Skip to content

Chapter 2

Part dinshi tashiga domin tagyara amma abin duniya yadameta jikinta bbu qwari.

16,919 words 0 views Progress saved
Download Book

************

Daqer tasamu tayi wanka dukda Mummy tanata faman lallabarta ko abincin kirki bataciba shima dan taga Mummy tatashi hankalinta shiyasa taci.

Zaune take porlour tayi tagumi abin duniya yadameta,Mummy ce tafito porlour tana ganin yanayin da Hanan take ciki jikinta yyi sanyi,ahankali taqaraso kusa da ita tazauna tare da dafata.

Da sauri tajuyo sakamokon jinda tayi andafata,tana ganin Mummy wasu sabbin hawaye suka zubo mata.

Mummy tasanyaya murya tace"Hanan,dan Allah kirage wannan damuwar"

Hanan taci gaba da kuka bata iya cewa komae ba.

Mummy tace"oh Hanan cigaba kikayi da kukan?"

Hanan tace"Mummy idan banyi kuka ba me zanyi arayuwana,yarabani da yarona,Mummy inason yaya Rafeeq amma shi bayasona bansan me yasaba"

Mummy tace"kiyi haquri Hanan,kuma maganar Sultan yanzu zanje innemi alfarmar abamushi,amma inaso kikwantar da hankalinki,kinji 'yata"

Hanan tace"toh Mummy"

Mummy tashiga cikin bedroom dinta tashirya cikin wani tsadadden lace milk tayi kyau sosae,sannan tadauki mayafinta tafito porlour bayan talalla6i Hanan sannan tayi mata sallama tafita.

Bisa hannun kujera takifa kanta taci gaba da kukanta daga qarshe takoma cikin bedroom dinta.

Da kanta take driving zuciyarta cike da tinani kala2,batasan yadda zata billoma Alhaji ba da wannan zancen gashi dama baya qasar.

Ahaka ta'isa gidan,bayan tayi parking din motarta aharabar gidan,cikin sallama tashiga main porlour dinsu.

Zuhra ce zaune aporlour tayi tagumi,bataji sallamar Mummy ba sbd tayi nisa cikin tinani.

Saida Mummy tayi sallama sau ukku sannan ta'ansa.

Zuhra taqaqaro murmushi tare da yimata sannu da zuwa.

Cikin fara'a Mummy ta'ansa,tare da samun wuri tazauna.

Zuhra tafita tadawo da ruwan roba da lemun kwali tare da glass cup guda biyu zubama Mummy.

Zuhra tagaishe da ita cikin girmamawa,Mummy ta'ansa sannan tadan kurbi ruwan dan kada Zuhra taga ko wani abu ne.

Mummy tace"Rafeeq yana nan ko?"

Zuhra tace"bayanan Mummy"

Mummy tace"toh shikenan bari intafi sae anjima"

Zuhra tace"toh Mummy kigaida gida"

Mummy tashiga mota da niyya tafiya gida amma tana jin komawa gida batare da Sultan ba irin halin da Hanan zata shiga.

Sae wani sashe na zuciyarta yace tatafi gidansu Rafeeq,haka kau akayi takarkata hancin motarta zuwa unguwarsu Haj. Maryam.

*************

Yaya Rafeeq yana shiga gidan zuciyarshi cike da fargaba,cikin sa'a lokacin Mami bata dade da dawowa daga wurin aiki ba.

Bayan yagaishe da Mami,Mami tana yima Sultan wasa tace"toh anfara yawo da shi ne shi daya"

Yaya Rafeeq yace"aah Mami"

Mami tadubeshi tace"ina Hanan din?"

Rafeeq yaduqar da kanshi qasa yace"Mami tana gidansu"

Mami tace"kamar ya tana gidansu Rafeeq?"

Rafeeq yace"Mami munsamu matsala da ita ne"

Mami tace"Rafeeq wane irin matsalane wanda agida bazaku iya shiryawaba har yakaiga tatafi gidansu?"

Rafeeq yace"Mami kugafarce ni amma nasaki Hanan"

Mami tace"subhanallah,Rafeeq kasan abinda kake fada kuwa?"

Abba ne yashigo da alama daga masallaci yake,suna ganinshi sukayi cirko2 suna kallonshi.

Bayan sunyi mashi sannu da zuwa,yazauna,yaya Rafeeq yagaishe da shi.

Abba ya'anshi Sultan yanayi mashi wasa yace"lfy Rafeeq naganka hankalinka tashe?"

Yaya Rafeeq bakinshi yana rawa yace"lfy la......"

Mami tace"inafa lfy Alhaji,wani tashin hankali da yaron nan yazomin da shi"

Abba yace"me ke faruwa ne?"

Mami tayi shiru,Abba yyima Rafeeq tsawa kai bakaji nane?"

Rafeeq yasadda kanshi qasa yace"Abba dan Allah kugafarce ni,nayi wani babban kuskure batare da shawarar ku ba,nasaki Hanan dazu"

Abba yyi salati yace"abinda kayimin kenan Rafeeq,amanar da aka bamuce kayima haka?"

Mummy ke tashigo porlour tare da sallama,fuskarta dauke da fara'a kamar yadda tasaba zuwa gida.

Mami da Abba suka ansa,ji yyi kamar yanutse cikin qasa sbd baisan yanajin kunyar Mummy ba sae yanzu,kasa dago kai yyi yakalleta.

Duk wanda yake kusa da Mummy yasan tanason Rafeeq sosae kamar yarta data haifa,kuma ko wurin aikinsu kowa yasani,shiyasa yakejin kunyarta sosae...............

*Miss j*🙋😘
[1/9, 22:23] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀A DALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITING BY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
_{United we stand nd success}_

*215-220*

Ganin Mummy yatasa hankalin Abba da Mami tashi bare uwa uba Rafeeq.

Mummy kenan,kamar yadda tasaba shigowa gidan cikin fara'a yauma haka tashigo,cikin rashin nuna damuwarta haka suka gaisa da su Abba..

Mami tace"Haj. Aysha bamuji ddin abinda yafaruba amma dan Allah ayi haquri,halin yaran yau sai addu'a"

Abba yarasa tacewa tinda suka gaisa da Mummy baiyi magana ba.

Mummy tace"haba Haj. Maryam ai nasan halin Rafeeq nasan kuma halin Hanan,nasan wani babban laifi zata aikata mashi,ai naji labarin irin zaman da suke,ko kadan Hanan bata da biyayya"

Rafeeq tinda yagaishe da Mummy kanshi aqasa yake har yanzu ko motsin kirki yakasa yi.

Mami tace"ae Haj. Aysha ba haka yakamata yyi ba ko kadan bai kyauta ba,shima baza'a rasa nashi laifin ba"

Mummy tace"ai qara yyi mata hankali may be tagyara halinta bataga yadda abokiyar zamanta take ba yarinya qarama amma da halin manya,amma dan Allah alfarmar da nake nema abamu Sultan mutafi da shi"

Abba yace"ni abin yadaure min kai,Rafeeq ne zaiyi irin wannan babban hukuncin batare da shawara na ba,ina jin kunyarku sosae Aysha,da wane ido zan dubi Alh. Lawal?"

Mummy tace"dan Allah ina roqon ku kada kutadama Rafeeq hankali sbd kunsan yanada heart attack already"

Mami tamiqama Mummy Sultan haryayi bacci,bata wani jima sosae ba tatashi tatafi gida.

Mummy nafita Abba yatashi ya shiga part dinshi,Mami tabi bayanshi sbd taga ranshi yabaci sosae,akabar Rafeeq zaune tsakiyar porlour yanata faman zubar da hawaye.

Zaune suke cikin wani madaidaicin porlour wanda yaji kayan more rayuwa da tsadaddun kujeru na zamani.

Mami tace"Alhaji, lalle Rafeeq ya aikata babban kuskure amma ayi haquri maganar haj Aysha abin dubawa ce yakamata mubinciki abinda yahadasu tare da yima Rafeeq uzuri sakamokon lalurar da yake da ita kada muxamo sanadiyyar tayar damashi da ciwon shi"

Abba yace"ya kikeso nayi da mahaifin yarinyar nan yadauki amanar yarsa yabamu,yarinyar na tana matuqar son yaronnan amma shi har yanzu bayasonta,narasa dalili why!!!?"

Mami tace"Rafeeq yanason Hanan tinda har tahaihu da shi Alhaji,babban matsalar shi,kasan yadda Rafeeq yatashi bayason raini,ita kuma Hanan batada ladabi batason zaman lfy,Islam tabani labarin komae kamar yadda sukaba Haj. Aysha"

Abba yakalli Mami yace"kinga Maryam ni yanxu inada abinyi plz"yatashi yabata wuri.

Bbu yadda Mami ta'iya dole tatashi tafita sbd tasan halin Abba man of policy ne baya sauya magana.

Jikinta bbu qwari tafito,tana fito taga Rafeeq cikin porlour kamar yadda tabarshi.

Hankalinta yaqara tashi,da sauri ta'isa wurinshi tana kallon cikin idanuwanshi sunqara ja kamar jini yakwanta..

Mami takama hannunshi suka shiga bedroom dinta da shi,Mami tazauna bakin gado yaya Rafeeq yazauna bisa carpet.

Mami tace"Rafeeq mahaifinka yyi fushi,nasara tayadda zan 6ullo mashi,nima kaina banji ddin abinda ka'aikata ba"

Rafeeq bakinshi na rawa yace"Mami nima nasan abinda na'aikata ba dai2 bane,amma rainane ya6aci kuyafemin dan Allah"

Mami tace"Rafeeq nariga nayafe maka amma kada kasake aikata irin wannan bbu kyau"

Rafeeq yace"yanzu ya zaniyi da Abba?"

Mami tadafa kanshi tace"insha Allah zanyi qoqarin nashawo kanshi,amma kada kasama kanka damuwa banaso ciwonka yatashi,kuma kakiyaye banaso irin haka tasake faruwa"

Rafeeq yace"insha Allah Mami"

Bayan wani lokaci yatafi gida.

*********

Tinda Mummy takoma gida da Sultan,Hanan tabude sabon shafin kuka,Mummy tarasa yadda zatayi da ita dukda irin rarrashinta da takeyi.

Gashi haryanzu takasa fadima mahaifin Hanan halin da ake ciki.

Mummy tace"Hanan idan ganin yaron ne bakiso zan maidashi wurin mahaifinshi,nayi tinanin idan nakawo maki yaon nan hankalinki zai kwanta"

Hanan tace"Mummy wlhy narasa yadda zanyi,inaso incire yaya Rafeeq cikin rayuwata amma nakasayin hakan"

Mummy tace"addu'a zakici gaba dayi Hanan kuma nima inayi maku addu'a"

Mummy tasa Larai tayima Sultan wanka aka shirya mashi sae bacci yadauke shi.

Bayan sallar isha'i,Daddy yakira Mummy awaya anan ne take fada mashi abinda yafaru tsakanin Hanan da Rafeeq.

Daddy baiji dadin abinda yafuba amma bbu yadda ya'iya,Mummy tayi mashi bayanin irin zaman da sukeyi Hanan batason zama lfy da shi da kuma abiyar zamanta,sannan yafahimta.

Bayan wata daya ds faruwar hakan,ba Rafeeq bbu labarinsa kullum Hanan tanata sa idon ganinshi amma shiru.

Ahaka Daddy yadawo daga thailand shima yyi mata fada sosae,kuma sannan ba wani shiga harkarta yakeba sbd tayi hankali.

Zaman gidan ba wani yima Hanan ddi yakeba,sbd bbu wanda yake sakar mata fuska cikin iyayenta har qara Mummy,amma Daddy daga gaisuwarta da yake ansawa,bbu abinda yake mata amma yana daukar Sultan yyita yimashi wasa.

Koda Abba yazo wurin Daddy bashi haquri,daddy bainuna komae ba,yace ai yyi dai2 dayayi mata haka,zanyi tayi hankali.

Rafeeq kullum sae yaje wurin Abba yabashi yahaquri amma bayako kallonshi,haka Mami da tayi mashi maganar Rafeeq saiya tashi yabata wuri.

Saida Mami tafadima Alh. Lawal halin da ake ciki sannan fa Daddy yasamu Abba yyi mashi magana sannan yyi haquri.

Yanzu hankalin Rafeeq yakwanta sosae bbu wani abu dayake damun Rafeeq yashi zamansu lfy shi da Zuhra dinshi.

Kusan kullum sai ankawo mashi Sultan har gida yagani.

Hanan dai taga abin bayi,wataranar monday Hanan tashirya wai itama zatabi Mummy zaria,sbd Mummy tacema daddy 1week zatayi a skul sbd sunada wani meeting da zasuyi.

Hakanan dai daddy ya yadda suka tafi,Hanan ko dadi takeji zataga yaya Rafeeq...............

*Ina sauraron comment dinku followers din wannan buk,nasan zakuce wane irin so ne Hanan takeyima Dr.Rareeq??...*

*Miss j*🙋😘
*🎀ADALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITTEN BY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*EDIT BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*

*230-235*

Bayan sun fito, Zuhra tace "su taso suje suci abunci".

