukar mayafi ta yafa akanta,
Tayi gaba yabi bayanta. daidai lokacin da suka fito daga entry hall, suka hango mai gadin gidan Ya buɗe gate, a jere motocin suka kunno kai cikin gidan,
Bayan sunyi parking, hajiya adama ta nufi motocin da sauri kafin ta karaso anila ta rigata fitowa da sauri ta nufe ta suka rungume juna fuskar kowannansu dauke da annurin farin ciki.
Abie da Uncle dan iya suka nufi uncle abdalla dake tunkaro su, suka fara yin gaisuwarsu ta manya” Sassannun ku, da zuwa, ku ƙaraso ciki”, Mamie da hajiya adama suka rungume juna fuskar kowan nan su ɗauke da murmushi, bayan sun raba jikinsu, Ummi ta miƙa mata hannu suka gaisa a mutunce,kafin ta janyo zahra tayi hugginta dinta, daga bisani suka haɗu gaba daya suka shiga falon gidan, yau ne karo na farko da su anila suka fara zuwa, zahra sai yan kalle kalle takeyi gidan ya burgeta ginine babba, ita kanta anila tayi mamakin haduwar gidan surukan nata, an wadata gidan da duk wani abu na biyan bukata.
Bayan kowan nan su Ya zauna kan sofa, Uncle dan Iya yace"masha Allah, kunsan ni bani gani inyi shiru, abdalla kayi kokari wannan dankareran gida haka kamar dubai"? ya fada Yana bin falon da kallo, hakan ba karamin dariya ya basu ba,
Mami tace"naso ace tuntuni mukazo ganin gida Allah bai nufa ba sai yau, gaskiya bamu kyauta ba.." hajiya adama tace"ay kun goge laifinku, tun da kuka zo yau gaba dayanku don ma babu jikalle na..."
Mami tace"Allah sarki, Ya tafi school, abunda yasa ma bamu tsaya jiran shi ba, sai marece suke dawowa.."
Fira ce ta barke tsakaninsu yadda kasan dangi ɗaya, daga bisani bayerabiyar dake a gidan ta shirya masu abinci akan dining, suka hallara gaba daya suka zauna suna ci, uncle dan iya sai santin abincin yakaye yi, ita dai anila hankalinta kamar ba akwance yake ba, ta kasa cin abincin, saboda wani irin faduwar gaba da take ji..
"Anila meke damunki ne? Naga kamar bakison cin abincin" cikin kulawa hajiya adama tay maganar, cikin sanyin jiki Anila tayi murmushi tace"babu komai mommy, abincin ne yayi min dadi shiyasa nake santin shi" dariya hajiya adama tay"karki damu idan ma baki koshi ba zansa akara maki ne nafi so ku ci ku koshi dama saboda ku akai girkin dayawa" murmushi kowan nan su yayi, zahra ba baka sai kunne Hankalin ta na akan plate din fatan doyan da take ci......
_______________________________✍️
A hankali motar dr shureim ta kunno kai cikin entrance gate din asibitin, bayan yayi parking din motar, Ya dan juya ya kalli zeenatu data langwa6e kanta kan shoulder dinshi, kwata kwata batasan inda suka zo ba, ta nutsu tana shakar kamshi turaren shi ta wani lumshe idanunta...
Cikin sanyin murya ya furta"zeenatu mun ƙaraso" buɗe idanunta tayi tare da gyara zamanta, kwata kwata bata lura da inda suka zo ba, kusan atare suka fito daga motar, kamar ance ta kalli saman ginin karaf idanunta suka sauka akan sunan asibitin da aka rubuta da manyan haruffa masu daukar ido, wani irin bugu kirjinta yayi da sauri ta dafe saitin zuciyarta,
"Yaya shureim! Ina ne nan? Kamar asibiti nake gani? Dama nan zaka kawo ni"? Cikin rawar murya tay maganar tana ja da baya
"Zeenat ki kwantar da hankalin ki, kamar yadda kika gani asibiti ne, wurin auntynki benazir na kawo ki, kullum saita tamabayi kina ina meyasa baki zuwa dubata...." bai ƙare maganarba, zeenatu ta juya a firgice ta damƙi murfin motarsu ta kutsa kai zata koma ciki da sauri Ya cafki hannunta ya fiddo da ita yana fadin meya haka zeenatu? Meke damunki ne? Benazir din ke bakison gani" wani irin kakarwa jikinta ya farayi ta ɗaura hannu biyu akai ta fasa wata iri gigitacciyar ƙara wadda tajanyo hankulan visitors din dake zarya a harabar asibitin, gaba daya hankalin mutane ya dawo kansu wasu har sun fara tambayar meya faru? wasu kuwa sunyi tunanin wani mugun abun akai mata...."
Cikin shesshekan kuka da murya mai ƙaraji take fadi "bazan shiga ba Yaya shureim ka maidani gida, wayyo Allahna na shiga uku, na bani ya shureim...." tsantsar tashin hankali ne akan fuskarshi gaba daya tabi ta rikitashi, ga jama'a da suka tasa shi gaba suna tambayar me akai mata...bai san sa'adda ya janyota kan kirjinshi ya rungumeta sosai kamar zai maida ita cikinshi, idanunshi sun kaɗa jawur yai saurin kai la66anshi saitin kunnanta, A hankali ya fara zuba mata kira'ar alqur'ni wohoho zokaga idanu mutane sun nutsu suna ba idonsu abinci, wasu sai santin karatun shi sukeyi, yayin da wasu kuma suka kokwanton watakil aljanu gare ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyar zeenatu, gaba ɗaya ta narke mashi tana faman sauke ajiyar zuciya, tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa shi, tayi shiru sai ƙara nutsa kanta cikin kirjinshi takeyi, mutanan dake kallonsu sunyi masu ƙawanya hada masu daukarsu hotuna da video hakan yasa shi kare fuskarshi ya ƙara ƙanƙame zeenatun shi, ahaka yajata suka nufi cikin asibitin don bayajin zai iya juyawa da ita gida.💔
Duk ta kankame shi, mutane sai kallonsu sukeyi, nurses har tambayar shi suke yi patient ce? Yace masu a'a lafiyarta lou,
hajiya layla dake tsaye tana waya bakin kofar privet room juyowar da zatayi keda wuya ta hango su, arude take binsu da kallon har suka karaso inda take
"Shureim wacece wannan ka rungumo haka"? Ta fada tana kallonta sam bata gane wacece ba saboda ya rufe fuskarta.
"Mami zeenatu ce, tazo duba jikin benazir ne"
A ruɗe tace"meke damuntane? Ke zeenatu ya akai? Ko bakison zuwane aka matsa maki? Muryarta kasa kasa ta furta"bana jin dadin jikina..."
"Haba shureim kasan bata da lafiya ka taso ta? Ko likita kukazo gani ne"?
"A'a mami, lafiyarta qalou, zanyi maki bayanin abunda ke damun ta, mu shiga daga ciki....."
___________________________________✍️
A lokacin Unaisah tana zaune kan chair din gaban gadon Benazir, hannun ta ruke da glass na ruwa, magani take bata in ta sanya abaki saita bata ruwan ta sha, ta maida kanta kamar ƙaramar yarinya agaban unaisah, har yanzu bata daina binta da kallon kurullan ba...
"Mommy ki maida hankali kan ruwan da kike sha, kada ki shake" murmushi taskar mata"bana gajiya da kallon ki ne, Kin sace min zuciyata" da mamaki unaisah take kallonta, kalaman matar suna sanyata kokwanton kamar ta dawo hayyacin ta
Shigowarsu dr shureim dakinne Yaja hankulansu ga kallon kofar,
"Benazir yau Allah yayi, zeenatu tazo dubaki, sai dai kamar bata jin dadin jikin ta,..." da wani irin yanayi benazir ke kallon zeenatu wadda ta 6oye fuskarta jikin shureim...cikin sanyin murya ta furta"Zeenatu...."! shiru bata amsa mata ba, Unaisah dai ta zuba ido tana kallon matashiyar dake kankame da shurem, jikinta sai kerma yakeyi kuma taƙi dago da fuskarta...
"Zeenatu bakiga auntyn naki ba"? In a low voice ta furta"bana son ganinta" waro ido waje benazir tayi sam ta manta da pretending din da takeyi saboda ruɗewar da tayi, lamarin ya daure masu kai, arude hajiya layla ta kalli shureim suka hada ido, unaisah dake kallon su abun ya bata mamaki aranta ta ayyana kowacece wannan take ta wani boye fuskarta? Yanzu haka bawani kyan kirki gareta ba, in banda wulakanci hada wani cewa bata son ganin mamanta, yanzu haka yar kishiya ce... Acikin zuciyarta take wannan sambatu
Banezir kuwa jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya da jin kalmar da zeenatu ta furta abun Ya girgizata sam takasa magana sai motsa la66anta take
"Pls kada hakan Ya dame ku, bayin kanta bane, Ina tunanin iska ne suka shiga jikin ta..." calmly ya zayyana masu komai dangane da abun da ya faru ranar farko da ya koma gida har yayi mata maganar benazir ta share shi, har zuwa ga abunda ya faru yau, mami ta tafa hannu tana ambaton "inna lillahi wa'inna ilaihirraji'in zeenatu Allah ya baki lafiya, Allah ya yaye maki abunda ke damunki, baiwar Allah ashe shiyasa tadaina zuwa asibitin, sannu zeenatu ta faɗa tana leƙen fuskarta, banza tayi da ita, benazir dai takasa magana kallon su kawai takeyi, ita dai unaisah ta baza kunne tana sauraron su bakomai ya bata haushi ba face Yarinyar da take ta boye fuska.
"Yaya shureim ka maidani gida! Kada daddy ya dawo ya iske bana nan!..."
Cikin kwantar da murya yace"ko ya dawo ba abunda zaiyi maki, ai ni na fito dake, da anjima zan maidaki, mu karasa ciki ki zauna..." yai maganar yana kokarin janyota cikin dakin, aikuwa ta turje tana yan fizge fuzge Hankali atashe mami tace"shureim abun da ban tsorofa kamar ba zeenatu ba, pls ka maida ita gida, tunda ta nuna bata son zama nan din..
Shi dai baison Ya maida ta gida saboda bai shirya komawa ba
"Mami babu kowa gidan, ita da kanta ta nuna batason zama ita kadai shiyasa na taho da ita..." ya fada fuskarshi ayamutse...
Saukowa Benazir tayi daga kan gadon ta tsaya agabansu cikin karyayyar murya ta furta"zeenatu! dagaske bakison gani na"? da wata irin tsiwa ta furta"Bana son ganin ki, ki daina yi min magana...." kafin ta ƙare maganar, Benazir takai hannu ta damƙi shoulder dinta dakyar ta rabata daga jikin dr shureim ta jijjigata da karfi har mayafin daya rufe fuskarta ya zame kan kafaɗarta....
Kamar daga sama sukaji Sautin fashewar glass kusan atare suka kai dubansu ga Unaisah wadda ta miƙe a sukwane tana faman zazzare idanun ta, tsantsar tashin hankali da rudani ne akan fuskarta
"Azeezaty meya faru...." hada baki sukayi wurin tambayar ta, la66anta sai kerma sukeyi gaba ɗaya ta rikice ta kasa magana, gabanta na faduwa ta nufi zeenatu wadda ke ta kerma tana zare blue eyes dinta akan fuskar Unaisah
Wani irin gumi ne ya wanke fuskar Angel duk da sanyin A.c din dake a dakin, ta sanya tafukanta ta murza idanunta saboda tana kokwanton ko dai gizau takeyi mata ne? In ba haka ba tayaya mutumin daya mutu zai dawo araye? Ta kasa yarda da abunda idanunta ke nuna mata, kusan sau uku tana murza su don su dawo dai dai, Hankulan su dr shureim na akanta, sun rasa gane meke damun ta! Ko dai tasan zeenatu ne? Meyasa ta razana da ganin zeenatu harta fasa water glass din hannun ta! Dukansu kansu ya daure
Agaban zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai unaisah tayi da hannayenta biyu saboda wani irin sara mata da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta*"UNAIZA❗❓*
*Daga Alkamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
[14/10, 6:05 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite
Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 35 Complete
by
Novels Elite Admin
August 31, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️💋✊🔥
Agaban Zeenatu ta tsaya suka fuskanci juna, ido cikin ido, dafe kai Unaisah ta yi da hannayenta biyu saboda wani irin sara matan da yayi, zuciyarta ta fara dakan uku uku, Muryarta adabarbace ta furta"UNAIZA❗❓
Arude Hajiya Layla ta maimaita sunan Unaisah
Dr Shureim yace"wacece Unaizah"? Cike da fargaba Unaisah ta nuna Zeenatu da yatsan ta"ita ce, Yar uwarmu Unaizah...." gaba daya ta rikita lissafin ƙwaƙwalwarsu, Zeenatu da ta gama ruɗewa idanunta Azazzare ta furta"bani bace! Ni bansan ki ba, ban ta6a ganin ki ba. ..." Sautin muryar Zeenatu ya ƙara rikirkita ta, runtse idanunta tayi brain ɗinta ta fara tariyo mata muryar Unaizah idan tana magana! Tabbas wannan Unaiza ce ta dawo...."
fashewa tayi da kuka ta cakumi hannayen zeenatu"wallahi ke ce, Unaizah din mu, yar uwarmu wadda ta rasu tayaya akai kika rayu bayan kin mutu ..."? Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana.
Al'amarin yayi matuƙar ɗaure masu kai, Hankali atashe Benazir ta furta"babyna wacece Unaiza? Shiru Angel ta yi hawaye na sintiri kan fuskarta...
Dr shureim yace"kodai tayi maki kama da yar uwarki ne? Ita wannan sunan ta Zeenatu ba Unaizah ba, bayan haka naji kin ambaci yar uwarku wadda ta mutu in banda abunki wanda ya mutu ay baya dawowa watakil sunyi maki kamane...." kalaman dr Shureim Sunyi tasiri a cikin zuciyarta, amma taya haka zai yiwu? Komai nasu iri ɗaya kamar mutun ɗaya! farar fatarsu, da launin idanunsu blue, hatta blonde hair dinsu iri ɗaya, bugu da ƙari surar jikin su, tun daga kan sirantakar su har big boobs din iri ɗaya.
Gaba ɗaya ta jefa kanta aruɗani, su Benazir sun kafe ta ido suna kallonta,
Kokwanto ta fara yi kodai gizau fuskar Unaizah takeyi mata akan fuskar yarinyar? Nan take tayi believing da abun da zuciyar ta ke fada mata saboda tasan ba mai yiwuwa bane, wanda ya mutu ya dawo, abu ɗayane zaisa ta yarda da abun da idanunta suka gane mata, wanda bakomai bane face Ƴan uwanta suga yarinyar nan! muddin suka ruɗe suka ambaci sunan ta da unaizah to anan ne zata gasgata abunda idanunta suka gane mata...."
Lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya, sam takasa janye idanunta daga kallon fuskar Zeenatu, A hankali ta kau da idonta tare da kallon su shureim wata irin kunyarsu ce ta kama ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah, ku yi hakuri, na ruɗe ne, wallahi tayi min kama da wata dana sani, amma ita tama mutu tun da jimawa...." nannauyar ajiyar zuciya suka sauke, har suna hada baki wurin furta"Allah yajiƙanta da rahama.."
Yawu Unaisah ta haɗiya mai zafi a makoshin ta, kafin ta sake kallon Zeenatu dake kallon ta"sister kiyi hakuri dan Allah, na tada maki hankalin ki, kuskuren fahimtane...." murmushi zeenatu ta sakar mata, su kansu saida sukayi mamakin murmushin da tayi ma Unaisah
Cikin sanyin murya ta ce"Kada ki damu, babu komai...." miƙa mata hannu Angel tayi don su gaisa, da sauri zeenatu ta zira hannunta acikin nata sukayi musabaha, yau ne karo na farko da suka fara sanin junansu amma ga dukkan alamu sun kamu da kaunar juna, tabbas da ace lokacin da aka kawo masu Unaiza ta fada mata twins ne su wlh da ba abunda zai hana ta dafe alkur'ani tayi rantsuwar wannan Yarinyar Twin sister din Unaizah ce!! Ta dai bar abun aranta har zuwa lokacin da Allah zaisa ta hadu da su Batool sune zasu kara tabbatar mata da abunda take zargi na kamannin ZEENATU da UNAIZAH.........💔.
Kafin wani ya ƙara furta kalma a cikin su, wayar shureim ta fara ringing, a hanzarce ya curo wayar daga aljihu yai picking call ɗin
"Shureim! Ka dawo da zeenatu gida, Ina jiran ka" rass yaji gaban shi ya faɗi, tun daga kan yanayin muryar Alhaji musa ya fahimci ba lafiya, ko jiran amsar shi baiyi ba ya katse kiran.
"Wanene Ya kira"? Hajiya layla ta fada tana kallon fuskarshi
"Uncle ne, Yace in maida zeenatu gida"
Ta6e baki hajiya layla tayi ba tare da tace komai ba
Har lokacin Zeenatu bata cire hannun ta daga na Unaisah ba, sun ƙurawa juna ido kowa da abun da yake saƙawa aranshi......
"Muje zeenatu" muryarshi ce ta katse shirun nasu, sallama yayi masu hajiya layla, ya ruƙo hannun zeenatu suka tafi, Unaisah bata daina kallon su ba, har leƙen su tayi abakin kofar dakin itama zeenatun suna tafiya tana waiwayon ta hada ɗaga mata hannu tayi mata bye bye...💔
*CHIEF OWAIS🔥✊*
Slowly dankareriyar motar shi ta kunno kai cikin villa dinsa, yana daga zaune ya hakimce a backseat, su biyu ne a mazaunin baya big guy dake a gefen sa, kowan nansu kaki ne a jikin shi, da alama sun kwaso gajiyar aiki duba da yadda kowan nan su ya lumshe idanun shi kamar masu jin bacci.. .. bayan sun karasa parking space agent din dake driving nasu yayi parking
A hanzarce Wani agent daga cikin jami'an dake kai komo a harabar ya karaso ya buɗe masu murfin motar.
"Sir, mu shiga daga ciki" ya faɗa yana leƙen fuskar shi yayi shiru, soft lips dinsa sun bushe sun ɗan ciza kalarsu pink kamar bazai motsa ba, big guy yayi tsammanin bacci yakeyi hakan yasa shi kai hannu ya dafa shoulder din shi, da wata irin kasala ya buɗe reddish eye dinsa tare da kallon big guy
"Mun ƙaraso gida, nayi tsammanin bacci kake yi.." yamutsa fuskar shi yayi, da zolaya big guy yace"ka bani dama in goya ka mana.." harara chief ya jefa mashi tare da zura kafar shi ya fito daga motar, da sauri jami'an dake a wurin suka buga kafa tare da sarah mashi, ko ta kansu baibi ba ya nufi cikin gidan, big guy yana abiye da bayan shi....
Har ya kusa shiga main falo, wayarsa ta fara ringing, gajiya ta hana ya dauki wayar, kaitsaye ya nufi upstairs Yana shiga daki, Ya rage kayan jikin shi ya fada toilet....
Ganin ya shiga ciki yasa big guy yin kwana ya fita daga dakin..
After some mins, ya fito daga wanka waist dinsa a ɗaure da towel ya nufi walk-in closet dinsa ya shirya kanshi cikin hanley shirt tare da black trouser na shan iska..
Bakomai yake son gani ba face Danish, Yau da tunanin shi ya wuni a office, Yaron ne ya tsaya mashi arai, baisan meyasa yake jin shi sosai acikin ranshi....
Yana ƙoƙarin zama gefen gadonsa, phone dinsa ta fara ringing sai time din ya tuna da kiran da akayi mashi dazu
Ɗaukar wayar yayi daga kan pillow Ya duba sunan mai kiran nashi
Yayi mamakin ganin kiran ta! saboda basu cika yin waya ba...daidaita nutsuwarshi yayi kafin yai picking ya kara wayar a kunne tare da yi mata sallama ya gaishe da ita cikin girmamawa.
On the other hand muryar sheikha mujeedat ta amsa mashi sallamar shi cike da dattako ta fara yi mashi magana cikin harshen turanci tana hadawa da arabi
"My in-law, did you see the message I sent you on WhatsApp"!
"I just got back from work, ban kaiga dubawa ba..."
"Okay, ka duba yanzu, ina so zamuyi magana dakai" amsa mata yai da toh ta katse kiran..
Zama yayi gefen gadon kafin ya shiga whatsapp dinsa, kaitsaye idanunsa suka sauka akan sakon gimbiya mujeedat, calmly ya fara karanta abun da ta turo ma shi
_*DNA Paternity Test Report* _
A tsanake yake bin bayanan da result din ya kunsa har yakai karshen sakamakon
_"DNA Profile Match: 99.99%. Paternity Index: 100,000,000:1 (extremely high probability). Conclusion: The DNA analysis conclusively confirms that Danish is the biological son of Sheikha Mujeedat bin khalid AlMaktoum._
Lokaci ɗaya chief ya zabura ya miƙe jikinshi na tsuma, tsantsar ruɗani da al'ajabine akan fuskarshi, A kalla ya maimaita karanta sakon yafi sau ashirin kamar irin bai fahimci me aka rubuta ba saboda tsabar kiɗima da mamaki! Tayaya haka zai yiwu? wai ma Wani Danish din ne? Na wurin shi da yake ruƙo ko wani ne daban"?
Gaba ɗaya ya ruɗe tayaya ma akai gimbiya mujeedat tayi DNA test din? A yaushe? kuma daga ganin result din original ne daga babban asibitin toronto"
Wahallan Yawu ya hadiya da sauri yai scrolling ya shiga contact ya buga mata call yana faman fitar da numfashi mai ɗumi.
Kiran na shiga Gimbiya Mujeedat ta ɗaga..." la66ansa na kerma ya furta"mommy, ki yi min bayani, ki fahimtar dani! Na gaza yarda da abun da nagani I can't believe! I was confused, is this DNA test true? ya fada hankali atashe.
Sanyayyar muryar gimbiya Mujeedat ce ta ratsa kunnanshi
"Owais, kamar yarda hankalinka Ya tashi ka shiga rudani, nima haka na shiga, zanma iya cewa fiye da yadda ka shiga! Owais tun arana ta farko danayi tozali da yaron nan naji a jikina ɗana ne! Jini na ne shi, duk da bani da tabbaci But what strengthened my suspicions is the unconditional love Hateem has for him"
Shiru ta ɗanyi kafin taci gaba da cewa" na san zakayi mamakin tayaya akai nayi gwajin!" bayani ta fara kora mashi dangane da yadda ta yanki gashin danish batare da sanin shi ba.
jikin chief yayi mugin yin sanyi kamar wanda aka zarewa laka, gaba ɗaya yasha jinin jikin shi, ya girgiza bilhakki..."
"My trusted doctor conducted the test. When the results came out, I was shocked, wlh har zazzabi nayi owais..." muryarta na rawa ta ƙare maganar cikin rauni na murya
"Owais ka fadamin me kake tunani akan yaron? Kaima kana zargin jininmu ne"?
Numfasawa chief owais yayi wata juwace ta nemi daukar shi da sauri ya koma ya zauna, yana faman jan numfashi sam ya kasa bata amsar tambayar ta, abunne ya rikirkita shi.
"Owais naji kayi shiru bakace komai ba! Ni raina yana bani Omair dinmune, jinjirin dana haifa ba araye ba, amma in shine tayaya zamu iya gano gaskiyar lamarin? ni dama tun time din dana haifi yaron hankalina baikwanta da yadda aka hana mu ganin koda gawarsa ba, na dade da radadin abun a zuciya ta..."dakyar chief ya samu kwarin gwiwar furta"kin fadama uncle sakamakon DNA test din"?
"Ban fada masa ba, saboda bana so in daga mashi hankalin.." jinjina kanshi yai kafin ya furta"bazan boye maki ba, tunaninmu yazo ɗaya, nima ina zargin babyn da kika haifa ne! Amma har yanzu bamu da ƙwaƙƙwaran hujjar da zamu tabbatar da hasashenmu in gaskiyane! Dole saimun fara yin bincike mun gano tayaya akai jinjirin daya mutu ya rayu! Sannan su wanene suka sace shi daga asibitin da abun ya faru❓
"yanzu muna da shaida ɗaya a hannu, ki ajiye result din dakyau, kibar komai a hannuna nayi maki alkawarin zan binciko komai, in har yaron nan ɗankune zai dawo gare ku in sha Allah, sannan pls mommy kada ki bari uncle yaga result din nan..." ta amsa mashi da toh, kwantar mata da hankali yaci gaba da yi, daga bisani su ka yi sallama.
Shiru yayi jim yana tunani! idan har ya tabbata dan uncle dinsa ne to wanene ya sadaukar da shi? Yana jin fargaban ace hateem dinne ko wani daga cikin uncles dinsa tun da sadaukarwar na jininka ne kadai zai iya bada kai. ❗
Yana jin fargaban ranar da zai gano koma wanene! A sukwane ya fito ya nufi bedroom din Danish saboda ya yi maraicin ganin shi ya ƙara jin ƙaunar yaron a zuciyar shi fiye da kullum
Baijima da fita ba, sai ga big guy ya hauro up hannun shi ruke da wooden tray na kayan abinci, knocking kofar yayi jin shiru ba'a bude ba yasa shi tunanin koya yi bacci ne ko yana toilet
Yanke shawarar shiga ciki yayi, ya danna code din kofar ta bude kafin ya shiga da kayan abincin.
A bakin door room din Danish ya tsaya tare dakai hannu yayi knocking almost 3 times ba'a buɗe mashi ba, baya jin zai iya juyawa batare daya sanya shi a cikin idanun shi ba.
Tura kofar yayi tare da sakai ya shiga da sallama, yana zura ƙafar shi ya fara cin karo da papers din da ya kacaccala ya kekketasu akan floor, murmushi chief yayi aranshi ya furta hmm dakin ɗan koyo.
Ya yi ma bedroom din nashi kaca kaca, kamar ance ya ɗago da idon shi karaf Ya hango zanen da yayi akan white board din da yake koya mashi rubutu da shi, wata halitta ya zana kamar jagwalgwalo daya ƙura ido saiya gane maca ce, yar diyar roba da marker yayi zanan, kafafuwanta kamar na cokula, ga gashin kanta a haukace ko wacece wannan?
Murmushin gefen fuska chief ya saki kafin ya wurga eye balls dinsa kan bed dinsa a kwance ya hango shi, sai sharar bacci yakeyi kamar matacce, yar singlet ce a jikin shi fara kyal, tare da short ja, yayi wani fresh dashi.
Gaba ɗaya ya barbaza papers din da yayi amfani da su, ga notebooks dinsa daya watsar, hannun shi yana aruke da pensil da alama yana cikin yin practicing na rubutu bacci yayi awon gaba da shi.
Cikin takun sanɗa chief ya ƙasa daga gaban gadon ya zauna tare da sunkuyar da kanshi saitin fuskar danish ya ƙura mashi ido yana kallon shi, wani irin bugu zuciyarshi ta fara doka mashi, kamannin shi sun 6aci da yaron hatta dogon hancin su, da launun hair dinsu, da shape din bakinsu iri ɗaya sak, uwa uba reddish eyes dinsu masu kyan gaske da jan hankali, yadda yake yin baccin cikin kwanciyar hankali ba karamin kayatar da chief yayi ba, har baisan sa'dda ya manna masa peck a forehead dinsa, ya daura zira ziran yatsunsa saman tattausar farar fatar fuskar Danish mai kama data jinjiri saboda hasken ta da laushinta ya shafa ta a hankali..
In a low voice ya furta"I hope you will be my cousin, I will be proud of you. I will give you all my care. If it is confirmed that you are my blood cousin, I myself cannot describe the joy I will feel. I will hug you tightly, I will shed my tears on you, kuma nayi maka alkawarin zan ƙwatar maka duk wani hakkinka na rayuwa da aka tauye maka! Waɗanda sukayi silar sadaukar dakai zansa suyi danasani mara amfani....." cak ya tsaya da magana ganin ya fara motsi, da sauri chief ya dago da kanshi batare daya dauke ido daga kallon shi ba, gyara kwanciyar shi yayi.
Ajiyar zuciya ya dan sauke ganin bai farka ba, hakanan yai sha'awar karanta rubutun da yayi a jikin papers din daya watsar kan mattress, paper din farko jagwalgwalone yayi bai iya gane komai ba, paper na biyune yaga ya rubuta I miss you, my Angel. Come back home..."
yayi mamakin handwritting dinshi cos yayi kokari ba kadan ba, har kokwanto yayi anya shi ya rubuta? ɗayar paper din ya dauko ya duba rubutun dake akai.
"I'm waiting for you, chief. Come back home..." murmushi chief yayi har dimple dinsa ya lotsa...
Next paper daya duba sunan Daddy hateem ne ya rubuta duk da akwai kuskure amma yayi kokari..." bayan ya kammala reading dinsu, ya ajiye mashi abun shi gefe daya, har zai mike yaji ya damƙi hannun shi, ya ɗan furgita saboda bai tsammaci zai farka ba..a hankali ya buɗe idanunsa sunyi ja dakyar yake ware su akan fuskar chief, da wata irin kasala ya furta"You're back." jinjina mashi kai yai alamar eh..
Miƙewa zaune yayi tare da yin miƙa chief ya bi shi da kallo, ya jinjinama girman jikin shi, ba karamin kato bane ko'ina na jikin shi a murɗe yake irin na majiya karfi masu jini ajika.
"Fadamin kayi missing dina"? Daga mashi gira yai"nayi missing dinka sosai, tun dazu nake jiranka don muyi karatu baka dawo ba..." cheif yace"ai naga ka fara" ya fada yana nuna zanen dake akan white board din.
sunkuyar dakai danish yayi hadi da yin murmushi.
Da zolaya yace"abunda na koya maka kenen"! Girgiza kai yay "a'a!
"Wacece ka zana? Na kasa gane fuskar, Jemaima ce ko Azeeza"? Dagangan ya kira sunan su don ya bugi cikin shi...
Kasa ƙasa da murya ya furta"Angel" dariya ce ta kubce ma chief, danish ya kura mashi ido yana kallon shi.
"Haba my bro, Unaisah ce wannan Aljanar? Abu kamar agidan mahaukata, Ai ni dana ganta ƙarama nayi zaton jamaimah ne ." sunnar dakai kasa yayi batare dayace uffan ba...
nan take chief ya fahimci halin damuwar da yake aciki harya ɗan rame ta wurin kwarin idanun shi sunyi ja.
"Fadamin meke damunka.."?
Shiru yayi jim kamar mai tunanin wani abu
"Ina so Unaisah ta dawo gida, I miss her, I want to see her. She forgets me, Bata nema na..." kasa ƙarasa maganar yayi da sauri ya cusa kanshi cikin pillow.
wani irin tausayin shine ya kama owais cikin sanyin murya ya furta"am sorry danish, unaisah zata dawo gobe in sha Allah, kuma ka daina tunanin ta manta dakai, kana aranta...." muryarshi da rauni ya furta"har yanzu fushi take dani, bata sona"
har yau chief baisan soyayya ce atsakaninsu ba, yafi tunanin shakuwace mai karfi shiyasa ko kusa abun bai damun shi.
"Ina wayarka"?
"Tana akan mirror," ya faɗa batare daya dago da kan shi ba
Miƙewa chief yai ya nufi mirror din ya dauko wayar, ya danna power ta kawo haske
Wayarsa ya curo yayi copying contact din Unaisah ya saka awayar Danish...
Kiran sunan shi yayi, dakyar ya amsa mashi na'am
Na sanya maka contact din angel a phone inka, zaka iya kiranta ku gaisa, ko ka tura mata text message kamar yadda na koya maka..." dago da kanshi yayi wani irin dadine ya lullu6e shi, mika mashi wayar chief yayi yatsun hannun shi na kerma tsabar zumudi ya karba saida ya shiga wurin rubuta sakon ya kasa tabuka komai.
Miƙa ma chief wayar yayi"ka rubuta min..." girgiza kai chief yayi"kai ya kamata ka rubuta...yamutsa fuska yayi kafin ya fara kokarin rubuta mata sakon saida ya kammala chief ya duba abunda ya rubuta dakyar ya gane meya ke nufi a sakon ya hade kalmomin babu space babu ƙa'idojin rubutu irin dai na yan koyo,
"Kayi kokari" ya faɗa tare da mika mashi phone"ka danna send" ya amsa mashi da toh...
"Zan shiga gym ko zaka bini? Daga mashi kai yai akamar eh, da sauri ya mike chief ya ruko hannun shi kamar wa da kani suka fita a tare.💞
_________________________________✍️
Meya faru bayan komar dr shureim gida?
Tsaye yake gaban sofa ya goya hannayen shi kan kirjinshi, fuskar shi babu annuri idanunshi sun kaɗa jawur tsabar 6acin rai da fusata, abun da ya faru bayan fitar shureim da zeenatu kwatsam Motar su Alhaji musa ta kunno kai cikin gidan tunkafin bodyguard din dake driving dinsu yayi parking saiga kira daga likitan shi dr Mark, bayan yayi picking ko sallama baiyi ba muryar mark ta katse shi"yalla6ai! Da sanin ka dr shureim Ya fita da zeenatu...." lokaci ɗaya yanayin fuskar shi ya canza zuwa tsantsar bacin rai
Saida ya mula yasha iska kafin ya furta"bada sani na ba"!
Dr mark yace"yalla6ai, dole fa sai kayi takatsantsan idan ba haka ba zamu iya samun gagarumar matsala, saboda mutane sun ɗauki hotunan dr shureim tare da zeenatu rungume da juna, a bainar jama'a sai yaɗa shi sukeyi a social media..." a kiɗime Alhaji musa ya furta"what! Are you sure"?
"Ƙwarai kuwa yalla6ai, ka duba whatsapp dinka, zan tura maka hotunan ka gani da idon ka..." katse kiran yayi, wani irin gumine Ya wanke fuskarshi saboda bacin rai! Har shi zai sanya doka agidan shi a karya"?
Alhaji ubaid dake zaune gefen shi Ya lura da yanayin shi
"Musa lafiya? Meya faru ne"? Ko kallo Alhaji ubaid bai ishe shi ba, Ya buɗe murfin motar Ya fito tamkar mayunwacin zaki Ya nufi gate security officers, suna ganinshi suka miƙe suna jiran tsammani
Wata irin tsawa ya daka masu da ta gigita dodon kunnuwansu, yana huci ya furta"da iznin ubanwa kuka bari dr shureim Ya fita da zeenatu huh!? Kafin in fita basaida na gargadeku akan kada ku kuskura ku bari ko kofar falo ta leƙo ko ba....." ya ɗage sai masifa yake zazzaga masu ta inda yake shiga batanan yake fita ba.
Alhaji ubaid Har ya fara kokarin lallashin shi aikuwa Ya daka mashi tsawa kamar ɗan cikin shi Ya nuna shi da yatsa yace"karka kuskura kasa baki, magana nake akan ƴata, ka wuce ka shiga ciki" jikin Alhaji ubaid na 6ari kamar mazari Ya juya ya nufi cikin gidan abisa umarnin Alhaji musa wato ƙanin shi 🤣
Hankulan gate officers din ba karamin tashi yayi ba, tsantsar tashin hankali da firgici ne akan fuskokinsu.
Dakyar wani daga cikin su ya samu kwarin gwiwar fadin"yalla6ai har tambayar shi mukayi da iznin wa zai fita da ita yace mana da izninka, munyi kokarin tuntu6ar layinka amma baka ɗaga ba...." bai ƙare maganar ba sakamakon zazzafan marin da Alhaji musa ya wanka mashi wlh daga tsaye duk girman jikin mutumin saida Ya durƙushe kan gwiwowinsa.
Kallon sauran gate officers din yayi waɗanda tuni sun sha jinin jikin su, babban tashin hankalinsu taya zasu fahimtar da shi cewa su ba laifin su bane? Alhaji musa bala'e ne, wani irin bauɗaɗɗan mutunne, bahago mai wuyar sha'ani.
Wani mai rabon shan duka daga cikin su ne Yayi shahada wurin furta"yalla6ai, har kiran hajiya sarah mukayi awaya muka tambayeta da izininta zasu fita tace mana eh, ta kuma ce kaima da sanin ka...." bai kare maganar ba, Alhaji musa ya daddage Ya kwashe shi da mari da tafukan hannayenshi biyu nan take bakin officer din ya fashe jini ya fara bulbulowa.
kallon sauran yayi yana jiran jin bayani daga gare su, sai tsuma suke yi suna ja da baya da alama sun razana....
"Ban ta6a sanin ku dakikai bane sai yau! Wallahi ku kuka da kanku! ....." zubewa sukayi akan gwiwowinsu suka dinga rokonshi sunayi mashi magiya don ya yafe masu, ko ta kansu bai bi ba, Ya nufi cikin gidan cikin takun nan nashi na izza,
bawan Allah Alhaji ubaid Ashe yana la6e ta window yana leken abunda Alhaji musa yakeyi ma masu gadin gidan, Yaji haushi ranshi Ya 6aci sai.......💔
Adaidai lokacin da motar dr shureim Ta kunno kai sai ga motar hajiya sarah yau ta dawo da wuri, atare suka nufi parking space bayan sunyi parking, kusan atare shureim da zeenatu suka fito, kafin hajiya sarah ta fito da sauri zeenatu taje ta rungume ta
"Sannu da dawowa mommy, ya aiki"?
Shafa kanta hajiya sarah tayi"lafiyalou my baby,..." ta fada tare da kallon shureim murmushi suka sakar ma junansu,
"Sannu da dawo Aunty, ya aiki?
"Lafiyalou shureim ya mai jikin"?
"Mai jiki Alhamdulillah, taji sauƙi sosai, gobe muke sa ran za'a sallame ta...
da fara'a tace"Alhamdulillah, amma naji dadi, gobe in sha Allah tare dani zaku tafi..." atare suka jera suka nufi falon gidan, basu san bomb yana nan zaune yana jiran su ba.
Lokacin da suka shiga falon kusan atare suka ci burki suna kallon shi, akace labarin zuciya atambayi fuska, tundaga kan yanayin shi suka sha jinin jikinsu, Yana zaune kan sofa ya haɗe fuska kai kace bai ta6a dariya ba, ya murtuke fuska ga wani gumi da ya jike gaban rigar shaddar jikin shi, tsabar fusata zufa ta ko'ina take tsastsafo shi."
Kallon kallon suka fara jefa wa junansu, tsakanin dr shureim da hajiya sarah, kamar an dasa masu aya sun gaza ƙarasa shiga ciki....
"Daddy, yaushe ka dawo..."? Zeenatu ce ta ambaci sunan shi, da sauri ta nufe shi har takusa isa, Hajiya sarah tayi saurin cafko hannunta, shigowa ciki dr shureim yayi kamar jira yake su shigo ciki Ya miƙe agadarance ya nufi shureim Yana huci Ya furta"shureim da iznin ubanwa ka fita da zeenatu"?
Har saida gaban shureim ya fadi saboda kalmar ubanwa da alhaji Musa ya furta.
dakyar ya iya buɗe baki Yace"bada iznin kowa ba, ni na fita da ita saboda ta fada min tagaji da zama ita kadai agidan...." bai kare maganar ba Alhaji Musa ya damƙi gaban rigar shi ya jijjiga shi idanun shi jawur Ya kalli cikin idanun shureim.
Hankalin su hajiya Sarah ba karamin tashi yayi ba, Allah kadai yasan mai yayi niyar yi mashi amma sai ya fasa ya saki kwalar rigar ya cije la66ansa a zafafe ya ce"shureim ni kayiwa karya? Ka ce da iznina ka fita da ita? Dama malamai suna karya? Kai ko kunya baka ji ba? Ina tsoron Allahn da addinin naka huh? Runtse ido dr shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin furucin Alhaji Musa ba, kuma bai ta6a tsammanin zai iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi hakan ba.
"Ka bani mamaki shureim? A bainar jama'a ka rungume zeenatu a kirjinka, ƙato dakai baligi salon kaja min zagi a idon jama'a, so kake ka zubda min mutuncina da kimata..."? Fasa ƙara zeenatu tayi ta fashe da kuka tana fadin"Daddy ka daina yi mashi faɗa! banaso, Ka kyale shi! ba laifin Shi bane nice na rungume shi.."
bata ƙare maganar ba, Ya dankara mata ashariya kamar bamaguje
watsawa tayi da gudu ta nufi upstairs tana kuka tamkar ranta zai fita, tsautsayine Yaja Hajiya sarah ta buɗe baki furta"Yakamata kasan irin kalaman da zaka gaya mashi, wannan ba dacewa bane, shureim baiyi abun kunya ba kaine kayi abun kunya! Akan wani dalili zaka rufe shi da fada saboda kawai ya dauki yar uwarshi ya fita da ita! Shi ne laifi?...." kafin ta kare maganar Alhaji musa ya yai kukan kura ya ɗaga hannu zai ɗebe ta da mari da sauri Dr shureim ya shiga tsakaninsu, kai tsaye marin sauka akan fuskar shi, ji kake tasss! Waro ido waje hajiya Saratu tayi, zuciyarta ta hasala, Idanunta sun kaɗa jawur batasan sa'adda hawaye suka wanke fuskarta.
Dr shureim dake atsaye hannunsa dafe da kuncinsa, tsabar radadin marin da yaji har wasu taurari masu wutsiya ya gani suna gilmawa a cikin idanun shi, zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshin shi, cikin karyayyar murya ya dubi Alhaji musa Ya furta"ni kadai yakamata ka hukunta saboda ni nayi maka laifi, saboda na ɗauki zeeenatu na fita da ita, kuma ni ne nayi karyar cewa da saninka, saboda ni a tunanina zeenatu yar uwatace ina da right din da zanyi iko da ita.." ya fada yana kallon cikin idon Uncle din nasa.
"Duk akan Zeenatu kake tada jijiyoyin wuya? Meyasa? Kawai saboda na fita da ita munje asibiti duba yar uwarta! Wai duk kullan nan na menene? Ya jefa mashi tambayar, gaba ɗaya ya daure Alhaji musa da mamakin shi
"Uncle yakamata ka sani, mu fa ba makafi bane, duk wani motsinka akan yadda kake tafiyar da rayuwar Zeenatu muna lura, Wallahi abinda ka aikata yau ya sa na fara kokwanto! sannan inaso ka sani don munayi maka biyayya ba hakan yana nufin muna jin tsoronka ba, ni bana tsoron kowa sai mahallici na......"
waro idanu waje Alhaji Musa yayi jin furucin shureim, yayi mamakin yadda ya iya kallon tsabar idon shi ya gaya mashi magana batare da jin shakkar shi ba, Hajiya Sarah taji dadin martanin da Shureim ya mayar masa.
gaba ɗaya kalaman dr Shureim a kunnan Alhaji Ubaid dake a la6e yana sauraron su, yaga komai daya faru akan idonshi, har hawaye saida ya zubar saboda yaji zafin kalaman da alhaji musa ya jefi shureim da su, sannan baiji dadin marin da yayi mashi ba, yaji takaici kamar ya binne kan shi. Yasan bazai iya yin komai ba shiyasa ya hana kan shi zuwa wurin su.
"Idan ka cigaba da yanke hukunci cikin fushi, wallahi zakayi danasani"! Kamar sakarai haka Alhaji musa Yabi shureim da ido wato ta ko'ina ya daure shi da mamaki, Ya kasa furta kalma, ga wani gumi dake tsastsafo mashi...
"Shureim ka yi hakuri dan Allah!.." hajiya sarah ta faɗa idanunta cike tab da kwalla,"kada ki damu Aunty", A fusace Ya haura kafa ya nufi room din shi, girgiza kai hajiya sarah tayi rai a6ace ta nufi dakin ta.
Lokaci ɗaya Alhaji musa yaji jiri na niyar ɗibar shi, da sauri ya zauna kan sofa, ya dafe kanshi dake sarah mashi da hannu biyu"
_________________________________💋✍️
Lokacin da motocin su Baba Obie suka ƙaraso asibitin, a gaggauce nurses suka fito da Stretcher, Hajjaty da Abla suka ɗauko marwa da taimakon nurses suka kwantar da ita kan Stretcher, kaitsaye suka nufi cikin asibitin da ita, da sauri su Hajjaty suka mara masu baya tare da su Baba Obie, mutane sai miko gaisuwa suke yi cike da girmamawa musamman da ya shiga ciki Nurses da Docs kamar zasu durƙusa ƙasa tsabar yadda suke gaishe da shi cikin girmamawa, tuni labarin zuwan shi asibitin ya isa kunnan Md Dr. Jidenna dama mutumin shine, yare ɗaya ƙabila ɗaya sai gashi ya fito da sassarfa ya nufi Baba Obie tare da wasu daga cikin docs na asibitin, barka da zuwa suka yi mashi daƙyar yake amsa masu duk sun fahimci baya acikin kwanciyar hankalin....., a Waiting Area su Hajjaty suka zauna kamar masu zaman makoki, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya suke yi na sakamakon ciwon marwa, babu wani mai kwanciyar hankali acikinsu, fuskokinsu sunyi jawur ruwan hawaye ya jiƙe su.Pravin kuwa Yana ruƙe da qugu ya haɗa uban gumi duk da sanyin A.c ɗin dake a wurin, ya kasa zaune ya kasa tsaye kamar mai fama da ɗan kanoma...
Su kan su likitocin da sukayi arba da Marwa saida suka ruɗe saboda basu ta6a ganin patient mai irin lalurar ta ba, ba wai kuturtar ba toshewar bakin nata kamar ba'a ta6a halittarta da shi ba!! Wasu ƙwararrun Medical team ne suka fara bincikarta, kafin su fara aikinsu sai da suka fara tambayar me ya jawo mata ciwon!! nan fa su Hajjaty da su Abla suka kora masu bayani dalla dalla dangane da yadda marwa ta tashi dare ɗaya da lalurar suka ce su kansu basu san menene makasudin ciwon nata ba...bayaninsu ya ƙara rikita Docs din, wannan wani irin ciwo ne farat ɗaya?
A ƙalla Medical team din sun ɗauki tsawon awanni wurin duba lafiyar marwa, abun ya fara basu tsoro, saboda sunyi gwaje gwaje da aune aune but every result came back inconclusive. No trace of infection, no signs of trauma, lamarin Ya rikirkita su, sunyi iyakar bakin kokarinsu amma still babu wani sakamako daya nuna cewa Marwa tana da wani ciwo ko wata lalura, saima wani abun ɗaure kai lafiyarta qalou....'! Babu irin kokarin da likitocin basu yi ba akanta sun baje fasaharsu da kwarewarsu amma ba wani cigaba sakamakon dai ɗaya ne....❗
tun safe har wuraren karfe biyar na yamma babu wani abu da likitoci suka gano,
Lokacin da likitocin suka fito, sun hada uban gumi akan fuskokinsu kai kace ba A.c a dakin, su kan su sun jigata basu ta6a cin karo da patient din da ya basu ɗan banzan wahala irin marwa ba, duk irin kwarewarsu da kwazon su basu iya gano komai ba....
Su Hajjaty suna a zaune bayin Allah, A asibitin sukayi sallah, ruwa ne kawai ya gifta ta makoshin su, tsabar tashin hankali Ya sa sun manta da yunwar cikin su, koda ganin Docs din sun fito jikinsu na 6ari suka miƙe suna kallon su, ganin sun nufi inda su Baba Obie suke yasa suka bi bayan su, kora mashi jawabi suka shiga yi cikin harshen turanci ɗaya daga cikin su ya fara bayani,
"Duk da irin ƙoƙarin da muka yi, mun kasa samun nasara." ya fada yana ɗan girgiza kan shi, "munyi iyakar bakin kokarinmu, munyi duk wasu gwaje gwaje amma bamu ga komai ba, babu wata cuta da tayi silar kamuwarta da ciwon kuturtan da kuma toshewar bakin" tsantsar rudani da tashin hankali ne akan fuskokinsu.. Dr din dake a gefen wanda ya yi maganar ya ɗaura da cewa, "sakamakon binciken da muka yi ya nuna tana da koshin lafiya....." A ruɗe Baba Obie ya ce, "Bangane me kake nufi ba doc! ta yaya haka zai yiwu? Ga abun nan kuna gani da idonku zahiran! amma kuce baku gano komai ba"? Su Hajjaty dake sauraron su sai faman zare idanu suke yi duk sun bi sun ruɗe jin bayanan Docs.
"Mun shiga uku! dan Allah docs ku taimaka mana, wallahi rana ɗaya ta kamu da cutar...." kallon su docs din sukai ɗaya daga cikin su softly ya furta, "We're sorry, but we cannot offer more help, ba abunda zamu iya yi mata......! su kan su Likitocin damuwace ƙarara akan fuskokinsu..
"Dama saida raina ya bani jinnu ne suka shafe ta, Baba abun da yakamata mu koma da ita gida a kira manyan malamai su taru akanta watakil a dace..." Hajjaty ce ta yi maganar tana matsar ƙwalla, idanunta akan Baba Obie wanda yayi jigum saboda damuwa....gaba ɗaya sun yi amanna da maganar Hajjaty dama tun kafin su zo asibitin babu wanda baiyi tunanin jinnu bane, saboda ciwo ne kwatsam Ya afka mata a dare ɗaya ba tare da dalili ba.....
"Dr ba yadda za'ay ku buɗe mata bakin ta? Baba obie ya faɗa yana kallon docs ɗin,
Girgiza kai ɗaya daga cikin su ya yi, "Sorry Sir, We cannot perform any surgery to open her mouth, because we don't know what is causing her illness. Without knowing the cause, we could potentially make things worse. Shawarar da zan baku shine a maida ita gida a nema mata magani." Sautin shesshekar su Abla Ya cika wurin bayin Allah duk sun bi sun ruɗe ga tashin hankali......
Dafa kafaɗar Baba Obie MD Doc Jidenna yayi cikin kwantar da murya ya ce, "Kada ku sanya damuwa in sha Allah zata ji sauƙi, kamar yadda Docs din suka bada shawara kuyi kokarin nema mata magani, saboda rayuwarta tana a cikin hatsari zata iya rasa ranta..." cikin harshen igbo ya yi maganar,
numfasawa Baba Obie ya yi kafin ya ce "To amman yanzu ni babbar damuwata ta ya zamu koma da ita a wannan halin, bamu san ta ya zata ci abinci ba hakan kuma ka ga babbar matsala ne ace mutum ya zauna ba cin abinci balle kuma ya sha ruwa, ina ganin kamar zai fi a barta a nan tun da likitocin baza su rasa dubarar da zasu yi ba su bata abincin, zamu san abun yi kafin gobe" jinjina kai MD ya yi kafin ya juya kan ɗaya daga cikin likitocin cikin harshen turanci ya yi mashi bayanin buƙatar Baba Obie in zai yuwu, amsa ya bashi da bazasu rasa hanyar da zasu yi hakan ba dama da suna bincikar lafiyarta sun saka mata ƙarin ruwa da wasu allurai da zasu ƙara mata karfin jiki ganin ta galabaita. Duk sun ji daɗin hakan, Baba Obie ya roƙesu kan su bata kulawar da ta dace kafin zuwa gobe, cike da girmamawa suka amsa mashi da zasu yi ƙoƙarin hakan. Su Hajjaty sunso su ƙara ganinta kafin su tafi, saidai basu son ƙara karya mata zuciya don sun san yanzu dole tana cikin matsananciyar damuwa ba kamar da aka kasa shawo kan matsalar tata, ba don sun so ba suka tafi kowannan su da tsananin tausayinta a zuciyarshi.
Suna a kan hanyarsu ta komawa gida Baba Obie ya tuntu6i layin Sheikh Imam Malik ya sanar da shi cewa yana son ganin shi idan yana kusa, Sheikh Imam ɗin ya sanar da shi baya a gari, amma zuwa gobe da asuba zai shigo Abuja...lokacin da Baba Obie yake yin wayar Pravin yana zaune a gefen shi, tun da yaji Baba Obie ya ambaci yana son ganin Shiekh Imam cikin shi ya katsa, ƴan hanjinshi suka motsa, wata irin kiɗima yayi ga sanyin A.c a motar amma wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, sai faman zare na mujiya yake yi....!
_______________________________✍️
A 6angaren su Aneelerh, tun Bayan sun gama kwasar girkin da akayi ma su, saida kowan nan su yayi kulu wash rabu hani'an kafin suka koma falon, firar yaushe rabo suka fara dama an kwan biyu ba ahadu ba.
Wuni su kayi agidan, kiran sallar azahar ne ya tadasu, dakin baki hajiya adama ta kai Aneelah da Zarah su mami kuma dakinta ta kaisu don suyi sallah, wato su mami sun shagaltu da kallon dakin hajiya adama an zuba kayan alatu kamar dakin wata basarakiya..
yayin da mazan suka tafi masallaci bayan sun dawo a falo suka ƙara hallara, akaci gaba da hira ga launch an kawo masu ita dai aneelah tun zuwansu gidan hankalinta ba kwance yake ba, Ana sai faɗo mata arai take, ga wannan faduwar gaban data dameta hakanan dai take daurewa, zarah ta lura da ita duk wani motsin Anila akan idonta, ta fahimci babu kwanciyar hankali atare da ita, so take su ke6e taji ko lafiya, kiran sallar la'asar ne ya sake tadasu inda kowa ya nufi dakin da yayi sallah dazu
Bayan sun gama sallah ta juyo da kallonta ga Aneelarh da dan yanayin damuwa tace "aunty aneelah miyake damunki tun zuwanmu gidan nan ina lura da ke kwata kwata kamar a takure kike ko duk tunanin Aunty benazir ne" yamutsa fuska tayi "A'ah zarah wlh Ana ce ta tsayamun a rai sannan tunda mukazo gidan nan gabana keta faduwa na rasa dalili raina ya bani kamar wani abu zai faru" cikin sanyin murya ta kare maganar, ruƙo hannunta zahra tayi a cikin mata suka kalli juna
"In sha Allah auntyna babu abunda zai faru sai alkhairi, ki daina sanya damuwa aranki sannan kicigaba da yin addu'a"
Numfasawa tayi kafin tace"nagode da shawararki zahra, bari na kira Ana in tuna mata ta dafa ma baby junaid indomie dan kinsan daya dawo ita yake fara tambaya" murmushi zarah tayi "ina ruwan sarkin rigima" yar dariya Aneelarh tayi, tare da ɗaukar phone ta danna ma Anah kira tashin farko aka sanar da ita layin akashe yake!
kallon zarah tayi"na kira baya shiga!"
Zahra tace"maybe tana a kitchen tana aiki shiyasa ta kashe wayar, ki bari ɗan anjima kadan saiki sake kira"ta fada tare da cewa muje kar a jimu shiru"ruko hannun Aneelah tayi suka fito daga dakin, addu'a anila ta dinga karantawa a zuciyarta amma kamar ana kara mata faduwar gaban. Wannan karan tamkar ana mata dakan sakwara a kirjin ta.. A falo suka tarar da su ummi jiki asanyaye Aneelerh ta zauna tana ambaton sunan Allah, sam hankalin ta baya atare da su mami dake ta fira ko gajiya basayi, can ta tsinkayi muryar mami a kunnanta
"Anila ya kamata ki kira mahboob ki tuna mashi kar ya manta yaje da wuri ya dauko baby junaid, kinsan bayasan jira muma yanzu zamu tashi mu tafi yamma tayi"dariya sukayi su duka ummi tace"gaskia kam" tashi Anila tayi ta koma gefe ɗaya ta kira layin mahboob yana ɗauka tace" please karka manta kaje ka dauko baby junaid da wuri...
Katse ta yai da cewa "ohhh Aunty Aneelah saikace karatu kusan kullum sai an tunamin inje dauko sa? to ki kwantar da hankalinki baby junaid tun ƙarfe 2 yana a gida, yau da wuri aka tado su, saboda za'ayi wani taro a school dinsu, nima abokina ne dake koyarwa a school din ya kira ya fada min an tada su shine naje na dauko shi, halan bakuyi waya da Ana bane"?
Wani irin bugu zuciyar Anila tayi rass! Taji gabanta ya fadi zuciyarta ajagule ta furta"wai kana nufin tun karfe biyu junaid yana agida"?
"Kwarai kuwa, naga kamar kin daga hankalin ki, idan ma don saboda shine kada ki damu kanki yana atare da Ana ita na damka ma amanar shi"
Still hankalin ta bai kwanta ba tace"mahboob na kira layin Ana a kashe, pls ko zaka duba min su"?
voice dinta kamar zatayi kuka ga wani faduwa da gabanta keyi "ki sake kira kiji ni yanzu bana agidan na tafi kallon match" sallama sukayi ta kashe wayar hannunta har kyarma yake wurin kiran layin Ana still dai a switch off, cikin sauri ta koma falo ta gayama su ummi yadda tayi da mahboob mikewa mami tayi tare da kallon su uncle abdallah "to mufa baki zasuyi halinsu" ta fada tare da yar dariya, hajiya adama tace"wlh kamar ku kwana banso ku tafi Allah, kun ɗebemin kewa yau, Anya bazan biku ba" da zolaya uncle dan iya yace"shi kuma abdallan ina zamu kai shi? aikuwa su duka suka sa dariya, Aneelarh kamar jira take ta yafa mayafinta zarah ma haka gaba ɗaya suka fito compound din gidan inda sukayi parking car dinsu...
"Allah ya kiyaye hanya, mungode sosai, in sha Allah zanzo ganin jikana, agaida min shi..." Uncle abdalla yayi masu sallama akan idon su motocin suka fuce daga gidan hajiya adama hada kwallarta saboda bataji dadin tafiyar su ba, ruke hannunta uncle Abdalla yayi a cikin shi, suka koma cikin gidan su...
Nima na ruƙe hannun alƙalamina✍️
(Mu haɗe Jibi Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya🔥)
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions[14/10, 6:05 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 36 complete
by
Novels Elite Admin
August 31, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE✍️
tun da motocinsu suka haura kan titi Aneelerh take ta tsuma ji take kamar ta ƙwace driving din daga hannun Abie don gani take kamar bai sauri, tsigar jikin ta sai tashi take, gaba daya ba ta da kwanciyar hankali..
Tsawon mintuna kafin suka ƙaraso anguwar su, baba mai gadi ya taso ya buɗe masu gate, motar abie ce farko ta uncle ɗan iya na abiye da bayan su, abie nayin parking hannunta na kerma ta buɗe motar ta fito ta nufi cikin gidan.
Mami tace ohni Aneelerh ko irin alkunyar nan babu, baka lura da yadda ta ɗaga hankalin ta ba tun agidan hajiya adama..." mami ce tay maganar tare da buɗe motar ta fito abie na dariya yace"ya'yan zamani kenan, ay su ba ruwansu da wata kunya indai akan ya'yan su ne idon su rufewa yakeyi.
Da sauri zahra ta fito tabi bayan Aneelerh, bayan ummi da uncle sun fito baba mai gadi ya karaso inda suke yayi masu barka da dawowa...
Lokacin da Aneelerh ta shiga falon ko sallama batayi ba saboda idon ta ya rufe, yaronta kaɗai takason gani muryarta na rawa ta furta"Ana! Ana! Ana...! Shiru ba'a amsa mata ba, a kan sofa ta wurgar da handbag dinta, ta nufi bedroom dinta da sauri don taga ko baby junaid na anan tana shiga ta iske dakin wayan babu kowa, fitowa tayi a fujajen ta nufi kitchen"Ana! Ana! Wai ina kika shiga ne?...." tana shiga kitchen ta taras babu kowa ranta ne ya bata kodai yana adakin Ana suna bacci"? Hakan yasa ta juya da sauri ta nufi hanyar dakin Anah
"Aunty Anila..." zahra ce ta kira sunanta, shigowarta kenan ta hango Aneelerh ta nufi dakin Ana da sauri tabi bayanta, kafin ta karaso Aneelah ta ture kofar dakin, cike dasa ran zata gansu kwance kan gado, zura kafarta keda wuya idanunta suka sauka akan gadon Ana babu kowa akai, dakin gaba ɗayanshi a haukace yake kamar anyi dambe a cikin shi, fululluka har biyu ta gani kan floor, ga zanin gado a yamutse yayi uban squeezing, wani abu da ya ƙara rikirkita Anila, dressing mirror din dakin data gani ya kife ƙasa, Wa'iyazubilla wani irin jiri jiri ta fara gani a cikin idanunta da wani irin azababban faduwar gaba ta ƙarasa shiga ciki kamar wadda aka zare wa laka, zahra tana abiye da bayanta sai faman zare idanu sukeyi cike da tashin hankali, tun daga kan yanayin dakin suka fahimci wani mugun abunne ya faru❗
"Mun shiga uku Aunty Anila! Meya faru da dakin Ana? Ta ina? Ina baby junaid..."? Aruɗe zahra take magana ita Anila gaba daya rudani Ya hana ta furta kalma, jikinta na kerma tasa hannu tayi knocking toilet door din dakin cike da sa ran Ana zata amsa mata, almost 3 times tana kwankwasa kofar toilet din babu alamun za'a tanka mata ko za'a buɗe kofar, da iya karfinta na karshe ta bangaje kofar da kafadarta nan take door din ta buɗe a slow ta bada wani sauti kiiiiiiiiii!
Da wani irin faduwar gaba ta zura kafarta cikin toilet din, A hankali take bin ko'ina da kallo, bata ga kowa ba, sai shower da tagani a kunne ruwa yana ta kwararowa ya malale kan floor, ga faucet ma a kunne ruwan dake 6ul6ulowa ta cikin shi Ya cika sink din harya fara gangarowa ƙasa.
Hankali atashe Anila da zahra suke karewa toilet din kallo..
Muryar Anila na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Zahra na shiga uku? Bangan su ba! Banga baby junaid ba! Ina Ana takai shi? Ina suka shiga!...
Ruƙo hannunta Zahra tayi"Auntyna ki kwantar da hankalinki, muje mu duba sauran dakunan watakil taje gyara dakin wani a cikin mu, ko kuma sun fita backyard.
Da sauri suka fito daga dakin, adai dai lokacin Su mami sun shigo suna zaune a falon suka hango zahra da Anila zasu gifta ta falon
Muryar Mami ce ta katse su"Kai Ina zuwa haka? Kusan atare suka juyo muryar Anila na rawa ta ce"mami ba mu ga Ana da baby junaid ba, su muke nema..." jin wannan maganar Yasa ummi da su Abie suka mike tsaye
Ummi tace"kun duba ko'ina"? Zahra tace"yanzu zamu karasa dubawa..." ta fada tare da ruƙo hannun Anila suka nufi hanyar dakunan su Abie...
Abu kamar wasa sai da takaiga ko'ina na gidan sun duba saƙo da lungu amma ba su gan su ba, nan fa hankulan mutanan gidan Ya tashi, hatta su abie saida suka tayasu neman Ana, kowan nan su Ya hada uban gumi kan fuskarshi, sai da suka tabbatar babu su agidan sannan suka dawo falo suka tsaya cirko cirko.
Fuskar mami A yamutse ta furta"to ina suka shiga ne? Ko dai sun fita daga gidan ne? Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, watakil ta fita da shi"
Abie ne Yace"bari nayi magana da baba mai gadi, in ma fitar su kayi zamuji a wurin shi, A hanzarce Ya fuce daga falon Uncle dan Iya yabi bayan shi da sauri.
Baiwar Allah Aneelarh, tafi kowa jin jiki, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita gaba ɗaya ta gama sarewa, tana zaune kan sofa, hannayenta biyu daddafe da kanta, tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta.
Zahra dake a gefenta itama damuwarce akan fuskarta, ta dafa kafaɗar Anila tana kokarin kwantar mata da hankali, ganin yadda ta canza fuskarta tayi jawur cheeks dinta har kerma suke, dama abunda take ta zullumi kenan, tunkafin barinsu gidan hankalinta bai kwanta da yanayin da taga Anah ba! shiyasa take ta jin faduwar gaba dama sau dayawa in wani abu zai faru da bawa Allah na bashi haske kan al'amarin.
Mai gadi na zaune kan kujera Ya kure sautin radio dinshi, sam baiji Kiran da su Abie suke kwala mashi ba, har saida suka karaso gaban kujerar tukunna ya lura da su, da sauri Ya kashe radio din Ya miƙe yana kallon su
"Bayan fitar mu daga gidan nan! Wani ya ƙara fita ne"? Abie ne ya jafa mashi tambayar, girgiza kai yayi"yalla6ai babu wanda Ya fita..." can kuma yace au na tuna Mahboob ya dawo tare da junaidu, bayan shigar shi ina zaune sai ga mahbob ya fito ya shiga mota ya fuce, bayan shi babu wanda Ya ƙara fita...." bai kare maganar ba Uncle ɗan iya ya tari numfashi shi da cewa"kana nufin baga ka lokacin da Ana ta fita da junaid ba..." girgiza kai baba mai gadi yayi yace"a'a gaskiya ni banga gifcinsu ba, Ina zaune na kasa na tsare ko sauro bai isa Ya haura gate din nan batare dana kama shi ba..." hankali atashe Abie da uncle dan iya suka kalli Juna.
"Yalla6ai wani abu ya faru ne"? Baba mai gadi ne yayi tambayar ganin kamar damuwa akan fuskokinsu...
Abie ne ya zayyana mashi abunda ke faru, baba mai gadi yace"ikon Allah! Amma yalla6ai kun duba ko'ina? Saboda wallahi ni banga fitarsu ba, Allah shine shaidata, ko gyangyadin bacci banyi ba, lokacin sallah kadai ke tada ni, kuma sallar ma abakin gate din nayita...." ba su tsaya jin karashen maganar shi ba, da sauri suka koma falon gidan, su mami na ganinsu suka mike har suna hada baki wurin tambayar abunda me ganin yace Abie ne ya kora masu jawabi.
Kaf a kunnan Anila lokaci ɗaya ta rushe da kuka tana fadin"inna lillahi wa'inna ilahirraji"un..." daga kan sofa ta sauko kan floor ta zauna dirshan, taci gaba da kuka"wallahi saida raina ya bani wani abu zai faru da su, tun lokacin da muka bar gidan nan naketa jin faduwar gaba, ashe wani abu ne zai faru da junaid dina, na shiga uku mami ku taimaka mun! Ku nemo min Ana ta kawo junaid dina.."!! Da sauri Zahra ta rungumota a kirjinta, ta cigaba da lallashinta..ita kanta zahran kukan ne ke shirin kubce mata.
"Haba Anila meye abun kuka? Kamar dai bakiyi tawakkali ba? Wayace maki wani abu ya faru da su? Uncle ɗan iyane ya fara mata magana cikin tausasa harshe.
Ummi tace"ni abunda nake tunani kodai Mahboob ne Ya fita da su yakamata akira shi aji" da sauri Abie ya zaro waya ya danna ma mahboob kira yana dagawa ko sallamar shi abie bai amsa ba yace"mahboob kana ina"?
On the other hand mahboob yace"ina akan hanyar dawowa gida..."
"Ana tana atare dakai"?
Da mamaki mahboob yace"ana kuma abie? Ba tana agida ba? Ko bata nan ne"?
Katse kiran Abie yayi, tare da kallon su mami dake kallon shi
"Baya atare da su..." sautin kukan Anila ne Ya ƙara karaɗe kunnuwansu...
Mami tace"amma abun da daure kai! Ina Ana taje da shi? Ke zahra kira layin Ana muji..." sai yanzu dabarar kiranta yazo masu arai, cikin shesshekar kuka Anila tace"ko kun kira akashe zaku same ta, tun muna agidan hajiya adama inata kira baya shiga.." Zahra tace"bari dai a akara kira watakil ta kunna wayar" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Anah kira, nan take aka sanar da ita wayar akashe take, nan fa hankalinsu Ya ƙara tashi, Cire hula abie yayi zufa ta ko'ina ta fara tsastsafo mashi ta kan goshin shi, idanun mami tuni sun rune sun koma Ja, al'amarin yayi matuƙar ɗaga hankulan su
fashewa zahra tayi da kuka tana fadin"Allah yasa Ana ba guduwa tayi da baby junaid ba! Raina yana bani itace ta gudu da shi..." cikin shesshekar kuka Anila tace"ni bana zargin Ana, bazata ta6a daukar min babay junaid ba, na yarda da ita sai dai idan wani abunne ya faru da su duka biyun."
Ummi tace"Anila raba kanki da ɗan adam ba abun yarda bane, na jikinki ma zai iya cutar dakai balle ita da take yar aiki bare, Allah kadai yasan meya faru! Ina suka shiga"?
Girgiza kai mami tayi hawaye nabin kuncinta tace"dan Allah ku daina waɗannan maganganun, dukkan mu babu wanda yasan meya faru da su? Ko ina suka shiga, bai kamata mu yanke mata hukunci batare da mun san ainihin abunda ya faru ba, dududu ba yanzu muka dawo ba, mu ɗanyi hakuri kafin dare yayi watakil ta dawo da shi, mu kyautata mata zato dan Allah..." dakyar ta kare maganar daurewa kawai takeyi
Ita dai ummi hankalinta bai kwanta da Ana ba, tafi zargin itace ta gudu da junaid, dama tun lokacin da ta fada masu tana yin mummunan mafarki tafara zarginta, yanzu gashi ta 6ace babu ita ba junaid, wama yasani ko yar kungiyar asiri ce shiyasa ta sace shi har baba mai gadi baisan da fitar su ba.
Ta dai bar abun a zuciyarta gudun kada ta daga masu hankali
"Anya baba mai gadi gaskiya ya fadi? Taya za'ay su fita batare da sanin shi ba? Ga shi mun duba ko'ina babu su babu alamar su! In har bata kofar gate suka fita ba ay babu wata kofa da mutun zai iya fita daga gidan nan in ba dai 6acewa tayi da shi ba kamar yadda naga yan kungiyar asiri sunayi"
Maganar ummi ba karamin firgitar da su tayi ba, cak Anila ta dakata da yin shesshekar kukan Idanunta jawur ta dubi ummi"bangane me kike nufi ba ummi! Dan Allah ki fahimtar dani!" kafin ummi ta buɗe baki, Uncle dan Iya ya wurga mata harara, Rai a6ace yace"baki da hankali ne? Ko so kike zuciyarta ta buga ne? meya kawo wannan maganar? Maimakon ki kwantar mata da hankali saima kara dagula mata tunani kike kokarinyi! Wallahi kar in kuskura in kara jin bakinki!!" faɗa sosai yakama yi mata kamar zai rufeta da bugu, har saida Abie ya dakatar da shi kafin suka samu yayi shiru.
Miƙewa Anila tayi, zuciyarta ta karaya, jikinta yayi mugun sanyi, ga wani azababben zazza6i da ciwon kai mai raɗaɗi da tafara ji, gaba ɗaya suka bita da kallo ganin ta miƙi hanyar fita daga falo kamar bata a cikin hayyacin ta.
da sauri Abie yabi bayanta ya damƙi hannunta fashe wa tayi da kuka tamkar ranta zai fita tadinga kokarin ƙwace kanta tana sambatu cikin fitar hayyaci ta furta"wayyo Allahna abie, dan Allah ka sake ni inje in nemo baby junaid dina, bana so na rasa shi, bana so acutar min da shi, kabarni abie, Junaid shi kadai ne jinin uzair da nake da shi, idan na rasa shi bansan inda zan tsoma raina ba..."
Tana cikin yin magana ta sarƙe kwatsam ta yanke jiki zata faɗi da sauri abie ya kwanto da ita kan kirjin shi, sai lokaci mami ta fashe da kuka kalaman Anila sun karya mata zuciya, zahra ma kukan takeyi haka itama ummi gida ya zama kamar na masu zaman makoki, adai dai lokacin mahboob ya shigo falon ko sallama baiyi ba sautin koke kokensu Ya cika kunnuwanshi, hankali atashe ya karasa shiga ciki yana faman raba idanu akansu, arude yake fadin mami! Ummi! Zahra! Me..me ya faru? Daddy..bai kaiga kiran sunan abie ba yai arba da anila wadda ke rungume jikin abie, kamar ba numfashi atare da ita, tsabar kiɗima Yasa mahboob sakin key din hannun shi ya faɗi ƙasa.
La66ansa na kerma ya furta"dan Allah kuyi min bayani meya faru kuke kuka? Meke damun Aunty Aneelerh?
dakyar Zahra ta shanye kukanta muryarta a disashe ta kwashe komai ta sanar da maboob da buɗar bakinsa sai cewa yayi"ban yarda ba, wallahi bazai yiwu ba! Ni da kaina na ɗauko yaron nan daga school kafin ma mu iso gida bacci ya dauke shi, bayan nayi parking din motata na goyo shi abayana na shigo da shi cikin gidan banga kowa ba a falo, raina ya bani watakil kun tafin unguwar da naji kunce zaku je, sai na wuce da shi dakin Ana, bayan nayi knocking din kofar ta buɗe min naga idanunta jawur kamar daga bacci ta tashi, har na tambayeta ina mutanan gidan tace min ai kun tafi tun ɗazu, sai na miƙa mata junaid nace ta kwantar da shi idan ya tashi daga bacci ta yi mashi wanka ta bashi abinci, ta amsa min da toh, ta tambaye ni ni bazan ci abincin bane nace mata sauri nake zan tafi kallon match idan na fita zan tsaya agidan su abokina zanci acan, mukayi sallama da ita na juya cikin sauri har nakusa fita falon naji ta kwala min kira na jiyo na kalle ta, a lokacin ta rungume junaid dake bacci a kirjinta, ganin tana kallona da murmushi akan fuskarta yasa nace mata lafiya? Ko akwai wani abu da take son fadamin ne? Ta girgiza min kai tace a'a wai nayi mata kyau ne, bance mata komai ba, na dai ɗaga mata hannu na mayar mata da martanin murmushin da tayi min kafin nasakai na fuce daga gidan...." gaba ɗaya su mami sun kasa kunne suna sauraron mahboob dake basu labarin rabuwar shi da Ana har yakai karshe.
"Tayaya za ku ce min ba ku gan su ba fisabilillahi? Idanunshi cike tab da kwalla yayi maganr, duk da bai tabbatar da abunda suka fada mashi ba, amma zuciyarshi ta karaya dama tunda ya damka ma Ana amanar junaid ya fita daga gidan yake ta jin wani iri, idanunshi suka dinga tariyo mashi murmushin da ta sakar mashi.
Zahara tace"wallahi mahboob babu su, ko'ina mun duba, ba Ana ba baby junaid, ni abunda ya daure min kai, dakin Ana da muka gani a haukace babu gyara, duk an jefar da pillows ƙasa dressing mirror dinta ya kife ƙasa, daga gani wani abunne ya faru, maganar zahra ta ƙara jefasu a rudani...."
Girgiza kai mahboob yayi cikin tashin hankali ya watsa da gudu ya nufi dakin Ana, don ya gane ma idon shi kafin fitowar shi Abie ya kwantar da aneelerh kan doguwar sofa, mami ta ɗauko robar ruwa a fridge mai sanyi ta buɗe murfin ta yayyafa mata akan fuskarta, dogon numfashi taja tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur ta dubi fuskokin su, biji biji take ganin su daƙyar ta iya motsa la66anta da suke bushe ƙamas ta furta"mami ina junaid ɗina? Ana ta dawo min da shi"
shiru sukayi fargaban halin da zata shiga ya hana wani ya bata amsar tambayarta...
Abie ne yai karfin halin furta"kiyi hakuri Anila, basu dawo ba, amma yanzu zamu tafi neman su, in sha Allah zamu dawo maki da yaronki..." runtse idanunta tayi wasu irin zafafan hawaye suka wanke fuskarta...fitowa mahboob yayi daga dakin Ana yana tafiya kafafun shi suna harɗewa saboda rashin kwanciyar hankali, dawowa cikin falon yayi ya tsaya yana kallon fuskokin su.
"Zahra kun kira layin Ana ɗin"? ɗaga mashi kai tay"mun kira akashe" tsoki Ya buga tare da ruƙe qugun shi kafin wani ya kara magana a cikin su, sautin kiran sallar magrib Ya karaɗe kunnuwan su
Uncle ɗan iya yace"dan Allah ku kwantar da hankalinku, in sha Allh zasu bayyana cikin koshin lafiya, yanzu ku je kuyi sallah kuyi masu addu'a duk inda suke Allah Ya kare mana su, in sha Allah idan muka fita zamu bi gidajen makwabta mu duba watakil adace ko sun shiga ciki"
__________________________________✍️
*💋UNAISAH ANGEL💓*
Wunin ranar Unaisah bata jin dadin jikin ta, kamar mai fama da zazzabi tun da idanunta sukayi tozali da zeenatu bata ƙara samun nutsuwa ba, Yarinyar ta tsaya mata aranta tunanin zeenatu yayi mata ƙatutu a cikin zuciyarta, ta rasa meyasa take ta faɗo mata aranta, har takai ga da zarar ta rufe idanunta fuskar Zeenatu take gani.
Tana akwance kan darduma wani guntun baccine Ya ɗauketa bayan ta kammala sallar magrib, gaba daya ta kudundune kanta cikin hijab....
Benazir tana zaune gefen gadonta tana ta kallon ta, yayin da hajiya layla ke azaune kan sofa..
"Benazir..." dagowa tayi tare da kallon mami data ambaci sunan ta, kallon kallo suka shiga jefawa junansu, tuni benazir tasha jinin jikinta, dama tun dazu da abun nan ya faru na zuwan zeenatu ta lura da irin kallon da mami takeyi mata ga wani annurin farin ciki da take gani atare da ita...
"Ya jikin naki? ɗazu naga kamar kin samu lafiya.."
shiru tayi jim tana tunanin ta yadda zata 6ullowa mommyn nasu don bata shirya bayyana masu ta samu lafiya ba, tana da dalilinta nayin haka..
Jin tayi shiru yasa mami ta sake furta"dake fa nake magana? Hannu tasa ta ɗan sosa gashin kanta tare da kyafkyafta idanunta irin yadda masu tabin hankali sukeyi sam ta kasa buɗe baki tayi magana, hajiya layla ta kura mata ido tana kallon ta, ta ɗan rude da yanayin ta aranta ta ayyana ko dai har yanzu da sauranta"?
"Mami ina baby na? Ban ganta ba? ta faɗa tare da saukowa daga kan gadon ta fara ɗaga pillow tana nemanta, hada kokarin yaye zanin gado duk don tayi pretending kada hajiya layla ta gane ta samu lafiya.
Shesshekar kukan karya ta farayi hada yarfa hannu ta juyo ta kalli hajiya layla da ta saki baki sototo tana kallon ta.
"Mami kodai wani ya sace min ita ne? na duba banganta ba.." abun ya ɗaurewa hajiya layla kai, yanzu fa take zaune tana kallon yarinyar amma farat ɗaya ta nuna bata ganta ba.
Jinjina kai tayi aranta ta ayyana lallai haryanzu da sauranta, ganin yadda tabi ta ruɗe ne yasa mami yin saurin kiran sunan ta, a hautsine ta juyo tare da kallon ta
"Gata nan a kwance kan darduma.." girgiza kai tayi"mami ba itace ba, wannan ƙatuwa ce, babyna karama ce" waro ido waje mami tayi can kuma tayi tunani kodai don taganta nannaɗe cikin hijabine, mikewa hajiya layla tayi taje gaban prayer mat din, a hankali ta cire ma Unaisah hijabin ta fiddo da fuskarta.
"Kin ganta"? washe baki Benazir tayi tare da sanya tafukan hannunta, ta rufe fuskarta tana fadin"ashe itace ta lullu6e da hijabi, shiyasa bangane ta ba, mami gobe zamu koma gida da ita ko"? Shiru hajiya layla tayi gabanta na faduwa, jin abunda Benazir tace, yanzu ya zatayi gobe idan zasu tafi? Tasan dole Benazir ta sanya masu rigima muddin su ka ce zasu raba ta da yarinyar ba karamin daga za'ay ba.
"Mami kinyi shiru..." murmushi yaƙe ta sakar mata"kinji ki da wata magana, in bamu tafi da ita ba, a asibitin zamu barta ta kwana ne"? Yar dariya benazir tayi tare da jujjuyawa tana fadin"wayyo Allahna naji dadi mami, nayi farin ciki, zamu tafi da babyna gida...." ita dai hajiya layla jikinta yayi sanyi, Da harta fara murnar Benazir ta dawo hayyacin ta ashe har yanzu bata gama wartsakewa ba.
Ringing ɗin wayarta ne Ya farkar da ita, kaitsaye sautin ya daki kunnanta, a hanzarce ta tashi zaune ta cire hijab din jikin ta, idanunta har sun ɗan kumbura, ganin hajiya layla agabanta yasa ta ɗan firgita kaɗan.
"Yanzu nake shirin tada ki daga bacci naga ko dinner baki ci ba, sai gashi kinma farka da kanki..." hajiya layla ta fada da murmushi akan fuskarta.
"Babyna..."
Benazir ce ta kira sunan ta, a hankali ta dube ta muryarta da kasalar bacci ta furta"na'am mommyna..." murmushi Benazir tayi"naji wayarki tana ringing, ki duba ki ga wanene ke kiran ki" amsa wa tayi da toh, ta mike ta nufi backpack dinta ta curo wayar a lokacin har kiran ya katse.
kallon su hajiya layla tayi sam bata son yin waya agabansu, kamar mara gaskiya ta zura wayar a aljihun rigarta, ta juya ta nufi toilet ta shiga daga ciki taja kofa ta datse.
Call ta danna mashi yana yin picking tace"daddy, barka da marece? Ka wuni lafiya"?
On the other hand taj Yace"lafiyalou daughter, halan daga bacci kika tashi naji muryarki wani iri"
"Eh, bayan na kammala sallah ne bacci yai awon gaba dani"
Okey, dama na kirane don in kara kwantar maki da hankali, daga gobe ne in sha Allah za'a sallame ku da wuri, mun ma yi magana da chief ya fada min shi zaizo daukarki...." murmushi tayi har cikin ranta taji dadin jin hakan
"Allah yakaimu lafiya daddy, amma zanyi kewar mommyna..." ta fada kamar zata sanya mashi kuka, dariya yayi"ke fa da kanki kikace kingaji da kallon ki da matar keyi..."
"Wallahi daddy ina sonta sosai, bansan rabuwa da ita, jiyan ma dana fada maka ta bani tsorone ina fa bacci ta tsareni da ido amma ni ina kaunarta"
"Kada ki damu, ko bayan kin dawo gida zan iya kaiki gidan su ki gidan ta" dadine Ya lullu6e ta, sun ɗan jima suna waya kafin sukayi sallama.
Tana sauke wayar daga kunnanta, idonta ya sauka akan text message din da aka turo mata da bakuwar number, cike da mamaki ta danna sakon ya buɗe kura ido tayi tana kallon jagwalgwalon rubutun
Daya bayan ɗaya ta fara karanta shi.
_Deer swit angil, I mis yu soooo mutch Pleeease come hom to me, and I promis to met awl your condisions I wuv yu soooo mutch_
Dafe kai tayi da hannu daya zuciyarta cike fal da tunanin wanene yayi mata sakon? aranta ta ayyana daga gani ƙaramin yarone ya ɗauki wayar babarsa batare da sanin ta ba, ya danna wrong number shine aka tura mata sakon, tuntsirewa tayi da dariya da sauri ta toshe bakinta tunawa da su hajiya layla acikin dakinta...
Murmushin gefen fuska tasaki cike da nishadi ta ƙara maimaita sakon saboda nata fahimci me aka rubuta ba, nutsuwa tayi sosai tana kallon rubutun tiryan tiryan lokaci ɗaya taji gabanta yaɗan faɗi ganin kamar nick name dinta wato Angel
_My sweet Angel, i miss you so much, please come home to me, and i promise to meet all your conditions i love you_
Tabbas sakon ba kuskuren akayi ba, ita aka turo ma shi, ko wanene? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, a kalla ta maimaita karanta text din yafi sau ashirin batare data iya gano wanene ya turo mata shi ba, reply ta mayar masa"Please, may I know who you are? Bayan ta tura mashi sakon ta fito daga toilet din, a lokacin dr jazz ya shigo duba jikin Benazir yana ganin ta ya sakar mata murmushi da sauri ta gaishe da shi ya amsa mata da fara'a, bayan ya kammala dubata, yayi masu sallama ya fuce daga dakin da sauri hajiya layla tabi bayan shi.
"Dr. Jazz! Ina son yin magana dakai" tsayawa yayi tare da juyowa yana kallon ta, agaban shi ta tsaya suka fuskanci juna
"Dr mungode sosai, kana kokari akan Benazir, ubangiji Allah Yasaka maka da alkhairi, Allah yabiya maka bukatunka..." addu'oi tadinga yi mashi yana amsa mata da ameen, da alama yaji dadin addu'arta
Jin tayi shiru kamar akwai wani abu dake damuntane yasa shi furta"naji kinyi shiru ko akwai wani abu" yarfa hannu tayi fuskarta ayamutse tace"dr bansan ya zanyi da benazir ba! Ta ƙwallafa rai akan yarinyar nan, Ni damuwata halin da zata shiga idan aka raba ta da yarinyar kar akoma yar gidan jiya"
ta faɗa tana marairaice mashi fuska, yama rasa amsar da zai bata don ya fahimci kamar so take abar masu yarinyar su tafi da ita abune da bazai yiwu ba"
Calmly yace"na fahimce ki, amma gaskiya sai dai kuyi hakuri, iyayen yarinyar nan sunyi kokari da har suka iya baku ita na tsawon kwanakin nan, saboda ba karamin so sukeyi mata ba, itace kadai yar su tilo" dafe kai hajiya layla tayi da hannu ɗaya, sai yaji ta bashi tausayi.
"Nasani dr, wlh sunyi mana halaccin da ba zamu iya biyan su ba, ni damuwata taya zamu rabata da yarinyar? Kana gani zata hakura"?
"Kada ki damu, ni nasan ta yadda zan raba su batare da an samu matsala ba, in sha Allah komai zai tafi dai dai" gyaɗa kai tayi"mungode dr, agaida mutanan gidan," sallama yayi mata kafin ya juya da sauri ya nufi hanyar fita daga asibitin.
______________________________✍️
Bayan tafiyar su Abie masallaci, mami ta kalli Aneela dake kwance tana faman share kwalla"kiyi hakuri ki daure anila, bana son kukan nan da kike yi, ku tashi kuje kuyi sallah kuyi masu addu'a...." jiki asanyaye ta miƙe kwata kwata babu kuzari kamar zata faɗi kasa da sauri zahra ta taimaka mata suka nufi bedroom dinta...
Cike da jimami ummi da mami suka nufi dakunansu domin yin sallah....
Bayan shigarsu dakin, Anila ta zame hannunta daga na zahra, ta zauna gefen gadon, wani iri gumi ne Ya wanke fuskarta, Numfashin ta da hucin zafi yake fita. tsananin tausayinta ne Ya kama zahra, cikin sanyin murya tace"Aunty Anila dan Allah ki daure ki tashi ki shiga toilet kiyi alwalar, idan muka kammala sallar sai muyi masu addu'a...."
idanunta jawur ta kalli zahra, Cikin disasshiyar murya ta furta"Zahra ki barni kawai, Ni kadai nasan raɗaɗin da zuciya takeyi min! Zahra in har Ana bata dawomin da junaid ba, wallahi zaku iya rasa ni, saboda bazan iya rayuwa batare da yaron nan ba, zuciyata zata iya bugawa in mutu...." kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya sarƙe makoshinta, fashewa da kuka zahra tayi"Aunty Anila ki daina wannan maganar! Bana jin dadi, Kina karya min zuciya ta! In sha Allah babu abunda zai faru dake, ba zaki mutu ba, kuma in sha Allah ba abunda zai faru da junaid, Zasu dawo cikin koshin lafiya..." lallashinta zahra ta ci gaba dayi dakyar ta samu ta shawo kan Anila, harta hakura ta mike ta shiga toilet yin alwala, bayan shigarta zahra ta nufi wardrobe din kayan Anila, don ta ɗauko mata hijabi, bayan ta bude murfin ta zura hannu cikin jerin hijaban Aneelarh dake a jere ta ruƙo ɗaya tana kokarin janyota kwatsam! ba zato ba tsammani idanunta suka sauka akan ɗan mutun dake kwance cikin shelve din wardrobe Ya kudundune kanshi atakure jikinshi duk ya sandare.
Rass taji gaban ta ya faɗi nan take ta saki hijabin dake ruke a hannunta ya faɗi ƙasa ta runtse ido ta daddage ta fasa ƙara tana ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un jikinta ya fara kakarwa gaba daya tabi ta ruɗe takasa gane wanene ma ita dai kawai taga dan mutun kamar aljani, banko kofar toilet anila tayi da gudu ta fito jin sautin karar zahra, gabanta na faduwa ta furta"Zahra! Meye faru? Lafiya kike ihu? La66an zahra na kerma sam ta kasa magana sai nuna mata cikin wardrobe din takeyi da yatsan hannunta wanda ke ta kerma..
Adabarbarce ta furta"Aun...Aun... aunty Anila mutun! Ɗan mutun a ciki! ...." a matuƙar ruɗe Anila ta nufi wardrobe din ta kai idonta inda zahra ke nuna mata lokaci ɗaya ta waro idanunta waje da karfi ta furta"baby junaid..." sai lokaci zahra ta sake kallon shi dakyau taga fuskarshi sharkaf da gumi ya sandare kamar matacce duk ya takure kanshi a cikin shelve din da alama ya dade a ciki, wani abun daure kai towel ne ɗaure a jikin shi daga gani har wanka anyi mashi.
Allah kadai yasan meya faru da har ya 6oye kan shi cikin wardobe.. " A hanzarce Anila ta ɗauko shi ta zauna kan floor tare da kwantar da kanshi saman kirjinta, ta shasshafa fuskarshi, muryarta na rawa tace ma zahra ta dauko mata ruwa, da sauri zahra ta fuce daga dakin jim kaɗan ta dawo hannun ta ruke da bottle water mai sanyi ta miƙa ma Anila, yatsun hannunta na kerma ta buɗe murfin ta gumtsi ruwan abaki ta watsa mashi saman fuskarshi, wata irin firgita yayi jikin shi ya fara kakarwa kamar wanda sanyi ya kama...nannauyar ajiyar zuciya anila da zahra suka sauke. Cikin sanyin murya anila ta ambaci sunan shi junaid! Firgigit ya ware idanun shi waɗanda suka kaɗa jawur har saida suka tsorata, Yana ganin fuskar mommynsa Ya ƙanƙameta ya cusa kanshi cikin kirjinta Ya fashe da kuka mai sautin gaske ya dinga sambatu na fitar hayyaci, hakan ba karamin ɗaga masu hankali yayi ba...lamarin yayi matuƙar daure masu kai? Meya faru da shi? Ya akai ya shiga cikin wardrobe ya boye kanshi❓hatta bugun zuciyarshi bana lafiya bane❗
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
[14/10, 6:05 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite
Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 38 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 02, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
"Junaid Dan Allah ka daina kuka! Me ya faru dakai? Meyasa ka 6oye a cikin wardrobe? ina Anah? Kwata kwata baya fahimtar me take cewa, kuka yakeyi na fitar hayyaci hada kai hannu ya dunga bugun bayan ta, fashewa sukayi da kuka daga ita har zahra wani irin tausayin shine ya kama su, gashi sun rasa gane kan shi.
banko kofar dakin ummi da mami su ka yi daga waje suka jiyo sautin kukan junaid hakan yasa suka watso aguje suka fado dakin, lokaci ɗaya suka ci burki suna kallon Anila dake a rungume da junaid, waro idanu sukayi hadi da buɗe baki tsabar mamaki da al'ajabi ne ya kama su! Sam sun kasa furta magana na dan wani lokaci kafin mami ta matsa kusa da su, muryarta da rudu ta furta"ikon Allah kamar junaid nake gani! a ina kuka gan shi ne"? Shuru ba wanda ya bata amsa har saida ta ɗan daka masu tsawa saboda akagareta"bakuji ina magana bane? A ina kuka gan shi"? Dakyar Zahra ta tsagaita da yin kukan tana faman jan numfashi ta labarta masu komai.
Mami ta zagba salati tana tafa hannayenta, gaba daya sun shiga rudani, lamarin yayi matukar rikirkita tunaninsu sun rasa tunanin me zasuyi, kowa da abunda yake sakawa aranshi..."
Mikewa Aneela tayi ɗauke da shi, ta nufi mami tana kuka Yana kuka an rasa me lallashin wani"mami ku taimaka ku lallashe shi yaƙi yin shiru na rasa gane meke damun shi, junaid baya a cikin hayyacin shi, idanunshi sun kaɗa jawur sai sambatu yakeyi mana"
miƙa hannu mami tayi zata dauke shi aikuwa ya maƙe kafaɗa ya ƙara shigewa jikin mamanshi, sautin kukan shi ya cika kunnuwansu, sun rasa ya zasuyi da shi, gaba ɗaya suka yi mashi ƙawanya suna kokarin shawo kanshi ta hanyar lallashin shi kwata kwata baya sauraron su, adai dai lokaci su abie sun dawo daga masallaci kwatsam sukajiyo kukan junaid mai ƙaraji, wani irin faɗuwar gaba ne ya darsu a zukatan su, mahboob har yana tuntu6e garin saurin ya shiga ciki, gudu gudu sauri sauri uncle Ɗan iya da Abie Sukeyi suka nufi dakin Anila, suna shiga suka iske su mami tsaitsaye cirko cirko fuskokin su sharkaf da hawaye, kusan atare su abie suka kai dubansu ga junaid, arude mahboob Yace"Junaid! Aunty Anila a ina kuka gan shi? Ko Ana ce ta dawo da shi"? Abie ne yayi hamdala Yana fadin Alhamdulillah sun dawo kenan, dama saida raina ya bani wani wurin sukaje, Ina Anan take ne? Me kuma akayi mashi yake kuka.. "? Uncle ɗan iya yace"lafiya kuke kuka?Shima Yana kuka babu mai lallashin wani? Ina ita Anan"?
cikin shesshekan kuka zahra ta sanar da su inda suka gano junaid
"Abie, junaid baya sauraron kowa, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, kuka kawai yakeyi, mun rasa gane kan shi..." tsantsar tashin hankaline akan fuskokinsu har sun fara murnar ganin shi azatonsu Ana ce ta dawo da shi ashe ba haka bane.
"Bani shi nan" abie Ya fada tare da miƙa ma Anila hannu, a firgice baby junaid Ya ƙankameta alamar bazai je gurin abie ba, cikin murya kuka tace"abie ya ki yarda da kowa, su mami sunyi kokarin lallashinshi amma Yaki sauraron su...."
Girgiza kai abie yayi tare da ambaton Inna lillahi wa inna ilahirraji'un kafin daga basani ya kalli anila dake ta sharar kwalla, tana jijjiga junaid
"Anila ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, ki daina kukan nan, Kina kara ɗaga mashi hankali, je ki zauna ki lallashe shi, ke kadai ce zaki iya shawo kan shi, kiyi mashi addu'a ita yake bukata ayanzu..." amsa mashi tayi da toh, da sauri ta koma gefen gadon ta zauna, tare da sanya hannu ta talla6o kan shi, ta fara yi mashi kira'ar alkur'anin a cikin kunnanshi, su mami sunyi zungudum suna kallon su gwanin ban tausayi, cikin ikon Allah taji ya fara tsaitsayawa da yin kukan kafin a hankali taji yayi shiru ya nutsa kan shi a kirjin ta, fuskarshi tabi da kallo kumtunsa sunyi jawur, la66ansa sun kumbura suntum, hatta ƙwarin idanun shi sunyi jajir, siraran hawayene ke ta zarya kan kun cin shi, lokaci ɗaya taji ya fara sauke ajiyar zuciya a jere jere, nunfashin shi ya fara daidaita ba kamar ɗazu ba.
bata dakata da yi mashi kira'ar ba har saida ta tabbatar ya daina shesshekar kukan kafin tayi shiru tana duban shi, ajiyar zuciya su mami suka sauke hankalin su ya dan kwanta jin yayi shiru
Cikin sanyi murya ta furta sunan shi"junaid" motsa la66ansa yayi batare daya firta kalma ba...
"Dan Allah ka daina kuka, kasan bana son 6acin ranka, nasan nice na bata maka rai na tafi anguwa nabarka, ka yi hakuri ka yafe min junaid, wallahi bansan za'a tada ku da wuri ba..." shiru yayi bai tanka mata ba...
"Babyna, bazaka mun magna ba? Fadamin meke damunka? Kanka yanayi maka ciwo? Ko kana jin yunwa? Ina Ana? Meyasa ka yin kuka..." duk tabi ta rude sai surutu takeyi mashi, shidai yayi shiru bawan Allah shi kadai yasan bala'in da idanun shi suka gane mashi.
"Kada ki takura mashi Aneelarh, tun da mun samu yayi shiru, ki kyale shi Ya huta, Allah kadai yasan meya faru da shi wanda yayi silar rikicewar shi"! Mami ce tayi maganar
Ummi tace"ni ban ma san tunanin me zanyi ba wallahi, hankali na Ya tashi! abun da ya ɗaure min kai meya faru da su? Taya akai junaid yayi wayon 6oye kan shi a cikin wardrobe? To ko dai wani mugun abunne Ya faru da su bayan tafiyar mu, gaskiya ina ji araina Ana ce ta boye shi don kada a cutar da shi ko kuma shi ya boye kan shi sakamakon wani mugun abun daya gani, Allah daga ganin halin da junaid yake a ciki bana lafiya bane, Yaga wani abune daya razanar da shi" ta ƙare maganar tana kallon su
Jinjina kai uncle dan iya yayi"nima abunda nake tunani kenan, amma taya za'ay mu san ainihin abunda ya faru bayan tafiyarmu? Cikin shesshekar kuka Anila tace"Junaid zai iya fada mana idan Allah yasa ya dawo hayyacin shi"
Mahboob daya gama razana dakyar ya iya bude baki yace"ni damuwata yanzu ina Ana? Ga junaid ya bayyana saura ita baiwar Allah, bamusan meya faru da ita ba! Bamu san awani hali take a ciki ba..." bai kare maganar ba, Abie yace"in har wani abunne ya faru da su, zai iya yiwuwa itama ta boye awani wuri kamar yarda ta 6oye junaid..." jin wannan maganar yasa mahboob ruko hannun zahra yace mata tazo suje su kara nemo ta, da sauri suka fuce daga dakin bedroom dinta suka shiga, suka fara nemanta sako da lungu har karkashin gadon ta, da cikin wardrobe dinta amma basu ganta ba, sun duba ko'ina tun suna sa ran zasu ganta har suka fidda rai, kafin su fito daga dakin sai da mahbbob ya shiga toilet dinta Ya kashe shower din da aka bari a kunne da faucet, ruwa harya fara taruwa sosai har cikin dakin ta ya fara gangarowa, basu bar dakin ba sai da mahboob ya taimaka ma zahra suka gyara mata shi, kafin suka fito da sauri suka nufi sauran dakunan suna duddubawa, duk wani wurin sirri da mutun zai iya 6uya saida suka duba ko zasu ganta sai dai kash bata nan, ceilling ne kadai basu tsaga sun bincika ba don sunsan ba tayadda za'ay ta iya shiga ciki ta buya.
Badan sunso ba dole suka hakura da nemanta, jikinsu yayi mugun yin sanyi, zuciyarsu ta karaya, gani suke kamar ba zasu kara ganin Ana ba.
Anila taso takai baby junaid asibiti adaren saboda aduba mata lafiyar shi amma abie ya hanata yace mata ta cigaba da yi mashi addu'a in sha Allah zai samu lafiya, taruwa sukayi akan shi ɗaya bayan ɗaya kowannansu saida yayi mashi addu'a suka tottofa mashi a jikin shi, har indomie zahra ta dafa mashi ta kawo masu a plate amma yaƙi ci, ta koma kitchen ta haɗo mashi tea dakyar anila ta samu yasha tea din, jikin shi ya danyi sauki, zuciyar shi dai ce take bugawa da karfi, duk yadda taso ya bata hadin kai suyi magana don taji meke damunshi yaƙi mata magana kamar kurma sai dai yabi ta da ido, don dole ta hakura, gashi ya hanata sukuni ya manne mata kamar anta da jini, ko da zata shiga toilet ta karasa alwala sai dai ta shiga da shi, bayan ta fito ta goya shi abayanta ahaka tayi sallah 💔
___________________________________✍️
*ALHAJI MUSA💪*
Da sassafe ya shigo katafaren falon gidan, jallabiya ce a jikin shi grey colour, ta ɗanyi tighting arms dinsa, kamar kullum fuskarsa a daure ba fara'a, ya zuba hannayenshi cikin aljihun jallabiyar.
Cikin takun izza yake tafiya yan aikin gidan dake kai komo suna yin aikace aikacen gyara falo dakai abinci dining suna ganin shi, suka fara gaishe da shi, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye ya nufi dining room ya tsaya bakin glass door din yana kallon zungureran table din dake a kewaye da kujeru ancika shi da kayan breakfast, wani abu da ya ɗaure mashi kai babu kowa a kan kujerun yayi mamaki sam ya manta da abunda ya faru jiya, saboda bayan ya gama balbalin bala'in shi gidan ya bari gaba daya bai ƙara dawowa ba, sai yanzu daya shigo da safen nan,baisan awani hali mutanan gidan suka kwana ba.
Agogon hannunsa ya duba don yaga ko time na yin breakfast dinne baiyi ba sai kuma yaga lokaci yayi
Ta6e baki yayi kafin ya dago ya kalli yan aikin, Tani ya hango da hannu yai mata alamar tazo, jikinta na bari ta nufe shi"yalla6ai gani"
"ya akai banga mutanan gidan ba? Ko baku fada masu an shirya masu breakfast ba"?
"Wallahi mun yi masu magana, ita zeenatu tace mun bazata ci ba, nayi nayi da ita taki kula ni, shi kuma shureim da naje dakin shi na iske shi kudundune cikin bargo kamar baida lafiya nayi mashi maganar breakfast yace min baijin yunwa in tafi kawai..."
bata kare maganar ba, rai a6ace ya ɗaga mata hannu da sauri taja baki tayi shiru duk tabi tasha jinin jikin ta, wucewa yayi azafafe Ya nufi upstairs, ya ture kofar dakin zeenatu ya shiga daga ciki, tana a zaune kan prayer mat, hannunta ruke da al'kur'ani tana karantawa sam bata ji motsin shigowar shi ba.
"Zeenatu"! Kakkausar muryarshi ce ta daki kunnanta, bata kula shi ba, tamkar bataji kiran da yayi mata ba, hakan ba karamun fusatashi yayi ba, kwatsam taji ya dauke kur'anin dake a hannunta, azabure ta mike idanunta sharkaf da hawaye ta furta"Daddy, give me my Qur'an..." ko kula ta baiyi ba ya rufe kur'anin ya nufi bookshelf din dakin ya daura shi asama kafin ya juyo ya kalle ta"fushi kike dani? Rai a6ace tace"daddy ba iya fushi nake da kai ba, haushin ka nake ji, dan Allah ka kyaleni in cigaba da karatuna ko na samun saukin abunda ke damuna..." fashewa tayi da kuka gaban hijab din jikin ta ya jike sharkaf da ruwan hawayen ta
"You don't want my happiness, Daddy. You don't want peace kullum burinka ka 6ata min rai, a haka kake son inyi alfahari dakai amatsayin mahaifina!"
ta faɗa tana zare mashi blue eyes dinta wadanda suka kaɗa jawur, ko kadan baiyi mamakin kalaman data furta mashi ba, ya riga da yasan meke damunta, wato saboda ya bata ma shureim rai jiya shiyasa take fushi da shi.
Matsawa yayi kusa da ita da sauri taja da baya tana girgiza mashi kai, wani irin fargaba da tsoron shi ne suka kamata tayi zaton zaiyi mata wani abune. Batai aune ba taji ya damƙi arm dinta ya janyota kan broad chest dinsa yayi hugging dinta.
softly yace"fadamin laifin me nayi maki? Meyasa kike fushi da daddynki? Cikin shesshekar kuka tace"ka 6ata ma ya shureim rai, jiya banji dadin kalaman daka gaya masa ba, daddy ya shureim baiyi maka laifin komai ba, amma ka rufe shi da fada harka shake wuyan rigar shi, baka dubi girman shi ba..." dakyar ta ƙare maganar, shafa bayanta yayi cikin sigar lallashi yace"yanzu me kike so nayi? Don in wanke laifina"? Ya faɗa tare da dago da fuskarta suka haɗa ido sai taji yayi mata kwarjini da sauri ta kau da idonta gefe murya na rawa tace"kaje ka bashi hakuri, idan yace ya yafe maka nima zan daina fushi dakai" ɗaure fuska alhaji Musa yayi jin abunda tace wai shi zaije yaba shureim hakuri, girman kanshi ba zai barshi ba, amma dayake shu'umun kanshi ne sai yace mata"okey, mu sauka down, muje kici abinci" maƙe mashi kafada tayi"bazan iya ci ba, in ba atare da ya shureim ba"
"It's okey, muje sai in bashi hakurin" tace toh, ya ruko hannunta suka sauko downstairs.
A dining room ta tsaya kamar yadda ya bata umarni, Shi kuma Ya nufi dakin shureim time din daya shiga da sallama abakin shi, bai taras da kowa ba adakin, sautin ƙarar zubar ruwa yajiyo daga bathroom, alamar yana aciki yana wanka, zama yayi gefen gadon shi yana jiran fitowarshi,
Almost 15 mins yana jiran shi, har ya mike zai tafi don bayason jira arayuwarshi sai dai ajira shi, jin motsin buɗe toilet door dinne yasa shi dakatawa ya tsaya yana kallon shureim dake fitowa waist dinsa daure da towel, gefen fuskarshi yayi jawur kamar jini ya kwanta, hada sahun yatsun Alhaji musa shatunsu ya fito rudu rudu, sai yaji ba dadi aran shi, ganin irin illar daya yi mashi kuma yayi imanin zafin marin da yayi mashine ya haifar mashi da rashin lafiya a jikin shi kamar yadda yaji Tani tace bashi da lafiya.
Kwata kwata shureim bai lura da Alhaji musa ba, cikin rashin kwarin jiki ya nufi dressing mirror.
"Shureim"!Ya kira sunan shi, ɗaure fuska yayi batare daya kalli inda yake ba, duk da yayi mamakin jin Muryarshi a cikin kunnanshi aranshi ya ayyana kome yazo yi dakin shi?ya dai san ba hakuri yazo bashi ba abune mawuyaci.
"Da kai fa nake magana"! ya faɗa fuskarshi adaure, da farko yaso ya shareshi don yaga iya gudun ruwan shi amma sai ya fasa saboda mutunne shi mai matukar ladabi da biyayya yana ganin girman nagaba da shi bayan haka akwai na annabawa wato hakuri.
Juyowa yayi suka fuskanci juna
Muryar shi kasa kasa ya furta"Uncle, barka da safiya? Ka tashi lafiya"? ya dan yi mamakin tarbar da shureim yayi masa, amma bai nuna a fuska ba,
"ka zauna inason magana dakai" kasa kasa ya amsa da toh, kafin ya juya ya shiga wurin closet dinsa, jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya fara, a kan couch suka zauna shureim ya kau da idanun shi gefe ɗaya yana jiran jin dame yazo!
"Shureim dangane da abun da ya faru jiya bana a cikin hayyacina, kasan inada bad temper idan raina ya 6aci bana iya controlling kaina..." yanayin yadda yayi maganar ya ɗaurewa shureim kai har saida Ya juyo dakai ya kalle shi don ya tabbatar idan dagaske uncle musa ne ke yi mashi magana ba wani daban ba.
haɗa ido su kayi da juna da sauri dr. Shureim ya kau da idon shi gefe ɗaya, hakan bai dame shi ba yaci gaba da magana cikin tausasa harshe"inaso komai ya wuce shureim, ni bana son duk wani abu da zaisa mu samu sa6ani atsakanin mu..." sai da yai wannan maganar shureim ya dube shi dakyau yace"uncle ni wannan duk ba damuwata bace, bana ruƙe mutun a zuciyata, tabbas banji dadin kalaman daka jife ni da su ba, sun bata min rai, saboda ban ta6a tsammanin zaka iya furta min su ba, da ace wani na waje ne ya gaya min su bazan ji komai ba, amma kai da kanka uncle why? Saboda na fita da zeenatu yar uwata? Ko dan saboda rungumar da nayi mata wanda nikaina bada son raina nayi ba.." idanun shi cike tab da kwalla ya fada yana kallon cikin idon shi"saboda zafin kalaman daka furta min jiya ko bacci banyi ba, da bakin cikin su na kwana azuciyata" mood din fuskar Alhaji musa Ya canza sosai, kalaman shureim sun karya mashi zuciya sai yaji duk ba dadi.
Ruƙo hannun shi yayi a cikin nashi ya ruƙe su gam na ɗan wani lokaci kafin ya fara magana a tsanake"Allah ya huci zuciyarka shureim, na gane kuskurena kuma in sha Allah zan gyara.."ya faɗa yana ɗan jinjina kan shi.
"Da akwai wata tambaya da kayi min ajiya, dangane da kullan da ni ke yiwa zeenatu, kace ka fara kokwanto akaina! Shureim ina son jin dalilin dayasa kace haka? Wani irin kokwantone kake yi akaina..." ba tare da jin shakkar shi ba yace"ban yarda da kullan da kake yi mata ba, raina yana bani kamar akwai wani abu da kake 6oyewa shiyasa nake kokwanto akanka, ka hanata cigaba da karatu, ka hanata yin kawance da kowa, sannan ka hana ta fita, kamar baka son kowa ya ganta, ita kanta zeenatun ta fara korafi kan kullan da kake yi.
Shiru Alhaji musa yayi tamkar bazai yi magana ba, can kuma ya saki Murmushin gefen fuska kafin yace"zan fada maka dalilin dayasa nake kullanta, in har hakan zai goge zargin da kakeyi akaina.." ya fada yana kallon shi.
Kafin ya ɗaura da cewa"Dalilin dayasa nake kullan zeenatu, is that I'm a famous politician with many enemies who want to harm me. Zeenatu is my weakness, bayan haka itace ƴa ɗaya tak da nake da ita akusa dani, in har ban bata kariya ba, rayuwarta tana a cikin hatsari saboda akwai masu bin diddiginta, bana so inyi ganganci da rayuwarta, makiyana sun sha turo min sako akan zasu halaka zeenatu, shureim taya bazan killace ta agida ba"? Maganar Uncle musa tayi tasiri a cikin zuciyar shureim jikinshi yayi sanyi zuciyarshi ta karaya, hankalin shi ya tashi da jin abunda ke faruwa da rayuwar zeenatu!
"May be zeenatu ta manta bata fada maka ba, lokacin da tana zuwa high school, kusan kullum in zataje makaranta sai an samu wadanda suka kai mata farmaki, don ma Allah yasa akwai bodyguards da suke kula min da ita ay da tuni zeenatu babu ita araye" ya faɗa tare da dukar da kan shi ƙasa ya marairaice fuska kamar ba Alhaji musa ba.
Cikin sanyin murya Dr shureim Ya furta"Uncle, hankalina ya tashi da jin maganar nan, yanzu na fahimci dalilin dayasa kake kullanta, ni kaina bazanso abun da zai cutar da ita ba, amma kullan yayi yawa tun da har ta fara takura, bai kamata saboda wasu ahanata jin dadin rayuwarta ba, bayan haka Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake, kuntata rayuwarta agida bashi bane mafita ba, wlh duk tsaron dake agidan nan bazai hana a cutar da ita ba, amma idan muka cigaba dayi mata addu'a, in sha Allah makiyanka ba zasu ta6a yin nasara akanta ba!" wasa wasa dr shureim ya 6uge dayi mashi nasiha har saida ya tabbatar Ya samu nutsuwa Kafin yayi shiru yana jiran jin me zaice..
"Shureim nagode da shawararka, zanyi tunani akai in sha Allah, sannan akwai magana da nakeson yi dakai idan na samu lokaci..." bai kare maganar ba, wayar shureim ta fara ringing,
"Zan ɗaga kira"
"Okey, pls ka sameni a dining, zeenatu tana jiranka, tace bazata iya cin abinci in ba atare dakai ba..." jinjina kai shureim yayi bayan fitar Alhaji musa ya nufi gaban mirror ya dauki phone dinsa Ya duba sunan mai kira, mommyn su ce da sauri yayi picking ya kara a kunnanshi
Tunkafin yayi sallama muryar hajiya layla ta katse shi"shureim wai lafiya tun jiya inata kira bana samunka ko wani abu ya faru ne?
Cikin sanyin murya yace"a'a mommy, kiyi hakuri, wayar tana a kashe ne ban jima da kunnata ba"
Yanayin muryarshi ya sa ta tunanin kodai ba lafiya gidan?
"Ya jikin Benazir din? Ko har dr Ya sallame ku"
"Abun da yasa na kira ke nan, don in tuna maka, karfe 11 da rabi za'a sallame mu"
Agogo Ya kalla karfe 9, ajiyar zuciya ya sauke"In sha Allah yanzu zan shigo asibitin" amsa mashi tayi da toh, da sauri ya karasa shiryawa cikin shigar larabawa, ya ɗauki facemask ya zura a aljihun shi da niyar in sun fita zai sanya ma fuskarshi, don baison mommyn su taga tabon marin da Alhaji musa yayi mashi yasan muddin tagani sai ta tada 6alli.
Adai dai lokacin daya fito daga dakin, sai ga Hajiya sarah ta kimtsa cikin riga da skirt na atampa, ta kashe daurin kallabi mayafinta akan kafada ta daura shi, ta ruke purse dinta a hannu, kasa karasawa tayi gare shi ganin tabon dake akan fuskarshi cos tun jiya da abin ya faru kowa ya shiga dakin shi basu kara haduwa ba, taji nauyin hada ido da shi duk saitaji ba dadi.
"Aunty, barka da safiya, kin tashi lafiya" fuskarshi dauke da murmushi ya nufe ta.
Tuni taji idanunta sun ciko tab da kwalla cikin sanyin murya tace"shureim ka yi hakuri da abunda ya faru jiya, wlh bakin cikine Ya hana in leko dakin ka, banji dadin ganin yadda tabon marin ya bata gefen fuskarka..."
Cikin sauri yace"pls komai ya riga daya wuce, kada ki damu kanki, lafiya kalou, ay uncle dinma yazo har daki ya bani hakuri harma mun sasanta kanmu" kallon shi kawai takeyi gwanin ban tausayi, ta dade bata ga mutumin mai saukin kai da hakuri irin dr shureim ba.
Ganin tayi tsaye tana kallon shine yasa shi furta"nayi waya da mommy ta fadamin karfe goma za'a sallame su, yakamata muyi sauri muyi breakfast sai mu wuce..." girgiza kai tayi da sauri ta share kwallar data zubo mata, tabi bayan shureim suka nufi dining
___________________________________✍️
Around karfe 10 na safe, Unaisah tana a zaune kan kujerar gaban gadon Benazir, har ta kammala shirin ta cikin abaya maroon colour, tayi rolling veil akan ta, baiwar Allah jikinta yayi sanyi, zuciyarta batayi mata dadi, sam bata son rabuwa da Benazir ta kamu da kaunarta, duk yadda take zumudin son tafiya don taga yan uwanta, saida taji ba dadi, sabo kenan turken wawa...
Gaba ɗaya ta shiga zurfin tunanin rabuwa da ita, benazir dake zaune gefen gadon ta ƙura mata ido tana kallon ta ko kyaftawa batayi, ta fahimci kamar wani abu yana damun yarinyar, ita kan ta faduwar gaba take ji kuma ranta yana bata kamar wani abu zai faru
"Babyna me kike tunani"! Cikin kun nanta ta tsinkayi muryar Benazir, wadda tayi silar dawo da ita daga duniyar tunanin data lula..
Numfasawa tayi a hankali take kallonta, tuni taji hawaye sun cika tab da idonta, hajiya layla tana a tsaye bakin kofar toilet tana kallon su fuskarta duk ayamutse, damuwarta halin da Benazir zata shiga idan aka raba ta da yarinyar, ita kanta ta shaku da yarinyar tana son ta, sai dai ba yadda suka iya dole su yi hakuri su rungumi kaddara.
Tattausar murmushi Unaisah ta sakar mata, tare da miƙa mata kwayar maganin dake a hannun ta"mamana ki sha maganin ki," dakyar ta ƙare maganar tamkar zata fashe da kuka saboda tasan maganin bacci ne dr jazz ya bata don ta ba benazir tasha, duk don su samu tayi bacci ko sun tafi da unaisah....
Baiwar Allah Benazir kamar tasan me suke kokarin yi gabanta sai faduwa yakeyi, buɗe baki tayi unaisah ta sanya mata kwayar maganin, ta kanga mata glass din ruwan hannunta ta shanye shi, ƴan mintuna ƙalilan Benazir ta fara gyangyaɗi idanunta suka fara kokarin rurrufewa wani irin karfi maganin ke gare shi dr jazz ya iya aika aika...cikin karyayyar murya ta furta"babyna, kada ki tafi ki barni, inaji ajikina kamar tafiya zakiyi..." ɗan zaro ido unaisah tayi da sauri tace"ki daina wannan maganar mamana, ina atare dake babu inda zanje" dafe kai benazir tayi da hannu ɗaya, dakyar take buɗe idanun ta masu ɗauke da matsanancin bacci ta ƙurama unaisah ido cikin sanyin murya tace"dan Allah ki yafe min Angel, nasan ban kyauta maki ba, amma kada kice zakiyi fushi dani, kada ki tafi ki bar ni, wallahi ina sonki, Allah shine shaida ta bada son raina na tafi nabar ki ba, nayi maki alkawarin zan baki gatan da kika rasa na rashin uwa atare dake, zan tarairaye ki in baki kulawa Angel" a matuƙar ruɗe Unaisah ke kallon Benazir, kalamanta sun ta6a mata zuciya, sun fama mata ciwon dake a zuciyar ta, amma sai tayi tunanin watakil tana sambatune akan yarta da ta rasa.
Kukane Ya kwacema Hajiya layla da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta saboda batason ta ɗaga masu hankali.
Baccin ne Ya rinjayeta, jikinta ya saki a sukwane ta kwantar da kanta saman pillow, ta lumshe idanunta har lokacin bata daina yin sambatu tana ambaton sunan Angel.
A hankali unaisah take binta da kallo zuciyarta na harbawa da karfi da karfi gani take kamar in ta tafi ba zasu ƙara haduwa ba, lokaci ɗaya taji tsantsar tausayin matar ya kamata, tayi fatan ace zata cigaba da kula da ita sai dai tasan daddynta bazai barta ba, after that yan uwanta suna bukatarta ita kanta bazataso tayi nesa da su ba, ruwan hawayen da suka taru acikin idanunta ne suka fara yar tseral kan kuncin ta.
"Azeezaty! Ke nake jira muje ko"? Dr jazz ne yayi maganar yana daga tsaye bakin kofar ɗakin, miƙewa tayi daga kan kujerar, kamar wadda aka zarewa laka, ta sunkuyar dakanta saitin fuskar Benazir ta manna mata sumbata har sau biyu kafin ta juya taje ta ɗauko backpack dinta, ta kalli hajiya layla miƙa mata hannu tayi alamar tazo, da sauri unaisah ta ƙarasa gareta, hajiya layla ta rungumota a kirjinta.
"Toh Azeezaty, mungode Allah yasaka maki da alkhairi, Allah ya baki ilimi mai amfani duniya da lahira, Allah ya baki miji nagari, zamuyi kewar rashinki, ɗan zaman da mukayi dake mun saba dake, benazir zatayi kukan rashin ki, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarki, Allah yasakama iyayenki da alkhairi..." amsa wa tadinga yi da ameen kamar kar su rabu da juna.
"Ki gaida min da mutanan gidan, in sha Allah zamu zo wata rana har gidan naku"
Murmushi Unaisah tayi"Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ƙara ma mamana lafiya, nima daddyna yace zai kawo ni gidan ku" murmushi hajiya layla tayi taji dadin maganar, sallama sukayi da juna, A hankali take tafiya tana waiwayon Benazir dake kwance tana ta sharar baccin ta....
Dr jazz harya fara gajiya da jiranta, sai faman duba wrist watch dinsa yake yi baya son chief ya karaso don yasan bai son jira.
Har fa ta kusa fitowa daga dakin sai kuma ta juya da sauri ta koma gaban gadon Benazir ta manna mata peck a goshin ta.
Ganin abun nata bame karewa bane yasa dr jazz shigowa dakin Ya tasa keyarta gaba suka fito, baiwar Allah tana tafiya tana waiwayon dakin hajiya layla tana tsaye bakin kofar room din, hawaye sun cika idanunta har saida suka bace ma ganin ta kafin ta juya ta koma ciki zuciyarta cike fal da kewar Azeezaty.
A dai dai lokacin da suka fito, hamshakiyar motar chief ta kunno kai ta entrance gate din asibitin yar uban su launin ash colour har salƙi take da daukar ido, yanayin yadda motar take tafiya slowly yayi matuƙar jan hankalin visitors dake zarya a arean wurin, suka bi da ido har saida ta tsaya a parking sace.
"Muje, Ina tunanin shi ne ya karaso" jaz ya fada tare da jan hannunta, tunkafin su ƙarasa take ta kallon hamshakiyar motar, tayi mata kyau, lokacin dayazo kawota ba irin wannan suka hau ba.
Bayan sun ƙarasa gaban motar, ta ciki aka buɗe mata cardoor din wani daddaɗan fragrance ne Ya daki hancinta, mai haɗe da sanyi A.c.
"Ki shiga ciki" jazz ya faɗa tare da nuna mata hanya, sunkuyar dakai tayi tare da shiga ta zauna, wurga ido tayi akan shi har saida taji gabanta ya fadi saboda wani kyau da taga yayi mata, ya kare gefen fuskarshi da phone dinsa, da alama waya yakeyi, fuskarsa tana asanye da mask.
Hadadden yard din dake ajikin shi Senator cotton material ne light sky blue, rigar short sleeve ce ta bayyana strong arms dinsa, na karfafan maza masu ji da kan su, lallausar sumar kanshi ta sha gyara, ya sabunta military hair cut din sa
Sunnar da kanta ƙasa tayi ganin yana ƙoƙarin juyawa, janye wayar yai daga kunnanshi, Ya ɗago suka haɗa ido da jazz sai faman sakar sakar mashi murmushi yakeyi
"babban yaya, sannu da zuwa barka da safiya"
Calmy ya furta"lafiyalou jazz, ina fata kaima haka"
"Alhamdulillah"
"Ya mai jikin?
"Taji sauƙi sosai"
"Naji dadin jin hakan, zamuyi magana anjima" amsa mashi yayi da toh, har time din bai kalli Unaisah ba, kamar baisan da zaman ta ba sai bayan da jazz ya rufe murfin motar, ta kamo belt zata daura taji ya ruko yana kokarin sanya mata ita wani irin shock taji, muryarta na ɗan rawa ta furta"ina kwana"
"Ina lafiya" atakaice Ya amsa mata, agogon hannun shi tabi da kallo kirar rolex daytona tayi bala'en yi mashi kyau....bayan ya kammala sanya mata ya gyara zaman shi,
A hankali ya dago ido ya kalli senior Agent din dake zaune a driver seat"zamu iya tafiya" cikin girmamawa ya amsa mashi okey Sir,
Key yayi ma motar tare da yin reverse ya karya kwana motar ta fuce daga asibitin.
Ajiyar zuciya ta ɗan sauke idanun ta akan window glass din motar, asibitin take kallo cike da jin kewar Benazir matar ta kwanta mata aranta, amma idan ta tuna yar uwar chief ce sai taji hankalinta ya kwanta, ta wani bangaren ta kosa su koma gida ko dan taga yan uwanta almost one week tayi kewarsu"
Fragrance din turaren chief Ya hana ta sukuni, ta wutsiyar ido take satar kallon shi, dogon hancin nan nashi ba karamin tafiya yake da ita ba. Hankalin shi na akan phone dinsa da yake scrolling
Tayi tsammanin gida zasu wuce kaitsaye amma sai taga kamar sun canza hanya, ba wadda suka biyo ba aranar da zai kawo ta, aranta ta ayyana watakil wata hanyar ce da bata sani ba.
Tana tsaka da yin zancen zucinta, suka karaso wani katafaren Obie mall luxury plaza
Tayi mamakin haduwar wurin tunani ta farayi ko me zasuyi a mall din? Ta dai zubama sarautar Allah ido.
bayan shigar su ciki agent din yai parking a katafaren parking space na mall din.
Shiru tayi zuru tana jiran jin me zaice, sai da ya shafe 5 mins kafin taji ya furta"Let's go inside." fitowa sukayi atare, da sauri senior agent din ya fito ya take masu baya, Hankalin Ta ba karamin tashi yayi ba ganin wayayyun ƴan mata da samari yan gayu suna zarya a wurin duk sai taji ta raina kanta, wata irin kunyace ta kamata, takasa motsawa daga inda take ganin idon mutane ya dawo kansu, duk da facemask din dake akan fuskar chief hakan bai hana mutane kallon shi ba musamman yan matan dake gifta wa wasu kamar zasuyi tuntu6e tsabar yadda suke kallon shi, ga shi ba halin tunkarar shi saboda senior agent din dake atare da su, wani basamuden mutun ne ƙarƙarfa babu annuri kan fuskarshi, ga bindigu dake soke a qugun shi.
Ganin bata da alamun motsawa ne yasa shi ruko hannunta a cikin nashi, rass taji gabanta Ya faɗi duk sai ta kama yan kame kame tana faman noke kai, duk da yadda taso ta daure kada tai kauyacin saida ta kasa a hankali take satar kallon mall din yayin da suka nufi main entrance, Security guard din dake tsaron wurin sun gane chief, sai miko gaisuwa sukeyi cikin girmamawa kamar zasu durkusa kasa, tun da taga haka sai ta fara jin kanta wata hajiya gata ga chief, murmushin gefen fuska ta dan saki tana wani tafiya taku dai daya tana hura hanci.
Senior agent din ne ya ruke mata shopping cart, ganin taki daukar komai sai kalle kalle takeyi ne yasa agent din yi mata gyaran murya ta kalle shi"ki dauki abunda kikeso, sannan ki daukarwa yan uwanki"
waro ido ta danyi tare da juya kai ta kalli chief, yana tsaye gefenta ya goya hannayen shi kan kirjin shi in a low voice ya furta"Do what he said" amsa mashi tayi da toh, nan fa tafara ruwan ido ta rasa me zata dauka ba sabon ba, ga mutane suna ta yin shopping dinsu hankali kwance ita ko kamar an daure mata hannayenta,
Sun lura da yanayin ta ganin zata 6ata masu lokacine yasa chief kallan agent din ya bashi umarnin duk abunda yaga idanunta sun kalla ya daukar mata shi ko da mara amfani ne, ya amsa mashi da okey sir.
juyawa chief yayi a hanzarce ya koma mota ya zauna saboda baison kallon da mutane sukeyi mashi.
Bayan fitar chief, Unaisah ta miƙi hanya, agent ɗin yana abiye da ita jira yake yaga me idonta zai kalla, ita kuma taki yarda ta kalli komai tunda taji umarnin da chief ya bada, tafi son tayi ta kallon yan mata da samarin dake shopping a wurin.
Adaidai wurin Confectionery, ta tsaya tana kallon chocolates din dake a jere ga cookies kala kala, da sauri agent din ya fara jidar mata su iri iri yana turawa a cart din duk abunda ta kalla saiya dauke shi, har saida ta kau da ido tukunna ya dakata. Tafiya ta cigaba dayi ta nufi gurin data ga an rubuta Female Fashion Floor, kayayyakine kala kala na mata da zarar ta kalli abu, cikin sauri agent din yake daukar mata shi koda kuwa mara amfanine kai har bras da pads saida ya kwasar mata saboda umarnin boss dinsa yake ki.
Gabanta har faduwa yakeyi ganin cart din ya fara cika, ita fargabanta ba tasan kudin kayanba kada su yi almubazzaranci.
Hakan baisa ta juya ba sai ta nufi Boys' Corner kayan mazane tundaga kan suturu masu kyau da tsada har izuwa takalma, shades, caps, watches komai fa babu ce kadai ke babu, da sauri agent ɗin yafara jidar kayan da yaga idanunta suna kallo, saida yaga ta kau da ido kafin ya dakata, cart din har ya cika yayi sauro, hakan yasa agent din yayi magana da wani sales assistant dake akusa da su yace mashi ya dauko masu wani cart din da sauri yaje ya dauko ya ruke mashi suka cigaba da take mata baya, aikin yi fa ya samu, ita fa hankalinta ma baya akan kayan, kawai gurin ne ya burge ta shiyasa taƙi tafiya, idonta take ba abinci, a wani Tech zone ta tsaya tana kallon kayan dake gurin da sauri ta juya duk suna abiye da ita kamar wata sarauniya, mutane sai kallon ta sukeyi suna mamakin kayan da ake kwasar mata, ko yar wacece?
Har zata gifta gaban wani education hub ta dakata tana kallon writting material din dake a gurin, bakomai ta tunaba face yan uwanta bata da burin dayawuce su iya karatu da rubutu, yanzu ne taga abu mai amfani da zata iya nuna tana so..harta buɗe baki zatayi magana idonta ya sauka akan agent din da assistant din sun dage sai kwasar mata kayan sukeyi, tun daga kan notebooks, Dictionary, pens, pensil, markers, drawing book, duk wani abu da idonta ya kalla saida suka ɗaukar mata shi, gaba daya sun kashe mata baki, kamar sakarya haka ta saki baki tana kallonsu, ganin abun nasu bame karewa bane yasa tayi saurin furta"dan Allah ku dakata Ya isa haka! wadannan kayan sunyi mana yawa.."
Agent din yace"banga alamun sun isa ba, Ni umarnin chief nake bi, in kina so mu dakata to ki kau da idonki daga kan kayan da sauri ta juya baya ta fara kokarin neman checkout counter dakyar ta gano gurin ta tsaya tana faman sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha gudu, har cashier din sai da ta dan bashi mamaki, ganin yadda ta fado gaban counter din, bayan ya auna kayan da suka siya total 800k har saida taji yan hanjin cikinta sun kaɗa murya na rawa ta kalli agent din"dan Allah ku rage kayan su koma na dubu goma" maganarta taso ta basu dariya agent din yace"da alama bakisan wanene chief ba, idan duka kayan mall din kikeso zaisa a mallaka maki su, babu abunda zai ragu na daga tarin dukiyar da yake da shi.." jinjina kai cashier din yayi" amma dai yalla6ai, ita din bakuwa ce a family din su? Daga mashi gira agent din yai, murmushi cashier din yayi a lokacin har an kammala sanya masu kayan a cikin shopping bags har kusan huɗu,
Agent din ya zaro master card din da chief ya bashi ya miƙa ma cashier din don ya ciri kudin, ƙin kar6a yayi fuskar shi dauke da murmushi yace
"Grandpa dinsa Ya hana a kar6i kudinsa, ku tafi kawai" girgiza kai agent din yayi"ka kar6a ka ciri kudin, chief baya son siyan kaya batare da an kar6i kudinsa ba, gani yake kamar sadaka aka bashi" dariya sukayi cashier din yace"nasan halin shi ay, har yau bai canza ba kenan, kudin ay duk nasu ne ko an kar6a hannunsu yake komawa, pls ka bashi hakuri ni bazan iya cirar kudinsa ba, zaija min ne..." duk yadda agent din yaso ya kar6i card din yakiya dole suka hakura yace ma unaisah su tafi, ita dai hankalinta yaki kwanciya, ta ruɗe da alamarin, taya zasu sayi uban kayan nan kuma aki kar6ar kudinsu? Abunda bata sani ba, mall din mallakin famiy dinsu ne, juyawa tayi da sauri ta nufi hanyar fita agent din yabi bayanta, ma'aikatan mall din suka bi bayansu da shopping bags din..
Bayan sun sanya masu kayan a boot din motar, agent ya bude mata car door din ta shiga ta zauna tare da kallon chief ya nutsu yana daddana wayar hannunsa, shigowa ciki agent din yai ya zauna a driver's seat ta mirror ya kalli chief.
"Sir, we've completed the purchase, and the goods are in the boot."
Fuskarshi babu annuri Ya furta"Why didn't I receive a debit alert?
"Sir, grandpa ɗinka Ya hana su kar6i kudinka, ba yadda banyi da cashier din ba amma yaƙi kar6a yace baya son yaja ma kan shi" ta6e baki chief yayi kafin a hankalli ya dan juya suka hada ido da unaisah dake ta kallon shi, da sauri ta sunnar da kanta ƙasa cikin sanyin murya tace"mungode Allah yasaka da alkhai..." bata kare maganarba ya toshe mata bakin ta da yatsan hannun shi..idanunsu acikin na juna ko kyaftawa basayi wani irin kallo suke jefawa junansu hatta agent din dake driving dinsu sai satar kallon su yakeyi ta cikin mirror fuskar shi dauke da murmushi yajima baiga macen data dace da chief irin yarinyar nan ba, sun burge shi.
da sauri ta sauke idonta kasa ta kama yin yan kame kame kamar zata nutse kanta cikin cinyoyinta, zame yatsansa yai daga kan la66anta, laushinsu ba karamin fusgarshi sukayi ba, muryar shi tamkar tame jin bacci ya furta"kada ki ƙara yi min godiya bana so" daga mashi kai tay"bazan ƙara ba"
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
[14/10, 6:05 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 39 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 03, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️
"Good" ya furta tare da gyara zaman shi, babu wanda ya ƙara furta kalma a cikin su, shiru motar baka jin sautin komai sai sanyin A c dake ratsa fatar su, aranta Allah Allah take su karasa gida don ta nuna ma yan uwanta tsarabar da tayi masu tasan zasu ji dadi.
Gaba ɗaya ƴan aikin gidan suna atsaitsaye gaban door room din marwa, fuskokinsu babu walwala idanunsu sun kumbura saboda rashin isasshen bacci da basu samu ba adaren jiya, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya sukeyi tun wuraren karfe shida sheikh imam ya karaso gidan, tunkafin karasowarshi bayan kammala sallar asubahi baba obie ya tura su hajjaty tare da security suka dauko marwa daga asibiti yanzu haka tana acikin dakinta tare da sheikh imam malik sautin ruƙiyar da yakeyi mata ya cika kunnuwansu bayin Allah sunyi zuru zuru, hankalinsu atashe tun safe ake abu ɗaya har yanzu ba wani labari mai dadi, a kalla sun shefe awanni abakin kofar dakin suna jiran sheikh imam malik.
"Idan har ya tabbata aljanune suka ɗaura mata ciwon, ni dai inaga zan tattara kayana in koma kauyenmu da zamane, zaifi min kwanciyar hankali don bana jin zan iya cigaba da zama agidan nan...." cikin rawar murya safa tayi maganar.
Abla tace"ni kaina na tsorata wallahi, jiya a zaune na kwana saboda fargaba da zullumin abunda ya faru da marwa, wlh ta bani tausayi baiwar Allah rana daya mutun ya tashi ba baki ga kuturta!"
Sofia tace"nifa saboda tsoro jiya bayan mun dawo gida, dana shiga daki karatun kur'ani na kunna awayata sai da asuba na kashe"
kowa yana tofa albarkacin bakinshi banda hajjaty dake tsaye ta goya hannayenta kan kirjinta, ita dai hankalinta bai kwanta da ciwon marwa ba!
Jin motsin buɗe kofane yasa sukayi shiru suna jiran tsammani, A hankali sheikh Imam Ya fito daga dakin, farar jallabiya ce a jikinsa, ya ɗaure kanshi da rawani, hannun ɗaya ruƙe da cazbaha.
cikin girmamawa suka fara yi mashi sannun da fitowa da fara'a ya amsa masu
tambayoyi suka fara jere mashi kamar yan jarida
"Malam ya ake ciki? Ya jikin marwan? Ta samu lafiya? Dagaske aljanune suka shafe ta? Sheikh zamu iya shiga ciki mu duba ta?
Ɗaya bayan ɗaya sheikh Imam Yake kallonsu, Ya rasa wa zai fara amsa ma tambayar shi sun ƙi bari Yayi magana, ya fahimci sun matsu da su san awani hali take ciki.
har ya buɗe baki zai yi magana Saiga baba obie tare da pravin sun nufo wurinsu.
Miƙa mashi hannu baba Obie yayi suka yi musabaha"sannu da kokari sheikh, Ya mai jikin? An dace kuwa"? Fuskarshi da fara'a yace"mu shiga daga ciki ku gani da idonku.." da sauri suka nufi dakin su hajjaty suna abiye da bayansu, agaban katifar marwa suka tsaya cirko cirko, tana a kudundune cikin bargo jikinta sai makekketa yakeyi, tuni pravin Ya haɗe fuska tamkar bai ta6a dariya ba, ga wani gumi mai ɗumi daya wanke goshin shi, Hanky ya zaro ya fara goge zufar.
An rasa wa zai fara cire bargon murmushi sheikh imam yayi don ya fahimci tsoro suke ji, da zolaya yace ma baba obie"baba kai yakamata ka fara cire bargon mu gani" waro ido baba obie yayi haɗi da girgiza kai yace"ya zakai min haka? dan Allah kadaina wannan maganar, kai dai daka fara aikin kai yakamata ka karasa ladarka.."
yar dariya Sheikh Imam yayi tare dakai hannu ya ruƙo bargon ya fara jan shi ahankali, pravin kamar ya daura hannu akai ya fasa ihu haka yakeji duk ya rasa sukuninshi kamar wani munafiki sai cizon yatsa yakeyi..
Su hajjaty sun baza na mazurai suna jiran ganin marwa, gabansu sai faduwa yakeyi .
Lokaci da sheikh Imam ya ƙarasa cire bargon, gaba ɗaya suka zabura suna kallonta idanunsu azazzare cike da mamakin ganin bakinta Ya buɗe sunyi matukar razana da lamarin, ta ko'ina zufa ce ke tsastsafowa ajikinta kamar wadda aka tsamo daga cikin tafki, kafafunta sun miƙe daga lauyewayar da sukayi, amma yatsun hannayenta basu dawo daidai ba har yanzu da kuturtar sai dai yatsun sun ɗan saki ba kamar farko da suka matse ba har suna fidda ruwa mai yauƙi yanzu babu ruwan.
Kusan Atare su hajjaty suka ambaci sunanta da karfi Marwa.
buɗe baki tayi zatayi magana sai dai ta kasa sautin muryar baya fita dakyau gura gura take magana kamar wadda harshenta ya ƙone kwata kwata ba'a iya gane me take cewa, har sun fara murna taji sauki ashe da sauranta, pravin har zai fita daga dakin jin takasa magana yasa shi dawowa ya tsaya yana kallon marwa afakaice yake sakin murmushin mugunta.
Jikin su hajjaty yayi sanyi lakwas, har sun fara sharar kwalla
Baba obie yace"Ikon Allah! sheikh dagaske dai jinnune suka shafe ta? Ya fada cike da son jin karin bayani, a tsanake sheikh imam ya ce
"Eh, bakaken aljanune a jikin ta, sune suka haddasa mata ciwon..." waro idanu waje su hajjaty sukayi wani irin tsorone Ya kamasu murya na rawa abla tace"dama Aljanu suna iya canza ma mutun halittar shi" jinjina mata kai sheikh imam yayi"fiye da haka ma zasu iyayi.." kallon kallo suka jefawa junansu.
Aruɗe baba obie ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!
Zuƙunnawa sheikh imam yayi daga gaban katifar marwa idanun shi akan fuskarta Ya soma magana"kada ki sanya damuwa aranki, Allah yana atare dakai, duk wani abu da kika ga ya faru dake mukaddarine daga Allah, bana so ki kuntata kanki, ko ki ƙyamaci kanki, balle kiyi tunanin illata kanki saboda wannan lalurar data same ki, kiyi kokarin cinye jarabawarki kada ki gaza, Aljanun da suka haddasa maki ciwon nan suma bayin Allah ne, babu abunda ya fi karfin mahaliccin mu...." tun da ya fara magana idanun marwa suka cicciko tab da kwalla ita kadai tasan me take kitsawa aranta.
"nayi alƙawarin zan taimaka maki amma fa dole sai kema kin taimaki kanki, kiyi kokarin bin abun da Allah da Manzonsa sukace ayi domin samun kariya daga sharrin su, da zuciya ɗaya in sha Allah zaki ji sauƙi, jikinki zai dawo kamar yadda kike ada" jinjina mashi kai tayi alamar ta gamsu da maganar shi.
"Ma.. malam muma ataimaka mana dan Allah, ka faɗa mana hanyoyin da zamu kare kan mu daga sharrin su"
cikin shesshekar kuka abla tayi maganar.
murmushi sheikh imam yayi tare da kallonsu ɗaya bayan daya sai yaji sun bashi tausayi ganin yadda jikinsu ke ta kerma kamar mazari
"Ku samu wuri ku zauna zanyi maku bayani" da sauri suka kewaye sheikh imam suka zauna kan ƙasa suna jiran jin me zaice.
Miƙewa yayi da sauri ya ɗauko kujerar mirror Ya ajiye agaban baba obie don ya zauna.
"Nagode sheikh" ya fada tare da zama kan kujeran.
Tun shugowar pravin dakin sheikh imam bai ɗaga ido Ya kalle shi ba, sarai ya san da zaman shi, dama tunfil azal basa jituwa tsakanin su ko gaisuwa bata ta6a haɗasu ba,
Shiru yayi kamar akwai abunda Ya hana shi fara magana, wayar pravin ce ta fara ringing daga cikin aljihunsa da sauri ya fuce daga dakin don ya amsa kira.
Fitar shi keda wuya sheikh Imam Ya fara magana yana duban marwa cikin tattausa harshe yace mata"kiji tsoron Allah! Rass gabanta Ya fadi, su hajjaty suka kalle shi da alamun rudani akan fuskokin su.
"Idan akwai wani abu da kike aikatawa badai dai ba to ki daina! Sau dayawa mu muke ja ma kanmu shiga cikin masifa, Allah ya gatanta mu ya bamu hanyoyi da dama da zamu iya ba kanmu kariya amma muna wasa damar mu...." ga dukkan alamu Sheikh imam Ya canza maganar daya dauko da farko hannunka mai sanda yayi mata kuma ta fahimce shi hakan yasa ta duƙar da kanta ƙasa hawaye suna cigaba da wanke fuskarta.
"Kina yin azkar? Girgiza mashi kai tayi alamar a'a
"Baki iya ba ne"? Ɗaga mashi kai tay alamar eh.
"Ya salam! Wannan wani irin ganganci ne? Da ranki da lafiyarki? Wallahi da ace kina kokarin kiyayewa babu wani mahalukin daya isa ya cutar dake in ba Allah ne ya kaddara za'ayi galaba a kanki ba, azkar garkuwa ne agare mu, ita kuma addu'a da kike gani takobin mumuni ce kuma ita addu'a tana iya canza kaddarar mutun, daga mummuna zuwa mai kyau.
Nasiha ya fara yi mata jikinta yayi sanyi lakwas, su abla tuni ido ya raina fata don su kansu bakowane keyi ba har kwara hajjaty itada ta musulta daga baya tana kokarin yi akai akai
"Gaba ɗaya inaso ku bani aron hankulanku, ku saurari abunda zan fada maku..." amsa mashi sukayi da toh,
Shiru yayi jim kafin ya fara magana"abunda ya kamata ku sani shine, Zikirin safe da yamma yana da matuƙar mahimmanci sosai, wanda inda Musulmi yasan mahimmancin sa da kuma kariya da yake bashi da bai barshi ba koda na kwana ɗaya ne, don haka ina ƙara jan hankulan ku da Ku yawaita Lazimtar Zikirin safe dana yamma.." atare suka hada baki wurin furta in sha Allah malam zamu kiyaye
Shiekh imam ya ɗaura da cewa"abu na gaba Yin alwala, mutum ya kasance yana yawaita zama cikin tsarƙi domin hakan na bada kariya, bayan haka akwai Qiyamul laili, da kuma Neman tsari yayin shiga bayan gida (toilet) idan zaku yi bacci ku yi alwala, sannan ku karanta ayatul kursiyu bayan ita sai falaki da nasi suna da Muhimmanci sosai..." jinjina kai kowan nan su yayi sheikh imam ya numfasa yana dubansu kafin ya dasa da cewa
"Sannan Faɗin La’ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa Ala kulli shai’in kadir sau ɗari safe da yamma
Faɗin Bismillahillazi la ya durru Ma’asmihi shai’un fil ardi wala fissama wahuwa ssami’ul alim” sau uku safe da yamma, Faɗin “A’uzi bikalimatillahit-tammat min sharri ma khalaka” sau uku safe da yamma"
baba obie ya nutsu yana sauraron sheikh imam har cikin ranshi yaji dadin yadda ya zaunar da yan aikin gidan yana koyar dasu yadda zasu kare kansu hakan ba karamin faranta ranshi ranshi yayi ba, shi kanshi ya karu da sheikh imam.
"Malam, wallahi ni yawan mantuwa gare ni, kona yi kokarin yi sai wani abun yaja hankalina..." Sofia ce tay maganar, shiekh imam Yace"akwai islamic apps na waya, da zaki iya sauke wa.." da sauri hajjaty tace"ina da shi zan tura mata nima dashi nake amfani, shi yake tunasar dani lokacin yin ibadata da kuma lokacin yin azkhar" murmushi sheikh imam yayi idon shi akanta yace"kinyi masu wayau, zaman tare baice haka ba, meyasa tuntuni baki sanar da su ba"?
Sunnar da kanta ƙasa tayi
Calmy ta furta"ay ni bansan ba su amfani da shi ba"
Gyaɗa kai yai"haka ya dace, In ka san abu na karuwa ne, to ka yi kokarin sanar da wasu suma su amfana, na tabbata da ace shirin labarina ne aka saki jiki na rawa zaki fada masu koba haka ba"? Gaba daya suka sanya dariya.
Murmushi baba obie yayi, shima sheikh imam din murmushine akan fuskarshi.
Baiwar Allah marwa duk da halin da take aciki saida tayi murmushi fuskarta sharkaf da hawaye...
Nasiha ya cigaba dayi masu akan su daina shagala duk runtsi duk wuya kada su yi sakaci da ibadarsu da kuma neman tsari daga gurin Allah, cike da gamsuwa suke sauraran shi daga bisani yace Idan har ku ka kiyaye zikirorin dana faɗa maku, sannan ku ka kuma ƙaurace wa saɓon Allah toh haƙiƙa Allah zai kare ku daga kowani irin sharri, kuma zaku yi rayuwa cikin kwanciyar hankali domin da Ambaton Allah ne da yimasa biyayya ake samun natsuwa. Allah yasa mudace" atare suka amsa mashi da ameen haɗi dayi mashi godiya
Baba obie yace"sheikh muna godiya sosai, jazakallahu khairan..." da fara'a ya amsa mashi da ameen...
Kafin ya kalli Su abla"ina bukatar mutun ɗaya da zai dinga kula da marwa"
shiru su ka yi kowa tsoron kusantarta ya ke yi, yanzu ma da suke adakin don sunga sheikah imam ne ga baba obie shiyasa suka saki jiki.
"Kada ku bani kunya mana! Kun riga da kunsan lalurar nan ba ita ta daura ma kanta ba! idan har kuka ce zaku juya mata baya ko ku ƙyamace ta zaku sa ta tsani kanta ne harta aikata ma kanta abunda bama fata, ayanzu bata da wasu yan uwa na kusa da ya wuce ku, ku take gani amatsayin yan uwanta wadanda zasu share mata hawaye...."
cikin sanyin murya hajjaty tace"wallahi bani ƙyamar marwa, kawai abune da bamu saba gani ba, muna jin tsoro amma in sha Allah zamuyi kokarin bata kulawa, ni nayi alkawarin zan dinga zuwa dubata...."
Shiekh imam yace"Alhamdulillah, naji dadin jin hakan daga gare ki, zuwa anjima in sha Allah zan aiko maki da magunguna na musulunci, sannan kafin in tafi zan kar6i contact dinki saboda in tura maki addu'o'in da zaki dinga tofa mata aruwan wankanta dana shanta,.."
"Toh malam, muna godiya Allah ya saka da alkhairi..."
miƙewa yayi bayan yayi masu sallama baba obie ya ruko hannun shi suka fita daga dakin....
Kamar jira suke sheikh Ya fita daga dakin da sauri su abla suka gudu zuwa kitchen Ya rage saura Hajjaty adakin.
Bata san sa'adda ta fashe da kuka ba, gashi ba halin Yin magana, da hannu ta dinga bugun katifa tana kuka, da sauri hajjaty ta rukota tana lallashin ta idanunta cike tab da kwallo, wani irin tausayintane Ya kamata.
"Marwa ki daina kuka, In sha Allah zaki ji sauki ki dawo kamar yadda kike ada, nayi alkawarin zan taimaka maki muyi duk abunda sheikh imam yace"
tunda hajjaty ta fara magana marwa tayi shiru tana kallonta wallahi tayi danasani yafi sau a ƙirga, kuma tayi mamakin yadda hajjaty ta amince zata kula da ita sa6anin sauran yan uwansu da suka gudu daga dakin.
Bata ta6a tsammanin hajjaty tana da saukin kai, da tausayi ga mutunci irin na yau ba, sai taji ta tsani kanta, hakanan batai mata laifin komai ba mace mai kyakkyawar zuciya amma saboda abun duniya ta amince zata yi mata leƙen asiri don abata matsayinta akuma koreta daga gidan wa'iyazubullah, bakomai ta tuna ba face hajiya saratu, ita da tayi silar jefata halin da take aciki, amma kwata kwata bata nuna damuwarta akanta ba, ko kalmar sannu ay ya kamata ta furta mata, ayanzu ta gane wasu mutanan sai kana da amfani agurinsu suke kula ka da zarar sunga bazasu amfana dakai ba sai su watsar dakai, tayi danasani taso ace tana da baki da yau saita fallasa asirin wanda yayi silar jefata halin da take a ciki ko da zata rasa ranta ne❗
Amma duk da haka bata makaro ba, ta ɗauki alwashin saita tona asirin wanda ya cutar da ita!
"Marwa"! Muryar hajjaty ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula
"Kiyi hakuri Kinji yar uwata, bana son ganin hawayenki, nasan kina jin yunwa bari na kawo maki abinci in kika kammala ci sai in taimaka maki kiyi wanka..." kifa kai marwa tayi jikin pillow ta rushe da kuka mai tsuma zuciya, tamkar ranta zai fita, zuciyarta ta karaya, a halin yanzu ba rayuwarta ta ke jima tausayi ba, rayuwar hajjaty itace abun tausayi....dakyar hajjaty ta shawo kanta har ta samu marwa ta daina kuka, da sauri ta mike taje kitchen donta haɗo mata abunda zata ci.
___________________________________✍️
*Hajiya Saratu*
A zaune take kan mirror chair jikinta sanye da sleeping gown ta manyan mata, fuskarta sam babu walwala ta zabga tagumi da hannunta ɗaya bata jima da farkawa daga bacci ba, ko wanka ta gaza shiga tayi, saboda rashin kwanciyar hankali, duk bayan yan mintuna saita duba wrist watch din hannunta, lumshe idanunta tayi yayin da acan ƙasan zuciyarta take tariyo maganganun da suka tattauna ita da Hajiya laurat a jiya, bayan ta taso daga office tsoro da fargaba suka hana ta dawo gidan, tace ma driver dinta ya wuce da ita aso villa acan suka haɗu da hajiya laura tun daga kan yanayin fuskar Hajiya saratu ta fahimci babu lafiya akwai wani abu da yake damunta, bayan sun zauna a pool yard masu yi masu hidima suka kawo masu coffee da kayan marmari tace mata bismilla su fara sha, girgiza kai tayi alamar bazata sha ba, hajiya laura tace wai meke damunki ne? kiyi magana mana, a shirye nake da in taimaka maki don mu shawo kan matsalar, ajiyar zuciya hajiya saratu ta sauke tana faman yamutsa fuska ta kwashe komai daya faru dangane da ciwon marwa ta sanar da hajiya laura.
"Wallahi ina cikin tashin hankali, zama gidan ma ya gagareni, yanzu haka da kika ganni daga office ko gida ban wuce ba nayo nan don in fada maki halin da nake ciki"
Shiru hajiya laura tayi jim da alamun ruɗani akan fuskarta tace"ni abunda bangane ba, kina nufin dare ɗaya ta farka da lalurar"?
ɗaga mata kai hajiya saratu tayi, al'amarin ya ɗaure mata kai
"Kuma an kaita asibiti?
"Bani da masaniya, amma bari na kira baba naji halin da ake ciki" tay maganar tare da curo waya ta danna ma baba obie bayan ya ɗaga, ta tambaye shi awani hali marwa take a ciki, ya sanar da ita abun da likitoci suka ce, tayi mashi sallama ta ɗago ta kalli hajiya laura da tayi zugudum tana kallonta, ta sanar da ita abun da baba obie ya faɗa mata, ga mamakinta sai taga hajiya laura ta saki murmushin gefen fuska takai hannu ta dauki cup of coffee ta kurba still da murmushi akan fuskarta, hakan ba karamin ɗaure ma hajiya Saratu kai yayi ba fuskarta a ɗaure tace"bana son iya shege meye abin murmushi aciki?
Yar dariya laura tayi"kwantar da hankalinki mutuniyata, kinsan wani abu"? Girgiza kai tay alamar a'a
"Wallahi ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba yarinyar nan marwa silar ciwonta yana da alaƙa da aikin leƙen asirin da kika sanya ta!! Hankali atashe Hajiya saratu ta zaro ido tana kallon laura aruɗe ta furta"ban..ban gane me kike nufi ba?
"Ke yanzu har sai nayi maki bayani? Yakamata ki gane mana, kiyi amfani da brain dinki, ciwon yarinyar nan aikin asiri ne, wlh ture akayi mata, in ba haka ba taya za'a ce rana ɗaya mutun ya tashi da cutar kuturta sannan ba baki, ai ke daga ji kinsan ɗaura mata ciwon akayi, Ni abun da na fahimta watakil hajjaty ta kama marwa tanayi mata leƙen asiri, shiyasa ta kulle mata baki don kada ta iya furta magana, bayan haka ta ja mata cutar kuturta don kada ta samu damar da zata yi rubutu da hannayen ta balle harta tona mata asiri...."
Dafe kai hajiya saratu tayi yayin da zuciyarta ke bugawa da karfi da karfi gaba ɗaya tabi ta ruɗe.
Hajiya laura taci gaba da cewa"hmmm wallahi ɗan adam ba abun yarda bane! Dama na jima ina zargin hajjaty, indiyawan nan basu tsoro Allah, ko a fina finan su zakiga suna yawan zuwa wurin bokaye don ayi masu asiri, matar nan munafuka ce wlh, tana amfani da rauhanai shiyasa ta mallake mutanan gidanku har ta samu gindin zama take iya shegen data ga dama, yanzu gashi ta kassara rayuwar marwa....."
Runtse idanu Hajiya saratu tayi, hankalinta Ya tashi har wani dishi dishi take gani a idanunta muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku"!
hajiya laura tace"ay mun sha ja maki kunne akan ki kori hajjaty daga gidan kika ƙiya, ay ni banma san ya akai kika yi gangancin da pravin ya ɗauko maki bakauya yar kauyan india masu bautar shanu ya ajiye maku agida, to wallahi kwara tun wuni ku dauki mataki akanta in ba haka ba hmmmm nan gaba Allah kadai yasan me zata aiwatar.." maganganun hajiya laurat sun tsaya mata arai sun kuma ɗaga mata hankali, bata ta6a jin faɗuwar gaba da tashin hankali irin na jiya ba, ta jima a vila suna tattaunawa da hajiya laurat har shawarwari ta bata dangane da yadda zata kare kanta daga sharrin hajjaty da kuma hanyar da zata bi don ta gano ainihin wacece ita.
Bayan sunyi sallama da juna, hatta shiga motarta tana zullumi da fargaban hajjaty, ta tsorata da ita ba kadan ba, ko bayan data dawo gida kasa shiga bedroom dinta tayi saboda tsoro, dakin baba obie ta fara shiga ta zauna wurin shi har saida aka fara kiran magrib ya tashi zai tafi masallaci kafin ta dawo dakinta sam ta kasa sukuni wani irin tsorone Ya kamata babban tashin hankalinta kada hajjaty tayi silar kassara rayuwarta kamar yadda ta kassara rayuwar marwa ya ilahi abin ya ɗaga hankalin ta, ba ita ta runtsa ba adaren jiya har saida pravin ya dawo ya fara mata faɗa akan rashin dawowarta da wuri, baiwar Allah saboda tsoro ta kasa mayar mashi da martani saima ta rungumeshi ta ƙanƙame shi hakan ba karamin daure mashi kai yayi ba, yaja hannunta suka zauna gefen gadon ya tambayeta meke damunta cikin sanyin murya tace mashi bata jin dadin zuciyarta tsoro take ji saboda abun da ya faru da marwa shiyasa taki dawowa gidan..
murmushi pravin yasaki har cikin ranshi yaji dadin tsoratar da tayi saboda shi agurinshi damace ya samu da zai dinga juyata son ranshi, tun da ya gano lagwon ta, a daren ranar sai da ya biya bukatar shi da ita, son ranshi ta sakar mashi jiki yayi abunda yakeso dama ya kwana biyu bata bashi hakkin shi ba.
Bayan ta dawo daga duniyar tunanin ta miƙe tana zagaye ɗakin tana tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin dole ta ɗauki mataki! Ta tsani hajjaty fiye da yadda ta tsani mutuwarta❗
__________________________________✍️
Lokacin da Benazir ta farka daga bacci, da wata irin kasala ta buɗe idanunta wadanda suka kaɗa jawur muryarta na rawa ta fara ambaton sunan Angel mikewa zaune tayi kan gadon, hannunta ɗaya dafe dakanta, ga wata faduwar gaba da take ji
"Babyna! Where are you? Mami Ina Angel dina? Bata nan ne? dakyar ta iya saukowa daga kan gadon tayi miƙa haɗi da yin hamma kafin ta fara baza ido tana neman Unaisah, ita kadai ce adakin, hajiya layla taje office din dr jazz domin amsa kiran da yayi mata.
"Angel! Angel! Can't you hear me calling you? Where are you?" Da karfi tayi maganar tare da nufar kofar toilet ta kwankwasa"pls idan kina ciki, Ki amsa min babyna kinji..." ta fada tare da kanga kunnanta jikin kofar, shiru taji ba a amsa mata ba, da alama babu mutun aciki, hakan yasa tay pushing door din ta shiga ciki tana bin ko'ina da kallo kwata kwata bata ga kowa ba, ji tayi kamar ta daura hannu akai ta fasa ihu, gaba ɗaya tabi ta rude dama saida ranta ya bata cewar ba lallai ta ganta ba
Fitowa tayi daga toilet din, ta nufi bed dinta, ta zukunna tana leƙen karkashin gadon don taga ko anan ta buya
Adai dai lokaci hajiya layla ta shigo dakin hannun ta ruke da takardar sallama kaitsaye idonta suka sauka akan benazir.
rass taji gabanta Ya faɗi ganin yadda tabi ta ruɗe tana ambaton sunan babynta, tuni taji hawaye sun ciko idonta sam takasa karasa shiga ciki saboda fargaban amsar da zata ba benazir idan ta tambayeta Ina babynta, batasan ya zatayi da ita ba, ga tsananin tausayinta da take ji.
"Mommy"! Muryar dr shurieim ce ta katse mata zancen zucin ta, aɗan firgice ta juya baya tana kallonsu, a jere suka nufo ta su uku ne, Shureim da Alhaji ubaid tare da hajiya sarah fuskokinsu dauke da murmushi, dakyar ta haɗiye damuwarta ta nufe su tana fara'a suka rungume juna ita da hajiya sarah bayan sun raba jikinsu, shureim Ya matsa kusa da mommynsu Ya rungumeta tare da manna mata kiss gefen fuskarta.
"Sannun ku da zuwa"
hajiya sarah tace"ay min afwa wlh banji dadi ba, jiya banzo na duba jikin benazir ba, ban kuma kira naji ya kuke ba" murmushi hajiya layla tay"kai haba ba komai wlh, ay kinama kokarin zuwa dubata, wlh kada kiji komai benazir tana cikin koshin lafiya.." tai maganar tare da kallon Alhaji ubaid dake kallonta, harara ta ɗan watsa mashi afakaice saboda taji haushin rashin kiransu da baiyi ba jiya, cikin sanyin murya yace"kiyi hakuri jiya bana jin dadin jikina ne shiyasa ban kira ba, naso ma inzo dubaku" ta6e baki tayi"ay kwara da kukazo gaba ɗayanku, ga Benazir can tana neman yarta, kuma yarinya masu ita sun dauki abunsu, dama likita ne ya bada maganin bacci aka bata tasha kafin aka rabata da yarinyar yanzu gata can ta hargitsa dakin tana neman yarta"
Hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Dr shureim yace"baiwar Allah, na tausaya mata, wlh dama saida naji fargaban zuwan ranar nan, gashi sun shaku da yarinyar"
Alhaji ubaid yace"yanzu ya zamuyi jama'a? ay ni nayi zaton ma zamu taras da su ashe har sun tafi, gaskiya banji dadi ba, ban ta6a haduwa da yarinyar ba balle inmata godiya ita da iyayenta da sukai mana halacci.."
Hajiya layla tace"wannan duk mai saukine tunda aneelah tasan gidan iyayenta, wata rana saimuje muyi masu godiya, yanzu dai muji da maganar benazir! Menene mafita"!
Hajiya sarah tace"ni nama rasa ta cewa wlh, amma ni aganina, abun da yakamata shine mu lalla6ata mu fada mata cewa daddyn yarinyar yazo ya dauke ta sun tafi mall, da anjima zai dawo da ita, saboda mu samu mu bar hospital ɗin da ita, in ba haka ba dakyar zata amince ta bi mu" gaba daya sunyi amanna da maganar hajiya sarah, atare suka nufi dakin, suna shiga suka isketa zaune gefen gado duk ta yamutse gashin kanta kamar na mahaukaci, ga fuskarta sharkaf da ruwan hawaye.
Atare suka hada baki gurin yi mata sallama, da sauri ta miƙe tana kallonsu, muryarta na rawa ta furta"mami! Ya shureim! Daddy! aunty Sarah! Ina babyna? Tana ina? Na duba ko'ina banganta ba! Dan Allah ku fadamin waya daukar min babyna? Wlh in har ba'a dawo min da itaba, zuciyata zata buga in mutu kowa ya huta"!
kusan atare suka haɗiyi yawu kowa yasha jinin jikinshi, dakyar hajiya Sarah tayi karfin halin furta"haba Benazir? Meyasa zaki daga hankalinki akan yarki? Waya isa Ya rabaki da ita? Ki kwantar da hankalinki, Yarinyar nan takice halak malak.."bubbuga kafafunta tayi saika rantse da Allah batasan me take ba, bayan da hankalinta tsabar pretending ne
"Ni kawai ku fadamin tana Ina? Meyasa banganta ba"?
"Benazir, daddynta ne ya dauke ta, sunje mall zasuyi maki siyayya da anjima zai dawo da ita gida..." cike da fargaba hajiya layla tayi maganar, shiru tayi jimm na ɗan wani lokaci kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya fuskarta ayamutse tace"mami dagaske Taj yazo nan? Shi ya dauki Angel dina"? Murmushi suka sakar mata, dr shureim yace"kwarai kuwa dagaske shiyazo ya dauketa.."
"Amma bai tambayeni ba? Ko ya daina sona? Ta fada tana zare masu eyes dinta
Alhaji ubaid yace"ya tambayeki mana, ay saboda ke sukaje yin siyayyar, yana son ya faranta miki rai.." wani irin tsallan murna ta daka tana dariya.
kallon kallo su hajiya layla suka jefawa junansu hankalinsu atashe, wato akwai gwarama idan suka koma gida taji shiru taj baizo mata da yarta ba.
"Mommy zamu jiraku a mota" dr shureim ya fada tare da kallon daddynsu atare suka fuce,
Badajimawa ba, saiga su sun fito tare da benazir har ta canza kayan jikinta ta maida kayan da aka kawota asibitin da su, a backseat na motar dr shureim ta zauna, yana agaba tare da alhaji ubaid, Hajiya layla kuma a motar hajiya sarah ta zauna, a jere motocin suka fuce daga asibitin.
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 40 Complete
by
Novels Elite Admin
September 03, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
Ex-Prisoners💓
Gaba ɗayan su suna zaune kan sofas na falo.
"Aunty ummi wai yaushe angel dinmu zata dawo gida ne? Jemimah ce ta faɗa tana faman haɗe fuska.
Sajeed yace"ni ma na damu da rashin dawowarta gashi tun jiya ko awaya bata kira munji muryarta ba.."
Batool tace"dan Allah aunty ummi ki kira mana ita mu gaisa, ko hankalinmu ya kwanta" tayi maganar tana kallon Ummi, gaba ɗaya hankalinta yana akan wayar hannunta da alama chatting takeyi batasan ma me suke cewa ba..
"Dama kun daina wahalar da kanku gurin yi mata magana, saboda hankalinta ba akanku yake ba.." acewar Parvin.
ɗaga murya batool tayi"Aunty Ummi..." aɗan firgice ta ɗago da ido tana kallon ta"batool! Lafiya kike kwala min kira kamar baki san ina akusa ba"? Dariya su naufal sukayi
Batool ta marairaice mata fuska"aunty ummi muna ta yi maki magana kin yi shiru baki amsa mana ba.." maida hankali tayi akansu
"Okey, Ina sauraronku lafiya"?
Kafin wani ya furta magana acikinsu ba zato ba tsammani, sallamar Unaisah Ta katse masu hanzarin su, kusan atare suka miƙe da gudun gaske suka nufeta hada masu tuntu6e garin sauri, Batool ce ta fara karasawa gareta ta faɗa jikinta suka rungume juna kamar zasu koma mutun ɗaya sai faman tikar dariyar murna sukeyi, gaba ɗaya sukayi mata rumfa kamar zasu lasheta yadda kasan sunyi shekara basu ganta ba,
Bayan ta raba jikinta daga na Batool, tabi su ɗaya bayan daya tayi hugging din yan mata, sajeed Ya buɗe hannu zai rungumota tayi saurin ja da baya tunawa da maganar aunty ummi itafa yanzu tsoran hada jikinta da namiji take yi saboda gudun kada ta samu ciki.
*_______________________________Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
Bayan ta raba jikinta daga na Batool, tabi su ɗaya baya daya tayi hugging din yan mata, sajeed ya buɗe hannu zai rungumota tayi saurin ja da baya tunawa da maganar aunty ummi itafa yanzu tsoran hada jikinta da namiji take yi, gani take kamar ciki zai shiga, har naufal ya kai hannu zai yi hugging dinta again ta ƙara ja da baya hadi da girgiza kan ta, mamaki ne ya kama su Naufal ganin yadda ta hana su ta6a ta kamar taga wani mugun abu.
"Meyasa mu bazaki rungume mu ba, ko bakiyi kewarmu ba"? murmushi ta sakar masu"kuyi hakuri ba haka bane, nayi missing dinku gaba ɗayanku.." girgiza kai sajeed yayi ni ban yarda ba Allah, naufal yace"kinfi son su batool shiyasa kika rungumesu ko"? Javed ma yace"ni banji dadi ba, wariya kike nunawa atsakanin mu.." gwalo parvin tayi masu, Sarah tace"nan fa ba prison bane, mun riga da mun gane jinsin mu, ku maza mu mata don haka kuyi hakuri no more hugs atsakanin mu ehe" dariya suka sanya.
Batool tace"bayan haka aunty ummi ta fada mana babu kyau mace ta rungume namijin da ba muharramin ta ba, koda ruke hannunsa ne" wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Unaisah dake sauraronsu taji dadin yadda suka fara gane abunda ake koya masu.
Gaba daya kalamansu akan kunnan chief dake abakin kofar shigowa falon maganar Batool ta faranta ranshi dama yajima yana son a fahimtar dasu game da mannewa juna da sukeyi amma yanzu alhamdulililah sun fara hankali
Mubeen yace"amma ay a prison mu na yi kuma baku ta6a hana mu ba"
Harara Parvin ta watsa mashi"ay lokacin muna a jahiliya period ne, yanzu kan mage ya waye..."
maganarta ta basu dariya, fashewa ummi tayi da dariya ashe tana tsaye abayansu.
Unaisah na ganinta tayi sauri nufarta suka rungume juna
"Oyoyo my babe Unaisah, welcome back home munyi kewarki abar kaunarmu"
"Nima nayi kewarku aunty ummi fatan na same ku lafiya..." ta fada tare da dago da kanta
"Lafiyalou Unaisah, ya jikin patient din? Ko har an sallame ta"!
"Yau za'a sallame shiyasa na taho gida, taji sauƙi sosai, tama ce in gaishe mata da ku" murmushi ummi tayi"Allah sarki muna amsawa, wlh naji dadin samun lafiyarta..."
Kallon su Naufal tayi sun haɗe fuska babu annuri duk don saboda taƙi hugging dinsu, jemimah ta tuntsire da dariya tana fadin wai ma haushi suke ji don kinki rungumarsu jibar su ma kattai da su.."bata ƙare maganar ba, Sajeed Ya tallabi keyarta nan take ta fara ta6e baki zatayi kuka,
Naufal Ya ɗaga hannu zai buge bakin da sauri ummi ta ruƙo hannun shi tana dariya tace"ya isa haka pls, wasa takeyi maku"
"Pls Angel, To mu gaisa da hannu" Sajeed Ya fada tare da mika mata hannu shi, shiru tayi jimm har ta miƙa hannu zata ruko nashi ba zato ba tsammani chief ya shigo falon yayi hanzarin daura hannunshi akan na Sajeeed, gaba daya suka shiga nutsuwarsu sam basu san da zaman shi ba.
cikin girmamawa suka fara gaishe da shi, ummi ma ta gaida shi ya amsa mata, Sajeed baki ya ki rufuwa saboda sunyi musabaha da chief, yaƙi sakar mashi hannu.
"Pls chief can you hug me"? Ɗaga mashi gira chief yayi tare da yin huggin dinshi, wani irin dadi ya lullu6e shi.
"Nima pls" acewar Naufa, miƙa mashi hannu yai da sauri naufal ya rungume chief harwani bude hanci yakeyi yana shakar kamshin turaren shi
Kunya ta hana Haris yin magana, lura da hakan yasa chief mika mashi hannu da sauri ya matsa kusa da shi suka rungume juna, bayan ya saki haris Ya rungume javeed da mubeen wayyo dadi, tsabar murna kamar anyi masu albishir da gidan Aljanna, Ummi sai satar kallonshi takeyi saboda kyan da yayi mata, kai ko amafarki bata ta6a tsammanin zata haɗu da chief face to face ba sai gashi cikin ikon Allah ƙaddara ta haɗa ta zama da shi agida ɗaya, ta yaba da hankalinshi, nutsuwarshi, wayewarshi, saukin kanshi da ilminsa komai Allah Ya bashi uwa uba ga tarin Dukiya.
Gaba ɗaya yan matan sun ɗaure fuska, ganin su naufal sun fara yi masu gwalo saboda chief ya rungumesu..." bubbuga ƙafa Jemimah tayi muryarta da shagwa6a tace"wayyo Allah, mu ma dan Allah yaya chief ka rungumemu..." dariya sajeed yayi tare da cewa"no bazai rungumeku ba, jinsin ku daban namu daban, kowa ya rungumi jinsinsa koba haka ba guys"? Ya fada cike da shakiyanci yana kallon su Javed,
Naufal yace"haba kamar dai a jahiliya period? ay haramunne na mijin ya rungume mace, nan fa ba prison bane kan mage ya waye.. " gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Unaisah hada dafe ciki, chief dake atsaye ya goya hannayenshi kan kirjin shi, idanunshi na akan fuskarta wani irin kallo yake binta da tashi ta saki baki tana ta dariya fararen hakoranta tass da su bata ta6a jan hankalinshi irin na yau ba.. Babu wanda Ya lura da irin kallon da chief yakeyi mata gaba daya ya shagala
A hankali ya kau da idon shi Ya juya Ya nufi part din shi.
"Wallahi inason ku yan uwana, kuna faranta min raina, Allah yabarni daku, wallahi mai rabani daku sai Allah, shiyasa naketa zumudin in dawo gida saboda nasan anan ne kadai zan samu farin ciki da kwanciyar hankali...." cikin jin dadi tayi maganar,
Ummi ta ruko hannun"mu shiga daga ciki, mun barki atsaye.." gaba ɗaya suka nufi Sofas din falon, kowan nan su Ya samu guri Ya zauna, shi dai sajeed kalmar muharram ta tsaya mashi arai, so yake yaji wanene muharramin nan da shi kadai zai iya rungumar mace, abun da bai sani ba ita kanta Batool din batasan wanene muharram ba, tabbas ummi ta ta6a faɗa mata amma karatun bai zauna akanta ba.
"Kinyi breakfast acan asibitin" cikin kulawa ummi tayi mata maganar,
"Eh, nayi" labari ta fara basu na Benazir duk suka kasa kunne suna sauraranta
"Matar tana sona nima ina sonta aunty ummi, mun shaku da juna, har grandma dinta muna mutunci da ita dayake adaki daya muke kwana kuma kinsan wani abu aunty ummi.." girgiza mata kai tay alamar a'a
"bata gane cewa ni ba yarta bace, bansan wani hali zata shiga ba idan ta farka daga bacci taga bani akusa da ita..." cikin sanyin murya tayi maganar.
Ummi tace"baiwar Allah, wallahi ta bani tausayi, ubangiji Allah Ya bata lafiya, inayi mata fatan Allah ya bata wata yar" suka amsa mata da ameen
"Wani abu daya bani mamaki aunty ummi, matar tana kama da Batool yadda kikasan ita ta haifeta Allah..." murmushi ummi tayi, batool ta washe baki jin an ambaci me kama da ita"wallahi har naji ina son ganinta" murmushi unaisah tayi"hmmm ai ba ita kadai ke kama dake ba, ranar dana fara ganin yayanta dr shureim saida na ɗan razana, yadda kikasan yayi kakinki, ke gaba dayansu kamar family dinki ne..." wani irin faduwar gabane Ya darsu a zuciyar Ummi, sunan dr shureim da Unaisah ta faɗa ya tsaya mata aranta.
"Dan Allah daske kike? Acewar batool,
"Wallahi dagaske nake, Allah ya zuba masu ruwan kyau, grand ma dinta balarabiyace..."
dafe kai ummi tayi da hannu ɗaya, gabanta na cigaba da faduwa.. Gaba daya sun lura da yanayinta,
"Aunty ummi lafiya" da sauri ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace ba komai unaisah, can kuma tace.
"Unaisah, kikace sunan yayanta dr shureim! Ita kuma Ya sunan ne"?
Murmushi Unaisah tayi kafin tace"Aunty Benazir" ummi tayi jimm kamar mai nazarin wani abu.
"Namanta ban fada maku, wani abun farin ciki daya faru ba.." har suna hada baki wurin furta"menene" dariya ta danyi kafin tace"kun tuna auntyna da nake yawan baku labarinta a prison" kallon juna sukayi batare da sun iya gano wacece ba.
"Duk wanda ya tuna sunanta zan bashi kyauta ta musamman" ta fada cike da nishadi
Nan fa suka fara canki canka,
Hawwa tace"na tunata, sunanta Aunty adama" girza kai unaisah tayi"a'a ita wannan mommy adama take"
"Kamar aunty bahijja ne" acewar hibba, dariya unaisah tayi"no ba haka sunan yake ba"
Sajeed yace"Sunanta aunty laila" dariya unaisah tayi"no ba haka bane Allah indai baku fada ba, bazan baku tsarabar da nayi maku ba.." ta fada tana karkaɗa kafarta gaba ɗaya kamar ta manta da zancen Danish kamar an goge mata tunanin shi a brain dinta.
"Sunanta Aunty Aneelerh, indai ba haka sunan yake ba to kuyi min dundu abayana" dariya Unaisah tayi tare da kallon batool"kin canka dai dai, aranar kafin in bar gida kunsan meya faru...."? Girgiza mata kai tayi, nan fa tafara basu labarin zuwan aunty Anila ko gajiya batayi, sai surutu takeyi kamar parrot, gaba daya hankalin ummi baya atare da su, kamar bata acikin nutsuwarta har saida kunnuwanta suka jiyo mata muryar Unaisah tana fadin"ashe ita aunty aneelerhn kawar aunty Benazir dince, atare mukaje asibitin abun da ya farantamin rai Aunty Aneelah ta haifa min dan kani sunan shi baby junaid, tama yi min alkawarin zata kawo min shi har gida..." wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Su Batool.
"Wayyo Allah Angel maimakon ta shigo mu gaisa da ita, meyasa baki fada mata irin kaunar da muke yi mata ba.." parvin ce tay maganar, batool tace"Yaushe zata kawo mana ɗan kaninmu junaid mu gan shi, wlh munji dadin haduwar ki da aunty Aneelerh, saura muma mu hadu da ita amma dai zatazo nan ko"? Daga masu kai tayi"don ma namanta ban kar6i number dinta ba, amma zan ma daddyna magana nasan bazai rasa layinta ba"
"Unaisah! da sauri Ta kalli ummi na'am
"Wai ni kam dama can anan abuja kuke zaune keda daddynki"? Girgiza kai tayi"a'a a joss muke" gaban ummi ne ya ƙara faduwa, karfin hali tayi wurin furta"okey, amma ita auntyn naki Aneelerh, ya kike da ita ne? Ta fada cike da son jin karin bayani
"Matar uncle dina ne Uzair"
Shiru ummi tayi bata kara yin magana ba
Motsin shigowar mutun a falon ne Yaja hankulansu ga kallon kofar, Senior agent din da ya kai su Unaisah mall ne ya shigo hannun shi ruƙe da shopping bags, ya goyo backpack dinta abayan shi, miƙewa tsaye sukayi suna jiran ya karaso
A tsakiyar falon Ya ajiye mata shopping bags din kafin Ya sauke backpack din bayanshi ya ajiye ta"i'm sorry na tsaya amsa kira ne"_ murmushi tayi tare da cewa nagode sosai"
Yace"Never mind" ya fada tare da juyawa ya fuce daga falon
Gaba ɗaya suka zagaye bags din suna kallon su ummi tace"tsarabar mu ce wannan"? Unaisah tace"eh nakune, nima akwai nawa ciki"
Zukunnawa ummi tayi agaban shopping bags din A hankali ta fara curo kayan tana ajiyesu kan rug, su Azeeza sai tsalle suke suna murna ganin cookies da chocolates kala kala dama mayinsu ne, kamar shazu mamu suke wurin shan zaki.
Tun kan aje ko'ina suka fara kokarin kai hannu zasu ɗauka, ummi tace su tsaya ta raba su.
"Unaisah wadannan uwayen kaya haka? Wanene ya siya maki su? da mamaki ta fada tana kallon fa.."
"Atare da chief mukaje shopping mall, bakiga wurin ba ya hadu, ni fa bani na zabi kayan ba, shi yace mutumin daya kawo kayan komai yaga idanuna sun kalla ya daukar min shi ko da mara amfani ne" jinjina kai ummi tayi cike da mamakin maganar ta maida dubanta ga kayan, gasunan tili guda.
ta fara ɗaga kayan tana ambaton sunayen su a fili, Fragrance set, hair accessories, gel nail kit, skincare set, jewelry box, lace robes, slippers, diary with a lock and key, throw blankets, shaving kit, smartwatches, earbuds, sports jersey, bluetooth speaker, da sauran su ga Writting material kala kala, can idon ta ya hango mata bras har kala uku da yan panties biyu, dagowa tayi tare da kallon unaisah baki asake tace"waɗannan fa"? Dariya Unaisah tayi tare da sunnar da kanta ƙasa wata irin kunyace ta kamata"wlh Aunty Ummi bansan hada bras acikin kayanba, sune suka daukarmun" dariya ummi tayi"ah toh ni dama nasan bada saninki ba, wannan ay sai dai Batool duk da bansan size dinta ba amma nasan zasuyi mata, ke kuma saiki bari in naki sun kara cukowa" gaba ɗaya su Naufal suka tsuntsire da dariya, daure fuska tayi rai a6ace take aika masu da harara, ummi tace"ku kuma meye nayi mata dariya kawai daga anyi abu cikin raha" kumshe dariyar sukayi
"Sorry my babe, kada ranki ya 6aci, ni da wasa nayi maganar" ta6e baki tayi tana faman wurga masu naufal harara.
Ummi tace"abun dai da yawa wlh, ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi.." ta fada tare dakai hannu tana kara dudduba kayan"suma dai waɗanda suka daukar maki kayan sun iya taya 6era barna.."ta fada tana yar dariya.
"Hada phone, bayan kina da waya? Da sauri unaisah ta kalli phone box din"
Da sauri batool tace"dan Allah sister ki bani dama bani da waya..." saejeed yace nima inaso dan Allah, haris yace wlh na riga ku dan Allah ni za'a ba, rigima suka sanya da sauri unaisah ta ɗauke phone box din, ta ruƙe a hannunta, ummi tace"kin raba gardama, ki ajiyeta agurin ki" ta amsa mata da toh,
Kwashe kayan Unaisah da Ummi sukayi atare su ka maida su cikin bags din, ummi ta dibar masu chocolates da cookies ta rarrabamasu kowa ya buɗe nashi yana ci, sauran tace"za'a ajiye su adakin unaisah, duk rana zamu dibi kaɗan mu sha idan ba haka ba nasan ba zaku raga masu ba, duka zaku shanye su" amsa mata sukai da toh.
"Unaisah ke da Batool, Ku kwashe kayan ku kai dakin ku, ku ajiye su dakyau" atare suka amsa mata da toh, kafin suka fara kwashe jakukku nan suka kai su dakin su.
*UNAISAH ANGEL*
Around karfe biyu na rana, tana a kwance kan bed dinsu ta ɗaura kanta bisa pillow, ta ɗan lumshe idanunta bakomai take tunani ba face Aunty Benazir, tun bayan data dawo gida hankalinta yaƙi kwanciya ta damu da son sanin awani hali take a ciki? Meya faru bayan ta farka daga bacci?
