WANE NE SHI? Na Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) Ya Allah! Yanda na zan fara wannan labarin lafiya, Ka sa na gama lafiya. Ka tsarkake min alkalamina daga rubuta abin da bai dace ba. Kasa abin da zan rubuta ya zama hujja gareni ba hujja a kai na ba. Allahumma Ameen Ya Rabbi. Wamnan labarin kirkirare ne. banyi dan ɓatawa wani kowata ba, idan ya yi kamance ce niya da labarin wani arashi ne. YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION Yota no...019 Pg 1and 2 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Monday, August 16th. Kuje Medium Security Custodial Centre. Wata sassanyar iska ce ta ke kaɗawa sakamakon hadarin da ya gangamo, babu abin da a ke yi sai walƙiya da cida . A hankali ya zuro ƙafarsa wajen gate ɗin gidan yarin,wata irin iska ya shaƙa ya kuma fesar iskar ƴanci kenan.Shi dai ya san an faɗa masa saura wata uku ya bar gidan yarin, amma kawai ɗazu aka zo a kace umarni ya zo daga sama wai a sake shi . Ɗaya daga cikin jamii'an gidan yarin ne ya koma gefe sannan ya kara waya a kunnensa,ƙasa ya yi da muryarsa ya ce " Hello yallaɓai an saki BARDE fa !" Wata irin zabura mutumin ya yi har yana watsar da wayoyinsa." Uban waye ya bada umarnin sakinsa lokaci bai yi ba"? .Amsawa Gandiroban ya yi ya ce "Wallahi ban sani ba nima abun ya ba ni mamaki !." Cikin tashin hankali da tsawa mutumin ya ce" Ka kira team ka ce musu abun farauta ya fito! A farauce shi tun kafin ya farauce mu ,domin shi ɗin mayunwa ciyar damisa ce da ta daɗe tana neman abin da za ta ci yanzu babu zato babu tsamani an sako shi,ka ce musu a kashe shi!". "Ok" Ya furta yana kashe wayar. A take ya fara kiran mutanensu ya na sanar musu BARDE ya fito!. Takawa ya ke yi ba tare daya san takamaimai inda zai je ba ,tunani yake shi dai ya san wani lokaci ya kan ji shi mai hankali wani lokacin shi kansa ba ya gane matakin da ƙwaƙwalwarsa take. Cak, Ya tsaya. Zubawa Wani mutum Ido da ya ke tsallaken titin Daga can dayan ɓangarensa a tsugunne ya na gyaran mashin. Tafiya ya cigaba da yi,ya tafi wajan wata ƴar tireda, da ake sayar da katin waya. Tsugunnawa ya yi, yayi zane a ƙasa sannan ya wuce da sauri, ya bar gurin. Me sayar da katin ya fito ya kalli bayansa domin a zaton shi ma ko mahaukaci ne . Rubutun da ya yi ya zuba wa ido , wata irin zabura ya yi har yana ƙokarin faduwa . ko tsayawa rufe gurin bai yi ba ya hau mashin ɗinsa, sannan ya kara wayarsa a kunnesa Jim ya ɗan yi sannan ya ce "Boss Wallahi ya fito!" Daga cikin wayar a kace masa , ka gudu daga gurin ko kuma ka mutu! A rikice ya ja mashin ɗinsa a ya tafi ya bar gurin da gudun gaske. Sannu a hankali ya ci gaba da tafiya, can kuma ya ƙara juyawa hagu da damansa,wasu ƙarti ya gani da baƙaƙen kaya a jikinsu sun rufe fuskokinsu da bakin ƙyalle, sun kuma zuba masa ido. Juyawa ya yi ya kalli tazarar da ke tsakaninsu akwai tazarar, amma ba sosai ba. Yinƙurawa ya yi ya tafi da gudu kamar haɗin baki haka suma suka biyo shi. Wani irin gudu ya ke yi iya karfinsa. Ganin da gaske sun kusa cin masa ga shi ya na da tabbacin idan suka kama shi sai dai wani bashi ba , ya sa ya fara waige -waige domin tseratar da rayuwarsa. Wata farar mota ya hango kirar G.L.K ta shararo da wani mahaukacin gudu, tana zuwa dai-dai inda yake aka yi wani irin burki. Daga ciki a ka ɓuɗe masa, ba tare da ya yi wani tunani ba ya faɗa cikin motar ya na sauke numfashi . Ɗan kwantar da kansa ya yi a kan kujerar motar ya na mai da numfashi,ganin ya tsira daga hannun waɗanan mutanen lumshe idonsa ya yi kamar me bacci can kuma ya buɗe, ya kai kallonsa kan direban dake tuka motar zabura ya yi ! cikin wata iriyar tsawa ya ce "dakata" "Sauke ni" maimakon ta tsaya sai ma gudu da ta ƙara wa motar, yunkurawa ya yi da nufin bude motar ya ji ta a kulle . A haukace ! yace "wai ba magana nake maki ba.?" " kenan ka zaɓi ka sauka mutanen nan can su illata k..." "Na ce ki sauke ni ko" Ma...Maci.... Maciya...Amana! Kawai. "Ya faɗa cike da in'ina, saboda yadda ya daɗe be magantu ba. Murmushin gefen baki ta yi, sannan ta ɗan kaɗa hanunta . Daga bayan Motar a ka zuro hannu a ka shaƙa masa wani abu a hankicif. A take kuwa lumfashinsa ya dauke,ya zube a gurin.Kuramasa ido ta ɗan yi sannan takarawa motar wuta. *** Misalin karfe 2:30 na dare. Daji ne me wani irin duhuwa da surƙuki. Wani irin gudu take yi saman miƙaƙiyar kwaltar da ta biyo ta cikin dajin, wadda ba ta da tabbacin idan za ta kai ta. Wasu bakaƙen motoci ne guda uku suke bin ta da wani irin gudu . Wata number take ta kira amma ba a ɗaga ba!. Jifa tai yi da wayar. , ta ci gaba da tuƙa motar cikin tsananin tashin hankali da ruɗani. Harbin motar mutocin da su ke biye da ita suka fara yi.Cike da ƙwarewa ta ke gocewa wasu daga cikin harbin nasu, amma duk da haka harbin ƙokarin samun ta ya ke yi. Gangarawa cikin ai nihin dajin ta yi ,mai cike da wani irin duhuwa da surƙuƙi. Cak ! Motar da tsaya taƙi gaba taƙi baya. Fitowa ta yi daga cikin motar da wani a bu rike a hannunta, gudu ta cigaba da yi tamkar makahon dokin da bai san gabansa ba bare bayansa ,tana jin yadda ƙayoyi suke ratsa kafafunta amma hakan be hana ta gudun ba ,sai ma karfi da ta kara masa. Tuntube ta yi da wani abu da ba ta da tabbacin dutse ne ko kuma a'a , ai kuwa ta hantsila ta fadi da rubda ciki ! Kanta ya gwaru da dutsen da yake gabanta, jini ! Ya wanke mata fuska ,rintse idonta ta yi wata irin a zaba tana ratsata tun daga kwakwalwarta har zuwa tafin kafarta Hawayene ya gangaromata, da kyar ta iya yunkurawa ta tashi cigaba ta yi da gudun duk da yadda ta ke gani dishi- dishi saboda jinin da take ta zubarwa. Wani surkuki ta shiga tana jin yanda ƙayoyi suketa kartatta,amma bata kula hakan ba saboda tashin hankalin da ta ke ciki ya wuce tunanin me tunani. Zubewa tayi a bayan wani dutse, a cikin wani irin mugun hali me kama da suma ko mutuwa tana jin hayaniyar su suna kusanto inda ta ke, amma ta gagara motsawa wani irin jiri ne yake ɗibarta, ita ba damuwarta su kasheta ba a'a damuwarta abin da yake hannunta,damuwarta ka da aci galaba a kan cikar buri da muradinta. Da ƙyar ta iya motsa hannuta ta na laluben abin da zata kare kanta, amma ba ta samu ba, saboda ko gani bata yi sosai. Rarraba hanya mutanen suka yi, wasu suka yi wani bangaren dajin, wasu sukai wani. Buyi daga ciki ne su ka yo inda ta ke , ɗayan ya yi wani gurin ya na haske-haske .Ɗaya daga ciki ne ya karaso wajen dutsen, hasketa ya yi da wata fitilla me masifafen haske, baki ya buɗe da nufin yin magana, amma babu hali saboda wata kalar shaƙa! Da a kai masa daga bayan sa .,duk da girmansa amma ya gagara kwacewa. Murɗa wuyansa ya yi da karfi wani irin sauti ne ya fita mara daɗi, karar da mutumin ya yi ne ta jawo hankalin yan uwansa,da gudu suka yo wajen. A hankali yake takowa inda take ja ta farayi da baya harta fito sarari ,ji ta yi suna cewa gatacan-gatacan, ku harbe ta shugabansu ya basu umarni . Cikim wani irin sauri da zafin nama mutumin ya sa hannu ya janyota bayan dutsen. Harbi suka din gayi har suka karaso gurin. Duba bayan dutsen sukai amma abin mamaki ! Babu ita babu dalilin ta.Sosai suka bincika dajin amma basu gan ta ba. Daddanna wasu numbers shugaban su ya yi,sannan ya kira cikin gurbataciyar hausarsa yace" Shugaba ta ɓata" Daga cikin wayar aka amsa masa da "ina da tabbacin tana cikin dajin nan, dan haka kusa ka ma sa wuta ."Da yes sir ya amsa sannan ya sauke wayar. Haka su ka sawa dajin wuta .Suka haɗa harda gawar dan uwan nasu ! Sannan suka bar wajen. ★★★ ABUJA. Darul Fiyya Federal Medical Center (FMC Darul Fiyya) 8:30 pm. Zaune yake cikin ƙayataccen office ɗinsa wanda ya ji kayan alatun rayuwa. Dr Hammad Mansur Ilyasu mai Dollars kenan . shahararen, matashin likita me ji da samartaka da kuma kuɗi . Computer ɗin gabansa yake kallo ,Idonsa sunyi jajur kamar garwashin wuta,zuciyarsa ce ke wani irin tafasa, hannu ya sa ya daki gillas cup ɗin daya ke kan tebur din gabansa,tarwatsewa ya yi a kasa ya bada sautin haduwar sa da tayis. Da sauri wata Nurse ta shigo ta na fadin yallabai Lafiya ? Kuw.. . "Fita".!! ya ce cikin tsawa jijiyoyin kansa duk sun miƙe tsaye. Jiki na rawa ta bar office ɗin. Kurawa bango ido ya yi yana taune lips ɗinsa da karfi .Wayarsa ce ta dau ringin juyawa ya yi ya kalli screen din wayar. Hannu yasa ya dauki wayar , Ya ɗaga be ko yi sallama ba ya ce "barrister kana ina ne? Akwai matsala babba fa" Ɗan jim ya yi sannan ya ce "eh yanzu zanbar Asibitin muhaɗu a gidan gonata." Shiruu ya ɗan kara yi,da'alama sauraren abin da ake faɗa masa ya ke ."Ok" ya ce sannan ya katse wayar. Key din motarsa kawai ya dauka da wayarsa ya fito. Tun da ya fito a ke ta gaisheshi hannu kawai yake ɗaga musu Ƙarasawa ya yi gurin da motarsa take ya shiga ya fizgi motar da mugum gudu ya bar Asibitin. Bai yi wata tafiya mai nisa ba ya'iso gidan gonar.A waje ya yi parking ɗin motar ya fito ya shiga ciki. Yana shiga ya tarar da Barrister Ramadan har ya'iso, gaisawa suka fara yi. "Likita bokan turai " Barrister ya faɗa yana murmushi. Shima dan murmushi ya yi wanda iya laɓansa suka tsaya. Zama suka yi a harabar gidan. Cikin damuwa Dr Hammad ya ce "Barrister a bun nan fa ya fara ba ni tsoro, abu kullum kara ta'azzara yake babu sauki . A cikin shekara shidan nan da fara aikina, ban san a dadin sau nawa aka kawo mana matan da a kayi musu fyaɗe ba. Wai mene ne matsalar ne?Ina masu ruwa da tsaki akan wannan lamari ?Ko kuma duk ba mu da sune? Abun ya ta'azzara da yawa. Akwai wata alamar hoton kunama da na ke gani a damtsen yawancin matan da ake kawowa da wani cukurkudaɗen rubutu da juyin duniyarnan na kasa karanta abin da aka rubuta, .kuma abin tashin hankalin kala ɗaya ne babu abin da yake raba su. Musamman kusantowar zaɓen nan." "Ka ga jiya ma an kawo wata yarinyar an yi mata mummunan fyaɗe abun ya ƙazanta ,don ba na tunanin za ta rayu, saboda anyi mata illa sosai. Kuma fa yarinyar bata wuce shekara 14 to 15 ba, an yi mata wulakanci sosai sai da na yi mata hawaye. Wallahi yanayin cin zarafin da a ka yi mata ya tunamin da wata yarinya, da a ka yi wa cin kashin nan, shekarar da na fara aiki, abun nan ciwo ya ke mun sosai. Na kasa mantawa saboda itace ta farko da na fara ganin tambarin a jikinta. Narasa wai sai yau she ƙasata zata gyaru ji nake kaina kamar ya fashe.Na tsani kalmar nan ba na sonta ko kaɗan idan na ji kalmar fyaɗe ! Zuciyata tafasa ta ke." "Mene ne amfanin ku a ƙasa mudin baza ku shiga cases ire-iren waƴen nan ba.?" Numfashi Barrister Ramadan ya sauke sannan ya ce "ba kai ka ɗai ba wannan ni ma ciwo ya ke min sosai, cases ɗin da aka kawo min a cikin wannan watan ya fi a shirin, Har na rasa yadda zan yi da su abun ya yi ya wa ai. "Naa daɗe da fara zargin anya babu sa hannun wata ƙungiyar da take aika-aikan nan kuwa? Ko kuma ya zama masu yin suna da daurin bayan manya?." Ramadan ya faɗa cike da damuwa. "Amma na ji ka ce yawan cin matan da ka yi wa aiki akwai wani tambari a damtsen hannunsu, mai ka fahimta a kai?" Ya tambaya ya na kallon Dr. Zazzafan numfashi ya sauke, sannan ya ce" abin da na fahimta shine akwai wata ƙungiya ko rukuni da suke yi,ko kuma wata haɗaka da suke yin wannan barnar,da su ke so a ankara dasu. Kamar yadda ka faɗa."ɗan jinjina kansa ya yi yace "lallai maganar ka za ta iya yiyuwa yanzu abin da ya kamata zan fara bincike akan wannan tambari ,saboda ta hakan zamu iya kamo bakin zaren matsalar, amma fa Dr wannan abu zai'iya zama mai haɗari sosai". Musamman daya zama ba ka da hurumi akan binciken,a matsayinka na likita. Da sauri Dr Hammad ya ce, "nasan da haɗari ba sai ka gayamin ba " Harararsa Barrister ya yi ya ce, " Can maka dai. zan fara bincike akan hakan duk abin da muke bukata ta gurin ka ina fatan zamu same shi. Akwai wata abokiyar aikina Barrister Safna , ta na ji da kalar cases din nan sosai dan yawanci shine wandaa tafi amsa tana aiki sos..." Katse shi Hammad ya yi da cewa , "kamar ya abokiyar aikinka tana da gaskiyar da da za ta iya shiga ciki ? Dan da alama akwai sarkakiya alamarin. Ka san za a iya samun matsala idan maganar ta fita."Dariya barrister ya yi sannan ya ce "tafi ka gaskiya ai " Taɓe bakinsa ya yi ya ce "habade wane ita takamo ni ta dai tsaya iya tata. Bari kaga hoton tambarin na dauka ya faɗa ya na zaro wayarsa,daga aljihu , mika masa wayar yayi ya ce, " kalli kaga" Amsar wayar ya yi ya na ɗora idonsa a kan screen din wayar ya zabura ! Ya mike tsaye ,har wayar tana kokarin subucewa. Ayeeshat Kissar ✍🏼✍🏼 08135210129 WANE NE SHI ? Na Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION 009 Bismillahir-Rahmanir-Rahim Page 3____4 Mikewa Dr Hammad ya yi da sauri shima. " lafiya kuwa Barrister?" Ya tambaya yana zuba masa ido. Girgiza kansa ya yi ya ce "ina zuwa." Ya faɗa ya na yin gaba . Ɗaga murya Dr ya yi ya ce "wayar fa? " Dawowa ya yi ya bashi wayar ya tafi da sauri. Shiga motarsa ya yi ya fita daga gidan gonar da gudu. Da kallo ya bi motar har ta fita. Jim ya ɗan yi sai kuma ya ɗan dage kafaɗar sa.fita shima ya yi ya hau motarsa ya nufi gida ,zuciyarsa cike da saƙe-saƙe. ★★★ Zaune su ke cikim babban ɗakin taron. manyan mutane ne sosai waƴen da suka ci su ka tada kai.Miƙewa Shugaban taron ya yi gyaran murya ya fara magana dacewa ."Ba komai ne ya taramu a wajen nan ba har ya sa a ka katse ayyukan da mu ke yi ba, sai sanarwar da kungiya ta ba da a kan mu faɗa muku Barde ya fito !. Fitowar yaron nan babban haɗari ne, zai'iya kawo ma na cikas babba." Ɗaya daga ciki ne ya miƙe cikin izza ya ce ,"wai shi wannan wani irin mutum ne WANE NE SHI ?Da har a ka haɗa taron gaggawa a kan shi? Ɗan gidan ubanwaye? Ko ya gagari kungiya ne?Da har ya tayarwa da ƙungiya hankali har ya yi san....." A fusace mutumim ya daka masa tsawa cikin ɗaga murya ya ce "shiɗin ba kowa ba ne , ba kuma dan kowa bane, amma babbar matsala ne, barazana ne ga mutuncinmu da kuma rayuwarmu ." "Idan har mu ka yi wasa yaron nan yana gaf da tarwatsamu. Idam baku manta ba shekarun baya ta dalilin sa kungiya ta kusa kwacemin kujerata. Kuma umarni ne daga Shugaba." Jiki a sanyaye mutumin ya koma ya zauna saboda tuna abin da shugaban nasu ya faɗa musu .Haka suka cigaba da tataunawa domin samun matsayar kawo karshen Barde. *** Barde A hankali ya ke ƙoƙarin ɓuɗe idanunsa da suka yi masa dauyi . Da sauri ya mai da idon ya rufe,saboda hasken da ya yi masa yawa. Ƙoƙari ya cigaba da yi har ya samu suka tsaya. Sannu a hankali yake ƙarewa ɗakin kallo kafin idonsa ya sauka a kan robar karim ruwan da take sarkafe, alamar angama kara masa ne.Yunkurawa ya yi da nufin tash,i ji ya yi ɗayan hannun nasa ya ƙi motsawa, hannun ya bi da kallo ganin shi ya yi a daure da sarƙa an kuma sawa sarkar kwaɗo,juyawa ya yi ya kalli kofar da a ka turo. Da sauri mutumin ya karaso gurinsa jiki na rawa ya ce "sannu Abokina ya jikin?" "Ka ganeni ? "Ya jero masa tambayoyin yana kallonsa . Zuba masa ido Barde ya yi, kamar wanda yake son ya gano wani abu akan fuskar tasa.Sai dai bai ce masa komai ba,bai kuma fasa kallonsa ba.Matsowa ya ƙara yi kusa dashi cikin tashin hankali ya ce"dan Allah ka ce wani abu,ni ne Ahmad fa ka ce ka gane ni dan Allah."Ya faɗa yana haɗe hannayensa guri ɗaya alamar roƙo. Bakinsa ya bi da kallo ba tare da ya yi maganar ba."Wai ko ka daina magana ne?Toh ko alama ce ka yi min dan Allah." Kau da kansa ya yi daga kallon Ahmad. A hankali ya ce " Abokina ɗan halak nake ba na manta hallaci." Rugume shi ya yi yana dariya ba tare da ya damu da datin da yake jikinsa ba. "Barka da dawowa Abokina" Sun ɗan jima rungume da juna kafin Barde ya ɗago ya ce, " Ina ne nan Abokina? Nasan tabbas ka na da masaniya a kan daukoni da a ka yi miyasa dole sai ita ? " "Gidana ne" Ya faɗa yana kallonsa, ba tare da ya ba sa amsar tambayarsa ta biyu ba. Jinjina kai ya yi ya ce" ka yi aure ne ?" "Eh shekara biyu kenan" Jinjina kamsa ya yi ya ce "kwance ni " Toh ya ce sannan ya kwance shi. Miƙa a yi ya na ambaton sunan Allah, jingina ya yi da bango ya lumshe idonsa . Banɗaki Ahmad ya shiga ya ɗan ji ma a ciki sannan ya fito, kallon Barde ya yi ya ce " Barde na haɗa maka ruwan wanka, ka tashi ka yi ."Bai ce komai ba ya tashi ya shiga banɗakin . Abakacin ya yi wankan sai kawai ya yi alwala ya fito. Tsayawa Ahmad ya yi yana kallonsa "ina wankan ? "Bai bashi amsa ba sai ma tambayar daya jefo masa. "Kwana nawa na yi a nan ? Ina ne gabas? " Dafe kai Ahmad ya yi yana tuna halayar Barde. Gabas din ya nuna masa ,sannan ya ce "yau kwanan ka biyu. Bai ce komai ba ya juya ya ta da sallah . Zama ya yi ya na jiran ya idar da sallar. Bayan ya gama biyan duka salolin da ake binsa, bai ta shi ba ya cigaba da tazbihi da ya tsuun hannunsa. Ya kai mintuna shabiyar yana tazbihinsa.Ganin ba shi da niyyar gamawa ya sa ya ce masa "Barde jiran ka fa nake." Juyowa ya yi ya kallesa da alamar tanbaya a idonsa . "Wankan " Ahmad ya faɗa ya na kallonsa . Banza ya yi da shi ya cigaba da abin da ya ke yi . Lallaɓa sa Ahmad ya shiga yi amma ya yi burus da shi .Da kyar ya samu ya yarda zai yi wankan, sai da ya sake haɗa masa ruwan . Miƙewa ya yi ya na harararsa ya shige ban ɗaki. Wankan ya yi da ya manta rabon shi da ya yi irinsa, dan bai san adadin saɓin da ya yi wa jikinsa ba . Ko da ya fito bai sami Ahmad a ɗakin ba amma ya ga kaya a kan gadon. Sai da ya gama shirya wa tsaf, kafin Ahmad ya sake shigowa wata matshiyar budurwa tana take masa ba ya .Mikewa Barde ya yi da sauri, " fita!" ya faɗa a zafafe yana zazzaro mata ido.Girgiza masa kai tashiga yi hawaye na cika idonta. "Na ce ki fita "ya kara maimaitawa a tsawace . Dan Allah ka saurare ni koda sau...." Kanta ya yo cikin kururuwa ya ce "zan kasheta....! " "sai na kashe ta ...!" Da sauri Ahmad ya rirrikesa iya karfinsa, amma sai kokarin kwacewa ya ke yi . Da gudu ta fita daga ɗakim ta na toshe bakinta da kuka ke shirin kubce mata..Ganin ta fita kuma Ahmad yaƙi ba shi damar riketa yasa faɗan ya ko ma tsakanin sa da shi . Wani irin naushi Barde ya kai masa da iya karfinsa aikuwa ya same shi a ciki ,ji ya yi cikin nasa ya kulle ba shiri ya sakesa ya durkushe ya rike cikinsa yana murƙususu . Hanyar fita ya nufa amma ya rasa ganeta, saboda yadda kansa yake juyawa wata iriyar hayaniya yake ji a kan nasa. Durƙushrewa ya yi ya rike kansa iya karfinsa ya shiga kwarara ihu ji yake kansa kamar zai fashe. Babu shiri Ahmad ya rarrafo inda yake "Abokina " "Abokina" ya faɗa yana girgiza shi ."Sai na kashe ta..!" " Saina kashesu..!" "zan kashe ta" Shi kawai yake maimaitawa . A hankali sautin kururuwar sa take raguwa ,rungume sa ya yi hawaye yana wanke masa fuska wani irin tausayinsa ne ke ratsa zuciyar sa. *** Maitama District, Abuja Municipal Area Council (AMAC), Federal Capital Territory (FCT) Abuja. Tun kafin ya ƙarasa gate din gidan u yake ta danna uban hon, saboda ya tsani jira.Ya ɗan jima kafin Mai gadin ya fito da gudu daga banɗaki ya buɗe masa . "Oga sir ka yi hakuri na dan zagaya ne, small Alhaji ." Ya fada cikin gurbataciyar hausarsa yana jinjina masa hannu alamar girmamawa. Ko kallo bai ishe shi ba, dan ba ya yanayi mai dadi,kuma gashi ya ɓata masa lokaci a bakin kofa. Parking ya yi sannan ya fito.Kiciɓus ya yi da Minal tana kokarin giftashi . " Ina zaki ?" Ya faɗa ya na bin ta da kallo. " Birthday din bestyna ake yi yau,wai ba ka sani ba ?Ta karasa ta na ɗan murmushi .Wani banzan kallo ya bita da shi,kafin ya ce da wannan banzar shigar zaki fita?" Bin jikin ta tayi da kallo . Wata Shegeyar riga ce a jikinta,wadda ta bi jikinta sosai iya gwiwa. Da wani ta kalmi me mugun tsini a ƙafarta, kanta ko arziƙin dan kwali babu sai gashinta da ya sha gyara . Turo baki ta ɗanyi. " toh me shigar nan ta yi nace mak....Wuce kibar gurinan tun kafin na kakkaryaki" Ta tsaya tana turo baki. Ransa ne ya sake ɓaci dama kuma a bacen yake . A hassaale ya yunkura da nufin kamo ta ai kuwa da gudu ta koma falon tana ƙwala kiran "Mommy.....!" "Mommy.." Da sauri Hajiya Saudat ta fito "lafiya" Da gudu minal ta koma bayanta "mai ya faru ne wai?" Ta kara tambaya tana kallon Hammad daya biyo bayan ta. "Wai mene ne ina ta muku magana duk kun yi shiru ta faɗa fuska ba annuri. " A harzuƙe ya ce "Mommy kalli shigar jikin yarinyar nan wai a haka za ta fita saboda rashin tarbiyya." janyo Minal Mommy ta yi gaban ta tana karewa shigar jikin ta kallo. "Me shigarta ta yi na ga mota za ta shiga ba wani a buba ." "Haba Mommy dan Allah kalleta fa kamar ba ƴar musulmai ba,kuma idan a mota za ta je ai ba a motar za ta zauna ba." "Ni fa gaskiya ba za a takuramin ba,a hanani yin abin da nake so tunda nima ban hana kowa ya yi rayuwarsa yadda ya ke so ba." Ta faɗa tana murguɗa masa baki. Kallon ta kawai ya ke yi, wani ƙululun bakin ciki ya tokare masa maƙoshi, saboda ya san Mommy ba za ta taɓa bari ya dake ta ba .Tariq daya fito daga kichin hannun sa rike da kofin tae ne ,ya ce "Ni fa Dr wannan halayar taka ta na bani mamaki, kabar ta ta yi rayuwarta yadda take so,tana da ƴancin yin rayuwar da take so,ba ka da ikon da zaka takure ta ko a dokan ce, kuma ma me shigarta ta yi haba ." Kallon su kawai yake idon sa har wani duhu-duhu yake yi masa. Ya kwaso bacin rai da tashin hankali daga gurin aiki yazo gida dan ya huta amma sai kara linkamasa bacin ran suka yi . Abin da yake faruwa a cikin wannan birkitacen a halin na daure masa kai . Sun dauki rayuwar turawa abun koyi da sha'awa. Kwata-kwata ba su daura yaransu a kan tarbiyar islama ba. Kallon Minal ya yi,ya yi ƙwafa . Juyawa ya yi ya nufi bangaren sa kansa na masa wa ni irin ciwo .Yana shiga ɗakin nasa ya wuce bandaki ya sakarwa kansa ruwa ko ze samu sa'ida . Tariq kuwa yana ganin ya shige ya kalli Minal ya ce "wuce ki tafi inda zaki Minal, mutum sai shegen shishshigi" Ya faɗa ya na neman guri ya zauna ya cigaba da shan shayinsa . Murmushi ta yi ta ce "Mommy sai na dawo" Babu ko alamar damuwa a fuskar mahaifiyarta ta ce mata "Ok Auta kar ki yo dare sosai" Toh ta ce,ta sa kai ta yi ficewar ta. Ya na fitowa daga wankan ko mai bai shafa ba, ya nemo kaya marasa dauyi ya saka ya sha magani ya nemi guri ya kwanta. Amma damuwa ta hana bacin zuwa sai juye-juye ya ke yi. Ganin barcin ya ƙi zuwa ne ya sa ya janyo wayarsa ya kamo hoton kunaman nan. Zuba masa ido ya yi sosai ya kare masa kallo gani yake kamar ya sansa a wani gurin na musamman ,amma ya kasa tuna gurin , ganin idan ya takura wa kansa da tunani, zai'iya samun matsala ya sa ya ajiye wayar. Alwala ya dauro ya tada sallar nafila.Bayan ya idar ya janyo Alƙur'ani ya daɗe yana sosai yana addu'oin kafin ya shafa . yana shirin miƙewa ya ji wata iriyar ƙara mara daɗin sauraro. Da sauri ya tashi yana kokarin fita daga ɗakin saboda ya duba . Kafin ya karasa wutar gidan ta dauke ji ya yi kamar ana wulgawa ta gefensa . Ihun Tariq ya ji a firgice ya kwala kiran sunan da wata kalar murya me amo Ayeeshat Kissar ✍🏼✍🏼 WANE NE SHI ? Na Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION YOTA 019 Bismillahir-Rahmanir-Rahim Page 5 ___ 6 Da gudu ya tunkari ɗakin,duk da tsananin duhun da yake gani . Yana ƙarasawa ya sa ƙafa ya harbi kofar ɗakin da take a rufe. Kamar hadin baki sai wutar gidan ta dawo . A tsakiyar gado ya same shi jikinsa sai faman rawa yake. Ririkesa ya yi ya na tofa masa addu'a . "help me.." ""Help me, please" Ya faɗa cikin fita hayyaci. "Tariq !!Tariq...! Kanatsu mana " Hammad ya faɗa da ɗan karfi yana rungume sa. Kanƙamesa ya yi sosai. Yana jin yadda zuciyarsa take wani irin bugu. Kara bakinsa ya yi saitin kunnensa , ya na bubuga bayansa ya ce "Zip your lips mana " lamo ya yi saifaman sauke a jiyar zuciya yake. Ɗagosa ya yi ya ce"Mai ya faru " Ɗagowa ya,yi fuska sharkaf da hawaye , "tsoro nake ji ,dan Allah ka taimaka min" A ɗan hasale ya ce"Wani irin taimako zan yi maka alhalin ban san mai ya faru ba?" Baki ya buɗe da shirin gaya masa abin da ya faru , sai dai abu ya faskara, saboda yadda ya ji an shaƙe masa wuya kamar za a rabashi da duniya. Ido Hammad ya zuba masa yana kallon sa, shi dai shegen tsoron nan nasa yana bashi mamaki, sai rashin jin tsiya gashi da shegen tsoro. Ɗakin ya bi da kallo rabon daya shigo harya manta. Shisha ya gani ta yi nata gurin da alama ita yake shama . Da sauri Mommy da Daddy suka ƙaraso suna tambayar lafiya meyasa meshi "gashi ku tambaye shi"Ya faɗa ya na harararsa ." "Bai iya addu a ba sai ihun tsiya, duk ya bi ya tadawa mutane hankali." Ya furta a kasan ransa kuwa tausayinsa yake ji . Juyawa ya yi ya nufi hanyar fita. Ai kuwa Tariq ya taso ya biyo bayansa . juyowa ya yi ya kallesa ya ce "meye ? " "Tsoro nake ji " Tsaki ya ja, ya ci gaba da tafiyarsa. "Mommy dan Allah ku saka baki tsoro na ke ji ." "Hammad ka tausaya masa mana dan Allah " Daddy ya faɗa yama kallon Tariq cike da tausayawa. Jinjina kansa kawai ya yi ya fice.Yana shiga dakinsa ya yi wuff ya datse kofar. Daga ciki ya ce masa. "Iskancinka ya ƙwace ka dan ubanka,na barka ka yi rayuwarka yadda ka ke so." Bubbuga kofar ya shiga yi yana yi masa magiya, saboda wani irin a zababen tsoran da yake ratsashi. Ammaa Hammad ya yi burus ya ƙyale shi. Zama ya yi a bakin kofar ya dasa masa kuka, ya kai mintuna talatin a gurin,kuma ya ki tafiya. A hasale ya buɗe masa kofar ba tare da ya ce masa komai ba. Da sauri Tariq ya tashi ya shiga yana sauke a jiyar zuciya. Ya san ko wani abun ne ya faru Dr zai yi masa addu'a,shi kuma bai ma iya wata addu'ar kirki ba. Mommy da Daddy kuma a can suka barsu sai juyawa sukai suka koma sashin su. ★★★ Around (1:30) am . Motarta take tukawa hankali kwance, tana ganin kiiran Mommy amma ta share saboda ta san faɗa za ta yi mata. A gefen wata bola ta yi parking din motar. Fitowa ta yi jikinta sanye da kayan ɗazu. Ta taka ta nufi inda bolar take tana toshe hanci , amma hakan bai hanata karasawa can gefan bolar ba. Tsugunnawa ta yi ta ɗago ta, da alama jiranta take zaman yi bacci ya dauke ta. Ta na zaune ta haɗa kai da gwiwa. Ɗagowa ta yi ta buge maata hannu alamar ta yi fushi. Kama kunnenta ta yi ta ce "I'm so sorry " ta faɗa tana miƙamata kular hannunta. Tun ɗazu ya kamata a ce ta zo amma shaf ta manta. Amsar kular matar ta yi ta kama jujjuyata tana dariya. Mota ta koma ta dauko ruwa ta dawo. Hannunta ta kama ta wanke mata, sannan ta ɓuɗe mata kular. Da sauri da sauri take ci wani yana zubowa. Tsayawa Minal ta yi tana kallonta, tuni hawaye ya cika idonta. Ruwa ta miƙa mata ganin abincin na kokarin shaƙeta. Amsa ta yi a bakacin ta sha kai tsaye , sai ta juyeshi a cikin abincin sannan ta kafa kular tana shan ruwan a haka. Ta na gamawa ta yi jifa da kular ta nemi guri ta yi kwanciyar ta . ta ɗan daɗe ta na kallonta kafin ta kama hanyar komawa inda motarta take. Tana shiga ta kifa kanta saman Steering motar ta fashe da kuka,sai da ta yi kuka mai isarta,kafin ta kunna motar ta dau hanyar gida. Ta rasa me yasa take kauna da tausayin matar nan. Ba ta taɓa tausayin wani abu kamar yadda take tausayin ta ba. Ita rayuwarta take yadda take so yadda taga dama. Ba tun yau take kawo mata abinci ba,gashi juyin duniyar nan ta yi tabar wajen bolar amma taƙi . Ta share hawayen daya gangaro mata. A hankali ta furta "ya Allah Ka kula da ita domin isar ka." ★★★ Kaduna state. Sahaba model college secondary school Wasu haɗaɗun zaratan motoci ne, suka faka a bakin kofar makarantar. Da gudu wasu murdaɗun guards suka fito hannunsu rike da bindugu,suka buɗe kofar farar motar dake tsakiyar motocin. A ƙalla an kai mintuna biyu, kafin Mutumin ya fito daga motar. Wani hadaɗen datijone, mai matukar kwarjini da haiba,wanda ba zai gaza shekaru saba'in da biyu a duniya ba. Ka na ganin sa kaga kamili . Tun kafin ya fito daga motar tuni malaman makarantar sun karaso , domin tarbarshi. Babu wulakanci ko nuna shi wani ne, haka ya ringa mika musu hannu su na gaisawa. Hatta da mai gadin Makarantar sai da su ka gaisa kafin malaman makarantar su musu jagora suka shiga cikin makarantar. A gaggauce aka tara daliban makarantar domin nuna girmamawa a gareshi . Gyaran murya shugaban makarantar ya yi. sannan ya fara magana cikin harshen turanci ,duk da bawani jin yaren suke ba. Sallama ya fara yi kafin kai tsaye ya wuce abin da yasa aka tara su . Cikin madaukakin farin ciki ya shiga gabatar da wannan datijon "Wannan bako ba kowa ba ne face datijon arziki .ALHAJI JUNAID ALI.Baya goya marayu. Shahararen dan kasuwa mai jinkan talakawa da tausayinsu , wanda sanadiyar wannan halin nashi ne Allah ya jefo mana shi wannan makarantar tamu me albarka ,domin ya share mana hawayenmu dana iyayenku". Risinawa shugaban makarantar ya yi ya miƙa masa abun maganar,saboda muryarsa bata fita da kyau. "Baya goya marayu harda ma masu iyaye uban marasa galihu da masu galihun ma. " Ya farucin ya jinjina masa hanayyensa. Cike da son ya burge sa. Gyaran murya Alh Junaid ya yi. A hankali ya yi wa tarin daliban sallama. Ya cigaba da magana da cewa "Yaku ƴaƴana ko na ce jikokina. Ina me baku shawara da ku ji tsoran Allah a duk abin da zaku yi,ku tsaya kai da fata wajen bauta masa da gaskiya kada ku haɗa sa da kowa domin shikaɗai ne. Ina kara shawartar ku da ku tsaya ku yi ilimi domin shine gishirin zaman duniya. A zamanin nan idan ba ka da ilimi ba a daukar ka mutum mai daraja,ku nemi ililmi iyakacin iyawarku, ka da ku bari a bar ku a baya,ka da ku ga kamar ba za ku iya ba, tabbas za ku iya." " Ba iya ilimin boko ba, ku haɗa dana addini. Domin ilimin boko shikaɗai yana iya hallaakar da musulmi .Kada ku kwanta ku ce kuna so ku zama kaza ku tashi ku yi aiki tukuru. Ka da ku yi wasa da damar da Allah ya baku zaku yi alfahari da kanku a gaba. Ilimi shine ginshikin zaman duniya, ilimi shine rayuwa, ku zama masu dagiya, ka da ku zama daga cikin kasalalu, ko kuma marasa manufa a rayuwa." " Ku yi rayuwa da buri da kuma manufa, kar ku gina burin ku akan tafarkin bata ." "Kada ku hangi abun wani, ku hangi naku. Ku zama jajirtattu kuma hazikai.Babu wanda aka haifa da iyawa, kowa sai da ya zo duniya ya koya har ya iya, domin haka babu abin da zai gagara sai wanda Allah bai nufa ba. Ku nemi ilimi kuma ku nemi kudi,ku dage da izinin Allah burin ku zai ci ka. Ku fawwala wa Allah lamuranku, kuji a ranku komai na Allah ne. Ina muku fatan alkairi da fatan gamawa lafiya a rayuwa, da kuma sa a cikin ta. Bissallam " Ya kai aya yana mikawa shugaban makarantar abun maganar ya koma ya zauna. Rap..! Rap ..! Kawai shine ke tashi na tafi tako ina . Tuni baki sun iso saboda zuwan nasa duk da cewa ba a shelanta zai zo ba,amma hakan be hana makarantar cika ba. Haka akai ta fitowa ana yi masa godiya da taya murna ga makarantar. Sosai jama'a suka taru kafin ya tafi. Dahike lokacin ana gab da zana jarabawar NECO/WAEC. Nan ya musu alkawarin duk wanda yaci jarabawar zai dauki nauyin karatunsa har ya gama. Sannan duk wani guri daya lalace a makarantar za a gyara musu a yi musu sabbabin bancina da kayan karatu . Ba karamin alkairi malaman makarantar suka samu ba, sakamakon zuwan sa. Sosai zuwan Alhaji Junaid Ali ya zamewa dalibai Alkairi saboda dayawa iyayen su ba su da halin ɗaukar dauyin karatunsu.. ★★★ Da sallama ya turo kofarr ɗakin ya shiga. A zaune ya same shi, ya ɗaga kansa sama yana kallon silik. "Abokina ya jikin?" Bai kalle saba kuma bai amsa ba. "Barde magana fa na ke yi" "Ba sauki " Ya faɗa fuskar nan babu alamar wasa . Dariya Ahmad ya yi ya ce " A'a yasin da sauki Alhamdulilah ,a dinga godewa Allah dai,ka yi wankan ne?" " Eh " Ya ce yana kokarin kwanciya. "Tashi mu je mu ci abinci ,a aske wannan sumar " Na koshi." " Me kaci? " Ahmad ya tambaya yana dan hararar sa . Banza ya yi bai kulasa ba, sai ma gyara kwanciyarsa da ya yi. "Ko na kawo maka nan ne ?" Daga kwancen daya ke ya ce, "bani wayar ka ." Shiru Ahmad ya yi kamar ba zai ba shi ba, sai kuma ya mika masa . Fita ya yi bai wani jima ba ya dawo, hannusa dauke da plet din abinci. "Yauwa tashi ka ci ." "Ba ka da kunne hala? Na ce bazan ci ba " A ɗan fusace Ahmad ya ce "wai kai miyasa ba a yi maka gwaninta ne? Duk yadda na ke son naga na burgeka sai ka nuna min ban kai ba." Sai kuma ya sassauta muryarsa ya ce "dan Allah ka ci Aki...!" Ɗagowa ya yi da sauri ,ya zubawa Ahmad Jajayen idanunsa. Hakan ya sa Ahmad katse maganar da ya yi niyyar yi. Hannunsa ya miƙa a hankali ya karɓi abincin ya hau cusawa cikinsa badan ya na so ba. Miƙewa Barde ya yi bayan ya gama cin abincin, ya ce "muje " "Ina?" "Gurin askin " Mikewa Ahmad ya yi ya nufi hanyar fita Barde na take masa baya. Tsakar gidan suka fita. Ya tsaya yana karewa tsakar gidan kallo. Madaidaiciya ce babu wani tarkace,sai Mota guda daya daga gefan dakim da suka fito. Suna kokarin shiga motar sai ga Safna. Da sauri ta karaso imda su ke. Tsayawa Ahmad ya yi suna gaisawa . "kibar gurin nan" Barde ya faɗa yana nuna mata hanya. Jiki a sanyaye ta ce " dan Allah ka saurareni ko da sau ɗaya ne " Ta furta tana haɗe hannuwanta biyu alamar roƙo. "Ah...Ahm...! Ahmad zan kashe ta! Ka ce ta bar gurin nan na ce " Ya faɗa cikin hargagi . Da fa kafadarsa ya yi a taushashe ya ce "Abokina ka saurare ta dan Allah ka ji abin da za ta ce, ba kamar yanda kake zato ban... !" "Na tsane ta !" Ya fada yana yowa kanta. Zabura Ahmad ya yi ya rikeshi,saboda ya san idan ya riƙe ta, zai'iya ilatata ne. "Ki tafi Safna za mu yi magana" Bata motsa daga inda take ba, sai ma gyara tsayuwar ta da ta yi. Ta na kallon sa,hawaye kuwa sai aikin su suke. A hankali ta ce" duk abin da za ka ce ko za ka min,na san na cancanci fiye da haka. Amma ina roƙonka ka bani dama koda sau ɗaya ne na maka bayani" Cikin tashin hankli Ahmad ya ce "No Safna ki sani wannan ba Bardem da ba ne,komai ya na iya faruwa ,idan ki ka cigaba da tsayuwa anan" Kokarin fita yake daga hayyacinsa,idan ya ga fuskarta. Abubuwa da yawa yake tunawa. So yake ya hana kansa tunawa amma abu ya faskara. Wani irin ihu ya kwarma ,ya yunkura ya maka Ahmad a jikin motar ,sannan ya yi kanta ganin ya yo gurim da take ne , ya sa ta zabura tana kokarin guduwa . Sai dai kash,kafin ta yi wani kyakykyawan motsi tuni ya damƙo ta. Haɗa kanta ya yi da bango iya karfinsa. Wata irinyar gigitaciyar kara ta yi,saboda jin azabeben zafi na ratsa kwakwalwarta . Shaƙe ta ya yi da karfin gaske ,kafin ka ce me, idanun ta sunyo waje kamar zasu faɗo kasa . Jin da ta yi ta fara jiyo kamshin mutuwa ne yasa ta fara kokari kwacewa, amma ko motsa hannun sa ta kasa yi . Da kyar Ahmad ya iya tashi, saboda kansa ya bugu sosai. Hankali tashe ya yo kansu ya na kokarin kwace ta amma abu ya gagara. Don ba ƙaramin ruko Barde ya mata ba.Ganin dai da gaske idan ya yi wasa kisa za 'ayi, yasa ya tattaro dukkan karfinsa ya daki hannun da ya shake ta. Babu shiri ya sake ta ,saboda ji ya yi kamar hannun ya karye. Ita kuwa ba ta ma san duniyar da take ba dan ta daɗe da sumewa . Ai kuwa ya dawo kansa a haukace yana wani gurnani, jijiyoyin kansa sun wani miƙe tsaye, idanunsa kamar garwashin wuta . Wani irin jiri ne yake ɗibar sa. Amma hakan be hana shi tunkarar inda Ahmad yake ba. Tsayawa Ahmad ya yi ya na jiran karasowar sa, don ya ga alamar gudu ba zai yi mai ba. Toro kofar gidan a kai. Ta Shigo da sallama a bakinta. Fararen kaya ne a jikin ta, kalar na malam jinya, wato nurse. Da alama ita ma ɗaya daga cikinsu ce. Cili ta yi da jakar hannun ta kayan ciki suka watse. Da gudu ta karaso inda Ahmad ya ke,ganin yadda jini yake zuba a kansa. Kwata-kwata ba ta lura da Barde ba ,bare ta ankara da ba a cikin hayyacinsa yake ba. . Ya na isowa bai yi wata-wata ba, ita ma ya shake ta,sannan ya hada kanta da jikin gini. Idan hankalinsa ya gushe yana daukar duk wanda ya yi masa katanga da cikar burinsa a makiyin sa ne kuma abun ya farauci rayuwar sa ce . Jiri ne ya ɗibe shi ya durkushe a gurin,ya rike kansa da karfi. Kalamanta ne suke maimaito kansu. Alƙawarin daya yi mata yake tunawa komai ya kasa goguwa "A'a....!A'a....! " Ya fada da karfi yana gwara kansa jikin bango . A hankali ya sulale ya faɗi a gurin, yana zubar da jini. WANE NE SHI ? By Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION YOTA 019 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Page 7____8 A gigice Ahmad ya yi kan matarsa, tuni ya manta da wani ciwo ko jiri. Zubewa ya yi a gabanta,ya shiga jijigata "Hafsat..!" "Hafsat..! Ki tashi dan Allah. " Ya Miƙe tsaye ,ya yi inda Safna take. "Safna..! Safna...! Dan Allah ki tashi" Da gudu ya koma gurin da Barde yake kwance, babu alamar rai a jikinsa. Jijjigashi ya shiga yi shima. "Abokina...! Abokina... Dan uwana,Barde dan Allah ku tashi ,karku barni ni ka ɗai ba zan iya ba. Ka da ku tafi kubar ni" Da sauri ya miƙe kamar an tsikaresa. karamar wayarsa ya ɗauko,wasu lambobi ya daddanna ya kara a kunnensa. Ana ɗaga wayar bai tsaya yiin sallama ba. Ya ce "Salim dan Allah ka zo gidana yanzu akwai matsala,Ka zo da kayan aiki. Ka yi sauri dan Allah." Ya Kashe wayar, hawayen da ya ganganro masa ya share , yace "Ya rabbi ka kawo mana dauki ya mai iko da komai da kowa ." ★★★ Hammad Sannu a hankalo yake takowa jikinsa sanye da riga da wando na shadda ash, ya daura hula silba . Ya rataya ( Lab coat) ɗinsa a saman kafaɗarsa. Sosai ya yi kyau, babu abin da ke tashi a jikimsa sai kamshin turare. karasawa cikin parlourn ya yi fuskar nan ba annuri. Guri ya nema ya zauna akan kujera. Yana sane bai karasa kan dining din ba, duk da yunwa ya ke ji, saboda ya hango Minal, kuma ya san indai ya karasa sai ta masa magana, gashi haushinta yake ji tun abin da ta yi mai jiya. Da sauri wata mata ta zo ta zube a gabansa . Ciike da ladabi take tambayar mai za a kawo masa,sai da ya gama shan kamshinsa, sannan ya gaya mata.