Islam kunya ta Kama ta sosae, ji take kamar tace ta k'oshi, to tasan halin 'yan kayansu, tana cewa ta k'oshi zai fara hararar ta.

Iman ko ajiki nta, ai dama so take yaji, cikin zuciyar ta take fad'in hakanan a matsa ma mutum yayi ta karatu, dan kuma ka fad'i abinda yake ranka sai aji haushinka.

Suka isa dinning area, kowa yasamu kujera yazauna, Zuhra ce tayi serving dinsu sannan ta zuba nata ta zauna kusa da mijinta.

Islam ta kasa cin abinci, ko motsin kirki ba tason yi, saboda kunya.

Iman ko babu ruwanta abincin ta take ci hankalin ta kwance.

Bayan sun gama cin abinci, suka koma parlour suka zauna suna firarsu, jefu jefi yaya Rafeeq yana d'an saka baki idan t akama dole yayi magana.

Iman dai tayi tagumi tana jiran yace su tashi ya kaisu gida dan ita ji take kamar saman k'aya take.

Tunda ta zauna babu abinda tace sai Islam da Zuhra ke firarsu dama basu wani saba da hira da yaya Rafeeq ba.

Yaya Rafeeq ya tashi yanufi part dinshi yabar su a porlour.

Yana fita Iman kamar jira take ta turo baki tace "ni fa wlhy na gaji, so nake naje gida, haka kawai an kawo mutun wuri kuma sai faman d'aure mashi fuska ake".

Islam tace "haba Iman, wai me yasa baki da haquri ne, yana fa sane da mu fa".

Zuhra tace "au ba zaku yi min weekend din ba?".

Iman ta ware ido tare da bud'a baki tace "a ina zamu yi weekend din?, ki bari duk ranar da wannan mijin naki ya tafi unguwa to ni da kaina zanzo yi maki hutu bama weekend ba".

Islam tace "ni fa kunyar shi na keji wlhy duk bana jin dadi".

Zuhra tayi murmushi tace "ai sak'o na nan zan bashi".

Islam tace "dan Allah abar sak'on nan wlhy wasa nake yi".

Iman tace "wane wasa, ni fa da gaske nake, amma dai kada a fada mashi".

Gaba dayansu sukasa dariya.

Da marece yaya Rafeeq ya kaisu gida, bayan ya gaishe da Mami da Abba sukayi fira sosae sannan ya dawo gida cike da k'aunar matarshi.

Ranar saturday Islam da Iman sukaje GRA gidan su Aunty Hanan suka d'auko Sultan, sai bayan sallar isha'i sannan driver ya maida shi gida tare da tsaraba mai tarin yawa, dan tin a school duk abinda suka gani na yara sai sunsaima Sultan, ga kuma Mami tasa driver yayima Sultan shopping aka hadashi dasu aka mai dashi gida.

Sultan yaro qarami tare da tarin masoya da farin jini, daga dang n uwa harna uba, yanzu yana da wata goma sha daya haqoranshi hudu biyu sama biyu qasa, kuma yadan fara tafiya kadan, yanayi taku daya biyu saiya zauna.

Kayan wasa wurin Sultan da kayan sawa ba'a magana, Mami ta saya, Mummy, daddy, Abba, Aunty Hanan, yaya Rafeeq da kuma Zuhra, har iyayen Zuhra idan taje gida suna ba dawa akawoma Sultan, amma Hanan bata sani ba saboda da ta sani baza ta ta6a sakama yaronta bayan Zuhra ba.

Ranar Sunday Mummy tasa driver yakai Sultan gidansu,yaya Rafeeq na kwance shida Zuhra sukaji door bell, ya saka jallabiya yafita, yana ganin Sultan dadi ya kamashi dan dama tunaninshi yake.

Shima Sultan yana ganin mahaifinshi ya bude haqoranshi guda hudu yana dariya,yaya Rafeeq ya'anshi Sultan tare da yima driver hasahi kamar yadda yasaba, driver yayi ta godiya yana wangale baki, yayi mashi sallama yatafi.

Tinda yaya Rafeeq yashiga da Sultan, Zuhra ta'anshe shi tanatajin dadi,ta nayi mashi wasa,ta saka shi cikin keken yara tana turashi, Sultan sai dariya yake.

Yaya Rafeeq ya tsaya kusa da ita tare da kwanciya bisa gadon bayanta,yace "kin mance da ni ko?".

Zuhra tayi murmushi tare da juyowa tace "kaima zoka shiga ciki in turaka".

Gaba daya sukasa dariya hada Sultan da bai san abinda aka ce ba.

Yaya Rafeeq yayi kissing din goshinta yace "saidai ki shiga in turaki".

Ya koma bisa kujera ya zauna yanata kallonsu, sai Zuhra ta bashi tausayi cikin zuciyarshi yace "ya Allah ka nunamin 'ya'yan Zuhra, Allah yashirya mani su da sauran yan uwa musulmai".

Zuhra tadauko Sultan tadawo tazauna kusa da Rafeeq tare da rugume Sultan bisa jikinta tana wasa da yatsun hannunshi.

Zuhra tayi murmushi tace "yayana komai na Sultan irin nakane fa, gaskiya kayi ma Aunty Hanan wayau".

yayi murmushi tare da kallon cikin idanuwan ta cike da qaunarta yace "kema ai wayau zanyi maki".

Zuhra takalleshi tayi murmushi cikin zuciyarta tace "ai da naji dadi wlhy".

Yaya Rafeeq yamatso kusa da ita yace "tunanin me kike kuma?".

Zuhra tace"babu komae".

Ya d'aura hannunshi bisa cikinta yace "Allah yasa ina da ajiya cikin cikin nan".

Zuhra tayi murmushi tare da boye fuskarta bayan Sultan.

yaya Rafeeq yayi murmushi yace "ni fa kullun addu'ata Allah ya nuna min yaran ki mata na Zuhra beauty".

Zuhra tace"Allah yakawo nagari toh my only".

Yace"ameeen my wife".

Yace "kinga dama ina so yau muje mu gaishe da su Mama".

Tuni fara'a ta cika fuskar Zuhra tace "kai amma naji dadi wlhy, dama abinda nakeso na tambaya kenan".

Yaya Rafeeq yace "kinga daganan sai muje ki gaishe da Mummy ko?".

Fuskarta tayi gwanin tausayi tace "wlhy yaya Rafeeq ina tsoron Aunty Hanan".

Ya kama hannunta ya hada da nashi ya rintse ya fara lallashinta cikin kulawa yace "babu abinda zata yi maki Zuhra, ki kwantar da hankalinki".

Zuhra tafara shiri, bayan taqara yima Sultan wanka ta saka mashi kaya, yayi bacci itama taje tayi wanka ta shirya cikin wani swiss boyel lace pick mai zanen flower black tayi kyau sosae.

Bayan tagama shiri tana fesa turaruka masu qamshi yaya Rafeeq yashigo cikin shirin tasa shadda galila ruwan sararin samaniya hada hula yayi kyau sosai, kamar wani balarabe.

yana ganin Zuhra dasauri ya rungumeta tabaya yace "kinyi kyau sosae,inama zama zamuyi agida inta kallon wannan kwalliyar taki".

Zuhra tayi murmushi tace "k'amshinka shine ya tababbatar min da kaine mijina na haqiqa da ban sameka ba da sai an ta yimin jaje, amma nagode ma Allah daya bani kai mijina mai qaunata tsakani da Allah, ina sonka sosae,bani fatan abinda zai rabani da kai".

ya lunshe ido biya bayanta kafin yasaketa, suna yin ido hudu, Zuhra tace "masha Allah, gaskiya har kishi ya kamani".

Yaya Rafeeq yace "nami fa?".

Zuhra tace "na matan da zasu ganka mana".

Yayi murmushi yace "ki kwantar da hankalinki, Rafeeq naki ne ke daya".

Zuhra tace "idan kan ya faru zanji dadi, amma yaya Rafeeq kasan Aunty Hanan tana sonka sosae, kuma idan nabar Sultan a haka iyayenshi na rabe ban yima kaina adalci ba.......".

Badan ta so ba dan dole tayi shiru sakamakon d'aga mata hannu da yayi, ya daure fuska yace "idan kin gama shirin ina jiranki a house premeses" yafita ba tare da yaqara cewa komai ba.

Mayafinta ta dauka tare da jaka, sannan ta sa'bi Sultan a kafad'arta ta fita, ranta babu dadi.

Koda ta'isa house premeses, zaune yake cikin mota Anaconda 2018 ruwan sararin samaniya, ta bude motar tare da sallama tashiga, sallamar kawai ya'ansa amma bai kalli inda take ba.

A haka suka yita tafiya babu wanda yayi magana, har suka tsaya wani supermarket tayi parking ya fita, yakawo abinda zai sawo masu aiki suka saka mashi akin boot sannan ya sallamesu ya shigo mota suka tafi.

Zuciyar Zuhra cike da tunanin yaya Rafeeq daga fad'in gaskiya sai fushi, ita ta rasa inda zata saka kanta.

Fuskar Sultan take kallo wanda yake ta faman baccinsa, tausayinshi ya kamata, bata san lokacin da hawaye suka zubo bisa fuskar Sultan ba daga cikin idanuwanta.

Tasan tabbas idan Aunty Hanan ta dawo, itace za tasha wahala, amma duk da haka, tana son tazo tariqe yaron ta, saboda cikin abubuwan da suke ma Zuhra tausayi, su tada mata hankali harda taga yaro baya tare da mahaifiyarsa gashi yaya Rafeeq yace da an yaye shi zai anshi abin shi.

Zuhra tasa hannu tagoge hawayen da suka qara zuboya mata,sannu hawayenta,tada Sultan daga bacci.

Yaya Rafeeq ya samu wuri yayi parking din motarshi a bakin titi.

Bayan yayi parking ya busar da wani iska mai zafi daga cikin bakinshi sannan yabige sitiyari, ya juyo yana kallon Zuhra ranshi babu dadi.

A hankali yake magana yace "amma kin san babu abinda na tsana irin zubar hawayenki ko?".

Zuhra ba taace mashi komai ba, ta fara qoqari tsaida hawayenta amma ina, dama gata sarkin kuka ga tausayi.

yace"kinga idan bakibar wannan kukanba wlhy zani juya motar inbaidake gida sannan ni intare ingaishe da su".

Tasamu hawayen suka tsaya,sannan yatada mota yatafi.

Suka isa unguwarsu Zuhra, mai gadi ya bud'e masu gate suka shiga, Alhmdllh gidansu Zuhra yyi kyau babu laifi dan in ba wanda ya sani ba, ba wanda zaice su Zuhra sun ta'ba talauci a duniya.

ya samu wuri yayi parking, sannan suka shiga, Mama ce suka tarar a porlour tana kallon tashar Africa tv 3.

Murna cike da fuskarta ta'anshi Sultan, suka zauna cikin jin dadi.

yaya Rafeeq ya zauna qasa tare da gaishe da Mama cikin girmamawa, Mama ta'ansa tare da saka masu albarka.

suka dan taba hira, Mama tace "gashi kun yi rashin sa'a Baban naku baya nan".

Rafeeq yace "ai zan dawo daukarsu zuwa anjima insha Allah".

Mama tace "Zuhra tashi kawo mashi abinci da lemu".

Rafeeq yace "Alhmdllh Mama nagode".

Zuhra tace "idan yadawo zamuci Mama".

Mama tace "toh Allah ya dawo da shi lafiya".

Bayan yayi masu sallama yafita, yayi ma mai gadi magana, ya fara shigo da kayan da ya sawo masu, kayan lashe lashe da tande tande da ruwan roba da sauransu.

Mama tai ta saka mashi albarka, tare da godia.

suka shiga firar su irinta tsakanin uwa da diyarta, nan mama ke fad'a mata duk ranar juma'a sai Rafeeq yazo gaishe da su tare da kud'i masu yawa.

Zuhra taji dadi sosae ko babu komae yaya Rafeeq ya damu da iyayenta kuma bai ta'ba fad'a mata cewa yana zuwa gaishe da su ba.

Mama tace "Zuhra, ya naga idanuwan ki kamar kinyi kuka?".

Zuhra tace "wlhy Mama yanzu da zamu taho daga nayi ma yaya Rafeeq maganar dawowar Aunty Hanan,shikenan yayi fushi".

Mama tace "banda wannan kuma fa?, akwai abinda yake yi maki?".

Zuhra tace "wlhy Mama idan nace ga abinya yaya Rafeeq yayi min marar kyau nayi qarya, wannan dai maganar ce kuma itama yaune mukayi ta da shi".

Mama ta tausasa murya tace "Zuhra tunda baya son wannan maganar, kibar yi mashi ita, ke dai ciki gaba da addu'a Allah ya tabbatar maku da alkairi, kuma idan Allah ya qaddara Hanan zata dawo to babu makawa zata dawo, idan kuma babu rabon dawowarta to ba zata dawo ba, kedai ciki gaba da addu'a".

Zuhra tace "toh Mama, insha Allah zan ci gaba da addu'a".

Mama tace "Allah yayi maku albarka, kema kuma Allah yabaki zuri'a tagari".