"Ya Allah kasa kada aunty Benazir tayi kukan rashina, bana son tayi maraicina rashina akusa da ita! Zuciyarta ce ta raya mata me zai hana taje wurin chief ta tambaye shi awani hali Benazir din take a ciki tun da yar uwar shi.
da sauri ta sauko daga kan gadon, ta dauko mayafi ta yafa akanta, taje gaban Shopping bags din da suka ajiye ta ɗauki ɗaya ta zazzage kayan cikinta a gidan drawer, ta ɗebi turare biyu ta hada da chocolates da cookies kala shida ta sanya a ciki tasan ma ba lallai ya kar6a ba, kawai tayi tunanin takai mashi ne.
Miƙewa tayi hannunta ruƙe da ledar da sauri ta fuce daga dakin atsanake take tafiya..
Adaidai lokacin Danish Ya fito daga bedroom din shi yana daga tsaye a second floor, ya sanya singlet da boxer shorts a jikin shi, ya dafe handrail da hannayen shi, yana bin down stairs da kallo kwatsam idanun shi suka hango mashi ita, kamar a mafarki Yake kallonta, kwata kwata baisan ta dawo gidan ba, saboda bai fito waje ba, yana adakin shi yana karatu bacci ya ɗauke shi bayan ya farka ya shiga bathroom yai wanka hakanan yaji yana sha'awar fitowa waje yasha iska cikin ikon Allah yaci karo da ita...
Yaji dadin ganinta sosai, har saida yaɗanyi murmushi dimples dinsa suka lotsa, ji yayi kamar yaje gurinta yayi hugging din ta ya faɗa mata irin kewarta da yai, sai dai yasan ba abune mai yiwuwa ba, saboda sharuddan data gindaya mashi, kuma yayi alkawarin bazai ta6a karyawa ba, in har ba ita da kanta ta janye kudurinta ba.
Yanayin fuskarshi ne Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai, zuciyar shi ta karaya ganin ta nufi upstairs kuma yasan bai wuci part din chief zataje ba, duk yadda ya kwallafa rai akan son ganinta amma ita bata damu da shi ba kamar ma ta manta da shi, da ace lokacin bayane kafin su samu sabani yasan shine mutun na farko da zata fara nema idan ta dawo daga wani guri.
Kifa kan shi yai jikin handrail din yana jin wani irin ɗaci aran shi....
Lokacin da ta je part din chief bata iske shi ba, sau uku tana yin knocking bai buɗe ba, ranta ne ya bata ya fita hakan yasa ta juyo ta nufi stairs a hankali take taka matakalar, ranta ne ya bata kamar ana kallon ta, da sauri ta wurga eye balls dinta tana bin downstairs da kallon ganin ba kowa yasa ta maida dubanta ga second floor ganin zata ganshi yasa shi sauri juyawa ya buɗe room door dinsa zai shiga tsayawa tayi cak da yin tafiya tana kallon bayan shi har saida ya shige..
"Danish" acikin zuciyarta ta ambaci sunansa, sam takasa karasa cigaba da tafiya sam ta manta da shi sai taji wani irin a zuciyarta kamar bata kyauta ma shi ba.
ganin shi da tayi yasa taji kewar shi ta mamaye ta sai dai bata jin zata iya zuwa gurin shi, ta san dalilin dayasa shima baizo gurin ta ba, saboda alkawarin da ya daukar mata, tun a prison tasan halin shi da ruƙe alkawari in har ba ita ta janye sharuddan ba, danish bazai ta6a kusanta kan shi da ita ba koda hakan zaiyi silar da zuciyarshi zata daina bugawa ne, shiyasa ta matsa mashi akan ya daukar mata alkawarin don tasan ta hakanne kadai zasu nisanta da juna.
Ƙwallace ta cicciko idanunta jikinta yayi sanyi lakwas ji take kamar bazata iya jure rayuwa guri ɗaya da shi, batare data kusanta kanta da shi ba, har yanzu akawai kaunar shi a zuciyarta kuma har abada bata jin zata iya daina son shi, la66anta na kerma ta furta"I'm Sorry Danish, bani da mafita ne, nasan dagani har kai zamu cutu amma muyi hakuri da juna na ɗan wani lokaci..." karasa saukowa tayi daga kan stairs din ta nufi bedroom dinsu, tana shiga ta iske Batool zaune kan mirror chair, da alama ita take jira
Jin motsin shigowarta yasa batool ta kalle ta
"Sister ina kika je? Muna ta jiranki a adining, kizo mu yi lunch"
In a low voice ta furta"pls basai kun jira ni ba, kuje ku ci abincin ku, zan zo"
"Toh" Batool ta amsa tare da saukowa ta fuce daga dakin
Zukunnawa tayi agaban drawer chest, ta buɗe ta karo chocolate da cookies masu yawa ta tura a jakar hannunta, ta dauko shaving set tana tunanin ko zai bukace su? mezaiyi da su, danish bashi da gashin da zai aske cos ta san shi tun a prison haka halittar shi take bai da underarm hair, hatta fuskarshi smooth take ba gashi, hakanan dai ta sanya mashi a jakar, ta ɗauki sport jersey ta sanya mashi, gani take kamar kayan sunyi mashi kaɗan, sai da ta kara mashi wasu akai, ta curo paper da pen ta rubuta mashi
"I'm back, my man. I hope I find you safe. nayi kewarka, ga tsarabarka nan, Take care of yourself for me."
acikin shopping bag din ta sanya mashi letter din, sam ta manta bai iya karatu ba, ita a tunaninta ya fara iyawa tunda daddynta ya fada mata chief ya fara koya ma shi, mikewa tayi da sauri ta fito ta nufi upstairs, a bakin kofar dakin shi ta ajiye mashi kayan, ta sanya hannu tayi knocking kafin ya fito ta watsa da gudu ta sauko down ta dawo bakin room door din su ta tsaya tana leken shi.
Lokacin daya fito baiga kowa ba, har zai juya yai tuntu6e da shopping bag din da sauri ya dubi jakar, yayi mamakin ganin ta baisan wanene ya ajiye mashi ba.
Zukunnawa yayi tare da buɗe jakar, ya fara zaro kayan yana kallon su, akan idon shi letter din ta fado ƙasa da sauri ya dauka ya buɗe yana kallon rubutun shiru yayi jim ya rasa gane me aka rubuta bawan Allah, Ya shafe mintuna yana harhada haruffan amma ya gaza karantawa, handwritting ɗin ta ya haɗu saika rantse da Allah babban mutunne Yayi rubutun saboda ƙwarewarta.
Unaisah dake a la6e tana leƙen shi fuskarta ɗauke da murmushi sai dadi take ji amma data fahimci ya kasa karantawa sai taji wani iri aranta, daga inda take ta yi mashi gyaran murya kafin ya ɗago da ido ya kalleta tayi saurin juya mashi baya ta ruke qugu da hannu, ta yi mashi hakanne don yasan cewa itace ta kawo mashi kayan.
Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskarshi, nutsuwa yayi yana kallon bayanta har saida ta shige daki kafin ya tattara kayan ya maida a cikin jakar ya mike da sauri ya shiga dakin shi bayan ya daura jakar kan gado, ya ɗauko paper da pen ya daura kan bedside drawer ya fara kokarin yin rubuta, bawan Allah idan yana so ya rubuta Ni sai ya fara daga Na ni no nu ne kafin ya canko wadda ta dace ya sanya..
Dakyar ya samu ya rubuta mata letter ɗin ya mike da sauri ya fito ya sauko down Yaje bakin kofar dakinsu Ya ajiye mata tare da yin knocking ɗin kofar, kafin ta fito yayi saurin komawa upstairs Ya tsaya yana jiran ganin ta
Tana fitowa taci karo da letter din daya ajiye mata, zukunnawa tayi tare da daukar takardar ta buɗe ta...
"Welkam bak hom, i miss yu so much, tanku" hawaye ne suka ciko idanunta wani irin tausayinshi ne Ya kamata da sauri ta dago ta kalle shi hannu ya ɗaga mata, a hankali itama ta ɗaga mashi hannu sai yanzu ta gane ashe shine ya tura mata text message awayarta lokacin da tana a hospital, hartana dariya tayi zaton karamin yarone ya dauki wayar babarsa..
Juyawa tayi da sauri ta koma cikin dakin su, ta dauki wayarta dake kan mirror, ta kwanta kan gado ta fara scrolling ta shiga messages dinta, murmushi tasaki tana kara karanta sakon shi bata san sa'adda kuka ya kubce mata ba...cusa kanta tayi jikin pillow tay kuka mai isarta kafin ta share hawayenta ta dago, ta kalli screen din wayar, yanke shawarar kiran shi video call tay, da number din daya tura mata sako ta danna mashi call yana shiga yai picking"Turn on your Wi-Fi, I'll call you on a video call." ta faɗa tare da katse kiran bata jira amsar shi ba, fatanta Allah yasa ya iya kunna wi-fi din, ta kunna na wayarta har zata danna mashi video call, Unexpectedly, taga kiran shi ya shigo via facetime.
Picking tay tare da kanga wayar saitin fuskarta ta ƙura ido tana kallon doguwar fuskar shi abun da ya ɗaure mata kai ya lumshe idanun shi, da alama akwance yake kan gadon shi ya tada kai saman pillow kamar yadda tayi.
Ta ɗan yi mamakin canzawarshi, kamar akwai rama ta wurin kwarin idanun shi fatar wurin tayi jajir ga zira ziran eye lashes dinshi da suka ƙawata kewayen idanun, la66an shi sun bushe ƙamas launinsu ya ƙara ciza wa, ga wani haske da yayi skin dinshi har salki take, gaba ɗaya ta shagala da kallon shi har saida taga ya fara kokarin buɗe idanun shi kafin tai saurin kau da nata gefe, kallo ɗaya da yayi mata saida yaji wani irin yanayi atare da shi, ta canza mishi ta ƙara yi ma shi kyau kamar yaune rana ta farko daya fara ganin ta haka ya nutsu yana kallon soft pink lips dinta, kafin ya maida duban shi ga grey eyes dinta, taƙi yarda su haɗa ido sai dai ta wutsiyar idonta take satar kallon sexy face dinsa ta screen din wayar..
"Tell me, have you forgotten me? Are you still angry with me? Or have you stopped loving me?"
Sanyayyar muryar shi ce ta ratsa kunnanta, har saida ta sauke ajiyar zuciya kafin ta furta"bana fushi da kaina, ban manta da kai ba, kana araina, kana tunanin daina sonka abune mai sauƙi agare ni"?
Lumshe idanun shi yayi, yana jin nutsuwa tana shigar shi, kalamanta sun sanyaya zuciyar shi.
"If you're even thinking about that, you should stop" ajiyar zuciya ya sauke kafin yace"kamar yadda nayi maki alkawari bazan ta6a karyawa ba, amma inaso mu dinga yin magana ko da ta waya ne pls give me permission to call you every day" ya faɗa yana kallon fuskarta yadda kasan suna aguri ɗaya.
"Okay, I give you permission, but you will call me only two times, and you can send me a message anytime, idan na gani I will reply to you immediately. After that, I don't want anyone to know what is going on between me and you, in har muka haɗu a falo ko hanya ta haɗamu indai ina atare da wani zan iya yi maka magana kaima haka..." tana magana idonta na kallon gefe ɗaya kwata kwata bata son su haɗa ido saboda yanayin da yake jefata kuma idon tana kallon shi, sai zuciyarta ta dinga tariyo mata abunda ya faru adaren ranar daya shugo dakin su.
Shiru taji bai amsa mata ba, sai ma motsin buɗe leda da taji a kunnanta, aranta ta ayyana ko meyake ki? ko dai ya ajiye wayar ne? A hankali ta ɗan saci kallon screen din karaf idanunta suna shiga cikin nashi lokaci ɗaya taji faɗuwar gaba.
Hankalinshi kwance yake kallon ta, Yana cin chocolate din data kawo mashi, yanayin yadda yake moving lips dinsa, sai taji wani iri zuciya da sake sake sai taga kamar da gangan yake don ya rikitar da ita cos he looks so sexy a yadda yake shan chocolate ɗin har wani lumshe idanun shi yakeyi alamar dadin yana kai mashi karo, sam takasa janye idanunta daga kallon lips dinsa, hatta yanayin fitar numfashin ta saida ya canza lokaci ɗaya ta nemi zaucewa da sauri ta kifa wayar jikin pillow tayi shiru tana jin wani irin abu mara misaltuwa ta rasa gane me yasa take jin hakan? chocolate kawai ya bude yana sha duk ta rasa sukununta har wani shauƙi take ji a jikin ta.
"Hello, Angel? Are you there? Muryarshi ce ta fargar da ita
Numfasawa tayi har ta fara motsa lips dinta zata bashi amsa muryar daddynta ta katse ta"daughter! Kina ina? Shi ne kin dawo ko ki neme ni ko"?
Cutting din kiran tay, ba don ta gaji da kallon shi ba, ta miƙe da sauri ta sauko daga kan gadon, ta nufi door room din ta buɗe, yana atsaye bakin kofar fuskarshi dauke da murmushi yake kallonta"welcome back, my Angel" hugging dinshi tayi, fuskarta dauke da murmushi ta zagayo da hannayenta kan bayanshi"daddy ina wuni ya aiki, Ya aunty danejo na, wlh nayi missing dinka, kana araina tunda na dawo nake ta dakon zuwan ka.." dago da kanta yai daga kirjin shi ya dubi fuskarta dakyau"nima nayi kewarki, ay na yi zaton zaki kira ko awaya ne ki fadamin kin dawo gida, ni gaskiya ban yarda kinyi missing dina ba, kina can kin samu uwa kin manta dani ko"! Ya faɗa da zolaya
Girgiza kai tay"a'a daddy, ba haka bane, ay bani da tamkarka a duniyar nan, mu shiga ciki kaga kayan da chief ya siya min..."
Taja hannun shi suka shiga dakin, cike da zumudi ta dauko shopping bags din ta buɗe ta fara curo kayan daya bayan daya tana nuna mashi
Waro ido ya ɗanyi alamar mamaki yace"Eyeh gayu mutanan Allah, duk ke kadai wannan? Amma naji dadi ubangiji Allah Ya saka mashi da alkhairi Allah Ya ƙara mashi buɗi da daukaka"
Fuskarta dauke da fara'a tace"ameen daddyna, wlh nima nayi mamakin kayan daya siya min amma fa bani kadai ba hada su Batool yace in daukarmawa inyi masu tsara..".
"Kin nuna ma auntynku"
"Eh, harma ta dibar mana chocolates da cookies sauran kayan tace mu ajiyesu adaki kafin lokacin da zata raba mana"
Murmushi yayi har cikin ranshi yaji dadin jin chief ne ya je da ita mall da alama burin shi Ya kusa cika na ganin Ya kulla alaka mai karfi atsakanin su.
"Daddy, na jima banga mutun mai mutunci irin chief ba, yana da saukin kai, ga shi wayayye ni dama can inason mutum irin haka..." ta saki baki tana surutu cikin rashin sani ta zazzago bras daga cikin shopping bag din dake ruke a hannun ta.
Waro ido taj yai cike da zolaya ya furta"Subhanallah, daughter wannan fa na wanene"? da sauri ta dube su, wata irin kunyace ta kamata, da sauri ta sunkuyar da kanta kasa sam ta kasa kawar da su"
Taj dake kallonta dariya ce kumshe abakin shi bai ta6a tsammanin Angel tana da kunya har haka ba.
Tunawa yai lokacin da tana karama har fadi mashi take dan Allah ya siya mata ƴar bra irin na aunty anila idan ta girma boobies dinta suka fito itama ta dinga sakawa, ranar yaci dariyar maganarta, komi tagani anila tayi itama sai tace zata yi idan ta girma, anila itace silar da Angel ta fara kwadayin tayi aure ay gani take babu rayuwar da tafi dadi irin ta gidan aure. Tasha fada ma taj itafa house wife takeso ta zama, kuma bazata auri talaka ba, saboda ita matar manya ce, hamshakin mai kudi zata aura, inda zata sakata ta wataya bata aikin komai sai dai yan aiki suyi mata ita tana daga kwance, shiyasa taj yakeso yacika mata burinta, bawai don kwadayin abun duniya ba sai don baya son yakaita inda zata sha wahala, saboda ta cancanci tayi rayuwar farin ciki, ta auri miji nagari nagartacce.
Jin yayi shiru bai ƙara tanka mata bane yasa ta dago da ido ta saci kallon shi, hankalin shi kwata kwata baya akanta, yayi zurfi cikin tunanin shi, da sauri ta kwashe bras din ta tura a cikin shogging bag din, kafin tace"daddy! " kallon ta yai"meye faru naga kamar kana tunanin wani abu" murmushi yayi mata.
"Ke nake tunani" farfari tay mashi da ido"me kake tunani akaina" calmly ya furta"inaso ki faɗamin gaskiya kina son aure har yanzu"? Rass taji gabanta ya faɗi da sauri ta cusa kanta tsakankanin gwiwowinta, yar dariya yayi"wai ni waya koya maki jin kunya? Kamar ba Angel dina ba, ko dai anyi min musayarki ne"?
Muryarta kasa kasa tace"a'a dadi ni din ce dai daka sani, Angel dinka,"
"Okey, fadamun amsar tambayar da nayi maki'!
Miƙewa tayi da gudu ta shige toilet, taja kofa ta datse, murmushi yayi yana kallon kofar.
Daga cikin toilet din yajiyo muryarta"daddy zan baka amsa ba yanzu ba, ka ɗibar ma aunty danejo tsarabar da nayi, kaima ka dauka..." dariya yayi haɗi da girgiza kan shi yana kallon kofar toilet din.
Chocoletes da cookies ya dibar masu a dakin ya samu plastic bag, ya sanya a ciki, kafin ya mike yana fadin"ni zan wuce toh, ba zaki fito muyi sallama ba"
Dakyar ya samu ta fito daga dakin, tana faman noƙe kai taje gaban shi ta tsaya"na manta ban tambayeki ba, ya mai jikin?
"Taji sauƙi sosai, wlh kamar kar in barta, ina kaunarta sosai, lokacin ma da zan tafi, saida dr jazz ya bani sleeping pill na bata tasha saboda bazata bari atafi dani ba.." muryarta na rawa ta kare maganar kamar zata sanya mashi kuka"daddy dan Allah zuwa jibi ka kaini gidansu daga nan sai muje gidan su aunty anila inason inga babynta.." tun da tafara magana ya kafe ta ido yana kallonta, mood din fuskarsa ya canza sosai, tsantsar tausayin su ne ya kama shi, dama yasan dole su kaunaci juna, jini ɗaya ba wasa ba, tsakanin uwa da ɗa sai Allah.
Cikin sanyin murya yace"ki kwantar da hankalinki, kada ki sanya damuwa aranki, zan yi kokarin kaiki gurin ta, amma ba yanzu ba, ki ƙara hakuri, ita kuma auntyn naki zan baki contact dinta, ki kira ta waya ku gaisa sai kiyi mata maganar junaid din nasan zata kawo maki shi"
Nagode daddy,"da murna tay maganar, Taje ta dauko wayar ta bashi ya sanya mata layin aunty Anilah
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
KURKUKUN KADDARA
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 39 Complete by Boss Bature
September 03, 2024
KURKUKUN KADDARA
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 38 Complete by Boss Bature
September 02, 2024
KURKUKUN KADDARA
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 37 Complete by Boss Bature
August 31, 2024
KURKUKUN KADDARA
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 36 complete
August 31, 2024
KURKUKUN KADDARA
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 35 Complete
August 31, 2024
KURKUKUN KADDARA
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 34 Complete
August 30, 2024
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
OPINION
Opinion: A Beacon of Integrity and Leadership in Public Service
by
Novels Elite Admin
August 21, 2024
YOU CAN ONLY GIVE WHAT YOU HAVE GOT
June 12, 2024
Corruption:Legal forum Calls to investigate EFCC Boss over selective treatment
November 17, 2022
FACEBOOK
COMMENTS
Anonymous
Pls Ina naiman Hadamu mu Akayi
Anonymous
Matar so please
Anonymous
Don Girman Allah insamiki number na zaki turamini ...
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 40 Complete
September 03, 2024
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 39 Complete by Boss Bature
September 03, 2024
Kuskure Ɗaya page 9 Complete by Jiddah S Mapi
September 02, 2024
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 41 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 04, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
Shigowa dakin hajjaty yayi bakin shi dauke da sallama, tsayawa yayi ganin bata a cikin ɗakin har ya juya zai fita ya jiyo saukar ruwa a toilet, ajiyar zuciya ya ɗan sauke ya nufi gefen gadon ta har ya yunkura zai zauna idanunsa suka hango mashi plastic bottles dake ajiye kan mirror drawer, miƙewa yayi tare da nifar mirror din ya tsaya yana kallon robobin kamar na ruwa haka suke, rubutun larabci ya gani a jikin su baisan me aka rubuta ba saboda baya jin harshen, zuciyar shi bata kwanta da su ba, ɗaya ya ɗauka ya buɗe murfin ta yakai hancin shi zai shinshina da sauri ya kawar da shi gefe ya yamutsa fuska haɗi da ta6e baki yana ɗan jan numfashi..
Motsin buɗe kofar toilet ne yaja hankalin shi ga kallon ta, fitowa tayi daga ciki, tayi ɗaurin gaba da towel, ta naɗe black hair din ta da wani towel ɗin
Suna haɗa ido da juna ta sakar mashi murmushi.
"mere pyaar, sai yanzu zan sanyaka a idanuna? Ina ka shiga ne ka barni da kewarka"?
Lumshe idanun shi yayi a hankali ya buɗe su yana bin ta da kallo mai cike da jin shaukin ta.
Ta baya tayi hugging din shi ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa, ta ɗaura hannayenta kan chest din shi.
"Wifey, i'm sorry wani kira akai min mai mahimmanci shiyasa ban samu damar zuwa gurin ki ba, amma kina araina" kwanto da kanta tayi kan shoulder din shi, nuna mata robar hannun shi yayi"menene wannan?
Fuskarta dauke da murmushi tace"maganin da sheikh imam Ya bada ne don adinga ba marwa tana sha, yace in sha Allah zataji sauƙi nan bada jimawa ba..." ta fada tare da manna mashi kiss kan cheek dinsa, gogan ya haɗe fuska sam bata kula da yanayin shi ba, taci gaba da cewa"
"Nayi ma sheikh imam alkawarin zancigaba da kula da ita, har zuwa lokacin da zata ji sauƙi"
ajiye robar yayi tare da janyota ta dawo ta gaban shi
Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Meye alakarki da marwa ne"? Fuskar shi adaure yayi mata maganar
"Yar uwata ce musulma, kuma tana bukatar taimakonmu saboda mune danginta ayanzu..." bata ƙare maganar ba ya rufe mata baki da yatsan shi
Calmy yace "Kingane ni bazan hanaki yin aikin lada ba, kawai bana so kina shisshige mata ne, ke ko kyamarta ba ki ji? kuma baki gudun ta goga maki lalurarta"? Zame hannun shi tayi daga kan bakinta
"Haba pravin, meya kawo wannan maganar? Ita ma fa ba ita ta daura ma kanta ba, bayan haka sheikah imam ya fada mana hanyoyin da zamu kare kanmu daga sharrin aljanu...." bata ƙare maganar ba yai saurin janyota kan kirjinshi yakai bakin shi saitin kunnanta, in a low voice ya furta"ni dai hankalina bai kwanta ba, kinsan bana son duk wani abu da zai cutar min dake, pls ki taimaka min ki aje aikin kula da marwa..." yanayin yadda yakeyi mata magana ba karamin kashe mata jiki yayi ba.
cike da shagwa6a tace"dan Allah kabarni inyi aikin nan, indai kayi imani da cewa Allah shi yake tsare bawansa, nayi maka alkawarin zan kula da kaina, amincewarka kadai nake bukata..."
Badan yaso ba ya amsa mata da toh.
ƙara matseta yayi a jikin shi, a hankali ya fara manna mata hot kisses kan wuyanta har ya zuwa kan kirjin ta..tuni ta fara jan numfashi tana lumshe idanunta, daukarta yai gaba ɗaya ya kwantar kan mattress ya zame kayan jikin shi ya rage daga shi sai short, ya fada kanta yaja bargo ya lullu6e su...romancing dinta ya cigaba da yi, gaba ɗaya ya rikitata, tsawon mintuna shabiyar kacal, wani irin kasalallan bacci ya yi awon gaba da hajjaty.
Fitowa pravin yayi daga cikin bargon ya sauko daga kan gadon Ya haɗa uban gumi a jikin shi, shu'umin murmushin gefen fuska ya saki tare da kallon hajjaty dake bacci...A hankali Ya furta"I'm sorry, zan yi maki laifi, saboda bazan bari kiyi silar tona min asirina ba," ya faɗa tare da juyawa ya nufi robobin maganin ya kwashe su, Ya shige toilet da su, Allah kadai Yasan meya yi masu, jim kaɗan Ya fito da robobin a hannun shi yana faman sakin shu'umun murmushi ya ɗaura su kan mirror.
Kafin ya fita daga dakin saida ya fara hawa gadon Ya sumbaci la66anta kafin ya sauko shaf shaf ya maida kayan jikin shi ya juya cikin takun tantirai Ya fuce daga dakin.
Fitar shi keda wuya hajjaty ta fara mutsu mutsun farkawa daga bacci, wata irin kasalace ta mamaye jikinta dakyar ta lalla6a ta miƙe ganin babu sutura ajikinta yasa tayi saurin kai hannu ta janyo towel dinta ta lullu6e jikinta, muryarta adisashe ta fara ambaton sunan shi shiru taji bai amsa mata ba alamar baya adakin, lumshe idanu tayi tare da jingina kanta jikin headboard, A hankali take tariyo abunda ya shiga tsakaninta da pravin wani irin shaukin son shi take ji, dai dai da minti ɗaya bata ta6a gajiya da shi ba, saboda soyayyar gaskiyace a tsakaninsu, bata ta6a haɗa son shi da wani ba.
Tunawa da marwa yasa tay saurin saukowa daga kan gadon ta shiga toilet, donta tsarkake jikin ta, bayan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ta feshe jikinta da turare, ta yafa mayafi akanta, da sauri ta dauki robobin maganin ta tura su cikin ledar da aka kawo su, ta fito ta nufi dakin marwa, da sallama ta shiga dakin fuskarta dauke da murmushi take kallon marwa dake akwance kan mattress ta rufe idanunta.
Zama hajjaty tay gefen katifar ta ajiye jakar agaban marwa.
"Sannu marwa ya jikin naki? a hankali ta buɗe idanunta waɗanda suka kaɗa jawur ta dubi hajjaty, dakyar ta kakaro murmushi tana kallon ta
tayi kyau abunta, ɗazu da safe hajjaty ta taimaka mata tay wanka har kaya ta canza yar doguwar rigace a jikin ta, jikinta sai kamshin turaren da hajjaty ta fesa mata yakeyi.
"Sheikh imam ya aiko da maganin ki,"
ta fada tare da ruƙo kafadun marwa ta taimaka mata ta zauna tare da jingina bayanta jikin pillow
"Kina jin yunwa" girgiza mata kai tay alamar a'a,
"Dama nasan ba lallai kiji yunwa ba, saboda dazu kin cika cikin ki da abinci" ta fada yayin da take bude murfin robar farko mai ɗauke da sunan zam zam..
"Kiyi bismilla ki sha, kur6a ɗaya zakiyi" ɗaga mata kai tay alamar toh
Lokacin data kurbi maganin kiris ya rage ta amayar da shi saboda zaurin da ya buso hancin ta.
Lura da yanayin ta yasa hajjaty cewa"am sorry halan maganin bai da dadi? Ɗaga mata kai tay alamar eh
Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Eyyah sai kin daure,kinsan yadda magungunan gargajiya suke akwai ɗaci, wani zakiji shi da bauri wani kuma tsami" ta faɗa tana yamutsa fuska, bayan ta kammala bata magungunan, tace"wannan ɗayan daya rage, a cikin ruwan wanka za'a ɗiga maki shi, zuwa anjima in sha Allah zan sake dawowa, sannan pls kada ki manta kiyi evening azhkar"
tun da ta fara magana marwa keta kallonta so take ta faɗa mata wani abu tarasa taya zatai mata magana daga ta yunkuro zatai magana sai ta kasa saboda muryarta babu dadin ji
Hajjaty sam bata lura da hakan ba, bayan ta maida robobin maganin a cikin ledar, ta ajiye gefen katifar marwa"ni zan tafi, da anjima zan shigo kawo maki dinner" ta fada tare da sakar mata murmushi ta mike ta tafara tafiya har ta kusa fita kunnuwanta suka jiyo mata marwa dake ta kokarin yi mata magana.
Juyowa tay tare da kallonta da alamun rudani akan fuskarta, da hannu take yi mata alama, hajjaty ta kasa gane me taje nufi, ita dai taga marwa sai nuna mata dunkulallun yatsun hannunta takeyi
"Marwa akwai wani abu da kike bukata ne"? Ɗaga mata kai tay alamar eh, komawa tayi gaban katifar ta zukunna tana kallonta, ruwan hawaye tagani kwance akan fuskarta"pls ki daina zubda hawayenki dan Allah, ki fadamun abunda kike so zanyi maki" da hannu marwa ta dinga goga floor tana kokarin kwatanta mata abunda take so ta dauko mata sai dai takasa fahimtarta
Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Marwa kiyi hakuri, wallahi bansan me kike nufi ba" buɗe baki marwa tayi ta fara mata gura gura.. tsoron maganarta hajjaty take ji nan take ta tuna da maganar pravin dayace mata ita bata tsoron marwa ta goga mata lalurarta, tuna wannan yasa tay saurin mikewa gabanta na faduwa ta fara ambaton sunan Allah acikin zuciyarta.
Cikin rawar murya tace"marwa sai anjima zan dawo in sha Allah" da sauri ta fuce daga dakin, marwa ta kifa kanta cikin pillow ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tamkar ranta zai fita 💔
________________________________✍️
*(AFTER 3 DAYS BAYAN KWANA UKU)*
A kalla yau kwana uku kenan da zuwansu Anila gidan hajiya adama, har ila yau ba su ƙara jin duriyar Ana ba, babu ita babu labarin ta, abun ya ɗaga hankulan mutanan gidan sun damu da rashin ta, kusan kullum sai anila da mahboob sun kira layinta a switched off suke samun shi, Lamarin ya ɗaure masu kai, basu da wata hanya da zasu Iya tuntu6ar wani nata, saboda ba su ta6a kar6ar layin yan uwanta dake a joss ba, abu biyu ya haɗe ma Aneelerh ga damuwar halin da junaid yake a ciki, kwata kwata baya sakin jiki da kowa ga ƙiwuya bai yarda da kowa na gidan ita kadai yake manne mawa, kuma har yau yaƙi buɗe baki ya tanka mata ya zama kamar kurma sai dai yabi ta da ido ko in yana jin yunwa sometimes yana bude baki ya furta kalmar yunwa, wani abu daya fi daure mata kai idan dare yayi zasuyi bacci ta rungume shi a jikin ta, sai ya dinga firgita yana sambatu kwata kwata bata gane me yake cewa.
Har su mami ta sanar ma abunda yakeyi suka ce taci gaba dayi mashi addu'a in sha Allah zaiji sauki, ita dai hankalinta bai kwanta da yanayin shi ba, ranta yana bata wani abu ba dai dai ba agidan dole akwai wani abu daya faru wanda yayi silar guduwar Anah da kuma rikicewar baby junaid! Kwana biyu da baije school ba sai ga kira daga class master din su junaid, bayan sun gaisa da anila ta ta tambayeta meyasa kwana biyu junaid baizo school ba, tace mata baida lafiya ne amma idan yaji sauki zai cigaba da zuwa
Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Cikin kwana uku anila duk ta fita hayyacinta har faɗawa tayi saboda damuwar rashin Ana da kuma halin da baby junaid yake a ciki, abie har kiranta yayi shi da uncle dan iya da su ummu suka taru akanta suka yi mata nasiha cikin lallami da lallashi donta kwantar da hankali saboda kowa ya fahimci bata acikin nutsuwarta, ko abinci sai zahra tayi dakyar take samu ta ci ta zama abun ban tausayi daga ita har junaid din harma kwara ita akan shi saboda ya takura kan shi ya kuma takura mata ya hanata sukuni ko toilet zata shiga sai ya sanya rigima zai bita, dakyar take samu ta lalla6a shi da wayarta don yayi game kafin ta samu ya kyale ta, idan salla zatayi sai dai ta goya shi abayanta, har yau babu abunda ya canza, yanzu girkin gidan ya dawo hannun mami da ummi saboda rashin Ana, zahra kuma ba azaune take ba, tana zuwa aiki, ita kuma anila kota nemi su bata ta tayasu aiki sai suce taje taji da junaid zasu kula da komai...💔
________________________✍️
Shin Ya labarin Benazir? Ay tun ranar da suka dawo gida ta kasa ta tsare tana jiran taj da Angel su dawo daga kasuwa, shiru shiru taji basu dawo ba har marece ya nutsa hankali atashe tace ma hajiya layla ta kira mata layin taj awaya taji meya hana su dawo! Hajiya layla tana yan kame kame tace mata ta manta bata da layin taj, kuma dayazo asibitin daukar Angel bata kar6a ba, sai dai ko dr shureim watakil shi yana da layin shi, ko da ta yi ma dr shureim magana akan ya kira mata taj cikin rashin kwanciyar hankali ya kira wrong number da gangan saboda ta tsare shi da ido tana jiran shi ya kira mata mijin ta, a dole yayi pretending ya ci gaba da magana yana fadin pls taj marece yayi ga benazir tana jiran ku, dan Allah ku dawo hakanan okey toh sai anijima Allah ya dawo daku lafiya, bayan ya katse kiran yace mata tayi hakuri ta kara jira suna akan hanya, baiwar Allah jiki asanyaye ta zauna kan sofa tana jiran dawowarsu, hankalinta kwata kwata ba a kwance yake ba, gani take kamar bazata sake ganin angel din ta ba...
Abu kamar wasa har dare yayi babu taj ba angel, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, lokacin da zasu yi dinner bayan su tani sun kammala shirya masu abinci a dining hajiya layla tace tazo su ci abinci, tace mata bazata iya ci ba, in har taj bai kawomata Angel din ta ba
hankulansu ba karamin tashi yayi ba, gaba ɗaya suka taru akanta suka fara lallashinta suna bata baki duk don su samu su taci abincin amma taƙiya, babu wanda baiji tausayinta ba musamman da karfe goma sha ɗaya ta buga na dare, a lokacin ta gama gane karya sukeyi mata, zuciyarta ta karaya a karshe ta fashe da kuka tace su daina boye mata gaskiya, kawai su fada mata ina yarta Angel? Saboda tana ji aranta ba taj bane ya dauke ta, babu wani siyayyar da suka je yi mata duk plan ne .." gaba daya aka rasa wanda zai faɗa mata gaskiya saboda fargaban halin da zata shiga, ranta yayi mugun 6aci zuciyarta ta hasala ganin sun zuba mata ido an rasa me magana a cikin su, idanunta suka kaɗa jawur, zafafan hawaye suka wanke fuskarta, tsabar fusata jikinta har kerma yakeyi tana faman jan numfashi tace"mami! Ya shureim, aunty sarah ku fadamin gaskiya ina babyna take? Wanene Yake son rabani da ita? Yarinyar nan ƴata ce fa halak malak, akan me zaku yi min karyar taj ya dauke ta sunje shopping mall? Meyasa har yanzu basu dawo ba? Kusan karfe goma sha ɗaya na dare, wlh idan har baku dawo min da babyna ba, komai zai iya faruwa..." dakyar ta kare maganar tare da sanya tafukan hannayenta ta dafe kanta kamar yadda take yi idan zatay pretending ta fara yi masu kuka na fitar hayyaci kamar zata rotsa dodon kunnuwansu, gaba ɗaya tabi ta furgita su, zeenatu tsabar tsoro daki ta shige ta kulle dama tunda Benazir din ta dawo ko gaisuwa bata hada su ba, bayan ta shiga dakinne ta fara tariyo fuskar Unaisah yarinyar data kira sunanta da Unaizah, har cikin aranta tana son ta kara haduwa da ita kuma tana son tasan wacece Unaizar su data mutu? ya akai komai nasu yazo iri ɗaya? Tabbas tana son tasan komai dangane da ita bayan haka tana son su kulla kawance da Unaisah saboda ta kwanta mata aranta tun a kallo na farko da idanunsu suka shiga cikin na juna.
Daga cikin falo ta dinga jiyo sautin muryoyinsu Hajiya layla suna ta kokarin lallashin Benazir, hada alhaji ubaid a lokaci baijima da shigowa gidan ba, gaba daya mutanan gidan suka taru akanta, in ka cire Alhaji musa saboda baya nan baisan budurin da sukeyi ba
Adaren ranar dakyar suka samu bacci ya ɗauketa, jikinta hada zazza6i.
har ila yau tana akwance ba lafiya, saboda rashin Angel dinta, tayi kukan harta gaji, kowa na gidan tausayinta yake ji, yau kwana uku kacal da rabuwarsu da unaisah tana jinyar zuciyarta bata son cin abinci ko wanka ta dainayi ta zama kamar mahaukaciya, kusan kullum sai hajiya layla ta matsa ma shureim akan ya kira anila yayi mata magana ta fada masu ina ne gidan iyayen yarinyar, dr shureim yace tayi su yi hakuri bazai iya ba, bayaso ya takura ma anila bayan haka babu amfanin suje gidan iyayen yarinyar tun da ko sunje yarinyar fa ba yar benazir bace ganinta bazai amfani benazir da komai ba saima ya ƙara ɗaga mata hankali tunda ba basu ita za'ae ba, adole hajiya layla ta hakura da yi mashi maganar Azeezaty
_________________________✍️
Idan muka koma bangaren Marwa, jikinta ya ƙara tsauri babu wani cigaba a lafiyarta, yatsun hannunta sai ƙara matsewa sukeyi ga wasu kananun kuraje da suka fara feso mata akan fuskarta, baiwar Allah ita kadai tasan halin da take a ciki, wani lokaci idan hannunta suka fara mata radadi kamar zata zauce, duk da halin da take aciki kokari take ta fallasa asirin wanda yai silar ɗaura mata ciwon, sau uku hajjaty ke xuwa dubata kuma tana kokarin kiyaye duk wasu sharudda nayin amfani da maganin da sheikh imam ya bata sai dai takasa gane an canza ruwan maganin rashin sani ya fi dare duhu batasan tana ƙara wa marwa ciwon ta ba takasa lura da yanayin ta, gashi duk in ta shigo daki sai marwa tayi mata alama da hannu har yau takasa fahintar me take nufi, idan tayi yunkuri takura kanta akan tay magana wani irin radadi take ji a makoshin badan taso ba ta hakura, wani lokaci idan tayi ma hajjaty alama da hannu ta kasa ganewa saita buga kanta jikin pillow tayi ta kuka kamar ranta zai fita, dakyar hajjaty take samu ta lallasheta har ta shawo kanta.
Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
A cikin yan kwanakin nan hajiya saratu bata bari hanya ta haɗata da hajjaty saboda tsoranta da take ji, hajjaty harta fara lura da ita, ranar da ta shiga kaima baba obie abinci hajiya saratu tana adakin, tun da taji sallamar hajjaty da sauri ta mike ko sallama batayi mashi ba ta fuce daga dakin, tun daga nan hajjaty ta fara lura da ita, abun ya ɗaga hankalin ta, tarasa gane laifin me tayi mata? Duk da dama tasan ba sonta take yi ba akwai tsanarta a zuciyarta amma yanzu abun ya karu fiye da lokacin baya
Idan muka koma bangarensu twins tun ranar da suka ga iftila'in daya faɗawa marwa basu ƙara marmarin komawa gidan ba, saboda kyankyami da kyama suke ji, a hotel suka koma da kwana, daga bisani da hajiya saratu takira zayn awaya ta fara zazzaga mashi masifa akan rashin dawowarsu gida yace mata su fa bazasu dawo ba in har ba an fidda mai aikin nan daga gidan su ba, bata musa masu ba, saima cewa tayi su bata lokaci zatayi magana da baba obie akan a maida marwa garin su indai hakan zai kwantar masu da hankali, sunji dadin maganarta hada yi mata godiya
✊Boss Bature💋: ________________________✍️
A kishingiɗe yake saman lallausan rug din dakin baba obie ya ɗaura head dinsa kan pillow, jikinshi na sanye da jallabiya fara kyal, fragrance dinsa ya haɗe da sanyin A.c din dakin, ba su jima da dawowa daga sallar asuba ba yabiyo baba obie dakin shi...A hankali yake danna phone dinsa Kira ne ya shigo ganin sunan commender james yasa shi picking call din tare da kara wayar a kunne, cikin girmamawa suka gaishe da junansu kafin daga bisani commender james ya sanar da shi sun samu izni daga manyan su, za su shigo Nigeria da shi da sauran sojojin da suka tsinci su Angel a dajin evil forest
Chief yace"I'm very happy to hear that, I can't wait to see you"
Commender james yace"I'm also very happy, this is the first time I'll be coming to Nigeria because of the children we found in the forest.
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
Our website uses cookies to improve your experience. Learn more
Accept !
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite
Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 42 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 05, 2024
Takun Ƙarshe
Boss Bature
A kishingiɗe yake saman lallausan rug din dakin baba obie ya ɗaura head dinsa kan pillow, jikinshi na sanye da jallabiya fara kyal, fragrance dinsa ya haɗe da sanyin A.c din dakin, ba su jima da dawowa daga sallar asuba ba yabiyo baba obie dakin shi...A hankali yake danna phone dinsa Kira ne ya shigo ganin sunan commender james yasa shi picking call din tare da kara wayar a kunne, cikin girmamawa suka gaishe da junansu kafin daga bisani commender james ya sanar da shi sun samu izni daga manyan su, za su shigo Nigeria da shi da sauran sojojin da suka tsinci su Angel a dajin evil forest
Chief yace"I'm very happy to hear that, I can't wait to see you"
Commender james yace"I'm also very happy, this is the first time I'll be coming to Nigeria because of the children we found in the forest, naji dadi saboda abun alfahari ni agare ni"
sun ɗan jima suna tattaunawa kafin daga bisani su ka yi sallama da juna.
Fitowa baba obie yayi daga toilet, jikinshi sanye da jallabiya fara, ya dago da ido ya dubi owais fuskarshi da fara'a yace"jikallena, nabarka zaune kana jira na, uziri ne ya ruƙe ni a ciki" dagowa chief yai tare da kallon shi suka haɗa ido da juna"barka da fitowa,"
"Yawwa owaisu na, fadamin me kakeson ci insa akawo mana, yau atare zamu yi breakfast.."
ya faɗa yayin da yake nufar bedside drawer chief yace"duk abunda kakeson ci nima shi zan ci "
Landline din kitchen baba obie ya kira, bayan an daga kiran ya isar da sakon abunda za'a kawo masu na breakfast bayan ya ajiye wayar
Ya samu guri kan lallausar rug din ya zauna haɗi da daura kan shi saman laps din chief yadda kasan uba da ɗansa.
ya ɗago ya kalli fuskar Owais dake kokarin saita shi da phone camera"me zaka min haka"?
"Hoto zan ɗauke ka, naga ka yi min kyau"
murmushi baba obie ya sakar mashi"duk kyau na nakai ka"?
"Eh mana, mu da mukai gado agurin ka, gaba ɗaya kamanninka muka ɗauko"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Na tsufa owais, yanzu babu wannan kyan da kake faɗin ina da shi"
"Kai kake ganin haka, ni tun da na taso rayuwata ban ta6a ganin mutumin daya tsufa da kyan shi irinka ba" ƙayataccen murmushi baba obie ya saki yana kallon fuskar chief, yaji dadin kalaman shi sun faranta ran shi.
"Baba, ɗazu kace zamuyi magana, ya fada bayan ya kammala daukar shi hoton.
shigowar hajjaty dakin ne ya katse firar su, ta ɗauki wankan material, hannunta ruƙe da tray na kayan breakfast dinsu agabansu ta ajiye tray din cikin girmamawa ta gaishe da su suka amsa mata har ta juya zata fuce daga dakin muryar baba obie ta dakatar da ita.
"Ya jikin marwa"?
"Da sauƙi baba,"
"Okey, ubangiji Allah ya bata lafiya" ta amsa mashi da ameen bayan ta fuce daga dakin chief ya dubi baba obie"wacece marwa"?
Ba halinsa bane tambayar abunda bai shafe shi ba, just saboda yaji ya ambaci ya jikin ta.
"Ɗaya daga cikin masu aikin gidan nan ce, bata da lafiya" iya abunda ya fada masa kenan saboda baison ya ɗaga mashi hankali, kamar yadda su twins sukai hijra saboda kyamar marwa.
"Allah ya bata lafiya" ya amsa mashi da ameen
Tea pot baba obie ya dauka ya tsiyaya masu shayi a kananun kofuna suka dauka suna sha
"Ka tambaye ni dangane da maganar da nace maka inaso muyi ko" ɗaga mashi kai yai alamar eh
"Nasan bazaka ji dadi ba, amma kada ka hanani tafiya" janye cup din hannunsa yai daga kan lips dinsa"tafiya zakayi"! Jinjina mashi kai yayi"lagos nakeson zuwa gurin aminina, kasan na daɗe ban ziyarce shi ba, kuma shi yana kokarin zuwa akai akai ya dubani har gida" jinjina kai chief yai"yaushe ne zaka tafi"?
"Karshen watan nan, 3 weeks zanyi in dawo" ɗaure fuska chief yayi"har sati uku baba, ina laifin one week" murmushi yayi"dama sai da nayi fargaban fada maka nasan da wuya ka kyale ni, indai bazaka barni ba to saidai muje atare" girgiza kai chief yayi"ba zan iya binka ba, naso muje atare amma ayyuka sunyi min yawa, amma fa bazan bari ka tafi kai kadai ba,"! Yamutsa fuska baba obie yai"to ni da wa zan tafi owais? Kowa yana da aikin yi, bana son in takura masu"
Shiru yayi jim kafin yace"zanyi magana da pravin, ya ɗauki hutun aiki Ya bika ku tafi, don gaskiya ni bazan bari ka tafi kai kadai ba"
"Haba owais kamar wani karamin yaro, sai kace bakasan wanene kakan naka ba, waɗannan kafafuwan nawa ba inda basu taka ba, har birnin sin sunje, nafa yi yawan duniya fiye da tunaninka, tun ina matashina nake fita kasashen waje ni kadai abuna."
Murmushi chief yayi"da da yanzu ba ɗaya ba, ka manyanta sosai ga tsufa, shiyasa nake tattalinka bana son wani abu ya same ka, duk da nasan Allah ke tsare bawansa."
kalaman chief sun kara faranta ranshi murmushi yayi yana kallon fuskar shi"anya akwai wanda yakaini dacen jika a duniyar nan"? chief yace"ni yakamata nayi wannan tunanin, cos bana tunanin akwai wanda yayi dacen kaka irina, ina alfahari dakai," dariyar farin ciki baba obie yasaki idan owais na yabon shi dadi yake ji kamar ya zuba ruwa kasa ya sha.
"Owais Mu fara cin abincin nan kada ya huce.." Chief ne yayi serving dinsu atsanake suke cin abinci ya lura duk dagowar da zaiyi sai sun haɗa ido da baba obie wani kallon so da kauna yakeyi mashi.
"Naga kana kallona, ba zan canza maganata ba, zanyi magana da pravin din atare zaku je nasan zai baka kulawa ta musamman kuma zai dinga sanar dani duk wani motsinka" dariya baba obie yayi"oh ɗan leken asiri zaka hada ni da shi kenan" ɗaga mashi gira chief yayi"bakomai nasan saboda kaunar da kake yi min ne, naji na amince muje atare da shi din" ya fada yayin da yake tura abinci abakin shi.
Knocking room door din akay daga waje, baba obie yace shigo ciki"
muryar hajiya saratu ce ta katse masu cin abincin nasu, atare suka dago suna kallonta, shugowa tayi jikinta sanye da swiss code lace, idanunta sanye da farin glass, ta aza veil a kafadarta, ta kashe daurin ture kaga tsiya, hannunta na aruke da handbag dinta.
Kwata kwata babu annuri akan fuskarta saida taga chief ta ɗan saki fuskarta.
"Shalelena barka da safiya, har anyi shirin xuwa office.. " murmushi ta sakar mashi"barka da safiya babana, ina fata ka tashi lafiya" tay maganar tare da samun guri ta zauna tana fuskantar su..
"Lafiyalou auta,"
"Barka da safiya auntyna, kin tashi lafiya? murmushi tasakar ma chief da fara'a tace"lafiyalou my son, ina fata kaima haka ya aiki"?
Yace"Alhamdulillah"
"I'm sorry na shiga busy, kwanaki nace zan shiga asibiti in duba patient din nan banje ba, Ya jikin nata? Ya kuma babynta Unaisah ina fata suna lafiya"? cikin kulawa tayi maganar tana duban shi.
"She's feeling better, almost 3 days da sallamarta, unaisah tana lafiya"
"Masha Allah, naji dadin jin hakan"
tun da suka fara magana baba obie ke kallonsu cike da mamakin taya akai suka sasanta tsakaninsu, shi dai yasan tsakanin jikallan nasa da autarsa ba sa jituwa.
gaba ɗaya sun fahimci kallon da yakeyi masu, murmushin gefen fuska ya saki har cikin ranshi yaji dadin shiryawarsu"tun yaushe kuka sulhunta tsakaninku bansani ba"? Ya faɗa yana kallon su
Murmushin dattako hajiya saratu tayi batare data furta kalma ba, chief ne ya bashi amsa da cewa"me ka gani baba?
Nuna su yayi da yatsan shi"ga abunan azahiri, ku fadamin wani ɗan arzikin ne ya hadamin kanku? Ni dai nasan baku jituwa"
tattausan murmushi sukayi
Hajiya saratu tace"Allah ne ya hada kanmu, dama can shaidan ne ya shiga tsakaninmu amma muna kaunar juna, ko ba haka ba my son" ta faɗa tana kallon shi
"Hakane baba, kuma in sha Allah ba za'a kara jin kanmu ba" har cikin ranshi yaji dadin maganarsu, dama baya son sabanin da suke samu atsakaninsu.
"Alhamdulillah, naji dadi ubangiji Allah ya cigaba da hada mun kanku, Allah ya kara dankon zumunci atsakaninku, shi kuma shaidanin daya shiga tsakaninku Allah Ya kare mu daga sharrinsa"
A tare suka amsa mashi da ameen, kwata kwata baiyi masu maganar mara lafiyan dayaji sun ambata ba, hankalin shi ya karkata akan jituwar da suka samu.
Miƙewa chief yayi da sauri baba obie yace"Grandson ina zuwa bamu gama yin breakfast ba"?
"I'm sorry, Grandpa. I'll come back later"
ya faɗa tare da russinawa ya sumbaci forehead dinshi hajiya saratu dake kallonsu ba karamin burgeta sukayi ba, sabanin da da take jin haushi intaga baba obie da owais suna bama junansu kulawa kamar uba da da, abun yana 6ata mata rai saboda ita aganinta baya son twins saboda ubansu ba jinsinsu bane shiyasa yake nuna wariya tsakaninsu, abun da ta fahimta ayanzu owais yana matukar girmama baba obie biyayya yakeyi mashi sau da kafa dama ita zuciya tana son mai kyautata mata.
Tayi zurfi a tunaninta, muryar baba obie ta katseta, firgigit tayi tare da kallon shi, har chief ya fita daga dakin bata lura ba.
"Fada min meke damunki? Tun shigowarki na lura da yanayinki kamar bakya jindadi ko"? Gyara zama tayi, kafin ta fara kora mashi jawabi.
"Baba akan marwa ne! Naga ciwon nata yayi tsauri shine nace me zai hana amaida ita garinsu gaban iyayenta? Ita kanta zataso ta kasance a karkashin kulawarsu hankalinta sai yafi kwanciya, ba kamar nan ba, ba dangi iya bana baba, kuma kaga ciwon nan nata bana lafiya bane, zata iya goga ma wani...." fuskarta ayamutse tayi maganar, kamar irin ta damu da ita din nan.
Shiru baba obie yayi jim kafin yace"Auta, kin taba zuwa duba lafiyarta ne"? ɗaure fuska tayi
Murmushi yai"nayi mamakin jin maganarki, inace tin ranar farkon da ta fara lalurar baki kara leƙawa ba, aranar ma guduwa kikayi daga dakin ko"? Ya faɗa da zolaya, sunnar da kanta kasa tayi batare da tace komai ba.
"Meyasa zaki ce amaida marwa garinsu? Ko dan saboda lalurarta? Da can da take mana hidima bamu guje ta ba sai yanzu da Allah ya jarabce ta? Munyi mata adalci kuwa? Yamutsa fuska tayi"baba ka fahimce ni, nasani ba ita ta daura ma kanta ba, babu wanda yafi karfin Allah ya jarabce shi, amma ni dai aduba mana, saboda lalurarta su twins suka daina kwana gida, kasan su da kyankyami kuma abune da basu saba gani ba, shiyasa duk suka firgice, ni kaina hankalina ba akwance yake ba, wlh dakyar nake iya bacci agidan nan gani nake kamar nima abun zai shafe ni..." da mamaki baba obie ke kallonta, ta haɗe rai ba annuri akan fuskarta, duk zaman nan da ake baisan cewa su twins sun bar gidan ba sai yanzu da yaji a bakinta ay da tuni yasa an dawo da su.
"Indai akansu twins ne zansa su dawo gida, amma marwa bazata koma gurin iyayenta ba, har sai ta samu lafiya, saboda anan ta samu lalurar, kuma anan zata samu warakarta in sha Allah, Ni ba zan bari mutuncina ya zube a idon jama'a ba, yarinya da lafiyarta ta fara aiki agidan nan sai kuma in maida ma iyayenta don amfaninta ya kare uhyum? Kiyi tunani mana, su kansu iyayenta ba za su ji dadi ba, su ga mun maida masu yarinyar su da nakasa a jikin ta.. "
Ran hajiya saratu ya 6aci muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"baba ban taba neman abu agurinka kaki yi min ba, sai yau saboda kawai na nuna bana son zaman marwa agidan nan! Yakamta ka duba lamarin nan baba fisabilillahi saboda ita su twins sun kasa zama gidan nan, nima na rasa kwanciyar hankali, baba kafison farin cikin marwa akan namu kenan..." yunkurawa tayi zata miƙe da sauri ya dakatar ta ita"saratu koma ki zauna" zama tayi fuskarta ba fara'a...
Bottle water ya dauka me sanyi ya tsiyaya mata ruwa a cup ya mika mata, tana faman haɗe rai ta kar6a ta kurbi ruwan sau uku kafin ta ajiye tana kallon shi.
Yayi shiru yana nazarin maganar ta, arayuwarshi baya son bacin ran ya'yan shi, sannan baya son duk wani abu da zai haifar da rashin kwanciyar hankali atsakaninsu, sai dai bayajin zai iya mayar da marwa garinsu ahaka batare da taji sauki ba, yanajin tausayin ta, bayan haka bazaiso mutuncin shi ya zube agurin iyayenta ba.
"Baba nasan me kake tunani, indai akan iyayenta ne, wlh daga mun basu kudi zasu ja baki suyi shiru, kaga sai suci gaba da yin jinyarta, ni nayi alkwarin zan dauki nauyin duk wani abu da za'a kashe gurin nema mata lafiya, ni kawai gidan ke banaso ta zauna" gauran numfashi yaja kafin ya dubeta"auta" tace"naam baba"
"Kada ki makara, ki tashi ki tafi aiki, zanyi tunani, in sha Allah idan na yanke shawara zan sanar dake" amsa mashi tayi da toh, kafin ta mike tayi mashi sallama ta fuce daga dakin.
__________________________________✍️
Lokaci ɗaya Zuciyarta ta fara bugawa da matsanancin ƙarfi tamkar ana buga ganga, numfashinta ya fara fita cikin sauri, yayin da kirjinta ke harbawa yana sama da ƙasa da kokarin jawo iska a cikin hunhunta, wani irin gumine ya fara tsasstsafowa ta cikin hudojin gashin jikin ta, zufa ta soma gangarowa ta cikin nannaɗaɗdiyar sumar kanta tamkar yayyafin ruwan sama jikinta ne ya fara kakkarwa, Yatsun kafafunta dana hannunta suka kama kerma, idanunta suna arufe gam ta matsesu, fatar kwarin idanunta sai kerma take sakamakon kwayar idanunta dake jujjuyawa, kokari take ta buɗe idanunta takasa saboda raunin da sukayi, jikinta tamkar babu jini saboda rashin kuzari, ga wata matsiyaciyar kasala data daskarar da ita daga yunkurin da take yi na son farkawa, Allah kadai Yasan tsawon makonnin da ta dauka bata acikin hayyacin ta sakamakon duguwar sumar da tayi.
A kalla ta shafe awa cikin mayuwacin hali tana kokarin ƙarfafa kanta donta samu damar buɗe idanunta, ta ko'ina ba sauƙi, jikinta tamkar an daddaure shi da igiyar kaca, sai faman jijjiga jikin takeyi donta samu kwarin gwiwar tada kanta.
La66anta dake a bushe ƙamas fatarsu ta faffashe hada busasshan ɗigon jini, da ƙyar ta iya moving dinsu ta furta"GABRIEL" kwata kwata sautin muryarta baya fita, cigaba da ambaton sunan tayi duk da radadin da makoshinta keyi mata mai azabar zafi, meyasa ta ambaci sunanshi? A karo na farko data dawo hayyacinta? Saboda shi ne aranta.
Lokaci ɗaya ba zato ba tsammani kwatsam tayi wani yunkuri da iya karfin ta na karshe ta daddage ta banbare kanta daga jikin abunda take a kwance tayi wata irin zabura ta miƙe zaune tana faman jan numfashi, sannu A hankali ta buɗe idanunta wani irin duhune bakikkirin ya mamaye ganinta, bata ganin komai tamkar ta makance, batasan a ina take ba? Meya faruwa da ita? ta manta komai, kamar tayi loosing memory din ta, tayi matuƙar rudewa ta rikirkice tunaninta ya gushe, daddafe kanta tayi da tafukan hannayenta cikin rawar murya ta furta"A ina nake? wa ya kawo ni nan? Meya faru dani? Babu mai jina ne? Kuyi min magana bana ganin komai, ko dai na makance ne...." sautin muryarta baya fita dakyau.
Kamar ta fasa ihu haka take ji, saboda takasa gane meke faru da ita? A ina take.
A lokacin da batay tsammani ba, kwatsam ba zato ba tsammani, wani siririn haske ya kurdado ta saman gurin da take, Waro idanu waje tayi cikin tashin hankali da tsantsar rudani take kallon hasken, A hankali hasken ya fara mamaye ɗakin har saida ya karaɗe cikin sa tamkar da rana.
Idanunta suka washe, amatuƙar ruɗe take kallon inda hasken ya fito ashe fitilune na saman ceilling din dakin, da sauri ta dubi inda take a zaune, Metal bed ne (gadon ƙarfe) irin kirar zamanin da na kaka da kakanni, Gadon Yana da girma da tsayi, ga wata lumbutsetsiyar katifa tattausar gaske mai dadin zama hada matassan kai guda biyu, daga saman gadon Yana da rumfa hada labulaye a kewaye da shi, kamar irin gadon sarakuna
Gaba ɗaya ta ruɗe ta rasa gane waya kawo ta dakin? Da sauri ta kalli kayan jikinta, farar riga ce shara shara kamar matacin kwakko, komai na jikinta ana gani, rigar tana da dogon hannu, tsayin ta bai wuci Iya gwiwar ta ba.
Sumar kanta kamar an kifa mata yayi, ta bushe ba gyara duk gashin ya yamutse, ƙoƙarin saukowa tayi daga kan gadon sai dai ta kasa saboda tsayinsa bata san ya zatay ba, matsawa tayi daga bakin gadon ta leƙa ƙasa cikin sa'a ta ga matakala irin ta bene mai hawa shida, numfashi ta ɗan ja tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ɗaura ramammun kafafuwanta kan matalar farko ta yunwa zata miƙe aikuwa wani irin jiri ya kwashe ta saboda rashin kwarin jikinta gaba ɗaya ta kundumo ƙasa timmm! ba karamin dakuwa tayi ba, amma saboda karfin hali da kwarin gwiwa irin nata ta daddage ta miƙe tana faman fitar da numfashi mai haki kamar wadda tasha uban gudu
miƙewa tay tsaye tana kallon katafaren ɗakin mai girman gaske, gado ɗaya ne aciki sai book shelve ma'ajiyar littattafai, da tsoffin akwatinan karfe daga gani tsohuwar ajiya ce, ga wardrobe mai girma ta jikin bango, wurga idanu tayi kan tukwanan kasa da ta gani girke a kasa, ɗaya saman ɗaya an jera su daurin ɗaurin sunyi sauro a jikin bangon da suke, hada kwaryaye rufe da faifan su, hada tukwanan furanni masu ban sha'awa daga gani koma wanene mamallakin ɗakin ma'abocin son kayan laka ne ko kuma makerin su ne.
A hankali ta ɗauke idanunta daga kan tukwanan ta bi bangon dakin da kallo, zanunnuka ta gani masu ban sha'awa, a hankali take tafiya tana nufar tsakar dakin tana cigaba da kallon abun mamaki da al'ajabi gami da rudani ita dai batasan waya kawota cikin shi ba! Ta manta komai.
tana cikin jujjuya idanu karaf ta hango Madubi zagayayye yana da mariƙi dake ajiye kasa...takawa tayi cike da fargaba ta nufi madubin yayin da zuciyarta ke cigaba da harbawa da karfi da karfi..tsayawa tayi agaban madubin tana kallon fuskarta, ta tsorata da ganin ramar da tayi, kashin wuyanta ya kwambare kamar zai fasa fatarta, ziraran yatsun hannunta ta daura akan wuyan tana shafa kashin kafin ta motsa yatsun a hankali ta shafa fuskarta, manyan idanunta dara dara launin brown ta zare su tana bin kanta da kallo, tana iya hangen dukiyar fulaninta sun rame sun kanjame bayan ada ba haka take ba, tana da kira irin ta karfafan mata masu jini ajika amma yanzu ta rame ta bushe ta faɗa kamar ba ita ba.
da zata iya tuna mummunan abunda ya faru da ita har zuciya zata iya hadiya ta mutu saboda tana da fusatacciyar zuciya, idan ta rikice babu mai iya sarrafa ta.
ta jima tana kallon kanta a cikin madubin, jiri jiri ta fara gani a idanunta da sauri ta dafe cikinta dake yi mata kukan yunwa ga wani kishin ruwa na fitar shari'a, makoshinta ya bushe ƙamas ko yawun da zata hadiya ta samu relief din kishin babu shi abakinta.
juwa ce ta kwashe ta gaba ɗaya jikinta ya rinjayeta ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume..
Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Cikin abunda baifi minti ashirin ba kacal, taji safkar ruwa mai sanyi kan fuskarta, dogon numfashi taja haɗi da sauke ajiyar zuciya sam takasa ta6uka komai, ko yatsan hannunta bata iya motsawa saboda rashin kwarin jiki.
cikin mawuyacin hali ta ɗan yi karfin halin buɗe idanunta biji biji take kallon mutumin dake tsaye akanta batasan wanene ba.
Cikin disasshiyar murya ta furta"ruwa!ruwa!ruwan, zan sha! Kishi nake ji..." dakyar sautin muryarta ke fita tana tsaka da sambatu taji an kanga mata wani abu kamar bakin gorar ruwa saitin bakin ta, wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, lokacin da ruwan ya jiƙe makoshinta nan da nan ta fara kwankwaɗarshi makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat...!!
"Ki sha A hankali kada ki shaƙe" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar dattijuwar dake mata magana.
Sai dai kwata kwata bata fahimtarta, tafi buƙatar ruwan fiye da komai ayanzu kamar rayuwarta ta dogara akan shi.
saida tasha mai isarta kafin ta fara numfarfasawa tana haki, wata irin nutsuwace ta shige ta, hatta bugun zuciyarta da fitar numfashinta sun daidaita, ganinta dawo daidai sannu a hankali take kallon fuskar tsohuwar da ta tallabe kanta akan kirjinta, hannunta yana ruƙe da gorar ruwa, tana asanye da alkyabba fara sol mai hula, tsohuwace tukuf fuskarta duk tamoji tamoji, gashin kanta fari fat hurhura ta mamaye ko'ina na gashin, hatta gashin jagirarta fari ne fat, daga ganin tsohuwar tayi gwagwarmaya a duniya, tsufanta bai boye kyawunta ba, bakowa bace wannan face Tsohuwa
*KHALA* dattijuwar arziƙi, fara mai farar aniya, tsohuwa mai zuciyar imani, macace mai tausayi da jinkan mutane, abun da zai baka mamaki tana ɗaya daga cikin Elders na kurkukun ƙaddara sune masu fada aji, tana da ƙarfin iko, amma meyasa ta fita daban acikin su⁉️
Gabriella ta tsareta da idanu tana binta da kallon kurulla, fuskarta da alamun ruɗani
kamar yadda take kallonta haka itama tsohuwa khala take kallon ta.
la66anta na kerma ta furta"wacece ke? Wa ya kawo ni nan? Meya faru da ni? Ki fadamin ina son sani" shiru tsohuwar tayi nata ce mata komai ba.
"Kinyi shiru baki ce mun komai ba, meyasa kike kallona? Wacece ke?....." ta faɗa arude tana tararraba idanu.
Tattausan murmushi ne ya bayyana akan fuskar dattijuwar, cikin sanyin murya ta furta"Sunana Khala, nasan baki sanni ba, kuma baki ta6a jin labari na ba, yau ne karo na farko da kika fara ganin fuska ta..." cike da dattako tayi maganar.
Ta ɗan dakata tana kallon gabriella.
"Yau tsawon makonni Ina jinyarki, Due to the traumatic brain injury that put you in a coma, I know you can't remember what happened to you because you've lost your memory..." tun da ta fara magana Gabriella ta nutsu tana kallonta.
"naji dadin samun lafiyarki, inatayaki murna"
Saurari Littafin Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
ta fad'a fuskarta ɗauke da annurin farin ciki, ita dai gabriella takasa gane komai, gaba daya arude take da tsohuwar, bata fahimtarta
"Naji kin ambaci nayi jinya tsawon makonni bana acikin hayyacina, meya faru dani"? Girgiza kai khala tayi"I won't tell you because I don't want you to remember what happened to you, ko dan saboda lafiyarki, a yanzu nafi bukatar kwanciyar hankalinki, saboda ina da buri akanki"! Aruɗe Gabriel take kallonta, harta buɗe baki zata tambayeta wata irin yunwa ta murɗa cikin ta, da sauri ta dafe cikin da hannu tana faman yamitsa fuska ta kalli khala"ki taimaka min da abinci, yunwa nake ji..."
Ajiye gorar ruwan hannunta tayi, tare da taimaka mata ta zauna dakyar, Sandar ta dake ajiye kasa ta ɗauka, ta mike tare da juyawa ta nufi wani teburi dake a dakin hada kujeru biyu a kewaye da shi, daga saman teburin kwanukan abinci ne.
Ta ɗauko bowl ɗaya ta juyo tare da kallon Gabriella
"Bansani ba ko kin iya cin zogale da kuli..." tunkan ta ƙare maganar gabriella tace"Ina ci, koma menene zanci.." murmushi khala tasaki ta nufo gurinta ta miƙa mata kwanon, Hannunta na kerma ta cire murfin ta fara dibar zogalen tana ci, duk da babu ɗanɗano abakinta, kunnuwanta har motsi sukeyi tsabar dadi, hannu baka hannu kwarya take duma loma tana turawa a karamun bakin ta kamar zata shake, kamar kyaftawar ido ta lamushe shi tass hada sanya harshe tana lasar kwanan..dariya khala tayi"kin koshi ko kina bukatar kari" da sauri ta ɗaga mata kai, juyawa khala tayi cikin takun dattako ta koma gaban table din ta buɗe wani kwano mai ɗauke da tsokokin nama taje ta mika mata kwanon"kalacina ne na safe, da naci na rage, bansan yau zaki farfadowa ba, shiyasa ban tanadar maki abinci ba, amma kiyi hakuri da wannan, idan aka kawo min lunch dina zan baki kici ki koshi" kar6e kwanon gabriel tayi hannunta na kerma ta fara daukar tsokar tana ci, sai da tacinye tass khala ta ɗauki gorar ruwan ta miƙa mata, ta kar6a ta sha.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wani irin relief taji a jikin ta, duk da bata koshi ba, taji ɗan dama dama a cikinta.
Kokarin mikewa tayi da sauri khala ta taimaka mata ta mike tsaye kan kafafunta, cikin sanyi murya tace"har yanzu baki bani amsar tambayoyin da nayi maki ba, na ruɗe na kasa tuna komai, wanene ya kawo ni nan? Ko kece? Sannan meya faru dani? A ina nake?
"Ki manta da komai, sai ki zauna lafiya, tunawar baida amfani, idan kika bani hadin kai, kuma kika bi sharuddan da zan fada maki zaki tsira da rayuwarki, idan kuma kikayi min gaddama zaki dawwama awahala..." kalamanta sun rikita gabriela cikin rawar murya tace"meyasa zaki hanani tambayarki? Ina son nasan wacece ni! Meya faru dani, ina ji araina kamar na manta wani abu arayuwata, dan Allah ki tuna min..." dafa kafadarta tsohuwa khala tayi"nayi maki alƙawarin zan baki amsar tambayoyinki amma ba yanzu ba, har sai zuwa lokacin da tunaninki ya dawo dai dai..." shiru gabriella tayi gaba daya jin kanta take kamar ba ita ba, kamar ma ba aduniyar mutane take ba.
Tafiya khala ta soma yi tana nufar cikin dakin calmly ta cigaba da magana tana kallon fuskar gabriel
"Sharuddan da zan gindaya maki, na farko koda gigin wasa kada ki ƙetare iyakarki! Ma'ana kada kiyi yunkurin nema ma kanki hanyar da zaki fita daga dakin nan! Babu ruwanki da komai da zaki gani adakin nan! Ki zama tamkar makauniya, bana son mutum mai karanbani da kafiya..." ta faɗa tana jinjina mata kai, ita dai gabriela tayi zuru tana binta dana mujiya saboda batasan komai ba sai yadda akai da ita.
"Idan kika bani hadin kai, zaki tsira da ranki, kuma zan gatantaki, babu abunda zaki nema ki rasa adakin nan.." fuskarta da murmushi tayi maganar, kafin ta juya ta ɗaga sandar hannunta tayi mata nuni da wata ƙofa
Sannan tace"wannan kofar, makewayina ne, idan uziri ya kamaki zaki iya shiga, harma wanka zaki iyayi don kiji dadin jikin ki, arana zaki ci abinci sau uku, idan kadaici ya dame ki, zan baki story books da zaki dinga karantawa, suna da dadi zasu debe maki kewa, ga kuma furanni abun sha'awa zasu faranta maki rai" ta faɗa still da murmushi akan fuskarta.
Gabriella tayi sototo tana kallonta kamar sakarya, wuce wa tsohuwa khala tayi agaban bookshelve ɗin ta tsaya tare da kai hannu cikin shelve tana neman storybooks din da zata bata guda uku ta curo ta juyo ta nufi Gabriel ta nuna mata su.
"su kadai na baki iznin ki karanta, bayansu ban laminta ki ta6a sauran littattafan dake a cikin shelve din ba" jinjina mata kai tay alamar toh, bayan ta kar6i books din khala tace"ki samu guri ki zauna, har yanzu jikinki ba kwari," cike da ladabi ta amsa mata da toh, don yanzu ganinta take kamar mamanta saboda itace mutun na farko data fara gani a idanunta bayan tsawon lokaci data ɗauka a coma..
Ruƙe hannunta khala tayi, taja ta har zuwa gaban table din ta zaunar da ita kan kujera"idan kika gaji da karatun, ki koma kan gado ki kwanta kiyi bacci ki huta" cikin sanyin murya ta amsa mata da toh.
"Akwai inda ke yi maki ciwo a jikin ki"? Girgiza kai tay alamar a'a
"Okey, ko bayan na fita daga dakin, kika ji wani guri nayi maki ciwo a jikin ki, ki kira sunana sau uku, zan ji ki"
"Toh,"
"Good girl" ta faɗa tare da shafa fuskar Gabriella da yatsun hannunta.
"Ki kula min da kanki" lumshe ido gabriela tayi kafin ta buɗe su tuni tsohuwa khala ta bace ma ganinta, har saida taji gabanta ya fadi ganin babu ita, akan table din ta ajiye books din data bata.
ta mike tsaye jikinta na kerma take bin ko'ina da kallo a kokarinta nata gano ina ta shiga, ganin babu ita adakin, yasa ta hakura da nemanta, ta juya ta nufi kofar makewayin da ta nuna mata, ta buɗe ta shiga, makewayine irin na zamani ya hadu komai cikinsa fari kyal, a tsaftace ba kazanta, a hankali take kallon cikinsa, bathtub ta gani ga shower, ga toilet seat, da cabinet, bata tsaya bata lokaci ba, ta cire rigar jikinta ta rataya a hanger, ta zukunna zatay fitsari taji gabanta amatse dakyar fitsarin ke fita nishi ta dinga yi a wahalce ta samu ta kammala.
ta miƙe tana faman sauke ajiyar zuciya, Takura kanta tayi da tunani har saida kwakwalwarta ta fara neman rikicewa tukunna ta hakura tana faman jan numfashi, ta nufi kwamin wankan ta shiga ta kwanta tare da kai hannu ta kunna bathtub faucet ta cika kwamun da ruwa mai ɗumi wata irin ni'ima taji mai dadin gaske.
Ta daɗe acikin ruwan tana ɗumama jikinta kafin tayi wanka ta maida rigarta, ta fito ta zauna kan kujerar, ta dauki storybook ta fara karantawa.
Murmushine ya bayyana akan fuskarta, da alama labarin da take karantawa ya faranta ranta, babi huɗu ta karanta, ta fara jin kasalar bacci, miƙewa tayi tare da kwashe books din ta nufi book shelves din dakin inda taga khala ta dauko mata su, tana kokarin ajiyesu ta hankaɗe wasu jerin littattafai dake a shelves tana kokarin tallabe su biyu suka rikito ƙasa, wani irin faduwar gaba ta ji, tsoro ya kamata tunawa da gargadin da tsohuwar tayi mata akan kada ta ta6a komai na dakin, jikinta na kerma ta zuƙunna tana kokarin tattara books din kamar diary suka an kulle su da makulli tayadda baza'a iya buɗe su ba.
Akan laps dinta ta daura books din kamar ance ta kalli covers dinsu karaf tayi tozali da hoton abunda ke akan diary na farko, zanan kananun yara ne su uku sanye da jajaye kaya, mata biyu sun sanya namiji a tsakiyar su, kayan matan rigace dai dai gwiwa launin ja, shi kuma namijin riga da wandone jajaye, abun da ya ɗaure mata kai da hoton cover din, duka yaran an daure masu hannayensu da igiya, an toshe bakinsu da jan kyalle, ga hawayen jini kwance kan fuskokinsu, da rubutun larabci aka rubuta sunan books din kokarin karantawa tayi A hankali ta furta sunan shi *sijill al-sujnā* bata san menene ma'anar sunan shi ba, janye na farkon tayi ta dubi sunan ɗayan diary din *tārīkh sijnil qadar* miƙewa tayi da sauri ta maida su gidan da suka fadowa, ta gyara su dakyau ta yadda ba azagane dun faɗo ba, da sauri ta nufi matakalar gadon ta haye ta kwanta tare da lumshe idanunta.
___________________________✍️
*HAJJATY*
Safa da marwa takeyi atsakar dakinta, Hannun ta ruƙe da wayarta, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita, saboda fargaba da tashin hankalin ciwon marwa jiya taga abunda ya rikitar da ita, kusan kwana tayi adakin marwa tana kokarin shawo kanta saboda kukan da takeyi abun yayi yawa kamar zata kashe kanta, hajjaty ga tsoronta da take ji amma ahaka ta daure ta zauna adakinta har saida ta shawo kanta ta hanyar kunna mata karatun kur'ani kafin ta samu jikin marwa yayi sauƙi har bacci ya ɗauke sannan ta dawo daki, yau tun da safe ta buga ma sheikah imam kira awaya ta sanar da shi halin da marwa take aciki, tace mashi ta kasa gane meke damunta, sheikh imam ɗin yace zai shigo in sha Allah.
A yanzu haka shi take jira, ta kasa shiga dakin marwa saboda bata jin dadin ganin ta a mawucin hali, yarinyar ba karamun tausayi take bata ba.
Kira ne ya shigo wayar da sauri ta duba screen din wayar ganin sunan sheikh imam ne yasa ta daga da hanzari ta daidata nutsuwarta gurin yi mashi sallama bayan ya amsa mata yace"na iso gidan" amsa mashi tayi da toh, da sauri ta dauki mayafi ta rufawa kanta, ta zura flat shoes a kafarta, ta fito ta nufi main falo din gidan tasan anan yake tsayawa idan ya shigo.
Tunkafin ta karasa ta hango shi zaune kan sofa as usual cikin shiga ta magadan annabawa.. masu aikin gidan dake ta kai komo cikin girmamawa suke gaishe da shi, har abunsha sun kawo mashi da snack, har ya fara shan lemun ya hango hajjaty, mikewa yayi tare da tunkararta, da fara'a tace"barka da safiya malam, ya gida ya iyali" murmushi yayi jin ta tambaye shi ya iyali.
bayan sun kammala gaisawa tayi gaba yabi bayanta har zuwa dakin Marwa saida ta fara shiga kafin tayi mashi iso ya shiga daga ciki, a lokacin marwa tana kwance kan katifarta, bacci mai nauyine ya dauke ta sai faman jan numfashi take yi, daga gani awahalce takeyin baccin.
"Malam, ni dai narasa gane kanta cikin kwanakin nan, in ta fara kuka kamar ranta zai fita, kuma wlh ina kiyayewa gurin bata maganin kamar yadda ka ce.." tay maganar tana kallon shi.
Matsawa yayi daga gaban mattress din Ya zuƙunna Yana kallon yatsun hannayen marwa da fatar fuskarta, farat ɗaya ya gane babu lafiya, ciwon nata ma ƙara ha66aka yakeyi babu alamun sauƙi, lamarin ya ɗaure mashi kai, a kalla ya shafe mintuna yana kallonta yana nazari akan yanayin ta.
Hajjaty dake kallon fuskarshi sheikh imam tuni tasha jinin jikinta ganin yanayin shi ba walwala.
mikewa yayi tare da kallon hajjaty"anya kuwa kinbi sharuddan bata maganin dana fada maki dai dai? Ko dai kinyi kuskure ne" arude ta girgiza kai"wallahi ban ta6a kuskureba, ina kokarin kiyayewa kamar yadda na fada maka..." bayani tayi mashi yadda take bata maganin, dalla dalla kamar yanda ya fada mata, tabbas ya yarda da maganarta, abunda bai gane ba ta ina matsalar take! Shiru yayi jim yana kara bin marwa da kallo
Muryar hajjaty na rawa tace"malam akwai matsala ne"?
Ya fahimci hajjaty bata lura da habbakuwar ciwon marwa ba ..
Numsafawa yayi kafin ya furta"ina maganin nata yake"?
Jikinta na 6ari tace"ga su can akan mirror, bari in dauko maka" dakatar da ita yayi da hannu tsayawa tayi, tana faman zare idanunta, juyar da kai sheikah imam yayi tare da kallon gaban mirror din marwa A hankali Ya nufi gaban madubin Ya tsaya tare da kallon robobin maganin, ɗaya ya ɗauko ya buɗe ya kalli ruwan dake a ciki, yakai hancin shi ya shinshina da sauri ya kawar da kanshi gefe saboda zaurin daya buso hancin nashi.
Hankalin hajjaty ba karamin tashi yayi ba ganin yadda ya haɗe rai sosai, ɗaya bayan ɗaya ya buɗe murfin robobin cikin matsanancin tashin hankali ya juyo a sukwane ya kalli hajjaty dake ta zare idanunta
"Ya akai haka"? Ya faɗa yana dubanta
Muryarta na rawa tace"meya faru shiekh? Ban gane me kake nufi ba" haɗe rai yai tamkar ba sheikh imam ba, da kakkausar murya yace"wanene ya canza ruwan maganun dana baki"! Rass taji gabanta Ya faɗi ta fara zare na mujiya, jikinta ya hau yin kerma abunka ga matsoraciya kamar wata mara gaskiya sam takasa bashi amsar tambayar da yayi mata.
Hakan ba karamin bata mashi rai yai ba"baki ji ina magana bane! Wanene Ya canza ruwan maganin? Saboda ni ba haka na baki shi ba, gaba ɗaya an canza ruwan cikin shi, bayan ni a iya sanina launin ruwan maganin baya canzawa..." A fusace ya fada yana binta da kallon tuhuma
Hankalin ta idan yai dubu toh ya tashi, Gabanta ya dinga faduwa gaba daya tabi ta rude, ta rasa amsar da zata bashi, wlh kwata kwata bata lura da hakan ba, sai da yayi maganar ta tuna da lokacin da ɗan aiken shi ya kawo mata maganin tabbas da ta buɗe tana dubawa taga launin ruwan ya banbanta.
Wahalallan yawu ta haɗiya cikin rawar murya ta furta"wallahi na rantse da wanda raina yake a hannunsa bani na canza ruwan maganin ba! Wlh bani bace, bansan wanene ba, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji"un..." gaba ɗaya tabi ta ruɗe wata irin zufar tashin hankali ce ta wanke fuskarta, gani take kamar shiekh imam yana zargin ta.
Girgiza kai shiekh imam yayi"kin bani mamaki! Meyasa zakiyi mata haka? Ko dan kin gaji da jinyarta ne? Ni fa ban tursasa maki ba, aikin lada ne tun lokacin dana bukaci wanda zai kula da ita da kin fadamin bakiso ay da ba haka ba"
Runtse idanunta tayi, wasu zafafan hawaye suka wanke fuskarta, kalaman sheikh imam sunyi mata tsauri, taji ɗacin su azuciyarta.
"ka yarda dani, wlh ni ba muguwa bace, bazan iya cutar da marwa ba, ina da zuciyar imani, ko kiyashi bazan iya cutarwa ba, balle ɗan adam, wlh bani na canza ruwan maganin ba, na shiga ukuna"
ta fada tare da dafe goshinta da hannu daya.
tunda sheikh imam yaga yadda ta rikice nan take ya fahimci ba ita bace, dama da biyu ya furta
"Ya Isa haka, Na yarda bake bace, amma wanene toh? Dole akwai yarda akai aka canza ruwan, kuma koma wanene mutunne, lokacin da dan aikena ya kawo maki maganin a ina kika ajiye shi"? Waro ido waje tayi murya na rawa tace"a dakina"
Sheikh imam yace"hakan na nufin anan aka canza ruwan maganin kenan? To wanene? Akwai wanda ke shiga dakin ki ne"? Shiru tayi jim gabanta na faduwa da matsanancin karfi, hankalinta ya tashi, kwata kwata bata kawo ma ranta pravin ba, tasan bazai ta6a yi mata hakan ba, me ma zai kaishi canza maganin marwa? Har abada ba za ta bari wani yasan akwai alaka tsakaninta da pravin ba.
Tayi zurfi cikin tunaninta muryar sheikh imam ta katse ta"kinyi shiru baki bani amsa ba? Wakike tunanin ya canza ruwan maganin? In har baki fadamin gaskiya ba, zanje in fada ma baba obie abunda ke faruwa"
a firgice ta zare mashi dara daran idanunta, wani irin faduwar gaba ta ji daram kamar ana mata lugude a kirjin ta, arude ta girgiza mashi kai"kayi hakuri sheikh, wlh bani da masaniya, amma nayi maka alkawarin zan binciko koma wanene" jinjina kanshi yayi"kinyi alkawari? Ɗaga mashi kai tay"in har kika sa6a hmm kinsan sauran, keda baba obie ne" matse kwalla tayi, cikin sanyin murya tace"in sha Allah ba zan saba ba, amma sheikh meyasa kake tunanin wani ne ya canza ruwan? Baka tunanin bakaken aljanun jikinta ne sukayi mata hakan don kada ta samu sauki? In ba haka ba taya za'ay wani ya canza ruwan? Akan wani dalili"? Ta faɗa tana kallon fuskar shi.
Murmushi shiekh imam yayi tare da dan girgiza kanshi kafin yace"ba al'janu bane suka canza ruwan, mutunne, dole akwai yadda akayi, ki zauna kiyi tunani dakyau..."
Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh,
"Sannan sheikh, akwai wani abu da marwa takeyi min, ni dai nagaza fahimta, duk in na shugo dakin zan bata magani, sai ta dinga goga hannunta a kasa, taita yunkurin yi min magana idan taga na kasa gane me take nufi saita kifa kanta jikin pillow...." bata ƙare maganar ba sautin tarin marwa ya katse hanzarin su, sam sun manta da ita dakin, maganganunsu su ne suka farkar da ita
Atare suka kalle ta, tana a zaune kan mattress din, ta jingina kanta jikin bango, idanunta suna rufe ga siraran hawaye dake zarya kan kuncinta, gwanin ban tausayi
"Marwa"! Jin muryar sheikh iman yasa tay saurin bude idanunta.
tana ganin shi ta fara kokarin yin magana donta gaishe da shi sai dai takasa.
"Basai kinyi min magana ba, na fahimce ki," ajiyar zuciya ta sauke, idanunta sun kaɗa jawur da su
Zukunnawa yai agaban katifar yana dubanta yace"Hajjaty ta faɗa min da akwai wani abu da kike yi mata nuni da hannu ta kasa gane menene ko zaki nuna min in gani"?
da sauri ta ɗaga mashi kai, jikinta na kerma ta matso bakin kafitar, ta daura hannunta akan floor ta dinga goga su tana kallon sheikh imam cike da sa ran zai fahimce ta, ita dai hajjaty sai faman zare ido takeyi fatanta Allah yasa shikeh imam ya gane menene marwa ke son fada mata abun yana damunta.
A kalla marwa ta kwatanta mashi yafi sau biyar ganin kamar baigane ba yasa ta fara matsar kwalla.
zurfin tunani ya shiga can yace"wani yana zuwa dakin nan? Girgiza mashi kai tay alamar a'a"
"Ko ana tsoratar dake ne"? Still ta girgiza mashi kai, shiru yayi yana kara hasasowa can yakuma cewa"kodai kina son kiyi rubutu ne.. "Ga mamakin sa sai yaga ta daga mashi kai alamar eh hada ɗan murmushin ta.
Hajjaty tayi mamakin jin hakan sosai, da sauri ta nufi drawer din marwa ta fara neman littafi dakyar ta zakulo wata jotter tare da pen, ta dawo bakin katifar ta buɗe mata jotter din ta ajiye agabanta, ta zira mata pen din dakyar ta matse biron da hannayenta, ta soma kokarin gogawa paper din, lamarin ya daure masu kai, daga hajjaty har sheikh imam din, sun kagara da suga me ta ke son rubutawa.
Duk yadda taso ta rubuta sunan wanda yayi mata aika aikar takasa, biron yaki zama a hannunta duk ta cakalkala paper din akarshe ma ta yayyage, jefar da pen din tayi kasa ta fashe da kuka tare da kifa kanta jikin pillow, gaba daya jikinsu yayi sanyi, zuciyarsu ta raunata da tausayinta.
Cikin sanyin murya shiekh imam ya ce"kiyi hakuri, na fahimce ki, akwai wani abu da kike son fada mana, amma kin kasa, abunda nakeso dake ki kwantar da hankalinki, in sha Allah nan badajimawa ba ciwonki zai zama labari, zamu tayaki da addu'a sannan zan canza maki wasu magungunan.
tun tana shesshekar kuka hartayi shiru ta hakura musamman da taji maganar sheikh imam hankalinta ya ɗan kwanta, har taji zata iya hakura har zuwa time da zataji sauki tunda bata da mafita.
Mikewa yayi tare da kallon hajjaty,
"ki zubda ruwan maganin dake a cikin robobin, zan kawo maki wani amma fa dole kiyi takatsantsan, kada ki kuskura ki bari wani yasan inda kika boye su ko kuma wani yasan na canza mata maganin nan daga ni sake wannan maganar, In kuwa kikai gangancin da wani ya sani har aka sake samun matsala to ki kuka da kanki domun kuwa bazan kyale ki ba...." a kausashe yayi mata maganar saboda ta ɗauki maganar shi serious, baiwar Allah duk tabi ta rude jikinta har kerma yakeyi sai taji dama bata kar6i aikin ba saboda bata son abunda zai hana ta kwanciyar hankali.
Sallama shiekh imam yayi mata, ya fuce yabarta da jimami
________________________✍️
Zaune yake a gefen gadon shi, jikinshi sanye da voile fari, tafukan hannayenshi tallabe da qur'ni, Ya tattara dukkan nutsuwarsa akan kira'ar da yake yi, acan kasan zuciyar shi damuwa ce cunkushe baya jin dadin zuciyarshi saboda halin da Benazir take a ciki ya damu ita, yana matukar jin tausayin ta.
Yana tsaka da yin kira'ar, sautin knocking Ya katse shi
Ɗaga murya yayi"wanene"?
"Ya shureim ni ce, Ina son yin magana dakai" jin muryar Benazir yasa shi saurin miƙewa ya ajiye kur'anin Ya nufi kofar ya buɗe mata, A hankali ta shigo ciki, jikinta sanye da abaya, tayi rolling veil akanta, hannun ta ruƙe da yar purse dinta, ga wasu highhill da ta saka a kafarta, aruɗe yake kallon ta ganin hada make up akan fuskarta.
"Ina kwana ya shureim ka tashi lafiya..."
"Lafiyalou sister, Ya jikin naki"?
"Naji sauki sosai" shiru sukayi fargaban shi kada tace yakaita gurin azeezaty ya san halinta in rigimarta ta motsa.
"Lafiya? Naga kamar kinyi shirin zuwa anguwa,"?
Murmushi ta sakar mashi
"Eh, gidan su anila nake son zuwa, jiya munyi waya da ita, ta fadamun yaronta baida lafiya, ashe shiyasa bata kira ta yi min ya jiki ba.." tun da tafara magana shureim ke kallonta gani yake kamar karya ta shirga mashi don ta samu yakaita gidan.
Ganin irin kallon da ya ke yi mata ne yasa tai saurin furta"wallahi dagaske nakeyi maka, bari in kira maka anilan ku yi magana" tay maganar tare da kai hannu ta buɗe purse dinta, ta curo wayar ta kira layin anila tana fara ringing, ta miƙa mashi fuskarta dauke da murmushi.
"Assalamu alaikum, Anila barka da safiya"!
On the other hand tace"ya shureim ina kwana ka tashi lafiya? Ya jikin benazir din? Wlh junaid ba lafiya shiyasa ban samu na kira naji ya ku ke ba ashe ma har an sallame ta" ajiyar zuciya ya dan sauke.
"Lafiyalou anila, Benazir taji sauki, itace ma ta kira min ke, tace tana so tazo duba junaid, ubangiji Allah ya bashi lafiya, in sha Allah yanzu zamu zo"
"Allah Ya kawo ku lafiya, ngde" sallama sukayi ya mika ma Benazir wayar
"Ki bari sai anjima muje, yayi wuri yanzu" girgiza kai tay haɗi da ɗaure fuskarta"ya shureim itafa ta nuna tana son inje yanzu"
"Naji, amma dan Allah idan mu ka je gidan, kada ki yi mata maganar yarinyar nan Azeezaty, nasan hada hakan yasa kike zumudin zuwa gidansu, kiyi hakuri Benazir yarinyar nan ba yarki bace idan kika sa hakuri in sha Allah kema zaki ga taki yar.."
dukar dakai kasa tay, idanunta suka ciko da kwalla.
"Kiyi hakuri idan maganata batayi maki dadi ba" girgiza kai tay'na fahimce ka, in sha Allah bazanyi mata maganarta ba, ay na hakura tuntuni" ajiyar zuciya ya sauke "haka nakeson ji, Kin fada masu mommy zaki fita" girgiza kai tay"a'a yanzu in zamu tafi sai mu gaya masu" amsa mata yai da toh
Kafin ya juya ya shiga ciki ya ɗauko carkey dinsa Ya fito suka jera atare suka nufi dining room, mutanan gidan duk suna azaune suna yin breakfast, mutumin ya haɗe fuska sai shan kamshi yake kamar iska tana mashi wari, abincin ma da aji da izza yake cin shi tamkar baya son tauna shi..
A fakaice hajiya layla take aika mashi harara kamar zata rufe shi da bugu, shi dai Alhaji ubaid ya nutsu Yana cin abin cin shi, yayin da zeenatu take fuskantar mommyn ta, sam takasa cin abincin ruwan lemu kawai take ta aikin durawa cikin ta, hankalinta da tunaninta suna akan Azeezaty, jiya har mafarkinta tayi, bata da burin daya wuce su haɗu da ita, don ta tambayeta wacece Unaizah mai kama da ita❓
Takun tafiyar su shureim ne yaja hankulansu ga duban su,
Bayan sun karaso cikin girmamawa suka gaishe da su kowa ya amsa masu banda Alhaji musa hakan bai dame su ba, sun riga sun dan halinshi
mami ta dube su"ina zuwa haka shureim"?
"Zamuje gidansu anila ne, yaronta baya jin dadi" hajiya sarah tace"Allah sarki, itace kawar benazir wadda suke zuwa asibiti dubata ko"? Benazir ta amsa mata da eh"Allah ya bashi lafiya" mami tace"ay da kun fada min tun dazu dana shirya mun tafi atare, amma idan kun isa gidan ku kirani dan Allah" suka amsa mata da toh, Alhaji ubaid yace"ku gaishe min da mutanan gidan, ace ma anila inayi mata yamai jiki, Allah ya bashi lafiya, idan na samu lokaci zan shigo gidan" ya amsa mashi toh.
"Ya shureim zan biku dan Allah" zeenatu ce tayi maganar, har zata miƙe Alhaji musa ya jefa ta da wani kallo tuni tasha jinin jikin ta, muryarta na rawa ta furta"dan Allah daddy ka bari su tafi dani, mommy kice ya shureim ya tafi dani inaso in bi su" atsawace Alhaji musa ya furta"karki kuskura ki ƙara magana! " a tsorace taja baki tayi shiru, idanunta akan fuskar shureim dake kallon ta, wani irin tausayinta ne ya kama shi, yana so su tafi da ita sai dai yasan daddynta bazai barta ba.
"Musa ka barsu su tafi da ita tunda tana son zuwa..." Alhaji ubaid ne yai maganar,
Banza yayi da shi tamkar baiji abunda yace ba, hakan ya sosa zuciyar Alhaji ubaid musamman layla ranta ya 6aci, harara ta galla mashi akan idonshi, ita day hajiya sarah tayi shiru batace komai ba.
"Shureim ku tafi, Allah ya tsare hanya.." ta fada tare da yi masu alamar su je, ruko hannun Benazir yayi suka kama hanyar fita daga falon yana jiyo sautin shesshekar kukan zeenatu, har waiwayowa yayi sai kallon shi takeyi duk sai yaji ba dadi amma idan ya tuna abunda alhaji musa ya fada mashi sai yaji kwara zamanta agidan duk da shi baiga amfanin hakan ba saboda yayi imanin cewa Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake.
Har suka shiga mota, bai daina tunanin zeenatu ba, ta tsaya mashi aranshi yana jin tausayin rayuwarta
Tsawon mintina kafin suka karaso anguwarsu anila, motarsu ta na shigowa layin gidan suka hango anila atsaye cikin shiga ta abaya fara ta goya baby junaid abayanta, hannunta ruƙe da wayarta..
Tunkafin su karaso ta ɗaga masu hannu alamar su tsayar da motar, agabanta yayi parking, ta nufi backseat ta buɗe ta shiga ta zauna kafin ta warware goyan junaid ta kwantar da shi kan kirjin ta.
Dr shureum yayi zaton gidan zasu shiga har zai tada mota benazir ta ruƙe hannun shi ya dubeta da mamaki"ba ciki zamu shiga ba, Anila ki faɗa masa inda zamuje"
Cikin sanyin murya tace"ya shureim obie estate zaka kaimu" aruɗe yake kallonsu da mamaki yace
"Bangane ba, me zakuyi acan? Anila fada mun ina fata dai ba gidan iyayen yarinyar nan zakuje ba"?
"Ya shureim muje kawai, zamuyi maka bayani daga baya, wani abune mai mahimmanci zai kai mu can" bai musa masu ba, yayi reverse ya miƙi hanyar fita daga unguwar
"Anila ya jikin junaid din! Ko dai shima duk plan dinku ne"? Murmushi suka saki, Anila tace"a'a ba plan bane, dagaske baida lafiya, amma jikin nashi da sauƙi.."
"Meke damun shi ne"? Kafin ta bashi amsa junaid ya fara mutsu mutsu kamar zai farka hakan yasa tay shiru tana kokarin lalla6a shi don ya koma baccin.
Cikin kulawa dr shureim yace"Allah ya bashi lafiya" ta amsa mashi da ameen.
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MAY LIKE THESE POSTS
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite
Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 43 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 05, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE
Bayan ta samu ta lalla6a junaid ya koma bacci, tun da motarsu ta haura kan titi suke ta satar kallon juna tsakaninta da Benazir ta cikin mirror din motar kamar wasu munafukai, kwata kwata hankalin dr shureim baya akansu ya tattara nutsuwarsa akan driving din da yakeyi, hakanan ranshi ya raya mashi ya dubi fuskar Benazir, ta wutsiyar idanun shi ya ke kallon ta adaidai lokaci sun kura ma juna ido ita da Anila da alamun rashin gaskiya atattare da su, duk dagowar da zaiyi sai ya kama su suna kallon juna ta mirror, gyaran murya yayi masu da sauri suka dube shi.
"Ban yarda daku ba! Ku faɗamin gaskiya meke faruwa ne? Meyasa kuke satar kallon juna ta mirror? Ina fa lura da duk wani motsinku acikin motar nan, kamar baku da gaskiya, ku ji tsoron Allah ku sanar dani abun da kuke boye min"!
Shiru su ka yi suna ta ƴan kame kame an rasa me bude baki ya bashi amsa duk sun sha jinin jikin su.
"Da ku nake magana? Me zamuje yi a obie estate? In har baku fadamin ba zan dakata da yin driving din..." fuskar shi adaure yayi maganar batare daya kalle su ba, kallon juna suka sake yi ta mirror, kafin su yanke shawara da junan su dr shureim ya yi parking din motar a gefen titi Ya kashe ta tare da jingina kanshi jikin headrest.
"In har ba zaku fadamin abunda kuke boye min ba, to kuwa zamu kwana anan ne.."
yawu Anila ta hadiya tare da kallon benazir da hankalinta ya gama tashi,
Cike da fargaba benazir tace"yaya shureim..dama ummm gidan su Azeezaty zamu je..." Dakyar ta ƙare maganar ganin ya juyo dakai ya kalle ta tuni ya hade rai, annurin fuskarshi ya gushe rai a6ace yace"meyasa baki jin magana ta? Har nasiha nayi maki nace ki yi hakuri tun da yar nan ba taki bace ki hakura mana, ni dama tun da naga take takenku raina ya bani gidan su yarinyar nan zaku je, to wlh bada ni ba, da nasan gidan su azeezaty zamuje da ban biye maku ba." kallon juna sukayi hankalin su atashe damuwa ce ƙarara akan fuskokin su.
Juyawa yai tare da kallon Anila cikin sanyin murya yace"haba anila! Meyasa zaki biye mata? Ni nasan bada son ranki ba, itace ta matsa maki, Benazir bata da hakuri ta fiye kafiya da naci, ba irin lallashin da ban yi mata ba akan ta hakura da yarinyar nan amma taƙi jin maganata"
kifa kai Benazir tayi jikin seat din da take azaune ta fashe da kuka tana fadin"yaya shureim na hakura da ita, nasan ba yata bace na yarda da hakan, Anila tayi min bayanin komai dangane da ita kuma na fahimce ta...." ta ƙare maganar tana shesshekar kuka, kafin yayi magana Aneelerh ta riga shi cewa"ka yi hakuri yaya shureim ban nemi shawararku ba nayi gamon kaina, saboda ina tausayin halin da Benazir take a ciki" ta fada tana kallon fuskar shi"shekaran jiya ta kirani awaya take faɗa min ita fa tun a asibiti ta fahimci yarinyar nan ba yarta bace kun ce mata taj ya dauketa sunje mall shiru basu dawo ba kun hana tasan gaskiya kun boye mata saboda baku san 6acin ranta, ni kuma abunda nayi tunani duk daran dadewa dole Benazir tasan gaskiya tun da gashi harta kirani awaya ta fadamin tagane ba yarta bace shiyasa kawai na faɗa mata gaskiyar zance, sannan na kwantar mata da hankali nayi mata nasiha nace tayi hakuri da boyen matan da akai munyi hakanne saboda gudun kada mu rasa ta"!
tun da ta fara magana dr shureim yayi shiru yana sauraronta, jikinshi yayi mugun yin sanyi zuciyar shi ta karaya.
Benazir ta ɗaura da cewa"Yaya shureim bayan Anila ta fadamin gaskiya, nayi kokarin cire azeezaty araina saboda a lokacin na hakura da ita, nasan inda rabo wata rana nima Allah zai bayyanar min da ƴata Angel, amma wallahi nakasa ya shureim Inason Azeezaty, Allah Ya jarabce ni da kaunarta, kai shaida ne akan irin Son da nake mata, ko bayan dana gane ba ƴata bace, ina sane nake yi maku pretending saboda kada ku rabani da ita, shiyasa ko bayan da muka dawo gida na ɗaga hankalina sosai saboda na fahimci kun rabani da Azeezaty" ta ɗan dakata da yin maganar tana kallon dr shureim dake kallon ta,
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
numfasawa tayi kafin taci gaba da cewa"jiya batare da sanin kowa ba, na kira Aneelarh awaya na fada mata halin da nake a ciki na rashin azeezaty, na roƙe ta akan ta taimaka min ko sau daya ne in ganta, saboda na kasa cire ta araina, shine tace min in jira zata yi magana da iyayen yarinyar idan sun amince muje gidan zata sanar dani, sai yau da safe ta kira ni ta fadamin tayi waya da daddyn azeezaty yace muzo gidan mu ganta, har ce mata yai ita ma yarinyar tana son ganina tun bayan data koma gida kullum sai ta yi maganata kaga itama kenan tana jin abun da nake ji agame da ita, ko da bamuje gidan ba, zata sa daddynta ya kawota gurina ne saboda itama ta damu dani"
Muryarta adisashe tayi maganar tana kallon dr shureim, ajiyar zuciya ya sauke har cikin ranshi yaji dadi da Benazir ta hakura abunda ya kara kwantar mashi da hankali jin cewa da sanin iyayen yarinyar zasuje gidan dama shi abun da yake jima fargaba kada su kwasa su je gidan ba tare da sanin iyayen yarinyar ba, benazir ta sanya masu rigima akan su bata ƴarta, tun da ba hankali gareta ba, yanzu kuma yaji daga bakinta tasan me takeyi ashe dagangan takeyi masu pretending don kada su raba ta da yarinyar, baiyi mamakin jin hakan ba, cos ya riga da ya san halin Benazir tun tana ƙaramarta idan ta kwallafa rai akan abu har aljanun karya take yi masu don ta ɗaga masu hankali kan abun.
yayi zurfi acikin tunanin shi, Benazir ta katse shi cikin rauni na murya tace"ya shureim dan Allah ka taimaka ka kai mu gidan, nasan me kake tunani, in sha Allah bazan bamu matsala ba, nayi maka alkawarin hakan, Ni kawai burina inga Azeezaty, kona samu kwanciyar hankali"
nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanun shi yayi shiru jimmm yana nazari kafin ya buɗe su akan fuskar Anila"ba ki yi laifi ba Anila, kinyi abunda ya dace ne, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani gurin yi maki godiya ba saboda naji dadin yadda kika damu da Benazir, wlh kin faranta min rai, saboda kwanakin nan dakyar nake bacci saboda damuwar halin da Benazir take a ciki, amma yanzu kin sama mana maslaha atsakanin mu da ita, ubangiji Allah yasaka maki da mafificin alkhairinsa."
Ajiyar zuciya Aneelarh ta sauke, fuskarta dauke da murmushi tace"ameen ya shureim, ay ba godiya atsakaninmu, mun riga mun zama ɗaya, zan iya yin komai saboda farin cikin ku" har cikin ransu sunji dadin maganar Aneelerh.
Kallon Benazir yayi suka haɗa ido da juna, fuskarta tayi jawur saboda kukan da tayi"kiyi hakuri kinji, ki share hawayenki, yanzu na fahimce ku, kuma naji dadin yadda kika ɗauki dangana, in sha Allah kema zaki gana da yarki wata rana, zamu ci gaba da yi masu addu'a ubangiji Allah ya bayyanar mana da su" suka masa mashi da ameen
Daga bisani ya tada motar ya cigaba da yin driving dinsu, Hankalinsu Ya kwanta sosai, Yanzu basu da sauran damuwa, har yanzu junaid bai farka daga bacci ba, maganganun da sukayi baisa ya farka ba, wani irin bacci yake yi mai nauyin gaske.
_________________________________✍️
*UNAISAH ANGEL💓*
Tana a zaune tsakiyar Bedmattress dinsu, kayan baccin jiya ne a jikinta riga da wando da alama ko wanka batayi ba, gaba daya hankalinta na akan notebooks din da ta jera kan katifar, ta sanya farin glass a idanunta kamar wata malaman makaranta, ta ruƙe red pen a hannunta, ta nutsu tana dudduba notebooks din data kar6a a hannun su Parveen, Assignment ɗin da ta basu jiya shine yau take dubawa, ta rasa gane me suka rubuta, duk jagwalgwalo ne, wani rubutun kamar na ƴan china wani shigen na thailand, tun da tafara checking note books din fuskarta ɗauke da murmushi wani lokacin saita kwashe da dariya hada kifawa kan katifa ba karamin nishadi suka sanyata ba, ta fahimci kwata kwata basu gane abunda take koya masu, kwakwalwarsu bata daukar karatu, bayin Allah sai taji ta karajin tausayinsu da kaunar su.
Motsin buɗe toilet door ne Yasa ta ɗago dakai ta dubi kofar, Batool ce ta fito daga ciki, ta sanya bathrobe kafafuwanta sanye da slippers, ta nannaɗe sumar kanta da farin towel, dakatawa tayi da yin tafiya ganin irin kallon da Unaisah ke yi mata duk saita sha jinin jikinta, da sauri ta bi kanta da kallo don ta ga ko tayi wani abu badai dabai ba, ganin lafiyalou babu wani aibu yasa tace"Sister, meyasa kike kallona? Akwai wani abu ne"? Murmushi ta ɗanyi tare da girgiza mata kai"bakomai wlh, You look so gorgeous, like a pearl" kayataccen murmushi Batool ta saki har dimples dinta suka lotsa, taji dadin yabon da unaisah tayi mata.
"tun dazu nake jira ki fito nima in shiga inyi wankan," ta faɗa tare da saukowa daga kan gadon ta fara tattara notebooks din ta ɗaurasu kan bedside drawer.
"ki zauna ki jira ni, idan na fito zan za6a mana kayan da zamu sanya, har make up zamuyi" dadine ya lullubeta"amma pls kada ki daɗe"
"Toh" da sauri ta nufi mirror chair ta zauna tana jiran fitowar ta.
Tsawon mintuna kafin ta fito daga toilet din, tayi ɗaurin gaba da towel fari, ta naɗe sumar kanta da towel kamar yadda Batool tayi...tsayawa tayi tana kallon batool ganin ta daura kanta gaban mirror idanunta arufe alamar bacci takeyi da alama taji dadin wankan da tayi shiyasa ta 6uge da bacci
Karasawa tayi gaban mirror din ta ɗauko hairdryer ta jona ta a socket, takai hannu ta tum6uke towel din da batool ta ɗaure kai da shi, ta saita hairdryer din akanta iska ta fara busowa buuuuu a firgice Batool ta farka tana kokarin buge dryer din hannunta.
Dariya Unaisah tayi"Sorry na katse maki baccin ki, inaso na gyara maki gashin ne naga kin wanke shi, ajiyar zuciya ta sauke tare da jingina bayanta jikin kujerar ta dafe saitin zuciyarta da hannu"kin bani tsoro sister, wallahi nayi azan wani mugun abunne"
Still fuskar Unaisah da murmushi ta cigaba da cakuɗa sumar kanta tana busar mata da ita
"Duk in na tuna farkon haduwar mu a prison, sai inji na kara kaunarki a zuciyata, saboda kin so ni a lokacin da kowa ke guduna, bakisan wacece ni ba, amma ki ka kirani da sunan sister dinki, duk da irin ƙyarar da nake maki hakan baisa kin juya min baya ba, har saida kika dasa min kaunarki a cikin zuciyata"
Murmushi Batool tayi"nima har yau idan na tuna farkon haduwarmu sai inji na kara kaunarki, abun da ya daure min kai a lokacin ya kuma bani mamaki, irin masifar son da nake yi maki, wallahi ko yan uwana da muka taso atare da su tun kafin mu mallaki hankalin mu ban yi masu irin son da nake maki ba, Allah ya jarabce ni da kaunarki a zuciyata..." ta fada tare da runtse idanunta.
Unaisah dake kallonta ta cikin mirror, tuni taji kwalla ta cika idanunta wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta..
Shiru sukayi na wani lokaci kafin batool ta ce"sister akwai wani abu dake damuna"!
"Menene"? ta tambaya tana kallon fuskarta
Cikin sanyin murya ta furta"Danish, wallahi na damu da shi, bansan meyasa ya canza mana ba, ba kamar lokacin da muna a prison ba, gaba ɗaya, baya son kowa yaje kusa dashi, ko magana nayi mashi dakyar yake amsa mini, har tambayar shi nayi meke damun shi yace min bakomai..." yanayin yadda tayi maganar tamkar zata fashe da kuka..
"Hatta su Haris sun fahimci baya son suna zuwa dakin shi, shiyasa suka janye jikin su, ni so nake naji idan wani abu muka yi mashi sai mu bashi hakuri ya yafe mana" shiru unaisah tayi batare data iya furta komai ba, Dama tasan dole su damu da halin ko in kulan da yake nuna masu, batasan meyasa yake takura rayuwarshi ba, kwata kwata baya son kowa ya ra6e shi in ba ita ba, yanzu da suka samu sa6ani atsakanin su abun Ya ƙara ta6ar6arewa, har cikin ranta bata jin dadin hakan
Kokarin kwantar mata da hankali tayi"pls kada hakan Ya dameki, sai kace bakisan halin shi ba tun a prison, dama can shi ba mai san shiga mutane bane, kinfi kowa sanin halin danish, baya son hayaniya, shi indai zai samu gado ya kwanta yayi bacci toh bashi da wata damuwa, ki daina tunanin ko kunyi masa laifi ne, wlh babu abunda kukayi masa abun a jininsa yake, kuma bawai ya daina damuwa daku bane, kuna aran shi" ajiyar zuciya Batool ta sauke, kalaman unaisah sun kwantar mata da hankalin ta.
Bayan ta gama gyara ma Batool gashin, ta zauna itama ta gyara mata nata daga bisani Unaisah tayi masu make up, powder suka shafa da lip gloss mai kyalli launin pink.
Bayan sun gama suka koma gaban closet ɗin su, inners suka fara sanyawa, Unaisah ta ɗauko mata sabuwar bra ta miƙa mata don ta sanya ta kar6a tafara kiciniyar sakata kamar zatai dambe saboda bata saba ba, batasan ya zata sakata ba, dariya unaisah tayi"bari na taimaka maki" ta faɗa tare da ruƙo hannun bra ɗin ta saƙala mata shi, ajiyar zuciya ta sauke da sauri ta koma gaban mirror tana kallon kirjinta, Yau ne karo na farko data fara sanya bra, tayi mata cuf cuf yadda kasan wadanda suka ɗauko bras din sun san size din ta.
Unaisah dake kallonta ji tayi dama ita, yamutsa fuska tayi"idan kin kammala kallon madubin ga kayan da zaki saka nan na zabo maki" ta faɗa tare da daura mata su kan gado.
Batare da bata lokaci ba, kowan nan su ya sanya kayan shi, tsayawa sukayi agaban mirror suna kallon tsantsar kyan sukayi
gaba ɗayansu Long sleeved gown ce a jikinsu launin Ice blue sai kyalli take da ɗaukar ido, ga wata hadaddiyar Silver necklace da suka saka a wuyan su, yayin da wrists din hannunsu ke asanye da Beaded Bracelets, sun saki curly hair dinsu ya lullu6e gadon bayan su, yadda kasan wadanda zasu halacci gasar miss word su kansu sun jinjina ma haɗuwarsu, sun tasa madubi gaba sai jujjuya jikinsu sukeyi.
Saida suka gama kallace kansu kafin unaisah ta dauko masu fragrance set suka fara barin ruwan turare ajikinsu saida kamshin ya gauraye dakin su tukunna su ka dakata da shafa shi.
"Wlh munyi kyau, Allah Ya zuba mana ruwan kyau sister" batool ce ta fada tana yarfa hannayen ta,
murmushi unaisah tayi tana kallon kanta ta cikin mirror
"Sai yau na kara ganin kamanninmu Allah, dukanmu tubarkalla dogaye ga dogon hanci, ɗan bakin mu heart shaped, gaskiya mungode ma Allah..." proudly ta faɗa
"Bari na dauke mu hoto" da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan pillow, ta dawo kusa da batool suka hada kai ta fara daukar su pics har kusan kala ashirin..
"Bari inje in nuna ma aunty ummi wankan dana dauka nasan zata ruɗe da kyawuna" da gudu ta fuce daga ɗakin hannayenta ruke da bazar rigarta kamar wata amarya, har ta fuce daga dakin unaisah bata daina kallonta ba har saida phone dinta ta fara ringing kafin ta kau da idonta, screen din wayar ta duba ganin sunan My man yasa ta ɗan yi murmushin gefen fuska kamar yasan jiran kiran shi takeyi girman kai ne ya hana ta fara neman shi, zama tayi daga gefen gadon ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta
Tayi shiru bata ce komai ba, tana jiran jin me zaice mata.
"My Angel..." bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa"ɗazu na tura maka message, nace ka sauko down muyi breakfast why didn't you come?"
Ta faɗa tana haɗe fuska kamar tana agaban shi.
Softly ya furta"Naga sakon da kika tura min, amma ban fahimci me kika rubuta ba, shiyasa ban zo ba" jikinta ne yayi sanyi lakwas duk sai taji ba dadi
"Meyasa baka kira ka tambayeni me na rubuta maka ba? Shiru yayi bai bai tanka mata ba.
"I have no answer,"? Still baice mata komai ba.
"Okey, kayi breakfast dinka"?
Sai lokaci taji ya ɗan sauke ajiyar zuciya"nayi, Haris ne ya kawo min adaki"
Lumshe idanunta tay, wani irin yanayi take jin kanta, Sautin muryarshi ba karamin rikita ta ya ke yi ba, A hankali ta kwantar da bayanta jikin pillow, dadin muryar shi take ji, idan suna yin waya har bata son suyi sallama da juna
______________________________✍️
Lokacin da motar dr shureim Ta biyo kan titin Obie Estate tun kafin su karasa Benazir take bin ganin da kallo yau ne karo na farko da ta fara zuwa, ta ruɗu da ganin haɗuwar katafaren entrance gate din dake abuɗe ga wasu fusatattun sojoji dake tsaron ƙofar cikin taku na majiya karfi suke kai komo abakin gate din sun kasa sun tsare babu mahalukin daya isa ya ƙetare kofar batare da an basu izni ba.
Hatta dr shureim bai ta6a zuwa ba, ya dai san estate din amma bai ta6a shiga ciki ba.
rage gudun motar yayi slowly yayi parking dinta gefe guda, don yasan ba lallai su barsu su shiga ciki ba.
."Anila kina ganin zasu barmu mu shiga"? Benazir ce tay mata maganar tare da dubanta
"Eh, amma dole saida iznin wani daga cikin mutanan gidan," ta fada tare da daukar wayarta daga cikin handbag, A hankali ta kwantar da baby junaid kan seat ta dubi dr shureim"bari na kira daddyn azeezaty din" amsa mata yai da toh, ta bude murfin motar ta fito daga waje ta danna ma shi kira, bayan ya ɗaga ta kara wayar a kunne.
"Taj, munzo yanzu haka muna a bakin entrance gate na estate din"
On the other hand taj yace"tare da wa kike zo"? Lokaci daya taji gabanta Ya fadi, tunawa da gargadin da sukayi mata sam ta manta.
Dakyar tay karfin halin ce mashi"tare da Benazir, sai yayanta dr shureim shine ya kawo mu..." bata kare maganar ba taj ya furta"why Anila? Why? Kin manta kashedin da chief yayi maki? Akan me zaki zo da su gidan nan? Ke kadai fa nace kizo saboda Angel tana son ganin junaid"
Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba duk tabi ta rude, ta fahimci ranshi ya 6aci
"Kina atare da su ne"?
"A'a na fito daga cikin motar ni kadai ce, Zanyi maka bayani, nasan zaka fahimce ni"!
Shiru yayi yana sauraron ta
cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri idan na bata maka rai, nasan ban kyauta ba, amma ba yadda zanyi ne, bazan iya jure ganin Benazir cikin mawuyacin hali ba, wlh baka ga yadda ta koma ba, saboda rashin Unaisah bata da kwanciyar hankali, ko abincin kirki bata iya ci duk ta rame, Kai kace min da zarar ta dawo hayyacin ta, in sanar da ita cewa yarta ce, yanzu tasan komai..." bata kare maganar ba, Taj yace"kina nufin kin fada mata har abunda ya faru da mu"? Yamutsa fuska tay tamkar zata saka mashi kuka tace"na faɗa mata, amma na gargadeta akan kada ta bari kowa yasan kuna araye, sannan nace mata kada ta bari unaisah ta gane itace mamanta kamar dai yadda kukayi mana bayani haka itama na sanar da ita, kuma tayi min alkawarin ba zata sanar da kowa ba"
"yayanta fa kin fada mashi? Shiru tayi gabanta na faduwa
Har saida ya sake maimaita tambayar da yayi mata kafin tace"A'a bai sani ba, mun dai fada mashi zamu zo gurin Azeezaty ne, kuma kasan dr shureim bai son ka ba, bazai iya gane komai ba, balle shi da bai cika shiga sabgar da bata shi ba wlh baida matsala, mutunne mai kamun kai"
saida takai aya kafin yace"Anila na fahimce ki, amma Bana so Benazir ta yi wani abu da zaisa unaisah ta gane cewa mahaifiyarta ce, pls komai ya tafi yadda muka tsara shi, idan kika bari aka samu matsala ke da chief ne"
"In sha Allah baza asamu matsala ba, zamu kiyaye"
Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar shi"okay, zanyi magana da chief, ku ƙara hakuri," amsa mashi tay da toh, bayan sunyi sallama ta buɗe murfin backseat ta shiga daga ciki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya, atare dr shureim da anila suka kalle ta
"Ya ake ciki"?
Murmushi ta danyi tare da kallon benazir tace"yace mu jira, za'a bamu iznin shiga" ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke.
Dr shureim yace"junaid har yanzu bai farka ba, ko dai kin bashi sleeping pill ne" yar dariya tayi"a'a wlh, nima nayi mamakin baccin shi kamar wanda yasha ƙwaya, may be ko dan jiya bai samu isasshen bacci bane..." ta faɗa tare dakai hannu ta shafa gefen fuskarshi.
Benazir tace"Allah nafara gajiya da jira, Allah yasa kada su shanya mu awaje, nifa naƙosa naga babyna" cike da zolaya dr shureim yace"bari maman babyn taji kina kiran sunan ƴarta da sunan taki, kotu ce zata rabaku" dariya sukayi gaba dayan su.
Kafin wani daga cikinsu Ya ƙara furta kalma, Suka ji anyi knocking window glass din motar
da sauri dr shureum ya sauke glass din
Wani soja ne tsaye fuskar shi a murtuke ba annuri ya furta"Who is Anila?" Yawu ta hadiya muryar ta na dan rawa tace"I am sir"
"Okay, ku shiga daga ciki, an baku izni" kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, dr shureim ya tada motar ya nufi drive way din da zai sada su da cikin estate ɗin, Anila ce ta dinga nuna mashi hanyar da zai bi har suka karaso gidan chief, basu sha wahala ba, motarsu na karasowa bakin gate din jami'an dake tsaron shi suka basu iznin shiga ciki bisa umarnin mammallakin gidan hakan na nufin an san da zuwan su, tun da motarsu ta shiga benazir ta ke ta jinjina kai wato sunyi mamakin haduwar katafaren villa din, daga gefen wani stunning fountain dr shureim ya tsayar da motar.
Rungume baby junaid anila tayi akan kirjinta, ta buɗe murfin motar ta fito, kafin dr shureim da Benazir suka fito daga ciki, A hankali suke karewa tamfatsetsen ginin kallo, ba su ta6a zaton za'a samun daular data kai ta Alhaji musa haduwa a birnin abuja ba, sai gashi yau Allah ya haɗasu da gidan director general Of Isod.
Jikin motar suka jingina bayan su, kowa da abun da yake sakawa aran shi, musamman Benazir ta kosa ta ga taj da Angel dinta murmushi kawai take saki ita kadai tasan dadin da take ji
"Bani junaid din in ruke maki shi" miƙa mata shi anila tayi bayan Benazir ta kar6e shi ta rungume a kirjin ta, Jami'an dake kai komo sai kallon su suke yi.
"Ina zamu nufa"? Benazir ta fada tana kallon Anila, tayi shiru saboda batasan ina zasu dosa ba, har ta yanke shawarar kiran Taj, kwatsam Horn din mota Ya karaɗe kunnuwan su, kusan atare suka dubi hadaddiyar motar dake tunkaro kirar black Mercedes
Agaban su motar tayi parking, sun ƙura ido suna jiran ganin wanene mamallakin ta.
Ta ciki aka buɗe car door din, gently ya fito daga ciki gaba daya suka bi shi da ido, yana sanye da kayan kakinsu na isod ya rufe fuskan shi da mask, zagayawa yai ta other side ɗin motar ya buɗe murfin, slowly chief ya fito daga cikin, hannun shi ruƙe da wayar shi, fuskarshi sanye da face mask, gaba daya dr shureim Ya kasa dauke ido daga kallon su, musamman Benazir gabanta har faduwa yakeyi gani take kamar taj ne sai dai takasa gasgata hasashenta saboda face mask din dake akan fuskar shi yasa ta kokwanton anya shi ne? sai kallonshi take yi shi kuwa ya haɗe fuska yama ki yarda su haɗa ido da juna don kada ta samu sararin da zata gane shi ne, Hankalin Anila ba karamin kwanciya yayi ba, aranta ta ayyana ashe ma suna atare da chief din tasan already ya fada mashi kwa6ar da tayi masu, fatanta Allah yasa kada ya tuhumeta.
Cikin girmamawa Anila ta gashe da su, chief ya amsa mata, dr shureim Ya mika masu hannu sukayi musaba a mutunce suka gaisa da juna.
Anila ta lura da taj, dama tasan za'a rina, ita ta gane shine kuma tasan saboda Benazir ya sanya face mask, sannan yaki tanka masu don kada taji muryar shi.
"Ya jikin naki" muryar chief ce ta katse mata zancen zucin nata, da sauri ta kalle shi har saida taji gabanta ya fadi, kwata kwata bata kalli fuskar shi ba, sai da yayi mata magana, ta so ta ruɗe sai taji kamar muryar Zaki.
jin tay shiru bata amsa ba yasa Aneelerh tayi saurin ce mashi"jikinta da sauki, Alhamdulillah" A hankali ya dubi taj sarai ya fahimci dagangan yaƙi magana saboda ex-wife dinsa, ita kuma baiwar Allah ta tsareshi da ido saboda ta gane shi ne.."
"Bismilla..." ya fada tare da nuna masu walkway din da zasu bi
Gaba yai tare da taj su Aneelerh suka bi bayansu, baiwar Allah Benazir ta zama kamar mutun mutumi, jikinta duk yai sanyi laƙwas cikin muryar raɗa tace ma anila"taj ne ko"? Jinjina mata kai anila tayi" shine amma kiyi hakuri dan Allah, kada ki sanya damuwa aranki, har yanzu yana akan dokin zuciya ki bashi lokaci nasan zai kula ki." hawaye ne suka cicciko idanunta, ganin shi da tayi ya fama mata ciwon son shi dake a cikin zuciyarta.
Gaba ɗaya ya canza mata, ba kamar taj din da ta sani bane ada, Ya zama babban mutun dashi, ga kyawun sura da cikar kamala, har wani ƙwarjini yayi mata, lallai da da yanzu ba ɗaya ba, cos ba zata taba manta yadda ta azabtar da shi da soyayyarta ba, ta gasa mashi aya hannu, ta raina shi kamar bawanta haka take sarrafa shi sai abunda taga dama akeyi agidan su, yanzu kuwa taj yafi karfinta, ita kanta ta shaida hakan, dr shureim dake abiye da su kwata kwata bai lura da halin da Benazir take a ciki ba, hankalin shi baya akan su
abakin wata glass door suka dakata da yin tafiyar, Chief ya buɗe masu kofar, Sanyin a c ne ya fara busowa ta cikin ɗakin mai dadin gaske, atare chief da taj suka shiga, Benazir da Aneelarh suka shiga daga bayansu kafin dr shureim ya shigo, sitting room ne Ya gaji da haduwa, a saman sofas suka zauna, anila da benazir da dr shureim suna akan sofa mai mazaunin mutun uku, yayin da chief da taj suke a zaune kan 2 seater dake fuskantar su.
Miƙewa taj yai ya nufi benazir, tayi azan zaiyi mata magana ne harta fara dan sakin murmushi bai ko kula ta ba, ya sanya hannu ya kar6i junaid daga hannunta, Ya koma ya zauna tare da kwantar da shi kan kirjin shi.
Da ido Aneelah tayi mata alamar tayi hakuri ta kwantar da hankalin ta, dukar da kanta kasa tay tamkar zata sanya kuka ba dan bata so dr shureim ya gane gaskiya ba ai da tuni ta cakumi rigar taj ta rungune shi.
Takun tafiya ne Yaja hankulan su ga duban mai shigowa, wani jenior agent ne Ya shigo hannun shi ruƙe da wooden tray mai ɗauke da softdrinks and snacks ya ajiye masu akan table kafin ya juya ya fuce
"Bismillah, zaku iya sha" Taj ne ya fada tare da yi masu nuna da table din, Anila ta ɗauki juice ta zuba masu a cups ta miƙa ma dr shureim ya kar6a, koda ta mika ma Benazir girgiza mata kai tay alamar a'a, jiki asanyaye Anila ta fara shan wanda ta zuba mata.
falon yayi tsit baka jin sautin komai sai sanyin a.c din dake ratsa fatar jikin su.
Gaba daya hankalin benazir na akan taj, Ta kasa janye idanunta daga kallon fuskar shi, so take ya ɗago su hada ido yaƙi yarda, sai ma Ya maida hankalin shi akan junaid dake rungume a kirjin shi, a hankali yake shafa sumar kan shi da hannun shi, son yaron yake kamar yadda yake son Angel dinsa.
"Dan Allah kuyi min bayani wanene daddyn Azeezaty a cikin ku? ina son nasan shi" dr shureim ne ya katse masu shirun nasu.
Da hannu chief ya nuna mashi taj,
murmushi dr shureim yayi"Allah sarki, dama inaso ne in ƙara yi maku godiya, wallahi munji dadin taimakon da kukayi mana, Allah ya saka maku da alkhairi..." atare suka amsa mashi da ameen.
"Daddyn Azeezaty, Ina tayaka murna, ka ƙara gode ma Allah daya baka yarinya mai hankali irin na manya, ga kaifin basira gata da saurin shiga rai" murmushi taj yai har cikin ranshi yaji dadin yabon da shureim yayi ma angel dinsa"thank you so much," ya faɗa yana mai nuna jin dadin shi.
"You should call her" chief ne ya faɗa tare da mikewa Ya nufi hanyar fita daga dakin.
Curo waya yai daga aljihun kakinsa Ya kira layin Unaisah
Bayan ta ɗaga yace"daughter kina ina ne"?
On the other hand tace"ina adakin mu" ɗagowa yai tare da kallon su anila, gaba daya hankalinsu na akanshi.
Kwantar da baby junaid yai kan sofa, yai ma anila nuna da hannu da sauri ta mike taje ta dauki baby junaid ta rungume a jikinta.
Miƙewa taj yayi ya nufi bakin kofar dakin ya tsaya saboda baison su ji abun da zasu tattauna, muryar shi kasa kasa ya ci gaba da yi mata magana
"Auntynki tazo tana son ganinki" yana juyo sautin ihun farin cikin data saki
"Daddy, atare da baby junaid tazo"?
"Eh, harma da aunty Benazir dinki,"
"Wayyo Allahna, gani nan zuwa daddy" da sauri yace"ban gama magana ba" nutsuwa tayi tana sauraron shi
"Ina yan uwanki suke"?
"Suna a falo"
"Okay, bana son kizo da kowa, ke kaɗai zaki zo..."
"Amma daddy suna son ganin baby junaid, na riga na fada masu mun hadu da aunty anila kuma sun kwallafa rai da son ganin ta"
"Look, kija baki kiyi shiru, kada ki fada masu game da zuwanta, kin riga da kinsan komai ba sai nayi maki bayani ba, idan har yaran nan suka zo zasu iya furta wata kalma da zaisa agane wani abu game daku, kuma hakan ya sa6ama dokar aikin mu, shiyasa nace kizo ke kadai, ke ma din dakyar na samu chief ya amince su ganki, Ina fata kin fahimce ni"? Shiru tayi da alama bata ji dadi ba
Fahimtar yanayin ta yasa shi sassauta muryar shi"Idan ki ka kwantar da hankalin ki, next time zasu sake dawowa ne in yaso sai su hadu da su"
ajiyar zuciya ta sauke"toh daddy, na fahimce ka, amma ya zanyi da batool? Ta riga da taji komai, namanta tana adakin, dan Allah daddy kabari in zo da ita"
shiru yayi baice mata komai ba
"Daddy, naji kayi shiru, pls ita kadai, batool ba zata bamu matsala ba, tana da hankali, zan ja mata kunne akan kada ta furta komai da zaisa su san wani abu dangane da rayuwar mu, nasan zata fahince ni"
Numfasawa yai kafin yace"ya zanyi dake tunda kin matsa akan son zuwa da ita, kuzo amma kinsan Allah idan aka samu matsala ki kuka da kanki" ya fada da zolaya, dariya tayi"ba abunda zai faru in sha Alah"
"Okay," ya fada tare da yi mata kwatancen inda sitting room din yake.
"Pls kada ku dauki lokaci, suna jiranku" cike da zumudi ta amsa mashi da toh, katse kiran yai tare da juyawa ya dubi su dr shureim sunyi shiru suna jiran tsammani, kallon benazir yayi ta kifa kanta kan sofa hand, idan yace baiyi kewarta ba yayi karya, almost 17yrs rabon shi da ita, ta canza mashi ba kaɗan ba, ya danyi mamakin girmanta, ta zama babbar mace ba kamar lokacin daya aureta ba, yar siririya da ita sai rashin kunya cike da kai, daurewa kawai ya ke yi ba ya san ta gane ya yi kewarta yafi so ta ɗanɗani irin ɗacin da ya ji aran shi na irin bakin cikin da ta kunsa mashi, Abun Ya ta6a zuciyar shi ba kaɗan ba, ƙwara itama taji ajikinta kamar yadda yaji, batare da sanin su ba, Ya fuce daga sitting room din Ya koma waje Ya tsaya zuciyar shi cike fal da tunaninta, Allah sarki tsohuwar zuma, yajima yana tambayar kanshi meyasa zatay mashi haka? Laifin me yayi mata? bai ta6a tsammanin tsanar da tayi mashi takai harta haifa mashi jinjira ta ajiye acikin kwamin wanka ta gudu tabar su, kusan shekara goma sha bakwai, bata ta6a waiwayarsu ba, taya zai iya yafe mata cikin sauƙi? Idanunshi ne suka ciko tab da kwalla, da sauri ya jingina kanshi jikin bango, Allah kadai yasan radadin da yake ji acan kasan zuciyar shi,
Maganar anila ya fara tariyowa inda take ce mashi bafa yin kanta bane, shiga akayi tsakaninsu, bada son ranta ta gudu ba, har yanzu tana son su, girgiza kai yai cikin karyayyar murya ya furta"ban yarda ba, nasan wacece Benazir, zata iya aikata fiye da haka ma, dama ba sona takeyi ba..." shi kadai yake sambatun shi abunne ya dame shi.
"Har yanzu shiru basu ƙaraso ba, ko dai Azeezatyn tana a school ne"? Dr shureim ne yayi maganar
Anila tace"nima nayi tunanin hakan, watakil sai an daukota daga school, mu dan kara hakuri" ta fada tare da kallon Benazir da ta langwa6e kai jikin sofa, ta lumshe idanunta... Tsantsar tausayinta ne ya kamata, dr shureim yayi tunanin saboda azeezaty ta shiga halin damuwa hakan yasa shi yi mata gyaran murya ta buɗe ido ta kalle shi"meke damunki ne? Tun da muka shigo na lura da yanayinki! Nasan bai wuci saboda azeezaty bane ko"! Murmushin yaƙe ta sakar mashi cikin sanyin murya tace"kamar ka sani ya shureim,
wlh na ƙagara da in ganta, kamar zan zauce" yar dariya yayi tare da miƙa hannu kan table din gaban sofa din, Ya dauki juice Ya zuba a cup, yana kokarin kaiwa bakinsa Ya ɗan dakata Yana sauraron muryoyin da kunnuwanshi suke jiyo mashi
"Mu je ciki mana"
"Dan Allah ki fara shiga, ni wallahi kunya nake ji,"
"Meye abun kunya a ciki, Aunty Anila ce fa, tare da aunty Benazir, ni ki wuce mu shiga..."
Kusan atare Anila da Benazir suka dubi ƙofar sitting room din, su biyu ne ɗaya ta rurruƙe ɗayar da ta turje akan ba zata shiga ba, Kamar zasu yi dambe, kwata kwata basu ga fuskokin su ba, Ita Batool mayafin da ta yi rolling akanta ne ya warware ya rufe fuskarta, sakamakon ingizatan da unaisah takeyi, Yayin da ita kuma Unaisah take abayanta tana kokarin tursasa mata akan ta shiga, murmushi Anila da benazir suka saki suna kallon ikon Allah
Cikin sanyin murya dr shureim Ya furta"Ki bi ta a hankali pls, kada ki ja ta fadi taji ciwo"
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(300)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 44 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 06, 2024
Sponsored Link
BOSS BATURE✊
Jin maganar dr shureim yasa ta saki Batool da ke ta faman yin haki, tana ta ƙoƙarin Gyara veil ɗinta daya rufe fuskarta Unaisah taja hannun ta suka nufi Ciki, Gaba ɗaya idanun su Benazir na akan su, Yadda suke tafiya a tsanake cikin nutsuwa yayi matuƙar burge su, Tamkar tagwaye komai na jikinsu kala ɗaya, gwanin ban sha'awa suke kallon su, Batool sai kiciniyar gyara mayafin takeyi takasa ga ɗan kunnanta da ya maƙale gashinta kwata kwata Unaisah bata lura da halin da take a ciki ba, sai janta ta ke yi.
"Babyna" Benazir ce ta kira ta da sauri ta dubi inda take atsaye lokaci ɗaya ta saki murmushin farin ciki, ta saki hannun Batool cike da zumudi ta nu fe ta Benazir ta rugumota a kirjinta kamar zasu koma mutun ɗaya, wani irin sanyi ne Ya ratsa zukatan su, kamar sun yi shekara ba su haɗu ba sunyi kewar juna.
Fuskar Aneelerh ɗauke da murmushi take kallon su har cikin ranta taji dadin faranta ransu da ta yi...
"Babyna, nayi kewarki, shi ne kika tafi kika barni, fushi nake dake baki damu dani ba" ta fada tare da ɗago kanta ta haɗe fuska alamar bata ji dadi ba' rufe fuska unaisah tay da tafukan hannayenta cike da jin nauyinta ta furta"i'm really sorry mommy na, wallahi na damu dake, ban manta dake ba kina araina"
Murmushi Benazir tay, tare da manna mata peck a forehead ɗinta, ta tallabo fuskarta da tafukan hannayenta, wani irin kallon so da kauna take bin ta da shi kamar zata maida ita cikin cikinta, tuni Unaisah tasha jinin jikin ta da ganin irin kallon ƙurullan da take yi mata.
Bakomai take tunawa ba face lokacin data barta a kwamin wanka yar jinjira da ita cikin jini, sai gashi Allah ya raya abun shi, ta girma ta zama ƴar budurwa da ita, tsakaninta da taj sai godiya yayi namijin ƙoƙari gurin rainon Angel, har abada bazata ta6a rabuwa da shi ba, ko da bazai kula ta ba sai ta san yadda tay ta maida auran su ko dan saboda Unaisah, ganin bata da alamun daina kallonta ne yasa ta ƙara rudewa muryarta adabarbace ta furta"Ya jikin naki? Kin ji sauƙi"? Yar dariya Benazir tay don ta fahimce unaisah ta gano ta
Ɗaga mata gira tay"Alhamdulillah my baby, naji sauƙi sosai..."
"Yanzu kin gane ni wacece" dariya suka yi gaba ɗayan su, Hakan Yasa ta fahimci taji sauƙi yanzu tasan ita ba ƴarta bace.
.
"Ki ɗauka har yanzu ban dawo cikin hayyacina ba, saboda bana so ki daina kira na da sunan mamanki, kuma bana so na rasa kulawar da kike bani" tattausan murmushi unaisah tay"in dai wannan ne baki da matsala dani, zan cigaba da kiranki mamana, babu abunda zai canza"
Gaba ɗaya Sun maida Hankali akan Unaisah, In ka cire dr shureim wanda gaba ɗaya ya tattara Hankalin shi akan Batool dake ta ƙoƙarin gyara mayafinta ga raɗaɗin da kunnanta ke yi mata duk tabi ta burkice, ajiye cup din hannun shi ya yi kan table tare da miƙewa ya je gabanta ya tsaya ya ruƙo Veil ɗin Zai gyara mata jin hannun mutun yasa muryarta na rawa ta furta"Earring ɗina Ya maƙale gashina za fi nake ji"
'Okay, calm down, I'll help you."
jinjina mashi kai tay, ruƙo mayafin yai tare da zame shi Ya sauko kan kafaɗarta bai kalli fuskarta ba sai da Ya Cire mata earring ɗin da ya sarƙe gashin, kafin ya ɗago da idanunshi slowly ya dubi fuskarta adai dai lokacin ta buɗe idanunta kaitsaye suka shiga cikin nashi bai san ya akai ya tsinci kan shi da jin matsanancin faduwar gaba hatta yanayin bugun zuciyarshi saida ya canza tamkar ana buga ganga.
wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarce shi, kamar yadda yake kallon ta haka itama ta ƙura mashi kyawawan idanunta sai faman kyafkyafta su takeyi kamar Yaji ya shiga cikin su, gaba daya ta razana da kallon da ya ke yi mata ga wani yanayi da ta tsinci kanta mai wuyar fassaruwa, hankalin ta ya ɗan tashi, duk tasha jinin jikin ta aranta ta ayyana wanene wannan? Meyasa ya ke kallona? Ko dai jira yake in yi mashi godiya ne"? Muryarta adabarbarce ta furta"Um... thank you.'
sam Ya kasa tanka mata sai kallon ta ya ke yi, yau ne karo na farko da suka fara ganin juna, amma dukansu sun ji wani baƙon al'amari a zukatansu
Hankalin su Unaisah kwata kwata baya akan su..
Abunda yaɗan ɗaure mashi kai kaman nin shi da yarinyar, tun da Allah ya halicce shi bai ta6a ganin ɗan adam din da yake bala'en kama da shi irin Yarinyar nan ba! Ko Benazir da take kama da shi kamannin su bai kai haka ba, ita wannan kamar anyi photocopy din fuskar sa ne don ma ya ɗan manyanta.
"Baby na Who is she? Is she your sister?' muryar Benazir ce ta katse Kallon kallon da suke jefa ma juna su, ajiyar zuciya dr shureim ya sauke tare da juyawa ya koma kan Sofa Ya zauna yana mai mamakin kaman nin shi da yarinyar yau yaga abun al'ajabin daya rikita shi.
"Sunan ta Batool Sister dina ce" da alamun rudani Benazir take kallon fuskar Batool Ta ɗan razana da ganin kaman nin su, aruɗe ta dubi Dr Shureim ta kuma juya ta kalli Aneelerh hankalinsu gaba ɗaya ya koma kan fuskar Batool, itama Aneelerh tayi mamakin ganin fuskar yarinyar kamanninta sun 6aci dana dr shureim.
Sun yi matuƙar ruɗewa da ganinta, Hankalinta ba karamin tashi yayi ba ganin irin kallon da su ke yi mata Jikinta har Ya fara kakarwa, Unaisah ta ɗan rude da ganin kallon da su ke yi ma Batool amma sai tay tunanin ko dan sunga kamanninta da dr shureim ne hakan yasa ta ɗan yi murmushi tare da ruƙo hannun Batool dake kerma tace"Sister, kinga aunty Benazir, ga yayanta Dr Shureim da nake baki labarin kamannin ki da shi, dama nasan za ku yi mamaki idan kuka haɗu" dakyar Batool ta ƙaƙaro murmushi akan fuskarta hankalinta sam ba'a kwance yake ba.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
'
Miƙa mata hannu Benazir tay jiki asanyaye ta matsa kusa da ita, ta yi hugging dinta tightly a kirjinta lokaci ɗaya ta fara jin bugun zuciyarta na ƙarfafa haɗe da faduwar gaba, nan take fatimar dr shureim ta faɗo mata aranta Ƴar jinjirar da ta rasu bayan haihuwar ta da watanni ita kanta batasan ya akai ta tsinci kanta da tunanin yarinyar ba, sam ta kasa raba Batool daga jikinta kamar zata maida ita cikin ta a hankali take shafa bayanta da tafukan hannayen ta, Batool ta yi shiru tana jin wani irin sanyi da kwanciyar hankali Yana ratsa zuciyarta.
Gyaran murya dr shureim yayi masu, A hankali Benazir ta raba jikinta daga na Batool
"Kun barsu a tsaye ku zauna mana" ya fada tare da nuna masu Sofa, ruƙe hannun Batool Benazir tay acikin nata suka zauna suna fuskantar dr shureim.
Unaisah ta nufi Aneelerh tun shigowarsu take ta ɗaukin son taga baby junaid, ta ɗanyi jinkiri ne don kada ta 6ata plan din su..
"Aunty Anila ina wuni? Ya su Mami da zahra" Magana takeyi ma anila amma hankalinta na akan baby junaid da anila ta rungume a kirjin ta, wani irin kaunar shi take ji kamar ta ƙwace shi daga hannun Aneelerh, ta yi kokari kame kanta ne kada ta cika zaƙewa agane sun san juna da jimawa
fuskar Aneelarh da fara'a tace"lafiyalou, Zahra tana gaishe dake, ina fata mun same ki lafiya.."
"Lafiyalou Aunty Aneelerh"
Dr shureim Yace"Babyn Benazir, Ni baki ganni bane, tun da kika ga mamanki kin manta da mu ko" ɗan murmushi tay"ba haka bane ya shureim, kana araina, ina wuni, ya su mami? ina zeenatu"?
"lafiyalou Azeezaty, su mami suna gaishe dake, ina fata mun same ki lafiya.."
"Lafiya lou, naga jikin mamana yayi sauƙi, ubangiji Allah ya ƙara mata lafiya"
"Ameen babyn mamanta" yar dariya sukai, kafin wani ya kara magana wayar hannun shi tay ringing daga cikin aljihunsa, a hanzarce Ya curota Ya duba sunan me kiransa, mikewa yai tare da kallon Benazir dake kallon shi"Mami ce"?
"A'a bakuwar number ce, bari na ɗaga naji" cikin sauri Ya nufi hanyar fita daga sitting room din, zuciyar shi cike fal da tunanin yarinyar daya tsaya ma shi aran shi, baiso kiran ya katse mashi kallonta da yake yi ba, bai kula ba tun da ya miƙe Batool tabi bayan shi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, harya kusa fucewa ya ɗan juya don ya saci kallonta karaf suka haɗa ido da juna, sanyayyar murmushi ya sakar mata tare da ɗaga mata hannu, kunyar shi ce ta kama ta da sauri ta juyar da kan ta gefe ɗaya, mutumin ya kwanta mata aranta tun da Unaisah ta bata labarin kamannin su, yau da ta gan shi face to face sai taji ta kamu da ƙaunar shi.
Da ido Unaisah tay ma Batool nuni da data gaida su Aunty Aneelerh muryarta na dan rawa ta furta"Aunty Anila Ina wuni" da fara'a Anila ta ce"lafiyalou sister fatan mun same ku lafiya"
"Muna lafiya"
Bata kau da ido daga kallon fuskar Batool ba, tana so tasan wacece ita? Ko itama ɗaya ce daga cikin yaran da zahra ta bata labarin badakalar da aka sha akan su ranar dinner din prime minister, ko kuwa dai yar uwar chief ce? Ta ayyana acikin zuciyarta, Ta dai bar abun aranta har zuwa time da za su yi magana da unaisah, tayi zurfin acikin tunanin ta taji hannun unaisah akan nata a hankali ta kau da ido daga kallon batool ta dubi unaisah, kar6ar junaid tay daga hannunta ta kwantar da shi kan laps ɗinta, ta ƙura ma shi ido tana kallon shi kamar zata lashe shi..
"Yau dai na kawo maki babynki, da kike ta zumudin son ganin shi, Ina fata na wanke laifi na" ta faɗa tana leƙen fuskarta, jinjina kai Unaisah tay"da har nayi fushi, da ace baki kawo min shi ba, zansa daddyna ne ya kawo ni har gida don inga ɗan ƙanina, amma yanzu kin wanke kanki agurina" ta faɗa da murmushi akan fuskarta
Anila tace"Tun acikin mota yake ta sharar bacci, Kamar wanda Yasha ƙwaya"
"ay ko dai yanzu zan tada shi, saboda ba karamin missing din shi nayi ba...." kafin ta ƙare maganar Baby junaid Ya fara mutsu mutsu alamar zai farka lura da hakan ya ɗaga hankalin Aneelerh, fargabanta kada junaid ya kwafsa masu, tasan muddin ya farka zai yi wuya in bai gane Angel ba kamar yadda kwanaki ya shaidata a hoto sauƙin ta ma dr shureim ya fita daga ɗakin dama shine damuwarta bata da matsala Benazir tasan komai already sunyi plan.
burinta Ya farka su haɗa ido da juna matsawa tay da fuskarta saitin ta shi ta kurama shi idanunta, miƙewa batool tayi ta dawo gefen Unaisah ta zauna tana kallon junaid ba ta son ta nuna zumudinta akan shi saboda unaisah ta kwa6eta, shiyasa taƙi sakin jiki kada tay wani abu ba dai dai ba.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Da wata irin kasala Ya karasa buɗe idanunshi, sun kaɗa jawur da su, biji biji yake ganin fuskar mutun a saitin tashi, red lips dinsa na kerma ya furta"mommy," shiru yaji ba'a tanka mashi ba, a hankali ya ɗaura yatsun hannayen shi akan fuskar Angel ya shafata har zuwa saitin la66anta ya ɗan matsa su kamar ya samu abun wasa, sam bai gane wacece ba saboda idanunsa sun disashe
"Mommy" ya sake ambaton sunan yana faman yamutsa fuskar shi.
Jin shiru taki amsa mashi ne yasa shi murza idanunshi da yatsunsa suka washe ya sake duban fuskar Unaisah dake yi mashi murmushi, shiru yayi yana kallonta yanayin fuskarshi ya nuna kamar ya ruɗe da ganin ta, tsawon mintuna bai tanka mata ba, kowa yayi shiru suna jiran ganin me zai yi
Tsinin hancinta Yaja da hannun shi, ta lumshe ido tana dariya, shima sai ya kama dariya kamar sun san juna, lamarin ya daure ma su anila kai, da alama junaid yayi azan mafarki yakeyi
Cikin sanyin murya ta furta"My little bro"
Lokaci ɗaya yanayin fuskarshi Ya canza Ya kura mata ido Yana kallonta ba tare da ƙyaftawa ba,
Unexpectedly taji ya furta"ANGEL"? Waro idanu waje tay tare da buɗe baki ta dubi Batool itama mamakinne Ya kamata saboda ta faɗa mata basu ta6a haɗuwa da juna ba wannan ne karo na farko
Sam Ta ƙasa furta kalma har sai da taji Ya ce"Angel uhm? Angel ɗina ne? Yayata" Sautin muryarshi baya fita dakyau ta fahimci kamar baya jin dadi, ruwan hawaye ne suka taru akan fuskarta, cike da jin dadi ta jinjina mashi kai la66anta na kerma ta furta"ni ce"
Aneelerh sai faman sakin murmushi ta ke yi dama tasan zai yi wuya in bai gane ta ba.
Still da ruɗu akan fuskar shi, kokwanto yake, kamar bai yarda ba, Lumshe idanun shi yai tare da buɗe su.
ɗago da kan shi tay tare da kwantar da shi saman kirjinta, ta tallabe shi tare da manna mashi sumbata har sau uku kan cheeks dinsa
Gyaran muryar da Aneelerh tay mata ne yasa ta ɗago adabarbarce ta dube su sam ta manta da Benazir duk saita kama kanta tana faman rarraba idanu akan su, Basarwa Benazir tayi tamkar bata ji me Junaid yace ba sarai ta fahimci ruɗewar da Angel tayi tasan don saboda ita ne kada ta gane wani abu.
Tun da Aneelerh tay gyaran murya junaid ya kalle ta tayi azan zai sanya rigima akan ta ɗauke shi kamar yadda ya sa6a yi ma kowa ƙiwuya amma wani iko na Allah sai ta ga bai yi ba, aranta ta ayyana watakil ya ga ne Angel dince shiyasa ya yarda da ita, miƙa hannu Batool tay da niyar ta dauke shi Ya maƙe kafaɗa alamar ba zai je ba.
Anila tace"sai kunyi hakuri da shi, baya da koshin lafiya" atare suka haɗa baki gurin furta"Allah ya bashi lafiya" ta amsa masu da ameen
"Kana buƙatar wani abu"? Cikin kulawa unaisah tay maganar tana kalon fuskar shi Ya nutsu Yana ta kallonta
"Batool zubo mashi juice a cup" unaisah ta fada tare da kallon ta da sauri batool ta ɗauko juice din da dr shureim Ya aje a cup bai sha ba ta miƙa wa Angel ta kar6a ta kanga mashi abaki A hankali ya fara sha.
"Naji shiru yaya shureim bai dawo ba" ta faɗa tare da kallon Anila
"May be bai kammala Yin wayar ba" acewar Anila
Sauke ajiyar zuciya ta ɗanyi har yanzu da sauran damuwa akan fuskarta.
Wrist watch din hannunta ta duba karfe ɗaya da rabi
"Bansan lokaci yaja har haka ba," Anila tace"nasan mami zata neme ni"
"Batasan kin fito bane"?
Ta sani amma ce mata nayi gidan ku zanje"
Da zolaya Benazir tace"Mai karya dan wuta dai," dariya Anila tay..
"Naji shirun yayi yawa, bari naje na duba Ya shureim" ta faɗa tare da miƙewa ta fuce daga dakin
Ajiyar zuciya Aneelarh ta sauke tare da kallon su Unaisah, Hankalinta Ya kwanta da ganin yadda junaid Ya saki jiki da ita.
"Aunty Anila ki bani wayarki mu dauki hoto, Na bar nawa a daki.'
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Okay" ta faɗa tare da zaro wayar tace"bari nayi maku pics din da kaina, ku gyara" hotuna ta fara ɗaukar su kala kala wani daga zaune wani daga tsaye wani kuma sukayi atare su uku junaid dai yana a maƙale da Unaisah Batool tay kwakwar ta ɗauke shi Yaƙi yarda da ita, bayan sun gama ɗaukar hotunan Anila ta ɗibi snacks a dan plate ta ba unaisah" ki bashi yaci, da safe baici abincin kirki ba" kar6ar plate din tay ta fara bashi abaki Yana ci.
Lokacin da Benazir ta fito waje neman Dr shureim A tsaye ta hango shi jikin Motar shi yana yin waya, da sauri ta nufe shi adai dai time din ya kammala yin wayar"ya shureim lafiya naga ka dade baka dawo ba" fuskar shi babu walwala Ya ce"Zeenatu ce ta kira ni da layin tani, tana kuka bata jin dadin jikin ta tace inzo gida tana son gani na"
"Baiwar Allah, dole taji ba daɗi ya shureim, Banji dadin yadda Uncle yake takura rayuwarta, ni nasan hada damuwar hakan"
ta fada cikin sanyin murya tana kallon shi
"Ka tafi ya shureim, Inyaso sai mu tsaida me abun hawa Ya kai mu gida" girgiza kai yai"a'a bazan iya tafiya nabarku ba, zan bata hakuri ta jira zuwa lokacin da zamu koma gida" ya fada yana kokarin danna mata kira da sauri Benazir ta ruƙe hannun shi amarairaice ta furta"a'a ya shureim kada ay haka, tunda kaga ta kira ka da akwai wani abu dake damunta, tana son ganinka, kuma kaima nasan hankalin ka bazai kwanta ba in har ba zuwa kai gurin ta ba..."
shiru ya yi jimm yana nazarin maganarta, aranta Allah Allah take Ya tafi duk don saboda ta samu taj yace zai kaisu a motar shi
ɗagowa yai da ido Ya dube ta"zan tafi amma zan dawo zuwa anjima in ɗauke ku" Amsa mashi tay da toh ka kula min da kanka" murmushi ya ɗanyi mata harga Allah baiso tafiyar shi ba, saboda yarinyar nan mai kama da shi ta tsaya mashi aranshi.
Akan idon Benazir motar dr shureim ta fuce daga gidan, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da duƙar da kanta ƙasa, damuwa ce cunkushe a cikin zuciyarta, ga dai yarta Allah ya nuna mata da ranta da lafiyarta kuma tayi farin ciki mara misaltuwa sai dai bata jin zata samun sukuni da kwanciyar hankali in har taj bai yafe mata ba, har yanzu tana son mijinta kuma bata jin zata iya rayuwa da wani ɗa namiji a duniyar nan in ba shi ba, zurfin tunani ta shiga da ace tun farko da ya aureta sunyi zaman lafiya zai iya yi mata uziri amma Yanzu koda yaji cewa Asiri akai mata ta gudu tasan bazai ta6a yarda ba saboda yasan wacece ita
Cikin karyayyar murya ta furta"Halina ne Yaja min, Ni na ja ma kaina..."
batai aune ba taji safkar hawaye kan kuncin ta, da sauri ta sanya tafin hannu ta share ƙwallar, kafin ta juya ta nufi hanyar koma wa sitting room din tana ta ƴan waige waige cike da sa ran zata ga 6ullowar taj sai dai har ta shiga babu shi babu alamar shi...
__________Ummin America
Futowa tay daga bedroom din ta jikinta sanye da bubu gown ta material, tay rolling akanta, flat shoes ne a kafarta, matsawa tay gaban handrail ta dafa tana kallon downstairs, A falo ta hango su gaba ɗayan su banda mutun uku, kowan nan su yana azaune kan rug sun haɗa kai suna rubutu a cikin notebooks din su, Sajeed ne kadai ya zauna kan sofa da alama shi ke koya masu rubutun.
Zura hannayenta tay acikin aljihun rigarta, ta nufi stairs cikin nutsuwa take taka matakalar ta sauko down ta nufe su babu wanda Ya lura da ita a cikin su har sai da tay masu gyaran murya tukunna suka dago da kai suka kalle ta har suna haɗa baki gurin furta"Aunty Ummi zo ki ga Rubutun mu, Ki za6i nawa yafi kyau" kusan atare suke mike tare da kewayeta kowa Ya miƙa mata notebook din shi.
ƙin kar6a tay gudun kada ta haɗa rigima kallo ɗaya da tai ma rubutun su sai da taji gaban ta ya faɗi ganin wani jagwalgwalo, a fakaice ta kalli sajeed karaf suka haɗa ido da juna da sauri Ya kumshe dariya yai mata alamar ta duba mana.
"Aunty ummi nawa zaki fara dubawa, nafi su abun kirki"
Jemimah ce ke rokon ta, kar6ar book din tay tare da duba rubutunta itace ke yin rubutu shigen na thailand ka rasa ta yadda take jagwalgwala shi
"Aunty ummi in kin gama duba nata saura nawa" acewar Azeeza, Deeja tace"wlh na riga ki nawa zata duba" kamar zasu sanya mata rigima.
Jinjina kai ta yi"Jemimah Kinyi ƙoƙari ki dage kin ji, idan kika maida hankali har kyauta zanyi maki" uban tsalle ta daka na murna hada yi ma Azeeza gwalo ta kar6i notebook dinta tana ta murna
"Muga naki azeeza' mika mata tay aranta ta ayyana tab lallai wlh da a school suka rubuta Iya shegen nan, jakkin duka zasu ci' amma a fili sai ta ɗan murmusa tace"kema kinyi kokari, Ki ƙara himma" dadine Ya lullu6e azeeza ta kar6i book dinta ta juya ta nufi jemimah.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Ɗaya bayan ɗaya saida ummi ta duba notebooks din Har ƙwara Naufal Ya iya rubuta ba laifi tayi mamaki har saida ta tambaye shi ya akai yafi su iyawa, Da hannu ya nuna mata Sajeed"kullum A ɗaki kafin mu kwanta bacci, Shi yake koya min rubutu da karatu..." jinjina kai tay"Sajeed sannu da kokari, amma yakamata suma sauran ka dage da koya masu kamar yadda kake koya ma naufal" amsa mata yai da toh.
Deeja sai haɗe rai take don ba'a yabi nata ba, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"rubutun ma bazan ƙara yi ba" ta faɗa tana kokarin keta littafin da sauri Haris Ya ruƙe hannunta"wayace maki rubutun baiyi kyau ba, ay naki yafi na kowa" kwa6e fuska tay tare da kallon Aunty Ummi tana faman zum6ura baki tace"amma ayni baki yabi nawa ba ko" yar dariya ummi tay"oh wai saboda ni zaki keta littafin, toh kiyi hakuri mantawa nayi amma naki yafi na kowa" washe baki tay har taji dadi..
"Ni rubutun ma yai kyau ko kar yayi ba damuwa ta bace, indai ba za'a hanani cin abinci ba" ta faɗa tana hura hanci, gaba ɗaya suka sanya dariya, girgiza kai Ummi tay"Allah ya shiryeki foodie, ke dai indai zaki samu abinci baki da sauran damuwa" ɗaga mata gira tay.
Sarah da ta gama haɗe rai wurga notebook dinta tay kan sofa ta juya zata tafi
"Hey! Where are you going?' muryar ummi ce ta katse mata hanzarin ta, yamutsa fuska tay"nagaji da rubutunne zanje na kwanta" murmushi ummi tay"nasan me kike ma fushi don ban yabi rubutunki ba ko" girgiza kai tay"a'a kawai nagaji ne" daga yanayinta ummi ta fahimci zatai rawar kawai dama tana lura da ita, ta iya raina abu in baiyi mata ba.
"Okey, kije ki kwanta ki huta, da anjima, da kaina zan koya maku rubutun"
"Okay, thanks" ta faɗa tare da juyawa ta nufi dakin su tana tafiya kamar zata balle tsabar tsawon ta har yanzu bata da ƙiba.
"Kuma idan kun gaji ku aje karatun, kwakwalwa tana buƙatar hutu, amma fa dole ku dage ilmi yana da matuƙar amfani, you have to endure and persist before you succeed." ta6e baki parvin tay"Allah aunty ummi da kin daina wahalar da kanki gurin yi mana bayani, bamu gane komai.." sakin baki tay sototo tana kallon parvin abun ban haushi abun dariya
Rubina tace"nima Allah bani ganewa, Nifa nafison in kwanta inyi bacci ko inci abinci" kallon ta ummi tay
Hibba tace"dama girki kika koya mana, da yafi, kin ga sai mu dinga girka abun da ran mu yake so"
Harara ta ɗan watsa mata"hauka nake in kai ku kitchen da sunan zan koya maku girki? A haka? Ku fara samun ilmin kafin in yi tunanin koya maku girkin"
Hannah tace"wai komai saida ilmi, to a jika abamu musha sai mu haddace" tuntsirewa ummi tay da dariya, Sajeed dake sauraron su baisan sa'adda ya fashe da dariya ba
"Aunty ummi dama kin daina wahalar da kanki gurin yi masu bayani, ba zasu fahince ki ba, har yanzu da sauran su" acewar Sajeed, tsagaitawa tay da yin dariya cike da nishadi tace"wani lokacin kamar masu hankali, wani lokacin kuma wlh kamar in hada ku da tsumagiya inta jibga" dariya sukayi gaba dayan su
"Ina Unaisah da Batool? Banga gifcinsu ba, ko suna adaki ne"?
Hawwa tace"basa nan tun dazu muka je neman Unaisah don ta bamu notebooks dinmu mu yi karatu bamu ganta ba kuma bata a toilet sai dai muka ɗauko books din"
"Kun duba ko'ina baku gan su ba? Ko dai sun je dakin Danish ne"? Haris Yace danish Yana atare da chief suna karatu bana tunanin sun je dakinsa"
"To Ina suka je ne"? Ta fada tana kallon su
Yasmin tace"kila sun fita waje ko dai muje mu nemo su"!
Shiru ummi tay bata amsa ba tunani tay ko dai sun shiga bangaren daddyn unaisah ne"?
Da sauri ta zaro wayarta daga aljihu ta lalubo contact din unaisah ta kira layinta tana ta kira ba'a picking har ta katse almost 3 times
Yanke shawarar kiran taj tay har wayar ta ƙare ringing ba'a ɗaga ba
"Nafi tunanin suna acikin gidan nan, ku tayani neman su" amsa mata su kai toh, da gudu wasu suka nufi bangaren hagu wasu dama Suka fara bin sako da lungu suna neman su.
_________________________✍️
Bayan dr shureim ya isa gidan, a hanzarce Ya fito daga motar Ya nufi Cikin main falo Yana ta sauri saboda Hankalinsa Ya tashi Da halin da Zeenatu take a ciki Ya kosa Ya ganta ko hankalinsa ya kwanta har ya kusa fita daga falon muryar Tani ta katse mashi hanzarin shi.
"Shureim har an dawo" dakatawa yai tare da kallonta"Tani na same ku lafiya" da fara'a tace"lafiyalou, "
"Ina mutanan gidan"?
"Hajiya layla tana aɗaki, zeenatu kuma bata jin dadi amma na kira daddynta awaya na faɗa mashi, Yanzu haka ya turo family doc din su Yana aɗakin Yana duba lafiyarta..."
tun kafin Ta ƙare maganar dr shureim Ya furta"Ya Salam! Mami tasan bata da lafiya"? Girgiza kai Tani tay"dana je faɗa mata na iske tana bacci shiyasa ban tadata ba"
Hankalin shi atashe Yayi saurin nufar upstairs, azafafe Yake taka stairs din harya haura second floor, Yana isa gaban ƙofar ɗakin yajiyo wata Murya irin ta giggan tantira daga cikin ɗakin
"Don't waste My time, idan baki bani haɗin kai ba, zan kira daddyn naki awaya in fada mashi,"
shesshekar kukan zeenatu yajiyo tana fadin"ni wlh banso, ka kyaleni, ka kyaleni nace banaso" zuciya da sake sake ta raya mashi wani mugun abunne ke shirin faruwa, gabanshi na faduwa Ya ture ƙofar ɗakin da hannu kai tsaye idanun shi suka sauka akan jibgegen katon nan Ya haye kan gadonta yayi mata rumfa da gabjejen kirjin shi ta maƙure kanta jikin headboard, jikinta sai kakarwa yake yatsun hannunta dana kafafuwanta sai kerma suke, ta rufe kirjinta da tafukanta, Yar rigar wanka ce a jikinta da bata wuci gwiwar kafarta ba, sumar kanta duk ta rufe fukarta....wani irin kishi ne Ya rufe dr shureim baisan sa'adda yai kukan kura daga inda yake yai wani ƙwaƙƙwaran taku Ya damƙi kafar dr mark A firgice Zeenatu ta ware idanunta akan fuskarshi la66anta sai kerma suke.
Dr mark ko ajikin shi, Fuskarshi a murtuke ba annuri Ya dubi Dr shureim da ya ruke kafar shi.
A gadarance yace"malam Lafiya ka ruƙe min ƙafa" ya faɗa yana bin shi da wani kaskantaccen kallo
Rai a6ace dr shureim yace"uban me kake yi akan gadon ta"? ta6e baki dr mark yai tare da nuna mashi Syringe ɗin hannun shi"Ubanta ne Ya kira ni don in duba lafiyar yar sa, ko kana da Ja ne" ya faɗa tare da ɗage mashi gira, ƙarfin halin mutum ya ɗaure mashi kai ko kunya bai ji ba Ya kure karamar yarinya kan gadon ta.
"Amma dai baka da hankali, Don ubanta Ya kiraka ka duba kafiyarta sai yace maka ka shigo har dakinta saman gadon ta? meyasa ba zaka tura me aiki ta kira maka ita ka dubata a falo ba? Hakan da kai ka kyauta?
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Ganin dr shureim zai raina mashi wayau yasa shi saukowa daga kan gadon Yana wani buɗe kafadunshi Ya tsaya agaban shi"meye naka aciki huh? Yakamata kasan irin kalaman da zaka furta min, Ni ba sa'an yin ka bane, kada kace zaka shiga hurumin aikina, ba yau na fara ba! kuma umarnin mahaifinta nake bi"
A harzuke dr Shureim yace"oh shi uban natane Yace ka shigo dakinta har kan gadon ta don kayi mata allura kuma haka ake allura abi a danne mutum"? Ya jefa mashi tambayar yana binsa da kallon tuhuma.
"Malam ka tsaya a iya matsayinka, nima in tsaya a nawa, tun wuri ka fuce daga dakin nan tun kafin na 6ata maka rai"! A kausashe Ya faɗa Yana Huci saboda baya ɗaukar raini, daga gani yana ji da karfi, juyawa yai da niyar ya koma kan gado saboda kunya bata ishe shi ba, a zafafe dr shureim Ya damƙi Strong Arm dinsa, a sukwane dr mark yai mashi wani kallo mai nuni da kashedi
"Sakar min hannuna! Karka kuskura ka bari na maimaita abunda nace"! Girgiza kai dr shureim yai duk da ya ɗan sha jinin jikin shi amma baya jin zai iya bari dr mark Ya koma kan gadon zeenatu da sunan zai mata Allura, ko ba dan kishinta da yake ba hakan bai dace ba kwata kwata
Hankalin Zeenatu ba karamin tashi yayi ba jikinta sai kerma ya ke yi kamar wadda sanyi ya kama cikin shesshekar kuka tace"yaya shureim ka ƙyale shi dan Allah, wlh idan daddy ya ji ka hana ya dubani ranshi zai 6aci, ni allurar ce bana so tun da akwai magani ya kyale ni in sha" idanunta sun kaɗa jawur
Wata irin zufar 6acin rai ce ta wanke fuskar dr shureim
Ido cikin ido suke kallon kallo tsakanin su, Taurin kan dr shureim da kafiyarsa sunyi matuƙar daure mashi kay, mutane da dama suna jin shakkar shi sai gashi yau Allah Ya hada shi da shureim
"Yaya shureim na roƙe ka, ka sake shi, bana son tashin hankali"
"Wallahi ba zaka dubata ba! Muddin ina numfashi, wannan wani irin yahudanci ne? Daga kai sai yarinya adaki saboda rashin ta ido har kan gadonta"?
Dr mark ya gama hasala Har yayi wani yunkuri Zai kai mashi naushi Zeenatu tay saurin saukowa daga kan gadonta, ta faɗa tsakanin ta riqe dr shureim tana kuka.
Da ace Zeenatu bata yi gaggawar raba tsakanin su ba, da Allah kadai yasan me dr mark zai yi mashi saboda ya fusata shi.
Sassauta fushin fuskarshi yayi, tare da kallon zeenatu da ta kankame shi, hankalin shi ya ɗan tashi da jin zafin jikin ta
Ganin mayen kallon da mark ke binta da shine yasa shi juyawa da zeenatu suka bashi baya.
Shu'umin murmushin gefen fuska ya saki tare da zaro wayar shi ya danna ma Alhaji musa Kira bugu uku Ya ɗaga.
"Sir, Wannan balaraben na gidan ka ya hana in duba lafiyarta saboda kawai Ya iske ni akan gadon ta ina kokarin yi mata allura shine ya rufe ni da faɗa yana gaya min magana mara daɗi" ya faɗa yana kallon bayan dr shureim, sarai yasan sunan shi amma saboda girman kai Ya kira shi da sunan balarabe
on the other hand Alhaji musa yace"Dr shureim Ya dawo gidan ne"?
"Yeah, shi nake magana akai, Yanzu haka muna adakinta"
"Okay, mark ka tafi kawai, i will call you later" ba don yaso ba ya amsa mashi da Okay"
duk suna sauraron shi abun da ya ƙara bata ma dr shureim rai jin ya fada ma alhaji musa yadda ya iske shi adakin batare da jin nauyin hakan ba, hakan na nufin dama ya saba zuwa dakin zeenatun ya hau gadon kuma da sanin Alhaji Musan.
Harara dr Mark Ya watsa ma bayan shi, tare da jan Tsoki ya fuce daga ɗakin.
Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, tallabo fuskarta yai da tafukan hannayen shi, idanunta amarairai ce ta kalle shi wani irin tausayinta ne ya kama shi, kumatunta sunyi ja, pink lips dinta sun kumbura daga gani ta jigata taji jiki ba kaɗan ba
"Me ke damunki"?
Muryarta da shagwa6a tace"ciwon ciki, daga fitowana daga wanka, na fara jin ciwon ciki yaya shureim nasha wahala kamar zan mutu har fadowa nayi daga kan gado, sai da Tani ta shigo ta iske ni kwance kasa ina murza cikina.. Shine ta kira daddyna awaya ta fada mashi shi kuma ya kira mark don ya dubani ni, ni kuma bana son allura"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Calmy yace"amma zeenatu why baki ce ya jira ki fito falo ba? Hakan ya dace ya shigo har dakin ki kan gado zai duba ki"? La66anta na kerma tace"yaya shureim ni banma san lokacin daya shigoba, ina kwance kawai na gan shi akaina, dama haka yake yi min in dai zaizo dubani baya tsayawa falo ɗaki yake shugowa, kuma daddy da mommy sun sani..."
Girgiza kai yai sha'anin rayuwar gidan uncle nasa sai du'a i, yafi jin haushin Tani da ta kira Alhaji musa, sai kace mami bata agidan ay da ta sani ta tada ta daga baccin da duk hakan bata faru ba.
Ganin kamar damuwa akan fuskarshi yasa tace"ya shureim ranka ya 6aci ko"? Dakyar take magana saboda cikinta dake mata radadi, Girgixa mata kai yai"bakomai, ina maganin naki" da hannu ta nuna mashi kan mirror
Juyawa yai ya nufi closet dinta ya dauko mata abaya ya miƙa mata, hannunta na kerma ta kar6a tasaka a jikin ta.
"Kin ci abinci"
"Bana jin yunwa ɗazu da safe na cika kina"
"Okey, ki zauna ki jira ni"
make mashi kafada tay"dan Allah kada ka tafi kabarni ni kadai"
"Ba tafiya zanyi ba, ruwa zan dauko" amsa mashi tay da toh ta zauna gefen gadon tana jiran shi, badajimawa ba ya dawo hannun shi ruke da Cup din ruwa ya zauna ya taimaka mata tasha maganin ganin yadda hannunta ke kerma bayan ta kammala sha, yasa Yace ta kwanta ta huta, marairaice mashi fuska tay da shawaga6a tace"so kake inyi bacci donka tafi kabarni ko"
Yanayin yadda takeyi mashi magana ba karamin kashe mashi jiki ya ke yi ba, ba zai juri kallon ta ba.
"Ba tafiya zanyi ba, zan koma falo," miƙewa tay"nima zanje falon"
"Pls ki kwanta ki huta, babu lafiya a jikinki"
Kuka ta saka mashi"haba ya shureim nagaji da zama ni kadai, ya kake so nayi da raina? nasan tafiya zakai kabarni..." lallashinta ya farayi"ya isa haka ki daina zubda hawayenki bana so, Idan saboda ni ne muje falon tare saiki kwanta kan sofa, in har hakan zai kwantar maki da hankali" ajiyar zuciya ta sauke ya zaro hanky daga aljihu ya share mata tears din fuskarta, ya ruƙo hannunta suka fito daga dakin
________________________________✍️
A bangren su Aneeleerh har wuraren biyu na rana suna agidan, Sun Mori lokacin su tare da su Unaisah sallah kadai ta tadasu, sun sha fira da su kamar ƙawayansu, sun ɗebe masu kewa ba kadan ba, musamman Aneelerh taji dadi tayi farin cikin ganin yadda Junaid Ya saki Jiki da Unaisah in a short time su ka shaku da junan su, wasan doki suka dinga yi mashi ita da Batool, akan bayanta ta ɗaura shi ta dinga rarrafe tana zagaye sitting room din batare da gajiyawa ba, Sai murna yake yana fadin doki sukuta sukuta.
Aneelerh tasha ruwan mamaki Ganin Yadda Yake tiƙar dariyar, yaushe rabon da ta ga dariyar Junaid tun ranar da Ana ta 6ace ko murmushi bayayi ga ƙiwuya amma yau ya sake kamar bashi ba, har ta fara tunanin in suka koma gida zata lalla6a shi cikin lallami ta tambaye shi meya faru da ana aranar watakil ya fada mata tun da taga bakin shi ya buɗe.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
har video Benazir ta ɗauke su da wayarta saboda sun burgeta taji daɗin walwalwar da su ke yi cikin nishaɗi bayan sun gama yi mashi wasan dokin, Unaisah ta daure idanunta da mayafinta ta dinga zagaye dakin tana neman su, Batool taja hannun junaid suka dinga garata sai da suka wahalar da ita dakyar ta cafko baby junaid ya dinga ihu Yana tsalle yace mata shima ta ɗaure mashi ido yayi wasan, ta cire mayafin ta ɗaure mashi idanunshi yadda bazai ji zafi ba, kamar makaho haka ya rinƙa miƙa hannu ya na laluban su da gangan Unaisah ta je gaban shi ta tsaya don kada su wahalar da shi, cafko rigarta yai da hannayen shi ya ƙankameta yana fadin ya kama ya kama.
Duba agoga Aneelerh tayi kafin ta kalli Benazir"yakamata mu tafi, kada mami taji na dade" sai lokacin Benazir tace"yanzu abun hawa zamu hau mu koma? nasan ko na kira dr shureim ba lallai yazo ba saboda rashin lafiyar zeenatu..." ta fada tare da ta6e baki
Murmushi Aneelerh tay saboda ta gano me take mawa
"Pls ki kira mijina ya maida mu gidajen mu" cike da zolaya tace"ki dai iya bakinki, Kada babyn naki taji kina kiran sunan ubanta da sunan mijinki, Yanzu ki tada mana 6alli" murmushi Benazir tay tare da kallon su Unaisah dake a zaune kan rug sun gaji da wasan hutawa suke.
Waya ta curo ta danna ma Taj kira tana fara ringing yai picking,
Tunkafin tay magana Yace"Aneelerh ykk ya su Unaisah, Ina fata kunji dadin kasancewa da su"
"Alhamdulillah, gasu nan zaune sun gama shan wasa da baby junaid, shima yau yaji dadin ganin yar uwarsa"
ta fada tana kallon su
"Masha Allah, Naji dadin jin hakan, Yanzu nake kokarin, kiranki,yakamata su koma yan uwansu sun fara neman su"
"Allah sarki, Nima abun da yasa na kiraka kenan, mun shirya tafiya kuma dr shureim bayanan Ya tafi ɗasu aka kira shi daga gida har yanzu bai dawo ba, mun kira layin shi baya shiga" ta faɗa tana kallon Benazir data tsare ta da ido fatanta Allah yasa ya amince yazo ya dauke su.
Shiru yayi jimm na ɗan wani lokacin kafin yace"Okay, Naso na maida ku gida amma bana a kusa, zansa jami'en mu ya kai ku" haɗe fuska Benazir tay tuni idanunta suka ciko tab da kwalla, gani take kamar ya ɗago su ne shiyasa yace zai turo jami'en su ya kaisu amaimakon shi
"Shikenan, Mun gode ssai," tay mashi sallama,
Kallon juna su ka yi ita da Benazir
"Nasan saboda ni ne yace bazai maida mu ba" ruko hannun ta Aneelerh tay"pls ki yi hakuri kamar yadda na fada maki, bana so yaran nan su fahimci wani abu kwara mu rabu lafiya, ki daure idan muka shiga mota zamuyi magana, nayi maki alkawarin zan taimaka maki mu shawo kan shi"
A hankali Benazir ta share hawayen ta, har ga Allah bata son tafiya tabar gidan ji take kamar su kwana anan sai dai tasan ba abune mai yiwuwa ba.
Suna azaune jami'en da taj ya turo yayi masu sallama Yace su fito Yana jiran su.
Hankalin Unaisah ba karamin tashi yayi ba ganin za'a rabata da baby junaid, bawan Allah sai ƙara kankameta ya ke yi duk don kada su raba shi da ita, bayan sun fito abakin motar suka tsaya, Aneeleeh ta kar6i junaid yana kukan rabuwa da Angel tace mashi yai hakuri za ta zo har gida ta same shi, dakyar tayi mashi wayau ya hakura.
"Toh Mu zamu wuce, zamu tafi mu bar ku da kewar mu" Anila ta fada tana kallon su, duk sun ɗaure fuska saboda basu son su tafi
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Dan Allah yaushe zaku dawo"? Cikin sanyin murya batool ta yi maganar, Benazir tace"in dai mune kusha kuruminku, har sai kun gaji da ganinmu" dadine ya lullu6e su, miƙa masu hannu tay da sauri suka matsa kusa da ita ta haɗa su duka ta rungume su, Cikin kunne ta yi ma Unaisah raɗa"zan kar6i contact dinki a gurin Aneelerh, Ki kula min da kanki, Ina kaunarki sosai" murmushi unaisah tasaki"nima zanyi kewarki mommyna"
Bayan sun raba jikin su daga na juna ta dubi Batool ta shafa gefen fuskarta da tafin hannun ta
"zanyi kewarki, Yau na fara ganinki amma kin kwanta min araina, kamar yadda Babyna ta sace zuciyata, Ina kaunarki, Ki kula min da kanki" dariyar farin ciki batool tayi"in sha Allah, nagode sosai aunty Benazir, nima ina sonki, " taso ta tambaye su dr shureim amma saita kasa saboda kunyarta da take ji.
Miƙa masu hannu Aneelerh tay, itama tay hugging dinsu baby junaid ya haɗe rai Idanunshi sun ciko tab da kwalla.
Sumbatar kumatun shi Unaisah tay, cikin sigar lallashi tace"I'm sorry my little bro, Zanzo har gidan ku, Aunty aneelerh pls ki kwantar masa da hankali bana so yayi kukan rashi na" ta fada tana kallon fuskar junaid
"Kada ki damu bazan bari yai kuka ba, ku gaida mana mutanan gidan" atare suka amsa masu da toh
Akan idonsu Motar su ta fuce daga gidan, fitar su keda wuya Ummi ta fito daga kofar falon har bayan motar saida ta gani yayin da take karasa fucewa daga gate din
Sun yi tsaye cike da jimamin tafiyar su, baby junaid Ya tsaya masu aransu.
Kwata kwata basu lura da ummi ba har saida ta ambaci sunayen su da sauri suka dube ta
"Daga ina kuke? Motar waye naga ta fita yanzu? Kallon ta su ka yi ba tare da sun furta kalma ba
"Ba ku ji Ina magana bane"?
Ajiyar zuciya suka sauke atare Unaisah tace"bamu san motar wanane ba, muma yanzu muka fito"
"Daga ina"? Kallon juna su ka yi
"Kamar baku da gaskiya, ku fada min mana daga ina kuke" ta fada tana jifansu da kallon tuhuma.
"Mun je part din daddyna ne, daga can muke" ba dan ta yarda da su ba tace"shine ko ku fadamin ay dana shirya mun je tare, gaskiya baku kyauta min ba" ta fada tana jifar su da harara dariya sukai atare..
"Ku wuce mu shiga ciki," gaba tay suka bi bayan ta hannun su ruke cikin na juna
*💋BOSS BATURE✊*
Da marece tana a zaune gaban mirror chair tana yin wani makeup ɗin akan fuskarta, saboda kwalliyar da ta yi ɗazu ta goge.
gown ɗin ɗazu ce a jikinta da alama bata gama gayun ba, ko kuma wanda akayi dominsa bai gani ba, ita kaɗai ce a ɗakin, sai ƴan shafe shafe take ma fuskarta, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama tayi matuƙar yin kyau, ta nutsu tana kallon fuskarta ta cikin mirror, pink lips dinta sun jiƙu da lip gloss sai shinning su ke.
Knocking ɗin kofar da akai ne Yasa ta ɗan juya ta kalli room door ɗin su.
