[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing* ✍🏻 *By* *Salma Mas'ud Nadabo* 👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest ```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera-speed-dial&_tn--=H-R Email:realhausafulaniwriters@gmail.com Facebook: www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *GARGAƊI* ```Ban yadda a juya min wannan labarin ba, ta kowace hanya, ba tare da izini na ba. Don haka a kula a kiyaye. ``` *TUNATARWA* ```Labarin dake cikin wannan novel ɗin ƙagaggen labari ne dan faɗakarwa da nishaɗantarwa haka kuma suna yanda ke ciki|``` ```BISMILLAHIRAHAMANIN RAHIM``` *Page: 01* Wanke wanke ne jibge a tsakar gida Wanda ko gidan biki ne sai haka, yarinya ce wadda baza ta wuce shekara goma shahudu ba, zaune saman kujera tayani gulma, ta tasa wanke wanken gaba, sai sharar ƙwalla take inda sabo ya kamata a ce ta fara sabawa da wannan baƙar wahalar, kallo ɗaya zaka mata kasan a wahale take, ko kayan jikin ta sun sha ruwa har sun gaji, yar riga da zanine sun mata yawa saboda tsabar rama, ko ba'a fadama ba kasan yunwa na galabaitar da ita, fara ce amma saboda tsabar wahala tayi jirwaye bama a gane farin sai ta daga wuyan ta, tana ɗauke da dan siririn hanci da baki dan qarami pink, duk da kodewar da tayi hakan be hana aga kyan da Allah yayi ma *Nihal* ba, Tsawar da aka daka mata ce ta sata ɗagowa a razane, cikin ɗaga murya indo tace, "dan uwar ki uban mi kike da har yanzu kin gagara gama wanke wankenan." "Shegiya mai ruwan maita, kiyi ƙoƙari kisa na rasa cinikin safe, dan wallahi bazan lamunta ba" goge hawaye Nihal tayi tare da cigaba da wanke wanken da takeyi, dan sarai tasan wacece Gwaggo indo, dan ba yau ta saba rufe ta da duka ba. Cikin sauri ta samu ta sauke kwanikan ta kai su ma'ajiya, qoqarin bude daki take, gwogo ta daka mata tsawa keeee!!!.. Birki Nihal taci ta juyo cike ta fargaba tana zare ido, harara Gwaggo ta aika mata tace, "mikike nufi da haka? sai kin gama taɓa ƙazamar uwar taki, sannan zaki dawo ki sheƙamin koko"? "Masu siya susha su mutu kenan tunda ba uwar ki keda asara ba ko, aiko zan gwada maki kuskuran da ki kayi na ƙoƙarin shiga ɗakin Hansatu." Janyo ta gwogo tayi ta soma jibga sai da ta mata lilis sannan tayi kwallo da ita kanta ya daki bango, qara sakin kuka Nihal tayi, Gwaggo kuma sai faman haki take tace, "narantse da Allah daga ke har Hansatun ba wadda ta isa ta ƙasarani wallahi uban kuma ya ja da mu ya zama gawa bale ku wallahi ƙarya kuke," "Bari malam ya dawo shima zanji dalilin aje min ku a gida, da bai watsa Ku almajiran ci ba daga ke har uwar taki" "Na baki nan da yan mintina ki sheƙa koko, in kuma ba haka ba jikin ki ya gaya maki" sannan gwogo ta ja dogwan tsaki tana qoqarin shigewa ƙurya ɗakin ta, lallau san murmushi ta saki kamar ba ita ke hargowa ba tace, "a'a yar baba har antashi kenan"... "Eh wallahi Gwaggo" Saratu kenan ɗiyar Indo wadda ta daurawa san duniya ko tsinke bata so ya taba ta bale mutum Kuka ne ya kubucewa wa Nihal tace , "astagafirilla Wannan wani irin *SAUYIN RAYUWA* ne ," jiki ba ƙwari ta miqe tare da Shiga madafa tana sharar ƙwalla, Saratu ta bita da harara. Duk Wannan tijarar da Indo ta gama, duk a kunan umman Nihal tayisu wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata. Ba ta taɓa tunanin ko a mafarki Ahalin *Tanimu* zasu wulaƙanta su ba amma sai gashi yau mutuwar malam taja masu tabbas sun ga *Sauyi Rayuwa* ```Taku ce har kullun Salma Mas'ud Nadabo ```✍🏻 [1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 *Edit by:* *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the best ```) https://mobile.Faceook.com/Real-hausa-fulani-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=operaspeed-dial&-tn_-=H-R Email:realhausafulaniwriters@gmail.com Facebook: www.Facebook.com/REALHAUSA FULANIWRITER'SFORUM.com *Page: 02* Kamala tatar kokon Nihal keda wuya, ta juye shi a bokitin da take zuwa talla da shi. Ganin Gwaggo na ɗaki yasa tayi sauri ta shige ɗakin su, cike da sallama ta Shiga ɗakin tana mai kallan umman ta, dake kwance saman tabarma wadda ko motsi ba tayi daga idanuwan ta sai bakin ta, dake motsawa sakwamakwan ciwo da take, kallo ɗaya zaka mata kasan mahaifiyar Nihal ce, a hankali Nihal ta matso kusa da ita, duk da warin da take tabbas abinda Gwaggo ta faɗa gaskiya ne, babu abinda ummi keyi inbanda tashin wari kasancewa uwa uwa ce shiyasa ko jin warin ba tayi. murmushi ta kuma saki tare da daura hannun ta saman gashin umma, Wanda ya cukurkude amma duk da haka ana ganin tsawan shi da laushin shi, wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo ma umma, girgiza kai Nihal tayi tace, "umma na abin alfahari na, ki daina zubar da hawayan ki insha Allah zaki warke umma, ki rinƙa yawo kamar kowa kinji rabin raina," ta idar daal zancan tare da shafa gefen fuskar umma. murmushi Umma tayi ta buɗe baki a hankali wadda ya mata nauyi tace,"Allah yasa maki albarka Nihal," "Amin Umma, sai kinyi hakuri yau Umma na naso ace tun kafin asuba na tashi, har na maki wanka amma yanzu lokaci ya ƙure," murmushi kawai Umma tayi Nihal ta miƙe har ta kai bakin ƙofa ta juyo tana kallan Umma sannan ta fita da sauri. Cikin sa'a ko da ta fita Gwaggo na ɗaki sai shewarta da ke tashi ita da yar lelan ta, bokitin koko kawai ta ɗauka, sannan ta sa kai ta fita tana tafe tana sauri kansancewar har yanzu gari bai waye ba sosai, gashi ƙafar ta ko arziqin takalmi bata samu ba, sai zafi da fasan ƙafar ta ke mata haka dai ta samu har ta kai tasha, wato inda suke sai da koko. "Nihal". "Nihal" sunan ta da ake ta kira ne ya sata waigowa cike da fara'a, "jummala".. "na'am".. "me yasa yau baki biyo min ba?. rausaya kai jummala tayi, "ina san zuwa Nihal amma abinda Gwaggo ke maki ne bana jin dadi shiyasa Nihal." Rausaya kai Nihal tayi tace, "karki damu jummala lokaci ne ya kawo haka tare da sauyin rayuwa, yau kusan shekar hudu kenan raban dana tsinci kai na cikin fari cikin jummala" ta ida zancan wasu hawaye na sulalo mata hannu jummala tasa ta goge mata hawayan, ba komai ƙawata Allah yana tare daku ke da Umma , a haka suka ƙarasa har gaban bishiya suka zauna. Wani ɗan matashin saurayi ne ya ƙaraso gaban su, cike da murmushi yana kallan jummala yace samin dan wakyan 50, sannan ya samu guri ya zauna yana kallan Nihal yace, ni ko jummala na rasa mi nayi ma ƙawar ki, bata min magana kullun fuskar ta daure ya fada yana kallan fuskar Nihal cike da fara'a, girgiza kai jummala tayi tace, "laaa wallahi baka fahimci Nihal bane shiyasa" "To shikenan yanzu dai duka nawa ne kudin koko dana dan wakyen? "Bana so ina ganin Ku anan kuna talla" duk Wannan zancan da saurayin keyi kan Nihal na ƙasa ko Kallan inda saurayin yake ba tayi, murmushi jummala tayi tace, "Ni ko kana bani mamaki, har yau ka kasa faɗa mana sunan ka, amma kullum sai ka siye kayan mu duka kuma da alama kai ɗan birnine ko?" "Jummala Ashe ana gane yan ƙauye irin mu kenan"? dariya Jummala tayi ita da Nihal wadda sai a lokaci ta dan dara. Wannan ɗan saurayin da ke zaune kusa da su Nihal ba yau ya far zuwa tasha ba, kuma kullun fes zaka Ganshi shi dai baza'a kira shi da fari ba amma dai ruwan tarwada ne, daka kalle shi kasan dan Hutu ne dan beyi ruwan dan kauye ba, har wa yau dai bai taɓa faɗa masu suna shi ba, duk sanda Jummala ta tanbaye shi sai yace mata sunan shi bawan Allah, hakan yasa Jummala ke Kiran shi da dan uwa haka itama Nihal duk da ba wata magana ke Shiga tsakanin su ba, amma duk san da ya zo sai ya kafe ta da idanuwan shi, hakan yakan sata jin nauyin shi, haka ya ƙirgo kuɗin ya basu sauran yace sunyi sadaka haka suka rinqa mai godiya, har yayi gaba Nihal tace, "yaya Allah ya biya maka buƙatunka na alheri, lalausan murmushi ya saki yace, amin Nihal, sannan suka cigaba da Raba talla, har Nihal ta dibar masu dan idan zata iya tunawa raban su da abinci tunda jiya. Kasancewa juye sukayi yasa tun karge 10:00pm ta kamo hanyar gida jummala tayi hanyar gidan su, har ta shawo kwana taci karo da Mudi da alama ya sha ya bugu kallo ɗaya zaka mai kaji baka marmarin maimatawa, shine babba ɗan Gwaggo daga shi sai saratu wadda yayi mata nisa sosai ko wajan haihuwa, rabawa tayi ta gefan shi zata wuce, fisgota yayi ya kifa mata mari yace, "dan ubanki har kin isa na wuce ke ma ki wuce baki bari na gama wuce wa yo ko uwar ki Hansatu ta isa na wuce itama tazo zata wuce, tunda Mudi ya wanke ta da mari ta kafe wasu hawaye masu zafi na bin kuncin ta ko kallon ta bai kuma yi ba ya wuce, yana zuƙar sigarin da ke hannun shi zamewa tayi ƙasa tare da sakin kuka me cin rai sai da tayi kuka ta gaji sannan ta ja jiki ta Shiga ciki, muryar Gwaggo da dillaliya kawai ke ta shi a gidan. "Haba Indo ke kanki kin sani ina maki sauƙin kayan nan kinfa san ke ka ɗai nake ma sauƙin kaya Indo" "To shinkenan yanzu dai ki ajiye min su idan Malam ya dawo daga birni zan faɗa mai"."yauwa ko ke fa ƴar gari. Sallamar Nihal ce ta katse masu zancen su ko ta kanta basu bi ba, sai hirar gaban su da sukeyi, gaishe da Talai dillaliya tayi cikin ladabi kawar da kai tayi kamar bata ji ba, ganin haka yasa Nihal aje bokitin koko, ta Ciro kudin dake habar zanin ta tace, Gwaggo gashi , wartar kudin tayi ta irgasu tsaf sannan ta kalli Nihal tace, wallahi naso ace kuɗin nan kabo ta bace kiga yadda zan kusa kashe ki a gidan nan", Sun kuyar da kai Nihal tayi tana wasa da yan yatsun hannu ta sannan taja jiki zata shige daƙin su, tsawa Gwaggo ta daka mata tace, "baki gamamin aiki ba ai da har zaki Shiga ciki, kayan Sara nan na jiran ki idan kin gama ki Shiga ɗakin Mudi ki gyara inda yayi amai fes, sannan ki kwaso kayan shi masu dati ki wanke, idan kin gama ga alalan rana najiranki kuma duk Wannan aikin da zakiyi karki wuce karfe ɗaya da rabi 1:30 na rana Sara Gwaggo ta Shiga kwallawa kira fitowa tayi tana miƙa tace, "Gwaggo ina bacci duk kin bi kin dameni da kira dan Allah, kawai kin katsemin jin dadi ko kallon Talai bata ishe ta ba, bale kuma gaisuwa, murmushi gwogo tayi tace, "haba ƴar lele aini ban san bacci kike ba dama kayan wankin ki zaki ɗauko Wannan yarinyar ta wanke maki," tsaki taja sannan ta shige ɗaki ta dauko kayan ta watsawa Nihal a fuska tare da gyara tsayuwa tace, "kuma ki wanke min kaya da kyau kin ji na faɗa maki sannan ta shige daki abin ta ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```✍🏻 [1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo* *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest ```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&ref=opera_speed-dial&-tn_-H-R *Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page:* 3_4 Duƙawa Nihal tayi ta kwashe kayan wankin da Sara ta Watson mata, ta kai bakin rijiya, ta ɗau guga ta soma jawo ruwa a rijiyar, kasancewar lokacin na damuna ne hakan yasa garin yayi lulumin, gashi garin hadari ya haɗu sosai, Gwoggo ce ta buɗi baki tace, "Allah yasa kar ruwan nan ya sako ya hanani cinikin rana," dillaliya ta amshe zancan da cewa, "aiko dai kinyi asara ƙullin wake gashi shi wake baya kwana," kafin ta ida rufe bakin ta aka fara yaiyafi, "a'a" Tatare kaya dillaliya ta fara tace, "to ni dai na wuce", Gwoggo da haɗa ƴan kayan da ke waje, tare da juyowa ta kalli Nihal tace, "ban ce kuma in ruwa ya sako ki shige daki ba nama faɗa mi ki, dan sai kin gama aikin ki tsaf" sannan tayi shigewar ta cikin ɗaki, Haka aka fara tsuga ruwa kamar da bakin ƙwarya, babu yarda Nihal ta iya haka take wankin nan cikin ruwan, ga wani sanyi dake ratsa ta wasu hawaye ne suka sulalo mata masu zafi, ga kyarma da take hakuran ta na haɗiyewa, sallamar da'aka rangada ne ya sata waigowa, ba kowa bane sai Baffa, ko kallo bata ishe shi ba, sai ma Nihal dake gaisheshi, ta ƙaraso dan ta amshi kayan hannu shi, "Baffa sannu da zuwa" ta fada tare da miqa hannu zata amshi kayan, wata uwar tsawa ya daka mata, wadda tasa Gwoggo fitowa tana gyara tsayuwar zanin ta ita da Sara. "In ban da iskanci daga dawowa na zaki tasani gaba kina cikani da surutu mara anfani, wannan ai iskanci ne," Gwoggo dake bakin kofa tace, "haba malam kayi haƙuri ka barmin ita daga dawowar ka ta saka surutu da hayaniya, ai haka take ba hankali kamar uwar tata," ta idda zancan tana shu'umin murmushi, kallon banza ya aikawa Nihal sannan ya miƙawa Sara kayan hannu shi, Gwoggo kuma ta janyo Nihal ta fara kila "dan uban ki daga dawowar miji na zaki tare shi da bakin hali dama haka bokan naku yace kuyi kenan,? shine aikin dana saki ne,? kuka Nihal take tana cewa, "wallahi gwoggo kayan hannun Baffa kawai naje amsa ba wani abu ba," uban ki ne da zaki amshi kayan shi" sai da ta mata lilis sannan ta hankaɗanta kan ta ya daki bokitin wanki, ƙarfin kukan Nihal ne ya tsananta saboda zafin da ya ziyarci ƙeyar ta kafin kace mi jini ya fara zarya, gwoggo kuma ta shigewar ta cikin, duk irin azabar da Nihal ke sha cikin gidan duk a kunnan Umma, babu abinda Umma ke anbata sai sunayan Allah, ga wata irin yunwa da ke dawainiya da ita gashi fitsarin jiya da kashin yau duk sun hade mata guri guda. Jan jiki Nihal tayi ta miƙe duk da jirin dake ɗibarta, baƙar ledar dake gefen ta ta kalla wadda ta debowa umma danwake gashi har ruwa ya cima ledar, kauda kai tayi ta cigaba da wankin, haka ta gama wankin tana diga, ta dauraye su ta shanya, sannan zubar da ruwan wanki ta debo wani ta aje, Ɗakin Mudi ta Shiga in banda tashi kayan barasa ba abinda ɗakin keyi, sai tabar wiwi da ke yawo da kalbar giya a dakin, haka ta Shiga ta fara gyara dakin ga wata dauɗa dake cike a ɗakin haka ta share dakin tas, ta kwashe aman da yayi na barasa dakin ya fita fes, ta tattaro kayan shi ta wanke su tas har amai sai da tayi saboda tsabar warin giya da kayan maye. Bayan ta kamala ne ta shige ɗakin su har lokacin ruwa bai tsaya ba, ɗakin ta Shiga gyarawa ta janye Umma ta cire mata kaya ta fidda su waje, da ƙyar ta iya jan Umma ta kaita waje ta wanke ta tas, da dan ragowar sabulun wankin, sannan ta age ta gefen rumfa ta shige dakin ta wanke duk inda umma ta bata, sannan ta dauko mata wasu kayan ta sa mata, in ban ido babu abinda Umma ke bin ta da shi gata yarinya ƙarama sai aikin manya, wasu hawaye ne suka zubo ma Umma, girgiza mata kai Nihal tayi sannan tasa hannu ta share mata hawayan ta, da ƙyar ta iya janta ta mai data ɗaki ta jinginar da ita, sannan ta ɗauko danwaken Allah yaso ruwa bai Shiga ledar ba, ta bude ta fara bata a hankali tana amsa itama tana ci sai da suka koshi sannan ta bata ruwa itama ta sha da fita ledar waje. Dawowa tayi ta wanke kayan umma, da ta fido su duk irin qazantar dake jikin su haka ta wanke su tas ta shanya tana gamawa wani irin zazzabi ne ya lullube ta da kyar ta iya komawa ɗaki ta canza wasu kayan ta shanya jiqaqun, sannan ta zo ta kwanta kusa da Umma tana rawar ɗari, Anyi ruwa sosai kamar da bakin ƙwarya dan ruwa bai tsagaita ba sai gab da magriba, garin yayi lum sai kukan kwaɗi dana tsintsaye ke tashi. Kiran sallah magriba ne ya fidda ta daga ɗakin su tana kallon Baffa ya gama alwalar shi ya wuce masallaci, sannan itama ta duƙa tayi alwala ta shige ɗaki, yau dai kusan ruwa ya hana ta zuwa tallan rana dana dare dadi fal a cikin zuciyar Nihal. Ɓangaran Gwoggo ji take kamar ta tsayar da ruwan, tsarabar da Baffa ya kawo ko har dillaliya ta dabar mawa, amma ko su Nihal bata warewawa ba, dan bata ƙiba a wayi gari sun mutu ba, da sai tafi kowa murna da jin hakan. ```Taku har kullu salma mas'ud nadabo```✍🏻[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=operaspeed trial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwritersforum@gmail.com *Facebook*:www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 5_6* Tun kafin asuba yau Nihal ta tashi, babu abin da ta soma yi face tsaftace muhallinsu sannan ta fito da Umma tayi mata wanka, ta shirya ta sannan ta jinginar da ita jikin bango, sai da ta kammala komai sannan aka fara kiraye kirayan sallah asubahi a lokacin ne al'fijir ya soma ketowa, wani irin dadi ya lulluɓe ta yau zata tafi talla ba tare da fargabar ta bar Umma cikin wani hali ba. Fitowa tayi daga ɗakin dan daura alwala, da Baffa ta ci karo shima yana alwalar, gaisheshi kawai tayi ta cigaba da tsayuwa har ya gama alwala, banza yayi da ita kamar be ji ba har ya idar ya fita, yana fita ta janyo ruwa a rijiya tasa abuta tayi alwala. Bayan ta gabatar da sallah tana zaune tana lazimi, duk wannan abinda takeyi Umma na jingi ne tana bin ta da idanuwa, murmushi Nihal ta zaki tace, "Umma na ina kwana," A hankali umma ta budi baki tace, "lafiya lau," matsowa tayi kusa da Umma tare da ɗora kanta saman kafaɗar Umma tace, "Rabin rai na kullun sai nayi mafarkin Abba na, yana cewa na kula mashi dake a duk halin da muke ciki," ta idar da zancan cikin sanyi murya, jin ɗigowar ruwa a fuskar tane ya sata ɗagowa, girgiza kai Nihal tayi tace, "Umma na bana so a duk lokacin da nake baki labarin Abba na ki rinƙa kuka" hannu ta kai a hankali ta share ma Umma hawayan ta ta cigaba da cewa a duk lokacin da nake baki labarin Abba na, so nake ki kasance cikin farin ciki, babu abinda Abba ke buƙata a wujen face addu'a, kuma hakan shi zai sa yayi al'fahari damu kin ji Umma na," Allah sarki Umma ji take dama hannuwata na motsawa da ba abinda zai hanata rungume ɗiyar tata, buɗe baki tayi tace, "Allah yasa maki Albarka Nihal,". "amin umma na," "ko bayan ba rai na ina so ki kasance mai aika ta aiyukan ki na alheri karki canza daga halin dana sanki dashi ƴata," Kwalla mata kiran da Gwoggo keyi ne ya katse masu farin ciki, rausaya kai Nihal tayi cike da shagwaba da nuna gajiyawar ta da irin kewar mahaifiyar ta da zatayi, ɗaga labulan ɗakin da akayi ne ya sanya ta miƙewa da sauri, Gwoggo ce ta aika mata kallan banza tace, "yau ga ƴar jakar uba, ina ta ƙwalla maki kira kinyi zaman ki ko kin manta yau littinin Sara na da makaranta, maza fito kiyi aikin da ke gaban ki, da sauri Nihal ta fito Gwoggo ta bita da ranƙwashi tare da aika wa Umma kallon ƙyanƙyami. Ko da Nihal ta fita itacuwan duk jike suke da kyar ta samu ta hura wuta ta daura ruwa, bayan ƴan daƙiƙu ruwan ya tafasa ta juye a bokitin wanka ta hadawa Sara ruwa ta kai mata har toilet, sannan ta dawo ta tsaya bakin ƙofar ɗakin Gwoggo tace, "Gwoggo na haɗa ruwan wankan," banza akayi da ita kamar basu ji ba gajiya tayi da tsayuwar ta koma bakin murhu ta daura ruwan koko, can sai ga sara ta fito tana miƙa ta yi shige warta cikin kewaye. Bayan ta sheƙa kokon ta juye shi a bokitin, ta dauka, kusan a tare suka fita da sara ita ta wuce makarantar boko ita kuma ta wuce talla. Tafiya take a hankali cikin nutsuwa, jin kamar ana binta a baya yasata ɗaga ƙafa, shima Wanda ke bintan ɗaga ƙafa ya sake yi a karo na biyu, shan gaban ta da akayi ne ya sata razana saura kadan bokitin kokon ta ya kife, wata uwar ajiyar zuciya Nihal ta saki tace, "yaya," "na'am matsoraciya" dan murmushi Nihal ta saki tace, "Allah na ji tsoro," murmushi ya ɗan saki daga bisani yace, "nayi laifi a min haƙuri," murmushi kawai Nihal tayi, kanwata, "ina jummala na ganki ke ka dai yau,? "Ai jummala na makarantar boko dama asabar da lahadi ne kawai take zuwa talla da safe," "ke kuma me yasa baki zuwa,? rausaya kai Nihal tayi idanuwan ta suka kawo ruwa ta kauda kai, "Eyya sis am sorry na bata maki rai ko,? girgiza kai Nihal tayi alamar a'a, "yanzu kin san mi za'ayi bari na sauke maki bokitin nan sai ki fada min kudin bokitin na baki kiyi sadaka da kokon sai ki koma gida," zaro idanuwa waje Nihal tayi tace, "na koma gida yanzu ai Gwoggo ka sheni za tayi," "to matsoraciya, muje to sai ki ta yani hira "to" kawai tace mai. A hankali suke takawa suna tafiya yaya na jan ta da hira sama sama, sai da su kayi tafiya mai ɗan tsayi sannan suka isa wata ƙatuwa gona wadda ta sha shuke shuke da ababan ban sha'awa shin kan shi gurin abin kallo ne, kukan tsun-tsaye ne ke tashi gashi komai na gurin green sai ratsin flowers pink and white sai ruwan dake gudana a gefe samu kyau da haske, gonar kuma na zagaye da ƙarafuna kana hango wani dan qararamin gida wanda yasha ginin sarauta gefe ga mota mai tsada fake a gurin, sakin baki Nihal tayi tana mamaki dama Ashe akwai irin wannan gurin a kauyan shanono, ganin yaya, ya amshi bokitin hannun ta ne, ya sata dawowa daga duniyar mamaki, gaban wani babban mutum yaje Wanda, da alama shike gadin gurin ya miƙa mashi bokitin yana masa magana fararan haƙoran sha na baiyana, sai a lokaci Nihal ta ƙarewa yaya kallo sanye yake da jeans n t-shirt, riga mai gajeran hannu blue light sai Jean's dark blue ga sumar kanshi ta kwanta sosai tasha gyara, ganin yana tahowa ne ya sata sunkuyar da kai tana wasa da ƴan yatsun Hannun ta, "ƙanwata na barki tsaye ko? murmushi kawai Nihal tayi, dan taku biyu zuwa uku su kayi suka ƙarasa bakin ƙoramar dake gudana a wurin zama yayi sannan Nihal itama ta zauna. Kallon shi Nihal tayi tace, "yaya na tanbaye ka,? "Eh mana" ya faɗi hakan yana smile kasancewa yaya mutum ne mai fara'a, "yaya wai dan Allah nan wurin wake da shi?. "ni da nake garin shanono ban taɓa zuwa wurin nan ba," yadda Nihal take maganar ne ya bashi dariya, ɗan darawa yayi, yace, "Nima nan gurin oga nane kuma aboki na shine nace mai zan zo kauye shine ya baki keys din gurin na sauka," langwabe kai Nihal tayi tace, "shima yana da kirki kamar kai,? "sosai ma, yama fini kirki duk wasu hallaye masu kyau gurin shi nake koya," "kai yaya, ni dai nasan a duniya nan babu Wanda ya kai ka kirki" dariya yaya, yayi yace, "idan na fara faɗa maki kirki irin na aboki na sai mu kwana mu tashi Bamu gama ba," ko yaya? "eh mana" "to ya sunan shi,? kallon ta Yaya, yayi yace, "suna shi bawan Allah" Dan bata fuska Nihal tayi tace, me yasa yaya baka son faɗa mana sunayan yan birni, da mun tanbaye ka, ni da jummala sai ka ce bawan Allah," lokaci nan zaki sani kin ji ƙanwata" rausaya kai kawai Nihal tayi sosai suke hira da yaya dan zaman da sukayi yaya ya gano Nihal na da son fira da raha, amma sai dai da akwai abinda ya lura yana damun ta, bangaran Nihal ko ji take ta samu wani ɗan uwa, dan har wani gurbi na ɗan uwa yaya, ya samu azuciyar Nihal, sallama baba mai gadi ne ya katse masu tunani miƙawa Nihal ɗin bokitin yayi tare da yi ma yaya godiya, amsar bokitin Nihal tayi, tare da miƙewa yaya ne yace, "lokacin tafiya gidan har yayi? daga mashi kai kawai tayi kusan a tare suka taho suna tafe suna kara wata hira idan Nihal tayi wani ƙauyancin sai ya kece da dariya har sai da suka karyo kwanar gidan su, sannan ya ciro kudin ta ya bata har da ƙari akai, zare kudin ta Nihal tayi ta miƙa masa ƙarin da ya bata harara wasa ya mata yace, "ki aje shi ko ba yau ba wata rana zai maki anfani," "to" kawai tace ta shige gida da sauri. Cike da sallama a bakin ta, ta shigo gidan, Baffa da Gwoggo na zaune saman tabarma ba Wanda ya amsa mata sallamar ta, duƙawa tayi tana gaishe su ba Wanda yace ƙala sai ma Gwoggo ce data miƙa mata hannu alamar ta bata kuɗin ta, ciro kuɗin tayi cas ta bata, sannan gwoggo tace, "ki hura wuta ki daura ruwan shinkafa da wake ga wake na jiran ki, ki tsince shi tsaf idan kin gama ki tsince shinkafa, ga kuma yaji na jiran ki, ki daka "to Gwoggo" Madafi ta shige ta fara hura wuta ga wani irin hayaki da ke tashi, saboda ɗanyan icce ne gabaki daya madafar ta gauraye da hayaki, da sauri Nihal ta fito tana tari Gwoggo dake zaune ce ta hankada ta tace, "ko zaki mutu sai kin hura min wuta nama faɗa maki," malam dake gefe yace, "dolen ta ma ai" Da ƙyar ta hura wutar ta tashi, ta daura tukunyar tare da zuba ruwan da ta ɗebo, ta fito da wake ta fara tsincewa bayan ta kammala ta fara tsintar shinkafa lokaci ɗaya ta gama tsince shinkafar yayi dai-dai da tafasar ruwan, wanke waken tayi ta zuba a tukunya ta fara dakar yaji cikin yan awani ta kamala abincin ko da ta gama lokacin su Gwoggo sun bar tsakar gida, zuzzuba abinci tayi a roba, roba daya ta ɗauko ta juye a leda tayi sauri ta kai dakin su tana fitowa tayi kicibis da Gwoggo gaban tane ya yanke ya fadi, ta kowa ta fara yi a hankali ta duƙa zata dau tray talla, saukar mari taji wanda ya hardasa mata zaman yan bori, cikin masifa Gwoggo tace, "idan har baza ki fasa shiga ɗakin Hansatu ba lokaci dana saki aiki ba, ni kuma bazan fasa cin uwar ki ba na rantse," sallamar da akayi ne ya katse mata zance wangale baki tayi tana sakin murmushi, "oyoyoyo yan bokoko an dawo," Sara dake wani zunbure zunbure tace, "Gwoggo wani kuma dabbanci tayi maki hala," "ke dai bari ai indai wannan ce kullun cikin yin halin tumakai take, ki shiga kiyi wanka ki shirya abincin ki na jiran ki, kin ji "to Gwoggo" sannan Gwoggo ta bita a baya har ta kai bakin kofa ta juyo tace, "karkiyi ƙoƙari ki tashi ki tafi idan na zo na same ki nan na lahira sai ya fiki jin dadi Allah sannan ta shige ciki. Wani irin kuka ne ya kubuce wa Nihal kuka take sosai kamar ranta zai fita haka ta dau tray ɗin talla tana tafiya tana kuka, ga zafin rana da haska fuskar ta, ta kunbura saboda marin da tasha, a haka take tafiya ga wata uwar yunwa dake dawainiya da ita haka ta ƙarasa tasha. Kasancewar rana ce yasa duk samarin tashar nan dan haka anata siyan shinkafar da wakyan, kafin ka ce mi har ta gama ciniki, sai duk babu dadi zaman ba jummala ba yaya. Ɗauke da sallama a bakin ta, ta shigo gida Mudi ne zaune saman kujera tayani gulma yana zuƙar wiwi ko inda yake Nihal bata kalla ba sai ɗakin Gwoggo ta nufa cikin sanyin murya tace, "Gwoggo na dawo," shuru tayi kamar bata ji ba, can sai gata ta fito ɗauke da tray gyara tace, "idan rana tayi sanyi ki kai wannan wajan danbe" "To Gwoggo" sannan ta miƙa mata cinikin rana. Aje tray ɗin tayi tsakar gida ta ɗauko buta, ta fara dibar ruwa a rijiya ta juye abuta sannan ta shige kewaye dan kama ruwa, har ta shige Mudi na binta da kallo da jajayan idanuwan shi. Bayan ta fito alwala ta ɗaura ta shige ɗakin su, Allah sarki Umma tunda ta jinginar da ita da asuba har yanzu a haka take, tausayin Umma ne ya lullube ta kwantar da Umma tayi, Allah yasa yau batayi fitsari ba bale kashi, gabatar da sallah tayi bayan ta idar ta fita waje ta debo ruwa a kofi ta dawo dakin, jinginar da Umma tayi ta janyo ledar shinkafa da wakyan data ɓoye masu a hankali ta fara ba Umma tana ci itama tana ci har suka cinye ruwa ta ba Umma sannan itama tasha, labari ta shiga ba Umma masu sanya nishaɗi tana bata labarin Umma na murmushi ganin yamma yayi ne yasa ta miƙe ta fito dan zuwa talla yamma. ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ``` ✍🏻 [1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=operaspeedsdial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwritersforum@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 7_8* Tafiya take a hankali ɗauke da farantin ta na talla, ƙwalla mata kiran da akeyi ne ya sata waigowa tana sakin murmushi, jummala ce ta qaraso kallan ta Nihal tayi tace, "jummala ina tray din talla ki? fadada murmushin ta Jummala tayi tace, "ai yanzu Inna ta daina ɗaura min talla tun ranan dana dawo kawu Sani ya zo gida ya rinƙa yima inna faɗa yace idan kuɗi take buƙata duk wata zai rinƙa turo mata idan sana'ar take sha'awa to tayi a gida ba sai na fita ba," rausaya kai Nihal tayi tace, "gaskiya na taya ki murna Jummala rayuwar talla bata da daɗi," ta idda zancan idanuwan ta sun ciko da kwalla, "insha Allah Nihal zan taya ki da addu'a in Allah ya yarda sai kin daina talla sai kin samu ƴancin ki kamar kowa ce ƴar gata" hawayan dake maƙale a idanuwan tane suka sulalo Jummala tasa hannu ta goge mata, "Bari nayi sauri na wuce," "to shikenan Nihal ki kula da kanki kin ji," "to Jummala nagode" ta faɗa da ƙarfi lokaci da tayi ma Jummala nisa da ƴar tazara. Dandazon maza ne birjik majiya ƙarfi, in ban da warin taba dana wiwi babu abinda ke tashi gurin danbe, sai kururuwa da kirari da akewa ƴan danben haka Nihal ta raba wajan ƴan uwan ta ƴan talla ta zauna tana kallon yadda majiya ƙarfi ke danbe. Wani rusheshan ƙato ne ma'abocin ƙarfi ya zauna gefen Nihal bisa tebiri, tare da janyo tire din gyadar Nihal yana dauki ɗai ɗaya yana ci yana kallon danbe, haka ta rinƙa ciniki kasancewar akwai mutane da yawa a wajan, wannan rusheshan ƙaton dake zaune kusa da Nihal sai da yaci gyadar saba'in zaman sa. Gab da magrib Nihal ta gama cinikin ta tsaf, cikin sanyin murya tace, "malam nagama cinikin kai nake jiyara ka bani sauran kuɗin," wata irin dariya ya saki yace, "wani kuɗin gyada kuma,? "wadda ka ci yanzu ta naira saba'in," dariya ya kuma saki tare da zunguro bangis dake kusa da shi, shima wani murɗaɗɗan ƙato ne guda yace, "Bangis wai naci mata gyaɗa sai na bada kuɗi," bushewa da dariya Bangis yayi yana kallon Nihal da jajayen idanuwan shi yace, "yo ke ko cinki yayi kina tunanin biya zaiyi balle gyaɗa" ya ƙara sakin dariya abokin banza yace, "faɗa mata dai, ni wannan tama min kaɗan ban iya cin ta sai dai na ci uwar tata mai ɗaura mata tallar," dariya Bangis ya saki tare da miƙawa abokin banza hannu suka kashe, kuka Nihal ta fara tare da rokwan su Allah annabi su bata kuɗin ta daga ƙarshema wuka abokin banza ya curo yace, idan ta ƙara damun shi sai ya farka mata ciki. Haka Nihal ta biyo hanya tana kuka maicin rai duk gurin da ta samu sai ta zauna tayi kuka san ran ta, Allah sarki rayuwar, yau Nihal ta zama abin tausayi, yau ita ke ganin Sauyin Rayuwa, har kusan bayan magriba tana yawo ta kasa komawa gida, ta fuskanci horo wajen Gwoggo wani dutsi ta gani dake bakin hanya ta zauna tare da ɗaura kanta zaman ƙatatunta tana kuka saboda tsabar kuka muryar ta ta dashe. Dafatan da akayi ya sata razana ta miƙe da sauri tana ƙoƙarin arcewa, jin an riƙe mata hannu ya sata tsayawa tana sauke ajiyar zuciya, cikin sanyi murya tace, yaya tare da sakin marayan kuka tace, "yaya" faɗawa jikin shi tayi tare da sakin kuka, lallashin ta Yaya ya shiga yi cikin shissheƙar kuka ta labar ta masa abinda ya faru, ta cigaba da cewa "wallahi yaya na koma gida ba kuɗinn Gwoggo kashe ni zatayi" "shhhh ya isa daina kukan haka kinji" zaunar da ita yayi saman dutsin yana facing nata sai sauke ajiyar zuciya take muryar ta duk ta dishe, "nawane kuɗin,? naira saba'in ta faɗa da shaƙaƙiyar muryar ta, "Ƙanwata bana so kina kuka kin ji, kwata kwata baki dace da talla ba, insha Allah sai kin zama wani Abu aduniya wadda kowa zaiyi al'fahari dake kanwata, daga yau idan an baki talla ki rinƙa zuwa kina samuna a wurin nan," murmushi Nihal ta saki mai nuni da farin cikin ta. Naira dari ya curo ya miƙa mata sannan ya riƙe hannun ta ya rakota har ƙofar gida sannan ya juya yana tausayawa irin rayuwar da Nihal keyi. Ɗauke da sallama a bakin ta tashigo, kusan duka ƴan gidan suna tsakar gida suna hira cikin nishaɗi kallo ɗaya zaka masu kasan basu da wata matsala, gaban Gwoggo Nihal ta ƙaraso tare da duƙawa zata bata kuɗin Mudi dake kusa da Gwoggo yace, "Gwoggo ya maganar kuɗin da kika ce zaki bani," murmushi Gwoggo ta saki tace, "dama waƴannan kuɗin kai nayi niyar bawa su, tunda kana kusa sai ka amshi abinka, jin haka yasa Nihal miƙawa Mudi kuɗin hannu ya kai tare matse hannuwan ta yana mata wani shu'umin kallo rawar jikin Nihal ya ɗauka ganin irin yadda yake matsa mata hannuwan ta cikin wani irin salo kuma yaki sakin su wani irin ƙarfi ne ya zo mata ta fizge hannunta ta tashi, da Sauri tayi ɗakin su, tana shiga ta zame bakin ƙofa tare da sakin marayan kuka marar sauti. *_TUNA BAYA_* Malam mamman haifaffen ɗan wani kauye ne da ke cikin ƙauyen Shanono yana zaune da matan sa biyu Larai da Lantana, malamin Al'majirai ne sannan yana noma sosai kasancewar sa bafulatani haɗe da kiwon dabobi. Lantana itace uwar gida tana ɗa ɗaya mai suna Tanimu wanda shine ɗan fari a gidan malam , tunda Lantana ta haifi Tanimu bata sake haihuwa ba har tanimu yayi wayo sosai kasancewar, malam mutum ne ma'abocin son yara sai ya ƙaro aure ba irin kishin da Lantana bata zubaba haka Larai ta zauna zaman haƙuri har Allah yasa ta samu ciki malam yayi murna sosai da jin labarin Larai tana ɗauke da juna biyu. Bangaren Lantana ko ji take kamar ta hadiyo zuciya ta mutu, A kwana a tashi ba wuya wajen Allah har cikin Larai ya isa haihuwa. Ta haifi santalelan ɗan ta ranar suna yaci Abubakar ana kiranshi da Habu Duk irin rigingimun da Lantana ke nema wajen Larai ta ƙi bata fuska sai ma Ladabi da biyaya da take mata hakan yasa ta zubar da makaman yaƙin ta suka zauna lafiya, haka Larai ke kula da Habu da Tanimu duk da Tanimu ɗan kishiya ne amma haka take kula da shi tare da ɗan ta ba tare da nuna ban banci ba, hakan nayi ma mahaifiyar Tanimu daɗi sosai sai dai tun tasowar Tanimu yaro ne Marar jin magana da San abin duniya. Bayan wasu ƴan watanni Larai da Lantana suka fara laulayi, murna wajen malam ba'a cewa komai saboda tsabar farin ciki. Kulawa sosai suke samu wajen mijin nasu inda suke ƙoƙari wajen haɗa kan ƴa-ƴan nasu Tanimu da Habu Yau ta kama asabar ranan ne su Larai suka tashi da naƙuda... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```✍🏻[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest ```) https://mobile.Facebook.com/Real hausa-fulani-Writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 9_10* Ko da unguwar zoma ta shigo cikin gidan ɗakin Lantana ta fara shiga saboda ta riga Larai soma naƙuda tasha matuƙar wahala sosai, daga ita har abunda yake cikin ta basu rayu ba, Lantana ta rigamu zuwa gidan gaskiya ko da Labari ya riski Malam yayi kuka sosai, Allah sarki Ashe haihuwa ce ajalin Lantana haka ya rinƙa sunbatu ga fargabar itama larai kar ya rasata. Tun kafin unguwar zoma ta isa ɗakin larai, larai ta haifi ƴan biyu maza masha Allah daga nan murna da rashi suka haɗe wa malam, wunin ranar zungur ba Wanda ya iya labarta wa Larai mutuwar Lantana, da tace zata je ganin abunda lantana ta Haifa sai ace mata ta bari ta huta tukun. Bayan an kai Lantana ma kwancin tane malam ya dawo gida, ya shigo ɗakin larai Duk ƴan zaman barka suka fita, zama yayi a saman gado tare da fuskantar ƴaƴan nasa ya amshe su yayi masu huɗuba sannan ya kalli Larai tare da gyara murya yace, "kin san duk mai rai mamaci ne Larai kuma Allah daya fimu so ne yake amsar bayin shi," shuru Larai tayi Duk jikin ta yayi sanyi, sannan malam yace, "Allah yayima Lantana rasuwa daga ita har abinda ta haifa." Kuka larai ta saki tana sanbatu "Allah sarki Allah ya jiƙanki yaya, Allah yasa mutuwa hutuce a gare ki" daƙyar malam ya lallashe ta, tayi shuru haka dai akayi zaman barkar uwar jego ba wani Kuzari. Ranar suna yara suka ci suna Hassan da Hussaini. Tun da Lantana ta bar duniya Larai ke kula da Tanimu da ƴa-ƴa ta bata gwada masu ban-banci komai tare take masu da ƴa'ƴan ta, sai dai Tanimu yasa ma ranshi baƙin hali Don gani ma yake kamar baƙin cikin Larai ne ya kashe masa mahaifiya, shiyasa kullum a ƙullace yake da ita, gashi bugu da ƙari Habu ya fishi komai tun daga ladabi da biyaya da iya zama da mutane, shiyasa malam yake nuna mai so ba Wai Dan baya San Tanimu ba, sai dan ya gyara halaiyar shi, hakan sai ya dasawa tanimu hassada a zuciyar shi da baƙin ciki gami da kyashin ɗan uwansa Habu. Bayan wasu ƴan watan ni ma, inna ƙara samun wani cikin tayi tasha wahala sosai sannan ta haifi ƴa mace tun daga nan bata ƙara samun wani cikin ba, saboda wahalar data sha. *Bayan Shekara Goma (10)* "Yanzu saboda Allah Tanimu abinda kake kana kyautawa? Malam ya cigaba da cewa, "kai kaƙi boko saboda Wai baka iya zarya daga shanono zuwa ƙauyen nan, sannan ƴar nomar ma baka iyawa har sai Habu ya dawo sannan shi zaiyi ta kai kana can kana yawon banza wannan ba rayuwa bace tashi ka ban guri," malam ya faɗa cikin tsawa. Tanimu kansa dake duƙe gaban malam ne ya miƙe yana gunguni yana cewa, cikin gunguni, "tun da su uwar na da rai ai dole a fifita su akai na." Inna dake bakin rijiya ce tace, "mikake cewa,? Tanimu Wai kai me yasa baza kayi hankali ba kullun in malam nama faɗa sai kaita magana kasa ƙasa bayan nace maku yin hakan tamkar zagi ne kake ma iyayan ka" ko saurarata beyi ba yana huci ya fita. Inna tace, "Allah ya shirya min kai Tanimu, sannan yaji kan Yaya". Yana fita yaci karo da Habu ya dawo daga makaranta janye da kekyan shi, murmushi Habu ya saki yace, "Yaya" Ɗaure fuska tanimu yayi yana ji kamar ya kashe shi, "shi Wai mai tarbiya Ai wallahi wata rana shi da kanshi zai ga bayan shi" maganar da Habu yayi ne ya katse mai tunanin da cewa, "dama Yaya dazu ne muka haɗu da malam Barau, rediyon sa ta lalace shi ne nace ya bani na gwada, ko zan iya gyara mai tun da ana koya mana sana'oi a makaranta, aiko ina kwancewa na gyara ta gyaru, shine ya ban narai hamsin." Tanimu ne ya ƙara hade rai a karo na biyu tare da nuna hassada shi yace, "to sai akayi yaya Dan ya baka hamsin.? "Dama hamsin ɗin zan baka, ka ɗau talatin ka bani ashirin tunda kai Babba ne" washe baki Tanimu yayi yace, "kai amma nagode ina ma laifin ka bar min hamsin ɗin tunda na fika buƙatar kuɗi" Murmushi Habu yayi mai nuni da jin daɗi shi yace, "ka ɗauka yaya na baka" sannan ya shige gida bai tsaya saurara godiyar da Tanimu Ke mai ba. Ɗauke da sallama ya shigo a bakin shi malam da inna na zaune a tabarma har ƙasa ya duƙa ya gaishe su sannan ya shige ɗakin su, ya cire uniform ɗin shi ya fito ɗauke da kayan zuwa gona, murmushi malam yayi yace, "haba malam Habu daga dawowa ba hutawa bare cin abinci zaka tafi gona, dawo ka zauna ka huta zuwa yamma ka je," ba musu ya dawo ya zauna inna ta zubu mai tuwo da miya ya ci ya sha ruwa yana ƙoƙarin miƙewa ne su Hassan suka shigo da gudu gida, tare da ƴar ƙanwar su Haulatu da alama daga makarantar allo suke. Idi ne zaune da Tanimu saman tabirin mai shayi, Idi yace, "gaskiya Tanimu kayi ma kanka faɗa, na lura habu so yake ya ƙwace girman ka ya zama nashi, tun wuri ka tashi tsaye, in ba haka ba ka sha mamaki, nan gaba gonar malam sai ta zama tashi indai kana zuba ido, gashi har shanono yake zuwa makarantar ya hudawa" wani bakin ciki ne Tanimu ya hadiye yace, "in dai ina numfashi a duniya zaka ga yadda zan mai da Habu sai ya zama marar anfani daga shi har ƴan uwan nasa da yake taƙama da su". "ai ɗan kishiyar uwa ba ɗan uwa bane" inji Idi ya idar da zancan yana afa ƙuli a bakin shi. ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ```✍🏻 [1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest ```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 11_12* Yau ma kamar kullum Habu tunda safe ya tashi kasancewa yau ma yana da makaranta gashi dama sune manya a makaranta wato aji shida, kallon yaya Tanimu yayi dake ta sharar bacci har zanin da yake rufa da shi ya yaye janyo zanin yayi tare ficewa daga ɗakin ya rufo masa ƙofa. Kai tsaye ɗakin Inna ya wuce zaune ya tarar da ita da alamu tasbihi take, tsugunawa yayi har ƙasa ya gai sheta, amsawa tayi cike da fara'a, sannan ta janyo damammiyar fura dake ƙarƙashin gado ta miƙamai, kusan a tsatsaye ya karya sannan ya mata sallama ya ɗau kekyan shi sai shanono. Lamarin Tanimu ko Habu na fita, ya miƙe ya wuce Gona saboda tunda Idi ya bashi shawarar jiya ya daina wasa da zuwa gona da kiwo, dan shi bai ga dalilin da Habu zaiyi babakere a gonar mahaifin su ba. Ko da Habu ya isa makaranta aji ya wuce, be wani daɗe ba malamin su na lissafi ya shigo, ya fara darasi tunda ya fara darasi Habu ne ke bashi amsa, a gaskiya Habu ba ƙaramin mai hazaƙa bane, shiyasa ko malamin makarantar naji da shi ko wata gasa za'ayi a birni da habu ake zuwa, har ya lashe kambun gasa, hakan yasa kowa ganin girman shi yake, gashi bugu da ƙari ga fasaha gyara a bubuwan ƙarafuna. Akwana a tashi ba wuya wajan Allah, yau dai su Habu sun kammala karatun su na secondary, inda aka haɗa kwarya-kwarya walima haɗe malamai, inda Habu ya amshi kyaututtuka sosai a matsayin shi na dalibi mai hazaƙa, hatta Malam sai da ya samu tashi kyautar a matsayin shi na mahaifin Habu, haka suka baro shanono cike da ɗunbin farin ciki. Suna isowa gida Habu ya shiga nunawawa Inna kyaututtukan da ya samu, albarka ta cigaba da Samai da fatan samun cigaba. Sallamar Tanimu ce ta katse masu zance, cikin murna da sauri Habu ya tari tanimu yana nunamashi kyaututukan daya samu, wani ɗan abu ne ya janyo yana nunawa Tanimu Wanda yafi kowacce kyauta soyuwa a gareshi, gabaki ɗaya abun zagaye yake da kwalba yana sheki, ganin yadda Habu ke tattalin abun da ririta shi yasa Tanimu shu'umin murmushi, yana ayyana yadda zai watsa abun amsar abun yayi yace, "kai Habu amma dai wannan Abu da kyau yake," Murmushi Habu yayi yace, "shiyasa duk nafi sonshi, ba komai ke birgeni da shi ba sai wannan kwalbar da kyal kyalin da yake ciki, da yanayin yadda aka tsara rubutun dake cikin sa." Murmushi Tanimu yayi gami da kallon Habu da gefan ido, kawai ya saki hannu sa kamar cikin rashin sani glass din ya tarwatse, rausaya kai Tanimu yayi tare da saurin duƙawa yana kallon Habu da gefan ido yace, "wayyo Allah Habu nama ɓarna," Habu dake tsaye sai da yaji babu dadi duƙuwa yayi yana kallon glass ɗin, ganin yadda tanimu duk yabi ya ruɗe ne ya sasa tausayawa ɗan uwan nasa saboda wani abu dabam sai tadawa kanshi hankali yake sannan yace, "haba yaya sai wani tada hankalin ka kakeyi saboda ɗan wannan abun ya fashe karma ka damu kan ka, tsautsayine kuma yana faɗawa kan kowa." Ko inna? Inna da fitowar ta yanzu tace, " aiko dai, Tanimu ka zo ka zauna ka ci abincin ka, kabar tada hankalin ka, tun ɗazu ma nayi ma kwaɗan zogale nasan kana so" murmushi na gefan baki Tanimu yayi tare da ƙara taka glass ɗin ya wuce ɗakin Inna. Duƙawa Habu yayi yana kallon glass ɗin har ga Allah yana son abun amma ya zaiyi tunda ya tashi aiko Gaba ki daya, tsintsiya ya dauko ya share gurin tsaf, sannan ya kai sauran kyaututtukan ɗakin Inna. Tunda Habu ya gama makaranta ya koma gona yana aiki sosai, wata rana Tanimu shi yake bari da aikin. Kasancewar yana da sha'awar gyara gyaran kayan wuta sai ya zama na da ya dawo daga gona sai ya wuce gurin malam bala mai gyaran rediyo da keke, tunda habu ya fara zuwa ya fara aiki albarka ke sauka a wurin gashi komai nashi cikin zamani da boko yakeyi saboda yayi makaranta so duk wata waya yasan sunata shiyasa yake cin ribar aikin. Kafin kace mi sunan Habu ya fara canzawa, an fara Kiran shi da habu injiniya saboda ƙwarewar shi wajen iya gyara ridiyo da keke. ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo`[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the best```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email* realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 13_14* Kamar kullum yauma suna gona duk sun haɗa zufa sun gaji, bakin wata bishiyar mangworo suka yaɗa zango suna hutawa, Tanimu na gefe yana ɓallar rake, wasu ƴan matane su biyu kowace ɗauke da talla, suka nufo gurin kallo ɗaya zaka masu kasan basu da tsinki, musanman ƴar farar wadda da alama mai ta shafa tayi haske saboda kafar ta baƙin ƙirin take fuskar ta fara, bakin nan ya sha jan baki ana tafe ana taunar ciwing gum, sai da suka zo bakin bishirya sannan ido tayi wata tsayuwar ƴan talla tana fashe kwai tana cewa, "zaku sai gyaɗa" tana faɗa tana fari da ido tana karkarye karye, kau da kai Habu yayi saboda shi kwata kwata mata masu irin wannan dabi'ar ba burge shi sukeyi ba. Tanimu ko duk ruɗewa yayi yana bin ido da idanuwa, dan shi bai taɓa ganin macen da ta kwanta mai a rai ba kamar ido ba, murmushi Tanimu ya saki tare da cewa. "Ƴan mata da saukar da farantin gyaɗar kika yi sai muyi magana ko" fari tayi da idanuwan ta, tare da juya dan ƙugunta kamar marƙin lema ta duka, "yauwa ko ke fa nawa-nawa gyaɗar" yana faɗar zancan tare da kallon fuskar ta wadda taji hoda kamar an tono ta daga ƙasa, cikin kissa da kisisina tace, "naira biyar biyar," haka Tanimu ya zaro naira goma ya ba ido tare da jan ta surutu kasancewa ido irin yaran nan ƴan talla masu bin maza har suyi masu juye shiyasa ta saki jiki da Tanimu tana mai malƙwashe-malƙwashe, kuma dama tunda ta ganshin taji ya kwanta mata a rai. Basu rabu ba har sai ta kwatanta mashi gidan su sannan yayi mata alƙawarin idan dare yayi zai zo zance, shi ko Habu mamakin irin wawtar da yayan nashi yayi yake dan shi ko a cikin kayan miya yaga mai kama da ido tsame ta zaiyi ya zubar, ko da yake hausawa sun cewa shan koko ɗaukar rai. Tun daga wannan rana soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin Tanimu da ido dan kusan duk kauyan ba Wanda be san soyayyar da ido ke zubawa da Tanimu ba, magana har taje ga iyaye, ko da Inna ta ji labari taji daɗi sosai koma dai yayane Tanimu zaiyi hankali amma ta so ace ya samu wadda tafi ido natsuwa da tarbiya, amma yaran yanzu baka iya masu shiyasa taja bakin ta tayi shuru tana fatan Allah ya tabbatar da alheri. Habu ko babu abinda yake samu sai cigaba dan yanzu haka ya koma shanono da aikin kanikanci, duk wata mota ko mashin da zaizo daga birni talalace sai an kira habu injiniya sannan zata tashi cikin ikon Allah dan ya samu kuɗi sosai don yanzu haka yana da tumakai da yawa da ake mai kiwo da su a shanono, yanzu haka ya tare a shanono a ɗakin maigidan shi Balele, zaman lafiya suke sosai da Balele, gashi Balele mutumin kirki ne, sannan Allah ya ɗaura mai san Habu shiyasa Habu ke jin daɗin zama da balele. Malam ko da labarin soyayya Tanimu ta same shi, cikin Gona kin shi ya dau ki daya yaba Tanimu sannan ya haɗa shi da dabbobi yayi kiwo, dan ya fara cin gashin kan sa tunda yanzu Shi ba yaro bane, Tanimu ko yaji daɗi haka sosai ko ba komai ya mallaki wani Abu daga gonar mahaifin shi. *Bayan Watanni Uku (3)* Shirye shiryen bikin ido da Tanimu ake kowani ɓangare ka leƙa hidimma ake. Ɓangaran ido ko duk ta ruɗe saboda ta ɓarar da budurcin ta tun a wajan talla, shiyasa duk hankalin ta, a tashe yake. Kamar kullun yauma tana ɗaki ta zabga uban ta gumi tani ta shigo, tana ta doka sallama amma kamar bayi take ba har sai da ta taɓo indo tace, "ke lafiyar ki kuwa indo kin zabga uban ta gumi, ke ɗaya kamata a gani kina murna indo," taɓe baki indo tayi tace, "ke dai bari Tani kema kin san ta tsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi ke kan ki kinsan ba yau na fara bin maza wajan talla ba, gashi satin biki na ya matso, ban san da wace fuska zan kalli Tanimu ba, idan aka kaini gidan shi." Tani ce tayi shewa tace, "yanzu saboda ɗan wannan abun kike tada hankalin ki Indo, to bari ki ji yanzu haka cikin gare ni, kuma ko za'a ɗauramin wuƙa a wuya bana iya cewa ga uban dan ko yar saboda kullan cikin harka nake, ki kwantar da hankalin ki dama yanzu gidan mai tafasa zani ta kulo min maganin zubar da ciki, sai muje tare idan akwai magani gyarawa ai sai a gyara nasan baza a rasa ba, tunda tasan har kar" shewa suka ɗauka tare da kashewa ido ta dauko maliliɓin ta suka fice da Tani. Sun kuwa yi sa'a suna zuwa mai tafasa taba Indo kayan matsi wanda duk nacin mutum ba zai ya gano ta taba lalata ba, ita ko tani a nan aKa haɗa mata magungunan ta sha ko Minti goma ba tayi da shan maganin ba ta fare murqususu sai ga bari sannan suka curo mata kudin ta cas suka kamo hanyar gida cike da farin cikin. Balele ne ya shigo ɗakin su da alamar gajiya a tattare da shi Kallon Habu yayi yace, "ina zuwa kuma Habu,? murmushi Habu ya saki yace , "kamanta jiya na sanar da kai gobe ake ɗaurin auran yaya na Tanimu ," "Kai amma Allah yasanya alheri wallahi na manta naso ace naje bikin ko dan yadda kake ji da yaya Tanimun nan," faɗaɗa murmushi Habu yayi yace, "ba komai oga ai nasan dalilin daya hana" "toh shikenan ga dubu Biyar ka bashi gudumowa ta," "ah yallabai har da ɗawainiya ai ba komai duk yima kai," godiya habu yayi sosai sannan ya kama hanyar zuwa ƙauyen su. Ko da ya isa gida cike yake da ƴan biki duk sun hallara, da zuwansa bai ko huta ba yaya Tanimu ya shiga tanbaya Inna tace mai yana ɗakin dake kusa da waje nan zai gyara masu shida matar shi , kai tsaye ɗakin ya nufa, cikin daya ne sai dai babban ne sosai sannan gefen ɗakin akwai dan ƙaramin ɗaki wadda bai kai Girman wancan ba, ko da Habu yaga gyaran da akayiwa ɗakin bai mai ba dan haka ya ciro kuɗi masu yawan gaske ya ba masu gyara su gyara ɗakin ya fito sosai, Tanimu sai gadiya yake, duk da shi za'ayiwa aikin sai da yayi hassada da baƙin cikin yau habu ya fishi abun hannu, sannan ya bashi gudumuwar da ogan shi ya bashi, shima ya ƙara masa goma akai. Masha Allah ɗaki yayi kyau duk Wanda ya kalli ɗakin sai ya yaba da namijn ƙoƙarin da Habu yayi wajen kashe maƙudan kuɗaɗe. *Washe Gari* A yaune ɗunbin mutane suka sheda ɗaurin auren *Muhammad (Tanimu) Ja'far* *Da Aisha (Indo) Kabiru (Malan Bala)* sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya.. ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ```✍🏻🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-Writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page:15_16* *A gaskiya ina jin daɗin yadda kuke comment kan wannan labarin wannan shafi naku ne masoyya SAUYIN RAYUWA ina yin Ku irin sosai ɗin nan* ❤ An kai amarya ɗakin mijin ta lafiya, inda Tanimu ya zuba wa amaryar sa soyayya duk da gaban Indo yana faɗuwa saboda bata da tabbacin maganin mai tafasa yayi aiki, jin Tanimu bai mata magana ba, kuma bai mata Kallon banza ba yasa ta sauke ajiyar zuciya ta cigaba da zuba masa shagwaɓa. Kafin Habu ya koma shanono sai da ya tabbatar yasa su Hassan a makarantar boko tare da siya masu sabon keke, sannan ya tabbatar masu da cewa, idan suna da matsala su same shi a gareji inna tayi murna sosai da jin daɗin irin yadda Habu ke kula da ƴan uwan sa, sannan ya siyowa Haulatu kayan wasa kafin itama lokacin fara zuwa makarantar ta yayi, bai tafi ba sai da ya aje masu shatara na arziki, Malam sanya masa al'barka sosai, ba'a wani jima ba Habu ya koma shanono. Ko da ya koma shanono aikin tuƙuru yake yana samun buɗi don yanzu har mashin ya siya mai kyau na zamani, Bangaran amarya da ango ko sai zuba soyayya suke yayin da Tanimu ke tattalin Indo ita kuma tana ƙara narke masa, tunda akayi auren ya rage zuwa gona da kiwo, malam ko zuba masa idanuwa yayi har sai ya gama cin amarcin sa. Kwanci tashi asarar mai rai yau dai Indo tashi akayi da masassara ko tsakar gida ta kasa fitowa, shurun da Inna taji ne ya sata, leƙa ɗakin kwance ta hango Indo sai kyar ma take inna ce tace, "a'a Indo ba lafiya ne" ta ƙaraso ɗakin tare da taimakawa Indo har sai da Indo taji dama-dama sannan Inna ta fita, ta damomata fura ta kawo mata, kurba ɗaya zuwa biyu tayo aman ta saboda tashin zuciyar da take fama da ita, inna ce ta gyara gurin tsaf ta taimaka mata da ruwan wanka, ko ba'a fada mata ba ta gano Indo juna biyu gare ta, wani irin daɗi ne ya lulluɓe Inna dan haka ta zage tana tattalin Indo, ko da Tanimu ya dawo Inna ta bashi labari ya ji daɗi sosai yayin da ya cigaba da kulawa da Indo. Kamar kullun suna zaune a tsakar gida Indo na gefe tana Kallan su Hassan yana karatun boko sai taɓe baki take, sallamar Habu ce tasa yara miƙewa da sauri suka rungume shi hannu shi dauke da baƙaƙyen ledoji, Indo ce ta kwaɓe baki tana zancen zuciya, "hmm aikin banza kawai da yake shi yana da abin duniya tunda ya dawo ai dole su rinƙa rawar ƙafa a kanshi shi kuma Tanimu ko irin kishin nan beyi," Habu ne ya katse mata tunanin da cewa, "yaya ina wuni mun same ku lafiya," washe baki Indo tayi tace, "lafiya lau Habu" yar baƙar ledar dake hannu sa ya miƙa mata "gashi wannan naku ne" "a'a har da mu a tsarabar Habu aiko mun gode" "ba komai yaya" jin irin godiyar da Indo ke zubawa Habu ne yasa Inna fitowa tana washe baki, "Habu sannu da zuwa," "yauwa Inna" sannan yabi inna ɗaki shida yara aka bar Indo a tsakar gida dogon tsaki taja tare da shigewa ɗaki ta wurgar da tsarabar cikin ɗaki. Sai yamma likis Tanimu ya dawo daga gona yana shigowa yaga saban babur fake a kofar gida mamaki ne ya cika Tanimu ko Babur ɗin waye wannan ya faɗa yana ƙarasawa ciki, da Haulatu ya haɗu da ita tana tsalle-tsalle zata fita yace, "ke" tsayawa tayi tana raba idanuwa yace, "wake da wannan babur ɗin,? wangale baki Haulatu tayi tace, "na yaya Habu ne" take annurin Tanimu ya ɗauke bangaje Haulatu yayi saura kaɗan ta kife ya shige ɗakin su yana shiga Indo ta miƙe tare da riƙe ƙugu, kallon ta Tanimu yayi yana ƙoƙarin ajiye fatanyar dake hannun sa Indo ce ta jeho masa tanbaya dacewa, "anya Tanimu kai ɗan gidannan ne kuwa,? juyowa yayi a razane yana binta da kallo kawar da kai tayi ta cigaba da cewa, "na lura a gidan nan baka da wani gata, kai da karen gidan nan baku da maraba, Tanimu babu abinda ka iya sai dai kayi noma da kiwo kayi naka kayi na Malam, shi kuma ɗan gata ya je shanono ya samo kuɗi ya dawo a rinƙa rawar ƙafa a kan shi, yanzu haka yana nan cikin gida ana ririta shi ana tatalin shi sannan dan wani ƙarin wulaƙanci wata ƴar leda ya ɗauko ya miƙa min wai ga tsaraba, sauran ya shige da ita ciki tunda ga matsiya ciya matar faƙara'u ga ladan ganin Indo, to wallahi bazan ɗau irin wannan iskancin ba, da akeyi idan kai ana maka kana shanye wa to ni ba zan ɗauka ba," ta idda zancan tana haki, idanuwan Tanimu ne suka kada sukayi ja yace, Indo kenan baki san gabar da ke tsakanina da muta nan ba ni da kai na nayi alƙawarin sai naga bayan su, ki zuba ido kiyi kallo Indo kuma da kike cewa ni da karen gidan su bamu da maraba lokaci na zuwa da Habu zaiyi haushi kamar kare, naji daɗi sosai da kika gano gabar da ke tsakanina da ahalin gidan nan tunda mahaifiyata ta, ta bar duniya uwar Habu ta maida gurbin mahaifiya ta kina tunanin zan bar sune, bari nayi ya gama Tara mana arzikin sai na kawar da shi na share tarinhin sa a duniya Habu Jatau ya faɗa yana sheƙewa da dariyar mugun ta zaki ga yadda ake tarwatsa iyali Indo" ya idda zancan yana shafar tulelan cikin ta murmushi ta saki tace, "ai gara ka ƙwato mana ƴancin mu mai gida" "shiyasa nake sanki ido" *Bayan Shekaru Goma (10)* Abubuwa da yawa sun faru ciki ko har da auren da Habu yayi , auri kyakyawa kamila kuma haziƙar matar sa Hansatu sannan yayi ginin shi mai kyau, na gani na faɗa a shanono don duk shanono ba gidan bulo kamar na Habu, Hassan ma yanzu ya dawo shanono yana taya habu aiki saboda yanzu Habu ya buɗe garejin shi na kanshi. Kamar kullum yau ma ya dawo daga gareji, ɗauke da baƙar ledar shi da Hassan, wata ƴar yarinya ce da baza ta wuce Shekara biyu ba a duniya, tana sanye da English wear's Jean's and t-shirt rugowa tayi dagudu tana cewa, "oyoyo Abba," caɓe ta Habu yayi yana ɗagata sama yana cewa, "ƴar Abban ta, cikin tsamin murya tace, "kawu ina alƙawarin mu" "yana nan Nihal amma ki bari ina komawa gida na dawo," "yaushe zaka tafi kawu? " yau insha Allah" ya ida zancan yana ja mata hanci , "ka gaishe min da Inna" "to zata ji Nihal," Umma ce ta fito daga madafi tana murmushi tace, "daga dawowar Ku ta fara cika ku da surutu, ban san ranar da Nihal zata dai na surutu ba" murmushi Abba yayi tare da ɗaura Nihal a cinya yana cewa, "zata bari ne da zarar, ta girma" "Allah yasa to," Ɗauke da jakar shi Hassan ya fito Umma tace, "Hassan ina zuwa kuma,? "La Umman Nihal ba jiya na faɗa makin zani ƙauye ba," "eh na tuna bari na baka wasu kaya daza ka kai wa maman Saratu tare na siya masu da Nihal" "to shikenan" haka Umma ta jido kaya kusan kala Biyar ta baiwa Hassan ya kai ma Indo. Sannan ya ɗau hanyar ƙauye, lafiya lau ya isa gida ko da ya tanbayi Inna ina Husaini sai tace, mai yana Gona ɗakin Indo ya shiga ya miƙa mata kayan da Umma ta bashi sai murna take da washe baki da godiya, yana fitowa ɗakin su ya shige ya rage kayan jikin shi dan shiga wanka, yana fitowa suka haɗu da yaya Tanimu ya dawo daga gona, murmushi Tanimu ya saki yace, "Hassan har an dawo ganin gida kenan," "Eh wallahi yaya" "ai hakan na da kyau" "dama yaya Habu ya bani saƙo na baka bari na ɗauko ma," ayi haka kai da zaka shiga wanka," "ai yanzu zan ɗauko ma" ɗakin su ya koma ya irgo kuɗin da yaya Habu ya bashi yayi ya kawowa yaya Tanimu sannan ya ƙara mai da nasa a kai, godiya yaya Tanimu yayi ya shige ɗakin su. Hassan na shiga kewaye, wata irin ƙara akaji wadda gabaki ɗaya gidan sai daya amsa, baki ɗaya ƴan gidan fitowa sukayi Tanimu ne yayi ƙoƙarin buɗe ƙofar kewayan, kwance yaga Hassan ya kakafe kwayar idon shi tayi fari fat sallati Tanimu ya ɗauka tare da sabar Hassan sai ɗaki ya kwantar da shi kafin ka ce mi gida ya ruɗe hankali duk ya tashi, Tanimu yace, "bari nayi Sauri na kira malam ata ya duba shi ko lafiya da Sauri ya shige ɗakin su yana shiga ya bushe da dariya yace, "yanzu muka fara indai wannan wasan ne yanzu muka fara, saura Husaini ya ƙara kecewa da dariya daga shi sai Haulatu daga Haulatu sai Inna daga Inna sai ya ƙara kecewa da dariya, jin an taɓa shine ya sasa razana ganin Indo ce ya san ya shi murmushi dariya indo tayi tace, "aikin ka yana kyau mai gida" ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo``` ✍🏻🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 17_18* Labari na iske Husaini yana gona, ko ɗaukar keke bai tsayayi ba saboda tsabar ruɗewa, a rikice ya iso gida yana isowa ɗakin Inna ya shiga wanda ya cika da maƙota ture su ya shiga yi kamar sabon kamu, ya isa gaban Hassan dake shinfiɗe kamar gawa sai launin idanuwan sa da suka sauya, duƙawa yayi gaban shi yana cewa, "Hassan dan Allah ka tashi wannan wani irin ciwo ne Inna" yana faɗi hawaye na sulalo masa bayan numfashi da Hassan keyi baka taɓa ce mai rayayye ba, Malam Atta ne ya iso shi da Tanimu lokacin ne mutane suka fara fita sunayi ma inna Allah ya sauwake, magunguna Malam Atta ya shiga haɗawa tare da addu'oi ya shafawa Hassan sannan Husaini ya talaɓo shi aka bashi nasha wasu na shiga wasu na fita, haulatu ko ba abinda take sai kuka Gwoggo na bata haƙuri da Inna bayan malam Atta ya fito ne yaba inna addu'oin da zata rinƙa yima hassan, dan ya lura kamar gamo yayi a kewayan godiya Inna ta shiga jera mai ita da Tanimu kamar gaske, Allah sarki ba su san makashin su yana tare da su ba. Sallamar Habu da Hansatu ne ya katse masu zance Nihal na kwance a kafadar Umma da alama bacci take, har ƙasa suka duƙa suka gaishe da Inna amsawa tayi cikin kulawa Habu ne ya miƙe ya shige ɗakin da Hassan ke kwance, shi kanshi Habu abin ya firgita shi ya tausayawa halin da Hassan yake ciki tare da yin alƙawarin duk inda magani yake zai nemomai, Gwoggo ce tasa hannu ta ɗauki Nihal tace, "ƴan'mata ana ta bacci," "aiko dai bata daɗe da dawowa daga makarantar allo ba muka taho to iskar mashin na kaɗawa bacci ya ɗauke ta," inji Umma, "Allah sarki" Gwoggo tace tare da cigaba da zancan zuciya,"lallai dole iskar mashin ke kaɗa ta tunda ga ƴar gata sannu a hankali zaku shugo hannu," mutsu mutsun da Nihal keyi ne ya katse mata tunani murmushi ta saki tare da cewa, "bari na dako mata damamiyar fura da Malam ya sha ya rage ta sha" "alalai Gwoggo kina ji da Nihal" inji Inna mudi da shigowar shi yanzu yace, "ko dai ta cuceta ba," bige mai Baki Gwoggo tayi tace, "kai dai duk wani tunani namasu hankali baka ciki"taja tsaki ta wuce ƙurya. Ciwo hassan ko kullun ƙaruwa yake ba raguwa yake ba, komai sai amai gashi yayi wata irin rama da fari kamar ana ɗibar mai jini duk Wanda yaga halin da Hassan ke ciki sai ya tausaya mai, Malam ma duk wata addu'a da sauka ba wace ba'ayiwa Hassan ba amma kullun ciwo tsanani yake, haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasu na farin ciki wasu na baƙin ciki, idan Habu sai samun buɗi yake yana kula da iyalan shi da ƴan uwa haka kuma duk inda yaji wani magani sai ya nemo ya kawo wa Hassan a gwada, sannan duk ya kwashe yaran Tanimu daga saratu har mudi ya zubasu makaranta da Nihal dan sun isa a sasu, duk wani jin daɗi na rayuwa haka Habu ke ma yaran ya ɗauke su tamkar shi ya haife su ko ƴa ƴan me gari baza su gwada masu jin daɗi da Hutu ba saboda Habu na zuwa birni duk wani Abu na birni na birgewa zaka Ganshi a gidan habu ko a hannu ƴa ƴan shi dan gabaki ɗaya su Mudi sun tare gidan idan ka gan su a ƙauye to weekend ne ko kuma sun je ganin kawu Hassan. Yau dai ciwo Hassan ya ƙara rikicewa fiye Dana kullum sai dai abin mamakin bakin shi ya buɗe dan har ya fara magana babu abinda yake Sai sanbatu yana ihu da gurnani, Allah yaso duka mutanan gidan nan dan shima Habu ya zo ganin jikin nashi da iyalan shi, da gudu suka shige dakin suka rirriƙe shi kallan Tanimu yake wasu hawaye masu zafi na sulalo mai shi kan shi Tanimu sai da ya tsargu da kallan da Hassan ke mai, saboda kallo ne mai cike da ka cin amanar mu wani irin gurnani ya fara yi launin idanuwan shi na yunƙurin komawa yadda suke can kuma yayi shuru yana motsa baki a hankali, Husaini ne ya fashe da wani kuka dan ba zai iya jurewa ba, ko ka ɗan can jikin Hassan yayi sanyi ya dawo kamar be taba ciwo ba, innalillahi wa'inna'illaihi raju'un rai yayi halin sa dai muce Allah ya ji kan Hassan ya gafarta masa gabaki ɗaya gidan ruɗewa yayi da kuka ba mai lallashin wani, Habu ne ka ɗai yayi namijin ƙoƙarin fara lalashi Inna, har Tanimu sai da yayi kukan munafunci haka Gwoggo har da suma take Tanimu na kamota malam yayi kuka sosai saboda Hassan mutum ne mai kyawawan halaya kamar ɗan uwan shi Habu shiyasa kowa ya ji mutuwar shi, wanka aka mai aka suturtashi aka kai shi makwancin sa, bayan an dawo aka fara zaman makoki. ```Taku har kullu Salma mas'ud nadabo ``` ✍🏻🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 19-20* Ranar sadakar uku ƴan uwa da abokan arziƙi kowa ya watse aka bar ƴan gida, malam ya tarasu yayi masu nasiha mai shiga jiki shi kan sa Tanimu sai da jikin sa yayi sanyi, amma malam na sallamar su ya watsar da nasihar a tabarmar, haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasu na farin cikin wasu na baƙin cikin, bangaran karatun su Nihal Alhamdulilla suna mai da hankali, Mudi kuma yana aji biyar (5) Nihal da saratu suna aji ɗaya (1) hakan nayi ma Habu daɗi matuƙa yarda yaga yaran sun haɗa kansu. Yau kamar kullun sun taso daga makaranta Mudi yana janye da hannu su Nihal tace, "yaya Mudi dan Allah mu biya ta gareji muga Abba kaji" lakuce ma Nihal hanci Mudi yayi yace, "to uwar yawa mun dawo daga makaranta maimakwan mu wuce gida sai mu wuce gareji ko to bamu zuwa" Saratu ce ta fara dire-dire ita da Nihal a kan dole sai ya kai su ba yadda ya iya haka ya wuce da su garejin Abba, ko da suka je gyaran tifa yake shida yaran sa da gudu Nihal da Saratu suka faɗa jikin shi suna dariya, murmushi ya saki tare da cire safar hannu sa ya ɗau Sara yana cewa, "ƴan mata ya karatu ana maida hankali ko? daga mai kai Sara tayi, taɓa shin da Nihal tayi ne ya sanya shi ɗaukar su a tare yana yi masu wasa, sai da ya cika su da kayan zaƙi sannan ya ce su wuce gida. Wannan shekarar gonar malam tayi albarka fiye da na da can baya sosai Dan Husaini ya zage yana noma duk Wanda yaga tsaruwar Gona sai ya kira Husaini ya mai ya biya shi, Husaini mutum ne Wanda yayi masifar iya noma kamar a kanshi aka tsara yadda noma take shiyasa ko da suka gama makaranta shi ya tsaya a ƙauye, saboda yafi wayau a gona shi kuma Hassan ya bi Habu, Haulatu ko anzama ƴan mata sosai Dan sai mane man auran ta ke zuwa daga ƴa ƴan manyan ƙauyan har na talakawa dan cikin ƴa ƴan manyan har da ɗan maigarin shanono kuma a gaskiya duk cikin samarin ta hankalin ta yafi kwantawa da shi saboda natsatsene, yanzu haka yana karatun jami'ar shi a kano, tunda suka ƙulla soyayya da shi duk ta watsar da samarin ta ya zamana shine zakaran gwajin dafi, shima bangaran shi ba ƙaramin so yake ma Haulatu ba dan har Inna shi ya faɗawa kuma tayi mashi alƙawarin faɗawa mai gari, duk wannan abinda ke faruwa a kan idanuwan Tanimu akeyin su da Gwoggo Inda ya ƙara lasar takobin watsa iyalan dan shi har wa yau yana baƙin ciki da su tare da hassada gashi Allah ya bashi mata ingiza mai kantu ruwa shiyasa kullun abin ƙara tabarbarewa yake. Bayan ƴan kwana ki dangin Salisu suka zo ne man auran Haulatu ranar Haulatu ba ƙaramin farin ciki take ba domin ji take kamar tafi sauran mata idan ta sami Salisu a matsayin miji, bayan angama komai dangin Haulatu sun amince kuma sun bada Haulatu ga Salisu sai dai kawai a fara shirye shiryen biki, farin ciki wajan ƴan uwa ba acewa komai kamar ace Salisu yafi kowa farin ciki a wannan rana. Yau ma kamar kullun Husaini ya je kiwo tun a wurin kiwo ƙafar sa ta fara mai wani irin zugi ga wata kasala da yake ji, jin jikin sa yake kamar ba nashi ba musanman kafafun shi dake mai ciwo da kyar ya ƙaraso gida ko da ya ƙaraso ƙafafun sun fara kunbura, ɗaure dabbobin shi yayi sannan ya wuce ɗakin Inna zaune ya sameta suna ta lisafi da Gwoggo kasancewa bikin Haulatu nata matsowa, gaishe su yayi a taƙaice tare da cewa, "Inna" "na'am Husaini" langwaɓe kai yayi yace, "Inna duk yau na rasa gane kanƙafa ta sai zugi take min da radaɗi da kyar na iya yin kiwo yau saboda ciwon da take min" wani malalacin murmushi Gwoggo ta saki dan tasan shima tashi ta zo, Inna ce tace, " sannu Husaini bari na baka magani kasha" "to Inna" sannan Inna ta miƙe ta ɗauko mai magani ya shafa yasha sannan ya koma ɗakin sa saboda masassara dake sa ko mai. "Nihal" "Nihal" dagu ta fito ita da Sara daga ɗakin Umma, wani irin ihu suka saki ganin Abba ya siyo masu kayan wasa faɗawa jikin shi su kayi ya caɓe su yana masu wasa, sai dariya suke sannan ya mika masu kayan suka ruga da gudu ɗakin Umma sannan Abba ya kalli Mudi yace, "ga naka kai ma shima wani irin daɗi ne ya lullube shi kayan sawane na zamani Wanda sai ƴa ƴan mai gari ke sawa ya siya mashi fadawa jikin sa Mudi yayi yana cewa," "Abba na gode Allah ya ƙaro buɗi" "Amin Mudi, gobe kushirya tunda anyi hutun makaranta zaku je ƙauye hutu" "to Abba Allah ya kaimu" "amin " sannan Abba ya wuce ɗakin Umma yana murmushi. Ciwan ƙafa dai ya faskara dan kamar be sha magani ba dan saboda yau ko iya tashi Husaini beyi ƙafar ta kunbura suntum sai faman zugin da take mai, sai kuka Husaini yake, saboda a zabar da yake ji ba irin maganin da ba'a samai ba, sallama su Habu ce ta ƙatsewasu Inna zancan, galala yayi yana kallan Husaini da mamaki, ƙarasowa yayi ɗakin da Sauri yana cewa, "Husaini mi ya same ka? "innalillahi wa'innailaihi raju'un wannan wace irin musifa ce" Habu ya faɗa idanuwashi na kawo ruwa saboda kallo ɗaya zakayi ma kafar tsigar jikin ka ya tashi, yaya tanimu yace, "kai ma ka faɗa Habu Allah ya yaye mana" malam dake gefe yace, "tamu ƙaddarar haka ta zo sai dai mu karɓe ta hannu bibiyu," Habu ne yace, "bai kamata mu zuba idanuwa muna kallan Husaini ba akwai asibiti a shanono muje muga ko za'a dace" Umma tace, "gaskiya kayi magana haka ya kamata ayi" Haka aka ɗauki Husaini aka sashi a amalan ke Tanimu da habu na biye da shi a babur, Allah sarki Haulatu sai kuka take Dan gani take kamar zata rasashi shima yaya Husaini gashi bikin ta sai matsowa yake, Umma ce ta janyo ta jikin ta tana lallashin ta, Gwoggo ta haɗa kan yaran sai masu wasa take dan ita ko a haɓar zanin ta Dan hakan da Tanimu keyi ba ƙaramin birge ta yake ba a gaskiya bokan dake masu aiki ba ƙaramin boka bane ita kanta Indo tana mamakin aikin shi kamar yankan wuka. ```Taku hat kullun Salma Mas'ud Nadabo` [1/7, 2:23 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-Writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com *Page: 21_22* Suna isowa asibiti aka basu ɗaki kasancewar asibitin ƙauye ba wasu kayan aiki ke akwai ba gado aka bashi sai ƙarimn ruwa da aka ɗaura mai da allurar barci sannan doctor ya kira su office da sauri suka ƙarasa ya nuna masu wajan zama tare da gyara zama yace, "A gaskiya ina tunanin wannan ciwo bana nan asibitin bane saboda bamu da masaniyar kwaran daya cije shi kuma nan ba kayan aikin da dayawa kamar birni, sai dai ku je birni amma duk da haka zamu bashi magunguna da kulawa na kwana biyu idan har lokacin abin ya gagare mu zamu tura ku birni domin samamai lafiya" sannan ya gyara zaman glass din shi ya rubuta masu magunguna ya miƙawa Habu, kuɗin gado ya fara biya sannan ya wuce siyan magungunan ya bar yaya Tanimu yana kula da shi, ranar Habu yasha zarya sannan ya dawo asibiti ɗauke da ledojin magunguna dana fruit, da kulololin abinci ajewa yayi a gefe tare da shafa sumar husaini Wanda har yanzu bacci ga ƙarin ruwan da akayi mai idanuwa shi ne suka kawo ruwa da kyar ya samu ya saita kan shi ya zauna gefan gadon yana facing din yaya Tanimu Wanda tuni ya fara ƴan ciye-ciye, cikin sanyin murya Habu yace, "Allah yasa Husaini ya samu lafiya" "amin habu" "ina mamaki irin ciwo da sukeyi ka duba ka gani yaya haka fa shima Hassan rana ɗaya ya kamu da ciwo amma sai gashi yayi ajalin shi hankali na yana tashi yaya Tanimu, anya ba akwai sa hannu wani ba" Tanimu Wanda ya kai lomar shinkafa da wake tari ya shigayi da zazare ido saboda ƙwarewar da maganar Habu ta sasa da sauri Habu ya miƙa mai ruwa yana jera mai sannu sannan ya numfa sa yace, "Habu bai kamata kana irin wayan nan maganganun ba sai ka ce baka da ilimi, insha Allah zai samu sauƙi Husaini ya warware" daga kai Habu yayi tare da share ƴar ƙwallar data tarar mai a ido shi ko Tanimu ko wannan ƴar damuwar da Habu ya shiga daɗi ya ji, dan indai damuwa ce yanzu ya fara shiga. Kwanan su Habu biyu a asibiti amma kullun ciwo Husaini ƙaruwa yake Dan har kafar ta fara Neman riɓewa, hakan ne ya zaburar da Habu ya nemi kuɗi masu yawa dan akai Husaini birni magani, dan ko yau Husaini na kwance kamar gawa dan be cewa ƙala sai in ciwo ya mai tsanani ya fara sanbatu yana kuka har sai anmai allura, shata mota habu yayi wadda zata kai su har kano dan duk ya gama tsare tsaran tafiya gobe insha Allah zasu wuce dan nemawa Husaini lafiya. Kusan da yama likis ya dawo gida ya ɗaukar masu abinci ko da ya je asibiti su inna sun zo duba husaini, sai gab da magrib suka ɗau hanyar ƙauyen bayan sunyi sallah isha yayi ma Tanimu sallama saboda shi zai kwana da Husaini a asibiti ya wuce gida. Cikin sallama ya shigo gida yara duk sunyi bacci sai Umma ka dai zaune a ɗaki tana jiran dawowar shi, murmushi ta saki tare da cewa, "sannu da zuwa abban Nihal" "yauwa matata" tashi tayi tana yunƙuri da komai kayan abincin riƙo hannu ta yayi yace, "Ina zuwa" murmushi Umman Nihal ta saki tace, abinci zan ɗaukoma nasan da yunwa ka dawo," ko daya bana jin yunwa naci abinci a asabiti" "to shikenan" gyara zama tayi tare da kallan shi kwana biyu duk yabi ya canza Allah sarki Habu akwai San ƴan uwa, a hankali ya ɗaura kan shi saman cinyar Umman Nihal yayi shuru wasa ta Shiga yi da sumar kanshi,cikin natsuwa cikin sigar lallashi tace, "abban Nihal" yace, "na'am" yana maiƙara gyara kwanciya a cinyar sahibar tashi "kwana biyun nan duk ka sauya saboda kasawa kanka damuwa miji na addu'a ya kama mu rinƙa yi ba tunani ba kaji miji na" ta faɗa cikin raunanniyar murya, dago idanuwashi yayi yana kallan Umman Nihal yace, "baza ki gane bane wannan abun yana ɗauremin kai yana bani tsoro, idan kika lura kamar ɗauki ɗai-ɗai akeyi mana umman Nihal inajin tsoran mu rasa Husaini," insha Allah ze warware kaji" Hirar su suka cigaba da yi maicike da so da ƙauna daga nan suka lula duniyar ma aurata. Tun da safe Habu ya fara shiri bayan Umman Nihal ta shirya shi sannan ta shirya yara zuwa makaranta kusan a tare suka fita, be zame ko ina ba sai tasha, yana zuwa ya iske Badamasi har ya iso motar kawai ya shiga suka wuce asibiti Dan ɗauko Husaini,suna Shiga asibitin dakin da aka kwantar da Husaini ya nufa yana shiga yayi turus, sakwamakwan ganin doctor kan Husaini ana ƙoƙarin ceto ran shi yunƙurin ƙarasawa yake Tanimu ya riƙe shi gam in ban da jijjiga babu abin Husaini keyi can yayi shiru girgiza kai doctor yayi tare da rufe husaini da mayafi, zaro ido Habu yayi yana girkiza kai cikin ruɗewa yace, "karka faɗa min shima ya mutu Dan Allah yaya Tanimu ka ce ƙarya ne Husaini na da rai" kuka ne ya kubuce mai ya sulale a kasa yana zabgar kuka, zuciyar Tanimu fes take dan ji ya ke kamar ya rage mugun iri a ganin shi, lallashin Habu ya shigayi shima yana matsar kwalla, shurun da badamasi yaji ne yasasa ya shugo ganin halin da suke cike yasa badamasi jikin shi yayi sanyi haka aka tattaro gawar Husaini aka sa a motar Badamasi sai ƙauye , suna isa gida ya ruɗe da koke-koke, ko da labari ya sami Umma tataro su Nihal tayi daga makaranta suka wuce ƙauye, ba Wanda beyi kukan mutur husaini ba, inna ko hada sanbatu sai da tasha rubutu aka samu sauƙin sunbatun, bayan sadakar uku ƴan uwa da abokan arziki kowa ya koma gida, gidan ya ƙara shuru, Allah sarki malam yana ƙara tsufa yaran nashi masu ƙarfi suna tafiya yayi kuka sosai ya share hawayan shi. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, anata shirye shiryen bikin Haulatu, lokacin Mudi ya kammala secondary ya dawo gida hutu, kafin ya cigaba shine ya fara taimakawa malam da kiwo, dan kusan tare suke zuwa. Bangaran Habu suna zaune lafiya sai buɗi da yake ƙara samu, duk wata soyayya da gata Nihal na samu gashi kullun ƙara kyau take, duk Wanda ya kalleta sai ya ƙara saboda yarin yar akwai kyau da Shiga rai gata kullun tsaf da ita. Yau ta kama laraba bikin Haulatu saura kwana uku gyara amarya ake sosai tunda satin bikin ya tsaya umma ko har sun iso suma anata haɗa hada su Gwoggo ko sai Kai kawo ake kowa ka gani cikin farin ciki yake, daran da yayi ne yasa kowa ya natsu ya samu makwaci ana sa ran gobe za'a sa amarya a lalle. Haulatu dake kwance kusa da Umma ji tayi kamar anmintsine ta tashi tayi tare da miƙewa kiran sunan ta ake, kantane yayi mata nauyi ko mayafi bata dauka ba ta fita daga gidan da gudu ba Wanda ya sani. *Asuba Ta Gari* Tashi akayi ba amarya ba dalilin ta abin kamar wasa ya zama gaske sama da ƙasa ba amarya, ne manta aka fara tare da sanar da su Habu tashin hankali, haka aka bazu dangin amarya Dana ango neman amarya inna ko sulalewa tayi ta sume gida ya ɗau salati sauran mazan dake gidan ne suka ƙaraso cikin gida saboda ruɗewar da matan sukayi ɗaukar inna akayi aka shin fide saman gado yayyafa mata ruwa akayi ko da ta farfaɗo hawanjinin ta ya tashi sakwamakwan faɗuwar da tayi idanuwan ta suka makance bari daya na jikin ta ya murgude, kuka gidan ya dauka ƴan biki da ƴan uwa malam a rikice ya shigo yana Kiran inna saboda gabaki ɗaya ya ruɗe, inna ko anmakance ga idanuwa bude amma ba'a gani, malam ruɗewa yayi da kyar aka samu ya dawo hayyacin sa. Birni da ƙauye babu inda ba'a je neman Haulatu ba harda police station anje ba labarin Haulatu haka su Habu suka dawo gida, duk ba daɗi suna isowa suka fara jin koke-koke a riki ce suka shige gida mi zasu gani inna ba idanuwa gashi ta murguɗe, Habu gabaki ɗaya komai ya mai cak kwakwalwarshi ce kawai ke juyawa wani irin jiri ke dibar shi da kyar ya samu wuri ya zame ya zauna hawaye suna sulalo mai, azuciyar shi yace, "wai meke faruwa da sune wannan wace irin ƙaddara ce ta sauko masu Haulatu ta ɓace inna ta makance gefen jikin ta ya murgude. Tanimu ɗaki ya shige ya rinƙa kawar dariya shi Gwoggo " kai maigida wallahi kai mugune na ƙarshe dubu Dan Allah yadda ka tarwatsa su kamar kiyashi, ni wallahi inna duk tafi ban dariya kaga yadda ta burgude ne," Tanimu yace, "saima kin ga ta mutu murus," ya ƙara kwashewa da dariya ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo``` ✍🏻 [1/7, 2:24 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 *Edit by* *Aliyu miko Muhammad* https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com *Page: 23_24* Haka ƴan biki suka watse saboda har yau ba'a ga amarya ba, sai inna dake ta faman jinya komai ya tsakulewa dangin yanzu ba'a wani samun nutsuwa, duk dako har yanzu Habu yana samun rufin asiri amma duk wata walwala da jin daɗi ya daina kullum cikin tunanin halin da Inna ta shiga yake, ko da suka je asibiti magunguna aka basu amma har yanzu jiya a yau, Tanimu ko da Gwoggo duniya ta masu daɗi saura mutum ɗaya su rage mugun iri. Yau tunda safe Tanimu ya shirya ya wuce daji saboda sun yi da boka ya dawo yau, haka ya miƙe hanya yana bin daji ba motsin kowa sai tsuntsaye da mugayan haluttu, bukkace ƙwali ɗaya a dokar daji sai dariri ku dake tashi, da baya da baya Tanimu ya shige yana shiga ya zauna boka ya kece da dariya yace, "nasan komai Tanimu ka kwantar da hankalin ka nan da kwana uku Habu ya zama tarihi" ya ƙara bushewa da dariya, "yanzu haka yayi sanyi da addu'a sakamakon tunani da wasi-wasi da muka tura masa sannu a hankali zamu cimmasa, amma fa kasan idan na gama aiki na zaka bani kaso mai tsoka kuma duk abinda na tanbaye ka daga baya zaka bamu," ya ƙara bushewa da dariya, insha... Dakawa Tanimu tsawa boka yayi, "kamanta mu ba'a kira mana Allah anan, Tanimu jiki na rawa yace, " to to" "yanzu ka amshi wannan laya tayi kwana biyu a bakin ka ba tare da kaci abinci ba ko kayi sallah ba," sannan Tanimu ya miƙake da baya da baya ya fita tare dasa laya a bakin shi. Tunda Inna ta kwanta ciwo ta fara Dan ɗan-ɗana kudarta saboda ko abinci Gwoggo ba ta bata sai idan malam na cikin gida idan ko malam nan faran faran bata samun wata kyakyawa kulawa, Habu ko be san meke faruwa ba, saboda gabaki ɗaya abubuwa sun riki ce mai suke, yau ma kamar kullun Inna ta fito daga kewaye tana tafiya a hankali, Gwoggo ta fito wani irin shu'umin murmushi Gwoggo ta saki kofar gida ta leƙa taga ba kowa sai malam shima ɗin yana ne sa da gidan, dawowa tayi ta zauna saman kujera ta yani gulma ta miƙe kafafuwa Inna ta ci karo da kafar gwoggo ta kife kasa ko kwakwaran numfashi bata sakeyi ba ɗaura hannu Gwoggo tayi a kai ta zunduma uban ihu Wanda ya jawo hankalin malam da maƙota kafin ka mi malam ya shigo gida tare da maƙota kuka Gwoggo take tana cewa, "mun Shiga uku Inna ki tashi, malam ka zo ka ga ikwan Allah," ko da malam ya ɗaga Gwoggo rai yayi halin shi take anan ya yanke jiki ya faɗi sumamme, malam Baraune da sauran muta nan dake tsaya ne suka ɗauki malam aka ida sa cikin dakin sa. Inna ko su liman ne suka ɗauke ta har aka kai Inna makwancin ta malam bai san inda kanshi yake ba, da labari ya sami Habu yayi kuka dan har kusan zaucewa yayi kafin ka ce mi gida ya kuma rikicewa da koke-koke Tanimu ko daɗi fal a zuciyar shi. Sai da akayi kwana biyu da rasuwar Inna sannan malam ya fara dawowa dai-dai Habu ko tunanin duniya sun mai ca ga mugayan mafarke mafarke da yake wani lokacin a ranazane zai tashi sai Umma ta riƙe shi tana mai addu'oi sannan zasu koma bacci. Kasancewa yau litinin tunda safe Umma ta tashi ta fara shirya Nihal da Sara domin zuwa makaranta bayan ta kammala shirya sune ta dawo ɗakin jingine jikin gado ta sami Habu hawaye na mai zarya a kunci, girgiza kai Umma tayi tare da dafa shi a dan razane ya waigo, cikin sauri ya fara goge hawayan fuskar shi, a hankali Umman Nihal ta fara murza mai hannuwan shi, kallan Umma Habu yayi ya aƙaro murmushin da iya karshi laban shi, buɗe baki Umma tayi zatayi magana idanuwan ta tap da ƙwalla ɗaura hannun Abba yayi saman laban ta tare da ƙara janyo ta jikin shi cikin sanyi murya yace, "mata na insha Allah bazan ƙara tada hankali na ba kin ji matata, " lamo Umma tayi a fafaɗan ƙirjin Abba tayi tana sauke numfashi a hankali dago ta Abba yayi, ya kallan ta sun daɗe a haka sannan ya ƙara matse ta a jikin shi kamar za'a sace mashi ita, "Umman Nihal wai ina Nihal ? Langwaɓe kai Umma tayi, " har ka manta yau Monday ko" murmushi ya saki yace, " mijin naki ne gabaki ɗaya ya ruɗe matana amma insha Allah zan dawo dai-dai ya ida zancan yana lakuce mata hanci, haka su Umma suka sha soyayya da Abba kamar ba zai fita wajan aiki ba amma haka ya shirya ya fita, ko da ya fita bai zame ko Ina ba sai makarantar su Nihal office din principal ya wuce tare da shedawa principal yana San ganin diyar shi Nihal principal ya sha mamakin hakan saboda ba halin Abba bane zuwa katsewa yara karatu ba, aika yaro yayi ya kira Nihal tunda aka ce mata Abba na nemanta sai jikin ta yayi sanyi, ko dai malam ne ya rasu ko kawu Tanimu duk hankali ta a tashe ta fito, tun daga nesa abba ke zabga mata murmushi hakan yasa ta saki ranta da Sauri ta ƙaraso tare da faɗawa jikin Abba, rungume ta yayi tsam a jikin shi sannan ya samu ɗaya daga cikin kujerun dake harabar makarantar suka zauna, kallon Nihal Abba yake cike da so da ƙauya na yace, "rabin raina" "na'am abba na" kin san miya kawo ni makaranta" girgiza kai Nihal tayi alamar a'a, "ba komai ya kawo ni ba sai dan na faɗa maki ki kasance mai haƙuri a rayuwar ki da ruƙo da addini rabin rai na duk halin da kika tsinci kanki ko da SAUYIN RAYUWA ne saɓanin abunda kika saba gani, bana su a duk sanda kika shiga wani hali ki manta da Allah na tare da ke Nihal " duk jikin Nihal sanyi yayi duk da a lokaci bata wuci shekara goma ba sai da hankali ta ya tashi da irin nasiha da Abba ke mata, a hankali ta buɗe baki tana sakin murmushi tace, "insha Allah Abba nama alƙawarin zan kiyaye , "yauwa ƴar Abba sannan a duk Inda kike ki zamu mai kula da Umman ki" "Abba na zan kula da ku insha Allah ko Abba" lakace mata hanci Abba yayi yace, "shiyasa nake ji dake Rabin rai na" "yeee Abba na" kyakyawar runguma ta kaima Abba ya rungume ta tsam ajikin shi wasu hawaye masu zafi suna sulalo mai saboda gabaki ɗaya ya rasa me ke damun shi, ganin Nihal na ƙoƙarin zame jikin ta yasa yayi saurin goge hawayan fuskar shi yana sakin murmushi, itama murmushi ta saki cikin shagwaɓa tace, "Abba na kaga duk kayan break ɗina sun ƙare, yaushe zaka siyo min wasu? kaga yau ma Umma kudi ta bamu ni da sara" "to shikenan Rabin raina idan na dawo daga gareji tare zamu je Ku zabi duk abin kuke so" " yee Abba bari naje na faɗawa Sara" haka Abba ya rinƙa Jan Nihal da hira mai cike da so daga nan yayi mata sallama tare da bata sweet da yawa ita da Sara. Ko da ya isa gareji yaran shi na ta gyara, wata mota aka kawo gyara kowa ya kasa gyarata shitu ne ya ƙaraso da Sauri yace, "yallaɓai tun ɗazu Muke jiran ka an kawo gyara, yau baka fito da wuri ba," "wallahi ko Shitu Ina wurin ƴar lele tana ta zuba min surutu shiyasa ban zo da wuri ba," murmushi Shitu ya saki tare da shafa kai, suka ƙarasa har gaban motar gyaran ta suka Shiga yi, gyara motar suke sosai, kan Habu ne ya fara sarawa fitowa yayi daga ƙarƙashin motar yana dafe kai gabaki ɗaya yaran shi ca sukayi a kan shi suna tanbayar shi lafiya, shitu ne ya riƙe shi zai zaunar da shi Dan ya samu Hutu wata irin dariya ya saki yana Neman kwacewa daga ruƙon da shitu ya mai ganin abin ya wuce na hankali ya fara kiran sauran yaran gantsara mai cizo Habu yayi ya ranta a na Kare, da gudu suka bishi hauka tuburan Habu yake kamashi sukayi sai gida Umma dake zaune tana cintar wake ta juyo sallama a Zaure mayafi kawai ta yafa, mi zata gani Abba ne ke hauka tuburan su shitu sun ririƙe shi gashi ɗaure da igiya wani irin kuka ne ya kuɓucewa Umma tana kuka tana salalami, daki aka wuce da shi aka daure, sai sanbatu yake yana kecewa da dariya can sai ya fashe da kuka, Umma ko addu'oi Shiga jeramai, sallamar limana ce ta katse mata zance , shigowa yayi mai addu'oi ya bashi yasha sannan yayi shuru yana gurnani ni. Ko da labari ya sami Tanimu yayi murna dan yau burin shi ya cika shi da Gwoggo baki har kunne Allah sarki Habu malma ne ka dai ya damu, shiryawa Tanimu yayi shi da Gwoggo zuwa shanono, kullin maganin da boka ya bashi ya zura a jaka shi da gwoggo suka ɗau hanya 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwritersforum@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 25_26* Ko da Tanimu suka iso shanono kukan munafunci ya soma yana mai cewa, "oh ni Tanimu wannan wane irin SAUYIN RAYUWA ne Habu, kai kuma taka ƙaddara da hauka ta zo munbani," Gwaggo ce ta amshe zancan da cewa, "Allah ya yaye mana," ƙullin maganin da boka ya bashi ya ciro a cikin jakar su yana cewa, "bari mu gwada wannan maganin muga ko zaiyi aiki" Umma dake gefe tana sharbar kuka ta miƙe ta dauko mai kwano yayi sulkulan shi ya matse bakin habu yana tirje-tirje ya ɗura mai wani malalacin murmushi ya sakar wa Gwoggo itama ta maida mai, ko da Nihal ta dawo daga makaranta taga yadda Abba ya koma tayi kuka kamar ran ta zai fita haka Sara kafin Gwoggo ta jata ta hure mata kunne, tunda Abba ya kwanta hauka komai ya lalace, shi ko Tanimu da ya zo jinya sai ya tare a garejin habu yana sa yaran habu abinda yake so, Gwoggo ɗaki guda ta hakince kafin su mamaye gidan duk wannan abinda ke faruwa Umma ko ta kansu bata bi ita dai fatan ta mijin ta ya warke. Yau dai haukan Abba yayi tsanani dan har igiyar da aka ƙulleshi da ita ya kunce kulle ɗakin akayi saboda tsoran abinda yake, gabaki ɗaya ɗakin sai da ya mai fata-fata Umma da Nihal kuka kawai suke sharɓa Gwoggo ko da Tanimu lamo sukayi a ɗakin su da ƴa ƴa su, sai abu yayi Abu ya kwashe da dariya ƙasa-ƙasa har dare ana Abu ɗaya daga Umma har Nihal ba Wanda ya rintsa, safiya nayi aka kira malam ko da ya buɗe ɗakin yasha mamaki Dan duk wani Abu dake ɗakin ya tashi aiki can raɓe bayan gado Abba ya laɓe kamar ƙaramin yaro yana kuka, murmushi malam jafaru yayi yace, "taso kaji Habu" tasowa yayi yana raraba ido ya zauna bakin gado ya takure yana satar Kallan Tanimu Wanda yake ta rausaya kan munafunci, addu'oi malam jafaru ya mai sannan ya bada magunguna karya asirri dan ya gano kamar asirri aka mai maganin da Tanimu ya kawo mai malam jafaru ya gani yashe a kasa hannu ya kai zai dauka Tanimu yayi Sauri riga shi ɗauka yana yaƙe yace, "ah wannan maganin yana da kyau amma tunda anfara wannan sai ya daina shan wannan na garin dama malam ne ya bani na kawo mai" kada kai malam jafaru kawai yayi ya fita, lokacin har bacci ya ɗauke Abba yana fita Tanimu ya cije leɓe yana tunanin ta ina zai ɓullo wa wannan al'amari dan wallahi ko ana ha maza ha mata sai Habu ya bar duniya tunda duniyar bata uban shi bace fita yayi a fusace har yana bangaje Gwoggo. Umma ko ɗakin da Habu ya ɓata ta gyara shi tsaf har lokacin yana bacci bai San wainar da ake toyawa ba, Nihal ce ta zauna kusa da shi tana kallan fuskar mahaifin nata tayi fayau daka gani kasanciwo na cin mutum a hankali ya ware idanuwan shi ya sauke su a kan Nihal wani irin lalausan murmushi ya saki ya miƙa mata hannu kamar jira take ta faɗa jikin shi tana kuka cikin sheshekar kuka tace, " Abba Dan Allah ka tashi Allah bana so ina ganin ka haka Umma na ta rinƙa kuka nima kana sani kuka Abba" ta ƙara rushewa da wani sabon kukan Abba shima kukan yake dan bame lallashin wani Umma ce ta shigo itama tabi layi ƙanƙame su Abba yayi suna kuka na yi bamai lallashin wani, sai da sukayi mai Isar su sannan suka ta shi, yau dai ba laifi jiki yayi sauƙi Dan maganin da malam jafaru ya bada masu kyaune, Gwoggo ko ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda yana yin da taga Habu a ciki, bangaran Tanimu ko yana fita bai zame ko Ina ba sai wajen boka Tal'udu Sabon Yanka zaiyane mai halin da ake ciki yayi dariya boka ya saki sosai sannan yace, "Tanimu sai kayi wanka da jinin jinjiri Dana bunsuru dana kare sannan zaka samu abinda kake so sannan kayi kwana biyu kana sallah tsirara, saboda a gaskiya Habu mutum ne mai ƙarfin imani idan ko kayi abinda na faɗa ma zamu tura mai baƙaƙyen al'jannu wadda ba yadda malam jafaru zaiyi dasu, Abu na ƙarshe da zan sanar dakai shine kayi zina da jaka da dare a gaban matar ka," zaro ido waje Tanimu yayi yace, "yanzu dole sai a gaban matata malam bani tunanin indo zata yadda da wannan zancen" "Tanimu baka shiryawa Habu mutuwa ba kenan cikin ƙunci da wahala ba, baka shirya Habu yayi wulaƙantacciyar mutuwa ba" boka Tal'udu ne ya faɗa yana kiran suna yan aljanu rausaya kai Tanimu yayi "idan dai dan naga bayan Habu ne babu abinda ba zan iya ba," "yanzu kayi magana Tanimu Idan dai kayi abinda na saka dai-dai zaka ga aiki da cikawa Tanimu" sannan ya janyo wasu magunguna a cikin kwalba yace, "Tanimu ga wannan ka canza mai da su a matsayin maganin shi, sannan ka tabbata bayan ka gama zini da jaka kajewa Habu a haka ka faɗa mai duk abinda ka shuka kana fita labari zai canza zani," "ina fajin tsoro karya zo ya warware " Tanimu tun da muke da kai ka taɓa ganin nai maka aiki ya warware yanzu Ina sauran suke kai dai aka kayi abinda nace ma," "abinda ka lissafa ban san inda zan samo jariri ba" "kai dai Tanimu wani lokacin sakarai ne, ka bada kuɗi ayima komai kai dai naka anfani da kayan aiki" sannan Tanimu ya dawo gida cike da farin cikin a zuciyar shi amma yana jin tsoran yadda zai tinkari Gwoggo da zancen yin anfani da jaka a gaban ta shi dai wannan Abu da kunya, yana shigowa Gwoggo ta tare shi tana huci ganin ya haɗa rai ne yasa jikin ta yin sanyi zama tayi kusa dashi nata gunguni, "yanzu saboda Allah malam sai kafita tun da safe sai yanzu ka dawo kana cika kana batsewa, gashi wancan karfan kafan ya tashi Dan yau garas ya wuni cikin gidan ba alamar ciwo," "daɗi na da ke Indo rashin haƙuri da jin bayani sai ki buɗe kunnan ki da kyau kiji idan ba haka ba sai dai mu koma gefe muna cizan yatsa" natsuwa Indo tayi kamar me ɗaukar karatu Tanimu ya zaiyane mata zance, amma saboda tsabar San abin duniya da rashin imani sheɗan ya riga ya gama da su ta amince. Allah sarki Habu tunda ya tashi yake neman Tanimu har dare yayi, ko daya tanbayi Umma Nihal ce mai tayi ya je samu mai magani wani irin daɗi ne ya lilibe Habu, ko da safe da Habu ya tashi jiki da sauƙi sosai, bayan gari yayi sha, Tanimu ya shigo ɗakin Habu yana ta washe baki, "a'a masha Allah jiki yayi sauƙi gaskiya magani yayi aiki," "ai bani da abinda zance ma yaya sai Allah ya saka da alheri ya baka mafifinci gida a gidan aljana" "ai duk yima kai ne Habu idan ban maka ba wazanyi wawa ya" ida zancan yana hawaye "yanzu ka duba yadda kake kula da Sara da Mudi ai bani iya saka ma da abinda kayi min a duniya Habu"yana faɗa yana sharar ƙwalla, " haba yaya tsakanina da kai ba yar haka nima ai ƴa ƴa nane" Umma da Gwoggo suka amshe zancan da cewa, "aiko dai," bayan sun gama tattaunawa, Umma ta wuce madafa Gwoggo ta wuce ƙurya Habu ya shiga wanka, yara na waje suna wasa ɗakin Habu Tanimu ya Shiga ya canza magunguna ya aje Wanda boka ya bashi sannan ya fito da sauri, Da yamma likis ya wuce wajen boka yayi wanka da jinin jinjiri dana kare Dana bunsuru, sannan boka ya bashi laya da ze daura a ƙugun shi, saboda inyaje anfani da jaka karya sha wahala, sannan ya taho gida yana isowa aka tare shi da labarin tunda Habu yasha magani bakin shi ya kulle sai dai ya rinƙa bin mutane da ido wani irin daɗi ne ya lulluɓe shi sannan ya leƙa ɗakin Dan ya tabbatar a zuciyar shi kuwa cewa yake Abu yayi kyau saura aikin dare. Dare nayi Tanimu da Indo suka fito dama ya taho da jakar shi tunda rana, Indo na kallo Tanimu ya gama sheke ayarshi da jaka, sannan ya wuce ɗakin Habu haihuwar uwar shi yana Shiga ya kunna haske ya gwaraye ɗakin, Habu dake kwance har yanzu bacci be ɗauke shi ba tashi yayi zunbur yana bin yaya Tanimu da kallo ko shima ciwon haukan ya same shi ne, dariya Tanimu yayi yace, "ɗan uwa nasan zakayi mamaki ko,? to kwantar da hankali ka lafiya ta ƙalau" ya idda zancan tare da zama yace, "Habu idan akwai Wanda na tsana a duniya to ya biyo bayan ka ya faɗa yana daga gira duk wata mutuwa da akeyi a cikin gidan mu nine nan ke aikatawa ya tintsire da dariya ni na masu asirri yanzu haka kai ma nama asirri ka ga wancan maganin na canza ma, saura kaɗan ka tafi barzahu, kaga dukiyar daka tara ta zama tawa da ƴa ƴa na, matar ka da ƴar ka su gane," idanuwan Habu cukowa sukayi da ƙwalla yana kallan Tanimu maganganun shi na mai yawo wani irin kukan kura yayi zai shaƙe Tanimu amma mi sai ya faɗi yana wani irin kuka yana kafe wa da Sauri Tanimu ya bar ɗakin, ya Shiga ɗakin su ya zauna, yana sauke ajiyar zuciya, ba gidan ba kadai gabaki daya unguwar ta ɗauka da irin kukan da Habu keyi na ban tsoro, Umma ce ta fito da gudu tana kuka shima Tanimu ya fito lokacin har ya sa kaya, Shiga ɗakin su yayi har da manyan