Zuhra tace "ameen Mama".

Zuhra ce ta dafa masu abincin dare, tuwon shinkafa da miyar agusi tare da farfesu yan ciki da kan rago, sai lemun kwakwa wanda yaji madarar gwangwani da ruwa da lemun ayaba wanda yaji youghout.

Haka su ka sha yinin su sannan sukayi wanka, ita da Sultan dama tasaka mashi kayanshi da pampers cikin jaka.

Bayan sallar magrib sai ga yaya Rafeeq ya dawo daukarsu, dama su sunci abincinsu yaya Rafeeq yaci nashi har ya gama Baba bai dawo ba.

Bayan yaya Rafeeq ya gama, saiga Baba yadawo cikin motarshi 406 baqa, suka gaishe sosae cikin jin dadi, sannan Mama ta fada ma Baba abin da kawo masu.

Baba yace "yo kai Rafeeq baka gajiya da hidima da mu?".

yaya Rafeeq yace "wlhy Baba babu komae, idan banyi maku ba wazai yi maku".

Baba yayi ta saka masu albarka sannu sukayi sallama suka tafi.

Saida suka fara zuwa gida wajen Mami, Zuhra ta gaishe da Mami cikin girmamawa Mami ta'ansa tare da jin dadin ganinta, ta d'auki Sultan.

Islam da Iman suka ja Zuhra dakinsu suka dan fara hira, Mami da Rafeeq suna porlour, Sultan ne yafara rigima, Mami ta kira Islam.

Mami tace "zoki dauki abinku".

Islam tayi dariya tace "kaji abinda matarka tafadi wai in dauki abinmu ko?"

Sultan kamar yana jinta sai yafara qoqarin zuwa wurin yaya Rafeeq, wai wajenshi zaije.

Islam tace "iyeh kaga masu uba, to tafi".

Tare da miqashi tana fadin kaqara zuwa gidan kasameni ai.

Mami tace "ai ni da mai gidana bamu rabewa har yaqi Aunty saboda ni".

Islam tayi dariya tace "Mami saboda daddy din dai".

Mami tace "gobe da safe Katsina zani je dan haka da mijina zanje".

Mami tace"yawwa kaga sai ka biyo ka tafi da su school ko, gashi Iman ta matsa abamu mota sutafi da ita".

yaya Rafeeq yace "Mami kema kin goyi bayan a basu mota?".

Mami tace "ai Abban ku yace sai anji ta bakin ka".

Yaya Rafeeq yace "wa zai ba wa'annan yaran mota, yaran da basu san ciwon kansu ba".

yaya Rafeeq yaqi ba da goyon bayan a basu mota.

Bayan sallar isha'i Abba yadawo lokacin yaya Rafeeq yadawo daga masallaci, bayan sun gaisa Abba ya dauki Sultan,sun dan dad'e a gidan sannan sukayi sallama suka tafi.

Babu inda suka tsaya sai gidansu Hanan, duk da dama Hanan tana ta zaman jiran dawowar Sultan amma ranta bai ba ta harda Zuhra za'azoba.

koda sukayi parking harabar gidan, suka shiga cikin parlour, babu kowa sai Asabe mai aiki ta dake ta fatan gyaran porlour.

Bayan ta gaishe da su, tayi ma Mummy magana.

Babu 'bata lokaci Mummy ta fito fuskarta d'auke da fara'a tare da murnar ganin Zuhra a gidansu.

Mummy ta samu kujera ta zauna tare da cewa ''ku dawo bisa kujera ku zauna mana kamar wasu baqi.

suka zauna bisa kujera sannan suka gaishe da Mummy, Mummy ta'ansa cikin jin dadi.

Bayan sun dan taba fira, Mummy ta'aika akira mata Hanan.

Bata jima sosae ba sai gata ta fito, cikin shigar riga da wando na bacci dan ita har tayi shirin kwanciya.

Sultan yana ganin Hanan yafara qoqarin kwace kanshi daga hannun Mummy yanason zuwa wajenta.

Hanan tana ganin d'anta tafara murmushi tace "babyna tun d'azu kai nake jira muyi bacci" tasa hannu ta'anshi Sultan dan ita bata lura da wasu mutane ba.

Mummy tace "Hanan baki ga yayanki ba da kuma Zuhra?".

Da sauri Hanan takalle su tace "sannunku da zuwa".

Zuhra ce ta'ansa tace "yawwa, Aunty Hanan kin wuni lfy?".

Hanan tace "lfy ya karatu?".

Zuhra tace "Alhmdllh"

Hanan ta kalli Rafeeq tace "yaya Rafeeq ina wuni".

Yace"lfy".

Yace "Mummy mu zamu koma gida".

Mummy tace "ko ruwa baku sha ba, Hanan a kawo masu ruwa mana".

Yaya Rafeeq yace "Alhmdllh Mummy daga gidansu Mami muke".

Zuhra ta fiddo turaruka guda biyar masu tsada ta bada aba Sultan.

saida Mummy tayi da gaske sannan suka sha lemu da ruwa suka tafi.

Bayan sun koma gida sunyi wanka sukayi shirin kwanciya dama sunci abinci gidan Mama, suka d'an taba fira sannan suka kwanta.

Da asuba Mummy ta kira wayar yaya Rafeeq, ta fada mashi suna asibiti Sultan babu lafiya.

Hankalinshi ya tashi sosae, dama yayi sallah, ya fadi ma Zuhra sannan ya tafi, Zuhra tayi yunqurin bin shi, amma yace tabari idan ya dawo sai su tafi idan ba'a sallamesu ba.

Zuhra harda kukanta, tausayi Sultan take ji sosae.

Yaya Rafeeq yana zuwa asibitin su Mami da Islam da Iman suna isowa.

Idanuwan Hanan sunyi luhu luhu sunyi jajir abin tausayi, Islam da Iman suna ganin Aunty Hanan suka fara kuka.

Mami ta fara yi masu fad'a, su da za suyi addu'a kuma su kwantar ma da Hanan hankali shine zasu qara saka mata damuwa.

yaya Rafeeq ya rude, hankalinshi ya tashi da yake yasan likitan dake kula da yara kuma asibitin Mami ne, ya bi bayan Mami suka shiga cikin office din likitan.

Suka tambaya zasu iya shiga su ga Sultan?.

likitan yace "eh amma banda hayaniya plz".

yayi masu jagora suka shiga dakin, likitoci biyu ne kan shi, amma ba hausawa ba, lokacin da suka shiga sun gama gwaje gwajensu,suka fito su Mami suka shiga.

TUni d'akin ya cika ciki da dangi da abokan arziqi, duk wanda yaga Sultan sai ya zubar da hawaye irin yadda cikin dare daya Sultan yakoma.

Hanan ko saida aka riK'eta saboda juwa take ta gani.

likita yace "yana son ganin iyayen Sultan".

Rafeeq da Hanan suka bishi office, likita ya dafa Rafeeq yace "Rafeeq kayi haquri sakamokon chlora da taci qarfinshi sai dai kuyi haquri Allah ya anshi abin shi".

Ai Hanan tuni ta zube qasa a sume, yaya Rafeeq jingina yayi da bango dan shima yanada niyyar fad'uwa, sai dai likita ya zaunar da shi bisa kujera.

likita ya danna wata qararrawa saiga Nurse guda biyu suka kama Hanan suka d'aurata gado sannan suka nufi wani daki da ita da sauri likita yana biye da su.

Dakin da Sultan yake kwance babu wanda yayi tunanin Sultan babu rai har Mami bata gane saboda bata kawo mashi mutuwa ba ko daya.

Saida wata Nurse tashigo tana basu haquri tasa farin kyalle ta lullube gawar Sultan.

*Real Miss J*🙋😘*🎀ADALILIN KANE🎀*

[5/11, 22:04] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀ADALILIN KANE🎀*

*235-240*

Saida wata Nurse tashigo tana basu haquri tasa farin kyalle talullu6e gawar Sultan.

Islam ji tayi kamar saukar aradu,kamar wani mafarki,hankalinta yayi mugun tashi sosae.

Iman kuwa kuka tafasa mai bantausayi,tarasa inda zata saka kanta.

Mummy ce tarungumeta tana lallashinta tare da bada haquri duk da irin d'acin da rad'ad'in da takeji cikin zuciyarta.

Mami banda salati babu abinda takeyi takasayin komae,ga wasu zafafan hawaye da suke zubo mata.

Mummy ce tafiddo wayarta daga cikin jaka,tashiga kiran layin Daddy domin tasanar da shi rassuwar,dama kuma yayi tafiya zuwa Abuja,amma tinda Mummy takirashi da asuba tafadi masa rashin lafiyar Sultan yafara neman biza zuwa Kano.

Tinda aka fita da Hanan,yaya Rafeeq yake tsaye yakasa ko motsin kiriki.

Doctor yayita fama da shi akan yazauna saboda yaga kamar yanada niyyar fad'uwa.

Amma yaya Rafeeq yace zai'iya tafiya babu komae.

Dole Doctor yabarshi yafita.

Jikinsa babu qwari yake tafiya,kamar wanda qwai yafashe mawa ciki.

Yana isa bakin room din da Sultan yake,yakasa shiga yayi kamar 5mins agurin kafin bude qofar,yayi sallama sannan yashiga.

Yana shiga kowa yamaida attension din kansa,cike da tausayawa.

Mummy tace"Rafeeq kuyi haquri kaji,Allah yabamu haqurin rashinsa".

Mami ce takira wayar Abba tafada mashi rassuwar Sultan.

Hankalin Abba yatashi sosae,lalle rayuwar duniya abin tsoro ce.

Wayar yaya Rafeeq ne yashiga ruri,hannunshi yayi mashi nauyi hakanan yasamu yad'auki wayar.

Zuhra ce hankalinta duk yabi yatashi tinda yaya Rafeeq yafadi mata,Sultan babu lafiya take kuka har yanzu ko breakfast batayi ba.

Takira wayar Mama tafad'a mata Sultan yana asibiti,itama Mama hankalinta yatashi sosae.

Cikin disashshiyar murya take magana tace"yaya Rafeeq tin d'azu nake kiran wayarka baka daukaba,ya jikin Sultan din ne?,Dan Allah yaya Rafeeq inason inzo inganshi,ince driver yakawoni?".

Yaya Rafeeq yadan saki murya yace"Inacan wurin Doctor ne,kawai driver yakaiki gidan Mami,jikin Sultan da sauki yanzu zamu dawo amma gidan Mami zamuje kinga saimu had'u acan".

Zuhra tace"toh shikenan bari inyima driver magana,Allah sarki Sultan d'ina kace inayi mashi sannu kafin muhad'u".

Yaya Rafeeq yace"zaiji sosae"tare da kashe waya.

Mami tace"Rafeeq ina Hanan?,naga ban gantaba ne".

Yaya Rafeeq yace"anyi admitting dinsa".

Mami tace"lafiya me yafaru kuma?".

yaya Rafeeq yafadi mata duk abinda yafaru.

Saboda kawaici irin na Mummy komae bata ceba,saida Mami takama hannunta suka tafi room d'in da aka kwantar da Hanan.

Babu 6ata lokaci Zuhra tasa driver yakaita gidan Mami,amma abin mamaki tararar da gida cike da mutane,maza awaje ansaka Canopy.

Kanta yakulle hakanan take tafiya,ranta sai fama saqa mata abubuwa yake.

Hakanan tashiga cikin gidan,tana shiga porlour taci namma taga mutane anyi jigun jigun,bayan tagaishe da su tamu wuri tazauna.

Abba yazo asibitin tare da driver aka tafi da gawar Sultan tare da su Islam da Mummy.

Mami ce tazauna asibiti jinyar Hanan.

Haka su Mummy suka tarar da mutane daga qofar gida har cikin gidan.

Islam da Iman na ganin Zuhra suka qara fashewa da kuka,hankalin Zuhra yaqara tashi saboda tinda tazauna babu wanda taji yayi maganar rassuwa.

Zuhra tatashi taje kusada Iman,zuciyarta a razane tazauna.

Idanuwanta na zubar da hawaye,mata da yawa sai kallonta sukeyi,wasu na tausaya mata, wasu kuma sunajin haushinta yan uwan Hanan kenan.

Ahankali take magana tace"Iman lafiya?, dan Allah kifada mani abinda yake faruwa".

Iman tana kuka tace"Sultan yarassu Zuhra saidai muyi haquri,Sultan yatafi yabar...........".

Tin kafin ta'ida fadin abinda yake bakinta,Zuhra tafadi asome.

Iman taqara sautin kuka tana kiran sunan Zuhra,rabin matan dake zaune porlour sukayo kanta.

Haka akayima Sultan wanka aka kaishe makwancinsa(Allah yasa mucika da imani,amin).

Lokaci kad'an yaya Rafeef yafita hayyacinta,ya rame fuskarshi cike da damuwa.

Zuhra tana farkawa taganta bedroom din Mami kwance bisa gado,Islam da Iman ne kusa da ita sunyi tagumi.

Fuskarsu takunbura idanuwansu sunyi jawur da su.