Jemimah ce ta shigo jikinta sanye da Overall, ta ɗaure blonde hair ɗinta da ribbon ta fito ɗass Farar fatar ta gwanin sha'awa.
"Little Sis halan dalili ne Ya shigo dake dakin mu"?
Ta faɗi hakanne don tasan bai wuci chocolate tazo roƙo a gurin ta ba.
murmushi tayi"Aunty ummi ce tace In kiraki, kizo mu yi dinner, in ba zaki ci ba sai mu cinye naki" dariya Unaisah tay"su acici mala'ikun tauna, Ku da baku gajiya da Cin abinci, Har wani fadi kike zaku cinye abinci na ai ko dana karanta maku Charman dudu cikin kowa ya kumbure"
waro idanu Jemaimah tay"Wlh wasa nake maki fa" miƙewa Unaisha tay daga kan chair din"oho in ma dagaske ne bismillah, ku ci ku ga abun da zai biyo baya"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Veil ɗinta dake ajiye kan bed ta dauka ta yafa akan kafadarta, ta koma gaban mirror ta dauki turare ta fashe jikin ta da shi.
"Sis Unaisah Kin yi kyau wallahi"
"Thank you, ki tafi ki ce masu su jirani Yanzu zan fito"
Maƙe kafada Jemimah tay"wlh ba inda zanje, so kike muje muyi ta jiran ki kiqi fitowa yawun mu yai ta tsinkewa ko"?
Girgiza kai Unaisah ta yi ba tare da ta tanka mata ba
"Kamar dole saida ni zaku ci, kullum sai anzo kirana"
Kafin ta ankare Jemimah ta buɗe drawer chest, Ta Saci Chocotes biyu ta tura a aljihun rigarta.
"Sis Unaisah mu tafi pls, suna jiran mu"
"Kada ki takura min pls" ta faɗa tare da juyawa ta nufi shoe rack ta ɗauko wasu hadaddun cone heel ta zura a ƙafafunta.
"Aunty Ummi tace Ki ɗauko mata wannan abun jin kiɗan zata kunna mana music"
Girgiza kay tay"Aunty ummi ta iya Taya beraye 6anna" ta faɗa tare da nufar inda ta ajiye bluetooth speaker din ta ɗaukota a hannu tace ma jemaimah mu tafi
Adaidai lokacin da suka fito daga dakin Danish yana atsaye gaban handrail din bene jikinshi sanye da kaftan maroon colour, muryar jemimah ce taja hankalin shi ga kallon su bai sauke idanunshi akan kowa ba sai kan Unaisah, wankan data ɗauka yayi matuƙar ƙayatar da shi, musamman data ju ya baya tana ta fi ya, kwata kwata basu lura da mutun ba, kuma ba su ji ajikin su ana kallon su ba.
Tun kafin su karasa Dining din, Ta hango Su gaba ɗayan su sun hallara A zazzaune kan dining chairs, an cika masu table din da lafiyayyan abinci.
Tana shigowa sautin takalmanta Ya karaɗe kunnuwansu, kusan atare suka ɗago suna kallonta kamar sun samu tv, kwalliyarta tayi masu kyau Nan fa suka fara Santi suna yaba kyan da tayi.
Ummi tace"lallai yau ƴan matanci ake ji, faɗa min wa kikayi ma kwalliyar nan" farfari tay mata da idanu"Someone special" ta fada da zolaya
sajeed yace"Zan Iya cankan wanene"? Ɗaga mashi gira tay murmushi yayi kafin Ya firta
"Chief" waro idanu waje su ka yi gaba dayan su, Praveen tace"baka da hankali Sajeed, chief dinne zata ma kwalliya, Mutumin da ko kallon mutane ma bayayi.
Ummi tace"ba abun mamaki bane, Ni dama na fara tunanin akwai wani abu tsakanin su, shiyasa ran nan yaje dake shopping mall ya yi maki siyayya..." ɗaure fuska Unaisah tay"kai aunty ummi, saboda inyi tsaraba yayi min siyayyan ba dan wani abu ba" ta faɗa tare da miƙa mata speaker ɗin hannunta, kar6a ummi tayi ta kunna ta kafin ta ajiye ta under chair ɗin da take a zaune, ta zaro wayarta daga aljuhun rigarta, tayi connecting ɗinta da speaker din.
sai daɗi suke ji za'a kunna masu music, kallon su Unaisah tay sun cika dogon table din ba space, Shima ɗayan mai mazaunin mutun shida babu space, sai ɗayan dining table ɗin daya rage mai mazaunin mutun Uku Javed yana zaune kan ɗaya daga cikin kujerun dake a kewaye da shi, anan ta samu guri ta zauna.
"Ku fara Cin abincin mana" ummi ce tay maganar.
Sajeed yace'wai da jira muke ki fara kunna mana music ɗin, zaifi armashi muna ci muna sauraro" ummi tace"na lura dakai mayen kiɗa da rawa ne, wa ya koya maka ne, cos ka fita daban ko acikin yan uwanka"
Murmushi yayi batare daya ce mata komai ba, don bazai Iya tuna komai ba dangane da yadda Ya iya rawa ya dai san abun a jinin shi yake.
"Wata waƙa zan sanya mana"? Ta tambaya tana kallon su,
Har suna haɗa baki gurin faɗin baby calm down, dama itace wakar da suka fi sani.
bayan Ta kunna masu wakar suka fara cin abincin suna gyaɗa kawunansu, wasu daga cikin su har wakar suke bi kamar su suka rairata saboda yadda suka Iya bin baitikan tiryan tiryan ba kuskure.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
babu wanda Ya lura da shigowar shi, abakin kofar dining room ɗin ya tsaya yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, ba zai iya tuna rana ta karshe daya shigo dining ɗin da sunan zaici abinci ba, Sai yau da dalili ya kawo shi.
"Danish"! da ƙarfi Haris Ya ambaci sunan shi, bai tsammaci wani zai gan shi ba, adaidai lokacin da wakar da suke sauraro ta ƙare hakan Yasan duk suka ji Kiran da Haris yayi mashi, da sauri suka kalli Inda yake atsaye da alamun mamaki akan fuskokin su.
Kusan kowan nan su saida Ya ambaci sunan shi, In ka cire Unaisah da tay shiru tana kallon shi
Ummi tace"Sannu da shigowa, ina fata kazo kaci abinci tare da mu ne" shiru yai bai tanka mata ba,
"Pls danish kazo muci dinner atare, Munyi missing ɗinka" Batool ce tay maganar,
Naufal Yace"Yau kawai dan Allah, baka ga dadin da muka ji ba na ganinka"!
gaba daya suka haɗa baki suna yi mashi magiya don ya shigo su ci abincin atare.
"Dama kun daina wahalar da bakunan ku, Idan so kuke Yaci cikin sauƙi, Unaisah zaku roƙa ba shi ba"
Sajeed ne yai maganar fuskar shi da murmushi, gaba ɗaya suka maida dubansu Ga Unaisah"pls Kiyi mashi magana, ya shigo muci atare" kau da ido tay gefe ɗaya tay shiru bata tanka ma su ba tayi mamakin maganar sajeed ko taya akai ya gane baya jin maganar kowa in ba nata ba.
"Aunty Ummi ki sa baki, Ta yi mashi magana" duƙar dakai ƙasa Unaisah ta yi, girman kanta Ya hana ta yi masu abunda suke so, ita kanta so take ya shigo ya zauna suci abincin atare amma bata jin zata iya yi mashi magana.
Calmly ummi tace"Unaisah, pls ki masa magana mana, Ƴan uwansa suna son suci abinci da shi.."
sai da ta mula ta sha iska, kafin ta wurga eye balls dinta kan Danish kamar me jin shakkarta, tasan saboda ita ne yaki shigowa gudun kada ya sabama sharuddan ta, ba ta yi niyar yi masa magana ba amma saboda batasan su fahimci sun samu sabani atsakaninsu yasa ta canza ra'ayin ta.
Har Ya juya zai fuce, sanyayyar muryarta ta dakatar da shi
"Big bro, ka zo mu ci abinci atare" a wayance ta faɗa tana kallon shi
har saida ya maimaita sunan data kira shi acikin zuciyarsa
"Ga wuri Na tanadar maka" ta faɗa tana nuna Kujerar dake facing ɗin ta.
baiyi niyar zama ba, amma saboda muradin ransa tayi mashi magana, Ya fasa tafiya Ya jiyo ya shiga cikin dining room ɗin, yan uwansu sai murmushi su ke yi saboda sunji dadin shigowar shi.
Ummi dai ta yi mamakin shakuwar dake atsakanin shi da Unaisah, aranta ta ayyana ko meyasa yake jin maganarta fiye da kowa! Yafi fifita ta akan yan uwansa tana lura da shi, abun da ta fahimta itama Unaisah din tafi ji da shi akan yan uwan shi, don tana lura da ita lokacin da ta ke ji da shi, duk in zasu ci abinci sai tace ma Haris ya kaima Danish nashi aɗaki bayan haka wasu lokuttan tana ganin Unaisah tana satar hanya ta shiga dakin shi, tabbas tana son tasan meke atsakanin su amma tasan ko da ta tambayi Unaisah zaiyi wuya ta faɗa mata gaskiya, aranta ta ayyana yanzun nan zan gano da kaina.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Zama yai kan chair din dake fuskantar Unaisah, ya jingina bayan shi jikin kujerar, ya ɗan lumshe idanunshi ba tare daya kalle ta ba, don baya son abin da zai ja ya karya alkawarin daya ɗaukar mata.
Sun yi shiru babu mai magana a cikin su.
Har saida ummi tace"me kuke Jira Unaisah? Ku fara cin abincin mana" A hankali ta ɗan saci kallon fuskar shi Har saida ta ɗanji faɗuwar gaba saboda kyan da yayi mata, tayi missing din ganin shi a kusa da ita.
a hankali take cigaba da kallon shi ganin ya lumshe idanun shi tasan ba lallai ya buɗe su ba, aranta ta ayyana wani irin kyau ne wannan kullum kamar ana ƙara mashi..."
gudun kada wani ya zargi wani abu tsakanin su yasa ta ɗauki glass of milkshake ta tura mashi agaban shi, ta haɗa mashi da plate of grilled steak with roasted vegetables ta aje agaban shi.
Cikin sanyin murya tamkar tame yin raɗa ta firta sunan shi, A tsanake ya buɗe reddish eyes dinsa dake lumshewa tamkar na mai jin bacci ya kalle ta da su, gaba ɗaya suka tsinci kansu da kallon juna ba tare da kyaftawa ba ya rasa a ina zai tsayar da eye balls dinsa, lip gloss din data shafa ma soft lips ɗinta ba karamin rikitan shi yake ba.
makeup din fuskarta ya tafi da imaninsa, kamar yadda yake kallonta haka itama take bin shi da kallo, tun daga kan dogan wuyansa ta fara har iya zuwa soft lips din sa a hankali tay moving eye balls dinta zuwa ga dogon han cin shi wani irin yanayi take ji ajikin ta mara misaltuwa, sam takasa ta6uka komai, Javed dake akusa da su baisan wainar da suke toya ba hankalin shi na akan abincin da yake ci.
Babu wanda Ya lura da su sai ummi da ta sanya masu ido duk wani motsinsu akan idanunta
Yawu ta haɗiya tana ƙoƙarin kau da ido daga kallon shi, ba zato ba tsammani sautin daddadan kiɗa Ya karaɗe kunnuwan su taken waƙar Ko wuya ko dadi adai dai inda baifin Ya fara da
Ko wuya ko dadi
Ni dake ba zamu rabe ba
Ka zamo ni na zama kai
Ba ranar rabuwa
Ko wuya ko dadi
Ni dake ba zamu rabe ba
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Ka zamo ni na zama kai
Ba ranar rabuwa..
gaba ɗaya jikinsu Ya mutu, wata irin kasalace ta mamaye sassan jikinsu, hatta yanayin bugun zuciyar su saida Ya canza.
Kasa ƙarasa cin abincin ta yi A hankali Ta jingina bayanta jikin kujerar batare da ta daina kallon shi ba, waƙar ba karamin shagalar da su tayi ba, sun shagala da kallon juna, sun kasa ta6uka komai, kowa na cin abinci ban da su..."
Cigaba waka tay sun nutsu suna sauraran baitin
Dani dake soyayya ta ginu
A zuciya ta ke na saka kin sanu
Kice dani kin barni na banu
Shine kadai zai sanya ayi mini duren kunu
Kiji ni dai zama dake daram dam-dam
Na rike ki ta kam kam-kam
Makiyan mu suje chan
Banda son ki bansan komai ba...
Lumshe idanunta ta yi a hankali ta dan numfasa ba tare da buɗe idanun ba, wani irin bakon abu take ji a jikin ta, mara misaltuwa, sai taji tamkar saboda su aka yi waƙar saboda yadda wakar take shigarta.
yatsun hannunta sai kerma suke, gaba ɗaya ta shiga yanayi ba zata iya jurar cigaba da kallon shi ba.
Danish dake kallonta wata irin nutsuwa ce ke shigar shi, musamman data rufe idanunta hakan ya bashi damar kallon ta son ran shi, farar fatar dogon wuyanta yabi da kallo Silver necklace ɗin data sanya tayi matuƙar ƙawata wuyanta, moving eyes dinsa yai slowly izuwa kan kirjin ta sam ta manta bata ɗaure boobs ɗinta ta ciki ba kamar yadda ta sa6a, yau yaga abun da take boye mashi, duk da ƙarantar su nipples dinta ba karamin girma ne da su ba.
hannun shi na dan kerma ya dauki milkshake din data ajiye mashi ya fara shan shi ba dan yana jin dadin shi ba, saboda kallonta da ya ke yi yafi mashi komai.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
baitin Wakar ne Ya ƙara rikirkita tunanin shi ya ɗan runtse idanun shi yana sauraron daddadar muryar da kunnuwan shi ke jiyo mashi sai yaji kamar Angel dinsa ce ke raira mashi ita.
Na rike ka hannu biyu baby na
Kai kazam fitila annuri na
Ko ana fizgemin nama na
Zan yabe ka da karfin harshe na
Sai da kai
Ba ya kai
Ka sarkafe mini a zuciya ta
Ba ya kai
Ummi tasan takan tsiya, dagangan take maimaita wakar saboda ta ƙara rikitar da su, yau taga abun da Ya ɗaure mata kai, tun daga kan yanayinsu ta fahimci irin tsantsar kaunar da suke ma junan su, don ita abun da tagani ma ya wuce A kira shi da so hada shaukin junansu da suke ji, yar wakar da ta kunna masu kadai ta jefa su awani hali dama da biyu ta kunna ta
Kasa jurewa yayi da wata irin kasala Ya miƙe zai bar dining din gudun kada yayi wani abu ba dai dai ba da zaisa su sake samun sabani da ita, da sauri ummi ta dakatar da wakar ta dube shi.
"Danish Ina zakaje? Naga ko abincin baka fara ci ba" tamkar baisan furta magana yace"bana jin yunwa" marairaice mashi fuska su Haris sukayi"pls danish, kada ka tafi ka zauna ka ci abinci" girgiza kai yai, Shi kadai yasan me yake ji ajikin shi, In har ya cigaba da zama Yana kallon Unaisah komai zai iya faruwa a yanzu haka jikin shi sharkaf Yake Ga gumi da ya wanke shi duk da sanyin a.c din dake a dining room din, su basu lura ba amma ita Ummi tasan me yake ji a wayance tace"ko dai kana da uziri ne"? ya ɗaga mata kai alamar eh.
Shu'umun murmushi Tasaki Okay, Muna jiranka idan ka gama uzirin naka, ka dawo kaci abincin" bai kula ta ba Ya fuce daga dinning din ba don ya gaji da zaman shi ba, sai don bayason yaja ma kan shi bala'e.
Fitarshi keda wuya Unaisah ta buɗe idanunta da suka kaɗa jawur da su, ga wani zafi da temperature din jikinta ya dauka kamar mai fama da zazzabi.
ta rasa gane meke mata dadi, fitar Danish daga ɗakin yasa taji batasan cin komai, mineral water kadai ta sha ta miƙe jikinta na tsuma ta nufi hanyar fita daga dakin muryar aunty Ummi ta katse ta"Wai lafiya? Shi ya fita baici komai ba, kema kin miƙe zaki fita? Meke damunku ne"? Ta tambaya kamar batasan meke wakana ba.
Yamutsa fuska Unaisah tay tare da kallon Ummi datay maganar
"Wayata zan dauko adaki, yanzu zan dawo" ta fadi hakanne don kada su zargi wani abu.
kumshe dariya ummi ta yi abakinta, tana lura da yadda jikinta ke tsuma.
"Okay, muna jiranki" fucewa tayi daga dining din tana tafiya da nawa kamar wadda kwai ya fashe mawa, tana shiga dakin su ta faɗa toilet taja ƙofa ta datse, zama tay akan toilet seat tayi shiru tana tariyo abunda ya faru a dining room.
Ta rasa gane dalilin dayasa take tsintar kanta awani yanayi duk idan tagan shi ko taji muryarshi! Batasan menene ba, ta kasa ganewa.
bata gama zancen zucin ba, zatayi tsarkin fitsarin da tayi taga wannan farin ruwan mai yauƙi wani irin kyankyami da kyamane suka kamata, da sauri tayi tsarkin ta fito ta tsaya abakin kofar toilet tana faman sauke ajiyar zuciya, bayanin aunty Umminsu ta fara tariyowa a lokacin da take faɗa mata dalilin dake kawo shi, abun da ya daure mata kai kallon juna kawai sukayi ba wani abu ba amma sai gashi ta gan shi, dole ta nemi ƙarin bayani agurin Aunty ummin su.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
ga yunwa tana ji sai dai bata jin zata iya komawa dining room din, faɗawa tayi kan bedmattress ta janyo pillow ta rungume shi a kirjinta, wani sanyine ke ratsa zuciyarta, ga wani dadi da take ji a jikin ta.
ta shafe tsawon mintuna shabiyar a kwance ba tare data motsa ba.
"Sister, Aunty Ummi tace kizo wai" muryar hawwa ce ta katse mata zancen zucin ta, ba tare da ta bude idanunta ba tace"okay, gani nan zuwa" bayan fitar hawwa daga dakin ta sauko daga kan gadon ta, ta gyara mayafinta, tana ƙokarin fitowa daga dakin kamar daga sama taji Sallamar Salsabeel da sauri ta juya ta dubi kofar falon, a tsaye yake ya ɗauki wankan shadda kamar ba shi ba, hannun shi ruƙe da trolley, kwata kwata bai lura da ita ba.
"Yaya salsabeel," muryar ta ce ta fargar da shi, murmushi yayi tare da nufarta yana jan trolley ɗin.
"Unaisah ykk"
da fara'a tace"lafiyalou, ya salsabeel kwana biyu baka leko mu ba, munyi fushi"
ta fada tana haɗe fuska yar dariya yayi"i'm really sorry, wlh kuna araina, yanzu hakama da kika ganni saboda ku nazo"
Miƙa mashi hannu tayi"kawo na ruƙe maka trolly din" miƙa mata yai tasa hannu ta ruƙe handle din"Menene aciki? Ko kayanka ne"? Girgiza kai yai" mu karasa ciki, zan nuna maki abunda ke a cikin shi" amsa mashi tayi da toh suka nufi cikin falon akan sofa Ya zauna, Ta aje trolley din agaban shi Yace mata ta kira sauran yan uwanta ya faɗa yana hangen su a dining room suna cin abinci sam basu lura da shi ba, da sauri ta juya ta nufi dining room din ta shiga ta kira su, tun da suka ji ta ambaci ya salsabeel ya zo kowa ya ajiye spoon din hannun shi, Cike da zumudin son ganin shi suka fito daga dakin su dukan su hada Ummi.
Kafin su karaso ya mike fuskanshi dauke da fara'a ya gaishe da ummi ta amsa mashi da fara'arta, kallon su Haris yayi daya bayan ɗaya aranshi yana tariyo lokacin da suke a prison, rayuwa ta canza sun wadatu da kwanciyar hankali
Hannu ya miƙa ma mazan sukayi musaba, Ya dubi Yan matan dake ta faman hade rai
Dariya yayi"fushi kuke dani"? Khadeeja tace"eh mana, tun yaushe rabon da kazo gurin mu, ka manta damu.."
Mubeen Yace"kullum sai munsa ran zuwanka amma saika ki zuwa"
gaba daya suka rufe shi da korafe korafen su dakyar Ya samu ya shawo kan su, har suka hakura da fushin da sukeyi da shi bayan sun gama gaisawa da junansu yace su zauna zasuyi magana mai muhimman ci.
Bayan Kowan nan su Ya samu guri Ya zauna kan Sofas suka nutsu suna jiran jin me zaice masu.
"Ya salsabeel, Wannan akwatin fa? Ko tsaraba ne ka kawo mana" parveen ce tay maganar tare da nuna akwatin da hannu
"Eh tsaraba ce amma bata abun ci ba, Kayan sawa ne" kallon juna su kayi da mamaki akan fuskokin su.
"Ina Danish"? Ya tambaya yana kallon su
"Yana a daki" suka haɗa baki gurin bashi amsa"
Yace"okay, wani ya kira min shi" Haris ne Ya mike da sauri Ya je kiran shi.
falon yayi tsit baka jin hayaniyar komai, duk sun ƙagara da son ganin menene acikin trolly din me kuma ya Salsabeel zai fada masu mai mahimman ci'?
Jim kaɗan saiga Haris Ya dawo tare da Danish, Har ya canza kayan jikin shi yanzu silk pyjama ne a jikin shi na bacci.
Tun shigowarsu Falon, Unaisah take satar kallon shi, bayan sun rungume juna da salsabeel a amutunce suka gaisa da junan su kafin daga bisani kowan nan su Ya zauna suka nutsu suna kallon salsabeel
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Mu farayiwa Annabi salati" suka amsa mashi da toh, bayan sun gama yayi shiru yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya kamar mai nazarin wani abu, Azeeza da Jemimah sai faman kumshe dariya su ke yi kamar wasu zautattu.
Ɗaya bayan ɗaya ya fara kiran sunayen su, duk wanda ya kira sunan shi sai ya amsa mashi da Na'am, ummi dai tayi shiru tana jiran jin me zaice ma su
Numfasawa yayi kafin ya fara magana cikin nutsuwa
"Gobe Idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya, za'a tafi daku Isod headquarter...."
Kallon juna su ka yi arude suka maimaita sunan Headquarter, Sajeed Yace"me za mu yi acan ɗin"? Da alama sun ruɗe, murmushi Salsabeel yayi kafin yace"zaku gana da manyan jami'an Isod" Hankali tashe Unaisah tace"mu ɗin"? Jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, Lokaci yayi da zasu gana da ku, don suji daga bakin ku, Suna bukatar bayani game da rayuwarku a gidan kurkukun ƙaddara, zasuyi maku tambayoyi da suka shafi rayuwar da kukai agidan kurkukun ƙaddara da kuma shi kanshi gidan kurkukun"
Ya fada yana duban fuskokin su sunyi shiru suna sauraronshi kowa da abunda yaƙe sakawa aranshi.
"Nazo ne don in ƙarfafa maku gwiwa, nasan akwai masu jin tsoro har yanzu acikin ku, to inaso ku aje tsoron nan gefe ɗaya da duk wani shakku da zakuji, yanzu lokaci ne da zaku bada gudummuwa ku taimaka masu gurin kawo karshen kurkukun kaddara, bayanan da zaku basu da su zasuyi amfani wurin yin binciken waɗanda suka azabtar da rayuwar ku, kada ku 6oye masu komai, duk mun ƙanƙantar abu da kuka sani ku faɗa masu zai iya zama mai amfani agare su"
tun da salsabeel ya fara magana Danish Ya rufe idanunshi gam kamar baya atare da su, sarai salsabeel Ya lura da yanayin shi.
"Ku faɗa masu irin kuncin rayuwar da kukayi, Ku faɗamasu azabtarwar da sukayi maku da kuma wulakanta rayuwarku da su ka yi, ku kaɗai kuka san meya faru arayuwarku, tunkafin ku mallaki hankalinku kuke a kulle ba shige ba fuce, idan har kuka 6oye wani abu baku fada ma su ba, kanku zaku cuta, kwara ku tona masu asiri don uban su kowa yasan me suke aikatawa" ya faɗa tare da bugun sofa din da yake zaune akai da hannun shi.
"ku daina ganin ayanzu kun tsira kun samu rayuwar ƴanci wallahi har yanzu rayuwar ku tana acikin haɗari saboda ba zasu ƙyale ku ba, suna nan suna bibiyar rayuwarku don su salwantar daku saboda kune prisoners na farko da suka fara karya dokar kurkukun kaddara, tayaya ku ke tunanin zasu ƙyale ku? Ay ko dan kada ku tona masu asiri dole su nemi hanyar da zasu shafe babin ku"
Maganar salsabeel ta ɗaga hankulansu, Tuni ido ya raina fata, wasu daga cikinsu har sun fara sharar kwalla,
ya faɗa masu hakanne don Ya tsoratar da su ya kuma tunzura su don su fusata su samu kwarin giwar tona masu asiri idan jami'an sirrin suka tambaye su.
"Ko ba don saboda ku ba, Ku tuna ƴan uwanku da kuka bari agidan kurkukun ƙaddara! Waɗanda basu ji ba basu gani ba kamar ku dai, suna can ana azabtar da rayuwarsu, Sun maida su kamar dabbobi sai azabtar da su sukeyi, meye ribarku idan ku kun samu jin dadin rayuwa su kuma suna awahala? Baku da burin ku dauki fansar abunda akayi maku? Sannan ku cecei rayuwar yan uwanku? Za ku ja baki ne kuyi shiru acigaba da salwantar da rayuwar kananun yara da basu ji ba basu gani ba"? Ranshi a6ace yayi maganar yana kallon su, Jiki asanyaye sajeed Ya sauko daga kan sofa, Ya dawo ƙasa ya zauna hannayen shi biyu tallabe da kan shi, Idanunshi sun ciko tab da kwalla.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Shesshekar kukan su ne Ya cika falon, kalaman salsabeel sun fama raunin dake acikin zuciyar su..."
Salsabeel bai dakata ba saida ya tabbatar sun fusata sun harzuka kafin ya tsagaita da yin maganar Yana jiran jin me zasu ce.
Cikin shesshekar kuka sajeed yace"wallahi ko ba ka fada mana ba, ba zamu raga masu ba, ni ashirya nake da duk wata tambaya da za'ayi min, nayi alkawarin zan fadi iya abunda nasani saboda nima twin sister dina tana can, bana so su kashe min yar uwata duk da bani da tabbacin tana araye kota mutu...." kuka ne Yaci karfinshi, Ya kifa kanshi saman sofa.
Wani irin tausayin su ne Ya kama Ummi, Tuni taji hawaye sun cika idanunta, lamarin rayuwar yaran tana matuƙar tada mata hankali, har yau tana jin labarin su tamkar a mafarki saboda abun yafi karfin tunaninta.
Fashewa jemimah tayi da kuka tana fadin
"nima wlh saina tona masu asiri, mugaye azzalumai kawai, hadama wannan tsohuwar data kusa kashe mu nida su Azeeza, Inaji ina gani majnoon dina ya mutu, wlh saina daukar mashi fansa, koda zan rasa raina ne..." rai a6ace tay maganar, idanunta sunyi jawur ga ruwan hawaye dake zarya kan kuncin ta,
dafe kai Deeja tayi da hannunta tamkar zata fasa masu ihu, idanunta sun rune zuwa ja, kwata kwata bata son jin maganganun da su ke yi,
miƙewa tayi da sauri ta fuce daga falon, duk suka bi bayanta da kallo babu wanda yayi yunkurin dakatar da ita.
"Bazan ta6a manta irin azabtarwar da sukayi mana ba, wallahi rantsuwar ɗan musulmi ba gudu ba ja da baya sai mun fallasa su kwara duniya tasan me suke aikatawa, ay yaya Salsabeel ba sai ka sha wahalar yi mana bayani ba, dama mu lokaci kawai muke jira in ma takama har prison din aje damu ayi faɗan da mu, wallahi zamu bada goyan baya ɗari bisa ɗari ko da silar hakan zai ja mu rasa ran mu wlh sai inda karfin mu Ya ƙare, Kome suke son ji zamu faɗa masu...."
tun da Unaisah ta fara zazzaga masifa, suke kallonta jikinta har jijjiga ya ke yi tsabar fusata da 6acin rai, an ta6o inda keyi mata ƙaiƙayi.." bata ƙare maganar ba, Danish Ya miƙe daga zaunan da yake kan Sofa, gaba ɗaya suka bi shi da kallo Salsabeel Yace"Danish Ina zakaje ban gama magana ba"? Ko kallo bai ishe shi ba, Ya fuce daga falon, sam unaisah takasa karasa maganar,
Da tsantsar mamaki suka bi bayan shi da kallo har ya 6ace ma ganin su.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Haris Yace"ka gani ko ya salsabeel? Danish Ya canza kamar bashi ba, Yanzu ji muna magana mai mahimmanci Ya tashi Ya tafi kamar abun bai shafe shi ba, haka muke fama da shi baya son shiga cikin mu kuma baya son muje gurin shi..." cikin jin kunar rai Haris yayi maganar yana kallon Salsabeel.
Korafe korafe suka dinga fada mashi akan danish,
Unaisah tace"nasan ma zai yi wuya ya bamu hadin kai, kuma yafi mu sanin komai dangane da gidan kurkukun ƙaddara"
a marairaice tay maganar,
Shiru salsabeel yayi jim yana ɗan jinjina kan shi kafin cikin sanyin murya yace"sai kun yi hakuri da shi, saboda ba yin kan shi bane, sau dayawa wasu abubuwan da za ku ga yanayi wallahi ba shi bane"! A matuƙar ruɗe suka kalli Salsabeel, Musamman Unaisah Maganarsa Ta jefata a ruɗani, Har dai tagaza jure tace"Ya salsabeel ban fahimci me kake nufi ba! Naji kace wani lokaci ba shi bane"! Kallon ta salsabeel yayi"ina nufin wani abun da ya ke yi bayin kan shi bane, shaidanun dake a jikin shi ne, su ne suke Controlling din shi, zai iya wuni ba acikin hayyacin shi ba, nasan baku taba lura da hakan ba, shiyasa baya son shiga cikin ku, kuma baya son wani yaje gurin shi, idan ba wanda yake son gani ba, amma abun da yakamata ku cigaba da taya shi addu'a, In sha Allah idan mukayi nasarar raba shi da evils din jikin shi, zaku sha mamaki, zai dawo ainihin wanene shi...."
"Yaya salsabeel amma dai bazai manta damu ba ko"? Batool ce tay mashi maganar,
"Taya zai manta daku? Abokan kuruciyar shi, sai dai wasu abubuwan da yake yi zai daina su, zai canza sosai fiye da yadda baku ta6a zata ba.."
Hankalin Unaisah Ya tashi ba kaɗan ba, Aranta ta ayyana idan har maganar Salsabeel ta tabbata tabbas akwai damuwa ba kadan ba, sai dai ta hana zuciyarta gasgata maganar shi.
Buɗe trolley din gaban shi yayi duk suka kura ido
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite
Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 45 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 06, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
Zama ya yi daga gefen gadon tare da kallonta Ya kashe mata ido ɗaya ya ɗage gira cike da izza yace"me kike tunani ne? Kinyi mamakin ganina ne"? Shiru tayi bata tanka mashi ba, saboda ita har yanzu bata yarda cewa dagaske shine take gani ba, kokwanto take anya bata samu ta6in hankali ba
Sarai ya fahimci Halin da take aciki, Ko ajikin shi, saima kwantar da kanshi da yai saman pillow
"Ummi!, Haƙuri na ya ƙare, bazan iya jurewa ba, sha'awar son kasance wa dake tana neman tayi min illa, kin san ke kadai ce macen da ke iya gamsar dani, shiyasa na tako da kaina nazo don in kar6i hakkina agurin ki!" ya faɗa yana bin ta da wani shu'umin kallo
"Tun zuwan karshe da ki kai gidana ban ƙara ganin ki ba, in har ba zaki dinga zuwa kina bani hakkina ba, toh ni zan dinga zuwa ina kar6a, kin riga da kin san wanene ni indai akan bukatar kaina ne bana ji bana gani"
gaba ɗaya ta ruɗe, La66anta na kerma ta furta"dagaske kai nake gani? Ɗaga mata gira yai.
"Tayaya akai ka shigo gidan nan"?
"Kin san bana son tambaya, Last time, I warned you to stop asking me questions. If you believe me, babu bukatar ki tuhumeni akan duk wani abu da zan yi"
dafe kai tayi da hannu ɗaya, lamarin shi ya fara bata tsoro ba kaɗan ba.
"I'm waiting for you, come and satisfy me." ya faɗa yana shafa sajen fuskar shi.
Girgiza kai ta yi"kayi hakuri bazan iya ba, ina jin fargaban wani yagan mu zan iya samun matsala, ko kamanta a gidan wa muke? Ta faɗa atsorace tana kallon shi.
A gadarance ya furta"gidan director general of Isod, Sai me"? Idan naga dama har gidan ubansa sai in shiga inyi abun da naga dama, bawai iya gidan sa ba, ina da ƙarfin ikon yin hakan"
ya faɗa tare da ɗago kan shi daga jikin pillown ya miƙe zaune, ya fara cire front buttons ɗin jallabiyar shi, kafin ya miƙe ya zame rigar gaba dayanta ya rage daga shi sai short black colour..
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Gabanta ba karamin faduwa yayi ba, har ila yau ta gaza sabawa da Zanan dake akan fatar shi, daurewa kawai takeyi saboda Allah ya jarabceta da kaunar shi ya riga daya mallake zuciyarta, ya zama wani bangare na rayuwarta, shi din kaddararta ne.
"Inaso ki zautar dani har in manta wanene ni..." ya faɗa yana sakin wani ɗan iskan murmushi irin na fasikan tantirai da suka kai matakin degree a tashanci.
ba yau suka saba yi ba amma duk lokacin da zai kusance ta, ba karamar azaba take ci ba saboda yanayin halittar shi bakowace mace zata iya jurarta ba.
Adabarbace ta furta"nayi maka alkawarin zanzo har gidanka da anjima dan Allah ka tafi yanzu bana jin dadi ne, kuma bana so yaran nan su dawo su iske ni awani yanayi da zai sa su zargi wani abu" ta faɗa tana zare mashi idanunta dake kara rikita shi.
"After that, it's risky to have sex in this house."
Dakyar ta ƙare maganar ganin yadda ya tunkarota gadan gadan, juyawa tayi da niyar ta buɗe kofa ta fuce, sai dai ina tuni ya cimmata, wata irin damƙa yayi ma waist dinta da faffadan tafin hannunshi, Ya matseta jikin ƙofar yana fitar da numfashi mai hucin zafi, jarabar tashi ta motsa zai iyayin komai awannan lokacin.
Tun da taji jikin shi anata gaba daya ta shiga yanayi na bukatarshi dama tayi kewarshi kawai tana tsoron wani ya gansu shiyasa ta nemi bijire mashi, batasan meyasa bata iya yakice shi daga gare ta ba, ya riga da ya saba mata da kanshi, Ya 6ata ta ba kaɗan ba, Ya zamar mata karfen kafa.
can ƙasan makoshi Ya furta sunan ta Ummi..." kamar shi ya raɗa mata sunan saboda yadda yake furta shi da wata irin siga ta jan hankali.
Sam takasa motsawa sun manna ma kofar kamar zasu shiga cikin ta
"Mahaifin ki Yaja min bala'e, Yayi min baki Ummi, na gaza mallakar ki amatsayin mata na, Ya hana ni jin dadin rayuwana na har abada, yayi min illa ba kaɗan ba har yanzu ina jin ciwon abun a zuciyata duk yadda nayi kokarin ganin na mallakeki abun yaci tura..." ya faɗa yana ƙara cusa kanshi tsakanin wuyanta yayin da tafukansa ke adaddafe da kirjinta.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
zuciyoyin su atare suke bugawa, numfashin su na fita da sauri da sauri, kwata kwata ta fara fita hayyacin ta sam bata ji kalaman shi ba, batai aune ba taji ya ɗauketa ɗungururum gaba ɗayanta ya nufi shimfideden gadonta ya kwantar da ita akai yabi ya rufa mata ƙirjin shi
😳
_______________________________✍️
Lokacin da motocin su ka ƙaraso Head quarter A parking space su ka tsaya, kusan atare jami'an dake driving ɗin su suka fito daga ciki tare da buɗe masu cardoors ɗin.
Big guy da Taj ne Suka fara fitowa A hanzarce Jami'an Dake a harabar gurin suka buga ƙafa tare da sara ma su cikin girmamawa suka gaishe da su.
Ɗayan bayan ɗaya Prisoners suka soma fitowa daga cikin motocin, gaba ɗaya sun rufe rabin fuskokin su da Cotton Scarfs ɗin su, umarnin chief ne tun suna acikin mota, ya ce A sanar su rufe fuskokin su.
tun da suka fara fitowa Matasan
Isod soldiers dake kai komo a filin harabar suka fara satar kallon su kamar za su yi tuntu6e, kura taga nama sai dai ba halin tunkarar shi, hankalin maza ya tashi da ganin zankaɗa zankaɗan matasan ƴan mata masu jini a jika, rainon mai girma Chief Owais.
sun ruɗu da ganin kyawun Unaisah saboda launin idanunta sun ƙara ƙawata kyawun ta, gaba ɗaya hankali ya dawo kan su, su kuwa duk sun sha jinin jikin su ganin yadda gwarazan Jami'an ke bin su da kwallo, Jami'an Isod da mata basa agaban su yau dai alkadarinsu ya karye ganin prisoners.
Lura da yanayin yadda jikin wasu daga cikin su ke kerma alamun rashin nutsuwa da kallon jami'an yasa big big yai masu dakuwa da hannu da sauri suka kau da idanun su, abakin motocin suka tsaya, Batool tana ruke da hannun Unaisah, Azeeza ta ruƙe hannun Jemimah, Hawwa ta ruƙe hannun Yasmin, Parveen da Hanna sun ruƙe hannun juna, Sarah da Hibba sun ruƙe nasu hannun, itama Rubina ta ruƙe hannun Deeja gam a cikin nata, haka suma mazan Haris ya ruƙe hannun Javed, Naufal yana ruƙe da hannun Sajeed.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Taj ne ya buɗe backseat na Cardoor din Chief, Gently ya fito daga ciki, ya ruƙo hannun Danish, wato tun kafin suga hannun wanene chief Ya ruko Jami'an dake sintiri suka ƙura idanu suna jiran ganin hannun wani hamshakin ne tsabar kyawun yatsunsa kamar na mace aran su suka ayyana koma wanene ba karamin jan wuya ba ne tun da har chief ya ruƙo hannunsa, lokacin ɗaya ya ƙarasa fitowa kusan suman tsaye jami'an su kai bakomai ne ya ruɗar da su ba face ƙirar jikin shi, ba su ta6a ganin saurayin daya ja hankalin su irin Danish ba, saboda sun haɗa komai suna ji da kan su amma yau sun ga wanda ya take su akan komai in ka cire Chief ɗin su wai ahakan ma da suka ganshi Ya rufe fuskar shi da Hanky, tun a cikin mota chief ya rufe mashi fuskar, kyawawan idanun shi ne kaɗai a bude ya ɗan lumshe su saboda bai cika son kallon da mutane suke yi ma shi ba hatta chief da su big guy sun lura da kallon da jami'an ke yi mashi har sun manta basu sara ma chief ba balle aje ga batun yi mashi sannu da zuwa.
"Zamu iya tafiya" big guy ne ya faɗa tare da nuna masu hanya, cikin takun nutsuwa suka soma tafiya suna ta ƴan waige waige suna ƙarewa head quarter din kallo don ba ƙaramin burge su ginin ya yi ba kamar ba'a 9ja ba wasu tankama tankaman floor to ceilling glass windows ne ta ko'ina launin sky blue daga waje kana iya ganin cikin Secure Operation Center ɗin su kamar reception,
Gaban su sai faɗuwa ya ke yi saboda kakin jami'an isod ya yi shige dana Giant din kurkukun ƙaddara, gani suke kamar Prison suka koma, duk sun sha Jinin jikin su kamar marasa gaskiya, sai ƙara ƙankame hannun junan su suke yi, zuciya da sake sake wasu har sun raya aransu in wani mugun abun ya faru zasu arce da gudu.
Lokacin da suka shiga SOC ɗin, Muryar Na'ura ta karaɗe kunnuwan su, bayani take bayawar dangane da zuwan Chief, tsayawa sukayi kamar an dakatar da su, A tsorace suke bin tsakar gurin da kallo, matasan Isod agents ne bila adadin sanye da kakin su, hankalin su kwance suke gudanar da ayyukan su agaban Computers yan bala'e Na'urori ne kala kala har ta jikin Glass din gurin.
"Wallahi tsoro nake ji, ganin su nake kamar giant din kurkukun ƙaddara" murya na rawa Batool tayi magana tana faman rarraba idanu akan jami'an, Cikin muryar raɗa unaisah tace"ki kwantar da hankalinki pls, kakin su ne irin na giant nima na ɗan tsorata kaɗan"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
ta faɗa tare da satar kallon fuskar Danish, kamar baisan da zaman su ba, kwata kwata yaƙi sakewa ya ƙi yarda ya haɗa ido da kowa.
Suna atsayen nan jami'an suka dinga miƙo gaisuwa gurin su chief kamar zasu durƙusa mashi ƙasa tsabar yadda suke girmama shi.
"Meyasa kuka dakata da tafiya? Akwai wani abu ne"? Big guy ne ya tambaya yana kallon faces din. su, hankalin chief na akan Phone dinsa da ya ke daddanawa.
Kafin wani ya ba shi amsa daga cikin su, Hankulansu suka karkata akan Lift dake saukowa down ta glass dinta suka hango wasu gungun ƙarfafan Jami'an Isod abin da da ya firgitar su, zubin siffar jami'an dake a cikin lift din sak irin ta Giants na gidan kurkukun ƙaddara, Aikuwa suka fara kokarin tarwatse wa
hankulan kowa ya dawo kan su, ganin yadda jikinsu ke kerma yasa Taj yi masu magana cikin kwantar da murya yace"pls ku kwantar da hankulan ku, Ku nutsu nasan me kuke tunani, duk wanda kuka gani anan jami'en Isod ne ba masu cutarwa bane" ajiyar zuciya suka sauke still wasu daga cikin su hankalin su bai kwanta ba, a tsorace suke da jami'an.
Lokacin da suka ƙarasa saukowa down, Lift din ta buɗe kusan su shida ne, cikin takun majiya karfi suka tunkaro su, fuskokin su rufe da face mask, suna karasowa agaban su suka tsaya azafafe suka buga ƙafa tare da sarah ma Chief, kafin suka hada baki gurin gaishe da shi ya amsa masu daga gani na hannun damar shi ne.
Kamar sun lura da yanayin yaran dake ta kallon su atsorace hakan yasa suka fara cire face mask din dake akan fuskokin su.
Su Unaisah sun nutsu suna jiran ganin su wanene, sun ɗan yi mamakin haduwar su matasan samari majiya karfi masu ji da karfin ikon su, Allah ya zuba masu baiwa da fasaha ga wayewa, wasu daga cikin su farar fata ne yayin da wasun su kuma suka kasance bakar fata.
"Introduce yourselves to them"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
chief ne ya faɗa tare da nuna masu prisoners, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskokin su, wani black american ne daga cikin su ya fara magana cikin harshen turanci idanun shi akan fuskar Unaisah.
"Greetings, I'm Ahmed Hassan, Chief of Operations. I oversee all field operations and tactical decisions. Welcome!" he said cheerfully.
Na gefen shi wani fari fat hatta sumar kan shi yayi Dyeing ɗinta ta koma fara daga gani ɗan yankin asia ne awayan ce yace"I'm Commander Haroon, Chief of Intelligence. I gather and analyze intelligence and advise the DG and COO" ya faɗa tare da nuna Chief Owais da Big guy kafin yace"We've been expecting you" da fara'a ya nuna su Unaisah
Gaba ɗaya sun nutsu suna sauraron su duk wanda yayi magana idanunsu na akan la66ansa.
'I'm Dr. Zara Saeed, head of Counter-Terrorism Division and leader of high-risk missions."
"Agent Ethan Kim, Tactical Expert, your go-to guy for high-risk missions."
"Agent Jabeer Osman, mid-level operative specializing in infiltration and surveillance."
Bayan sun gama gabatar da kan su, atare suka hada baki wurin yi masi barka da zuwa.
Murmushi kowan nan su ya saki, Har sun ji hankalin su ya kwanta.
"Mu karasa daga Ciki" big guy ne ya faɗa tare da nuna masu hanyar da zata sada su da inda zasu je.
Taj da big guy ne agaba prisoners suna abayan su, Chief da Danish suna abiye da su, yayin da Manyan jami'an ke take masu baya Har suka ƙara so wani katafaren guri kamar falo Ya haɗu ba kaɗan ba, jami'an da suka iske aciki girmamawa suke gaida su chief.
A saman hadaddun sofas din da ke agurin Taj yace su zauna, dama agajiye suke da tsayuwa da sauri suka zauna, daga gefen Danish ta zauna saboda ta lura da mood dinshi kamar baijin dadin shi, tana so ta ɗan kwantar mashi da hankali gudun kada Yaƙi basu hadin kai.
tuni ƙamshin turaren junansu ya shiga hancinan su sosai su ke shakar shi, ga ni'imar sanyin A.c din da ke ratsa jikin su.
Idanunsu na akan su Big guy dake atsaye tare da manyan jami'an nan sun haɗa kai suna tattaunawa atsakanin su daga inda suke basa iya jin me suke cewa.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
A lokacin da bai yi tsammani ba, Yaji ta ruƙe yatsun hannun shi a cikin nata, aruɗe ya dube fuskarta tamkar batasan tayi ba, ta wani Basar ta kalli gefe ɗaya.
"Meke damunka"? Ta fada batare data kalli fuskar shi ba
"Na lura tun da mu ka zo kamar babu walwala atare da kai, ka ki sakin fuskarka kamar wani abu na damunka ko baka jin daɗi ne?
Ta tambaya ba tare data kalli fuskar shi ba, Saboda ƙwarjinin da yayi mata.
lumshe idanun shi yayi tare da jan numfashi har saman fuskarta taji saukar iskar numfashin sa wani irin yanayi taji atare da ita.
"Nayi maka magana kayi shiru baka tanka min ba, ko dan na damu da kaine"? nutsuwa yayi yana kallon kyawawan idanunta kwata kwata taƙi yarda su haɗa ido saboda sunyi kusa da juna kuma bata son ta jefa kanta cikin irin halin da suke tsintar kan su duk in su ka haɗu da juna.
Ba zato ba tsammani taji ya shigar da yatsunsa a cikin nata ya yi tighting din su wani irin shock taji har tay kokarin zame hannunta daga nashi amma ya ƙara ƙanƙame su ta yadda bazata iya kwatsar kanta ba.
Arude ta furta"pls ka sakar min hannuna! Kada wani gan mu," can ƙasan makoshi ya furta"Ke kika fara ruƙe min hannu, don haka bazan saki ba" ya faɗa yana kallon idanun ta so yake ta juyo su fuskanci juna ko ya samu nutsuwar da yake samu agurinta amma taki bashi haɗin kai.
Babu wanda ya lura da halin da suke a ciki, Hankalin yan uwan su na kan su Taj da mutanan su.
Bayan wasu ƴan mintuna, taj Ya nufo su gurin su suna ganin shi suka fara sauke ajiyar zuciya dama duk sun takura da zama su kadai
"Batool, Unaisah da ku zamu fara, Bismillah ku taso ku shiga daga ciki" ya fada tare da nuna masu ƙofar Questioning Room din.
Batool harta fara jin faduwar gaba amma da taji tare da Unaisah ne sai taji hankalinta ya kwanta.
Ƙoƙari take ta miƙe Danish Yaƙi sakin hannunta, fargabanta kada daddynta ya gani dakyar ta samu ta ƙwace hannunta daga nashi ta ta ruko hannun Batool suka bi bayan daddyn ta.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
bayan sun shiga ɗakin suka tsaya suna ƙare mashi kallo, wasu hadaddun kujeru ne biyu suna fuskantar ɗaya daga tsakiyar su madaidaicin table ne.
ga wani two-way mirror a jikin bangon dakin, wanda anyi shine saboda masu duba wanda ake tambaya su samu damar kallon shi daga Observation Room, tsabar tsaron ɗakin hada Surveillance Cameras (Kyamarorin sa ido) Nau'o'in ɓoyayyun kyamarori masu daukar video recording, ta kowace kusurwar dakin har ta cikin fitilun kwai da jikin kofa duk sune a makale ba zaka ta6a ganin su ba in ba an fada maka akwai ba,
gaba daya sun shagala da kallon ɗakin har saida taj yayi masu gyaran murya kafin suka yi saurin kallon shi
Murmushi yayi masu"ku zauna mana" muryar Unaisah da yar shagwa6a tace"daddy zamu iya cire mayafin daga kan fuskar mu? Wlh ya takura mana"
da kan shi ya cire mata mayafin, Ya yi mata rolling akanta, Ya matsa gaban Batool ya warware mata na kan fuskarta itama ya naɗa mata akan ta, sai dadi takeji ganin yayi mata yadda yayi ma Unaisah.
Bayan sun zauna ya ɗan dafe table din gabansu da tafukansa Ya dubesu da kyau
"Pls kada ku bamu kunya, ku natsu ku kwantar da hankulan ku gurin amsa mashi tambayoyin da zai yi maku, Mutun ɗaya ne zaiyi maku tambayoyin dan haka ku kwantar da hankalinku" kallon juna su ka yi atare kafin suka dube shi.
Murmushi ya sakar masu "ina fatan zakuyi min haka" atare suka haɗa baki gurin first"Eh" yar dariya yayi"lokaci yayi zan tafi, ku kula mun dakan ku"
amsa mashi su kayi da "toh"
Bayan fitar shi daga dakin kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, kowa da abun da yake sakawa aran shi, damuwar Unaisah akan Danish tana ji aranta zaiyi wuya ya basu hadin kai.
"Sis Wai wanene Zai yi mana tambayoyin"? Batool ce tayi mata tambayar kafin ta bata amsa suka ji motsin shigowar mutun atare suka kalli kofar ɗakin.
har sai da gaban su ya fadi saboda ba su tsammaci ganin chief owais ba, ta wani bangaren sunji dadi saboda sun san wanene shi sun kuma yarda da shi ɗari bisa ɗari.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Walking Slowly yabi ta bayan kujerun su Ya nufi frigde ya buɗe ya dauko juice mai sanyi ya haɗo da cups biyu ya daura akan table din gaban su, duk wani motsin shi akan idanun su yanayin yadda yake tsiyaya masu ruwan lemun a cup ba ƙaramin tafiya ya yi da imanin su ba, komai nashi cikin aji, ƙasaita da nutsuwa yake yin shi"
kwata kwata bai ɗago Ya dube su ba, har sai da ya gama zuba masu juice din mai sanyi a cups Ya tura ma su agabansu kafin a hankali Ya zauna tare da ɗaura kafarshi ɗaya kan ɗaya, ganin sunƙi daukar cups din yasa shi tunanin ko basu san su ya zubawa ma ba, kamar ya sani kuwa ai gani suke basu kai matsayin da chief zai zuba masu lemu a cup ba.
Da index finger din shi ya nuna masu Cups din, Hakan yasa suka fahimci nasu ne, a tsanake suka ɗauka suka fara sha a hankali don kada yaga sun yi ƙauyanci musamman Unaisah da aji take shan juice din yayi mata dadi ga sanyi.
A gayun ce ta rage kaɗan a cup din ta ajiye kan table, Batool kuwa duka ta shanye shi har tana shaƙe wa cikin raɗa unaisah ta yi mata magana don kada ya ji su
"shashasha, Ki yi irin na yan gayu ki rage kaɗan, kada yaga hadamarki"
baiwar Allah idanunta amarairaice ta kalli cup din ta shanye kaf tsoronta kada Unaisah tayi mata faɗa sunnar dakai ƙasa Unaisah ta yi ganin chief na kallonta wata irin kunyarshi da nauyinshi ne suka kamata.
mayar da idanun shi yayi kan Batool in a cool voice ya furta"kin koshi ko in ƙara maki"? Maimakon ta bashi amsa sai ta kama kallon unaisah, nan take ya fahimci tana jin tsoron tayi mata fada.
bai jira amsarta ba, ya ƙara mata juice ɗin a cup"ki dauka" jikinta asanyaye ta kar6i cup din takai baki saida ta shanye kafin ta ce"thank you"
"Neva mind," ya faɗa tare da gyara zaman shi
"Can we start?" ya fada yana kallon su
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Atare suka amsa mashi da Eh, tun kafin su zo head quarter din an sanar da su da harshen turanci za su yi magana saboda duniya ce zata saurari tattaunawar su.
Shiru ya yi yana duban su da alama nazarin wani abu yake yi tsawon mintuna kafin kasaitacciyar muryarshi ta katse shirun na su
"Da farko Inaso ku gabatar da min da kan ku" Unaisah ce ta fara gabatar da kanta kafin batool ta yi nata introduction din.
"Tayaya akai kuka tsinci kan ku agidan kurkukun ƙaddara"? Kallon juna su ka yi, kafin Unaisah ta fara bashi labarin lokacin da ta gudu daga rigar fulani da yadda Bakar mota tayi parking agabanta aka zuro hannu daga ciki suka dauketa.
"Daga nan ban kara sanin inda kaina yake ba.." tiryan tiryan ta labarta mashi, bayan ta kammala nata cikin kuka saboda duk lokacin da ta tuna rayuwar da sukayi a kurkukun kaddara sai taji zuciyarta ta kare musamman mutuwar unaizah da majnoon dinsu, Ya mai da duban shi ga Batool jikinta sai kerma yake duk ta rasa nutsuwarta gaba daya sun fahimci halin da take a ciki.
Jin tayi shiru yasa Unaisah ingiza kafadarta, Muryarta na rawa ta fara magana.
"Ni bansan lokacin dana tsinci kaina agidan kurkukun kaddara ba, tsohuwar da ta raine mu wadda muke kira tsohuwa Tamira ta ta6a faɗa mana tun muna jarirai aka kawo mu gidan kurkukun, itace ma ta shayar da mu ta kuma raine mu har muka mallaki hankalin mu"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
dakyar ta ƙare maganar duk tabi ta ruɗe saboda kwarjinin da chief ke yi mata duk in ya ɗago da ido ya kalleta tun bai fahimta ba har ya fara ɗago ta, shi dinne akwai jan hankali dole mace ta ruɗe agaban shi kamshin turaren shi kadai ya isa ya susutar da su balle kuma shi din gaba ɗayansa.
Kamar ɗan jarida haka ya tsare su da tambayoyi tun suna amsa mashi cikin dadin rai har suka fara galabaita tuni Gumi ya fara wanke goshin su duk da sanyin A.c din dake dakar fatar su, numfashin su har sauri sauri yake gurin fita musamman Batool kirjinta sai sama da kasa ya ke yi ta fara rikicewa, wata tambayar ma da kunya suke amsa mata saboda nauyin amsa mashi da suke ji.
"Bayan sun ɗauke ki na tsawon watanni me su ka yi maki" ya fada tare da nuna batool da girarsa, sunnar da kanta ƙasa ta yi gaban ta na faɗuwa.
"Ina sauraron ki" ya fada cikin aji yana duban Batool
"Can I help her"? Unaisah ce tay maganar, tana faman jujjuya eye balls dinta
"Rasa kunya 6eran tanka, nasan zata aika" big guy ne ya faɗa da zolaya yana kallon Taj, ashe suna atsaye gaban Mirror suna kallon su tare da su COO, CI, and Senior agents daga observation Room.
harara Taj Ya jefa mashi"bana son Iya shege wlh"
Big guy yace"gaskiya ke bakaso jarin ka bata da kunya, ita sister dinta tana jin kunya shine ita rasa kunya take fadin zata taimaka mata..." murmushi Taj yai batare daya ƙara tanka mashi ba.
Girgiza kai chief yayi "No, I prefer her to tell me herself, kinsan ance waƙa bakin mai ita tafi dadin sauraro ko ba haka fa"? Ya faɗa tare da daga mata gira, cike da jin kunyar shi ta sunnar da kanta kasa tana dan sakin murmushi.
Kayataccen murmushin gefen fuska ya dan saki tare da kallon Batool da ta tsare shi da idanunta.
Yawu ta haɗiya kutt sautin Ya fita, cikin rawar murya ta fara en ena hakan yasa shi dakatar da ita"ki fara daidaita nutsuwarki" tuni tasha jinin jikinta muryarta na rawa ta amsa mashi da toh, shiru su ka yi na tsawon mintuna kalilan kafin yace da ita kin shirya amsa min"? Yanayin yadda yayi mata magana yasa taji wani bakon abu ya ziyarceta wanda batasan menene shi ba.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Jinjina mashi kai tay alamar eh kafin atsanake ta fara bashi labarin abin da ya faru da ita bayan giants sun dauketa na tsawon watanni.
runtse idanun shi yayi tare da dafe forehead din shi da hannu ɗaya, wani irin tsantsar bacin rai ne ya ziyarci zuciyar shi, hatta su taj dake kallon su jikin su yayi mugun yin sanyi, sauran jami'an dake kallon su babu wanda ran shi bai 6aci ba, jikin su har tsuma yake yi tsabar fusata.
Lokacin da ta karasa bashi labarin, dakyar ya iya buɗe idanun shi ya dube fuskarta suka hada ido cikin na juna
"Iya abunda su ka yi maki kenan? cikin sanyin murya da yar sheshshekar kuka tace Eh
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kafin ya furta"idan kunayin jinin al'ada ne kadai suke daukar ku"? Tace eh
Mayar da duban shi yayi kan Unaisah"ke fa"? da gira yai nuna da ita.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Cikin sanyin murya ta fara bashi labarin abun da ya faru lokacin da ta saci hanya ta fita daga dakin su na gidan kurkukun ƙaddara ta tafi neman Neman Danish har tsautsayi ya rutsa da ita ta haɗu da tsohuwa zafreeen.
Bata boye mashi komai ba, sai da ta sanar dashi, abun da yafi kona mashi rai wankan jinin da matsafan su ka yi mata bayan sun tu6e mata kayanta, ga kuma azabtarwar da suka yi mata cikin shesshekar kuka tace"ta karfi ta tsiya suka sa ni na farke mace mai tsohon ciki da wuka har jaririnta saida wukar ta yanka, bayan haka suka tursasa min saida suka bani naman mutun tafasasshe suka sa karfi gurin banbare bakina kafin suka tura min naman, har ciwo saida naji gurin ya dinga bleeding...."
wani irin tsantsar tausayin su ne ya kama shi da sauran jami'an da ke kallon su, chief baisan sa'adda Ya ruko yatsun hannunta a cikin nashi ba, saboda ta bashi tausayi sai yaji kamar ya yi huggin din ta da alama ya manta da jami'an dake kallon su.
*DAGA ALƘAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*_______________________________________✍️💋✊
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
POST A COMMENT
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(302)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite
Home
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe chapter 46 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 07, 2024
Takun Ƙarshe
Calmly yace"share hawayen bana son ganin su" jinjina mashi kai tay alamar toh
Ya zuba mata juice A cup Ya miƙa mata, Yatsun hannunta na kerma ta dauka takai baki ta yi kur6a ɗaya ta aje, ta nutsu tana jiran tambaya ta gaba
"Sun ta6a yin raping ɗin ki"? Dakyar yai mata tambayar saboda fargaban amsar da zata ba shi.
Shiru tayi jimm tana tunanin meye ma raping din? Ko yana nufin irin abun da matsafan su ka yi ma su Deeja kamar yadda ta bata labari.
Shirun da ta yi ba karamin kayar mashi da gaba tayi ba, hankalin shi ya tashi matuƙa.
"Ko baki gane me nake nufi ba" da sauri tace"na gane, ni ba su ta6a yi min ba, saboda sai wanda ya fara jinin al'ada suke yi mawa"
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanunshi wani irin sanyine ya ratsa zuciyar shi ita kanta ta lura da yanayin shi tayi mamakin hakan.
Sun ɗauki tsawon lokaci Yana jera masu tambayoyi Cikin ikon Allah suka amsa mashi duk wata tambaya da yayi masu babu abun da suka boye mashi saida suka faɗa mashi komai da suka sani dangane da rayuwarsu agidan kurkukun kaddara daga farko har zuwa lokacin da suka tsira daga kurkukun.
gaba ɗaya jami'an dake kallonsu saida zuciyarsu ta karaya da tausayin rayuwar yaran musamman wadanda basu san labarinsu ba, abun ya girgiza su ya yi matukar ɗaure masu kai da al'ajabi, suna sauraran abun kamar amafarki saboda al'ajabin da ya rufe su, abin da yafi karya masu zuciya labarin Unaizah, wlh hankalinsu yayi mugun tashi sun girgiza da jin rashin imanin da matsafan suka yi mata, duk irin dauriyar jami'an isod sai da idanunsu suka kaɗa jawur tsabar fusata sunji zafin mutuwar yarinyar da yadda uban ta ya yaudareta ya salwantar da rayuwar ta tsabar mugunta da zalunci.
"Menene Sunan mahaifinta"? Ya jefa ma Unaisah tambayar.
Wani ikona Na Allah gaba daya ta manta da sunan kamar an shafe mata shi a kwakwalwarta.
Girgiza kai tay"na manta sunan shi, amma idan na tuna zan sanar dakai, ta dai ta6a fadamin babban mutun ne a Nigeria" jinjina kai chief yayi"A cikin backpack din dinta da sojojin america suka ba mu, munga textbooks, jotter da diary kun ta6a buɗe su"? Shiru ta yi jimm kafin ta girgiza kai"bazan iya tunawa ba, amma yan zu backpack din tana adakin mu tun lokacin da na kar6a agurin daddyna"
"Okey, Idan muka koma gida zan kar6a" amsa mashi tayi da toh
Sara ma su yayi da hannun shi kafin ya jinjina masu da babban yatsan shi, gaba ɗaya suka saki murmushi
"Thank you for your cooperation, Unaisah and Batool, The information you provided will help us find the oppressors and put an end to them In sha Allah" ya fada yana kallon su, at same time suka sauke ajiyar zuciya, dama aƙagare suke da ya kammala yi masu tambayoyin don ba karamar gajiya su ka yi ba.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Miƙewa ya yi ya nufi room door suka bi bayan shi, suna fitowa daga dakin da sauri Yan uwan su suka nufo su suna tambayar su me aka tambaye su.
"Ku bari idan ku ka shiga zaku ji abunda muka ji amma fa akwai juice me sanyi zaku sha dadi" unaisah ce tayi maganar.
Tun fitowarsu Chief Ya Bar wajen Ya nufi Observation room saboda ba shi ne zaiyi ma sauran tambayoyi ba.
Tayi mamakin ganin Danish yana bacci ya langwa6e kan shi saman kujera da alama yaji dadin sanyin a.c din dake ra6ar shi, hakan ba karamin tada mata hankali yayi ba, gani take kamar baccin nashi bana lafiya bane da sauri ta nufi Sofa din ta zauna daga gefensa ta ƙura ma shi ido tana fuskar shi.
Taj ne ya fito daga dakin da suke Ya nufo gurin su, Mutum uku Ya kira Parveen, Jemimah da Azeeza su uku aka shiga da su dakin tambayar, ahaka aka dinga dibar su ɗaya dayan duk wanda ya fito daga ɗakin jikin shi ba kuzari ga zufa saboda galabaita da tambayoyin da akeyi masu saukin su akwai Juice da ruwa me sanyi ita jemimah uwar son banza daga anyi mata tambaya daya sai tace ta gaji abata lemu ta jiƙa makoshin ta, ahaka aka samu ta amsa tambayoyin, haka itama parvin Jami'en da yayi mata tambayoyi yasha bakar wahala saboda shiririta da ta saka ga rashin nutsuwa kafin agama yi mata tambayoyin saida tasha juice yayi cup goma, Deeja kuwa dama basu sanya ran zasu samu wani abu daga gareta ba saboda ta6in hankalin ta, kamar ma bata jin dadin jikinta ko irin haukan da takeyi masu agida batayi a headquarter din ba tana zaune kan sofa ta yi shiru tana kallon duk wani mai giftawa.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Ɗaya bayan daya saida suka amsa tambayoyin da akayi masu, mutun huɗu da jami'an suka ji dadin tattaunawar su da yaba kokarin su Unaisah da Batool sai mazan cikin su duk da bakomai suka iya tunawa ba kamar abun da ya faru da su lokacin da aka ɗauke su na tsawon watanni sun kasa tuna abun da akayi masu sun dai san sunci baƙar azaba kuma duk wanda yaji alamomin da suka dawo hayyacin su da su a jikinsu zai fahimci hada homo su ke yi da su.
Jami'an Sun firgita da jin irin rashin Imanin da matsafan suke yi ma su, sunji abun da Ya gigita tunanin su ba dan juriya irin tasu ba da kuwa sun fashe da kuka saboda bakin ciki da takaicin abunda akayiwa yaran da ba su ji ba basu gani ba, suna ji aransu idan ya'yansu ne hakan ta faru da su ya zasuyi? Wlh har zuciya zasu iya hadiya su mutu.
Bayin Allah gaba ɗaya sun dawo kan kujerun sun zauna, fuskokin su sharkaf da ruwan hawaye saboda an fama masu raunin dake a cikin zuciyar su, idanunsu sun kaɗa jawur kamar jan gauta, sun yi shiru suna tuna rayuwarsu ta prison babu mai magana a cikin su, yanzu saura mutun ɗaya ya rage a shiga dashi dakin tambayar, sun ma rasa taya zasu farkar da shi daga bacci, ya hakimce kan sofa Hankalin shi kwance yake fitar da numfashi shi baisan meke wakana ba.
Agaban kujerar da ya ke zaune jami'an suka tsaya suna kallon shi daga cikin su hada chief da taj da big guy.
"Sir, Mu tada shi daga baccin"? taj ne ya faɗa tare da kallon chief
"Bana so mu takura mashi, Mu jira zuwa lokacin da zai farka inaga zaifi" girgiza kai big guy yai"Sir ni anawa shawarar mu tada shi, saboda yaron yana da nauyin bacci, bamu san lokacin da zai farka ba ga baƙin mu na america da muke jiran ƙarasowar su, bayan haka yan uwanshi akagare suke da su koma gida, saboda sun gaji suna bukatar hutu"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
cikin tausasa harshe ya ƙare maganar yana duban chief, maganar big guy ta tuna mashi da nauyin baccin Danish, zai iya kai magrib bai farka ba, wrist watch din hannun shi ya duba kusan karfe ɗaya da rabi.
"Sir, Nima anawa shawarar Atada shi daga baccin" acewar COO,
Ci yace"nima na goyi bayan a tada shi daga baccin duba da lokaci"
gaba daya jami'an sun goyi bayan a farkar da shi daga bacci.
Duk abun da ke faruwa akan idanun su Unaisah suna kallon ko me ke faruwa.
Kamar za su tada jariri daga bacci cikin muryar raɗa Taj ya furta sunan shi"Danish! Danish"! Kamar ya yi magana da bango, babu alamun zai farka
A hankali ya dan bubbuga kafadar"pls danish ka tashi" still bai farka ba
CI yace"amma dai yaro ne da jikin manya ko? Cos ni lokacin da aka turo mana hoton fuskar shi banyi tsammanin yakai haka girma ba"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Yar dariya Big guy yai"adinga hadawa da tubarkalla, dama nasan sai ka tanka, kai da baka iya gani ka yi shiru, to yaro ne shekaran shi 20" da zolaya yai maganar, murmushi Su ka yi tare da maida hankalin su akan Taj dake kokarin tada Danish.
Big guy yace"Dama na faɗa ma ku Nauyin bacci ne da shi, a samu ruwa me sanyi a yayyafa masa a fuska watakil Ya farka" girgiza kai chief yayi"ban amince asanya mashi ruwa ba, bari na jaraba tada shi" mikewa taj yayi don ya bashi damar zama kusa da Danish.
Bayan ya zauna ya kai hannu ya ɗan bubbuga kafadar shi"Danish? Ka tashi ina so zamu yi magana!.." a kalla ya ambaci sunan shi yakai sau biyar har Senior agents din sun fara jin fargaban anya lafiyar shi kalau.
Ba zato ba tsammani, suka ga ya fara motsa yatsun hannayen shi alamar zai farka, kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, A hankali ya ɗan bude idanun shi waɗanda suka kaɗa jawur ya dubi fuskar chief.
"Sannun da bacci, ka barmu muna ta jiranka" yamutsa fuskar shi yayi ba tare da ya furta kalma ba.
Ruko hannun shi chief yayi"ta shi mu shiga ciki, mun gama yi ma yan uwanka tambayoyi saura kai kadai ka rage, Ina fata zaka bamu hadin kai kamar yarda suka bamu" Cikin kulawa ya yi maganar yana duban shi.
Da wata irin kalasa Yake kallon chief dake masa magana, hanky din da ya rufe rabin fuskar shi tuni ya jima da warwarewa.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Tun daga kan yanayin shi Jami'an suka fahimci zaiyi ji dakai, Aransu suka ayyana kamar kanin chief saboda kamannin su da suka gani.
Sunyi mamakin ganin yadda chief ke lalla6a shi kamar zai durkusa mashi mutumin da suke ma biyayya sau da kafa suke tarairayarshi yau shi ne dakan shi yake tarairayar wani, ba komai ne yasa shi yin hakan ba face don ya samu ya shawo kanshi ya amsa masu tambayoyin su baya son Danish ya bashi kunya.
Dakyar Ya samu Danish Ya miƙe chief ya ruke hannun shi Yaja shi suka nufi Questioning Room ɗin yasan yadda yake da wuyar sha'ani shiyasa ya zabi kan shi a matsayin wanda zaiyi mashi tambayoyin yasan da wuya in wani ne Ya saki jikin shi.
Gaba ɗaya burin jami'an Suga tattaunawar chief da Danish, sun ƙwallafa rai akan son jin bayanan da zai bayar, Suna atsaye gaban mirror din suna kallon su ta cikin Observation room din.
Bayan sun zauna kan Chairs dake fuskantar junan su, Chief Ya zuba masu juice a cup ya miƙa mashi.
kin dauka yayi har saida chief yace"na ka ne kadauka" kafin ya cira hannu ya dauki cup din Ya kur6i juice ɗin wani irin sanyi ne ya ratsa throat dinsa.
bayan ya kammala sha ya aje cup din ya mayar da hankalin sa akan chief dake kallon shi, bai ta6a jin fargaban tambayar wani dan adam a duniyar nan ba irin yadda yaji fargaban tambayar Danish sun kurama juna ido an rasa me magana a cikin su.
Jami'an dake kallonsu sunyi matukar ƙagara, Yayin da taj da Big guy hankalunsu ke atashe saboda zullumin kada Ya basu kunya.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Idan muka koma 6angarensu Unaisah, tun da suka shiga da Danish ta rasa nutsuwarta, Hankalinta atashe Yake saboda ita tasan mawuyacin abune Danish ya basu hadin kai, idan ta tuna rayuwarsu ta baya yadda kwata kwata bai ta6a fada mata wani abu daya shafi kurkukun kaddara ba duk irin mutuwar son da ya ke yi mata, haka ya dinga boye mata ko ta tambaye shi baya fada mata ita da take kaddararsa balle su da har yanzu bai yarda da su ba kallon su kawai ya ke yi saboda ba yadda zaiyi da su.
Tun tana daga zaune har dai ta miƙe ta fara zarya a tsakar gurin da suke, hatta su Sajeed sai da suka lura da yanayin ta, ko da suka tambaye ta meke damunta sai tace masu ba komai ta kosa su koma gida ne.
"Zamu iya farawa"? Ya tambaya yana kallon sa, tamkar baisan furta maganar Yace"yeah..." ajiyar zuciya chief ya ɗan sauke kafin ya fara magana
"Ka fara gabatar mana da kanka, muna son muji sunan ka da takaitaccen tarihin rayuwarka"
kalma ɗaya tak ya furta"Danish" daga nan bai ƙara magana ba, kuma baida niyar yin ta.
Hakan bai damu chief ba, yayi mashi uziri saboda yasan ba lallai yasan me ake nufi da gabatar da kai ba.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Tun kana jariri ka tsinci kanka agidan kurkukun kaddara hakan na nufin kai rainon su ne, tun da a hannun su ka mallaki hankalin ka, kasan komai dangane da elders kuma kasan duk wani abu da suke aikatawa agidan kurkukun kaddara a matsayinka na prison shield dinsu..." ya faɗa yana kallon fuskarshi, yadda kasan yana fahimtar shi ya nutsu yana sauraron shi.
Numfasawa chief ya yi kafin ya ɗaura da cewa"ɗan uwanka Salsabeel ya fada min kafi shi sanin su wanene shuwagabannin kurkukun kaddara ka kuma san komai dangane da su, bayan haka kaima kana ɗaya daga cikin Giants masu babban muƙami agidan kurkukun kaddara, saboda suna ji dakai kuma sun yarda da kai shiyasa har suka baka mukamin garkuwar su hakane"?
Ya tambaya yana bin shi da kallo, ɗaga mashi gira Danish yai alamar eh ba tare da ya furta ba.
"Bayan haka munji bayani daga bakin yan uwanka, kaine kayi masu hanyar da suka fita daga gidan kurkukun kaddara shima hakane"! Again ya ɗaga mashi gira.
Ran Big guy yayi mugun 6aci saboda a gurinsu disrespecting ne Chief Yana magana Ka amsa mashi da gira ji yake kamar ya fada dakin Ya kifa mashi mari dama shi akwai zuciya.
Chief kuwa bai kawo komai aran shi ba dangane da yadda Danish Yake amsa mashi.
"Who are the Elders? Do you know their faces? cike da sa ran zai amsa mashi yayi tambayar.
Girgiza mashi kai yai alamar a'a, Sai a lokacin Ya lura da yadda yake amsa mashi ba ɗa'a kwata kwata ranshi ya sosu.
Muryarshi da sanyi ya furta"ba zaka iya yi min magana ba"? ɗaga mashi gira yai alamar eh, runtse idanun shi ya yi ranshi ya ɗan baci amma sai yayi kokarin sarrafa temper dinshi saboda bayason ya bi shi ta karfi yafi son ya lalla6a shi su rabu lafiya.
"Kana nufin tsawon lokacin daka dauka agidan kurkukun kaddara bakasan su wanene elders ba? Ko fuskokin su baka sani ba"? Yamutsa fuska ya yi dakyar ya furta"nasan su amma ban san fuskokin su ba"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Don't lie to me, Nasan ba halin ka bane"
"Why should I lie? If I don't want to tell the truth, I'll just shut my mouth." fuskarshi adaure yayi maganar.
Jinjina kai chief yayi"sunayen su fa? Ka sani"
Shiru yayi bai tanka mashi ba, hakan na nufin yasani baison fada mashi.
Bai matsa mashi ba Har cikin ran shi baiji dadi ba, daurewa yayi ya canza mashi wata tambayar.
"Ina so ka fadamin komai dangane da gidan kurkukun ƙaddara, da kuma abunda ake aikatawa a cikin sa"!
Wani kallo Danish Ya jefa mashi mai wuyar fassaruwa, A kalla sun shafe mintuna Danish bai amsa mashi tambayarba, kuma bai da niyar amsa mashi.
Jikinshi yayi mugun yin sanyi, bai ta6a zaton zaiyi mashi haka ba, duk irin yadda ya aje girman shi Ya kaskantar da kai agurinshi duk don ya samu ya basu hadin akai ashe shi ba ayi mashi gwanin ta.
Cikin karyayyar murya ya furta"Ka yi shiru ba ka amsa min ba ko baka ji me nace ba"? Kawar da kan shi gefe yayi alamar bazai amsa mashi ba
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Softy chief yace"kada kayi min haka, idan ka fadamin ba iya mu zamu amfana ba, ku ma zaku amfana, Danish baka da burin daukar fansa akansu? Meyasa zaka rufa masu asiri? Mutanan da suka raba ka da iyayenka tun kana jariri suka sace ka, bayan haka suka tauye maka hakkinka na rayuwa tun baka mallaki hankalin ka ba, idan ma kana yi masu kallon iyayen ka masu kaunar ka toh ka dauna, Yakamata ka farka Danish! Mutanan da kake gani amatsayin wani naka basu ta6a sonka ba, sun raine ka ne saboda biyan bukatar kan su, duk ranar da ka mutu zasu manta da kai ne, tsawon shekara ishirin suka kuntata rayuwarka sun cutar dakai sun kuma raba ka da iyayenka saboda tsabar zalunci, kai baka tunanin ina nasu ya'yan suke? Nasan ba lallai kayi wannan tunanin ba amma inaso ka sani wallahi suna da ya'ya suna acikin mu suna rayuwar yanci cikin kulawa da gatantawar su, kai kuma sun wulakanta ka da sauran yan uwanka" a faɗace ya faɗa yana duban shi.
"Rayuwata ba ta ta6a burge ka ba? Lokacin da ka shigo cikin mutane amatsayin wanda baison komai ba, shin baka yi tunanin sun yaudare ka ba? Ya tambaya rai abace yana kallon shi, Maimakon yaga rauni atare da shi saima yaga ko ajikin shi, maganganun chief basu karya mashi zuciya ba, su Taj dake kallonsu duk sun fahimci hada jahilci ke damun Danish, Elders sun kashe mashi rayuwa sun yaudareshi ta yadda bazai iya gane cutar da shi sukayi ba. Sun riga da sun yi mashi hudubar su, sun gatanta shi sun nuna mashi cewa su kadaine gatan shi a duniya.
"ba gaskiya kake faɗi ba, they've never hurt me. Suna sona kuma sune iyayena, bayan su bani da wasu iyaye a duniyar nan"
bai ƙare maganar ba chief owais daya gama harzuka rai a6ace ya ɗaki gaban table din ko gizau Danish bai yi ba.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Muryarshi a kausashe Ya furta"kai wani irin bauɗaɗɗan mutunne? Baka da tunanine? Ko bakasan ciwon kanka bane? Tayaya ina kokarin in fahimtar dakai kana kauce hanya? Meyasa kake yaudarar kanka? duk abunda mu ke yi munayi ne saboda mu daukar maku fansar cin zalunku da akayi mu kuma ceto rayuwar sauran yaran da ke a hannunsu sannan mu kawo karshen miyagun da suka kafa kurkukun ƙaddarar! Kai kadai zaka iya taimaka maka Danish! Don haka dole ka bamu hadin kai..." Ran shi yakai makura agurin 6aci baima san yayi mashi tsawa ba. idanunshi sun kaɗa jawur saboda bai ta6a neman abu agurin wani ya rasa ba Danish shi ne mutun na farko da yayi rejecting din bukatarsa.
Jami'an dake kallonsu sun harzuƙa Musamman big guy Yafi fusata ganin yadda Danish ke wahalar da chief duk basu ji dadi ba
Ga mamakinsu murmushin gefen fuska Danish yayi tare da furta"I'm respecting you, so please don't pressure me. If you want peace with me, stop asking about the prison of destiny and stop insulting the elders, bayan haka inaso ku sani bazan ta6a baku hadin kai ba indai akan su ne, saboda ku ba kowa bane agurina, ban hada alakar komai daku ba, duk da bani da ilmi amma nasan me na ke yi, Ina da hankali baku isa kuyi min wayau ba yan uwana kadai na sani su kadai zan bawa kariya kuma ina tare dasu babu wani wayau da za ku yi min"
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
maganar Danish ta yi matuƙar daure masu kai, Hankulansu yayi mugun tashi, gaba ɗaya chief ya rasa bakin magana saboda Danish Ya sagar mashi da gwiwa, yanayin fuskarshi ya nuna tsantsar mamaki da al'ajabi gaba daya ya fara sare da lamarin shi.
"Zan iya tafiya" ya fada yana kallon fuskar chief dake kallon shi kamar gunki haka Ya kame sam ya kasa magana, idan har ya biyewa zafin zuciyarshi ba karamin faɗa zasuyi da junan su ba, sai dai bazai ta6a biye ma shi ba saboda shi ba ajin yin shi ba ne, bayan haka yana yi mashi Uziri duba da irin rayuwar daya taso still akwai tsantsar tausayin Danish a cikin zuciyar shi.
bai jira Amsar da chief zai ba shi ba, Ya miƙe Ya nufi hanyar fita daga room ɗin, yana ruƙe handle din kofar yaji ta adatse.
juyowa yayi tare da kallon chief, bawan Allah Ya dafe kan shi da tafukan hannayen shi, tsabar bacin rai da takaici ne ya addabe shi, wata irin zufar 6acin raice ta fara tsastsafo mashi, la66ansa har kerma suke shima sam bai iya fushi ba, zuciya ce da shi.
"Ka buɗe min kofar zan fita" babu wasa akan fuskarshi yayi maganar
A fusace chief yace"I'm not done talking to you! Come back and sit down. If you don't answer my questions, we'll spend the whole day here."
kwatsam Yaji alamun buɗe kofar, aruɗe ya ɗago yana kallon shi yayi mamakin yadda ya iya bude kofar bayan computer ce ke controlling din ta, dole saida izninsu kofar zata buɗe.
har ya ɗaga kafa zai fita kenan chief ya yi hanzarin mikewa ya bi bayanshi yana isa gaba daya ya faɗa kan bayanshi yayi hugging dinshi tighly kamar zasu koma mutun ɗaya.
Cikin rauni na murya ya furta"Danish, I'm really disappointed in you.You embarrassed me, I never thought you'd do this to me you're hurting the heart that's trying to save your life. ban ta6a zaton za ka yi min haka ba"
ya faɗa yana jan numfashi haɗi da ƙara cusa jikin shi ana Danish, wlh tsabar bacin rai ne yasa shi yin hakan saboda gaba ɗaya ya fara sarewa da lamarin shi, kafin su baro gida adakin Danish sai da ya roƙe shi akan ya ba su hadin kai yace mashi ya amince amma sai gashi yanzu ya bijire ma su, Bai ta6a zaton zai kunyata shi ba.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Rungumar da chief yayi mashi ba karamin kashe mashi karfin jikin yayi ba, Zuciyar shi taso ta karaya sai dai baya jin zai iya amincewa da su, kalaman chief sun tsaya mashi aranshi sun kuma sanya mashi kokwanto a tunanin shi, ga wani irin yanayi da yake ji mara misaltuwa atare da shi yana ji kamar suna da connection da chief, sam ya kasa ta6u ka komai yanayin fitar numfashin shi sam babu kwanciyar hankali.
Lumsassun idanunshi ya ɗaura akan hannayen chief daya dafe flat tommy din sa, Har cikin ran shi baiji dadin bijire ma shin da yayi ba, baisan ya akai yake jin mutumin aran shi ba, Yana matuƙar ƙaunar Chief baya son bacin ran shi.
Komai dake faruwa akan idonsu big guy, sun yi shiru suna jira suka ga martanin da zai mayar wa chief.
A hankali Danish ya daura tafukan hannayen shi akan na chief ya damƙe su sosai yana mai jin wani irin yanayi mara misaltuwa, In a weak voice Ya furta"Ka yi hakuri, bazan iya ba ku hadin kai ba, pls kada ku tursasa min akan abun da banyi niya ba.." yana faɗan hakan ya 6an6are hannun chief daga ruƙon da yayi mashi ya fuce daga dakin, wani irin jiri ne ya kusa ɗibar shi da sauri ya dafe ƙofar da tafin hannun shi.
Da ƙarfi Big guy ya ture kofar Observation room Ya futo Yana huci Ya nufi Danish dake kokarin komawa gurin su Sajeed, da sauri sauran Jami'an dake a tare da shi suka biyo bayan shi ganin yadda ya fusata, sun san halin shi yana da bad temper.
Taj dake abiye da su hankali atashe Ya ke danna wayar sa layin Salsabeel ya kira cikin sa'a ya ɗaga ko sallama baiyi ma shi ba ya faɗa mashi abunda ke faruwa, salsabeel ya zabga salati dama sai da yai fargaban faruwar hakan, saboda shi yasan wanene Danish, mutum ne mai kafiyar tsiya ga girman kai da rashin yarda.
"Yanzu haka ina acikin head quarter din, wallahi nasan za'a rina shiyasa na yanke shawarar zuwa saboda shi" acewar salsabeel bayan sunyi sallama taj ya mayar da dubanshi ga big guy wanda tuni Ya cimma Danish wani irin kukan kura yayi tare da kai hannu Ya damƙi kwalar rigar shi, Jami'an dake a kewaye da su suka rurruƙe hannun big guy suna kokarin su raba tsakanin su.
Tashin hankalin da ba'a saka ma shi rana, Kusan atare su Unaisah suka miƙe idanunsu azazzare suke kallon su cike da faduwar gaba.
Da wata irin kakkausar murya ya furta"Who the hell are you? ɗan uban wanene kai a kasar nan? Me kake taƙama da shi ne huh? Kana da wani gata ne daya wuce Allah da shi chief din ne? Saboda tsabar rainin wayau yana magana kana amsa mashi da gira tsaran wasan ka ne shi"? Ya faɗa yana bin shi da wani ƙasƙantaccen kallo, big guy irin bauɗadɗun mutanan nan ne masu saurin fushi, wani lokaci sai daga baya su yi dana sani, shiru Danish ya yi batare daya tanka ma shi ba.
Big guy yaci gaba da fadin"Da kasan wanene chief da ba ka yi mashi haka ba, in ba dan aikin shi ba kai ka kai matsayin da zai kula ka ne? Ka rasa wa zaka yi disrespecting sai mutun mai kima da daraja a idon mutane, mutumin da ya ke hana idon shi bacci don ya taimaki rayuwar al'umma, mutun mai tausayin da jin ƙan na ƙasa da shi..." ya faɗa A harzuke Yana kallon cikin idanun Danish wanda yayi kasaƙe yana kallon shi, karfin halin mutumin ya bashi mamaki yadda ya damƙi kwalar rigarshi batare da jin shakkar yin hakan ba.
"Sir, ka yi hakuri ka daina yi mashi faɗa, me zai hana mu lallashe shi ni inaga idan muka bi shi ta lallama zai bamu hadin kai kodan abunda muka ji wurin yan uwanshi dole muyi mashi uzuri" CI ne yai maganar cikin kwantar da murya
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Agent zahra Yace"sir Please, ka kyale shi, He's still young, it's not your place to argue with him, He doesn't know anything, We need to persuade him gently." cikin tausasa murya ya faɗa yana kallon fuskar Big guy tamkar baisan suna magana ba Ya haɗe rai ba annuri ko kaɗan akan fuskar shi.
Dafa kafaɗar shi COO yai"Allah Ya huci zuciyar ka Yalla6ai, mu kan mu bamu ji dadin abun da yayi ba amma yakamata muyi mashi Uziri saboda baisan komai ba..."
bai kare maganar ba Unaisah ta fashe da matsanancin kuka, kamar jira su Batool su ke ta fara kuka suma suka fashe da kukan gaba daya sautin shesshekar kukan su Ya karade kunnuwan jami'an dake agurin, tsabar tashin hankaline Yasa suka fashe da kuka dama tun da suka fito daga dakin tambayar zuciyarsu araunace take saboda raunin da aka fama masu
ga kuma wani tashin hankalin da suke kallo duk da basu san meya faru ba amma sun fahimci Danish ne yayi wani abu badai dai ba.
"OMAR, pls ya isa haka! Ka sake shi, nayi magana da Salsabeel awaya ya faɗa min yana acikin head quarter din yanzu zai shigo"
idanun shi jawur Ya dubi Taj a fusace Yace"Taj I won't let him go. He must return and answer the chief's questions, ya 6ata min rai ya rasa wazai disga sai chief din mu? Tsaran wasan shi ne? duk kokarin da ya ke yi akan su shi baya gani ne? Ni bana son mutun mara ɗa'a irin shi ..."
Ya fada tare da cije le6en shi ya maida dubanshi ga Danish wanda tuni Jikin shi Ya fara kakarwa wata irin zufar 6acin rai ce ta fara tsatstsafo mashi, Numfashin shi ya fara hauhawa yana fita cikin sauri, lokaci daya temperature din jikin shi ya ɗau wani irin zafi, idanun shi suka rune zuwa Ja.
"Yaya Omar dan Allah Ka sake shi, nayi maka alkawarin zan shawo kan shi" cikin shesshekar kuka Unaisah tayi maganar
Haris yace"dan Allah Ya Omar ka ƙyale Danish, Idan laifi yayi maku ku yi hakuri zamu fahimtar da shi" magiya suka dinga yi mashi akan ya yi hakuri Ya saki Danish
Adaidai Lokacin da Salsabeel Ya faɗo arean da suke yana faman wurga idanu don ya gano inda suke kwatsam idanun shi suka sauka akan gungun jami'an da su ka kewaye su.
Gaban shi ne yayi wani irin faduwa aguje ya nufe shi har yana bangaje jami'an dake sintiri kamar mahaukaci haka suke kallon shi
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Yana ƙarasawa ya sanya karfi ya raba tsakanin big guy da Danish Yana faman haki ya dubi Danish wani irin faduwar gaba yaji ganin sa6ar majici akan wuyan shi babu wanda Ya lura da sabar sai shi da Allah ƙaddara zai ganta, wahalallan Yawu ya haɗiya la66anshi na rawa ya furta"Danish, please...don't. Please, Danish, try to control your anger.."
gaba ɗaya jami'an sun ruɗe da ganin yadda Salsabeel ke lallashin shi, Musamman Big guy ranshi ya ƙara 6aci a faɗa ce yace"meya sa ka ke bashi hakuri"?
Salsabeel bai tanka mashi ba saboda tashin hankalin da yake tunkaro su batare da su sun sani ba, In har evil heart dinshi ta motsa zai rikiɗa ne ya canza halitta, ya tarwatsa head quarter din gaba ɗayanta ba ƙamar 6arna zai yi ma su ba.
Da hannu ya dafe saitin zuciyar Danish, Ya marairaice mashi fuska tare da girgiza mashi kai alamar A'a...
gaba daya jami'an sun kasa fahimtar me Salsabeel Ya ke nufi!
Wani irin dogon numfashi Danish Yaja cikin zafin nama Ya bangaje hannun Salsabeel daga kan kirjin shi yana faman fitar da huci mai zafi ya miƙi hanya, aguje su Unaisah suka bi bayan shi suna kwala mashi kira ko kallo ba su ishe shi ba, bai sha wahalar gano kofar da suka shigo Soc din ba Ya fu ce daga ciki Ya nufi main enterance gate na head quarter din.
Kafin karasawar shi big guy ya kira layin ɗaya daga cikin jami'an dake tsaron gate din Ya basu Umarni karsu kuskura su bar shi Ya fita.
Lokacin daya karaso Yana tafiya kamar baya acikin hayyacin shi, hankulan jami'an dake sintiri gaba daya ya dawo kan shi, fisatattun jami'an dake tsaron gate din suna ganin shi suka gane shi ne matashin da aka basu umarni karsu bari ya fita, aikuwa azafafe suka yi mashi ƙawanya kamar zasu rufe shi da bugu.
Yan uwanshi sai kuka suke suna ambaton sunan shi hadi da yi mashi magiya akan ka da ya tafi ya bar su, babban abunda suke ma fargaba in ya fita ina zai dosa?
Dakyar chief ya iya lallashin zuciyarshi cike da rashin ƙwarin jiki ya fito daga ɗakin Ya nufi su big guy dake atsaitsaye curko curko sun kasa kunne suna sauraron Bayanin da Salsabeel ya ke yi masu dangane da Danish
"Ga chief nan" taj ne Ya fada kusan atare suka kai duban su gare shi, damuwa ce karara akan fuskar shi.
Bawan Allah da buɗar bakinsa sai cewa"Ina Danish? Ina sauran yaran"? Kafin wani daga cikin su Ya bashi amsa sautin ringing wayar big guy ya katse hanzarin su
Da sauri Ya kara wayar a kunnan shi.
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
"Sir, Yaron nan fa Ya fita! Mun yi kokarin mu dakatar da shi amma mun kasa, gaba ɗaya ya watsar da jami'an da sukai kokarin hana shi fita..." a kidime Big guy ya furta"what? Ya fita! Garin yaya hakan ta fadu"?
Wani irin faduwar gabane Ya ɗarsu a zuciyoyin su, sunyi matukar mamakin jin hakan shin tayaya akaima har ya iya fin karfin jami'ansu Ya fuce daga head quarter din?
"Yaran suna nan, amma ɗaya daga cikin ƴan matan mai launin ido ruwan toka ta kubce mana, yanzu haka wasu daga cikin jami'an mu sun bi bayan su"
Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, Salsabeel bai tsaya yaji karashen zancen ba, Ya watsa aguje Ya fuce, Agaggauce Senior agents din suka rufa mashi baya, ya rage saura big guy da chief atsaye suna fuskantar juna
"Meya faru Omar? Meyasa Ya tafi? Wani ya 6ata masa rai ne ko abunda ya faru tsakanin mu ne"?
Dakyar big guy yai karfin halin zayyana mashi abunda ya faru bayan fitowar Danish
Girgiza kai yayi cikin sanyin murya yace"meyasa Omar? Meyasa zaka yi mashi haka? Kamanta wanene shi? Yaron da bai san komai ba yanzu daka bata mi shi rai ina kake tunanin zai dosa? Wa ya sani agarin nan"?
Saurari Littafin >>>>Kurkukun Ƙaddara Takun farko Kada a manta ayi mana subscribe like da kuma comment sannan a yi share. Domin samun sabbin littafi idan Mun ɗora.
Yanayin yadda chief ke yi mashi magana araunace ba karamin karya mashi zuciya yayi ba.
"Duk abun da nayi nayi ne saboda kai, kasan irin kaunar da nake maka, zan iya jure komai amma wlh muddin wani yayi kokarin bata maka rai bazan kyale shi ba, koma wanene.."
"Nasani Umar, amma ni baka kyauta min ba, yakamata kayi amfani da hankalin ka, rayuwar shi abun tausayi ce, tabbas raina ya 6aci da abun da yayi min amma wlh ko kusa ban ji haushin shi ba, saima son shi da ya ƙara ninkuwa acikin zuciyata, yakamata mu yi mashi Uziri bai kamata mu ga laifin shi ba yaron da har yanzu suna iya control dinshi..." bai ƙare maganar ba ya juya cikin takun sauri Ya nufi hanyar fita daga Soc din da sauri big guy yabi bayan shi
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
YOU MAY LIKE THESE POSTS
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(23)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(302)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(3)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: _________________________________✍️
Sautin ringing ɗin wayarta ne ya farkar da ita daga dogon baccin daya ɗauke ta, tana a kudundune cikin lallausan duvet dinta.
da wata irin malalaciyar kasala ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta da su kai mata nauyi saboda baccin da tasha ga wani irin tsami da jikin ta yayi mata, lalube ta fara yi tana shasshafa bedmattress din don taji idan yana nan har ta ƙare lalubawa bata ji mutum akan gadon ba, hakan na nufin ya jima da tafiya.
Tunawa da yanayin da take a ciki yasa tay saurin ware idanunta cike da fargaba ta dubi jikin ta zir take ba sutura, lumshe idanunta tayi cike da jin shaukin shi take ɗan jan numfashi, yayin da ƙwaƙwalwarta ke tariyo mata abun da ya faru tsakanin ta da shi a lokacin da suke tsaka da jin daɗin su.
A hankali ta miƙe zaune ta ja duvet din ta lullu6a kirjin ta da shi, kafin ta jingina bayan ta jikin headboard, sumar kanta ta yamutse saboda damƙar da tasha a hannun big boss, ko ina na jikin ta zafi ya ke mata.
idanunta sun kumbura sun kaɗa jajawur, haka la66anta ma sun kumbura don ba karamin tsotsa suka sha ba, ta galabaita sosai har wani jirin kasala take ji a jikin ta.
Kifa kanta tayi kan gwiwowinta tunawa da nasihar da mahaifinta ke yawan yi mata.
"Ke kadai Allah Ya bani mamana, tun kina ƙaramarki bani da burin daya wuce in inganta rayuwarki ki zama hafizar alkur'ani mai ilimin addini da zamani saboda inyi alfahari dake sannan ki zama abun kwatantace, Alhamdulillah cikin ikon Allah sai gashi kin cika min burina ko'ina zancenki ake duk in na shiga cikin jama'a sun dinga yabonki suna fadin ƴata malama ce hafiza mai cikar kamala da kamun kai ga kyautatama al'umma da son taimako, kowa yabon ki yakeyi, burin kowace mace tayi koyi da Aishatu bintu imam malik mace ɗaya tamkar da dubu, Ummi nasihar da zan maki ko bayan ba raina kiji tsoron Allah, kada ki canza daga yadda nasanki, abun da zaki min wanda zaki biyani shi ne Ki karemun martabana da kimata a idon duniya, kada kiyi abun da zai zubda min mutuncina Aishana"
Rushewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, a duk lokacin da ta tuna nasihar mahaifinta zuciyarta ba ƙaramar karaya ta ke yi ba, tana jin tsanar rayuwar data ɗaukarwa kanta, tana mai danasanin abun da yayi silar rabuwarta da mahaifinta, saboda bata da abu mafi soyuwa da ya wuce shi a duniyar nan, kai duk wani gata da ya zata samu agurin ubanta ta samu ninkin baninkin sa.
tana jin raɗaɗin karya alƙawarin mahaifinta da ta yi na kare mashi martabarsa.
kifa kanta tayi jikin pillow, ita kadai baiwar Allah babu mai lallashin ta.
Ba halin ta bane, ba laifin ta ba ne, tana da ilmi tasan zina ba kyau ta kuma san hukuncin wanda ke aikatata amma meyasa takasa dainawa ko da tayi nufin ta tuba ta koma ga Allah? Tasha yunƙurin yin hakan amma aduk lokacin da big boss ya buƙace ta bata iya bijire ma shi.
Ta yi kuka tamkar ranta zai fita kamar ƴar dambe ta dunƙule hannayenta ta dinga bugun mattress kamar zatai hauka ta tsani abunda take aikatawa bata so ta mutu batare da yafiyar mahaifinta ba, kuma batason ta mutu tana aikata sabon Allah tana matukar jin tsoron makomarta.
Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita hayyacin ta, fuskarta sharkaf da hawaye ta janyo wayar daga kan drawer ta duba sunan me kiranta.
Maji daɗina shine sunan daya bayyana akan screen din, kasa picking call din tayi saboda fushin da zuciyarta ke yi.
Text message ne ya shigo on the top of the screen din wayar, cikin zuciya ta soma karanta abunda ya rubuta mata
_"ummi, na tafi ba tare da nayi maki sallama ba, ki yi hakuri da hakan nasan zaki tashi da kewana, anyi min kiran gaggawane, ba dan nagaji da jin ɗumin jikin ki ba, bazan iya misalta daɗin da kika jiyar dani ba, kin bani cikakkiyar gamsuwa da zan iya ɗaukar kwanaki ban nemi matana ba, bazan iya biyanki ba Ummi, ki fadamin me zanyi maki don in faranta maki"_
Runtse idanunta tayi gam, siraran hawaye suka dinga shararowa kan kuncin ta..
"Ya Allah Ka cire min jarabar son bawan nan naka, Ina neman tsari da shi...."
bata kare maganar ba kwatsam taji dirar motoci acikin gidan, a firgice ta jefar da wayar ta faɗa kan mattress ta duro daga kan gadon, tafin hannunta a tallabe da bargon ta faɗa toilet taja ƙofa ta datse, tana faman zare idanunta, sam ta manta da su Batool tasan bai wuci sune suka dawo gidan ba, abunda take jima fargaba kada wani ya shigo ɗakinta tasan in har suka ga gadonta sai sun zargi wani abu saboda ya 6aci ba kaɗan ba.
Cikin Takun sauri Chief Ya faɗo Falon Ya nufi upstairs, agurguje taj da big guy suka biyo bayan shi, kwata kwata babu kwanciyar hankali akan fuskokin su damuwace ƙarara saboda jami'an da suka tura su nemo Danish kusan awanni har yanzu ba wani labari, har tracking layin sa sukai a karshe suka gano location din da wayar take agida yabar ta baije da ita head quarter din ba, wannan dalilin ne yasa suka yanke shawarar su dawo gidan, watakil su gan shi.
bai nufi ko'ina ba sai bedroom din Danish Yana isa bakin kofar yayi knocking ɗin ta cike da fargaban kada su ki ganin shi.
Jin shiru ba'a buɗe kofar bane yasa shi tureta da hannun shi ya faɗa ciki Yana haki saboda gudun daya sha, bazai iya tuna when last yayi irin shi ba.
da matsanancin faduwar gaba yake bin dakin da kallo wayam babu kowa adakin dafe kan shi yayi da hannu ɗaya idanunshi sun kaɗa jawur babban tashin hankalin shi Ina Danish yaje? ya zai yi da yan uwan shi? Me zai fada ma Uncle hateem idan ya kira yana son yin magana da shi"?
"baya aciki ko"? muryar boss ce ta katse mashi zancen zucin shi
Big guy duk ya rasa kuzarin shi Ya daura ma kanshi alhakin 6atan Danish saboda shi ne silar daya ja har ya yi zuciya Ya tafi, sai yanzu ya ke danasanin bata mashi rai da yayi ganin yadda ya ɗaga hankalin chief Owais.
"Taj bansan ya zanyi ba, baya nan, ya tafi, ya zanyi da raina, bana so na rasa yaron nan wallahi danasan abun da zai faru zuwan mu headquarter da ban tursasa mashi akan yabi mu ba..."
dakyar yake magana saboda damuwar data cika zuciyar shi.
jikinsu yayi mugun yin sanyi.
Cikin raunin jiki ya dubi big guy"Omar, kaga abunda kaja min ko? Idan har yaron nan bai dawo gida nan ba, bazan yafe maka ba..." gaba ɗaya ya rikice masu.
"Sir kayi hakuri, na kar6i laifina, kuma nayi danasanin 6ata mashi rai da nayi, bada son raina ba ya 6ata min rai ne amma nayi maka alkawarin zanje in nemo shi duk in da ya shiga agarin nan..."
yana faɗan hakan ya juya azafafe ya haura kan stairs ranshi ya 6aci da furucin Chief, kalmar daya furta mashi ɗazu daya ce Son danish na kara ninkuwa azuciyar shi yaji haushinta bayan irin cin mutuncin da yaron yayi mashi amma ko kadan ransa bai 6aci ba, shi arayuwarshi bayason wanda zai shiga tsakaninsa da chief, yana matuƙar jin kishin yaga chief yana nunama wani so fiye da shi hakan na kona masa rai yafi so koda yaushe ya zamana na hannun daman shi.
Dafa kafadar chief yai da hannun shi"dan Allah ka kwantar da hankalin ka, bana so kana sanya damuwa aranka, in sha Allah Danish zai dawo ..." lallashin shi ya cigaba da yi, bawan Allah gaba ɗaya ya rasa ƙwarin gwiwar shi.
"Nima Zan bi Omar, Zamuje mu binciko shi"
Numsafawa yai kafin ya dubi Taj da rinannun idanun shi
"Ina sauran Yaran? Sun shigo?"
bai ƙare maganar ba, suka jiyo sautin tafiyar su da sauri taj ya dubi kofar shigowa falon, ɗaya bayan ɗaya suke shigowa kamar yan gudun hijra saboda jigatar da su ka yi, fuskokin su sharkaf da hawaye sun sha kuka bayin Allah har sun gaji sun gode ma Allah, Unaisah tafi su jin jiki har wani jiri take gani acikin idanunta, sun ruke hannun Juna ita da Batool suma sauran sun rurruka hannayen junan su.
"Sun shigo,"
"Pls, Calm them down, I don't want them to worry about losing their brother, ka cigaba da lallashin su, Sannan ashirya masu lunch dinsu"
"Sir kaima kana bukatar hutu, ka koma daki ka kwanta ka huta zanyi magana akawo maka lunch din ka" girgiza kai yai"wallahi bazan iya cin komai ba in har Danish bai dawo gidan nan ba"
Taj yayi mamakin kalaman shi, bai ta6a zaton son da chief yake ma Danish yakai har haka ba, aranshi ya ayyana watakil ko dan saboda sabon da sukai da junan su cikin kwanakin nan.
"Da ka daure.."bai kare maganar ba ya katse shi"Boss ka tafi kawai, Ka kula da sauran yaran, Ka kira auntynsu ka fada mata halin da suke a ciki"
Cike da jin tausayin shi ya amsa mashi da toh.
Lokacin da ya sauko down, A kan sofas Ya hango su zazzaune sun yi shiru kamar masu zaman makoki, tsayar da idanun shi yayi akan Unaisah da ta kwantar da kanta saman kafadar Batool, tayi matukar bashi tausayi, bakomai yake tunawa ba face lokacin data bi bayan Danish ta haura kan titi mota takusa hankadeta ba dan Allah yasa Jami'an su sun yi gaggawar Kai mata agaji ba da tuni rai yai halinsa saboda ta furgice idanunta sun makance bata ji bata gani danish kawai take nema ido rufe, har wani zazza6i take ji ajikin ta mai azabar zafi, ga ciwon kai daya fara takura mata, ta rasa meke mata dadi duniyar nan, ita damuwarta ina Danish ya shiga? Baisan kowa ba agarin abuja, abun da take jima fargaba kada yace zai koma Gidan kurkukun kaddara duk in zuciyarta ta raya mata hakan sai taji matsanancin faduwar gaba ga tashin hankali da firgici.
kwata kwata babu wanda Ya lura da Taj a cikin su saboda damuwar data rufe idanun su.
Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka kalle shi in ka cire Unaisah wadda ta rufe idanunta hawaye sai suntiri suke yi kan kuncin ta.
Jiki asanyaye ya zauna yana dubansu
"Unaisah! " dakyar ta buɗe idanunta da suka rune zuwa ja ta kalle shi
"Meyasa baki jin maganata? Bana hanaki yin kukan nan ba? Ko shi zaisa ya dawo ne"? Yawu mai ɗaci ta hadiya tamkar bata son yin maganar tace"daddy, bana jin dadin jikina ne"
"Ba dole jikinki yaki dadi ba, duk kinbi kin daga hankalinki uhyum! Sai kace ba kisan tawakkali ba Unaisah! Ce maki akai Ya bace ba zaki kara ganin shi ba ne? ya fada yana kallon fuskarta, shiru tayi tana sauraron shi tasan ba lallai ya fahimce ta ba tun da shi a zaton shi sabo ne kadai atsakanin su.
Sassauta muryar shi yayi cikin sigar lallashi yace"kuyi hakuri nima na damu da rashin shi, amma bai kamata ku zauna kuyita kuka ba, ba zai yi maku maganin komai ba saima ya kara jaza maku wani ciwon, ku tayashi da addu'a in sha Allah zai dawo ko dan saboda ku..." sun yi shiru suna sauraron shi.
"Allah Ya kare mana shi aduk inda yake, Allah Ya karkato mana da tunanin shi ya dawo gida .." cikin sanyin murya suka amsa mashi da Ameen
Miƙewa Parveen Tayi boss yace"ina zuwa"?
hannunta dafe da cikinta tace"fitsari ne Ya matse ni" ta fada tare da kama hanyar ta nufi dakin su,
"Nima fitsarin nake ji, tun ɗazu ya matse ni" murya na rawa jamimah tayi maganar tare da mikewa daga kan sofa ta watsa da gudu ta nufi dakin su.
"Time din sallah azhar har ya wuce, Ku tashi ku tafi ɗaki, ku yi wanka ku yi sallah kafin ku fito zanyi magana a shirya maku lunch din ku nasan kuna jin yunwa" cikin kulawa ya faɗa yana duban su.
Bata jin zata iya cin abinci in har Danish bai dawo ba, cike da rashin kuzari ta miƙe idanun ta akan daddynta dake kallon ta bakomai ne ke daure mashi kai da ita ba face haukan da tayi ɗazu ya rasa gane meke a tsakaninta da Danish!.
Ta ɗan tsargu da kallon da yake yi mata, in a weak voice tace"Zan shiga daki, bansan ko zan dawo na iske ka ba, ka gaida min aunty Danejo" bata tsaya taji amsar shi ba, ta juya ta nufi dakin su tana tafiya a harharɗe kamar zata kife ƙasa har sai da ta shige dakin tukunna ya ɗauke ido daga kallon ta.
Knocking door room dinta da akayi ne yasa tayi sauri fitowa waist ɗinta daure da towel, hannun ta ruƙe da wani short towel da take tsane sumar kanta da shi.
Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Batool daga waje tana fadin
"Aunty Ummi ni ce, Mun dawo, ki buɗe min ƙofa..." wani irin sanyi ne taji ya ratsa zuciyarta, taji dadin jin muryar Batool saboda a halin da take a ciki tana bukatar wanda zai kwantar mata da hankalin ta.
"Batool, ki jira ni, Ina shiryawa ne"
"Toh"
Cikin kankanin lokaci ta kammawa shiryaw cikin abaya baƙa mai kyan gaske, ta yi rolling headscarf, ta nufi door room din tana buɗewa Batool tayi sauri faɗawa kan kirjinta, tayi mata wata irin runguma kamar zata koma cikin ta wani irin faduwar gaba taji saboda kunnnata sun jiyo mata shesshekar kukan batool, dama tun da ta rungume ta taji aranta ba lafiya ba.
Aruɗe ta furta"My Babe, meya faru? Baki da lafiya ne"? Ta faɗa tare da tallabo fuskar Batool da hannunta, hankalinta ya ƙara tashi da ganin yadda fuskarta ta yi jawur ta jike da ruwan hawaye
Jijjiga kafaɗarta tayi"meke damunki ne? Wani abu ya faru ne? Fadamin mana waya ta6a min ke"? Ta fada akagare da son jin amsarta.
La66anta na rawa ta labarta mata abunda ya faru a head quarter dangane da batan Danish.
Hankalinta Ya tashi matuƙa muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa inna ilaihirraji"un Amma banji dadin abun da big guy yayi mashi ba, bai kyauta ba Allah, da hankalinshi da komai sai kace baisan wanene Danish din ba..." rai a6ace tay maganar.
"Yanzu Ina su Unaisah din"?
"Duk suna adakin su, gaba ɗaya basa jin dadin jikin su saboda abunda ya faru, munyi kuka har mun gaji"
tsantsar tausayinsu ne Ya kamata ga damuwar bacewar Danish tana jin shi kamar kaninta saboda kaunar da takeyi ma su
Da tafukan hannayenta ta share ma batool hawayen dake sintiri kan fuskarta.
"Ki daina zubda hawayenki, bana so pls, ni nasan zai dawo ne in sha Allah, mu tayashi da addu"a" ta fadi hakanne saboda tasan bazai iya jure rashin Unaisah ba, tun shekaran jiya data ga abunda ke tsakaninsu tasan ba karamin abu ne zai iya raba su ba.
"Aunty Ummi ko sallah banyi ba.."
"Okay, ki shiga ciki ki yi, bari naje gurin yan uwan naki, nasan zasu neme ni" a hanzarce ta fuce daga dakin, sam ta manta bata gyara gadon ba, saukin ma ta bar bargon a toilet.
_________________________________✍️
*ANEELERH💓*
a Zaune take kan gadonta jikinta sanye da riga bubu, ta yi shiru tana kallon baby junaid dake zaune gefen ta hannun shi ruƙe da plate din wainar fulawa wanda zahra ta soya mashi ita, sai tsantsani yake saboda dadin da tayi mashi dama ya iya kwaɗayi, kadan yake balla ya ɗan dangwala yaji saiya tura a cikin karamin bakin shi
Shekaran jiya izuwa yau ya ƙara samun lafiya walwalar shi ta dawo tun da yaga Angel dinsa ta cika shi da farin ciki, ko bacci yake yana ambaton sunanta, tun da suka dawo gida ya addabeta akan ta kira Angel awaya tace mata tazo yana son ganin ta, dakyar take samu ta shawo kan shi, sai dai har yanzu bakowa yake yarda ya ɗauke shi ba, daga momynsa sai zahra da mami amma su abie kam ƙiwuya yake yi masu abun yana daure mata kai, har mahboob bai cika yarda ya dauke shi ba.
Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar shi ta katse ta
"Mommy, wannan sauran wainar dana rage na Angel ne, wa zai kai mata? ko ni zakisa mahboob yakaini a mota in kai mata..."ya faɗa yana nuna mata rabin wainar da ya rage a plate din
Murmushi tasakar mashi"na fada maka ba Angel bace, bana so wani yaji kana kiran sunan Angel, ita yarinyar da ka gani sunan ta Azeezaty suna kama ne da Angel din mu"
yamutsa fuska yai tare da maƙe mata kafada"wallahi wayo zaki min, Angel dina ne ita ay har tambayarta nayi tace mun eh itane ko" ya faɗa da shagwa6a yana hade fuska.
Ƙura ma juna ido sukayi batasan ya zatay da shi ba tana son ta tambaye shi meya faru amma tana jin fargaban kada akoma yar gidan jiya, zai iya birkice mata tun da ta fahimci baison maganar kwata kwata.
"Mommy kina kallona ko zaki ci wainar ne in ɗan maki" ya fada yana kokarin 6allo mata da sauri ta furta"a koshe nake my baby boy, na fiso ka ci ka koshi..." farfari yayi mata da idanun shi
"Yaushe zaka koma school"?
Maƙe mata kafaɗa yai"shaina ƙara samun lafiya" yar dariya tayi "junaid na ganoka gudun school kake, Allah next week zan maida ka, ay naga kaji sauki jikin ka ya murmure" yamutsa mata fuska yai tare da zumbura mata baki
"Allah in kinasho in koma ki sani makarantar su Azeezaty, sai mu runka yin wasa da ita"
ya faɗa tare da 6allo wainar da ya rage ma Angel ya tura abaki yana ci, murmushi tayi tare yin kasa da muryar ta"babyna" ya amsa mata naam
Takai hannu ta shafa sumar kan shi.
"Zaka iya tuna abun da ya faru ranar da muka je gidan Hajiya adama"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda ya ware idanun shi da karfi, Jikin shi ya fara kerma kamar mazari.
da sauri ta janya plate din wainar ta daura kan table, ta saukowa daga kan gadon ta zukunna agaban kafafuwan shi kamar mai neman gafara.
"Dan Allah junaid ka fada min, kaga ni mommynka ne, duk duniya baka da tamkar ni, idan ma kana jin tsoron ka fadi ne wasu suji nayi maka alkawarin bazan bari kowa yaji ba daga ni sai kai...."
tatta6e fuskarshi yayi ruwan hawaye suka taru acikin idanun shi labbanshi suka kama kerma taji faduwar gaba da ganin yanayin shi sai dai bata jin zata iya hakura a wannan karan, saboda tayi matukar ƙagara da son jin meya faru da su aranar!.
Ruko hannun shi tayi cikin sigar lallashi da wayau da dabara ta karya murya tare da marairaice mashi fuska duk don ya tausaya mata ya fada mata, magiya ta dinga yi mashi yayi shiru yana kallonta da tsantsar tashin hankali akan fuskarshi.
can dai ta ɗan bugu cikin shi da wayau tace"Ni dama na sani Ana guduwa tayi junaid, sai da nace mata kada ta tafi tabarmu amma shine ta tafi, ni bansan laifin da nayi mata...."
bata ƙare maganar ba, sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata daga bakin junaid
Cikin shesshekar kuka yace"mommy bafa guduwa tayi ba, Allah dodone Ya kashe ta a cikin gidan nan, ni na ganshi da idona kuma itane tace in gudu in 6oye"
kamar an dasa mata aya ta tsaya cak tana kokarin tariyo maganar shi acikin zuciyarta lokaci ɗaya ta saki dariya tana fadin"haba junaid, abun naka hada zolaya, karya fa babu kyau, In ba zaka fadamin gaskiya ba ay basai ka shirga min karya ba..."
girgiza mata kai yai babu alamun wasa akan fuskarshi ya furta"wallahi mommy dagaske nake faɗe maki, dodone Ya cinye ana adakinta, tana ta kuka hada jini a jikin ta..."
yadda kasan kanzon kurege haka take sauraron shi sai tikar dariya takeyi irin ya raina mata wayon nan shi kuwa ya haƙiƙance yana faɗa mata iya gaskiyar shi sai ma ta maida maganar tashi abun nishadi.
"Mommy ki daina dariya, ba abun dariya bane wlh dagaske nake maki" wani kallon rainin wayau ta wurga mashi kafin tace"junaid bana hanaka yin rantsuwa akan karya ba..."
kuka ne Ya ci karfin shi wannan karan ta ɗan ji faduwar gaba duk da bata yarda da maganar ba ta dauki abun shiririta arude ta ke lallashin shi cikin shesshekar kuka yace"mom.. my ba karya bane, ki daina min dariya, ni banaso dodon daya kashe ana ya kashe mu mommy, dan Allah mu gudu mubar gidan nan ni wlh tsoro nake ji..."
bata san sa'adda ta rungume shi a kirjinta ba, hankalinta yayi mugun tashi saboda kukan da junaid yake yi mata tasan halin kayanta ba karamin abune zaisa junaid yin kuka ba irin haka, tabbas wani mummunan abu ya faru da ya yi silar zaucewarshi sai dai zuciyarta taki yarda da maganar shi, gani take bame yiyuwa bane.
_______________________________✍️
A ƙalla ta fi karfin mintuna a tsaye tana kallon Unaisah dake a kwance kan darduma ta nannaɗe kafafunta cikin hijab, idanunta suna a rufe gam sai yan siraran hawayen da ke sintiri kan fuskarta tayi kukan tayi addu'ar amma har yanzu zuciyarta taki sarara mata daga radadin da take mata, gani take kamar ta rasa Danish.
aranta tana ji in har kurkukun ya koma tabbas zata bishi ne ko da hakan zaiyi silar rasa ranta don ji take bazata iya rayuwa batare da shi ba.
"Unaisah!" ummi ce ta kira sunan ta, tayi shiru tamkar bata ji ta ba
"Nasan kina ji na, ni bansan ya zanyi dake ba, duk irin kokarin da nayi gurin kwantar maki da hankali kinki daina kukan nan, ga abincin ki dana sa akawo maki shima kinki ci, to wai kukan da kike shi zaisa ya dawo ne? Tun da kinyi addu'ar sai kibar ma Allah komai In sha Allah zai dawo...." cikin sigar lallashi ta faɗa tare da zukunnawa gaban prayer mat din
"Dan Allah ki tashi ki ci abincin ki..." da wata irin karyayyar murya ta furta"aunty Ummi, ba zaki gane ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, zuciyata bata min dadi ji nake kamar zan rasa raina ne, yaya Omar ya 6ata min rai, shine silar komai, wallahi Aunty ummi naji zafin kalaman daya gaya ma Danish, duk da baida ilmi ko jahili akayi ma gori sai yaji ba dadi"
jikin Ummi ba karamin sanyi yayi ba, ga wani irin tsantsar tausayin Unaisah daya kamata, tasan bai wuci hada soyayyarshi ke azabtar da ita ba.
"Kiyi hakuri Unaisah, In sha Allah Danish zai dawo, Allah shi zai tsare sa aduk inda yake, mu taya shi da addu'a ni inaji araina ko dan saboda kaunar da yake yi maki zai dawo"
dakyar ta buɗe idanunta wadanda suka kada jajawur ta dubi ummi duk da halin da take a ciki tayi mamakin kalmar kaunar data furta.
fahimtar hakan yasa ummi tay saurin furta"naga kamar yafi kaunarki a cikin yan uwanki, kema haka shiyasa nace haka, kada ki ɗauka ko ina sanya maku ido ne"
shiru tayi bata tanka mata ba.
"ni abun da nake tunani watakil ya ke6e kanshine awani guri don ya gusar da bacin ranshi in ba haka ba Danish ay ba za ace ya 6ace ba, mutumin da ba shi kadai bane tsaf zai iya kawo kan shi gidan nan..."
bata kare maganar ba ta dakata tana kallon Unaisah ganin yadda ta zabura ta miƙe tsaya kamar zata fadi saboda rashin kwarin jikin ta
"Ina zuwa"?
"Yanzu zan dawo aunty ummi, wani abu zan duba" tana fadan hakan tasa kai ta fuce daga dakin cike da sa ran hasashen ta zai zama gaskiya, maganar da ummi tayi ta tuna mata da wani abu daya ta6a faruwa.
________________💋Chief Owais💪
Kwance yake akan gadon shi, yar singlet da short ne ajikin shi, damuwa ta hana shi ta6uka komai, ya dade bai shiga tashin hankalin daya shiga a yau ba, wayarsa dake akan bedside drawers sai ringing ta ke yi daga kiran ya katse wani ke shigowa sautin ya cika kunnuwan shi, amma baya jin zai iya picking din su yasan bai wuci Na hannun damansa bane suke kira don suji ko an ga Danish.
Shaf ya manta da bakin da za su yi, saida tunanin Ya faɗo mashi aran shi kafin ya mike ya janyo wayar shi tare da duba screen din My dad shine sunan daya gani saida ya fara daidaita nutsuwarsa kafin yai picking call din
"My Son, Ya kake Ya aiki, ka manta da daddyn ka ko"?
Duk da halin da yake aciki sai da yaji nutsuwa ta shige shi jin muryar daddynsa
lumshe idanun shi yayi cikin sanyin murya ya furta"lafiyalou daddyna, ni na isa in manta da bugun zuciyata? Mutumin da nake kwana in wuni da tunanin shi araina saboda kaunar da nake masa"
Sautin dariyar mai girma sharafuddeen ce ta ratsa kunnan shi cike da nishadi yace"My Son kasan duk wata hanya da zaka kare kanka agurina, ka faranta raina, but meke damunka ne? Naji muryarka kamar baka jin dadi..."
Shiru yayi jim dama yasan zai yi wuya in daddyn nasa bai gane wani abu ba, dayawan lokutta ta muryar shi kadai yake gane halin da yake a ciki.
"Babu komai, yanzu na tashi daga bacci ne, shiyasa kaji voice dina wani iri"
"Hmm owais kenan, har ni zaka boye ma damuwarka"?
"Daddy, ka yi hakuri zan iya kiranka anjima mu yi magana"?
"Okay, in ba baka kira ba, Ni zan kiraka, ko inzo gidan naka da kaina kasan bana wasa da lafiyarka" yar dariya chief yayi saboda yaji dadin maganar shi ba wani jimawa sukayi ba sukai sallama
layin Omar ya danna ma kira kusan sau uku tana ringin bai ɗaga ba sai a kira na hudu yayi picking.
Kara wayar yayi a kunnan shi"Omar, kana Ina"?
On the other hand big guy yace"na tafi neman bugun zuciyarka saboda bana so in rasa ka" shiru yayi jimm yana maimaita maganar big guy harya fahimci ranshi ya 6aci saboda yayi mashi karya, location dinshi ya nuna yana agidan kamar ko ya sani yana akwance kan gadon bai jima da tashi daga bacci ba.
"Omar zamuyi magana, nasan meke damunka, pls don't forget to get the soldiers ready and go to the airport, jirgin su commender yakusa yin landing nan da minti talatin "
"Consider it done, sir, amma ya yakamata kaima ka shirya mu tafi airport din atare, zasu fi jin dadin tarbar da zamuyi ma su"
"Just do what I say" ya umarta, bai bari big guy ya kara magana ba yayi rejecting call din don baya jin zai iya fita daga gidan a halin da yake a ciki.
*Unaisah Angel*
Bayan fitowarta daga dakinsu bata nufi ko'ina ba sai upstairs tana tafiya jiki duk ba kwari ta tura kofar ɗakin ta shiga daga ciki bata ga kowa ba.
Gadon shi tabi da kallo sai ta dinga ganin kamar zata gan shi kwance yana bacci, kau da idanunta tayi ta juya ta nufi toilet dinsa.
A hankali ta daura tafukan hannayen ta, ta tura ƙofar ta buɗe ta, dira ƙafarta ke da wuya taci karo da abunda yayi silar razanar da ita ta daddage ta fasa kara tana ambaton sunan Allah ta dafe kanta da tafukan hannayenta, hadi da runtse idanunta jikinta ya fara kakarwa, wani irin faduwar gaba taji tamkar ana dakan sakwara a kirjin ta.
dukkan ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari tayi matuƙar firgita da abunda idanunta suka gane mata, tayi matukar razana, yatsun hannunta na kerma ta bude kofar ɗakin garin saurin ta fita cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da ƙasan hijab dinta dake ja da kasa gaba ɗaya ta wuntsila ta yi kundunbale ta kife ƙasa hankalinta yayi mugin tashi jikinta yadau zafi rau wata irin zufar tashin hankali ce ta fara tsastsafo mata.
Tana ta kokarin mikewa donta gudu taji motsin buɗe ƙofar tuni tasha jinin jikin ta, ta ƙame a durkushe ta kasa ɗagowa yayin da ƙwaƙwalwarta ke tariyo mata Halittar da tagani a cikin toilet dinsa kamar Wolf (kerkeci) jibgegen gaske.
Ƙamshin turaren Chief ne Ya ziyar ci kofofin hancin ta, Kafin Daddaɗar muryarsa ta katse zancen zucin ta
"Unaisah? Are you Okay"? Ay tana jin muryarshi ta yi wani irin yunkuri da iya karfinta na karshe ta zabura ta miƙe, gaba ɗaya ta faɗa kan broad chest dinsa ta ƙanƙame shi, cikin shesshekar murya take faɗa mashi abunda ta gani a cikin toilet din tare da yi mashi nuni da yatsan ta.
Sam ya kasa fahimtar me take nufi, sai kallonta yake yadda ta kankame jikinshi ta hanashi motsawa daga gani ta tsorata ba kadan ba.
"Unaisah, what's wrong? Who's in the toilet?"
Batare data ɗago ba ta furta"dodo ne a toilet din sa,"
"Okay, zanje na duba, ki jira anan" ya fada tare da ruko hannayenta a hankali ya banbare su daga kan waist dinsa.
yayi mamakin uwar zufar daya gani akan fuskarta kamar an yayyafa mata ruwa ga zafin da jikinta ya ɗauka yaji shi har jikin shi da ta rungume shi sai faman jan numfashi take tafin hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta.
"Ki kwantar da hankalin ki, Ina atare dake, ba abun zai faru..."
yawu ta haɗiya tana faman zare idanunta acikin nashi ta amsa mashi da toh.
har ya ɗaga ƙafa zai nufi toilet din Yaji ta damƙo upper arm dinsa, slowly yakai duban shi gare ta.
Girgiza mashi kai tay a tsorace tace"Don't go alone, I don't want anything to harm you"
murmushin gefen fuska ya sakar mata har cikin ranshi yaji dadin nuna damuwa da ta yi akan shi hakan ba karamin faranta ranshi yayi ba.
"Kada ki damu, ba abun da zai faru dani in sha Allah" ya fada yana kallon Heart shaped lips dinta da suka jiƙu da ruwan hawayen ta.
Taƙi sakin rigar shi saboda ta tsorata da abunda tagani tana jin fargaban wani abu ya same shi, shi da bai saba da wahala ba.
Maƙe mashi kafada tay kamar ƙaramar yarinya cikin sanyi murya tace"hankalina bai kwanta daka shiga ba, pls kada kaje, ka kira salsabeel awaya yazo ya gani ko ka kira sheikh imam malik"
A hankali ya cire hannun ta daga kan arm dinsa
Kamar ta sanya mashi kuka, bai jira ya kara jin me zatace ba, Ya nufi toilet din sai da ya fara karanta addu'ar shiga kafin ya sa tafin hannunsa ya ture ƙofar A hankali ta buɗe.
Without feeling nervous ya fada cikin toilet din, Yana shiga idanunshi sukayi mashi kyakkyawan gani yayi matuƙar mamakin ganin shi kwance cikin kwamin wanka Ya cika shi da ruwa, ko kayan jikin sa bai cire ba ahaka ya kwanta a ruwan Kamar ma bacci yake yi.
_Tsantsar mamaki da al'ajabi ne suka bayyana karara akan fuskar shi, Ikon Allah mutumin da suke ta wahalar nema kamar zasu tada garin abuja, ba irin neman da jami'an su basuyi mashi ba sako da lungu na garin saida suka bincika basu gan shi ba ashe yana acikin toilet dinsa kamar al'jani, ko taya akai ya shigo gidan? Bayan har gate officers ɗin gidan sai da ya tambaye su koya dawo gidan suka ce mashi bai dawo ba, gani yake kamar amafarki yake kallon shi saboda zuciyarsa taki aminta da abun da idanunsa ke nuna mashi_
Da tsantsar ruɗani ya furta"Danish! Is that you?"
*DAGA ALKALAMIN BOSS BATURE✍️*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: __________________________________✍️
"Danish is that you"! Ya faɗa yana bin fuskar shi da kallo, babu alamun yaji maganar shi, babu inda ke motsi a jikin shi in ka cire numfashin shi dake fita cikin nutsuwa.
Walking slowly chief ya isa bakin bathtub ɗin ya zuƙunna kan kafafunsa ba tare daya kau da ido daga kallon fuskar Danish ba.
Allah kadai yasan farin cikin da ya mammaye zuciyar sa wanda misalta shi ma bazai yiwu ba, Yau da ya rasa ɗan tahalikin nan Allah kadai yasan halin da zai shiga.
Abun da ya faranta ranshi da baije ko'ina na, ko da suka bata mashi rai bai yi fushi ba, bawan Allah sai ya dawo gida yayi kwanciyar shi cikin ruwa hakan na nufin bazai iya rayuwa ba tare da yan uwansa ba, duk runtsi duk wuya yana atare da su.
Cikin sanyin murya ya sake ambaton sunan shi"Danish" Shiru bai motsa ba, cike da fargaban kada ace wani abun ne ya faru da shi chief ya daura tafin hannunsa na dama saman forahead dinsa ya shafa shi har zuwa kan karan hancin sa.
Ba zato ba tsammani yaji Danish Ya damƙi wuyan Hannun sa, eye lids dinsa na kerma dakyar ya buɗe idanun shi da su kai mashi nauyi ya dubi chief.
Da wata irin kakkausar murya yace"saboda yan uwana na dawo nan"
Wani irin faduwar gaba Unaisah taji, yayin da take kokarin shigowa toilet din cike da fargaban me zata taras jin shiru chief bai fito ba shiyasa ta yanke shawarar bin bayan shi.
Lokaci ɗaya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata muryarshi, tayi matuƙar yin mamaki saboda ita lokacin data shiga toilet din jibgegen wolf tagani zaune cikin bathtub ɗin shiyasa ta raza, yanzu ta gane shi ne ya rikiɗa ya dawo mutun.
wani irin tsantsar farin ciki ne mara misaltuwa ya wanke zuciyarta, dama saida ranta ya bata zai dawo, hasashen da tayi ya tabbata maganar da ummi tayi ce ta tuna mata da ranar daya rikiɗa kafin ya zama maciji da jikin shi ya dauki zafi rau cikin kwami ya shiga ya tsuma kanshi da ruwan sanyi.
yanzu ta gane idan ranshi ya 6aci yana son yayi cooling temper dinsa ruwan sanyi yake shiga, taji tausayin shi, shi dai rayuwarshi wani sa'i kamar bata mutane ba.
"Danish, ka tada min hankalina, daga ni har yan uwanka da abokan aikina, babu irin neman da ba ayi maka ba a garin nan, saboda kai ko abinci na gaza ci, ban ta6a tsammanin damuwar da nayi dakai takai har haka ba..." ya faɗa yana kallon cikin idonshi.
"Da na san ranka zai 6aci da ban matsa maka mun tafi head quarter ba, banji dadin abunda big guy yayi maka ba, na tsawatar mashi kuma ya gane kuskuren shi, bazai ƙara gigin bata maka rai ba"
yanayin yadda chief ke yi mashi magana da sigar lallashi ba karamin kwantar mashi da hankali yayi ba, zuciyarshi taso ta karaya da jin irin kaunar da yake yi mashi, tun daga kan facial expression dinsa yaji ya yarda da duk wani abu daya faɗa masa.
"Kayi hakuri idan na bata maka rai, sannan inaso Ka faɗa min duk wasu sharrudda da zamu bi don mu zauna dakai lafiya batare da mun 6ata maka rai ba saboda naji jiki ba kaɗan ba lokacin da aka sanar dani ka fita nayi zaton bazan ƙada ganinka arayuwata ba" softy ya fada tare da tsamo hannun Danish daga cikin ruwan ya haɗe yatsun hannun su cikin na juna, yayi shiru yana sauraron shi.
"Sannan Alfarmar da zan roko a gurinka, nasan baka yarda da ni ba, amma dan Allah ko dan saboda yan uwanka kada wata rana kayi fushi ka koma inda ka fito.." ya ɗan dakata yana kallon yanayin fuskar Danish.
"nasan za ka yi tunanin kodan saboda ina son ka bamu hadin kai shiyasa nake lallashin ka, ba haka bane, Kamar Yadda Allah ya jarabci Uncle dina da kaunarka nima haka nake jinka a zuciyata"
Unaisah dake atsaye bakin toilet door din gaba daya tana sauraran maganar chief, zuciyarta ta karaya da tausayin su, aranta ta ayyana wannan wata irin zazzafar kaunace suke yi ma shi? Anya Danish bai da alaƙa ta jini da su?
Lumshe idanun shi yayi tare da numfasawa slowly ya ware eyes dinsa akan fuskar Chief
Baiyi tsammanin zai tanka ma shi ba, in weak Voice Danish Yace"ban ruƙe ka a zuciyana ba, amma ku daina bata min rai in na nuna bana son abu kada ku tursasa min, ni bana so na cutar da kowa, shiyasa na ke6e kaina saboda in sanyaya zuciyata, kamar yadda kake jina a zuciyarka nima haka nake jinka, haɗin kaine kawai bazan baku ba, sannan ka yi hakuri da bata maka rai da nayi, I didn't realize I was rude to you and disrespected you until he told me."
runtse idanu chief yayi gam na dan wani lokaci bai furta komai ba, har cikin ranshi yaji dadin maganar da Danish Ya furta mashi na cewa shima yana jin shi kamar yadda yake jin shi, yasan sannu a hankali wata rana zai samu amincewar shi.
Phone ringing dinsa ne Ya sa shi hanzarin buɗe idanun shi tunawa da bakin su, wrist watch din hannun shi ya duba.
"Danish, Ka fito daga cikin ruwan nan haka, Inaso Ka shirya, nasan kana jin yunwa, zan sa ashirya mana dinner"
Amsa mashi yayi da Okay
Fitowa Chief yayi daga toilet din, Ya zaro wayar daga trouser pocket dinsa, misscalled ya gani da layin big guy.
Kira ya danna masa bayan yayi picking, big guy ya sanar da shi cewa yanzu haka suna akan hanya sun dauko su commender daga airpot.
fuskar shi da fara'a ya furta Alhamdulillah Allah Ya kawo ku lafiya, bai sanar dashi game da ganin Danish ba, ya bari sai in ya zo gidan ya ganshi.
Bayan sun yi sallama, Ya kira layin Ci ya sanar da shi game da ganin Danish yace ya sanarma sauran abokan aikin su, Ci yayi farin ciki sosai harya shawarce shi akan su lalla6a shi kada su yi duk wani abu da zai 6ata ma shi rai.
Sai da ya kammala yin wayar ya lura babu Unaisah a dakin, ranshi ya bashi may be ta fita ne don ta sanar da uwanta.
bayan fitar Chief da yan mintuna, A hankali Danish Ya futo daga ciki, har ya cire kayan jikin shi, short kadai Ya bari, sumar kanshi dake a jike ta manne ma fatar bayan shi da gefen fuskar shi, tamkar babu kuzari a jikinshi da wata irin kasala yake taka kafafun shi, a duk lokaci daya rikiɗa ya dawo suffar shi ta mutane ba karamin jiki yake ji ba.
Gaban dressing mirror ya dakata da tafiya ya dafe gaban mirror ɗin da tafin hannun shi ɗaya.
Kunnuwan shi ne suka soma jiyo ma shi motsin mutun a dakin shi, yayi zaton chief ne hakan yasa bai damu daya ɗago da ido ya kalle wanene ba.
"Meyasa ka tafi batare da ka fada min inda zaka je ba? Kasan irin tashin hankalin dana shiga na rashin ganin ka"? Da sauri ya kalle ta ta cikin madubin
Tana tsaye abayan shi ta goya hannayenta kan kirjin ta, abayan labulen dakin shi ta la6e saida taga chief ya fita tukunna ta fito don ta samu damar zazzaga mashi masifa.
Har sai da gabanshi ya ɗan fadi ganin yadda idanunta suka kumbura sun kaɗa jawur ko ba afada masa ba yasan tasha kuka tamkar ranta zai fata.
tuni yasha jinin jikin shi yasan ba zai tsira daga fushinta ba dole ta hukunta shi.
Bai aune ba, yaji ta faɗa kan faffaɗan bayanshi ta zagayo da hannayenta kan broad chest din shi ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta rufe idanunta da ke tsiyayar da ruwan hawaye ta dunkule yatsunta kamar yar dambe ta dinga bugun kirjin shi da karfi, duk da hakan bata huce ba sai da ta gartsa mashi ciwo har sau uku akan fatar bayan sh
Ko kaɗan baiji zafin abun da tayi mashi ba, ya fahimci irin radadin da taji na rashin shi yasan tayi tunanin Ya koma kurkuku ne. Cikin shesshekar kuka take fada mashi abunda ya faru bayan tafiyar shi.
Zuciyar shi ta karaya ya kara jin tsantsar kaunarta da sonta acikin zuciyar shi, yadda takusa salwantar da rayuwarta saboda shi! Duk da fushin da take da shi na abunda ya faru tsakaninsu hakan baisa ta daina damuwa da shi ba, kamar ma ana kara mata zazzafar kaunar shi.
yayin da yake wannan tunanin idanunshi sun cicciko tab da kwalla a hankali yake kallon hannuwanta dake akan kirjin shi ta gama naushin nashi yanzu tsunkulin kirjin shi ta ke yi duk fa don ta huce radadin daya kunsa mata, zuciyar shi tayi matuƙar karaya saboda tausayin rayuwarsu daya kama shi, yana jin tsoron ranar da mutuwa zatayi masu yankan kauna, yasan dole wata rana ɗaya ya riga ɗaya mutuwa acikin su, fatanshi Allah yasa in ma mutuwarce ta fara daukar shi saboda baisan yaga mutuwar Unaisah, ko ma ta ɗauke su atare saboda yasan ba lallai ta iya surviving batare da shi ba, yana ɗaya daga cikin dalilin dayasa yaki yarda ya bada hadin kai saboda shi ya san me zai biyo baya.
Lumshe idanun shi yayi yayin da siraran hawaye suka fara yar tseral kan kuncinsa, shesshekar kukan ta da yake ji a kunnansa ba karamin karya masa zuciya ta ke yi ba.
Sai da tayi mai isarta, tayi shiru tana kara makalkale jikin shi yana jin duk wani motsinta a jikinshi harta bugun zuciyarta da dumin jikinta duk yanaji anasa jikin..
In a weak voice ta fara magana taja jan numfashi
"Ban hana ka tafi duk inda zaka je ba, amma ka fara tunanin wani hali zan shiga kafin ka yanke shawarar tafiyar, sannan in ma zaka tafi toh ka tafi dani, idan ba haka ba zan hadiyi zuciya na mutu ne"
bata kare maganar ba, yai saurin ruko hannunta acikin nashi ya janyota ta dawo ta gabanshi yayi saurin rungumeta tightly a kirjin shi kamar zasu koma mutun daya.
hijab din jikinta ta jiƙe sharkaf da gumi kamar babu a.c adakin tsabar hucin da jikinta keyi mata ba, da alama Unaisah ta manta da hudubar aunty umminsu ta kuma manta da sharuddan data gindaya mashi na kusantar inda take sai gashi yau saboda halin data shiga na gudun kada ta rasa shi yasa ta kunsata kanta da shi ta kuma rungume shi saboda tana bukatar jin dumin shi a jikinta, tausayinshi da kaunarshine suka rufe mata ido har tagaza gane abunda take badai dai bane ta manta.
Sunyi shiru babu mai magana acikinsu, ko motsi basa sonyi saboda yanayin da suka tsinsu kan su mai wuyar fassaruwa ji suka inama zasu dawwama ahaka sai dai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi ko ba mutuwa akwai kaddara da zata iya raba su 🥺
Da wata irin kasala Yasa hannu yaja hijab din jikinta ta zame ta dawo kan kafadarta.
ya cusa hannunshi cikin lallausar sumar kanta ya nannaɗeta gefe guda ya fiddo da kunnnata na dama.
Saitin kunnan ya daura tausasa red lips dinsa cikin sanyin murya mai dadin sauraro ya furta"kamar baki yarda da kaunar da nake maki ba? Meyasa zaki ɗaga hankalinki bayan kinsan cewa bazan iya rayuwa batare da ke ba, idan ma kina tunanin hakan toh ki daina...." ya faɗa cike da bata tabbaci har cikin kunnnata take jin iskar numfashinsa..
"mutun yana rayuwane tare da ƙaddararsa sannan bai isa ya guje mata ba, nima haka take agurina, bazan taba tafiya nabarki ba in har bake kika bani iznin in tafi ba, ke kadaice zaki bani umarni in bi, gaba ɗaya burin rayuwana akanki ne da yan uwana, bazan ta6a rabuwa babu ku ba, duk runtsi duk wuya zan kasance atare daku"
bai ƙare maganar ba ta tari mumfashin shi da cewa"ka yi hakuri da abun da ya Omar yayi maka, nasan shine ya bata maka rai, nima raina ya 6aci zanyi mashi magana yadaina bata maka rai" ta fada ba tare da ta dago kanta ba.
Murmushi ya danyi har cikin zuciyarshi yaji dadin maganarta shiyasa yake kara kaunarta saboda kaunar da take masa, zata iya bata mashi rai amma wani bai isa ya daga masa yatsa ta kyale shi ba.
"Ki kyale shi, ba laifinsa bane, ni ne na 6ata masa rai, komai ya faru ni naja ma kaina.."
Hankalin shi Yayi mugun tashi da abunda idanunsa suka gane mashi, tsabar kidima da tashin hankali har wani jiri jiri yake gani acikin idanunshi, da sauri ya dafe kofar dakin gudun kada jiri ya kwashe shi ya kife ƙasa, Yayi danasanin zuwa dakin Danish dayasan zaiga abunda zai jijjiga
kwakwalwarsa da tashi hankali da baiyi gigin zuwa ganin Danish ba!.
Ya gaza yarda da abunda idanun shi ke nuna mashi da kuma abunda kunnuwanshi suke jiyo mashi.
Angel dinsa ce kwance ajikin namiji sun kankame juna kamar anta da jini? Wlh bai ta6a zaton zatay mashi haka ba, ta karya zuciyarshi ba kadan ba.
bazai juri kallon su ba, adaddafe Ya juya yabar kofar dakin dama yazo ne donya ga Danish Chief ne Ya bashi labarin sun ganshi, bawan Allah da farin cikinshi ya zo don ya bashi hakurin abunda big guy yayi mashi ashe da rabon yaga abun da zai hana shi runtsawa adaren yau.
shi mamakin shi tayaya Unaisah har tasan dadin ta rungumi namiji? A tunanin shi batai wayon da za ta yi hakan ba, bayan haka yana yi mata kallon mai hankali bai ta6a zaton zatay abunda tasan haramun ne ba.
yana tafiya kamar zai kife kasa saboda jirin dake shirin kwasar shi, babban tashin hankalinshi ya zaiyi ya raba alaƙar su? Saboda ya fahimci azababbiyar kaunace atsakaninsu ko romeo da juliet albarka, kai wannan har layla da majnoon sun shallake sai yanzu ya gane dalilin dayasa ɗazu ta haukace tabi bayan Danish har mota takusa hankadeta ashe sone Ya makantar da ita.
shi azaton shi shakuwace atsakaninsu ashe shine bai fahimta ba, bakomai yake tunawa ba face alkawarin daya daukarwa kanshi na mallaka ma chief Unaisah, tun kafin ma ta bayyana ya bashi ita, sadakine kadai bai biya, ba yadda za'ay ma ya amince ma soyayyar Unaisah da Danish! Ko ta halin ƙaƙa sai ya raba su, bama zai ta6a yiwuwa ba, ay bata isa tasa shi zubda girman shi ba, bare aje ga batun bashi kunya.
Acikin zuciyarshi yake ta sambatu kamar wani zautattace.
Peck ya manna mata akan forehead dinta ta lumshe idanunta tana jin wani irin abu yana ratsa tsigar jikin ta.
numfashi ta ɗanja tare da sauke shi kan kirjin shi iskar ta daki fatar shi.
tana kokarin ɗago da kanta kamar daga sama tajiyo muryoyinsu Batool daga waje suna ambaton sunan Danish a ruɗe ta raba jikin ta daga nashi tayi saurin komawa bayan curtain ta 6oye tana faman sauke ajiyar zuciya.
Bin labulan yayi da kallo baiso suka katse masu hanzarin su ba, murmushi yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba, daga gani yaji dadin faranta masa rai da tayi.
Kamar an korosu suka fado dakin ko sallama babu, da karfin suka hada baki gurin furta"Danish"! Juyowa yayi tare da kallonsu, gaba ɗayan su ne babu wanda babu acikin su.
Wani irin annurin farin ciki ya gani akan fuskokinsu, bayin Allah tun da suka dawo daga headquarter tashin hankalin bacewar shi Ya hana su canza uniform din jikinsu ko wanka ba su yi ba.
harya motsa lips dinsa zai yi magana bai yi aune ba gaba daya suka nife shi suka fada kan jikinshi kamar zasu kayar da shi kasa, saboda yadda suka baibaye shi kamar ƙudajen zuma, gaba daya sautin kukan su ya cika dakin nashi.
dayasan halin da zai jefa su da bai tafi yabarsu ba, a zaton shi sun daina damuwa da shi ashe har yanzu ba abun da ya sauya na daga kaunar da su ke yi ma shi.
Dakyar ya samu suka kyale shi cikin shesshekar kuka suka fara korefe korafe akan tafiyar da yayi yabar su.
Haris daya fara zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu kowa yana fada masa irin tashin hankalin daya shiga, murmushi yadinga sakar masu kamar zaiyi dariya saboda sun bashi nishadi sun kuma faranta ranshi, ita Batool da tafi su jin jiki pillow ta dauko ta fara buga mashi kan kirjin shi aikuwa kamar jira suke gaba daya suka fara wasa da pillows suka dinga kwala mashi ta ko'ina.
tun yana murmushi yana kokarin kare kanshi harya fara tiƙar dariya kamar sakarkaru haka suka saki baki suna kallon shi cike da mamakin ganin Dariyar shi.
Duk abun da ke faruwa akan idon Unaisah gaba daya ta shagala da kallon fararen hakoranshi masu kyau da tsari sai dariya yakeyi kamar zai shaƙe.
ba su kyale shi ba har saida ya faɗa kan gadon shi yana fadin ya isa haka na kar6i laifi na bazan kara tafiya nabarku ba.." jefar da pillows din su ka yi kan mattress din sai haki suke suna kallon shi sun kewaye gadon shi.
"Waya faɗa maku na dawo" ya tambaya yana kallon su,
Atare suka hada baki gurin furta"daddy Taj"
"Banyi zaton kun damu dani har haka ba..." bai kare maganar ba suka fara naɗe hannayen shirts dinsu alamar zasuyi bugu dabi'arsu ce tun a prison..
"Ku kyale shi ya gane kuskuranshi" muryar Unaisah ce ta dakatar da su, atare suka jiyo tare da kallon ta, tana tsaye atsakiyar dakin duk a tunaninsu daga waje ta shigo ba su san cewa tana la6e jikin labule ba.
Haduwa sukayi gaba suka zauna gefen gadon shi, ba zasu iya tuna when last suka nishadantu da Danish irin na yau ba, ya sakar masu fuska sun yi fira cikin raha sunyi nishadi kamar lokacin da suke a prison.
Jin shiru Unaisah bata dawo ba, tun da tace ta jira har yanzu bata ji duriyar ta ba, gajiya tayi da zaman dakin shiyasa ta fito don ta neme ta, sai kuma ta taras babu su a falon har zata juya idanunta suka sauka akan taj dake zaune kan sofa ya zabga uban tagumi kamar wanda ya rasa mafaɗi a duniya, tun daga kan yanayin fuskarshi ta fahimci babu lafiya atare da shi, kamar akwai wani abu na damun shi.
Karasawa tayi gaban sofa din da yake ta ambaci sunan shi shiru bai tanka mata ba, har saida ta maimaita kusan sau uku na karshen ne ta ɗaga murya a ɗan firgice ya dago da ido ya kalle ta, murmushi tasakar mashi, da sauri ya fara kokarin danne damuwar shi ya ɗan saki murmushin yake yace"Ummi ya kike, kin wuni lafiya" bata amsa mashi tambayarba sai cewa tay"yalla6ai meke damunka ne? Kusan sau uku ina kiran sunanka baka amsa min ba, anya lafiya" still da murmushi akan fuskarshi ya furta"ummi ba komai lafiyana lou, ba abun da ke damuna"
Tunani tayi kodai rashin Danish ne yasa shi shiga halin damuwa hakan yasa tace"Ya mukaji da abun da ya faru na 6atan Danish? Wlh nima ɗazu Batool ke fadamin, Hankalina ya tashi ba kaɗan ba.." bata kare maganar ba taj yace"oh bakisan An gan shi ba..." waro idanu waje tayi"dagaske"?
"Eh, ay yanzu haka su Unaisah suna acan dakin shi" wani irin ihun farin ciki ta saki tare da firta Alhamdulillah kusan sau uku tace"wlh naji dadin ganin shi da akayi, saboda hankalina ya tashi musamman ganin yadda yan uwanshi suka gaza cin abinci saboda rashin shi.
"bari naje naganshi" har zata jiya taj ya kira sunan ta tajiyo ta dube shi.
"Idan kin shiga dakin, pls ki kirasu, su zo su shirya akwai baki da zasu zo bayan sallar magbrib"
amsa mashi tay da toh, zumudin son ganin Danish Ya hana ta tambayi su wanene bakin da sauri ta juya ta nufi upstairs.
Bin ta da kallo taj yayi har ta 6ace ma ganin shi, sunkuyar da kan shi ƙasa yai kamar bawan dake neman gafara, abun duniya ya ishe shi tun dazu bakin cikin abunda yagani yake ta nanukarsa, idanunshi sunki daina tariyo mashi abun takaicin daya gani....
Lokacin da takarasa bakin kofar dakin tunkan ta shiga ta fara jin hayaniyarsu yadda kasan gidan biki ko suna sun cika ko'ina da surutun su.
knocking kofar tayi almost 3 times ba wanda ya buɗe mata, zafin dumi Ya hana su ji bugun kofar, murmushi tasaki tare da tura ƙofaf ta shiga ciki
Tsayawa tayi tare da goya hannayenta kan kirjinta tana kallon ikon Allah sun cike dakin shi, wasu akan couch wasu gefe gadon shi har saman gadon.
ta fahimci yau ba karamin nishadi suke ji ba.
Kokari take ta hango Danish din duk sun rufe shi dakyar idanun ta suka hango mata bayan shi ya kifa kanshi jikin pillow, Unaisah tana kishingiɗe gefen shi sun shagala da kallon juna, sun bar su Batool sai ɗumin surutu suke .
Yanayin fuskartane Ya canza zuwa tsantsar mamaki da rudani, tun da take rayuwa agidan bata ta6a lura da zanan tottoo din shi ba, tasan yana da shi amma bata ta6a ganin dukanshi ba, sai yau datayi arba dashi babu riga a jikin shi, abunka ga farar fata zanan ya fito 6aro 6aro bakomai ne ya rudar da ita face ganin zanan tattoo dinsa sak irin na big boss kamar anyi copying tattoo din big boss an manna mashi abayan shi.
wannan abu ya bata mamaki har ta gaza yi masu magana saboda kallon Abun al'ajabin daya ruke ta..
__________________________💓✍️
Safa da marwa take yi atsakar dakin ta, fuskarta babu walwala ga dukkan alamu akwai wani abu dake damunta wanda yayi silar shigarta halin da take a jiki...
Sallamar dr shureim ce ta katse zancen zucinta, kamar dama jiran shi takeyi da sauri ta nufe fuskarta ayamutse tace"shureim fita zaka yi ne"?
Girgiza mata kai yai"a'a, wurinki nazo inaso muyi magana ne" ya fada tare da wuce ta ya zauna gefen gadonta, itama ta zauna tana kallon shi cike da son jin wata magana ne zasuyi....
"Meke damunki ne? Yanayin fuskarki ya nuna kamar bakya jin dadi"?
"Shureim lamarin Benazir yana ɗaga min hankali, kai baka lura ba har yanzu da yanayin ta ba? Wani lokaci tana abu kamar mai ta6in hankali ni tsorona kada ta haukace..." ta faɗa sukuku babu walwala, maimakon taga tashin hankali akan fuskarshi sai taga ya saki tausasan murmushi arude tace"lafiyarka kuwa? Ko bakaji abun da nake magana akai bane" ruko hannayenta yayi acikin nashi, fuskarshi da fara'a tace"mommy zan fada maki gaskiya amma kada ki fadamawa kowa..." cike da mamaki tace"toh, Ina sauraronka" ta fada tana kallon cikin idanun shi
"Benazir taji saukin abinda ke damunta, haukan da kika ga tanayi pretending ne, har tambayarta nayi meyasa take yin hakan? Sai ta nuna min bata son asan ta samu lafiya... Baki asake hajiya layla take sauraron shi tayi mamakin jin hakan aranta ta ayyaba lallai benazir ashe haryanzu tana nan da dabi'arta nayin karyar ciwo.
"Amma shureim baka tunanin akwai wani dalili dayasa benazir take pretending? In ba haka ba taya mutun da lafiyarshi zai za6i zama mai ta6in hankali" ta jefa mashi tambayar
Shiru yayi jimm shi kanshi yayi wannan tunanin amma koda ya tambayeta sai tace mashi bakomai.
"Gaskiya bana tunanin akwai dalilin dayasa yakeyin hakan cos na tambayeta tace min bada wata manufa ba saina rashin son a rabata da azeezaty"
Girgiza kai hajiya hajiya layla tayi"ni nasan kayana shureim, Benazir bata ta6a yin abu batare da dalili ba, dole akwai dalili, ni fa najima ina zargin da akwai wani abu da Benazir ta sani ko ta aikata wanda har yaja akayi mata asiri..."
maganar hajiya layla ta ɗan ɗaga hankalin shi tunawa da bibiyar rayuwar Benazir da akeyi acikin gidan dama kuma yana zargin wanda yayi mata asiri ne yake son karasa kasheta bayan haka itama Benazir din zai iya yiwuwa maganar hajiya layla ta zama gaskiya.
amma saboda bayason ɗaga mata hankali shiyasa yaki sanar da ita zancen bibiyar rayuwar Benazir da akeyi sai dai ya yanke shawarar zai je dakin Benazir don ya tambayeta meya faru da ita aranar data kulle dakin ta.
Yayi zurfi acikin tunaninshi muryar Hajiya layla ta katse shi"kaima kana tunanin abunda nake tunani ne ko kuwa" murmushin yaƙe ya sakar mata"mami bana so ki sanya damuwa aranki, hasashen da kike ba lallai ya zama gaskiya ba, zai iya yiwuwa wani tayi ma rashin kunya kinsan wasu mutanan da bakar zuciya ga mugunta arai watakil ita ta manta da ta bata masu rai shine su kuma da babu Allah aransu suka yi mata asiri don su kuntata rayuwarta, ko kuma wanda ya aikata mata hakan yayi ne da niyar ya ɗauki fansar wani abu da ku ka ta6a yi masa..." dafe kirji hajiya layla tayi da tafin hannunta alamar ta shiga uku itama fa tayi rashin mutunci lokacin da Alhaji ubaid Yake akan mulki tunma kafin ya hau kujerar gomna ba mutunci ne da ita ba, yanzu ne tayi hankali ta gane Allah ɗaya ne.
"Ni fa ban fada maki donki tashi hankalinki ba, inaso ne na kwatanta maki ba lallai hasashen ki ya zama gaskiya ba, banaso ki matsa ma benazir kan ta ta fada maki meyasa take pretending, mu kyaleta kawai iyakacinmu da ita addu'ane kawai ubangiji Allah Ya kare mana ita daga sharrin duk wani abin cutarwa..." amsa mashi tayi da Ameen ita dai hankalinta bai kwanta da lamarin benazir ba.
sun jima suna fira adakin harya bata labarin zuwansu gidan su Azeezaty duk don ya kara kwantar mata da hankali taji dadi kamar ta zuba ruwa akasa tasha tsabar farin ciki.
__________________________💓✍️
akwance take kan gadonta, jikinta sanye da night dress, ta ruƙe wayar ta a hannunta, ta nutsu tana kallon hoton fuskar Unaisah dake akan wallpaper din ta... bata gajiya da kallon fuskar ƴarta, takan wuni tana kallon hotunan su Unaisah ba tare da gajiya ba.
kwantar da wayar tayi kan kirjinta ta ɗage kai sama tana kallon ceilling.
bakomai take tunawa ba face shawarwarin da Aneelerh ta bata akan yadda zata shawo kan Taj ta hanyar kyautata mashi tun shekaran jiya take tura mashi love messages har yau yaki mata reply kamar tay hauka, ta rasa ya za ta yi ta shawo kanshi har jaraba kiran shi tayi tun da ya ɗaga sau ɗaya yaji muryarta bai kara picking call din ta ba.
ɗago wayar tayi ta shiga cikin whatsapp dinta, a chat dinsu da Anila tayi copying contact din Unaisah data turo mata..
Cike da marmarin son Jin muryarta ta sanya number din tana kokarin yin saving kwatsam ba zato ba tsammani taga number din already akwai ta a contact list dinta da sunan God gift, Yarinyar da ta kira wrong number a matukar rude ta kurawa contact din ido batare da kyaftawa.
lamarin ya daure mata kai tunani tayi ko dai Aneeleerh wrong number ta tura mata?
zuciyarta ce ta raya mata bakya tunanin duk itace? Dama kuma sunansu iri ɗaya Unaisah hakan na nufin yartace yarinyar da suke waya? Ta jefa ma kanta tambayar, kokwanto ta farayi anya kuwa itace? Yarinyar fa ta fadamata ba abuja suke ba.
"Bari dai na jaraba kira inji" call ta danna almost 20 times ba'ay picking ba, damuwace karara akan fuskarta, jin knocking ɗin room door dinta yasa ta yin saurin aje wayar kan side drawer ta fara haɗe rai zatay pretending...
A hankali ta shigo dakin, Jikinta sanye da dogon hijabi, a tsakar dakin ta tsaya tana kallon Benazir kamar tana jin shakkar tunkararta, tayi mamakin Ganin zeenatu adakinta yau wata rana tun lokacin da aka sallameta ba ta kara kusanta kanta da ita ba.
aranta ta ayyana watakil iskokan dake akanta ne suka saketa shiyasa ta fara neman su shirya da juna
Kurama juna ido sukayi batare da kyaftawa ba, har na tsawon mituna kafin zeenatu tay karfin halin firta"Aunty Benazir, zan iya shigowa ciki"?
Ɗaga mata gira Benazir tay ba tare data furta mata kalma ba, wucewa tayi kan gadon ta haye tare da juya mata baya
sunyi shiru kamar basu ta6a sabawa da junan su ba
"Aunty benazir ina Azeezaty? Nasan kuna waya da ita, ba ta6a tambayarki ni ba"? Kallon bayanta Benazir tayi kafin tace"kina nufin babyna"? Tace Eh
"Tana tambayarki, duk in mu ka yi waya sai tace in gaida mata ke.." dadine ya lullu6e zeenatu har batasan sa'adda ta aje kunyar gefe guda ta juya suka fuskanci juna ita da benazir
"Itama ta damu dani, kamar yadda na damu da ita kuma tana so na" ta tambaya tana kallon benazir dake kallon ta..
Ɗaga mata gira tay alamar eh
Murmushi tasaki"yaushe zaki kiramin ita mu gaisa"?
"Gobe in sha Allah" washe baki tayi tana faman kyafkyafta blue eyes din ta...
Ita yanzu tausayi zeenatu ke bata, shiyasa kwata kwata bata ruƙe ta aranta ba.
Ganin kallon da Benazir ke yi mata yasa tay saurin rufe idanunta, cike da jin nauyinta tace"Aunty benazir dan Allah ki yi hakuri da abun da na maki" murmushi Benazir tayi"zeenat laifin me kika min"?
"Banje asibiti na duba lafiyarki ba, bayan kin dawo ban kula ki ba" yar dariya Benazir tayi"haba karki wani damu wlh, nayi maki uziri ya shureim ya fada min bakyajin dadi .." ajiyar zuciya ta sauke har taji sanyi aranta, ta ɗan buɗe idanunta akan fuskar Benazir miƙa mata hannu tayi"nayi missing dinki ba kaɗan ba sisterna rabin raina, da naganki adakina naji dadi, dariyar farin ciki zeenatu tasaki tare da kama hannun Benazir ta ruƙe shi gam a cikin nata.
_________________________________✍️
Bayan sallar Mabrib, gaba dayan su sunyi wanka sun shirya cikin shiga ta mutunci yan matan sun sanya abaya sunyi rolling kamar larabawa, mazan kuma sun sanya jallabiya kusan kalar shigar da su kayi aranar dinner din Hateem sun yi kyau sosai.
a falo suka hallara mutun ɗaya ke babu acikin su Danish da har yanzu bai karasa shiryawa ba, Ummi ma tana atare da su ta dage sai daukar su pics take yi saboda sunyi mata kyau
"Wai su wanene bakin da zasu zo ne"? Sajeed ne yai tambayar idonshi akan Unaisah, yasan dakyar in batasan su wanene ba,
"Nima bansani ba, na kosa naga su wanene mu kara hakuri su karaso Allah yasa muga alkhairi"
su ka amsa mata da ameen, su jemimah sai yan guje guje suke atsakar falon ita da azeeza da parvin kamar wasu tsararrakin juna har saida ummi ta tsawatar masu kafin suka daina wasan..
"Ku nutsu pls, manyan bakine su zasu zo.."
"Aunty ummi su wanene wai"? Akagare Hanna ta tambaya tana kallonta
Ummi tace"nima bansan su wanene ba, amma boss ya fadamin bakin chief ne, tun da naji hakan nasan ba kananun mutane bane, shiyasa nace ku nutsu kada ay abun da za'aji kunya..."
kallon juna su ka yi, duk sun kagara da su ga su wanene...
Shigowa falon Taj yayi hannayen shi zube cikin aljihun jallabiyar shi, kwata kwata babu annuri akan fuskarshi kamar wanda aka fada ma sakon mutuwar shi.
Kwata kwata basu lura da shi ba har saida Javed Ya ambaci sunan shi kafin hankalinsu yakai gare shi, Unaisah na ganin shi ta nufe shi da sauri donta fada mashi abun farin cikin daya faru na bayyanar Danish azatonta bai sani ba.
tana karasowa Taj yayi saurin kauce mata kamar bai ganta ba, fuskarshi a haɗe ya nufi su Naufal Ya mika masu hannu daya bayan daya ya yi musabaha da mazan kafin Ya maida hankali kan su sarah da fara'a yake amsa masu gaisuwar da su ke yi mashi.
gaba ɗaya ta gaza ɗaga kafafunta saboda faduwar gaban da taji, hankalin ta ya tashi da ganin abun da daddynta yayi mata, kokwanto tayi anya ya ganta? Ko dai bai lura da ita bane? In ba haka meyasa zai shareta ya nufi yan uwanta?
ta sanyawa ranta cewa bai ganta bane saboda bai ta6a mata hakan ba, cike da kwarin gwiwa ta nufe shi a lokacin yana tsaye, ta fada bayan shi ta rungume shi tana fadin"daddy ni baka ganni ba ne..." rai aɗan bace ya furta"unaisah ki sake ni, tun kafin na bata maki rai" ya fada tare da janye hannunta Ya jefar da shi gefe ɗaya.
aruɗe ta kalli fuskar shi, ya haɗe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne.
Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su
Duk da haka bata kawo komai aranta ba, ta kuma cewa"daddy, chief ya fada maka an ga danish a cikin toilet dinsa..." banza yayi da ita tamkar baiji maganar ba, hakan ba karamin ɗaga mata hankali yai ba.
komawa tayi cikin yan uwanta ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba.
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: ________________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️😈😳👹
..." bai kare maganar ba General Noah Ya katse shi da cewa"Dole saida shi zamu iya farmakarsu? Shi ɗan uwan nashi salsabeel bazai iya yi ma sojojinmu jagora ba" girgiza kai big guy yai"saboda laifin daya aikata masu, sun ɗauke garkuwar sihirin shi, Salsabeel bai da karfin ikon da zai iya jagorantarmu, dole sai dai shi Danish din"!
A kalla sun shafe tsawon awa da rabi suna tattaunawa a karshe dai ba su tsayar da ranar kai farmakin ba, har sai zuwa lokacin da Danish zai basu haɗin kai....
A yammacin ranar Su uku ne zaune saman kujerun backyard din gidan, sunyi shiru babu mai magana acikin su, yanayin fuskokinsu kadai zai tabbatar maka da akwai wani abu dake damunsu, kowan nan su da abunda yake sakawa cikin ran shi..
Muryar chief ce ta katse shirun nasu"Ina salsabeel din? Ka kira shi? Naji shiru baizo ba"
Cikin nutsuwa big guy yace"yace min yanzu zai shigo, mu kara hakuri nasan yana akan hanya"
jinjina kai chief ya yi tare da kallon Taj, wanda gaba ɗaya hankalin shi baya akan su, Ya langwa6e kai jikin sofa, har yanzu damuwar Unaisah ta hanashi sukuni baida wata walwala.
"Taj"! A hankali Ya dubi Chief daya kira sunan shi Na'am..
"What's wrong with you? tun zaman mu anan banji kayi magana"!
murmushin karfin hali yayi in a cool voice yace"Sir bakomai, idan ma akwai abunda ke damuna bai wuci tunanin yadda zamu kawo karshen kurkukun kaddara ba"
murmushi chief yayi wanda bai wuci fatar la66ansa ba.
"In sha Allah komai ya kusa zuwa karshe, bi'iznillah mu ne da nasara"
da kwarin gwiwa ya furta maganar, suka hada baki gurin faɗin"Allah Ya tabbatar mana da alkhairinsa"
kafin wani yakuma magana, sallamar Salsabeel ta katse su atare suka dago tare da kallon shi, cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa amsa mashi
"Ay min afwa, Uziri ne Ya ruke ni, nabarku kuna ta zaman jira na" big guy yace"kada ka damu bismilla zauna mana" zama yayi kan kujerar dake a gefen Taj, ya maida duban shi ga chief ya nutsu yana jiran jin me zai ce.
Big guy ne ya zayyana ma shi komai da suka tattauna agurin meeting, ya ƙara da cewa"ko yau muka samu wanda zaiyi mana jagora zuwa gidan kurkukun, a shirye muke da mukai farmaki, yanzu haka da nake maka magana mun riga da mun tadani rundunar dakarun Sojoji, da kuma makaman yaƙi, ku kadai muke jira Salsabeel! We don't need to waste time!.
Chief ya ɗaura da cewa"nayi alkawarin bazan ƙara takura ma Danish game da zancen kurkukun ƙaddara! Salsabeel kai kadai ne kasan ta wace hanya zamu iya samun haɗin kanshi, saboda kafi mu sanin wanene shi, pls ka taimaka mana Salsabeel, muna so muje mu gane ma idon mu abunda suke aikawata mu kuma kawo karshen su...."
yanayin yadda chief ke yi mashi magana da raunin murya ba karamin karya mashi zuciya yayi ba, ji yake inama ace zai iya yi masu jagora da kan shi basai sun bukaci Danish ba wlh da babu abunda zai hana koda hakan zai yi silar rasa rayuwarshi..yayin zurfi cikin tunanin shi muryar Taj ta dawo da shi hayyacin shi
"Kayi shiru baka ce komai ba, gaba dayanmu mun ƙagara da muji daga gareka, Salsabeel mun yi imanin zaka sama mana mafita in sha Allah, pls kada ku sagar mana da kwarin gwiwar mu, hatta commender james shima ya shirya bada gudummuwarshi gurin kai farmaki, haka zalika Rundunar Sojojin Nigeria suma sun shirya tsaf lokaci kadai suke jira mu faɗa masu"
ya faɗa yana duban Salsabeel"saura kai Salsabeel ka bamu gudummuwarka mun san ka yi kokari amma muna bukatar ƙari"
Dukar da kanshi ƙasa yayi lamarin na nema yafi karfin shi baisan ya zaiyi da Danish ba, shi kadai zai kawo masu cikas, baisan yadda zaiyi ya tankwara shi ba, amma tabbas yana da tabbacin mutun ɗayane duk duniyar nan zai sa shi abu yayi, Cikin karyayyar murya.
yace"Yalla6ai, Ku bani mintuna shabiyar In ba damuwa, inaso zanyi magana da Danish din"
big guy yace"muna jiranka" miƙewa yayi cikin takun sauri Ya nufi cikin gidan.
Yana shiga falon Ya hango Unaisah tare da Danish su biyu zaune kan rug, sun tasa notebooks agaba tana koya mashi karatu, tsakanin jiya izuwa yau, ta janye sharuddan data gindaya mashi duk da bata sakar mashi fuska.
Sam basu lura da shi ba, har saida yayi masu gyaran murya kafin suka dago tare da kallon shi, suna ganin shi suka mike tare da gaishe da shi ya amsa masu sam ba walwala ya dubi Danish.
"Inason yin magana dakai" ya faɗa tare da juyawa ya nufi upstairs
sai da ya fara kallon Unaisah tace"yana jiranka, ka tafi, ni zan tsaya anan idan kun gama maganar sai mu ci gaba da karatun"
amsa mata yai da toh kafin Ya bi bayan Salsabeel, a dakinsa Ya same shi tsaye, cikin lalama Salsabeel Ya fara magana.
"Danish ka bani mamaki! Ina hankalinka da tunaninka suke? Kamar baka da zuciya a kirjinka ka rasa su wa zaka rufa ma asirin sai waɗanda suka cutar da rayuwarka? Danish baka da burin daukar fansa akansu? Ko dan saboda mu kawo karshen zaluncin su mu kuma ceto rayuwar sauran yaran dake a hannunsu yakamata ka basu hadinkai, mutanan nan sun shirya tsaf don sukai farmaki a mutu ko ay rai kai kadai suke jira pls Danish kada ka bani kunya mana, a yadda nasanka kai mutunne mai tausayi da son taimako kuma da kake cewa sune iyayenka masu sonka karyane elders baxasu taba zama masoyanka ba iyayenka daka kullata a ranka zai iya yiyuwa basu suka sadaukar da kai ba suma suna cen suna kewarka ka wani ne a danginka kayi tunani mana. .." tunda ya fara maganar facial expression din Danish bai nuna ya karaya da kalaman Salsabeel ba.
Bai ma bari Ya karasa maganar ba, Ya katse shi da cewa'I can't, please don't pressure me i don't want anything to disturb my peace of mind, Salsabeel you know who the elders are! basai nayi maka bayani ba, ka kuma san su wanene Evil giants, sannan ka san kurkukun kaddara gaba da baya, tayaya kake tunanin zasu iya kai masu farmaki su yi nasara akansu? Inajiye masu tsoron su rasa rayukansu saboda basu da karfin da zasu Iya cin galaba akan su"
bai kare maganar ba Salsabeel Ya katse shi cikin marairaice fuska yace"Danish! Wannan ba hujja bace! Allahn daya halicci elders din shi ne zai basu nasara, saboda sun dogara da shi kuma sunyi imanin zasu iya cin galaba akansu, kawai ka yi abun da suke so"
"Bazan ta6a fahimtar abunda kake fadi ba, ka daina wahalar da kanka salsabeel, banaso mu samu sabani atsakaninmu pls na roke ka ka kyaleni, kaima kuma ka fita sabgarsu in har ba so kake rayuwarka ta salwanta ba..."
duk yadda Salsabeel yaso ya shawon kanshi Yaki fahimtarshi ya kangare ya sanya taurin kai da kafiya, tun yana lallaba shi ta lallama har takaiga Ya cakumi Gaban rigarshi da hannayenshi cikin jin kunar rai ya dinga zazzaga mashi masifa kamar zai rufe shi da bugu ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a karashe yace tunda na bika ta lallama ka ki bani hadinkai, zan bi dakai ta tsiya ne, hanyar da baka isa ka guje mata ba, dole kaje ko kana so koba so.."
bayan ya fita daga dakin akan stairs ya tsaya yana faman fitar da hucin bacin rai, yaji haushi da takaicin hali irin na Danish, duk da yanayi mashi Uziri saboda sanin cewa bashi kadai bane har yanzu elders suna iya sarrafa shi amma A halin Yanzu daga zuciyarshi ne bawai Evils din jikinshi bane.
Abunda ya fahimta dangane da Danish baya son rabuwa da Unaisah shiyasa yaki basu hadin kai, gani yake kamar in yabisu suka je kai farmakin rayuwarshi zata Iya salwanta batare daya cika burin shi akan Unaisah ba gyaɗa kai yai da alama ya kamo bakin zaren saukowa down yayi bai ganta a falon ba, kaitsaye ya wuce bedroom din su, yayi knocking almost 3 times kafin ta buɗe mashi kofar yaci sa'a ita kadai ce a ciki.
"Ya salsabeel yau kai ne adakin mu" dakyar ya kakaro murmushi kan fuskarshi yace"ni ne Unaisah, tun da kika ganni kinsan abune mai mahimmanci ya kawo ni gurin ki"
cike da mamaki tace mashi toh, daga gefen gadon suka zauna suna fuskantar juna, ta tsare shi da idanunta cike da ƙagarar son jin wata magana zai mata
"Unaisah Kin san meya faru lokacin da chief ya shiga da Danish Questioning room a headquarter wanda yayi silar fusata Omar har suka samu sabani..." aɗan ruɗe ta girgiza mashi kai"ba komai na sani ba, kaɗan na fahimta daga furucin ya omar"
Nan take Salsabeel Ya labarta mata abun da Ya faru tsakanin Danish da Chief,shi ma abakin big guy yaji komai.
ranta ya sosu da jin abunda Danish yayi ma chief, babban abunda ya fi bata takaici daya ce ma chief ba gaskiya ya ke faɗi ba, they've never hurt him Suna sona shi kuma sune iyayen shi, bayan su bashi da wasu iyaye a duniyar ranta yayi mugun 6aci ba kaɗan ba, sam ta kasa magana sai jinjina kai take.
"Unaisah babu irin magiyar da banyi ma Danish ba, akan ya amince ya basu hadin kai yakiya, nayi lallashin nayi roƙon duk abanza wlh da raina ya baci kamar in rufe shi da bugu saboda ya bata min rai..." ya faɗa rai a6ace ya ɗan dakata Yana kallon unaisah dake kallon fuskarshi
"Wallahi da ace zan iya jagorantarsu zuwa gidan kurkukun kaddarar da tuni nayi hakan Unaisah, sai dai ni yanzu bani da wani karfin ikon da zan iya yin hakan, bayin Allahn nan sun shirya tsaf sun tanadi rundunar sojoji da makaman yaƙin da zasu farmake su abu ɗaya ne zaiyi masu cikas wanda zai yi masu rakiya zuwa gidan kurkukun kaddarar, Unaisah basu san hanyar da zasu bi ba, ba su san a daidai ina ginin yake ba! Shin akan ƙasa Yake ko karkashin kasa Yake? Bayan haka ke kinsan yadda ginin yake wani irin kurman ginine mai rikitarwa da tsoratarwa in har mutun baida ilmi akan shi wlh tuni zai zauce, Danish shine makamin da zamu iya tunkararsu da shi ..." da yai wanann maganar bakomai ta tuna ba face lokacin data saci hanya ta fita matakalar bene ta dinga mayar da ita baya, ga wannan rudin mai rikita kwakwalwar mutun ya dinga ganin abun da babu azahiri.
"Kinyi shiru baki ce komai ba, yakamata Mu ne mi mafita Unaisah, In ba haka ba elders zasu cigaba da aikata zalunci, kwara muyi amfani da wannan damar kada muyi gangancin da zata kubce mata..'
tsantsar damuwace akan fuskarta cikin sanyin murya tace"Yaya Salsabeel menene mafita? Kafi kowa sanin halin Danish, Yana da taurin kai da kafiya, Idan ya fadi abu babu wanda Ya isa Ya canza ra'ayin shi...." bata ƙare maganar ba, Salsabeel yai saurin furta"akwai mafita Unaisah" a kagare tace"menene mafita" shiru yayi jim yana jin shakkar yadda zata dauki abun amma daya tuna irin burin da take dashi na son ruguza kurkukun kaddara sai ya samu kwarin gwiwar ce mata"Unaisah, duk duniyar nan mutun ɗaya ne kacal zai iya tursasa mashi Ya bashi umarni kuma Ya bi shi sau da ƙafa..." da ruɗu akan fuskarta tace"wa kenan"?
Nuna ta yai da index finger din shi waro idanu waje tayi kamar wadda taji wani mugun abu
"Ke Unaisah! Basai nayi maki dogon bayani ba, kin riga da kinsan irin tsantsar kaunar da Danish ya ke yi maki, wanda ko sauran yan uwanshi da suka taso atare bai ta6a yima kwatankwacin shi ba, wlh nayi imanin in har kika bashi umarni yaje zai je..."
da matukar tashin hankali ta girgiza mashi kai labbanta na rawa tace"I can't... I can't change his mind Danish won't listen to me ya Salsabeel kai fa ka fadamin wasu lokuttan ba shi bane zai iya wuni baya a hayyacinsa taya kake tunanin zan iya bashi umarni ya bi"?
Ta fada idanunta azare take kallon shi, ita babban tashin hankalinta a haɗa ta dashi don ta shawo kanshi bataso su sake samun sabani bayan haka tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar masoyinta cikin haɗari, da alama soyayyarshi na nema ta rufe mata idanunta..
"Unaisah Zaki Iya, Ko ba don saboda son da yake yi maki ba, idan ba zaki manta ba na ta6a fada maki dalilin dayasa suke kiranki da kaddarar kurkuku" kura mashi ido tayi batare da kyaftawa ba.
"Ma'anar hakan shine ke kaɗaice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara! Kamar yadda yazo a allon tsafin su, duk da bamu da tabbaci Allah kadai yasan gaibu amma In Allah Yasa hakan ya zamana gaskiya ne kinga kenan wannan wata hanyace da zaki yi amfani wurin kawo karshen su, Ki zamar masu mummunar ƙaddarar da zatayi silar tarwatsa su.
maganar salsabeel ta farfado da tunaninta na son kawo karshen kurkukun ƙaddara amma bataji zata iya tursasa danish don ya yi masu jagora.
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"ya Salsabeel na fahimce ka, amma bana jin zan iya tursasa ma Danish, Ina matuƙar jin tsoron in jefa rayuwar shi cikin hadari, in har wani abu ya faru dashi bazan ta6a yafe ma kaina ba, idan ma zuwan ya zama dole sai da shi to ku haɗa da ni.
kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya tokare makogwaronta nan hawaye suka dinga zarya kan kuncinta.
Zuciyarshi taso ta karaya da maganarta,
Shesshekar kukan tane Ya fargar da shi, Cikin sigar lallashi yace"in har kin yi imanin cewa Allah shi ke tsare bawansa bai kamata kina tunanin Zai rasa ransa a gurin Yaki ba, ay bashi kadai zaije ba Unaisah baga mu ba ko mu baki damu mu mutu ko muyi rai ba? Wlh Unaisah jininmu akan akaifa yake babu gudu ba ja da baya ko da zamu rasa ranmune sai mun yi yaƙi da dukkan karfin mu, mun dogara da Allah kuma munyi imanin shine zai bamu nasara akan kyakkyawar niyar da muke da ita na ganin mun kawo karshen zaluncin kurkukun kaddara...."
Kwata kwata bata gane me yake cewa ba, ita fa damuwarta akan Danish ne cikin karyayyar murya tace"ni abun da nafi jimawa har yanzu shi ba musulmi bane, I don't want him to lose his life as an unbeliever! ya makomarsa zata kasance?..." ta faɗa tana kallon fuskarshi da idanunta wadanda suka kaɗa jawur da su
shi kanshi abun na damun shi, baida burin daya wuce Danish ya musulunta ko dan ya tsira da imaninsa, amma yasan bamai yiwuwa bane in ba wani iko na Allah ba, saboda wadannan evils din na jikin shi.
"Mu cigaba da taya shi addu'a in sha Allah zai musulunta, ni dai yanzu damuwana ki yi kokari kisa ya amince mana..." kifa kanta tayi jikin pillow, sam bata son maganar gani take kamar tursasa mata yakeyi don ta ingiza danish ga fadawa halaka..
Sarai ya fahimci daga ita har Danish din Giyar soyayyace ke dibarsu, shiyasa har suke neman su bijire..
Gwiwar shi ta sage, cike da rashin kwarin jiki Ya miƙe ba tare daya kauda idanun shi daga kallon ta ba Yace"banzo nan donna bata maki rai ba, kodan na tursasa maki nazo ne don mu hada hannu gurin cimma burin da muka dade muna jiran ranar da zamu aiwatar da shi, kada ki manta nayi ma mahaifiyata alkawarin zan kawo karshen zaluncin Elders bayan haka kema kin min alkawari watakil Yanzu kin manta nasani..." wani irin radadi take ji acikin zuciyarta tana maijin bakin cikin gaza amsa mashi bukatar shi
"Zan tafi Unaisah, ki zauna kiyi nazari da hankalin ki, Zan jira har zuwa lokacin da zaki aiwatar da abun da na sanyaki, bana so kiyi danasani mara amfani..." ya fada tare da juyawa ya nufi kofar fita daga dakin Harya ruke handle din Ya dan dakata tare da juyawa ya dube ta, still bata dago da kanta ba sai kuka take yi
"Kina tunanin zaman Danish agidan nan shi zaisa Ya tsira da ranshi? Abunda baki sani ba dokar elders ce duk wanda ya san sirrinsu dole su kashe shi, in har baije Ya farmakesu ba, to su zasu farkama ke shi ne akowani lokaci" ya na fadan hakan yasa kai ya fuce
Fitar shi keda wuya ta kuma fashewa da wani sabon kukan kamar ranta zai fita, maganar salsabeel ta fara tariyowa farkon haduwarsu agidan kurkukun ƙaddara
_inaso ki ɗaurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ƙarshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matuƙar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ruƙo a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka_
_"NAYI MAKA ALƘAWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ƙarshen su, Bi'iznillahi_
Tuna wannan yasa ta ƙara sautin kukan nata.