Ɗan kishingiɗa ya yi yana danna wayarsa. "Oh god ! Dr ka yi kyau wallahi " Ta fada daga tsayen da take . Ɗagowa ya yi yana harararta, amma ita ko a jikinta. Hoto ma kawai take faman yi masa. "Minal !" Kallon shi ta yi,ta sake sakar masa murmushi. Dawowa ta yi kan kujerar da yake zaune. "See it" Ta fada tana nuna masa hotunan da ta yi masa . Badan yana so ba haka yake kalla ,saboda ya san baza ta barshi ya huta ba. Gashi kansa har yanzu ciwo yake. Ta na cikin nuna masa su kaji motsi daga bayan su. Juyawa suka yi a tare . Tariq ne ya fito, ya yafo ubba bargo, sai faman jan kasa ya ke yi. Juyawa Hammad ya yi dariya tana son kubce masa saboda tuna sambatun da ya yi masa jiya. "Me ye haka?" Minal ta faɗa tana kallon sa. Zabura ya yi yana kallon bayansa . Hammad ta kalla ta ce "Dr wai mai ya same shi ne?" "Tambaye shi mana" Ya faɗa ya na shan shayinsa kamar bai san da zaman saba . Mikewa ta yi ta karasa inda yake ta janyosa har kan kujera. Zama ya yi sai faman zare idanu yake. Kallon Hammad ya yi ya ce "good Morning yaya hammad " Zaro ido Hammad ya yi yana kallon sa, har yana shirin ƙwarewa, saboda ya manta rabon da ya gaishe shi ma. Dariya ce ta kwace masa sosai ya dara. Ita kuwa Minal kallom Tariq ta yi sannan ta ce "wai meyafaru ne ?" Kallon ta ya yi, tuni idunsa sun cika da hawaye, domin shi dai a rayuwarsa Allah ya daura masa masifafen tsoro. ya ce " jiya ba ki ji karata ba ?" Ya mutsa fuska ta yi ta ce "kasan dauyin bacci na ,ban ji ba, kuma dama ban dawo da wuri ba, ina zuwa na kwanta.,sai da safe ma na yi sallar isha'i " "Ba ki yi sallah isha 'i ba sai da safe?" Hammad ya tambaya yana kallon ta, cike da mamaki duk da ya san zata aikata wanda ya fi wannan ma. Turo baki ta yi ta ce "toh bacci nake ji koda na dawo, ka san kuma ita salla anfi son a yi ta cikin natsuwa" Buɗe baki ya yi har zai yi magana, sai ya yi shiru kawai yana kallon ta. "Sallar ce ba ki yi ba sai da safe, wato kin je birthday party kin dawo,kuma kin gaji. " "Ai na yi istigfari da na gama." Ta bashi amsar maganar zucin da yake yi ,bai san ma ta fito ba. Ko a jikin ta,wai an zunguri kakkausa. Labari ma ta cigaba da bawa Tariq . Shi dai Tariq duk a tsorace ya ke,har yanzu ya kasa sakin jikinsa, sai faman raɓe-raɓe ya ke. Shi kaɗai ya san abin da ya gani jiya . Miƙewa Minal ta yi ta ce "bari na je gurin Daddy, tun jiya da safe bangansa ba" Kallon ta Hammad ya yi , shima yana mikewa " Wai ke ba ki da hankali ne ?A haka za ki je gurin su Daddyn" ?Bim jikimta ta yi da kallo. T-shirt ce a jikin ta fara, sai wandon da ya wuce gwiwa kaɗan kofi. kanta ko arzikin hula bai samu ba. Kallon sa ta yi, ta yi masa murmushi, sannan ta ce " ba fa fita zan yi ba, wajen Daddy kawai zan je,kuma ma ni ban ga aibun shigarnan ba Dr " Wata muguwar harara ya watsa mata. Ta Basar ,kamar ba ta gani ba. Wucewar ta ma ta yi ,ta daukowa Tariq (break fast)ɗin shi . Ta na a jiye masa ta nufi hanyar sashin Daddy. Dafe kansa ya yi dama ya san hakan zata faru, ya kamata ace zuwa yanzu ya fita daga sabgar yarinyar nan, akan wannan shigar da take yi. Amma abu ya gagara indai zai ga ta yi banzar shiga bakinsa ba ya iya yin shiru. Bin bayan ta ya yi da kallo , ya rufa mata mata baya, dom shima yau bai ga momyy ba kuma yasan tana can sashin . Da sallama ya shiga ya nemi guri ya zauna. Ita kuwa Minal babu sallama kawai fadawa ta yi. Tana shiga ta yi tsalle ta ɗane bayan Momyy ta na dariya. "Barka da safiya rabin ran." "Yauwa barka dai Auta, kin tashi lafiya?" "Fine Mommyna, ina Daddy? " "Bai sauko ba tukuna" Tashi ta yi ta nufi hanyar bedroom dinsa. Dafe kansa ya yi ,a hankali ya ce "wannan yarinyar kuwa za ta yi hankali ?" Murmushi Mommy ta yi sannan ta ce "za ta yi mana,kasan har yanzu yarinya ce " "A hakan Momyy ? Minal fa ta san abin da take yi , kullum ke da Daddy sai ku ringa cewa yarinya ce. Toh yaushe za girma? Ko jiya ba ta yi sallar i sha'i ba, sai da safen nan, haba Mommy" "Lokaci yana nan zuwa da za ta yii " Mommy ta faɗa babu alamar damuwa a fuskarta , Sai ma dan danna wayarta da take yi. "Hmmmm" Kawai ya ce .Sai kuma ya ce "Mommy ina kwana ? " ".likita bokan turai,ba kusan a mutu, ba kusan a samu lafya. Ka tashi lafiya" "Alhmdulilah Mommyna, da fatan kin wayi gari cikin koshin lafiya?" Ƴar dariya ta yi ta ce "Lafiya kalau Alhamdulilah .Ya jikin Tariq ?" Ya mutse fuska ya ɗan yi sannan ya ce "Ai kalau yake,kawai tsoro ne yake sawa kansa" "Yanzu yana ina ?" "Gani Mommy" Tariq ya faɗa daga tsayenn da yake a bakin kofa. Juyawa Hammad ya yi yana kallon sa,saboda yazaci yana can , ya na karyawa . Harara ya watsa mai, yace "wai kai ba ka da hankali ne? ba za ka je ka a jiye bargon nan ba?" A jiye bargon ya yi a hankali, kamar wanda zai kare shi daga wani abu. "Kai komai sai an fada maka? Toh dauke shi daga kasa " Tsugunnawa ya yi ya dauke, ya mai da shi kan kujera.sannan ya zo ya zauna a gefan Mommy. A jiyar zuciya Momyy ta sauke, mamaki ya hanata magana. Ta san Tariq,ta san rashin kunyar sa, ta san wane ne shi. Amma yau ladabi kawai yake zubawa . Dariya ta yi a zuciyarta ta ce "idan ka ji ana ki gudu, toh tabbas sa gudu ne bai zo ba." "Wai ni Tariq mai ya same ka jiya ?" Shagwabe fuska ya yi idonsa suka ciko da hawaye. Ya ce "Mommy wallahi jiya ba karamin tsoro na ji ba, har yanzu zuciyata ba ta daina bugawa ba. " Gyara zama Momyy ta yi ta ce"ba ni labari,mai ya fara?" Ɗan shiru ya yi kamar zai gaya mata,sai kuma ya tuna abin da ya ji jiya,da ya tashi faɗawa Hammad. Kara marairaicewa ya yi ya ce"Ni duk na manta komai,Kawai dai na ji tsoro sosai.Rarrashin shi Mommy ta shiga yi shi kuma ya cigaba da tabara,kamar yaro karami. Takaici ne ya cika Hammad a hasale ya tashi tsaye. "Amma kai dai Allah ya wadaran wannan dan iskan gemun ,geme- geme da kai, ka zauna kana mana kuka" "Kuma wallahi idan ba ka yi min shiru ba, yau baza ka kwana a dakina ba." "Sorry Dr, na hadiye Wallahi ." Babu shiri Hammad ya saki murmushi, yau shi yake juya Tariq yadda ya so." "Tariq " Mommy ta kira sunansa, a tausashe. Ɗogowa ya yi yana kallonta "ka yi Breakfast kuwa?" "Ban yi ba Mommy, amma na ƙoshi" Uhmmm kawai ta ce taciga ba da karyawar ta,kasancewar ba ta jira Dadday ba. Matsowa ya yi kusa da abincin,Sannu a hankali ya zura hannunsa ya fara ci. Kallon sa Mommy ta yi suka hada ido. K Ya kawar da kansa ya cigaba da cin abincinsa. Murmushi Mommy ta yi , ta ajiye cokalin hannun ta. Dama jira take ya fara ci . Dan gyaran murya Hammad ya yi ya ce"Ni fa na fara gajiya, na yi latti . Ina ga yarinyar nan ce ta tsare shi da surutu ,bari na je na gani . " Ya ce yana nufar hanyar badroom din Daddy. ★★★ Minal A hankali ta tura kofar ɗakin a buɗe ta jita. Wani murmushi ta saki, ta ce "Alhamdullah " Shiga ta karasa yi.A zaune ta hango shi a gefen gado,ya sunkuyar da kansa ƙasa,da alama wani abu yake kallo. Cikin sanɗa take takawa har ta isa bakin gadon, hawa ta yi a hankali har ta iso kusa dashi. Hanayeta ta saka ta rufe masa idanu . Zabura ya yi da sauri ya miƙe yana boye abin da yake kallo. Hannunta tabi da kallo, tana zazzaro ido, ruwa ta gani "hawaye" Ta fada tana kallon Daddy. Saukowa ta yi daga kan gadon da sauri . "Daddy mai aka yi maka? Waya ya taba ka?Meyasa ka kuka? Me ya sameka ka ke kuka?Me ka ke boye min ?" WANE NE SHI ? By Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION 019 Page 9 _,10 Bismillahir-Rahmanir-Rahim Shiru ya yi yana kallon ta. leka bayansa ta yi domin taga me ya ke boyewa. Duk kokarinsa na boyewa sai da ta fahimci mene ne.. "Daddy wannan hoton wa ye? " "Nagani " Ta fada ta na kokarin karbar hoton. Girrgiza kansa ya yi sannan ya ce "Auta karki damu ki je ina zuwa." "Haba Daddy kuka fa ka ke yi,ban taɓa ganin hawaye ya zubo daga idanunka ba sai yau,meyasa Daddy?" Gani ta yi ya bi inda ya tashi da ido. Da sauri ta juya ita ma.Ɗayan hoton ta gani, da sauri ta dauka ta hau dubawa. Su hudu ne a jikin hoton, hoton na da ne sosai. Ita dai Daddy kawai ta iya ganewa a cikin su ,shima da ƙar saboda hoton na dane ya yi duhu sosai. "Su waye waƴenan Daddy?Meyasa kake kuka da ka ga hoton su?" Wani murmushin yaƙe ya yi , sannan ya ce "su ɗin rayuwata ne " Ido ta zuba masa amamakance ta ce "kuma ban san su ba?"Ƴan uwan kane su ?" "Minal...!" Daddy ya kira sunanta da karfi. Ba ta amsa ba,ba kuma ta daima kallon sa ba. "Ki dai na yawan tambaya, kuma ki dai na tsananta bincike .Ba kowanne ne yake zamowa alkairi ba. Duk abin da ki ka gani ki barshi a inda ki ka ganshi.Ba lallai ɗaga shi daga gurin ya zama alkairi ba." "Toh Daddy in sha Allah , amma ba ka gaya min meyasa ka ke kuka ba!" "Auta yana daya daga cikin abin da na ce ki dai na. Yanzu ki saka aranki kamar ba ki taɓa ganin hoton nan ba, barantana har zuciyarki ta kawo miki wasu tambayoyi a kan sa kin ji ko?" Ɗan turo baki ta yi ta ce "gaskiya Daddy ba zan iya jin kamar banga hutunan nan ba. Kawai dai ka ce karna zurfafa bincike akai." 'Zan gayawa Mommy kuma" Zaro ido Daddy ya yi ,tsoro ya bayyana saman fuskarsa. A tausashe ya ce mu yi ciniki nawa zan biya a rufamin asiri " Ba shiri murmushi ya kwace mata,ɗan juya idonta ta yi. Ta ce "ehh toh bari na yi tunani." Guri ta samu ta zauna ta ɗaga kanta sama ta lumshe idonta. Ta kai minti daya kafin ta buɗe idon. Kallon Daddy ta yi daya zuba mata ido shima yana murmushi . Murmushi ta sakar masa ita ma, sannan ta miƙe " yauwa Daddy a samu matasa guda biyar , kamar ni ko waƴen da suka fini, masu karamin karfi sai ka dauki nauyin karatunsu ko kuma ka basu jari .x Murmushin da yake yi ne ya kara faɗaɗa. Allah ya zubawa Minal tausayin na kasa da ita ,da son a taimaka musu. Shiyasa yake jin ta har cikin ransa. "Daddyy..! Ka yi shiru " "Toh Minal shikenan, ko kuma akwai wani abin da ki ke so? Ku ma wannan ai aikina ne ki faɗi wani abun daban." "Daddy wannan ɗin ka yi shi da nufin ni na yi idan kudin sunyi saura akai gidan marayu." "Aminatun Daddy, kuma Auta a taba ki aka sa bacci mai daɗi, yar Daddy da Mommy" Rufe idonta ta yi da tafukan hanayenta,ta na dariya."Abar yabon haka kar kaina ya yi nauyi ." Dariya Daddy ya yi shima ya girgiza kansa. Abin da ya tohkare masa kirji ya faɗa. A fili ya ce "Allah na gedo maka daka azurtani da Minal, Allah ya miki albarka. Sabuwar mota zan siya miki in sha Allah." Tsalle ta daka ta ɗane bayansa tana dariya, ba karamin farinciki ta shiga ba.Amma Abin mamaki ba ta yi masa godiya ba,hakan kuma bai dame shi ba. Turo kofar ɗakin Hammad ya yi ya shigo da sallama a bikinsa. Wata uwar harara ya watsawa Minal , daman ya san ita ce ta tsaidashi , ta barshi yana jira har lokaci ya kure masa . Murguɗa masa baki ta yi ta kara rike malinmalin din Daddy. "Doctor Hammad Mansur Iliyasu Mai Dollors." Dadddy ya fada yana miƙa masa hannu Dauke idonsa ya yi daga kan Minal, ya karasa shigowa cikin dakin.Hannu ya miƙawa Daddy shima "Barka da safiya ya Alhaj." Dariya Daddy ya yi sannan ya ce "yauwa barka dai ɗan gidan babansa." Sakin Daddy Minal ta yi ta zagaya tashiga cire musu zafafan pictures.Saboda ba karamin kyau ɗa da uban suka yi ba. "Wow..! Kun ga yadda ku ka yi kyau, ma sha Allah." "Daddy Wallahi ka aurar da wannan mutumin ya girma da yawa fa " "Gaskiya ne Aminatu ,kin kawo shawara mai kyau ,ina Hammad?" Daddy ya tambaya yana ɗan daure fuska. "Gani Daddynmu" "Yauwa ka nemo mata ko na nemo maka, Malam Dr" Lumfashi ya sauke yana yiwa Minal wani mugun kallo, ta ƙasan ido. Aran shi ya ce "Ni yanzu Daddy wane aure zan yi kuma? Wacce naso na aura ta tafi ta bar ni,yanzu aikin da na saka a gaba nake yi ,kuma shi nake da burin cinma ." "Dr ka yi shiru ka na tunani, idan baza ka iya gayawa Daddy.n ba, ka zo ka faɗa min a kunne, sai na faɗa masa. Ka san ni bana jin kunyar Daddy. Ko Daddy" Ta faɗa tana langwabar ta kanta gefe . "Wallahi Daddy ka shiga tsakanina da wannan yarinyar mara kunya,ko jikinta ya fada mata. Ke manya suna magana kema kina yi?" "Ah... ! Aha...! A'a A'a ina..! Mai ta yi maka da jikinta zai faɗa mata ?Toh wallahi ahir din ka, kuma ai gaskiya ta faɗa ka ke ta zaremin ido,shine ka koma kanta dan ta yi magana?. Toh li'ilafi ƙuraishi aniyar ka ta bika .Wuce muje Auta " Ya kyalle sa ya ce "gaskiya ce dole mu gaya maka." Ya ja hannuta suka wuce gaba. Girrgiza kai kawai Hammad ya yi, aransa ya ce "za ku ga ranar cewa da nake ku tsaya ku kula da tarbiyar ƴaƴanku, Allah ya kai mu dai . Bimsu ya yi a baya" Suna tafiya tana nunawa Daddy hotunan da ta yi musu. Shi kuma ya biye mata,sai faman santi yake yi . Ko da suka koma parlourn, tuni Mommy ta gama cin abincin jiran fitowar su take, don ita ma fita zata yi. Shikuma Tariq har yanzu bai gama ba, sai fama yake shida ya ce ya koshi. "Wai kai acici mala'ikun tauna, har yanzu ba ka gama ba ?" Ko ɗagowa bai yi ba bare ya tanka mata . "Hammad ka tattara duka ma'aikatan gidan nan, ɗan anjima police za su zo, za su yi bincike akan abin da ya faru jiya.Dan tun da sassafe na yi magana da su, komai zai tafi akan tsari ,saboda ko ni ina zaton da akwai lauje cikin nadi, akwai abin da ya faru da ni nima." " Sannan a satin nan zanbar kasar nan ,akwai wani meeting da zamu yi na manyan yan kasuwa in sha Allah." " Zan bar maka wasu abubuwan kafin na dawo ,dole sai ka rage shiga Asibitin nan." Ɓata fuska Hammad ya yi ya ce , "Daddy ga Tariq nan ka bar masa mana,zai iya ,ni kawai a barni da aikina" Ya furta yana dan satar kallon Daddy ya san ba zai taba yarda ba . Haɗe fuska Daddy ya yi ya ce "Wai har sai yaushe ne zaka mai da hankalinka akan kasuwanci?Ni ma yanzu ya kamata ace na huta, ka tsaida hankalinka guri ɗaya mana" "In sha Allah Daddy very soon ka yi hakuri ,Sauban yana iya ƙokarinsa fa" Jinjina kansa ya yi murmushi dauke a fuskarsa ya ce"Sauban uban ƴan aiki,ina ka je aiki ina zaka aiki." Mai da idanunsa ya yi kan Tariq,ya san idan ya yi kuskuren sakar masa manyan abubuwansa,kafin ya dawo ba karamar ɓarna zai masa ba,saboda duk inda akai maganar lazy toh ya kai har ma ya wuce. Babu abin da ya sani ban da kashewa mata kudi, da zuwa mashaya, shi dai kawai ya shana. Yana da yancin yin rayuwa yadda yake so. Ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da kurbar black Tea ɗin sa,ba tare da ya tanka maganar Hammad ba. Wani abun mamaki a gidan Hammad ne kawai ya damu da rayuwar da Tariq ya ke yi. "Daddy ni yanzu bari na je Asibitin akwai tiyatar da zan yi ,idan sun zo sai ka kira ni madawo ." "Amma Daddy da zaka yarda da shawarata, da na ce ka bar ma'aikatan nan ,tunda ba yau aka fara ba,kuma zuwan su babu abin da yake ƙarawa.Dama Malamai ka samu suka yi sauka ko Allah zai kawo sauƙi." Jinjina kai Daddy ya yi ya ce"ka ga kuwa ban yi wanna tunanin ba,gaskiya ka yi magana mai ma'ana..Zan yi magana su Malam Ilyas da suke yi duk ƙarshen wata , sai su zo. In sha Allah sai anyi sati kullum a yi sauƙa da addu'o'i. Kafin karshen wata su ɗaura." "Ok ,Allah ya ba da sa a " Ameen ya ce ya yi hanyar fita ya na cewa" Mommy sai na dawo addu'ata yi masa ita ma. Ficewa ya yi sai faman sauri ya ke, saboda baya san wasa da lokaci. Da sauri ya shiga motar, ya yi Reverse ,ya nufi hanyar gate ɗin. Da gudu mai gadin ya tashi ya buɗe masa yana ta faman zabga masa kirari, bandir din yan ɗari bibbiyu ya cila masa. Da sauri ya cabe kudin yana taka rawa bayarwar smalll Alhaji ɗaya tana tsunduma mutum cikin farin ciki. A guje ya fita daga gidan ya dauki hanyar zuwa Asibitin shi. Sai yanzu ma yake ganin tarin miss calls din Ramadan,da Dr Fahad Abokin aikinsa. Dafe kansa ya yi yana tauna gefen lips dinsa. Shaf ya manta da wayar a cikin motar jiya.Ramadan ya fara kira bugu uku ya daga wayar daga cikin wayar ya ce " Hammad lafiya kuwa ? Na yi ta kiran wayarka, ba ka dagawa.Har na ɗakko hanya zan zo gidan, sai na tuna halinka na barin waya a mota , kawai na yi kwanciya ta. Nasan ba zaka cutar da kan ka ba.." Ɗan guntun murmushi ya yi ya ce "toh mai ka mai da ni, yanzu inda wani abun ya same ni fa sai ka ce mai kuma? "Dallah karka dame Muhammad Ramadan , ina aiki ne, na ji alamun tuki ma ka ke yi , amma kana waya. Maza-Maza ka ajiye wayar nan * Ya fada cike da shakiyanci. Dan haɗe girarsa ya yi kamar bai ji shi ba. "Hello.. Helllo ,Dr kana jina kuwa?" Ramadan ya ce jin ya yi shiru kuma bai katse kiran ba. "Ramadan jiya ina ka je da muna magana da kai a gidan gona ? Na san akwai dalilin kiran da kai min saboda ya wuce ƙa'iɗar karin da ya kamata ace ka yi min. " Shiru ya yi bai ce komai ba,Parking din motar Hammad ya yi sannan ya ce "Ramadan ina jinka ka yi shiru. Meyasa na ga tsantsar tsoro da firgici a cikin idon ka? Ka rude da yawa nasan wane ne kai, fada min mai yake faruwa ka san wani abu game da tambarin nan?* Da sauri ya ce " No..! A'a ban san komai ba,sai dai zan zurfafa bincike, amma fa" "Amma me?" "Ba wani abun zan ce ba dama" Jinjina kai Hammad ya yi , ya fahimci,akwai abin da yake boye masa "Kana ina ne?" Jim ya dan yi har sai da Hammad ya ce "ko shima baka sani ba ?" "A'a ina abin nan, Office" "Oho maka dai abin da zan iya ganewa shine, na same ka a Office ɗin" "Ok Abba za ka same ni" Dariya hammad ya yi ya shafa kwantacen sajensa . Ya kunna motarsa yana kokarin barin wajen wata mota ta zo da gudu ta za wuce ta kusa da shi. Rage gudu motar ta yi, da ta zo kusa da shi. Cillo masa wata envelope aka yi Sannan suka kara gaba da mugun gudu . Da kallo ya bi bayan motar sannan ya dauki envelope ɗin. Buɗe ta ya yi ya zaro hoton ciki. zabura ya.yi yana zazzaro ido saboda abin da ya gani a ciki . WANE NE SHI ? By Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION 019 Page 11___12 Bismillahir-Rahmanir-Rahim Da mugun. gudu ya bi bayan motar, amma babu ita babu alamun ta ,ta ɓace bat. Duk da haka bai gamsu ba, hakan bai hana shi cigaba da dube -dube ba a ƙalla ya kai rabin awa yana abu ɗaya. A matukar hasale ya gangara gefan ttiti ya yi parking. "Kai...! Kai ...!! Ohh my god..! " Ya faɗa yana dukan stearing motar da karfi. " suwa ne ne waƴan nan ne ? Ya aka yi suka san na san da wannan hoton ?Bibiya ta suke?" Ya tambayi kansa." Ina suka sanni." Dafe kansa ya yi yana tunani, iya kacin tunanin sa ya yi amma ya kasa tuna inda wani ya san da maganar nan.Jin bai tuna komai ba yasa ya sauke zazzafar ajiyar zuciya .Hoton ya sake daukowa, Tsantsareran zanen Hoton kunama ne baƙiƙƙirin. Wayarsa ya dauko ya haɗa su tabbas kalar su ɗaya sosai ya kare musu kallo ,kafin ya fesar da zazzafan huci. "Ya rabbi" Ya furta ya marasa me zai yi . Haka dai jiki babu kwari ya dauki hanyar zuwa Asibitin zuciyarsa ciki da sake-sake kala-kala . Yana shiga cikin hospital ɗin bai tsaya daidai ta parking ɗinsa yadda ya kamata ba,ya kashe motar ya fito . Wata yar farar takadda ce ta faɗo kasa don shi bai ma kula da ita ba,da alama a tare su ke da hoton kunaman nan. Da sauri ya durkusa ya dauke ta. Jefata ya yi a aljihu ya nufi ciki. Tun daga harabar Asibitin ake ta miƙa masa gaisuwa,saboda irin kyautatawarsa gare su,duk da kasancewar ba wani babba bane,amma hakan bai hana har manya girmama shi ba saboda Dr Hammad mutum ne har mutum.Yana shiga cikin Office ɗinsa ya nami guri ya zauna akan ƙayayaciyar Kujerarsa.Ya lumshe ido. So yake ko yaya ne ya samu natsuwa. A hankali ya ɓuɗe idonsa,farar takar darnan ya zaro ya warwareta. Manya-manyan rubutu ne a jiki da aka rubuta da jar kala. "(Stay in your lane)." Ya maimaita ya kai sau biyar, kafin ya miƙe ya fara zagaye, ya rasa waaye zai zarga,saboda ya yi maganar nan a gurin wani meeting da suka gabatar a ciki satin nan. Amma ai bai yi maganar tambarin kunamar nan ba, kawai maganar fyaɗe ya yi. Toh amma WANE NE SHI ? Wanda ya sa aka kawo masa wannan sakon ,ya san tabbas waƴancen turo su aka yi shi dai ba zai zargi Ramadan ba saboda yasan ko a mafarki ba zai cutar da shi ba . Wucewa ya yi inda madaidaicin Firdge din sa yake ,ya bude ya ɗako gorar ruwa me sanyi sosai . Tunda ya kafa kansa bai sauƙe ba sai da ruwan ciki ya kare . Komawa ya yi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Gabaɗaya ya rasa abin da yake masa daɗi. Turo kofar Dr Fahad ya yi ya shigo da sallama a bakinsa. Amsawa Hammad ya yi ya dafe kansa gabaɗaya ya manta da tiyatar da za su yi, sai da ya ga Fahad ya tuna. "Bisimillah mana, Hammad ya faɗa yana kallon Dr Fahad. Murmushi ya ɗan sakar masa ya karaso ya zauna Hannu Hammad ya miƙa masa suka gaisa."Am Dr Lafiya kuwa na kira wayarka ba ka daga ba,kuma tun ɗazu nake kallon hanya amma shiru ,na yi mamaki saboda sanin ba ka wasa da lokaci." Ajiyar zuciya Hammad ya yi ya ce"Ba na jin dadi ne gabaɗaya tun jiya " "na yi tunanin dama ba ƙalau ba ,ashe ma babu lafiya ne ,toh Allah ya sauwaƙe." Ammasawa ya yi da Ameen sannan ya bashi uzirin ba zai iya (Opretoin)yanzu ba.karɓar aikin ya yi sannan ya tashi ya fita. Iya ƙokarinsa ya yi dan ya samu ya yi aiki yadda ya kamata,amma abu ya gagara. Miƙewawa ya yi cike da kasala ya ya dauro alwala,sakamakon kiran sallah da ya j. Masalacin cikin Asibitin ya nufa. A can ya yi sallah.. Ya daɗe yana addu'a kafin ya tashi Ya fita. ★★★ A gabar nan ina so na yi wata yar magana. Sai ka ga mutum mai kuɗi, idan an yi sallah ya zauna ya yi dogon azkār, ya roƙi Allah bukatunsa.Amma da yawa daga cikin talakawanmu idan aka sallame, kamar jiran a sallame suke.Za si tashi su bar masallacin.Ko uban me za su yi idan sun tashi? Babu cikakkiyar sallah, babu cikakken azkār, balle roƙon bukatu wajen Allah. Sai ma su zauna suna gulmar masu kuɗin,da munana musu zato. An ce maza ba sa gulma, amma yanzu duniya ta koya musu. Ya kamata mu koma ga Allah, ba wai mu zauna muna cewa wane azzalumi ba. Sai ka ga mutum ya zauna yana zagin shugabanni, amma wallahi idan shine ya samu damar da suka samu, abin da zai yi ma sai ya fi nasu. Cuta da zalunci sun yawaita. Cin amanar juna da zubar da jini sun yi yawa. Wallahi ko saka ka aka yi ka yi wani abu, kai kuma ka yi domin ka samu kuɗ,i kada ka manta, shi sharri kare ne. Hassada ta yi yawa. Matsalar ƙasar nan ba daga shugabanni kaɗai take ba, har mu ma muna da rawar da muke takawa. Duba,mutum nawa ne a cikinmu ya taɓa cutar da mu? Idan ba mu gyara halayenmu ba, can ji kam sai dai Allah. Duniya ta rufe mana ido, mukan manta duk abin da muka shuka shi za mu girba. Allah ya kawo mana mafita, ya datar da mu, ya daura mana adālan shugabanni. Allah ya sa mu dace. Kuma ban ce masu kuɗi ba sa aikata laifi ba,suna yi,kuma idan muka tashi faɗar aibunsu,muna faɗa Sannan kuma mu kula da ibadar Allah, musamman sallah a kan lokaci, da yawan karanta Alƙur’ani. Da yawanmu sai Alƙur’ani ya tuhumemu a ranar ƙiyāmah game da ƙaurace masa da muka yi, muka rungumi kafafen sada zumunta na zamani (social media). Wallahi, da yawanmu sai mu daɗe ba mu ɗauki Alƙur’ani muka karanta shi ba. Mun fi bawa wayoyinmu tsadaddun lokutanmu fiye da Alƙur’ani. Social media ta wawure kusan dukkan lokacin da muke dashi na yini da dare. Wallahi, lamarin ba wai mu karanta wannan saƙon kawai mu wuce ba. A’a, nazari ya kamata mu tsaya mu yi, mu ɗauki ɗamarar gyarawa. Domin haƙiƙa, kullum rayuwarmu raguwa take yi, kullum kuma ƙara kusantar ƙabarinmu muke yi. Abin kunya ne a gare mu,mu matsayin M musulmi,mu je lahira a ce mun fi bawa social media lokutanmu fiye da Alƙur’ani mai girma. Mu yi ƙoƙari mu taimaki kanmu, mu rage yawan ta’ammuni da social media, mu dawo mu rungumi Alƙur’ani. Domin Alƙur’ani ne zai cecemu a ranar gobe ƙiyāmah, saɓanin social media.” Allah ya samu dace Ameen. Dawo wa labari ★★★ Kai tsaye ( Emergency) ya wuce ya tura daƙi mai lamba 17, da sallama ɗauke a bakinsa.Wata dattijiwar mata ce zaune akan kujerar gefan gadon,sai faman share hawaye take da gefan mayafinta. "Au Mama wai har yanzu baki dai na kukan nan ba ?Sai kin jawa kanki wata cutar ? Kuma mama abin da bai faru ba shi aikewa gudu, wanda ya faru ya riga ya faru ." Rushewa ta kuma yi da kuka kamar cewa ya yi ta ci gaba . Cikin shashshekar kuka,ta ce "haba ɗan nan, ya za ka ce kar na yi kuka? Ya za ayi na ƙi yin kuka, yarinyar nan ita kaɗai nake gani na ji sanyi,na samu natsuwa. Ƴaƴana bakwai ita ta takwas, amma yau duka babu su,sun tafi sun bar ni ." A cikin wata ɗaya Allah ya amsar min su dukansu,har banganmu wato mijina. Ita ƙa dai ta rage min, ita ka ɗai ta rage min, na daura duk wani fatana da burina akan ta. Ita ma antarwatsa min komai, an cutar da rayuwata an cutar da ta ƴata, an ruguza min tarbiyar dana dauki tsawan shekaru ina ba ta, saboda ita nake rayuwa har farin ciki ya dawo cikin rayuwata amma ita ma yanzu tafiya za ta yi ta barni ancutar damu. Allah ya isa wallahi ." "Shin mene ne aibu na dan na turata,ta nemi ilimi? Mai muka yi musu?Duk matan duniya ,sai Rumaisa ,laifi ne don ta je ta nemi ilimi?" " Mijina ya tafi ya bar ni,ƴaƴana gaba ɗaya sun tafi sun barni. Saura yar auta kuma ita ma yanzu..." Kasa karasawa ta yi ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi taɗaura kan ta gefen gadon . Hawayen ya ciko idonsa. Ya tako inda take. Tsugunnawa ya yi ya rike hannunta cike da dauriya ya ce," Mama komai da ya faru dake kin dauke shi kaddara. Kin rasa yaranki kin rasa mijinki,kuma duka kina kaunarsu, yanzu a kan wannan abin da ya faru ya kamata shima ki amsheshi da hannu bibbiyu,ki kuma godewa Allah a duk halin da kika tsinci kanki a ciki,Allah yana sane dake ." "Kuma ni ba ki dauke ni ɗan ki ba ?" Girgiza kanta ta yi da sauri ta ce "badan da kai ba da Jamalu, da yanzu mun tozarta saboda ba mu da karfi, ba ni da yadda zan yi " Girgiza kansa ya yi da sauri shima. Ya ce "ki saka a ranki Allah ne ya kawo miki dauki, saboda addu'ar da ki ke yi,ki kwantar da hankalinki dan Allah . Yanzu idan ta farka wane ne zai rarrashi wani a cikinku? Dole ki tsaya ki karfafi gwiwarta, wannan kaddarar bashi yake nuna rayuwar ka tazo karshe b....." Maganar shi ta katse, sakamakon jijjigar da yarinyar dake kan gadon tafara yi, har gadon yana motsawa. Da sauri ya miƙe ya kira Abokan aikinsa kafin su zo tuni ya karasa inda take ya shiga bata taimakon gaggawa ko da suka zo,rufuwa sukai akan ta cike da ƙwaire wa da sanin makamar aiki. Kallon mama ɗaya daga ciki ya yi "ya ce dan Allah ki ya hakuri ki je daga waje." Girgiza kai ta yi ta ce "a'a ɗana, ka barni na ga mutuwar ƴata akan idona." . Ganin saikuka take ya sa aka lallaɓata daƙyar ta fita. Tana ji tana gani ta fito tabar Rumaisa,ba ta da tabbacin rayuwarta ko akasin haka. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Allahumma ajurni fii musibati wa'akliflii kairan min ha Ita kawai take maimaitawa, Saboda inba ita ba ba ta san mai za ta yi ba. ★★★t Minal Tunda Hammad ya fita Daddy bai daɗe ba shima ya fita, Mommy ma haka. Don haka suna zaune a falo ita da Tariq ,suna ta hirarrakinsu,da kallace kallacem su, Sosai Tariq ya warware,don har ya yi wanka ma ya canza kaya saboda indai kana tare da Minal ba za ta bari ka yi kaɗaici ba . Wani koriyan film suke kallo. Ta ɗago ta kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,da sauri ta tashi zaune daga kishingiɗen da take. Zuciyarta ce ta gaya mata matar kan bola dagowa Tariq ya yi ya ce "lafiya ?" Girgiza kanta ta yi sannan ta ce "ina zuwa" Ta tashi,ta yi ciki da sauri . Kusan mintina talatin ta dauka kafin ta fito. Ta shirya cikin blue jins da bai wani kama ta ba, da farar T-shirt sai blue jaket da ta daura, saman kanta ta daura wani. kyale da bai boyo gashin kanta ba. Sosai ta yi kyau abin ka da farar fata. Ƙarasawa wajen Tariq ta yi da bai san ma da zuwan ta ba saboda hankalinsa gabaɗaya yana kan kallon da yake yi. " ya kaga wankan ?" Ta faɗa tana jujjuyawa "Wow very nice, kin fita tawan" Murmushi ta sakar masa ta miƙa masa hannu suka tafa sannan ta yi gaba tana cewa "sai na dawoTariq,ka kula da kanka" Ɗaure fuska ya yi ya ce "sai ka ce yaro kumaa" Kamar bashi ne ya gama kyarma ɗazu ba. Ita dai dariya kawai ta yi ta fita. Tana fita harabar gidan kai tsaye inda motarta take ta nufa,da ta sa aka wanke mata ita tun dazu da safe. Shiga ta yi ta kunna ta. Da sauri mai gadin ya miƙe ya buɗe mata kofa. Ita ma sai faman kirari yake mata, dama daga ita sai Hammad ne suke bada kyauta, shi kuwa Tariq wataran ma da a buge yake shigowa babu abin da yake hadasu da shi sai zagi . Dakatawa ta yi a bakim gate ɗin . Da sauri Danial ya karaso yana cewa "Aunty Madam Ta yi dariya ta ce ina sauran ma'aikatan suke,dudubawa ya yi ya ce "madam yanzu nam fa suna nan bansam inda suka yi ba . WANE NE SHI ? By Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION 009 Page 13___14 Bismillahir-Rahmanir-Rahim Kuɗi ta dakko, ta mika masa . Ta ce "ku raba kai da sauran " Jiki na rawa ya karɓa yana zuba mata godiya .Cikin gurɓataciyar hausarsa ya ce "yar Alaji yar gidan ajiya Allah ya cigaba da baki ki bamu. " Ita dai ba ta ce masa komai ba, ta kara gaba. Kuɗi kwata-kwata ba matsalar ƴaƴan Alhaji Mansur ba ne .Saboda haka suke wadaƙa yadda suke so. Hankali kwance take tuƙin ta, sai faman shan Music take . A hanya ta tsaya inda ta saba sai mata abinci,ta karɓa,ta wuce. Tana isa ta fito daga motar,ta tufi inda ta saba ganin ta. Sai dai abin mamakin babu ita babu dalilinta. Zagayawa ta yi ta duba, amma ba ta ganta ba. Ba ta saba zuwa taga bata nan ba,saboda haka hankalinta ya tashi sosai da sosai . Ta duba ta sosai bata ganta ba. Dawowa ta yi ta samu guri ta zauna hankali tashe, ta ma rasa abin yi gabaɗaya. Sai faman share hawaye take yi . Yanzu a ina zata ganta ita dai ta san ba ta yawo,inda take zama a nan take anan rana zata sameta harta fadi .Sai idan ta ga dama take matsawa. Ji ta yi an cakumota ta baya a figice ta juya. Kuka ne ya kuɓce mata aikuwa ta saki abinta.Rumgume ta ta yi ba tare da la'akari da tarin dauɗar dake jikinta ba . Ɗagowa ta yi cikim kuka ta ce "ina ki ka je ? Kika bar ni na yi ta neman ki,na yi zaton wani ya sace min ke." Shiru matar ta yi tana kallon bakinta. Kamar tana fahimtar abin da take cewa. Kawai sai ta fashe da dariya sai da ta yi mai isarta, kafin ta fashe da kuka. ita dai Minal yar kallo ta koma, saboda ba ta taba ganin kalar kukan nan ba. Kuka ne cikin gurnani mara daɗim ji. Mikewa wa matar ta yi cikin kukan ta riƙe hannun Minal ta ja da karfii,babu shiri ta bi bayanta, tiryan- tiryan takai ta har inda take kwanciya. gefen bolar ne, ruwa duk ya jiƙa mata inda za ta kwanta, gurin ya yi kaca -kaca sai wari yake. Girgiza kanta ta yi sannan ta ce "na ce kibiyo ni mu je gidanmu kin ƙi. Ki zo na kai ki gurin Mommy kin ji. " Ita dai ba ta amsa mata ba, sai ma ɗaɗɗago mata tsummokaran da take kwanciya a kai,ta na miƙo mata wai ta karba. Miƙewa Minal ta yi har wani jiri take gani saboda yadda wari yake tashi a gurin . "Ki taso mu tafi " Miƙewa matar ta yi,ta biyo bayan Minal da ta yi gaba. Cike da mamaki Minal ta juyo,ganin ta biyo ta . Murna ce ta kama ta ta ce " ki na gane abin daa nake cewa ? " Kallon Minal ta yi sannan ta fashe da dariya mai karfi don ita a zaton ta wasa take yi mata. Wucewa ta yi don ta ɗako mata abincinta Biyo bayanta ta yi, ta na cigaba da ɓaɓaka dariya,sai dai ba ta karasa inda motar take ba, daga baya-baya ta tsaya tana dariyarta. Ɗaƙo abincin ta yi ta dawo inda take. Gabaɗaya yau ba ta jin daɗin abin da take yi. Kamo hannun ta ta yi, ta kaita kan wani dakali dake gefan bolar. Ta zaunar da ita,ta a jeye ledar hannunta, ta ɗako ruwa ta baɗe, sannan ta kama hannunta ta wanke mata sosai. Abincin ta mika mata , da cokalin robar da aka sako a ciki,duk da ta san balalle ta ci bada shi ba. Ai kuwa hakan aka yi, don cilli ta yi da cokalin, ta zira hannu ta hau cin abincin tana dariya wani yana zubowa. Ruwa Minal ta ɗako ta buɗe mata, sannan ta miƙa mata,ganin abincin na kokarin shake ta. Karɓar ruwan ta yi kamar zata sha, sai da ta kai shi saitin bakinta kafin ta juye ruwan a cikin abincin ta ɗaga robar abincin ta kafa kai tana shan ruwan,wani yana shiga wani yana zubewa. Ido Minal ta zuba mata,tana ganin yadda take cin abincin,tausayin ta yana ratsa zuciyarta . Ta yi wani mugun datti,tun sanda ta fara ganinta da wayen nan kayan ta santa, gashi ta ƙi yarda ma ta bi ta ba rantana ta kaita a gyara mata jiki. Cillin da ta yi da robar abincin ne, ya sa ta fahimci ta koshi . Miƙewa ta yi ta kama hannunta ta kai ta ɗayan tsalaken,ba inda bolar take ba gurin ana buga bulo. Duk da shima dai sai a hankali amma akwai rumfa a gurin . Ciki ta kaita ta zaunar da ita,da yake ma'aikatan duk sun watsae saboda antashi daga aiki . Kallon wani matashin saurayi ta yi wanda ba zai gaza ta a shekaru ba . Sallama ta yi masa. Ya amsa yana kare mata kallo, ganin shigar jikin ta duk da yana yawan ganin ta tazo wajen matar,amma bai zaci musulma ba ce ba,saboda yanayin shigar da take yawan zuwa da ita. "Lafiya ?" Ya tambaya yana kallonta,yana kuma kallon matar da ta yi kwanciyarta ta fara bacci . Dan jim ta yi can kuma ta ce "dan Allah so nake ka kulamin da wannan matar karka bari ta je yawo, kuma ka bata abinci anjima.." A harzuke ya bude baki zai fara yi ma ta masifa, amma sai ta koma ganin kuɗin da ta zaro, badir din yan dubu-dubu ne guda biyu, mika masa ta yi, ta ce "ka rike amana " Jiki na rawa mutumin ya karɓi kudin,yana zabamata godiya cikin ma daukakin farin ciki . Sai da ta ɗan tsaya tana kallonta, kafin ta juya da nufin komawa inda motarta take. Ji ta yi an rike hannunta da sauri ta juya. Matar da ta fara bacci ya ma aka yi ta tashi?. Ido ta waro ganin hawaye kwance a idonta."Mene ne?Ta tambaye ta amma shiru,ba ta daina kallonta ba, ba kuma ta ce komai ba.A hankali matar ta zame hannunta daga na Minal ta koma ta kwanta. Da kallo tabita mamaki ya cika ta,kallon nan ya tsaya mata a zuciya A kallon da ta yi mata kamar mai hankali. Jiki babu ƙwari ta juya ta bar wajen. Haka dai ta nufi gida,zuciyarta duk ba daɗi tana ta sake-saken wace hanya ta zabi ta shawo kanta tabar wannan mumunan wajen. Wannan kenan ★★★ Tsaye yake cikin tsakiyar sihara,babu gida gaba,babu a baya. Wata iriyar masifafiyar kishirwa ce take barazanar illata rayuwarsa. Ba karamar galabaita ya yi ba,kafafuwansa sun gaza daukar ganganjikinsa,saboda haka ya zube a gurin cikin mugun hali. Wani irin huci ya ji a saman kansa. Kamar ance ya buɗe idonsa,ya bude a hankali. Dishi-dishi yake gani,kafin idanun shi su watsake. Wasu gabza- gabzan mutane ya gani a kansa bakunansu na ci da wuta,ga wasu kacoci a hannunsu. Cikin tsananin firgici da tsoro,ya shiga ja da baya daga kwancen da yake, tsoro ya hana shi tashi. Wata mahaukaciyar tsawa aka daka masa, daga bayansa. Firgici da tsoro ne yasa ke kama shi, da kyar ya iya juyawa domin ganin mene ne a bayansa. Wasu mutane ya gani su biyu. Hannunsu rige da mashi, wanda yake kamar garwashin wuta, saboda jan da ya yi. Wuyansu yana ta mafan tsartar da jini. Bakinsa yake so ya buɗe ya yi musu magana,amma ya gagar, ji yake kamar ansaka masa gam a jikin bakin. So yake ko ihu ne ya yi amma abu ya faskara. Tsakiya suka sa shi cikin wani irin karaji da tsawa mutanen suka fara magana a tare. "Kun yi sake ɗan zaki ya girma lokacin girbar abin da kuka shuka ya yi" "Zaku girba tabbas, zaku girba tabbass" Ɗaga masun hannunsu suka yi a tare ,suka caƙa masa a kirjinsa daidai saitin zuciyarsa. Wata kalar hantsulowa ya yi daga kan gadon, yana maimaita kalmar shihada . Wani mugun bugu zuciyarsa take masa jikinsa ya yi jagalab da gumi. Duk da yadda A.C take aiki a ɗakin . Har yanzu kishirwa yake ji. Miƙewa ya yi kafafunsa sai faman rawa suke yi. Idonsa ya kai kan agogon bangon ɗakin,karfe 3:20 am. Gefen gado ya dawo ya zauna kamar me tsoran hawa kan gadno zuciyarsa sai sake -sake take masa. Ya rasa gane shin mai zai girba . Wani mummunan mugu zuciyarsa ta yi, sakamakon tuna wasu al'amura da suka faru shekara 27 da da suka wuce. Dafe kirjinsa ya yi yana maimaita "Innalil-lahi wa'inna ihi raju'un" Dama barcin bai daɗe da sace shi ba, saboda yana cikin tsananin tashin hankalin batar yarsa zahra. Gashi jami'an tsaro sun dakatar da fitar da rahoton batan nata. Bakin cikin abin da ya faru yasa ya killace kan sa a ɗaki shikaɗai. Jiki babu kwari ya miƙe ya dauro alwala kawar da komai ya yi ya tada sallah. Ya daɗe yana nafilfili kafin ya zauna ya jima yana rokon Allah don har a ka yi asalatu idonsa biiyu. Dan haka ya miƙe ya ɗora raka'atanulfajir. ★★★ Barde Turo gate din gidan ya yi ya shigo da sallama a bakinsa. Da sauri Ahmad ya miƙe duk da jirin da yake gani ."Yauwa Salim dan Allah taimaka " Hannun shi ya kama yace" ka kwantar da hankalin ka babu abunda ze faru me ya same su ne wai?" Cikin tashin hankali Ahmad ya ce "zan,yi maka bayani " Karasawa su kai inda suke amamakance yake duban su, duka su ukun azube. cikin daurewar kai ya ce "Mai amm mai ya faru dasu hak....." Wani wawa burki ya ci maganar shi tan katse ganin fuskar wanda yake kwance a a gabansa "Ba...Bar Barde..! Ya aka yi hakan ta faru ?yaushe ya dawo hayyacinsa ma? " "Nima na yi mamakin farkawarsa da wuri, shine ya yi wannan ma" Ya faɗa yana nuna masa su Safna. Jinjina kansa ya yi cike da gamsuwa ya ce "toh ai ba zai yiyu na iya wannan aikin ni kaɗai ba, bari na kira sister Halima da sister Maryam,amma kafin nan mu ɗauke Oga daga nan " Toh Ahmad ya ce sannan su kai kama -kama suka miƙashi ɗaki . Taimakon gaggawa ya fara basu tun daga nan saboda jini da Safna take zubarwa, ita da Ahmad. Ko da su Sister Halima suka zo haduwa suka.yi akan su, kafin kace mai tuni sun gama komai tsaf. Allurar bacci ya yi musu ,amma Ahmad ya ce shi ba sai an yi masa ba. Haka su sister Halima suka tafi cike da sake-saken meyafaru akai wannan karamin hatsarin,amma babu amsa saboda basu ga fuskar tambaya ba . Sai da su Salim suka tabbatar da sun fita tukunna Ahmad ya rufe gidan. Suka shiga ɗakin da Barde yake yadda suka barshi haka suka koma suka same shi . Duk wani taimako da ya kamata ya bashi ya bashi, amma haryanzu bugun zuciyarsa yaƙi dawowa. kallon shi Ahmad ya yi da runanun idonsa sannan ya ce "ko dai ya mutu ne?" WANE NE SHI ? By Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION 019 15__16 Bismillahir-Rahmanir-Rahim Girgiza kai Salim ya yi da sauri ya ce " a'a ina iya kokarina dai" Gyaɗa kai kawai ya yi ya fita daga ɗakin. Falon gidan ya nufa dan duba halin da su Hafsat suke ciki. Haryanzu bacci suke yi. Zama ya yi saman ɗaya daga cikin kujerun daƙin,ya dafe kansa da yake masa ciwo . Anya zaman Barde ya kamata a cikin gidan nan ? Ya tambayi kansa yana zabga ta gumi. Toh amma idan ba nan ɗin ba, ina ne zai samu kariya daga hare-hare da ake kawowa rayuwarsa? A yanzu rayuwar Barde da ta Safma tana da amfani fiye da tasa. Tarin da Hafsat ta yi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya faɗa,da sauri ya miƙe ya nufi inda take . "Hafsat Hafsat sannu" Ya faɗa yana kama hannunta. Damƙe hanayensa ta yi cikin nata, hawaye yana zubo mata, saboda kanta da yake mata ciwo. Ya bugu sosai. ita ma cikin kuka ta ce "wannan shine Barden? Wannan shine halin na shi na gari ? Shine wanda ka ke ta ba ni labarin,dama Barden mahaukacine ? " Rufe mata baki ya yi yana girgiza mata kansa. Ture hannunsa ta yi ta yumkura ta tashi zaune da kyar . Tana jin jiri yana ɗibartaa sama-sama,sakamakon allurar bacin da aka yi mata,ta fara aiki. Cikin bacin rai ta ce "ba ka ba ni amsa ba ." Cikin matukar damuwa ya ce "ban yi miki bayani tun farko ba? Da amincewar ki aka wo shi gidan nan. Kuma sai da na miki bayanin halin da yake ciki,ke kika bani kwarin gwiwar na kawo shi nan ba wani ba. "Amma ni dai yanzu dan Allah ki yi shiru kin ga dai ba ki da lafiya idan kika warke za mu yi magana ." Komawa ta yi ta kwanta zuciyarta cike da tsoron kar Barde ya tashi ya illatasu ,ita ta tabbatarwa kanta kwata-kwata bashi da hankali. Zuba mata ido Ahmad ya yi sonta yana kara tsumashi . A tsawan shekara biyu da aurensu bai taɓa yi mata magana ta yi masa musu ba,shiyasa yake matukar girmama uzirinta,da ita kanta ma. Wani irin so yake mata wanda ko shi bai san kalarsa ba. Bai taɓa tunanin zai so wata mace bayan Suhaima ba,amma yanzu lokaci yana kokarin canza komai. ★★★ Rugar Baffa arɗo. Da sauri wata matashiyar yarinya,da baza ta haura shekaru goma (13) a duniya ba, ta fito daga cikin wata madaidaiciyar buka,tana ƙwala kiran "Baffa Baffa kaɗon nan ya farka" Da sauri Baffa ya ajiye bakar hannunsa ya nufi bukar. A zaune ya same ta,sai faman kale-kale take. "Sannu ko sannu ka ji jinina kai kawai ta yi tana kallonsa da tarin tambayoyi a ranta. "Ya a kai ta zo nan gurin? Meyafaru da ita ne? " So take ta tuna. Lumshe idonta ta yi,a hankali komai yake dawo mata kamar