Zuhra tafara qoqarin tashi zaune,da sauri Iman tazo tatemaka maka tashi zaune.

Zuhra tafara magana cikin muyar kuka tace"ya Allah kasa mafarki nake,wannan mummunan mafarki,Islam dan Allah kada kuyi fatan kuyi irin mafarkin da dani har qarshen rayuwarku,ina Sultan yake?,dan Allah kukawomin shi".

Iman tafasa sabon kuka,har saida Mummy da Mama suka shigo cikin bedroom din.

Islam tace"Zuhra ba mafarki kikayi ba,da gaske ne Sultan ya'ansa kiran mahalicci,saidai muyi haquri".

Zuhra taci gaba da kuka kamar ranta zai fita,Mummy da Mama suka shiga lallashinsu amma sunqi suyi shiru.

Ashe dama amfadima Baba rassuwar,shi kuma yasanadda Mama,amma koda sukayi waya da Zuhra basu nuna mata cewa sun sani ba.

********

Asibiti ko da Hanan tafarka saita fara surutai kamar wadda tasamu ta6in hankali.

Saida akayi mata allura tasamu bacci sannan aka samu sauqi.

Har'aka gama zaman ukku Hanan tana asibiti sauki saiga Allah,hankalin kowa yatashi sosae ga kuma tausayinta da mutane sukeji,ga rassuwar Sultan ga kuma ciwon dake damunta.

Bayan sati daya,Mummy da Daddy suka yanke shawarar afiddata abroad.

Hanan tasamu mental retarded,aka fara shirye shiryen fitarda ita waje domin aduba lafiyarta.

Sun shirya komai tsaf, tare da Mummy suka tafi duk wanda yaga Hanan saiya tausaya mata cikin halin da take.

Duk abinda Zuhra tad'auko na Sultan shikenan ranar babu zama lafiya.

Ita da yaya Rafeeq sunfita hayyacinta ,sun rame kamarba suba duk farin cikin da suke ciki ada yanzu babu.

Iyayensu sun lura da halin da suke ciki,Abba da Mami da kansu sukazo har gida sukayi masu nasiha akan suyi haquri,Allah yasan dalilin yin hakan,sannan Abba yace duk abinda sukasan na Sultan ne suje suyi sadaka da shi ko zasu samu sauki.

Bayan tafiyarsu,yaya Rafeeq yashiga parking din kayan Sultan domin yabi maganar da mahaifinsa yafada mashi.

Nanfa Zuhra tashiga kuka tana roqonshi akan yabarmata kayan bazata qara tada hankalinta bayi mashi alqawari.

Yaya Rafeeq yace"Zuhra nalura kayan nan suna qara tada maki hankali,kamar fiddasu zaifiye mana".

Zuhra tace"dan Allah yaya Rafeeq kataimaka min kada kafidda kayan nan,wlhy idan ina ganinsu suna d'ebemin kewar Sultan d'ina".

Yaya Rafeeq yace"ai banda pic dinsa zan fidda fa,kayan wasa akawai da kayan sawa".

Zuhra tace"toh shikenan,mijina yadda kace haka zakayi"

Haka aka kwashe kaya masu yawa akayi sadaka da su.

Watan Hanan biyu a asibiti qasar turai,ana kula da lafiyar Hanan,Alhmdllh dan yanzu da sauki ba kamar da ba.

Dukda ana waya da Mummy,amma saida Mami da Abba sukayi shirin zuwa ganinta,Abba yacema yaya Rafeeq yashirya atafi da shi.

Ba dan ranshi nasoba haka yashirya aka tafi da shi,kwansu ukku suka dawo,jikin Hanan yayi sauki sosae har amfara maganar sallamarsu.

Watansu ukku a London suka dawo gida Nigeria,amma har lokacin Hanan saita dauko kayan Sultan tarungume tayita kuka kamar qaramar yarinya.

Yan uwa da abokanan arziqi sukayita zuwa yimata ya jiki.

Hakama Mami da Abba da su Iman da Islam sukaje ganinta da yake lokacin anyi hutun second semester suna gida.

Zuhra kau saida tayita roqon yaya Rafeeq sannan yakaita taganota tare da yimata ya jiki.

Hanan tarame sosae,saida jikinta yayi kyau sosae taqara fari kamar ba itaba.

Mummy da Daddy sunji dadin zuwansu,sukayita saka masu albarka.

Bayan wata hudu da dawowarta asibiti jikinta yakoma normal tayi kyau saidai tari damuwa da tinani,masoya sai faman zuwa sukeyi masu sonta da aure kuma masu kudi masu ji da kansu hada dan ministan kudi amma basu dameta ba.

Mummy tayita fama da ita akan tafita sugaisa amma bata zuwa,saidai tarabu da ita,gashi dama likita yace kada abarta cikin damuwa,saboda ciwon zai iya dawowa sabo.

Kullum addu'ar Mummy itace Allah yakawo masu tafita akan wannan al'amari.

Yanzu zaman Zuhra da yaya Rafeeq yadawo normal saidai abinda ba'arasa ba.

Haqiqa Zuhra tanajin tausayin Hanan,dan wani lokacin idan tazauna tayi tinanin irin yadda Hanan keson yaya Rafeeq tin tana yarinya kafin tasan me nene so,da kuma irin yadda yake nuna rashin damuwarsa akanta ga kuma rashin yaronta da tayi ga kuma ciwon daya sameta duk adalilin yaya Rafeeq har kuka takeyi.

Tana tinanin da itace haka tafaru da ita ya zatayi,sai taji wani sabon tausayinta yakamata.

Aunty Hanan taqi sauraron ko wane d'a namiji tindaga yarintarta har zuwa yanzu duk adalilin yaya Rafeeq.

Wannan wane irin sone haka,sanin gaibu sai Allah,amma duk wanda yaji irin wannan labarin yasan ba qaramin so bane.

Wata ranar asabar Abba yana gida yakira wayar yaya Rafeeq yace"yasameshi agida"

Babu b'ata lokaci yatafi,yasamu Abba da Mami cikin porlour din Abba suna fira da alama firar tashice.

Yashiga tare da sallama,bayan yagaishe da su,Abba yanuna mashi kujera kusa da shi.

Abba yafara magana ranshi b'ace yace"Rafeeq ina ganinka kamar mai hankali ashe baka da shi,kai bakasan kawaici bane?,dama dalilin da yasa nakiraka,inason baka umarni indai nine nahaifeka to inaso kamayar da Hanan gidanka,saboda tanason ka kuma taqi sauraron kowa sai kai,kai kuma baka kula da ita,iyayenta sunsa maka ido kanayin yadda kakeso ko,kuma likita yace lalle idan tashiga cikin damuwa ciwonta zaidawo sabo,yanzu nayanke shawara nan da sati biyu za'a daura aurenku kai da ita,kuma daganan gidansu zaka nufa domin kufara shiri kuma ku daidaita kanku,dafatan kafahinci abin mafad'i?".

Yaya Rafeeq ranshi babu dadi yace"eh Abba insha Allah zanyi hakan".

Mami tace"yawwa dama abinda mukeso muji kenan,Allah yayi maka albarka,ai yakamata atausaya mata Rafeeq,Hanan har ciwon hauka tayi duk *Adalilin kane* mu munsani ga kuma rashin yaronta da tayi aiko dan hakan antausaya mata".

Suka shiga yimashi nasiha,tare da saka mashi albarka.

yajima kafin yabar gidan,babu inda yayi parking da motarsa sai house premeses din su Hanan,qananan kayane jikinshi black jeans nd red shirt gaban shirt din anrubuta DON'T TOUCH da baqin fenti,yayi kyau sosae dan shima yanzu yaqara kyau da fari dan yanzu business yakeyi yanada wurin sayar da motoci da kamfanin takalma a India.

Tin kafin yayi parking din tsadaddiyar motarshi,yaga wata qatuwar mota new modern dan hada irinta akayi mashi order daga waye satin da yawuce.

Motar nada bala'in tsada sosae,yamayi tinanin ko Daddy na gida,yana fitowa daga cikin mota yaga hango Hanan zaune da wani acikin wata rumfa ta shaqatawa,wani takaici yaji yakamashi kamar yahad'iyi zuciya yamutu,yabude mota yashiga da niyyar tafiya gida..........................

*Real Miss j*🙋🏻‍♀😘
[5/11, 22:04] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀ADALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITTEN BY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*

*240-245*

Kasa tadarya motar yayi shima kanshi yarasa me yake damunshi.

(ni Miss j nace me ke shirin faruwa ne?,shin kodai yaya Rafeeq yanason Hanan?,ko kuma yafara sonta ne?).

Hakanan yasamu yatada motarshi aguje yabar gidan ranshi babu dad'i.

********

Hanan batasan da zuwanshi ba bare kuma tafiyarshi saboda ko Abdulhameed yazazo wurinta yasamu yau tafito ba sauraronshi takeyiba zuciyarta cike da tinani tare da qosawarta akan takoma cikin gida.

Duk irin yadda Abdulhameed yake lalla6ata baisamu tashawo kanta ba,saboda ita take duk yabi yatakura mata,kamar yana mata ihu acikin kunnuwanta.

Abdulhameed yamatashi wanda bazai wuce 32yrs ba,1st born din minister of finance ne,matashi ne kyakykyawa maiji da kanshi,amma baya gaban Hanan hasalima haushinsa takeji.

Yaya Rafeeq baifi 3mins da fita daga house premeses dinsu ba,Hanan tatashi tsaye tace"Abdul ni zan shiga cikin gida,nabarka lafiya".

Shima yasan halin yakanshi dama yasamu yau tafito yasamu ganinta,yayi murmushi yace"my queen kihuta lafiya".

Bata ko juyo takalleshi ba taqara gaba,kallonta kawai yake tare da tausaya mata wani sonta ne yake qara shigarsa.

Mahaifiyar Abdulhameed itace qawar Mummy tin America da sukaje wani semener acan suka had'u da Mummy,tin daganan suke zumunci har yau ba'a yada ba.

Wurin mahaifiyarshi yaji labarin rassuwar yaron Hanan wato Sultan,shikuma Abdulhameed ranar yadawo daga Germany,yaji tausayin Hanan sosae,musamman daya samu labari tasamu rashin lafiya har London aka fidda ita.

Hanan tana shiga porlour ta tarar da Mummy zaune bisa kujera one seater tana karanta Magazine,fuskarta d'auke da farin glass da alama naqara lafiyar ido ne.

Hanan tafashe da kuka tafada bisa Mummy,da sauri Mummy ta'ajiye magazine din dake hannunta bisa centre table,tare da cire glass din dake fuskarta hankalinta tashe.

Mummy tafara tambayarta arazane tace"lafiya Hanan?,me ke faruwa?".

Hanan batayi magana ba sai farashin kuka data qara.

Mummy cikin muryar lallashi take mata magana tace"haba baby na me kuma akayi?,waya ta6amin ke ne?".

Tafara share mata hawayenta taci gaba da lalla6arta,babu abinda yake tadama Mummy hankali ayanzu,irin taga hawayen Hanan suna zuba.

Haqiqa sunason Hanan,amma Allah yasa iyayenta suna da kawaici sosae,dan sau tari zakuga iyayen Hanan basu ganin laifin yaya Rafeeq ko kad'an.

Tashin hankalin Hanan babban abune agurinsu musamman yadda Doctor yasheda masu lalle idan tana shiga cikin damuwa ko tana yawan tinani ciwonta zai iya dawowa sabo har yafi nada.

Hanan ita d'aya suka mallaka,tinda suka sameta ko 6ari bata sakeyi ba.

Ta tashi cikin gata tare proper care,kowa yana sonta,duk abinda takeso shi akeyi mata more especially Daddy yanaji da ita sosae.

Mummy nisa tace" 'yata fadamin me ke faruwa mana".

Hanan tatashi zaune tace"Mummy wai yaya Rafeeq bazai qara dawowa gare ni ba ne?,bayajin tausayi na Mummy".

Sai kuma tafashe da kuka taci gaba da cewa,tin bayan rassuwar Sultan d'ina ban qara sakashi cikin idanuwana ba Mummy,banison ko wane d'a namiji sai shi,shi kuma bayaso na,baya kulani,Mummy ya zanyi ne?,ko dai mutuwa zanyi imbi d'ana inhuta da wannan duniyar?".

Tad'ago jajayen idanuwanta tana kallon Mummy,itama Mummy dukda irin juriyarta hawayene ke zubowa gada cikin idanuwanta.

Hanan tarud'e saboda bata saba ganin idon Mummy yana zubar da hawaye ba.

Hanan tace"Mummy dan Allah kada kiyi kuka,kiyafemin Mummy na".

tafara gogema Mummy hawayenta.

Mummy tayi murmushin qarfin hali tace"Hanan,yayanki yanason ki,kuma zai dawo gareki kici gaba da haquri,amma kiyi qoqarin gyara halinki abinda bayaso kibaryi mashi kinji".

Hanan da sauri tatashi zaune tace"Mummy da gaske yaya Rafeeq zai dawo gareni?".

Mummy tace"insha Allah zai dawo dawowa nahar abada amma fa saikinyi haquri".

Hanan tayi murmushin jin dad'i tace"i love u Mum".