A bangaren Salsabeel bayan ya koma backyard din kamar yadda yabarsu Chief haka ya taras da su zaune suna jiran shi.
Bawan Allah duk Ya rasa kuzarin shi, su Unaisah sun bata mashi rai ba kaɗan ba..
Hankalin su baya akan shi har saida yai masu sallama kafin su ka dube shi, zama yai kan kujera ya sunkuyar da kan shi ƙasa tun daga yanayin shi suka fahimci akwai damuwa..
"Salsabeel ka yi shiru baka ce mana komai ba! Ya kuka ƙare da shi"? Cikin kulawa Taj yai maganar..
Cike da jin nauyin su ya girgiza kai,
"Danish ya bani kunya, ban ta6a zaton zai bijire min ba..." tun da suka ji hakan damuwa ta bayyana akan fuskokin su don sun riga sun hasaso karashen zancen na shi..
Rai a6ace Omar yace"meyasa zamu wahalar da kanmu akan shi? Yaron nan fa ɗan rainin wayau ne, idan muka ce zamu bishi ta lalama bazai ta6a bamu haɗin kai ba, kwara mu bi shi ta ƙarfi da yaji mu ci ubanshi har sai ya miƙa wuya..."yana huci ya faɗa kamar zai haɗiyi zuciyarsa saboda bacin rai..
Chief ya ɗaga mashi hannu badan Ya ƙarasa maganar ba yaja baki yayi shiru fuskar shi a murtuke..
"In har bashi yayi niya ba, ko da zamu rasa damar da muke da ita na zuwa gidan kurkukun bazan bari a tursasa masa ba, itama Unaisah ban amince ayi amfani da ita gurin shawo kan shi ba, cos zai ga kamar ni na sanya ta ne" Salsabeel ya ɗan kalle sa cos shi harya riga daya tuntu6i Unaisah.
Cike da takaici Big guy ke kallon chief da yai maganar
"Haba Owais, Saboda shi kawai zamu fasa niyar mu"?
"Omar, ba ina nufin zan fasa aikin mu bane, sai dai mu nemi wata hanyar..." bai ƙare maganar ba, Big guy ya mike yana huci ya kama hanya zai bar backyard din..
Damuwa ta hana Taj furta kalma baima san me suke cewa ba.
Miƙewa chief yayi da sauri yabi bayan Omar, don bazai bari su sabamu sabani tsakaninsu ba dama kwanakin nan yana jin haushin fifita Danish da yake yi.
Bayan tafiyar su, ya rage saura Taj da Salsabeel sunyi shiru babu mai magana acikin su.
Ganin yadda Taj ya zabga uban tagumi ne yasa Salsabeel furta"Sir are you Okay"?
Yamutsa fuska yai"kada ka damu, i'm okay, just banji dadin yadda ɗan uwanka yaƙi bamu haɗin kai ba" ya fada yana kallon Salsabeel
"Amma Salsabeel babu dabara da zamu iya yi don mu shawo kan shi"?
Shiru Salsabeel yayi yana nazarin maganar shi, wata dabara ce ta faɗo mashi arai da sauri Ya dubi Taj
"Akwai hanya ɗaya" akagare Taj yace"Ina sauraronka"
"Ƴarka Unaisah, Ita kaɗai ce zata Iya sa shi dole yayi..." lokaci ɗaya Taj ya haɗe rai, annurin fuskar shi ya ɗauke, saboda zafin maganar Salsabeel daya ji.
"Meyasa kace haka"?
Murmushi Salsabeel ya ɗanyi kafin ya fara zayyana masa dalilinsa nacewa haka!
"in har ta umarce daya je zai je, saboda ya mutu akan Sonta, ba irin magiyar da banyi mata ba akan taje ta rokar mana shi amma taƙiya saboda gudun kada ta yi silar da zai rasa ranshi, amma ina da tabbacin in har ka yi mata magana zamu iya cin galaba akan ta saboda kai mahafinta ne, bazata ki bin umarninka ba"...
Tun da ya fara magana Taj ya tsare shi da ido batare da kyaftawa ba, bakomai yake tunawa ba face abunda idanun shi suka gane mashi, ɗari bisa ɗari ya yadda da maganar Salsabeel saboda shi shaidane akan mahaukacin son da suke ma junan su, duk da ya ɗauke ƙafa akanta amma yana jin zai iya zuwa gurinta don ya jarabata"
Har salsabeel ya ƙare maganar Taj bai sani ba, gyaran muryar da yayi mashi ne ya fargar da shi
"Pls, ka taimaka koda sau ɗaya ne ka jaraba yi mata magana.." fuskar shi amarairaice ya fada..
Wayar Taj ce tay ringing, kallon Salsabeel yayi"it is Okay, zan jaraba" ya faɗa tare da miƙewa Yai picking call din
"Sir, ina fata lafiya, naji shiru baku dawo ba"
"Boss, Ka sallami Salsabeel ya tafi, kaima zaka iya tafiya..." amsa mashi yai da toh..
"Chief yace ka tafi, zai neme ka" mikewa yayi"pls sir, sai naji daga gare ka" jinjina mashi kai yai batare daya fur ta kalma ba.
_________________________________✍️
Su Batool na zaune a falo suna fira kusan su dukkansu in ka cire Unaisah da Danish sai ummi su kadai ke babu a cikin su...
Sam basu lura da shugowarshi ba fira taja hankalin su, ganin babu Unaisah yasa shi juyawa ya nufi bedroom din...
Adai dai lokacin ta fito daga bathroom, sanye da yar rigar wanka, zuciyarta cike fal da tunanin abunda suka tattauna da Salsabeel
Wayar ce ta fara ringing, har zata dauka taji anyi knocking din kofar
"Wanene"?
"Ki buɗe kofar ki gani" ras ta ɗan ji gabanta ya fadi jin muryar daddynta, tana jin shakkar shi yanzu ba kadan ba saboda canzawar da yayi mata.
"Unaisah ba zaki buɗe min ƙofar bane"! Jikinta na 6ari ta je ta buɗe ƙofar, shigowa ciki yai tare da aza idanun shi kan fuskarta wani irin tausayinta ne ya kama shi.
Cikin rawar murya tace"daddy Ina wuni" ta fada tana kallon shi
Shiru yayi bai tanka mata ba hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.. Kasa jurewa tayi batasan sa'adda ta faɗa kan kirjin shi ta kankame shi tana tana kuka tace laifin me na maka daddy? Meyasa ka canza min? Ka daina sakar min fuska, idan na gaishe ka dakyar kake amsa min idan na kira wayarka baka ɗagawa, daddy don soyayyarka da manzon Allah ka fadamin laifin me nayi maka sai in nemi yafiyarka, wlh bana so kana fushi dani Daddy, kaifa mahaifina ne kasan hukuncin wanda iyayensa ke fushi da shi ...."sambatu taci gaba dayi batare data raba jikinta daga nashi ba..
Zuciyarshi ta karaya da jin furucinta, ta bashi tausayi ba kadan ba, ga kaunarta dake kara ninkuwa cikin zuciyarshi, jiya dakyar ya runtsa hatta Danejo saida ta lura da yanayin shi ba irin magiyar da batai mashi ba akan ya fada mata gaskiyar abunda ke damunshi amma yakiyi saboda bazai iya tona ma yarsa asiri ba, kamar tona ma kansa ne..
Baiwar Allah muryarta harta disashe, Unxpectedly taji ya ɗaura tafukan hannyenshi akan sumar kanta ya ɗan shafa bayanta cikin sigar lallashi
Kafin ya fara magana
"Unaisah, kin bani mamamki, kinyi min abunda ban ta6a zato ba..." a firguce ta dago tana kallon fuskar shi
"Ina yi maki kallon mai hankali, kuma mai jin tsoron sabawa Allah ashe nayi kuskure Unaisah, na yaudari kaina.." cike da tashin hankali ta furta"daddy ni din? Me nayi maka"? girgiza kai ya danyi cike da takaici ya zayyana mata abunda Ya taras sunayi adakin Danish...
Dafe kai ta yi da tafin hannunta, wani irin faduwar gaba da tashin hankali taji
"Idan shi jahili ne baida addini, ke ay ba irinsa bace, Kinsan babu kyau unaisah, ina tarbiyar dana baki? Baki ji komai ba kika biye mashi kuka rungume juna, haba Unaisah baki kyauta ma kanki ba, nima kuma baki kyauta min ba, wlh kin karya min zuciyata, kin samin fargaba saboda zullumin kada ya lallata min rayuwar yata...."
kusan suman tsaye tayi, jikinta ya fara kakarwa kamar mazari ga kunyar shi data lullu6e ta, tasan bata da gaskiya shiyasa ta sunnar da kanta ƙasa cikin sanyin murya ta furta"daddy, na kar6i laifina, amma dan Allah kada ka zarge mu, wlh bamu ta6a aikata wani abu daya sabama Allah ba, duk da Danish baida addini ba ɗan iska bane daddy, bazaiyi abunda zai cutar dani ba, idan yayi ba daidai ba ina faɗa masa babu kyau a addinina kuma baya musa min, abun da ya faru ranar bana a cikin hayyacina daddy, hankalina ya tashine naji matuƙar tausayin shi kuma naji tsoron kada na rasa shi shiyasa na rungume shi, amma wlh ba shine ya fara rungumata ba, ni ce daddy...."
yanayin yadda take yi mashi magana jikinta na kerma ba karamin rauni ta sanya mashi ba, yayi niyar yayi mata fada sosai amma sai yaji bazai iya ba, ya yarda da maganarta yasan Unaisah bazatai mashi karya ba.
"Meke atsakaninki da shi"? Ya tambaya yana kallon ta
Kamar mai in ina ta fara yan kame kame tana fadin"amm..umm..dama.."ta ɗan kau da idonta gefe kamar bazata karasa maganar ba tace"bazan boye maka ba, dama najima inason in faɗa maka, nasan zaka goya min baya akan abunda nakeso...." tashin hankali idanun shi aware yake kallon ta.
"Daddy Allah ya jarabce mu da son juna ni da danish, soyayyar dake tsakaninmu bazata misaltu ba, har rayukan mu zamu iya sadaukarwa akan junanmu, daddy wlh ina son danish, shi kadai ne namijin da nake da burin in aura..." bata ƙare maganar ba, sakamakon tsawar da Taj Ya daka mata wadda tay silar rikicewarta arazane Ta zazzare grey eyes dinta akan fuskar shi Yana faman fitar da huci yace"Impossible Unaisah! Wlh bazan lamunta ba, ba zaki sa nayi karamar magana ba, baki isa ki kunyata ni ba, kina hauka ne unaisah? Meye abunso atare da shi? Yaron da baida adinini arne ne, ga jahilci cike da kai, sannan bashi da wani galihu, bayan haka ina yake da halin da zai iya ruke min ke!?
wani irin jiri jirin tashin hankali ta gani acikin idanunta kalaman daddynta sunyi matuƙar ɗaga hankalin ta, tayi mamakin furucin da yayi akan danish kamar dai ya manta cewa komai ya faru arayuwar shi bayin kan shi ba ne...
"Unaisah Ina burin da kike shi na son auran attajirin me kuɗi? Mai ilmin addini dana zamani mai cikakken asali wanda zai gatantaki Ya tarairayeki ya baki kyakkyawar kulawa?
"Daddy, na jima da soke wannan burin, ba dole sai na auri miji mai kudi zan samu farin ciki ba, sau dayawa wasu masu ilmin basu aiki da shi daddy, ni kawai miji na gari nake nema kuma na samu daddy, duk abunda ka lissafa Danish zai iya bani fin su, saboda yanayi min soyayyar da bazai iya cutar dani ba, yana yi min son da zai iya hana kanshi farin ciki saboda farin ciki"
Ta ɗan numfasa kafin taci gaba da cewa" ka kira shi jahili daddy banji dadi ba, bayan kasan ba shi yaja ma kanshi hakan ba, idan ka amince min, zanyi amfani da son da yakeyi min in musuluntar da shi..."
bata ƙare maganar ba, Ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu! wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makogwaronsa, Ya ma rasa me zaiyi ya huce haushin sa, Yayi mamaki wai har Unaisah ta iya gaya mashi da bakinta bata ji kunyar shi ba lallai ba karamin so take ma shi ba, zata iya komai akan shi..
Kafadunta Ya dafa da tafukansa Ya jijjigata har saida Sumar kanta ta yarfo ta gaban fuskarta fashewa tayi da kuka don ta gane bai fahimce ta ba..
Da kakkausar murya ya furta"Bazan ta6a amince ma soyayyarku ba, ba son shi kike ba, tausayin shi kike ji, tun wuri ki cire zancen zaki aure shi, saboda na riga da nayi maki miji sadakinki ne kadai bai biya ba, kuma yana sonki, shine za6ina unaisah in har ba bijiremin zakiyi ba, bana so ki bani kunya kada kisa na karya alkawarin da nayi masa, ki cika min burina Unaisah, danish ba dole saida ke zai iya rayuwa ba, ga sauran yan uwanki nan sai ya zabi daya acikin su, Unaisah burin kowace uwa ta sama ma ya'yanta uba nagari ba jihili ba.
abun da Taj bai sani ba tuni tajima da sumewa, idanunta daya gani a kakkafe shi yasa shi gane hakan..cikin jin faduwar gaba ya hadiye sauran maganarshi da bai amayar ba, saboda tashin hankali, Ashe nashi wasane bai ta6a ganin true love ba sai yau, ay yayi zaton daga layla da majnoon andaina samun irin soyayyar nan, sungumarta yayi kan fadar shi ya kwantar da ita kan gadon su, Ya fito daga dakin jiki na kerma Ya tafi dauko ruwa kafin dawowar shi, Batool ta shigo dakin fuskarta dauke da murmushi ta zauna gefen gadon tana kallon wani sabon salon kwanciya agurin Unaisah, tayi zaton dadin baccine yasa ta dauki tsawon lokaci bata leko waje ba.
"Sister Ya kamata ki tashi, Aunty Ummi ta hanamu baccin marece.."
ta fada tare dakai hannu ta ɗan bubbuga ƙafar Unaish shiru bata farka ba,
"Unaisah wani irin bacci ne wannan kamar mai fama da cutar bacci" ta fada tana kara bubbuga legs din ta.
Adaidai lokacin Taj ya fado dakin hannun shi ruke da robar ruwa me sanyi, Yana ganin Batool yaci burki gaban shi na faduwa yasan muddin tasan Unaisah suma tayi sai ta yi kukan da zai jawo hankalin sauran yan uwanta.
Jin motsin adakin yasa Batool ta juyo ganin daddyn Unaisah yasa ta miƙe da fara'a tace"ina wuni daddy, i'm sorry watakil ka yi sallama banji shigowarka ba..." yawu ya haɗiya dakyar ya tattara nutsuwarsa yana kokarin danne damuwar shi yace"lafiya lou daughter.." da alamun rudu kan fuskarta tace"daddy naga water bottle a hannunka.." washe baki yayi"eh ni zan sha ne, kishi nake ji" murmushi tayi"ko kazo ganin Unaisah ne" a kagare ya daga mata gira"bacci take, yanzu nake kokarin tadata" da sauri yace"kinga bari ni in tashe ta, kije gurin ummi naji kamar tana nemanki..." kamar taso ta ɗago shi, ta lura kamar wani abu badaidai ba, amma sai batayi mashi gaddama ba, ta fuce daga dakin, ajiyar zuciya ya sauke bayan ya datse ƙofar dakin, ya zauna gefen gadon da sauri ya cire murfin robar ya yayyayafa mata ruwan kan fuskarta.
dogon numfashi taja tare da sauke ajiyar zuciya..
"Unaisah, Pls ki yi hakuri ki tashi, kinji! I won't hurt you anymore..."
dakyar ta iya buɗe idanunta wadanda suka kada jawur ta dube shi
Wani irin ciwon kaine Ya far mata...
Cikin disasshiyar murya tace"daddy, kada ka raba ni da Danish, zan iya rasa raina.."
Kwata kawata baya son tana fadin zata rasa ranta akan Danish, Ranshi baci yake kamar ya hadiyi zuciya, kuma yana akan bakanshi bazai janye ba.
"I'll think about it, Yanzu bana son duk wani abu da zai ɗaga hankalinki, kwanciyar hankalinki nakeso..." hankalin ta ya ɗan kwanta, gani take kamar daddynta zai duba mata ne.
"Amma daddy, baka son Danish ko"? Girgiza mata kai yai"Ina son shi Unaisah, Kuma ina jin tausayin rayuwar shi, maganganun da kikaji nayi ɗazu rainane Ya 6aci bawai don ina nufin hakan ba, ni kawai banaso kina sakar mashi jikin ki ne"
cikin kwantar da murya ya faɗa.
Ruko hannun shi tayi a cikin nata"daddy pls ka min alkawarin ba zaka raba ni da shi ba"!
Dafe kai yai da tafin hannun shi, ji yake kamar ya kifa mata mari saboda haushin da yake ji in ta ambaci sunan Danish
"Kina so In amince ma Soyayyarku?In kuma ba shi damar Auren ki"? jin wannan maganar daga bakin daddyn nata yasa ta miƙe zaune cike da zumudi tace"Eh daddy..."
Numfasawa yayi kafin yace"Zan baki Umarni, If you do what I say, I promise to fulfill your dream of marrying your choice".
gabanta ne ya ɗan faɗi duk da batasan umarni da zai bata ba, taji fargaba sosai..
"Daddy, wani irin Umarni ne? Ka faɗa min in sha Allah zan yi maka biyayya" ta faɗa cike da jin fargaban amsar da zai bata..
Ido cikin ido su ke kallon jun.
"ki bashi Umarnin, ya yi mana jagora zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara..."
wata irin razananniyar faduwar gaba taji, kamar zata zauce ta daddafe kanta da tafukanta dama saida ranta ya ayyana mata abun da zai umarce ta da tay...
"Inaso in tabbatar da kaunar da ya ke yi maki, ta hakanne zan gane shin jarumtakarsa takai in mallaka mashi lu'u lu'u na?
ya faɗa yana kallon idanunta da suka rune zuwa Jajawur kamar Jan gauta.
Cikin shesshekar kuka tace"daddy, pls ka bani wani umarnin daban, wannan is too hard for me! I can't force him I don't wanna put his life in danger"
Kwata kwata babu annuri akan fuskarshi, ya haɗe rai sosai saboda yana son ta ɗauki maganar shi serious
"Unaisah, karna kuskura na ƙara ji kin furta kalmar kada ki jefa rayuwarsa cikin hadari! Ke ba musulma bace? Ba kiyi imani da Allah ba? Ko baki yarda da ƙaddara ba? Ko kuwa ƙarancin tawakkali ne ke damunki"? Runtse idanunta tayi tana jin wani iri yanayi a zuciyarta mara dadi
"Ba haka nasanki ba Unaisah! Kin canza min! Ina zuciyar imaninki take? na fahimci so ne ke nema ya rufe maki ido, Unaisah kin manta mummunar ƙaddarar data rabamu? Kin ta6a tunanin zaki ku6uta daga kurkukun ƙaddara? Kin ta6a tunanin zamu sake haɗuwa? Ikon wanene yin hakan"?
In a weak voice tace"Allah"
"Toh inaso ki sanya ma ranki, duk wani abu da zai faru da shi muƙaddari ne daga Allah, tun zuwan shi kurkukun kaddara bazai hana Allah ya jarabce shi da wata ƙaddarar ba, har kwarama yaje can yayi jahadi gurin ceton rayuka...."
nasiha ya cigaba dayi mata tun bata fahimtar shi har ta fara yin amanna da maganar shi...
"Daddy, ni damuwana he's not a muslim, banson ya mutu batare daya kar6i kalmatusshada ba"
ta faɗa hawaye na bin fuskarta...
Ruko hannayenta yayi acikin nashi ya ruƙe su gam kafin yace"In sha Allah zai musulunta Unaisah, idan sheikh imam yazo zamu nemi taimakon sa"
"Amma daddy, nima ina neman alfarma agurinka"!
"Wace alfarma"?
"Ku tafi dani, Nima ina son in bada gudummuwata..." waro idanu waje yayi aranshi ya ayyana bazai yiwu ba, amma a fili sai yace"Zan yi magana da chief, kinsan dokar aikinsu babu mace, amma in har ya amince zamu tafi dake" ajiyar zuciya ta ɗan sauke, fatanta Allah yasa Chief ya amince mata, dalilin dayasa ta za6i tabisu saboda abu biyu, na farko don ta kashe Jan wuya, duk da batasan wanene shi ba, kuma batasan ko yana ɗaya daga cikin members na kurkukun ƙaddara ba, sai dai taji aranta dakyar in ba ya cikin Elders, abu na biyu donta ba Danish kariya, koda Ajali zai riske shi, toh su mutu atare zaifi mata kwanciyar hankali.
Kiraye kirayen Sallar isha'i da aka fara yi ne, yasa Taj miƙewa ya dube ta"zan tafi, kiyi kokarin aiwatar da umarnina, in sha Allah silar biyayyar da zakiyi min, ba zaki ta6a danasani ba, saima ya zama silar farin cikin ki na har abada" cikin sanyin murya tace "in sha Allah daddy, zanyi masa magana, duk yadda mukai zan sanar dakai"
"Gobe da safe, in tashi da labari mai dadi" jinjina mashi kai tay
Miƙa mata hannu yayi da sauri ta sauko daga kan gadon ya rungumota, yana ƙara lallashinta da bata baki har saida ya tabbatar taji hudubarshi kafin su ka yi sallama da juna kamar karsu rabu..
_________________________________✍️
Idan muka koma bangaren Benazir sam ta kasa walwala, maganganun Zaki sun tsaya mata arai, sun hana ta sukuni gani take kamar batayi masa adalci ba, tayi kuka sosai har zazza6i saida ya lullu6eta, Wlh Yabata tausayi bata ta6a ganin rauninsa ba sai awannan lokacin, yayi mata taimakon da har abada bazata ta6a mantawa da shi ba, ya bata lokacin shi! Ya bata kulawarshi! Ya bata ci da sha Da suturu harma da aikin yi, ya kuma ruketa agidan sa na tsawon shekara goma sha bakwai bai ta6a goranta mata ba, sun shaku da juna, ya zama tamkar uba agare ta!
babu wanda yasan wani abu dangane da zuwan Zaki, daga Ita sai Alhaji musa suka san da maganar, fatanta Allah yasa kada Uncle musa yayi ma Daddynta maganar don batason duk wani abu da zai daƙile maganar komawarta dakin Mijin ta, taso taji daga bakin uncle me Zaki ya fada masu sai dai takasa ma tunkarar shi saboda bata son taji abunda zai hana runtsawa.
Har kiran Layin Zaki tayi don ta kara bashi hakuri amma kwata kwata kiran baya shiga..
Tunani ta somayi me zatayi don ta saka mashi?
Zuciyarta ta bata amsa da cewa me zai hana ta hada shi da Aneelerh! aranta kuma ta ayyana zaiyi wuya su sasanta cos zaki bazai kara gangancin fadawa tarkon son macen da kaddara ta rabata da mijinta, kamar dai ita 💔
_________________________________✍️
Har wuraren ƙarfe shaɗaya na dare bata runtsa ba, saboda matsananciyar damuwar data addabi zuciyarta, sai faman juyi takeyi kan matress kamar me fama da ciwon ciki, maganganun daddynta dana Salsabeel ne suka dinga dawo mata cikin kwalwar kanta, bata san ya zatayi ba, bata da wata mafita daya wuce ta amsa bukatarsu sai dai tana jin tsoron tayi silar jefa rayuwar man dinta a cikin haɗari amma idan ta tuna burin da take da shi na kashe jan wuya, da kuma nasihar daddynta sai taji kamar ana kara mata kwarin gwiwarta.
*CHIEF OWAIS*
Bacci ya ƙauracewa Idanun shi, Ina zai sa ran shi yaji dadi? chief irin mutanan nan ne waɗanda idan suka kwallafa rai ga abu suka saka buri da naci da komai in har ba su ga sun Cimma nasara ba to fa hankalin su bazai ta6a kwanciya ba..
Ya ƙuntata kanshi Ya hana zuciyar shi sukuni, baisan taya zai 6ullowa lamarin ba, Danish Yana nema Ya zamar ma shi ciwon kai...
Yayin da yake wannan tunanin safa da marwa yake a tsakar bedroom ɗinsa, boxer short ne kaɗai a jikin shi, fuskarshi a yamitse ba annuri..
Jefi jefi in damuwar ta addabe shi tafin hannunsa yake cusa cikin sumar kanshi ya yamutse ta kamar ɗan mahaukaci wani lokaci da karfi ya ke bugun iska da hannayen shi.
Phone ringing dinsa ne ya katse hanzarin shi, kamar bazai duba mai kira ba, zuciyarshi ta takura mashi akan ya duba, juyawa yayi a sukwane cikin rashin kuzari ya dauko wayar dake aje kan mirror chair, yayi mamakin ganin almost 16 missed calls, picking call din yayi tare da kare wayar a kunnan shi yai shiru yana jiran jin me zaice
"Owais, ya ake ciki game da kai farmakin?..."
"Only a few days remain"
"Ko zaka Iya faɗamin menene shirin ku a yanzu ni kuma zan ƙarfafa maku gwiwa"
Har yanzu bai yarda da mutumin ba, shi mugu bashi da kama, zai iya bayyana ta suffar mutanan kirki don ya shiga jikin mutun...
"I'm sorry to say, bazan iya faɗa maka ba, in har dagaske kana son taimakona ba dole sai kaji me muke shiryawa ba"
"Hakane, Ka faɗi gaskiya, Owais, shawarar da zan baku shi ne, Ku sanya malaman addini su tayaku addu'a, sannan ku ma iyayenku magana su tayaku da addu'a, ku kuma yawaita sadaka ga marayu da mabuƙata suma su tayaku da addu'a, ku nemi kariya daga wurin Allah, in sha Allah badai mutun da Aljan ba sai Allah...." bai ta6a jin 6oyayyan mutumin ya burge shi irin na yau ba yaji dadin shawarwarinsa
Har ya buɗe baki zai yi mashi godiya yaji ɗuff yai rejecting call din..
Hakanan Yaji Yana ra'ayin ganin Unaisah, wall clock Ya kalla ƙarfe 11 na dare, yasan i war haka tayi bacci
Jaraba kiran layinta yayi, tana fara ringing ta yi picking yayi mamaki bai zata zata ɗaga ba ..
Kara wayar yayi a kunnan shi yama rasa me zai ce mata.
Sanyayyar muryartace ta ratsa kunnanta
"Barka da dare chief, ka wuni lafiya"?
"Why are you still not sleeping"
"I woke up for the night prayer" yaji dadin jin hakan
"Okay, if you dont mind I want you to bring me the girl's backpack"
"Toh" rejecting call ɗin yayi, sai da yayi unclocking ɗin kofarsa don ta samu damar shigowa, kafin ya shiga bathroom don yayi wanka.
Saukowa tayi daga kan gadon ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta ta cikin madubin.
Silk Pyjama ne a jikinta, riga da wando launin blue sky, rigar tana da dogon hannu sun yi matuƙar yi mata kyau.
Lallausar Curly hair dinta tabi da kallo, duk Ya har gitse saboda rashin kwanciyar hankali ta manta when last tayi fixing dinsa.
Fragrance set ta ɗauko ta feshe ko'ina na jikinta da shi, cikin kankanin lokaci daddadan kamshin turarenta ya buɗe ɗakin
ta ɗauko veil ta yafa ma kanta kafin ta saka flat shoe a kafarta.
Back pack din ta dauko, ta daurata kan mattress, ta curo wasiyar da Unaizah ta bata guda biyu ta boye su cikin diary ɗinta, don bata jin zata iya rabuwa da su tunda kamar amana ta bata, tafison ta damƙa ma iyayenta da hannunta.
Goya jakar tayi abayanta, ta fito daga ɗakin, gidan shiru babu kowa a falon alamar duk sunyi bacci adakunansu..
Bata nufi ko'ina ba sai ɗakin Chief, tana ƙarasa bakin kofar takai hannu zatayi knocking sai taji ƙofar ta fara kokarin buɗe kanta ta ɗanyi mamaki
Almost 3 times tana yin sallama ba'a amsa mata ba, ta kutsa kai ta shiga ciki, bata ga kowa ba, sai dai taji sautin safkar ruwa daga toilet dinsa, wurga ido tayi tare da kallon glass wall din toilet nasa yayi duhu sama ka dai take iya gani..
Gajiya tayi da tsayuwa, ga wata kasala da take ji, wasa wasa ta fara gyangyaɗin bacci, har ta saki backpack din hannunta ta fadi kan floor ba tare data lura ba..
Lokacin daya fito waist dinshi ɗaure da towel fari kyal, fatar shi tayi freshi danshin ruwa ya jiƙata...yana kokarin ɗaga kafa ya nufi dressing mirror ba zato ba tsammani ya hango mutun kwance kan rug kamar an jefar da ita a gurin ta baje sai sharar bacci take yi, ga backpack ɗinta yashe gefe ɗaya...
Yayi mamaki cos bai tsammaci zai iske ta adakin ba, ya daisan ya cire security din kofar, abun da ya fi daure mashi kai ta yadda bacci yayi awon gaba da ita akan rug dinsa, kamar wadda tasha kwaya..
Walking slowly ya nufi rug din Ya zuƙunna daga gabanta, ya nutsu yana kallonta, yanayin yadda take fitar da numfashi cikin nutsu kirjinta na sama da kasa ba karamin tafiya tayi da imaninsa ba, kamar jinjira la66anta sai kerma suke.
Sai yanzu yayi tunani me ya hanata bacci da wuri? tabbas akwai damuwa aranta wanda silar hakan ta kuntata kanta ta hana idanunta bacci shiyasa da tazo dakinshi baccin yaci karfinta har yai awon gaba da ita batare da sanin ta ba..
Baya jin zai iya tada ta daga baccin, bai shirya katse mata jin dadin ta ba, baccin da takeyi sauki ne agare ta.
Yanke shawarar canza mata gurin kwanciya yayi, A hankali ya sanya hannayen shi biyu ya tallabota ya dago da ita tare da miƙewa Ya nufi katafaren gadon shi da ita, kusan itace mace ta farko da zata kwanta akan shi,
A tsakiyar mattress din Ya shimfidar da ita, duk da baccin da takeyi hakan bai hanata jin dadin sauyin gurin kwanciyar da akayi mata ba, numfashinta har canzawa yayi, lallausan duvet ɗinsa ya janyo ya lullu6e ta shi har zuwa kan kirjinta, kasa janye idanun shi yayi daga kallon ta gaba ɗaya ya shagala da kallon kyakkyawar sexy face dinta wani irin yanayi ya fara ji a jikin shi hakan yasa shi saurin miƙewa Yabar gaban gadon, badan bai yarda da tsoron Allahn shi ba sai don gujewa sharrin shaidan...
Can cikin bacci kunnuwanta suka soma jiyo mata daddaɗar kira'ar karatul qur'anin shi, kamar amafarki take sauraron karatun a lokaci yana zaune kan darduma jikinshi sanye da farar jallabiya, raba dare yayi yana kai kukansa gurin Allah, bayan ya kammala ya buɗe kur'ani yacigaba da karantawa.
Yana tsaka da karatun, tayi wani kwakkwaran juyi cikin bacci ta dinga mirgino kiris Ya rage ta kundumo ƙasa, yana gani yai hanzarin miƙewa yai saurin tallabota da hannayen shi biyu..
Zuƙunnawa yayi gaban gadon ya bi ta da kallo, ganin kamar tana kokarin buɗe idanunta, biji biji ta fara ganin kamar mutun a kusa da ita aranta ta ayyana anya ba mafarki take ba"?
Murya na rawa ta furta"Batool" shiru ba'a amsa mata ba
"Aunty ummi" still ba amsa mata ba
"Sajeed" nan ma shiru ba'a amsamata ba
Murza idanunta tayi da yatsunta, don ta samu damar ganin wanene...wani irin faduwar gaba taji lokacin da idanunta suka washe ganinta ya dawo normal, kokwanto ta farayi anya Chief ne? Ko dai mafarki ta ke ba? Taya za'ai chief ya shigo dakin su"? Kwata kwata ta manta abun da ya faru.
Tunani tayi ko Danish ne ya koma mata Chief,
Cikin disasshiyar murya ta furta"Danish"
Jin shiru bai amsa mata ba, yasa ta fara kokarin miƙewa da wata irin kasala a jikin ta, zama tayi tare da jingina bayanta jikin headboard.
"Kin tashi lafiya"? sexy voice dinsa ce ta ratsa kunnanta, firgigit ta ware idanunta sosai akan fuskar shi wani irin faduwar gaba taji, a rude ta kalli bedroom din sai yanzu ta gane adakin wa take..nan take ta tariyo abunda ya faru daren jiya bayan ta zo dakin shi bacci yaci karfinta adakin shi...tsabar rudu jikinta na kakarwa ta zabura zata sauko daga kan gadon ai kuwa gaba ɗaya jiri ya kwasheta kiris ya rage ta kifa kasa da sauri Chief Ya janyota ta fado kan laps dinsa, wata irin kunyace ta kamata, ta runtse idanunta la66anta na kerma tace"i'm really sorry, I didn't know I fell asleep in your room dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini"
Ƙamshin turarenshi ya hana ta ƙarasa maganar saboda ratsa makoshinta da yayi.
Batai aune ba taji numfashin shi na kokawa da nata numfashin
Jin shiru bata ji move dinsa ba yasa ta ɗan kyalla ido ɗaya don ta ga wani hali yake ciki
Unexpectedly suka haɗa ido cikin na juna, sam ta kasa runtse idanunta..
gani take kamar amafarki wai yau gata ga chief, ya ɗauketa kamar yar jinjira..bakomai take tunawa ba face maganganun daddynta, duk da bai fito fili ya faɗa mata wanene mijin da yayi mata ba, taji aranta Chief ne, kuma tabbas taga abunda yake kokarin ankarar da ita, Chief ya haɗa komai da zaisa mace ta so shi.
Matsawo yayi da fuskarshi saitin tata, har tsinin hancinsu ya gogi na juna anata wautar tayi azaton kiss zai mata abaki, gaba ɗaya tabi ta dabarbarce kamar wadda electric shock ya kama, ƙayataccen murmushi ya sakar mata har dimples dinsa ya lotsa aransa ya yi mamakin kamun kanta cos yadda mata ke hauka a kanshi da wata ce ta samu kusancin nan da shi tuni zata ƙwaye masa.
Ya riga da ya fahimci me zuciyarta ke raya mata..
A hankali ya sauke ta kan floor din. da sauri ta miƙe tare da sunnar dakanta kasa.
Veil dinta dake ajiye kan gadon shi ya dauko ya yafa mata akai tare da naɗe mata shi.
"Thank you.." tafiya tasoma yi zata bar dakin ya dakatar da ita"ban gama magana da ke ba" tsayawa tayi tare da juyowa ta dube shi
Zama yayi gefen gadonshi, da yatsan shi Ya nuna mata backpack din data kawo ma shi
"Buɗe min jakar" da sauri ta dawo ta zukunna ta bude backpack din..
"Ki curo komai dake aciki" ta amsa mashi da toh, bayan ta kammala curo kayan dake a cikin jakar ta jerasu kan floor.
"Ki buɗe min textbooks din, Inason ganin meke a cikin su.."zama tayi dirshan kafin ta fara bude shafukansu harta kammala Ya rage saura Diary din Unaizah..
"Zaki iya karanta min" ɗaga mashi kai tayi alamar eh a gogo ya kalla saura rabin awa afara kiran sallah asubahi.
Kasa kunne yayi yana sauraronta, yayin da idanunshi ke akan tausasan pinkish lips dinta ta zaƙe sai karanta mishi takeyi da zazzaƙar muryarta.
Kafin ta kammala karantawa tuni idanunta sun cicciko tab da kwalla, saboda akwai chapters na rayuwar Unaizah da suka ta6a zuciyarta, duk wani abu daya faru da ita mai dadi ko mara dadi sai da ta rubutashi.
shi kanshi chief dake sauraronta zuciyarshi ta karaya da jin irin rayuwar sharholiyar da yarinyar tayi tare da iyayenta batare da sun tsawatar mata ba, saima suka bada gudummuwar gur6ata rayuwarta, hakan na nufin dama cen mahaifinta ya sadaukar da ita shiyasa ya wulakanta rayuwarta ya hana tasan addinin shi don kada Allah ya tuhumeshi aranar gobe kiyama saboda shi jaki ne.
Cikin shesshekar kuka tace"na gama karantawa"
Mika mata hannu yayi ta bashi diary ɗinta, shafin farko ya duba shi anan yaci karo da corners na hotuna guda uku babu biyu sai ɗaya daya rage na Unaizah.
A cikin zuciya ya karanta sunayen dake akasan gidan hoton
_My lovely dad, Red Neck, and my first love, my momma, and me, Unaizah, Yar gidan daddy_
ya shafe mintuna Yana kallon hoton Unaizah ya rasa a ina ya ta6a ganin fuskar nan!
"Red neck, sunan wanene"? Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar shi
Sai lokacin ta tuna da sunan mahaifin Unaizah, da sauri tace"Nickname din daddynta ne, Jan wuya" jinjina kanshi yayi
"Kin ta6a buɗe diary din nan"?
"Eh, amma ban ta6a karanta rubutun ciki ba sai yau" Ya juyo mata shafin farko da yatsa ya nuna mata wurin da ya kamata hotuna su kasance.
"Ina waɗannan hotunan suke, ko lokacin da kika fara buɗe diary din haka kika gan shi da hoto ɗaya"?
Bata san ya akai ta tsinci kanta da jin faduwar gababa, shiru tayi tana kokarin tunanowa sai dai ta kasa,
ganin kamar ta rudene yasa chief aje diary din, Ya janyo drawer chest din gadon shi, Ya curo diary dinshi hadadden gaske, mai gidan key a jikin shi ya buɗe tare da nuna mata shafin farko, Hoton daddynsa ne mai girma sharafuddeen tare da Mommynsa Malikat sarauta, Ga hoton shi a tsakiyar nasu lokacin baifi shekara shabiyar ba.
"Kinga yadda nawa ɗiary din Yake! Kuma naga kamar kusan iri ɗayane da nata, zai iya yiwuwa akwai hutanan a jiki cos ga shaidanan alamar an ta6a manna hotuna a jikin corners din, watakil cikin rashin sani kin ta6a buɗe diary din hotunan suka faɗi without your knowlegde" ❓❗❔❕
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: __________________________________💋✍️💋🌹🔥🫀💘
a ruɗe ta kalli fuskar shi, ya haɗe rai kamar ba daddynta ba, ta rasa gane meke faruwa da shi ne.
Babu wanda Ya lura da abunda Ya faru tsakaninsu, Hankalin yan uwanta baya akan su
Duk da haka bata kawo komai a ranta ba, ta kuma cewa, "Daddy, Chief ya fada maka an ga Danish a cikin toilet ɗinsa...." banza yayi da ita tamkar bai ji maganar ba, hakan ba karamin ɗaga mata hankali ya yi ba.
komawa tayi cikin yan uwanta jiki a mace ta tsaya zuciyarta cike fal da tunanin sauyawar daddyn nata, fatanta Allah yasa ba wani abu ke damun shi ba.
Walking slowly yake taka stairs, da karfi Jemimah ta furta sunan Danish hakan yaja hankulansu gaba daya suka kalli stairs din bakunansu a buɗe saboda tsantsar kyan da yayi, wata hadaddiyar light grey thobe ce a jikinsa ta bi surar jikin shi, ya ɗaure sumar kan shi with hair ties, gaba daya sun shagala da kallon shi, ƙasa-ƙasa da murya ummi ta furta Tabarakallahu ahsanil khalikin, Allah yayi halitta..."
A second to the last step na stairs ɗin ya ɗan dakata da yin tafiyar jin alamun kamar ana kallon shi kafin ya ɗago da ido ya dube su, motsin buɗe kofar falo yaja hankulan su.
Gaba ɗaya hankalinsu ya koma kan masu shigowa, Big guy ne ya shigo da sallama a bakin shi, kafin U.s armies din suka shigo kowannansu suit ne a jikin shi...zuba masu idanu su ka yi kamar ba su gane su ba, sun yi shiru suna kokwanton anya su ne? Saboda basu tsammaci zasu gan su ba.
Dakatawa su ka yi da yin tafiyar suna kallon su kusan su shida suna jira suga reaction din su, Wani irin ihun farin Ciki Gabriel Ya saki, da gudu Ya nufi Lieutenant thompson Sojan daya taimake shi a dajin evil forest saboda sarkar cross din shi, kafin Ya ƙaraso thompson Ya bude mashi hannayen shi ya fada jikin shi yayi hugging din shi gaba daya suka fashe da dariya.
Wayyo Allah daɗi da wani irin farin ciki sauran ex-prisoners suka nufe su kafin su ƙaraso suka miƙa masu hannuwansu don su yi hugging din su, aiko suna ƙarasawa ƴan matan suka ƙi bari su yi hugging ɗinsu sai dai suka yi shaking hands, in ka cire jemimah da ta maƙalƙale Commender har saida ya ɗauke ta, mazan cikin su suka yi hugging dinsu ɗaya bayan ɗaya, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, sunyi mamakin zuwan bazatan da suka yi ma su.
Da tsantsar mamaki Unaisah ta furta"Commander James! Captain Lewis! Major Smith! Jackson Lee! Canal Harry! Lieutenant Thompson! What an astonishing reunion! Is this really a chance encounter?"
Dariya suka saki gaba dayan su, da fara'a commender james ya ce, "Indeed, it's us! We hope you're overjoyed to see us. We've come specifically because of you, and we hope you'll welcome us with open arms." (Yeah mu ne, muna fata kunyi farin cikin ganin mu, munzo ne saboda ku, fatan zaku kar6e mu hannu biyu..." )
bai ƙare maganar ba suka haɗa baki gurin furta, "We welcome you, most warmly! We're truly elated to see you!"
Daɗi ne Ya lullu6e sojojin, sai kallonsu sukeyi gwanin ban sha'awa sunji dadin sauyin da sauka samu sun kuma jinjina ma Chief, su Hibba da basu san su wanene ba sai faman baza masu na mujiya su ke yi cike da son sanin su wanene su ɗin.
Captain lewis ne ya nuna su da hannunshi cikin harshen turanci ya ce, "waɗannan sune sauran yan uwan naku"? A tare suka haɗa baki gurin furta Eh, Tambayar sunayen su yayi Sajeed ne ya gabatar masu da su..
Yana zuwa daidai kan Deeja Commender Ya dubi Haris, "Is she your sister cos you look alike"
Yana murmushi yace Eh sister ɗinsa ce.
"She's the cause of his heartbreak" Unaisah ta faɗa da zolaya, dariya sojojin su ka yi.
Major smith Ya ce,"Dear Angel, where is that handsome young man, mai nauyin bacci ban gan shi ba ko baya nan .." bai ƙare maganar ba Thampson Ya ce, "nima abunda nake so na tambaya kenan, Ina Danish"? da yatsa Unaisah ta nuna ma su shi, yayi tsaye kan stairs, idanunsa na akan su, gaba ɗaya suka kai duban su gare shi Commender ya ce, "Har yanzu yana nan da ƙyuiyarsa?"
ganin kamar baida alamun zuwa gurinsu ne yasa Unaisah yin saurin cewa,"may be bai gane ku ba ne," major ya sake cewa, "Mun riga da munsan halin shi ai, Ya bacci har yanzu yana yi ko ya daina?
Dariya suka saka gaba ɗayan su, da ido Unaisah tayi mashi alamar ya zo gurinsu ganin kamar sun damu da son ganin shi.
Saukowa down ya yi ya nufe su, commender ya miƙa mashi hannu, "Danish, come here, I'm thrilled to see you! I hope you're safe and sound," ya faɗa tare da yin hugging ɗin shi, In low voice ya furta, "I'm fine, ina yi maku barka da zuwa" ya faɗa tare da raba jikinshi daga na commender ya bi sauran yayi hugging ɗinsu tare da yi masu barka da zuwa hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ma su ba.
Big guy ne yace da su, "Mu shiga ciki, ku zauna ku huta." Hannayen su ruƙe dana prisoners suka nufi falon, kafin su ƙarasa Taj dake tsaye yana kallon su, Ya matso kusa da su suka gaisa da junansu, big guy ya gabatar masu da Taj a matsayin mahaifin Unaisah sun yi murnar jin hakan sosai, duk budurin da ake Ummi tana can gefe ɗaya tana yin waya har sai da commender ya hangota yana ganin bayanta ya gane itace, nufar ta yayi yana isa ya rungume bayanta, a ɗan firgice ta juya don ta ga wanene ta haɗe rai amma koda ganin commender James sai ta waro idanu cike da mamaki ta ambaci sunan shi, "Sir James, is that you? I'm surprised," ta faɗa tana yar dariya
Sir james ya ce, "It's me, dear. Yesterday when we called, I hid the point of my coming because I wanted you to be surprised."
Murmushi ta sakar mashi, "I welcome you wholeheartedly I'm at a loss for words to express my happiness and how much I've missed you."
"I've missed you too, dear one. I'm overjoyed to see you." Ya bata amsa.
Ya yi zaton za ta yi hugging na shi amma sai ya ga akasin hakan, Taj da Big guy kuwa tun rungumar farko da commender yayi mata suka kalli juna, dama sun san za'a rina tun da su dabi'ar su ce yin hakan, a kan sofas suka zauna gaba dayan su, nan fa ex-prisoners suka fara cika su da surutu suna basu labarin abubuwan da suka faru bayan dawowar su Nigeria, suna tsaka da yin fira Chief Ya sauko down shima ya kimtsa tsaf cikin suit nasa, suna ganin shi suka miƙe da sauri commender ya nufe shi suka rungume juna a mutunce suka gaisa ya yi mashi barka da zuwa, kafin ya nufi sauran sojojin ya miƙa masu hannu suka gaggaisa.
Kowa na gidan tun daga kan Gate security Officers har Chefs na kitchen saida suka shigo falon domin yi ma baƙin Chief barka da zuwa, hakan ba ƙaramin faranta ransu yayi ba ganin yadda kowa ke ɗokinsu sai girmama su ake.
Batare da bata lokaci ba, Chefs suka shirya masu dinner a dining, duk girman table ɗin saida suka cika shi da kayan abinci kala kala.
Yau gaba ɗayansu su ka yi dinner a tare da baƙin su, gwanin ban sha'awa su commender sun ji daɗin karramawar da akai ma su, abun da yafi burge su yadda prisonsers suka saki jiki da su kamar irin sun haɗa alaƙa ta jini da su, hakan yasa suma suka samu walwala kamar suna a gidajen su na America, ga jemimah da ta yi ta basu nishaɗi da surutunta, ta maida commender kamar kakanta, har abinci take bashi a baki, ta yi kane-kane akan laps din shi, Danish kuwa hankalinshi na akan Unaisah ya lura kamar akwai wani abu dake damunta saboda yadda take cin abinci kaɗan kaɗan kuma hankalin ta yafi karkata akan daddynta saboda shine damuwarta.
Bayan sun kammala cin dinner ɗin, wata sabuwar firar ce ta 6arke a tsakanin sojojin da su Chief har kusan ƙarfe goma kafin Big guy ya raka su masaukin da za su zauna, duk yadda Unaisah taso ta gana da daddynta a daren ranar abun yaci tura tana ta jiran zuwan shi tasan ya saba duk in yana gidan dare yayi sai ya zo dakinsu yayi mata sallama kafin ya tafi amma yau taji shiru, koda ta fito bata iske kowa a falon ba, shima yayi tafiyar shi, da damuwa ta kwana a ranta.
Gidan Kurkukun Ƙaddara🔥
_____________________________✍️
Meke faruwa a gidan kurkukun ƙaddara? Saboda gabatowar gagarumin shagalin da zasuyi na black Night, sun fara shirye-shiryen tarbar wannan dare mai daraja a gurin su, Yanzu sun dakata da yin duk wani mugun abu da suke yi a gidan kurkukun, hatta fursinonin su sun yi mamakin sauyin da suka gani, lafiyayyan abinci suke basu mai rai da lafiya har sau uku a rana, bayan haka sun tsaftace ɗakunan prisoners din da makewayin su sun kuma canza masu sabbin Uniform.
Duk da sauyin da suka samu, hakan bai saka su yin murna ba, saboda sun san da wata manufa a ƙasa, wata wutar bala'en ce zata kunno kai, kamar ko sun sani dalilin dayasa suka sauya masu cimarsu daga ganye zuwa lafiyayyan abinci mai gina jiki, saboda albarkatun jikinsu su cicciko suyi ƙiba fatarsu tayi kyau don su ji daɗin aikata fasiƙanci da su, a cikin abincin da ake kawo masu hada wata kwayar sihirin da suke saka masu a cikin dafaffen kwai, kamar sha ka fashe take aiki a jikin ɗan adam walau mace ko namiji, cikin kankanin lokaci Yake ciko da duk wata ramar jikin su ya ha66aka jinin jikin su.
Lallai Elders Sun shirya ma Black Night..💔
Yau gaba ɗaya Sun fiddo da Prisoners din dake a kurkukun zuwa tsakar prison din, ko ina ka kalla sune birjik, sun jera layi, as usual jajayen uniform ne a jikin su, a yanzu babu masu black Uniform na ƴan baiwa tun daga kan su Unaisah.
A ƙalla fursinonin da suka rage agidan kurkukun ƙaddara zasu kai kimanin ɗari uku da hamsin, daga ciki harda jariran da suke raino.
Yan matan suna asanye da short gown wadda bata wuci gwuiwarsu ba, mazan kuma riga da wando ne ajikin su, babu mai magana a cikinsu kamar gumaka sun ƙame a tsaye ko motsi basa yi, Iya ƙwayar idanun su ce kadai take kyakkyaftawa sai numfashinsu dake fita.
Bakomai ne yasa suka nutsu ba, fa ce Giants ɗin dake a kewaye da su, Wasu irin gabza-gabza masu jini a jika.
sun kasa sun tsare sai suntiri suke umarni kawai suke Jira su aiwatar.
Cikin takun Izza Tsohuwa Inno ta nufo gurinsu hannun ta ruƙe da sanda, kamar kullum a cikin shiga ta red gown take, daga bayanta Giants ɗin dake take mata baya ne, kan matakalar benan dake fuskantar prisoners ɗin suka dakata da yin tafiya, ta tsaya tana bin su da ƙasƙantaccen kallo.
har na tsawon mintuna batare data furta kalma ba, sai da ta mula ta sha iska kafin ta fara magana a a gadaran ce
"Duk wanda na kira lamba ɗin shi a cikin ku, Ya koma gefe ɗaya" ta faɗa tare da nuna masu inda zasu tsaya da sandar hannun ta..
"Prisoner no twelve, Thirteen, Fourteen...' duk wanda ta kira sunansa, Jikinsa na kerma yake fitowa daga cikin layi ya tsaya gefe ɗaya, daga gani masu kyawun surar cikin su take zaƙulowa waɗanda suka zama matured.
Kusan fursinoni arba'in da takwas ta kira, mata sunfi yawa acikin su, saida ta kammala kiran lambobin waɗanda ta zaba kafin ta furta prisoner no 100 shiru ba'a amsa mata ba, da alama ta manta aika aikar dasa giant yayi mata, tsawa ta daka masu, "baku ji ina magana bane? Where is she?"
Murya na rawa wata young adult daga cikin su ta yi ƙarfin halin furta, "tun lokacin da kika sa Giant Ya tafi da ita, bamu ƙara ganin ta ba"!
Shiru tayi jim sai da yarinyar tayi magana kana ta tuna abun da tasa aka yi mata.
Giant ɗin dake a gefenta ta kalla, "Tana raye ko ta mutu?" Cikin girmamawa da wata irin buɗaɗɗiyar murya ya ce, "Bani da masaniya, bayan na kaita ɗakin fiɗa kamar yadda kika bani umarni, ban ƙara bi ta kanta ba"
Murmushin gefen fuska ta saki, "If she dies, I will be sad because I want her to witness the black night,
Even though I know even if she is alive, she will not be useful anymore."
Cike da shaƙiyanci ta faɗa kafin ta sake ce ma giant ɗin,
"Ina ji a raina bata mutu ba, amma bayan da ka kaita ɗakin fiɗa ka tabbatar sun feɗe sassan jikin ta? Ta jefa mashi tambayar.
"Bayan na kaita ɗakin fiɗar, ban ƙara komawa ba, saboda ba hurumina bane"
Bata tsaya taji ƙarshen zancen nashi ba, ta juya cikin takun sauri giants din suka rufa mata baya.
bata nufi ko'ina ba sai dakin fiɗa, koda ta shiga ta tambayi Gigantes Medici ɗin dake a gurin game da Gabriella, basu iya tuna meya faru bayan an kawo ta ba, ta nemi su bata records na fursinonin da su ka cire sassan jikin su, kwata kwata babu sunan ta.
Babu inda bata duba ba, kamar zata yi hauka, har records ta kar6a na dead prisoners nan ma bata ga sunan Gabriella ba, nan take zuciyarta ta raya mata cewa wani ya ceci rayuwarta.
Wani irin ƙululun baƙin ciki da takaici ne suka mamaye zuciyar tsohuwa Inno, tsabar fusata har wani hayaƙin huci take fitarwa ta kofofin hancin ta, rai a 6ace ta furta, "duk inda kika shiga zan gano ki ne, koma wanene ya ceci rayuwarki yayi babban kuskuren da bazai iya kubcema azabata ba! " da karfi ta buga sandar hannunta tare da furta sunan Gabriellah da wani irin amon murya mai amsakuwa..
A matuƙar firgice Gabriella ta farka daga dogon baccin da ya ɗauke ta, kanta ne ya fara sara mata da ciwo.
da tafukan hannayenta ta daddafe kan, wani irin gumin zufa ne ya fara tsattsafo mata, Kakkausar muryar dattijuwarne ya fara dawo mata a cikin kanta.
_"Faɗa da aljani ba riba, wannan somun ta6i ne, nan gaba idan kika kuskura kika sake yunƙurin yi min rashin ɗa'a farfesun namanki zansa ayi min shashasha kawai_
waro idanunta waje tayi, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, ta fara jan numfashi da karfi da karfi
_bakin ki ne ya ja maki! Nayi mamaki da har kika iya rayuwa, ai nayi zaton zan zo na same ki awargaje babu rai, amma saboda taurin kai har yanzu numfashin ki bai daina fita ba_
Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, cos she recovered her memory, ta tuna komai, abun ka game zuciya ta dinga buga kanta jigin karfen gadon har saida goshinta ya fara barazanar fashewa, wani tafarfasa zuciyarta ke yi mata saboda bakin cikin abunda dattijuwa inno tasa aka yi mata.
Ba dan Allah yasa tsohuwa khala ta faɗo dakin ba, da tuni Gabriella ta jima da kashe kanta, tana shigowa sautin kukan da take saki ya tari hanzarinta, ta waro ido waje tana kallon yadda Gabriella ke buga kanta, Cike da tashin hankali ta yi kukan kura tayi dirar mikiya kan gadon ta damƙi wuyan rigarta, ta jijjigata da hannayenta ta fara kokarin rarrashinta amma saboda bad temper dinta ta makance bata iya fahimtar komai da khala ke faɗa mata, sai kuka take tana fadin, "Let go of me! Let go of me! Why am I still alive? why didn't you kill me? You wicked oppressors, Jesus will never forgive you, you will all go to hell!
cikin fitar hayyaci take zazzaga masifa tana kokarin kwace kanta daga hannun tsohuwa khala don ta ƙarasa kashe kanta, tausayinta ne ya kama tsohuwa Khala duk da tayi mamakin zuciyar dake gare ta, in wani ne ya ga ya tsira zai zauna cikin salama ne amma ita so take ta kashe kanta ta karfi da yaji, da tasan zata dawo cikin hayyacinta da bata bar dakin ba, yanzu gashi tana neman ta dawo da hannun agogo baya, don bazata manta lokacin da ta ɗauka gurin yin jinyarta ba, har ɗinki sai da tayi mata a gabanta saboda raunin da taji.
Allah ne ma ya nufa zata rayu don da wuya giant su kwanta da mace ta tashi da lafiya batare da ta haukace ba ko ta mutu.
Kamar zasu yi dambe ita da Khala, saboda ta sanya karfi dama Allah yayi ta da ƙarfi kamar doki, da ƙyar khala tayi nasarar buga kanta jikin pillow ta tamurshe ta, ta yadda numfashinta bazai rasa hanyar fita ba, kasa ɗagowa ta yi da kanta saboda khala ta tokare kanta da tafin hannunta, zafafan hawayene suka fara yar tseral kan kuncin ta, cikin disasshiyar murya ta furta, "Bana so na mutu, kada ki kashe ni, Ina son ganin ɗan uwana Gabriel," Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa khala ta kwashe da ita tuni jikin Gabriella yayi sanyi lakwas.
Da kakkausar Murya khala ta ce, "Kinsan baki son ki mutu me yasa kike kokarin kashe kanki? Yar ƙarama dake sai baƙar zuciya kamar ta kafuran farko! Dame kike taƙama ne? Ina karfin naki yake uhm!"? Nishi ta dinga yi tana huci kamar zata iya ta6uka wani abu.
Sassauta murya Khala tayi, "Ba duka muka taru muka zama ɗaya ba, kasancewata a gidan kurkukun ƙaddara, ba hakan yana nufin nima muguwa bace, kamar yadda kika zata, kinyi min mummunar fahimta, amma nayi maki uziri saboda bakisan komai dangane dani ba..."
ta faɗa tana kallon idanun Gabriella da suka kaɗa jawur.
Numfasawa tayi kafin ta ɗaura da cewa, "Da ace ni muguwa ce da ban taimaki rayuwarki ba, nasan yanzu tunaninki ya dawo, dama abunda na ke gudu kenan saboda nasan za'a rina, yanzu da ban zo ɗakin nan ba da tuni kin jima da kashe kanki saboda ɗamsil basira, idan kina tunanin mutuwa mafita ce a gareki toh ki daina, shi jarumi ba'a san shi da karaya ba, kada ki zama raguwa ki zama jaruma mai iya tankwara zuciyarta me kuma burin ɗaukar fansar zaluncin da aka yi mata.
Tana jan nishi da ƙyar ta furta, "Who are you? Where did you find me? and Why did you help me?"
"Sanin wacece ni baida amfani, iya abunda zan iya sanar dake shi ne ba a haife ni a gidan kurkukun ƙaddara ba, bada son raina na kasance a cikin shi ba, ta karfi da yaji aka kawo ni nan, bazan iya misalta maki ƙunci da raɗaɗin da na ji a lokacin dana buɗe idanuna na tsinci kaina a gidan kurkukun nan ba, na ga musiba da bala'e da idanuna, abunda ban ta6a zaton ko a mafarki zanga makamancin shi ba, zuciyata a karye take saboda anci amanata an yaudare ni, bayan haka an nuna min fin karfi ba yadda na iya,...." idanunta ne suka ciko tab da kwalla.
"Kamar yadda kika so kashe kan ki, nima nasha yin yunkurin yin hakan amma idan na tuna menene makomata? Sai inji na gaza! Mutuwa bazata hana su cigaba da aikata fasadi ba, saboda su ɗin 6atattu ne in har bamu haɗa hannu mun kawo ƙarshen su ba, babu abunda zai canza na daga zaluncin da suke aiwatarwa, bayan haka babban abunda yasa nake so na rayu shi ne ya'yana inason na sake ganin su ko da da numfashina na ƙarshe ne".
muryarta na rawa ta ƙare maganar, hawaye suka cigaba da sintiri kan fuskarta, Gabriella dake sauraran khala, itama hawayene kan fuskarta, tana da wuyar sha'ani a rayuwarta bata yarda da mutane amma karo na farko ta yarda da tsohuwa Khala, maganarta ta karya mata zuciya.
A hankali ta zame tafinta daga kan Gabriella, hakan ya bata damar miƙewa ta zauna da ƙyar tana duban fuskar khala da tausayawa
"Ke ɗan uwan ki ɗaya ne, ni kuma jikokina da suka salwanta agidan kurkukun ƙaddara yawa ne da su, inaji ina gani ban iya tsinana masu komai ba saboda an nuna min fin ƙarfi...." fashewa ta yi da kuka kamar ƙaramar yarinya.
Itama Gabriella din kukan ta fashe da shi saboda tausayin khala da ya mamaye zuciyarta ashe ita bata ga komai ba tayi mamakin haƙuri da juriyar tsohuwar da har ta iya kai tsawon lokacin nan bata haɗiyi zuciya ta mutu ba.
"Yau kimanin shekara ashirin cuf, rabon da in shaƙi iskar duniya saita gidan kurkukun ƙaddara, bani da burin da ya wace in tona masu asiri, kullum ne sai na roƙi Allah dare da rana ba fashi, duk da har yanzu ba wani sauyi, ban ta6a gajiyawa ba, saboda nasan Allah ne kadai zai iya cika min burina kuma yana sane dani, wani jinkirin Alkhairi ne kuma ina ji araina ƙarshen kurkukun nan ya zo" ta faɗa tana jan magina.
"Kin tambayeni Ina na tsinto ki?" A ranar bayan na fito daga fadar Elder naji ina sha'awar in kewaya kurkukun duk da bana so nayi tozali da abunda zai hanani kwanciyar hankali, har zan gifta na hango tsohuwa inno tare da giant din da ya ɗauko ki babu sutura a jikin ki raina ya 6aci ba kaɗan ba, nayi zaton ma kin mutu ne, kwatsam idanuna suka hango min yatsun ƙafarki na motsi, wani iko na Allah ni da bana shiga huruminsu bansan ya akai zuciyata ta azalzala min akan in taimaka maki ba, cikin sanɗa na bi bayan su, har suka aje ki a ɗakin fiɗa, tafiyar su ke da wuya, nayi 6adda kama ta hanyar amfani da sihiri na, na shiga cikin Gigantes Medici din batare da sanin su ba saboda hankalinsu ya karkata akan aikin fidar da sukeyi, kafin su zo kanki cikin abunda bai fi daƙiƙa talatin ba, na sace ki na kawoki ɗakina, na fara kokarin tsayar da bleeding din da kike yi kafin na dinke raunukan jikin ki...." tiryan tiryan khala ta zayyana mata komai, wani irin son tsohuwar ne ya kamata har batasan sa'ar da ta faɗa kan kirjinta ba, ta rungumeta cikin shesshekar ta furta, "Ki yi haƙuri nayi maki mummunar fahimta, ki yafe min"
Ɗan murmushi khala tayi kafin ta daura da cewa, "Tun kafin ki dawo hayyacinki na ji kina ambaton sunan ɗan uwanki Gabriel, na kwallafa rai a kan son sanin wanene shi? a cikin bookshelve ɗina ina da littafin register na fursinoni (Sijil al-sujna) a cikin littafin na buɗo ina bincikawa don inga wanene me suna Gabriel, ban sha wahala ba, saboda nayi nazari na gane cewa ku ɗin ba tsoffin prisoners bane cikin waɗanda aka kawo ne a ƙarshen shekara ta dubu biyu da ashirin da uku, cikin sa'a na ga sunayen ku, a fahimtana ɗan uwanki ne ko?..." cikin sanyin murya tace, "twin brother ɗina ne."
"Zaki iya tuna tayaya akai kuka tsinci kanku a gidan kurkukun ƙaddara?" Girgiza kai ta yi har lokacin bata raba jikinta daga na khala ba.
"Bazan iya tuna komai ba, ɗan uwana kadai na sani, pls ki taimaka min in gan shi..." Shiru tsohuwa khala ta yi saboda tasan me zai biyo baya in har ta faɗa mata cewa baya a cikin kurkukun, cos ta ga sunan shi cikin list na escaped prisoners, ta lura da yadda take mugun son shi in har ta faɗa mata, zuciyarta zata karaya ne kuma zata ga kamar ya manta da ita ne shiyasa ya tafi ya barta batare da ya taimaki rayuwarta ba"
Ɗagowa tayi da kanta, "kinyi shiru baki bani amsa ba, bana so na rasa ɗan uwana, nasan yana cikin wahala kuma yana nemana, pls ki ɗauko shi ya dawo nan mu rayu atare"
Dafa kafadarta khala tayi, "Zan iya jefa rayuwarmu da tashi cikin haɗari, abunda yasa nake 6oyenki saboda a yanzu haka dattijuwar da ta kusa kashe ki, nemanki take ruwa ajallo, amma in har Allah yayi mana tsawancin kwana gaba na yi maki alƙawarin zan hadaki da ɗan uwanki..."
cikin karyayyar murya ta ce, "ya mutu ko"? Girgiza kai tsohuwa khala ta yi, "A'a yana raye, "
"Ta ya kika san yana a raye"?
"Zan nuna maki"
Ɗaga mata kai ta yi alamar toh, saukowa suka yi daga kan gadon, ta ɗauki sandar ta, ta nufi gurin furannin dake a ɗakin, Gabriella tana a biye da bayanta, da sandar ta nuna mata fure kore shar da shi a cikin wata tukunyar shi mai kyan gaske.
"Ɗan uwanki yana a cikin ƙoshin lafiya, kin gan shi nan" aruɗe ta dubi khala, "tayaya hakan zai yiwu! Mutun ya zama fure??"
Dariya khala tayi, "It's a magic trick kema idan naso sai in mayar dake fure, Ko kina da ja ne?" Ta faɗa da zolaya, da sauri ta girgiza kai,
Zuƙunnawa tayi a gaban furen ta ƙura ido tana kallon shi, cikin sanyin murya ta furta sunan shi abun mamaki sai ta ga furen ya motsa ganyayyakinsa kamar iska ta kaɗa shi.
Murmushi ta saki,"Da gaske kaine?" again ya ƙara motsa ganyen shi, wani daɗine ya lullu6eta har ta buɗe baki zata ƙara magana kwatsam ba zato ba tsammani taji kamar an jeho mata wuƙa a kirjin ta,
dafe shi ta yi da hannun ta, radadi ya hana ta motsa, nan take ta fara yin aman jini,
Hankalin Khala kwata kwata baya akanta batasan meke faruwa da ita ba, saboda tayi zurfi acikin tunanin ta, sai kokari Gabriella take ta ruƙo rigarta amman ta kasa saboda kermar da yatsunta ke yi....🥺
__________________________________✍️
*BENAZIR💔*
Suna a zaune kan darduma su biyu ita da Zeenatu, sun haɗa baki suna karatun kur'ani da suka buɗe akan qur'an stand
Wayar tace ta fara ringing, bayan takai aya ta dakata da yin karatun ta miƙe da sauri ta nufi wayar dake ajiye saman gadonta
"Aunty Benazir, Azeezaty ne?" Zeenat ta tambaya tana kallon ta
Bata ba ta amsa ba, har saida ta dauki wayar, ta dubi sunan me kiranta, tayi mamakin ganin sunan Uncle ya bayyana yau wata rana Alhaji musa ya kira ta, a ranta ta furta Allah yasa alkhairi ne.
Ɗaga kiran ta yi ta kara wayar a kunnanta, tana kokarin yi mashi sallama ya katse ta da cewa, "Ki same ni a garden yanzu" amsa mashi ta yi da toh.
Aje wayar tayi gaban mirror, ta juya suka haɗa ido da Zeenatu ta ƙura mata ido tana kallon ta.
"Daddynki ne ya kira ni, ki cigaba da yin karatun yanzu zan dawo" tace toh"
Bayan fitar Benazir, cike da zumuɗi ta miƙe, ta ɗauko wayar Benazir ta fara laluban layin Azeezaty, sam ta kasa ganowa saboda batasan sunan da Benazir tay mata serving ba, amma da ta tuna Benazir ta fada mata jiya ta kira layinta bata samu ba, hakan yasa ta shiga call logs, lambar farko da akai ma saving da God Gift ta danna Call almost 3 times tana kira baya shiga, ba dan ta so ba ta hakura.
Lokacin da Benazir ta ƙaraso Garden ɗin tunkan ta ƙarasa idanunta suka hango mata mutun uku zaune kan lallausar darduma kowannan su shadda ce a jikin shi.
bata iya tantance su wanene ba, saida ta isa wani irin burki ta ci ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya da tsantsar mamaki ta furta, "ZAKI!"
Yana Jin muryarta da sauri ya ɗago ya kalle ta, zumbur ya miƙe tare da ambaton sunan ta "Benazir!"
Hawaye ne suka ciko idanunta, tayi mamakin ganin shi, kuma tayi farin cikin ganin bawan Allahn nan ba zata ta6a manta halaccin da yayi mata ba..
Gaba ɗaya hankalin Sir mubarak, da na Alhaji musa ya dawo kan su, Sir mubarak na ganin Benazir a ranshi ya ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa Zaki ya ruɗe akanta, da alama dai Sir Mubarak ya yaba da kyanta.
Jinjina mashi kai tayi, "Yayana ni ce,"
Cikin sanyin murya ya ce, "Benazir baki kyauta min ba, kinsan irin tashin hankalin dana fuskanta saboda rashinki a kusa da ni.. " bai kare maganar ba, Sir Mubarak ya yi mashi gyaran murya atare suka kalle shi.
Cikin sauri Zaki Ya gabatar mata da Daddynsa, Cike da jin kunyarshi ta gaishe da shi, fuskarshi a sake ya amsa mata, tare da yi mata fatan alkhairi.
"Benazir, ki shiga da shi ciki." Alhaji Musa ne ya faɗa fuskarsa a sake kamar ba shi ba, amsa mashi ta yi da toh, bata yi aune ba ta ji ya ruƙo hannunta a cikin nashi kamar yadda ya saba yi lokacin da suna tare.
Fita su ka yi daga garden din, yace mata ba zai shiga gidan ba, yafi so suyi magana a cikin motarsa, ya buɗe back seat na motar shi yace ta shiga, ji ta yi bazata iya yi mashi musu ba hakan yasa ta shiga ta zauna bayan shima ya shiga ya datse car door din, suka Ƙurama juna ido kamar yau suka fara haɗuwa, sunyi kewar junan su sosai.
"Da ranki da lafiyarki Benazir, baki neme ni ba, kamar kin manta dani a rayuwarki, baki yi tunanin damuwar da zan shiga ba, kin tafi kin barni da kewarki kullum zullumina kina ina? Kin isa gidan iyayenki lafiya ko kuwa?"
Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, bata ji dadin halin da ta jefa shi ba, tasan shaƙuwar dake tsakaninsu dole ya damu da ita..
"Ka yi hakuri Yayana na kaina, wlh kana a raina, ban manta da kai ba, kamar yadda ka damu da ni nima haka na damu da kai..." katse ta ya yi, "Amma meyasa ba ki neme ni ba?
"Ka manta wayata tana a hannunka?"
"Ba hujja bace Benazir, kin riga da kinsan wanene mahaifina a ƙasar nan, kinsan family estate dinmu, why baki je can kin neme ni ba in har dagaske kin damu dani?"
Fuskarshi a yamutse ya yi maganar, kwarjini ya yi mata ta sunnar da kanta ƙasa, tasan bata kyauta mashi ba..
"Me nayi maki dana cancanci hakan daga gare ki? Ko kin daina ƙaunar yayan naki ne?" Yanayin yadda yake magana ba ƙaramin karya mata zuciya yake yi ba, ga kamshin turarenshi da ya kanainaye hancin ta.
Da ƙyar ta furta, "Na kar6i laifina, ban kyauta maka ba, amma ka yafe min, bazan ƙara maimaita kuskuren da nayi ba." Lumshe idanunshi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta, matsawa yayi dab da ita da sauri ta ja da baya, har saida ya ƙureta jikin murfin motar .
Shafa fuskarta ya yi da tafin hannun shi, yana kokarin haɗe bakinsu ta yi saurin kauce mashi, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin shi yayi ba, saboda ta sauya mashi.
"Kin canza min, meyasa?" Muryarta na kerma ta ce, "Yayana ka yi haƙuri, ba halina bane, ko a lokacin da nake amince ma hakan bada son raina bane, sai don bani da mafita ne, kewar mijina ne yasa nake biye maka saboda in samu relief..." wani irin kishi ne ya ziyarci zuciyar shi, idanunshi suka kaɗa nan da nan suka fara yin ja...
"Kin haɗu da mijin naki?"
Ɗaga mashi kai ta yi alamar eh,
Hankalin shi idan yayi dubu toh ya tashi, damuwa ce ƙarara kan fuskarshi, ita kanta ta sha jinin jikinta da ganin yadda numfashin shi ke fita..
"Tayaya akai ka gano inda nake?"
Da ƙyar ya furta, "Uncle ɗinki, abokin Daddyna ne,..." ta yi mamakin jin hakan.
A takaice ya bata labarin tun farkon dawowarshi abunda Ya faru har zuwa lokacin da Sir Mubarak ya kira Alhaji musa ya fada mashi lokacin da zasu zo ganin ta ..."
ƙiris Ya rage ta fashe da kuka saboda tausayinshi da ya kamata, bata ta6a sanin yana sonta ba sai yanzu da ya ke faɗi mata, tayi mamakin zurfin cikin shi...
Ruƙo hannayenta ya yi acikin nashi.
"Ki taimaki rayuwana, ban saba da wahala ba, bansan menene so ba, sai akan ki, ke shaida ce, mata basa a gabana, aikina kawai nasa a gaba, wlh bazan 6oye maki ba tun rana ta farko da na fara ganin ki naji na kamu da ƙaunarki, shiyasa koda kika faɗamin kina so ki yi nesa da kowa naki ban yi maki faɗa ba, saima nayi maki hanyar da zamu bar ƙasar atare saboda idanuna sun makance akan sonki, a ranar da kika faɗamin kina da aure, ban runtsa ba saboda hankalina ya tashi kuma duk da sanin hakan ban ji son ki ya ragu ba saima ƙaruwa...."
dafe kanta ta yi da tafukan hannayenta, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, kalaman Zaki sun tsuma zuciyarta da tausayin shi, ba dan Taj ba da ba abunda zai hana ta amince mashi saboda gayen ya haɗa komai da mace zata buƙata a gurin namiji, sai dai kash bata jin zata iya rabuwa da Uban ƴarta.
Muryarta na rawa ta ce,"kai ne ka tura ma mijina saƙon ya sake ni?"
Girgiza kai ya yi, "Ba ni bane, bazan iya aikata hakan ba." numfashi ta ɗan ja, kafin ta runtse idanun ta, ya zuba mata ido yana kallonta kamar zai hadiyeta saboda tsantsar son da yake yi mata...
"Daddyna ya bani goyon bayan in nemi soyayyarki, In har kika amince min zai yi magana da iyayenki, on friday za'a ɗaura mana aure, Next week zan koma dake Canada, na yi maki alƙawarin ba zaki ta6a danasanin aure na ba, kin riga da kinsan wanene ni kin san halina, kuma ko bayan auren bazan hana yarinyarki ta zo inda kike ba, har shi kanshi ex-husband din naki bazan raba zumuncin dake tsakanin ku ba..."
Kuka ne ya kubce mata, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalinshi ya yi ba, bazai juri kallon hawayen ta ba, da sauri yayi hugging dinta, halin da take a ciki ya hana ta kwace kanta daga gare shi.
Cikin shesshekar kuka ta ce,"In har da gaske kana so na kuma kana son farin cikina, to ka barni in rayu da mijina, wallahi bazan iya rayuwa da wani ɗa namiji in ba shi ba, ba dan ƙaddara ta raba ni da shi ba, babu abunda zaisa na juya mashi baya, ko dan darajar ƴar dake tsakaninmu bazan Iya rabuwa da shi ba..."
kusan suman zaune yayi jin maganar ta, raba jikinta ta yi daga nashi, fuskarta ta jiƙe sharkaf da hawaye taci gaba da cewa, "Ka taimaki rayuwana, ka rufa min asiri, in har taimakon da kayi min kayi ne don Allah, toh ka haƙura da ni, mu cigaba da zumunci har ƙarshen rayuwarmu, amma maganar aure babu ita tsakanin mu..."
Maganganunta sun karya mashi zuciya, wani irin zafi ne ya mamaye jikinshi, duk da sanyin A.c din motar hakan bai hana shi fitar da gumi ba.
kifa kanshi ya yi kan kafaɗarta yana ambaton Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan min ha..." sambatu ya ci gaba da yi kamar ya fara zaucewa..
Tasan irin radadin karya zuciya ba kowa ke iya jurar shi ba, fargabanta kada tayi silar da Zaki zai rasa rayuwarsa amma ya zata yi? Bata da mafita da ya wuce ta lallashe shi taci gaba da bashi hakuri...
"Yayana nakaina, matsayinka bazai ta6a canzawa agurina ba, bazan ta6a juya maka baya ba, ina jinka tamkar ɗan uwana na jini, ina mai takaici ƙin amsa bukatarka, bawai don baka kai in aureka ba, wlh kowace mace zata yi burin ta auri namiji jajirtacce nagari irinka, saboda ka haɗa duk wasu kyawawan dabi'u da halaye wanda zaisa mace ta so ka, sai dai kash Allah bai kaddara kaine mijina ba, muyi haƙuri mu rungumi kaddara, zan tayaka da addu'a Allah ya baka mace tagari, wadda zata maye maka gurbina...." cikin karyayyar murya ya furta, "Benazir bazan Iya rayuwa batare dake ba, zan roƙi Allah ya dauki raina in huta da radadin rasa ki da nayi" da sauri ta ce,"In sha Allah bazan zama silar da zaka mutu ba, sai dai in zama silar farin cikin ka na har abada, zan tayaka da addu'a Allah ya baka ikon cinye jarabawar soyayyata, Allah ya cire maka sona acikin zuciyarka..." cikin rawar murya ta ƙarashe maganar.
shiru yayi bai ƙara magana ba, sai bugun zuciyarsa da take ji a jikinta.
"Alfarmar da zan roƙa a gurinka, don darajar manzon Allah SAW, ka rufa min asiri yayana nakaina, kada ka faɗama Daddynka komai da ya faru tsakanin mu, saboda zai iya sanar da Uncle ɗina shi kuma zaiyi min dole ne, nasan bazaka so abunda zai 6ata raina ba..." wani irin zazza6i ne ya lullu6e jikin shi, kamar ya fasa ihu haka yake ji, So bala'ene, duk maganganunta akan kunnanshi sai dai ya kasa furta kalma.
Shafa sumar kanshi tayi da tafin hannunta cikin sigar lallashi ta ci gaba da kwantar mashi da hankali maimakon yaji sauƙi a ranshi saima yaji kamar tana ƙara rura wutar sonta a zuciyar shi..
Tayi fatan ace zata iya share mashi hawayenshi ta aminta da auren shi sai dai kash bazata Iya ba, kamar yadda yake jin azabar sonta itama haka take jin azababbiyar soyayyar Taj, duk namijin da zai aure ta sai dai ya auri gangar jikinta amma ruhinta yana agurin Taj.
Bayan wani lokaci, ta fito daga cikin Motar, da gudu ta nufi cikin gidan tana shiga daki bata iske Zeenatu ba, saman gado ta faɗa ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai ita.
Hanky ya zaro daga front pocket dinsa ya share fuskar shi, saboda baisan daddynsa ya gano abinda ya faru da shi, saboda yayi mata alkawarin zai rufa mata asiri, ka ji masoyi na gari samun irinsu zaiyi wuya aduniyar nan.
Zaki mutum ne mai haƙuri ga tawakkali.
Bayan ya goge fuskar shi, Ya rufe murfin motar, ya zaro shades ya sanya ma idanunsa.
Bayan tafiyar Benazir da yan mintuna Sai ga Sir Mubarak da Alhaji Musa sun fito daga garden din gidan, fuskokinsu ɗauke da fara'a da alama sun ji daɗin firar da suka yi.
"Naji daɗin karramawar da aka yi mana, yanzu sai yaushe mahaifin nata zaizo Abujan ko mu zamu je can Jos dinne? cos ina son ganawa da shi game da zancen auransu"
Alhaji Musa ya ce, "kada ka damu, basai kunje can ɗin ba, tun da har ni na amince da aurensu, shima zai amince ne." murmushi Sir Mubarak yayi, "Mutumina ka faranta raina, Allah ya ƙara dankon zumunci a tsakaninmu," Ya amsa mashi da ameen.
"Ba zaka shiga ciki ka gaisa da madam ɗina ba"
"Ban shirya haɗuwa da surukata ba, sai zuwa na gaba in sha Allah." Ya faɗa yana bin compound din da kallo yana ci gaba da yin murmushi.
Fitowa Zaki ya yi daga motar, fuskar shi da fara'a ya ce, "Daddy, mun riga da mun gama magana da ita, harma ta koma ciki."
Farin ciki ne ya lullu6e Sir Mubarak,
"Uncle, ina godiya da damar da ka bani, Allah ya ƙara girma da ɗaukaka" ya faɗa yana kallon Alhaji musa,
Murmushin gefen fuska ya sakar ma shi, "Kada ka damu, na dauke ka kamar ɗana, komai zan iya yi saboda farin cikin ka."
Bayan sunyi sallama da juna, Alhaji Musa Ya koma gidan, su kuma suka shiga motar su.
Kwata kwata Sir Mubarak bai lura da yanayin fusakarshi ba saboda shades din da ya sanya ya rufe idanun shi ya hana yaga eye balls dinsa waɗanda suka kada jawur tamkar garwashin wuta.
"Bani labari mana my son, ya kuka yi da ita?"
Shiru yayi jim kafin ya cije ya ce, "ta amince Daddy, "
"Alhamdulillah, yanzu da yaushe zamu zo nema maka auren ta?"
Tamkar baison furta maganar ya ce, "Ba yanzu ba daddy, mun yi da ita sai bayan na sake samun hutun aiki zan zo Nigeria sai a ɗaura mana auren" farin cikine ya cika Sir Mubarak.
"Ina tayaka murna my son, ni dama nasan da wuya a samu macen da zata yi rejecting dinka, saboda kai din na musamman ne." Murmushin takaici ya ƙaƙalo kan fuskar shi ba tare da ya iya furta kalma ba, a ranshi ya riga da ya yanke shawarar barin ƙasar gobe, kwara ya nisanta kanshi da ita in ba haka ba zai iya zaucewa.
*MEETING ROOM*
Around ƙarfe 11 na safe hamshaƙan motoci suka fara kurɗaɗowa ta entrance gate din Isod headquarter, jigunannun gaske da matsakaicin gudu suke tururuwar shigowa a jere har kusan guda shida, kowace mota tana da tinted.
A parking space motocin su ka yi parking, a hanzarce Jami'an dake sintiri su ka yi saurin ƙarasawa bakin car doors ɗin suka bubbuɗe masu kofar....
Chief Owais ne ya fito tare da Big guy, motar bayan tasu Senior agents ɗin su ne.
Bayan su sai Commender james Ya fito shima tare da sauran sojojin da suka zo, kowannansu yana asanye da kakinsa..
Motar ƙarshe General ɗin sojoji ne.
A gaggauce Jami'an dake kewaye da su sukayi hanzarin buga kafa tare da sara ma su cikin girmamawa suka gaishe da su kamar zasu zuƙunna masu tsabar ladabi.
Basu tsaya 6ata lokaci ba, Cikin takun dattako suka nufi Secure operation center duk inda suka gifta sai ƙamshin turarensu ya gauraye da iskar gurin daddaɗan gaske, kuma duk hanyar da suka bi jiki na 6ari jami'an dake a gurin ke sara masu, sai dai kawai su ɗaga masu hannu alamar sun kar6i gaisuwar tasu.
Bayan sun hau lift ta sauke su a third floor, A bakin awani Katafaren Meeting room (ɗakin taro na sirri) wanda gaba ɗayan shi a kewaye yake da zallar glass launin blue sky, wanda ke a waje bazai iya ganin na ciki ba, bayan haka bangon gilashin ɗakin soundproof ne irin wanda ke hana sauti fitowa waje, duk wani abu da za'a tattauna iya cikin ɗakin sautin ke tsayawa na waje bazai ta6a iya ji ba..
Gaba ɗaya sun nutsu suna jiran kofar ta buɗe ma su, biometric authentication ce sai ta tantance mutun kafin ta bashi iznin shiga..
Tafin hannu Chief ya ɗaura kan saitin na'urar ta yi screening din shi ta haska kwayar idanun shi kafin ƙofar ta fara sliding slowly har ta ƙarasa zuge kanta..
Walking majestically suka fara shiga ɗaya bayan ɗaya cikin katafaren Meeting room din, U.s armies din dake a tare da su sai faman jinjina kai suke saboda ƙawatuwar dakin taron yayi matuƙar burge su, cos ba su tsammaci zai kai haɗuwar meeting room ɗin su na America ba, wata irin ni'imtacciyar iskar A.c ce mai fita da ɗumi ta fara ratsa hudojin gashin jikin su irin mai sanyaya zuciyar mutun ta kwantar masa da hankali yaji shi a wata duniyar daban.
Wani katafaren zunguraren table ne a tsakiyar ɗakin shape ɗinsa kamar rectangle ya ke iya jikinshi abun burgewa ne sai salƙi da daukar ido yake, ga wasu high-end Chairs kewaye da shi ga wasu haɗaɗɗun Microphones da Laptops a gaban kowace kujera, bangon dake fuskantar table ɗin wani tafkeken large screen ne.
Komai na yin meeting an tanade shi a ɗakin.
A tsanake kowannan su ya ja kujera ya zauna, suka fuskanci junan su, bayan sun daidaita nutsuwarsu ɗakin yayi tsit na ɗan wani lokaci, kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyar shi...
Abu na farko da suka tsara yi ma junansu barka da zuwa da kuma gabatarwa..
Dakin taron ya yi tsit a daidai lokacin da Chief Owais ya miƙe daga kan kujerarsa tare da tawagarsa, domin fara gabatar da kan shi cikin dattako ya fara magana yana duban kowannansu....
"Good morning everyone, i'm director Owais Sharafudeen Obinna, the Chief of Isod, With me are my team members," ya faɗa tare da yin nuni da su,
"Deputy Director General Omar Musa Wadata, Chief of Operations Ahmad Hassan, Chief of Intelligence Commander Haroon, and Senior Agents Dr. Zarah Saeed, Agents Ethan Kim and Jabeer Osman."
yanayin yadda yake gabatar da su ba ƙaramin burge su yayi ba komai nashi cikin aji yake yin shi, duk wanda ya ambaci sunanshi zakaga ya saki ƙayataccen murmushi kan fuskar shi..
"Muna yiwa kowa barka da zuwa" ya fada tare da komawa kan kujerarsa ya zauna suma duk suka zauna.
The next person General Noah ne wani bayerabe baƙi mai jiki ya miƙe yana gyara necktie ɗinsa,
"Hello everyone, nice to meet you all, I am General Noah the General Officer Commanding the Nigerian Army, It's an honor to be here today." ya faɗa fuskar shi da murmushi kafin ya koma ya zauna.
Cike da kwarin gwuiwa Commender James Ya miƙe tare da tawagarsa su shidda,
"Hello everyone, I am Colonel James, the U.S. Commander of the Joint Task Force. I am joined by my team.." ya faɗa tare da nuna U.s armies din dake gefen shi,
Ya fara zayyana sunayen su,
"Major Smith, Captain Lewis, Canal herry and Lieutenant Thompson tare da Jackson lee, munayi ma kowa barka da zuwa, mun ji daɗin gayyatar mu da ku ka yi" gaba daya sunji dadin gabatarwar da yayi bayan sun zauna ɗakin yayi shiru na ɗan wani lokaci.
Kafin Chief ya numfasa calmly ya cigaba da kora jawabi, "Thank you, everyone, Let us proceed with the agenda, we are gathered here today to discuss a grave and urgent matter, already mun riga da mun san abun da ya tara mu, dangane da yaran da sojojin America suka tsinta a dajin Evil forest suka damƙa case dinsu a hannun hukumar mu ta Isode..."
gaba ɗaya sun nutsu suna sauraron shi hadi da kallon fuskar shi,
Ɗan dakatawa yayi kafin ya daura da cewa, "...bayan bincike da hukumarmu tayi mun samu bayanai daga gurin yaran, wato wasu miyagun matsafa ne suka ƙirƙiri wani gini a karkashin ƙasa wanda suke kira da Gidan Kurkukun kaddara! Inda suke kulle mutanan da basu ji ba basu gani ba ta ƙarfi da yaji suke killace su, anan suke aikata duk wani fasadin su.." gaba ɗaya hankalin Jami'an ya karkata akan shi cos ba komai suka sani dangane da yaran.
"But that's not all, bayan ƙuntata rayuwar yaran, suna azabtar da su azaba mai raɗaɗi, ta hanyar yin amfani da karfin sihirin su gurin sarrafa su, su yi amfani da su ta ƙarfi da yaji..."
"But that's still not the worst of it. They use these innocent children as sacrifices for their dark magic rituals, draining their blood and exploiting their suffering for their own gain. And, tragically, they have been known to target young girls during their period, subjecting them to... unspeakable atrocities..."
kasa ƙarasa maganar yayi saboda takaici da baƙin ciki da ya mamaye zuciyar shi, tuni gumi ya fara tsartsafo mashi akan fuskar shi,
haɗa ido su ka yi da commender kasancewar suna fuskantar juna, tun daga kan yanayin yadda ya ƙura mashi ido ya fahimci maganar da yayi tayi matuƙar girgiza shi, a ƙagare yake da son jin karin bayani, hatta sojojin sun yi matuƙar girgiza da jin maganar kurkukun ƙaddara.
Mamakinsu wai har za'a samu yan adam da zasu iya shirya mugunta da zalunci a ƙarƙashin ƙasa na tsawon lokaci batare da asirin su ya tonu ba?
"Owais, kai muke sauraro, Muna bukatar ƙarin bayani daga gurin ka." General Noah ne ya yi maganar...
Cikin sanyin murya ya amsa mashi da Okay, kafin ya kunna laptop din gabanshi ya fara operating ɗinta nan take large screen ɗin dake a jikin bangon dake fuskantar su ya kawo haske kamar tv nan take ya yi displying video ɗin su Unaisah a Questioning room wato ɗakin tambayoyi, lokacin da suke bada bayani dangane da rayuwarsu agidan kurkukun ƙaddara komai da suka tattauna camera ta naɗe shi.
Yayin da suka nutsu suna sauraron tattaunawar su, wata irin zufar bacin rai da tashin hankali ce ta wanke goshin su kamar ba A .c a dakin, wlh sun yi matuƙar kiɗima da jin labarin kurkukun ƙaddara da kuma irin mugunyar azabar da ake yi ma matasan yaran da basu ji ba basu gani ba... tsabar fusata da baƙin ciki da takaici yasa jikin commender ya fara tsuma yana zubda gumi.
Bakomai yafi Karya masu zuciya ba face Labarin Unaizah da Majnoon duk irin dauriyar Soja saida ruwan hawaye suka cika idanuwansu kamar zasu fashe da kuka,
Dunƙule hannu General Noah yayi ya dinga bugun gaban table din yana cizon lower lips dinshi, saboda tsabar fusata.
Commender James kuwa da shi da tawagar shi tsantsar mamaki da al'ajabi Ya hana su ko motsa, sai faman jinjina kawunansu suke yi al'amarin ya girmi tunaninsu, su mamakinsu yadda har matsafan suka share tsawon lokaci suna aikata 6arna a ƙasa batare da an iya kama su ba, a ganinsu sakacin shuwagabannin ƙasarne da kuma waɗanda keda alhakin kula da tsaron ƙasar"
Jikin kowannansu yayi mugun yin sanyi lakwas, ɗakin taron yayi tsit baka jin sautin komai saina muryoyin su Unaisah.
Murya na rawa General Noah Ya furta"Owais, I can't believe what I'm hearing. Am I not dreaming? What cruelty and evil? I have never heard of such a thing before! a kasar nan wannan tashin hankalin ke faruwa batare da saninmu ba? Toh meye amfaninmu? Nayi danasanin mukamin da nake dashi tun da har ban iya kawo karshen ta'addanci a kasar nan ba, bamu ba al'umma tsaron da ya dace ba..."bai ƙare maganar ba saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare maƙoshin shi. da sauri Canal dake gefen shi ya dafa kafaɗarshi cikin sigar lallashi ya fara ƙoƙarin kwantar mashi da hankali.
Cikin sanyin jiki chief Owais Ya zaro hanky daga front pocket ɗinsa Ya miƙa ma general Noah ganin yadda yake zubda gumi yatsun hannunsa na kerma Ya kar6a ya fara share hawayen dake sintiri kan kuncin sa..."
"Owais lamarin Ya ɗaga hankali na! Wai dagaske ne Yana faruwa?"
Commender James ne ya yi maganar tsabar ruɗin tashin hankali yasa shi jin al'amarin kamar almara.
Jinjina mashi kai ya yi alamar eh ba tare da ya iya furta kalma ba.."
Gaba ɗaya saida ya kunna masu videos ɗin prisoners lokacin da aka zo kan nasu Jemimah kifa kai general Noah yayi kan table ɗin kamar zai fasa ihu saboda tsananin tausayin yaran, kukan zuci yake mai azabar radadi.
Babban abun takaicin da ya haddasa matsananciyar damuwa a zuciyarsu yadda matsafan suke lalata rayuwar ƙananun yaran saboda rashin imani a lokacin da suke tsaka da raɗaɗin ciwon cikin jinin al'ada.
Bayan haka sun karaya da jin irin kullan da suke yi masu tun suna jarirai babu shige babu fuce, abinci sau ɗaya a rana, kaya kala ɗaya, sun ƙasƙantar da rayuwarsu sun tauye masu hakkinsu na rayuwar duniya sun maida su kamar dabbobi.
"Wlh, na rantse da wanda raina yake a hannun shi, mutanan da suka ƙirƙiri gidan kurkukun ƙaddara ba zasu ƙara shaƙar numfashi cikin kwanciyar hankali ba, ɗaya daga cikin su bazai sha ba, idan har suka kuskura suka zo hannu wlh sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwayensu suka yi a duniyar nan, sai sun ɗanɗani kuɗarsu sai sun manta da duk wani jin daɗi da suka ta6a ji a duniyar nan..." a harzuƙe Noah ya faɗa kamar ana tunzarashi da ƙyar suka lalla6a shi ya koma ya zauna yana faman yin haki kamar wanda yasha gudu...
Shiru suka yi na ɗan wani lokaci, batare da wani ya ƙara furta uffan ba, ƙoƙari suke su kwantar da hankalunsu don su samu nutsuwar faɗin ta cikin su, tashin hankali ya hana ko ruwan sanyi su kora ma maƙoshin su.
Muryar Big guy ce ta katse shirun nasu
"Abunda muka gano dangane da kungiyar matsafan, sadaukarwa da su ke yi, dole sai danginka, mutun ba zai iya sadaukar da wanda bai haɗa alaƙar jini da shi ba".
Girgiza kai Dr. zahra ya yi, "Banma san me zance ba, mutanan nan sun san me suka taka, kuma daga ji manyan mutane ne a ƙasar nan, shiyasa suka daɗe suna aikata ta'addanci batare da asirin su ya tonu ba..." Maganar Dr. Zahra ta ɗaga hankalin Chief Owais da Big guy saboda sunsan su wanene ke ruƙe da ƙasar wato family ɗin su.
"Mutane ne masu hatsarin gaske, tunkarar su ba abune mai sauƙi ba, ta ya za'ae ma mu san su wanene su balle har mu iya kawo ƙarshen su? Babban abun da ya ɗaure mana kai yaran gaba ɗaya ba su ta6a ganin fuskokinsu ba, hatta shi babban cikin su Salsabeel da ya fi su daɗewa a gidan kurkukun, kai hatta yaron da ke ruƙe da muƙamin garkuwarsu, ya rayu tsawon shekaru baisan fuskokinsu ba amma yasan Nicknames ɗin su, saidai yaƙi faɗa mana komai dangane da su, yana da taurin kai, mutunne mai wuyar sha'ani, ɗan uwansa Salsabeel ya faɗa mana cewa yafi shi sanin su wanene elders..." Big guy ya ƙare maganar yana dubansu.
Ci ya ɗaura da cewa, "Har yanzu suna sarrafa shi, mawuyacin abune ya bamu haɗin kai, ɗan uwansa yace in har muka tursasa mashi zai iya ja mana gagarumar matsalar da bazamu iya magance ta ba..."
Agent Jabeer Osman ya ɗaura da nashi bayanin, "Matsafan suna da kaifin basira da wayau, sun san cewa wata rana asirin su zai iya tonuwa shiyasa basu ta6a yin kuskuran da wani zai san fuskarsu a cikin yaran da suke raino ba, sun iya takun su..." ya faɗa yana jinjina kan shi.
"Garkuwar nasu Yaro ne mai kafiyar tsiya, bai yarda da bare ba, yan uwansa kaɗai ya sani, amma abun ɗaure kai shine silar ɗaukar yarinyar da suka ruƙa matsayin ƙaddararsu suka kaita gidan kurkukun wanda silar kasantuwarta a gidan ya ja har suka samu shaƙuwa mai ƙarfi tsakaninta da shi garkuwar nasu ta yadda su kan su suka gaza raba shi da ita, silar hakan yaja har ya ku6utar da su daga kurkukun.
Big guy ne ya kora jawabin, bayan ya kai karshe Commender James Ya ce"That means Unaisah is his weak point, she can be used to control him, right?"
Jinjina mashi kai chief yayi murmushin gefen fuska James ya saki, "Everything will be easy for us if we can use her to control him"
"Da buƙatar mu san ya ƙarfin ikon su Yake? Menene rauninsu? da kuma Location ɗin da gidan kurkukun kaddarar Yake kafin mu fara shirye-shiryen kai masu farmaki" A cewar Captain lewis...
Chief Owais yace, "Karfin ikon su, suna iya 6acewa, bayan haka harsashin bindiga baya iya fasa fatarsu, makami ko wuta basa tasiri akan su, In har ba an ta6a lafiyar idanunsu ba, wanda kuma yin hakan ba abu ne mai sauƙi ba, saboda kakin Gaints ɗin dake a jikin su garkuwa ne, makami irin namu bazai iya yi masu illa ba..." gaba ɗaya hankalinsu ya tashi da jin bayanin Chief! Tunaninsu ta ya za'ai su farmaki mutanan da basa jin bullet, ko wuta balle wani makamin irin nasu.
Big guy ya ɗaura da cewa, "Bayan haka, su basa faɗa da makami sannan da bugu ɗaya suke kashe mutun." Waro idanu waje su commender suka yi gaba ɗaya sun kiɗima da jin zancen nan,
"Sanin inda gidan kurkukun ƙaddara yake mutun ɗaya ne zai iya yi mana jagora kuma shi kaɗaine zai iya taimaka mana gurin sanin ta yadda zamu iya kashe su cikin sauƙi"
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 & 08103884440*[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: _____________________________✍️🔥☠️🌹💋💔☠️💘😈❓❗
Ya faɗa yana ƙoƙarin taimaka mata don ta tuna.
Shiru tayi fuskar ta da alamun ruɗu sam takasa tunawa, Girgiza kai ta ɗanyi"bazan iya tunawa ba, dama hoto ɗaya ne akai..." bata ƙare maganar ba ya katse ta da cewa"zan baki lokaci, ki nutsu kiyi tunani a ina hotunan suke, cos inaji araina akwai hotunan nan biyu da babu jikin diary din, pls ki kokarta ba karamin taimako zaiyi mana ba gurin gudanar da binciken mu"
jinjina mashi kai tayi"in sha Allah zanyi kokarin in tuna" rufe Diary dinsa yai tare da maida shi cikin drawer.
Kiran Sallar asubahin farkone Ya karaɗe kunnuwansu, mikewa tayi da sauri tace"zan iya tafiya" ɗaga mata gira yai alamar eh..
Juyawa tayi da sauri ta nufi kofar fita, bai daina kallonta ba, har saida ta 6ace ma ganin shi.
Cikin tafiyar sanɗa take taka matalar benan gudun kada wani ya ganta ta fito daga ɗakin Chief a irin wannan lokacin, kamar wata munafuka.
Kwata kwata bata lura da mutun agabanta ba, sai yan waige waige takeyi kamar wuyanta zai balle Unexpectedly tayi tuntu6e da faffaɗan kirjin shi.
tsabar tashin hankali kusan suman tsaye tayi tunkafin ma ta kalli fuskarshi ta riga da ta gane wanene!
Ja da baya ta ɗanyi tare da sa tafin hannu ta dafe handrail ta ɗago tare da kallon shi from head to toe tayi mamakin ganin sleeping dress dinsa kalar na jikinta launi ɗaya, idanun shi manne da shade fari ya ɗaure sumar kan shi ta baya, ba karamin kyau yayi mata ba sai dai ta ji shakkar yanayin shi, ya haɗe rai kamar bai ta6a murmushi ba, Allah kadai yasan tun yaushe yake tsaye.
Ido cikin ido suke kallon juna batare da kyaftawa ba
tayi mamakin ganin fuskarshi a yamutse idanunshi sun dan kumbura da alamun rashin bacci atattare da su, ko me ya fito da shi a wannan lokacin? Ko dai damuwar maganarsu Salsabeel ce ta hana shi runtsawa ne"? Aranta ta ayyana hakan.
Shiru babu wanda yayi magana sai sautin numfashinsu dake fita har na tsawon mintuna biyar kafin ta katse shirun nashi da faɗin"My man, me kake haryan zu ba ka yi bacci ba"?
Shiru bai tanka mata ba
"How long have you been here"?
"Tun lokacin da kika shiga bedroom ɗinsa" waro idanu waje tayi sam ta kasa magana sai yan kame kame ta ke yi.
"Me kike yi adakinsa? Har na tsawon awanni hudu"? He asked throwing her a suspicious look She could see the jealousy on his face
Muryarta da inda inda tace"am..um..dama ɗazu ne da dare naje kai mashi backpack ɗin Unaizah daya bukaci yana son ganin ta saboda binciken da suke yi, shi ne da na shiga dakin na iske ya shiga toilet wanka, bansan bacci ya dauke ni ba, sai yanzu na farka..."
kasa karasa maganar tayi ganin yadda ya matso kusa da ita kamar zai rufe ta da bugu tuni tasha jinin jikin ta, bakomai yake kallo ba face kayan baccin jikinta sunyi uban squeezing kamar an kwatosu daga bakin kura, zuciya da saƙe saƙe saita dinga hasaso mashi abinda ya shiga tsakaninta da chief har wani jirin 6acin rai yake gani a cikin idaninsa.
Da wata irin kasalalliyar murya tamkar tame jin bacci ya furta"na yarda dake nasan ba zaki iya cin amana ta ba, amma meyasa zaki je dakinsa ki ɗauki lokaci har haka? Ki rasa inda zaki bacci sai dakinsa"?
Dafe kai tayi da hannu ɗaya harta fara tunanin lallashin shi ta bashi hakuri amma da ta tuna maganar daddynta sai ta samu kwarim gwiwar cewa"Sai me Danish in nayi bacci dakinsa? Fiye da haka ma zan iyayi!" gabansa ne ya fadi cike da mamaki yake kallon ta
"Ka bani kunya my man, ka rasa wa zaka butulce mawa sai Chief? Da ya Salsabeel? i heard everything daya faru tsakaninka da Chief" ta fada tana galla masa harara
"Wai har elders kake ikirarin basu ta6a cutar da rayuwarka ba, kuma sune kake kallo amatsayin iyayenka! Are you crazy? Ko ka fara shaye shaye ne"? Ta fada tana kallon cikin idanunshi, babu alamun zai tanka mata, kamar ana tunzurata ta cigaba da cewa
"Saboda me zaka ƙi ba su haɗin kai? Meyasa zaka rufawa Elders asiri? Ko dai kun haɗa baki da su? In ba haka ba, tayaya zaka rufa asirin miyagun da suka kaskantar da rayuwarka saboda muguwar manufarsu akanka"! Runtse idanun shi yayi gam maganarta ta daki zuciyarshi bai ta6a zaton zaiji kalaman nan daga bakin ta ba.
"Hmmm, dama nasan ba zaka ce komai ba, saboda baka da gaskiya Danish! I have been suspecting you for a long time since we were in prison baka ta6a faɗamin komai dangane da kurkukun ƙaddara ba, ni ban ma ta6a sanin me ake aikatawa a cikin kurkukun ba sai da karanbani na yakaini na gani da ido, meyasa ka boye min a lokacin uhyum"?
Bata jira amsar shi ba ta daura da cewa"Bayan haka ranar da Giants suka zo daukar Batool da hannunka ka miƙata, ta rayu ko ta mutu, baka damu ba, hakan na nufin kaima da sa hannunka ake akaita komai, watakil ma ɗan leƙen asirin su ne halan...." kasa karasa maganar tayi sakamakon bugun handrail da yayi da tafin hannun shi, saboda zafin maganarta dayaji, buɗe idanunshi yayi sun kada jawur ita kanta sai da taji gabanta Ya faɗi amma ta dake ta jajirce don ta harzuƙa shi tayi karfin hali cigaba da magana
"Ka sha faɗamin kai garkuwane agareni, mai bani kariya, zaka iya komai dan farin cikina, Danish Ina son na tabbatar da son da kake min, shin zaka Iya sadaukar da farin cikin ka saboda nawa" ta fada batare da ta kau da ido daga kallon shi ba..
Jinjina mata kai yai alamar eh, murmushin gefen fuska ta dan saki kafin ta haɗe fuskarta tamkar bata ta6a dariya ba.
"Danish, Inaso ka yi masu jagora zuwa gidan Kurkukun ƙaddara..."
bata kare maganar ba Yai hanzarin furta"bazan Iya ba, pls kada ki tursasamin inyi abunda banyi niya ba..." a rude yake maganar
da kakkausar murya tace"nasan zaka Iya ne shiyasa na umarce ka da kaje, saboda ni nasan wanene Man dina, kada ka bani kunya, bansan ka da tsoro ba.."
"Bazan je ba, bana son duk wani abu da zaiyi silar raba mu, suma ina jiye masu haɗarin da zasu jefa rayuwarsu, Ja da Elders ba abune mai sauƙi ba, basu da karfin da zasu iya farmakarsu please understand me..."
fuskarsa ayamutse yayi maganar
"Danish Idan har bazaka je ba, to inaso ka sani zan yanke duk wata alaƙa dake a tsakanin mu! Saboda bazan ta6a auran ragwon namiji ba, matsoraci wanda bazai iya jefa rayuwarshi cikin hadari don ya ceci rayukan Al'umma ba ya kuma kawar da masu aikata zalunci a doron ƙasa.."
waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata faɗo ƙasa.
"Chief yafika jarumtaka, yana da zuciyar imani da tausayi, baisan mu ba, bai hada alakar komai damu ba, amma saboda kyakkyawar zuciyarshi burinshi Ya taimaki rayuwarmu data sauran yaran dake agidan kurkukun kaddara sannan ya kawar da miyagu a cikin al'umma bai damu daya rasa ranshi ba! a shirye yake da ya sadaukar da ranshi saboda ya ceci rayuka kaifa? Ta jefa mashi tambayar shiru yayi bai tanka mata ba
"Saboda kai na hakura da burina na ganin na auri attajirin mai kuɗi mai asali ɗan babban gida, mai ilmin addini dana zamani, naji zan iya rayuwa dakai ahaka saboda kaunar da nake maka, amma meyasa kai ba zaka iya hakura da ra'ayinka akan nawa ba"?...dakyar ta ƙare maganar saboda hawayen da suka kubce mata tana mai jin takaicin tilasta masan da take kokarin yi.
"Danish baka da komai, in banda kyan da Allah yayi maka, If I marry you, how will I be proud of you"? Cikin shesshekar kuka ta faɗa
"Ace na auri ragon namiji mai tsoron zuwa yaki? Ko arne mara addini? Ko kuwa jahili dabaisan komai ba? Ko matsafi mai goyon bayan matsafa wurin aikata zalunci"!
Kiris Ya rage Ya yanke jiki ya fadi saboda wutar bacin rai data ziyarci zuciyar sa
Maganganunta sun ta6a zuciyarshi ba ƙadan ba, Yaji zafin su sosai, ita kanta ta tsorata da ganin yadda gumi ke tsastsafo ma shi, duk da tana jin tsoron kada Evil's heart dinsa ta motsa, amma dayake idanunta sun rufe burinta kawai ya amsa bukatarta.
Da wata irin karyayyar murya mai cike da 6acin rai ya furta"Angel, mafarki nake ko gaske? Da kanki kike jifana da waɗannan munanan kalaman? ni Angel? Your Shield"? numfashi ya ɗan ja kamar bazai iya karasa maganar ba yace"meyasa zaki min haka? Lafin me nayi maki da cancani cin mutunci daga gareki? Angel kema Kina min kallon jahili? Mara asali? Kuma kika kira ni da matsafi"?
ɗaga mashi gira tai"Hell fucking yeah, ko nayi ƙarya ne"? Kasa magana yayi,
"abu ɗaya ne zakayi wanda zai wanke ka daga gareni, shine Ka cire tsoro, Ka basu haɗin kai akai farmaki gidan kurkukun kaddara, ta hakanne kaɗai zan yarda dakai in kuma har ka bijire min kaki bin Umarnina, wlh na rantse da wanda raina yake a hannunsa muddin baka bada goyon baya ba, na kwammace in mutu da ciwon sonka, akan in aure ka"! Da sauti mai karfi tayi maganar tare dakai hannu ta daki handrail..
duk abunda ke faru tsakanin su babu wanda ya sani
"In kuwa har ka bari Chief yayi nasarar ruguza kurkukun ƙaddara batare da taimakonka ba, zan mallaka mashi kaina..." bata kare maganar ba sakamakon zazzafan marin daya kwasa mata wanda shi kanshi bada sanin shi ba, a karo na farko data fara jin tafin hannunsa akan fuskarta da sunan mari, wa'iyazubillah wani azababben radadi taji ya ratsa sassan jikin ta kamar an watsa mata wuta jirine Ya kwashe ta, ta tafi zata kife ƙasa cikin zafin nama Ya taro ta da hannunshi ya dawo da ita kan kirjin shi, yayi hanzarin daukarta kan kafadarshi Ya nufi bedroom dinshi da ita gudun kada wani ya riskesu a halin da suke a ciki.
Yana shiga ɗakin Ya kwantar da kan gadon shi, kamar matatta, da alama suma tayi saboda azabar da taji.
Hankalin shi idan yai dubu toh ya tashi, Jikinshi sai kerma yake kamar wanda sanyi Ya kama, zafin Kishi Yaja mishi bala'e..
Duk da sanyin A.c din dakin hakan bai hana gumi tsastsafo mashi kan fuskarshi ba, zukunnawa yayi daga bakin gadon yana kallon gefen fuskarta, shi kanshi Ya tsorata da ganin yadda fatar gurin tayi ja sosai, shatun fingers in shi ya fito ruɗu ruɗu.
Yatsun hannayen shi Ya zuba ma Idanun shi Yana kallon su cike da danasanin marin da yayi mata, ya san yadda marin Evil giant yake da zafi, zata Iya kai Sati da radadin dafin marin a jikin ta.
cike da takaici ya dinga bugun kanshi da hannayen shi kamar zai zauce saboda zafin abun da ya yi mata
Tuni hawayen da suka taru cikin idanunshi suka fara Yar tseral kan kuncin shi, abu biyu ya haɗe mashi ga zafin munanan kalaman data jefe shi da su ga takaicin marin da yayi mata.
Cikin karyayyar murya ya furta"ba laifina bane, ke ce kika bata min rai, gashi kinja na mareki bada son raina ba" ya faɗa tare da daura tafin hannunsa saitin inda Ya mare ta, dabara ce ta fado mashi da sauri ya saita fuskar shi saitin tata, sihiri gaskiyar mai shi, ruwan hawayensa dake ɗiɗɗiga kan fuskarta sune suka goge tabon marin da ya yi mata cikin kankanin lokaci fatar ta dawo fara sol kamar ta jinjira, numfashi Yaja tare da sauke ajiyar zuciya a hankali launin idanunsa suka dawo yadda suke.
kallonta da yake yi ahaka yafi masa kwanciyar hankali akan Ya farfaɗo da ita saboda fargaban masifarta.
Daga gefenta Ya raba jikin shi, Ya kwanta tare da lumshe idanun shi, bai ta6a fuskantar tashin hankali irin na yau ba, tayaya zai iya shawo kan Unaisah ta fahimci abunda yake nufi"?
Kwatsam yana a cikin mawuyacin halin nan ba zato ba tsammani ya tsinkayi Muryar Khala a cikin kunnanshi..
"Uhum Garkuwa Namu"
A rude Ya mike zaune yana bin dakin da kallo, cikin sauri Ya share hawayen fuskarsa, jikinshi har 6ari yake garin zumudin ya sauko daga kan gadon, Hasken ɗakin shi ne Ya dauke ɗuff Duhu Ya mamaye ko'ina, bai nufi ko'ina ba sai gaban mirror Ya yaye madubin idanunshi su ka yi mashi tozali da tsohuwa Khala zaune kan armchair, Cikin shigarta ta gado fuskarta a yamutse ba annuri.
Zama yayi kan Mirror chair din with respect ya gaishe da ita, da fara'a ta amsa mashi
Kafin Ya nutsu Yana jiran jin me zata ce ma shi
"Ina fata kun fara shirye shiryen kawo farmaki"? shiru ya yi baice mata uffan ba.
Yanayin dake a kan fuskarshi ta nazarta nan take ta fahimci baida matsaya
Yar dariya tayi"jikana, faɗamin ba, me ake Ciki ne"? dakyar Ya labarta mata abinda ke faruwa bai boye mata komai ba
Girgiza kai tay"yaro man kaza, Har yanzu Jinin Elders ne a jikin ka, amma Alhamdulillah naji dadi da Allah Ya bani ikon ganawa dakai a karo na biyu, saboda na fahimci ka na bukatar in wayar maka dakai, in kuma yi maka karatun ta nutsu ta yadda zaka fahimci su wanene Elders da kuma dalilin dayasa suka raine ka..." aruɗe Yake kallon fuskarta...
"Kasan wacece ni, ka kuma san matsayina agidan kurkukun kaddara, nafi ka sanin komai Danish, duk wani abu da suke aikatawa a tafin hannuna yake" ta faɗa tana nuna mashi tafin hannun ta.
"Abu na farko da baka sani ba, Elders Mayaudara ne, Maha'inta, maciya amana, bansan ko ka san da labarin nan ba, amma inaso ka sani tun kana jinjirinka cikin tsummanka suka sace ka daga wurin iyayenka, suka rabaka da su batare da saninka ba, sannan suka sadaukar da kai zuwa gidan kurkukun ƙaddara, Ni nasan su wanene Iyayen ka, wallahi basu san kana araye ba, an yaudare su ne da sunan ka mutu...." dafe kanshi yayi da hannu ɗaya zuciyarshi cike fal da ruɗanin maganarta, bazai ce tayi karya ba sai dai kokwanton da zuciyarshi keyi bazai bari ya aminta da ita ta cikin sauƙi.
"Bani da isasshen lokacin da zan yi maka bayani, amma atakaice ka zauna kayi nazari Danish, kai ganau ne ba jiyau ba, kasan komai, har yau zubda jinin mutane suke yi kamar kwari, Laifin me suka yi masu? Ahaka zaka rufa masu asiri uhyum? Ita kanta yarinyar da kake gudun rabuwa da ita ba zasu kyale ta ba, wallahi in har baka bada goyon baya an kawo karshen su ba, da kai da ita sai kun salwanta, saboda suna nan suna shirin yadda zasu kashe ku.."
waro idanun shi waje yayi jin abinda tace.
Murmushin gefen fuska ta saki tare da jinjina mashi kai"hmm wai kana tunanin Suna kaunarka? To wallahi ko ɗaya basu ta6a kaunarka ba, sun raineka ne don biyan bukatar kansu, idan kai me hankali ne ga misali nan, Yanzu da suke ganin sunci moriyarka amfaninka ya kare kana neman tona masu asiri ba ga shi har sun ɗauke mukamin da suka baka na garkuwarsu ba, sun ba Jeremiah, kai kuma nema suke su salwantar da rayuwarka saboda kai kadaine kasan sirrinsu dakai kadai za'a iya farmakarsu...."
wani irin gumin tashin hankaline Ya wanke fuskarshi, Maganar tsohuwa khala tayi matuƙar yin tasiri a zuciyar shi.
Kusan sau uku Tana ambaton sunan shi bai amsa mata ba, saboda zuciyarshi ta lula duniyar tunani
Har saida tayi mashi gyaran murya kafin ya dawo hayyacin sa
"Ina Gabriel? Ya rayu ko ya mutu"? ya ɗanyi mamakin jin ta tambayi gabriel ko a ina ta san shi"?
"Yana adakinsa, bacci yakeyi"
"Masha Allah, Naji dadin jin hakan, sai dai, Yar Uwarsa daya bari agidan kurkuku tana acikin mawuyacin hali..."
"Who's she? ya tambaya don sam ya manta da cewa Gabriel Yana da sister.
"His twin sister Gabriella...." a takaice ta labarta mashi rashin imanin da tsohuwa inno tasa giant yayi mata, tsabar 6acin rai jikinshi har tsuma yakeyi
"ta rokeni akan Tana son ganin ɗan uwanta, nayi mata alkawarin ko zan rasa raina ne in dai muna da tsawaicin kwana zan haɗa ta da ɗan uwanta" cikin rauni na murya tayi maganr tare da mikewa daga kan kujerar da take, ta haske mashi Gadon da Gabriella take akwance kamar babu rai a jikinta, sai jan numfashi take dakyar dakyar
"Nayi zaton ta samu lafiya, amma wani abu ya faru jiya wanda Ya ɗaga hankalina, tana daga zuƙunna tayi aman Jini, ta dafe ciki tana faɗin Yan hanjinta suna konewa, Inaji araina Inno ce tayi mata asiri, nadai yi kokarin yi mata yan dabaruna ahaka Jikin da sauƙi amma tana bukatar taimakon gaggawa daga gare ku idan ba haka ba da wuya ta rayu.."
Jikin shi yayi sanyi saboda tsantsanin tausayin yarinyar daya kama shi, yanzu ya tuna ranar farko da aka kawo su har tsohuwa Zafreen tasa aka raba su.
"Danish Ahaka zaka rufa masu asiri? Shikenan babu wani wanda zai kawoma bayin Allah dauki! Haka zamu barsu su cigaba da azabtar da rayuka? Ba zamu ɗauki mataki ba"? Sam ya kasa magana saboda raunin da zuciyar shi tayi
*Da wata irin kakkausar murya ta firta"YA RAGE NAKA GARKUWA, DOLE ƊAYA CIKIN BIYUN NAN YA FARU! KO DAI KA BADA GOYAN BAYA AKAWO MASU FARMAKI, KO KUMA SU SU KAWO MAKU FARMAKI SU GA BAYAN KU..."*
Sau Uku ta maimaita Hakan, kafin ta cigaba da ƙarfafa mashi gwiwa daga bisani bayan ta ƙara jaddada mashi kwanan watan da zasu yi black night, ta bashi wasu muhimman bayanan da zasu amfane su, daga nan ta 6ace ma ganin shi, kifa kanshi yayi gaban mirror ɗin Zuciyar shi cike fal da damuwa, anan wani wahalallan bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.
Lokacin da Batool ta farka daga bacci taga babu Unaisah adakin, bata damu ba, bayan tayi sallar asuba, taji shiru bata dawo ba, hakan yasa ta miƙe ta fito daga dakin tafara neman ta, sai da tabi ɗakunan Yan uwansu duka ta duba taga babu Unaisah, Hankalinta ba karamin tashi yayi ba,.
Da sauri ta nufi ɗakin Aunty Ummunsu, tayi knocking almost 3 times, kafin ta samu Ummi ta buɗe kofar, tana miƙa hadi da yin hamma ko kayan baccin jikinta bata kaiga cire wa.
"Babe, Har kin tashi"? Daga mata tayi"Aunty Ummi sister tazo nan? Na farka banganta ba"
Girgiza kai Ummi tayi"Bata zo ba, kin duba ko'ina"?
"Eh," ta fada da damuwa
"Kada ki damu, nasan duk inda taje tana acikin gidan nan" ta faɗa tare da ruko hannunta"mu shiga daga ciki, Ki jira ni in shirya sai mu fito tare" amsa mata tayi da toh.
Bayan shigar su ɗakin, Ummi ta kunna mata kallo a laplop ɗinta, kafin ta shiga bathroom don tay wanka.
Nutsuwa tayi kan gadon tana kallon drama, ta shagala da kallon wayar Ummi ta fara ruri.
Ɗauko wayar tayi daga kan pillow, ta duba screen ɗin bata gane me aka rubuta ba saboda bata iya karatu ba..
Da karan banin ta tayi picking call ɗin kamar yadda taga Unaisah nayi, ashe video call ne, yanayin yadda ta ruke wayar yatsan hannunta yayi hiding front camera, wanda Ya kira bazai Iya ganin ta ba, kura idanu tayi aka fuskar mutumin dake kwance cikin bathtub, ruwan kumfa ya rufe Jikin shi fuskar shi kaɗai take Iya gani yayi shiru yaki magana itama tayi shiru taƙi furta kalma zuciyarta cike fal da tunanin wanene Wannan ƙaton.
"Ummi meyasa kike boye fuskarki? jira kike saina maki magana"? Muryar shi ce ta katse shirun ta..
Jin motsin buɗe kofar toilet, yasa ta danna end Call, da sauri ta mayar da wayar kan pillow ta aje.
Ta yi hakanne saboda Ummi ta ta6a gargaɗinta, akan in ankira wayarta bata akusa kada tayi picking dama bata ta6a kuskuren daukar mata waya ba saboda ta fahimci bataso.
Koda Ummi ta fito bata faɗa mata an kira wayar ba, bayan ta kammala shiryawa atare suka fito daga dakin.
Har wuraren ƙarfe tara, basu ga Unaisah ba, gashi Har time ɗin Yin breakfast dinsu ya yi gaba ɗaya yan uwansu sun hallara a dining ita kaɗai su ke jira sun yi neman har sun gaji kuma babu wanda yai tunanin tana adakin Danish.
Can cikin kunnuwanshi suka soma jiyo mashi sautin tarin ta, firgigit Ya farka da kasala Ya miƙe zaune Yana kallon ta da idanunsa waɗanda suka kumbura.
A hankali ta miƙe zaune tana Hamma Wata Irin Yunwa take ji, kwata kwata bata iya tuna abun da ya faru ba, fitsari ne Ya matse, saukowa tayi daga kan gadon da sassarfa ta shige toilet ɗinshi sai da ta gama tana kokarin fitowa idanunta suka sauka akan shi, Ya zafga Uban tagumi da tafukansa kamar wanda Ya rasa gata a duniya.
Nan take komai daya faru tsakanin su Ya dawo mata acikin tunaninta, gefen fuskarta daya mara ta shafa da tafin hannun ta, harara ta watsa mashi taja tsoki, kafin ta juya zata bar ɗakin.
takun tafiyarne Ya fargar da shi, da sauri Ya miƙe ya shagabanta kiris Ya rage kirjinta Ya bangaji na shi
"Bani bukatar Jin komai daga gare ka, bani hanya na wuce"! tana huci ta faɗa tana neman rabawa ta gefen shi don ta wuce
Cikin sauri ya ruƙo Arm ɗin ta, hakan yasa ta dakata da tafiyar
"I want to ask you one question."
shirun da tayi ne yasa shi fahimtar jiran shi takeyi
"baki tsoron ki rasa ni"?
"Danish, ko da Ina jin tsoron In rasa ka, Ka tuna ranka ɗaya ne tak! da shi kadai zaka Iya taimakon dubban rayuka, ka kuma yi silar tarwatsa gang din azzalumai"
"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"? jinjina mashi kai ta yi"nafi maka kwaɗayin ka mutu a filin yaƙi, kwara mu hakura da duk wani buri da muke da shi, mu bada rayukanmu donmu taimaki bayin Allah, in sha Allah ko bamu ji dadi anan ba, zamuji acan, in ba haka ba mutanan nan bazasu ƙyalemu muyi rayuwar farin ciki ba, saboda mun san sirrin su kuma mune na farko da muka gudu daga gidan kurkukun ƙaddara, mun tona asirin su, zasu nemi hanyar kashe mu ne, ka fada min taya zamuji dadin rayuwa da fargaba a zukatan mu? Kaima fa har yanzu suna atare kai, Ka tuna abunda kayi min rannan, wata rana har kashe ni zaka iya yi ba acikin hayyacin ka ba, dan Allah ka fahimce ni, rayuwa bazata yiwu ahaka ba, kana bukatar ka zama cikakken mutun"❗
duk yadda taso ta jure saida idanunta suka cika tab da kwalla kwata kwata bataso Yaga rauninta, tafi son yasan da gaske take don ta samu ya amince.
Batai aune ba, Taji Ya zube kan gwiwowinsa, A hankali ya jinginar da kanshi jikin laps dinta, ya zagayo hannayen shi kan waist ɗinta ya ruƙe ta gam, da wani irin hucin zafi numfashin shi ke fita ya riga daya sadaƙas Angel had already won him over, dole Ya mika wuya, abu ɗaya da bazai ta6a mantawa ba, munanan kalaman da ta furta mashi, tabbas Yana son wata rana ya bata mamakin da zaisa tayi danasanin abunda tayi masa.
Cikin karyayyar murya tamkar ta majinyaci Ya furta"Na amince, zan basu haɗin kai, all because of you, Whatever happens to me, blame yourself .." kasa ƙarasa maganar yayi saboda raunin da zuciyar shi tayi..
Angel dake tsaye kamar gunki tana kallon sumar kanshi, ruwan hawayen ta dake gangarowa kaitsaye suka ɗiɗɗiga saman sumar kan shi, baiwar Allah duk sai taji ba daɗi, Zuciyarta ta karaya da kalaman shi,.
Ta rasa farin ciki zatay da amincewarshi ko bakin ciki? ita dai tasan Ita da kwanciyar Hankali sunyi bankwana.
Yatsun Hannunta na kerma Ta shafa sumar kan shi, dakyar ta banbare hannayenshi daya ruke waist ɗinta da su, ta fuce daga ɗakin, akan flooe Ya kwanta tamkar babu jini ajikin shi.
maganganun mutun biyu ne sukayi tasiri akanshi, Tsohuwa Khala and his Destiny, yaci alwashin duk runtsi duk wuya sai yaga bayan Elders sannan Yana son yaje kurkukun kodan Ya haɗu da tsohuwa khala saboda yana son ta faɗa mashi su wanene iyayen shi saboda ya fahimci su kadai ne zasu iya bashi abun da akeyi mashi gori akai❓
___________________________________________✍️
Idan muka koma Gidan baba Obie, tun da Owais Ya faɗa ma Pravin zancen tafiyar da yake so suyi tare da baba Obie, Hankalin Shi ya tashi haiƙam, gaba daya ya rasa nutsuwar shi saboda bakin ciki Ya tafi batare da ya ƙarasa aiwatar da mummunar kudirinsa ba, wunin ranar a daki yayi saboda damuwa har hajiya saratu saida ta lura da yanayin shi har tambayar shi tayi meke damun shi yace mata bai da lafiya zazza6i ke damun shi ga owais ya nemi alfarmar ya raka baba Obie lagos, baisan ya zaiyi ba yana jin nauyin yace bazai je ba
Hajiya saratu tace bazaima yiwuwa ba, zatayi ma baban magana anemi wanda zai bi sa suje tunda shi ba koshin lafiya gare shi ba.
kafin hajiya saratu tayi ma baba Obie magana Pravin yaji labari awurin hajjaty, a jiya daya shiga ɗakinta ya iske ta zaune tsakiyar gado tana ta kuka ya tambayeta meke damunta, nan take labarta masa baba obie ya kira ta adakinsa ya sanar da ita gobe kafin ya tafi zaisa jami'ai su maida marwa garin su gurin iyayenta, zata fi samun kulawa agurin su su kuma zasu cigaba da bata tallafi.
Da jin wannan maganar, pravin ya washe baki, bai ma tsaya ya karasa jin karashen zancen ba, Ya fuce daga dakin Ya koma dakin hajiya saratu ya tambayeta shin dagaske ne za'a maida marwa garin su tace mashi eh, ay itace ma tayi ma baba obie magana amayar da ita saboda su twins tana son su dawo gidan da zama.
farin cikine ya lullu6e parvin harya manta da karyar ciwon da yakeyi yace mata ay yama ji saukin zazza6in zaibi baba obie suje lagos din, tace mashi a'a gaskiya tafi son ya wartsake in yaso daga baya sai ya bishi, yasa naci akan shi dai zaije tace meyasa zai takura kansa bayan ba koshin lafiya gare shi ba, ya marairaice mata fuska da dadin baki ya shawo kanta harta amince bazata fada ma baba Obie ba.
Washe gari da sassafe, jami'an da za su tafi da marwa, suka doko sallama, a lokacin hajjaty tana adakinta tare da sauran yan aikin gidan sun hadu suna shirya mata kayanta, Baiwar Allah sai kuka take yi su kansu kukan sukeyi na rabuwa da ita, bayan sun kammala shiryata Hajjaty da Abla suka daukota sauran masu aikin na abiye dasu A harabar ajiye motoci su ka iske mutanan gidan sun hallara domin yi mata bankwana.
A lokacin bakowa marwa ke kallo ba face pravin dake ta kashe mata ido yana sakin wani dan iskan shu'umin murmushi duk idan ya fakaici idon mutane, marwa tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda bakin cikin zata tafi batare da ta tona asirin wanda yai mata aika aika ba..
har suka shigar da ita cikin mota bata daina gunjin kuka ba, haka ta dinga bugun window glass din motar da hannayenta kamar zata fasa shi.
babu wanda ya fahimci mai marwa take nufi, gaba daya sunyi tunanin zafin rabuwa dasune yasa take yin haka, har alkawari hajjaty tayi mata akan kullum zata dinga kiranta awaya sosai ta kwantar mata da hankali, bayan sunyi mata bankwana Akan idonsu Motar ta fuce daga gidan bayin Allah sunyi kukan Rabuwa da marwa.
Pravin kau ranshi fari tass Kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha Hankalin shi ya kwanta baida sauran damuwa, Ya kira zaid awaya yayi masu albishiri na tafiyar marwa, Ya kuma labarta masu maganar tafiyar da zai yi tare da baba obie, sannan Yace su dawo gida Yana son ganinsu kafin su tafi.
Bayan dawowar su twins, murna awurin hajiya saratu kamar ta shekera bata gan su ba, cos tayi kewarsu ko kaɗan batai masu fadan zaman su a hotel ba, haka shima Uban saima tarairayarsu da ya ke yi.
Wuraren ƙarfe shabiyu na yau, gaba daya Yan family din dake a estate din suka yi ma baba Obie rakiya zuwa Airport kamar wanda zai bar kasar, hada Owais da su Senate Lateef kowa da kowa, kamar karsu rabu da shi saboda kaunar da suke ma mahaifin su.
________________________✍️
(After One Day, Bayan kwana ɗaya)
Yana tsaye gaban Dressing Mirror, har ya kammala shirin xuwa Office, jikin shi sanye da kakin shi, fuskarshi kwata kwata babu walwala tamkar bai ta6a dariya ba, saboda matsananciyar damuwar data yi mashi ƙatutu a zuciyarshi, Ga rashin isasshen baccin da baiyi ba jiya idanun shi sunyi ja sun ɗan kumbura.
Har ya miƙa hannu zai ɗauki watch daya daura gaban mirror kamar ance ya ɗago da idanun shi ya kalli mirror Unexpected ba Ya hango shi tsaye ta cikin madubin Ya goya hannayen shi akan kirjin shi, Jean da t.shirt ne a jikin shi.
wani irin faduwar gaba yaji saboda bai tsammaci zaiga mutun adakin shi ba! Taya akai ma ya shugo bayan kofar tana da security? Zuciyarshi ce ta bashi amsa da cewa ka manta sihirin dake ajikin shi? A sukwane ya juyo tare da kallon shi..
Yadda kasan wanda Ya ku6uto daga gidan mahaukata, Sumar kanshi ta yamutse, Fuskarsa ba annuri kamar bai ta6a dariya ba.
hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, ganin yanayin da Danish Ya faɗo ɗakinsa, ya rasa meke damun shi? Yayi rashin lafiya ne? Kai daga ganinsa ba lafiya ba.
muryar shi da ruɗani Ya furta"Danish? Meke damunka? Baka da lafiya ne"? Ya faɗa akagare da son jin amsar shi.
Cikin sanyin murya yace"zan baku haɗin kai, and I will lead you to the Prison of Destiny, I will help you fight them"
kamar amafarki yaji kalaman Danish saboda mamakin daya mammaye shi, hannu yasa ya ɗan murza kunnan shi don ya tabbatar ba makuwa yayi ba yace"dagaske kake ko wasa"?
"I'm serious..." tsabar farin Ciki yasa chief zubewa kan gwiwowinsa yayi sujjada domin nuna godiyarsa ga Allah.
a daren jiya ya raba dare yana yin Nafilfili akan Allah ya shiga lamarinsu ya kawo masu hanya mafi sauki da zasu farmaki Elders sai gashi cikin ikon Allah yau da safe Allah ya kar6i addu'arsa.
Lokacin daya ɗago daga sujjadar tsantsar farin cikine akan fuskarshi, miƙewa yayi tare da nufar Danish yayi hugging ɗinsa tighly kamar zai maida shi cikin shi saboda faranta masa da yayi bai ta6a jin masifar kaunarsa ba irin na yau.
Dagowa yayi tare da dafa kafadunsa suka fuskanci juna.
"Danish, bazan Iya misalta maka farin ciki da nake a ciki ba, Ka faranta min raina, amma kai da kanka kayi ra'ayin ka bamu hadin kai ko wani ya tilasta maka? Saboda yanayin ka ya nuna kamar bada son ranka ba"
Girgiza mashi kai yayi ba tare daya furta kalma ba.
"Kamar baka da lafiya"? Ya kuma tambayarsa
"Lafiyana lou, just ask me anything you want to hear from me, and I'll tell you."
abun nema ya samu da sauri chief ya ruko hannun shi ya zaunar da shi gefen gadon shi.
Kafin ya dauki wayarsa Ya kira landline din kitchen Ya isar da sakon akawo mashi breakfast ɗinsa da baiyi niyar ci ba, amma saboda suji dadin tattaunawa da danish shiyasa ya umarci akawo mashi.
Ba'afi mintuna biyar ba, kuku ya shigo hannayenshi ruke da wooden tray shaƙe da kayan abinci ya aje masu kan table kafin ya fuce daga ɗakin.
"Nasan kana jin yunwa, mu fara yin breakfast, kafin mu fara tattaunawar tamu" girgiza mashi kai yayi"bazan iya cin komai ba.." bai ƙare maganar ba chief ya katse shi"pls kada muyi haka dakai, ko kaɗan ne ka ci"
matsa mashi yayi dakyar chief ya shawo kanshi, bayan sun kammala yin breakfast ɗin, Chief ya cire Coat dinsa Ya rage daga shi sai vest, babu zancen zuwa Office, zuwan Danish Yafi komai mahimmanci a halin yanzu.
A tsakiyar gadonshi suka zauna suna fuskantar juna kamar malami da dalibinsa, sai da ya fara kunna audio recording din wayarsa, kafin ya tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan Danish
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 & 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: ________________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️❓😈👹💞💘
"duk da ɗan uwanka Salsabeel da sauran Yan uwanka sun fada mana komai dangane da gidan kurkukun kaddara, Ina neman ƙarin bayani daga gare ka, saboda kafi su sanin komai"
A tsanake Danish ya fara kora mashi jawabi tiryan tiryan bai 6oye mashi komai ba.
"Inaso Naji tayaya su ke mayar da mutun ya zama Giant ɗin su"? Ya tambaya yana kallon cikin idanun shi"
Wa'iyazubillah, Tunkan Ya karasa labarta mashi, chief Ya runtse idanun shi saboda fusatar da zuciyarshi tayi tamkar zata tarwatse tsabar bacin rai, bakomai yafi karya mashi zuciya ba face irin azabtarwar da suke yi masu kafin su mayar da su Giant, matasan yaran da basu ji ba basu gani ba, abu mafi muni rashin imanin da suke sanyawa su aikata abun ya munana sosai.
wani irin tsantsar tausayin Danish Ne ya ƙara ninkuwa cikin zuciyarshi, abun ya ɗaga hankalinshi matuƙa.
la66anshi na rawa ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"! Ya ambaci hakan Yafi sau talatin..
Danish dake kallon shi Ya fahimci matsanancin tashin hankalin da ya ke a ciki.
Numfashi ya ɗanja yayin da siraran hawaye suka fara zarya kan kuncin shi..
Cikin raunanniyar murya ya furta"I can't describe the pain I felt in my heart, it saddened me hakika sun cutar da rayuwarku, yanzu da kananun shekarun ka, ahaka suka sanyaka ka aikata duk wadannan abubuwan, Wa'iyazubillah, what kind of disaster is that?"
Jinjina kai ya yi "Allah baya barin hakkin wani akan wani, akwai sakayya, In sha Allah tun agidan duniya zasu fara gir6ar abun da suka shuka kafin su fuskanci mutuwar su.."
Danish yayi shiru yana sauraron shi, bawan Allah Ya zama kamar saƙago jikinshi duk babu karsashi shi kadai yasan damuwar dake adabbarsa..
"ka faɗamin gaskiya dagaskene bakasan fuskokin su ba? Abun ya tsaya min araina tsawon shekara 20 tun kana jariri harka mallaki hankalinka amma baka ta6a ganin fuskar su ba"? Ya faɗa fuskarsa ayamutse yana mai dubashi.
"ba sanin su ke banyi ba, nasan fuskokin su amma bazan ta6a iya shaida su ba acikin mutane, saboda suna amfani da karfin sihirinsu gurin canza kamanninsu dama halittar jikinsu shiyasa nace maka bansan fuskokin su ba"
gyaɗa kai chief yayi na yarda dakai amma miye sunayen su daka san suna amfani da shi"?
"Elder, shine shugaban kurkukun ƙaddara, Da iznin sa komai ke faruwa, bayan shi sai mataimakinsa Jan harshe shine mai zartawarwa, na ukun su Jan Wuya shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon Giant, na hudun su Jan Ido shike kula da bangaren safarar yaran da ake kaiwa gidan kurkukun ƙaddara.........."
Tun daya fara magana Chief Ya nutsu yana sauraron shi har sai da yakai aya kafin yace mashi"Alfarmar da zan nema agurinka, kafin mu kai farmakin Inaso ka dinga bin mu zuwa headquarter donka taimaka ma Isod soldiers din mu da horon yadda zasu yi faɗa da Giants.."
Amsa mashi yayi da toh sannan ya faɗa masa date din daya kamata su je, kamar yadda tsohuwa Khala ta shawarce shi da su kai farmaki adaren ranar, amma bai sanar da shi daren menene ba.
Da tsantsar farin ciki Chief Ya ruƙo hannayen Danish a cikin nashi ya ruke su gam.
"Bansan taya zanyi maka godiya ba, kalmomi sunyi kadan Danish, Ka faɗamin duk wani buri da kake son cimmawa, Ni kuma na maka alƙawarin In har baifi karfina ba zan cika maka shi"
ya faɗa da ɗan murmushi kan fuskarshi, Danish bai furta komai ba, sai faman lumshe idanun shi yakeyi kamar gyangyaɗin bacci ya ke yi.
Lura da hakan yasa Chief ya ruƙo hannayen shi Ya taimaka mashi Ya kwanta kan gadon, wani irin bacci ne mai nauyin gaske yayi awon gaba da shi.
(Lallai Gadon Chief Yayi albarka, Unaisah ta kwanta, Ga Danish ma Yayi bacci akan shi😂 saura ni ma zan ɗana)
_________________________________✍️
Da yammacin Ranar, Chief Ya kira Meeting din gaggawa wanda su kayi A headquarter din su tare da Manyan jami'an Isod dana Sojoji, da kuma U.s army, gaba ɗayan su suka hallara a meeting room ɗinsu, bayan Chief ya kunna masu audio ɗin daya dauka na tattaunawar shi da Danish, sunyi matuƙar yin mamakin amincewar shi, musamman big guy, sun kuma ji dadin yadda ya basu hadin kai cikin sauki batare da sun sha wahala ba, ba tare da 6ata lokaci ba, kowa Ya fara kawo shawarar shi dangane da yadda zasu kai farmakin, babu wanda bai tofa albarkacin bakin shi ba, basu suka tashi meeting din ba, har saida suka tsayar da kwanan watan da Danish Ya faɗa ma chief amatsayin Ranar da zasu kai farmaki.
Tun daga ranar su ka fara shirye shiryen tafiya Yaƙi babu kama hannun yaro, basu da wani hutu, gagarimin shiri suke na musamman kuma komai nasu cikin sirri suke yin shi saboda tsaro ba don tsoro ba, sun tanadi Miyagun Makamai da zasu yi amfani da su agurun gabzawar.
Tawagar Dakarun sojoji Uku ne zasu je kai farmakin, tawaga ta farko Isod Soldiers ne, bayan su sai Tawagar Sojojin Nigeria, Tawaga ta uku ta U.s Soldiers ce.
a bangaren Unaisah Da Danish tun ranar da ta tursasa mashi akan ya amsa zai basu hadin kai, basu ƙara haɗuwa da juna ba, walwalarsu ta ragu, rayuwarsu ta ƙuntata saboda tsantsar damuwar da suka shiga na fargaban kada su rasa junan su, bayin Allah ta ko'ina ba sauƙi, kokari sukeyi su saba ma kansu rayuwa batare da juna ba don su saukaka ma kansu radadin son juna da suke ji a zukatansu, sai dai abun yaci tura, abun sai ya zamana kamar suna kara rura wutar son da suke ma junansu ne.
Ba karamin maraicin shi takeyi ba, saboda shirya shiryen da sukeyi na tafiya yaƙi yasa baya zama gidan, atare da chief suke zuwa headquater saboda taimakon da yakeyi masu gurin ƙara wayar masu da kai game da kurkukun ƙaddara, Saida takaiga idan Chief yaje da shi headquarter din su jami'ansu ji suke da shi suna masa biyayya kamar dai chief din, wani irin farin jini gare shi, abunda yafi burge su da shi karfin da Allah yayi mashi, ga kaifin basira da Allah ya bashi, har jaraba shi sukayi ta hanyar haɗa shi da ƙarfafan Isod soldiers don suyi wrestling da shi, saboda su tabbatar idan giant basa jin bugu aikuwa sun sha ruwan mamaki, Isod Soldiers din da suka hada shi da su gurin damben su kusan hamsin saida Ya sumar da su, a hakan ma baiyi masu bugun da zasu raunata ba saboda baison yai masu illa shiko ko kwarzane ba su yi ma shi.
Idan suka tafi Basu tashi dawowo gida, sai marece idan ya dawo agajiye daya samu yayi wanka ko abinci bai nema bacci yake yin awon gaba da shi, baya tashi farkawa sai lokacin da dare ya tsala kowa yayi bacci tukunna ya ke tashi yaci Dinner din shi.
dauriya kawai yakeyi amma kewarta na neman tayi mashi illa, haka itama ko abincin kirki bata ci, ta rame tayi haske sosai kamar babu jini a jikinta, kullum a bedroom ɗinsu take killace kanta bata son kowa ya ra6e ta, tafi son kadaici duk da ba karamin azabtuwa takeyi ba na rashin ganin shi, tun tana 6oye abun da ke damunta idan yan uwansu suka matsa mata musamman auntyn umminsu har takaiga sun gano da kansu saboda kauracewa junan da sukayi ita da Danish, nema take ta zauce kullum ciwo ba koshin lafiya, abinci sai aunty ummi tayi mata dole take cin shi akarshe ma ta amayar da shi a toilet ba tare da sanin su ba, bacci Ya kaurace ma idanunta idan dare yayi haka zatay ta juyi kan gado rungume da pillow a kirjinta, idan abun ya isheta nafilfili take tashi tayi kuma duk akansu takeyin sallar, wani lokacin akan prayer mat baccin ya ke yin Awon gaba da ita. wannan wani irin Azababben So ne❓
Gaba daya abunda ke faruwa Taj baisani ba, saboda shima ba zaune ya ke ba, ummi har yunkurin kiranshi tayi don ta fada mashi halin da Unaisah take a ciki na rashin Lafiya amma Unaisah ta dinga rokonta akan kada ta sanar da shi saboda gudun faɗan da zaiyi mata, dakyar ta samu Ummi ta fasa kiranshi bayan ta gindaya mata sharadi akan bazata ƙara fashin cin abinci ba, tace mata eh ta amince ahaka ummi ta samu ta ɗan shawo kanta.
Kamar yadda boyayyan mutumin nan Ya ba Chief shawarar su sanya manyan Malaman addini suyi masu addu'a, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tuntu6i shiekh Imam malik awaya, Ya nemi alfarmar yana son su haɗu anan gidan shi.
Shiekh imam yace mashi in sha Allah zai shigo gidan.
After Magbrib Bayan sun kammala yin dinner din su, ba suje sun kwanta ba, gaba ɗayan su suna zaune a falo, sunyi shiru babu mai magana acikinsu, kwata kwata babu annuri akan fuskokin su, gashi dai sun sanya kayan baccin sai dai baccin Ya kauracewa idanunsu saboda damuwar da zuciyoyin su suka shiga, babban tashin hankalinsu jin za'a tafi da Garkuwarsu, babu irin magiyar da basuyi ba akan suma atafi da su amma Salsabeel yace bazai yiwu ba, suyi hakuri su biyu sun isa suyi ma Sojojin jagora.
Unaisah ta ƙwallafa rai akan son aje da ita kuma har yanzu tana akan bakanta don bazata bari su tafi da Danish batare da ita ba, abun daya daure masu kai har yau babu wanda ya faɗa masu date din da zasu je kai farmakin, duk in suka tambayi Taj ko big guy sai suce masu basu fidda lokaci ba, haka shima Danish yake fada masu, gaba daya sun yarda da maganarsu, Unaisah ce kadai hankalinta bai kwanta da zancen ƙin bayyana masu kwanan watan ba, ta fahimci sun haɗa baki ne, ranta yana bata tafiyar bazata zasuyi batare da sanin su ba shiyasa suka shirya hakan, tun da ta fahimci hakan kusan kullum sai ta addabi daddynta da Salsabeel akan su faɗa mata date ɗin amma suka ƙiya, tayi magiyar tayi rigimar duk abanza, harta hakura tadaina tambayar su, ta dai zuba ma sarautar Allah ido.
Fitowa Ummi tayi daga Bedroom dinta, jikinta sanye da doguwar rigar bacci, ta zuba hannayenta cikin aljihun rigar,
Daga inda take ta hango su zazzaune kan sofas na falo, sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki.
Girgiza kai tayi tare da zaro waya daga aljihu ta kira Layin Boss.
Bayan yayi picking suka gaisa cikin girmamawa kafin tace"yalla6ai akwai matsala fa, Yaran nan sunƙi zuwa su kwanta ga su can zaune falo sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, Ni nasan bai wuci zancen tafiyarku bane Ya ɗaga hankalin su..." ta fada fuskarta ayamutse.
Muryarshi da damuwa ya furta"Ya sallam, Ummi pls ki yi koƙarin kwantar masu da hankalin su"
"Wallahi ba irin lallashin da banyi masu ba, amma duk abanza"
"Ummi, ki zauna dasu, yanzu zamu shigo gidan In sha Allah"
"Okay, Allah ya dawo daku lafiya"
"Ameen" da ga haka Su ka yi sallama.
Saukowa down tayi, har ta shigo falon ba su ankara ba.
Sau uku tanayi masu sallama babu wanda Ya amsa mata saboda Hankalinsu baya atare da su.
Binsu da kallo ta yi, daga wanda ya ɗage kai sama, Sai wanda Ya langwa6ar da kan shi jikin Sofa, kowa dai da alkibilarsa da ya kalla
Bakowane Yafi bata tausayi ba, face Unaisah, baiwar Allah ita kadai ce kwance Kan rug, yadda kasan tsumma, ta nannaɗe guri guda kamar kifin gwangwani ko motsi batasan yi.
Kware murya tayi da karfi ta furta"wai bakwa ji nane"? A firgice suka zabura kowannan su Ya gyara zaman shi, kusan atare suka dube ta, In ka cire Unaisah wanda ko gizau batay ba, tana nan yadda take a kwance..
"Aunty ummi har kin bamu tsoro," hanna ce tay maganar.
Haris Yace"wai har yanzu basu dawo ba"?
"Aunty ummi, ko zaki kira mana su? Mun yi ma Unaisah magana tace wai batasan inda ta jefa wayar ta ba, kuma mun duba bamu ganta ba" acewar Batool..
Naufal yace"pls Aunty Ummi, nasan ba zaki rasa sanin ranar da zasu tafi ba, dan Allah ki faɗa mana wlh munyi maki alkawarin ba zamu faɗa masu mun sani ba"
Bata tanka masu ba, wuri ta samu kan Sofa ta zauna, batare data kauda ido daga kallon su ba.
Calmly tace"yanzu nayi waya da boss, Yace min suna akan hanyar su ta dawowa gida.."
"Aunty ummi duk ba wannan ba, kawai ki fada mana ranar da zasu tafi, in ba haka ba hankalin mu bazai kwanta ba" acewar Naufal.
"ku yarda dani, wlh nima bansan date din da zasu tafi ba, har tambayar boss nayi yace min basu fidda rana ba, kunsan yanayin aikinsu na jami'in sirri, kuskure kadai zai iya lalalata shirin su, yakamata mu fahimce su ko"
ta fada cikin kulawa tana kallon su.
Sarah tace"amma ay ba laifi bane in mun sani, zamu tayasu da addu'a ne kawai,"
Murmushi ummi ta ɗanyi"in zaku tayasu da addu'a ay ba dole sai kun san ranar da zasu tafi ba, wannan baya daga cikin sharuddan yin addu'a"
"Look aunty ummi, kin san komai, kawai kina boye mana ne" fuska a daure Sajeed Ya faɗa.
Yar dariya tayi"dama nasan zaiyi wuya ku yarda dani, in ma baku yarda ba toh kada Allah yasa ku yarda" ta fada tare da yi masu dakuwa da hannunta, tuntsirewa su Ka yi da dariya itama dariyar tayi
"Kun fiye taurin kai Allah, haba mana, kusan karfe tara, Yakamata kuje ku kwanta, ga little sisters dinku nan sai gyangyadin bacci sukeyi nasan saboda ku yasa suka ki zuwa su kwanta bacci" ta fada tana nuna Azeeza da jemimah da hannunta sun manne ma juna sai gyangyadi su ke yi..
"Hmm aunty ummi kenan, Salon muje mu kwanta bacci, lokacin da zamu farka ace mana sun tafi ko? Da fa wayon mu" dariya tayi sosai maganar javed ta sanyata nishadi.
Mikewa tayi ta nufi sofa din da su jemimah suke a zaune, ta dauki jemimah ta goya abayanta, kafin ta tada Azeeza tana layi ta mike kamar wadda tasha kwaya..
Ruko hannunta tayi, ta nufo bedroom dinsu dasu, sai da ta tabbatar sun kwanta bacci ta kashe masu switch din dakin tana kokarin fitowa unexpectedly Jiniyar motocin dake shigowa gidan ta karaɗe kunnuwan su.
Kusan atare suka mimmiƙe tsaye suna jiran shugowar su, Unaisah ce kaɗai bata motsa ba tana nan inda take akwance..
Cikin takun sauri suka fara shigowa falon, Chief ne agaba hannun shi ruƙe dana Danish daga bayan su Shiekah Imam Malik ne, Yayin da Boss da big guy hada ma Salsabeel su ke abiye dasu, mutun biyune babu kaki a jikin su, Danish da Salsabeel, black jean da white shirts ne a jikin su kala ɗaya.
Tun da Ummi taji Sallamar shiekh Imam malik, ta kasa fitowa daga dakin su Jemimah..
Kusan atare suka ci burki suna kallon su, sun yi mamakin ganin su a tsaitsaye curko curko suna ganin Danish jikinsu har 6ari yake garin saurin su karasa gare shi, daya bayan daya saida yayi huggin din su duk da agajiye yake har wani jiri jiri yake gani acikin idanun shi..
Atare suka hada baki gurin yi masu sannu da dawowa, kafin suka gaishe da shikeh imam malik cikin girmamawa..
"Sheikh, mun jima bamu ganka ba, kamanta damu" sajeed ne yai magana
Tattausan murmushi shiekh imam Ya sakar masu"masha Allah na ji dadin ganinku cikin koshin lafiya, Yan jikokina, ban manta daku ba, kuna araina, duk in zanyi addu'a saina sanyaku a ciki" murmushin farin ciki suka saki..
Gaba daya hankalin Taj baya akansu, Yar shi Yake nema Yaga babu ita a cikin su, baisan awani hali take ciki ba, ya yi kewarta ba kadan ba..
"Bismillah, mu shiga ciki" big guy ne ya fada tare da nuna masu hanya
Kafin su karaso, da sauri Unaisah ta mike cike da rashin kwarin jiki ta zauna.
Bayan sun karaso cikin falon Prisoners gaba daya suka zauna kan rug, su Chief suka zauna kan sofas din.
Kwata kwata basu lura da ita ba, ganin daddynta ya miƙe yana kokarin nufar dakinsu yasa tay karfin halin furta"sannu ku da dawowa, ya gajiyar aiki" atare suka dago suna kallon ta, haduwar idanunsu Cikin na jina yasa Danish yin saurin kawar da fuskarshi gefe daya saboda kallonta da yakeyi ba karamin karya mashi zuciya yakeyi ba, hakan da yayi ya sanyata jin wani iri a azuciyarta, gani take kamar fushi yake da ita..
"Unaisah Lafiyarki kuwa? Meke damunki"? Taj ne ya tambaya yana kallon ta..
Murmushi ta kakaro kan fuskarta"bakomai daddy, idan ma akwai abinda ke damuna, bai wuci zullumi da fargaban tafiyar ku bane"
Jiki asanyaye Taj ya zauna gefenta, tare da ruko hannayenta acikin nashi.
Hankalin Chief gaba daya yana akansu, shi kanshi Ta bashi tausayi ya lura da ramawar da tayi.
"Pls ku bamu aron hankalin ku nan" big guy ne yai maganar, gaba daga suka dube shi, a lokacin Unaisah ta kwantar da kanta saman kafadar daddynta..
"Ina Auntyn naku take"?
"Taje ta kwantarsu da su jemimah dakin su, har yanzu bata fito ba"
"Okay, wani ya kira mana ita"
Har mubeen Ya miƙe zaije kiranta, sai gata ta fito komawa yai ya zauna..
Tana karasowa, cikin sanyin murya tayi masu bangajiyar aiki, kafin ta dubi sheikah Imam malik kallon juna sukayi ido cikin ido daga gani sunyi kewar ganin junansu
Muryarta na dan rawa ta furta"ina wuni sheikh ya fama da jama'a.." tamkar bazai amsa mata ba, ya furta Lafiya..daga haka Ya kau da idanun shi gefe ɗaya.
"Bismillah, Ki zauna" big guy ne ya fada tare da nuna mata sofa, bayan ta zauna falon yayi tsit baka jin motsin komai kamar mutuwa ta gifta.
Gyaran murya sheikh Imam Yayi tare da duban Chief yace"Owais, meke faru ne? naga kamar wani abu na damunku, daga ku har yaran babu mai walwala, ince dai ko lafiya"? Jinjina mashi kai chief yayi"kada ka damu, babu wani abu." ya fada tare da kallon Omar batare daya furta mashi komai ba, da ido ya fahimci me chief yake nu fi..
A tsanake ya fara labarta ma Sheikh Imam, dangane da shirye shiryen da suke yi nakai farmaki, sai dai ba komai ya faɗa masa ba, ya dai ce mashi miyagun yan'ta'addane kuma matsafa ne masu hadarin gaske zasu je kaima farmakin a kurmin daji..
Sheikh Imam Malik Ya jinjina lamarin, tun da big guy ya fara zayyana mashi, Yake ta dan jinjina kan shi alamar ya girgiza da jin zancen.
Chief Owais Ya daura da cewa"baba, alfarmar da muke nema agurinku, munaso ku haɗa kai da manyan malamanmu na addini don ku yi mana addu'o'i, sannan zamu bada abun sadaka abawa mabukata da marayu suma su taya mu da addu'a."
Numfasawa sheikh Imam yayi fuskar shi dauke da matsananciyar damuwa yace"Owais, Kunyi tunani mai kyau, tabbas tunkarar miyagun matsafa ba abune mai sauki ba, mutanene masu haɗarin gaske, amma ta inda kuka fi su ku kun dogarane ga Allah ne, kuma kun yi imanin shi ne zai baku nasara akan su..." ya fada yana ɗan jinjina kanshi
"In sha Allah Owais, tun da har kuka nemi mu taya ku da addu'a zamuyi aiki tukuru, bi'iznillahi ba zasu ta6a cin galaba akan ku ba, saboda kyakkyawar niyar da kuke da ita na ganin kun kawar da masu aikata fasadi adoron kasa.." gaba daya sunji dadin furucin sheikh Imam malik
"Zan iya sanin yaushe ne zakuyi tafiyar"? prisoners duk sun baza kunne suna jiran jin amsar da chief zai ba shi.
"bamu fidda rana ba, amma a kowani lokaci zamu iya tafiya"
"Okay, in sha Allah zuwa gobe da safe zan sanarwa yan uwana malamai yan team dinmu wadanda nayi imanin in har muka hada kai da su gurin yi maku addu'a babu wani mahalukin daya Isa Ya ci galaba akan ku, Sihirinsu bazai ta6a tasihiri a kanku ba, in ba wani iko na Allah ba....."
Gaba ɗaya sunji dadi maganar shiekh Malik,
"Amma, malam, Danish har yanzu bai musulunta ba" gaba daya suka maida hankali akanta, sunnar da kanta kasa tay, ganin irin kallon da daddynta yayi mata.
A hankali suka maida duban su ga Danish, wanda ya dafe goshinsa da tafin hannun shi
Salsabeel Yace"kamar kin shiga zuciyata Unaisah, wlh tun dazu nake ta zucci zuccin inyi mashi maganar shi, gaba daya mun damu da rashin addininsa"
Chief yace"nima abun na damuna, ataimaka mana sheikh, a karkato mana da hankalin shi Ya kar6i shahada, kafin lokacin da zamu tafi"
Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, babu wanda baiyi magana ba, akan damuwar su na rashin addinin Danish In ka cire Big guy ko kadan bai sanya baki a maganar ba.
"Danish, Har yanzu baka da ra'ayin kar6ar addinin musulunci"? Shiekh imam ne ya tambaya yana kallon shi..
Gaba daya sun kagara da su ji me zai ce
Sai da ya mula ya sha iska kafin ya firta"bani da ra'ayi,"
"Meyasa"? Shiru yayi bai tanka ma shi ba.
Hakan ba karamin karya zuciyoyin su yayi ba..
"Inason Yin magana dakai, a ɗakin ka" bai yi mashi musu ba, Ya mike sheikh Imam Yabi bayan shi suka nufi second floor har dakin danish bayan sun shiga Shiekh Imam Ya kulle Kofar.
Gaba daya sun kagara da su fito, fatan su Allah yasa Ya kar6i musulunci.
Kasa kasa da murya Taj yace ma Unaisah"kun ci abincin daren ku"?
"Eh daddy,"
"Pls ki daina sanya damuwa aranki, banason ganin ki a rame haka babu walwala, in har saboda tafiyar da zamuyi ne addu'arki muke bukata ba damuwarki ba.."
"Toh daddy, zan daina, amma pls ka fadamin date da zaku tafi na maka alkawarin bazan sanar da kowa ba"
Aranshi ya ayyana ay ko da zan fada ma kowa Unaisah bazan fada maki ba, ni nasan me zai biyo baya in kikaji, rigima zaki sa sai mun tafi da ke ..
"Daddy ka yi shiru"
"Unaisah, Chief Yana kallon mu, kuma shi Ya hana asanar da kowa, kuma mun yi mashi alƙawarin zamu ruke amana, kinga bai kamata in zama mutun na farko da zanci amanar shi ba, amma ki ƙara hakuri zan nemi izni daga gurin shi In har Ya amince zan sanar da ke"
yamutsa fuska tayi tamkar zata sanya kuka tace"ran nan ma haka ka ce min zaka yi mi shi magana akan in biku amma baka yi masa ba"
Shiru yayi bai tanka mata ba, ta fahimci wayou ya ke yi mata gashi takasa tunkarar Chief din da maganar wani irin nauyinsa ta ke ji.
Agogon Hannunsa ya duba karfe goma na dare, ɗagowa yayi tare da kallon Chief, Wanda Hankalinsa ke akan Phone dinsa da yake daddanawa..
Har saida suka fara gajiya da jiran sheikah Imam, A kalla sun shafe mintuna talatin Cuf, Wasu daga cikin Prisoners har sun fara bacci.
A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga sheikh Imam Ya fito daga dakin batare da Danish ba, tunkafin ya karaso su ka lura da yanayin damuwar dake akan fuskarshi, nan take suka fahimci ba ay nasara ba...
Har ya zauna ba su daina kallon shi ba, yayi shiru babu walwala akan fuskarsa
"Baba an dace kuwa"? Kallon chief yayi tare da girgiza mashi kai yace"ban ta6a yi ma wani ɗan adam da'awa irin wadda nayi mashi ba, kuma da wuya inyi har in gama mutun baiji imani ya shige shi koda bai musuluntan ba, amma banaso hakan Ya dame ku, kowa ni dan adam da irin tashi Jarabawar, wani har ya mutu baiyi imani da Allah ba, amma fa kada ku yanke kauna da shi, idan Allah yaso shi da rahama koda da numfashi na karshe ne in Allah ya nufa sai kuga ya furta kalmatusshahada..." bai ƙare maganar ba, Unaisah ta mike da gudu ta bar falon, gaba daya suka bita da kallo har ta 6ace ma ganin su.
Suma sauran yan uwan nata, kuka suka kamayi, shiekh imam ne yayi masu nasiha mai tsuma zuciya harya samu ya shawo kan su,
Kafin tafiyarshi, sai da Ya ƙarfafa masu Chief gwiwa, Ya jima agidan har wuraren karfe sha daya kafin yayi masu sallama ya tafi.
Bayan tafiyar shi, Taj Yace suje su kwanta, jikin kowan nan su asanyaye suka mike ko sallama ba su yi ma su ba, kowa ya nufi ɗakin shi Ummi ma ta yi ma su sallama ta nufi nata ɗakin.
(After two days da zuwan Sheikh imam, Bayan kwana biyu)
Yau tunda sanyin safiya, kiran Taj ya farkar da Ummi tana tsaka da yin baccin ta, bayan ta daga sun gaisa Yace Ta shirya su Unaisah, tare da ita kanta, yana son su kawo ziyara part dinsa gurin Danejo, Ummi taji dadi dama Ta gaji da zama guri daya tafi son tana ɗan yawata.
Batare da 6ata Lokaci ba, taje dakunansu ta tada su daga bacci ta isar masu da sakon Boss, duk da halin da damuwar da suke a ciki hakan bai hanasu jin dadin zasu je part din daddy taj ba, Unaisace kadai Hankalinta bai kwanta da zancen zuwansu part din daddynta, saboda ranta yana bata yau ne kwanan watan da zasu je kai farmaki, shiyasa akayi masu wayau don a kawar masu da tunanin su, aikuwa ko brush batayi ba, wankan ma ta kasa yi, A karkashin gado ta boye kanta duk don kada tabisu.
"Sister! sis! Where are You, Mun fa shirya, ke kadai muke jira" muryoyin su Batool tajiyo a cikin kunnanta, shiru tayi bata amsa masu ba.
Can tajiyo muryar Ummi tana fadin"Unaisah Ina kika shiga ne? Kun duba toilet ɗinta kuwa"? Ta fada tana kokarin tura kofar toilet dinta, koda Ummi ta buɗe kofar ta shiga ciki bata ga kowa ba, tayi mamakin ganin babu ita a ciki, rufe kofar tayi, tare da kallon su, sunyi tsaitsaye.
"Aunty ummi ki kira daddyn nata, Muji idan taje can ɗin" acewar Sajeed
Waya ta zaro daga Cikin Yar purse ɗinta, ta danna ma Taj kira almost 3 times tana kira baya shiga har ta gaji ta hakura da kiran nashi..
"Mu tafi, may be tana can din" fitowarsu keda wuya daga dakin sai ga big guy ya shigo part din su
Kaitsaye idanun shi suka sauka akan Ummi, from head to toe Yabi ta da kallo, fitted gown ce a jikinta ta material launin ash colour kamar ajikinta aka dinka kayan, ta kashe daurin dankwalinta sai ɗan gyalen data yarfa a kafadarta, ko makeup batayi ba amma tayi matukar jan hankalin shi.
Gaba daya sunyi mamakin kallon da big guy keyi ma Auntyn ummin nasu, ita sam bata lura ba da fara'a tace"Gm Sir, ya gajiyar aiki? dakyar ya haɗiye abunda ke ransa Yace"lafiyalou Ummi, Ina zuwa haka"? Ya tambaya kamar baisan da plan din su ba
"Zamuje kai ziyara a Part din Daddyn Unaisah" murmushin gefen fuska Ya sakar ta, kafin Ya dubi prisoners.
"Guys, Kunyi kyau, Muje na raka ku part din nasa" ya fada tare da nuna masu hanya, su ka yi gaba shi kuma Yajera da Ummi cikin nutsuwa suke yin tafiya.
"Kinyi mini kyau, badan Ina busy ba, da na daukeki mun fita yawan buɗe ido"
"Banyi zaton kana Kula mata ba.." ta fada tare da kallon shi..
Murmushin gefen fuska yayi"nima fa banajin magana, tubabbe ne, daga baya na shiryu silar Owais.."
"Allah sarki Chief, Mutumin kirki, har kasa na kara jin kaunar shi saboda shi din na dabanne samun irin shi da wahala" still fuskarshi da murmushi yace"That's why I'm proud of him..."
"Kasan wani abu"? Girgiza mata kai yai saikin faɗa
"najima ina yi maka kallon sani, hatta muryarka tayi min kama data wani mutumina Allah, kuma kun ɗanyi kama da shi"
"Zan iya sanin sunanshi"?
"A'a, bana faɗi, amma ka fadamin sunan Family dinka"
Yar dariya yayi yana binta da wani shu'umin kallo, kamshin turarenta duk ya kashe mashi kuzarin shi musamam Yadda qugunta ke gogar nashi ba karamin tsuma shi take ba..
"Wayau zaki min Ummi, Ke kin ki faɗamin sunan mutumin naki sai ni zan fada maki sunan family ina, bazai yiwuwa ba Allah"
Murmushi tayi"na yarda kowa ya ruke nashi, amma kai ba hausa bane zalla ko? Cos kayi kama da ruwa biyu" ɗaga mata gira yayi.
"Meye Full name ɗinka"?
har ya buɗe baki zaiyi magana Muryar Sarah Ta katse su"Aunty Ummi, ke muke jira fa" Gaba daya sun shagala sunata fira sam sun manta da su, har sun karasa bakin kofar part din...
Karasowa sukayi, big guy ya kwankwasa kofar, almost 3 times kafin suka ji motsin bude kofar ta ciki
Taj Ne Ya fito Jikin shi sanye da kakinsa Yana ganinsu ya saki fuskar shi da fara'a suka gaisa da juna cikin girmamawa.
"Bismillah Ku shiga, madam Tana a ciki tana jiran ku..." murmushi suka saki gaba dayan su, har sun fara shiga ciki Taj ya lura babu Angel acikin su..
Da sauri Yace"Ina ita Unaisah din"?
Ummi tace"wlh bamu ganta ba, mun duba ko'ina har cikin toilet dinsu, mun yi zaton ta riga mu karasowa ne"
Big guy yace"ni banma lura babu ita a cikin su ba, sai yanzu da kayi maganar nan.." fuskar Taj A yamutse Yace"ku shiga daga ciki, Bari naje na dubota" ya fada tare da kallon Big guy"muje" sai da ya fara kallon ummi Yai mata waving kafin Yabi bayan Taj, suna fitowa daga falon,yayi locking door din dama da biyu suka turo su nan.
Bin falon su ka yi da kallo, jin shiru matar gidan bata fito ba, ummi tace mu zauna mu jira ta.."
da sauri kowannansu ya samu guri kan Sofas suka zauna.
Badajimawa ba, sautin takalamanta Ya karade kunnuwansu, kusan atare suka kalleta yayin da take saukowa down, ta dauki wankan abaya baƙa, tayi rolling akanta.
jinjina kai ummi tayi aranta ta furta masha Allah.
Sallama tayi masu, kamar tana jin shakkarsu, har yanzu bata saba da mutane ba..
A wayance Ummi ta mike tare da ruko hannayen Danejo Acikin nata, ta sakar mata murmushi"sannu madam, fatan mun same ku lafiya.." sai faman rarraba idanu takeyi akansu Rubina
Dakyar ta firta"lafiyalou"
Ummi tace"kamar baki gane su wanene ba, Ko dai Mijin naki bai fada maki zuwan mu bane" sai lokaci tayi murmushi"wlh ya fadamin, na shafa'a ne, da yake banganku tare da ƴartawa ba shiyasa na ɗan ruɗe amma yanzu nagane ku" Hugging ɗinta Ummi tayi, Kafin suka zauna kusa da juna.
Da sauri Prisoners suka gaishe da ita.
Da fara'a tace"tabarakallahu ahsanul khalikin, Kune Yan uwan Angel ɗin? Atare suka amsa mata da eh
"Masha Allah Jinsin kyawawa Naji dadin haɗuwa daku, amma Ina Unaisah ɗin take"?
Ummi tace"bata karasa shiryawa bane, shiyasa muka tafo, amma dadynta Yaje ya taho da ita"
"Ke ce mommynsu ne"? Yar dariya ummi tayi"kina nufin wadda ta haife su? Daga mata kai tay, dariya ta kumayi kafin tace"kin iya zolaya, ni ina zan iya haifan wadannan har su goma sha, ko nayi maki kama da matar aure ne"?
Ta tambaya tana kallonta, murmushi Danejo tayi"A'a amma dagaske baki ta6a yin aure ba"?
ɗaga mata gira ummi tay, waro idanu waje Danejo tayi da mamaki tace"tab lallai, aradun Allah da a rigarmu kike da tuni Kin aje tatta6a kunne, Ko kina so ko bakisho dole ay maki aure" tuntsirewa sukayi da dariya gaba dayansu, hausarta ba karamin nishadi ta basu ba, kana jin maganarta zaka gane bafullatanar daji ce.
Sai dadi takeji ganin yadda ta sanya su nishadi
Maimakon ta dauko masu abunsha, sai ta kama basu labarin haɗuwar ta da Taj, har zuwanta birni da irin wautar da tadinga yi mashi, sunci dariya kamar zasuyi kuka.
Ta zaƙe sai zuba takeyi masu kamar aku, Har saida Parveen ta gaji da zuba na mazurai taji shiru bata kawo masu abinci ba, gashi ko breakfast basuyi ba suka taho
Hannunta dafe da cikinta tace"Aunty Danejo, mufa Yunwa muke ji, bamu ci komai ba muka taho" dan zaro ido ummi tayi tana kallonta, sarai parveen taga kallon da ummi tayi mata amma saita kawar da idonta gefe.
Mikewa Danejo tayi"i'm really sorry, na cika ku da surutu, kunsan mutumin dake zama cikin kadaici in ya samu abokin fira komai ma mantawa yakeyi, kuma fa tun dazu Nayi maku girki tunda daddyn angel ya sanar dani zuwanku..."
har ta fara tafiya ta juyo tare da kallon su"wa zai bini kitchen din mu dauko kayan abincin"? Da sauri Parveen da Yasmeen suka mike atare suka nufi kitchen.
Ajiyar zuciya sajeed Ya sauke tare da kallon aunty umminsu yace"da farko dana ganta kyakkyawa nayi zaton miskila ce ashe ta iya dan banzan surutu" dariya ummi tayi tana fadin"Pls kadaina maganar nan kada taji ka, amma fa kamar ka shiga zuciyata, Nima nayi zaton hakan"
Jemimah tace"gulma haramun, Allah In tadawo saina fada mata abunda kuka ce" Harara sajeed Ya galla mata"dako Kin ci na jaki Allah, Yar sa ido kawai" gatsina mashi hanci tayi tare da hararar shi, Ya janyo throw pillow Ya ɗan buga mata akanta.
Azeeza tace"Aunty Ummi, wai itace maman angel ne? Wadda Ta gudu tabarta acikin kwamin wanka" waro idanu waje sukayi
Batool tace"ke fa baki gane komai, Kin manta bafullatar dajin da Angel ta bamu labarinta? Wadda ta tsinceta acikin ruwa.." ta faɗa tana kokarin fahimtar da ita can tace"Yanzu na gane ta" ummi dake kallonsu a hankali ta sauke idanunta kan Deeja, data daura kanta saman kafadar Haris, hannunsu ruke cikin na juna tun zuwansu basuyi magana ba, aranta ta ayyana"Mun baro romeo da juliet agida, ga kuma layla da majnoon"
Fitowar su Danejo daga kitchen ne Ya katse firarsu, kowan nan su ruke da farantai shake da kayan abinci , akan rug suka ajiyesu,
kowannansu ya sauko kan rug din suka kewaye farantan,tun da kamshin abincin ya daki hancinsu suka fara hadiyar yawu
Har sun fara Cin abincin, Batool tace"ba zamu jira Unaisah ba"? Ummi tace"nima dai naji shiru bata karaso ba"danejo tace"kada ku damu, itama na ajiye mata abincin ta, duk lokacin data karaso sai taci"
daga haka ba su kara magana ba, Kowa ya maida hankali kan abincin da yake ci da alama yayi masu dadi, su parveen ba baka sai kunne, Hannu baka hannu kurya, kwata kwata bata Iya bakunta ba. Ummi har alama tayi mata da ido donta daina loma amma ta wani basar kamar bata ganta ba
Danejo ko sai fadi take kuci ku koshi in ma bai isheku ba, akwai saura abincin dana aje mana..
_________________________________💔
Around ƙarfe 2 na rana da matsakaicin gudu motocin su suka kunno kai Cikin Villa din..
Su biyune zaune a back seat din Motar Chief, babu mai magana a cikin su, sunyi shiru daga gani ba karamar gajiya suka kwaso ba ..
Gently yake daddana wayar hannun sa, yana kokarin kiran daddy dinsa sai ga kiran shi ya shigo, yayi mamaki kamar yasan shi yake shirin kira..
Picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnansa yana niyar yi mashi sallama miryar Mai girma sharafudden Ta katse masa hanzarinsa"Owais Inason ganinka Yanzun nan..." har saida gabansa yadan fadi da jin yanayin muryar daddyn nasa.
"Am...daddy, Ina fata lafiya" bai kare maganar ba Yace"idan kazo zaka ji koma menene" daga haka Ya katse Kiran
Lamarin Ya daure mashi kai! Bai ta6a jin muryar daddynsa cikin fushi irin Na yau ba, fatan shi Allah Yasa ba wani abun bane ya taso.
A hankali Ya dubi Danish dake a hakimce kan seat, Ya langwa6e kan shi, Idanun shi suna a lumshe kamar ma bacci ne yayi awon gaba da shi.
"My Boy, Bacci kake Yi"? Cikin kunnanshi ya tsinkayi muryar chief a wahalce ya buɗe rinannun idanun shi batare daya iya furta kalma ba.
Adaidai Lokacin Motocin suka yi parking, agent Ya buɗe masu cardoors ɗin. .
Atare suka fito, adai dai lokacin Taj da big guy sun fito daga motarsu..
Gaba daya suka maida Hankali akan Chief da Danish..
"Daddy Ya kira ni yanzu a mota, Yace Yana son gani na, zan tafi.." ya fada yana kallon su
"Pls take care of my baby boy, he's very tired and needs your care. Ensure he bathes, eats, and then goes to bed and rests before the time is full..."
yamutsa fuska Omar yayi kasa kasa da murya ya furta"sai kace wani jinjiri, kowa ma agajiye yake ay"
"Magana kake yi ne"? Chief ne ya fada yana kallon shi, Girgiza kai yayi"a'a," ya fada tare da kallon Danish baima san yanayi ba, hankalin shi baya atare da su..
"Sir, Allah ya dawo mana dakai lafiya, agaishe mana da mutanan gidan" amsa masu yai da ameen Kafin Ya koma cikin motar, basu bar gurinba, har saida motar chief ta 6ace na ganin su.
"Guy ina zuwa, Ka manta amanar da Chief Ya bamu"? Da zolaya ya fada yana kallon shi, a lokacin Danish Har yayi gaba abun shi..
Harara Ya galla mashi"Ya 6ata min rai, tarairayar da yakeyi masa tayi yawa sai kace wani jinjiri? Bai da magana sai ta Danish..." Yar dariya Taj yayi"wlh Omar Ka fara bani tsoro! Bana tunanin ko matar da zaka aura zaka yi kishinta makamancin wanda kakeyi ma Chief, kai dai bakaso kowa ya ra6e shi, bazan manta farkon zamana agidan nan ba, kiri kiri Ka fara jin haushina saboda kyautatamin da chief Yakeyi, naci wuyarka kafin muka saba da juna.."
kayataccen murmushi Big guy yayi"ba zaka gane ba Taj, duk yadda zanyi maka bayani ba lallai ka fahimce ni ba, wlh ina tsananin kaunar chief son shi nake, fiye da yadda nakeson kowa nawa, nifa ji nake dama mu Twins ne ni da shi..."
ɗan zaro idanun yayi maganar Omar ta bashi mamaki"nifa wlh ban ta6a zaton kai mataimakinsa bane saida na fara kar6ar training na isod, nayi mamki cos kamar ɗan aikinsa baka gajiya dayi masa hidima" yar dariya Big guy yai"kauna ce kawai, shima yayi fama dani akan indaina amma nakiya sbd banaso wani ya samu kusanci da shi."
Murmushi Taj yayi" Allah yabar kauna tsakaninka Da Chief, Allah yasa mutuwace kadai zata rabaku"
ya kar6e da cewa"ita ma mutuwar bana fata ta rabamu, nafison ta dauke mu atare ni da shi"
murmushi Taj yayi bakomai ya fado mashi arai ba face ɗan uwansa kuma amininsa Ozair, har abada bazai samu abokin da zai maye masa gurbinsa ba.
tuni Yaji Kwalla ta cike idanunsa a fakaice Ya share Hawayen don kada Omar Ya gani raba hanya su ka yi da Omar, Ya nufi part din chief don Ya cika Umarnin sa na ba Danish Kulawa.
A lokacin Danish Har Ya shiga bathroom, Koda ya shigo bedroom dinsa bai iske shi ba, landline din kitchen ya kira ya isar da sakon su kawo ma Danish lunch dinsa.
Yana katse kiran saiga kiran Ummi Ya shigo Layinsa, Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnansa.
"Boss, Har yanzu Unaisah batazo ba, har jaraba kiran layinta nayi amma akashe, kuma naga kofar falon anyi locking ɗinta already.."
dafe kai yayi da hannu ɗaya sam Ya sha'fa'a da batun Unaisah..
"Ummi, i'm really sorry, dazu mantawa nayi wlh, amma yanzu zan dubota"
"Okay, sai naji daga gare ka"
Rejecting call din yayi, Cikin sauri ya fito daga dakin Danish, Ya nufi Bedroom dinsu shigarshi Keda wuya adai dai lokacin Tana kokarin fitowa daga karkashin gado ashe tun bata fito ba, anan bacci yayi awon gaba da ita sai yanzu ta farka.
Wani irin burki Yaci Yana kallonta cike da mamaki, Yarinya ta zama kamar aljana, kwata kwata bata lura da shi ba, dakyar take jan numfashi saboda zazza6in dake nema yafi karfin ta, ga wata matsiyaciyar Yunwa da take ji, Sleeping Gown ɗin jikinta tayi squeezing, Kamar yadda sumar kanta ta yamutse.
Gyaran Muryar da yayi mata ne, Yasa tay firgigit Ta juyo ta fuskance shi da idanunta wadanda suka ƙankance...
Wani irin faduwar gaba taji, girgiza kai taj yayi"Unaisah, Irin Rayuwar da kika zaba ma kanki kenan? Bakya jin maganata Unaisah, soyayya ta rufe maki Ido kinbi duk kin hana kanki kwnaciyar hankali" jikinta na kerma ta girgiza mashi kai batare data Iya furta kalma ba
A faɗace Yace"Zoki wuce Kibi Yan uwanki, tun safe suke ta jiranki"
Make mashi kafaɗa tayi cikin disasshiyar murya ta furta"daddy, ni bazan bi su ba, anan zan zauna, kuma ko wanka ma banyi ba"
Ɗaure mata fuska yayi"Uban me Ya hana Kiyi wankan tun dazu? Ai kina sane kika boye karkashin gado, kega mai wayau ko"? Marairaice mashi fuska tayi"Dan Allah daddy, Ka ƙyaleni bana son zuwa, nafison na zauna nan, Ni bazan bi su ba..."
Ganin Yana tunkarota gadan gadan Yasa Ta fara kokarin gudu, yana kokarin Cafkota, ta kufce mashi ta watsa da gudu Ta fuce daga dakin, Aguje yabi bayanta sai dai koda ya fito baiga gifcin ta ba, kamar walkiya ta 6ace ma ganinsa, Ranshi Ya 6aci ba kaɗan ba.