yanzu ake yin sa . Da sauri ta ɓuɗe idanonta,da suka canza launi daga fararen da suke, zuwa launin bacin rai da tsananin damuwa. " Mairamu zo ga shi nan Allah ya yi zai tashi" Baffa ya faɗa cikin fulatancii,da maɗaukakin farin ciki . "Waye ya kawo ni nan ? Ina akwatina take?" Ta faɗa cike da tashin hankalin kada ta rasa akwaitn da ta sadaukar da rayuwarta da dukkanin farin ciki da fata na rayuwarta akan ta. Cikin tausasawa Baffa yac e "ni na kawo ki nan, kuma akwatin ki tana nan lafiya.Yanzu ki watsa ruuwa tukuna ki kara hutawa kafin ki yi mana bayanin wace ce ke." Jinjina kai ta yi ceke da son ta danne komai . Kallon Inna mairamu Baffa ya yi da tuni ta shigo ya ce "yauwa sai ki taimaka mata ta yi wankan,ta ci abinci ta kara shan magani ,zuwa gobe sai mu yi maganar da ita,idan ta kara samun cikakiyar natsuwa ." Da toh Inna ta amsa. Fita baffa ya yi ya basu guri. Ita kuwa faɗime tana gefenta, ta manne mata, saboda ita mugun burge ta take. Tana son ta ga mutum dan birni, gashi yau kwana da kwana ki suna tare,kuma ɗaki daya babu abin da take saki sai murmushi ,cike da farin ciki Fita Inna ta yi don hada mata ruwan wankan. Da sauri Fadime ta sake matsowa kusa da ita. Ta yi ƙasa da muryarta saboda kar ajiyo maganar da za ta yi, Inna ta shigo ta kore ta . Ta ce " Kai kaɗo ya sunanka ?" Juyowa ta yi ta kalle ta,da fulatanci ta yi mata tambayar. Haka kawai ta ji yarinyar ta kwanta mata. Ɗan murmushi ta sakar mata, ta ce "sunana Zahra kuma ni mace ce ba namiji ba" Ta mai da mata da fulatancin ita ma. "Ni kuma sunana Fadime" Jinjina kai ta yi sannan ta ce "Wow nice name ki ce ke takwara ta ce" Zaro ido fadime ta yi amamakance ta ce "mene ne Nice ? Kuma ni sunana Faɗime ba Zahra ba " Murmushi ta yi ta ce "turanci ne na miki,kuma ai da Zahra da faɗime duk ɗaya ne kawai ɓata miki suna ake yi" Juya kyawawan idanunta ta yi ta ce "Nice,amma fa ni ba zan ce miki zahra ba,sai dai na ce miki Addana,idan Baffa ya ji na kira sunanki gatsal duka na zai yi" Ƙara gyara zama Faɗime ta yi saboda yadda hirar take mata dadi. "Kin san kwanan ki nawa a gurin nan ?Ba ta jira ta ba ta amsa ba ta cigaba, "yau kwanan ki bakwai ba mu yi zaton zaki tashi ba,har ciwan naki ya warke kin sha wahala ko?Duk Baffa ya shiga damuwa wai baya so ki mutu akwai tarin tambayoyin da yake so ya mi..... " Maganar ta ce ta katse, sakamakon ankara da zagin da Inna take auno mata daga bakin kofa . Babu shiri ta miƙe tsaye ta dauki ƙwaryar dake gefenta. Ɗan satar kallon Inna ta yi sannan ta kalli Zahra ta ce "bari na tatso miki nono kafin ki shiirya " Ta Wuce ta fita da gudu. Da Kallo Zahra ta bi ta,cike da burgewa . Hawaye ne ya gangaro mata,da sauri ta share cikin dabara saboda kar Inna ta gani. Karasa shigowa ɗakin Inna ta yi,tana ƙara yi mata sannu,da ba ta hakuri akan shirmen Fadime. Haka dai Inna ta taimaka mata ta yi wanka. Sai kayanta Inna ta ba ta tasa ,saboda na Faɗime sun mata kadan. Gashi ita daga ita sai kayan jikinta da suka yayyage, saboda wahala. Sai da ta yi salloli kafin,Inna ta kawo mata abinci. Kasa cin abincin ta yi saboda ba ta saba dacin irin shi ba. Sai nonon da Fadime ta kawo mata ta iya sha, shima bada yawa ba. Wani jikaƙen magani Inna ta bata ta ce tasha,babu musu ta amsa ta sha. Tana zaune a nan har fadime ta dawo daga aiken da Inna ta yi mata gidan su Jangudo,ta karɓo mata garin tuwo nasu ya ƙare,kuma bata ankara ba har sai da ta yi ruɗen tuwan. Shine ta ba ta kwarya ta ce ta yi gudu ta amso mata. Ta kai kusan rabin awa kafin ta dawo. Ta shigo sai faman raɓe -raɓe take yi da ƙwaryar a hannun ta,amma anrabata biyu,jikinta ya yi butu-butu ta garin. Juyowa Inna ta yi da take tuƙa tuwo, ta kalle ta ta ɗauke kanta kawai,ta cigaba da aikinta. Tun ɗazu yaron makota ya shigo , ta tura shi ya amso mata dama ta yi tunanin Faɗime ba zata dawo mata da abin arziki ba . Ajiye kwaryar ta yi a wajen wanke -wanke sannan ta dawo ta ja ta tsaya. Sosa kanta ta yi kamar ankunna ta haka ta fara magana . "Wallahi Inna ba ni na tsokane su ba. Su habu ne da ɗan gidan mai gari ,kawai na shanyo kwana zan taho suka tare ni, wai sai sun dake ni,dan ranar nan da kika aike ni sun tare hanya sun ce ba wanda zai wuce, ni kuma dana zo sai na wuce da gudu, shine yau suka tare ni suka barar da garin, kuma Wallahi Inna sai da na ce kin hana ni fada amma ba su ji ba ." A fusace Inna ta ce "faɗan da na hana ki shine ba za ki daina ba ko? Ba ni da ikon na aikeki sai kin salwantar da abin da na aikeki ko? Wai ni yaushe za ki yi hankali ?" Cike da rashin gaskiya ta ce "Wallahi Inna ban yi faɗa ba,su ne ma suka dake ni" Ta faɗa tana matso hawaye. Hmmm kawai Inna ta ce tana mata addu'ar shiriya a zuciyarta. Kiran salar magaribar da ake yi ne yasa Inna ta ajiye aikin da take yi, ta daura Alola tashige. Ita dai Zahra kallon Faɗime kawai take yi,tana murmushi . Kafin Inna ta shiga daki sai da ta zubawa Zahra ruwan alola . Cikin sanɗa Fadime ta je ta leƙa Inna, ganinta ta da sallah yasa ta dawo da sauri ta zuba ruwan wanka tashige ba yi. Dama raɓe-raɓen da take yi tasan faɗan Inna bai kare ba. Bayan ta fito daga wankan alwala ta daura, ta shiga ɗaki . Riga da zani tasaka kafin ta tada sallah. Ta duddun gura kawai ta sallame. Babu maganar addu'a haka ta tashi ta fito harɗaki ta samu Inna,ta tsugunnawa ta ce "Inna ina wuni " Banza ta yi mata kamar ba ta jita ba. Ta dan daɗe a gurin tana gaya mata ta yi ladamar abin da ta yi kuma ba zata sake ba. Ita dai Inna carbin hannun ta kawai take ja. A hankali ta tashi ta koma bukarta . Kabar Inna ta ɗaibo,ta dawo tsakar gida ta shiga haɗa mafici. Cike da mamaki Inna take kallonta,kwata -kwata ba ta yarda da wannan kame-kamen na ta ba. Tana tsaye a gurin wata mata ta shigo afujajan. Hannunta rike da wani matashin yaro wanda zeɗan girmewa Faɗime, amma ba sosai ba. Zabura Fadime ta yi ta mike tsaye ta ce "shi kenan asirina ya taunu." WANE NE SHI ? By Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION . YOTA 019 Page 17 ____ 18 https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Bismillahir-Rahmanir-Rahim "Sannu da zuwa ku karaso" Inna ta fada tana dan faɗaɗa fuskarta da murmushi . Turowa Inna yaron ta yi gaban ta,cike da rashin mutumci ta ce "kalli abin da wannan azalumar yarinyar nan, ta yi wa Habu ta fada da fulatanci Kallon Habu Inna ta yi, kansa ya fashe ,ga gefen fuskarsa ya kumbura. Hankali tashe Inna tashiga bawa Hafsii hakuri ,a kan za ta hukunta fadime. Amma matar nan ta tsaya tana ta zage-zage,tana gayawa Inna magana. Sosai ran Inna ya baci, a ƙalla ta san ta girmi matar nan, nesa ba kusa ba. Amma Faɗime ta ja mata zagi. Kan Fadime Inna ta yi a zafafe da nufin dukan ta. Ta cafko ta. Rintse ido Faɗime ta yi da sauri,ta san dama idan ta shiga hannun Inna ba za ta ji da daɗi ba. Ɗaga hannu ta yi ta sauke mata lafiyayen mari ,hannu ta sake ɗagawa da shirin kara mata. Ta ji an riƙe hannunta daga baya,a zafafe ta juya dan ganin wane ne . Baffa ta gani tsaye fuskar nan babu annuri. Ba ta ce komai ba ta saki fadime ta ja da baya. Kan Fadime ya yi da tuni ta zube a kasa tana burgima . Ɗaga ta ya yi ,ta mike tsaye sai ihu take, kamar wadda ake zarewa ruhi. "Ki i rufe min baki " Ya faɗa ba alamar wasa. Kamar an yi ruwa an dauke haka ta shanye kukanta tas. Tasan wane ne Baffa ba ya magana biyu. Hafsii ya kalla da ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta. Kwata-kwata ba ta lura da shigowarsa ba, masifa ta rufe mata ido har sai da ya zagayo. Sarai ta san halin tijarar Baffa,yanzu sai ya yi mata wankin babban bargo. A fusace Baffa ya ce "Ina alfahari da jinina,na san babu rago a ciki. Ki bi hanyar da ki ka biyo ki koma, idan ba haka ba." Ƙwafa ya yi ya juya ya ja hannun Fadime. Zaunar da ita ya yi a gefen Zahra, da take ta kallonsu ita dai ba ta ce komai ba. Tashi ya yi ya debo mata ruwa. Babu musu ta karɓa ta sha,saboda ta maru da kyau. Sai da tasha ruwan sosai kafin ta dire kofin, ta cigaba da shashekar kukan. Inna kuwa bakin ciki ne ya daskarar da ita, ta rasa wane kalar hali ne da Baffa, sai ka ce ba fillo ba. Shi kwata -kwata ba shi da kawaici akan faɗime, duk da cewa ba ita ce yarsu ta fari ba, amma ita kaɗai ce ta yi tsayin rai, sauran duk ba su tsaya ba . Shi ya sa yake lalaɓata,baya son bacin ran ta, duk da hakan ba ya hana shi hukuunta ta idan ta yi masa laifi,sai dai bai yarda wani ya taɓa masa yarsa ba. Baffa ko ta kan Inna bai bi ba, sai faman rarrashin Faɗime yake da sai daga baya kukan ya dawo. Da kyar ya samu ta yi shiru. Ranar ko abincin dare ba ta ciba. Haka ya lallaɓata ta je ta kwanta, kamar ita a ka yi wa laife,ba ita ta yi ba . Ita ma Inna banza ta musu,ta cigaba da ayyukan ta, ranta duk babu dadii. So ta yi ta zane faɗime sosai,kuma ta san yanzu shikenan dukan ya sha ruwa. Sai da ta gama duk abin da take, kafin ta kama Zahra da har yanzu take ɗingishi, saboda ƙayoyin data taka. Ita ce ta ce Inna ta barta a tsakar gidan, har ta gama, saboda ganin taurarin ya saka ta cikin nishaɗi sosai . Ko da suka isa cikin buka,kwanciya ta yi akan shimfiɗar da aka yi mata. Ta jima akwance bacci ya gagara abubuwa da dama take tunawa . Yanzu ta ya ya za ta bawa su baffa labarin nan,mai cike da ruɗani da tsantsar bakin ciki, da takaici . Girggiza kanta ta yi da sauri ,a hankali ta ce," zan manta komai na ɓuɗe sabuwar rayuwa". Haka dai ta cigaba da sake-sake, har bacci ya yi awan gaba da ita . Koda garin Allah ya waye,tana ta sauraren su baffa su yi mata magana, a kan sanin wace ce ita amma shiru. Haka aka haɗa mata kayan karyawa. Inna ta kawo mata,cike da karamci irin na fulanin usili. Yau ta dan samu ta ci cike da dauriya. Kallon fadime ta yi da take ta faman zankaɗe kayanta. Kamar ta tambaye ta kawai ta ƙyale ta . Ba ta ma daɗe da tashi daga bacci ba,don sai da Inna ta shigo kawomata abin kari ta ganta,ganin ba ta da niyyar yin sallah ya sa ta rarakata. Shine ta ɓige da duba kaya. Jin motsi ya tunkaro ɗakin nasu ne , yasa faɗime zabura ta taɗa sallaar. Daga bakin kofa Baffa ya tsaya, yana tambayar ko ta tashi Lafiya. Ba ta amsa ba sai gaisuwar da ta mai da masa cike da ladabi . Ya amsa murmushi kwance a kan fuskarsa. Ya tambaye ta ya karfin jikin nata . "Na ji sauki" Ta ba shi amsa da hausa,saboda shima da hausar yake mata magana, duk da ba ta fita sosai. Cikin natsuwa da tausasawa Baffa ya ce "muna ta son mu yi magana da kai, amma babu dama,har Arɗo ya aiko a kira ni,na san dalilin kiran ba zai wuce akan ki ba, amma zan je idan na dawo ,ko zuwa anjima ne, sai mu yi magana " Jinjina kanta ta yi hawaye yana cika idonta. Da sauri Faɗime ta fito hannunta riƙe da ɗan kwalinta. Kaya ne irin na Baffa a jikinta, riga ce ta mafarauta iya gwiwa , sai bakin dogon wando. "Baffa tsaya ni mu tafi" Galala ya yi yana kallonta "mu tafi ina ?" "Yau da ni za a je farautar " Baki ya buɗe da shirin yin magana, da sauri ta katse shi . "Ka manta alƙawarin da mu kai da kai" Ta faɗa tana langwaɓar da kanta . Daga zaunan da Inna take ta ce "baza ki je ba,namiji ce ke?" Kallonta Baffa ya yi ya ce "toh yanzu idan ban tafi da ita ba, sai ki ce ta dauko miki magana, ki yi hakuri na je da ita Innarmu" Ya karasa maganar cike da raha. Dan murmushi kawai Inna ta yi ta cigaba da aikin da take yi. Don ita halin Baffa ya dai na ba ta haushi dariya yake ba ta . Haka Baffa ya sa Faɗime a ga ba suka yi daji . Ita dai Inna jiran dawowarsu take yi, ta ga ko goyo ta ɗin zai yi,dan ba yau ya fara ba. Zaune suke a kan tabarmar kaba. Yanayin da ake ciki na damina ne ya kawata gurin, duk da cewa dare ne amma hakan bai hana hasken farin wata wadatar gurin ba. Ga wata sassanyar iska mai haɗe da kamshin kasa tana kaɗawa . Gurin ya dauki shiru na wani lokaci. Kafin Baffa ya yi gyaran murya,ya mai da hankalinsa kan Zahra sosai ,da ta yi kasa da kanta ,tana wasa da ya tsunta. Cikin harshen fulatanci ya fara yi mata magana ,saboda ya lura tana jin yaren. "Alhmdullah ,Allah muna ƙara miƙa godiyarmu gareka. Tabbas ban da iko da ƙudira ta Allah babu abin da zai tashe ki daga wannan dogon suma,da kuma raunikan da kika samu a mabanantan sassa na jikinki. , Amma ki godewa Allah da ya sa kika kubuta har kika samu lafiya ." Numfashi ya sauke sannan ya cigaba . "Yanzu zamu so jin tarihinki,da abin da ya raba ki da iyayenki har ki ka shigo daji kina gudun ceton rai,saboda musan ta wace,hanya zamu mai da ki ga iyayenki" Dara-daran idanunta ta lumshe sakamakon yadda suka bushe mata. A take wani irin gumi ya shiga tsatstsafomata . Zuciyarta ta shi ga wani irin bugu tarihinta, labarinta, so take ta yi magana, so take ko ya ya bakinta ya buɗe amma abu ya gagara . A hankali zuciyarta take curewa tamkar curin dawo,ji take kamar za ta faso ƙirjinta ta fito. Da ƙyar take iya fizgo numfashinta daga cikin huhunta. "Abiii.." Zuciyarta ta shiga maimaita mata sunan. "Muna sauraranki " Baffa ya fada gannin ta shafe lokaci mai dan tsawo ba tare da ta yi magana ba, gashi ita suke jira Da kyar ta iya haɗiye yawun bakinta, domin ta samu ta jika makoshinta da ya bushe,amma a banza domin kuwa babu aikin da ya yi mata. Kallon Baffa ta yi ta kuma mai da idonta kan Inna. Kamar an fisgo maganar daga,bakinta,ta ce "labarina ba shida dadin ji ba shida dadin tunawa . " Ina neman afuwarku ina mai baku hakuri,ba zan iya baku labarina a halin yanzu ba,saboda ina da tabbacin kafin na gama baku labarin wace ce ni , zuciyata za ta iya bugawa na mutu,kuma a yanzu ina bukatar na rayu saboda dalilai masu karfi ." "Abin da zan iya faɗa muku shine a kwatin nan ita ce sanadiyar komai" Ta ƙare maganar tana nuna wata madaidaiciyar a kwatin da take gefenta. A jiyar zuciya Baffa ya sauƙe sannan ya ce "kin ɗaure mana kai da yawa,akwai bukatar ko ya ya ne musan wace ce ke,saboda musan yadda zamu zauna dake,ba za mu ji natsuwa da kwanciyar hankalin zama dake ba ,alhalin ba musan wace ce ke ba." Jinjina kai ta yi ta ce "sunana Fatima Bintu Zahra,ana kirana da Zahra. kaddarata rikitacciya ce,kuma rudadiya . Kusa a ranku ba zan taba cutar da kuba" "Ina son zama daku,saboda a ɗan zaman da na yi a gidan nan, na lura ku nagartatu ne,domin na ga karamci. Baku san ko wace ce ni ba kuka tainake ni,ina son ku dauke ni kamar ƴarku wadda kuka haifa da cikinku,na yi muku alƙawarin yi muku biyayya tamkar yar cikinku." "Amma ba zan muku dole,domin ku zauna da ni ba, ba zan taɓa komawa gida a yanzu ba, saboda farautar rayuwata ake yi ta ko ina." Gyara zama Baffa ya yi, yana kallon ta cike da mamakin furicinta, "toh mahaifinki fa? Iya sunanki kawai kika fada mana" "Mahaif i " Kalmar ta yi dirar mikiya a kwanyarta. A take zuciyarta ta sake matse mata a kirjinta ,i take kamar zat a iya bindiga a ko da yaushe . "Mahaifi "t Ta mai maita a fili "ba ni da shi ba ni da baba ni" WANE NE SHI ? By Aisha Isah Musa (Ayeeshat Kissar) https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH YOUNG TALENTED WRITER’S ASSOCIATION . https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z I-D No....019 Pg 19 _____20 Bismillahir-Rahmanir-Rahim Baki Baffa ya bude yana kallonta, "kamar ya baki da mahaifi ? Ai ko shege yana da uba sai de aki jingina shi da kalmar." Wani bushashshen murmushi ta yi, wanda iya saman laɓɓanta ya tsaya . "Ku dauke ni a matsayin wadda ba ta da uban,ko kuma wanda ba a jingina ta da kalmar ba, ko kuma wadda wata ƙaddara ta yanke tsakaninta da mahaifinnata ". "Ka da ku matsa a kan sanin ko ni wace ce ni ko kuma abin da ya raba ni da gida, saboda bashi da amfani hakan." Shiru suka yi cike da mamakin kalamanta. Abun ya daure musu kai da yawa. Cike da fahimta Baffa ya ce "na fahimci zancen naki duk da akwai boyayyan al'amari,a cikin rayuwarki cike take da sarkakun zarurukan da ke kanki baki son suba,kuma ba za ki iya warwaresu ba,sai dai Allah ya warware miki." "Tabbas kaddararki ta na jone da ta mu ko kuma na ce da ta fadime amma lokaci zai bayyana mana komai ." "Kuma ni shaida ne a kan yadda ake farautar rayuwarki, ganau ne ni ba jiyau ba.Domin haka zamu zauna dake da zuciya daya ruwanki ne ki zauna damu haka,ruwanki ne ki ci amanarmu. A jikina nake jin kinsan ɗaci da zafin cin amana don haka,riko da ita ko facali da ita yana hannunki ." Juyawa ya yi kan Inna da take kallon Zahra, kallo me dauke da amalar tambaya da fassarori kala-kala. "Ko akwai maganar da ta yi karo da zaɓi ko son ranki,a cikin maganar da na yi ?shin kin aminta ta zauna tare damu ko kuwa?" ★★★ Hammad Cike da natsuwa yake tuƙa motarsa. Sassanyan kiɗa ne na tashi,a cikin motar.Fuskan nan babu walwala ko kaɗan,damuwa ta yi masa yawa ,ya rasa abin yi ,shine ya zaɓi kunna kidan ko zai samu sauki amma a banza. Cika bakinsa ya yi da iska mai zafi ya fesar . Ya rasa meyasa wasu mutanen ba su da adalci. A kan biyan bukatarka saika rusawa waƴen da ba su dogara da komai ba sai Allah,sai wannan farin cikin. Watakila ma shi kaɗai ya rage musu a rayuwa, amma haka zaka sa kafa ka murje shi. Lumshe idonsa ya yi a hankali ya buɗe ya karya kwanar da zata sada shi da gurin aikin su Ramadan . Ko da ya isa bai ko tsaya gyara praking ba,haka ya fito ya nufi ciki. Tun kafin ya karasa aka sanar masa da ya tafi tun ɗazu. Mugun ɓaci ransa ya sake yi. Ya koma cikin motar ya bar gurin . Tuƙi yake amma ya sha banban dana dazu,domin yanzu kamar motar ce ta yi masa laifin. Kafin ka ce mai kuwa ya isa gidansu Ramadan,saboda babu wani nisa tsakanin gidan da gurin aikin nasu. Kai tsaye bangaren nasa ya nufa. Yana shiga kuwa ya hangesa ya juyawa kofar baya da alama wani abun yake. Yana zuwa inda yake ya kai masa wa naushi iya karfinsa,cikin mugun zafin nama Ramadan ya yi kasa. Ai kuwa ya samu bango a take hunnunsa ya fashe, Ya shiga tsatstsafar da jini. Hankali tashe Ramadan ya yo kansa yana masa sannu .Juyowar da zai yi ya sake kawo masa daushin. ciki sa'a ya sameshi . Zubewa Ramadan ya yi yana dafe cikinsa. Tsayawa ya yi yana kallonsa,ganin yana ƙokarin raina masa hankali. Shi ya san ba cikinsa ya sama ba . Ganin yadda yake ta birgima a kasa yasa hankalinsa ya fara tashi, ya isa inda yake, ya dago shi cike da tsoran ka da wani abun ya sami abokim nasa,yasan ba wata cikakiyar lafiya ce da shiba . Ga ni ya yi jikinsa ya sake. Ya zazzaro idonsa yana jijjiga shi "Ramadan wai me ka ke yi hakane ka tashi mana , ba nason kalar wasan nan fa," Duk maganar da ya yi a banza saboda ko motsi bai yi ba. Kafin kace me ya haɗa uban gumi duk ya rikice. A hankali Ramadan ya bude idonsa guda ɗaya,ganin yadda duk ya koma kalar tausayi ne yasa ya kasa rike dariyarsa. Tuntsurewa ya yi da dariyar ,ya matsa daga kusa da shi da sauri. Kasaƙe ya yi yana kallonsa "amma wannan gayen ya raina masa wayo da yawa" Mikewa Ramadan ya yi ya cigaba da dariya. Shi dai Hammad bai tashi daga idan yake ba,kuma bai daina kallonsa ba. Kan kujera ya ɗane sannan ya ce "Sorry man, na san halinka da shegiyar zuciya kamar kuturu,ba ka ƙi a tashi hankalin ɗakin nan ba, shine na zaɓi na yi maka haka ,amma ka yi hakuri ka ji dan albarka ." Ya furta cike da shakiyanci . Mikewa Hammad ya yi ya jinjina kansa ."Ka yi da dan halak ka ji " Ya nemi guri ya zauna a daya daga cikin kujerun falon. "Mu yi zancen hankali ba na son shirme ka ji". Kau da wasa Ramadan ya yi daga kan fuskarsa sannan ya ce ina jin ka Boss. Meyasa da ka ga hoton nan,na ga tsoro da firgici a fuskarka? Ya a kai na ga yanayinka ya canza a lokaci guda? Kuma na kira ka kake mun kame-kame har ka gudo daga gurin aiki.?" "Duk saboda tsoranka ne Alhajinmu" Ramadan ya fada yana harararsa. Ɗan gyara zama ya yi ya ce" abin da yasa ka ga na shiga cikin wannan halin shine,na taɓa ganin wannan tambariin a zahiri!." Gyara zama Hammad ya yi da sauri yana kallonsa. Dan sauke numfashi Ramadan ya yi sannan ya ce "kasAn a ina? kuma gurin waye?" Girgiza kai ya yi da sauri cike da zakuwa ya ce a " gurin wa ka gani.?" "A gurin Barrister Safna! Wadda na yi maka maganar za ta shiga cikin case ɗin" Da sauri ya mike tsaye ya ce "ya a kai ka gani kuma ka tabbatar da irin shine sak?" Jinjina kai Ramadan ya yi ya ce "na tabbatar irin sa ne kuma na je gurin aikin ne saboda na kara tabbatar wa amma ita Safnar ba ta zo ba kuma na kira wayarta a kashe ." "Gashi ni ba sanin gidansu na yi ba,ya kamata mu samu cikaken bayani game da na hannunta tukuna." "Ya jikin yarinyar nan ta asibiti,zan je na duba ta anjima " A take fuskar Hammad ta sake canzawa,malolan takaici ya tsaya masa a nakoshi. Wani yawu ya haɗiye me kauri da daciya ce "Ramadan an cutar da rayuwar baiwar Allahn nan sosai, hakinsu kadai ya isa ya rusa wa wanɗanda suka yi duk wani shiri ko burinsu ." "Idan na kalli yarinyar sai na yi tunanin inda da Minal ya faru ya zan yi?" "Wai su masu yin wannan rashin kirkin basu da ƴaƴane ? Idan basu da su,basu da ƙanne? idan su ma babu,dole suna da iyaye mata, amma saboda rashin imani su tattala nasu su boyesu, su wulakanta na wasu sai kace su ba ƴaƴa bane ." "Wallahi wallahi Ramadan inda ina da damar kama ire-iren mutanen nan saina gana musu a zabar da sai sun yi nadamar rayuwa a doran duniya.Su din anoba ne rayuwarsu ba ta da amfani a doran kasa" Da fa kafadarsa Ramadan ya yi ya ce "suna da ƴaƴa,suna da ƙanne kuma suna da iyaye,rashin sanin darajarsu ne da burin duniya da yake rufe musu ido" Ina jin abin da ka ke ji amma ina so ka gane wani abu, komai sai an bishi a hankali and hannu daya ba daukar jinga,kuma komai sai idan akwai hujja,ba mu da masaniyar akan su waye suka lalata rayuwar yarinyar nan, amma ina ɗan sandan da aka kawo ta da shi?." Taku biyu Hammad ya yi daga inda yake yana jinjina kansa "na sani na kuma fahimci nufin ka. Jamal Abdulazez ne fa." Zaro ido Ramadan ya yi a take wani murmushi ya subuce masa ya ce "Wow amma wannan abu ya kayatar da ni, Jamal dai dana sani wai Zaki fa?" Taɓe baki Hammad ya yi ya ce " sai ka ce wani abu duniya,shine ma ya tsinci yarinyar fa" "Yanzu ta ina za a fara ne?" "Da hannunka da ya fashe zamu fara." Harara ya watsa masa sannan ya ce"wai kai dole sai ka saka wasa a komai naka shege kawai" "wasan me na saka Malam Sardauna ? Kawai dan nace a duba maka hannunka ?" "Eh nawa ne ko naka ?Ai ni najiwa kaina karka dame ni ni ba karamin yaro bane zan iya kula da kaina." Ɗan taɓe baki Ramadan ya yi ya ce "kana likita amma kana wasa da lafiyarka,ko dan kana da ishashiyar lafiyar shine baka san darajar taba oho." "Zan sake kiran Safnar idan anjima,dan ta kama ma har gidansu zan nema dan ban taba zuwa ba ." "Kuma sai na gayawa Mami na ce yau kusa halaka mata tilon danta namiji kayi ." Kafaɗarsa ya daga alamar ko a jikinsa "Idan ka fasa zuwa din,nasan ba za ta taɓa yarda ba,idan ka sameta duk yadda ku ka yi zamu yi magana." "Yanzu bari na je gida Daddy zai sani aiki,kasan jiya Tariq tsorata ya yi ta yi cikin dare,sai a dakina ya kwana. Kasan shi da shegen tsoro shine wai Daddy Police zasu zo su yi bincike a kan abin da ya tsorata shi sai kace yau a ka fara." "Duk da na. ce masa ya barshi kuma da alama ya yarda,amma gwara na je kar ya turosu ɗin" "Ana yawan yi fa a sashin masu aiki ,kuma ana zuwa a bincika ɗin,amma a banza babu abin da ake samu sai takaicin tambayoyin da suke addabata da su kamar ni a ka tsorata." Yar dariya Ramadan ya yi "Malam Tariq kenan kura ga tsoro ga ban tsoro. Ya ya tashi ne? Na sansa da shegen tsoro ". Dariya shima Hammad ya yi duk da halin da yake ciki . "Yau biyayya yake min ba kama hannun yaro,ya musulinta ai ,sai kuma nan da ƴan kwanaki zai koma Tariq din shi wanda ya san yancin kansa. " Dariya Ramadan ya yi ya ce"Tariq nawa inda yake burge ni ya san ƴancin kansa. amma lamarin gidan nan naku ya na daure kaina anya babu wani abu a ƙasa?" WANE NE SHI ? AYEESHAT KISSAR https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z YOTA....O19 Pg 21____22 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Numfashi Hammad ya sauƙe ya ce"Ni ma na yi tunanin hakan,koma mene ne Allah ya bayyana mana abin da yake a ɓoye." "Ameen ya rabbi, mu je gidan na duba oga Tariq " Motar su ka shiga su ka dauƙi hanyar zuwa gidan . A hanya Hammad ya yi (dressing)ɗin hannun nasa . Sun ɗan daɗe suna danna hon kafin Mai gaɗin ya zo ya ɓuɗe. Tun kafin Hammad ya yi magana Inyamurin Mai gadin ya fara magana, "I'm sorry oga na shiga toilet ne cikina ne ya Autsine " Harararsa Hammad ya yi ya ce" Ina gab da canza ka a gidan nan tun da baka da amfani, kashi-kashi kamar fara,ba ka da wani amfani ba dan guards ɗin da,suke zagaye da gidan nan ba ban san mai za ka yi ba ." "Sorry Sir" Ya faɗa yana ƙara rage tsawonsa. Girgiza kansa ya yi kawai ya wuce ciki, dama tuni ya fito daga cikin motar. Lekowa Ramadan ya yi ya ɗaga ma sa hannu. Da sauri ya karasa inda yake. "Oga Oga" Ya ce yana miƙa ma sa hannu su gaisa. Riƙe hannun nasa Ramadan ya yi cike da tsokana ya ce "An zo aiki an bige da zagayen banɗaki a canza hali dai." Dariya Danial ya yi ya leƙa bayan Hammad . Ƙasa ya yi da murya ya ce"Oga fadansa ya yi yawa ka ce masa ya dai na .." "A'a sai dai kai ka gaya masa da kanka ko na baka number dinsa ?Idan ba za ka iya fada masa gaba da gaba ba ." Da sauri Danial ya bar gurin ba tare da ya ce komai ba. Tuntsirewa Ramadan ya yi da dariya ya ce"Hammadu mazan gaske" . Gyara parking ɗin ya yi kafin shima ya shige falon da sallama a bakinsa. Tariq ya samu a kwance saman kujera ya na danna wayarsa. Hannu ya miƙa masa su ka gaisa,cike da raha ya ce"Malam Tariq ya jiki na ji labarin abin da ya faru jiya, Allah ya kiyaye gaba ya kauda bacin rana". Zaune Tariq ya tashi ya kara ɓata fuska "kai dai bari jiyan nan ni ka ɗai na san abin da na gani,ka sa bacci na yi ni kaɗai nasan abin da na ga ni wallahi" Ya yi furucin yana ya mutse fuska, kamar ze fashe da kuka. Gyara zamansa ya yi ya haɗdiye dariyar da ta ke ƙokarin subuce ma sa, ya ce "Babbar magana abin har ya kai haka kenan ,sannu Tariq don ma kai jajirtacen jarumi ne,wanda yasan ƴancin kansa. Shi wannan tsoran bai san kai degree holder) ba ne? Abun sam babu daɗi Allah ya sa mudace." "Zaro ido Tariq ya yi ya ce "don Allah ka rufa min asiri kar ka ja min,ni tsoro ma na ke ji " Kwashewa ya yi da dariya sai da ya yi me isarsa sannan. ya ce"Na bari "Ina Mommy da Minal?" "Mommy ba ta nan Minal kuma ba ta daɗe da shigewa ɗakinta ba." Miƙewa Ramadan ya yi ya ce"Bari na duba ta killa ma ta na can Ta na baccin bayan la'asar. Bai bi ta kan Hammad ba ya nufi ɗakin Minal. Karo suka kusa yi. Ya ja baya da sauri. "Mee" Murmushi ta ɗan sakar masa itama ta ce "Barrister" "Na'am kiin daina son Barrister naki ko?" Taɓe baki ta ɗanyi ta ce"Wai ba ne ce ma ka ni babu aure a tsarina ba?Ta fada ta na baro inda yake ta nufo hanyar Falon. Biyo bayanta ya yi yana faɗin "haba rabin ran yanzu idan baki yi aure ba ya zaki yi ki samu magaji? Dariya ta yi ta ce" wannan ya daina dumunka ai Dr zai yi aure idan ya haifi ɗa sai ya bani na raini yaron ko yarinyar" Ta furucin da iyakar gaskiyarta . "Eh ga Muhammad Hammad sarkim mahaukata ko?" Hammad ya faɗa yana zama acan gefe. Waro ido ta yi ta ce "yanzu Dr ba za ka bani ɗanka na rainan maka shi ba? Ni ce fa." "Eh kedin,kowa ya haifi nashi" Zunburo baki ta yi ta ce"Mommy da Daddy amd Tariq da su Sauban,sun isheni rayuwa, tun da na fahimci kai ba kauna ta kake ba." Ta ɓe bakinsa ya yi ba tare da ya tanka mata ba."Tariq ko ka ga laifina?"No kina da freedom na yin rayuwarki yadda kike so" . Murmushi ta yi masa ta jinjina ma sa hanunsa alamar like. Kafin ta lumshe idanunta ta jingina da jikin kujera. Kallon Tariq Ramadan ya yi ya ce "mutumin ya wasa kwana biyu mu na ta baku kaya ko?" Kallonsa ya yi ya ce "Ai har abada Barcalona ta na ƙasan Madrid,ku gama duk abin da zaku yi mun ara muku wannan shekarar kafin mu juyo kanku." Dariya Ramadan ya yi ya ce"ka ce dai kawai kun yi laushi a hannun yara masu aikin manya. "Ai har abada jinin messi ba zai taɓa faɗuwa ba,Yamal ya riga da ya sha gaban duk wani ɗan ƙwallo dake Madrid" Dariya Tariq yi ya ce " Mai ya kawo maganar Messi kuma? Ko so kake na tuna maka da shugaba ne?Minal na so ace a zamanin Pepe da Ramos, wannan yaron ya zo wallahi, da tuni sun share mana hawayenmu a kansa" "Waƴenan ai mahaukata ne, kwata-kwata ba su da kai" Ramadan ya faɗa yana ɗan ya mutse fuska. Haka dai suka cigaba da musun ball,Ramadan sai shakawa Tariq ya ke yi, saboda a shekaran jiya aka yi wasa tsakanin Real Madrid da Bacarlona, Bacarloma suka ci 4 0. Shikuma Tariq ya na ta ƙoƙarin kare kansa. Wani iri ta ke jin zuciyarta,,wannan kallon da ta yi mata ya tsaya mata a zuciya..Duk da yanzu ba daɗewa ta yi waya da gayen nan ,ya ce mata babu matsalar komai, amma haka kawai ta kasa natsuwa, ji take kanar wani abu zai faru. Gabanta ne ya tsananta bugu da sauri -sauri. Shiru ta yi tana jin yadda zuciyarta take dokawa amma ba ta yi koƙarin yin addu'a ba .Ta na jin yadda Ramadan yake ta zuba amma ta kasa tanka masa,duk surutu irin na ta. "Mee ki na lafiya?"Ramadan ya tambaya ya na kallonta,ganin sai surutu ake yi ban da ita, kuma sare yasan halin ta,da yanzu sai ta fi kowa zaƙalkalewa,musamman da ya zama team ɗin su daya da Tariq. Buɗe idanun ta ta yi da suka kaɗa suka yi ja ta ce "eh mai ka gani?" Ta fada tana son ɓoye damuwarta. Babu komai yanayin kine na ga ya sauya." Murmushi ta ɗan yi ta ce"bana jin dadine kaina ne ya ke min ciwo" "kin sha magani?" Ya muste fuskarta ta yi ta ce"ba na son shan magani" "Dan Allah ki sha kin ji" "Zan sha idan na tashi'" "Ok ki sha dan Allah" Jinjina masa kai kawai ta yi don ba za ta shaɗin ba.Wata uwar harara Hammad ya watsawa Ramadan, haushin zaƙewar nan tashi yake ji. Ai dodonsa ta kusa dawowa. Mai da idanunsa kan Minal, ya yi amma bai yi magana ba, ya cigabaa da abin da yake. Jin hayaniyarsu tana hau mata kai ne yasa ta miƙe ta nufi ɗakinta.Sai da ta zo saitin da Hammad yake ya ce "meke damunki" Juyowa ta yi ta kallesa,ta girgiza masa kanta, ba tare da ta yi magana ba ta wuce. A hankali ta tura kofar ɗakin ta shiga . Kai tsaye ta wuce inda kayayyakin zanenta suke. Samun guri ta yi ta zauna. A natse take bin ɗakin da kallo,komai na ɗakin pink ne me haske . Ba ƙaramin kyau ɗakin ya yi ba. Don kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da annarka dukiya wajen shiryashi.Ɗaki ne kamar duniyar katun. A hankali ta mai da idonta kan abin da take ta soma zanen. Wannan shine abin da yake ɗebe nata kewa mudin tana cikin kunci . Ya kuma saka ta farin ciki da walwala. Raywar gidan Alhajji Mansur kenan, babu mai kula da mai kake yi, ko meza ka yi a cikin gidan, komai ka yi daidai ne,babu ruwan Mommy ko Daddy.Haka kawai duk abin da ka yi daidai ne. Sosai ta duƙufa ga abin da ta ke yi, ta bada dukkanin natsuwartta a kan shi,kafin kace me kuwa murmushi ya maiye damuwar da take ciki. Ta ɗauƙi tsawon lokaci tana abu ɗaya kafin kiran wayarta ya katse abin da take yi . Video call ne Ɗagawa ta yi fuskarta ta kara faɗaɗa da murmushi. Ba ta ce mata komai ba har tsawon wasu mintuna.Hannu Minal ta kai saitin idanta,da sauri ta kiftasu.Ta kuma zubawa Minal ido ba tare da ta yi mata magana ba. Kawar da fuskarta Minal ta yi a sanyayeta ce "say someting mana"Sannu a hankali ta buɗe bakinta cikin faransanci ta ce "Meke damunki?" I don't know,kawai dai bana jin daɗi ne,ki dawo dan Allah". "Kin yi kewata ne?" Matar ta faɗa tana kallonta "Sosai ma ki dawo, ina son na ganki" Karo na farko da matar ta dan saki murmushi ta ce" ni ma ina son ma ganki,kin yi sallah?" Shiru ta yi ba ta tanka ba "Ok ajiye min waya" I"m so sorry zan yi" Miƙewa ta yi ta ce"Kalli "ta faɗa tana nuno mata zanen matar da ta yi. Fuskarta ta fito raɗau. Matar kan bola ce,ta yi kyau sosai. Kallon hotom ta yi a take zuciyarta ta buga da masifaffen karfin da sai da ta dafe ta ta ce "Wace ce wannan?" WANE NE SHI ? AYEESHAT KISSAR YOTA....O19 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. 23____24 https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z "Ba ki santa ba,idan kika dawo zan baki labari." Jinjina kai Nihal ta yi,ba tare da ta ce komai ba. Kashe kiran ta yi ta nufi banɗaki dan dauro alwala. ★★★ Rugar arɗo "Adda..! Adda..!Adda..! Ki fito mu tafi kar a cike gaba-gaba a nan zamu zauna" Fitowa ta yi daga bukar jikinta sanye da riga da zani na saki. Fitowa Baffaa ya yi shima daga baɗaki,hannunsa rike da buta. Ya ce"Faɗime saura ki je ki yi dambe,ki kula sosai kema"Ya faɗa yana kallonsu cike da burgewa,sun yi kyau sosai.Kama hannu Zahra Faɗime ta yi ta ce"kar ka damu Baffa ko dukana aka yi ba zan rama ba" Dariya Baffa ya yi ba tare da ya tanka maganarta ba,saboda ya san karya take."Ina nan dawowa nima" Tom suka ce suka nufi hanyar fita. A hankali ta zura kafarta waje. Wannan shine karo na farko da ta fara fita daga cikin gidan. Ba a ainihin Rugar suke ba, sun ɗan fita daga gefe. Kallon Zahra Faɗime ta yi da take ta zabga murmushi ta ce "Wai Farin cikin duk na zuwa kallon shaɗin ne?" Shiru Zahra ta yi ba ta tanka ba saima cigaba da murmushin da ta yi?" Kin yi shiru" Ta faɗa tana ɗan jijjiga hannuta da take riƙe da shi. Zabura ta ɗanyi dan ita gabaɗaya hankalinta baya kanta. "Tunanin me kike yi?"A bakacin ta ba ta amsa sai ta ce"garin ku yana da kyau sosai"Dariya Faɗime ta yi ta ce"ina kaunar rugarmu sosai ba na son wani abu ya yi sanadiyar da zan bar ta,ko aurar da ni Baffa zai Allah ya sa ɗan rugar nan ne zai aure ni" "Dan ma baki shiga cikin dajin sosai ba,ko mu bi ta baya ne? Ta fi sauri ma" Girgiza mata kanta ta yi ta ce "A'a mu bi ta cikin garin ina so na ga yanayin garin naku" Jinjin kai Faɗime ta yi suka cigaba da tafiya ta cikin rugar. Sai suka zama abin kallo wajen tsirarin mutanen da ba su je kallon shaɗin ba. Duk inda suka gifta sai a bisu da kallo ba a san Zahra ba, gashi babu damar yin magana,yanzu Faɗime sai ta zazzaga maka rashin mutunci. Ita ƙa'idarta kowa ya santa a cikin rugar nan ba a shiga shirginta,idan ba haka ba ta yi maka wani shirmen sai dai ka yi hakuri. Mudin dai da wanda ta girma ta yi faɗa,toh Baffa cewa yake yi ai shi bai haifi raguwa ba.Idan ma ita aka zane sai ya ce babu ruwan shi. A haka suka karasa gurin da ake yin gasar shaɗin. Gurin ya cika sosai da sosai. Tsuka Faɗime ta yi dama ta sani mutane za su yo sauri su cike gurin,domin akwai dabi tsakaninsu.Ta shiga kutsawa har sai da ta samu guri suka zauna. Kamar yadda ta ce da faɗa da komai a gaba-gaban suka zauna. Kallon Zahra Faɗime. ta yi ta ce"Adda kin ga wancen sune ƴan rugarmu,su kuma wayen can ba yan rugar nan ba ne." "Wanna shi ne ɗan gidan sarkin shanun yankin nan,kuma fa ba sa shiri kwata-kwata,wani lokacin ma yaƙi ne yake raba su da juna,faɗan tun kan iyayensu ne ba tun yanzu ba." Cigaba da nuna mata ta yi ga Mai gari da jama'arsa,dama kuma shine baban Jaeh. Can gefe guda kuma ga Baban Buba can sarkin shanun yankin.Shima da tawagarsa,ga kuma tawagar Buba da ta Jaeh, ga sauran dattijan rugar,da sauran mutane abin gwanin sha'awa. "Kin ga wancen shine Jaeh, babban ɗan Baffa arɗo, shi nake so ya cinye saboda shi take so.Buba ba shida mutunci ko kaɗan sai ya yi tayiwa manya tsawa,don ma baki gani ba, kin gane?" Gyada kai Zahra ta yi ta ce "na fahimta sosai,sarkin surutu" Ta ƙare maganar tana maida hankalinta kan bulalen da ake ta gyarawa ana jiran alƙalin wasa ya bada umarni a fara. Umarnin farawa a ka ba da. Ƙa'ida za a yi maka bulala amsin ne idan ka yi ihu ko hawaye ko guduwa ka faɗi,ko da kuwa ana na 49 ne. Nan aka fara,mamaki da tsoro ne suka cika Zahra ganin yadda ake yin duka babu alamar tausayi ko jinƙai,amma haka wanda ake duka yake shanyewa, ba zai ko motsa ba. Ba iya alkale bane ke irga bulalar da ake shimfiɗawa babban ɗan mai gari ba ,har da mutanen rugar Mamaki da al'ajabi ne ya sake cika zahra, ganin har an yi masa bulala 35 ba tare da ya nuna alamun yana jin dukan ba, kasancewar ba ta taba kallon gasar ba. Faɗime kuwa sai tsale take yi,tana kara koɗa Jaeh. A tare suke lisaafi "arba'in da biyar, arba'in da shida,arba'in da bakwai da takwas da tara hamsin." Wani irin ihuuuu gurin ya dauƙa aka shiga tsale- tsale da kiɗe-kiɗe,ana ƙara koɗa jarumtar Jaeh. Wani irin farin ciki ta tsinci kanta a ciki mara misaltuwa. Nan alkalin gasa ya fito ya ba da sanarwar, Jaeh ya cinye gasa zagaye na farko,za kuma a ƙara saka ranar da zai rama dukan nan a jikin abokin takararsa,domin banbance gwanin da zai iya karɓar ragamar rayuwar masoyiyarsa. A hankali aka fara watsewa zuciyoyin mutanen rugar cike da farin ciki. Miƙewa su Faɗime suka yi domin komawa gida. Kallon Zahra ta yi ta ce "Adda mu je gidansu Chubaɗo mana,ban ganta a gurin shaɗin nan ba" Girgiza kai ta yi ta ce ba ta yarda ba. Magiya ta yi ta mata daƙyar ta amince suka nufi gidan nasu. Da sallama suka shiga sai dai babu wanda ya amsa kasancewar duk ba su dawo ba. Kai tsaye suka shiga cikin ɗakinta. Zaune take ta sunkuyar da kanta ƙasa,tana wasa da ya tsunta. Da sauri ta ƙarasa inda take,ta sunkuya ta ɗago ta. Hawayen da ke kwance a kan fuskarta ta shiga share mata. "Waye ya ta ɓaki? Me aka miiki?Ko Dada ce?" Girgiza kanta ta yi da sauri, ba tare da ta kalle ta ba ta ce"babu wanda ya mata komai" Harara ta watsa mata. Tasan Dada ce zata yi mata wani abun. "To ya baki je gurin shaɗin da aka yi ba?" Gyara zamanta ta yi,ta kalli turtsetsen cikinta, ɗam kimanin wata shida,sai dai kamar ya yi wata 8 ta ce"ba na son shiga cikin mutane,ba na jin daɗin abin da suke yi min kin san mutanen rugar nan ai" Waro ido Faɗime ta yi ta ce "ba su ji gargaɗin da na yi musu a kanki ba ko?Cigaba suka yi?" "Ba za ki iya hana mutane faɗar abin da ke ransu ba,za dai ki iya yin iya ƙokarinki,ni babu wadda ta sake yi min wani abu,ni ce nake tausayin kaina,da abin da zan haifa,ban san irin rayuwar da zai yi ba." Ta faɗa tana ƙokarim danne kukan da ya zo mata. Mai da idonta ta yi kan Zahra da har yanzu take tsaye bata zauna ba ,sai ma bin su da ido kawai da take yi. Murmushi ta sakar mata,ta matsa mata kusa da ita domin da zauna.Sannan ta gaisheta amsawa ta yi cikin sakin fuska. Sai da suka gama gaisawa sannan ta kalli Faɗime ta ce,"Kin manta kin zo da baƙo ne ?" Girgiza kai ta yi cike da takaicin abin da ake yi wa Chubaɗo ta ce"Ina sane ke ce ki ka dauke min hankali" Ta faɗa sannan ta ja bakinta ta tsuke,kamar ba ita take magiyar a zo gidan ba. Hira suka ɗan cigaba da tabawa sama-sama,kafin Faɗime ta ce ta tashi su tafi. Miƙewa Zahra ta yi, ta yi wa Chibaɗo sallama suka fito.Hanyar gida suka yi babu wanda ya kula wani a cikinsu. A jima A jima,sai Faɗime ta ja tsuka.Ita dai Zahra bata kula ta ba har suka kusa kaiwa gida. Tsayawa Fadime ta yi cak! Saboda yanayin da take ji yana ratsa ta. Gabanta ne ya faɗi. Ta Basar ta ce "Kin san wani abu?"Gigiza kai Zahra ta yi ba tare da ta tanka ba. "Mutanen rugar nan ba suda mutunci da tausayi ko kaɗan" Zaro ido ta yi , ta kasa kunne tana jiran karin bayani. Dafe kanta ta yi, ta cigaba. ''Kaf rugar nan babu wanda yake ƙaunata ban da su Baffa irin Chubaɗo,ita kaɗai ce take cewa kar na yi na hakura na ƙi yi." Share hawayen fuskarta ta yi ,ta cigaba "Su basu san kaddara ba ,daga kaddara ta faɗawa mutum shi kenan sai a hukunta shi da abin da ba shi da ikon canzawa kansa ,ba kuma shi ya daurawa kansa ba" Shiru Zahra ta yi ba ta tanka ba,sai mamakin kalaman Fadime da suka cika mata zuciya. "Kin san mai ya faru da ita?" "A'a sai kin faɗa" Zahra ta fada tana kallon Faɗime da take ta sauke numfashi kamar mai wani ciwon. "Sule shi ya fara neman aurenta,sai wani ya zo daga rugarsu Adda (mamanta)shima yana sonta,shine aka shirya shaɗi,da aka yi sai wancen ya cinye,na manta sunansa,bayan sati daya aka daura auren ya tafi da ita can rugarsu.." "Ranar da a ka kaita ƴan bindiga suka shigo rugar tasu suka kora shanayensu, suka kashe dayawa daga cikin mazan rugar. Ita kuma suka keta mata haddi,a gaban angonta,shi kuma suka kashe shi" "Hakan bai ishesu ba suka sakawa rugar wuta suka ƙona ta kurmus." "Suka tarkata su suka yi daji da su,cikin ikon Allah wasu daga ciki suka kubuta sakamakon baccin da suka kwanta saboda kayan mayen da suka sha." A cikin waƴen da suka kubuta har da ita,ta dawo gida baki ga jinyar da ta yi ba. Bayan ta ji sauƙi kuma sai aka ce wai tana da juna biyu , babu yadda Dada ba ta yi ba na son ta zubar da cikin amma yaƙi zubewa, wai saboda kar ta ja mata abin kunya,shi ma fa sai da ta yi cuta sosai, kamar za ta mutu kuma ta ji sauƙi. "Shine mutanen rugar nan suke ta tsangwamar ta duk inda ta je sai an zageta,ba ki ga irin cin mutuncin da suke yi mata ba, har da jifa da zuba mata ruwa wani lokaci, ba ta da damar ta fita ko nan da can wani ko wata ba su yi sanadiyar zubar hawayenta ba.Wai ta yi abin kunya,sai da na fara rama mata idan suka yi mata wani abun tukunna suka rage " *Amma a haka Dada take nuna mata bata sonta baki ga abin da take yi mata ba wai duk dan saboda cikin ya fita." "Baffa yana yawan gaya min karda na bari wani ya cutar da ni mudin a kan gaskiyata nake." "Na taimaki wanda zan iya da abin da Allah ya ba ni" "Baki ji tausayimta ba don Allah?" WANE NE SHI ? AYEESHAT KISSAR YOTA....O19 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. 