Daddy ne yashigo cikin manyan kaya fuskarshi d'auke da fara'a yace"only ur mum?".

Mummy da Hanan suka saka dariya,Hanan tatashi tataroshi tace"i really love u with all my heart".

Daddy yayi murmushi yace"same 2 u my daughter".

Yazauna sukad'an ta6a hira,Hanan tatashi tanufi room d'inta da niyyar canza kaya tayi sallah.

Wayar Daddy ce tad'auki ruri babu 6ata lokaci yad'auka tare da sallama.

Suka gaisa tare da ta6a d'an barkonci irinna abota sannan,Abba daga dayan 6angaren yace"dama maganar auren Hanan ne yataso".

Daddy yace"Alhmdllh Alhaji Khaleel,gaskiya naji dad'i Allah yasa alkairi".

Abba yace"baka tambayeni inda tasamo mijin ba?".

Daddy yace"ai nasan wannan miji tinda kaine taza6oshi to lalle gwarzo ne sosae,amma wanene sirikin namu?".

Abba yace"Hmmm,Rafeeq dai nawajenka,yakamata amaida auren nan tinmunada rammu".

Daddy yace"toh amma,Alhaji Khaleel,Rafeeq ya amince ne?"

Abba yace"haba Alhaji Lawal yaushe zamu jirashi ai tini ya amince".

Daddy yace"gaskiya naji dad'i sosae,Allah yatabbatar da alkairi yasa ayi da mu".

Abba yace"nan da sati biyu za'ayi komae agama,dan bazamu 6ata lokaci ba".

Daddy yaji dad'i sosae ahaka sukayi sallama tare da addu'ar Allah yakaimu lokaci yabasu zaman lafiya.

nanfa Daddy yake fad'ima Mummy duk abinda ke yafaruwa,Mummy taji dad'i sosae kamar tazuba ruwa qasa tasha,tayi masu addu'a sosae,nanfa aka shiga sanar da yan uwa da abokan arziqi amma uwar gayya Hanan batasan me ke faruwa ba.

**************

Yaya Rafeeq yana isa gida ko part dinshi bai shigaba yawuce part din Zuhra,lokacin tagama abinci tana gerawa saman dinning table.

Tana ganinshi tagane yanayin da yake ciki ranshi ne a6ace,Zuhra ta'ajiye komae dawo kusa da shi tanayi mashi sannu da zuwa tare da tambayarshi abinda yake faruwa.

Ya kalli Zuhra tare da shafa fuskarta mai santsi,nan yake fad'amata abinda yafaru shi da Abba.

Cikin farin ciki tace"kai Alhmdllh,amma Allah yayima Abba albarka yaqara yawancin rai,wlhy dana iya guda ya nayi wannan abin farin ciki haka".

Yaya Rafeeq yamiqe tsaye yace"me kike nufi Zuhra?".

Zuhra tatashi tsaye ganin yad'aure fuska yana kallonta tace"haba my only nifa ba wani abu naceba,kawai dai Abba yayi gaskiya ne".

yaya Rafeeq yace"da kyau,bari nabar maki gidan".

Zuhra tabi bayanshi tare da rungumeshi tanayi mashi kukan shagwa6a wai yayi haquri,tasamu yasamu wuri yazauna.

Saida talalla6ashi yaci abinci yayi wanka sannan yatafi masallaci sallar la'asar.

Zuhra tasamu wuri tazauna tana tinanin inama Sultan nanan tafi farin ciki fiye da yanzu,sai hawaye suka fara zubo mata,kewar Sultan tadawo mata sabuwa,tashi tayi tad'auko pic din Sultan tana kallo tana kuka.

Haka yaya Rafeeq yasameta,cikin irin wannan yanayin nanfa yashiga lallashinta yana taba haquri,har yasamu tad'an saki jikinta.

Nan fa Zuhra tasamu damar shimashi maganar Aunty Hanan akan yayi haquri komae yawuce.

Yaya Rafeeq yafada mata Abba ya umarceni da cewa daga gidanshi inwuce gidansu Hanan,amma ina zuwa natar da ita tare da wani qato.

Zuhra kamar tayi dariya sai kuma tad'aure tace"haba yaya Rafeeq amma kasan yadda Aunty hanan take masifar sonka bazata saurari kowaba sai kai".

Yaya Rafeeq yace"hmm,Zuhra kenan".

Zuhra tace"toh kunyi magana da ita ko?".

Yadan tamutsa fuska yace"batasan najeba kuma nayi tafiya ta".

Zuhra tace"toh amma gobe zaka koma ko yayana?".

Yaya Rafeeq tace"me zanyi idan nakoma?".

Zuhra tashagwa6e fuska kamar zatayi kuka tace"haba yayana me yasa kaqi fahimtar Aunty hanan ne?".

Yace"zamu iya canza wani maganar ne?".danshi yanzu Hanan haushinta maganarta yakeji bare kuma ita.

Fuskar Zuhra dauke da damuwa tace"yadda kakeso yayana".

Yatsaya yana kallon cikin idanuwanta,haqiqa bayason ganin fuskar Zuhra cikin damuwa dan ji yake kamar baiyima kanshi adalci ba,kamar wani sashe na jikinshi ne yake cikin damuwa,dan yanzu Zuhra babban abuce agurinshi.

Yakamo fuskarta yayi kissing din goshinta yace"toh yanzu me kikeso ayi my wife?".

Tad'anyi murmushi tace"inaso dan Allah,ina neman alfarma akan gobe kaje kuhad'u da Aunty hanan,kuma sannan ku faminci juna idan kayi haka kayimin komai".

Badan ranshi yasoba yace"toh shikenan,insha Allah gobe zanje".

Da sauri Zuhra tatashi tana murna tafad'a jikinshi,yaya Rafeeq yana mamakin irin halin Zuhra,kodai har yanzu yarinta gareta ne?.

Kullun son Zuhra qara shigarshi yakeyi ji yake kamar ya had'iyet,bayason abinda zai 6ata mashi rai ko kadan,maida Hanan ma dan yazama dole maganar Abba ne da bazai mayar da itaba,duk dan Zuhra,amma yaga Zuhra kamar farin ciki takeyi da jin maganar auren.

Washe gari ranar sunday,yaya Rafeeq yafito wanka,Zuhra da kanta tashiryashi sannan taza6a mashi kayan da zai saka,shadda ce fara sul tare da babbar riga wanda taji aikin yan qasar singhel tare da takalma da hula,wani tsadadden agogo na gold ne tasaka mashi ahannu,Zuhra tasaka masa kaya sannan tafesheshi da turaruka masu dad'in qamshi,ya saka takalma Zuhra sai faman yaba kyaun da yayi takeyi har tarakashi harabar gidan,taza6a mashi mota fara sul Rangerover 2018,har yabar harabar gidan Zuhra tana d'aga mashi hannu,saida yafita sannan tadawo cikin gida.

Daddy ne yakira Hanan yake fad'a mata Abbanta Alhaji Khaleel yasama mata miji,nan da sati biyu za'a d'aura mata aure kuma ranar zata tare gidan mijinta.

Hanan batace komae ba,saidai kawai tayi given up rayuwarta tazo qarshe.

Tinin ranar Hanan cikin damuwa take,kowa yafahinci hakan saidai,Daddy ne yabada umarnin kada wanda yafad'a mata saboda ayi surprise nata.

Ko da Yaya Rafeeq yashiga harabar gidansu Hanan,yayi parking kamar kullun ma aikata suka fara kawo gaisuwa,shi kuma yanayi masu hasahi kamar yadda yasaba.

Abba yana kallon yaya Rafeeq ta up stairs,saidai kawai yayi murmushi kowa yasan Rafeeq mutumin kirki ne amma bayason raini kuma yana kaucema duk abinda za'ayi masa magana akai ko yakawo mashi raini.

Yaya Rafeeq ya'aiki wani ma'aikaci yayi mashi magana da Hanan,babu 6ata lokaci yatafi.

Koda Idi yafadi ma Mummy ana kiran Hanan,Mummy tashiga tinanin ko waye yake neman Hanan kuwa?.

Daddy ne yasauko daga upstairs yace"tana zuwa"

Mummy tace"waye kuma yake nemanta?".

Hanan ce tafito tanata faman mazurai dan taji Mummy tana fad'in sunanta.

Ganin Hanan atsaye Daddy yace"Yaron da zai aureta nan da sati biyu shine yazu,taje tashigo da shi mana".

Ran Hanan yayi mugun 6aci amma babu yadda ta'iya dole tatafi.

Tana tafe tana ququni,Daddy da Mummy suka bita da kallo,Mummy kamar zatayi dariya.

Haka Hanan tafita harabar gidansu,qamshin tiraren da bazata ta6a mantawa da shi ba,yacika mata hanci har zuwa brain d'inta.

Dukda yajuya baya bazata ta6a qin ganeshi ba saboda yadda zuciyarta tariqe mata komae nashi har abada..............................

*Real Miss j*🙋🏻‍♀😘
[5/11, 22:04] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀ADALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITTEN βY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*

*245-250*

Jikin babu qwari take tafiya,zuciyarta cike da tinani iri daban daban,shin yaya Rafeeq wa yazo nema?,kuma me yasa yatsaya awaje?.

Bata samu wanda zai bata wannan amsar ba,kuma ko zuciyarta batada amsar da zata bata.

Ahaka taqarasa inda yake,tana kuma tinanin waye yake nemanta?,waye kuma wanda zata aura?.

Wani 6angare na zuciyarta yake riya mata,yanzu Hanan shikenan ke da yaya Rafeeq wani daban zaki aura.

Me yasa Abba zai za6a mata wani daban,bayan kowa yasan ga wanda takesu duniya da lahira,yanzu ya zanyi in'iya zama da wani d'a namiji ba yaya Rafeeq ba?.

Dan dole ta tattara natsuwarta tamaida guri d'aya ba dan komai ba,saidan takusa isa inda yake tsaye ajikin motarshi.

Cikin natsuwa muryarta har rawa yake tayi sallama.

Ya d'auki 3mins kafin ya'ansa,bayan ya'ansa sallamar cikin isa yace"sai yanzu kikaga damar zuwa?".

Hanan gabanta ne yafad'i,batasan lokacin da tafad'i kalmar yaya Rafeeq dama kaine kake kirana?.

Yaya Rafeeq yace"u thought,baqonki najiya ne?".

Hanan tatausasa murya tace"i'm extremely sorry,yanzu kazo mushiga daga ciki".

Ahankali yajuyo yana kallonta fuskarshi babu alamar wasa,sai Hanan taqara tsurewa ganin sai faman 6ata rai yake.

Yace"ai nasan da cikin gidan,waye yazo wurinki jiya?".

(Ni miss j nace kaiji yaya Rafeeq da tado fitina ko meye ruwanshi aciki😏).

Hanan tabayi magana ba,dukda tanason gano laifinshi na tambayarta da yayi amma zuciyarta takasa bashi laifin.

Yaya Rafeeq yace"dama zuwa nayi nafada maki kirubuto duk abinda kike buqata,zaki iya aikamin da shi,kuma ina sauraron labari idan wani qato yaqara zuwa wurinki kuma kika fito".

Yana gamawa yashiga mota,baiko bari yaga tafiyarta ba yayi tafiyarshi abinshi.

Takai 10mins atsaye agurin kafin tatafi.

Tinaninta duk akan yaya Rafeeq ne,yanzu aurenta za'a maida da yaya Rafeeq,amma kuma yanayi mata haka.

Wai yaushe ne yaya Rafeeq zai dawo gareta yagane irin son da takeyi mashi?.

Yaushe ne yaya Rafeeq zaibar tsanarta ne?,bayajin tausayinta,ko dan rashin da tayi ai yatausaya mata.

Da wannan tinanin ne Hanan tashiga cikin gida zuciyarta babu dad'i.

Tana shiga porlour taga Daddy azaune shi da Mummy,gaba dayansu sun lura da yanayin da Hanan take ciki.

Daddy baiji dad'in yanayin da yana Hanan ciki ba.

Mummy ce tace"Hanan,Rafeeq din yatafi ne?".

Jikinta babu qwari tad'aga kai alamar eh.

Mummy tace"kuma Hanan,bakice mashi yashigo cikin porlour ba saiki barshi awaje,kamar wani baqo".

Hanan tad'an kalli inda Mummy take tace"yana sauri ne Mummy,shine wanda zan aure ne?".

Mummy tayi murmushin qarfin hali tace"Hanan kenan,dama mun6oye makine domin muyi surprise naki".

Hanan tad'anyi murmushi tace"Mummy,Daddy nagode sosae da nuna so da kulawarku agareni".

Daddy yace"kada kidamu Hanan ai wannan aikimmu ne,yanzu kije kihuta kinji".

Hanan ta'ansa da toh,sannan tashiga cikin room d'inta.

Bayan tafiyar Hanan,Daddy yakalli Mummy yace"yarinyarnan kamar tana cikin damuwa fa".

Mummy tace"tana mamakin wanda zata aura ne".

Daddy yace"babban burina kuma farin cikina shine inga Hanan agidan aurenta tare da wanda takeso suna zaune lafiya".