________________________________✍️💔
Fitowa yayi daga Cikin toilet, waist ɗinsa ɗaure da white towel, motsin mutun yadinga ji acikin kunnanshi, hakan yasa shi dakatawa da tafiya, slowly yake bin bedroom ɗin nasa da kallo Unexpectedly eye balls dinsa suka sauka akan Curtain dakin dake motsi, alamar akwai mutun a ciki..
Yatsun kafafunta Ya hango ta ƙasan labulen daya ɗage sai kerma suke ...farat ɗaya Ya gane itace..yayi mamakin ganinta adakinsa bayan kwanakin da suka shafe batare da sun nemi junan su ba, kome ya kawota bedroom dinsa? Aransa ya ayyana hakan.
Yi yayi tamkar baisan da zamanta adakin ba, shaf shaf Ya shirya kan shi, Cikin Singlet fara da short.. kafin Ya koma gefen gadonsa Ya zauna tare da maida hankalinsa kan breakfast din da Taj yasa aka kawo mashi..
A tsanake Yake Cin abincin ta wutsiyar idanunshi Yake satar kallonta yayin da take buɗe labulen Tana leƙensa ji take kamar taje garesa tayi hugging dinsa sai dai ina wani irin shakkar tunkararshi takeji, saboda maganganun data gaggaya masa marasa dadi ita kanta bata tsammaci zai dyauki tsawon kwanaki bai kula ta ba ko kiranta awaya bayayi..
Gajiya tayi da tsayuwar, ta fito daga bayan curtain din tayi tsaye tana kallon shi.
Tayi zaton baiganta ba, cikin sanyin murya tace"My man, fushi kake dani?
Banza yayi da ita hakan ba karamin karya mata zuciya yayi ba.
"Baka ga halin damuwar dana shigaba, saboda kai ko bacci bana iyayi,nasan komai ya faru laifina ne, nina ja ma kaina amma ka yi hakuri ka yafe mim, I don't know if we'll meet again, maybe this will be our last meet, duk da bansan date da zaku tafi ba, amma inaji araina yau ne, shiyasa daddyna yace mu tafi part dinsa mu zauna, ni kuma na boye saboda inason muyi bankwana kafin mu rabu..."
ta faɗa idanunta cike tab da kwalla, So hana ganin laifi, duk yadda yaso Yaki jin tausayinta hakan ya gagare shi, kalamanta sun ta6a zuciyar shi.
slowly ya dubeta daga kasa Ya fara kallonta, Hankalinshi ya tashi da ganin irin ramar da tayi, daga gani bata samun isasshen bacci ko bata cin abinci yadda ya kamata ga shi babu gyara a jikinta, kamar zai zubda mata kwalla saboda matsanancin tausayinta dayaji yasan duk akan shine ta shiga halin Damuwa...
Da spoon din hannun shi ya nuna mata gefen shi, cike da rashin kwarin jiki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya batare da ta kauda ido daga kallon shi ba..
Cup din tea Ya dauko Ya kanga mata abakinta, ganin taki buɗe baki yasa shi furta"kisha" la66anta har kerma suke da sauri take kur6ar shi, nutsuwa yayi yana kallon throat dinta dake moving slowly.
sai da ta shanye shi kaf kafin ya dauki fork duk tana kallon shi Ya nannaɗo noodles ya tura mata abaki, kamar yasan yunwa take ji, sakin jiki tayi ya dinga bata tana ci saida ya tabbatar taci ta koshi kafin ya aje spoon ɗin.
Ya ruko yatsun hannayenta a cikin nashi, bata ta6a jin kunyar hada ido da shi irin na yau ba, saboda rashin mutuncin data zazzaga mashi, sunnar da kanta kasa tayi
Cikin nutsastsiyar muryarsa ya ce"Ni ban ruƙe ki a zuciyata ba, baki min komai ba, amma yanzu kin min abunda banji dadin shi ba..." a rude ta kalle shi
"Meyasa zaki takura kanki akaina"?
Cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, nasan nina tursasa maka akan kaje aman wallahi ni kadai nasan radadin da zuciyata keyi min saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya idan ka tafi, wallahi bana so na rasaka, kuma wallahi bada son raina na gaggaya maka magana ba, nayi ne kawai don in fahimtar dakai amma kaima kasan irin son da nake maka zan iya rayu wa dakai ahaka yadda kake, koda kuwa zaka makance ne ka kuturce, ka gurguce wlh zan rayu dakai bazan ta6a canza maka ba"
bata kare maganarba, ya rufe la66anta da yatsan shi, hakan yasa ta haɗiye sauran maganar da bata amayar ba..
Nutsuwa yayi yana kallon siraran hawayen dake sintiri kan kuncin ta..
"Basai kin yi min bayani ba, na fahimce ki, ina jin abun da kike ji..." lumshe idanunta tayi tana jin wani iri aranta...
"Listen to me carefully, now I need your peace of mind because that way, I'll have the confidence to do everything, maganganun da kika gaya min tabbas banji dadinsu ba, amma ta wani bangaren sun taimakamin gurin Farfado da tunanina..." Ya ɗan dakata Yana duban fuskarta, sill bata bude idanunta ba.
"Abu ɗaya da nakeso Kiyi min alƙawari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, and even if I don't come back, be patient, Endure a life without me"
(sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba)
bai ƙare maganar ba, ta katse shi cikin shesshekar kuka tace"Bazan iya daukar maka alkawarin nan ba, saboda bazan iya jurewa ba, bazan ma iya rayuwa batare dakai ba.."
fuskarta ya tallabo da tafukan hannayensa"meyasa zaki karaya Unaisah? Kin manta abunda kike ce? ...girgiza kai tayi"ka manta da abunda ya wuce, ba acikin hayyacina na fada ba.." murmushi takaici yayi
"Ki sama ranki zan dawo da raina da kuma Lafiya na, Nayi maki alkawarin hakan, zan kare kaina bazan bari na mutu ba.." bai kare maganarba tay saurin furta"baka ce In sha Allah ba"? Shiru yayi bai amsa mata ba.
Gyada kai tayi"tunda ba zakace ba, ni zanyi maka addu'a, Allah ya kare mun kai, Allah ya dawomin dakai da ranka da lafiyarka, in sha Allah, ko bayan kun tafi zan raba dare na biyu, rabi inyi baccin awanni kadan rabin In tashi tsakar dare inyi maku addu'a...." har cikin ranshi yaji dadin maganarta, kuma, Har time din bata buɗe idanunta ba.
Batai aune ba, Taji safkar Yatsunsa agaban rigarta, a firgice ta bude idanunta, wata irin kunyace ta kamata ganin Yana maida mata front buttons ɗin rigarta, sakamakon gudun da tayi ɗazu gaban rigar ya buɗe batare da ta ankara ba, tun da yafara bata abinci yake ta kokarin gyara mata rigar saidai ya kasa saboda gudun masifarta.
Sunkunyar da kanta kasa tay, tasan yaga abun da take 6oye masa..
"Ranar dana dawo, what will you do when you see me?"
Ya fada tare da zame yatsunsa daga gaban rigarta ya maida tafukansa kan shoulders din ta kamar kanwarsa.
"I can't imagine how happy I'll be, I'll cry for joy and hug you tightly"
ha6arta Ya ɗago da hannun shi"shi kadaine abunda zaki min"? Jinjina mashi kai tay,
"That won't be enough for me.."
"Faɗa min me kake so"?
Kunnanta ya ruko tare da yi mata raɗa bai ƙare maganar ba, tay sauri toshe bakin shi da tafin hannunta, kamar wadda taji wani mugun abu, jikinta har rawa yake, His shyness enveloped her, and his sexy words made her burn with desire he also set his soul on fire, lumshe idanun shi yayi tare da ware su cikin nata, harara ta ɗan watsa mashi tare da murguɗa mashi small lips din ta.., kashe mata ido ɗaya yai tare da ɗage mata gira batasan sa'adda ta saki murmushin gefen fuska ba, wato son da takema Danish irin unconditional love ne, idan tana tare da shi takan manta da komai, kamar dai yanzu da suke atare ta manta ma da hudubar da daddyn ta yayi mata kan hada jiki da sukeyi indai tana tare dashi mantawa take da komai shi kadai take gani kuma takeso ta kasance dashi.
Yana kokarin janye hannunta daga bakinshi, ba zato ba tsammani suka ji anyi knocking ɗin kofar, kallon juna sukayi wani irin faduwar gaba taji, sam ta sha'fa'a ta manta da daddynta da ke neman ta.
Muryarta nawa tace"nasan baiwuci daddyna bane, ni bana so naje part dinsa nafiso Inga tafiyarku tukunna, pls kada ka fada masa ina aciki, Ni zan boye..." wani irin kallo yake binta da shi, jikinta na kerma ta mike da sauri ta boye bayan curtain
Daga waje sukajiyo muryar Taj Yana fadin"Danish, Ka bude min ƙofa" mikewa yayi yaje gaban room door din Ya bude mashi.
shigowa yayi fuskarshi babu walwala Yace"Unaisah tazo nan"? Danish dabai Iya karya ba, Ya nuna mashi Curtain din da hannun shi"tana ciki" cike da takaici Taj Ya nufi labulen Ya ɗage shi, wata irin gigitacciyar ƙara ta fasa kamar zata zauce, ta dinga ihu tana fadin daddy bazanje ba, Ka kyale ni, kabarni inga tafiyar ku"!
ga tausayinta yanaji amma ji yake kamar ya rufeta da bugu.
bai bata lokaci ba, Ya sungumeta kan kafadar shi, Ya juya ya nufi kofar dakin kuka ta dinga Yi tana mika ma Danish Hannu don Ya kawo mata dauki bawan Allah Yana ji Yana gani Taj Ya fuce da ita, baisan ko wannan zai kasance rabuwarsu Ta karshe ba, yana jiyo sautin muryarta daga waje cikin shesshekar take sambatu
_"I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_
Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor.....
Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin jikinta duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa..
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: _______________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️❓😈👹💞💘
Zubewa yayi kan gwiwowinshi a karshe Ya yada kafadunsa kan floor.....
Yadda take a haukace, Ahaka Taj Ya nufi part dinsa da ita, sautin koke koken da takeyi ne yaja hankulan jami'an dake kai komo A compund din gidan zuwa ga kallon ta, gaba daya hankalinsu ya dawo kan su, Kamar mazurai haka suka zuba ido suna kallon Unaisah dake ta kokarin kwace kanta daga jikin daddynta, sun kwadaitu da ganin santala santalan cinyoyin ta, Yar rigar baccin duk ta nannade dama bata wuci gwiwarta ba...Bacin rai Ya hana Taj Ya lura da abunda ke faruwa..
Agaban kofar shiga falon part dinsa, Ya danna Password din ƙofar, ta bude kafin Ya shiga da ita ciki, adai dai Lokacin Yan uwanta sun kabbara sallar La'asar da ake ta kira, anan falo Danejo ta shimfiɗa masu prayer mat sun daidaita sahun su.
Kwatsam su ka jiyo kukan Unaisah hakan Ya ɗaga hankulansu a rude suka katse sallar, gaba daya suka kai dubansu ga Taj, sun firgita da ganin yadda Ya daukota a saman kafadarshi, sai hauka ta ke yi mashi, har suna hada baki gurin tambayar Taj meya faru da Unaisah.
bai bi takansu ba, Ya nufi bedroom dinshi da ita, adai dai lokacin Ummi da danejo sun sallame sallamarsu kusan atare suka mike tare da bin bayan shi.
Sai dai kafin su ƙaraso Taj ya datse ƙofar ɗakin.
A saman gadon shi Ya wurgar da ita gaba ɗaya ta kife kan mattress din gashin kanta ya tarwatse
Yana huci Yace"shashasha, wlh kin bani kunya, wlh badan kaunar da nakeyi maki ba da yau saikin yabawa aya Zakin ta, bugun tsiya zanyi maki, wawuya kawai, ban ta6a zaton za ki min haka ba, har yanzu kina nan da kafiyarki ta kuruciya, saboda soyayya bakya ganin kowa da gashi, shi kadai kike tsoron ki rasa, na fahimci ma kinfi damuwa dashi akaina, nima fa hadani za'aje kurkukun, amma kwata kwata bata ni kike ba..."!
Daƙyar ya ƙarasa maganar saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare makoshin sa.
A hankali Hawaye masu ɗumi suka wanke fuskarsa.
Dagowa tayi agalabaice tana kuka ta girgiza mashi kai muryarta ashake ta furta"daddy ba haka bane, ka fahimce ni, kaifa mahaifina ne, wallahi na damu dakai, har abada bazan ta6a samun madadinka ba..."
bata kare maganar ba, Ya juya zai bar dakin yana huci, durowa tayi daga kan gadon da gudu ta nufe shi harya ruke handle din ƙofar, tay saurin rungumeshi ta baya ta zagayo da hannayenta kan stomach dinsa, ta maƙyalƙyleshi cikin shesshekar kuka take lallashin shi tare da bashi hakuri..
su ummi sai bugun kofar sukeyi don ya bude masu.
Hakan da tayi masa ba karamin sanyaya zuciyar shi tayi ba, tuni ya sauko daga kan dokin zuciyar da ya hau, A hankali Ya ruko hannunta tare da janyo ta ya dawo da ita ta gaban shi, Yayi hugging dinta tightly, a hankali yake shafa sumar kanta, duk da halin damuwar da take a ciki sai da taji sauƙin radadin da take ji a cikin zuciyarta.
cikin sanyin murya yace"komai ya wuce Unaisah, na daina fushi dake, raina ne ya 6aci amma yanzu na fahimce ki, kiyi haƙuri dukkanmu addu'arki muke bukata, amma kukan nan da kike yi da sanya damu aranki bazai ta6a canza mana kaddararmu ba, saboda addu'a ce kadai take canza kaddarar bawa, Ki yi mana addu'a Unaisah In sha Allah, zamu dawo cikin koshin lafiya.."
cikin kwantar da murya yakeyi mata nasiha, su Ummi dake tsaye bakin kofar dakin sunyi shiru suna jiran ya bude masu ƙofa..
daga bisani ya ruƙo hannunta suka shiga toilet, Ya wanke mata fuskarta, suka fito daga toilet din still hannun shi ruke cikin nata suka zauna kan gadon shi..
"Daddy, bazan kara kuka ba, zanyi maku addu'a, Allah ya kare min ku ya dawo min daku lafiya" tsananin tausayinta ya kama shi damuwar shi a haka zai tafi yabarta gashi yaji alamun zazza6i a jikin ta.
"Yawwa my daughter, yanzu kin share min kokwantona akanki, ni dama nasani, ƴata mai biyayya ce, zatayi abunda daddyn ta yake so.."
ya faɗa tare da shafa gefen fuskarta data kumbura jawur, wlh shi kadai yasan irin yadda yakeji azuciyarshi duk in ya tuna inda zasuje da kuma yarsa tilo da yake da ita, bayason wani abu ya faru kawai dai yayi imanin komai zai faru da su mai kyau ko mara kyau mukaddari ne daga Allah, Bawa bai isa ya guje ma kaddararsa ba.
"Banaso sauran Yan uwanki, su gane wani abu, pls kija baki kiyi shiru, ko da sun tambayeki me yasa kike kuka, ki fada masu wani abun daban, nasan kina da wayau basai na maki bayani ba "
jinjina mashi kai tay,
Rungumota yayi akan kirjinshi, ya fara janta da fira Yana tariyo mata kuruciyarta duk da halin damuwar da take aciki saida taji sanyi aranta.
"Nan dakina ne, Zaki Iya zama aciki kafin mu dawo, ga toilet ki shiga kiyi wanka.." amsa mashi tayi da toh..
Sumar kanta yaci gaba da shafawa, yadda ya sabayi mata tuntana yar kankanuwarta, ahaka yake samu tayi bacci, aiko cikin sa'a yaji alamun bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya ya sauke a hankali Ya kwantar da ita kan gadon, sai da yayi mata addu'o'i kafin Ya mike da baya da baya yake tafiya yana kallon ta idanunsa cike tab da kwalla.
Jiki asanyaye yajuya tare da buɗe room door ɗin Ya fito su ummi na ganin shi suka kewaye shi kamar yan jarida suka tsare shi da tambayar meya faru da Unaisah...
"bata Jin dadin jikinta ne, zanyi magana da dr, zai zo ya duba ta, yanzu bacci takeyi pls idan ta farka ummi ki taimaka mata tayi wanka taci abinci sannan ki sanya mata ido sosai.." basu kawo komai aransu ba, Ummi tace in sha Allah zanyi duk abunda kace.
Kallon Danejo yayi"My wife, Pls ki taimaka ma Ummi, Ku kula da su, " fuskarta dauke da murmushi tace"toh, daddyn Angel, kaima ka kulamin da kanka" sallama yayi masu, kafin fitarshi daga part din a ƙalla ya shafe mintuna biyar yana tunani kafin Ya fuce..💔
_______________________________✍️
*CHIEF OWAIS*
A Hankali Motar shi ta kunno kai cikin wani katafaren Resting Home na mai girma sharafudeen, tun kafin SA din dake driving dinsa yayi parking ta window glass din motar Ya hango Jami'an DSS kewaye da Courtyard din gidan dama kafin su shigo yaga sojoji tsare da gate din gidan hakanna ya dinga jin faduwar gaba.
Motarsu nayin parking bai jira an bude mashi car door ba saboda sauri da kanshi ya bude ya fito, with respect Dss din dake tsaye suka sara mashi, ko kallo basu ishe shi ba Ya nufi main door din falo.
Walking quickly ya haura Uptairs a gaban ƙofar katafaren Master suite na mai girma sharafudden ya ɗan dakata da yin tafiyar.
"Come In" daga cikin ɗakin Ya juyo muryar daddynsa
Da sallama ya shiga ciki a seating area ya hango shi A zaune kan wata katafariyar Sofa, ya dauki wankan tailored suit a jikin shi, yayin da idanun shi ke a manne da farin glasses, Hankalin sa na akan Apple Ipad din da yake pressing.
Madaidaicin table din gabansa na ɗauke da cups na cofee ...Ya daura kafa daya bisa daya.
Tun daga kan yanayin fuskar daddynsa Ya fahinci akwai damuwa, Karasa shigowa yayi tare da zukunnawa kan kafafuwansa agaban daddynsa Cikin girmama Ya gaishe da shi, sam babu walwala atare da shi Ya amsa mashi tare da nuna mashi sofa din dake facing dinsa
"have a seat," ya fada batare daya dago ya kallesa ba.
Jiki asanyaye Chief ya mike ya zauna kan sofa din, Kafin ya maida hankalinsa kan daddyn nasa yana jiran jin me zaice ma shi..
Da ipad din hannunsa ya nuna cup of coffee yace"ka ɗauka kasha naka ne"
yana cikin shan coffeen Muryar daddynsa ta katse shi"Owais, dagaske ne zakuje kai Farmaki.."
Ƙiris Ya rage ya saki cup din hannun shi, A matukar ruɗe yake kallon daddynsa, kwata kwata bai dago ya kalle shi ba, Still Hankalin shi na akan Ipad dinsa.
"Kayi shiru baka ce komai ba, Inaso naji daga bakin ka ne"!
Dakyar Ya iya furta Eh daddy, dagaske ne, amma tayaya akai ka sani? Bayan asirrince muka shirya komai ban sanar da kowa nawa ba..."
Sai da yai wannan maganar mai girma sharafudden ya dago da idanunsa ya dubi cikin idanun shi.
"hmm owais kenan, kada ka manta, tun kafin ka mallaki hankalinka nake sanya jami'ai su bibiyi rayuwarka, sai yanzu da ka girma ka ke tunanin zan daina sanya ido akanka"?
ya tambaya yana kallon shi, lamarin ya daurewa chief kai kuma hankalinsa ya dan tashi.
"Owais, meye hadinka da zuwa kai farmaki? dama shugaba Yana zuwa Yaƙi ne?
"Daddy, Ni na za6i da naje..." bai kare maganarba, ya katse mashi hanzarin shi
"Owais, bazan ta6a yin gangancin da zan rasaka ba, ka riga da kasan irin kaunar da nake maka, kai kadaine ɗa namiji tilo da nake da shi, taya zan zuba maka ido ka dinga yi min wasa da ranka"? A fadace ya fada.
Hankalin chief ba karamin tashi yayi ba, ganin dad dinsa na nema Ya jaza mashi matsala.
"Daddy, pls wanene Ya fada maka zancen zuwa kai farmakin nan! Inaso na sani.." fuskarshi ayamutse ya faɗa
Girgiza kai Sharafudeen yayi"ba bu bukatar ka sani, kuma kada kayi tsammanin cikin jami'an ku ne, a'a ko ɗaya, dan leken asiri nane ya fada min"
"why pls? Daddy kasan banaso!, a matsayina na jami'in sirri bai kamata ka sanya dan leken asiri yadinga bibiyar rayuwana ba, hakan ya sa6ama dokar aikina"!
Ya fada rai abace
"Naji Ubana Obinna, zan dakatar da ɗan leken asirin, amma ka sani, babu kai babu zuwa Kai farmaki, bada yawuna ba wlh..." saukowa yayi daga kan kujerar dayake azaune, Ya zukuna gaban daddyn nasa tare da ruƙe hannayensa acikin nashi.
"Daddy, dan Allah kada ka sage min kwarin gwiwar da nake da shi, daddy kamanta ne? Kaine fa kake karfafamin gwiwa akan aikina, tun da muke zuwa kai farmaki baka ta6a dakatar dani ba sai yanzu daddy"? Ya fada fuskar shi amarairaice.
"pls Kada ka hanani Yin aikin da zan taimaki rayuwar bayin Allah, in kuma kawar da mugun iri a cikin al'umma, daddy, Kasan ni mai biyayya ne agareka, ban ta6a maka gardama ba, amma dan Allah daddy, ka barni inje, na kwallafa rai akan son zuwa, Inaso naje daddy...."
Tamkar zai saka mashi kuka, Ya jima baiga damuwar dayagani yanzu akan fuskar shalelensa ba, idanunshi sun kada jawur kamar jan gauta.
Saidai bayajin zai yarje masa yaje don shi bai shirya rasa shi ba.
"Owais, Ni bawai zan hanaku yin aikin ku ba, kawai hankalina Ya tashi da jin inda zaku je kai farmakin, saboda ɗan leƙen asirin nawa ya fadamin inda zakuje gurin matsafa ne masu hadarin gaske, inajin tsoron Su cutarmin dakai, gaskiya ban amince kaje ba, saboda kai yanzu director General ne, babu zuwa Yaƙi a aikinka, ba dole saida kai zasuyi nasara ba, kawai ka tura Yaranka suje mana"_
ya faɗa babu wasa akan fuskar shi, harya buɗe baki zai kara furta kalma ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"na gama magana Owais," ya faɗa tare Ya duba agogon hannunsa
"I have a meeting, I don't want you to go anywhere, you'll spend the whole day here" yana fadan hakan yasa kai ya fuce.
Dafe kanshi Yayi da tafukan hannayen shi, kamar zai fasa ihu saboda tashin hankalin da zuciyarshi ta shiga! Mamakinsa taya akai daddynsa yasan da zancen farmakin da zasu ƙaddamar? Wai har yasan gurin matsafa zasuje? Bayan haka meyasa tunda Yake zuwa Yaki bai ta6a dakatar da shi ba sai wannan karan❓
Sun riga da sun gama tsara komai, tafiya kadai ta rage masu amma daddynsa na neman Ya kwafsa mashi.
Wayarsa dake acikin Trouser pocket dinsa sai ringing takeyi, yasan bai wuci na hannun damansa ne ke nemansa ba.
Kifa kan shi yayi, jikin Sofa wani irin sarawan Ciwon kai Yake Ji, Ji yayi bazai Iya bari damar nan ta wuce shi ba, Shi kadai ne zai bada Umarni su tafi kai farmakin nan In har basu ji daga gare shi ba, gaba daya plan dinsu zai lalace.
Yana tsaka da tunanin nan kwatsam lokaci ɗaya ya fara Jin wani irin matsanancin bacci na neman yaci karfin shi lokaci daya ya zare idanun shi cike da tashin hankali Ya ke duban Cup din da daddynsa Ya bashi Yasha cofee yunkurawa yayi da wata irin kasala Ya nufi kofar dakin Yaja handle din Yana kokarin bude ta sai dai ga mamakin shi Ya datse kofar ta waje, Kuma dole saida fingerprint ɗin daddynsa ko na mommynsa za'a iya unlocking ɗinta, tashin hankalin da ba asaka masa Rana.
Gwiwowin ƙafafunsa ne suka sage, wata irin juwa ta ɗebe shi gaba ɗaya Ya kife kan floor kamar wanda yasha giya takai mashi karo bai ta6a zaton daddynsa zaiyi masa haka ba, dama saida boyayyan mutumin nan yace mashi kada ya yarda da kowa saboda kowa zai Iya cutar da shi a halin Yanzu da alamun kamshin gaskiya amaganar shi.
Still bai daina kokarin mikewa ba, dakyar Ya zaro wayar shi daga trouser pocket dinsa, yanata faman kiciniyar bude idanunshi dake lumshewa, dakyar Ya lalubo layin Mommynsa Ya danna mata Call, cikin sa'a tayi picking.
"My baby boy, how are you"?
Kokari yake ya buɗe labbansa sai dai yayi masa nauyi, kamar harshen shi ya karye, dakyar ya iya furta"mom... myyy ... in.. Ina a resting home din dad... he locked me in his master suite...I can't open the door...I need your help...come quickly, Mommy."
yana faɗan hakan wayar ta sulbe daga hannun shi.
Yana jiyo muryarta da karfi take ambaton"hello Hello, Owais! Kana ji na? Me ka yi masa ne?
Kalmar karshe da kunnansa su ka ji ta furta kafin kiran Ya katse, bai ƙara sanin inda kan shi Ya ke ba..
(TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASHI RANA🤔❓)
__________________________________✍️
Yayin Da Chief Owais ke a garƙame Cikin ɗakin Mai girma sharafuddeen, acan Gidansa kuwa Ƙarfe biyar na maraice dai dai ba ƙari, Dankara dankaran Motocin suka fara shararowa Cikin gidan, kamar a filin daga, Wasu irin Dakarun Sojojine Majiya karfi, masu kirar samudawa, sunyi tsayuwar jarumtaka kan motocin, gaba dayansu Army Combat Uniform ne a jikin su, baka iya ganin fatar su saboda ta ko'ina sun rufe jikin su with protective gear, kowan nansu yana sanye da helmet(hular kwano) Bayan motocin sun yi Parking, cikin zafin nama sojojin dake akan motocin suka diddiro tare da bubbbuɗe Cardoors din, U.s Armies ne su ka fito kowan nan su yana a sanye da kayan yaƙi sun shirya tsaf.
Ta glass door din Falo, Big guy ya hango su, shima harya kammala shirinsa cikin Isod Combat Uniform.
Wata irin damuwace ta bayyana akan fuskarshi Ganin har su commender james sun karaso amma chief bai dawo daga Villa ba, Ya riga daya san halin turawa basu wasa da lokaci, kuma basa sa6a alƙawari, In har suka ji Chief bai nan Bazasu ji dadi ba, zasu ga kamar ba'a ɗauki abun da mahimmanci ba ne.
Kusan sau Hamsin Yana danna mashi Call baiyi picking ba, Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, cike da takaici ya furta"Ya salam,! Chief Ina ka shiga! Pls kada ka 6ata mana shirin mu, dan Allah ka ɗaga kirana, bana so mutanan nan suga gazawar mu"
ya faɗa idanun shi akan screen ɗin wayar shi dake ruƙe a hannun shi..
Layin Boss Ya danna ma Kira, bayan yayi picking Ya ce"boss, akwai matsala fa" on the other hand Taj Ya furta"meya faru Omar"?
"Chief Har yanzu bai dawo ba, Ina ta kira wayarsa baya picking, gashi har tawagar su commender sun karaso..."
Hankali atashe Boss Yace"Ya salam, Yanzu ya zamuyi Omar? Ko dai zaka jaraba kiran daddynsa"
"Har layin daddyn nasa na kira baya shiga"
"To ka jaraba kiran layin mommynsa watakil aci sa'a ta ɗaga"
"Okay, zan jaraba, but pls kuma Ya kamata ku fito Yanzu" ya amsa mashi da toh kafin Ya katse kiran
Yana kokarin kiran Gimbiya malikat Sai ga sako Ya shigo wayar shi da bakuwar number..
Buɗe sakon yayi tare da karantawa
_Omar, I won't be able to come; inform every team of fighters. I have canceled the attack_
(Omar, bazan samu damar zuwa ba, Ka sanar da kowace tawaga ta mayaƙan, Na soke kai farmakin)
Tsabar bacin rai, tuni idanun big guy sun kaɗa jajur, kamar zai fashe da kuka baima san sa'adda Ya jefar da wayar Ta fada kan sofa.
jiri Yaji Yana niyar dibar shi adaddafe ya zauna kan sofa, adai dai Lokacin, yaji Motsin Buɗe kofar main Falon, zumbur Ya miƙe Yai saurin daidaita nutsuwar shi don kada su gane wani abu...
ɗaya bayan ɗaya suka soma shugowa falon, dakyar Ya kakaro murmushi kan fuskarshi ya nufe su da sauri suka sara ma junansu, a mutunce suka gaisa da juna..
Cikin harshen turanci Commender James yace"Omar me kuke Jira ne? Naga banga sauran ba, Ina Chief Yake"?
Fuskarshi da matsananciyar damuwa kamar mara gaskiya sam Ya kasa bude baki Ya basu amsa saboda nauyin maganar da zai furta masu
gaba daya sun fahimci kamar akwai wani abu dake damun shi
"Omar kayi shiru bakace komai ba, Ina Chief dinne"? Yawu mai ɗaci Ya haɗiya, adabarbarce Ya furta"Am..sir.. dama dazu ne daddynsa Ya kira awaya yana son ganin shi, Har yanzu dai bai dawo ba, shi muke jira"
Yamutsa fuska Commender James Yayi da alama ranshi Ya 6aci bai dai ce komai ba.
"Pls mu shuga daga ciki" ya fada tare da nuna masu Cikin falon..
Girgiza kai Commender Yayi"ba zama ya kawo mu ba, bamu da lokacin da zamu 6ata, ka kira Chief kace mashi Yazo Mu tafi"
"Na kira layin shi baya shiga"
"Me hakan ke nufi"? Ya tambaya yana kallon Big guy.
Kafin Ya furta Kalma sai ga Boss Ya na saukowa Down daga second floor, jikinshi sanye da kakin yakinsa karasowa yayi tare da sarah masu commender suma suka sara mashi.
kallon big guy yayi
"Har yanzu baka same shi ba"?
Jinjina mashi kai yai alamar eh..
Cike da damuwa Taj Ya dubi su commender"sir, pls ku ƙara hakuri, watakil wani Uzirinne Ya ruke shi, idan ba damuwa mu shiga daga ciki"
"Taj kuyi kokari ku nemo Chief, idan ba haka ba zamu rasa damar da muke da ita"
ya fada tare da kallon yan tawagarsa"mu je" bin bayan shi su ka yi a kan sofas suka zauna.
ya rage saura Taj da big guy atsaye suna fuskantan juna sam sun kasa magana duk basu ji dadi ba.
"chief bai kyauta mana ba, Ni dama saida raina ya bani da wuya mukai farmakin nan lafiya batare da an samu matsala ba" rai aɗan bace Yai maganar.
Kafin Taj Ya furta kalma, wayar Big guy Ta fara ruri, da sauri Ya duba screen din tamkar zai fashe da kuka Ya dubi Taj"mun shiga Uku, General ne ke kira, may be Suma sun shirya tawagar su"
"Omar, ka kwantar da hankalinka, In sha Allah, komai zaifi daidai, Yanzu ka ɗaga kaji me zaice maka"!
Picking call din yayi tare da kara wayar a kunnanshi bayan sun gaisa
General Noah Yace"Ya ake ciki ne? Na kira layin chief baiyi picking ba, Already mun shirya tawagar Sojojin mu, Umarnin shi kadai suke jira"
yamutsa fuska big guy yayi, da ido Taj yake karfafa mashi gwiwa dakyar Ya furta"Sir, nan badajimawa ba, zakuji daga gare mu" daga haka su ka yi sallama.
Dagowa yayi tare da kallon Taj" hmm kasan meya faru"? Girgiza kai Taj yayi
"Chief ya turo min message, na boye ne saboda inajin nauyin in furta, amma chief Ya soke kai farmakin ayau"
wani irin faduwa gaban Taj yaji arude Ya firta"tayaya hakan zai yiwu Omar? Anya kuwa ka karanta sakon da kyau"
Mika mashi wayar yayi don ya karanta da kanshi bayan ya kammala karantawa Ya kalli Omar"ka yarda Chief ne ya rubuta sakon nan? Girgiza kai Omar yayi"ina kokwanto wlh, saboda Chief kaifi ɗayane baya sa6a alkawari in ba wani kakkauran dalilinne zai hana shi zuwa ba, bayan haka meyasa bai turo min sakon da layin shi ba"? Boss yace"uhum ni nasani ay, Allah kadai yasan meke faruwa, gaskiya ƙwara muje villa din.."
Da sauri Omar Yaje ya sanar da su commender cewa zasuje Villa donsu ga meya tsayar da Chief, commender Yace suyi kokari kada a bata lokaci.
gudu gudu sauri sauri suka fito daga Falon da karfi Big guy Ya kwaɗawa Jami'an dake akusa da parking space Kira Yace su buɗe masu mota, agaggauce jami'an suka bude, Taj ne ya fara shiga big guy na kokarin shiga, ba zato ba tsammani, saiga Motar Chief ta kunno kai cikin gidan da gudun gaske kamar zata tashi sama.
wata irin nauyayyar ajiyar zuciya Big guy ya sauke.
"Boss Ga chief din nan" da sauri boss Ya fito daga motar suka nufi motar Chief, motar Na tsayawa Big guy ya buɗe mashi car door din, kaitsaye idanunsu suka shiga cikin na juna, Ya jigata ba kadan ba.
Huggin dinsa Yayi kamar zasu koma mutun ɗaya a kalla big guy ya sauke ajiyar zuciya yafi sau uku..
"Ka tada min hankali Owais, meyasa ka dade? Ina ta kiran layinka baya shiga" ya fada tare da dago da kan shi har saida yadanji gabanshi ya fadi ganin yanayin fuskar Chief sam babu walwala kamar wanda yayi jinya.
Hatta boss Yasha jinin jikinshi da ganin yanayin nasa.
"Wani abu ya faru ne? arude Ya fada Yana kallon shi
Baya Jin zai iya sanar dasu abun da daddynsa yayi mashi.
dakyar ya iya shanye damuwarshi Ya kakaro walwala kan fuskarshi kafin Yace"bakomai, lafiyana lou, bacci ne ya dauke ni acan, kuma na sanya wayar a silent batare da sanina ba" badan sun yarda da maganar ba suka amince.
boss Yace"Sir mu shiga daga Ciki, tawagar su commender sun karaso, Suna a falo suna jiranka, bayan haka tawagar sojojin nigeria suma sun shirya, gaba dayanmu Umarninka muke jira..." numfasawa yayi kafin ya furta"okay Danish da salsabeel fa? Suma sun shirya"?
"Eh, duk sun shirya" ajiyar zuciya ya sauke.
Bayan sun shiga Gidan, atsaitsaye Ya gaisa da su Commender kafin Ya nufi bedroom dinsa, don Ya shirya...
(Tayaya akai Chief Ya ku6uta daga tarkon da Mahaifinsa Ya ɗana masa"?)
Bayan da ya kira Mommynsa awaya, ba'a fi minti biyar ba, sai ga hamshakiyar motarsu ta shigo a parking space security din dake driving dinsu yayi parking, A hanzarce Gimbiya Malikat ta fito daga mazaunin baya na motar, Jikinta sanye da tsadaddiyar Lafaya lace, hadadden shade din data sanyawa idanunta ba karamin kawatasu yayi ba, takalman kafarta kadai abun kallo ne, tana tafiya p.a ɗinta na take mata baya, wata katuwar mace karkarfa, Jikinta sanye da Suit, tasha kitson zane akanta.
Cikin takun qasaita take tafiya, yanayin fuskarta sam babu walwala, saboda Hankalin ta ya tashi da jin abunda Owais Ya fada mata.
Kaitsaye suka Nufi master suite din Mai girma sharafudden.
Abakin kofar Room ɗin suka dakata da yin tafiya, Gently ta ɗaura Thumb ɗinta akan Biometric scanner ɗin dake jikin handle din kofar, nan take kofar tayi Unclocking ɗin kanta...
Juyawa tayi tare da kallon P.a ɗinta, abunka ga masu Izza a jini, da ido tayi mata alamar ta tsaya anan, with respect ta amsa mata da okay ma'am..
shigarta keda wuya kofar tayi locking kanta..
Ɗakin tabi da kallo, kwatsam idanunta suka hango mata shi kwance kan floor kamar matacce kwata kwata baya motsi.
Numfashin shi ne kadai ke fita.. Hankalinta yayi mugun tashi, a sukwane ta zare shade din dake akan fuskarta..cikin sauri ta nufe shi ta zukunna agabanshi ta sanya hannayenta biyu ta dago da kanshi ta kwantar saman laps ɗinta.
shasshafa fuskarshi tayi muryarta na rawa ta furta"My son! Lafiya ka kwanta kan floor kamar wani mara gata? Meke damunka ne? Owais kana Ji na kuwa?
tariyo maganar da sukayi awaya tayi lokaci ɗaya zuciyarta, ta raya mata ba baccin lafiya yakeyi ba, saboda yanayinsa yafi kama da na wanda yasha kwayar maye.
a hankali ta kwantar da kan nashi kan floor, ta mike tare da kai idonta kan coffee table din dake a seating area.
Cups ta gani biyu akai, matsawa tayi gaban table din, ta dudduba cups ɗin, ita dai bata ga komai ba har ta juya zata koma wurinshi kwatsam idonta ya hango mata packet na pills daga gefen table din kiris ya rage ya shige karkashin sa.
Yatsun hannunta na kerma ta dauki packet din ta soma karanta rubutun dake a jikin shi zaro ido tayi saboda ta gane sleeping pills ne.
Hankalinta ya tashi ba kadan ba! tamkar zata fashe da kuka ta furta"why Owais! Why! Me ya hadaka da maganin bacci mai hadarin gaske.." juyawa tayi tare da kallon shi bawan Allah baimasan inda kanshi yake ba..
fitowa tayi daga dakin hannunta ruke da fakitin, P.a na ganinta tay saurin russina mata..
"Duba min maganin nan" ta fada tare da mika mata roban
"Inaso akawo min antidote dinsa Yanzun nan.."
Jinjina mata kai p.a tay, tare da juyowa ta bar gurin, tana atsaye tana jiran ta, badajimawa ba saigata ta dawo hannunta ruke da Injection ta miƙa mata.
Tasa hannu ta kar6a, tare da juyowa ta koma ɗakin, kasancewar tana da ilmin abun bata sha wahala ba, bayan ta kamma yi mashi allurar.
Zama tayi gefen shi, tana kallon shi, zuciyarta cike fal da tunin meya faru tsakanin shi da mahaifin shi..
Tsawon mintuna ashirin, Ya fara zubda gumi a jikin shi, kamar an yayyafa mashi ruwa, yatsun hannunsa dana kafafunsa suka fara kerma kamar wanda sanyi ya kama, ajiyar zuciya ta fara saki ganin ya fara dawowa hayyacin shi...a hankali ya bude idanunshi wadanda suka kaɗa jawur ya kurawa ceilling din dakin ido kamar ya manta da abunda ya faru.
"Owais,"
jin muryar Mommynasa yasa shi saurin kai idonshi gare ta..wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, da kyar ya tattara karfin jikinshi Ya samu ya mike tare da matsawa kusa da ita, cikin sauri ta rungumoshi kan kirjinta, hannunta daya acikin sumar kan shi..
"My son, are you Okay? ta fada cikin kulawa.
Jinjina mata kai yai alamar eh, bata kara tanka mashi ba, yayi shiru yana faman jan numfashi har saida Ya ƙarasa wartsakewa Ya dawo hayyacin shi kafin ta tambayeshi dangane da kwayar maganin baccin daya sha!
"Kai nake sauraro Owais, ka daga min hankalina, kuma meya hadaka da daddynka, dayaja harya kulle ka adakin sa"?
ta fada tana kallon fuskarshi, still bai dago daga jikinta ba.
Cikin disasshiyar murya ya furta"mommy, zanyi maki bayani, amma ba yanzu ba, pls ki kwantar da hankalinki, ba abunda ya faru tsakanina da shi..."
fuskarta ayamutse tace"meyasa bazaka fadamin yanzu ba"?
A gajiye ya girgiza kanshi"mommy, tafiya zanyi, abokan aikina suna jira na, I don't want to lose the opportunity I have, In har banje ba, all our plan will be ruined"
gefen fuskarshi ta shafa da hannunta"shikenan, Na fahimce ka, bazan matsa maka ba, nasan yanayin aikinku, amma pls, ka kula mun da kanka Owais..." lumshe idanunshi yayi tare da jinjina mata kai, ya ruko hannayenta biyu acikin nashi"mommy, Ina barar addu'arki, nasan kinayi min, amma kwanakin nan ina bukatar ƙari akan wadda kike yi min, bama ni kadai ba, hada abokan aikina .." cikin sanyin murya tace"in sha Allah Owais, zanyi maka addu'a, ay bana mantawa dakai, amma kayi ma daddynka magana akan yayi maka addu'a ?
girgiza kai yayi"a'a mommy, nafi bukatar taki, in har kikayi min kamar yayi minne, and pls, bana so daddy yasan kin bude min dakin nan, kiyi min hanyar da zan fita daga gidan nan batare da wani ya ganni ba..."
ta ɗan rude da jin abunda Yace amma sai bata kawo komai aranta ba, saboda ta yarda da ɗan nata da kanta tayi mashi hanyar barin gidan batare da security officers din da mahaifinsa yasa tsaron gidan sun tuhume su ba.
Kunji yadda akai Chief Ya ku6uta daga tarkon daddynsa ✍️
Fitowar Chief daga Part dinsa tayi daidai da fitowar Danish Da Salsabeel.
Gaba ɗaya Hankulan U.s Army din Ya dawo kan shi, yayi matuƙar jan hankalinsu yadda kasan Diamond a sararin samaniya saboda kyan da yayi Cikin shigar Isod Combat Uniform, Ya rufe fuskar shi da Mask, hadaddiyar sumar kan shi ya daure ta da head ties jelar gashin ta sauka agadon bayansa.
Ƙafafuwansa suna asanye da wasu hadaddun Combat boots ko a kakin yakin bakomai ya sanya ba babu protective gear saboda baya bukatar su.
har ya sauko down basu daina bin shi da kallo ba, tun da Allah ya halicce su basu ta6a ganin Matashin sarauyin da kakin Yaki su kayi ma kyau irin Danish ba ya fita daban acikin su, ya fito a suffar jarumtakarsa, sadaukin namiji mai ji da karfin sa..
Kallo ɗaya big guy yai masa ya kau da kai gefe, taj kuwa sai da yadan sha jinin jikin shi aranshi ya ayyana ba mace ba ko namiji ya kallesa sai ya burge shi, ina ma amfanin kyau irin nashi ba ilmi wannan ay masifa ne bakaramar 6arna zaiyi ba, a ganinsa kyawun shi ne ke ruɗar Unaisah da kuma tausayinsa shiyasa ta ke nema ta zauce akan son shi.
A hankalin Salsabeel Ya ruko hannun Danish acikin nashi.
Bayan sun karasa saukowa down U.s Armies suka fara zuzuta kyawun da kakin su ka yi mashi hatta chief sai da ya yaba, gaba daya suka dunguma zuwa harabar ajiye motocin gidan.
abun daya 6ata ma big guy rai Yana niyar ya shiga Motar da chief zai hau Chief ya ja hannun Danish suka shiga motar, Yaji zafin hakan sai dai Ya hakura Ya shiga Motarsu Taj.
bayan us armies din sun shisshiga motocinsu, da gudun gaske suka fuce daga Estate din saboda Lokaci.
A cikin Mota Chief Ya kira Sheikha Mujeeda, Aransa yana Allah Allah ta ɗaga Yasan ba ta daga kira in ba an fara tura mata sakon neman izni ba amma cikin ikon Allah tayi picking yadan yi mamaki amma da ya tuna maganar da sukai akan Danish sai ya gane dalilin dayasa ta daga kiransa bayan sun gaisa yace mata ɗanta na barar addu'arta zasu yi wani aiki mai hadarin gaske.
yanayin muryarta da damuwa tace In sha Allah zanyi mashi addu'a, In yana kusa ka bashi wayar"
mika ma danish wayar yayi baisan wanene ba Ya kar6a ya kara a kunne yayi shiru baice komai ba har saida gimbiya Mujeedat ta furta"My Son kana lafiya"? arude Ya kalli Chief tare da tambayar who is She? Murmushi Chief yai tare da cewa"matar daddy minister" nan take ya tariyo lokacin farko daya fara ganinta, bazai ta6a manta yadda ta cire mask din fuskarshi ba ta zuba mashi kyawawan idanunta.
Cikin sanyin murya ya gaishe da ita with respect, ta amsa mashi kafin tace"chief ya fada min zakuyi wani aiki mai hadarin gaske, In sha Allah zan tayaku addu'a..." yace mata ya gode, har tana zolayar shi da cewa tasan da daddy minister ne suke waya sai yafi sakin jiki saboda sun saba amma ita kamar baison yi mata magana..
Ko gama wayar basuyi ba ya mika ma Chief saboda wani yanayi dayake ji atare da shi, Zuciyarshi Ta kasa samun sukuni tun kafin su bar garin Ya fara jin matsananciyar kewar Unaisah.
Tafiya yankin azaba sun ɗauki tsawon awanni akan hanya, da misalin sha biyun dare, suka qaraso cikin Dajin da suka haɗa katafaren sansaninsu, dajin yana a kusa da evil forest, katafaren Military base ne mai girman gaske ga wasu Irin Dakarun Sojaji masu ƙira irin ta zakuna kowan nan su yana asanye da army combat uniform dinsa, Cikin takun majiya karfi suke sintiri a cikin sansanin tamkar da rana saboda hasken electricity din dake a ko'ina na sansanin.
Bayan sun fito daga cikin motocin su, duk inda suka gifta cikin girmamawa sojojin ke sara masu tare da yi masu maraba da zuwa, a haka har suka shiga inda masaukinsu yake domin su dan hutu na wucen gadi.
THE DAY👹👺
Asubahin fari suka farka daga bacci, musulman dake acikin sukayi sallah awani ke6a66en wuri dake a cikin sansanin, bayan sun yi kalacin su, gaba ɗaya sojojin suka hallara a filin dambe, suka fara motsa jikin su har dambe sai da su ka yi a tsakaninsu wanda ya kasance kamar gasa ce su ke yi, Danish ya zama zakaran gwajin dafi a wurin an kasa samun wanda zai kayar dashi dayawa sun kara samun kwarin gwuiwa da ganin irin kwazon shi, bayan sun gama damben suka ɗan huta har wuraren ƙarfe shida na marece kafin daga bisani suka fara shirin shiga evil forest.
A helipad din dake a wani sashe na cikin Sansanin Wasu dankara dankaran Jiragen yaƙi ne a jere masu saukar ungulu da aka tanadar masu, ko da ido ka kalle su sai gabanka ya fadi, already fighter Pilots ɗin da zasu Yi jigilar daukarsu tuni sun shige cikin helicopters din.
Bayan komai ya daidaita, har dakarun sojojin sun gama shiga cikin jiragen, Kafin wani Lokaci jiragen suka lula sama, yayin da trucks ɗin makamai dake tafiya akasa suke bin su.
*FATAN NASARA*
____________________________________✍️
*🔥GIDAN KURKUKUN ƘADDARA🔥☠️*
Farkawarta kenan daga bacci, A hankali ta buɗe idanunta tare da kallon rufin gadon, Har na tsawon mintuna, har rama ta qara saboda azabar rashin lafiyar da tayi.
ta wutsiyarta idanunta ta hangi mutun kwance gefenta, da sauri ta wurga idanunta akanta, ajiyar zuciya ta sauke ganin tsohuwa khala, da alama tayi nisa acikin baccin ta, ta ɗan yi mamaki don tunda ta tsinci kanta a dakin khala bata ta6a kwana kan gadon ba, a saman kujera take yin baccin ta a zaune kamar dogari.
Kasa kauda ido tayi daga kallonta, wani irin kaunar dattijuwar take ji acikin zuciyarta, batasan sa'adda ta matsa kusa da ita ba takai hannu ta shafa gefen fuskarta mai tarin tamoji tamoji, ta manna mata sumbata kan goshin ta ta danyi murmushi har chin dimple dinta Ya motsa.
"Bayan ɗan uwana gabriella, bani da abu mafi soyuwa daya wuce ke, Inasonki Khalana.." kamar daga sama ta tsinkayi muryar Khala acikin kunnanta"Nima Ina sonki Jikata" zare brown eyes dinta tayi fuskarta dauke da annurin farin ciki ta furta"Khala, Idonki biyu"? Ta fada akagare da son jin amsarta..
A hankali Khala ta buɗe idanunta akan fuskar Gabriellah.
"Ya jikin naki Jikata"? still da murmushi kan fuskarta tace"Naji sauki, yanzu babu inda keyi mani ciwo"
Tattausan murmushi khala ta sakar mata"haka nake sonji, Na lura kamar Kina farin ciki Yau, saboda tunda nake dake banta6a ganin murmushin ki ba..." yar dariya Gabriel tayi
"khala, kece silar farin cikina, da na yanke kauna da rayuwar duniyar nan, amma silar haduwana dake da kuma alkawarin da kika daukarmin na haɗani da ɗan uwana Yasa naji Ina son na rayu, Ina son na zama jajirtacciya jaruma kamar ke, kuma ina son na ɗauki fansar abunda akayi mana" tunda tafara magana khala ke binta da kallo, arayuwarta tana Son ya'ya musamman idan tagan su cikin nishadi da walwala shiyasa aduk lokacin data ga ana azabtar da rayuwar su take jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu saboda baƙin cikin da takaici.
"Amma khalana, Idan muka yi nasarar ku6uta daga kurkukun nan, atare zamu rayu ko"? Murmushi khala tayi"Idan na fita bansan inda zanje ba, bani da kowa, ko kina da inda zaki ajiye ni"?
Shiru gabriella tayi tare da ta6e bakinta kamar zatay shagwa6a tace"nima bani da kowa, amma dani da ɗan uwana Gabriel, zamuyi aiki tukuru, donmu gina gidan da zamu zauna, nayi maki alkawarin zamu baki kyakkyawar kulawai..."
cike da nishadi khala ke sauraronta..
Kwatsam suna tsaka da yin fira, ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka jiyo masu wani irin sautin Bugun ganguna dumdum kamar dodon kunnan su zai fashe, tsabar sautin bugun gangar Ginin Har girgiza yakeyi, hatta gadon da suke kwance akai ya kama girgiza.
gaba daya Gabriella tabi ta ruɗe, baiwar Allah dama ba lafiyar kwalwa gare ta ba, da sauri ta toshe kunnuwanta da tafukan hannayenta.
Tsohuwa Khala kuwa tashin Hankali da farga Ya hana ta motsa sai faman zare idanunta takeyi.
Lokaci ɗaya suka daina Jin bugun gangar, sai kuma suka fara jiyo ɗaddaɗar Busar sarewa tana tashi
lokaci ɗaya yanayin fuskar Khala Ya sauya, aruɗe ta furta"ELDERS"
Cikin ruɗu Gabriellah ta kalle ta cike da rashin fahimtar me take nufi..
Damƙo hannunta tayi acikin nata"akwai abunda na manta ban fada maki ba, daren yau dare ne mai hadarin gaske, bugun gangar da kika ji alama ce dake nuna ƙarasowar ELDERS.
"abunda nakeso dake ki 6oye karkashin gadon nan, kada ki kuskura ko tari kiyi idan ba haka ba zaki jefa rayuwar ki cikin haɗari ne.."
Hankalin Gabriella ba karamin tayi yayi ba, muryarta na rawa ta furta"Dan uwana fa? kada su kashe min shi..."
katse ta khala tayi"babu abunda zai same shi, kiyi abunda nace maki kawai"
saukowa sukayi daga kan gadon da sauri Gabriella ta shige karkashin gadon, ba laifi Yana da faɗi da tsawo, kamar ƙaramin ɗaki, tayi mamakin ganin buhun huna kusan Biyar a karkashin gadon ga wasu akwatinan ƙarfe, jikinta na kerma amma saboda karanbani saida ta yi kokarin kwance buhun don ta ga menena aciki, Sai dai takasa saboda mugun ɗaurine akayi masu, tatta6a jikin buhun tayi sai taji kamar Makamai ne a cikin su...
Komawa tsohuwa khala tayi kan gadon ta kwanta tare da lumshe idanunta, zuciyarta cike fal da fargaban abun da zai biyo baya don tasan muddin Elder ya ƙaraso adakinta zai huce gajiyar shi.
bakomai yafi damunta ba face zuwan Garkuwa, Allah Allah take su karaso saboda batason Elders suyi nasarar Salwantar da rayuka a wannan daren, In har daren yau ya wuce Bata cimma burinta ba, bata jin zata Iya jure rayuwa adoron duniyar nan, saboda in har ta kuskura asirin ta Ya tonu na abunda take kullawa Allah kadai Yasan Mummunan hukuncin da zasuyi mata, donma saukinta daya Elder Yana Ji da ita.
Bata kare zancen zucinta ba, Kamar daga sama Taji dirar wani abu adakinta,
Sautin shu'umar dariyar shi ce ta karaɗe kunnuwanta, Tuni tasha jinin jikin ta.
"Da wata irin Murya irin ta tantiran ƴan'duniya Ya furta"Idan ma bacci kike, toh ki farka..." yunkurawa tayi ta miƙe zaune, tare da kai dubanta gare shi, Yana atsaye cikin wata rantsattsiyar alkebba launin Ja mai adon duwatsu irinta sarakuna..ya lullu6e kanshi da hular alkyabbar, rabin fuskarshi arufe yake da takuntumi, kafafunshi suna asanye da wasu hadaddun takalma na alfarma, yayin da hannunsa ke aruke da sanda ta zallar Zinari.
ba'a Iya ganin fatar jikin shi saboda ya lullu6e ko'ina hatta yatsun hannunsa safa ya sanya masu.
Gabriella dake labe ta kasa kunne tana sauraronsu, da ga inda take tana Iya hangen kafafuwan Elder..
"Taya zan Iya bacci batare dana sanyaka acikin idanuna ba, tun bayan daka tafi kabarni da kewarka, idanuna sunyi maraicin ganin ka, sanyin idaniyata, mijina uban ya'yana, sarki ɗaya tak da ke mulkar zuciyata..." cike da qasaita yake sakin dariya yayin da yake tinkarar gadonta cike da dattako yake taka matakalar gadon.
"Meyasa soyayyar mu bata tsufa ne? Aduk lokacin dana ganki sai inji kamar ana rura wutar sonki a cikin zuciyana, bazan Iya misalta kewarki da nayi ba.
yayin da yakeyin maganar, wani irin kallo khala take binsa da shi mai wuyar fassaruwar, ta tsane shi fiye da yadda ta tsani mutuwarta, shine silar komai 💔
gaba daya tayi zurfi a tunaninta sam ta manta da shi akusa daita, batai aune ba taji ya janyota jikin shi, wani ɗaci taji aranta, sai taji kamar ta hada jikinta da wuta saboda tsanar da tayi mashi..
Sumbatar kuncinta yayi, cikin wani irin salo ya fara sarrafa ta.
Gabriella dake la6e a karkashin gadon, gabanta sai faduwa yakeyi ganin yadda gadon ke girgiza kamar zai rubzo mata, gani take kamar mutumin dayazo ne ke cutar da Khala.
kasa jurewa tayi duk tabi ta rude jikinta sai kakarwa yakeyi bata san sa'adda ta saki ƙara ba, da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta.
Lokaci ɗaya Elder Ya raba jikin shi daga na Khala, ido cikin ido suke kallon juna..tun daga yanayinta ya fahimci akwai wani abu da take boye masa.
Kamar daga sama taji Ya furta"kamshin mutum nake ji adakin nan..." arazane ta ware idanunta akan fuskar shi, jinjina mata kai yayi
"Ke da wanene Kuke rayuwa adakin nan? Kuma Yana ina"? Ji tayi kamar ta fasa ihu saboda tashin hankali, batasan ya akai ya gane akwai mutun ba..
.
"Kinyi shiru baki bani amsa ba, Ko kin bani za6i In gano da kaina"?
Yawu mai daci ta hadiya muryarta na rawa tace"bakowa, Ni kadai ce, nayi mamaki da naji kace kaji kamshin mutun bayan ni kadai ce mutum da ke rayuwa a cikin dakin nan.."
"baki saba min karya ba, Amma yau kinyi min, kinsan na tsani makaryaci, saboda alamace dake nuna mutun zai Iya cin amanarka wata rana"
idanunta ne suka ciko tab da kwallo, cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri, na gane kuskurena, kasan ba halina bane, dama yarince daga cikin prisoners, inason yarinyar ne shiyasa na taimake ta..."
tun kafin ta kare maganar Ya daka mata tsawa a faɗace Ya furta"meke damunkine? Kina cikin hayyacinki kuwa? Kin manta gargadin da nayi maki?
Kamar ƙaramar yarinya ya rufe ta da faɗa.
"Ki rasa wa zaki kawo cikin dakina sai ƙasƙantacciya Prisoner? Ɗakin Elder? kefa sirrina ce, sai da na fada maki banaso kowa ya rabeki in bani ba"
kokarin bashi hakuri tayi, ko kallo bata ishe shi ba, saukowa yayi daga kan gadon da kakkausar murya ya furta"Tana ina"! Jiki na rawa tsohuwa Khala ta sauko daga kan gadon.
"Pls kada ka rabani da ita, Inasonta, wallahi bada wata manufa na ajiyeta adakin nan ba.." magiya ta dinga yi mashi amma dayake zuciyar irin ta fir'auna ce ko kadan bai saurare ta ba.
Tsoro Ya hana Gabriella fitowa, kirjinta kamar ana luguden ta6are..
"Zaki fito da kafafuwanki, ko kuwa Ni kikeso In fito dake..." cikin karyayyar murya khala ta kira sunanta..
Jiki asanyaye ta fito daga karkashin gadon, wani dan iskan kallo Elder yabita da shi, farat ɗaya Ya gane ƴar wacece.
Dariyar shaƙiyanci Ya saka kafin Yace"wannan Ay yar gurin Jan wuya ce, sadaukarwar Jini ce, bazan Iya barmaki ita ba, dama wata ce daban, Ko ubanta Yaji kin dauke ta sai yazo ya kar6eta ya mayar da ita cikin prisoners, kinga kuwa babu amfanin boyeta agurin ki...."
Gabriel ta ruɗe da jin maganar shi, ta fashe da kuka, idanunta akan fuskar Khala dake kallon ta.
cikin shesshekar kuka tace"kada ki bari arabani dake, kashe ni zasuyi, bana so na koma gurin su, kada ki manta da alkawarin da kikayi min pls...."
Da kallon tuhuma Elder Ya dubi Khala"wani alkawari ne kikayi mata"
"Zan hada ta da ɗan uwanta" ta fada rai a6ace..
"Ku shigo ku dauke ta" suka ji ya fada, kafin wani Ya furta kalma sai ga Giants biyu karfafa sun fado cikin ɗakin, wani irin faduwar gaba Gabriella taji, jikinta na bari kamar mazari ta la6e bayan Khala, ta rurruke hannunta tanayi mata magiya kan kada ta bari su tafi da ita.
shiru khala tayi jikinta yayi sanyi lakwas, Zuciyarta ta karaya.
"Ku maida ta, Cikin Ƴan uwanta,"
Duk yadda Gabriella taso ta kubce masu abun yaci tura, tana ji tana gani suka nuna mata fin karfi akan idonta Giants suka fuce da Gabriella...
Jiki asanyaye ta koma kan kujera ta zauna, idanunta suka cicciko tab da kwalla...
Matsawa yayi kusa da ita tare da sunkuyar da kanshi gab da fuskarta"fushi kike dani"? Ya faɗa tare da ɗage mata gira..
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: _______________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️❓😈👹💞💘
Yar dariyar takaici ta yi, "Elder kenan, ka jima kana nuna min fin ƙarfi, wlh tun ranar dana gane asalin wa nene kai, na ji ka fita araina, wlh na tsaneka kamar mutuwa, babu abunda nake kwaɗayi da ya wuce inga bayanka, dan Allah ka mutu mana, na gaji ! na gaji !! da irin baƙincin da kake ƙunsa mini, wai kai wani irin mutunne? ko sau ɗaya baka ta6a jin nadamar irin zunubban da kake aikatawa ba? Na jima ina kokwanton anya kai mutunne? Saboda babu zuciyar imani a ƙirjinka... "
Bata ƙare maganar ba, ya daka mata tsawar da tayi silar rikicewarta tuni tasha jinin jikinta, nuna ta yayi da yatsan shi, "Bansan a ina kika samu ƙwarin gwiwar gaya min magana cikin idona ba, koda yake dama haka kike da kafiyar tsiya, ke kin sani bada son raina na jefa ki cikin kurkukun nan ba, kece sila, shisshiginki da bin kwakkwafinki ne suka ja maki, naso mu dawwama acikin farin ciki amma kin 6ata komai, wallahi ba don son da nake maki ba da tuni najima da kashe ki, amma saboda ƙaunar da nake maki shiyasa na killaceki anan saboda kada ki tona min asirina..."
Cike da taikaici ta yi murmushi haɗi da ɗan girgiza kai ta ce, "Ai ni tuni kajima da kashe ni, me kuma ya rage? Tsawon shekaru ashirin rabona da inga hasken rana, tsawon shekara ashirin rabona da inga wani dangina, dan Allah ka kashe ni in huta, na roƙe ka Ka kashe ni mana...!" cikin jin kunar rai ta faɗa.
Lumshe idanunshi yayi akan fuskarta tare da buɗe su, da wata irin siga ta jan hankali yace,
"Idan na kashe ki, kamar na kashe kaina ne, nafison in ma mutuwar zakiyi mu mutu atare."
"Elder kenan, makomarmu ba zata ta6a zama ɗaya ba, ni da nake so In mutu Cikin rahamar ubangiji, taya za kai min fatan mu mutu atare?"
Tuntsirewa ya yi da dariya, cike da tsana take kallon shi....
"Bazan bari ki 6ata min ranata ba, yau ina cikin farin cikin zagayowar ranar da muka kafa gidan kurkukun ƙaddara, ko murna baki tayani ba..."
Wani kallon rainin wayau ta jefa ma shi a cikin ranta ta furta, "In Sha Allah yau ce rana ta ƙarshe da zaku yi black night a duniya, Ubangiji Allah Yasa su kawo maku farmaki su tarwatsa tawagar azzalumai..."
"Me kika ce?" Firgigit ta kalle shi cike da fargaban kada ace Yaji ta, duk da ta dai san a zuciya tayi maganar amma tasan yana iya karantar abunda take saƙawa acikin zuciyarta.
"Kaji nayi magana ne?" Girgiza mata kai yayi.
"Ni zan Shiga fadata, ko zaki raka ni?" Banza tayi da shi,
"Ki kula min da kanki." Bai tsaya yaji amsarta ba, Ya 6ace ma ganin ta..
Me ya faru bayan Giants sun tafi da Gabriella?
Tana ta kuka tana tirjewa, a haka suka miƙi hanyar komawa cikin Kurkukun da ita, adaidai zasu karya wata kwana kwatsam saiga Tsohuwa Inno ta fito daga fadar elders karaf idanunta suka hango mata Gabriella...
A sukwane ta dakata da yin tafiya ta zuba mata idanu, yarinyar da take nema ruwa ajallo sai gata yau Allah Ya haɗasu..
Dariyar mugunta ta saki mara daɗin ji kamar haniniyar jaki, A firgice Gabriella ta kai dubanta ga tsohuwa Inno jin sautin dariyarta, Lokaci ɗaya yanayin fuskarta Ya canza ganin matar da ta tsana fiye da mutuwarta.
Ƙarasowa Inno tayi gaban su da sandarta ta tsaya cike da shaƙiyanci ta ce, "Wanake gani kamar Gabriella? Yarinya mai ran ƙarfe, ashe rai kanga rai? dama saida raina ya bani baki mutu ba, Kina nan da ranki, kai! amma fa nayi mamakin tayaya akai kika rayu bayan tiyatar dana sa giant yayi maki? Wani mai imanin ne yayi jinyarki?
Banza tayi da ita, ta6e baki Inno tayi tare da kallon giants din dake a ruƙe da ita, "A wace Bola kuka tsunto sharar nan"? Wannan kalma ta ƙona ran Gabriella, ta ƙulu sosai.
Ɗaya daga Cikin Giant ɗinne Ya ce, "Daga ɗakin Khala, Elder ne ya bada Umarnin mu dawo da ita cikin yan uwanta." Ta6e baki Inno tayi, "Dama nasani, duk cikin kurkukun nan babu mai zuciyar imanin da zai iya jinyarki in ba ita khala ɗin ba, amma fa na tayaki baƙin ciki, da kin mutu da kin huta."
Ta faɗa tana leƙen fuskarta, warin bakinta duk Ya cika hancin Gabriella, wani irin yunƙurin amai ta fara Ji..
Bin ta da kallo tayi daga ƙasa har sama, saboda tsabar fitsara hada sanya hannu ta ɗage rigarta ta tura kai tana leƙen gabanta don taga aikin da akai ma wurin, duk tayi shiru bata hanata ba...
Ɗagowa tayi fuskarta dauke da shu'umin murmushi ta ce, "Kin ɗinku da kyau, wuri fa yayi kyau, naji dadi kinga yau Manyan Baƙin mu zasuyi badago a kanki..." ta faɗa tana sakin dariya.
Ƙululun baƙin cikine Ya tokare makoshin Gabriella sai huci take kamar zakanya, kashe mata ido tsohuwa Inno ta yi kafin ta kalli giants din dake a ruƙe da Gabriella ta basu Umarnin su tafi.
Kamar jira take Giants ɗin subar wurin dama zuciyarta ta kawo wuya, aikuwa tayi wani irin kukan kura da iya ƙarfinta na karshe ta daka uban tsalle tayi zaman yan bori akan Tsohuwa Inno, kamar Allah ya aikota ta dinga gartsa mata cizo da yakushi tsohuwa inno ta dinga kokarin Kayar da ita ƙasa amma takasa, sai da ta kekketa fatar ƙwalƙwalin kanta, duk ta ciccisge mata yar hurhurar dake a kan, tayi ma kwallan kan rantali da akaifarta duk ya yi jaga jaga da jini...
Wa'iyazubillah! Wata irin kururuwa tsohuwa inno ta saki tare da jijjige jikinta silar hakan yasa Gabriella ta kundumo ƙasa timm! nan take Inno ta rikiɗa ta zama wata mummunar halitta mai razanarwa, gurnaninta kaɗai Ya isa ya rikita kwakwalwar mutun.
Da mugunta ta durfafi Gabriellah, a lokacin so tayi ta kasheta ta hanyar handameta, aikuwa ta watsa aguje ta nufi wata doguwar hanya mai duhun gaske, bin ta Halittar ta yi aguje duk inda ta taka sai floor ɗin gurin ya girgiza saboda girman halittar, gaba ɗaya Gabriella ta rude ta razana ta rasa ina zata boye kanta, don tasan muddin Tsohuwa Inno ta kamata Sai dai buzunta...
Saƙo da lungu ta dinga bi, tana tsaka da yin gudun ta faɗo cikin wani ke6a66en wuri mai tarin komatsai ga shi babu wadataccen haske,
Gurnanin dabbar da ta jiyo ne yasa ta furgice ta soma ja da baya, cikin rashin sani tana ƙara ɗaga kafarta ta taka wani wuri gaba ɗaya ƙasan gurin ya rubza da ita ta zurma cikin wani rami wanda bakomai ne a cikinsa ba face zallar jini mai ƙarnin gaske ga ɗoyi, shi wannan tafkin asalin samuwar shi daga ɗakin fiɗa ne na gidan kurkukun ƙaddara, jinin mutanan da suke feɗewane idan ya gangaro ta cikin pipe kai tsaye yake shiga cikin tafkin anan ya ke taruwa in suka tashi amfani da jinin zuwa suke su dibe shi a cikin tuluna.
Wa'iyazubillahi! kamar zata haɗiye zuciya saboda azabar ƙarnin da ya toshe ƙofofin hancinta, jinin ya mamaye jikinta Iya wuyanta ne awaje sai ihu take tana kokawar fitar da numfashin ta.
Ko da tsohuwa Inno ta faɗo wurin ta hango Gabriella tana ihu cikin jini, nan take ta Rikiɗa ta dawo ainihin suffarta ta mutane, wata irin mahaukaciyar dariya ta saki, ganin haƙarta ta cimma ruwa, Saboda zalunci maimakon tabarta haka sai da tayi mata sihiri ta ƙarasa nutsar da ita cikin jinin kanta ya shige gaba ɗaya, tasan bazata rayu ba, sai dai a fito da ƙasusuwanta in namanta ya gama zagwanyewa.
A bangaren Tsohuwa Khala Hankalinta Yaƙi kwanciya, saboda fargaba da zullumin abun da zai biyo baya in har su Garkuwa basu kawo farmaki ba, baiwar Allah ta kwallafa rai akan zuwansu, ta kasa tsaye ta kasa zaune har gaban madubin ɗakinta ta je ta zauna kan kujerar gabansa, tayi siddabarun da ta saba yi donta samu damar yin magana da shi amma bata ga komai ba a cikin madubin, nan fa hankalinta ya ƙara tashi ganin har dare yayi❗
_______☠️👹☠️BLACK NIGHT💀👹☠️_______
Ƙarfe Goma daidai agogon Gidan kurkukun ƙaddara ta buga, adai dai wannan Lokacin, Dubban shahararrun matsafa suka fara tururuwar fitowa daga masaukin su na gidan kurkukun ƙaddara, adaren ranar duk wata halitta dake bacci a cikin dajin Evil forest da kurkukun saida ta farka saboda sautin bugun ganguna da busar sarewa daya karaɗe ko'ina tamkar za'a fasa ginin saboda Yadda kiɗan ke tashi..
takaitaccen tarihin Daren Black Night, shidai wannan dare, ya samo asaline aranar da Elder Ya Ƙaddamar da gidan kurkukun ƙaddara, Dare ne mai daraja a gurin su, suna alfahari dashi, kuma suna ɗokinshi saboda dare ne na sharholiya, kowa zaiyi bushasha suci karensu babu babbaka sannan a daren suna ƙara ƙarfin tsafinsu, agurinsu kenan, amma agurin Prisoners Daren black night kamar guguwar annobace saboda tashin hankalin da suke fuskanta adaren, kada na cika ku da surutu bari mu leƙa muga meke wakana adaren Black Night❗❓
Ɗaya bayan ɗaya matsafan ke fitowa daga masaukinsu, Wasu a hawa na ukun bene, wasu suna a hawa na biyu yayin da wasu suke a hawa na farko, kowani matsafi Ya ƙure kuri adakansa, ƙarshen wanka na kece raini, matsafan ma jinsi jinsi ne.
Tawagar matsafan yankin Asia ne a hawa na farko, sunyi anko shigar su kamar irinta kayan gargajiya launin jajaye na ƙasar China, ga wani dogon gemu har kan tulun tumbinsu, uban goshin su kamar jirgi ya yi asubanci, ga wani uban sanƙo dake gare su, idanuwan nan nasu mitsi mitsi kamar na kifaye.
A hawa na biyu kuwa tawagar Matsafan India ne, Sun buga adon su kamar malaman majami'u, wasu irin mutane ne masu ƙaton tumbi da manyan mazaunai burguza burguza ga wani uban rantali akawunan su, Munanan gaske, duk sun yi fentin ja da baƙi a jikin su, kwata kwata babu sutura a jikin su, zir suke haihuwar uwar su sai jan fentin da suka shafe jikinsu da shi, ga mutum mai ƙyanƙyami in ya kallesu sau ɗaya bazai sake marmarin kallon su ba.
Tawagar matsafan kurkukun ƙaddara, Su kuma nasu wankan wasu dogayen rigunane a jikinsu baƙaƙe har ƙasa suke ja, sun lullu6e kawunansu da hulunan rigunansu, sun rufe fuskokinsu da mask mai suffar ƙwarangwal.
Tawagar matsafan yankin Europe da America suma ba'a barsu baya ba, suma sunyi ankon su na kece raini.
Gaba ɗayansu sun hallara a tsakar kurkukun, ƙwansu da ƙwarƙwatar su ko'ina ka kalla sune birjik.
Babu masaka tsinke, saboda shagalin yau, ko'ina na kurkukun saƙo da lungu wasu irin dakarun Giants ne majiya ƙarfi ke sintiri sai mazurai suke, Jira suke kawai suga badaidai ba su aiwatar da aikin su.
Ko sauro bai isa Ya ratsa kurkukun ba batare da sun gan shi ba, hatta dakin maduban tsafinsu makil yake da giants sun kasa sun tsare suna kallon komai dake wakana a kowace kusurwa ta kurkukun da dajin Evil forest don tabbatar da tsaro, duk da basu sama ransu wani zai kawo masu farmaki ba, saboda ba'a ta6a gigin yi masu kutse ba, shiyasa suka daɗe suna sheƙe ayar su.
Surutunsu Ya karaɗe ko'ina, da wani irin Yare mara daɗin Ji suke magana cikin harshen su na matsafa, sai raha suke suna hira cikin nishaɗi.
Daga kan ground floor ɗin gurin wani haɗaɗɗen red carpet ne aka shimfiɗa tun daga fadar mai girma Elder har zuwa ƙarshen bango inda aka ƙawata wurin kamar karagar sarakuna, ga wasu jigunannun Armchairs guda shida an ƙawatasu da kayan ado.
Daga can gefe ɗaya a tsakiyar Ground floor din wani zungureran Table ne ɗauke da tsadaddun kayan shaye-shaye masu haɗarin gaske ga tulunan Jini da aka girke kan table ɗin, ga farfesun nama cike da farantai nau'ika daban daban irinsu, farfesun naman ɗawisu, na naman shanu kai hada farfesun yan cikin mutun, soye soye kala kala da kayan maƙwalashe.
Yayin da makaɗan suke ta yan kiɗe-kiɗe da raye rayen su, wasu gungun yan rawa manyan mata masu dirin jiki suka fara fitowa Kwata kwata babu sutura a jikinsu zir suke haihuwar uwarsu, wata irin rawar qugu sukeyi mai jan hankali, nan fa matsafan suka fara washe haƙora suna kallon su..
Gaba ɗaya sun ƙagara a fara shagalin, fitowar Elders kaɗai suke Jira..
Idan muka koma cikin fadar Elders kuwa, tattaunawa su ke yi a tsakanin su, Elder yana a zaune kan kujerar mulkinsa yayin da sauran Elders din suka kewaye shi suna a zaune kan carpet din fadar, Gaba ɗayansu sunyi shiga ta alfarma irin ta mai girma Elder, sun rufe ko'ina na jikin su baka iya ganin koda akaifar su ce, su shida ne cuf ba ƙari.
Cike da nishadi Ya soma magana Yana dubansu, "Me ya rage mana"? Ya faɗa yana bin su da kallo..
"Babu komai Elder, Mun riga da mun toshe kowace Hanya da za'a Iya kawo mana farmaki, dama duk burga ce, wane yaro! rijiya ay ba wurin gaɗar makaho bace, ƙananun kwarine su, in banda ma hauka ina su ina ja da mu? sunyi tunanin sauƙi ne Ja da mu, ko Dajin Evil forest basu isa su ƙetare ba, mune masu ƙarfin iko, da izinin mu komai ke wakana, in muka so Da kalma ɗaya zamu shafe babinsu mu mayar da su tur6aya!"
Gaba ɗaya suka tuntsire da dariyar shaƙiyanci, bayan sun tsagaita da yin dariyar Elder Ya dubi wanda yayi maganar Jan Le6e, "Na ji daɗin bayanin ka.." Ya faɗa tare da maida dubanshi kan Elder din dake zaune gefen Jan Le6e ya ce, "Mutumina Jan wuya, Ko akwai labari? Ko kuwa sai mun sha mun bugu don nasan halinka da miskilanci kafi sakin baki idan ka hau kan network..." Cike da shaƙiyanci ya furta, "Musamman in akwai mata da giya anan linzamina yake kwancewa..." Dariya suka saka gaba ɗaya....
"Baka da matsala mutumina, yau ranarmu ce, saika za6a ka darje," Ƙasaitacciyar dariya jan wuyan ya saki.
"Jan kunne na ji ka yi shiru baka ce komai ba"? Ya faɗa Yana duban shi.
Muskutawa ya yi ya gyara zaman shi, "Elder, Ni bani da abun cewa, Hankalina Ba a kwance Yake ba, ban ta6a tsintar kaina a yanayi na jin faɗuwar gaba irin na yau ba..." gaba ɗaya suka maida hankali kan shi.
Da kakkausar Murya wani mai zafin rai a cikinsu wanda suke kira jan harshe Ya ce, "Wannan wani irin zancen banza ne? Ka kuwa san me hakan Yake nufi? Faɗuwar Gaban Elder yana nufin mummunar ƙaddara zata Iya afka mana, tun wuri Ka dakatar da zuciyarka, ba'asan Elder da raunin zuciya ba..."
Yana ƙare maganar Jan Wuya Ya ce, "Ka gafarce ni, kaima kayi kuskure a maganarka Jan harshe, Elders sunfi ƙarfin mummunar ƙaddara, ita kanta ƙaddarar tsoron mu take ji, shiyasa bata ta6a gigin afka mana ba..." Da gadara suke magana.
(Duniya budurwar wawa, Wanda Ya 6ace Ya 6ace.....)
"Jan wuya, kai ɗin na dabanne, namijin duniya, wanda bai ta6a karaya ba, ina son ƙwarin gwiwarka mutumina..." Ya faɗa tare da yi masa alamar jinjina da babban yatsansa, kafin Ya dubi Jan Kunne "Kai kuma, kada na kuskura na ƙara jin ka ambaci faɗuwar gaba, nasan me ke damunka, da zarar kaga mata masu manyan mazaunai zaka wartsake..." Dariya suka saka gaba ɗayan su.
Kafin wani ya ƙara furta kalma a cikinsu, Evil Giants masu ƙirar samudawa har su Goma suka kewaye kofar shiga Fadar...ɗaya cikinsu mai wata irin ƙatuwar murya ne Ya ce, "Elders baƙi sun hallara, lokacin shagali ya yi, zamu iya tafiya..." jinjina kai Elder yayi tare da miƙewa suma sauran Elders din suka Miƙe cikin takun dattako suke tafiya akan jan carpet din da aka shimfiɗa masu, hannuwan su ruƙe da sandunan su na alfarma.
Lokacin da suka 6ullo ta ground floor ɗin makaɗan dake kiɗa suka ƙara kaimi gurin buga gangunan kamar zasu fasa su, ga wata daddaɗar busar sarewa dake tashi, wani irin kirari suka fara yi masu suna kurantasu da hura masu kai har wani rausayawa suke yi alamar kirarin yana kai masu karo.
Gaba ɗaya Hankulan matsafan Ya dawo kan Elders, Taurari masu haskaka duniyar matsafa, kowa burinsa ya ga Elders, musamman sababbin matsafan da basu jima da shiga harkar ba, saboda wani irin farin jini ne da su, sun shahara a fadin duniya.
Cikin girmamawa matsafan suke miƙo gaisuwa kamar zasu durƙusa masu saboda biyayya....bayan Sun ƙarasa gurin da aka ƙawata masu, kowan nan su ya zauna kan armchairs ɗin da aka tanadar masu.
Ɗaga hannu Elder ya yi cikin sauri masu buga gangar da masu raye rayen suka dakata ...
Duk faɗin girman gurin idan ya yi magana sai kowa Yaji shi kuma a hankali yake yin ta cikin nutsuwa.
"Ina yi ma kowa barka da zuwa, haƙiƙa bazan Iya misalta farin cikin da nake a ciki ba na ganin kowannanku, abun alfahari ne a gareni, ace waɗannan dubban mutanan saboda ni suka baro muhallinsu suka zo don su taya ni murnar zagayowar ranar dana Kafa GIDAN KURKUKUN ƘADDARA....."
Ya ɗan dakata Yana bin matsafan da kallo tun daga kan hawa na Uku har izuwa na farko, sun kasa kunne suna sauraron shi..
"A daren yau, muna taya juna murnar nasarorin da muka samu, bamu ta6a faɗuwa ba, dukkan abunda muka sa gaba sai mun cimma shi, ina fata abokan harkar mu zaku tayamu murna." Sowa suka sanya da ƙarfi suke amsa mashi da, "Yeho! Yeho!! yehoo!!
Gyaɗa kai ya yi kafin ya ɗaura da cewa, "Kamar yadda kuka zo domin mu kuka faranta mana, muma zamu faranta maku, wannan yasa muka tanadar maku shirye shiryen da muka saba yi A kowane black night..."
Bayan Elder Ya gama kora jawabin shi, Jan Harshe Ya ɗaura da nashi...
"Gasar da zamu gabatar, faɗan gwada karfin iko ne, team da suka zo na ɗaya suka yi nasarar lashe gasar, zamu basu santala santalan yan mata har guda goma sha biyar, waɗanda suke tsaka da Yin jinin al'adarsu, don su biya buƙatarsu da su, bayan haka zamu basu matasan maza goma sha biyar suma su biya buƙatarsu da su..." Wani irin ihu matsafan suka sanya har sun fara saƙa buri akan suyi nasara saboda tsananin kwaɗayin mace mai jinin al'ada su ke yi..
Dakatawa yayi da yin bayanin, kafin ya ɗaura da cewa, "Tawagar da ta zo a mataki na biyu, mun tanadar masu jarirai goma sha biyar, tare da Tulunan jinin al'ada da muka tsuma, bayan haka zamu basu mata masu ɗauke da juna biyu su yi amfani da su sannan su sha jinin abunda ke acikin su..."
Tunkan Ya ƙare maganar matsafan suka sake sheƙewa da shewar Murna.
"Tawagar matsafan da suka zo na uku, mun tanadar masu sabbin gawawwakin da muka tsuma, sannan zamu basu sassan jikin fursinonin mu." Wani irin ihun farin Ciki matsafan suka saki, su fa yau shar kakarsu ta yanke saƙa...
"Saura waɗanda basu yi nasara ba, suma ba zamu barsu hakanan ba, kamar yadda muka yi alkawari zamu faranta ma kowan nan Ku...."
Yana ƙare maganar Ya ɗaga hannu nan take masu buga gangunan suka ci gaba da gashi.
________________________________________✍️
Shigowa ta yi cikin katafaren Hall din da suka tara za6a66un prisoners da suka tanada saboda faranta ma baƙin nasu.
Hall ne mai faɗi da tsawon gaske ta cikin shi akwai ƙofofin ɗakunan dake a jere jikin bangonshi, Yana da dogayen benaye, a wani sashe na hall ɗin akwai wasu tsoffin rijiyoyi da suke a garƙame da murafen ƙarafuna, ga wasu kaskwayen wuta dake ci, hall ɗin ya kasance inda suke bada horon zama Giants zanunnukan dake a jikin bangon hall ɗin kadai ya isa ya razanar da mutun..Anan suke killace duk wani abu da suka tanada saboda baƙin su.
Tana ƙarasa shiga ta iske female giants ɗin dake shiryasu su ukku cikin kakinsu.
Sun tu6e masu uniform dinsu, saboda basu buƙatar su shiga da su gurin taron da sutura, jikinsu sai kerma da kakarwa yake yi, daga ka kalli idanunsu zaka ga tsantsar tashin hankali, a ƙalla prisoners ɗin sun kai su arba'in da wani abu.
Female giants din na ganinta suka russina tare da gaishe da ita, ko kallo ba su ishe ta ba..
Zama tayi kan kujerar dake fuskantar su tana ƙare masu kallo, bayan ɗan lokaci ta kai hannu ta kware ƙasan rigar ta, tsamurarrun cinyoyinta ne suka bayyana,wani ƙyalle dake naɗe da ɗaya daga cikin cinyoyin nata ta fara warwarewa, Ya ilahi! wani irin uban wari ne ya buso yadda kasan gunyar ƙwai ta fashe lokacin data ƙarasa kwance wurin, wani irin ciwo ne ya mamaye wurin har wurin can ƙasanta kamar dai gyambo, da ƙyar in baza'a rasa yan ƙananun tsutsotsi a wurin ba, gyara wurin ta shiga ƙoƙarin yi,
Hankulan Prisoners din ba ƙaramin tashi ya yi ba, yunƙurin amai suka soma yi sakamakon ɗoyin ciwon da ya bugi hancinan su, aikuwa da kakkausar murya tace, "Duk ɗan iskan da ya kuskura ya yi amai a gurin nan sai na sa ya lashe shi da harshen shi...!"
Waro idanu waje suka yi da sauri suka toshe bakunan su da tafukan hannayen su...
Tsautsayi ne Ya ritsa da wasu ƴan biyu maza dogaye sirara da su, irin masu ƙyanƙyamin nanne, duk yadda suka so su hana aman fitowa daga bakinsu saida ya kubce masu aikuwa suka fara amayar da abunda ke cikin su.
Murmushin mugunta tsohuwa Inno ta saki, "Ku ko wani tsautsayin ne Yaja maku yin amai?" Hankali a tashe suka fara yi mata magiya akan tayi haƙuri, Tsawa ta daka masu tuni suka sha jinin jikin su, da yatsa ta nuna masu wurin, "Ku zo ku sha daɗi.." Fashewa suka yi da kuka suna kallon sauran yan uwan su, wani irin tausayin sune Ya kamasu.
"Kada kubari in maimaita abunda nace!!" Ba yadda suka Iya, sun riga da sun san bala'en da zai biyo baya idan suka bijire mata..
Cike da jin shakkarta suka nufe ta, zuciyoyin su na tashi haiƙam suka durkusa kan gwiwowin su agabanta, Idanun su na kallon tashin hankali!
Da yatsa ta nuna na tsakiyarsu, "Kai zaka fara, Kafin na buɗe idanuna kayi hanzarin kafa bakinka..." Tana faɗa ta kulle idanunta.
Yawu Ya haɗiya, cike da kyankyami yake kallon wurin ga azababben warin yafi yawa da suka matso gab da ita gaba ɗaya ya kanainaye hancinsu..
Tsohuwa Inno har wani murmushin mugunta take saki jin hucin Numfashin su a jikinta.
Kwatsam! ba zato ba tsammani, kamar daga sama taji an buga mata wani abu mai azabar zafi a wurin, bugun har agaban ta.
Wata irin zabura ta yi ta miƙe tsaye, cikin ruɗu ta zare tsoffin idanunta akan Giant din dake tsaye a gabanta, hannun shi ruƙe da Ƙatuwar guduma ta ƙarfe.. tuni Jini Ya 6alle mata kamar pipe din ruwa ya fashe...
A tsananin ruɗe take kallon shi kafin ta dubi yan ukun dake tsaye bayan shi..da sauri ta dubi female giants din dake a wurin, wata irin razana ta yi ganin gawarwakinsu baje a ƙasa, Cike da al'ajabi ta furta, "Kai! wanene kai??"
*"GARKUWAR FURSINONI"*
Ya faɗa tare da sanya hannu ya zare Mask ɗin fuskar shi, Tsabar mamaki da al'ajabi hadi da razana ya hana ta furta kalma, kusan suman tsaye tayi ganin Garkuwar Kurkuku, Zance ya 6aci! daƙyar ta haɗiye al'ajabinta, Muryarta na rawa ta furta, "Garkuwarmu! Kai nake gani dagaske ba mafarki nake ba?tayaya ka shigo kurkukun nan eye? Ka dawo gurinmu ne? Ni dama nasan bazaka Iya rayuwa batare damu ba...." Sai sambatu take yi mashi kamar wata zararra, abu biyu ya haɗe mata ga azabar zafin da gabanta keyi mata.
Wani ƙasƙantaccen Kallo Ya wurga mata mai tattare da ƙyama, cike da ƙwarin gwiwa ya furta, "Na dawo, amma ba a matsayin Garkuwarku ba, a matsayin garkuwar fursinoni." jikinta na kerma kamar mazari kafin ta furta wani abu ta jiyo sautin takalmansu ɗaya bayan ɗaya suke shigowa cikin Hall ɗin, ba zaka ta6a gane ba giants din kurkuku bane saboda kayan jikinsu sak irin Na giants ne.
Ɗaya bayan ɗaya suka soma cire mask din fuskarsu, waro idanu waje tsohuwa Inno tayi Ganin baƙin Fuskoki a gidan Kurkukun Ƙaddara.
Kallo ɗaya Chief Owais ya yi ma Prisoners din dake a gurin ya yi saurin kawar da idanun shi, Haka shima Big guy kasa jurewa yayi ganin babu sutura a jikin su, Taj da zuciyarshi ta gama karaya da tausayinsu ji yayi kamar ya fashe da kuka, a ranshi ya ayyana wai anan yarsa Angel tayi rayuwa har na tsawon shekaru, Ya salam!!!.
Salsabeel kuwa tun shigowarshi idanun shi na akan Inno wani irin kallo mai cike da tsana yake jefa mata....
"Su wanene ku!.." bata ƙare maganar ba, sakamakon wani zazzafan Mari da Chief Owais Ya kwasa mata har saida wuyanta ya nemi jirkicewa, Kafin ta ɗago Ya daddage ya sakar mata mahangulba kan mummuƙenta...gaba ɗaya ta kife ƙasa a susuce ta furta,"kai, kai, kai, kai....."
Prisoners din dake a gurin gaba ɗaya sun ruɗe sun rasa gane su wanene wadannan baƙuwar fuskar? shin sun zo ne da niyyar taimakonsu? ko kuwa suma mugaye ne..?
"Kai ku maida Kayan ku" Big guy ne ya faɗa ba tare da ya kai idonshi kan su ba, jikinsu na kerma suka ɗauki uniforms dinsu dake yashe kasa suka shiga zirasu a jikin su.
Ƙululun baƙin ciki ne Ya tokare makoshin tsohuwa inno, tun da take wani ɗan adam bai ta6a gigin ta6ata ba da sunan bugu sai yau da Allah Ya haɗata da Chief, yunƙurawa tayi ta miƙe tana layi ta soma rarraba idanunta akan Salsabeel da Danish.
Tana huci ta ce, "Maciya amana! saina tona maku asiri gurin Elders"
Ta faɗa tana kokarin Yin sihiri don ta 6ace sai dai wani iko na Allah kamar an ɗauke mata sihirinta, A ruɗe take kallon hannayenta ganin sun ƙi tasiri.
"Kina mamaki ne?" Danish ne ya faɗa tare da ɗaga mata gira, takaici ya ishe ta..
"Wai dama haka matsafan suke, munana, gasu ƙazamai, gwanin ban ƙyama." Fuska a yamutse Big Guy ya faɗa tare da watsa mata yawu kan fuskarta ya ce, "Daƙiƙiya, dama karfin naki na sihiri ne, yanzu da babu shi taya zaki faɗa ma Elders dangane da zuwan mu? Bayan mun riga da mun mamaye gidan kurkukun da dakarun sojojinmu, munyi basaja mun saje da Giants ɗinku, Yanzu haka ɗaya bayan daya sojojinmu suke bi suna yi masu kisan mummuke batare da sanin ku ba."
Dafe kai tsohuwa inno tayi da hannayenta ta fara jijjiga jikinta tana kokarin ta rikiɗa nan ma dai abun ya ci tura.
Batai aune ba Sai dai taji safkar wuƙa a makoshinta, Big guy ne ya farke ta har saida ya dire ƙasa, Jini ya dinga tartsatsi kamar pipe din ruwa ya fashe, gaba ɗaya gangar jikinta ta zube ƙasa tana bullayi ta dinga sakin wata irin kururuwar azaba har rai ya yi halin sa....
"Har yanzu nagaza yarda da abunda idanuna suke nuna min! Ina jin abun kamar a mafarki ashe dagaske komai ke faruwa!" cikin jin ƙunar rai Chief Ya faɗa kafin Ya dubi Sojojin dake a bayansu ya ce, "Ku tafi da yaran!" Cike da bada Umarni Chief Ya faɗa.
Kuka suka fara Yi masu jikinsu sai kakarwa yake yi, sun yi zaton cutar da su zasu yi, fahimtar hakan yasa Taj yi masu bayani ya ce sun zo ne don su taimakesu su ba masu cutarwa bane.
Waro idanu waje suka yi, wlh alƙalamina bazai Iya mistalta irin yadda suka yi mamaki da al'ajabin jin za'a taimaki rayuwarsu ba, batare da 6ata lokaci ba, huɗu daga cikin Isod soldiers dinsu suka tafi da yaran..
Duk wannan abun dake faruwa Babu wanda Ya san da zuwan su cikin kurkukun, sai mutun ɗaya wato tsohuwa Khala.
Saboda sautin bugun gangunan da makaɗa suke yi Ya hana Matsafan su jiyo sautin abun da ke faruwa..
Ajiyar zuciya suka sauke batare da jin fargaba ba, suka fito daga Hall din cikin tafiyar sanɗa suka nufi wata doguwar hanya mai kwana-kwana..
Duk Giant din da ya ankara dasu kafin yayi wani yunƙuri tuni suke fille kanshi da adda, Kisan Gilla su ke yi masu...
(SHIN TAYAYA AKAI SUKA SHIGO GIDAN KURKUKUN ƘADDARA?)
Bata nufi ko'ina ba sai hall ɗin da madubban tsafinsu suke, tana shiga ta iske giants din dake kan duty, tasan muddin Su garkuwa suka ƙaraso sune na farko da zasu fara kawo masu cikas saboda suna kallon komai dake wakana a cikin kurkukun ƙaddara da kuma dajin evil forest, gyaran murya tayi masu, cikin girmamawa suka gaishe da ita, tace meya hanasu shiga filin taro? Bayan yau rana ce mai mahimmanci da buƙatar kowa dake a kurkukun ya halacci wurin shagalin, Giants din su ka bata amsa da ba'a basu umarnin subar aikin su ba, tsohuwa khala tace a matsayinta na matar Elder tana mai umartarsu da su aje aikinsu, suje suma ayi shagalin da su, ba suyi mata musu ba, saboda sun san wacece ita, kuma Elder ya gargaɗesu akan suyi mata biyayya sau da ƙafa, in har ta buƙaci wani abu kada suyi mata jayayya su dauka kamar shi ne ya basu umarni, tuna wannan yasa Giants din suka bar bakin aikin nasu.
Murmushi Tsohuwa khala tayi, tana ganin fitarsu, ta bi madubban tsafin ɗaya bayan daya ta jefar da su gaba ɗaya suka faffashe.
Fitowa tayi daga hall din tana cikin tafiya cike da fargaba, kwatsam ta hango wasu gungun matsafa a cikin baƙinsu kusan su takwas sun nufo wurin kamar dai suna ƙarewa ginin kallo ne, gyaran murya ta yi masu da sauri suka dubeta, fuskarta da fara'a ta nufe su bayan sun gaisa ta gabatar masu da kanta a matsayin Matar Elder, sai faman washe baki suke yi suna ƙara gaishe da ita tace masu in ba damuwa su biyota zata nuna masu wasu bangarori na kurkukun tasan zasu so su gani.
Basu kawo komai a ransu ba, suka bi bayanta ta nufi wani ɗaki da su, suna shiga ta datse ƙofar a ruɗe suka kalle ta ganin ta rufe ƙofa, kamar sun fara zargin wani abu, sai dai kafin su gano hakan Tsohuwa Khala ta yi hanzarin zare ƙaramar wuƙarta gaba ɗaya ta kashesu, ta zuƙunna ta cire kayan dake a jikinsu dama shine abun da take so..
6acewa tayi, bata dira a ko'ina ba sai a cikin ɗakinta, ta jefar da kayan saman gadonta kafin ta kuma 6acewa ta bayyana a wani ke6a66an guri inda Danish ya faɗa mata ta nan zasu biyo idan suka ƙaraso.
Tana tsaye hannunta ruƙe da sandar ta, zuciyarta cike fal da zullumi, Allah Allah take su ƙaraso kamar ta fashe da kuka saboda bugun barazanar da zuciyarta ke yi mata, ta aikata 6arna ba kaɗan ba, har ta fidda rai da zuwansu zuciyarta ta fara raya mata ta kashe kanta kawai tun kafin Elders su ankara da 6arnar da tayi masu.
A lokacin da bata yi tsammani ba, ta fara jin motsi ta saman ceilling din da take, A hanzarce ta kalli silin din ta sauke idanunta kan wasu tsofaffin tagogine dake a kulle jikin shi.
Cike da sa rai take kallonsu, Unexpectedly taga Murfin windows din na motsi wlh tsabar farin ciki bata san sa'adda takai goshinta ƙasa tay sujjada domin nuna godiyarta ga Allah, tunkafin ma ta tabbatar in su ɗinne, Kafin ta ɗago daga sujjadar kunnuwanta suka jiyo mata ƙarar 6allewar murfunan tagogin, a zabure ta miƙe tana kallon kafafuwansu, ɗaya bayan ɗaya suka fara dirowa ƙasa, kamar ana jeho su.
Dariyar farin ciki ta saki duk da mask din dake akan fuskar Danish hakan bai hana ta gane shi ba, shima yana ganinta ya nufeta gaba ɗaya ta rungumeshi kamar zata maida shi cikinta, kai ƙarshe ma sai ta fashe mashi da kuka, cikin shesshekar murya ta ce,"Alhamdulillah, nagode ma Allah da ya nuna min wannan ranar da raina, har na fidda rai da zuwanku.."
Ta faɗa tare da raba jikinta daga na Danish ta dubi sauran sojojin dake atsaitsaye ga wasu dake ta durowa ƙasa.
"Khala" Salsabeel ne ya ambaci sunanta, bata gane shi ba saboda mask din da ya rufe fuskarshi, cikin sauri ya matsa kusa da ita, ta rungumeshi nan ma ta kuma fashewa da wani kukan farin ciki, Allah abun godiya..
Bayan ta raba jikinta daga na Salsabeel, Danish ya gabatar mata da Chief Owais, wanda tun da ya duro hankalinsa ke akan ginin yana mai jinjina girmansa, amma lokacin da kunnuwansa suka jiyo mashi muryar Khala da ruɗu ya tsayar da idanunsa akanta, kamar yadda take kallon shi haka shima yake kallonta, muryarta na rawa ta furta, "Owais, kaine ka girma haka?" Tayi zaton a cikin zuciya ta yi maganar, gaba ɗaya sojojin sun ɗan ruɗe da jin yadda tayi maganar kamar tasan shi, shi kanshi Chief din ya ruɗe da jin muryarta kamar yasanta, sai dai ya kasa gane wacece saboda ta rufe fuskarta da tukunkumi.
Idanunta kaɗai suke iya gani...
Bai aune ba, yaji ta cakume shi da hannayenta biyu ta rungume shi sosai fiye da yadda ta rungume su Salsabeel...Allah kaɗai yasan me take ji acikin zuciyarta..
Idanunta cike tab da kwalla, ta ɗago tare da kallon su,
"Ku kaɗai ne"? Ta faɗa ganin kamar sun gama shigowa kuma duka basu fi su hamsin ba,
Salsabeel ya ce, "Ba mu kaɗai bane, akwai sauran sojoji sama da ɗari biyar, suna akan hanyar shigowa." Ajiyar zuciya ta sauke, still idanunta akan Chief Owais, duk yasha jinin jikinshi da ganin irin kallon da tsohuwar take yi mashi,
"Ina yi maku barka da zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara, a yanzu haka sun fara gudanar da shagalin Black Night basu san komai dake faruwa ba, saboda na toshe duk wata hanya da zasu iya ganinku ta madubin tsafin su, sannan akwai tanadi da nayi maku, ku biyo ni."
Ta fada tare da juyawa suka bi bayanta, har suka isa ɗakinta basu ci karo da kowa ba.
Bayan sun shiga, Ta umarce Salsabeel da Danish da su fiddo kayan dake a karkashin gadon ta..
Bayan sun fiddo Buhunhunan da akwatinan ta ce, "Makamai ne acikinsu, a gidan kurkukun nan ake ƙera su, na daɗe ina tara su a 6oye saboda burin da nake dashi na ganin na kawo ƙarshen zaluncin su."
Ta ɗan dakata tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa, "Makaman dake a hannunku ba za su yi tasiri akan su ba, amma in har kukayi amfani da makaman nan cikin sauƙi zaku kashe su"
Farin Ciki ne Ya cika su, a hanzarce Salsabeel da Danish suka kwance buhunhunan, sun yi mamakin ganin yawan makaman, Wuƙaƙe ne da adduna, harda takubba da kibiyoyi, ga gatari da manyan gudumomi, nan kowan nansu ya ɗauki makamin da ya kwanta masa arai, bayan sun kammala ɗauka, ta ce, "Ku fara kokarin ceto rayukan fursinoni dake a ciki kafin su ankara da shigowarku, Danish da Salsabeel kuyi masu jagora zuwa daƙunan da fursinoni suke." suka amsa mata da toh.
Ta ƙara da cewa, "Duk yaran da kuka taimaka, ku kawosu nan, zan taimaka masu su fita daga kurkukun..."
With respect suka amsa mata da toh.
Akwatinan ƙarfen ta nuna masu, "Kakin giants ne a ciki, na tanadar maku sune saboda kuyi 6adda kama ku saje da su, duk da naga kakin ku sunyi shige da nasu."
Ta kuma nuna masu kayan Matsafan da ta kashe, "Ga wasu kayan nan ma."
Big guy yace, "Ba dukkanmu keda irin kakin ba, akwai sauran tawagar sojojin da zasu ƙaraso, in yaso sai wasu daga cikinsu suyi amfani da kayan." Jinjina kai ta yi, "Hakan yayi, zaku iya tafiya, Ina yi maku fatan nasara" Har cikin ran su sunji dadin taimakon da tsohuwar tayi masu, yaune karo na farko da suka fara ganinta amma ta kwanta masu a rai.
(Kunji yadda akai suka ƙaraso Cikin gidan kurkukun ƙaddara)
Suna cikin tafiya suka ci karo da wani bene mai kanannaɗa, Kwata kwata babu fargaba a tare da su, suka hau benen ya 6ula da su cikin wata hanya mai tarin kofofi, har zasu gifta ta wani ɗakin kwatsam wani gabjejen Giant ya fito sanye da lab coat fara a jikin shi gaba ɗaya suka sha jinin jikin su..
Da farko da ya kallesu yaso ya ruɗe amma sai ya ji a jikin shi ba Giants din su bane.
"Su wanene Ku?" Da wata irin ƙatuwar murya ya yi maganar, Yan hanjin cikinsu ne suka kaɗa aka rasa wanda zaiyi mashi magana acikin su..
kamar yaso ya ɗago su amma sai yayi azan daga cikin baƙinsu ne da suka zo.
Ƙarfin Hali Chief ya yi wurin furta, "Daga cikin baƙin kune, muna ƙarewa ginin kallo ne" Maraba ya yi masu tare da nuna masu ƙofar dakin da ya fito ya ce, "Ɗakin fiɗa ne, zamu iya shiga ciki idan kuna neman ƙarin bayani dangane da yadda muke gudanar da aikin mu."
Ya faɗa tare da buɗe kofar dakin ya shiga suka bi bayanshi, sun yi matuƙar girgiza da ganin fursinonin dake a kwance kan gadajen ɗakin, Hada mata masu ciki, jikinsu sanye da fararen kaya, Ga wasu gungun Gigantes medici dake tsaka da yin aikin fiɗa a gaban gadon fursunan da suka farke cikin shi, har sannu da aiki suka yi masu, giant doctor din da ya shigo dasu ya gabatar dasu ga sauran yan uwansa likitoci kafin yace masu su ƙarasa ciki, Ya nufi gaban wasu manya-manyan furizozi Ya bubbuɗe su, sun razana sosai da ganin sassan jikin mutanan da suka feɗe masu yawan gaske..
Hankulansu sun tashi matuƙa sai dai basu yi gangancin da zai sa a gano su ba, bayani ya fara kora masu game da yadda suke feɗe mutun su cire sassan jikin shi da yadda suke amfani da shi har safarar sassan suke yi zuwa wasu ƙasashen su siyar da su.
Chief da Big Guy sun harzuƙa matuƙa, jikinsu sai tsuma yake yi saboda tsabar fusata kamar su rufe shege da bugu.
Kwatsam yana tsaka da kora masu bayani Taj ya yi su6ul da baka gurin furta, "Amma dai baku da imani" kaitsaye maganarshi da dira cikin kunnan Giant doctor din.
Nan take ya dakata da kora masu bayanin da tsantsar ruɗani Ya furta,"Who are you?" Shiru suka yi, hakan ya ƙara ƙarfafa zarginsa akan su.
Wata irin gigitacciyar tsawa ya daka masu tamkar zai fasa dodon kunnansu da karfi ya ce,"baku ji ina tambayarku bane? Su wanene ku huh?" Maganar da yake yi ce ta janyo hankulan sauran Giant doctors
din dake aikin fiɗa, suka ajiye tiyatar da suke yi gaba ɗaya suka zagayesu kamar zasu rufe su da bugu, safunan hannayensu jaga jaga da jini..
Jin sunyi shiru sun ƙi basu amsa ne yasa ɗaya daga cikinsu ya kai hannu zai cire Mask din dake akan fuskar Chief, bai kaiga ƙarasa cirewa ba, Danish Ya zaro addarsa azafafe Ya datse hannunsa ya 6alle biyu jini ya dinga tartsatsi, koda ganin hakan sauran giants ɗin suka harzuƙa matuƙa, suka afka masu faɗa ya kaure atsakanin su, sun ci wahala kafin suka yi nasarar kashe su gaba daya suka zubar da gawarwakinsu akan floor.
Sai haki suke suna nishi, Big guy ya dubi Taj da ya dafe cikin shi, "Next time kada ka ƙara maimaita kuskuren da ka yi, yanzu da ka ja mun rasa rayukanmu." daƙuwa Taj ya yi masa batare da ya furta kalma ba.
Fursinonin dake a kwance kan gadajen suna ganin abunda ke faruwa saidai sun kasa tashi zaune saboda alluran da suka banka masu sun kashe kuzarinsu, kwayar idanunsu ce kadai ke motsi..
"Ya zamuyi dasu"? Big guy ne ya tambaya.
Salsabeel Ya dubi Danish, "ka yi wani abu pls" duk suka maida hankali kanshi, shi kadai yasan me ya yi masu sai gasu sun miƙe kan ƙafafunsu.
Basu tsaya 6ata lokaci ba, wasu daga cikinsu suka tafi da fursinonin...
Fitowa sukayi daga ɗakin fiɗar, Suka faɗa dakin dake akusa dashi, nan fa suka ga abun da ya ƙara ɗaga hankulansu, jarirai suka gani a cikin containers, kamar bakwaini gwanin ban tausayi...Taj har ƙwalla saida ya zubda masu, Big guy ya ce, "ya zamu yi da su?"
"Dan Allah mu taimaka masu, kada mu barsu anan" Taj ne ya faɗa.
Salsabeel ya bashi amsa da, "Bazai yiwu ba, don ta yanzu, mu barsu kawai Allah yana atare da su."
Fucewa suka yi daga ɗakin suka shiga ɗakin dake a gaba, rasss! gabansu ya hau faɗuwa ganin ɗarurrukan kwarangwal na mutane sagale jikin igiyoyi ga wasu nan zube a ƙasa har jikin bangon ɗakin ko'ina su ne na mutanan da suka kashe, wa'iyazubilla zuciyoyin su sun karaya ba kadan ba. Wata shari'ar dai sai A lahira wallahi.
Kusan zagaye kurkukun suka yi saƙo da lungu suka dinga shiga, sune har cikin treatment rooms din kurkukun, anan suka ga majinyatan fursinonin da suka kwantar, sun ci baƙar azaba a hannun masu jinyar su wurin yin faɗa dasu, da ƙyar suka kashe su kafin suka ceci majinyatan suma.
Saida suka gama kwashe fursinonin, kafin suka dawo baya, har sun kusa 6ula ground floor din da ake shagalin Chief Ya dakata da yin tafiya, kallon shi su ka yi, duk da basu san me ya hana shi cigaba da yin tafiyar ba, sun fahimci kamar Yana jin fargaban yaga wani dangin shi a cikin matsafan, dama da zargin mahaifinsa aransa ga kuma abun da ya faru tsakaninshi da tsohuwa Khala na furucin da ta yi akanshi.
Idan muka koma bangaren Elders, sun shagala suna kallon karawar da matsafan su ke yi a tsakar fili, kowani matsafi ya zage damtse gurin nuna ƙarfin sihirin shi, dambe ne na fitar shari'a suke yi kamar zasu kashe juna, idan bala'e yayi bala'i har rikiɗa suke yi su koma dodanni su cigaba da dambatawa a tsakanin su.
Saida aka zo zagaye na ƙarshe a wasan, Elders suka ji shiru ba'a zo da prisoners ba babu su babu alamar su...
Da yatsa Elder Ya yi ma ɗaya daga cikin Evil giant din dake bayan shi alamar Ya matso kusa, sunkuyar da kanshi yayi saitin fuskar Elder...
Cike da bada Umarni Ya ce, "Ka yi ma Giantesses magana, suzo da yaran da sauran kayan da aka tanada Yanzun nan...!" da buɗaɗɗiyar murya Giant din Ya amsa mashi da angama sir, daga Inda Yake bai matsa ba ya 6ace ma ganin shi.
Bai dira a ko'ina ba sai a hall din da suka tara prisoners, Nan Ya ga abunda Ya tada hankalinsa, gawarwarkin da ya gani baje ƙasa na female giants dinsu, Ga Gawar tsohuwa Inno...aruɗe da yana yi na mamaki Evil Giant din Yake bin ɗakin da kallo kamar a mafarki, Fitowa yayi daga Hall din saboda dakakkiyar zuciya irin nasu, neman waɗanda suka kawo masu hari ya shiga yi, don Ya aika su lahira.
Yana Cikin tafiya suka bangaji juna shi da wani giant, tun daga yanayin yadda yayi tangal tangal zai faɗi Evil giant din Ya gane ba nasu bane saboda giant basa bangazar juna.
Da kakkausar murya ya furta"Wanene kai?" Rasss ya ji gabanshi ya faɗi, yan hanjin cikin shi suka kaɗa, baima san ubanda ya janyo shi wurin ba shi kaɗai batare da kowa ba gashi sam ya kasa yin wani yunkuri don ya ce ci kan shi, ware faffaɗan tafukansa evil giants ɗin ya yi da niyar Ya tarwatsa ƙoƙan kanshi sai dai kafin ya yi hakan baiyi aune ba Yaji dirar Zarto saman kan shi, kwatsa kwatsa Ya faffasa kan nashi Kafin Ya ƙwalƙwalo idanunshi yabar gangar jikin shi yashe a ƙasa, ajiyar zuciya Taj ya sauke wlh har ya fidda rai da rayuwa badan Allah Ya hankaɗo Danish ba da tuni evil giant ɗinnan Ya aikasa Barzahu.
Duk da bawani sabawa suka yi da juna ba saida yaji kaunarsa ta shiga ranshi, cikin sanyin murya ya furta, "Thanks" Jinjina mashi kai ya yi tare da nuna mashi hanya, "Zamu iya tafiya." Bin bayanshi Taj yayi suka nufi sauran jami'ansu da sukai Basaja..
Jin shiru Evil giant din da suka aika bai dawo bane yasa Elder Sake tura wani, a karo na biyu yaji shiru bai dawo ba, wasa wasa har giant biyar suka aika basu dawo ba, lamarin ya ɗaure masu kai, Miƙewa elder ya yi Jan Wuya ya ce, "Ina zaka je?"
"Ina so naje na duba Hall din, tayaya zamu aika mutun biyar shiru basu dawo ba, kada a yi abin kunya!"
Girgiza kai Jan Wuya ya yi, "Ba kai yakamata ka je ba, bari na je na duba.." ya faɗa tare da miƙewa cikin takun ƙasaita ya fuce daga filin taron, bayan tafiyarshi, Elders suka Ji shiru shima bai dawo ba, hakan yasa Jan Harshe ya miƙe Ya tafi neman shi, shiru shima bai dawo ba, har saida ta kaiga gaba ɗaya Elders sun bar filin shagalin, Fitarsu keda wuya kwatsam! ba zato ba tsammani wata irin kururuwar Fashewar bamabamai ta karaɗe gidan kurkukun, Gaba ɗaya taron matsafan da ke a gurin shagalin babu wanda Ya tsira da ranshi, saboda mamayarsu aka yi sihirinsu bai amfane su da komai ba, Haka wuta ta dinga balbali tana Cin naman jikinsu, suka runƙa sakin wata irin kururuwar radadin azaba mai amon gaske.
Har Cikin Kunnan Elders yayin da suka je hall din don su ga meya hana giants din da ake aika dawowa.
Kowa ya shiga ciki wani irin burki yake ci sakamakon abun al'ajabin da idanunshi ya gani, a haka har suka haɗu su duka, Cak duk suka yi sun kasa yin wani ƙwaƙƙwaran motsi, da wani irin matsanancin mamaki da al'ajabi gami da ruɗanin tashin hankali suke duban junansu....ganin abunda basu ta6a zaton ga ni ba, ga kuma sautin da kunnuwansu suka jiyo masu. Wannan shi ake kira bazata!!!
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: _______________________________✍️🔥💋💔🫀🌹☠️❓😈👹💞💘
Kowa ya shiga ciki wani irin burki yake ci sakamakon abun al'ajabin da idanunshi ya gani, a haka har suka haɗu su duka, Cak duk suka yi sun kasa yin wani ƙwaƙƙwaran motsi, da wani irin matsanancin mamaki da al'ajabi gami da ruɗanin tashin hankali suke duban junansu....ganin abunda basu ta6a zaton ga ni ba, ga kuma sautin da kunnuwansu suka jiyo masu. Wannan shi ake kira bazata!!!
Sun sha ruwan mamaki! Elder da ya gama ruɗewa ya ce, "Ni kaɗai nake ganin abun da idanuna ke nuna min? What the hell is happening? Who killed them? Where are our prisoners?" A tsawace ya ƙarashe maganar.
Jan kunne Ya ce, "Abun da ɗaure kai! Anya ba farmaki aka kawo mana ba??"
Jan wuya yana huci ya furta, "This can't be happening, it's not true. Ƙarya ne, I can't believe it! how is this possible?"
"Zance Ya 6aci! Tabbas an kawo mana farmaki! Wasu sun shigo kurkukun nan, Kuma Ni na jiyo ƙara wadda ba tantama ta fashewar Bomb ce." Cike da tabbaci Jan le6e ya yi maganar..
"Kai! Ina ba zata ta6a sa6uwa ba, Ta ya ma har wani zai iya ƙetare dajin Evil forest ya shigo kurkukunmu bayan tsaron da muka sanya? Wannan zancen bazai ta6a zama gaskiya ba!"
Jan harshe ne ya furta cikin ruɗanin zuciya.
Gaba ɗaya sun ruɗe sosai ganin abun suke kamar a mafarki, bama su gasgata abunda idanunsu suka gani ba, da abun da kunnuwansu suka jiye masu ba.
"Ina! bazai yiwu ba, wannan ba gaskiya bane, Muje Mu duba..." A cewar Jan Ido.
Suna ƙoƙarin Juyawa katsam suka yi arba da Dakarun sojojin da ke shigowa cikin hall ɗin runduna guda suka yi masu ƙawanya, Hannuwan su ruƙe da muggan makaman da Khala ta rarraba masu.
Wlh an shammace su, sun girgiza matuƙa, Ko a mafarki Elders basu ta6a tsammanin wannan ranar zata zo ba, Al'ajabi da rudani Ya hana su Iya furta kalma, sai jinjina kai sukeyi kamar wasu ƙadangaru.
Mamakinsu tayaya akai har aka yi nasarar kawo masu farmakin bazata a gidan Kurkukunsu! Abunda ba'a ta6a gigin yi masu ba, Lallai yau alkadarin su Ya Karye, gaba ɗaya sun ruɗe da lamarin.
Ɗaya bayan ɗaya suke kallon Dakarun Sojojin, Hankalinsu fa Ya ɗugunzuma ainin, amma saboda dakakkiyar zuciya da ƙarfin hali irin na Elders kawai sai suka fashe da wata irin mahaukaciyar dariya mai razanarwa, kai daga gani sun san me suka taka..
"Kun aikata babban kuskure!! Da har kuka shigo gonar mu! Wani tsautsayinne Yasa kuka kawo mana farmaki huh?" Jan Harshe ne ya faɗa yana huci.
Jan Le6e ya amshe, "Rabon ajaline Ya kawo ku..."
Bai ƙare maganar ba, dakarun sojojin suka dare tare da buɗe hanya, Ɗaya bayan ɗaya suka fara shigowa, ba su iya tantance fuskokinsu ba saboda masks da suka saka.
Kallon kallon suka fara jefawa juna tsakanin su da Elders, tsabar yadda zuciyar Chief Owais ke bugawa kamar zata fasa ƙirjinshi saboda zullumin wanda zai gani a cikin danginsa tun kafinma ya ga fuskokinsu, haka shima Big guy hankalinsa ba a kwance yake ba.
"Kune na farko da kuka fara kawo mana farmaki, amman hakan ba yana nufin kun ci galaba akanmu bane, ba zamu ta6a ƙyale ku ba, sai kun yi danasanin kuskuren da kuka tabka!!!"
Da kakkausar Murya Jan Ido ya yi maganar.
Tun da suka fara magana basu tanka masu ba, wani abu da suka lura da shi, Wasu daga cikin Elders ɗin sun ƙi yin magana, wannan yasa su zargin sanannu ne shiyasa suka ƙi magana don kada aji muryoyin su..
Big guy ne ya yi ƙarfin halin furta, "ELDERS, nayi farin Cikin ganinku, ashe dama ana iya ganin ku cikin sauƙi haka?" Ransu Ya 6aci da jin maganar shi,
"Dalla dubeku, wasu bajimaye daku, ko kunya baku ji ba! Mutane marasa imani, wlh da ace tuntuni munsan da zamanku a doron duniyar nan wallahi da tuni mun jima da shafe babinku, mugaye, azzalumai marasa imani, yau dai dubunku ta Cika, wlh saikun ɗanɗani kuɗarku...!"
Kalaman Big Guy sun yi matuƙar fusata zuciyoyinsu, tun da uwayensu suka haife su a duniyar nan wani ɗan adam bai ta6a tunkararsu gaba da gaba Ya faɗa masu kalaman 6atanci ba sai akan Big Guy.
"Ni bansan ma da wani jinsi zan misalta ku ba, saboda ku ɗin Jakkunane, dabbama tafi ku kyan kai, gaku dai ƙazamai, saboda shafewar basiri da ruɗin duniya da son kai da zalunci kun manta cewa wata rana dole ku mutu kubar duniya ku koma ga mahaliccin ku, Wai ku anya kuna da zuciya a ƙirjinan ku? Wasu irin mugaye ne ku.......!"
Taj da ya ɗauko maganar bai ƙare ta ba, sakamakon wata irin razananniyar tsawa da Jan wuya Ya daka mashi, tuni Ya haɗiye sauran maganar da bai idasa amayarwa ba..
Girgiza kai Chief ya yi, wlh takaici da baƙin cikin ganin Elders Ya hana zuciyarshi salama, Rai a matuƙar 6ace ya ce, "Mai kuke jira ne!" Ya faɗa tare da kallon dakarun sojojin su.
"Ku kama su! Da ransu muke son su, dole su fuskanci hukunci mai tsanani!!!"
Kamar Jira Sojojin su ke yi ya basu umarni suka fara ƙoƙarin kama Elders aikuwa kwatsam! Ba zato ba tsammani suka fara ganin wasu irin samudawan Evil Giants suna faɗowa cikin Hall ɗin masu yawan gaske, Kai da ganinsu sai gaban mutun Ya faɗi saboda ƙirar karfin su, gaba ɗaya su ka cika Hall ɗin, Sai gurnani su ke yi tamkar mayunwatan zakuna..
Sai lokacin Elder Ya buɗe baki ya ce, "Garkuwa, kayi tunanin bazan gane ka bane?" Sautin muryarshi ta canza kamar ta matashin saurayi, A hankali Danish ya cire Mask ɗin fuskarshi, Ya fuskance su da ainihin suffarsa ta jarumta, gaba ɗaya sun girgiza sun kuma kiɗima da ganin shi....
Cikin karyayyar murya Elder Ya kuma cewa, "Ni nasan ba yin kanka bane, tursamaka suka yi, kada ka manta baka da gata da ya wuce mu a duniyar nan, mune rufin asirinka, mu muka raineka muka gatanta ka, mu ka inganta rayuwarka. Ka manta irin gatanci da muka yi maka ne? Kada ka ce zaka Ci amanarmu.."
Elder bai kai ga ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Chief Owais ya daka masa yana huci, bai kaiga furta kalma ba Jan Harshe Ya ɗaga masa hannu, "Karka kuskura ka ƙara maimaita kuskuren da kayi!! Ba a yiwa Elder tsawa! Idan Yana magana ba'a katse shi!" Wlh ƙarfin halinsu ya yi matuƙar ɗaurewa Chief kai.
Cike da takaici Garkuwa ya ce, "Babu wanda ya tursasa mini, Ni nasa kaina, maƙaryatan banza, you've been deceiving me for a long time under the guise of privilege"
( ka daɗe kana yaudarata da sunan kune gata na!")
Tuni idanun shi sun cicciko tab da ƙwalla, ga wani ɗaci da yake ji a ranshi.
"Yanzu na riga da na gane cin zalun da kukayi mini, tsawon shekara ashirin tun ina jinjiri na kuka raba ni da iyayena, batare da sanin su ba, kun yi masu ƙaryar na mutu bayan ina raye, laifin me na yi maku??" Ya faɗa a tsawace kamar zai rufe su da bugu, wlh sun razana da jin abun da ya ce, basu yi zaton zai gano gaskiya ba.
He was extremely angry, maganarsa ma daƙyar take fita saboda 6acin rai,
"You never loved me, you hurt me and violated my right to live. Kun raine ni saboda biyan buƙatar kanku, da ace nasan gaskiya tuntuni, hmmm, da yanzu babu ku a doron duniyar nan, na tsaneku Elders...."
Bai ƙare maganar ba, Jan le6e Ya tari numfashin shi da cewa, "Kai har ka kai matsayin da zaka Ci amanarmu? Ka manta duk wani abu da kake taƙama dashi agurinmu ka same shi! Ba don mu ɗin ba ina zaka samu ƙarfin halin tunkararmu har ka rako wasu don ku farmake mu? Dube ka dallah! Sun maida ka sauna, shashasha, sakarai sai yadda suka yi da kai..."
Murmushin takaici ya yi batare da ya furta kalma ba, su Taj da ke sauraronsu kamar su rufe shaggu da bugu suke ji saboda zafin maganarsu, Salsabeel da ya gama fusata rai a 6ace ya zame mask ɗin fuskar shi don su ganshi da kyau.
Nuna shi Elder ya yi da yatsan shi batare da ya iya furta kalma ba saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare maƙogwaron sa...
Cikin zafin rai Jan Harshe Ya furta, "Maci Amana, dama nasan kana acikin su, bakasan cewa nemanka muke yi ruwa a jallo ba? Hmmm, na ji daɗin ganinka ɗan maciya amana, tun da har kayi kuskuren kawo kanka cikin kurkukun nan, to ka sani mun tanadanar maka azaba mai raɗaɗiii..."
"Ta Allah ba taku ba, dama nasan kun ƙullace ni, naji daɗi dana dasa baƙin ciki a cikin zukatanku, ko ba komai mahaifiyata ta yi nasara akanku saboda itace silar komai...." tiryan-tiryan Salsabeel ya labarta masu shirin da suka daɗe suna yi akan ɗaukar fansar mahaifinsu Habibullah da suka kashe har izuwa taimakon da suka yi ma prisoners gurin tseratar da su,
Haƙiƙa Elders sunji zafin cin amanar da suka yi masu, sai dai basu nuna hakan ba.
Yar dariya Big Guy ya yi tare da cewa, "Na fahimci haushin su kuke ji saboda sun tona maku asiri, idan ku masu hankaline kuyi nazari mana, gaba ɗaya duk wani shirinku lalacewa yake yi...."
"Ga misali nan kun gani, Danish yanzu namu ne, kun raine shi mu kuma zamu ci moriyar shi, garkuwar ku Ya juya maku baya yanzu mu yake goyon baya, kuma dashi zamu yi amfani gurin kawo karshen zaluncin ku"
Ya faɗa tare da yi masu gwalo, aiko ransu Ya 6aci, zuciyarsu ta harzuƙa, Big Guy da ƙarfin hali Ya kuma cewa, "Wai ashe Elders ɗinma matsorata ne, naga kun rufe fuskokinku, In ba tsoro ba, ku buɗe mu ganku mana, Ko kuna jin tsoron kada mu gane su wanene ku?"
Shiru suka yi basu tanka mashi ba.
Sai da ransu ya kai maƙura a 6aci, suka harzuƙa ainun kawai Elder ya ba Evil Giants umarnin su farmake su, Kafin kace me faɗa Ya kaure tsakanin Sojojinsu da Evil Giants, wata irin ƙura da kururuwa ta karaɗe tsakar Hall ɗin, Bugun mutuwa suke yi ma junansu, Abu fa ya ture don ginin wurin har girgiza ya ke yi saboda bala'e, baka jin komai sai sautin naushi da ƙarar buge buge da sukar kibiyoyi.
Lokaci ɗaya Hankulansu Chief ya fara tashi ganin yadda Evil Giants suke kashe sojojinsu, Jini sai ambaliya yake yi, Wani irin kisan rashin imani suke yi masu, cikin ƙanƙanin lokaci sun kashe sojojin sama da hamsin.
Yayin da su kuma ko ƙwarzane babu wanda ya yi masu saboda Garkuwar kakin dake a jikinsu, bayan haka suna amfani da sihiri gurin 6acewa, sai dai mutun ya ji sun dira a bayanshi kafin ya ankare tuni suke farke cikin shi da akaifun su, Evil Giants Bala'e ne...!
Shu'umin murmushi Elders suka fara saki, dama sun san bazasu iya karawa da Evil Gaints ɗinsu ba.
Ganin suna neman su rasa Sojojinsu yasa Danish yin wata irin suka ya dira a tsakiyarsu, Da gudumar hannunsa Ya dinga tarwatsa kawunan su, da bugu ɗaya yake kashe su, kamar Allah Ya aiko shi, ganin haka yasa su Omar fara sakin kabbara da ƙarfin gaske suma suka afka cikin filin dagar, Cikin Ikon Allah sai gashi sun Ci ƙarfin Evil Giants ɗin, sun bada ƙaimi haiƙan a filin dagar, wani zungureran mashi ne a hannun Chief Idan ya saita shi ya jefa shi kaitsaye mashin yake soƙe kawunan Giants, a lokaci ɗaya sai mashin ya kashe giants sama da goma, da Evils din suka ga haka sai suka rikiɗa suka koma wasu irin mugayen dodanni masu zaƙo zaƙon akaifu suka fara farka cikin Sojojin da ƙwalƙwale idanuwansu.
Duk fa abunda ke faruwa akan idanun Elders suna a tsaye suna kallon su, Abun da ya ɗaure masu kai, ganin makaman da suke faɗa da su yana tasiri akan Evil Giants ɗinsu, kuma abun mamakin da ya sha masu kai sun lura makaman kamar irin wanda maƙeran kurkukun ƙaddara suke ƙerawa ne, har sun fara 6ata rai ganin ana kashe nasu amma da suka ga Evil Giants din sun cigaba da kashe sojojin sai suka fara sakin dariyar mugunta.
Bayin Allah sun ci baƙar wahala, kusan sau biyar Evil Giants suna kokarin kashe Taj sai dai Danish ya hana, duk yadda zaiyi ya kare shi ko ya kawar da shi sai ya yi don baison Unaisah ta rasa mahaifinta, Ya gwammace shi su dake shi akan su ta6a Taj, ba don shi ba da tuni Taj ya sheƙa barzahu.
Big Guy kuwa da yake Allah ya zuba mashi ƙarfi shi da Chief Owais kuma sun ƙware wurin sanin dubarun yaƙi sosai hakan yasa ko ƙwarzane basu yi masu ba, kamar ana ƙaro masu Giants ɗin don daga sun kashe su wasu ke ƙara kurɗaɗowa ta jikin bango suke shigowa, Kun san ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, Kwatsam! Suna tsaka da yin artabun nan wani shaiɗanin Evil Giant ya damƙi Big guy Ya daddage ya ɗaga shi sama kafin ya buga da ƙasa nan take Kan shi Ya fashe jini Ya fara bulbulowa..
Karaf akan idanun Chief, wani irin Ihu Chief Ya fasa ganin zai rasa amininsa, ya yi kukan kura Ya dira agaban Giant ɗin ƙazamin faɗa ya kaure tsakanin su, gaba ɗaya hankalin Sojojinsu baya akansu saboda kowan nan su hankalinshi ba a kwance Yake ba ganin abun na neman fin ƙarfin su koma a ce yafi ƙarfinsu, Giants sun mamaye su ba kaɗan ba....
Duk yadda Chief ya so ya kashe shi abun ya faskara, saboda wani kafirin ƙarfine da shi, da mugunta Giant ɗin ya sakar mashi naushi a tsakiyar cikin shi, nan take ya fara aman jini, duk da haka bai ƙyale Chief ba, Ya daddage ya buga kan shi jikin wani ƙarfe nan take goshinshi ya faffashe jini ya fara bleeding ta hancin shi.
Hakan bai yi mashi ba, saida ya kai shi ƙasa ya damƙi wuyan shi ya fara jan shi a ƙasa ya tunkari wani kaskon wuta da niyyar ya tura kan shi ciki, gaba ɗaya Chief ya fita hayyacin shi ya kasa taimakon kan shi, a dai dai lokacin Danish ya ankara da abun da ke faruwa, ai baisan sa'adda Ya fasa ihu ya saki gudumar dake a hannunshi, sai dai me, kafin Ya kai mashi taimakon gaggawa wasu gungun Evil Giants suka rufe shi da bugun mutuwa suka hanashi motsawa, dama raunin shi suke jira, kamar zaiyi hauka.
A can bangare guda kuwa Taj shima Ya gamu da nashi bala'en, wani ƙasurgumin shaiɗanine ya take cinyar shi da basamudiyar ƙafarshi, nan take kafar ta bada wani sauti rukukus kamar zata cizge, har fashewa saida tayi jini ya fara bulbulowa, Azaba goma da tara Ihun ma ya kasa yi sai juyi yake yi a ƙasa.....
Salsabeel yana tsaka da yin faɗa ya zage damtse sai kashe su yake yi, bai aune ba yaji an damƙi damtsen hannun shi, da sauri ya juyo don ya ga wanene, rass! ya ji gabanshi ya yanke ya faɗi ganin ɗaya daga cikin Elders dama haushin shi suke ji..
Kafin ya yi wani yunƙuri Elder din da ya damƙesa ya murɗe hannun shi, azabar raɗaɗi ya hana ko ihu ya yi, naushi ya sakar mashi a gefen fuskar shi nan take jini ya wanke bakin shi, duk da haka bai ƙyale shi ba, sai da ya damƙi kanshi ya ja a ƙasa ya nufi matakalar bene ya buga kan a ƙasa, bawan Allah Salsabeel radadi ta ko'ina yake ji, saboda rashin Imani hakan bai masa ba, ya ɗaga ƙatuwar ƙafarsa da niyyar ya take kan nasa sai kuma ya fasa sakamakon wani abu da ya ja hankalin shi wanda ya ja har ya bar gurin salsabeel.....
Evil Giant ɗin da ya damƙi wuyan Chief yana ƙoƙarin tura kanshi cikin kaskon wutar, Unexpected ya ji an damƙi hannun shi, Yana huci ya juyo karaf suka haɗa ido da elder, kafin ya furta wani abu Elder ɗin ya murɗe kanshi nan take ya kife ƙasa matacce, ba tare da sun ankara ba ya janye Chief daga filin dagar ya nufi ƙofofin dake a cikin hall ɗin ya wurga shi a cikin wani daki kafin ya ja ƙofar ya datse ta, babu wanda ya lura da hakan.
Daƙyar Danish yafi ƙarfin Evil Giants ɗin da suka rurruƙe shi ya yi kukan kura ya watsar da su, jikinshi ya yi rauni sosai, sun faffasa kakinsa da ƙumbunansu har sun ta6a fatar shi, fuskar shi duk ta 6aci da jinin raunukan da suka ji ma shi.
Wata irin jijjiga ya yi ya rikiɗa ya zama jibgegen Zaki.. Ya afkawa Giants, cikin zafin nama ya dinga kakkashe su ta hanyar farke Idanunsu, cikin ƙanƙanin lokaci ya kashe Giants sama da ɗari, gaba ɗaya ya zubar da gawarwakinsu ƙasa.
Koda ganin haka nan fa Elders suka fara shan jinin jikin su.. ganin yadda Danish Ya salwantar da rayukan Giants ɗin su, ta ko'ina jininsu ne ke tartsatsi yana sauka ƙasan wurin kamar ƙoramar jini...ga yan hanjin cikin su waje sun zazzago, ransu ya 6aci matuƙa har ƙoƙarin sarrafa shi suka yi da sihirinsu don ya koma yana kashe sojojin don mugunta, sai dai wani iko na Allah Evils ɗin Danish sunƙi responding umarnin da suke basu, lamarin ya girgiza su ba kaɗan ba, sun rasa gane tayaya zasu shawo kan shi.
Basu gama kaɗuwa ba sai ga tawagar U.s Army sun faɗo Hall din, Sun gama da matsafan da sukai saura sun dawo nan don su tayasu yaƙi, ashe duk wani bomb da ya fashe a filin shagalin U.s Armies ne suka dasa su. Bayan sun yi 6adda kama sun saka kayan matsafan da Khala ta basu, suka shige cikin matsafan dake a filin shagalin, Cikin hikima da ƙwarewa suka dasa bombs a saƙo da lungu na ground floor ɗin kurkukun, bayan sun tabbatar da Elders sun fita daga cikin filin dama haka suka tsara saboda basa son Elders su mutu a raye suke son su, da ganin fitarsu a hanzarce suma suka nisanta kansu da filin taron kafin suka danna remote din dake a hannuwan su nan take bama baman suka faffashe.
Hankulansu ba ƙaramin tashi ya yi ba, ganin yadda aka kashe Sojojinsu, koda Elders suka ga sun ƙaru kuma zasu iya yi masu 6arna ba kaɗan ba ga Danish ya zamar masu masifa sai zubda jinin Giants yake yi, hakan yasa suka fara tunanin buɗe rijiyar da Jeremiah yake a ciki, saboda shi kaɗai ne zai iya ƙarar da su kaf cikin mintuna ƙalilan.
Bawai don su basu da ƙarfin yin faɗa dasu bane, kawai rainine a gurinsu su yi gogayyar kafaɗa dasu gurin yin faɗa, sun fi so su nuna masu ƙarfin ikon su.
Kafin su aiwatar da mummunan ƙudurinsu, tuni U.s armies sun haɗa hannu da Danish duk da ba a suffarshi yake ba sun fahimci shine sanin yana iya canza suffa kamar yadda aka sanar masu kuma gashi sun ga yana farmakar Giants, nan fa suka ci gaba da bada ƙaimi suka ci gaba da kashe Giants ɗin.
Kafin ka ce me, tuni sun wanke Hall ɗin da jinin Giants ya malale ƙasa kamar ambaliyar ruwa...hakan ba ƙaramin tada hankalin Elders ya yi ba, ransu ya kai maƙura a gurin 6aci, Zuciyoyinsu sai tafarfasa suke yi saboda tsabar fusata, ga wani gurnani da suke saki kamar mayunwatan zakuna.
Saida suka ƙarar da Giants ɗin, hankalin Danish ya karkarta akan su Taj, gaba ɗaya sun razana da ganin su cikin jini kamar babu rai, Cikin sauri ya nufi Big guy dake yashe ƙasa, ya taimaka mashi gurin ɗaure mashi kan shi da wani jan ƙyalle da ya tsinta a nan, sai nishi yake yi bawan Allah, Shi kaɗai yasan irin azabar da yake ji, daƙyar ma ya rayu.
Jini duk ya wanke fuskarshi, cikin fitar hayyaci Ya furta,"Danish.... Chief, help him! I don't want him to die, go find him, I want to see him before I die...."
Tsantsar tausayinshi ne ya kama su, duk da halin da yake a ciki damuwar shi akan Chief ne, wannan wata irin ƙauna ce 💔
"Danish ! Ina Chief?" Commender ne ya tambaye shi, Girgiza kanshi ya yi yana huci ya furta, "Bansan ina ya shiga ba, amma zan binciko shi."
Ya faɗa tare da miƙewa, juyawar da zai yi keda wuya yaci karo da Taj wanda ke kwance cikin gawarwaki kamar ba numfashi a jikin shi, Hankalin shi ya tashi matuƙa, cikin sauri ya nufe shi ya taimaka mashi ya miƙar da shi zaune tare da jinginar da shi gefen Big guy, bawan Allah sai sambatu yake yi yana faɗin yar shi, ya bar masa amanarta, ya ruƙe mashi ita, baya so ta yi maraicin rashin shi, kalaman Taj sun karya zuciyar Danish, bai san sa'adda ya ji hawaye sun wanke fuskar shi ba.
In a weak voice ya furta, "Ba zaka mutu ba, zaka rayu, Angel tana buƙatarka, bana so ta rasa ka...."
Ƙafar Taj da ta lanƙwashe ya jata da ƙarfi ta bada wani irin sauti, tsabar raɗaɗin da Taj ya ji ne yasa shi sakin ihun azaba, nan take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme, duk Danish ya bi ya ruɗe, ya kasa gane yana raye ko ya mutu ne? Ya dai samu ya tsayar da bleeding ɗin cinyarsa.
Miƙewa ya yi tare da kallon su Commender da sauran sojojin da suka rayu, gaba ɗayansu babu wanda bai raunata ba, sun jigata sosai, gaba ɗaya sun sare da lamarin.
"Salsabeel!" Hankali a tashe Ya furta lokacin da idanunsa suka hango mashi Salsabeel kwance rai hannun Allah, da gudun gaske ya bi takan gawarwakin dake zube a ƙasa ya nufi gaban benen, yana isa ya zube kan ƙafafuwansa tare da tallabo kan Salsabeel, wasu irin zafafan hawayene suka wanke fuskarshi ganin hannun shi dake a karye ƙiris ya rage ya 6alle biyu, ƙashi har ya 6ullo ta fatar, da ƙarfi ya fasa ƙara mai sautin gaske shatun jijiyoyin goshinshi suka fito ruɗu ruɗu kan fatarsa, Su Commender dake kallon shi jikinsu ya yi sanyi sosai kamar su zubda mashi ƙwalla saboda tausayi.
Unexpectedly Ginin kurkukun Ya fara Jijjiga kamar zai 6a66ako, lokaci ɗaya kunnuwansu suka fara jiyo masu sautin wata shu'umar dariya ta tantirin shaiɗani mara daɗin saurare.
Tunkafin ma su ga wanene suka sha jinin jikin su, saboda tashin hankali gaba ɗaya sun shafa'a sam sun manta da zaman Elders a hall ɗin waɗanda tuni sun jima da 6acewa, 6at babu su babu alamarsu, sun riga da sun san tsiyar da suka shuka, sun tafi sun bar su da masifa.
Cikin hanzari Danish ya miƙe tsaye, zuciyarsa na dakan uku uku, yayin da rinannun idanunsa ke akan rijiyoyin dake a hall ɗin saboda yasan yana ciki.
"Ina Elders suke? Sautin dariyar da muke ji ta wanene?" Canal Herry ne ya yi tambayar a ruɗe.
"The Elders have disappeared, the only way to escape is to run away before the evil giant emerges from the wall, He's the most dangerous evil giant in the prison of Destiny, and their new prison shield, ba zaku iya ja da shi ba, Ku barni da shi, In ba haka ba, zaku rasa rayukan ku ne!"
Wani irin faɗuwar gaba suka ji, kafin wani daga cikin su ya motsa, Unexpectedly murfin ɗaya daga cikin rijiyoyin ya 6alle da karfi tattare da iska ya yi sama kafin ya ƙundumo ƙasa, gaba ɗaya suka zare ido suna jiran ganin menene zai biyo baya.
A firgice Danish Ya dinga yi masu tsawa yana faɗin su tafi! su barshi da shi, amma suka ƙi tafiya saboda bazasu Iya barinshi shi kaɗai ba.
Lokaci ɗaya wani irin hayaƙi mai haɗe da tartsatsin wuta ya fara fitowa daga cikin rijiyar tuni suka sha jinin jikin su, ashe basu ga komai ba, lokacin da basamudan shaiɗanin ya duro daga cikin rijiyar kusan suman tsaye suka yi tsabar razana da kiɗima.
Wani irin zabgegen mutun, kwata kwata babu sutura a jikin shi, zir yake haihuwar uwarsa, gaba ɗaya jikinshi zanen tattoo ne da zanan aka yi mashi sutura, Ga wasu zaƙo-zaƙon akaifu masu kama da tsinin mashi, lokacin da ya buɗe idanun shi ƙiris ya rage su commender su arce a guje saboda wani irin jajayen idanu gare shi, Idan ka kalleshi sau ɗaya ba zaka ƙara marmarin haɗa idanu da shi ba saboda tsoratarwar da gare shi.
Bakowa bane wannan face sabon Garkuwar kurkukun ƙaddara wato JEREMIAH.
Da ƙarfi commender ya ba sojojin da suka rage umarnin su fara harbin shi, saita shi suka yi da bindigu suka dinga sakar mashi wuta ta ko'ina sai dai ko gizau baiyi ba, har bomb suka wurga mashi ya gangara agaban shi, ya ɗaga faffaɗan tafin ƙafarsa ya murje bomb ɗin, koda ganin haka ai saifa jikin taƙaura ya yi La'asar!
Tun fitowar shi daga rijiyar idanun shi na akan Garkuwa shi kaɗai yake hari, dama da niyyar ɗaukar fansa suka ƙirƙire shi, girgiza jikin shi yayi tare da sakin tsawa mai kuwar gaske, tamkar zai fasa dodon kunnuwansu, duk saida suka girgiza.
Tsautsayi ne ya kai wani soja gaban shi ya ɗaga wuƙa zai caka mashi aikuwa ya damƙi wuyanshi, nan take ya tsinka shi biyu, jini ya dinga tartsatsi ya jefar da gangar jikinsa gefe ɗaya, ai koda ganin hakan nan fa suka fara Ja da baya In ka cire Danish shi kaɗai ne bai motsa daga inda yake ba, ƙarasowar shi kawai yake jira.
Da gudu wasu sojojin suka nufe shi, tunkafin su karasa ya matse yatsun hannayenshi nan take jikinsu ya faffashe kamar anyi jajjagen kayan miya...
Waro idanu waje su Commender suka yi, lamarin ya gigita tunanin su, basu ta6a ganin bala'e da musiba ido da ido ba sai yau da Allah Ya haɗa su da Jeremiah.
Gaba ɗaya gurnanin Jeremiah ya addabi kunnuwan su, Danish dake atsaye ya rasa abun yi, yasan muddin Jeremiah ya baro bakin rijiyar wlh sai ya kashe su kaf ɗinsu da ido kadai zai iya salwantar da su.
Shiru ya yi yana yanke shawara da zuciyar shi lokaci ɗaya ya fara tariyo kalaman Unaisah sai ya ji kamar a lokacin take furta mashi su,
_I love you, Danish! I really love you, i wanna be with you for the rest of my life, I can't live without you, My heart beats for you alone, My soulmate, I'm yours, I don't want you to go and leave me! Please come back to me! don't die! I'll wait for you..."_
Yana so ya gana da tsohuwa khala saboda yaci burin ta faɗa mashi su wanene iyayensa yana matuƙar son ya gansu fiye da komai na duniyar nan, yana kuma son ya rayu saboda Unaisah, amma ya zai yi? Baida wata mafita da ya wuce ya aiwatar da abun da yake ganin dai dai ne.
Su Commender sai kiran sunanshi suke yi don su ji me yakamata su yi kafin Evil din ya farmakesu, Hankalin shi baya atare da su, gangan jikinsa kaɗai suke gani amma ruhinsa yana atare da Unaisah...
Wata irin jijjiga Jeremiah ya yi, A lokacin ya gama daidaita jikin shi, dama abunda ya tsayar da shi kenan, babban kuskuren da zasu yi shine su bari Jeremiah ya baro bakin rijiyar, domin kuwa in har ya dira ƙafarsa duk wani mai sauran rai da babu sihiri a jikin shi sai ya mutu in ba wani iko na Allah ba, aikuwa yana ɗaga ƙafarsa kafin Ya dire ta ƙasa, Danish ya watsa da gudun gaske ya durfafe shi, yana ƙarasawa gaban shi ya daka uban tsalle ya haye kanshi ya cakumeshi da hannuwan shi biyu, da iya ƙarfin shi na ƙarshe ya ingizasu gaba ɗaya suka rubza cikin rijiyar, nan take murfinta ya maida kanshi ya rufe makullinta ma ya datse kan shi, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!😭😭😭
Da ƙarfi suka dinga ambaton sunan Danish kamar zasu fasa ihu saboda tashin hankalin kada su rasa shi, da gudun gaske su Commender suka nufi rijiyar, suka haɗa hannu duka Sojojin suka fara kiciniyar 6alle murfin, saida ina, abun ya ci tura saboda murfin rijiyar mugun ƙarfene da aka tsaface shi, haka suka dinga zubda gumi suna ta haki tare da jan murfin don ya buɗe amma duk a banza. Duk irin jarumtakarsu ta sojoji saida suka fashe da kuka tamkar ransu zai fita, babu irin makamin da basuyi amfani da shi ba don su buɗe murfin rijiyar abun yaci tura, har bomb suka ɗaura saman murfin don ya buɗe suka ja da baya tare da duƙewa ƙasa, sai dai koda bomb ɗin ya fashe babu abunda murfin rijiyar ya yi.
A gaban rijiyar suka zuzzuƙunna cike da takaicin rasa Danish da suka yi, Suna tsaka da tashin hankalin nan, saiga Chief ya duro ta tagar ɗakin da Elder Ya garƙame shi, daƙyar yake jan ƙafar shi, jini duk ya wanke fuskarshi da gaban kakinsa, babu inda bai raunata ba ajikin shi, hankalin shi ya tashi da ganin gawawwakin rayukan da aka salwantar, nan take ya fara jin matsanancin faɗuwar gaba da tashin zuciya gami da ruɗani...
Kalmar farko da ta fara fitowa a bakinsa shine Ina Danish? Ina Omar? Ina Taj da Salsabeel?" Shiru sojojin suka yi an rasa wa zai bashi amsa saboda fargaban halin da zai shiga, cikin rauni na murya ya furta, "Wai baku ji ina magana ba? Ina Danish ne?" Cikin karyayyar murya Commender James ya ce, "Omar, da Taj da Salsabeel, sun raunata sosai, bamu da tabbacin suna a raye ko sun mutu," Ya faɗa tare da nuna mashi inda suke, daƙyar ya iya hangosu,
Cikin sanyin murya ya ce, "Shi fa Danish yana ina?" Kallon juna su ka yi batare da sun furta kalma ba..
"Kada kuce min ya mutu! Meyasa nake ganin hawaye akan fuskokinku?" A wahalce yake yin magana, daƙyar Major ya bashi amsa da cewa, "Kayi haƙuri Sir, bamu da tabbacin yana araye ko ya mutu...."
"Yana Ina ne??" Ya faɗa kamar zai saka masu kuka, da hannu lieutanant Jackson ya nuna mashi rijiyar.
Kafin ya labarta mashi abunda ya faru na baiyanar Jeremiah ya ƙara da cewa, "Mun yi iyakar bakin ƙoƙarinmu, sai dai mun kasa buɗe murfin rijiyar, gaba ɗaya bamu ji daɗin abunda ya faru ba, saboda mu rayu, ya sadaukar da kan shi...." Ya faɗa hawaye cike tab da idanun shi.
Cikin rauni na murya Thompson ya ce, "I've never seen a braver person than him, He's the real hero"
Captain ya ɗaura, "Ni kaina na jima banga mutun mai jarumta irin nashi ba, Ya cancanta ya rayu amma tayaya zamu iya taimakon shi..."?
Idanunshi cike tab da ƙwalla ya ƙare Maganar, jiri Chief ya fara gani a cikin idanun shi, duk irin juriyarshi saida ya fashe da kuka mai sauti kamar ƙaramin yaro, a sukwane ya zube kan gwiwowinsa ya kifa kanshi ƙasa kamar zai haƙa ƙasa ya binne kanshi saboda wutar baƙin cikin da ke ruruwa acikin zuciyar shi, da sauri su commender suka kewaye shi don su lallashe shi amma ina zuciyarshi ta kai maƙura, Yunƙurawa yayi ya miƙe da sauri suka rurruƙe shi, idanun shi a rufe yake tambayar Ina Elders? Suna a raye ko sun mutu?" Commender Haroon Yace, "Sun 6ace ma ganin mu, ina da tabbacin sun gudu daga gidan kurkukun nan." Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya, ji yake kamar ya kurma ihu ko ya samu ya fitar da abunda ke ranshi, bakowa ya faɗo mashi a rai ba face tsohuwa Khala yasan zata iya taimakon su.
Sai da ya fara umurtar wasu daga cikin sojojin yace su ɗauki su Taj su tafi da su, a kafaɗa suka rataya su, basu tsaya 6ata lokaci ba, cikin sauri suka nufi hanyar da zata sada su da ɗakin tsohuwa khala, sai dai me, kwatsam! suna tsaka da yin tafiya gaba ɗaya hasken gidan kurkukun ya ɗauke ɗuff, wani irin duhu baƙiƙƙirin Ya mamaye idanun su, Cikin sauri suka zaro Torchlight ɗin su tare da kunna su haske ya ɗan wadata kaɗan.
Dakatawa Chief yayi da yin tafiya, gaba ɗaya suka kalle shi, tsantsar tashin hankali suka gani akan fuskarshi, a ruɗe ya furta, "Kun kira pilots ɗinmu dake a waje" Gabansu ne ya faɗi, wlh sham sun shafa'a basu tuntu6e su ba, balle su ji meke faruwa a can, sun san tabbas za'a iya farmakarsu tun da Elders sun 6ace.
Cikin sauri Commender ya zaro tactical radio ya kanga a bakinsa, kusan sau uku yana kiran sunayen matuƙan nasu shiru ba'a amsa mashi ba..
A hanzarce Chief ya ciro wayarsa ya kanga a baki da ƙarfi ya dinga furta sunayensu nan ma shiru, wa'iyazubillah!
Tamkar zai fashe da kuka ya furta, "Taya zamu san meke faruwa da sauran sojojinmu da muka bari a waje!"
Dafa kafaɗarsa James ya yi, "Ku kwantar da hankalinku, ba lallai abunda kuke hasashe ya zamana gaskiya ba, zai iya yuwuwa matsalar network ne, saboda na fahimci network da suke amfani da shi iya cikin kurkukun ne yake aiki, wanda ke a ciki bazai iya kiran na waje ba, haka shima wanda ke a waje bazai iya kiran wanda ke a cikin kurkukun ba..." Commender da ya yi maganar ya faɗane don ya kwantar masu da hankali amma shi kanshi yasha jinin jikin shi.
Cike da takaici chief ya ja tsoki kafin suka cigaba da tafiya, a ƙalla sun karya kwana ya kai takwas kafin suka kawo kan dogayen benayen nan, aikuwa suna hawa benayen suka fara maidosu baya, idanunsu suka fara yi masu gizon yan uwansu da suka bari a gida suka dinga ganin su a kan hawa na uku Giants sun rurruƙe su suna kokarin wurgo da su ƙasa.
"Daddy, don't let them kill me! Help me, Daddy" Dafe kai commender Jemes ya yi jin muryar yarsa tilo, saboda ruɗu da tashin hankali ya fara kokarin komawa hawa na ukun don ya taimaketa, damƙar hannunsa Chief ya yi, sai hauka hauka yake yi yana faɗin ya sake shi zai je ya ceci ƴarsa...
Chief yana fitar da huci ya ce, "Ka manta abunda Danish Ya faɗa mana, kafin zuwanmu gidan kurkukun nan? Abun da kake gani ba gaskiya bane, sun yi hakanne don su razanar da mu..."
Yana ƙoƙarin shawo kan Commender James batare da sanin shi ba, Major smith ya watsa da gudu ya haura hawa na uku, ganin giants ruƙe da matarshi mai tsohon ciki sai kuka take yi tana miƙo mashi hannu don ya taimake ta.
Yana ƙarasawa gaban benan Giants ɗin suka jefo da ita, aikuwa cikin fitar hayyaci ya daka suka ya bi bayanta don ya ceto ta, kafin su ankara tuni Major Smith ya kife ƙasa nan take kanshi ya fashe ko shurawa bai yi ba ya mutu, matar da yabi dama babu ita gizaune kawai Giants ɗin ma duk sun 6ace babu su.
Zuciyar Chief ta karaya sosai, commanders da sauran sojojin jikinsu yayi mugun yin sanyi, wlh sun ji baƙin ciki da takaicin rasa sojan su, Kamar su ɗaura hannu akai su fasa ihu, don ma jarumta irin na sojoji ba yau suka fara ganin irin tashin hankalin nan ba..
Dafa kafaɗar Commender Chief ya yi in a cool voice ya furta,"I'm really sorry..." Girgiza kai Commender ya yi, "Kada ka damu, ajalinshi ne ya yi, ba mu isa mu hana shi mutuwa ba, balle muda muke sojoji dama saida muka bayar da rayukanmu kafin muka kar6i aikin, sannan duk rashi da muka yi bai kai naku ba..."
Da ƙyar suka shallake benan suka ci gaba da tafiya suna haska hanya da torchlight ɗin hannunsu, wani abun tashin hankalin duk in suka haska bango sai sunga inuwar Evils.
Wani sa'in har gifcin shaiɗanun suke gani...amma da yake zuciyar su ta kangare sun ma daina jin fargaban komai...gaba ɗaya ginin nema yake ya juye masu lissafin ƙwaƙwalwar su sun kasa gano hanyar da ɗakin tsohuwa khala yake lalube kawai suke a duhu, suna tsaka da tafiya kwatsam saiga wata tsohuwa kamar mahaukaciya ta faɗo ta gabansu hannunta tallabe da tsohon cikinta, sai kuka take yi tana roƙonsu su taimaka mata naƙuda take yi, abunka da me tausayi Chief har ya yi niyyar taimaka mata zuciyarshi ta raya mashi, "karka kuskura! kai baka ga ta yadda ta faɗo gaban ku ba..." Kafin ya yanke shawara da zuciyar shi tsohuwar ta daka suka ta haye kan Thompson ta dinga yakushin shi da cizon fuskar shi, cikin xafin nama Chief Owais ya damƙi ƙeyarta ya 6am6areta daga jikin Captain ya daddage ya buga kanta da ƙasa, kafin ta ɗago Commender James ya sakar mata harsashi a tsakiyar kanta, nan take ta sheƙa...
Kallon Thampson suka yi, fuskarshi ta yi jaga jaga da jini gwanin ban tausayi, haka suka dinga cin karo da tsoffin mata matsafa sai hari suke kawo masu, ɗaya bayan ɗaya suke kashe su. Sai da suka gama shan baƙar wahala duk sun jikkata daƙyar suka gano ɗakin tsohuwa Khala, tun kafin su shiga gabansu ke faɗuwa ganin ɗiɗɗige-ɗiɗɗigen jini kan benan da zai kai su ɗakin nata.
Kallon kallo suka jefawa junansu, an rasa wanda zai fara shiga ɗakin saboda zullumi da fargaban abunda zasu taras..
Sun shafe mintuna biyar a bakin ƙofar ɗakin batare da sun iya ta6uka komai ba. Daƙyar Chief ya yi ƙarfin halin tura ƙofar da sunan Allah a bakin shi ya zura ƙafarshi, su Commender suka bi bayan shi.
Wani irin burki suka ci, ganin babu khala aɗakin ta, abun da ya jefa su a matuƙar ruɗani gaba ɗaya ɗakin nata a hargitse yake, hatta gadonta ya jirkice, tukwanan furannin dake a ɗakin duk an faffasasu, Ga jinin da ya malale kasa... YA ILAHI❗❗
*INA TSOHUWA KHALA❓* INA PRISONERS DIN DA SUKA KU6UTAR❓*IN BAKU MANTA BA ITA TA CE SU KAWO YARAN DA SUKA KU6UTAR WURIN TA GASHI BABU ITA❓*
*MEKE SHIRIN FARUWA NE❓* *MEKE FARUWA TSAKANIN JEREMIAH DA DANISH BAYAN SUN FAƊA RIJIYA❓KUNA TUNANIN ZAI RAYU❓*SHIN YA BATUN BIG GUY, TAJ DA SALSABEEL WADANDA A HALIN YANZU BAMU SAN TAƘAIMAIMAI SUNA A RAYE KO SUN MUTU❓😭*
*SU CHIEF ZASU FITA LAMI LAFIYA DAGA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA❓*
*INA ELDERS*❓
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: ______________________________🔥💫
Wani irin burki suka ci, ganin babu khala adakin ta, abun daya jefa su arudani gaba ɗaya dakin nata a hargitse yake, harta gadonta Ya jirkice, tukwanan furannin dake a dakin duk an faffasasu, Ga jinin dayake malale kasa.. YA ILAHI❗❗
Alkalamina bazai Iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba.
Sun rasa gane meya faru da tsohuwa khala? Jinin wanene suka gani a kasa? babban abun da suke ma zullumi Fursinonin da suka turo akawo gurin ta, basu san awani hali suke ciki ba, fargabansu kada ace jinin fursinonin ne!
badan zuciyar Imani ba da tuni Chief Ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin da Elders suka kunsa masu.
La66ansa na kerma ya furta"La'haula walaqu wata Illah Billa, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un....." wani irin zafi jikinshi ya dauka rau...
Cike da ruɗu Commender James Ya furta"ni fa bangane ba, meke faruwa ne? Ina prisoners din da muka kubutar? Ina tsohuwar take? Jinin menene wannan"? ya faɗa yana nuna jinin dake malale kasa...
Yawu mai ɗaci thompson Ya hadiya ga radadi daya addabe shi, cikin sanyin murya yace"bana fata abunda nake hasashe ya zamana gaskiya, Zai iya yiwuwa Matsafan ne suka kawo mata farmaki watakil sun gano hada sa hannunta gurin kawo masu farmaki..."
bai ƙare maganar ba, Chief yai hanzarin katse shi ta hanyar girgiza kai yana fitar da numfashi mai ɗumi ya furta"in kuwa hakane Elders sun kashe ni, sun gama dani..."
kamar zautacce ya dinga nanatawa
Kanshine ya fara juya mashi wata irin juwace ta fara kokarin daukar shi da sauri Ya dafe bangon dake abayan shi, Yana huci hadi da jan numfashi kamar mayunwacin zaki..
"Ba zamu bar Nigeria ba, har sainaga bayan Elders, dole su fuskanci mummunan hukunci mai tsanani"
rai a6ace commender James ya fada...
"Me yakamata muyi yanzu? Bana bukatar mu 6ata lokaci gurin nemo su"! Commender haroon ne ya fada...
Captain lewis Yace"Where should we begin searching for them? Do you think they're still in this prison?"
Dukansu fa arauna ce suke, gabban jikinsu duk sun raunata ga yunwa da bacci dole su jigata tun dare ake gabzawa har gari ya waye batare da sanin su ba, amma saboda karfin hali irin na soja, burinsu su karasa aikin da suka dauko bata kansu suke ba, dare guda ba bacci sai zallar tashin hankali...."
"I don't think they're here, We should return to Nigeria and devise a new plan, we've lost our soldiers, and we're too weak to fight them now. We need to know what's happening with the soldiers we left outside"
(bana tunani suna nan, ni dai shawarar da zan bamu shine mu koma Nigeria, In yaso saimu sake sabon shiri, tunda yanzu duk mun rasa sojojin mu, Mu kanmu a raunace muke bamu da karfin da zamu iya yin faɗa da su a halin yanzu" acewar lieutanant Jackson)
Numfasawa Chief yayi"in sha Allah, karshensu ne yazo tun da har mu ka yi nasarar shugowa kurkukun nan, kuma mun yi masu barnar da ba zasu iya gyarata ba, nasan sun tsoratane shiyasa suka gudu, hakan ma wata nasarace...."
ya faɗa yana jan numfashi kafin Ya ɗaura da cewa"Zaku Iya tafiya amma ni bazan Iya barin kurkukun nan ba, saboda ɗan uwana Danish, zan jira har zuwa lokacin da Allah zai fiddo dashi daga cikin rijiyar zamu dawo tare da shi..."
ya faɗa idanun shi cike tab da kwalla, tsananin tausayin shi ne Ya kamasu, commender james Ya dafa kafadarshi Cikin kwantar da murya yace"ka yi hakuri Chief, bana tunanin zai rayu acikin rijiyar nan, ka daure kayi hakuri ka lallashi zuciyar ka, Mu tafi kawai..."
Zafafan hawayene suka wanke fuskar sa, wlh kallonsu kawai yakeyi yasan bazasu ta6a jin irin kunar da zuciyarshi keyi mashi ba.
cikin karyayyar murya ya furta"Bazan Iya tafiya ba, tayama zan tafi in bar Danish acikin rijiya tare da wannan Shaidanin? What if he kills him?"
Girgiza kai yai"Idan Nayi haka banyi mashi adalci ba, saboda mu rayu ya jefa kanshi cikin haɗari, sai kuma mu tafi mu barshi?
Dakyar ya kare maganar, daurewa kawai yakeyi, cike da tausayinshi su ke kallon shi, su kansu hawayen ne cike tab da idanunsu.
"Abun da nakeso ka fahimta, Danish Ya sadaukar da kan shine don mu rayu! Idan har muka bari muka rasa ranmu hakan na nufin burin shi bai cika ba, pls ka jure ka rungumi kaddara" acewar Commender Haroon.
Girgiza kai yai"ba zaku fahimce ni ba! But Danish deserves to live, wai shi mema Ya mora a rayuwarsa ta duniyar nan? Ya zo awahalce yanzu kuma kuna nufin in barshi Ya mutu? Shikenan fa ya mutu baisan iyayen shi ba, Bai ta6a jin dumin mahaifiyarshi ba, Baisan menene dadin iyaye ba, idan Uncle hateem Ya kirani ya tambayi ina yaronsa wata amsa zan bashi? kai Ina, wlh bazai yiwu ba dole naje na ceto rayuwar sa koda zan rasa rainane..."
da alama chief owais Ya fara zaucewa sai sambatu yakeyi masu marasa kan gado, kafin su gama yanke shawara da zuciyarsu chief yai hanzari juyawa da gudu Ya fuce daga dakin da niyar ya koma gurin rijiyar, da gudun gaske suka bi bayan shi cike da tashin hankali suke ƙwala mashi kira haɗi dayi mashi magiya akan ya tsaya kada yaje amma ko waiwayen su baiyi ba, saboda Idanun shi sun makance Danish kawai ya ke son gani, bawan Allah kusan sau hudu yanayin tuntu6e Ya fadi kasa ahaka zai mike Ya cigaba da gudu, Yana kokarin shan wata kwana kwatsam ba zato ba tsammani ginin Kurkukun Ya fara Jijjiga kafin kace me tuni ginin ya fara tsastsagewa, hankalin Su commender ba karamin tashi yayi ba, akan idon su komai ke faruwa yayin da Chief kwata kwata bai lura ba saboda baya acikin hayyacin sa.
wannan shi ake kira da tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, wasu irin marmarar duwatsun da akayi ginin ne suka fara 6a66akowa daga sama Kaitsaye suke rubzowa ƙasa da wani sauti suka tartwasewa, duk wanda kuwa tsautsayi yasa suka afkwa kanshi tofa Ya tashi aiki.
Chief daya rikice bai kaiga isa hall din ba, Wani Gingirimeman dutse Ya yanko mai girman gaske Gaba daya ya zube ƙasa, ya shiga tsakanin chief da hall din, ras gaban shi ya faɗi ya zare reddish eyes dinsa sam ya kasa motsawa, Wlh zuciyarshi ta gama karaya ya riga daya fidda rai da Danish.
Saboda ya rude kokari yake ya nemi hanyar da zai bi ya karasa ga hall din, wani ginin ne ya zazzago daga saman ceilling din dayake batare daya ankara ba, Cikin zafin nama commender james Ya damƙi damtsen hannun shi ya jefar da shi gurin Su captain da sauri Suka rurruke shi Yana kuka Yana kokarin fisge kan shi daga hannunsu ahaka suka sanya karfi gurin ingiza shi.
bawan Allah sai waiwayon ginin hall din daya rushe yakeyi..Yana ji Yana gani ahaka suka tafi da shi kamar yayi hauka sai sambatu yakeyi
_tun da na fara aiki ban ta6a faduwa ba sai yau da nagaza taimakon ka, Naji kunya Danish, i'm a looser, ka sani ba kai kadai bane danish, Kana da Allah kuma kana da dani, Danish bazan bari ka mutu ba, zan dawo Danish, zan dawo dole na ɗaukar maka fansa..........😭😭😭_
(Finally Su Chief Sun yi nasarar fita daga kurkukun kaddara bayan kalubalen da suka fuskanta)
*__________________________ELDERS 🔥*
A zazzaune suke kan Sofas cikin wani Daki mai duhu, saika kura ido zaka Iya ganin su da taimakon wutar Candles dake Ci, round table din dake agaban su shake Yake da kwalaben Giya sun sha sun bugu har ta kai masu karo.
Idanunsu sun kaɗa jawur kamar jan gauta, fuskokinsu babu annuri ko miskala zarratin basu taba fuskantar barazana da tashin hankali irin na wannan lokacin ba, sunyi babbar asara ba kaɗan ba.....❗
"Sune na farko da suka fara kawo mana farmaki! sun latata ginin da nayi wahalar kafawa tsawon shekaru! Sun san komai da muke aikawata, sun san sirrin mu, sun gani da idanunsu, sun kuma kashe rabi da kwata na Giants din mu, bayan irin 6arnar da sukayi mana na, sun 6ata shagalin black Night, sun kashe dubban matsafan da basu ji ba basu gani ba..."
ya faɗa yana jan numfashi cikin fushi, kafin ya daura da cewa"hakan bai ishe su ba, sai da suka kwashe Fursinoni da muka raina tsawon shekaru don mu amfana da su, sun tarwatsa duk wani shirin mu"
"Yaron da muka raina da hannun mu don ya zama garkuwar mu yaci amanar mu ya koma garkuwar su, tsohuwa Tamira da Salsabeel haka suma suka ci amanarmu, abunda yafi karya min zuciyata, wadda na damƙa ma yarda ta da amanata, hada ita cikin waɗanda suka bada gudummuwar kawo mana farmaki! meke shirin faruwa da mu ne? Meyasa waɗanda muka yarda da su suke cin dunduniyar mu"?
bai karasa maganar ba Yana huci Ya ɗaga kwalbar giyar dake a hannun shi Ya rotsa ta kan table din gaban shi nan take ta tarwatse.
Ran Elder yayi mugun 6aci, a wannan gabar komai zai iya faruwa.
Hankulan sauran Elders din ba ƙaramin tashi yayi ba, wata irin kururuwar ihu Ya fasa tare da tallabe kan shi da tafukan sa.
Lallashin shi suka fara yi cikin kankan dakai da girmamawa dakyar suka shawo kan shi.
Gyaran Murya Jan harshe yai kafin ya furta"Karaya ba tamu bace, Ba'a san elders da rauni ba, har yanzu muna da damar da zamu Iya dawo da ran kurkukun ƙaddara...."
bai ƙare maganar ba, Elder Yana huci Ya tari numfashin shi da cewa"tayaya zamu iya yin hakan? Bayan sun riga da sunsan komai, sanin ka ne muddin wani yasan sirrin inda muke yin tsafinmu abu na farko da zai faru lalacewar ginin kuma ya riga daya faru, abu na gaba shine karyewar sihirinmu In har hakan ta faru cikin sauki zasu shafen tarihin da muka daɗe muna kafa shi...."gaba daya sukayi shiru suna sauraranshi, da alama sun kadu sosai.
dakatawa yayi da yin maganar wani irin kululun bakin ciki da takaici ne ya tokare makoshin shi"a matsayin mu na mashahuran da duniya tasan da zamammu, abun kunyane asan me muke aikatawa, Ina jin tsoron mu rasa kimarmu da darajarmu fiye da yadda nake jin tsoron mutuwata, mutuncinmu zai zube a idon duniya, girmamamu da mutane suke yi suna ganin martabarmu zai tashi abanza, daga nan basai nayi maku bayanin abun zai faruwa ba, kun riga da kunsan sakamakon bazai ta6a yin kyau ba..." ya fada yana binsu da kallo daya bayan daya.
bakowane daga cikin su ya karaya ba, shi dama Elder mutunne mai wata aƙida tun fil azal baya son duk wani abu da zaisa mutuncin shi ya zube yana girmama ƙimarsa.
muzkutawa Jan le6e yayi kafin da wata irin muryar mai tattare da zafin fusata Yace"garkuwar kurkuku Ya zama garkuwar Fursinoni, ƙaddarar kurkuku ta zama mummunar ƙaddara agare mu, babban kuskuren da muka tabka shine barin tsohuwa Tamira da ranta, a lokacin da muka kashe Habibulllah, da mun sani mun haɗasu duka mun kashe su, shima garkuwarmu da ace bamu kawo ƙaddara gidan kurkukun mu ba, nayi imanin bazai ta6a cin amanar mu ba" ya ɗan dakata da yin maganar yana mayar da numfashi kafin yaci gaba da cewa"ita kuma Khala Elder Kayi hakuri da abunda zan faɗa, tunkafin zuwan wannan lokacin saida muka baka shawarar ka kasheta saboda ita din tana da kyakkyawar zuciya kuma tana ƙyamatar abunda muke aikatawa amma saboda kaunar da kake mata, shi yaja har ka gaza Yanke mata hukuncin daya dace"
Cike da danasani Elder ya sunkuyar da kan shi ƙasa, tunda suka fara magana, Jan wuya Yana a kishingide Yana binsu da kallo babu alamun kaɗuwa atare da shi, shi kuwa Jan kunne kamar yafi su shiga damuwa dama duk cikinsu shine mai raunin zuciya.
Jan Ido Yace"kada ku bani Kunya, duk wani abu daya faru ya riga daya faru, Mu fa Elders ne, babu wani mahalukin daya isa yaga bayan mu, abun nawa muka aikata bamu ta6a karaya ba sai wannan lokaci don kawai wasu kananun kwari sun kai mana farmaki? Rai nawa muka salwantar? Ya fada cike da gadara.
"sai wadannan zasu gagaremu! In har muna so mu dawo da karfin ikonmu dole mu bi abun da allon tsafinmu ya nuna mana, dole mu aiwatar saboda itace dama takarshe da ta rage mana wadda zamuyi amfani da ita gurin dawo da ran kurkukun ƙaddara"
Ya faɗa tare da dan dakatawa yana dubansu"a wannan karon dole mu cire sonkai atsakaninmu, bi'amana mu kashe duk wanda Yasan sirrinmu koda mafi soyuwa ne agaremu..."
sarai Elder Ya fahimci da shi yake magana.
"ita kuma dama ɗayan nan data rage mana itace mu cire Zuciyar Yarinyar nan, Mu ba dodon tsafin mu Ya handame ta, sannan mu kashe ƙaddarar kurkuku, ta hakane kaɗai gidan kurkukun ƙaddara zai farfaɗo...."
wata irin mahaukaciyar dariya suka kwashe da ita, ganin har yanzu suna da saura damar da zasu cigaba da aiwatar da shaidancin su.
Cike da izza Jan wuya yace"abun farin ciki, Garkuwar da suke taƙama da shi, Ya rasa ranshi saboda shi wawane shashasha, Ya sadaukar da kanshi saboda ya basu kariya, duk da muma munyi babban rashi amma wannan duk ba wata matsala bace da zamu daga hankalinmu akai, Ni ta inda najiye mana dadi gaba dayansu wadanda suka san sirrinmu basu san fuskokin mu ba, tayaya suke tunanin zasu iya yin nasara akanmu? In banda ma sudin dakikai ne iya fa sunayen mu suka sani, sai kuma sirrinmu amma azahirin rayu basu san su wanene Elders Ba...."
Maganar Jan Wuya ta faranta masu rai, ganin sun samu mafita...
"Yanzu wanene Zai kawo mana Yaran?" Jan harshe ne yayi tambayar, Cike da isa Jan wuya yace"kubar komai a hannuna"
tuntsirewa suka kuma yi dariya hahaha
_________________________________✍️
Shin Ya Labarin Tsohuwa Khala❓
*Bayan wani lokaci*
Farfaɗowa tayi daga dogon suman da ta yi na tsawon awanni, A hankali ta buɗe idanunta wani irin duhu ne ya mamaye ganin ta, tana ƙoƙarin motsa jikinta taji kamar an daddaureta.
gumin zufa ne Ya wanke fuskarta, bata gama wartsakewa ba sai nishi take yi tana jan numfashi..
takun tafiyar mutun taji a cikin kunnanta yana tunkaro ta, cikin disasshiyar murya ta furta"wanene"?
Kakkausar murya Elder ce ta razanar da ita yayin daya furta"me nayi maki dana cancani cin amana daga gare ki"
Shiru tayi bata furta kalma ba, Hankalinta dai idan yai dubu toh ya tashi, zuciyarta sai dakan uku uku take tasan yau sai buzunta, mai kwatarta a hannun Elder sai Allah.
A hankali Hasken fitilun dake saman ceilling din ɗakin ya haskaka ko'ina tana a zaune kan Kujerar ƙarfe, a rude take kallon igiyar kacar da suka ɗaɗɗaure jikinta da ita, ko yatsanta bazata Iya ɗaga wa ba, Da sauri takai dubanta gare shi yana a tsaye Ya juya mata baya, tun da taganta adakin da suke hukunta wanda yaci amanarsu na gidan kurkukun kaddara Ta tsinci kanta da jin matsanancin faduwar gaba, ga wasu karfafan Evil giants data hango tsaye abakin kofar dakin..
"Tun da naga irin makaman da sukai amfani da su gurin kashe giants nasan cewa koma wanene ya basu makamin acikin mu yake, saboda mu kadai keda irinsu acikin gidan kurkukun nan ake ƙera su, bakowa yazo min araina ba face ke dama kin jima kina gaya min zaki dauki fansa akaina"
Cike da karfin Hali tace"banyi mamakin abun da kayi min ba Elder, Ni angaya maka bani da zuciya a kirjina ne? Taya kake tunanin bazan ci amanarka ba? Dama akwai amana tsakaninmu? Kaida ka rabani da kowa nawa, har kana da bakin furta naci amanarka? Akwai maci amanar daya wuce kai mugu, Hakanan kawai saboda nasan sirrinka bisa kuskure ka rabani da dangina, ya'yana, Jikokina, ka kafe ni da asirinka cikin kurkukun nan."
idanunta jawur ta faɗa yayin da hawaye ke shararowa kan kuncin ta..ta daura da cewa
"tun lokacin dana nasan sirrinku, a ranar na daukar wa kaina alwashin saina yi silar Tonuwar asirinka, kowa yasan wanene kai, da miyagun ayyukan da kake aikatawa, shiyasa na dinga satar makamanku ina boye su saboda tanadin zuwan wannan ranar"
bata ƙare maganar ba, Taji Ya sheƙe da dariya, cike da izza Ya juyo ya fuskance ta, batare daya furta kalma ba, gently yake jujjuya sandar hannun shi.
"Dariyarka ta bazance Elder, Ni nasan Ayanzu haka Ƴan hanjin cikinka kaɗawa sukeyi saboda zullumi da fargaban mezai biyo baya, Na kunsa maka bakin cikin da har abada ba zaka manta ba, naja maku babbar asara, koba komai Yau kaga wadanda suka fi karfinka"
ta fada da murmushi akan fuskarta.
Wata Yar iskar dariya Ya saki, Kafin Ya furta"dame kike takama ne? Da ido Ta nuna mashi sama tace"Allah, shine abun tinƙahona, koken dana daɗe ina kai mashi akanka Yau ya amsa addu'ata, daga Yanzu ka kasance cikin shiri akowani yanayi mutuwa zata Iya riskarka, zaka wukalanta ka zama kaskantacce, kimarka da darajarka zasu zube a idon duniya....."
bata ƙare maganar ba Elder Ya buga sandar hannunsa ta daki ƙasa har saida ƙura ta tashi, wani irin radadi taji acikin kanta hakan yasa ta dakata da yin maganar.
Yana Huci Yace"kina tunanin kinyi nasara akaina ne? Bayan Duk wani shirinki Ya tashi Abanza, wadanda kike takamar zasu ga bayan mu a yanzu haka babu ko daya acikin su, duk sun mutu a hannun giants din mu, suma fursinonin da kika ku6utar basu tsira ba zamu kashe su ne"
Wani irin faduwar gaba taji arazane Ta furta"kana nufin Danish da Owais sun mutu su ma" jinjina mata kai yayi" gaba daya sun mutu...Don haka kidaina farin ciki, saboda haryanzu baki kamo hanyar da zaki ga bayana ba, kashe Elder ba abune mai sauki ba, Ita kanta mutuwar tsorona take ji..." a gadarance yai maganar.
ta kiɗima da jin maganar shi, idanunta cike tab da kwalla ta furta"saboda shafewar basira da jahilci kamanta kafin kai anyi wasu azzaluman da suka gabata yanzu duk suna ina ? Ta jefa mashi tambayar bai furta kalma ba.
"mutuwa bata tsoronka Elder Lokacin ka ne baiyi ba, Allah yana sane da duk wani abu da kake aikatawa dama ce ta dan wani lokaci kuma kajira ka gani wlh karshenka bazai kyau ba" ta faɗa tana sharar kwalla
"kuma karya kake min, Danish dina bai mutu ba, owais dina ma bai mutu ba ina ji araina suna araye..."
Fashewa yayi da dariya"ki yarda ko karki yarda matsalarki, Kina kurarin kin tona asirina, bayan Har yanzu asirina arufe yake saboda babu wanda yasan ainihin Elder, ko fuskata basu sani ba, taya zasu iya tona min asirina? Bayan Ko tuhumata basu isa suyi ba saboda basu da wata shaida...." ya fada yana sakin dariyar shakiyanki.
ranta a 6ace ta furta"ni zan tona maka asiri..." ta faɗa tana huci.
Da buɗar bakinsa sai cewa yayi"kin ta6a ganin gawa tayi magana"?
Cike da tashin hankali ta zare ido tana kallon shi, matso da fuskarshi yayi saitin tata"Oh wai kina tunanin zan barki araye? Bayan kece kika san su wanene Elders, Ko da can da kika san sirrina nabarki araye nayi danasani da ban kasheki ba, da nasan zaki zamarmin masifa da tuni najima da fille kanki...."
gaba daya tabi ta rude da jin maganar shi muryarta nawa ta furta"kada ka kasheni, Kabarni da raina, Ina son naga ya'yana da jikokina, Ina so na koma gurin dangina, ko dan son da kake min da zaman amanar damukayi da juna ka kyaleni da raina.."
Girgiza kanshi yayi"ke da ganin su, Sai a lahira, nasoki tamkar raina amma tunda kika nunamun tsantsar kiyayyar da kike min naji nima kin fita araina, Inasonki amma nafi son mutuwarki ayanzu idan nabarki zaki zamarmun annoba"
Ya faɗa tare da dafe saitin zuciyarshi, batay mamakin ganin hawaye da suka cika idanun shi ba..
"bazan ta6a son wata halitta kamar yadda nasoki ba, nasan zanyi bakin ciki da takaicin rasaki arayuwata, zanyi maraicin rashin ki, zan dawwama da radadin kashe ki da zanyi, Bazan ta6a yafe maki abunda kikai min ba, kece silar komai, Kin Ci amanar kaunar dake atsakaninmu, meyasa tun farko kika tsananta bincike akaina? Meyasa Kika san sirrina? Kinyi silar lalata Farin cikin rayuwarmu, kema kin sani nasoki fiye da yadda nakeson kaina...." zubewa yayi agabanta kan gwiwowinshi...sosai ta fashe da kuka cikin karyayyar murya ta furta"komai ya faru mukaddarine daga Allah, sirrinka dana sani Allah ne Ya kaddara zan sanin, shiyasa har nasan komai, da ace kai musulmine kayi imani da Allah da ka gane abunda nake faɗa maka..
"duk yadda na karya maka zuciya bai kaiga yadda ni ka karya min tawa ba, ina farin ciki na auri miji nagari mai sona da bani kulawa ashe mugun mutum na aura, da kanka ka musuluntar dani ashe kai din kasungumin arnene matsafi da baiyi imani da Allah ba, sannan ka ciyar damu haram, wlh ko bayan ba raina sai Allah ya tona asirinka, in sha Allah Elder saika yi kaskantacciyar mutuwa, duniya gaba daya zata juya maka baya, komai daka mallaka zai lalace.."
bata kare maganar ba, Ya zabura Ya mike tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki...tuni ta hadiye maganarta, Hankalinta atashe take kallon shi.