25__26 https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Mamaki ne ya cika Zahra, ta ce "waye ya gaya miki wannn maganar haka?" Jim ta ɗanyi sannan ta ce Adda Chubaɗon ce ta gaya min komai" Share ƙwallar da ta gangaro mata ta yi. Ta ji matukar tausainta, amma meyasa ta zaunar da Faɗime ta bata wannan labarin?Gaskiya ta yi wauta,ko da yake ita ma yarinya ce karama,don a ƙalla ba za ta wuce shekaru sha biyar ba,tabbas bawa baya taɓa kwaucewa kaddararsa,wannan zagayawar kawai da ta yi ta fahimci akwaitsantsar jahilcin dake dawainiya da mutanen rugar. Zubawa Fadime ido ta yi da take ta faman rangaji kamar zata kifa, ta ce"Kina lafiya?" Ta ɗago idanunta da suka canza launi daga farare zuwa wani irin launi da ta kasa tantance wane irin nau'i ne. Damƙe hanunta Faɗine ta yi da take riƙe da shi da karfin gaske,ta rufe idanunta ta buɗesu a hankali ta juyasu,ta cije gefen bakinta,sakamakon azabar da take ratsa ta. Jini ne ya zubo mata dagaa hancinta da gefen kunenta.Bata tanka mata ba ta zare hannunta daga nata ta nufi kofar shiga gidan,sai dai kafin ta ƙarasa jiri ya ɗebeta ta yanke jiki ta faɗi,wani irin abu mai yauƙi yana fita,daga bakinta. ★★★ MAFARI. Zaune suke cikin babban falon gidan kowa yana harkar gabansa,duk da sanyin damunar da ake yi sakamakon ruwan sama da aka sheƙa cikin dare. Kasancewar yau weekend ce duk suna gida. Kalon Minal Tariq ya yi da ta takure saman kujera ta yi shiru, duk da ba wata hira ake yi ba, amma suna yi sama-sama,abin mamakin yauma shiru kamar ba Minal ba . "Tawajena ya dai" Ɗago runannun idanuwanta ta yi,tta zuba masa,sai dai ba ta ce da shi komai ba,ba kuma ta yi masa murmushin da ta saba yi masa a duk lokacin da ta kalli wani ko za ta yi magana da kai ba. Mai da kanta ta yi ta kwantar ta lumshe idanunta,zuciyarta ce take yi mata wata iriyar dokawa ga fargabar da take ratsata tun jiya, ba ta wani samu ishashshen bacci ba. ji take yi kamar zata rasa wani abu mai mahimmaci a gareta, kamar wani abun zai faru,kamar zai faru da ita ko waninta.Sosai ta tsunduma duniyar tunani da har ba ta san Tariq ya cigaba da tambayarta ba. "Auta kina lafiya kuwa?"Tariq ya faɗa ganin sai magana yake yi mata ta yi shiru ,kuma yasan hakan ba halinta ba ne . "Eh ina lafiya"Ta faɗa a ɗan hasale. Girgiza kansa ya yi ya ce"ni na tambayeki ai" "Toh ina ruwanka da damuwata?Ko rayuwata,mai ya dameka da duk wannan ɗin?" A fusace ya ce" dan na tambayeki shine zaki gaya min magana?Babu ruwana dake dama" "Eh ina ruwanka dani?" Faɗa suka cigaba da yi,sai dai babu wanda ya tanka musu.Minal daga kwancen da take rungume da Mejor(magenta) take ta faman yi nasa rashin kunya,shi kuma abin har ya kai masa tashi tsaye. Daddy bai tashi shiga faɗan ba sai da ya ga Tariq ya yo kanta da nufin dukanta, Hannunsa ya sa ya kareta sannan ya ce"Ahirr ɗinka karka kuskura ka taɓa min ƴa" "Amma Daddy ka ji abin da take cemin fa,daga tambayarta" "Toh ina ruwanka da ita ɗin?Kuma kamata ya yi ka yi mata uziri,tunda ka ga ba ta yanayi mai daɗi" "Amma Dadd..." Hannusa Ya daura a kan bakinsa ya ce"Ka yi hakuri, ni na wakilceta, kasan mace ce tana da rauni" A fusace ya yi hanyar fita, a ransa yana tunanin anya ba zai fara saka kayan mata ba, idan Minal ta yi masa rashin kunya su daku su fidda raini. Har ya kusa kaiwa bakin kofa, ya ji sautin tsukarta.Dawowa ya yi ya ce"Daddy ka ji ko,Mommy kina jinta ko?" Sai a lokacin Mommy ta ɗago daga karatun jaridar da take yi,ta ce "Auta ba kyaji,kai kuma ka yi haƙuri" Guri ya samu ya zauna yana jiran ya ji ta sake tanka masa ya sauƙe mata abin da yake kansa. Harara Daddy ya watsa masa,shi ba zai iya yiwa ƴar uwarsa uziri ba?Kuma mace ce ai tana da rauni. Minal dai bata tanka ba sai ma juya masa ƙeya da ta yi,ita kanta ba a sanranta ta biye masa ba,kawai dai ranta ne a ɓace. "Minal kin yi magana da Nihal kuwa?Kwana biyu ba ta daga wayata,ta yi fushi da ni, don na ce ta dawo Najeria" "Eh Daddy na yi magana da ita jiya ,tana lafiya"Jinjina kai Daddy ya yi ya cigaba da amsawawi Yar dariya Mommy ta yi tace"Nihal manya ni kuma ta ce.min ta na nan zuwa karshen watan nan." Hammad dai yana gefe , bai ko kalli inda suke ba,bare ya tanka su. Sai yanzu ma da ya ji anyi maganar Nihal ya ji kamar ya tofa,amma kawai ya sharesu.. A ranshi yana burin ta dawo don ya yi kewarta sosai. A zuciyarsa ya ce"na daɗe ban ga yar rainin wayo irin Nihal ba. Wayar Minal ce dauki ruri,,ba ta daga ba,har kiran ya katse,aka sake kira,banza ta sake yi da wayar,domin ko ɗagowa ba ta yi ba bare ta duba wake kiran. Hankalinsu ne ya koma kan T.V ɗin dake banne a bangon ɗakin sakamakon abin da yake fita daga cikinta. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! A dai-dai lokacin da aka buga gangar siyasar ƙasar nan,tare da tabbatar da Alhaji Abubakar Yakubu Ɗan Gaske,, mataimakin shugaban ƙasa, a matsayin zaɓaɓɓen ɗan takarar shugabancin ƙasar nan, sai dai kash! A dai-dai wannan lokaci ne aka samu rahoton ɓatan tilon ‘yarsa, Zahra Abubakar Yakubu Ɗan Gaske. Wannan labari ya tada ƙura matuƙa a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ikirarin cewa shi yasan inda ya ɓoye ta kuma zai fito da ita a lokacin da ya ga dama. Wasu kuma na cewa tsafi ya yi da ita domin samun nasara a zaɓen da ke tafe. A yayin da wasu ke ci gaba da yi mata addu’ar Allah Ya bayyana ta. Kowa dai na faɗin albarkacin bakinsa game da lamarin." Numfasawa matar dake karanta rahoton ta yi, sannan ta ci gaba da cewa: “Abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa abin mamaki ! Rundunar ‘yan sandan F.C.T Abuja ta fitar da rahoton kubutar wani babban ɗan ta’adda, Mahmud Abdullahi, wanda aka fi sani da Barde, ko na ce Tiger, daga gidan gyaran hali na Kuje Medium Security Custodial Centre, ba tare da wa’adin fitowarsa ya cika ba.” "Rundunar ‘yan sandan ta ƙara da cewa suna nemansa ruwa a jallo, tare da saka gagarumar kyauta ga duk wanda ya yi nasarar kama shi ko ya bayar da sahihin bayanin da zai kai ga damƙeshi." "Anan ma sai dai a ce: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. A daren jiya ne ‘yan bindiga suka kai hari a ɗaya daga cikin ƙauyukan Jihar Katsina, inda suka kashe manyan magidanta har guda 23, sannan suka tafi da mutane sama da 35. Muna kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su tashi tsaye domin ganin an kubutar da waɗanda aka sace. Ana wata ga wata, salati za mu yi ko kuka? A daren jiya ne aka kai hari ofishin jakadancin Jamus, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata.A cikin waƴen da suka jikkata harda ɗan gidan shugaban hafsun sojojin ƙasar nan. Tsit falon ya yi na tsawan sakan ɗaya, biyu ,uku, kamar mutuwa ta gifta. Miƙewa Daddy ya yi da sauri kamar an tsikare shi ya ce"Ya ya aka yi maganar nan ta fita ,wannan wane irin hauka Abubakar ya yi?Zai samu matsala babba fa akan batan yarinyar nan wallahi" Daƙyar Mommy ta kalli Daddy ta ce"Yaushe Zahran ta dawo da har aka sace ta ? Ima jin wancen satin Hajiya Rukayya ta turota ta gaishe ni" Numfasawa Daddy ya yi ya ce"sun hana asanar ne"A fusace ta ce"kamar ya yanzu ƴar Abubakar ɗin ce bamu da ikon sanin ta ɓata sai dai mu ji a duniya? Girgiza kai Daddy ya yi ya ce" ba za ki gane ba Hajiya,mukanmu bamu tabbatar da sace ta aka yi ba sai daga baya,mun yi zaton wani gurin ta tafi,sai daga baya aka turowa Abubakar sako,kuma sun ce kashe ta za su yi" "Sannan kuma sun gargaɗi ka da mu kuskura mu gayawa wani, ko da kuwa iyalanmu ne , faɗan na iya janyo matsala. Shiyasa ban fada muku ba,amma ku yi hakuri ,bari na je gidan Habun" Numfasawa Mammy ta yi ta ce"Tariq ɗako min makolin mata na je gidan Hajiya Rukayyar" Toh ya ce ya tafi ɗakin domin ya dauko. Hammad da ya miƙe tsaye ne saboda mamaki, jikinsa duk y yi sanyi ya ce "Allah ya bayyana ta ya tauna asirin waƴen da suka sace ta" Tarkacensa ya shiga kwashewa yana maganar zuci, yanzu abun ya yi girman da ƴar mataimakin shugaban kasa za a sace,toh talaka ya ce mai?Gabaɗaya mamaki ya cika shi. Kira ne ya sake shigowa wayar Minal a karo na huɗu,a hasale ta ɗaga don ta ji waye haka. Kara wayar ta yi a kunnenta ba tare da ta ce komai ba. Secon ɗaya,biyu,ta miƙe a raza ta ce "Me...ka ce me!Mai ya same ta ?suwaye? Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un,wane hospital ne?O..Ok..ok gani nan" ★★★ Tsaye yake saman dogon tsaunin da za ka yi mamaki idan aka ce maka ɗan adam zai iya ƙetare rabinsa, bare a kai samansa,ya zuba hannayensa a bayansa da suke rufe da ɓakar safa. Sannu a hankali ya juyo ya fuskanci hasken farin watan da da bayansa kawai yake haskawa, sai dai fuskarsa a rufe take, a taƙaice ma babu wata gaɓa ta jikinsa da ta yi saura a buɗe . Wasu irin baƙaƙen kaya ne a jikinsa, rigar daga baya akwai tambarin kunama, har kasa,daga gaba kuma rigar ta tsaya iya gwiwa ne. Cikin wata iriyar murya mai amon gaske ya fara magana. "Lokacin amsar duk abin da kuka shuka ya yi, lokacin yiwa al'umma gashin ƙuma ya yi, wannan ita ce wasa mafi kyau da za a taɓa bugawa a duniya,ya zama dole na mallaki duniya,ko ta hali ƙaƙa!A rayuwa kowa da sila da dalilin rayuwarsu,lokaci ya yi za a fara " Wata iriyar mahaukciyar dariya ya shiga ɓaɓɓakawa, cikin dariyar ya ce" fansata tana kan duk wata mace ta duniya sai na karya lagonku, sai na kawo karshenku!Sai na cika burina koda kuwa kowa zai mutu! I'm the best!" WANE NE SHI ? AYEESHAT KISSAR YOTA....O19 27___28 https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Barde Da sauri Ahmad ya fito daga ɗaki yana ƙwala kiran "Barde..!Barde...Barde fa!Kana ina ne wai?" Fitowa ya yi daga ɗakin yana neme -neme, gabaɗaya ya zagaye gidan amma babu shi babu alamun shi,mutumin da ba shi da lafiya toh ina ya je?. Ya ja ya tsaya a tsakar gidan ya jingina da bango cikin matsanan cin tashin hankali.Yanzu karfe 11:30 ne na dare ya ma rasa ya zai yi. Gabaɗaya kansa ya kulle,sace shi a ka yi ko me? Inuwa ya gani saman kansa,a razane ya ɗaga kai ya kalle shi. Yana zaune a saman katanga kamar yana zaune a cikin ɗakisa,hankali kwance. Harara Ahmad ɓalla masa ya ce"amma ka mai dani ɗan iska, kasa ni sai gantali nake yi kamar mara amfani" Ko kallonsa bai yi ba bare ya amsa maganar shi.Ya cigaba da motsa bakinsa alamar wani abun yake ci. Sai da ya gama abin da Allah ya nufe sa da yi sannan ya diro. Kallon Ahmad ya yi ya ce"mai ka mai da ni da zaka ce kana nai mana,nufin ka ni mahaukci ne ko?" "Zan cutar da kaina ko wani?" Haɗe fuska Ahmad ya yi ya ce " ai kai matsalarka kenan,juya magana,dan na duba ka banganka ba shine zaka wani ce saboda kai mahaukaci ne?" Taɓe bakinsa ya yi kamar ba zai yi magana ba kuma sai ya ce" Ai matarka a mahaukaci take kallona" Ya faɗa sannan ya shiga ɗakin da yake matsayin nashi. Bin bayansa Ahmad ya yi suka shiga daƙin tare,guri ya samu ya zauna ya durkusar da kansa kasa . "Barde " "Hmmm" "Ɗazu na kalli labarai,ban ji daɗin maganar da na ga gida jaridar sun yi a kanka ba" "Mai suka ce?" Shiru ya ɗan yi sai kuma ya ce "wai kai ɗan ta'adda ne,kuma rudunar yan sanda ta bada umarin kama ka a duk inda aka ganka" A hankali ya ɗago da kansa ya kallesa a kalla ya ja mintuna biyar yana kallonsa,har sai da gaban Ahmad ya faɗi,jijiyoyin kansa sun miƙe idanunsa sun sake cizawa. "Toh karya suka yi ni ba dan ta'addan bane?Maganarka ta biyo kuma kasan ko sun fito sun bayyana ko ba su fito ba suna nema na." "Sai dai abin da ba su sani ba shine ni Barden Mamah na wuce kamu,na wuce da saninsu, na tsani duk wani mutum mai kaki,na yi alƙawarin farautarsu tamkar mayun waciyar damisa." "Ni ɗan ta'addane!Yanzu na fara idan akwai wani maiji da gashin bakin yana iya hanani" Miƙewa ya yi tsaye ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa,ya ce "Ahmad lokacin bari na gidan nan ya yi tabbas an fara wasan ya zama dole sarki ya hau karagarsa kafin kujerarsa ta kubuce daga hannunsa" A raza ne Ahmad ya miƙe yana ƙarewa agogon hannunsa kallo,domin ba shi da masaniyar lokacin daya sa shi ya ce"Barde kana da hankali kuwa?Ba kada lafiya fa,ina za ka je a haka?" "Ina ka samu agogon nan?" "Ni mace ne da kake son kullum sai ka ɓoyeni? ka sani boyewar ba mafita ba ce, domin kasan sauran idan a ka fahimci ina nan" "Ka kawo ni gidanka ba tare da izinina ba,don haka tafiyata ba ta bukatar izininka" "Dama na sani ni mahaukacin ne,ina kuma alfahari da haukar tawa! " "Zan tafi domin fuskantar abubuwan da suka yi saura,zan tafi domin na shayar da wasu azaba,zan tafi domin na yi wa kasa ado da jinin mutane da dama." Girgirgiza kai Ahmad ya yi ya ce"A'a lokaci bai yi ba, ka jira,da saura" "Karyane wallahil azim babu wani mahalunƙin da ya isa ya hana ni aiwatar da cikar buri da muradi na a duniya" "Sai na tabbatarwa duniya abin da tun farko na taso na ginu a kai" "Hakane zaka yi ni kaina za a yi dani, amma abim da nake so ka fahimta maƙiyanmu sun fimu yawa da ƙarfi,kuma ko da yaushe cikin neman rayuwarka ake yi. "A'a yanzu za a yi sai na tabbatarwa da duniya ni ɗan ta'addane!" Shiru Ahmad ya yi ganin ransa ya baci da yawa kar ciwonsa ya tashi. Sai da ya gama zagayen shi a ɗakin sannan ya nemi guri ya zauna ya kallesa ya ce "bari na baka saƙo ka gaya matarka." "Ka gaya mata kowa da kaddararsa,na sani ban taɓa yiwa kaddarar wani dariya ba balantana na ce hakki ke bibiyata,kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa,kowa da yadda ƙaddara ta zaɓi ta zo masa. Dauka ta mahaukaci kuma wannan zaɓin yana hannunta ta dauke ni duk abin da ya zo ranta ba ni da damuwa da haka." Sanin tun da ya ce zai tafi sai ya tafi ne ya sa ya ce"Barde dan girman Allah zan roƙi wata alfarma guda biyu" "Allah ya ba ni ikon iyawa" "Za ka iya sai dai idan ba ka yi niyya ba" Bai jira amsarsa ba ya cigaba. "Meyasa ka zaɓi barin gidan nan a halin da ka ke ciki?" "Ina zaka je daga nan?Kuma dan Allah am am ka abin nan" "Uhhhm" Barde ya faɗa yana kallon Ahmad da ya ɗan daburce. "Am dan Allah Barde ka yafewa Safna" Ya yi furicin shi kansa yana jin kamar ya yi kuskure. Shiru Barde ya yi yana kallonsa ya ja sakanni sannan ya ɗan ja fasali ya ce"Ahmad ka damu dani dayawa ,rayuwata kuma ba ta da wani amfani, tambayarka ta farko,saboda na gaji da zama a nan alhalin akwai abubuwan da suke jirana,kana zamana zai lalata maka tsakaninka da matarka,babban dalilin kuma zan faɗa maka." "Tambayarka ta biyu kuma gidana zan je mana." "Alfarma ta uku kuma ba zan iya ba" Miƙewa tsaye Ahmad ya yi da sauri ya ce "ina ka ce zaka?Mai kake ɓoye min ? Meyasa ba za ka iya ba?" Wani abu ya yi mai kama da murmushi ya ce"ɗayan gidan ba wanda kake zato ba ne" Saitin kunnane shi ya matsa ya raɗa masa wani abu,sannan ya dawo ya zauna ya cigaba da mgana "tambaya kake meyasa ko?" "Faɗa maka kake so na yi kamanta ko?" Shiru ya yi duk damuwar abin da ya faɗa masa ta baibayesa,ya sani zai yi duk a bin da ya faɗa. Bai iya tanka maganarsa ta karshe ba saboda ba shi da amsar ba shi. Miƙewa Barde ya yi ya ce "ka kula sosai ya faɗa sannan ya nufi hanyar fita daga ɗakin harya kai bakin kofa. Ahmad ya ce "dan darajar Allah da manzonsa kar ka yi abin da zai bata komai, na san halinka komai a hankali a ke binsa,zan zo gidan idan na kammala wannan aikin, ka kula da maganinka dan Allah. "Kuma wannan sumar yaushe za ka rage ta?" Gyaɗa kai ya yi ya ce "wannan sumar ba zan asketa ba har sai shirin farko ya tabbata" Fitowa tsakar gidan ya yi Ahmad ya biyosa yana jin kamar ya hana shi tafiya,sai dai ya san azabeben taurin kai irin na shi, kawai ya yi shiru. Juyowa Barde ya yi ya miƙawa Ahmad hannu suka yi musabaha ,sannan ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba ya kama katangar gidan ya haura ya dira ta bayan gidan. Da sauri Ahmad ya juya ya koma ɗakin da ya fito cikin tsananin sauri yake tattara duk wani abu da zai shaida Barde ya taɓa zama a nan sai da ya tattaro su kaf ,sannan ya fito da su tsakar gidan,fetur ya zuba musu ya ƙyatta ashana. Yana tsaye a gurin har suka ƙone. Sai da ya tabbar sun kone kaf sannan ya kwashe tokar ya fita,sai da ya dan yi tafiya mai dan nisa tukunna ya zubar da ita ya dawo gida. Cike da zulumi. Shiƙaɗai ne a gidam don yau Hafsat kwana za ta yi a asibitin. Barde kuwa yana dira ya cigaba da tafiya cikin sassarfa,babu abin da zaka iya gani a jikinsa sai idanunsa domin kuwa ya rufe ko ina na jikinsa. Tsayawa ya yi cak! Na yan wasu sakanni ,sannaan ya cigaba da tafiya . Wani loko ya samu ya shige. Wani mutum ne ya zo ya gifta shi ba tare da ya kula da shi ba. Cikin azama ya yi wuf ya kwarfesa. Faɗuwa mutumin ya yi kasancewar bai yi zato ba. Shake wuyansa Barde ya yi ya zazzaro masa ido ya ce "Waye kai" Daga hannu mutumin ya yi alamar saranda,da kyar ya iya cewa"Ni...Nii...Ni ɗan aike ne." Ya faɗa da kyar saboda azabr shakar da ya ji. Sassauta shake shi ya yi,saboda ya san dan aike ba ya laifi. Sai dai bai sake sa ba. Ya ce "wane ne ya aikoka" "Ban san WANE NE SHI ba nima kuɗi ya biya ni ya nuna min kai ya ce na baka wannan" Ya fada yana nuna masa jakar da take gefe sa. Jakar ya dauka ba tare da ya damu da mene ne a ciki ba, ya yi wa mutimin nan kyayawan naushin da zai jima bai gane inda kansa yake ba. Sannan ya cigaba da tafiya cikin sassarfa. Fita ya yi daga ainihin unguwar da gidan Ahmad yake ya fito titi,unguwar a can ƙarshen gari take sosai domin kuwa babu gida je da yawa ma. Tsayuwarsa ke da wuya ,wata bakar mota ta shararo da gudun gask,e ba ta ci burki a ko'ina ba sai a gabansa. Babu ɓata lokaci ya shiga cikin motar ta bar gurin da matsiyacin gudu. ★★★ Zaune yake cikin kayataccen office dinsa wanda ya ji kayan alatun duniya. Juyi yake kan kujerar da yake kai cike da izza. Yana cikin wannan halin ne wayarsa ta dauki rurin neman agaji. Sai da ya gama shan kamshinsa sannan ya daga kiran da har ya katse wani ya shigo. "Yautai" Mutumin ya faɗa ba tare da ya yi sallama ba. "Daga cikin wayar Yautai ya ce"BALBELA SHEGEN KA YA GABANKA FARI BAYANKA ƁAKI.Mai gida game da maganar aikin nan da ka ce a yi ne,mun jefa fatsarmu cikin babban tafkin domin kamo ƙosasun kifaye,sai dai kash!Yawancinsu raunatattu ne, lafiyayun sun yi kasan ruwa sosai,sai dai akwai wani bijimi da na samu labarin ya taso sama domin shan iska,ina ganin zamu jefa masa mugani ko za mu iya kamo shi.Amma fa shi ba kowane masinci ne ke iya kamo sa ba domin kuwa yana da tsananin santsi ,babu lallai mu iya ka mosa." "Amma akwai shawara,za ka iya tattaro masuntan da kake da su domin su gwada bajinintar su a kansa ." Wata iriyar dariya ya yi ya ce"komai sanstinsa ya yi kaɗan na haɗa masa kafatanin masuntana . WANE NE SHI ? By AYEESHAT KISSAR YOTA....O19 29____30 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z "Cike da girmamawa Yautai ya ce "A'a yallaɓai,ba a ko da yaushe yake da santsi ba wani lokacin gautsine da shi,a taƙaice ma zan iya ce maka Hawainiyya ne,yana iya canza kala a duk sanda ya so" Cikin ɓacin rai mutumin ya daki tebur ɗin dake gabansa ya ce"ƙarya ne !Ƙarya kake wallahi,ni nafi karfin wani kifin da yake ɓoye kansa a cikin ruwa.Na fi karfin kifin da yake buya a kasan ruwa,ya bani tsoro har abada, na gama ganin abin da wani mahalukin zai ba ni tsoro." Idan ba za ka iya ba na san wanda zai iya kamo shi." Cikin murya tsageru Yautai ya ce"Mai gida kasan wane ne Yautai duk abin da na fada ina da daliln fadar shi." "Ba wannan ba tun dazu na gama kimtsa amaryar nan,amma abokan angon har yanzu ba su kawo motar dibar amaryar ba." Jinjina kai mutumin ya yi ya ce"Yautai iya harkallar da ta hadamu kasa ni ba ka san wane ne Abdallah Muhammad Tasi'u Doro ba,Abokan Angon suna hanya . Ya karasa yana kashe wayar. Ya yi murmushi a hankali ya ce"Yautai maganar nan taka ta janyon maka bakuntar rami ko da kuwa lokacinka bai yi ba" ★★★ Rugar Baffa arɗo. A tsorace ta karasa inda take tuni fuskarta ta canza kala daga fara zuwa wani launi shuɗi-shuɗi. Cikin tashin hankali ta yi kokarin ɗaga ta amma abu ya gagara,ta yi wani irin nauyi na ban mamaki. Tana cikin kokuwar ɗaga ta Baffa ya fito,jikinsa jiƙe da ruwa alamar ya yi alola ne. Wani irin faɗuwa gaban Baffa ya yi.A take zucoyarsa ta shiga haska masa taswirar wani abu. Wani abu da yake sirri ne a gare shi! Da sauri ya ƙarasa inda take,ɗaga ta ya yi ya shiga da ita cikin gidan. Cikin tashin hankali Zahra ta bishi a baya,tana ta faman sharar ƙwalla. A tsakar gida Baffa ya shimfiɗe ta,sannan ya shiga ɗakinsa babu jimawa ya fito hannunsa riƙe da jakar magungunansa. A jiye jakar ya yi ya shiga harhaɗa nagunguna. Duk da tashin hankalin da Zahra take ciki, hakan bai hana yadda Baffa yake aiki cike da ƙwarewa da sannin makamar aiki. burgeta ba. Wani mai mai kamar manshanu ya shafa mata a fuska,ya dauko wani baƙi kuma ya shafa mata a goshi . Cikin ikon Allah fuskar ta fara washewa daga kalar da ta yi. Addu'a ya cigaba da yi mata yana tofa mata a goshin yana kuma murzawa a hankali. Tari ta fari yi a hankal ,cikin yan daƙiku jikinta ya fara wata iriyar kakkarwa. . A fusace Baffa ya ce"Ya muka yi dake?" Matar dake jikin Faɗime ce ta fara magana. "Ni bana karya alƙawari Abduu,lokacin da na ce maka zan dawo ne ya yi,kaddarar ta tun karo ta yadda babu wani hatsari da zai iya dakatar da ita,lokaci ne ya yi shiyasa har na zo na bawa bakuwa labari." "Ƙarya kike " "Ke ki ka ce min sai nan da shekaru mai yasa kika canza?" Cikin yanayin ɓacin rai ta ce"ina ƙara maimaita maka ni bana karya alƙawari,ban san ka da wannan hali ba,karka fara,kuma idan ma na karya alƙawarim yarjejeniyar za ta nuna." "Zan tafi dama na zo na faɗa maka ka shirya domin karɓar abin da duk ta zo maka da shi,ina kara yi maka tuni bazan taɓa mantawa da alƙawari ba. A take gumi ya fara tsatstsafo wa Baffa har lokaci ya yi? Cikin ikon Allah bayan atshawar da faɗime ta yi a take jiikinta ya sake ta hau bacci. Kallon Zahra Baffa ya ce"Mai ta ce miki?" Jim ta dan yi ta ce"ni babu abin da ta ce min hira muke da Faɗime,ba da ita ba." "Hirar me?" "Labarin Chubaɗo ta ba ni da yadda yan garin nan suke tsangwamar ta." Jinjina kai Baffa ya ce" ba Faɗime ba ce ita ce." "Zaro ido ta yi ta ce"ita wa?" "Haƙabiya sunanta,ta dawo ne sakamankon wani rikitaccen al'amari ." "Abin da ya sa na ce miki ita ce shine,idan ki ka kula zaki ji maganganun da ta faɗa miki sunfi karfin yarinya kanar Faɗime,kuma yanzu ma ba ki ji ta ce ta kawo miki ziyara ba?" Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa da kalaman shi. Jiki babu ƙwari Baffa ya miƙawa Inna jakar maganin ta mayar ɗaki,shi kuma ya wuce ya fita domin zuwa masallaci. Zahra ma da kyar ta miƙe ta iya gabatar da sallah gani take kamar ita ta yi sanadiyar rashi lafiyar Faɗime,sai dai abin da ba ta sani ba larura ce wadda take bin jini. Haka dai suka kwana jiki duk babu ƙwari,Inna ce ma mai daddagewa. Bayan sati ɗaya. Faɗime ta ware tsaf,don har rashin mutunci ya dawo,yanzu darun da a ke yi da ita wai a dole sai ta raka sale kiwo. A fusace Inna ta ce"ku kuke lallaɓata,yarinyar da ko yanzu ta samu miji aure za a yi mata ita ce kuke lallaɓawa haka?" Kifkifta ido ta shiga yi tana jiran ta ji abin da Baffa zai ce. Sai kuwa ya ce "Yanzu mai ya kawo maganar aure?Yarinyar da ba ta da lafiya." Kama hannuta Baffa ya yi yayi mata raɗa a kunne, jinjina kai ta yi ,ta kalli Sale ta ce "jeka kawai watarana na je" Harara ya watsa mata ya ce"dama ko ance na je dake ai watsar dake zan yi a hanya na ƙara gaba" Murguɗa masa baki ta yi ,sai dai bata tanka ba gudun kar Inna ta hukunta ta idan Baffa ya fita. Ƙwafa ya yi ya fice. Bayan Baffa ya fita.Tabarmar kaba Fadime ta shimfiɗa musu a karkashin bishiyar tsakar gidan,suka zauna suna hira gwanin sha'awa. "Adda ina ta magana kin yi shiru" Ɗan murmusawa Zahra ta yi wani abu yana zarge mata zuciya. Domin tunani take,tuninanin da ta gagara hana kanta yinsa. Ɓoyayiyar ajiyar zuciya ta sauƙe. Ta ce "Na tambayeki mana" Jinjina kai Faɗime ta yi da dama labarin take so. "Dama Baffa ya daɗe yana sana'ar bada magani?" "Eh ,don ni ban ma san lokacin da ya fara ba,kilan ba a haife ni ba ya fara." "Amma meyasa kika tambaya?" "Baki ga shi ya miki magani ba?" "Kawai ranar ne yadda ya haɗa miki magani sai da na ji nima inason na iya " Dariya Faɗime ta yi ta ce"bari Baffan ya dawo zan gaya masa" Zaro ido Zahra ta yi ta ce "kar mu yi haka dake mana,ni fa kawai ji na yi ya burge ni shi ya sa na faɗa miki" "Yaushe zamu fara darasin?" Cike da murna ta ce" ko yanzu" "A'a bari dai ki kara warwarewa haɗe rai ta yi ta ce"wai me ya same ni don Allah?Ni dai nasan mun dawo daga gurin shaɗin nan sai ma me?Sai muka je gidan su chubaɗo daga nan dai ban san mai ya faru ba" Bayani Zahra ta yi mata amma ta ce ita fa sam ba ta yarda ba,ita ba ta da aljanu,Inna dai tama jin su ta sharesu. Ana cikin haka suka tsinkayi salamar Chubaɗo ,da sauri Faɗime ta miƙe. Cike da mamaki Inna da Faɗime suke kallonta,domin kuwa rabon da ta shigo ta daɗe. "Chubaɗo ke ce a gidan namu ?" Sunkuyar da kanta ta yi ta gaishe da Inna cike da girmamawa,ansawa Inna ta yi fuska a sake,ta nuna mata inda suke ta ce ta je ta zauna. Takawa ta yi a hankali,sakamakon cikin ta daya girma sosai,ta zauna . Ta kalli Faɗime da har yanzu mamaki bai sake ta ba,ta ce"Ya dai?" Sai a lokacin Faɗime ta sauke numfashi ta nemi guri ta zauna ita ma. Mai da kanta ta yi ga Zahra ta miƙa mata gaisuwa. Fuska a sake Zahra ta ce"Lafiya ƙallo ya jikin?" "Da sauƙi" Ta faɗa tana sunne kanta ƙasa,gabaɗaya kunya ta cika ta don rabon da ta fito daga gida har ta manta,saboda muddin za ta fito sai an tsangwame ta,wannan dalilin ne ya sa ta janye daga cikin mutane,sai da a ka gayawa Dada Faɗime ba ta da lafiya,tukunna yau ta samu ta fito. "Ya jikin?" Ɗan ɓata rai Fadime ta yi ta ce"ni lafiya ta ƙalau,waye ya ce ba ni da lafiya?" Harararta Zahra ta yi ta ce" ba gidanku ta zo ba?Shine ko gaisuwa babu" "Zaki hau ta da tambaya?" "Kifta ido ta yi ta ce"Mamaki na ji rabon da ta fito har na manta,amma ina yini" Murmushi ta yi ta ce"ban amsa ba ya karfiin jikin?Gari ya ɗauka ƴar gidan Baffa ba ta da lafiya" "Ni lafiyata kalau babu abin da ya same ni"ta faɗa sannan ta miƙe ta ehbo mata ruwa a cikin randar kasa mai sanyi ta dawo ta zauna. Dama ruwan ta ɗaibo ne saboda gudun kar Zahra ta yi mata faɗa , ta ɗan muskuta ta ce"ya a ka yi Dada ta barki kika fito?" Rausayar da kai ta yi ta ce"Da ƙyar ta bari, yanzun ma ba ta san na fito ba,na san kuma ba za ta ne gane ba" Hira suka cigaba da yi sosai, tuni Chubaɗo ta warware ,ita ma Zahra ta shiga tana ta yi musu tambayoyi game da mutanen rugar,suna ba ta amsar abin da suka sani,ta fahimci akwai raunin ilimin addini sosai bare maganar na boko,so take ko yaya ne kamar yadda rugar nan suka tamake ta da mafaka,daya daga cikinsu ya taimaki rayuwarta,har kuma suka yi nata alfarmar gurin zama,ita ma ta taimake su,sai dai ba ta san ta yaya zasu karɓi abin ba musamma da ya kasance har yanzu wani irin kallo suke yi mata kamar wadda ba su yarda da ita ba, ko kuma su ka ga wata baƙuwar fuska. Abin da ya sa ma a ke ɗaga mata ƙafa shine Baffa da yake matukar taimakon mutanen rugar,duk da shima ba wani hali ne dashi can ba,ga Oga Faɗime yanzu sai ta rikita maka lissafi. WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR YOTA...019 Page 31___32 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Ruwa Faɗime ta iba da shafa mata a gefen fuskarta tana dariya. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce"Bakya ji Faɗime,kamar ni a da,koma na fiki" "Toh me ya sa ko magana ba kya yi sosai?Wani irin murmushi ta saki mai ciwo ta ce"lokaci ya kan iya canza komai,daga ciki kuwa har da abin da ƙwakwalwarka ba ta taɓa lissafa maka shi ba,rayuwa ta koyar da ni darasin da a gaba ba na tunanin akwai abin da zai iya girgiza min tunani ko zuciya " Kallonta Faɗime take, sai dai ta kasa fahiimtar manufarta. Kawai ta ɗan taɓe baki ta ce "ni ban gane ba" Murmushin ta sake sakar mata ta ce "lokaci dai zaki fahimci abin da nake nufi" Chubaɗo kuwa jikinta duk ya gama yin sanyi,ita kanta ta rasa gane a wane mizani zata daura maganarta ta,sai dai ta fuskanci wani abu,wani abun da sai wanda yake kan fuskantar kaddara ko ya gama fuskantar ta, shine zai iya ganewa. Jiki a sanyaye ta ce "bari na tafi kar Dada ta neme ni" Ɗan kallonta Zahra ta yi ta ce" Faɗime bari na miki nasihar" Ta faɗa ne badon Fadime ba,Chubaɗo take so ta ji,ta kuma ɗauka. Ba tare da ta jira jin ta bakinsu ba ta cigaba. "A rayuwar duniya kar maganar mutane ta hana ki sukuni, kar ki kuskura ki dauki damuwar wanda bai damu dake ba ki saka a ranki, duk wanda ki ka ga zai kawo miki matsala a farincikinki ki yi koƙari ki ja ba ya da shi, saboda farinckinkii yana da matukar amfani a rayuwarki. "Indai kin yarda ba ɗan adam ne ke iya tsara miki taswirar rayuwarki ba , toh kar ki yarda dole sai da shi zaki rayu ko zaki yi farinciki, ki yi farinciki ko da kuwa babu kowa a kusa dake . " Karki yarda sanadiyarki wani ya zubar da hawaye ko ya yi bakin ciki komai ƙanƙantar sa, muddin kina sane, ka da kuma ki yarda wani ya cutar dake haka kawai." Nasihohi ta cigaba da musu masu ratsa jiki. Jikin Chubaɗo ya yi sanyi sosai,ji take kamar Zahra da ita take. Kuma hakan take, domin kuwa da ita ɗin take,ta kuma yi nasarar saka mata ƙwarin gwiwa da karsashin za ta iya rayuwa kamar ko wanne ɗan adam, za ta iya yin farinciki ba sai tare da wani ba. Faɗime kuwa ko a jikinta don ita ba wani fahimtar abin da take cewa take ba. Abin da dai ta riƙe shine ka da ta bari wani ya cutar da ita,wannan maganar ta zauna mata a kai tsaf. So take idan Baffa ya dawo ta yi masa magana, game da kudirinta, na son ta fara koyar da yaran rugar tun da tana da karatunta daidai gwargwado. Jiki babu kwari Chubaɗo ta miƙe ta yi musu sallama ta tafi. Da daddare bayan sun gama cin abinci Zahra ta samu Baffa da maganar ƙudirinta a kan mutanen rugar. Ajiyar zuciya ya sauƙe a fili ya ce"duk na ji bayananki, kuma kin yi tunani mai kyau domin mu na bukatar hakan sosai da sosai, sai dai mutanen rugar nan suna da matsala sosai don ba lallai su amince lokaci ɗaya ba, musamman ke da kike bakuwa a garin nan" "Amma gobe idan Allah ya kaimu zan samu Baffa arɗo da maganar duk yadda muka yi da shi sai ki ji" Jinjina kai ta yi ta yi matukar farimciki da ta ga Baffa ya amshi maganar da hannu bibbiyu.Godiya ta yi masa ta miƙe taje ta kwanta cike da fatan Allah ya sa mai gari ya amince. Da safen kuwa kamar yadda Baffa ya yi mata alkwari ya je ya samu Baffa arɗo ya gaya masa komai, cikin ikon Allah shi ma ya karɓi abim da hannu bibbiyu, duk da ya ɗan ja maganar da farko. Cikin satin a ka tara jama'a ya yi sanarwa, wasu sun yarda wasu kuma sunƙi. A haka ta fara koyar da ƴan mata da ƙananan yara, cikin ɗan lokaci har tsirarun manya take koyarwa, ba ƙaramin taimako ta yi musu ba domin kuwa wasu sai a lokacin suka san ana wani wankan tsarki,kawai kwaɗa sallarsu suke ita ma sallar akwai gyara sosai. Ganin yadda cikin ƴan kwanaki ta samu karɓuwa ne ya sanya mata ƙwarin gwiwa sosai, ta fi mai da hankali kan koyar da su salllah yadda ya dace da kuma yadda za su tsarkake jikinsu daga najasar da wanka ya wajaba a kanta Cikin yan watanni abubuwa suka fara canzawa kusan rabin mutanen rugar sun amsheta da hannu bibbiyu musamman da ko maganar karatun boko ba ta taɓa gwada musu ba ,duk da akwai masu hassada da baƙinciki sai dai sun gaza hana mutane yi wa Zahra mubaya'a . Faɗime kuwa fankama ta ƙaru domin idan mutum bai mata ba za a koyar da shi ba, shiyasa take yadda ta ga dama. Chubado ma ba a barta a baya ba tana iya ƙokarinta, don da ita a cikin ɗalibai masu kwazo. Wata iriyar sassanyar iska ce take kaɗawa sakamakon hadarin da ya taso ta ko'ina,dajin ya yi duhu. Dire salkar ruwan da take hannunta ta yi ta kalli yadda hadarin ya yi ɓaki walik,ta kalli Zahra da ta miƙe tsaye itama tana kallon yadda iska mai ɗan karfi take kaɗawa,ta ce "Hadarin nan fa yana iya samun mu a nan idan ba mu yi sauri ba. Gyaɗa kai Zahra ta ce "na ga alama sai mun yi sauri. Ta faɗa sannan ta dauƙi salkar ruwan ta rataya. Harhaɗo kan shanayen suka yi suka kaɗa su hanyar da za ta sada su da rugarsu. Cike da nishaɗi take kaɗa shanayen,ba ta taɓa tunanin bayan waccem rayuwar za ta sake samun rayuwar da za ta yi farinciki ba, cikin ikon Allah gashi tana rayuwa mai cike da nishaɗi. Gabanta ne ya ɗan faɗi ganin iskar tana kara karuwa, ga shi da alama ruwa ya na gaf da sauƙowa. Ta kalli Faɗime da ko a jikinta, ganin hadarin bai wani ɗaɗata da kasa ba ta ce"wai ba za ki yi sauri ba?" Saurin ta ƙara don ta san Kwata-kwata Zahra ba ta son ruwa ya taɓa ta,saboda ba karamar wiya take sha ba. Duk da haka sai ta ce"so nake kafin muje gida ruwan ya sakƙo na yi wanka" Harara ta watsa mata tana tuna wani lokaci da daɗewa da ta shiga cikin ruwa ta yi wanka, duk da Mami ta hana ta amma ba ta hanu ba,ta tuna yadda ta sha walaha sosai. Murmushi daɗan saki hawaye na ƙokarin ƙwashe mata. Sai da ta tabbatar da mai da kukan sannan ta ce"uban wanka" Ɗan taɓe baki Faɗime ta yi ta ce" sai yanzu zaki amsa kenan,fatana dai kafin muje gida ruwan ya saƙƙo" Duka ta kai mata da sandar da take hannunta ta kauce da sauri tana dariya. Cikin ikon Allah har suka isa gida ruwan bai tsuge yadda suka yi zato ba, sai dai ana ta yayyafi mai haɗe da iska. Sale da ya dawo yanzu ne ya daure dabobin,su kuma suka wuce ciki. Kamar jira ruwan yake su shige ya sauƙo da karfin gaske. Bayan sun ci abinci sun yi sallah ne Faɗime ta ce "Adda yau babu darasi ne?" Daga kwancen da take ta ce"Eh mana ai yau ba ranar darasi ba ce, kuma na gaji wallahi,jikina ma duk ciwo yake" "Toh Allah ya ba da lafiya" Ta faɗa sannan ta cigaba da bitar karatun da ta biya mata. Safiyar juma'an ta zo wa da matanen rugar Baffa arɗo a wani irin yanayi na ban mamaki. Rugar ta yi wani irin shiru na ban mamaki tamkar babu wani mai rai dake rayuwa a cikinta. Sai bishiyo da suke kaɗawa a hankali ,iska mai haɗe da kamshin ƙasa tana ta kaɗawa. Ko ina luf-luf ni'imar Allah ta lulluɓe dajin da mutanen ciki. "Baffa dan Allah ina so zan raka Adda mu zagaye rugar nan" Faɗime ta faɗa tana kallon Baffa da yake ta gyaran bakarsa da ta lalace. Ba tare da ya dakatar da abin da yake yi ba ya ce "a'a" Magiya ta shiga yi masa, duk da yadda take jin jikinta gabaɗaya babu ƙwari . Da ƙyar ya barsu. Har Baffa ya yi wakan ya shirya domin halartar sallar juma'a Faɗime ba ta tashi daga inda ya bar ta ba,ta kuma yi shiru. Sai bin tsakar gidan take yi da ido can kuma sai ta lumshe idon. "Kin fasa fitar ne?" Ɗagowa ta yi suka haɗa ido da Baffa kawai sai ta ji idanunta sun ciko da kwalla. Mai da kanta ta yi ta kwantar a hankali ta ce "Eh "Cike da mamaki Baffa yake binta da kallo, ya ce "lafiya kuwa?" Girgiza kanta kawai ta yi. Gabansa ne ya faɗi wani abu ya shiga yi masa yawo . Har ya buɗe baki zai yi magana ya tuna lokaci zai kure masa, da sauri ya fita. Dama ya gama shiryawa fita kawai zai yi. Fadime kuwa wani irin yanayi take ji,ita dai tun da take ba ta taɓa jin yanayi makamacinsa ba. Ko wankan juma'an da take dauki duk sati yau ta kasa yi. Da kyar ta samu ta gabatar da sallah . Fitowa ta yi ta nufi inda Inna da Zahra suke zaune itama ta zauna ta gaishe da Inna ta amsa tana kallonta duk ta yi wani zuru-zuru. "Inna" "Na'am" "Inna don Allah na kwanta a kan cinyarki?" Kallonta Inna ta yi ta kalli cinyarta ta, kawai sai ta samu kanta da gyaɗa mata kai. Zamewa ta yi a hankali ta kwanta zuciyarta tana ƙara yi mata nauyi Inna kuwa hankalinta na kan Zahra da take raira karatun Suratul Kahfi,cikin zazzaƙar muryarta. Ta daɗe a kwance a kan cinyar kafin ta tashi ta kalli Zahra da ta gama karatun ta ce "Adda ina son rugar nan bana so na rabu da ita ina matuƙar kaunarta." Shiru Zahra ta yi na ƴan wasu sakanni, gabaɗaya jikinta a sanyaye yake ita ma ta rasa dalili, ga gabanta sai faɗuwa yake yi lokaci zuwa lokaci. Ajiyar zuciya ta sauƙe ta dafa kafaɗarta haka kawai sai ta tsinci kanta da tausaya mata, tabbas a iya zaman da ta yi da Faɗime ba ta taɓa jin muryarta dauke da rauni muraran ba sai wannan karon, ta hango wani abu mai wuyar fassara a cikin idanun nata. Ita kanta sai yanzu take jin so da kaunar zama a wannan dajin Allahn,Allah ya wadata shi da wata irinyar ni'imar da muddin ka zauna a gurin sai kaunar shi ta cika ma zuciya. Ta ce"Namesake na san kina kaunar rugar nan toh amma mene na irin waƴennnan maganganun duk me ya kawo su?" "Ban sani ba Adda nima ban sani ba kawai na ji ina so na faɗa ne!" WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR YOTA...019 Page 33___34 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. Ganin gabaɗaya ba ta da natsuwa ne ya sa ta janyo ta jikinta tana tofa mata addu'a, cikin ikon Allah kuwa ta fara samun natsuwa har ba ta san lokacin da bacci ya dauke ta ba. Ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da karatunta. Ko da Baffa ya dawo ya zo musu da tsarabarsu kamar yadda ya saba, ya samu Faɗime tana bacci ya tambayi lafiya take? suka ce masa eh. Lokacin da aka tashi cin abincin dare, wani irin mamaki ne ya cika Zahra da Faɗime, ganin Baffa ya umarci Inna da ta zuba musu abinci a tire ɗaya, yau gabaɗaya yake son suci abincin. Wani abin mamakin da ya ƙara faruwa shine, daɗewar da suka yi suna hira, hadarin da ya taso bai katse musu hirarsu ba. Wasa-wasa har kusan karfe ɗaya da rabi suna zaune. "Baffana ina sonku wallahi!" Shiru Baffa ya yi yana kallonta, kawai sai ya samu kansa da ƙarewa filin Allah da suke zaune kallo. Murmushi ya yi ya ce "ya kamata a kwanta haka dare ya yi, balantana ke Zahra akwai karatu gobe". Miƙewa suka yi a tare har za su shige Baffa ya kira su ya umarci kowa da ya yi alwala. Bayan sun yi ne ya ja su suka yi sallah raka'a biyu a nan inda suka tashi ,suka yi addu'o'i kafin suka kwanta. Bayan awa ɗaya da rabi da kwanciyarsu, bacci suke yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sama-sama suka fara jiyo hayaniya a cikin baccin. Cikin wani irin firgici suka farka, sakamakon wata irin razananniyar ƙara da suka ji ta karaɗe dajin ta ko'ina. Babu abin da kake ji sai ƙarar babura ta ko'ina, a take iface-ifacen jama'a da gije-guje ya gauraye rugar Shiru ta yi na wasu ƴan sakenni, tana so ta tabbatar da ko mafarki ne take yi. Sai dai kashh! Abin da take ji ba a mafarki ba ne zahiri ne. A hankali ta ce "Ya Allah, me yake shirin faruwa ne? Wannan ƙarar ta me ye?" Zabura ta yi ta tashi zaune da sauri sakamakon ƙarar da ta ji tana barazanar fasa dodon kunnenta. Cikin tsanin kaɗuwa da tashin hankali ta fara faɗin "lnnalillahi wa'inna'ilaihi raji'un". A take kanta ya fara juya mata, idonta ya haska mata wani abu mai ban tsoro. Cikin rawar murya Faɗime ta ce "Adda mene ne? Ƙarar me nake ji ne? Adda tsoro nake ji". Idanunta ta kai kan Faɗime dake kwance tsoro ya hana ta motsin kirki, ta takure a wuri ɗaya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Ita ko da ta kwanta ba baccin ta yi ba, ta nan tana karatun wasiƙar jaki. Wannan hayaniyar ce ta tashe ta. So take ta gasgata zuciyarta da gaske su ɗin ne? Damƙar da Baffa ya yi wa hannunta ne ya dawo da ita daga duniyar mamaki, tsoro, da tsananin firgicin da ta lula. Cikin tashin hankali ya ce "ƴan bindiga ne". Dimm! Ta ji ƙirjinta ya buga da ƙarfi, dafe zuciyarta ta yi tana kallon Baffa "Ƴan bindiga kuma?" Ta tambaya tana zaro ido waje. Zuciyarta na ƙara tsananta bugawa. "Shikenan komai ya ƙare? Komai ya zo ƙarshe? Shikenan rayuwarmu cikin wannan ni'imtaccen garin ta zo katshe?". Faɗime ta faɗa a fili sakamakon abin da ta ji yana fitowa daga bakin Baffa. Cikin wani irin yanayi Baffa ya saka hannunsa a aljihu ya ɗauko wani abu mai kamar ƙwai ya damƙawa Zahra ya ce "Ba muda wani isheshshen lokacin magana a yanzu, amma wannan shine fitilarki domin samun cikar burinki. Allah bai ƙaddara zaki gyara Rugar nan kamar yadda kika so ba, komai na Allah ne, kuma shine mai sakayya kan wanda aka zalunta, in dai kun rayu na baki amanar gudan jinina, da matata, ki zame musu bango abin jingina, na baki amanar ta, na bar miki ita duniya da lahira, na sani tabbas ba zan rayu ba. Wannan shine abin da Haƙabiyya ta zo faɗa min amma na ɗauki maganar da wasa". Ita dai Inna kallonsa kawai take yi, ba don tana fahimtar abin da yake faɗa ba, ƙwaƙwalwarta ta kasa fassara mata mai take ji. Ba ta dawo hayyacinta ba bare ta samu zarafin tambayar Baffa abin da ke zuciyarta. Ƙarar babura dana bindugu ya ƙara tsananta, ba abin da kunnenta ke ji sai guje-gujen mutane da koke kokensu. Hannun Zahra dana Faɗime ta ja ta nufi ɗakinta da gudu da nufin ɓoye su. Kafin ta ƙarasa. Sale ya faɗo gidan da wani irin gudu sakamakon biyo sa da ƴan bindigar suka yi, ƙarar fitar harsashe ne ta karaɗe gidan, ɗaya daga cikin su ne ya sakar masa harsashi a tsakiyar kansa. Wani irin feshi jini ya yi ya wanke fuskar su Inna dake tsaye a gurin. Ihu Faɗime ta kwarma tana ƙoƙarin zuwa gurin gawarsa. Tsawar da ɗaya daga cikinsu ne ya daka mata ya sa ta tsaya cak. Saita su suka yi da bindiga suna tabbatar musu da duk wanda ya motsa sai sun harbe shi. Babu alamar tsoro ko misƙala zaratun a fuskar Baffa, kallonsu yake ɗaya bayan ɗaya, kallo irin na rainin nan. Babban cikinsu ne ya umarci Baffa da ya ketawa Zahra da Faɗime haddi a gabansu.Yana maganar yana ƙyaƙyata dariyar mugunta. Cikin baƙin ciki da takaici Baffa ya kalle su, wani abu mai ɗaci ya cakar masa zuciya. Yana da tabbacin idan zai musu kuka da magiya ba za su fasa kashe shi ba, don haka ya zaɓi shihada. Ya fara takawa a hankali babu alamar yana tsoran harsashi, kasancewar mutumin a kusa yake da shine ya sa taku huɗu ya ƙarasa inda yake, yana huci kamar wani zaki. Ya kalli fuskarsa ya ce "Me muka yi muku da kuka zaɓi sabauta rayuwarmu ta hanyar ƙasƙanci? Shin mun tare muku wani abu ne? Meyas...." Maganar shi ce ta katse sakamakon buga masa kan bindigar da ɗaya daga cikinsu ya yi. Cikin rashin sa'a ya faɗi akan wani dutse, dake tsakar gidan a take haƙorinsa ya fita. A fusace mutumin ya ba su umarnin su ɗaure Baffa, ɗauresa suka yi kamar wani huhun goro. Rai a ɓace mutumin ya fara magana da hausa. "Da ban yi niyyar taɓa tsohuwar nan ba, kawai so na yi in kasheta salin alin, amma yanzu ka ja mata bala'i tun da ba ka da kunya". Ya ƙarasa maganar yana janyo Inna da take ta tsuma kamar wadda aka fitar daga ruwan ƙanƙara, jefar da ita ya yi a gurin, ya kalleta ya ce "babu laifi da ɗan kyanta har yanzu". Ya faɗa yana wata iriyar dariyar shaƙiyanci. "Ku juyo min da fuskar yaran nan ina so suga abin iyayemsu ke ɓoye musu" . Kakkauran inyamurin mutumin ya faɗa, sannan ya saka ƙarfi ya yagawa Inna rigarta ya fara koƙarin janye mata zanin jikinta. Riƙe zanin ta yi tana kuka mai ban tausayi. A hasale ya ɗaga hannu ya kifamata gigitaccen marin da sai da bakinta ya fashe da jini. Ɗago runanun idanunta ta yi ta kallesa, ba ta damu da marin da ya yi mata ba ta ce "Dan girman Allah kada ka wulaƙanta ni a gaban ƴaƴana". Bai kulata ba ya fizge zanin jikinta da ƙarfi, da sauri Faɗime ta damƙe hannun Zahra da take riƙe da shi jikinta yana wata iriyar kyarma. Ita dai Zahra komai ganin shi take kamar bacci take yi kuma za ta farka nan ba da daɗewa ba. Da sauri Baffa ya rintse idanunsa da wani irin ƙarfi, saboda ganin mutumin nan yana ƙokarin cire wando, ina ma ace ajalinsa ya riskesa kafin zuwan wannan baƙar ranar me cike da baƙin duhun da har abada ba zai goge ba. Shin me suka yi musu da suka cancanci wannan cin zarafin?Meyasa dole sai su?Shin gwamnatin da ake faɗa tana sane da halin da suke ciki? Haka mutumin nan ya ci mutumcin wannan salihar dattijiwa, ya keta mutunci da alfarmarta a gaban yaranta da mijinta. Bayan ya kammala aika-aikarsa ya miƙe ya zo kusa da Baffa ya tsugunna ya ce "wannan shine hukuncin duk wanda zan faɗa ya faɗa ". Lumshe ido Baffa ya yi zuciyarsa tana gaya masa kafin ya mutu zai iya yin wani abin. Motsawa ya yi ya ji hannunshi zai iya motsi don haka bai ɓata lokaci ba ya fakaici idonsa, ya ɗakko wani ƙarfe da yake gefensa, cikin zafin nama ya caka masa shi a wuyansa. A take mutumin ya saki wata irinyar razananniyyar ƙara, ya dafe gurin yana kakari, idonsa na kakkafewa. Murmushi Baffa ya saki yana da tabbacin sai dai wani ba shi ba. A hankali ya ce "Alhamdulillah". Daga haka ya fara maimaita kalmar shihada. Ba su jira konai ba suka buɗewa Baffa wuta ta ko'ina aƙalla harsashin da ya shiga jikin farin datijon ya kai talatin. Wani irin yanayi Fadime take ji kamar gaske kamar wasa,wani abu ne yake mata wayo a kanta tamkar tsuta,ta sandare a guri ɗaya sai ka ce saƙago. Ko kifta idanunta ba ta yi. Tabbas Baffa a ka harbe,toh me ya yi musu?Kawai don sun zauna a ruga kawai don ya tambaye su laifin me suka yi? Me Inna ta yi musu? Runtse idanunta ta yi a hankali ta buɗe tamƙe hannun Faɗime ta yi da yake cikin tana. Karar harbice ta gauraye dodon kunnemsu a tare suka lumshe idanunsu suka buɗe sakamakon jini da ya wanke musu fuska. Sun kashe Inna sun harbeta ita ma. Wanda ya yi harbin ne ya kallisu yana wani irin huci ya ce "sai kun shiga bala'i tun da tsohon nan ya kashe mana hamana ya faɗa da hausa." Kallon na kusa da shi ya yi ya ce"kusawa gidan wuta shima. Tankaɗa ƙyeyarsu uka yi suka fita da su. Suka bar gawar Baffa da Inna a yashe a gurin Ba iya su kaɗai bane suna da yawa domin ba iya natan rugarsu bane har da wasu daban. Kora shanayensu suka yi suka suka rugar baki ɗaya wuta.. Sai a yanzu ta samu ikon jiyowa ta kalli gari mafi soyiwa a zuciyarta,garin da duk abin da take so shi take ci. Garin da duk abin da take so shi take yi. A yau ta bar Innarta mai yi mata faɗa idan ta yi laifi, ta bar Baffanta mai goya mata baya idan ta janyo fitina. Ta barsu ta barsu ba don za ta sake ganinsu ba ta barsu bari na har abada. Tana ganin ƙyalin watar tana tashi har tana jin wucinta. Da gaske dai Inna tana cikin wutar nan bayan cin mutuncin da a ka yi musu. Mangarin da ɗaya daga cikinsu yake mata ne ya sa ta juyar da kanta ta cigaba da tafiya. Har yanzu babu ko alamar hawaye a idanunta,gani take ma kamar za ta tashi daga bacci a ce mata duk mafarki ne. Me ya rage?Yanzu me ya rage? Kawai ta bi su Baffa,meyasa ma ba ta faɗa wutar ba meyasa ta bari suka ƙome su kaɗai. Tafiya suke babu kama hannun yaro babu tausayi babu imani haka suke dukan duk wanda ya tsaya kamar dabba. Wanda suka ga alamar ya gaji sosai kuma su harbe shi. Tun cikin dare suke tafiya har alfijr ya keto,har gari ya yi haske,har rana ta take ba su kai inda za su kai ba. Mutane da yawa sun fita hayyacinsu . Yan bindigar kuwa: Kaɗan daga cikin su ne suke tafiya a ƙasa shima suna yi suna canzawa . Zubewa Faɗime ta yi a kasa a karo na babu adadi, cikin yanayi na fita hayyaci. Da sauri Zahra ta tsugunna tana ƙokarin ɗaga ta amma ina. Tsayawa wani gabjejen mutum ya yi a gabansu ,ya ya ce "bari a harbe ta tana tsaidamu ita da wannan ya faɗa yana nuna wata mata da ta yi wata iriyar galabaita. Ga tsohon ciki ga tafiya ga tashin hankali. Tana faɗuwa tana tashi suna dukanta. Ya saita bindigar a kanta. Rungumeta Zahra ta yi cikin wani yanayi ,tabbas ba za a ta iya b su hakuri kar kashe ta ba amma ba za ta tashi daga nan ba har sai sun harbeta ita ma. Tasss ! Tasss !Tassss ! Ka ke ji ƙarar harbin da ya yi. Runtse idanunta ta yi da karfi,sakamakon jinin da ya wanke mata fuska. WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR YOTA...019 Page 35__36 Bismillahir-Rahmanir-Rahim. https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH?mode=gi_t https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z A hankali ta fuɗe idanunta domin ganin wane irin kisa suka yi wa Amanarta. Sai dai me babu alamar harbi a jikinta ta kura mata ido tana neman inda jini ya yi wannan zubar. Wata iriyar razanar niyar tsawa ya daka mata,duk da jikimta ya amsa amma ba ta ji ta a cikin zuciyarta ba. Matar dake bayansu ya harbe . Ashe jinin shi ne ya wanke mata fuska. Cikin tsawa mutumin ya ce "tashi ki wuce!" Kallonsa ta yi sosai sanye yake da kaya irin nasu babu abin da a ke gani a jikinsa sai ƙwayar idonsa. Sai dai shi baƙin rawani ne a kansa saɓanin su da suka saka jajaye. Tsugumnawa ta yi da nufin daukar Faɗime amma ta kasa saboda yadda jikinta da ya yi wata iriyar gajiya . Zubewa ta yi kan gwiwarta ita kanta ba ta san me take faɗa ba, ta dai san tana magana"Dan Allah ku kashe mu ,me muka yi muku,meyasa dole sai m...." Ai ba fa ƙarasa ba sakamakon wawan dukan da mutumin ya kai nata a baki,da kan bindigar,ya yi nasarar samunta sosai,jini kuwa a samu hanya. A hankali ta fara lumshe idanunta da suka yi mata dauyi,tun tana gani dishi-dishi har duhu ya cike gurbin sauran hasken da ya rage. A hankali ta fara motsa fatar idanta tana ƙoƙarin buɗe ta,sakamakon sasanyar iskar da ta ji tana ratsa ta. Karewa gurin kallo take cike da mamaki ,kwakwalwaeta ta yi mata dauyi,ta kasa tunanin komai. Kawai sai ta samu kanta da ƙarewa gurin kallo Wani irin katon fili ne iya ganinka ga dakurun wajen sai kaiwaa da komowa suke,wasu kuma suna zaune suna shirya wasu abubuwa,suna zuba su a manyan kwalaye. Ɗan motsawa ta yi da nufin gyara kwanciyarta,domin wacen ba ta yi mata daɗi ba. Riƙe ta da taji anyi ne ya sa ta kai magananta gurin,Faɗime ce a zaune a kusa ta ita ta zuba mata ido cike da yankewar tsammani,domin ita ƙadai ce ta rage mata a yanzu,ita kaɗai ce karshen karfin gwiwarta. Sai a yanzu komai yake dawo mata ,tabbas ta tuna komai. Da sauri ta miƙe zaune tana kara bin wajen da kallo. Mutane ne kashi-kashi ,wasu a bangaren da suke wasu kuma a dayan bangaren,da alama dai wannan babbar runduna ce. Saka hannun Faɗime ta yi cikin na ta ganin sai sauƙe ajiyar zuciya take,ta kwantar da ita a kan cinyarta. Kwanciyar ta yi,ta yi shiru, har yanzu kwakwalwarta ta kasa tunani,zuciyarta ma jinta takr fayau tamkar babu ita a kirjinta. Zahra kuwa cigaba da ƙarewa gurin kallo ta yi,tama kallon shige da ficen su Wasu suna kuka,wasu kuma sun yi shiru jugum-jugum,wasu kuma kallonsu kawai suke ,dan da alama sun saba da zaman gurin. Tana cikin wannan halin ne idanunta suka kai kan wata mata a yashe a kasa,tamkar babu rai a jikinta. Kare mata kallo ta cigaba da yi ganin kamar ta santa. Gabanta ne ya faɗi ,kamar Chubaɗo?Kai tabbas ita ce ma,ba ta ganin fuskarta amma tana da tabbacin ita ce. Sai dai akwai tazara a tsakaninsu me ɗan tsawo,gashi ba za ta iya tashi i ba,domin daga zaunen nan da take ma jiri take gani,bare ta karasa inda take. Idanunta sun bushe sosai babu alamar hawaye,sai wani irin zafi da kirjinta yake mata kamar zai tsage. A yanzu ta fahimci komai kwakwalwarta ta ba ta haɗin kai,ashe karya ta yi da ta ce ta gama ganin abin da zai girgiza zuciyarta,tabbas ɗan Adam ba shi da sani a kan gaibu,da ta sani da ta zauna tun farko an kasheta ɗin,da ba ta zo rugar nan ba. Da ba ta saba da matanen ciki ba. Da ba ta saba da garin da take jin shi har cikin ranta ba. Da ba ta saba da mutane masu karmci irin iyayen Faɗume ba. Lumshe idonta ta yi wani abu me ya ji yana zagaye maƙoshinta. "Yanzu a haka za a ce baki ɗaya Fulani azzalumai ne?A haka a ke haɗa su a yi musu kuɗin goro?Me ya sa wasu mutanen ba su da adalci?. Fulani sune idan ka je daji za su baka gurin kwana,za su taimaka maka,su baka abinci su mutanta ka. Amma dan wasu sun zama azzalumai a cikinsu sai a haɗa su duka a yi musu kuɗin goro,anya muna yi wa junan mu adalcu kuwa? A lokacin da suke da damar wulakanta ka domin kuwa a cikin daji Fulani suke da sarauta,a lokavin wasu daga cikinsu za su taimake ka. Kamar dai yadda ya faru akanta. Tabbas ko a yanzu a kwai Fulani a nan amma abin da wasu ba sa ganewa shine ba iya Fulanin ba ne ƴan garkuwa da mutanen,har da inyamurai da sauran kabilu akwai. Wannan abin fa Fulani a ka yi wa,babu matakin da za a dauka musu kuma,an cutar da su. Ya ubangijina ubangijin kowa da komai,ya Allah ya ga bayinka nan suna zaluntar bayinka Allah ba su fi karifinka ba,idan mu sun fi karfinmu. Ya Allah bakina ya gaza roƙarka ya hayyu ya kayyum ka saurari zuciyata . Idonta ta buɗe sakamakon karar cida da ta ji,kallon sararin samaniya da ta yi wanda hadari yake haɗowa da sauri. Idanunta ta mayar kan sauran mutanen da suke gurin. Akwai alamar tashin hankali a gurin wasu, wasu kuwa ko a jikinsu. Iska me ƙarfi ce ta fara kadawa tana shigarwa jama'a ido da hanci. Ana cin haka suka ji karar babura ta cika gurin. Ba a fi mintuma biyu ba,sai ga wasu mutanen jikinsu sanye da kaya irin na su. Jeruwa suka yi sai kuma suka dare,daga tsakiyarsu wani mutum ya fito shima dai ba ka iya gainin komai a jiikinsa,domin kuwa har ƙwayar idonsa ba a gani a rufe ta da tabarau. Tum kafin su yi magana wasu daga cikin mutanen griun duka miƙe tsaye. Cikin tsawa wani daga cikinsu ya ce ku mike tsaye!. Duk da galabaita da yunwa bai hana su miƙewa ba. Wasu suna faɗuwa suna tashi , Bin su ya ringa yi da kallo yana takawa a hankali. Cak ya tsaya ya zubawa guri ɗaya ido Guri dayan da ya zubawa ido ne ya ja hankalin sauran jama'ar gurin. Me za su gani Zahra ce zaune ba ta ko motsaba. "Ke!Ba ki ji abin da a ka ce miki ba. Shiru ta yi ba ta motsa ba. Tsoro ya ne ya bayyama a fuskar sauran jama'ar da suka daɗe a gurin,domin kuwa sun san tabbas zaman nan da ta yi ba zai haifa mata da ɗa mai ido ba. Suna tabbacin abin da zai biyo baya ba mai daɗi bane ba. Faɗime da baccim wahala ya fara biga ce ta farka a firgice saboda ƙarar tsawar da ta dake ji a saman kanta. Zaune ta tashi ganin ido ya dawo kamsu kowa su yake kallo. Ga sauran matanen duka a tsaye. Kallon Zahra ta yi da ko a jikinta,ba ta ma ɗago kai ba bare ta lura da suwa ye suke kallonta. Motsa bakinta ta yi da ya yi mata dauyi saboda daɗewa ba ta yi magana ba,ga kuma tashin hankali.. Ta ce "Addaa! Kallonta ta yi ba tare da ta tanka mata b a. "Ke wace kalar yarinya ce wai?Shugaba wannan ita ce Babansu ya kashe mana Hamana." Hannu Shugaban nasu ya ɗaga da sauri suka ɗaura masa bindiga a tafin hannun. Takawa ya yi ya karasa inda suke,ya tsugunna a gabansu yana kallonta. "Wace ce ke?" Ya faɗa yana shafa bindigar da take hannunsa Sai a lokacin ta ɗago da jajayen idanunta ta zubawa mutumin. Zuciyarta ce ta buga da sauri,har sai da ta ji tana son ta dafe ta. Ta so mai da kanta ta sunkuyar amma sai ta ji kamar an hana ta,ta ji tana son ƙarewa mutumin kallo Ta ƙura masa ido kuwa ko kiftawa ba ta yi. A bangaren Shugaban nasu ma,gaban shi ne ya yanke ya yi wata iriyar faɗuwa. Mamaki ne ya baibaye shi. Wace e wannan toh? Dakewa ya yi Ya ce "Ke kaɗai ce ba za ki bi umarni ba ko?Lallai akwai bukatar kisan kin zo fadar da mubaya'a a cikinta wajibi ne." "Babanku ne ya kashe min amintacen yarona ko?" Ya faɗa yana ƙare mata kallo gabansa yana cigaba da faɗuwa. Tun ɗazu take so ta yi addu'a amma ji take kamar an daure mata harshe. Gabaɗaya ma addu'ar taƙi zuwa kanta. Sai yanzu Allah ya ba ta ikon faɗar ,"La'ilaha'illah anta,subahanaka inni'kuntu minazzalimin." A cikin zuciyarta. Miƙewa mutumin ya yi ya ja da baya taku uku. Su dai jama'ar gurin da sauran yaransa,kallonsu kawai suke suna jiram suga me zai faru. Ɗaga bindigar ya yi har zai har ba wayarsa ta dau ruri,dakatawa ya yi ya ɗaga wayar,jinjinna kai ya yi da sauri ,sannan ya juya. Kallon yaran na sa ya yi ya ce"ka da ku kasheta ajiyata ce,ni ne wanda zai hukunta ta da kaina. A faɗa sanna ya juyo ya ƙara kai idanunsa kan Zahra da har yamzu shi take kallo. Jinjina kansa ya yi ya juya ya tafi da sauri. Gabadaya jikin waƴen da suka daɗr a gurin ya yi sanyi mamaki da tsananin al'ajabi ya cika su. Domin kuwa Shugaba bai taɓa karɓar bindiga bai yi kisa ba. Komawa suka yi suka zauna suna kara girmama abin. A ɓangaren Zahra kuma jikinta ne ya dau wata iriyar kyarma,sakamakon abin da idonta ya gane mata. So take ta tabbatar shin da gaske ne ko ƙarya,tabbas idanunta sun yi baƙin ganin da suka tuna mata da da. Lumshe idonta ta yi tama jin kamar rauni zai kamata kamar hawaye zai zubo. A daidai lokacin kuma ruwa ya saƙo da wani irin karfi,ruwa mai feshi da iska. Ƙanƙame jikimta ta yi da sauri,ba ta son ruwan sama ya taɓa mata fata ko.kaɗan,amma a yanzu tana.ji tama gani ruwa yana dukanta,babu yadda za ta yi. Babu alamar gurin fakewa hasali ma ko bishiyun kirki babu a gurin. Jama'a suna zaune a muhalansu haka kawai an rabosu da su an zo an killace su a guri ɗaya saboda son zuciyar wasu da wata manufa tasu ta daban. Ruwan sama a ka cigaba da yi kamar da bakin kwarya,kafin ka ce me tuni ta fara fita daga hayyacinta,ruwan baya bari ka shaƙi iska yadda ya kamata. Ko da a ka gama shekan ruwan tuni zazzaɓi ya rufeta,dama ga yunwa ga wahalar tafiya,gashi har yanzu ba su ba su komai ba. A haka suka kwana har garin Allah ya waye ba a daina yayyafi duka ba ga ruwan ya kwanta a inda suke. Dafa ta Faɗime ta yi cikin rawar sanyi ta ce"Adda yunwa nake ji,kuma sanyi nake.ji" Ɗa kyar ta buɗe idonta ta da suka yi mata dauyi ta kalleta,ta ce "Faɗime wannan ita ce kaddararmu mu amsa da hannu bibbiyu,mu ce alhamdulilah,Allah shine abin godiya a kowa ne hali... Maganarta ce ta katse sakamakon ganin ɗaya daga cikin ƴan ta'addan ya tun karo inda suke Gurasa ya shiga raba musu guɗa ɗaiɗai. Sai da ya gama bawa kowa sannan ya koma ya zauna. Bin guras da kallo Faɗime ta yi a bushe take sosai gata yar karama,ba ta tunanin guda biyar za ta rage mata yuwanr da take ji ma. Amma a haka har da zumuɗi wasu suke ci saboda azabar yunwa. Chubaɗo da ruwan da a ka yi ya sa ta farka har ta dawo kusa da su ne ta miƙa mata ta ta gurasar ta ce"Haɗa da tawa ki ci." Girgiza kai Zahra ta yi ta ce"a'a bari na ba ta tawa ke ki ci ko dan saboda ɗan cikinki. Kallonsu Faɗime ta yi a take hawaye ya cika idonta,su sun yarda ta ci su kuma su zauna haka,alhalin tare sa duka suka sha wahalar,amma ba su daina tausayinta ba. Kallon hannun Zahra ta yi da ta kawo shi saitin bakinta.A hankali ta buɗe bakin ta saka mata gurasar.Lumshe idonta ta yi hawaye ya zubo,ashe har yanzu da saura,har yanzu da sauran wanda zata kalla ta kira shi da masoyi. Daukar ta ta ta yi itama ta rana biyu ta bawa Zahra rabin a baki,kamar ba za ta amsa ba sai kuma ta karba. Ɗayar rabin kuma ta bawa Chubaɗo Murmushi Chubaɗo ta yi wanda ba ta shirya masa ba. Ganin mutane suna da zuwa gefe kaɗan daga inda suke ne suna shan ruwa,gurin ruwan da a ka yi ya taru a gurin sosai. Suma suka miƙe suka karasa domin sha.. ɗibar ruwan Zahra ta yi ta kai bakinta,ya mutse fuska ta ɗan yi,saboda yadda ta ji cikinta ya daure sosai,ta san kwana kin da ta yi ne ba tare da ta saka masa komai ba. "Ki daina yi wa waƴen nan mutanen taurin kai ba a yi musu,domin ba su da imani ko misƙala zaratun,nan ba kamar ko wanne gurin masu garkuwa da mutane bane. Nan din na musamman ne,ba su da imani ko tausayi ,a shawarce ka da ki kuma,ki yi abin da suka ce miki kawai shine mafitarki" "Idan naƙi fa?" WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR YOTA...019 PAGE 37__38 https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH?mode=gi_t https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z BISMILLAHIR_RAHAMANIR__RAHIM. "Shin idan na yi abin da suka ce za su sake ni?Ko za su gyara abin da suka ɓata." "Idan kika ƙi,za su gana miki ukuba, wadda ko a labari ba ki taɓa jinta ba." Ɗago ido Zahra ta yi ta kalli matar da a kalla zata haifeta Itama tana tsugunne tana shan ruwan. Bushashshen murmushi ta sakar mata ta ce "Ai daɗi abin duk wahalar da za su gana min iya duniya ce,ko za su iya bi na lahira su cigaba da gana min azabar?" Jinjina kai matar ta yi ,tana yi wa Zahra kallon tausayi,lallai da ta san ina ne inda ta shigo da ta shiga taitayinta,akwai da yawa wayen da suka yi ra oshin kunya amma ba su kai labari ba. Ita gabaɗaya abin da Shugaba ya yi ne yake bata mamaki,lallai wanan yarinyar mai tsananin sa'a ce,amma tana tsorace mata me zai faru idan har ya dawo,domin kuwa ba ya yafiya a rayuwarsa. Ehbar ruwan ta yi ta zuba a fuskarta duk da sanyi da take ji cikin wani irin yanayi Ta ce "Mene ne abu mafi tsoratarwa ga dan adam? "Mutuwa?" "Kwanciyar kabari?" "Tsayuwa a gaban mahaliccinmu,ranar da abin da ka aikata ba ya ɓuya,ranar da gabɓanka za su yi bayanin abin da ka aikata.?" Baka littafinka,karɓa wala da hagu ko da dama. Tsalakar siraɗi. "Sakamakon karshe wuta ko aljanna ?" "Ina ga sune abu mafi tsoratarwa ga duk wani mai rai ko? "Faɗa min wanne daga ciki za su sa a fasa?Ko kuma har kabarina za su bini su cigaba da gana min zabar?So kike mu cigaba da tsoronsu kullum su cigaba da azabtar da mu,suna bautar damu? Ba suda imani ba su da tausayi,dan miyasa za mu yi musu biyayya?Ku kuke tsoran mutuwa ni bana tsoranta".. "Idan suna ganin sun fi mu karfi ai ba su karfin Allah ba" Jinjuna kai matar ta yi Tace "Duk na san da wannan ,ba za ki gane abin da nake faɗa miki ba sai kin gani da idaonki". Miƙewa Zahra ta yi ta ja hannun faɗime suka nufi inda suka tashi ba tare da ta sake tankawa matar nan ba.. "Zainab ,Fateemah,mu yi addu'a addu'a ita ce takobin mumini,ba muda wani wayo ko da barar da ta wuce mu nemi daukin ubangiji,yana sane da mu,ya san halin da muke ciki,muna kuma kyautata zaton zai kawo mana dauki a kowa ne lokaci" "Shin kuna tare da ni?" Jinjina kai Chubaɗo ta yi ta ce "Adda kin kasance haske a cikin duhu a gare mu,kin kasance inuma me kare mana rana,tabbas kin zame mana abin alfahari,kin fara tsamo mahaimata daga duhun jahilci zuwa haske na islama.A lokacin da muka karɓe ki da hannu bibbiyu domin gyara kura-kutanmu a kan addinin mu,a lokacin a ka shigo a ka tarwatsa mana komai a ka kashe iyayenmu a ka ƙona gawawwakinsu,a ka kora dabbobinmu a ka ci mutunci masu mutimcin,a ka keta rigar alfarmar da take lillaɓe da mu ,a ka ƙona mana rugarmu" Adaidai lokacin da komai ya kare sai ya zamana ke ce abin da muke kallo a matsayim jigonmu,ni dai ina tare da ke,ina tare da ke har zuwa bugun numfashina na ƙarshe!" Ta faɗa tana ɗaura hannunta akan nata,Hawayr ne ya zubowa Faɗime ta buɗe baki a hankali ta ce"Inna,Baffa,Adda!Ita ma ta daura hannunta a kan nata. "Mu yi addu'a mu faɗawa Allah zai sauraremu fiye da yadda wani mahaluƙin zai ji mu ." "La'ilah ha'illa'anta subhanaka innikuntu mina zalumin" Mu yi addu'ar nan domin ita ce addu'ar da Allah ya kubtar da Annabinsa Yunus,A.S. daga cikin kifi,mu yi ta da yaƙini in sha Allah Allah zai duba mu. Addu'ar suka shiga maimatawa cike da yaƙi ni. Kallon ƴar ranar da ta fita Zahra ta yi lokacin sallar azahar ya yi,ba ta ga kowa daga cikin mutanen da suke tsare sun yi sallah ba. Ta kalli Chubaɗo ta ce"Zainab lokacin sallah ya yi fa,ban ga kowa ya yi ba,ɗazu ma da asuba ban ga kowa ya yi ba.Nima ɗazu da na ji bazan iya tashi ba saboda zazzaɓi a inda nake na yi sallar. "Amma ina zuwa bari na je na yi alwala" Jinjina kai Chubaɗo ta yi ta ce"idan kin yi nima zan yi,amma ba kya ganin gwara kawai mu yi taimama?" Bata kai ga ba ta amsa ba, suka tsinkayi muryar wani datitjo da da alama shima ba a daɗe da kawo shiba,don kayan jikinsa masu kyau ne. "Dan Allah ina ne gabas?" Shiru a ka yi ,tsoro ya bayyana a fuskar dayawa daga cikin mutanen gurin. Sake maimaita tambayar ya yi wadda ta jawo hankalin wasu daga cikin ƴan bindigar,Shiru ne ya kara ratsa gurin gabaɗaya mutane a tsora ce suke. Cike da mamaki Zahra ta kai dubanta kan matar da ta yi mata magana ɗazu,amma sai matar ta kawar da kanta gefe. Mutumin nan bai gajiya ba ya sake tambaya,ba da karfi ya yake maganar ba,amma ana ji. A fusace Basiru dake naɗa wiwi ya taso ,ya kai masa mari,da sauri dattijon ya kauce,hakan ya sake fusata shi,ya kai masa mangari da bindigar da ke hannunsa Ya ce "Uban wa ya gaya maka ana sallah a gurin nan da zaka damemu?Toh ba a yi,ka koma ka zauna inda a ka ce maka. Mamaki ne ya bayyana a fuskar Dattijon,mai damu da dukan da ya yi masa.ba,duk da yadda yake ganin jiri. Ya ce "Ku yi hakuri gaskiya ba zan iya yi muku biyayya a kan abin da ka ce ba" Ya juya ya kalli inda zuciyarsa tafi ayyana masa gabas ce ya tada sallarsa. A fusace ya rufesa da duka yana yi yama zaginsa,da harbinsa da kafa. Bai daina yin sallar ba,a haka ya kai ruku'u,ya ɗago ya kai sujjada,ya kuma miƙewa. Wanda ya harbe Inna ne ya ce ka harbe shi kafin Shugaba ya zo,laifin ya dawo kanmu." Kan bindiga Basiru ya sa ya maka nasa a ƙeya,sannan ya saita shi da bindiga. A galabace mutumin ya kallesu sannan ya fara magana. "Ina miƙa godiyata ga Allah da ya sa ban sha wahala ba yadda ake cewa kuna bada wahala.Ina so ku san wani abu a har kullum har kuma abada gaskiya ita ce saman karya,duk adonda za a yi mata ,bare taku da a bayyane take. Babu inda wannan zaluncin da kuke kira da sana'a zai kaiku face tamkin ladama,da danasa..." Bai karasa ba ya ƙara maka buga masa bindiga a baki. Ya ce Allahn da kake cewa ba za ka saɓa masa ba,me yasa bai hana mu kamaka ba?Me yasa kuma bai kubutar da kai ba?" "Yanzu zan kashe ka,idan ka je can sai ka gayawa Allahn" Murmushi mutumin ya yi ya ce"Ina mara da wamnan kisan da za ka yi min,amma ka sani ka yi kuskure,lallai Allah zai nuna muku buyarsa da karfin mulkinsa." Ya faɗa sannan ya fara maimaita kalmatu shihada. Tasss!!!!Tasss!!!Tasss!! Shine sautin da ya tashi kafin jinin mutumin ya yi feshi. Da sauri Basiru ya juya domin ba shi ya yi harsbin ba. Shugaba ne tsaye hannunsa riƙe da ƙaramar bindiga yana wani murmushi,na rashin imani,babu wanda ya lura da ya zo,sai da ya yi harbin. Da sauri mutane suka mimmiƙe. Takowa ya yi ya karasa inda gawar mutumin take,ya ɗebo jininda da yake zuba ya ce "Wannan shine hukuncin duk wanda xai karya mana,doka . Ya kalli Basiru ya ce"ku kira iyalensa a karɓi kuɗin fansarsa,sannan a tura musu gawarsa" Ya karasa faɗa sannan ya juya ,har ya tafi sai ya tsaya ya juyo ya kalli Zahra sannan ya juya ya cigaba da tafiya. Ko motsin kirki mutane kasa yi suka yi,saboda tsoro,da firgici. Ba a wani jima ba ya dawo ,wasu mutane suna biye da shi, jikinsu sanye da suit,sai wani babban mutum da ya sha malinmalin,da alama wani babbane a kasar. Suka karasa suna tattaunawa. Wani irin firgici ne ya sake bayyana a fuskar mutanen da suka daɗe a tsare. "Mutum nawa kuke so yanzu toh?" "Jaririn da ya kai haihuwa wanda ba a haifashi ba,da kuma jinin uwar ɗan,kuma uwar ɗan ka da ta haura shekara ashirin,sai kuma maganar Odojin da muka yi,idan za a samu ta mutum goma muke so,sai kuma jinin budurwar,da a ka kwanta da ita,ma'ana jinin da ta zubar lokacin saduwar" Jinjina kai ya yi ya ce"babu damuwa amma kasan dokar ai,babu maganar saɓa alƙawari,dole sai ka cika" Rass!Rass!Rass! Haka zuciyar Zahra ta buga tabbas ba za ta taɓa manta wannan muryar ba sannanniya ce a gare ta,toh me ya kawosa nan?Kuma ne yasa yake neman wayen nan abubuwan?Gabaɗaya kanta ya kulle. Zuciyarta ce ta yi mata wani irin dauyi,ta tsananta bugu lokacin da ta tsinka yi muryar bafulata nin mutumin yana umartar wannan alhajin a kan ya duba suwa ye za su yi a cikinsu. Kara sun kuyar da kanta ta yi ,ashe da gaske wayen nan mutanen suna tare da masu riƙe da madafan iko,ashe da gaske aiki suke musu,inkuwa hakane babu shakka su kansu masu aiki,wawaye ne,sune suke buya a cikin daji,suna rayuwa a kankance a wulakance,idan a ka kashe su kuma an kashe banza,kuma sun yi musu amfani,su suna zaune da fuskar na kirki,lallai akwai gyara a ƙasar nan. Tunanin ta ne ya katsse l lokacin da ta ji,kukan mutane ya gwairaye gurim,a wulakance masu Suit ɗin nan suke janyo duk wanda a ka nuna musu su fito da shi sarari. Babu abin da jikjn mutanen gurin yak3 sai raya,saboda sun sani gwara a harbe su da a yi musu irin wannan kusan.Ga shi kowa bai san a za a zaɓa daga cikinsu ba. "Yauwa ga wara can za ta yi" Mutumin ya nuna Chubaɗa da take zaune ita ma a tsorace. Ido ne ya dawo kanta,da sauri ta kalli Zahra irin kallon nan me nuna da gaske da ni yake? Shiru ZAhra ta yi zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri,tun da ta zo gurin nan wannan ne karo na farko da ta ji faegaba ta ratsata. Tsanan nin sin rayuwa ne ya bayyana a fuskar Chubaɗo,domin sare ta fuskanci ita ce irin macen da a ke kwatantawa. Ai ba ta gama tunanin ba mutana nen suka ƙara so inda take,da sauri ta miƙe tama ja da baya,fugota ɗaya daga cikin su ya yi,cike da rashim imani. Da sauri Zahra da ta miƙe ta riƙe Chubaɗa,Faɗimr ma tuni ta fara kuka. Wani irin kasaitacen murmushinr ya bayyana a fuskar Shugaba,ganin kamar da sabo a tsakanin ta da.Chubaɗo,amma har yanzu wani abin mamaki,da Zarar ya kalli sashjn da take sai gabansa ya yake.ya faɗi. Tumi ta manta da mutumin da take ɓoyewa fuska,ta shiga kokuwa da su suna wular da ita ,tana kuma ta shi ta kama ta ,domin ba ta taba sanin da gaske ta shaƙu da Chubaɗo ba sai yanzu da ake.koƙarin raba su,rabuwa ta har abada,rabuwa mafi muni. Kasanceawar akwai bambanci tsakankn karfin mace da namiji ne.ya sa ɗaya daha cikinsu ya falla mata wani gigitacen marim da sai da wasu taurari suka gibta a kanta,ya hanƙaɗ ta gefe ta faɗi a galabaice. HankLin Alhajin nan ne ya koma kanta,hanin sai kai ruwa rama a ke da ita a kan kawai an ɗauki Chubaɗo,duk sauran babu wanda ya yi koƙarin rigima sai ita. Shi abin ma mamaki ya ba shi,ai ya yi zaton baki ɗaya mutanen gurin Balejo ya riga ya rufe musu baki,amma sai ya ga Zahra tana wannan abun. Gabansa ne ya yanke ya faɗi lokacin da idonsa ya kai kan gefen fuskarta, kamar ya san me wannan fuskar!!! Toh amma a ina? WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR YOTA...019 PAGE 39 and. 40. https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Bismillahir_rahamanir_rahim. Kawar da tunanin ya yi sakamakon kiran wayarsa da aka yi. Ya ɗaga ya koma gefe yana amsawa. Wata budurwa aka dauka wadda take tare da mahaifiyarta,maman nata sai kuka take tana ba su hakuri ,amma ko saurarta sunƙi yi. Chubaɗo na kuka,Zahra na yi,Faɗime na yi haka suka janye ta daga cikinsu,suka saka ta cikin mutanen da za a karkashe. Wani Murmushi shugaba ya yi ya ce"yau a nan za a yi aikin ku dauko kayan aiki" Ya faɗa yana ƙara sakin murmushin mugunta. Zahra da babu abin da take sai a jiyar zuciya,ba ta ma ankara da kallon da yake mata ba,tana hanun matar nan da ta yi mata magana ,lokacin da suka je shan ruwa,ta yi mata kyakykwan riƙo ta kasa kwacewa kawai sai ta koma ajiyar zuciya. Da sauri suka kawo wukake da wasu makamai,,da wata freezer babba sosai .Mamaki ne ya kama Zahra,dama a irin wannan dajin har za a samu waƴan nan abubuwan ne? Tunanin ta ne ya katse ganin an buɗe freezer nan.Kawunan mutane ne a ciki,da wasu sassan jikinsu,sai kuma kasanta,ƙoda ce,da kwayar ido,da abubuwa makamantan su. Da sauri ta rufe idonta ta buɗe toh su kuma ban da garkuwa da mutane,har mafiya suke yi? Ko safarar sassan jikin ɗan adam suke? Tashin hankali,firgice,tsoro ne suka bayyana a fuskarta,da sauri da kalli Chubaɗo da ta zuba mata ido ita ma.A cikin idanunta ta hango kaumar rayuwa,kanta ta maida kan Fadime da ta zubawa gurin da ta gama kalla ido.Da sauri ta rufe mata idonta,hannu ta saka a hankali ta zame hannu Zahra ta kalle ta,sannan ta girgiza mata kai,alamar ta ƙyaleta,ta mai da kanta kan Chubaɗo ba tare da ta furta wata kalma ba. A take wani abu da ya faru dazu ya shiga dawo mata. Suna cikin yin addu'ar nan da ta ce su yi,Chubaɗo ta kaleta ta ce"Addarmu gabana faɗuwa yake,cikina sai juyawa yake" Ba ta jira ta ba ta amsa ba ta cigaba "Adda dan Allah na roƙeki wata alfarma?" Jinjina kai Zahra ta yi ba tare da ta yi magana ba. "Dan Allah ki miƙe kafarki na kwanta!" Ta faɗa tana kallon ta,a ɗarare,domin ba ta saba da ita kamar yadda Fadime ta saba ba. Jinjina mata kai ta yi alamar eh. Zamewa ta yi a hankali ta kwanta. "Wash!Na ji daɗin kwanciyar nan,kamar kar na tashi" Ɗan murmushi Zahra ta yi ta ce "kuma sai kin tashi ba" Ɓata fuska ta yi ta ce "kai Adda ni ce fa,Adda na miki wata tambaya ranki ba zai ɓaci ba?" Farat Faɗime ta yi ta ce "Eh ki tambayanni babu matsala". "Harara ta watsa mata ta ce waya saka dake?" "Ni na saka da kaina" "Faɗan za ku yi ko tambayata za ki yi?" "Tambayarki zan yi Addarmu" "Toh Zee tambaye ni" Murmushi Chubaɗo ta yi ta ce"Adda yanzu ku kadai kuka rage min,Allah ya sa kar wani daga cikinku ya rigani mutuwa" Haɗe rai Zahra ta yi ba tare da ta ce komai ba,ta fahimci yau kuma surutu dake ji da shi,ita kuna addu'a ce a gabanta.. Hannunta ta kama da take tazbihi da shi ta ce"Adda ki bar tambayar kawai na fasa,kar ranki ya baci." "Tambaye ni" Ta fada a taƙaice tana kokarin sakin fuskarta. Ta fahimci so take ta rage musu damuwa ne koyaya.. Maganar da ta fito daga bakinta ce ta yi sanadiyar,gushewar murmushin da yake kan fuskarta. "Adda dan Allah wace ce ke?Daga ina kike yar wane gari ce?Me ya sa ki ka zo Rugarmu?Ina iyayenki?Me ya sa bakya son yin maganarsu?"Dan Allah ki ba mu labarinki ko da ba duka ba." Ta fada tana riƙe hannunta.. Lumshe idanunta ta yi,a take hotunan komai yake gibta mata a cikin idonta,tamkar a yanzu ake yi. Da sauri ta buɗe idonta da suka sauya daga launinsu zuwa ja,dama har yanzu akwai zazzaɓi a jikimta. "Ba shi da daɗi fa!" Ta fada a hankali kamar mai koyan magana. A yanzu har da faɗime gurin haɗa bakin "eh muna so a hakan".. Wani murmushi ta yi da yafi kuka ciwo ta ce"Zan baku labarin Zahra yar gayu,ƴar gata,shalelen Ammi da Abbi,yadda kaddara ta sauya komai rana daya.Na san ba ku taɓa jin labari makamcin wannan ba,toh zan baku,amma ba yanzu ba,sai ranar da muka kubta daga nan gurin,ina ji a jikina zamu kub.." "Idan ba mu kubuta ba fa?Ko suka kashe wani a cikinmu fa?" Chubaɗu ta furta Zuciyarta ce ta buga da karfi,amma sai ta daure ta ce"Muna da Allah,mun dogara da shi. "Hakane Adda amma kaddara ta riga fata!" Harara ta wurga mata ta maida kanta gefe alamar ta ji haushi. Damke hannunta ta yi ta ce"ki yi hakuri,shiyasa na ce ba zan tambayeki ba." Jinjina mata hannunta ta yi alamar babu komai. Faɗime ma jikinta duk ya yi sanyi don har ga Allah tana son ta ji wace ce Addarta. Kamar daga sama ta fara magana "Sunana Fateemah Bintu zahra,na san kusan wannan." Lumshe idonta ta yi tana jin kamar abin da za ta fada saɓo ne, a hankali ta ce "Fateemah Abubakar Dan Gaske!" shine full name ɗina,ni ƴa ce ga mataimakin Shugaban kasa,a Abuja nake da zama" Shiru ta yi,su kuma suka zuba mata ido,suna jiran karin bayani. "Ki cigabaaa" Faɗime ta fadi a shagwaɓe. "Ki rabu dani Teema,ba yanzu ba,yanzu lokacin addu'a ne, ban san sanda zan gama muku labarin nan ba idan na fara." Jinjina kai Chubaɗo ta yi ta ce hakane,amma zuciyata na tsananin so,amma yanzu addu'a ita ta fiye mana" A firgice ta dawo daga duniyar tunani. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta faɗa a bayyane tana ƙoƙarin kwace riƙon da matar nan ta yi mata,sakanakon abin da ta gani,a take kanta ya fara juyawa. Mutum aka yanka da wata adda,abin mamakin shine ba a bari jinin mutumin ya tafi a banza ba,don wani katoton ƙoƙo suka saka suna tare jinin,wani irin shiru gurin ya dauka bayan da aka gama. Juyowa Shugaba ya yi ya kalli Zahra,da ta sandare a guri ɗaya,murnushi ya kuma saki domin ganin alamun abin ya taɓa ta,a ranshi ya ce"tun yanzu?" sai kuma ya kara fuskantar ilahirin jama'ar gurin da yaren fullanci y ce"Ki akwai me magana" Shiru suka yi babu wanda ya tanka,tih su tanka su ce me? Yarimyar nan aka janyo wanda aka kama tare da mahaifiyarta,a gaban mahaifiyarta da sauran mutane,suka rabata da rigar mutuncinta,su ka keta alfarmarta ta ƴa mace,samman suka ɗebi abin da suke so .. Wani irin kuka Mamanta ta fashe da shi, mai taɓa zuciya,ta musu magiya ta yi kuka amma ba su saurara ba,ta roƙe su,su kyale mata yarta,ita su yi abin da za su yi da ita,amma inaa,ba su daina abin da suke so ba,daga karshe ma Shugaba ya sa suka rirriƙeta,ya kuma ce a gabnta za a yi. Ganin sun gama ne ya sa suka saki maman nata,da gudu ta karasa inda tilon ɗiyarta take,wadda ba ta samu arzikin ko zani su yafa mata ba. Dan kwalin kanta ta cirre ta yafa mata,saboda zanin nata shi suka shimfiɗa suka ci mutumcinta.. Rungumeta ta yi ta cigaba da kukanta. Ko kallo ba ta ishi su ba suka cigaba da abin da suke yi. lumshe ido ta yi ta buɗe a hankali,zuciyarta tana wata iriyar tafasa,kenan haka za su yi wa Chibaɗo ma?So take ta juya ta rufe wa Faɗime ido, don karta ga abin da ake yi,sai dai ta san ta makara,domin ba ta jin za ta iya juyawa ma bare su hada ido. Ai ba ta san lokacin da ta yunkura ta miƙe,ta kwace rukon da matar nan ta yi mata ba.Da gudu ta yi inda suke,suna jan Chubado da take tiirjewa. Riƙe ta ta yi irin ruƙon nan na duk abin da za ku yi mata,sai dai ku haɗa da ni. Juyim duniyar nan ta hana su yin aikinsu.Chubaɗo kuwa har ta fara fita daga hayyacinta,ga tsoro da fargaba duk da ta kudirta a ranta duk abin da ya faru da ita Allah yana sane da ita. Wani gigitaccen mari Basiru ya kifa mata,shiru ta ji wajen ya ƙara dauka don tabbas ta maru,sai dai babu alamr za ta sake ta,duk da yanzu iya hannunta ne ta riƙe. Murmushi Shugaba ya kuma saki"Yarinyar nan tana da taurin kai"Ya fada a ransa ,kafin ya fara takowa ya nufo inda take gabansa yana tsannanta bugu. Mamaki ne ya bayyana har a kan fuskarsa,domin ji ya yi kamar zuciyarsa za ta fito waje. Tsayawa ya yi a gabanta sannan ya miƙa musu hannu,wata sharɓebiyar adda aka daura masa.. Cak numfashinta da idanunta,da kukan da take gunjin yi suka tsaya. Ba komai ne ya tsayar da su ba face ganin hannun Chubaɗo da take riƙe da shi ya bar gangar jikinta. Wasu abubuwa ta ji suna mata yawo a kai kamar kiyashi,ai bata tsinke da al'amarinsu ba,sai da ta ga Shugaba ya daura addar nan saman marar Chubaɗo ya ja,a take kuwa jini ya fara aikinsa. Da sauri ɗaya daga cikinsu ya kawar da kansa gefe domin magana ta Allah tun da ya shigo harakar nan, bai taɓa haɗuwa da abin da ya daki zuciyarsa ba irin kisan mai cikin nan. Dishi dishi Faɗime ta fara gani,tabbas abin nan ya mata girma. Mutum aka kashe a gabanta mutun ɗin ma Addar? Bayan kashe mata Inna da Baffa? A hankali ta sulale a gurin,numfashinta na kokarin barin gangar jikinta. Zahra kuwa kamar gunki ta zama ita dai ta san ba ta mutu ba,ba kuma ta suma ba,amma ta gagara motsa ko da farcenta ne.Addu'ar ma ta kasa bare wata magana,kawai kallomsu take. Sai wani irin buɗewa da zuciyarta take yi. Mai yasa bata ba ta labarin tun ɗazu ba?Mai yasa ta ce mata sai sun kubuta?Ta ce ta gaya mata wace ce ita ko da shi kaɗai ne ya rage a abin da zata sani kafin ta bar duniya. Amma ta yi watsi da maganarta. Me yasa !? Me yasan!? Why !? Su kuwa cike da rashin imani suka ciro dan cikinta.Namiji ne a halittarsa babu abin da bai bayyana ba. Ba karamin tsorata ilahirin jama'ar gurim suka yi ba,don da gaske an aitaka rashin imani,yau abin nasu na musamman ne. ★★★ Mai Dollars Family Minal. Ba ta saurari kiran da Mommy take mata ba, ta yi ɗaki da gudu ta dauko keyn motarta ta fito. "Lafiya kuwa?Tariq ya tambaya,ganin tashin hankalin da yake fuskarta. "Aminatu" Hammad ya faɗa yana bin ta da kallo,gabaɗaya ta rikice. Hannun Tariq ta riƙe numfashinta har wani sama da ƙasa yake yi Ta ce "Tariq sun ce ba ta numfashi!Idan ta mutu ni ma mutuwa zan yi,ita kaɗai ce farincikina" Assalamu alaikum jama'ar kwarai fatan kuma lafiya?Allah ya sa haka.Na ce duk wanda yake karanra littafin nan ya min magana ina son na buɗe group naku na musamman Nagde WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR YOTA...019 PAGE 41___42 https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Bismillahir_rahamanir_rahim. "Wace ce ?" Ya tambaya yana kallonta cike da mamaki. Sakin hannunsa ta yi ta yi hanyar fita da gudu,ba tare da ta sake tanka masa ba. Kallonsu Hammad ya yi ya ce "ku je kawai bari na bi bayanta" Jiki a sanyaye Mommy ta gyaɗa kai ta ce "mu je Tariq" "Amma Mommy kalli halin da take ciki fa" Ba ta ce masa komai ba ta yi hanyar fita,zuciyarta tana bugawa. Juyawa ya yi jiki a sanyaye ya bi biyanta. Da sauri Hammad ya bi bayanta yana kwala mata kira,amma Inaa,ko da ya fito ma lokacin ta danna hancin motarta waje a guje. Da sauri ya shiga ta shi motar ya bi bayanta. Mamaki ne ya bayyana a kan fuskar Danial,Idi me bawa fulawowi ruwa ya kalla ya ce"Hausa man Mai Dallors Family babu lafiya,na ga Alhaji ya fito ankali a tashe ga ƴar Ajiya ga Oga" Harara Idi ya watsa masa ya ce"Ina ruwanka? C.T.V camera,wai kai aiki ka zo yi ne ko sa ido? Turbune fuska ya yi yana shirin ba shi amsa ,Musa ya ƙaraso gurin ,ya ji abin da Idi ya ce don shi bai iya magana a hankali ba ya ce Kai fa Idi ba ka da kirki ya zaka ringa gwasale mutum,Danial ina jinka ni faɗa min." Wani banzan kallo Idi ya watsa masa cikin ɗaga murya ya ce"Ni ba zan yi munafurci ba,don ina tsoron Allah,ina kuma tsoran azabarsa." "Mutane su ba ku ku ci ku ƙoshi,su baku makwanci,su kuma biya ku albashi ,amma ku ɓige da cin namansu" Kwashewa da dariya Musa ya yi ya ce"Sannu sarkin masu tauhidi,da tsoran Allah na duniya,ai da suke ba mu albashi aiki muke musu,gurin kwana kuwa silar aikin ne" "Kuɗin ma da namu ne, duk babakere ake mana da dukiya" "Dake ubanka ne ya nema musu ko?" "Ko ba ubana ne ya nema ba,ina da tabbacin cikin wamnan uwar dukiyar anyi babakere da hakkin talakawa,kuma kasona Allah ya isa" Juyawa Idi ya yi ya tafi ba tare da ya tanka masa ba,don indai munafurci ne a barwa Musa da Danial a cikin gidan nan. Kasa da murya Musa ya yi ya ce "shege fuska annabi musa zuci fir'auna,kai Danial tsegunta min" Gyara tayuwarsa ya yi ya shiga kora masa yanayin da ya ga Familyn Waro Ido ya yi ya ce"kai haba?Allah ya sa lafiya kasan ƙarar fitar motar Auta ne ya sa na fito,na ga me ke faruwa" "Fatan mu dai koma mene ne ayi shi a cikin gidan nan,dan da a baka labari gwara ka bayar.Ladidi take tsegunta min wai wannan me kama da turawan ta kusa dawowa" Waro ido Danial ya yi cikinsa ya kaɗa ,shi dai Allah ya zuba masa tsoram matar nan,kwarjininta ke sa shi rikicewa wani sa'in. Da gudu ya yi hanyar banɗaki ya ce wait Musa cikina ba daɗi bari na fito." Da harara ya bi shi yana ganin ya shige ya ce"shege ɗan inyamura masu kashi a leda,a haka zaka kare kullum cikin zagayen banɗaki" Ya faɗa sannan ya yi gaba da sauri tunawa da abin da yasa cikin Danial ya hautsina. ★★★ Wani irin gudu take saman titin tamkar don ita kaɗai aka yi shi. Allah ne kawai yake kare ta don ba ta san sau nawa ta kusa haɗa haɗari ba. Da sauri ta dauki wayarta da take ruri "Gani nan saura kaɗan na ƙaraso" Ta faɗa sannan ta ajiye wayar Cikin ƙanƙanin lokaci ta ƙarasa Danna hancin motar ta yi cikin Darul Fiyya Federal Medical Center (FMC Darul Fiyya) Motar ƴan sanda ta gani a tsakiyar Asibitin da mutane sun yi carko-carko. Bata tsaya daidaita parking yadda ya kamata ba ta fito,duk da abin mamaki ne ganin yan sanda dayawa haka a asibiti,da kuma mutane masu yawa ,amma ba ta bi ta kansu ba dan ba shine abin da ya dame ta ba. Tana shirin kiran numbern da a ka kira ta,kawai sai ta ɗaga kanta wannan mutumin da ta bashi kuɗi ta hango,shi da wasu mutane da ba ta iya tantance ko suwaye ba.Da sauri ta karasa gurinsa tana tambayarsa tana ina ?Me ya same ta. Tsayawa suka yi suna kallonta kowa yaƙi magana musamman wanda ta bawa kuɗin nan sai inda-inda suke yi. Hankalinta ne ya ƙara tashi sosai,kama hannun mutumin nan ta yi ta ce"Ina Mamahna?Ko ta mutu ne?Ku faɗa min dan Allah,kun ce sai na zo gani na zo,dan Allah,dan Allah" Ta faɗa wasu hawaye masu zafi suna gangaro mata. Dama ita ko a banza hawaye ba ya mata wahala,bare ta yi dalili. Mamaki ne y kama mutanan gurin aka fara kallon kallo Sai a lokacim Hammad ya ƙaraso gurin hankali tashe,dan bai san akan wa Minal za ta tayar da hankalinta har haka ba. Ɗaya daga cikinsu ne ya kalleta cike da mamaki,ya ce" Mamanki tana nan ba ta mutu ba,amma tana cikin mugun halin da gwara mutuwa da shi,dama tana da ƴa amma ki xka barta take rayuwa a ƙaskance,har hakan ya yi sanadin rayuwarta ta kusa salwanta,aka kuma ci mutuncinta haka?" A dake Hammad ya ce sharhi aka tambayeka yi? Kallom Hammad ya yi yana hura hanci sa kuma ya kawar da kansa ganin babu wargi saman fuskar. Cike da gatsali da jin hushin maganar da ya gaya masa ya ce "Can muka tsintota gefen bola wasu matasa su biyar sun ci mutuncinta yadda suke so,da alama ma ko gurin boka suka je ya ba su sa'a,amma duk sun mutu a gurin bayan da suka gama . Dummm dummm haka zuciyar Minal da Hammad ta buga a tare.. "kamar ya sun ci mutuncinta?". Hammad dai bai ce komai ba,sai bugun da ya ji zuciyarsa tana yi,ya tsani wannan kalmar. Ba tare da ya shiryawa maganar ba ta fito " Rape??" Jinjina kai mutumi nan ya yi ya ce "eh fa, kasan burim duniya ya rufe mana ido ,kowa burinsa ya samu abin duniya,yanzu dai gashi sun yi mummunan ƙarshe sun bar duniyar ba su cika burin nasu ba" "Gawarwakin nasu suna hannnun hukuma yanzu." Kallon bakinsa kawai yake ba tare da yana fahimtar a abin da yake faɗa ba. Wani irin buɗewa ta ji zuciyarta tana yi,wai fyaɗe mene ma haka? A take kwakwalwarta ta wasko mata manufar maganar tasa. Kanta ta ji ya fara juyawa,idanunta suna ganin duhu,numfashinta ya shiga sarƙewa. Ai ba su ankara ba suka ji karar faɗuwarta. Da sauri su ka yi kanta suna salati,ɗaga musu hannu ya yi ba tare da ya ce musu komai ba. Inhaler dinta ya fara lalube sai dai kwata+ kwata bai ganta ba da alama ma bata fito da ita ba. Tsugunnawa ya yi ya kara hannunsa a saitin hancinta don tabbatarwa. Ɗagowa ya yi ya kalli mutumin nan da ya yi maganar ya ce"idan wani abun ya same ta,ka kuka da kanka. Wani ɗan sanda ne y kara so inda suke ya ce"Lafiya?". "Eh lafiya,ciwonta ne ya tashi" Ya faɗa a taikaice Cak ya ɗaga ta ya nufi ciki da ita. Dayan hannunsa ya sa ya zaro wayarsa ya danna kiran Dr Hafiz, don dazu sun yi waya ya ce masa yana nan, kafin ya ɗaga ya hango shi yana tahowa da sauri da alama wani abu zai yi. Da sauri Dr Hafiz ya nufo inda yake ganin shi riƙe da mutum ya sa bai tsaya wata doguwar magana ba,ya yi wa wasu nurses magana suka dauko gadon mara lafiya aka daurata suka shiga da ita. Babu ba ta lokaci ya je ya yi duk abin da ya kamata sannan ya dawo. Sosai hankalinsa ya tukunzuma saboda ya san tana da matsalar numfashi,ga shi Hafiz ya hana sa shiga ɗakin wai ya jira a waje,wannan ba aikinsa ba ne. Babu abin da yake sai kaikawo kiran Mommy ne ya shigo wayar.Gabansa ya sake faɗuwa kamar ba zai ɗaga kuma sai ya ɗaga. A hankali ya ce "Mah" "Ya aka yi ne Hammad?Ina Auta a kan wa take kuka? Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba,har ta yi zaton ko wayar ce ta katse sai kuma ya ce "Gamu nan a Asibiti,ban san kuma akan wa take kuka ba,na dai san mace ce" "Kamar ya?Yi min bayani yadda zan gane mana,kuma me ku ke yi a asibitin?Gamu fa har mun dawo gida,akwai matsala ne?" "Am Mommy komai lafiya anjima kaɗan zamu dawo ,asmarta ce ta ɗan tashi" Ya faɗa a hankali don yana da tabbacin numfashinta ne ya sarƙe ta. Cike da tashin Hankali ta ce"kuma sai ka ce komai lafiya?Gamu nan zuwa asibitin" "Ok, sai kun zo" Ya faɗa sannan ya katse wayar. Bai daɗe da gama wayar ba Dr ya fito yana share gumi. Miƙewa ya yi da sauri ya yi ya ce"Yah" Alama ya masa da ya biyosa. Jinjina kansa kawai ya yi,amma sai ya fara shiga ɗakin hutun da aka kai ta.Bacci take yi,ya ɗan daɗe yana kallonta kafin ya juya ya fita. Kai tsaye office ɗinsa ya nufa ya shiga da sallama a bakinsa,ya nemi guri ya zauna. Amsawa ya yi yana ɗan rubuce rubucensa,bai ɗago ba sai da ya karasa.Ya kallesa ya ce" Dr ya haka?Meke damun yarinyar nan,jininta ya hau da yawa har haka ,gashi kasan yanayin lalurar nan ta ta,a ringa kulawa sosai Dr" Jinjina kansa ya yi ya ce "in sha Allah" Yanzu dai ba wata matsala hutu take buƙata,zuwa anjima ma idan ta tashi shikenan. Miƙewa ya yi tsaye ya ce"na gode sosai Hafiz za ka ji ni in sha Allah,za a kiyaye kuma" Hannu ya mika masa suka gaisa sannan ya yi hanyar fita,har ya kai bakin kofa sai kuma ya tsaya,ya juyo ya ce"kasan wata da aka kawo asibitin nan ɗazu?" Jim Ya dan yi sai kuma ya ce "ai yau an kawo mata da yawa,faɗa min wata alama ko zan gane" Ya tsani koda da kwatan ce kalmar nan ta fito daga bakinsa,dan haka sai ya ce"a gefen bola aka tsince ta" Take Hafiz ya harbo girjin Jinjin kai ya yi ya ce "Na shigo dazu na ji ana ta kace na ce akan ta,amma ina ga Auwal ne ya jagoranci karɓar ta,tun ɗazu muka rabu dashi za su shiga da ita tiyata,so ban sani ba yanzu ko an fito da ita ba. Ba ka ga police da mutane a waje ba?Ai duk a kan case ɗin ne." "Amma kasan ta ne?Na ji ana cewa wai mutanen da suka yi aika-aikan duk sun mutu,abin ya matukar daure min kai,matar ma an zaci ta cika da farko saboda yanayin halin da take ciki" "Kasan maganar ta girma sosai,media ta shiga sosai,na za ci ma ko ka ga posting ɗin" Maganganun Hafiz ya shiga jujjuya su a ƙwakwalwarsa yana musu ma'auni,toh amma meye haɗin Minal da matar nan,har ya ga soyayyarta me tsanani a idanunta,bayan ya san Minal rayuwarta ba ta damu da kowa ba sai Familynta .Amma toh ya aka yi haka zuciyarsa ta tambaya .. "Dr ya dai" Ɗagowa ya yi yana ƙokarin boye mamakin da ya shiga Ya ce "dama haka ta ringa faruwa ko da kuskure ka wulakanta rayuwar wata ka fadi ka mutu a gurin" Zaro ido Hafiz ya yi ya ce"kai abin da tashin hankali da mamaki su biyar fa aka ce,kuma ma ni ban yarda ba,waye ya gansu lokacin da suna aikatawa?Ya aka yi aka san sunne?Kuma babu wanda yake da tabbacin ba kashe su aka yi ba". Harara ya watsa masa ya ce "ba ka yarda ba ko?Ya za a yi ace sune idan ba a ga alamomi ba?Ko bayansu ka ke goya?Ko kuma ba su cancanci mutuwa ba?" Sanin halin Hammad na daukar zafi musamman a wannan fagen ne ya sa ya ce"ya za a yi na goyi bayansu kawai dai abun ne akwai daure kai sosai,fahimta ta ce baka yi ba." Amma ina ka sa wayarka ana ta nemanka ɗazun,ba a same ka ba nima na kikkiraka." Kafaɗarsa ya ɗage cikin halin ko'inkula ya ce "oho dai gaskiya za ta yi halinta ai.Bari na je kar su mommy su karaso ba su ganni ba.Wayata kuma ban san inda na jefa ta ba ɗazun,amma ai da ɗayan layin kuka kira zan gani,don ga ta a hannuna." Kuma Idan matar ta tashi ina so naga yanayin jikinta" Jinjin kai ya yi ya ce"Toh in sha Allah Dr me zamani" WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR YOTA..019 Page 43_44 https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Bismillahir_rahamanir_rahim Murmushi ya dan yi sannan ya ƙarasa fita daga office ɗin. ★★★ A harabar asibitin kuwa ce-ce-ke-ce ne ya kaure a gurin,mamakin dayawa daga cikin mutanen shi ne,kiranta daa sunan mahaifiya da Minal ta yi.Tuni wasu sun sa musu cemera a lokacin dan haka suka shiga daurawa a media.Gefe guda kuma,hankalin mutumin nan ya tashi sosai tun furucin da Hammad ya yi masa.Ya kalli na kusa da shi ya ce "Aminu gida zan tafi"Rike rigarsa Aminu ya yi ya ce"idan ka isa Allah ya kwashe min albarka,mu zaka bari a ruwa,Ba dai bakinka bashi da linzami ba?Toh bari ya fito mu ji,idan Kuma yarinyar ta mutu wallahi ka shiga uku,Dan ban ma sanka ba.Cewa zan yi a hanya muka hadu." Ya juya ya kali Abokanensa waƴenda tare suke dama ya ce "ko ya kuka ce?Idan wata matsala ta samu yarinyar nan zaku nuna kun san shi?" Kusan a tare suka shiga girgiza kai,"ba mu sanshi ba wallahi" Hannun ya daura aka, gumi yana yanko masa.Ya ga alamar wannan mutumin me kudi ne,dama an ce masu kudin nan ba su da mutunci.Ya ce"Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un,daga taimako?Na rantse da Allah Legos zan gudu" Kara rikesa Aminu ya yi,da yake jin kamar ya yi dariya,saboda ganin tsurewar da ya yi,amma sai ya daure,ya ce "sai ka bari ya fito mu ji ko rai ya yi halinsa,sai ka tafi libiya ma ba loges ba" "Dan ya rasulillahi ka daina maganar mutuwa,wallahi ba ta mutu ba,au in sha Allah,Aminu ni ne fa murtala abokinka" Ya fada yana marairaice fuska. Kwashewa da dariya wasu daga cikinsu su ka yi,Aminu har da dafe ciki.Cikin dariyar ya ce"Murtala ai sarai na gane ka ka,addu'a ita ta fiye maka ba sambatu ba" Addu'o'i ya shiga jerowa iri-iri,wasu ma be san me yake fada ba,gabadaya ya tsure. Sabi'u Wanda shine Minal ta bawa kudi dan ya kula da matar nan ,yana gefe,gabadaya ya shiga damuwa,musamman ganin halin da Minal ta shiga.Dama tun ganin abin da ya faru babu Wanda ya fado masa a rai sai Minal,ya yi zatom za ta shiga mawuyacin hali dama. Haka suka cigaba da jira a gurin tsawon lokaci ★★★ Kai tsaye dakin ya koma,Bai Dade da zama ba aka kira sallah mikewa ya yi ya fito,yana amsa Kiran mommy da take sheda masa sun iso ya zo ya shiga da su. Harabar asibitin ya fito yana dube-duben inda su mommy suke,bai yi aune ba ya ga mutum a gabansa.Ɗan ja baya ya yi yana kallonsa. "Yallabai ya me jiki?Ina fatan ta tashi?Wallahi Me gida tsautsayi ne da sharrin harshe" Shi gabadaya ma ya manta da ya bar wasu mutane a waje, sai yanzu da ya fito,ya ga Kuma sun karaso. Girgiza masa kansa ya yi alamar eh,sannan ya ce"Ina matukar baka hakuri a kan abin da na gaya maka dazu raina ne ya baci" Kallon sauran da suka tsaya carko- carko a gabansa ya yi ya ce "ta farfado bacci take,na gode sosai da kulawa." "Yallabai toh ya jikin mahaukaciyar?"Sabi'u ya fada yana jin kamar harda gudumawarsa a kan abin da ya faru.Watakila inda ya tsaya ya kula da amanar da aka ba shi da hakan ba ta faru ba,duk da dai cikin dare suka yi aika aikar da suka yi. Jim ya dan yi sai ya samu kansa da amsa masa "da sauki ita ma" Ya fada yana yin gaba. Duk da maganar dake bakin Sabi'u ba ta kare ba,sai ya zabi sawa bakin nasa linzami ya yi shiru. Dan ya ga mutumin kamar baya son mutane. Gefe ya koma ya yi tagumi. Shi kuwa Aminu kallon Murtala ya yi ya ce"na Taya ka murna abokina,Allah ya kare gaba sai ka ringa kiyaye bakinka. Harara ya watsa masa ya ce"Abokinka a gidan ubanwa?Shege kawai" Kwashewa da dariya ya yi ya ce"Kai ka sani Kuma.Yanzu ya maganar tafiya Loges din?" Banza ya yi masa,yana harare harare. Kauda wasa daga fuskarsa ya yi ya ce"ya kamata fa mu nemi likatan can,domin ta inda aka hau ice ta nan ake sauƙa." "Mu ji ya jikinta sannan kowa ga kama gabansa,Tun da mune gaba-gaba wajen kawota." ★★★ Tun kafin ya karaso su mommy suka hango shi don haka kawai suka fito. "Ya jikin Minal din?" Tariq ya fada hankalinsa a tashe. "Da sauki mu shiga ka ganta mana" Wai ya na ga hankalinku duk ya tashi?Ku kwantar da hankulanku mana, Asmarta ce fa kawai ta tashi shine ta fadi." Jinjina Kai Mommy ta yi ta ce "ai yadda hankalinta ya tashi komai ma na iya faruwa da ita" "Wai a kan wa take wannan tashin hankali ne?Na san kuma,dole akwai abin da ta gani ko aka fada mata da ya sa ta faɗi,me ya faru?". Adaidi lokacin suka karaso bakin kofar dakin da take ciki,dan haka ya yi amfani da wannan damar ba tare da ya amsa tambayar mommy ba ya tura kofar dakin suka shiga. Har yanzu bacci take yi dan haka suka samu guri suka zauna. Da sauri ya ja Tariq suka fita jin ana ƙokarin tada sallah. Bayan sun dawo Kusa da ita Tariq ya koma ya kama hannunta guda,yana kallon fuskarta da ta yi fayau. Shiru dakin ya dauka tsawon yan mintuna. Sare Mommy ta fuskanci Hammad ba ya son amsa tambayar da ta yi masa,don haka sai ta kyale sa kawai. Wayarsa ce ta fara kara ,zaro ta ya yi ya duba,Nihal ce shi gabaɗaya ya manta ya bar datarsa a buɗe.Dagawa ya yi da sallama a bakinsa.A bakacin ta amsa sai ta ce"Muhammad Hammad"Harara ya watsawa wayar kamar yana ganinta ya ce"kya de fara amsa min sallamar ko?" Shiru ta yi ba ta tanka ba Murmushi ya yi mai sauti ,dama ya san tun da ya ce ta amsa ko tana da niyyar amsawar ba za ta amsa ba. "Wai ke bakya missing ɗinmu?" "Eh ba na yi,ina missing wanda yake missing dina ne kawai" Shiru ta dan yi sai kuma ta cigaba "Ina babyta?Zuciyata tana buga min fiye da kima a kanta,na kira wayarta kuma ba ta ɗagawa" "Ba ki ban ajiyar babynki ba,ina ga ta ɓata ki je ki siyo wata amma" Ya faɗa cike da nishaɗi Katse kiran ta yi,ta kira vedio call Mommy ya miƙawa wayar shiru,Mommy ta yi kamar me nazarin wani abu,can kuma ta karɓa. Lokacin da ta karfa har kiran ya katse wani ya sake shigiwa. A sanyaye ta ɗag kiran. Fuskarta ce ta bayyana saman screen din wayar Ba ta yi zaton ganin Mommy ba,da ba za ta kira ba.Ido Mommy ta zuba mata na wasu yan sakanni,zuciyarta tana matsewa a kirjinta. Allah shine sheda tana matukar kaunar Nihal. Kaf cikin ƴaƴanta babu wanda yake da ƙawazucin uwa irin ta. sai dai ta gagara ba ta kulawar da take bukata. Murya can kasa ta ce" Mommy"!Da sauri ta dago ta kalle ta,a bakar zuciyarta da ta sani ba ta yi zaton za ta yi mata magana ba. "Nihal ki na lafiya? Jinjina kanta ta yi a hankali ta ce"eh fatam kema haka?Ina Auta?". Ɗan murmusawa Mommy ta yi ta ce"Ba ta da lafiya muna asibiti,asamarta ce ta tashi". Zaro ido ta yi fuskarta tana bayyanar da tashin hankalin da ta shiga Ta ce "Ina take" Da sauri Hammad ya mika hannunsa ya karbi wayar.Gwalo ya yi mata,ya ce "ba za ki ganta ba,sai anjima." "For what reason" Ta fada tana harararsa. "ra'ayina" Ya ce yana murmushi. Kunnenta ta kama tana marairaice fuska Shima shagwabe fuska ya yi ya ce"Ni a'a" Mommy har ta daina mamakin shakuwar Hammad da Nihal,duk gidan ta su tafi zuwa daya idan ka cire Minal,kodan sabida halinsu ya zo daya oho. "Muhammad" Nihal ta kira shi a hankali tana kallon cikin kwayar idonsa. Kawar da Kansa ya yi murmushi yaki barin fuskarsa. Bai amsa kiran ba sai ma ya canza magana da cewa"Yaushe za ki dawo ne?Ina bukatar ganin ki" Fuskarta ce ta canza sosai Kamar ba za ta tabyi magana ba sai Kuma ta ce"Ba na son dawowa,na fi son rayuwa ni kadai. Daure fuska ya yi shima ya ce "ai ko ba ki dawo dan kowa ba ya kamata ki dawo ko dan su Daddy " Cikin yanayi na kunar zuciya ta ce"dama su Daddyn suna sona da har za su damu da zamana ko tafiyata?Inda wasu ka ambata sai na fi damuwa da kalamanka a kan wannan" Jikinsa ne ya mutu murus,ya rasa kwarain gwiwar sake magana. Musamman da ya dago ya ga idanun Mommy a kansa. Da kyar ya iya motsa lips dinsa ya ce"Idan ki na son ganinta ki zo har inda take" Tari Minal ta fara yi Wanda ya sa shi katse kiran.Da sauri suka rufu a kanta suna jera mata sannu. "Tariq kira Hafiz" Toh ya ce ya fita Hammad ya faɗa Da ido ta bisu zuciyarta tana wassafo mata tambayar me ya kawo ta nan. "Sannu Auta" Mommy ta faɗa tana riko hannunta. Jinjina kanta ta yi tana kallon ta Zaune ta tashi da sauri tana ƙokarin sauƙa daga kan gadon. Riƙe ta Hammad ya yi . "Tana ina?" Ta tambaya cike da tashin hankali. Shiru ya yi yana kallonta,ba tare da ya ba ta amsar tambayarta ba. "Dr ka yi shiru,ka gaya min inda take ganinta nake so na yi" "Zan gaya miki inda take amma da sharaɗi" Be jira abin da za ta ce ba,ya cigaba. "Sai kin natsu,kin yi mana bayanin inda ki ka santa". "Hawaye ne ya ciko idonta ta ce "Dan Allah ka faɗa min ba zan iya natsuwa ba". Hannunta ya saki ya yi hanyar fita yana cewa baki shirya ganinta ba ashe" Miƙewa ta yi za ta bishi Tariq da ya shigo yanzu ya riƙe ta. Cike da rararashi ya ce "kin san halinsa ki zauna ki natsu kafin ya dawo,sai ki sa Mommy ta saka baki" Komawa ta yi ta zaune,amma gabaɗaya ta kasa natsuwa zuciyarta sai luguden daka take yi. Ya ɗan dade kafin ya dawo Shigowa ya yi hannunsa rike da magani, da kallo suka bishi Ruwa ya dakko ya zo ya zauna a kusa da ita,sannan ya buɗe ya miƙa mata tare da maganin. Ba musu ta karɓa ta sha. Mommy dai tana zaune tana kallonsu amma ba ta tanka ba,dama kuma ba gwanar magana ba ce . Kiran Daddy ne ya shigo wayarta,sai a lokacin ta dauke idanunta daga kansu,ta ɗaga kiran. Jim ta ɗan yi tana sauraren sa,sai kuma ta ce"Muna Asibiti amma yanzu zamu dawo" Tana cikin wayar Dr ya shigo Minal ya kalla ya ce sannu ko". Jinjina masa kai ta yi tana kare masa kallo . Guri Hammad ya ba shi,ya duddubata.Bayan ya gama ne ya kalle su ya ce"Yanzu dai ba wata matsala,saura sallama.Bayan wasu cike-cike ya ba su sallamar, tare da basu shawarwari a kan kula da lafiyarta. Dr Hafiz yana fita Minal ta sauƙo daga kan gadon da take ta kama hannun Hammad cikin wani irin yanayi ta ce "Zuciyata tana bugawa sosai,dan Allah ka kaimi gurinta Ko ta mutu ne?Nima musulma ce,kuna ance musulmai sun yadda da kaddara ko?Na yarda da ita nima" Hannunta ya matsa da dan karfi yana kallon ta,gabaɗaya ta zama abin tausayi. "Da gaske ne abun da aka ce ya faru da ita" Ta faɗa tana kallon sa,tana son ta ji a'a ta fito daga bakinsa sai dai ina.A hankali ya jinjina mata kansa ,ya ƙara da cewa" eh kwarai da gaske". Gyara mata mayafin doguwar rigar da take jikinta ya yi,sannan ya kama hannunta ya ja ta suka yi gaba. Biyo bayansu su Mommy suka yi,Tariq na faɗin "toh me ƴar uwa ai ko ba komai sai ka ce mana ku taho ko?" "Kar ka taho ka zauna" Taɓe baki ya yi ya ce"ka de canza hali wallahi" Banza ya masa ya cigaba da tafiya Mamaki ne ya kama su ganin ya dauki wata hanya abakacin ya fito waje kai tsaye. "Ina za mu je" Minal ta tambaya "Siyar da ke zan yi" Ya ba ta amsa ba tare da ya kalle ta ba. Yanayin da take ciki bai barta ta tanka masa ba. "Mommy siyar da Auta za a yi" "Ai ba za ta saidu ba.kwantar da hankalinki Auta" "Kuma fa yasin Mommy wannan figigiyar ba za ta yi tsada ba,wai tsaya Dr idan ita Minal saida ta za ka yi to shi Tariq fa?" "Mommy ce ta karɓe zancen ta ce"Ai kai ko siyanka ba za a yi ba,inde Auta ba za ta yi tsada ba,ji kanka kwatoto,sai dai a ba da kai alakoro" Zaro ido ya yi ya ce"alakoron me?Wallahi Mommy idan ki ka ga yadda mata suke rawar jiki a kaina sai kin yi mamaki" Daidai lokacin suka iso kofar ɗakin. Hakan ya sa babu wanda ya tanka maganarsa. Tura kofar ya yi .A hankali ta taka kafarta cikin ɗakin kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Duk yadda take son ganinta sai ta ji,wani irin tsoro ya mamaye ta. Shigowa ɗakin suka yi suna baza idon ganin wace ce wadda Auta ta tada hankalinta a kanta. Akwai Nurse guɗadaya a dakin da take ta kici-kicin canza mata wani ruwan dan wannan ya ƙare. Sakin hannunsa ta yi ta ƙarasa inda take da gudu. Zubewa ta yi kan gwiwarta tana kallonta fuskar nan ta yi fayau,an kuma sa mata robar hanci. Fuskar ta duk bandeji wanda ya sa ba za a iya tantance ainihin wace ce ita ba. Rasa bakin magana ta yi sai kuka. Duk shiru su ka yi,su ka yi carko-carko tambayoyi fal ransu. Daurewa Hammad ya yi ya taka inda take durƙushe,rankwafowa ya yi da zummar ɗago ta karaf idonsa ya gane masa abin da ya sa zuciyarsa tsayawa na wucin gadi!. Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH WANE NE SHI? BY Ayeeshat Kissar. Page. 45__46 YOTA...019 https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH?s=cl&p=a&ilr=2 https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Bismillahir_rahamanir_rahim. Tashin hankali tsora, da firgici, ne suka bayyana saman natsatstsiyar fuskarsa. Da sauri ya miƙe tsaye ya kara matsawa gab da ita Tsugunnawa ya yi daidai saitin wuyanta yana ƙara kallon zanen kunamar da ya fito raɗau saman fatarta,sai dai ita a wuyanta ne,maimaikon sauran da ya sani duk na su a damtsen hannu ne. "Ka santa ne?" Mommy ta tambaya tana takowa inda yake. Cak!Ta tsaya tana kallon yatsun kafar matar,a take zuciyarta ta fara zagaye ƙirjinta,kafin ta cure, bugunta ya tsananta. Hayyacinsa ya dawo,da sauri ya ce "am a'a ban santa ba ganin na yi dai kamar na santa,ashe ba ita ba ce" Ya faɗa yana ɗan ja da baya ya kuma kasa dena satar kallon gefen wuyanta. Mamaki ne ya kusa kashe nurse ɗin dake tsaye,ta ji ance matar ba ta da kowa,kuma ta ga waƴen nan mutane,gashi ga dukkan alama daga gidan arziki suka fito,ga kuma wannan yarinyar tana kuka sai ka ce mamanta ce ta rasu. Dan haka ta yanke shawarar tambayarsu. Ɗan gyaran murya ta yi ta ce"Amm sannunku,na ce kun santa ne,na ji ance ba ta da kowa a bola ma take rayuwa,ko a gari kuka ji abin da ya faru da ita?" Ɗago kai Hammad ya yi ya kalle ta kawai sai ya sami kansa da girgiza mata kai. Ya ga alamar sabuwar zuwa Asibitin ce,dan ba ta nuna alamar ta san shi ba. Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa ta sake cewa"Nifa ince na ji mamaki ai,an hana masu san su ganta ganinta ma kwata-kwata,saboda kar su yi mata vedio,kasan halin mutanenmu" Ta kare maganar tana maida idonta kan Minal da take kuka bilhakƙi,duk da kukan ba mai sauti ba ne,amma kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci daga ƙasan zuciyarta yake fitowa. Tariq dai yana gefe yana kallonsu,dan sare ya ga halin da Hammad ya shiga,har ma da Mommy.Wannan dalilin ya sa shi jin tsoran zuwa inda suke,dan bai san me suka gani ba. Da ƙyar Minal ta iya tashi ta zauna saman kujerar dake gefen gadon,da taimakon nurse din nan. Duk rarrashin da Nurse din ke mata ta kasa tsaida hawayenta. "Shin mai baiwar Allahn nan ta yi musu?A halin da take ciki ba ta san komai ba,tana rayuwa ne kawai ba tare da buri ko mafarki ba .Me ya sa?Ma ya sa ?Saboda me?" Muryar Hammad ce ta dawo da ita zahiri. "Inda na san kukan nan za ki yi da ban kawo ki ba,ba ki san halin da ki ke ciki bane?Ko ita baki ga halin da take ciki ba? Shikenan ki kashe kanki ai rayuwarki ce ba ta wani ba". Da ido kawai take bin sa,ta kasa tanka masa. "Tashi mu tafi" "A'a ku je kawai,zan cigaba da zama a nan" Wani banzan kallo ya watsa mata.A fusace ya ce "wallahi ba ki isa ba,ba ki ga tana karkashin kulawar Asibiti ba?Me za ki yi.mata ma idan kin zauna?" Shiru ta yi ba ta tanka ba,babu kuma alamar za ta tashi ɗin. Har yamzu Mammy ba ta dawo normal ba,hasali ma ba ta fahimtar abin da suke cewa. "Ai da ƙyale ta ka yi Dr,tun da ta ce tana so,tana da yancin yin abin da take so,Mommy ki zo mu tafi ni dai" Ko kallonsa bai yi ba bare ya tanka maganarsa. "Mommy Mommy Mommy fa" Tariq ya faɗa cike da ƙosawa. Zabura ta ɗan yi ta ɗaga idonta tana kallonsa "Lafiya kuwa" Jinjina masa kai ta yi dan bakinta ya gagara buɗuwa Matsawa inda take zaune ya yi, a natse ya ce"Wallahi idan baki tashi ba,sai na saɓa ki a kafaɗa" "Dan Allah Dr ka kyale ni". Sassauta muryarsa ya yi ya shiga rarrashinta,baki nurse din nan ta saka suka hadu suna lallaɓa ta.Da ƙyar suka samu ta yarda za ta tafi. Haka ya taso ta gaba suka fito tana ta faman sharar ƙwalla. Ruƙo hannun Mommy Tariq ya yi suka fito suma ,ban da taɓe baki babu abin da yake yi. Ya rasa meke damun Hammad gabaɗaya dole sai ya shiga rayuwar mutum yake jin daɗi,mugun hushin halin nan nashi yake ji. Dole sai barin motar Minal suka yi,dan Hammad be yarda ta shiga ko motar Tariq ba. Sai da ya kaita har cikin ɗakinta sannan ya fito ya sake fita . Ɓangarem su Tariq kuwa tambayar duniyar nan ya yi wa Mommy meke damunta,amma ta gaza ba sa gamsashshiyar amsa,kamar ma ba a hayyacinta take sosai ba ,shi tsoro abin ya koma ba shi ma. Ko da suka isa gidan sai da ya zagaya ya buɗewa mata motar,sannan ta fito. Da taimakosa ya haura da ita sama. Aƙalla ta kai kusan mintuna talatin bata motsa daga inda take ba. Mikewa ta yi ta taka gaban madubin ɗakin ta tsaya Cire mayafin da ke kanta ta yi ta ajiye a gefe ,sannan ta zauna tana ƙarewa fuskarta kallo.Ko alamar hawaye babu saman fusakar,sai dai akwai wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Dama tana nan?Tana raye har yanzu?Toh ina ta shiga?Amma ita ɗin ce ma? Da sauri ta girgiza kanta cike da son tabbatarwa ta ce"eh kwarai ita ce,babu yadda za a yi na kasa gane alamar nan. Toh amma ina Minal ta santa? Dafe kanta ta yi saboda yadda ta ji yana sara mata. A hankali ta ce "Allah ya kaimu gobe zan tabbatar na samu dukkanin amsoshina" ★★★ Fitowa ya yi,bayan ya kai Minal ɗaki,ya sake shiga mota ya bar gidan.Kai tsaye Asibitin ya sake nufa zuciyarsa tana yi masa sake-saƙe iri-iri,ya yi matukar kaduwa ganin wannan tambarin a wuyar matar nan,zai so ta tashi ,ze so ya gana da ita,amna ai ance mahaukaciya ce . Dafe kansa ya yi zuciyarsa tana bugawa da sauri. Tun yaushe wannan tambarin yake a jikinta?Me ya sa nata ya kasance a wuya saɓanin sauran da dukan su a damtsen hannunsu yake?" Zuciyarsa ce ta tuna masa da wannan matasan da aka ce sun mutu,kilan sune suka yi mata tambarin,idan haka ne lallai a gawarwakin su ba za a rasa wata alama ba . "Wannan ba aikinka ba ne amma,naka kula da marasa lafiya" Zuciyarsa ta tunatar da shi Girgiza kansa ya yi yana karya kwanar da za ta sada shi da Darul fiyya,a bayyane ya ce "Allah ya ga zuciyata ba da wata manufar nake yin duk wannan ba,ya ubangiji indai akan kan daidai nake ka tabbatar da ni,ka taimake ni.Ko zan shiga hurumin da ba nawa ba ya kamata na san amsoshin tambayoyina,amma ta yaya?". "Jamal Abdulaziz!" ƙayataccen murmushi ya yi ya ce"Ta kwana gidan sauƙi,sai dai matsalarsa dan iska ne,ba lallai y bani abin da nake so ba. Daidaita parking ya yi sannan ya lalubo wayarsa,da nufin kiran Jamal. Kiran Ramadan ya gani burjik,hararar wayar ya yi kamar ita ta yi masa laifi,sannan ya yi ƙwafa. Numbern Jamal ya shiga nema,sai dai bai ganta ba. Yamutsa fuska ya ɗan yi ashe ba shi da numbern. Yana ƙoƙarin kiran Ranadan sai gashi ya kuma kira. Bai ɗaga ba sai da ta kusa tsinkewa,sannan ya ɗaga. A fusace Ramadan ya ce"wai kai wane irin mutum ne?Kira nawa na yi maka ba ka ɗaga ba?Kasan wace magana zan faɗa maka ne?Yanzu idan ina cikin wani halin na neman taimako kenan bazan neme ka ba?' Shiru ya yi yana saurarensa sai da ya kai aya sannan ya ce"ka gama ubana?"Indan magana ka ke son yi dani baka san inda nake ba ashe" A matuƙar fusace Ramadan ya ce"Ni nake nemanka dole ka wulakanta ni yadda ka ke so,idan na sake nemanka ka yi min abin da yafi haka" Ya kai aya yana yanke kiran Bin kiran ya yi saida ta kusa tsinkewa ya ɗaga,ya yi shiru yaƙi yin magana. Murmushi ya ɗan yi,ko banza shima ya ɓata masa rai.Ya sassauta muryarsa ya ce"I'm very sorry,ban san ka kira ba,ɗayar wayar kuma na manta ta a mota." Shiru ya yi yaƙi tankawa alamar dai ranshi ya ɓaci. "Wai kai dallah mace ne kai da zanta lallaɓa ka,ko ba kasan kai ma me laifi ba ne?" "Uban me ka kira zaka faɗa min" Ajiyar zuciya ya sauƙe duk da bai huce ba ya ce"Idan ka ga dama ka canza hali,idan ba ka ga ni ba,ka ci gaba" Ya ci gaba "na yi magana da Safnar yau,ashe ba ta da lafiya ne,amma ta ce monday za ta dawo aiki,kuma Jamal ya kira ni,wai yana san magana da kai akan cese ɗin Rumaisa, ba shida contact ɗin ka". Jinjina kai ya yi ya ce Allah ya kaimu monday ɗin sai mu je mu same ta,nima ina bukatar yin magana da shi,da kuma kai.Ka yi masa magana gobe ya fi kamata mu haɗu,tun da monday ba mu da time " "Ok,bari zan gaya masa,sai mu san inda za mu haɗu". Sallama suka yi sannan ya fito daga motar. Kai tsaye ɗakin majinyatansa ya fara bi daya -bayan -ɗaya. Yana matuƙar jin daɗin yadda yake ganin annuri a fuskokin masu kulawa da majinyatan,dama su kan su.Duk da wannan ba Asibitin shi ba ce,yana kuma shigowa sau biyu a sati ne ,amma yana matukar jin daɗin yadda yake ganin fara'a a fuskokin jama'ar da suka shigo da kuka . Da sallama ya shiga ɗakin,be samu Rumaisa a kan gadon ba,mamanta kuma tana sallah. Guri ya samu ya zauna saman daddumar da ya gani a gefe. A hankali ta zuro kafarta daga banɗakin ta fito. Sannu a hankali take ɗaga kafarta,tana yi tana cije bakinta. Samsam ba ta kula da Hammad ba,dan ba ta yi tunanin wani zai zo yanzu ba. Ba ta san wane likita ne yake duba ta ba kwata-kwata.Ita a iya saninta mata masu fararen kaya ne kaɗai suke dubata. Shima bai taɓa dacen samunta ido biyu ba,duk lokacin da zai dubata bacci take yi. Da ƙyar ta iya karasowa baƙin gadon ta zauna tana ɓata fuska. Buɗe baki ta yi za ta yi magana ta ji muryarsa me kauri da zurfi,irin ta cikakkon maza ta daki masarafar sautinta".Sannu Ruma ya jikin hope da sauƙi?" Zabura ta yi da sauri har tana ƙokarin faɗowa daga kan gadon dama ba ta zauna da kyau ba. Rintse idonta ta yi ta saki karar azaba. Da sauri ya saka hannunsa ya taro ta.Ware madaidaitan idonta ta yi,suka faɗawa cikin shanyayen idonsa. Kara ta ƙwalla da iya karfin ta,a take jikinta ya ɗau mazari. Sakinta ya yi da sauri,hakan ya sa ta ƙara fama ciwonta. Ihu ta kuma saki me karfi tana fashewa da kuka.Da sauri Mamanta ta katse addu'ar da take yi ba tare da ta shirya ba. Gabaɗaya Dr sai ya nemi natsuwarsa ya rasa. Babu abin da idanunta suke iya hango mata sai idonsa ha ta ga wata maraba da idon wannan ba. A take ƙirjinta ya fara kasa da sama,ta fara kokawa da numfashinta da yake mata wahalar shiga da fita. Riƙe ta Mananta ta yi tana tambayarta lafiya.Rumgume ta yi wani irin tsoro na ratsa ta. "Mah..!Mam..!Mamah". Ta furta da kyar "Rumaisa".. "Ki natsu mana,ki kira sunan Allah." Girgizan kanta ta shiga yi hawaye na mata sintiri. "Tsoro nake ji Mamah" "Mamah shine! Shine..!" Ta faɗa tana kara ƙanƙame ta. Zaro idanunsa ya yi da sauri,haɗi da ja baya ya ce"What?Ni ne wa?" Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR PAGE 47__48 Bismillahir_Ramanir rahim Murmushi Mama ta Dan saki ta ce"Haba Kai kuwa,sai kace ba likita ba,ka manta da halin da take ciki?" Ta fada tana gyara Mata kwanciya. "Bari na turo sister Maryam tun da tana yarda da mata" Hanyar fita daga Asibitin ya yi, bayan ya kira Sister Maryam din kamar yadda ya ce . Tunanin yarinyar da ya fara ganin tambarin nan a hannunta ne ya fado masa.Tabbas a lokacin ta ba sa tausayi,ba ita kadai ba da mamanta da Kuma yayanta,har ya koma ga Allah ba ya tunanin zai manta fuskarta.Amma ko Mai ya hana yayan nata dawowa har yau oho. Tsaida tunanin ya yi lokacin da ya kara so bakin mota . Ya shiga ya bar Asibitin.Tunani ya yiwa kansa yawa har ya rasa wanne zai yi,hakan ya sa ya yi ta shawagi Saman mikakiyar kwaltar garin Abuja,ba tare da ya san takamaimai inda zai je ba.Ya dade yana zagaye kafin ya koma gida. Kai tsaye bangarensa ya nufa.Yana shiga ya faɗa banɗaki . ★★★ A bangaren Daddy kuwa ,Kai tsaye Private retreat,din Alhaji Abubakar ya nufa,domin ya san ba zai same shi a ko ina ba sai nan. Kamar yadda ya yi tunain samunsa a can ya same sa ɗin.Da sallama ya shiga falon,babu kowa a nan dan haka ya haura sama yana ƙwala masa kira. Turus ya ja ya tsaya yana kallonsa, ganin sa zaune amma duk kiran da yake kwaɗa masa bai amsa ba. Ƙarasawa ciki ya yi ya tsaya a gabansa,cike da ɓacin rai ya ce "meye kai haka?" Shiru bai amsa ba,ɗan taɓa sa ya yi,hakan ya sa ya zabura,don gabaɗaya bai ji shigowarsa ba. ""A'a am Mansur "Ya furta yana kallonsa dan ya san ya masa laifi. Harara Alhaji Masur ya wurga masa,duk da jikinsa ya yi sanya ganin halin da yake ciki.Ya ce"Me kake yi haka?Ko na ce me kai haka?Ina hankalinka Abubakar?Ina yawan nazarin kafin yanke hukunci?Ba ka ganin hakan zai janyo mana matsala?" "Kwata-kwata zaɓe saura kwana nawa?" A natse Alhaji Abubakar ya ce"Zauna mu yi magana ". Zama ya yi yana fuskantarsa. Sai da ya ɗan ja fasali kafin ya fara magana"Ba ni na fitar ba,Hajiya ce,sai da na yi mata gargaɗi a kan kar ta fitar,saboda gudun matsala da kuma tunanin yan adawa za su yi amfani da wannan hanyar wajen yaƙarmu,dama wasu matsalolin da dama waƴenda nake hango su,amma fur taƙi yarda sai ma cewa ta yi"ran ƴarta ya fi mata mulki." Numfashi ya ja sannan cigaba"Wai ni tun da ban damu ba,ni Mansur ni ne ban damu da batan diyata ba,wanda na mallaka ciki da waje a duniyar Allahn nan" Ya faɗa yana nuna kansa da alamar ɓacin rai a muryarsa. Shiru Daddy ya yi yana kallonsa,ya rame sosai kamar wanda ya yi dogowar rashin lafiya. Cije gefen bakinsa ya ce"Mansur ina kewar su Muhammad sosai,ina matukar kewar ku."Murmushi ya ɗan yi ya zarce da faɗin"Kai ma na rasa ka,na rasa Mansur ɗin da,kamar yadda kai ma ka rasa ni,anya ba hakƙi ba ne ya fara bibiyata?Batan Zahra ya fama min tabon da na ɗau dogon lokaci bai warke ba" Ya kai aya idonsa na cikowa da ƙwalla Girgiza kai Daddy ya yi cike da dauriya ya ce"Haba kai kuwa meye ka ke yi haka ne?Muna da laifi a cikin abubuwan da suka faru,amma ka sa ni ƙaddara ta riga fata,inda muna da iko da mun dawo da baya domin gyara kurakurenmu,sai dai ba mu da wannan damar,dan haka mu fuskanci gaba ,mu kiyaye " "Kuma ba ka rasa ni ba,har yanzu ina nan a Mansur ɗina kawai yanayin aik..." "Kana ganin mun ki yaye anya?" Alhaji Abubakar ya yi maganar yana kallonsa Miƙewa tsaye ya yi ya ce"ka ga yanzu ba lokacin wannan maganar ba ce,akwai abubuwan da suka fi waƴennan maganganun naka mahimmanci". Ya furta cikin son ya kawo karshen maganar gudun ka da rauninsa ya bayyana kamar yadda na Alhaji Abubakar ya fito fili. "Yanzu wace mafita ka yi tunani dan gane da ɓatan Zahra?" Girgiza kansa ya yi,alamar babu komai Murmusawa Alhaji Mansur ya yi ya ce "ni na san mafita na kuma san inda zan same ta " "Ka daina murnushi,domin inda ka ke tunanin samun,maslaha daga nan matsalar ta faro". Alhaji Abubakar ya faɗa,sannan ya maida idanunsa ya lumshe. Wannan shine abin da ya faru, a ɓangaren Daddy,da Alhaji Abubakar. ★★★ Mai Dollars Family. Tun sassafe Minal ta yi shirin tafiya Asibiti,Falo ta fito ta zauna tana jiran gari ya gama washewa. Fitowa Hammad ya yi zai dauki ruwa ya ganta a zaune ,tana kallon agogon dake daure a hannunta. "Ya dai" Ya tambaya yana binta da ido "Na shirya ne". Ta bashi amsar hankalinta na kan Agogon. Tausayi ta bashi da dariya. Ruwan ya je ya dauko sannan ya dawo ya zauna a gefenta. Ya ce"ko kin je yanzu ba za su buɗe miki ba,kuma ko sun buɗe ba za su bari a ganta ba,saboda halin da take ciki,sai da na nemi alfarma kafin aka bari jiya muka ganta." "Ki na ji?Ki yi hakuri zuwa anjima lokacin sun buɗe sai na kai ki,kin ji Auta" Jinjina kai ta yi ba tare da ta yi magana ba. Sai da ya tabbatar da ba za ta fita ba,sannan ya yi sauri ya shirya cikin ƙananan kaya. Dawowa ya yi y same ta a falon,tana ganinsa ta miƙe tsaye. Hannunta ya kama ya nufi ɓangarem Daddy da ita.Kamar ta ce wani abu,sai ta share kawai. Ba wanda ya sake magana a cikin su,sai can ya ce" kin gaishe da su Mommy?" Girgiza kanta ta yi alamar a'a Kofar ɗakin Mommy suka fara isa don ita ce farko kafin ta Daddy. Minal na shirin danna kai ya riƙo ta,sannan ya sa yatsansa ya kwanƙwasa. Sai da ta ba da umarinin shigowa sannan suka shiga Gaisheta suka yi ta amsa babu yabo ba fallasa,ta tambayi Minal jiki. Ta amsa da da sauƙi. Mamaki ne ya ɗan kama su,sanin ba haka halinta yake ba,duk da ba ta kasance mutum me yawan dariya ba,sai dai kusan ko da yaushe fuskarta a sake take. Kare mata kallo Minal ta yi sannan ta ce"meke damunki Mommy" Girgiza kanta ta yi cike da son ɓoye damuwarta ta ce"Babu komai me ki ka gani" Shiru ta yi ba ta ce komai ba,sai Hammad ne ya yi magana"Bari mu je Mommy,idan mun karya zan kaita ta duba matar nan" "Da sauri ta miƙe ta ce ku jira ni bari na shirya" Kallon juna suka yi,mamaki ya ƙara bayyana a fuskokinsu. Mommy ba ta cika damuwa da abin da ya dame su ba,iya kaci ta yi maka fatan alkairi. Ganin suna kallon juna ne ya sa ta yi sauri ta ce"Matar ta ban tausayi sosai ne,da ita na kwana a raina." Kai suka jinjina a tare sannan suka fito daga ɗakin. Ɗakin Daddy suka je suka gaishe shi,suka sauƙo suka wuce dining area. Izuwa yanzu Minal kam ji take kamar ta ƙwarma ihu,daurewa kawai take,don ta san halin Dr,yanzu sai ya mata tsiya. Ko da suka je tuni Tariq ya iso,dan shi baya wasa da harakar ci. Hannu Hammad ya mika masa suka gaisa sannan ya zauna. "Auta ya jikin?" Ba tare da ta kallesa ba ta ce "da sauƙi"taɓe baki ya yi jin yadda ta amsa ya ce"ke de ba a miki abin arziƙi" "Ya ishe ka haka Malam ka san dai ba lafiya ce da ita ba ko?" Hammad ya furta yana harararsa "Au Allah?Toh sannu me ƴar uwa,nuna min iyakata ka ji" Suna cikin haka Daddy da Mommy suka fito dukkan su cikin shiga ta alfarma. Sun yi matukar kyau. "Wato Daddy ka yi dacen mata wallahi,ka ga yadda kuka yi kyau." Tariq ya faɗa yana murmushi. Zama suka yi a tare suna suna yar dariya. Gaishe su Hammad ya ƙara yi suka amsa masa da kulawa. Babu ɓata lokaci suka fara karyawa ba tare da wani ya kuma magana ba,dan gabaɗaya idan ka cire Tariq kowa da abin da ya dame sa. Dan gyaran murya Tariq ya yi ya ce "Daddy na tambaye ka mana" Jinjina masa kai Daddy ya yi yana ƙurbar haɗaɗen baƙin shayin da yake hannunsa. "Wai Daddy dama kana da ƙani,amma ba ka taɓa gaya mana ba. Ƙwarewa ya yi dan jin tambayar ya yi tamkar saukar guduma . Ruwa Hammad ya yi miƙa masa da sauri Yana masa sannu,shima gabaɗaya mamakin abin da Tariq ya faɗa ya kama shi. Ɗakƴar tarin ya tsaya,tuni idonsa sun kaɗa sun yi jajur. Sai da ya ɗan samu natsuwa sannan ya kalli Tariq ya ce"wa ya gaya maka" Hajiyar kano ce,wai sunansa Abdullahi,ta ce ina kama da shi sosai,shi ne nake mamaki na ga ko labarinsa ba ka taɓa ba mu ba". Guntun murmushi ya yi wanda ba shi da alaƙa da nishaɗi ya ce"eh,hakane ya rasu da ɗadewa sakamakon gobara,shi da matarsa." "Allah sarki Allah ya jikansu,dan Allah Daddy ka ban hoton shi,ina so na ga kamar da nake yi da shi" Shiru ya yi bai tanka ba,ya cigaba da shan shayinsa "Haba mana Daddy ka taimaka". Wani irin hargittsatsten kallo ya watsa masa,wanda ya sa shi shan jinin jikinsa. "Ba ni da hoton shi" Ya faɗa yana ɗaga kiran da ake masa. "Minal ba ki ci komai ba " Hammad ya furta dan yana ankare da ita. Share hawayen da ya zubo mata ta yi, ta ce"Yaƙi shiga" Kallon ta Daddy ya yi dan shi bai san abin da ya faru ba ya ce"Auta ko jikin ne?" "A'a Daddy na koshi ne kawai" "Ƙarya take yi wallahi a kan wata mata fa take damun kanta tun jiya,matar tana Asibiti,ni ban san me ya faru da ita ba,shine dalilin tashin asmarta" Harara ta wurga masa sannan ta maida kanta ta cigaba da wasa da cokalin hannunta. "Wace mata ce Auta?Me ya faru da ita kuma.". Shiru ta yi ba ta yi magana ba,dan tana da tabbacin tana buɗe baki za ta fashe da kuka. Hammad ne ya ce"Ban san takamaimai alaƙarsu ba,amma dai da alama sun shaƙu sosai,ya kamata ka je ka duba matar Daddy,idan ka samu time.Wai ba ta da cikaken hankali,tana bukatar a tsaya mata an cutar da ita wallahi". Ya faɗa cike da kunar zuciya. Jinjina kai Daddy ya yi ya ce"ko ita ce ɗazu na gani a news,a unguwar zuba take ko?Abin ya taɓa ni sosai,wai maza biyar ne suka haike mata,kuma duka sun rasa ransu." "Lamarin akwai daure kai,amma na ji Alhaji Junaid ya ce zai tsaya mata a kan neman lafiyarta,kasan bawan Allahn nan ba daga nan ba." "Zan je na ga halin da take ciki ko zuwa gobe ne,sai mu ga me ya kamata na yi" Ɗan waro ido Tariq ya yo ya ce"au dama wai ita ce?Ai yanzu maganar ita ce take ta yawo a media tun jiya,Allah ya saka mata." Tun ɗazu Minal take ankare da Mommy babu abin da ta ci ko ta sha,ta fuskanci tana cikin damuwa amma wacce ?" Miƙewa Daddy ya yi ya shafa kan Minal sannan ya yi mata kiss a goshi ya ce"Auta ki rage damuwar nan kin ji,ki shirya anjima zan baki wani hadaɗɗem labari." Jinjina kai ta yi ta ce"Toh Daddy" Yauwa Aminatun Daddy ba ta Monmy ba,mama ga Mansur mai Dollars,in sha Allah za ta samu lafiya duk da baki faɗa min wace ce ita ba" "Zan gaya ma sai anjiman" Murmushi ya yi ya ce "ki ce zan sha labari?Toh Allah ya kaimu" Taɓe baki Tariq ya yi ya miƙe a zuciyarsa ya ce "Auta ko hauka". A zahiri kuma harararta ya yi ya ce "ni kam bari na yi nan." Sai a lokacin Mommy ta ce"Allah ya tsare" waje ya yi yana amsawa. Shima Daddy fita ya yi bayan ya gama rarrashin Minal. Sai ya rage saura su uku Minal da ta gama ƙosawa ta ce"Dan Allah ku tashi mu tafi" Yunkurawa Mommy ta yi za ta miƙe,Dr ya yi saurin dakatar da ita da cewa Mommy ai ba ki ci komai ba" Tsaye ta tashi tana gyara zaman mayafin ta ta ce "Kar ku damu,zan ci ko zuwa anjima ne" Shiru ya yi yana nazartar ta Minal kam tuni ta dangana ga waje dan ta matsu ta je ta ganta. Fitowa suka yi suma a tare. "Hammad ba ka san komai a kan matar nan ba,ban da abin da ka gayawa Daddynku?" https://chat.whatsapp.com/JVl9RkCU8EjJmSNCuAeIlH?s=cl&p=a&ilr=2 https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z WANE NE SHI? AYEESHAT KISSAR YOTA..019 PAGE 49__50 https://chat.whatsapp.com/Eh2iSk99O6jKbZQDbkZQfS?s=cl&p=a&mlu=4 https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z BISMILLAHIR_RAHAMANIR_RAHIM. Da sauri ya kalleta,sai kuma ya sauƙe kansa ya ce"Eh iya abin da na gaya masa ne,amma lafiya?". "Lafiya kalau kawai dai na tambaye ka ne,na san ka da bincike kamar ɗan sanda" Ta faɗa tana basarwa . Buɗe mata mota ya yi ta shiga,Minal ma ta shiga. Sai da ya yi wa motar key ya fita daga cikin gidan sannan ya ce"Ni ban san dalilin da ya sa na zama likita ba,kawai dai kaddara ce,amma ina matukar son sanin abin da ban sani ba,musamman wanda ya shigewa mutane duhu,ko wanda ba su damu su sani ba. Ɗan murmushi ta yi ta ce komai nufin Allah ne,ya riga ya tsara maka abin da za ka yi ne,kasan ɗan adam ba shi da iko da kansa yana tafiya ne a kan abin da Allah ya tsara masa " Jinjina kansa ya yi cike da jin daɗin yadda ta amsa maganar tasa ya ce"Mommy dan Allah ki taya ni da addu'a ina shirin yin wani aiki me haɗari,kin san dan naki" "Allah ya taimaka ya shige gaba ya ba ka ikon aiwatar da alkairi" Ta faɗa a sanyaye tunanin matar nan yana kara cika mata zuciya Shiru ta yi na tsawom lokaci,har ba ta san an iso ba. Fitowa ta yi daga motar jikinta a sanyaye Minal ba ta tsaya jiransu ba ta shige ciki abinta dan ta haddace ta inda suka biyo. Yauma akwai motar ƴan sanda a tsakiyar asibitin. Kallon ta kawai Hammad ya yi ya girgiza kai,ko da ta je ba su barta ta shiga ba,har ta fara yi musu kuka. Suna ganinsa suka fara gaishe sa dan fuskarsa ba ɓoyayyiya ba ce a gurinsu.Sun yarda Minal za ta shiga ganin kukan da take yi,sai dai sun hana Mommy. Tsuka Minal ta yi ƙasa-kasa ta ce"sai yanzu suka zo ba ta kariya kenan?Ga sunan dai a haka kamar masu amfani,amma ba su da wani amfanin ba a ganin su a guri sai bayan faruwar masifa. Ta shige tana banka musu harara Ba karamin tashi hankalin Mommy ya yi ba,don tana bukatar ta sake ganinta. Fita ta yi harabar asibitin hankali tashe tana kiran wata number ★★★. Barde "Mahaukaciyar uwa zama dake sai hakuri a baki ci,a ba ki sha,idan kin ci kin rage ba me ci.Katarar uwa makarar kallo yaro in ya leƙa sau guda ba zai koma ba.Gafiya me ado da gashin baki.Bindin kunama me kama da sirdin doki,ko wa hauka zai rika tashi.Yaro ba shi raina manya ya daɗe,ko ya daɗe ba zai ƙarko ba,yaro in bai mace ba zai lalace,dakalin majina a hauka a zame,ka hau mutum ka zauna daidai". Mutumin dake durkushe a gabansa ya kai aya yana ƙara yi masa jinijina,da hannayensa guda biyu. Ganin bai yi alamar ya san yanayi ba ya sa ya cigaba . "Zaki dan Mama namiji uban mata,sunfika dukiya kafi su nasara,ka riƙe wahabu sun riƙe ibilish .." Katse shi ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce"Salis"Da sauri mutum ya ɗago ya ce"Na bi Allah na bika garkuwa Mamansa" Hannu ya miƙa masa.Ya miƙa masa kwati,ya ƙarɓa ya buɗe. Bindiga ce a ciki,fito da ita ya yi ya kare mata kallo ya ce"lokacinka ya fara Barde,ka yi wa kasa ado da jinin maƙiyanka." Murmushi yake so ya yi sai dai ya manta yadda ake yinsa.Saka bindigar ya yi a kugunsa. Daga yau masu nemana za su fara naman hanyar gudu,ta inda matsalar ta samo asali ta nan zan fara magance ta" Ya kalli Salis da gar yanzu yake a duƙe Ya ce "Ka cika alƙawari,kar ka karya,ka haɗo.komai ka ajiye a ma'ajiya zan zo na dauka" "Zan neme ka idan da bukatar hakan JInjina kai Salis ya yi ya miƙe tsaye. Ya ce "Ina tare da kai gwanki,komai ya kamnalla ma tun daren jiya,aikinka ne kawai ya rage" Jinjina kansa kawai ya yi,ya sauƙo daga saman dutsen da yake kai, ya yi gaba,ya bar Salis a gurin. Bin bayansa ya yi da kallo,kafin ya dau box ɗin da ya bari a gurin ya kara gaba da sauri,yana jin kwarim gwiwa game da aikin da yake yi,duk da ya san va daidai ba ne,ya kuma tabbatar a ko da yaushe yana iya rayuwarsa ko wani muhimmin abunsa,amma alƙwari ya dauka,bai kuma san yadda ake karyasa ba ma. Bai yi wata tafiya me nisa ba ya karaso inda motar da ya zo take,buɗe baya ya yi ya shiga aka figi motar da mugun gudu. Ba su fi mintuna uku da barin wajen ba wasu baƙaƙen motoci suka iso gurin.Fitowa nutanen suke yi suna dube-dube.Bakaƙen kaya ne a jikinsu,babu abin da ake iya gani a jikinsu,sai ƙwayar idonsu. Bayan sun gama duben-duben su ba su ga komai ba ne suka shiga motocinsu suka bat gurin. ★★★ Ɓangaen Ahmad kuwa Tun da ya dawo daga zubar da tokar ya je ya kwanta zuciyarsa na luguden daka Bai fi mintuna talatin da dawowa ba ya ji alamar ana durowa cikin gidan.Jinjina kai ya yi a zuciyarsa ya ce"gaskiya Barde na musamman ne ko ya ake yi ya san da wannan shiri na su oho" Kawar da tunanin ya yi ya fara ambatar duk addu'ar da ta zo bakinsa dan ya san tabbas rayuwarsa tana cikin haɗari. Bai daɗe a wannan halin ba suka shigo har ɗaki suka taso ƙyeyarsa zuwa tsakar gidan . Gigitacciyar tsawa ogansu ya daka masa ya ce"Kai ina Barde?" Bai dago ba ya ce"Ban san wanda kuke magana a kai ba." Kwaɗa masa mari ɗaya daga cikinsu ya yi ya ce,"kai kaɗai ka san inda yake,duk binciken da muke yi nan yake nuna mana" Girgiza kansa ya yi fuskarsa tana bayyanar da tsananin tsoro ya ce" ku bincika ban taɓa sanin ko me irin sunasa ba" Banzan kallon Shugabansu ya watsa masa.Gabaɗaya bai yarda da shi ba ya ce "ku ƙara bincikawa,ko alamunsa kuka gani yau sai mun yi watanda da namanka" Ya yi maganar yan kallon Ahmad Babu inda ba su duba a cikin gidan nan ba,amma ba su same shi ba. Cike da ƙosawa da neman Barde da suke yi tun fitowarsa ya ce"Kaii!Wai shi wannan Barden wane ne shi? Me ya sa ya zama abin farauta ga mutane da yawa?Me ya sa ya gagara kamuwa?" Ya kare maganar yana wani irn huce,don a tarihin rayuwarsa da ta aikinsa bai taɓa yin kwana uku yana aiki akan mutum bai ga bayansa ba,amma wannan banzan ya gagara kamuwa. "Wane ne shi?" Ya faɗa da karfi Kallonsa Ahmad ya yi da wutsiyar ido,a ransa ya ce" Barde mutum ne,amma ba kamar kowa ba,shiɗin na musamman ne,abin tausayi,abun tsoro abun ban mamaki,ɗan baiwa tun daga haihuwa" "Ku daure min shi" Ya faɗa yana ƙiyasta irin kisan da zai yi wa Barde duk ranar da ya haɗu da shi. Wayarsa ce ta fara ƙara,ya ɗaga ya koma gefe yana amsawa. Da sauri ya dawo ya kalli yaransa ya ce "Ku taho an kama sa inji Oga" A ɗaɗaure suka bar Ahmad suka yi tafiyarsu. Duk da gabansa ya faɗi lokacin da ya ce an kama Barde ya san karya ne wasa ya yi musu da hankali sai kuma ya ɗan saki murmushi ya ce "shege Abokina har yanzu kwanyar tasa tana nan.* Motsawa ya yi y ji babu ta yadda zai iya kwance daurin Dariya mara sauti ya ƙara saki "Yanzu inda sun kama Barde a nan kilan fa ko ƙashina ba za a gani ba,da yanzu sunana margayi Ahamad." Ya furta Motsawa ya kuma yi ya ji babu yadda za a yi ya iya kwance kansa,sai kawai ya gyara kwanciyarsa Ya ce bari na barwa safiya na ga ya Allah zai yi da ni kuma. Har garin Allah ya waye yana nan a haka ,sai wajen 8 sannan Hafaa ta dawo,ba ƙaramim tashi hankalinta ya yi ba,da ta ganshi cikin wannan halin. Fita ta yi ta samo maza a waje suka kwancesa Motsa kafarsa ya yi da ta yi masa tsami ya ce "Alhamdulillahi ubnagijin musa da haruna,Allah na gode maka da ka kubutar da ni daga hannun waƴen nan miyagun" Hankali tashe Hafsa da mutanen da suka kwance sa suka haɗa baki gurin faɗin" wai me ya faru ne?" Gyara zamansa ya yi don jikinsa gabaɗaya ya yi tsami ya ce"Wallahi ban san ko su waye ba,sun ce dai na basu kuɗi na ce musu ba ni da shi,shine suka daure ni,suna da shirin saka min wuka aka kira ogan nasu,shine suka bar ni a haka suka tafi." Wani kallo Hafsa ta watsa masa don ko kaɗan ba ta yarda da abin da ya faɗa ba. Allah ya ki yaye gaba suka masa sannan suka tafi inda za su. Tana ganin sun fita ta ce "ina mai laifin da ka ɓoye?Wallahi ban yarda da haka kawai suka zo ba,Barde suka zo nema " Miƙewa tsaye ya yi ya daure fuskarsa sosai ya ce"ai da hike kin san na saba da yi maki ƙarya,ki je ki duba idan kim ga Barden burinki ya cika tun da ya bar miki gidan" Baƙi t a ɗan tabe ta ce "Ni a wa da zan kore shi,ya dai tafi,kuma dama ya za a yi ka ajiye mana kato a cikin gida?" Murmushi ya saki,ya taka a hankali zuwa inda take.Ya daura hannayensa saman kafadunta ya ce "Hafsa kenan,wallahi ko raina na bawa Barde ban faɗi ba,ban biyashi ba.Hafsa kin san wane ne Barde?Kin san wace iriyar rawa ya taka a rayuwata?" Kanshi ya ɗaga sama wani irin dauyi ya danne masa ƙirji Ya ce "Wallahil azeem Hafsa inda habu Barde a duniyata da ba ki ganni ba har ki ka ji ki na sona" "Gani ki ke kamar kin wuce kaddara ko?Toh a kan Barde zan iya rabuwa da kowa ! Idan na ce kowa ina nufin kowa,ciki kuwa har da ke!" "Idan akwai abin da ya fi sadaukarwa zan yi masa,idan akwai abin da ya fi goyan baya zan ba shi,idan da rai ba guɗa ne ba,zan sadaukar masa da dukkanin rayukan da nake da shi.Amma ko yanzu ba ta ɓaci ba,rayuwa ɗaya ce ko?Toh ki sa a ranki zan sadaukar da ita gare shi,muddin bukatar hakan ta ta shi." Ƙirjinta ta tafe cike da mamaki ta ce "Ahmad da bakinka ka ke cewa za ka iya rabuwa da ni a kan Mahaukacin abokinka,kuma mai laifi wadda hukuma take nema ruwa a jallo" Ƙaɗa kai ya yi ya ce "ai za ki iya zuwa ki sanar da masu neman nasa ga inda yake,sai su zo su kama shi" Cike da madaukakin mamaki ta ce "Ahmad ni ce fa,Hafsarka,dama akwai wani mahaluƙi da zai iya shiga tsakaninmu har ya yi galaba ?" Zame hannuwanta ya yi daga kan fuskarsa,tya dauke nata daga kam kafaɗarta.Ya wuce ciki,yana jin babu daɗi a zuciyarsa game da abin da take faɗa a kan Barde,duk da shima bai so gaya mata maganganun nan ba,amma abun nata ya yi yawa. Ta daɗe tsaye a gurin zuciyarta tana mata zafin kalaman da Ahmad ya faɗa mata,babu abin da kalmomin suka ƙara mata sai tsanar Barde. "Ba zan taɓa bari na rasa mijina ba don ina sonsa,na yi alƙwarin yin duk me yiyyiwa na kawo ƙarshen wannan tsinananiyar abotar" Ta yi maganar cike da ƙunar zuciya Takawa ta fara yi a hankali ta yi hanyar falon Sai kuma ta tsaya ta kalli kofar ɗakin da yake zama a ciki Kafin tattausan murmushin samun mafita ya kubce mata Ta ciji gefe lips ɗinta Ta ce "Barde ko hmmm"WANE NE SHI? BY AYEESHAT KISSAR YOTA...019 51_52 https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z https://chat.whatsapp.com/Eh2iSk99O6jKbZQDbkZQfS?s=cl&p=a&mlu=4 Daga wannan ranar Hafsa ba ta kuma ta da maganar Barde ba,saɓanin da da kullum cikin mita da rigima suke. Yau ta kama talata,kasancewar an tashi da ruwan sama,mai marka-marka ya sa jama'a suka ɓoye a cikin gidajensu. Zaune yake a cikin falonsa yana kallon T.V sai dai sam hankalinsa ba a kan kallon yake ba.Yau tsawon sati biyu da tafiyar Barde.Tun daga wannan ranar bai sake jin ɗuriyarsa ba.Ya je duk inda yake tunanin yana can sai dai bai same shi ba. Ga shi babu wata hanyar sadarwar da za su yi magana. Ga takurar Safna da kullum cikin kiransa da zarriya take,ita gabaɗaya ba ta yadda da bai san inda yake ba. Babban tashin hankalinsa shine:ba shi da tabbacin yana lafiya ko a'a. Duk da zai iya yin haka duk don ya ƙwaracewa ganin Safna. Kiran Safnar ne ya dawo da shi duniyar mutane Ya ɗaga jiki a sanyayaye,da kuma sallana a bakinsa Daga cikin wayar ta amsa Bayan sun gaisa ne ta ce "Har yanzu dai ba wani labari ko?" Jinjina kansa ya yi kamar tana gabansa ya ce"shiiru har yanzu Safna,amma da na samu wata masaniyar za ki ji ni" Jiki a sanyaya su ka yi sallama ta kashe wayar. Yana kashe wayar kira ya sake shigowa,kamar ba zai ɗaga ba,dan a tunanin shi ko costomers ɗinsa ne,,kuma sai ya ɗaga. Da sauri ya miƙe tsaye Ya ce " Shi Barden!?Yanzu kana ina?" Mikewa ya yi da sauri ya yi hanyar fita yana faɗin."Gani nan zuwa,ka kula dai kar ya ganka". ★★★ Hammad Kusan tattare motarsu ta shiga ƙayattacen Garden ɗin.Babu wanda ya fito daga motar sai bayan wajen minti biyu.Kamar haɗin baki suka fito a tare. Nufar inda Ramadan yake zaune suka yi a tare,bare da wani ya kula ɗan uwansa ba. Zama suka yi sannan suka gaggaisa. Harara Jamal ya watsawa Hammad ya ce"wato kai ba za ka iya miƙo hannu mu gaisa ba sai dai na miƙa maka ko?Kai ka san wane ne ni?" Taɓe baki Hammad ya yi ,ya rama kallon banzan da ya yi masa ya ce"Ni kasan wane ne ni da ka ke faɗa min duk kalmar da ta zo bakinka? Karɓe zancen Ramadan ya yi da cewar "su wane ku kuwa,ban da banzaye" "Wai ku ko yaushe ku ka haɗu sai kun yi faɗa?Ku canza hali dukanku wallahi,babu wanda zan aurar a haka" "Ba mu da ishashshen lokacin ɓatawaa,mu je kan abin da ya tara mu" Shiru suka yi ba su tanka ba,tsawon ɗan lokaci. Sai can Jamal ya ce "Mene ne yasa ka ke nemana haka?" Ya yi tambayar yana kallon Hammad. Hankalinsa ya maida kansa sosai ya ce "abubuwa da yawa!Amma kai ma mai ya sa ka ke nema na" "Bai kamata ka maido min da tambaya ba,ya fi dacewa ka fara bani cikakkiyar amsa". Ya ɗan ja numafashi ya cigaba "Ni abin da ya sa nake nemanka mun daukko mara lafiya ne,wannan wadda ake magana a kanta yanzu ,toh ganin jiya weekend ne ya sa na nake nemanka,saboda na san ba za mu samu kwararrun likitoci ba.Sai kuma akan maganar yarinyar nan Rumaisa" "Wato sai da amfanina ya tashi sannan za ka neme ni" Hammad ya yi maganar Kafaɗa Jamal ya ɗage ya ce"nima ina da tabbacin sai da amfanina ya tashi sannan ka neme ni,dan banza ba ta kai zomo kasuwa" Ajiyar Zuciya Hammad ya sauƙe gaskiya ya faɗa,don haka bai ja maganar ba. Ya yi gyaran murya ya fara magana"D.S.P ina so na fara yi maka wata tambaya kafin mu shiga ainihin maganar da ta tara mu" Jinjina kai ya yi alamar yana saurarensa Ya ce "Mene ne burin rayuwarka kafin yau?" "Burina shine na zama jami'in ɗan sanda,sai dai a da burin ne kawai sai da na ƙara hankali tukunna na gina mokamar burin,ma'ana dai da kawai ɗam sanda nake son zama ban banbance ɗan rashawa ko me aikata gaskiya ba." Ban sake tabbatar da na dauko aiki mai hatsarin gaske ba sai da na zama cikakken jami'i. A tunanina na da kowanne jami'in tsaro mutumin kirki ne mai kare kasarsa da dukiyarta da ma yin hukunci na adalci,sai dai kash! Ba haka abin yake ba, ainihin ƴan ta'addan ba na daji ba ne,manyan jami'anmu ne. Sune suke goyan bayan yan siyasarmu wajen aikata komai,ashe abubuwa da yawa na ta'addancin dake faruwa da saka hannunsu dumu-dumu." "Babu ja a zancenka,masu riƙe da madafan iko sune ƙashin bayan ta'addancin kasar nan,sune ginshiƙin rusa kasar.Amma a ganinka su manyan sun fi karfin hukunci ne ?" Ramadan ya yi furicin yana kallon Jamal. "Eh,A'a a bayyane ba su fi karfi ba,a ɓoye sun fi karfi,don masu hukuncin ke aita laifukan.Ko kuma ma na ce a bayyanen ma sun fi,a inda ba su fi ba,shine a rubuce.Ba sai na faɗa maka ba Barrister kai ka san meke tafiya ai,kana daga cikin masu bada labarin sun fi karfin hukuncin ko a'a" "Kun san wani abu" Girgiza kai suka yi a tare Ya ce "idan kai karamin ɗan sanda ne tamkar sarki da bawa haka abin yake.Tsakaninmu da shugabanninmu,su sun zama annoba a ƙasa,sun maida kansu kaji,kullum yan siyasa cikin watsa musu tsaɓa suke ,su kuwa su tsatstsage.Sun maida ƙananan yan sanda bayi,ba ka da ikon yin aiki yadda ya dace,mudin ka taɓo manya,idan ka ga an barka ka yi abin da ya dace toh ɗan talaka ka ke wa hukunci " "Shiyasa yanzu ba ni da zaɓin rayuwa ko mutuwa,aiki kawai nake yi dan tabbatar da adalci a dukkan cases ɗin da na ɗauko.Kamar yadda C.S.P ya yi kafin su salwantar da rayuwarsa." "Wane ne C.S.P ka ce manyan duk mutanen kawai ne?" Hammad ya tambaya cike da son sani,don bayanin nashi ya ƙayatar da shi ainun,ya sake jin ƙwarin gwiwar tunkararsa da maganar. "Murmushi Jamal ya yi". Ya dan yi shiru sai kuma ya cigaba "Na san maganar da na yi bai kamata na yi ba,don zan iya taƙaita maku tambayar amma na ji na faɗa muku ne saboda abin yana damuna,kuma abokin kuka shi ake fadawa mutuwa" "Na san shi da Tager,na san aikinsa,na san zafin kansa, na san an cutar da shi,sai dai har yanzu na gaza gane wane ne shi.Ina buri da muradin ganawa da shi muddin yana raye.Babu abin da ya fi ƙayatar da ni irin salon aikinsa,ko da hike ba shine maƙasudin maganarmu ba" "Maganar Shugabanninmu kuma ai ba a taɓa zama ɗaya a rayuwa sai dai bangare daya ya rinjayi ɗayan." Ya maganar yarinyar nan da kuka kawo asibiti,an samu wani cigaba ne?" Hammad ya furta "Wace yarinya?" Ya tambaya "Kai fa Shege ne Jamal ina jin haka ka ce min kana son ganin Hammad saboda ita" Ramadan ya faɗa yana hararsa "Shi kuma Abdulaziz din ya za ka yi da shi?Gaya min idan sunan uban wani nake karawa a gaban nawa" Sai kuma ya ce Suhaima wai?Har yanzu dai ina bincike,shiyasa nake son ganawa da ita,don maganarta za ta iya taimaka mana" "Anma kana bincike akan Tambarin kunamar nan" Girarsa ce ta tattare alamar rashin fahimta ya ce"wane tambari ?" Ba ka lura da tambarin kunamar dake damtsen hannunta ba? Ya zarce "Akan shi ne nake neman ka Jamal ni ba dan sanda bane ba kuma lauya ba,sai dai zuciyata ta kasa natsuwa shekara 6 kenan da na fara ganinsa,tun ranar farko dana gansa na ɗaura ayar tambaya akan zanen,musamman maganganun da ita yarinyar take yi,wannan ya sa na daɗe da tunaninta.Dalilin fyaɗen da aka yi mata ya sa ta rasa ranta,mahaifiyarta ma ta rasa nata ran,dalilin abin da ya faru da yarinyar.Yayanta kuma tun da ya ce zai je ya dawo har yau da nake baka wannan labarin bai dawo ba." Katse shi Ramadan ya yi da cewar "Wannan keta haddin iyayenmu matan da ake ya yi yawa,yawan daya zarce tunan.Maza da yawa sun dauki cin zarafin ƴa mace a matsayin karamin laifi,na rasa mene ne akan wasu mazan" Murmushi mai ciwo Hammad ya yi,an taɓo masa inda yake mai ƙaiƙayi. Ya ce "Ko kunsan cewaa ya kassara rayukan yara da dama Ya kassara al'umma da dama Ya sa iyayen yara zubar hawaye .Ya ruguza fata buri da makomar wanda aka yi wa.Ya sarewa dayawa daga cikin waƴenda a kaiwa gwiwa.Shin kun taɓa tunanin abu daya zai iya illata jiki,zuciya da ma rayuwar mutum gabaɗaya cikin dan ƙanƙanin lokaci?Fyaɗe na daga cikin manyan matsalolin al'umma a duniya,anyiwa mata anyiwa maza,anyiwa yara masu kananan shekaru,an lalata gobensu.An yi wa matasa masu tasowa an ruguza makomarsu.An yi wa manya masu iyali an ruguza karfin gwiwarsu,an tarwatsa farincikinsu da na wanda suke zagaye da su." Zazzafam huci ya fesar ya cigaba "Tambayta ga masu yin wannan aika-aikar,shin suna da mahaifiya kuwa,don wanda ya san darajar mahaifiyarsa ba zai wulakanta ta wani ba.Suna da kanwa,yaya,ko ƴa,ko kuwa mata?Za su so ayi musu anya?"Ko da hike bari na koma kan labarin da nake baku,don babu mai ba ni amsar tambayata" Tun da ya fara koro Jawabin,Jamal yake kallonsa har ya dasa aya,ya daɗe bai ji tsikar jikinsa ta tashi irin yau ba.Kai tsaye zuciyarsa kalaman suke isa" "Bayan haka an kawo mana yara mata masu karancin shekaru irin nata dan ba za da wuce shekaru 16 ba a lokacin,dama masu shekaru 14,15 ba zan ce maku ga adadin ba,amma na san da yawa,kuma dayawa akwai wannan tambarin a damtsen hannunsu,kana yanayin Fyaɗen ɗin iri ɗaya muddin akwai wannan tambari a hannunsu.Yawancin su kuma sun rasa ransu,sai dai babu abin da ya tsaya min a zuci irin na yarinyar farko." "Wannan lamari ya sani cikin matukar damuwa,da tashin hankali." "Yanzu kusan shekara daya da rabi ba a sake kawo wata yarinya mai wannan tambarin ba .Har na ajiye zancen,don da na fara bincike akan tambarin sai dai ban samu wata masaniyar komai ba." Ya ja numfashi kafin ya ci gaba. "Kwatsam! Sai ku ka kawo Rumaisa,ba karamin tashi hankalina ya yi ba.Gashi ban taɓa faɗawa kowa ba tsawon shekarun nan,ranar da na ji damuwa na shirin yi min illa, babu shiri na samu Ramadan nake faɗa masa, yanayinsa ya nuna ya san wani abu akan tambarin,sai dai tambayar duniyar nan na yi masa yaƙi ba ni gamsashen bayani,sai da na je har gida tunkunna yake faɗa min wai a gurin wata abokiyar aikinsa ya taɓa gani. "Gobe idan Allah ya kaimu za mu za mu je office ɗinta." "Na ga dacewar na faɗa maka saboda kai kafi cancanta ka san wannan lamari,ima so dan Allah ka tsaya akan wannan case ɗin,har abin da yake boye ya bayyana.Da kai da Ramadan" Buɗe baki Jamal.ya yi zai yi magana ya katse shi da cewar "Yauwa na manta kwanaki wasu mutane sun wullo min wannan takardar a cikin envelope " Ya fada yana zaro ta daga aljihunsa. "Sai kuma matar nan mai fama da larurar taɓin hankalin nan,itama jiya na je duba ta,na ga tambarin , Amma ita a wuyanta ne saɓanin sauran Gashi ance waƴenda suka aikata sun mutu,amma fa na ji daɗi" "Amma dai kai ba ka da mutunci Hammad yanzu ace tsawon shekara shida ba ka taɓa faɗa min ba sai wannan karan?Kuma ko lokacin da abin ya faru me ya sa ba ka faɗa min ba?" Ramadan ya furta,fuskarsa na bayyanar da rashin jin daɗi. "Ra'ayi " Ya ba sa amsa cikin halin ko inkula. "Sai kuma ya ce"lokacin kuna ijift,jinyar hajjo" Ajiyar zuciya Jamal ya sauƙe me karfi Ya ce "Gaskiya lamarin akwai ban mamaki sosai,ni ban taɓa kula ba ,amma na ji abin ya dau hankalina,akwai hoton a gurinka?" Gyada kai ya yi ya dauko wayarsa,ya lalobo haton ya miƙa masa. Karɓa ya yi ya zubawa hoton ido,kusan minti 2,kafi. ya ce "Na kasa karanta rubutun ƙasa fa" "Ni ma na kasa,waƴenda suka rubuta ne kawai suka san ma'anarsa Kallon Ramadan Jamal ya yi ya ce "Ramadan mai ya sa lokacin da yake neman bayanai a wajenka ka ringa yi masa wasa da hankali?". Jimmm ya yi can kuma ya ce"Ina ta tunanin ta ina zan fara yi masa bayani ne,kuma ka ga ban san wannan labarin da ya ba da yanzu ba.Kana ina ta kiran wayar Barrister Safnar ba ta shiga. wannan shine dalilin". Taɓe baki Jamal ya yi ya ce "Barrister kenan!" WANE NE SHI? Ayeeshat Kissar Yota/019. Page 53_54 https://chat.whatsapp.com/Eh2iSk99O6jKbZQDbkZQfS?s=cl&p=a&mlu=4 https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Bismillahir-rahamanir rahim. "Jamal kenan " Shima ya faɗa da irin sigar da ya yi furucin. "Dr., a matsayinka na ƙwararre, me kake ganin ke haddasa yawaitar fyaɗe a cikin al'umma? Kuma wace hanya ce kake ganin ya kamata a bi don daƙile wannan matsalar?" Muskutawa Hammad ya yi ya gyara glass ɗin idonsa ya ce "Ni dai a tunanina, ba dalili daya ne ke haddaawa ba,amma bari na baka wasu daga cikin dalilan a takaice." "Rashin sanin darajar ɗan Adam da mutunta haƙƙinsa.Rashin tarbiyya da ƙin bin koyarwar addini. Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da na iya haddasawa,domin sai kana da hankali zaka iya banbance abu me kyau dbmar kyau Amfani da ƙarfi ko iko a kan mara ƙarfi,ba saina tsawita ba,kunsa yadda manya ke take hakkin na ƙasa da su. Rashin hukunta masu laifi yadda ya kamata. Rashin ilimantar da mutane game da mutunta iyakokin wasu da neman yardarsu. Rashin kulawar iyaye da al'umma wajen tarbiyyar yara. Waɗannan su ne manyan abubuwan da ke taimakawa wajen yawaitar fyaɗe a cikin al'umma a nawa ganin." "Ba iya naka ganin ba har da namu,amma saka sutura me bayyanar da tsiraici baka ganin yana daya daga ciki?" Jamal ya kai aya yana kallonsa... "Eh kaima ka yi magana Jamal yana ɗaya daga ciki musamman tsakanin yammata da samarin wannan zamanin.Amma kar a rinjayar da shi gabadaya idan aka yi la'akari da masu yiwa jarirai da kananan yara. Wasu kuma hijabin da ki ke sawa ke jan hankulansu,dama masu yi wa maza abin dai sai hamdala." "Hanyar magance su kuma tana ga daƙile wayenan matsalolin ko kuma rage musu tasiri." A tare suka shiga tafa masa suna dariya "Wato likita kai na daban ne,maganganunka abun a duba ne wallahi" Ramadan ya faɗa bayan gama tafa masan "Kar ka daman malam" "Na wani tunani yanzu ku matso ku ji" Jamal ya faɗa Matsawa suka yi ya yi musu raɗa Da sauri Hammad ya ɗago Ya ce "Kai amma ba ka taɓa burge ni irin yau" Harararsa ya yi ya buɗe baƙi da nufin magana,wayarsa ta hau ruri,fasa maganar ya yi ya ɗaga wayar "Subhannalah ku na ina yanzu?" Ya yi furincin yana miƙewa tsaye Ku miƙa shi Asibiti mafi kusa ,ku tabbatar komai ya tafi daidai gani nan zuwa. Ya faɗa sannan ya kashe wayar Kallonsu ya yi ya ce"Ni kam dai zan tafi dama akwai ayyuka da yawa da zan yi yau,ga lokaci ya riga ya tafi. "Su kuma wayen nan na aika su karshen gari su yi min wani bincike,shine suka yi hatsari ". "Amma duk yadda ake ciki za ku ji ni,ban gama faɗar abin da na so ba,duk da hakan ba matsala ba ne" Miƙewa suka yi suma Hammad ya ce"ai mu ma ina ga zaman ba shi da amfani tun da ga abin da ya taramu kuma angama" A tare suka jera suna tafiya,har Jamal zai shiga mota ya juyo ya ce"maganar da na faɗa muku,a kula sosai,za mu yi zama na musamman a kanta" "In sha Allah" Suka amsa a tare Kafin kowa ya shiga motarsa,ya yi nasa gurin ★★★ Zahra Tun bayan jin duniyarta ta tsaya,ba ta sake tantance ainihin abin da yake faruwa,a duniyar zahiri ba. Sai yanzu da ta ji sassanyar iskar da take da tabbacin ta dawo mata da ruhinta da ta yi zaton ko ya tafi ne. Ko da ta farka din,kwakwalwarta ba ta tafi hutun wucin gadin nan da take tafiya ba. Sai dai ta kasa buɗe idonta don ba ta son ace komai da ya faru a gaske ne,kamar yadda zuciya da kwakwalwarta suke ba ta,tabbaci . Shiru ta yi tana sauraren bugun zuciyarta. Sunnu a hankali ta fara ware manyan idanunta,sararin subhanaha ta zubawa ido da a ka yi masa ado da taurari.Da alama dai dare ne sosai don ba ta jin motsin komai,sai na kaikawon masu tsare su da daddare. Ta juya gabas da yamma ba ta ga Chubado a raye ba,ta sake dubawa ba ta ga gawarta ba,ba ta ganta ba.shikenan?Shikenan sun rasa ta ita ma?Ba fa ta bata labarin nata ba. Ina suka kai dan cikinta?Me za su yi da shi?Chubaɗon ita ina suka kaita?Shikenan ita ma?Ko darajar sallar gawa ba za ta samu ba?Wai mai suka yi wa mutanen nan ne? Juyaar da kanta ta yi gefe tana kallon tarin jama'ar da aka rabo su da muhallansu bisa son zuciya,aka zube su anan,saboda cikar muradai. Duk iskar nan da ake yi ba su da wata mafaka da ta wuce nan gurin,rana ko damina,duka suna nan.Babu maganar abun rufa,don ko suturar arziki babu a jikinsu,wahala ta tasa sun yayyage. A hankali ta yunkura ta tashi zaune. Idonta ta shiga bazawa tana neman Amanarta,can gefe ta hangota ta takure jikinta guri ɗaya,tana bacci.Sai dai ga dukkan alamu a wahale t take yinsa. Rarrafawa ta yi gurin da take,don ba ta jin kafafuwanta za su dauketa,ko da ta miƙe.. Karasawa inda take ta yi,ta daura kanta saman cinyarta,sannan ta cire yalolan hijabin dake jikinta ta rufa mata. Jikin nata ya dau zafi sosai Dama hijabin ne yake dan taimakonta ya rufe mata jiki duk da ya gaji da yawa. Kwata-kwata sanyin da ake yi baya damunta duk da tana jin shigarsa har cikin ƙashinta. Sai dai suyar da zuciyarta take yi ya kore sanyin. Zuba mata ido ta yi tana jin wani irin zafi a ranta,shikenan yanzu sun rasa chubaɗo,rasawa ta har abada,rashin da ba za su taɓa mantawa da shi ba Me ta yi musu da ta cancanci irin wannan kisan na cin mutiunci? Shafa lallausan gashin Fadime ta yi da ya ci uban datti Ta ce "Yanzu ke kaɗai ki ka rage min,kamar yadda ni ƙadai na rage miki. Ba na so ki riga ni mutuwa dan ban san halin da zan shiga ba. Ba na son na rigaki nutuwa Faɗine,dan ban san yadda za ki yi da rayuwarki ba,a matsayin da ki ke yanzu." "Ina da burin gina miki rayuwa Fateemah,kamar yadda Baffa ya ba ni amanarki,in sha Allah ba zai yi dana sani ba,mudin ina raye" Kanta ta ɗaga sama wani irin abu me yaji yana zagaye nakoshiita Ta ce "Ya Allah!Ya rabbi! Ya hayyu ka ƙayyum,ka fi mu sanin halin da muke ciki,kafi mu sanin abin da ya dace da rayuwarmu,ya ubangijin rahama, ga bayinka Allah suna zaluntar mu,ubangiji ba mu musu komai ba,Allah ka yi mana sakayya da gaggawa a kansu,ya rabbi ba mu da wani iko,ba mu da karfi ba mu da dabara,Allah da kai kaɗai muka dogara,ya rabbi ka kawo maba daukinka" Shiru ta dan yi sai kuma ta cigaba "Allah ga baiwarka nan,ubangiji ka tsaya nata lokacin da babu me tsaya mata,ya rabbi ka ji tausayinta,ka agajeta.Idan ba ni da rabon kubuta Allah ka kubtar da ita " "Ya rahim salihan bayinka suna da yawa a duniyar nan ya rabbi idan ba ni da rabon fita ubangiji ka jefa ta hannu na gari,inda za ta yi dariya ba kuka ba,Allah ka share mata hawaye dan darajar manzon Allah." "Ke!" ɗaya daga cikin masu tsare su ya faɗa yana hasketa da fitilar hannunsa me mahaukacin haske.. Tsawar da ya yi mata be sa ta ji ko gezau ba bare hasketan da ya yi. Me ki ke yi a nan . Mutumin ya sake faɗa cikin tsawa,yana kara haske ta Ba ya iya ganin fuskarta gabadaya,sai dai gefe ɗaya dan haka ya nufi.inda take a fusace cike da mugun nufi. Cak ya tsaya yana kallonta daga dan nesa da ita Ita ce aka kashewa ƴar uwa,ita ce tabbas ya gane ta,ita ce muhaluƙi na farko a doran duniya da ta fara ba shi tausayi,tun da ya shigo harakar nan . Tabbas zuciyarsa ta karye har bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba a lokacin. Ashe yana da sauran imani,ya yi zaton har abada wanin abu ba zai sake dakar masa zuciya ba.Ashe ba haka ba ne. Jiki a mace ya ci gaba da jan kafafunsa ya karasa inda take "Me ki ke yi har yanzu ba ki yi bacci ba?" Ya faɗa a tausashe Ɗagowa ta yi a hankali ta zuba masa ido,ta gane shi, shi ne mutumin da ya taimke su lokacin da aka kaɗo su daga ruga,mai baƙin rawani. Ta kawar da kanta a hankali ba ta ce komai ba.Baki ya buɗe zai sake mata magana Basiru ya ƙwala masa kira.Juyawa ya yi da sauri ya bar gurin zuciyarsa tana azalzalarsa ya juyoya sake kallonta.. Ko kaɗan ba ta jin bacci,toh wacce natsuwar ce da ita wadda za ta barta ta yi wani bacci. A nan ta cigaba da zama har ketowar alfijir.Da ta daidaici lokacin sallar asuba ya yi sai ta kalli Fadime ta fara bubbugata. "Fateemah!Fateemah!Tashi lokacin sallah ya yi ta faɗa a sanyaye Buɗe idonta ta yi ta kalleta sai ta mai da idon ta rufe bare da ta ce komai ba.Ta tashi zaune.Nuna mata yadda ake taimama ta yi. Suka yi Zahra ta karɓi hijabin da ta rufa mata daren jiya ta tayar da sallah. Fadime kam zuciyarta sai bugawa take,saboda kar su Basiru su ga Addarta tana yin sallar su yi mata wani abun. Allah ya taimaka har ta idar babu wanda ya zo Hijabin ta cire ta bata,ita ma ta yi sallar Bayan ta gama ne ta rarrafa ta kwanta a kan cinyar Zahra,tana sauƙe wata iriyar ajiyar zuciya. Cikin wata iriyar murya mai sanyim da bata taɓa jin ta da ita ba ta ji ta ce"Adda!Shikenan itama ko?Ina son Inna,suka kashe min ita,ina son Baffa sosai,shima suka kashe.Adda ina son Adda Chubaɗo ita ma sun kashe ta,saura mu ko?" Haɗiye wani abu me daci ta yi.Idanunta a lumshe suke dan haka ba ta buɗe su ba. Ta ci gaba da cewa "Adda bana so na mutu yanzu,amma kin san mene?Ina so su fara kashe ni kafin ke,ba zan iya jura ba." "Ina so na yi kuka,amma yaƙi zuwa Adda nan ɗina na min ciwo sosai" Ta faɗa tana nuna mata saitin zuciyata Zahra kam ta rasa abin da za ta faɗa mata zuciyarta ta yi sanyi shiyasa ta zaɓi ta saurareta kawai,jin maganganunta take tamkar wuta don ba karamin ƙona zuciyarta suke yi ba. Bata damu ta tanka mata ba "Adda ina ta so ki farka na hau kan cinyarki,ko zan ji sanyi,ko ina ya min zafi Adda.Lokacin da na tashi na ga kin ƙi tashi,na za ci ko kema kin tafi kin barni."Hannunta ta kamo ta ɗaura saitin zuciyarta ta ce"Lokacin ji na yi kamar nan zai buɗe min.Wai dama wannan ce rayuwar da Baffa yake cewa zan fahimce ta idan na girma?Amma ai har yanzu ban girma ba ko?" Jim ta ɗan yi maganar da za ta faɗa tana mata dauyi ,ta ce "Na gaji Adda, ko dai Allah ba ya son mu ne?." Rufe mata baki Zahra ta yi cikin wani irin yanayi ta ce "Allah yana son mu,jarabawa yake mana,ya ga ko zamu iya cinyewa.Ki yi shiru kuma maganganunki suna ƙona ni" Gefen bakinta ta cije da karfin gaske,inda ta san abin da take ji,da bata hanata magana ba,inda ta san yadda fitar maganar yake rage mata nauyin da zuciyarta ta yi,da ta ce ta yi. Ba ta sake magana ba,ita ma Zahran haka Bayan wasu awwani Aka fara rarraba musu gurasa hannu baka hannu kwarya jama'a suke cinyewa saboda tsananin yunwa da wahala. Ko da ya zo kan Faɗime sai ya miƙo mata guda hudu a bakacin ya bata guda biyu,da mamaki Zahra ta ɗago ta kallesa,har za ta yi magana sai ta fasa. Mai da kallonta ta yi ga Faɗime da ake miƙawa amma taƙi karɓa kamar ma ba ita ake bawa ba. Hannu ta sa ta karɓar mata ta zube mata akan cinyarta.Shi kuma ya yi gaba ya ci gaba da rabawa ba tare da ya bawa Zahra ba. Ita kam Zahra ko a jikinta,don a zatonta ma su biyo ya bawa Ki ci mana Ta faɗa Girgiza kanta ta yi ta ce "Mutuwa nake so na yi" "Idan ki ka mutu na yi yaya ƴar Baffa?" Buɗe idonta ta yi Ta ce "Sai ki koma garinku,ki tafi gidanku wajen ƴan'uwanki" "Ni kin ga yanzu ba ni da gida ba ni da gari,ba ni da Inna ko baffa,babu komai sai ke" *Hannunta ta kama ta rike tsawon wasu dakiku kafin ta ce"ki na da ni Faɗime,ni ce ruga,ni ce inna ni ce baffa,ni ce kowa ,ki sa a ranki kina da kowa idan kina da ni,koma ko babu ni,kina da Allah shine me komai mai kowa." Miƙa mata gurasar ta yi ta ce Kin amince da abubuwan da na ce?Kin yarda duka zan iya maye miki gurbinsu?Idan eh,ki karɓa ki ci,idan kuma a'a ne ki faɗa min kin ji" WANE NE SHI? Ayeeshat Kissar YATO 019 Page:55_56 https://chat.whatsapp.com/Eh2iSk99O6jKbZQDbkZQfS?s=cl&p=a&mlu=4 https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Karɓar gurasar ta yi, ta fara dannata a baki ba tare da ta ce komai ba.Jinta take kamar ƙaya,idan ta sauka cikinta kuwa sai ta ji tamkar wuta ta zuba a cikin.Shekarunta ba su kai ta tantance ainihin me take ji ba,Amma ta san tana jin ciwo a cikin kirjinta.Akwai wani Abu mai nauyi da take jin kamar yana rinjarta,yana rinjayar sauran karfin da ya rage a gangar jikinta. Miƙa mata gurasar ta yi,ba tare da ta ce uffan ba. Karba ita ma ta yi,duk da ba ta tunanin akwai wani Abu da zai iya wucewa ta makogaronta. Amma idan ta ce mata ba za ta ci ba, sanin kanta ne rigima ta janyo,tun da itama ba don tana so take cin ta hannunta ba. Ta gutsira ta Kuma tauna. Sai dai hadewa ya zama yaki,don ta kasa. Juyowa ta yi ta kalli Fadime da alamar gajiyawa a fuskarta Za ta yi magana ta girgiza Mata kai alamar a'a. Rintse idonta ta yi ta haddeye da kyar Mano ne ya karaso gurin ya mika mata abu a leda baka sannan ya wuce. Kai tsaye bayan wani dutse ya zagaya ya samu guri ya zauna. Ya ɗan dade a zaune kafin ya dakko gurasar Zahra da ta yi saura ya saka ta a baki,kasa hadewa ya yi saboda boshewar da ta yi ,babu shirin ya curo pure water daga aljunusa ya kora ta,don taki wucewa a haka. A haka ya cigaba da ci ba don ba shi da abin da zai ci ba,kawai dai na Zahran yake son ci,domin shi ma abin karyawarsa ya bata,wani irin tausayin ta yake ji,gashi tun daga ranar da aka kashe mata y'ar uwa yake samun kansa da zuba mata ido na tsawon lokaci ba tare da ya san dalili ba. Ya daɗe zaune a kafin ya tashi ya bar gurin,yana jin nishadi har cikin ransa.Ya san yau Zahra za ta ci wani abu bayan wannan bushashshiyar gurasar. Gefe guda Kuma zuciyarsa tana raya masa abin da yake da tabbacin yin shi halaka ne a gareshi,da ma duk wanda ya yi wannan kokarim ★★★ Mamaki kwance a fuskarta ta bude ledar.Biredi ne a ciki sai kunu me dan zafi mamaki ya sake mamaye ta. Na mene ne wannan?Kuma ya aka yi ya bata ita kadai bai bawa sauran Jama'ar gurin ba?. Kafadarta ta dan dage kafin ta mikawa Fadime biredin,ita kuma ta dauki kunun ta fasa ledar da bismillah a bakinta. Kunun ya yi mata dadi saboda babu sugar kuma da d'an zafinsa. Ko dar ba ta ji ba game da kunun don ta san idan cutar da ita za su yi ba sai sun ba ta wani Abun ba. Duk da har yanzu ba ta daina mamaki ba. Mikawa Fadime ta yi ta karba ta d'an kurba ta mikawa wata mata mai cikida ta lura tun da ya basu ledar take bin su da kallo.Da sauri matar ta karba tana zabga godiya. Haka rayuwa ta cigaba da garawa bayin Allahn nan a cikin wannan hali. Kullum cikin kawo sabbin mutane ake. Suna kuma bada fansa amma sai sun yi niyya,ko da sun kira gidanku idan suka jinkirta suna iya kasheka kuma su karɓi kuɗin fansar. Wani lokacin ma ko ba a yi jinkirin ba suna kashewa. Yanzu kam sun samu sauƙi ta ɓangaren abinci,don ana kawo dawa susa matan gurin su yi tuwo a ciki gaya. Saɓanin da da suke wajen kwana biyu ba su basu abinci ba,idan suka tashi kuma su ba su gurasa 1 ko 2. Duk da hakan idan dawar ta kare suna kwana uku ba su ci abinci ba. Bangaren Zahraa tun tana tunanin kwanankinsu a wajen har ta hakura ta daina ta fawallawa Allah lamarinta don ta san me ji ne kuma me gani. Haryanzu ba ta daina sallah ba ba kuma su daina dukanta ba idan suka ga tana yi. Tun daga ranar da Shugaba ya yi kashe Chubaɗo bai kara dawowa ba. Izuwa yanzu hantsi ya daga sosai,zafi ya fara damun jama'a,da alamar yau rana za a Yi sosai. Wasu karafuna Basiru ya zo ya zobe a gaban tarin al'ummar annabin da suke zazzaune a gurin.Da ya gama zazzage su a bai cewa kowa komai ba ya juya ya tafi.Can ya dawo ya sake.zube tsintsiyoyin kwakwa. Daya-bayan-daya .jama'a suka fara tashi suna dauka suna jeruwa a layi. Mata kuma tsintsiyar suke dauka Ganin haka ya sa wayenda ba su taɓa ganin anyi ba,suka ringa zuwa suna dauka,suna kuma hawa layi,gudun kar su yi laifi. Ba tare da sun san me za'ayi ba. "Adda ki tashi mu dauka muma" Fadime ta yi furincin cikin harshen fulatanci.Ita gabadaya ta tsinke da lamarin way'en nan azzaluman mutanen,babu abin da ba za su iya aikatawa ba.Ta Kuma san Addarta da taurinkai,ba kuma ta shirya rasata ba. Shiru Zahra ta yi kamar ba za ta tashi ba,can Kuma ta mike,suka je suka dauka suma. Sai da karafan da tsintsiyoyin suka kare sannan mutane suka daina zuwa suna dauka. Sun kai Rabin awa a tsaye a gurin kafin wasu.daga cikin su suka shiga gaba,wasu suka tsaya a baya wasu kuma a tsakiyarsu,don ba su kariya ta musamman. Suka tasa su.gaba tamkar ba mutane ba.A cikin wannan tafiyar,duk wanda ya yi gangancin tsayawa hutu,to ɗayan biyu ne,ko ya yi ta rayuwarsa ko kuma jikinsa ya gaya masa.Shiyasa duk tafiyar da ake jama'a suke ta kaffa-kaffa duk da sun gaji,ga rana ta take sosai. Tafiya suka yi sosai kafin suka iso,tuni mutane sun fara fita hayyacinsu,saboda tsananin yunwa da wahalar tafiya. Da kallo Faɗime ta bi gurin. Katon fili ne sosai ga bishiyoyin da aka fito da su daga cikin kasa,ma'ana tun daga tushiyarsu. Ga kuma itatuwa manya da ƙanana,wasu an faskarasu, wasu kuma ba a sara ba. Gefe guda kuma gona ce iya ganinka. Babu bata lokaci maza suka fara saran bishiya,ba sa kyale ta sai sun jijjigota gaba ɗaya daga tushe,wasu kuma wanda aka riga aka fito daga cikin kasa suke sassarawa. Mata kuwa shara suka dauka suna ta yi,wadda ba su san 'okacin da za su gama ta ba. Nan ma.akwai yaran Shugaba sai dai ba su kai na can yawa ba,suna ta lissafin kuɗaɗen,suna shirya su, su da wasu mutane jikin su sanye da kakin sojoji, fuskokinsu a rufe da rawani,makamai iri-iri a zube a gefensu. Rana ta ƙwalle a kansu babu mafaka babu hanyar gudu,toh ka gudu ka je ina ma? "Adda na gaji,zan faɗi" Faɗime ta faɗa a wahale idanunta ko gani ba sa yi sosai. "Kar ki yarda ki ajiye sharar nan ko ki faɗi,,ki daure,kin ji" Da sauri Zahra ta juya ta kalle ta,har za ta yi magana sai ta fasa ta cigaba da shararta. "Faɗi abin da yake ranki yammata na fiye shiga abin da babu ruwana za ki ce ko?" Ta tambaya sannan ta ɗan yi murmushi ta ce "Na san zaki yi mamaki ganin ban sanku ba,ban san daga ina ku ke ba,amma ina ta yi muku shishshigi a cikin lamuranku,alhalin bai shafe ni ba" Shiru Zahra ta yi ba ta tanka ba,don abin da ta faɗa gaskiya ne. Matar ta cigaba "Sunana shine Baba Karime,ba yau na zo gurin nan ba, shi yasa na san dayawa daga cikin tsiyar da mutanen gurin nan za su iya aikatawa." "Kin san me yasa nake cewa ki daina musu taurin kai idan suka ce ki yi abu ko ki bari?Saboda a gabana an salwantar da rayuwar masu hali irin naki,waƴen da bazan iya tantance miki yawansu ba" "Ko kuma ko ban faɗa miki ba ai kin gani,tun da sun gwada misalin rashin imanin a kan ƴar uwarki" Gurin nan suna sakin mutane,amma sai sun yi niyya.Idan ki ka ga an dauke mutane daga gurin nan,toh mata ne,kuma sai bayan wasu mutane sun zo,waƴenda ba zan iya ce miki su wane ne su ba.Sai su zaɓi matasa su tafi da su" Ta wannan hanyar ce kawai na san ana fita,ta sauƙi,kuma shima ba mu da tabbacin ina suke kaisu. Shiyasa nake gudar miki hakan ta faru dake,don ke matashiya ce,daidai iba." Tari ne ya sarƙeta,sai da ya lafa kafin ta ce Ni ko a labarin da nake ji ban taɓa jin guri irin wannan ba " "Abin da ya sa nake miki shishshigi kuma na ga kamar akwai sauran buri da fata na yin rayuwa a gaba a tare da ke, shiyasa nake shishshige miki idan na ga ki na musu taurin kai.Kin ga wannan Shugaban ki ji tsoron Allah ki ji tsoron sa, wallahi shaiɗani ne na gasken gaske" Babu abin da Zahra ta ce har yanzu,ita dai baba Karime ba ta damu ba,ta cigaba. "Wallahi baiwar Allah ban san ki ba amma haka nan Allah ya dasa min kauna da tausayinki a raina,musamman lokacin da ɗayar nan take raye,dukkansu sun jingina gare ki ne,duk da kananan shekaru irin naki,kuma a hakan ki ke dauke dauyinsu ki hada da naki ,ga ki yarinya karama,wadda ba ta wucce a saurari damuwarta ba" " Mutanen gurin nan ba su da imani ko tausayi,ba su dauki ran dan adam matsayin abu me daraja ba,sun dauke shi tamkar ran kiyashi ko cinnaka,wanda za a mitsike a wuce" Me yasa suke hana ayi sallah?Dn Allah kuma ina ne nan" Ta tambaya ba tare da ta tanka maganganunta ba. Ɗan ɗaga kai Baba Karime ta yi ta kalli gurin kafin ta sauke kan kasa Ta ce Idan na ce miki ga dalilin na miki karya saboda,nima ko da suka kamo ni sun hana yi,amma nafi tunanin" Sai kuma ta yi shiru "Kin fi tunanin me?". Girgiza kai ta yi ta ce zargi ne,za ki gani da idonki kuma" "Nan gurin ma ba zan ce miki ga shi ba,amma na san shima gurin su ne.Duk bayan wani 'okaci sukan sawa mu zo mu yi wannan aikin,wanda ba shi da wata ma'ana,suna yi ne kawai don zalunci.Sai dai suna kashe mutum 5 zuwa 7 kafin mu gama da sun gama kai adadin nan suke dakatar da aikin. Jinjina kai Zahra ta yi tunane-tunane suna zagaya ƙwaƙwalwarta. "Abin da ya sa na ce kar ƙanwar nan taki ta tsaya da sharan,za ki gani da ido ki" Daga haka ta ja bakinta ta tsuke. Kafin wani 'okaci yunwa da ƙishirwa da tsananin wahala ta sa jama'a sun fara zubewa a kasa a galabaice. Duk da halin da mutane suke ciki bai sa sun tausaya musu ba,duk wanda ya faɗi dukansa suke yi duka na wulaƙanci,suna taka su.Idan suka lura mutum ya galabaita da yawa kuma su harbesa. Ganin suna kashe jama'a ne ya sa mutane da yawa suka ƙara dagewa suna aikin ba don komai ba sai don tsairatar da rayuwarsu. Kamar Zahra ba za ta kuma magana ba,kuma sa ta kalli Baba Karime ta ce'Gaskiya mun gaji da yawa kalli numfashin da ƙanwata yadda yake fita, kin ce kar mu ajiye sharar kuma " Ku yi hakuri ina da tabbacin mun kusa ajiyewa,ba ki lura sun kashe wajen mutum 5 ba,ka da ki yi wani motsi za ki iya zama ta karshe ko ta biyun karshe" Murmushi ta yi ta ce " mun galabaita da yawa gwara na kawo karshen wasan." Ba tare da dogon tunani ba ta saki tsintsiyar a ƙasa ta faɗi sannan ta mike tsaye jiri yana diɓarta. WANE NE SHI? Ayeeshat kisssar Page 57_58 Yota/019 Under Yota's amazing pens https://chat.whatsapp.com/Eh2iSk99O6jKbZQDbkZQfS?s=cl&p=a&mlu=4 https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z Barde Zaune yake cikin ƙaton falon yana fuskantar mutumin da yake gabansa. Fuskarsa sanye da mask ya kuma ɗaura p-cap a saman kansa. Yana ɗan kaɗa yatsunsa da suke zube kan teburn d ya raba tsakaninsa da mutumin. A tsanake yakenazartar yanayin falon,da mutanen ciki. "Aiki za ka min a kan wannan mutumin" Inyamurin ya furta yana kallonsa. Bai ce komai ba sai idanu da ya zuba masa. Wani hoto ya mika masa ya ce "Shine wannan" Sai kuma ya tura masa wata jaka kan tebur ɗin,ya ce, 'Akwai hatsari a cikin aikin,duk da kaima mai hatsari ne. Wannan shine ladan zai iya canja rayuwarka na har abada" Kuɗi bai isa ya canza min rayuwa ba,kuma ba kai zaka fada min tukuicina ba,ni zan faɗa ma". Ya miƙe sannan ya cire bakin tabaron da ya rufe idonsa da shi,ya daura kafarsa saman tebur ɗin. Ya ce "Ka faɗi sunan kawai. Ni ba na yawan tambaya. Aiki ne nawa ba labari ba. Idan ban karɓa ba, akwai dalili. Idan na ce na karɓa shikenan" Mutumin ya saki murmushin da ya ƙara bayyana muninsa,ya miƙe tsaye shima. Ya ce "Sanyi mana Bro, ba ka yi mamakin ya aka yi na san inda kake ba?Ko kuma na san yadda zan yi na same ka ba?Duk da yadda ka ke ɓoye kanka?Toh kar ka yi mamaki don na harsaso abin da zai iya canza rayuwarka" Jakar ya ja baya kaɗan.ya ce"Indai ka karɓi aikin kana da zaɓin faɗar adadin tukuncinka" Gira ɗaya Barde ya ɗage mai ya ce""Accepted your project" "Tukuicin zai iya zama kai ne da kanka,mudin buƙatar hakan ta tashi. Kamar dai haka " Ya yi furucin tare da harbin mutumin dake gefen damarsa da sauri. Kafin mutumin ya yi wani yunkuri ya saita sa da bindigar hannunsa. Ya ce za ka iya tsaida shirin da ka fara,kona tsaida bugun zuciyarka na har abada" Saita sa yaran mutumin suka yi suma da bindigogin hannayensu. Suna jiran umarni daga Shugabansu. "Ku dakar da komai" Mutumin ya faɗa a ɗan tsora ce. Ja baya suka yi kowa ya koma matsayarsa. " Na jinjinawa basirarka,da ka gane wanda nake farauta,ka sauƙaƙa aikina." Ya fesar da numfashi ya ce."Ka sa a ranka kamar an kammala aikinka ne,zan kuma neme tukucina kamar yadda na ce". "Amma ka sani Barde sawun keke ne,watakila ka na yin dukkan shirinka a tafin hannuna ne." Ya sauƙe bindigar daga kan mutumin,ya maida ta mazauninta,sannan ya nufi hanyar fita hankali kwance. Sai da ya je bakin ƙofar falon ya ji muryar mutumin yana faɗin"Anya hakan da ka yi ba zai kai ka ga nadama ba?" Cak ya tsaya ,ba tare da ya juyo ba ya ce"Cika baki ba naka bane,domin sanin gobe sai Allah,sai kuma wanda ya ganta" ★★★ Mai Dollars Family Yau ta kama rana ta musamman a cikin gidan Alh Mansur.Domin yau ne Biyu daga cikin ƴaƴansa za su dawo kasa Nageria,bayan shafe dogon lokaci ba sa nan. Duk da hankulan jama'ar gidan ba a kwance yake ba,hakan bai hana su yin hidindimu da kaikawo ba. Cikin takunsa na cikkakun maza masu jini a jika ya shigo falon yana ta faman baza kamshi. Ya shirya tsaf cikin dakakkiyar farar shadda,ya ɗaura baƙar zanna a kansa,sai faman walƙiya take. Babu abin da fuskarsa take fitarwa ban da annuri. Agogon hannunsa ya kalla kafin ya fara kiran "Minal Minal" Falon ta ƙaraso tana amsa kiran nasa a sanyaye,sai dai kallo guda za ka yi mata ka karanto farincikin da take ciki..Zuba mata ido ya yi har ta ƙaraso inda yake.Ta faɗa sosai gabaɗaya ta canza kamar ba ita ba.Ta yi kyau sosai cikin baƙar abayar da ta saka ta yi rolling kanta da mayafin abayar. "Ya dai" Ya faɗa yana kallonta. Ta kallesa kafin ta ce "Babu" Kansa kawai ya jinjina ya yi gaba yana faɗin "mu je toh" "Ina Tariq?" "Gani nan Allah ya sa samu ne" Hannusa ta kama ba ta ce komai ba "Sakannni dallah tun da ni ba ɗanki ba ne." Ta mai banza ta kuma ƙi sakinsa. "Mommy bari mu je" "Har lokaci ya yi kenan?Allah ya tsare.Amma fa kun yi kyau ma sha Allah" Mommy ta faɗa da shigowarta falon kenan. Mommy ba ki ganni bane? "Na ganka mana Tariq" Shagwaɓe fuska ya ɗan yi kafin ya ce"Amma ai sai ki ce na yi kyau ko" Da karfi Minal ta ja hannusa suka yi waje tana faɗin ba ka yi kyau ba ko kaɗan." Dariya ya yi har sai da kyakykyawar wushiyarsa ta bayyana . Har yanzu yarinya ce ke ba ki san rayuwa ba,bari sai kin girma zan fara musayar yawu dake" Motocinsu suka shiga suka nufi airport. Motar Hammad ta shiga ta ƙyalle Tariq da yake ta sababin ta yaudare shi,inda ta sani tun farko sai ta ce ga motar da za ta shiga. Firfitowa suka yi daga motocinsu bayan da suka isa,suka nufi Arrival Hall, inda mutane da dama ke zazzaune,wasu a tsaye, suna jiran fitowar 'yan uwansu. Suka zauna a kujerun da aka tanada a gurin. Miƙewa Minal ta yi cike da zumuɗi ta ce"Ohh Allah !" Murmushi Hammad ya yi wanda ya ƙara bayyana haibarsa. Flight display board ɗin ya nuna mata da ya tsansa.Ta kalla. ɗan tsalle ta daka ganin jirginsu ya yi landed. Ta rungume Dr tana dariyar farinciki da ta daɗe ba ta yi ba. Farincikinsa ne ya karu ganin yadda take ta fara'a. Ko yanzu sai kin jira kusan rabin awa yarinya". Tariq ya faɗa shima yana murmushi "Idan mintuna 30 ɗin ta cika za su fito ai" Tsaye Hammad ya miƙe bayan da fasunjoji suka fara fitowa.Ya zubawa hanyar ido don ganin futowar ƴan uwansa. Sannu a hankali take takowa tana jan trolley ɗinta.Sanye take da farar T-shirt da farin wando,ta ɗaura jacket mai launin rairayi (beige) a samansu wadda ta kai mata har wajen gwiwarta. Gefenta wani matatshin saurayi ne mai kama da Minal sosai. Sanye da farar polo mai ɗan tsawo da baƙin wando, ya saka fararen sneakers. Ya kuma rataya ƙaramin backpack a kafaɗarsa, yayin da yake jan trolley ɗinsa Shima. Ga su can Tariq ya faɗa yana dariya,ya juya zai yi wa Minal magama sai dai bai ganta ba. "Ina Minal ?" Da ido ya yi masa nuni da inda take.Har ta kusa ƙarasawa inda suke. Sakin trolley ɗinta ta yi, ta buɗe hannayenta tana kallon Minal. Da gudu Minal ta ƙarasa gare ta, suka rungumi juna gam,Minal na dariya ita kuma tana murmushi. Ɗago ta Nihal ta yi ta kalli fuskarta kafin ta ce"Baby gurl a sassauta riƙon kar a karya ni" Sakinta Minal ta yi ta koma kan Sauban ta rugume shi tana dariya murna.Ita dai Allah ya ɗaura mata ƙaunar ƴan uwannata,ba ta iya son wani abu ba bayan su,da su kaɗai take rayuwa.Duk da yanayin gidan nasu. Sai kuma matar nan da ta yi wa rayuwarta shigar bazata. "Me kama dani kin girma fa" Sauban ya faɗa yana jan hancinta. Rararsa ta dan yi ta ce "Ni da ka manta da ni ma" Hannyensu ta riƙo suka karaso inda su Hammad suke. "Ke dai ki canza hali,komai sai kin min shigege haba" Dariya suka yi gabadaya sannan suka gaisa da shi shima. "Zo na sa miki albarka " Hammad ya faɗa yana nufo inda take. "Amma ka raina ni gayen nan,yushe ka yi wayo ma?" "Ranar da aka haife ki." "Idan kun gama, sai ku tuna da ni. Ni ma ai ɗan uwanku ne." Sauban ya faɗa yana harararsu. "Kai da ka ke dani,me za ka yi da su?Kyalesu su je can da yawarsu" Tariq ya faɗa. "Karka haɗani da ɗan uwana dallah" "Taho taho shehin ƙwallo". Karasowa ya yi ya haɗasu duka ya rumgume. "Barkanku da dawowa kasarmu ta gado kun ji " Ya faɗa kafin ya janyo trolley ɗinsu ya nufi hanyar waje "Ai da na ji kasar babu daɗi zan koma inda na fito " Sauban ya faɗa Kai a wa?Ai kun dawo kenan sai dai ziyara yara" "Wai ina Mommy ne?" "Ba ta jin daɗi shine Dr ya ce za zauna kawai." Motar Hammad Nihal da Minal.suka shiga shi kuma Sauban ya shiga ta Tariq "Wai tsaya na tambayeku,ni direbanku ne?" "Kamanta ne,idan ka cika magana kuma zan kore ka." Nihal ta ce hankalinta na gefen titi tana ganin sauye-sauyen da da ba ta san da su ba. Jinjin kai ya yi ya ce "Kin karo wulaƙanci yarinya, kin daɗe bakya nan fa,ina ga 3 years fa" Kai ta gyaɗa ta ce"Eh yanzun ma Minal ce ta sa na dawo,kar ka cire ram komawa ta nam kusa. Ta kalli Minal da ta saka hannunta cikin nata ta lumshe idanuwanta kamar me jin bacci. "Ameenatu lafiya?Ko dai jinkin ne?Ko kuma kin yin hankali ne?" "Babu ɗaya,damuwa ce ta sawa ranta ji yadda ta ƙara figewa dan Allah" "Akan me?" "Akan maganar nan dai,na baki labari ai" "Ya jikin matar".. Ta ce tana tuna maganat da suka yi da Hammad ɗin. "Da sauƙi amma har yanzu ba ta san waye yake kanta ba,amma dai ana ta samun ci gaba. "Mene ne amfanin saka.damuwar har haka?Ko saka kanki cikin wani hali zai sa ta ji sauƙi?" Ta girgiza kai "Buɗe baki ki amsa min" Amsawar ta yi da" a'a ." "Shikenan toh ki ci gaba da saka damuwar a ranki kin ji" Ta faɗa sannan ta lumshe idanunta,alamar ta gama magana. Daga haka babu wanda ya sake cewa wani abu har suka kai gida. A harabar gidan suka iske Mommy da masu aikin gidan,dama wasu daga cikin ƴan uwanta duka.Tuni su Tariq sun iso su kawai ake jira. Ta daɗe zaune a cikin motar kafin a hankali ta zura kafafunta waje ta fito da ganganr jikinta gabaɗaya. Zuciyarta ce ta motsa mata a cikin kirjinta Mommy ta hango tana kallonta.Kallo irin na uwa ga ƴaƴanta,ta tsinto so kauna,bege kewa a cikin idanunta, da wani irin rauni. Da sassarfa ta je gareta ta yi mata kyakykyawar ruguma ba tare da ta ce komai ba.Sai dai ita kanta ta san ta yi kewar wannan kirjin ta yi kewar samun kula daga me shi.Ta yi kewa yadda ba ta iya faɗuwa. Ko da ta saki Mommy sai ta ga tan sharar ƙwalla,ta zuba mata ido tana kallonta,kamar ta akwai abin da yake damunta,kamar ta rame,kamar tana buƙatar ta amayar da wani abun da yake ci mata tuwi a ƙwarya. Hannunta ta riƙe suka nufi cikin gidan ba tare da ta kula da sannu da zuwan da ake mata ba. Biyo su Hammad suka yi suma Jinjina masa kai kawai ya yi,hankalinsa na kan Mommy. Sai da ta zaunar da Mommy a kan kujera,sannan ita ma ta zauna. Ta ƙi yin magana,har sai da Mommy ta ce"Tashi ki watsa ruwa mana. Ta miƙe ta nufi bangaren da zai sadata da bedroom ɗinta.. Bayan gama gashe-gashe Sauban ya kalli ya ce " bari nima na ɗan watsa ruwa tukunna" Wanka suka yi,sannan suka hallara a dining gabaɗayansu . Bayan sun yi nisa da cin abincin ne Hammad ya ce"Ya na ji ba ku tambaya Daddy ba?* "Yanzu nake shirin tambayarka na ji shirun ya yi yawa" Cewar Sauban Ita kuwa Nihal da take cin abincinta hankali kwance cewa ta yi"Na san yana meeting ko?Ko kuma yana wani aikin me mahimmancin da ya fi mu" Ta yi furucin cikin halin ko in kula Shiru suka yi duka don sun fahimci ma'anar maganarta ta. Sai can Sauban ya ƙatse shirun da faɗin Tariq ya rashin ji,fatan ka daina".. Kansa ya ɗan shafa ya ce"A'a wallahi ana nan ana yi " A zahiran ce Nihal abinci take ci sai dai a ɓadilance hankalinta na kan Mommy da Minal da kuma mikin da Hammad ya fama mata. Hammad kam ya fahimci halin da take ciki dan ya santa sosai,musamman yadda ƙwayar idonta da ta kasance shuɗi (blue)ta ƙara cizawa.. Minal kuwa hankalinta gabaɗaya ya koma asibiti,so take ta je ta duba ta,sai dai tana da tabbacin Nihal ba za ta barta ta je ko'ina ba. Bayan sun gama cin abinci fali suka koma aka daura hirar yaushe gamo. Minal na kwance kan cinyar Nihal ,ita kuwa bin kowa da ido kawai take. Idan ka ji ta yi magana toh an saka a ciki. Miƙewa ta yi jin hayaniya neman dmsa mata ciwon kai ga gajiya,so take ta ɗan kwanta. Ta kalli Hammad ta ce "Daddy ko Hmmm" WANE NE SHI? Ayeeshat kissar. PAGE 59--60 Yota/019 Under Yota's amazin pens https://chat.whatsapp.com/Eh2iSk99O6jKbZQDbkZQfS?s=cl&p=a&mlu=4 https://whatsapp.com/channel/0029VbAzYbJDDmFcfb5WOQ3z A daidai lokacin Daddy ya shigo.hakan ya sa ta juya ta kallesa. Cikin takunsa na manyan mutane masu ji da kuɗi ya karaso tsakiyar falon. Ya dubi ƴaƴan nasa murmushi kwance a fuskarsa ya ce"Sannunku da dawowa ahalin Mansur.Wallahi tun safe muke wani meeting sai yanzu muka gama,na so ace da ni aka je tarbarku" Daddy ya faɗa yana kallon Sauban da Nihal. "Na yi tunanin haka Daddy" Sauban ya furta babu alamar damuwa a muryarsa.Ya miƙe ma ya zo inda Daddy yake suka gaisa. Gaishe da shi mutanen falon suka shiga yi, kafin suka fara zamewa suna fita. Har yanzu Nihal ba ta ce komai ba. Kallon da ta lura Hammad yana yi mata ne ya sa ta ce"Barka da wannan lokaci,fatan na same ku lafiya". Bai nuna alamar damuwa ba ya amsa "Alhamdulillah mun gode Allah,ya U.S ɗin?" Ya maida dubansa kan Sauban ya ce"Dama aiki ya min yawa ga Hammad ya ƙi maida hankalinsa yadda ya kamata.Shi kuma wancen" Ya nuna Tariq "Sai dai addu'a.Amma Alhamdulillah agogo sarkin aiki ya dawo." Dariya Sauban ya yi ya ce"Toh Alajinmu" Ɗage kafaɗa Tariq ya yi alamar ko a jikinsa.Shifa dama duk harakar wahala ba sonta yake ba,su je can su karata da aikinsu.Wanda yake yi ma yanzu ma ba don yana so yake yi ba. Daddy ya daɗe a tsaye suna hira kafin ya wuce sashinsa Sai da ya tafi sannan Nihal ma ta yi bangarenta,tana ankare da irin hararar da Hammad yake auna mata,amma ko a jikinta. ★★★ Karfe biyu na dare. Tsaitsaye suke cikim katon filin da yake zagaye da doguwar katanga,ta farin dutse. Gabaɗayansu sanye suke da wata jar duguwar riga har ƙasa, mai hula. Hannayensu riƙe da ƙoƙon kan mutum.Sun jeru a layi sahu sahu. Yau rana ce ta musamman a garesu,rana ce ta fargabar abin da zai je ya dawo,na zulumin me zai faru. Rana ce ta farinciki kuma ga wasu daga cikin su. Gurin ya yi tsit babu sautin komai sai na kukan mujiya da yake tashi. Sannu a hankali itama kukan nata ya lafa,shiru ya sake wanzu a wajen. Can wata iriyar busar sarewa mara daɗin sauraro ta gauraye ilahirin gurin. A tare suka ɗaga hannayensu sama,sannan suka fara tafiya suna rangaji suna wasu irin harɗadɗen yare. Suka isa gaban wata katuwar ƙoramar jini,wadda take ta tafasa. Yadda suke a kan layin haka suka ringa ɗibar jinin da ƙoƙon hannunsu suna sha sau uku,sannan su wuce gaba inda wata dodonniya take,su yi mata sujjada. Duk wanda ya yi sujjadar ya kasa dagowa toh yana cikin waɗanda kungiya ta sadaukar da jininsa. Hakan ya sa kowa ka gani zaka ga fargaba kwance a kan fuskarsa. Wata iriyar tsawa aka yi da walƙiya mai karfi,kafin wata wuta fara da baƙa ta fara ci tana tsiri a sama,ƙoramar jinin nan ta kama wata iriyar ambaliya.Kusan mintuna biyar ana haka kafin komai ya dawo daidai. Muryar dodanmiyar ta fara tashi mai kama da kukan jaki. "Ya ku mabiya duniya masoyanta,a yau kungiya ta tashi da wani bakon al'amari wanda ba ta saba ganin shi ba,hakan ya sa muka kara yawan mutanen da za a yi sadaukarwa da su." Shiru ya gifta,can kuma ta ci gaba "Kamar yadda kungiya take yi yau za a karawa wasu matsayi,saboda kwazonsu,da kuma yawan sadaukarwar da suke mana,za kuma a rage wa wasu matsayi,sabodalaifi na bijirewa umarnin kungiya,ko kuma rashin yin sadaukarwa a kan lokaci. Muna yi wa baƙi barka da zuwa da fatan za ku bi dakokin kungiya." Bayan ta gama magana ne masu manyan muƙaimai suka taso daga kan kujerunsu zuwa gaban madogararsu. Wani mutum me sanye da baƙaƙen kaya saɓanin sauran da kowa jajaye ne,sai dai banbancin numbern da take nuni da matsayinka. Suka iso gabanta. Mai baƙaƙen kayan ne ya fara yin sujjada,sannan suma suka yi. Shi ya fara ɗagowa ya tashi ya isa gaban Madogarar,ya durkusa ya dauki ƙoƙon kan mutum ya ehbi.jinin da yake zubowa daga ƙasanta ya sha,sannan ya kuma yin sujjada ya ɗago.. Ya buɗe baki zai yi magana aka daka masa tsawa,cikin tsawar sautin murar ɗazu ya fara tashi. " "Bala'ai da masifu suna tunkaro kungiya sanadiyarka,tabbas badanda ka kawowa kungiya cigaban da babu wanda ya kawo mata ba,da tuni kungiya ta dauki tsatstsauran mataki a kanka ." A firgice ya ɗago ya ce,"amin aikin garafa ya madogarata,amma ban san kuskuren da na yi ba. "Kalli can" Ya daga kai yana kallon bangon da ya bayyanar da tasiwirar da ba za ta taɓa gogewa a idonsa ba domin ita ce silar komai. A firgice ya tashi tsaye ya ce "Madogara an kashe su fa,da idona na ga gwarasu." Cikin tsawa madogara ta ce "Ka yi babban kuskure lokacin hauhawar matsayinka ka saɓa dokar kungiya,wanda muma ba mu sani ba sai a wannan ranar. Kungiya ba ta daukar asara don haka ka je ka gyara kuskurenka,kafin ya shafi kungiya,idan ba haka ba,tsiniwar kungiya za ta hau kanka. Magiya ya shiga yi yanawa dodanniyar kirari.. "Ya isa haka,kungiya ta ji kukanka,kuma za ta sama hannu " A jiyar zuciya ya sauƙe.Jiki a sanyaye ya kuma yin sujjada ya mike ya koma mazauninsa zuciyarsa na bugawa kamar yadda ya yi haka suma waƴenda suke bayansa suka yi. Suka faɗi bukatunsu kungiya ta amsa. Ta kuma ragewa wasu matsayinsu ta karawa wasu. Sannan aka yi sadaukarwa da mutanen da kungiya ta zaɓa. ★★★ Mommy Sosai ta rame kallo ɗaya za ka yi mata ka karanto damuwa a kan fuskarta duk da tana koƙarin ɓoyewa.Tun daga ranar da ta ɗaura ido a kan matar nan ba ta kuma yin cikakken bacci ba,burinta ta farfaɗo ta gana da ita,domin a yanzu ta tabbatar da ita ɗin ce,so take ta tabbatar mata da bakinta,amma abu ya ci tura. Tana ta kokarin kar ta yawaita tambayar Hammad amma abun ya gagara. Ta share hawayen da ya gangaro mata sannan ta miƙe ta ɗauko wayarta.Wata number ta kira sai dai har ta katse ba a. ɗaga ba. Bugu zuciyarta ne ya tsannanta ,ta kuma kiran wayar ta miƙe tsaye tana zage a ɗakin. Sai da wayar ta kusa katsewa sannan a ka ɗaga.Ta sauke nannauyan ajiyar zuciya ta fara magana. "Har yanzu shiru ba ta tashi ba,ina gaf da gazawa ƙarfina ya kusa karewa" Ta faɗa kuka na kubce mata. Daga cikim wayar aka ce " Saudat,ba ki fi mu damuwa da wannan lamarin ba. Ki kwantar da hankalinki idanunmu yana cikin asibitin,duk abin da yake faruwa muna da sani a kai.Dom haka da ta farka za mu sani,ki kama kanki,ki kuma.iya takunki,kin san da cewa kuskurenki ɗaya tal yana iya ruguza mana burin da muka daɗe muna muradin cika shi,ki kiyaye" Da azama Mommy ta katse kiran jin motsi a bakin kofar,a hanzarce ta nufi kofar tana faɗin waye. Da sauri ta shiga ja da baya daga bakin kofar,zuciyarta na wani irin bugu. ★★★ 1:39 am A sukwane motar take tafiya,burinsa ya karasa mahaɗarsu kafin lokaci ya ƙure. Cike da ƙosawa ya dubi direbansa ya ce"Ka kara sauri Bala,lokaci yana neman ya ƙure fa." "Toh ranka shi daɗe" Bala ya amsa daga haka babu wanda ya sake magana a cikinsu. Sai dai mutumin lokaci bayan lokaci yake kai dubansa kan agogon hannunsa. Ɗagowa ya yi da sauri ya ce"a'a ya na ga ka tsaya ne?Ba ka ji na ce ina sauri ba ne?" Cikim girmamawa bala ya ce"Wallahi ban san meyafaru ba,nima kawai na ga ta mutu ne" Dafe kai mutumin ya yi yana fesar da iska me zafi Iya kokari Bala ya yi amma motar nan taƙi tashi,don haka ya fito don duba ko wani abun ne. Cike da damuwa mutumin ya fito daga motar jikinsa sanye da kayan yan sanda. Ya kalli Bala da yake ɗan taɓe-taɓe ko zai gano matsalar. "Wai ya aka yi ma kasan motar ba ta da lafiya ka bari muka taho da ita?Kasan abin da yake gabana ne?" "Wallahi yallaɓai motar nan lafiyarta kalau,don ɗazu ma sai da na kaita Sabi'u ya kuma dubata,ya tabbatar da lafiyarta ƙalau. Sai da sharrin karfen nasara kawai" Mutumin ya bude baki zai yi magana wayarsa ta kama haske alamar ana kira . Ya ɗaga ya ce"Hello Abdallah ka ganni a hanya mota ta mana tsiya wallahi" Jim ya dan yi alamar yana sauraren abin da ake cewa daga cikin wayar... Ya kalli gurin da yake wajen gari sosai kafin ya ce"A'a ai ba mu fi ma rabi ba,kasan yanayin hanyar, kuma ni ban san ya za a yi ba ma" "Yanzu ya za a yi yallaɓai?Motar nan fa taƙi tashi" "Ina ga kuɗin mota zan baka sai ka je ka taho da masu gyara,ni kuma zan jira yanzu haka an turo a ɗau..." Maganarsa ta katse ganin wasu baƙaƙen motoci sun zagayesu,ga wasu mutane da suke fitowa daga duhuwar ciyayi. Da sauri ya zaro bindigarsa da nufi yin harbi,sai dai ko kafin ya yi wai yumkuri wani daga cikinsu ya daki hannun da bindigar take.. Da karfin tsiya suka kamasa suka danna sa a mota.Bala kuwa wanda ya daki hannun mutumin ne ya dauki bindigar da ta faɗi ya harbe sa... Sai da suka dan yi tafiya a cikin dajin da suka shiga da shi sannan suka tsaya,suka fito da shi waje. Ɗaɗɗauresa suka yi a jikin bishiya da karfin tsiya sannan babban cikin su ya iso gabansa ya dan duka ya ce "Oganmu ne ya samu aiki,kuma sai mun cika" Da ƙyar mutumin ya ce" mai na yi muku?Su wane ne ku?Waye ya turo ku?" "Ba mu ya kamata ka tambaya ba,amma ka bari kafin ka mutu za ka ga fuskar wanda ya samui" "Ku kwance shi mu fara aikinmu." Suka kwance shi sannan suka daddanne shi da karfin tsiya ya sa wata ƙaramar wuka ya yanke masa harshe.. Ya goge jinin a jikin mutumin,yana ƙyaƙyata dariyar mugunta ganin yadda mutumin yake shure-shuren azaba. Ganin kamar ya suma ne ya sa ya sake umartar su da su ƙara danne masa shi. Suka yi yadda ya ce,shi kuma ya sa kuwar ya yanke masa kunnuwa duka biyu. Tsananin azaba ta sa ya sake suma ya farfaɗo. Mikewa ogannasu ya yi ya zaro wayarsa daga aljihu ya yi kira,ba a dauki dogon lokaci ba aka ɗaga. Video ne hakan ya sa fuskar mutumin daga wancen bangaren ta bayyana Ya saita mata wayar a fuskarsa yanda zai gani. Duk da a kwance yake cikin jini da raɗadin da yake da tabbacin ba zai tashi ba,sai da ya zaro idanunsa,da dama can sun yi ƙuru-ƙuru ya buɗe baki zai yi magana sai dai babu wannan Damar.Kawai ya fashe da kukan tsananin baƙin ciki. Daga dayan ɓangaren kuma mahaukaciyar dariya mutumin yake ƙyaƙyatawa,ganin yadda yake gunjin azabar fitar rai. "Ga dayar kala ta yau ka gani,dama rayuwarka ba ta da wani amfani maci amanar kasarsa." "Ku kashe sa da bindigarsa" Ya kare maganar dariya na kuma kuɓce masa. "Good bye" Ya faɗa yana ɗaga masa hannu sannan ya katse wayar. Babu bata lokaci ya sa bindigar tasa,kamar yadda aka umarcesa ya harbe shi" Motocinsu suka shiga suka bar wajen da mugun gudu. Da wani irin mahaukacin gudu ya iso wajen,sai dai shi daga cikin dajin ya fito. Ya sa kafa ya daki narfin motar ya fito hannunsa riƙe da wani makami kamar gatari,sai dai shi daga samansa ya na da faɗi sosai da kaifi,daga tsakiyarsa kuma ya tsuke.. Da sassarfa ya ƙara so inda mutumin yake a yashe cikin jini. Wani irin ihu ya kwarara sai da dajin ya amsa. Ya sari wata bishiya da makamin hannunsa har sai da ya lume. ★★★ Mai Dollars Family Minal Gabaɗaya hankalinta ya koma asibiti,duk ta bi ta rasa natsuwarta.Zuciyarta sai buga mata take yi. Babu abin da take sai juyi. Gabaɗaya daren ba ta yi bacci mai daɗi ba. Ta rasa wace iriyar kauna take wa baiwar Allan nan,a ƙasan zuciyarta take jinta. Washegari da wuri ta shirya don ita ganin daren ta yi ya mata nisa. Kasancewar a ɗakin Nihal ta kwana ne ya sa,ta yi sallar asuba,don ita ba ta wasa da sallah sam. Kamar yadda ta daukarwa kanta kwanan nan yau ma hakance ta faru,duk a falo suka tarar da ita. Hammad dai murmusawa kawai ya yi,zuciyarsa na mamakin wannan irin kauna da Minal kewa matar nan. Ta kalli Daddy da yake shan shayi yana tunani ta ce"Daddyyy shine ka ce za ka je ka dubo ta kuma ba ka je ba" Ajiyar zuciya Daddy ya sauke yana dan faɗaɗa fuskarsa da murmushi ya ce"Afuwan Autar Daddy abubuwa ne suka sha kaina,kin san zaɓe yana ta ƙaratowa ga ɓatan Zahran nan.Abubuwa dai duk sun min yawa.Amma anjima in sha Allahu ina nan tafe" "Siyasa ka fara Daddy?" Sauban ya tambaya yana kallon Daddyn "Eh,a'a,Abubakar ke siyasa ka sani,kuma Abubakar Mansur ne,Mansur Abubakar ne" "Tabbas Allah dai ya bar ƙauna ya bada sa'a" Ya faɗa yana dariyarsa me sanyi,dan kaf gidan ya fi kowa yanayin shiru-shiru,amma akwai surutu idan ya samu waje. "Wai Daddy har yanzu ba a gano Zahran ba?Ina ta zuci-zucin tambayeka na manta" Hammad ya faɗa "Eh wallahi Hammad har yanzu shiru,babu wani labari,amma har yanzu ana kan bincike" Baki ya buɗe zai yi kuma magana,wayarsa ta hau ruri. Dagawa ya yi bakinsa dauke da sallama Daga cikin wayar Jamal ya ce"Yau za ka shigo Afiyya?An ji ma ina nan zuwa zan gana da Rumaisa tun da ta samu sauƙi.Zan kuma duba jikin baiwar Allan nan" "Eh,zan shigo in sha Allah sai ka zo.Amma fa an camza mata ɗaki ka sani?" Daga cikin wayar Jamal ya ce"Eh na san ancanza,amma ban san inda aka maida ta ba" Faɗa masa ɓangaren ya yi da numbern ɗakin sannan suka yi sallama ya ajiye wayar. "Yauwa ka ga nima ba sai na sha wahala ba, da na je na san inda zani,don zan iya zuwa lokacin da kake aikin da dole sai na jira. Daddy ya yi furucin yana kokarin tashi tsaye. "Ai ko baka sani ba,kana da Auta,ta haddace hanyar dakin " "Kwantar da hankalinka zan ma kira idam na zo" ★★★ Suna tafiya a hanya Minal na addabarsa da ya ƙara sauri "Ke kin ishe ni,ko na baki ki tuƙa ne?" "Eh,bani.ka ga yanda ake tuƙi" Ya yi murmushj ya ce"ni ha dan iska bane,ina da burin ganin anjima lafiya". Ta taɓe baki cikin halin ko in kula da maganarsa Kafin su isa Ramadan ya kira sa yake shaida masa zai zo anjima,ya duba jikin majinyaciyar nan,don tun da suka yi maganar nan sai yau ya samu kansa. Suna isa Minal ta fito za ta yi ɓagaren da zai sada ta da ɗakin da zuciyarta take muradin zuwa . Dakatar da ita Hammad ya yi yana faɗin "Jira ni mu shiga tare,yanzu dakin nata zan fara" "Toh mu je" "Amma sai na fara zuwa office ɗina tukunna" Girgiza kai ta yi da sauri,ta ce"Ka same ni a dakin" Ta yi gaba ba tare da ta jira jin abin da zai ce ba. Kansa kawai ya girgiza ya yi hanyar ofishinsa. Yanzu babu yan sandan da suke tsaron kofarDuk da akwai idon hukuma a kanta har yanzu. Karfe uku na yamma Tana zaune a gefen gadonta hannunta da babu karin ruwa riƙe a hannunta kamar yadfa ta saba Yanzu ciwon fukarta ya warke sai abun da ba a rasa ba.Ta zuba mata ido tana kallonta,kamar ta kira ta ta amsa . Ita so take ta farka ko haukar ta cigaba da yi mata,za ta fi samun kwanciyar hankali fiye da kullum da ganta a haka. Wayarta ta yi kara amalar shigowar message.Ta duba Nihal ce take nemanta. Ta miƙe badon tana son ta tafi ha,sai don sanin halin Hajiyarta ta. Ta dubi nurse ɗin da take yawan zama tare da ita ta ce"Bari na je,sai gobe" Murmushi nurse din ta mata ta ce"Toh Allah ya kaimu, Jiki a sanyaye ta fita,sai da ta biya office ɗin Hammad kafin ta wuce gida.Zuciyarta cike da tunanin rigimar da za ta yi wa Daddy yau tun da yaƙi zuwa. Ba ta daɗe da shiga ba nurse ɗin ta lura da hannun matar da kafafuwanta suna motsi,ta fita da sauri don kiran Dr. A hankali ta fara koƙarin buɗe idonta da suka yi mata nauyi,da ido kawai take bin ɗakin tana tunanin me ya kawo ta nan kuma. Daidai lokacin aka turo kofar da sallama za a shigo,sai dai me?Cak ya tsaya jin bugun zuciyarsa ya dakata na dan wani lokaci,wayar hannunsa ta subuce ta faɗi. Ita ma idanunta suka sauƙa a kan fuskarsa,ta zabura da mugun karfin da sai da ta faɗo daga kan gadon. Ba za taɓa mantawa da wannan fuskar ba har abada,ko da kuwa baccin mutuwa ta yi ta tashi,kuma tabbas shine. Ta shiga nuna shi hawaye na mata suntiri a fuska,sai dai ta kasa cewa komai,sai ma numfashinta da yake ƙokarin daukewa Wayarsa ya ɗauka da mugun sauri ya bar ɗakin yana kiran wata number. Fitar mutumin ke da wuya wasu mutane suka shigo jikinsu sanye da kayan likitoci suka daura ta a kan wani gado suka fita da ita,don tuni da suma. Alhamdulillah! A nan na kawo karshen book 1,mu haɗe da ku a book 2 don warware muku zare da ababa,da kuma samun amsoshin tambayoyimku.