Mummy tace"farin cikinta shine namu,badason rammuba Hanan tafad'a cikin wannan hali na lalura".

Daddy yace"munyi waya da Doctor yace bayan shekara daya amaida ita,za'a qara dubata".

Mummy tace"Allah yaqara lafiya".

Hanan ce kwance bisa lafiyayyen bed dinta wanda yaji bedshirt mai taushi,babu abinda take tinani sai halin yaya Rafeeq,daga qarshe tayi addu'ar Allah yasa yaya Rafeeq yafahimci irin son da takeyi mashi suzauna lafiya.

Kullun Zuhra cikin lalla6ar yaya Rafeeq take akan yakula da Aunty Hanan kada taqara samun wani ciwon akan rashin kulawar da yakeba.

Da marece Islam da Iman sukazo,sunsha firarsu sosae,Zuhra kenan babu wanda zai ganta yace wai ana shirin yimata kishiya,batasama ranta komae ba,ita dai tayi imani da Allah,kuma tasan shine zai kawo mata sauki cikin wannan lamarin.

Haka suka gama yininsu bayan sallar magrib suka tafi gida,zuciyoyinsu cike da tinanin irin halin Zuhra,gaskiya samun irin Zuhra cikin mata sai'antona.

Haka sukaje gida sunaba Mami da Abba labarin irin halin Zuhra,kwata kwata bata damu da aurennan ba illama itace take qara qarfafama yaya Rafeeq gwaiwa ajan auren.

Mami dama tadad'e da fahimtar halin Zuhra mutuniyar kirki ce,kuma tasamu tarbiya tindaga gidansu.

Nanfa kowa yashiga yabon halinta,Abba yayi farin ciki sosae dajin irin halin matar d'anshi guda daya tilo namiji kuma wanda yafiso.

Kowa ya qara sonta tare da ganin girmanta da kuma qara d'aukaka martabar iyayenta.

Ana saura kwana ukku aurin aure,Abba ne yahad'a lefe dozen biyu,d'aya aka kai gidansu Hanan,dayan ko na Zuhra ne,kuma komae iri daya ne saidai color yabanbanta.

Mami ma tayi masu akwati guda biyar biyar,sannan ga kuma wanda yaya Rafeeq yayi masu.

Yaya Rafeeq yarasa me zaiyima Zuhra arayuwa,yayi mata kyautar mota JAGUAR XF 2018 fara sul,tare da saka mata albarka da tarin kalamai masu dad'i wanda yaqara tabbatar mata da lallai yaya Rafeeq yana qaunarta fiye da kansa.

Kudine yabata miliyan d'aya yace tayi hidimar biki,idan kuma tana buqatar qari ya cheque yabata yace tarubuta ko nawatakeso zaiyi waya akawo mata.

Gidansu amarya ma biki akeyi babu kama hannun yaro kamar wata budurwa wanda zatayi sabon aure.

Daga gidansu amarya aka hada masu dinner a wani katafaren hall na manyan mutane masuji da kansu,amarya taji gyara tasha dilka harwani yellow takeyi,daqer Zuhra tasamu ango yahalarci taron amma ita bata samu zuwaba saboda batajin dad'in jikinta sosae.

Zuhra ce tahada masu kamu a wani babban hall na masu kud'i,abinci ne na turawa sai wanda kakeso lemuna,snacks da dao sauran kayan tand'e tand'e dana more rayuwa.

Kowa sai yabama Zuhra yake akan qoqarinta,hakanan dai take hidimarta amma batajin dad'in jikinta,tin jiya da daddare yaya Rafeeq yaketa tambayar me yake damunta amma tace ita lafiyarta qlau fa,dan dole yarabu da ita badan yayarda ba.

Haka aka d'aura auren Hanan da yaya Rafeeq,d'aurin auren da yatara manyan mutane,yan siyasa,yan kasuwa,masu fada aji da malamai da sauran yan uwa da abokan arziki,anatayi masu fatan alkairi.

Hanan tana zaune gaban Mummy da Aunty Saudat qanwar Mummy da mama sa'a yayar Daddy anayi mata fad'a wata sabuwar number ce tadame da kira.

Mummy tayi mamaki saidai bata nunama ko komae ba,saida aka gama fadan Hanan tashiga bedroom din Daddy domin ta'ansa waya.

Hmmmm,Khubra ce,tauraruwa mai wutsiya kenan,Hanan tad'auka suka gaisa.

Khubra tace"naji labarin rashin lafiyarki da rassuwar Sultan ga kuma bikinki anayi,ban samu zuwaba saboda kinsan Mummy batason ganina da ke Hanan,amma ina mai baki haquri".

Hanan tace"haba Khubra wannan ba hujja bane,aiko a wayane kin nemeni har afad'i maki rassuwar yarona amma kiyi shiru?".

Khubra tayi murmushin irin na gogaggun yan bariki tace"hmmm, ai baikatama kiga laifina ba Hanan,laifin kishiyarki Zuhra zaki gani saboda malamina yafad'amin itace tayima Sultan asiri yamutu,dan haka kada ki yadda,Allah yabaki damane domin kiga bayan Zuhra,ki bima yaronki haqqinshi".

Hanan tace"Khubra kina nufin Zuhra ce takashemin Sultan d'ina..............."

Ganin Mummy datayi atsaye kusa da ita shine yasa maganarta tamaqale bata samu damar fitowa ba.

Mummy tayi murmushin takaici tace"hmmm da kyau Hanan,kicemin ga inda nake tifqa anayimin warwara,ga wadda take qara baki tarbiya ko?".

Hanan hannunta na rawa tini takashe wayar,tarasa bakin magana tinin tafara kuka.

Mummy tace"kukan name nene kuma?,Hanan idan har kikace tarbiyar da wannan shed'aniyar ta baki itace zaki d'auka,toh kitina wannan itace damarki taqarshe a gidan Rafeeq wlhy duk abinda yabiyo baya babu hannummu aciki ni da mahaifinki domin zan fad'a masa komai".

Hanan cikin muryar kuka tace"wayyo Allah na Mummy na wlhy natuba,babu ni babu Khubra har abada,ku yafemin dan Allah".

Mummy tace"Hanan tin kina university narabaki da yarinyar nan amma ashe nice kika d'auka mutuniyar banza baki rabuda da itaba,yarinyar da take aikata manyan laifika,tabi maza tabi mata,Hanan bazan zargekiba amma baki kyauta minba".

Hanan hannunta na rawa tazare layinta takarya agaban Mummy,sai faman zubar da hawaye take.

Mummy tadafa kafad'arta tace"Hanan keba musulma bace?,baki yadda da qaddara ba?,baki yadda Allah ne mai kashewa ya kuma raya ba?".

cikin muryar kuka Hanan tace"nayarda Mummy".

Mummy tace"toh Allah shine wanda yarabaki da Sultan ba Zuhra ba,ki ajiye maganar waccen jahilar,kuma boka jihiline Hanan,inason fad'i maki gaskiya Zuhra tana sonki,tana qaunarki,nason d'anki,tanason ki Rafeeq,tanason farin cikinku,tanason yan uwanki da iyayenki,ita yarinyar kirki ce kuma mai tarbiya,daga qarshe inaso kiyi koyi da kyawawan halinta idan har kinason zama lafiya,kada kinuna mata abu marar kyau saboda tana sonki sosae".

Hanan tace"Mummy insha Allahu nad'auki maganarki kuma ina da Khubra har abada,ki yafemin,wlhy ban ta6a aikata wani mummunan abuba kamar yadda Khubra take aikatawa".

Mummy tace"toh Allah yayi maki albarka,kije kizauna da mijinki da abokiyar zamanki lafiya kuma da zuciya d'aya,yanzu kije iyayenki na jiranki zasu kaiki gidan mijinki".

Hanan tasha kuka tafin tatafi,daqer aka rabata da Mummy sai kace wata qaramar yarinya.

Tin daga lokacin Hanan tayi alqawarin babu ina ba Khubra hargaba da abada kuma tad'auki qaddara akan mutuwar Sultan,da kuma zama da mijinta tare da Zuhra da zuciya d'aya.

Babban al'amari,tin bayan sallar la'asar du abinda Zuhra taci saiya dawo ga kuma wani ciwon kai da take fama da shi,amma babu wanda tafad'i mawa.

Duk da su Islam da Iman nata faman yi mata surutu akan me ke damunta,saidai tace babu komae batajin magana ne.

Aka kai amarya gidan mijinta,bayan sallar insha kuwa yawatse,gidan shiru dan Zuhra tana part dinta kwance biya kujera 3seater saboda abinda yake damunta.

Yaya Rafeeq yana gidan Abba,Mami da Abba sunafa faman yimashi nasiha tare da nuna mashi yanayin rayuwa da kuma haquri.

Abba yace"Alhmdllh yau dai Allah yanuna mana abinda muka dad'e munason gani,toh Rafeeq ga Hanan a gidanka,kayi adalci atsakaninsu,kasan dai halin da Hanan take ciki,ko ince ciwon da yake tare da ita,toh ka kula sosae,idan har kazama sanadin tashin ciwon Hanan bazan yafemaka ba,yarinyar nan tana sonka tana qaunarka kuma ba rasa masoya tayiba hakanan abin Allah,Allah yanufeta da sonka,idan har katadama Hanan ciwonta kagama kunyatani a idon duniya saboda iyayen yarinyar nan suna da kawaici sosae, kuma son gamamin komae tinda suka nunamin suna son abinda nahaifa,bawai ina nufin kafifita Hanan akan Zuhra ba,aah banaso awulaqanta kowa acikinsu,kuzauna lafiya,hakan zaisa hankalina yakwanta inyi farin ciki ko bayan raina,Allah yayi maku albarka,yabaku zuri'a tagari".

Mami ta'ansa da ameen ya rabbi.

Mami tace"toh,duk abinda zan fad'a mahaifinka yarigani Rafeeq,hakika Zuhra yarinyar kirkice samun irinta sai antuna dan haka kariqesu da kyau,itama Hanan idan tanada wasu halaye wa'anda bakaso,zaka iya gyarata cikin hikima,da haka hartazama kamar kowa,banaso wani abu marar dad'i yafaru atsakaninku,Allah yarufa asiri,ya albarkaceku ya kuma baku sa'a"

Suka ansa da ameen.

Abba yace"yanzu saika tashi katafi gida dare nayi.

yaya Rafeeq yayi godia tare da fad'in insha Allah yayi alqawarin adalci,atayashi da addu'a Allah yahad'a kansu.

yaya Rafeeq baibar gidanba sai wurin 9:30pm.

Suka rakashi har wurin mota hadasu Islam da Iman sannan sukayi mashi addu'ar asuba tagari.

Yabiya wani supermarket yayi shopping dinduk abinda yake buqata sannan yatafi gida.

Ango yasha qamshi,yasha farar shadda fara qar tare da babbar riga,wadda tayi aiki irin na yan ghana,ya qara kyau da kwarjini.

Hannunshi d'auke da manyan ledoji guda biyu,part din Zuhra tafara shiga yatarar da ita kwance biya kujera.

Yayi sallama amma bata ansaba yasan bacci takeyi,a fili yace"oh my God,my wife abisa kujera kike bacci kuma?".

Ya isa wurinta da niyyar yad'auketa yakaita bedroom dinta bisa gado.

Fuskarta yafara shafawa mai tarin taushi tamkar fatar jariri sabuwar haihuwa,ahankali tabude kyawawan idanuwanta kamasu shining kamar zaiba.

Suna had'a ido tayi mashi murmushi,shima murmushin yamaida mata tare da kissing goshinta.

Zuhra tace"yaya Rafeeq nayi tinanin kunyi bacci fa".

yace"ya zanyi inyi bacci batare da naga wannan kyakykyawar fuskar takiba,yanzu nadawo daga gidansu Mami".

Tace"ina abokan naka?"

Yayi murmushi yace"ko auren farko ban yarda abokai sukayimin rakiya ba bare kuma nabiyu,yanzu haka kece zaki rakani ai".

Zuhra tace"ni kuma yaya Rafeeq?".

Yace"taso mujema,ni naga kindan fad'a Zuhra kuma kinqi kifad'amin abinda yake damunki".

Zuhra tayi murmushin qarfin hali tace"kai dai ke ganin haka amma ni babu abinda yake damuna".

Tatashi suka tafi part din Hanan,har ciki bedroom dinta sua shiga saboda bata porlour.

Zaune take tsakiyar gado,dakin yayi kyau sosae,sai Zuhra taga komae na part din Hanan iri dayane da kayan da yaya Rafeeq yacanza mata,color ne kawai yabanbanta,kayan part din Hanan komae purple tin daga porlour dinta har bedroom da kitchen,ita kuma Zuhra komae pinks colour ne nata.

Tana ganin kafin ta'ansa sallama tayi masu kyakykyawan murmushi tare da ansa sallamarsu.

Suka zauna yaya Hanan tagaishe da yaya Rafeeq babu yabo ba fallasa ya'ansa,Zuhra tagaishe da ita tare da yimata sannu da zuwa,cikin kulawa Hanan ta'ansa.