Giants ɗin dake abayanshi Yaba Umarnin su ɗaure mashi ƙafafuwanta da igiya jikin fankar dake liƙe saman ceilling din dakin, fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita ita ba mutuwar take tsoro ba, abu biyu take ma bakinci zata mutu bata tona asirin Elder ba, abu na biyu zata mutu bata gana da ya'yanta ba bayan tsawon shekaru ashirin da Ya garkameta akurkukun basu san tana raye ba.
tana ji tana Gani, giants din suka kwance igiyoyin da suka daureta a jikin kujerar, daya ya ruketa sai kuka take tana kallon Elder Ya saddar da kanshi kasa don baya son raunin zuciyar shi ya hana shi kashe ta.
a jikin fankar Suka ɗaure kafafuwanta gangar jikinta da kanta suna kallon ƙasa, Da ido yayi sihiri Nan take Kasan inda kanta ke kallo ya wawake ya zama katon rami
wata irin wuta mai balbali ta kama ci...lokacin da hucin wutar Ya fara ta6a kanta, wani irin azababben kuka ta fashe da shi kamar ana zare ranta, wani irin radadin azabane ke rabar kowani sashe na jikin ta, cikin shesshekar kuka Ta dinga yi mashi magiya akan ya kwance ta, Kada ya kasheta ko dan darajar ya'yan dake tsakaninsu amma saboda rashin imani irin na Elder cikin sauri Ya juya Gints suka rufa take mashi baya basu kai ga isa kofar dakin ba suka 6ace ma ganin ta.
Ita kadai baiwar Allah ga wutar sai kokarin kama jikinta ta ke yi, bata da wani sauran sihiri ajikinta balle tace zata kwance kanta, saboda elder ya riga daya karya garkuwar sihirin dake a jikin ta.
sambatu tadinga yi cikin fitar hayyaci take ambaton duk wata addu'a da tazo bakinta ahaka har numfashinta Ya fara kokawar daukewa zufar jikinta ta dinga tsastsafowa kamar yayyafin ruwan sama kafin wani lokaci bugun zuciyarta Ya tsaya cak, numfashinta Ya dauke da alama dai Khala rai yayi halinsa, wutar harta rufe ta....Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un 😭😭😭
____________________________________✍️
After One week (bayan sati ɗaya dakai farmaki Gidan Kurkukun ƙaddara❓
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋🌹
~__________________________~✍️
After One week (bayan sati ɗaya dakai farmaki Gidan Kurkukun ƙaddara❓
Hankalin Unaisah ba ƙaramin tashi yayi ba, Jin shiru har tsawo sati ɗaya basu dawo ba, lamarin Ya ɗaga hankalin ta ba kadan ba, dauriya kawai takeyi kamar yadda tayi ma su alkawarin zata daina kuka, kuma bazata sanya damuwa aranta ba, sannan ba zata hana idanunta bacci da kuma cin abinci.
Abu ɗaya ne bata wasa da shi, Tashi Yin nafilfili takai kukanta gurin Allah, idan dare yayi, biyu take raba lokacin ta, rabi tayi bacci rabi ta tashi tayi nafila, wani sa'in in ta fara tsayuwar daren Har sai kafafunta sun fara raɗaɗi tukunna take dakatawa.
mafi yawan lokutta akan prayer mat bacci ya ke yin awon gaba da ita, Unaisah da Aunty Umminsu sai batool ne kadai sukasan da tafiyarsu kai farmaki sauran yan uwanta babu wanda ya sani abu daya da suka sani shine har yanzu suna shirye shiryen tafiya amma basu tafi ba, kamar yadda Unaisah ta sanar da su, tayi masu hakanne don kada su daga hankulansu yayin da ita kuma hankalin nata ba akwance yake ba, sai dai suna yawan tambayar meyasa Danish baya leƙo su? kuma su an bar su anan ko nan zasu ci gaba da zama ne kuma yaushe ne zasu je kai farmakin, dakyar suke samu su shawo kansu ita da ummi, harta Danejo batasan komai ba dangane da kai farmaki ta dai san zasu je yin wani aiki kamar yadda Taj ya faɗa mata, abunda yafi damunsu babu wanda ya kira su awaya balle su san awani hali suke a ciki....💔
A daren jiya ne ta farka tsakar dare da matsanancin faduwar gaba sakamakon wani mummunan mafarki da tayi, Hankalin ta ya tashi matuka jin yadda tsigar jikinta da zuciyarta ke tashi, gaba daya tarasa samun nutsuwarta saboda tana ji aranta wani mummunan abu ya faru da su, a lokacin idanunta sun makance burin ta kawai ta ganta a part din Chief don taga idan sun dawo ko basu dawo ba, hijab ta zura a jikin ta, batare da sanin kowa ba ta fito daga dakin daddyta dama anan suke kwana ita da Batool bayan tafiyar su.
Ta sauko down ta nufi main door ta falo, ta dinga ƙoƙarin buɗe ƙofar ta kasa saboda security din dake a jiki, batasan menene password din kofar ba, har jaraba sanya numbers tayi sau biyu ana nuna mata wrong code tare da warning message.
zukunnawa tayi bakin kofar tafukan hannayenta toshe da bakinta don kada yan uwanta sujiyo ta, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, sai da ta gama hasala can zuciyarta ta ayyana mata me zai hana ta jaraba sanya kwanan watan da aka haife ta, cos ta sani tuntana karama mahaifinta baida password da ya wuce date of birth inta, cikin hanzari ta miƙe ta danna numbers din fortunately ƙofar ta buɗe batai wata wata ba ta fuce aguje ta nufi part din Chief, ko tsoro bata ji dare ne fa sosai donma akwai hasken Electricity tamkar rana.
Fitarta keda Wuya Batool ta farka sakamakon fitsari daya matseta Bayan ta fito daga toilet din ta dawo dakin Sai lokacin ta lura babu Unaisah, hankalin ta ya tashi tana fitowa ta hango Ƙofar Falon abude kasancewar Unaisah bata datse ƙofar ba, nan take ranta ya bata fita tayi cikin sauri ta nufi kofar harta kusa Isa kwatsam Ta tsinkayi muryar Ummi cikin Kunnanta.
"Babe Ina zuwa" cak ta tsaya da tafiya, Ummi ta nufo ta cike da mamaki take duban kofar falo data gani abuɗe.
"Ina zaki haka da tsakar dare ko mayafi babu akanki? Wanene kuma Ya buɗe kofar nan? Ko wani ya shigo ne?
cikin rawar murya ta fada mata babu Unaisah adaki, Da jin haka Ummi ta ruko hannunta suka bi bayan Unaisah, fitarsu keda wuya kofar falon ta datse silar bangazar da sukai mata..
Suna fitowa suka hango Unaisah tsaye agaban Security officers din gidan ta ruƙe qugu, ashe sun ganta lokacin da take gudu tana kokarin karasawa ga kofar shiga bangaren Chief.
a hanzarce suka kewata suna tambayarta ina zataje da tsakar daren nan? Gaba daya sun fahimci bata acikin hayyacinta sai haki take muryarta na rawa ta furta wurin Chief zataje.
Officers din sukace mata ay basu dawo ba, don haka ta koma inda ta fito, ta fashe da kuka tana fadin ba inda zataje, ita ta gaji da zama cikn fargaba kawai su kaita inda suke.
rigima ta saka masu duk yadda suka kaiga zare mata ido da yi mata tsawa akan ta koma takiya har takaiga wani Soja yai kokarin kai hannu da niyar ya ɗauke ta aikuwa ta gartsa mashi cizo har saida ta fasa mashi fata, ranshi ya 6aci matuƙa harya daga hannu zai kwasa mata mari cikin zafin nama officer din dake a gefen shi Ya damƙi hannunsa da kakkausar murya yace"karka kuskura, In har ba so kake ka rasa aikin ka ba"
Yana huci Ya fusge hannun shi ya juya yabar wurin, lallashin ta suka cigaba dayi don su samu ta koma tace masu in har suna so ta koma su bude mata kofa ta shiga ta dauko wayarta data bari, Officer din yace ta fada masu inda ta ajiye wayar zasu kawo mata zuwa gobe yanzu dare yayi taje ta kwanta, kin fada masu tayi tace itama batasan inda ta ajiye wayar ba sai ta shiga zata duba, kuma a yanzu take son wayar"
Ba yadda suka iya da ita adole suka kira Layin Agent zahra saeed daya daga cikin na hannun Chief amintattunsa, saboda ba wanda zai iya bude kofar idan ba su din ba.
Saboda rigimar Unaisah yana bacci tare da iyalinsa yayi recieving call din su, bayan sun sanar da shi abunda ke faruwa yace su dauke ta su mayar part din, Officern yace mashi yalla6ai ba fa yadda zamuyi da ita, abokin aikinmu da yai gigin ta6a ta cixo ta gartsa mashi har saida ta fasa Fatar shi, yana can yana jinyar kan shi" da jin hakan agent zahra yace"tafi karfin ku ne? wai ma wacece acikin yaran" kallon ta officern yayi meye sunanki" muryarta ashake tace Unaisah..
"Sir sunan ta Unaisah, tana launin ido ruwan toka" da jin hakan okay yace su jira shi.
Adai dai lokacin su ummi suka karaso tayi mamakin ganin Unaisah tsaye gaban Security Officers, Hijab din jikinta ta jike sharkaf da gumi ta hade rai kamar bata ta6a dariya ba, tambayarsu tayi meke faruwa ne, anan officers din suka sanar dasu komai daya faru, batai mamaki ba ta riga tasan halin kayanta in taso abu kamar zawo take bata da uziri ko kaɗan.
Batool ta tausaya mata sosai, ganin yadda ta fita hayyacin ta, jikinta sai kerma yake, rungumota tayi a jikinta, officers din suna ta kallon su kamar zasu hadiye su...
Bayan yan mintu, Sai ga kiran agent zahra ya shigo wayar officer din daya kira shi, bayan yai picking yace suje bakin kofar ya buɗe ta.
Unaisah ta danyi mamaki jin hakan amma da ta tuna kofar tana da security sai taga ai bakomai bane may be yai amfani da computer ne gurin buɗe kofar daga can inda yake.
Suna zuwa bakin kofar ta zuge da kanta, ajiyar zuciya kowannnasu ya sauke kafin suka shiga ciki baiwar Allah idanunta na akan Second floor ta dinga kallon door room dinsa dake a datse, har gizau ya dinga yi mata ta hango shi tsaye ya dafe handrail fuskarsa ɗauke da murmushi, jikinta yayi sanyi lakwas zuciyarta ta karaya, gaba ɗaya ta shagala da kallon shi, har saida ummi tace tayi sauri ta dauki wayar suna jiran ta kafin ta nufi Bedroom dinsu Batool tabi bayanta, ummi tana a falo tana jiran su.
Suna shiga ɗakin suka bazama neman wayarta, Batool tace sis ki yi kokari ki tuna inda kika ajiye ta, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace wlh na manta inda na saka ta, har zanin gado suka yaye tare da kakka6e shi duk basu ganta ba, Har closet dinsu suka duba basu ga wayar ba, suka duba under bed nan ma basu gani ba, cikin hanzari Batool ta zazzago da mirror drawer chest tana lalubawa unexpectedly hotuna suka faɗo kan floor, cikin sauri ta dauƙi hotunan ta kura masu ido tana kallon su farat daya ta gano inda ta ta6a ganin Faces din mutanan dake akan pics din, cike da zumudi ta furta kai Ina kika samu hoton mutumin aunty Ummi da kawarta"
Kaitsaye maganar ta daki dodon kunnan Unaisah a lokacin ta gaji da neman wayar har zata zauna gefen gado ta tsinkayi maganar Batool, mikewa Batool tay da sauri ta nufe ta tare da mika mata hotunan tace ina kika same su"? Da ruɗu ta kar6i hotunan ta soma duba su tana kokarin tunano inda ta gan su sai da ta zurfafa tunanin dakyar ta iya tuna ranar da ta gansu a karkashin gado a lokacin tana cikin neman wayarta.
Numfasawa tayi kafin ta furta" ran nan ne nagansu a karkashin gadon mu shine saina boye su a cikin drawer"
"To ay mutumin aunty Ummi ne wannan" ta fada tana nuna mata hotonsa" Ita kuma wannan kin tuna ƙawarta baturiya wadda sukazo airport atare wata fara sol launin idanunta blue"?
Da mamaki Unaisah ta ƙara duba hotunan dakyau tabbas ta gane fuskar baturiyar kawar aunty Ummin su, farko data fara ganin hotunan sai da tay mata kallon sani sai dai bata iya gano a ina ta ta6a ganin ta ba.
"Amma taya akai kikasan Mutumin aunty ummi ne wannan"? Ta jefa mata tambayar..
"Zan faɗa maki, amma dan Allah kada ki fada ma aunty Ummi, saboda ta ta6a buga min warning, akan kar in daukar mata waya in an kira..." Unaisah tace taji ba zata fada ma Aunty ummin ba..
Nan Batool ta labarta mata ranar da ya kira video call tayi picking, abun daya ɗaure ma Unaisah kai ta yadda har Batool ta iya ruƙe fuskarshi a karo na farko data fara ganin shi a video call.
"Kin tabbata shine"?
"Wlh shine, watakil kuma mai kama da shi ne, amma gaskiya kamanninsu ya 6aci sosai.."
lamarin ya ɗaure mata kai taya akai hoton kawar aunty ummi da saurayinta yazo dakinsu? Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, Ta dai san aunty ummi baza ta yi gangancin kawo hoton saurayinta adakin su ba tunda har ta gargadin Batool akan daukar mata waya thats mean bataso asan komai dangane da abun da ya shafi phone dinta.
Kafin wani ya ƙara furta kalma daga cikinsu suka jiyo muryar Ummi daga waje tana fadin Wai har yanzu baku ga wayar ba ne.
Cikin sauri Unaisah tace ma Batool kada ki fada mata komai dangane da hotunan, nima bazan faɗa mata ba, inaji araina hotunan nan akwai wani abu atattare da su, zanyi kokari insan daga inda suke"
kafin Ummi ta shigo ɗakin su ka yi hanzarin mayar da kayan cikin drawer din, hotunan ma cen cikin wasu notebook dinta dake qasan drawer din ta boyesu.
Adaren ranar basu koma part din daddynta ba, bayan da taga wayar officers suka ce su fito su koma part din daddynta, aikuwa ta sanya masu rigima akan bazata koma ba anan takeson kwana, ganin dare ya nutsa sosai yasa suka kyale ta, taso ta kwana adakin Danish sai dai takasa bude room door dinsa saboda an kulle kuma bata san code din kofar ba, adole ta hakura suka kwana adakinsu ita da Batool, Ummi kuma ta kwana adakinta.
Morning🌄
Zaune suke su Uku akan dining Chairs, sun tasa Abincin breakfast din da aka jere masu kan table agaba sai dai sun kasa ci, saboda rashin kwanciyar hankali tun kayan baccin jiya ne a jikin su babu wanda Ya cire nashi.
"Unaisah, ku ci abinci mana" ummi ce ta faɗa tana kallon su, kamar wadanda sukayi amai da gudawa duk sun faɗa, sai uban kasusuwan wuya..
In a cool voice Unaisah tace "Aunty Ummi, wlh abincin ma bayayi min dadi, turawa kawai nake yi.."
Batool tace"kamar kin shiga zuciyana wlh nima dai babu dadi..." shiru ummi tayi cike da damuwa take kallon su to ita ma dindai ba dadin abincin take ji ba, turawa kawai takeyi..
"Yau tsawon sati guda Aunty Ummi, babu labarinsu, kullum da zullumi muke kwana, tunanin mu meya faru da su? Sunyi nasara ko kuwa? Tayaya zamu sani Aunty Ummi? Ko awaya babu wanda Ya tuntu6e mu...." dakyar ta ƙare maganar saboda kukan dake kokarin 6alle mata, dakyar ta haɗiye shi.
"Jiya har mafarkin Danish nayi, da daddyna, Amma mafarkin baiyi min daɗi ba, shiyasa ban ma baku labari ba..." ta faɗa arauna ce, dafa kafadarta Ummi tayi"mu kara hakuri Unaisah, tun da bamusan meya tsayar da su ba, amma wani jinkirin Alkhairi ne In sha Allah zasu dawo cikin koshi lafiya..." yamutsa fuska tayi batare data furta kalma ba,
Wayar Ummi ce tayi Ringing daga cikin aljihun wandonta, zaro wayar tayi tare da duba sunan me kiranta, kamar mara gaskiya ta dago suka hada ido da su Unaisah har suna hada baki gurin furta"Daddy ne"?
Girgiza kai tay"ba shi bane, Friend dina ne" kafin tay picking call din ya katse mayar da wayar tayi cikin aljihu kafin ta maida dubanta gare su.
A fakaice Unaisah ta kalli Batool suka hada ido batare da ta lura ba, gaba ɗaya sun fahimci bata son yin waya agabansu in har ba daddyn Unaisah ne ya kira ba ko big guy.
"Guys yanzu dai mu daure mu ci ko rabin abincin ne kada ay almubazzaranci"..." matsa masu tayi dakyar ta samu Suka ci kaɗan.
mikewa Unaisah tayi daga kan dining din ta nufi dakin su.
Bayan tafiyarta Batool ta dubi aunty Ummi"yaushe zamu koma part din daddy, kada suji mu shiru"
Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, Bari na kira Danejo awaya in fada mata don ta kwantar masu da hankali" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Danejo kira.
zama tayi gefen gadon Su hannunta ruke da iphone dinta data dauko, messages ta shiga ta buɗo Sakonnin daya ta6a tura mata, nutsuwa tayi tana karanta su fuskarta ɗauke da murmushi, bayan ta gama karanta sakonnin ta shiga gallery ta bude hotunan da ta ta6a yi mashi batare da sanin shi ba, yayi mata kyau a pics din har wani lumshe idanu takeyi idan tana kallon su, ta kosa ya dawo ko dan ta cika mashi burin shi, idan ta tuna alkawarin daddynta dayace in har ta bi umarninsa zai bari ta auri zabin ranta sai taji wani dadi ya lullu6e zuciyarta, fatanta Allah yasa suyi nasarar ruguza kurkukun kaddara su dawo cikin koshin lafiya.
Kira ne Ya shigo wayarta, murmushi ta dan saki ganin sunan mommyna ya bayyana akan screen din wayar, picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta..
"Haba my baby, kin daga min hankali kullum saina kira bana samun ki, Almost a week?! Meke damun ki ne? sautin muryarta da damuwa ta tambaya.
"I'm sorry mommy, school ne ya boye ni, bayan haka wayar ma ta samu matsala sai jiya aka gyara min ita"
On the other hand, Benazir kiris Ya raga ta sanya dariya, ta rasa gane meyasa Unaisah take son yi mata karya, bayan ba halin ta bane, since last week ta riga da ta gane itace Unaisah yarinyar da ta kira wrong number tay mata karyar a kano suke yanzu kuma tace tana school bayan a labarin da Aneelerh ta bata Unaisah bata zuwa School.
basarwa tayi tare da cewa"Okay, kada ki damu, nima bazanso na takura maki ba, am babyna Ina daddynki ne? Almost a week bana ganin shi a online.." su6ul da baka tay What's your connection with him?"
yar dariya benazir tayi"son shi nakeyi, tun ranar dana fara yin tozali da shi, don ma yaƙi kulani ay da tuni mun yi maki ƙani..." waro idanu Unaisah tayi can kuma tadan saki dariya, har cikin ranta taji dadin maganar Benazir don kuwa time da ta fara ganin ta saida tayi ma daddynta sha'awar auranta, tadaiyi shiru ne saboda tana kokwanton ko tana da aure bayan haka bata son yayi ma Danejo kishiya ga kuma aunty Aneelerh da take burin ya aura saboda kaninta junaid ya samu Uba nagari.
tayi zurfi a tunaninta muryar Benazir ta katse ta"kinyi shiru babyna, kin san nima na rasa mijina da yata, ina maraicinsu, Aneelerh ta fadamin baya tare da mommynki, shiyasa nakeso nazo na maye gurbinta, ko bakya son in auri daddynki"
murmushin yaƙe tayi kamar tana agabanta tace"inaso, amma bata faɗa maki yana da au..." bata ƙare maganar ba, sakamakon dirar motocin data jiyo acikin kunnanta, rejecting call ɗin tayi tare da jefar da wayar Kan gado, ta fito da gudu ko Mayafi bata ɗauka ba ta nufi hanyar fita daga falon jikinta sai kerma yake tsabar zumuɗi, kafin ta ƙarasa Ummi da Batool suka bi bayanta da ɗan gudun su.
At same time motocin su ka yi parking, a gaggauce Officers dake tsaron gidan suka Yi masu kawanya tare da yin hanzarin buɗe cardoors, Adai dai lokacin Unaisah ta zuro kofarta waje wani burki Taci idanunta azare take Kallon motocin Cike da fargaban wa zata fari gani.
CO ne Ya fara fitowa cikin hanzari ya zagaya bayan motarsu ya buɗe boot ya cure folding wheelChair ya ajiye ta kasa ya fara kwancewa sai da ya daidaita wheelchair din kafin Ya furta"zaku iya fitowa da shi"
Wani irin faduwar gaba taji gaba daya tabi ta rude jin ya furta za'a iya fitowa da shi ko wanene? sai faman rarraba idanu takeyi akan motocin, lokacin da idanunta su kayi mata tozali da mutumin da SA suka rurruko daga backseat na ɗaya daga cikin motocin, jikin shi sanye da patient uniform blue yar riga ce mai tsayi, Cinyar kafarsa ɗaya gaba dayanta a nannaɗe take da bandage daga gani aiki akayi masa a tsakiyar cinyarsa, A hankali suka zaunan dashi kan wheelChair din sai nishi yake yana fitar da numfashi mai huci daga gani babu lafiya atattare da shi.
Cike da tashin hankali ta zare idanunta, la66anta na kerma ta furta"inna lillahi wa'inna Ilaihirraji'in! Daddy"! Da karfi ta furta sunan shi, bawan Allah a firgice Ya dubi inda take har rama yayi saboda azabar ciwo, suma Jami'an suka maida hankali akan ta..
watsawa tayi da gudu tana karasawa gaban shi a slow ta zube kan gwiwowinta, ta fashe da matsanancin Kuka tamkar ranta zai fita Cikin shesshekar kuka ta furta nashiga ukuna! daddy Meya faru dakai? Meya faru da kafarka?
tsantsar tausayinta ne Ya kama shi, Ummi da Batool sun kasa motsawa saboda tashin hankalin da idanunsu suka gane masu, daya bayan daya sauran dake acikin motocin suke fitowa, Chief owais ne jikin shi sanye da Singlet fara sai short, gaba ɗaya goshinshi bandage ne, fuskokin su duk sun 6aci da tabonnin raunukan da suka ji, Wa'iya zubilla, dafe kirji ummi tayi cike da tashin hankali ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Batool kuwa Fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita musamman data lura babu Danish a cikin su, daga cikin sauran da suka fito daga cikin motocin U.s armies din da suka rage ne su Biyar, babu cikon ɗayansu, sai wasu daga cikin na hannun daman Chief wadanda ba'aje Kai farmakin da su ba.
Akace labarin zuciya atambayi fuska, tunkafin suyi masu bayani suka karanci komai daga yanayin su, Dakyar Taj yai karfin halin janyo Unaisah Ya rungumeta akan kirjin shi, tare da shafa sumar kanta yana faman sauke ajiyar zuciya, har cikin ranshi yaji dadi da Allah yasa ya rayu ashe da rabon zai sake ganawa da yarsa? sai dai abu daya da yake ma fargaba.
hannun Ummi ruke dana Batool suka karaso Gurin su Chief, Fuskokinsu sharkaf da hawaye Murya Na rawa Batool ta furta"Ina Danish din mu"? Shiru sukayi don basu shirya komawa asibiti da wanin su ba.."dan Allah ku faɗa min Ina danish? Meyasa bangan shi ba..." cikin shesshekar kuka tayi maganar, Sunyi shiru suna kallon ta, Chief ma Hankalinsa baya akan su, saboda matsananciyar damuwar data mamaye zuciyarsa.
Unaisah data kwantar da kanta a kirjin daddynta, Hankalinta Idan yai dubu toh ya tashi, tin da taji muryar Batool tana tambayar Danish ta fahimci babu shi su ka dawo! Babu!!babu!! Hasbunallahu wa'ni imal wakeel, acikin zuciyarta ta dinga maimaita duk wata addu'a datazo cikin bakin ta.
Ummi kuwa Jikinta yagama mutuwa Cikin sanyin murya ta wanda Ya kara tayi masu Chief barka da dawowa da tambayar ya jikin su, fuskokin su kwata kwata babu walwala suka amsa mata, Kafin Commender james ya nemi su shiga ciki saboda majinyatan jikinsu da suka jigata, dakyar Chief yake Tafiya saboda rashin kuzari, bawan Allah shi kadai yasan me yake ji a cikin zuciyarshi bazai ta6a mantawa da Danish ba Har abada ya kafa tarihi acikin zuciyar shi, gaba daya abun da suke jima fargaba yadda yan uwan shi zasu kar6i abunda zasu fada masu saboda su sunsan irin kaunar da suke ma Junansu komai zai iya faruwa idan suka ji cewa Danish ya mutu.
"Commender pls, meya faru ne? Hankalina Ya tashi, Ina son nasan Ina Danish ne? Ina Omar? Ina Major"? Suna Ina"?
Girgiza kai commender yayi cikin rauni murya da harshensa na turanci ya furta"Ummi, muje ciki zamuyi maku bayani"
yana fadan hakan yabi bayan Su Chief suka nufi ciki.
mutun uku ya rage a harabar, gaba daya suka zukunna Agaban Taj, Cikin rauni na murya Unaisah ta furta"daddy, Ina Danish"?cike da fargaban amsar da zai bata tayi maganar, tare da dago kanta daga kirjinshi, fuskarta ta 6aci da hawayenta, gwanin ban tausayi ya ke kallon ta.
"Dan Allah Daddy Ka fada mana, Ina Dan uwanmu Danish"? batool ce ta fada still bata daina kukan ba...
Ummi ma tace"tun da kuka tafi, Hankalinmu ba akwance yake ba, saboda zullumi da fargaban awani hali kuke ci, gashi kun dawo ba yadda muka zata ba, babu wasu daga cikin ku, sannan ku kanku araunace kuke, that means something bad happened."?
Ta fada idanunta cike tab da kwalla, yayi shiru yana binsu da kallo...
"Daddy, pls ka fada min, yana raye koya mutu, kada kace zaka boyemin, saboda duk mun daren dadewa dole naji, kwara ka fadamin ayanzu inyi jinyar zuciyata idan ina da rabon cigaba da rayuwa, ay ma nayi imani da kaddara, in ma ya mutun Zanyi hakuri in rungumi ƙaddara..."
wani kallo Taj yayi mata bakomai yake tunawa ba face abubuwan da suka faru kafin tafiyarsu irin haukan da tadinga yi na zai raba ta shi, shine yanzu take kokarin yi mashi burga salon Ya fada mata Ya rasata na har abada.
ganin kallon da ya ke yi mata yasa ta kama in-ina hawaye na cigaba da tsastsafowa kan fuskarta tace"wlh daddy bazan damu ba, ka fadamin kawai.." tana kuka tana dariya tayi maganar kamar zautacciya.
hmmm baiwar Allah bashi ba, hatta ummi ta karaya da ganin yanayinta, kodan saboda Unaisah zataso ace Danish Yana raye.
Da ido tayi mata Taj alamar karya kuskura ya fada mata, don ita tasan me ta gani wlh, Shafa fuskarta yayi da tafukansa Ya kakalo murmushi kan fuskarshi"meye naga kun wani daga hankulanku"?
"Daddy taya hankalinmu bazai tashi ba, kun dawo gaba dayanku ba lafiya, kuma babu Danish da ya Omar"
jinjina kanshi yayi"hakane daugher, amma inaso ki sani dan uwanku yana nan cikin koshin lafiya.."
ba dan sun yarda da maganar ba, Tace"yana ina"? kafin ya bata amsa Ummi ta katse su da cewa"Haba Unaisah, dudufa Yanzu suka dawo, baki ga halin da yake a ciki ba, ki bari Ya shiga Ciki Ya huta mana, inyaso sai muji komai daga bakinsu," dakyar Ummi ta lallashe su suka hakura da yi mashi tambayoyin.
Unaisah da Batool ne suka gungura Wheelchair din Taj ganin ya raunata sunsan ba lallai ya iya gungura kan shi ba, suka nufi main falo din ummi na abiye da bayan su, anan suka iske su commender zazzaune kan Sofas, gaba dayansune da suka shigo, a tsakiyar sofas din Su batool suka dakata da gungura shi, kan floor suka zauna kamar masu zaman makoki, ummin ma ta zauna gefen su.
saida suka huta nutsuwa ta shige su sosai, kafin chefs din gidan suka shiga jera masu Abinci, kamar sarki haka suka dinga lallashin chief donyaci abinci yace masu bazai iya ba, ko yaci bazai ji dadin shi ba, subar shi kawai shi kadai yasan halin da yake aciki, cikin kwantar da murya commender yace"in har bakaci abincin ba, taya zaka samu karfi ajikinka balle harka Iya Karasa aikin ka"!
"What you need now is peace of mind because your brain needs rest to function, Chief worry won't solve anything, it will just lead to loss and regret, just Forget about every bad thing that happened in the prison of destiny, Strengthen your heart and face what lies ahead, that's how you'll achieve success ka fuskanci abunda kasa agaba, ta hakane zaka cimma nasara..." kalamai masu karfafa zuciya Commender james Yaci gaba da furta mashi sauran na hannun damanshi duk suka saka baki gurin kwantar masa da hankali har saida suka samu Ya ɗan lafa, cikin sanyin murya ya furta"nagode da shawarwarinku, in sha Allah zanyi abunda kuka ce, amma Yanzu nafi bukatar wanka, zan shiga ciki, idan na fito zanci abincin.."
yana faɗan hakan Ya miƙe cike da rashin kuzari Ya nufi part dinsa.
Yana shiga Ya faɗa kan gado Idanunsa na fuskartar ceilling, komai daya faru a gurin Yaƙin Ya fara tariyowa Hannunsa daya dafe da saitin Zuciyarshi, Yafi jin Danish Fiye da kowa sai kuma amininsa Omar wanda a halin yanzu yana agadon asibiti rai hannun Allah As a result of his brain injury, ya shiga coma ba lallai ma ya dawo da cikakkiyar lafiyarsa ba, a bayanin da docs su ka yi ma shi kenan.
abu na biyu da ya kwallafa rai akai Shine Elders, Alwashi ne ya daukarwa kanshi Elders ba zasu kai karshen watan nan ba batare daya gano su ba, abun da Yafi tada mashi hankali tsohuwa Khala matar ta tsaya mashi aranshi! Kalmar data fara furta mashi "owais kaine ka girma haka"? Meyasa yake jin kamar ya san muryarta? Meya faru da ita? Hakika tsohuwa Khala tayi masu kokari, ba wai iya makamai ta taimaka masu da shi ba, ta taimaki fursinonin da suka ku6utar, shi Kanshi ya jinjinama jarumtakarsu Ita da Danish sun cancani a yaba masu, don shi ji yake da ace Danish yana raye ba abun da zai hana Ya sauke mukamin shi na director general Ya damƙa mashi saboda ya cancan ta.
A hankali siraran hawaye suka wanke fuskar shi ya ɗan numfasa tare da lumshe idanun shi yana jin wani irin yanayi mara dadi a tattare da shi
aranar da suka kwana a sansani kasancewar a masauki daya suka zauna kafin suyi bacci sun dan ta6a fira da shi har ya dan bugun cikin shi yace ya fada mashi meke a tsakanin shi da Unaisah kar yai tsammanin yana sanya masu ido ne, kawai Ya lura da yadda suke kaunar junansu, a lokacin har saida yai murmushi kafin yace ma shi ya dauka Unaisah bugun zuciyar shi ce, yana tunanin mutun zai iya rayuwa batare da zuciyarshi tana bugawa ba? Dariya chief yai ya girgiza kai yace a'a bama zai ta6a yiwuwa ba, yace mashi toh haka Yake jin Unaisah, a lokacin Chief ya sake tambayarsa ya fada masa wani buri yake so ya cika masa idan suka dawo bayan sunyi nasara, ya danyi jim kamar yana nazari kafin yace baya bukatar komai, kawai shi abunda yake so yai masa alkawarin koda bai rayu ba idan sukaje kai farmakin Ya ruke Unaisah da mahaifinta da sauran Yan uwan shi yabar mashi amanar su ita kadaice alfarmar da zai nema agurinsa.
Bayan ya dawo daga duniyar tunanin daya lula A hankali ya Kife kanshi jikin pillow, fuskarsa ta 6aci da hawayensa..
_______________________________✍️
"Dan Allah ku faɗa mana ina dan uwanmu Danish meya faru daku"? Batool ce ta kuma tambaya...
Cikin sanyin murya Commender Haroon yace"ku kwantar da hankalin ku, Danish bai mutu ba, saboda bamu shaida mutuwarsa ba"
A takaice Ya labarta masu abunda Ya faru a ranar da suka kai farmakin bai boye masu komai ba"
Canal herry yace"munyi babban rashin na har abada ba zamu ta6a warkewa daga radadin da muka ji ba na rashin Danish, zai yi wuya asamu jarumi irin shi a duniyar nan" Ya fada tare da saddar da kan shi ƙasa.
mikewa Unaisah tayi kamar bata acikin hayyacinta kafafunta sai kerma sukeyi ruko hannun ta Taj Yayi"My angel, zauna muyi magana, bafa mutuwa yayi ba, ni nasan zai dawo ne da kanshi In ma bai dawo ba zamu koma ne"
gaba daya hankalinsu Commender na akanta, ta runtse idanunta sosai, jikinta kakarwa yakeyi kamar wadda sanyi ya kama, dakyar ta furta"daddy, Danish Yana acikin rijiya ta gidan kurkukun kaddara tare da evil giant me hadarin gaske? ku ka tafo ku ka baro shi!, sannan Elders basu mutu ba sun yi nasara kenan? ta faɗa tare da dafe goshinta tana huci tace"shiyasa nace ku tafi dani, ni dama saida raina ya bani wani mummunan abu ya faru ashe mafarkin da nayi gaskiya ne"
"Unaisah, Ki fahimta bamu da yadda zamuyi ne, Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, bamu isa mu canza mashi kaddarar shi ba, yakamata ki godema Allah Unaisah baki yi farin ciki ba? Saboda sadaukarwar da Danish yayi Mun ceto rayukan Yan uwanku dake a kurkukun kaddara yanzu haka suna a asibiti a karkashin kulawar likitoci, bayan haka mun ku6uta da ranmu da ba don shi ba da tuni mu kanmu mun rasa rayukanmu"
Bata jira karashen zancen shi ba, ta zame hannunta daga Nashi Cikin sauri ta nufi dakinsu ta shiga ta fada toilet, ta kunna shower da faucet don kada sauti Ya fita, da hannu biyu ta daddafe kanta dake sara mata, Ta daddaga ta fashe da wani irin kuka mai cin rai kamar ranta zai fita, ihu tadinga Yi tana hauka hauka gaba daya shatun jijiyoyin goshinta Ya fito rudu rudu kan fatarta, hatta wuyanta shatun jijiyoyinne, wani irin mahaukacin zafi temperature din jikinta Ya dauka, Idanunta suka kaɗa jawur kamar garwashin wuta, kamar ana rura wuta Cikin zuciyarta saboda bala'en radadin da takeyi mata, sau uku tana buga kanta Jikin sink, har saida fatar goshinta ta faffashe jini ya wanke kyakkyawar fuskarta, nan take Hancin ta ya fara bleeding, lokaci daya tafara jin wani irin azababben ciwon kai mai azabar radadi, juwace ta kwasheta gaba daya ta yanke jiki ta faɗa kan floor, wani irin duhune Ya mamaye ganinta, Ji take kamar ta tsaga kirjinta ta ciro zuciyarta ta jefar saboda tafarfasar da ta ke yi.
Maganganunshi ne suka fara dawo mata acikin kanta ..
_"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"?_
_"Abu ɗaya da nakeso Kiyi min alƙawari shine, Ko bayan tafiyana kada kiyi kukan rashina, kada kiki cin abinci, ko ki hana idonki bacci saboda ni, sannan koda ban dawo ba, kiyi hakurin Jure rayuwa batare dani ba..."_
"Meyasa zaka yi min haka? Ta fada acikin ranta
"Don nace ka bada ranka ba ina nufin ka mutu ba, taya kake tunanin zan iya rayuwa batare dakai ba? Na rasa farin cikin rayuwata, me rage min? ya Allah Ka dauki raina in huta"
Lokaci ɗaya ta fara tariyo farkon haduwarsu agidan kurukukun kaddara, at sight da sukayi tozali da juna sai da ta razana da ganin kyawun shi...In har Danish bai dawo ba, to kuwa tabbas zata dawwama da bakin ciki arayuwarta.....💔
Tana jiyo sautin bugun kofar da suke yi mata, sama sama muryoyinsu ke yi mata yawo akai Unaisah ki bude kofa, pls ki bude, wai baki ji Ina magana! Ba zaki bude ba"?
ko yatsanta bata iya dagawa, saboda halin da ta shiga...
Lokaci ɗaya ta fara jin matsanancin ciwon kirji, hudojin fatar jikinta suka fara fitar da gumi ta ko'ina zuface Ke tsatsafo mata kamar an yayyafa mata ruwa, numfashinta yayi karanci dakyar take Jan shi bata kara sanin inda kanta yake ba💔
*Bayan Wani Lokaci*
*OIH*
Da matsakaicin Gudu Motar su ta shigo asibitin tunkafin suyi parking, Nurses suka fito a gaggauce hannayensu ruke da Stretcher agaban motar suka aje, Jikinshi na rawa ya fito daga backseat na motar, Ya zura hannu Ya dauko Unaisah dake a rungume Jikin Ummi, kwata kwata babu Numfashi a jikinta, Batool sai kuka takeyi kamar ranta zai fita, da kanshi Ya kwantar da ita kan Stretcher din, Nurses suka gungura ta zuwa Emergency ward yayin da Su ummi ke abiye da bayan su.
A waiting Area Ummi da batool suka tsaya Suna jiran tsammani, Chief yana a zaune kan seat Ya dafe forehead dinsa da tafin hannunsa, idanunsa sun kaɗa jajur saboda tashin hankalin da yake fuskanta.
Bayan yan mintuna, Motar Us armies da ta Senior agents ta karaso asibitin, visitor din dake kai komo a harabar asibitin sai kallonsu sukeyi, gaba daya suka fito daga Cikin Motocin hada Taj wanda gaba daya fuskarsa ta jike da hawaye kamar karamin yaro yayi kuka sosai, ga shi ba koshin lafiya gare shi ba, dama ko sallamar shi ba ay ba Ya matsa lamba akan a sallame shi saboda yar shi, dakyar ya samu Chief ya sanya hannu suka sallame shi acan inda aka kwantar da su a (Combat support hospital)
gaba dayansu babu wani mai kwanciyar Hankali, Sun rasa ina zasu sa ransu suji dadi a duniyar nan, Na hannun daman Chief suka kewaya batool da Ummi suka fara lallashinsu da kwantar masu da Hankali, Shima Taj haka suka dinga tausarshi yana azaune kan wheelchair dinsa ya sadda kan shi kasa, Kasa jurewa yayi a karshe ya gungura kujerarsa Ya koma bakin Kofar dakin da aka kwantar da ita, Kasancewar Kofar ta glass ce yana iya hangen Docs din da suka kewaye gadon ta, sun dage damtse suna ta kokarin ceto rayuwarta, leken ta ya dinga yi tana a kwance kan medical bed Sai jan numfashi take duk da sun sanya mata Oxygen mask akan fuskarta.
Addu'o'i Ya dinga yi mata acikin zuciyarsa akan Allah ya bata lafiya..💔
Wunin ranar suna asibiti Har lokacin likitoci suna aiki akanta, Kafin marece docs din suka kammala bincike sakamakon ya nuna tana fama da severe depression and Heartbreak Syndrome, She's in a critical situation, dealing with two major issues simultaneously, docs din ma sunce in har ba'ay kokarin shawo kanta ba, Zuciyarta zata bugawa ne, amma zasuyi iyakar bakin kokarinsu don ganin ta samu lafiya.
Hankalin su Ya tashi matuƙa sun shiga matsananciyar damuwar abunda ke damun Unaisah, duk wannan abun dake faruwa Danejo da sauran Yan uwansu dake agida basu sani ba.
(Get well Soon Unaisah Angel)
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞💓💔💞🫀🌹
~✍️~
~__________________________________~
gajiya tafari yi da tsayuwa charging kwata kwata baya sauri, zama tayi gefen gadon su ta dan fara gyangyadi kafin wani lokaci bacci yai awon gaba da ita.
A hankali ya ke saukowa down ya zuba hannayensa Cikin aljihun wondon baccin sa, sam ya kasa runtsawa saboda tunanin a wani hali Unaisah take a ciki? Ta yi bacci ko idonta biyu? Ya damu sosai akan ciwonta, direct ya nufi bedroom dinsu Yana gab da zai shiga ya jiyo shesshekan kukan ta kasa kasa.
Almost 3 times yana kwaɗa sallama shiru tare da knocking door din, ba'a amsa mashi ba Har zai juya sai kuma ya kasa jurewa saboda baya son damuwarta ga kuma kukan da ya ji ta na yi.
A hankali ya tura kofar ɗakin Ya shiga da sallama abakin shi, babu wadataccen haske a dakin sai na bedside lamp da suka bari a kunne, Batool ya hango a kwance kan gadonsu tana ta sharar baccin ta ita kadai abun ta.
Wurga eye balls dinsa yai saitin inda yake jiyo shesshekar kukanta, wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi ganinta a cikin prayer corner tana a zaune kan prayer mat, jikinta sanye da dogon hijabi, hannunta ruke da prayer beads tana lazami, yayin da idanunta ke akan qur'anic stand din data buɗe.
tabbas tajiyo kamshin turaren Chief sai dai bata kawo aranta cewa shine ba kuma kwata kwata ba ta ji motsin shigowar mutum ba saboda tayi nisa a cikin ibadarta.
Unaisah ta yi Namijin kokari ba lafiya gare ta ba, amma saboda ta nema masa rahama gurin Allah yasa ta hana idonta bacci ta tsaya tsayin daka don ganin tayi masa addu'a dama alkawari ta daukar masa zata raba daren ta biyu rabi ta yi bacci rabi ta yi addu'a, samun masoyi mai sonka tsakani da Allah da zai iya yi maka addu'a batare da sanin ka ba zaiyi wuya a duniyar nan.
Hakika ta burge shi sosai, Har ya zagayo ta gabanta bata lura da shi ba, saboda ta ɗan lumshe idanunta, dogayen eye lashes din ta sun jiƙu da ruwan hawayenta.
Kyakkyawar fuskarta ta 6aci da hawayen ta, ɗaga hannayenta tayi sama Cikin harshen larabci ta fara karanta addu'o'i duk akan Danish dinta.
Lumshe idanun shi yai a hankali ya sake bude su kan fuskarta, ya jinjinama irin kaunar da take ma Danish yayi fatan ace shi ya samu soyayyarta, saboda samun mace tagari irin ta zaiyi wuya a fadin duniyar nan, yarinyar da zata iya tashi in the middle of the Night tayi nafilfili don ta yi maka addu'a Omg😘
A hankali Ya zukunna ta gefen ta, Ya zuba mata lumsassun idanun shi masu ɗauke da bacci.
Bakomai yake kallo ba fa ce eye lashes dinta da soft lips dinta dake kerma sun jiku da hawayen ta sometime har tongue take zurowa ta lashe su baisan ya akai ya tsinci kan shi da kallon ta ba.
A hankali ya mayar da eye balls dinsa kan kwantaccen gashin forehead dinta dark brown ya nannade gwanin ban sha'awa kai komai nata abun ban sha'awa ne.
Kasa yi mata magana yai cos yai tunanin she may feel uncomfortable if she sees him in front of her.
Slowly ya miƙe tare da juyawa ya nufi hanyar fucewa daga dakin
Kamar daga sama yajiyo muryarta a cikin kunnan shi"Wanene" dan dakatawa yai ba tare da ya juya ba, Zumbur ta mike gabanta na faduwa cos tajiyo motsin tafiyar shi.
waro idanu waje tay lokacin da tay arba da faffadan bayan shi, wlh sai taga kamar Danish ne yanayin tsayuwarsa banbancin Danish yafi sa tsayi da kuma doguwar sumar kai, uwa uba launin fatarsu ba daya ba.
"Wanene"? Ta ƙara faɗa cike da fargaba, gudun kada ya tsoratar da ita yasa shi juyowa a hankali suka fuskanci juna tana ganin chief tay saurin share hawayen ta saboda ya hanata kuka, tayi mamakin ganinsa a wannan lokacin a cikin dakinsu, arude ta furta"barka da dare" ya fahimci rudani dake akan fuskarta hakan yasa shi cewa"I'm sorry na shigo dakin ku batare da izninku ba, na fito ina zagayawane najiyo shesshekar kukanki, Hankali ya tashi sau uku ina yin sallama ba'a amsa min ba, har knocking nayi shiru shiyasa na yanke shawarar shigowa ciki amma ba halina bane"
Cikin sanyin murya ta furta"na fahimce ka, kuma nagode da kulawarka agare ni, ka damu dani sosai"
Sam taki bari su hada ido tun kallon farko da tay mashi ta kawar da idanun ta.
"Kin manta sharaddun da dr ya gindaya maki? I thought I would find you sleeping, although you are doing good thing, but you should continue resting until you've fully recovered, ban hana ki masa addu'a ba, zaki iya yi masa addu'a aduk lokacin da kikai sallah, amma yanzu dare ne Unaisah"
with respect ta amsa mashi da toh.
Shiru suka ɗanyi na wani lokaci, takun tafiyarsa taji da sauri ta dago matsowa yai dab da ita..
Ta sadda kanta kasa tana dan jin faduwar gaba.
In a cool voice yace"a ranar da mu ka kwana a sansanin mu, Danish ya nemi in yi masa alkawarin ko bayan ransa In kula da rayuwarki data mahaifinki da yan uwanki, and I vowed to fulfill his request"
jin wannan maganar yasata kusa fashewa da kuka jikinta ya kama kerma.
"Ban fada maki don in fama maki raunin dake a cikin zuciyarki ba, sai don inaso ki taimakamin Unaisah, Ki bani hadinkai gurin ganin na cika masa alkawarinsa, in har kika bani dama duk da ina shiga busy saboda aiki zan yi kokarin ware mana lokacin da zamu dinga ganawa da juna, in sha Allah I'll support you in overcoming the pain that's troubling you."
dakyar ya ƙare maganin ganin yadda hawaye ke yar tseral kan kuncinta aranta ta ayyana wata irin kauna Danish yakeyi mata? Ya Ilahi, Shi damuwar shi wanda zai kula da rayuwarsu in baya nan wayyo Allah hakika tayi babban rashi arayuwar ta.
batai aune ba taji safkar yatsun chief kan fuskarta gently ya soma share mata hawayen ta.
Muryarsa tamkar ta me yin raɗa ya furta"If you give me a chance, I will replace him, despite knowing I may never fully replace him in your heart" ya ɗan dakata yana mayar da numfashi, ta nutsu tana sauraron shi.
"Na riga shi sanin ki amma ya riga ni haduwa dake, nasan da ace tun lokacin na bayyana kaina agurinki da nima na samu gurbi acikin zuciyarki, sai dai kash na makaro amma har yanzu ina da sauran dama Unaisah, nasan kun shaku da juna ke da shi, kun sha wahala a tare, kun yi rayuwa a guri ɗaya, kun san sirrin juna, nikuma bansan komai dangane dake ba, amma idan kika bani dama nayi maki alkawarin zan canza maki rayuwarki...."
da wata irin siga ta jan hankali yai mata maganar, har saida taji wani irin yanayi atare da ita, kalamansa sun ta6a zuciyarta.
Ɗagowar da zatay keda wuya karan hancinsu ya gogi na juna razanar da ta ɗanyi ne yasa ta ɗaga ƙafa zatay baya aikuwa gaba daya ta tafi zata kife kasa saboda rashin kwarin jikinta.
Cikin zafin nama yai hanzarin damko waist dinta Ya janyota gaba daya ta fada kan broad chest din shi, wani irin faduwar gaba taji, She could feel his heart beating rapidly, lumshe idanunta ta danyi sam ta kasa motsawa daga jikin shi, ta rasa gane me take ji? Amma tabbas taji wani irin sanyi da kwanciya hankali yana ratsa zuciyarta.
har ga Allah bai janyota da wata manufa ba, gudun kada ta fadi yasa shi rukota sai kuma abun ya nemi ya jefasa a wani yanayi mara misaltuwa, nutsuwa yai yana kallon fuskarta tay lamo a jikin shi kamar jinjira.
Damuwar rashin Danish ta fara affecting brain din ta, komai ya faru Danish take gani a yanzu haka ji take kamar a jikin Danish ta faɗa shiyasa ta kara narke masa.
abunka ga mabukacin dake bukatar duk wani abu da zai sanyaya mashi zuciya.
"Unaisah" shiru bata amsa mashi ba.
"are you sleepy? Ya tambaya yana leken fuskarsa.
Still bata motsa ba, Batool ce ta fara mutsu mutsu kamar zata farka, hakan yasa shi raba ta daga jikin shi ya ɗan jijjigata dakyar ya samu ta buɗe idanunta wadanda suka kaɗa jawur kamar an watsa masu barkono.
"Muje ki kwanta" kamar gunki tay shiru babu alamun zata ɗaga ƙafarta, kamar bata jin me yake cewa.
Sungumarta yai kan Shoulder inshi Ya nufi bed da ita, Cikin kulawa ya kwantar da ita..
"Kada Ki kwana Da hijab a jikin ki, Ki cire sannan ki yi addu'a" sai lokacin ta dan jinjina ma shi kai.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin Yai hanzarin juyawa ya fuce daga dakin.
Sai bayan daya fitane ta samu kanta, maganganunsa ne suka dinga yi mata yawo akai a haka har bacci mai dadi yai awon gaba da ita.
"ANEELEERH🌹*
ba ita ta tashi farkawa ba sai wuraren ƙarfe huɗu na dare dayake tasa abun aranta har mafarki saida tayi, idanunta biji biji ta buɗe su ta dubi agogo, kafin ta curo wayar daga chargy harta cika, Kunna wayar tayi Haskenta na kawowa taga abunda ya karya zuciyarta hoton Ana ne da baby junaid akan wallpaper dinta sunyi murmushi a hoton.
Bata samu wayar da password ba, lalube ta cigaba dayi mata ta shiga whatsapp dinta, tana tsaka dayin scrolling ta fada Archived anan taga wani Group da Ana ta bude ita da sisters dinta,, Shiga ciki tayi ta soma karanta firarsu.
_sister, ke da kike zaune cikin rufin asirin Allah, meyasa kika ce kin gaji da zama gidan? Bayan irin sabon da kikayi da Aneelerh, gashi muma ta silarki mun samu taimako a gurin ta_
_ba zaku gane ba, Ni kadai nasan halin da nake aciki, bawai don son raina nakeso In bar gidan ba, kawai hankalina ba akwance Yake ba, ni dai kawai inaso nabar gidan ne_
_kinga in wani abu ke damunki, ki fada mana, mu nemi mafita a tare_
_kada ku ɗaga hankulanku, babu komai, kawai inaso nadinga ganinku kullum akusa dani, saboda kuka dai ne dangin da kuka rage min a duniya_
_idan kina so mu dawo kusa dake, toh ki sama mana aiki anan abujan mana, sai mu dawo, muma munfiso mu zauna kusa da ke_
_bazan bari ku dawo nan ba, sai ni kusa ma min aiki in dawo nan_
_meyasa_
_nafison zama a Jos din fiye da nan_
Dakatawa Aneelerh tayi da karanta sakon, aranta ta ayyana meyasa Ana take gudun zama abuja? Bayan kafin zuwansu tafi kowa daukin zasu dawo nan"! Girgiza kai ta danyi kafin ta yanko wata firar tasu ta ci gaba da karantawa..
_janet tace"Ana! Kina cikin hayyacinki kuwa? Meyasa kike magana kamar wata musulma"? esther tace"Na fara zarginta, cikin kwanakin nan kullum in zakiyi magana a group chat dinmu sai kin sanya mana abun addinin musulunci bayan mu ba musulmai bane_
_Voice note ta tura masu"nagaji da 6oye maku da nake yi, ku yan uwana ne babu wani sirri atsakanin mu, nasan zaku goyi bayana" su kace muna sauraronki"Na musulunta, Yau wata biyu kenan, amma babu wanda ya sani, ko Aneelerh ban fada mata ba, A boye nake yin sallah ta"_
_"Dagaske kike ko wasa" janet ce ta fada_
_"Na ta6a maki wasa irin wannan"?
Janet tace"a'a"_
_Ana Tace"toh, Dagaske nake Ana ɗinku Yanzu musulmace ni, na yi imani da Allah kuma nayi imanin cewa Jesus da muke bautamawa bawan Allah ne kuma manzon sa ne"_
Esther tace"nagaza yarda Ana, kamar dai kin haukace, taya zaki bar addinin iyayen mu da kakannin mu"?
_Dogon voice note ta tura masu mai dauke da bayanin abunda Yaja hankalinta harta musunta tace ita kawai ta kaɗaitu da son addinin musulunci saboda kyawawan dabi'un Aunty Anila, tana burgeta tana sonta tana son yadda take janta ajiki, da yadda take kyautata mata, bata ta6a nuna wariya tsakaninsu ba, tana son tayi koyi da komai nata, yanayin mu'amalarta, kyawawan halayanta, da yadda take karatun al'qur'ani, hatta shigarta ta musulunci burgeta takeyi dama kuma ta ta6a yi mata tayin addinin tun farko farkon fara aikinta gidan Uzair ta nuna bataso, tun daga nan bata kara takura mata ba, tadaice mata tayi bincike sosai akan addinin musulunci zata gane abunda take son fahimtar da ita, kunji abunda yasa na musulunta kuma sai nagane shine addinin gaskiya, kuma Inaso ku musulunta don mu gudu tare mu tsira a tare_
wani chat nasu da Anila ta duba, yan uwan Ana ne su ka yi mata voices da murnarsu suka fada mata sun musulunta, tayi murna kamar kamar me sukace ta za6a masu suna tace ita sunan data canza ma kanta sunan nana Aisha, Ita kuma janet ta sanya mata sunan Khadija, sai Esther Zainab, bayan ta raɗa masu sunan janet tace sufa ko alwala basu iya ba, bayan haka basu san komai ba, tace kada su damu zata dinga koya masu kur'ani da hadissai acikin group din nasu itama da apps na musulunci take amfani da kuma sauraran karatun malamai da wa'azinsu ta haka ta ke samun Ilmi.
Lokacin da Aneelerh ke karanta Chat din, hawayene Cike tab da idanunta, wani irin murmushin farin ciki tadinga saki kamar wata zautatta, aranta ta ayyana ashe ana ta musulunta bata sani ba? Allahu akhbar, Abunda yafi faranta ranta, hada Yan uwanta ta musuluntar.
taji dadi da Ana ta musulunta ta silar ta, A hankali ta furta"Alhamdulillah Ya Allah na gode maka..." har sujjada saida tayi.
yanzu A ina zan samu ana? Ta jefa ma kanta tambayar? yanke shawarar kiran layin Yan uwanta tayi sam ta manta dare ne ta shiga danna masu kira babu wanda yayi picking, Zuciyarta cike fal da farin ciki ta jingina bayanta Jikin gadon su, kiraye kirayen sallar asubahi da aka fara ne yasa ta aje wayar, ta mike ta shiga toilet don tayi alwala.
Bayan ta sallame sallar, ta zauna tayi addu'o'in da ta saba yi daga cikin harda Ana tayi ma addu'a sosai, kafin ta mike ta dauko wayar Ana ta koma kan gadonta, Gallery ta shiga ta dinga budo hotunan Ana dana yan uwanta.
Ta shagala tana kallon su Unexpected yatsan ta ya danno video ba tare da sanin ta ba, shesshekar kukan da tajine Yasa Ta mayar da hankali akan videon..
wani irin faɗuwar gaba taji, Lokaci daya ta zazzare idanunta wadanda bakomai ne acikinsu ba face tsantsar tashin hankali da rudani gami da al'jabi, ta yi matukar razana da jin abun da kunnuwan ta suke jiye mata, gaba daya ta rude, gumin tashin hankaline Ya fara tsastsafo mata ta ko'ina a jikin ta, kafin kace me Tsigar jikinta ta fara tashi haikam, La66anta na kerma ta shiga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allahumma ajirni fil musibati...
tsabar kiɗimar da ta yi ne Yasa tadinga sambatu kowace addu'a tazo bakinta furta ta kawai takeyi, har saida takaiga junaid dake bacci ya farka a firgice sakamakon sallallamin dayaji Mommynsa nayi.
Yana buɗe idanunshi suka sauka akan fuskar Aneelerh wadda ta jike sharkaf da gumi, Idanunta sun kaɗa jawur har wani zazza6i zazza6i take ji a jkin ta..."
Kusan sau uku Junaid yana ambaton sunanta bata ji shi ba, saboda kwakwalwarta ta tafi hutun wacin gadi, abune da bata ta6a zata ba.
"Aunty Aneelerh? Kina ina ne nake jin kukan baby junaid" muryar zahra ce ta fargar da ita, a firgice ta zabura ta sauko daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja ta rufe.
lokacin da zahra ta shigo junaid kadai ta gani zaune sai kuka yakeyi idanunshi akan kofar toilet din dakin.
da sauri ta nufe shi ta zauna gefen gadon tare da daukar shi ta rungume a kirjinta"junaid lafiya kake kuka? Ina mommyn naka kota shiga wanka ne"? Da yatsa Ya nuna mata toilet door din"nan ta shiga da gudu, inata kiran shunanta bata amsa ba..." da ɗan mamaki ta dubi kofar toilet din kafin ta maida dubanta ga junaid"i'm sorry, Yi shiru, mu jira ta fito" kwa6e fuska yayi "to ai jiya nace ta hada min tea bata kawo ba, har bacci ya ɗoke ni" kallon cup din dake ajiye kan Table tayi"Ko shi ne wannan ta ajiye maka" sai da tay maganar ya lura da cup of tea din da Aneeleeh ta ajiye.
Zahra tace"shine ma, amma naga Ya huce, Bari naje na hado maka wani hada noodles zan dafa maka"
Aneelerh dake acikin toilet tafukan hannayenta biyu toshe da bakinta gudun kada kukan ya kubce mata, tana cikin halin ha'ula in nan tajiyo muryar junaid daga waje yana kwankwasa kofar toilet din"mommyn ki fito"
gaban faucet taje ta wanko fuskarta ta buɗe kofar ta fito, a tsaye ta same shi ya ruƙe qugun shi fuskar shi a daure kamar wani babban mutum.
"Junaid, i'm sorry, jiya na kawo maka tea din sai na iske kana bacci" da shagwa6a yace"tea dinma ya huce, aunty zahra zata haɗo min wani kuma ma zata dafa min noodles..."
"Yawwa, Yanzu mu shiga toilet inyi maka brush, kafin ta dawo" amsa mata yai da toh, cikin sauri taje ta ajiye Wayar Ana Cikin rigar pillownta ta zuge ta, kafin ta dawo ta ɗauki junaid ta shiga toilet da shi.
da shigarsu ba'afi minti talatin ba, sai ga zahra ta shigo hannunta ruke da madaidaicin tray mai dauƙe da plate biyu na noodles da zafinta tare da cups of tea ta ajiye kan table din gaban gadon, ta zauna tana jiran fitowar su don taji motsin ruwa a toilet.
Wayar hannunta ta cigaba da dannawa, Har zuwa lokacin da Aneelerh ta fito bayanta a goye da baby junaid, har wanka tayi mashi ta lullu6e shi da towel dinsa.
Yana ganin abunda zahra ta kawo masa ya fara Washe baki, tun da ta fito take ta kokarin kaukauce ma zahra don kada su hada ido..
"Auntyna Barka da safiya kun tashi lafiya?
"Lafiyalou zahra, Hope kina lafiya" da fara'a tace"lafiyalou"
"Sannun da kokari zahra, baki gajiya dayi mana dawainiya" ta fada tare da daura junaid kan gadon.
"Haba Aunty Aneelerh, wata irin dawainiya"? Ta faɗa tare da mikewa ta nufi closet din kayan junaid"Yaushe zai koma school ne?
Ta fada yayin da take dauko mashi kayan da zai sanya
"In sha Allah next week zai koma"
Riga da wando ta dauko mashi, da kanta ta sanya mashi, Aneeleeh dake a zaune ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa mafaɗi a duniya
Zama zahra tayi kusa da ita, ta daura junaid kan laps dinta, tea ta fara bashi Ya shanye duka kafin ta dauki fork ta soma nannado noodles tana tura mashi abaki yana ci.
sam bata lura da Halin da Aneelerh take aciki ba, sai surutu takeyi tana fadin"Aunty Aneelerh ba zaki ci bane,? Shiru taji bata amsa bata ba, juyowa ta danyi tare da leƙa fuskar ta, gabanta ne ya faɗi ganin tsantsar damuwa akan fuskarta, idanunta sun kaɗa jawur.
Da karfi zahra ta furta"Aunty Aneelerh"! Firgigit tayi tare da kallonta razanar da tayi yasa Zahra jin fargaba.
Adabarbarce ta furta"am...um...zahra.. Har kin sa mashi kayan..." a ruɗe zahra ke kallon ta duk tabi tasha jinin jikinta..
"Aunty Aneelerh, Lafiyarki kuwa? Kinga yadda idanunki suka kumbura, kumatunki sun yi ja, kamar kinyi kuka, gaba daya ma kin sauya min kwata kwata babu nutsuwa atare dake"
dakyar ta daidaita nutsuwarta cikin sanyin murya tace"bakomai wlh, lafiyana lou, kawai tunanin duniya ne..." girgiza kai zahra tayi"wlh kallo daya mutun zaiyi maki ya fahimci baki cikin nutsuwarki, auntyna in akwai abunda ke damunki, ki fadamin dan Allah sai mu nemi mafita a tare..."
murmushi ta danyi"Zahra ki yarda kawai babu komai" gyaɗa kai tayi"shikenan, ga noodles din nan ki ci pls, kada ki zauna da yunwa ni zan tafi gurin aiki har na kusa yin late"
"Nagode da kulawarki zahra, ki kula min da kanki" tana murmushi tace"kema haka" kar6ar junaid anila tay don taci gaba da ba shi abincin.
Zahra Harta kusa ficewa daga dakin ta tsinkayi muryar Aneelerh"Uncle na nan ne"? Zahra bata kawo komai aranta ba tace"Eh, yana nan dakinsa"
"Okay, " fuce wa zahra tayi daga dakin..
Bayan tafiyar zahra, da rabin awa ta fito Hannunta dauke da baby junaid ta nufi dining area, tunkafin ta karasa ta hango mutanan gidan gaba daya sun hallara akan dining chairs zahra ce kadai babu atare da su.
tsayar da idanunta tayi akan Uncle dan iya daya hakimce kan kujera Ya ƙwama wani uban glases akan idanunsa, Ya tasa farfesun yan ciki shake da plate sai sharbar romo ya ke yi kamar ƙaramin yaro, yanayin fuskarta ne ya canza zuwa matuƙar bacin rai, fusata, da tsantsar tsana Aranta ta furta Mugu bashi da kama, Cike da rashin kuzari ta karasa cikin girmamawa ta gaishe da su da fara'a suka amsa mata, mami ta mika hannu ta kar6i junaid ta zaunar da shi kan laps dinta nan fa ya fara zuba mata shagwa6a.
Tun da ta zauna mami ta yi serving dinta duk cokali daya idan tay sai ta dago ta kalle shi gabanta sai faduwa yakeyi, hakanan yaji kamar Ana kallonsa yana kokarin dagowa tay saurin kawar da idanunta, a dabarbarce ta shiga tura chips abakinta, Mayar da kansa yai ganin ba abunda ya zata bane.
"Aunty Anila ya maganar komawar Junaid School ne? Tun da yaji sauƙi ya kamata amaida shi, karatu yana ta wuce shi"
"Zahrama ta tambayeni dazu, in sha Allah sati mai zuwa zai koma"
Mahboob Yace"Allah Yakaimu lafiya" ta amsa da ameen
Junaid dake zaune saman Laps din mami tana bashi abinci tuni ya haɗe fuskar shi muryarshi da shawaga6a yace"Allah ni bazan koma ba, dodo zai ɗauke ni in naje.." dariya su ka yi Abie yace"jikana mai abun ban mamaki! Wani irin dodo ana zaman lafiya"? Yana faman zumbura baki yace"wanda Ya kashe..." a firgice Anila tay sauri katse shi da karfi ta furta"junaid! Ya isa haka, kamanta abunda na fada maka" da sauri ya rufe bakinsa da tafin hannunsa, dariya su ka yi inka cire Uncle ɗaya wanda hankalinsa kwata kwata baya akan su, Anila kam Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba su ɗago komai ba sun maida abun wasa, agogon hannunsa ya duba kafin ya mike Abie yace"har za'a fita"?
Uncle yace" Yau hutu nake har gobe ina gida" Ya fada tare da juyawa ya nufi bedroom dinsa.
Mami tace"wai nikam Ina zahra ne? Ko har an tafi aikin"?
Ummi tace"eh tun dazu ta wuce, tazo tayi min magana cikin bacci naji ta" ummi tace"nima kam naso naji ta tana knocking yau fitar wuri akayi kenan, Abie Yace"zahra badai hankali ba, bata iya tafiya aiki batare dabi kowannan mu tayi mashi sallama ba" Mahboon yace"dama tayine don afada" dariya sukayi, Ummi tace"na fahimci kana kishi kaji an yabi zahra" ta6e baki yayi Anila dake kallonsu daya bayan daya wani irin tausayin su ne Ya kamata.
A Obie Estate kuwa, Yau shirye shiryen Tarbar baba Obie su ke yi, kasantuwar yau ne ranar da zasu dawo daga Lagos, maids din gidan tun safe suka fara gudanar da aikinsu.
Tsaye take a gaban dressing mirror tana ɗan jujjuya jikin ta, wani hadadden Saree ta sanya launin ja mai adon duwatsu sai sheki suke, yayi bala'en yi mata kyau kamar amarya, ta zuba adon Zabba da awarwaro a hannayen ta, ga wasu jerin gemstone necklaces a wuyanta masu daukar ido, ta saki doguwar sumar kanta a abayanta baka wulik sai sheki take, A hankali take kokarin gyara Earrings din dake a kunnanta, yayin da idanunta ke kallon cikin madubin, Ita kanta ta yaba da haɗuwarta, Sareen jikinta ya nadu sosai ya zauna mata, ɗan light makeup tay akan fuskarta tayi kyau, daddaɗan ƙamshin turarenta dana bakhhoor burner din data Kunna Ya gauraye iskar ɗakin da wani irin kamshi mai dadin shaka.
Murmushi ta dan saki har dimple dinta Ya lotsa, ta fito sak ba'indiyarta ta usili, wani irin annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskarta, bakomaine yasa ta farin ciki ba face murnar dawowar Pravin Jiya sunsha waya da shi yana fada mata irin kewarta da yai yace mata ta shirya mashi kanta don idan ya dawo sai ya fanshe kwanakin da baya nan.
Cikin harshen indianci ta furta"Ina jiran ƙarasowarka my lovely husbad"
ta faɗa tana yar dariya.
High heels ta ɗauko ta zura a kafafunta ta fito ta nufi kitchen don ta duba masu aikin gidan.
*HAJIYA SARATU*
Tana a kwance kan katafariyar bedmatress dinta tayi nisa a baccin ta, Ta wawware kafafuwanta daya tay dama daya tay hagu sai jan minshari takeyi, Sleeping gown ce a jikin ta, zanen kitson da ke akanta ya kara fiddo da kyawun fuskarta duk da babu annuri akanta.
Iphone dinta dake ajiye saitin kunnanta ce ta fara ruri da karfi sautin ya addabi kunnanta, har saida ta fara kokarin farka cikin magagin bacci da bacin rai ta dinga katse kiran almost 4 times a na hudu ne ta fusgo wayar ta kara kunne rai a6ace ta furta"wai wanene ke son takura mini ne"?
"Jatuminki ne" ras taji gabanta Ya fadi jin muryar baba Obie, a rude ta zabura ta miƙe fuskarta ya amutse cike da jin nauyin furucin da tay sam takasa magana saboda kunya.
Murya na rawa ta furta"baba i'm sorry, wlh bansan na furta ba, Kiran wayarka ne ma ya tashe ni daga bacci bansan kai bane ka kira..."
bata kare maganar ba ya katse ta"Auta Ko da bani bane abun da kikai ya dace? Idan abokan aikin ki ne fa"?
"Baba ka gane mana, daga bacci na tashi, ban gama wartsakewa ba"
"Pravin bai fada maki yau zamu dawo bane"? Yamutsa fuska tay"ya fada min"?
"Shi ne kuma kike ta baccin asara, ba zaki tashi kije ki gyara kanki ba"?
Haɗe rai ta yi "baba wani irin gyara kuma"?
sautin dariyar shi tajiyo"its Okay, yanzu haka muna akan hanyar zuwa airport"
"Okay, zan zo in tarbe ku, Yanzu zan shirya Allah ya kawo ku lafiya" ya amsa mata da Ameen kafin sukai sallama.
Saukowa tay daga gadon tana ƙuƙuni kan maganar gyara da baba obie yai mata.
"Haba Akan me zan takura kaina, Gyara ya wuce mutun Ya dawo ya iske iyalinsa daya bari cikin koshi lafiya, Nifa ba baiwar Namiji bace ehe.." ta ƙarashe kukunin tare da bude toilet door ta shige.
Lokacin da ta ƙaraso Kitchen din kamshin abinci ne ya daki hancin ta har can cikin makoshinta kamshin ya ratsa.
Sam basu lura da zuwanta ba, gaba daya Hankulansu na akan girke girken da sukeyi.
Gyaran muryar da tay masu"Aikinku na kyau" atare suka dube ta, kamar yau suka fara ganinta tayi masu kyau, murmushi suka saki tare da gaishe da ita cikin girmamawa, da fara ta amsa masu.
"Ya kamata kuyi sauri ku kammala, sun kusa karasowa"
Sofia tace"in sha Allah kafin su karaso zamuyi kokari mu gama"
Hajjaty tace"yanzu dame dame ku ka kammala"? Safa ce ta lissafa mata.
"Okay, naji kince hada dambun Nama, pls Ki dan zuba min shi tare da juice, wlh yunwa nake ji" ta fada tana shafa cikin ta, dariya sukai cikin raha tana lura da satar kallonta da sukeyi tasan da wuya in basuyi gulmarta ba kamar ko ta sani gulmace ke cin su.
Bayan Safa ta zuba mata dambun naman a plate ta haɗo mata da glass na juice a kan madaidaicin tray ta daura mata tare da muka mata tasa hannu ta kar6a tare da yi mata godiya ta juya ta fuce.
fitarta keda wuya Abla tace"wannan gayu haka hajjaty, Kamar wadda zataje gasar kyau"? Ta fada baki asake, sofia tace"ni dai wlh tana burgeni, inason mace mai tsafta da iya daukar wanka, amma abunda bangane ba Wa takeyi ma kwalliya ne? Naga dai ba wani guri take zuwa ba kullum tana a gida"
"Kun cika sa ido, Nifa bansan gulma wlh, naga dai ba yau ta fara yin kwalliya ba" safa ta fada tana jifarta da harara.
"Ba yau ta saba ba amma na yau yasha banban, yau fa baba Obie da pravin zasu dawo meyasa zata ca6a adon nan sai kace wadda zata tarbi Mijinta, ko dai hajiya saratu batay gayun nan ba bana tunanin ma ta tashi daga bacci, sai ita zakakka abun nata na nema ya wuce gona da iri ya kamata ta tsaya a matsayinta na yar aiki" Ta kare maganar tana hura hanci
Fashewa sukayi da dariya..
"Pls Ya isa haka Sofia, nasan meke damunki, Bakin cikine da hassada, Saboda kinga hajjaty Allah ya zuba mata ruwan kyau gashi tafi ki matsayi shiyasa kike kishin ta"
tsoki Sofia taja"Allah ya kiyaye inyi mata hassada Ni kawai na fara zargin akwai wanda takeso ta mallaka agidan nan shiyasa take caba ado nan don taja hankalin sa, In kuwa hakan ta faru mu zamu zama bayinta, kuna gani dai haka Harriet ta aure Sir mubarak to wai mu ko bamu da farin jini ne a gurin mazan family din nan" ..fashewa sukayi da dariya.
"Duniya tayi maku dadi, wato Na lura gaba daya kun manta da marwa" acewar Abla, Atare suka hada baki gurin furta Alah sarki marwa ko awani hali take? Safa tace"jiya nayi waya da innarsu ta fada min jikin nata da sauki har ta fara kokarin yin magana"
Sofia tace"baiwar Allah tadaiji jiki sosai, Alah ya bata lafiya, ko ta samu ta dawo bakin aikin ta, In sha Allah nima da anjima zan kira inji ya jikin nata"
_____________________________________✍️
A hankali take tafiya cikin takun dattako, wata hadaddiyar egyptian abaya ce a jikinta mai tsadar gaske, tay rolling head scarf, yayin da Idanunta ke amanne da farin glases, Ko hoda bata shafa ba amma ba ƙaramin kyau ta yi ba, hannunta daya na a ruke da purse dinta, ga wani daddadan fragrance dinta dake tashi.
Har zata gifta idanunta suka hango mata hajjaty, wani uban burki ta ci ganin yadda ta caba ado kamar wata amarya.
"Ke zonan" ta fada da ɗaga murya, hajjaty bata san da zamanta ba, har takusa shiga part dinsu na maids ta tsinkayi muryar Hajiya saratu rass taji gabanta Ya fadi arude ta juya tana kallon ta, da hannu tay mata alamar tazo.
Hankalinta ya tashi don tasan kiran hajiya saratu ba alkhairi bane.
Jiki asanyaye Ta nufe ta aranta tana ta ambaton la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin.
Koda ta karasa nesa da ita ta tsaya cikin sanyin murya tace"gani aunty saratu" harara ta galla mata har saida tasha jinin jikinta.
"Uban wa kikai ma wannan adon"? sunkuyar da kanta kasa tay, aranta ta furta"mijinki nayi mawa, a fili kuma tace"Aunty, kamar dai yau kika fara ganin nayi kwalliya"? Ji tay kamar ta kwasa mata mari saboda fusata"karki kuskura ki kara kirana da sunan aunty, in banda munafurci sai da kika saisaici ranar da kikasan mijina da baba zasu dawo tukunna kika caba adon nan ko? A cikin su wa kikai mawa"? Ta fada tana cije lips dinta hadi da matsowa kusa da hajjaty, jikinta sai kerma yake tray din hannunta kamar zai kife kasa, Cikin rawar murya tace"Allah shine shaidata, Ni banyi kwalliyar nan don daya daga cikinsu ba, nayi ne saboda in burge kaina" idanunta cike tab da kwalla ta kare maganar.
Da hannu hajiya saratu ta cafko pallu din sareen data laga kan kafadarta..
Ta soma goge mata kwalliyar fuskarta ran hajjaty ya 6aci sosai duk ta cabe mata kwalliyarta.
Murmushin mugunta hajiya saratu ta saki da alama ta manta da abunda hajiya laura ta fada mata"Idan kin koma ɗaki, Ki cire sareen nan, Yau nafi son naganki cikin uniform na ma'aikatan gidan nan fatan kin fahimce ni" jinjina mata kai tay"Toh"
"Yawwa zaki iya tafiya" har zata juya ta kuma kiranta
Da yatsa ta nuna tray din hannunta"meye a ciki"?
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"dambun nama ne"
"Samun wuri, Wato ke har kin riga masu gidan dandana girki ko? Ta fada tare da kai hannu ta buɗe plate din Ta duma hannu ta dibi dambun naman ta tura abaki tana tauna, bakinta a cunkushe tace"kafin in dawo kisa a shirya min Lunch dina, komai da aka dafa za'a zuba min.." ta fada tare da kara dumbuzar dambun naman ta tura abaki, kafin ta dauki Juice ta kur6a, duk hajjaty tana atsaye tana kallonta.
Tsoki taja"duk na bata hannuna da maiko ni da zanje airport tarbo mijina" cikin sanyin murya hajjaty tace"yakamata ki wanke" ta fada tare da nuna mata Sink din dake a kusa da in da suke.
harara ta galla mata"nifa komi zakiyi ba zaki taba burgeni ba.."
Ta fada tare da zaro hanky daga purse dinta ta mutsustsuke hannun dashi duk don kada hajjaty taji dadin ta bi shawarar ta, juyawa tayi ta nufi hanyar fita daga falon.
Binta da kallo Hajjaty tayi har ta bace ma ganinta, murmushi ta saki ta danyi mamaki da ta ci abun hannunta musamman a kwanakin nan data lura kamar batason ko hanya su hada, tabbas ta bata mata rai amma har yau Allah bai sanya mata tsanarta ba, Ita dai tana so su dinga mutunci da juna.
Juyawa tayi jiki asanyaye ta nufi dakinta.
kaitsaye hajiya saratu ta nufi hamshakiyar motarta, a hanzarce Officern da zaiyi driving dinta yai hanzarin bude mata cardoor har ta zura kai zata shiga muryar Twins ta katse mata hanzarin ta"Mommy" gently ta juyo tare da kallonsu, yayin da suke fitowa daga Entry hall sun dauki wankan suit kamar a turai.
Murmushi ta sakar masu, Suna karasowa ta haɗa su duka tayi hugging dinsu gwanin ban sha'awa..
Bayan sun gaishe da ita ta amsa masu tare da cewa"my twins Ina zuwa haka? Yau dai ba aiki na sani ko za'a fita yawon bude ido ne" zaid yace"No, daddy ya fada mata time da jirginsu zai karaso shiyasa muka shirya don muje tarbo su"
"Kunyi tunani mai kyau, Nima yanzu haka airport din zanje, me zai hana mu shiga mota dina"
Bayan sun shiga suka sanyata tsakiya suna zaune a gefe da gefenta.
Sai da motarsu ta haura kan titi kafin ta dubi zayn"ya zahra? Two days ban tuntube ta ba, amma nasan kai kana waya da ita"
yamutsa fuska yai a dakile ya furta"may be tana lafiya" wani kallo ta wurga mashi"oh baka da tabbaci ma? Thats mean baka kiranta awaya"!
"No ba haka bane mommy, Kinsan yanayin aikina bakasafai nake samun lokacin yin waya ba" girgiza kai tay"banji dadi ba, yakamata kana bata kulawa zayn, nan bada jimawa ba zata zama matarka" daure fuska yai, zaid sai faman kunshe dariya yakeyi..
"Mommy hannunki kamshin nama yakeyi ko hancina ne" Ya fada tare da ruko hannunta Yakai saitin hancin shi yana shinshinawa.
"Kai Zayn Allah ya wadaran naka ya lalace, ka cika sa ido" ta fada tare da dago purse din hannunta, ta kwala mashi akai" dariya suka sanya gaba dayansu da alama dai suna acikin farin ciki.
__________Hajjaty___________
Bayan da ta dawo daki, zama tayi daga gefen gadonta, ta ajiye din akan table din gabanta, A tsanake ta fara cin dambun naman fuskarta dauke da murmushi wato abunda hajiya saratu tay yabata dariya, aranta ta ayyana in da ni muguwace kamar yadda kike fadi wlh da abinci kadai zan iya kashe ki saratu.
Wayarta ce ta soma ringing, tayi azan Pravin ne cike da zumudi ta janyo wayar daga kan pillow ganin ba pravin bane yasa murnar ta koma ciki amma taji dadi data ga kiran daga kayin marwa ne.
Picking call din tay tare da kara wayar a kunnnata.
"Ina wuni inna, ya jikin marwan"? Bata kare maganar ba, Muryar Marwa ta katse ta da cewa"Aunty Hajjaty Nice marwa dakai na"
Da mamaki ta furta"Wai dagaske Marwa kece? Allahu akhbar amma natayaki murna naji dadi da bakinki Ya bude Marwa Ya jikin naki"
"Da sauki, yatsun hannayena ma sun warke har abinci Ina ci dakaina" tsantsar farin ciki ne Ya cika hajjaty"Alhamdulillah Ya Allah mungode maka, Allah ya kara maki Lafiya marwa, Allah ya kara tsare ki daga sharrin Aljanu".
"Ameen aunty, nagode da kulawarki agare ni" shiru sukayi na dan wani lokaci kafin hajjaty tace"kinji kwana biyu ban kira na tambayi lafiyarki ba, wlh na shiga busy ne amma kina araina, bari na hada ki da su Abla ku gaisa" har ta yunkura zata mike Marwa tay saurin katse mata hanzarinta"Aunty akwai wani abu da nake son fada maki sirri ne" jin wannan maganar yasa hajjaty ta koma ta zauna ta nutsu tana sauraronta.
"Kiyi hakuri ki yafe min, Abunda ya faru dani hakkinki ne ke bibiyana, baki min komai ba, amma saboda kwadayin abun duniya na rufe ido na kar6i tayin aikin leken asiri da aka sani akanki" wani irin faduwar gaba hajjaty taji gaba daya tabi ta rude murya na rawa tace"ban.. bangane me kike nufi ba!"
Marwa bata boye mata komai ba ta sanar da ita zargin da hajiya saratu takeyi akanta da kuma aikin data bata don tayi mata leƙen asiri don ta gano me take kullawa.
"Marwa Dama kece kike tsoratar dani"?
Cikin shesshekar kuka marwa tace"wallahi nice, nayi danasani hajjaty, baki min laifin komai ba hasalima kin kaunace a lokacin da wasu ke kyamatata, da zuciya daya kikai jinyata, na dade banga mace mai kyakkyawar zuciya irinki ba, kina da hakuri ga son taimako...."
kasa karasa maganar tay saboda kukan daya kwace mata.
Zafafan hawayene suka wanke fuskar hajjaty tabbas hankalinta ya tashi da jin abun da hajiya saratu tasa ay mata ashe tsanar da tay mata har takai ta sa adinga bibiyarta? Laifin me tay mata?
Numfasawa tay kafin ta furta"marwa ki daina kuka, wlh na yafe maki, har ita hajiya saratun, Allah ya yafe mana baki daya, kuma naji dadi da kika gane kuskurenki"
Bayan Marwa ta tsagaitawa da yin kukan tace"bawai iya wannan ne abun da na kira in fada maki ba..."
A kagare hajjaty tace Ina sauraron ki marwa.
"Bansan ya zaki ɗauki abun ba, amma kiyi hakuri ban fada maki don in tada maki hankali ba face sai don In ceto rayuwarki saboda Kyautatamin da kika yi, Da farko nayi danasanin aikin da hajiya saratu ta sakani amma daga baya Naji dadi saboda silar aikin Allah ya nuna min wani mugun abu dake rayuwa agidan nan" Yawu hajjaty ta hadiya kutt zuciyarta cike fal da fargaba ta furta"marwa menene? Fada min dan Allah!
Numfasawa marwa tay kafin ta daura da cewa"Aunty PRAVIN shine silar ciwo na, Saboda Ya gano nice nake yi maku leken asiri shine Ya daura mini cutar kuturta Ya toshe min bakina"
bata kare maganar ba sakamakon tsawar da hajjaty ta daka mata"Ya isa marwa! Bana son karya ki rasa wa zaki wa kazafi sai pravin? Taya pravin zai iya daura maki ciwo? Sai kace dai Aljani"!
"Saboda shi din mugun matsafine, kece bakisan wanene Pravin ba, tun farkon fara aikina gidan nasan munanan dabi'unsa, Ya saba Bibiyar mu yana laluban jikinmu dayi mana barazana akan in muka tona masa asiri zaisa a koremu daga aiki....."
wani irin faduwar gaba hajjaty taji daram dararam kamar ana mata luguden ta6are a kirjinta, Jikinta sai kerma yake kaf kaf idanunta azazzare cike da tashin hankali wlh ji take kamar a farmaki sam takasa yarda da maganar marwa taya ma wai pravin dinta zay aikata hakan?
"Naji kin shiru, dama nasan ba lallai ki fahimce ni ba, amma ki sani wlh rantsuwar dan musulmi ba kazafi nayi masa ba, Halinsa ne, a daren ranar dana tashi da ciwon kuturta shine mutun na karshe daya shigo dakina, bayan na fito daga wanka naje gaban madubi kwatsam na hango mutun abayana ya goya hannayensa akan kirjinsa a razane na zabga salati na jiyo na dube shi nace pravin taya akai ka shigo dakina bayan na kulle kofa? Yana dariya yace min Nice na kira shi, daban shiga gonar shi ba da abunda zai kawo shi dakin, Hankalina ya tashi nayi azan yazo ya yi min abunda ya saba yi mana ne amma sainaga akasin haka yana matsowa kusa dani naja da baya har saida ya kure ni jikin bango, Ina zare ido nace in har bai fita ba, zan yi ihu in tona ma shi asiri kowa yasan ya shigo dakina still yana dariya yace ko nayi ihu abanza babu wanda zaiji, da naga bani da wata mafita yasa na fara rokon shi akan kada ya ta6a ni yace shi ba wannan ya kawo shi ba, yana so in fada masa wanene ya sanyani aikin yi maki leken asiri? Nayi mamaki jin yai magana akanki saboda ni a iya sanina farko daya kawo ki gidan nan ya kira ki da sunan yar uwarsa marainiya wadda ta rasa mijinta bai ma nuna kina da mahimmanci agare shi ba, A lokacin sai nace mashi Meye alakarka da ita? Kuma taya kasan Ina yi mata leken asiri? Yace saboda ke matarsa ce, maganar taya akai yasan ina yi maki leken asiri bata shafeni ba kawai yana son yaji waya sanya ni, na watsa mashi harara nace Munafukin banza wlh saina tona maka asiri agurin hajiya saratu, maciya amana, yace taya za'ay in tona mashi asiri Ina tunanin zai kyale ni ne bayan nasan sirrin shi, injira inga abunda zai faru dani, yana fadan hakan Ya juya ya fuce yana huci, bayan fitarsa na fara zumudin gari ya waye saboda na kudiri aniyar da sassafe zanyi sammako inje in fadawa hajiya saratu alakar dake atsakaninku dama abunda nake nema kenan"
Ta dan dakata da bata labarin tana mayar da numfashi kafin ta daura da cewa"Aunty kwatsam tsakar dare ina tsaka da bacci na fara jin yatsun hannayena sunayi min kaikayi, a furgice na farka ina kikarin motsa labbana naji sunki budewa aunty adaren ranar naga bala'e ban kara komawa bacci ba....."
kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota..."
Tunda tafara labarta mata abunda ya faru gaba daya Ta rude tabi ta rikice ta rasa tunaninta, ta razana matuka idanunta azare take jujjuya eye balls dinta, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata akan goshin ta..wa'iyazubilla bata san sa'adda wayar ta zame daga hannunta ta fada kan floor.
fadawa tay kan mattress Ta lumshe idanunta da suka kaɗa jawur, Hakika hankalin ya tashi Ahakama bata gasgata maganar Marwa ba, saboda ta yarda da pravin ta cikin sauki bazata yarda don afada mata wani mugun abu daya shafe shi ba, Ita tasan wanene Mijinta, In har bashi ya bude baki ya fada mata da kanshi cewa ya aikata ba to ba lallai ta yarda ta cikin sauki ba, kawai tayi believing marwa karya takeyi mata sai dai abu daya dayasa ta jin farga harya haifar mata da kokwanto shine taya akai Marwa tasan akwai aure a tsakaninta da pravin❓
Fashewa tayi kuka tana fadin wallahi karyane, Ni nasan wanene Mijina, pravin ba matsafi bane, kuma baya bin mata, sharri ne kawai akeso ayi masa wlh marwa dana san zaki fadamin wannan maganar da banyi jinyarki ba saboda ke din ba mutuniyar kirki bace, Makira algunguma kawai kinaso ki shiga tsakanina da mijina ne..." kamar mahaukaciya ta dinga sambatu tana bubbuga mattress da hannayenta gashin kanta duk ya hargitse..."
_________________________________✍️
*Chief Owais🔥🌹*
Time da motarshi ta kunna kai cikin gidan baba Obie, tunkafin SA din dake driving dinsa yayi parking Idanunsa suka sauka akan Security details din daddynsa ta window glass din motar yake hango su, sunyi tsayuwar dakaru agaban dankara dankaran motocin su.
Tuni yanayin fuskarsa Ya canza zuwa tsantsar bacin rai, yanzu baida abu mafi tsana a duniyar nan daya wuce mahaifinsa! Baya son ganin shi, ko sunan shi baya son ji, yanzu har takaiga ba zarginsa yakeyi ba tabbaci yake da shi akan cewa yana ɗaya daga cikin Elders na gidan kurkukun ƙaddara shiyasa kwata kwata yanzu baya jinsa amatsayin Uba, Ya toshe duk wata hanya da zata hada su, yanzun ma daya san yana agidan da baizo ba.
Fitowa Yayi daga Cikin Motar, Farar jallabiyace a jikin shi ya naɗe kanshi da arab turban saboda baya son wani yaga raunin dake akan goshinsa, saboda baya son ya daga masu hankali, Walking slowly Ya nufi main palour, with respect maids din dake sintiri suke gaishe da shi bai ko kula su ba ya nufi part din baba Obie tunkan Ya karasa Ya dinga jiyo muryoyin Uncles dinsa suna fira cikin raha ..
Knocking door din yayi,"wanene"? Hajiya saratu ce ta tambaya daga cikin dakin.
"Owais ne"
"Okay, Come In" tura kofar yayi tare da sa kai Ya shiga da sallama abakin shi, kusan a lokaci daya suka dube shi.
baba obie yana daga kishindige kan Tattausan Rug Ya tada kansa saman Pillow, daga gaban shi wooden tray ne na fresh fruits da aka kawo ma sa, Hajiya saratu ce ka bashi Kayan marmarin a baki Yana sha.
yayin da Senate Lateef da Sir Mubarak suke a zaune kan Sofa, Mai girma sharafudeen Yana a zaune kan arm Chair, Ya dauki wankan suit...
"Zauna mana," Hajiya saratu ce tay maganar ganin yayi tsaye kamar mai nazarin wani abu.
A hankali Ya zauna cikin girmamawa Ya gaishe da su, da fara'a suka amsa mashi, kafin ya matsa kusa da baba Obie ya sumbaci forehead dinsa.
"Sannu da dawowa baba, Ya gajiyar tafiya"? fuskar baba Obie da murmushi Yace"Yawwa shalelena, gajiya tabi jiki musamman da na ga rabin raina" dan murmushi yayi"nayi kewarka, bayan haka Naji dadi da Allah ya dawo min dakai cikin koshin lafiya" still fuskar baba obie da murmushi yake kallon shi, Har cikin ran shi yaji dadin maganarshi.
Tun shigowarshi bai bari sun hada ido da daddynsa ba, shi ko Ya kura masa ido fuskarsa ba walwala ganin yanda Owais yaba banza ajiyar shi, Ko irin gaisuwar nan da suka saba yi in suka hadu da juna baiyi mashi ba, hakan ya jefa shi a yanayi na damuwa.
Hajiya saratu tace"owais ina ka shiga ne? Kusan two weeks bama ganin gifcinka, ko an kira ba'a samunka"! Senate yace"abunda zance kenan, Kwata kwata baya leƙo mu, ko dan kaga kakan naka baya nan ne? Dama albarkacinsa muke ci halan"
"Ba haka bane, wlh kuna araina, aikine ya boye ni"
Sir mubarak yace"kufa haka kuke dakai da dan uwanka baku da magana sai ta aiki kamar agogo bakwa gajiya" dan murmushi yayi Baba Obie yace"karfa ku takura ma shi tom, in ba haka ba yanzu zan kora ku waje, kowa Ya kama gabansa kubarni da abun kaunata"
dariya suka sanya banda mahaifinsa wanda ya zabga ubam tagumi.
"Baba Ya aminin naka, na lura kaji dadin zama agurinsa, kai da kace zakai 3 weeks sai ga shi har ka kara kwanaki akai" yar dariya yayi Owais"ba zaka gane ba, wlh kamar kar mu rabu, dakyar fa escords dinshi suka rabamu a airport, wlh har kwalla saida na zubda saboda tausayinshi daya kamani"
dakyar ya kare maganar, kwalla cike tab da idanunshi.
Jikinsu duk yayi sanyi, tausayin baban nasu Ya kamasu
Sir mubarak yace"har yau har gobe ina mamakin amintakarku baba, na dade banga abokai masu rukon amana da kaunar juna, da suka taso tunkuruciya batare da wani abu ya raba su ba irinku, Ina alfahari da ku, Allah ya ƙara dankon zumunci atsakaninmu da shi"
kalaman Sir Mubarak sun faranta ranshi da fara'a yace ameen
Senate Lateef Yace"baba mezai hana ya dawo nan mana, tunda shi ba iyali gare shi ba, a legos dinma ba wani dangine da shi ba, kai kadaine dai danginsa" numfasawa baba Obie yai kafin yace"ba yadda banyi da shi ba akan ya dawo nan mu zauna, amma yaƙiya shi dai yafi sha'awar zaman legos, hada sabo ke dawainiya da shi amma in sha Allah idan ya halarci family meeting din da zamuyi zanyi kokarin jan hankalinshi akan Ya dawo nan din.."
"Ina pravin dinne? Ina so inyi mashi bangajiya" chief ne ya fada, hajiya saratu tace"Yana adaki"
"Okay, ya fada tare da kallon Sir mubarak"Uncle, Ina zaki? Tsawon kwanaki banji duriyarsa ba, ko na kira bana samun layin sa"
"Ay Zaki tun satin daya wuce suka koma canada.." hajiya saratu tace"ba sallama"? Ta fada ranta adan bace.
Senate Yace"gaskiya ba a kyauta mana ba" Sir mubarak yace"kuyi hakuri, ai ba jimawa zaiyi ba, Idan za'ayi family meeting zai halarta ne"
gaba daya hankalin sharafuddeen baya atare da su, bawan Allah Hankalinsa na akan dansa dake ta kakkauce masa..
"Baba Ina neman alfarma, agurin kowannanku" acewar Chief, gaba daya hankalinsu ya dawo kanshi..
Baba Obie Yace"ina sauraronka fadi kaitsaye"
Shiru ya ɗanyi jimm kafin ya ce"inaso a yi family meeting a ranar birthday dina"
da dan mamaki suke kallon shi, basu ta6a canza date na family meeting din su ba.
"Alfarma nake nema, Idan kowa Ya amince min, amma idan bazai yiwu ba, ba damuwa"
Numfasawa baba obie yayi tare da cewa"owais, wannan ai ba wani abu bane, canza date bazai zama matsala ba, nidai bani da damuwa na amince maka, sai dai bansan ra'ayin iyayen naka ba" ya fada tare da nunasu da hannun shi.
Hajiya saratu tace"haba bakomai wlh, nidai na amince masa"
"Nagode Auntyana" murmushi tasakar mashi
Senate lataeef Yace"ka yi tunani mai kyau owais, kaga kowa zai halarci birthday dinka har ma wadanda basa kasar saboda family meeting, Nima ta bangarena na amince"
fuskarshi asake Yace"nagode Uncle senator" ya maida dubansa kan sir mubarak wanda ya hade rai
"Thats impossible, akan me za'a canza date da aka saba yin family meeting saboda kai? Gaskiya ni ban amince ba," hankalin Chief ba karamin tashi yayi ba, hatta sauran Uncles din nasa sunyi mamakin maganarshi haka baba Obie ma baki asake yake kallon shi, cikin sanyin murya chief yace"Shikenan, tun da baka amince ba, na hakura nima abarshi a kwanan watan da akeyi" dariya Sir mubarak yayi"zolayarka kawai nakeyi, kasan ni bani da matsala Owais, tun da har baba ya amince nima na amince maka, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya" sanyine ya ratsa zuciyar chief cike da jin dadi Yace"ameen Uncle dina thank you"
"Sharafuddeen Me ke damunka ne"? Muryar Baba Obie ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula, murmushi ya kakaro kan fuskarsa babu komai baba,"
"Ina fata kaji alfarmar da ɗan naka yake nema agurinmu"? Jinjina kanshi yayi"naji baba, Allah ya nuna mana lokacin" iya abunda ya furta kenan.
Wayar Chief ce tayi ringing, mikewa yayi da sauri Yayi masu sallama Ya fuce daga dakin don Ya daga kiran da aka yi mashi..
Bayan ya kammala yin wayar juyawar da zaiyi keda wuya yayi arba da daddynsa bawan Allah fuskarsa A yamutse yake duban shi.
"Owais, Laifi me nayi maka? Meyasa kake guduna ko kallona baka son yi? Why Owais kayi blocking duk wata hanya da zan iya magana dakai" ya fada amarairaice.
kallon tuhuma Owais Ya doka masa da kakkausar murya yace" ka daina boye true colour din ka, yanzu na riga da nasan ainihin wanene kai! kuma wlh alwashi na dauka saina tona maka asiri kowa yasan abunda kake aikatawa..."
waro idanu waje mai girma sharafuddeen yayi da tsantsar rudani akan fuskarshi yace"owais wannan wani irin zancan banza ne? wani irin asirine kake ikirarin zaka tona min"?
Banza yayi dashi bai tanka ma shi ba, matsawa Yayi kusa da shi"owais Ka fadamin dan Allah, me na aikata? Idan ma saboda Sleeping pill din dana bakane yasa kake zargina wlh banyi da wata manufa, nayi ne saboda naji tsoron in rasa ka"
harara Chief Ya galla masa, ji ya ke kamar ya shaƙe wuyan uban nasa saboda tsanar da yayi masa.
Hannu yakai yana kokarin ta6a turban din dake akansa da sauri Owais Ya cafke wrist dinsa a tsawace ya furta"Don't even think about touching me, or you'll face unforeseen consequences"!
Hankalin Sharafudeen ba karamin tashi yayi ba, He couldn't believe that wai owais ne ke yi masa magana kamar zai doke sa? Babu tausasa harshe? Anya bai fara shaye shaye ba? Ko dai har yanzu ƙwayar maganin bancin daya bashi ce ke aiki ajikin shi❗❓
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹
~✍️~
~______________________________________~
Cikin sanyin murya ya furta"Owais, bayan dana hana ka zuwa kai farmakin sai da kaje ko? Ka daina jin magana ta Owais! " ya faɗa idanunsa akan ciwon goshinsa daya ɗan leƙo batare da saninsa ba.
"Lafiyata bata shafeka ba! Kuma Daga Rana Irin ta yau babu ni babu kai! Ni ba dan ka bane, kakane shine mahaifina mutumin kirki ba irinka ba, Kuma na rantse ka jira ka gani..."
yana ƙarasa maganar Ya jefar da hannun sa daya ruƙe, Ya juya azafafe Yabar Part din Ko sallama bai je yayi ma baba Obie ba.
Ya tafi Yabar Sharafudeen cikin rudani, bai taba zaton owais zaiyi masa haka ba, Kai ko a mafarki, Ji yayi bazai Iya jurewa ba, Cikin sauri Yabi bayanshi Yana fitowa Ya hango Motar Owais dake fita, da sauri ya nufi Security Details dinsa tunkafin ya karaso suka bude mashi cardoor din motarsa Ya shiga ciki, ya basu Umarnin su kai shi Gidan owais.
Chief yana zaune seat din baya na motar, ya rufe gefen fuskarsa da hanky, Idanunsa sun kaɗa jawur, bai ta6a karaya da rayuwar duniya ba irin wannan karan yayi fatan ace ba'a halitto shi acikin ta ba, wai mahaifinsa matsafi ne! fasiki mai shan jini da cin naman mutun, Ya Ilahi!
"Sir, motocin mahaifinka suna abiye da bayan mu" SA din dake driving dinsa ne yayi maganar, aransa ya furta wato mutumin nan saida ya biyo ni!
Motarsu na shiga main gate na villa dinsa Ya ba Security officers Umarnin karsu kuskura su bar kowa ya shigo gidan.
Bayan ya fito daga Motar, Cikin sauri Ya Part dinsa Yana kokarin Haura wa kan stairs Unexpectedly muryar Shi ta katse hanzarinsa"Owais? Lalacewar taka har takaiga ni kake bada Umarnin a hana shugowa gidan ka"?
Dafe kanshi yayi da hannu ɗaya wani irin kululun bakin cikine Ya tokare makoshin shi Ya tsani jin koda muryarsa.
a cikin kunnansa yake jiyo takun tafiyar shi bai motsa ba har ya karaso ya zagayo ta gaban shi suka fuskanci juna.
Gabansa ya dan fadi ganin hawaye na sintiri kan kuncin mahaifinsa.
Cikin raunanniyar murya yace"owais, Dan Allah ka fadamin Laifin me namaka? Wlh Hankalina bazai ta6a kwanciya ba in har baka fadamin ba..." Zuciyarshi taso ta karaya, amma In ya tuna wanene Mahaifinsa nasa sai yaji kamar ana kara rura wutar ƙiyayyarsa a zuciyarshi.
Bai ko kula shi ba, Ya nemi ra6awa ta gefen shi zai wuce, cikin sauri Sharafudeen Ya damƙi Arm dinsa.
Cikin karyayyar murya yace"Owais, in har ba so kake zuciyata ta buga in mutu ba, ka fadamin laifin me nayi maka da yaja har kake zargina! wai ni owais, mahaifinka"!
Kallo mai cike da tsana Chief Ya watsa mashi kafin yace"kafi kowa sanin laifin da ka aikata min, zaifi ka fita sabgata, don bazan taba fahimtarka ba, kawai ka jira lokacin da zan fallasa asirinka a bainar jama'a.."
ya faɗa tare da bangaje hannun sharafudeen Ya kara gaba Ya shige part dinsa Yayi locking room door dinsa rai a6ace.
A bangaren Mai girma sharafudeen Kasa motsawa yayi, al'ajabi da bakin Cikin maganganun da Owais ya gaggaya masa sun ruƙe zuciyarshi tamau sun hana kafafunsa motsawa, Ya rasa ya zaiyi bai ta6a sanin Owais yana da kafiya da taurin kai ba Sai yau da Allah ya nuna masa, tunani ya soma yi waya kamata Ya kira ya fada masa halin da yake a ciki!.
Tsadaddar Wayarsa Ya zaro Ya daga aljihu ya shiga call logs Ya danna ma Number din da yayi saving da jini ɗaya kira, Tana fara ringin yayi picking..
A mutunce suka gaisa da junansu kafin Yace"pls ko zaka kira Owais, kuyi magana, akwai wani abu da ke damunsa yaƙi fadamin may be kai ya sanar dakai" tun daga yanayin muryarsa prime minister Hateem Ya fahimci dan uwan nasa yana acikin damuwa.
Othe other hand prime minister yace"Okay, Don't worry, I'll call him Just calm down and take care of yourself for me"
"Okay, Nagode kaima ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama ya juya ya tafi zuciyarsa a hautsine..
*ANEELERH*
Ta fi karfin rabin awa tana safa da marwa a tsakar dakin ta, tana ta tufka da warwara akan yadda zata bullowa lamarin, tun da ta saurari maganganun Ana gabanta keta faduwa, Hankalinta yaƙi kwanciya, damuwarta Ina Ana? Tana raye ko ya kashe ta? batajin zata Iya hakura taja baki tayi shiru batare da tayi gaggawar daukar mataki ba ko dan ta kwatarwa Ana hakkinta, ta kuma ku6utar da family dinta, zuciyarta ce ta dinga azalzalarta da tunzurata akan taje ta tunkare shi kaitsaye ta fada masa ta san komai sannan tayi masa barazana in har bai fada mata ina take ba zata tona masa a asiri uban kowa yasan me ya ke aikatawa sannan ta kaishi kara gurin hukuma.
Kwakkwaran Numfashi taja, fuskarta babu annuri ta fito daga dakin bata iske kowa a falo ba, Mami da ummi suna a kitchen suna aikin lunch.
Bata nufi ko'ina ba sai ɗakin Uncle dan Iya, da kwarin gwiwa take tafiya yayin da bugun zuciyarta ke ƙaruwa Ga tsoro tanaji amma ahaka ta dage ta durfafi dakin nasa har takusa kutsa kai Cikin ɗakin taji kamar an ruke kafafunta dakatawa tayi da yin tafiyar, nan take brain dinta ta fara tariyo mata maganar Ana.
_watakil lokacin da zaku kalli video din nan, bana a raye na mutu, saboda yace bazai kyaleni ba dama yake jira da zai kashe ni, kuma kunga ni kadaice agidan, yanzun nan naga shigowar shi shiyasa na gudo daki don in samu damar yi maku video, dan Allah don sonku da manzon Allah saw Aduk lokacin da kuka kalli videon nan kuyi gaggawar kaishi ƙara gurin hukuma, sannan ku gudu daga gidan nan, kada ku bata lokaci, saboda shi din mutum ne mai hadarin gaske, ya sha yi min barazana akan In har na kuskura na fada ma wani abun da ya ke min wlh sai ya kashe ni bayan haka zai kashe duk wanda na fadamawa shiyasa nakasa sanar daku_
Tuna wannan maganar yasa Aneelerh taji tsoro ya mamaye zuciyarta, tayi shiru tana sauraron gargadin da zuciyarta ke yi mata.
_Kada ki kuskura Anila! Ba zaki Iya ja da shi ba, in har yasan kin san sirrin shi kashe ki zaiyi, mutane irinsa basu da imani zasu iya aikata komai donsu rufawa kansu asiri, Kwara ki nemi wata mafitar...."
tayi zurfi cikin tunaninta kwatsam Ta tsinkayi muryar mutum abayanta
"ANEELERH"! Ras gabanta Ya fadi jin muryar mutumin datazo nema, tuni taji tsigar jikinta na tashi, Yan hanjin cikin ta suka hau kadawa.
"Ko ba ita bace"? Zazzare Idanu tayi, Cikin sauri Ta daidaita nutsuwarta, A hankali ta juyo ta fuskance shi, Yana atsaye Cikin riga yar shara da gajeran wando, Junaid Ya jima Yana fada mata Uncle dinta mummuna ne ba ta6a ganin muninsa ba sai yau data gano mugun halinsa.
zuba mata jajayen idanun shi yayi, Cikin rawar murya ta furta"am.. um..un uncle barka da rana, dad..dama kai nake nema, um.. inaso ne dama in tuna maka maganar...."
cike da rudani yake kallonta Jin yadda take yin magana a dabarbarce kamar mara gaskiya amma bai kawo komai aransa ba yasan Anila da kunya may be tana jin nauyin yi masa magana ne shiyasa ta ruɗe.
Murmushi yayi tare da cewa"Anila kenan, to meye abun rudewa aciki? Kawai don zakiyi min magana? Waini sai yaushe zaki daina jin kunyata? Sai kace ba Uncle dinki ba"? kakaro murmushin yaƙe tayi kan fuskarta batare da ta tanka masa ba.
Dafe kai yai"kash Kiyi hakuri kinji shiru tun da kika tura min credentials ɗin ki, har yanzu ba'a neme ki ba, kema ce baki tuna min, kinsan uncle din naki da mantuwa abubuwane sunyi yawa akaina bakasai nake tunawa ba, In sha Allah zan tuntubi Md din asibitin mutuminane ai..." washe baki tayi tace"bana so na takura maka ne, nasan uzirurrukane sukai maka yawa, shiyasa bana yi maka magana, yau ma don naji kace kana gida shine nace bari na tuna maka"
"Allah sarki, nasa maki rai kina ta faman jirana, ki kara hakuri In sha Allah yanzun nan dana shiga daki zan kira shi awaya in tuna ma shi, Ki ma fara shirye shiryen fara zuwa aiki"
ya fada tare da tafa hannayen sa.
Washe baki ta kumayi alamar taji dadi tace"nagode uncle, Allah yasa ka da alkhairi Saina Ji daga gare ka, Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa"
"Ameen Anila, ai baki da wata damuwa, ke da kike dani? Asibitin Obie ai namune ke sai ma kin zabi albashin da kike so a yankar maki Allah wallahi" fashewa tayi da dariya tana fadin"kai uncle, Ina kara gdy da kulawarka agare ni" batai gangancin da zai gano ta ba, lokacin da ta baro gurinsa wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tafin hannunta dafe da saitin Zuciyarta.
Tana shigowa falo taja tunga ta tsaya tana tunanin meya kamata tayi? dafe kai tay kamar mai fama da ciwon kai.
Aranta ta ayyana Ko dai ta sanarma Mami? Can kuma ta girgiza kai ba lallai su yarda ba, ko da ta nuna masu video din tun da bayani ne Ana tayi bawai videon abun da ya ke yi mata ne ba, Bakowane zai gasgata maganarta ba kai koda zasu yarda hadari ne Ta gaya ma wani acikin gidan hankalinsu zai tashi a karshe ma garin nukunuku Ya gano su.
Gaba daya Aneelerh ta ruɗe, kwakwalwata na neman rikicewa..
Juyawar da za ta yi ke da wuya tayi arba da mami dake ta kallon ta.
Washe baki tayi adabarbarce ta furta"ma.. mi dama yanzu nake niyar shigowa kitchen din don in tayaku aiki"! Wani kallo mami ta yi mata.
"Aneelerh lafiyarki kuwa? Tun dazu Ina tsaye abayanki baki lura dani ba har kiran sunanki nayi kusan sau uku baki amsa min ba, meke damunki ne!" yawu ta haɗiya ƙut jikinta na tsuma tace"mami ki yarda dani babu komai, ba abunda ke damuna"
"Anya Anila? Ko dai baki da lafiya? Ta fada tana karewa fuskarta.
girgiza kai tay"lafiyana lou mami"
Ba don ta yarda da maganarta ba tace"toh," har zata juya ta dan dakata"Kunyi waya da mahboob ne"?
"A'a,"
"Kinsan ba kai gare shi ba, kada yabar mana yaro da yunwa, Ki kira shi ya dawo da junaid gida" amsa wa tay da toh.
"Naji kince zaki ta ya mu girki, mun kammala ay, ga gidan nan ki kara gyara shi" ta amsa mata da toh.
Mami na barin gurin ta sauke ajiyar zuciya.
________________________________________✍️
*PRAVIN*
Cike da zumudin son ganin ta, ya shigo dakin tashin farko yai arba da awarwaron ta akan floor inda ta watsar da su, Hankalinsa ba ƙaramin ta shi yai ba, a yadda yasan Hajjaty da tsafta ba karamin abu zaisa tabar dakinta a yamutse ba gyara ba, hakan yasa shi fahimtar babu lafiya.
Sam bai lura da ita ba, har saida ya karasa tsakiyar dakin, Idanunsa suka sauka akanta tana a kwance kan gadonta bayan data gama koke koken bacci ne yai awon gaba da ita, from head to toe yabi ta da kallo kamar mahaukaciya, naɗin sarin jikinta duk ya warware, har inners din ta sun fito, ga gashin kanta a hargitse kamar bata gyara shi ba, aransa ya ayyana meya faru da ita? Meke damunta"?
damuwace karara akan fuskarta, hawa yai kan gadon ya matsa kusa da ita, da ya dubi fuskarta sai da yaji gabansa ya fadi, Gaba daya kwalliyar da tayi ma fuskarta ta baci da jan bakin data shafa ma lips dinta.
Lumshe idanun shi yayi tare da sake buɗe su kan fuskarta
A hankali ya Shafa fuskar da yatsun sa har izuwa kan wuyanta ya dire su kan kirjin ta.
Numfashi ta ɗan ja tare da sauke shi da hucin zafi.
Baya so ya katse mata baccin ta, amma yana son yaji meke damun ta.
Can kasan makoshi ya furta"My lovely wife, am back, nayi kewarki sosai"
ya faɗa tare da manna mata sumbata kan lips dinta.
ya saba duk in ya dawo daga aiki ko ya dawo daga tafiya ya shigo dakinta zai taras da ita tayi gayu ta gyara ko'ina na dakin don ta faranta masa kuma zata watso da gudu ta rungume shi sannan ta yi kissing din shi amma yau sai yaga akasin hakan taya ba zai damu ba?
Hannunshi ya zura ta bayanta yana kokarin kwance igiyoyin rigarta bai aune ba yaji ta damƙi hannunsa, da sauri ya kalle ta, A hankali ta buɗe idanunta wadanda suka kada jawur ta sauke su a cikin nashi, gaban sa ne ya ƙara faɗuwa ganin yadda idanunta suka yi ja kamar an watsa barkono acikin su.
Arude ya furta"kin tada min hankalina, meke damunki ne? Gaba daya dakin a hargitse babu gyara, ke kanki ba acikin nutsuwarki kike ba, wai meke faruwa ne"?
Maganganun marwa ne suka soma dawo mata a cikin zuciyarta, Siraran hawaye ne suka wanke fuskarta, hakan ba karamin daga hankalinsa yai ba, duk yabi ya rude cikin rawar murya yake yi mata magiya akan ta fada masa damuwarta..
Lumshe idanunta ta danyi kafin ta kuma bude su akan fuskarta.
Zuciyarta naci gaba da tariyo mata abun da marwa ta faɗa mata akansa.
Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar Pravin ta katse ta ransa adan bace ya furta"wai ba zaki fada min abun da ke damunki ba ne? Kina ji ina magana kin share ni"!
Numfashi taja tare da sauke shi da karfi.
Ta yi saurin daidaita nutsuwarta cikin disasshiyar murya tace"sannu da dawowa.
"Ba wannan na tambayeki ba, ki fada min meke damunki"
"Kada ka damu, babu komai"
"Karya kike yi, Dole akwai abunda ke damunki"
"Hakane, bana so na tada maka hankali ne, wlh Cikina ke ciwo, kasan halin da nake shiga idan na fara ciwon ciki" girgiza kai yai"ban yarda ba, kawai ki fada min abunda ke damunki"? Ya fada fuskarsa a daure.
Tunani ta soma yi ya zatay da shi? Don bata jin zata iya fada masa abunda marawa tace akan shi, tasan bazaiji dadi ba in yaji anyi masa kazafi kwara ta bar abun acikin zuciyar ta.
Kurama juna idanu sukayi har na tsawon mintuna goma, sai da ransa ya gama baci jin tayi shiru taki tanka masa, yana huci yace"yau ni kike boye ma abunda ke damunki? kina da wanda yafi ni ne? Okay, kada Allah yasa ki fada"
Saukowa yai daga kan gadon Har ya kusa fucewa daga dakin tayi saurin mikewa ta duro daga kan gadon ta nufe shi da gudu ta faɗa bayanshi tare da zagayo hannayenta kan kirjin shi
Dakatawa yai da yin tafiyar da kakkausar murya ya furta"kin shirya fadamin"?
"eh" batare daya juyaba yai shiru yana sauraronta.
"Hajiya saratu ce ta bata min rai, taci mutuncina pravin, ni bansan wata irin tsana tayi min ba..."
karya ta shiga shirga mashi abun da ba halin ta ba, duk don ta samu ta kawar masa da tunanin abunda ke damun ta.
Ransa ya baci da jin abunda hajiya saratu tayi mata.
Cikin shesshekar kuka ta kara da cewa"ita ce ma ta cabemin kwalliyar da nayi maka"
ta fada tare da ruko sareen dai dai Inda hajiya saratu ta goge mata kwalliyar da shi ta nuna mashi da yar shagawaba tace"ka gani ko"?
Runtse idanun yai ji yake kamar yaje ya shake wuyan hajiya saratu.
Yana huci yace "bazan ƙyale ta ba, dole In rama maki cin zalun da takeyi maki, mara mutunci kawai.." still da shagwa6a ta tallabo fuskarsa da tafukanta"babe, Ni ban fada maka don ka rama min ba, wlh na yafe mata, kawai banji dadi bane, amma komai ya wuce, mu kyale ta kawai"
Jinjina mata kai yai tace"ina fata kun dawo lafiya? Ya baba Obie? Ya kuka baro aminin nasa"?
"Mun baro shi lafiya, Baba Obie Yana a part dinsa, da anjima ki shiga kiyi ma shi barka da dawowa"
"Okay, fada min me kake son in kawo maka"?
"Bana jin yunwa, Naci abinci agurin hajiya saratu, A yanzu nafi bukartar ki"
ya fada tare da daukarta kamar Yar baby, Dariya ta saki tana kallon shi..
Jujjuyata yai kafin ya nufi gadon su da ita, ya jefa ta a hankali, tana daga kwance tana kallon shi yayin da yake a tsaye yana Unbuttoning din rigarsa.
"Ba zan raga maki ba, almost one month, dakyar nake Iya bacci saboda rashin ki"
Tace"nima haka, ba raga maka zanyi ba, ka tafi ka barni da kewarka"
_________________________________✍️
Shigowa dakin ta yi, tana kokarin Yaye veil din da tay rolling, taga wayam babu pravin data bari yana cin abinci adakin.
"Ina ya shiga ne? Ko ya shiga toilet"! Ta fada aranta, tare da nufar toilet door ta danyi knocking shiru ba'a amsa mata ba, sai dai taji sautin safkar ruwa alamar ana amfani da shi.
Watsa hannayenta tayi, ta koma ta zauna daga gefen gadon, Ta curo waya daga cikin yar purse dinta ta danna na Hajiya laura Kira.
"Mara mutunci, Sai yau kika tuna dani?
"Banson iya shege matar Yaya, don kar in tuhume ki shine kika rigani magana ko"?
Fashewa hajiya laura tayi da dariya"Sorry aminiyar arziki, bana fada maki zanje dubai ba? Sai jiya na dawo agajiye wlh" hajiya saratu tace"kai haba, Ashe kun dawo, Ya gajiyar tafiya"
"Alhamdulillah, gajiya tabi jiki, akwai fa kaya, munyi sabuwar ɗauka, Na tura maki videos ta whatsapp yakamata ki hanzarta zabar wanda kikeso tunkafin akwashe kizo kina cizon yatsa"
Hajiya saratu tace"Amma naji dadi wlh, dama ga hidima muna da ita, dazu Owais ya nemi alfarmar ayi family meeting a birthday dinsa, kuma kinsan In Owais zaiyi birthday, ko biki albarka saboda yarda baba Obie ke ji da shi ina mai tabbatar maki za'ai harka ta arziki" dariya suka sanya gaba dayansu
Laura tace"amma da mamaki Owais daya saba yin birthday a canada inda aka haife sa kice wannan karan A Nigeria za'ae, Amma fa naji dadi wlh, Allah ya nuna mana lokacin lafiya"
Sun dan jima sunayin waya da hajiya laura kafin su ka yi sallama.
Gallery ta shiga ta buɗe hotunan da tayi ma Parveen aranar dinner din Hateem batare da sanin ta ba.
Kamar ibada kullum saita kalli hotunanta, ta6e baki ta ɗanyi.
_____________UNAISAH ANGEL
Tana a kwance kan gadonsu, Ta lumshe idanunta yayin da brain dinta ke tariyo mata memories dinsu da Danish, wani sa'in ta yi murmushi wani sa'in ta zubda kwalla, Amma yau tunanin nata ya kasu gida biyu, saboda kalaman da Chief ya furta mata adaren Jiya da su ta wuni aranta, bata ta6a zaton mutun me matsayi irinsa zai iya aje girmansa da komai donya ja ta a jiki ba.
"Unaisah" muryar Ummi ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula
Su biyu suka shigo dakin, Hannun Batool ruke da wooden tray mai dauke da dinner dinta akan table ta daura mata shi.
"Su daddy sun dawo"
Ummi tace"a'a may be sun tsaya yin sallar isha'i ne naji an fara kira, yanzu dai ki daure ki tashi kije ki yi wanka"
Maƙe kafaɗa tayi"Pls aunty Ummi, dan Allah kibarni, Bana son maganar wankan nan nafi jin dadin jikina a haka, Ni wlh tsoron ma taba ruwan nake"? Baki asake ummi ke kallon ta.
Batool tace"pls Ki daure kiyi wankan zaki ji dadin jikin ki, baki ga yarda kika koma ma ba? Kamar yar mahaukaciya"
Ummi tace"fada mata dai, Gashin kanki ko kyan gani babu, Pls ki tashi kiyi amfani da ruwan zafi zaki fi jin dadin jikinki" girgiza kai tay
Ummi ta dubi Batool"in muka bita ta lalama bayi zatay ba, Abun da za'ay ki kama hannunta ni in kama kafafuwan mu shiga da ita ciki muyi mata wanka" kafin ummi ta karashe maganar suka ga ta zabura ta mike tsaye tana girgiza
dariya suka kwashe da ita.
"Dan Allah ku kyaleni, tun da nace bana son wankan, Ba jikina bane wai"
Basu tsaya sauraronta ba, Ummi ta haye ta cafko ta tare da daukarta saman kafadarta, tana ta zabga mata masifa akan ta kyaleta hada ambaton sunan daddy.
Shigewa Ummi tayi da ita cikin toilet.
Jim kadan ummi ta fito bayan ta wanke mata gashin kanta, ta barota a cikin toilet din, kafin ta fito Batool ta dauko mata kayan da zata sanya.
Bayan ta shafe mintuna, sai gata ta fito tana ta faman daure fuska, Jikinta a sanye da bathrobe..
Kallo daya tay masu ta wuce ta nufi gaban dressing mirror ta zauna, ummi ta fara gyara mata gashin kanta cikin kankanin lokaci ya fara sheƙi.
"Zaki iya shafa lotion din ko in shafa maki" yamitsa fuska tay"zan iya" murmushi suka saki, kamar babu laka a jikin ta kwata kwata bata da kuzari, dakyar ta shafe jikinta da body lotion bayan ta kammala tace su fita zata saka kaya ummi tace"wani dare ne je mage bai gani ba Unaisah? Time da baki a hayyacin ki kin san sau nawa inayi maki wanka"?
Ras gabanta ya fadi waro idanu waje tay har zata fasa zazzaga masifa Batool tace"zolayarki takeyi"
cije le6e ta yi, dakyar ta mike ta nufi kayan da Batool ta aje mata kan bedmattress ta dauka ta nufi wurin closet dinsu can cikin dakin ta shige don kada su ganta.
Jim kadan suka jiyo takun tafiyarta a tare suka dube ta, oversized shirt ce tare da wando plazzo Green colour, ta daura veil din kayan a saman shoulder dinta.
Ummi tace"ku dai Allah yayi maku ruwan kyau, dama kika rame sai kika kara kyau, musamman Collarbone dinki ya kara kawata kyawun kirjin ki" yamutsa fuska tayi cikin sanyayyar voice dinta tace"Anya aunty Ummi ba sharri kike min ba? Kashin wuya ne abun kyau"?
Batool tace"wlh dagaske yayi maki kyau" tabe baki tayi
"Kizo ki zauna ki ci abincin ki" ta fada tana nuna mata tray din.
Jiki asanyaye ta nufi gafen gadon ta zauna, Batool tayi serving dinta, sam takasa Cin abinci, ko kamshin shi bata son Ji.
"Pls ki daure ki ci ko kin samu karfi a jikin ki" girgiza kai tay"bana jin dadin shi, Ko naci amayar da shi"
Duk yadda sukaso taci abinci takiya, Suna tsaka da rarrashinta su ka ji yo dirar motoci a cikin gidan.
Jikinta na kerma ta mike tsaye ummi na tambayarta ina zataje tace"Su daddy sun dawo zataje gurin su"
"Batool taimaka mata ku tafi, kwarama da suka dawo watakil idan shi ya yi maki magana asamu ki ci abincin"
Fitowar su daga dakin yayi daidai da shugowar su falon.
Taj ne Agaba kan wheelChair dinsa Sai faman gungurata yakeyi, Chief da sheikh Imam suna abiye da bayansa A masallaci suka hadu da shi bayan sun kammala sallah Anan harya yai mamakin ganinsu yace ashe sun dawo sau uku yana zuwa gidan neman sa saidai ace mashi baya nan ya kuma tambayi meya faru da su? Ganin rauni a kafar Taj, Chief yace in ba damuwa yazo su tafi gida sai su karasa magana acan.
Takun tafiyarsu ne Yaja hankulan su Chief ga kallon direction din da suke, kaitsaye idanunsa suka sauka a cikin nata, kayan jikin ta sunyi mashi kyau.
Karasowa sukayi Cikin girmamawa suka gaishe da sheikh Imam
Kasa amsawa yayi saboda hankalinsa daya tashi ganin goshinta a nade da bandage, ta rame ba kamar yadda yasanta ba ita.
"Subhanallah, Unaisah meke damunki"? Murmushi tay,
"Bani da lafiya, amma naji sauki"
Chief yace"mu karasa ciki" gaba daya suka nufi falon kowa ya samu guri ya zauna, Ummi tana a labe bakin kofar dakin su..
"Chief, Hankalina ba akwance yake ba, Inaso nasan meya faru daku? Farmakin da kuka je kaiwa anyi nasara ko kuwa? Naga Taj da rauni a kafa, ga Unaisah ma ba lafiya, kaima haka naga ciwo a goshinka, Sannan Ina sauran yaran suke ne"?
aruɗe ya tambaya yana dubansu.
Gyaran murya Chief yai kafin ya soma magana calmly.
"Ba zamuce bamuyi nasara ba, Alhamdulillah munci rabin yakin munga tasirin addu'a, abubuwa da dama sun faru masu dadi da marasa dadi..."dan dakatawa yai yana kallon Unaisah dake a zaune gefen daddynta ta daura kanta saman kafadarsa lumshe idanun ta tayi don batason jin karashen zancen na shi.
"We lost Danish, Salsabeel ya samu karaya a hannunsa, Umar has a brain injury, gaba daya an kwantar da su a asibiti, su Commender ma Sunyi rashin daya daga cikin sojijin su, sauran yaran suna a part din Taj..."
Muryarsa na rawa ya furta"danish Ya mutu ne"?
"Bamu da tabbacin ya mutu ko yana raye, saboda bamu ga gawarsa ba" tashin hankalin da damuwane tsantsa akan fuskar Sheikh Imam, Ya girgiza da jin basu dawo Danish ba, wlh yaji zafi acikin zuciyar shi..
Girgiza kai yai idanunsa cike tab da ƙwalla.
Ya dan jima batare daya furta kalma ba, Can ya numfasa cikin karyayyar murya yai masu nasiha akan suyi hakuri da rashin da sukayi Su mika lamuransu gurin kada su sare, Danish kuma zasu tayashi da addu'a in ya mutu Allah yajikan shi In kuma yana araye Allah ya bayyanar da shi.
Sannan Ya bukaci yana son yaje ya duba su Salsabeel chief yace idan suka tashi zuwa zai kirashi sai suje atare su duba jikin su saboda asibitin ba a kusa yake ba.
Shiru sukayi falon yai tsit kowa da abunda yake sakawa acikin zuciyar shi.
"Ina auntynku? Ko itama tana a dayan bangaren ne"? Kaitsaye maganar shi ta dira a kunnan Ummi tayi mamakin Jin sheikh Imam ya tambayeta.
"Tana anan tare da mu" Batool ce ta bashi amsa..
Batay niyar fitowa ba amma saboda maganar sheikh Imam yasa ta fito jikinta sanye da dogon hijabin data dauko a cikin closet din su Unaisah.
Har kasa ta zukunna ta gaishe da shi fuskarsa da fara'a ya amsa mata, ta danyi mamaki mutumin da ko kallonta baisonyi amma yau haryake tambayar tana ina.
"Hateem Yasan da maganar"! Girgiza kai chief yai"ban sanar da shi ba ko da zaiji ba yanzu ba,"
Sheikh yace"Allahu akhbar, Allah baya barin wani don wani yaji dadi, Hateem yaso yaron nan kamar dan cikinsa, nasan in yaji hankalinsa ba karamin tashi zaiyi ba"
ya fada fuskarsa da damuwa jikinshi duk yai sanyi, Zuciyarsa ta karaya, saboda shi kan shi yaso yaron kuma bakomai yafi daga masa hankali ba face kin kar6ar shahadar da baiyi ba.
"Sheikh ga Unaisah nan, Har yau bata daina sanya damuwa aranta ba, dakyar muke samu tayi bacci, dan Allah ay mata nasiha.." Taj ne yai maganar.
Ya tambayi meye silar ciwonta, Taj ya fada masa komai.
Tsananin tausayin su ne Ya kama shi, Cikin sanyin murya ya farayi masu Nasiha har na tsawon mintuna talatin kafin Ya gama gaba daya jikinsu yayi sanyi lakwas, Imani ya kara shigarsu sosai.
Har wurare karfe 9 Shiekh Imam yana agidan daga bisani yai masu sallama Chief Ya rakasa Har cikin motarsa sai da yaga tafiyarsa kafin ya juyo.
Time daya shigo falon ya tsinkayi muryar Ummi tana fada ma Taj Unaisah taki cin abinci.
Da damuwa akan fuskarsa yace"Why Unaisah? Baki so ki samu lafiya ne? Ai ta fama dake akan kici abinci"
Muryarta kasa kasa ta furta"Zuciyata ke tashi,duka abincin da naci da safe dana rana saida na amayar da su a toilet, ban fadi maku bane saboda bana son in tada maku hankali, abincin ma bana jin dadin shi ..."
Kafin wani ya furta kalma muryar Chief ta katse su.
"Gobe idan dr yazo duba ki ki fada masa aman da kike yi, amma bazan bari ki kwana da yunwa ba, Fada min me kike son Ci"
ya fada tare da dafe Sofa da hannayensa Yayin da idanunsa ke akan fuskarta.
Saboda nauyin shi da take jine yasa ta ce"zan daure naci wanda aka kawo min"
"Ina abincin nata yake" Batool tace"yana a daki"
"Je ki ɗauko min" mikewa ta yi da sauri ta nufi dakinsu.
Jim kaɗan sai gata ta dawo hannayen ta ruke da tray ta ajiye shi kan rug.
Zagayowa yayi tare da samun wuri Ya zauna a gaban tray din, mamakin chief ya rukesu Musamman daya Kira Unaisa Ya nuna mata gaban tray din Yace tazo taci abinci"
Ta dan zaro idanu tare da kallon Taj fuskarsa ɗauke da murmushi yai mata alamar taje mikewa tay jiki ba kwari ta zauna tana fuskantarsa, yayin da tray din ya raba tsakanin su.
Coconut water ya dauka da sauri ta mika yatsun hannunta dake kerma da niyar ta kar6i Glass din
Batai aune ba taji ya kanga mata strawa din a baki, wata irin kunyace ta kamata, adan rude ta saci kallon su ummi da Taj fuskokinsu dauke da murmushi..
Ganin ta ki motsa lips dinta yasa shi furta"ki sha" yawu ta hadiya ƙutt kafin a hankali ta fara zukar shi, abunda tagaza sha dazu sai gashi ta kwankwade shi duka batare da ta ankara ba har saida ya janye straw din daga bakinta.
Spoon ya dauka Murya na rawa ta furta"zan iya ci da kaina" ta fada tana kyafkyafta gray eyes din ta
Hakan ba karamin Jan hankalin shi yai ba.
"Ki bari ya baki mana Unaisah, Baki ga yadda hannunki ke kerma ba taya zaki iya ruke spoon" Ummi ce ta yi maganar aranta ta ayyana Samun wuri.
Batool sai faman hadiyar yawu take yi, ba yunwa take ji ba, Amma yadda taga Chief na ciyar da Unaisah yasa taji dama ya bata itama.
Taj kuwa Ransa fari fat da farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha, Burinsa yana daf da cika, abun da ya daɗe yana jira abunda yafi burgesa yadda Chief ya nuna kulawa agare ta agaban shi inaga idan sukai aure? Allah kadai yasan gatancin da zata samu a gurin sa, Shi yasan Unaisah ta gama morewa.
Tun tana jin kunyar ya bata abaki har ta dan saji jiki ganin daddynta bai nuna wani abu ba..
duk in ya bata one spoon sai sun haɗa ido da juna launin idanunsa da take kallo bakomai yake tariyo mata ba face kyawawan idanuwan Danish kasancewar launin idanunsu daya hatta shape dinsu kamar an zana saboda kyau.
"My Angel" muryarsa ce tay mata gizau a cikin kunnanta...
Lumshe idanunta ta danyi wasu zafafan hawayene suka taru a cikin su sam bata son kowa ya gani.
Nutsuwa ya yi yana kallon fuskarta, tuni Ya dakata da bata abincin ganin halin da ta shiga.
"Unaisah" muryarta na rawa tace"Naam"
"Pls don't shed your tears"!
jinjina mashi kai ta yi.
"Na koshi da abincin, Ina so zan shiga toilet" bata jira amsar shi ba, Ta mike har zata fara tafiya taj yace"har kin kammala cin abincin ne"? danne damuwarta tayi"Eh, Inaso zan shiga toilet"
Da sauri ta nufi dakin su, Tana shiga toilet taja kofa ta datse, tare da jingina kanta jikin bango wani jiri jiri take gani kamar zata kife kasa, sai faman jan numfashi takeyi tare da zare gray eyes dinta.
Har yanzu ta gaza yarda cewa man dinta baya atare da ita, bata taba zaton zata iya rayuwa batare da shi ba.
Duk irin burin da ta ci akan shi in sunyi aure zata kyautata mashi saboda halaccin da yai mata yanzu gaba daya plan dinta Ya lalace.
Saitin Zuciyarta ta dafe da tafin hannunta"My man, na gaza yarda cewa ka mutu, Ina ji araina kana raye, shiyasa har yanzu zuciyata take harbawa, don da ace baka raye babu makawa saina bika nima"
*Mr President*
Around ƙarfe shabiyu na dare bai runtsa ba, ya wuni da bakin cikin da owais ya kunsa masa, har ciwon kai saida yai, kayan bacci ne a jikin shi ya zuba hannayensa a cikin aljihunsa wandonsa, Sai sintiri ya ke yi a tsakar katafaren bedroom din Hajiya laura, ya rasa meke masa dadi? Komawa yai window Ya dafe glass din da tafin hannunsa Ya zuba ma sararin samaniya idanunsa da suka kaɗa jawur..
"Why Owais? why? girgiza kai ya danyi"Ni nasan bayin kanka bane Owais, akwai wanda ke son Ya shiga tsakanina dakai, amma meyasa zaka zargeni kamar bakasan wanene mahaifinka ba"?
Bai aune ba Yaji tayi hugging dinsa ta baya tare zagayo hannayenta kan flat tommy insa.
"My big boss, pls ka fada min meke damunka? gaba daya yau nakasa gane maka, kwata kwata babu walwala a tare dakai.
"Ina da damuwa amma bazan iya fada maki ba kawai ki tayani da addu'a Allah ya kawo min mafita"
Kwantar da kanta tayi kan shoulder dinsa"in sha Allah zanyi maka addu'a, amma pls muje mu kwanta, dare yayi sosai kana bukatar hutu"
"No kije ki kwanta bana jin bacci yanzu" zagayowa tayi tagan shi tare da jinginar da bayanta jikin window glass din a hankali yake dubanta, Nightgown ce a jikinta shara shara rigar.
Kashe murya tayi"ko dai kazo muje mukwanta ko kuma In kira Sarauta In fada mata abun da ke faruwa tunda ni kaki sanar dani" tana fada ta juya zata nufi cikin dakin donta dauko waya da sauri yakai hannu Ya damƙi waist dinta Ya janyo ta ta dawo Jikin shi.
"Ba sai kin kirata ba, naji zan kwanta" kashe mashi ido daya ta yi"ai da ka bari na kirata, kai kasan me zai biyo baya"
Baisan ya zaiyi da laura ba, sometimes indai yana tare da ita koma mashi take yarinya duk da yana jin dadin hakan sosai.
Lallaba shi tayi harta samu yabita suka kwanta.
______________________________bayan wani lokaci
A kwana A tashi ba wuya wurin Allah, yau Wata daya Cuf dakai farmaki gidan kurkukun Kaddara.
meya faru a yan kwanakin nan a kowani Family?
A bangaren Aneelerh cikin kwanakin da suka gabata, ta kasance cikin tsananin damuwa abun duniya ya ishe ta, ta rasa ya za ta yi, kullum tunanin ta wa yakamata ta tunkara da maganar? Ga shaida tana da ita a hannu sai dai tasan mawuyacin abune a yarda da ita, bayan haka tana jin tsoron ta sanarma wani maganar ta koma masa, akarshe ta jefa rayuwarsu cikin hadari.
tuntana 6oyewa har sai da ta kai ga kowa na gidan Ya fahimci Akwai abunda Ke damunta saboda yawan razanar da takeyi da zarar ankira sunan ta, In tana cin abincin Yatsun hannunta kerma suke kaf kaf, bayan haka takan raba dare bata runtsa ba.
Babu irin magiyar da basu yi mata ba akan ta fadi abunda ke damunta tace itafa ba bakomai lafiyarta qalou, Har abie Yasa aka kirata a falo suka zauna duka mutanan gidan Ya matsa mata akan ta fadi meke damunta a karshe tayi masu karya tace dama a kwanakin nan tana yawon yin mafarkin Uzair da Taj shiyasa ta shiga damuwa, har kuka ta yi masu, duk don su ɗauki maganarta Serious, tausayin ne ya kama su, gaba daya suka haɗu suna lallashinta hada uncle dan iya shine kan gaba, har ila yau bata ta6a yin kuskuren da zai gane tasan wani abu game da shi ba.
___________________________________✍️
Idan muka koma bangaren Unaisah, sai dai muce Alhamdulillah, jikinta ya fara murmurewa, damuwarta ta ragu saboda gatancin da take samu agurin mutan dake bata kulawa, Aunty Ummi, Batool, Taj uwa uba Chief, cikin kankanin Lokaci Shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu, baya gajiya da bata lokacin shi, kulawar shi, soyayyar shi.
kullum ne sai sun haɗu da juna, mafi yawan lokutta atare su ke yin breakfast da dinner agaban kowa yake bata abinci abaki tun tana jin kunyarsa yanzu har ta saba da wayewar shi ganin Taj bai taba nuna ya damu da hakan ba saima dadi da ya ke ji.
Haƙiƙa Chief yayi namijin kokari gurin samun lafiyarta, kullum cikin faranta mata rai ya ke yi, Yanzu atare suke motsa jiki a gym room dinsa, bayan haka atare suke yin Kallo a tv room dinsa, har garden din gidan suke zuwa atare su yawata ba karamin nishadi take samu ba, komai ta ke so shi ya ke yi mata, saboda tsantsar kulawar da yake bata ko tari tayi wanda bai kwanta masa arai ba sai ya kira dr don yazo ya duba ta, saboda baya wasa da lafiyarta.
duk wani abu da daddynta Ya fada masa wanda tafi so tuntana Yarinya sai da Chief yasa aka kawo mata shi agidan.
Saboda kyautatawar da yake yi mata ne yasa ta fara Jin shi sosai a cikin ranta, da tunanin shi take kwana da shi take ta shi, In ta farka daga bacci shine mutun na farko da take kwaɗayin ta hada ido da shi.
Har yanzu Danish Yana aranta sai dai ta rage damuwa da rashin shi, ta dauki dangana tama fidda rai da shi, saboda ya taba fada mata bazai iya tafiya yabarsu ba, tabbas da ace yana a raye da tuni ya dawo gare su amma yau har one month shiru babu alamun shi.
Abu daya da bata fashi shine yi mashi addu'a har yau bata fasa tashi tsakar dare tayi nafilfili saboda shi ba 💔
A bangaren yan uwanta dake a part din Taj Har yau basu san meke wakana ba, abu biyu ne ke damun su, Kulle su da akayi a part din taj da kuma rashin dawowar su Unaisah Part din, amma saboda yawan kiransu video call da sukeyi Yasa hankalinsu Ya dan kwanta In suka bukaci suna son yin magana da Danish ita keyi masu wayau ta gyara muryarta ta koma irin tashi da yake ta kware gurin iya kwaikwayon muryar Danish Ba zaka taba gane ba shi bane, Ta hake take shawo kan su, ko da sun nuna suna son suyi video call da shi sai tace masu sun manta Danish baya kallon camera? In ta fadi hakan sai suce eh sun tuna fa.
wani sa'in kamar zasu saka mata kuka su dinga mata magiya akan su dai suna so su dawo nan su zauna atare da su, tace su kara hakuri suma suna jirane sai su Danish sun tafi sai su dawo nan.
Alhamdulillah duk da suna a kulle part din Taj suna samun kulawa chief bai barsu hakanan ba, ya sanya masu duk wani abu na more rayuwa da zai shagalar da su ya kawar masu da damuwarsu, Basu da matsalar komai, Hutu kawai suke sha, rana ta farko da Unaisah tayi video call da su saida ta yi mamakin ganin yadda Kumatun parveen suka cuccuko, sunyi kiba sunyi haske kamar ya'yan turawa, Duk in zasu yi waya sai sajeed Ya tuna mata akan ta fada ma Danish Yar uwarsa dake a prison dan Allah kada su manta da ita su taimaka su ɗauko ma shi ita...💔
__________________________________
✍️
Idan Muka Koma Obie Estate tuni sun fara shirye shiryen Bithday din Owais da family meeting kasantuwar saura kwanaki kalilin ya rage, prime minister harya kira baba Obie awaya ya fada masa ranar da zai shugo Nigeria yakuma ce su fara shirin tarbarsa.
saboda gabatowar ranar Baba Obie Yasa aka fara gyara Estate Din tare da ƙawatasa yadda kasan Masarauta saboda kayan alatun da aka wadatasa da su.
A bangaren Hajjaty tuni tayi watsi da maganar Marwa, kuma tayi blocking contact dinta saboda bata bukatar ta karajin koda muryarta, tun da tayi ma Praveen kazafi taji ta fita aranta.
BENAZIR💔
A Zaune take kan Mirror chair, Hannunta ruƙe Da wayarta, hotunan Unaisah take kallo Idanunta sun cuccuko tab da kwalla, Baiwar Allah Hankalin ba akwance yake ba, ta damu da rashin samun su awaya, In ta kira Unaisah kiran baya shiga, shi kuma, Taj ko ta kira baya picking sometimes rejecting call din yakeyi har sako ta tura ma sa tace dan Allah idan ma bazai kula ta ba, ya hada ta da Unaisah tana son yin magana da ita, shiru bai kirata ba kuma bai mayar mata da reply ba, ta rasa ina zata tsoma ranta taji dadi! Gashi since last da sukai waya da Unaisah Bata kara bacci Cikin kwanciyar hankali ba, saboda munanan mafarke mafarken da ta ke yi akan ta da kuma tana ji aranta wani abu na faruwa da su, Har tunanin zuwa estate din ta yi sai dai tasan Ba lallai ta samu hanyar shiga ba ko da taje, tunda ba wani gareta ba, Taj da take takama da shi baya kula ta amma tasan indai ta nemi Anila da maganar zata taimaka mata suje tunda dama ita ta hadata da su kuma ta san Taj yana ganin girman Aneela.
Kifa kanta ta yi gaban mirror tana shesshekar Kuka.
"Aunty Benazir" Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Zeenatu, Kasa dagowa tayi saboda bata son yanayinta ya jefa zeenatu a hali na damuwa
Shigowa dakin zeenatu tay, jikinta sanye da jallabiya fara.
Ganin Benazir zaune ta kife kai gaban mirror yasa ta nufe ta.
"Aunty Benazir, lunch is ready, we're waiting for you" ta fada tare da karasawa gaban ta.
Jin shiru bata dago ba yasa zeenatu tayi tunanin ko bacci ta ke yi.
Dafa bayanta tayi"aunty Benazir, Wake up pls, " taji tayi shiru bata tanka mata ba.
tasan in har ba magana ta yi mata ba, ba tafiya za ta yi ba, a yanzu bata son kowa a kusa da ita tafi son kadaici.
"Zeenatu! Pls ki kyale ni, basai kun jira ni ba, Ki tafi kawai ku ci abincinku,"
ras gabanta ya dan fadi jin yadda Benazir take magana cikin shesshekar kuka arude ta furta"Aunty Benazir! Meke damunki? Baki da lafiya"?
Bata san sa'adda ta daka mata tsawa ba"bansani ba, Zeenatu! Nace ki kyaleni, Ki rabu dani, bana son ganin kowa akusa dani..."
zazzare blue eyes dinta tayi, abunka ga shagwababba ta fashe da kuka ta juya ta fuce da gudu ta nufi dining area.
A lokacin Mami da Hajiya sarah tare da Dr shureim da Alhaji Ubaida suna azaune kan dining Chairs har sun fara cin abincin, Kukan zeenatu ne yaja hankulansu ga dubanta, azabure suke mike suna kallonta, Ta na karasawa ta fada jikin mommynta tana ci gaba da kuka, Hankali atashe suka dubi juna kafin suka maida idanunsu akanta.
" Zeenatu meya faru? Ina Benazir din? Wa ya tabaki"? Alhaji ubaid ne ya tambaya.
Mami tace"ki bude baki kiyi magana mana! Wani abunne Ya hadaki da Benazir dinne"?
Dago da ita Hajiya sarah tayi"Daughter, Daina kuka, Fada min meya faru"! Cikin kula tayi maganar tana share mata hawayen fuskarta
Cikin shesshekar kuka tace"Ah.. an.. aunty Benazir ce take kuka, Nace tazo muci abinci shine ta daka min tsawa tace in tafi bata son ganin kowa a tare da ita"
Dr shureim bai tsaya ya karasa sauraron maganar Zeenatu ba, Ya zame jiki Ya nufi dakin Benazir tunkafin Ya karasa shiga Ciki yajiyo sautin kukanta, gabansa na faduwa ya afka ciki Ta cikin madubi Ya hango fuskarsa sharkaf da hawaye ta zabga uban tagumi kamar wadda ta rasa gata a duniya, da sauri ya nufe arude ya furta Benazir! Lafiya kike kuka? Meke damunkin ki ne?
mikewa tayi ta nufe shi ta kwantar da kanta saman kafadar shi tana kuka, bubbuga bayanta ya somayi da hannunsa cikin sigar lallashi yace"pls ki fadamin damuwarki, Zan taimaka maki mu nemi mafita, amma kukan nan bazai amfane ki da komai ba, saima yajaza maki ciwon kai"
dakyar ta hadiye kukan tace"yaya shureim ina ma mutuwa zata zama hutu agareni wlh dana mutu na huta, nagaji nagaji da azabtarwar da zuciya keyi min akan rashin mijina da yata, yaya shureim bana jin dadin komai, hankalina ba akwance yake ba, Ina so nagan su..." dakyar ta karashe maganar..
Gaba daya a kunnan su Mami da basu dade da shugowa dakin ba, Gaba dayansu sunyi tsaitsaye cirko cirko suna sauraron maganar Benazir, tausayinta ne ya kamasu mami tuni idanunta sun ciko tab da kwalla, batasan ya zatay ba, ita kanta zataso Benazir ta hadu da bayin Allahn nan ko ta samu nutsuwar hankali..
Zeenatu dake kuka kalaman benazir sun karya mata zuciya, wani kukan takuma fashewa da shi.
"Benazir, Kiyi hakuri, Ki kara jurewa dan Allah, Na roke ki, sanya damu arai bazai haifar maki da komai ba, saima ta fama maki raunin dake a cikin zuciyarki, bana so a koma yar gidan jiya, dan Allah Benazir kiyi hakuri zamu tayaki da addu'a kema ki dage in sha Allah zasu bayyana"
Hajiya sarah ce ta yimaganar cikin sanyin murya.
Girgiza kai Alhaji ubaid yai shi kanshi abun na damun shi.
"Kinga kukan Ya isa haka, Kiyi shiru, in sha Allah Idan Uncle dinku ya dawo zanyi magana da shi ya taimaka yasa a yi cigiyar su agidan jaridu watakil adace..."
gaba daya tunaninsu har yanzu babu labarinsu ita kadai tasan Da zaman su..
A hankali ta dago daga kan kafadar dr shureim Idanunta sun kada jawur ta dube su ji take kamar ta fada masu Taj da Unaisah suna nan kuma tasan inda suke, ko dan ta samu su tayata neman yafiyarsa.
Girgiza kai tayi"nagode da kulawarku agareni, Amma basai an yi cigiyarsu a gidan jaridu ba, Aneelerh ta fada min sunyi iyakar bakin kokarinsu gurin yada hotunansu a social media da Gidan jaridu amma har yau babu labarinsu...." ta dan dakata kafin ta daura da cewa"dan Allah kada ku damu da halin da nake a ciki, bawai don banyi imani da kaddara ba, wlh nayi kokarin In manta da su a cikin zuciyata amma abun Ya faskara..."
ta faɗa tana matse kwalla.
Kallonsu Dr shureim yayi"pls Ku barni da ita, ku je ku ci abincinku, Zan yi mata nasiha" Alhaji ubaid yace"yawwa shureim pls kayi kokarin shawo kanta, bana so ciwonta ya tashi" amsa mashi yai da toh, fita su ka yi ya rage saura su uku
Kallon zeenatu yayi, Tana atsaye bakin kofar sai shesshekar kuka take.
"Calm down your mind, Ki kawo min lunch din ta a daki" ta amsa da toh ta juya ta fuce..
Ruko hannunta yai suka zauna kan gadon ta.
Nasiha ya farayi mata cikin kwantar da murya har saida taji zuciyarta ta dan lafa da radadin da takeyi mata.
Sai da yaga ta samu nutsuwa sosai kafin yace"akwai inda ke maki ciwo" girgiza ma shi kai tay"a'a ya shureim, lafiyana lou"
"Okay, " ya fada tare da sauke ajiyar zuciya.
Shigowa zeenatu ta yi cikin dakin, hannayenta ruƙe da tray mai dauke da lunch ta mika ma dr shureim Yasa hannu ya kar6a yadago ya dube ta"thanks, yanzu sai hankalin ki ya kwanta, tunda auntyn naki ta daina kuka" murmushi tadan saki.
"Ki je ki ci abincin ki"
Cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh.
Bayan fitar Zeenatu daga dakin Ya maida hankalinsa akan Benazir, A baki ya soma bata abincin tana ci, sai kallon shi takeyi har saida Ya tsargu da kallon Yace"Akwai wani abu ne"?
"Yaya shureim dan Allah ka taimaka ka kaini gidansu Anila Inason ganinta."
"Da yaushe"?
"Ko yanzu kace sai in shirya mu tafi"
"Kin fada mata ne"?
Shiru tayi jim don rabon da suyi waya da Aneelerh kusan two weeks babu wanda ya tuntubi wani amma saboda tana son Taje din yasa tay mashi karyar sunyi waya harma ta fada mata zasu zo
Yace toh idan sun kammala Cin abincin zai kai ta.
Dadine Ya lullubeta bayan sun gama cin abincin, Ya fita don yaje ya shirya.
Jikinta na rawa ta dauki waya ta danna ma Anila kira, don ta sanar da ita batun zuwansu, almost 3 times tana doka mata kira ba'a picking a karshe ta hakura da kiran nata ta fada toilet don tayi wanka.
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: Novels Elite
Health College
Home
Kurkukun Kaddara
Kurkukun Ƙaddara Takun Ƙarshe page 61 Complete by Boss Bature
by
Novels Elite Admin
September 29, 2024
Sponsored Link
Takun Ƙarshe
Zaune yake a mazaunin driver na motarsa, ita kaɗai ya ke jira su tafi, har ya fara gajiya da jiran ta, wayarsa ya zaro daga front pocket din rigarsa ya danna mata Call.
"Idan kika ƙara minti ɗaya baki fito ba zan koma ciki ne." Yana fada yayi rejecting call ɗin, jingina kanshi jikin headrest ya yi tare da lumshe idanun shi.
Sam bai ji tahowarta ba, sai dai ya ji motsin buɗe cardoor din, buɗe idanunsa yai tare da kallon ta baki a buɗe ganin yadda ta ca6a ado kamar wadda zata je gidan surukanta, Wani hadadden Code lace ta saka orange riga da skirt sun ɗan kama jikinta, mayafin kayan a kafaɗa ta daura shi, ga wani hadadden daurin dan kwali da ta yi, baƙar sumar kanta ta sauko har mid back dinta, fuskarta ta sha make up....,sunkuyar da kai ƙasa ta yi ganin kallon da Dr Shureim ɗin ke yi mata.
"Benazir, wa ki kai ma kwalliyar nan? sai ka ce wadda zata je bikon mijinta?" Tuntsirewa ta yi da dariya, ta yi mamakin jin ya canki abunda ta shirya, don wannan kwalliyar da ta yi saboda Taj ta yi ta, yau ta ɗaura ɗamarar janyo hankalin shi gare ta.
"Zai iya yiwuwa."
ta faɗa tana sakin murmushi, ta6e baki ya yi tare da ɗan girgiza kan shi ba tare da ya kawo komai a ransa ba, Kafin ya yi wa motar key a hankali ya yi reverse, a tsanake Ya ke yin driving ɗin su...
"Zeenatu ta ganki da zaki fito daga gidan?"
Ya tambaya yayin da yake juya sitiyari.
"Eh, amma bata nuna zata bini ba, naji tace zata bi Aunty Sarah Office, may be shiyasa bata damu da ta biyo mu ba."
Tafiyar mintuna ƙalilan Suka ƙaraso layin su Aneelerh, Bayan Baba mai Gadi Ya buɗe masu gate Dr Shureim ya shigar da motar ciki, a parking space ya dakata.
"Mu shiga ciki" Girgiza kai ya yi, "ki fara shiga zan shigo daga baya" amsa mashi tayi da toh,
Fitowa ta yi ta nufi cikin gidan, bakinta ɗauke da sallama ta shiga...
"Muryar wa nake ji kamar Benazir?" Murmushi ta saki tare da sauke idanunta akan Mami da Ummi dake zaune a falo suna kallo a tv, gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta bayan sun amsa sallamar da ta yi...
"Wlh ni ce Mami, na yi maku zuwan bazata ban kira na faɗa ba" ta fada tare da karasawa ta dan duƙa gaban sofa ɗin da suke a zaune ta gaishe da su.
"Ina wuninku, fatan na same ku lafiya"
A tare suka haɗa baki "lafiya lou, ya mutanan gidan naku?"
"Suna nan lafiya, Sun ce agaishe masu da ku."
"Ina Zeenatu da Shureim namu"? A cewar Mami,
"Yaya Shureim shi ya kawo ni, yana a waje, shi ya ce in fara shugowa zai biyo ni, mun baro Zeenatu a gida za su je office tare da Mommynta."
Mami tace"Allah Sarki, na ji kin ce kin yi zuwan bazata baki kira kin fada ba, nan ay kamar gidan ku ne Benazir, naji dadin zuwanki..." Still fuskarta dauke da murmushi..
Ummi ta ce"Ga mutuniyar taki can, ta ɗaura aure da zaman ɗaki, dan Allah Benazir in kin shiga ki yi kokarin kwantar mata da hankali, kwanakin nan mun rasa gane kanta,"
"Bata da lafiyane?"
Mami ta ce, "Hmmm, ta sanya damuwa a ranta ne, wai kwanakin nan tana yawan yin mafarkin su Uzair shine fa duk tabi ta hana kanta sukuni..."
"Subhanallah!" Fuskarta da damuwa ta faɗa tare da miƙewa ta nufi dakin Aneelerh..
A bakin kofar dakin ta tsaya, kusan sau uku tana doka mata sallama shiru ba'a amsa mata ba, har saida ta fara gajiya da tsayuwa, a ƙarshe ta yanke shawarar shiga ciki.
Tana Shiga idanunta suka sauka akan Aneelerh dake a kwance kan gado, ta ƙurawa Ceiling idanunta ko kyaftawa bata yi, lamarin ya daurewa Benazir kai, a ranta ta ayyana wannan wata irin damuwace da zata sa aita maka sallama baka ji?
Ta karashe zancen zucin tare da kai hannu saman kafar Anila ta 6aka mata bugu, wata irin zabura ta yi, a firgice ta miƙe zaune tana zare idanunta muryarta na rawa ta furta,"Na shiga ukuna!" hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta.
Hankalin Benazir ba karamin tashi ya yi ba, ganin yadda Aneelerh ta rame kwata kwata bata a cikin nutsuwarta.
"Ni ce fa..." Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta sauke Idanunta akan Benazir don sam bata lura da ita ba.
Numfashi ta dan ja tare da sauke ajiyar Zuciya ta ƙaƙaro murmushi kan fuskarta..
"Benazir ke ce? Meyasa baki fada min zaki zo ba?" Bata tanka mata ba har saida ta samu guri ta zauna daga gefen gadon kafin ta maida hankalinta kan Aneelerh.
Duk tabi ta dabarbarce ganin irin kallon da Benazir ke yi mata, washe baki ta shiga yi tana kokarin danne damuwarta ta ce, "Sannu da zuwa Benazir, ya ki ke? Ya su Mami? Ina ya Shureim da zeenatu?"
Cike da damuwa Benazir ta furta, "Don Allah meke damunki haka Aneelerh? sau uku ina doka sallama baki amsa ba, nama yi zaton kin shiga toilet ne ko bacci kike yi, ashe idonki biyu kina a kwance kin takura kan ki, why pls dubi yadda kika rame? Fuskarki duk ta yamutse kamar wata tsohuwa" Ta fada tana ƙare mata kallo..
A rude Anila ta girgiza kai muryarta da in-ina ta ce,"Lafiyana lou ba abun da ke damuna..."
Kaitsaye Benazir ta ce, "ƙarya ne wallahi, Dole akwai abunda ke damunki sai dai idan baki son fadamin ne."
Murmushi ta dan yi,"Bafa wani abu bane, kawai ina yawon yin mafarki akan Uzair...." tunkan ta kare maganar Benazir ta tari hanzarinta, "Mami ta faɗa min hakan, amma ban yarda ba Anila, Look, nifa nasan wacece ke, mafarkin Uzair bazaisa ki shiga damuwa har haka ba, bayan kinsan mafarki ba gaskiya bane, in ma hakanne a yadda nasanki da tawakkali Addu'a zaki dage kina cigaba da yi masa bawai ki tsananta damuwa ba, kawai ni yanzu ki fadamin meke damunki kinsan tsakanina dake babu 6oye-6oye, Kinsan sirrina nasan naki, kuma dai abokin kuka shi ake fadawa mutuwa, pls In har kin yarda da ni...."
Shiru Anila ta yi jim tana tunanin kodai ta fadawa Benazir watakil ta taimaka mata su nemi mafita, ruƙo hannayen Benazir ta yi acikin nata, suka ƙurawa juna ido..
A hankali hawaye suka fara zarya kan kuncin Anila, hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Benazir ya yi ba.
"Zan fada maki saboda na yarda dake, amma dan Allah ki rufa mini asiri Benazir, bana so kowa ya sani mu barshi a matsayin sirri tsakanina da ke.." A ƙagare Benazir ta jinjina mata kai.
Nan take Anila ta fayyace mata komai, tun daga ranar da suka je gidansu Hajiya Adama da abunda ya faru bayan dawowarsu game da 6atan Ana, da inda suka ga Baby Junaid a sume cikin drawer shelve da yadda Junaid ya burkice masu suka rasa gane kanshi, komai saida ta sanar da ita, har wayar Ana ta curo daga cikin pillow case ta kunna mata videon ta mika mata don ta gani da idanunta.
tunkan ta Ƙarasa kallo yatsun hannunta keta kerma kamar wayar zata kife kasa, idanunta azazzare cike da tashin hankali ga wani irin faduwar gaba da take ji, labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairan minha..., bata ƙare sallallamin ba Anila ta yi saurin toshe mata bakinta da tafin hannunta gudun kada wani ya ji yo su.
Tuni hawaye sun wanke fuskar Benazir, Sai faman girgiza kai ta ke yi.
Cikin muryar rada Anila ta ce,"Allah abun tsoro dan adam abun tsoro, muna nan sake da baki ashe muna a tare da mugun iri acikin mu! Benazir ki fada min taya hankalina zai kwanta? Wai Uncle dina shi ne yake aikata wannan fasikancin a cikin gidan nan? Babban tashin hankalina Ina Ana? Yau kusan wata uku babu ita Benazir, ina jin tsoron ace ya kashe ta...." Ta fada tana kuka ƙasa kasa.
A hankali Benazir ta zame hannun Anila data toshe mata baki da shi.
Hawaye wasu na bin wasu akan kuncinta ta ce, "Anila dama Ana ta 6ace shine baki fadamin ba tun lokacin da abun ya faru?"
"Na yi zaton da son ranta ta gudu shiyasa ban fadamaki ba saboda na saka ran zata dawo."
Jinjina kai Benazir ta shiga yi.
"Mugu bashi da kama Anila, munafuki kamar na Allah, wlh bazamu kyale shi ba, dole mu ƙwatarwa Ana hakkinta sannan mu maka dan iska gurin hukuma...."
bata kare maganar ba Anila ta yi saurin katse ta, "Pls ki daina ɗaga murna bana so wani ya ji, yanzu me yakamata mu yi? Kin dai ji ta ce mutunne mai hadarin gaske in har muka yi kuskuren da maganar ta koma masa zai iya salwantar da rayuwarmu tunda ba imanine da shi ba, Allah kaɗai ma yasan munanan ayyukan da yake aikawata bayan wannan da Ana ta fada."
Jinjina kai Benazir ta yi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abubuwan dake faruwa da ita a gidan Uncle Musa, yunƙurin kashetan da ake yi ga kuma kurciya da aka yi mata, tun rana ta farko da aka fara yi mata take zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta.
Anila da ta zuba mata ido ganin ta yi shiru bata da niyar yin magana yasa ta dafa kafadarta, "Benazir kin yi shiru ba ki ce komai ba?" Numfasawa Benazir ta yi kafin ta ce, "Aneelerh, akwai damuwa, nima fa akwai wanda ke bibiyar rayuwata a gidan Uncle Musa, kusan sau hudu ana yunkurin kashe ni....."
Waro idanu waje Anila ta yi, cike da ruɗani take kallon Benazir ya yin da gabanta ke faduwa rass rass!!!
Nan Benazir ta labarta mata komai da ya faru da ita tun farkon zuwanta gidan..
"Aneelerh wallahi ba don Allah yana kawo min ɗauki ba, da tuni an jima da kashe ni, don ma yanzu babu tabon yatsun hannun mutumin a wuyana ya goge dana nuna maki kin gani"
Hankalin Anila fa ya tashi sosai, duk tabi ta rude, "Benazir! anya ba iska bane? In ba haka ba wanane zai yi maki hakan agidan Uncle Musa? Gidan dake a tsare da Security Officers taya wani bare zai iya shigowa har dakin ki ya yi yunƙurin kashe ki??" ta fada tana zare idanunta...
Girgiza kai Benazir tayi, "Wlh Anila ba iska bane, mutunne! Abunda yasa na kara karfafa zargina saboda abu biyu, na farko kurciyar da aka yi mini! Aka rabani da dangina, Na biyu labarin da Ana ta bada, Shine ma ya farfaɗo da tunanina, koma wanene mutunne kuma yana amfani da sihiri kamar yadda Ana tace Uncle ɗan-iya yana amfani da sihiri gurin sarrafa ta"
Da ƙwarin gwiwa ta yi maganar tana duban Anila wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa yake yi kamar mazari.
"Ina zargin mutumin da yayi min kurciya shine yake son kashe ni.."
Cikin shesshekar kuka Anila tace, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'iun! Banazir mun shiga Uku! Wanene wannan? Laifin me ki ka yi masa da ya ja har ya ke son raba ki da rayuwarki? Wai dan Allah meyasa hakan ke faruwa da rayuwarmu? Daga wannan sai wannan?"
Maganar Anila ta sake tuna mata abunda ta faɗa mata game da Taj, cikin saurin ta ce, "Anila! Kinsan tunanin da nake kuwa??" Girgiza kai tayi da sauri, "A'a."
Gyara zama Benazir ta yi,
A labarin da kika bani na abunda ya faru da su Uzair, kin tuna Alhazawan da suka yi ma leƙen asiri? Har suka rikiɗa suka handame uba da ƴa'yansa saboda yayi masu leƙen asiri...?" Cikin sauri Anila ta jinjina kai,"Kwarai kuwa haka ne!"
"To baki tunanin ko halin da nike ciki nada alaƙa da hakan, sai nike ganin kamar idan muka fada ma Taj komai zai taimaka masu gurin yin binciken da su ke yi akan Alhazawan nan da kuma 6atan Uzair? Kuma kinga Taj yanzu jami'e ne shi, sannan yana a gidan Director General In har muka je masu da maganar wallahi ina mai tabbatar maki zasu dauki mataki akan Uncle dan-iyan, tunda su jami'ai ne sun fi mu sanin ta yadda zasu bullowa lamarin, ko ya kika gani?" wata irin nannauyar ajiyar zuciya Anila ta sauke, Wlh sham ta shafa'a ta manta da cewa Taj jami'in bincike ne ai da tuni ta sanar da shi komai.
"Ban ta6a sanin ni shashasha bace sai yau da kika ankarar dani, Mu da muke da jami'i a hannu, Wlh gaba ɗaya kaina ya kwance tsawon kwanakin nan inata neman mafita, kwata kwata tunanina bai bani in tuntubi taj ba, nama manta da cewa shi jami'i ne sai yanzu da kika tuna min."
Murmushi suka sakar ma Juna.
"Yanzu ya za a yi? Babu buƙatar 6ata lokaci, da zafi zafi ake bugun ƙarfe, ƙwara muyi amfani da damar da muke da ita tunkafin lokaci ya kure mana" A cewar Anila.
Benazir ta ce, "Ay daga nan sai gidan DG, Nifa dama da shirina nazo wlh, na ma manta ban fada maki abunda ya kawoni ba saboda halin dana riskeki..."
"Anila kusan One month bana samun Unaisah a waya! Shima Taj kona kira baya picking? Baki ga na rame ba nima? Damuwa ce wllh, Gashi kwanakin nan sai munanan mafarke-mafarke na ke yi akanta da ni kaina, Ina ji araina kamar wani abu na faruwa da su..."
Fuskarta a marairaice ta faɗa, Anila ta ce, "Ai bake kadai ba, Ni kaina Idan na kira bana samun su a waya, wlh hankalina ba a kwance yake ba, don ma tashin hankalin videon nan da na gani ya dauke mun hankalina almost 2 weeks ban neme su ba."
"Ba surutu yakamata mu tsaya muna yi ba, na baro Dr Shureim a waje yana jirana, ki tashi ki shirya mu tafi."
_________________________________✍️
"Shiru Har yanzu basu fito ba," A cewar Ummi, Mami ta ce, "Kinsan ƙawaye In aka haɗu ba'a gajiya da fira,"
Ummi ta kuma cewa,"Kuma na ji ta ce ita da yayanta ne, shi ba zai shigo bane? An bar shi a waje yanata jira."
"Nima abunda na gani kenan, bari na je na yi masu magana su je suce ya shigo." tana kokarin mikewa sai ga Benazir da Anila sun nufo falon hannunsu ruƙe cikin na juna.
Ba zaka ta6a gane sun yi kuka ba, kowaccensu ta gyara fuskarta ko alamun hawaye babu, dubai abaya Anila ta saka ta yi rolling veil akanta ko makeup bata tsaya yi ba.
"To fa Ina zuwa kuma? Ai da yanzu nake niyyar shigowa inji me ake kitsawa ne, Kun yi zamanku shiru a ɗaki."
Murmushi suka saki, Mami ta kuma cewa, "Yakamata kuyi wa Shureim magana ya shigo ciki mana."
Sai lokacin Anila ta ce, "Dama zamu fita unguwa ne."
"Ina zaku je ne?" Kallon juna suka dan yi kafin Benazir tayi saurin cewa, "Gidan Hajiya Adama, tuntuni ni ke ta so inje Allah bai nufa ba, sai yau na yanke shawarar zan zo Anila ta rakani, dama itace ta fadamin sun dawo nan da zama...." Fara'a Mami tasaki, "Kai Amma kinyi tunani mai kyau, nima nayi kauron baki ne amma wlh abun na araina, tuntuni nike ta so in shawarci Anila ta raka ki ku je su gan ki, ni nasan zasu yi murnar dawowarki."
Ummi ta ce, "Nifa wlh na yi zaton ma sun san da dawowarta, ashe ba'a fada masu ba, gaskiya ba'a kyauta masu ba"
"Ai yau zamu wanke laifinmu, zan basu mamaki, har gida zan kai masu Benazir" A cewar Anila, dariya su ka yi, Mami ta ce, "Ku tafi yana ta jiranku gashi ko ruwa ba a kai mashi bama, in kun isa ku gaishe mana da su, sannan kada ku daɗe dan Allah, zan ma kira Abie dinku in faɗa masa"
"Zasu ji, in sha Allah bazamu dade ba."
A bangaren Dr Shureim, har ya gaji da jiran Benazir jin shiru bata fito ba, buɗe motar ya yi tare da fitowa da niyyar ya bisu, ƙarar horn din motar da ya ji ne yasa shi ɗan dakatawa ya juya yana kallon motar dake kunno kai cikin gidan.
Ta gaban shi motar ta wuce ta yi parking a gaban entry hall, bayan ta kashe motar ta fito tare da zagayawa other side din motar ta buɗe backseat, ta ɗauko baby Junaid dake ta sharar bacci jikin shi sanye da uniform dinshi, dayan hannunta ruke da food basket dinsa, Two weeks kenan da komawarsa School.
"Yaya Shureim ina wuni?" Ta faɗa da fara'a akan fuskarta,
Fuskarshi dauke da murmushi yace, "lafiya lou Zahra, ya kike? Ya gajiyar aiki?"
"Alhamdulillah, Kai kadai ka zo ne"?
"Benazir na kawo tana ciki." ya fada tare da kallon Junaid, "Junaid bacci ake yi, ankwaso gajiyar school."
Murmushi Zahra ta yi tare da cewa, "Mu shiga daga ciki" Ta faɗa tare da yin gaba yabi bayanta, har sun kusa shiga falon sai ga Benazir da Anila sun fito suka yi kacibus da juna.
Da fara'a Zahra ta gaishe da Benazir ta amsa mata da fara'a itama akan fuskarta.
"Aunty Benazir why zaki bar ya Shureim a waje fisabilillah?"
Yar dariya Benazir tayi, "Bafa ni na hana shi shigowa ba, shine ya ce in fara shiga zai biyoni daga baya."
Bayan Anila ta gaisa da Dr Shureim ta ce ma Zahra unguwa zasu fita, ta kula da Junaid, sai zuwa anjima zasu dawo."
Bata nemi sanin inda zasu je ba ta ce, "Allah ya dawo daku lafiya."
Suka amsa da ameen, bayan Zahra ta shige ciki Dr Shureim ya dubesu da dan mamaki yace"Bangane ba! ina zaku je ne?"
"Yaya Shureim mu je zamu faɗa maka."
Bai yi musu ba suka nufi motar, bayan duk sun shiga ya tasheta suka tafi.
_____________________Obie Estate🔥
Koda suka ƙaraso main gate na estate din basu sha wahalar shiga ba, Security Officers basu dakatar da su ba, Saboda sun gane fuskar Anila kuma tayi masu bayanin cewa gurin Hajiya Saratu suka zo, suna jin hakan suka basu permission din shiga.
Bayan Motar su ta shiga cikin estate din kaitsaye suka nufi villa ɗin Owais, Tunkan su ƙarasa Security Officers din dake tsaron gate din suka nufo motar hakan yasa Dr Shureim yin packing din ta.
Officers shidda ne suka yiwa motar tasu ƙawanya,
Knocking window glass din aka yi, "Get out of the car!" ɗaya daga cikin su ne ya umarta.
Bayan sun fito suka fuskance su.
"Su wanene ku? Daga Ina kuke? Wa kuka zo nema?"
Da hannu Dr Shureim ya nuna Benazir da Anila, "Ai sai ku yi masu bayani, Ni dama ban so zuwa ba, don nasan ba lallai mu samu shiga ba, amma kuka matsamin, yanzu ba ga irinta nan ba." ya faɗa fuskarsa a haɗe don shi baya son abunda zai haɗa shi da masu kaki...
"Ki kira Taj din a waya, Ni nasan kona kira ba lallai ya ɗaga ba."
Benazir ce ta faɗa idanunta akan Officers din da suka zuba mata ido har saida Dr Shureim ya ankara da mayataccen kallon da suke binta da shi, ransa ya 6aci cikin harshen larabci yace ta lullu6e jikinta da mayafinta.
Da sauri ta gyara mayafin ta lullu6e kirjinta da kanta sa6anin da da yake akan kafadarta, duk da haka basu daina kallonta ba, ta ji haushi ita da ta yi kwalliya don Taj ya gani sai gashi wasu na nema su riga shi gani.
Almost 3 times Anila tana doka masa kira baya picking, hankalin su ba ƙaramin tashi ya yi ba..
"Ya zamu yi Benazir! Ya ƙi ɗagawa wlh"
"Keep trying, idan ba haka ba wadannan masu fuskar shanun ba bari zasu yi mu shiga ba."
Cikin harshen larabci ta yi maganar..
Murmushi Dr Shureim ya yi tare da ɗan girgiza kanshi jin abunda yar'uwarsa ta fada, jami'an kuwa sun baza kunne da yake ba arabi da ace da hausa ko da turanci ta fada da taci na jaki.
Taj na ƙoƙarin fitowa daga toilet yana ta gungura wheelchair dinsa ya jiyo muryar Batool tana kwaɗa masa kira,"Daddy, wayarka tana ringing, wani ne ke kiranka"
Har ya nufi ƙofar dakin sai gata ta faɗo ko sallama babu, tana ta haki ta miƙa masa wayar tana fadin, "A falo ka barta saman hannun kujera."
Bai kar6i wayar ba sai cewa ya yi ta karanta mashi sunan me kiran, ɗan zare ido ta yi kafin ta dubi sunan da ya bayyana akan screen din wayar.
"An..An..Antin Yu.. nai..sah.." daƙyar ta ƙare karatun a lokacin har kiran ya katse, Murmushi Taj ya sakar mata, "Auntyn Unaisah ne, kin yi kokari daughter, Allah ya yi maki albarka."
Ya faɗa tare da kar6ar wayar, sai faman sakin murmushi ta ke yi, tana son taji an yabeta in ta yi abu.
"Ina ƴar uwar taki ne?"
"A ɗaki na barota kudundune cikin bargo."
"Bacci ta ke yi ne?"
Girgiza kai ta yi, "Waya ta ke yi da Chief, Daddy baka ji yadda take kashe mishi murya ba hada shagwa6a fa," fashewa yayi da dariya har fararen hakoransa suka bayyana.
"Shaƙa mini in ji me take ce masa?"
Da biyu ya yi maganar saboda yana son yadda Batool take kwaikwayon maganar Angel dinsa, aiko da yar shagwa6a ta ce, "Shine ka tafi baka jira na tashi daga bacci ba, pls kada ka daɗe ka dawo gida bazan jure zama batare dana sanyaka a idanuna ba"
Tuntsirewa Taj ya yi da dariya, Itama dariyar ta kama yi yadda kasan uba da ƴarsa.
"Daddy, ka ji daɗi?" Ɗaga mata kai ya yi, "Sosaima, kema da kika bani labarin ga wannan" Ya fada tare nuna mata robar peanut din da ya aje kan drawer bai kaiga fara ci ba, da sauri taje ta dauka tare da yi ma shi godiya.
Fitowa ta yi daga ɗakin jikinta a sanyaye, kwata kwata babu walwala, a saman stairs ta zauna hawaye cike tab da idanunta take kallon Peanut din da daddy Taj ya bata, A hankali ta soma ɗebowa tana afkawa a baki tana ci, hawaye na sintiri kan kuncin ta, Allah kaɗai yasan me ke damun ta.
Fitar Batool ke da wuya, wani kiran na Anila ya sake shigowa wayar tasa, picking ya yi tare da kara wayar a kunne.
Bayan sun gaisa ne Anila ta fada masa gasu a bakin gate na gidan security sun hana su shiga ya taimaka ya yi masu hanya su shigo.
Shiru ya yi yana tunanin hanyar da zai dakile shigowarsu saboda baya son suga halin da yake a ciki, ga Chief ma baya nan, bayan haka ba'a son ma kowa yasan wani abu dangane da farmakin da suka kai, in har su Anila suka gan shi zaune kan wheelchair dole hankalinsu zai tashi harma su nemi jin me ya faru da shi..
"Taj na ji ka yi shiru baka ce komai ba?" Muryar Anila ce ta katse tunanin da ya ke.....
Muryarsa a dabarbarce ya furta, "Anila meyasa baki kira kin fadamin zaku zo ba?"
"Banyi tunanin yin hakan ba, saboda na ga Almost weeks kona kira bana samunka."
"Anila, sai dai ku yi hakuri ku koma gida, yanzu bama nan mun je yin meeting a headquarter ɗin mu."
On the Other Hand Anila ta zabga salati tana fadin, "Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, dan Allah Taj ka taimaka ka bada iznin a barmu mu shiga ciki, wlh zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo gidan, Don Allah Taj, wlh wani abune mai mahimmanci ya kawo mu, It's urgent, please help."
Ta fada tana kallon Benazir data yamutsa fuska kamar zata sanya kuka.
Shiru Taj ya yi yana nazarin maganarta, tun daga kan yanayin muryarta ya fahimci da akwai wani abu da ya kawota gidan,
"Okay, ku ɗan jira"
Ta amsa mashi da toh, rejecting call din ya yi, ya shiga tuntu6ar layin Chief, almost 5 times tana ringing bai yi picking ba, ana shidda ne ya ci sa'a Chief ya ɗaga kiran..
"Yalla6ai mun yi baƙi, Anila ce tare da Benazir, Wlh bansan da zuwansu ba saboda basu faɗamin ba, sai dai kawai ta kira a waya ta fadamin suna a bakin gate an hanasu shigowa, wlh da nasan da zuwan da bazan bari suzo ba, amma na ji Anila tace matsalace ta kawo su."
Koda jin wannan maganar Chief ɗin ya ce zai yi magana a basu iznin shigowa ciki.
Godiya Taj ya yi masa bayan sun yi sallama, ya zura wayar Cikin aljihun jallabiyar sa.
A hankali Motar Dr Shureim ta karaso cikin parking space, bayan ya tsayar da ita. suka fito daga ciki, kallon kallo Benazir da Anila suka jefawa junan su.
"Yaya Shureim ko zaka jira mu anan?" Benazir ce ta yi maganar saboda basa son su shiga dashi ba don komai ba sai don kada su ƙetare iyakarsu ga kuma gargadin da aka yi masu.
"Ba damuwa, ku shiga zan jira ku, but pls kada ku daɗe."
Amsa mashi su ka yi da toh kafin suka nufi main door na falo, suna ƙarasawa ƙofar ta zuge suka shiga bakinsu ɗauke da sallama, wani sanyayyan sanyin Ac ne na daban ya ratsa fatar jikinsu har wani lumshe idanu suka yi.
Time da suka buɗe idanun nasu kaitsaye suka sauka akan Taj dake a zaune kan Sofa ya nutsu yana jiran ƙarasowarsu, Ba zaka ta6a gane yaji rauni a cinyarsa ba saboda ya lullu6eta da jallabiyar jikinshi, Sofa ɗin ma daƙyar ya samu ya yi dubarar da ya zauna akanta, da ɗayar ƙafarsa me lafiyan ya tura wheelchair din ta koma tsakankanin sofas saboda baya son su ganta.
Ta wutsiyar idanunshi ya ke hangosu yayin da suke nufo shi.
Anila ta yi mamakin ganinsa bayan ya ce mata basa nan ashe yana nan, komi yasa ya boye mata da farko? Ta ayyana a cikin ranta.
Har saida suka ƙaraso kafin ya ɗan ɗago da niyyar ya kallesu karaf idanun shi suka shiga cikin na Benazir, har saida ya ɗan ji gaban shi ya faɗi saboda kyan da ta yi ma shi, amma da yake namijin duniya ne sai ya haɗe rai tare da kawar da idanun shi.
Murmushi Anila ta yi kafin ta gaishe shi ya amsa mata fuskar shi asake.
Cikin sanyin murya Benazir ta gaishe da shi a daƙile ya amsa mata..
"Ku zauna."
A kan Sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna suna fuskantar shi....
Gaza jurewa Benazir tayi idanunta cike tab da ƙwalla ta ambaci sunan shi"Taj!" Shiru bai tanka mata ba..
"Nasan har yanzu fushi kake dani, amma meyasa idan na kira baka picking? Har saƙo na tura maka akan ka taimaka ka haɗani da Unaisah saboda idan na kira bana samun layinta amma kwata kwata ba response..."
Hannu ya ɗaga mata tuni ta haɗiye maganarta, "Dama wannan ne abun da ya kawo ku?"
Ƙasa-ƙasa da murya Anila ta raɗa mata "pls ki aje wannan maganar gefe, ki yi haƙuri mu yi abinda ya kawo mu, kinga daƙyar muka samu aka bamu damar shigowa ciki." Jinjina mata kai ta yi alamar ta gamsu.
Mayar da dubanta ta yi akan Taj, "Dama issue ne akan yar aikin gidan mu Ana data 6ace yau wata Uku kenan."
Jin wannan maganar Yasa Taj ya maida hankali akan Aneelerh.
Dakatawa ta ɗan yi ganin kuku ya nufo su hannun shi ruƙe da wooden tray na fruit da cool drinks ya ajiye masu kan table, bayan ya tafi Aneelerh ta cigaba da zayyana masa komai da ya faru har izuwa kan videon da ta gani...." tunkafin ta kai ƙarshen zancen yanayin fuskar Taj ya sauya zuwa tsantsar mamaki, tashin hankali da kuma ruɗani...
"Zan iya ganin Videon??"
Da sauri tace "Eh," Ta faɗa tare da zaro wayar daga cikin handbag dinta ta shiga pressing dinta, bayan ta kunna masa video ta miƙe taje gaban shi ta miƙa ma shi.
Bayan ya kar6a, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi matuƙa, saboda tsabar girgiza da kidima duk da sanyin A.c din falon saida ya fara zubda gumin zufa lamarin ya ɗaure masa kai, Lallai sun zo da case mai girma, abun da ya ɗan jefa shi a rudani a bayanin Ana ya fahimci shi Uncle ɗin Anila matsafine kuma abun da yake yi ma Ana yayi kamanceceniya da cin zarafin da Elders su ke yi wa prisoners a lokacin da suke yin jinin al'ada.
A dabarbarce ya furta, "Anila dama Ana tana nan?"
Idanunta cike tab da ƙwalla tace, "Eh, atare da ita muka dawo gidan Uncle din"
Jinjina kanshi ya yi Idanunshi sun kaɗa sun ɗan yi ja,
"Ku sha lemun" Ya faɗa yana nuna masu drinks din..
Miƙa hannu Anila tayi ta dauki Juice ta tsiyaya masu a glass cups, saboda dadin da ya yi masu kusan duka suka shanye..
"Tanimu Ja'afar Falgore, inkiya Ɗan-iya shine full name na uncle dinki ko?"
Ya tambaya yana kallon Anila, Jinjina mashi kai ta yi alamar eh, a ransa ya furta karen yan siyasa zai aikata fiye da hakan, ya ƙarashe zancen zucin nashi tare da aje wayar Ana a gefen sa.
Har ya zaro waya zai dannawa Chief kira maganar Anila ta dakatar da shi...,
"Benazir na ji kin yi shiru baki ce komai ba? ba zaki fada masa abunda ke faruwa dake ba?"
Cikin karyayyar murya ta wanda ke shirin saka kuka tace,"Ba ki ga ko kallona bai son yi ba, Even if I tell him, he won't take me seriously."
A hankali Taj ya dubi Benazir da tayi maganar, idanuwansu suka shiga cikin na juna, da sauri ta kawar da nata idanun gefe ɗaya.
"Ina sauraronki! Faɗamin me ke damunki?" Wani sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta jin ya kula ta, aikuwa ta gyara zama ta fara labarta masa abun da ke faruwa da ita, nutsuwa ya yi yana sauraronta, dan dakatawa ta ɗan yi tana haki kamar wadda tasha gudu.
Da hannu ya nuna mata Mineral water,"Ki sha" da sauri ta dauka ta ɗan kur6a.
Bayan ta ajiye taci gaba da bashi labari..
*bari mu koma baya don jin meya faru a ranar da Benazir ta dawo daga gidansu Anila bayan ta fada mata komai dangane da batansu Angel harta kulle kanta a daki, a ƙarshe da aka bude dakin aka iske ta kwance a ƙasa rabin jikinta a cikin toilet👇*
Bayan da ta gama shan kukanta tamkar ranta zai fita, lokaci ɗaya ta fara Jin azababben ciwon kirji, tana jiyo bugun kofar da suke yi mata haɗi da yi mata magiya akan ta bude amma taƙi saboda bata son ganin kowa a kusa da ita, a kan floor ta kwanta tana cigaba da sharar ƙwalla.
"Pls idan kina saurarena ki tashi ki kunna karatun alkur'ani kada ki kwana a haka, yakamata ki yi hada nafila..." Muryar Dr Shureim ta jiyo acikin kunnanta.
Daƙyar ta iya tattara ƙarfin da ya yi saura a jikinta ta mike ta nufi toilet don tayi alwala kamar yadda Dr Shureim ya shawarce ta.
A gaban sink ta tsaya tare da kunna faucet, ta soma yin alwalar sai dai gaba ɗaya hankalinta baya a tare da ita, ta lula duniyar tunanin ina zata ga Taj da ƴarta? Tana tsaka da yin alwalar hasken electric bulb din dake a saman ceilling ya fara wasa ya kawo ya dauke, bata kawo komai aranta ba ta yi tsammanin electricity din gidan ne ya samu matsala, hakan yasa taci gaba da yin alwalarta.
Bata yi aune ba, unexpectedly glass din madubin da take fuskanta ya fara tsattsagewa, a razane ta ƙura ido tana kallon abun mamakin gani take kamar idanunta ne ke nuna mata ba dai dai ba, dama bata a cikin hayyacinta damuwa ta fara zautar da ita, miƙa hannu ta yi da niyar ta shafa madubin don ta tabbatarwa kanta abunda take gani gaske ne ko ƙarya kwatsam! madubin ya tarwatse da kan shi glass din ya zubo kan floor, har ta kware baki zata fasa ƙara ta ji an fusgo hannuwanta izuwa cikin madubin, ta ƙarfi da yaji ake kokarin janta cikin shi, fashewa ta yi da matsanancin kuka na tashin hankali ta dinga yan buge-buge tana ƙoƙarin kufcewa yayin da hannayen da suka rurruke nata suka ja kusan rabin jikinta cikin madubin, daddagewa tayi da iya ƙarfinta na ƙarshe ta shiga karanta ayatul kursiyu bata kaiga direta ba ta ji an wurgo da ita gaba ɗaya gangar jikinta ta dawo cikin toilet ɗin kanta ya daki floor, A zabure ta miƙe ta watsa a guje ta nufi ƙofa sai dai me? Kafin ta ƙarasa ƙiiiii taji kofar ta datse kanta, fasa ƙara ta yi da ƙarfi take ambaton sunan Yaya shyureim dana Mommyn su don su kawo mata a gaji, bugun kofar ta dinga yi kamar zata 6alle ta, gurnanin mutun ta jiyo a bayanta jiyowar da zata yi keda wuya tayi arba da wani gabjejejn mutun ƙaƙƙarfa jikinshi sanye da baƙaƙen kaya ya rufe ko'ina na jikin shi, zazzare mashi idanu ta yi kamar mai fama da farfaɗiya ta dinga farfari zuciyarta na bugawa da tsananin fargaba ta dinga sambatu tana fadin, "Na shiga Uku!!! Wanene kai? Wallahi kada ka ta6a ni, kada ka matso kusa dani, zan ƙona ka da ayar Allah..., bata ƙare maganar ba ya ɗaura gabjejen tafin hannunsa kan wuyanta ya damƙe shi ya jata tana kuka da yan buge-buge ya nufi bathtube da ita, wani irin ruwan zafi ne ya kwararo ta cikin faucet har tiriri yake yi kamar za'a zabka kaza haka ya soma ƙoƙarin tura kanta cikin ruwan, wanda hucinsa kaɗai bala'e ne tsaf zai ƙona fatar mutun, fashewa tayi da kuka tana ihu ga bleeding da hancinta ya fara yi,
Sai yakushin hannunshi take yi don ya saketa, yana gab da zai tsumbula kanta cikin ruwan, ta furta wata addu'ar neman tsari da Dr Shureim ya koya mata, wallahi ko second ba a ƙara ba mutumin ya 6ace 6aat hasken toilet din ya daidaita, madubin ma ya maida kansa yadda yake, hannunta dafe da wuyanta dake mata raɗaɗi take kallon Ikon Allah, Wato addu'a tayi a rayuwa musamman in kayi imani ba tare da kokwanto ba, ganin ya 6ace yasa ta zabura aguje ta nufi kofar toilet ɗin ta dinga bugunta daƙyar ta samu ƙofar ta buɗe sai dai kafin ta fuce wani irin jiri ya ɗebeta gaba ɗaya ta yanke jiki ta faɗi yaraf har goshinta ya fashe sakamakon dakar floor da kanta ya yi.
Hankalin Anila dana Taj ba ƙaramin tashi ya yi ba, Sun yi matuƙar girgiza da jin abunda ke faruwa da Benazir.
"Kin taba faɗa ma wani?" Ɗaga kai ta yi,"Eh, Yaya Shureim ne kadai ya sani, amma ban faɗa masa na ranar dana shiga toilet ba saboda ban farfado cikin hayyacina ba.
Cike da al'ajabi yake ɗan jinjina kanshi yayin da zuciyarshi ta cika fam da tashin hankali, Komai da suka faɗa yayi shige da case din da suke aiki akai, yanzu ya fara yarda da abunda Anila ta faɗa masa akan Benazir.
Chief ya kira bayan ya yi picking gaba daya ya fayyace masa abun da su Aneelarh suka sanar da shi, tashin farko ya ce wannan babban al'amari ne, kuma ya ji dadin zuwan su, in ba damuwa su jira shi ya dawo yana son yin magana da su.
Ɗagowa ya yi tare da kallon su Aneelerh, "Ya buƙaci yana son magana daku, zaku iya jira har lokacin da zai dawo?"
Aneeleerh ta ce, "Ba damuwa zamu jira shi"
Faɗa mashi ya yi kafin su ka yi sallama ya aje wayar gefen ta Ana...
"Naga baku sha fruit din ba," Ya ɗan tambaya idanunsa akan Benazir dake ta kallon shi..
"Ni wlh hankalina kwata kwata ba a kwance yake ba, bana jin cin komai"
"Look Aneelerh, Ki kwantar da hankalin ki, tun da har ku ka yi dubarar tuntu6armu in sha Allah komai zai tafi dai dai" jinjina kai ta yi ..
"Ina su Unaisah ne?" Benazir ce ta tambaya
"Suna a daki" ya bata amsa batare da ya dubeta ba...
"Zan iya ganin ta" girgiza mata kai ya yi"A'a!"
"Meyasa? pls Taj, almost one month ban ji muryar ƴata ba? Dan Allah meyasa ka ke yi min haka? Laifin da na yi maka tsakanina da kai ne, banga dalilin da zaisa ka shiga tsakanina da ƴata ba, saboda ni na yi wahalar naƙudarta na kuma haifa maka ita..." ranta a 6ace ta yi maganar tana aika masa da harara.
"Sau nawa kina yunƙurin zubar da cikin nata don kada ya 6ata maki shape?"
Bai ƙare maganar ba Anila ta yi saurin furta, "Dan Allah Taj ku daina, ba girman ku bane, bai kamata aji maganar nan daga bakin ka ba, Benazir koda da son ranta ta gudu tabar Unaisah amma ai tayi nadama ko? Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana yakamata kaima ka yafe mata."
Murmushin gefen fuska ya ɗan saki, "Ni zolayarta nake yi, amma komai ya wuce awurina, sannan ni ba hanata Unaisah na ke yi ba, tayi rashin lafiyane har kwantar da ita asibiti saida aka yi, bana so na ɗaga maki hankali ne shiyasa ko kin kira bana ɗagawa ....."
Bai ƙare maganar ba sakamakon kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji"un da Benazir ta furta tare da miƙewa tana yarfa hannu ta furta "Meke damunta ne? Wani irin ciwo ne ta yi? Don Allah ka haɗa ni da ita! Dama saida na ji a raina wani abu na faruwa da ita, har mafarkinta nake yi ashe bata da lafiya...." Ta faɗa har hawaye sun zubo kan fuskarta,
Da damuwa akan fuskar Anila ta ce, "Taj, meke damun Unaisah ne? Meyasa baka sanar dani ba?"
"Calm down your mind, Unaisah ta ji sauƙi yanzu, bari na kirata ku gaisa."
Ya faɗa tare da ɗaukar wayarsa yana ƙoƙarin danna mata kira Unexpectedly suka jiyo shesshekar kukanta!
Kusan a tare suka kai duban su gare ta, tana a tsaye jikinta sanye da Satin fitted gown black colour tabi shape dinta, bata ɗaure sumar kanta ba,ta sake ta har mid back dinta, ƙafafunta na sanye da highhill masu ɗan banzan tsini....
Jikinta sai kerma yake yi kamar mazari, yayin da idanunta dake fitar da hawaye ta tsayar da su akan Benazir, ashe tunda Taj da Benazir suka fara sa'insa ta fito daga daki kaitsaye maganganunsu suka sauka acikin kunnanta.
"Daughter meyasa kike kuka? Ko jikin ne?" Da damuwa akan fuskar Taj ya tambaya.....
Da index finger ɗinta ta nuna Benazir,
"Dama kece mahaifiyata wadda ta haifeni a wulakance! ta barni a cikin kwamin wanka sannan ta gudu ta tafi ta barni! Dagaske kece Aunty Benazir?"
Rai a matuƙar 6ace ta faɗa da tsiwa tana fitar da numfashi mai huci.
"Ki amsa min tambayata??" Ta faɗa tana zare mata gray eyes dinta...
Tsabar ruɗu da tashin hankali ya hana Benazir furta kalma, wani irin shakkarta take ji....
"Shirun da kika yi ya tabbatarmin da abunda kunnuwana suka jiye min."
Ta faɗa tare da maida kallonta akan Aunty Aneelerh cikin jin ƙunar rai ta ce,"Aunty Aneelerh, I know you won't lie to me tell me, who is she?"
Yawu Aneelerh ta haɗiya ƙutt, cikin sanyin murya ta ce,"Pls Unaisah, zo ki zauna za mu yi maki bayanin komai..."
Fashewa tayi da kuka tare da girgiza kanta, "Daddy, Aunty Aneelerh meyasa kuka 6oyemin cewa itace matar nan data gudu ta barni? Kuka sani na je nayi jinyarta a asibiti, bayan kunsan irin tsanar da tayi mini, bata taba sona ba, wallahi dana san kece bazan taba yin jinyarki ba koda zaki rasa ranki ne" with a burning heart ta faɗa tana aika mata harara.
"Why didn't you kill me at birth if you couldn't care for me? You left me in the bathtub and abandoned me for years, You never thought to return and check on the child you left behind!, wlh hakkina kaɗai bazai bari ki gama da duniya lafiya ba...."
Bata ƙare maganar ba sakamakon tsawar da Aunty Aneelerh ta doka mata, "Unaisah ya isa! Ya isa haka!! Har yanzu ita mahaifiyar kice, karna kuskura na ƙara jin kin gaya mata maganganu marasa daɗi"
Fashewa da kuka Benazir tayi, baiwar Allah tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi.
"This woman will never be my mother! I don't like her, I hate her, I don't want to see her, You're heartless and don't deserve to be called a mother! Dan Allah na roƙe ki ki fuce daga gidan nan in har ba so kike ni in bar maki gidan ba"
Cike da takaici Taj ya dafe forehead ɗinsa da tafinsa, dama saida yayi fargaban zuwan ranar nan, shi yasan za'a rina saboda Unaisah ta ƙullaci Benazir aranta, haushinta take ji sosai, tsanar ta samo asali ne tun daga kuruciyarta.
Bata saurari kowannan su ba ta juya a zafafe ta nufi kofar dakinsu, da gudu Benazir tabi bayanta ta kai hannu tare da ruƙo hannun rigarta, aikuwa cikin fushi Unaisah ɗin ta bangajeta har saida ta yi taga taga zata faɗi, cikin sauri Aneelerh da ta biyo bayanta tayi saurin tallabota.
Rushewa ta yi da matsanancin kuka tana fadin wai ƴar da ta haifa ce ta ke gaya mata magana kamar zata doke ta? "My own daughter calls me heartless! Na shiga Uku Aneelerh ta tsaneni bata son ganina! Wayyo Aneelerh zuciyata zafi ta ke yi min..."
Gaba ɗaya hankalinsu ya tashi da abunda Unaisah ta yi, abun da ya ƙara ƙona ma Benazir rai yadda Taj ya yi banza da su ko motsawa baiyi ba daga kan kujerar da yake balle ma harta sa ran zai taimaka mata su shawo kan Unaisah, tayi masa mummunar fahimta, batasan lalurace ta hana shi miƙewa ba, dama da haushin shi aranta saboda tasan shine ya cusa ma Unaisah tsanarta acikin zuciyarta shiyasa harta ƙullaceta arai in bashi ɗin da ya fada mata ba, Uzair da Aneelerh ba zasu ta6a tona mata asiri a gurin Unaisah ba dole sai in a wurin Taj ta ji.
Bawan Allah Taj damuwa ce ƙarara akan fuskarshi, kwata kwata bai ji daɗin abun da Unaisah ta yi mata ba.
"Aneelerh, Ku dawo ku zauna, ku barni da Unaisah, zanyi magana da ita."
Rai a6ace Benazir ta nufe shi kamar zata doke shi ta damƙi gaban jallabiyar shi da hannyenta biyu tana huci ta ce, "You caused everything Taj, I hope you're happy now, kaine ka cusawa Unaisah tsanata a cikin zuciyarta, saboda kaine ka faɗa mata cewa na haifeta nabarta acikin kwamin wanka, wai laifin me na yi maka ne? Wace irin tsana ka yi minne???"
Runtse idanun shi ya yi batare daya iya furta kalma ba, cikin sauri Aneelerh ta damƙi hannun Benazir ta soma kiciniyar 6am6are shi daga wuyan Taj, "Wai miye hakane Benazir? Idan rai ya 6aci ai hankali bai kamata ya gushe ba, Taj bazai ta6a faɗa ma Unaisah abun da ki ka yi don yasa ta tsane ki ba..."
"Ki barni Aneelerh, wlh bazan ƙyale shi ba, yadda ya saka mata ƙiyayyata acikin zuciyarta dole ya je ya saka mata soyayyata a cikin zuciyarta, saboda shine ummul aba'isin komai, wlh he must fix what he ruined."
Ta ƙarashe maganar tare da bangaje Aneelerh, ta ƙara kakkama gaban rigarshi, ɗaurin kallabin kanta tuni ya jima da zamewa, doguwar sumar kanta duk ta hargitse kamar mahaukaciya, yana jan numfashi da ƙarfi ya furta, "Benazir ki sakar min rigata, mara kunya, har yanzu bazaki ta6a canzawa ba, tsakanin ni da ke wanene mai laifi? Da har zaki ce ni ne silar komai? Bayan kece ummul aba'isin duk wani abu da ya faru..."
Ya faɗa yana buɗe idanunsa da suka kaɗa jawur ransa ya 6aci ganin Benazir na neman ta ɗaura masa laifi.
"Tabbas, Ni na faɗa ma Unaisah, kuma Allah shine shaidata ni ban faɗama Unaisah don ta tsaneki ba, fa ce sai don ta tausayamin ta daina azabtar da ni, saboda a lokacin da tana ƙarama mugun halinta sak irin naki ne, bata jin maganata kusan kashe ni ta yi da baƙin cikinta, kin tashi kin tafi kin barni da jinjira ke baki yi tunanin taya zan iya rainonta ba ne? Benazir in bazaki iya godemun ba bai kamata kiji haushina ba!"
Yana huci ya ƙare maganar, fashewa tayi da kuka tamkar ranta zai fita, Still taƙi sakin gaban rigarshi.
Hankalin Aneelerh ba ƙaramin tashi yayi ba, ganin takasa shawo kan Benazir ne yasa ta watsa da gudu ta nufi hanyar fucewa daga falon don ta je ta gaya ma Dr Shureim, tasan shi kaɗaine zai iya dakatar da Benazir saboda bad temper dinta in takai maƙura a 6acin rai ko mai iskokai bazai nuna mata yadda ake bori ba.
*UMMIN AMERICA🔥*
Su biyu ne a zaune kan rug din dakinta, ita da Batool sun ƙurawa laptop screen idanunsu, wani korean drama ne su ke kallo ita da Batool, Ummi ta toshe kunnuwanta da Headset kwata kwata bata jin wani sauti daga waje saina abunda take kallo.
Batool ce ta fara jin hayaniyar mutane a cikin gidan, tun tana jin maganganun nasu ƙasa-ƙasa har ta fara ji da ɗan karfi.
"Aunty Ummi" Shiru bata amsa mata ba, bubbuga kafaɗarta ta yi, a ɗan firgice ta dube ta, "Babe lafiya?"
"Kina jin hayaniyar mutane acikin gidan nan?"
"Banji me kika ce ba," Ta faɗa tare da zame headset din ta maida hankalinta akan Batool, "Kamar wasu ne ke faɗa acikin gidan nan, naji hayaniyarsu a cikin kunnena, ki saurara ki ji" Ɗan zare ido Ummi ta yi tare da yin shiru ta kasa kunne a hankali ta fara jiyo maganganunsu...
"Su wanane? Ko munyi baƙi a gidan ne?"
Girgiza kai Batool ta yi, "Wallahi nima bansani ba, kawai yanzu na jiyo hayaniyar su kamar faɗa su ke yi...."
Da sauri Ummi ta miƙe, mayafinta data bari akan gado ta ɗauka tare da yafa shi kan kafaɗarta...
"Ki ci gaba da yin kallon, bari na je na gano mana meke faruwa." Ta amsa mata da toh da sauri Ummi ta fuce daga ɗakin......✍️
Dira ƙafarta keda wuya unexpectedly ta tsinkayi muryar Dr Shureim a cikin kunnuwanta..
"Benazir baki da hankali ne? Meye haɗin ki da shi? Mutum da girmansa zaki shaƙe gaban rigarsa!"
Ya faɗa yayin da yake shigowa falon cikin sauri idanunsa akan Benazir da har lokacin bata saki kwalar Taj ba, Anila tana abiye da bayan Dr. Shureim gaba ɗaya hankalinsu ya tashi sosai, batai aune ba Dr shureim Ya damƙi hannunta ya fusgeta gefe ɗaya har saida tayi taga-taga kamar zata faɗi.
Rai a matuƙar 6ace ya dubeta kamar zai kife ta da mari.
"Uban meya haɗa ki da shi? Dama dalilin da yasa kika matsamin in kawo ki gidan kenan? Saboda kawai ki tada husuma?"
Tana shessheka ta ce,"Yaya Shureim Taj ne fa, My Ex-husband, Uban ƴata dana haifa, Azeezaty itace yarinyata Unaisah....."
A ruɗe Dr shureim yake kallon Benazir sam ya kasa furta kalma saboda yadda maganar ta dira a cikin kunnansa ta rikita lissafin kwakwalwarsa.
Juyawa ya ɗan yi tare da kallon Anila wadda jikinta keta kerma saboda fargaban kato6arar da Benazir ta yi masu, bayan irin gargadin da aka yi masu akan kada su fallasa asirin Taj yana a raye.
"Inna lillahi! Benazir meyasa kika faɗa masa? Meke damunki ne? Kin manta amana na faɗa maki, kuma kika yi alƙawarin ba zaki faɗa ma kowa ba!" Ta faɗa a faɗace kamar zata doke ta.
Taj dai tun da ya sunnar da kan shi ƙasa bai ƙara ɗagowa ba saboda halin damuwar da zuciyar shi ta shiga.
Tana kuka ta ce, "Ai wallahi ƙwara kowa ma ya san yana a raye, in ba haka ba baƙin cikin shi zai kashe ni ne! "
Gaba ɗaya Dr Shureim ya gama ruɗewa, sai faman rarraba idanunsa yake yi akan Taj da Benazir da Anila.
Dakyar ya shanye mamakinsa da wata irin raunanniyar murya ya furta, "Dan Allah ku fahimtar dani! Na kasa ganewa, shin dagaske shine Taj mijinki! Azeezaty kuma itace ƴarki Angel?" Ya tambaya yana kallon su...
Cikin sanyin murya Anila ta ce, "Hakane Yaya Shureim." Ɗan zare idanunshi ya yi tare da maida idanunshi kan Taj da tsantsar mamaki yake kallon shi.
"Bawan Allah, ka ji tsoron Allah ka faɗamun gaskiya, da gaske kaine Taj mijin Benazir?" Jinjina mashi kai Taj ya yi alamar Eh.
Baki asake ya kuma mayar da duban shi akan su Anila kamar waɗanda suka yi ma sarki ƙarya sunyi zuru zuru...
Gaba ɗaya sun kasa furta kalma sai kallon kallo suke jefawa junansu...
"Yaya Shureim! Benazir!! Aneelerh!!!
Muryarta na rawa ta furta sunayen su, Kaitsaye sautin muryarta ya daki dodon Kunnuwansu, wata zabura suka yi a firgice suka kai dubansu inda take a tsaye saman stairs fuskarta sharkaf da hawaye idanunta sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono acikin su, yanayin fuskarta ya nuna tsantsar ruɗani da tashin hankali gami da al'ajabin ganin bayin Allahn nan, Tayaya zata manta fuskokin su? Bayan irin haddar da ta yi masu...
"Is that really you? Or am I dreaming? I can't believe my eyes!"
Tashin hankalin da ba'a saka mashi date! Al'ajabine ya ɗaure zukatansu ya hana la66ansu motsawa sai dai idanu da suka bita da su batare da ƙyaftawa, Yau tsawon shekara goma sha takwas da ɗauriya rabon su da yar tahalikar nan tun da ƙaddara ta raba su da ita, ba zasu ta6a mantawa da Aishatu bint Sheikh Imam Malik ba! Ba zasu ta6a manta raɗaɗin da suka ɗanɗana na abun da ya rabasu da ita ba.
"Dama Kunsan Juna ne?"
Daƙyar Taj ya furta maganar yana dubansu, yayi mamakin ganin yadda suka ƙame atsaye idanunsu azazzare kamar waɗanda suka ga wani mugun abu.
Benazir ce ta yi ƙarfin halin furta, "ƘAWATACE AMINIYATACE, ITA ƊIN TAMKAR YAR UWA TA JINI TAKE A WURINMU! YAU SHEKARA GOMA SHA TAKWAS RABON MU DA ITA, TUNDA ƘADDARA TA RABA MU❗❓
*(WAIWAYE ADON TAFIYA)*
*WACECE AISHATU BINT IMAM MALIK? MENENE DANGANTAR AISHA DA ANEELERH DA BENAZIR DA KUMA DR SHUREIM? WACE ƘADDARA CE TA RABA SU❗❓👇*
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
Sponsored Post
Tags
Kurkukun Kaddara
YOU MIGHT LIKE
1 COMMENTS
Idan kuna da tambaya akan abinda Baku game ba ko kuma kuma Neman littafin da babu a nan kawai ku ajiye tambayarku a ta comment ko wani shawara da Zaku bamu.
Anonymous
30 September 2024 at 10:52
Thank you and jaxakillahu Khairan
Reply
Previous Post
Next Post
GET IN TOUCH
Facebook
twitter
YouTube
Instagram
Whatsapp
SUBSCRIBE US
OPINION
FACEBOOK
COMMENTS
CATEGORIES
Africa
(1)
Al'adu
(1)
Alkamawa
(3)
Article
(3)
Blogger Tips
(1)
Economy
(5)
Education
(2)
Entertainment Gist
(1)
Gyaran-Jiki
(5)
Health
(13)
Jikar Iya
(11)
Kimiya
(1)
Kiwon Lafiya
(54)
Kukan Zuci
(5)
Kwalliya
(4)
Labaru
(25)
Lifestyle
(1)
Ma'aurata
(1)
News
(304)
Nigeria
(5)
Noma
(1)
Opinion
(4)
Picture
(3)
Politics
(15)
Profile
(2)
Q&A
(1)
Ramadan
(9)
Ramadan Tafsair
(1)
Siyasa
(1)
Sports
(72)
Tarihi
(5)
Technology
(1)
Tips
(3)
Video
(3)
YouTube
(5)
Zain Abeed
(1)
Zamantakewa
(1)
Novels Elite
Get the Most Exciting News and Read Your Favorite Hausa Novels. Let us be your source for exciting news reports worldwide, as well as access to a wide variety of blogs and blogging tools. We also offer novels in different languages including Hausa so you can easily read what interests you! Plus with our Google Adsense partner program, monetize when readers engage with your content.
Novels Elite
SUBSCRIBE
Posts
Comments
Links
Post a Job
LATEST POSTS
ADVERT
Novels Elite
Copyright © 2024 Novels Elite | All Rights Reserved
DMCA.com Protection Status
Disclaimer |
Privacy Policy |
Terms and Conditions
Our website uses cookies to improve your experience. Learn more
Accept ![14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹
~<✍️~
~___________________________________~
Sheikh Imam Malik Shahararren malamin addinin musulunci ne, kuma babban alkalin Kotun Musulunci, Haifaffen jihar jos ne, wayayyen malamin addinin musulun ci ne kuma dan boko maiji da kanshi, ga wadatar arziki da Allah ya yi mashi, sheikh Imam ya yi suna wajen yin adalci, rukon amana tausayi da jinƙai, yana da ƙwarewa ta fannin shari'ar musulunci, mutunne shi mai tsastsauran ra'ayi akan addininsa, kuma kaifi ɗaya ne In ya furta magana baya canza ta, da dama mutane masu aikata mugayen laifuka suna jin tsoron shari'ar sheikh Imam Malik saboda sun san Halinsa baya kar6ar Cin hanci, dole mutun Ya kar6i hukunci dai dai da abunda ya shuka ko ɗan uban wanene, sannan yana da zuciya idan ranshi ya 6aci, sai dai duk da hakan Yana da sauƙin kai ga wanda ya iya zama da shi.
Matarsa Ta farko Malama Fatima Batool wadda ta kasance Yar uwarsa diyar wan mahaifinsa mazaunin Sudan, Auren zumunci iyayensu suka haɗa su, Kuma cikin Ikon Allah jininsu ya haɗu soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu har takai su ga yin aure, Sunyi zama Na amana saboda Ra'ayinsu yazo ɗaya, Yaji dadin zama da ita saboda kyawawan halayenta, tanayi mashi biyayya sau da kafa, A lokacin data samu ciki yayi murnar da bazata misaltu ba, baya gajiya dayi mata addu'a akan Allah ya sauke ta Lafiya, bayan data haihu ne ta koma ga Mahaliccinta yayin da tabar masa Yar jinjiran da ta haifa masa, Shiekh Imam Yaji rasuwar ta, duk irin juriyarshi da tawakkalinsa sai da ya zubda ƙwalla saboda babban rashin da yayi.
Rainon yarsa ya koma hannun gwaggwansa kanwar Mahaifiyarsa, A lokacin iyayensa duk basa araye, itace ta kula masa da Yarsa Har ta dan fara tasawa.
daga bisani Kawunsa na sudan ya bashi auren kanwar Matarsa Aunty Laura, a wani zuwa da yai sudan kai masu ziraya, A lokacin sheikh imam baida niyar ƙara aure saboda bai warke daga radadin rasa matarsa da yayi ba, amma saboda aunty laura ta kasance Jinin Malama Batool yasa shi amincewa da aurenta.
Bayan auransu da wata daya Rainon Aisha ya dawo hannun Aunty laura, ta rike ta da amana kamar yar cikinta, tana bala'en Son Aisha, saboda jininta ce ita uwa uba kamanninta sak dana Yayarta Malama Batool, saboda yadda take bata kulawa ba zaka taba gane ba yarta bace sai an fada maka.
hakika sheikh imam malik yayi namijin kokarin gurin tarbiyantar da rayuwar yarsa, ya tsaya mata tsayin daka don ta nemi duniyarta da lahirarta, gaba daya halayanta da dabi'unta irin nashi ne, abu daya da bata ɗauko na shi ba shine Zuciya, tana da tsantsar hakuri kamar Mahaifiyarta Malama Batool, hausawa sukace kyan ɗa ya gaji ubansa itama hakan ta ke Aisha tagaji mahaifinta da kuma mahaifiyarta malama Batool.
Sheikh Imam ya ɗaura mata burin duniya, Bai taba son wata aba kamar yarda yaso Aisha ba, ita kadai ce ƴa daya tilo da Allah ya albarkace shi da ita, Babu irin gatan da sheikh Imam bai yi mata ba.
Aishatu macace mai cikar kamala, mai tsantsar kamun kai, samun matashiya mai irin baiwar ilmin da Allah ya bata zaiyi wuya a fadin duniyar nan, ta haddace alkur'ani mai girma tun tana da shekara goma sha uku a duniya, mutane dayawa suna yabonta saboda kyautatawarta a gare su, kyawawan dabi'unta da halayanta abin koyi ne ga duk wata ya mace, kuma burin kowani namiji ne ya mallaki mace kamarta.
duk wani abu da zai sabama Mahaliccinta gudun shi takeyi, tana da jinƙai da son taimako bata gajiya da hidimtawa addininta.
Abun burgewa iyaye mata da matan aure suna karuwa da ita, also she's a role model for young women.
tun tana yar matashiyarta take koyawa a islamiyar Mahaifinta mai suna madarasatul Fatima Batool dake a kusa da gidan su, tana yin wa'azi ta kuma yi da'awa ga waɗanda basuyi imani ga Allah ba, ta dalilin Aisha, Sheikh imam malik Ya samu daukaka fiye da zaton shi, ta kare mashi martabarshi da kirmarshi ta kuma daukaka darajar shi a idon duniya, sau dayawan lokutta baya sanin tayi wani abun, sai dai akira shi awaya ko azo har gida ayi mashi godiya akan alkhairin da Aisha tayi, yai ta mamaki farin ciki ya cika shi, sai ya kirata ya tambayeta me tayi tukunna take fada masa Alherin da take samu a gurin Gasar karatul al'qur'ani da wadanda mutane suke bata kyauta saboda dadin wa'azinta da suke ji, dama A duk lokacin da ta kawo mashi kudin don ya dauki wani abu baya kar6a, kudinne take tarawa in suka taru dayawa da su take amfani gurin tallafawa marasa karfi, tana yawan ziyartar asibitoci, gidajen yari, da gidajen marayu ta basu tallafin kayan abinci da suturu in kuma bata da kudin da zata basu zatayi masu wa'azine da nasiha mai ratsa zuciya, shiyasa sheikh imam ya ke bala'en ji da Aisha, yana matukar son Yar shi, itama bata da abu mafi soyuwa dayawuce Mahaifinta, tana yi mashi biyayya sau da kafa, batason bacin ran mahaifinta, tana kokarin yin duk wani abu da zai faranta ran shi.
Dangantar da ke a tsakanin Benazir da Ayshah da Dr shureim ta samo asali ne tun daga kan Iyayen su Maza, Sheikh Imam malik baida amini daya wuce Alhaji ubaid Wadata sun kasance makwabtan junane, Gidansu Yana a jikin na juna, Akwai zumunci mai karfi a tsakanin Iyalansu, atare suka taso tun kuruciya, kasantuwar Alhaji ubaid Dalibin Mahaifin sheikh Imam ne agurinsa yake ɗaukar karatun addini kafin Allah yayi masa rasuwa, Alhaji Ubaid dan babban Gidane, Family dinsu yayi shura A jihar, saboda Arzikin Mahaifin su marigayi Alhaji mu'azzam wanda akeyiwa lakabi da wadata babban dan kasuwane a zamaninsa.
Benazir da Aisha Ƙawayen junane kuma aminnai tun kuruciya, atare suka taso kuma atare su ka yi primary da secondry a makarantar Sheikh Imam Malik wadda Har Islamiya ake koyawa a cikin ta, abun da zai ɗaure ma kai, kwata kwata halin Aisha dana Benazir baizo daya ba, sun sha banban, Benazir tana da girman kai, rashin kunya kuma bata iya shigar mutunci ba, duk suturar da zata sanya sai ta matse jikin ta.
Sarai Sheikh Imam yasan da Halin Benazir Ya kuma san Gado tayi agurin Hajiya layla, mutane suna yawan kawo mashi tsegumi akan ya raba yar shi da Benazir In ba haka ba zata bata masa tarbiyar ƴa, Bai ta6a ɗaukar maganarsu ba, saboda Shi ya yarda da tarbiyar daya ba Aisha yasan bazata ta6a bari Benazir ta rinjaye ta ba, sai dai ita ta rinjayi Benazir gurin karkato da hankalin ta don ta shiryu, bayan hakan Yayi Wa Benazir farin sani, Yasan Bata Jin magana kuma bata da kunya sai dai ita din ba Yar iska bace, bata shaye shaye, bata bin maza, Rashin ɗa'arta abaki ne da kuma yanayin Shigarta, sai kuma yawon gantali da take fita a kowani dare ne sai taje Night club, gata yar hana biki maraici, kuma zabaya ce a fagen rawa, amma Sheikh bai ta6a gigin raba ƙawancen su ba, saboda yana son duk wani abu da Aisha ke so.
bayan haka baya son abunda zai raba zumuncinsu da makwabtan shi.
Wadannan dalilan ne suka sa Shiekh imam Ya amince ma ƙawancen Aisha da Benazir, Amma sai da ya gindaya mata sharudda akan bai lamunta tadinga fita yawo ba, kulle ya ke mata daga makaranta sai gida, In har zasu hadu da Benazir sai dai tazo gidan su, Ko kuma In Aunty laura zataje gidan gurin Hajiya layla ta tafi da ita, sai kuma in sun haɗu a school, amma sam bai yarda ta dinga bin Benazir suna fita yawon gantali ba bayan haka ya hanata kula kowani saurayi saboda akwai wanda yake burin ta aura har sa'insa su ke yi da Aunty laura akan ya hana Aisha kula samari ita ta rasa gane ma manufarsa akan Aisha kamar ba yar cikinsa ba, maganganu marasa dadi take fada masa bai ta6a biye mata ba.
Aunty laura wayayyiyar macace Yar boko kwararriya ta fannin business, ta inda suka sha banban da Imam ita tana da karancin addini akai, kwata kwata halinta ba irin na yayarta mariganya Batool bane, shiyasa basu jituwa da sheikh imam malik, sa'insa suke da junansu saboda ta tsani yadda yake zafafawa akan addini kuma A ganinta kullan da ya ke yi ma Aisha takura ce.
shi kuma yanayi ne saboda Farin jinin da Allah yayi mata, Babban abunda Ke ci mashi tuwo a ƙwarya yadda wasu mazan basa iya kau da maitarsu akan Aisha, saboda Dirin da Allah yayi mata, tun tana ƙanƙanuwarta wani irin dirin jiki ne da ita mai jan hankali, duk taku daya idan tayi sai jikin ya girgiza koda kuwa ta sanya dogon hijabi ajikinta ne sai shatun dirinta Ya bayyana wani irin farin jinin samari gare ta kuma mafi akasarinsu ba don Allah suke son ta ba sai don kwaɗayin Surar ta.
wannan dalilinne yasa shi tsananta mata tsaro ko fita za ta yi dole ta sanya dogon hijab da niƙab, daga makaranta sai gida makarantar ma shi ke kai su da kanshi In an tashi ya dauko su ita da Benazir, wani sa'in In aikin yayi mashi yawa ko zaiyi zaman shari'a Aunty Laura ce ke dawainiyar kaisu wani lokaci in ta samu damar dauko su daga school in an tashe su sai ta saci hanya takai su Shopping mall tayi masu siyayyar kayan amfanin su na mata.
Awata rana ne Aisha tana a zaune kan darduma sai ga Benazir ta shigo gidan da rawar jiki ta shigo har dakinta ta ruko hannunta da farin ciki take fada mata tazo taga Uncle musa da Yaya shureim sun dawo Nigeria, kasantuwar su dukansu A lokaci ba mazauna Nigera bane, Shi Alhaji musa harkar kasuwancin shi yakeyi a kasashen ketare yayin da Shureim ke karatu a kasar egypt can gurin ammin su ya ke da zama.
da fara'a Aisha tace meyasa bata fata mata ba, Benazir tace kawai tana son tayi suprising dinta ne, cike da farin ciki tace ta jira ta a falo zata shirya, Benazir na fita daga dakin Aisha ta soma shirya kanta cikin abaya, sai ga Aunty laura ta fito daga daki ta iske Benazir zaune kan sofa, da fara'a suka gaisa da juna har ta tambaye ta meya sanyata farin ciki nan take fada mata yaya shureim da Uncle musa ne suka dawo Nigeria shine ta zo don ta fada ma Aisha, washe baki aunty laura tayi tana fadin Ah lallai manya manyan baki, shine ba'a fada min ba? tana cikin magana sai ga Aisha ta fito sanye da dogon hijab hada nikab akan fuskarta.
fuska adaure Aunty laura tace kefa matsalata dake kenan, kamar kinfi kowa tsoron Allah, kullum cikin nikab, yanzu nan da gidan makwabtan namu sai kin saka hijab da nika..." a karshe ta korata daki tace taje ta sako Mayafi..da damuwa tace ita bazata iya ba, saboda hijab mutuncin ya mace ne, bayan haka baba ya hanata fita ba hijabi har ta soma janyo mata aya, aunty Laura ta mike rai a6ace taja hannunta suka koma daki, adole saida ta tursasa ma Aisha ta saka Wani guntun veil a kafadarta, baiwar Allah duk sai taji ba dadi ganin yadda abaya din ta ɗame jikinta, dirinta nan nata mai jan hankali ya bayyana muraran musamman ta gurin mazaunanta sun fito rudu rudu..
ahaka Banezir taja hannunta suka tafi gidansu, shigarsu keda wuya ta gate din adai dai Lokacin Alhaji musa Yana atsaye gaban dankareriyar motarsa ya dauki wankan shadda hannunsa ruke da waya, kallo daya da Aisha tayi mashi saida gabanta ya fadi saboda ƙwarjinin dake gare shi, wata irin kirar jiki gare shi irin ta yan dambe.
Benazir ce ta gabatar mata da Uncle dinta, duk irin izzar Alhaji musa da yayi tozali da Aisha saida Ya rasa nutsuwarsa saboda shi irin mazan nan ne masu kwadayin mace mai kyawun sura, sanin da yayi mata tuntana karamarta yanzu kuma ta girma, wani irin kallo yadinga binta da shi harya kasa amsa gaisuwar da ta ke yi mashi, A lokacin rudewa Aisha tayi saboda bai kwanta mata arai ba, musamman da ta ga hakoransa ya sanya masu Gold-plated teeth..
ita kanta Benazir ta lura da yanayin da ya shiga. Hakan yasa taja hannun Aysha suka nufi cikin gidan, Uncle musa yabi bayanta ta da kallo yanayin yadda take tafiya jikinta na girgiza ba karamin tayar masa da maitar sha'awarsa tayi ba, kuma tun daga lokacin ya kudiri aniyar saiya mallake ta.
Bayan sun shiga babban falon gidan, anan suka iske Hajiya layla tare da Alhaji ubaid suna zantawa tsakaninsu, bayan sun gaishe dasu hajiya layla tace su shiga ciki su gaida shureim..
Tun da Allah Ya Halicci Aishatu Bintu Imam bata ta6a ganin mutumin daya kwanta mata aranta ba, da kallo ɗaya ta fada tarkon son shi sai akan dr shureim yanayin da suka same shi adakin shi yana zaune kan darduma Ya buɗe al'kurni yana karatu cikin nutsastsiyar Muryarsa ba karamin jan hankalin ta yayi ba, tayi mamakin girman daya ƙara tsawon shekaru a lokacin rabon shi da Nigeria.
Sai da yakai aya, cikin sanyin murya yace masu su shigo yaga sun yi tsaye bakin kofar dakinsa, Jan hannunta Benazir tayi suka zukunna agaban dardumarsa ta gabatar masa da aminiyarta yar makwabtansu diyar sheikh Imam, ganin kamar bai gane ba don tun suna kanana Yabar Nigeria, Aisha ta gaishe da shi tare da yi mashi bangajiyar tafiya, da murmushi akan fuskarshi ya amsa mata, abunda bata sani ba Dr shureim yasan da zamanta, Yana yawan sauraron kira'arta da take yawanyi a taron musabaka, wanda mutane ke yaɗa videon a social media amma saboda miskilancinshi sai ya nuna kamar bai gane ta ba.
sun ɗan jima Yana jan su da fira, lokacin da ta tashi tafiya dr shureim ne ya yi mata rakiya tare da Benazir har kofar gidansu, saida suka ga shigarta kafin suka koma gidan su.
a daren ranar Alhaji musa Ya kira Benazir ya soma tambayarta dangane da Aisha, ko tana da tsayayyan da zata aura"? Benazir tayi mamakin tambayoyinsa saboda tasan Uncle din nata mugun miskiline bai cika shiga sabgar da bata shi ba, In fact mata basa agaban shi bata kawo komai aranta ba ta fada masa komai dangane da Aisha, Hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba jin cewa bata kula samari, fargabansa daya Sheikh Imam malik saboda basa ga maciji.
A bangaren Aisha tun bayan data koma gida tunanin dr shureim Ya hana zuciyarta sukuni, Kwana take da shi aranta, haka zalika in tana koyama dalibanta karatu wasu lokuttan shagala take da tunaninsa har sai daliban su ankarar da ita.
ta bayan fage Uncle musa ya fara ba Banezir makudan kudi masu auki don suje yin siyayya da Aisha, kuma yace mata baya son Aishar ta sani, Benazir bata ta6a fada mata Uncle musa ne ke bata kudi ba, Sai ma in ta tambayeta ina take samun kudi sai tace dr shureim ne ya bata, hakan ya sa ta saki jiki duk da bata da kwadayin abun duniya tayi azan yaya shureim yana son ta ne shiyasa yake ba Benazir kudi don suyi siyayya.
kusan kullum sai Aunty laura tayi masu hanyar fita daga gidan batare da sanin Shiekh Imam ba, don suje Mall suyi siyayya harma da yawon buɗe ido koda Aisha ta nuna bata son fita Aunty laurace ka tursasa mata in ta turje sai ta fashe mata da kuka tana fadin bata mata biyayya saboda ba ta ɗauketa uwa, don taga ita bata haihuwa, in ta fadi hakan jiki na rawa Aisha take bin Umarninta.
Tun bata sake ma Uncle musa in suka haɗu harta fara sabawa da shi, tana matukar girmama shi tanayi mashi kallon Uncle dinta.
Haka zalika shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da dr shureim, Benazir tayi mamaki saboda sanin da tayi ma Aisha bata Kula maza sai gashi dr shureim ya ciri tuta, sun saba da juna, Benazir ta sanya masu ido sosai, Ta fahimci dukansu suna son juna, ita Aisha Kunya ce ta hana ta furta mashi Kalmar so, yayin da shi kuma miskilanci ne Ya hana shi bayyana mata, bayan haka Yana jin nauyin yayi soyayya da Aisha saboda yanayi mata kallon Kanwarsa.
A duk lokacin da Benazir taso Ta bugi cikin shureim don ya fada mata In yana son Aisha sai yace mata shi babu soyayya atsakaninsu kallon kanwa ya ke yi mata, haka In ta bugi cikin Aisha don taji in tana son ya shureim sai tace mata ita fa ba son shi ta ke yi ba, kawai tana yi mashi kallon yayanta ne saboda zumuncin dake a tsakaninsu, In Benazir zata shekara tana tambayarsu amsa daya suke bata.
Bayan da suka kammala Secondry School, Alhaji Ubaid ya sama masu admission a wata Jami'a dake a birnin hagen na kasar Jamus batare da sanin sheikh Imam Malik ba sai daga bisani ya same shi har gida ya sanar da shi.
shiekah Imam bai nuna amincewarshi ba, Yace shi bazai bari yarsa ta tafi uwa duniya karatu ba, duk Universities din dake a Kasar har sai an fita waje neman ilmi? Alhaji ubaid ya ce yayi hakuri da bai nemi shawarar shi ba ya tashi ya yanke hukunci dama yaga Benazir ta kwallafa rai ne akan son zuwa can tayi karatu kuma ta nuna tana son suje tare da Aisha shi kuma yayi la'akari da shakuwar dake a tsakaninsu In aka rabasu ba zasu ji dadi ba shiyasa ma har ya nemi Benazir data kar6o ma shi Academic record din Aishah.
A ranar da su ka yi maganar, bayan Alhaji ubaid yayi mashi sallama ya tafi, ranshi a bace Ya kira Aisha ya fara mata fada akan takardun karatunta data kai ma Alhaji ubaid don ya sama mata admission, tace mashi wallahi ba ita ta bashi takardun ba, hasalima ita batasan da maganar ba, ko da jin hakan nan take ranshi ya bashi da sa hannun Aunty Laura, Har daki Yaje ya same ta da maganar, maimakon ta kar6i laifin ta saima ta dinga masifa tana fadin taje ta bada kuma wallahi bai isa Ya hana Aisha taje karatu kasar waje ba, shi ko dan zumuncin dake a tsakanin shi da Alhaji Ubaid bazaisa Ya amince be? Idan Ma yana jin tsoron wani abu ya same ta acan din Ba Allah ke tsare bawansa ba, bayan haka tun da Ba ita kadai zataje ba hada Benazir ya bar ta mana, shiekh imam yace mata ya gama magana bata isa tasa shi canza ra'ayin shi ba.
Ganin da gaske Shiekh Imam zaiyi mata bukulun kudin da take samu agurin Alhaji musa yasa ta kwashi kafa taje gidan kakarsu ta bangaren Uba da ta rage masu mai Suna Hajjo, ta tsara mata karya da gaskiya akan kullan da Sheikh imam ya ke yi ma yarsa, ta ce ita bakin cikinta gorin da ya ke yi mata akan Aisha sai kace ba diyar yayarta ba, In da kara aisha ai yar ta ce tana da ikon juyata son ranta, bayan haka ta fada mata Alhaji Ubaid Ya sama ma Aisha gurbin karatu a kasar germany ita da Benazir amma Ya hana bai dubi zumuncin dake a tsakanin su ba, Hajjo da ranta ya 6aci ta sa Aunty laura ta kira mata imam a waya tace yazo tana son ganin shi, koda yazo ta balbaleshi da fada kamar zata rufe shi da bugu kasancewar shi mai biyayya yadinga bata hakuri kamar zai durkusa mata kasa tace mashi in har yana son farin cikin ta yabar Aisha ta tafi karatu kasar germany, Shiekah imam yayi kokarin ankarar da ita illar dake akwai na tura ɗa karatu kasar waje balle ita da take mace amma Hajjo ta rufe ido tace itafa ta gama magana, kawai yabi abunda tace mashi, ta ko'ina ta matsa mashi lamba ba dan yaso ba ya amince zai barta, don yasan halin Hajjo rikicin tsufa ne ke damunta.
bayan komawarsu gida baibi takan Aunty Laura ba Ya kira Aisha ya tambayeta da son ranta zataje kasar waje karatu? Aisha tace aa bata so saboda batason tayi nesa da shi, amma benazir ta nuna tana so suje suyi karatun atare acan tun da ba wasu shekaru ne masu yawa ba" a maganarta shiekh ya fahimci bada son ranta ba amma tana son ta bi aminiyarta ba yadda ya iya hakanan ya amince.
Bayan Alhaji Ubaid Ya kammala yi masu travel arrangement, ana i gobe zasu tafiya sheikh imam bai iya runtsawa ba, saboda zazza6in tafiyar da Aisha za ta yi, wannan ne karo na farko da zatayi nesa da shi, bawan Allah akan dardumarsa Ya raba dare yana yin nightprayers duk akanta, washe garin ranar aunty laura ta shirya ta tsaf, a motar sheikh imam suka tafi, acan airport suka hadu da Benazir tare da family dinta da su ka yi mata rakiya, Aisha tasha kuka na rabuwa da Baba imam, har nasiha yayi mata akan ta ji tsoron Allah, kada ta canza a yadda yasan ta, sannan ta kare mutuncin kanta, karatu yakaita daga shi bai amince tayi wani abu da zai sa6awa mahaliccinta ba.
Baba imam bai ƙyale Aisha hakanan ba saida Ya hadasu da Benazir ya karayi masu nasiha mai tsuma zuciya sannan ya damƙa ma Benazir amanar Aisha yace ya yarda da ita bai ta6a barin Aisha ta kula wata kawa in ba ita ba don haka ya bata amanar yar shi, ta kula mashi da ita.
Benazir jikin ta ba karamin sanyi yayi ba, har kuka saida tayi saboda tausayin baba Imam, Alhaji ubaid ma yayi masu nasiha, bayan ya gama dr shureim Ya kirasu agaban shi Yayi masu addu'o'i tare da yar nasiha A lokacin Aisha ta dinga kallon shi, tayi fatan Ya furta yana sonta kafin su tafi amma sai baiyi ba saboda shi kallon kanwa ya ke yi mata, bawai don baya sonta ba sai don kasancewarsa miskili da zurfin ciki ko kallonta bai cika yi ba, bayan Aunty laura da hajiya layla sun sanya masu albarka tare da fatan alkhairi a karatun su, daga nan suka yi masu bankwana.
Silar hawan su jirgi Allah Ya ƙaddara haduwarsu Da Aneelerh Muhammad falgore itama a lokacin za ta je yin karatu kasar germany, ta zauna a seat daya da Benazir taga ta burgeta ta ɗan fara janta da fira har Benazir ta dan saki jiki da ita, A lokacin Aneelerh batasan da zaman Aisha a cikin jirgin ba tana a seat din bayansu ta rufe fuskarta da mayafinta zuciyarta cike fal da tunanin mahaifinta data bari da kuma muradin ranta.
Bayan jirginsu yayi Landing a airport na birnin hagen, Alhaji Musa Ya turo wani escord ɗinsa Yazo daukarsu a hadaddiyar mota, sukayi sallama da Aneelerh suka shiga mota, a zaton su kaitsaye escord din zai wuce da su Jami'ar da zasuyi karatu acan, amma sai suka ga akasin hakan, a wani katafaren gida da Alhaji musa Ya kama masu haya a kusa da Jami'ar, Anan Escord din yakai su a matsayin gidan da zasu zauna, Aisha tayi mamakin haduwar katafaren Gidan, tayi azan a hostel zasu zauna amma sai taga akasin hakan, tsabar gatanci hada masu aiki Ya aje masu agidan, kamar ba karatu suka je yi ba Aisha ta ɗanji shakkun ta zauna agidan saboda gudun kada ta shagala ta kasa ta6uka abunda ya kawota amma saboda Benazir yasa ta amince ta zauna, rana ta farko da suka fara shiga jami'ar, ba zato ba tsammani sukayi arba da Aneelerh ashe itama a nan zatayi karatu, Sunyi farin ciki da ganinta duk da ba'a department ɗaya suke da ita ba, rayuwarsu a jami'ar gwanin ban sha'awa shiga class kadai ke rabasu amma da zarar sunfito zasu hadu da Aneelerh a karshe ma da kawancensu yayi karfi da Aneelerh sai suka yi mata tayin ta baro hostel ta dawo gidansu da zama, Aneelerh bata musa ba ta amince masu toh ita kanta data ga inda suke rayuwa saida ta girgiza da mamaki saboda haduwar Gidan.
Uncle musa ba karamin gatanci yayi masu ba, shi ke daukar dawainiyar komai nasu, tun daga cinsu shansu suturarsu masu kyau da tsada har account ya sanya yaronsa ya bude masu na kasar germany, baya gajiya da tura masu dollars kamar baison zafin neman su ba, lamarin shi ya fara daurewa Aneelerh da Aisha kai ganin yadda ya ke ji dasu yana tarairayarsu, wani abun daure kai Duk weekend sai yazo kasar germany daga America, kuma agidansu Yake sauka anan zai kwana su yi breakfast lunch dinner duk tare da shi, har yawon buɗe ido Yake zagayawa dasu a motar shi, da abun ya fara damun aisha ta dai gaza hakuri ta fada ma Benazir itafa zata koma hostel da zama saboda tana jin tsoron baba Imam Yaji labarin ba a jam'ar take zaune ba zai iya yi mata fada bayan haka bata son yadda Alhaji musa ke kashe masu kudi abun yayi yawa, sannan meyasa yake zarya duk week end sai yazo ya kwana agidansu? A ganinta hakan bai dace ba, a matsayinsu na musulmai kuma mata su dinga barin Namiji yana kwana a gidan su, Benazir ta nuna kin amincewarta da komawar Aisha Hostel, ta dinga lallashinta akan tayi hakuri ta zauna, na dan wani lokaci ne, kada ta damu da Alhaji musa halinsa ne shi mutum ne mai son yin alheri yana da wayewa don haka kada ta dauka da wata manufa ya ke zuwa kawo masu ziyara, sannan kuma kada ta damu sheikh Imam bazai ta6a sani ba.
dakyar Benazir ta shawo kanta har ta hakura da komawa hostel ɗin, kusan kullum ne saita kira babanta a waya hakan ba karamin kwantar masa da hankalinsa ya ke yi ba, kuma duk in ya kira sai yayi mata nasihar daya saba yi mata, haka aunty laura ma suna yawan yin waya da ita, wasu lokuttan da dama tana son ta kira Yaya shureim amma idan ta tuna bai ta6a nemanta ba sai ta fasa saboda bata son ta zubda ajinta
Sai dai taji labarinsa awurin Benazir idan tayi waya da shi wani lokacin Benazir tana bata wayar don ta gaisa da shi hakan ba karamin dadi yakeyi mata, haka itama Aneelerh silar Benazir ta san Yaya shureim har suka saba da shi, itama Aneelerh duk in zatayi waya da mami da Abie sai ta hadasu da aminnanta donsu gaisa ta haka suka ƙarfafa zumuncin su.
har whatsapp group suka buɗe na sada zumunci da family dinsu harta baba Imam saida Aisha ta sanya shi aciki, Aneelerh ta saka abie da mami, itama Benazir ta sanya Alhaji ubaid da hajiya layla tare da dr shureim Wani irin zumunci mai karfi ne ya shiga tsakanin family din su duk time da suka hadu online fira suke sha ba kadan ba, har hotunansu suke tuttura masu.
Duk idan suka samu hutun School Nigeria suke dawowa tun a airport family dinsu zasu harhadu domin tarbarsu har party Uncle musa Yake hada masu, idan hutu ya kare zasu koma germany har kuka sukeyi saboda basu son rabuwa da family din su.
Akwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin sa'a suka kammala degree dinsu, duk da Benazir da Ummi sun riga Aneelerh kammalawa saboda ita nata course din almost 6 years ne medicine and surgery su kuma Business Administration ne shekaru uku ne, Amma saboda shakuwar da tayi da su yasa ta matsa lamba akan zata ajiye karatun saboda bata jin zata iya cigaba da zama a germany batare da su ba, tasan in suka gama tafiya zasuyi su barta, suma sun damu da hakan, a wani zuwa da Uncle musa yayi gidansu, Benazir ta same shi da maganar Aneeleerh, Sai cewa ya yi karsu damu, zai sa arage mata shekarun karatun ta ya koma daidai da nasu, sunyi matukar yin mamakin hakan, aikuwa sai gashi Ya yi mata hanyar da zasu kammala a shekara daya da ita, Amma duk da haka In ta dawo Nigeria sai ta kara karatu akan wanda tayi.
Uncle musa yayi masu halaccin da bazasu taba mantawa da shi ba, Kyautatawarshi agare su bata misaltuwa, da Ayshah tana kokwanton dukiyar shi ganin yadda yake masu barin kudi kamar baisan wahalar nemansu ba, Benazir ce tayi brainwashing dinta, ta fayyace mata cewa kudinsa na Halal ne, babban Dan kasuwane kamar dai mahaifinta Alhaji Ubaid.
ranar da zasu yi graduation celebration (bikin yaye dalibar) wanda shuwagabannin jami'ar ne suke daukar nauyin yin shi a cikin makarantar, gaba daya family din kowan nan su saida Ya hallara hatta sheikh Imam saida Yaje masu aiko Aisha tayi murnar ganin baba Imam, Ranar sunyi farin cikin da basu ta6a yin makamancinsa ba saboda Yadda yan uwa da abokan arziki suka dinga basu kyaututtuka da yi masu fatan Alkhairi arayuwa, aranar ne sukayi hotuna sosai, abunda yafi basu sha'awa Yadda Family dinsu suka hada kai kamar yan uwan juna, musamman Aisha tayi murna da ganin yadda ya yadda Shikeh Imam ya yarda da Abie din Aneelerh sun zama abokai, haka iyayen su mata sun hada kai sai zumunci suke sadawa a tsakanin su.
(Bayan dawowarsu Nigeria, da sati biyu kacal)
A yammacin wata rana Sheikh Imam Yana zaune akan Sofa dake a cikin katafaren Sitting room din gidansa, yana tsaka da karanta Jarida, daya daga Cikin security Officer na gidansa yayi masa sallama bayan ya amsa Ya isar da sakon Ana sallama da shi, bai motsa daga Inda yake ba ya tambaye sa wanene ke nemansa? Officer din yace Kanin makwabcin su ne Alhaji Musa, Shiru ya danyi jim aransa yana mai mamakin karfin Halin Alhaji musa da har ya iya takowa yazo gidansa neman shi, daga bisani yace ma Officer din ya shigo da shi.
sallamar Alhaji musa ce ta katse zancen zucin nashi, dakyar ya sakar mashi fuska suka gaisa har ya taya shi murnar kammala karatun su Aisha, bayan sun yi shiru na dan lokaci kowa da abunda yake sakawa aranshi, daga bisani Alhaji musa yai gyaran murya ya ce"dama nazo ne don in nemi alfarma agurinka" bai jira jin ta bakin sheikh imam ba ya cigaba da cewa"Ina son ka bani auren Aisha, saboda ta kwanta min araina"
wani kallo shiekh Imam ya watsa masa mai kama da harara.
Tashin farko Yace"sai yau na tabbatar da baka da Hankali Musa, kai baka ji kunyar tunkarata ido da ido ka fadamin wannan maganar ba? an gaya maka ni mahaukacine da zan dauki ƴata mai daraja in hada ta da fasiƙin mutun, irin ka"?
Maganar imam Ta sosa zuciyar Alhaji musa amma dayake shike nema agurinsa sai ya shanye bacin ransa, yace"bai kamata ka gaya min maganganun nan ba, wanda yace yana son naka ai masoyinka ne, saboda nasan mutuncinta shiyasa na tako nazo da kaina don in nemi aurenta agurin ka..."
murmushin takaici Sheikh Imam yayi"Haba Musa, ko kayi zaton namanta wanene kai"? Ya fada tare da miƙewa daga kan kujerar da yake ya juya ya nufi bookshelves din dakin mai ɗauke da kundin dokoki dana tarihi, da sauransu.
A cikin kundaddakin Ya curo Criminal record Na Alhaji Musa, Ya wurga masa akan kirjinsa, Kafin Ya dafe table din gabansa da tafukansa Ya soma magana Yana kallon Cikin idanunsa..
"Mara Kunya fitsararre, Sau nawa Muna yanke maka hukunci a kotu akan mugayen laifukan ka, amma da zarar kaje prison sai dai muji labarin ka fita, saboda kasan me ka taka kana da manyan mutanen da suke daure maka gindi, sune suke sama maka mafaka a kasar waje, shiyasa kake sheke ayarka" ya faɗa yana kallon Cikin idanun shi.
"Tayaya har kake tunanin Ni Imam malik zan iya baka auren yata aisha bayan nasan Halinka ciki da bai? Musa kaine Dealer mai fataucin miyagun kwayoyi a kasar nan, kai ne Cin zarafin mata masu rauni gurin tilasta masu don suyi karuwanci a kasashen waje, baka gajiya da keta haddin mata, last shari'ar da nayi akanka, yara masu talla kayi ma fyade sannan ka binne su da ransu don kada asirinka Ya tonu, cikin rashin sa'a aka samu wani bawan Allah dayaga lokacin da kake aikatan hakan harya kaika kara police station bayan sun gama bincike akanka suka mika ka kotu abun takaici bayan mun yanke maka hukuncin daya dace dakai mun tura ka prison sai dai muka ji labarin babu kai a kurkuku harma Ka gudu ka koma America da zama, saboda bakin zalincin ku, kai da ubayen gidan ka kuna amfani da haramtacciyar dukiyar da ku ka tara gurin toshe bakin shaidu da bawa jami'ae cin hanci...." Ya karashen maganar yana huci tamkar zai doke sa.
Alhaji Musa ya sunkuyar da kansa kasa, ya dunkule yatsunsa, ransa ya baci matuka da jin maganganun da Sheikh Imam ke gaya masa saboda kawai ya nemi auren yarsa.
"ka yi haƙuri ka nemi wata, amma sam ba ka cancanci ka mallaki aisha ba, nafi sha'awar ta auri mutun mai tsantsar ilmin addini musulunci, mai jin tsoron Allah, mai kuma kyawawan halaye da dabi'u wanda zai ruke min ita amana, Wallahi idan har na aura ma Aisha kai banyi mata adalci ba, Allah ma bazai barni ba saboda ita din amana ce agare ni"!
yanayin fuskar Alhaji musane Ya canza ganin wahalar shi na niyar ta tashi abanza.
Cikin kankai dakai yace"kada kayi min haka, wallahi inason Aisha itace mace ta farko da nayi burin in mallaka don mu raya sunnah, idan har don saboda halayena ne, nayi maka alkawarin zan shiryu in har zaka bani auren ta"
cike da takaici Sheikh imam Yace"Oh har saina baka aurenta zaka shiryu! Ba zaka shiru don Tsoron mahaliccinka ba"?
"Naji zan shiru saboda Allah, Kawai ni ka amince min in aure ta, komi ka ke so zan baka ina da tarin dukiya wanda zai ishemu muyi rayuwar mu" Da gadara yakeyi masa magana,
Dariya sheikh imam yayi"Musa kenan, Kai abun duniya ya dama, ni dukiya bata agaba na, ban damu da kyalekyalen duniyar nan ba, wanda wata rana zaka mutu kabarsu ne, daga kai sai halinka za'a binne ka, sannan ka duba kaga gidan da nake rayuwa cikin rufin asirin Allah, babu abunda na nema na rasa don haka kadaina yi min bagu da dukiyar daka tara ta hanyar Haram.."! hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, abunka ga mutumin da bai ta6a neman abu ya rasa ba, babban takaicin shi yadda ya aje girman kansa da komai yazo don ya nemi auren ta amma Sheikh imam Ya watsa mashi kasa a ido.
"Amma ai ka bari ita yar taka ta furta bata sona ko"? Ya fada tare da ɗage masa gira...
Shiekh Imam Yace"Wallahi koda Aisha tana sonka ba zata aure ka ba! Balle ma nasan Jinina bazai ta6a kaunar fasiki irin ka ba, in sha Allah kaida Aisha sai dai hange daga nesa amma aure har abada, nayi fatan ma ace shureim ne yazo min da maganar auren ta, wallahi jiki na 6ari zan aura mata shi, saboda Ya cika duk wasu sharuddan da zan Iya mallaka masa Aisha..."
cikin rauni na murya Uncle musa yace"da me shureim yafi ni? wasu sharuddane ya cika wanda ni ban cika su ba"
Sheikh Imam Yace"ko ban fada maka ba, kai ka sani, shureim hafizi ne mai dumbin tarin ilmin addini, mutum mai tsoron Allah, mai koyi da sunnar manzon Allah SAW, ba kamar kai ba, daka sa duniya agaba...." wani irin zafin kishine Ya rufe idon Uncle musa, Yaji zafin maganar Shiekh Imam Ko sallama bai yi mashi ba Ya mike azafafe Ya fuce daga sitting room din.
Bayan Uncle musa Ya koma gidan yayansa damuwa ta hana shi sukuni, Yana ji aransa in har bai mallaki aishaba har ransa zai iya rasawa, bakomai yake hadama ba face surar jikin ta..
Dayaga bashi da wata manufa sai ya yanke shawarar tunkarar Aisha don ya nemi soyayyarta, yasan in har ta amince mashi Shiekh imam bai isa Ya raba su ba, Har court zai iya kai shi ƙara.
Da taimakon Aunty laura ta shirya mashi ranar da zaizo gidan donsu gana da aisha aranar shiekh Ya tafi gurin aikinsa. .
Agarden suka zauna, tana asanye cikin dogon hijab dinta cikin girmamawa ta gaishe da Alhaji musa ta kara yi mashi godiya bisa ga kokarin da yayi akan karatunsu, yaji dadin tarbar da tayi masa har yaji aransa ba zata ta6a ƙin amsa bukatarsa ba.
Cikin nutsuwa Uncle musa ya fayyace mata irin kaunar da yakeyi mata, tashin farko Aisha tace"kayi hakuri da amsar da zan baka, wallahi bawai bana sonka bane, kawai ban ta6a yi maka so daya shafi aure ba, Ina jinka kamar Uncle dina saboda zumuncin dake atsakanina da Benazir, amma ni inada wanda nakeso..." bata kare maganar ba Yai saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga nata hannu har saida tadan sha jinin jikin ta.
"Karya kike kice bakisona, babu macen dana ta6a nuna inaso tayi rejecting dina, don haka kema akwai soyayyata acikin zuciyarki, idan ma kina jin kunyata ne to ki daina, ni ba Uncle dinki bane, ashirye nake da in aure ki, Aisha kiyi tunani akaina kafin ki yanke shawara, zan jira naji daga gare ki"
yana fadan hakan yayi tafiyarsa, gaba daya tashiga halin damuwa kuma ta kasa sanarma kowa, hatta Benazir da Aneelerh basu san da maganar ba, kusan sau biyar Alhaji musa yana tuntubarta a waya don yaji in ta canza ra'ayi amma ta nace akan ita bazata iya auren shi ba, tana da wanda takeso, daya matsa mata akan ta fada masa wanene takeso sai tace mashi yaya shureim ne, a lokacin ji yayi kamar ya binne ta da ranta saboda bakin kishine da shi, ya ji zafin furta sunan shureim da tayi, zuciyarshi ta raya mashi cewar ba ra'ayinta bane Shiekh imam ne ya cusa mata nasa ra'ayin dama ya nuna yafi sha'awar ta auri shureim daga nan ne ya kuduri aniyar saiya shiga tsakanin su.
Har gida yaje ya samu shureim Ya tambayesa meke a tsakaninsa da Aisha, dr shureim yace babu komai face mutunci, shi ya dauke ta kamar kanwarsa.
Uncle musa yace bai yarda ba, in har yana son ta ya fada mashi zaiyi mashi hanyar auren ta, daya matsa mashi da tambaya kawai sai yace mishi eh yana sonta amma bai ta6a sanar da ita ba.
Hankalin Uncle musa ba karamin tashi yayi ba, saboda ya fahimci dukan su suna son juna, kuma In har Shureim Ya furta yana son Aisha tofa babu makawa sai Sheikh imam Ya bashi ita.
hakan yasa shi yanke shawarar komawa gurin imam malik don ya kara rokonsa akan ya bashi ita, kusan sau biyar yana zuwa gurin imam amma ya rufe ido akan bazai ta6a aura masa aisha ba, ta ko'ina babu sauki, har aunty laura yaba cin hanci na makudan kudi donta karkato da hankalin sheikh imam akansa amma duk abanza, itama aishar ba irin magiyar da baiyi mata ba akan ta amince da soyayyar shi akarshe sai tayi blocking duk wata hanya da zata haɗa ta da shi, hatta gidansu Benazir ta daina zuwa sai dai Benazir tazo gidansu ta same ta, ranshi ba karamin baci yayi ba, shi a ganin shi bata yi mashi halacci ba, kodan saboda dawainiyar da yayi dasu yaci ace ta saka mashi amma saita butulce dama shi baya abu dan Allah sai idan yasan zai samu riba.
bayan wasu kwanaki Uncle musa ya ɗauke ƙafa da zuwa Gidan yayansa kwata kwata suka daina jin duriyarshi, da Benazir ta sanar da Aisha baya kasar Ba karamin dadi taji ba, kuma ta saki jiki ta cigaba da zuwa gidan, wani lokaci atare suke zuwa gidansu Aneelerh wani sa'in kuma Anila ce ke zuwa gidajen su ta kawo masu ziyara, har takaiga iyayen su na ziyartar junan su.
Daga baya da soyayyar Aisha ta fara addabar Dr shureim har takaiga dakyar yake runtsawa saboda tunaninta, baya da burin daya wuce ya aureta, aranar daya shirya tunkararta don Ya fada mata irin kaunar da yake yi mata, A lokacin Aysha da Aneelerh sunzo Gidan su suna a dakin Benazir Suna fira, A bakin kofar dakin ya tsaya yana tunanin taya zai tunkareta da maganar? Zata kar6i tayin soyayyar shi ko kuwa? yana jin fargaban Aisha taki amincewa da shi shiyasama tuntuni yaki sanar da ita saboda fargaban amsar da zata ba shi.
Har ya zaro waya daga Aljihu da niyar Ya kirata don ta fito su ke6e, kwatsam kunnuwansu suka jiyo mashi firar da su ke yi..
"Yanzu tun da mun kammala karatu me ya rage mana"? Benazir ce tayi tambayar.
Aneelerh tace"Aiki da kuma Aure, amma Abie yace bazai bari in fara aiki a private hospital din daya buɗe min ba har sai na tsayar da miji"
Benazir tace"Why not Ki ba Uzair damar ya turo da magabatansa? Tun da naga Jininku Ya haɗu da shi"
Murmushi Anila tayi"Wai da Ke nake Jira, Idan Kinba Taj damar Ya tura da nasa magatan Gidan ku nima sai in ba Uzair Damar Ya tura gidan mu..." wani kallo mai kama da harara Benazir tayi mata..
"Pls mana ki amince masa nasan fa Kin mutu akan kaunarsa amma sai ki ta wani Ja mashi Aji"
"hmmm nifa ba aji nake ja masa ba, Ina tunanin ta yadda zan tunkari mommy da wannan maganar, daddy baida matsala nasan zai amince min, amma mommy bansan ya zata dauki abunba kinsan Mommy bata son dan jarida sannan shi ba dan wani Hamshakin mai kudi bane..."
Tun da suka fara magana Aisha bata tsoma baki ba, tayi shiru kamar hankalin ta baya akansu, har saida Benazir ta ɗan dafa kafadarta tukunna ta mai da hankali akansu.
"Meke damunkine? Tun dazu kin yi shiru ba ki ce komai ba, ko baki ji abunda muke magana akai bane"
Murmushi tayi"Naji mana, mamakine ya kamani, Naji kuna maganar Taj da Uzair su wanene su din? Yanzu duk kawancen mu daku ashe har akwai wani sirri naku da bansani ba"?
Dariya su ka yi, Anila tace"Ay mana afwa Ustatha, ba haka bane, wlh mu ma bamu dade da sanin su ba, kin tuna ranar da muka fada maki zamuje shopping mall? One week da dawowarmu"?
"Hakane na tuna, Ay ranar na fadamaku Uzirin daya hana ni fita"
Benazir tace"toh A ranar muka hadu da su, kyawawan Samari kuma sun kwanta mana arai"
Taya su murna tayi Allah ya sa su zama Alkhairi agare ku
Suka amsa mata da ameen.
Anila tace"pls muna so muji ra'ayinki, Donni bana so mu riga ki yin aure, nafi so yadda muke aminnan juna, Muyi aure atare ya'yan mu su taso a tare"
Benazir tace"Aisha fa bata da matsala, Kinsan Allah yayi ta da farin jinin samari iri iri, attajiran masu kudi, Manyan Malamai sai ta zaba ta darje, Ko yau ta fidda miji baba Imam aurar da ita zaiyi Allah"
ta fada tana dariya, Murmushin takaici malama Aisha tayi Cikin raunanniyar murya tace"Bazan boye maku ba, dani daku mun riga da mun zama daya, Munsan sirrin Juna, Wallahi bana alfahari da farin jinin da nake da shi, saboda mafi akasarin mazan da suke sona ba dan Allah bane sai don Surar Jikina, Wlh Benazir da wuya namiji yazo gurina da sunan soyayya batare daya neme ni ba, Ina jin bakin ciki da taikacin hakan, ni nasan zaiyi wuya asamu wanda zai soni dan Allah..." dakyar ta kare maganar saboda kukan daya ciyota, Kalamanta sun karya masu zuciya.
Cikin shesshekar kuka tace"Inason Aure fiye da tunaninku, inaso in raya sunnar manzon Allah SAW amma taya zan samu wanda zai soni dan Allah"? Gaba daya tausayinta ne ya kamasu.
Lallashinta suka somayi tare da kwantar mata da Hankali, su ka ce In sha Allah zasu tayata da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zaiso ta tsakani da Allah.
Dr shureim dake a labe yana sauraronsu tun dayaji maganganun Aisha sai jikinsa yayi sanyi zuciyar shi ta karaya, Har Yaji shakkar furta Yana sonta saboda gudun kada tayi tunanin shima surar jikinta ya ke so.
Bayan wani Lokaci, Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa kuma cikin sa'a ya shiga da kafar Dama, Arziƙin shi ya habbaka sosai, Rawar kai a wurin Hajiya layla har ba'a fada, dama ta jima tana cusa mashi ra'ayin ta akan ya shiga siyasa saboda taga yadda Alhaji musa ke fantama da dukiya abunda take ma kwadayi kenan, dama arayuwarta ta tsani taga Alhaji musa yafi Alhaji Ubaid Arziƙi tana jin haushin hakan sosai.
Dr shureim ya so ya kalubalanci siyasar da mahaifinsa ya shiga, Amma Hajiya layla ta take mashi burki ta hana shi magana adole yaja baki yayi shiru.
Alhaji musane yayi mashi hanyar da ya shiga Jam'iyarsu, a Karon farkon da Jam'iyar JDP ta tsayar da shi a matsayin Dan takararsu Na Gomna sunyi murnar da bazata Misaltu ba.
Saboda Farin Cikin hakan yasa Hajiya Layla ta shirya masu gagarumin Party don taya Alhaji Ubaid murnar takarar da aka tsayar da shi da kumayi mashi fatan Alkhairi.
Kafin Shigarshi siyasa saida ya fara tuntubar Shiekh Imam don ya bashi shawara, Sheikh yace shi bazai hana shi yin siyasa ba amma da zai bashi shawara yacigaba da kasuwancinshi sai yafi zama alkhairi a gare shi, saboda yawancin yan siyasa sai sun kauce hanya suke samun mulki, Nasiha sosai yayi mashi har yace ya dauki shawarar shi amma daga baya sheikh imam sai dai yaji labari agurin mutane cewa Alhaji Ubaid Ya tsunduma a harkar siyasa yayi mamaki sosai saboda bai ta6a bashi shawara bai dauka ba sai a wannan karan, abun daya kara ɗaure mashi kai, ɗauke kafa da Alhaji Ubaid yai kwata kwata ya daina shigowa donsu gaisa sai in sun hadu a masallaci, daya fahimci kaukaucewar da yakeyi masa sai ya kyale shi don ya gano baya son ya hana shi yin siyasa shiyasa ya janye jiki da shi.
Lokacin da Celebration din Ya matso, Hajiya Layla ta gayyaci yan uwa da abokan arziki don su tayasu Murna, daga cikin wadanda ta gayyata hada Aunty Laura, Benazir kuma ta gayyaci Anila da malama Aisha, koda Aisha ta nemi izni agurin baba Imam yace bai amince taje party ba saboda yahudancine babu shi a addinance, bata ta6a musa masa ba sai akan maganar Party din nan, ta dinga rokonshi akan yabarta taje saboda ta yi ma Benazir alkawarin za ta je, In har ba ta je ba Benazir ba za ta ji dadi ba, Shiekh imam Yace tayi hakuri kawai, don bazai ta6a bari taje ba, wunin ranar kwata kwata babu walwala akan fuskarta, Har Aunty laura ta roka akan ta nema mata alfarma agurinsa aunty laura tace ita bazata sanya masu baki ba, saboda an nuna mata iyakarta don haka suje can su karata ita da uban nata, abunda yasa tace haka saboda taji haushin bukulun da shiekh imam yayi mata akan kudin da Alhaji musa yayi mata alkawarin zai bata intaja hankalin imam da Aisha suka amince da auranshi amma gaba daya suka watsa mata ƙasa a ido abun ya kona ranta.
Ana i gobe za'ayi partyn, Tafiya ta kama sheikh Imam malik, manyan abokansa wadanda suka kasance shahararrun malaman addinin Islam yan kasar sudan dayake acan yayi karatu lokacin daya zauna gurin Kawunsa, abokanne suka gayyace shi wani taron karrama malamai da za'a gabatar a kasar sudan, kafin tafiyarshi saida ya kira Aisha ya kara gargadinta akan bai lamunta taje partyn nan ba, tace mashi toh in sha Allah bazata je ba, bayan tafiyarsa Aunty laura tace ma Aisha ay yanzu tunda mai gadin nata bayanan, sai ta shirya ta tafi tace ta fasa zuwa saboda batason ta sa6ama mahaifinta, bata matsa mata ba amma da Alhaji musa Ya kira ta waya yace mata yana son Aisha ta halarci Partyn in har tasa tazo zai bata Dala dubu goma sha biyar, Jiki na 6ari Aunty laura taje har dakin Aisha ta tunzurata akan ta shirya su tafi, baiwar Allah duk yadda taso ta hana zuciyarta bijirema mahaifinta saida takasa saboda tana son zuwa itama.
Wuraren ƙarfe biyar na marece dai dai, suka shigo gidan Alhaji Ubaid, Aunty Laura ta dauki wankan shadda, Ta coge daurin dan kwalin ture kaga tsira, Ita dai Aisha Abayane a jikin ta doguwa har kasa, sai nikab din da ta sanya.
Anan suka iske manyan bakin su Hajiya layla, babu masaka tsinke, Yan uwa da abokan arziki duk sun hallara a katafaren garden din gidan da aka kawata shi da kayan ado da kujerun da baki zasu zauna an tanadi duk wani abu da baki zasu bukata don jin dadin su, Ga mawaka da Maroka sun Cika gidan sai kaɗe kaɗe sukeyi da yan raye raye.
Tunda suka shigo gidan gaban Aisha keta faduwa rass rass, kwata kwata hankalinta ba akwance yake ba, duk sai taji ba dadi saboda ta sabawa mahaifinta.
Lokacin da ta lula duniyar tunani Yayin da Aunty laura ta shige Cikin mutane tabarta.
Sam bata ji takun mutun ba, sai dai taji an rungumeta, har firgita saida tayi amma da taga Benazir ce sai ta sauke ajiyar zuciya, cike da farin Ciki suke kallon juna, Banezir ta ɗauki wankan tsadadden leshi ko arzikin dan kwali babu akanta..
"Amma wallahi naji dadin zuwanki Aminiyar, har na fara fidda rai, ashe zakizo, ya ki ke ya baba imam? Cikin sanyin murya tace"baba bayanan ya tafi sudan, atare da aunty laura mukazo" ruko hannun ta Benazir tayi "mu shiga ciki, ki gaishe da Uncle Musa, tun Shekaran Jiya ya dawo Nigeria, tare da matar daya aura baturiya, amma baizo da ita nan ba, acan gidansa na Abuja yabarta, bai sanar da kowa game da auransa ba sai dai muka ji abakinsa jiya daya zo"
tun da Benazir ta fara surutu Hankalinta ba akwance yake ba, wani irin faduwar gaba taji jin ta ambaci sunan Uncle musa fuskarta babu walwala tace"kina nufin Uncle musa yana acikin gidan nan"?
Jinjina mata kai tay"eh," tace toh tabari da anjima in an gama partyn sai suje su gaida shi, Benazir ta amsa da toh, damuwace karara Akan fuskarta, Benazir bata lura da halin da take a ciki ba.
bayan sun shiga falo ta iska kawayen Benazir Hada Anila kowaccen su ta dauki wanka na mutunci Aneelerh na ganinta cikin sauri taje ta rungumota, Sauran kawayan Benazir sai murna suke yi Aisha bintu imam tazo, har rige rigen daukar hotuna sukeyi da ita, baiwar Allah tadinga kakkauce masu saboda gudun kada baba Imam yaga hotanta agurin partyn daya hana ta zuwa, Aneelerh ce ta lura da yanayinta hakan yasa taja ta gefe daya ta tambayeta meke damunta? Bata boye mata komai ba ta sanar da ita, ta kara da cewa ita kawai hankalinta bai kwanta ba, tana ji aranta kamar wani abu zai faru, cikin sigar lallashi Aneelerh ta soma kwantar mata da hankalinta har saida taga ta saki jiki...
tun da aka fara gabatar da shagalin hankalin Aisha ba kwance Yake ba, ga kawayen Benazir sai cashewa suke yi suna tikar rawa ga abinci kala kala ko kadan batay sha'awar ci ba.
Tana zaune kan kujera Wayarta ta fara ringing, tayi picking tare da karawa kan kunnanta
Muryar shureim Taji yana fadin ta same shi a upstairs yana son yin magana da ita"
Bata kawo komai aranta ba, ta yi azan zai bayyana mata soyayyar shi ne Hakan yasa ta mike batare da sanin kowaba Ta nufi upstairs, abakin kofar dakin dataga takalmansa tayi knocking ana bude kofar dakin aka janyota ta fado ciki, a firgice ta dago don taga wanene rass taji gabanta Ya fadi ganin Alhaji musa atsaye fuskarsa babu annuri daga shi sai short a jikin shi, wani irin faduwar gaba taji, da tsantsar mamaki ta furta"uncle kaine"? Daga mata gira yayi"nine Aisha.."arude tace"amma yaya shureim ne Ya kira ni, yana ina"
"Ni ne nayi muryarsa, saboda nasan idan kikaji ni ke kiranki ba zuwa zaki yi ba" matsawa yayi dab da ita tayi saurin ja da baya cikin sanyin murya yace"aisha, inaso ki dubeni daga kasa har sama ki fadamin me Allah ya rageni da shi"? Kawar da kanta gefe tayi muryarta na rawa tace"bakomai"
"In har hakane meyasa baki sona?..
"Saboda bakai nake so ba,"runtse idanun shi yayi saboda jin zafin maganar shi
"Aisha idan kikai min hakan baki min adalci ba, kin hana zuciyata sukuni saboda ke na kashe makudan kudi donki samu rayuwa mai kyau, Harta karatun da kukayi a germany nine na dauki nauyin shi ba Alhaji Ubaid ba, kawai nayi amfani da shi ne saboda nasan Halin mahaifinki da tsautsauran ra'ayi ba lallai in yaji nine nayi hakan Ya amince kije ba, kuma nayi hakanne saboda in dinga samun ganinki akai akai, saboda Imam bazai bari ina zuwa zance gurin ki ba, amma da kuna karatu a germany ba karamin morewa nayi ba saboda ina ganinki a duk lokacin dana so"
Hankali atashe tace"Dama duk dawainiyar da kayi mana a germany ba dan Allah kayi ba? saboda son da kake min ne" jinjina mata kai yayi...
"Wallahi da ace nasan kaine ka dauki nauyin karatunmu a kasar germany, da ba abunda zaisa inje"
tana fada ta juya zata fuce yayi saurin ruƙo qugunta da tafin hannun shi ya janyota da karfi ta faɗo kan kirjin shi, ya soma matsa mazaunanta yana sakin nishi, For the first da ta fara hada jikinta da namijin daba muharramin ta ba, rai a6ace ta banbare jikinta daga nashi ta daddage ta wanka mashi zazzafan mari ji kake fasss!.
dafe kuncinsa yayi da tafinsa, idanunsa suka kada jawur cike da bacin rai yace"ni kika mara"? Tana haki tace kadan ka gani, Nan gaba idan ka kara gigin ta6a jikina wallahi saina yi maka abunda har abada ba zaka manta ba, dama ba don Allah kakeso na ba, sai don wata mummunar manufa taka" tana fada ta buɗe kofa ta fuce...
Tun da yake wani dan adam bai ta6a daga hannu ya maresa ba sai akan Aisha, yaji zafin marin nan adaddafe Ya fada kan gadon shi yana juyi, ransa ya baci matuƙa jikin shi har gumi yake zubdawa.
abangaren malama Aisha bayan fitarta daga dakin a jikin bango ta Jingina bayanta, fuskarta sharkaf da hawaye taji takaicin rungumar da Uncle musa yayi mata, kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta ke ji, Ya dasa mata kiyayyarsa a cikin zuciyarta.
Tana cikin tafiya wani irin ciwon mara Ya turnuke ta, da sauri ta dafe cikinta da tafin hannunta, sam takasa cigaba da tafiya a nan ta durkushe tana faman fitar da huci...
Adai dai lokacin dr shureim Ya hauro Upstairs din domin amsa kiran da Uncle Musa yayi ma shi, Yana ganinta Jikinshi na rawa ya karaso gurinta Yana tambayarta meke damunta? muryarta na rawa ta furta"cikina yaya shureim ciwo yake min, ka taimaka ka maida ni gida" ganin halin da take a ciki yasa shi ruko hannunta, ya taimaka mata ta miƙe suka sauko down, A lokacin babu kowa a falon gaba daya sun Koma garden can inda akeyin shagalin.
Har suka fito harabar gidan basu ci karo da kowa ba.
Sai nishi takeyi tana jan numfashi, dr shureim sai sannu yakeyi mata har suka karaso Cikin Gidan Imam, Ya tambayeta tana da maganin ciwon cikinne ko yaje ya siyo mata ne? Dakyar ta bude baki tace mashi bata da shi ya kare" Cikin sauri Dr shureim Ya fita Ya nufi chemist din dake a kusa da su don ya siyo mata maganin, tausayinta duk ya kama shi..
Lokacin daya dawo gidan hannun shi ruke da leda ta maganin daya siyo mata, a bakin kofar falo yai ta ƙwala sallama shiru bata amsa mashi ba, Kuma Yan aikin gidan duk basa a kusa, wayar sa ya zaro ya danna mata call tana fara ringing, tayi picking yanayin yadda yaji Muryarta ba karamin ɗaga masa hankali tayi ba.
Cikin shesshekar kuka take fadin"ya shureim mutuwa zanyi, ka taimaka min, " adabarbarce ya furta"Aisha kina ina ne? Ga maganin na kawo maki" shiru yaji bata amsa mashi ba, a rude Ya mike Ya soma neman bedroom dinta saboda bai taba shiga dakinta ba, duk zuwan da zaiyi gidan A falo ya ke tsayawa.
Dakyar ya gano bedroom dinta, saboda tsabar rudu ya afka Ciki, a kwance ya taras da ita tsakiyar gadonta, sai juyi takeyi tana murkususu, tafukan hannayenta adaddafe da mararta, sam babu abaya ajikinta zafin daya taso matane yasa ta cireta cikin fitar hayyaci batare da saninta ba, sai Camisole data rage a jikinta shara shara gaba daya surar jikinta ta bayyana muraran.
Bai kula ba saboda hankalinsa ba akwance yake ba burinsa kawai ya taimake ta, Aje maganin yai akan bedside drawer Ya fito da sauri jim kadan ya dawo hannun shi ruke da bottle water Ya zauna daga gefen gadon..
Sai da Ya ballo kwayar maganin Ya juyo don ya taimaka mata tasha, kwatsam Idanun shi suka sauka akan Santala santalan Cinyoyinta lokaci ɗaya tunanin shi ya gushe, ya fara jin wata irin matsananciyar sha'awa na taso mashi kamar ransa zai fita, Zuciyarshi ta dinga azalzalarshi kanshi ya fara juya mashi kamar hankalinshi na barin jikinshi, Bawan Allah a lokacin yaita kokari kaucewa sharrin shaidan amma abun Yaci tura saboda yadda surar ummi ke fusgarsa har baisan sa'adda Ya afka mata ba, ga zafin ciwo tana fama da shi a haka dr shureim ya keta mata haddi, taji radadin da bazai misaltu ba, cikin fitar hayyaci ta dinga Sakin kukan azaba, tana yi masa magiya akan ya kyale ta, kada ya kashe ta, kada ya rabata da mutuncinta, amma duk abanza saboda a lokacin shureim yayi nisan da baya jin kira. Ya Ilahi!
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹
~✍️~
~___________________________________~
Bata tashi farkawa ba, sai Bayan sallar Magrib, bakinta dauke da sunan Allah, tana kokarin motsawa don ta miƙe taji wani azababben zafi agabanta, ga wata kasala data baibaye sassan jikinta, tunani to soma yi meya faru da ita? A ina take"? jin iska na ratsa jikinta yasa tay saurin shafa jikin nata, lokaci daya gabanta Ya soma faduwa jin babu sutura a jikinta cikin sauri ta yunkura ta miƙe zaune, tana kallon kanta kafin ta yi saurin kallon gefenta, shureim ta gani a kwance kan gadon batare da sutura a jikin shi ba, sai dan bargon daya lullu6e ass dinsa, sam ta kasa tuna komai amma tabbas taji a jikinta raping ɗinta yayi Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ana zare ranta, Koken da ta ke yi ne ya farkar da shi, a firgice ya bude idanun shi da suka kada jawur ya dube ta da su, baiyi aune ba yaji saukar zazzafan mari kan kuncinsa ta shaƙe wuyanshi tana kuka ta furta"nashiga uku! yaya shureim ka kashe min rayuwata, ka gama dani! Ka wulakanta martabar jikina ka goga min ƙazantar Zina, Allah Ya isa tsakanina da kai, bazan ta6a yafe maka ba..."
zafafan hawayene suka wanke fuskarshi kwata kwata baiji zafin marin da tayi mashi ba saboda ruɗun da kwakwalwarsa ta shiga gaba daya yabi ya rikice yana kokarin tariyo abunda ya aikata mata, saboda baya a cikin hayyacinsa komai ya faru, wlh ko a mafarki bai ta6a sha'awar ya kusanci macen da ba muharramarsa ta aure ba, balle Aisha da yake yi mata kallon kanwarsa, tana kuka Yana kuka Yace"Aisha bayin kaina bane, ba halina bane aisha, ke shaidace akaina, wlh ni ba mazinaci bane..."
bai ƙare maganarba ta Fasa tsawa tana huci tace "babu abunda zaka fada min ya shureim, wlh sai Allah yayi min sakayya, da kasan irin burin da nake dashi akanka da ba kai yi min haka ba, da tunfarko ka fadamin kana son Jikina, Ni mai iya aurenka ce don in dinga biya maka bukatarka saboda son da nake maka, amma ka rasa ta hanyar da zaka neme ni sai ta hanyar Zina"?
Tana magana Jikinta na kerma, Idanunta sun kada jawur kamar an watsa mata barkono.
Cikin disasshiyar murya tace "ka karyamin zuciyata yaya shureim, ka cuceni, ka zalunce ni, Inayi maka kallon mutun mai tsoron Allah, ashe kaima fasiki ne, kana daya daga cikin mazan da basa son mace don Allah sai don surar jikin ta, kaja mun aikata zunubi, Yanzu da wani ido kakeso In kalli Babana, da mutanan da sukeyi min kallon mutuniyar kirki! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..." duk yadda yaso ya shawo kanta ya kasa, taki ta saurareshi balle ta fahimce shi, saukowa tayi daga kan gadon jikinta duk ba kwari dakyar ta mayar da rigarta da gudu ta shuge toilet tana kuka ta kulle kofar, tabar shureim a zaune kan gadonta yana ta kuka kamar karamin yaro, sau uku yana marin kanshi saboda bakin ciki da takaicin abunda ya aikata ma Aisha, Matar da yayi burin ya aura.
"Ya Allah ba halina bane, Kafi kowa sanin bawan nan naka, Ni maijin tsoronka ne mai gudun saba maka ne, kullum ina rokonka akan ka kareni daga sharrin zuciya da sharrin shedan amma meyasa Hakan ta faru dani? Meyasa na aikata ma Aisha haka"?...
Cikin shesshekar kuka yajiyo muryarta daga cikin toilet tana fadin"Yaya shureim ka tashi ka tafi tunkafin Aunty laura ta dawo"..
Jiki asanyaye Ya sauko daga kan gadon Cike da danasani Ya mayar da suturarsa, Wlh Yaji kunya mara misaltuwa, Yaji radadin da har yau In ya tuna sai yaji ɗaci aran shi.
______________________________________✍️
Lokacin da su Benazir suka lura babu malama Aysha a gurin partyn nanfa hankalinsu ya tashi suka dinga nemanta sako da lungu na gidan, har layin wayarta suka kira akashe.
Hankalin su atashe suka tuntu6i Aunty Laura da maganar, tace kada su damu, ta koma gida dama bada son ranta tazo ba, bayan Kammala partyn suka biyo Aunty Laura gidan don suga idan ta dawo, bayan sun shigo gidan suka Nufi dakinta, adatse suka iske kofar, Knocking su ka yi tare da ambaton sunanta, Tana jinsu tayi shiru bata amsa masu ba, har saida suka fara gajiya da bubbuga kofar su ka fara tunanin ko bata nan ne.
A lokacin da basuyi tsammani ba, sai ga kiran ta ya shigo layin Benazir, cikin sauri Benazir tayi picking up tana tambayar ina ta shiga ne? Suna ta neman ta.
Cikin raunanniyar murya Aysha tace kada su damu, tana acikin dakin, ta kwanta ne saboda bata jin dadin jikinta amma da sauki.
Cike da tausayinta Benazir tayi mata sannu da jiki kafin ta mika ma Anila itama tayi mata sannu.
Daga bisani su ka yi wa Aunty Laura sallama suka tafi, zuciyoyinsu cike fal da tunanin yanayin da sukaji Muryar Aisha.
Tun daga Ranar Aisha ta ɗauke Kafa da zuwa gidan aminnanta, Babu wanda yasan abunda ya faru tsakaninta da dr shureim, ita kadai tayi ta nukunuku ta ki yarda Aunty laura ta gane halin da take a ciki, saboda bata son kowa ya sani ta fiso ta rufawa kanta asiri.
Tsawon kwana uku bata bude wayarta ba, baci ba sha, ba bacci, ta killace kanta adaki, wani irin depression ne Ya kamata ga ciwon rabin kai da take fama da shi, In ta fara kuka har sai hawayenta sun kafe tukunna take dakatawa, kusan kwana ta ke yi tana yin istigfari tare da kai kukanta gurin Allah.
Saboda tayi imanin shi kadai ne zai kawo mata mafita, Hankalin Aunty laura ba karamin tashi yayi ba, ganin Aisha na neman ta halaka kanta, Ta rasa gane meke damunta gaba daya ta hana kanta sukuni, ta rame tayi duhu, idanunta kullum a kumbure suke saboda kukan da take sha, ba irin magiyar da batayi mata ba akan ta faɗa mata meke damunta amma taki sanar da ita, sai dai tace ta tayata da addu'a Allah ya yaye mata abunda ke damunta, tace toh In sha Allah zatayi mata addu'a.
Idan muka koma bangaren Dr shureim tun washe garin ranar da abun Ya faru, Yabar Kasar, Ya tafi Egypt saboda bazai Iya cigaba da jurar zama yana ganin Aisha da abun kunyar daya aikata mata ba.
Bayan makonni da afkuwar Lamarin, Sheikh Imam Ya dawo Nigeria, Bayan ya huce Gajiya a dakinsa, Aunty laura ta jera mashi abincin shi akan rug din dakinsa, Kasa cin abincin yayi saboda faduwar da gaban shi keyi, kuma yaji shiru Aisha bata leko ta yi mashi sannu da zuwa ba, kamar yadda ta saba yi mashi.
"Ina mamana? Ko taje islamiya ne, Aunty laura tace aa tana adaki Yace ta kira ma shi ita.
Fitowa tayi daga dakin ta shiga dakin Aisha, tayi mamakin ganinta a kudundune cikin bargo jikinta sai kerma yakeyi kamar wadda sanyi ya kama.
Hankali atashe Aunty Laura ta haye kan gadon tare da yaye bargon, gabanta ne ya fadi rass, ganin yadda idanun Aisha suka juye, tsabar zafin da jikinta ya dauka tamkar naman da aka gasa da wuta, arude Aunty laura ta zabga salati Ta watso aguje ta nufi dakin sheikh Imam Ta sanar da shi halin da Aisha take aciki, abincin da bai ci ba kenan, jikinshi na 6ari yabiyo bayan Aunty laura suka nufi dakin Aisha, Suna shiga suka taras da Amai na fita daga bakinta.
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un" arude Sheikh Imam Ya furta, baiyi wata wata ba, Ya sungumi Aisha Ya fuce da ita da gudu Laura tabi bayanshi, Suka shiga mota.
Kaitsaye Suka Nufi Asibiti da ita, aranar saida aka kwantar da ita saboda jikinta yayi tsauri.
A asibitin suka kwana, Sheikh Imam bai runtsa ba, Yadda Ya ga rana haka yaga dare, har fada saida yayi ma Aunty Laura akan sakacinta na rashin kula da Aisha, gaya nan har ciwo yakamata batare da ita ta sani ba, Aunty laura dai sai hakuri take bashi tace ba laifin ta bane, nan ta fayyace masa halin da Aisha ta shiga bayan tafiyarsa, ta kara da cewa ba irin magiyar da banyi mata ba akan ta fadamin meke damunta amma takiya sai dai tace Intaya da addu'a, Sheikh Imam ya damu sosai, Babban abunda ya kara daga masa hankali ramewar da tayi, kamar ba Aisharsa ba.
Basu sanar da kowa game da ciwonta ba, a duk lokacin da su Benazir suka kira Aunty Laura su kai mata korafin sun kira layin Aisha basa samu sai tace masu su yi hakuri ayyuka ne su ka yi mata yawa, kwanansu ɗaya a asibitin baci ba sha saboda damuwar Halin da Aisha take a ciki, Bayan dr din dake kula da Aisha ta gama bincikenta akan lafiyarta, ta kira Sheikh imam don suyi magana acikin Office din ta.
Bayan sun shigane Dr din Ta dube shi dakyau fuskarta da damuwa tace"Sheikh, naji dadi da Ya kasance Ni Ce amintacciyar Likitar dake duba Iyalanka, Saboda kai malamina ne, ni kuma dalibarka ce, ni me rufa maka asiri ce don kare martabarka" Cike da gamsuwa sheikh Imam Ya jinjina mata kai da alamun rudu akan fuskarsa.
Takardar dake a hannunta ta miƙa masa jiki asanyaye ya kar6a har zai buɗe muryar Dr din ta katse shi.
"Sakamakon gwajin da mukayi ma Aisha ne"
A hankali Ya soma karanta sakamakon, abun mamaki sai taga yana dariya maimakon taga tashin hankali akan Fuskarshi don ta san muddin Ya karanta sai Hankalinsa ya tashi ba kadan ba.
"Sheikh Lafiya naga kana dariya" mika mata takardar yayi"Ki duba dakyau, wannan sakamakon bana Aisha bane, watakil kunyi mistake ne, Aisha da bata da aure, Ina ita Ina ciki"? Ya fada da murmushi akan fuskarta, Idanun Dr dinne suka cicciko tab da kwalla saboda tsananin tausayin shi daya kamata.
"Dan Allah, Ki bani na Aishana inaso in san meke damunta, wannan kuma ku nemo mai shi ku bata, kada asamu matsala..."
girgiza kai Dr din tayi cikin rauni na murya tace"Kayi hakuri Sheikh, kai malamine nasan kayi imani da Allah ka kuma yi imani da kaddara, wlh result din Aisha ne, Tana dauke da juna biyu, Nima dana ga sakamakon saida na karyata kaina saboda nasan Aisha bata da aure, sannan Aisha kamilar macace, amma dana zurfafa bincike na sai na gano dagaske Cikine a jikin ta...."
bata ƙare maganarba sakamakon Tsawar da Sheikh Imam Ya doka mata tamkar zai fasa dodon kunnanta, Tuni tasha jinin jikin ta.
Yana Huci Ya furta"Kin bani mamaki dr Husaina, kin kuma ji kunya wlh, baki taba yi min karya ba sai yau, wannan sakamakon da kika nuna min bana Aishana bane, mamana bazata taba aikata zina Ba, Ƴata kamila ce, mai jin tsoron Allah bazata taba aikata abunda zai sabawa Mahaliccin ta ba, Na yarda da ƴata Aisha bazata ta6a ruke koda hannun Namijin daba muharraminta bane, don haka ki gaggauta janye kazafin da kike kokarin yi mata, watakil biyanki akayi don kiyi mata ƙazafi, dama akwai masu jin haushin daukakar da Allah yayi mata watakil kema kina daga cikin su...'
kwata kwata Dr husaina bataji haushin kalaman Shiekh Imam ba, sai ma tausayin shi daya ƙara kamata.
Kekketa Takardar yayi, Tare da watsa pieces din saman table din gabanta, Ya juya afusa ce Yabar Office.
Yana tafiya Visitors dake zarya acikin asibitin sai kallon shi sukeyi ganin Sheikh Imam wasu har gaishe da shi sukeyi amma bai kula su ba, Yana shiga dakin da aka kwantar da Aisha Ya iske Aunty laura zaune kan kujerar dake a gefen gadon ta zabga uban tagumi..
Tana jin motsin shigowarshi ta mike tana tambayarshi me dr tace.
Rai a6ace yace"ba zamu cigaba da zama acikin asibitin nan ba, Gida zamu tafi inyaso sai muyi jinyarta acan"
"Amma ba'a sallame mu ba, kuma jikin nata har yanzu da sauranshi..."
bata ƙare maganar ba, Ya daka Mata tsawa"Ki ruko Aisha mu tafi" jikinta na bari ta taimaka ma Aisha ta mike baiwar Allah ko tafiya bata iyayi sai layi take kamar zata kife ƙasa a haka suka shiga mota da ita.
Bayan sun dawo gida Aunty Laura Ta matsa mashi akan ya faɗa mata me doc Husaina tace akan ciwon Aisha Nan ya kwashe komai da suka tattauna ya sanar da ita, itama a lokacin biye mashi tayi suka karyata maganar Dr husaina.
Cikin da laulayi ya zo ma Aisha, bakar wahala take sha, wani sa'in tana a kwance kan gado take fara kwarara amai ta sauko da gudu ta fada toilet ta karasa shi acan.
Gashi kullum Cikin yin zazzabi takeyi, daga bayane Aunty Laura ta gano Ciki ne da ita, Bazan Iya misalta tashin hankalin da Aunty Laura ta shiga ba, a daki ta same ta kwance kan gado tace taji tsoron Allah ta fada mata gaskiya! Akwai ciki jikinta ko babu? saboda ta fara kokwanto akan yanayin ta, Kafin ta sanar da ita saida ta fara rokonta akan karta fada ma baba Imam tabarshi a matsayin sirri atsakaninsu duk da tasan watarana dole ne Yaji, Aunty laura tace tayi mata alkawarin bazai taba ji abakinta ba.
Anan ta labarta mata komai daya faru tsakaninta da shureim, a lokacin Aunty Laura ta zabga salati tana sallallami, Jikinta Ya kama bari Saboda razanar da tayi, ta girgiza ba kadan ba, musamman dataji cewa Shureim ne yayi mata aika aikar, Babban tashin hankalinta Idan Sheikh Imam Ya gano Cikin ne dagaske, to fa itace mutun tafarko da zai fara tuhuma saboda ita ta matsa ma Aisha akan suje Partyn.
Aunty Laura tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda tausayin Aisha daya kamata, Yarinya Kamila da ita an zubar mata da mutuncin ta, dr shureim Yasha tsinuwa agurin Aunty laura, tace dan iska munafuki mai fuska biyu, kamar Na Allah, In sha Allahu sai yaga sakayyar abunda yayi mata, daga bisani ta lallashi Aisha taja ta ajiki sosai, ta dinga bata hakuri hadi dayi mata nasiha har hakuri ta bata akan Tursasa matan da tayi akan taje, gani take ma kamar itace Silar komai daya faru da Aisha.
A haka aka cigaba da rayuwa, Har Ila Yau sheikh Imam yaki yarda cewa Aisha ciki gare ta, wani'sa'in agaban shi zatayi amai amma ko kadan bai yarda ya zargeta da ciki ba, Iya bakin gwargwado tana samun kyakkyawar kulawa agurin Baba Imam, baya barinta cikin damuwa, Ya hana a kaita asibiti kuma Ya hana dr Husaina zuwa agidan, Ko tazo da niyar duba Aisha tun daga bakin gate security Officers ke korarta.
lamarin ya daure mata kai, ita burinta kawai ta taimaka ma sheikh Imam su nemi mafita gudun kada kimarshi ta zube sai dai Yaki bata damar ganawa da shi, Har court taje ta same shi a office dinshi Amma Yaki sauraronta, badan taso ba tahakura da bibiyar shi.
Saboda zullumi da fargaban abunda zai biyo baya In sheikh Ya san Aisha tana da ciki, yasa Aunty Laura ta rame, kamar mai fama da zazzabi har saida sheikh Imam Ya lura da canjin da tayi, ko da ya tambayeta meke damunta sai tace mashi Ciwon aisha shine silar damuwarta, hakuri kawai yake ba.
Dubarace ta fado mata arai, ta sami Aisha da zancen su zubda Cikin kawai, Aisha tace bazata iya ba, bata son ta kuma aikata wani zunubin na kisan kai bayan wanda suka aikata, ita bazata iya kashe rai ba, laifin da shureim ya aikata mata bazai shafi abun dake a Cikin ta ba.
Aunty laura taita kokarin tunzurata don ta amince asamu arufawa kai asiri amma Aisha ta yi kunnan Uwar shegu da maganarta, ganin tasa kafiya yasa Aunty laura ta dinga zuba mata maganin zubar da ciki aboye take barbada mata shi cikin abinci ko cikin abun sha, sai dai wani Iko Na Allah tun da tasoma yunkurin 6arar mata da ciki Allah bai nufa ba, saima kara lafiya da ta ke yi.
Lokacin Da Cikin Yakai wata Biyar, Ya fara bayyana a jikinta, daga ka kalle ta zaka gane tana da ciki Amma sheikh Imam Ya kasa Yarda Ciki ne saima yace ture akai mata, Ajiyar Aljanu ce, haka ya dinga banka mata ruwan addu'o'i tana sha, In zataci abinci sai ya tofe shi da addu'a in zata kwanta bacci sai ya shigo har daki gaban gadonta yayi mata addu'a, Zuciyar Aisha ta karaya da ganin irin Yardar da mahaifinta yayi da ita, shiyasa ta kasa buɗe baki ta furta mashi Ciki ne a jikin ta, sai dai in suna atare yanayi mata addu'a ko yana bata abinci abaki, tayi ta zubar da hawaye tana kallon shi, ya dinga lallashinta yana fadin mamana kiyi hakuri Allah yana tare da bayinsa masu Hakuri, ki jure ki cinye jarabawar nan, In sha Allah koma wanene yake nemanki da sharri kanshi zai koma, mutanene ba Allah aransu bakin ciki da hassada sunyi yawa azukatan mutane.
Wani sa'in in yanayi mata maganar sai ta dinga Yunkurin buɗe baki don ta fada mashi gaskiya amma sai ta kasa, In Aunty laura na akusa taga tana kokarin fada masa sai tayi saurin janye hankalin shi da tunanin wani abun.
Saboda Lalurar Aisha Yasa Sheikh Imam Ya hana ta fita ko kofar falo bata leƙawa, saboda baison wani yaga Aljiyar da aljanu sukayi mata a zargi ciki ne, duk wanda yazo nemanta gida sai dai suce mashi bata nan tayi Tafiya Sudan gidan Kawunta, babu wanda yasan Aisha tana agida har su Benazir.
Daliban Aisha na islamiya, Da abokananta malamai da duk wani mai sauraren wa'azinta sai da ya damu da rashin ganin Aisha, saboda Allah yayi ta da farin jinin mutane suna son Aisha.
A kwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin Aisha Ya Cika wata tara Cuf, tashi dakyar zama dakyar haka ta ke fama, a daren wata ranar Juma'a ne nakuda ta kamata, Aunty Laura ta matsa akai ta Asibiti ganin yadda take shan wahala, amma Sheikh Imam Ya hana yace ciwonta bana asibiti bane, sai dai ya bata ruwan addu'a tasha, a lokacin Aunty Laura, har yunkurin fada mashi gaskiya tayi amma saboda tsoron Kada ya saketa Yasa taja baki tayi shiru, ta bar shi ya gani da idon shi.
A falo ya zauna yana jan cazbaha, Ya baro Aunty laura adakin Aisha.
Bayan wani Lokaci, Kukan Jariri Ya cika kunnen shi, Wani irin Bugu Zuciyar shi tayi tamkar zata fasa kirjin shi, Tsantsar tashin hankali da rudanine Ya bayyana akan fuskarshi, cikin sauri Ya miƙe Ya shiga dakin Aisha, dira kafarshi keda wuya ba zato ba tsammani idanun shi suka sauka akan Jinjirin da Aunty Laura ta ruƙe a hannunta.
Lokaci daya yanayin fuskarshi ya sauya, A lokacin Ayshah tana a kudundune Cikin bargo Aunty laurace ta taimaka mata tayi wanka bayan ta kar6i haihuwarta.
Jikinshi na kakkarwa ya karasa shiga dakin a gaban Laura ya tsaya yana ƙarewa Jinjirar kallo idanunshi azazzare.
Babyn Fara Sol da ita, Idanunta dara dara farare kamar an diga zaiba, ga wata yalwatacciyar sumar kai har gaban goshinta gashin ne a nannaɗe, kallo daya zakai mata kagane Ba jinsin bakar fata bace.
A lokacin Jikin Aunty Laura kerma yake kamar mazari, Ga wani bugu da kirjinta keyi mata saboda tsoron Hukuncin da Shiekh Imam zai yanke mata.
Numfashi yaja tare da miƙa hannu Ya kar6i jinjirar daga Hannun Laura, Ya kura mata idanu Yana kallon ta.
Ya kasa yarda da abun da Zuciyarshi ke raya mashi, ya yi fatan ace mafarki ya ke yi ba gaskiya ba, wani kululun bakin cikine da takaici Ya tokare makoshin shi..
Muryarshi na rawa ya furta"Shegiya agidana? Gidan Alkali sheikh Imam? Sanannan malamin addinin islama! Me yi ma wasu fada da nasiha akan aikata Barna"? Yau agidana aka aikata barna? Ni sheikh? yata Aisha ce ta haifi Shegiya acikin gidana? Batare da Aure ba? inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..."
wani makokon bakin cikine ya mamaye zuciyarshi, hannayenshi na kerma Ya mika ma Laura yarinyar da sauri tasa hannu ta kar6a, jikinshi na kerma ya zauna Gefen gadon Aisha Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya ya furta"mamana, tayaya kika samu Ciki? Wanene yayi maki aika aikar nan"?
Kunya da bakin cikine suka sa Aisha tagaza furta kalma, taki fitowa daga cikin bargon jikinta sai kerma ya ke yi.
Shurun da tayi ne ya bata masa rai, Ya doka mata tsawar data firgitar da su, Har Jaririyar saida ta fashe da kuka
Yana Huci Yace"Ba zaki bani amsar tambayar da nayi maki ba"?
Aunty laura tana kuka tace"Abien Aisha tsautsayine da kaddara..."
Bata kare maganar ba, Ya zabura ya miƙe ya nufe ta gadan gadan, batai aune ba Taji safkar maruka zafafa kan kuncinta, Har saida shatun hannayensa suka fito rudu rudu akan kuncin ta, gefen bakinta ya fashe jini ya fara ɗiɗɗiga.
"Allah Ya isa tsakanina dake Laura, Kin cuce ni kin cuci kanki kin kuma Cuci Aisha, sannan kin Cuci malama Batool! Kin ci amanata, nasan komai ya faru da Aisha kece Sila, kece kika ja komai, shashasha mara hankali"
Fashewa tayi da kuka Jinjirar hannunta sai kuka takeyi.
"Kunyi tunanin bansan komai bane? Duk abunda ke faru agidan nan an fada min, Kece Kika matsa ma Aisha kuka tafi partyn dana hanata zuwa, kina amfani da biyayyar da takeyi maki gurin Cutar da rayuwarta.."
Cikin shesshekar kuka tace"wallahi Allah shine shaidana, Ni ban ta6a Cutar da Aishaba, na ruke amanar da ka bani, Kai ka sani in ba ni ba wa kake tunanin zata kula maka da yarka kamar yadda na kula maka da ita"?
Bai kula ta ba, Ya koma ga Aisha Ya sanya Hannu Ya yaye bargon data lulluba da shi wata irin zabura tayi ta mike zaune jikinta na kerma ta dinga girgiza kai batare data iya furta kalma ba.
"Ki gaya min wani fasikin ne yayi maki ciki"?
Cikin rawar murya ta zayyana mashi komai daya faru.
"Dan Allah ka yafe min baba, Ba laifina bane, bayin kaina bane, Na rantse maka da wanda raina yake a hannunsa Bada son raina komai ya faru ba, dr shureim shine Ya yi min fyaɗe, baba kayi hakuri kayi hakuri, nasan nakarya maka zuciya, Naji kunya baba, nayi abun kunya, har rokon Allah nayi ya dauki raina in huta saboda bakin cikin abunda yaya shureim yayi min..."
sambatu tadinyi yi mashi...
Bai san sa'adda hawaye suka cika idanun shi ba.
Cikin raunanniyar Murya yace"Aishana, meyasa lokacin dana hanaki fita partyn bakiji maganata ba? Meyasa? Har ni zansa maki doka ki karya saboda Wannan shashashar ta tursasa maki" ya fada yana nuna Aunty laura da yatsa.
"Aishana baki taba yi min gardama ba, ban taba hanaki abu kika ƙiyi ba sai akan Paryn nan! Kika bijiremin, Ni dama saida raina ya bani wani abu zai iya faruwa shiyasa Na hanaki zuwa, da ace kinbi maganata da duk hakan bata faru ba, Kinga illar Kin bin Umarnin Iyaye ko"?
jinjina mashi kai ta yi Jikinta nata kerma.
"Aisha, Kinbiyewa Son zuciyarki, Kin cuce ni Kin Cuci kanki, Kin kuma Cuci mutanan da suka yarda da mu, sannan Kin zubarmin da mutucina kema kuma Kin zubar da naki mutunci, kinja mana abun kunyar da shiga cikin mutane zai gagaremu, Kin karya alkawarin da kikayi min na kare mun mutuncina da kimata a idon duniya, masuyi maki kallon mutuniyar kirki da zarar sunsan abun kunyar da kika aikata zasu fara yi maki kallon fasika mai fuska biyu, da Ina alfahari dake amma A yanzu babu wannan Aishana, Kin lalata komai, farin Cikin da kika sama min tun ranar haihuwarki a yau kin bata shi, Kin dasa min bakin cikin da har abada bazan ta6a warkewa daga radadin da naji ba, Aisha Ina da makiya wadanda suke son ganin bayana, Idan har sukaji abun kunyar da kika aikata zasuyi min dariya, kuma zasu yi amfani da hakan gurin ganin raunina..."
fashewa tayi da kuka tana fadin"baba kadaina fadin maganganun nan bana jin dadi baba, Kaifa malamine, kafi ni sani baba, Abunda ya faru dani Kaddara ce, wata irin addu'ar neman tsari ce bakai min ba? Nima haka inayi ma kaina amma hakan bai hana kaddara ta afkamin ba, saboda Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan, babu wanda Allah baya jarabta baba, Annabawan Allah sun fuskanci jarabobin rayuwa basu taba gazawa ba, ya kamata kaima kayi koyi da su, baba wannan ne karo na farko daka fara fuskantar jarabawa mafi muni arayuwarka sau ɗaya tak yarka tayi ciki batare da aure ba, Dan Allah baba Mu dauki Hakan amatsayin Kaddararmu, muyi hakuri mu jure, baba Kafi jin kunyar duniya akan ta lahira? Mutane bazasu amfane mu da komai ba saboda basune zasuyi mana hisabi ba"!
Maganganun Aisha sun karya Zuciyarshi, har ya gaza yanke mata hukuncin da yayi niyar yi mata.
Mikewa yayi da sauri Ya fuce daga dakin, Yana fita Aunty laura ta mika mata Jinjirar dake ta kuka"ki bata nono Tasha yunwa take ji" Kar6ar jinjirar Aisha tayi, ta fara shayar da ita idanunta akan fuskar Jinjirar yayin da take tsotsar nono sai kallon fuskar mamanta takeyi, hawayen Aisha dake gangarowa ta cikin idanunta kaitsaye yake sauka saman fuskarta, tayi azan In ta haifi yarinyar zataji tsanar ta saboda bata sameta ta hanyar aure ba, amma sai ta ji tsantsar kaunar yarinyar fiye da komai na duniyar nan.
Aunty laura ta kara lallashin Aisha har saida ta kwantar mata da hankali.
"Aisha nayi danasani da nayita kokarin zubda maki Ciki saboda inajiye maki bakin mutane da kuma abunda zai biyo baya idan mahaifinki Yaji, wlh yanzu da kika tunasar damu sai naji jikina yayi sanyi, da na kashe yarinyar nan da nayi danasani na har abada, baiwar Allah gata kyakkyawa kamanninta sak dana Ubanta, Allah ya raya mana ke bisa tafarkin addinin islam, Allah yasa ki gaji Kyawawan halayan Mamanki"
aisha na murmushi ta amsa mata da ameen.
"Bari naje na shirya maki Abinci nasan kina jin yunwa"
"Aunty Laura, Baki gaji ba? Naga kin raunata" murmushi tayi kada ki damu Aisha, duk raunin da zan ji bai kai wanda kika ji ba.
Ta fada tare da fucewa ta shiga kitchen da kanta Ta hada mata farfesu bayan ta gama ta kawo mata adaki.
A bangaren Sheikh Imam bayan daya Koma dakinsa safa da marwa ya cigaba dayi, Zuciyarshi cike fal da tunanin ta yadda zai bullowa lamarin saboda bayason asirin abun da ya faru da yarshi aisha ya tonu a idon duniya, yana jiye masu tsoron tozarcin da zasu fuskanta agurin mutane..
A bangaren Dr shureim tun bayan daya Koma Egypt gurin aminsa, Bai kara samun kwanciyar hankali ba, saboda damuwar abunda yayi ma Aisha, Sai da ya shafe sati daya cur bai runtsa ba, abinci sai anyi dakyar ake samu yaci, ya yi duhu ya rame saboda tunanin A wani hali aisha take aciki, ga wani irin azababben sonta daya kara nunkuwa acikin Zuciyar shi, har takaiga baya iya bacci batare da yayi mafarkinta ba, Sometimes sai yayi tunaninta ya ke samun nutsuwa a cikin zuciyar shi, kusan kwana yakeyi akan darduma yana istigfar tare dayi ma Aisha addu'ar Allah yaye mata damuwarta ya kawo mata sauki acikin rayuwarta, saboda yasan zunubin daya aikata mata bazai barta ta zauna lafiya ba, dole su fuskanci kalubale ita da Mahaifinta.
tun yana boye abunda ke damunshi har amminsu ta lura da rashin walwalar shi ta dinga tambayarshi meke damunshi yaki fada mata, ta kasa jurewa ta kira iyayen shi ta sanar da su halin da Dan su ke a ciki, da jin hakan Hajiya layla ta bashi Umarnin ya dawo Nigeria, saboda ammi tace ta rasa gane kanshi, baya bacci baya son cin abinci, wanka ma saita matsa mashi ya ke yi kamar karamin yaro.
Bayan ya dawo Nigeria, Iyayenshi suka tasa shi agaba da tambayar meke damunshi? yaƙi ya sanar dasu, Ba irin lallashin da basuyi mashi ba amma duk abanza.
Saida Ya samu nutsuwa ya kira Benazir a dakinsa ta same shi ya tambayeta Ina Aisha? Tace mashi rabon ta da Aisha kusan wata tara da kwanaki, Aunty Laura tace masu ta tafi sudan gurin kawunta, Ko sun kira layinta basa samu kuma koda zata tafi ba ta yi masu sallama ba"
Hankalin shi ba karamin tashi yayi ba, Zuciyarshi ta karaya sosai.
Ana haka saiga kiran Sheikh Imam Ya shigo wayar shi, wata irin kunyace ta kama shi kamar bazai daga kiran ba sai kuma Ya daga, Ko sallamar shi sheikh Imam bai amsa ba Yace shureim Inason ganinka, Ka same ni agidana, Ya amsa mashi da toh.
Bai bata Lokaci ba, Ya shirya kanshi cikin shadda Ya nufi gidan Sheikh Imam A garden Ya taras da shi zaune kan kujera fuskarshi babu walwala kamar bai taba dariya ba, tuni Shureim Yasha Jinin jikin shi.
Bayan daya zauna kan kujerar dake fuskantar sheikh Imam Malik Ya yi shiru Yana sauraron shi..
Kallo ɗaya sheikh Imam yayi mashi Ya lura da irin ramar da yayi daga gani yana acikin damuwa.
"Akwai wata rana, dana farka tsakar dare, na fito daga daki Ina zagaye Gidana, dama Ina yawan yin hakan sometimes bana iya bacci batare dana tofe ko'ina da addu'a ba, ina gab da zan gifta dakin aisha Najiyo shesshekar kukan ta, Kasan me naji tana fadi"? ya tambaya da tsantsar bacin rai Yana kallon fuskar Shureim daya gama rudewa, Girgiza kai yayi"aa baba'
"Addu'a takeyi Allah ya cika mata burinta na ganin ta auri yaron makwabtana data mutu akan kaunarsa batare da sanin shi ba.."
wata irin karaya Zuciyar dr shureim tayi.
"Nayi mamaki a wannan lokacin, saboda Aisha bata taba bude baki ta fadamin ga wanda takeso ba, amma a lokacin danaji tayi addu'ar nan ni kuma sai nayi alkawarin zan aura mata yaron nan da take so saboda in cika mata burin ta.."
zafafan hawayene suka wanke fuskar Dr shureim.
"Yarinyar da tayi dakon soyayyarka acikin zuciyarta na tsawon shekaru, ta hana idonta bacci don ta roki Allah ya mallaka mata kai ita ka wulakanta rayuwarta Shureim? Ya faɗa rai abace.
"Inayi maka kallon mutumin kirki kamili, mai jin tsoron Allah, ashe na yaudari kaina! shureim ka sani ka take sani? Da yata ka aikata zina? Sannan baka taba waiwayonta ba, Ka haura kafa kabar kasar, Sai jiya na samu labarin ka dawo! Baka damu da halin da ka jefata ba shureim! Har yabonka nakeyi saboda na yaba da kyawawan halayenka amma ka tashi ka watsa min kasa a ido"
Fashewa da kuka dr shureim yayi kamar karamun yaro, shima sheikh Imam din hawaye ne ke zarya kan kuncinsa.
Cikin karyayyar murya mai tattare da danasani dr shureim Shureim Ya soma bashi hakuri Yace ya amsa laifinsa amma wlh baisan Ya akaita ba, Allah shine shaidarshi bai ta6a kusantar zina ba, bai ta6a sha'awar Ya kusanci Aisha batare da aure ba, Amma ya karbi laifinsa kuma Yana neman alfarmar ya bashi aurenta saboda su rufawa kansu asiri.
Sheikh Imam yace yaji amma yana so yaje gida Ya fada ma iyayensa abunda Ya aikata sannan Ya sanar da su zai auri Aisha, Duk abunda su ka ce Yazo ya sanar da shi, Jikinshi na 6ari ya mike har tambayar sheikh yai Aisha tana nan cikin gidan? Yace mashi eh, ya sake cewa zai iya ganinta? Imam Yace aa bai amince Yaganta ba, har sai bayan an daura auransu.
Bayan komawar Dr shureim gida ya kira Alhaji ubaid da Hajiya layla a falo Benazir ce kadai ke babu a cikinsu.
Bayan sun nutsu, Dr shureim Ya fayyace masu komai daya faru tsakanin shi da Aisha Sannan Yace Ya yanke shawarar zai aureta..
Tunkan Ya kare maganar Hajiya layla ta fara zazzaga masifa tana fadin wallahi bada yawunta ba, bai isa Ya bata masu suna agari ba, sai dayaga zabe ya kusa zai zo masu da wannan maganar mara dadin ji? Salon yaja masu zagi agurin Jama'a? ta inda take shiga bata nan take shiga ba.
Da farko Alhaji Ubaid yaso Ya fahimci dr shureim Har fada yayi masa akan abunda yayi ma Aisha, sannan yace ya amince masa zaije suyi maganar aurensu da sheikh Imam din, Shureim Yaji dadin maganar Mahaifinsa hajiya layla sai banbamin bala'i takeyi, Ita damuwarta ba akan abun kunyar da shureim yayi ma aisha bane, face Takarar da Alhaji ubaid Ya tsaya ga zabe ya kusa In har abokan adawarsu suka Ji abun nan zasu nemi bata masu sunane, a karshe su rasa kujerar da suke nema.
Bayan kwana daya da afkuwar Lamarin, Alhaji Ubaid Ya canza magana, ya kira shureim Ya fada masa yayi hakuri amma gaskiya bazai bari ya auri Aisha ba, saboda yayi bincike ya gano aisha ba mutuniyar kirki bace, dama can ta saba bin maza, har videos dinta na batsa wanda tayi tare da maza an tura masa awaya, sannan abun da ya faru tsakanin shi da ita ya yarda bayin kanshi bane, laifin Aishar ne itace shaidaniyar dataja Hankalin shi donta biya bukatar kanta.
Hankalin dr shureim ba karamin tashi yayi ba, ya dinga salati Yana karanto duk wata addu'a da zata sanyaya zuciyarshi, ranshi ya 6aci matuka da jin kazafin da mahaifinsa yayi ma Aisha, Yace wlh daddy karyane, wannan maganar ba gaskiya bace, kaji tsoron Allah, kaji tsoron ranar da zaka koma gare shi, Aisha ba fasika bace, mutuniyar kirkice ita, abunda aka fada maka akanta karyane, kai kasan wacece aisha tuntana karamarta kamilar macace mai kamun kai, daddy kada ka biyewa son zuciyarka! Nasan siyasa ce ke nema ta rufe maku ido shiyasa kuke gudun in auri Aisha kuma maganar nan har yanzu ma ba Wanda yasan da ita daga gidansu sai nan, dan Allah kubarni in aureta in rufa mata asiri, Nine fa nayi silar jefasu a halin da suke aciki ita da mahaifinta, meyasa ni ba za ku ga laifina ba sai laifinta ta? Ita da nayiwa fyade"?
hajiya layla Ta balbale shi da masifa tace"ko yaki ko yaso aisha ba mutuniyar kirki bace, abunda mahaifinsa ya fada akanta gaskiya ne, dama ita can bata yarda da ita ba, munafukar kullum tana yawo cikin hijabi kamar ta Allah, ashe maza take bi, gashinan zata bata mata tarbiyar ɗa, don haka ta yanke duk wata alakarsu da sheikh Imam malik, zumuncinsu Ya kare.
Gaba daya suka juya ma Dr shureim baya, duk wannan abun dake faruwa Benazir bata sani ba, Saboda bata agidan ta tafi Abuja gidan Uncle Musa.
Shiekh Imam malik ya yi ta Jiran zuwan Alhaji Ubaid Ko shureim don Yaji daga garesu amma Yaji shiru wai malam yaci shirwa.
Har dai ya yanke shawarar zuwa gidan da kanshi don yaji ya ake ciki.
Bayan ya isa Security Officer din dake tsaron Gidan Ya shiga yayi mashi sallama da Alhaji Ubaid.
Sai ga Jam'in ya dawo yace mashi Ya shiga daga ciki.
A falon gidan Shiekh Imam Ya zauna kan Sofa Yana Jiran fitowarsu, Tsawon mintuna Sai ga Alhaji ubaid da Hajiya layla sun fito daga part dinsu, akan sofa suka zauna suna fuskarshi, tun daga yanayin fuskarsu Ya fahimci babu lafiya, kamar basu taba yin dariya ba, Koma arzikin gaisuwa bai samu ba.
ya yi tsammanin zasu bashi hakuri kan abun kunyar da dansu yayi ma yarsa, amma sai yaga akasin hakan, bayan da ya kora masu jawabin abunda ya kawo shi Alhaji Ubaid Yace Yayi hakuri ya rungumi kaddara, Amma shureim bazai auri Aisha ba, saboda sun yi bincike akanta sun gano ba mutuniyar kirki bace ta saba bin maza.."
bai dire maganar ba Sheikh Imam Ya doka masa tsawa Rai amatukar bace Yace"amma baka da Mutunci Alhaji Ubaid, ka bani mamaki, mutumin banza mutumin wofi, yau da kanka kake yiwa aishana kazafi? Yarinyar data taso agabanka tuntana karama kasanta farin sani, har alfahari kakeyi da ita saboda kyawawan halayanta, ba kamar yarka Benazir ba da kowa yasan bakin halinta data gada awurin jatumarta, Ni ban ta6a aibata yayanka ba saini zaka aibata nawa Ubaid? Akwai dan iskan dayawuce danka daya keta mata haddi? Nayi zaton in masifa ta same ni kaine mutun na farko da zaka fara rufa min asiri ka sharemin hawayena ashe na yaudari kaina!!...."
Dakyar ya ƙare maganar hawaye wasu nabin wasu akan kuncinsa Yaji zafin maganar Alhaji Ubaid.
Hajiya layla ranta Ya 6aci matuka da jin yadda sheikh Imam Ke gaya magana akan ya'yanta, dama ba mutunci gareta ba, tana da sonkai, nata kadai ta sani, ko da take zumunci da su Albarkacin Alhaji ubaid suke Ci.
Nan ta shiga surfa mashi ruwan masifa zagi ta uwa ta uba kamar zata dokesa, saboda rashin kunya, kwata kwata sheikh Imam bai damu da maganganunta ba saboda yasan halinta, Bata da kunya fitsararriya ce, kuma dama ita tabarmar kunya da bori ake naɗeta.
Alhaji Ubaid kasa magana yayi, saboda Zuciyarshi da tayi rauni saboda maganar Sheikh Imam malik ta karya Zuciyar shi, Ya danji tausayin shi amma da ya tonu hudubar da shaidan yayi mashi saiya canza ra'ayin shi.
Ya mike Ya fara gaya ma sheikh Imam magana Yace"ya jira ya ga abunda aka tura masa, zaisan ba kazafi yayi ma Aisha ba" Ya juya ya nufi dakinsa sheikh Imam Yana atsaye jikinshi na kerma zuciyarshi cike fal da tunanin menene Alhaji Ubaid zai nuna masa"?
Bai karashe zancen zucin ba, sai Ga Alhaji Ubaid Ya fito hannun shi ruke da wayarsa Ya miƙa ma Sheikh Imam"gayanan ka gani da idonka"
Yatsun hannunsa na kerma Ya kar6i wayar lokacin daya daura idanunsa akan Screen din wayar saida Zuciyar shi takusa dakatawa da bugawa saboda tsabar firgitar da yayi, a lokacin Jikin shi yadinga tsuma idanunshi suka kada jawur, baisan sa'adda Ya saki wayar Ta fadi kasa Ya juya cikin fitar hayyaci ya fuce daga gidan Yana tafiya kafafuwanshi na hardewa kamar zai kife kasa.
Bayan fitarshi Zainab mai aikinsu Taje ta fada na Dr shureum abunda Iyayensa sukayi na sheikh Imam Malik, Ransa ya 6aci a zuciye yaje ya same su ya dinga yi masu fada kamar zai doke su, Yace basu kyauta ba, meyasa zasuyi ma sheikh Imam haka? Shifa makwabcinsu bayan haka sunyi zama na amana, amma saboda rashin adalci da son zuciya sun rufe ido akan rashin gaskiya suka ci mutuncin shi, babban abunda yafi kona mashi rai abunda suka nuna ma Sheikh Imam ya gani, yaji zafi sosai, amma su ko a jikinsu.
Aisha tana zaune cikin dakinta a kan gado, tana tsaka da shayar da babynta, Baba Imam ya fado dakin Afujajan ko sallama baiyi mata ba, Jikin shi na zubda Gumi Yakai hannu Ya damƙi ƙeyar Aisha da ita da yar duka Ya wurgo su tsakar falo Ta kife kasa Yarinyar ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, Da gudu masu aikin gidan suka fito sakamakon Kukan Aisha da suka jiyo, Aunty Laura dake a cikin dakinta tana tsaka dayin waya tajiyo kukan Aisha dana jinjirarta, batasan sa'adda ta jefar da wayar kasa ta watsa da gudu Ta shigo falon tana haki, Gabantane ya yanke ya fadi ganin Sheikh Imam tsaye yana huci kamar mayunwacin zaki ga Aisha da jinjirarta yashe a kasa suna kuka.
Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Ta faɗa tare da nufar Aisha donta taimaka mata ta mike sai dai kafin Ta karasa Sheikh Imam Ya doka mata tsawa Yace"karki kuskura ki taba ta! Idan ba haka ba, abakin aurenki" cak ta tsaya jikinta na kerma.
"Allah Ya isa tsakanina dake Aisha, Allah Tsine maki Albarka, In sha Allah sai kinga sakayyar abunda kikai min" waro idanu waje Aunty laura tayi, Hankalinta amatukar tashe, gashi ba halin tayi magana balle ta dakatar da shi, maids din suka daura hannayensu asaman kansu cike da tashin hankalin jin furucin sheikh Imam ga yarsa, ba su taba zaton zai yi mata haka ba, su din amintattunsu ne, koda asiri Ya tonu agidan suka gane Aisha tana da ciki basu ta6a nuna sun sani ba saboda basa son abunda zai zubar da martabar sheikh Imam da ita Aisha.
"Kin cutar da rayuwata kin yaudareni Aisha, Idan aure Kikeso Meyasa ba zaki fada min ba inyi maki!? Sai kika zabi ki zubarmin da mutunci na, inayi maki kallon mutuniyar kirki ashe ke din fasika ce, mara tsoron Allah, Dama tun farko banso Kika je Germany karatu ba saboda hankalina bai kwanta ba, ashe bayan da kika je karuwanci ki ke yi acan, naga komai Aisha an nuna min videos dinki da hotunanki tare da kato, Yau silarki An zageni anci mutuncina Aisha wlh nayi danasanin haihuwarki da akayi"❗
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥✍️*
*Game bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹
~___________________________________~
A bakin door room dinta suka tsaya, fuskokinsu ɗauke da damuwa.
"Aisha meyasa baki tuntube ni ba a lokacin da abun ya faru? saboda laifin ya shureim ya shafe ni? mun yi zaton kina a Sudan ashe kina a gida, da ace kin sanar dani ke kinsani ni me iya tsaya maki ce, wlh zan tayaki faɗa ne don ganin na kwatar maki hakkin ki, amma bansan komai ba, sai dai na ji labari bayan na dawo gida, abun da yafi ƙona min rai tafiyar da ki ka yi batare da kin neme ni ba, kuma baki yi tunanin kije gidan su Anila ba......"
daƙyar Benazir ta ƙare maganar tana jan numfashi saboda Zuciyarta dake tafarfasa.
Idanunta na akan door room din Aisha, suna jiyo shesshekar kukan ta daga cikin dakin.
"Lokacin da naji abun da ya faru tsakanin ki da ya shureim da kuma kazafin da akayi maki, Har jinya nayi gadon asibiti saboda baƙin cikin da na ji, wallahi Allah shine shaida ta, nayi bakin cikin da bazai misaltu ba, Na ji zafin hukuncin da baba Imam ya yanke maki cikin fushi batare da ya yi bincike ba, mu shaida ne akan ki Aisha sannan mu shaida ne akan Yaya Shureim abun da ya faru a tsakanin ku sharrin shaidan"
Aneelerh ta ɗaura da cewa,"Ni kaina sai dai naga sakon ki, har kiran ki na yi ba ki yi picking ba, har messages na tura maki akan ki faɗa min ina kike ko ki zo gidanmu amma babu amsa, Aisha meyasa ki ka zabi ki tafi ki bar mu? Bayan kinsan irin kaunar da muke yi maki, ko bayan tafiyarki bamu manta dake ba, a Kullum muna cikin damuwar rashin ki, tunanin mu ina kike? Kina raye ko kin mutu? Meke faruwa a cikin rayuwar ki.... "
Aneelerh bata ƙarasa maganarta ba, Dr Shureim ya katse ta, cikin sanyayyar muryarsa mai tattare da rauni ya ce,"Pls Aisha, mu manta da abunda ya wuce, ki yafe mini, Ki yi hakuri Aisha, dan Allah ki fito mu yi magana, gaba ɗaya ɗokin ganinki mu ke yi"
Babu alamun zata tanka masu.
"Pls Ku dawo ku zauna mana, indai Ummi ce tana a gidan nan, duk da bansan meya faru a tsakaninku ba amma na tausaya maku, in har kuka bamu hadin kai in sha Allah zamu yi kokarin sasanta ku da ita"
Taj ne ya yi maganar daga inda yake a zaune, Jikin su asanyaye suka baro kofar dakin Ummi ba don sun so ba, suka koma falo kowannan su ya zauna kan Sofa, kwata kwata babu walwala akan fuskokinsu, Idanunsu sun kaɗa jawur saboda kukan da suka sha, babu mai magana a cikinsu kowa da abunda yake saƙawa a cikin Zuciyar shi.
Taj dake fuskantarsu, A tsanake ya ke nazarin yanayin su sam ya kasa dauke ido daga kallon su.
"Pls ina son insan meye alaƙarku da Aisha ne? A nan take zaune?"
Murmushi Taj ya ɗan yi tare da kallon Dr Shureim da ya yi maganar.
A tsanake Taj ya zayyana masu alakar dake a tsakanin su da Aisha, tun daga kan aikin da U.s armies suka saka ta, ya ƙara da cewa,"Tamkar uwa take a gurinsu, tana kula da su sosai..."
Ajiyar zuciya suka sauke gaba daya hankalin su ya kwanta da jin a nan take da zama don basu son su kara rabuwa da ita.
A bangaren Ummi bayan data shige daki ta yi locking door din, tana kuka ta fada kan gadon ta, Batool dake a cikin toilet tana jiyo shesshekar kukanta ta fito hankalinta atashe ta haye kan gadon tana tattaba bayanta, "Aunty Ummina! Meke damunki? Meyasa ki ke kuka? Waya 6ata maki rai!"
Kwata kwata Ummi bata saurare ta ba, hakan yasa ta fashe da kuka itama tana fadin, "Dan Allah aunty Ummi ki daina kuka, bana so! Ki faɗa min meke damun ki?"
dakyar ta iya furta,"Bana jin dadin Zuciyata, zafi take yi mini! Babe na rasa Fatima na, I've lost my Batool ta mutu, na yi babban rashi! Baki ji radadin da nake ji ba..."
sambatu ta dinga yi mata, Batool data gama ruɗewa ta kasa gane inda maganganun ta suka dosa.
"Aunty Ummi, ban mutu ba, Ina a raye, ba ga ni a kusa dake ba?" ta faɗi hakanne saboda ta yi zaton ita Batool din take nufi.
Tana kokarin tallabo fuskar Ummi da tafukanta don ta miƙar da ita zaune saboda karfin hali irin nata..
Ba ta yi aune ba, Ummi ta janyota kan chest ɗinta ta rungumeta sosai, duk don ta samu relief na radadin da take ji, damuwace ta mamaye zuciyar Batool lokacin da fatar jikinta ta haɗu data Aunty Umminsu, saboda zafin da jikinta ya ɗauka har a jikinta tana jin shi.
Ruɗewa ta yi cike da tashin hankali take fadin,"Baki da lafiya Aunty Ummi, you're burning up, in wani abu ke damunki ki fada min zan taimaka maki har ki samu sauki.. "
ta faɗa tana ƙoƙarin ƙwace kanta daga rukon da Ummi ta yi mata don ta samu damar zuwa ta faɗa ma daddy Taj da Unaisah halin da take aciki sai dai sam Ummi taƙi bari ta motsa.
Tunawa tayi da addu'a, cikin sauri ta fara karanta yan addu'o'in da ta iya a cikin zuciyarta ta tottafa mata saman wuyanta.
Kafin Ta ɗaura hannayenta biyu akan bayanta cikin sigar lallashi ta ke ɗan bubbuga bayanta kamar ta samu karamar yarinya.
Ji ta yi inama ace Batool ce ɗiyarta, Murnar da za ta yi ba zata misaltu ba, tana son Batool sai dai ita bata fito daga mahaifarta ba, tasan duk mun daran daɗewa, wata rana Batool zata ga iyayenta ne.
Cusa yatsun hannayen ta ta yi acikin sumar kan Batool, yayin da zuciyarta ke tariyo mata fuskar babynta, bazata taba mantawa da suffarta ba, tana ji aranta tabbas da ace tana a raye kuma ta girma, ba abun da zai hana su yi kama da Batool saboda kamanninta da Dr Shureim, ta dade tana ganin kamanceceniyar su sai yau ta ƙara tabbatar da hasashen ta.
"Aunty Ummi da sauki?"
Cikin disasshiyar murya ta furta,"Ki cigaba da yi min addu'a, Allah yaye min abunda ke damuna" Da sauri ta amsa mata da toh .
Time da aka fara kiran sallar la'asar, Taj yace ma su Anila su shiga daki su yi sallah, bayan ya nuna masu ɗaya daga cikin bedroom dinsu Sajeed suka tashi suka shiga, Dr Shureim ya ce ya tashi su tafi masallaci, sam ya ma manta da ƙafarsa dake ciwo har ya yunkura zai mike kafar ta fara yi masa zogi ba arziƙi ya koma yana nishi, anan Dr shureim ya fahimci baida lafiyar ƙafa har ya tambayi meke damunshi ne? ya ce mashi ya samu rauni ne a cinyar sa ta dama amma da sauƙi, cikin nuna tausayawa Dr shureim ya yi masa sannu da jiki, har ya ce in bazai iya zuwa masallacin ba ya yi zaman shi tun da lalurace, Taj yace ma shi kar ya damu, zai iya zuwa ai yana da wheelchair, ya faɗa tare da kai hannu Ya janyo kan kujerar sa da ya 6oye tsakankanin Sofas, ya janyota ta dawo ta gaban shi, ya yi ta ƙoƙarin miƙewa yana kasawa har saida Dr. Shureim Ya taimaka mashi ya zauna a akanta, tukunna suka tafi.
__________________________________✍️
Tana a kwance tsakiyar gadonsu, ta ƙurawa ceilling idanunta da suka kaɗa jawur, hawayen da suka cika idanunta a hankali suke gangarowa kan kuncinta, bakomai take tariyowa ba face fuskar Benazir, wai dama itace mahaifiyarta da ta yi watsi da ita? Tana yi mata kallon mutuniyar kirki ashe ba haka bane ta yaudari kanta, abin da yafi ƙona mata rai, jinyar ta da ta yi, ta bata abinci a baki, ta yi hugging dinta har ma ta sumbace ta saboda kaunar da ta ke yi mata bisa rashin sanin wacece ita, but now that she knew the truth, she hated her more than anything in the world, abun da yafi tsaya mata a rai meyasa ta gudu tabarta bayan ta jefar da ita cikin kwamin wanka? In bata sonta meyasa bata kashe ta ba tun lokacin da ta haife ta, Laifin me ta yi mata da yaja har ta tsane ta?
Tabbas tana son ta tunkareta gaba da gaba don taji amsar tambayoyin ta.. ranta yakai maƙura a gurin 6aci, sai faman yin juyi ta ke yi akan gadon kamar mai fama da ciwon mara.
_______________________________🌹✍️
Around ƙarfe biyar na marece, motar Chief ta kunno kai cikin main gate, bayan driver dinsa ya tsayar da motar a parking space cikin hanzari ɗaya daga cikin security Officers din da ke sintiri yai hanzarin zuwa gaban car door ya bude masa motar, fitowa ya yi daga ciki jikinshi sanye da Suit.
With respect Security Officers din suka sara mashi, har zai juya muryar driver dinsa ya katse shi
"Sir, should I bring in the suitcases?" He nodded, then turned away, ya nufi falo.
Cikin sauri SA ɗin ya buɗe tanƙameman boot din motar Chief, ya soma fiddo wasu hadaddun akwatina, guda biyu bayan ya gama ya rufe boot din, ya ruƙo handles dinsu ya bi bayan Chief da su.
Chief bai taras da kowa a falon ba, Kaitsaye Ya nufi Upstairs saboda a gajiye ya dawo he needs some rest, duk da yafi bukatar ya gana da su.
Bayan shigar shi dakin, SA din Ya shigo mashi da akwatinnan ya ajiye su kafin ya fuce.
Shaf shaf ya rage kayan jikin shi Ya shiga bathroom don ya yi wanka.
Bayan wani Lokaci ya fito daga part dinsa ya dauki wankan blue sky voile, sai kamshi ke tashi a jikin shi, walking magestically ya nufo down.
tun kafin ya ƙaraso takun tafiyarsa yaja hankulansu ga duban shi, a lokacin sun dawo falo suna jiran shi.
A hanzarce suka mimmiƙe tsaye, kaitsaye ya nufi Dr Shureim, side hug ya yi masa tare da ruko hannunsa sukayi musabaha, Dr shurem ya ɗan yi mamakin saukin kan Chief yadda ya tarbe shi kamar sun saba da juna.
With respect Aneelerh da Benazir suka gaishe da shi tare da yi mashi sannu da dawowa, fuskarsa da fara'a ya amsa masu.
Gaba ɗaya Ya lura da yanayin fuskokin su kamar ba walwala akai.
Sarah mashi Taj ya yi daga zaunen da ya ke bai motsa ba ya yi mashi sannu da dawowa, mayar masa da martanin sarawar ya yi kafin ya amsa gaisuwar da ya yi masa tare da miƙa masa hannu suka gaisa da juna.
Daga bisani ya zauna gefen Taj, ya kasance suna fuskantar su Dr shureim..
"A yi mini afwa, na barku kunata jirana." Ɗan murmushi suka yi gaba dayansu.
Dr shureim ya ce, "bakomai wlh, Allah yasa dai bamu katse maka aiki ba"
Fuskarshi a sake ya ɗan jinjina kan shi,
Tunkafin ya tambayi wani abu Taj ya yi hanzarin daukar wayar Ana dake ajiye gefensa ya kunna masa videon tare da miƙa masa ya sa hannu ya kar6a tare da daura idanunsa akan Screen din wayar ya nutsu yana kallon videon, bayan ya gama kallo shiru ya yi yana ɗan jinjina kan shi.
Lamarin ya ɗaure mashi kai tamau, kuma tunanin su ya zo ɗaya dana Taj.
Gyaran murya ya yi masu a hankali suka mayar da dubansu gare shi.
Tambayoyi ya fara yi ma Anila dangane da Ana da kuma Uncle din ta, bata boye masa komai ba duk abunda ya tambaya sai ta bashi amsa.
Bayan Ya kammala yi mata tambayoyin, Taj ya ce, "Benazir, ki yi masa bayanin abun da ke damun ki" cikin sanyin murya ta amsa mashi da toh,
A tsanake ta kwashe komai da ya faru da ita a gidan Uncle musa ta sanar da Chief, ta ƙara da cewa, "Ban sanar ma kowa ba, Yaya Shureim ne kaɗai ya sani, bayan haka yanzu an ɗaga ƙafa da kawo min harin."
Yanayin fuskar Chief ya nuna tsantsar ruɗani da al'ajabi, kallon Dr Shureim ya yi wanda gaba daya hankalin sa baya akan su, duba da yadda ya sadda kan shi ƙasa.
"Za ki iya suffanta mini mutumin da ya kawo maki hari a cikin toilet?"
Ta amsa da eh, kafin ta fara siffanta mashi mutumin.
Kallon kallo suka jefawa juna tsakanin shi da Taj, lamarin ya daure masu kai, saboda gaba ɗaya yadda Benazir ta suffanta mutumin, baida bambanci da giant ɗin kurkukun Ƙaddara, amma abun tambayar anan meyasa ake son kashe ta? Zurfin tunani Chief ya shiga har na tsawon yan mintuna, kafin ya ɗago ya dubi Benazir suka haɗa ido cikin na juna.
"A lokacin baya, kafin ƙaddara ta rabaki da gidan mijin ki, babu wanda ki ka ta6a yi ma laifi kuka samu sa6ani a tsakanin ku har ta kai ya ci wani alwashi a kan ki?"
Girgiza kai ta yi,"Gaskiya ni ba wanda wani abu ya taba haɗa ni da shi..."
Bata ƙare maganar ba, ganin irin kallon da Taj ya yi mata, nan take ta fahimci me yake nufi wato yasan halinta ciki da bai.
Gyaran murya ta dan yi, "A lokacin baya nasan bana jin magana, idan nace ban taba samun sabani da wani ba to na yi ƙarya, amma bana tunanin na yi laifin da har za'ayi yunƙurin kashe ni"
"Bakya tunanin wanda ya yi maki kurciya shine yake nema ya kashe ki saboda ya ga kin dawo a raye, may be akwai wani abu da ya haɗa ku ko sanin sirrin wani wanda baya son asirin shi ya tonu ta silar bayyanar ki shiyasa yake nema ya halaka ki..."
Maganar Chief tasa ta jin faduwar gaba, zurfin tunani ta shiga yayin da ƙwaƙwalwarta ke kokarin tariyo mata abubuwan da suka faru a lokacin baya kafin ta gudu daga gidanta, sai dai ta kasa tuna komai kamar an wanke mata brain dinta.
"Ki yi kokari ki tuna Benazir, ba ƙaramin taimako zaiyi mana ba"
Taj ne ya yi mata maganar cikin kwantar da murya, har kallon shi saida tayi kamar wani abu bai shiga tsakaninsu ba, Chief yana lura da duk wani motsin su haɗi da karantar yanayinsu ta fuskarsu.
Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Aneelerh dake yi mata magana cikin raɗa, "Please ki tuna Benazir, ni nasan baza a rasa wadanda kuka taba samun sabani da su ba, ko ya ya ne ki yi tunani pls"
Wani abu da Chief ya lura da shi shine satar kallon Dr shureim da take yi, hakan yasa shi zargin akwai abun da ta sani, kuma tana so ta fada sai dai bata son Dr Shureim ya ji shiyasa take satar kallon shi a fakaice.
Fahimtar hakan yasa shi cewa, "Kada ki damu, zan baki lokaci, bayan kin koma gida kiyi kokari ki tuna in ya so sai ki kira Taj a waya ki sanar da shi"
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da ɗin murmushi ta ce, "In sha Allah idan na tuna zan kira in sanar da ku"
Shiru suka dan yi na wani lokaci.
"Meke damun shi ne?" Chief ne ya fada idanunsa akan fuskar Dr Shureim ƴan hawayen da suka cika idanun shi sai kokarin sauka kan kuncinsa suke yi.
Taj ya ce, "Yawwa Sir, namanta ban fada maka ba...." A hankali Chief ya mayar da hankalinsa akan Taj, komai da ya faru bayan fitowar Ummi Ya sanar da shi, jinjina kai ya yi tare da kallon su Anila, "Zan iya sanin menene alaƙar ku da ita?"?
Har suna haɗa baki gurin furta eh saboda suna son ya taimaka masu tunda agidanshi take da zama.
"Yaya Shureim," Benazir ce ta kira sunan shi, cike da damuwa ya ɗago ya kalle ta, a kunne ta yi masa raɗa, "Suna son sanin menene alakar mu da Aisha, zan iya faɗa masu komai da ya faru? tun da ka ga agurinsu take da zama may be idan su ka ji su taimaka mana"
Ya ɗan ji nauyin maganar, amma a halin yanzu baida za6i,
Cikin sanyin murya ya ce, "Idan kina ganin zasu sama mana mafita, ki fada masu komai,"
Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta maida dubanta akan Taj da Chief.
Nan ta fara basu labarin rayuwarsu, da alakar su da Aisha, da kaddarar data raba su da juna, bata 6oye masu komai ba, da yake ta iya bada labari ko mistake bata yi.
Lokacin data ƙarasa basu labarin idanunta cike tab da ƙwalla, yayin da su kuma tsantsar mamaki da al'jabine ya kamasu, A sanin su da Ummi tantiriyar Karuwace da ta yi ƙaurin suna a America, ashe kaddara ce ta canza mata rayuwa, sun ji tausayinta sosai, har ta kai ga sun yi shiru jimm suna ɗan jinjina heads din su, shi dama Taj ya daɗe yana yi mata kallon sani, sai yanzu da Benazir ta bada labarinsu, Ya tabbatar ma kansa Bintu Imam ce.
"Dan Allah ku taimaka mana, kada ku bari Aisha ta koma America, ku ruke mana ita har sai mun sansanta tsakaninta da mahaifinta da kuma mu, muna so ta koma kamar yadda take a da, sauyin da muka gani atare da ita ya tada mana hankali, wlh kallo ɗaya da nayi mata na fahimci ta canza rayuwarta"
Chief ne ya ce,"Na yi maku alkawari In sha Allah, Aisha ba zata koma America ba, zan cigaba da ruke ta anan har sai na cika maku burukan ku, saboda nima na damu da ita na tausayama rayuwarta sosai, na ji zafin abun da ya yi silar rabata da mahaifinta da kuma halin da ta jefa rayuwarta, wanda nayi imanin tsinuwar da mahaifinta ya yi mata ce ke bibiyarta, bayan haka Dr Shureim..."
Ya amsa mashi da na'am idanunsu acikin na juna.
"Kaima na tausaya maka sosai, labarinku ya ta6a zuciyata, kun bani tausayi, please ka cigaba da hakurin da ka saba yi, in sha Allah ni Chief na yi maka alƙawarin Ummi won't leave this house until everything is settled"
Maganar Chief ta kwantar masa da hankalinsa, wani dadine ya ji ya lullu6e zuciyar shi, Anila Da Benazir basu san sa'adda suka saki murmushin jin dadi ba, har suna hada baki gurin yi mashi godiya.
"Ina fata mun gama magana, ko akwai sauran wani abu?" Cikin kulawa Chief Ya faɗa yana duban su,
"Unaisah, ta ƙi kula ni...." gaba daya ta fada mashi abunda ya faru tsakaninta da Unaisah, har cikin ranshi bai ji dadi ba, amma ya fahimci Unaisah, baiga laifinta ba, dole ne dama ta ƙi accepting din ta saboda ta ƙullace ta aranta.
"Kada Ki damu, Ni zan yi mata bayanin da zata fahimta, In sha Allah"
Ita dai Anila tunaninta ya fara komawa gida fargabanta kada Junaid ya saki baki ya furta dodon da ya kashe Anah a gaban Uncle.
"Akwai gargadin da nake so na yi maku gaba dayanku, daga rana irin ta yau inaso ku dauki kanku a matsayin jami'an sirri, kada ku kuskura ku faɗa ma wani damuwarku, sannan kada ku bari yanayin ku ya nuna! Duk wani abu da muka tattauna anan to mu binne shi anan!" Ya faɗa yana nuna floor da index finger ɗinsa.
"Sirrinku a cikin zuciyarku, In zai yiwu ma, ku daina tunanin abun cos kuskure kaɗan zai iya jefa rayuwar ku cikin hadari. Tun da har kun fada mana komai, from now on Case din yabar hannun ku, yanzu yana a hannunmu, kuma in sha Allah zamu cigaba da yin bincike akai"
Gaba ɗaya sun yi amanna da maganar shi, kuma sun daukar mashi alƙawari zasu kiyaye.
"Yakamata mu tafi, na ga an kusa fara kiran Magrib" Aneelerh ce ta faɗa tana duba wrist watch din hannunta.
Taj ya ce, "Zamu ruƙe wayar Ana a hannun mu, har zuwa time da zamu kammala bincike. Mungode sosai, Allah ya maida ku gida Lafiya"
Atare suka hada baki gurin furta Ameen muna godiya muma da aka kar6e mu hannu bibbiyu tare da fatan nasara.
Dakyar Dr shureim ya mike fuskarsa sam ba walwala, ya so ace zai iya ganin Aisha kafin su tafi.
Daƙyar ya iya furta,"Please zan iya samun phone number din Aisha?"
Taj ya ce, "Mi zai hana." ya ɗauko wayarsa ya lalubo layin Ummi ya mika masa, yatsun hannunsa har kerma suke saboda zumudin ya kar6a, shaf shaf yayi copying dinta bayan ya gama ya mika ma Taj tare da yi mashi godiya.
Benazir dake kallon shi ta kasa gane me ya hana shi mikewa? A ganinta ko rakiya ne yakamata ya yi masu.
"Muje nayi maku rakiya" Chief ne ya fada tare da mikewa, ya ruko hannun Dr shureim a cikin nashi suka yi gaba, Aneelerh da Benazir suna a biye da bayan su.
Bin su da kallo ya yi har saida suka 6ace ma ganinsa, lumshe idanun shi yayi a hankali yake tariyo komai da ya faru tun farkon zuwan su Benazir.
Unexpectedly ya ji an sumbaci forehead dinsa, a firgice ya buɗe idanun shi, har saida gaban shi ya fadi da ya yi tozali da Benazir ta sunkuyo da kanta saitin fuskarshi, nan da nan ya haɗe rai,
"Baki tafi ba?"
"Taya zan tafi kana fushi dani" Ɗaure mata fuska ya yi.
"Pls abunda ya faru ɗazu ka yafe mini, raina ne ya 6aci," Ta fada tana kashe mashi murya.
"Na ji, ya wuce."
"Yaushe zaka maida ni ne? Na gaji da jira." Wani kallo ya yi mata mai kama da harara ya ce, "Toh rasa kunya 6eran tanka, ke baki ji kunyar furta in maida ki ba? Hauka nake da zan dauki macen da take ruƙe kwalar rigana kamar zata doke ni!"
Ya fada babu wasa akan fuskarsa.
Marairaice fuska ta yi kamar zata fashe da kuka ta ce, "Pls ay na baka hakuri, wlh na gane kuskure na, don Allah ka daina wahalar da ni mana, nafa san kana sona har yanzu." ta faɗa tana yi mashi farfari da idanunta.
Hakan da tayi ba ƙaramin sace zuciyar shi ta yi ba.
"Ka yi shiru bakace komai ba," Ta fada da yar shagwa6arta.
Ɗagowa ya yi suka hada ido cikin na juna wani kallon so da kauna suke jefawa junan su, bakomai take tuna mashi ba face Unaisah.
"Wallahi wannan karon idan ka mayar dani, zan yi maka biyayya sau da ƙafa, zan tarairayeka kamar jinjiri, yanzu fa na canza ba Benazir din da ka sani ada bace, ka ga yanzu na iya girki, na iya gyara gado, na iya wanki, wlh har wanka zan dinga yi maka...."
Duk yadda ya kai ga hana kanshi sakar mata fuska baisan sa'adda ya tuntsire da dariya ba, saboda kalamanta sun bashi dariya, kuma dagaske take fada masa babu wasa akan fuskarta.
"Oh, kina nufin yanzu kin gane an halicci hannayenki don ki girka ma ƙato abinci?" Ya fada tare da ɗage mata gira, dariya ta saki har dimples dinta ya lotsa.
"Bama iya girki ba, komai zanyi masa." Tabe bakinsa ya dan yi.
"Yakamata ki tafi suna jiranki." Ɗan bubbuga kafafunta ta yi kan floor, "Taya zan tafi baka bani amsa na ba?"
"Zamu yi magana a waya" Ba don ta so ba tace, "ka yi mini alƙawari?" Jinjina mata kai ya yi.
"Okay, ka rama min kiss da na yi maka." Zare idon shi ya ɗan yi bata jira amsar shi ba ta manna mashi peck ta juya tana dariya ta nufi Kofa, bin bayanta ya yi da kallo har ta bace ma ganin shi.
________________________________________✍️
Around ƙarfe tara na dare, Benazir ta fito daga bedroom dinsu, hannunta a ruƙe da wayarta, har ta sanya kayan bacci a jikin ta, sai dai baccin ya ƙauracewa idanunta, a hankali take tafiya yayin da zuciyarta ke ta azalzalarta akan ta kira Taj ta faɗa masa abunda ta kasa sanar da su ɗazu, sai dai tana matuƙar jin shakkar ta fitar da sirrin gani take kamar zai koma masa ne, amma in ta tuna halin da Aisha ta shiga, da irin uƙubar da Dr Shureim Ya sha akan yarinyar sai kawai ta ji ƙwara ta fada kawai ko da hakan zai yi silar rasa rayuwarta ne, ta ma san ko bata fada ba, hakan bazai hana a cigaba da yunƙurin kashe ta ba.
Tana Ƙoƙarin juyawa ta koma ɗaki ta ji motsin shigowar mutun Falon, da sauri ta kai idanunta ga duban shi, Alhaji Musa ne ya shigo cikin takun nan nasa na izza yake tafiya fuskarsa ba annuri, ya zuba hannayensa cikin aljihun wandon shaddar Jikin shi, hakanan ta tsinci kanta da jin faduwar gaba, cikin sauri ta juya da sauri ta faɗa bedroom din ta, kamar munafuka ta dinga leƙen shi, waro ido ta yi ganin ya dan dakata da yin tafiyar, alamun ya ji ajikin shi ana kallon shi, jikinta na kerma ta datse kofar ɗakin.
A hankali yake bin ko'ina da kallo, ganin ba abunda ya yi zata bane yasa shi gyaɗa kai ya cigaba da tafiya Ya nufi part dinsa.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da hadiyar yawu, tunani ta soma yi a ina yakamata tayi wayar cos bata so wani ya ji koda kalma ɗaya da zata furta ne.
Ɗaura idanunta ta yi akan Zeenatu da ke a kwance kan bedmatress tayi nisa acikin baccin ta, Cikin tafiyar sanɗa ta nufi gadon ta janyo duvet ta lullu6e mata jikinta gaba daya.
har ta nufi toilet zata shiga sai kuma ta fasa, tunawa da babu kyau yin magana acikin toilet.
Gaba daya kanta ya ɗaure, tsoro take ji, ga shi abun ya dameta so take kawai ta fallasa sirrin da ta daɗe da shi a cikin zuciyarta, ba zata iya jira gobe ta yi ba.
Akan Mirror Chair ta zauna, ta fara danna wayar ta kira layin Taj ta kurawa screen din wayar idanunta tana jiran ya yi picking.
Lokacin da kiran ya shigo layin Taj, yana a kwance kan gadonsa har ya fara bacci kiran ya katse shi.
Kasantuwar ya aje wayar a kusa da kunnansa, ransa a ɗan 6aci ya janyo wayar ko da ganin kiran Benazir cikin sauri ya daidaita nutsuwar shi.
Bayan yayi picking ya kara wayar a kunnansa.
Ko sallama bata yi mashi ba ta ce, "shine ko ka kira ka tambayi mun isa lafiya ko?"
Cikin disasshiyar muryarshi ta wanda bacci bai ishe shi ba yace, "I'm sorry Ummu Unaisah, wlh kuna araina, tun dazu nake ta zucci zuccin in kira ku.."
Da shagwa6a ta ce, "Hankalinka kwance ma bacci kake yi, Ni gani nan damuwar rashin ka a kusa dani ta hanani runtsawa sai faman tunanin ka nake yi" Har cikin ranshi ya ji dadin kalamanta, murmushi ya yi, "Waya fada maki ni ban damu dake ba? Nima kin tafi kin barni da tunanin ki, da zarar na rufe idanuna ke nake gani,"
Sautin dariyarta ne ya cika kunnan shi.
( Allah sarki tsohuwar Zuma😂 har wani ƙara kankame pillow yake yi a kirjin shi, da alama Benazir tayi winning heart din Taj.)
"Ina babynmu?"
"Tana a bedroom din su, may be ta yi bacci"
"Okay," shiru su ka dan yi jimm har saida ya furta, "Akwai wani abu da kike son fada mini ne?"
Cikin sauri ta ce, "Eh dama dazu akwai tambayar da ku ka yi mini ban samu na amsa maku ba, saboda Yaya Shureim yana a wurin bana so yaji..."
Cike da zumudi Taj ya ce,"Okay, Ina sauraron ki Ummu Unaisah"
Calmly Ta soma ba shi labari.
"Kafin dawowar mu Jos, A lokacin ina a gidan Uncle Musa, ban kai ga sanin komai da ya faru tsakanin Yaya Shureim da Aisha ba, na ta6a kama Uncle yana yin wata waya ta sirri, wuraren karfe ɗaya na dare ban runtsa ba, dama dabi'atace idan ina yin Chatting bana yin bacci da wuri, to adaren ranar na fito daga ɗakina dake a cikin gidan sa, hannuna ruke da wayata ina tafiya ina yin chat da niyyar daukko ruwa, gaba daya na shagala har na sauko down batare dana ankara ba, Na shiga zagaye falon gidan kafin na nufi walkway din da zai sadani da backyard din gidan na tsaya, kwatsam kunnuwana suka soma jiyo mun muryar mutum yanayin waya ƙasa kasa kamar baya son wani ya ji shi, a firgice na kalli saitin inda nake jin maganar sa a hankali cikin sanda na karsa bakin kopar da zata 6ula da kai bayan gidan, a zaune na hango shi kan ɗaya daga cikin kujerun shaƙatawar dake a wurin, a lokacin na dan ji tsoro saboda ban tsammaci zanga mutun a irin wannan lokacin ba, amma sai na dake saboda ina son in san wanene kuma ina son jin wayar mecece ya ke yi a tsakar dare! Ni abunda yafi daure mun kai duk rooms din dake acikin gidan da falo ya rasa inda zaiyi waya sai a backyard, hakan yasa na dasa masa alamar tambaya, aikuwa cikin sanɗa na matsa gaban tukwanan furannin da ke a bayanshi na zukunna tare da kasa kunnena ina sauraron shi.
"Kada ku bari ta yi 30 Mins a cikin ramin, zamu iya rasata ne, ku kasance a ankare, da zarar kun ga jami'an sun tafi da shi, kuyi hanzarin haƙa ramin ku ɗauko Jinjirar, Sannan bayan kun cire ta daga ciki, Ku kashe daya daga cikin karnukan ku, Ku je ku zuba ƙasusuwan shi a cikin ramin"
Lokacin da naji wannan maganar wani irin faduwar gaba na ji duk da ban fahimci inda zancen nashi ya dosa ba, gaba daya nabi na rude amma a haka na toshe bakina na cigaba da sauraron shi saboda ina son inji karashen zancen na shi.
"Bana so a samu matsala, dole sai kun yi taka tsantsan! ka da ku yi gangancin da wani zai gan ku, idan ba haka ba kun sauran sauran,"
Ya faɗa tare da yin rejecting call din ganin ya miƙe yasa na yi saurin zuƙunnawa ƙasa da rarrafe na dinga tafiya cikin sanɗa sai da na ga nayi nisa da backyard din, tukunna na mike da sauri na koma dakina na ja kofa na datse.
Aranar na kwana da tunanin wacece naji Uncle Musa yana bada umarnin a haƙa ramin da take a ciki a curo ta? Kuma yace a kashe kare a zuba ƙasusuwan shi a cikin ramin? Menene manufarsa ta yin hakan?"
A lokacin gaba daya na ruɗe, na kasa gane komai, dakyar bacci 6arawo ya yi awon gaba da ni, tun daga ranar ban kara samun kwanciyar hankali ba, saboda tunanin wayar dana kama Uncle musa yanayi atsakar dare, zuciyata ta dinga azalzalata akan in tunkare shi in tambaye shi game da wayar da na ji yanayi, sai dai tsoro da fargaba sun hanani yin hakan, bayan haka bansawa raina wani mugun abun ya ke yi ba saboda na yarda da Uncle Musa, daga baya ma sai na watsar da zancen na cigaba da yin harkokin gabana.
Taj da ya kasa kunne yana sauraronta, tuni ya mike zaune saboda mamakin daya daure zuciyar shi.
Benazir ta ɗaura da cewa, "Lokacin da na kudiri Aniyar saina gano koma wanene ya shiga tsakanin Ya shurem da Aisha, da kuma munafukin da ya ƙulla mata makirci a ƙasar Germany, Lokacin da na saci hanya na shiga dakin Aunty Zainab na tambaye ta meya faru a tsakanin Dr Shureim da iyayen mu saboda ina zargin bakomai suka faɗa mana ba, bayan zainab ta fayyace mini komai, Hankalina atashe na koma ɗaki na, inata wasi wasi akan wayar nan dana ta6a kama Uncle Musa yana yi a bayan gidan sa, sai da na zurfafa tunanina nayi dogon nazari kafin na gano wayar nan fa da Uncle musa yake yi akan babyn Ya Shureim ce.
Amma abun da ya ɗaure min kai shine Meyasa Uncle Musa zai yi haka? A raina na ayyana ko dai yana son ya yi mashi hankaline saboda rashin hankalin da ya yi na binne ƴarsa, amma kuma dana kara yin tunani sai na gano wannan fa yafi karfin abunda nake hasashe, ganin an dauki kwanaki Uncle Musa baida niyar fallasa shi ya dauki yarinyar, bayan da kunnanshi ya ji irin bakar wahalar da Ya Shureim yasha bayan ya binneta kuma ya yi danasani, to amma meyasa da farko Uncle Musa ya nuna baisan komai ba?
Bayan mun yi waya da Ya Shureim har ya fada mini yasha jaraba kiran layin wayar Uncle don ya nemi taimakon sa, amma baya samun shi, tun daga nan ne na fara zargin da akwai wata mummunar manufa atare da shi.
Ban tunkare shi da maganar ba, saboda a lokacin ka zo mini da maganar zaka turo magabatan ka ayi maganar auren mu, shiyasa na watsar da maganar na bar komai araina. Bayan mun yi aure da kai, A lokacin Daddyna har ya samu nasarar lashe zabe ya zama gwamnan jihar wanda tun da ya hau mulkin bai ƙara lafiya ba, saboda ciwon ƙafa da ya matsa mashi, ba irin maganin da ba'ayi mashi ba amma ciwon yaki ci yaƙi cinye wa. Wani iko na Allah da zarar an fita da shi kasar waje don a nema masa lafiya sai ciwon nashi ya warke, amma da zarar an dawo da shi Nigeria ciwon na shi yake komawa sabo, a karshe da yan jam"iyarsu suka fahimci ciwon nashi bame ƙarewa bane, sai suka shawarce shi da ya aje mulkin yaje ya nemi lafiyarsa, Shekara daya yayi kafin ya sauka, zaman Jahar ya gagare shi silar hakan iyayenmu suka koma Dubai da zama, Ni kuma saboda auren da na yi ne yasa suka barni a Jos.
A lokacin Uncle Musa ya zama Shahararran dan siyasa, ganin sa yayi mini wuya saboda bai cika zuwa Jos ba tun da iyayen mu suka koma Dubai, ya ɗaga ƙafa da zuwa Jos daga Abuja sai ƙasashen waje, Kuma duk in na kira phone numbers dinsa bana samu.
A ƙarshe na yanke shawarar tura mashi text message, na rubuta mashi komai dana ji ya fadi a cikin wayarsa, sannan na yi mashi barazanar ko dai ya dawo da babyn Shureim, Ko kuma in tona masa asiri a gurin Daddy da Mommy har da ma Ya Shureim din.
Da tura mashi saƙon ko minti biyar ba'ayi ba, sai ga kiran Uncle Musa ya shigo wayata, na yi mamaki sosai saboda tunda nake kira ba'a picking.
Bayan na ɗaga ko sallamata bai amsa ba ya ce, "Benazir! Ni za ki yi ma kazafi? Yaushe kika ji ina yin wannan maganar? Bayan haka ni miye haɗina da yarinyar Shureim da har zansa a binno ta daga rami? Me zanyi da gawa..."?
Bai ƙare maganar ba na ce, "Haba Uncle, wlh baka isa ka raina mini hankali ba! Da kunnena na ji ba gaya min a ka yi ba, Wlh babyn Shureim tana araye kuma ta na a gurin ka, Kai kasan inda ka kaita, kuma na rantse idan har baka dawo masa da ƴar sa ba, saina tona maka asiri.."
Ina ƙarashe maganar na kashe wayar, cike da saran zai neme ni.
Aikuwa ba zato ba tsammani a yammacin ranar da na yi waya da shi sai ga kiran shi ya shigo waya ta, a lokacin baka a gida, bayan na ɗaga kiran na ji yace in fito wajen gidana ya turo da escort dinsa yana jirana a cikin Mota.
Na ɗan ji fargaba amma da ya ke lokacin ina jin tashen rashin ji, bana jin fargaba kuma bana jin tsoron tunkarar koma uban wanene.
Batare da saninka ba, na bi Escort dinsa acikin mota ya kawo ni guest house din Uncle Musa dake anan Joss.
Bayan na fito daga motar, escort din ya rakani har cikin falon gidan, Ina shiga na taras da shi a zaune saman Sofa ya ɗaura ƙafa daya kan ɗaya, fuskarsa kwata kwata babu annuri kamar bai taba dariya ba, Nima na haɗe rai fiye da yadda ya haɗe ta shi fuskar, tunkafin ya bani iznin in zauna na samu guri kan sofa din dake fuskantar shi, na zauna tare da ɗaura ƙafata ɗaya kan ɗaya hakan ba karamin daure mashi kai ya yi ba.
Tambayar farko da ya yi min shine in fada masa gurin wa na ji maganar dana fada masa?"
Na ce in har yana so in fada masa to ya fara kawo min Babyn Shureim.
Lallashina ya fara yi duk dan in faɗa masa, na sanya kaifi nace wallahi ya daina wahalar da kanshi saboda bazan faɗa ba, dole sai ya fara kawo mini yarinyar.
Shu'umin murmushi ya saki tare da cewa bai damu ba in je in fada ma duk wanda zan fadamawa, saboda bani da hujjar da zan iya tuhumar shi, balle har in tona masa asiri, kuma in bi a hankali in ban iya kama barawo ba sai barawon ya kama ni.." na yi dariya hada shewata na ce, "Ka bani mamaki Uncle, ina yi maka kallon mutumin kirki ashe kai din mutumin banza ne! Ka yi zaton bansan komai ba?"
Na faɗa ina zare mashi idanuna, a lokacin yanayin fuskarsa ya sauya zuwa tsantsar al'ajabi da rudani.
"Benazir Ni kike kira mutumin banza? Ido cikin ido batare da jin shakkata ba? Kin manta matsayina agurin ki?"
Harara na galla masa, "Na je na fada Uncle, Wallahi Hakkin Aisha bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba, Ka cuce ta Ka cuci Yaya shureim ka kuma cuci Babyn da suka haifa"!
Ina magana hawaye na shararowa kan kuncina.
"Ashe dama duk kyautatawar da ka yi mana ba don Allah bane, sai don saboda wata mummunar manufa taka, baiwar Allah Aisha saida ta nuna batason zama agidan da ka kama mana haya a kasar germany saboda hankalinta bai kwanta da shi ba, sannan ta nuna rashin jin dadin ta akan zaryar da kake yi cikin gidan duk weekend sai ka zo ka kwana ga kudi da kake kashe mana, ni da kaina na kare ka agurinta na nuna mata cewa kada ta damu Uncle dina mutunne mai son yin alheri kuma dukiyar ka ta halal ce kasuwanci kake yi, sai daga baya na gano komai, arzikin da kake taƙama da shi ba ta hanyar halal ka tara shi ba, mu ka raina ma wayau da sunan kasuwanci kake yi, bayan haka ina zargin kana a ƙungiyar asiri ta yan shan jini, kuma kaine ka haɗa Aisha da mahaifinta, wato ka yi amfani da damar da kake da ita, a lokacin da kake zuwa ka kwana a gidanmu, sai ka bari dare ya yi sai ka saci hanya batare da sanin mu ba ka ke shiga ɗakin Aisha, ka dauketa video da hotuna, wama ya sani ko asiri kake yi mata shiyasa har batasan kana yi mata hakan ba, wallahi ka ci amanar yardar da na yi maka! kuma na rantse da wanda raina yake a hannunshi in har baka dawo mana da babynmu ba saina fallasa asirin ka...."
Tun kafin in ƙarasa maganar, Uncle Musa ya doka min tsawa yana huci kamar mayunwacin zaki, saboda tsabar fusata da bacin rai jikin shi ya dinga fitar da gumi, abun da ya daure mashi kai ya kuma ɗaga hankalinsa shine ta yaya akai duk nasan abunda yake ƙullawa?" Sam ya kasa magana sai huci yake fitarwa, Idanunsa sun kaɗa jawur.
Ganin baida niyar yin magana yasa naci gaba da cewa, "Kuma kaine ka shiga tsakanin Yaya Shureim da Aisha, ka yi masa asiri kasa yayi mata fyaɗe ba'a cikin hayyacin sa ba, komai dake faruwa kana bin diddiginsu kana samun information a gurin yan leƙen asirin ka, Hatta Mahaifinmu baka ƙyalesa ba, kana amfani da sihiri gurin juya shi don yabi ra'ayin ka, bayan haka kaine ka turama Daddy videos din Aisha daka dauka tare da kai sai ka 6oye fuskarka don karsu gane kaine kabar fuskar Aisha saboda tsabar mugunta da zalunci irin naka! kuma kai ne shaidanin da ya tunzura mahaifinmu akan karya kuskura ya yarda Shureim ya auri Aisha in ba haka ba zai rasa kujerar da yake nema kuma mutane zasu juya mashi baya saboda abun kunyar da Shureim ya akaita, munafukin Allah kaita faɗa masa kauli da ba'adi har saida ka shiga tsakanin daddy da Ya Shureim...".
Ban kai ga ƙarasa maganar ba ya katse ni ta hanyar bugun table din gabansa da hannunsa, Jikinshi har wani jijjiga yake yi saboda bacin rai.
"Benazir! Bana so ki jefa rayuwarki a cikin hadari! Ina mai gargadin ki, Tun wuri ki yi gaggawar janye zargin da kike yi mini, tun kafin ki yi danasani" Na yi tsalle na dire na ce, "Wlh Uncle bazan janye ba, saboda ni akan gaskiyata nake, ba zargin ka ni ke yi ba, tabbaci gare ni, kai baka yi mamakin tayaya akai nasan sirrinka ba uhum? Na faɗa ina kallon cikin idanunshi, wlh a lokacin ya razana dani ba kadan ba, amma da yake shu'umin mutunne sai ya dake ya tirje akan cewa ba gaskiya nake fada ba, ƙazafi nake yi masa.
raina a 6ace na juya zan bar falon ban ma jira ya karasa maganar shi ba, har na kusa fucewa Ya dakatar dani ta hanyar kiran sunana na tsaya ina jiran jin me zai ce.
"Ki fada mini komai kike so a duniyar nan zan yi maki shi, amma maganar zaki tona min asiri bata taso ba, Ki yi watsi da maganar nan, nifa Uncle dinki ne, In kika tona mini asiri kamar kin tona ma family din mu ne, ki dawo mu sasanta tsakanin mu" A hankali na juyo na fuskance shi.
"Baka so zaman lafiya ba Uncle, ai wlh in har kana son sasanci to ka dawo mana da babynmu, ni kuma nayi maka alkawarin babu wanda zaiji maganar nan! Ni ita kadai nake so bandamu da abunda kake aikatawa ba, wannan tsakanin ka da Allah ne, duk wanda ya yi da kyau ya sani, kuma dai akwai mutuwa akwai hisabi kowa zai girbi abunda ya shuka ne..." Dafe kanshi ya yi da tafin hannunsa kamar mai fama da ciwon kai,
"Meyasa kin fiye taurin kai da kafiya ne? Yakamata ki iya bakinki Benazir! Har yanzu bakisan wanene ni ba! Sabo da kaza bai hana in yankata! Wlh zan iya salwantar da rayuwarki, kuma idan na kashe ki na kashe banza."
A lokacin gabana ya faɗi na kuma sha jinin jikina amma ban bari ya gane hakan ba, saima na yi dariya na ce, "Idan ma kana tunanin kashe ni shine mafita agare ka, to ka daina, saboda hujjojin dana fada maka ina da su, bani kadai ke da su ba, Nima ina da mutanene da nake yin aiki tare da su, idan yau ka kashe ni, wlh zasu fallasa asirin ka ne duniya tasan me ka ke aikata, ka ga kuwa baka da wata mafita da ya wuce ka bini ta lalama"
Maganar da na yi ta ɗaga hankalinsa matuƙa, Zuciyarshi ta hasala kamar ya rufe ni da bugu haka yake ji.