Yaya Rafeeq ne yayi masu nasihohi akan zama lafiya da kuma bin umarni da order,yayi masu bayani sosae akan zaman mataye na mazan Allah(s a w),daga qarshe yace yana fatan zasuyi koyi da su.

Yace"ga dinner dinsu nan Hanan,tajera masu a dinning area,babu 6ata lokaci Hanan tatashi,a part dinta sukaci abinci,pizza ne da tsire da lemuna da wani cake mai shegen dad'i,sai kuma wasu manya donut wanda sukaji kayan had'i,da fresh milk da dai sauransu.

Bayan sungama sukad'an fara fira,har 10:45pm,Zuhra tace"idan nabiye maku bazanyi bacci ba yau dan haka nabarku lafiya".

Tamiqe zata tafi,Hanan tace"kai Zuhra badai har kinfajin bacci ba?".

Zuhra tace"wlhy Aunty Hanan bacci nakeji,bari intafi inkwanta".

Yaya Rafeeq,Aunty Hana,
Ina maku fatan alkairi,
Asuba tagari.

Yaya Rafeeq ai bari murakaki mana,yatashi tsaye,Hanan ma tatashi suka fita.

Dama Zuhra nata ganin jiri,daurewa kawai take,saboda batason sugane wani abu dan hankalin yaya Rafeeq zai tashi sosae,qarshe wannan daren nasu ya6aci.

har cikin bedroom dinta suka kaita,yaya Rafeeq ne yakwantar da ita,yanada niyyar lullu6eta sai amai,duk yabi yarud'e yaqara rungumeta ajikinshi,hankalinshi yatashi sosae duk yabi yarud'e.

Gaba d'aya kayan jikinshi sun 6aci amma baidamu ba,yaqara rungumeta ajikinshi kamar wadda za'a qwace mashi ita.

Yadda Zuhra keyin aman dile duk wanda yagani yarud'e,sai abin yayi m Hanan yanayin irin yadda Sultan yariqayi agida kafin sutafi asibiti aranar da zai mutu.

Itama Hanan tarud'e sosae,yaya Rafeeq yace"Hanan tafi part dina kidauka car keys mutafi asibiti.

Da gudu Hanan tafita har tinti6e takeyi,kafi tadawo yaya Rafeeq yacanza ma Zuhra riga,sannan yacire babbar rigar da ke jikinshi.

Yadauketa yafita da ita,a porlour yaci karo da Hanan,suka tafi harabar gida sai asibiti.

Allah dai yakaisu lafiya dan irin gudun da yakeyi,Hanan ce rungume da Zuhra a baya,shikuma yana driving.

Suna zuwa asibiti emergency aka ansheta,akayi cikin wanda room da ita,drip aka fara saka mata,sanna aka shiga dubata.

Yaya Rafeeq ko zama baiyiba haka itama Hanan takasa zama,tausayin Zuhra yakamashi dama yasan daganinta batajin dad'i,Allah kadai yasan irin yadda takeji.

Saidai Hanan taga Yaya Rafeeq yana zubar da hawaye kamar wata mace,tinda take bata ta6a ganin kukan yaya Rafeeq ba,ko mutuwar Sultan baiyi kuka ba,wannan wane irin sone yaya Rafeeq yakeyima Zuhra?.

Lalle Zuhra tayi sa'a arayuwa,ko kuma ince halintane yaja mata wannan martabar.

Idanuwan yaya Rafeeq sunyi yajur kamar garwashi,gashi cikinsu babu wanda yazo da wayarshi bari afad'i a gida.

Bayan 2hrs Doctor yafito tare da sauke farin glass din dake fuskarshi fuskarshi babu annuri da walwala,gaban Yaya Rafeeq ya yanke yafad'i.

Hatta Hanan saida taji hankalinta yayi mugun tashi,itama har kuka saida tayi dan tausayi gashi kuma angon nata sai zubar da hawaye yake.

Doctor yakalli yaya Rafeeq cikin tausayawa yace"kasame ni a office yanzu"...........................

*Real Miss j*🙋🏻‍♀😘
[5/11, 22:04] ‪+234 813 019 3077‬: *🎀ADALILIN KANE🎀*

*STORY & WRITTEN BY JAMILA SAMAILA YUSUF*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*

*250-255*

Hankalin yaya Rafeeq yaqara tashi,Hanan dake zaune tatashi tsaye.

Yaya Rafeeq zuface fara keto masa duk da irin A/C dake cikin asibitin.

Yaya Rafeeq yabi bayan Dr. Hashim,har zuwa office.

Zaune yake agaban Dr. Hashim bisa kujera.

Yaya Rafeeq addu'a kawai yake,Allah yasa Zuhra tasamu lafiya kamar yadda take abaya.

Dr. Hashim yayi gyaren murya yace"ranka ya dade matar tana dauke da juna biyu na tsawon 6months,congratulations".

Yaya Rafeeq yace"Dr. ya jikin matana yake?".

Dr. Hashim yace"kada kadamu ranka ya dade,insha Allah zuwa gobe zaku koma gida".

Yaya Rafeeq yayi ajiyar zuciya mai qarfi yace"Alhmdllh,hankalina ya kwanta sosae".

Dr. Yace"lalle kanaji da wannan matar taka sosae".

Yaya Rafeeq yace"Dr. Hashim kenan,ina sonta fiye da tinanin mai tinani,yanzu zamu iya shiga muganta?".

Dr. Yace"eh zaku iya shiga,amma fa zatakai zuwa 5:30am bata farkaba cuz alluran da akayi mata,Allah yabata lafiya".

Yaya Rafeeq yace"ameen ya rabbi,muna godia".

Sukayi sallama da Dr. yatashi yafita.

Tinda yabar Hanan ko zama bata sake yiba,saboda hankalinta atashe yake.

Anan yatarar da ita cikin farin ciki,Hanan tana ganinshi itama tayi murmushi tasan da alamar nasara.

Yaya Rafeeq yaqaraso ina take tsaye,Hanan tace"yaya Rafeeq ya jikin Zuhra?".

Yaya Rafeeq yace"Alhmdllh Hanan,Zuhra tana d'auke da juna biyu,Allah sarki,ashe ina da rabon ganin yaron Zuhra?".

Hanan tace"Alhmdllh Allah yaraba lafiya".

Yaya Rafeeq yace"ameen ya Allah,yanzu mushiga muganta".

Hanan tabi bayan shi har suka isa bakin qofar shiga room din,yaya Rafeeq ne yamurd'a qofar sannan yashiga tare da sallama,Hanan na biye da shi.

Kwance take bisa gado,tanata baccinta,cikin kwanaki kad'an tad'an fad'a,tausayinta yaqara kama shi.

Yazauna agefe gadon,Hanan na zaune bisa kujerar da ke kusa da gadon.

Kyakykyawar fuskarta yake kallo,yasa hannunshi na dama yafara shafar fuskarta da keda taushi kamar fatar jariri sabon haihuwa.

Wani masifaffen kishi yatasoma Hanan,ji take kamar ta'anshi car key tatafi gida dan dai dare yayi sosae,babu yadda ta'iya dole tarintse idanuwanta tana neman tsari daga shaidan.

Basu dade ba sukajiyo kiran sallar asuba,yaya Rafeeq yatashi yashiga toilet yadauro alwala sannan yatafi masallaci.

Bayan yatafi itama Hanan tayo alwala tayafa mayafinta tare da kabbara sallah.

Yaya Rafeea yana dawowa,yaga dai Zuhra bata farka yacema Hanan zaije yafadama su Mami.

Hanan tace''adawo lafiya".

Hanan ta'isa bakin gadon Zuhra tazauna zuciyarta cike da tinani iri daban daban akan Zuhra.

Hakika tasan tana kishin yaya Rafeeq,kuma tana sonshi sosae fiye da komae,batayi niyyar had'ashi da kowa ba,amma babu yadda ta'iya idan tanason zamanta lafiya tare da shi to dolene tazauna da Zuhra lafiya,saboda ba itaba hatta iyayenshi sunsan yanason Zuhra fiye da komae.

Dan dole taba zuciyarta haquri tare da addu'ar Allah yabasu zama lafiya,ya karesu daga sharrin mutun da aljan.

Tabbas Zuhra yarinyar kirkice bata nufina da komae sai alkairi toh dammi natsaneta,wannan duk sharrin shaidan ne tare da sharrin Khubra,Allah karagemin wannan kishin da yake damuna nazauna da Zuhra tamkar qanwata ciki daya.

Wannan tinanin shine tayitayi har Allah yayima Zuhra farkawa.

Ahankali Zuhra tadafa hannunta muryar asanyaye tace"Aunty Hanan tinanin me kikeyi haka".

Fuskar Zuhra kice da damuwa.

Firgigi tadawo cikin hayyacinta tace"Zuhra kintashi?,ya jikin naki?,bari nayima Doctor magana,ina zuwa yanzu".

kafin Zuhra tayi magana har Hanan tafita,tausayin Hanan yakama Zuhra,cikin zuciyarta take fad'in badai anan Aunty Hanan takwana ba.

Babu 6ata lokaci Hanan tadawo da Doctor,fuskarshi d'auke da fara'a yashigo tare da sallama,Hanan na biye da shi.

Bayan Zuhra tagaishe da shi ya'ansa,tare da yimata ya jiki,yashiga dubata.

Jikinta da sauki sosae,yatambayeta ya takejin jikin nata,Zuhra tace"lafiya qlau saidai rashin qwarin jikin".

yace"kada kidamu zaki samu lafiya insha Allah".

Yakalli Hanan yace"zuwa anjima za'azo abata breakfast dinta tare da magani,Allah yabata lafiya,Ina Rafeeq yajene?".

Hanan tace"yaje yadawo yanzu insha Allah".

yace"ok,shikenan".sannan yafita.

Hanan tadawo tazauna kusa da ita tace"ya jikin naki?".

Zuhra tace"nasamu sauki Aunty Hanan,amma kinyi qoqari da kika kwana awurin nan nagode Allah yabaki lada".

Hanan tayi murmushi tace"ameen,ai tare da shi muke yaje gidan Mami yadawo".

Zuhra tayi murmushi tace"Allah yadawo da shi lafiya".

Bayan sungaisa da Mami da Abba nan ne yake fad'a masu abinda ke faruwa,duk sukabi suka rud'e hadasu Islam da Iman da suka tashi bacci ba shiri sunyi cirko cirko.

Tare da Mami yataho asibitin tin cikin motor Mami taketa faman mashi fad'a dan tinlokacin da zasu tafi asibitin da ankira amfad'a masu,ambar yarinya kamar bata akowa.

Saidai yaya Rafeeq yayita bata haquri dan yaga ranta ya6aci sosai.

Suna zuwa suka tarar da Zuhra tafarka,har tana iya magana lafiya lau.

Bayan tagaishe da Mami,Mami ta'ansa tare da yimata ya jiki cikin kulawa tare da tausayawa.

Wata Nurse ce tashigo tare da wani dan keke naturawa wanda yake dauke da kayan break da kuma magunguna.

Cikin toilet din akwai sabon brush da maclearn,bayan tayo brush,lokacin Nurse din tagama had'a tea,da niyyar ita zata bata.

yaya Rafeef ne yace"kibar zanbata".

Nurse din tayi murmushi tace toh tare da komawa gefe.

Yaya Rafeeq ne yabata tea din da hannunta tare da cheaps da soyayyen kwai,bata wani ci sosae ba,dukda Mami tasa baki.

Bayan yagama batane,Mami tace"yanzu katafi da Hanan gida domin tashirya,kaima saika shirya,sannan kutahoma da Zuhra da kayanta da zata shirya".

Badan ranshi yasoba hakanan yatafi yabar Zuhra,haka yatafi da Hanan gida akabar Mami.

Mami ce taci gaba da kula da Zuhra tare da tattalinta kamar mahaifiyarta,Mami sai nan nan take da Zuhra kamar ba sirikarta ba.

Hakika Zuhra najin dadi tare da godema Allah daya hadata da Mami,saboda tinda Allah yahadata da yaya Rafeeq bazata iya cewa ga abinda Mami tayi bata marar kyau ba,tsakaninta da ahalin Mami da Abba sai godia tare da fatan alkairi.

Lokacin da Doctor yadawo qara duba Zuhra,nan yakeyima Mami murnar akan cikin Zuhra,itama Zuhra anan takejin abinda ke faruwa,Mami tashiga nuna farin ciki tare da godia ga Allah,ita kuma Zuhra banda kunya babu abinda takeji dan ji take kamar tagudu.

Bai wani 6ata lokaciba sai gashi yadawo,tare da iyayen fruits da juice da chocolate da dai sauransu.

Bai dade da dawowa ba saiga su,Islam da Iman driver yakawosu tare basket manya guda biyu ta abinci,nan fa Mami tatsare Zuhra akan saitaci abinci.

peppe chicken ne tazuba mata tare da soyayyen irish da source.

Zuhra tana faraci tayi da gudu toilet,yaya Rafeeq yabita amai kawai takeyi babu qaqqautawa,saida tagama sannan suka dawo.

Babu abinda takeso sai tea da cheaps shikenan abincinta.