Har na ɗaga kafa zan fuce na sake tsinkayar muryarsa a cikin kunne na, "Ko don saboda abun da ke a cikin ki, Yakamata ki yi takatsantsan idan ba haka ba, zaki jefa rayuwarsa a cikin haɗari ne..."
Wani irin faduwar gaba na ji, saboda a lokacin bansan ina ɗauke da juna biyu ba, cikin sauri na dafe cikina tare da zare idanuna akan fuskar shi, gaba daya na bi na ruɗe, Murmushin mugunta ya sakar mun saboda ya gano lago na..
"Benazir, nafi karfin ki nesa ba kusa ba, wlh baki isa ki ja dani ba, ƙaramar yar iska mai kwana da wando, saboda baki da hankali ki rasa wa zaki tuhuma sai ni? Kinsan wanene ni kuwa?? Ki fara sanin wanene ni kafin ki yi ja in ja dani, Sannan zan ƙara tuna maki, kina da miji, kina da juna biyu, kina da iyaye, kuma kina da ya ya mafi soyuwa a gare ki, Ina fata Kin fahimci abunda nake nufi???"
Yana karasa maganar ya juya ya nufi up batare da ya sake waiwaye na ba, har saida ya 6ace ma ganina kafin na kawar da idanuna daga barin kallon sa.
Har na dawo gida ban daina tariyo maganarsa a cikin kunnena ba, Saboda hankalina ya tashi sosai, Lamarin Uncle Musa ya fara bani tsoro, na riga da na gane mugun mutunne shi, mara imani, kuma tantirin shaidani nasan zai iya aiwatar da komai don ya rufawa kansa asiri..
Bayan sati biyu na je ganin likita batare da saninka ba, bayan doc yayi mini gwaje-gwaje sakamakon ya nuna ina dauke da ciki na sati biyu, nan fa hankalina ya ƙara tashi kwata kwata ban yi farin ciki da cikin ba a lokacin saboda zai zama rauni na, kuma ina jin tsoron in haife shi saboda fargaban kada Uncle Musa ya salwantar da rayuwarsa, Ko ya ɗauke sa kamar yadda ya dauke ɗiyar Ya Shureim, wannan dalilinne yasa nayita yunkurin in zubar da cikin Angel, wlh Allah shine shaidata badan bana son shi ba, Kawai a lokacin muna yawan samun sabani da kai saboda bani da kwanciyar hankali, Damuwa tayi mini katutu, kullum cikin zullumi da fargaba nake yi saboda nasan Uncle Musa bazai ƙyale ni ba, kamar yadda ya fada dole ya dauki mataki akaina, kuskuren da na yi shine ƙin sanar da kai, Na ƙi faɗama kowa nabar abun a matsayin sirri, saboda gudun kada na faɗa ya koma mashi karshe inja ma kaina da kuma dangina don har lokacin ban saduda na kyaleshi kan fito da yarinyar Yaya Shureim ba, ka ji dalilin da yasa a duk lokacin daka kamani ina yunkurin zubar da cikinta ka tuhume ni dalili, sai ince maka bana son ya'ya, kuma bana son cikin saboda zai bata mini shape ɗin jikina, Amma a zahirin gaskiya bada son raina ni ke yin hakan ba, gaba daya rayuwar aurena da kai wani abun sai daga baya na gane bayin kaina bane, nasan bana jin magana, amma wlh Taj na so mu yi zaman lafiya sai dai na kasa faranta maka, saima cuzguna makan da nake yi hakanan bakai mini komai ba, kawai sai inji haushin ka, da tsanarka acikin Zuciyata, hatta mai aikin gidanmu Janet na ji na tsane ta, laifin da bai kai ya kawo ba idan ta yi mini bana ƙyale ta, saina azabtar da ita...."
Kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan da ya ƙwace mata, Haƙiƙa Zuciyar Taj ta karaya, tsantsar mamaki da al'jabi sun ruke zuciyar shi tamau, duk da sanyin A.c din dake a dakin hakan bai hana shi fitar da zufa ba, jikin shi har tsuma yake yi, wani irin tausayin Benazir ne ya kama shi ya yi danasanin zarginta da ya dinga yi, ashe bayin kanta bane, makircine aka shirya mata.
Numfasawa ta yi, cikin shesshekar kuka ta ci gaba da cewa, "Bayan wani lokaci, ban ƙara jin ɗuriyar Uncle musa ba, har lokacin da cikin Unaisah Ya cika wata tara cuf, nima kuma ban ƙara tuntubarsa ba ko in yi tunanin sanar da wani game da sirrin, a tunanina saboda bana son in jefa rayuwar ahalina Cikin hadari ne, a daren ranar da naƙuda ta kama ni, da ni da kai muna a kwance kan gadonmu mun yi nisa a cikin baccinmu, kwatsam ba zato ba tsammani, na fara jin naƙuda na taso mun, a firgice na farka daga baccin hannayena daddafe da cikina, ina ta faman cizon le6e saboda radadin da nake ji a jikina.
Zufa duk ta wanke jikina, naita kokarin kai hannu don in tashe ka daga bacci amma nakasa, na yi kokarin in yi koda addu'a ne nan ma abun ya ci tura saboda haƙorana sun game gam, Taj ban ƙara sanin me ya faru dani ba, nadaisan bana a cikin hayyacina na sauko daga kan gado ina jan ƙafa na tura ƙofar toilet na shiga. Wlh Taj haihuwar Unaisah ikon Allah ne, kwata kwata bana a cikin hayyacina a haka na kar6i haihuwana da kaina amma bansan na yi ba, bansan dame na yi amfani gurin yanke cibin ba, a lokacin dana haifeta saida na kalleta cikin jini, na rungume abuna ina kuka tana kuka, abun da nake ta gudun in haifa sai gashi na haifeta, kuma sai na ji na kamu da ƙaunarta fiye da komai na duniyar nan, ina tsaka da kallonta, Kwatsam na fara jin ana ambaton sunana da wata iriyar murya mai matuƙar tsoratarwa, kuma nan take na dinga jin bakin ciki a cikin zuciyata, na ji na tsani komai in har ban je na amsa kiran da bakuwar muryar ke yi mini ba zan iya rasa raina ne, saboda yadda tsigar jikina ke tashi kamar ana tunzurani, yadda kasan ana zare raina ban ma san sa'adda na kwantar da Unaisah cikin bathtube ba, cikin hanzari duk da rashin ƙwarin jiki na fuce daga cikin toilet din, ko waiwaye ban yi ba na nufi gate, baba mai gadi yana adakinsa yana bacci baisan na fita ba, saboda wani ƙarfine ya zo mini bangaza ɗaya na yi wa kofar jikin gate din mu dake a kulle nan take ta buɗe nasa kai na fuce da gudu na bi santar mu. Ban ƙara sanin meya faru ba, sai dai na wayi gari na ganni a kwance kan gadon asibiti magashiyan rai a hannun Allah, bayan dana dawo hayyacina na tambayi nurses din dake kula dani akan meya faru da ni? anan suke faɗamin wani matashi ne ya bankaɗe ni da motarsa akan titi shine ya kawo ni asibitin, abun da ya ɗaure mini kai, ni da na ke a Jos meya kawo ni Abuja? Ban sanya damuwa araina ba saboda lokacin burina kawai in yi nesa da dangina saboda bana son su a kusa da ni.💔
Tun kan ta ƙarasa bashi labarin ya soma ambaton Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! cikin karyayyar Murya ya ce, "Benazir! Dama haka komai ya faru baki ta6a sanar da ni ba? Kika sa nayi ta zargin ki, Ya Salam!! Pls ki yafe mini"!
In a cool voice ta ce, "Ba laifin ka bane, rashin sanine ya jawo hakan, Nima ka yafe mini 6ata maka rai da na yi a zaman mu na aure.."
"Ki manta da komai ya wuce, saboda ke ma bayin kanki bane, Ina tunanin Uncle dinki shine Ummul aba'isin komai da ya faru, yanzu ina so ki faɗa mini kece kika tura min sakon In sake ki!"
"Bani bace Taj, saboda ni ban tafi da waya ba, ni bansan wanene yayi mini hakan ba amma ina zargin Uncle Musa, saboda bayan na dawo gida Daddy da Mami sun faɗa min ana tura masu sakonni ta layin wayata, wai hada sakon da nace ni na gudu da son raina kuma na shiga duniya kada suyi tunanin zan dawo gare su kuma kada su sha wahalar nema na..." Dafe kai Taj ya yi da tafin hannunsa, Idanunsa sun kaɗa jawur da su.
"Benazir, Ni kuma saƙon da aka tura mini da bakuwar number ne, Idan bazan manta ba, abun da aka rubuta a cikin sakon shi ne ka sake ni Taj, kuma kada ka yi tunanin zan dawo na tafi kenan har abada, har kiran layin na yi amma saina ji shi a kashe kuma daga ranar ba'a ƙara tura min saƙo ba, tun ina sa ran dawowarki har dai na fidda rai"
Fashewa ta yi da kuka tana fadin, "Shiyasa kowa ya ƙullace ni aranshi saboda ana zargin da son raina na tafi, Koma wanene ya yi min hakan bazan ta6a yafe masa ba, Allah ya isa wlh sai Allah ya yi min sakayya, lallashinta ya shiga ya har ya samu ta yi shiru, shima ya yi shiru na ɗan wani lokaci, sai sautin Numfashin junan su da suke ji ta cikin wayar, so yake ya bata labarin rayuwar Unaisah a gidan Kurkukun ƙaddara saboda Yana zargin dasa hannun Uncle dinta sai dai ya kasa saboda baya son ya ƙara ɗaga hankalinta, ganin halin damuwar da ta shiga, gaba daya ya fahimci bibiyar rayuwar su ake yi, tun daga kan Benazir, da Aisha da Dr Shureim, da kuma Iyayensu suma ba'a ƙyale su hakanan ba.
Jin shirun ya yi yawa ne yasa shi tunanin ko ta yi bacci ne .
"Benazir?"
In a low voice ta ce, "Na'am'
"Pls, Ki kwantar da hankalinki, nasan ba zaki rasa ciwon kai ba saboda kukan da kika sha, dan Allah kada ki sanya damuwa a ranki, maganar Uncle din ki zan faɗa ma Chief in sha Allah, duk yadda mu ka yi da shi zamu tuntu6e ku, yanzu ki kwanta ki yi bacci..."
Bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa, "Don Allah Taj, ku taimaka mana, har yanzu ina ji araina Babyn Shureim tana a raye, kuma tana a gurin Uncle, shi kadai yasan inda ya aje ta, amma nasan in har kuka yi bincike akan shi zaku gano komai..."
Kwantar mata da hankali ya cigaba da yi saida suka raba dare suna yin waya kafin suka yi sallama, A daren ranar Taj bai iya runtsawa ba, saboda maganganun da suka tattauna da Benazir sun hana shi sukuni, har dai ya gaza jurewa ya kira layin Chief saboda yasan ba lallai bane idan ya yi bacci ba saboda a irin lokacin yana yawan tashi yin nafila, Cikin sa'a Chief ya yi picking call dinsa, a nan ya sanar da shi sun yi waya da Benazir, ya ce ya duba whatsapp dinsa ya tura mashi recording din da ya ɗauka na tattaunawar da suka yi, Chief ya amsa mashi da toh.
Bayan Chief ya kammala sauraron audio din da Taj ya tura masa, har sujjada saida yayi saboda nuna godiyarsa ga Allah da ya fara kawo masa sauƙi a cikin lamuransa ya kuma ƙara yin addu'ar neman nasara akan abun da suka sa a gaba.
After Two days, ana gobe za'a yi family meeting, kiran sallar asubahin farko Private jet din Prime minister ya yi landing a Airport, Mai girma Sharafuddeen tare da Security details dinsa ne suka je dauko su acikin dankara dankaran motocin su, wannan karon daga shi sai Escorts dinsa suka zo Nigeria batare da iyalinsa ba, kuma bakowa ne yasan da zuwan nashi ba sai family dinsa, ko yan jarida ba a bari sun san da zancen zuwan na shi ba.
Kaitsaye suka wuce Vila da shi, Sai da ya fara huce gajiyar da ya kwaso, Har bacci ya yi a dakin ɗan uwansa Sharafudden kafin zuwa marece suka shigo Estate.
Gaba daya yan'uwansa suka hallara a main falo din baba Obie don su tarbe shi, Yana shigowa falon suka nufe shi cike da tsantsar farin cikin ganin shi, ɗaya bayan daya suka dinga yin hugging dinsa, burinsa ya ƙarasa ga mahaifinsa sun hana shi motsawa kowa ɗokin ganinsa yake yi. Daƙyar ya samu suka kyale shi ya nufi Baba Obie dake ta sakar mashi murmushi ya rungume shi kamar zai maida shi cikin jikin shi, su Hajiya Saratu baki yaƙi rufuwa saboda murnar ganin Yaya Hateem, kowa ya buɗe baki sai ya tambaye shi ina iyalinsa? Meyasa bai zo da su ba? Ya ce masu su kwantar da hankalinsu suma zasu zo ne, amma a halin yanzu gimbiya da su Yazrin sun tafi Dubai gurin danginta hidima ce gare su, ita kuma Faryat bata samu hutun makaranta ba, shiyasa bata samu damar zuwa ba.
Lokacin da marece ya nutsa, sai ga kiran his excellency Abdul razak ya shigo wayar Baba Obie ya sanar da shi sun ƙaraso Abuja yana a aiport, Batare da 6ata lokaci ba Baba Obie ya tura da motocin Escorts suka dauko shi, bai jima da ƙarasowa ba sai ga motocin His excellency Deen na Kaduna sun iso cikin Estate din. Sun yi farin cikin sake haduwa da yan uwansu saboda sun yi kewar juna, Baba Obie sai haba haba yake da su, saboda murna bakinsa ya ƙi rufuwa. A daren ranar saida suka raba dare suna hira da mahaifinsu kamar ba zasu yi bacci ba har saida Baba Obie ya ce suje su kwanta su huta tukunna suka yi sallama da shi, Hateem dai ruƙe shi ya yi a ɗakinsa yace tare zasu kwana saboda ya yi kewarsa, hakan ba ƙaramin dadi ya yi ma Prime minister ba, a kan gadon Baba Obie suka kwanta, zai kwana da tunanin mutumin da ya kwallafa rai da son ganinshi, ɗazu da Chief ya zo gaishe da shi har tambayar shi ya yi ina baby boy dinsa? Yana lafiya? A lokacin hankalin Chief ba karamin tashi ya yi ba, amma saboda baya son ya ɗaga masa hankali yasa shi cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya, amma baya a gidansa yanzu, yana a camp din su na isod, yana kar6ar training.
Dakyar ya samu ya shawo kan Hateem har ya haƙura da maganar Danish amma fa yace duk yadda za'a yi kafin ya koma yana son ganin sa.
~________________________________🍁~
*_🔥🔥🔥The Chief Owais Birthday Celebration and Family Gathering🔥🔥🔥_*
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹
~___________________________________~
fashewa tayi da matsanancin kuka sam ta kasa buɗe baki ta yi magana saboda bakin cikin tsinuwar da mahaifinta yayi mata, bata taba zaton zaiyi mata haka ba ko da kuwa ta aikata abunda ya ke zargin ta da shi, ta rasa gane wanene yayi mata kazafi? Laifin me tayi masa"?
A lokacin Aunty Laura kasa jurewa tayi, tana jin koda zai sake ta ne sai tayi magana, Cikin fushi da nuna bacin rai tace"wallahi ka bani mamaki baban Aisha! Idan rai ya baci ai hankali bai kamata ya gushe ba, shin Ina ilminka ya ke da har zaka bari shaidan da zuciya su rinjaye ka! Kai fa ba mahaukaci bane, Da hankalin ka amma tayaya za'ay wa yarka kazafi ka yarda harka dauki mummunan mataki akanta...." bata kare maganar ba, sakamakon Marin daya kifa mata akan kuncinta, tuni hawaye sun cuccuko tab da idanunta, taji zafin marin da yai mata.
Ganin hakan Yasa Maids din gidan suka sha jinin jikinsu, daya bayan daya suka bar falon zuciyarsu cike fal da tausayin Aisha da babynta.
Murmushi Aunty laura tayi tana kallon cikin idanunshi da suka kada jawur sai tsuma yakeyi yana huci..
"Bazan fasa magana ba wlh, ko da zaka kashe ni ne! Wlh ka bani kunya kuma ka bani mamaki, sannan kaji kunya wlh, Tun wuri kayi gaggawar janye hukuncin da kayi ma Aisha tunkafin kayi danasani! Abune da ka sani na sani, kai da Aisha kuna da makiya masu jin haushin daukakar da Allah yayi maku kai baka tunanin sune suke kokarin 6ata maku suna? Bayan haka videos din da kake ikirarin an nuna maka ka ganta da ƙato Ka duba dakyau ba fuskarta aka dauka akayi editing ba"? Ta jefa mashi tambayar tana akai masa harara sam baya fahimtarta, ya riga daya hau kan dokin zuciya..
Sassauta muryarta tayi"yakamata ka dinga amfani da kwakwalwarka da kuma saninka, idan Aisha batayi abun kunya ba, to kai ne zakayi babban abun kunya, haba Imam ko da ace Aisha ta aikata laifin da kake zargin ta, kai ba maiyi mata uziri bane kaja ta ajiki don ta shiryu, korarta da za ki yi shi ne mafita? Hmm duk dai inda Aisha zataje Yarka ce, Kuma kowa yaganta zai ce diyar imam malik ce, Kaga kuwa babu ribar korarta! bana so kayi danasani mara amfani ...."
Kalaman Aunty Laura sunso suyi tasiri acikin Zuciyarshi, Amma duk idan Ya tuna abun da idanunsa suka gane masa sai yaji wani irin kunci a cikin zuciyar shi, saboda shi yasan wacece Aisha, yana da tabbacin videos din da aka nuna mashi ba editing bane itace da kanta"
Sheikh Imam bai dauki hudubar Aunty laura ba, ya ce ma Aisha ta tashi Tabar mashi gidan shi! baya bukatar ganinta, yana karashe maganar ya fuce yabar gidan.
Maids din da Aunty Laura suka kewata sunata aikin lallashinta da bata hakuri, bata taba ganin bakar rana irin ta yau ba, har addu'a tayi Allah ya dauki ranta ta huta amma dayake Lokacin mutuwar nata baiyi ba sai bata mutun ba.
Kasa tafiya tayi saboda bata son ta tafi, mahaifinta Yana fushi da ita, ga tsinuwar da yayi mata, tafi son Ta roki yafiyarsa inyaso saita tafi.
Tsawon kwana uku tana zuwa dakinsa donta bashi hakuri bai ta6a sauraronta ba, Ko gaisuwarta baya amsawa, gaba daya ya ɗauke ƙafa da yi mata magana, ko kallon ta bai son yi.
Aunty laura ta yi kokarin ta tunbi Hajjonsu don ta sanar da ita abunda ke faruwa don tasan ita kadaice zata iya take mashi burki A lokacin da take kokarin kiran layin Hajjo batasan sheikh Imam Ya shigo dakin nata ba, aiko batai aune ba, taji ya fusge wayar ya Maka ta da kasa ya take ta da kafarsa, yana huci ya gargadeta akan in ta kuskura ta fada ma wani wlh abakin auren ta, ba arziki taja bakinta tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.
Aisha ta shiga tsaka mai wuya, damuwa takusa tayi mata illa ko ma ince tayi mata illa, da abun ya ishe ta, ta kunna wayarta sakonni sukai ta tururuwar shigowa, ko ɗaya batayi sha'awar budewa ba ta lulubo layin Anila ta danna mata kira, don bata jin zata iya fadama Benazir saboda sun fita aranta batason komai daya shafe su.
Lokacin da Anila taga kiran malama Aisha tayi mamaki bayan tsawon watannin data dauka bata neme su ba.
Bayan ta daga kiran tayi ta tambayarta meyasa ta yada su? In sun kira basu samun layinta, kuma tayi tafiya ko sallama ba ta yi masu ba.
Cikin shesshekar Kuka Aisha ta kwashe komai daya faru ta sanar da Aneelerh, Aneelerh Tayi kuka taji bakin ciki da takaicin abunda dr shureim yayi mata, Duk da tasan ba halinsa bane, kuma taji zafin Hukuncin da baba Imam yayi ma Aisha, sannan taji tausayinta sosai, Aisha tace mata tayi danasanin zuwanta germany karatu saboda anyi mata kazafi an daura mata laifin da bata aikata ba, Hankalin Aneelerh ya tashi sosai har tace mata zatazo gidan tare da Abie da Mami donsu tayata bashi hakuri ya yafe mata.
Cikin sauri Aisha tace karta kuskura ta fada masu halin da take a ciki, Baba Imam yana da bad temper idan ransa ya 6aci baya ji baya gani sai daga baya ya ke yin danasani, Idan har yasan ta fada mata abunda ke faruwa da ita, to kuwa zai kara hukuntata ne, amma ta roke ta akan ta tayata da addu'a in sha Allah komai zai tafi daidai.
badan Aneelerh taso ba tace mata toh amma dan Allah kar ta tafi ta zauna agidan, idan ma ya matsa mata akan ta bar masa gidan toh toh tazo gidan su ta zauna, Aisha tace mata toh.
Bayan sun kammala waya Aneelerh bata ƙara samun kwanciya hankali ba, saboda zullumi da fargaban kada Aisha ta tafi, gashi ta hana ta faɗa ma Benazir halin da take a ciki ta kuma hana itama tazo gidan saboda gudun kada laifinta ya shafe su.
Tayi azan Baba Imam zai sassauta hukuncin daya yanke mata, Ganin har anyi kwana biyu bai kara yi mata maganar ba, haka Aunty Laura ma tayi tunanin yaji nasihar ta ne shiyasa ya ƙyale Aisha, Hankalin su har ya dan kwanta.
a daren wata ranar Alhamis, tana tsaka da yin bacci, ta rungume babynta da ke bacci akan kirjinta, Sai ga sheikh Imam Ya fado dakin Yana huci Ya tashe ta daga bacci Yace ta tashi tabar gidan bai son ganinta, Ta yi nesa da shi idan ba haka ba zai kashe yarta, Ya tsaneta baya son ganinta kuma wlh in har ta bari wani yasan tayi cikin shege ta haihu Sai Ya lahantata, tace mashi baba kada kayi min haka! Idan ka kore ni a cikin daren nan ina kake tunanin zan tafi? Bayan ka hana in nemi taimakon dangin mu, nifa yarka ce baba, amana ce agare ka, nasan da mahaifiya ta, tana araye wlh koda ace ni karuwace ba zata kore ni ba, saima taja ni a jikin ta don in shiryu, balle kai da ka taso tare dani ka sanni ciki da bai, ka tarbiyantar dani, kuma ka yarda dani amma a yau kaine kake korata? Saboda kaddara ta afka min? Bai Saurareta ba, Tana kuka ta sauko daga kan gadon, ko Aunty laura bata sani ba adaren ranar shekh imam Ya kori aisha daga gidan Har bakin gate Ya rakata Bata dauki komai nata ba sai yar wayar data tsira da ita.
a bakin gate din gidan Alhaji Ubaid ta tsaya hannayenta rungume da jinjirarta dake ta sharar baccinta.
Tana kuka Ta kalli sararin samaniya taga hadari ya hadu bakikkirin Babban tashin hankalinta kada a barke da ruwa sama batasan Ina zata sanya yarta ba.
Anan ta yanke shawarar kiran dr shureim duk da bata da tabbacin yana nan ko bai nan don tunda abun nan ya faru bata kara jin duriyarshi ba tun da ba fita ta ke yi ba, wayarta kuma akashe take, ko ya kira ba sani zatayi ba.
sau uku tana Kira baya Picking, sai ana hudune taci sa'a yai picking tace"shureim ina a kofar gidanku, Baba Imam ya kore ni daga gida, Ka zo ka kar6i yarka, idan ba haka ba zaka rasata ne"! Tana karasa maganar, ta kashe kiran.
Ko mintuna biyar ba ayi ba sai ga dr shureim Ya fito jikin shi sanye da jallabiya, kallo daya da yayi ma Aisha saida gaban shi ya fadi ganin yadda ta rame idanunta sun kaɗa jawur sun kumbura, A lokacin yaji kunyar hada ido da ita kamar ya haƙa ƙasa ya binne kanshi, tsantsar tausayintane ya kama shi sam bai ma lura da babyn hannunta ba.
Karasawa yayi kusa da ita, harya bude baki zaiyi mata magana ta dakatar da shi"ban kiraka don muyi magana ba, Yaya shureim nagode da abunda ka saka min da shi," ta fada tare da manna mashi yarinyar da ke a nannaɗe cikin towel dinta a kirjin shi yai sauri rungumeta wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyar shi.
"Gatanan Itace abunda muka samu, nabar maka ita amana, badan bana sonta ba na baka ita, sai don bana so tasha wahala tunda ni yanzu bani da kowa banma san inda zan tafi ba, wata rana zan dawo in kar6i abuna, Inaso kayi mata huɗuba da sunan mahaifiyata FATIMA BATOOL, Idan har kabari rayuwarta ta cutu ka sani Allah yana sama yana Kallonka, Nima kuma bazan yafe maka ba, akwai ranar hisabi"
maganganun Aisha sun karya mashi zuciya, baisan sa'adda ya fashe mata da kuka ya dinga yi mata magiya akan kada ta tafi tabarshi wlh yana sonta ashirye yake da ya aureta yayi mata alkawarin zai wanke laifinsa zai share mata hawayenta, zai kula da rayuwarta, tace mashi ya makaro, Lokacin daya kamata ya furta mata hakan ya riga daya wuce, sai bayan daya 6ata komai, sannan ita bazata taba auren namijin daya santa ba.
Ba yadda baiyi da ita ba amma ta kafe, har cewa yayi ta shigo ta kwana agidansu amma takiya, ta juya zata tafi yabi bayanta yace sai dai su tafi atare saboda bazai iya rayuwa batare da ita ba, sannan Yar da tabar masa, shi baida abunda zai shayar da ita ta taimaka ta dawo suyi aure su rufawa kansu asiri da kuma yarsu.
Aisha bata saurare shi ba, da taga dagaske Dr shureim binta zaiyi sai ta watsa da gudu Shima yabita aguje a karshe ta bace ma ganin shi... 😭
Tun daga wannan Lokacin dr shureim bai kara ganin Aisha ba, babu wanda yasan Ina ta dosa, Anila saidai taga sakon data tura mata.
_Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu."_
A daren ranar bayan Dr shureim Ya koma da baby cikin gidan, batare da sanin kowa ba, Ya nufi daki da ita Ya kwanta kan gadonshi yayin daya rungume Yarshi a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da bakin cikin abunda yayi ma Aisha shine silar komai, yaji takaicin tafiyarta, yaji kunci da radadin rasata da yayi.
Dakyar ya samu nutsuwa, ya buɗe fuskar babyn ya zuba mata idanunshi da suka kada jawur yadinga kallonta kamar zai hadiyeta, A hankali ya sumbace ta a saman forehead dinta da cheeks dinta, wani irin tsantsar sonta ne ya lullu6eshi kamar ya mayar da ita cikin shi, a kalla ya shafe rabin awa yana kallonta, aranshi ya ayyana inama ace ta hanyar aure suka same ta da sai yafi kowa farin cikin zuwanta duniya, amma ahakanma Ya gode ma Allah daya bashi ita, addu'o'i sosai yayi mata har yai mata huduba da sunan*FATIMA BATOOL*
Bai tashi sanin yana a cikin musibaba, Saida Ta farka tsakar dare ta fara tsala kukan Yunwa, A firgice ya farka ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi duk yabi ya Ruɗe, ya sungumeta akan kafadarshi ya sauko daga kan gadon ya dinga zarya da ita a tsakar dakin yana lallashinta haɗi da jijjigata.
Sakamakon kukan data dinga tsalawane Yaja har mutanan gidan suka farka daga bacci, Cike da mamakin jin kukan jinjira a cikin gidansu.
Da gudu Suka nufo Dakin Dr shureim Alhaji ubaid da hajiya layla sai Mai aikinsu zainab, suna shigowa suka iske shureim ya rungume baby a kirjin shi.
Cike da mamaki suka tambaye shi yar wacece? Donsu kwata kwata basu san Aisha ta haihu ba, sun dai san abunda ya faru tsakaninta da shureim.
Jin yayi shiru bai basu amsa ba yasa hajiya Layla ta doka mashi tsawa tace shureim ba kaji ina magana ba? Yar uban wacece wannan"?
Cikin sanyin murya yace"ƴata ce, babyn da Aisha ta haifa mince, Baba Imam ya koreta daga gidansa, shine ta kawo min ita jiya da daddare"
Bai ƙare maganar ba Hajiya layla tayi tsalle ta dire tace"Wlh bazata sa6u ba! Shegiyar zaka kawo mana acikin gida? So kake kaja mana surutu agurin mutane? Wato shi uban nata ya koreta saboda gudun abun kunya sai mu zaka jajubo mana annoba ka kawo mana agida? Saboda baka da hankali"?
Ta inda take shiga bata nan take fita ba, Kamar zata rufesa da bugu, Kalamanta sun Kona ransa, musamman data kira yarsa da sunan shegiya, bai kula ta ba hankalinsa na akan fatima dake ta kuka surutunsu Ya kara hargitsa kwakwalwarta duk tabi ta rude ga yunwa tana ji.
Alhaji Ubaid Yace"shureim, kayi hakuri da abunda zance, badan bana son jininka ba, sai don gudun abun kunya, kuma kaga an kusa fara zabe in har maganar nan ta fita wlh za ka ja min asara ne, don Allah ka dauki yarinyar nan ka kaita gidan marayu su kula maka da ita, Inyaso sai ka dinga zuwa kana dubata..."
sai a lokaci Ya fuskance su da wata irin fusatacciyar murya yace"ɗan ku ne shegen da yayi wa uwarta ciki ta haifeta, wallahi ba inda zan kaita! Ban taba sanin baku da imani ba sai yau da kuka nuna min, Yarinyar nan koba dan kasancewarta jinina ba Yakamata ku tausayamata, Jaririya ce fa? Ta rasa mahaifiyarta, ni kadai na rage mata, ya kuke so tayi da rayuwarta ne"? Idanunsa cike tab da kwalla yai maganar.
Aunty Zainab tayi kokarin tayashi fadan amma Hajiya layla ta koreta daga dakin ta fuce tana kuka saboda sun bata tausayi.
Kusan dare suka raba ana abu daya, kowa yana akan bakanshi.
Hakika dr shureim Yaci wahalar Iyayenshi, kullum sai sunyi barazanar kashe mashi ƴa in har bai fitar masu da ita daga gidan ba amma Yakiya.
wulakancin yau daban na gobe daban Sun daura mata karan tsana ba gyaira ba dalili, Aunty zainab ce ke shayar mashi da ita a boye batare da sanin su ba.
Hajiya layla har ɗaukar babyn tayi batare da sanin shi ba, ta fuce da ita daga cikin gidan, a lokacin yaje masallaci yin sallah sai da ya dawo ya duba dakin shi bai ganta akan gado ba, ya fito arude yana nemanta, Aunty zainab ce ta fada mashi taga hajiya layla ta shiga dakin shi, tana da tabbacin itace ta ɗauke ta, hankalinsa ya tashi, ya dinga kiran layinta bata picking, time data dawo cikin motarta ta shigo gidan ya nufeta yana huci yace ina yarshi tace tabada ita sadaka.
Ji yayi kamar ya dauketa da mari, ya dinga rokonta akan ta dawo mashi da yarshi tayi banza ta kyale shi, yai hakuri Ya jira time da Alhaji ubaid ya shigo gidan, ya tuntube shi da maganar ya dinga rokonsa akan ya yi ma mommynsu magana ta dawo masa da yarsa, Alhaji ubaid bai kulasa ba saima yace tayi abunda ya dace.
rai a6ace Ya nufi Kitchen Zainab tana a ciki tana yin girki taga yashigo ya dauki wuka Ya fita da ita aguje tabi bayanshi.
A lokacin Hajiya layla tana a zaune kan kujera tana danna waya batai aune ba, taji ya ɗaura mata wuka a akan wuyanta, ta zare ido gabanta na faduwa, shureim yana huci yace"kodai ta fada mashi inda takai mashi baby, ko kuma ya kasheta"
adabarbarce tace"nashiga uku shureim ni zaka kashe? Mahaifiyarka? Saboda kawai na kawar da ƙazantar zina daga cikin gidan mu"?
Ihunta da Alhaji Ubaid ya ji yo ne yasa shi watso wa da gudu Yafito daga dakin shi ganin abun da Shureim ke kokarin yi ne Ya tada hankalinsa kafin Ya karaso Shureim Yace"kana karasowa zan hada dakai in kashe!" ba arziki Alhaji ubaid Yaci burki yana lallashin shi akan ya aje wukar zasu dawo mashi da yar shi, Zainab tana kallon komai dake faruwa, ko kadan bata sa baki ba, saboda taji dadin barazanar da Shureim yayi masu, tun da su ba Allah aran su.
Hajiya layla data gama tsorata cikin shakakkar murya ta fada mashi sunan gidan marayun data kai Batool.
Sakin wukar yayi da gudu Ya fuce daga gidan Cikin motar shi Ya tafi.
Kafin marecen ranar sai gashi ya dawo da babynsa, ya rungume abunsa a kirjin shi, baiwar Allah tayi kuka har ta gaji idanunta sun kada jawur dakyarma ya samu Caregivers din dake rainon yaran suka bashi ita, saida ya basu cin hanci harna Dubu dari shidda kafin suka damka mashi ita.
Abun da ya ɗaurewa shureim kai, Mugayen halayan da iyayensa suka sauya wanda ada ba haka suke ba, har kwara hajiya layla yasan tunfil azal bata da mutunci, batason talaka, ta tsani talauci, ga girman kai, amma mahaifinsu Alhaji ubaid ba halinsa bane, Shi shaidane babansu mutumin kirkine amma tunda ya faɗa harkar siyasa ya canza shima, Ya rasa gane meke faruwa ne? Duk wannan badakalar da aka sha Benazir bata sani ba, ko awaya inta kira su don su gaisa ko suka kira donsu gaisa da ita babu wanda ya taba gigin faɗa mata.
don wlh da ace ta sani zasu sha ruwan mamaki saboda masifarta, har hajiya layla data gado shakkarta take ji, zata tsayama shureim ne kuma babu wanda ya isa ya ɗaga ma yarsa yatsa agidan.
Shureim harya fara tunanin sun hakura, ganin kwana biyu basu bi takanshi ba, hakan ba karamin dadi yayi mashi ba, ashe wata wutar bala'en ce zasu kunna mashi.
Alhaji Ubaid yasa aka kulle mashi bank account dinsa, Ya hana shi abincin gidan shi, duk wani abu da yayi mashi a matsayin uba saida ya kwace shi, hada key din motarsa ya kwace ya kasance baida ko sisi, ita kuma zainab da hajiya layla ta gano tana shayar da yarsa kuma tana satar abinci aboye takai ma shureim aikuwa tayi mata shegen duka da girmanta da komai ta kuma koreta daga gidan gashi bata da kowa a nigeria danginta da komai suna a egypt haka tayi ta gagari cikin gari.
Dr shureim ya shiga matsananciyar damuwa, da shi da yarshi suna a tsaka mai wuya, Ya rame yayi duhu, Itama jinjirar ba lafiya, ga yunwa da rashin bacci, kwana su ke yi idon su biyu har rokon su yayi kan su taimake shi kada ya rasa yarshi suka kiya saima su ka ce In har yana so su mayar masa da komai nashi da suka kar6a to ya mayar da Batool gidan marayu, kusan kullum sai ya jaraba kiran layin Uncle musa don ya fada masa halin da ya ke a ciki saboda yasan shi kadai ne zai goyi bayansa sannan ya taimaka masa amma ko ya kira layin a kashe ya ke samun shi, baisan ya zaiyi ba, ga Hajiya layla tace in har ya kuskura ya kira wani nata don ya taimaka mashi Allah ya isa bata yafe ba shiyasa ya kasa kiran Ammin su.
Baida wata mafita daya wuce ya gaya ma Allah, A karshe ya dauki yarsa yabar masu gidan.
Ko a jikinsu damuwarsu daya kada su rasa dan su amma donta yarinyar basu damu ta mutu ko tayi rai ba.
Baisan Ina zai nufa da ita ba, a wannan zamanin bakowane zai kula maka da dan ka tsakani da Allah ba, gashi bakowa ya sani a joss ba, saboda rabi da kwata na rayuwarsa a gurin amminsu yayita can Kasar egypt.
Tafiya ya ke yi Jikin shi ba kuzari, ya rungume babynsa a kirjin shi, Zuciyarshi cike fal da tunanin makomar rayuwar yarsa.
Tuntana kuka har ta gaji tayi shiru bacci ya ɗauketa, kwatsam aka fara ruwan sama tamkar da bakin kwarya, ya rasa ina zai sama masu mafakar da zasu zauna, Baiwar Allah tana tsaka da baccinta ruwa ya farkar da ita, Ta dinga tsala kuka ya rasa ina zai kaita don kada ruwan yai mata illa.
a karshe dai ruwan gaba daya akansu ya ƙare, Har dare ba adaina ruwan ba, saida daren Ya tsala ruwan Ya dauke a lokacin Ya ma fidda rai da ita saboda Zuciyarta ta daina bugawa Jikinta ya saki.
Anan ne ya yanke shawarar binneta, Saboda yaga baida wata mafita, in har ya barta wahala zata cigaba da sha, mutane ma ba zasu kyale ta ba za'acigaba da tsangwamarta ne tunda har iyayensa sun shegantata sun kirata da kazanta inaga mutanan waje?
Kowa ma zai samu kwarin gwiwar cuzguna mata ne idan ta girma, kwara ya saukaka mata ta huta itama, yasan in ta mutu Allah zaiji kanta.
A lokacin kwata kwata baya acikin hayyacin shi kamar ya fara zaucewa, Da hannayenshi Ya haƙa rami, Ya sakata a ciki ya kwantar da ita yayi mata addu'a, Yana kallon yatsun kafafunta dake motsi alamar bata mutuba, amma Ya rufe ido saboda bayason taci gaba da shan wahala Ya rufe mata kasa a jikinta ya daddale gurin da kafafuwan shi, anan ya zauna kamar mahaukaci yaci gaba da sambatu shi ka ɗai daga bisani ya suma akan kabarin ta.
Bayan sati Biyu da afkuwar lamarin, Dr shureim Ya farka a gadon asibiti, ya fara lalubar Yarsa Yaji shiru babu ita a jikin shi, Yabi ya rude hankalin shi Ya tashi, ya sauko daga kan gadon Yana fadin Ina yarsa! Ina fatimarsa! Ina batool dinsa! Tana Ina"?
Likitan dake dubashi Ya rurruke shi Yana kokarin kwantar masa da hankali, aikuwa ya bangaje shi da karfi har saida doc din Ya kife kasa.
Hajiya layla Da Alhaji Ubaid da ke a waje suna jiran tsammani, muryarsa da suka jiyo daga cikin dakin yana kwala ma batool kira yasa suka yi saurin shigo cikin dakin, yana ganin su ya nufe su yana tambayar su Ina yarsa take? Ta na ina? Hajiya Layla tace suma basu san Inda ya kai ta ba, abun da ya faru bayan ya bar gida suka baza jami'ae don su nemo shi, cikin sa'a jami'an suka tsintoshi a sume a gaban wata bishiya, amma basu ga yar shi ba, shine suka garzaya da shi asibiti, Yau sati biyu kenan baya a cikin hayyacin shi.."
sai da tayi wannan maganar ya tuna da abunda ya aikata ma Batool, wani irin jiri jirin tashin hankali Ya gani acikin idanun shi, ya dinga ambaton inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un kamar maganarsa zata kare! wai mike faruwa da rayuwarshi kamar wanda akayima jifa? bala'i daga wannan sai wannan.
Bai karasa jin zancen ba, Ya watsa da gudu Ya fito daga asibitin, suka biyoshi a cikin motar su, Ya dinga gudu kamar zai fadi kasa, har titi Ya hau mota ta kusa bankade shi Allah ne dai Ya tsare shi dakyar Ya gano gurin da ya binne ta, Ya zube kan gwiwowinsa, Jikinshi na kerma Ya haƙa ramin wani irin faduwar gaba Yaji ganin kasusuwanta, Harta mutu ta rube kashinta kadai ya rage, daddafe kanshi yai da tafukan hannayen shi saboda matsanancin ciwon kan da yaji, nan Take Ya yanke jiki ya fadi a sume.
A lokacin motorsu Alhaji Ubaid ta karaso gurin da yake, bayan sun fito suka taras da shureim rai hannun Allah, ga ramin daya haƙa abude sai kasusuwa birjik a cikin sa.
Basu tsaya bata lokaci ba, Alhaji ubaid Ya dauke shi ya shigarshi da shi cikin motar, suka koma asibiti da shi.
Tun daga wannan Lokacin shureim bai kara hankali ba, ya zama mahaukacin karfi da yaji, bayagajiya da sambatu yana fadin wayyo Allahana, na kashe Batool, da hannuna na binne ta acikin rami, Batool ta mutu ta zama kashi, Naci amanar da aisha ta bani, Allah bazai barni ba"
sai da takai ga ko sallah shureim bai iyayinta cikin nutsuwa, A lokacin Hajiya layla da Alhaji Ubaid sun ji tausayin shi sun kumayi danasanin tilasta mashin da sukayi akan yarinyar gayanan sun ja ya binneta ta mutu, shi kuma Ya haukace.
saida ya shafe wata daya bai dawo daidaiba, A lokacin Hajiya layla ta dawo da zainab mai aikinsu gidan tana daya daga cikin masu bashi kulawa duk da baya acikin hayyacin shi tayi kokarin tambayarshi meya faru? A haukan nashi Ya fayyace mata komai, tayi bakinci sosai sai dai bata ga laifin shi ba, saboda tasan me yaja mashi ya aikata hakan, haka ta dinga kokarin kwantar mashi da Hankali.
Ganin za6e ya kusa ga mutane sun fara yi masu surutu akan Halin da shureim ya shiga duk da kullan da sukeyi mashi amma an asamu wasu daga cikin ma'aikatan gidan sun fitar da sirrin su a boye, Hakan Yasa suka yanke shawarar tura shi Egypt, to a lokacin ya ɗan fara dawowa hayyacin shi tunkafin ma suje mashi da maganar ya tattara yanashi yanashi batare da saninsu ba ya tafi egypt saboda bayason zama tare da su sun fita aranshi, bayan ya isa ne ammin su ta kira hajiya layla ta sanar da su shureim yazo sai dai bata gane meke damun shi ba, ko magana ba ya iya yi mata.
Hajiya layla tace ta taimaka ta lallashe shi sannan ta bashi kulawa, ya samu tabin hankali ne sakamakon buguwar da kanshi yayi garin tukin mota ya yi accident har jinya yayi a asibiti.
Karya da gaskiya ta dinga fada mata har ammi ta yarda da maganarta tace in sha Allah zatayi kokarin bashi kulawa, hakan ba karamin dadi yayiwa hajiya layla ba.
Bayan komawarsa egypt ya gaza jure radadin da zuciyarshi keyi mashi kullumne sai yayi mafarkin Batool a cikin rami tana kuka, Hakan ya ƙara dagula mashi lissafi har takaishi ga fadawa harkar shaye shaye ya zama cikakken dan kwaya.
_(Kunji alakar dake atsakanin Ummi da su Benazir da kuma shiekh Imam malik, da kuma kaddarar datayi silar rabuwar su da ita, Bayan haka duk wata sa'insa da dr shureim yakeyi da iyayenshi bayan dawowarshi daga egypt a lokacin dayaji sauƙi ya dawo hayyacin shi ya kuma daina shaye shaye, wannan rashin jituwar ta samo asaline daga abunda sukayi mashi, yana yawan furtawa hajiya layla sune silar masifar daya shiga, ita kuma tace basu bane saboda lokacin da zai aikata bai yi shawara da su ba, bayan haka Hotunan da yake yawan kallo acikin wayarshi hoton mutun biyune! Hoton Aisha da kuma hoton Yarsa Batool daya ta6a dauka a wayarsa, ko bayan dawowarsa Nigeria bai yarda yarsa batool ta mutu ba, saboda a lokacin duk in zaiyi mafarki da ita araye yake ganinta ba amace ba, sannan kasusuwan daya gani a cikin kabarinta yana kokwanton bana mutun bane kamar na kare ne, bayan haka yana mamakin yarda tayi saurin zama kashi in two week da binne ta❗ shiyasa yake zargin akwai wata makarkashiya, amma daga baya ya hakura da tuhumar iyayensa Ya dauki dangana, Benazir bata tashi sanin abunda Ya faruwa ba saida ta baro gidan Uncle musa aranar ma tare da shi suka zo joss din da iyalinsa Sara da kanwarsa Hajiya laura dake zaune agidansa, anan sukaji komai daya faru abakin Alhaji ubaid sai dai bai bayyana masu ukubar da su ka yiwa shureim da yarsa ba, sun dai fadi laifin shureim na binne Batool da yayi, Uncle musa ya nuna rashin jin dadin shi har fada saida yayi masu akan sakacin da sukayi har suka bari shureim ya binne yarsa, Benazir kuwa saboda bakin cikin abunda shureim yayi ma Aisha da kuma yar daya binne saida tayi jinya gadon asibiti saboda tana da fusatacciyar Zuciya, bayan da aka sallame ta daga asibitin ne, ta taka taje har gidansu anila ta rufe ta da fada akan boye matan da tayi, anila tay ta kokarin fahimtar da ita cewa ba laifinta bane, Aisha ce ta hana ta sanar da ita saboda gudun abun da zai biyo baya in mahaifinta yaji ta fitar da sirrin, aranar saboda fadan daya kaure tsakanin Benazir da anila saida mami da abie suka rabasu dakyar bayan sunci uban juna, abie ya tambayi meya hadasu faɗa, anan Anila ta fayyace masu komai, hankalinsu ya tashi matuka basuji dadin abunda ya faruwa ba, Ita kuma Benazir acikin labarin da Anila tabada nan taji wani abu daya ɗaure mata kai tamau har ta kudiri aniyar saita gano koma wanene ya shiryama Aisha da yaya shurem makirci, saboda ta gane ba laifinsu bane, tuggune aka shirya masu, musamman ita Aisha da aka yi mata kullalliya tun a kasar germany, bayan Benazir ta dawo gida, batare da sanin kowa ba, ta shiga dakin zainab mai aikin su ta tsare ta da tambayoyi akan ta fada mata meye faru tsakanin shureim da iyayen su saboda taji aranta bakomai suka sanar da su ba, anan zainab ta fayyace mata komai, bayan ta baro dakin zainab din ta koma nata dajin ta dauki waya ta kira dr shureim a lokacin duk yana a egypt, cikin sa'a ya daga kiran bayan tayi ma shi ta'aziyar babaynsu da suka rasa ta bashi hakuri tare da lallashin shi, har ya tambaye ta agurin wa taji nan ta labarta ma shi komai, har tace yaya shureim meyasa baka sanar dani ba? bayan haka meyasa da suka matsa maka baka dauki yarinyar ka kaima Aneelerh don ta ruke maka ita ba? Yace mata baiyi tunanin hakan ba, saboda a lokacin baya acikin hayyacin shi komai ya faru, ta kuma tambayar shi meyasa me kira uncle musa ya nemi taimakonsa ba, yace mata ya kira amma baya samun shi, a karshe tace mashi kada ya damu, in sha Allah zata dawo mashi da farin cikin shi, a lokacin bai gane maganar ta ba, har dai su ka yi sallama da juna Sauran bayani game da abun da ya faru zamu ji ne abakin wanda ya dace muji👍)_
Gaba ɗaya suka bita da kallo yayin da take ƙarasa saukowa daga kan stairs ɗin ta nufe su Jikinta na 6ari yayin da hawaye ke cigaba da wanke fuskarta.
cikin raunanniyar murya dr shureim ya furta"Aisha dama Kina nan"!
Muryar mutumin da yai silar tarwatsa rayuwarta, tun kallo daya da tayi ma shi tayi saurin kawar da idanunta akan su Benazir.
Anila data gama rudewa tace"Aisha kece dagaske Nake Gani? Aisha dama Kina nan da ranki da lafiyarki baki ta6a tunanin ki waiwaye mu ba? ko awaya baki taba kiran mu ba, ko mun kira bama samunki! kullum layinki a kashe! aisha Kinsan Irin radadin danaji saboda tafiyarki? Laifin me mukayi maki Aisha dayaja har Kika manta damu arayuwarki, kika zabi kiyi nesa damu bayan alkawarin da mukayi ma juna duk runtsi duk wuya zamu kasance atare, Why Aisha? Kinbar mu da zullumin ina kika tafi? Kina araye ko kin mutu? Awani hali kike Ciki...."?
Kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya kwace mata kamar ranta zai fita.
Idanunta akan na Aisha wadda gaba daya ilahirin jikinta rawa ya ke yi kamar mazari, ga hawayen dake yar tseral kan kuncin ta.
Cikin shesshekar Kuka Benazir tace"baki kyauta mana ba Aisha! Kinci amanar amintakar mu, a zatona In matsala ta same ki nice mutun ta farko daya kamata ki fara tuntuba sai bakiyi hakan ba, tsawon shekara goma sha takwas baki waiwaye mu ba, ban ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zatazo ki juya mana baya ba, sai gashi tazo Aisha.."!
Kasa karasa maganar tayi saboda zafin da zuciyarta tayi mata ta fashe da kuka, Taj dake ta kallon su duk da baisan me ya faru da su ba, jikin shi yayi sanyi kawas, zuciyarshi ta kwaɗaita da son jin labarin Alakar dake a tsakanin su, Ummi tana ƙarasowa gaban su Benazir da Anila suka rungumeta kamar zasu mayar da ita cikin su, Jikinta ne yayi sanyi lakwas tausayin junansu ya kamata, they had deeply missed each other, more than words could express cike da sanyin jiki a hankali ta daura hannayenta akan bayansu, suka haɗa kawunansu Jikin na juna suna ta kuka babu mai lallashin wani, idanunsu arurrufe sai ruwan hawayen da ke shararowa ta cikin su.
"Aisha, ashe da rabon zan sake ganin ki a rayuwata"? Ya faɗa yana kallonta har time din bata raba jikinta daga nasu Benazir ba, tsawon mintuna kafin a hankali suka raba jikinsu daga na Juna.
Komai daya faru arayuwarta take tunawa, gani take kamar a yanzu komai ke faruwa, Kallon kallo suke jefawa Junansu tsakaninta da Anila da Benazir, sunyi mamakin haduwar bazatan da sukayi.
Taj dai Ya rasa gane takan maganganunsu, duk yabi ya rude sai binsu da kallo yakeyi ..
Dr shureim duk ya Sha jinin jikin shi ganin kamar bata son kallon shi, fargabansa kada ace har yanzu bata yafe masa ba.
Lokacin da Idanunsu suka shiga cikin na juna, wani irin yanayi suka shiga mai wuyar fassaruwa, tayi mamakin manyantakarsa, ba kamar yadda ta tafi ta barshi ba, Ya ƙara girma ya kuma ƙara kyau, su ma sunyi mamakin Sauyawar da Aisha tayi, ta zama babbar mace, dirin jikin nan nata yana nan ya ma kara ninka na da.
Dakyar ya iya furta"Aisha, na gaza yarda cewa kece nake gani, dan Allah ki yi min magana ko na gasgata kaina" Ya faɗa idanunsa cike tab da kwalla.
"Nice ya Shureim..." bai jira ta karasa maganar ba, ya furta "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! ya ambaci hakan Yafi sau a kirga kafin ya zube kan gwiwowinsa tare da daura goshinsa kasa yayi sujudusshukur cikin harshen larabci yake yiwa Allah kirari tare da hamdala saboda bayyana masa Aisha da yayi,.Lamarinsu Ya daurewa Taj kai Ya rasa gane meke faruwa, sun bar shi a duhu.
Mikewa yayi ya mayar da duban sa agare ta, Cikin karyayyar murya dr shureim Yace"ba irin neman da banyi maki ba, Allah bai nufa zan ganki ba, har yau bandaina kallon hutunanki ba, kuma har yau bandaina jaraba kiran layin wayarki ba don inji ko zai shiga amma ban ta6a samun ki ba Aisha, Kin manta damu, amma ni ban manta dake ba, You're always in my nightly prayers"
Lumshe Idanunta tayi tare da bude su A hankali kan fuskar shi, Ji yake kamar yayi hugging din ta ko ya samun sassauci nadaga abunda Zuciyarshi ke ji a game da ita, Sam sun kasa Daina kallon juna, ita kadai tasan me take ji
"Dan Allah Aisha ki bude baki kiyi magana ko munji sanyi a cikin ranmu" Aneelarh ce ta fada tana share kwalla.
Numfasawa tayi kafin ta furta"Ya shureim Where's my baby, ina Fatima Batool dina? Has she grown up? Is she attending school? Have you told her about me? Does she know about me?"
Gabansu ne Ya faɗi rass! gaba daya suka sha jinin jikinsu, Da jin abunda tace sun fahimci bata su take ba, Yar da ta bari itace aranta.
Sunkuyar da kanshi yai kasa sam Ya kasa bude baki Ya furta kalma saboda fargaban halin da zata shiga! Hankalinta ne Ya tashi jin yayi shiru bai furta mata kalma ba.
"Ya shureim kayi shiru bakace komai ba? Inason ganin ta fiye da komai na duniyar nan! Nasan yanzu ta girma, a lissafina zata kai shekara goma sha takwas...."
bata ƙare maganar ba, ganin hawaye na shararowa kan kuncinsa, aruɗe ta dubi su Benazir daga yanayin fuskarsu ta fahimci wani abu ya faru.
"Benazir, Ina fatima na? Nasan kin kula min da ita, saboda na yarda dake, nasan ba zaki taba bari jinina ya wulakanta ba, dan Allah ki fada min ina take? Inason naganta! Ku kai ni gurin ta! Sunkuyar dakai kasa Benazir tayi, idanunta cike tab da kwalla.
Hankalin Ummi ba karamun tashi yai ba, hannayen Anila ta ruko a cikin nata..
"Anila, nasan ba zakiyi min karya ba, pls ina babyna dana barma ya shureim? Keda Benazir wanene Ya shayar min da ita uhm? Waye ya raine ta har ta girma? Na yarda daku nasan ƴata tana samun kulawa a gurin ku, Dan Allah ku fada min tana ina"?
Kamar mai faman da tabin hankali, sam babu nutsuwa atare da ita, Yar ta kawai take son gani.
Gaba daya maganganun Aisha sun ruɗa Taj, sai binsu yakeyi da kallo daya bayan ɗaya, ya rasa gane inda suka dosa.
Dakyar ya iya furta"pls ku zauna, sai kuyi magana atsanake! Kukan Ya isa Haka, bana so inganku a cikin damuwa, duk da bansan meya hada ku ba"
"Daddyn Angel, kace suyi min magana Ina babyna take? Sunyi banza sun kyale ni suna ji ina magana"!
Tausayin ta ne ya kama Taj, yace"dan Allah ku fada mata Ina babynta ta ke"!
In a cool voice shureim yace"kiyi hakuri Aisha, fatima ta koma ga mahaliccinta tun bayan da kika bani ita, badajimawa ba ta rasu....."
kasa ƙarasa maganar yayi ganin yadda ta dafe kanta da tafukan hannayenta labbanta na kerma take ambaton Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un..
"Kiyi hakuri Aisha, wlh Yaya shureim yayi iyakar bakin kokarinsa gurin ganin ya ruke amanar da kika bashi, amma Allah bai nufa Batool zatai zawaicin kwana ba..."
Benazir bata ƙarasa maganar ba, Aisha ta soma ja da baya tana girgiza kanta, wani irin kuncine Ya mamaye zuciyarta, Taji zafin mutuwar yarinyar data kwalla fa rai akai, tayi azan ta girma har ta zama budurwa ashe ma ta rasu.
"Pls Aisha, Ki tsaya zamuyi maki bayani, pls, kiyi hakuri ki jure, mu ma munji zafin mutuwar ta, ba yadda zamuyi ne Allah ya riga daya kaddara faruwar hakan.."
Aneelerh da ta dauko maganar, bata kaiga dire ta ba, Aisha ta juya da gudu tana kuka kamar zatayi tuntube yayin da take taka stairs, cikin sauri suka bi bayanta sai dai kafin su karasa tuni ta shige daki ta kuma datse ƙofar.
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹
_*~....................................................................~*_
~___________________________________🌹✍️~
Around Ƙarfe 10 na safe, Kiran Chief Ya shigo wayar ta, a lokacin tana a zaune kan prayer mat ta nutsu tana yin karatun alkur'anin da ta buɗe akan qur'anic stand, bayan da ta kai aya miƙewa tayi daga kan Prayer mat din, ta ɗauko wayarta da ɗaura kan Pillow ta yi picking Call din tare da kara wayar a kunnanta.
"My babe, how're you? i hope you slept well "?
Sa'ilin da muryarsa ta ratsa kunnanta wani sanyi taji ya ratsa zuciyarta.
"I'm doing well, thanks hubby,
"Okay, Idan baki komai ki same Ni a part ɗina"
"Okay Sir" rejecting call din ta yi.
da sauri taje gaban prayer mat din ta rufe qur'anin, Bayan ta saka High heels dinta ta fuce ta nufi part dinsa.
yana a kishingiɗe kan bedmattress dinsa, single da short ne a jikin shi Ya mike kafafunsa yayin da idanunsa ke a lumshe kamar na mai jin bacci, yau tun da ya farka daga bacci Omar ke ta faɗo masa arai, saboda a duk ranar birthday dinsa Omar ne mutun na farko da ya ke fara turo ma shi happy Birthday greetings tare da Birthday gift, Omar baya so wani ya riga shi taya Chief murnar birthday dinsa, wannan karan Allah bai nufa za'ayi da shi ba.
Lokacin da ta karaso bakin Door room din, sau ɗaya tayi knocking kofar ta buɗe, sallama tayi mashi daga ciki tajiyo voice dinsa ya furta"Come In babe"
Walking slowly ta nufe shi ta dan tsaya daga gaban Gadon, idanunta akan fuskar shi still bai buɗe eyes dinsa ba suna a lumshe.
sumar kan shi tabi da kallo ganin hadadden ducktail haircut din da akayi masa, ya ƙara ƙawata kyawun fuskar shi, ya yi mata kyau daga gani yau akayi masa shi.
Sau uku tana gaida shi bai amsa mata ba, tayi azan bacci yakeyi amma sai ta tuna before ta shigo saida ya bata izni.
"My Chief, ko ka yi bacci ne? Nayi magana naji ka yi shiru, pls kayi min magana"
bata ƙarashe maganar ba, taji ya furta"kin bata min rai Unaisah, fushi nake da ke" Ya faɗa tare da buɗe idanunsa akan fuskarta.
Gabanta ne ya fadi adabarbace tace"I'm sorry ban fahimce ka ba, Meyasa ka ke fushi da ni? Laifin me nayi maka"?
Saukowa yayi daga kan gadon, hannun sa ruke da wayar sa, ya juya ya nufi tattausan rug din dakin sa, a ruɗe tabi bayan shi da kallo, gently ya zauna akan rug din tare da nuna mata gabansa da yatsan shi"sit here Babe"
jiki asanyaye ta zauna tana fuskantar shi, jikinta duk yayi sanyi ganin mood dinsa ba walwala.
Kasa jure kallon da ya ke yi mata tayi, slowly ta kawar da idanun ta gefe daya..
"Meyasa kika tsani mahaifiyar ki? Laifin me ta yi maki?
nan take bacin rai ya wanzu akan fuskar ta, her voice barely above a whisper tace"Because she doesn't love me, she hates me, That's why lokacin da ta haife ni ta jefa ni a cikin bathtub, sannan ta gudu ta tafi batare da ta sake waiwaye na ba...."
tun da ta fara magana ya nutsu yana kallon smooth pinkin lips dinta har saida ta kai aya tayi shiru tana jiran amsar shi..
"You were rude to her, banji dadin maganganun da kika gaggayawa mahaifiyar ki ba!" ya fada yana mai nuna bacin ran shi
"uwa uwa ce koda ta banza ce It's not acceptable to disrespect her!"
"Amma bata sona meyasa tayi watsi da ni"?
"Ki daina cewa bata sonki Unaisah"!
Da yar tsawa ya fada, har saida ta zare mashi gray eyes dinta hakan yasa shi sassauta muryarsa saboda baison ya daga mata hankali
"I know you're intelligent and thoughtful, Don't you think there's a reason your mother ran away from you? pls kiyi tunani ta haife ki a tsakar dare a cikin toilet ta kar6i haihuwarta da kanta, ta saka ki a cikin bathtub ta gudu daga gidan ba tare da sanin mahaifin ki ba..."
arude ta dube shi gabanta na faɗuwa
"Nasan bakomai kika sani dangane da tafiyarta ba, kamar yadda shima mahaifinki bakomai ya sani ba, rashin sani ne yasa kuke fushi da ita saboda kunyi tunani ta gudu ne saboda bata son zama da ku bayan ba haka bane....." gaba daya Unaisah ta rude da jin maganar shi.
Audio Recording din da ya ɗauka na Labarin Ummi da Benazir ya kunna mata a wayarsa, ashe ya yi recording batare da sanin su ba.
Tun da ta fara sauraran shi yanayin fuskarta ya canza zuwa rudani da tashin hankali, aranta ta ayyana dama Aunty Ummin su Malama ce? Bata taba jin mace mai tausayi da kamun kai da tsantsar ilmin addinin islama irin ta ba, baiwar Allah ashe kaddara ce ta yi silar canza rayuwar ta.
Hawaye ne suka cika idanunta tab, tsananin tausayin Aunty ummin su ya kamata, ga wani kaunarta daya shiga zuciyarta, abun daya yafi ta6a zuciyarta a cikin labarin Hukuncin da sheikh Imam ya yanke ma ta, da kuma binne yarinyar da wan mahaifiyar yayi, Abun ya ta6a Zuciyarta sosai, muryarta na rawa tace"ban ta6a jin labarin daya taba zuciyata ba, irin wannan, kuma banyi zaton sheikh Imam zai iya yin hakan ba, a matsayin shi na malami, Aunty ummi ta bani tausayi ita da ya ya shureim, amma banji dadin binne yarinyar da yayi ba" muryarta na rawa ta ƙarashe maganar.
"Yanzu inaso ki fadamin, Kafin ki saurari wannan labarin Wani irin kallo ki ke yi ma Aunty Ummin ku"?
tamkar zata fashe da kuka tace"tun kafin na santa, Dr. Laura ta america ce ta fara bani labarin ta, tace min karuwace ita, bata da kamun kai, kuma tayi kaurin suna a america, kawai dai ba mutuniyar kirki bace, amma da zama ya hada mu da ita sai na gane tana da sauƙin kai, ba kamar yadda na zata ba, a ranar da ta fara yin karatun al'qur'ani agabana, na razana sosai, har nayi tunanin meya sa bata amfani da saninta take aikata sabon Allah ashe ba halin ta bane, kaddara ce ta afka mata...." ta karasa maganar cikin sanyin murya.
"Yanzu fada min meyasa ki ke yi mata kallon mutuniyar banza"!
"Rashin sani ne,"
Gyaɗa kai Chief yayi"haka zalika, itama mahaifiyarki rashin sanine yasa ki ke tunanin ta gudu ta bar ki saboda bata sonki, bayan ba haka bane, itama bada son ranta ba"
waro idanu waje tayi, jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, ni na hana mahaifinki yayi maki magana, saboda na daukarwa mommynki alkawarin zan sasanta tsakanin ki da ita, tun shekaran jiya da su ka zo bayan sun tafi, a daren ranar mommyn ki ta kira dad din ki, ta fada masa komai da ya faru da ita, har ma sunsasanta tsakanin su saboda ya gane ba laifin ta bane, may be bai fada maki ba, saboda nace yabar komai a hannu na"
ya ƙarasa maganar tare da kunna mata audio din da Taj ya tura masa ya mika mata wayar
"Calm down and listen, zaki samu amsoshin tambayoyin da kike nema a gurin mommyn ki..."
yatsun hannunta na kerma ta kar6i wayar daga hannunsa tare da kangata saitin kunnanta don ta samu damar ji da kyau.
A hankali Chief ke kallon fuskarta yadda take zazzare gray eye balls dinta tare da moving lips dinta ba ƙaramin tafiya yake da shi ba.
Bai aune ba Yaga ta zabura ta miƙe, Jikinta na kerma yadda kasan wadda Electric shock Ya kama, wayarsa dake a hannunta sai kerma take saboda jikinta dake kakarwa, Dafe kanta tayi da tafin hannunta, Labbanta na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un"!
Ganin ta juya arude yasa shi sauri kiran sunanta"Unaisah Ina zaki je ne"?
Yarfa hannun ta ɗaya tayi, ta kamo gaban hijab din jikinta ta soma fifita da shi saboda zafin daya taso mata gaba daya ta rude.
"Calm down babe, dawo ki zauna muyi magana mana"
Calmly ya faɗa idanunsa akan fuskarta dake fitar da gumi kamar babu A.c a dakin.
Lokaci daya ta fashe da kuka tana fadin wayyo Allah na, na shiga uku, ina son naga momnyna, Ina son in nemi ya fiyarta, Inaso na bata hakuri! i love her, i really wanna see her..."
ganin yadda ta daga hankalinta yasa Chief Ya miƙe tare da kar6ar phone din gudun kada ta kayar da ita kasa, Cikin boxer pocket dinsa Ya zura phone din, kafin ya tallabo fuskarta da tafukansa.
"Kalli cikin idanuna Unaisah" dakyar ta iya buɗe idanunta da suka cika da hawaye, cheeks dinta sunyi jawur da su.
"Ki daina kuka, Ba laifin ki bane Unaisah, rashin sanine yajawo hakan, nasan yanzu kinyi danasani, saboda kin gane gaskiya" Jinjina mashi kai tayi alamar Eh.
"Ki gode ma Allah Unaisah, mommyn ki jaruma ce, I've wondered who gave birth to this remarkable child, cos you're different, with a sharp mind and loving, Ina alfahari da mommynki, saboda tayi bajinta, tayi abunda ya cancanta a jinjina mata..."
tun daya fara magana ta ɗan sassauta da kukan sai shessheka da ta ke yi, Kalaman Chief Sun ƙara sa ta jin wani irin masifaffan son mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan.
"Uncle din mommynki Shine silar komai daya faru, shine munafukin dake ƙulla makirci atsakanin su, bayan haka muna zargin yana da sa hannu a kungiyar matsafan kurkukun kaddara, yanzu haka mun fara bin diddiginsa nan bada jimawa ba zai shigo Hannu"
In a low voice tace" I think he's the one who sacrificed me, kuma ina zargin yarinyar Aunty Ummi daya dauka in dai basu kashe ta ba, zai iya yiwuwa tana a cikin fursinonin kurkukun kaddara, watakil ma tana atare da mu"
"Tunanin mu yazo ɗaya Unaisah ..."
"Amma, Ina jin fargaban mommy na taƙi kula ni"
"Zata kula ki Unaisah, a yanzu haka jiran ki ta ke yi, na fada mata zaki neme ta da kanki, ki kira ta awaya ki bata hakuri sannan ki nemi yafiyarta hakan zaisa taji dadi acikin zuciyarta"
cike da zumudi ta juya zata tafi yai saurin dakatar da ita"ina zaki je"
Fuskarta a yamutse tace"i wanna call her"
kayataccen murmushi Chief ya dan saki"Okay, ga kayanan ki tafi da su"
ya fada tare da nuna mata suitcases din dake ajiye gaban Couch, arude take kallon su a lokacin harya juya ya nufi ƙofar da zata kai shi gym room dinsa Ya shige ciki.
Kasancewar akagare take da ta kira mommynta, bata tsaya yin wani dogon tunani akan akwatinan ba, cikin sauri ta nufe su, taja handle din daya ta fuce da shi.
______________________________🍁✍️
Tana shiga Bedroom dinsu, ta ɗaura akwatin saman gadon su, Ta dauko wayarta dake ajiye kan bedside drawer ta danna ma layin da tayi saving da Aunty Benazir kira, saboda zumuɗi sam ta kasa zama sai zarya ta ke yi a tsakar dakin, almost 3 times tana kira ba'a picking, jikinta ne yayi sanyi saboda ta yi zaton fushi take yi da ita shiyasa bata daga ba.
_Message ta tura mata mommy, dan Allah ki daga kirana akwai abun da nakeso In fada maki_
Ba'afi minti biyu data tura sakon ba, sai ga kiran Aunty Pretty ya shigo wayar ta, kwata kwata batayi farin ciki da ganin kiran ba, saboda a halin yanzu bata son ganin kiran kowa in ba na Aunty Benazir ba, har ya katse batayi picking ba, sai da aka ƙara kira, ta haɗe rai ba annuri ta ɗaga kiran tayi shiru batayi mata sallama ba.
On the Other hand jin tayi Shiru yasa Benazir tace"daughter, kin bukaci kina son yin magana dani, kuma na kira kinyi shiru"?
Waro idanu waje ta yi saboda rudanin da ta shiga, sai da ta fara janye wayar daga kunnanta ta duba number ɗin da kyau taga ta aunty pretty ce da sauri ta shiga messages ta duba number ɗin data tura ma saƙon, taga ba kuskure tayi ba Aunty Benazir ne ta turamawa amma ya akai Aunty Pretty ta kira ta sannan tace taga sakon ta?
Nan take zuciyarta ta bata amsa da cewa zai iya yiwuwa mutun ɗayane ke amfani da layi biyu, Ras taji gabanta Ya dan faɗi, labban na kerma ta furta"Aun.. Aunty pretty, dama kece Mommyna Aunty Benazir"?
Sautin Dariyar Benazir ce ta ratsa kunnanta, cike da nishadi tace"ni ce mana, layin da kika turama sako na Uncle din ki ne da nake amfani da shi, bayan na kar6i contact dinki agurin Aneelerh, ina saka number din Unexpected naga sunan da nayi maki saving ya bayyana akan screen din wayata nayita mamaki nace ashe da daughter dina nake waya batare da sanina ba, daga nan na yanke shawarar kiran ki da layin ya shureim saboda bana so ki gane ni ce...."
wata irin kunyace ta kama Unaisah, tayi shiru tana zare idanun ta.
"Kin daina fushi dani..."? Benazir ce ta tambaya akagare da son jin amsar ta.
Kwatsam taji ta fashe mata da kuka kamar ranta zai fita, Hankalin ta ba karamin ta shi yayi ba, muryarta na rawa tace"Unaisah lafiya kike kuka? Meke damunki ne? Waya taba min ke"?
Cikin shesshekar Kuka tace"Forgive me, Mommy I realize my mistake I apologize for hurting you, I love you more than anything in this world, I want Daddy to remarry you and bring you back to me, cos I need you in my life...."
tana jiyo muryar Benazir dake ambaton Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya nuna mini ranar da nake ta jiran zuwanta Unaisah dagaske Kina sona yanzu? Kina son mommynki ta dawo kusa dake"?
Jinjina kai tayi kamar tana agabanta tace"seriously, I love you so much, i want you to take care of me, I thought since Daddy had done everything for me, bazan bukace ki ba amma ayanzu na gane ke ce cika makon farin cikin rayuwata, bani da tamkar ki har abada..."
Bata karasa maganar ba sautin kukan Benazir ya cika kunnan ta, hankalinta ne ya tashi da rawar murya tace"dan Allah ki daina kuka, bana son ji, pls, Allah zaiyi fushi dani idan kina kuka akaina..."
cikin shesshekar murya Benazir tace"ba kukan bakin ciki bane Unaisah, kukan Farin Ciki ne, kin faranta raina, Kin sani jin kamar nafi kowa farin ciki a duniyar nan, yanzu bani da sauran damuwa, Mijina ya daina fushi dani, yata ma ta daina guduna, Alhamdulillah..."
"Ba ki ce kin yafe min ba"?
Benazir bata bata amsar tambayarta ba, sai taga ta canza call din zuwa Video Call, picking tayi lokacin da idanunta suka sauka akan fuskar Benazir wata irin kunyace ta lullube ta, fadawa tayi kan gado wayar na a hannunta tayi saurin janyo pillow da dayan hannun ta lullu6e fuskarta tana dariya, itama Benazir din dariya take ma yi.
Cike da zolaya tace"rasa kunyan 6eran taka, Lemme see your face, kin tuna karyar da kikai min, Kina zuwa school sannan a kano kike da zama uhum"? Ƙyalƙyalewa tayi da dariya ba tare data furta kalma ba.
"Oh ni Benazir, mamaki nake wai ni ce na haifi zankaɗeɗiyar balarabiyar nan tubarkalla kamar hurul ain"
fashewa ta kumayi da dariya, Hakan ba karamin faranta ran Benazir ya yi ba, dama tayi ne donta saka ta farin ciki ganin ta damu sosai.
"Aneelerh ta bani labarin kuruciyarki, yadda kasan ni agari, nima haka nayi kuruciyata amma fa ban kaiki rashin ji ba, gaskiya ni ban taba sa an kai daddyna cell ba" ta fada tana kallon Unaisah data kare fuskarta da pillow sai dariya ta ke yi.
"Taya zamuyi magana bayan kinki bari inga fuskarki uhm? Pls let me see your face, " A hankali ta zame pillow din, ta matso da screen din wayar saitin fuskarta suka zubawa juna ido gwanin ban sha'awa.
"Wow, ƴata tafi ta kowa kyau, launin idanunki irin na Ammin mu ne ta eygpt, kinsan me har yanzu tana araye ta tsufa tukuf..."murmushi Unaisah ta yi tana faman sauke ajiyar Zuciya.
"Fadamin waya sa ki kirani awaya"?
"Chief ne, shine ya fada min komai daya faru da ke"
"Mutumin kirki, ya taimake ni, Allah ya saka sa masa da mafificin Alkhairin sa"
Ta amsa mata da ameen..
"Kina da saurayi" cike da jin kunyarta tace"shine ai"
"Wa"?
"Zan fada maki ba yanzu ba"
"Okay, abun da nakeso dake, Ki manta da komai daya faru, na yafe maki Unaisah, kuma ba laifin ki bane, rashin sanina yasa kika ƙulla ce ni aranki, amma ni ban ruke ki a cikin zuciyana ba, in ma akwai mai laifi to ni ce Unaisah, duk da nima bada son raina na tafi nabarki ba, amma naji dadi da ban tafi dake ba, watakil da yanzu baki araye tunda bana acikin hayyacina zan iya jefar dake akan titi...."
kasa karasa maganar tayi saboda kukan dake kokarin balle mata, cikin karyayyar murya Unaisah tace"pls kada kiyi kuka mommy, bana son ganin hawayen ki,..."
jinjina mata kai tayi"bazan yi ba tun da bakya so....." sun dade sunayin waya akalla sun shafe awa daya da rabi a hakan ma basu gaji da yin wayarba, sai da Benazir tayi mata alkawarin zata zo gidan tukunna ta hakura su ka yi sallama da junansu.
miƙewa tayi tsaye kan gadon, ta dinga tsalle kan matress din fuskarta dauke da murmushin Farin ciki.
Shigowa dakin Batool tayi, jikinta asanye da kayan bacci riga da wando ko mayafi babu akanta.
burki ta ci ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda Unaisah ke daka Tsalle tana dariya kamar karamar yarinya.
Baki asake da mamaki tace"Sis Meke damunki ne? Meyasa kike yin tsalle akan katifa sai kace karamar yarinya"?
Bata amsa mata ba, ta duro daga kan gadon ta nufe ta, tare da rungume sosai, Batool duk ta rude ta rasa gane kanta fatanta Allah yasa ba tabin hankali ta samu ba.
"Sis meyasa ki farin ciki ne uhm"? Ta fada tare da raba jikinta daga na Unaisah
Fuskarta dauke da annurin farin ciki tace"Batool ki tayani farin ciki, na gano wacece mommyna wadda ta haife ni" waro idanu Batool tayi"are you serious? Ta ina? Wacece"?
Murmushi tayi"Aunty Benazir, mai kama dake, Itace Mommyna, kuma itace Aunty pretty da mukeyin waya da ita.."
farin ciki ne ya lullu6e Batool"ina tayaki murna sis, Kinji dadin rayuwarki, Mommynki da daddynki suna nan, Baki rasa kowa naki ba..."
maganar Batool ta taba zuciyarta, jikin ta ne ya yi sanyi sosai, tsananin tausayinta ne ya kama ta, su da basu taba sanin dangin su ba.
"Sis amma kin yafe mata laifin da tayi maki ne? Kuma taya akai kika gane itace mommynki uhum"? Ta fada akagare da son amsar ta.
"Shekaran jiya bana baki labarin Aunty Benazir da Aunty Aneeleeh sunzo ba"?
"Eh na tuna, ay time din na fada maki aunty ummi bata jin dadi, atare ma bacci ya dauke mu adakin ta.." ɗan girgiza kai Unaisah tayi"baiwar Allah, Aunty Ummi, ta bani tausayi, naji labarin rayuwarta ashe kawaye ne su, da ita da mommyna da Aunty Anila, kaddara ce tayi silar raba su, nima mommyna bada son ranta ta gudu tabar ni ba" ta fada fuskarta. amarairaice.
"Waya fada miki pls, nima ina son ji"?
"Zan baki labarin komai daya faru amma ba yanzu ba, saboda nasha kuka wlh har zazzabi nake ji a jikina, amma da nayi waya da mommyna sai naji sauki acikin zuciyana.."
badan taso ba tace"Toh sis zan jira ki, wlh har na kagara naji, kuma ina ƙara tayaki murna Unaisah"
"Nagode my own sis,"
"Lah! Akwatin wanene wannan"? Ta faɗa tana nuna suitcase din da Unaisah ta aje, bata jira amsarta ba ta nufi akwatin dake ajiye, ta zauna daga gefen gadon ta soma kokarin bude shi tana fadin"wallahi yayi kyau sosai..." sai da tayi maganar Unaisah ta tuna da akwatin, da sauri ta dawo gaba gadon ta zauna, suka saka akwatin a tsakiyar su..
Kasa bude akwatin tayi, dakyar Unaisah ta buɗe shi waro Idanu waje su kayi ganin jigunanun Laces dinkakku tare da Materials da atampopi hada shaddoji, ɗaɗɗaga kayan suka somayi bakunansu sun ki rufuwa saboda mamaki.
"Dan Allah waya baki su"
"Ɗazu da chief ya kirani naje dakinsa shine yace min in dauka, dama ya kar6i awona ran nan, amma naji dadi wlh dama bamu da kayan hausawa acikin kayan mu..."
sai murna ta ke yi tana yaba kayan, Batool dai jikinta yayi sanyi ganin kamar kayan na Unaisah ne kadai banda nata a ciki.
"Bai ce hadani ba"?
Da budar bakin Unaisah sai cewa tayi"Anya, kamar nawa ne ni kadai, amma kada ki damu zamu dinga sanyawa atare, ai abuna naki ne"
mood din fuskarta kamar bataji dadi ba, in a cool voice tace"a'a ni bazanyi amfani da su ba, naki ne saboda ke ya siye su, kada ki damu..."
ta fada tare da saukowa daga kan gadon, ruko hannun ta Unaisah tayi"meya faru ne naga kamar bakya farin ciki"?
Murmushi ta kakalo kan fuskarta"don't mind your self, Am ok, inaso zan je dakin Aunty Ummi"
tana ƙarasa maganar ta juya ta fuce daga ɗakin, Unaisah bata kawo komai aranta ba, ta maida kayan cikin akwatin kafin ta datse shi tare da ruko handle dinsa, ta sauko ta fito daga dakin ta nufi dakin Aunty Ummi.
_💘UMMIN AMERICA💘_
Fitowa tayi daga Toilet jikinta sanye da bathrobe, wayar ta dake akan gado sai ringing takeyi, da zarar kiran ya katse wani ke shigowa.
Hararar wayar tayi bata da niyar daukarta.
Sai da ta gama shirya kanta cikin Jallabiya, kafin ta dauki wayar tare da yin picking ta kara a kunne.
Kakkausar muryarsa ce ta ratsa kunnanta " Ummi, why haven't you been answering my calls for two days? I've even sent you messages, but you didn't respond."
Batasan ya akai ta tsanci kanta da jin haushin shi ba.
"Bana jin dadi ne, wayar ma ban san inda na jefa ta ba, sai yau na dauko ta"
"Okay, ya jikin naki"
"Da sauki"
"Inason ganin ki, zanzo da anjima.."
bai ƙare maganar ba ta katse shi da cewa"Sorry, basai ka zo ba, ka bari idan na samu time zanzo gidan ka"
muryarsa da mamaki yace"Ummi kin canza min, wani abu ya faru ne"?
"A'a ba abunda ya faru, kawai bana so kazo nan dinne,"
"Okay.." ya na faɗa yai rejecting call ɗin.
nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, har zata aje wayar saiga kiran dr shureim ya shigo wayar, tun shekaran jiya da suka zo yake ta kiran ta, sau daya ta taba picking tana jin muryar shi ta katse kiran amma tayi saving contact dinsa.
A kalla tana da missed calls dinsa kusan dari da hamsin, daga shekaran jiya izuwa yau, ga messages da ya ta turo mata na ban hakuri da rarrashin ta akan rashin da su ka yi na yar su.
Wi-pi din wayar ta kunna kafin ta shiga whatsapp, ta bude chat din shi, A hankali ta zauna daga gefen gadon ta soma karanta last message da ya tura mata.
_Aisha ba zaki yafe ma yayanki ba? Pls bani baki tausayi, tsawon shekara sha takwas ina dakon soyayyarki a cikin zuciyata, dan Allah ki taimaki bawan Allahn nan, gani da ƙoƙon barata agare ki, ko bacci bana iyayi saboda tunanin ki, nasan da babynmu tana araye watakil inci albarkacin ta, saboda kina son ta, amma baki son mu sake samun wata atare? Kiyi tunani Aisha ni kadai ne zan iya baki irin ta_
A hankali ta furta"nasani ya shureim, kai kadai ne zaka iya bani irin ta, tabbas ina so na sake haihuwar mai kama da ita, but I can't marry you! I've already told you I won't marry the man who raped me, I can forgive you, but I can't marry you, even though I still love you amma meyasa kayi mini haka?
jefar da wayar tayi kan gado kafin ta kifa kanta jikin pillow, kuka take ji sai dai hawayen sunƙi zubowa, sai dai takama yin kukan zuci.
"Aunty Ummi" cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Unaisah, Da sauri ta shanye damuwarta ta mike zaune tana kallon Unaisah dake shigowa ciki hannunta ruke da akwatin ta.
"Ina Batool din? Tace min zatazo gurin ki, "
"Batool bata shigo nan ba, akwatin wanene wannan"? Ta fada tana nuna akwatin hannun ta
"Kayan da Chief ya siya minne"
ta fada tana murmushi, Ummi tace"Masha Allah, amma na taya ki murna, gaskiya Chief yana ji dake.."
ta fada yayin da take buɗe akwatin data kar6a a hannun ta, tayi mamakin kayan masu kyau da tsada.
______________________________✍️
bayan ya kammala motsa jikin shi, ya fito daga Gym room din ya nufo dakin sa, hannun shi ruke da bottle water me sanyi, ya rataya farin towal akan shoulder dinsa, kwata kwata babu riga a jikin shi sai Boxer short dinsa, gaba daya jikin shi gumi yake fitarwa..
Harya bude murfin robar zai kai baki da niyar yasha ruwan, wayarsa ta doka alert, dan dakatawa yayi ya nufi wayar dake akan couch, ya danna unclock button, bai jira yaga wanene zai shigo ba ya juya baya ya kanga bottle din abakinsa ya fara shan ruwa.
can cikin kunnansa yajiyo takun tafiyar mutun, abun ya daure kansa aransa ya ayyana wanene ya shigo masa daki batare da sallama ba? A sukwane ya juyo don yaga wani isasshen ne, da dan mamaki akan face din sa ya ke kallon ta, tayi tsaye idanunta na kallon floor, kamar mara gaskiya sai wasa takeyi da yatsun hannunta..
*~_____________________________////////////////////🔥🌹~*
*Daga Alkalamin Boss Bature🔥🫰*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*[14/10, 6:06 PM] Amin@ M Yusuf Yol@: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹
_ *The Unexpected Guest *_
~___________________________________🌹✍️~
Da ace wani ne ya shigo masa daki haka zai tuhumesa ne amma da yake yasan wacece ita, da irin rayuwar da tayi sai bai damu ba.
"Me ke damun ki"? Ya fada ganin kayan baccin jikinta sunyi squeezing, ga sumar kan nan nata a haukace ba gyara.
Sam ta kasa bashi amsa, wani irin shakkarshi take ji, batasan ma ta shigo dakin ba, saboda bata a hayyacin ta,
Nufo ta yayi jikinta na bari ta juya zata fuce, tana ruke handle din kofar taji ta adatse, wani irin faduwar gaba taji, ta dinga jan handle din amma taki buɗewa kamar zata saka kuka.
Mamakine ya kama shi, ya rasa gane kan ta, aransa ya ayyana ko dai tana da tabin hankali? If not why zata shigo dakinsa ba sallama kuma yayi magana tayi shiru, sannan ya nufo ta tana kokarin guduwa"?
Daga bayanta ya tsaya yana kallon yalwatacciyar suman kanta data cika bayanta.
"Fada min meke damun ki? Baki da lafiya ne? Ai ko ki akayi guri na? Ko kinzo ne don ki gaishe dani'?
Cikin rawar murya tace"am sorry, bansan na shigo ba, ba wanda ya aiko ni, "
"Look, ni nasan ba hakanan ki ka zo ba, dole akwai abunda ya kawo ki daki na, just Calm down and tell me "
Batare data juyo ta dube shi ba tace"ka ba Unaisah akwati, ni baka bani ba kuma inaso"
Murmushin gefen fuska ya saki"Akwati biyu nace ta dauka, daya nata daya naki"
"Ai daya ne tazo da shi, kuma tace nata, ita kadai ka ba mawa"
juyawa yayi tare da kallon inda ya ajiye akwatinan daya ya gani.
"Oh, ina tunanin ta manta bata ji ni dakyau ba..." ya juya ya nufi akwatin ya janyo handle dinshi ya mika mata"ga naki kema" maimakon ta juyo ta kar6a sai ta mika mashi hannun ta ta baya don ya bata.
"It's improper ki juya mun baya ina magana, if you wanna me to give it to you, Turn around and face me"
sarai ya fahimci shakkar shi take ji, kuma tana da kunya.
Dakyar ta juyo ta fuskance shi idanunta na kallon floor.
dayasan haka zai ganta inya matso kusa dabai ce ta juyowa ba, saboda gaba daya shatun nipples dinsa sun fito sosai ta jikin rigar baccin ta, bata saka bra ba, da sauri ya kawar da idanunsa gefe ɗaya, Ya mika mata akwatin hannunta na kerma ta ruƙe handle dinta cike da zumudi ta juya zata fuce ya dakatar da ita.
"Kar in kuskura in ƙara ganin kina yawo babu mayafi akanki! Ki dinga suturta jikinki dakyau"
gabanta na faduwa ta amsa mashi da toh, Ya raba ta gefenta Ya danna code din kofar ta buɗe da sauri ta fuce, tsayawa ya yi yana kallonta yayin da take jan akwatin ta nufi stairs, sai dadi take ji har zukunnawa tayi kan stairs ta shasshafa jikin akwatin batasan yana kallonta ba, sai da tagama kalle shi ta mike cike da zumudi ta karasa sauka down ta nufi dakinsu don taje ta gwado ma Unaisah itama ya bata suitcase.
Sakin kofar yayi ta yi locking kanta, har zai juya idanun shi suka sauka akan siraran gashin kanta da ya kakkaba a kan floor, wasu irin dogaye masu kanannaɗa.
juyawa yayi ya nufi tissu box dinsa dake ajiye gaban mirror ya yago tissue ɗin ya dawo ya zukunna gaban gashin Ya daura tissue din Ya nannaɗo su aciki, Kafin ya mike ya nufi drawer, ya bude Ya sanya Tissue din a ciki.
______________________________🔥🔥🔥
Bayan Kammala Sallar Juma'a around ƙarfe biyu da yan mintuna, Hamshakan Motoci Suka fara tururuwar shigowa Obie Estate, bakowane a cikin su ba face yan uwa da Abokanan Chief Owais yan team dinsa na isod tare da U.s Armies.
Raba hanya motocin su kayi wasu suka nufi Gidan Baba Obie yayin da wasu suka nufi Gidan Chief Owais..
*CHIEF OWAIS🔥💪*
Yana atsaye Cikin Lift, ya dauki wankan tuxedo suit, anyi masu adon Gold Gem stone dark blue, sai kyalli su ke yi, kayan sunyi fitting dinsa, ga wannan hadadden ducktail hair style din da yayi ma sumarsa.
idanunsa na akan wrist watch dinsa kirar patek philippe wanda sai dan wane da wane suke sanyata.
Time yake kallo, Yana karasa saukowa down Lift din ta buɗe Ya fito Ya nufi Dining area Tun kan ya karasa fragrance dinsa Ya daki kofofin Hanci nan su kusan atare suka dago suna kallon shi, ya yin da su ke a zaune kan Dining Chairs suna cin lunch din su.
kasa haɗiye kingin abincin dake a bakunan su sukayi saboda rudewar da sukayi na ganinsa, Ya tafi da imanin su, Ba ummi ba ba taj ba har Unaisah da Batool sun shagala da kallon shi..
Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka gyara nutsuwar su..
Cikin girmamawa Ummi da Taj suka gaishe da shi, fuskar shi asake ya amsa masu kafin ya mayar da dubansa akan Unaisah dake ta kallon shi a fakaice Ya kashe mata ido ɗaya, gaba daya ya ƙara dagula mata lissafi, sai ta dinga ganin kamar Danish ne.
"Happy birthday Chief namu, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka, Allah ya kara girma da daukaka, Allah ya kare mana kai daga sharrin makiya da mahassada"
"Ameen, Thanks, Allah yabar zumunci atsakanin mu"
"Bangane ba, Yau ne birthday din Chief, shine ba'a fada mana ba"? Ummi ce ta faɗa tana duban Taj
"Am sorry, Laifi na ne da ban fada maku ba, yau ne Birthday dinsa, ya ƙara shekara daya, saura kaɗan ya cike 40yrs" ya fada da zolaya yana murmushi.
"Amma dai banji dadi ba, da an fada mana da wuri ay da mun shirya muma anyi celebration din da mu"!
ta faɗa tana kallon Chief, tattausar murmushi ya sakar mata.
"ay min afwa, Idan na dawo da anjima zamuyi wani celebration din agida.."
"Allah yakaimu anjima lafiya, sannan nima ina tayaka murnar birthday dinka, Allah ya cika maka burikanka na rayuwa, Allah ya wanzar da farin ciki da zaman lafiya mara yankewa arayuwarka, Allah ya ƙara maka lafiya, Allah kuma ya baka mata tagari wadda zata zama cika makon jin dadin rayuwar ka..."
a hankali yake amsa mata da ameen ameen, Unaisah tun da taji an ambaci mata tagari kuma taga ya kalle, ta dan saki murmushin gefen fuska tare da kawar da idanun ta gefe ɗaya.
"Happy Birthday Chief, Allah ya faranta maka rai kamar yadda kake faranta mana"
Batool ce ta faɗa da murmushi akan fuskarta, kallonta yayi ganin ta yi rolling mayafi akanta hakan ya tabbatar masa da taji warning din da ya yi mata.
"Thank You,"
Wani kallo Taj yai ma Unaisah hakan yasa tace"happy birthday My husband to be, Allah ya baka nasara akan abunda kake nema, Allah kuma ya cika maka burikan ka"
Waro idanu Ummi tayi"What"? cike da jin kunya ta sunnar da kanta ƙasa, Batool ce kadai bata fahimci me tace ba, shi kuwa Chief ƙayataccen murmushi Ya saki idanun shi akan fuskarta, Taj sai faman sakin murmushi yakeyi Yaji dadin abun nan.
"Amen, shukran laki wife to be, Allah ya cika mana burin mu" cike da jin kunyar daddynta ta amsa mashi da ameen.
"Zan kai karfe shida, pls kafin na dawo Ku shirya kanku, zan ma Chefs magana su hada maku Cake..."
haɗa ba ki su ka yi gurin yi mashi godiya, tare da fatan Alkhairi.
har ya juya baya basu daina kallon shi ba, yadda yake tafiya cike da aji ba karamin kayatar da su yayi ba, kafin taj ya dawo da duban shi gare su tuni Unaisah ta gudu zuwa daki saboda kunyar kada ta hada ido da shi.
Yana fitowa Falo Yayi Arba da motocin da ke shigowa Villa Dinsa, a jere suka tsaya a parking Space.
Ɗaya bayan ɗaya suka soma fitowa daga Cikin motocin, Kowan nan su Ya ɗauki wankan expensive Suits na kece raini, tun daga kan CO, CI, Agent zahra and Osman, tare da U.s Armies, fuskokinsu dauke da farin ciki suka nufe shi, aransu sai yaba kyawun shi su ke yi su kansu wankan shi ya tafi da imanin su, Gaba daya sai yaji bakin Ciki Ya mamaye zuciyar shi saboda rashin Ganin Omar atare da su, Farin cikin shi ragagge ne, suna karasowa suka sara mashi, shima Ya sara masu, tare da mika masu hannu daya bayan daya sai da ya yi Musabaha da su, a mutunce suka gaisa da junansu, bayan sun yi mashi happy birthday, Saida suka fara shigowa Cikin gidan suka duba jikin Taj kafin suka fito, ahanzarce security officers suka bude masu Cardoor suka shiga cikin motocin a jere suka nufi Cikin Obie Estate.
Daidai Lokacin da za'a fara gudanar da Shagalin, gaba daya Hall din a kewaye yake Da sojoji harma da Isod Soldiers, baka jin komai sai sautin kidan Isod Anthem dake ta shi.
A gaban Hall din motoci suka dinga yin parking.
Ahanzarce Jami'an suka soma bude masu cardoors...
Yana ƙoƙarin fitowa daga Cikin motar, Idanunsa suka sauka akan Daddynsa dake fitowa daga cikin motar shi, Karaf idanunsu suka shiga cikin na juna, nan da nan Ya haɗe rai tare da kawar da idanun shi gefe ɗaya.
Girgiza kai sharafuddeen yayi duk sai yaji ba dadi, badan ya damu da shi ba, da ba abunda zai sa shi zuwa birthday dinsa sai dai shi bazai biye mashi ba.
gaba ɗaya Uncle dinsa sun fito daga cikin motocin su hada Baba Obie, jikokin family din bakowane Ya samu damar halarta ba, wasu uzuri ne ya ruke su, kowan nan su Ya dauki wankan shadda geztner blue sky, sai ya zamana kamar sunyi anko da Chief ne.
Akan Idon shi Chief Ya nufi Baba Obie yayi hugging dinsa tighly tare da manna masa peck a cheeks dinsa, bayan sun gama gaisawa ya nufi Hateem Yayi hugging dinsa kafin Yabi sauran Uncle dinsa da Yan uwansa duk yayi hugging dinsu, amma shi ko arzkin gaisuwa bai samu ba, hakan ba karamin taba zuciyarshi yayi ba.
babu wanda ya lura da hakan sai Hateem dama tunda yazo ya fahimci akwai wani abu dake damun Dan uwansa, bai dai tambaye shi ba, sai yanzu yaga amsar tambayar shi lamarin ya daure mashi kai sosai.
Gaba ɗaya suka dunguma izuwa Cikin Hall din da aka kawata shi da decoration, makada da mawaka da akayi inviting Sun hada kai sai kirari suke yi ma Chief.
basu dade da shiga Ciki ba, Saiga Mommynsa gimbiya malik tare da hajiya laura da kanwarsa hindu sun shigo, gaba dayansu Laces ne a jikin su, yana ganinsu ya nufe su, tun kafin Ya karaso hindu ta riga shi isa tayi hugging dinsa tighty tana fadin"happy birthday Big bro, we're so proud of you"
fuskarshi dauke da murmushi Ya dan bubbuga bayanta da tafin sa.
Kafin ya dago ya rungume mommynsa, shafa sumar kan shi tayi"happy birthday, my beloved son, You're the light of our family, and I'm so grateful for your kindness, compassion, and leadership, May this year bring you happiness and success."
"Ameen mommy, I can't thank you enought, kin gama min komai, kece silar daukakana" ya fada tare da raba jikin shi daga nata, murmushi suka sakar ma Juna.
Kafin ya dubi Hajiya laura, suka gaisa a mutunce itama ta yi mashi fatan Alkhari.
Shigowa Hall din Hajiya Saratu tayi, jikinta sanye da pakistan na manyan mata riga da wando, tayi rolling veil akanta, ga wani hadadden shade fari data saka, ta wanku iya wankuwa, pravin Yana a gefen ta, yayin da su twins ke abiye da bayansu, gaba dayansu Indian outfits ne a jikinsu, sunyi bala'en kyau, sun fito da ainihin suffar su ta indiyawa.
Hajiya laura na ganinta ta nufe ta da fara'a suka yi hugging din Juna sai yaba kyanta Hajiya laura take yi, bayan su twins suna gaishe da ita suka wuce Gurin Chief, suna karasowa Ya yi hugging dinsu atare sukayi mashi happy birthday.
Pravin ma Yaje yayi mashi, kafin Hajiya saratu itama ta matso kusa tayi hugging dinsa tare da yi mashi fatan Alkhairi, Kafin kace me tuni Hall din ya cika da yan uwa da abokan arziki, Sai yan gaishe gaishe suke yi atsakanin su,
Hatta U.s Armies da Senior agents saida Chief ya kai su gurin baba Obie suka gaishe da shi, ya kuma kaisu gurin Mommynsa suka gaishe da ita cikin girmamawa, haka sauran Uncles dinsa duk saida su ka gaisa da abokan aikin sa mahaifinsa ne kadai bai kai su wurin shi ba.
daga bisani Mc ya hau kan Stage, hannun shi ruke da mic, ya farayi ma Baki maraba da zuwa, tare da gabatar masu da kan shi, dayawa sun gane fuskarshi shine yayi mc A farewell dinner na hateem, Baba Obie ne ya yi inviting dinsa a wannan karo ma.
Bayani ya soma korawa, Hankulan Kowa Ya dawo kan shi.
_"Ladies and gentlemen, esteemed guests, family, and friends, welcome to Chief Owais's birthday celebration!"_
_Today, we gather to honor a remarkable leader and an extraordinary individual"_ ya fada yana nuna Chief Owais.
gaba daya suka fara tafa mashi, bayan ya kammala Speech dinsa Yayi inving Iyayen Chief don suyi speech dinsu, bayan Gimbiya Malikat Ta kammala nata mutane sunata tafa mata, Mai girma sharafuddeen ma yayi nashi Speech din mai ratsa zuciya, sai dai ko kadan Chief bai nuna Yaji dadin yabon da yayi mashi ba, saima yaki dagowa su hada idanun su, hakan ba karamin bata ran Mai girma shafuden ya yi ba_
Time da Mc yayi inviting Chief don yayi speach dinsa, Hankalin Kowa na hall din ya dawo kan shi...
Cikin nutsastsiyar muryar shi mai Jan hankali Ya kora jawabi mai matuƙar taba zuciya, abun da ya kara daurewa Uncles dinsa Kai Jin ya yabi mahaifiyarsa tare da su, amma bai sanya sunan mahaifinsa ba, basu kawo komai aran su ba, saboda sun yi tunanin ba dagangan ya yi ba.
Bayan Ya kammala speech dinsa Mc yace"I'm inviting his wife to give a speech on stage"
Tunkan Ya kare maganar Hajiya saratu ta ɗaga murya tace"ai har yanzu bashi da aure, tazuru ne"
gaba daya hall din suka kama dariya cikin nishadi, sun sa shi jin kunya.
Cike da zolaya Mc Yace"Chief what are you waiting for? Me ka nema ka rasa? Zankadedan saurayi kamar ka, burin kowace ya mace uhm? Ya faɗa yana kallon sa, kamar baisan yanayi ba, idanunsa na akan wayarsa da yake dannawa..
"Cikin yan matan nan da suke hauka akanka ya kamata aba daya dama mana" dariya suka sanya,
Hajiya saratu tace"He has a fiancee, Insha'Allah, we will soon invite you to his wedding celebration"
Gaba daya jama'ar dake acikin Hall din suka sanya shewar murna.
Daga Bisani Labulan daya Lullube ke6ataccen gurin da aka tanada saboda Chief ya soma ɗagewa sama a hankali gaba daya hankulan mutane ya koma kan shi
Wata katafariyar throne Chair ce da aka kawatata saboda shi, daga gaban kujerar wani hadadden table ne anan aka daura katon cake din da akayi domin sa, mai hawa 10 hada sunan shi a jikin Cake din da wani salon rubutu me jan hankali akayi shi, daga saman silin din gurin an kawata shi da navy blue balloons da steamers, wurin Ya burge mutane, friends dinsa ne suka yi mashi rakiya Ya hau kan kujerar Ya zauna tare da daura kafarsa ɗaya kan ɗaya like a King on his Throne.
Minti 30 aka ware saboda baki su samu damar Cin abinci, bayan kowa yaci yasha anyi kullu wash rabu hani'an Mc Ya sa Mawaka suka fara wake Cheif Owais, wakar tayi mashi dadi hatta yan uwansa sunji dadin wakar birthday din da akayi masa.
Lokacin da Mc Yayi inviting Yan uwa da abokan arziki donsu fito tsakiyar filin su taka rawa, nan fa suka fara hawa kan dancer floor din cike da nishadi suke taka rawar girma, kowa saida Ya taka In ka cire Mutun daya Mai girma sharafudden da ransa yagama 6aci, Jira yake kawai agama shagalin su shiga family meeting don Ya fallasa abun da ke faruwa tsakaninsa da owais, saboda hakurinsa ya ƙare ya ƙwammace kowa ya ji.
Lokacin da aka kusa kammala shagalin, Yan uwa da abokansa suka taya shi Yanka cake, ya 6allo cake din Yaba momynsa abaki, bayan taci itama ta debo ta saka mashi abaki yaci.
ya bi Uncle ɗin sa daya bayan daya ya gutsuro cake ɗin ya sanya masu abaki suka ci, ko da yazo kan sharafudeen Saida Ya fara aika masa da harara kafin Ya bashi cake din, badan idon mutane ba da ba abun da zaisa ya ci cake din nan, hakanan ya jure ya bude baki Ya sanya mashi cake din kamar anyi masa dole.
Bayan ya gama basu Hindu ta debo cake din ta bashi abaki, shima ya bata abaki, Baba Obie Ya ballo Ya tura masa abaki, kowa ka kalla fuskarsa dauke da farin Ciki banda mahaifinsa.
Mintuna talatin da suka rage kafin A kammala Birthday din, photographers suka fara daukar su Hotuna da videos, sai da Chief Ya dauki hoto da kowa daya halarta amma banda mahaifin sa, Ko kusa da shi Yaƙi bari Yazo, balle yasa ran zai yi hoto da shi.
Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, Yan uwa da abokan arziƙi sun gwangwajeshi da Kyaututtuka na ban mamaki, bayan kammala addu'ar tashi daga taro da Mc ya gabatar tare da yi ma Baki fatan sauka gida lafiya.
*HAJJATY🍁*
Tana akwance kan gadonta, Ta lullube kanta cikin bargo, Jikinta sai makekketa yakeyi saboda zazzabin daya lullu6eta, duk yadda taci burin ta halarci birthday din Owais, Allah bai nufa ba, Tun safe take fama da zazzabin har magani tasha amma yaƙi sauka, har kiran layin Pravin ta yi don ta fada mashi halin da take aciki amma bai yi picking call din ba, rabon ta da shi tun bayan kammala sallar asubahi daya leko dakin ta bata ƙara ganin ƙeyarsa ba.
Yan aikin gidanne kadai suka san bata da lafiya, Har abinci suka kawo mata amma takasa cin shi, burin ta kawai taga pravin saboda shi kadai ne zai iya kwantar mata da hankali.
________________FAMILY MEETING🔥
"Owais meya haɗa ka da Mahaifinka? Meyasa kake zarginsa? wani laifine kake tuhumarsa da shi Ya fada min ba yadda bai yi dakai ba akan ka fada masa amma ka ƙi sanar da shi why pls"?
Hateem ne Ya faɗa Idanunsa a kan Chief owais dake a tsaye yana fuskantarsa, Suna a cikin dakin Baba Obie.
Fuskarsa babu walwala ya furta"zanyi maka bayani anjima"
girgiza kai Hateem yayi ransa abace yace"No, Yanzu nake son ji Owais, Dole ka amsa min tambayata idan har ba so kake raina Ya baci ba"!
Shiru yayi saboda ya rasa ta ina zai fara kora masa jawabi.
"Hateem meke faruwa ne? Har an fara shirin Family meeting bangan ku ba, yanzu nake tambayar kuna ina, auta take fadamin taga shigowarku dakin baba "
Sir mubarak ne ya yi maganar yayin da ya ke shigowa dakin idanun shi akan su.
Kafin wani daga cikin su Ya furta Kalma suka ji an banko kofar dakin gaba daya suka kai dubansu ga mai shigowa.
Mai girma sharafuddeen ne Ya shigo dakin fuskarsa kwata kwata babu annuri, sai huci Yake yi kamar mayunwacin zaki, kaitsaye ya nufi Owais yana karasawa gaban shi, Ya damƙo Arm dinsa da ƙarfi Ya fusgoshi Ya nufi kofar dakin da shi...
Hankali atashe Hateem da Sir Mubarak suka bi bayanshi suna kokarin dakatar da shi.
Bai nufi ko'ina ba sai falon, A lokacin Baba Obie tare da sauran Uncles dinsa da Hajiya saratu duk suna a Falon kowan nan su yana azaune kan sofa, shigowar Shafudden ne Ya ɗaga hankulan su a razane suka mimmike tsaye , cike da rudu suke kallon su..
"Dad.. let go of arm" yana huci ya fada sharufudeen Yace"bazan saki ba Owais, kayi duk abun da za ka yi..."
"meke faru ne? Yaya sharafuddeen? Owais! Me ya hada ku ne"?
Hajiya saratu ce ta yi maganar, bai ko kula ta ba, ya nufi baba Obie da ya gaza miƙewa agaban shi Ya wurgar da chief owais, gaba daya ya tafi zai kife ƙasa baba Obie yayi hanzarin ruko kafadunshi Ya janyo shi ya dawo kan laps dinsa.
Yana haki Yace"gayanan baba, ka tambayesa Uban me nayi masa! watakil kai ya iya faɗa maka"
ya faɗa yana nuna Owais da yatsan sa, Kafin Ya dubi yan uwansa cikin bacin rai yaci gaba da cewa"Owais Ya ɗaura min karan tsana, yau wata ɗaya kenan, rabon da in yi bacci cikin kwanciyar hankali saboda shi, gaba ya ke yi da ni! ya juya min baya, yana zargina akan laifin da ban aikata ba, ba yadda banyi da shi ba akan ya fadamin me nayi masa amma yaki ya faɗa...."
Daura hannu biyu hajiya saratu tayi akanta..
Uncles dinsa gaba daya sun rude da jin abunda ke faruwa tsakanin Owais da mahaifin sa.
Cikin sanyin murya Baba Yace"meyasa baka fadamin ba tun lokacin daya juya maka baya"?
"Saboda bana so na daga maku hankali, shiyasa nabar abun araina, yau ma dana fada maku naga abun nashi ya fara wuce gona da iri, nema yake ya daura min hawan jini, Baba Hakurina ya kare, Owais Ya kona min rai" ya fada idanunsa cike tab da kwalla.
Gaba daya basu ji dadin abun da Owais ya yi masa ba.
Senate lateef Yace'baka kyauta ba, owais, ka bani mamaki, ina hankalin ka ya ke? Da har ka bari mahaifinka Yana kwana da fushinka acikin zuciyar shi"?
Ya faɗa yana kallon chief wanda har lokacin bai ɗago ba, tunda Baba Obie ya daura kanshi asaman laps dinsa.
"Owais, ka tashi kayi mana bayani, wani laifi ne kake tuhumar mahaifin ka da shi? " His excellency abdul razak ne yayi maganar..
His excellency deen daya gama fusata da kakkausar murya yace"ba kaji ana magana bane? Ka tashi ka fada mana meya hada ka da shi"!
Cikin sanyin murya Hateem Yace"pls, Kubi shi a hankali, "
ya fada tare da kallon Owais"My son, pls, ka tashi kayi mana bayani, in sha Allah zamu fahimce ka,"
Pravin da ke ƙoƙarin shigowa falon har zai saci hanya ya nufi dakin hajjaty ganin abunda ke faruwa yasa shi cin burki Ya karya kwana ya nufi gurin su ya tsaya tare da ruke qugun shi da hannu daya ya kasa kunne Yana sauraron maganganun su.
A fusace Owais Ya miƙe tare da juyawa ya nufi daddynsa gadan gadan Kamar zai dokesa, lamarin ya daure masu kai owais bai taba basu mamaki irin na yau ba, har sun fara kokwanton anya ba Aljanu ba ne a jikin shi.
Hannu yasa Ya daki kirjin shi yana faman fitar da hucin bacin rai idanunsa sun kaɗa jawur tamkar an watsa barkono a cikin su, wlh a lokacin Sharafuddeen Yasha jinin jikin shi saboda bai taba ganin owais acikin bacin rai irin na yau ba, Batare da jin shakkarshi ba ya fuskance shi gaba da gaba.
Da farko yayi zaton Dukanshi zaiyi, ganin yadda Ya tsaya a gabansa Yana huci.
Gaba daya kawunnansa sun zubawa sarautar Allah ido, suna jira su ga iya gudun ruwan shi.
Dakyar ya haɗiyi ƙululun bakin cikin daya tokare Zuciyar shi..
Sautin muryarsa dakyar yake fita"ka za6i in tona maka asiri agaban su"?
Ya jefa mashi tambayar, muryar sharafuddeen tamkar zai fashe da kuka Yace"Sai me owais? Ka fada masu suji, wlh da Allah na dogara, ni nasan ban aikata komai ba..."
Gyaɗa kai Chief Owais yayi tare da cewa"kana ɗaya daga Cikin Elders na gidan KURKUKUN ƘADDARA❗...."
Aruɗe Sharafuddeen yace"bangane me kake nufi ba Owais, su wanene Elders? What Prison of Destiny are you talking about"?
Kallon kallo Uncles dinsa suka fara jefawa Junansu gaba daya sun rude da jin abunda Owais Ya faɗa! Su kansu sun kosa suji su wanene Elders? Kuma wani gidan kurkukun kaddara ne ya ke magana akansa?
Hateem har ya buɗe baki zaiyi magana baba obie ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu"kabarsu suyi magana atsakanin su, kada wanda ya sa masu baki"! ya umarta, batare daya motsa daga kan kujerar da ya ke ba.
Wani makirin murmushi Pravin ya saki tare da cizon leben shi saboda dadin da yaji.
"ka riga da kasan me nake magana akai, ina da tarin hujjoji akanka, kawai ka amsa min tambayata, Idan har baso kake In fallasa asirinka agaban su ba..."
bawan Allah Sharafudden Ya rasa Ina zai tsoma ranshi yaji dadi, murmushin takaici ya saki, tare da kai hannu Ya damƙi kwalar Chief yana huci yace"ka dade baka tona min asirin ba dan ubanka! ka fada kowa yaji Owais..."
"Haba yaya Sharafudeen pls Owais.."
Hajiya saratu da ta ɗauko maganar, bata kaiga dire ta ba, baba obie Ya daka mata tsawa tuni taja baki tayi shiru, da rudu take duban baban nasu ta razana ba kadan ba.
Kasa hakuri Hateem yayi don bazai juri kallon Dan uwansa Da dansa a yanayi irin wannan ba, Nufarsu yayi da niyar ya raba su, bai kai ga isa ba Baba Obie Ya ambaci sunan shi da kakkausar murya"Hateem!"
fuskarshi dauke da damuwa yace"baba pls kada ka hana ni! Bazan iya jure kallon dan uwana ahali irin wannan ba, ɗan sa fa ne, wannan ba abune da zamuja baki muyi shiru ba muna kallon uba da ɗa suna faɗa atsakanin su.."
fuskar baba Obie adaure Ya nuna masa sofa"ka koma ka zauna, Umarni nake baka"! Badan yaso ba ya nufi sofa din daya nuna masa ya zauna ransa abace.
Hajiya saratu data gama hasala juyawa tayi rai abace ta nufi part dinta don bazata juri kallon abunda ke faruwa ba.
"Ba zaka fada ba"? ya fada batare daya saki kwallar rigar shi ba..
Yaso Ya rufa mashi asiri saboda koba komai mahaifinsa ne shi, amma ganin yadda ya matsa ma shi akan ya fada ne yasa shi ya zuciya har baisan sa'adda Ya fara gaya masu irin miyagun ayyukan da Elders suke aikatawa..
Lokaci ɗaya yanayin fuskokinsu Ya canza zuwa tsantsar tashin hankali da rudani mara maisaltuwa hadi da tsantsar al'ajabi.
bai karasa maganar ba, Sakamakon Tsawar Da Hateem Ya doka masa, tamkar zai fasa dodon kunnansa.
wannan karon bai saurari baba Obie ba ya mike cikin fushi Ya nufi Owais yana fadin
"zaka tabka kuskuren da zakayi danasani arayuwarka! Idan ma zarginsa kakeyi to ka daina, Ka sake bincike akan wadanda kake zargi, amma mahaifinka baya daya daga cikinsu, sai dai idan kazafi aka yi masa...."
girgiza kai Chief yayi hawayen da suka taru acikin idanunsa tuni sun fara sauka kan kuncinsa.
"Uncle Ba zarginsa nakeyi ba, tabbaci nake da shi, Yana daya daga cikin Elders, saboda shine mutumin da ya janye ni daga fagen fama, Ya jefani acikin daki don kada a cutar dani, bayan haka aranar da zamuje kai farmaki, saida ya kira ni a resting home dinsa, Ya gargadeni akan kada inje kai farmakin, ashe ya saka min maganin bacci mai hadarin gaske acikin coffee din da ya bani nasha...." a takaice ya fayyace masu dalilan da sukasa ya ke zarginsa.
Maganganun Owais sun so suyi tasiri a cikin zuciyoyin su, har sun fara jifar sharafudeen da kallon tuhuma.
Dafe kai sharafuddeen yayi da tafin hannunsa, wani irin kululun bakin cikine ya tokare makoshinsa, sam ya kasa magana, dakyar yake iya furta Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un..
"Baba dan Allah kasa baki a maganar nan! Kai kadaine zaka iya tsawatar masa..."
His excellency deen ne ya fada yana kallon Baba Obie, wani abun daure kai, kwata kwata fuskarsa babu alamun damuwa.
"Me ku keso ince? Sharafuddeen shi yakamata ya kare kansa agurin Owais, Ni banga laifin Owais ba, kubar yaro yayi aikinsa, ko kun manta cewa shi jami'en bincike ne"?
Cike da rudani suke kallon baba Obie, jin abunda yace, sun fahimci shi ko ajikin shi bai damu ba,
"Ba ku kai shi son mahaifin shi ba, Hakanan dai owais bazai tuhumi mahaifinsa batare da yana da kwakkwarar hujja akan shi ba, kunsan dai ba zai yi maku karya ba....."
Bai kare maganar ba, sharafudeen Ya katse shi, Cikin raunanniyar murya yace"baba, da bakin ka kake fadan hakan? Ka yarda da maganar owais, kaima kana zargina? Baba kaifa mahaifina ne kafi kowa sanin halina, kasan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya aikatawa ba, wlh banji zafin kazafin da owais yayi min ba, kamar yadda naji zafin maganar ka..."
dakatar dashi baba Obie yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu"Ni bance ina goyon bayan Owais ba, kuma bana goyon bayanka saboda bansan wanene mai gaskiya acikin ku ba, amma in har zaka iya kare kanka agaban yan uwanka nayi alkawarin zan dauki mataki akan Owais, In kuma ka gaza yin hakan hukuma zatayi aiki akanka, donni bazan bari ka zubarmin da mutuncina ba...."
juwace ta kusa dibar Hateem da sauri Ya nemi sofa ya zauna tare da dafe kanshi dake sarah mashi.
Sir mubarak sam Ya kasa magana, saboda yana da fusatacciyar zuciya in har ya bude baki ran kowa zai 6aci ne.
Sun rasa wa zasu goyama baya a cikin su? owais da baba Obie sun haifar masu da kokwanto akan sharafuddeen, aganinsu son owais ne ya rufe mashi idanun shi shiyasa ya goyi bayan shi.
Munafuki Pravin sai ya fakaici idon mutane yake sakin makirin murmushin nan nashi, Ji yake kamar ya zuba ruwa kasa Yasha saboda farin cikin sabanin da owais ya samu da mahaifinsa dama yajima yana jin haushin Owais..
Fuskar Sharafudeen amarairaice ya dubi Yan uwansa..
"Kuma Kuna zargina akan abunda owais ke tuhuma ta"?
Shirun da su ka yi ne yasa shi tunanin suma sun goyi bayan Owais da baba Obie, zubewa yayi kasa kan gwiwowin sa, hawaye suka wanke fuskarsa, ga wani matsanancin ciwon kai da yake ji, zuciyarshi ta karaya.
"ba mu zargin ka, saboda mu shaida ne akan ka, mun san wanene dan uwan mu, amma abun da muke so da kai shi ne ka fada mana, meyasa ka sanya mashi sleeping pill a cikin coffee? After that! Why ka hana sa zuwa kai farmaki bayan baka taba hana shi ba! sai wannan karon? Sannan Yace ka yi fitar sirri a daren ranar da suka je kai farmaki, Sharafuddeen Ina kaje"? his Excellency abdul razak ne ya jefa mashi tambayar.
Shiru yayi batare daya iya kare kanshi daga abunda suke tuhumar shi ba.
A hankali Chief owais Ya sadda kanshi Kasa ko kallonsa baison yi saboda baison tausayin shi ya kama shi, gaba daya komai dake faruwa akan idanun Hajiya saratu dake atsaye bakin kofar shiga part dinta, taji komai daya faru saboda bata kaiga shiga ciki ba..
Hannayen shi dake kerma ya ɗaga sama cikin karyayyar murya ya ce
_"Ya Allah, bani da mafita daya wuce kai! Kaine shaida ta, kafi kowa sanin wanene bawan nan naka...."
bai kaiga ƙarasa maganar ba, sakamakon muryar dattijuwar data karaɗe kunnuwan su
*_"NI INA DA JA AKAN MAGANAR KA OWAIS, JINI NA BAZAI TABA AIKATA MIYAGUN LAIFUKAN DA KAKE TUHUMARSA DA SU BA"!*_
~*_________________________________*~
*Daga Alƙalamin Boss Bature🔥✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
[14/10, 8:15 PM] Amina Musa Mustapha💕💕: 🔥💋💞☠️💔💞🫀🌹
_ * *_
~___________________________________🌹✍️~
A matuƙar ruɗe suka juya tare da kallon mai shigowa...
Sandar hannunta ce ta fara zurowa cikin falon, Kafin ta kunno kai, farar jallabiya ce a jikinta ta lullu6e kanta da head scarf ta rufe fuskarta da takunkumi, haka zalika idanunta suna asanye da shade fari, daƙyar ta ke dogara sandar hakan ya bayyana rashin kuzari a tattare da jikin ta, daga gani bata da koshin lafiya duba da yadda jikinta ke kerma.
Cike da tsantsar ruɗani suke kallon ta daga ƙasa har sama, basu san wacece ba, amma maganar da ta furta ta tsaya masu a ƙahon zuciya.
A sukwane Sharafudeen Ya miƙe yana duban ta, Muryarta ta yi masu kama da ta mahaifiyarsu da suka rasa tsawon shekaru wanda basu mance da yanayin sautin muryar tata ba.
Pravin sai faman zazzare Idanunsa ya ke yi burinsa kawai ya ga wacece ita duk da fargabar da ta shige shi saboda muryarta ta yi masa kama da ta wata da ya ta6a sani..
Baba Obie sam ya kasa motsawa, zuciyar shi ta ƙi aminta da abunda kunnuwanshi suke juyo mashi, haka kuma ya kasa yarda da abunda idanunsa ke nuna mashi, kokwanto ya ke aransa ya ayyana hakan ma bazai ta6a yiwuwa ba, wanda ya mutu ba ya ta6a dawowa, duk da yanayin fuskarsa ya nuna tsantsar ruɗani, sai dai babu alamun fargaba atare da shi saboda ya yi imanin hakan bazai taba yiwuwa ba, sai dai idan fatalwarta ce ta dawo...
"Wace ce ita? Da izinin wa ta shigo estate din nan?" Tambayar da ta cika zuciyoyinsu kenan, gaba ɗaya sun ƙagara da su ji dame ta zo musu.
"Baiwar Allah daga ina ki ke? Wa kike nema ne? Kuma tayaya akai kika shigo estate ɗin?" His excellency Deen ne ya tambaya fuskarsa a murtuke.
Hajiya saratu dake a tsaye bakin kofar shiga part dinta tayi sototo tana kallon Ikon Allah..
Kusan atare Sir Mubarak Da Hateem suka miƙe daga zaunan da suke akan Sofas suka bi ta da kallo...
"Wacece wannan dattijuwar ne? Me ya kawo ta nan? Da iznin wa ta shigo Estate din nan uhum"! Acewar His excellency Abdul Razaq...
"Dan Allah ku yi wani abu akai, matar nan ba mutun bace, ku duba ku ga yadda jikinta ke kerma," Pravin ne ya faɗa yana zare idanun sa..
"Ku kira Security Officers ku tambaye su ta ya akai suka bar bare ya shigo mana estate! Da iznin Uban wa..."
Senate Lateef ne ya ɗauko maganar yana huci idanunsa akan tsohuwar, ƙoƙari take ta cimmusu sai dai rawar da jikinta ke yi da rashin kuzari ya hanata yin saurin.
Tana gab da zata ƙarasa gaban Sofas ta ɗan dakata tana mayar da numfashi.
Cikin sauri Chief ya nufe ta, a hankali ya sanya tafin hannunsa ya dafe bayanta ya taimaka mata ta ci gaba da tafiya suka ƙaraso tsakiyar Sofas ɗin, rai a 6ace Sir mubarak Ya ce,"Kana acikin hankalinka kuwa? Ko ka san ta ne?...."
Bai ƙarasa Maganar ba tsohuwar ta yi kukan kura ta dira agaban Baba Obie ta jefar da sandar hannunta, bai aune ba ta wanka masa zazzafan mari tare da cakumar gaban rigarshi da yatsun hannayenta dake ta kerma.
Tashin Hankalin da ba'a saka masa rana! zazzare idanunsu suka yi cikin tsananin al'ajabin karfin halin dattijuwar nan take ran su ya 6aci, ta tako har cikin estate ɗinsu ta mari mahaifinsu a gaban idanunsu!!'
Ransu ya yi mugu mugun 6aci har sun harzuƙa za su kai mata bugu Sharafuddeen ya yi hanzarin kare ta.
Sir Mubarak yana huci ya ce, "Don Ubanki wacece ke?? Uban me ya kawo ki estate din nan? Da me kike taƙama ne?"
Senate ya amshe da fadin, "Sharafudeen ka matsa ka bamu guri! Baka ga abunda ta aikata bane? mahaifinmu fa ta mara agaban idanunmu!"
Cikin rawar murya Pravin ya ce, "Wallahi mahaukaciya ce, daga gani irin mahaukatan nanne masu yin hauka tuburan a dawanau ta gudo Allah Ya hankaɗo mana ita nan, wlh ku yi gaggawar korarta daga estate din nan idan ba haka ba zata manna maku hauka ne..."
Baba Obie bai motsa ba amma fa ya girgiza sosai, da ruɗu yake kallon fuskarta da idanunsa wadanda suka kaɗa jawur, sam ya kasa magana saboda rudewar da ya yi ya rasa gane wacece ita meyasa ta mare shi?"
"Ba zaku ɗauki mataki ba? Kuna gani a gaban idonku ta mari Baba? Matar nan fa mahaukaciya ce wlh, babu lafiya a tare da ita, da gani tana tattare da baƙaƙen aljanu shiyasa har ta yi nasarar shigo mana nan..."
Pravin ne Ya faɗa Yana zare idanunshi yadda kasan na kwarton mazuru.
Ran Hajiya Saratu ya 6aci ganin abun da dattijuwar ta yiwa mahaifinsu, cikin fushi ta nufe su tana ƙarasowa bata bi takan Sharafudeen ba, ta damƙi mayafin tsohuwar kokawa ta barke a tsakaninsu, tana huci ta ce, "Wlh bazata sa6uba, na rantse sai kin yabawa aya zaƙinta, ki shigo har estate dinmu ki mari ubanmu a gaban idanunmu? Kina acikin hayyacinki kuwa? Na shiga ukuna! Wai dan Allah uban wanene ya gayyaci tsohuwar najadun nan acikin gidan nan? Da iznin Ubanwa Securities suka bari ki ka shigo.."
Balbaleta da faɗa Hajiya Saratu ta yi ta inda take shiga bata nan take fita ba.
Sai da suka gama harzuƙa kowa zuciyarshi ta zo a wuya.
Pravin yana ƙoƙarin zaro waya daga aljihu don ya kira Security Officers din gidan, Kwatsam ba zato ba tsammani Hajiya Saratu ta yakice takunkumin dake akan fuskarta, Ta fusge shade din dake akan idanun tsohuwar ya faɗo ƙasa ta bi tasa ƙafarta ta take shi ya faffashe.
Ɗagowar da za ta yi da niyyar ta wanka mata mari har ta ɗaga tafin hannunta, idanunta suka sauka akan fuskar tsohuwar cak ta tsaya tana zare idanunta, Gaba ɗaya suka daura idanunsu akan fuskarta, Wani irin faduwar gaba suka ji ya ɗarsu acikin zukatansu, Sun ruɗe da ganin fuskarta kamar sun so su gane ta sai dai sun kasa gane wacece ita.
Sai lokacin ta yi ƙarfin halin buɗe baki murya na rawa ta ce, "Saratu, bani bace tsohuwar najadu, kin ga tsohon najadu nan, ubanku Obinna!"
Ta faɗa tana nunasa da yatsanta sai lokacin ya shaida fuskarta, Wata irin zabura Baba Obie ya yi jikinsa na 6ari ya miƙe tsaye a kiɗime yana zazzare idanunsa! lokaci ɗaya yabi ya rikice, Hankalinsa yayi mugu mugun tashi, kanshi ya daure, Ya yi matuƙar razana da ganinta, tsantsar al'ajabine ya ruƙe shi, ganin abun yake kamar a mafarki sam ya kasa gasgatawa..
Hajiya saratu ta daka mata tsawa tana fadin "Ke! Mahaifin namu ne tsohon Najadu? Baiwar Allah dame kike taƙama ne, wace ce ke wai..."!
Bata ƙare maganar ba Hateem ya daka mata tsawa a ruɗe ta ja baki ta yi shiru, matsawa ya yi kusa da Khala ya dafa kafaɗunta da tafukan hannayen sa, ya kafe ta da idanunshi yana ƙoƙarin gano wacece ita..
Cikin sanyin murya ta ce, "Baku gane ni ba? Hateem! Sharafudeen! Ni ce fa, *AURORA EDWARD* Momman ku!"
Ta faɗa tana ƙoƙarin tuna masu ta juya ta dubi su Saratu ta ce, "Saratu! Lateef! Mubarak! Deeni? Razak! Baku gane ni ba ku ma?" Ta fada idanunta cike tab da ƙwalla.
Cikin shesshekar kuka ta ce, "Ba laifinku bane, laifin ubanku ne, Mugu azzalumi, Kun ganshi nan..., Shine ya ɗauke ni tsawon shekara ashirin ya raba ni da ku, ya yi maku ƙaryar na mutu bayan ina a raye...."
Waro idanunsu waje su ka yi suna kallon fuskarta yayin da ƙwaƙwalwarsu ke ƙoƙarin tariyo masu wacece ita saboda ta canza musu sosai, tayi tsufan da bazasu iya gane ta ba cikin sauki.
Saboda tsabar tashin hankali, duk da sanyin A.c din dake a falon hakan bai hana baba Obie fitar da gumi ba, jikinshi Ya jiƙe sharkaf kamar wanda aka tsamo daga teku, Firgici da tsoro sun mamaye zuciyar shi, duk yabi yasha jinin jikin shi.
Pretending ya yi duk don ya ƙara dagula masu lissafin ƙwaƙwalwar su ya ce, "This can't be Aurora Edward, bazai ta6a yiwuwa ba, matata ta mutu kuma mun shaida mutuwarta, wanda ya mutu baya dawowa sai dai idan Aljana ce ke!"
Ya faɗa a tsawace kamar zai doke ta, bata ko kula shi ba ta mayar da dubanta akan ya'yan ta burinta su gane ta saboda hankalinta ya tashi ganin sun kasa yarda cewa ita ce.
"Hateem, Sharafudden nasan ko kowa bai gane ni ba, Ku zaku gane ni..."
Ta faɗa tare da tallabo fuskar Hateem da tafukan ta, wata matsananciyar damuwa ce mai tattare da ruɗani ta mamaye zuciyar Hateem da Sharufudeen, kokwanto su ke yi akanta, abu ɗaya da ya yi masu kama dana mahaifiyarsu ajikin ta, shine launin ƙwayar idanun ta.
In a broken voice, Hateem yace "Momma... Is that really you I'm seeing? But how is that possible after you died? Ni dai a iya sanina wanda ya mutu baya dawowa ..." Ya faɗa yana girgiza kansa.
Bai ƙare maganar ba Sharafuddeen ya ce, "Don Allah ki fahimtar damu, kin jefa mu a ruɗani! gaba daya mun ruɗe, tabbas ba zamu manta da mahaifiyarmu ba, amma taya kika rayu bayan kin mutu? Dan Allah ki fada mana! Mafarkine wannan ko gaske..." Ya faɗa fuskarsa sharkaf da hawaye.
Murmushin takaici ta saki tare da juyawa ta dubi baba Obie da ya yi tsaye sototo kamar mutun mutumi.
"Ku tambayesa ina ya kai maku mahaifiyarku tsawon shekaru ashirin bayan ya yi maku ƙaryar na mutu, shine ummul aba'isin komai, shine ya azabtar da mahaifiyarku, wuya ce ta sa na yi tsufan da basu kai na shekaru na ba..."
La66ansa na kerma ya ce, "Kada ku yarda da ita! Ƙarya take gaya maku, Fatalwa ce ba mutun ba ce, dan Allah ku kawar da ita daga cikin gidan nan, ku kira Security officers su fitar da ita, Ku kore ta bana son ganinta" Ya faɗa yana nunata da yatsansa dake kerma..
"Don't believe her! I don't want to see her, Crazy ghost, hypocrite, get her out ba mutun bace Aljana ce ku kira sheikh Imam ya yi mata ruƙiya zaku tabbatar da abunda nake faɗa maku..."
Kamar zararre sai sambatu ya ke yi, duk yabi ya dabarbarce ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.
Murmushin takaici ta sakar mashi, ga wani ƙululun bakin ciki da ya tokare maƙogwaronta, "Haba Obinna, idan har ni aljana ce to kai kuma bakin shaiɗani ne, wannan bawan Allah da kuke gani ba mutumin kirki bane, fasiƙi ne mara imani, daga shaidan sai shi, daga shi kuma sai fir'auna a wurin aikata zalunci...."
bata ƙare maganar ba suka daka mata tsawar da ta razanar da ita, gaba daya sun ruɗar dasu, da ita da baba Obie sun rasa maganar wa zasu ɗauka sai dai sun yarda da mahaifinsu fiye da yadda suka yarda da kansu.
Komai dake faruwa akan idanun Chief Owais da ya ƙame a tsaye kamar gunki sam ya kasa motsawa, tsantsar rudanine da fargaba akan fuskarsa.
Damƙar hannunta baba Obie ya yi ya dinga janta yana faɗin, "Zo ki fice ki bar mana Estate, wuce ki tafi, mahaukaciya, makira annamimiya mai son haɗa uba da yayansa, ni nasan maƙiya ne suka turo ki don ki yi mini ƙazafi..."
Fashewa ta yi da kuka tana kiran sunan Hateem dana Sharafudeen don su kawo mata ɗauki.
"A'uzu billahi minasshaiɗanir rajim tuf tuf, wa innahu min sulaimanu wa'innahu bismillah! Aniyarki ta biki makira algunguma baƙar munahika"
Ya faɗa yana tottofa mata yawu akan ta, sam sun kasa tsayar da shi, al'amarin ya rikita zukatansu.
Tana kuka haɗi da waiwayonsu cikin shesshekar murya tana magana tana miƙa masu hannu,
"Hateem kada ku bari ya fitar dani, Sharafudeen ka taimaka mini, kada ku bari ya ƙara raba ni daku! Na yi kewarku, Wlh ni ce mahaifiyarku Aurora Edward! Your momma, ban mutu ba, ba fatalwa bace ni, Owais Kada ka bari ya kore ni, Ni kaɗai ce zan iya fayyace maku komai akan shi, Owais kaima ba ka tuna ni ba kakarka momma? ...." Ta faɗa idanunta cike tab da ƙwalla, tana ta ƙoƙarin ƙwace hannunta daga mugun ruƙon da baba Obie ya yi mata sai dai ta kasa saboda babu karfi atare da ita.
Hankalin Pravin Idan yayi dubu toh ya tashi, murnar da yake yi tuni ta koma ciki, ya murtuke fuska, hannayenshi biyu ya ɗaura a saman kanshi alamar ya shiga uku, ƙirjin shi kamar ana luguden ta6are, kafin ka ce me tuni ya haɗa uban gumi, jikinshi ya kama makyarkyata kamar wanda farfaɗiya ta kama.
Har ya kusa fucewa da ita daga falon Sharafudeen ya yi kukan kura ya watsa da gudu ya nufe su, yana ƙarasowa ya bangaje baba Obie gaba daya ya kife ƙasa kafin ya ɗago Sharafudeen ya damƙo hannun Khala ya juyo da ita suka dawo Falon.
Da sauri Hateem ya nufe su ya kar6e hannun Khala dake acikin na Sharafuddeen ya yi hugging ɗin ta akan broad chest dinsa, ya ƙanƙameta sosai kamar zai mayar da ita cikin cikin shi, wani irin sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta kamar yadda shima ya ji sanyi a ranshi, rungumar da ya yi mata tasa ya ƙara yarda mahaifiyarsu ce saboda wani yanayi da ya tsinci kan shi wanda uwa da ɗa kadai ke jin irin shi idan jikinsu ya haɗu da na juna.
"Yaya kun yarda da ita? Kun yarda cewa momma ce?" Hajiya saratu ce ta faɗa a ruɗe
"Ta yaya bazamu yarda da ita ba, koda kowa bazai yarda ba mu mun yarda mahaifiyarmu ce, ni tun lokacin da idanuna suka shiga cikin nata, raina ya bani momma ce..." A cewar Sharafuddeen.
"In hakane taya akai ta rayu bayan ta mutu? kuma mun ga gawarta da idanunmu?" Ta jefa ma su tambayar .
Sharafuddeen ya ce, "Shi yakamata ku tuhuma.." Ya faɗa tare da nuna baba Obie
"Saboda na fara kokwanto akan shi! kuma dama shi borin kunya da hauka ake naɗe shi, in ba haka ba meyasa zai ɗaga hankalinshi don kawai ya ganta? Bayan haka a gabanku baba ya juyamin baya ya hana kowa ya yi magana akan tuhumar da Owais ke yi mi ni, wai har ni zai ce in kare kaina agurin Owais!....." Ya faɗa yana jifar shi da kallon tuhuma.
Bai ƙarasa maganar ba Baba Obie Ya nufo su cike da rashin kuzari, yana fitar da huci kamar mayunwacin zaki ya nufi Khala da Hateem ya rungume, har ya miƙa hannu da niyyar ya damƙo ta, Sharafuddeen ya yi saurin damƙo hannunsa ya jefar da shi gefe ɗaya baima san sa'adda ya daka mashi tsawa ba, dama da haushinshi a cikin zuciyar shi.
Gabansa ne ya yanke ya faɗi jin yadda Sharafudeen ɗan cikinsa ya daka masa tsawa kuma ya jefar da hannunsa, hankali a tashe ya furta, "Na shiga uku..!!!"
"Baba, don't dare touch our momma! Don't touch her! Let her talk, Idan har kana da gaskiya meyasa zaka ɗaga hankali akanta huh? Ka barta ta yi magana mana!" rai abace Sharaudeen ya faɗa yana kallon cikin idanun shi.
Zare idanu baba Obie ya yi with pure confusion on his face,
Tsantsar mamaki ya hana su Sir mubarak furta magana sai binsu da idanu su ke yi.
nuna kanshi ya yi da yatsan shi, "Sharafuddeen ni kake yi ma tsawa? Ka na cikin hayyacinka kuwa? Inna lillahi wa'inna ilahirraji'un.." ya faɗa yana dafe kanshi da tafukan hannayensa..
"Baka ga komai ba Obinna...."
Tsohuwar ce ta faɗa tare da raba jikinta daga na Hateem ta dubi baba Obie da wani ƙasƙantaccen kallo mai cike da tsana..
"Dama bana faɗa maka ba akwai ranar ƙin dillanci? Shin ban fada maka duk min daran daɗewa asirinka zai tonu ba? Dama hausawa sun ce rana dubu ta 6arawo rana ɗaya ta me kaya, yau dubun taka zata cika...."
Girgiza mata kai ya dinga yi idanunsa sun kaɗa jawur tamkar ya fasa ihu haka ya ke ji, ya rasa ya zai yi ya dakatar da ita.."
Cikin raunanniyar murya ya furta, "Kada ki yi min haka! Na roƙe ki, kada ki tona mini asiri, Kada ki raba ni da ƴaƴa na, kada ki raba ni da mutuncina, Ki rufe mini asiri ki agazama rayuwata, ki taimake ni kodan saboda darajar ya'yan mu, In kika fallasa asirina kamar kin fallasa asirin ahalinmu ne, zaki ja mana tozarci a idon duniya...."
Zubewa ya yi akan gwiwowinsa yana ci gaba da girgiza mata kai hadi da marairaice mata fuska don ta tausaya mashi.
Kallo Ya koma sama, kalaman Baba Obie sun ɗaga hankulansu, sun jefa zuciyoyinsu acikin rudani tunma kafin su ji wani asiri ne nashi da baya son ta tona.
"Lokacin da na dinga roƙonka akan kada ka kashe ni ka barni da raina baka yi hakan ba saboda zuciyarka ta ƙeƙashe babu ɗigon imani a ranka, zalunci kadai kasa a gaba, ba irin magiyar da ban yi maka ba amma ka toshe kunnuwanka kuma ahaka kake tunanin ni zan rufa maka asiri bayan Allah ya tseratar da ni uhm?"
Ta faɗa tana kallonshi da raunatattun idanunta. Ruƙe ƙafafunta ya yi da hannayenshi ,"Dan Allah ki rufa mun asiri, kiyi min rai, kada ki kashe min rayuwata, na yi maki alƙawarin zan shiryu..."
cikin jin ƙunar rai ta haɗiyi yawu mai ɗaci tare da kawar da idanunta daga barin kallon shi ta dubi sama hawaye na cigaba da zarya kan kuncinta, ranar da ta daɗe tana gargadinsa akan zuwanta, ba irin jan hankalin da bata yi mashi ba amma yaƙi ji yanzu wa gari ya waya?
"Dan Allah ki faɗa mana dagaske momma ce ke? Dama baki mutu ba kina a raye? Kuma me ya faru dake? Me babanmu ya akaita? Dan Allah ki faɗa mana, kun ɗaga mana hankali, Kun ruɗar damu..." Hajiya Saratu ce ta fada fuskarta a yamutse, Sir Mubarak ya ce,"Momma ki faɗa mana gaskiya, muna son mu ji taya akai kika rayu bayan kin mutu? Kuma me mahaifinmu ya akaita maki? Sannan wani asiri ne nashi da baya son ki faɗa?"
Tsantsar tausayinsu ne ya kamata, saboda tasan in ta faɗa su da farin ciki har abada, watakil ma baƙin cikin mahaifin nasu zai yi silar rasa ran wasu daga cikin su.
Amma ya zata yi bata da mafita da ya wuce wannan, saboda alwashine ta daukarwa kanta, Allah ne ya amsa addu'arta shiyasa har ta rayu don ta tona masa asiri don haka bazata butulce ba, mutun azzalumi irin sa bai cancanci a rufa masa asiri ba.
Cikin karyayyar murya tana kuka ta ce, "Ku yi haƙuri! ku yi haƙuri!! ku yi hakuri!!! da abun da zan faɗa, nasan abun da ciwo amma ya zaku yi ubanku ne ya ja maku, shine silar komai...."
Ta faɗa da tsawa tana kuka jikinta har jijjiga ya ke yi, Chief Owais ya kasa furta kalma, sai rarraba idanunsa ya ke yi akan fuskar Obie da Khala haƙika sun jefa shi a ruɗani.
"MAHAIFINKU OBINNA SHINE ELDER NA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, SHI DIN MUGUN MATSAFI NE, BAIDA IMANI, MUGUNTA DA ZALUNCI YASA A GABA, TUN FIL AZAL, DUKIYARSA BATA HALAL BACE, KUMA SHI BA MUSULMI BANE, ARNE NE, IDAN BAKU SAN KURKUKUN KADDARA BA, ZAN FAYYACE MAKU KOMAI, GIDAN KURKUKUN KADDARA GIDAN MATSAFA NE, YA KAFA SHI TSAWON SHEKARU TALATIN DA DAURIYA, ME AKE AIKATAWA A GIDAN KURKUKUN ƘADDARA? ƘANANUN YARAN DA BASU JI BA BASU GANI BA SUKE KULLEWA A CIKINSHI, BA FUCE BA SHIGE, TUN SUNA JARIRAI SUKE RAINONSU HAR SU GIRMA, ZASU TASO BATARE da addini ba, ba salla ba sallati, sai tsantsagwaran jahilci cike da kansu, basu san wanene mahaliccinsu ba, gaba daya sun tauye masu hakkinsu na rayuwa, abu mafi muni suna azabtar dasu azaba mai radadi, su yi lalata da su, su sha jininsu, su kwanta da gawa, su cire sassan jikin su, kai har jarirai basu bari ba da mata masu ciki suna kwanciya dasu, matasan yan mata da suke tsaka da shan azabar Jinin al'ada a haka suke saduwa dasu duk watan Allah idan ya kama, Ni kaina bazan iya misalta rayukan da suka salwantar ba, Nima ina ɗaya daga cikin fursinonin kurkukun kaddara, saboda tsautsayi yasa na yi masu leƙen asiri nasan sirrinsu shiyasa ya shirya makirci ya dauke ni daga gare ku,....."
Bata ƙarasa maganar ba Sir mubarak ya doka mata tsawar da ta yi silar firgicewarta, Yana huci ya ce, "Ƙaryane! Bazai ta6a zama gaskiya ba, kazafi ki ke yi masa, mahaifinmu bazai ta6a iya aikata munanan zunubban nan ba, mahaifinmu mutumin kirki ne, Mai jin tsoron Allah, mutun ne mai zuciyar imani da tausayi, bazai taba aikata abunda kike zarginsa da shi ba...."
Bai ƙare maganar ba senate Lateef da ya gama harzuka zuciyarshi a wuya yai kukan kura zai shaƙe wuyanta, Sharafuddeen ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar damƙe wuyan hannunsa, yana huci ya ce, "Ka sake ni Sharafudeen!! Wannan mahaukaciyar matar ta rasa wa zata yi ma ƙazafi sai mahaifinmu? Baka ji munanan kalaman da ta jefe shi da su ba? Wai mahaifinmu ne matsafi? Ɗan kungiyar asiri???" Ya faɗa yana zare idanunsa da suka kaɗa jawur.
Cikin jin ƙunar rai His excellency Abdul Razak ya girgiza kai yana fitar da numfashi mai ɗumi ya ce, "Wlh kodai ku fitar da tsohuwar nan ko kuma in kashe ta a gurin nan, ta ya zaku bar mahaukaciya tana cin zarafin mahaifinmu a gaban idanunmu, wannan ai zancen banza ne, wlh sai munyi shari'a dake dole ki fuskanci hukunci mai tsanani...."
Deen ya amshe, "Ai ga irinta nan! tun farkon shugowarta yakamata a kore ta, ni bansan uban waye ya bata iznin shigowa ciki ba! Ku kuma kun yi tsaye kamar wasu sakarkaru a gabanku ake yi wa mahaifinmu ƙazafi, daga gani abokan adawarmu ne suka turota don ta tarwatsa zaman lafiyar mu...." Ya faɗa yana nuna su Hateem.
Kalamansu sun cika kunnan baba Obie, wata irin karaya mai haɗe da faɗuwar gaba ce ta ɗarsu acikin zuciyarshi dake yi mashi wani irin mahaukacin bugun barazana, wani kallo yake binsu da shi mai wuyar fassaruwa ganin yadda suka haƙikance akan kazafi ne ake yi masa saboda yardar da su ka yi da shi.
Cikin raunanniyar murya Khala ta ce, "Koda zaku kashe ni bazan fasa faɗar gaskiya ba, na yi maku uzuri saboda nasan irin yardar da ku ka yi wa mahaifinku, hakika ya cutar da rayuwarku, ya zalunce ku, tsawon shekaru kuna tare da mugun iri acikin ku batare da kun sani ba, Ya daɗe yana munafurtarku...."
Ta ɗan dakata tana jan numfashi, sai ƙoƙarin kai mata bugu suke yi amma Hateem da Sharafudeen sun hana, sai ma suka katangeta ta yadda bazasu iya ta6ata ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, tana a tsakiyar su taci gaba da magana.
"Dukiyarsa bata halal bace, Haramun ce tsantsa, ya ciyar daku da haram! Ya tufatar daku da haram!! Ya gina ku da haram!!! Mahaifinku mutunne mai neman duniya ido rufe, baidamu da lahirarsa ba, koda ya ke baiyi imani da Allah ba, burinshi ya shahara, darajarsa ta ɗaukaka duniya tasan da zaman shi, shiyasa ya jefa kanshi cikin halaka da ku kanku saboda kuma bai barku hakanan ba, duk wata nasara da kuka samu, da duk wata ɗaukaka da kuka samu, sun samo asali ne daga abunda mahaifinku ya ke yi maku, shiyasa baku ta6a faɗuwa ba a rayuwarku, ya sanya maku farin jinin da in har kuka shiga mutane sai kun shahara acikin su, haka zalika in kuka ta6a abu zai yi albarka......"
Wannan karon bakinsu ya mutu bawai don sun yarda da maganar ba, sun dai fara wasiwasi acikin zuciyoyin su.
Yanayin fuskokinsu ya nuna tsantsar tashin hankali da damuwa haɗi da rudanin al'ajabin maganarta.
Baba Obie dake a zuƙunne kan gwiwowinsa ya kasa motsawa ji yake kamar an rufa masa bargon azaba a bayanshi saboda tashin hankalin da ya shiga, da wani ido zai dubesu a wannan baƙar ranar, gaba daya ya ɗimauce ji yake kamar ya haƙa rami ya binne kansa, babban abun takaicin sihirinsa ya ƙi tasiri a kanta, ya so tun farko ya dakatar da ita sai dai Allah bai yarda ba, this time around jikinta akwai kariyar ubangiji.
Tsohuwa Khala bata dakata da yin magana ba taci gaba da cewa, "Sau nawa matayenku suna haihuwar ya'ya su zo babu rai a jikinsu ko bayan sun haihu jariran su mutu?" Ta faɗa tamkar tana yi masu tambaya,
Ta ɗaura da cewa, "To waɗannan yaran ba mutuwa su ka yi ba, ku tambayi ubanku Obinna ina yaran ku suke! Ta faɗa a tsawace tare da nuna shi da yatsan ta.
Tashin hankalin da ba'a saka mashi date!, Wlh alƙalamina bazai iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba, zuciyarsu ta karaya da ganin yadda ya yi shiru ya kasa kare kanshi daga abunda tsohuwar ke tuhumarsa."
Cikin shesshekar kuka Hajiya Saratu take fadin, "Nashiga Uku! Na bani na lalace! Baba dan Allah ka yi magana! Baba ka ƙaryata tsohuwar nan! Baba ka agazamana zuciyarmu ta raunata! al'amarin nan ya fi karfin zukatanmu! Baba mu mun yarda da kai munsan bazaka iya aikata abunda take jefanka da shi ba, wlh kazafi ta ke yi maka, Mahaifinmu ba fasiƙi bane, mahaifinmu ba matsafi bane, mahaifinmu bazai taba iya aikata rashin imanin da kike tuhumarsa da shi ba, dan Allah baba ka tashi ka ƙaryata tsohuwar nan....!"
Tana cigaba da kuka ta nufe shi ta dafa kafaɗunsa tana kokarin mikar da shi tsaye don ya yi magana sai dai ya ƙi bata haɗin kai, wasu irin narka narkan shatun jijiyoyine suka fito saman fatar goshinsa..
"Baba ka taimaka min, Ka agazama rayuwarmu, baba ka yi magana, na roƙe ka, dan Allah dan soyayyarka da manzon Allah SAW......"
Murmushin takaici khala ta yi, "Hmmmm Saratu dama kin daina wahalar da yawun bakin ki, saboda a halin yanzu mahaifinku baida bakin magana, wannan kaɗai ya isa yasa ku gasgata magana ta..."
Ta faɗa tana kallon fuskar baba Obie dake fitar da gumin zufa, shatun jijiyoyin wuyansa sun fito ruɗu ruɗu, jikinshi ya ɗauki wani irin mahaukacin zafi.
"Duk wani jariri da matayenku suka haifa ya zo ba a raye ba sune suke ɗauke shi daga gare ku, da haɗin bakin munafukan likitocin asibitinsa, Ku tambayi munafuki MD Dr Jidanna, da Dr Adam da kuma Dr chisom, da sa hannunsu ake yi maku wannan aika aikar...."
"Zaku haifi ɗa ku ganshi a mace alhalin ba shi bane rufa ido su ke yi maku su yi musayar shi da aljani su ɗauke na gaskiyar su tafi da shi gidan kurkukun kaddara, ku kuma ku dauki aljanin ku yi jana'izarsa ku rufe a ƙabari da sunan jinjirinku ku ka rufe...." ta faɗa cike da takaici,
"Haƙiƙa Obie ya zalunce ku wlh wata shari'ar sai dai a lahira, amma fasiƙin mutumin nan ya daɗe yana aikata luwaɗi da zina da jikokinsa da ya sadaukar a gidan kurkukun kaddara, ya sha jininsu, ya kashe su saboda neman duniya, bashi kaɗai ba harda sauran fasiƙan da suke aikata fasadi a bayan ƙasa, Elders din suna da yawa sune miyagun dake sadaukar da jininsu matsayin fursinoni, da yawa ma ƴa'ƴan naku azaba ce ke kashe su, cikin ka so ɗari baifi ka so goma ne ya rage daga cikin su ba...."
Numfashinta ne ya fara tsaitsayawa, jini ya fara bleeding daga cikin hancinta hakan ba ƙaramin ɗaga hankalin Sharafudeen da Hateem ya yi ba..
Daurewa ta yi duk da azabar da ta ke ji a jikinta a haka ta cije ta ci gaba da cewa, "Na rantse da wanda raina ya ke a hannunshi duk abunda na faɗa maku ba ƙarya bane, idan baku yarda ba, gayanan agabanku ku turkeshi ya fada maku gaskiya...."
Tsayawa ta yi tana haki fuskarta ta jiƙe sharkaf da gumi, ta dafe saitin zuciyarta da tafin hannunta...
"Kamar yadda na faɗa maku, bashi kaɗai bane Elder, akwai muƙarrabansa da suke take masa baya, Amininsa Ifeanyichukwu inkiya Jan kunne amma a gidan kurkukun kaddara jan harshe shine nickname dinsa, shine Mataimakinsa a tare suke aikata fasadi, abun takaici sun auri junansu tun da daɗewa saboda tsantsagwaran jahilci da tumasanci...."
Kutumar U! Zaro idanu suka yi kamar ƙwayar zasu faɗo ƙasa, sun shiga matsanancin tashin hankali, maganarta ta ƙara dagula masu lissafi, jin abun suke kamar wasan kwaikwayo.
"Bayan haka, surukinku mijin Saratu, shine Jan kunne na gidan kurkukun ƙaddara..." Tunkan ta ƙarasa maganar hajiya Saratu ta daddafe kanta da tafukan hannayenta, ta dinga girgiza kanta, tsabar kiɗimar da ta yi ne yasa ta dinga sambatu kowace addu'a ta zo bakinta furta ta kawai ta ke yi..
Runtse idanunta ta yi ruɗu yama hana ta iya tantance me Khala take nufi, buɗe idanunta keda wuya Unexpected ta hango Pravin da ya arta a guje ya nufi sashen yan aikin gidan, aikuwa jikinta na 6ari tabi bayan shi...
Khala bata dakata ba, ta ci gaba da cewa, "Sir Benjamin baturen amuruka, abokin mahaifinku wanda suka yi tashen yawon duniyarsu atare da obie da amininsa, shine jan le6e na gidan kurkukun ƙaddara, mugun fasiƙi ne....."
"Bayan shi sai baƙin shaidanin da taƙadarancin sa yafi na fir'auna, zan iya cewa tun da Allah ya halicce ni ban ta6a ganin mugun bawa irinsa ba, bazan iya misalta mugayen zunubban da yake aikatawa ba, shine mai bada shawara kuma head na kula da bangaren bada horon giants ɗin kurkukun ƙaddara, baida imani ko misƙala zarratin, asalin shi bawan Obie ne daga baya da likafa ta ci gaba sai ya bashi muƙamin Elder...shish.. Shish.....
Kasa ƙarasawa ta yi saboda abun da ya sarƙe maƙoshinta, dama ba koshin lafiya ne da ita ba, jiri ne ya kwasheta a galabaice ta yanke jiki zata faɗi, cikin sauri Sharafudden ya sungumeta ya kwantar da ita akan doguwar kujera, sai kokarin ƙarasa maganar take yi amma ta kasa...
Wai shin Ina Chief Owais? bawan Allah Komai dake faruwa akan idanunsa kuma kunnuwansa na sauraro, kwata kwata baya acikin hayyacin shi, zufar dake tsastsafowa ta saman fatarsa ta jiƙe jikin shi sharkaf, kwata kwata ya gaza yarda da abunda Khala ta faɗa, Gani yake kamar mafarki yake yi ba gaske bane, duk da ya gama raunana zuciyarshi ta karaya da ganin yadda baba Obie ya yi shiru bai tanka ba! Hakan na nufin da gaske ne ba kazafi aka yi masa ba tun da ya kasa kare kan shi, inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! La'haula wala quwata illa billah, da wannan ranar ƙwara mutuwarsa, addu'o'i yake ta nanatawa acikin zuciyar shi..
Jiki a mace Sir mubarak ya zauna kan Sofa, zafi ne ya taso mashi har ta kai ga ya tu6e rigar shi ya jefar da ita ƙasa, ya ɗaura gwiwar hannunsa akan hand sofa ya zagba uban tagumi, kamar wanda ya rasa gata a duniya.
"Deen! kana jin abun da nake ji kuwa? Deen Ka tsunƙule ni dan Allah inaso na tabbatar in ba mafarki nake yi ba..."
Cikin raunanniyar murya His excellency Abdul Razak ya faɗa yana kallon His excellency Deen da ya haɗa uban gumi a jikin shi, girgiza kai ya yi cikin karyayyar murya ya ce, "Ba mafarki bane, kada mu yaudari kanmu! Da gaske ne komai ke faruwa, baba da muke sa ran zai kare kansa daga ƙazafin da tsohuwar nan ta yi masa ya kasa, gashi nan yana ji ya yi shiru..." Ya faɗa yana nuna Obie..
Muryar Sharafuddeen ce ta katse shi da cewa, "Abun da momma ta faɗa akansa ba ƙarya bane, ya aikata ne shiyasa ya kasa kare kansa....."
"In kuwa hakan ya tabbata gaskiya ne, Baba ka kashe mana rayuwa, ka gama da mu, mun mutu, mun bani mun shiga Uku! Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un......"
Senate Lateef da ya ɗauko maganar bai kaita karshe ba Ya yanke jiki ya faɗi a sume, a firgice Deen da Abdul Razak suka rufa akan shi suna ambaton sunan shi haɗi da bubbuga jikin shi don ya tashi..
"Ruwa, tana buƙatar ruwa..."
Hateem ne ya yi maganar, cikin sauri Sharafuddeen ya je ya dauko bottle water me sanyi yana gab da zai ƙaraso Ya lura da Owais dake a tsaye baya motsi da alama suman tsaye ya yi, wuce shi yayi ya nufi Hateem ya miƙa masa robar ruwan Ya kar6a yatsun hannunsa na kerma ya kanga ma tsohuwa Khala a baki, kusan rabin ruwan ta shanye sam ta kasa magana idanunta ma sun rufe gam bata iya buɗe su.
Kar6ar robar Sharafuden ya yi daga hannun Hateem cike da rashin kuzari ya nufi su Deen Ya mika masu bayan sun yayyafa ma Senate Lateef ya farfado yana sambatu kamar mai tabin hankali har yana fadin Allah yasa mafarkine abunda ya ji.
Kar6ar robar ruwan ya yi daga hannun Deen ya je gaban Owais ya daddage ya watsa mashi ruwan a saman fuskar shi, lokaci ɗaya yaja dogon numfashi ya furzar da shi da wani irin zafi.
Kamar mahaukaci haka ya damƙi gaban rigar Sharafudeen hawaye na zarya akan kuncinsa da wata irin karyayyar murya ya ce,"Ka faɗa min kaima kana ɗaya daga cikinsu?"
Ya fahimci ba ya acikin hayyacinshi, tsigar jikinshi duk ta tashi haiƙam zuciya ta riga da ta tsinke.
Tsananin tausayin shine ya kama shi, Cikin sanyin murya ya ce, "Bana ɗaya daga cikin su Owais..."
"Meyasa ka kasa kare kanka lokacin dana tambayeka?"
Girgiza kanshi ya yi, "Saboda na daukarwa baba alƙawarin bazan faɗa ma kowa ba..." Katse shi ya yi, "Wani alƙawari ne ka daukar masa?"
"Shine ya kira ni a waya ya faɗamin zaku je kai farmaki gurin matsafa masu haɗarin gaske, ya gargade ni akan kada in kuskura in barka ka je, nace mashi ai yafi kusa da kai kafi jin ma maganarshi, me zai hana ya yi maka magana, sai ya ce min ba ya son bacin ranka ne yasan idan ya hana ka zuwa baza ka ji daɗi ba, shiyasa ya kasa amma yasan ni idan na yi maka magana bazaka ji komai ba, kawai in baka umarnin kada ka je, nace mashi baba ban ta6a hana Owais ya je kai farmaki ba, hasalima ni nake ƙarfafa masa gwiwa akan aikinsa idan na hana sa wannan karan dole zai ji ba daɗi ne, sai ya fara min faɗa yana fadin har shi zai bani umarni in ƙi bi! Yana magana ina magana, da ni da owais din duka ba a ƙarƙashin ikon shi muke ba? Na dinga bashi haƙuri har saida na amince zan yi maka magana tukunna ya haƙura, Sannan ya ce zai turo da ɗan saƙo da maganin bacci in saka maka a cikin Coffee, saboda in kasa kafiya ka turje akan ba zaka bi umarnina ba, sai in baka kasha coffee din, kuma baya son kasan shi ya sakani, nayi masa alkawarin bazan bari ka sani ba, kaji dalilin da yasa lokacin da na kira ka a resting home dina ka ƙi bani hadin kai ni kuma na baka coffeen dana zuba maganin baccin ka sha...."
Gaba ɗaya maganganun Sharafudden a cikin kunnuwansu sun ji komai, hankulansu sun ƙara tashi, cikin rawar murya Owais ya ce, "Kana nufin baba shine ya hanani kai farmaki, kuma shine ya sa ka bani maganin bacci, amma a daren ranar ina ka je saboda an faɗa min ba a gan ka ba?" Ya fada a ƙagare da son jin amsar shi..
"Owais ni ban je ko'ina ba, ina a villa, adakin mommynka na kwana zaka iya tambayarta ka ji, bayan haka sanin kowannanku ne Villa tana da tsaro, ba yadda za'a yi shugaban ƙasa ya yi fitar sirri in the midst of the night batare da wani daga cikin security ya bi shi ba, Allah shine shaida ta..." Ya fada fuskarsa a yamutse.
"Hakan na nufin Baba shine ya ƙulla maka makirci saboda ya ɗaura maka laifin sa? Ko don ya shiga tsakanina da kai?"
Jinjina kai Sharafudden ya yi,"Babu tantama Owais, baba shine Master planner ɗin da ke shirya maƙarƙashiya atsakaninmu, bansan meyasa ya yi hakan ba..."
Cikin shesshekar kuka ya ƙarashe maganar, wata irin juwa ce ta ɗibi Chief ya yi taga taga zai kife ƙasa cikin zafin nama Sharafudeen ya janyoshi ya rungume abunsa akan kirjinshi, atare suka fashe da matsanancin kuka tamkar ransu zai fita.
Haƙiƙa baba Obie ya muzanta, kunyar duniya ta kama shi, ya shiga matsananciyar damuwa, bai ta6a zaton wannan ranar zata zo ba, Wani irin azababben ƙunci da bakin ciki da takaici ne suka turnuke zuciyar shi, jin kanshi yake kamar ba mutun ba saboda tashin hankali.
A zabure ya miƙe kamar mahaukaci ya juya jikinsa na 6ari zai bar wurin sai dai kafin ya kai ga tafiya Owais ya hango shi, a zuciye ya 6an6are jikinsa daga na daddynsa ya nufi baba Obie cikin zafin nama ya damƙi damtsen hannunsa ya juyo da shi suka fuskanci juna gaba da gaba, kunya ta hana baba Obie ya haɗa ido da Owais saidai ya sadda kanshi ƙasa.
Cikin raunanniyar murya ya ce, "Baba kai kaɗai ne zaka share min shakku na, Ina so na ji daga bakin ka, da gaske kaine Elder na gidan kurkukun ƙaddara? Kuma kaine mutumin da ya fitar da ni daga fagen yaƙi ya jefa ni a daki uhum??"
Ya faɗa cike da fargaban amsar da zai bashi, wlh ya yi fatan ace zai iya kare kansa sai dai ya kasa saboda asirinsa ya riga da ya tonu.
Gaba ɗaya idanunsu na a kan fuskarshi amsar shi kawai suke jira su ji, batare da ya ɗago da idanunshi ya dube shi ba ya jinjina mashi kai alamar Eh, a lokaci ji ya yi kamar ya haƙa ƙasa ya binne kansa saboda baƙin cikin da ya ziyarci zuciyarshi, raɗaɗin da suka ji yafi na ƙunar wuta zafi..Ya Ilahi!
Zuciya ce ta ɗibi Owais baisan sa'adda ya ci kwalar rigarshi ba, da hannu biyu ya damƙe shi sosai jikinshi na 6ari.
Hakan ba ƙaramin karya zuciyar Obie ya yi ba, duk irin jarumtakar namiji hakan bai hana sun fashe da kuka ba kamar ƙananun yara, gaba ɗaya sautin koke kokensu ya cika falon, wasu suka dafe kawunansu da tafukan hannayensu saboda azabar radadin da zuciyarsu ke yi musu, wlh sun yi danasanin zuwansu duniya a lokacin, sun ji ɗaci a ransu, ranar ta zame masu mafi muni a rayuwarsu. Gaba daya suka kewaye shi suna tambayar shi don me zai yi musu haka? Meyasa ya ci amanarsu ya ha'ince su? Wannan wani irin neman duniya ne? Me yasa ya aikata musu hakan? Wlh Hankalinsu ya tashi matuƙa, duk sun fita hayyacin su, kuka kawai suke yi kamar ransu zai fita..
Hakan ba ƙaramin karya zuciyar Obie ya yi ba, bai ta6a danasanin irin rayuwar da ya daukarwa kansa ba irin yau, saboda Allah ya jarabce shi da masifar son ya'yan shi, Koda ya ke sadaukar da jikokin shi bai ta6a sadaukar da ya'yan shi ba.
daƙyar ya iya haɗiye baƙin cikin shi, da wata irin karyayyar murya ya furta, "INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN!!! Na shiga Uku! wlh na daɗe ina fargaban zuwan wannan ranar, dama nasan duk mun daran daɗewa asirina zai tonu ne sai dai ban ta6a zaton zai tonu ta wannan hanyar ba! Ranar da nake jin zullumi da fargaban zuwanta, ranar da nake jiye ma kaina tsoron zuwanta, ya zan yi da rayuwana? ya zan yi da rayuwarku? Nasan na cutar da rayuwarku cuta mafi muni, na zalunce ku, na kuma zalunci kaina, Amma koma dai menene bakin alƙalami ya riga da ya bushe, na riga dana tabka babban kuskure, ban kuma san da wasu kalmomi zan roƙe ku gafara ba, banma cancanci in nemi yafiya agurinku ba, wlh na muzanta, na tozarta, na ji kunyar haɗa idanuna da ku, kaicona!...."
Bai ƙarasa maganar ba ya fashe da kuka, hawaye suka wanke fuskar shi, mutumin da sun manta when last suka ga hawaye ya zuba daga cikin idanunsa saboda jarumtakarsa ashe tsantsagwaran matsafine, Yana kuka suna kuka an rasa me lallashin wani, daƙyar yake kallon fuskokinsu cike da jin nauyin abun kunyar da ya aikata musu.
"Nasan na biyewa son zuciya, amma wallahi ba laifina bane, Nima gado na yi, tun kakanninmu da iyayenmu na taso acikin matsafa, shine hanyar samunmu, na yaudare ku da musulunci amma ni ba musulmi bane, arne ne ni kamar yadda ta faɗa muku, tun da na taso rayuwata bansan mai kyau da mara kyau ba haka iyayena suka tarbiyantar da ni, duk abubuwan da suka faru son zuciya ne da son ɗaukaka, buri na in tara dukiya, in ɗaukaka in zama shahararre a duniya, ƴa'ƴana ma su ɗaukaka a idon duniya, wannan dalilinne yasa gaba ɗaya kuka ɗaukaka kowannanku na nema masa duniya kuma ya same ta..." Bai ƙare maganar ba HATEEM ya katse shi ta hanyar cakumar shi cikin tsananin tashin hankali ya furta, "Baba! Baba!! baba!!!...." Idanuwansu cikin na juna a marairaice yake kallon shi..
"Meyasa ka za6i ka ciyar da mu haram? Baba duk irin ƙaunar da muke yi maka, kullum burinmu mu kare maka mutuncinka sai gashi kai ka zubar mana da namu mutuncin, ɗaukakar daka sama mana ta tashi a banza wlh! Saboda da zarar mutane sun ji abunda kake aikatawa wlh mun zama abun gudu, za'a juya mana baya ne a tsangwamemu zamu zama abun ƙyama, makiya zasu samu damar cuzguna mana, Baba ka bar mana mummunan tabon da mutane zasu dinga cin zarafin mu da shi! Haba baba! Wlh ka bamu mamaki baba, wai mahaifinmu ne yake aikata munanan zunubban nan?" Ya faɗa yana haɗiyar yawu mai tsananin ɗaci cikin mutuwar jiki ya sake shi..
Sharafudeen ya ɗaura da cewa, "Baba yanzu ina amfanin irin wannan? Wace riba ka samu baba? Ina hankalinka yake? Tayaya ka bari shaidan da zuciya suka rinjaye ka? Kamanta da wata rana zaka mutu ka koma ga Allah, baba Idan ka nema mana duniya lahirarmu fa? Ya kake so mu yi baba? Muna alfahari da kai, kaine abun tunƙahon mu, kaine silar ɗaukakarmu ashe mun yaudari kanmu baba, A yau mutuncinka ya zube acikin idanunmu baka da sauran daraja baba, wlh da wannan bakin cikin daka ƙunsa mana da kashe mu ka yi kamar yadda ka saba kashe ya'yan mutane...!"
Kuka ne ya ci ƙarfinsa har ya kasa karasa maganar..
Baba Obie sai kuka yake yi babu ƙaƙƙautawa..
Senate Lateef ya ce, "Baba wace shafewar basira ce ta same ka? Ni abun da ya dauremin kai yadda har ka iya kashe mutun ka sha jinin shi, ka kuma lalata rayuwar yaran da basu ji ba basu gani ba, baba wa ya koya maka zaluncin nan? Har yanzu na gaza yarda kaine kake aikata hakan Baba, Tsawon shekara nawa kana aikata fasadi a doron ƙasa! Wallah baba da ace ka yi hakuri tun fil azal ka yi rayuwarka cikin talaucinka da sai ya fiye mana kwanciyar hankali, shi arziki da daukaka na Allah ne, sai wanda ya so yake bawa, watakil ma kana ɗaya daga cikin wadanda Allah ya tsaga da rabonsu kaine baka sani ba, ka biyewa son zuciyar ka baba, gayanan ka jefa rayuwarmu a halaka, bayan haka jin dadin duniya ƙalilan ne baba, gaba dayanmu mutuwa zamu yi, komai muka mallaka anan gidan duniya zamu barshi, lahiri itace dawwamammiya, wlh da wannan masifar daka jefa mu a ciki wlh gara ace mun taso rayuwarmu a matsayin musakai marasa gata a duniya da dai irin wannan rayuwar, baba yanzu da ka ɗaukakamu ya zaka yi da mu? sai da ka bari duniyar tasan da zamanmu ana yi mana kallon mutane masu daraja da ƙima, masu martaba a idon duniya, yanzu idan suka ji miyagun laifukan da kake aikatawa me kake tunanin zai biyo baya?" Ya jefa mashi tambayar yana kuka yana girgiza kai.
kafafunsa ne suka gaza ɗaukarsa ya zube kan gwiwowinsa, idanunsa sun rune jawur, kumatunsa sun yi jajir, duk ya faffasa labbansa da haƙoransa, gemunsa ya jiƙe sharkaf da ruwan hawayensa, Ko'ina na jikinsa zufa ce take tsattsafo masa kamar babu A.c a falon.
Wlh ya sadaƙas bai ta6a zaton zai ji kunyar zunubban da yake aikatawa ba sai yau da Khala ta fallasa asirin sa a gaban ya'yansa mafi soyuwa a gare shi.
Dukkan ilahirin jikinsa kerma ya ke yi, ga wani irin azababben zazzabi da ya lulllu6esa, mutumin da sai ya yi shekara da shekaru bai yi ciwo ba saboda ƙoshin lafiyar dake gare shi to yau dai hada matsanancin ciwon kai, bazama a raza ciwon zuciya na farat daya ba saboda depression din da ya kama shi, gaba ɗaya suka zauna kewaye da shi kamar malami da almajiransa kuka hada majina, sun kasa tsayar da kan su. 😭
Daƙyar ya iya furta, "Idan na ce ku yi hakuri ban yi maku adalci ba, iya cutarwa na cutar da rayuwarku, ban cancanta na ci gaba da rayuwa ba, nasan a halin yanzu da kuka gano wanene ni kun tsane ni fiye da komai na duniyar nan, don haka na miƙa wuyana a gare ku, nasan na aikata maku ba dai dai ba, Ku yanke mini duk wani hukunci da kuka ga ya dace dani, ku azabtar da ni, sannan ku kashe ni, idan ba haka ba, Ni zan kashe kaina, saboda bazan iya cigaba da rayuwa da abun kunyar da na aikata muku ba..." Yana faɗa yana kuka haɗi da tari.
Sama sama khala dake a kwance kan Sofa take jiyo maganganunsu, baiwar Allah ita kadai tasan halin da take a ciki, ta tona masa asiri burinta ya cika sai dai bata yi farin ciki ba, saboda halin da ya'yan shi suka shiga shiyasa kafin ka fara aikata wani abu mara kyau ka fara tunanin makomarka da kuma halin da zaka jefa wanda ya yarda da kai abun yana da ciwo.
"Ku kashe ni, in har baku kashe ni ba mutane bazasu ƙyale ni ba, ku kashe ni kawai nafi so na mutu a hannunku, ko dan saboda ku dauki fansar abun dana aikata maku, ku kashe ni na ce, in ba haka ba zan kashe kaina..."
Zumbur ya miƙe jikinshi na kerma, Lokaci daya gabansu ya fadi ganin jinin da ya wanke gaban wandon shi.
Har suna haɗa baki gurin ambaton sunanshi, Allah sarki duk da abun da ya aikata hakan bai hana su ɗaga hankalinsu a kanshi ba,
"Mu kai shi asibiti kada ya rasa ranshi!" Sharafuddeen ne ya yi maganar a ruɗe.
Har sai da baba Obie ya dube shi da raunatattun idanunsa, ƙasa ƙasa da murya ya ce, "Duk abunda na yi maka baisa ka daina damuwa da ni ba Sharafuddeen....?" Girgiza kai ya yi, "Ku yi hakuri bazan je asibiti ba, ku barni a gida, in ma mutuwace ta riske ni a cikin ku...." Yana ƙarasa maganar ya shallake su ya juya a hanzarce ya nufi part ɗinsa, da gudu suka bi bayanshi kafin su ƙaraso tuni ya shige ɗakin ya ja ƙofa ya datseta ta yadda ba zasu iya buɗeta ba. 😭
Yanke jiki ya yi ya faɗi kan floor ya dinga birgima yana bubbuga goshinsa kan floor har saida ya fashe jini ya 6alle masa, daga waje suna juyo kururuwar azabar da yake fitarwa mai kuwar gaske kamar zai fasa dodon kunnuwansu.
Da iya ƙarfinsu na karshe suka dinga bubbuga ƙofar hadi da ambaton sunan shi da karfi.
Chief kamar zai 6alle ƙofar da kafaɗarsa ya dinga bangazarta duk da raɗadin da ya ke ji.
"Baba ka buɗe mana ƙofa, bamu gama magana da kai ba, baba kada ka mutu kabar mu, baba dan Allah ka buɗe bamu gaji da ganin ka ba, akwai tambayoyin da baka bamu amsoshinsu ba, baba! baba!!, zamu iya yafe maka amma ka buɗe mana kofar, baba pls, baba pls, idan ka tafi ka barmu a cikin wannan mawuyacin halin daka jefa mu ya kake so mu yi da rayuwarmu! Ka taimaka mana baba, ka fitar damu baba.. "
Ba irin bugun da ba su yi ma kofar ba amma ta ƙi 6allewa, a karshe da suka galabaita a gaban kofar ɗakin nashi suka zazzauna suna cigaba da yin kuka kamar masu zaman makoki.
Gaba ɗaya abun da ke faruwa ƴan aikin gidan basu sani ba, saboda anyi masu iyaka da shiga falon dama ƙa'ida idan za'ayi family meeting ba'a buƙatar bare agurin shiyasa kwata kwata basu leƙo ba kuma basu ji sautin koke koken da ake yi ba, saboda akwai tazara tsakanin sashen su da main falo.
_____________________PRAVIN 🥵
Tun lokacin da khala ta fara fallasa asirin su, cikin rawar jiki ya bar falon batare da sanin kowan nan su ba, bai nufi ko'ina ba sai sashen yan aikin gidan.
A lokacin Hajjaty tana a ƙudundune cikin bargo har ta samu bacci ya ɗan dauke ta, kwatsam ba zato ba tsammani kamar daga sama ta ji an cakumeta, ta fasa ƙara tana kokarin kwache kanta cikin ruɗu da tashin hankali, kwata kwata batasan wanene ba saboda bargon da ya lullu6e fuskarta, a saman kafaɗarshi ya sa6e ta, tana kuka tana ihu tare da ambaton sunan pravin don ya kawo mata ɗauki, juyawar da zai yi keda wuya ya yi arba da hajiya Saratu dake shugowa ɗakin afujajan nan take gabanshi ya yanke ya faɗi ya zazzare idanunshi yana kallon ta kamar yadda take kallonshi da tsantsar tashin hankali akan fuskarta..
Numfashinta na fita da hucin bacin rai ta ce,"Munafiki, Gidan ubanwa zaka kai ta eye? Yan iska maciya amana, wato Kun daɗe kuna cin amanata, yanzu da ka ga asirinka ya tonu shine ka lalla6o ka saci jiki ka shugo don ka dauki kwartuwarka don ku gudu ko?" Ta faɗa tana zare idanunta.
Tsawa ya daka mata har saida ta razana, muryarsa na rawa ya ce, "Ki matsa ki bani wuri in wuce tunkafin in yi maki illah!"
Cikin fusatacciyar murya ta ce, "Illah kuma ta nawa? Ka bani mamaki pravin, Ka karya min zuciyata, munafuki dama na daɗe ina zargin Hajjaty ashe tare kuke aikata fasiƙanci, wai a haka na aure ka na haifa maka ƴa'ƴa, Ka cutar da rayuwata pravin, hakkina da na ya'yanka bazai ta6a bari ka gama da duniya lafiya ba wlh, kuma na rantse babu gidan ubanda zaku je, mayaudaran banza, dole ku gurbi abun da kuka shuka..."
Bata ƙarasa maganar ba, sakamakon naushin da ya sakar mata akan kuncinta, nan take gefen bakinta ya fashe ta fara bleeding, azabar zafin da ta ji ne yasa ta dafe gefen bakin, da mamaki ta furta,"Pravin! yau da hannunka ka dake ni? Inna lillahi..! " Rai a 6ace ta yi kukan kura ta haɗa su duka biyun da shi da Hajjaty ta hankaɗa su gaba ɗaya suka kife ƙasa, bargon jikin Hajjaty ya warware baiwar Allah tuni ta jima da sumewa sakamakon buguwar da kanta yayi dama ya lafiyar gwiwa.
Ransa ya 6aci matuƙa, a harzuƙe ya yunƙura ya mike Ya nufi hajiya Saratu batai aune ba, ya damƙi ƙeyarta da hannunshi ya jata ta karfi ya nufi mirror tana ta kokarin ta kwace kanta sai dai ta kasa saboda raunin da zuciyarta ta yi yasa ta kasa ta6uka komai.
Yana isa gaban madubin ya buga kanta jikin shi nan take madubin ya fashe, duk ya sossoke fuskarta, tuni ta fara bleeding, kukan ma ta kasa yi saboda zogin azabar da ya ratsa sassan jikin ta, ya ɗago da kan nata ya wurgar da da ita a galabaice ta kife kan floor ta mirgina numfashinta yana ta kokawar ɗaukewa.
Hakan bai masa ba sai da ya take yatsun hannayen ta da tafin ƙafarsa duk ya murjesu suka faffashe jini ya soma tsastsafowa.
kwata kwata babu imani a zuciyarsa, ga idanun nan nasa sun kaɗa jawur kamar an watsa barkono a cikin su, Ya na huci ya furta, "Allah ya isa tsakanina da ku, Dangin matsafa masu arziƙin jini, Duk ubanku ne ya ja min shiga halin da nake a ciki, shine mugun da ya sa na jefa rayuwata cikin halaka ina zaman zamana lafiya, dama ni ban ta6a son ki ba, dukiyarki ce tasa na aureki da kuma kwaɗayin surar jikin ki, Kin daɗe kina baƙanta min rai ke ga mai arziki ɗiyar ƙaruna, ki yi ta min gorin arziƙi don ina zaune a gidan ku, to ai ga irinta nan, yanzu ai kin gane arzikin naku bana halal bane ko? Ya faɗa yana tottafa mata yawu a kan fuskarta.
"Kuɗin jini ne kuke tunƙaho da su, wlh badan ƴa'yan dake tsakanina dake ba da ba abun da zai hana in huce haushina a kanki, zan bar ki da ranki ne ba don na so ba.."
Ya faɗa yana kallon fuskarta da ta jiƙe sharkaf da jini kamanninta har sun sauya saboda azaba ta gama fita hayyacinta, juyawa ya yi da sauri ya nufi bargon Hajjaty ya janyo shi ya rufa mata a jikinta tare da nannaɗeta a cikin bargon ya mayar da ita kan kafaɗarsa, Ya tsallake hajiya Saratu dake a kwance rai hannun Allah cikin sauri ya fuce daga ɗakin, batare da sanin kowa ba ya gudu daga Estate ɗin......💔
___________________________________✍️
*_(SHIN ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN AHLIN FAMILYN SUKA KARASO SUKA JI ABUN DA KE FARUWA❓GA HAJIYA SARATU AKWANCE RAI HANNUN ALLAH! WA ZAI KAI MATA DAUKI❓ YA RAYUWAR BABA OBIE ZATA KAYA ZAI KASHE KANSHI NE KO KUWA❓ ME KUKE TUNANIN ZAI BIYO BAYA IDAN SAURAN ELDERS SUKA JI LABARIN ASIRIN ELDER YA TONU❓YA LABARIN PRAVIN DAYA GUDU DA HAJJATY GIDAN UBAN WA ZAIJE❓ DA WANI IDO YA'YAN BABA OBIE ZASU FUSKANCI DUNIYA? KUNA TUNANIN BA ZASU FUSKANCI KALUBALE BA AKAN MUKAMAN SU❓ TAYA ZA'A HADA KOWANI PRISONERS DA IYAYENSA❓ TAYA ZA'A KAMA SAURAN ELDER❓ TO WAINI TAYAYA MA AKAI TSOHUWA KHALA TA RAYU?😳 YANZU NE LOKACIN DA ZAKU ƊAURA ƊAMARARKU TAMAU DON JIN YADDA ZATA KAYA🔥💪_*
*Gani ga wane Ya ishi wane Jin tsoron Allah😭 page din nan ya taba zuciyata)*
*DAGA ALƘALAMIN BOSS BATURE🔥🔥🔥🔥😭*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*
Table of Contents