Wajen 11am saiga Mummy tazo ganin Zuhra tare da abinci kala kala da fruits da ruwan roba,tatausayama Zuhra sosae,anan tazauna har lokacin da aka sallamesu suka tafi gida.

Saboda kawai irin na Mama cewa sukayi tinda Mami tana tare da Zuhra basai sunzo ba dan itama uwace zatayi komae.

Mami taji dadin da irin kalaman iyayen Zuhra,sun bata girmanta sosae.

Babu irin gatan da Mami batayima Zuhra ba,lalle Zuhra mai sa'a ce.

Sai bayan sallar isha'i sannan Mami da su Islam suka tafi gida.

Dan Yaya Rafeeq da Hanan anan suma suka wuni.

Saida lokacin kwanciya yayi,yaya Rafeeq yabi Hanan har part dinta yace"tayi haquri yakwanta agurin Zuhra tinda batada lafiya.

Hanan dukda bataji dadi ba saidai tadanne tace mashi babu komae,Allah yabata lafiya.

Zuhra har bacci yafara daukarta taji alamar mutun yashigo bedroom dinta,da sauri tabude idanuwanta wa'anda suke cike da bacci,yaya Rafeeq ne tagani yana qoqarin rufe d'aki.

Fuskarshi cike da murmushi yace"maman twins ko akwai abinda kike buqata?".

Zuhra tayi murmushi tace"babu abinda nake buqata mijina,saidai katafi kakwanta da Aunty na".

Yaya Rafeeq yaqaraso kusa da ita yazauna gefen gado yana kallon cikin idanuwanta yace"tasan baki da lafiya kuma tahaqura inkwana anan ko zaki buqaci wani abu".

Zuhra taji tausayin Aunty Hanan sosae,fuskarta cike da tausayin Hanan tace"yaya Rafeeq zamana anan kamar zan takura maku,kaga Aunty Hanan tana buqatar kulawarka,ina son intafi gida ko zaku samu damar cin amarcinku".

Da ranshi ya6aci baici da ita komai ba saidai yakwanta kawai tare da kashe beside lamb din dake kusa da shi.

Hankalin Zuhra yatashi tasan fushi yayi,ahankali tamatso inda yake tare da kiran sunanshi.

Tace"yaya Rafeeq lafiya?".

Baiyi mata magana ba,ranta babu dadi saidai taji hawaye suna zuba bisa fuskarta.

Dajin yadda take mayar da numfashi yasan kuka takeyi,da sauri yatashi zaune tare da kunna wutar dakin,ya juya yana kallonta.

Yace"amma kinsan banason ganin kukanki ko,kuma kinji abinda Mami tafada maki banda yawan tinani da 6ata rai ko?".

Zuhra tajuyo takalleshi,sai kuma batashi tausayi,yasa hannu yashare mata hawaye,fuskarshi cike da ladamar abinda yayi.

Yace"amma kinsan ko Hanan anan gidan tayi komai,Zuhra nasan idan kika tafi gida za'a kula da ke,amma nafison nakula da ke Zuhra kullun ina ganinki".

Zuhra tace"yaya Rafeeq fushinka yana tadamin hankali kayi haquri da maganar da nafada maka,kuma bazan sake maganar zuwana gida ba".

Yaya Rafeeq yace"my real wife,saboda haka nake qara sonki,i luv u to d square of infinity".

Ahaka sukayi baccinsu kike da so da kauna,hmm yaya Rafeeq kenan.

Hanan dukda irin yadda take tausayin Zuhra amma saida taji bataji dadin wannan lokacin ba,amma babu yadda ta'iya dole tayi haquri ahaka bacci yadauketa.

Washe gari dan dole Zuhra tatake badan komai da saidan yaya Rafeeq yana iya cewa anan zaiqara kwana dukda Hanan bazatace aah ba amma ai babu dadi.

Haka Zuhra taci gaba da rainun ciki har tabar laulayi,aka koma skul da yake suna 4 hundred level ne,cikinta nada wata 6 suka gama exam na 1st semester.

Zaune suke lafiya da Aunty Hanan,dan itama tasamu yadda takeso yanzu yaya Rafeeq yana kulata sosae fiye da da,tanajin dadin zama gidan sosae.

Duk abinda yakeso shine takeyi,dan itama tana kula da Zuhra sosae dan tagane zama lafiyarta agidan shine tazauna da Zuhra lafiya.

Kusan duk baya sati 1 sai Mami tazo gidan ganin Zuhra tare da yimata ya jiki.

Su Islam da Iman sungama A.B.U lafiya da yake suna gaban Zuhra da 1yr sakamokon abinda yafaru da ita.

Aka fara shire shiren saka masu rana wata 6.

Bayan su Zuhra sun kamala 2nd semester exams dinsu da sati 3,wani ranar juma'a tana kwance adaki ita da yaya Rafeeq matsanancin ciwon nakuda yakamata,tanata faman nishi yaya Rafeeq yatashi arude,yakira wayar Mami yafada masu,sannan yakira wayar Hanan babu 6ata lokaci sai gata cikin shirinta nazuwa asibiti.

Cikin daren nan suka tafi asibiti,acan suka tarar da Mami da Islam da Iman driver yakawosu.

Bayan andauki Zuhra cikin gadon daukar marassa lafiya akayi dakin haihuwa da ita.

Zuhra tasha wahala dan acan suka kwana,kowa sai addu'a yake Allah yasaketa lafiya.

yaya Rafeeq dan tausayin Zuhra hada kukanshi,Zuhra tasha wahala da saida marece sannan tahaihu har amfara shirin yimata c.s.

Abu kamar amafarki Nurse tayi masu albishir da tahaihu lafiya,amsamu twins babies,murna wurin dangi ba'a magana take yaya Rafeeq yayima Nurse kyautar kudi masu yawa,Mami kuwa yan hannun gold din dake hannunta takire tasakama Nurse din.

Nurse tayita godia,bayan kamar 1hr aka fito da jarirai farare tas da su mace da namiji.

kowa sai farin ciki yake,Islam tace"ai dama daganin wannan cikin yadda yayi girma kasan sai yan biyun".

Mami tace"Alhmdllh,Allah yaraya manasu".

Nurse tafito tace"ranka ya dade ku kwantar da hankalinku nan da 30mins zaku iya shiga kuganta".

Nanfa murna taqaru sosae.

Lafiya qlau Zuhra tahaihu babu wata matsala,bayan 2hrs aka sallamesu suka tafi gida.

Duk wanda yaga babies sai ace ai namijin da yaya Rafeeq yake kama macen kuwa Zuhra.

Hanan kuwa babu zama itama tana cikin farin ciki sosae.

Yaya Rafeeq yayi masu huduba da Umar da Maryam.

Da satin yadawo akasha biki wanda ba'a ta6a yiba dan shanu biyu da raguna hudu banda kaji da talo talo da aka yanka,anraba abubuwa kamar ba asan ciwon kudi ba,irinsu carpet,jikkuna,bedsheet,hijabai,cooler,alkur'anai da sauransu.

Ana kiran yaran da Sultan da Afra,kullun yaran suna wurin Aunty hanan dukda andauko Nannies guda biyu da zasu riqa kula da su.

Arziqi wurin yaya Rafeeq yafi da dan yanzu hada kamfanin atamfofi yake da shi a Ghana,ga kuma kamfaninshi na takalma da jakuna a thailand,ga kuma motoci da ake shigo mashi da su ana sayar mashi.

Tini yafara gina qaton gidanshi a g r a,katon gida mai dauke da part hudu,gidane na alfarma kuma namasu kudi masu jida kansu.

Ahaka bikinsu Islam yazo,akasha biki a gani nafada,lokacin su Sultan da Afra nada wata ukku sunyi wayau ga kyau,kamar Sultan harta 6aci da mahaifinsa,Afra kuma mahaifiyarta.

Haka taro yatashi lafiya qlau aka kai amare gidajensu,Islam ana kano aka ajiyeta,Iman kuma katsina.

Saida yaranta suka kusa iya yaye sannan suka fara service dinsu dayake acikin kano aka ajiyeta.

Ana cikin hakane Allah yaba Hanan ciki mai laulayin fitina dan dan dole yaya Rafeeq saida yabari tatafi gida,dan har cikin yayi qwari batajin dadi dukda anata zuwa asibiti.

Suna zuwa ganin akai akai,dan Sultan da Afra kamar gidan suke aisu kullun suna gidansu Hanan.

Bayan wasu watanni Allah yasauketa lafiya tahaifi diyarta mace wadda taci sunan Aysha,sunan Mummy kenan ana kiran baby da Farhat,yarinyar tana kama da Hanan sosae itama tana da kyau sosae.

Tini Zuhra ta manta da tayaye wasu yaranta,har ta kusa gama sevice dinta.

Amma yaya Rafeeq haryafara maganar wai babu wani labari dan shifa so yake gidan yacika da yara,Zuhra dai saidai tabishi da ido,abin mamaki kamar dai haihuwar babu wahala.

Ahaka Allah yabata ciki baifi wata hudu ba,Iman tahaihu suka dauki hanyar Katsuna ta dikko,tahaifi babyboy nanma asha taro baby yaci suna Aliyu suna kiranshi da Haidar.

Ahaka cikin Zuhra yatsufa,har lokacin haihuwarta yayi,bayan haihu da wata daya tasamu namiji yaci sunan Abba ana kiran baby da Khalipha suka tare a sabon gidansu.

Ba'a jimaba Islam tahaihu ita kuma baby girl tasamu mai suna Ayda.

Bayan Zuhra ta'anshi result dinta,yaya Rafeeq yafara shire shire yayesu yatafi da su England domin ci gaba da karatunshi da kuma na Zuhra zatayi Masters dinta acan,ga kuma su Sultan da Afra suma aka sakasu school tare da yaran turawa.

Rayuwa kenan,haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin jin dadi da kwanciyar hankali,kamar basu ta6a wani tashin hankali ba,Nigeria saidai suzo da yawo.

Bayan shekara biyar sun gama karatunsu da yaya Rafeeq turarawa sun daukeshi aiki a wata babbar jami'ar dake England zama yakamsu acan.

Wata shekara sunzo gida suna ahanyarsu tadawo gida driver yadaukosu airport nan sukaga wata almajira tanata faman bara jikinta duk quraje da yagaggun kaya da kuda sai faman binta sukeyi yaran sai faman janta sukeyi wai mayya mayya,adaidai inda danja tatsaida motarsu dan motoci biyune da daya tayi masu kadan,mota daya Zuhra da Hanan da Khalipha da Farouq na wajen Hanan da Suhaila tawurin Zuhra,dayar motar kuma Yaya Rafeeq da Afra da Sultan da Abiyad.

Matar tazo tana bara,Zuhra ce taji tausayinta taciro dubu biyar taba driver yabata,kamar daga sama matace takira sunan Hanan saikuma tafara kuka.

Dan Hanan bata wani ganeta ba,matar tace"Hanan baki ganeni ba?,ni ce fa Khubra,Khubra qawarki".

Hanan tayi salati tace"Khubra kice kika koma haka?".

Khubra tace"ni ce,banida lafiya Hanan kitaimaka min".

Tini motoci suka fara tafiya saboda ambada hannu,Hanan sanan tayima Mummy alqawarin itada Khubra har abada,kuma bazata karya wannan alkawarin ba,saidai taciro kudi masu yawa tamiqa mata hannunta na rawa ta'ansa kafin tayi magana har motarsu Hanan tayi gaba,nab Khubra tafadi tana kukan bakin ciki da ladama.

Yaya Rafeeq ne zaune cikin family dinshi porlour yaran duk sunbi sun hayeshi yana wasa da su.

Zuhra ce tafito tace"wa'annan yaran bakuji gaskiya".

Yaya Rafeeq yace"ni da nakeso Allah yaromin yara da yawa kinfasan yadda nakeson yara".

Ai Zuhra tace komai taqara gaba saboda tasan halinshi da son yaran kamar yadda yafada.

Rayuwarsu abin sha'awa cike da kwanciyar hankali,ga jin dadi sunje makka yafi sau nawa ga umara sunata zuwa,gashi kowace nada shoprite da kamfaninta.

Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin jin dadi,gashi ko wani lokacin cikin aikama iyayenshi da na matanshi abin arziqi tare da yan uwa da abokan arziki.

Arziki yaci uban nada dan yanzu yaya Rafeeq yasha kwana yayi kudi sosae yayi qiba daidai misali haka matanshi.

Yaranshi suna da tarbiya sosae ga kula da suke yamu tako'ina gasu kyawawa abinson kowa.

ALHMDLLH,INA GODIYA DA ALLAH DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI MAI SUNA ADALILIN KANE WANDA NI JAMILA SAMAILA YUSUF NABADA LABARI KUMA NARUBUTA.
08130193077

SAI KUJINI ASABON LITTAFINA MAI SUNA FURUCI NA NE!!!!!!!!!.

*REAL MISS J*🙋🏻‍♀😘

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Table of Contents

Chapters

2 chapters
  1. 1 Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
  2. 2 Part dinshi tashiga domin tagyara amma abin duniya yadameta jikinta bbu qwari.