unguwa da suka tashi daga bacci saboda kukan da Habu keyi, mi zasu gani yankan jikin shi habu yake ta ko Ina jini na zuba kowa tsoro sai da ya Shige shi ririke shi malam jafaru yayi yana mai addu'a jinin ya fara zubo mai ta hanci ta baki yana kallan Tanimu yana mutsu mutsu can yayi shuru yana motsa baki a hankali yana kalmar shahada innalillahi wa'innailaihiraju'un ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ``` ✍🏻 ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo✍🏻 ```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by* *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwritersforum@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 27_28* Innalillahi wa'innailaihiraju'un ko wanne mai rai yakan zama mamaci Umma dake bakin ƙofa ce ta sulale sumammiya, Gwoggo tayi kanta da maƙota malam Jafaru ko kankame Habu yayi yana shara ƙwalla babu Wanda yayi tunanin Habu zai iya furta Kalmar shahada a halin da yake ciki, babu wanda beyi kuka ba ko Tanimu sai da jikin shi yayi sanyi saboda bayan asarrin yaci Habu baƙin cikin yasa ya haɗiyi zuciya ya mutu, gabaki ɗaya gida ya rikice da koke-koke Umma ko ana kai ta ɗaki sakwamakwan suman da tayi, tayi bari Wanda ko ita kanta bata san da zaman cikin ba, Nihal ko gabaki ɗaya ta gigice kafewa kawai tayi saboda tunda take bata taba ganin mutum yayi irin mutuwar da Abban ta yayi ba, har sai da aka sheka mata ruwa sannan ta dawo dai-dai ta daɗe tana zarana, malam Jafaru ne yayi ma Abba wankan gawa sai dai muce Allah ya jikan Abba ya gafarta masa ya saka mai abinda Tanimu yayi mai har aka kai Habu makwancin shi na gaskiya manyan unguwa na kuka yaran shi kuka ba irin Wanda basuyi ba, Wanda be san gaskiyar mutuwar su Abba ba sai suka shiga tausayawa Tanimu tare da fatan Allah ya tsare shi labari na isa wajen malam baƙin ciki da takaici ya sanya shi haɗiyi zuciya ya mutu wani saban kuka ne ya ɓalle, Umma ko har akayi kwana uku da rasuwar Abba bata san inda kanta yake ba gata nan kawai kullun cikin kuka take Nihal ko, ko bacci batayi na kirki data kwanta zata tashi a razane, Gwoggo da Tanimu duniya tayi masu daɗi dan ji suke kamar sun sauke wani nauyi a haka har akayi bakwai da rasuwar Abba da malam sannan kowa ya tafi gidan sa. Tunda Abba ya rasu suka fara ganin SAUYIN RAYUWA duk wata dukiya da Abba ya malaka Tanimu ya Tattare ya mallake, Gwoggo ko tayi babakere a kowani ɗaki na gidan sai ɗaki daya na Abba nan Umma ke zama tana takaba, sannan Gwoggo tayi zama na musanman ta fara hure wa Sara kunne da Mudi gabaki ɗaya yanzu Sara ba ruwan ta da Nihal kowa har karshi yake ko makaranta zasu komai ya cakuɗewa Nihal gashi books ɗin ta na makaranta duk sun fara ƙarewa, dan a lokaci suna aji huɗu (4) ita da Sara. Yau a gajiye likis ta dawo daga makaranta daƙin Umma ta shiga, Umma ta hango zaune tana sana'ar kuka wadda ta zamar mata jiki tunda Abba ya rasu faɗawa jikin ta Nihal tayi ta kwaɓe fuska ganin hakan ne yasa Umma share hawayen fuskar ta tana murmushi "Rabin rai na har kin dawo? " na dawo tun ɗazu amma naga kina ta kuka Umma dan Allah ki dai na kuka kinji" "insha Allah ba zan sake ba kin ji" cire uniform din ta Nihal take tana cewa, "Umma gabaki ɗaya books ɗina na makaranta sun ƙare dan Allah kiyi ma baffa magana ya siya min naga ya siyawa Sara sababbi kuma fa nata basu ƙare ba kuma naga idan Abba zai siya mani Abu tare yake siya min da Sara amma naga baffa ba haka yakeyi ba" ta idda zancan idanuwan ta sun cuko da ƙwalla, janyo ta Umma tayi jikin ta tana murmushi "haba Rabin rai na karki damu insha Allah idan Baffa ya dawo zan faɗa mashi nima ina buƙatar kuɗin kashewa ina so na wanke makin kayan ki masu datti," murmushi Nihal ta saki mai nuni da jin daɗin ta, ko da Baffa ya dawo da yamma da dare yayi Umma ta same shi ta mai bayani sai ya hauta da masifa da bala'i har abin ya ɗaure mata kai su da hakkin su amma ze rinƙa ci mata mutunci dan ta tanbaya haka Umma ta dawo ɗaki tana sharar ƙwalla, ga wata masassa data rufe ta ko da Umma tatashi da safe ko miƙewa bata iyawa saboda ciwo hakan yasa Nihal bata je makaranta ba tun daga wannan rana Umma ta daɗe bata tashi Nihal kuma ta fara ɗanɗana kudarta ta koma kamar baiwa a gidan ƴar makarantar boko da allo Gwoggo ta kashe mata zuwa saboda wahala gidan da talla, Umma ko in banda kuka babu abinda take, gashi Baffa Tanimu yasa an kullewa maƙota baki a wurin boka haka yasa bame tanbayar su wannan kenan. *CIGABAN LABARI* A hankali Nihal ta raba gefan Umma ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. *Asuba Ta Gari* Yau ma kamar kullun tun kafin asuba Nihal ta tashi tayi aiyukan da ta saba na yau da kullun bayan ta kammala ta hura wuta ta ɗaura ruwan koko, yana tafasa ta sheƙa tana ƙoƙarin ɗaukar bokitin Gwoggo ta fito tana muzurai, har ƙasa Nihal ta duƙa ta gaishe ta harara ta aika mata, ",da ban kwana lafiya ba ai baza ki ganni ba, tunda nasan har fata kike mubi sahun uban ki Habu mstww, tashi ki ban gu ban san munafunci" simi simi Nihal ta ɗau bokiti ta fita, a hankali take takawa saboda fasan kafar ta dake mata zafi, tun daga ne sa ta hango yaya zaune a ɗaya daga cikin kujerun dake harabar wajen da yace ta same shi yau, tattausan murmushi ta saki tana jin yaya har cikin ran ta shima dake zaune hango ta yayi yana ta sakin smile sanye yake da jallabiya black mai hula yayi kyau har ya gaji gashin kan shi sai sheƙi yake da walwali kana gani Kasan ankashe mata kuɗi, tun da Nihal ta taho yake binta da kallo tausayin ta na ƙaralulluɓe shi ganin ta zo kusa da shine ya lumshe idanuwan shi, kamshin turaran shine ya doki hancin Nihal sauke ajiyar zuciya tayi tare da dukawa ta gaishe shi har ƙasa, "ƙanwata mi ya sami idanuwan ki sukayi ja bayan nace karki sake zubar da hawayan ki" rausaya kai Nihal tayi wasu hawayan na sulalo mata daga ta yaya, yayi yana kallan fuskarta wadda tayi ja saboda tsabar kuka janyo ta jikin shi yayi ya rungume ta tsam kamar jira take ta saki kuka mai cin rai lallashin ta ya shigayi cikin sanyin murya, " "haba sister tun jiya fa nake lallashin ki amma har yau kin kasa daina kuka please ki dai yin asarar hawayan ki Nihal" ya idda zanca yana ɗago ta daga faffaɗan ƙirjin shi yasa hannu yana share mata hawaye ,murmushi ta saki Allah sarki RAYUWA ba wanda ke damuwa da ita sai yaya ita ko a duniya da mai zata saka mai tana wannan zancan zucin baba mai gadi ya amshi bokitin dake hannu ta , zama su kayi bakin ruwa suna hira mai daɗi Nihal sai dariya take kamar ba ita ke kuka dazu ba. *fan's am too busy kuyi haƙuri da wannan page ɗin Please* ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ```[1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by* *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwritersforum@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 29_30* Nihal ce ta kalli yaya Wanda shima kallan ta yake tace, "gaskiya yaya wajan nan yana da kyau sosai, ina san wurin nan dubi yadda tsuntsaye ke shawagi yaya ga wata ni'ima da sanyin daɗi, amma nasan duk daɗin wurin nan bai kai birni ba yaya ko, ina so naje birni naga ƴan gayu abba ya sha faɗa min cewa wata rana tare zamu je birni naga gari amma sai ga..." lumshe idanuwa Nihal kawai tayi saboda rawar da muryar ta keyi, "ƙanwata kenan shiyasa na zaɓa mana nan dan kirinƙa samun hutu da natsuwa, maganar zuwa birni ko ki kwantar da hankalin ki insha Allah zaki je birni har ki zama wani Abu na alfahari," "yaya na kenan bana tunanin akwai ranar da zan zama haka, ka duba ka gani tallan safe da ban na rana da ban na dare da ban kabata ganin in da dan talla ya samu cigaba sai dai ya ƙare a yawo a titi" Nihal ta idda zancan hawaye masu zafi na wanke mata fuska, girgiza kai yaya yayi, "Nihal ba'a fidda rai ga rahamar Allah ƙanwata ki daina saurin yanke ƙauna akan rahamar ubangiji ki rubuta ki aje komin rintsi komin wuya zaki samu cigaba a rayuwa Nihal" murmushi Nihal ta saki tana tila dutse cikin koramar dake gudana, a gaskiya kalaman yaya na mata daɗi ko ba komai a duk sanda tana tare da shi tana samun nutsuwa, Yaya ne ya katse mata tunani da cewa, "ni ko ƙanwata ina jummala ƙawar ki? " Jummala nan bamu haɗuwa shiyasa saboda bana samun wani lokaci bale har mu haɗu da ita kuma makaranta ta boye ta, duk da nasan Jummala tsoran Gwoggo ke hana ta zuwa wuri na" "duk sanda kuka haɗu kice mata ina gaishe ta" zata ji insha Allah." Baba mai gadi ne ya ƙaraso da bokitin Nihal ya aje yana jerawa Yaya godiya sannan ya miƙawa Yaya kola dake hannu shi mai kyau ya koma wajan zaman shi miƙawa Nihal kula yaya yayi yana cewa, "ga wannan idan kin koma gida ki samu ki ci ke da Umma karki barmin kankin da yunwa" Yaya ne ya faɗi hakan cikin sanyin murya, idanuwan Nihal ne suka kawo ruwa jikin ta na rawa tasa hannu ta amshi kular, idan zata iya tunawa raban su da abinci ita da Umma tun jiya, girgiza mata kai Yaya yake alamar kar tayi kuka buɗe baki tayi da niyar gode mashi hannu ya daura saman lips din ta alamar baya so sun Daɗe suna kallon junan su sannan Nihal ta kauda kanta, ɗan sosa ƙeya Yaya yayi yace, "lokacin tafiya gida yayi ko? daga mai kai Nihal tayi cike da shagwaɓa miƙewa su kayi a tare maƙale ƙafa Nihal tayi saboda tsamin da ta mata ga fason ƙafar ta dake ta mata zafi, yayane ya lura da yanayin da take ciki, kwala wa Baba mai gadi kira yayi yace ya siyo mashi silifas da Sauri baba mai gadi ya ƙarasa shago ya siyo yana miƙawa yaya yayi godiya sannan ya miƙawa Nihal wani irin daɗi ne ya lulluɓe ta godiya ta shiga jera masa tana tsalle tsalle dariya ta ba shi sosai saboda yadda takeyi. ***** Bayine ke ta zarya acikin babba Masarautar *MATAWALE* kowani bawa na sanye da kaya launi iri ɗaya mata nasu rawaya doguwar riga maza ɗinki mai sulke wanda aka sarrafa shi da yadin haɗa da hular wangale geta ɗin da akayine yasa bayin suka jera layi kowa ya sada kanshi ƙasa, tunda motocin suka fara kunno kai babu motar tai ƙasa da miliyan ashirin (20) a ƙalla motocin zasu kai biyar biyu gaba biyu baya daya a tsakiya wadda tafi kowace Motar dake ciki ƙayatuwa gami da kyan gani, murfin motocin huɗu aka buɗe a tare dogarai ne da security's majiya ƙarfin dantse waƴanda sun sha suit black da baƙin glass dogarai na sanye da riga malin-malin da sharɓeɓiyar bulala wasun su harda tsofaffin taɓaryu kai kace wanda zasu yaƙi, busar da aka fara ne da algaita shi zai tabbatar maka da dan sarki *SULTAN* ya dawo daga ƙasa mai tsarki wato Makka warda ke zaune a nahiyar Saudiya, ɗaya daga cikin security's ɗinne ya ƙaraso da Sauri ya buɗe murfin motar tsakiyar ya ja gefe ya tsaya, a hankali ya turo kafar shi wadda ke sanye cikin takalmin sarauta ruwan zaiba mai matuƙat kyau sai da jinjina sannan ya idda fitowa gabaki ɗaya bayin dake harabar wurin zubewa sukayi suna masu kwasar gaisuwa, wow masha Allah haɗuwar guy ɗin har kusan sumar dani tayi duk da a lokacin fuskar shi na cikin rawani, zabuni ne sanye a jikin shima mai ruwan sulki wanda yasha aiki da milki zare sai alkyabba milk Wanda tasha aiki ta gaji kanshi na sanye da rawani white idanuwan shi na sanye da dan siririn glass fari gabaki ɗaya gurin haskyan shi kawai ke baiyana yana ɗauke da ɗan siririn hanci da jajayen laɓɓansa wanda suka kasance ƙanana kamar ya shafa janbaki, taku uku zuwa biyu yake cikin isa da mulki fadawa da security's na bayan shi, Isar su bakin wata haɗaɗɗiyar ƙofa yaja ya tsaya badawan dake bakin ƙofar ne suka buɗe mai ƙofa, daga wa fadawan bayan shi hannu yayi alamar su tsaya bakin ƙofa shi kan shi hannu abin kallo ne fari yake tas yana ɗauke da agogo ruwan haɗalashi na azirfa mai tsadar gaske yatsun hannu shi na sanye da zoben azurfa, Haɗaɗɗan parlour ne Wanda ya amsa sunan shi yasha Royal chair's ash and black bayine keta kaikawo, gimbiya ce zaune saman ɗaya daga cikin kujerun tana sanye da doguwar Riga lace mai tsaɗar gaske green ana mata massages, a hankali Sultan ya ƙaraso yayi hugging nata tabaya wani irin lallaunsan murmushi gimbiya ta saki bayin dake ɗakin ne suka shiga kwasar gaisuwa hannuwa kawai ya daga masu cikin calm voice din shi cike da shagwaɓa yace, "habibty I really missing you" ya idda zancan tare da zagayowa miƙa mashi hannuta tayi yayi kissing nashi sannan ya zauna da nuna alamar gajiya murmushi gimbaya ta saki dan tasan halin ɗan na ta yanzu yana iya cewa kayan sun isheshi tun kafin ta gama zancan zuci Sultan ya fara ƙorafi "habibty ni dai gaskiya kayan nan sun isheni bana iya 1hour da su ya faɗa yana furzar da iskar bakin shi, bari na wuce part ɗina nayi take shower na dawo" murmushi gimbiya ta saki, "amma kafin kaje part naka ya kamata kaje part din maimartaba da part ɗin second mom ɗin ka first" cike da isa yace, to. Kai tsaye be zame ko ina ba sai fadar maimarta ba security da fadawa na biye da shi dai-dai bakin ƙofar ya daga masu hannu alamar su tsaya, shiga yayi yana faɗaɗa murmushin shi Wanda ke fito da laka kyan shi, cikin rawani face ɗin shi take amma ana ganin kyata inaga ya cire rawanin, sarki dake saman kujera shi ta mulki datijo mai natsuwa da adalci da Sanin ya kamata, Sultan na isa gaban shi ya zube yana kwasar gaishuwa , a hankali sarki ya mike ya dago shi ya rungume tsam shi kan shi sarki yasan yayi missing dan na shi sun dau lokaci suna rungume da juna sannan Sultan yayi break up din hugging din yana smile, maimartaba ne yace, "masha Allah Sultan ka ganka ko cikakyan babba mutum mai natsuwa da kamala" ya mutse fuska Sultan yayi yace, " Allah ya taimake ka nifa kayan nan duk sun isheni ya fada a shagwabe," murmushi maimarta ba yayi irin nasu na manya yace, "a hankali zaka saba," sun Dade suna hira da maimarta ba sannan ya wuce part din gimbiya jalila wato second mom din shi step mother din shi, shiga shi part din ta, bayi suka fara kwasar gaisuwa suna mai kirari, gimbiya jalila dake zaune saman Royal chair ta wani hada rai tayi zaman yan sarauta tana cin fruit ganin bayin ta na zube wane ya sheda mata dan gold din ya zo Wanda ake fifita shi akan ya'ya ta da sauran yaran gidan, tabe baki tayi tare da mikewa badan ta so ba tana sakin murmushin yaƙe, murmushi Sultan ya saki irin Wanda take ji kamar ta kashe shi dan haushi hannu ta miƙa mashi yayi kissing ɗin shi sannan yayi kissing goshin ta tare da yin hugging din ta cikin sweetest voice din shi yace, "ruhi I really miss u" break up din hug din yayi gimbiya jalila na murmushi mai cike da ma'anuni mai cike da dunbun munafurci na gidan sarauta. ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ``` ✍🏻 [1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma Mas'ud Nadabo*👑 *Edit by*: *Aliyu Miko Muhammad* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R *Email*:Realhausafulaniwriters@gmail.com *Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com *Page: 31_32* Gimbiya Jalila ce ta koma saman kujerar ta, ta alfarma tare da yiwa Sultan nuni daya zauna, murmusawa Sultan yayi tare da cewa, "Ruhi na ba zama ya kawo ni ba zuwa nayi kawai dan ki san na dawo gida lami lafiya" yana faɗa yana sakin wani ƙayataccen murmushi har dimple ɗin sa yana lomawa ciki, "ai hakan na da kyau ɗan sarki jikan sarki mejiran gado" haɗe rai Sultan yayi tare da kissing din goshin Gimbiya Jalila ya fita da sauri fadawa na bin shi a baya da security's, dogwan tsaki Gimbiya Jalila ta ja tana tunanin irin taurin rai da wayau irin na Sultan, sauke ajiyar zuciya Gimbiya Jalila tayi. Sultan na isa turakar sa ya nufa fadawa suna biye da shi a baya da security's buɗe mai kofa akayi cikin isa ya shige tangameman pralourn shi wanda yasha kayan alatu Royal chair's ne maroon masu kyau da tsada da lallausan carpet in banda ƙamshi da sanyi AC ba abinda ke tashi faɗar tsaruwar parlour ɓata lokaci ne komai na parlour ɗin ya hadu iya haɗuwa duk wani kayan mulki da saurata parlour ya haɗa, wani irin lallausan murmushi Sultan ya saki saboda ganin ƙannan shi Jere a parlour su biyar, suna jiran isowar shi mata uku maza biyu, gabaki ɗayan su sada kai sukayi a ƙasa suna mai sannu da zuwa kowanne a cikin su yasha kayan sarauta dan gabaki ɗayan su alkyabbace a jikin su, a hankali ya tako zuwa gare su kowanne ne su mika hannu yayi Basmal ce da ta farko hannu ta ya fara kissing ta mai sannu da zuwa tare da kissing din goshin shin shi sai Ashada dake ƴan harare-harare da zafin kai ke ɗibar shi, da badan Gimbiya jalila ta matsa mashi ba da ba abinda ze sa shi ya tarbar yayan nashi, mutum se shege iyayi ta tsirfa, hannu shi da Sultan ya kama ne ya sasa dawowa daga duniyar tunani murmushi Ashada ya saki suna kallan juna shi da Sultan ido cikin ido ganin ba ze iya ja da kwarjinin Sultan ba yasa ya janye idanuwa shi tare da zare hannuwan shi daga cikin na Sultan, ƴar dariya Sultan yayi irin na yaro man kaza, sannan yayi kissing hannun Nawwara dana Minal, Nasim ke washe baki wato ɗan autan su wanda jinin su ya hadu da Sultan, Sultan na ji da shi kamar kawai yana zuwa setin shi daga shi sama yayi yana kissing nashi ta ko ina yana cewa, "I miss u my boy" dariya Nasim yake yana San kai hannu kan hanci Sultan dan dariya Sultan yayi tare da kawar da kanshi janyo kan Nasim yake yana cewa cikin tsamin murya" Uncle kissing naka zanyi this time around ba jama hanci zanyi ba Allah" ya fada yana rauyasa kai shi me wayau "to naji sarkin wayau wata rana se naga hanci na a hannu ka na lura Darling, washe haƙori yayi Wanda ya fara fanfara, a hankali ya ɗaura lips ɗin shi saman goshi Sultan yayi masa kiss, sannan Sultan ya sauke Nasim Lumshe idanuwa yayi tare da daga masu hannu alamar su fita cikin natsuwa suka bi layi suka fice. Suna fita bayin Sultan suka shigo *Sinbul aga* da *Barma* wato ƴan tsali-tsali Sultan Dan kusan kullun se sun kusa sa mashi headache, harara ya aika masu sannan ya shige ɗakin shi shima dakin iyakar haduwa ya hadu royal bed yasha bedsheets me kyau da tsada gefe ɗaya dressing mirror tasha kaya kala-kala daga man gashi har na shafawa da turarur ka ba'a magana gefe guda kuma mirror ne babba tsayayye jingi ne Wanda idan ka tsaya kana ganin kanka a tsaye, dakin in ban da sanyin AC ba abinda ke tashi da kamshi, Gaban tagameman mudubin ya tsaya ahankali ya zare takalmin dake ƙafar shi bayin dake bayan shi suka ƙaraso cikin ladabi a hankali suka fara cire mashi rawanin dake kanshi masha Allah iya kar haɗuwa Sultan ya haɗu kamar balarabe sumar kanshi luf ta kwanta tasha gyara har ta gaji ga saje fuskar shi ya kwanta luf ga thick eye lashe, eye brown din shi kamar yayi carving looking extra ordinary black ga dimple kamar ansa nail da hammar anyi nailing cheeks nashi, Sultan mutum ne mai tsaho kuma murɗaɗɗe ne yana da faffaɗan ƙirji fari ne sosai har wani ja-ja yake yellow-yellow saboda tsabar fari da hutu, iya kar haɗuwa Sultan ya haɗu hannun shi ya miƙa aka zare mashi agogon dake maƙale a hannun shi da zoben shi, a hankali suka daga alkyabba dake jikin shi suka aje gefe ya rage daga shi se zabuni, daga masu hannu yayi alamar su dakata da kanshi ya idda cire zabunin ya rage daga shi se singlet itama cirewa yayi tare da miko hannu Sinbul aga ya bashi bathrobe yasa sannan yayi hanyar toilet biyo shi sukayi a baya wata uwar tsawa Sultan yadaka masu yana cewa, "wai Ku wace irin ƙwaƙwalwa gare Baku da hankali ne? Nasha faɗa maku ba yau ba, bana buƙatar wani ya biyo ni bathroom ni yaro ne da zaku biyo? Cikin rawar jiki Simbul aga da barma suke bashi haƙuri tsaki yaja sannan ya shige haɗaɗɗan bathroom ɗin shi. Ashada na shiga part din Gimbiya Jalila yayi tili da rawanin shi yana huci juyowa yayi yana Kallan bayin shi dake take mashi baya yace, " banzaye ƴa ƴan matsiya ta ƴan iska," fisgo mawar yayi ɗaya daga cikin bayin shi yayi, ya kifa ma marwa mari har gudu uku yayi wurgi da shi gefe yace, " tsinanne kawai ni zakayi wa bariki kaga *Sultan Saleem* har da yi mashi kirari ko? fusgo shi yayi tare da matse mashi baki yana huci yace idan ka ƙara mai maita abinda kayi wallahi se na kashe ka nama faɗa ma banza" Gimbiya Jalilia ce tayi masu alama da su fice, da sauri suka fita har suna tuntuɓe, janyo shi Gimbiya tayi ta zaunar da shi tare da Koran bayin dake parlour gabaki ɗaya, wata uwar harara Gimbiya ta aika mashi tana cewa, "sokake ka gwadawa duniya halin da muke ciki ina anfanin wannan haukar da kake, dan farin jini da isa Sultan yafi babba abinda yayi ya cuce ka shine ya girme ka nace ka barmin komai a hannu na amma ka ƙi se wani zafin rai kake da na zuciya mtsww tashi ka bani guri" ta faɗa a tsawace da sauri Ashada ya tashi yana baza alkyaba yana huci. Sultan na fitowa daga wanka ya shiryawa yayi cikin suit din shi Ash masha Allah yayi wani irin kyau har ya gaji barma ne yasa mashi cover shoe din shi black sannan ya ƙara gyara masa gashin kan sa Simbul aga ne ya miƙo mashi glass ɗin shi fari me kyau tare da ɗaura mashi agogo ya feshe shi da turare me kamshi da sanyin daɗi wani irin masifar kyau Sultan yayi, sannan barma ya dau ko briefcase din shi suka fito daga part ɗin security's na tsaye bakin ƙofa barma ne ya miƙawa ɗaya daga cikin security's din briefcake din Sultan, ajere suka fito da security's, fadawa ne suka biyo shi a baya cikin sweetest voice din shi yace, "kunsan bana buƙatar idan zani asibiti naje da fadawa ko" jin hakan yasa fadawa suka ja gefe. Bude mashi murfin mota akayi har ze shiga ya juyo muryar Basmal tana cewa, "yayana!!. yayana!!.. tsayawa yayi cak da Sauri ta ƙaraso bayi na take mata baya, ɗan ɓata fuska tayi data zo kusa da shi tare da langwabe kai cike da shagwaba ɗaura hanuwan tayi saman face din Sultan tana cewa, " yayana baka ci abinci ba kuma har ka fito gabaki ɗaya kowa yana babba parlour yana jiran ka amma se ka fita, gashi tun ɗazu Ramlat ke San ganin ka yayana kuma na mata promise daka dawo ita zaka fara gani, daura hannun Sultan yayi saman na Basmal yace, "karki damu sweetheart zan dawo da wuri har muyi dinner tare, yanzu Ina da marasa lafiya da yawa kuma kin ga saboda su na dawo Nigeria kuma kin sani sweetheart, maganar Nazili kuma iskanci ne ya hana ta zuwa, fin Ku tayi da bazata zo tare da Ku ba part ɗina ba, ban San ranar da zata yi hankali ba mtsww," "yayana kasan tana daɗewa bata gama shiryawa ba shiyasa bata biyo mu ba" "ko" sannan yayi kissing goshin Basmal ya shige mota, a hankali motocin suka bar harabar gidan dan gwaɓe fuska Basmal tayi tare da juyawa suka shige ciki gida ita bayin ta. ```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo``` ✍🏻 [1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Ashe dai haka SAUYIN RAYUWA ya tara d'inbin masoya naji dadi sosai da kulawar Ku a gare ni kuma hakan ya qaramin karfin gwiwa yadda zan cigaba da suburbudo maku posting kamar yadda kuke so_*🤪 *Page: 35_36* Da kyar Nihal ke takawa saboda wani irin jiri dake d'ibar ta ga wani irin nauyi da farantin talla ya mata a haka ta samu ta k'araso har inda suke haduwa da yaya, ko da ta zo wajan ba kowa se baba mai gadi data hango yana zaune saman kujera shi kamar kullun, da kyar ta iya takowa har wurin shi tunda baba mai gadi ya hango ta yake ta washe baki saboda da ya hango Nihal yasan yau gidan shi ba kwanan yunwa, ganin ta k'araso wajan shi ya sashi tashi a kid'ime saboda yanayin da ya ganta a ciki gefen bakin ta a fashe jini na zuba fuskar nan tayi jawur ta kunbura, tausayin tane ya lulub'e shi tare da tanbayar ta cikin nuna tausayi yace, " Nihal mi ya sameki ? maganar da yayi ma Nihal ce tasa ta sakin kuka a hankali ya Shiga bata hakuri duk da bai San dalilin yin kukan nata ba amma dai koma minene yasan irin bak'ar wahala da Nihal ke sha a hannu marik'in nata, janyo hannu yayi tare da zaunar da ita saman tabirin da yake zaman sannan ya aje farantin ta gefe dan ya lura tsayuwar gagarata take nemanyi, har Nihal ta zauna bata ce ufan ba se ajiyar zuciya da take faman saukewa, baba mai gadi ne yace, "sannu kinji Nihal bari na kira maki yayan naki ai yana ciki" daga mashi kai Nihal kawai tayi da Sauri shi ya k'arasa yana ayana yadda aka maida fuskar Nihal kamar lauje dan duka a dai-dai bakin kofar parlour yaci karo da yaya Wanda ke k'ok'arin fitowa sanye yake da shada light brown tasha aiki da dark brown zare haka hula dake kanshi light brown colour ne da ratsin dark brown ba k'aramin kyau ya zaubaba se kamshi yake zubawa ganin baba mai gadi ne ya sasa tsayawa yana sakin k'ayatacan murmushi Wanda fararan hak'oran shi suka bayana, ko da baba mai gadi ya k'araso jiki shi a sanyaye kamar an zare mashi laka ganin haka yasa yaya tambayar shi lafiya tun kafi yayi magana yace, "baba Allah yasa lafiya dai," "Eh to lafiya ba lafiya ba yarinyar nan ce Nihal ta zo kamar wadda tayi hadari," ko ida ji zancan yaya beyi ba ya wuce baba mai gadi da Sauri ya fita, ida baba mai gadi ya bar Nihal har yanzu nan take sai dai wannan karan kanta na bisa cinyoyin ta, ta dunk'ule waje d'aya tana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri yaya ya k'araso tare dayin kneel down dai-dai setin Nihal a hankali yasa hannu yana dago da fuskar Nihal wadda a lokaci ta k'ara kunbura rintse idanuwa yaya yayi tare da ware su kan fauskar Nihal cikin rudewa yana cewa, "k'anwata waya makin haka? duk wadda ya maki haka be kyauta ba wannan wani irin laifi kika aikata da za'a maki irin wannan horan" kuka kawai Nihal ke shek'awa musanman taga yayan nata wanda take mashi shagwaba yadda take so kukan da Nihal take shi ya k'ara rikita yaya sai fama lalashin ta yake, cikin sanyi murya yace, "ya isa mana kukan kiyi hakuri kijin k'anwata bari na fito da mota na kai ki asibiti kijin" daga mashi kai Nihal tayi ciki gida yaya ya koma ya ya janyo hadadiyar motar shi luxus me tsada gaske baba mai gadi ne ya wangale mashi gate ya fita sai da ya zo dai-dai saitin Nihal yayi parking tare da zagayowa ya bude mata murfin mota, zaro idanuwa Nihal tayi tana kallan motar duk da zafin ciwo da take ji qin tasowa tayi sai idanuwa da dake ta faman rabawa ganin irin yadda take yasa yaya k'arasawa tare da kamo hannuwata sai fama titila idanuwa take cikin rawar murya tace, "yaya na warke wallahi," dariya abin ya so bama yaya amma sai ya hade rai yace, "shiga muje asibiti zan kai ki kijin" make kafa ta kumayi tana San zame hannuwan yaya daga rukwan da ya mata, ita Allah na gani bata iya Shiga wannan motar ace Mota duk bak'i har da window's ai bama zeyu ba ta bishi duk Nihal na wannan zancan azuciyar tane, kamar yaya yasan tunanin da Nihal take yace, "tsoran Shiga motar kike ko? Saboda bakin tinted" kallan shi Nihal tayi dan ita bama tasan me tinted din ba, cike da kauyanci Nihal tace, "me kuma hakan yaya" dariyar da yaya yake ta boyewa ce ta kubuce masa sakin baki Nihal tayi tana kallan shi ganin be daina dariyar bane yasa Nihal sakin kuka shuru yayi yana kallan Nihal murmushi ya saki tare da ja mata hanci yace, " ke ko wallahi kin iya rigima wannan mijin ki ya bani da rigima Shiga muje a duba min lafiyar ki haka nan za'a lalatawa yar k'anwata kyakyawar fuskar ta da duka," murmushi Nihal tayi bata ce ufan ba ta shige motar tana dari-dari rufe murfin motar yayi tare da zagayowa ya shige motar ya ja su, a hankali yake tukin duk bayan mintina yana kallan Nihal Wanda sanyi AC motar ke San sata bacci, isowar su harabar asibitin yasa yaya gyara parking sannan ya b'ale murfin motar ya zagayo ya budewa Nihal, ko da suka shiga asibiti office din Dr suka Shiga dressing aka mata sannan aka mata alura wadda sai da aka sha fama dan da kyar ta tsaya, sannan Dr ya basu magunguna tunda Nihal tasha alura take aikawa yaya harara da murguda mashi baki sai faman kumbure-kumbure take a dole fushi take da shi, abinma dariya yake bashi Hakan ma da take ba k'aramin k'ara mata kyau yake ba, har suka zo Shiga mota ba Wanda yace k'ala bude mata murfin motar yayi ta Shiga sannan shima ya shige be zame da so ko ina ba sai wurin shitu me tsire a nan ya siyi tsire sannan ya shiga shagwan kusa da shi ya siyo lemo masu sanyi, ya dawo bude back seat yayi ya aje ledojin sannan ya dawo ya zauna mazaunin driver har lokacin Nihal fushi take da shi, a hankali ya daura hannuwa shi saman na Nihal dago idanuwa tayi suna kallan juna shagwabe fuska yaya yayi ya zama abin tausayi yace, "please ayima yaya hakuri a daina fushi da shi haka mana please" ya ida zancan yana shagwabe fuska dariya Nihal ta saki tana cewa, "dama manya na shagwaba yaya? " Eh mana manya na shagwaba musanman idan yaya yayi ma k'anwa laifi ya ida zancan yana Jan cheeks din Nihal, dariya Nihal ta kuma tintserewa da ita tana cewa, "amma gaskiya yan birni ke haka gaskiya mu nan kauye ba namijin dake shagwaba" murmushi yaya ya saki yace, "Dan Allah? "Allah kuwa" "tab muko birni kowa na shagwaba yayi maganar cikin sigar wasa kamar yaro washe baki Nihal tayi tace, "Kasan wani Abu yaya? " a'a sai kin fada" "gaskiya yaya ni dan birni zan aura," dariya yaya ya saki yana mai cigaba da tukin da yake yace, "alalai k'anwata ta fara zama yan'mata rufe fuska Nihal tayi ala dole tana jin kunyar yaya dariya sosai yaya yake yace, "karki damu indai dan birni ne kin samu ni da kaina zan zaba maki miji ko ki fada min irin Wanda kike so na samo maki me hankali da natsuwa wadda zai kulamin dake," murmushi kawai Nihal tayi, janta fira sosai yaya yayi har suka k'araso gida tunkafin ya Shiga da mota cikin gida Nihal ta sauka shi kuma ya k'arasa da motar ciki, bayan yayi parking ya dawo Inda suka saba zama dauke da ledoji a hannun shi sai da suka k'ara gaisawa da baba mai gadi ya k'ara tanbayar shi me jiki sannan shima ya mik'a mashi ledar dake hannu shi guda daya sannan ya k'arasa wajan Nihal wadda ke zaune tana wasa da yar tsutsuwa isowar yaya ne yasa yar tsuntsuwar tashi sama, murmushi ta saki ganin yaya zama yayi sannan ya bude Leda d'aya yace, "oya matso ki sama cikin ki wani Abu nasan kina jin yunwa washe baki Nihal yi tare da janyo ledar lafiyayan tsirene yaji albasa da tumatur da k'uli gefe guda kuma ga mango juice , wani miyau Nihal ta hadiya tare da gyara zama ta faraci hannu baka hannu k'warya yaya na kallan ta wani irin tausayin tane ya lulube shi insha Allah sai ya fida ta daga cikin wannan kuncin wannan promise yayi ma kanshi, daina cin da tayine yasa yaya tanbayar ta yace, " kanwata kar dai ki ce min har kin koshi so kike na maki dure ko," idanuwan Nihal ne suka kawo ruwa tace, "yaya inata cin dadi na manta da umma na gaskiya ban kyauta ba ko yaya,? Murmushi yaya yayi yace, " to yar umma ai umma ba taki bace ke ka d'ai nima na aje mata karki damu ki cinye wannan nakine," murmushi Nihal ta saki ta mai godiya a gaskiya bata da abinda zata ce ma yaya shiyasa ta aje shi waje na musanman ita ko tayi ma kanta alk'awari duk randa yaya ya nemi wani Abu a wajanta zata mashi sai dai inya sabawa shari'a musulinci ne ba zatayi ba. Wayar yaya ce ta fara ringing da Sauri ya miqe tare da matsawa gefe yana wayar Abu daya na karshe Wanda yace shine insha Allah 1 week na cika zan dawo zan zo maka da labari me dadi , duk da ba'a jin abinda na wayar ke cewa amma da ka lura da yanayin wayar zaka Kasan aminan junane wayar su ke cike da kauna sai da yaya ya gama wayar tsaf ya dawo yana kallan Nihal wadda har ta gama cin abinci sai kunsan yama likis sannan yaya ya rako ta kamar yadda suka saba ya bata Kudin ta cif da qari sannan ya bata ledar magunguna ta yana kallan ta har ta shige gida. Cikin k'warewa Sultan ke duba patients yana basu kulawa sosai yauma kamar kullun yana tsaye bakin gadan wani datijo smile Sultan ya saki tare da taba goshin shinshi yace, "Ahamdulillah baba jiki yayi sauki sosai insha Allah gobe zamu baka sallama kai ma ka huta da alururin da kakesha" Dan murmushi datijan ya saki yace, "amma dai Allah yasa ma albarka ya baka mata ta gari, ai k'ara na bar asibitin nan na gaji da zama kullun sai an soke min mazaune da karfan bature ina ma anfani" gyara glass din shi Sultan yayi Wanda ke mak'ale a hadadiyar fuskar shi Wanda in ka kalla sai ka maimaita kalla saboda haduwar ta Sultan yace, amma fa yauma sai namaka wata alura," jikokin baba dake gefe ne suka tintsere da dariya,drama Sultan da tsoho naba mutane dariya kwata-kwata tsohon baya San alura gashi dole ayi mashi shiyasa kullun suke shan drama da Sultan, haka yauma da kyar ya tsaya aka mashi alura, sannan Sultan ya fita daga dakin patient din direct office d'in shi ya shige tare da daukar briefcase din shi a bakin kofa suka hadu da Alex na jiran fitowar shi mik'a mashi briefcase din yayi suka tako har bakin motoci shi sannan aka bude mashi murfin motar back seat ya zauna, a hankali motocin suka bar harabar asibitin basu zame ko Ina ba se gida yana isa part nashi ya shige Barma da Sinbul na biye dashi suna k'arasowa bakin kofa yace, "Sinbul yau bana buk'atar Ku biyo ni ciki bedroom, ai ni ba yaro bane da kullun zaku rink'a bina kamar jela wai zaku shirya ni da San da bana Nigeria Ku ke shirya ni, dan wata tsirfa za'ace Ku rink'a shirya ni wannan ma ai rainine da anyi wannan amma yanzu bazan dauka ba" sannan bayin dake bakin kofa suka bude mashi kofa barma da sinbul kallo suka bi Sultan da shi suna mamakin irin halina Sultan Jan k'afafuwa sukayi suka bar part din zuwa Nasu na bayi yana Shiga kaya kawai ya cire ya shiga toilet ya Dade yana wanka sannan ya fito sanye da bathrobe da Dan k'aramin towel yana goge gashin kanshi , lotion ya janyo ya fara shafawa bayan ya kamala shafa ya gyara gashin kanshi ya kwanta luf-luf kayan da su barma suka aje mashi ya sa hannu tare da sakin Dan gutun tsaki blue shada ce tasha aiki da dark bleu zare k'ara daga kayan yayi tare da bata fuska, "nifa gaskiya ban fiya San manyan kaya ba fa sun wani aje mani shada se ka ce Wanda ze je daurin aure ko sallah juma'a mtww, Dan dai kawai da memartaba zeyi dinner da ba abinda ze ja mani sa wasu manyan kaya kiran sallah magrib da akeyi ne yasa Sultan zura kayan cikin sauri tare da feshe jikin shi da turare me sanyi da kamshin dadi dama ya dauro alwala shi a toilet, tare suka Shiga masalaci da security's din shi har se da akayi sallah isha suka dawo cikin gida. Direct men pralour ya nufa lokaci kowa ya halara a dining area dauke da sallama a bakin shi ya shigo men parlour gabaki dayan su amsawa sukayi maimartaba ne ya kuma fad'ad'a murmushin shi yana cewa Sultan har ka dawo" Eh yace ataikaice tare da kallan ammi wadda tacika fam saura kiris ta fashe, dan murmushi Sultan ya saki tare da karasawa wajan ya rungume ta baya zame hannuwan shi yar datijowar tayi, fara ce sosai kallo daya zaka mata kasan cewa Sultan jikanta ne, Dan shagwabe fuska Sultan yayi yace, "ammi am so sorry ba laifi na bane da ban zo ba dear kin ji ammi" "ni dai ka kyale in ai ka kwadamin iya kata tunda har ka iya dawowa k'asa ka kasa zuwa ganina se yanzu, yanzu ma a wajan dinner hakan is good ai" kara shagwabe fuska Sultan yayi kamar karamin yaro yana ba ammi hakuri amma tayi Biris da shi maimartaba ya kalla yace, "Abba please kasa baki a magana nan," abinci ze kai bakin shi ya tsaya yana cewa ai kunfi kusa gabaki daya dariya suka saki su basmal d'aurewa Sultan yayi yace, "kin gani ko ammi dama abinda suke so kenan nama fasa yin dinner din" ya zame hannu washi da suke sama shoulder din ammi rik'e hannuwan shi ammi tayi tace, "haba mai gida ni na isa nayi fushi da kai murmushi Sultan ya saki har dimple din shi na lomawa pack ya mata a cheeks nata sannan ya ja kujera ya zauna kusa da ita Nazili na gefe sanye take da t-shirts me santsi milk se sket black ta nade gashi ta waje d'aya daga karshan jela ya nanade ta gaba Kuma dan sisiri gashi ya zubo yana reto bakin ta sanye da jan baki, murmushi ta saki tare da mikawa Sultan plate , Basmal ce ta katse ta da cewa Nazili bani plate din nasa ma yayana abinci mika mata plate din tayi ta fara zuba mashi itama sanye take da gown red ta raba gashin kanta biyu, ( *ohni salame duka yan'matan gidan nan gashi gare su*🙄) Gimbiya jalila ce ta tabe baki cike da munafurci tace, "Hmm Sultan dai Dan gata ne kowa so yake ya faran ta mashi ai hakan na da kyau" Sultan da tunda Gimbiya ta fara magana suke kallan juna ido ciki ido kauda kai Gimbiya jalila tayi tare da kallan maimartaba tana smile, daga haka ba Wanda ya karama magana, Ashada dake gefe ya cika fan yar wuk'ar da take hannu shi wadda yake cin abinci da ita yake ta jujuya yawa jiya ke kamar ya tashi ya luma ma Sultan wuk'ar kowama ya huta. Bayan sun gama dinner kowa ya wuce part din shi Sultan da Nasim zaune suna game a dakin Nasin kallo daya zakayi ma dakin Kasan dakin Dan gatane, shafa kanshi Sultan yayi yace, "my boy dare yayi ya kamata kaje ka kwanta ba musu Nasim ya mike har bakin bed Sultan ya raka shi sannan ya lulube shi da blanket tare da yi mashi pack a goshi ya kashe haskyan dakin ya fita. Dakin ammi ya shiga ammi ya hango zaune saman bed ta jingi na bayan ta, bayin nata mata hidama ganin Sultan yasa Suka zube suna kwarsar. gaisuwa tare da ficewa murmushi ya sakar wa ammi tare da karasawa ya zauna bakin gado tare da taba goshin ammi yace, "matar amma yau baki sha maganin ki ba ko" shuru ammi tayi dan bata San shan maganin kwata-kwata, ta fara gajiya da shaye-shayen magunguna janyo bedside drower Sultan yayi yace, "magain ya b'alo wa ammi sannan ya bude Dan karamin fridge din dake dakin ya janyo robar ruwa ya tsiyaya a glass cup ya mika mata amsa tayi tare da sha tana Smile duk da bata San magani amsar cup din yayi ya aje a gefe sannan ammi ta kwanta, ja mata blanket yayi tare da yi mata pack a goshi ya fita, yana tafiya bayi na kwasar gaisuwa har ya isa part nashi bude mashi kofa akayi ya shige yana shiga ya rage kayan jikin shi saboda dama ya gaji da su kawai hakuri yake toilet ya shiga ya sakarwa kanshi shower ya fito sanye da bathrobe turus ya ja ya tsaya yana kalla Asiya baiwar shi tsaye da cup din coffee da alama yanzu ta shigo kallo da ya mata ya watsar sanye take da gown brown me stones tana sanye cikin alkyabba mara kwaliya ta karan misk ga hannu dauke da d'an karamin tray da cup a sama har ya gama shiryawar shi Asiya na tsaye kamar gunki se da ya zauna saman daya daga cikin Royal chair's din shi sannan yayi zama irin na mulki ya lumshe ido a hankali ta karaso tare da aje tray din saman stool ta dau cup din tace, cikin sanyi murya "ranka yadade ga coffee din miqa hannu yayi ya amsa yana kalla ta ta k'asan ido har yakai cup din baki shi se ya mika mata yana smile tare kallan agogan dake mak'ale a bangwan dakin yace, "amshi ki fara sha se nasha ware idanuwa waje Asiya tayi cikin in....in..a baki na rawa ran ka yadade bana tunani akwai had'a idan nasha wani Abu da cup din da kake anfani da shi" murmushi Sultan yayi har dimple din shi na lomawa yace, "Hmm aini nace ki sha yana maganar yana tsare ta da idanuwashi, amsa cup din Asiya tayi jikin ta na rawa Sultan yace, "relax Asiya" ya fadi maganar yana Jan ta ya k'ara da cewa, "kada ki kuskura ruwan tea din nan ya kife a k'asa nama fada maki" idanuwan Sultan sunyi jawur kamar garwashi lumshe idanuwa yayi kamar me bacci yana kallan Asiya ta daura cup din a baki ta, ta fara sha tana sha hawaye na wanke mata fuska jikin tane ya fara rawa cup din dake hannu ta ya fadi k'asa ya tarwatse, Sultan na kallan ta wuya ta kama tana wani irin kakari tana hawaye har ta durkushe a wajan jini ya fara bi mata hanci se da tayi wata irin shak'uwa ta fadi matata, Sultan Wanda idanuwashi sunri ne ja abinka da fara bata kafi kace mi jikin yayi jawur jijiyoyi sun fito sun mai rudu-rudu saboda bacin rai mik'ewa yayi tsaye ya maida hannuwashi bayan shi yana zagaye dakin cikin daga murya yace, " Alex!!! Alex!!!" *_kai fan's wala typing akwai wahala_*🤧 ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 *_Alhamdulillah a yaune zan cigaba da rubuta wannan littafi nawa SAUYIN RAYUWA naji dadi sosai da nuna soyayya Ku a gare ni fan's masu biyo ni private yau dai zamu cigaba wannan shafin naku ne masoya na_* *Page: 33_34* A cikin katafarin asibitin motocin suka faka Wanda daga sama an rubuta *SULTAN TEACHING HOSPITAL* se walk'iya rubutun yake a hankali daya daga cikin security's d'in shi Alex shi ya bude mashi murfin motar tare da riqe briefcase d'in sultan yana take mashi baya sauran suka dakata a harabar asibiti. ******* Nihal da yaya ke tafiya suna fira har sai da suka k'araso kwanar gida sannan ya Ciro kud'in ta cif har da k'ari ya bata, murmushi Nihal tayi tare da jerawa yaya godiya, sannan ta daga kafa a dai-dai bakin kofa taci karo da mudi wanda yasha ya bugu sai warin wiwi yake. fad'ad'a murmushin shi yayi tare da fisgo Nihal ta fada fafadan kirjin shi yana wani cije lips a razane Nihal ta dago suna kallan nuna ido cikin ido tana mutsu mutsu tana neman kwacewa a jikin shi, wani irin karfi ne ya zo mata ta bangaje shi ta shige gida da saurin tana zancan zuci, "ta rasa mike damun mudi da alama barasar da yake sha ta fara gaya mashi karya" muryar gwoggo ce ta katse mata tunani da cewa, "tunanin uban mikike ko sallama babu saboda yanzu kin k'una baki tara k'wari ko, to yayi kyau ki zo ki bani kudi na, kafin na matso nan na maki wulak'anci." gaban Nihal ne ya yanke ya fad'i da Sauri ta tura kula da yaya ya bata cikin bokitin koko ta aje a gefe, simi-simi Nihal ta k'araso ta mik'awa gwoggo kudin rank'washi gwoggo ta sakarwa Nihal a kai idanuwan Nihal ruwa suka kawo sosa kanta take Wanda take jin zafin rakwashin gwoggo har tsakar kanta, daka mata tsawa gwoggo tayi cikin kakakausar murya tace, "maza-maza ki bani guri ga wanke-wanke na can na jiran ki idan kin gama ga talla rana na jira shashashar banza," Nihal na hawaye ta qarasa wajan wanke-wankyen Wanda rana ta haska wajan tarwai babu alamar inuwa a hankali ta mik'e ta jawo ruwa a rijiya ta zuba a roba ta fara wanke kwanukan tanayi tana had'a zufa, sai da ta gama wanke-wankyen tas sannan tayi wuf ta d'auke kula dake cikin bokitin koko ta shige d'akin su da Sauri, umma na kwance saman ta barma kamar kullun sai faman zarni ke tashi saboda tasha ruwa da yawa shiyasa tayi fitsari sosai inda Allah ya taimaki Nihal batayi kashi ba, murmushi Nihal ta saki tare da jinginar da umma zaune, cikin fara'a Nihal tace cike da shagwaba, "Allah sarki umma na, nasan kin gaji da kwanciya ko ? Girgiza kai umma tayi alamar a'a k'ara fad'ad'a murmushi Nihal tayi tace, "umma kin ga abinda yaya ya bani yace muci Wanda nake baki labarin shi Dan birinin nan me hankali," cikin zakuwa Nihal ta kuma cewa kamar yasan muna fama da horan yunwa umma, gaskiya yaya na da kirki" ta idda zancan tana washe baki, murmushi umma ta saki me nuni da jin dad'in ta tace cikin sanyin murya, "Rabin raina ki dai kama kanki kinga maza ba abin yadda bane Nihal ina tausayawa rayuwar ki Nihal" Umma ta idda zancan hawaye na wanke mata fuska, daurewa Nihal tayi tare da hadiye hawayan dake mak'ale a idanuwan ta, a hankali tasa hannu tana gogewa umma hawayan ta cikin rawar murya Nihal tace, "umma bana so kina zubar da hawayan ki idan kina zubar da hawayan ki hakan na karyar min da zuciyar umma na, hakan na jefa ni cikin wani hali, nasan cewa Allah yana tare da mu umma na, insha Allah se mun fita daga cikin k'uncin nan da rashin gatan nan umma na" Nihal ta idda zancan tana had'iye wasu hawaye dake San sulalo mata, cikin rawar jiki Nihal ta fara bude kula da yaya ya bata saboda tsabar yunwar dake dawainiya da ita, lafiyayan soyayya doya ce tsoman akwai da pepper chicken a sama tun kafin su fara ci miyan su ya tsinke idan zasu iya tunawa raban da suci abinci me lafiyar haka tun Abba na da rai, a hankali Nihal ta shiga bama umma itama tanaci har suka cinye sannan Nihal ta ba umma ruwa itama tasha, tana sakin murmushi tace, "umma na bari nayi sauri na tafi talla rana kafin gwoggo ta biyo ni," "to Nihal Allah ya tsare min ke", "amin umma na" Bud'e labilan Nihal ke da wuya aka wanke ta da lafiyayyan mari har guda uku gabaki d'aya wutar jikin Nihal d'aukewa tayi tana ganin wasu taurari bin gwoggo da idanuwa Nihal tayi wasu hawaye na wanke mata fuska, se huci gwoggo take kamar kumurci wata uwar tsawa ta dakawa Nihal tace, "dan uwar ki ban hanaki Shiga da kin wannan tsinaniyar uwar taki ba idan na saki aiki ba,? in ban da wulak'anci sai kin gama taba k'azamar uwar taki sannan se ki zo ki taba min kayan sana'a," fisgota gwoggo tayi tare da wurgi da Nihal kanta ya daki bangwan tsakar gida, sulalewa Nihal tayi tare da sakin wani irin kuka me cin rai, gwoggo bata saurara mata ba, haka ta rufe Nihal da duka kamar zata kashe ta umma dake d'aki sai kuka take tana jiyo irin wulak'anci da Nihal ke fuskanta, sai da gwoggo ta mata lilis Wanda ko motsi da kyar take sannan ta sake ta, tana sauke ajiyar zuciya, cikin masifa gwoggo tace, "maza-maza ki d'auki farantin nan kafin na taka maki ruwan ciki na k'arasa ki, ita kuma uwar taki zata gane kuranta tunda saboda ita kike yin yadda kikaga dama da ba ita ai da Baki rink'a tsalake min dokokin dana shinfid'a maki ba," wani irin kuka Nihal take har murya ta bata fita jan jiki Nihal tayi tare da d'aukar faranti talla baki ta sai zubar jini yake, a haka ta fita tana dingishi jiri na dibarta. Tunda Sultan ya shige asibiti ma'aikatan asibitin ke kwasar gaisuwa fuskar nan d'aure ba alamar wasa, yana isa bakin k'ofar office din shi Alex ya bud'e mashi kofa tare da mik'a mashi briefcase din shi, ya koma wajan sauran security's d'in, lumshe idanuwa Sultan yayi tare da bin office din da kallo komai neat yadda yake so, ba k'aramin haduwa office din yayi ba in ban da sanyi AC da kamshi ba abinda ke tashi, a hankali ya k'arasa bakin table tare da aje briefcase din shi ya zauna saman kujera ya lumshe idanuwa yana juya kujera a hankali ya ware idanuwan shi janyo briefcase din sultan yayi yana k'ok'arin budewa Knocking din kofar da akeyi ne yasa Sultan saki dan guntun tsaki yana ce wa, "ai fa na dawo yanzu zan fara yawo da headache saboda takura," a Dan hassale yace, "come in" a hankali aka bude kofar office din, kyakyawar budurwa ce ajin k'arshe fara take tas tana dauke d'an siririn hanci tana da yar doguwar fusaka me dauke da baki me dan girma Wanda yasha red janbaki sanye take da alkyabba white tasha aiki da Golding zare cikin alkyabbar doguwar Riga ce a ciki Golding me zananan flowers da dishi dishin stone's se kyalkyali take gashin kanta a bude yake sha gyara da wasu flowers masu kyalkyal kala-kala se kamshi take zubawa kirjin nan cike cif yake haka hips din tama cif yake ba k'aramin kyau ta zubaba k'afar ta na sanye da takalmi me tsini har se da ta shigo tsakiyar office din sannan tayi ma bayin ta nuni da su fita, kauda kai sultan yayi tare da d'aukar allura dake saman table yana k'ok'arin fita, dai-dai setin Nazili da Sauri Nazili ta fada jikin Sultan tare da k'ankameshi, kauda kai Sultan yayi ya k'ara had'e rai yana qoqarin banbare Nazili daga fafadan qirjin shi, dan murmushi ta saki tare da zamewa daga cikin Sultan tare da nad'e hannuwa ta a k'irjin ta, tana wani jujuyawa tana k'arewa office din kallo tana wani yauk'i tace, "fushi ko? dariyar gefen fuska Sultan yayi har dimple din shi na lomawa tare da k'ara matsowa kusa da Nazili har tana Shakar kamshin turaran shi da bugun zuciyar shi me rikitata yace, " "mi ze sani nayi fushi dake umm? Kawai Dan baki zo tarbana ba, idan kin ga ana fushi da Abu to an damu da shi kin gane," ya idda zancan yana killing smile din shi me rikita yan'mata, hade rai Nazili tayi tace, "kana nufin baka damu dani ba Sultan saboda ni ba Basmal ba ce ba ko , koma dai minene nima sister din ka ce kuma se na fadi ma ammi abinda ka ce," ta idda zancan tana bata fuska, ciki calm tune Sultan yace, "ba wai ban damu dake bane Nazili halin ki ne bana so," yana maganar yana shafa lalausan gashin kanta Wanda ya sauko har kafadar ta ya cigaba da cewa, you have to change your habit Nazili," tabe Baki tayi tare da zame hannu sultan dake gefen fuskar ta tace, " yanzu dai ba wannan ba ina *Ammar* tunda kayi tafiya shima yasa k'afa ya kama gaban shi Dan bana tunanin yana zuwa ma asibiti saboda da ciwo ammi ya tashi bashi ya duba ta ba," ta ida zancan cikin yanga," yamutse fuska Sultan yayi yace, "ban tanbaye ki wannan ba, kuma muyi magana da shi nasan da tafiyar kuma insha Allah ze dawo nan da 1 week ya ida zancan yana dagawa Nazili gira, fari da idanuwa Nihal tayi ciki mulki da nuna isa tace, " "to ai shikenan tunda ka sani na d'auka shirman nashi da shashanci nashi ne ya tashi," wata uwar harara Sultan ya watsawa ma Nazili yace, "look Nazili yanzu akwai aikin da nake kuma kin San bana bari ana biyo ni office da wasu surutu you have to leave and ammar ba mate din ki bane so ya kamata kisan irin maganar da kike a kanshi duk rashin kunyar da kika mashi nima zaki min so you have to be very carefully, idan kin koma gida ki ce ma ammi am so sorry da ban shigo ganina taba, am to busy shiyasa amma idan na dawo tare zamuyi dinner" ya ida zancan tare da yima Nazili light kiss a goshi ya ficewar shi ya bar Nazili kamar gunki tsaye zama tayi tana cije lips din ta, a gaskiya guy din nan Dan rainin senses ne wai yaushe ne Sultan ze daina mata wulak'anci tana fadin zancan cikin cijewar hak'ori dafe goshin ta Nazili tayi tana ce wa dole ka soni *SULTAN SALIM* dole " a fusace ta fito daga office din bayi na take mata baya kowa na asibitin bin ta yake da kallo se Sauri take alkyabba ta na tashi sama saboda Bacin rai inda sabo ya kamata ma aikatan asibitin su saba da hali Nazili dan kullun ta zo se sunyi fada da Sultan amma har yau ta kasa yin zuciya da shi maganganun kasa-kasa ma aikatan asibitin suke. ```Taku had kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo* 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 37_38* Ba Alex ba hata bayin da ke bakin kofa se da suka tsorata da irin kiran da Sultan keyi ma Alex da sauri Alex ya bude kofar part din sultan tare da fadawa suka shigo, turus suka tsaya suna bin gawar Asiya da kallo suna kallan Sultan da sauri Alex ya k'araso gaban Sultan yana taba jikin shi wanda a lokaci Sultan ranshi a bace yake ko ufan ya kasa cewa Alex ne yace cikin damuwa, "Sultan hope dai ba abinda ya same ka? Katse shi Sultan yayi ta hanyar daga hannu ya fara magana cikin sanyin murya da nuna gajiya yace, "ina anfanin ku? babu ace duk security's din dake bakin part dinna har kofar daki na babu wanda yamin anfani, wai me yasa baza a barni na huta ba why tunda na taso da wayau na ake bibbiyata tunda ina 10 year na bar Nigeria saboda irin haka, aka kaini inda ba Wanda na sani se security's da na k'ara girma na fada ma yan'uwa inda nake tunda na fadi ban k'ara samun peace of mind ba, har rana me kamar ta yau mi yasa ake bibbiya tane why" Sultan ya ida zancan cikin sanyin murya Alex ne yayi hugging nashi yana shafa bayan shi yana cewa, "relax Sultan everything will be ok" sannan ya zauna da shi saman kujera lumshe idanuwa Sultan yayi yace, "miko min wayana iPhone din shi Alex ya mika mashi fadawa da bayin part din shi dake tsaye abin tausayi da security's Alex yace masu kowa ya koma bakin aikin shi sannan kada Wanda ya kuskura ya bari cikin gida sannan kowana su ya koma bakin aikin shi, DPO Sultan ya shiga kira bugu d'aya ya dauka tare da sallama dauke a bakin shi yace, "Ranka ya dade yau kai da kanka kake kira cikin daran nan Allah yasa lafiya" dan shuru Sultan yayi yace, "DPO Bilal ina San ganin ka ne yanzu a gida idan zaka so ka zo da yaran ka" ok kawai DPO yace, tare da katse kiran aje wayar shi Sultan yayi yana kallan gawar Asiya wadda ke kwance har yanzu cikin honey voice din shi yace, "Asiya mi yasa zaki min haka bayan se dana yadda dake cikin bayi na mata, har zuciya ta ta fara rayamin wani Abu a kanki sannan zaki min haka miyasa mutanan da nafi yadda dasu suke cutata, idan zan iya tunawa Asiya ke ce mutum ta ashirin dana kashe da hannun idan anzo kashe ni" yana yin maganar kamar Wanda ya zauto, wasu hawaye ne masu zafi suka wanke wa Sultan fuska a hankali Alex ya dafashi yana nuni ya kamata ya zama me dauriya kauda kai Sultan yayi shi kan shi yana ba kanshi tausayi yasan da cewa ko bayin dake gidan su da talakawan dake karkashin shi sun fishi kwanciyar hankali, yaushe ne zan samu *SAUYIN RAYUWA* yaushe goge hawayan shi yayi ya cigaba da kallan kyakyawar fuskar Asiya tare da lumshe idanuwan shi, shigowar DPO ce ta katse mashi tunani mik'ewa yayi tsaye tare da yima DPO iso turus DPO yayi tare da kallan Sultan ko ba'a fada mashi ba yasan tatsuniyar gizo mata wuce k'ok'i zama yayi sannan Sultan ya zauna tare da mika mashi hannu suka gaisa yace, " Bilal na taso ka dadare ko, haba-haba Sultan ai ba komai tunda dama aiki nane" nuna mashi gawar Asiya Sultan yayi tare da yi mashi bayani d'aya daga cikin yaran DPO ya rubuta statement akan abinda Sultan ya fada gyaran murya DPO yayi yace, "to yanzu ya za'ayi da gawar tunda nasan bakaso hankalin yan gida ya tashi," "da na yanke shawara ku tafi da gawar gobe se amata sutura a kaita makwancin ta, Hakan ma yayi Sultan Allah ya tsare ka daga sharin mak'iya" "Amin Bilal" "Amma fa gaskiya ya kamata security's din ka su dage, ya suke sake irin haka na faruwa" cikin honey voice din shi Sultan yace, "ba laifin su bane laifi nane dana ba Asiya yadda ta shiyasa tayi anfani da wannan damar, Toh shikenan kai ma ya kamata ka rage saurin yadda da mutane Sultan please wallahi aka rasaka anrasa babba mutum" dan smile Sultan yayi yace, "k'aramin mutum dai" "Lalala kai ke ganin haka amma mu ganin babba mutum muke ma" "Toh shikenan" "Nifa Sultan jiki na bani yake kamar wani a cikin gidan nan ke bibbiyar ka" "I think so nima, amma har yau na kasa tabatarwa" "Toh Allah ya shige mana gaba" "Amin Bilal" "Bari na lalaba na wuce sani ku dauko gawar mu fita da ita" to suka ce tare da ficewa da gawar Asiya. Sultan na zaune saman kujera har yanzu idanuwa shi a lumshi Alex ne yace, "Sultan you need to rest, be kamata kasa ma ranka tunani ba gode ma Allah ya kamata kayi, Asiya kuma kanta tayi mawa akwai yan'mata da yawa wayan da zasu so ka because of god you have to cool down my man" daga kai kawai Sultan yayi tare da hawa saman bed Alex ya ja mashi blanket ya kashe haskyen dakin ya fita ya Dade yana juye-juye kafin bacci b'arawo ya sace shi. ***** Ko da Nihal ta koma gida su gwoggo basu nan hakan ya mata dadi tana aje hijabin ta, aka fara kiraye-kirayan sallah magrib hakan ba k'aramin dadi ya mata ba ta San yau ba talla dare, alwala ta dauro ta fara jera salolin da ake binta bayan ta idar ta fito da umma da kyar ta zauna da ita a tsakar gida sannan ta shige daki, ta fara sharewa da gyarawa se da tayima dakin fes sannan tasa ruwa ta wanke simintin dakin ta fido tabarma umma ta wanke ta tas da abin shinfidar, bayan ta kamala ta jawo ruwa a rijiya ta juye a bokitin wankan ta cirewa umma kaya, ta mata wanka tare da wanke mata kai ta nanade ta da sani sannan itama ta ja ruwa ta shige toilet ta fara wanka se da ta wanke jikin ta tas sannan ta kwance dankwalin kanta gashin ta ya zubo har gadan baya sabulu tasa ta wanke gashin tas, dama duk ya ishe ta da tsami jima take kamar ta yanke shi ta huta, wani irin dadi ya lulube ta data fito wanka wani irin wasai taji idan zata iya tunawa rabanta da wanka ta kai sati biyu kunya ce duk ta rufe ta a fili tace, "yaya dai yana shan kamshi" hhhh lol😂, tana gama shiryawa aka fara kiraye-kirayen sallah isha sallah ta gabatar sannan ta janyo ledar tsiran umma dana magunguna ta sai da suka ci suka koshi har da gatsa sannan Nihal ta debo ruwa tasha magani, kasancewa yau anyi tsaf ta kuma dama gashi cikin magunguna har Dana sa bacci kafin kace mi wani lafiyayan bacci ya sure ta. *Asuba ta bari* A hankali yasa hannu ya zame blanket din dake jikin shi, tare da sauko da santala-santala kafafuwan shi k'asa wata iska ya murzar tare tura hannu shi cikin sumar kanshi yana barbazawa sannan ya mike yana kallan mirror tare riqe k'ugu, bude kofar da akayi ne ya sasa juyowa sinbul ne da barma Kansu a sunkeyi be ce masu k'ala ba ya fara cire bottle din rigar shi ya mik'a hannu Sinbul ya bashi bathrobe ya saka sannan ya shige toilet, kafin ya fito bayi mata har sun gyara part din sai kamshi yake da zanyin AC a hankali ya fito daga toilet yana goge jikin shi da k'aramin towel, yadda aka gyara dakin ya mashi kyau sosai dressing mirror ya nufa tare da zama saman sofa ya janyo lotion ya fara shafawa bayan ya gama, ya tsaya barma ya karaso riqe da suit din shi dark blue da yar riga ciki light blue riga barma ya fara saka mashi sannan ya bar Sultan yasa bottle din rigar da kanshi kusan dai da taimakwan su barma Sultan ya shirya sannan ya feshe jikin shi da turaran shi me kamshi da tsada Al-Haramain tuni dakin ya gauraye da kamshi dadi, zama yayi Sinbul ya sa mashi covered shoes din shi black, ya Allah Sultan looks breathtaking handsome, mikewa yayi Barma ya bashi briefcase din shi masha Allah wani irin kyau Sultan ya zuba ga sajan face din shi ya kwanta luf-luf dan siririn glass din shi ya zura tare da sa agogo shi silver na azurfa da zube. duk inda ya wuce bayi ke zubewa suna kai gaisuwa d'aga masu hannu kawai yake, part din Habibty ya fara shiga bayi nata hada-hada su minal cikin shirin su na zuwa school suka rugo da gudu suka rungume Sultan suna cewa, "morning yaya, morning too" pack ya Shiga yi masu d'aya bayan d'aya can se ya tsaya yana cewa, "ina Nasim? Minal ce tace, "yana dakin momi shi, ok oya kuyi sauri ku wuce school ku shafa min kan Nasim," to suka ce tare da ficewa da gudu daga parlour, k'arasawa dakin habibty yayi tana zaune saman wata kujera kamar gado tayi kwanciyar sarauta gashin ta ya baje saman kujera kayan ta sun baje har k'asa wani k'ayatacan murmushi Gimbiya Nadiya ta saki umma Sultan kenan, k'arasowa yayi tare da cewa, " habibty hannu ta mik'a mashi yayi kissing hannu tare da zama gefen ta yace, "Habibty ina kwana, shafa gefen face din shi habibty tayi tace, " lafiya lau Sultan, my boy kullun k'ara girma kake fa, kaga ammi har ta fara min magana kak'i fito da mata kayi aura" bata fuska Sultan yayi yace, "Habibty ni fa har yanzu ban shiryama aure ba har yanzu ban samu wadda hankali ya kwanta da ita ba habibty," harara wasa Gimbiya ta sakarwa Sultan tare da ja mashi kunne yar k'ara ya saki yana cewa, "aushhhh habibty am sorry" sakin kunnan tayi tace, "yadda kunnan ka yaji zafi haka nake so ka samu min inlow" d'aga kai Sultan yayi yana cewa, OK Habibty pack ya mata a cheeks nata sannan ya fita, direct part din ammi ya shiga tana dining area tana breakfast k'arasowa yayi tare da kissing forhead din ta yana cewa, "matar kinsha maganin ki kuwa harara ta aika mashi cike da tsiwa ammi tace, "bansha ba kuma bazan sha ba ni fa na gaji da wannan shaye-shayen anwani maidani kamar yar k'waya" yar dariya Sultan yayi har dimple din shi na lomawa yace, "yi hakuri please kisha kinji, Dara ya kwalawa kira wato jakadiyar gida da sauri ta k'araso tana washe baki, gaishe ta Sultan yayi sannan ya ce ta daukowa ammi magunguna ta, da sauri tashige daki ta kwasosu murmushi ya kuma saki tare da amsa yana kallan ammi wadda tayi kicin-kicin rai, balo su yayi tare da bata ruwa a cup yace, " please matar yi sauri ki hadiya" harara ta kuma watsa mashi tare da shan magunguna, pack ya mata a goshi yace, "good" ko k'ala bata ce ba ta cigaba da breakfast din ta Nazili ce ta fito sanye da wado da riga riga, orange Wando milk irin budade me kamar fantalo yadin me laushi se riga me wuya me dan fadi gefe daya kafad'ar ta ta fito, gashin kanta tayi parking nashi waje daya tasha Jan bakin hannu rike da fost milk kafar ta na sanye da takalmi me tsini irin me igiyoyin dinan sai zubaba kamshi take cikin isa take takowa komai na jikin ta amsawa yake saboda yanayin tafiyar da take, bayi na gaishe ta, tana yamutsa fuska dining area ta nufa hango Sultan da tayi tsaye ya sata sakin murmushi tare da k'arasawa wajan Sultan hannu ta zagaya a waist din Sultan tare da yin dage tayi kissing goshin shi tana smile ta dan zame jikin ta tace, morning Sultan, morning Nazili, shafa cheeks din ammi tayi tana smile ta aje fost din ta saman table tare da daukar cup din coffee ta kai baki, ammi tace, "Har kin fito, Eh Ammi na fito ta fada tana k'ara kurbar coffee, ammi ta k'ara katse da cewa Nazili amma dai ba haka zaki fita ba, ya kamata ki sa veil kafin ki fita," kwabe fuska Nazili tayi tace, " Ni fa.. Wani kallo da Sultan ya watsa mata ne yasa ta yin shuru sannan yayi ma ammi pack ya fice, Nazili ta bishi da kallo. Sara ce ta fito tana mika da misalin karfe 7:00am ware idanuwa tayi ganin murhu ba alamar wuta gwoggo ta fara kwalawa kira cikin tsiwa tana cewa, "gwoggo!! Gwoggo!!, gwoggo dake baccin gajiya jiya ce, ta tashi a zabure tana gyara zanin ta ta leko kamar an watso ta tana cewa, "lafiya Sara" murhu Sara ta shiga nunawa gwoggo wata uwar ashar gwoggo ta saki tana cewa, "kutumar uba amma yarinyan nan anyi tsinaniya kenan itama bacci take dan uwarta" Sara dake gefe tace, "shikenan gwoggo tajamin lati dama bakin ciki take da karatun nawa, ke takewa bakin ciki ko ni so take ta haram tamin cinikin safe". Ruwan randa gwoggo ta juye a bokiti me sanyi ta nufi dakin su Nihal wage labilan dakin tayi tana kallan su Nihal suna ta shara bacci bokitin ta daga ta shek'a masu su Nihal a razane Nihal ta mike umma kuma nata zare ido. ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo ``` [1/7, 2:25 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏽 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the among the rest```) *Page: 39_40* Gwoggo ce tsaye ke huci kamar kumurci tana bin Nihal da mugun kallo wadda ta jik'e sharkaf, cike da masifa gwoggo tace, "yo in ban da iskanci ke ma se kin kwanta kiyi bacci ki Hutu ko tunda ga abiyar wasan ki na bacci, maza-maza wuce ki daura ruwan koko kafin inci uban ki la'ada waje," jikin Nihal na rawa simi-simi ta rab'a ta gefen gwoggo zata wuce wani irin wawan k'uli ta sakar mata a baya har sai da Nihal ta gantsere ta fito da sauri waje kamar an tulo ta, Sara ce ta watsa mata harara cike da tsiwa tace, "wallahi tallahi naje makaranta aka min dukan lati na dawo gida kanki zan sauke, shashashar banza wadda bata San anfanin ilimin ba, mtsww kuma ga kaya na can sunyi dati ki tabata indan kin dawo daga talla ki wanke min su in ba haka ba jiki yayi tsami," idanuwa Nihal taf da hawaye ta duka tana hura wuta ko cikan ki bata ce ma Sara ba se ma umma ce da ta fado mata a rai, "Allah sarki umma na bata iya tashi bale har ta canza kaya ko ta tsane ruwan da gwoggo ta watsa masu, wasu siraran hawaye ne suka wankewa Nihal fuska da ace Abba nada rai da zasu kasance cikin gata da jin dadi Allah sarki rayuwa bayan hannun ta Nihal tasa ta goge hawaye da ke zubo mata a fuska kamar ruwa duk tana wannan zancan a zuciyar tane, a haka ruwa ya tafasa ta juyewa sara na wanka sauran ta shek'a koko da su. Duk yadda taso ta lek'a dakin su kafin ta tafi talla abin ya gagara saboda gwoggo ta kasa ta tsare tana bin ta da mugun kallo mai cike da tsana, a haka ta ja yan'mata kafafuwan ta bakin kofa taci karo da baffa yana k'ok'arin shiga gida dukawa tayi har k'asa tana gaisheshi wani kallo ya watsa mata tare da Jan dan siririn tsaki, shi wallahi har mantawa yake iyallan Habu na raye se da yaga wannan maya sannan ya tuna, haka dai zasu k'are a rayuwar su wannan fadar malam ce ya ida shiga gida, wani irin kukane ya kubucewa wa Nihal zaman dirshan tayi a k'asa tana shekar kuka Wai ita yaushe ne zata samu *SAUYIN RAYUWA* Allah sarki Abban cikin yar siririyar muryar ta Nihal tace, "Allah ya ji k'anka Abba" sannan ta tashi da kyar ta fara takawa. A harabar asibiti motocin Sultan suka faka kamar kullun, Alex ne ya zagayo ya bude mashi murfin mota a hankali ya zuro k'afafuwan shi tare da fitowa gabaki daya, cikin isa da mulki yake takawa Idan ka kalle shi se ka sake kallan saboda kyan irin na sultan da natsuwar shi Alex na biye da shi da briefcase din shi, suna isowa bakin kofa Sultan ya amshi briefcase din shi ya k'arasa cikin office. Gimbiya jalili ce zaune yakumbo na zuba mata kirari wato baiwar ta, kuma yar gaban goshin ta wadda suke hada makirci tare, tabe baki Gimbiya jalila tayi tare da gutsura Apple din da ke hannu ta yakumbo na mata massage tace, "Allah ya k'ara nisan kwana Gimbiya ba Wanda ya isa ya ja dake, ke ce a gaba ke ce a baya kinyi babakere kin hana yan' uba," wani irin murmushi Gimbiya jalali ta saki tace, "Na baki kujera makka yakumbo," godiya yakumba ta shiga jera mata daga mata hannu tayi Alamar ya isa tana murmushi tace, "kin San Matsala ta yakumbo? girgiza kai yakumbo tayi gimbiya ta lumshe idanuwa tana shakar iska tace, " Sultan shine matsala ta yaran nan Allah ya zuba mashi taurin rai kamar fir'auna, na rasa yadda zanyi naga bayan shi, kwata-kwata Gimbiya Nadiya bata dace ta zama mahaifiyar sarki ba, ni na dace na zama ki duba ki gani yakumbo ya'ya na maza biyu mace daya," "Haka ne ranki yadade" "Ita fa nadiya namijin ta daya mata biyu, wacece a cikin ta dace ta zama uwar maza" Gimbiya Jalila ta ida zancan tana lumshe idanuwa, murmushi yakumbo ta saki tace, "ranki yadade ba wadda ta dace da ta zama mahaifiyar sarki kamar ki Gimbiye" tabe baki Gimbiya jalila tayi tace, "Ni fa kashe sarki a waje na Abu me sauki ne, amma kashe Sultan shine babba tashin hankali na tun yana ciki yake zuba min taurin kai gashi kuma har ya zo duniya, dana kashe shi zan kawar da sarki Ashad ya hau kujera Mulki Nadiya da ya'ya ta mata suyi waje" ta ida zancan tana sakin dariya tare da saka faru a bakin ta murmushi yakumbo tayi tare da tasowa dai-dai saitin Kunnan Gimbiya jalili tana mata rad'a sannan taja kefe kai sunkuye murmushi Gimbiya jalila ta saki tace, "Na baki kit d'ina daya na gold" zubewa k'asa yakumbo tayi tana godiya Gimbiya jalila ta d'aga mata hannu. A hankali Nihal take takawa har ta karaso wajan da suke haduwa da yaya tun daga nesa ta hango yaya zaune saman resting chair, ba k'aramin kyau ya zuba mata ba sanye yake da jeans n tshirt Jeans din black riga white me dan k'aramin hannu gashin kan nan nashi luf-luf yasha gyara ga wani irin ni'imatacan kamshi da yake zubawa tun kafin ka k'araso wajan sa, tun da ya hango Nihal yake ta washe fararan hakoran shi k'arosawa Nihal ce ta sashi mik'ewa har lokacin Nihal kanta na k'asa, a hankali ya karaso daf da ita tare da sakin smile yana k'ok'arin sauke ma Nihal bokitin koko har a lokaci Nihal bata dago idanuwa taba, a hankali yaya yasa hannu ya dago da habar Nihal yana kallan kyakyawar fuskata, wasu siraran hawaye ne ke sulalo mata, cikin calm tune yaya yace, "k'anwata mi aka maki waya taba min ke hala gwoggo ce, mi ya sami kayan ki suka jik'a duk wannan tanbayoyin yaya yake jerawa Nihal wani irin kuka Nihal ta saki tare da fad'awa jikin yaya ta kankame shi tana sakin kuka, gabaki d'aya jiki yaya sanyi yayi, ji yake kamar an sare mashi laka tsayuwar ma neman gagare shi take, daurewa yayi ya janyo kuzarin shi cikin kasalaliyar murya yana shafa bayan Nihal tayi shuru yace, "k'anwata kiyi hakuri kinji wata rana se labari insha Allah everthing will be ok my dear kin ji" d'aga kai kawai Nihal tayi tana sauke ajiyar zuciya, sannan ta zame jikin ta daga na yaya hannuwa ta ya rik'e har suka k'araso resting chair suka zauna yaya na kallan ta cike da tausayi. Zaune yake yana dana system idanuwan shi manne da glass knocking din da ake ne yasa Sultan yace, "come in" cikin honey voice din shi sister Naja ce hannu ta dauke da files tana smile tace, "yallabai ina kwana dago idanuwa Sultan yayi tare da amsawa ya zuba wa files din hannu Naja sexy eye's ball din shi yace, " Naja ya kamata Ku fara sa tausayi alamarin nan ban gama da wasu ba se a k'aro wasu, please Ku aje sauran Idan ammar ya dawo ya amsa," "to shikenan Doctor yadda ka ce haka za ayi" "Ga files din nan na saman file din na Alhaji barau ne Wanda za'ayima operation da misalin karfe 10:00am" hannu Sultan yasa ya amsa tare da gyara zaman glass din shi ya bude file din yana dubawa sannan ya aje a gefe, tare da mik'awa Naja wasu file's din yace, ga wad'an nan na gama da su a ki kai su store ki je" "Ok" "Sannan ki fada masu doctor bashir su shirya kafin 10:00am" "OK Doctor" har tayi gaba Sultan yace, "and kema ki shirya tare zamu shiga theater room" "Toh shikenan" sannan Sister Naja ta ja mashi k'ofa ta fice. Agogo dake mak'ale a bangwan office din ya kalla kusan karfe goma saura minti 15 suit din shi ya cire tare sasauta nicktie din shi ya nanad'e hannu rigar shi toilet ya shiga ya dauro Alwala, sallah ya gabatar raka'a biyu ya dad'e yana addu'a Allah ya basu nasara kan operation din da zamuyi sannan ya sallame sallah. A hankali ya murda handle din kofar office din shi ya fice wani daki ya Shiga dake kallan office din shi, gabaki d'aya d'akin zagaye yake da mirror kowani zing d'aya yana da mirror tare da yar k'aramar loka a gefe, murmushi Sultan ya saki ganin sauran doctor's din suna shiryawa yace, "Har kun shigo kenan" bashir yace, "Eh" a takaice, makule Sultan ya Ciro ya bude loka shi sannan ya Ciro kayan da suke sawa Idan zasu shiga operation, se da ya fara cire zube hannun shi da agogo ya tura a loka sannan ya fara shiryawa, masha Allah haka suka shirya tsaf kallo d'aya zaka masu kasan sunsan abinda suke, Sultan ne ya fara fice wa sannan su bashir suka biyo bayan shi abin sha'awa, dakin da aka kwantar da Alhaji barau ya shiga Hajiya ikilima na gefe Alhaji ta zabga uban tagumi sallamar sultan ce ta katse mata tunani amsawa tayi, sannan Sultan ya tanbaye ta me jiki, da sauki tace a taikece bakin gadan Sultan ya k'arasa yana sakarwa Alhaji barau murmushi yace, "Insha Allah yau zaka samu sauki" yana maganar yana zuk'o alura dake Hannun shi, murmushi Alhaji barau ya saki yana cewa, A hankali "dana ji dadi," alura Sultan ya mashi yana murmushi sannan yazo setin fuskar shi yana nuna mashi finger's din shi daga d'aya zuwa biyar ganin bacci yayi gaba da shi yayi mu bashir magana su dauke shi, gado suka canza mashi tare da Jan wancan suka shiga theater room suna shiga red danja ta kama, hajiya ikilima se zarya take a waje Allah ya ganin tsoran aikin yan Nigeria take Dan dai ba yadda zatayi Alhaji yace se nan Wai likitin k'wararene wacece wata tsiyace, to wallahi ta dau alwashi duk abinda ya sami mijin ta kotu ce zata rabasu da asibitin. Gabaki daya yau Nihal sukuku tayi shi ba wata walwala sosai, hankalin yaya ko duk ya tashi se faman Jan ta da labarai masu dadi yake tana binshi da idanuwa, kwata-kwata yau hankalin ta yana kan umma da halin da ta barota a ciki duk shi ya hana Nihal sukuni, daura hannu washi yaya yayi saman na Nihal cikin sanyin murya yace, " k'anwata please ki daina yawan tunani karki samama kanki wani ciwo please " murmushi Nihal tayi Wanda iyakarshi lab'an ta tace, "Insha Allah yaya zan dena" "Good girl" Cikin k'warewa suke aiki baka jin motsin komai se na injina da suke aiki a jikin Alhaji barau mik'a hannu Sultan yayi Sister Naja ta bashi kayan aikin ba me cewa k'ala cikin su, bashir ne ya rik'e hannun Alhaji barau dai-dai Inda jijiya shi ke harbawa tare dagawa Sultan hannu, idan zufa ta karyo mashi se sister Naja tasa tissue ta goge mashi , se da suka gama aikin tsaf sannan Sultan yabi ya dinke Alhaji yana kallan yadda machine din ke Nuna yadda ran Alhaji barau ke harbawa, k'irjin Sultan ne ke dukan uku-uku bama shi ka d'ai ba hata sauran haka k'irjin su ke bugawa, ganin abun ya dai-dai ta ne yasa suka cire abin da ke manne a hanci su, tare da sakin a jiyar zuciya suka furta Alhmadulillah kunsan a tare murmushi suka saki tare da nufar Sultan su kayi hugging nashi gabaki d'aya suka rufe shi Dan murna. ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo ``` [1/7, 2:26 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Wannan shifin nakune fan's ina jin dadi yadda kuke nuna soyayya ku a gare ni da yadda kuke suburbudo comment hakan namin sugar irin sosai din nan_* *Page: 41_42* Ba komai bane ya janyo wannan murna ba se kasancewa su suka fara irin wannan aikin a Nigeria sakin Sultan su kayi suna murmushi, amir yace, "masha Allah we didn't" gabaki d'ayan su murna suke sannan suka chanzawa Alhaji barau gado aka fito da shi ana fitowa da shi iyallan shi suka biyo ganda da sauri Dr amir ne ya dakatar da su tare da cewa, "ku d'an yi hakuri da shiga dakin yanzu yana buk'atar hutu," daga mashi kai hajiya ikilima tayi tana hamdala gaskiya ko ta yadda da maganar Alhaji, Sultan babba likita ne Wanda yasan abinda yake, direct waiting room suka wuce da Alhaji barau tare da sa mashi k'arin ruwa da manna mashi oxygen, sannan suka fito suna ta sakin smile. Room suka shige kowa ya cire kayan theater dake jikin shi, bashir ne yace, "you guys ni fa banyin break ba I am Hungary wallahi," Amir yace, ",Nima yunwa nake ji duk da madam ta bani break kafin na fito" Dan siririn tsaki Sultan yaja yana wanke hannu shi a zing yace, "Ku dai kun fiye raki se kace ba maza ba se cin tsiya ko auki baku k'arawa" Sister Naja tace, kai ma ka gani yallabai se ci ba auki" tabe baki amir yayi yace, "Ni fa ban San surutu kowa ya samu guri ci zeyi" bashir ya daga kafad'a yace, "aiko dai" Sultan yace, "ok muje muyi break din first se kowa ya koma bakin aikin shi," a tare suka jero abin sha'awa suka wuce gun cin abinci, suna isa suka sami seat suka Zauna bashir da amir founded yam with egusi soup aka kawo masu, Sultan da Sister Naja fish pizza da cottage pie with coffee, cikin natsuwa suke cin abinci, Amir ne ya katse shurun da cewa, "Sultan wai ina ammar ya je ne? nayi missing nashi kuma ina kira wayan shi baya shiga," "Ya tafi range har yanzu be dawo ba nima na rasa mi ya zauna dashi haka, kamar be so ya dawo" bashir da amir ne suka had'a baki wajan cewa, "ko dai yayi new crush ne" hhhhhh, "I don't think so, kauye ne fa kawai se ya rasa ina zeyi new crush se a kauye" Sultan ya fada yana goge bakin shi da tissue, dariya su bashir suka saki tare da cewa, "idan tayi tsami zamu ji" sannan suka tashi kowane su ya koma bakin aikin shi. Yau ma kamar kullun yaya har kwanar gida ya rako Nihal, yana kallan ta har ta k'urewa ganin shi, dauke da sallama ta shigo gida gwoggo da dilaliya na zaune saman kojera tayani Gulma suna cinikin wasu kaya, har k'asa Nihal ta duka ta gaishe su, kallo daya dilaliya ta mata ta watsar gwoggo ko hannu ta mik'a alamar ta bata kudin ta kudin ta irgo cif ta mik'a mata har se da ta hada da hannu Nihal wajan amsa Dan masifa, hanyar daki Nihal ta nufa gwoggo ta daka mata uwar tsawa tace, "ina kuma zaki bayan ga wanki na jiran ki dalla malama wuce ki fara aikin gaban ki," kallan kayan wanki Nihal tayi tana mamaki irin yawan su tun daga na gwoggo har na baffa dana Sara zata wanke gobe kuma na mudi na jiran ta, bakin rijiya ta dawo tana jan ruwa kafin ta fara wankin. Sultan na fitowa harabar Asibiti yan' jarida suka mai cha kasancewa labari ya kai masu a kan aikin da yayi ma alhaji barau babba d'an siyasa mai fada aji, ganin haka ne yasa security's din sultan suka k'araso suna kare shi gudun kar a samu matsala har ya shige mota, a hankali motocin suke tafiya har suka iso gida mai gadi ya wangale masu gate shugowar motocin yayi dai-dai da shigowar motar Nazili bale murfi mota tayi, ta fito tare da k'arasawa bakin kofar motar Sultan bale murfin motar yayi ya fito, kallo d'aya ya mata ya watsar yayi gaba, cikin siririyar murya ta Nazili tace tare da rik'e kugu tace, "Sultan" cak ya ja ya tsaya tace, "amma dai kasan haka nan ba zan zo na tsaya bakin kofar mota ba ko ina san muyi magana da kai ne," juyowa Sultan yayi ya watsa mata wani kallo na baki da hankali yace cikin honey voice din shi, "yanzu ne lokaci da ya dace muyi magana, ke makauniya ce? yanzu na dawo daga office idan ke baki gaji ba to ni a gajiye na dawo kin gane mtsww," Jan dan siririn tsaki Nazili tayi tare da shigewa part din ammi da sauri, ammi dake zaune saman three star Nazili ta zo wucewa rai bace ko Kallan inda ammi dake batayi ba ta nufi bedroom din ta, ammi ce tace, "Nazili cak taja ta tsaya bata juyo ba, ammi tace, " waya b'ata maki rai naga kin shigo rai bace," Nazili tace, ba kowa," "Amma shine se ki shigo rai b'ace kuma ko sallama babu" juyowa Nazili tayi a hasala cikin daga murya cike da rashin kunya tace, "Na ce maki ba komai amma sai wani tanbaya kike a'a tsohowa da ke amma se San jin k'wak'waf" sannan Nazili ta juyo tana kallan baiwar ta Aziza tace, "se nace ki bude min kofa zaki bude mtsww" da sauri Aziza ta bude mata kofa tare da bin bayan ta, ammi ko girgiza kai tayi ta rasa ranar da Nazili zata daina wannan zafin kan ko da yake k'uruciya ke dibar ta. Rungume Sultan da kayi ta bayane yasasa sakin murmushi tare da janyo Basmal ta dawo gaban shi tana facing nashi tace, "yayana gabaki daya kamata da little sis naka ko" ta ida zancan cike da shagwaba shafa cheek din ta Sultan yayi yace, "Sweetheart ba laifi na bane laifin aiki ne gabaki d'aya ya rik'e ni har yanzu ban samu Hutu ba amma kin ga gobe weekend muna tare kijin" murmushi Basmal ta saki tare da cewa to yayana sannan ta mashi pack a goshi tace, "yayana lunch na jiran ka a men parlour nasa an dafa ma abinda kafi so," murmushi Sultan yayi har dimple din shi na lomawa tare da lumshe idanuwa sannan ya d'an ja cheeks din Basmal yana cewa, "shiyasa nake ji da ke little sis kin San favorite thing's d'i yayan ki, Allah ya baki miji na gari musha biki" rufe fuska Basmal tayi tare da sakin dariya ta rab'a ta gefen Sultan ta wuce, girgiza kai Sultan yayi sannan ya k'arasa Shiga part nashi. "Ki zo ki cire min takalman nan sun isheni" Nazili ta fada cikin Jan magana duk'awa Aziza tayi tana cirewa Nazili takalmi bayan ta gama cire mata Nazili ta cire kayan ta tare da mik'a hannu Aziza ta bata towel, kwata-kwata Nazili bata jin kunyar cire kayan ta gaban bayi wani lokacin ma su take cewa su cire mata saboda tsabar sangar ta da mulki Nazili ta rai na kowa a gidan, Sultan ne ka d'ai ke gyara mata zama shima dan tana bala'in San shi kuma tana ganin k'war jinin shi se kuma maimartaba su ka d'ai take gani da gashi toilet ta shiga tare da zura santala-santalan k'afafuwan ta cikin kwamin wanka tare da zame towel din jikin ta lumshe idanuwa Nazili tayi cikin ruwan tana tuno irin kyau da k'war jini na Sultan gabaki daya Sultan ya gama tafiya da ita, hango irin yadda Sultan yake smile dimple din shi na lomawa hakan ba k'aramin tafiya da imanin ta yake ba, gashi da body building kamar shi yayi kanshi, ware idanuwa tayi tare da cigaba da wanka kusan wanka duk da tunanin Sultan tayi shi sannan ta fito sanye da bathrobe kan ta nanad'e da towel zama tayi d'aya daga cikin Royal chair's din ta, ta lumshe idanuwa ko bata fada ba Aziza ta gane massage za'a mata k'arasowa tayi ta fara yi mata massage a hankali gefe ga fruit ana mata tana sha, ware idanuwa Nazili tayi tana kallan Aziza tace, "Aziza ni da Sultan ko mun da ce? Washe baki Aziza tayi tace, "fadi barna baki, Gimbiya ai wallahi kun da ce musanman shi Sultan din shi za'a cewawa yayi dace da samun zuk'ek'iyar budurwa kamar ki ga kyau ga ilimi, aiko shi yayi dace babba" far da idanuwa Nazili tayi tare da gutsara gwaba da ke hannu ta. Cikin shirin shi Sultan ya fito na Jean's n t-shirt, t-shirt din black me d'an k'aramin hannu jean's blue, ba k'aramin kyau ya zubaba kafar shi na sanye da Booth black, se shek'i yake, direct garden ya wuce, ihu bayi maza ke tashi, iya kar haduwa garden din ya hadu ko ina malale yake da grass carpet, gefe guda kuma swimming pool ne da kujerin shan iska, gefe d'aya kuma kujeri ne na Alfarma, ihu da aka kuma sawane ya janyo hankalin Sultan wajan ya nufa inda fadawa da bayi ke shewa da alamar abinda ake na masu dadi, murmushi Sultan ya saki ganin Ashad ne ke wasa da wuk'a tare da fadawa majiya karfi duk Wanda ya bige se ya fadi ya cinye shi se bayi da fadawa ke shewa, saboda haka aladar wasan yake, suna ganin Sultan suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa, hakan ne ya Ankara da Ashad kallo d'aya Ashad yayi ma Sultan ya watsar, gabaki d'aya bayin gurin suka dauka da cewa Sultan ya shigo suyi da Ashad daga masu hannu Sultan yayi yace, to murmushi Ashad ya saki Wanda iyakar shi laban shi, zaro wuka Sultan yayi ya Nufo Ashad yana smile, fara wasan wukar suke cikin k'warewa Wanda Ashad da gaske yake binshi da wuk'ar ganin abin Ashad da gaske ne yasa Sultan wani irin juyi tare da dukan habar Ashad hakoran shi da lips din shi suka hade ya tafi taga-taga Sultan ya kaima k'irjin shi duka da wuka ya fadi k'asa warwas, sultan ya bishi da wuk'a a wuya suna kallan juna ido cikin ido kowana su na maida numfashi murmushi Sultan ya saki irin na rainin wayau yace,"aushh" ya taba gefen bakin Ashad Wanda jini ya fara zuba, ihu fadawa ne ya dawo da su Sultan murmushi Sultan ya saki tare da mik'awa Ashad hannu ya mik'e, bubuga bayan Ashad yayi ya matso dai-dai satin kunnan shi kamar me rad'a yace, "har yanzu da sauran ka, tsakanin ka da *SULTAN SALIM* akwai tazara mai tsaho" sannan Sultan ya biki kafad'ar Ashad yana shu'umin murmushi ya k'ara gaba ya bar Ashad yana binshi da mugun kallo me cike da tsana . Yau dai Nihal tasha wanki sosai dan kusan se yama likis ta gama tana shanya aka fara kiraye-kirayen sallah magrib, ruwan dauraya ta juye a maguji sannan ta shige dakin su, dakin in ban da wari ba abinda yake da sauri ta k'araso kusa da umma, tausayin umma ne ya kama Nihal da kyar Nihal ta janyo umma waje sannan taja ruwa a rijiya ta juye abokiti tayi ma umma wanka, sannan ta shige dakin su ta gyara shi fes, gurin umma ta dawo ta dafa jikin umma, zafi jikin umma yayi rau sakwamakwan ruwan da gwoggo ta shek'a masu ya haifar wa umma da zazzabi, hakan ne yasa Nihal rudewa tana, cewa umma na zazzabi ke damun ki sannu kin ji da kyar ta ja umma ta maida ta daki, sannan ta debo ruwa tare da b'alo panadol taba umma tare da k'ara tab'a goshin ta tace, "sannu umma na" sannan Nihal ta fita waje dan dauro alwala. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 43_44* Daran yau daga umma har Nihal ba Wanda ya rintsa saboda zazzabi dake damun umma a hankali Nihal ta daura kan umma a saman cinyar ta, tana shafa kanta Wanda jikin yayi rau kamar garwashi, wasu hawaye ne ke sulalowa Nihal tana sa bayan hannun ta tana gogewa kwantar da umma tayi ta fita ta debo ruwa ta dawo ta dau zani ta nufo umma tare da maida ta bisa cinyoyin ta tana danna mata ruwan a hankali tana cewa, "umma sannu kin ji Allah ya baki lafiya" se dai umma ta daga kai ita ka d'ai tasan abinda take ji. Sultan nashiga part nashi wanka ya sake ya fito sanye da bathrobe da dan k'aramin towel yana tsane jikin shi knocking din kofar da a keyi ne yasa shi tsayawa da goge gashi kanshi yana kallan kofar, cikin honey voice din shi Sultan yace, koma waye ya jira ni a parlour na gama shiryawa jin hakan yasa, khalifa tsayawa a parlour tare da zama saman kujera ya b'oye wuk'ar dake hannu shi cikin riga, janyo lotion Sultan yayi ya shafa sannan ya bude wardrobe ya curo fara jalabiya me kyau ya saka masha Allah tuni kyan Sultan ya fito, yayi kyau kamar balarabe sannan ya feshe jikin shi da turare a hankali ya bude handle din kofar daki tun da ya hango khalifa yake sakin murmushi tare da k'arasowa cikin takun shi na mulki hannu wanshi na hard'e a baya, da sauri khalifa ya mik'e kan shi a k'asa yace, "Ranka yadade barka da wannan dare dama na zo na taya ka hira ne," Murmushi Sultan ya saki yana bin khalifa da kallo yace, "amma fa ka kyauta khalifa, se dai kuma kash main parlour zani dinner yau sweetheart tasa an dafa min favorite food dina, ko zamu je tare muyi dinner tare? Murmushi khalifa ya saki yace, " ranka yadade ban dade da cin abinci ba na gode da tayin ka, Allah ya k'ara maka tsawan cin rai," gajeran murmushi Sultan ya saki yana kallan khalifa yace, "mu tafi ko" Sultan na gaba Khalifa na baya zaro wuk'ar yayi har ya d'aga ze cakawa Sultan wuk'ar ya ga alamar ze juyo se ya maida wuk'ar yana maida dawa Sultan ya juyo yana murmushi ya matso kusa da khalifa kamar me rad'a ya rungume shi tsam a jikin shi yace, "a duk inda kake ka iya takun ka, saboda mak'iya na zagaye da kai , so dayawo ana kashe mutum ta hanyar Wanda ya yadda da shi, amma ka sani mutane da yawa nayi ma kallan biri kai kuma kanayi masu na ayaba shiyasa nake san ka, kasancewar ka jarumi, " Sultan ya shafa k'ungu shi yace yana sakin murmushi, "saboda kullun kana yawo da makamin saboda mak'iya idan nine kai da mindiga zanyi yawo" wani irin miyau khalifa ya had'iya me d'aci, take a nan jikin shi ya fara rawa, amma se yayi ta maza ya daure yana murmushi yak'e, Sultan ya katse shi da cewa, "idan mak'iyin ka ya shigo gidan ka idan kai ne mi zaka mashi,? baki khalifa na rawa yace, "kashe shi zanyi" dariya Sultan yayi yace, "Ni bana kashe mak'iyi a ranar farko se a rana ta biyu" sannan Sultan ya kakab'e rigar khalifa yana shu'umin murmushi yace, "muna iya tafiya" jiki a sab'ule khalifa ya fito duk se ya ji ya tsani kanshi. Direct main parlour Sultan ya wuce lokaci kowa ya halara a dining area shi kad'ai ake jira, dauke da sallama a bakin shi ya shigo Gimbiya jalila dake zaune sai da tasha jinin jiki ta, tana bin Sultan da kallo Jan kujera yayi tare da zama kusa da ammi yana murmushi yace, "ya dai matar na ga duk kin wani bi kin tsure ko tsoran kar na ce ki sha maganine," yana maganar yana kallan Gimbiya jalila ko ba'a fad'a mata ba tasan wannan magana da biyu akayi ta an jefi akuyar kishiya, murmushi maimartaba yayi yace, "Ku dai baku gajiya kai da ammi," murmushi ammi tayi tana jawa Sultan kumatu tace, "wannan bokan turan wallahi ya ishe ni," basmal tace, "mu dai bamu shiga tsakanin Ku, ka shiga kasha kunya" tana maganar tana saving din Sultan waina da biyar taushe wadda taji yan'ciki da kaji da naman rago ga man shanu ya ji, tun kafin ta ajewa Sultan ya fara lashe baki yana cewa, "sweetheart wannan shagalin duk ni ka d'ai gaskiya zan baki tokwici," murmushi basmal ta saki tana aje mashi plate din, Nazili da mom suka hada baki wajan cewa wannan abun har da San kai shine kika wareshi shi kad'ai kika mashi wannan shagalin ko," Nasim yace, "nima yaya zanci" minal tace, "nima" ita da shukura suka had'a baki wajan fad'i dariya Basmal tayi tana cewa, "ai shi yayana be san cin abinci shiyasa na yi mashi favorite nashi ko ya samu ya ci," Ashad dake gefe sai aika masu da harara yake da ya sannan da wannan abinci da guba ze sa mashi ko shinkafar b'era yaci ya mutu, a haka suka gama dinner din wasu na farin ciki wasu zuciya cike da mugunta. Bayan sun gama dinner Sultan ya ruk'o hannu ammi suna tafiya suna tab'a hira har suka k'araso dakin ta ta zauna saman sofa tana cewa, "Sultan wai yaushe ne zaka kayi aure ka ga mun zuba maka idanuwa amma har yanzu shuru, naga alamar ma maimartaba be damu da zancan kayi aure ba ya zuba maka na mujiya, hade rai Sultan yayi tare da daura kan shi saman cinyar ammi yana cewa, " shi fa aure lokaci ne ni har yanzu ban samu wadda ta kwanta min a rai ba," ture shi ammi ta shiga daga cinyar ta tana cewa, "kai kullun aka yima maganar aure se ka hau wa mutane wasu jawabi, ko dai baka da lafiya ne? dariya Sultan ya saki yana Jan bedside drawer yana cewa, "lafiya ta lau ammi garas nake lokaci dai nake jira" yana maganar yana balo mata magani, duka ammi da kai mashi ya goce tana cewa, "ja'iri indai da gaske kake mu gani a k'asa," to Sultan yace yana mik'a mata glass cup ta amshi glass cup din ta kora magani, Sultan yayi kissing goshin ta yace, "matar Allah ya baki lafiya" tace, "ameen," sannan ya fito. direct part nashi ya wuce yana shiga bedroom ya iske night dress din shi saman bed zurawa kawai yayi ya fad'a bed yana tunanin maganar da ammi ta mashi, shi kan shi be samu peace of mind ba yama za'ayi yayi aure, shi kwata-kwata aure baya gaban shi ma yanzu hasali ma mata haushi suke bashi tunda Asiya taci amanar shi, aka had'a baki da ita wajan kashe shi, watsar da zancan yayi bacci me dadi yayi awangaba da shi. Sanyi-sanyin Asubane yasa umma yin bacci gyara mata kwanciya Nihal tayi sannan ta fito ta dauro alwala ta koma ta gabatar da sallah bayan ta idar ne ta sake tab'a jikin umma har yanzu jikin da zafi amma ba kamar jiya da dare ba. Fita tayi ta fara aika ce aika canta na yau da kullun kasancewa yau wanki jiya zata k'arasa dan haka yau ba talla, ruwan koko ta daura sannan ta koma bakin rijiya tana Jan ruwa, se da ta gama cika ko ina na gidan sannan ta shek'a koko ta juyewa su gwoggo nasu abokiti ta d'ibi nasu, ta d'umama tuwo ta aje da sauri ta kwashe Nasu ta kai daki tana fitowa suka hade da gwoggo ko kallo bata ishe ta ba ta dau kayan kalacin su ta shige daki, sauke ajiyar zuciya Nihal tayi ta koma dakin su lokaci umma ta tashi murmushi ta saki tare da jinginar da umma ta zuba koko a cup ta fara ba umma kurba d'aya zuwa biyu umma tayi fara kakarin amai sai da ta amaye kokon tas tana mai numfashi. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 45_46* sannu Nihal ta shiga jirawa Umma da sauri fita ta dauko ruwa da tsunma ta goge ma umma jikin ta, sannan ta goge k'asan dakin tana cewa, "Umma sannu kin ji Allah ya baki lafiya, anjima ina samu dama na fita zanzo maki da maganin zazzabi ki samu ta sauka sannu," tana maganar tana taba goshin umma Wanda yayi zafi sosai har zata mik'e umma tace, "Nihal cikin raunaniyar muryar ta dawowa Nihal tayi ta zauna tana k'ak'aro murmushi da iyakar shi laban ta, cikin sanyin murya umma tace, "Allah yayi maki Albarka Nihal Allah yasa ki gama da duniya lafiya, insha Allah Nihal rayuwar bazata cigaba da zama a haka ba jiki na, na bani se kin zama wani Abu a duniya, ni fata na dake a duk inda kike ki zamo mai gaskiya da ruk'wan Amana, nasan cewa ke Nihal macece mai hakuri amma ina so ki k'ara a kan Wanda kike yi," jikin Nihal ne yayi sanyin wasu hawaye suka zuba mata cikin rawar murya tace, "umma na Dan Allah ki daina fad'a min irin wannan kalaman suna sani shiga rud'ani" Nihal ta ida zancan tare da sakin kuka ta k'ank'ame umma tana cewa, "insha Allah umma na zaki samu sauki wand'an kalaman da kike fadi tare zamu cigaba da yin su bani kad'ai ba tare zamu rayu" Nihal ta k'ara she maganar tare da fashewa da kuka, umma idanuwan ta taf da hawaye take girgizama Nihal kai alamar tayi shuru, tana cewa, "bana so naga kyakyawar d'iyata tana kuka umma na tare dake Rabin rai na kijin insha Allah zan samu sauki har na fara tafiya da k'afafuwa na kuma har naga jikoki na" dariya Nihal ta saki tana goge hawayan ta da bayan hannun ta umma kuma ta kafe ta da idanuwa tana murmushi, sannan Nihal ta tashi tare da daukar tsumma da robar ruwan ta fita, fitowar ta keda wuya aka wurgo mata wasu kaya masu cike da warin giya dana wiwi ko ba'a fad'a ba tasan na mudi ne, Sara ce rik'e da kugun tana yan' harare-harare tace, "malama ga kayan yaya se a samu damar wanke su, ba wai kije ki tsaya gaban shingin gawa ba," wani irin kallo Nihal ta watsawa Sara saboda bata had'a kowa da umma ba, itama gwoggo tana d'aga mata kafa ne saboda matsayin ta a gurin ta da kuma girman dake tsakanin su shiyasa idan ta taba umma take shuru, "keeee!! Malama wakike watsawa irin wannan kallan? karya nayi ne uwar taki ba shingin gawar bace," Nuna ta Nihal tayi da yatsa tana cewa, "duk irin rashin mutuncin da zaki min zan dauka, amma ban da ki tab'a min uwata shuru-shuru magana ce game hankali dan ina shuru ina kyale ki ba shi ze baki damar cima uwata mutunci ba," sannan Nihal ta matso daf da Sara idanuwan ta taf da k'wala sunyi jawur kamar gar washi, matsawa Sara tayi saboda abin da Nihal keyi ya fara bata tsoro sannan tace, "idan yau na so dole Ku had'a ina Ku ina Ku, ku barmin gida saboda gidan nan na uba nane bana uban ki ba, kuma kud'i na kika ci kika girma ba da kud'in uban ki ba idan baki sani ba yau ki sani shashashar banza" fitowar gwoggo daga kewaye ne yasa Nihal sakin kuka tana tatare kayan da Sara ta watso mata, mamaki cika Sara yayi bata tab'a tunanin Nihal na da baki ba se yau Ashe itama ta iya munafirci kenan tab akwai Jan aiki a gaban su, lalai kam ya kamata ta fad'awa gwoggo abin da Nihal ke cewa bayan idanuwan ta, tsawar da gwoggo ta dakawa Nihal ce ta dawo da Sara daga duniyar tunanin, gwoggo cike da masifa tace, "yau ga yar iska yarinya kuka uban mi kike tun da safe sai ka ce uban wani ya tab'a ki ko wanki mudin ne bakiyi yanzu inci uban ki la'ada waje" shuru Nihal tayi tare da aje kayan mudi bakin maguji. A hankali ya yaye lalausan blenket din dake jikin shi yana kallan sinbul da barma da suke gyara mashi wardrobe, a hankali ya sauko daga saman bed yana cewa Sinbul cikin muryar bacci da sauri suka k'araso gaban Sultan harara ya watsa masu, yayi ma barma nuni da ya matso kai a sunkuye ya matso kusa da Sultan nanade hannu riga gashi Sultan yayi yace, "duk'a" duk'awa Barma yayi Sultan ya saki karfin shi ya sakarwa barma k'uli yana cewa, "na hana ana shigo min bedroom lokaci da ina bacci Baku ji ko cikin masifa Sultan yace, "oya sinbul kai ma zo nan" raraba idanuwa sinbul yake yana cewa, "Ranka yada....! Janyo shi Sultan yayi ya sakar mashi k'uli tare da ja masu kunne yana cewa, "gobe ma idan ina bacci Ku shigo" ya jasu kiii!!! har bakin kofa ya wurgo su parlour kamar kayan wanki yace, "stupid kawai" sannan Sultan ya wuce bathroom ya dade yana wanka sannan ya fito sanye da bathrobe da d'an k'aramin towel yana goge jikin shi, direct gaban dressing mirror ya tsaya lotion ya fara shafawa sannan yasa hand dryer ya busar da gashin shin tare da shafa mashi mayuka masu kamshi da sa gashi kyali masu tsada, wardrobe ya bude ya curo kayan shi jeans n t-shirt, rigar Apple green colour se jeans blue cikin natsuwa ya shirya tare da gyara sajan shi ya kwanta luf-luf masha Allah tuni Sultan ya fito yayi kyau lips din nan na shi yayi kamar ansa Jan baki sannan ya saka booth nashi black masu kyau, masha Allah he looks handsome, a hankali ya bude handle din kofar Dara ya hango da sauran bayi suna jera mashi breakfast a dining kasancewa yau a part nashi zeyi break, suna ganin sultan suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa har ya iso dining babu Wanda ya dago cikin su se jakadiya Dara, murmushi Sultan ya saki tare da jan kujera yana, "cewa ina kwana Dara," "Lafiya lau ranka yadade" "Ina matar kina dai kula min da ita ko? Murmushi Dara ta saki tana saving Sultan chips with pepper soup din yan'ciki, tana cewa, "Eh amma yau se da nasha fama da ita kafin ta sha magani" tana fadin zancan tana turawa Sultan plate a gaban shi, "Wannan tsohowar akwai rigima"Sultan ya fad'a yana amsar coffee a hannu Dara cikin natsuwa Sultan yake breakfast din shi suna tab'a hira da Dara kasancewar jinin su ya zo d'aya da jakadiya shiyasa har Sultan ke tsayawa suyi hira musanman yadda take kula mashi da ammi duk duniya bayan mahaifiyar shi to ammi ce mace ta farko da yafi so duk wani abin da take so Sultan na nema mata ko da hakan ze sa shi ya cutu musanman da take fama da hawan jini Abu kad'an ze b'ata mata rai jinin ta ya hau shiyasa Sultan ke nema mata farin ciki duk inda yake, bayan ya kalama breakfast din direct part din maimarta ba ya wuce. Dauke da sallama a bakin shi ya shigo fadar maimartaba, maimartaba yana zaune da waziri suna tattaunawa murmushi sarki ya saki shi da waziri har k'asa Sultan ya tsugunna yana gaishe su, maimartaba yace, "yau kuma shigar yahudawan a kayi kenan" dariya Sultan ya saki tare da zama, waziri yace, "ai su basu ganewa manyan kaya sunfi yi masu kyau," Maimartaba yace, "Ai k'ara Ammar naga shi yana d'an k'ok'arin kamantawa amma shi wannan dayasa ze fara raki wai zafi, se kace kan shi turai ta dira," shi dai Sultan bin su kawai yake da idanuwa kawai se yasa manyan kaya se ka ce Wanda ze je sallah juma'a ko daurin aure saboda su kawai ya siyi manyan kaya, waziri ne ya katse mashi tanani da cewa, "tunda ammar yayi tafiya Sultan shima ya dauke k'afa a gida na Adda har tayi maganar ta gaji," Sosa keya Sultan yayi yana cewa, "Wallahi Abba aiki ne ke rik'e ni tun da nima na dawo yau ne d'ai na samu Hutu insha Allah zan shigo mu gaisa da Adda ka ce mata ta daina fushi dani" dariya waziri yayi yace, "ai kunfi kusa" Maimarta ba yace, "aiko dana San Ammar zeyi wannan dad'ewar dana matsa wa governor sosai a kan maganar yin titi na akauyan nan dan gabaki d'aya titinan sun ji jiki" "Kuma kaga ze tsaya har a gama ya dawo" "Ai yanzu lokaci ya k'ure tun da naji ka ce jibi ze dawo" murmushi Sultan ya saki ji yayi kamar an zuba mashi ruwan sanyi da aka ce jibi ammar ze dawo, da har ya fara tunanin ya bishi yaga waca uwar yake a kauyan har kusan wata, har shi ya dawo shi yana can kauye, sun dad'e sosai suna hira sama-sama sannan Sultan ya masu sallama ya fita. Yana fitowa suka had'e da Basmal tana sanye da riga da wando, rigar pink jeans blue kan nan nata yasha gyara tayi parking nashi waje d'aya bakin nan yasha jan baki tasha kyau sosai, kafafuwan ta na sanye cikin booth White tace, "yayana tun dazu nake Neman ka na kira wayan ka baya shiga, murmushi Sultan yayi yace, " "Bama na iya tuna ina na aje phone din," "Yayana nasa an gyara mana dawaku nan mu" "Wow sis kamar kin San abinda ke rai na kenan muje toh," Direct wajan aje dawaku na suka nufa wani k'atan doki ne fari tas tunda ya hango Sultan yake haniniya yana tsale da alama murna ganin Sultan yake, gefe kuma brown doki ne be kai girman na Sultan ba, Jan linzamin dokin Sultan yayi yana shafa wuyan shi yana cewa, "I miss u Azir," sannan Sultan ya hau dokin basmal ta hau nata a hankali suke tafiya da dawaku nan cikin filin da aka tanada dan wasa da dawaku na su. Bayan Nihal ta gama wanki dakin mudi ta shiga ta gyara shi tsaf sannan ta fito, dakin su ta shiga ganin halin da umma ke ciki ne yasa Nihal k'arasawa wajan umma da sauri tana k'walawa umma kira cikin kuka, inban da jijiga ba abin umma keyi farin kunfa na bi mata baki Nihal tace, "na shiga uku umma" wani irin kuka Nihal ta saki tare da fita da gudu tayi dakin gwoggo, gwoggo na zaune tana yankan akaifa Nihal ta fad'a dakin ta rike kafafun gwoggo tana kuka tace, " gwoggo umma dan Allah gwoggo ki taimaka mu kai umma asibiti dan Allah" tana maganar tana kuka har da majina "ko taimaka min kar umma na ta mutu," fisge k'afar ta gwoggo tayi cike da masifa tace, "ta mutu mana se mi dan ta mutu ko ke bank'i ki mutum ba aikin banza kawai ai dama gawace tak'i rami ko karya nayi mtsww," ta ida maganar tana kallan Sara kuka Nihal ta kuma saki duk ta rud'e da gudu ta fito daga gidan ko takalmi babu tana kuka gidan su jummala ta nufa kofar gidan kule kuka Nihal ta saki tana cewa, "na shiga uku umma na bazaki mutu ki barni ba wallahi ki ka mutu bin ki zanyi" yayane ya fad'o mata a rai, gudu ta cigaba dayi har ta k'araso gidan yaya baba mai gadi ta wuce da gudu ta shiga gidan shima bin bayan ta yayi, ammar dake zaune a parlour da alama waya yake yana kallan news, sanye yake da three quite black da fara t-shirt banko kofar Nihal tayi ta shigo tana kuka ta riqe k'afafun yaya tana kuka tana cewa, "yaya dan Allah ka taimake ni umma na ba lafiya dan Allah" tana maganar tana kuka mik'ewa ammar yayi tare da mik'ar da Nihal, car key din shi dake saman stool ya dauka tare da Jan hannun Nihal ta na kuka baba mai gadi da ya biyo ta jin abin da ta fad'a ne yasa shi yin sauri yaje bude gate, cikin mota suka shige ya ja motar da sauri yana tuk'in yana kallan Nihal wadda ke kuka kamar ran ta zai fita, dai-dai kofar gidan su yaya yayi parking, b'ale murfin motar Nihal tayi da sauri ta fito yaya ya bi bayan ta shima cikin sauri, gwoggo dake tsakar gida tana daka se ga su Nihal sun shigo wata uwar ashar gwoggo ta saki tana cewa, "wannan Gardin kafirin fa ina kika samu shi har ya shigo mana cikin gida? ba Wanda ya tanka mata suka shige dakin yaya ya dauko umma cak suka fice Nihal na kuka, back seat yaya ya aje Umma Nihal ma ta shiga back seat din tana kuka har a lokacin umma kyar ma take yaya ya ja Mota. A dai-dai harabar Asibiti yaya yayi parking suka fito da umma suna shiga asibitin aka amshe ta duk da asibitin kauye ne likito cin sunyi k'ok'arin ba ma umma kulawa, Nihal ko k'asa ta zame tana sakin kuka jikin ta in ban da rawa ba abin da yake ita kanta tana buk'atar likita ya dubata, a hankali yaya ya k'araso ya dafa kafad'ar ta yana cewa, "insha Allah umma zata samu sauki addu'a zaki mata Allah ya bata lafiya ba kuka ba Nihal," d'aga mashi kai kawai Nihal tayi ta na sauke ajiyar zuciya. Fitowar doctor ce tasa Nihal da yaya mik'ewa da sauri har suna yar rige-rigen tanbayar jikin umma Nihal tace, "ya jikin umma na? Goge zufa dake goshin shi doctor yayi yana bin su da kallo ba Nihal ba hata yaya k'irjin shi na dukan uku-uku, " Doctor yace, "am sorry to say Hajiya Allah yayi mata rasuwa se dai kuyi hakuri," wani irin ihu Nihal ta saki taci kwalar likitan tana cewa, "wallahi k'arya kake umma na da rai na shiga uku innalillahi wainnailaihiraju'un wallahi karya kake wasa kake ko," janyo ta yaya yayi jikin shi yana cewa, "Nihal" kuka Nihal ta saki har da majina tana cewa, "wallahi yaya Karya yake ka ce ya bani umma ta" juyo da fuskar ta yaya yayi suna kallan juna yana girgiza mata kai take a nan Nihal ta sulale.....🙆🏽‍♀ ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo ```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 47_48* Take a nan Nihal ta sulale sumamiya yaya rud'ewa yayi yana cewa, "Nihal ki tashi ka da ki barni" daukar Nihal akayi cak Dan a bata taimakwan gagawa, kwatar da ita kayi tare da k'ara mata ruwa sannan doctor ya tabatar wa yaya sumane tayi zata iya farfad'o kowani lokaci hamdalla Ammar yayi sannan ya wuce d'akin da aka kwatar da Nihal kwance take fuskar ta tayi fayau se busasun hawaye dake kwance a fuskar ta lumshe idanuwa yaya yayi tare da zama kusa da Nihal. Bayan sun gama wasani da dawaku na, direct Sultan dakin shi ya wuce ya sake wanka sanye da towel ya fito se d'an k'aramin towel yana goge jikin shi lotion ya shafa sannan ya shirya cikin three quite brown da white armless gashin nan nashi ya kwanta luf-luf, ya feshe jikin shi da turare me k'amshi, part din mom ya wuce tun da ya shigo bayi ke kwasar gaisuwa d'aga masu hannu kawai yake ya wuce bedroom din Gimbiya Nadiya, zaune take saman sofa baiwa na mata massage gefe kuma ga fruits tana sha, murmushi mom ta saki ganin Sultan a hankali ya k'araso yayi mata pack a goshi cikin honey voice din shi Sultan yace, "mom sannu da hutawa" "Yauwa Sultan" Gimbiya Nadiya nuni tayi ma baiwar ta data basu guri mik'ewa tayi kai a sunkuye ta fita Sultan yace, "wash mom na gajiya" Sultan ya fad'a yana daura kanshi a cinyar mom murmushi mom ta saki tare da shafa lalaushan gashin kan shi tace, "mi ya saka gajiya haka" Dan tabe baki Sultan yayi cike da shagwaba yace, "doki kawai na hau" murmushi mom ta saki tana cewa, "son karfa ka zama rago" d'an tasowa Sultan yayi yana kallan mom ya langwabe kai yace, "mom rago no no gaskiya Sultan ba rago bane ko mom," light kiss mom ta mashi a kumatu tace, "Nima da wasa nake tana fadin zancan tare da maida kan Sultan bisa cinyar ta tace, " "yauwa Sultan tun d'azu Nazili ke Neman ka tana so kuyi magana" tabe baki Sultan yayi yace, "Ai tasan inda nake ni zanma bita kenan," "Haba son wai mi yasa kake haka ne kai da k'anwar ka itama fa kamar su Basmal take tunda d'iyar k'anin baban ka ce amma kullun baka fad'in magana me dadi a kanta, kai dai na lura duk Wanda ya damu da kai kafi mashi wulaqanci," kwab'e fuska Sultan yayi cike da shagwaba yace, "Ni fa ba wulaqanci nake mata ba, daka sakar mata fuska se ta nemi ta raina ka" ja mashi kumatu Gimbiya tayi tana cewa, "kai kuma baka San raini Allah ya nunamin matar ka Sultan nasan se tasha fama da halin ka wallahi" Hmmm kawai Sultan yace, tare da gyara kwanciyar shi a jikin Gimbiya. "Yakumbo wannan shawara taki har yanzu tak'i ci ni fa na fara gajiya da jiran kawar shanu, yakumbo," "Ki kwantar da hankalin ki Gimbiya komai ze tafi dai-dai kamar yadda na fad'a maki," D'aga mata hannu Gimbiya jalila tayi tace, "kin ga yakumbo zan baki dama ta k'arshe Idan dai har naji shuru da hannu na zan kashe shi komawa ya huta" "Haba rai ki yadad'e ai kwata-kwata aikin nan be dace dake ba k'ara ki bari mu muyi ko nasa ayi," d'an siririn tsaki Ashad ya saki yana cewa, "Na lura yakumbo sanyin takewa aikin nan idan har bazata iyaba a barmin komai a hannu na tunda dama ni ya shafa ba Ku ba" harara Gimbiya jalila ta maka mashi tare da cewa, "wato mu baka dama salan kaje kayi sob'ancin naka har a gane kai ka aika ta, ko kuma ya kashe ka yayi mursisi se dai kawai a neme ka a rasa kamar yadda aka rasa Asiya mtsww," "Momi wai mi kika dauke ni? ku bani dama Ni kuma nayi maku promise se kunga gawar Sultan ko kuma yaji jiki ko be mutu ba" dariya suka saki na mugunta momi tace, "to shikenan na baka dama ai dama barewa bazatayi gudu ba d'anta yayi rarafe" haka suka zauna suna k'ula makirci suna warwarewa. A hankali Nihal ta ware idanuwan ta kalaman doctor na dawo mata kamar a mafarki mikewa tayi zaune tare da cire k'arin ruwan da ake mata, sakowa tayi daga kan gado a hankali tana dakawa saboda jikin ta ba k'wari wasu hawaye masu zafi na bin kuncin ta, tana bude k'ofa taci karo da yaya Wanda ke k'ok'arin shigowa hannu shi dauke da ledar magunguna, kallan-kallo sukewa juna su cikin raunaniyar murya hawaye sirara na bin fuskar Nihal tace, "yaya Dan Allah ka ce min mafarki nake ba gaskiya bane abinda kunne na ya ji , ka ce min umma doguwar suma tayi," Nihal ta ida zancan tare da zamewa a k'asa tana gunjin kuka hannuwa ta had'e kamar me neman gafara, a hankali yaya ya duk'a ya d'aga Nihal tsaye ya zaunar da ita saman gado sannan ya tsugunna ya rik'e hannuwan Nihal suna facing din juna yace cikin sanyin murya, "Nihal na san cewa ke musulmace ya kamata kiyi imani da k'addara mai kyau da Mara kyau Nihal, duk wani me rai mamaci ne ko umma bata rasu yau ba dole wata rana zata rasu, ke kanki baki wuce Allah ya dauki ran ki ba Nihal umma ba abinda take buk'ata a wajan ki se addu'a Nihal ba kuka ba, yima mamaci kuka be da wani anfani kin ji" daga kanta Nihal tayi wasu hawaye na sulalo mata, sannan yaya yace, "tashi mu tafi " to Nihal tace tare da mik'ewa Yaya ne ya bude mata murfin mota sannan shima ya zagayo ya shige, a hankali yake tukin yana yi yana kallan Nihal wadda ta rakub'e gefe d'aya tun da suka doso hanyar gida ta fara hango mutane, wasu siraran hawaye ne suka zubo mata, yaya na parking Nihal ta b'ale murfin motar tare da fashewa da kuka sakwamakwan ganin gawar umma za'a mata sallah inna jummala ce ta rungume Nihal kuka Nihal take sosai sannnan ta jata zuwa cikin gida yaya kuma yabi yan kai gawa, gidan cike yake da yan amsar gaisuwa har da yan'uwan umma wayan da ta dad'e bata gansu ba, gwoggo ko sai kukan munafirci take kamar gaske, haka shima bangaran baffa se share k'wala Gulma yake. Kusan duk yinin yau Sultan a part din mom yayi shi kiran Sallah magrib ne ya sasa ya fito daure da alwala, direct ya wuce masalaci se bayan sallah isha Sultan ya dawo, part din ammi ya wuce dauke da murmushi ya shigo ammi na zaune saman three star Nazili na zaune saman one star tana shan coffee sanye take da pink doguwar Riga dai-dai gwiwa se gashin ta da ya zubo har gadan baya, a hankali Sultan ya zauna saman three star kusa da ammi murmushi ammi ta saki tana cewa, "ya dai mijin" tana maganar tana shafa gashin kan shi, murmushi Sultan yayi yace, "lafiya lau ammi fura na zo sha" "Toh shikenan, Nazili d'akowa Sultan fura," har se da ammi ta k'ara maimaitawa sannan ta dawo daga duniyar tunani saboda tun da Sultan ya shigo take kallan shi saboda irin Kyan da ya k'ara mata, cikin isa ta mik'e tare da kawo fura ta ajewa Sultan sun dad'e suna fira da ammi sama-sama yana shan fura Nazili na Dan tsoma bakin ta, Sannan yayima ammi se da safe tare da manna mata kiss a goshi. A hankali yake takawa duk Inda ya wuce bayi na gaishe shi jin kamar ana bin shi a bayane ya sasa tsayawa tare da waigowa ganin ba kowa bayan shi ya sashi cigaba da tafiya, fisgo shi akayi da karfi tare da to she mashi Baki rigima suka Shiga yi yana kiciniyar bude fuskar Wanda ya to she mashi Baki , beyi auni ba yaji an Luma mashi wuk'a har so biyu zaro idanuwa Sultan yayi duk da zafin da Sultan ke ji be hana shi zaro wuk'ar dake cikin shi ba yana maida numfashi ya lumama wadan ya Luma mashi wuk'ar yana k'ok'arin bude mashi fuska ban kad'e sultan yayi tare da Jan jiki ya bar wajan da Sauri, da kyar Sultan ke bin Bango rike da cikin shi yana maida numfashi Alex ne daya hango Sultan a sukwane ya sasa saurin k'arasowa tun kafin yayi magana Sultan ya fad'a jikin shi sumame ```Taku hat kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 49_50* D'ago da fuskar Sultan Alex yayi yana jinjiga shi yana cewa, "Sultan...!!!! Cikin d'aga murya gabaki d'aya gidan se da ya amsa da muryar Alex Daukar Sultan yayi cak fadawa na biye da shi, Sinbul ne yayi sauri daukar waya Dan kira Doctor, tuni labari abinda ya faru ya gwaraye gidan sarki da gidan waziri, waziri na kwance yana bacci matar shi na mak'ale a jikin shi ya fara jin bugun k'ofa zame Adda yayi daga jikin shi tare da mik'ewa a hankali ya nufi k'ofar ya bud'e ganin bafadan shi Hassan ne yasa waziri zuba mashi idanuwa yana saurare cikin rawar murya yace, " Ranka yadad'e Sultan," be ida jin Sauran bayani ba ya koma ciki ya sanyo kayan shi Adda na cewa, "lafiya" tabi bayan shi cikin sauri suka nufi cikin gidan sarki, sarki na zaune da Gimbiya jalila a turakar sa kasancewar yau ita ke da kwana tana ta zuba mashi kisa da kisisi na k'wankwasa kofar da akayi ne yasa Sarki zame jikin shi daga na Gimbiya jalila kasancewa suna like da juna light kiss ya mata a lips din ta sannan ya mik'e, jin alamar takowar shi yasa waziri wangale kofar kanshi a k'asa idanuwan taf da kwalla yace, "ran ka yadad'e Sul....!! bakin sarki na rawa yace, " don't you tell me wani Abu ya sami d'ana" Sarki ya fad'a cikin d'aga murya, bakin waziri na rawa yace, "mai...!! D'aga mashi hannu sarki yayi tare da komawa bedroom ko ta kan Gimbiya jalila be biba mik'ewa tayi tana cewa, "lafiya kuwa ran ka yadad'e ? Alkyabba shi ya zura yana ce mata, "Sultan ne ba lafiya," waro idannuwa tayi tana cewa, "bari na biyo ka" ko saurara ta beyi ba ya fice fadawa na take mashi baya, yana fita Gimbiya jalila tayi far da idanuwan ta ta bushe da dariya tare da fad'awa saman bed tayi d'ai-d'aya tana cewa, "aikin ka na kyau Ashad Ashe dai d'ana bana wasa bane jar uba hhhhhh, duk wannan maganar a fili take yin ta alkyabba ta janyo da sauri ta daura ta saman night dress din ta, ta murza idanuwan ta dan sunyi ja tana fitowa suka had'e da yakumbo far tayi mata da idanuwa tare da sakar mata murmushi kusan dai duk maganar da sukayi da idanuwa da baki sukayi ta saboda tsabar mugun hali. Bangaran Sultan doctor Amir har ya zo ya fara bashi taimakwan gagawa dan Sultan ya zubar da jini da yawa sannan Dr amir ya mashi dinkin har a lokaci Sultan be San inda kanshi yake ba, sannan Dr amir ya daure mashi cikin da bandeji, Maimarta ba na isowa umma Sultan ta, ta fad'a jikin shi tare da sakin kuka tana cewa, "kaga za'a kashe min Sultan d'ina maimartaba" ta ida zancan tare da k'ank'ame sarki, rungume ta sarki yayi tsam a jikin shi yana shafa bayan ta yana cewa, "shhh ya isa insha Allah Sultan will be ok my dear," Gimbiya jalila da isowar ta yanzu ganin yadda sarki ya k'ank'ame Gimbiya Nadiya se da hakan ya b'ata mata rai kukan munafirci itama ta saki maimartaba ganin haka yasa ya dafa goshin shi yace, "Oh Allah" janyo Gimbiya jalila yayi itama fad'ad'an kirjin shi yana lalashi su haka sukayi lamo a jikin shi Gimbiya jalila ko yau zuciyar ta Fes ba tak'i Sultan ya mutu a daran yau ba kowama ya huta fitowar doctor amir ne ya katsewa Gimbiya Jalila tunani da Sauri maimartaba ya k'arasa yana cewa, "ya jikin Sultan? Dan murmushi Amir ya saki tare da cewa, "Alhamdulillah insha Allah daya farfad'o komai ze zama Normal," murmushi sarki ya saki yana cewa, "masha Allah" sannan suka d'unguma suka shige dakin Sultan Wanda yake kwance bema San duniyar da yake ba. Labari na kaiwa ammi hawan jinin ta ya tashi har se da Doctor Amir ya dubata tare da yi mata Alura bacci jakadiya Dara na zaune da ita, Nazili na kwance Azizi ta bude kofar bedroom din ta a hankali ta Shiga tashin ta, a hankali Nazili ta bud'e idanuwan ta cike da masifa tace, "lafiya malama kin zo kina tashi na daga bacci da wannan daran ni sa'ar ki ce," Jikin Aziza na rawa ta zayanewa Nazili abinda ya faru, A zabure Nazili ta janyo sleeping robe din ta tasa tare da nanad'e gashin ta, ta fita daga bedroom d'in da ta sauri, a dai-dai shiga part din Sultan ta hade da Basmal da Minal da Shukura suna sharbar kuka zasu shiga itama kukan take Nasim ne kawai babu da Ashad, Nasim ko nisan bacci yayi Ashad ko yana can hankali kwance, suna shiga dakin Sultan bakin bed din shi Suka nufa, maimartaba yace, "ya kamata kowa ya koma part nashi tunda Sultan abin ya zo da Sauki" sannan ya kira waziri tare da sheda mashi yana so abin ci ko mashi koma waye yake kawowa Sultan hari tun yana k'aramin kuma wannan karan ya d'au alwashi ba inda ze fida Sultan se dai ayi kare jini biri ji da masu kawo mashi hari kuma duk wanda ya kama da sa hannu shi a gidan se ya fuskan ci horo mai tsanani . Da kyar jabir ya k'araso wajan Ashad yana dafe da ciki yana maida numfashi a hankali zame abinda ya rufe fuskar shi da shi yayi, kan shi Sunkuye yace, "Ran ka yadad'e" juyowa Ashad yayi tare da zame hula Alkyabba dake kanshi yana shu'umin murmushi, ganin halin jabir yake ciki yasa Ashad had'e rai tare da cin kwalar jabir cikin huci yana cewa, "karka ce min ba abinda ya sami Sultan, yanzu na aika ka lahira tunda kai ka kasa" dariya jabir ya saki duk da zafin da yake ji ya zame hannu Ashad daga Wuyan shi yace, "ban tab'a zuwa aiki na dawo ba nasara ba kuma bazan fara a kan Sultan ba" yana maganar yana cije hak'ora ya cigaba da cewa, "se dai wannan jarumi ne munyi kare jini biri jini nasan yanzu in dai ba'a kawo mashi d'auki gagawa ba nasan ya mutu, so d'aya ya caka min wuk'ar ji halin da na Shiga bale shi har sau biyu kuma da karfi na, na caka mashi" dariya Ashad ya bushe da ita yana shafa gemun shi kamar na bunsuru yace, "aiki ka yayi kyau jabir'' jakar kudi Ashad ya mik'awa jabir yana cewa, komai da komai na cikin jakar gobe da Asuba flight din ka ze tashi sannan ka tabata ba Wanda ya San wannan magana zan turo ma da likitan sirri ya duba ka ga car key dina akwai driver a waje yana ganin ka ze gane," sannan ya bibigi kafad'ar shi yana cewa, "Good job my man" ya maida hula Alkyabba shi ya bar wurin da sauri. *Washe gari* Yau sadakar uku da rasuwar umma sai dai mu ce Allah ya ji k'anta yan'uwan umma ne zaune a parlour baffa su duka har dama baffa Aunty Aisha ce tayi magana kasancewar daga umma se ita se k'anna su maza biyu Aunty Aishi a birni kano take aure kuma mijin ta d'an kasuwa ne yana da rufin asirri cikin sanyin murya aunty Aisha tace, "mi zai hana tunda umma ta rasu abani Nihal mu tafi birni tare zan bata kyakyawar kulawa kamar yadda zan ba ya'ya na" gwoggo ce ta rushe da kuka tayi tsale ta dire ta ce ba inda Nihal zata, tabar dangin uban ta koma na uwar ta to mi akayi kenan, baffa ne ya share kwalla munafirci yace, "Haba Aishatu kika dauke min Nihal ai baki kyauta min ba ita zan rink'a gani ina jin sanyin ina tunawa da d'an uwana, Aisha karfa ki manta mu ka d'ai ne ke Raye se diyar Dan uwan nawa idan kin ga Nihal ta bar hannu na to se dai aure na mata" baffa ya ida maganar yana rushewa da kukan k'arya, Nihal dake gefen aunty Aisha wasu hawaye na wanke mata fuskar tabas yau ta tabatar da tsanar da su gwoggo suke masu itama so suke bak'in cikin su ya kashe ta kamar yadda ya kashe umma kuka Nihal ta saki sosai tare da fita daga pralour da gudu, gwoggo tab'e Baki tayi tana zancan zuci, da Nihal ta je birni ta waye tayi wayau k'ara ta nak'asa ta, ko tun wuri su samo wani kwakin su bata, Aunty Aisha ce ta katse mata tunani da cewa, " toh shikenan baffa naji maganar ka kuma na tausaya maka Allah ya ji k'an magabata, sannan insha Allah zan rink'a waiwayar Nihal dani da su khabir sannan in baza Ku damu ba Nihal zata rink'a zuwa mana Hutu birni" kad'a kai baffa yayi yace, "indai wannan ne baku da wata matsala kuma ai Nihal d'in yar ku ce, Dan dai ban iya jurewa rashin ta kusa da nine" ya ida zancan yana matsar kwalla kad'a kai aunty Aisha tayi tare da curo dubu ashirin a jaka ta, ta mik'awa baffa se faman antayo mata godiya yake sannan suka fito direct dakin da Nihal ta shiga aunty Aisha ta bita jiki ba kwari, a hankali ta dafa Nihal d'ago rinanin idanuwan ta Nihal tayi tana kallan aunty Aisha, murmushi Aunty Aisha ta saki Wanda iya karshi lab'an ta ta janyo Nihal jikin ta, ta daura kanta saman cinyar ta tana cewa cikin sanyin murya, "ban san Nihal d'ita da rashin tawakali ba, kuma basan Nihal d'ita da karya ba, bana so ki boye min duk abinda ke damunki Nihal ko bakya jin dadin zama da su baffa ne? idan har haka ne ni kuma na maki alk'awarin daukar ki mu tafi ko da hakan ze janyo cece kuce," murmushi Nihal ta k'ak'oro tana kallan aunty Aisha tace, "babu abinda su baffa ke min kawai dai ina kewar umma nane, kuma naso na biki ko Dan naga su ikilima," kallan ta Aunty Aisha take tana San karantar wani Abu amma Nihal tak'i bata fuskar hakan tashi tayi tare da janyo trolley d'in ta, sannan ta curo takada ta rubuta number wayar ta tace, "Nihal ga wannan number ta ce duk abinda ke damunki ki kirani ki fad'a min kinji d'iya ta," d'aga kai Nihal tayi sannan ta amshi trolley din a hannu Aunty Aisha suka fito su gwoggo na tsakar gida, washe da baki gwoggo tace, "Allah ya kiyaye hanya" "Ameen" har bakin kofa gida Nihal ta rako ta su baba khabir na tsaye bakin kofar mota, murmushi baba khabir ya saki yana cewa, "k'araso mana yar leleta" murmushi Nihal ta saki idanuwan ta taf da hawaye ta shige jikin baba khabir, shafa kan ta yayi yace, "insha Allah da anyi hutun makaranta zanzo daukar ki muje Hutu ko," Nihal dake ji kin baba khabir mamaki ne ya kamata saboda irin k'aryar da baffa ya sharto mashi zame jikin ta, tayi tana murmushi tace, "toh baba" "Yauwa yar albarka" baba sani yace, "Ni wallahi Nihal d'in duk sai naga ta wani yamutse ta k'oke" ya fad'a yana kallan aunty Aisha tabe baki tayi tace, "Hmmm" tare da mik'awa baba sani trolley Aunty Aisha ta mik'awa Nihal 1k cikin hannu ta tace, "gashi kin sha sweet" bude baki Nihal tayi zata mata godiya, daura yatsanta Aunty Aisha tayi tare da girgiza mata kai murfin mota suka bude suka shige, Nihal nata d'aga masu hannu har suka k'ule sannan Nihal ta soke dubunta a zani. Bayan Ashad ya tsala wanka ya wuce dining area yayi break yau zuciyar shi fes kamar anzuba mashi k'ankara goge bakin shi yayi da tissue ya wuce part din Sultan hannu shi dauke da kwalbar guba wadda idan yasa ma Sultan a ciwo, ciwo zai cigaba da girma har ya mutu, yana isa bakin kofar parlour Sultan ya watsawa fadawa harara jiki na rawa suka bude mashi kofar ya shige ba abinda parlour keyi se kamshi turare da k'ara AC dake tashi murmushi ya saki na farin ciki ya nufi dakin Sultan, yana bude kofar ya hango Alex zaune saman sofa ida shigowa Ashad yayi tare da watsawa Alex wani irin kallo hannuwan shi na zube a Aljihu yace, "zanyi magana da yayana privacy ya kamata ka bamu guri" tabe baki Alex yayi yace, "bacci yake" harara Ashad ya maka mashi yace, "a hakan nake so ka bani guri, saboda bana zama waje d'aya da matsiya ta" se da Alex ya zo zai wuce Ashad se kuma ya dawo yace, "be carefully kar wani Abu ya biyo baya bayan ka fita," ya ida maganar yana kallan Ashad tsoki Ashad ja tare da nufar bakin bed din Sultan, ya zauna yana kai aika mashi da harara yana shafa gemun shi, Sultan dake kwance idanuwan shi lumshe eye's lashes din shi sunyi Zara-zara a hankali ya bude kwalbar ya dibi maganin ya nufi saman ciwo Sultan da maganin, rike a hannuwa shi akayi kam gaban Ashad ne ya yanke ya fad'i, ware idanuwa shi Sultan yayi suna kallo-kallo da Ashad murmushi Ashad ya k'ak'aro yace, "bros ya jiki" smile Sultan yayi yace, "da sauki" "Masha Allah" mik'ewa Ashad yayi tare da daukar cup yana had'a coffee, Sultan na binshi da idanuwa Ashad yace, "yaya kwata-kwata banji dad'i wannan Alamari ba" yana fad'a yana jeba sugar me k'waya a tea, Sultan yace, I think shima Wanda yamin haka shima yana can yana jinya, sannu baya hana zuwa se dai a dad'a ba aje ba wata rana da hannu zan kama Wanda ke aiko min su," tabe baki Ashad yayi yace, "aiko dai da se nafi kowa murna da wannan rana," d'an murmushi gefen fuskar Ashad yayi yace, "Na ji kamar waziri na cema maimartaba Azir ya mutu jiya saboda ya ci guba" a zabure Sultan ya mik'e ya ce wani Azir d'in? kake nufi karka ce min doki na" tab'e baki Ashad yayi yace, "waka sani Azir bayan dokin ka" dafe ciki shi Sultan yayi tare da sa sleeping robe din shi ya fice da sauri, dariya Ashad ya saki yana cewa, "huhuhu yanzu muka fara," sannan ya aje cup din coffee a table tare da bin bayan Sultan, sultan yana fitowa parlour Alex dake zaune saman three star ya mike tare da rik'e hannun Sultan yace, "Sultan what wrong" zame hannu Alex Sultan yayi ya fice yana d'ingishi, kallo Alex ya bi Ashad da shi yace, "mika fad'a mashi? Alex ya fad'a cikin d'aga murya tsawa Ashad ya daka mashi yace, heeee!!! ya nuna shi da yatsa yace, " ya kamata Kasan matsayin ka malam, fad'a mashi halin da dokin shi yake ciki nayi saboda ban ga anfanin b'oye mashi ba nonsense mtwss" sannan ya bala ma Alex harara janyo shi Alex yayi ya mak'ure shi a bango fisge hannu Alex yayi ya fita yana gyara kwalla rigar shi, Duk Inda sultan ya wuce bayi na kwasar gaisuwa wasu na Gulma saboda a yanayin daya fito direct wajan kiwon dawa kunan gidan ya nufa waziri da sarki ne a tsaye a wajan se fadawa, gefe d'aya kuma dokin sultan kwance yana hawayan wahala likitan dabobi na duba shi, da sauri ya k'arasa wajan tare da duk'awa yana shafa dokin idanuwan shi jawur waziri ne ya d'aga shi yana cewa, "take it easy Sultan" yana magana yana shafa gashin Sultan, maimartaba ne ya ja hannu shi kamar sakar ya bi maimartaba har fadashi Suna isa Sultan ya fashe da kuka tare da fad'awa jikin maimartaba yana cewa, "why all this Abba mi yasa laifi na ke shafar abinda nake so why Abba me yasa aka haife ni tunda ansan ba'a so na Sultan ya k'ara rushewa da kuka shafa bayan shi maimartaba yake yana cewa, "sorry Sultan be are strong man my son kuka Sultan yake yana sauke ajiyar zuciya yana magana a hankali yace, "I hate Nigeria Abba da duka mutanan dake cikin ta toshe mashi baki maimartaba yayi tare da zaunar da shi sannan ya daura kan Sultan a cinyar shi yana shafa gashi Sultan yana cewa, "take it easy ban sanka da saurin karaya ba Sultan be are man my boy" shi dai Sultan yayi lamo yana sauke ajiyar heart. Wanke-wanke take bakin maguji gwoggo na gefe tana tsintar wake, almajiri ya shigo dauke da Sallama a bakin shi yace, "wai yaya na sallama da Nihal," gwoggo dake tsintar wake ce ta tsaya cak tace, wa... !! Bata ida maganar ba Nihal tace, ka ce mashi ina zuwa hannu ta, ta tsame daga cikin ruwan d'auraya ta janyo hijabin dake saman igiya, gwoggo tace, "gidan uwar wa zaki? Ko saurara ta Nihal ba tayi ba tasa k'afa ta fice, tsaye jikin mota Nihal ta hango yaya har se da gaban ta ya fad'i saboda yanayin data gashin sanye yake da farin yadi me sharara yana sanye da b'akar hula yasha kyau har ya gaji murmushi Nihal ta saki Wanda iya karshi lab'an ta gaishe da yaya tayi ya amsa fuskar shi dauke da fara'a yace, " ya muka ji da hakuri," "Hakuri angode Allah" Dan jum kad'an yaya yayi yace, "kin ganin zuwan bazata ko? d'aga kai Nihal tayi alamar Eh, murmushi yaya yayi yace, " wallahi tafiya gida ne ya taso min yau da tun ranan zan tafi to se ga rasuwar umma ya hanani tafiyar da niya ta se gobe zan koma, to se d'an uwana ba lafiya kuma bana iya hakuri se gobe, " hawayan dake mak'ale a idanuwan Nihal ne suka sulalo yanzu shima yayan tafiya zeyi ya barta duk tana maganar ne a zuciyar ta yaya ne ya katse mata tunani da cewa, "duk abinda kike buk'ata kiyima baba mai gadi magana, idan kin kai mashi abinci kamar yadda kika saba ze baki kudin kin ji, insha Allah zan dawo ba zan wani dad'e ba kin ji k'anwata" yana maganar tare da bude back seat ya curo Leda viva ya mik'awa Nihal amsa tayi hawaye na wanke mata fuskar girgiza mata kai yaya yayi alamar tayi shuru sannan ya bude murfin mota ya shige yana d'agawa Nihal hannu itama tana d'aga mashi cike da tunanin Nihal ya d'au hanya da kewar Nihal duk'ewa Nihal tayi a wurin tare da sakin kuka. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```we are the best among the rest```) *_godiya gare ku masoya na abin alfahari na ina mik'a gaisuwa a gare ku masoya, wannan littafi nima ina sanku irin sosai din nan damu biyo ni ta private da masu comments ta group duk ina gaishe ku wannan shafin naku ne kuyi yadda kuke so da shi_* *Page: 51_52* Gidan waziri shirya-shirye ake sosai na tarbar ammar se hada-hada bayi suke suna kai kawo, waziri ne ya fito yana gyara zaman rawanin shi tare da kallan Adda yana murmushi yace, "yau fa ba zama tunda ammar ze dawo ko shirya ni kin kasa yi nama fara kishi," Murmushi Adda ta saki tana cewa, "haba ranka yadad'e ni na isa nak'i shirya d'an tsoho miji na kawai dai ina so in ya dawo ya ji dadi tarbar da zan mashi tunda ya dad'e baya gida," "Kuma fa haka Dan gaskiya kuni ina missing din ammar," "Yauwa dama ina so anjima na lek'a Sultan da jiki" "Toh shikenan, ni wallahi yaran nan tausayi yake bani ace aita farautar ran mutum kamar wata daba" "Nima dai abin nan na daure min kai ran ka yadad'e ace aita Abu yak'i ci yak'i cinyewa kamar cin k'wan makauniya" "Ke ma dai kin fad'a bari na k'arasa fada" "A dawo lafiya Allah ya tsare min kai" "Ameen Gimbiya ta" Bayan Nihal ta sha kukan ta ta gaji ta ja jiki , ta shige gida, wani irin mugun kallo gwoggo da Sara suka watsa mata gwoggo tace, "uban waye shi Wanda ya zo duba ki,? har nake jin ana fad'i mashi wani suna," shuru Nihal tayi tana raraba idanuwa tana wasa da yatsun hannuwanta, wata uwar ashar gwoggo ta antaya mata tare fisgo ta, ta warce ledar hannu ta, ta fara kila ta tana cewa, "wato abokanan watse warki wajan talla har sun fara biyo ki cikin gida, aiko uwar ni zanci" duka Nihal take kamar Allah ya aiko ta tanayi tana masifa, mudi ne da shigo warshi yanzu yabi gwoggo da Nihal da kallo tare da tanbayar lafiya gwoggo na haki ta d'ago, Nihal ko ta samu ta runtama da gudu d'aki tana kuka gwoggo tace, "ai wallahi indai ni dake ne yanzu muka fara yo in ba iskanci ba, a ce har aboka nan watsewar ta sun fara biyo ta gida wato wata rana a gaban idanuwan mu za'a ci ko," mudi ko tunda gwoggo ta fara magana ya Lula duniyar tunani Ashe dama Nihal yar hannu ce alalai dama ya dad'e miyan shi na tsinkewa musanman yanzu da yan'matan ci ke bayana a jikin ta ba komai ke tafiya da imanin shi ba kamar hips din ta da d'an k'aramin bakin ta lumshe idanuwa yayi tare da kad'a kai shima k'wallan shi ta kosa shiga raga, ko ida saurara gwoggo beyi ba ya shige daki yana tufka da warwara yana hango sura Nihal Wanda yanzu ta fara zama cikakiyar budurwa, bude ledar da yaya yaba Nihal gwoggo ta shiga yi kayan zak'ine kamar suyi magana bak'in cikine ya tokari zuciyar gwoggo dan tasan bame kawo mata wannan abin arzik'in se wannan d'abir nin sannan ta d'au alwashin se ta masu waman farak'a idanma shi ke sata rawar kai, haka Nihal taci kuka ta gaji Wanda kuka yanzu ya zamar mata jiki, jakar ta dake sak'ale jikin b'usa ta janyo ta Ciro wasu hoto na Wayan da sukayi da su umma tana kallan pics din tana hawaye a haka har wani wahalalan bacci ya kwashe ta. Horn yayi mai gadi ya wangale mashi gate ya sakin murmushi a hankali ya sako hancin motar shi cikin compound d'in gida tare da parking motar parking lot a hankali ya bude murfin motar bayi na ta zubewa suna kwasar gaisuwa kai tsaye main parlour ya shige ba kowa cike da murna da zumud'i yake cewa, "Adda your son is back" Adda dake shiryawa gaban dressing mirror ta juyo muryar Ammar murmushi ta saki tare da feshe jikin ta da turare ta fito da Sauri shima ammar da sauri ya k'arasa gaban Adda tare da kai mata hug yana cewa, "I miss u Adda" d'an ture shi Adda tayi tare da had'e ran wasa tace, "ba wani you miss me kaje kauye kayi zaman ka kai kad'ai, wai mi ake haka a kauyan nan ne? har yasa ka manta gida" far ammar yayi da idanuwa tare da kashewa Adda idanuwa yace, "Akwai story amma first lemme take bath tukun na," murmushi Adda ta saki tana cewa, "Allah yasa naji Alheri" "Alheri mane Adda ga car key dina kiba sani ya curo kaya a boot ya kaimun su bedroom din na" "OK" Part nashi Ammar ya shiga kayan shi ya rage sannan ya shige toilet ya dad'e yana wanka cike da tunanin Nihal se da ya kamala wanka tsaf ya fito sanye da bathrobe da k'aramin towel yana goge jikin shi, trolley din shi ya kalla Wanda sani ya aje tare da kauda kan shi, shiryawa yayi cikin black yadi me d'an kauri sannan ya feshe jikin shi da turare yasha kyau har ya gaji, a hankali ya bude handle din kofar bedroom ya fito kallan parlour shi yayi shi kan shi yasan yayi missing d'in gida, fita yayi daga part d'in ya wuce na Adda zaune take tana kallo Arewa24 ana program din akoshi da rufi rungume ta Ammar yayi ta baya yana cewa, "Adda bari naje wajan Sultan I miss him wallahi," "Ka bari ka fara yin lunch se ka je mana" d'an kwab'e fuska Ammar yayi yace, " nafi so na fara ganin shi sannan zan samu peace of mind" "Toh shikenan ka ce mashi ina gaishe shi Allah ya bar soyayya" dariya Ammar yayi tare da ficewa zuwa gidan maimarta ba, Bude kofar da akayi ne yasa Sultan dake kwance saman three star kamar me bacci yace cikin kakausar murya, "bana ce kar Wanda ya shigo min part ba, bana buk'ar kowa get out komawa waye" dariya ammar saki yana cewa, "laifin kuma har da mu ya shafa" mik'ewa Sultan yayi tare da bin Ammar da kallo can kuma se ya bala mashi harara tare da kwasar wayoyin shi ze shige bedroom shan gaban shi Ammar yayi tare da rik'e kunnuwan shi yace, "Am sorry Sultan nasan ni me laifi ne amma ai ya kamata ka saurare ni first" "Ka ga malama matsa min kuma gobe in kaje office takardar dakatarwar ka na saman table tunda ka gaji da aikin Hutu kake so mtwss" zaro idanuwa Ammar yayi yace, "Kar ka ce min wannan ciwo ne yasa ka fara koyan rashin imani," dariyar dake neman kubucewa Sultan ya had'eye tare da cewa malama just leave me alone I need to rest," zagaya shi Ammar yayi sannan ya matso kusa da shi ya lek'a idanuwan shi dariya Sultan ya saki yana cewa, "zan ci uban ka fa mi ka d'auke ni" duka ya kai ma Ammar ya kau ce yana cewa, "gani nayi abin kamar saban kamu" duka Sultan ya shiga k'okarin kai mashi parlour suka fara zagayewa suna dariya rik'e cikin shi Sultan yayi saboda gudun da yayi har ya fama ciwo shi ya fara jini, Ammar ne ya d'aga gira yace, "ya dai" murmushi Sultan yayi yana dafe cikin shi yace, "Nothing" k'arasowa Ammar yayi tare da hug din Sultan yace, "I miss u dude" smile Sultan yace, "me to" zame hannuwan Sultan Ammar yayi daga cikin shi yace, "aushh Sultan sorry ciwo ka na buk'atar new dressing naja ka fama ciwo ka am sorry" dariya Sultan yayi kawai, Ammar ya cigaba da cewa, koma waye yama haka Allah ya tuni a sirrin shi dude" "Ameen" Dressing Ammar ya mashi cikin k'warewa sannan ya b'alo maganin shi da ruwa a cup ya ba shi ya sha, yace, "Saura abinci na lura yau ko breakfast ba kayi ba, ga abinci a dining har na rana ya sami na safe please ka dai na yin haka Sultan ai mak'iyan ka abinda suke so kenan kai kuma kana basu dama Sultan" Sultan kawai saurara Ammar yake sannan ya biyo shi dining area ja mashi kujera Ammar yayi sannan yayi saving nasu plantain porridge Wanda yasha kidney da liver na yan'ciki gefe kuma fresh juice ne na coconut with milk, suna ci suna taba hira yaushe gamo, shigowar da akayi ne ya sasu dagowa Nazili ce dauke da sallama a bakin ta, tana sanye da riga da skert riga red me hannu d'aya bud'ad'e se mine skert black tasha kyau har ta gaji gashin nan yasha parking bakin nan yasha Jan baki, murmushi ta saki tare da k'arsowa tayi ma Sultan pack a goshi tace, "ya jiki Sultan" "Da Sauki Nazili" kallo d'aya ammar ya mata ya kauda kai kasancewar basu shan inuwa d'aya, kallan up and down Nazili ta mashi tare da Jan kujera kusa da Sultan kamar zata shige jikin shi tare da amsar spoon din da ke hannu Sultan tace, "lemme feed you" murmushi Sultan ya saki tare da tura mata plate din dama Sultan ba dai San jiki ba, A hankali take feeding nashi yana amsa can se tayi murmushi ta kalli ammar tace, "Umm se yau ka dawo kenan" d'aga gira ammar yayi yace, "me idanuwan ki suka ganni," harara Nazili ta maka mashi tace, "Ai na 'd'auka can zaka zauna tunda dama daga nan aka fito," ta ida zancan tana kallan Sultan Wanda ke mata wani irin kallo na baki da kunya aje spoon din hannu ta tayi tare da langwabe kai tace, "Sultan zuwa nayi muyi magana amma privacy tana maganar tana kallan ammar mik'ewa Ammar yayi yace, "bari naje na gaishe da ammi," wani kallo Sultan ya watsa mashi yace, "idan baza ta iya fad'i a gaban ka ba to tabar maganar" kwab'e fuska Nazili tayi tare da cewa, "dama gobe zan bar Nigeria zan je UK akan maganar business dina, so ina so ka turo min kudi ko 5 million ne please" ta ida zancan tana wani kif-kif ta idanuwa, "OK toh shikenan ki turo min da account number d'in ki, amma daga wannan angama saboda wancan zuwan ni na Baki ina kike kai kudin? shagwabe fuska Nazili tayi tare da k'ok'arin kai mashi hug yace, "ke zaki famamin ciwo ," "oh wallahi na manta ne" take a nan Sultan ya tura mata kudi sannan Nazili ta bar part din cike da murna da soyayya Sultan fal a zuciyar ta, tare da daukar wa kanta alwashi da ta dawo zata fad'awa ammi abinda ke ranta, ko ta samu ta mallaki muradin ran ta. Sun dad'e sosai suna hira kiran sallah magarb ne ya tashe su alwala suka dauro a tare sannan Sultan yasa jalabiya , suka wuce Masalaci se bayan sallah isha suka dawo part d'in ammi suka wuce zaune suka same ta saman three star tana shan fruit tana kallo , dauke da sallama a bakin su suka shigo murmushi ammi ta saki tana cewa, "wana ke gani kamar ammar? dariya Ammar yayi yace, "nine nan da kai na" ya ida zancan tare da zama shima Sultan ya zauna, "sannu da zuwa ya mutanan shanono,? "lafiya lau Ammi" "masha Allah, se kuma da ka dawo ka ji mumuna labari," "Wallahi ko ba kiji ba da aka ce min ke ma ki na can ciwo ya kama ki da har ina murna ze mutu ya barmu tare musha soyayya Ashe bin shi zakiyi" dariya Ammi ta saki tana cewa, "ja'iri" sun dad'e suna hira sama-sama sannan Ammar ya wuce gida Sultan kuma ya wuce part din Mom. A Kwana a tashi ba wuya wajan Allah yau kusan sati d'aya da tafiyar yaya , duk wata walwala da farin cikin Nihal ya dauke, dama ganin umma da yaya ne ke sata jin dadi, ta k'ara ramewa ta lalace tayi baki, baba mai gadi ne kad'ai ke kwantar mata da hankali, kullun cikin fargaba take saboda mudi ya sako ta gaba, kullun da Kala salan iskanci da zai bijuro mata da shi, yauma kamar kullun ta dawo daga talla dai-dai kofar gida suka had'e yana bin ta da shu'umin kallo idanuwan shi jawur rab'awa tayi ta gefen shi zata wuce fisgo ta yayi ta fad'a fafad'an kirjin shi wani irin kallo Nihal ta watsa mashi tana kiciniyar kwatar kanta tace, ciki masifa da d'aga murya, "dala yaya mudi wai me haka? malam ka sake ni" k'ara k'ank'ame ta yayi a jikin shi yana wani shinshina ta bankad'a shi Nihal tayi ya tafi taga-taga zai fadi tace, "banza d'an iska kawai" ta shige gida da gudu tana kuka. K'wafa mudi yayi wato tafi bawa yan' birni jikin ta shi kuma zai gwada mata k'aryar iskanci da har take ce mashi d'an iska to wallahi ko ta k'arfi se yayi anfani da ita" Tana Shiga ciki gwoggo taba kudin ta sannan ta cigaba da aika ce aika can ta na yau da kullun ba ita ta gama ba sai da aka fara kiraye-kirayen sallah magrib , alwala tayi tare da shigewa d'aki ta gabatar da sallah bayan ta idar ta cigaba da sana'ar kukan nata Wanda ya zamar mata jiki yanzu, kiran sallah isha ne yasa ta tsagaita kukan tare da mik'ewa ta gabatar da sallah ta dad'e tana Addu'a Allah ya kawo mata dauki sannan wani bacci me dadi ya kwashe ta. Wani murmushi mudi ya saki ganin ba kowa a tsakar gidan da alama kowa yayi bacci wani irin dad'i ne ya lulube shi fitowa yayi daga d'akin shi gaba d'aya, a hankali ya bud'e d'akin Nihal kwance ya hango ta tayi d'ai-d'aya a tabarma da alama baccin ya mata dad'i gashin ta ya wani baje ga santala-santalan cinyoyin ta sun bayana wani irin miyau mudi ya had'iye sha'awar Nihal na dad'a fisgar shi lumshe idanuwa yayi tare da matsowa kusa da Nihal ya kwanta yana shafa santala-santala cinyoyin ta, cikin bacci Nihal taji kamar ana shafata a zabure ta mik'e tana wurwurga idanuwa ta bud'e baki zata zun duma ihu toshe mata baki mudi yayi yana k'ok'arin cire mata riga, girgiza mashi kai Nihal take hawaye na wanke mata fuska ganin Abun mudi da gaske ne yasa Nihal fara cizan shi da yak'ushin shi rigama sosai suka fara tsakanin su Nihal na k'ok'arin k'watar kan ta amma mudi ina kamar be ji har ya kai ta k'asa ya danne Nihal na hawaye, lalib'e tashiga yi da hannu ta ko Allah ze sa ta samu makamin jin wata kwalba yasa Nihal sauke a jiyar zuciya ta d'aga kwalbar ta bugawa mudi a k'waryar kan shi take a nan ya fad'a jikin ta jini na zuba ture shi Nihal tayi tana kuka Kallan jinin dake hannu tayi tana cewa, "na Shiga uku Nihal na kashe yaya mudi na Shiga uku wallahi nima nasan gwoggo kashe ni zatayi" ta ida zancan tana kuka me cin rai jakar dake gefen ta ta dauka ta fita daga gidan da gudu ko takalmi babu bare d'ankwali ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 53_54* Gudu Nihal take ko waigowa ba tayi se da tayi nisa sannan ta tsaya tana maida numfashi, sannan ta cigaba da gudun duk taji ciwo a k'afafuwan ta jini se zuba yake tsayawa tayi ta nad'e gashin ta saboda yana tare mata fuska ga kayan ta duk sun yage saboda rigima da suka sha da mudi sai da ta k'ara nisa da gida je, ta fara hango gonaki sannan ta samu natsuwa dan tayima kanta alk'awari daga yau tabar kauyan shanono mahaifar ta, wata gona ta hango nesa da ita a hankali ta ja jiki ga wani irin jiri dake d'ibar ta, tana shiga gona cikin ciyayi ta shige tare da yin pillow da jakar hannu ta, ta kwata cike da tsoro da fargaba a haka bacci b'arawo ya sace ta. *Asuba ta gari* Sanyi-sanyin Asuba ne ya tashi Nihal a hankali ta mike tana waige-waige jakar ta ta janyo tare da fita daga cikin gonar da sauri ba kowa a wajan se sautin kiran sallah da kukan zakaru dake tashi, gudu Nihal ta cigaba tayi dan gani take kamar har yanzu su gwoggo zasu biyo bayan ta cikin sa'a ta isa tasha motar kano da kaduna taji ana kira, aunty Aisha ce ta fad'o mata a rai tasan taje kano ta koma cikin dagin mahaifiyar ta kuma Dama tana da number ta, 1k din da Aunty Aisha ta bata ita ta curo ta mik'awa kwandasta sannan ta shige, kallan na cikin motar take kamar yadda suma suke Kallan ta kauda kai tayi saboda ta San dalili baya wuce ganin ta kaca-kace, kasancewar dama mutum d'aya ake jira yasa Nihal na shiga mota ta tashi mota na tashi Nihal bacci ya kwashe ta. Tsaye yake gaba dressing mirror yana shiryawa cikin wata armani royel blue suit da white inner tie d'in shi kala suit d'in, ta kama jikin sa sosai wando jikin shima pencil ne sannan yasa cufflinks masu diamond royel blue stone hannu shi na sanye da agogo silver, k'afar shi na sanye cikin cover shoe black, gashin kanshi se shining yake sajan shi yayi luf-luf yayi bak'i hakan ba k'aramin fido mashi da haskyan fatar shi yayi ba kallo d'aya zakayi ma Sultan ka sake masha Allah Sultan looks so...huh yayi kyau sosai, A hankali ya tako ya bude handle d'in kofar parlour, Barma da Sinbul na zaune zaman jiran shi briefcase din shi ya mik'awa Sinbul sannan ya fito suna biye da shi se da suka fito compound sannan yace cikin honey voice din shi, "Sinbul ka wuce da briefcase dina car zan shiga part d'in mom da ammi," "Toh" Sinbul yace, sannan ya k'arasa parking lot. Cikin natsuwa ya iso main parlour Mom na zaune a dining area tana break murmushi ta saki ganin Sultan, k'arasowa yayi tare da yi mata pack yace, "morning habibty" "Morning too habibi How was ur night" "Calm mom" "Good amma za kayi breakfast kafin ka wuce office? ta ida zancan tana tsare shi da idanuwa saboda ta San halin shi kwata-kwata Sultan be San cin abincin gida, ta wani fanin bata ganin laifin sa ta wani fanin kuma tana damuwa sosai tabas d'an ta na fuskan ta RAYUWA Allah ya kawo mashi *SAUYIN RAYUWA* cikin gagawa Sultan ne ya katsewa Gimbiya Nadiya tunanin da cewa, "um zanyi break amma kad'an zanci" "Good boy ko kai fa" Murmushi Sultan ya saki har dimple din shi na lomawa ya ja kujera ya zauna kusa da mom yana cewa, "Basmal fa" "Tana school yau tana da lecture din safe" tana maganar tana saving din Sultan paper soup din chicken with Araf bread, tura mashi plate din mom tayi tana had'a mashi tea me kauri, Kallan abincin Sultan yake kamar me jin tsoro, a hankali yake juya spoon d'in shi cikin plate d'in, mom ce ta rike hannu shi cikin calm tune tace, "ya dai my son? tsoran cin abincin kake? Girgiza mata kai Sultan yayi yana murmushin yak'e yace, " Nop kawai bana so naci da kai nane" murmushi mom ta saki sarai ta gane tunanin Sultan cikin sanyin murya tace, "OK lemme feeding" murmushi yayi har dimple d'in shi na lomawa, a hankali mom ta gutsuro bread d'in ta kai mashi baki ya amsa se da ya fara ci sannan ya wani lumshe idanuwa yana cewa, "wannan abinci kamar habibty tayi shi " dariya mom tayi tare da ja mashi cheeks tana cewa, "Ashe dai my son be manta girkin maman shi ba" ware idanuwa sultan yayi yana cewa, "na manta girkin mom d'ina ai na manta kaina" haka mom ta rink'a feeding nashi har ya cinye ya goge bakin shi da tissue, yana k'ok'arin tashi mom tace, "Sultan" "yes habibty" "Mi yasa baka zuwa gaishe da second mom d'in ka,? zaka je gaishe da ammi da maimartaba amma baka shiga gaishe da momi ya kamata ka gyara," canza fuska Sultan yayi yana cewa, "ita ta fad'a maki bana Shiga gaishe ta? Girgiza kai mom tayi, "toh shikenan yanzu dai inna dawo naje na gaishe ta" "A'a gaskiya yanzu nake so ka je" "Toh" Sultan yace tare da kissing cheeks d'in mom ya fice, part d'in ammi ya shiga zaune ya same ta saman three star tana kallo, sallama d'auke a bakin shi ya shigo murmushi ammi ta saki tana cewa, "d'an halak yak'i anbato yanzu nake ma jakadiya maganar ka" smile Sultan yayi yace, "se kuma gani na zo baki abinda baki so" tabe baki ammi tayi tana cewa, "nasan kala maitar ka ko ka tafi se ka dawo ba dai k'waya bace a cigaba da d'irkamin ai ba laifin ka bane laifin shi tsohon naka ne da be damu da uwar shi ba ana maidata yar k'waya" dariya Sultan ya ke sosai yace, "Ashe dai ammi kin San kala maitata to masha Allah tunda kin sani, kinga ba anfanin tanbayar zanzo ko ba zan zo ba," jakadiya ya kwalawa kira ta kawo mashi maganin ammi haka ammi ta rink'a sababi amma sai da Sultan ya bata magungunan tasha, har ya mik'e ze fita ammi tace, "yauwa dama ina so naje gidan hakimi bari na shirya se ku aje ni," ware idanuwa Sultan yayi yace, "Ammi da safiyar nan zaki je wa mutane gida yanzu in soyayya suke se ki katse masu jin dad'i" harara ammi ta watsa wa Sultan tana cewa, "gidan k'anin nawa ne gidan mutane? Allah ya kawo mu toh yanzu shi hakimi har wata soyayya zeyi tsofai-tsofai da shi" dariya Sultan yayi yana cewa, "ammi ko ke ce na samu wani tsoho na lik'a maki Allah ka d'ai yasan soyayya da zaki zuba mashi" d'aga hannuwa ammi tayi tana tafawa tace, "Ni bilkisu na bani rarumo pillow kujera ammi tayi ta Shiga gefawa Sultan da Sauri ya fita yana dariya yace, "ki shirya inna dawo se muje. Part d'in Gimbiya jalila ya Shiga tana zaune da d'an lelan na ta suna break dauke da sallama a baki shi Sultan ya shigo, Gimbiya jalila da Ashad suka bishi da idanuwa, k'ak'aro murmushi Gimbiya jalila tayi cike da munafirci tace, "yau za'ayi ruwa da k'ankara" ta ida zancan tana mik'awa Sultan hannu ta kissing din hannu yayi yana murmushi, "Aini wallahi son nayi fushi kwata-kwata Baka zuwa ganina ko dan ina mahaifiyar k'annan ka ai ka zo tunda ni ban kai matsayin mahaifiyar ka ba, "Ba haka bane hidimomi ne sun min yawa but am sorry," "Amma ai hidimomin basu hanaka zuwa wajan ammi ba" "Ammi ai patient ce" "Toh shikanan naji ka zauna muyi break mana" ta fad'a tana murmushin gulma, "Nayi break ai " "OK" Kallan Ashad yayi yace, "yau baka da aiki ne" tabe baki yayi tare da d'an jingi da kujera dining yace, "kowane a ka ce ma wahalale ai kaima d'in ina ganin k'ok'arin ka da kullun kake yawan zuwa, ni dai ban iyawa tunda ni ba bawa bane, murmushi Sultan ya saki tare da had'e rai yana cewa, "Allah yasa yau karka zo wajan aiki, ka ga aiki da cikawa I don't care kana k'anina what ever takarda sallama zan baka, Se ka dawo gida ka cigaba da zama, ya fad'a tare da watsawa Ashad Harara yace, stupid boy kawai kana girma kana cin k'asa, na baka just a second kafin na isa office na ganka if not a bakin aikin ka mtsww" Sultan yasa kai ya fice. Jar uba amma wannan yaran anyi tsinane ko mutuwa na kunyar idananuwan uwa bale wannan, kwata-kwata yaran nan be da mutunci, "Hmm fad'i b'ana baki" inji Ashad "rabu da shi inya tsinci kan shi a kabari ze gane kuran shi" "Yanzu dai tashi ka tafi ai dan yasan takadun ka suna da yar Matsala shiyasa yake haka, ba kowani asibitin ne zaka samu babba matsayi ba se dai a baka k'aramin matsayi, yasan da haka shiyasa yake so ya sallame ka dan bakin ciki" tsaki Ashad ya ja tare da fita ya bar Gimbiya jalila nata kunfar Baki. Motar su Nihal a tasha ta sauka ganin fasinjas nata sauka yasa Nihal sauka rungume da jakar ta tana raraba idanuwa mutane se hada-hada suke da kai kawo, kowa harkar Gaban shi yake ko yanayin tsarin tasha ya isa ya nunawa Nihal yau ta bar kauye ta bar mahaifar ta, ta dawo birni wani wuri ta hango ida mutane ke d'an zama da alama wajan me saida abinci ne k'arasawa Nihal tayi wajan ta zauna saman tebirin rungume da jakar ta, wata yar budurwa ce zaune gefen ta da alama d'aya daga cikin yaran me se da abincin wurin ce tana ta latsa waya, cikin sanyi murya Nihal tace, "baiwar Allah Dan Allah wata number nake so ki kira min da wayar ki, ki taimaka min" Kallan Nihal tayi da niyar ta mata rashin mutucin ganin kala tausayin da Nihal tayi da yanayin da take se yasa mero jikin ta yayi sanyi tace, "toh fad'i min number" jikin Nihal na rawa ta curo takardar number aunty Aisha taba mero, ko da mero ta kira Layin kashe, haka ta rink'a kira saboda ta tausayawa Nihal musanman da Nihal ta fad'a mata daga a kauye take ita bak'uwace, haka Nihal ta rink'a zama mero na janta da hira kusan tare suka ci abincin mero har yamma tayi shuru Layin aunty Aisha ba ya Shiga har su mero suka tashi. Sultan ne zaune a office idanuwan shi manne da glass yana duba files d'in marasa lafiya da sister Naja ta kawo mashi, knocking d'in da akeyi ne yasa Sultan cewa, "come in" ammar ne ya shigo sanye da suit Ash yana smile hannu shi rik'e da wasu files , b'ata fuska Sultan yayi yana bin files d'in hannu Ammar da kallo har ya zauna, Sultan yace rai a had'e, "Karma ka ce ni ka kawowa wannan abun na duba, dan wallahi yanzu ma zan bar office d'in gida zani fita zamuyi da Ammi aha" dariya Ammar yayi yace, "maida wuk'ar Sarkin hawa, ni zan Cuba ba kai ba na patients d'in nane" "Hmm thank god Baka San gajiyar da nayi bane tunda na zo nake duba patients, theater biyu nayi fa Allah na gaji naso ace kai kayi theater amma se ka zo late" Sultan ya ida zancan yana aikawa Ammar Harara, "bari na fita tunda harara ta kake yi," Mik'ewa Sultan yayi yana cewa, "Nima yanzu zan wuce se mu wuce tare" briefcase d'in shi ya daukar a tare suka bar office d'in. Yana isa gida part nashi ya wuce, wanka yayi a gurguje saboda yasan ammi da k'orafi shiryawa yayi cikin wata fara shada tasha aiki na sarauta da brown zare sannan yasa brown hula, yayi kyau sosai abin ka da fara fata se haskyan shi ya k'ara fitowa, direct part d'in ammi ya wuce ko da yaje dama ta shirya cikin wata gown d'in lace me tsada maroon shi take jira, Alkyabba ta Sultan ya amsa yasa mata, silver an mata aiki da bak'in zare sannan suka fita security na biye da su suka shige mota. suna isa gidan hakimi a parking lot sukayi parking Sultan da ammi suka fito bayi da fadawa nata kwasar gaisuwa dayima Sultan kirari, dauke da sallama a bakin su suka shige main parlour hajiya dake kallo ce ta d'ago tace, "A'a sannu da zuwa ammi" larai ta Shiga kwalawa kira ta kawowa su ammi abin motsa baki, kallan Sultan tayi tace, " yau za'ayi ruwa da k'ankara, shiyasa naga hadiri ya had'u" Sosa keya Sultan yayi yana murmushi, hajiya tace, "ammi yaushe me suna Abba ya fara zuminci? Dariya ammi tayi tace, " wato sharin da akewa mai gida kenan" "Toh shi d'in ne baya zuminci bari hakimi ya shigo kiji mi ze ce" bata ida rufe Baki ta ba hakimi ya shigo shi ma tsokar Sultan ya Shiga yi sun dad'e suna hira Kiran Sallah magrib ne yasa hakimi da Sultan suka wuce masalaci, se bayan sallah isha suka dawo se da sukayi dinner sannan su Sultan suka fito tafiya gida har bakin mota hajiya da hakimi suka rako su. Saman tebir Nihal ta samu ta kwanta tana tunanin yadda RAYUWA ta sauya mata ba uwa ba uba , ba wajan kwana kuka take sosai, ga wata yunwa dake azalzalata, gashi gurin shuru ba motsin kowa se kukan karnika dake tashi wani mugun tsoro ne ya lulub'e ta, tare da nadamar gudowa daga gida dama ta tsaya gwoggo ta kasheta, surutan da take ji k'asa-k'asa ne yasa zuciyar Nihal k'ara tsinkewa da wata fargaba, wasu mazane su uku suka nufo wajan da Alama yan shaye-shaye ne ganin mutane tayi tsaye a kanta mik'ewa tayi zaune jikin narawa tana bin su da idanuwa taf da kwalla, kuka Nihal tasa tare da duk'ewa ta had'a hannuwa tana cewa, "dan Allah kuyi min rai karku kashe ni" Dariya babba cikin su yayi yana magana cikin maye yace, "ba maganar kisa a nan bamu lokaci zakiyi mu huta," share hawayan ta Nihal tayi saboda bata gane hausar ta su ba tace, Indai guru ne gashi nan na Baku" tana maganar tana k'ok'arin rab'awa ta gefe d'aya daga cikin su fisgo ta yayi ya maido ta k'ara Nihal ta saki hawaye na bin fuskarta manna ta yayi da bango se matsawa Nihal take kamar zata shige bango jin shi daf da ita har suna jin numfashin juna yasa Nihal ware idanuwan ta wani irin k'ara ta saki tare da gantsara mashi cizo ta bankad'e shi ta runtuma da gudu suma da gudu suka bita godi Nihal take har da fad'uwa tana tashi tana cigaba da gudu har ta iso bakin titi ko gani batayi samarin nan na biye da ita ji kake kiiiiiii!!! Mota ta tashi da Nihal take a nan ta zube, birkin da aka ci ne yasa Sultan cewa,"what's wrong? Ammi ma shuru tayi tunanin ta yan bashine suka tare su lokaci d'aya security's d'in Sultan da shi kanshi suka bud'e murfin motocin su, gabaki d'ayan su da mindiga a hannu su Alex ne yace, " Audu what's wrong? Cikin ina... ina.. yace, "Accident" da sauri Sultan da Alex suka k'araso tare da had'a baki wajan cewa, "mutum ko mi? mutum yace jikin shi na rawa, dafe goshin shi Sultan yayi yana cewa, " Ya Allah yau kuma ta nan aka b'ulo min" k'arasawa yayi gaban Nihal Wanda ke kwance shame-shame jini na zuba kota ko ina, Wuyan ta Sultan ya tab'a tare da cewa, "Masha Allah tana numfashi" daukar ta Sultan yayi cak aka sata a back seat d'in mota ammi ko duk ta rikice musanman da taji wata aka kad'e komi ya fido mace da wannan daran ganin gilmawa samari yasa Sultan bin wajan da kallo *_typing akwai wahala walla da kyar na ida wannan_*😫🤕🤧 ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo ```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Ina ba masoya hakuri a kan jina jiya shuru na gode sosai da kulawar a kai naji dad'in sosai da kuka tanbaya ta lafiya akan jin shuru Allah ya bar kauna wannan shafin naku masoya SAUYIN RAYUWA_* *Page: 55_56* Cikin takunshi na isa da mulki ya k'araso gaban ammi ya zauna, murmushi ammi ta saki tana cewa, "yanzu nake maganar ka naga tunda ka tafi baka dawo ba," d'an tabe baki Sultan yayi se hakan ya k'ara fito da dimple d'in shi yace, "um bani da doti da rana yau se dare hope dai Dr amir ya zo ya duba ta,? " Eh ya zo ya cire mata k'arin jinin sannan yace, "da dare za'a mata allura," "Good tana cin abinci? Ammi tace, "Eh amma se dai bata jin dad'in bakin ta da kyar take tura shi," Mikewa Sultan yayi ya nufi gadan Nihal dake zaune, cikin honey voice d'in shi kamar me rad'a yace, "mi ke maki ciwo? Ya zuba mata idanuwan shi masu rikita yan'mata, gabaki d'aya Nihal ji tayi jikin ta ya hau rawa saboda wani k'war jini da Sultan yake mata ga kyan shi dake rikitata cikin sarkewar harashe tace, " ba komai se dai jiki nane ba k'arfi ji nake kamar ba nawa ba" lalausan murmushi Sultan ya saki yana cewa, "insha Allah a hankali jikin naki ze dawo kamar nakin, ki rink'a taimakawa kanki kina cin abinci komai ze zama Normal" ya fad'a yana tsare ta da idanuwan shi, k'asa da kai Nihal tayi tana wasa da yatsun hannu ta, Basmal ce ta katse shurun da cewa, "Ammi ya kamata mu wuce gida yama yayi yanzu a fara kiran sallah magrib, tunda yayana ya zo nasan ze bata kulawa sosai" ta ida zancan tare da rik'e hannun Nihal tana kallan Sultan tana Smile, wani kallo Sultan ya watsa ma Basmal na rashin fahimata Dan shi duk a tunanin shi Basmal ce zata kwana da Nihal, bud'e baki yayi da niyar magana ammi ta katse mashi zance da cewa, " Na San ze ba maki kulawa Nihal duk abinda kike buk'ata ki fad'a ma Sultan kin ji" ta ida zancan ta shafa cheeks d'in Nihal, d'aga mata kai Nihal tayi tana satar kallan Sultan Wanda yayi kicin-kicin da rai, basket din abinci Basmal ta d'auka ammi na gaba Sultan ya bisu a baya a hankali suke tafiya ammi na bashi labarin Nihal da yadda ta tausaya mata, se da ta kai aya Sultan yace, "Than se mu maida ta inda muka d'auke ta fine," ya fad'a rai bace, ammi tace, "Ai na riga dana yanke shawara tabi mu gida kawai saboda yarinyar ta bani tausayi" Sultan yace "Ammi ! Tare da Jan fasali yace, "babu idan zamu da ita, ni kwata-kwata ban yadda da ita ba, kuma wannan labari banga abin tausayi a cikin shi ba, ai ba kanta aka fara almajiran ci ba, kuma bata da families ne,? wannan maganar ba tayi kama da hankali ba," Ammi tace cike ta tsiwa, "na Riga Dana yanke shawara hakan, kuma ai ba gidan ka zan aje ta ba, gidan d'ana zan aje ta," Dafe goshin shi Sultan yayi idanuwan shi sun rine sunyi jawur ya juyo da ammi suna facing juna cikin sanyi murya yace, "ammi you have to no mutane ba abin yadda bane how comes za'a ce bata da families ammi you have to think about this matter," zame hannu Sultan ammi tayi daga jikin ta tace. "me anfanin matsayin naka ? Dana mahaifin ka ?ai Dan Ku taimakawa marayu da marasa k'arfi ne Allah ya baku matsayin Sultan, ina tananin zaka zama shugaba mai adalci Ashe ba haka abin yake ba, da ina tunanin zaka fi mahaifin ka tausayi da adalci Ashe ba haka abin yake ba, Sultan na riga Dana gama magana Nihal tare damu zata zauna ko kana so ko baka, ko shi mahaifin naka bai isa ya hanani aje Wanda nake so a Inda nake so a cikin gidan ba, bale kai Sultan" sannan Ammi ta bar wajan da sauri, Sultan ya bita yana cewa, "Ammi you have to understand" ko saurara shi ba tayi ba aka bud'e mata murfin mota ta shege. Rike k'ugun shi Sultan yayi tare da furzar da iska me zafi ya wuce cikin asibiti. Arabar gida motocin ammi su ka faka, a hankali ta bud'e murfi Mota ta fito ganin ammar ne ya sata Smile gaisawa sukayi a tsaitsaye ta wuce Fada maimartaba Dan fad'a mashi shawara da ta yanke kan zaman Nihal a cikin su, A hankali Basmal ta k'araso gaban ammar cikin takunta na Jan hankali duk wani d'a namiji me lafiya, far tayi da idanuwan ta tana gyara veil din kan ta a hankali take motsa lips d'in ta tace, "ya ammar ni fa fushi nake da kai amma ka kasa ganewa ko," ta ida zancan tana jefa mashi wani kallo da kwayar idanuwan ta murmushi ammar ya saki yana tataro natsuwar shi yace, "ya za'ayi nayi ma gimbiya laifi kuma na kasa bata hakuri tunda ki kaga haka ban san laifin Dana Aikata ba" yana maganar yana makin funny face, tab'e baki Basmal tayi tace, " Kullun se na kira phone na ka tunda kayi tafiya amma bata Shiga, sannan da ka dawo ko ka fara zuwa ka gani baka zo ba ko? se da kowa ya gama ganin ka yauma Dan dai kawai-kawai" tana maganar tana making face nata kamar za tayi kuka, hannuwa ta Ammar ya rik'e a hankali ya furta "am sorry, ban San ki damu dani haka ba dear shiyasa" kukan shagwaba basmal ta Shiga jerawa Ammar janyo ta yayi jikin shi ya rungume ta tsam yana cewa , "Why those tear,? am sorry am here for you dear, ban kyauta ba nasa princess kuka, ya kamata a bani punishment me tsauri" yana maganar yana shafa bayan ta lumshe idanuwa Basmal tayi tare da yin lamo a chest d'in ammar gabaki d'aya su kawo da abinda yake sak'awa a ran shi, ammar yace, miyasa matsayin da ya aje Basmal ada a yanzu babu shi me yasa yanzu baya tananin ta se na Nihal watsar da zamcan yayi tare da kiss forhead d'in Basmal sun dad'e a haka suna juyo harbawa zuciyoyin juna su sannan Basmal ta zame jikin ta a hankali dariya suka saki su duka Basmal tace, "laa har an gama Sallah magrib muna nan" rufe fuskar ta tayi tana dariya tare da shigewa gida da gudu, murmushi ammar yayi tare da barbaza gashin kan shi sannan ya wuce part d'in maimartaba. D'an siririn tsaki Sultan ya saki tare da kwaso alulurin dake saman table direct d'akin Nihal ya nufa a hankali ya bud'e kofar d'akin tsaye ya hango ta da alama daga toilet ta fito, a hankali take takawa jin kamar ana Kallan ta yasa ta d'agon idanuwan ta, kauda kai Sultan yayi tare da yin magana can k'asan mak'oshi yace, kin ci abinci, "Zama Nihal tayi saman gado tana cewa, "na kasa ci saboda hannuna ya kunbura" ta ida zancan idanuwan ta taf da kwalla, k'arasowa cikin dakin Sultan yayi tare da zama gefen gado yace, "muga hannun" mik'a mashi hannuwata Nihal tayi ya dad'e yana Kallan santala-santala yatsun hannun ta masu tsaho dasu masu kyau duk da hannun ya kunbura be hana aga kyan su ba, sakin hannu yayi tare da janyo warwer da plate, shinkafa da miya ce taji naman rago da kaji ga coslow ya zuba a plate tare daukar spoon, ran nan nashi a had'e kawai zeyi wannan abune saboda tana patient nashi kuma saboda ammi, a hankali ya d'ebo abincin ya kai bakin Nihal kallan-kallo suka shiga yima juna su sun kusan kawashe Rabin sa'a a haka sannan Nihal tayi k'asa da idanuwan ta a hankali Sultan ya ke feeding nata tana amsa, can ta kware ta fara tari ruwa Sultan ya dauko yana bubuga bayan ta a hankali yana cewa, "sorry ! Aje plate d'in Sultan yayi sannan ya bata ruwa tasha tana sauke numfashi, janyo plate d'in yayi Dan ya cigaba da feeding nata, girgiza kai Nihal tayi cikin kasalaliyar murya tace, "na koshi Allah," tab'e baki Sultan yayi tare da aje plate d'in ya dauko alura ya fara zuk'o magani a Sirinji ware idanuwa Nihal tayi a hankali ta fara zamewa daga saman gado ta yunkura zata ruga Sultan ya dam kota, kuka Nihal ta fara tana cewa, "Wallahi ban San allura ka bani magani Dan Allah" shuru Sultan yayi Nihal se mutsu-mutsu take a jikin shi , hannu ta ya tataro gabaki d'aya ya manna su a chest nashi ya rungume ta sosai a jikin shi kuka Nihal ta fara duk yadda taso ta k'waci kanta daga rukwan da Sultan ya mata ta kasa, cikin sanyi murya Nihal ke cewa, "Dan Allah karka min da zafi" ta ida zancan tare da daura kanta saman fafad'an k'irjin Sultan, tana sauke numfashi a hankali, a hankali Sultan ya tsula mata allura zafin da ya ziyar ce tane kad'an yasa Nihal cikwikwiye Sultan tare da sakin kuka me cike da shagwaba ta k'ankame sultan , lokaci d'aya Nihal ta sakar wa Sultan da kasala abinka da lafiyayan namijin, sun dau lokaci me tsaho a haka Nihal idanuwan ta a rintse tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tayi tsere. A hankali Sultan ya zame jikin shi daga na shi, yana sakin Nihal ta fad'a saman gado tana sauke a jiyar zuciya, Sultan kuma ya ja yan k'afafuwan shi tare da zama saman kujera ya lumshe idanuwan shi. Ammi nashiga fada maimartaba bayan sun gaisa da ammi, take sheda mashi ra'ayin ta kan Nihal tare da fad'a mashi rayuwar Nihal kamar yadda Nihal ta zayana mata, sosai maimartaba ya jinjina maganar Inda yaba ammi goyan baya d'ari bisa d'ari, shiyasa a kullun yake alfahari da mahaifiyar tashi musanman yadda take kyautatawa marayu da marasa karfi, shiyasa wani lokacin yake ganin kamar tare da ammi suke mulkin kuma hakan na mashi dad'i sosai, ammi taji dad'in amincewar d'an nata zuciyar ta fal da farin cikin tabar fada tana sak'e-sake a zuciyar ta. ***** Bangaran su gwoggo ko da safiya tayi gwggo taji shuru ba motsin Nihal a fusace ta debo ruwa mai sanyi a randa tayi d'akin Nihal tana huci, ganin mudi a d'akin yasa gwoggo zunduma ihu tare da sakin bokitin hannun ta tana k'walawa baffa kira, da gudu baffa ya fito daga d'aki shi da Sara, daukar mudi yayi se asibiti gwoggo se kuka take tana antayawa Nihal zagi tana kuka, baffa ko yara ya tara yan'daba yace su nemo mashi Nihal duk Inda take a kauyan ko a Raye ko a mace. ```Taku had kullun Salma mas'ud nadabo```[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 59_60* Jijiga Sultan ammar yake yana cewa, "Sultan.!! Sultan.!! gabaki d'aya ya rud'e cikin d'aga murya yace, "guards !! security d'in sultan suka k'araso, daukar Sultan ammar yayi jikin shi na rawa har yayi gaba ya tsaya cak yana cewa cikin murya me rawa, "ina so ku bi samarin da suka kawo ma Sultan hari a raye ko a mace Ku kawo min su," yana ida zancan ya wuce da Sultan cikin part nashi, jikin ammar se rawa kawai yake yana tsoran Allah yasa Sultan be samu wata matsala ba yana shiga part d'in sultan fadawan shi sukayi ca suna tanbayar mi ya faru ko saurara su Ammar beyi ba se daya shiga da Sultan d'akin shi ya shin fid'e shi har a lokaci jini na zuba a kanshi duk yawan gashin shi se da jini ya jika shi, a hankali ya tako bakin kofar yace, "bana so ku sanar da kowa cewa ga halin da Sultan ke ciki" d'aga kai su Sinbul su kayi suna zubar da kwalla rufe d'akin Ammar yayi tare da daukar wayar shi ya kira Dr amir saboda baya iya kula da sultan shi kad'ai Amir na daukar wayar ammar yasa kuka kamar k'ara min yaro yana cewa, "Amir ana so a kashe min dude" kuka ammar yake sosai tare zamewa k'asan wajan yana korawa Dr amir bayani Alex dake gaban Dr amir yana mashi dressing ne ya mashi wayar hannu amir Wanda yayi kasake, kuka Alex ya saki yana cewa, "no ! nasan ba abinda ze sami Sultan" Ya mik'e da sauri duk da alokacin k'arin ruwa ake mashi rik'e hannu shi Dr amir yayi yace, "you have to rest Alex," cikin sanyin murya Alex yace, "bana iya jurewa dole na bika" a tare suka bar Asibitin tare da daukar kayan aikin da za'ayi anfani da su bama komai suka kwasa ba saboda A cikin masauratar akwai asibiti, Gimbiya Nadiya ce ta fito hannu ta dauke da cup d'in coffee subucewa yayi a hannu ta ya fad'i gaban tane ya yanke ya fad'i tana bin cup d'in da kallo, guri ta samu ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, Sultan ne ya fadu mata a rai addu'a ta shiga jera mashi duk da bata San halin da yake ciki ba, jin a dafa ta ne ya sata sakin murmushi tunanin ta Sultan ne ganin maimartaba ne yasa ta mikewa tsaye tare da k'ara sakin wani murmushi bayin dake part nata tuni sun fice, jikin maimartaba ta fad'a ta rungume shi tsam ita kanta bata San dalilin canjin nata ba, A hankali Nihal ta zauna saman kujera bugun zuciyar ta na k'aruwa ta rasa dalilin hakan, lumshe idanuwan tayi a hankali Dara ta mik'e kafafun Nihal tana mata pedicure, su Yasmin suna mata tausa bayan Dara ta gama ta shafa mata wasu mayi ka na musanman a k'afar ta saboda fasan k'afar ta yayi saurin bacewa, mamaki ko hana Nihal magana yayi saboda yadda take gani ana mata cikin zuciyar ta kuwa hamdala take Allah ya kawo mata *SAUYIN RAYUWA* daga ta inda bata tab'a tsanmani ba, Amir na shigowa part d'in Sultan ammar ya fad'a jikin shi tare da sakin kuka yana cewa, "zasu kashe min Sultan wallahi na rasa Sultan na rasa good friend" kwalla dake idanuwan Amir yasa hannu ya goge yana shafa bayan Ammar yana cewa, "haba aboki na bi a strong man mana insha Allah Normal ze tashi ai Sultan namiji ne" Alex da kuka ke Neman kubuce mashi ne da sauri ya bar part d'in Sultan yana goge hawayan shi, kafin kace mi Ammar da Amir sun fara bama Sultan taikwan gagawa, banko kofar da kayi ne yasa Ammar d'agowa bashir ne tsaye murmushi Ammar ya saki yana cewa, "Leda nawa na jini ka bada bashir? yace "biyu! aje lider k'arin jini bashir yayi tare da k'arasowa ya taba jijiyar Sultan na hannu d'aga masu ammar hannu yayi alamar komai na tafiya dai-dai cigaba su kayi da aikin su cikin ikwan Allah suka kamala aikin sannan aka daura mashi k'arin jini, komawa gefe suka yi tare da zaunawa suna duba agogo, kowa cikin su fata yake Sultan ya mik'e lafiya lau. ***** B'angaran Nazili ko business d'in ta na tafiya yadda ya kamata company d'in ta se k'ara samun cigaba yake, ta k'ara kyau tayi fresh wayewa se abinda ya k'aru musanman taje inda take da freedom amma se dai tunanin Sultan ya hana ta sakat da shi take kwana tana tashi, san shi se lunkuwa yake a zuciyar ta, duk ta matsu ta gama aikin ta dawo Nigeria taga sanyin idanuwa ta babba damuwar ta ko ta kira shi se yaga dama yake dauka, lumshe idanuwa Nazili tayi tare da ware su saman pic d'in dake manne a d'akin ta, iyayan tane murmushi ta saki tare da cewa, "I miss u," duk da iyayan Nazili sun rasu hakan baya hanata sauka gidan su idan ta zo uk, mahaifiyar Nazili baturiya ce sun had'u da k'anin maimartaba ne sanda ya zo karatu soyayya me karfi ta shiga tsanin su, sakwamakwan Auran su yasa family d'in mahaifiyarta musulinta , mamar ta na haihuwar ta, ta rasu haka Abban ta ya rink'a kula da ita yaki aure tana da shekara 14 mahaifinta shima ya rasu haka yasa ta dawo Nigeria hannu maimartaba yana kula da ita, tunda ta kyala idanuwa ta kan Sultan ta kamu da San shi, shi kuma matsayin kanwa ya aje ta kamar su basmal haka yake ganin ta sauke ajiyar zuciyar tayi Tara da kallan k'anwar mamatar lusi wadda ta dafa ta, murmushi lusi ta saki tare da cewa, "ya dai my baby" murmushi Nazili ta saki tare da cewa, "lafiya lau," zama lusi tayi tana cewa, "kin ki zuwa ki auri family d'in mahaifiyar ki ko Nazili? dariya Nazili ta saki tare da cewa, "Sultan yafi min kowa shi nake so shi nake tunani," tabe baki lusi tayi tana bin Nazili da kallo, car key d'in ta Nazili dauka tare da fita daga gidan. *** Wata hadadiyar daguwar riga Dara ta dauko light blue se alkyabba dark blue tasha aiki da gold zare, cikin natsuwa ta shirya Nihal nanad'e mata gashin ta akayi ya zubu har gadan bayan ta bakin Nihal ko ya kasa rufuwa saboda kauyanci da murna, make up aka mata sosai sannan aka sa mata alkyabba tayi kyau sosai, wuyan nan nata yasha sakar gold hannu ta ko yasha zoben gold, tare suka fito da Nihal ammi dake saman kujera ce ta bud'e baki tana cewa, "masha Allah" gabaki d'ayan yaba kyan Nihal suke ammi tace, "Ku kaita wajan gimbiya Nadiya ta sa mata albarka," bayi na biye da Nihal tana tafiya a hankali har suka k'arasa part d'in umman Sultan Se da Gimbiya ta masu iso suka shigo a lokacin maimartaba ya bar part d'in murmushi mom ta saki tare da kallan Dara ta mike tsaye Gimbiya ta bin Nihal da kallo, zubewa Nihal tayi tana kwasar gaisuwa murmushi mom tayi tare da cewa cikin muryar ta mai dad'i da mulki tace, a bud'e mata fuskar Nihal wadda ke sunkuye cikin hula alkyabba a hankali Dara ta bud'e fuskar Nihal murmushi mom ta saki tare da d'ago da habar Nihal ta furta "masha Allah" da yaba kyau na Nihal, mom tace, "Na ba kyautar gold" mom ta fad'a tana kallan Dara sannan tace, "na k'ara mata bayi mata uku, wannan zab'i yayi ina nan shigowa na kawowa Ammi gworan godiya mun amsa hannu bibiyu" dariya Dara tayi me sauti, shuruka da Nasim da minal dake tsaye gafe d'aya a hankali Dara ta shiga nuna mata su da matsayin su, jikin Nihal ne yayi sanyi saboda alamarin su Ammi ya fara bata tsoro gaban ta se dukan uku-uku yake bata k'ara rudewa ba se da ta ga duk d'an da ka ce mashi ga Sultana se ya washe baki tare da kissing hannu ta, Nihal ji tayi kamar ancire mata laka, kyaututuka mom ta dauko da yawa taba Nihal tare da cewa, "na sa albarka a wannan abin jiki na na bani Alheri ne," murmushi Dara tayi tare da ruko hannu Nihal suka fita wadda ta kasa gane inda zancan nasu ya dosa. A hankali yake bude idanuwan shi abinda ya faru dashi ne ya dawo mashi kamar yanzu akayi, a hankali ya maida idanuwan shi tare lumshe su yana nazari duk da kanshi na sara mashi, yana cewa yaushe ne ze samu peace of mind, ya kusa wata ba a kawo mashi hari ba, ta hanyar wa aka samu damar shigowa wajan wasa da dawaki, Nihal ce ta fado mashi a rai, tabas wannan yarinyar ce ta shigo yau cikin gidan kenan aiko ta akayi Dan taga bayan shi saboda ita ka dai ce ta shigo Bak'uwa, da ita akayi anfani aka shigo gidan kenan tana da had'in baki da masu cutar da shi acikin gidan tsanar Nihal ce ta k'ara ratsa zuciyar sultan da duk wata mace, ganin tunani na Neman dawo mashi da ciwo sabo yasa sultan ware idanuwan shi a hankali, ammar dake bakin gadan ne ya saki murmushi yana cewa. "Sultan ! murmushi Sultan ya saki da sauri Alex da Amir suka k'araso da bashir rungume Sultan sukayi suna murna shima dariya yake Dan ya kwantar masu da hankali. Tsaki gimbiya Jalila ta saki tana cewa, "har yanzu ban fara jiyu sautin kukan Nadiya da Ammi ba ya kamata a binci ko mana gaskiya" "Ki kwantar da hankali ki Gimbiya ni nasan an buga mashi iccan se dai in rufa-rufa za'a mana" "Toh shikenan ki fita kije ki binci ko mana ya ake ciki Dan na fara gajiya da jiran gawar shanu" da Sauri yakumbo ta fita Dan itama tana so taji k'arin bayani. Kwana biyu Sultan ya kwashe yana jinya ya warware sosai su Ammar sun ji dad'i Dan suke bashi kulawa har ya warware, kwata-kwata basu bari labari ya je cikin gida ba, se dai duk Wanda ya zo Neman Sultan se ace mashi yana wajan aiki haka suka rink'a rabawa su Gimbiya jalila hankali in ranta yayi dubu to ya baci, Ashad ko labari mutuwar jabir na zuwa mashi yayi bak'in ciki sosai tare da k'ara tsana Sultan da Alex Dan yasan su ne zasu kashe jabir tare daukar wa kan shi alk'awari wannan karan se Sultan ya mutu ko ana ha maza ha mata. Had'a kayan shi Ammar yakeyi a trolley Adda ce ta shigo bedroom d'in tana murmushi tace, "Duk wannan sanmakwan na zuwa shanono ne Ammar? Sosa keya yayi yana dariya yace, "kawai Adda ina so na isa da wuri ne bana so dare yayimin a hanya," "Hakan na da kyau ai tafiya dare ba dad'i idan ka gama had'a kayan ka, ka zo breakfast na jiran ka" kai ammar ya d'aga tare da cigaba da had'a kayan shi Dan duk ya matsu yaga Nihal he Miss her so much. Gyara Nihal take sha sosai duk wani abinda bata iya ba koyawa mata ake ta murje ta k'ara wani kyau kullun se an mata wanka so biyu kuma ko wani wanka da ruwan turare ake mata, k'afar ta ko tuni fasan k'afar ta sun bace, yau ma koya mata cin abinci ake da spoon da fork, da ta d'ebo abinci se ya zube, dariya Basmal take tana nuna Nihal da yatsa kuka Nihal ta fara tare da bin Basmal da gudu , gudu suke suna zagaye dakin ammi da shigowar ta kenan basmal ta boye bayan ta, tana yima Nihal gwolo, Ammi tace, "mi ta makin Sultana? kwabe fuskar Nihal tayi tana cewa, "Basmal ce da taga ana koyamin Abu se ta hau min dariya" " rabu da ita kin ji Nihal" daga kai Nihal tayi ammi ta ruko hannun ta tare da rankwan shi Basmal, yar k'ara ta saki tana cewa, "zamu had'e ne anjima, " gwolo Nihal ta mata tare da bin ammi parlour, Dr Amir ne zaune Ammi tace, ga ta nan zaunawa Nihal tayi kusa da ammi Amir yayi murmushi gwaje-gwaje yayi ma Nihal tare da d'ibar jinin Nihal a Sirinji yasa a cikin jaka yana cewa, "na san insha Allah komai nata lafiya lau ne se dai muce Allah ya Nuna mana rana ammi," murmushi Ammi tayi me sauti tana shafa gefen fuskar Nihal wadda itama murmushi tayi duk da bata gane dalilin da yasa ake mata hakan ba, godiya ammi tayi ma Dr Amir sannan ya fita, sosai Nihal ke samun kulawa Matsala ta d'aya ce ilimin boko shima ammi tace se ta gama abinda take zata sama mata makaranta boko da islamiya. Sanye yake da inner white shirt me uneck da three quarter black ya kama jikin shi sosai yayi kyau kwarjinin shi ya k'ara fitowa a hankali yake takawa kamar me tausayin k'asa a haka har ya k'arasa part d'in mom zaune ya hango ta saman kujera murmushi ya saki har dimple d'in shi na lomawa a hankali ya k'arasa ya rungume ta baya murmushi Gimbiya tayi tana cewa, "my son" kissing forhead d'in ta yayi tare da zagayowa ya zauna tare da daura kanshi saman cinyar mom shafa kanshi take tana cewa, "my son kana cin abinci kuwa" "Eh mana" "Se naga kamar ka rame son" d'an murmushi Sultan yayi yana cewa, "kawai dai kinyi kwana 2 baki ganni bane shiyasa" ya fad'a yana mikewa "bari na je wajan ammi nasan yau zamu sha drama" dariya Gimbiya tayi tace, "kai dai baka ji" dariya Sultan yayi. direct part d'in ammi ya wuce ammi da fitowar ta daga dakin Nihal kenan taga Sultan saman kujera zaune ya lumshe idanuwa kamar me bacci, harara ammi ta maka mashi tace, "kai miya kawo ka nan? A hankali ya bud'e lumsasun idanuwa shi, har a lokacin ammi na harara shi yace, "zuwa nayi na gaishe ki ," oh na dauka b'atan kai kayi ai" a zuciyar ta kuwa wani irin dad'i ammi taji ta dauka Sultan na fushi da ita ne, amma yanzu ta yadda ba fushi yake da ita ba, Sultan yace, "kina shan maganin ki kuwa matar" had'e rai ammi tayi Dan raban da tasha maganin ta har ta manta, harara ammi ta maka mashi tace, "ai yanzu se ka zo ka cigaba da duramin kwayoyin tunda ka zo" murmushi Sultan yayi tare zauna da ammi yace, "maganin fa is good for you ammi yanzu Abu kad'an na iya faruwa ki samu Matsala saboda baki shan maganin ki please ki rink'a sha ko bana nan kin ji matar, ni fa lafiyar ki nake so ba komai ba," murmushi ammi tayi tace, "toh zan rink'a sha ta ida maganar tana shafa gefen fuskar Sultan smile yayi yana cewa, "ammi zan sha fura" ja mashi ceeks tayi tace, "dama shi ya kawo ka. ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 57_58* A kwana a tashi ba wuya wajan Allah yau dai aka sallamo Nihal daga Asibiti masha Allah ta murmure ta d'an k'ara kyau saboda natsuwar da ta samu na kwana biyu, Ammi da Basmal se nan suke da ita a harabar gida motocin suka faka. Nihal ko tunda suka nufo bakin gate gidan bakin ta ke hangame, bata k'ara rud'ewa ba sai da aka bude masu murfin mota, baki a sake take bin gidan sarauta da kallo wadda zata iya cewa raban da taga mulki da sarauta mai tsarin irin na gidan har ta manta, Basmal ce ta janyo hannu ta ganin ta tsaya tak'i gaba tak'i baya, binta Nihal tayi kamar rakuma, duk inda suka wuce se bayi sunyi k'asa da kai tare da zubewa suna kwasar gaisuwa, wani miyau Nihal ta hadiya tana cewa a cikin zuciyar ta Ashe dama da manyan mutane irin haka nake tara, lalakam kirkin su ammi ya kai tunda har suka iya bata lokacin su a kai na, Ashe dama duniya akwai masu kirki bayan yaya, ba abinda zata iya cewa ammi se dai Allah ya k'ara bud'i, shigowar su part d'in Ammi ne yasa Basmal sakin hannun Nihal ta zauna saman kujera tana murmushi tana bin Nihal da kallo wadda ta tsaya cak a parlour kamar wadda ruwan jikin ta ya tsotse, Jakadiya Dara dake goge-goge ce tabi Nihal da kallo, kallan Nihal take sosai tana so ta tuna ina ta san fuskar ko ba yau ba tasan wata me fuskar jin k'anta ya mata nauyi yasa Dara watsar da tunanin ta na murmushi Dan Nihal ta mata, murmushi ammi ta saki tana cewa Dara, "ya kika gani" tace ma Dara murmushi Dara tayi suna magana da ammi cikin mulki da sarauta Wanda se Wanda ya taso a cikin su ze gane manifar su, Dara ce tayi murmushi tace, "yadda kike so haka za'ayi ranki yadad'e komai ze tafi dai-dai" dariya Basmal tayi ita da ammi, janyo Nihal ammi tayi ta zauna da ita saman kujera kusa da ita ammi tace, "ki saki jikin ki Nihal nan ma kamar gida ne, duk abinda kike buk'ata kimin magana" sannan ammi ta nuna Dara tace, "wannan da kike gani jakadiya ce ita ce shugabar bayin gidan nan duk abinda kike so ki mata magana" kai Nihal ta d'aga ta cigaba da bin parlour da kallo kamar k'war idanuwan ta zata fito, hannun ta Ammi ta rik'e su ka Shiga wani d'aki fad'in tsaruwar dak'in b'ata lokaci ne komai na d'akin pink and white ne se royal bed yana sanye da bedsheet White se royal chair guda biyu pink da table a tsakiyar su se tangameman mirror tsaye, gefe kuma dressing mirror ne da drawer k'asan d'akin carpet ne me laushi pink and white, wasu hawaye ne su ke k'ok'arin sulalo wa Nihal ta had'iya Ashe tana da raban shiga rahamar uban giji, Ashe zata samu SAUYIN RAYUWA goge hawayan tayi dake gangaro mata tayi tana k'ara bin d'akin da kallo kamar a film, ammi ce ta katse mata tunani da cewa, "Wannan d'akin ki ne Nihal idan be maki ba ko baki San colour d'in dakin kimin magana" ware manyan idanuwan ta Nihal tayi tana cewa, "Bani da abinda zance se dai nace na gode Allah ya k'aro bud'i" girgiza mata kai ammi tayi tace, "bana san wannan godiyar taki kin ji kamar Basmal kike a guri na" kwalawa wasu bayi mata guda biyu Ammi kira tayi, cikin rawar jikin suka k'araso kan su a k'asa kowace cikin su gashin kanta ya sha two baby's cikin ladabi Yasmin da Barira suka ce, "Barka da zuwa Sultana, Allah ya k'ara nisan kwana Gimbiya" kallan-kallo ammi da Nihal suka shigayi watsar da abinda kunnan ta ya ji mata Nihal tayi tare da sakin murmushi, Ammi tace, "daga yau Ku zaku rink'a kulawa da Sultana kamar yadda zaku kula da Basmal" d'aga kai su kayi a tare sannan Ammi ta basu izinin fita. Bakin mirror Dara ta janyo Nihal tana k'are mata kallo daga sama har k'asa, ita dai Nihal bin su take dana mujiya Dara ce tace, "Yasmin ki had'awa Nihal ruwan wanka" da Sauri Yasmin da Barira suka shige toilet Dan hadu ruwan wankan Nihal, ruwan wanka suka had'a na sosai a cikin kwamin wanka sannan suka fito da wani zani sharara d'an k'ararami, Dara ce tasa hannu tana k'ok'arin cirewa Nihal kayan ta ware idanuwa Nihal tayi tana kallan ammi idanuwan ta taf da kwalla tana kallan ammi, girgiza mata kai ammi tayi tace, "karki damu duk abinda za'a maki haka tsarin yake kin ji" tana maganar tana murmushi sannan Ammi da Basmal suka bar d'akin suna smile, haka dara ta cirewa Nihal kayan ta duk da kunyar da Nihal ke ji tana nok'e-nok'e zanin da su Yasmin suka dauko shi suka nad'awa Nihal sannan suka nad'e mata gashin ta suka so ke shi da wata yar kibiya, jakadiya Dara na rike da ita suka shige toilet su Yasmin na bayan ta rik'e da bathrobe da towel haka Nihal ta bi su kamar gunki, suna shiga toilet d'in tayi mutuwar tsaye saboda haduwar toilet d'in da tsaruwar shi, cikin kwamin wanka Dara tayi ma Nihal nuni da ta shiga a hankali ta zura santala-santalan kafafuwan ta janye zanin jikin ta Yasmin tayi, yar k'ara Nihal ta saki tare da yin zaman yan buri a cikin kwamin wankan, Barira da Yasmin dariya suka saki lokaci d'aya jakadiya ta watsa masu harara simi-simi suka fice daga toilet d'in suna dariya k'asa-k'asa, in tak'aice maku Dara ce tayi ma Nihal wanka ciki da bai sannan ta mata wanka da ruwan turare daga nan tasa ta cikin hayaki na turare ta lulube ta zani se da hayakin ya ratsata turaran ya kamata sannan ta yaye zanin tare da bata bathrobe tasa sannan ta nad'e mata jik'akyan gashin ta da towel duk kunya ta lulub'e Nihal. Gudu suke a doki suna dariya Sultan ya mik'e saman dokin yana yima Ammar gwalo yana dariya saboda yayi ma Ammar nisa, Jan lizamin dokin shi Ammar yayi yana cewa, "Sultan zan kama Kane, wallahi wannan lamarin akwai San kai kayi ban yadda da wannan tseran ba ka dawo a sake," dariya Sultan saki har dimple d'in shi na lomawa ya k'ara ma dokin shi gudu yana magana da karfi saboda yayima ammar nisa sosai yace, "ba wani San...!! Be ida magana ba aka duke mashi kai da wani k'atan icce wutar Sultan ce ta dauke ya tafi taga-taga tare da sasatau ruk'wan da yayi ma linzamin dokin shi kafin yayi wani yunk'uri an k'ara maka mashi ta gaba k'okarin rik'e na gaban yake aka k'ara maka mashi iccan a keya rike keyar shi Sultan yayi yana fida numfashi sama-sama yana ganin biji-biji, haniniya dokin Sultan ya fara da karfi, ammar gudu ya k'arawa dokin shi jin haniniyar dake tashi isowar shi wajan yayi dai-dai da guduwar samarin da suka kawowa Sultan hari da sauri ammar ya sauko daga doki yana isa gaban Sultan yana fadowa daga duki sumame. Dariya Gimbiya jalila ta bushe da ita tare da mik'ewa tsaye tana zagaye d'akin ta tace, " woooo!! Ke yakumbo shiyasa nake yin ki" Gimbiya jalila ta tsaya cak daga zagaye d'akin da take ta na cewa, "Aikin ki yana min dad'i yakumbo, Ni ko Gimbiya jalila mi zan ba yakumbo yau na kyautata mata kamar yadda ta faran ta min rai yau," murmushi yakumbo ta saki tana gyara tsayuwar ta, kanta a k'asa tace, "Ranki yadad'e bani da wani buri da ya wuce na faranta maki, na kasance yar gaban goshin ki, na kasance baiwar ki na dawama ina bauta maki ke da ya'yan ki" watsa hannuwa Gimbiya jalila tayi ta waigo tana kallan yakumbo wadda kanta ke k'asa har a lokaci tace, "Indai wannan ne yakumbo kin samu bani da mahalukin dake sani farin ciki kamar ke yakumbo, me zai hanani baki wannan matsayin ke ce fa kikamin albishir da cewa ga halin da Sultan ke ciki ko ze shiga hhhhhhhh, lalala! Idan ko Sultan ya mutu yau" Gimbiya tayi far da idanuwan ta tace, "Ni da kai na zan ya'taki yakumbo ! Murmushi yakumbo ta saki tana fari da idanuwan ta na farin ciki tace, "nasan ma wannan mulelan iccan da yasha a kai, ko be je lahira ba ze iya haukacewa hhhhh" "Um hakan yayi kyau yakumbo anjima kije ki biya samarin da sukayi aikin kuma karki ci ko sisi idan kin dawo zan baki naki kasan . Alex ne daure saman kujera an rufe mashi baki da fuska cikin wani d'aki me tarkace se mutsu-mutsu yake yana gunguni , dariya jabir ya saki yana kallan Ashad, murmushi Ashad yayi a hankali k'araso setin jabir cikin rad'a yace, "idan be bamu had'in kai ba ka kashe shi kawai idan ka gama aikin ka kudin ka na jiranka, ni zan wuce gida nasan yanzu duk halin da ake ciki gidan mu an fara zaman makokin" dariya jabir ya saki yana juya kwalbar giya dake hannu shi sannan Ashad ya dafa kafad'ar shi tare da sa hula alkyabba shi ya fita da sauri shi, bayin shi na take mashi bays zuciyar fes. A hankali jabir ya k'arasa gaban Alex tare da cire mashi abinda ke fuskar shi, ware idanuwa Alex yayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mashi yana girgiza kai yana gunguni, gira jabir ya d'aga yana dariya yace, "kana mamaki ne ko Alex,? um karkayi mamaki Alex Dan ka ganeni wato kai ne kake hana ruwa gudu ko? Jibir ya ida zancan yana takewa Alex kafafuwan shi ihu Alex ya sa duk da ba'a jin ihu idanuwan shi na zubar da kwalla bakin ciki, ba komai ne ke sa Alex hawaye ba se saboda jabir na d'aya daga cikin yara Sultan dake bashi kariya San da suna Uk ko a lokaci Sultan yafi ji da shi a kan Alex saboda addinin su d'aya yaran su d'aya shiyasa a lokaci Sultan ya bashi waje na musanman, shi ko Alex kiris ta ne kuma bature ne basu fara shiri da Sultan ba se da suka zo Nigeria shima dalilin da yasa hakan Alex ne ya tura kanshi da karfi cikin zuciyar Sultan har ya koyi Hausa saboda shi wannan dalilin yasa ko sanda ze dawo Nigeria ya biyo shi gabaki d'aya, shi kuma jabir yace ze zauna a can idan Sultan ya dawo UK ya rink'a bashi kariya Ashe duk munafirci ne ya hanashi biyo su, jabir ne ya katsewa Alex tunanin ta hanyar k'ara taka mashi kafafuwa k'ara Alex ya saki, jabir yace, "tanbayar ka nake banza me Jan kunne, idan kana San kanka da mutunci ka had'a kayan ka, ka koma UK my gay," jabir ya ida zancan yana matsewa Alex fuska, cire mashi salataf d'in dake bakin shi Jabir yayi, yana saki Alex ya saki k'ara jini nabin bakin shi saboda dukan da yasha kafin a sumar da shi a kawo shi wajan, cikin murya kuka Alex yace, "Why jabir me yasa kake so kaga bayan Sultan mi yasa? Sultan be tab'a cutar da kai ba hasalima yafi sanka a kanmu mi yasa kuke muzgunawa RAYUWAR Sultan" Alex ya fad'a cikin d'aga murya, matse mashi baki jabir yayi yana cewa, "malam daina min ihu" yana maganar yana zubawa Alex Giya saman ida ya ji ciwo ihu Alex ya saki fuskar shi ta k'ara ja abinka da bature, jabir yace, "Dalla malam rufe min baki, ce maka nake ka fita harkar Sultan ka koma k'asar Ku tunda nan ba k'asar uban ka bace ko kuma na kashe ka, ko kuma kabi ra'ayina muga bayan Sultan shine magana banza," sauke ajiyar zuciya Alex yake kamar ze shid'e yace, "Never jabir Allah bazan cutar da Sultan ba se dai ka kashe ni," yana maganar yana kwance hannu shi ta baya da glass d'in da ke zube a wajan, taso mashi jabir yayi hannu shi dauke da bindiga ya seta Alex, k'undinbala Alex yayi, ya ida kwance kafar shi rigima suka Shiga yi tsaka nin su karya mashi hannu Alex yayi jabir ya saki ihu sannan ya amshe bidigar dake hannu jabir ya harbe shi a zuciya a nan jabir ya duk'e yana fitar da hawayan wahala Alex ya cigaba da Harbin shi yana kuka yana cewa, "I hate u jabir, I hate u" ya k'ara fad'a cikin calm tune, nan jabir ya fad'i matace, Alex yayi kwallo da shi yana cewa, "fuck u, son of a bitch" ya tofa mashi yawu ya ja k'afafu shi yana tafiya yana ganin jiri yana kashe yaran jabir har ya fito ya shige motar su ya bar dajin. ```Taku had kullun Salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing* *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 61_62* Tuki yake sauti k'ira'a AlQur'ani na tashi yana a hankalin har ya iso shanono ji yake baya iya sauka masaukin shi se ya fara ganin Nihal ko ze samu natsuwa, tunda ya shigo cikin garin bugun zuciyar shi ke k'aruwa ya rasa dalilin hakan, a haka har ya k'arasa kofar gidan su Nihal kasancewa yasan duk halin da ake ciki yanzu ta gama talla faka motar shi yayi tare da fad'ad'a murmushin shi ya bud'e murfin mota, wani Almajiri ya hango cikin sanyi murya ya cema Almajirin ya kira mashi Nihal, aiko Almajirin ya shiga, gwoggo dake daka ce ta d'ago tana kallan Almajirin, Almajirin yace, "Ana sallah da Nihal," tsaida dakar gwoggo tayi baki sake tace, "wake Neman ta" Almajirin yace, wani d'an birni ne murmushi Gwoggo ta saki tace, "kace mashi ya shigo," Almajirin na fita gwoggo ta shige d'akin bak'i ta gyara shi sannan tayi sauri taje ta tada sara dake bacci tace, "ke tashi Dan uban ki alheri ya zo mana tunda ita tatafi ke se ki maida gurbin ta," mikewa Sara tayi zaune tana kallan gwoggo cikin rashin fahimta, gwoggo tace, " ki tashi mana ko se ya shigo ya ganki kaca-kaca," "gwoggo wai wa? "Wannan d'an birnin nane fa ya zo neman Nihal tunda bata nan ke se ki maida gurbin ta, ki tafi birni ki huta" far da idanuwa sara tayi dama tunda ta kyala ido da rasuwar umma taga ammar ta mutu da san shi, da sauri ta duro daga kan gado ta shige toilet dan watsa ruwa, Ammar na shigowa gwoggo ta mashi iso har parlour b'aki tana murmushi zama yayi tare da gaishe ta har a lokacin yana mamakin sauyin gwoggo ruwa da sob'o ta aje mashi, amma kwata-kwata hankalin shi na kan kofar d'akin ko ze ga Nihal sanyi idanuwan shi amma shuru sunkunyar da kai k'asa yayi zuciyar shi na tsanan ta harba, Gwoggo ce ta katse mashi tunanin da sakin kukan munafirci tana kuka tana cewa, " ba komai bane yasa na ce ka shigo gida ba se saboda maganar da zamuyi bata fad'uwa a waje," ta ida zancan tare da share hawayan ta da bayan zani, zuciyar Ammar k'ara tsinkewa tayi ya tattaro hankalin shi kan gwoggo ta cigaba da cewa, "se dai muce Allah ya shiryi Nihal saboda bayan tafiyar ka, Nihal ta fetsare k'afafuwata, ta shiga bi maza har ta kai ga ankamata da kwarto a d'aki suna shek'e aya," gwoggo ta k'ara rushe wa da kuka ta cigaba cewa, "ko da baffa ya kamata dumu-dumu se da yanke jiki ya fad'i, ba'a nan ta tsaya ba Ashe tana dauke da juna biyu data lura mun gane se ta had'a kayan ta, ta gudu yau kimanin wata guda kenan bamu ga Nihal ba , ba irin neman da bamuyi mata ba, amma ina tafigewa taitabin maza" zuciyar Ammar ce ke harbawa, zuciyar na fad'a mashi k'arya ne ya za'ayi Nihal ta aika ta haka yariyar da ko ida girma batayi ba, gwoggo ce ta katse mashi tunani da cewa, "sai dai ka nemi yar'uwar ta sara shi kad'ai ne adalacin da zamuyi maka, Nihal kuwa ta riga da ta cuceka se dai ka barta da Allah" gwoggo ta ida zancan tana kuka kamar gaska, ta fice lumshe idanuwa Ammar yayi wasu hawaye na zubu mashi wato se dai suka ga bayan Nihal yanzu ina ze shiga Neman ta a duniya gashi bashi hotan ta ko d'aya. Dariya gwoggo ta saki tana fita tare da cewa sara tayi sauri ta sami Ammar a d'akin baki aiko ta shirya cikin shada yellow ansha hoda kamar ta shiga cikin gari, ga uban jan baki kamar akuya taci dusa, sallama Sara ce ta katsewa Ammar tunani da sauri ya goge hawayan shi saboda ko tashi ya kasa yi bin sara yake da kallo Dan kusan tsoro ta bashi, washe mashi hakora tayi. Ji yayi kamar ya ranta ana kere da kyar ya tattaro natsuwar shi tare da daukar car key d'in shi ya aje masu bandil d'in dubu d'aya tare da watsawa sara harara yace, "ga abin kuke so nan na aje maku, "insha Allah Nihal tana hannu na gari mtsww" sannan Ammar ya sa kai ya fice ya bar sara sake da maki tana jujuya kud'in da Ammar ya aje masu. Shigewa mota yayi cike da tunanin Nihal dan ko kasa k'arasawa yayi masaukin shi, k'ara kawai ya juya kano se yafi samun natsuwa yanzu shi ta ina ze fara neman Nihal Allah ya hada fuskokin su, ya Allah haka Ammar ya rink'a wannan tunanin da Sanbatu anya ze iya jurewa rashin Nihal kuwa a haka har ya iso kano, jiki ba kwari yana parking motar shi a parking lot lokacin yayi dai-dai da fitowar Basmal daga mota ta dawo daga makaranta sanye take da gown milk kanta na sanye ta veil black tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ba, mamaki ne ya rufe ta ganin Ammar har ya dawo yau, cikin siriri murya ta tace, "ya Ammar tsayawa yayi cak be juyo ba be kuma yi magana ba, A hankalin ta k'araso wajan shi tare da kallan fuskar shi wadda ke cike da damuwa tace, "my dear waya b'ata ma rai, har ka dawo daga shanono ne? be ce komai ba se ma rungume ta da yayi tsam a jikin shi, ya lumshe idanuwa yana tunanin wani hali yanzu Nihal take ciki sun dau lokaci a haka sannan ya sake ta za tayi magana ya daura finger d'in shi saman lips d'in ta yace, "bana san wata tanbaya please" sannan yayi gaba bin shi tayi da idanuwa tare da kad'a kai tayi cikin gida. Zaune yake saman kujera yana sanye da jallabiya fara idanuwan shi na manne da glass yayi kyau har ya gaji kamar shi yayi kan shi dan kyau yana shan coffee yana danna system da alama abinda yake mai muhimmaci ne saboda gabaki d'aya hankalin shi na kanta, knocking d'in da akeyi ne ya sasa d'ago idanuwan shi tare da cewa, " come in" cikin honey voice d'in shi Sinbul ne ya shigo kan shi a k'asa yace, "Ranka yadad'e maimartaba na san ganin ka," gaban shine ya yanke ya fad'i take a nan yaji zuciyar shi na harbawa, a hankalin ya furta "ganin zuwa" toh sinbul yace, tare da ficewa ya maida k'ofar ya rufe a hankalin ya ture laptop d'in gaban shi tare da aje cup din hannu shi saman stool, a hankalin ya taso ya bud'e kofar ya fice, Direct Fada maimartaba ya wuce dauke da sallama a bakin shi ya shiga lokacin ba kowa se maimartaba, murmushi maimartaba ya saki, a hankalin Sultan ya k'araso tare da gaishe shi har a lokacin bugun zuciyar shi na k'aruwa zama yayi kan shi a k'asa maimartaba yayi gyaran murya tare da cewa, " *SALIM* ! Gaban Sultan ne ya k'ara fad'uwa a karo na biyu, saboda maimartaba bai fiya kiran suna shi na ainashin ba, jin hakan ya tabatarwa Sultan dacewa muhimmiyar magana zasuyi, tattaro hankalin shi yayi gabaki d'aya kan maimartaba sannan maimartaba yace, "Ba komai bane yasa na kira ka ba, se dan nashe dama ka, ka fara shirye-shirye bikin ka idan kana da abinda kake buk'ata seka fad'a min, mun riga da mun gama magana da Ammi kuma hakan yamin dad'in sosai, kasancewar zab'in daga hannu Ammi ya fito, insha Allah nan da sati d'aya za'a daura auran, dago jajayan idanuwan shi Sultan yayi yana tunanin wacece wannan me k'aran kwana haka, cikin sanyin murya Sultan yace, " Abba ni fa ban gane wace magana ake ba hasali ma bamu tab'a irin wannan magana da Ammi ba" jum kad'an maimartaba yayi tare da cewa, "Ai ba wata bace ta nesa bale hankalin ka ya tashi Nihal wadda Ammi ke ruk'o," Ware idanuwa Sultan yayi yana tunanin wacece ma Nihal A hankalin yace, "ranka yadad'e ni dai ban shirya ma aure yanzu ba ya ida zancan yana satar kallan maimartaba, "Ai mun riga da mun gama magana kaje Ku sasanta kan Ku kai da yarinyar," ya ida zancan tare da had'e rai, wani irin miyau me d'aci Sultan ya had'iya, yana bin maimartaba da kallo ko ze janye maganar ganin ba wasa a fuskar shi yasa ya fice jiki a sabule. Cikin zafin har ya nufi part d'in ammi fuskar shi murtike abinka da fara fata fuskar nan tayi jawur jijiyoyi duk sun fito, tun a bakin kofa yake kwallawa ammi kira, da sauri ammi da Nihal suka fito jin kiran yayi yawa Sultan tsaye idanuwa shi jawur yace cikin sanyi murya , "Ammi ina so ki je ki cewa maimartaba kin janye maganar had'i ni aure da Nihal, dan bana san ta bana san auran I don't like her ammi, idan kuma kina san bacin raina ayi k'ok'ari a daura min auran not ever in my dream auran nan ba zeyuyu ba Sultan ba ze auri bastard ba, se me asali wadda nasan daga ina ta fito ba tsintar ciyar mage ba," yana ida maganar ya fita fuuuu.. Kamar guguwa, ammi na kwala mashi kira ko saurarata beyi ba, Nihal ko da gudu ta shige d'aki tare da sakin kuka tana tunanin ta samu *SAUYIN RAYUWA* Ashe ba haka abin yake ba wata wahala ta tsoma kanta Ammi zata shigo dakin kuma se ta fasa tare da shiga dakin ta, tana sauke numfashi a hankalin dan har wani jiri take gani saboda kalaman da Sultan ya fad'a Ammi be taba ja in ja da ita ba se yau. Yakumbo dake mak'ala ce ta saki lalausan murmushi dan yau se gimbiya jalila ta ji labari me dad'i ammi da Sultan a samu matsala duk da ba duka taji zancan ba. Adda na zaune a parlour Ammar ya shigo jiki a sanyaye Adda ce ta mik'e tare da tanbayar shi lafiya jikin a sanyaye ya rungume Adda tare da sakin kuka lalashin shi Adda ta shigayi duk da bata san damuwar d'ana taba, se da yaci kuka ya gaji yana sauke ajiyar zuciya sannan Adda ta jashi tare da zaunar da shi saman kujera ruwan sanyi tasa ikilima ta kawo mashi, se da ya sha sannan ya daura kan shi saman k'afad'ar Adda, a hankalin ta ke shafa kan shi yana sauke a jiyar zuciya, A hankalin Adda tace, "Ammar ko zaka boyewa kowa damuwar ka ban dani ya kamata ka fad'a min abinda ke damun ka Ammar," cikin sanyin murya Ammar ya shiga bata labarin Nihal be boye mata komai daga rayuwar Nihal ba ya ida zancan tare da cewa, "Adda ina tausayawa Nihal ban san hannu suwa zata fad'a ba gata yarinya k'arama bazata wuce shekara 16 ba a irin wannan shekarun tana buk'arta me kula da ita musanman iyayan ta idan suna da rai" ita kanta Adda se da ta zubar da kwalla tare da yima Nihal Addu'a Allah yasa a hannu na gari take haka Adda ta rink'a lalashin Ammar har yayi shuru ya d'an warware har ya ci abinci tare da shigewa part nashi. Direct gidan waziri Sultan ya wuce saboda gidan so annoying ya shiga gaida Adda yayi dake jera abinci dare a dining ita da ikilima, kallo Adda ta bishi da shi tare da ganin damuwa k'arara a idanuwan shi amsawa tayi, sannan ya wuce part d'in Ammar, zaune ya gashi saman kujera yana kallan news amma kwata-kwata hankalin shi baya wajan Sallama Sultan ce ta katse mashi tunani murmushi ya saki tare da cewa dude, zama Sultan yayi tare da lumshe idanuwa shi yace, "na lura so ake abi ta hannu ammi aga bayana" Sultan ya ida zancan yana goge hawayan shi da bayan hannu shi, k'ara rudewa Ammar yayi ga tashi damuwar ga ta Sultan kuma anan Sultan ya kwashe yadda su kayi da maimartaba da ammi, murmushi Ammar ya saki tare da cewa, "Nasan ammi baza ta ma zabi mara kyau ba Sultan jiki na, na bani hakan Alheri ni", harara Sultan ya watsawa Ammar rike hannu shi Ammar yayi yace, "please stop making this so difficult insha Allah auran Alheri ne," fisge hannu shi Sultan yayi tare da mik'ewa ze fice, shan gaban shi Ammar yayi yana, yace, "Haba Sultan ban sanka da haka ba, kayi hakuri mana idan ma dan wani mugun abun akayi idan Allah ya dubi zuciyar Ammi Allah ze kare ka Sultan ni dai nasan ammi bazata zab'a ma abinda ze cutar da kai ba ya kamata ka daina irin wannan tunanin, Eh yes nasan kana da mak'iya a zagaye da kai amma be kamata ka rik'a zargin kowa ba Sultan please ka rink'a yiwa mutane kyakyawan zato, balan tana na san zab'in Ammi me kyau ne, please kayi hakuri komai ya wuce, ka zo muje muyu dinner," "Ban ci na koshi" "Ni kuma ina jin yunwa I can't allow you to go home with an empty stomach, na san can ma idan kaje ba ci zakayi ba, muje" harara Sultan ya k'ara sakar mashi yace, "gidan mu zan tafi tunda kai ma goyan bayan Ammi kake" Ba haka bane goyan bayan ka nake" Murmushi Sultan yayi har dimple d'in shi na lomawa, shiyasa a kullun yake san Ammar duk bakin cikin dake damun shi daya ga Ammar yake jin komai ya wuce, murmushi shima Ammar d'in yayi sannan suka wuce dining area Ammar ne yayi saving nasu tuwan shinkafa da miyar d'ayan kub'ewa tasha naman rago se kamshi take suna ci suna fira kamar basu bane matsala ke damu ba , can Sultan ya tsaya da cin abincin ya ja d'an siririn tsaki yace, "the most annoying thing yarinyar ko asali babu mtsww," murmushi Ammar yayi yace, "Ni dai ba ruwana nan gaba idan ka fad'a, ko aibinta baza rik'a gani ba," Ammar ya ida zancan yana dariyar shak'iyanci, harara Sultan ya watsa mashi tare da aje spoon d'in hunnu shi dariya Ammar yayi yace, "Sorry ! Sannan Sultan ya cigaba da cin abinci suna hira sama-sama bayan sun kamala dinner Sultan ya dad'e a gidan waziri sannan ya dowa gida. Bud'e mashi kofa akayi ya shiga parlour Mom ya gani zaune wadda tun d'azu take zaman jiran shi, murmushi ta saki shi kuma Sultan ya wani kwabe fuskar kamar ze yi kuka ya k'araso tare da daura kan shi saman kafad'ar mom, a hankalin mom take shafa kan shi sultan yace, " Mom please kiyi ma maimartaba magana ya janye maganar nan bana san ta, don't like her, she's annoying" kissing forhead d'in shi Mom tayi tare da cewa, "this is ammi decision let her be," kuma yarinyar tamin ba ruwan ta, kayi tunani akan zab'in kaji my boy, ka ga Saboda maganar da kayiwa ammi har hawan jinin ta ya tashi, baka kyauta ba," shuru Sultan yayi duk se yaji ba dad'i ko kowa ze k'i zab'in ammi ya kamata shi ya bi, mikewa yayi tare da cewa, "bari naje na dubata" "Bacci take yanzu Dr Amir ya zo ya dubata, ina ta kiran wayar ka bata shiga lokacin" shuru Sultan yayi can kuma yace, "kashe ta nayi saboda bana san a takurami" Mom ta girgiza kai tare da kiss cheeks din Sultan tace, "Sai da safe" murmushi yayi tare da rako mom har bakin part nata sannan ya koma nashi cike da tunani *_Muje zuwa yanzu aka fara labari,🤪 idan Nazili taji Sultan zeyi aure ya zata kasance zata barsu bayan auran su sha iska kuwa? wani hali Ammar ze shiga idan ya gane cewa Nihal ce matar da Sultan ze aura shin ze hakura ya auri Basmal,! yaya karshen gwoggo da baffa ze kasance, Gimbiya jalila mi zata ji idan ta gane Sultan be san Nihal kuma itama bata san shi wani irin zama za suyi gashi kowa ze zuba masu idanuwa ne shin Sultan ze daina zargin Nihal na da had'i baki da su Gimbiya jalila koko_*🤔 _yawan comments yawan posting_🤣😂🤣 Nima daga wannan page d'in zan zama yar duniya walla ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Kyal kyal🤣😂🤣 Ashe dai haka sauyin rayuwa yayi farin jini😍 karku damu fan's insha Allah zan rink'a posting kullun sai dai idan laruru ne ya kama ni kusan jiki da jini🤪 jiya dai naga masoya da masu kira da masu magana a group da masuyi ta prvt duk na gode insha Allah zan rink'a kwamuso maku story kamar ba gobe_*🤸🏽‍♀🤸🏽‍♀ *Page: 63_64* *Washe gari* Shiryawa Sultan yake cikin wata suit Apple green colour da black inner tie d'insa the same colour da suit d'in Cufflinks yasa tea green diamond stone ke da su, Suit d'in ta kama jikin shi kamar Dan shi akayi kayan making his figure perfect, wani silver bezel wrist watch ya saka da wasu covered shoes black, masha Allah he looks breath taking, ya b'ata fuskar nan, despite he look magical handsome, fashe jikin shi yayi da turaran Al-haramain tare da k'ara gyara gashin kan shi, kallan Sinbul yayi tare da cewa, "ka dau ki briefcase d'ina ka kai min parking lot ka ba Alex" to Sinbul yace, tare da ficewa A hankali yake tafiya kamar me tausayin k'asa, a haka har ya k'arasa part d'in ammi saboda da tunanin ta ya kwana a ran shi yana shiga yaci karo da Jakadiya murmushi ta saki tare da cewa, "Ranka yadad'e ka tashi lafiya" murmushi Sultan ya saki tare da cewa, "Lafiya lau Dara" d'aga kira yayi tare da rik'e kugun shi yace, "Dara ina matar ne" "Tana d'aki kasan jikin nata ya motsa" "Toh Sultan yace tare da wuce wa bedroom d'in Ammi cike da shagwaba. A hankali ya bude handle d'in kofar zaune ya hango ta saman gado gefe kuma Nihal ce zaune hannun ta dauke da plate din abinci tana feeding Ammi pepper soup d'in nama rago, sanye take da riga pink me hannu vest da mini sket black gashin kanta yasha gyara, tayi parking nashi da black ribbon daga k'asa ya nanad'e kamar taliya duk da ba kwaliya a fuskar ta tayi kyau sosai, kallo d'aya Sultan ya mata ya kauda kai tare da gyaran murya, gabaki d'ayan su juyowa sukayi a tare suka zuba mashi idanuwa, wani irin kyau Nihal taga Sultan ya k'ara mata har yafi lokacin da ta fara ganin shi, a zuciyar ta tace, " ya Allah wannan mutumin Akwai kyau masha Allah, amma daga ganin shi ba lalai yayi kirki ba ko fitsara da yayi ma ammi jiya ta nuna halin shi, shagwabe fuska Sultan yayi ya zama abin tausayi, Nihal na ganin haka ta aje plate d'in hannun ta saman bedside drawer tare da mik'ewa zata fita rik'e hannun ta Ammi tayi murmushi Nihal ta saki tare da yima Ammi pack a goshi tace, "bari na baku guri kuyi magana" murmushi Ammi ta saki tare da sakin hannun Nihal, A hankali ta taso har a lokacin Sultan na bakin kofa yana bin Nihal da kallo se da ta zo daf da shi sannan ya kauce tare da aika mata harara, kauda kai Nihal tayi dan baza ta juri kallan tsanar da Sultan ke mata ba tausayin kanta ne ya kamata, anya ko zata iya daukar irin cin kashin da tasha A hannu su gwoggo kuwa, lokaci yayi da ya kamata ta kwatar wa kan ta yanci lumshe idanuwa Nihal tayi tare zama saman kujera parlour tana tufka tana warwara. Karasowa sultan yayi bakin bed d'in ya zauna yana murmushi a hankali ya kama hannu Ammi yayi kissing nashi tare da cewa, "Am sorry Ammi nasan ban kyauta ba, abin da nayi maki ji Ammi" kama kunnuwanshi yayi biyu tare da cewa, "ki yafemin Ammi" ya ida zancan cikin raunaniyar murya, Sauke hannuwanshi Ammi tayi tare da cewa, "Ni ya kamata na baka hakuri na had'a ka da abinda baka so, kuma gaskiya ka fad'a a matsayin ka, ya kamata ace Kasan daga wani tushen wadda zaka aura ta fito ni ya kamata na nemi yafeyar ka sultan" daura d'an yatsan shi Sultan yayi a lips d'in Ammi yana girgiza mata kai yace, "Ki daina fad'in haka Ammi indai zab'in ki ne, na amsa hannu bibiyu zan nunawa duniya cewa Ammi ta isa da Sultan ba maimartaba kad'ai ba, zan nunawa zab'in ki so" ya ida zancan yana killing smile d'in shi har dimple d'in shi na lomawa, murmushi Ammi ta saki tana cewa, "Da har zan janye maganar" ware idanuwa Sultan yayi tare da cewa, "So kike na Shiga wani Hali, ban k'arewa zab'in ki kallo ba se yanzu" ya ida zancan yana kashewa Ammi ido, dariya Ammi ta saki tare da Jan cheeks d'in Sultan tace "kai ko" wani irin dad'i Sultan ya ji ganin yasa Ammi cikin farin ciki, bin Ammi da idanuwa Sultan yake yana murmushin yak'e kenan idan har yana so Ammi ta kasance cikin farin ciki ya zama dole ya auri Nihal wani bakin ciki ne ya tokare mashi wuya, janyo plate d'in dake saman bedside drawer yayi tare da cigaba da feeding Ammi tana ci yana bata labari har ta cinye sannan yayi kissing goshin ta tare da ficewa. A parlour ya ci karo da Nihal tana kallo tana ganin Sultan ta mik'e da Sauri zata shige d'aki, fisgo ta Sultan yayi har kan ta ya daki fafad'an kirjin shi gashin kanta ya gogi fuskar shi har yana k'ok'arin shige mashi baki matsar da gashi sultan yayi ga wani kamshi ta daya mamaye mashi hanci lokaci daya, ture ta Sultan yayi daga k'irjin shi, tafiya Nihal tayi taga-taga zata fad'i Sultan ya k'ara matse lalausan hannun ta kamar audiga, wata yar k'ara Nihal ta saki tare da rintse idanuwan ta, kafe ta Sultan yayi da idanuwa yana kallan ta be ma San yana yi ba of coz he can't resist to stop looking at her natural beauty face, jin shuru yasa Nihal ware manyan idanuwan ta tare da sauke su kan kyakyawar fuskar Sultan ture ta Sultan yayi da k'arfi, tare da gyara suit d'in shi, fad'awa saman kujera Nihal tayi idanuwan ta taf da kwalla tana sauke ajiyar zuciya, juya mata baya Sultan yayi tare da zuba hannuwashi cikin aljihu yace cikin honey voice d'in shi , "ina me baki shawara tun wuri ki cewa Ammi baki so na, baki yadda da wannan auran ba, ko kuma ki fad'a min nawa aka biya ki ! kika shigo rayuwar Sultan tun daga naira d'aya har zuwa billion ki fad'a min ni kuma na maki alk'awari zan baki, kwata-kwata baki dace da Sultan ba ya kamata ki San da haka, ga cheak nan zan baki na naira million 10k idan be maki ba ki fad'a min na k'ara maki, na baki nan da yamma ina so ki had'a ina ki ina ki kisan inda dare ya maki" sannan Sultan ya watsa mata cheak d'in kud'in ya fice, kuka Nihal ta saki tare yayaga cheak d'in da Sultan ya bata, ta shige daki da gudu jikin jakadiya ta fad'a dake jera mata kaya a drawer, juyo da ita Dara tayi suna facing juna a hankali ta zauna da Nihal saman gado, jin kukan Nihal take har cikin zuciyar ta a hankali Nihal ta daura kanta saman kafad'ar Dara tana cigaba da kuka ita kanta Nihal bata San me yasa take jin Dara kamar umma ta ba shafa bayan ta Dara take. A hankali tana sauke ajiyar zuciya tana jan majina kamar me mura, Dara ce tace, " ki k'ara hakuri da Sultan kin ji, nasan bame b'ata maki rai a wannan lokacin se Sultan tunda shi kad'ai ya shigo part d'in nan, duk wannan abun da Sultan ke maki na d'an lokaci ne Nihal, jiki na na bani auran nan Alheri ne kuma ki duba ki gani Sultan be da wata makusa yana da halaya masu kyau kowace uwa ta gari zata so ce yarta ta Sultan ze aura, shiyasa nafi kowa yi maki sha'awar na ga kin zama matar Sultan ina nan dake wata rana se kin bani labarin kulawa da Sultan ke baki, na san cewa yanzu ba lalai ki fahimci abinda nake fad'a maki ba Amma nan gaba zaki gane" kawai saurara Dara Nihal take Dan zuciyar ta ta fara raya mata ta gudu kamar yadda Sultan d'in ya buk'ata Amma ta gudu ina zata shine tunanin da take, lumshe idanuwa tayi, ta cigaba da tunani shin ta gudu ta kyautawa Ammi kuwa, murmushi Dara tayi tare da shafa kan Nihal tace, "Nihal karkiyi tunani Mara kyau saboda abin Sultan ya maki kin ji Sultana, kada kiyi k'ok'arin barin gidan nan ko dan ni, saboda inajin wani Abu game dake Nihal wadda har yau kasa gane me dalilin hakan, na rasa mi ya sami kwakwalwata bata tuna baya" hawayan dake mak'ale a idanuwan ta Dara ta goge tare da saurin tashi ta bar dakin, Nihal ko bin ta tayi da idanuwa tare da cewa, ya akayi ta gane tunanin da nakeyi kenan, gyara zama Nihal tayi tare da ware idanuwan ta yaya ne ya fad'u mata a rai Allah sarki shi ka d'ai ne ke gwada mata soyayya a duniya bayan umma da Abba se yaya se Ammi da Dara Wayan da suka shigo rayuwar ta yanzu, wai yaushe ne zata samu *SAUYIN RAYUWA* ne lumshe idanuwan Nihal tayi tare da kwaciya ta watsar da tunani dake damun ta. Sultan ne zaune cikin office ya lumashe idanuwan shi yana juya kujera a hankali, a zuciyar kuwa fata yake kafin ya koma gida Nihal ta tafi, dan shi kwata-kwata by know love doesn't exist in his dictionary, knocking d'in kofar da akayi ne yasa Sultan cewa, "come in" cikin calm tune har a lokacin idanuwan shi a lumashe, Ammar ne ya shigo hannu shi dauke da file kallan Sultan yayi Wanda har a lokacin idanuwan shi na lumshe suke, zama Ammar yayi tare da gyaran murya yace, "Sultan! Cikin calm tune d'in shi ya cigaba da cewa, "haba Sultan mun riga da munyi maganar nan jiya be kamata yau na gan ka cikin damuwa ba ya kamata ka rage to much of thinking nasan Ammi baza ta tab'a ma zab'in mara kyau ba, jiki na na bani cewa zab'in nan Alheri ne ya kamata ka daina maido hannun agogo baya abinda ya wuce ya wuce Sultan nasan kana jin tsora kar a kuma yin na Asiya I don't think wannan haka take please ka daina haka mana" A hankali Sultan ya ware lumsasun idanuwan shi ya zubawa Ammar su kamar TV yana kallan sa yace, " Ni fa kwata-kwata yarinyar nan bana san ta, ban san mi ya rufe wa Ammi ido ba, ko ra'ayi na bata tanbaya ba kan yarinyar nan, ina tunanin ko 17 year bata kai ba mtsww," "Kayi hakuri Sultan kowa na duniyar nan hakuri yake ni kai na hakuri nake dan ji nake kamar duniyar ta min nauyi" galala Sultan ke kallan shi yace, "Dama kana da wata damuwa ka kasa fad'a min! " ya za'ayi na fad'a ma bayan ga taka damuwar please ka daina tunani, yanzu dai ka tashi muje muyi lunch dan har na fara jin yunwa" "Bana ci na koshi, saboda bani da matsayi a wajan ka har Abu na damun ka kakasa fad'a min" "Ya hakaru Sultan ban San tadama hankali ne kuma nayi promise da mun gama lunch zan fad'a ma" Harara Sultan ya watsawa Ammar tare da cewa, " sarkin ci" a tare suka fice da Sultan yana kunbure-kunbure kamar ka ce kule yace cas. "Gimbiya Nifa k'inshin-k'inshin nake ji Sultan ze yi aure," date k'arjin ta Gimbiya jalila tayi tare da cewa, "au mi? Anya kunnan ki dai-dai ya ji kuwa yakumbo? " Wallahi Gimbiya jiya da kunne na naji se dai ban tabatar ba kamar ma basan auran yake ba Ammi ce zata lik'a mashi wata ya aura" "Kinga wannan jarababa tsohuwar ni ina k'ok'arin kawar da shi ita kuma tana k'ok'arin yi mashi aure ya Tara zuri'a kenan! Bari naje part d'in Ammin na gani da idanuwa. Alkyabba kawai Gimbiya jalila ta zura tare wuce wa part d'in umman Sultan dan tasan wajan ta kad'ai zata ji yadda zancan yake, dauke da sallama a bakin ta ta shigo, Gimbiya Nadiya na zaune saman kujera ana mata massage, murmushi mom ta saki ganin Gimbiya jalili tare da yi mata nunu da mazauni, tsayawa Gimbiya jalila tayi har se da yakumbo ta kakab'e mata wajan sannan ta zauna girgiza kai mom tayi tana mamakin rashin yadda na jalila, maganar Gimbiya jalila ce ta katse mata tunani da cewa, "Haba umma Sultan ban tab'a tunani haka ba," karkato hankalin ta mom tayi kan Gimbiya jalila tare da yima bayin d'akin Alamar su fita, yakumbo ko ji tayi kamar ta kifawa mom mari dan ta so ayi komai a gaban idanuwan ta, Gimbiya jalila ta cigaba da cewa, "Ashe dama irin zaman da muke kenan a ce abin Arziki ya sami Sultan se dai naji labari a wajan bayi na, ace me jiran gado zeyi aure bani da labari, ko da yake aini ban kai matsayin uwa a gare shi ba" Gimbiya jalila ta ida zancan tana matsar kwalla, duk mom se ta ji ba dad'i kuma haka ba laifin ta bane laifin Ammi ne tayi tunani tun ranar da aka kawo mata Nihal ranar an kai ta wajan momi, mom ce tace, "kiyi hakuri Gimbiya nayi tunanin an kai maki ita tunda nima Ammi ce ta aiko min da ita saboda zab'in Ammi ce, kuma yarinyar mai hankali se dai muce Allah ya tabatar da Alheri dan Sultan yayi sa'a" wata uwar harara Gimbiya jalila ta makawa mom bata lura ba sannan ta mik'e tana cewa, "bari na je na ga suruka tawa to" tana maganar tana washe hakoran munafirci, mom tace, da kinyi zaman ki se a kira maki ita " "Ba komai bari na k'arasa d'in" sannan Gimbiya jalila ta fita tana maimaita maganar da mom tayi tare da Jan d'an siririn tsaki. Part d'in Ammi ta wuce dauke da Sallama Ammi dake cin Ammi ita da basmal suka Amsa har k'asa ta duk'a ta gaishe da Ammi ta amsa ran nan sake, sannan Gimbiya jalila tace, "Na zo ganin suruka tawa da kai na dai" murmushi Ammi ta saki tana cewa, "nayi laifi amin hakuri da jiya zan turo ta se ban ji dad'i ba shiyasa bata zo ba" "Allah sarki Ammi muma haka jiya muka ji da kyar na samu na rintsa saboda tunanin halin da kike ciki" "Allah sarki ni ina nan ina bacci Ku na hana Ku" "Laa ba komai Ammi" "Ki shiga daga ciki Nihal d'in na bedroom d'in ta" harara Gimbiya jalila ta sakarwa Ammi a fakaice ji take kamar ta shak'eta kowama ya Hutu. Turus Gimbiya jalila ta tsaya tana bin Nihal da kallo wadda yanzu ta fito daga wanka tana sanye da bathrobe gashin kanta ya wani nanad'e ya kwanta a gadan bayan ta, ga santala-santalan kafafuwan ta sun bayana fuskar ta Gimbiya jalila ta k'arewa kallo tare da had'iye wani yawu me d'aci, tab d'i jam gaskiya wannan bata dace da sultan ba ko alama, wannan yarinyar da Ashad ta dace! Dan mugun Abu se aka zab'awa Sultan wannan zuk'ek'iyar yarinyar Wanda a shekaru ya tsere mata nesa ba kusa ba, lokaci da zata k'ara girma Allah kad'ai ya San kyan da zata zubu ni da nake mace na yaba bale namiji shiyasa Nadiya ta isheni dabkunfar baki, da kyar ta iya tataro natsuwar ta saboda bak'in cikin dake cin ta , Nihal da jakadiya ne suka duka har k'asa suka gaishe da Gimbiya harara ta makawa Jakadiya tace, "ina San yin magana da suruka ta se a bamu wuri ko! Jiki a sabule jakadiya ta fita, murmushi Gimbiya jalila ta Saki tare da rik'e hannuwan Nihal ta zauna da ita saman kujera tana sakin murmushi munafirci, ita ko Nihal duk kunya ta kamata cikin siririyar muryar ta, ta shigar munafikai tace, " ki saki jikin ki mana Nihal se wani noke-noke kike, ki dauke ni kamar umman ki kin ji dani da umma Sultan duk d'aya ne, ko wani ya hure maki kunnene a kaina? Girgiza kai Nihal tayi alamar a'a murmushi gefen fuska Gimbiya jalila ta saki tana cewa, "duk abinda ya shige maki duhu ko baki gane ba ki fad'a min kinji" d'aga kai Nihal tayi alamar toh, k'ara sakin wani murmushi Gimbiya jalila tayi tare da rike hannun Nihal duka biyu kamar wata ta Allah ta marairai ce cikin sanyin murya tace, "d'iya ta naga kamar baki san auran nan, idan har baki San sultan ki fad'a min, ni kuma na baki alk'awari zan hana amaki auran nan, saboda kwata-kwata Sultan be da hali shiyasa nake tausaya maki nasan zaki sha fama," ta ida zancan tana satar kallan Nihal wadda idanuwan ta sunyi ja, wani dad'i ne ya lulub'e Gimbiya jalila ta cigaba da cewa, "kina san sultan ko baki san shi? Shuru Nihal tayi zuciyar ta na harbawa da sauri da sauri lokaci d'aya jikin ta ya hau rawa anya ta fad'awa Gimbiya cewa bata san Sultan ta kyautawa Ammi kenan, to idan Ammi ce ta aiko ta Dan ta bigi cikin ta fa, wata zuciyar tace, a'a Nihal k'ara ki fad'a mata da wannan auran wahala da zaki tsoma kanki, lumshe idanuwan ta Nihal tayi tare da bud'e bakin ....... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rast```) *Page: 65_66* Lumshe idanuwa ta Nihal tayi tare da bud'e baki ta rik'e hannuwan Gimbiya jalali tare da sakin murmushi me sauti tace, "ina san Sultan! ina san shi kamar yadda yake so na" Nihal ta ida zancan tana tsare Gimbiya jalila da manyan idanuwan ta, ta Cigaba da cewa, "Umma duk wadda ta samu Sultan a matsayin miji tayi sa'a" galala Gimbiya jalila tabi Nihal da kallo tana antaya mata Ashar a zuciyar ta, kallan mirror Nihal tayi tare da cewa, " Umma dan Allah na dace da Sultan ko ban dace ba" ta fad'a cike zak'uwa takaici ne ya hana Gimbiya jalila yin magana se da Nihal ta maimaita tanbayar ta, sannan ta had'iye wani k'ulutun bakin ciki tace, "kun dace mana sosai ai dacewar ce tasa aka had'a ku amma! " bata ida zancan ba Nihal tayi wani irin juyi da idanuwan ta tare da washe baki tana k'arewa kanta kallo a mirror kamar gaske, takaici ne yasa Gimbiya jalali barin dak'in cike da tsanar Nihal, tana fita Nihal ta fad'a gado tare da sakin kuka, Allah ya gani bata san Sultan mi zaisa ma ta so shi mutumin da be da mutumcin. ********************* Shirye-shirye biki ake ba kama hannun yaro, Nihal se gyara take sha, ta murje tayi kyau ta k'ara haske har wata k'iba ta d'an k'ara komai na jikin ta ya ciko sosai musanman na fulanin ta, hips ko ba'a magana kullun cikin dura mata magunguna mata ake kala daban-daban se zuba kamshi take komi ta rik'e se ya kama kamshi saboda tsabar gyara da kamshi, ta k'ara kwarewa da shiga ta wayewa da iya make up idan tayi kwalliya da kanta yadda kasan yi mata akayi saboda yadda ta goge Duk wani takalmi me tsini ta iya sawa ta zagaye gari, ga wani mulki da saurata da Ammi ke koya mata idan ka ga Nihal baka tab'a cewa ita ce, waje d'aya ne take kwafsawa idan kayi mata turanci bata iya ba shima Ammi tace bayan biki idan ta gama cin Amarcin ta za'a Sata makaranta. Bagaran Sultan har mantawa yake da wata Nihal dan shi kwata-kwata mantawa yake za'ayi wani Abu wai shi aure, saboda ko ganin Nihal d'in bayayi saboda ko fita ba'a bari tayi, ba yadda Ammar da Amir ba suyi da Sultan ba dan ayi wani eventis yace a'a, a Cewar shi babu wani anfanin yin wani events da wadda ba so yake ba kuma mara tushu wannan dalili yasa Sultan kin amincewa da maganar su Ammar, dan ko IV yak'i rabawa kowa se Ammar ne da Amir suka zage se rabawa friend's IV suke, ranar da Ammar ya fara ganin suna Nihal a IV din se da ya sha ruwan jinin jikin shi Amma se ya watsar da zancan, amma ya dad'e yana kallan IV zuciyar shi na tsanan ta bugawa da kyar ya samu ya watsar da tunanin cewa ba Nihal d'in shi bace zata auri Sultan. Yau aka shigo da lefan Nihal akwati shabiyu kowa yayi mamakin kayan dake cikin an zuba mata kaya sosai, ita kanta Nihal tasha mamaki gwala-gwalan dake cikin kayan basu fad'uwa har da makulin mota, Nihal ganin abubuwan take kamar a mafarki, tare da mamakin irin dukiyar da ake narka mata, babba takaicin ta shine irin b'ata lokacin da ake wajan gyara ta, ga Wanda be san daraja ta ba, kyakyawa kulawa take samu wajan mom da Ammi Basmal ma ba'a barta a baya ba, suma sauran yaran dan basu nan ne su boarding School minal da shukara Nasim ne kad'ai ke gida shima kullun yana lik'e da Nihal kasancewar jini su ya zo d'aya, Gimbiya jalila ko shishigewa Nihal take dan ta samu dama turawa Sultan mugun Abu ta hannu Nihal , Allah sarki Nihal ita ko bata sani ba, amma duk da haka bata sakin jiki da Gimbiya jalila ita kanta bata san dalilin hakan ba, Sultan ne saman kujera zaune yana shan coffee, sanye yake da Jean's black and T-shirt red ta kama jikin shi sosai hakan se ya k'ara fito mashi da zala kyan shi, gashi kan nan nashi ya wani kwanta se shek'i yake, sajan shi ya kwata luf-luf ya wani k'ara haske da kyau, Sinbul ne ya shigo parlour tare da sanar mashi dacewa maimartaba na neman shi, cewa yayi gashin nan zuwa A hankali ya mik'e ya fito, bangaran Nihal ma maimartaba ya aika ta zo sanye take cikin red gown me Stone's ta kama jikin ta ba k'aramin kyau ta mata ba, kamar dan ita akayi rigar, ta wani k'ara haske dama ga gyara tana sha tana tafiya Albarkatun jikin ta na motsawa, black veil ta dauka tare da wuce wa fadda maimartaba, a dai-dai bakin kofa suka ci karo da juna kallan-kallo suka shiga aikawa junan su kowane cikin su bugun zuciyar shi na k'aruwa kauda idanuwan ta Nihal tayi tana k'ok'arin shigewa, kallan da Sultan yake mata ne ya haifar mata da tintibe luuu ! ta tafi zata fad'i Sultan ya mata masauki a fafad'an kirjin shi lumshe idanuwan Nihal tayi tare da yin lamo a kirjin Sultan tana sauke Ajiyar zuciya, duk tsoro ya kamata saboda bata san kala wulak'ancin da Sultan ze antayo mata ba shiyasa tayi lamo tana jiran saukar aradu, Shi ko Sultan gabaki d'aya ya rud'e saboda wani irin fitinan kamshi da Nihal ke zubawa ga wani laushi da ya ji jikin ta yayi kamar auduga, a hankali yake shinshina kamshi turaran ta yana k'ara riki ta shi veil d'in kanta ne ya zame kallan gashin Sultan ya shiga yi wanda yayi baki wulik se shining yake, wata kasala ce ta lulub'e Sultan da kyar yake tatare natsuwar shi dan kar ya watsa kanshi kauda kai yayi gefe zuciyar shi na harbawa da sauri da sauri, a hankali Nihal ta zame jikin ta daga jikin Sultan ta maida veil d'in ta cikin Siririyar murya ta tace, "Na gode da taimako " tana ida zancan ta shige fadda, d'an siririn tsaki Sultan ya saki a zuciyar shi yace, ba wani yar iska wannan iskancin duk cikin plan d'in da aka koya maki ne insha Allah ba zaki ci galaba a kai naba" sannan shima ya bi bayan ta, dauke da sallama suka shige fadda maimartaba, murmushi maimartaba ya saki shi da waziri dake zaune a gefen maimartaba, har k'asa suka duka suka gaishe su baki washe maimartaba da waziri suka amsa, nuni sarki ya masu da su zauna a hankali suka zauna a kujera har a lokacin kan Nihal na k'asa tana wasa da yan'yatsun hannun ta Wayan da suka sha bakin lale, Sultan se satar kallan su yake, be tab'a ganin wadda lale ya mata kyau a hannu ba kamar Nihal, maganar maimartaba ce ta katse mashi tunani da saurin ya kauda kan shi, maimartaba yace, "ba komai bane yasa na kira kuba se dan na baku kyautar kayan daza kusa ranar daurin auran Ku ranar da tafi kowace rana Albarka a rayuwar ku" yana fad'a yana murmushi Alkyabba waziri ya mikawa maimartaba Silver tasha aiki da gold zare da sark'ar gold da wata doguwa riga me kyan gaskya A hankali ya taso ya mik'a wa Nihal Wanda kanta ke a k'asa har a lokacin murmushi Nihal ta saki tare da bud'e baki zata tayi godiya, maimartaba ya girgiza mata kai tare da shafa kanta yace, "Allah yasa maki Albarka" sannan ya mik'a hannu aka bashi na Sultan, Alkyabba ce black anmata aiki da gold zare da fara shada a sama da zoben azurfa se kyali yake da agogwan silver me tsadar gaske murmushi yak'e Sultan ya saki tare da bud'e baki yayi godiya maimartaba, ya ja mashi cheeks yace, "Bana san godiya nan Allah yasa maku Albarka kuna iya tafiya," jikin Nihal ko sanyi yayi yanzu kenan Sultan zata aura wani irin zama zatayi da Wanda ya tsane ta kenan ita rayuwar ta a haka zata k'are cikin tsana da tsangwama, shi ko Sultan tsanar Nihal ce ta k'ara narke mashi a zuciya kenan shi rayuwar shi ba ze tab'a zamun jin dad'i a duniya ba, tun yana daukar auran wasa gashi har ya zama gaske tunda gobe ne d'aurin auran, har sukayi nisa kowa da abin da yake sak'awa wani takaici ne ya ciwo Sultan, fisgo Nihal yayi da k'arfi wata yar k'ara ta saki saboda matsar da Sultan ya mata toshe mata baki yayi suna kallan juna ido cikin ido, idanuwan Nihal taf da kwalla, Sultan yayi murmushi k'arfin hali har dimple d'in shi na lomawa idanuwan shi sunyi jawur yace cikin honey voice d'in shi, "Se ki zubar da ruwa a k'asa kisha zaki auri Sultan, amma ki sani bana san ki natsane ki! kuma ba zan tab'a zama dake a matsayin mata ba se dai a matsayin baiwa! ke ko baiwa ta fiki daraja a idanuwa na saboda nasan mi yasa kika aure ni saboda san abin duniya, tun yanzu an fara baki se kiyi murna, kuma ina mai sheda maki karki sake ki Shiga gona ta saboda kika shiga ilata ki zanyi kamar kiyashi ina fata kin gane bloody fool ! sannan ya saki Nihal yana aika mata kallan tsana kuka Nihal ta saki tare da barin sultan tsaye a wajan kamar gunki shafa sumar kan shi yayi tare da barin wajan. ************************************ A yau ne d'ibin mutane suka sheda Daurin Auran *SULTAN SALIM MATAWALE da NIHAL ABUBAKAR* wanda ya tara manya-manya masu kud'i da b'usushin gwabnati da yan' kasuwa da saraku na jahohi daban-daban, babu abinda ke tashi a babba masalacin Sarkin kano se bushe-bushe da alkaita da kirari Allah yasa Alheri ya bada zaman lafiya, marok'a sun zagaye Sultan suna mashi kirari, sanye yake cikin wata black Alkyabba ta sha aiki da gold zare daga cikin alkyabba fara shada ce tas tasha aikin sarauta na gani na fad'a da sirfani da brown zare, yana sanye da farin rawani yayi kyau masha Allah idanuwan shi na manne da d'an siririn glass ko ba'a fad'a ma ba kasan shine ango saboda haduwar shi da zala kyan shi daya bayana, se dai fuskar nan ba walwala se ma ya kalle Ammar sannan yake murmushi yak'e yana ba marok'a kud'i, shima Ammar d'in ba'a bar shi abaya ba dan ya sha kyau cikin brown shada malin-malin tasha aiki sarauta da dark brown zare se washe fararan hakoran shi yake kamar gonar audiga. Amarya tasha kyau wanke hannu ki taba saboda tsabar kyau da Nihal ta zuba, sanye take cikin Alkyabba silver tasha aiki da gold zare daga ciki gown ce gold da d'ishi-d'ishin Stone's masu kyali se walwali suke gashin kanta ya wani nanad'e ya zubo har gadan bayan ta daga cikin hula alkyabba ana hango shi yana reto, murmushi yak'e kawai Nihal take saki, se faman rangad'a bud'a ake anayi mata kirari ita da angwan nata Basmal ko se rawar kai ake zubawa itama tayi kyau har ta gaji pic kawai ake dauka kamar ba gobe. Shigowar ango ce gaida Ammi yasa busa ta k'aru bayan sun dawo daga daurin aure Nihal najin haka zuciyar ta shiga dukan uku-uku ita kanta bata san dalilin hakan ba, tunda Sultan ya shigo tsafin bayi keyi mashi kirari yana watsa masu kud'i kamar takada yana washe fararan hakoran shi dimple d'in shi na bayana har ya k'arasa gaban Ammi, Ammi na ganin shi ta fara hawayan dad'i dan yau Sultan ya cika mata burin ta daya auri Nihal musanman yadda taga yana nuna jin dad'in shi, a hankali Sultan ka k'araso dai-dai setin kunan Ammi yace cikin honey voice d'in shi, "Why those tear Ammi? Ke da ya kamata kiyi rawa har da tsale" d'an duka Ammi ta kai mashi tana girgiza kai, albarka ta shiga jera ma Sultan bayi da manyan hajiyoyi da matan sarakai na amsawa da Amin. Ammar dake tsaye bayan shi yana mitsinin shi yana dariya k'asa-kasa yace, "munafiki wallahi ka cuci yarinyar mutane se Allah ya kamaka" harara Sultan ya maka mashi a fakaice, Amm ce tace, "a fito da Amarya tayi pic a angwan nata" ana fad'in haka wayar Ammar ta shiga ringing dai-dai lokacin Nihal ta fito Ammar ya rab'a ta gefen ta ya fita se dai yaji wani irin shock, amma se ya basar tare fa ficewa yana waya. Azizi ce baiwar Nazili ke zarya cikin daki tana kiran Nazili Amma wayar bata shiga tunda satin bikin Sultan ya tsaya kullun se ta kirata, amma wayar ta ci ringing ba'a dauka, zagaye d'akin Azizi take tana cewa, "Aunty Nazili ki dauka mana" har wayar ta katse ba'a dauka ba k'ara kira tayi karaso na biyar, Nazili da ke zaune saman resting chair bakin Swimming pool gashin ta yawani baje daga ita se wata vest milk dai-dai cinyar ta santala-santalan cinyoyin ta waje tana shan juice d'in coconut,ta wani tarwai saboda tsabar haske idanuwan ta na manne cikin bakin glass, d'an siririn tsaki ta saki tare da mik'a hannu ta dau wayar ta cikin mafisa da tsiwa tace, "me wai Azizi ! Wani irin shock Nazili tayi tare da mik'ewa idanuwan ta waje😨 ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```` [1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *page: 67_68* Wurgi da wayar hannun ta Nazili tayi sakwamakwan ganin pictures d'in Sultan da Nihal Wanda Aziza ta turo mata dukewa tayi a wajan tare da fashewa da kuka tana cewa, "nooo! Sultan ni kad'ai ce na dace da kai" da gudu ta shige cikin gida ta wuce aunty lusi dake parlourt ta haura upstart's tana me cigaba da kuka drawer ta bud'e ta Ciro trolley d'in ta, ta fara loda kaya kamar mahaukaciya tana kuka aunty lusi ce ta biyo ta a baya tana cewa, "what wrong with you? Why are you crying? What happened to you? Haka aunty lusi ta rink'a jerawa Nazili tanbaya lokaci d'aya amma ko juyo ta k'iyi se kuka take tana faman had'a kaya cikin trolley, juyo da ita aunty lusi tayi suna facing juna, fad'awa jikin aunty lusi Nazili tayi tare da saki matsanan cin kuka tana cewa, " why Sultan! tana kuka tana cigaba da cewa, "se na kashe koma wacece ta auri Sultan se naga bayan ta bazan tab'a barma ta Sultan ba" tana fad'i zancan tana shashek'ar kuka, a lokacin ne aunty lusi ta gane halin da Nazili ke ciki lalashin ta shiga yi tare da zaunar da ita bakin gado tana cewa, "ya isa kukan haka kin ji daughter ai ba shi kad'ai bane namiji da zaki d'agawa kanki hankali ba, akwai maza da yawa masu kyau da mulki da komai wayan da suka fishi, kuma kema kina kyan nan zaki sami wanda ya fishi, tunda ki kaga haka Allah ya nufa ba mijin ki bane" mik'ewa Nazili tayi tare da jefawa aunty nata wani mugun kallo tayi, sannan t shigewar ta toilet tana wanka tana kuka da sanbatu, haka aunty lusi tayi zaune tana zaman jiran fitowar ta, tana fitowa ko kallan ida take batayi ba lotion ta shafa tare da janyo rigar ta doguwa peack colour me dogwan hannu sannan ta daura black veil ta saka takalman ta masu tsini ta manna bakin glass a idanuwan ta duk da ba wata make up a fuskar tatta tayi kyau sosai, trolley d'in ta ta janyo aunty lusi tace, "ina zaki da yamma nan Nazili? Take it easy mana" Nazili wadda ta juyawa aunty lusi baya tace, "Nigeria zan koma a yau se na katse masun jin dad'in se na watsa farin cikin da suka tanadar wa daran yau," sannan ta ja trolley d'in da karfi ta fice daga gida ko saurara aunty lusi ta k'iyi, zama Aunty lusi tayi saman gado tare da dafe kanta, direct airport Nazili ta wuce. Kasancewar yau ta kama walima cikin wata bleu Alkyabba aka shirya Nihal tayi kyau sosai kamar ita tayi kanta saboda tsabar kyau, da rana malama ta zo tayi wa'azi mai shiga rai akayi ciye-ciye da lashe-lashe. Bangaran ango ko yana zaune da friend's d'in shi a part nashi se had'a kaya suke saboda yau suke so subi flight d'in karfe 4:00pm su wuce Abuja wasu kuma su bar k'asar se godiya Ammar ya ke masu kan namijim k'ok'arin da sukayi na zuwa haka shima Sultan d'in ya rink'a zuba masu godiya kamar gaske, bayan sun kamala had'a kayan su Sultan ya kira Sinbul da Barma su fida kayan waje, har bakin mota ya rako su hannu shi na zube cikin aljihu yana murmushi, Alex ya kira wadda ke tsaye daga gefen yace, ya wuce da su airport, murmushi Alex yayi tare da bud'e masu murfi mota suka shige suna tsokanar Sultan wai se sun zo suna, dariyar shak'iyanci Ammar yake yana kallan sultan yace, "gashi zaku tafi ko bari yakiyi ku ga amaryar duk ya tatare ta ya b'oye" dariya su Ahmad suka saki suna cewa, "idan ta tsufa ya bari muganta" murmushin yak'e Sultan yake yana shafa lalausan sumar shi, har suka bar harabar gida harara ya makawa Ammar yace, "wallahi zan ma rashin M idan kana min haka" sultan nata kunfar baki har suka shige part d'in shi. ********** Bayan yan'biki kowa ya watse gida ya rage hayaniya, Nihal ce zaune saman gado babu abinda take se aikin tunanin da aiyana wa ranta baza juri walakanci da Sultan ze mata tunda itama ba san shi take ba daraja Ammi yaci ta aure shi, wulak'anci da tasha a hannun su gwoggo ya isa, wata gwagwamar ajiyar zuciya ta saki tana bin su yasmin da kallo da suke gyara d'akin ta, Jakadiya ce ta shigo d'akin hannun ta dauke da Alkyabba maroon da doguwar riga maroon a sama kallo Nihal ta bita da shi idanuwan ta taf da kwalla Dan tasan zancan, murmushi Dara ta saki tare da cewa, " ta so mana" shagwabe fuska Nihal tayi ba yadda ta iya haka tabi jakadiya toilet wanka ta mata tare da sata cikin tsimin turare, bayan sun fito dak'i ta zauna da Nihal saman kujera dake facing d'in dressing mirror wata madara ta dauko a cup ta mik'ewa Nihal ta shanye ta tas sannan ta shafe mata jikin ta da wani lotion me fitinan kamshi, a hankali jakadiya ta janyo doguwar riga ta zurawa Nihal maroon colour ce me stones daga gaban rigar zuwa bayan ta wani zare ne hakan se yasa ana ganin na fulanin ta sosai tun daga bayan rigar har zuwa k'ugunta zare ne, make up akayi mata tayi wani masifar kyau bakin nan yasha Jan baki ya k'ara k'ank'ancewa parking d'in gashin ta akayi ya wani nanad'e kamar taliya saman gashin an jera wasu abubuwa masu kyalkyali se daukar idanuwa suke, ita kanta se da ta yaba kyan da ta zuba se dai rigar da aka sa mata kunya take bata Alkyabba maroon Jakadiya ta sa mata tare da feshe ta da turare me kamshi da sanyin dad'i, ammi ce ta shigo tare da washe baki tace, "Masha Allah gaskiya Dara ya kamata na baki tukwici" Nihal ko kunya ta hanata had'a ido da Ammi bayan Ammi ta mata nasiha sosai kamar yadda tayima Sultan sannan tace, a wuce da Nihal part d'in Sultan jikin Nihal ne yayi mugun sanyi ji tayi idanuwan ta sun ciko da kwalla janyo hula alkyabba jakadiya tayi ta rufewa Nihal fuska, yasmin da bariri na bayan Nihal Jakadiya na gaba, Basmal ce ta zo saitin kunnan Nihal tace, "Nasan yau zaki rud'a yayana" waro idanuwan Nihal tayi kamar za tayi kuka tana bin Basmal da kallo, sai da akaje part d'in mom da Gimbiya jalila sannan aka wuce da Nihal part d'in Sultan suna zuwa bakin kofar jakadiya tacewa bafadan bakin kofar ya sanar da Sultan an kawo mashi Amaryar shi, ko minti biyu bafadan beyi ba ya fito yana cewa ya ce Ku shiga kama hannun Nihal jakadiya tayi tare da cewa, "Allah ya bada zaman lafiya" ta saki hannun Nihal a parlour sannan tace ki shiga daga ciki. Nihal na ganin fitar su jakadiya ta fara waro idanuwa tana bin parlour da kallo da mamakin had'uwar shi da tsaruwar shi ga wani kamshi dad'i take fita, ta dad'e a tsaye a parlour sannan ta taka a hankali ta Shiga d'akin, tsaye gaban dressing mirror ta hango Sultan ya juya mata baya hannuwan shi hard'e ta baya sanye yake da zabuni maroon yasha Aiki da gold zare, sanyi AC da kamshi d'akin se mamaye hanci Nihal yake ga wani irin sanyi da d'akin yayi kamar firdge, Nihal ta kwashe kusan 30 minutes tsaye Sultan be ce mata k'ala ba a hankali ya juyo yana bin ta da kallo har a lokacin kanta a kasa yake, saboda tsabar tsayuwa har k'afar ta tayi tsami, a hankali Sultan ya k'araso daf da Nihal har tana jin saukar numfashin shi da kamshin turaran shi da ya mamaye mata hanci, a hankali Sultan yasa lalausan hannu shi, ya dago da kyakyawar fuskar Nihal, kafe ta yayi da idanuwa yana mamaki irin halita da Allah ya tsara mata ya dau tsawan lokaci yana bin kyakyawar fuskar ta da kallo, A hankali ya sauke idanuwan shi akan na fulanin ta wayan da ke bayane ta cikin zaran dake cikin rigar yana kallan yadda numfashin ta ke sauka dana fulanin ta, Nihal ko lunshe idanuwan tayi eye lashes d'in ta sukayi kamar ansa na kanti, kauda kai Sultan yayi ganin bugun zuciyar na harbawa da sauri-sauri tab'e baki Sultan yayi tare da wuce ta, a hankali Nihal bud'e lumsasun idanuwan ta, tare da sakin gwagwamar ajiyar zuciya tana bin Sultan da kallo, can k'asan ma koshi Sultan yace, "ki je ki cire kayan nan saboda baki dace da su ba, ba ke nayiwa tana din kayan ba" ya ida zancan tare da mik'a mata kayan bacci riga da wando wani kunlutun bakin ciki ne yayi ma Nihal tsaye a zuciyar ta tace, to dama ce mashi akayi kayan sun dad'ani da k'asa ne da zaka fad'a min mara dad'i, kayan ma yan' iska mi zanyi da su, d'an siririn tsaki Nihal ta saki tare da mik'a hannu zata amshi kayan baccin dake hannu Sultan ran ta a had'e, kallan-kallo suke yima juna su Nihal ce ta kauda kanta ta gefe Sultan ya zubar da kayan baccin a k'asa ya fice jin shuru yasa Nihal tatare kayan bacci tare da sakin kuka ta shige toilet wanka tayi sannan ta shirya a toilet d'in riga ce pink me dogwan hannu tana dauke da zanan flowers manya, a hankali ta fito daga toilet tare da aje kayan da ta cire saman sofa tana bin d'akin da kallo, murd'a kofar d'akin da akayi ne ya sata waigowa Sultan ne ya shigo kauda kai Nihal tayi, ko kallan Inda Nihal take beyi ba, ya dau night dress d'in shi dake cikin drawer ya shige toilet shigar shi toilet yasa Nihal ta haye lafiyar gado tare da lulub'ewa da blanket, Sultan na fitowa daga toilet ya haye bed jin Nihal a saman bed d'in yasa Sultan cewa cikin d'aga murya, "what a fuck! A zabure Nihal ta mik'e saboda tsawar da Sultan ya daka ya cigaba da cewa, "How dare you zaki kwanta in the same roof with me" waro idanuwa Nihal ta kuma yi tare da k'ara kankame blanket d'in hannun ta Sultan yace, "baki jinane are you deaf oh what get the hell out of my sight," kef-kef da ido Nihal take tace, "Nifa ba gane abinda kake fad'i nake ba Idan zakayi yaran da nake ji kayi idan kuma ba za kayi ba , se da safe karka hanani bacci malam" Nihal ta koma ta kwanta tare da jan blanket wani irin tsaki Sultan ya saki tare da janye blanket d'in jikin Nihal ya dauke ta cak Ihu Nihal ta fara tana zulo a jikin Sultan jikin ta na gogar na Sultan, wata irin kasala Nihal ta sakar wa Sultan, wadda ita kanta bata sani ba, tana cewa, "malam ka sake ni wai me haka" wurga ta kasa Sultan yayi, wata yar k'ara Nihal ta saki Sultan yace cikin kasalaliyar murya shi, "nan ne ya dace da ke," mik'ewa Nihal tayi tace, "wallahi bazan kwana a k'asa ba se dai na koma d'aki na" wata uwar harara Sultan ya maka mata tare da tashi yasa key ya kule d'akin ya haye saman bed... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITES FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 69_70* Kiran sallah Asuba ne ya tashi Sultan a hankali ya zame blanket d'in jikin shi, k'ok'arin shiga toilet yake, ya kallin Nihal dake bacci saman sofa ta wani kudindine waje d'aya, toilet ya shige ya dauro alwala tare da yin brush har ya fito Nihal na kwance tana shara bacci kasancewa bata samu wani bacci ba saboda sanyin d'akin yayi mata yawa se gab da asuba bacci barawo ya dauke ta, dan siriri tsakin Sultan ya saki yana cewa, a zuciyar shi a haka Ammi ke cewa me hankali me natsuwa da addini ! ina addini a nan an saki baki saman sofa ana bacci ba sabanba mtsww" har yayi gaba ya dawo tare da bud'e fridge ya curo gora ruwa mai sanyi ya nufi kan Nihal rai had'e bud'e bottle d'in robar yayi ya fara zubawa Nihal, a zabure Nihal ta mik'e da gudu tare da fashewa da kuka tana k'ok'arin fita tana cewa, "gwoggo kiyi hakuri dan Allah wallahi ban san lokaci ya wuce ba" fisgo ta sultan yayi ta fad'a saman kujera tana cigaba da cewa, "gwoggo dan Allah kiyi hakuri karki ga laifi na kan abin da nayiwa Mudi" tana maganar tana sheshek'ar kuka duk ta gigice, sakatarare Sultan yayi yana kallan ta yana maimaita suna yan da Nihal ke fad'i wacece gwoggo waye mudi, fisgo ta Sultan yayi da karfi Nihal ta fad'a jikin shi cikin kakausar murya yace, " wacece gwoggo da mudi ? ya fad'a a tsawace Nihal da ta dawo daga hayacin ta, tayi tsif bakin ta na rawa tana bin Sultan da idanuwan ta wayan da suka rine da ja saboda tsabar kuka, fisge hannun ta Nihal tayi tare da gyara gashin kanta ya koma baya tana jan majina ta rab'a ta gefen Sultan zata wuce, cikin daka tsawa Sultan yace, "wacece gwoggo da mudi ? Gaban Nihal ne ya yanke ya fad'i da kyar tataro natsuwar ta tare da had'iya wani miyau mai d'aci ta zaro idanuwan ta waje, tare da juyowa ta hard'e hannuwan ta a k'irji tace, "ban gane mi kake nufi ba, suwaye kuma haka! wacece gwoggo a nan wanene mud,? ta ida zancan tare da k'ara gyara gashin ta daya rufe mata fuska, cije hakora Sultan yayi ya matso daf da Nihal a hasale har tana jin saukar numshin shi, waro idanuwan waje Nihal tayi a tunanin marin ta Sultan zeyi se kuma ya numfasa yace, "kada ki bari na gano kina boye min wani Abu game dake idan kika bari na gane hmmm" sannan yasa kai ya fice dafe goshi Nihal tayi tare da zama tace na shiga uku da yaushe na fad'i gwoggo da mudi Allah ka rufamin Asirri kar Sultan yasa abinciko koni wacece, idan ya gano cewa na kashe yaya mudi ne na gudu fa, wani kallo za'a min Allah ka rufa min Asirri ya Allah" Nihal ta fashe da matsananci kuka ta cigaba da cewa, yaushe ne zan samu sauyin rayuwa ne, da kyar ta iya tashi ta shige toilet dan dauro Alwala. Misalin karfe 7:00am flight d'in su Nazili ya sauka Nigeria a hankali take saukowa daga stairs d'in jirgi reception ta shiga ta zauna a saman resting chair wayar ta ta curo a jaka sabuwa wadda ta siya jiya a UK kafin ta wuce airport a jirgima tayi chajin wayar kasancewa number's d'in wayar ta a Email take saving nasu bata sha wata wahala ba wajan nemo number kabiru driver ba, bugu d'aya ta mashi ya dauka can k'asan ma koshi Nazili tace, "kabiru ina airport ka zo ka d'auke ni" ko 20 minutes ba'ayi ba Kabiru ya iso airport daukar trolley d'in ta yayi tare da sa mata boot, sannan ya bud'e mata back seat ta zauna sannan ya zagaya front seat ya ja su, tafiya suke amma gani take kamar kabiru driver be sauri. A harabar gidan kabiru driver ya faka mota yana parking Nazili ta fito har lokacin idanuwan ta na manne da bakin glass tafiya take komai na jikin ta na amsawa, bayi se zubewa suke suna mata sannu da zuwa ba Wanda ta amsawa har ta isa part d'in Ammi Ammi dake zaune a parlour tana kallan sunna TV kafin a gama breakfast jin motsi yasata juyowa kasancewa ko sallama Nazili ba tayi, sakin murmushi Ammi tayi tana cewa, "Nazili kin dawo? cire glass d'in idanuwa ta tayi tare da hard'e hannuwan ta a k'irji ta d'aga gira tace, "Eh na dawo Ashe kunyi bikin Sultan har an gama ba Wanda ya kirani ya fad'a min se dai naga pictures na yawo a media" Nazili ta ida zancan tana Jan fasali tana kallan Ammi ido cikin ido, Ammi ce ta sasauta muryar ta tana cewa, "Nazili ya kamata ki saurare ni first mana," Nazili tace "ko Ammi! sannan ta shige d'aki tana mai cigaba da cewa da karfi, "ina tunani Ammi ba ke kika haifi Abba na ba da ke kika haife shi ba za ayi bikin Sultan bana nan ba," tana shiga d'aki Nazili ta cire veil d'in kanta tare da rik'e kugu tana zagaye daki tana cewa, "se naga bayan koma wacece matar sultan, wace tsinaniyar ce ta aura shi" jin An murd'a kofa ne yasa Nazili juyowa hannuwa ta hard'e a kirjin ta cike da masifa tana kallan kofar ganin Aziza ne ya sata sakin tsaki ta d'aga kira tana cewa, "me? kada ki fad'a min cewa har yanzu Sultan na tare da Amaryar shi? "Uhmm Gimbiya ke ma kin san" d'aga mata hannu Nazili tayi cikin masifa tace, "bana San jin komai, wanene uban ta ! "Gimbiya nima kawai na gan..... ! Daka mata tsawa Nazili tayi tace, "fitar min daga d'aki bana san ganin ki, bama na buk'tar ganin kowa yanzu ina buk'ar hutu" cikin daka tsawa Nazili ta ida zancan, da sauri Aziza na fita har tana tuntub'e ta fice, zaunawa Nazili tayi bakin gado tana kuka tana cewa, "shikenan suna can suna jin dad'i suna soyayya, idan na kama koma wacece se na shak'e mata wuya mtsww" tana ida zancan tana kuka tare da goge hawayan ta da tissue tana mai cigaba da kuka, Ammi ce ta shigo dakin tana kallan Nazili duk se taji ba dad'i kuma itama ba laifin ta bane ba irin kiran da ba'a mata ba wayar ta baya shiga kuma dama gashi ba a ja bikin da tsawo ba Nazili ce ta d'ago jajayan idanuwan ta hata hancin ta yayi ja saboda tsabar kuka cikin masifa tace, "Ammi bana san ganin ki bana san ganin kowa" ta fad'a tana mai cigaba da kuka a hankali Ammi ta k'araso tare rungume Nazili tsam ajikin ta, tana faman bata hakuri se sauke ajiyar zuciya Nazili take Ammi tace, "kiyi hakuri Nazili nasan bamu kyau ta ba Amma,! "Amma mi ! Nazili ta fad'a tana Jan fasali tare da kafe Ammi da ido, ta cigaba da cewa, "mi yasa baza a jira na dawo ba, saboda bani da matsayi a cikin gidan saboda iyaye na basa raye ko Ammi, me yasa Sultan ze yi aure yanzu Ammi ! na fad'a maki bana buk'ar kowa a kusa dani yanzu, I wish iyayena na raye da baza a min haka ba" Nazili ta ida zancan tare da zuwa bakin kofa ta bud'e tace, "Ammi kina iya fita bana san ganin ki" idanuwan Ammi taf da kwalla suka ciko tana kallan Nazili wadda ta kauda kanta gefe a hankali Ammi ta tako har bakin kofa sannan ta fice tana fita Nazili ta maida kofar ta rufe da karfi sannan ta shiga zagaye d'aki tana tunanin ta inda zata bulo. Ammi na fita taci karo da Basmal k'arasawa wajan Ammi tayi tana tanbayar ta lafiya, Basmal tace, "Ammi waya b'ata maki rai? ke dawa kike hayani? Basmal ta ida zancan tana zaunar da Ammi saman kujera ruwa ta d'ebo a cup me sanyi ta ba Ammi, ammi ta shanye ruwan tas tana sauke numfashi Basmal tace, "ke dawaye Ammi? a hankali Ammi tace, " Nazili ! Waro ido Basmal tayi tace, "ta dawo ne Ammi? "Eh ta dawo tana ta fad'a a kan anyi bikin Sultan ba da sanin ta ba" "Oh fu ! ai ba laifin mu bane laifin wayar tane how many time's na kira bata shiga bari naje na mata magana" rik'e hannun ta Ammi tayi tace, "ki kyale ta idan ta huce zata fito koma wa akayi ma haka dole ya ji haushi musanman yadda take ji da Sultan, "Ammi Amma be kamata ta bata maki rai ba bayan tasan problem naki" "Naji dawo ki zauna with time zata huce" "OK" "Gimbiya ni fa ina ganin mun samu mafita tunda matar tashi kamar bata da wayau ko ya ki ka gani" d'an siriri tsaki Ashad ya saki yace, "dalla malama yi mana shuru ko breakfast ba muyi ba za'a fara bamu shawara mara anfan mtsw, kawai a aika yan' mashi su tare shi su kashe mu huta shine magana amma yanzu da yayi aure ya'ya ze fara jerawa fa" Gimbiya jalila ce ta numfasa tace, "da ina tunanin kamar maganar yakumbo ce mafita Amma na lura yarinyar kamar tana d'an banza wayau" "Bana tunanin haka ranki ya dad'e" "Allah yasa hak'ar mu tacima ruwa" Ashad yace, "zama ta cine Ku bani lokaci" dariya suka saki Gimbiya jalila tace, "shiyasa nake sanka son aikin ka na kyau dan dai ma akwai yan hana ruwa gudu" haka suka rink'a kula makirci suna warwarewa. A hankali Nihal ta mike daga saman sofa tana waige-waige bakin dressing mirror ta hango sultan yana shirya ciki wata suit yayi kyau har ya gaji ta dad'e tana kallan shi ganin ze juyo yasa tayi sauri mik'ewa tana k'ok'arin fita Sultan yace can k'asan makoshi, "ina zaki? Juyowa Nihal tayi tana kallan shi tare da cewa, "zan koma cikin gida ne" tsaki Sultan ya ja yace, "A haka zaki fita my friend dawo kiyi wanka sannan" ya ida zancan yana maka mata harara yace, "ko fita zakiyi tare zamu fita nama fad'a maki" sannan ya dauki bathrobe da towel ya watsa mata a fuska yace, "a wuce" gutun tsaki Nihal ta saki tare da shigewa toilet ta dad'e tana wanka tana gamawa tasa bathrobe ta daure gashin ta da towel kasancewa ta wanke shi, tana fitowa daga kwamin wanka santsin ya jata ta fad'i k'asa wata k'ara Nihal ta saki tare da sakin kuka Sultan dake zaune saman sofa yana latsa wayar shine ya ja tsaki wani ihun Nihal ta saki tana cewa, shikenan na kare kugu tana kuka, mikewa Sultan yayi a hasale ya nufi toilet d'in murd'a kofar yayi zaune yaga Nihal tayi zaman yan' buri had'e rai Sultan yayi yace, "lafiya kikewa mutane ihu? Kuka Nihal ta saki tare da cewa, " fad'uwa fa nayi na kasa ta shi" hannu sultan ya mik'a mata a hankali ta daura lalausan hunnan ta saman na Sultan, k'ara ta kuma saki ta koma ta zauna tare da cewa, "na kasa tashi" tsaki Sultan ya saki ya k'ara had'e rai, a hankali Sultan ya duka tare da daukar ta cak kamar baby, suna fitowa daga toilet lokacin yayi dai-dai da shigowar jakadiya tun a parlour ta fara jiyo ihun Nihal shine ta shigo tana ganin Sultan dauke da Nihal ta wani diririce zuciyar ta, tayi fes tunanin ta komai ya auko musanmam yadda taga Nihal d'in ta wani zagaye hannun ta a wuyan Sultan, shi ko sultan had'e rai yayi kamar gaske yana Smile saboda yasan halin gidan Sarauta dama da gangan ta shigo dan taga ya sukayi daran jiya, saman bed ya dire Nihal, kunya duk ta kamata ko gaishe da Jakadiya ta kasayi, sosa k'eya Sultan yayi tare da cewa, "Dara ina kwana" Amsawa tayi tana wurwurga idanuwa tana kalle-kalle cikin dak'in kamar barauniya Sultan ne ya katse mata tunani da cewa, "Nihal bata da lafiya bari na dubata idan na gama zan kira ki se ku fita tare" toh jakadiya tace tare da ficewa tana dariya k'asa-k'asa tana cewa, "d'an tselankwa duk ya gama zagayan ana kaita har ya ware," Dara na fita Sultan ya maka wa Nihal harara yace, Malama sako min daga gado" shuru Nihal tayi kamar bata jishi ba ta cigaba da matsar kwalla tana cewa, "kafata da kuguna zasu cire" tana maganar tana yarfe hannu bedside drewar Sultan ya bud'e ya juro wani magani a tuf yace, "gashi ki shafa" amsa Nihal tayi Sultan kuma ya koma saman sofa ya juya mata baya se da ta gama shafawa sannan ya juyo sannan bud'e drewar ya ciro wata jigida ta gold yace, "tashi ki sa wannan" tsoke fuska Nihal tayi tace, "mi zanyi da wannan" had'e rai Sultan yayi yace aladar gida nan ce duk wadda ta shigo part d'in mijin ta rana farko dole tasa kuma ki kula min da abuna dan bake na tana darwawa ba, kin gane malama idan kuma bazaki sa ba zan sa maki da kai na" Nihal na jin haka ta amshi jigidar ta da kanta sannan Sultan ya mik'a mata wata gwon green me zana flowers ta saka sannan ya kama hannu ta tana ingishi har suka iso parlour jakadiya na zaune murmushi ta saki tare da kallan k'afafuwan Nihal tana sakin Smile se sannu take jera mata haka shima Sultan d'in kamar gaske sannan suka fice. Bayan sun koma d'aki Dara da Nihal Dara tace, "hmmm yaran yanzu ba'a iya masu, ko jin kiri babu yanzu shi duk wannan kulunbotsan da ya gama maki ai na dauka se kinyi wata kafin ya neme ki se gashi har da kyauta da ya dace Abawa kowace cikakiyar mace ya baki hakan na nuna lafiya lau kika zo gaskiya Ammi zata ji dad'in labarin nan sosai," Dara na maganar tana yima Nihal gashi ita ko tayi fuska dan bata gane me jakadiya ke nufi ba aiko da suka fito lokacin har k'afar ta, ta saki ta fara tafiya Normal Dara se cewa take "gashi nan magani har yayi aiki sannu kin ji ai kin durzu wallahi" Nihal ko se d'aga kai take tana cewa, "baki ji d'a zu ba jikin se ciwo yake Amma yanzu ya saki" " ai dole tafiyar kima sauyawa tayi" Dara na maganar tana shirya Nihal cikin wata gwon dark blue me bud'adan kafad'a saman ta anjera stone's masu kyalkyal daga baya kuma tana da igiya shepa d'in ta ya fito sosai zubo mata tayi da gashin ta har gadan baya, tayi wani irin kyau Dara tace, "bari na kira Ranka yadad'e ku wuce dining area" tabe baki Nihal tayi tare da zama bakin gado. Aziza ce ta shigo d'akin Nazili tace, "Aunty Nazili Ammi tace kiyi hakuri ki zo kiyi breakfasat" tsaki Nazila ta saki tana cewa, "idan bazan yi ba fa," rufu kofa Aziza tayi cike da gulma tace, "Sultan da Amaryar shi yanzu zasu fito, tab'e baki Nazili tayi tare da cewa, "ganin zuwa," mikewa tayi ta shirya cikin wata orange riga mara hannu sannan tasa black skirt ya kama jikin ta sosai shepa ya fito se skirt d'in yayi kamar gwon tasa parking gashin tayi tare shafa red Jan baki a lips d'in ta direct dining area ta wuce. Murd'a kofar da akayine yasa Nihal d'agowa ta kalli bakin kofa Sultan ne tsaye shirya ciki wata armani royal blue suit da white inner tie d'insa kala suit d'in ta kama jikin sa hata wandon pencil ne ya saka cufflinks masu diamond royal blue stones yayi kyau har ya gaji he look masha Allah can kasan makoshi Sultan yace, " se ki ta so muje ko" a hankali Nihal ta tashi tasa flat shoe black sannan ta taso, har sunyi gama Sultan yace, "kada ki kuskura ki gwada ma wani cewa muna da matsala nama fad'a maki duk abinda zanyi inayi ne dan lafiyar Ammi to ki guji bacin ranta" ya ida zancan yana had'e rai, kallan shi Nihal kawai tayi tare da kauda kanta, a hankali suke tafiya a tare jigidar da Nihal tasa na amsawa duk wanda ya ji k'ara se ya gane cewa jiya sun kasance a tare, hakan ba k'aramin dad'i yayi ma ammi ba data ji k'ara, a haka har suka iso dining area kallo ya koma kasan su, Basmal tace, "masha Allah matar yayana kinyi kyau" murmushi yak'e Nihal ta saki tace, "Na gode" Nazili dake zaune ji tayi wani kulutun bakin ciki ya mata tsaye da kyar take had'iye miyau, Sultan jama Nihal kujera yayi ta zauna tana raraba ido sannan ya zauna kusa da ita a tare suka gaishe su Ammi da mom, amsawa sukayi cike da fara'a Gimbiya jalila da Ashad ko ji suke kamar su shak'e Sultan har se ya daina numfashi, haka itama Nazili ji take kamar ta kashe Nihal dan haushi musanman data ganta kyakyawa da kusan haske kawai Nazili zata nunawa Nihal nesa ba kusa ba, serving nasu plantain porridge Wanda yasha yan'ciki fara cin abinci sukayi cikin natsuwa, Nazili ce ta katse shurun da cewa, "Sultan Ashe kayi aure? "Uhmm" sultan yace yana mai cigaba da cin abinci" kallan mutanan dining Nazili tayi tare da kallan Nihal tace, "Amma naga saurin yin auran nan yaushe kuka had'u da Sultan ne dama kun dad'e tare ? Nazili ta jefawa Nihal tanbaya tare da tsare ta da idanuwa Shuru Nihal tayi tana kallan Nazili wadda ta kafe ta da idanuwa, sultan ne yace, "Nazili kin fiye tanbaya da yawa" Sultan ya ida zancan yana tsare Nazili da ido, maganar da Sultan yayi ma Nazili tayi ma Ammi dad'i saboda dama ba Wanda yasan wacece Nihal daga maimartaba se Basmal su kad'ai ne suka sani, aje spoon d'in hannu ta Nazili tayi tare da cewa, "daga tanbaya se ace na fiye surutu," murmushi Nazili ta saki ta k'ara cewa, "wanenen mahaifin kin a Nigeria wani aiki yake? Kema doctor ce oh what" Nazili ta ida zancan tana tsare Nihal da idanuwa, Gimbiya jalila uwar gulma tuni ta dago Nazili kishin Sultan take wani murmushi ta saki tana tunanin ga wata dama ta samu tana wani huhura hanci tana kallan Ashad Wanda shima ya d'ago Nazili, kwarewa Nihal tayi ta fara tari da sauri Sultan ya mik'a mata ruwa yana aikawa Nazili mugun kallo yace, "bakin San idan ana cin abinci ba'a magana ba," murmushi Nazili ta saki tare da cewa, "kamar na so nasan wata me kama da ita ne shiyasa nake tanbayar ai" gaban Nihal ne ya k'ara yankewa ya fad'i, a je spoon d'in hannu ta Nazili tayi, ta watsawa Nihal mugun kallo ta zo dai-dai setin Nihal tana cewa, "sorry dear nasa kin kware hala baki basa cin irin shi a gida ba ne" nata maganar tana kallan Nihal gabaki d'aya Nihal ta ji ba dad'i saboda ta gane cewa gasa mata magana Nazili take sannan ta dafa kafad'ar ta tare da bari dining area ta shige daki tana cewa, "Uhmm yanzu na gane saboda mi yasa Sultan ya aure ta saboda kyan fuskar ta ko to se na kona fuskar , se naga yan da za'ayi, se na had'a mata makircin da Sultan ze tsane ta har abada, am gonna make this house a living hell to you Nihal, se naga bayan ki, talaka kawai," ta ida zancan tana smile tare da janyo wayar ta dake bedside drawer..... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among rest```) *Page: 73_74* Bud'e murfin mota Sultan yayi ya shige jingine jikin seat d'in mota yaga Ammar idanuwan shi a lumshe tsare shi da idanuwa sultan yayi yana kallo ko bai fad'a ba fuskar shi ta nuna damuwa k'arara saboda fuskar shi ta canzan lokaci d'aya, cikin calm tune sultan yace, "Ammar ! A hankali ya bud'e lumsasun idanuwan shi Wayan da lokacin sun rine da ja, ya zubawa Sultan na mujiya, hankalin Sultan ne ya tashi ya cigaba ta cewa, "Ammar what wrong with you? Nazili ta b'ata ma rai ne? Mi ya same ka, shiyasa bana san yariyar nan bata da kunya" k'ak'aro murmushi Ammar yayi Wanda iya karshi lab'an shi yace, "Ba abinda Nazili ta min, kira na akayi a waya yanzu ake ce min friend d'ina ya rasu," langwabe kai Sultan yayi yace, "Eyya Ammar Allah ya ji kanshi, take heart, amma ya akayi ban san shi ba? Sultan ya ida zancan yana tsare Ammar da ido kasancewa duk friend d'in su d'aya, d'an daburcewa Ammar yayi tare da cewa, "San da naje kauye ba tare da kai ba shi ne lokacin muka zama friend sosai har muka saba" tab'e baki Sultan yayi yace, "OK Allah ya gafarta mashi" "Amin" ganin Ammar d'in duk yayi suku-suku yasa Sultan cewa, "bari nayi driver d'in na lura kamar baka cikin natsuwa" d'aga kai Ammar yayi tare bud'e mazaunin driver ya barma Sultan ya koma inda sultan ya bari har sultan ya ja mota Ammar ya kalli sultan tare da cewa, "please ka sauke ni gida bana jin zan iya komawa aiki yanzu," kallan Ammar Sultan yayi yace, "ba dai shanono zaka tafi yanzu ba? Girgiza kai Ammar yayi yace, " Se gobe zani" Da ace bani da theater gobe da munje tare," "Ku ma fa " Ammar yace tare da maida idanuwan shi ya lumshe, kofar gida sultan ya aje Ammar ya wuce dan tsakanin gidan waziri da gidan maimartaba ba wani tazara dan duk kusan cikin gida d'aya ne. Adda ce zaune a parlour tana kallo Ammar ya shigo jiki a sanyaye ko sallama ya kasa yi saboda nauyin da bakin shi yayi, har ya wuce Adda dan ko ganin ta beyi ba, Adda ce tace, Ammar! shuru Ammar yayi kuma ya kasa juyowa su had'a ido da Adda tasowa tayi tana k'arewa fuskar Ammar kallo wadda ke cike da damuwa cikin sanyin murya Adda tace, "Ammar lafiya...!! Adda bata ida rufe bakin ta ba Ammar ya fad'a jikin ta, tare da sakin kuka yana cewa, "Shikenan Adda yanzu Nihal ba tawa ba ce Adda, Ashe dama ita ce matar da Sultan ya aura, yau ido na ya gane min Nihal a matsayi matar sultan !! Ammar ya ida zancan ciki sakin kuka mara sauti, haka Ammar ya rink'a yima Adda sanbatu, lalashin shi Adda ta shiga yi kamar k'aramin yaro janyo Ammar tayi ta zauna da shi saman kujera suna facing juna, ita kanta d'an nata ya bata tausayi musanman yadda ya kwalafawa ran shi Nihal kama hannuwan shi Adda tayi duk biyu cikin nata, cikin sanyin murya tace, "Ammar! dago jajayan idanuwan shi yayi yana kallan Adda ta cigaba ta cewa, "nasan cewa Ammar kai mutun ne mai hakuri da tawakali ! ina so ka dauka cewa wannna k'adara ka ce Ammar Allah ya nufa Nihal ba matar ka ba ce, bana so ka sawa kanka damuwa ka ji, ka godewa Allah cewa Nihal d'in hannun na gari ta fad'a kuma aure tayi ba yawan banza ba idan haka ka gani se kafi jin zafin abin, Amma yanzu d'an uwan ka take aure kuma aminnin ka, kai kanka kasan Sultan mutumin kirki ne ze kula da Nihal d'in se dai muce Allah ya basu zaman lafiya kai kuma Allah ya baka wadda tafi ta," sauke ajiyar zuciya Ammar kawai yake yana zubawa Adda na mujiya yana tunanin rayuwar da sukayi a baya da Nihal lumshe idanuwan shi yayi wasu hawaye masu zafi suka sulalo mashi, ya san cewa ya rasa Nihal har abada, hannun Adda Ammar ya kama duka biyun tare da kissing na su, sannan ya mike ya wuce part na shi da kallo Adda ta bi shi ita ma duk jikin ta yayi sanyi dole ta san d'an nata ya shiga wani hali ita kanta data ga Nihal da biki ta yaba da kyawun ta da hankali ta, Allah yaba d'an nata wadda tafi ta, Adda ta fad'a a fili tana mai cigaba da yi mashi addu'a Allah ya cire masa San Nihal dan yanzu ta zama matar wani. Bayan Nihal ta ci kuka ta gaji ganin tunanin be fishe ta yasa ta shige toilet tayi wanka tana mai addu'a Allah ya rufa mata Asirri tana k'ara rokwan Allah maji rokwan bayin shi dan ta san cewa Allah yana sane da ita da irin wannan tunanin Nihal ta gama wanka sanye da towel ta fito, goge jikin tayi ta shafa lotion me kamshi sannan ta shirya cikin white Jean's da black t-shirt tayi kyau sosai tatare gashin kanta tayi ta maida shi gefe d'aya ta feshe jikin ta da turare , maroon Jan baki ta sama lips din ta d'an kad'an , sannan ta zurawa kafarta flat shoe silver me kyalkyali sannan ta fice daga part d'in sultan dan ta gaji da zaman shuru. part d'in mom ta wuce cikin sallama ta shiga parlour ba kowa se bayi dake hada-hada ko ba'a fad'a mata ba ta san mom na bedroom gaishe ta bayin suka shiga yi Nihal na amsawa rai sake har ta k'araso bedroom d'in mom, a hankali ta kama handle d'in kofar ta d'an leka kanta mom ta hango tsaye gaban drawer tana gyara wasu album's murmushi Nihal ta saki mom da juyawar ta kenan ta sakar wa Nihal da murmushi tace, "daughter shigo mana" shigowa Nihal tayi kai a sunkuye hannu mom ta mik'a mata Nihal ta kama tana washe baki, tace, mom ina wuni" "Lafiya lau daughter, yau an tuna da mom ko? daga kai Nihal tayi tana gyara gashin kanta murmushi mom tayi tace, " Ammi duk ta kwashe mun ku," ta ida zancan ta smile, washe baki Nihal tayi tana girgiza kai, janyo hannun Nihal mom tayi ta zauna da ita bakin gado suna facing juna aje Album's d'in hannun ta mom tayi tare da sa hannu ta d'ago da fuskar Nihal suna kallan juna Mom ta saki lalausan murmushi tace, "Masha Allah daughter kina da kyau, gaskiya my boy yayi sa'ar mata dan ma baki sakin jiki dani" mom ta ida zancan tana langwabe kai, washe baki Nihal tayi tace," mom na gode," waro idanuwa mom tayi tace, " son be taba fad'i maki kina da kyau ba ne" mom ta ida zancan tana k'arewa kyakyawar fuskar Nihal kallo, shuru Nihal kawai tayi tana yak'e a warwaran dake hannu mom na gold ta shiga cirewa tana cewa, "Nihal bani hannun ki" cikin zak'uwa Nihal ta mikawa mom hannun ta, a hankali mom ta Shiga sa mata a warwarayan a hannu tana cewa, "nima sun min kad'an dama nace duk ranar da son yayi aure matar shi zan ba mawa, duba ki gani yadda suka maki kyau Nihal, masha Allah komai naki mai kyau ne" mom ta ida zancan tana murmushi washe baki Nihal tayi tare da jujuya hannun ta cikin jin dad'i ta rungume mom tace, "na gode mom sun min kyau ina so" ta ida zancan ta zame jikin ta daga na mom, shafa fuskar Nihal mom tayi tace, "Nihal! A hankali Nihal ta d'ago idanuwan ta tana kallan mom wadda fuskar ta, tayi abin tausayi ta cigaba da cewa, "Ni dai fatana daughter ki zauna da Sultan cikin Aminci Nihal ki kulamin da Sultan," shuru Nihal tayi ta kafe mom da idanuwa a zuciyar ta tace, Allah sarki da yake shi d'an gata ne har wani cewa ake na kula shi mutumin da be San daraja ta ba, ni da bani da mai kula dani se dai ya rink'a cusa min bakin ciki ina shanyewa, jin idanuwan ta na kawo ruwa yasa Nihal lumshe idanuwa tana k'akaro murmushi yak'e, album mom ta janyo tana nunawa Nihal album d'in bikin su Wanda tunda akayi pictures d'in ranar biki ko marmarin ganin su batayi ba, mom se murmushi take tana nuna wa Nihal pictures d'in sun ma Nihal kyau sosai kasancewa daga ita har sultan d'in sunyi smile, har suka gama kallan pictures d'in mom bakin ta na dauke da murmushi, wani album d'in mom ta janyo tana cewa bari kiga pictures d'in son yana baby kiyi dariya bud'e pictures mom ta shigayi Nihal na gani tana murmushi duk da bata gane me mom tace da farko ba Amma jikin ta ya bata Sultan take nufi, wani picture suka kai Wanda aka dauki sultan yana kuka ya b'are baki dariya mom da Nihal suka saki, mom ce ta girgiza kai tana cewa, "sultan akwai rigima kin gan shi ko" wuce picture d'in mom tayi ta kai Wanda ita kadai ce da ciki tayi picture murmushi mom ta saki tace, "kalle ni nima san da ina yarinya kamar ki, nan ina da cikin Sultan ne zanyi haihuwa ta farko maimartaba ne yamin picture d'in lokacin munje Dubai, wata rana kema haka zaki haifi jikoki na, nasan Sultan ze ba grandchildren d'ina kulawa of coz shima yana san children" mom ta fad'a tana fadada murmushi ta, kirjin Nihal ne ya bada daram-daram a zuciya Nihal tace, tab d'in jam dawa zata haihun sultan kowa, ko a mafarki bata Fatan hakan ta kasance jiran lokacin take daza tace ya bata takarda sakin ta dan baza ta juri zama da shi ba kwata-kwata bale akai ga wani Abu wai shi ciki, dafatan da mom tayi ne yasa Nihal dawowa daga duniyar tunani, murmushi yak'e Nihal ta saki tana cewa, "mom bari na koma part d'in Ammi tun safe dana bata magani ban k'ara lek'a ta ba," murmushi mom ta saki tana mai kallan agogo tace, "ke dai ki ce min lokacin dawowar sultan yayi zaki gudu" rufe fuska Nihal tayi kamar gaske tare da cewa, "mom na gode da kyauta" pack mom ta mata a kumata sannan Nihal ta fice. Da fitowar Nihal daga part d'in mom taga motaci na shigowa bin motacin Nihal tayi da kallo tare da kau da kanta, motaci Sultan ne suka faka Alex ne ya budewa Sultan murfin mota kamar ance Nihal ta juyo tana juyowa sukayi ido hud'u da Sultan, da kallo sultan ya bi Nihal wadda itama kallan shi take k'asa tayi da kanta tare shigewa part d'in Ammi, tana shiga parlour taga ba kowa jin motsi a kitchen ne yasa Nihal nufar kitchen d'in tana mamakin mi ake a kitchen yanzu bayan ba'a girki a kitchen d'in kowani part se dai a kawo abinci daga babba kitchen, a hankali Nihal ke takawa maganar da taji anayi k'asa-k'asa ne yasa Nihal lafewa jikin bangwan kitchen d'in yakumbo ce da wata baiwa adama tsaye a kitchen yakumbo na cewa, "ki tabata kin zuba guban nan cikin Abinci Sultan ki san duk yadda zakiyi Dara ta matsa a kan Abincin Sultan se ki barbad'a, idan kika min haka kin gama min komai" murmushi Adama ta saki tana juya ido tace, "karki damu jakadiya ta yadda dani zan maki aiki yadda kike so amma da sharad'i se na ji dubus," murmushi yakumbo ta saki tare da yima Adama rad'a a kunne dariya suka saki tare da toshe baki, yakumbo ta cigaba da cewa, "yanzu na san ya dawo kiyi sauri ki aikata abinda na saki, saboda ke kawai na shigo part d'in nan wallahi," murmushi Adama tayi tace, "karki damu komai ze tafi dai-dai," Nihal dake manne jikin bango kitchen ce ta toshe bakin ta, numfashin ta na sama-sama zuciyar ta na tanbayar ta, to mi Sultan ya masu suke san kashe shi, motsin data jine yasa ta barin wajan da sauri Nazili ce ta bin Nihal da kallo tana aika mata harara tace, "mikikeyi a nan? Nazili ta tanbaya tana tsare Nihal da ido, tab'e baki Nihal tayi tare watsa hannuwa tace, "dan na zagaye gidan su miji na nayi laifi ne" Nihal ta ida Zancan tana hard'e hannuwan ta a kirjin ta, had'e rai Nazili yi tare da tab'e baki tace, "mijin ki? hehehe kiyi sauri ki kuskura bakin ki saboda Sultan yafi k'arfi ki malama, ina mai baki shawara kiyi gagawar fad'a mashi ya baki takarda ki dan se ya fi maki nonsense Almajira kawai," tsaki Nihal ta ja tare da shigewa d'aki ta maida kofa ta rufe, Nazili na huci ta wuce d'akin ta tana maimata kalaman Nihal, zagaye d'aki Nihal ta shiga yi tana cewa, mi sultan yayi ake san kashe shi, shafa gashin kanta Nihal tayi tare furzar da iska me zafi wata zuciyar tace ina ruwan ki, kika sani ko rashin mutunci daya saba yi maki ya masu, ko saboda wannan dalilin suke so su kashe shi su huta da halin shi, Amma idan ta lura ai baya wulakanta ma aikatan shi ita kad'ai ya rai na, wata zuciyar tace amma kuma se su kashe shi, wata zuciyar tace idan Sultan ya mutu ke ma ai kin huta da wannan auran mara anfani zaki samu damar jin dad'in to minene idan ya mutu zama Nihal tayi saman kujera ta dafe goshi. Sultan na shiga part na shi watsa ruwa kawai yayi, ya shirya cikin inner black shirt me uneck, da three quarter brown masha Allah yayi kyau sosai har ya gaji wayar shi ya dauka dake saman bedside drawer sannan ya wuce parlour jakadiya ya gani da Adama suna ta jera abinci a dining murmushi Sultan ya saki yana cewa, "Jakadiya ina wuni" sultan ya ida zancan yana Jan kujera dining, lafiya lau ranka ya dad'e, murmushi Sultan yayi yace, "yau mi aka dafa min" washe baki jakadiya tayi tana cewa, "abinda kafi so shina dafama, Adama a zuciyar tace shi kuma zeyi ajalin ka ba mtsww, wani irin dad'i sultan ya ji tare bud'e warmer miyar, miyar taushe ce tasha naman rago da kaji da yan'ciki se kamshin manshanu take lashe baki Sultan yayi tare da bud'e daya warmer waina ce an mata suya irin me kyanan gyara zama Sultan yayi tare daukar spoon ze d'ibi miyar tun tana warmer a hankali yasa spoon ya d'ebo miyar tare da kai........ ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *page: 71_72* Bayan kowa ya gama breakfast ba yadda Ammi ba tayi da Sultan kar ya je office ba se ya gwada mata cewa wata matsalace ta taso haka ya lalashe ta a kan cewa yana gamawa ze dawo wajan Amaryar shi of coz shima zeyi missing nata haka ya gama tsara Ammi ya fice. Nihal ta sha kyaututu ka hannu Ammi da mom haka itama Gimbiya jalila haka Nihal ta rik'a zuba masu godiya sannan ta wuce d'akin ta, tana shiga taga Nazili zaune ciki dakin ta, ruwan jinin jikin ta Nihal ta sha tana bin Nazili ta kallo yadda ta daura kafa d'aya kan d'aya saman kujera tana murmushi rai nin wayau mikewa tayi tare da takowa har gaba Nihal shafa fuskar Nihal tayi tare da sakin dariya tace, "oh no! Ashe dama ke Almajira ce hhhhhhh na tausaya ya maki amma" zagaye d'akin Nihal ta shiga yi tana cewa, "ya akayi Sultan ya auri almajira tsintar ciyar make i can't still believe cewa matar Sultan bata da asali bale tushe had'e rai Nazili tayi tare da nad'e hannuwanta a kirji tace, " Asirri kikayi wa Sultan Amma wani bokane me k'ok'ari haka ya maki aiki, kwata-kwata baki dace da rayuwar Sultan ba ina fata kin gane yar talaka Allah yasa ma ba wajan yawan bara ba mama kin tayi cikin ba dan nasan mabarata yadda kuke" ta ida zancan tana d'agawa Nihal gira Kafe ta da idanuwa Nihal tayi tana kallo idanuwan ta taf da kwalla ba kowa ya ja mata rayuwa haka ba se su baffa ya zama dole ta amshi matsayin ta haka, Nazili ce ta d'aga mata haba tana kallan ta tace, "ushhh karkiyi kuka fa gaskiya na fad'a maki baki dace da Sultan ba nayi mamakin yadda Sultan ya iya zama dake ma guri d'aya wallahi, ko baki fad'a min ba na san ciwan yunwa ne ya kashe baba ki da mama ki, kaf dangin ku nasan cewa bame arziki duk taran matsiya ta aka tara, karki damu yanzu kin shigo cikin arziki zaki rabu da tsiya da talauci, Allah yasa kuma baki da bak'ar kafa saboda shi talauci a jinin talaka yake, fad'a min daga naira d'aya har million zan baki ki rabu da Sultan kiyi gagawar cewa ya baki takarda sakikin if not" Nazili ta matsewa Nihal fuska ta cigaba da cewa, "if not se na wulak'an taki gaban jama'a se na tona ko ke wacece," Nazili ta ja tsaki tace, "bitch! kawai" sannan ta fice daga d'aki tare da buga mata kofa, a hankali Nihal take taka d'akin wani jiri na d'ibarta dressing mirror ta dafa hawaye na wanke mata fuska tana maimaita kalaman Nazili tabas ta san bata dace da Sultan ba, me yasa duniya bata san tane miyasa ma aka haife ta a duniyar ne , ko ta wani fani baza ta had'a kanta da Sultan ba shikan shi ya fad'a basu dace ba gashin yau ma ankara nanata mata Kalmar, ce mata akayi san sultan d'in take da zata rink'a jefa mata magana bayan su gwoggo to Sultan ne mak'iyina na biyu inda zan iya yakice shi dana yadda kwalan mangwaro na huta da k'uda, kuka Nihal ta saki tare da duk'ewa tana gunjin kuka babba tashin hankalin ta Allah yasa Nazili karta ta san dalili da yasa ta gudu daga gida kuka Nihal take baji ba gani. ******************* Akwana a tashi ba wuya wajan Allah satin su Nihal d'aya da aure babu abinda ya canza sultan ya mata Nazili ta mata har k'ara Sultan idan ta gaji tana ramawa gaban Ammi be nuna komai amma da Zara taje part nashi wulak'anci kala-kala. Shirye-shiryan fara zuwa makaranta Ammi ke tayi ba abinda ba'a siya mata ba Ammi tace surprise za'ayi ma Sultan se dai yaga Sultana ta fara zuwa makaranta kuma ta san haka ze mashi dadi sosai, Nihal ko se murna take komin banza zata samu ilimin boko dama gashin Ammi tace next week malamin islamiyya ze fara zuwa yana koya mata dad'i duk ya ishi Nihal, Nihal ce kwance saman sofa tayi shirin kwanciya, Sultan na saman bed idanuwan shi na manne da farin glass yana sanye da sleeping robe, dana laptop yake da alama aiki yake can ya d'ago idanuwan shi tare da satar kallan Nihal dake kwance saman sofa ta dunkule dan yau ko blanket yace baze bata ba tausayin tane ya kamashi k'adan, mik'ewa yayi tare da bud'e drawer ya ciro blanket ya k'arasa gaban sofa a hankali yasa blanket ya lulub'e Nihal yana k'arewa kyakyawar fuskar ta kallo, jin dumi ne yasa Nihal bud'e lumsasun idanuwan ta, ta sauke su kan Sultan da Sauri Sultan ya mik'e hannuwan shi na zube cikin Aljihu, juya mashi baya Nihal tayi tare da gyara kwanciyar ta. *Washe gari* Tunda Asuba Nihal ta tashi tayi wanka tare da dauro Alwala har ta gama shafan ta Sultan be dawo daga masalaci ba duk wannan shirin da take fuskar ta na dauke da murmushi maida kayan da cire tayi tare da ficewa daga d'akin, direct d'akin ta ta wuce tana shiga ta iske Dara na gyara d'akin Murmushi Dara ta saki tana cewa "yau litinin se makaranta kenan anya ko kinyi bacci kuwa? murmushi Nihal ta saki tana cewa, "kai umma ko bari na bakiyi na gaishe ki kin fara tsokana ta dan Allah" Nihal ta ida zancan tana turo baki dariya Dara tayi tace, "to ai gaskiya na fad'a Allah yasa kin ba mijin ki kulawa kika fito" tab'e baki Nihal tayi tare bud'e drawer tana Ciro Uniform d'in ta black and White, dariya Dara ta saki tana cewa kinyi wanka kuwa dire-dire Nihal ta fara ta tana cewa "kai Umma" dariya suka saki a tare ja mata kumatu Jakadiya tayi murmushi Nihal tayi tare da juyawa tana had'a kayan ta idanuwan ta taf da kwalla ta rasa mi yasa take samun natsuwa idan tana tare da Dara Allah sarki Allah yaji k'an umma Nihal ta fad'a a zuciyar ta, mini skert ne black da White shirt haka Nihal ta shirya cikin uniform d'in ta masha Allah tayi kyau sosai se d'an k'aramin hijab white, lipsticks kawai ta shafa a bakin ta, jakadiya tace, "Masha Allah Nihal kinyi kyau sosai da uniform d'in nan ni dai fata na kiyi abinda ya kaiki tunda kin san ke matar aure ce matar ma ba matar k'aramin mutum ba" murmushi Nihal tayi tace, "Insha Allah zan kiyaye" bata ida rufe bakin ta ba Nasim ya shigo sanye da uniform d'in shi yana cewa, "Aunty Nihal ki zo muyi breakfast mu tafi karmu makara" "to" Nihal tace mashi tare Jan hannun shi suka fice, a dining area suka iske Ammi na breakfast har k'asa Nihal ta gaishe ta murmushi Ammi ta saki tana cewa, "yan'makaranta har an fito kenan" d'aga kai Nihal tayi alamar Eh, washe baki Ammi tayi tana cewa, "Allah ya bada sa'a ayi Sauri a karya a wuce" "toh" Nihal tace, tare da fara cin abinci ita da Nasim suna ci suna taba hira kamar wani sa'anta. Ko da sultan ya dawo daga masalaci be yi mamakin rashin ganin Nihal ba dan shi yama fi san hakan, toilet kawai ya shige ya dad'e yana wanka ya fito sanye da bathrobe da towel a hunnu shi yana goge jikin shi, cikin sauri ya shirya cikin wata American rose colour suit yayi kyau sosai kamar shi yayi kanshi dan kyau briefcase d'in shi ya dauka tare da bud'e handle d'in kofa ya fito Barma ya mik'awa briefcase d'in suka wuce parking lot . Suna gama breakfast suka mik'e zasu fita Ammi tace, "Allah ya kiyaya," suna k'okarin fita ne Nazili ta fito daga d'akin ta sanye da wata gwon blue d'inkin rigar kamar bubu ta baza gashin ta Wanda ya nanad'e a gadan bayan ta bakin nan yasha jan baki k'afar ta na sanye ta takalma masu tsini hannu ta na rik'e da fost da alama company zata wuce, d'aga gira tayi tare da bin kofar da kallo tace, "Ammi suwaye suka fita yanzu" ta jefawa Ammi tanbayar tare da Jan kujera dining murmushi Ammi tayi tace, "Nihal! tab'e baki Nazili tayi tana cin abinci a zuciyar tana cewa, ni da kai na zan fidda ki macijiya maya yar talaka, Dai-dai za su shiga mota Sultan yana k'ok'arin shigewa tashi motar tsaye yayi yana k'arewa Nihal kallo mai cike da tuhuma maida murfin mota yayi cikin masifa tare da nufo idan Nihal take tana k'ok'arin shiga mota rike hannun ta Sultan yayi can k'asan mak'oshi yace, "kar ki kuskura ki shiga motar nan" da kallo Nihal ke bin Sultan da shi na rashi fahimta damke mata hannu yayi sosai ya fara tafiya da ita can k'asan makoshi Nihal tace rai a had'e, "Sultan! Ina zaka kai ni ka sake ni" tana maganar tana neman banbare hannu Sultan daga jikin ta har suka iso part d'in Sultan, wurgi yayi da Nihal ta fad'a saman gado yana huci ya rik'e kugu yana maida numfashi kamar wani zaki Nihal ce ta katse mashi tunanin da cewa, "me haka Sultan? me yasa zaka min haka? baka ganin makaranta zani" daka mata uwar tsawa Sultan yayi tare da cewa, "ban shirya fara fitar ki yanzu ba" durowa Nihal tayi daga saman bed tana kallan Sultan idanuwan ta taf da kwalla Sultan ya cigaba da cewa, "ina fatan kin gane ban baki damar ki fara fita ba, oh su kike ki fita ki had'e da mutanan na ki ko, Saboda bana baku dama a gida ku had'u ko toh hakan yayi kyau baza ki fita ba" Sultan ya ida zancan yana kafe Nihal ta idanuwa necktie d'in shi Sultan ya gyara tare da ficewa daga d'akin yasa ma kofar bedroom d'in key da Sauri Nihal ta k'araso bakin kofar tana duka tana cewa, "Sultan! Sultan ! Wai me yasa kafiya sankanka da yawa ne" zamewa Nihal tayi bakin kofa tare da sakin kuka, Sultan na fita mota ya shige aka jashi se office Sultan zaune a office yana juya kujera ran shi had'e knocking d'in kofar da akayi ne yasa shi cewa "come in" Ammar ne ya shigo fuskar shi dauke da murmushi yana cewa, "Ango! ango! Ango kasha kamshi harara Sultan ya watsa mashi yana cewa, " Wai yaushe ne zaka daina rai nani " dariya Ammar ya saki yana cewa seka fara aje ya'ya bud'e baki Sultan yayi zeyi magana Ammar yayi saurin cewa, "yanzu ba wannan ba ina files d'in dana baka ranar Friday kayi aiki da su,? dafe goshi Sultan yayi yace, "oh na manta da su a gida wallahi" washe baki Ammar yayi yana cewa, "Alalai wallahi kana jin dad'in ka ai da baka mantuwa yaushe ka fara haka" Ammar ya fad'a yana dariyar shak'iyanci tsaki Sultan ja yace, "ka ga malam ta so muje tare na dauko su," "Toh" Ammar yace tare bin bayan Sultan parking lot suka wuce Motar Ammar suka shige Ammar yana ja yana tsokanar Sultan har suka iso gida a parking space yayi parking, Sultan ya b'ale murfin mota ya fice Ammar na k'ok'arin fitowa ya ga Nazili murmushi Ammar ya Saki yana cewa Nazili Ashe kin dawo,? "Eh na dawo tunda gashi ka ganni" tana maganar ta bud'e murfin mota Ammar yace, "ban ganki da bikin Sultan ba" ya fad'a yana tsare Nazili ta idanuwa cike rainin wayau tsaki Nazili taja tace, "ina ruwan ka da rashin zuwa na, ko sa ido mtsww" sannan ta mai da kofa ta rufe dariya k'asa-k'asa Ammar yayi tare da wuce wa part d'in Sultan Sultan na bud'e kofa Nihal ta mike tsaye lokacin har ta cire hijab d'in kanta da takalmin kafar ta daga ita se mini skert da white shirt gashin ta ya zubo har gan bayan ta, a zabure Nihal ta tashi tana bin Sultan ta kallo mai cike da tsana tana cewa, "Sultan mi yasa zaka min haka Wai mi yasa baka da imanine umm, mi yasa baka saurara damuwar kowa se ta ka eeeh !!! Ni fa ba san ka nake ba na aure ka ya kamata kasan da haka Sultan abinda kake min ya fara isa a kanmi kake min haka, ka bari idan nace ina san ka se ka wulakanta ni san da na aure ka ai ba haka kace ma Ammi zaka rik'e ni ba ko" tana maganar cikin daga murya tana kuka, idan dutse na magana sultan yayi haka ya gama had'a file's d'in ze fice da sauri Nihal ta binshi wannan k'ara be kule mata kofa ba har ya iso parlour Nihal tace da karfi, "Sultan ! Na san kana....!!! abinda ta ganine yasata yin shock da waro idanuwan ta kasa k'arasa maganar da take sanyin tayi, Ammar dake tsaye bakin kofa ne ya daskare yana bin Nihal da kallo wadda a yanzu ta canza mashi a Nihal d'in daya sani, da ban dan yayi mata farin sani ba da baze iya gane ta ba, dan ta kira suna Sultan shiyasa ya gane murya ta yatabar da cewa ita ce, Jim kad'a Sultan yayi jin Nihal tayi shuru juyowa yayi suna facing juna dan shi har a lokacin be ga Ammar ba ya matso daf da ita ganin haka yasa Ammar fita da sauri dan gani yake duniyar na juya mashi, ciki masifa Sultan yace "Nihal na sha gaya maki cewa gidan nan idan ana magana ba'a daga murya, kada ki sake labari ya je kunnan Ammi ta gane wani irin zaman aure muke na fad'a maki kenan duk abinda ya sami Ammi saboda ke se uhmm" sannan Sultan yasa kai ya fice, Nihal da tayi mutuwar tsaye ce ta dawo hayacin ta tare da cewa, "na shiga uku yaya mi ya kawo yaya nan gidan asirri na ya tonu zagaye parlour Nihal ta shigayi tana shara kwalla duk hankalin ta ya tashi tsoran ta d'aya kar yaya ya fesawa Sultan ita wacece bayan k'arya data gama sakar masu, mi Ammi zata ji idan taji haka mi za'a dauke ta mutuniyar banza dafe goshi Nihal tayi zuciyar ta na dukan uku-uku jirin da take ganine yasa ta zama saman kujera tana maida numfashi. ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page:75_76* Banko kofa Nihal tayi da karfi tana maida numfashi cikin d'aga murya tace, "Sultan! Sultan dake kokari kai spoon bakin shi ne ya lumshe ido yana k'ara jin tsanar Nihal yau kuma da wani iskanci ta zo na kiran suna shi da karfi gaban bayi, ware idanuwan shi yayi tare da k'ok'arin kai spoon bakin shi karo na biyu, da sauri Nihal ta warce spoon d'in hannun Sultan, tayi tsuru-tsuru dan ita kanta bata san ta ina zata fara bayani ba, Adama dake gefe in ban da tsuma ba abinda take, zufa se karyo mata yake, dubare ce ta faduwa Nihal tace, "tsaka na gani cikin tukunyar miyar yanzu" ta ida zancan tana tsare Sultan da ido duk tabi ta riki ce sultan yace, "Tsaka kuma ! Murmushi Sultan yayi na rainin wayau yace, " Dara kwashe abincin nan" gwagwamar ajiyar zuciya Adama ta saki tare da jin tsanar Nihal, haka suka washe abinci, k'ok'arin fita Nihal take Sultan ya ruko hannu ta, gaban tane ya yanke ya fad'i Allah yasa kar sultan ya gano cewa lab'e tayi har ta ji, Sultan ne yace, "Na san cewa babu wata tsaka data fad'a cikin tukunyar abinci da zanci, kuma kada kiyi tunanin dan kinyi wannan abun shi ze sa na yadda dake, idan kina tunanin haka gwara tun wuri ki canza tsari, tanbaya ta a nan ya akayi kika shiga babba kitchen har ki kaga tsaka cikin tukunya ko kuma nace suwa ki ka gani suna zuba min guba a abinci,? Idan ko har baki fad'a min ba nafi tunanin wannan shirin ki ne," juyowa Nihal tayi ta fisge hannun ta daga rukwan da Sultan ya mata idanuwa ta taf da kwala murmushi yak'e Nihal ta saki tace, "Ai dama ba tsakar data fad'a nayi hakan ne dan na haram tama abincin, kamar yadda ka haram tamin zuwa makaranta d'azo" Nihal ida zancan tare d'aga gira ta cigaba da cewa, "yanzu nasan duk halin da ake ciki an zubar da abinci se kasa a dafama wani ko ka kwana da yunwa na san kai ma yanzu ka ji yadda na ji" sannan Nihal ta fice, ciki sumar kan shi Sultan yasa hannu shi yana zagaye parlour shi kan shi yasan karya take kawai dai tasan an zuba guba ne cikin abinci kamar yadda zuciyar ke ba shi, wata zuciyar na cewa karka ga dan tayi ma haka ka yadda da Nihal itama Asiya haka tayi ta shigo rayuwar ka Sultan, fad'awa Sultan yayi saman kujera ya lumshe ido. "Amma dai anyi tsinaniyar yariyar" Gimbiya jalila ta ida zancan tana huci kamar kumurci ta cigaba da cewa yarinyar nan Gona ta take so ta fara shiga in tasan wata bata san wata ba, ni mai iya sawa ce akawar da ita cikin d'an kankanin lokaci wannan Nihal d'in se naga bayan ta, ta fara shigar min hanci yakumbo " Gimbiya jalila ta ida zancan cikin d'aga murya, juyowa Gimbiya jalila tayi tace, "yama akayi tasan da an zuba guba cikin abinci? Gimbiya jalila ta watsawa yakumbo tanbayar, "nima wallahi Gimbiya abin da ke daure min kai kenan" murmushi Gimbiya jalila tayi tace, "ina so ki aika a kashe min Adama a daran nan" sannan Gimbiya jalila ta shiga d'aki ta bar yakumbo a parlour. *Washe gari* Shiryawa Nihal take cikin wata gwon maroon me dogwan hannu fuskar nan tata ba walwala tayi fayau da ita, bayan ta gama shiryawa ta fito parlour zaune ta samu Sultan saman kujera yana sanye da suit black yayi kyau sosai, cikin siriryar murya ta Nihal tace, " "ina kwana" tana k'ok'arin wuce shi ta fita, dan bata damu daya amsa ba da karya amsa, mik'ewa Sultan yayi yace, " ki jira ni mu fita tare akwai inda zamu" Sultan ya fad'a a tak'aice tsayawa Nihal tayi cak tana mai k'ara jin haushi Sultan da ya barta tana zuwa makaranta ai da yanzu tana can d'an siriri tsaki Nihal ta saki, k'arasowa da Sultan yayi ne yasa Nihal k'ara had'e rai kallan kasan ido sultan yake mata yana mamaki halin Nihal na karfin hali wani lokacin idan tana masifa ba abin da ke birge shi kamar yadda karamin bakin ta ke zakalkalewa kamar zata iya dukan shi, dan siriri tsaki Sultan ya saki tare da kauda kan shi, tafiya suke a jere gwanin ban sha'awa har suka karaso part d'in Ammi dauke da sallama a bakin su suka shiga Ammi da Basmal dake zauna ne suka washe baki Ammi tace, "Nihal ya akayi baki je makaranta ba, Ammi ta jefawa Nihal tanbayar, shuru Nihal tayi tana tsare Sultan da ido ja mata kujera sultan yayi yana murmushi yace, "Ammi bana so tana fita kullun ana gane min mata zan sama mata lesson teacher mace a gida" murmushi Ammi ta saki tana cewa, "hakan na da kyau sultan kayi tunanin mai kyau idan exam ya zo se taje ta zana" "Ai dama haka na tsara" ya ida zancan yana kallan Nihal wadda ta had'e rai daura hannu shi yayi saman na Nihal yana mata kallan shi me rikita yan'mata shi ga munafi ki tunda gaban Ammi ne, murmushi yake Nihal ta saki tana mai kasa da kanta Basmal tace, "yayana soyayya ka da Aunty Nihal na birge ni, Nima Allah ya bani Wanda ze min haka," murmushi Sultan da Nihal sukayi suna kallan juna, Nihal ko a zuciyar ta cewa take da ban ji maki dadi ba Basmal, Ammi ce ta katse masu tunanin da cewa, "se naga kamar fita za kuyi? murmushi Sultan ya saki yana cewa, "uhmm wani waje zata rakani" Sultan yana maganar yana shan coffee, washe baki Ammi tayi tace "Allah ya baku zaman lafiya da fahimtar juna wannan soyayya taku tana tuna min da tsoho miji na margayi" Ammi ta fad'a tana kallan Basmal dariya gabaki d'ayan su suka saki ban da Sultan da ya had'e rai yana washe bakin karya, Basmal tace, aunty na ya kamata ki canza kaya tunda tare da yayana zaki fita ya kamata kiyi gayun da yafi haka," d'an daburcewa Nihal tayi tana cewa, "ki barni haka ma bana sa...!!! "Haba aunty please ki tashi muje mana" Ammi tace, "ki tashi mana Nihal nasan Dara ta maki make up se kin zama looking take away my dear," kallan da Sultan ya mata ne yasa Nihal mik'ewa bedroom d'in ta suka shiga, shirya Nihal akayi cikin dark blue gwon me dogwan hannu me flowers da stones se walwali kayan suke nanad'e mata gashin ta akayi aka sokeshi da wata yar kibiya lips d'in ta yasha maroon Jan baki ita kanta Nihal ta yaba kyan data zuba se dai takaicin ta d'aya saboda Sultan akayi shi mtsww, black veil ta dauka da fost silver me kyau suka fito, fitowarta tayi dai-dai da fitowar Nazili ta shirya cikin jeans and t-shirt ta saki gashin kanta kallo tabi Sultan da shi Wanda ke kallan Nihal yana yaba kyan ta a zuciyar shi da ko ganin Nazili beyi ba da take mashi magana cikin iyayi, juyawa Nazili tayi nata kallan inda Sultan ke kallo wani kulutun bakin ciki ne yayi mata tsaye tana bin su da kallo, Basmal ce ta katse mata tunani da cewa, "Aunty na kinyi kyau masha Allah," kallan Nazili Basmal tayi tace, "yau fa yayana ze fita da Aunty outing ya kikaga ni Nazili, dama tunda sukayi aure basu samu damar fita ba saboda aiki" wani miyau Nazili ta hadiye tana mamaki irin kyau na Nihal take a nan idanuwan ta suka fara kawo ruwan mik'a ma Nihal hannu Sultan yayi a hankali ta daura lalausan hannu ta saman na Sultan yana tsare ta idanuwa shi masu rikitata suka fice, Basmal sakin baki tayi tabin su da kallo dan wani irin mugun birge ta suke, tunanin Ammar ne fad'o mata a rai murmushi ta saki ta shiga daki dan yau itama se taga sanyin idaniyan ta Nazili da ta cika tam idanuwan ta taf da kwalla Ammi na lura da yanayin ta. d'aki Nazili ta shiga da gudu tana kuka watsa kayan dressing mirror d'in ta Nazili take tana cewa, "se na kashe ki Nihal na tsane ki na tsane ki Nihal" tana kuka tana sanbatu Ammi ce ta turo kofa ta shigo taga yadda Nazili ke hauka rike ta Ammi tayi tana cewa, " Nazili! jikin Ammi Nazili ta fad'a tana cewa, "ta kwace min farin ciki na Ammi, ki na ganin irin kallan da Sultan ke mata me cike da so ko ganin mutane bayayi na tsane ta ammi, ta dauke min fari cikin Ammi," rugume ta ammi tayi tsam tana jin tausayin Nazili na shigar ta duk se ta ji ba dadi bata taba tunanin cewa Nazili nasan sultan ba ko tana san nashi ba tayi tunanin san ya kai haka ba, Amma yanzu lokacin ya riga ya kure se dai in shi sultan d'in ne yace yana san ta da kan shi. fisge hannun ta Nihal tayi a compound can kasan makoshi tace. "Na fad'a ma babu inda zan bika, ka kyale ni na koma cikin gida dan fita da kai babu wani Anfani na fad'a ma sultan," Nihal ta ida zancan tana tsare Sultan da ido, ko saurara ta sultan beyi ba ya bud'e mata murfin mota ya tura ta ya zagaya Alex ya bud'e mashi suka bar harabar gidan. Shiryawa Basmal tayi cikin wata brown gown me dan siriri hannu ta kama jikin ta parking gashin kanta tayi ta yafa veil tayi kyau sosai kallan mirror take tana cewa, "Allah yasa ya Ammar ya ga nayi kyau" wasu books ta dauka tana fitowa parlour ta had'e da Ammi murmushi Ammi ta saki tana cewa, "wannan gayun fa se ina? murmushi Basmal tayi tace, "gidan waziri zani ya Ammar ze koya min wani lesson," murmushi manya Ammi tayi tace, "yau be je office bane,? "ina tunanin haka saboda naga motar shi a waje" "Ok Allah ya taima ki gaishe min da Adda", sannan Basmal ta fice. Direct gidan waziri ta cewa, shiga parlour tayi da sallama Adda da fitowar ta daga kitchen kenan washe baki tayi tare da amsawa Basmal tace, Adda ina wuni" "lafiya lau daughter ya Ammi da mom naki" lafiya lau Adda Ammi tace na gaishe ki" murmushi Adda ta saki irin nasu na manya tace, "ina amsawa amma dai wannan zuwan ba nawa bane" dariya Basmal ta saki tana sunne kai, "Toh ai shikenan mutumin naki na part na shi yanzu nan ya shigo gidan" murmushi Basmal ta saki tana cewa, "toh Adda dama wani mathematics ze koya min" "hakan na da yau ai" mikewa Basmal tayi Adda ta bita da murmushi tana fatan Allah yasa Basmal da Ammar su sasanta kan su ayi tuwo na mai na dan ita Basmal ta mata, bakin kofa Basmal ta tsaya tana gyara kanta a hankali ta ke knocking d'in kofar amma shuru ba'a ce ta shigo ba a hankali ta murd'a handle d'in kofar ta shiga parlour ba kowa se sanyi AC da kamshi dake tashi, aje books d'in hannun ta Basmal tayi saman stool kofar bedroom ta nufa a hankali ta murd'a kwance saman bed ta hango ya Ammar ya luluba da blanket yana ta shara bacci wani irin kyau Ammar ya mata a hankali ta bud'e fridge ta dauko gora ruwa ta nufi kan Ammar tana leka fuskar shi tana bude bottle din gora a hankali, fisgo ta Ammar yayi ta fad'a jikin shi dariya Basmal ta saki ruwan ya bata masu fuska Basmal tace, "ya Ammar dama ba bacci kake ba ko? kallan ta Ammar yake kamar me Neman wani abu a fuskar ta dariya Basmal ta kuma saki tana cewa, "ya ammar ! tana maganar tana murmushi fararan hakuran ta na bayana tana bashi labari tana watsa hannuwa, Ammar dariya yayi, a hankali ya rik'e hannu ta shuru Basmal tayi tana bin Ammar da kallo a hankali ya matsar da gashin kanta daya kare mata fuska yace, "my dear kin yi kyau waya maki make up? zunburo baki Basmal tayi tace, "oh kana nufin ban iya make up ko to ni nayi da kai na" ta idan zancan tana turo baki, ja mata kumatu Ammar yayi yace, "am sorry gani nayi kinyi kyau da yawa" yana maganar yana tsare ta da idanuwan shi masu rikitata, setin kunan ta Ammar ya matso yana magana ciki rad'a, rufe fuska Basmal tayi tare mikewa ta fice da gudu dariya Ammar yayi ya zame blanket din jikin shi ya shige toilet Basmal ko bakin kofa ta tsaya tana mai da numfashi far da idanuwa tayi tana cewa, "wai da gaske ya Ammar yake yana so na," d'an mari fuskar ta Basmal tayi tare sakin murmushi, da sauri ta fito daga part d'in Ammar saboda tsabar murna Adda ta wuce A parlour, murmushi Adda ta saki tana cewa, "Basmal ! murmushi Basmal ta saki tare da cewa, "Adda bari na je na dawo" murmushi Adda ta saki ta girgiza kai. Direct office din sultan suka shiga Nihal ta cika fam, aje briefcase d'in shi sultan yayi Nihal ce ta katse mashi tunani da cewa, "me anfanin kawo ni wajan aikin ka ai ba wajan aiki ka cewa Ammi zaka kawo ni ba, sultan me yasa kake shiga rayuwa tane da yawa mi yasa,? harara sultan ya watsa mata tare da matsowa daf da ita rintse ido Nihal tayi tunanin ta marin ta Sultan zeyi, kallan kyakyawar fuskar ta Sultan ya shigayi yana mamaki rashin kunyar Nihal amma se tsoro, hade rai yayi yace, "ina tunanin ke kika fara shiga rayuwa ta, ni ya kamata na tanbaye ki haka kuma ki bani amsar haka kin gane sannan maganar zamuje wani wuri dake baki kai matsayin da Sultan ze fita dake ba wannan d'in ma akwai dalili kin gane" sultan ya ida zancan tare da sakin dogwan tsaki, alurori dake saman table ya dauka ze fice, Nihal ta bude lumsasun idanuwan tace, "Ai ni ban ce ina san fita da kai ba, kuma ina zaka tafi ka barni a nan sultan, Allah ka tafi ba zan zauna ba, ka hanani zuwa makaranta sannan ka kwaso ni ka kawo ni nan, nima fa mutum ce sultan, Wai me yasa baka saurara damuwar kowa se ta ka? ko saurara ta sultan beyi ba ya fice, kuka Nihal ta saki tare da zama saman kujera tace, "mugu kawai. Nazili na fitowa daga wanka taga Gimbiya jalila zaune saman sofa tana zaman jiran ta ta fito, kallo Nazili tabi Gimbiya jalila da shi na rainin wayau dan ita bata ganin kowa da gashi, cike da rashin kunya tace, "miya kawo ki daki na ba tare da izinin ba" ta fad'a tana tsare Gimbiya jalila da idanuwa murmushi Gimbiya jalila ta saki tana wasa da kwalin tissue dake saman stool tace, "zuwa nayi na magan ce maki matsala ki amma idan baki so, zan iya fita, mikewa Gimbiya jalila tayi zata fice, tana saurara mi Nazili zata ce har ta kai bakin kofa Nazili tace, "wace matsala? ta fada tana saurara Gimbiya jalila murmushi Gimbiya jalila ta saki tana cewa, "a kan Nihal mana! nasan cewa kina san sultan kuma ni kai na san da haka, mi zai hana na taimaka maki kiyi fad'a akan abinda kike so,? Gimbiya jalila ta ida zancan tana fatan samun nasara dan kar Nazili ta watsa ta, shuru Nazili tayi tana nazarin maganar Gimbiya can kuma tace, "idan aka samu matsala fa? Gimbiya jalila ta kyalkyale da dariya tace, "Indai kin yadda dani magana ta kare zantaya ki yakki a kan abinda kike so saboda ina maki fatan kasancewa da Sultan, anjima ki shigo part d'ina zan baki maganin da ze sa Sultan ya tsani Nihal a gabanki ze mata kora kare kwata-kwata Sultan be dace da Nihal ba dake ya dace," far Nazili tayi da ido tace, "zan shigo anjima amma bana san wasa cikin aiki na" murmushi Gimbiya jalila tayi tare da ficewa tana dariya k'eta dan ita burin ta Sultan ya bar doran kasa bata damu da damuwar Nazili ba. Koda Ammar ya fito daga wanka be ga Basmal ba beyi mamaki hakan ba Addu'a daya ce yake Allah ya cire mashi san Nihal shiyasa yayi sauri furtawa Basmal yana san ta saboda dama can yana san nata ganin Nihal yasa zuciyar Ammar mantawa da soyayyar Basmal ba wai baya san ta bane se dan san Nihal d'in yafi yawa, da kuma irin jan ajin da Basmal din ke mashi ada amma yanzu ya tabatar tana san shi auran sune ze cire mashi tunanin Nihal haka ya gama shiryawa yana wannan tunanin ya fito parlour books d'in da Basmal ta bari ya kalla jujuya su yayi tare furta cewa, "anjima na kai maki har gida my love. Iyakar shanyuwa Nihal ta shanyu haka ta rink'a zaman jiran sultan, wani takaici duk ya rufe ta ga wata yunwa dake dawainiya da ita, murd'a kofar da akayi ne yasa Nihal dago idanuwan ta a masifa ce, Ammar ta gani daskarewa tayi zaune tana bin Ammar da kallo juyawa yayi da sauri ze fita, zuciyar shi na dukan biyar-biyar dan ba k'aramin kyau Nihal ta zuba mashi ba har tana k'ok'arin goge mashi hada cikin siririyar murya ta Nihal tace, "yaya! tare da saki kuka kamar karama yarinya, shuru Ammar yayi yana saurara ta se kuma ta kasa cigaba da magana, can kasan makoshi Ammar yace, "mi yasa kika bar gida? wani dalili ne ya saki hakan har kikayi aure ba tare da sanin kowa na ki ba? kuka Nihal ta saki tana shasheka Ammar har cikin zuciyar shi yake jin kukan Nihal jiya ke kamar ya rungume ta tsam a jikin shi amma se dai yanzu ta riga ta zama matar wani, ciki sanyin murya Nihal ta fadawa Ammar abinda ya faru da ita, tana mai cigaba da cewa, "yaya na kashe mudi da hannu na ciki rashin sani kuma ba laifi na bane laifin shine yaya" Nihal ta kara rushewa da kuka tana cewa, "dan Allah yaya ka rufamin Asirri karka fad'awa Sultan ko ni wacece dan Allah" ta ida zancan tana rike kafafuwan Ammar janye kafar shi Ammar yayi ya lumshe idanuwa yana jin zafi rashin Nihal yace, "saboda ki san shi ne baki so ya sani ko mi? Shuru Nihal tayi can kuma tace, "yaya bana san shi kawai na yadda da auran ne da bani da inda zani yaya bani da kowa, bana so su dauke mutuniyar banza saboda tun farko na riga dana masu karya dan Allah yaya ka rufamin asirri" tausayin Nihal ne ya lulushe Ammar cikin sanyin murya yace, "tashi kin ji kanwata tsakanina da ke ai ba yar haka, sirrin k'anwata ai nawa ne, bana so kina zubar da hawayan ki" handkerchief yaya ya mikawa Nihal goge hawayan ta Nihal tayi tare da mikewa tana dariya mai had'e da kuka-kuka tana murmushi tana kara goge fuskar ta, lokacin yayi dai-dai da shugowar Sultan kallo ya bi Nihal da Ammar, gaban Nihal ne ya yanke ya fad'i ganin Sultan ta tsare shi da ido Nihal tayi tana fatan Allah yasa be ji su ba, Ammar ne ya wayan ce yana cewa, "yanzu na shigo Neman ka ashe da Amarya mu aka zo, yanzu nake tanbayar ta ina kake, tsare Nihal da ido Sultan yayi sannan yace kamar me koyan magana, " Eh tare muka zo" yana hadiye-hadiye ya kafe Nihal da ido itama jikin ta se rawa yake, Ammar ne yace, bari na ba masoya guri ya fice ya barsu, a hankali Sultan ya tako gaban Nihal rai a had'e ganin Sultan ya zo gab da itane ya sata rintse..... ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo ````🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Ina mika sakwan gaisuwa mai tarin yawa a gare Ku masoya na 🤗 Allah ya bar kauna da zuminci 😍 wannan shafin naku ne 🤗 ana mugun tare irin sosai d'inan 🤓 asha karatu lafiya na san cewa yau zuciyar masoyan wannan littafi zata kasance fes 💃💃 kamar yadda na suburbud'o maku posting_*😬 *Page: 77_78* Ritse idanuwa ta Nihal tayi sakwamakwan wani murdawa da mara ta tayi lokaci daya, ganin tsayuwa na neman gagarata yasa ta fashewa da kuka tare da rike cikin ta, cikin kuka Nihal tace, "Sultan ciki na,! durkushewa Nihal take neman yi a kasa Sultan ya riko ta tare da manna ta a jikin shi lafewa Nihal tayi a jiki sultan tana mai kara tsana ta kuka tana cewa, " Sultan mutuwa zanyi ciki na" rud'ewa Sultan yayi cikin sarkewar harshe a rud'e duk a lokaci daya musanman yadda Nihal ta cikwikwiye mashi suit tana rasgar kuka ciki ta, talabu da habar ta yayi har lokacin idanuwa ta na rintse tana kuka Sultan yace , "mi ya sami cikin naki Nihal kin ci wani Abu ne bayan fitata" sultan ya ida zancan a raunane kuka kawai Nihal take shekawa Sultan tana kara cikwikwiye mashi suit, Har a lokacin hannun su na mak'ale dana juna kwatar da Nihal yayi saman chest d'in shi yana shafa bayan ta a hankali kamar me rad'a yana cewa, "Sorry bari na baki magani ki daina kuka kin ji" Har a lokacin tana rike da cikin ta tana kuka tayi lamo a fafad'an kirjin Sultan, shurun da Sultan ya jine ya sasa d'ago da fuskar Nihal abin da ya ganine ya sasa razana wuyan Nihal ya taba wadda a lokaci bata dad'e da sumewa ba a jikin Sultan, daukar ta yayi a sume ya daura ta saman bed rest d'in office d'in shi a rud'e murza hannuwa ta Sultan ya shigayi Amma shuru har a lokacin Nihal bata numfashi bud'e drawer yayi Ciro alura guda biyu yayi ma Nihal a jijiya tare da bud'e idanuwan ta wayanda suke a lumshe kwanje-kwaje Sultan yayi ma Nihal tare da daura mata drip sannan ya fice daga office d'in, boutique ya wuce ya siyo mata kaya da pad da new pantries hankali shi duk yana kan Nihal duk se yaji tausayin ta ya kamashi, yasan idan ba magani take sha ba period wahala ze rika bata, har ya dawo bata tashi ba aje ledojin hannu shi yayi a hankali ya k'arasa bakin gadan yana karewa kyakyawar fuskar Nihal kallo a hankali ya kai hannu ze taba fuskar ta komiya tuna ya dauke hannu shi da sauri, komawa yayi ya zauna saman kujera yana fata Allah yasa data tashi ta ji ta normal babba abinda ke bashi mamaki Ashe Nihal din yarinya ce sosai tunda har wannan lokacin bata fara period ba, ringing d'in wayar shine ya katse mashi tunani a hankali ya sa hannu ya dauka suna dake jikin scream d'in ne ya sasa smile karawa yayi a kunne tare da cewa, "hello matar ba dai kishi kika fara ba" murmushi Ammi tayi daga dayan bangaran tace, "mun ji ku shuru ne Baku dawo ba naga har dare ya farayi baku dawo ba" jum kad'an Sultan yayi tare da kallan Nihal dake kwance yace, "Ammi bana tunani zamu dawo gida yau" murmushi Ammi tayi me sauti tace, "toh shikenan ina Nihal d'in? bani ita mu gaisa" kara kallan Nihal Sultan yayi tare da cewa, "Ammi tana toilet idan ta fito zan kira ki" "Toh ammi tace tare da katse wayar Basmal dake gefe Ammi ce tana jin me Sultan ke cewa dariya ta saki tana cewa, "Ammi yayana yau soyayya ake ta sha kenan" duka Ammi ta kai basmal ta kauce Ammi na cewa, "toh uwar gulma bari dai maimartaba ya dawo daga kasa mai tsarki ce mashi zanyi ya mika ki kema kafi ki zama abin da kika zama" dariya Basmal ta saki tare Da rugawa da gudu d'aki tana cewa, "Kai Ammi har kin fara gajiya da ni, to yau part d'in mom zan kwana idan kin fara kewata na dawo" girgiza kai Ammi tayi tace, "Allah ya shirya ki. Bangaran Nazili kowa tunda su Sultan suka fita ko wajan aiki ta kasa fita tana zaune gida tana faman leka window, ko zata ga motocin Sultan a compound amma shuru d'an siriri tsaki Nazili ta saki tare da zuge labilan d'akin ta, jin an murd'e kofa ne yasa ta juyowa a Hasale tana kallan kofar Aziza ce ta shigo dauke da tray d'in abinci ta aje saman stool har zata fita Nazili tace, "Sultan ya dawo shi da wannan Almajira koko," "Gimbiya har yanzu basu dawo ba," "mtsww kwashe kayan abincin ki bita da su bana jin yunwa" Nazili ta ida zancan a masifa ce jiki na rawa Aziza ta kwashe kayan abinci ta fice. "Momi har yanzu kin kasa gane Abu daya bana tunanin wata guba ko What ever da za'a sama Sultan cikin abinci ze kashe shi of coz Dr ne ya san abubuwan nan yana da brain sosai, Ni fa na riga dana gama shiri na time kawai nake jira na aika mugu lahira, kwata-kwata sa Nazili cikin wannan aiki be da anfani" Ashad ya ida zancan yana kora fresh milk d'in dake hannnu shi dan shuru Gimbiya jalila tayi can kuma tace, "ina da dalilin da yasa ni haka son, shiyasa na sako Nazili cikin har kanan ita kanta bata zan manufar mu ba, zan fi so ace Sultan ya mutu cikin ruwan sanyi, idan muka ka sheshi da makamin ana iya binci ke a gano cewa da sa hannun mu, kuma kasan aka gane kashin mu ya bushe" "Momi kenan! ai mutanan da zan ba aiki ba zaune suke a Nigeria ba, babu abinda ze faru amma for now zan baku dama kuyi anfani da Nazili naga yadda zata kasance amma bana tunanin wannan aiki ze tafi dai-dai" yakumbo dake rabe ce tace, "Ai sultan ya yadda da Nazili ba ze taba kawo ma ran shi zata cuce shi ba, ita kuma sakaryar ba tasan gadazaran da muka k'ulla mata ba, ka ga zata je babu fargaba ko tsoran ze mutu, se dai farin ciki samun nasara soyayyar ta a gare shi" dariya Gimbiya jalila da Ashad suka saki sannan Ashad ya mike yana cewa, "momi gobe zan wuce Dubai kan maganar takadun dana sace a office d'in Sultan bana so kowa ya sani bana kasa idan Sultan ko maimartaba sun tanbaya ki, ki ce masu naje range, kan maganar gona ta, saboda ina so na shirya ma sultan tugun da ko be mutu ba zeyi shekara talatin a gidan yari" dariya Gimbiya jalali ta saki tana cewa, "Ok son shiyasa nake sanka saboda kasan kan wannan harka" Gimbiya jalila ta ida zancan tare da rako d'an nata har bakin kofa suna hira. A hankali Nihal ke bud'e idanuwan ta k'ok'arin sakowa take daga gado Sultan ya k'arasa tare da rike ta, tsare shi Nihal tayi da lumsasun idanuwan ta tana kallan shi, dauke hannun shi yayi dake saman nata yana tanbayar ta ciki honey voice d'in shi yace, "mike maki ciwo yanzu" shagwabe fuska Nihal tayi tace, "ba komai" "Ok" Sultan yace mata tare da cire mata drip d'in hannu ta, sannan yace, "tashi ki shiga toilet ki yi brush ki fito, ki sama cikin ki wani abu," daga mashi kai Nihal tayi a hankali ta sako daga saman bed d'in ta shige toilet abinda ta ganine ya sata zuduma ihu ta fito da gudu daga toilet jiki ta na rawa karasowa Sultan yayi gaban ta, Nihal tace, "karka kuskura ka matso kusa dani, mugu Azalimi," Nihal ta ida zancan tana kuka tace, "Me kamin Sultan mi ya kawo jini a panti d'in na? Nihal ta jefawa Sultan tanbayar idanuwan ta taf da kwala ta tsare shi da ido, had'e rai Sultan yayi a zuciyar shi yana cewa me wannan yarinyar ta dauke ni ko iskanci zanyi se na rasa da wa zanyi se da wannan abar mtsww, da kyar Sultan ya dane Zuciyar shi ya kara takowa ihu Nihal ta saki tana cewa, "karka zo kusa wallahi ka zo se na kashe ka" Nihal ta ida zancan ta mannewa da kofar toilet tana fama raba ido tana kuka riko hannun ta Sultan yayi Nihal ta fara fisge-fisge rungume ta tsam Sultan yayi a jikin shi Nihal na fama dukkan Chest d'in shi tana cewa, "ka sake ni malam" hura mata iska bakin shi Sultan ya shigayi a hankali cikin kunnan ta me sanyi, lokaci daya ya sakarwa Nihal da kasala lamo tayi a chest d'in shi tana fama sauke ajiyar zuciya tana dukkan chest d'in shi a hankali, cikin rad'a Sultan yace, "ba wani Abu na maki ba wannan ne dalilin da ya saki ciwo ciki, kuma ba kanki aka fara ba kowace mace ta kai age d'in ki tanayi," shuru Nihal tayi tana saurara Sultan ga wani irin dadi da voice d'in shi ya mata kamar karya daina magana, can kasan makoshi sultan ya cigaba cewa, "idan ma kina tunanin wata rana zaki bani sha'awa ko wani Abu to ya kamata ki farka daga wannan mafarkin babu abin da ze ba Sultan sha'awa a jikin ki, Sultan yafi karfin ki ta kowace kofe" sannan Sultan ya ture Nihal daga jikin shi yana jifan ta da mugun kallo, tsare shi da ido Nihal tayi tana jin tsanar Sultan na ratsata tare da jin kunyar zargin da tamai dole ya gasa mata magana tunda ita tajawa kanta, Leda sultan ya dauka ya mikawa Nihal tare da yima ta bayani ran shi a had'e duk se ta ji kunya ta kamata. amsar ledar Nihal tayi ta shige toilet wanka ta farayi sannan tayi duk yadda Sultan ya fad'a mata canza kaya Nihal tayi cikin doguwar riga pink ta kama jikin ta Sosai kamar Sultan ya aunata kafin ya siyi rigar ita kanta tayi mamaki yadda riga ta zauna mata d'as, a hankali ta bud'e handle d'in kofar toilet ta leko zaune ta hango Sultan yana latsa waya, a hankali Nihal ta tako kanta a kasa ta zauna baki gado tana satar kallan Sultan dake zaune yana latsa waya jin kamar ana kallan shi yasa ya dago karfa suka had'a ido kauda kai Nihal tayi a zuciyar ta tana cewa wayo Allah na yanzu wannan mugun ze rai nani, mika mata cup d'in da Sultan yayi ne da bread rolls ne yasa Nihal dagowa amsa tayi har a lokacin Sultan ya tsare ta da idanuwan shi masu rikitata kasa tayi da kanta tana shan tea tana gyara gashin kanta da yake zubuwa yana rufe mata fuska tea din kawai Nihal ta iya sha dan bakin ta ko dad'i babu tana gama shan tea d'in ta aje cup din da ragowar bread rolls magani Sultan ya balo ya mike mata da glass cup na ruwa ran nan a had'e kwabe fuska Nihal tayi kamar za tayi kuka ganin ba wasa a face d'in Sultan ya ta amsa ta shanye bayan ta Shane ta ta aje glass cup d'in hannu ta, can kasan makoshi Sultan yace, "ki na iya tasowa mu wuce gida" to Nihal tace tare da daukar fost din ta, ta yafa veil d'in ta suka fito har a lokacin kan Nihal na kasa, parking lot suka wuce Alex ya bud'e masu murfi mota suka shige direct hotel suka wuce sakin baki Nihal tayi tana mamaki mutumin da yace zasu je gida miya kawo su nan zaune tayi ciki mota, dan ita a ganin ta babu inda zata da ya wuce gida, can kasan makosh sultan yace, "ki fito! tsare shi da ido Nihal tayi tana cewa, "ina ne nan mi ka kawo ni nan nayi dare fa yayi" "saboda daran yayi shiyasa na ce ki fito" shuru Nihal tayi har se da Sultan ya riko hannun ta suka fito a tare har suka k'arasa reception hannun Sultan na makale dana Nihal da kallo Nihal ke bin hotel d'in ATM card Sultan ya bada aka curo kudi sannan aka bashi key d'in dakin da zasu sauka, har a lokacin Nihal na raba idanuwa har suka iso bakin lift sultan ya dana ya bud'e makalewa Nihal tayi tana bin lift d'in da kallo tana kallan Sultan dai-dai setin kunan ta Sultan yace, "yar kauye kawai ba cinye ki za'ayi ba" had'e rai Nihal tayi tare da watsawa Sultan kallan da yafi kama da harara ta fisge hannun ta, ta shege lift d'in hard'e hannuwan tayi a kirji ta, ta ja gefe ta tsaya, shigowa Sultan yayi yana kallan ta ta kasan ido tare da danna lift din ya rufe har suka isa Nihal na gefe duk cikin dari-dari take lift na budewa Nihal ta fice da sauri tun kafin Sultan yace mata fita zasuyi murmushi Sultan yayi tare da biyo bayan Nihal tafiya kadan sukayi suka k'arasa dakin su, key sultan yasa ya bud'e se da ya kuna light a dakin sannan Nihal ta shiga tana bin dakin da kallo ciki da parlour ne tsaye Nihal tayi tana bin ko ina da kallo har Sultan ya cire suit d'in shi ya aje saman kujera ya rage daga shi se shirt harkokin shin ya shigayi har a lokacin Nihal na tsaye juyowar da zeyi suka kara hada ido da Nihal hannu shi daya na zube a cikin aljihu daya kuma cup d'in coffee kauda kai Sultan yayi tare da cewa, "tsayuwa zaki cigaba dayi ne" ya ida zancan yana kuna TV shuru Nihal tayi tare da zama saman kujera ta takure waje daya, kallan kasan ido Sultan yake mata sannan yace, "idan kina bukatar wani Abu ki shiga daki ki shirya kanki ki kwata" kamar jira Nihal take ta shige daki da saurin ta Sultan yabi bayan ta da kallo. Nihal na shiga bedroom Lafiyar bed kawai ta bi ta kwanta dan wani irin bacci take ji, bangaran Sultan ko a parlour ya kwanta saman kujera. *Washe gari* A hankali Nihal ta zame blanket din jikin ta tare kallan agogon dake manne a daki waro ido tayi ganin karfe goma, da sauri ta duro daga kan gado ganin Leda a gefen bedside drawer yasa Nihal budewa kayane da duk wani Abu da zata bukata toilet ta shige tayi wanka a gurguje dan burin ta be wuce ta ganta a gida ba daure da towel ta fito goge jiki tayi ta shafa lotion, gwon ce peach colour d'inkin girgar kamar bubu shape din ta ya fito sosai tayi kyau sosai duk da fuskar ta ba make up, kayan da ta cire ta tura cikin Leda a hankali ta bud'e handle d'in kofar hango sultan tayi tsaye gaban dining yana aje abinci sanye yake da suit Ash yayi kyau sosai sajan shi ya kwata luf-luf gashin kanshi se shining yake jin kamar ana kallan shine yasa ya dago da sexy eye ball din shi karfa suka hada ido da Nihal kauda kai Nihal tayi kamar me neman wani Abu ciki siriryar murya ta tace, "ina kwana," kamar me koyan magana sultan yace, "lafiya lau" sannan Sultan yace, "ki zo kiyi break" sultan ya fada a takaice "na koshi ni gida nake so na tafi" Nihal ta fad'a tana tsare Sultan da ido shima d'in kallan ta yake sun dau lokacin me tsawo suna kallan juna sannan Nihal tayi kasa da idanuwan ta saboda karjinin da Sultan ya mata kauda kai Sultan yayi tare Jan kujera ya fara breakfast din shi tare da yin dana sanin yi mata magana, jin yunwa na nukurku sata yana sa Nihal satar kallan plate din abinci gwiwa a sage ta karaso tare da Jan kujera ta zauna ran nan a had'e serving d'in kanta tayi chips with paper soup d'in yan'ciki hannu Nihal tasa ta fara tura abinci dan ba karamar yunwa take ji ba, ta kasan ido Sultan ke kallan ta yana mamaki taurin kai iri na Nihal na nuna isa kamar d'iyar wani, goge baki shi yayi da tissue sannan yace, "muna iya tafiya yanzu" ya ida zancan yana kallan Nihal dake k'ok'arin kai lomar abinci kunya ce ta rufe ta rasa yadda zatayi tayi gashi ita bata iya ce mashi ya jira ta idasa cin abinci dan karya raina ta Sultan ne ya tsare ta da ido alamar ta tashi ko ta koshi ko bata koshi ba wannan ba damuwar shi ba ce, fasa kai lomar abinci Nihal tayi tare da Ciro tissue ta goge hannun ta da bakin ta sannan suka fice. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau farin ciki gobe a kasin Nihal ta kara wayewa tayi kyau se dai kullun tunanin ta ina zata taga jakar da su Ammi suka tsince ta da ita ko Allah ze sa ta samu number aunty Aisha ta shiga, lokaci yayi da ya kamata taga dangin mahaifiyar ta ko ta samu natsuwa. kamar yadda Sultan yace wa Ammi ze nemama Nihal lesson teacher haka ya nema mata but Arabic da boko sosai Nihal ke mai da hankali tana mai kara jin itama zata san wani Abu game da addinin ta da boko dan ba wani samun ilimi tayi a hannu su gwoggo ba, in ban da ilimin talla. ******************************* Bangaran baffa duniya ta fara yi mashi zafi kullun cikin fargaba yake da mugayan mafarke-mafarke kullun a razane yake tashi cikin dare, gwoggo ko abinda yake ya fara isatar dan ko zaman lafiya yanzu yayi karanci a gidan, mudi ko tunda ya aika ta abun kunya, suna dawowa daga asibiti tunanin Nihal ya isheshi da takaicin abinda yayi mata had'a kayan shi yayi, yayima baffa karyar cewa ze je birni neman aiki ya gudu, sara ko ta lalace bin maza ba kama hannun yaro musanman yanzu da take SS 1 dama can da bokwan take anfani tana yawo banza malamai su matsa yan tasha su matsa indai za'a bata kudi musanman yanzu da gwoggo ta daure mata kungun iskanci dan yanzu wata ran ba a gida take kwana ba, abubuwa sun had'ewa baffa sun mashi yawa gashi asirri da yayi ma'aikatan gareji ya fara sakin su dan har sun fara cewa ya biya su albashin su yadda ya kamata ko su aje aiki ko su buga shi a kotu. Yauma kamar kullun bayan ya shirya ze fita daga gida gwoggo ta biyo shi da sauri ta cimai kwala tana cewa, "malam ni fa yanzu na rasa gane kanka ina zaka baka bada kudin cefane ba? jiyama haka kasa kafa ka fice, to wallahi sisin kwabo na! na gama sama cikin harkar gidan ka nama fad'a ma" gwoggo ta ida zancan tana hura hanci fisge kwala rigar shi baffa yayi yana cewa, "wallahi larai baki da mutunci baki San daraja miji ba kwata-kwata, wai me yasa baki da tunani dda ke keki cewa na baki kudi'n cefane, ke baki lura da wani irin hali mijin ki ya shiga ke dai burin ki a baki, ki shiga taitayin ki wallahi kin San bani da mutumci kisan hali farin sani," shewa gwoggo ta saki tana cewa, "tanimu kenan ka fad'i duk abinda zaka fad'i kudi ne se ka bada, kuma bilahilazi har da kudi na, na jiya zaka bani dan tsakanina da kai babu yar haka na gayama" bakin da baffa ze bud'e ne yayi magana Sara ta shigo cikin gida cikin shigar yan'duniya yan kauye tana taune-taune bakin nan yasha jan baki hannun ta rike da leda, baffa ne ya daka mata wata uwar tsawa yana cewa, "daga gidan uban wa kike Sara,? gidan uwar wa kika kwana jiya? baffa ya ida zancan tare da yin kukan kura kan sara, gwoggo ce tayi tsale ta shiga tsakiyar su tana huci tace, "dakkata malam karka manta wannan d'iya tace ba d'iyar Habu ba, ina ruwan ka da inda taje ga wadda ya kamata ka bi ka tanbayi gidan uwar wa ta je har ta kusa kashe ma d'a ta guda amma ba wannan ba, yo in ban da tanbayar rai nin hankali ai kasan bata wuce gidan mu ko ka mata katangar karfe da gidan kakanin tane? gwoggo ta ida zancan tana huci hannnu ta na rike dana sara ta boye bayan ta, tana kunbure-kunbure tana wani girgije-girgije ita ba wasu kaya na zo a gani ba, nunata baffa yayi da yatsa yana cewa, "Wallahi talahi yarinya nan ta kwaso abin kunya ba'a gida na ba na ma fad'a maki" wata irin shewa gwoggo ta saki tana buga zani tana cewa, "wallahi aniyar ka ta bika tanimu an fad'a ma kowa irin diyar kanin ka ce Habu ita ce yar iska wadda saboda tsabar iskaci ta gudu anneme ta sama ko kasa, ni ko d'iya ta tana cikin gida, saboda tsabar bakin ciki irin naka tunda yanzu babu dangin na ka, ka gama da su da bakin cikin ka shine yanzu ka dawo kan ya'ya na to wallahi dan gani da bari kurwar ka kur li'ilafikuraishi aniyar ka ta bika wallahi" kad'ai baffa yayi ya fice daga gidan gwoggo ta ja hunnun sara tana cewa, "yau mimuka samu d'iyar albarka" d'aki suka shige sara na yan surutai game da sa idan da baffa ke mata. ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo ```[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Assalamu alaikuma masoya na ina mai baku hakuri da rashin ganin posting dina jiya wani wani kwakwaran dalili ya hanani amma yanzu komai ya zama normal wannan shafi naku ne masoya sauyin rayuwa_* *Page: 79_80* Shiryawa Nihal take ciki black jeans and blue t-shirt tayi kyau sosai, turare ta feshe jikin ta da shi sannan ta sa Jan baki tare da yin parking gashin kanta, kasancewa Ammi na bedroom tana bacci basmal na School, Nihal tana gama shirin ta, ta wuce part din mom dauke da sallama a bakin ta tana shiga bayi ta gani suna ta hada-hada Dara na gwada masu aikin da ya dace suyi murmushi Nihal ta saki cikin siririyar murya ta tace, "Umma ina wani" "Lafiya lau, yau malama taki bata zo bane? Daga kai Nihal tayi tana murmushi tace, "mom fa? "Tana kitchen" dan waro ido Nihal tayi cike da surprise mi mom take a kitchen bayan ga ma'aikata a hankali ta karasa kitchen mom dake faman aiki kamar ba Gimbiya ba, bayi se taimaka mata suke da yanke-yanke vegetable cikin sanyi murya Nihal tace, " mom! Juyowa tayi fuskar ta dauke da murmushi tace, "daughter yau lesson teacher bata zo bane? Mom ta fada tana tsare Nihal da ido tana murmushi shuru Nihal tayi tana kallan mom cike da surprise musanman yadda taga tana soya miya, murmushi mom tayi tare a aje spoon d'in hannu ta, ta daura hannu ta saman fuskar Nihal tace, "daughter kina mamaki ne mom na girki ko, kamar ba yan'aiki karki damu kin ji" janye hannuwan ta mom tayi daga fuskar Nihal tana mai cigaba da cewa, "duk mulki mace da kyan ta da kudi ta idan bata iya girki ba se sorry daughter kin ganni nan duk san da aka ce ranar girki nane bana bari kowa yayi ma maimartaba girki da kaina nake yi, saboda ba masu aiki suyima mijin ka girki be da wata fa'ida tanan ake yawan samun matsala da matan zamani musanman ku masu tasowa" murmushi Nihal tayi tana mai taya mom bare magi mom tace, "kuma kisan wani Abu daughter? Girgiza kai Nihal tayi tana cewa, "mom se kin fad'a" "Iya girki nasa miji ya kara San matar shi fiye da tunanin ki daughter, yanzu haka na tabata idan maimartaba ya ci abincin nan ko ba dad'i ze kara ji na a cikin zuciyar shi tunda har bana bari bayi su mashi, ya kamata ace ke ma daughter kina kwatanta yi ma son hakan ki daina yadda bayi nayi mashi komai ko turaka shi ya kamata ki rinka sa ido ki daina bari ana shiga anyhow, ze ji dadi sosai musanman da baya yadda da kowa na San ze yadda dake tunda yana sanki kuma zeji dadi tsarin" mom ta ida zancan a raunane, of coz tana sane da musguna mashi da ake ta hanyar cikin shi da shan shi be da wani peace of mind Nihal kad'ai zata kawo karshan wannan lamari, shuru Nihal tayi tana nazarin maganar mom a zuciyar ta tana cewa nima watsani yake dan ba yadda yake yi dani ba amma se Nihal tayi murmushi yake tace, "mom ai ni ban iya irin wannan girki ba koko da tuwo na iya da shinkafa da wake San da ina kauye su kad'ai na iya, kuma insha Allah zan rika kula da part d'in shi" murmushi mom tayi tana juya miyar ta dake kan wuta tace, "daughter karki damu kin ji a hankali zan fara koya maki girki kala-kala har da na waje, naji dadi sosai da kika fahimce ni of coz part din mijin ki sirrin kine" wani irin dadi ne ya lulube Nihal da taji mom zata koya mata abincin yan gayu har tayi hugging din mom haka Nihal ta zage tana taya mom aiki a kitchen sunayi suna fira kamar uwar da diyar ta baka taba cewa uwar mijin ta ce, hakan kuma nayi ma Nihal dadi ko ba komai idan sultan ya mata wulakanci yan'gidan su na nuna mata kulawa. "Nazili ga wannan maganin ki tabata kin zuba ma Sultan a cikin abinci ko abin sha, na tabata zaki sha mamakin yadda ze wulakanta Nihal a gaban idanuwan ki" Gimbiya jalila ta ida zancan tana mikawa Nazili kulin maganin hannu ta, amsa Nazili tayi tana jujuya maganin kamar kashi tana wasu yatsine-yatsine can kuma se tayi murmushi tace, "idan magani be yi aiki ba fa,? Nazili ta ida zancan ta tsare Gimbiya jalila da ido, murmushi mugun ta Gimbiya jalila tayi tace, "ze mayi ne nina fad'a maki ! "Toh shikenan amma ya kama ki fad'a min nawa zan biya ki saboda ni Nazili ba'a min aiki kyauta, saboda bana layin matsiya ta" Nazili ta ida zancan tana fido bandil din dubu daya daga cikin handbag d'in, tsare ta Gimbiya jalila tayi da ido tana kara jin tsanar Nazili tare da jinjina irin rai nin da Nazili tayi mata Allah ya ga abinda ya gani ya hanata Sultan ko ta aure shi baza ta bada damar wani ya rabe shi ba, murmushi Gimbiya jalila tayi tare da daukar kudi da Nazili ta aje saman Stool tana jujuyawa tace, "amma kin San tsakanin uwa da diyar ta babu yar haka," juya idanuwa Nazili tayi tace, akwa kasuwanci tsakanin uwa da diyar ta, kuma nasan kina bukatar kudi ne saboda baki aikin fari bale na baki se dai ki ci na maimartaba da d'an ki, so wannan gashin kanki ne kina iya fara kasuwanci da kud'i," Nazili na gama fad'i haka ta fice wani dogwan tsaki Gimbiya jalila ta saki tare da watsawa yakumbo kud'in a fuska. Bayan su mom sun kamala had'a abincin kusan kala biyar suna jerawa a dining kafin akai turakar maimartaba mom ce ta kalli Nihal tare da cewa, "daughter ki je ki watsa ruwan na san yanzu son yana kan hanyar dawowa kar ya dawo yaji kina kaurin kitchen," yar dariya Nihal tayi tana cewa, "mom bafa da icce mu kayi girkin ba," "Laaa daughter dan bada icce bane se ki kasa yin wanka maza wuce kiyi wanka, ko nasa Dara ta maki" dariya Nihal ta saki tana rufe fuska tana cewa, "bari naje nayi" "yawa ko ke fa, anjima ke da son ku zo dinner tare," "Toh mom" sannan Nihal ta fice, Nihal na fitowa taci karo da Nazili taci kwaliya ciki wata gwon maroon har kasa rigar shape d'in jiki ta ya fito d'as bakin ta yasha Jan baki tana tafiya komai na jikin ta na amsawa gashin kanta ya nanad'e kamar taliya a gadan bayan ta, da kallo Nihal ta bi ta, ganin tayi part d'in Sultan ita da bayin ta na take mata baya yasa Nihal tab'e baki tana cewa a zuciyar ta aikin banza cusa kai ba kwarjini mtsww sannan Nihal ta kara gaba ganin motacin Sultan a compound ne yasa Nihal yin jum kad'an kamar me na zari juyawa tayi da sauri tabi bayan Nazili. Nazili na isowa bakin kofa bafade ya bud'e mata kofa bayin ta suka tsaya a waje, Sultan da dawowar shi kenan yana kokarin cire necktie d'in shi a parlour kafin ya karasa bedroom, Nazili ta shigo fad'ad'a murmushin ta Nazili tayi tana takowa cikin tafiyar ta me Jan hankali har ta karaso gaban Sultan rike waist d'in shi tayi tare da yi mashi light kiss a kumatu cike da shagwaba tana cewa, "tunda baka nemana yau na zo da kai na" smile Sultan yayi har dimple d'in shi na lomawa tare da furta "Nazili! ciki honey voice d'in shi ya cigaba da cewa, "ba haka bane aiki ne ya min yawa shiyasa" tsare Sultan da ido Nazili tayi wani kyan Sultan na kara rud'a ta musanman da yayi murmushin me kashe ta, gashi kullun kara kyau yake ya Allah Nazili furta a zuciyar ta tare da cewa, "kullun haka kake cewa se ka ce agogo sarki aiki" ta ida zancan tana tsare Sultan da ido da yake fama kokarin cire necktie, murmushi ta yi ta kara matsowa kusa da shi har suna jin saukar numfashin juna su ga wani kamshi turaran Sultan daya rikitata lalacewa tayi gurin kallan shi musanman da yayi kasa da idanuwan shi eyelash din shi sukayi kamar yasa, cikin kisa da kisisi na tace, "lamme help you," murmushi sultan yayi yana cewa, "ba se ki tayani ba," ya ida zancan yana cire necktie din ya zauna saman kujera tab'e baki Nazili ta kumayi tare da cewa, "Ni fa zuwa nayi musha coffee kwana biyu bamu sha tare" murmushi Sultan yayi yace, "kamar kisan shi zan had'a yanzu kafin nayi taking bath had'a mana" da Sauri Nazili ta nufi dining area jiki ta har rawa yake, kananan cups ta dauko tasa saman karamin tray tare da janyo flanks ta zuba ruwan zafi cikin k'ananan cups din kamala had'e coffee din tayi, a hankali ta zura hannu ta cikin gaban rigar ta, ta ciro kulin maganin da Gimbiya jalila ta bata, tana waigen Sultan dake ta fama latsa waya hankalin shi baya kanta, da sauri ta juye mashi duka maganin cikin coffee d'in da ta had'a ta juya da spoon dauko tray da ta yi yayi dai-dai da shigowar Nihal ta na sakarwa Nazili malalacin murmushi tace, "Sultan har ka dawo? dago da sexy eye ball d'in shi yayi yana karewa Nihal kallo Wanda shi kan shi be san yana yi ba of coz he can't resist to stop looking at her beauty face, ringing din wayar shine ya katse mashi tunanin, lokacin yayi dai-dai da mika mashi cup da Nazili ke kokarin yi Nihal ta amsa da Sauri tana cewa, "Nazili be kamata mutum na tare da yunwa ba yasha coffee ya kamata ya fara yin lunch sannan ko" ta ida zancan ta na tsare Nazili da ido tana addu'ar Allah yasa kar Sultan ya juyo ya watsa ta Nazili ce ta katse mata tunani da cewa, "amma dai kin san ina da ilimi bana yin abu up head," murmushi Nihal tayi tare da kallan Nazili hannu ta rik'e da cup din coffee d'in Nihal da Nazili na kallan-kallo Nazili tare da jefa ma juna su kallo me cike da tsana sakin cup din hannun ta Nihal tayi ya fad'i kasa tana murmushi mugunta Waro ido Nazili tayi tare da cewa, "Nihal ! Idanuwan ta waje Dukawa Nihal tayi tana cewa, "wayo Allah na, nayi barna" Sultan da tunda suka abun su hankalin shi na kan wayar da ya ke, kara mashewar cup ne yasa Sultan juyowa da sauri tare da katse wayar daya ke yana kallan Nihal wadda ke duke tana kokarin tatare glass cup, din dake a kasa tana faman ba Nazili hakuri, kamar bada gangan tayi ba, yankewa da Nihal tayine ya sata sakin yar kara da sauri Sultan ya karaso gaban ta tare da rike hannu Nihal dake zubar da jini kuka Nihal tasa cike da shagwaba tana kallan Nazili ta kasan ido hura mata iskar bakin shi Sultan yake yana cewa, "sorry! yana tsare ta da idanuwan shi ma su rikitata kallan juna suka shigayi, Nazili dake tsaye akan su tana kallan yadda Sultan duk yabi ya damu ji tayi kamar tayi hauka idanuwan ta taf da kwala cike da tsanar Nihal. ganin haka yasa Nazili fita daga part din sultan da gudu tana kuka Wanda cikin su ba Wanda ya lura da ita. Tana isa bedroom nata saman bed ta fad'a tare da sakin kuka tana cewa amma wannan anyi tsinaniya natsane ki Nihal natsane ki mekewa Nazili tayi tana mai cigaba da cewa lokaci yayi da ya kamata muyi fito na fito ba boka ba malam Nihal se na kashe ki, se na kona fuskar dakike takama da ita wadda take daukewa Sultan hankali se na kona ta share hawayan ta Nazili tayi tare da janyo wayar ta dake bedside drawer ******************** Ammar ne da Basmal cikin wani park suna zaune sama wasu resting chair suna facing juna tsakiyar su table da roba ice cream Ammar ne ya tsare Basmal da ido yana aika mata da kallan so tare da daura hannun sa saman na Basmal yace, "My love ni fa yanzu a shirye nake, so na ke su maimartaba su san muna tare nasan zasu ji dadin hakan, na matso na ganki a gida na" ammar ya ida zancan yana rike da hannun Basmal, murmushi ta saki har fararan hakuran ta na baya tare da cewa, "nima haka Darling amma zan fi so na kamala karatuna tunda saura shekara daya" bata fuska Ammar yayi yana cewa, "gaskiya baby bana iya hakuri har se shekara daya, ni fa idan san samu nane ayi bikin nan cikin satin nan" Ammar ya ida zancan yana d'an matse mata hannu yar kara Basmal ta saki tana cewa, "ya Ammar abun har da keta kuma" dariya Ammar yayi tare da cewa "Ni na isa nayima my princess keta" ya ida zancan yana smile tare da daukar spoon d'in ice cream yana feeding din Basmal yana bata tana amsa tare da zuba mashi shagwaba, haka suka rinka zuba soyayya mai cike da kauna. *** Bayan sun gama dinner da dare kowa ya wuce part d'in shi tsaye Nihal take gaban dressing mirror tana sharce gashin kanta a hankali tana kallan mirror, sultan da fitowar shi daga toilet kenan ya kafe bayan Nihal da kallo jin kamar ana kallan ta, ta baya ya sata juyowa karaf suka had'a ido da sultan sun dau lokaci me tsawo suna kallan juna su Wanda basa iya fassara kallan na minene kasa da idanuwan ta Nihal tayi tana wasa da gashin kanta kauda kai sultan yayi, karasawa Nihal tayi baki drawer zata Ciro blanket mika hannu Nihal tayi tana kokari janyowa amma ta kasa se dage takeyi Sultan ne ya karaso dai-dai lokaci Nihal ta daura hannu ta saman blanket din shima Sultan ya daura hannun shi saman lalausan hannun ta juyowa sukayi a tare suna kallan juna har a lokacin hannun Sultan na saman na Nihal janye hannun ta Nihal tayi da sauri tana gyara gashin kanta, kauda kai sultan yayi tare da mikawa Nihal blanket, yayi gaba se da ya hau saman bed sannan Nihal ta iya furta "na gode" shuru Sultan yayi kamar be jita ba ya ja blanket tare da kashe haskyan d'in kwantawa Nihal tayi saman sofa tayi lamo kamar me bacci haka shima Sultan sun dau lokaci mai tsaho kafin bacci ya dauke su. *Washe gari* Shiryawa Sultan yake cikin armani royal black suit da white inner tie d'insa kala daya da suit d'in ta kama jikin sa har wandon pencil ne, ya saka cufflinks nashi masu diamond royal silver stone kafar shi na sanye da black cover shoe, wayar shi ya janyo dake saman bedside drawar layin Ashad ya fara kira ya mashi kusan 3 miss call ba'a dauka ba d'a siriri tsaki ya saki yana kokarin daukar breafcase din shi karaf suka had'a ido da Nihal wadda ke sanye cikin wata gwan blue dai-dai gwiwa santala-santala kafafuwan ta a bayane kallo daya zaka masu kasan kafafun masu taushi ne tun daga kafafuwan ta Sultan ya fara binta da kallo har ya sauke su kan fuskar Nihal, kallan gashin ta dake baje a kafad'ar ta se shining yake dauke kai Sultan yayi da sauri tare daukar briefcase din shi ya fice, tabe baki Nihal tayi tana cewa mutum kullun cikin bakin rai kamar fir'auna mtsww. Daga labile window parlour shi Ashad yayi yana leka Sultan dake mikawa Alex briefcase d'in shi tsaki Ashad ya saki tare da cewa, "shashasha se ka gane kuran ka" wayar shi dake saman kujera ya dauka yana sakin murmush mugun ta number ya shiga kira bugu daya aka dauka tare da Sallama murmushi Ashad ya saki tare da cewa, "Nas ina so ka canza alururin da za'ayi ma Alhaji Adamu kafin a shigar da shi theater ka tabata kayi min aiki da kyau" "toh" Nas yace tare da kashe wayar yana kashewa ya wuce office d'in Sultan a hankali ya murd'a kofar ya shiga ya canza alururi ya fito da sauri. Jin an murd'a kofa ne yasa Ashad shigewa d'aki da sauri ya shige cikin blanket yana rawar d'ari, ganin ba kowa parlour yasa Sultan murd'a handle din kofar dakin Ashad saman bed ya hango shi kudidine da Sauri sultan ya karaso bakin gadan yana cewa , "Ashad! Tare da zame blanket din jiki shi bud'e ido Ashad yayi a hankali kamar Wanda yayi sati yana ciwo yana kallan Sultan ciki honey voice d'in sultan yace, "mi ke damu ka Ashad ? tunda safe nake kiran layin ka baka dauka ba, kuma kasan yau muna da operation me mahimmanci, kuma kasan muna bukatar ka a wajan," ya ida zancan yana tsare Ashad da ido jum kad'a Ashad yayi tare da shake murya yace, "yayana bana jin dad'i fever ke damuna amma bari na tashi mu tafi" "No kayi zaman ka amma ka daina bari ciwo na rufe ka haka" Sultan ya ida zancan yana tab'a goshin Ashad shigowa da bawan Ashad yayi da tray d'in abincin ne yasa Sultan mekewa ya amshi tray d'in ya daura saman ciyar shi yana cewa, 'oya taso ka ci abincin nasan halin ka idan kana ciwo baka san cin abincin" langwabe kai Ashad yayi yana maikara jin dad'i yadda Sultan ya yadda cewa ciwo yake Sannan yace, "bana jin yunwa" ya fad'a a takaice had'e rai Sultan yayi ba alamar wasa ya fara feeding Ashad yana amsa se da tabatar ya koshi sannan ya aje tray din yana cewa, "Allah ya baka lafiya bros" sannan sultan ya mashi pack a goshi, daga kai Ashad yayi yana wani langwabe wa sannan Sultan ya fice yana fita Ashad ya fushe da dariya tare da bud'e drawer ya Ciro wasu takadu ya janyo tray ya kuna masu light wuta ta kama ya kona takadun duka yana murmushi yana cewa a fili "la,la, la yau wani ze fara zaman gidan yari" Ashad ya ida zancan tare da saki dariya ya wani kwata saman bed yana karkad'a kafa. Sultan na isa office canza kayan shi yayi zuwa na theater dakin da aka kwantar da Alhaji Adamu ya shiga tare da sis Naja na dauke da tray din alura da za'a mashi, ana mashi alura bacci ya kwashe shi cikin d'an kankanin lokaci sannan Ammar da amir da Nas suka canza mashi gado direct aka wuce da shi theater room iyallan shi na waje suna faman zarya. cikin natsuwa da kwarewa suke aikin se da suka kamala aiki sultan na dinke shi sannan Alhaji Adamu ya fara wata jijiga ga jini na fito mashi ta baki da ido rud'ewa Sultan yayi yana cewa "oh my god wani ya canza Alura da akayi mashi" da sauri suka fara kokorin cire injinan dake jiki Alhaji Adamu ana canza wasu, zufa ce ta shiga karyowa Sultan, jin shuru numfashi Alhaji adamu ya dauke wuta yasa suka zaro ido lokaci daya suna kallan Sultan, Nas ne ya tab'e baki yana cewa, "Ashe dama abinda kuke aikawa a asibitin nan kenan duk Wanda ya zo be da lafiya se Ku karasashi, toh wallahi hukuma se ta sani cikin Ku ba Wanda yasan aikin shi" Nas ya ida zancan yana taba wuyan Alhaji Adamu Wanda ya riga da ya zama gawa, dago jajayan idanuwan shi Sultan yayi tare da cin kwala Nas yana cewa, "How dare you zaka gaya min magana Nas kasan dai na fika sanin abinda nake, kasan bana abu up head, Nas kadda ka kuskara ka kara fad'i min maganar banza if not" Sultan ya ida zancan tare da yin wurgi da Nas rike shi Ammar yayi yana cewa, " Wannan abun ba abin tadda hankali bane akwai sheda gwabti, ta yadda da aikin mu, kuma muna da files na sheda alura da aka mashi" Nas yace, "Ai dole kuke cewa akwai su tunda kusan zaku kashe shi wani irin kukan kura Sultan yayi ze kai ma Nas cafka Ammar ya ririke shi, shi da Amir safar hannu shi sultan ya cire yana maida numfashi da Sauri ya fita daga theater room, iyallan Alhaji Adamu na ganin shi sukayi cha a kan shi Sister Naja ce ta shiga basu hakuri a kan su jira insha Allah lafiya ze fito zama su kayi saman kujera suna fata ayi aikin a sa'a, Sultan na shiga office d'in drawer ya bud'e yana neman takudun daya aje suka ce daukar ni rikicewa Sultan yayi yana bud'e drawer's din office d'in shi, se daya birkita komai na office d'in, Jirin da ya fara ganine yasasa dafa table din office din shi yana furta "innalillahi wa'inna'ilaihiraju'um" wata irin zufa na karyo mashi had'a hannu washi biyu yayi a fuska yana cewa, "ya Allah! ina na aje takadun Allah ka rufa min Asirri" Sultan ya ida zancan yana sauke wahalala ajiyar zuciya, murda kofar da kayine yasa Sultan dago da jajayan idanuwan shi, ya sauke su kan Nas shi da yan sanda ya rik'e kugu yana cewa, "gashi nan a wuce da shi, irin sune ke kawo baraka a kasa dama da wannan aika-aika yake tara dukiyar shi" mikewa Sultan yayi yana bin Nas da ido har yan sanda suka karaso duk Sultan be cikin natsuwa hakan be hana shi nuna mulki da isa ba gyara suit din sultan yayi yace, "kar Wanda ya tabani cikin Ku ni da kai na zan mika kai na" sannan yan sanda suka tasa Sultan gaban iyallan Adamu kuwa tuni labari ya Isar masu kuka suke suna jerawa Sultan Allah ya isa har suna cewa saida sasan jiki mutane yakeyi tare da tsinewa asibitin kafin kace mi yan'jarida sun halara abin nema ya samu Ammar duk a rude ya karaso gaban Sultan tare da ce mashi ina takudun suke cikin calm tune sultan yace, "nima ban sani ba Amma ka bincika a gida" Sultan yayi kallan tausayi Allah sarki Shari kayan gwalba sannan suka tura Sultan cikin mota, ba a wuce da Sultan ko ina ba se wani hotel cikin daki aka sashi Wanda DPO Bilal ya bada umarnin a tsare shi a daki tun daga wayar shi agogo shi duka aka amshe su aka kule dakin police na baki kofa, zagaye daki Sultan yake yana mamaki Waze mashi wannan Abu waya zancan mashi alura waya sace mashi documents bashi da amsar tanbayar shi, dafa goshin shi Sultan yayi saboda tsabar juyawar da kwakwalwar shi keyi yanzu idan maimartaba ya ji labari me ze dauka Ammi wani hali zata Shiga ita da mom, kwantawa yayi saman kujera dakin ya lumshe ido yana tunanin wace rayuwa zeyi a gidan yari wannan wace irin musiba ce, murd'a kofar da akayi ne yasa Sultan mikewa da sauri DPO Bilal ne ya shigo daki komawa Sultan yayi ya zauna idanuwan shi a lumshe DPO Bilal yace, cikin calm tune, "Sultan! bud'e idanuwan shi Sultan yayi tare da zubawa DPO na mujiya DPO ya cigaba da cewa, "Sultan Allah ya taimaka anbani belinka amma hukuma ta ce tsare ka 24 hour ba shiga ba fita se ka kawo lawyer, ko kuma ka bada takarda sa hannun gwabtani akan Asibitin ka sannan zaka wanke zargin da akewa asibitin ka, nasan cewa ba da gangan kayi haka ba, amma se munyi bincike zamu gane haka sannan hukuma tasa a a dakatar da Asibitin ka har se gaskiya ta fito an hana yad'a labaran ka a kafafan yad'a labarai" DPO ya ida zancan tare mikawa Sultan wasu files a zabure Sultan ya mike yana cewa, "No, no, no can't be! wannan shari akayi ma Asibiti wannan karya ne Sultan ya ida zancan jiki shi na rawa saboda abin da ya gani, kafad'ar shi Bilal ya dafa yana cewa, "Sultan files d'in nan office d'in ka aka dauko su, kuma daya daga cikin ma'aikanta shi ya bada sannan ya sheda mana ba yau aka fara safara miyagun kwayoyi a Asibitin ka ba, da kashe marasa lafiya tare da cazasu kudi masu dunbin yawa saboda karfin ikwan ka, hakan na nuna cewa baku san aikin ku ba kuke yiwa mutane" Sultan Wanda ya hau kololiwa wajan hawa idanuwan shi sunyi jawur kamar garwashe kwala DPO yaci yana haki kamar Wanda yayi tsere yana cewa, "Bilal kasan kuni wanene kasan wanene Sultan tunda ba yau ba, ina so ka bani guri tun ina ganin sauran mutunci ka a ido na ka fita Idan ba haka" Sultan ya ida zancan tare da saki wuya DPO Bilal tare da watsawa Bilal takadun hannu shi a fuska tari Bilal ya shiga yi yana shafa wuyan shi yana magana da kyar yana cewa, "Sultan mi ya...!! Daga mashi hannu Sultan yayi yana cewa, "tun ina ganin ka a matsayin aboki na yanzu kada kasa na fara ganin ka a matsayin makiyi na kuyi duk bincikyan da zakuyi a shirye nake dana je gidan yarin na amshi duk wani horo da za'a min" Sultan ya ida zancan tare da rintsi idanuwan shi DPO Bilal ya fice da sauri daga dakin. A harabar gida Ammar yayi parking shida Alex suka fito da Sauri part d'in Sultan suka wuce, nihal dake ta faman goge dining area Wanda yanzu ta daina yadda bayi na gyara part d'in sultan saboda wasu abubuwa data fuskan ta a gidan musanman yadda taga mom nanuna mata cewa kara tayi ma Sultan komi da kanta, duk da bata San shi amma za tayi hakan saboda Ammi da mahaifiyar shi zata faranta masu, murd'a kofar da akayi ne yasa Nihal dagowa da sauri tunanin ta Nazili ce ta zo mata rashin mutunci data saba, aje tsuman hannu ta Nihal tayi tare da cewa, "yaya! tana kallan shi ji tayi kawai gaban ta na tsanata fad'uwa masanman yanayin data ga Ammar da Alex cike da tuhuma take kallan su sannan tace, "ina sultan? shuru Ammar yayi tare da tunanin ya fad'a mata ko karya fad'a mata Amma ya kamata ace ko kowa be sani ba matar shi ta sani a hankali ya tako har gaban Nihal Wanda ta tsare shi da ido tana kallan shi tana kallan bayan shi, cikin alamar lalashi Ammar ya kwashe duk abinda ya faru ya fadawa Nihal waro ido tayi tare da fashewa da kuka tana cewa, "Nasan Sultan ba zeyi haka ba Dan Allah yaya kasa a saki Sultan ya dawo gida ko dan farin cikin Ammi" Nihal ta ida zancan tana mai kara tsana ta kuka Wanda ita kanta bata San dalili damuwar ta kai ba, koma dai minene ta San Shari akewa Sultan ba ze aika haka ba, zauna da ita saman kujera Ammar yayi yana faman lalashi tare da cewa tayi shuru karta bari kowa ya sani "insha Allah yau Sultan a gida ze kwana kin ji Nihal" baiwar Allah Nihal duk ta rud'e, bedroom suka shige suka fara fido takadun Sultan suna bincikawa Nihal itama shiga tayi ana dubawa da ita hankali duk a tashe birki ta drawer's din dakin sukayi suna bincika kowani file. "Aikin ka yayi kyau Nas zan baka kudin ka cas sannan maganar cigaba da karatun ka a Dubai na gama shirya komai, gobe flight din ka ze tashi" wani irin dadi ne ya lulub'e Nas Gimbiya jalili dake gefe duniya tayi mata fes kamar an zuba mata ruwan sanyi haka suka riga hira su tare da kula wani makircin tunda labari yazo masu a kan inda aka tsare sultan. Haka Sultan ya rika zama cikin daki abin duniya ya isheshi da mamaki irin makirci da ake kula mashi Wanda har kanshi ke daurewa shigo mashi da lunch da akayi ne ya sasa juyowa yana kallan police d'in har ya aje mashi abinci ya fita, kallan abinci Sultan yayi tare da kauda kai ya shige toilet ya dauro alwala ya dad'e yana saloli Allah ya kawo mashi mafita, yana idar da sallah ya mike, makakin da yafara ji a wuyan shine yasasa dafe wuyan shi numfashin shi na fita da kyar ba komai bane ya janyo haka se gubar da aka sa mashi ta cikin AC ta fara aiki jiri Sultan ya fara ganin da kyar ya karasa bakin kofa yana dukan kofar yana cire necktie d'in shi saboda yadda wuyan shi ya mashi yana fida numfashi sama-sama duka kofar yake Amma ba Wanda ya bud'e har jini ya fara bi mashi ta hanci yana wani wahalalan tari take a nan ya sulale..... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWAN*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the among the rest```) *Page: 81_82* Daya daga cikin security da aka bari bakin kofa ne Bangis ya bud'e kofa da sauri toshe hanci shi yayi sakwamakwan warin wani gas na poising da yake tashi a dakin mara dadi, a rud'e ya karaso gaban Sultan Wanda ya sume wayar shi ya Ciro da sauri ya fara kiran DPO bilal, kafi kace mi ambulance har ta iso daukar Sultan akayi cak tare da daura shi saman gadan marasa lafiya aka manna mashi oxygen da duk wani taimakwan gaggawa tare da cire mashi bottel din rigar shi, DPO Bilal duk ya rud'e wayar shi ya ciro ya fara kiran Ammar da Maimartaba, da sauri aka wuce da Sultan cikin Ambulance tare da tsanata tsaro a hotel din yan'sanda na bincike. Wani file Nihal ta dauko da sauri tace, "yaya ina tunanin kamar wannan kuke nema! da sauri Ammar ya taso ya amshi files din hannun Nihal bud'ewa ya shigayi wani irin murmushi ya saki yana cewa, "masha Allah, Allah ya so guda biyu ne" da sauri shima Alex ya kara so yana dubawa ringing d'in wayar ammar ne ya katse masu tunani ciro wayar yayi daga aljihu tare da karawa a kunne abinda kunnan shi ya jine yasasa sakin wayar hannu shi a kasa, Alex ne yasa hannu ya dauka tare da karawa kunne da kyar ya iya furta "gamu nan zuwa Asibiti ! Nihal dake tsaye kamar gunki gaban ta na tsanata fad'uwa kamar zuciyar ta zata fasa kirjin ta da kyar ta iya cewa, "karku ce min wani abu ya samu Sultan Dan Allah" ta ida zancan tana saki kuka ta durkushe, kukan Nihal ne ya dawo da Ammar daga duniyar tunani da kyar ya iya saita kan shi ya dago da Nihal suna facing juna yace, "Haba Nihal ba kuka ya kamata kiyi ba addu'ar ki Sultan yake bukata kin ji Nihal" daga kai Nihal tayi tana goge hawayan fuskar ta, Ammar yace ma Alex , "mu wuce Asibiti" Nihal ce tayi saura tara numfashin Ammar da da cewa, "zan biku" shuru Ammar yayi tare da jin tausayin Nihal ji yadda ta damu da Sultan lokaci daya duk da ba wani san juna suke Allah sarki Nihal kina ganin rayuwa Ammar ya fada a zuciyar shi, veil d'in ta Nihal ta dauka suka fice. Gabaki daya su mom da Gimbiya jalila suna fadda Maimartaba sunayin lunch, Ammi ce ta aje spoon d'in hannun ta tare da cewa, " ina Nihal da Sultan yau tun safe ban gan su ba" ta ida zancan tana kallan mom, gimbiya jalila da Ashad kallan juna sukayi suna dariya kasa-kasa suna cin abinci, maimartaba ne yace, "ki san yanayin aiki su ba zama, kana zaune za'a kira ka," cikin sigar munafirci Gimbiya jalila tace, "Ai Sultan na kokari sosai" Ammi tace, "kuma har da Nihal din hankali ya kasa kwanciya ne, na saba duk safiya tare muke breakfast yau Nihal ko leke haka shima Sultan din" basmal ce ta katse masu zance da cewa, "tunda kukaga haka aunty Nihal bata nan hakan ya nuna suna can suna shan soyayya su, kunsan dai Nihal bata zama ita kadai se tare da yayana" ta ida zancan tana murmushi ja mata kunne mom tayi tana cewa, "ke ko Allah ya shirye ki" yar kara ta saki tana sosa kunnan ta tana cewa, "kai mom daga fadi gaskiya" ringing d'in wayar maimartaba ne ya katse masu tunanin shuru sukayi har maimartaba ya dau wayar Gimbiya jalila da Ashad se kallan juna suke ta kasan ido suna fatan Allah yasa mutuwa Sultan yayi, mikewa maimartaba yayi yana furta "what! Da karfi, "karka fad'in min cewa wani abu ya sami Sultan d'ina a wani asibiti aka kwatar dashi? A kan wani dalili za'a daure min d'a ba tare da sanina ba, what nonsense is this wallahi duk abinda ya sami d'ana kotuce zata raba ni da Ku", Ammi dake gefe maimartaba numfashin ta ne ya fara sama-sama yana neman daukewa saboda kalaman maimartaba sun fara juya mata kwakwalwa Gimbiya jalila da Ashad ko zuciyar su fes se fatan Allah yasa ya karasa daga can ayi can, mom mutuwar zaune tayi ita da Basmal Gimbiya jalila ce ta kallo Ammi ta tafi luuu sumamiya karasawa tayi gaba Ammi tana kiran suna da karfi tana cewa, "Ammi ! Ammi ! tana jijiga ta, rud'ewa maimartaba yayi zafi biyu ya had'e mashi daukar Ammi akayi aka wuce da ita bedroom aka kira Dr Amir ya zo ya dubata, kuka mom kawai take shekawa Basmal na lalashin ta Gimbiya jalila kukan gulma take Ashad na lalashi ta kamar gaske bayan an gama duba Ammi maimartaba yace, "su wuce asibiti suga wani hali Sultan yake ciki" Gimbiya jalila tayi karaf tace, "Ai ba'a bar Ammi ita kadai ba nida Ashad ma kula da ita" maimartaba yayi alamar ya gamsu da maganar ta hijab mom kawai ta zura Basmal ta yafa veil d'in ta direct parking lot suka wuce, mota su ka shiga bala driver ya ja su se Asibiti A harabar asibiti Ammar yayi parking motar shi a parking lot suka fito kai tsaye Asibiti suka shige DPO Bilal dake zarya bakin emergency ne ya dago da jajayan idanuwan shi ganin su Ammar yasasa karasawa da sauri ya rungume Ammar tare da sakin kuka, jikin Ammar ne yayi sanyi, Nihal da sauri ta karasa baki kofar emergency tana leka sultan ta cikin glass d'in kofar yadda likitoci sukayi cha akan shi tausayi shi ya lulube Nihal tare da saki kuka wai me yasa duk Wanda ta sani se ta rasashi wannan wace irin rayuwa ce, ba komai ke sata kuka ba, se tunawa da mutuwar umma da Abba yau mutuwar su ta dawo mata sabuwa musanma yadda daga sultan na shan jiki zamewa tayi bakin kofa tana mai cigaba da kuka, ciki kuka Bilal yake cewa, "yanzu da wani ido zan kalli Sultan na kawo shi waje na keb'e dan kar a samu matsala se gashi an samu, na San Sultan ze kalle ni a matsayin Wanda aka had'a baki da shi dan a cutar da shi" Bilal ya ida zancan yana sheshekar kuka yana mai cigaba da cewa, "wallahi ban san an sa poinsin cikin AC ba, Dana sani ba zan kai sultan ba," shuru Ammar yayi yana shafa bayan Bilal alamar lalashi tare da zauna da Bilal saman chair din dake harabar wajan yana cewa, "be kamata kana tunanin Sultan ze ma wannan kallan ba, ya san ko kai wanene," Ammar be ida rufe bakin shi ba aka fito da Sultan daga emergency mikewa sukayi, direct waiting room aka wuce da Sultan hancin shi na manne da oxygen da Karin jini da ake mashi, da sauri su Ammar suka bi bayan doctor zuwa office se da suka samu waje suka zauna sannan suka shiga tanbayar shi ya jiki Sultan, gyara zaman glass d'in shi Doctor nafi'u yayi tare da cewa, "ya kamata Ku bashi kulawa sosai da tsaro saboda saura kad'an poisin din nan ya mashi ila kuma matsala da ake samu irin shi bin jini yake, yanzu baza mu gane ciwo ya sake shi ba se ya tashi amma ze dad'e yana fama da wahala numfashi d'an kankanin Abu yana iya sawa numfashin shi ya dauke saboda huhun shi ya matse, idan zaku bi shawara ta a fida shi waje a mashi checkup bayan wata daya ! sannan doctor yayi yan rubuce-rubuce ya mikawa Ammar paper godiya suka mashi DPO ya wuce bakin aikin shi saboda har yanzu yana kan bincikyan dalili da ya kawo poisin ciki AC, direct dakin da aka kwantar da Sultan ya wuce, zaune ya sami Nihal saman kujera tana facing gadan da Sultan ke kwance mikewa Nihal tayi tana cewa, "mi doctor yace maku" kakaro murmushi Ammar yayi yace, "jiki da sauki karki wani damu kanki kinji" daga kai Nihal tayi tare da furta "Alhamdulillah! shigowar su mom ne ya katsa masu tunani, murmushi Nihal ta saki tare da karasawa wajan mom da sauri kama hannun ta mom tayi ta zauna da ita tana me kalla sultan tace, "daughter mi yasa Baku fad'a mana halin da kuke ciki ba,? shuru Nihal tayi tana wasa da yan yatsun hannun ta tana cewa, "bamasu mu tada maku hankali ne shiyasa" Nihal da ida zancan a raunane shafa kumatunta mom tayi tace, "daughter kunyi tunanin mai kyau, amma nan gaba karku kara boye mana wani abu" daga kai Nihal tayi, maimartaba da Ammar fita waje sukayi Ammar ya fad'a mashi abinda doctor yace shuru yayi can kuma yace, "Allah ya ba Sultan lafiya" "Amin! Ammar yace yana rufe bakin shi waziri da Adda suka karaso waziri ya mikawa maimartaba hannu suka gaisa yace, "inane dakin daka kwantar Sultan? maimartaba yace, "mu karasa tare muma ai yanzu zamu koma" suka shige cikin. Bayan sun gama duba sultan har a lokaci be tashi ba maimartaba yace ya kamata su koma gida tunda jikin da sauki se a bar matar shi da kula da shi mom tayi na'am da zancan shi haka suka baro Asibiti akan cewa za'a aiko Basmal da dinner. Zagaye parlour Ashad yake yana cewa, "ban so sultan ya farfado ba wannan mutumin Allah ya mashi taurin rai," Ashad ya ida zancan yana wurgi da cup din glass dake hannun shi yana mai cigaba da cewa, "Momi ni fa ban k'i na aika har asibitin a kashe shi ba, amma wannan banzan yakubu yana fad'a min cewa akwai security a kofar dakin shi, ni wannan labari be min dadi ba" Ashad ya ida zancan yana zama saman kujera, Gimbiya jalila ta numfasa tace, "Ni bama wannan ya dameni ba yanzu idan aka gane dasa hannu ka ya zamuyi,? Wata iri dariya Ashad ya saki tare da cewa, "Momi kenan ke kika haife ni Amma har yanzu kin kasa sanin wanene a salin Ashad, duk abinda zanyi ina anfani da kwakwalwata ina anfani da takuna ! babu Wanda ze gane da sa hannu na of coz ina gida bani da lafiya sanda Nas ya canza alururi ba Wanda ya ganshi, kuma tare da shi akayi operation din kuma yanzu haka baya kasa ya tafi karo karatu ta karkashin gwabnati, document d'in dana sace tuntuni na kona, san da naje Dubai lokaci nayi document din safara kwayoyi da sunan Sultan sannan na koyi singing din shi nayi na aje mashi a office ba Wanda ya sani" ya ida zancan yana saki dariya "amma ki san wani Abu sultan nada wayau komi zeyi biyu yake ajewa nasan tabas yana da wasu documents din aje, dole sultan ya mutum momi na tsane shi" ya ida zancan yana furzar da iska me zafi. Nazili ce ta shigo part din Ammi tana bin Gimbiya jalila da Ashad da kallo kasancewar suna part d'in Ammi a cewar suna kula da ita har zata Shiga dakin taci birki tana cewa, "lafiya na ganku yau a nan ina sauran mutanan gidan? Nazili ta fad'a tana tsare su da ido, lagwabe kai Gimbiya jalila tayi ta koma kala tausayi tare da kwashe duk abinda ya faru ta fad'awa Nazili bud'e baki Nazili tayi tace, "ya Allah ! da yaushe duk wannan Abu ya faru? juyuwo tayi da niyar ta wuce asibiti ganin sun mom sun shigo ya sata cewa, "kun dawo ina sultan ? Nazili ta fad'a tana leka bayan su Mom, mom tace, "Sultan na Asibiti,! "Shine ba Wanda ya zauna da shi? Nazili ta ida zancan a raunane, maimartaba ne ya katse mata zance da cewa, "daughter dawo karki damu Sultan na tare da wife na shi nasan zata ba shi kulawa sosai, shiyasa nace a basu space" tsaye Nazili tayi tana had'iye wani kulutun bakin ciki tana kallan maimartaba wato shima fada mata yake wannan almajira ta fita dacewa ta kula da Sultan ba ita ba wannan jahila mima ta sani da za'a barta da sultan ganin tayi shuru yasa maimartaba hugging nata yana shafa bayan ta tunanin shi shock ne ya kamata be san tsanar Nihal ya kara dasa mata ba a hankali yake cewa , "daughter kirki damu insha Allah sultan ze warware" daga kai Nazili tayi tana wani sunne kai sannan ta ja kafafuwanta ta shige bedroom d'in Ammi Gimbiya jalila ko da Ashad ta ciki na ciki haka kowa ya wuce part nashi yana jimami shiko maimartaba sawa yayi a tsanata bincike a gano suwa ke da sa hannu. ******************************* Sallama da akeyi ne yasa gwoggo gyara dankwali dake kanta cike da fargaba ta amsa ganin su aunty Aishe ne se da tasha ruwan jinin jikin ta had'e rai tayi tana cewa, "Ku shigo Ku shigo! aunty Aisha se leke take taga ta ina Nihal zata fito ita da baba sani da Ahmad dan baba sani, dake bayan su har suka karasa dakin baki suka zauna debo masu ruwa a randa gwoggo tayi tana mai cewa, "sannu Ku da zuwa ya hanya? "Alhamdulillah gwoggo" aunty Aisha ta fad'a tana mai cigaba da cewa, "se kika ganmu kwatsam ba sanarwa" gaban gwoggo ne ya kara yankewa ya fad'i tana raraba ido tace, "aiko dai" aunty Aisha ta katse mata tunanin da cewa, "Ina Nihal d'in tun dazu nake ta faman raraba ido ko zan ganta ko tana makaranta ne? aunty Aisha ta ida zancan tana tsare gwoggo da ido, had'e rai gwoggo tayi tare da zayana masu karya da gaskiya ta ida zancan da cewa, "yau kimanin shekara daya kenan raban dana sa Nihal a idanuwa na, ta fitsare kafafuwanta ta shiga duniya," aunty Aisha ce ta mike tsaye dafe da kirjin ta tana cewa, "wallahi karya ne Nihal bazata taba aikata haka ba, se dai ki ce kun musguna mata har ta guda na san d'iyar hansatu baza ta taba aika ta haka ba, wannan shari ne wallahi" mikewa gwoggo tayi tsaye tana kallan aunty Aisha shekeke tace, "A haye Ashe har wata sheda Nihal zaki iyayi, to Alhamdulillah a hannu na ta tashi Nina santa tunda ko uwar tata tun daga wayan Nihal har ta mutu a nad'e take, bale ke uwar gulma da kicifi zaki gayamin kabali da ba'adi , zanyiwa Nihal Shari ne ko mi? Idan baki sani ba yau kin sani watsatsace" dadagewa aunty Aisha tayi ta dauke gwoggo da mari tana huci baba sani ya rike aunty Aisha cike da masifa da bala'i aunty Aisha tace, "ban taba tunanin Sharin naku da muguntar ku ta kai haka ba wallahi ku dai kunji kunya insha Allah se kunga sakaya Allah" gwoggo dake tsaye ce kamar gunki hannu ta dafe da kumatu, Sara ta katse masu tunanin da cewa, "An fad'a Nihal din ba yawan banza tatafi ba" Sara dake bakin kofa ta fad'a tana mai daga hannu ta dauke aunty Aisha da mari tace, "uwa ta ba asarki bace," Ahmad dake tsaye ya dauke Sara da mari har guda uku yace, "banza k'azama har kin isa ki taba min fuskar uwa na tsaya ina kallan ki" Ahmad ya ida zancan tare da yin kukan kura kan Sara tana zunduma ihu saboda taurari da take gani gashi Ahmad ya bita da duka baba sani ne ya dauke shi da mari yana cewa, "Ashe Ahmad baka da hankali se ka biyewa mata suna shashanci idan baza ka bada hakuri ba ai baka hura wutar ba" Ahmad dake fama huci yana aikawa sara mugun kallo baffa da shigowar shi yanzu yace, "to tsoho munafiki ! a gaban ka an tasa min iyalli ana duka sannan saboda tsabar rashin mutunci a cikin gida na" baffa ya ida zancan yana cin kwala baba sani yana huci yace, "Nihal din diyar wani shege ce cikin ku diyar kanina ce, za'a zumin har gida ana tanbaya ta idan ma kwad'a ta nayi na cinye ai ba abinda ze dame Ku bale Ku karankad'a miya danki uwa! ina kuke sanda ita hansatu take ciwo uban wani ya zo cikin ku nemanta? oh wato se yanzu dana gama gina yarinya ta zabin yawo banza saboda gadan gida Ku ne dan mu zuri'armu babu wace tayi yawan daduro shine yanzu zaku zo min gida da zancan banza" aunty Aisha ta bud'e baki zata mulmulawa baffa ashar baba sani ya aika mata wani irin kallo taja baki ta tayi shuru tana maida numfashi gwoggo dake gefe tace, "fada masu dai malam tasha a nono ne" ta ida zancan tana gyara tsayuwar zanin ta tana aikawa aunty Aisha da harara sannan baffa yace, "ku tatara ina ku ina ku ku fice min a gida tun kafi na nuna maku kuni wanene" ya ida zancan yana jera masu takalma su aunty Aisha tace, "wallahi talahi kotuce zata rabu mu daku se kun fito mana da Nihal duk Inda ta shiga" aunty Aisha ta ida zancan tana kuka jan hannun ta baba sani yayi suka fice har suka shiga mota Aunty Aisha na kuka tana cewa, "duk wannan Abu da ya faru har da laifin mu yaya sani mun manta da Nihal har na tsawan shekara daya tunda yayata rasu basu sake dawowa ba, wannan Abu da mi yayi kama wallahi na san Nihal baza ta taba aika ta abinda suke fad'i ba" Ahmad dake driving yace, "Small mom kiyi hakuri ki daina zubar da hawayan ki, insha Allah duk idan take za'a ganta kuma komin daran dadewa zata nememo, su kuma su je Allah na sane da su" Ahmad ya ida zancan yana mai cigaba da driving share hawayan ta Aunty Aisha tayi tana cewa, "dole nayi kuka Ahmad nasan cewa Nihal taga rayuwa tanimu mugun mutum ne Allah seya sakawa Nihal" baba sani yace, " 'yanzu dai mu koma gida a sanarwa hukuma yan'sanda amma karki fada wa khabir halin da ake ciki kin san zafin zuciyar shi Allah dai ya kyauta yasa hannun na gari ta fada gabaki daya suka amsa da amin. ***** A hankali sultan ke bud'e lumsasun idanuwan shi juyawar da dakin ke mashi ne ya sasa kara lumshe idanuwan shi yana maida numfashi shi da kyar, linke dadumar hannu ta Nihal tayi ta aje tare leka fuskar Sultan a zuciyar ta tana cewa wannan mutumin Allah ya zuba mashi kyau kamar shi yayi kan shi, amma a haka se ka rantse be da masifa, ganin hannu Sultan na motsawa a hankali yasa Nihal saki murmushi tana me kara kallan fuskar shi tana addu'ar Allah yasa ya bud'e idanuwan shi, a hankali sultan ya bud'e idanuwan shi ya sauke su kan Nihal tsare ta yayi da ido yana kallo itama kallan shi take tana dariya mai kuka da sauri ta fita domin kira doctor ko 5 minutes Nihal ba tayi ba se gata ta dawo da doctor duduba sultan yayi tare da cire mashi a Karin jinin da ake mashi shi da oxygen din hanci shi, sultan bin su kawai yake da ido yana lumshe su, se da doctor ya gama komai sannan ya juyo yana kallan Nihal yace, "ki had'a mashi tea me kauri yasha banda bread" "Toh" Nihal tace sannan doctor ya fita a hankali Nihal ta karaso bakin bed d'in tare da yin kokarin jigina da Sultan lumshe ido sultan yayi yana shakar kamshi turaran Nihal dake mamaye mashi hanci veil din kanta ne ya zame gashin kanta ya zubo mashi a fuska ajiyar zuciya sultan ya saki tare da ware idanuwan shi ya sauke su kan Nihal dake juyowa suna facing juna dauke kai Nihal tayi zata mike veil din kanta ya tad'iye ta fadawa tayi luuu sama fadadan kirji sultan rintse ido Nihal tayi tare da cije hakora tayi loma a kirji Sultan sun dau lokaci me tsawo a haka, lumshe ido sultan yayi yana shakar kamshin Nihal tare da jin saukar numfashi Nihal a chest din shi a hankali Nihal ta dago kamar Mara gaskiya tana gyara gashin kanta cije hakora Nihal tayi tare da mikewa zunbur ta dauki veil din ta jikin ta se rawa yake ciki sarkewar harshe tace, "kayi hakuri dan Allah ba da gangan na fado...!!! Nihal tayi shuru saboda tsare ta da ido da Sultan yayi ciki rawar jiki Nihal ta fara had'a mashi tea hannun ta se kyarma yake Sultan ko bin ta kawai da ido yake har ta gama hada tea din ta mika mashi wajan amsa ya had'a da hannun ta me laushi yana mai kara tsare ta da ido ita d'inma kallan shi take, tiririn tea din ne ya fara kona Nihal yar kara ta saki tana cewa, "aushh hannu na ! rike hannun ta Sultan yayi yana hura mata da iskar bakin shi me sanyi tsare Sultan da ido tayi tana kallan red lips din shi ritse ido Nihal tayi tana cewa a zuciyar ta, ya Allah jin an murda kofa yasa Nihal fisge hannun tan kokarin tashi Basmal ce da Ammar suka shigo Basmal tace, "aunty na da sauri Nihal ta shige toilet Basmal ta kyalkyale da dariya tana kallan Ammar tana dariya kasa-kasa saboda yadda Sultan ya had'e rai ta aje basket din hannu ta ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWAN*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the among the rest```) *Page: 83_84* Kwana uku sultan ya kwashe a asibiti yana jinya duk wata kulawa Nihal ke bashi ita, har mamaki irin dawainiyar da take mashi yake hakan se yasa ya dan saki jiki da Nihal har ta dan fara bashi tausayi, bayan an sallamo su hukuma ta wanke sultan daga zargin da ake mashi sannan har yanzu tana kan bincikyan ta, Gimbiya jalila da Ashad ko kamar suyi hauka dan baki ciki dan sun so ace sultan ya mutu a asibiti. DPO Bilal haka ya rinka ba Sultan hakuri a kan abinda ya faru sultan gwada mashi yayi kwata-kwata be damu ba saboda ko so daya be kawo shi a rai ba, dan yafi zargi na kusa da shi ne ke mashi zagwan kasa wanda har yau ya kasa tabatar da zargin shi wannan kenan. Ammar ko bayan sultan ya warware ya samu waziri a kan maganar shi da Basmal sosai waziri ya ji dadi shi da Adda musanman Adda wadda kullun addu'a ta kenan yau Allah ya cika mata burin ta, koda waziri yayi ma maimartaba magana yayi na'am sosai ya nuna farin cikin shi kuma dama can ya so a hada shi da Basmal lokaci da za'ayi bikin Sultan se Allah be nufa ba, a haka suka gama maganar su tare da tsaida rana biki nan da wata daya murna wajan Basmal da Ammar ba a magana, Ammar ya so ace ma sati aka sa kamar yadda akayi na sultan of coz ya matso ya ga Basmal a matsayin matar shi. Bangaran karatun Nihal maida hankali take sosai bata wasa ita kanta aunty Biola tana mamaki kokari irin na Nihal komai ta mata nan da nan ta dauka ya zauna mata karatun se san barka haka na addini ba'a barta a baya ba, mom ko ta zage se koya mata girke-girke take kala-kala, kullun kara kyau take da fresh ga wani girma tada kara komai na jikin ta ya canza ya kara girma, ta zama da's da ita, ita kanta tana mamaki kanta kamar ba Nihal yar talla ba. Yauma kamar kullun bayan sun gama breakfast kasancewa yau weekend aunty Biola bata zo lesson ba, Nihal ce ke taya Dara kwashe kayan abinci da aka gama ci a dining suna kaiwa babba kitchen murmushi jakadiya tayi tana cewa, "Gimbiya ko gajiya bakiyi ya kamata ki je ki huta ba'a san Gimbiya da aikin wahala ba" Dara ta ida zancan tana aje warmer a zing, dariya Nihal tayi tana cewa, "wallahi umma idan kina ce min Gimbiya kunya nake ji dan Allah ki bari, damu da ku duk daya muke a wajan Allah bamu da wani banbanci" murmushi Dara tayi tana mai kara yaba natsuwa da hankali irin na Nihal tace, "toh Nihal diyar umma insha Allah zan daina kin ji" murmushi me nuni da farin cikin Nihal tayi tana taya Dara wanke plate din wanke-wanke kusan tare suka gama wanke-wanke sannan suka fara girki da sauran bayin, bud'e fridge Dara tayi ta ciro fruit tasa a boll zata wanke Nihal ta amshe tana cewa, "umma bari na taya ki gyarawa" "Nihal baki gajiya da aiki kwata-kwata ya kamata ki rinka samun Hutu wannan aiki ai se mu" murmushi Nihal tayi tana mai cigaba da wanke fruits, Jakadiya ta cigaba da nunawa sauran ma'aikatan yadda zasuyi su kan su mamakin aikin Nihal suke yadda take sakin jiki da su kamar ba bayin ta ba, bayan Nihal ta gama gyarawa ta yanka tace , "umma na gama" murmushi Dara tayi tace, "madallah da kokari ki kai wa Ammi daga nan karki dawo ki huta , dan na lura so kike sultan ya dau mataki a kaina ina sa mashi Sultana aiki" turo baki Nihal tayi tana cewa, "kai umma kora ta kike ko ! Ta ida zancan tare da daukar boll din ta fita, murmushi jakadiya tayi tare da girgiza kai san Nihal na kara shiga ran ta , duk lokaci da tayi kokari matsawa kanta ta tuna ina ta san fuskar se ta wuni tana fama da ciwo kai a hankali ta furta Allah ka bayana min boyayyan almarin nan. Direct bedroom din Ammi ta shiga koda ta shiga ammi na toilet saman stool ta aje boll din tana kokari fita idanuwan ta suka sauka kan Jakarta wadda ta leka daga karkashi gado wani irin dadi Nihal taji ta dad'e tana neman ta Ashe ammi ce ta aje mata, da sauri Nihal ta duka tare da zaro jakar tana murna bud'e jakar tayi tana duba abubuwan dake cikin ta lokacin yayi dai-dai da fitowar Ammi daga toilet, juyowa Nihal tayi tana murmushi tace, "Ammi dama ke kika aje min jakar nan kai amma na ji dadi, na dauka ta fadi shiyasa ko tanbayar ki bayi ba" murmushi ammi ta saki tana cewa, "Ai naga akwai abubuwa masu mahimmanci shiyasa na aje maki na so na baki tuntuni to mantawa nake" Murmushi Nihal ta kuma saki har fararan hakoran ta na bayana tare da cewa, "Ammi ga fruit ni da kaina na gyara maki idan kin gama ki sha magani ki na cikin drawer" harara Ammi ta makawa Nihal tana cewa, "toh ko shi mijin naki daya aiko ki se naga dama nake sha, wato shi yanzu ya daina matsamin ke kuma kin hau layi to ba zan sha ba na gaji," dariya Nihal tayi tana mai zama kusa da Ammi tace cikin sanyi murya, "Ammi please ki daure ki sha maganin ki kin ji, mu fatan mu ki samu lafiya ba komai ba kin ji kishiyar" Nihal ta ida zancan tana kashewa Ammi ido dundu ammi ta kaiwa Nihal ta kauce tana dariya ta fita da sauri. Part din sultan Nihal ta wuce koda ta shige baya part din bathroom ta shiga ta watsa ruwa sanye da bathrobe ta fito kanta nanade da towel goge jikin ta tayi tare da shafa lotion me kamshi, shiryawa Nihal tayi cikin wata yellow gwon me dogwan hannu rigar na dauke da manyan flowers White, Riga ta mata kyau sosai ta kama jikin ta ga hips d'in ta daya fito d'as da shi na Fulani ta kamar su fasa gaban rigar su fito sakin gashin kanta tayi ya zubo har gadan bayan ta duk da ba wata kwaliya tayi ba tayi kyau sosai kamar ita tayi kanta, har zata fita ta hango wayar Sultan dake saman bedside drawer da sauri tasa hunnu ta dauka tare da bud'e Jakarta ta Ciro takada da aunty Aisha ta rubuta mata number ta Allah yaso wayar ba key, numbers din ta kwafa tare da kira ringing wayar ke tayi ba'a dauka ba Nihal se addu'a take Allah yasa a dauka katsewa tayi sannan ta kuma kira a karu na biyu, fisge wayar da akayi ne yasa Nihal dagowa a razane Sultan ne ya amshe wayar ran shi a had'e tare da karasa a kunne, mijin aunty Aisha dake zaune saman kujera ringing ya isheshi kuma aunty Aisha na kitchen hannu yasa ya dauka tare da karawa a kunne yace "hello! Hello! Sultan dake bin Nihal da kallo ya daskare waje daya yana wasu hadiye-hadiye zuciyar shi na tsanata bugawa yana jin wani irin zafi Wanda be taba jin shi ba, shuru yayi be ce kala ba har mijin aunty Aisha ya gaji da cewa hello ya kashe wayar zame wayar Sultan yayi a kunna shi ya tsare Nihal da ido yana hadiye-hadiye can kasan makoshi sultan yace tare da kankance idanuwan shi, " wanene wanda naji kina waya da shi kuma da waya ta! Sultan ya jefa wa Nihal tanbayar yana mai kara matsowa daf da Nihal, tsare Sultan da ido Nihal tayi tana kallo, tare da furta "wani kuma ni ba wani na kira da wayar ka ba" Nihal ta ida zancan tana kokarin rabawa ta gefan sultan ta wuce, daka mata tsawa sultan yayi yace, "Idan ina magana ba'a juya min baya! tanbayar ki nake wanene shi wannan da kike kira? ya fad'a a taikaice shuru Nihal tayi tana raba ido can kuma ta had'e rai tace, "wani kuma ai na fada ma ba wani na kira ba" Nihal ta ida zancan tana tsare Sultan da ido sultan yace, "Oh ko toh murya wa naji kike nufi? had'e rai Nihal tayi tana kokari rabawa ta gefen sultan ta wuce fisgo ta Sultan yayi ta fad'a saman fafad'e kirjin Sultan taga-taga suka tafi tare da fadawa saman bed rintse ido Nihal tayi tare da ware su saman kyakyawar fuskar Sultan gashin kanta ya rufewa Sultan fuska a hankali sultan ya sa hannu ya matsar da gashin tare da daura idanuwan shi saman fuskar Nihal kasa Nihal tayi da idanuwan ta, duka hannu ta na bisa fafadan kirjin Sultan kafe ta sultan yayi da ido yana bin kyakyawar fuskar Nihal da kallo ba komai ya fi tafiya da imanin Sultan ba se pink lips din ta lumshe ido Sultan yayi wani bakwan Alamari na shigar shi lokaci daya a hankali suke sauke numfashi, sun dau lokaci mai tsawo a haka a hankali sultan ya bud'e jajayan idanuwan shi ya sauke su kan Nihal data ware idanuwan ta, da sauri Nihal ta zame jikin ta zata sauka janyo ta Sultan ya kumayi ya matse ta ajikin shi, yar kara ta saki me cike da shagwaba can kasan makoshi kamar mai rad'a yace, "wanene kika kira da wayata? Sultan ya tsare Nihal da idanuwan shi wayanda suka rine ja shuru Nihal tayi tana mutsu-mutsu dan sultan ya sake ta, wata irin kasala ta sakarwa sultan lokaci daya kara matse ta yayi cikin jiki shi yana shakar kamshin ta me riki tashi, cike da tsiwa Nihal tace, "ka sake ni! ta ida zancan tana turo baki hannu Sultan yasa ya murd'e mata baki ihu Nihal ta saki tare da fashewa da kuka kwata-kwata Sultan be damu da kukan ba yace, "tanbayar ki nake ba kuka na ce kimin ba, dawa kike waya? ya nanata mata tanbayar yana tsare ta da ido ciki kuka Nihal tace, "to ka sake ni se na fada maka" can kasan makoshi sultan yace, "bazan sakeki ba se kin fada min dawa kike waya first" ya ida zancan yana kafe Nihal da ido da kyar Nihal take sauke Numfashi saboda matse ta da Sultan yayi a jikin shi, Nihal tace, "kanwar umma na kira" murmushi rainin hankali Sultan yayi yana matsar da gashin Nihal daya rufe mata fuska yana cewa, "Amma naji murya namiji! kuma sannan bani da labari cewa kina da wasu family" sultan ya ida zancan cikin kakausar murya rintse ido Nihal tayi tare da toshe kunne tana kuka tace, "Ni fa gaskiya na fad'a ma! da kyar Nihal ta fisge jikin ta tare da cewa cikin masifa, "danna ce ni almajira ce ba shi ze baka damar kallo na mara asali da tushe ba kamar yadda kake fadi, idan baka sani ba yau ka sani saboda su na zo birni, ba saboda na zo na zama matar ka ba, har ka samu damar kallo na mara tushe" Nihal ta ida zancan tare da ficewa daga dakin, Shuru Sultan yayi zuciyar shi nayi mashi suya mi yasa ma ze damu dan tana waya da wani wata zuciyar tace saboda matar ka ce, dole ka kare hakkin aure, wayar shi ya janyo tare da kallan number danna number yayi da niyar kira kuma se ya fasa tare da yin wurgi da wayar ya lumshe ido. Aunty Aisha da fitowar ta daga kitchen kenan tana smile mijin ta yace, "honey yanzu nan aka kira ki da new number na dauka shuru ba ayi magana ba" "May be network ne kasan haka suke" "Bana tunanin haka ki sake kira ki ji" to Aunty Aisha tace tare da cigaba da cewa, "my love muje muyi lunch anjima ni da yaya sani zamu je police station kan maganar Nihal dole tanimu ya gane kuran shi na wufintar da Nihal da yayi" karawasa dining sukayi Abubakar na cewa, "Allah dai ya kyauta my dear, wani lokacin se ka rasa ina imanin muta ne yake zuwa Allah ya bayana ta" amin aunty Aisha tace tana feeding din mijin ta jallof din cuscus haka suka rinka maganar Nihal da yadda za su shawo kan alamarin. ********* Basmal da Nihal ne zaune a garden saman grass carpet suna lisafa abubuwan da za'ayi da biki dan har program zasuyi kala-kala, murmushi Basmal tayi tana cewa, "Aunty na! na ji dadi sosai da kike bani sports naki," murmushi Nihal tayi Basmal ta cigaba da cewa tana lumshe ido hannu ta na rike dana Nihal, "Aunty zan kasan ce da fari ciki na soon na san nima ya Ammar ze bani kulawa kamar yadda yayana ke baki, soyayyar ki da yayana yana birge ni aunty cikin fa d'ankakanin lokaci kuka fara soyayya gashin har kun shaku" Basmal ta ida zancan tana washe baki tana tsare Nihal da ido murmushi yake Nihal tayi tana cewa, "Um! Tsakin da aka saki ne yasasu dagowa Nazili ce sanye ciki gown light brown dai-dai gwiwa tayi parking gashin kanta hannun ta dauke da newspaper zama tayi sama resting chair tana cewa, "Basmal ya kamata ace duk programs din bikin ki ki samu Wanda ya san kan abubuwa, ma'ana masu ilimi wayanda suka dade cikin shi," ta ida zancan tana gefa wa Nihal kallo me cike da tsana tana mai cigaba da cewa, "sister bana so ki rinka shawara da gidadawa, na san kina da friends wayayu ya'ya manya ba ya'ya almajirai ba, idan ko kika ce da ya'ya almajirai zaki rinka shawara bikin ki ba ze bata light ba, karki manta bikin diyar sarki za'ayi ba bikin almajira ba mara tushe ko asali" na Nazili ta ida zancan tana kallan Nihal tana murmushi tare da bud'e newspaper tana cigaba da karantawa, jiki Basmal ne yayi sanyi bata ji dadi abin Nazili ta fada ba kamar gasawa Nihal magana take cikin magana, daura hannuwan ta Basmal tayi saman na Nihal tana yak'e tace, "aunty na kiyi hakuri haka halin ta yake ba wai ta fada bane saboda cin fuska" Basmal ta ida zancan tana kwabe fuska, murmushi Nihal tayi tana cewa, "dama ni ban dauke shi wani abuba, tunda na zama matar sultan bani da wata damuwa ko Bacin rai ko da an bata min da muje bedroom ze faran ta mi shiyasa a kullun yaya ki ke samun guri na musanman a zuciya ta" Nihal ta ida zancan tana murmushi tana kallan Nazili, Wanda ta cika fam fuuu ta tashi ta bar wajan tana aikawa Nihal mugun kallo. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 89_90* *ONE WEEK LETTER* Bayan sati daya abubuwa da yawa sun faru ciki har da shirye-shiryen exam da Nihal keyi duk wani abu daza ta bukata Sultan ya tanadarmata su. Yauma kamar kullun Nihal na zaune tana karatun exam dan yanzu karatun ya zamar bata jiki, dan bata so ta fadi jarabawa, murda kofar da akayine ya sata juyowa, sultan ne sanye cikin milk night dressing din shi wando da riga mai dogwan hannu, kallo daya Nihal ta mashi tare da kauda kanta tana bita karatun ta, drewar sultan ya bud'e tare da ciro wasu kaya dake cikin Leda a hankali ya tako gaban Nihal ya tsaya tare da aje ledar saman sofa dagowa Nihal tayi karaf suka had'a ido da sultan cikin honey voice din shi Sultan yace, "ki shirya gobe da safe zanyi dropping naki a school, insha Allah gobe zaki fara exam, zaku fara da English and basic technology ga uniform din da zaki saka komai na gama hadawa" har sultan ya kai aya Nihal na kallan shi wani irin dadi ya lulube ta ko ba komai gobe zata fita tasha iska dama ta gaji da zama waje daya, maganar da Sultan yayi ne ya dawo da Nihal daga duniyar tunani tsare ta da ido Sultan yayi tare da had'e rai yana cewa, "saura kuma idan kinje karkiyi kokarin ki dage ki ci exam's din idan har kika fadi bazan cigaba da biyan kudi na ba ana maki lesson mara anfani ba," wani irin kallo Nihal ta watsa ma Sultan tare da cewa, "Ni kuma idan naci bazan cigaba da zama ana min lesson ni kad'ai ba! se dai ka kaini makaranta nayi karatu kamar yadda kowa keyi idan ba haka ba, zan fadawa Ammi irin zaman da muke! shawara ta rage naka" Nihal ta ida zancan tana daukar littatafan ta dake saman sofa zata raba ta gefan sultan ta wuce fisgo ta Sultan yayi Nihal ta fada saman fafad'an kirjin sultan kallan juna suka shigayi mai cike da sakwanni mutsu-mutsu Nihal ta fara tana neman kwace kanta tana kallan Sultan fuskar ta daure, can kasan makoshi sultan yace, "Ai dama duk abinda zan maki ina yinshi ne saboda Ammi ba saboda ke ba, amma ki sani baki isa ki sani nayi abinda banyi niya ba, kuma dama kin aure nine saboda kin san cewa Ammi ce weakness dina! murmushi Sultan ya saki tare da cigaba da cewa, "hakan da kikayi is good, amma ki sani baza ki taba cin galaba a kaina ba" ya ida zancan yana kara matsewa Nihal hannu ta, da karfi Nihal ta fisge hannun ta har tana tafiya taga-taga zata fadi Sultan ya taro ta fadawa tayi saman fafadan kirjin sultan da karfi Nihal ta ture Sultan tana cewa, "Ai nima ina zaune da kai ne saboda Ammi kuma har yanzu ina jiran ranar da zaka bani takadata ma'ana ranar da zaka sakeni! saboda bana jin zan iya zama da mutumin da bana so baya sona! har karshan rayuwata kuma ida har baza kamin abinda nake so ba Sultan ni kuma se na fadawa Ammi irin zaman da muke,! Nihal ta ida zancan tana tsare Sultan da ido shima din kallan ta yake kamar yadda take kallan shi idanuwa waje kokarin rabawa Nihal tayi ta gefan sultan zata wuce kara fisgo ta Sultan yayi ya wurgata saman sofa saboda kalaman Nihal sun fara bata mashi rai har ita zata ce tana zaune da shi ne saboda Ammi, zaro ido Nihal tayi waje tare da kara shigewa jikin sofa dan wannan karan Sultan ya bata tsoro, cikin kakausar murya Sultan yace, "toh miyasa da aka tashi yin auran bakin fada wa Ammi baki so na ba,? se kikayi shuru da bakin ki saboda kin ga daula oh what? karki manta fa nasan mi yasa kika aure ni kin aure nine saboda kiyi ruining life dina do you think ban sani bane let me tell you something duk abinda za kiyi karki kuskura ki bari Ammi na ta shiga wani hali Nihal if not! Wani malalacin murmushi Nihal ta saki na rainin hankali tace, " Ni ban ce ana ruining life dina ba, daga taimako na zama matar ka ba tare da sanin family dina ba! an fada mana cewa ni shegiya ce ko bani da asali ne, se kai ne zaka ce ina ruining life naka da ni da kai wake ruining life din wani? me yasa baka fadawa Ammi baka iya zama da almajira a matsayin mata ba bari kaji Sultan kamar yadda baka so na nima haka bana sanka,! na san cewa auran nan kayi shine saboda Ammi idan har baka so Ammi ta shiga wani hali dole kayi min abinda nake so, maganar daula ko what ever karkayi tunanin kudin ka na dadani da kasa sultan ko daya kuma daga yau karka kara kashe min ko sisi cikin kudin ka! Maganar da Nihal keyi ma sultan ba karamin soya mashi zuciya take ba musanman idan ta furta bata san shi kamar yadda baya san ta, juya mata baya Sultan yayi zuciyar shi na kuna tana tafarfasa kamar zata fito waje saboda bacin rai juyowa ya kumayi lokacin idanuwa shi sun rine zuwa ja ya nuna Nihal da dan yatsa tare da sauke hannuwa shi ya fice da sauri daga dakin ya banko mata kofa da karfi kamar ze cire, lumshe ido Nihal tayi tare da dafe goshi tana sauke numfashi *********** bangaran minal da nawwara kannan sultan dake boarding school suma shirye-shiryen exam suke, kasancewar suma JSCE zasu zana murna wajan su ba'a magana dan sun matsu su gama exam su dawo gidan Hutu, musanman da suka ji cewa suna dawowa za'a fara bikin Basmal, minal ce dake kwance saman bed kasancewar dakuna hostel din mutum uku-uku ne daya ke makarantar ta ya'ya manya ce murmushi Minal ta saki tana cewa, "Nawwara na matsu naga mun gama exam's din nan mu koma gida, gaskiya this time around baza mu dawo boarding ba duk wani biki da suna wuce ka yakeyi haka akayi bikin yaya Sultan muna school har yanzu bamu San matar ba" Nawara dake duba littatafan ta ce ta dago tare da gyara zaman glass din ta dake manne a idan ta tana cewa, "I miss home so much minal kema kinyi magana this time around zamu matsa ma Abba ya barmu a gidan tunda mun zama yan'mata, ya kamata ace ko wani biki muna zuwa" shukura dake gefe dariya suka saki ita da minal ita kanta nawwara dariya ta saki suka kara kwashewa dariya sannan kowa ya cigaba da duba littafin shi. *WASHE GARI* Kiran Sallah Asuba ne ya tashi Nihal dauke da addu'a a bakin ta, ta mike zaune tana waige-waige a hankali ta sauke idanuwan ta saman bed din Sultan ganin baya saman bed din, yasa Nihal tuna rigiwar da sukayi jiya barbaza gashin kanta Nihal tayi tare furta "am so stupid yesterday! Jikin Nihal ne yayi sanyi a hankali ta zame blanket din jikin ta Nihal, ta nufi bakin kofa, a hankali ta kama handle din kofar ta murd'a tare da tura kanta parlour tana waige-waige kwance saman three star ta hango sultan ya kudindi ne cikin blanket gyara gashin kanta Nihal tayi a hankali take takawa har ta karaso bakin kujera tana leka fuskar sultan, motsin da Sultan ya ji a kanshi ne yasa sultan fisgo Nihal da karfi ta fada jikin shi tare da aza mata wuka a wuya zaro ido Nihal tayi tana kallan Sultan da idanuwan shi ke a rufe, a hankali Sultan ya bud'e lumsasun idanuwan shi ya sauke su saman kyakyawar fuskar Nihal yana bin ta da kallo tare da janye wukar daya kafa mata a makoshi, cike da tsiwa Nihal tace, "oh my goodness sultan kiyayar da kake min har ya kai ka fara kokarin kashe ni, what wrong with you Sultan? juyawa Sultan baya Nihal tayi tana yan'kame kame tana kakabe kujeri tana satar kallan Sultan shima har a lokaci idanuwan shi na kan Nihal juyowa Nihal tayi tana cewa, "um ya kamata ka tashi ina so na share parlour kafin mu fita bana so lokaci ya kure min" Nihal ta ida zancan tana wasa da yatsun hannun ta, kallan agogan dake manne jikin bango parlour sultan yayi kusan 5:00pm sannan ya kalli Nihal tare da kara kallan agogan itama kallan agogan tayi tare da juyowa karfa suka hada ido da Sultan wayancewa Nihal tayi tana cewa, "ka tashi mana" zuba mata sexy eye's ball din shi Sultan yayi tare da cewa, "ki bari kiyi sallah mana first se kiyi duk abinda zakiyi" juyawa Sultan baya Nihal tayi tare da cije lips tana cewa, "Allah yasa karya gane kallan shi nake ya rai nani, to mima ya sani fitowa oh pah," da sauri Nihal ta bar parlour ta maida kofar dakin ta rufe jingina Nihal tayi da kofa tana maida numfashin turo kofar da taji anayi ne ya sata zabura da sauri ta bar jiki kofar sultan ne ya shigo rike da pillow da blanket kallan Nihal din yake da alamar tuhuma sannan ya aje blanket din hannu shi saman bed yana kokarin shiga toilet da gudu Nihal ta karasa tana cewa, "aaah!!! Birki Sultan yaci yana kallan ta rabawa Nihal tayi ta gefen sultan ta shige toilet ta maida kofa ta kule dan siririn saki Sultan ya ja yana cewa, "wannan yariyar ta fara rai nani da yawa se na koya mata hankali mtsww" sannan ya fice daga part din gabaki daya Nihal na bakin kofa tana jin fitar Sultan , ta fito daure da alwala ta gabar da sallah. Misali karfe 7:00pm Nihal ce ke shiryawa cikin uniform din ta black and White skrt black dai-dai gwiwa da white shirt me dogwan hannu sosai kayan sun amshe ta tayi kyau se White hijab shirya tsab Nihal tayi cikin uniform ita kanta ta yaba kyan da uniform din ya mata, sannan Nihal ta fito daga bedroom zaune a parlour ta sami sultan saman kujera, a hankali sultan ya dago yana kallan ta wani irin kyau Nihal din ta mashi se ya ga ta kara zama to young da ita mikawa Sinbul briefcase din shi sultan yayi tare da cewa, "sinbul ka karasamin da briefcase dina cikin mota kafin na fito" to sinbul yace tare da amsa cikin ladabi ya fice sannan sultan ya kalli Nihal alamar su fita a tare suka fito da sultan gwanin ban sha'awa duk wanda ya kalle su se ya kara a haka har suka karasa main parlour lokacin kowa ya halara a dining area har da maimartaba dauke da sallama suka shigo, gabaki daya kallo ya koma kan su Ammi dake zaune ce ta saki murmushi tana cewa, "masha Allah Nihal uniform din nan ya maki kyau sosai Allah ya bada sa'a ya bada abinda aka je nema" gabaki daya yan' dining suka amsa da, "amin! har da Nihal dake jan kujera ta zauna karasowa sultan yayi tare da yima mom pack da Ammi a kumatu da maimartaba murmushi maimartaba yayi tare da cewa, "fushi nake da kai son! zaro ido Sultan yayi tare da langwabe kai yana jan kujera dake kusa da maimartaba, gimbiya jalila da Ashad kallan juna sukayi tare da tabe bakin suna kallan maimartaba, Sultan ne yake cewa, "am sorry Abba wallahi aiki ne ke boye ni shiyasa, insha Allah for now zan rinka kula da mutane na" kallan shi sarki yayi yana cewa, "Sultan ban san ranar da zaka fara shiga mutane ba, yaushe zaka saba dasu har su san cewa kaine shugaban su nan gaba kad'an, ko dai soyayya ce ta boye ka" maimartaba ya ida zancan ya kallan sultan dake yake, gabaki daya dining area kwashewa sukayi da dariya ban da Nazili dake aika wa Nihal da wani irin kallo, wani tunanine ya fado mata a rai lokaci daya, kayatacan murmushi Nazili ta saki tana fatan nasara furzar da iska mai sanyi tayi tana juya spoon din hannu ta sannan ta dauki wayar ta dake kusa da ita message ta Shiga rubutawa cikin dankakanin lokaci ta gama tare da tura shi tana murmushi, har sultan da Nihal suka gama breakfast suka fice, Nazili na zaune a dining cikin zuciyar ta tana cewa, "yau se na batar dake Nihal se na share tarihin ki a zuciyar Sultan se nasa sultan ya tsane ki" Nazili tana zancan zuci tana sakin murmushi, maimartaba ne dake zaune, kallan Nazili yayi tare da cewa, "daughter yau baki zuwa aiki ne? langwabe kai Nazili tayi tare da cewa, "Abba am not feeling much better am sick! shafa kanta Ammi tayi tare da cewa, " sorry my dear you have to take some rest" mom ce ta amshe zancan da cewa, "kin sha magani? girgiza kai Nazili tayi Gimbiya jalila dake gefe tana cin abinci a yangace tace, "Sorry dear" ita da Ashad mikewa Nazili tayi tare da sakarwa maimartaba pack a kumatu da Ammi sannan ta wuce bedroom. Zagaye daki Nazili keyi tana sakin murmushi murda kofar dakin da akayi ne ya sa Nazili hayewa bed da sauri ta lulube, Aziza ce ta shigo dauke da tray da ruwa se magani mekewa Nazili tayi tare da zabga tsaki tana cewa, "mi ya kawo ki daki na yanzu, bana bukatar ganin kowa idan ina san ganin ki zan nemeki" Nazili ta ida zancan tana amshe tray din hannun Aziza, cikin rawa jiki Aziza tace, "Ammi ce tace a kawo maki magani" harara Nazili ta watsa mata tare da cewa, "naji..! naji..! kina iya fita" jiki a sabule ta bud'e kofa zata fice Nazili tace, "Aziza! juyowa Aziza tayi kai a sunkuye Nazili tace, "ina so ki samin ido a kan abinda ke faruwa main parlour" daga kai Aziza tayi tare da ficewa tana fita Nazili ta janyo wayar ta dake saman bedside drawer kiran wata number ta shigayi bugu daya aka dauka daga dayan bangaran akayi sallamah murmushi Nazili tayi tare da cewa, "Tjee ina fatan ka ga sako na" murmushi Tjee yayi daga dayan bangaran yana cewa, "Gimbiya naga komai amma baki rubuto da suna makarantar ba? Wani malalacin murmushi Nazili ta saki tare da furta, " prime college! Shine suna makarantar TJee ina so kayi min aiki kamar yadda na saka ka! zan baka ko nawa kake bukata tun daga 1 million har 10 million TJee" "Baki da wata matsala Gimbiya zanyi duk abinda kike bukata amma ki aje min kudi na cas" "Kai ma kasan kudi ba matsalata bace ni dai fata na kayi min aiki da kyau TJee! "toh shikenan Gimbiya baki da wata problem a kaina" murmushi Nazili ta saki tare da kashe wayar Hannun ta, tana zagaye daki tana cewa, "yau Nihal na lahira se ya fiki jin dadi se kin dandana bacin ran da kika dade kina dasa min! murmushi Nazili ta kuma saki tana tunanin bakar wahala da Nihal zata sha hannun TJee ta kara tintsirewa da dariyar keta.. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITERS FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 87_88* Bayan Nihal da Sultan sun gama breakfast books din ta Nihal ta dauka tare da daura white veil din ta, Sultan se kallan ta yake briefcase din shi ya dauka suka fito a tare kasancewar da safe lesson teacher Nihal ke zuwa har suka fito compound idanuwan Sultan na kan Nihal, cikin natsuwa Nihal ta wuce lesson room, Alex dake tsaye kusa da Sultan ya dau 5 minutes yana mashi magana amma kwata-kwata hankali shi na kan Nihal ya tsare ta da ido yana kallan wani saban yanayi game da ita yana shigar shi wanda shi kan shi be san dalilin hakan ba, me yasa ya tsinci kanshi da tana birge shi kadan bada yawa ba, taba shi da Alex yayi ne yasasa dawowa dai-dai shafa sumar kanshi Sultan yayi yana sakin smile tare da mikawa Alex briefcase din shi da sauri ya shige mota ya zauna gidan baya tare da lumshe ido yana tuna moment din shi na jiya da Nihal, a haka motocin shi suka fara barin harabar gidan Alex dake front seat mazauni banza, juyowa yayi yana kallan Sultan yana smile daga mashi gira sultan yayi yace, "what? Dariya Alex yayi tare da cewa, "boss yau na lura kamar kana cikin good mood" murmushi Sultan yayi tare da lumshe ido yana cewa, "wani abu ka gani? aini kullun haka nake, ko kaga wani canji ne? sultan ya ida zancan yana tabe baki girgiza kai Alex yayi yana cewa, "uhm amma kad'an bada yawa ba! dafa goshin shi Sultan yayi yana cewa cikin zuciyar shi what wrong with me maida kanshi Sultan yayi bakin window yana sauke ajiyar zuciya. Maida hankali Nihal take sosai suna lesson ita da aunty abiola tana kara wayar mata da kai kan karatun ta tare da sheda mata cewa, next week za'a fara JSCE tayi magana da Sultan yace makaranta ze kai ta tayi exam ya kamata ta dage da karatun, to Nihal tace mata sannan suka cigaba da gudanar da lesson din su. Nazili ce tsaye gaban dressing mirror tana shiryawa cikin jeans and shirt, black jeans rigar white tasha kyau har ta gaji bakin nan yasha jan bakin tayi parking gashin kanta ya wani nanad'e daga kasa, fost din ta dake saman dressing mirror ta dauka tare da saka takalman ta black boot a hankali tasa Hannu ta bud'e handle din kofar dakin ta, tana tafiya komai na jikin ta na amsawa har ta karaso dining area lokaci sun Ammi har sun fara breakfast, kallan su take da alamar tanbaya sannan ta kalli inda sultan ke zama yana break jan kujera tayi ta zauna tana cewa, "morning grandma" Nazili ta fada tare da sakar wa Ammi pack a cheeks nata "Morning too Nazili" Basmal dake kusa da Ammi tace, "kin tashi lafiya? "lafiya lau" Nazili tace tana serving kanta plantain, kallan Ammi tayi tare da cewa, "Ammi ina Sultan? yau beyi break a gida bane? Basmal ce ta amshe zancan da cewa, "Ai yanzu yayana ya daina break da mu tare da wife nashi ya keyi yanzu nasan ya tsufa a office," daga gira Nazili tayi tana kallan Basmal takaici na rufe ta, Basmal ta cigaba da cewa, "Nihal naji da yayana sosai tana bashi kulawa shiyasa kullun soyayya su kara birge ni take Ammi" Basmal ta ida zancan cike da jin dadi, Murmushi Ammi tayi tare da cewa, "shiyasa nake san Nihal akwai natsuwa da biyayya! Wani irin kallan banza Nazili ke bin su Ammi da shi bakin cikin na shigar ta dan siririn tsaki ta saki ta turo plate din gaban ta, Ammi tace, "Nazili ba dai har kin koshi da abincin ba? "Eh na koshi" Nazili ta ida zancan a gadarance tare da barin dining da sauri cikin zuciyar ta tana cewa, wawaye se naga bayan wannan matsiyaciyar yarinyar nan natsane ki,Nazili ta fad'a da karfi, har Nazili ta isa parking space tana surutai da masifa, tana kokarin bud'e murfin motar ta suka had'e da Ammar, murmushi Ammar ya saki yana cewa, "Nazili ke dawo kuma tun daga nesa na hango ki, kina masifa Allah yasa lafiya" Ammar ya ida zancan yana rike kugu, kallan banza Nazili tayi ma Ammar tana cewa, "dan sa ido kawai mtsww, kaji da rayuwar ka malam mtsww! Ta ida zancan tare da shigewa cikin motar ta da karfi ta fisgi motar kamar zata tashi sama ta fice, girgiza kai Ammar yayi tare da cewa, "ko yaushe Nazili zatayi hankali oho! sannan ya karasa cikin gida a bakin kofar part din Ammi suka had'e da Basmal tana kokarin fita Hannun ta rike da books kasancewar tana da lectures din safe, murmushi Basmal ta saki tana kallan Ammar shima kallan ta yake mai cike da so da kauna, cikin siririyar murya ta tace, "ya Ammar ina kwana," Amsa mata yayi cikin calm tune tare da matsowa kusa da ita kamar me rada yace, "my love kinyi kyau sosai har kin sa na fara kishi, duk wannan kwalliyar school akayi mawa ita" kallan kanta Basmal tayi ba komai bane jikin ta se black after dress se black veil da lipstick da ta shafa ma lips din ta, amma duk da haka tayi kyau, murmushi Basmal ta saki har fararan hakuran ta na bayana tace, "sweetheart ina kwalliya a nan? ni ba kwalliya da nayi Allah" Basmal ta ida zancan cike da shagwaba, ja mata hanci Ammar yayi sannan yace, "toh shikenan amma fa kinyi kyau muje nayi dropping naki tunda naga kamar school zaki" to Basmal tace tare da bin bayan Ammar shi da kanshi ya bud'e mata kofar mota sannan ya koma ma zaunin drive a hankali ya fara jan motar se da sukayi nisa sannan Ammar ya daura hannuwanshi saman na Basmal yana cewa, "my love kin mantar dani ko gaishe da Ammi banyi ba saboda kin rud'a ni da yawa" dariya Basmal tayi mai sauti tana kallan Ammar dake kallan ta a hankali Ammar ya sakar mata light kiss a kumatu shuru Basmal tayi tana tsare Ammar da ido suna kallan juna, horn din da suka fara jine yasasu juyawa lokaci guda a dan razane birki Ammar yaci yana dariya yana cewa, "baby kin gani zaki ja mana hadari a kan titi! nidai gaskiya my love na matsu mu kasance tare da juna, ji nake kamar na jawo satin bikin mu nan kusa" harara wasa Basmal ta sakarwa Ammar tana cewa, "ba ruwana laifin kane na lurama so kake mu mutu kafin bikin" mintsinin ta Ammar yayi a hannu yana harara ta yar kara Basmal ta saki rufe bakin ta yayi dai-dai da parking din motar Ammar a harabar makarantar su Basmal murmushi Basmal tayi tana cewa, "Alhamdulillah mun iso lafiya" ta ida zancan cike da zolaya tace, "thank you sweetheart" dariya Ammar yake yana cewa, "matsoraciya kawai" Ammar ya ida zancan yana kama hannun Basmal fisge hannuwan ta tayi tana cewa, "cizo na zakayi tunda ka mintsineni" dariya Ammar ya saki yana ja mata kumatu yana cewa "no baby ko daya kawai dai" a hankali ya sakar mata light kiss a kumatu yana cewa, "ki kullamin da kanki kin ji my love" daga mashi kai Basmal tayi sannan Basmal ta bud'e murfin motar ta fice, tana kallan Ammar har ya ja mota ya bar harabar makarantar har se da ya kure ma ganin ta sannan ta shige cikin class. Sultan ne zaune saman kujera yayi relaxing a cikin office na shi yana juya kujera da yake zaune idanuwan shi a lumshe, ba abinda yake tunawa se Nihal murmushi Sultan ya saki yana tuna yadda Nihal ke zakalkalewa tana mashi masifa, murmushi ya saki Wanda shi kan shi be sani ba, har dimple din shi na lomawa hakan se ya kara mashi kyau, a hankali Sultan ya furta, "oh goshh why do I always have to think about her even since I set my eye's on her, I hate this! lumshe idanuwan shi Sultan ya kuma yi knocking din kofar da akeyi ne yasa Sultan cewa, "come in" cikin honey voice din shi Ammar ne ya shigo hannu shi dauke da file's aje su yayi saman table sannan shima ya samu waje ya zauna yana facing din Sultan ya zuba mashi idanuwa gyara zama Ammar ya kumayi yana kallan Sultan dake ta zuba smile, Ammar yace, "Sultan yau ka duba patient kuwa" ya fad'a yana tsare Sultan da ido zaro ido Sultan yayi yana cewa, "oh my god na manta" Sultan ya ida zancan yana kokarin daukar aluran dake saman table, kallan shi Ammar yayi tare da cewa, "yana ji voice kana with full of joy" murmushi Sultan yayi tare da cewa, "mi ka gani? dariya Ammar yayi yana kallan face din Sultan yadda ya canza yana tanbayar Ammar, Ammar yace, "am sure you having a good time with Nihal" Ammar ya ida zancan yana tsare sultan da ido shima din kallan shi yake zuciyar Sultan na dukan uku-uku me ke faruwa da shine duk yana wannan zancan ne a cikin zuciyar shi rintsi idanuwan shi Sultan yayi ba abinda yake gani se Nihal, a hankali ya sauke su saman fuskar Ammar da ya tsira mashi ido had'e rai Sultan yayi yana cewa, "Allah ya sauwake nayi good time da wannan yarinyar kawai ina cikin good mood ne", dariya Ammar yayi tare da cewa zakayi bayanine Allah ya nunamin ranar da Nihal za tayi wining heart naka Sultan,! had'e rai Sultan yayi tare da cewa, "enough! Ammar bana san irin wannan kidding din let change da subject please" Sultan ya ida zancan yana tatare file's din dake saman table jikin shi yayi sanyi yana fatan Allah karya nuna mashi ranar, taba shi da Ammar yayi ne yasa Sultan juyowa suna facing juna yace, "Na batama rai ko am sorry dude, to min ya hanaka duba patients da wuri wani abu na damun ka ne" murmushi yake Sultan yayi yana kallan Ammar yace, "Uhm wasu abubuwa na tsaya dubawa" Sultan ya fada yana kallan Ammar dake kallan shi da alamar tuhuma, kad'a kai Ammar yayi sannan suka fice tare daga office din. Misalin karfe 12:00pm lesson teacher Nihal ta tafi, part din Ammi Nihal ta wuce a gajiye, lokacin Ammi na zaune saman three star tana kallo, murmushi Ammi ta saki tare da cewa, "har an gama lesson din? aje books din hannu ta Nihal tayi saman kujera tana cewa "eh Ammi," "toh madalla, Allah ya taimaka" "Amin" zama Nihal tayi saman kujera Ammi dake kallan ta tace, "kin gaji ko?ai haka karatu yake se hakuri, ki shige bedroom ki samu hutu, zan turo maki Yasmin ta maki massage, yau ba se kin wani daura wani abuba dazu mom ta aiko da cewa kuje part nata ke da Sultan kuyi lunch" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "amma fa na ji dadi dama tunanin abinda zan dafa nake gashi yau na gaji sosai" Nihal ta ida zancan a shagwabe dariya Ammi tayi tana cewa, "to ai gashi yanzu kin samu hutu" cike da farin ciki Nihal ta hada books nata dama ta gaji dayi ma k'atan kawai abinci ya zauna yana ci ba godi bare na gode sannan Nihal ta shige bedroom, toilet ta shige ta sheka wanka ta fito daure da towel da karamin tana goge jikin ta Sultan ya fadu mata a rai murmushi Nihal tayi tana goge jikin ta, dressing mirror ta nufa ta shafe jikin ta da lotion sannan ta shirya cikin jean da pink shirt me dogwan hannu ta kama jikin ta sosai sannan tasa black boot Nihal tayi kyau kamar ita tayi kanta, jan baki ta shafa ma lips din ta gashin kanta ya zubo har gadan bayan ta yana ta shining sannan ta fito parlour, lokaci Ammi ta shige bedroom din ta, part din mom Nihal ta wuce, dauke da sallama a bakin ta ta shiga parlour, mom dake zaune ana mata massage gefe ga fruit tana sha murmushi mom ta saki cikin ladabi Nihal ta gaishe da mom tare da samun guru ta zauna, bayin mom taba umarni su zubawa Nihal abinci tuwan shinkafa miyar egusi taji vegetable se kamshi take zama Nihal tayi ta shara abincin ta bi da fresh juice me sanyi se da ta cinye abincin sannan ta dago ido kunya ce ta kamata ganin mom na kallan ta dariya mom tayi tace, "ki saki jikin ki daughter nima kamar mom naki nake babu wata kunya tsakanin mu" daga kai Nihal tayi suna taba hira da mom sama-sama kiran sallah la'asar ya tashi su mom, a dakin mom Nihal tayi sallah bayan sun idar mom ta bud'e karamin frigde ta ciro fresh milk ta zuba a glass cup ta mikawa Nihal, washe baki Nihal tayi tare da amsa ta shanye shi duka har da lashe baki saboda dadi sosai Nihal ta saki jikin ta, haka mom tasa akayima Nihal massage, Nihal taji dadi jikin ta sosai, bayan sun fito parlour tana zaune Nasim ya shigo da gudu parlour ya fada jikin Nihal yana cewa, "Aunty Nihal please ki zo ki tayani wasa bani da friends" ya ida zancan a shagwabe murmushi Nihal tayi tana kallan shi mom dake gefe zaune tace, "Nasim ina Momi? daga ido zama yayi yana cewa, "dazu ta fita ita da yaya Ashad takin fita dani" Nasim ya ida zancan kamar zeyi kuka yana cewa, "Gashi bani da friends aunty Nihal please ki tayani" kama hannuwan shi Nihal tayi tana cewa, "to shikenan zan taya ka" mom ce ta mike tana cewa, "bari na karasa part din maimartaba idan Sultan ya dawo abincin shi na dining area" to Nihal tace tana kallan mom har ta fita sannan ta juyo tana kallan Nasim tace, "wani wasa zamuyi? Nihal ta ida zancan tana daura shi bisa cinyar ta, washe bakin Nasim yayi yana cewa, "wasan b'uya zamuyi zan daure maki eye's naki da veil se ki nemo ni, idan kika kamani se ki boye na nemo ki" to Nihal tace cike zakuwa veil din ta tasa ta daurewa Nasim ido sannan ta boye bayan kujera zagaye parlour Nasim yake yana cewa, "Aunty Nihal zan kama kine fa," ganin Nasim ya zo bakin kujera yasa Nihal tashi a hankali ta boye bayan labile, jin kamar motsin mutum yasa Nihal fisgo hannun me shigowa dan karya tona ta,ba kowa bane se Sultan da shigowar shi kenan kwata-kwata Nihal bata lura da shi bane tunanin ta Basmal ce toshe mashi baki Nihal tayi tana cewa, "kiyi shuru karya jini" kamshin turaran Sultan ne daya doki hancin ta ne yasa Nihal juyowa kamar mara gaskiya zuciyar ta na tsanata bugawa idanuwan ta a rintse ta juyo a hankali ta sauke su saman fuskar Sultan, kallan juna suka Shiga yi har a lokaci hannun Nihal na saman lips din sultan, a hankali ta zame hannun ta tana cewa, " am..!! toshe mata baki sultan yayi yana cewa kamar me rada, "kiyi shuru Nasim nan wajan" tsare shi da ido Nihal tayi tana kallo daga labilan da kayi ne yasa Nihal karayin lamo tana kallan Sultan, cike da shagwaba Nasim yace, "aunty Nihal ina kika Shiga har yanzu ban gano ki ba" ya ida zancan kamar yayi kuka, fitowa Nihal tayi daga labalan ta bar Sultan a cikin daga Nasim tayi tana dariya tana cire mashi veil din dake idan shi, dariya shima yake yana cewa, "aunty Nihal kin boye waje menisa" a hankali sultan ya fito daga jikin labilan Hannun shi na zube cikin aljihu zamewa Nasim yayi daga jikin Nihal yana cewa, "uncle! da gudu ya karasa gaban Sultan daga shi sama sultan yayi yana mashi wasa yana cewa, "my boy! Murmushi Nihal tayi tana kallan sultan, moment din su na dazu na dawo mata lumshe ido tayi tana sakin lalausan murmushi. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITERS FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Assalamu alaikum bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan kuna lafiya, nasan da yawa masoya littafi na sun ji ba dadi sakwamakwan jina shuru da kukayi, ba komai ya janyo haka ba se losing phone dina danayi shiyasa but yanzu am back insha Allah zaku rinka ganin posting dina na gode sosai da soyayyar ku masu Kira kafin nayi waya da wayanda suka min message ta WhatsApp thanks for the caring fan's Ana mugun tare irin sosai din nan na sadaukar da wannan page din gare ku fan's_* *Page: 85_86* Ba karamin dadi Nihal taji ba ganin Nazili ta bar garden rai bace ko ba komai itama ta kona mata rai kamar yadda take mata, murmushi Nihal ta saki tare da gyara gashin kanta dake kare mata fuska tare da daura hannun ta saman na Basmal tana mai cigaba da sakin lalausan murmushi, cigaba da tattaunawa suke kan yadda zasu tsara program's din biki tare da ware ranar da zasu je shopping na musanman, kiran sallah magrib ne ya tashi su Nihal a garden part din Ammi suka wuce Kaitsaye kasancewar Nihal bata sallah se ta wuce babba kitchen dauke da murmushi Nihal ta shiga da sallama dauke a bakin ta, gabaki daya bayin dake kitchen din suka zube suna kwasar gaisuwa ciki fara'a Nihal ta amsa tare da matsawa kusa da jakadiya ba komai yasa Nihal shigowa kitchen ba se dan ta cikawa mom burin ta, dan ta lura kwata-kwata mom bata so bayi da ma'aikata nayiwa sultan girki, murmushi Dara ta saki tana mai cigaba da cewa, "ke dai gimbiya bakya gajiya da shigowa kitchen, kuma haka na da kyau Nihal! ita kanta jakadiya tana ji dadi yadda Nihal ta amshi ragamar girkin Sultan a hannun ta dan kar Sultan ya shiga wani hali! murmushi Nihal tayi tana cewa, "umma gajiya nake da zama bana aiki, na saba a gida kullun ina aiki" Nihal ta ida Zancan tana daura tukuya a gas, cikin dankankanin lokaci Nihal ta daura cuscus jakadiya tana yanka mata vegetable suna girki suna taba hira miyar kabej da dankali Nihal tayi taji vegetables se kamshi take zubawa, bayan ta kamala suka juye komai a wermar direct dining area Dara da Nihal suka wuce suna jerawa washe baki Jakadiya tayi tare da cewa, "gaskiya Nihal bani da abinda zance se dai nace sultan yayi sa'ar mata a wannan zamani kafin a samu Gimbiya me shiga kitchen tayi girki se an tona,! shuru Nihal tayi tana kallan jakadiya tana murmushin yak'e, murmushi Dara tayi tana mai cigaba da cewa, "Gimbiya a gaskiya ke da Sultan kun dace da juna sosai a cikin ku na rasa wanene yafi halin dataku," matsowa Dara tayi kusa da Nihal tare da rike hannuwan Nihal ta zauna da ita daya daga cikin kujerin dining shafa kumatun Nihal Dara tayi tana murmushi tace, "Nihal duk abinda zan fad'a maki da shawara da zan baki ki dauka Nihal ina jin ki tamkar ya'ta ta cikina, Nihal kisan cewa uwa ce kadai ke fadawa ya'ya ta shawara wadda baza cutar da suba," Dara ta ida Zancan tana tsare Nihal da ido tana mai cigaba da cewa, "Bayan Ammi da mom Sultan bashi da kowa se ke Nihal, na lura har yanzu kin kasa sakin jikin da Sultan karki manta fa mijin kine Nihal ya Kamata ki rinka sakin jikin ki da mijin ki kina sanin damuwar shi, Nihal tunda Sultan ya ta so a rayuwar shi be san wani abu kwanciyar hankali ba, Nihal kullun farautar rayuwar shi ake duk wani Abu da Sultan ze maki na dan lokaci ne inada yakinin cewa Sultan na sanki Nihal babu namijin da Kika dace da shi saman da sultan Nihal, Sultan amana ne a gare ki Nihal ke kad'ai ce zaki iya bashi kariya, naji dadi sosai da kike bashi wannan kulawar, amma ya kamata ki kara a kan wace kikeyi" tsare ta da ido Nihal tayi take nan tausayin Sultan ya lulub'e ta, zancan zuci Nihal ta shigayi tana cewa, mi yasa ake farautar rayuwar sa ya za'ayi mutumin daya taso cikin gata ya zamana ana farautar rayuwar shi idan ta lura kowa na gidan na nuna ma shi so, kuma bata taba ganin shi cikin damuwa ba, maganar cewa Sultan na santa wannan tunani umma ne, bata tunani akwai ranar da Sultan ze so ta ko a mafarki haka itama bata jin zata so Sultan dai-dai da rana daya se dai kalaman jakadiya sun sa jikin ta yin sanyi, taba kumatun ta da Dara tayi ne yasa Nihal dawowa daga duniyar tunani, kama hannuwan Dara Nihal tayi dake saman kumatun ta suna kallan juna murmushi yake Nihal tayi tare da lumshe idanuwan ta cikin sanyi murya tace, "umma zan shiga ciki" sannan Nihal ta mike har ta je bakin kofar bedroom jakadiya tace, "Nihal kiyi nazari a kan magana ta kinfi kowa kusa da Sultan a yanzu yana bukatar kulawar ki sosai! tsayawa cak Nihal tayi tana saurara maganar da Dara ke mata sannan ta murda handle din k'ofa ta shige bedroom din ta, jingina Nihal tayi da bakin k'ofa maganar Dara na dawo mata kamar yanzu take fada mata, lumshe ido Nihal tayi tausayin sultan na shigar ta da kyar ta iya jan yan'matan kafafuwan ta ta shige toilet ta watsa ruwa sanye da bathrobe Nihal ta fito daga toilet tana goge jikin ta da karamin towel, dressing mirror ta nufa ta shafe jikin ta da lotion me kamshi da sanyin dadi shiryawa tayi cikin black wando me kamar bagi se shirt orange me budadiyar kafad'a kayan sun mata kyau sosai kamar dan ita akayi su turare me sanyi dadi ta feshe jikin ta da shi sannan ta baza gashin kanta har gadan baya se shining yake ya wani kwana a gadan bayan ta, duk da ba wata kwalliya tayi ba amma tayi kyau sannan ta fito. direct dining area Nihal ta wuce lokacin kowa ya halara maimartaba ne kadai babu kasancewa tare da waziri zasuyi dinner cikin natsuwa Nihal ta karaso dining area tunda Sultan ya hango Nihal ya kafe ta da idanuwan shi yana kallan yadda Nihal ke takowa of coz he can't stop looking at her, muryar Nihal ce ta daki dodan kunna shine yasasa dawowa daga duniyar tunani, tana cewa cikin siririyar muryata "barka da war haka! Nihal ta fada tana mai jan kujera kusa da Sultan lumshe ido yayi saboda kamshin turaran Nihal daya ziyarci hancin shi iskar bakin shi me sanyi Sultan ya furzar zuciyar na tsana ta harbawa, gabaki daya yan dining suka amsa "barkan mu juna" ban da Nazili dake ta faman aika wa Nihal da mugun kallo, murmushi mom tayi tare da taba kumatun Nihal tace, "masha Allah daughter kinyi kyau," murmushi Nihal tayi tana sunkuyar da kanta kasa, Yakumbo dake gefe tana kokarin serving Sultan abinci ne Nihal ta kalla kalaman Dara ne suka shiga dawo mata a kwakwalwa bata san sada ta rikewa Yakumbo hannu ba kallan juna ido cikin ido suna Shiga yi yakumbo da Nihal take anan yakumbo tasha ruwan jinin jikin ta tana kallan Nihal, ita kanta Nihal ta rasa dalilin da yasa ta tsani yakumbo, ba yakumbo ba kad'ai har Gimbiya jalila da Ashad se da suka kalli juna, murmushi Nihal tayi tare da cewa, "na hutace ki zanyi serving nashi da kaina! Ammi dake gefe da mom ba karmin dadi suka ji ba Gimbiya jalila ko wani kulutun bakin ciki ne ya Mata tsaye a makoshi, me yarinyar nan take nufi da yin hakan! yakumbo data ja baya ta tsaya tsanar Nihal da Sultan na kara narkewa a zuciyar ta, tana kallan su ta kasan ido, Ashad ma kallan Nihal yake yana tufka yana warwara, kallan juna Ashad da Gimbiya jalila sukayi suna aika wa juna su sako ta kasan ido kamar haka lalai kam akwai jan aiki a gaban mu!, warmer Nihal ta bude tare da serving sultan abincin data girka da kanta Sultan dai shuru yayi yana tunanin dalilin da zai sa Nihal ta hana shi cin abincin da kowa ze ci, turo mashi plate din da Nihal tayi ne ya sasa dawowa daga duniyar tunani tsare Nihal yayi da ido itama din kallan shi take Basmal ce ta katse masu tunani dacewa, "gaskiya Aunty na kina ji da yayana yanzu wannan abincin da kanki Kika girka? na zo zanci Dara ta Hanani wai na yayana nane, gaskiya aunty na kina nuna mana launin fata shi se a dafa mashi nashi da ban gashi kamshin abincin duk ya cika mana hanci daga ji zeyi dadi, gaskiya nima zanci! Nasim dake kusa da Basmal yace, "nima! rufar ma wermar sukayi suna zubawa suna santi spoon daya Basmal tayi tare da lumshe ido tace, "gaskiya food din nan yayi sweet, Ammi ya Kamata ki dandana" to Ammi tace Dara na serving nata abincin, murmushi yake Nihal tayi tana kallan sultan a hankali ya sa spoon a plate din spoon daya yayi tare da lumshe ido ganin idanuwan su Ammi na kanshi yasasa saki smile tare da daura hannuwan shi saman na Nihal a hankali ya furta "thank you hayate! tare da manna mata pack a lalausan hannu ta, tsare shi da ido Nihal tayi tare da yin saurin ta zame hannun ta dake cikin na sultan tare da kauda Kanta tana mai cigaba da cin Abinci, Nazili dake zaune ta cika fam kamar ta tarwatse aje spoon din Hannun ta tayi ciki plate tare da sakin murmushi rainin hankali tace, "Nihal! Dago da idanuwan ta Nihal tayi tana kallan ta murmushi ta saki tare da daga gira tace, "amma nayi mamaki yadda kika iya girki dama gidan almajirai ana daura tukunya? Kuma ko ana daurawa, I think ba dai irin wannan ba se dai tuwon dawa miyar kuka! idan ansamu na Allah bani wahidi! Gabaki daya kowa na dining se da yasha ruwan jinin jikin shi Gimbiya jalila ko dadi ta ji sosai ganin tsinkin da Nazili kewa Nihal ko ba komai ta biya ta a daran nan, Mom ko ji tayi zuciyar ba dadi ita da Basmal da Ammi jikin su yayi sanyi, tsare ta da ido Nihal tayi tana kallo tana hadiye-hadiye d'aga gira Nazili tayi tare da cewa, "Na manta fa ashe almajirai d'ai-d'aya ne ke da gida amma ke nasan baku da shi saboda rashinshine...! Sultan ne yace, "Nazili ! Cikin angry voice saboda Kalaman Nazili sun fara sosa mashi zuciya, duk da cewa ba Karya Nazili take ba yes Nihal almajira ce but now she is my wife, yanzu ta tashi daga almajira ya Kamata Nazili ta dinga gyara Kalaman ta! tsare Nazili da ido Sultan yayi, lumshe ido Nazili tayi tare da ware su ta furta "Ni fa tanbaya kawai nake ina ta iya abincin nan" Nazili ta fada tana tsare sultan da ido lumshe ido sultan yayi saboda kalaman Nazili na bata mashi rai sannan ya bud'e idanuwan shi ya sauke su kan Nazili da suka sauya launi cikin lokaci daya zuwa ja, yace, Nazili! Shuru Nazili tayi tana kallan Nihal dake kallan ta Sannan ta kara jefawa Nihal da tanbaya da cewa, "dama gidan almajirai ana abinci? murmushin da yafi kuka ciwo Nihal ta saki, tare da kallan sultan tace, "almajirai suma suna rayuwane kamar yadda mutane ke rayuwar su, kamar yadda ma'aikata ke zuwa aiki haka suma suka dauki almajiranci kamar yadda kike samun gata gaban yan'uwan ki suma haka almajirai suke samu, suna rayuwa cikin jin dadi da walwala kamar yadda kowa yake yi, da almajirai da masu wadata duk daya suke a wajan Allah , Allah baya duba gatan da mutum ya samu ko daula da yake ciki da zuciya yake anfani, haka suma almajiran suna samun kyakyawar rayuwa tun da gashi nima na samu har na auri sultan kuma a haka ya ganni yake so,! Nihal ta ida zancan tana kallan fuskar sultan tana tsoran karya watsa ta, shima din sultan kallan ta yake yana hadiye-hadiye sannan yayi murmushi yana kallan Nazili Wanda ta canza lokaci daya kamar tayi kuka, maganar da Nihal tayima Nazili ammi taji dadin ta sosai shuru Nihal tayi tare da numfasawa ta cigaba da cin abincin ta, daura hannu shi Sultan yayi saman na Nihal tare da rike shi sosai, shi kan shi be san yana aikata hakan ba ture plate din gabanta Nazili tayi tare da cewa, "se da safen ku" ta bar dining area zuciyar ta a dagule da takaicin yadda sultan ke nunawa Nihal so ko a gaban waye tasan ba komai ke dibar shiba se Kyan fuskar ta, ta dau Alwashin se ya wayi gari ta kona fuskar ze dawo hayacin shi mtsww cikin zafi rai Nazili ta fada a fili, "tallaka kawai,! bayan ankamala dinner kowa ya wuce part din shi. Nihal ce zaune saman sofa tana sanye da pink sleeping dress din ta wando da riga mai dogwan hannu tana duba books din ta murda kofar da akayi ne yasa Nihal dago da idanuwan ta sultan ne sanye cikin night dress dark blue wando da riga kallo daya Nihal ta mashi ta kauda Kai saboda haushin sultan yake bata, saboda ta san a kan shi Nazili ke gasa mata magana akan mutumin dako damuwa bayi da ita ba, d'an siriri tsaki Nihal ta saki a zuciyar ta bata San ya fito fili ba sultan dake tsaye gaban dressing mirror can kasan makoshi sultan yace, "dawa kike? Galala Nihal tayi tana kallan sultan tana mamakin da yaushe ya jita shuru Nihal tayi tare da daukar books din ta tana ajewa a drawer dagowar da zatayi taga mutum tsaye a kanta had'e rai Nihal tayi tana kallan sultan shima sultan ranshi a had'e babu alamar wasa yace, "dawa kike? shuru Nihal tayi a karo na biyu takowa sultan yayi daf da ita matsawa Nihal tayi Sultan ya kara biyo ta har se da ya manna ta a bango had'e rai Nihal tayi cike da tsiwa tace, "wai me haka Sultan? ka matsamin na wuce," Nihal ta ida zancan a tsawace tsare ta da ido sultan yayi yana kallan lips din ta kamar me neman wani Abu, raraba hannuwan shi sultan yayi jiki bango yayi ma Nihal runfa har suna jin saukar numfashin juna su sultan yace, "idan naki fa what can you do hum? Are you going to beat me up or what! Nihal ce ta kara tsinkewa da lamarin sultan, tsare Nihal da ido Sultan yayi ba alamar wasa a face na shi, duk da zuciyar Nihal na dukan uku-uku saboda kwarjinin da Sultan ya ke mata hakan be hana Nihal had'e rai ba tana kokarin ture hannuwan sultan ta wuce ba, janyo ta sultan yayi ya Kara manna ta bango wata yar kara Nihal ta saki saboda matse mata hannu da Sultan yayi da hannun shi ya kara matsowa kamar ya shige cikin jikin ta rintse idanuwa Nihal tayi jikin ta na rawa tare da cewa, "Dan Allah kayi hakuri bada kai nake ba fa, wallahi ban masan tsakin ya fito ba dan Allah ka bani guri na wuce, bacci nake ji" had'e rai sultan yayi yace, "yau nan zamu kwana! zaro ido Nihal tayi tare da kallan sultan idanuwan ta waje tana kallan sultan dake kallan ta tsaki sultan ya saki tare da barin Nihal tsaye kamar gunki sauke ajiyar zuciya Nihal tayi tare da cewa mugu a zuciyar ta, saman bed sultan ya haye tare da kashe light din dakin gabaki daya zancan zuci Nihal ta shigayi tana cewa, "dan mugun Abu har da kashe min haske ban gama shiryawa ba to bazan ce ka kunna min ba, dana ce ka kunna min Kara na mutu, bin bango Nihal ta shiga yi tana neman haskyan dakin a hankali gashi dakin yayi duhu sosai tuntube Nihal tayi kanta ya daki center table Kara Nihal ta saki tare da fashewa da kuka saboda zafin da ya ziyarci goshin ta, a hankali sultan ya bud'e lumsasun idanuwan shi yana jin kukan Nihal har cikin ran shi duk yadda ya so yayi banza da ita ya kasa can kasan makoshi Sultan yace, "what's this Nihal you know I hate distraction! bayan kin ce kina jin bacci me na damuna kuma yanzu" Banza da shi Nihal tayi ta cigaba da sakin kuka kamar ma zuga ta Sultan yayi lumshe ido sultan yayi jin ba zai iya jurewa kukan da Nihal take ba ya tashi zaune tare da zame blanket din dake jikin shi ya kunna haskyan daki, duke a kasa ya hango Nihal tafe da goshi tana kuka zuba mata ido yayi yana kallo kana yace cikin calm tune, "what's wrong with you? dago da jajayan idanuwan ta Nihal tayi tare da fashewa da kuka, a hankali sultan ya sako daga saman bed cikin natsuwa ya karaso gaban Nihal tare da dukawa ya zame Hannun ta dake saman goshi ta ganin yadda goshin ta lokaci daya ya kunbura yayi ja yasa sultan rintse ido, bedside drawer ya bude ya ciro magani a dan tufu ya matso kusa da Nihal ya matsa maganin a Hannu shi bismillah sultan yayi yana kokarin daura Hannun shi saman goshin Nihal, ja baya Nihal tayi tare da cewa, "lafiya! karka tabani na fada ma" Nihal ta ida zancan tare da dunkulewa waje daya tana kuka tana jan majina, Kauda Kai Sultan yayi tare da kara matsowa kusa da Nihal dan bashi da lokacin musayar yawu da ita dan ya lura ta fara rai na shi, a hankali ya daura hannun shi saman goshin Nihal yana murza mata wata yar kara Nihal ta saki sakwamakwan wani irin zafi ne daya karu a goshin ta bata san lokaci data shige jikin sultan ba ta kara rushewa da kuka cikin shashekar kuka take cewa, "da zafi ka kyale ni please! hura Mata iskar bakin shi sultan ya shigayi me sanyi tare da cewa kamar me rada dai-dai setin kunnan Nihal yace, "ki bari na murza maki kin ji idan ya kai gobe kunbura zeyi sosai" dakyar Nihal ta iya daga mashi kai ta zame taga jikin shi murza mata goshin yayi karo na biyu kara Nihal ta kuma saki tare da shigewa jikin sultan ta cikwikwiye mashi night dress din shi hura mata iskar bakin shi sultan yake yana murza mata a hankali, cikin dankankanin lokaci baccin wahala yayi awan gaba da Nihal, tsare ta da ido sultan yayi yana kallo yadda ta lafe a chest din shi, a hankali ya dauke ta kamar baby ya shifid'e ta saman bed tare da gyara mata kwanciya ya ja mata blanket, tsare ta sultan yayi da ido yana kallo a hankali ya daura hannun shi saman kanta tare da matsar da gashin kanta daya rufe mata fuska a hankali ya furta "Nihal! cikin calm tune sannan ya mike a warwaran Hannun Nihal ne ya Kama rigar sultan juyowa Sultan yayi tare da dukowa yana cire awarawaran gyara kwanciya Nihal tayi tana facing Sultan tare da kama hannu shi tayi pillow da shi ta kankame hannu sosai sultan ya dau kusan 30 minutes duke yana kallan yadda Nihal ke bacci ga hannun shi da Nihal ta kankame kamar za'a kwace mata shi juyawar da tayi ne yasa Sultan zame hannun shi ya koma sama sofa ya kwanta ya dade yana juyi ya rasa meke damun shi kwana nan wani abu na tokare mashi zuciya da kyar ya samu bacci barawo ya sace shi. *WASHE GARI* Kiran sallah asuba ne ya tashi Nihal mika Nihal tayi dauke da addu'a a bakin ta kasancewar baccin jiya ba karamin dadi ya mata ba, ganin ta saman bed ne yasa Nihal zabura ta mike da sauri tana waige-waige tana tunanin me ya kawo ta bed ita dake kwana a sofa, abinda ya faru da ita jiya ne ya fado mata a rai murmushi Nihal ta saki tare da maida gashin kanta baya tace, ashe dai yana da kirki yaye blanket din jikin ta Nihal tayi ta fara takawa a hankali har ta isa bakin sofa ganin ba Sultan ya sata rike kugu tana waige-waige tabe baki Nihal tayi, kasancewar bata sallah gyara dakin ta shigayi yayi fes sannan ta Shige toilet ta sheka wanka ta fito lokacin gari ya fara haske sultan be dawo daga masalaci ba, shafe jikin ta da lotion Nihal tayi sannan ta bud'e drawer ta curo black rigar ta wanda akayi ma dinki kamar bubu, shiryawa Nihal tayi cikin kayan ba karamin kyau Nihal ta zubaba gaban rigar anjera ma shi white stone's masu masifar kyau lipstick Kawai ta shafa ma lips din ta tare da Karewa kanta kallo ta cikin mirror taba goshin ta Nihal tayi abinda ya faru jiyane ya fara dawo mata cikin kwayar idaniyar ta, murda handle din kofa da akayi ne yasa Nihal waigowa har gashin kanta iska na kad'a shi ido hudu sukayi da Sultan wanda shigowar shi yanzu kenan kallan ta sultan ya shigayi tun daga forehead din ta har kafafuwan ta wani irin kyau Nihal din ta Kara mashi, a hankali sultan yake takowa har ya Karaso daf da Nihal wanda itama din kallan shi take tamkar yau suka fara ganin juna su a hankali sultan yasa lalausan Hannun shi ya, talabo da fuskar Nihal yana kallan goshin ta lumshe idanuwan ta Nihal tayi, bin fuskar ta da kallo sultan yake yana kallan yadda eye lashes din ta suka wani kwanta kamar tasa na kanti a hankali Nihal ta bud'e lumsasun idanuwan ta, ta sauke su kan kyakyawar fuskar Sultan, kalaman Dara ne su ka Shiga yimata yawo a brain tana kallan Sultan take tausayin shi na shigar ta jin kamar tayi kuka ne yasa Nihal ja da baya tana maida gashin kanta Baya, kanta a kasa tace, "ina kwana" ko amsar sultan bata tsaya saurara ba, ta raba ta gefan shi ta wuce da sauri, babban kitchen Nihal ta nufa tana Shiga bayi suka zube suna kwasar gaisuwa amsa masu Nihal take cikin sanki fuska Sannan ta umarci Yasmin ta fere mata dankali ita kuma ta daura ruwan flaks cikin dankankanin lokaci ruwa ya tafasa ta juye a flaks lokacin har Yasmin ta gama fere dankalin Nihal bata wani dau lokaci ba ta soya dankalin tare dayin peper soup din yan'ciki ta juye a warmer Yasmin da bariri suka biyo ta da tray din abinci har part din su, suna zuwa bakin kofa Nihal ta dakatar da su tare da amsar tray din Karasawa da shi dining area ta jera komai umarni tabawa su Yasmin da suna iya tafiya idan tana bukatar su zata neme su to suka ce mata sannan kowa ya koma bakin aikin shi, zama Nihal tayi saman two star tare da kuna TV tana kallan MBC2 kamshi turaran Sultan daya mamaye mata hanci ne ya sata dagowa sultan ne sanye cikin suit din shi american rose color yayi kyau sosai sajan nan na shi ya kwanta luf-luf da shi red lips din shi yayi kamar yasa jan baki, Hannun shi na rike da briefcase, ya Allah Nihal kawai ta iya furtawa cikin zuciyar ta kauda Kai Nihal tayi dan kar sultan ya gane tana kallan shi ya raina ta ganin ya nufi dining area yasa Nihal bin shi a baya jan kujera sultan yayi tare da aje briefcase din shi ya zauna, plate Nihal ta janyo tana serving na shi abinci, tana serving nashi Sultan yana satar kallan ta ta kasan ido cikin zuciyar shi yana cewa, why this why do I always looking at her cute face, the most annoying thing yadda nake wasting time ina kallan ta I hate this , tura mashi plate din da Nihal tayi gaban shine ya sashi dawowa daga duniyar tunani a hankali Sultan ya fara cin abinci wani irin dadi abincin yayi ma Sultan jin testing din abincin yake kamar na jiya, amma yadda ya keyi da face na shi se ka rantse abincin ba dadi saboda yadda yake cin magani kamar yana cin mad'aci saboda baya so Nihal taga kamar abincin ya mashi ta raina shi, Nihal ko serving kanta tayi tana cin abinci a hankali da sun hada ido da Sultan se tayi kasa da kanta, shigowar yakumbo dauke da tray abinci ne ya Katse masu tunani lokaci daya itama yakumbo sakatarere tayi tana bin su da kallo tana mamakin waye ya kawo masu abinci, a haka har ta karaso tare da zubewa tana kwasar gaisu tana kokarin aje tray din Hannun ta da sauran bayin dake bayan ta suna kokarin aje na hannun su aje fork din hannun ta Nihal tayi tace, "yakumbo kuna yi tafiya da abincin aba ma wasu, daga yau bana bukatar ana kawo kowani kala abinci ba tare da izinina ba" galala yakumbo tayi tana bin Nihal da kallo tana Kara tabatar da zargin ta akan Nihal jan yan'mata kafafuwan su sukayi tare da kwashe Kayan abincin juyowa Nihal tayi tana kallan fuskar sultan a tunani ta ko ze watsa ta ganin kamar hankalin shi baya kan su yasa Nihal sauke ajiyar zuciya. Gimbiya jalila ce ke zagaye daki tana huci kamar kububuwa tace, "yau ma yariyar nan koroku tayi da kwanikan abincin! Gimbiya jalila ta ida zancan tana zagaye parlour rai bace "wai mi yariyar nan take nufi da amshe ragamar girkin sultan a hannu ta, hakan na nufin ta gano boyayan sirrin mune komi? idan ko haka ne lahira za tayi bakuwa, saboda na tabatar da zargina a kanta fa yau na aika da breakfast shine zata koroku da shi" "Ke ma dai Gimbiya kin gani, gabaki daya yanzu ta mamaye zukatan yan'gidan nan se abinda tace ga yaran nan na lura wani irin so yake mata ko dauke idanuwan shi baya iyawa a gaban mutane idan yana kallan ta se dai mu ce Allah ya kyau ta riga tayi kaka gida mtsww" "tabas ko wata yarinya ta kusa ta zama gawa danni ba'a Shiga gona ta a kwana lafiya, kawar da ita awajena abune mai sauki, idan na kashe ta kin ga se ya fadi ya mutu" Gimbiya jalila ta ida zancan tana dariyar keta can kuma se tayi shuru yakumbo ta dasa da cewa, "Gimbiya kinyi magana Dan yariyar nan kadangaran bakin tuluce me hana a sha ruwa! tsaki Gimbiya jalili ta saki tare da shigewa Daki a fusace. ```Taku har kullun salma mas'ud nadab``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 91_92* A harabar prime college school motar Sultan ta faka a dai-dai bakin hall din exam, a hankali ya dago ido yana kallan Nihal dake makure jikin kofa murmushi Sultan ya saki ganin se faman bud'e kofa take amma ta kasa matsowa yayi dai-dai setin ta har suna jin saukar numfashin juna su, raba hannuwan shi Sultan yayi tare da bud'e wa Nihal kofa yana juyowa karfa suka had'a ido tsare ta da ido Sultan yayi kalaman da Nihal ta fada mashi jiya da dare suka shiga dawo mashi kamar a lokacin take fada mashi, lumshe ido Sultan yayi jikin shi ya kara sanyi sannan ya janye jikin shi ya koma ya zauna tare da gyara zaman suit din shi, tsare shi da ido Nihal tayi tana kallo dagowar da Sultan zayi karfa suka hada ido kauda kai Nihal tayi da sauri zata fice, Sultan ya ruko hannun ta tare da daura mata 1k sannan ya saki hannun ta yana cewa, "zanzo na dauke ki idan kin gama exam" kallan shi Nihal tayi tare da bud'e lalausan hannun ta tare da cewa, "mizan yi da kudin ka sultan, ka amshi kudin ka bana so! Had'e rai Sultan yayi tare da tsare ta da ido yana cewa, "na baki ne saboda Ammi ba saboda kai na ba," tab'e baki Nihal tayi tana cewa, "Nima na amsa ne saboda Ammi kawai" sannan Nihal ta fice daga motar har ta fice sultan na kallan ta, sannan motocin Sultan suka bar harabar makarantar Murmushi Nihal ta saki tare da shakar iska me sanyi a hankali ta furta "Alhamdulillah alakuli hali,! cikin natsuwa Nihal ta karasa hall din da aka tanada dan yin exam tana shiga taga students duk zaune kowa na harkar gaban shi kujerin ne birjik kowani mutum yana da seat daya, a hankali Nihal ta karasa seat ta zauna kallo ne ya koma kanta kasancewar students din basu santa ba suka fara magana kasa-kasa mazan da matan, wadda ke bayan seat din tace tatabota juyowa Nihal tayi fuskarta dauke da murmushi Itama yariyar murmushi ta saki tare da cewa, "sannu ki" "yauwa! Nihal tace sannan yariyar tace, "suna na Nana, ke kuma fa? "Nihal..! Murmush Nana ta saki tana cewa, "amma dai ke external ce" "Eh.! Nihal tace sannan ta juya bata wani dade ba aka fara raba booklet har aka zo kanta, Nihal taji dadi sosai ganin duk abinda ta karanta ya fito cike da jin dadi ta gama exam din ta na English suka fito kafin a shiga basic technology. Fitowa Nihal tayi daga hall tare da zuwa wajan wata resting chair ta zauna tana kallan students dake wuce wa,nana ce ta karaso tare mikawa Nihal hannu suka gaisa murmushi Nana ta saki tare da zama kusa da Nihal tana cewa, "kema baki zuwa break ne" girgiza kai Nihal tayi tana cewa, "bana jin yunwa shiyasa" "Kamar ni kenan" daga mata kai Nihal tayi hira suka taba sama-sama sannan aka koma exam hall nan ma basu wani dade ba, exam tayiwa Nihal dadi sosai tare da Nana suka fito lokacin driver ta ya zo daukar ta kallan Nihal tayi tare da cewa, "tunda gida zaki tafi why not muyi dropping naki" murmushi Nihal tayi tana cewa, "na gode sosai Nana amma munyi da yaya na ze zo dauka ta" daga kai Nana tayi tare da cewa, "toh shikenan ki gaida gida" "Ze ji" Nihal ta fad'a a takaice, har Nana ta bale murfin mota ta juyo tana cewa, "gashi ban amshi number ki ba" "Eyya Nana bani da waya" "Toh shikenan se mun had'e gobe" murmushi Nihal tayi sannan Nana ta shige mota, guri Nihal ta samu ta zauna tana kallan mutane masu wuce wa, ta dau lokaci mai tsaho tana zaune zaman jiran Sultan shuru be zo ba. Motocin Sultan ne suka jeru dan zuwa makaranta daukar Nihal, daya daga cikin yaran Tjee ne dake jingine jiki bishiya ne ya leko ganin motocin Sultan ya sasa watsa busoshi kan titin ji kake tayoyi na bada tas! tus! Suna fashewa Sultan dake zaune a bayan seat ne ganin mota ta tsaya yasa Sultan cema musa driver "mike faruwa.! cikin ladabi yace, "ranka yadade taya ce ta bashe.! b'ale murfin motar Sultan yayi ya fito a tare suka fito da Alex kallan juna sukayi da Sultan sannan Alex, yace, "Sultan ya kamata ka shige mota wajan nan akwai matsala," ya ida zancan yana dukawa yana duba busar dake zube a kasa, shima sultan dukawa yayi tare da kallan busar sannan ya kalli agogan dake makale a hannun shi wayar shi ya ciro da sauri ya shiga Kiran driven shi na gida tare da shigewa cikin mota ya zauna yana duba agogan dake makale a hannun shi gaban shi na kara faduwa, ganin lawali driver be dauka ba yasa Sultan kiran layin Ammar bugu daya zuwa biyu be dauka ba, bangaran Ammar ko yana theater room hakan ne ya hana shi daukar kiran Sultan, hakan yasa dole Sultan ya jira aka gama gyara motar shi badan ya so ba. Iya kar kuluwa Nihal ta kulu ganin Sultan be zo daukar ta ba har students sun watse, dama yace ta jirashi ne dan ya shanya ta agogo dake makale a hannun ta Nihal ta kalla kusan karfe 12:30am dan siririn tsaki Nihal ta saki yanke shawara Nihal tayi kara ta hau kekenapap ta koma gida, dagowar da Nihal zatayi taga wani kato a kanta juyawa Nihal tayi daniyar canza hanya wani katan ne ya tare ta kallan su Nihal ta shigayi na rashin fahimta tsoro na kara shigarta, duk da tsoran da Nihal ke ji hakan be hanata kokarin rabawa ta gefe ta wuce ba, TJee ne ya damko hannun ta a razane Nihal ta juyo tana kokarin banbare hannun Tjee cike da tsiwa Nihal tace, "malam lafiya zaka rike min hannu" Nihal ta ida zancan tana kiciniyar banbare hannun TJee bud'e mata gaban rigar shi yayi tare da nuna mata bindigar dake sakale a kugun shi zaro ido Nihal tayi kafin ta iya furta komai BS ya shaka mata fara hoda, take a nan Nihal ta sulale jikin TJee a sume daukar ta yayi ya daura a kafad'a shi ya tura a mota, sannan shima ya shige suka fisgi motar da karfi suka bar harabar makarantar. Tunda Sultan ya nufo hanyar makarantar gaban shi ke tsanata faduwa har suka karaso harabar makarantar, ganin duk ba students yasa zuciyar Sultan kara tsinkewa har suka isa bakin hall din makarantar isar su tayi dai-dai da lokacin ana kokarin rufe hall din, bud'e murfin mota sultan yayi da sauri ya fito tare da yima security din dake kokarin kule kofar sallamah murmushi malam tukur yayi tare da cewa, "bakar da zuwa yallabai Allah yasa lafiya ai da ka karasa office din principal yana ciki" jikin Sultan ne yayi sanyi cikin honey voice din shi yace, "yariyar na zo dauka yau ta zo zana exam" sakatarere malam tukur yayi yana kallan sultan tare da gyara tsayuwa yana cewa, "Toh fa ai students din da suka zana jarabawa tun kusan karfe 12:00pm suka gama zana pepper, se kuma ta gobe idan Allah ya kai mu" shuru Sultan yayi yana nazari can kuma yace, "baka ga wata yarinya fara ba, yar siririya bata da tsaho sosai" "Gaskiya ban ga kowa ba tunda na zo nan wuri se dai ka dan zagaya cikin makarantar may be tana wani waje tana zaman jiran ka" godiya ya Sultan yayi ma malam tukur tare da komawa cikin mota, juyowa Alex yayi yana kallan sultan yace, "Allah yasa lafiya" shuru Sultan yayi tare da ce ma Alex su zagaya cikin makarantar ko zasu ganta haka suka zagaye makaranta tas ba Nihal ba alamar ta, ko da Sultan yaje office din principal yayi mashi bayani shima ce mashi yayi bega Nihal ba, iyakar tashin hankali Sultan ya shiga da kyar ya iya karasawa cikin mota zuciyar na tsanata harbawa, da kyar ya iya cewa Alex su koma gida may be Nihal din ta koma gida ya ida zancan tare da maida kan shi setin window ******* A cikin wani daji motar su TJee ta faka sannan yasa yaran shi ya dauki Nihal ya kai ta cikin wani gida sama da kasa da alama gidan ya dade ba'a shige shi ba, yana shiga ya aje Nihal saman kujera tare da daure mata hannuwan ta ya fice TJee ya shigo kujera ya ja ya zauna yana facing Nihal da har a lokacin sume take, ruwan dake kusa da shi na sanyi a bokiti ya janyo ya watsa wa Nihal a fuska wata irin ajiyar zuciya Nihal ta sauke a hankali ta sauke idanuwan ta saman fuskar TJee, TJee murdadan mutum ne dogo chocolate colour yana sanye cikin black jean da t-shirt White kafarshi na sanye da black boot, Hannun shi na rike da sigari yana busawa, kara maida ido Nihal tayi ta lumshe saboda har a lokacin idanuwan ta sun mata nauyi biji-biji take gani, dukan table din da TJee yayi ne yasa Nihal razana tana kallan TJee cikin sanyi murya Nihal tace, "inane nan, mi ya kawo ni nan, mina maku? Nihal ta ida zancan a raunane tare da cigaba da cewa, "please let me go! please" Nihal ta ida zancan tana kallan Tjee kamar za tayi kuka tana jijiga kujera da take bisa, matsowa kusa da ita TJee yayi yana murmushi rainin hankali yace "kina tunanin zan barki ki koma gida wajan Sultan ne ko? Toh kinyi kuskure ke da Sultan kunyi hannun riga kina jina! Tjee ya ida zancan yana matsawa Nihal fuska baya Nihal tayi cike da tsiwa hakoran ta a had'e tace, "ka daina tabani! dariya TJee ya saki tare da kallan Bs dake gefen shi yana cewa, "ka ji fa na daina taba ta" dariya suka saki lokaci daya suna kallan Nihal fisgo mata gashin kanta TJee yayi wata irin kara Nihal ta saki saboda azabar daya ziyar ci kanta tana mutsu-mutsu danna kanta Tjee yayi cikin bokitin ruwan sanyi me kankara mutsu-mutsu Nihal take tana neman ceto kanta saboda numfashin ta dake kokarin daukewa, fisgo mata gashi Tjee yayi Nihal ta biyo shi idanuwan Nihal sunyi jawur, tari Nihal ta shigayi saboda shakewa da tayi da ruwa tana maida numfashi hawayan wahala na bi mata kumatu, Tjee na kokarin dan nawa Nihal sigari a wuya, ringing din wayar shi ya katse mashi hanzari ganin number Nazili yasa shi dauka tare matsawa gefe yana cewa, "yanzu haka muna tare da ita duk yadda kike so haka za'ayi" "Zan kira ka Tj idan na gama tsara abinda na ke, yanzu haka nasa an kona kayan ta sannan zan turo maka Aziza da jakar kudi" murmushi jin dadi TJee ya saki yana cewa, "Allah ya ja da kwana Gimbiya" Amin Nazili tace a takaice tare da datse wayar tana murmushin ji dadi, har Tj ya gama wayar ya kashe Nihal na kallan shi tana sauke ajiyar zuciyar wahala Tun kafin drive ya gyara parking Sultan ya fito, part din shi ya wuce da sauri ya bud'e part din shi ganin wayam ba Nihal yasa zuciyar shi kara tsinkewa da sauri ya wuce part din Ammi, yana shiga lokacin yayi sa'a ba kowa parlour bedroom din Nihal ya bud'e ya shiga nan ma wayam kofar toilet ya murda nan ma wayam, bedroom din Ammi ya wuce kwance ya hango Ammi tana bacci kallan ta Sultan yayi take anan jikin Sultan yayi sanyi ya fara zancan zuci to ina yariyar nan zata,dama tayi amfani da zuwa exam ne dan ta gudu ta jefa rayuwar Ammi cikin matsala, me yasa zata aikata haka, da sauri Sultan ya maida kofar dakin Ammi ya kule gudun kar ammi taji motsin shi ta farka, part din mom Sultan ya wuce da sauri lokaci mom na zaune saman three star Sultan ko ganin ta beyi ba ya shiga bud'e daku na, nan ma wayam ba Nihal ba alamar ta wani irin jiri ne ya shiga dibar Sultan da kyar ya karaso parlour ya dafa kujera dan ji yake kamar ya kifa, mom ce ta dafa shi, kallan mom sultan yayi a raunane tare da rungume ta sosai a jikin shi shafa bayan shi mom ta shigayi alamar lalashi ta dago da shi suna kallan juna ta zauna da shi saman kujera sannan ta kama hannun Sultan tana cewa, "son mike damun kane, ina Nihal? mom ta ida zancan tana kallan bayan shi kalmar da mom ta fada se da tasa sultan sankarewa yana kallan ta saboda tsabar firgici tabas Nihal bata dawo gida ba tunda har mom ke tanbayar ta, taba kumatu shi da mom tayi ne yasa Sultan dawowa daga duniyar tunani yana kallan mom da kyar ya iya zayana mata abinda ya faru hankali mom ba karamin tashi yayi ba, a razane ta mike tana cewa, "kana nufin Nihal ta bata daga zuwa zana jaraba, ya Allah ka fadawa yan'sanda sultan? girgiza kai sultan yayi yana cewa, "mom gabaki daya na riki ce ne mom, ban san ta ina zan fara ba" mom ce ta kama hannu shi tare da zama tace, "I now my son dole ka shiga damuwa, ya kamata ka sanar da yan'sanda Sultan, hakan shine kawai mafita kaji" daga mata kai Sultan yayi tare da cewa, "dama yanzu abinda zanjeyi kenan amma mom please karki fadawa kowa saboda idan Ammi taji labari zata iya shiga wani hali" gefen fuskar Sultan mom ta shafa tana cewa ba wanda ze ji kaji" daga mata kai Sultan yayi saboda magana ma nauyi take mashi, Nazili dake makale jikin kofa dama tunda Sultan ya shigo gida ta biyo shi a baya saboda ta san ko be fadawa kowa abinda ke faruwa ba, ze fadawa mom abinda ke faruwa wani irin murmushi samun nasara Nazili tayi tana zancan zuci, lokaci yayi Nazili da hak'arki zata cin ma ruwa, girgiza kan jin dadi Nazili tayi tare da fitowa daga bakin kofa da sauri cikin sigar munafirci tace, "mom! mom da Sultan lokaci daya suka juyo suna kallan Nazili kwata-kwata Sultan be ji dadi ganin Nazili ba dan yasan tana iya fadawa ammi, dafa goshi Nazili tayi tana cewa, "oh my goodness mom karki fada min abinda kunnena ya jiye min da gaske ne" Nazili ta ida zancan tana zama kusa da mom tana cewa, "i new it ai dama na sani tsintaciyar mage bata mage mom, mi yasa zata gudu ta bar Sultan, gashi cikin mu ba wanda yasan gidan su bale kuma family nata, dama haka tallaka yake ka sashi a inuwa shi kuma ya jefa ka a rana na san wannan abun duk cikin plan din tane" Nazili ta ida zancan tana kallan Sultan ta kasan ido murmushi samun nasara Nazili tayi ganin yadda Sultan idanuwan shi sukayi jawur jijiyoyi duk sun fito dafa Sultan Nazili tayi tana cigaba da cewa, "na san duk abinda zan fada lokacin da akayi auran ba wanda ze fahimce ni amma gashi yanzu ta nuna maku true colour din ta, Allah yasa ma ba tayi sata ba kafin ta gudu" zame hannun Nazili Sultan yayi tare da cewa, "Nazili...! Nihal is my wife! ya kamata kisan irin maganar da kike fadi a kanta wannan maganar da kike fadi bata da mahali a nan wajan Nazili, taimako daya zakiyi min shine ki ja bakin ki, kiyi shuru bana so Ammi ta sani am sure kika min haka se kin fi birge ni" da kyar sultan ya mike ze fice daga part din Nazili tace, "Sultan..! ya kamata kayi nazari a kan maganar dana ke, wai me yasa idan nayi magana ba me saurarata yarinyar nan ba sanka take ba sultan kudin ka take so, amma gabaki daya idanuwan ku sun rufe, ya Allah wannan wace irin yariya ce" ko saurara ta Sultan beyi ba ya fice, rike kugu Nazili tayi tana murmushi tana cewa a cikin zuciyar ta idan kaje dakin ka, ka duba drewar kayan ta data kudi ka nan ne zaka iske wayam, daga nan ne zaka fara yarda da magana ta *Sultan salim* sannan Nazili ta juyo kusa da mom ta zauna tana kara ida nufin ta. Haka Sultan ya fito daga part din mom ya wuce na shi, drewar Nihal ya bud'e ganin wayam ba kayan ta yasa Sultan maida kofar da karfi sannan ya bud'e drewar da ya aje jakar kudin shi nan ma wayam, take a nan dakin ya fara juyawa Sultan cikin daga murya yace, "Nihal..! fatali da kayan dressing mirror sultan ya shigayi, yana tuna kalaman da Nihal ta fada mashi jiya da kalaman da Nazili ta fada mashi yau, cikin zafin rai sultan yace, "why Nihal mi yasa kike so ki jefani ciki tashin hankali, me yasa zaki gudu why Nihal" Sultan ya ida zancan yana kara fatali da kayan daki har ya yanke be sani ba, haka Sultan ya rinka sanbatu, murda kofar da akayi ne yasa Sultan tsayawa cak yana kallan kofa tunanin shi ze ga Nihal, ba kowa bane se Ammar da ya shigo da sauri Ammar ya karaso dakin yana kallan Sultan tare da karasowa gaban Sultan ya rike mashi hannun shi dake zubar jini ya zauna da shi saman bed har a lokacin sultan ran shi a bace yake yana maida numfashin Ammar ne yace, "sultan mi ke damun ka har ka ji ciwo baka sani ba, wai me yasa idan ran ka ya baci baka abu na hankali sultan? komai yayi zafi maganin shi Allah" mikewa Sultan yayi ya bud'e mashi drewar yana cewa, "mika gani a nan..! murmushi takaici Sultan yayi yana cewa, "mika gani ta tattare duka kayan ta da kudi na ta gudu, kasan wani abu Ammar ba satar kudin ke ban haushi ba guduwar da tayi saboda san zuciya irin nata tana so ta kashe min Ammi na mi yasa Nihal take so ta karamin tsana ta, da ace ta fadi min abinda ya kawo ta Ammar zan bata tun daga million har abinda yayi sama, tun kafin lamarin nan yayi nisa na tanbaye ta amma a lokacin ta rai na min hankali Ammar, saboda tana san ganin bayan mu nasha fada ma turo ta akayi amma ka ki fahimta kai da Ammi yau gashi ta nuna maku true colour din ta, yanzu se ku cigaba da yaban ta kai da Ammin" Sultan ya ida zancan yana kokarin barin dakin, Ammar da jikin shi yayi mugun sanyi ya san cewa babu inda Nihal zata of coz bata da kowa yanzu se Sultan lokaci yayi da ya kamata Sultan ya san wacece Nihal, daga gani wannan alamarin muta nan dake farautar rayuwar shi ne zasuyi anfani da wannan damar dan ganin cewa sun ruguza mashi farin ciki, cikin sanyi murya Ammar yace, "Sultan ya kamata kabi lamarin nan a hankali be kamata ka dau zafi dayawa ba! juyowa sultan yayi tare da watsawa Ammar wani irin kallo yace, "be kamata na dau zafi ba Ammar..! me idanuwan ka suka gani kana nufin shari zan mata oh what! Sultan ya ida zancan ze fice, "Sultan kwai dalilin da yasa nake tuhumar ka haka saboda na fika sanin wacece Nihal na fika sanin abinda Nihal zata aika ta, da abinda baza ta aika ta ba, babu inda yafi ma Nihal kwanciyar hankali sama da gidan nan sultan..! ko wani hali Nihal ta shiga yanzu ta shiga ne saboda kai ya kamata kayi tunanin sultan" birki sultan ya ci rike da handle din kofa sannan ya juyo yana kallan Ammar dake zubo zance... ```Ta Ku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Assalamu alaikum masoya SAUYIN RAYUWA ina mai baku hakuri da rashin ganin posting dina hidimomi ne suka min yawa shiyasa amma insha Allah komai ze zama normal na gode da soyayyar ku a gare ni_* *Page: 93_94* Babu abinda Ammar ya boyewa sultan a kan rayuwar Nihal yana bashi labarin yana mashi dressing a hannun shi daya ji ciwo Ammar ya ida zancan yana cewa, "Sultan Nihal tana bukatar ka, kai kadai ne gatanta duk yadda na so na fahimtar da kai a farko Sultan Nihal tace nayi mata promise bazan fadawa kowa ba ko ita wacece shiyasa na boye maka" sultan dake kallan Ammar jikin shi yayi sanyi idanuwan shi sun ciko da kwalla, shafa kumatun Sultan Ammar yayi yana cewa, "Nihal ta sha wahala rayuwa tana bukatar *SAUYIN RAYUWA* Sultan she need your help sultan," mikewa Sultan yayi tsaye hannu shi daya na cikin alhiju idanuwan shi sun ciko da kwalla, cikin zuciyar shi yana cewa, "Allah sarki Nihal na baki wahala na zarge ki a kan abinda ba haka bane ki yafemin, dafa shi Ammar yayi a hankali Sultan ya juyo yana kallan Ammar dake kallan shi zama yayi saman sofa saboda kan shi ya kule gaba daya be san ta inda ze fara neman Nihal ba ya kamata ya kira DPO Bilal shi kad'ai ne ze taimake su, Ammar ne yace, "Sulta...! be ida rufe bakin shin ba wayar Sultan ta hau ruri da sauri Sultan ya kai hannu ya dauka ganin bakuwar number yasa Sultan karawa a kunne yayi shuru Nihal ce rike da waya Tjee ya tsare ta da bindiga yana cewa, "idan kika bari sultan ya gane tirsasaki mukayi se na tarwatsa maki kai da harsashi zaki fada mashi abinda na ce maki koko..! wani irin miyau mai daci Nihal ta hadiye hawaye masu zafi na bin kuncin ta da kyar ta iya seta kanta tace, "hello..! sultan dake zaune mikewa yayi tsaye saboda ko a cikin magagin bacci ya ji murya nan seya gane bale kuma ido biyu, shima "hello..! yace, murya shi na rawa, marayan kuka Nihal ta saki me tsuma zuciyar me saurare ta kasa furta ko da kalma daya, ja mata gashi Tjee yayi tare da amshe wayar sultan na jin ihu Nihal zuciyar shi kamar ta fashe saboda jin kuka Nihal yake har cikin zuciyar shi, cikin daga murya yake cewa, hello..! Hello Nihal..! dif sultan yaji alamu an kashe wayar beyi kasa a gwiwa ba yayi saurin danna number amma me se ya ji kashe, a hankali Sultan ya dawo saman sofa ya zauna idanuwan shi sun ciko da kwalla yana jin kukan Nihal cikin ran shi, dafa shi da Ammar yayi yasa sultan dago idanuwan shi da kyar yana kallan Ammar da shima a rud'e yake yace, "muje police station Ammar! sultan ya ida zancan tare da mikewa yayi gaba Ammar ya bishi a baya, fashewa da kuka Nihal tayi fisgo ta Tjee yayi tare da haska Nihal da wawan mari ji kake tas, tas, har se da ta kifa saboda taurarin da ta gani, azaba ma ta hanata kuka se haki da take ta faman yi, fuskar ta tayi butu-butu da kura fuskar ta tayi jawur saboda azaba, a hankali Nihal ta dago tana wani irin ni shi idanuwan ta sunyi jawur a hankali ta kai hannu gefen bakin ta dake zubar jini saboda tsabar marin data sha, dariya Nihal ta saki kamar sabuwar kamu tana kallan Tjee idanuwan ta jawur, ba komai yasa Nihal dariya ba se ganin shima ta bata mashi rai, janyo gashin ta Tjee yayi tare tura mata kan bindiga yana cewa, "shegiya me kama da aljanu i wish an bani damar kashe ki da sena aika ki wallahi, ni zakiyi ma taurin kai na ce ga abinda zaki fadi se ki hau kuka," Tjee ya ida zancan yana bankada Nihal kanta ya daki bango yana cigaba da cewa, "ke da Sultan ko se dai ki ganshi da wata ba dai ke ba, munafuka na tabata sultan ba san ki yake ba keke san shi mima zeyi dake me sufar aljanu mtsww, banza yar matsiya ta wadda ta gaji tsiya" Tj ya ida zancan yana jan Nihal kiii..! ya wurga ta daki me komatsai ya kule, yana ta masifa. da kyar Nihal ta ja jiki ta jingina da bango wani irin kuka ya kubuce mata ga sanyi dake shigar ta saboda yau yini tayi Tjee na sheka mata ruwan sanyi take a nan Nihal ta hau rawar dari hakoran ta na had'ewa. A dai-dai bakin police station sultan ya faka motar shi abinda ya dade beyi ba driving da kanshi, a tare suka fito da Ammar suka shige police station, kai tsaye office din DPO Bilal sukayi masauki dauke da sallama suka shiga Bilal dake zaune yana duba file's ne ya dago fuskar shi dauke da fara'a yana cewa, "yau manyan baki ne a office din nawa" DPO Bilal ya ida zancan yana mikawa su Sultan Hannun suka gaisa tare da nuna masu mazauni kallan su DPO Bilal yayi tare da cewa, "Allah yasa lafiya dai dan naga fuskokin ku sun nuna akwai damuwa" numfasawa Sultan yayi tare da zayanawa Bilal komai ya ida zancan da cewa, "kafin mu zo nan an kira ni da number amma dana bi Layin kashe, please Bilal help me Nihal come back home save please Bilal" sultan ya ida zancan a raunane mika hannu DPO Bilal yayi tare amsar wayar Sultan ya duba number sannan ya kira office ya rubuta statement din sultan tare da rubuta number wayar, kallan sultan DPO Bilal yayi tare da cewa, "koma waye ya kira da Layin ze sake kira daga nan zamu sa tracker mu gane location din inda suke, yanzu zamu bika gida da tracker saboda kowani lokaci suna iya sake kira se muyi tracking wajan" kallan juna Ammar da Sultan sukayi sannan Sultan yace, "why not muje hotel bana so a sani a gida hankalin su ze iya tashi musanman Ammi" toh shikenan bayan sun gama tattaunawa a tare suka fito daga office din DPO Bilal da yaran shi guda biyar. Ammi ce da fitowar ta daga bedroom kenan kallan Dara Ammi tayi dake jera abincin dare a dining ita da Aziza tana cewa, "sannu da aiki jakadiya," sunkuyar da kai kasa jakadiya tayi tare da cewa, "yauwa Gimbiya" kallan parlour Ammi tayi tana cewa, "Ni ko tun da safe ban karasa Nihal a ido na ba" Ammi ta ida zancan tana karasowa dining, Dara dake jera kayan abinci tace, "Nima tun da safe data min sallama zata je zana jarabawa ban kara data a idanuwan ba" Basmal da shigowar ta kenan jan kujera tayi ta zauna tana murmushi tare da daura Hannun ta saman na Ammi tana cewa, "Na san cewa Nihal na tare da yayana saboda yayana baya bari Nihal tayi nisa da shi ko kad'an, nima tun dazu nake cigiyar ta ban gantaba gashi ina so ta rakani shopping," "Allah yasa lafiya" Ammi ta fada daukar wayar ta Basmal tayi tare da fara kiran layin sultan Amma shuru be dauka ba janye wayar tayi a kunnan ta tare da ajewa, murmushi Basmal tayi tana cewa, "Ammi nafi tunanin yayana yana tare da Nihal saboda tun dazu ban gan shi a gida ba, kin gama yaki daukar Kiran hakan ya nuna suna tare suna shan soyayya" lumshe ido ammi tayi tana cigaba da cin abincin ta, mom da shigowar ta kenan taji zancan da su Ammi suke jikin ta kara sanyi yayi Dara ce ta ja mata kujera ta zauna Ammi ce ta tari numfashin ta da cewa, "Ni ko Sultan ya fadi maki ina zasu je shi da Nihal..! Da sauri mom ta dau ruwa a glass cup tana sha ta aje tana yak'e tace, "be fada min ba Amma na san suna taran ma..! Mom ta ida zancan tana kawar da maganar. Turo kofar dakin da akayi ne yasa Nazili juyowa tana kallan Aziza hannu ta nad'e a kirji tana sanye cikin red shirt da black wando me kamar bagi kanta yasha parking tace, "kin kai ma Tjee kudin shi,? "Gimbiya na bashi" "ina fatan baki dau ko sisi ba," "Gimbiya ban dau komai ba, ya za'ayi na ci amanar ki" "Da kyau..! aikin ki na kyau" bedside drewar Nazili ta bud'e tare da ciro bandil din 1k tace, "gashi wannan naki ne" murmushi Aziza tayi tare da amsar kudin tana juyawa tace, "Allah ya ja da ran Gimbiya insha Allah sultan ya zama naki," murmushi jin dadi Nazili tayi tana cewa, "yama zama nawan..! dama can nawan ne" Nazili ta ida zancan tana tsare Aziza da ido ita kuma tana murmushi taya Nazili samun nasara, har zata fice ta juyo tana cewa, "Gimbiya naji dazu da muna jera kayan abinci a dining Ammi na tanbayar ina Nihal? Murmushi Nazili ta saki tana cewa, "Nihal..! Ai yanzu babu wata Nihal se dai sultan da Nazili" bakin window Nazili ta tsaya tana cigaba da cewa cikin zafin rai, "zanga waze ceci wannan yarinya Nihal se na batar dake a cikin zuri'ar gidan nan.! Nazili ta ida zancan tana cije hakora sannan ta juyo tana kallan Aziza tace, "kina iya fita idan ina neman ki zan kira ki ki samin ido a kan abinda ke faruwa," daga kai Aziza tayi tare da ficewa cike da murya. A harabar hotel motar sultan ta faka data yan'sanda a tare suka shige hotel din kasancewar tun kafin su iso sunyi bucking har an tanadar masu daki keys din suka amsa suka shige a tare, ciki da parlour ne da 2 bedroom, a parlour yan'sanda suka jera tracker su koda za'a kira layin sultan karo na biyu, su gane location din wajan, baki window sultan ya tsaya yana tuna moment din shi da Nihal lumshe ido yayi zuciyar na kara suya dafa shi da Ammar yayi ne ya juyo suna kallan juna mika mashi waya Ammar yayi tare da cewa, "Ammi..! cikin sanyi jiki Sultan ya mashi wayar ya kara kunne se da ya saisaita kan shi sannan yace, "Hello matar..! Daga dayan bangaran Ammi ta washe baki tana cewa, "Tun dazu nake kiran layin ka sultan shuru baka dauka ba Allah yasa lafiya..! Lumshe ido sultan yayi yace, "lafiya lau Ammi" "Masha Allah Nihal na kusa da kai ne? Idanuwan sultan tuni suka kawo kwalla da kyar ya iya furta "eh, kuma yau ba'a gida zamu kwana ba Ammi we need some space" murmushi manya Ammi ta saki na jin dadi sannan ta cigaba da cewa, "duk san da zakuyi nisa irin haka Ka rinka sanarwa sultan," "OK" sultan yace, Ammi ce ta katse mashi tunani da cewa, "bani Nihal naji muryar ta tun safe raban dana ji ta" wani irin miyau me daci sultan ya hadiye tare da cewa, "Ammi Nihal na bathroom idan ta fito zan gaishe maki da ita" sultan ya ida zancan tare datse kiran yana kallan Ammar, Ammar ne yace, "sultan ya kamata kasa ma cikin ka wani abu I think tun safe raban ka da abinci" "Bana jin yunwa Ammar fata na aga Nihal shine kawai, of coz saboda ni ta shiga matsala" sultan ya ida zancan yana goge hawayan da suke kokarin zuba mashi ya cigaba da cewa, "da kunne na naji kukan Nihal tana neman taimako amma bayan da zanyi saboda ban san ina take ba, ba san ta ina zan fara ba, me yasa duk wanda ya rabe ni se ya shiga wani hali Ammar,? Sultan ya ida zancan hawaye sirara na bin kuncin shi da sauri yasa hannun ya goge shima Ammar idanuwan shi sun ciko da kwalla yana kallan Sultan da tsantsar damuwa, cikin sanyin murya Ammar yace, " insha Allah Nihal zata dawo gida lafiya sultan ka rage damuwa insha Allah se asirrin wanda ke bibiyar rayuwar ka ya tonu," sultan yace, "Amin! cikin sanyi murya Ammar ya katse shuru da cewa, "Sultan you have to take some food" Ammar ya ida zancan yana mikawa Sultan glass cup daya hada mashi tea me kauri amsa sultan yayi tare da zama saman kujera kurba daya zuwa uku Sultan yayi ma tea din ya aje yana cewa, "Ammar dole na damu rayuwar mutum biyu aka jefa cikin matsala Ammar duk saboda ni, ban san wani irin hali Ammi zata shiga ba idan taji labari..! bana san abinda ze taba Ammi Ammar" Lallashin Sultan Ammar kawai yake da ban baki. ********* A hankali Nihal ta mike tsaye tana ingishi bakin kofar taje ta murd'e amma kule hawaye masu zafi ne suka zubo mata bubuga kofar Nihal ta shigayi tana cewa, "ku bude min please ina so na shiga toilet please" Nihal ta ida zancan tana zamewa bakin kofa tana hawaye bud'e kofar da akayi ne yasa Nihal mikewa da sauri tana kallan BS dake maka mata harara, kai a kasa Nihal tace, "ina so na shiga toilet" dan siririn tsaki BS ya saki tare da cewa, "biyo ni" simi-simi Nihal tabi bayan BS suka fito har parlour lokacin su Tjee na zaune suna shaye-shaye suna daririku, kallan ta Tjee yayi tare da tabe baki BS ya nuna mata toilet, shiga Nihal tayi tare da sakin kuka har Nihal ta gama abinda take tana kuka tare da dauro alwala, har zata fito ta leka window toilet din dan kararamine tsaki Nihal ta ja cikin sanyi murya tace, "Allah ka fidda ni cikin wannan tashin hankalin ya Allah" Nihal ta ida zancan tana goge hawayan ta da bayan hannun ta, simi-simi Nihal ta fito daga toilet tare da maida kofar ta kule cikin sanyi murya tace, "zanyi sallah please a taimaka min da waje inda nake bazeyi sallah ba" kallan juna BS da Tjee sukayi da sauran yaran Tj sannan Tj yace, "kaji min iyayi har wata damar sallah gare ki ji ta fa, malama ba mu waje kona babbala ki" TJee ya ida zancan cikin daka tsawa kuka Nihal ta saki saboda tsabar razana BS ya tasa keyar ta yana cewa, "wuce muje malama" Nihal na hardewa BS ya tasa ta gaba wayar da Nihal ta hango ne saman center table yasa Nihal rugawa da gudu tayi bakin kofa tana murdawa tana cewa, "somebody help me a taimake Ni dan Allah" dariya Tj da sauran yaran shi suka saki fisgo ta BS yayi ya wurgo ta tsakiyar parlour, Tjee dake zaune ne ya fisgo ma Nihal gashin ta kuka Nihal ta saki tana rike hannun Tj saboda azabar da take ji daka mata tsawa Tj yayi yana cewa, "kina tunanin zamu barki ki iya fita ne? Idan ma kina wannan tunanin ki daina" ya ida zancan tare da hanbare Nihal, kanta ya da ki center table kuka Nihal ta saki tana maida numfashin tare da fakar idanuwan su Tj ta janyo wayar Tj ta tura cikin rigar ta, fisgo hannuwan ta BS yayi yana ja Nihal na kuka har ya wurga ta daki, sauke ajiyar zuciya Nihal tayi tare da fido wayar tana rokwan Allah yasa wayar ba password cikin sa'a ko babu number's din wayar ta shiga dubawa da kyar ta iya gano number sultan da sauri ta danna kira, su sultan dake zaune suna jiran tsamani ringing din wayar shine ya ja hankali kowa na parlour har DPO Bilal alamar da hannu DPO Bilal yayi ma sultan da sauri Sultan ya kai hannu ya dau wayar ganin number da aka kira shi da ita dazu ce yasa yayi ma DPO bilal alama, a hankali ya kara wayar a kunne Nihal ce tace, "hello...! Sultan please help out sultan zasu kashe ni dan Allah ka taimake ni..! Nihal ta ida zancan tana sakin kuka muryar sultan na rawa duk ya rud'e ya rikice yace, " kina iya gane ina kike yanzu..! wawaigawa Nihal tayi tare da fashewa da kuka tace, "nima ban san inda nake ba Sultan ban sani ba..! Nihal ta ida zancan tana kara rushewa da kuka cikin calm tune sultan yace, "calm down Nihal ina nan zuwa na daukeki mu dawo gida kin ji Nihal" Jan majina Nihal tayi tare da kankame wayar tana cewa da "gaske sultan..! "Eh mana Nihal ki kwantar da hankali ki, ki daina kuka, Nihal kuka baya yima cute face naki kyau ko kad'an" murmushi jin dadi Nihal tayi take a nan ta shiga goge hawayan fuskar ta kamar Sultan na gaban tana sauke ajiyar zuciya har cikin ran shi Sultan yake jin Nihal shima da ze samu dama ba abinda ze hana shi zubar mata da hawaye saboda ta bashi tausayin cikin honey voice din shi Sultan yace, "kin ci abinci..! girgiza kai Nihal tayi kamar sultan na ganin ta tace, "ban ci komai ba tun safe" Nihal ta ida zancan kuka na kubuce mata, banko kofar da akayi ne yasa Nihal razana wayar hannun ta ta fadi tana juyo muryar sultan na magana damko ta Tj yayi ya kifa mata mari yana cewa, "amma dai ke anyi tsinaniya mu zakiyiwa ta yan'duniya" bangaran sultan ko rud'ewa yayi yana cewa, "hello Nihal..! yana juyo saukar marin da Nihal ke sha dif yaji wayar ta mutu baya-baya sultan yayi kamar ze sume saboda jirin dake dibar shi Ammar ya tare shi ya zauna da shi sultan da Ammar kuka suka saki bame lalashin wani saboda duk abinda ake kowa na ji DPO Bilal ko jikin shi yayi mugun sanyi shima kamar yayi kuka daurewa kawai yake da kyar ya iya furta "Sultan karka damu mun gane location din wajan ya kamata mu wuce can din..! DPO Bilal ya ida zancan yana bama yaran shi umarni da sauri Sultan da Ammar suka mike wani irin dadi ne ya lullube sultan da sauri suka fice. "Oh my goodness wannan yarinya ta gama damu wallahi we have to do something, BS daure min ita bari nayi sauri naje na dawo" parlour Tjee ya koma tare da cewa yaran shi, "you guys ku hada kayan ku yanzu zamu bar wajan nan," wayar BS Tj ya dauka ya fara kiran Nazili amma shuru bata dauka ba saboda lokacin tayi nisan bacci komawa dakin Tj yayi tare da finciko Nihal se ihu take tana cewa, "ka sake ni babu inda zani se Sultan ya zo..! Nihal na maganar tana kuka tana cigaba da cewa, "dan Allah Ku rabu dani wai me yasa baku da imani ne, mi na makune dan Allah..! mari Tj ya kara zabgawa Nihal yace, "saboda ki na san sultan shi yasa" Tj yayi maganar cikin daka tsawa idanuwan Nihal jawur tana kallan Tj ta dauke wuta Nihal tayi cikin zuciyar ta tana cewa waya ce maku ina san shi me ze sa na so mutumin da baya so na kenan shi yasa a cutar da ni haka, tura ta cikin mota Tj yake amma Nihal ta rike kofar motar tana kiciniyar guduwa kan bindiga BS ya makawa Nihal take a nan ta sulale sumamiya, ajiyar zuciya suka saki Tje yace, "good job my guy, yarinyar nan kwai taurin kai kamar karuna..! sannan suka shige cikin motar big boy ya fisgi motar da karfi suka bar harabar dajin. A cikin dajin motar sultan ta faka da sauri Sultan ya bud'e murfin mota ya fito DPO Bilal na kwalla mashi kira ko saurara shi beyi ba ya nufin gidan suka bishi a baya, DPO Bilal ne ya sha gaban sultan yana cewa, "Sultan ya kamata mu bi komai hankali be..! matsar da DPO Bilal yayi ya shige gidan zuciyar na tsana ta bugawa da karfi a hankali yasa hannun ya bud'e kofar gidan ya shiga, da kayan maye ya fara cin karo wuce parlour sultan yayi yana cewa, "Nihal..! Nihal..! da karfi yana bud'e daku na gidan a haka har ya karasa dakin da aka kule Nihal hijab din ta kawai ya gani da igiyar da aka daure ta, amma gida wayam ba mutane dukewa Sultan yayi kasan wajan hawaye Masu zafi na bin kuncin shi yana cewa, "Nihal duk Nina ja maki wannan wahala kwata-kwata baki dace zama da mutum irin na ba..! sultan yana maganar yana kuka haka sultan ya rinka sanbatu DPO Bilal ne ya riko Sultan dan da karya suka iya banbare shi daga gidan yana duke yana kuka rike da hijab din Nihal kamar karamin yaro, haka suka tura shi cikin mota yana suraitai kafin ka ce min zazzabi me zafi ya saukowa sultan haka suka karasa da sultan hotel kaitsaye daki aka kai shi aka kwantar da shi Ammar yaduba shi tare da yi mashi allura sannan ya kara mashi drip saboda rashin cin abinci da yake, Sultan na kwance hawaye na bi masha fuska yana sauke ajiyar zuciya jefi-jefi a haka allura baccin da Ammar ya mashi ta fara aiki a hankali bacci ya fara fizgar shi har bacci ya dauke shi. A dai-dai kofar wani gida na katako ginin turawa cikin daji gidan yake ba motsin kowa se kukan tsintsaye dana shanu dake tashi motar su Tj ce ta faka, BS ya dauki Nihal a kafad'a ya shiga da ita gidan tare da shin fid'e ta saman kujera, Tj da shigowar shikenan harara ya maka wa Nihal kamar tana ganin shi yace ma BS, "dauke min wannan abar ka kai min ita ciki na tsani ganin ta wallahi, Nazili ta had'a ni da aiki gashi na kira wayar ta dan wulakanci taki dauka mtsww" simi-simi BS ya dauki Nihal ya shige da ita daki ya fito ya kule ta, a hankali Nihal ta bud'e lumsasun idanuwan ta dafe da goshi jikin ta yayi rau saboda zazzabin dake damun ta a haka ta mike kamar yar'maye tana bin bangwan dakin haskyen dakin Nihal ta kuna tare zuwa bakin window dakin tana jijigawa tana kuka tana cewa, "se na fita daga gidan nan" amma ta kasa bud'ewa se ma yankewa da Nihal tayi yar kara ta saki tare da kama hannun tana kallo babu abinda ya fadowa Nihal a rai se sultan duk rigimar da suke baya bari ta shiga wani hali tunawa tayi da ranar da ta bige da center table sultan duk ya bi ya damu ko ba komai Sultan na da kirki share hawayan ta Nihal tayi ta jingi da bango a hankali bacci ya fara dauka Nihal tana rawar sanyin. *Washe gari* A hankali sultan ya bud'e idanuwan shi gami da zame blanket din jikin shi drip din da ya gani makale Hannun shi ya cire tare da sauke santala-sanlata kafafuwan kasa, kwata-kwata be jin kwarin jikin shi a haka ya mike ya nufi toilet har ze shiga ya sauke idanuwan shi saman center table dake dauke da tray din abinci saman, kallo daya yayi ma abincin tare da kauda kai ya shige toilet cikin kwamin wanka ya shiga ya lumshe idanuwan shi yana tuna abubuwan da suka faru jiya, a haka dai har ya kamala wankan ya fito sanye da bathrobe direct dressing mirror ya nufa ya shafe jikin shi da lotion sannan ya dau ash suit din shi da Ammar ya aje mashi saman sofa haka dai ya shirya babu wata walwala fatan shi daya yayi tozali da Nihal yana gyara necktie din shi aka turo kofar dakin a hankali ya dago ya sauke idanuwan saman fuskar Ammar da ya shigo, cikin sanyi murya Ammar yace, "ka tashi lafiya,? shuru sultan yayi dan be da amsar tanbayar da Ammar ke mashi wani irin ya tashi lafiya bayan yau kwana daya da bacewar yarinyar mutane har ya gama shiryawar shi be ce ma Ammar k'ala ba yana kokarin fita Ammar ya ruko hannun shi yace, "sultan ko break ba kayi ba ya kamata ka sama cikin ka wani abu be kamata ka zauna da yunwa ba please k a ci wani abu," "Ammar bana san cin komai bana jin yunwa," "kawai ka fada ne amma kana jin yunwa sultan jiya fa tea kawai ka sha bayan nan baka kara cin komai ba, I can't allow you with an empty stomach please ka daure ka ci wani abu" da ban baki da komai Ammar ya zaunar da sultan ya hada mashi tea mai kauri ya mika mashi tare da tura mashi plate din chips kad'an sultan ya ci abincin ya aje. ****** Turo ma Nihal plate din abincin BS yayi kallan abincin Nihal tayi tare da kauda kai wasu hawaye masu zafi suka sulalu mata a zuciyar tana cewa wannan wace irin rayuwa ce yaushe ne zata samu *SAUYIN RAYUWA* hannu tasa ta goge hawayan fuskar ta da bayan Hannun ta tsaki BS ya saki yana cewa, "ka ji min shegiya kin samu an kawo maki abincin ma har wani kauda kai zakiyi, oh ba irin shi kike ci ba ko, idan baza ki ci ba se in cinye dama wanda na ci be isheni ba," wayar shi dake ruri ce ta katse mashi tunanin sunan Nazili da ya ganine ya sasa ficewa da sauri dan ya mikawa Tjee zaune a parlour ya sami Tj tare da mika mashi waya yace, "Nazili ce..! hannu Tj ya sa ya amsa tare da cewa, "hello..! Nazili dake zaune Aziza na mata massage tana sanye cikin sleeping robe din ta white tace, "Tj Allah yasa lafiya ina tashi naga miss calls naka na kira wayar bata shiga ba," tsaki Tj ya saki yana cewa, "ke dai bari Gimbiya" nan da nan ya kwashe abinda ya faru ya fadawa Nazili mikewa tayi tsaye tana cewa, "amma dai anyi matsiyaciya idan ta san wata bata san wata ba, zan turo ma number sultan ka kira shi ka fada mashi inda kuke ka ce ya kawo 20 million kar ya zo da police yana zuwa ku kashe Nihal din a gaban shi ka ga shikenan na huta kuma kun huta" dariya Tj ya saki daga dayan bangaran yana cewa, "Gimbiya kin fini mugunta nima na so na gama da ita amma ba'a gaban shi ba amma tunda kin ce haka, to hakan za'ayi kin ga daga nan ze fidda rai a kanta tunda yaga gawar ta..! murmushi Nazili ta saki tare da katse wayar hannu ta tana murmushi a zuciyar ta tana cewa lokaci yayi da Nihal zata bakunci lahira ko tana so ko bata so dole da barmin sultan, sultan nawa ne ni kad'ai murmushi ta kuma saki tare bazar da gashin kanta sannan tace, "Aziza had'e min ruwan wanka yanzu zan fita ina da meeting" murmushi Aziza ta saki tare da shigewa toilet da sauri dan had'ewa Nazili ruwan wanka. ********** Ringing din wayar sultan ce ta katsewa su DPO Bilal hira da suke a parlour daukar wayar DPO Bilal yayi tare da nufar dakin da Sultan yake ya mika mashi wayar a hankali yasa hannu ya amsa ya kara a kannu ne tare da cewa, "hello..! Tj dake kusa da Nihal yace, "sultan..! ya ida zancan yana shekewa da dariya ya cigaba da cewa, "idan kana san matar ka ka zo ka amshe ta amma se k zumin 20 million cash idan kuma baka san ta," Tj ya ida zancan yana jawa Nihal gashi ya kara wayar a dai-dai Nihal Sultan na jiyo ihu Nihal da kukan ta, Tj ya kara wayar a kunnan shi yana cewa, "mi ka ji..! cikin rawar murya Sultan yace, "please ku daina taba ta duk abinda kuke so zan baku amma karku salwantar da rayuwar ta please" "Bazan mata komai ba idan zaka bada abinda muke bukata' amma idan baka kawo kudin ba se na kashe ta, sannan gargadi na biyu bana san ka zo min da police ko daya, ka zo min da police se na kashe ta nama fada ma," sannan Tj ya saki murmushi yana cigaba da cewa, "ko ban fada ma inda nake ba na san ka sani, saboda kana zagaye da police, na baka nan da 2 hours idan baka zo ba se na kashe ta..! Tj ya ida zancan tare da kashe wayar mikewa sultan yayi da sauri suka fice da DPO Bilal banking suka wuce su duka se da Sultan ya ciro kudin nan cas ya zubasu cikin briefcase din shi sannan yasa briefcase din a boot, DPO Bilal ya tari numfashin Sultan yana cewa, "Sultan ka kwantar da hankali ka muna biye da kai ga wannan abun kasa a kunnan ka duk abinda ke faruwa zamu sani," amsa sultan yayi yasa a kunne Ammar ya daga kafadar shi yace, "Allah ya maido ka lafiya" smile Sultan ya saki yana fatan Allah yasa ba abinda ya sami Nihal jin kamar idanuwan shi sun kawo ruwa yasa ya shige mota, tare da ja ya bar harabar Bank din DPO Bilal da yaran shi na biye da shi a haka Sultan ya karasa dajin ba motsin kowa se tsintsaye da bishuyoyi dake kadawa haka ya rinka shiga har se da hango gida sannan yayi parking motar shi ya tsaya, message Tj ya turo mashi yana cewa, "ka fito daga cikin motar kudin mu matar ka..! a hankali sultan ya fito daga mota ya bud'e boot ya fido briefcase din shi ya tsaya jikin mota yana waige-waige ina ze ga sun bulo , Tj ne ya damko Nihal fuskar shi a rufe ya tsare Nihal da bindiga suna tafiya tana mutsu-mutsu fuskar ta kumbura saboda tsabar duka uniform din jikin ta biyar baka siyan su saboda dati ga gefan bakin ta daya fashe jini kwance a bakin, sultan na hango ta ya taso da sauri kamar yayi kuka itama Nihal din kuka take ganin sultan, nuna shi da bindiga Tj yayi yace, "karka kara matsowa na fadama," daga hannun Sultan yayi yaci birki tare da aje briefcase din shi a kasa DPO Bilal da yaran shi na bayan bishiya suna kallan abinda ke faruwa sultan na aje kudin ya kara matsowa yana kallan Nihal dake shabar kuka shima da kyar yake controlling kanshi ji yake kamar yayi kuka alama Tj yayi BS dake gefe ya je ya dauki briefcase din da Sultan ya aje, rike da bindiga BS ya karasa ya dauki briefcase din big boy ya faka mota BS ya tura kudin cikin mota ya shige, tura Nihal Tj yayi ta tafi taga-taga zata fadi da kyar ta mike zata karasa wajan sultan tana kuka DPO Bilal da yaran shine suka fito da sauri kafin sunyi aune ji kake daram-daram harbin be sauka ko ina ba se gefan cikin Nihal tsayawa tayi cak hawaye azaba na bin kuncin ta Sultan dake jikin mota da karfi yace, "Nihal..! gabaki daya dajin se da ya amsa da gudu ya nufo Nihal gabaki daya yaran DPO Bilal fitowa sukayi suka bi Tj da yaran shi ji kake an kara dauke Nihal da wani harbin dukewa Nihal tayi dafe da ciki yana zubar jini, Sultan na karasowa Nihal ta fadi kasa dafe da ciki jini na bin bakin ta idanuwan ta na fidda ruwa janyo ta Sultan yayi jikin shi bakin shi na rawa yana shafa kumatu yace, "please Nihal ki bud'e idanuwan ki Nihal, dan Allah karki mutu " gabaki daya Sultan ya rud'e ya gigice idanuwan shi sunyi jawur jijiyoyi duk sun taso, a hankali Nihal ta bud'e idanuwan ta dake fidda hawayan wahala ta daura hannun ta saman fuskar sultan hawaye na bin kunci ta da kyar ta iya furta, "sultan bakin ta na rawa sannan ta saki smile a hankali idanuwan ta suka rufe wani ihu Sultan ya saki yana jijiga Nihal ganin bata motsi ya fashe da kuka......... ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 95_96* Daukar Nihal sultan yayi cak ya karasa da ita bakin mota back sit ya bud'e ya kwantar da ita, shafa kumatun ta Sultan yayi tare da goge hawayan shi da bayan hannu maida kofar yayi da sauri ya rufe ya zagaya front sit ya zauna da gudu ya figi motar ya bar harabar dajin, yana gudu ya juyawa yana kallan Nihal hawaye na zubu mashi yana cewa, "baza ki mutu ba Nihal insha Allah baza ki mutu..! a haka ya karasa asibitin shi yana isa harabar asibitin yayi wani wawan parking da sauri ya zagayo ya dauki Nihal har a lokacin tana zubar jini bata motsi, da gudu nurses suka karaso da gado aka daura Nihal aka karasa shiga da ita cikin Asibiti har a lokacin sultan na makale da Hannun Nihal dayan hannu shi na zaman kanta, har se da aka karaso theater room sannan doctor amir yace, "sultan ka kwantar da hankali ka zamu duba ta insha Allah zata warware" goge hawayan idanuwan shi Sultan yayi yana cewa, "da gaske Nihal zata tashi.? bana so ta mutu amir, dan Allah karka bari Nihal ta mutu dan Allah amir, Nihal ta mutu bazan yafewa kai na ba Amir," sultan ya ida zancan yana sakin kuka zauna da shi Amir yayi yana lallashin shi yana cewa, "Insha Allah lafiya lau zamuyiwa Nihal aiki ta mike insha Allah zamu samu nasara ceto rayuwar matar ka" daga kai sultan yayi yana kokarin tsaida hawayan dake neman zuba mashi, sannan doctor Amir ya wuce office da sauri ya shirya cike da tausayin abokin nashi, da sauri ya wuce theater room sultan na bakin kofar yana zarya yana hango operation din da akewa Nihal ta glass door, white shirt din shi ko duk ta baci da jini jirin da yake ganine ya sasa samun waje ya zauna ya jingina da kujera, Ashad da fitowar shi daga office kenan ya hango sultan, ko ba'a fada mashi ba yasan yana cikin matsala har ya taka ya karasa wajan shi se kuma ya ci birki, yana cewa, "to ina ruwa na da matsalar shi, nurse din da ya ganine zata wuce yasa Ashad cewa, "sister naja..! Juyowa sister naja tayi Ashad ya karaso wajan ta yana cewa , "Sister naja mike faruwa da yayana.! Ashad ya fada cikin sigar damuwa nan da nan sister naja ta kwashe abinda ya faru ta fadawa Ashad ta ida zancan tana cewa, "Boss ya bani tausayin yana san matar nan ta shi koma waye ya aika ta masu haka Allah se ya toni asirri shi" sister naja ta fada idanuwan cike da kwalla sannan ta wuce Ashad wani irin dadi ne ya lullube Ashad shafa gemun shi yayi yana cewa cikin zuciyar shi daga gira Ashad yayi yana cewa, to waye ze aika ta haka dama bamu kad'ai ke farautar rayuwar wannan shashashan nan ba, tura hannuwan shi Ashad yayi cikin aljuhu yana cewa, Amma na san wannan aiki Momi ce zata aika ta ba tare da ta sanar da ni ba yaushe ta fara abu ba tare da shawara ta ba? i wish tare dani aka shiga da ba abinda ze hanani aikata lahira se ya ida haukacewa gabaki daya, Ashad ya ida zancan yana ficewa daga asibitin da sauri dan be so Sultan ya ganshi ya katse mashi hanzari parking space ya wuce tare da shigewa back sit driver ya ja suka bar harabar asibitin zuciyar shi cike da gulma. Bangaran su DPO Bilal yankawa sukayi jeji suna bin su Tj kasancewar Tj be samu nasara shiga mota ba, gudu ya shigayi cikin jejin amma se dai kash su DPO Bilal sun cin mashi birki ya ci tare daga Hannun shi sama DPO Bilal yace, karka kara ko motsi daya ka tsaya inda kake" murmushi Tj ya saki yace, "A kan wani dalilin zan tsaya na tsaya a sani gidan yari tsawan shekaru har se na jigata kwata-kwata rayuwa ta bata dace da gidan yari ba ni bazani gidan yari ba na samu SAUYIN RAYUWA" juyawa Tj yayi ya cigaba da gudu DPO Bilal beyi kasa a gwigwa ba ya dauke Tj da harbi dukewa Tj yayi yana kallan DPO Bilal da kyar ya iya daga hannu ya nuna idan shi dana DPO Bilal take a nan ya sulale sumame yaran shi DPO Bilal yasa suka dauki Tj suka tura a mota dan wuce wa da shi asibitin, su BS da suke cikin mota suna jin saukar Harbin rintsi ido BS yayi yana cewa, "shit..! Ya ida zancan ya dukan sitiyarin mota yana cewa, "an gama da mu ya kamata na kira Nazili ta san halin da ake ciki..! har motar su DPO Bilal ta wuce motar su na fake a karkashin bishiya iyakar rud'ewa sun rud'e fisgar motar su sukayi da karfin dan barin wajan. Nazili dake zaune a kujera office din ta ta daura kafa daya kan daya tana sanye cikin white shirt da jeans blue kafarta na sanye cikin boot gashin kanta ya wani nanad'e ya zubo har gadan bayan ta, murmushi take tana juya kujera tana tunanin yanzu duk halin da ake ciki an aika Nihal lahira, ringing din wayar tane ya tashe ta zaune number BS data ganine ya sata sakin murmushi saboda ta san by now sun aika Nihal lahira hannu tasa ta dauka tare da kara wayar a kunne abinda Nazili taji ne ya sata mikewa tsaye tana cewa what..! kuna mi haka ta faru, shit what a fuch is this kun watsa min tsarin yanzu shi Tj yana hannu yan'sanda, na shiga uku..! katse wayar hannu ta Nazili tayi tare da aje ta saman table tana cewa, "shit..! shit..! Wannan wani irin shirya me ne" barbaza gashin kanta tayi tare da furta, "na shiga uku asirri na ya tonu, ya Allah wannan wani irin bazan ci ne irin na matsiya ta, suna mi har police su kama su" da sauri Nazili ta dauki car key din ta da handbag din ta tana cigaba da cewa, "ya kamata na tsaida Tj kafin ya tonamin asirri ya kamata nayi wani abu" tana fitowa ta ci karo da sakatariyar ta cikin ladabi tace, "Boss ina zaki je saboda inda an zo neman ki na fadawa masu neman ki" harara Nazili ta maka mata tace, "be zama dole duk inda zani se an sanarwa duniya ba kawai ki ce bana nan" haka Nazili ta baro cikin office din ta ta wuce parking space ta shige motar tare da fisgar motar da karfi kamar zata tashi saman. Ashad ne ya shigo part din Gimbiya jalila yana cewa, momi..! momi..! Gimbiya jalila da bayi ke mata tausa alamar tayi masu da hannu su fice sannan Ashad ya shigo bedroom yana kallan ta rike da kugu yana cewa, "i now it by this time zan same ki ciki nishadi da an nashuwa, tunda kin sa a kashe matar sultan ba tare da sanina ba..! mikewa Gimbiya jalila tayi zaune tana cewa, "bangane statement din ka ba kara maimaitawa na ji" dariya Ashad ya saki tare da fadawa saman sofa yana cewa, "yanzu dai tana asibitin plan din ki ya rushe se ki kara wani," harara Gimbiya. Jalali ta makawa Ashad tana cewa, "ban san shashanci ni yaushe na samu damar aika ta hakan bayan bana kasar munyi tafiya da maimartaba da yaushe hakan ta faru,? sakatarere Ashad yayi yana kallan Gimbiya jalila yana cewa, "Momi karki ce min ba ke kika kaiwa matar sultan hari ba" girgiza kai Gimbiya jalila tayi tana cewa, "gaskiya bani bace amma waye ya rigamu aika ta abinda mukayi niya dama ba mu kad'ai ya zamar ma kadangaran bakin tulu ba," murmushi Gimbiya jalila tayi tare da mikewa tsaye tana cewa, "zan so naga kowa wanene ko dan mu had'a karfi da karfi mu tarwatsa wannan yaro, koma waye ze aikata haka" dariya Gimbiya jalila ta saki tana cewa, "baya wuce Nazili ita kadai ce na san zata aikatawa Nihal haka amma bamu da tabas, idan ko ita ce ta cika mai zafin nama," Gimbiya jalila ta ida zancan tana shekewa da dariya mugunta, "kasan wani abu my son nasan cewa yanzu bame labarin abinda ke faru saboda san bakin yaran nan da boye-boye baze so kowa ya sani ba, saboda shi gashi me wayau baya so Ammi ta sani ko hehehe, ko ba komai se na rikita gidan da wannan labarin se nasa ammi ta rud'e, bari na shiga cikin gida na watsa labarin kowa ya sani" Gimbiya jalila ta ida zancan tana kokarin fita ruko hannu ta Ashad yayi yana cewa, "momi karki je ina tunanin be kamata ki fadi ba, bana so ki fadi ciwan ammi ya tashi," murmushi takaici Gimbiya jalila tayi tare da makawa Ashad harara tana cewa, "kai har damuwa ka keyi da matar bata damu da kai ba, matar data bud'i baki zata ce sultan Ashe har yanzu tsanar ta bata ratsa zuciyar ka ba, duk wanda ya nuna d'ana ba kowa bane se nuna mashi iya karshi, ta dadi ciwan be tashi ba, idan ta tashi ta mutu, ni ba damuwa ta ba ce, nuna Ashad Gimbiya jalila tayi da yatsa tana cewa, "ka kiyaye ni " Gimbiya jalila ta ida zancan tana fisge hannu Ashad a jikin ta sannan ta fice daga part din ta. Kukan munafirci Gimbiya jalila ta saki tare da shigewa part din Ammi tana cewa, "mun shiga uku yau kuma abun be tsaya kan sultan ba har da matar shi," ta ida zancan tana saki kukan gulma, Ammi da mom dake zaune suna hira mikewa sukayi a tare dafe da kirji musanman mom da hantar cikin ta kad'a kuka mom ta saki ta san cewa har shi ma Sultan din ba lallai ya tsira ba, wannan wace irin rayuwa ce aita farautar rayuwar d'an ka kamar wani naman daji, Gimbiya jalila ta cigaba da cewa, "sun kashe mu wannan wace irin rayuwa ce, yanzu haka suna Asibitin rai a hannu Allah yarinya karama da ita tasha harsashi tun yanzu bata tsiraba ta fara shiga taskwan rayuwa, shima sultan din ace ya gigice dan har karamar hauka yake, mun shiga uku" Gimbiya jalila tana zancan tana kallan Ammi da ta kasan ido take anan numfashin Ammi ya fara sama-sama tana dafe da kirji hayaniyar da Basmal ta jine ya fito da su ita da jakadiya taro Ammi sukayi ganin zata sume saboda tsabar rikici zauna da ita sukayi saman kujera har a lokacin dana maida numfashin ruwan Dara ta kawo mata a glass cup jikin ta na rawa ta amsa ta sha tana cewa, "na san ba abinda ze sami jika na Sultan da matar shi me yasa Sultan ze boye mana wannan rudanin shiyasa tun jiya hankali na yaki kwanci da rashin ganin su kusa dani, Allah ka tsare min su ya Allah" Ammi ta ida zancan tana sharbar kwalla, mom kuwa mutuwar zaune tayi tana tunanin wani hali ya'yan nata suke ciki, hawaye na gangaro mata, a hankali Basmal ke lallashin ta itama tana matar kwalla, Dara se goge hawaye take Allah sarki Nihal fita, da kyar mom ta iya cewa a kira driver ya kai su asibitin Ammi gani take har da laifin sultan da yaki sanar da su se dai su ji labari daga sama me yasa sultan yake haka ne hawayan idanuwan ta Ammi ta goge, kafin ka ce mi magana ta zagaye gidan, maimartaba dake fada shima labari ya cin masa iya kar rud'eni ya shiga dan kusan a tare suka dunguma zuwa asibiti har da waziri da Adda. Sultan dake tsaye bakin theater room ta glass door yana hango operation din da akewa Nihal a hankali ya daura hannu shi saman kofar yace, "Allah ya tashi kafadu kin Nihal" juyowa da sultan zeyi ya hango su maimartaba suna nufa shi, rudewa sultan yayi da sauri ya shiga goge hannun shi mai dauke da jini jikin white shirt din shi, ya goge hawayan shi yana kokarin janyo jarumtar shi baya su ko dan su gane halin da ake ciki, murmushi sultan ya kakaro yana kallan Ammi dake nufo shi zuciyar shi na tsana ta harbawa Ammi na isowa wajan shi ta dauke shi da lafiyayan mari dafe kunci sultan yayi, ya kallan Ammi, kuka Ammi ta saki tana, cewa, "mi yasa kake boye mana abinda ke faruwa da kai a tunanin ka bamu sani bane yaushe zaka fara fadin halin da ka shiga, tir da wannan zurfin cikin naka" Ammi ta ida zancan tana kuka tare da rungume sultan gam tana cewa, "bana san na rasa ka sultan dan Allah ka daina boye mana alamarin ka" shima sultan hayawe ne suka shiga yi mashi zarya a hankali Sultan yake cewa, "Ammi ki yafe min duk yadda na so na kare Nihal kar ta shiga wani hali nayi ina tsoran na fada maki bana so ki shiga wani hali amma ki yafe min Ammi," sultan ya ida zancan hawaye na mashi zarya ya cigaba da cewa, "me yasa duniya bata so na Ammi me na aikata haka ake bibiyar rayuwa ta, na tsani duniyar da abinda ke cikin ta" Sultan ya ida zancan yana rushewa da kuka, gabaki daya kowa na wajan se daya zubar da hawaye musanman mom da maimartaba ta, janyo mom maimartaba yayi a jikin shi musanman yadda yaga tana kuka har neman shid'ewa take saboda tausayin d'an nata shafa mata kai maimartaba yayi yana cewa, "ya isa kukan haka, Allah yana tare da d'an ki addu'ar mu kawai yake nema," sauke ajiyar zuciya mom tayi tana cewa, "yaushe ne d'a na ze samu SAUYIN RAYUWA ka duba ka gani tun yanzu an fara bi takan iyallan shi yaushe ne ze samu farin ciki me daurewa," mom ta ida zancan tana kuka tana cewa, "anjefa rayuwar yarinya a hadari saboda d'a na" Zame jikin ta ammi tayi daga jiki Sultan ta zauna da shi a hankali ya daura kanshi saman kafadar Ammi yana sauke ajiyar zuciya, Gimbiya jalila dake gefe murmushi ta saki a zuciyar tana cewa indai bibiyar rayuwar ka ne yanzu aka fara har se na aika ka lahira zan samu kwanciyar hankali da natsuwa, idan dai kuka ne yanzu kuka fara Allah yasa Nihal din ta mutu se na cigaba da ganin koke-kokyan Ku dan ni dadi yake min Gimbiya jalila ta zancan zuci tana tsare su da ido musanman yadda taga maimartaba ya wani kama mom zuciyar ta na cigaba da suya, fitowar doctor Amir ne ya katse masu tunani da sauri suka mike lokaci daya maimartaba ya karasa wajan shida Ammi suna cewa, "ya jikin nata.? shuru Amir yayi yana kallan Sultan da dake zaune fargaba da tsoro ta hana shi mikewa ya tsare Amir da ido zuciyar na tsana ta harbawa Amir yace, "Alhamdulillah mun samu nasara ceto ran ta but am sorry to say tana como, ba komai ya haifar da haka ba se saboda razana da tayi," Amir ya idan zancan yana kallan sultan da hawaye ke mashi zarya cikin zuciyar shi yana cewa, saboda ni kin tsinci kanji cikin tashin hankali Nihal ki yafe min kwata-kwata baki dace da mutum kamata ba kina bukatar SAUYIN RAYUWA ni ko bani da tabas kan rayuwa ta, Allah ka tashi kafadun Nihal ya Allah, Gimbiya jalila ko murmushi ta saki tana cewa, "no.! No.! ban jima wannan yaro dadi ba wanna ita da gawa ai basu da banbanci, kafin ta farfado kai ma zanyi kokarin aika ka inda take kokarin tafiya, gaskiya an ragemin aiki numfawa Gimbiya jalila tayi lokacin yayi dai-dai da fitowa da Nihal za'a wuce da ita waiting room hancin ta na makale da oxygen se Karin jini da ake mata gabaki dayan su dunguma sukayi zasu shige Waiting room doctor Amir yace suyi hakur da ganin ta se zuwa dare shima din se mutum daya zuwa biyu, daga kai maimartaba yayi tare da cewa, "idan akwai wata matsala a Sanar da mu idan aikin be yuyuwa a Nigeria se mu fidda ta please a bata kyakyawar kulawar," "Ba Ku da damuwa Abba insha Allah komai ze zama normal" godiya maimartaba yayi mashi tare da cewa, "Ku taso muje gida,". Ammi ce ta kalli sultan tana cewa me ze hana sultan ya je gida ni na zauna da Nihal ya kamata ya je gida ya samu natsuwa, murmushi manya maimartaba yayi tare da cewa, "samun natsuwa shi ai shine ya gan shi kusa da matar shi muje kawai" Jin haka ya sa su ammi wuce wa gida suna fatan Allah ya karawa Nihal lafiya aka barta da Sultan. A harabar gida Nazili tayi parking da sauri ta shigo gida da Aziza taci karo tana zagaye main parlour tana ganin Nazili ta karasa da sauri tana cewa, "Gimbiya karki ce min kema mumunanan labarin nan ya same ki" tsaki Nazili ta saki tana cewa, "ba dole ba tunda nina bayi a min aikin mtsww" "mun shiga uku wannan tsinaniyar yarinya bata mutu ba" dafe goshi Nazili tayi tare da cewa, "Gabaki daya kwakwalwata ta kule ban san ta ina zan fara ba, yanzu dai ina mutanan gidan, "suna Asibiti Gimbiya" "Oh my goodness Allah ka runfa min asirri, kin ji wani labari na tashi a kai na? girgiza kai Aziza tayi tana cewa, "kawai dai naga sun fice su duka gidan suna cewa Nihal na asibiti ba lafiya, kuma tunda naji kwana zancan na san hakar mu bata ci ma ruwa ba, gabaki daya na rud'e gashi ke ma kin zo da wani bakin labarin Tj na hannu yan'sanda, Allah ya tsagaita wannan bala'i" dan siririn tsaki Nazili ta saki tana cewa, "karki daga min hankali mana zan ji da komai karki manta ni ce Nazili duk abinda nasa gaba se cin mashi, bari na wuce asibitin na san a can zan ji labarin Tj ko ya mutu ko yana raye, ki kula da duk wani motsi na mutane nan gidan nan, ya kamata nayi sauri na tari numfashin Tj kafin asirri na ya tonu, mindin asirri na ya tonu na bani" Nazili ta ida zancan tare da ficewa da sauri ta koma cikin mota ta bar harabar gidan. Shiryawa Sultan yayi cikin kayan asibiti green har da hula da abin makalawa a hanci, direct dakin da aka kwantar da Nihal ya nufa, a hankali yasa hannu ya murda handle din kofar ya shiga, kallan Nihal sultan ya shigayi yana kallan injina dake aiki a jikin ta juya baya yayi yana kallan kofa lumshe ido yayi hawaye na bin fuskar shi a hankali ya furta saboda nikika shiga masifa, goge hawayan idanuwan shi Sultan yayi a hankali ya tako gaban gadan kneel down yayi tare da daura lallausan hannun shi saman kan Nihal yana kallan ta addu'a sultan ya shiga yi mata yana tofa mata a hankali ya daura mata kiss a goshin ta yana cewa, "Allah ya baki lafiya" a hankali Nihal ta fara bud'e idanuwan ta, ta sauke su kan kyakyawar fuskar sultan dake kokarin mikewa, kallan shi Nihal ta shigayi kamar me neman wani abu hawayan wahala na bin kumatun ta murmushi sultan ya saki tare da kama hannu ta yana dariya, lumshe ido Nihal tayi tare da bud'e su tana magana a hankali matsowa sultan yayi da kunnan shi dai-dai setin bakin Nihal a hankali Nihal ta ce, "Inane nan ban mutu ba Ashe zan rayu" Nihal ta ida zancan tana cewa, "Na gode da taimakwan rayuwa ta da kayi," tana maganar bakin ta na rawa saboda injina dake bakin ta da hancin ta girgiza mata kai sultan yayi yana shafa saman kanta yana murmushi yace, "Allah ne abun godiya" a hankali Nihal ta maida idanuwan ta ta rufe, sultan ko wani irin dadi ya ji ko ba komai yanzu hankali shi ya kwanta. A harabar asibiti Nazili tayi parking motar ta fitowar ta tayi dai-dai da fitowar Ammar daga cikin mota, har Nazili zata wuce se kuma ta ci birki tare da juyowa tace, "Ammar..! Ammar dake kokarin kule motar shi ya juyo yana murmushi yace, "yau kuma me Gimbiya ta zo yi asibiti" Ammar ya ida zancan yana fara'a kasancewar be san Nazili na da labarin abinda ya faru ba murmushi Nazili tayi tare da gyara tsayuwa tace, "na zo duba mara lafiya ne Ashe abinda ya faru kenan ina fatan Allah yasa a kama koma suwaye ke da sa hannun a cikin wannan abun," sakatarere Ammar yayi yana cewa, "ya akayi kika sani murmushi Nazili tayi tare da cewa, "baka da labarin cewa gida kowa ya sani yanzu dai wani hali ake ciki kun Sanar da yan'sanda" murmushi Ammar yayi yana cewa, "yanzu haka an kama daya daga cikin yaran amma yana asibiti yan'sanda saboda yayi kokarin guduwa aka harbe shi" tsare Ammar da ido Nazili tayi tana nazari sannan tace, "toh shikenan Allah ya kyau" sannan Ammar yayi gaba ya bar Nazili tsaye baya-baya tayi da sauri ta shige mota tare da daukar wa kanta alwashin da dare zata sa aje asibitin a dauke Tj ya bar kasa gabaki daya. Da dare BS ya shirya a matsayin likita ya shige asibiti idanuwan shi na manne da glass fuskar shi na dauke da abun hanci, Nazili kuma na bakin kofar asibitin tana cikin mota tana jiran shi har ya shiga asibitin, aiko yana zuwa bakin kofar kasancewar akwai security ID card din shi ya nuna masu sannan ya shige dakin, kwance ya hango Tj maida kofa yayi ya tura a hankali ya zare komai na injin dake jikin Tj murmushi Tj ya saki duk da yana jin jikina, bakin window BS ya leka lokacin big boy na bakin window yana jira ya miko mashi Tj, da kyar ya dauki Tj ya mikawa big boy ta window sannan ya koma dakin ya jera pillow ya fito fuskar shi dauke da murmushi har yayi nisa security yace, "doctor..! sankarewa BS yayi zuciyar shi na harbawa har ya fara kokarin ciro mindigar dake makale a kugun shi, daya daga cikin security's yace, "ka manta da ID card din ka baka amsa ba" da kyar ya iya juyowa murmushi security yayi yace, "gashi kana ta sauri zaka je duba Marasa lafiya Allah ya taimaka," murmushi BS yayi tare da mika hannu ya amsa yace, "na gode" da sauri ya bar wajan yana fitowa harabar asibitin ya nufi motar Nazili lokacin har big boy ya sa Tj cikin mota fisgar motar Nazili tayi da karfi suka bar harabar asibitin. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 97_98* A wani dan madaidaicin gida Nazili ta faka motar ta BS da big boy suka dauki Tj suka shige da shi cikin gidan Nazili na biye da su, se da suka shinfidar da shi sannan BS ya kalli Nazili dake bin su da kallo tab'e baki Nazili tayi tare da cewa, "Nasan nan ze ishe ku, ku zauna har se kura ta lafa, duk abinda zaku bukata na ci da sha akwai" sannan Nazili ta ida zancan tana kokarin ficewa BS ya biyo ta yana cewa, "Ranki ya dade ya kamata ki bamu sauran kudin da kika ce zaki bamu..! kin ga se a ida yima Tj magani da su, tunda sauran kudin yan'sanda sun amsa" waigowa Nazili tayi tana kallan BS a sheke tare da nad'e hannuwan ta a kirji tace, "Amma dai kai baka da hankali ko..! Nazili ta ida zancan tana murmushi rainin hankali tace, "cewa nayi idan aikin ku yayi kyau zan ida biyan kudi ina kuka gama aikin naku da har zan baku wani kudi bayan yarinyar dana ce ku kashe tana asibiti kwance tana samun kulawa a hannun sultan, maimakwan ace tana kwance a kabari gida ya cika da yan zaman makoki, let me tell you something BS babu kwaban sisi na da ze kara ciwo..! taimako daya zan maku shine na samo doctor ya cigaba da duba Tj shine kawai abinda zan iya, shima saboda ina dan jin tausayin shi amma da badan haka ba ko kallo baku isheni ba, saboda na riga na gama contract da ku" Nazili ta ida zancan zata bud'e murfin mota rike murfin motar BS yayi yana cewa, "kin san Allah dole ki idasa biyan sauran kudin saboda duk yadda kika ce muyi munyi kawai lokacin ta ne bayi ba bazeyo ki ce baza ki idasa biya ba, idan ko kika ki toh wallahi se na tona asirri..! BS ya ida zancan yana ciro wayar shi aljihu ya cigaba da cewa, "duk plan din da kika tsara yana cikin wayar nan ki bini a hankali if not se na kaiwa sultan din ya ji da kunna shi" dariya Nazili ta saki BS yayi sakatarere yana kallan ta sannan ta gyara tsayuwa tare da matsowa tab da BS tace "kasan kuni wacece kuwa? mu zuba ni da kai shege ka fasa..! abinda nasa aka aikawa Nihal zan sa a aikatama mafi muninshi kafin ka kira sultan ka fada mashi ni zan kira shi na fadi mashi, sannan ko ka tona min asirri kasan bazan yi zaman gidan yari ba tunda bani na harbe ta ba, hasalima ina iya cewa ban san ku ba, karka manta cikin gida na kake zaune yanzu an fada ma ni shashashace ka ga wannan gidan..! murmushi Nazili tayi tare da furta "zagaye yake da wayanda suka dame ka suka shanye a daba da daukar kisa ba bakin komai ba, shiyasa nayi dana sanin daukar ku kumin aiki, ina da yaran da suka fiko tantiranci..! idan kaji wasa ka juya baya kasha kallo..! da kyar BS ya iya juyawa murda-murdan kati ya gani rike da bindigu zagaye da gidan wani irin miyau ya hadiye yana jinjina bala'i irin na Nazili da mugunta lallaikam ta damasu ta shanye a makirci, dafa kafadar BS Nazili tayi tare da kakabe mashi kafada shi tana cewa, "kayi kokarin tona min asirri na san gidan tsoho har can zani na kawar da su ina fatan ka gane wani tsoho nake nufi" Nazili ta ida zancan tana babaka dariya har da hawaye sannan ta tsaya tana cewa, "har ka ji tsoro ko? cool down my friend se ka tona min asirri sannan" Nazili ta ida zancan tare da daurewa ta cigaba da cewa, "bani wayar nan ko na dauke ka da harbi..! Nazili ta ida zancan tana tsare BS da bindiga ba alamar imani atatare da ita jiki na rawa BS ya mika mata wayar warcewa Nazili tayi tare da aje wayar a kasa ta take da takalmin kafar ta me tsini, tana dariya wayar na fafashewa sannan ta aje bindigar tare da shafa kumatu BS wanda ya gama tsorata da lamarin Nazili lallai wannan yarinyar annobace cikin mutane hura mashi iskar bakin ta Nazili tayi a ido kif-kif ta ido BS yayi tare da sauke idanuwan shi saman fuskar Nazili, dauke hannun ta Nazili tayi dake saman cheeks din BS tare da goge hannun ta da tissue sannan tace, "fool kawai..! ta ida zancan tare da shigewa mota ta bar wajan Bayan yan mintoci da tafiyar BS doctor ya zo duba Tj security's basu kawo ma ran su komai ba, doctor ya shiga ganin shi wayam da doctor ya ganine yasa doctor ya shiga kwallawa security's kira a rude suka shigo daki, abinda idan su ya ganine ya sasu razana cike da tanbaya doctor yace, "ina patient din,? Bello dake gefe doctor yace, "shit kenan wannan ba doctor bane gaskiya an raina mana hankali" cike da tashin hankali suka kwashe abinda ya faru suka shedawa doctor, bello ya ida zancan yana cewa, "yanzu mi zamu cewa boss munyi sakaci da aikin mu shit..! a rude security suka kira DPO Bilal suka sheda mashi DPO Bilal be ga sakacin kowa ba se nasu fada dai sun sha shi har se da gwiwar su tayi sanyi, a daran suka bazama neman su Tj ko Allah ze sa zasu bar gari a kama su DPO Bilal ko ba karamin takaici yayi da irin sakacin da security's suka tafka ba. ***** Bayan kwana biyu sosai Nihal ke samun kulawa wajan sultan duk da cewa bata sani ba tana como, sultan kuwa ya daura damara kyautatawa Nihal da inganta rayuwar ta har se ta samu SAUYIN RAYUWA da farin ciki me daurewa ko da ze rasa komai nashi a kanta, saboda labarin Nihal ya bashi tausayi sosai, bangaran makaranta ko tuni yasa an zana ma Nihal exam har sun gama result kawai ake jira, su minal ko sun dawo gida cike da murna da san ganin matar yayan nasu labarin da suka ji cewa Nihal na asibiti basu ji dadi ba, duk yadda suka so suje su ganta sultan ya hana yace tana Como su bari a fido da ita, dan haka sun dukufa da addu'a cike da zakuwar ganin ta. Sultan ko kullun yana makale da Nihal a ganin shi hakan da yake tausayi ne ba soyayya ba, Ammar ko kullun cikin bashi gwarin gwiwa yake da kara jadada mashi labarin Nihal saboda yasan sultan mutum ne mai tausayi ta haka ze dasa mashi san Nihal din har ya wayi gari ya kamu, har Nihal ta fito daga Como sultan na bata kulawa har mamakin sauyawa sultan Nihal take ko tari me karfi baya bari tayi hakan yasa Nihal ta dan saki jiki da shi, minal da nawwara ko kullun suna kan hanyar zuwa asibiti, Nazili ko bakin ciki cin ta yake dan gani take abinda ta aikata yasa sultan ya kara san matar shi da bata tsaro na musanman hakan ba karamin hauka yasa Nazili ba. Yauma kamar kullun Minal ce zaune tana feeding Nihal pepper soup din yan' ciki dan bata fuska Nihal tayi tare da ture boll din da hannun ta tace, "na koshi" murmushi Minal tayi tana cewa, haba aunty Nihal ki kara mana baki ci da yawa ba, ki daure ki kara" harara wasa Nihal ta makawa minal tace, "matsala ta dake kenan kullun kika zo se kin cika min ciki da abinci ko nishi ya zamana da kyar nake gaskiya na koshi" Nihal ta ida zancan tana turo baki nawwara da Minal dariya suka saki aje boll din minal tayi tana cewa, "Allah yasa yayana ya shigo se ya dura maki da kan shi, tun tea din safe baki kara cin komai ba kuma se mun fadawa mom" nawwara bata ida rufe bakin ta ba aka turo kofar dakin gabaki dayan su juyowa sukayi a tare sultan ne ya shigo ya shirya cikin wata suit ta kama jikin shi Ash colour da inner blossom dark ash colour necktie dinshi kala suit nasa ya saka gem stone rose, sajan shi ya kwanta yayi luf-luf ya wani kara kyau, tsare shi da ido Nihal tayi tana kallo tana kara jinjina kyau irin na sultan da sauri minal ta mike daga saman gado tana cewa, "yauwa yayana gara da ka zo taki cin abinci bata san cin komai" Minal ta ida zancan tana yamutse fuska janyo hannun shi nawwara tayi tana cewa, "gara da ka zo se kayi feeding nata da kanka" Minal da nawwara suka ida zancan suna jan hannu sultan zuwa bakin gadan da Nihal take zaune kallan juna minal da nawwara sukayi suna dariya suna kallan Nihal "suka ce ai yanzu dole ki ci abincin tunda ga yaya" bata fuska Nihal tayi tana kallan su dariya suka saki harara sultan ya maka masu yana cewa, "abokiyar wasan ku ce kuke mata dariya, nasan zata ci ni take san gani shiyasa ta ki cin abinci" sultan ya ida zancan yana tsare Nihal da ido tare da shafa sumar kanshi, zama yayi saman bed din gefan Nihal yana cigaba da cewa, "kalle su dariya fa suke maki za'a maki dure" sultan ya ida zancan yana daukar boll din pepper soup din turo baki Nihal tayi tare da sakin kuka dariya minal da nawwara suka saki aje boll din sultan yayi ya bisu a guje da gudu suka bar dakin suna yima Nihal gwalo ai se ta kara fashewa da kuka a hankali sultan ya karaso kusa da ita daukar boll din yayi tare da nufar ta da spoon din abinci bud'e baki Nihal tayi tana amsa ganin ba wasa a fuskar sultan tana ci tana kuka tana harara shi har ta cinye, sultan ko murmushi yayi tare da kad'a kai tissue ya zaro tare da goge ma Nihal baki tsare shi da ido Nihal tayi tana mugun mamaki sauyin sultan tsare ta da ido sultan yayi shima yana kallo kamar me neman wani abu a fuskar ta murd'a kofar da akayi ne ya dawo da hankalin su nawwara ce ta shigo wurga ido nawwara ta shigayi tana cewa, "am sorry handbag din na namanta bazan kara takurawa Princess ba" ta ida zancan tana ficewa juyowa sultan yayi karaf suka had'a ido da Nihal gashin ganta Nihal ta shiga gyarawa tare da kauda kai a hankali sultan ya daura hannun shi a wuyan Nihal wani irin yar Nihal taji tana kallan sultan wani saban yanayi na shigar ta matsowa yayi har suna jin saukar numfashin juna su ga kamshi turaran shi daya mamaye mata hanci me sanyi dadi, a hankali ya kama gashin kanta ya nanad'e mata shi kamar ganmu sannan ya dawo ya zauna cikin honey voice din shi sultan yace, "na san daga yanzu baze kara takura maki ba, tunda na nanad'e shi ko" har a lokacin Nihal na kallan shi kamar a mafarki take ganin sauyin sultan ruwa ya tsiyaya a glass cup ya mika mata da magani amsa tayi tare da shanyewa sannan sultan ya mike ze fice, har ya isa bakin kofa ya kama handle din kofar Nihal tace, "na gode," bud'e kofa sultan kawai yayi ya fice, kwanciya NIhal tayi tana tunanin sauyin sultan watsar da tunanin tayi tare da lumshe idanuwan ta bacci me nauyi yayi gaba da ita. Bangaran sultan ko patients yaje yana dubawa yana dubawa su yana tuna cute face din Nihal, da moment din da suke kasancewa a yanzu murmushi sultan ya saki tare da cigaba da duba patients cikin kulawa da kwarewa. Da yamma Ammi da mom suka zo duba Nihal cike da kayan marmari wani irin gata Nihal take samu wajan su da kulawa dan zama tayi kamar gold cikin su Ammi ce tace, "Masha Allah jiki yayi kyau sosai se dai mu jira ranar sallama," mom tace, "gaskiya ko Allah abin godiya kwanaki biyu da suka wuce kallo daya zakayi ma yarinyar nan ka zubar da hawaye," shigowar Basmal da Ammar ne ya katsewa mom zance har kasa Ammar ya duka yana gaishesu dauke da fara'a mom da Ammi ke amsawa Basmal saman gadan da Nihal ke zaune ta nufa ta zauna tana cewa, "aunty Nihal ni kyau ma da fresh naga kinayi kamar asibitin ya amshe ki" Basmal ta ida zancan tana daga gira dariya Nihal tayi tana cewa, "bana san tsoka na ni asibiti ma ya isheni" murmushi Basmal ta saki tana cewa, "nayi missing naki gidan ba dadi bame rakani siyaya da raba IV se ni kad'ai yaran nan ko fita da su headache zasu sakar maka" Ammi ce ta cabe zancan da cewa, "ko tana gidan ba rakaki zatayi ba oh sokike Gimbiya ta rinka gantali, kuma sannan maganar sa headache ki nemi me sa maki, daga dawowar yara za'a sa masu kahonzuka" turo baki Basmal tayi tana cewa, "kai ammi yanzu se ki hanata, kuma maganar yaran ai ba karya nayi ba ita kanta Nihal kawaici take Masu da Wannan surutun na su" "Toh yayi maida min magana" Ammar dake kallan Ammi harara ta sakar mashi tana cewa, "katsare ni dana mujiya, ko rama mata fadan zakayi" dariya Ammar yayi yana cewa, "ni dai ban ce komai ba Ammi" "kama ce yanzu na zaune ka" dariya Ammar ya saki yana cewa, "ni dai na gano ki kishi kike" Ammar ya ida zancan tare da ficewa. Se kusan dare su Ammi suka koma gida Nihal ji take kamar ta bisu zaman asibitin ya ishe ta haka ga shirye-shiryen biki da ake tayi ban da ita, taso ta zagaya garin ace mutum tunda ya zo gari so daya ya taba fita shima tana iya kiran rana da bakar rana, mikewa tayi ta shige toilet wanka tayi tare da dauro alwala sanye da towel ta fito tana goge jiki ta kallo daya tayi ma kayan asibitin tare da bata fuska a hankali Nihal ta furta a fili "ni dai na gaji da kayan nan Allah ya gani" daga kayan Nihal tayi ta cigaba da cewa, "se warin asibiti nake kai jama'a" haka Nihal ta rinka surutai sannan ta saka kayan tare da saka hijab ta gabatar da sallah isha, bayan ta idar ta dade tana addu'a turo kofar da kayi ne yasa Nihal juyowa da sauri tunanin ta su nawwara ne se ta ga sultan ne mikewa Nihal tayi tana linke dadumar hannun ta, sultan se kallan ta yake ta kasan ido har ya zauna saman sofa, bayan ta gama ta aje dadumar tare da komawa saman bed ta zauna tana wasa da yan yatsun hannun ta, sultan ne ya katsa shurun da cewa, "mike maki ciwo yanzu? dago kai Nihal tayi tare da cewa, "ba abinda ke min ciwo ni gida nake san komawa na gaji da zaman asibitin" Nihal ta ida zancan tana tsare sultan da ido "kuma shine baki san cin abinci," zazzare ido Nihal ta shigayi can kuma tayi sauri tana cewa, "na koshi ne lokacin shiyasa amma ina cin abinci sosai ma" "Toh idan haka ne yanzu zan zuba maki abinci ki cinye duka a gabana" daga kai Nihal tayi cike da zakuwa warmer sultan ya bud'e ya zuba mata tuwan shinkafa miyar taushe se kamshi take zubuwa taji vegetable ga namomi mikawa Nihal yayi tare da cewa, "oya cinye yanzu" amsa Nihal tayi tare da kallan sultan tace, "ina zan kai abincin nan yamin yawa bazan iya cinye shi ba" daga kafada sultan yayi yana cewa, "toh shikenan bani na rage har yanzu cin abincin ki be koma normal ba, na fasa sallamar ki gobe" da sauri Nihal ta duro daga saman gado tana mika hannu zata amshi abincin hannun sultan sama sultan yayi da abincin yana cewa, "a'a ki bari na rage mana ai ya maki yawa" sultan ya ida zancan yana maida plate din bayan shi zagayawa Nihal tayi bayan sultan da sauri ya maido plate din gaban shi zagayowa Nihal ta karayi tana cewa, "ka bani mana" "zan baki amma se na rage shi" warmer Nihal ta dauka tare da bud'ewa zata fara ci, ganin sultan ya nufo ta yasa Nihal dubawa da gudu aje plate din Hannun shi sultan yayi zagaye dakin suka shigayi Nihal da sultan kamo Nihal sultan yayi dariya Nihal take saki saboda tsakulkulin da sultan ke mata har cikin zuciyar shi sultan yake jin dariyar da Nihal ke saki amshe warmar sultan yayi ya kule, kwabe fuska Nihal tayi kuka Nihal tasa tare da nufo sultan matsawa yayi rike da warmer zagaye dakin suka cigaba dayi sultan na mata dariya abinda Nihal bata taba gani ba har dimple din shi na lomawa bata fuska Nihal tayi tana kallan sultan karasowa tayi tana cewa, "dan ka ga ina san komawa gida shi yasa kake wanani" Nihal ta idan zan zata juya zantsi yaja ta luuu ta tafi zata fadi sultan ya taru ta sandar sa drip ta biyo su fadawa sukayi saman gado a tare sultan na saman Nihal rintsi ido Nihal tayi tana rike da riga sultan binta da ido sultan yake yana ganin yadda eye lashes din ta suka wani kwanta kamar tasa na kanti, a hankali Nihal ta bud'e idanuwan ta, ta sauke su saman kyakyawar fuskar sultan tana kallan shi, zabura tayi da sauri tana kokarin mikewa da sauri sultan ya mike yana gyara zaman suit din shi, ya juyawa Nihal baya gyara gashin kanta Nihal tayi tare da takurewa saman bed da sauri sultan ya dauki plate ya mika mata hannu Nihal tasa ta amsa ba tare da ta bari sun kara hada ido da sultan ba, har ta fara cin abincin ta cinye tas ta aje plate din, bolo magani da ruwa sultan yayi ya mika mata, haka Nihal ta amsa shima ba tare da ta kalli sultan ba se da ta shanye sannan sultan ya koma saman sofa tare da cire suit din shi ya rage daga shi se shirt, gabaki daya sun kwanciya sukayi tare dayin lamo ba abinda ke tashi se mugun zuciyoyin su lumshe ido sukayi a tare moment din da suka kasance ne ya shiga dawo masu a idanuwan su a tare suka mike zunbur suna kallan juna sultan dake saman sofa tsare Nihal yayi da ido itama din kallan shi take cikin zuciyoyi su suna cewa, "ya Allah mike shirin faruwa da nine me yasa nake ganin shi cikin idanuwa na..! "Mi yasa nake ganin ta cikin idanuwa na" gabaki daya yansu hada baki sukayi gurin cewa, "ya Allah" ya fito fili Wanda su kansu basu san maganar ta fito fili ba da sauri Nihal ta koma ta kwanta tare da dafe goshi shima sultan komawa yayi ya kwanta tare da kashe haskyan dakin dan ko magana ya kasa itama haka Nihal a haka bacci yayi awan gaba da su. Washe gari da safe Nihal na tashi bata sami sultan a dakin ba batayi mamakin hakan ba saboda ba ita kad'ai bace patient's, saboda wani lokacin har operation yana yi da dare kuma dama yau ta makara tashi sallah Asuba da sauri ta shige toilet wanka tayi tare da dauro alwala da yin brush tana fitowa tayi tozali da wata red gown saman bed tasha Stone's se kyalkyalki take da sauri Nihal ta karaso gaban gadan tana bin kayan da kallo, sauke idanuwan tayi saman black veil da fost black se kyalkyali take da flat sheo black wani irin murmushi ne ya kubucewa Nihal tana waige-waige daukar rigar Nihal tayi ta saka wani irin fitinan kyau rigar ta mata shape din ta ya wani fito das da shi, hijab ta zura tare da gabatar da sallah har ta idar da sultan be shigo ba mikewa Nihal tayi tana barbaza gashin kanta, sultan da shigowar shikenan lallacewa yayi wanjan kallan Nihal musanman yadda riga ta mata kyau ga gashin kanta da take mashi wani salo wanda ita kanta bata sani ba iska na kad'a shi juyowar da za tayi karfa suka had'a ido da sultan murmushi Nihal ta sakin se hakan ya kara mata kyau tace, "ina kwana" da kyar sultan ya saita kanshi yana gyara necktie din wuyan shi yace, "lafiya lau" yana bin Nihal da ido tun daga kasa har sama kauda kai sultan yayi yana cewa, "muna iya tafiya yanzu" washe baki Nihal tayi tace, "gida..! daga mata kai sultan yayi wani irin tsale Nihal tayi rintse ido sultan yayi ji yake wani bakwan alamari na shigar shi tare da ware idanuwan shi ya sauke su kan Nihal, sosa keya Nihal tayi duk se kunya ta rufe ta veil din ta ta yafa tare da saka takalmatan sannan ta dau fost, a hankali ta tako bakin kofa a tare suka fito da sultan kallo daya zaka masu ka sake saboda tsabar haduwa da tsantsar kyau kallo daya zaka masu ka dauka akwai tsantsar soyayya har suka karaso parking space Alex ya bud'e Masu kofa suka shige motar sannan driver ya ja mota. ******** Nazili da fitowar ta daga daki kenan zata office taga gidan anata hada-hada tab'e baki tayi tare da kiran Yasmin baiwar Nihal zata wuce da wasu flowers tace, "ke zo nan..! jiki na rawa ta karaso hard'e hannuwa Nazili tayi tana cewa, "mi ke faruwa baki zamuyi ne ko shirin bikin aka fara? washe baki Yasmin tayi tare da cewa, "yau sultana zata dawo gida shine ake gyara ko ina dan a tarbe ta," fasali Nazili ta ja tana kallan Yasmin kamar ta kife ta da mari da kyar ta iya hadiye kulutun bakin ciki tace, "kina iya tafiya" da sauri Yasmin ta bar wajan gyara gashin kanta Nazili tayi tana cewa cikin zuciyar ta yau zaki dawo gidan nan mu dasa daga inda muka tsaya, ko zanyi yawo tsirara se na rabaki da sultan saboda ba ajin ki bane Baku dace ba, da ni sultan ya dace, ina san sultan ko wace rana ta duniya san sa lunkuwa yake a zuciya ta, kullun wutar san sa ruruwa take a zuciya ta, ban k'i ba gabaki dayan mu mu mutu kowa ya rasa sultan din ba..! Nazili ta ida zancan zuci tare da shigewa dakin ta dan fitar da tayi niya ta fasa. Ashad ne ya shigo part din Gimbiya jalila yana sanye da jeans and Ash shirt fadawa yayi saman kujera yana cewa, "momi hidimar mi ake a gidan nan? gimbiya jalili dake cin kayan marmari tabe baki tayi tare da cewa, "kai ma dai ka gani matar sultan ce fa zata dawo shine dan fihila ake ta wannan ruguntsimin ba abinda ke ban haushi se kamar yadda minal keyi, tafi kowa rawar kai a kan sha'aninan mu nan da yara zasu dawo daga makaranta ba uwar da aka hada masu amma dayake matar dan gold ce ka ga rawar kafa" tsaki Ashad ya saki yana cewa, "karki ga laifin su yar matsiya tace shi shiyasa ake kokarin nuna mata arziki," ya ida zancan yana daukar Apple yana ci Gimbiya jalila ta cigaba da cewa, "ni bama hidimar ke kona min rai ba yadda Minal ke shige masu ko part din nan kafin ka ganta se Allah yayi ni dai Nadiya ta cuce ni wallahi..! "hmmm ai bata da kishi ko kad'an yadda kika san zuciyar kare ni kaina tafi fifita sultan a kai na se kace ni ba wanta bane uwa daya uba daya ba anya minal ke kika haife ta kuwa, ko da yake shima Nasim din duk can suke," Gimbiya jalila tace, "da bani nayi cikin su ba da se na ce ba ya'ya na bane, da ba a ido na biyu na haife su ba naga abinda na Haifa ba, da se na ce anyimin musaya a asibiti wallahi," kwafa Ashad yayi tare da cewa, "se na fara cin uban su zasu san annabi ya faku, bari naje na shirya na zo na zauna naga yadda za'a kare indan ta kama na watsa taran da bakin ciki wani ya kara komawa asibiti," dariya Gimbiya jalila ta saki tana cewa, "son baka da dama wallahi kafi ni iya shege" dariya Ashad yayi tare da ficewa Gimbiya jalila na kara hura mashi kai. A harabar gida motar sultan ta faka bud'e mashi murfin mota Alex yayi ya fito sannan ya zagoya gefan Nihal ya bud'e mata tare da mika mata hannu kallan sultan Nihal take tare da daura lallausan hannun ta saman na sultan gabaki dayan su shock suka ji lokaci daya, sannan Nihal ta kara fitowa daga cikin mota tana bin gidan da kallo sannan ta kalli sultan daya zagaye hannun shi a wast din ta ya kara Matso da ita jikin shi bugun zuciyar su na karuwa a hankali yayi mata rad'a kunne tare da cewa, "karki manta mun dawo gida idanuwan mutane na kan mu, duk abinda muke mu nayi ne saboda Ammi," murmushi yak'e Nihal tayi tare da cewa, "shine se ka hau kama ni da haka kake min koko wani saban salan ka bulo da shi na kamani anyhow ba zan dauka ba" Nihal ta ida zancan tana murmushi yake tana tsare sultan da ido kara dan matsa mata hips sultan yayi zaro ido Nihal tayi tana cewa, "me haka wai" dauke kai sultan yayi tare da had'e rai duk inda suka wuce bayi na masu sannu da zuwa da zubewa suna kwasar gaisuwa ganin yadda gidan ya canza yasa Nihal bin gidan da kallo duk a tunanin ta gyaran biki ne part din Ammi suka nufa a hankali Nihal ta zura kafafuwan ta main parlour wani abu ne ya fashe a raze Nihal ta rungume sultan cike da tsoro shima din rugunme ta yayi tsam a jikin shi yana shakar kamshi ta mai dadi, dariya mutanan parlour suka saki wani kyalkyali ne ya shiga zubo masu akai ita da sultan dago kai Nihal tayi tana bin kyalkyali da kallo tana sakin murmushi tana kallan yanayin decoration din da part din yasha daga jikin bango an rubuta welcome back home sultana, zamewa Nihal tayi taga jikin sultan tana bin ko ina da kallo tana murmushi minal da nawwara ne suka janyo hannu ta Ammi dake rike da plate din cake ta matso tare da gutsuro cake din tasa mata a baki tare da cewa, "barka da dawowa gida Gimbiya, Allah ya kara tsare mana ke" murmushi Nihal ta saki tare da rungume Ammi tana dariya idanuwan ta cike da kwalla ba abinda ya fado mata a rai se umma da Abba Allah ya ji kan su Nihal ta iya furtawa a ciki zuciyar ta haka mom ta Matso ta bata cake tare da bata gift murmushi Nihal tayi tare da amsa tace, "na gode mom" Gimbiya jalila ma gift ta bata murmushi Nihal tayi tare da cewa, "na gode Momi" Nazili dake gefe ta cika fam kamar ta fashe takowa tayi rike da gift tana murmushi rungume Nihal tayi dai-dai setin kunnan Nihal tace, "barka da dawowa almajira ba komai na sami cikin gift din nan ba se kudi na san shine burin almajiri" Nazili ta ida zancan tana murmushi tare da zame jikin ta a jikin Nihal kallan ta Nihal keyi tana murmushi yake sannan ta riko hannun Nazili tana cewa, "kuma a haka zan zama Gimbiya Nihal matar dan sarki na fari muna nan dake wata rana se kin zama baiwar almajira" Nihal ta ida zancan tana murmushi fisge hannun ta Nazili tayi daga rukwan da Nihal ta mata cikin zafin rai tana kallan Nihal dake murmushi, Minal da nawwara ne suka hada baki wajan cewa, "muma ga namu gift din" murmushi Nihal ta saki tare da sakar masu kiss a kumatu tana dariya sultan yana kallan Nihal dan gabaki daya ta tafi da imanin shi da salan ta, Nazili na lura da irin kallan da sultan ke bin Nihal da shi me cike da so da kauna, tsanar Nihal na kara shigar ta minal da nawwara ne suka ce, "saura na yaya ya kamata ya nuna mata nashi gift din ko Ammi ya fada mana yadda yayi missing nata da bata gida" minal da nawwara suka ida zancan suna janyo hannun sultan, dariya yayi yana ja masu kunne lokaci daya yar kara suka saki suna cewa, "wayo Allah yaya akwai zafi" cikin honey voice din shi sultan yace, "Allah ya ga abinda ya gani yasa kuke boarding da gida kuke da mun bani" dariya kowa na parlour ya saki yana cewa, "sun maida ka kakan su" sultan yace, "nima haka nagani" ya ida zancan tare da kiss kumatun su hadadan kit sultan ya ciro a aljihun shi karamin tare da bud'e kit din zube ne ciki mai kyau se kyalkyali yake zubawa a hankali ya kama hannun Nihal tsare shi da ido Nihal tayi shima din kallan ta yake yana sakin smile a hankali ya saka ma dan yatsan ta zoben wani irin kyau zoben ya kara yima hannun ta se sheki yake kallan zoben Nihal tayi tana murmushi dan zoben ba karamin kyau ya mata ba ko ba'a fada mata ba tasan me tsadane sosai saboda haskyan da shakin da yake zubawa, zame hannun ta Nihal tayi tare da dago Hannun tana murmushi tana nunawa muta nan parlour cike da jin dadi kuma tayi hakan dan ta gumama Nazili gabaki daya parlour ya dauka da "wow wannan zoben ya hadu" Basmal ta ce "gaskiya yayana ya iya siyayar masoya" dariya parlour kowa ya saki ban da Nihal dake kallan sultan dake kallan ta cikin siririyar muryata Nihal tace, "na gode sosai da wannan kyauta taka tafi ta kowa" Nihal ta fada tana murmushi yake maimartaba da shigowar shi kenan yace, "tawa kuma tafi tashi" dukawa Nihal tayi tare da gaishe da maimartaba kunya duk ta ishe ta da sauri da shige dakin ta mom tace, "ka kure ta kasa ta ji kunya" dariya maimartaba ya saki yana cewa, "nayi late har an gama tarbar diyar tawa idan ta fito ace na bata kyautar mota ga key din" cike da zumudi Basmal tace, yayana ya bita daki ya bata yanzu," Ammi tace, "haka ko za'ayi..! duk da sultan be so bin ta ba dan be san rai ni haka ya amshi key din. Nihal na shiga daki jakarta ta dauka tare ciro hotan umma da Abba tana kallo a hankali ta shafa hotan hawaye Masu zafi suka zubo mata a hankali ta furta "I wish kuna tare dani duk wannan farin cikin da aka sani yau naso a ce su baffa ne suke bani shi, Abba ka yafe min a kan guduwar da nayi daga hannun baffa rungume hotan Nihal tayi tare da cigaba da cewa, "ina missing naku umma da Abba ku yafe min nayi aure ba tare da sanin wani nawa ba" Nihal ta ida zancan tana sakin kuka sultan dake bakin kofa yana jin duk abinda Nihal ke cewa tausayin tane ya kara lullube shi duk bakar wahala data sha hannun su baffa har yanzu tana ganin laifin ta na guduwar da tayi murda kofa sultan yayi ya shigo, da sauri Nihal ta mike tana goge hawayan ta tare da boye hotan a bayan ta a hankali sultan ya tako gaban ta tare da dago da fuskar Nihal sisiraran hawaye ne suka shiga zubo mata juya mashi baya Nihal tayi da sauri tana goge hawayan fuskar ta cikin honey voice din shi sultan yace, "Mi ya saki kuka wani ya bata maki rai ne sultan ya fada" juyowa Nihal tayi tana cewa, "ba Wanda ya bata min rai farin ciki ne yamin yawwa family din ka suna da kirki" Nihal ta ida zancan tana bud'e bedside drewar zata tura hotan hannu ta, hannun shi sultan ya daura saman nata yace, "idan nace wannan hotan ne ya saki kuka karki musamin kinyi missing umma da Abbas ne ko" zaro ido Nihal tayi a birkice ta juyo tana kallan sultan. ```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo```[1/7, 10:14 AM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 99_100* Kallan sultan Nihal take zuciyar ta na tsana ta bugawa fatan ta daya kar sultan ya gano ko ita wacece, murmushi Nihal tayi tare da janye hannun sultan zata rufe bedside drewar duk da tsoran dake ziyartar zuciyar ta dama wannan sauyin na shi ba karamin daure mata kai yake ba Allah yasa ba damar tona mata asirri ya samu ba, tsare ta da ido sultan yayi tare da cewa, "ya kamata ki bani hotan nima nasan mother in low na da father in low na saboda yanzu mun zama daya iyayan ki kamar nawa suke duk da basu raye zan so na san su," jikin Nihal mugun sanyi yayi amma hakan be hanata bud'e baki tace tare da nad'e hannunwan ta a kirji tana cewa, "Bana tunanin almajirai zasu zama iyayan ka babu wani anfani kallan hotan iyaye na" matsowa sultan yayi kusa da Nihal dan ja tayi da baya zuba hannuwan shi sultan yayi cikin aljihu ya tsare Nihal da ido kauda kai Nihal tayi tana kallan gefe tana kokarin boye hawayan dake kokarin zubo mata saboda karyar da ta zauna tayi ma iyayan ta, juyo da fuskar ta sultan yayi tare da sa dan yatsan sa ya dangwalo hawayan Nihal cikin honey voice din shi sultan yace, "duk bani hotan ne ya janyo kukan gani nayi tunda ina auran diyar su ya kamata na san su ko a hoto ne," sultan ya ida zancan yana kallan Nihal dake kallan shi kauda kai Nihal tayi tare nufar drewar a hankali ta bud'e drewar ta ciro hotan ta mikawa sultan, amsa sultan yayi yana kallan hotan murmushi sultan ya saki tare da cewa, "Ashe Nihal da umma take kama" zama Nihal tayi bakin gado tana murmushi mai had'e da kuka Allah ya gani tayi missing iyayan ta a hankali sultan ya karaso bakin gadan ya zauna janyo Nihal yayi jikin shi daura kanta tayi saman kafadar sultan tare da fashewa da kuka shafa gashin kanta sultan yake cikin sanyi murya yace, "Nihal ki daina zubar da hawayan ki Nihal, kuka baya maki kyau duk abinda ya dame ki addu'a ce maganin damuwar ki, kuka baya yaye matsala" ya ida zancan tare da dago da fuskar ta suna facing juna kuka Nihal ta kuma saki tare da cewa, "ina missing umma da Abba Nihal bata da kowa ko kanne bani da su bani da yaya ni kad'ai ce, bani da wanda zan fadawa damuwa ta rayuwar maraya bata da dadi" daura finger din shi sultan yayi saman lips din Nihal shuru Nihal tayi tana bin sultan da idanuwan ta wayanda suka rine zuwa ja, sultan ya katse mata tunani da cewa, "baki da yaya sama da sultan kannan sultan kannan ki, ko bakya so? sultan ya ida zancan yana tsare Nihal da ido murmushi Nihal ta saki tana cewa, "ina so" murmushi sultan ya saki tare da mika mata hannu yace, "friends..! Murmushi Nihal ta saki tana kallan hannun sultan a hankali ta daura nata tana cewa, "friends..! hannu sultan yasa yana gogewa Nihal hawayan ta daukar hotan sultan yayi tare da kara shi a fuskar Nihal yana cewa, "da gaske fa Nihal da umma take kama" murmushi Nihal ta saki kallan ta sultan yayi ganin yadda taji dadi, sultan cigaba da cewa yayi "Umma Nihal na missing naki" yadda sultan yayi maganar cikin sigar shagwaba kamar a gaban umma yake dariya Nihal ta shiga yi tsayawa sultan yayi yana kallan Nihal yadda take sakin dariya yana jin dadin hakan ko ba komai ya fara dasawa Nihal farin ciki a rayuwar ta insha Allah Ammar se yayi alfahari da shi, ganin kallan da sultan ke mata ne yasa Nihal daga mashi gira murmushi sultan yayi sannan ya ciro car key a aljihu shi ya kama hannun Nihal ya samata a hannun yana cewa, "Abba ne yace a baki" bud'e hannu Nihal tayi ganin car key ya sata zare ido tana cewa, "wannan kyautar da Abba ya bani tayi yawwa, kyautar dana amsa yau tayi yawwa gashi ni ko motar ban iya ba" Nihal ta ida zancan tana kallan sultan ja mata kumatu sultan yayi tare da cewa, "se na koya maki..! yana gama fadar haka ya fice shafa kumatun ta Nihal tayi tare da sakin murmushi tana kallan kofa. Da daddare after an gama dinner Nihal da su nawwara dakin Nihal suka shige wasa suke yi da pillow suna goje-goje a dakin Nihal, se ihu suke suna dariri ku, Nihal ko yanzu gidan ba karamin dadi yake mata ba, musanman kasancewar ta tare da su minal duk da ta girme masu amma tsakanin su ba wani nisa bane sosai, Dara dake bakin kofa ce tayi gyaran muryar, gyaran muryar Jakadiya ne ya sasu natsuwa da sauri Nihal ta aje pillow hannun ta tana kallan jakadiya Dara ce tace, "dare yayi ku wuce daki, time din baccin sultana yayi" simi-simi minal da nawwara suka fice suna cewa, "se da safe Aunty Nihal, se da safe Dara" pack Dara ta masu a kumatu bayin su suka rufa masu baya, maida kofa Dare tayi ta kule, murmushi Nihal ta saki tana cewa, "umma ina wuni" "lafiya lau Nihal, ke dai har yanzu bakya jin jikin ki ki biye masu kuna tsale-tsale kin ji dadi Nihal baki da wata matsala wallahi kowa naki ne," murmushi Nihal ta saki tana sunne kai tace, "umma ina jin dadi zama da su, suna debemin kewa sosai" Nihal ta ida zancan tana daura kanta saman kafadar Dara, Dara ce ta katse mata tunani da cewa, "kin ga ba hira ya kawo ni ba, zuwa nayi na shirya ki, kin san yau zaki koma part din mijin ki" turo baki Nihal tayi tana cewa, "umma ni fa na dauka daki na zan kwanta" murmushi Dara ta saki tana cewa, "bana san fihili da can ba tare kuke kwana ba ko da kina Asibitin ai kullun kuna like da juna," turo baki Nihal tayi tana kallan Dara tace, "yau ina so na kwana dake ne ki tayani fira umma nayi missing naki" harara Dara ta watsawa Nihal tana cewa, "ka jimin fihili shi bakiyi missing nashi ba se ni, so kike sultan ya fara yimana zarya a nan, kwana ki nawa asibiti yaran nan ai yayi kokarin, ki godewa Allah kin samu miji mai natsuwa amma ke baki gani Allah ya shirya min ke Nihal" turo baki Nihal tayi tana cewa, "kullun umma se kin yabe shi amma ni bakya yabona dana aure shi" murmushi Dara ta saki tare da ja ma Nihal hanci tana cewa, "ke ma ina yaban ki a wajan shi" tab'e baki Nihal tayi tare da rungume jakadiya shafa kanta jakadiya take har cikin ran ta take jin san Nihal, jin ta take tamkar diyar da ta Haifa da cikin ta. Yasmin ce ta dauko bathrobe barira da ke tsaye tana zaman jiran Nihal mikewa Nihal tayi tsaye tare da mika hannu bathrobe aka bata kayan jikin ta ta cire tasa bathrobe ta shiga toilet Dara na biye da ita kasancewar yau ita zatayi mata wanka, saboda tsarin masaurata ne duk wadda zata shiga turakar mijin ta se ta sha gyara, cikin kwamin wanka Nihal ta zuru santala-santalan kafafuwan ta tare da sakin bathrobe din yasmin dake gefe ta dauka ta fice, wanka Dara tayi ma Nihal bayan ta kamala tasa ta cikin kayan kamshi kala-kala Nihal har mamakin gyaran da ake mata take se ka ce ta shekara ba tayi wanka ba, gashin kanta ma haka ya sha wanki sannan suka fito a tare, suna fitowa saman sofa Nihal ta zauna zaman sarauta barira na mata massage yasmin na shafa mata lotion me kamshi sannan akayi drying gashin kanta, mikewa Nihal tayi ta tsaya gaban tangameman mirror dakin ta, sakin bathrobe din jikin ta Nihal tayi wata yaloluwar riga bacci pink Dara ta dauko ta sakawa Nihal wadda ita da babu ba maraba dai-dai gwiwa rigar ta tsayawa Nihal kallan rigar baccin Nihal tayi ta cikin mirror tare da juyowa cike da kunyar rigar tana cewa, "Umma bana iya fita da wannan rigar dube ta fa, kunya nake ji Allah" harara Dara ta maka mata tare da cewa, "ki zauna nan har se an kwace maki miji..! mi wanna rigar tayi saboda Allah idan zaki farka ki farka ki rike mijin ji" Nihal ko cikin zuciyar ta cewa take su miji manya ita ina ruwan ta koma waza ta kwace shi ta kwace ita ba abinda ya dame ta, in banda yanzu ma daya sako ai ko kallo be ishe ta ba, shagwabe fuska Nihal tayi tana cewa, "Allah rigar kunya take bani dube ta shara-shara" ganin ba wasa a fuskar Dara yasa Nihal hakura tare da zama gyara mata gashi kanta akayi tare da jera wasu flowers masu kyau a kan gashi aka nanad'e kasan gashin kamar ganmu sannan aka tsantsara mata make up, har mamakin irin kwalliya da ake mata take maroon alkyaba Dara tasa mata tasha aiki da gold zare se kyalkyali take turare aka feshe Nihal da shi duk da kamshi da take zubawa, ita kanta Nihal data kallin kanta a mirror ta sheda kyada data zuba, wani magani Dara ta mikawa Nihal a cup amsa Nihal tayi ta shaye tas tana gama sha ta kwabe fuska sannan Dara ta ce, "muna yi tafiya" mikewa Nihal tayi tare da daura hula alkyabar a kanta Dara na gaba Yasmin da barira na bayan Nihal a hankali Nihal ke takawa zuciyar ta na tsana ta bugawa. Bangaran sultan ma shirya shi akayi cikin sleep robe maroon sumar kanshi tasha gyara se zuba kamshi yake yana tsaye gaban mirror sinbul da barma na shirya shi, lumshe ido sultan yayi yana tunanin Nihal a hankali ya bud'e idanuwan shi a lokacin su barma da sinbul sun gama aikin sun kai a sunkuye suka fice. Suna isowa bakin kofa Dara tace a sanar da sultan ta maido mashi matar shi koda bafade ya shiga be dade ba ya fito tare da cewa, "yana maku iso" tun a bakin kofa Dara da su Yasmin suka juya a hankali Nihal ta shige parlour ba kowa se kamshi da sanyi AC dake ta shi a hankali ta taka har ta shige dakin tsaye ta hango sultan gaban mirror hannun shi na hard'e ta baya tsayawa Nihal tayi tana bin dakin da kallo ta kasan ido ko ba'a fada mata ba tasan dakin yasha gyara saman bed dima abin kallo ne duk an zuba red flowers a sama ga wani kamshi da dakin keyi, a hankali sultan ya juyo ya dau mintoci yana kallan Nihal a hankali ya sauke idanuwan shi saman santala-santalan kafafuwan ta dake waje farare tas da su fara takowa sultan yayi har ya zo dab da Nihal har suna jin saukar numfashin juna su a hankali sultan yasa hannu ya bud'e hula alkyabar yana bin fuskar Nihal da kallo wani irin yar sultan ya ji tun daga babba dan yatsan shi har kan shi, ga wani kyau na daban daya ga Nihal ta kara mashi, a hankali ya daura hannun shi saman alkyabar yana kokarin cire mata alkyabar, Nihal ko gaban ta banda faduwa ba abinda yake kirjin ta se sama-sama yake yana dawowa rike hannun sultan Nihal tayi ganin yana kokarin cire alkyabar tsayawa sultan yayi yana kallan ta ga wani fitinan kamshi ta na riki ta shi dan a wannan lokacin shi kanshi be san yana hakan ba, matso da fuskar shi sultan yayi dai-dai wuyan Nihal tare da sa hannu ya saki gashin kanta ya zubo har gadan bayan ta, a hankali sultan ya fara bin Wuyan Nihal yana shinshinawa har ya karaso fuskar Nihal yana kokarin hada bakin su waje daya, Nihal kuwa jikin ta rawa ya dauka take a nan idanuwan ta suka kawo ruwa, tsayawa sultan yayi cak yana maida numfashin a hankali da sauri ya zame jikin shi zuciyar shi na tsana ta harbawa Nihal da hawaye sun fara yi mata zarya jin shuru yasa ta ware idanuwan ta tsaye ta hango sultan ya juya mata baya, hakan ba karamin dadi yayi ma Nihal ba, zuciyar sultan kuwa gargadin shi take karya aikata abinda yake shirinyi lumshe ido sultan yayi wani bakwan alamari na shigar shi wanda tun tasowar shi a yau ya fara jin shi kuma kan Nihal, Nihal kuwa na ganin haka drewar ta nufa da sauri dan canza kaya jikin ta koda ta bude drewar duk irin rigar baccin ne se wayanda suka fita lalacewa, juyowa Nihal tayi tana kallan sultan dake kokarin komawa saman bed ya kwanta tace, "Sultan ina kayana mi yasa aka canza min kaya? juyowa sultan yayi cike da kasala yana kallan Nihal ya tsare ta da ido da kyar ya iya cewa, "ki zo ki kwanta please ki bar kowa ce magana se da safe bacci nake ji" "bana iya kwana da wannan kayan ni dai ka fadi min ina kayan bacci na suke" takowa sultan yayi ya matso dab da Nihal tare da cewa, "to mi ya sami kayan jikin ki, idan ma saboda nine ba ki iya bacci da su ni da ke duk daya muke ni kallan hula nake maki" sultan ya ida zancan yana kauda kai zaro ido Nihal tayi tana cewa, "mi kace..! juyo da fuskar sultan Nihal tayi cike da bacin rai da tsiwa Nihal tace, "kalle ni" namujiya Sultan ya zuba mata tare da cewa, "Ni har yanzu kallan hula nake maki" hannun sultan na zube ciki aljihu yana kallan yadda Nihal ke maka mashi harara tsare sultan da ido Nihal tayi tare da cewa, "bari na nuna maka banbanci dake tsakanin hula da kalabi" dan a ganin Nihal sultan ba karamin ci mata fuska yayi ba ya kira ta hula ma'ana namiji nuna kanta da yatsa Nihal tace, "kalle ni da kyau ni da kai akwai banbanci, ni ba hula ba ce ka gane kalli kanka a mirror ka zo ka kalle ni" alkyabar jikin ta Nihal ta cire ta zame kasa tare cewa, "kallan ni da kyau" juyawa Nihal ta shigayi, gashin kanta ta barbaza tana juyawa sultan, ko ina na jikin ta, sannan Nihal tace, "yanzu ka ga banbancin" Nihal ta ida zancan tana kara juyi, sultan kuwa mutuwar tsaye yayi yana kallan na fulanin ta da hips din ta yadda take juya shi rintse ido sultan yayi tare da yin dana sannin kalma da ya fada dan iyakar rikitawa Nihal ta riki tashi, juyowar da Nihal zatayi ta fada saman fafadan kirjin sultan a hankali ya talabo da fuskar Nihal yana kallan ta itama Nihal kallan shi take, hada baki su sultan yayi waje daya yana mata wani rikitatan kiss, kissing din ta sultan yake kamar zakin daya shekara yana jin yunwa tsayuwar ma gagara su tayi kasa suka zube Nihal kuwa wani irin yana yi ta shiga na daban gaba daya jikin ta yayi sanyi gashi bata da karfin kwace kanta daga rukwan da sultan ya mata har suka zube kasa Sultan na kissing nata yana shinshina ta kota ko ina, a hankali ya daura hannun shi saman rigar ta yana kokarin rage mata rigar jikin ta tsayawa yayi cak idanuwan shi sun rine, kwace kanta Nihal tayi da gudu ta mike ta shige toilet ta kule kanta tana maida numfashin kamar wadda tayi tsare zamewa tayi kasan toilet dafe da kirji, jikin ta se rawa yake tsoran sultan ya lullube ta lokaci daya, sultan kuwa beyi yunkuri bin Nihal ba lumshe ido yayi yana sauke numfashin da kyar ya iya jan jiki ya hau saman bed yana jin kunyar abinda ya aikata Wanda shi kan shi be san mi ya shige shi ba, ba abinda yake bukata kusa da shi se Nihal lumshe ido sultan yayi yana cewa "Mi hakan yake nufi san ta nake koko dai sha'awar ta nake ya kamata nayi nisa da ita" rintse ido sultan yayi yana jin haushi kan shi. har dare ya raba Nihal na toilet se da ta daina jin motsi sannan ta fito a hankali taje bakin drewar riga kawai ta gani ko dubawa bayi ba ta cire na jikin ta ta saka tare da lalabawa ta kwanta zuciyar ta na harba dan duk a tsorace take, sultan kuwa duk yana jin motsin ta ganin ta kwanta ne ya sauke ajiyar zuciya bacci ya dauke shi. **** Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru ciki har da shirye-shiryen biki da ake ba kama hannu yaro Amarya gyara take sha sosai ta murje ta kara kyau da haske kun san tare da Nihal mom ta hada su ana masu gyaran jiki wani kyau Nihal ta kara, Nazili kuwa kullun bakin ciki na k'ume ta musanman yadda taga Nihal ta kara murjewa ga zalla kyau da take karawa, daga gidan waziri har gidan maimartaba hada-hada kawai ake na sha'anin biki angwaye ma ba'a barsu a baya ba suma hidama kawai su, sultan kuwa ban da tunanin Nihal ba abinda yake ko rintse ido yayi ita yake gani har mamakin kanshi yake da alajabi amma har yau ya kasa yadda da cewa ya fada kogin san Nihal. Sultan ne zaune saman sofa a dakin Ammar ya lula duniyar tunanin Nihal wanda ya fara zamar mashi jiki ba abinda yake tunawa se moment din da suka kasance 2days da suka wuce, Ammar ne ya shigo daki hannu shi dauke da cup na coffee, murmushi Ammar ya saki yana kallan sultan yasan he's in a good mood zama kusa da sultan yayi tare da mika mashi coffee amsa sultan yayi yace "thanks dude" kara kallan sultan Ammar yayi yace, "I can see that you are in a good mood sultan, the truth is that you're in love with Nihal..! coffee din da sultan ke Shane ya kusa kware shi aje cup din sultan yayi tare da cewa, "What..! No, no, ni fa kawai ina tausayin tane and..! "And what..! Sultan ya kamata mu fara serious magana I now kana san matar ka amma se turewa kake kana sama kanka damuwa" shuru sultan yayi tare da juyowa yana facing Ammar yace, "the problem is ban san ta yaya zance mata ina san ta ba kasan am not use to that stuff, I'm new in the system, kuma har da ina jin nauyi ta kar tayi tunani abinda ya faru 2days da suka wuce, kasan halin mata tana iya cewa ba san nake ba jikin ta nake so..! the truth is i love her from the bottom of my heart, i love Nihal so much Ammar bansan san da na fara san ta ba, I can't remember, I never thought it will be happen to me, not even in my dream Ammar" "Please stop making this so diffcult just Architech that's normal you will soon get used to it, and I now Nihal zata so ka sultan kuma matar ka ce kana da damar fada mata ko wani lokaci, nasan ma baza tayi wannan tunanin ba" shuru sultan yayi can kuma yace, "toh shikenan zan yi trying but not now yet" Yaune aka kawo wasu Nihal kayan ankwan da za'a sa na dinner material blue mai kyan gaske da head white daga kayan suke suna kalla kowa na gwada nashi, Basmal ce tace, "gaskiya aunty Nihal wannan rigar ta maki kyau dubi yadda ta kama jikin ki das kamar dan ke akayi ta" murmushi Nihal ta saki tana kallan mirror ita kanta kayan da dinkin sun mata dan ba karamin dinki aka mata ba minal tace, "wallahi kuwa riga ta zauna maki sosai, dayake aunty Nihal din me kyau ce" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "kema naki sun maki kyau minal kamar dake akayi su" "Saura mu jira lokaci" nawwara ta fada tana zuge zip din rigar ta, Aziza dake makale bakin kofa kwafa tayi tare da cewa naga yadda zaki sa kayan har ki je dinner anjima, kad'a kai Aziza tayi tare wuce wa daki Nazili. Nazili dake tsaye gaban dressing mirror tana gwada kayan ta murda kofar da akayi ne ya sata juyowa Aziza ce ta shigo dauke da tray din abinci ta aje a center table tana cewa, "sannu da hutawa Gimbiya" Juyowa Nazili tayi tana cewa, "yauwa zo ki zuge min zip din kayan nan ki shirya min komai nawa saboda anjima nima zani dinner" cike da gulma Aziza tace, "oh shiyasa dazu naga aunty Nihal na gwada wani dinki mai kyau kala naki Ashe itama dinner zata" juyowa Nazili tayi a fusace tana kallan Aziza cikin zafin rai tace, "se na haram ta mata zuwa dinner saboda bana anko da matsiyata a kan wani dalilin zan sa kaya iri daya da tallaka" tab'e baki Aziza tayi tana cewa, "dinkin ta ma naga ya so yafi naki Allah ya huci zuciyar ki" juyowa Nazili tayi tare da bigewa Aziza baki cikin masifa ta kankace ido tana cewa, "Allah ya sauwake ace wannan almajira kayan ta sunfi nawa, ya kamata ki iya bakin ki yar matsiya ta shashasha kawai" Aziza dafe da baki ta rakube a bango tana bin Nazili da kallo amma kamar masifa kullun tana like da Nazili, zagaye daki Nazili ta shigayi rake da kugu tana cewa, "ban san yaushe zan cin ma buri na a kan wannan shashar ba" murmushi Nazili ta saki tare da furta "se na haram ta maki sa kayan nan, Aziza ina so ki san duk yadda za kiyi ki dauko min kayan nan ki kawo min su a hannu na" Nazili ta ida zancan tana waigowa murmushi Aziza ta saki tare da cewa, "angama ranki ya dade" sannan ta fice Su Nihal na gama gwada kaya suka wuce part din mom dan dauko sauran kayan da za'a rabawa yan'mata amarya a dinner. Hakan ya ba Aziza damar shiga dakin Nihal linke ta ga kayan Nihal saman bed dauka tayi da sauri ta wuce da su dakin Nazili, lokaci Nazili na zaune zaman jiran ta amsar rigar Nazili tayi tana murmushi tace, "kin kyauta Aziza kin min dai-dai" lighter Nazili da dauko a bedside drewar tare da kunawa kasan rigar wuta, kama ci da huta rigar tayi se da tayi rabi Nazili tayi wurgi da rigar kasa tare da cewa, "bani ruwa Aziza" ruwa Aziza ta mika mata a glass cup ta zubawa rigar sannan tace, "ki maida ki aje inda kika dauke ta, ina so na sata bakin ciki a wannan daran se taje dauka taga ta kone" Nazili ta ida zancan tana dariya, daukar rigar Aziza tayi tare da cewa, 'idan ta gane ke ce fa Gimbiya" "Ko ta gane babu abinda zata iya kije ki kai mata ki aje kamar yadda nace maki" A gajiye likis Nihal ta dawo part din Ammi bedroom din ta kawai ta wuce ko lura da abinda akayi ma kayan ta ba tayi ba ta dauka ta wuce part din sultan, saman sofa ta aje kayan ta shiga toilet wanka Nihal ta sheke ta fito sanye da towel lotion kawai Nihal ta shafa kasancewar yamma tayi me make up na part din mom tana jiran ta rigar kawai Nihal ta janyo ta saka abinda ta ganine yasa Nihal shock tsare rigar tayi ta ido tare da damke ta a hannun ta tasan ba me aikata mata haka se Nazili saboda ita kad'ai ce ta tsane ta a gidan hawayan takaici ne suka fara zubowa Nihal share hawayan tayi tare da daukar rigar ta fita da sauri. Nihal bata zame ko ina ba se dakin Nazili tana shiga ta banka kofar da karfi Nazili dake zaune ce ta mike hannu ta nad'e a kirji tana bin Nihal da kallan wulakanci batayi auni ba Nihal ta dauke ta da mari har so biyu ji kake tas, tas........ ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/11, 10:19 AM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 101_102* *_wannan page din naki ne ke kad'ai aunty Khadija Hamu kiyi yadda kike so da shi,🤗 godiya ta musanman gare ku masoya SAUYIN RAYUWA yawan comments yawan posting_*🤪 azabure Nazili ta mike tana maida numfashin dafe da kunci sakwamakwan baccin daya dauke ta tayi mumuna mafarki Nihal ta tsinka mata mari maida gashin kanta tayi baya tana cewa, "god for bit..! da sauri ta duro daga saman gado kofar dakin ta ta murd'a tare da leka main parlour iska me zafi Nazili ta furzar dawowa tayi cikin dakin tare da daukar jug ta tsiyaya ruwa cikin glass cup ta shanye tas tana kallan mirror tana duba kuncin ta cikin zafi rai tace, "amma dai anyi mayar mata har ciki bacci bata saurara min ba, kafi ta ci mun fuska ni zan fara aikata mata hakan..! Nazili ta ida zancan tana zagaye dakin ta jin an murda kofa ne ya sata juyowa a razane tana kallan kofar, Ammi ce ta shigo tsare ta da ido Nazili duk tayi zuru-zuru kamar mara gaskiya Ammi ce ta matso gaban ta tana cewa, "what wrong with you naga kinyi suku-suku dake" juya baya Nazili tayi tana cewa, "nothing Ammi daga bacci na tashi shiyasa" Nazili ta ida zancan tana zama saman gado matsowa Ammi tayi bakin gadan ta zauna tana cewa, "har yau ba ki daina halin kwanciya da yamma ba ko bayan kin san hakan ba kyau, yan'mata se shirwa suke ban ganki a cikin su ba" tab'e baki Nazili tayi tare da cewa, "yanzu zan shirya Ammi" ta ida zancan zata mike ruko hannun Nazili Ammi tayi tare da cewa, "Nazili ina san magana dake..! maida hankali Nazili tayi kan Ammi, Ammi ta cigaba da cewa, "Nazili ya kamata ace kema by now kin fido miji kinyi aure na lura dake har yanzu kamar aure baya gaban ki, ki duba ki gani duk sa'anin ki suna gidan mijin su wayanda basu yi ba suna da tsayaye amma ke ba ko daya" zame hannun Ammi Nazili tayi tana cewa, "oh my goodness Ammi how many time zan fada maki ban shirya yin aure ba impact ma har yanzu ban ga namijin daya dace dani ba..! Nazili ta ida zancan zata shige toilet maganar da Ammi tayi ne yasa Nazili tsayawa cak "Nazili ya kamata kiyi ma kanki fada idan ma sultan kike zaman jira ya zo ya aure ki ya kamata ki farka daga wannan mafarkin, da be ce yana san ki ba se yanzu da yayi aure ze dawo maki Nazili, kuskure anriga da anyi shi Nazili ya kamata ki gane hakan" juyowa Nazili tayi rai bace tana kallan Ammi hannu ta nad'e a kirji tace, "yanzu na gane me ya kawo ki Ammi kin shigo daki nane saboda ki bata min rai, idan har kin san haka ne kofa a bude take kina iya fita, dan kowa nayin aure what ever bashi ze sa ki tirtse ni dole se nayi aure ba, koma me ya faru ai laifin ki ne me yasa baki hana sultan yin auran ba, bayan kin san da cewa ina san sultan tun tasowata amma kika rufe ido kika ba almajira, kika cusawa sultan san Nihal, mi yasa baki cusawa sultan so na ba,? baki da wannan amsar amma ni ina da ita saboda ba kya sona cikin jikokin ki, tunda kika aikata haka aikin riga kin rabani da sultan saboda i can't stay under the same roof with almajira Ammi" murmushi Nazili ta saki tare da matsowa kusa da Ammi suna kallan juna tace, "let me tell you something Ammi ni yanzu sultan baya gaba na saboda yana san matar shi Ammi a kan wani dalilin zan zauna zaman jiran shi, ke ma Ammi kinyi gaskiya da kika ce sultan be ce yana so na da ba se yanzu..! Nazili ta ida zancan hawaye na sulalo mata a kunci rungume ta Ammi tayi tana cewa, "Am sorry for that Allah ya maki albarka da kika gane hakan, amma dan Allah ki daina cewa bana san ki Nazili ina sanki Nazili ina jin ki har cikin zuciya ta" Ammi ta ida zancan tana shafa kumatu Nazili idanuwan ta cike da kwalla, rungume Ammi Nazili tayi kamar tayi sanyi ta saduda, murmushi Nazili tayi cikin zuciyar ta tana cewa, Ammi kenan kina tunanin zan zuba ido ne ina kallan su, nayi hakan ne kawai dan na fita daga zargi ko da na aikata wani abun baza a ganeni ba..! Nazili ta ida zancan zuci tare da numfasawa zame jikin ta Ammi tayi tana murmushi itama Nazili murmushi ta saki tare da cewa, "Ammi bari na shige toilet nayi wanka, ki daina tunanin san sultan ne ya hanani fida mijin kawai ban samu wanda muka daidaita bane" Nazili ta ida zancan tana shafa kumatun Ammi kissing hannu ta Ammi tayi sannan ta fice d'an siririn tsaki Nazili ta saki tare da shigewa toilet. Bangaran Nihal kuwa zama tayi saman gado tana kallan rigar siraran hawaye na zubo mata duk da ta san wacece zata iya aikata mata haka amma bata da tabas kan hakan, wai mi tayiwa Nazili ta tsane ta haka, idan ma kan sultan take mata haka ita sultan ba damun ta yayi ba kuma ai ba ce mata akayi arzikin gidan su ya d'ad'a ta da kasa ba ne da zata rinka wulakantata, ko da yake ba laifin ta bane rashin nuna tana da tushe ne ya janyo mata tsana wajan Nazili, amma ta kuji zuwa rafi wata rana tulu ze fashe jin kamar an tabata ne yasa Nihal juyowa a dan razane sultan ne tsaye kanta goge hawayan fuskar ta Nihal tayi da sauri ta rarumo hijab din dake kusa da ita, ta saka tana kokarin fita kama hannun Nihal sultan yayi ya tsare ta da sexy eyes ball din shi yace, "what's wrong with you, why those tear,? sultan ya jefawa Nihal tanbayar shuru Nihal tayi idanuwan ta taf da kwalla tana wasa da rigar hannu ta, matsowa sultan yayi gaban Nihal yace, "kinyi shuru Nihal waya bata maki rai? da kyar Nihal ta iya nunawa sultan rigar da aka kona mata tare da saki kuka tana cewa, "ban san waya min haka ba kawai naga rigar haka, yanzu ni shikenan bazani dinner ba tunda bani da ashobe" Nihal ta ida zancan a shagwabe hawaye na wanke mata fuska sultan ko a zuciyar shi yasan haka tana iya faruwa saboda ya lura yanzu kamar kan matar shi aka dawo dan a tarwatsa mata fari cikin ta, kamar ya sani ya dinka mata nashi dinki na daban murmushi sultan ya saki bin shi da kallo Nihal take sannan ta had'e rai tana cewa, "dadi ma ka ji..? ta ida zancan zata zame hannu ta daga rukwan da sultan ya mata janyo Nihal sultan yayi ta fada saman fafadan kirjin shi zaro ido Nihal tayi tana kokarin kwace kanta a hankali sultan yake magana kamar me rada yana cewa, "ba kina da karfi ba ki kwace kanki mana" sultan ya ida zancan yana kashe ma Nihal ido wiki-wiki Nihal tayi tana girgiza kai tace, "ya hakuri ka sake ni please" sasauta rungumar da sultan ya mata yayi da sauri Nihal ta ja baya ruko hannun Nihal sultan ta yayi, be zame da ita ko ina ba se bakin drewar Nihal na biye da shi, drewar ya bud'e tare da ciro gwon ya mikawa Nihal d'aga rigar Nihal tayi abin mamakin shine wannan riga ta fi wacan haduwa nesa ba kusa ba dinki ba karamin kyau yayi ba gaban dressing mirror Nihal ta tsaya tana kallan rigar wani irin murmushi ta saki da karfi Nihal ta furta, "wow..! dan bakin ta ya kasa rufuwa saboda murna, juyowa tayi tana kallan sultan cike da murna tace, "amma na gode wannan rigar tafi tawa kyau sosai sultan, duk wanda ya gani da wanna rigar se ya kalla ya kara kalla" Nihal ta ida zancan tana washe baki sultan yace, "saboda nasan zatayi ma princess kyau na aje mata dama can ita nake so ki sa" murmushi Nihal ta saki tare da shigewa toilet da sauri rigar kawai ta saka ta fito a hankali ta tako sultan dake zaune saman sofa bin ta yayi da kallo saboda kyan da rigar ta mata mikewa yayi a hankali ya tako gaban Nihal yana kallan ta wayar shi ce dake ruru ta katse mashi hanzari daukar wayar yayi tare da cewa, "kuna inayi shigowa" murda kofar da akayi ne yasa Nihal juyawa masu make up ne mata suka shigo washe baki Nihal tayi tana kallan su tana kallan sultan wani irin dadi na ratsa ta sultan ne ya katse mata tunani da cewa, "ki je suna jiran ki fa, bari naje na dawo" sultan ya fada tare da ficewa, cike da murna Nihal ta zauna anayi mata make up me kyan gaske tasha mamakin kyan data zuba su kan su masu make up din yaba kyan da Nihal tayi suke rose ce daya daga cikin masu make up din tace, "ran ki yadade wannan kyau da kikayi har kin so kifi amarya" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "rufa min asirri ina ni ina fin amarya" dariya rose tayi tace, "toh shikenan haka dai kika ce amma ni gani nake ta kusa fin amarya ko Rachel," Rachel dake hada kayan su cikin jaka tace, "wallahi kuwa har da ita din me kyau ce" haka suka gama hada kayan su suka fice, fitar su da yan mintoci sultan ya shigo ya shirya cikin shadda shi light blue tasha aiki da dark blue zare ba karamin kyau ya zuba ba kan shi na sanye cikin dark blue hula sajan shi ya kwanta luf-luf red lips din shi se shining yake Nihal ko mutuwar tsaye tayi tana kallan sultan, saboda kyan da ya mata shima sultan din kallan Nihal yake yana sakar mata kill smile din shi me sace zuciyar yan'mata har ya tako gaban ta Nihal na kallan shi da jinjina irin kyan da manya kaya ke mashi, hura mata iskar bakin shi sultan yayi a ido, lumshe ido Nihal tayi a hankali ta sauke idanuwan ta saman fuskar sultan, sultan ne ya katse mata tunani da cewa, "kallan fa?, na canza maki ne? sultan ya fada yana daga ma Nihal gira, da sauri Nihal ta juya har tana bari da kayan dressing mirror cije hakora Nihal tayi cikin zuciyar ta tana cewa, "karfa wannan mutumin ya rai nani me yasa ma na tsaya ina kallan shi" bayan ta sultan ya dawo ya tsaya tana hango shi ta cikin mirror sarka sultan ya ciro a aljihun shi ya matsar da gashin Nihal ya fara saka mata kallan sarkar Nihal take se kyalkyali sarka take a hankali Nihal ta daura hannun ta saman sarkar tana kallo tace, "wannan sarkar fa sultan" murmushi sultan ya saki yana cewa, "Ammi ce ta bani na saka maki, idan baki so se na maida mata" turo baki Nihal tayi tana kara shafa sarkar tana smile tace, "ya za'ayi na ce bana so bayan sarkar ta min kyau, kuma fa ammi ce ta bani amma na gode sarkar na da kyau sosai dubi yadda ta min kyau" Nihal ta ida zancan tana washe baki sultan kuwa dadi yaji saboda shi ya siya mata sarkar ba wata Ammi ya fada ne kawai, hata dan kunna sarkar sultan ne yasa mata kallan juna suke ta cikin mirror kamar kar su daina cikin siririyar murya ta Nihal tace, "na gode sosai sultan ka sani farin ciki a wannan daran" Nihal ta fada tana smile, hugging din Nihal sultan yayi ta baya a hankali ya sakarwa Nihal kiss a wuya ya furta "kinyi kyau..! kasa da kai Nihal tayi zuciyar ta na tsana ta harbawa cike da tsoro tana wasa da yan yatsun hannun ta a haka suka fito. compound mota na fake tana jiran su murfin mota sultan ya bud'e mata sannan ya zagaya ya zauna driver ya ja mota. Hall din dinner ya cika makil da yan'uwa da abokan arziki MC se zubu yake yanayi ma yan'uwa da abokan arziki sannu da zuwa, Amarya da ango tuni sun halara Ammar ya sha kyau har ya gaji yana sanye cikin brown shadda malin-malin tasha aiki da dark brown zare Basmal tasha kyau cikin red material da head red tasha kyau har ta gaji rigar se jan kasa take kallo daya zaka masu kasan sun dace da juna se smile suke sakarwa juna su mai cike da su da kauna, cikin sanyin murya Basmal tace ma Ammar, "har yanzu yayana da aunty Nihal basu zo ba Allah yasa lafiya" murmushi Ammar yayi yana cewa, "Rabin rai na suna kan hanya nasani kin ji" daga mashi kai Basmal tayi tana smile, Dr Amir ma ya zo tare da matar shi fatima Dr bello ma ya zo da matar Bilkisu biki dai se bidiri ake minal da nawwara sun zo se zuba rawar kai ake Nazili ma ta zo tana sanye cikin ashoben ta tasha kyau har ta gaji amma rashin ganin sultan ya sosa mata zuciya saboda tasan baya wuce yana wajan Nihal, irin yadda MC ya shiga wasa Nihal da sultan ne yasa gabaki daya hankalin mutane ya koma kan Nihal da sultan mutane se yaba kyan su suke da haduwa wasu mata har cewa suke dama su, a tunanin MC amarya da ango biyu ne a bikin shiyasa ya zage yana ta koda Nihal da sultan dake takawo se smile sultan yake tunda suka taho yake makale da Nihal, Nihal ko kunya duk ta ishe ta duk yadda taso sultan ya sake ta amma yaki itama murmushi yake kawai take, Nazili dake zaune mikewa tsaye tayi ta kafe Nihal da ido kallan kayan jikin Nihal din kawai take kishi ya rufe ta a fusace ta dau fost din ta zata fice, rike mata hannu da akayi ne yasa ta tsayawa cak a fusace Nazili ta dago Nihal ce ta rik'e mata hannu tana murmushi matsowa kusa da Nazili tayi cikin rada tace, "karkiyi tunanin bangane ke kika kona min kaya ba, saboda baki san gani almajira wajan dinner, kamar yadda kike fada kuma matar sultan, ina mai baki shawara kada ki kuskara sauran mutuncin dake tsakanin mu ya zube Nazili" matsowa Nihal ta kuma yi dai-dai setin kunna Nazili tace, "nasan cewa kina mamakin ina na samu kayan dake jiki na, anyway sultan ne ya dinka min saboda yana san farin cikin almajira...! kwace hannu ta Nazili tayi idanuwan ta a kankance tace, "what do you mean by tell me this nonsense Nihal, how dare you..! nuna Nihal da yatsa Nazili tayi sannan ta kad'a kai tace, "kinyi na farko kinyi na karshe, you must pay for this rubbish you have done to me Nihal" rike dan yatsan Nazili Nihal tayi tana cewa, "karki kara nunani da yatsa if not am gonna teach you a lesson, kuma ina so ki sani cewa sultan nawa ne ni kad'ai, sultan na almajira Nihal ne a haka ya gani kuma yake so I hope you get me right..! Nihal ta ida zancan tare da matsawa jikin sultan tana shumin murmushi idanuwan Nazili cikowa sukayi da kwalla tana kallan yadda sultan ya zagaye hannun shi a waist din Nihal, da sauri Nazili ta juya baya hawayan bakin ciki na bin kunci ta cikin zuciyar ta tana cewa, "Nihal you must pay, how dare you zaki sani kuka how..! da sauri ta bar hall din ko ganin gaban ta batayi, fadawa saman fafadan kirjin Alex da Nazili tayi ne ya sata tsayawa cak tare da rushewa da kuka, Alex dayake kokarin shigowa hall tsayawa yayi zuciyar shi na tsana ta harbawa da kyar ya iya banbare Nazili daga jikin shi yana cewa, "Gimbiya miya same ki..? ko saurara shi Nazili ba tayi ba ta ruga da gudu ta shige mota da sauri Alex ya bi ta a baya, amma ina ta figi mota cikin hight speed ta bar harabar wajan rike kugu Alex yayi tare furzar da iska me zafi juyowa Alex yayi ya dukawa ya dauki fost din da Nazili ta yadda a kasa yana kalla sannan ya maida ta ciki mota cike da mamakin yana yin daya ganta duk se be ji dadin hakan ba, har wata zuciyar na cewa ya bita. hoto dai Nihal da sultan sun shashi kamar dinner bikin su Minal da nawwara ban da yaba kyan Nihal ba abinda suke, matan abokan Sultan se nan suke da Nihal, Nihal ko ta saki jiki da su ana hira har tanbaya suke yaushe sultan ze kawo masu ita, ansha dinner an cashe anyi ciye-ciye da lashe-lashe naira tayi kuka har ta raina kanta dinner tayi kowa ya gwangwaje a haka taro ya watse ana fatan Allah ya maimaita. Washe gari ta kama ranar daurin aure a ranar ne misalin karfe 2:00pm na Asabar dinbin mutane suka sheda daurin auran *AMMAR MUSA WAZIRI DA MATAR SHI BASMAL UMAR MATAWA SARKIN KANO* manya-mayan kosushin gwabnati sun halari daurin auran da manyan yan'kasuwa da sarakuna na garuruwa daban-daban a nan ne hango ango sanye da fara shadda malin-malin shi da sultan sun sha kyau har sun gaji se murmushi suke saki suna mika gaisuwa ana masu kirari da bushe-bushe suna ta ruwan kudi da friends din su kowa ya gansu yasan cewa yau ranar farin ciki ce. Cikin gida ma ya kacame anata busa algaita Amarya na sanye cikin had'adan lace din ta Ash da ratsin pink tasha silver alkyaba tasha aiki da gold zare can na hango Nihal sanye da lace milk me ratsin blue a jiki, dinkin ya kama jikin ta sosai se hada-hada take busar daka fara ne ze sheda maka angwaye sun shigo, busa karu tayi a gidan har angwaye suka shigo main parlour suna ta kwasar gaisuwa ana hotuna, Nihal ce dauke da wasu kaya zata wuce da su dakin Amarya sultan ta gani bakin kofa kallo daya ta mashi ta kauda kai tana kokarin wucewa amma sultan ya tare mata hanya matsawa tayi sultan ya kara tare ta matsowa sultan yayi kusa da ita dai-dai setin kunnan Nihal kamar me rad'a yace, "kin yi kyau my dear kamar na sace ki" kiri Nihal tayi tana kallan sultan tana kokarin tantance maganar daga bakin shi ta fito harara Nihal ta maka mashi can kasan makoshi tana cewa, "ai dama ni din mai kyau ce, se yau ka fara gani kyan nawa, ka fara matsamin fa" Nihal ta idan zan tana tsare sultan da ido kokarin rabawa tayi ta gefan sultan ta wuce fisgo ta sultan yayi ta fada saman fafadan kirjin shi zaro ido waje Nihal tayi tana cewa, "sultan cikin mutane fa muke baka ganinene, wai mi yasa kake min haka ne" Nihal ta ida zancan tana waige-waige sakar mata kiss sultan yayi a kumatu zaro ido Nihal tayi tare da ture sultan ta bar wajan da sauri tana waigen sultan, alamarin sultan yanzu ya fara ba Nihal tsoro Nazili dake tsaye bayan sultan duk abinda ya faru a idanuwan ta ya faru hadiyar zuciya ne kawai ba tayi ba saboda takaici, tare da kudirtawa zuciyar yadda zata bulowa Nihal. Nihal ce ta shigo dakin Basmal tare da maida kofa ta kud'e da sauri ta jigina da kofar murmushi ta saki Basmal ce ta katse mata tunani da cewa, "Aunty Nihal me sirrin naga kin shigo kina murmushi," murmushi Nihal ta saki tace "ba komai kayan da zaki sa na amso maki" "Hmmm idan tayi tsami zamu ji" aje kayan Hannun ta Nihal tayi tana cewa, "bama..! bata ida rufe bakin ta ba Minal ta shigo tana cewa, "aunty Nihal yaya na kiran ki yace ki same shi a part din ku," jum kad'an Nihal tayi tana cewa, "ni kuma..? Basmal tace, "toh wacece matar shi a nan dake yake ko dan kin ga idanuwan mutane" Basmal ta ida zancan tana kashe mata ido murgudawa Basmal baki Nihal tayi tana cewa "ban taba ganin amarya me sa'a ido irin naki ba" Nihal ta ida zancan tare da ficewa tana cewa, "shi kuma wannan ya fara shiga rayuwa ta, ko mi zan mashi oho bayan ya gama kunya tani cikin jama'a, duk wata tsirfa ya iyata gaban mutane kuma hakan bashi ze hana a san irin zaman da muke ba..! haka Nihal ta fito tana surutai har ta wuce part din su kaitsaye zaune a parlour ta sami sultan a dining area tsayawa Nihal tayi tana cewa, "gani..! cikin kosawa Nihal tayi maganar dago ido sultan yayi yana kallan ta can kuma yace, "ki zo ki zauna mu ci abinci, nasan baki ci komai ba tun safe..! galala Nihal tayi tana kallan sultan yanzu har shi ke damuwa da cin abincin ta cikin rashin kulawa Nihal tace, "na koshi bana jin yunwa," murmushi sultan ya saki yana cewa, "tunda kin koshi se kiyi feeding nawa..! ni yunwa nake ji" sultan ya ida zancan ba tare da ya kalli fuskar Nihal ba sakatarere Nihal tayi tare da cewa, "kai yaro ne da zanyi feeding naka da can ni ke baka abincin uhm ka ga tafiya ta" Nihal ta ida zancan tana nufar kofar fita da sauri sultan ya sha gaban Nihal tare da sama kofa key ya kule ya tura key din cikin aljuhu a hankali ya shiga takowa Nihal na matsawa har ya manna ta jikin bango rintse ido Nihal tayi jikin ta na rawa ta rasa wannan bibini da sultan ke mata indai haka abota take toh wallahi ta kusa yanke ta ina dalili, a hankali Nihal ta bude ido tana kallan sultan daya raba hannuwan shi a bango ya mata runfa cikin sweet voice din shi sultan yace, "zaki bani abincin ko...! sultan ya ida zancan yana kokarin hada bakin su waje daya rintse ido Nihal tayi ta kauda kai jikin ta na rawa ta kara shigewa jikin bango tace, "aah zan baka dan Allah ka matsa zan baka, wai me haka kake sultan, wai me ke damun ka ne zan baka" ja da baya sultan yayi yana murmushi tare da shafa sumar sa yace, "toh shikenan" ya koma dining ya zauna kallan shi Nihal keyi gaban ta na tsana ta faduwa da alajabin sauyin da sultan ya samu kamar ba miskilin data sani ba, suna hada ido ta kauda kai tana cewa cikin zuciyar ta, "wannan bibini har ina" haka Nihal tayi serving sultan shinkafa da miya taji naman rago da coslow da vegetable, spoon Nihal ta dauka tare da zama sultan na kallan ta ta kasan ido har ta kamala zubawa a hankali ta debo abincin ta nufo bakin sultan kauda kai sultan yayi yana cewa, "mi ya sami hannu ki? da hannu zaki bani" aje spoon din hannu ta Nihal tayi tare da sakin shumin murmushi watsa hannun ta Nihal tayi cikin abincin tana wani juya abinci kamar me dama fura da hannu sannan ta ciro hannu ta daga cikin plate din ta tura ciki bakin ta tana lashe hannu tana yi tana kallan sultan daya tsare ta da ido yayi tagumi yadda Nihal take ma abincin duk dan ta bata mashi rai, yace ta tashi ta bashi guri, bata san komai nata birge shi yake ba se da Nihal ta lashe hannun ta tas sannan ta dagawa sultan gira tare da debo abincin ta nufo bakin sultan da murmushi sultan ya bud'e bakin shi tsare shi da ido Nihal tayi tana cewa cikin zuciyar ta ci zeyi kenan wiki-wiki Nihal tayi da ido tana washe baki taba sultan abinci a baki lumshe ido sultan yayi tare da ware su yana cewa, "abincin yau yafi na kullun dadi, duk san da zan ci abinci ke zan kira kiyi feeding nawa" had'e rai Nihal tayi tare da cigaba da feeding din sultan yana ci abincin hankali shi kwance mamaki kuwa ya hana Nihal kwakwaran motsi, debo abinci Nihal tayi karo na uku ta kai bakin sultan wannan karan har da finger din ta ya hada ya ciza, cikin sigar wasa da jan hankali yar kara Nihal ta saki cike da shagwaba ta mike tana matsar kwalla zata bar wajan, hugging din ta sultan yayi ta baya tare da daura kanshi gefan kafadar ta wani irin shock suka ji lokaci daya daga sultan har Nihal rawa jikin Nihal ya dauka cikin honey voice din shi sultan yace, "am sorry" sultan ya ida zancan yana kama hannun Nihal a hankali ya shiga hura mata iskar bakin shi me sanyi a finger's din ta lumshe ido Nihal tayi wani saban yana yi na shigar ta juyo da ita sultan yayi ya rungume tsam a jikin shi ya lumshe ido yana sauke numfashin a hankali san Nihal na kara shigar shi da kaunar matar shi, lamo Nihal tayi a fafadan kirjin shi zuciyar ta na tsana ta harbawa da kyar ta iya janyo jarumtar ta, ta ture sultan saman kujera sultan ya fada yana kallan Nihal door key Nihal ta dagawa sultan hugging nata da yayi shi yabata damar zare key din a cikin aljihun shi da sauri ta bud'e kofar parlour zata fice ta kara waigowa murmushi sultan ya sakar mata harara Nihal ta maka mashi tare da ficewa da sauri. Da yamma aka shirya Amarya aka wuce da ita fadda maimartaba ya mata nasiha mai ratsa jiki tun a nan Basmal ta fara kuka haka aka fito da ita Ammi ta dasa nata ta ida zancan da cewa, "mom zaki ce wani abu? mom tace, "to ni se dai nace Allah ya bada zaman lafiya yi nayi bari na bari, se dai ko momi zata ce wani abu," Gimbiya jalila tace "bani da abin cewa Allah ya bada zaman lafiya ya nuna mana na Ashad" daga nan aka wuce da Basmal gidan Waziri hannun bibiyu Adda ta amshi amare, a nan aka basu daki kafin washe gari Ammar ya dauki amarya shi su tafi honeymoon US. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/12, 7:41 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 103-104* Washe gari da safe waziri yayi ma Ammar nasiha mai ratsa jiki tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya shi da Amarya, kaitsaye part din shi ya wuce a bedroom ya sami sultan yana hada mashi kaya cikin trolley, murmushi Ammar ya saki yana cewa, "kai amma fa na gode dude, se hidima kake tunda aka fara bikin nan baka samu hutu ba," rufe trolley sultan yayi yana cewa, "kasan bana san irin wannan abun me kuma abin godiya a nan, da kai da amarya ai duk nawa ne to me abin godiya, kara ka tafi kuna huta da kai" dariya Ammar ya saki yana cewa, "hmm zakayi missing nawa ne wallahi na tafi, dama kai har yanzu a bisa iska kake yawo kai da gwaro baku da maraba" pillow sultan ya janyo ya shiga makawa Ammar yana cewa, "ka rai nani wallahi karka manta ni yayan ka ne yanzu, kanwata fa kake aure amma duk wani iskanci ya iya fitowa daga bakin ka, ni dai yanzu kama girmana zan rink'ayi" dariya Ammar yake har da hawaye harara sultan ya sakarwa Ammar yana cewa, "Wai mi ka dauke ni ne d'an rai ni hankali zan rama ne Allah zan baka mamaki, baza ka daina min dariya ba" toshe bakin shi Ammar yayi yana kallan sultan yace, "gwaro..! da gudu ya fice da gudu sultan ya biyo shi Adda dake dauke da tray din abinci zata wuce part din Waziri kafin ya wuce fadda, da gudu Ammar ya boye bayan Adda da gudu sultan ya karaso zagaye Adda suka shigayi Adda tace, "wai yaushe zaku girma ne, har yanzu baku daina wannan yarintar ba ko se kun aje ya'ya zaku bari" tsayawa sultan yayi yana aikawa Ammar harara dake bayan Adda, Adda ta cigaba da cewa, "kai ko kunya baka ji amarya ka fa na cikin gidan nan amma maimakwan ka natsu amma se kara balewa kayi, kuma duk ta kare kai ne mara gaskiya, meya hada ku? Ammar ne ya bud'i baki zeyi magana sultan ya fisgo shi ya toshe mashi baki se kokarin banbare hannu sultan yake girgiza kai Adda tayi tace, "Allah ya shirye ku" sannan ta wuce part din waziri rankwashe sultan ya sakarwa Ammar a kai sosa kanshi Ammar ya shigayi sultan kuma ya had'e rai, a haka sultan da Ammar suka fito sultan yana rike da trolley har suka iso compound dago kan da sultan zeyi ya hango Nihal tare da Basmal ta rako ta suna ta dariya kallo daya Nihal tayi ma sultan ta kauda kai Ammar ne yace, "amma dai na gode Nihal da kokari ke da kanki ki dauko min Amarya ta, har da ina cewa wannan ya tsaya na dauko abita" murmushi Nihal tayi tana cewa, "laaa ba komai Allah ya kiyaye hanya" ta ida zancan tana budewa Basmal murfin mota tana mata bye-bye harara sultan ya watsawa Ammar yana cewa, "zaka dawo ka same ni" sultan ya ida zancan yana bude mashi murfin mota sinbul yasa trolley a booth driver ya ja mota Nihal ko ganin motar su Basmal ta bar harabar compound da sauri Nihal ta wuce part din mom dan gani take kamar sultan ze biyo ta saurin da sultan ya ga Nihal nayi ne ya hana shi bin ta. *********** Aunty Aisha ce zaune gaban yaya sani tana matsar kwalla tace, "haba yaya sani yanzu haka zamu zuba ido kan yarinyar nan, yau kimani wata biyu kenan ina maka magana kan yarinyar nan Nihal, ya kamata tanimu ya d'andana kudar shi amma ka rintse ido ka ce a'a" aunty Aisha ta ida zancan tana rushewa da kuka ta cigaba da cewa, "da ace yaya hansatu na raye baza ta tab'a yafe mana ba, abinda muke aikatawa be dace ba, tun tana raye ba ruwan mu da ya ta kwana ya ta tashi gashi yanzu ma diyar tata mun watsar da lamarin ta, bayan muna da rufin asirri da zamu iya ja da tanimu ni dai ba zan cigaba da zuba ido ba wallahi," yaya sani ya katse mata hanzari da cewa, "Aisha wai mi yasa baza ki gane abinda nake nufi ba shima fa tanimu waya gari sukayi ba yarinyar nan, ban ga dacewar a kai tanimu ga hukuma ba, saboda shima tamkar mahaifin ta yake bana tunanin zeyi abinda ze cutar da diyar d'an uwan shi, idan ma da sa hannun su Allah na gani, kuma zanyi iya bakin kokarin yan'sanda su gani inda Nihal take nima abun na damuwa, amma maganar mika tanimu Hannun hukuma ban laminci da ita ba" "toh shikenan yaya tunda bazaka dau mataki ba ni zan dauki mataki duk inda Nihal ta shiga a duniyar nan dole tanimu ya fada mana, dan ba tsoran shi muke ji ba idan ma mutuwa tayi sai ya fadama, ni dai kam se inda karfi na ya kara akan maganar nan kaga tafiya ta..! Aisha ta dau jakarta tana kuka hajiya farida matar yaya sani tana cewa, "ban ga laifin ki ba wallahi ai bazeyu ba shima alhaji ban san kafewar nan ta micece ba, ya wuce asasu bayan kanta su ci duka ai zasu fadi inda suka kaita ina anfani mutane mugaye ina goyan bayan ki dari bisa dari" hajiya farida ta ida zancan tana rako aunty Aisha compound har ta shige motar ta, ta bar harabar gidan tana ciwan baki sannan Hajiya farida ta shigo cikin gida tana kokarin wuce alhaji sani yace, "farida..! tsayawa tayi cak sannan tace, "idan ba maganar yarinyar nan zaka min ba da irin matakin da zaka dauka ba ni da kai ba wata sauran magana, duk sanda ka janye wannan bakar al'adar taka zamuyi magana, koma haihuwar ta tanimu yayi aka neme ta aka rasa ai ma ji dalilin bale kuma a matsayin sa na wan uban ta sannan gobe idan Allah ya kai mu zamu wuce shanono da yan'sanda" sannan hajiya farida ta haye sama ta bar yaya sani. ******* Abubuwa sun rincabe sun tsakude a gidan tanimu dan abinda zasu ci yanzu gagara su yake saboda duk wata kadara daya mallaka ta kare wasu sun kone kanikancin ma yaran sun gane cutar su yake tuni sun bar aikin, komai ya rushe komai ya tabarbare yau kimani wata guda kenan yana kwance yana ciwo ko tashi be iyawa danasani da nadama sun rufe shi wulakanci babu wanda be sha a hannu gwoggo, turo kofar da gwoggo tayi ne yasa tanimu dago ido yana kallan ta cike da masifa tace, "ni dai wallahi na gaji da wannan masifa tanimu idan ma zaka mike ka mike, ko kuma kasan nayi ina dalilin kullun cikin fidda kayan gida nake ina saidawa saboda mu samu nasawa a bakin sallati na gaji wallahi kama san nayi wallahi dubi yadda na rame na lallace kamar bani ba indo, nan gaba kad'an sai mun koma almajiranci na sani, toh wallahi ka sani mindin na gaji gida zan koma cikin dangi da yan'uwa tunda ina dasu kuma nasan zasu amshe ni hannu bibiyu" hawayan wahala ne ke sulalowa tanimu dajin dacin maganganun da gwoggo take watso mashi masu kama da harshan damo, kwata-kwata gwoggo bata damu ba se cigaba da cewa tayi, "kai kuma da an fara magana se hawaye kai ga makwarara sarki tsiyaya kai ka sani shawaraki kawai" jin kakarin amai ne yasa gwoggo fita waje a guje Sara ce keta amayar da garin rogwan da suka sasak'a tunda safiyar Allah, se amai take kamar zata amaye yan'hanjin ta sallati gwoggo ta rafka tana tafa hannuwa tace, "Mi nake gani Sara karki ce min cikin shege kika dauko min nabani ni indo, tashi dan ubanki kimin bayani" Sara da ta galabai ta da kyar ta iya debo ruwa ta wanke bakin ta tare da share wajan gwoggo na tsaye tana kokarin wucewa gwoggo ta fisgo ta tace, "zaki fada min wani tsinanene ya maki ko saina kashe ki" gwoggo ta ida zancan tana kirbar Sara kamar Allah ya aikota kuka Sara take tana ihu da kyar ta samu gwoggo ta saurara mata tana haki tace, "zaki fada min koko? cikin kuka Sara tace, "wallahi gwoggo ban san waya min ciki ba" dokewa Sara baki gwoggo tayi tana cewa, "a ruwa kika sha cikin ko min dan ubanki" muciya gwoggo ta dauko zata makawa Sara ta zunduma ihu tana cewa, "zan fada..! cikin shashekar kuka tace, "wallahi gwoggo ban sani ba saboda ba mutum daya nake bi ba" "laaaha'ilaa gwoggo ta ida zancan tana cewa, "na bani ni indo yaushe raban ki da al'ada dan ubanki wanene na karshe wanda daga shi baki sake al'ada ba," sauke numfashin Sara tayi tana cewa, "Audu giya..! sallati gwoggo ta saki tana cewa, "wannan matsiya cin dan shaye-shayan wanda daya wuce se gori ya dauka, wanda nayi daduro da shi san da ina yan'matanci ki rasa wa zaki bi se shi tsoho sa'an uban ki wannan ma ai yama girmi uban naki, tallaka fitik fakara'u alalrurati na shiga uku ni indo..! zama gwoggo tayi tana matar kwalla tana cewa, "kin cuce ni Sara da ilimin ki da komai, ko cutar (S) aka ce Audu giya nada ita ban gardama a halin yanzu dai, nayi asara kudin tara dana baki da kika je boko dan ki waye ashe tukunya kike shiga" tanimu dake daki duk abinda gwoggo ke fadi yana ji yau ya tabatar da mi ya aura dai-dai da halin shi ya samu yayi kuka kamar zuciyar shi ta tarwatse yayi danasanin abinda yayima yan'uwan shi babu abinda yake gani sai su a idanuwan shi suna firgitashi tabas yasan karshan shine ya zo yana mai rukwan Allah ya taimake shi Nihal ta dawo ya nemi gafara ta kafin Allah ya dauki ran shi, Allah sarki kanwata haulatu ko tana ina yasan tana raye amma ya mata kurciya ko ina take a duniya yasan baza ta taba dawowa kauyan nan ba, sai dai idan asirrin daya mata ya kare kuma abinda be taba yuyuwa ne saboda boka yadade da mutuwa tun bayan rasuwar Habu kuka ne ya kubuce mashi. ***** misalin karfe 4:30pm jirgin su ammar ya isa US kaitsaye masaukin su suka wuce iyakar haduwa wajan ya had'u fadin tsaruwar shi bata lokaci ne bayan sun ci abinci sun dan huta Basmal ta wuce toilet dan watsa ruwa haka shima Ammar. Basmal ce tsaye gaban dressing mirror daga ita se towel ta nad'e gashin kanta da wani tana shafe jikin ta da lotion mai kamshi, turo kofar da akayi ne ya sata dagowa Ammar ne ya shigo gabaki daya rudewa Basmal tayi tana neman abinda zata rufe jikin ta da shi abin ma dariya ya bashi yace, "duk ke kad'ai" rintse ido Basmal tayi tare da rufe fuskar ta da tafin hannun ta Ammar kuwa gabaki daya ya rikice a hankali Ammar ya tako gaban ta ya rungume ta ya saukar da nannauyar ajiyar zuciya yana shinshina kamshi ta, cikin murya rada yace, "my love ki je ki dauro alwala ki zo muyi sallah mu godewa Allah daya nuna mana wannan rana" Basmal ko bakin ta ya mutu da kyar ta iya jan kafafuwan ta ta shige toilet ta dauro alwala ta fito a zaune saman daduma ta sami Ammar after dress kawai Basmal tasa tare da sa hijab sallah raka'a biyu suka gabatar tare da godewa Allah, bayan sun idar Ammar ya juyo ya kama kanta ya mata addu'a sannan ya saki murmushi yana kallan Basmal mikewa yayi ya bud'e fridge ya ciro fresh milk ya tsiyaya a glass cup tare da janyo Basmal jikin shi kunya duk ta rufe ta yana bata tana amsa har ta shaye shima ya sha sannan Basmal ta shirya cikin night dress din ta doguwar riga dai-dai gwiwa me d'an siririn hannu sannan ta haye bed ta kwanta kashe haskyan dakin Ammar yayi shima ya kwanta tare da janyo Basmal jikin shi wasa ya shiga yi da ita daga nan ya hada bakin su waja daya yana yi mata rikitantan kiss gabaki dayan su sun fita hayyacin su (ganin haka yasa na sulale na fice ba dani ba salalan kaza) ***** Yini yau duk yadda sultan yaso ya ga Nihal abun ya faskara dan kwata-kwata bata dawo part din su ba ganin baya iya jurewa rashin ganin nata, ya mike ya shirya cikin jeans and white shirt yayi kyau sosai har ya gaji se fitar da sanyayan kamshi yake kai tsaye part din Ammi ya wuce a parlour ya sami Ammi Dara nayi mata tausa dauke da fara'a sultan ya karasa tare da rungume Ammi ta baya ya mana mata pack a kumatu sannan ya dawo ya zauna yana kalle-kalle can kuma yace, "matar ina wife nane? tun safe ban kara sata a ido na ba," murmushi manya Ammi tayi tace, "tana garden dazu ina ji yara suna matsa mata suje garden tunda baka ganta ba to ta bisu" murmushi sultan ya saki tare da cewa, "bari na bi matata yaran nan basu bar min mata ta huta ko gajiyar biki bata sauke ba zasu daura mata tasu" sultan ya ida zancan tare da ficewa Dara dakeyiwa Ammi tausa wani irin dadi ne ya lullube tana jin dadin wannan kulawa da sultan yake nunawa Nihal Allah ya barsu tare ya tsare su daga sharin mahasada, Nazili dake bakin kofa tana kokarin fitowa magana data ji sultan yanayi ne ya sata juyawa ta fada saman gado tare da sakin kuka da tsinewa Nihal tana cewa, "se naga bayan ki Nihal natsane ki sai na raba ki da sultan har a bada" a haka baccin wahala ya dauke ta. Dariya da Nihal keyi shi ze tabatar maka da tana cikin nishadi ita da su nawwara tiyo Nasim ya dauko naba shukoku garden ruwa yabi Minal da Nihal yana masu barin ruwa suna dariya suna boyewa bayan shukokin dake garden janyo Nasim Minal tayi tana mashi cakulkuli yana dariya da sauri Nihal ta dauko tiyo din ruwan tana wanke Nasim da ruwa joyuwa da zatayi da tiyo ta wanke nawwara da ruwa, ruwan basu sauka ko ina ba se jikin sultan lumshe ido sultan yayi tsayawa Nihal tayi tana kallan sultan daya tsare da rikitatun idanuwan shi sakin tiyo din ruwan Nihal tayi tana kallan sultan bugun zuciyar ta na karuwa shima sultan kallan ta yake yana kallan yadda ta jike rigar jikin ta ta wani manne a jikin ta gashin kanta duk ya like a jikin ta, ture Nihal Nasim yayi batayi masauki ko ina ba se saman chest din sultan gabaki dayan su kasa sukayi saman grass carpet dariya Minal da nawwara suka saki Nasim kuwa cigaba yayi da jikasu da ruwa lamo Nihal tayi saman fafadan kirjin sultan suna kallan juna a hankali sultan ya matsar da gashin kanta daya rufe mata fuska ya daura finger din shi saman lips din ta yana yawa da shi mirginawa Nihal tayi da sauri ta bar jikin sultan tana kallan shi ganin Nasim ya biyo ta da tiyo da gudu Nihal ta shiga zagaye garden tana dariya ita da su minal janyo Nasim sultan yayi tare dayi mashi rada a kunne dariya Nasim yayi tare da cewa, "give me five..! tafawa sultan da Nasim sukayi amsar tiyo din sultan yayi Nasim ya dauko wani da gudu suka shiga bin su Nihal suna gudu suna dariri ku, daga Nihal sultan yayi cak Nasim na jikasu da ruwa Nihal na dariya faranran hakuran ta na bayana yadda sultan ke juya Nihal abin sha'awa ne cike da tsantsar so da kauna, Gimbiya jalali da yakumbo dake kokarin wucewa fadda maimartaba lalacewa tayi tana kallan su kwafa ta saki tana cewa, "ka ci lokacin ka ina sane da kai ba matawa nayi da kai ba, iska na bari ka sha fata na daya Allah yasa bata dauki ciki ba," murmushi yakumbo ta saki tana cewa, "idan ma ta dauka zubar da shi abu ne mai sauki" murmushi Gimbiya jalila tayi tare da matsowa saitin kunnan yakumbo tana magana murmushi yakumbo take saki sannan Gimbiya jalila ta janye jikin ta tare dagawa yakumbo ido ta wuce part din maimartaba. ****** Washe gari da safe bayan aunty Aisha ta gama kimtsawa tsaf ita da driver suka biya gidan yaya sani dan dauko hajiya farida ko da suka isa ta shirya su take zaman jira ita da Ahmad dan ta na fari amsar car key Ahmad yayi hannu driver suka dau hanya Shanono tare da yan'sanda, basu wani dade ba suka isa shanono a harabar kofar gidan tanimu Ahmad ya faka motar shi kallo daya zakayiwa gidan kaji baka marmarin sakeyi, Ahmad da aunty Aisha da hajiya farida a tare suka dunguma suka shiga cikin gidan a tsakar gida suka sami gwoggo da Sara gwoggo na dirkawa Sara magani zubar da cikin ganin su aunty Aisha yasa kwana sha dake hannu gwoggo sub'ucewa ya kife a kasa ba komai ya haifawa gwoggo haka ba se yan'sanda dake bayan su jiki na rawa gwoggo tace, "Allah yasa lafiya daga ina? tab'e baki aunty Aisha tayi tana cewa, "au baki gane mu ba kenan, tanimu na gida koko? bakin gwoggo na rawa tace, "yana cikin kurya amma baya jin dadi" "wannan damuwar ku ce ki shiga ki taso mana keyar shi, ko mu mushiga" inji aunty Aisha gwoggo wadda ta kid'ime ta rude tace, "baya iya takawa ko nan da can se dai ku shiga ciki" labinlan daki aunty Aisha ta daga warin daya doki hancin tane ya sata ja baya hanci dod'e tace, "office ku dauko shi tunda yana da rai kuma bakin shi be mutu ba, dole ya gayamana inda ya kai mana diya" haka yan'sanda suka kunna kai dakin Baffa yana matsar kwalla suka kinkimo shi yana cewa, "wallahi ban san inda yarinyar nan take ba ni kai na neman ta nake ido rufe kuyiwa Allah kuyi hakuri, kubar ni naji da wannan azabar nasan cewa sakaya Allah ke bibiya ta..! ko saurara shi basuyi su kayi waje da Baffa aunty Aisha tace, "idan ka je can kayi bayani" ihu gwoggo ta zunduma tana rike kafafuwan Aunty Aisha tana cewa, "kuyiwa Allah ku sakar min miji wallahi ko kun je da shi can se dai su karasa shi dan bashi da masaniya a kan inda yarinya nan ta shiga, na shiga uku ni indo" hanbare gwoggo Aisha tayi da kafa rarafewa gwoggo da Sara sukayi kafar hajiya farida wani irin hanbari hajiya faridda tayi gwoggo har se da kanta ya daki bango suka fice, haka gwoggo ta fito tana zunduma ihu tana bin su tana cewa, "na shiga uku ni indo kin cuce mu Nihal wai yaushe ne zaki barmu mu huta" har mota su ta tashi take a nan ta yanke jiki ta fadi daura hannu a kai Sara tayi tare da kwarma ihu tana kwallawa gwoggo kira..... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/14, 8:03 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_A gaskiya ina jin dadin comments na Ku masoya SAUYIN RAYUWA kuna zugani iri sosai din nan 😍Allah ya bar kauna_*🤸🏾‍♀ *page: 105_106* Haka Sara ta rinka zunduma ihu da kyar ta samu wani ya taimaka mata shima sai da ya gama yi mata tanadi har yana cewa Allah ne ya kama su, har aka kai gwoggo asibiti yana masu kunfar baki, tunda ya kai su ya juya gashi ba ko sisi a hannun ta nan zube aka bar gwoggo ba likitin daya bi ta kanta bale kuma a kai ga nurses, ganin ba sarki se Allah yasa Sara bin Layin kati ko Allah ze sa ta dace, har layi ya zo kanta mika hannu me raba kati tayi tace, "kudi? Cikin sanyin murya Sara tace, "Baiwar Allah bani da ko sisi dan Allah ki taimaka ki bani ko da bashi ne, ki taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ki," wata uwar harara sister rabi ta watsa mata tace, "da can kin san baki da kudin kati kika kwaso uwar taki kuka zo, ai se ki kwashe ta ku tafi gida malama in ban da san banza irin na matsiya ta, d'an abinda zaku bada din shi kukewa bakin ciki bayan asibitin ma na gwabnati ne, malama kama gaban ki ko nasa security's suyi waje dake" hawayan idanuwan ta Sara ta goge tana cewa, "keko bawar Allah ki taimake ni bani da ko sisi wallahi da ina da su zan ba ki, ki dubi halin da mahaifiya ta ke ciki mana baiwar Allah kamar baki da imani, ko bashin ne ki bani katin fata na mahaifiya ta taga likita" wata irin shewa sister rabi ta saki tana cewa, "Ai da yake uwar taki imani ya ishe ta ince ba indo bace matar tanimu kin ga malama ja kazamar uwar ki ku bace min da gani, ku je kuyi mata maganin gargajiya tunda ba halin yin na asibiti, ko ina taimakwan kowa na duniya an fada maki zan taimake ku ne? Naira biyar mutum ya rage ta kwana shinkafa sai kunbi tun har gidan kun mashi tanadi" ganin dai da gaske ci masu mutunci sister rabi keyi yasa Sara komawa gefe tana tsiyaya hawaye ita yanzu ya zatayi da gwoggo ko motsawa batayi gashi wanda ya kawo su sai da ya gama masu diba albarka, sai da Sara ta kwashe kwana biyu a asibiti tana neman taimako ba wanda ya saurare ta, haka ta tataro gwoggo suka dawo gida tana mata maganin gargajiya kallan gwoggo Sara tayi hawaye masu zafi suka zubo mata ita yanzu ina zata samo kudi, babu wani abinda yayi saura wanda zata iya dagawa ta saida a gidan, gidan ya zama tamkar kango babu abinda ya rage sai yar ya loluwar tabarmar da gwoggo ke kai kwance ita kanta tana bukatar kulawa saboda cikin dake jikin ta ba karamin laulayi yake sata ba ta rame tayi dan kai ga wani fari da tayi na yunwa goge hawayan idanuwan ta Sara tayi ta gyarawa gwoggo kwanciya ta zabga uban tagumi. ****** Bangaran su aunty Aisha sun isa garin kano lafiya kaitsaye suka wuce offishin yan'sanda aka watsa tanimu bayan kanta aunty Aisha ce tace, "idan yayi magana ku sanar mani, ina so ya dandana kudar shi har se ya fada mana inda ya kai mana yarinyar mu" offisa yace, "baki da matsala hajiya duk yadda kika ce haka za'ayi" sannan aunty Aisha ta kad'a kai ta shige mota suka wuce gida. A harabar gida driver aunty Aisha ya faka mota ta fito kaitsaye cikin gida ta shige zaune saman two star da sami mijin ta yana karanta newspaper murmushi ya saki yana cewa, "my dear har kun dawo? aje jakar hannu ta Aisha tayi tana cewa, "Eh mun dawo dan ma na tsaya gidan yaya sani na sauke hajiya farida, my love abun dai ba dadi wallahi yanzu haka tanimu yana hannun hukuma har se yayi bayani inda Nihal take za'a sake shi, na rasa wannan wani irin taurin kai tanimu yake, kuma duk ta kare ya san inda take har yanzu naki yadda da cewa be san ina Nihal take ba..! Aunty Aisha ta ida zancan tana matsar kwalla lallashin da mijin ta ya shigayi tare da cewa, "my dear ki bar daga hankalin ki insha Allah Nihal zata bayana, yanzu dai ki je ki watsa ruwa ki fito mun shirya maki abinci mai dadi ni da yaran ki" murmushi Aunty Aisha tayi tana cewa "da gaske mijina shiyasa nake sanka" aunty Aisha ta fada tana sakarwa Abban Nana pack a kumatu, "bari nayi sauri nayi wanka na fito, su Nana har sun tafi islamiyya hala? "eh sun tafi bama ta dade da fita ba dan duk a tunanin ta tare da Nihal za ku dawo," "Allah sarki Nana tana san ganin yar'uwan nan tata" aunty Aisha ta ida zancan tare da wucewa bedroom Duka dai tanimu yasha haka ya rinka zunduma ihu duk da kafafuwan shi na nad'e hakan be hana su jin azabar da yake sha hannun kuratan yan'sanda ba, yayi laushi sosai ya fita hanyyacin shi fuskar sa ta kunbura saboda tsabar kila, da kyar yake sauke numfashi garba ne dake tsaye rike da gora yace, "tsoho banza zakayi bayanine daga ganin ka mugun tsoho ne," tanimu dake ta sauke numfashi cikin gajiyawa yace, "wallahi ni bani na batar da yarinyar nan ba, nima waya gari nayi ban gan ta ba na rantsema da Allah offisa, bani da masaniyar inda take, ni kai na nemanta nake ido rufe a halin yanzu" tanimu ya ida zancan yana sauke numfashi ai kamar ya zuga garba cigaba yayi da duka kamar Allah ya aiko shi se da tanimu ya sume garba ya watsa mashi ruwan sanyi sannan ya fice yana cewa, "zan dawo na cigaba daga inda na tsaya har se ka fadi inda ka kai yarinyar mutane munafiki" kuka Baffa ya saki ya san cewa ko rabin abinda ya shuka be girbeba yanzu ya fara ganin SAUYIN RAYUWA. ****** Misalin karfe 7:00am Sultan ne ke shiryawa cikin wata suit American rose colour da inner blossom red colour tie din shi kala suit nasa ya saka gem stone rose yayi wani irin kyau masha Allah sultan looks breath taking handsome, briefcase din shi ya dauka ya fito parlour Nihal dake jera abinci a dining da bayi na taya ta, tana sanye cikin red gown wuyan rigar a bude yake gashin kanta ya rufe mata kafadar ta tayi wani irin kyau baki ta ya sha red jan baki haka se ya karawa lips din ta kankancewa, waigowar da zatayi karaf suka hada ido da sultan tsare ta da ido sultan yayi yana kallan ta ita ma shi take kallo cikin zuciyar su babu abinda suke yabawa se kyan juna su da sauri Nihal ta janye idanuwan ta bayin dake taya ta jera kaya a dining kai a sunkuye suka shiga zubewa suna gaishe da sultan sannan suka fice, a hankali sultan ya tako yana takowa yana bin Nihal da kallo har ya ja kujera ya zauna serving nashi Nihal tayi chicken and chips wrap sannan ta tura mashi plate din had'e rai sultan yayi yana cewa, "kin manta abinda na fada maki kenan? cikin kosawa da halin sultan Nihal ta shiga feeding din sultan abincin yana ci ko kallan fuskar ta ba yayi saboda yadda ta had'e rai har ta gama feeding nashi sannan yace, "dauki briefcase nawa yau ke zaki rakani bakin mota" had'e rai Nihal tayi tana gunguni sultan yace, "mi kika ce? Dauke kai Nihal tayi tana rike da briefcase din sultan har suka karaso compound bakin motar shi sannan Nihal ta mika mashi briefcase din shi a hankali sultan ya matso har suna jin saukar numfashin juna su ya sakarwa Nihal pack a kumatu sannan yace, "ki shirya anjima idan na dawo zamu fita" can kasan makoshi Nihal tace, "idan bani da lokaci fa" ta ida zancan tana tsare sultan da ido kauda kai sultan yayi tare da shafa sumar shi setin kunne Nihal sultan ya matso tare da cewa, "doka ce daga yau dole ki rinkayi lokaci na ko kina so ko baki so tunda karkashi na kike" tsare Sultan da ido Nihal tayi tana kallo sannan sultan ya bud'e murfi mota ya shige nad'e hannuwa Nihal tayi a kirji tana zancan zuci, "wai shi wannan mutumin me ya dauke ni, bazanyi lokacin na shi ba ko anayi dole" Nazili dake tsaye cikin shirin ta na zuwa office duk abinda ya faru a kan idanuwan ta ya faru wani dunkulan kunci ne ya rufe ta, da takaici yadda take ganin sultan na rawar kafa kan Nihal, takowa tayi gaban Nihal wadda ta Lula duniyar tunanin har motocin sultan sun bar harabar gidan, murya Nazili ce ta doki dodan kunna Nihal, "Ai se a koma cikin gida tunda ya tafi, ko baki gaji da ganin shi ba, oh ko kuma tunani satar da zaki mashi kike, saboda na san mi ya kawo ki kudi..! shi dama matsiya ci baya taba gajiya da abin duniya," maida gashin kanta baya Nihal tayi tana kokarin wuce Nazili damko hannun Nihal Nazili tayi juyowa Nihal tayi a fusace tare da fisge Hannun ta tace, "wai ke wace irin mata ce me yasa baki gajiya da ihu, bani da lokacin ki ba ko da yaushe nake kula karnika ba idan suna haushi ya kamata ki gane haka..! Daga hannu Nazili tayi zata dauke Nihal da mari rike hannu Nazili Nihal tayi idanuwan ta a kankance tana cewa, "fuska ta ba sa'ar wasan ki bace ko a mafarki karki kara wannan gigin bale a zahiri" Nihal ta watsar da hannu Nazili kasa har tayi gaba ta dawo tace, "tunda na malaki sultan ya kamata kin san cewa na malaki komai na gida nan so ba se na tsaya sata zan sami abinda nake so a wajan miji na ba, ina fatan kin gane" Nihal ta ida zancan tare da nuna Nazili da yatsa ta bar wajan, wata wawiyar ajiyar zuciya Nazili ta saki tana waige ko akwai wanda ya gan su cije yatsa Nazili tayi tana cewa, "sai na lallata fuskar nan se na gwada maki cewa ke ba komai ba ce lokaci yayi da zan nuna maki true colour dina, za ki san ni kike gasawa magana se na koya maki hankali Nazili ta ida zancan tare da shigewa motar. Koda Nihal ta shige cikin gida ta manta da wata Nazili ta cigaba da sha'anin ta ita da su nawwara dan har yau basu koma school ba, after sun gama lunch suka dunguma zuwa shopping saboda shirye-shiryan komawar su nawwara school kuma yau ake birthday din wata kawar su shiyasa zasu je shopping mom ta basu kudi masu yawa driver ya kai. Nihal ba karamin dadi ta ji ba a harabar shop right motar driver ta faka Nihal ta sha mamaki ganin garin kano Ashe dama haka waje yake sun shiga shop right sun judo kaya kala-kala har Nihal ta dauwa mom da Ammi da Dara nasu sannan suka dawo gida a gajiye likis part din Ammi suka wuce nan Nihal ta ba Ammi nata tsaraba da Dara sannan ta wuce part din mom ta bar su nawwara suna shirin zuwa birthday. Mom dake zaune a bedroom badiya na jera mata kaya a wardrobe a hankali aka turo kofar dakin ta Nihal ce ta shigo fuskar ta dauke da fara'a hannu ta na rike da leda turaren data siyawa mom a shop right murmushi mom ta saki tana cewa, "diyar albarka shigo" cikin ladabi Nihal ta shigo tare da gaishe da mom ta amsa tana cewa, "har an dawo kenan" daga kai Nihal tayi tana cewa, "mom kema ga naki tsaraba" washe baki mom tayi tana cewa, "har dani cikin siyaya to na gode, gashi turaran mai kamshi daughter kema kina san kamshi kamar ni" murmushi Nihal tayi tana sinne kai badiya dake jera kaya zubewa tayi tana gaishe da Nihal amsawa tayi tare da amshe kayan da badiya ke jerawa tace, "bari na jera kina iya tafiya," mom tace" "baza ayi haka ba daughter ki barta ta cigaba ke da kika dawo daga kasuwa ya kamata ki huta" shagwabe fuska Nihal tayi tana cewa, "mom ki bari nayi na saba a gida ni nakewa umma na komai bana jin dadi zama bana yin komai, kuma ban gaji ba" Nihal ta ida zancan tana gyarawa mom wardrobe ba yadda mom ta iya haka ta barma Nihal tanayi suna fira har ta gama sannan ta kule wardrobe din tace, "saura me mom? "ba komai daughter" zama Nihal tayi saman sofa rukwo hannuwan Nihal mom tayi tana cewa, "Allah ya maki albarka Nihal" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "amin mom" kiran sallah la'asar ne ya tashi su Nihal alwala Nihal dauro tare da mom suka gabatar da sallah bayan sun idar mom tace ma Nihal bari ta je fada maimartaba ta dawo. ********* Sara ko taga SAUYIN RAYUWA Ganin zaman ba abinda ze mata yasa Sara shiryawa zuwa gidan tabawa kawar gwoggo tasan zata samu wani abu wajan ta tunda tana siye da shiyarwa, kaitsaye gidan tabawa ta zame Tabawa dake zaune saman kujera tayani gulma ta turo dankwalli gaba tana kasa alalla saidawa ganin Sara ne ya sata had'e rai tamkar bata taba dariya ba tace, "Allah yasa lafiya idan ma zancan kudi ne ya kawo ki Sara gaskiya ki juya, danni bani da su bani da dalilin su, kuma har da laifin ku duk kadara da kuka tara kuna mi ta kare ko da yake sakaya Allah ce ke bibiya ai dama duk abinda ka shuka shi zaka girba sanda indo ke cikin daula ta manta da kowa se da yanzu iftila'i ya hauku kuke neman mutane to ban da su" kuka Sara ta saki tana cewa, "kiyiwa Allah inna ki taimaka gwoggo na can rai hannun Allah ko motsi batayi bani da ko sisi ko abinda zan daga na saida bani da shi, ki taimaka wallahi gwoggo kad'ai ta rage min," "Toh da ran hannuna yake ba hannun Allah ba, kin ga malama fita min daga gida kafin laifin da kukayi ya shafe ni, ai kin saba raba shakira ki se ki je ki kasa ayi a biya ki" "Haba inna dan Allah ki taimaka ko bashi ne ki bani, ina iya rasa gwoggo a halin yanzu" wata uwar ashar tabawa ta sakarwa Sara tace, "ta mutu mana sai me dama duk mai rai mamaci ne..! kiii Tabawa ta ja Sara ta watso ta waje wani irin kuka Sara ta saki tana cewa, "na shiga uku ni Sara ina zan tsoma rayuwa ta Ashe dama haka sakaya Allah take..! babu abinda ya fado mata a rai se san da Nihal ta zo rokwan gwoggo ta taimaka a kai umma asibiti fir taki kuma wannan dalilin shi yayi sanadiyar mutuwar ta itama yau gashi an mata, duniya kenan idan kai ne yau gobe ba kai bane tabas taga yadda sakaya Allah take haka ta ja kafafuwan ta zuwa kauyan su gwoggo ko Allah ze sa a dace ta sha bakar wahala a hanya ga laulayi da kyar ta karasa aiko cikin sa'a ta sami wan gwoggo ze je gona ta zayana mashi abinda ke faruwa, tasha ciwon baki kamar me sannan ya ciro naira dari biyu ya damka mata wadda ko abin hawa tayi da su sai sun kare haka ta yanko jeji ta dawo gida ta cigaba da yima gwoggo magani wanda da kyar take samo masu na sama bakin sallati har gwoggo ta mike sai dai bakin ta ya karka ce gefe guda. ********* Da yamma likis sultan ya dawo gida ko da ya dawo part na su ya wuce kaitsaye bathroom ya wuce yayi wanka ya fito sanye da towel yana goge jikin shi d'aya, ya shafe jikin shi da lotion sannan ya shirya cikin jeans and black t-shirt me dan karamin hannu ta kama jikin shi yayi kyau sosai sannan ya feshe jikin shi da turare, part din mom ya wuce kaitsaye kafin yaje na Ammi dauke da sallama sultan ya shiga part din mom ganin ba kowa parlour se bayi dake hada-hada, hakan yasa sultan wucewa bedroom din mom a hankali ya murda kofar kwance saman gado ya hango Nihal ta kudindine cikin blanket bayan mom ta fita bacci ya dauke ta, a hankali sultan ya tako bakin gadan ya tsare Nihal da ido yana kallan yadda dake bacci kneel down sultan yayi bakin gadan a hankali sultan ya kai hannun ze shafa saman cheeks din Nihal gyara kwanciya Nihal tayi tare da janyo hannu sultan tayi pillow da shi tana bacci, murmushi sultan yayi yana kallan ta dan ba karamin kyau Nihal ta mashi ba a hankali ya sakar mata kiss a goshi dan motsawa Nihal tayi a hankali ta bud'e idanuwan ta tare da maida su ta lumshe se kuma ta dan bud'e saboda kamshi turaran sultan daya doki hanci ta, a zabure Nihal ta mike tana kallan sultan shima se daya dan zabura saboda yadda Nihal tayi tamkar taga abin tsoro waige-waige Nihal ta shigayi ganin ba mom a dakin cike da masifa tace, "Mi ya kawo ka nan" Nihal ta ida zancan tana tsare sultan da ido shafa sumar kan shi sultan yayi yana wani kill smile nashi yace, "tanbaya ta kike mi ya kawo ni dakin mom? to zan fada maki na zo ganin matata ne..! tunda bata iya tarbar mijin ta ba idan ya dawo daga wajan aiki" galala Nihal ta tsaya tana kallan sultan tare da watsa mashi harara tace, miji..! Na wucin gadi ko, idan mafarki kake ya kamata ka farka, ni fa ka ishe ni da wannan bibini na gaji" sultan yace, "ni kuma yanzu na fara..! ya ida zancan yana hayowa saman gadan ja da baya Nihal tayi tana cewa, "karka kuskura ka matso na fada maka sultan na mana iya ka" har Nihal ta kai karsha gadan ta tafi luuu zata fadi kasa sultan ya taro ta a nanauyar ajiyar zuciya Nihal ta sauke idanuwan ta a ritse tare da kankame rigar sultan daukar ta yayi cak kamar yar baby har lokacin idanuwan ta na rintse murda kofar da akayi ne yasa Nihal ware idanuwan ta mom ce ta shigo zaro ido Nihal tayi da sauri ta duro daga rukwan da sultan ya mata cike da kunyar mom ta fita da gudu daga dakin, gogan na ka kuwa ko a jikin shi girgiza kai mom tayi tare da ja mashi kunne tana cewa, "baka ji kasa min daughter guduwa" yar kara sultan ya saki yana sosa kunne shi zama mom tayi sultan ya daura kan shi saman ciyar mom tana shafa kan shi tana cewa, "ka tada min daughter daga bacci ko, kuma ka zauna min tashi ka bi matar ka" lumshe ido sultan yayi yana cewa, "mom korata kike? yau nan zan zauna" yayi maganar cikin sigar shagwaba lakace mashi hanci mom tayi tana cewa, "Allah ya shirya min kai, shagwaba da kake min ko nawwara bata zaunawa tana min" rungume mom sultan yayi yana cewa, "tabar min shiyasa" murmushi mom ta saki tare da cewa "tashi ka bi matar ka" mikewa sultan yayi yana cewa, "mom ko baki ce ba bin Abita zanyi" pillow mom ta janyo ta bi sultan da shi tana cewa, "duk wata sauran kunyar ka ta fice" da gudu sultan fita yana dariya... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/15, 6:58 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 107_108* A kwana a tashi ba wuya wajan Allah yau su nawwara ke hada kaya dan komawa school Nihal kuwa duk jikin ta yayi sanyi ta san za tayi missing nasu ba d'an kadan ba, dama suke debe mata kewa nawwara ce ta shafa kumatu Nihal tana cewa, "Aunty Nihal ko zaki bi mu ne? murmushi Nihal ta saki tana cewa, "ina jin kamar haka zanyi missing na ku sosai" ta ida zancan idanuwan ta cike da kwalla, nawwara ta minal rungume ta sukayi a tare suna cewa, "ki daina damuwa aunty zaki rinka zuwa mana visiting mun san yaya ze kawo mana ke ko Aunty Nihal" daga kai Nihal tayi gabaki daya murmushi suka sakarwa juna su Dara ce ta shigo dakin tana cewa, "Ku fito an gama hada kaya suna compound driver na jiran Ku" a tare suka fito compound har da Ammi, Ammi tace, "iyallan rigima yau za'a tafi Allah ya kiyaye hanya" mom tace "ma huta kwana biyu kafin hutun ya kare" hugging din su mom sukayi suna dariya, minal na kokarin shigewa mota Gimbiya jalila ta jawa minal kunne tana cewa, "bana ce ku biya ta part nawa ba kafin ku wuce" yar kara minal ta saki tana cewa, "sorry Momi na manta ne" "Hmm ai ke kullun cikin manta uwar kike shashasha" warmer abinci Gimbiya jalila ta mikawa minal tare da yima minal da nawwara pack a kumatu sannan suka shige mota Nihal na masu bye-bye har motar su, ta bar compound sannan ta juyo cikin gida. *BAYAN KWANA BIYU* Nihal ce ke shiryawa cikin jeans white and black shirt tayi wani irin kyau gashin kanta ya wani nanad'e ya zubo har gadan bayan ta, murda kofar da akayi ne ya sata juyowa Dara ce ta shigo hannun ta rike da tray na fruit, murmushi Nihal saki tare da karasawa ta amshi tray din hannu Dara, murmushi Dara tayi tana cewa, "nayi tunanin kina part naku Ammi ke ce min kina nan shine nace bari na kawo maki kayan motsa baki," "Umma kina ji dani, na gode umma, yanzu na fito daga wanka dama niya ta dana gama shiryawa na je kitchen na taya ki aiki," "aiki da wannan kwalliyar wannan gayun na ganin mai gida ne, kuma se a shiga kitchen da shi" murmushi Nihal saki tana cewa, "kin ji ki umma wai kwalliyar gani mai gida, ina so na shiga na daurawa sultan wani abu bana su bayi na mashi girki kamar yadda kike so ke da mom" murmushi Dara tayi tana cewa, "hakan na da kyau akwai dalilin da yasa haka amma nan gaba zaki gane" daukar apple Nihal tayi tana ci tace "yauwa umma bari na nuna maki hotan umma da Abba dama na dade ina so na nuna maki," "haka fa dauko na gani, nima ina san gani su tun ba yau ba," da sauri Nihal ta nufi drewar kwalla mata kira da Basmal keyi ne yasa Nihal washe baki tana cewa, "Basmal sun dawo yau kenan" maida drewar Nihal tayi ta kule da sauri tayi waje Dara ta girgiza kai tace "af ta manta ta fice bata dako hotan ba, bari na fita nima wani jukwan na gani" Nihal ta na fita Basmal ta rugo ta rungume Nihal washe baki Nihal tayi tana cewa, "saukar yaushe amma na ji dadi dawowa nan taki" dariya Basmal tayi tana cewa, "akwai story baza ki gane bane shigowa ta kenan ko part din mu ban wuce ba, ba yadda my love beyi dani ba na bari na huta sannan na shigo amma na ki," Ammi ta shiga kwallawa kira, fitowa Ammi tayi daga bedroom tana cewa, "tunda naji kira da ihu nasan ke ce, haka ake se kin wanke kafafuwan ki, kin taho nan bayan mun bada ke gidan waziri zaki sauka ko part naku, shi Ammar din yana mi kika taho na" turo baki Basmal tayi tare da karasawa wajan Ammi tana cewa, "na lura tsohuwar nan bakiyi missing nawa ba, ko dai kishi kike mazajan naki sunyi aure sun barki" dariya Ammi ta saki tana cewa, "ka jimin ja'ira ai ni ina tare da su mutu ka raba ni ce on top" dariya Nihal da Basmal suka saki Basmal na cewa "ina zasu kai ki kin zama cus" Rufe mashi ido da akayi ne yasa sultan saki murmushi yana cewa, "rigimame ya dawo" dariya Ammar ya saki yana cewa, "wato har wani lakabi ka min" "Eh mana rigimar ka tayi yawwa amma fa nayi missing naka" "Ai dama na fada zakayi missing nawa kace a'a" "uhm naji ban da cika baki ai kad'an nayi" sun dade sultan da Ammar suna hira yau she gamo kiran sallah la'asar ya sasu wucewa masallaci. Bangaran Nihal da Basmal bayan sun gama fira part din Ammi suka wuce part din Basmal suka dasa wata sabuwa hira Basmal se zuba takewa Nihal har tana ce mata Ashe haka soyayya take ya kamata su ware lokaci ita da sultan su je honeymoon tunda akayi auran su basu sha iska ba kullun suna cikin family house, Nihal ko a zuciyar ta cewa take idan da wannan zan je honeymoon to za'a dade ba a je ba har duniya ta tashi kuwa, ruko hannu Nihal Basmal tayi tana cewa, "kinyi shuru Aunty Nihal ya kamata ki fadawa yayana, shigowar ki rayuwar yayana kin sauya shi da yawwa aunty Nihal, kuma na san ze amince da maganar, shifa yayana a kanki ya fara soyayya kuma yana ji dake sosai, aunty Nihal ya kamata kuje yawan bud'e ido ko saboda ke," "Basmal kenan zamu je ne karki damu aiki ne yama sultan yawa shiyasa" "uhm aunty kenan shikenan" sannan suka cigaba da hira su ta yaushe gamo Nazili ce ke shirya cikin duguwar riga ta peach colour rigar ta mata kyau sosai ta kama jikin ta Aziza ce ta turo kofa ta shigo Nazili dake shafa tana hango Aziza ta mirror cikin ladabi tace, "Gimbiya ki na da bako" tsayawa cak Nazili tayi da shafa huda da take tace, "bako wannan wani irin bako ne ya zo min ba tare da izinina ba,? "ba wani bako bane na mu zo mu gani ba Gimbiya, Alex ne ya zo neman ki da alama ya zo da muhimmiyar magana dan har ce mashi nayi baki da lokaci wani bako yanzu tunda weekend ne" murmusawa Nazili tayi tace, "ki ce mashi ina zuwa zan so naji mi ya kawo shi, kuma dami ya zo ina nan tafe na same shi" "to ranki ya dad'e" sannan Aziza ta ja mata kofa ta fice. Bayan fitar Aziza da yan mintoci Nazili ta fita a main parlour ta sami Alex zaune yana sanye cikin suit din shi black ta kama jikin shi sosai yayi kyau da shi gashi kan shi se shining yake Nazili na isowa Alex ya mike tsaye cikin ladabi murmusawa Nazili tayi tace, "mike tafe da kai ne, naji ance kana nemana lafiya dai ko,? "ba wani abu bane ya kawo ni dama kwanaki biyu da suka wuce a wajan dinner kin yadda fost naki, shine na gani kuma naga akwai abubuwa masu mahimmaci a ciki" d'aga kira Nazili tayi tace, "amma ka kyauta sosai ka san kan aikin ka, kamar kasan na dad'e ina nemanta amma na rasa ina na aje ta ashe, na yarda ita ban sani ba" mika hannun Nazili tayi ta amshi fost din tana jujuya ta bude fost din Nazili tayi komai nata na cikin babu abinda aka taba har Alex ze fice Nazili tace, "dan tsaya mana, ina zuwa" daki Nazili ta shiga ta debo kudi a drewar sannan ta fito ta karaso inda Alex ke tsaye tace, "ga wannan ka samu na kashewa..! tsare Nazili da ido Alex yayi yana kallo sannan ya tako inda Nazili take ya amshi kudi ya juya yace, "bana bukatar kudin nayi maki ne kawai saboda Allah" "Ka amsa ni na baka sometime tallakawa nada matsala nasan cewa kana bukatar kudin nan, amma saboda taurin kai irin tallaka baze bari ka amsa ba" Nihal ta ida zancan zata wuce dan ba karamin haushi Alex ya bata fisgo ta Alex yayi har sai ta fada saman fafadan kirjin shi ya matse ta gam SNA jin saukar numfashin juna zuciyar na harbawa lokaci daya cikin nuna isa Alex ke magana da nunawa Nazili ita ba komai bace yace, "ke kudi ya dama bani ba, of coz ni ma'aikaci ne, dan ina aiki karkashin sultan bashi ze baki damar dauka ta matsiyaci ba, idan ma kina tunanin haka kinyi kuskure, kasata ke biya na albashi, albashi na na wata daya shine albashin ki na rabin shekara, I hope you get me right akwai mabuka ta a waje da yawa kina iya basu" murmusawa Nazili tayi cikin sigar raini wayau tace, "wow..!hakan be mun ba da mari na kayi sannan zan gane ka ji zafi, maganar da na maka anyway ka ci lokacin ka" Alex be ida saurara zancan ta ba ya fice, zancan zuci Nazili ta cigaba dayi ji yadda yake magana se ka ce jakin kano kamar ba bature ba, anyway koma dai minene matsiyaci ne kai, saboda ba a canzawa tuwo suna, a kasar takuma ba wani dan shege bane amma se fihila mtsww sannan Nazili ta wuce bedroom din Ammi. Da daddare bayan kowa ya gama dinner ya wuce part din shi kamar yadda aka saba, Nihal ke sanye cikin kayan baccin pink riga mai dogwan hannu da wando, tana tsaye gaban dressing mirror tana sharce gashin kanta murda kofar da akayi ne yasa Nihal juyowa sultan ne ya shigo shima ya shirya cikin dark blue kayan bacci shi riga mai dugwan hannu da wando kallo daya Nihal ta mashi ta dauke kai system din shi sultan dauka ya hanye saman bed sannan yace, "Nihal..! Na kamala komai naki na fara zuwa makaranta insha Allah gobe zaki fara zuwa" a razane Nihal ta juyo tana kallan sultan tace, "makaranta..? Ni ba zan kara zuwa ko wace makaranta ba" "amma ai ke kika ce dole na maida ki makaranta idan ba haka ba zaki fadawa Ammi irin zaman da muke ko kin mata, sai kuma yanzu ki ce a'a" "Oh ta nan ka bulo kenan idan kai ka manta abinda ya faru dani ni ban manta ba, ba makaranta da zani aunty abiola ta dawo ta cigaba da min lesson kamar yadda aka saba, tunda fita wajan ya zamar min matsala" Nihal da ida zancan ta kokarin goge hawayan fuskar ta karasowa gaban Nihal sultan yayi ya ruko hannuwan ta yace, "duk abinda kikaga ya sami bawa kadara ce, kuma mutum baya gojewa kadara shi, Nihal karatu na da anfani sosai insha Allah babu abinda ze same ki zan baki kulawa yadda ba abinda ze cutar dake" sultan ya ida zancan yana dago da habar Nihal cikin sanyi murya Nihal tace, "promise..! "promise" sultan ya fada murmushi Nihal tayi tana cewa, "shikenan zan je makaranta Allah ya tsare" "amin.! sultan yace har Nihal ta kwanta sultan yace Nihal....! ina san magana dake" gaban Nihal se da yanke ya fadi saboda yadda sultan ya kira suna ta mikewa zaune Nihal tayi ta maida hankali ta kan sultan gabaki daya, sultan dake zaune saman stool yana facing din Nihal kanta a sunkuye tana wasa da yan yatsun hannun ta cikin wata irin murya me sanyi sultan yace, Nihal..! zuciyar Nihal kara tsinkewa tayi karo na biyu cikin honey voice din shi sultan yace, "kalle ni" dagowa Nihal tayi tana kallan sultan ganin bata iya jure kallan sultan saboda kwarjini da yayi mata yasa tayi kasa da kanta, zamawo sultan yayi daga sama stool ya durkusa gaban Nihal ya kama hannuwan ta duka biyu cikin nashi, jikin Nihal wani mugun sanyi yayi sultan yace cikin muryar shi me sanyi da dadin saurare, "Nihal..! Na jima ina fadin love doesn't exist, I never thought it will happen to me not even in my dream, na dade ina avoiding naki, ina karya ta abinda nake ji game dake Nihal but I just couldn't help it anymore, I must admit ita Nihal I fell for you, I love you Nihal with all my heart and am ready to give you the care and love a wife desires, ina so muyi zama kamar yadda ko wasu ma'aura suke cikin so da kauna na san cewa ni mai laifi ne a wajan ki Nihal, ina san ki Nihal, a kan ki na fara sani so..! Nihal ko wace rana san ki karuwa yake a zuciya ta, ki daure ko kwatan wanda nake maki ne ki min" a hankali sultan ya daura hannu Nihal setin zuciyar shi yace, "zuciya ta na tsana ta harbawa saboda dake Nihal so nake maki bana wasa ba" shuru Nihal tayi zuciyar ta na lugude idanuwan ta cike da kwalla, zame hannu ta Nihal tayi daga rukwan da sultan ya mata mikewa Nihal tayi tsaye ta juyawa sultan baya cikin dauriya Nihal tace, "sultan bana san ka..! Sultan ji yayi kamar Nihal ta harbawa mashi harshashi a zuciya shi ta cigaba da cewa, "kawai ina zaune da kai ne dan bani da yadda zanyi, ina zaune ne da kai ne saboda halacin da Ammi ta min, ta taimaka min a lokacin da bani da kowa bani da gata daga ni sai Ubangijina shiyasa nayi mata biyayya na aure ka, ba wai dan ina san ka ba, ba na san ka sultan..! Bana san ka..! kayi hakuri mu cigaba da zama haka idan kaji baka iya zama dani kana ka iya saki na" rungume Nihal sultan yayi ta baya muryar shi na rawa yana cewa, "I know I make you sad so many times Nihal am sorry for that, amma please karki hore ni da ciwan san ki na rokeki..! na san cewa ki na san mijin ki, na san cewa babu matar da zata ki mijin ta" rintse ido Nihal tayi hawaye na wanke mata fuska kwace kanta tayi daga rukwan sultan tace, "na ce bana san ka an taba so dole ne, Ashe akwai ranar da zaka so blood fool, toh ni ba ranar da zan so sultan d'an gata" Nihal ta ida zancan tana kwasar blanket zata fice parlour rike mata hannun sultan yayi yana control din hawayan dake kokarin zubo mashi yace, "karki fita idan nine baki san gani zan fita daga daki Nihal, "amma ki sani mijin ki na san ki, baze iya rayuwa idan babu ke ba duk horan da zaki min zan jure amma please ki daure ko kwatan san da nake maki ne kimin Nihal" sultan ya ida zancan tare da ficewa ya barma Nihal dakin ya koma parlour zamewa Nihal tayi tana kuka me yasa ma ta gasa mashi magana haka kuma tana jin san shi na yawo cikin jikin ta, bayan bata da wani gata da ya wuce mata sultan shine farin cikin ta, ya za'ayi tace ba ta san d'an muta nan da suka taimake ta amma ya zama dole ta nunawa sultan ba a samun mace daga sama ko tana amincewa da soyayya shi sai ta kwato wa kanta yanci a wajan shi wahala da be sha ba wajan auran ta, ita ze sha yanzu, kwantawa tayi saman sofa tana mai cigaba da tunanin bangaran sultan ko kasa rintsewa yayi ga san Nihal dake azalzala shi ji yake kamar ya karama wutar san ta gobara a zuciyar shi daya fada mata. *WASHE GARI* Kiran sallah Asuba ne ya tashi Nihal toilet ta shige tayi wanka tare da dauro alwala ta gabatar da sallah tana idarwa main kitchen ta wuce ta girka masu, yam kebabs with chicken se da ta kamala komai, yasmin da barira suka biyo ta da kayan abincin part din su suka jera a dining sannan Nihal ta basu umarni su tafi, bedroom Nihal ta shige dan shiryawa jin kara ruwa ya sheda mata sultan na toilet, a kurguje ta shirya cikin uniform din ta black and white rigar white skrt black tana kokarin bale bottle din rigar, sultan ya fito daga toilet yana sanye da bathrobe da kallo Nihal ta bishi da sauri ta kauda kanta tana kicinyar bad'e bottle din riga karasowa sultan yayi gaban ta zuciyar Nihal ko harbawa take da sauri da sauri ta kara tsuke fuska cikin sanyi murya sultan yace, "lemme help you" kif-kif ta ido Nihal tayi tare da janye hannun ta, a hankali sultan yasa hannu yana bale mata bottle din bin shi da kallo Nihal take tana kallan yadda sanja shi ya jike da ruwa sannan tabi fafadan kirjin shi da kallo da sauri Nihal tayi kasa da kanta lokacin yayi dai-dai da gama bale mata bottle din can kasan mako shi Nihal tace, "na gode" sannan ta fice da kallo sultan ya bi ta san ta na ruruwa a zuciyar shi. Har se da Nihal ta gama break sannan sultan ya fito yana sanye ciki black suit din shi ta kama jikin shi yayi wani fitinan kyau a tsaitsaye yayi breakfast sannan suka fice a tare, part din mom suka wuce suka gaishe ta kamar kullun sannan suka wuce na Ammi daga nan suka fito compound suka shige mota ba wanda ya kara ce ma wani kanzil se sultan dake satar kallan Nihal ta kasan ido ita ko ta had'e rai. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/16, 7:40 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Gaskiya mosaya SAUYIN RAYUWA bani da abinda zance se Allah ya bar kauna, ina ganin yadda kuke ruwan comment kamar ba gobe na gode sosai ina jin dadi hakan, hakan ya nuna cewa littafin yana kawo suger, ni kuma zan cigaba da suburbudo maku Page's kamar ba gobe_* *Page 109_110* A harabar makarantar motocin sultan suka faka shi da kan shi ya zagaya ya bude wa Nihal murfin mota ta fito, har a lokacin ran ta had'e yake, kaitsaye office din principal suka wuce, cikin fara'a ya amshe su bayan sun kamala komai yace ma wani uncle lawal ya gwadawa Nihal class din ta Ss1 wani irin dadi Nihal taji a tare suka fito da sultan har tayi gaba sultan yace, "baki ji ba" tsayawa Nihal tayi cak ba tare da juyo ba a hankali ya tako gaban ta ya sakar mata pack a goshi tare da tura mata kudi break a cikin school bag din ta yace, "ki kula min da kanki hayaty" tab'e baki Nihal tayi sannan tayi gaba ta bar shi nan tsaye se da ta dan yi nisa ta juyo ganin sultan kallan ta yake har a lokacin yasa Nihal juyawa da sauri ta shige aji shi kuma ya shige mota ya bar harabar makarantar. Uncle lawal da suka shigo da Nihal class yace, "ga sabuwar student kun samu saura ku koya mata surutu," dariya yan class sukayi suna yaba kyan Nihal wasu har ce mata suke balarabiya sannan ajin suka dauka da cewa, "ya suna ki" nan dai Nihal ta fada Masu suna ta Nana dake zaune a fornt sit tace, "Nihal..! dawo nan ki zauna na maki sit sabuwar kawata" dariya yan class su dauka suna cewa, "oh Nana daga zuwan ta zaki fara nuna mata halin naki" Nana ko kasancewa tare sukayi paper farko ta JSCE shiyasa ta gane Nihal sa rai, murmushi Nihal ta sakar mata sannan ta karaso sit din ta ta zauna, sannan Nana ta shiga jan Nihal da fira kafi uncle ya shigo saboda jinin su ya hadu har take tanbaya ta tunda ta zo exam bata kara zuwa ba shigowa uncle peter ne ya sasu natsuwa aka cigaba da lesson. Zaune yake cikin office idanuwan shi a lumshe yana dan juya kujera da yake zaune ya lula duniyar tunani duk yadda ya so ya cire tunanin Nihal ya kasa musanman yadda kalamanta na jiya da daddare daya ke mashi yawo cikin brain din shi, dan har ji yake tamkar yanzu take fada mashi, Ammar ne ya shigo office din hannun shi rike da files tsare sultan yayi da ido yana san gano abinda ke damun shi, dan ya kusa awa yana knocking kofa ba a bashi izini ba zama yayi ciki sanyi murya da nuna tsantsar damuwa yace, "sultan..! A dan razane sultan ya dago idanuwa ya zubawa Ammar tare da cewa, "da yaushe ka shigo? numfasawa Ammar yayi yana cewa, "ya za'ayi ka sani bayan kana duniyar tunani, mike damun ka,? Sauke nanauyar a jiyar zuciya Sultan yayi yace, "Nihal..! so take san ta ya min ila..! nan sultan ya kwashe yadda sukayi da Nihal daran jiya, dariya Ammar ya saki har da buka table galala sultan ya tsaya na kallan shi sannan yace, "amma baka da mutunci ina fada ma halin da nake ciki kana min dariya" tsaida dariya sa Ammar yayi yana cewa, "kai ma kasan ai dole haka ta faru ka manta irin zaman da kukayi, dama nasan wannan rana zata zo, shiyasa na rinka hana ka abubuwan da ka mata a baya amma ka rintse ido sultan, kawai kayi hakuri ka cigaba da lallaba ta, har ta amshi soyayya ka, na san cewa tana san ka sultan ka bar tada hankali" sauke numfashin sultan yayi tare da furta, "Allah yasa..! files din hannun shi Ammar ya mikawa sultan tare da cewa, "cikin files din har da takarda taran da za'ayi a Moscow gobe" bud'e files din sultan yayi yana cewa, "ni fa ban shirya ma wata tafiya ba, ina kokarin kashe wata gobara an kunnu min wata, ni dai ban ji dadin tafiyar nan ba" dariya Ammar ya tintsire da ita yana cewa, "kuma nima ba zuwa zanyi ba, dan ban gama cin amarci na ba, kai da baka fara ci ba sai ka lallaba ka je taran nan" had'e rai sultan yayi yana cewa, "dama wani yace ka je," ya ida zancan yana kokarin barin office din Ammar ya ruko hannun sultan ganin yadda ya bata rai sosai yace, "am sorry dude koma ze sama normal karka damu kaji kawai jan aji take ma irin nasu na mata" haka Ammar ya rika tausar sultan har suka wuce theater room. Makaranta tayi ma Nihal dadi sosai musanman da ta gane cewa Nana na gane karatu sosai se ta su ta zo daya suka kara kulewa, dan kusan tare sukayi break Nana na kara wayar mata da kai kan karatun da akayi ba ta nan, bayan komawar su break anyi lesson sosai kuma Nihal ta fahimta misalin karfe 3:30pm aka ta she su Nihal tana fitowa daga class ta hango daleliyar motar ta da Abba ya bata fake driver na zaman jiran ta ji tayi zuciyar ta ba dadi ta so a ce sultan ne ya zo daukar ta Nana ce ta daga mata hannu tana kokarin shiga motar su ita da kanna ta tace, "ki gaishe da su mama" "zasu ji Nana" sannan Nihal ta shige mota, A gajiye likis Nihal ta dawo gida part din su ta wuce kaitsaye watsa ruwa kawai tayi ta shirya cikin wata yellow gown dai-dai gwiwa duk da ba wata kwalliya tayi ba tayi kyau sosai da ita, sannan ta wuce part din Ammi, Ammi dake zaune ce ta washe baki karasawa Nihal tayi ta sakarwa Ammi pack a kumatu Ammi tace, "yan makaranta har an dawo kenan" "Eh..! zama Nihal tayi saman 1 star tace, "wash Ammi na gaji makarantar akwai dadi amma da gajiya, ji nake kamar anmin duka" murmusawa Ammi tayi tana cewa, "haka karatu yake sai hakuri bari Yasmin ta zo ta maki massage" dining Nihal ta nufa ta zuba jallop din taliya taji vegetable da naman rago Nihal ta zauna tana ci, bayan ta gama ta cigaba da rubuta note din da akayi bata nan. ************ Yau dai police station sun gaji da lamarin tanimu yau kwana uku kenan kafar shi na ruwa, tana wani irin wari mara dadi har wani baki kafar tayi tamkar abinci ya rube yayi funfuna, officer garba kiran aunty Aisha yayi ya shide mata halin da ake ciki dan shi a ganin shi tanimu shingin gawa ne nan Aunty Aisha ke shida Masu bata garin officer garba yace, to shi dai ze maida tanimu kauyan sun dan sunyi bincike iya bincike sun gano bashi da sa hannu a bacewar Nihal bashi da wata masaniya inda take, haka suka kwashi tanimu zuwa shanono suna isa shanono suka watsar da shi kofar gida Sara da fitowar ta kenan zata je neman masu abinda zasu ci cikin ta har ya dan fito tayi kamar lauge saboda tsabar rama da duhu da gudu ta karasa wajan Baffa tana cewa, Baffa..! Warin da Baffa yakeyi ne ya ziyar ci hanci Sara da sauri ta toshe hanci wani tukokin amai ya yunkuro mata take a nan ta hau amai tamkar zata amaye yan cikin ta tace, "Baffa wannan wace irin cuta ce a jikin ka, warin mi kake haka sai ka ce mushe ya mutu, ni Sara ina zan jefa rayuwa ta da gwoggo zan ji ko da kai ji yadda kafar ka ke ruwa kamar ma tsutsa ke bi, na shiga uku wannan wace irin musiba ce" kuka Sara ta saki tana kwalla wa gwoggo kira da kyar gwoggo ta iya fitowa da karka ta can bakin ta, kama baki tayi da sauri ta kara sa gaban Baffa wanda shi da matace babu mara ba ga hawayan wahala na bi mashi kunci ido duk kwantsa ga taban duka duk jikin shi ya farfashe, kuka gwoggo ta saki tana cewa cikin maganar ta wanda yanzu ta zama tamkar ta kutare, "malama haka ka koma, wannan wace irin cuta ce ta same ka mun shiga uku mun lallace, Allah na gode maka da baki nane kawai ya samu matsala," Baffa kuwa ko k'ala ya kasa cewa se tsiyaya hawaye da kyar gwoggo suka ja Baffa zuwa cikin gida hanci su na toshe bisa tabarma suka shinfid'e shi, da kyar ya iya cewa, "ruwan..! da sauri Sara ta debo mashi ruwa a randa ta talabo shi ta bashi wani irin ihu ya zunduma yana cewa, "jini..! jini..! ku taimake ni ku fitar da ni daga cikin gidan nan wallahi Habu baze barni ba, ku taimake ga hassan nan ze kashe ni, usaini ze shake ni, ku taimake ni" ja da baya Baffa yake yana cewa, "ba zan zauna ba ku fitar dani daga cikin gidan nan" Sara na kuka tace, "Baffa me suka maka abirni? gwoggo sun hauka ta mana Baffa shikenan rayuwar mu ta kara rushewa" kuka sara take tamkar ta shide gwoggo jin sunayan da tanimu ke kira ya sa yan hanjin ta kadawa tamkar mazari tana ja da baya tana zaro ido abubuwan da suka aikata ya fara yi mata zarya kamar yanzu suke aikatawa ihu da Sara ta saki ne yasa gwoggo sankarewa sakwamankwan sumewa da Baffa yayi. ****** Da daddare Nihal ce zaune dakin Ammi suna hira turo kamar da akayi ne yasa Ammi juyowa washe baki Ammi tayi tana cewa, "dan albarka kamar kasan naka rai na" murmushi sultan ya saki tare da zaman kusa da Ammi yace, "matar yanzu kin daina ji dani kin fi ji da kishiyar ki na lura," Nihal dake gefe tana jin abinda sultan ke cewa tunda ya zo ko daga kai ta kalle shi taki se shi dake fama satar kallan ta ganin bata da niyar kallan shi yace, "Hayaty ki shirya zaki rakani wani waje yanzu" dagowa Nihal tayi karfa suka had'e ido da sultan Ammi ce ta katse masu tunani da cewa, "yau fitar masoya za'ayi kenan" murmushi sultan ya saki yana cewa, "matar baki kishi na ma ko toh shikenan," murmusawa wa Ammi tayi tana cewa, "toh ya zanyi tunda kamin kari koma dai minene ni ce on top" sakarwa Ammi pack yayi a goshi yace, "kamar kin sani yar tsohowa" dariya Ammi tayi tana cewa, "ni ba tsohuwa ba ce" dariya sultan ya tintsire da ita tare da ficewa, Ammi tace, "Nihal tashi ki shirya kiyi kwalliya sosai daga gani fitar nan, na da mihimmaci, tunda fita da mai gida ne ya kamata ki kure a daka" murmushin yake Nihal ta saki tare da cewa, "toh..! zata fice Ammi tace "ko da yake dawo, wannan aikin se jakadiya" zaman Nihal tayi tana cewa a zuciyar ta fita da shima se anyi wasu iyayi shi yasa ya samu waje yana yadda yaga dama, dawowar Ammi da Dara ne ya dawo da Nihal daga duniyar tunani Dara ce tace, "muje ko" gyada kai Nihal tayi tabi bayan Dara zuwa dakin ta, shirya Nihal tayi cikin wata dark green gwon rigar ta kama jikin Nihal sosai bakin ta ya sha red Jan baki, bakin yayi dan karamin da shi parking gashin ta Dara tayi sannan ta bata veil Apple green colour da fost silver ta feshe mata jiki da turare me kamshi wani irin kyau Nihal tayi sannan suka fito, lokaci yayi dai-dai da fitowar Nazili zata wuce dining area birki ta ci tana kallan Nihal zuciyar ta na lugudan bakin ciki, bakin ta kasa shuru yayi tace, "jakadiya ina zaku je da wannan daran kusan 7:30pm" murmusawa Nihal tayi tare da katsewa jakadiya hanzari tace, "zan fita da muradin rai nane ma'a mijin na sultan" Nihal ta ida zancan tana tsare Nazili da ido irin ki mutu idan kin ta shi murmushi daya fi kuka Nazili ta saki tana cewa, "hakan na da kyau dama fitar masoya da daddare tafi, musanman sultan da bashi da lokaci da rana," murmusawa Nihal tayi tace, "kamar kin sani, kinyi tunani da kika gane haka..! Nazili na kokarin magana sultan ya shigo main parlour cikin wanka shi na suit kamar kullun yayi wani irin kyau, shock Nazili tayi da kyar take danne abinda ke yunkurin fito mata dan ji take tamkar tayi hauka, ga wani fitinan kamshin sultan daya wuce ta ta shaka wanda ko kallan ida take be ba yana can yana kallan Nihal dan ji yake kamar ya hadiye ta saboda so jikin Nazili rawa yake saboda baccin rai tana kallan Nihal dake mata alama da ido taga yadda gogan nata ya rud'e ko kallan kowa ba yayi tana malallancin murmushi har sultan ya karaso gaban yana smile ya kama Hannun ta tare da sakar mata pack yace, "hayaty kinyi kyau sosai" cikin yauki Nihal tace, "na gode," "muna iya tafiya" sannan suka fice suna makale da juna Nihal na waigen Nazili da tayi mutuwar tsaye suka fice. Suna isa compound Nihal ta zame jikin ta tare da daurewa tace, "ina zamu ne cikin daran nan baka san naje makaranta na dawo na gaji bane, lokacin hutawa nane yayi dan dai kawai a gaban Ammi kayi maganar nan shiyasa zan bika dan bazan iyayi maka musu a gaban ta ba, amma daga yau karka sake min haka Sultan", sultan ko zuba mata ido yayi yana kallo yadda take masifa da dan karamin bakin ta ji yake kamar yayi kissing nata, sannan Nihal tayi gaba, yana kokarin bud'e mata murfin mota tace, "bana so ina da hannu" sannan ta bude ta shige ta zauna sultan ya zagaya ya zauna. Hawayan bakin ciki ne suka fara zubowa Nazili gabaki daya kayan dining ta daga ta watsar tana haki gabaki daya bayin dake part din Ammi fitowa sukayi da gudu suna kallan barnar da Nazili tayi da sauri Aziza ta karaso gaban ta tana cewa, "Gimbiya me ke faruwa? dafe kai Nazili tayi tana cewa, "kai na ze fashe juyawa yake ina bukatar iska..! Nazili ta ida zancan a tsawace da sauri Ammi ta karaso ta kama Nazili tana cewa, " abar kauna ta mike damun ki, kika shiga wannan hali" Ammi ta ida zancan tana kwalla da kyar Nazili ke maida numfashi cike da tsiwa tace, "Ammi ku fida ni waje ina bukatar iska, kowa ni matsiyaci ya koma bakin aikin shi kunyi tsaye kuna kallo" janyo hannun ta Aziza tayi Ammi tace, "Ku fita da ita ta samu iska, abar kauna ta duk abinda kike so shi za ayi maki sannu kin ji" Ammi kuwa hankali ta duk ya tashi har da hawaye tace mi ke damun Nazili ne dan bata kawo ma ranta fitar su sultan bace ta gigitata haka ba, su na fita gander suka nufa suna isa Nazili tace, "ki tafi ki ban waje ban san ganin kowa kusa dani, natsani ganin fuskar kowa" Nazili ta ida zancan cikin tsawa Aziza na tuntube ta bar wajan zamewa Nazili tayi daga resting chair ta zunduba wani irin ihu tana kuka tamkar ranta ze fita cikin kuka tana cewa shikenan ta kwace shi har abada, bazan taba yadda ba se na kwato abuna, kuka Nazili take bana wasa ba tana sanbatun tamkar mahaukaciya dafa ta da akayi ne yasa Nazili dako da jajayan idanuwan ta ba kowa bane se Alex da ya shigo garden yana waya da family din shi ji kuka ne ya sashi nufo wajan, tsare shi Nazili tayi da jajayan idanuwan ta da kyar ta iya furta, "me ya kawo ka nan? na fada bana san ganin kowa, ka tafi ka bani guri bana san ganin kowa..! Nazili ta fada a tsawa ce Alex ko tausayi ta bashi ya rasa dalilin dake sata yawan kuka da shiga damuwa bata rasa komai ba amma ta jefa rayuwata cikin damuwa, mikewa tsaye Nazili tayi cikin shashekar kuka tace, "tunda baza ka bani guri ba ni zan baka tunda kai baka gane ya ran da nake maka" takawa Nazili ta fara tayi tamkar wadda tayi shaye-shaye saboda jiran dake dibar ta luuu ta tafi zata fadi Alex ya taro ta yana cewa Gimbiya..! Gimbiya..! Da karfi yana taba kumatu ta amma ta sume daukar ta cak Alex yayi ya nufi cikin gida a rude. A bakin wani hadadan restaurant motar sultan ta faka wanda ko ba'a fada ma ba kasan restaurant din manya mutane ne bana kanan mutane ba, zagayowa sultan yayi ya budewa Nihal murfin mota wajan Nihal ta tsaya kalla ganin a rubuta restaurant yasa Nihal togewa tana kallan sultan sannan ta juyo ran ta had'e tace, "Mi zamuyi a nan? abincin da akayi a gida ya zamuyi da shi, ni ba zan shiga ba gida zan koma" Nihal ta ida zancan tana kokarin juyawa ruko hannun ta sultan yayi ya maraire ce fuska cikin sanyi murya ce, "akwai maganar da nake so muyi ba wai abinci zamu ci ba" kwace hannu ta Nihal tayi daga rukwan da sultan ya mata sannan tace, "wace magana zamuyi wadda bama iya yi a gida" daura finger din shi sultan yayi saman lips din Nihal yace, "please..! ya ida zancan yana langwabe kai "Naji shikenan..! sauke nanauyar ajiyar zuciya sultan yayi yana jinjina rigima irin ta Nihal kallan shi ta kasan ido Nihal tayi tana cewa a zuciyar ta se kayi laushi zan sasauta maka sannan suka shige ko da suka shiga ba kowa kasancewa sun san da zuwan na su abin ma mamakin ya ba Nihal wannan wani irin restaurant ne ba mutane ja mata kujera sultan yayi ta zauna sannan shima ya zauna yana facing nata, welter ne ya kawo masu littafin da zasu duba abinda zasu ci, amsa sultan yayi ya duba sannan yace, "a kawo mana Brown past da fresh mango juice" sannan welter ya tafi, tsare Nihal da ido sultan yayi yana kallo ita ko ta hade rai welter na kawo abincin ya koma ya zauna kallan abincin Nihal tayi tace, "ka ce min magana zamuyi amma naga an kawo mana abinci" "Am sorry for that hayaty zamu dade muna magana ne shiyasa kuma nasan zaki iya jin yunwa" "Uhm.! Kallan abincin Nihal tayi tare da kwabe fuska da kyar ta dau fork tana juya abincin aje fork din tayi tace, "sultan bana iya cin wannan abincin bana san shi" ta ida zancan tare da ture plate din murmusawa sultan yayi yace, "to mi kike so hayaty bana so kina bata min cute face din nan taki, duk abinda kike so ki fadi min yanzu nasa su kawo maki" sultan ida zancan yana saki murmushin me kara mashi kyau wani shan kamshi Nihal tayi tace, "tuwo miyar kuka zanci" ta ida zancan tana kauda kai murmushi sultan yayi saboda yasan rigima kawai Nihal ke nema shiyasa take haka dan ta bata mashi rai shi kuma har yanzu ba tayi abinda yaji haushi ba se san ta dake ruruwa a zuciyar shi, dagawa welter hannu sultan yayi alamar ya zo sannan yace, "a canza abincin nan a kawo mata tuwo biyar kuka" "toh yallabai, hajiya asa maki amshanu" daga kai Nihal tayi sannan ya dauke plate din ya wuce da shi ya kawo mata tuwo miyar kuka da spoon a ciki har yayi gaba Nihal tace, "ba kwana wanke hannu ne" sultan da ze kai fork bakin shi ya tsaya yana kallan Nihal sannan yayi smile ya cigaba da cin abinci ruwa aka kawo Nihal ta wanke hannu sannan tasa hannu ta fara cin tuwo miyar kuka har wani lumshe ido Nihal take alamar abincin na kai mata har ta cinye welter ya kwashe plate din Sannan Nihal ta kalli sultan tace, "kace zamuyi magana amma baka ce komai ba, har na gama cin abinci" a hankali sultan ya daura hannun shi saman na Nihal kallan shi Nihal ta shigayi san shi na kara ruruwa a zuciyar ta da sauri ta janye hannun ta cikin murya shi me dadi sultan yace, "dama fada maki zanyi gobe zanyi tafiya da safe, zan kwashe tsawan sati biyu bana gida" jikin Nihal mugun sanyi yayi dan har ji tayi gaban ya fadi yana wani irin lugude lokaci daya taji bata san sultan yayi tafiyar haka nan, sultan ne ya katse mata tunani da cewa, "Na san cewa murna kike har cikin zuciyar ki zan tafi, dama na ta kura maki ko? a hankali sultan ya kama hannu Nihal ya cigaba da cewa, "Nihal ina san ki please ki yarda da cewa ina san ki mana koda so daya ne, tafiyar nan da zanyi jin nake kamar mu tafi tare, bana so kiyi nisa da ni ko kadan, ji nake kamar zan bar rabin jiki na ki daure ki so ni Nihal please dan Allah ki daina ganin laifi na a kan kiyaya da nuna maki a baya, ina da dalilin na mai karfi shiyasa na maki haka amma ki yafe min Nihal ki daure ki bari mu raya auran mu da so da kauna da zaman lafiya" Nihal da kanta ke kasa idanuwan ta sun ciko da kwalla wanda ita kanta bata san dalilin su ba da kyar Nihal ta daure ta dago tare da kwace hannun ta tace, "Allah ya kiyaye hanya" ta dauki fost din ta ta fice tana fita kafi ta shige mota ta fara anbaliyar hawaye ji take kamar kar sultan yayi tafiyar nan saboda hankalin ta be kwanta da tafiyar ba a haka ta shige mota, bayan shigar da yan mintoci sannan sultan ya shigo kauda kai Nihal tayi bakin window tana matsar kwalla wadda sultan be san tanayi ba amma hannun su na makale dana juna ta kasa kwace hannu ta wannan karan a haka drive ya ja mota. Koda suka isa gida Nihal bacci ya dauke ta daukar ta sultan yayi cak kamar baby ya wuce part din su da ita, a saman bed ya shinfid'e Nihal yana kokarin mikewa Nihal ta janyo hannun shi cikin bacci, dawowa yayi shima ya kwanta saman gadan tare da daura kan Nihal saman fafadan kirjin shi yana shafa kanta Nihal kuwa kara shige mashi tayi sosai, a haka bacci me dadi ya kwashe sultan ba tare da sun sa kayan bacci ba. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/19, 4:19 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 111_112* *WASHE GARI* a hankali Nihal ta bud'e idanuwa jinta makale jikin sultan ne ya sata waro ido zuciyar ta na tsana ta harbawa, jin sultan na motsawa yasa Nihal maida ido ta rintse ta kara yin lamo a kirjin shi kamar tana bacci, bud'e idanuwa sultan yayi ya sauke su kan Nihal dake bacci karya bilhaki a hankali yayi kissing forehead din ta tare da godewa Allah da yasa Nihal bata tashi ba, bare tayi mashi rigima a hankali ya zame Nihal daga jikin shi yana kallan agogan dake makale a bangwan dakin kusan karfe 6:00am d'an zaro ido sultan yayi a zuciyar shi yana cewa wani irin bacci ne ya dauke su, ko sallah Asuba ba suyi ba koda yake bacci na musanman ne tunda da abar kauna shi ya kwanta lullube Nihal yayi da blanket ya shige toilet duk abinda yake Nihal na jin shi se ma kara bin lafiyar gado tayi tamkar tana bacci da gaske. *BAYAN YAN MINTOCI* Nihal ce ta turo kofar daki ta shigo, a hankali ta sauke idanuwan ta kan sultan dake faman hada kaya cikin trolley jikin tane yayi sanyi karasowa Nihal tayi gaban sultan tana cewa, "ka barshi na hada ma kayan" dago ido sultan yayi yana bin ta da kallan so yace, "makarantar taki fa? bana so kiyi late a bige ki, ki shirya ki tafi karki makara nayi ma driver magana yayi dropping naki," "ya za'ayi naje school bayan zakayi tafiya ko ba komai zan tsaya saboda idanuwan mutane, ya kamata na ga tafiyar ka inya so gobe se naje, bani kayan na shirya ma" murmusawa sultan yayi yace, "Toh shikenan" yaji dadi kulawar da Nihal ta nuna mashi haka Nihal ta shiga hada mashi kaya jikin ta duk a mace duk inda sultan yabi idanuwan ta na kai daya juyowa se ta kauda kai tana yan kame-kame haka ta gama hada mashi kaya tsaf suka fito tana jaye da trolley din Sinbul dake bakin kofa ya amshe ya fice, main parlour suka wuce kaitsaye lokacin kowa ya halara. Gaishe da su mom da maimartaba suka shigayi, Gimbiya jalila dake gefe da Ashad wani malallacin murmushi suke sakarwa juna su Ashad cikin zuciyar shi yace ai kara ayi bankwana kafin a maido gawar taka yana tunani yana wasa da gemun shi wani nishadi na lullube shi haka sukayi break ana yima sultan Allah ya kiyaye hanya, Ammi ce tace, "Allah ya kiyaye hanya ayi taro lafiya a gama lafiya" gabaki daya dining aka dauka da "Amin..! Nihal ko se satar kallan sultan take a haka aka rako sultan compound ze wuce Nihal dake rabe jikin Ammi tana kokarin boye hawayan dake niyar zubo mata dan ita kad'ai ta san abinda take ji, ga wani irin faduwar gaba dake ziyar tata ganin kuka na neman cin karfin ta yasa Nihal jan jiki ba tare da kowa ya lura ba ta shige cikin gida. Daki Nihal ta shige tana kuka ita kanta ta san zatayi missing mijin ta ba dan kadan ba, me yasa ma jiya bata amsa mashi ba maganar data dokin dodan kunna Nihal ce ta sata juyawa a razane "Nihal..! me yasa kike min karya? Da sauri Nihal ta shiga goge hawayan idanuwan ta tana kallan sultan dake matsowa daf da ita har suna jin saukar numfashin juna su Nihal tace "karya kuma..! "of course Nihal you lied to me, kin ce baki so na bayan kuma kina so na gashi kina kukan missing mijin ki" "Waya ce maka kuka nake, you got this wrong bana san...! Nihal bata ida kai hayaba sultan ya hada bakin su waje daya yana yima Nihal wani iri rikitatan kiss duk yadda Nihal taso ta kwace kanta ta kasa se da ya gaji dan kanshi ya sake ta, suna maida numfashin tamkar sunyi tsere hada goshin shi sultan yayi dana Nihal waje daya yana sauke numfashi, a hankali yake magana kamar me rada, "Don't you lie to me again why can't you just admit kina san mijin ki, i can't read your mind na san ki na so na Nihal, kawai baki so ki fada min ne saboda wani dalilin naki" sultan ya ida zancan yana shafa kumatun Nihal, a hankali Nihal ta daura hannu ta saman hannun sultan siraran hawaye na zubu mata tana kallan idanuwan shi, murmushi sultan ya saki har dimple din shi na lomawa wata irin runguma sultan ya kai ma Nihal tare da daga ta yana dariya har suka fada gado murmushi Nihal take saki siraran hawaye na bi kuncin ta, numfasawa sultan yayi yace, "stop shading those tear hayaty" sultan ya ida zancan yana goge mata hawayan ta kama hannu Nihal sultan yayi yana cewa, "hayaty kin hora ni da yawa ji fa har dan wuya nayi just tell how much you love me, I now you fell to hayaty" turo dan karamin bakin ta Nihal tayi tana cewa, "ba yanzu ba se na samu time" shagwaba fuska sultan yayi yana cewa, "please mana just tell me" "Okey calm down, uhm" cakulkuli sultan ya shigayima Nihal tana dariya a har tana shidewa yana cewa, "tell me mana" numfasawa Nihal tayi tana sauke numfashi da sauri Nihal ta mike zata bar gadan janyo ta sultan yayi ta fada saman gado, kissing din ta ko ta ko ina ya shigayi yana cewe, "i love you so much hayaty, yanzu na gane ki, ana san miji ana kaiwa kasuwa" shafa kumatu sultan Nihal tayi tana mashi kallo me cike da so tace, "love..! Lumshe ido Nihal tayi san sultan da kaunar sa na kara narke mata cikin zuciya, kokari hada bakin su guri guda sultan yake ringing din wayar shi ya katse mashi hanzari daga Nihal yayi tare da zaro wayar a aljihun shi ya kara a kunne yana cewa, "Alex ka bani nan da 5 minutes zan fito" sannan ya datse kiran yana kallan cute face din Nihal ya lagwabe kai yace, "hayaty bari na wuce flight din na saura 20 minutes ya tashi kar nayi missing flight din na a samu matsala, Amma fa zanyi missing naki" shuru Nihal tayi tana wasa da zabe hannun ta kama hannu ta sultan yayi cikin siririyar murya ta Nihal tace, "Allah ya kiyaya hanya, Allah ya maido min kai lafiya" ba karamin dadi sultan ya ji ba da addu'ar da Nihal ta mashi, kissing forehead din ta yayi, wayar hannu shi ya mika mata tare da cewa, "ga wanna wayar ki rike kafin na dawo se na siya maki wata, zan kira ki idan na isa" daga mashi kai Nihal tayi sannan sultan ya fara tafiya da gudu Nihal ta rugo ta rungume shi ta baya tana kuka tana cewa, "ni daina ka hakura da tafiyar nan bana so kayi tafiyar" Nihal ta ida zancan tana kuka jikin sultan wani mugun sanyi yayi juyo da Nihal yayi suna facing juna numfasawa sultan yayi yana cewa, "hayaty me yasa baki so nayi tafiyar? sultan ya ida zancan yana talabo da habar Nihal, "kawai bana so ka tafi ne" "Hayaty tafiyar nan ta zama dole amma Dana gama abinda nake zan dawo kin ji, Ashe ana ji dani haka," sultan ya fada yana lakacewa Nihal hanci, dukan kirjin shi Nihal tayi cikin sigar wasa da shagwaba ta rungume shi a hankali ta furta, "I love you" shafa bayan ta sultan yake shima yace, "love you more hayaty" ji yake kamar ya suri abarshi su wuce tare amma hakan be yuyowa lokaci ya kore da kyar dai suka rabu da juna sultan ya fice. Zagaye daki Nazili ta keyi tana rike da kugu tana murmushi tace, "ya tafi gida ya rage daga ni se wanna yarinyar mi kike tunani Aziza idan nace maki aiki na yau ze fara zakiyi mamaki," murmushi Nazili ta saki tana mai cigaba da cewa, "zanyi abinda ze sa ta manta da ko ni wacece, se ta rai na kanta..! se ta san shayi ruwa ne, ni zata sama hawan jini tayi kuskure mafi muni Aziza matso ki ji" matsowa Aziza tayi Nazili tayi mata rada a kunne murmushi Aziza ta saki tana cewa, "Gimbiya kinyi dai-dai haka za'ayi" murmushi Nazili ta saki tana fari da ido tana cewa, "se na ji ki, ina saurara ki bana san ayi wasa da ganganci, kamar yarda na suma daran jiya itama zata dandana mafi muni abinda tamin wannan shi ake kira da somin tabi" Nazili ta ida zancan tana nad'e hannu a kirji ita da Aziza suna murmushi. "Tafiyar nan tamkar tafiya har abada take..! ina so a dauko min matar a tabatar da be bar ajiya ba, se nasa an bincika min ita tsaf" Gimbiya jalila ta ida zancan tana waigowa tana kallan yakumbo murmushi yakumbo ta saki tana cewa, "indai wannane aiki ne mai sauki ba se an dauko ta ba saboda kar tayi zargin wani abu, se mu isa part nata ba tare da mun razana ta ba muyi abinda ya kai mu" "kinyi magana yakumbo kinyi dogwan tunani a wanna gabar," Ashad yace, "Allah yasa this time around kar suyi mana shirme dan bana san shashanci, dama kauda ta akayi ko be mutu ba ya ji zafin mutuwar ta..! saboda sultan taurin rai gareshi so nawa ana kai mashi hari, amma se wanna munafikin Alex din ya tare ko Allah ya bashi sa'a ya kubuce" buga table Ashad yayi yana cewa, "shiyasa na tsani Alex shima ya kamata ya raka shi lahira se ya cigaba da tsare shi can ko kuma yaci wuta, yanzu haka kina kallo tare suka tafi wani lokacin har ji nake kamar na aza mashi wuka a wuya na tsinka jijiyar makoshin shi gabaki daya, Momi bazaki gane bane shike hana min ruwa gudu gabaki daya" "take it easy my son wanna karan se hakarmu ta cin ma ruwa" yakumbo kira doctor yanzu muje ya duba yarinyar can. ****** Misalin karfe 8:00am jirgin su sultan ya isa Moscow a hankali suke sakowa daga stairs din jirgi shi da Alex dauke da murmushi a fuskar su, baturan dake dagawa sultan hannu ne daga nesa sultan ya nufa yana smile flower ya mikawa sultan murmushi sultan ya saki baturan yace, "your welcome Dr sultan" "Nice to meet you to herry" yan labare sai dauka suke hugging din juna sukayi Herry na cewa, "long time sultan" murmushi kawai sultan ya saki sannan suka shige motocin dake fake wajan kaitsaye masaukin suka wuce kafin lokacin taran yayi. Wani hadadan gida suka sauka iyakar tsaruwa gidan ya tsaru gidan ko ina security's ne suna gadin gidan ba dan komai ba se dan sultan, gani su shiyasa sultan girgiza kai, dan shi ya fara gajiya da wannan rayuwar duk ida ze je se da security's daurewa kawai yake da wannan tunani ya shige toilet ya sheka wanka koda ya fito shiryawa yayi kamar yadda ya saba cikin black suit din shi sannan ya janyo wayar shi dan kiran Nihal kafi su fara taran. ********* Nihal dake kwance kasancewar yamma ne a Nigeria dan misalin karfe 5:00pm na yamma ne, ga wani irin suku-suku da take jin ta tunda sultan ya tafi, ringing din wayar tane ya sata mikewa cike da murmushi ta mika hannu ta dauki wayar ta kara a kunne daga dayan bangaran sultan yace, "hello hayaty..! lumshe ido Nihal tayi tare da kwantawa tana jin zazzakar muryar sultan har cikin ran ta ciki muryarta me dadi tace "kun isa lafiya? "lafiya lau hayaty ganin ina ta missing naki i wish tare muka zo, yanzu ma zamu shiga taran hope kina kula min da kanki" murmusawa Nihal tayi daga dayan bangaran tace, "Eh..! Sultan da Nihal su dauki some minutes suna hira masoya Nihal se dai ta bishi da eh da a'a dan kusan wayar duk shi ke zuba har mamakin Nihal take ashe yana da magana sannan sultan ya katse wayar. katse wayar yayi dai-dai da shigowar Gimbiya jalila dakin Nihal mamaki ne ya rufe Nihal saboda tunda ta shigo gidan Gimbiya jalila bata taba shigowa part na su ba Amma se gata yau murmushi Gimbiya jalila ta saki tana cewa, "daughter kina mamakin shigowa ta ko karki damu dan mahaifiya ta zo duba diyar ta ai ba wani abu bane tun ke da sultan ba ruwan ku dani na rasa laifin dana aikata maku" "Momi ki daina fadi haka, bana jin dadi idan kina nuna kamar bamu damu dake ba mun damu dake sosai ni da Sultan kuma muna alfahari dake, duk san da kika bukatar ganimu zaki ganmu, da kin bari na shigo ni ya kamata na zo na duba ki, idan kina bukatar ganina kawai ki turo yakumbo ko Yasmin zanzo ne" "ba komai daughter karki wani damu kanki nima din ina san ganin naki, ina so na kula da ke kamar yadda sultan ya bukaci hakan" Gimbiya jalila ta ida zancan tana kama hannu Nihal suka zauna murmushi Nihal ta saki tana sinne kai, dan jim kadan Gimbiya jalila tayi sannan tace, "yauwa daughter bani kad'ai na zo ba tare nake da doctor ze duba lafiyar ki" "lafiya na Momi? ai ni lafiya ta lau, babu abinda ke damu na" murmushi manya Gimbiya jalila tayi tana cewa, "oh laifin sultan ne be fada maki ana checkup a gidan nan ba duk bayan wata ina tunanin ya manta ne be fada maki ba, karki damu ba wani abu bane saboda kowa ana mashi" daga kai Nihal tayi tace, "toh Momi amma Ammi bata taba fada min ba ko itama ta manta ne" "Daughter kinfiye tanbaya, tsoro kike jine hala karki wani damu" daga kai Nihal tayi tana kallan yakumbo dake tsaye bakin kofa, alama Gimbiya jalila tayi ma yakumbo da ido sannan ta fita ta taho tare da doctor murmushi ta saki tana cewa, "gata nan abimin daughter a hankali doctor" gaban Nihal doctor ya zo ya fara yan gwaje-gwajan shi Nihal dai na bin su da kallo Gimbiya jalila na mata smile har ya gama sannan Gimbiya jalila tace, "ka jira ni a part din maimartaba" ta fadi hakan ne dan kar Nihal ta kawo komai a ran ta alhalin bakin su daya da doctor din sannan ya fice murmushi Gimbiya jalila ta saki tana cewa, "Dama ace daughter akwai rabo da se na fi kowa murna ni zanyiwa maimartaba albishir" raraba ido Nihal keyi wani irin rabo kuma sannan Gimbiya jalila ta fice Doctor dake zaman jiran ta a part nata tana shigowa tace, "me result din ya bada, akwai ko babu? "Gimbiya babu komai gaskiya" murmushi Gimbiya jalila ta saki tare da amsar result din tace, "masha Allah wanna albishir ya min ka je zan turo ma kudin ka" murmushi doctor yayi yace, "na gode ranki yadad'e" sannan ya fita. ******* Manya-manya likitoci na kasashe daban-daban sun halari wannan taro da shuwagaban ni kasashe daban-daban har dana Nigeria, inda shugaban kasar moscow ya fara bud'e taro sannan likitoci guda biyu sukayi jawabi, sannan aka kira Sultan yayi jawabi sosai a kan aikin shi ya amshi kyaututa ka da yawa a ranar aka nada shi shugaban likitocin Africa sosai sultan yaji dadi wanna karin girma daya samu, shikan shi shugaban kasar Nigeria yayi alfahari da sultan saboda darajar daya karawa Nigeria a idan mutane, daga nan aka fara ciye-ciye da lashe-lashe dan kusan taran anyi shine a cewar dan sultan akayi shi kuma ya ji dadi hakan, har ji yayi dama da Nihal din shi ya zo bayan taro ya watse ya wuce masaukin shi. Kokarin kwantawa sultan yake cikin kayan baccin shi yaji ana knocking din kofa "come in" yace Alex ne ya shigo mikewa zaune sultan yayi yana cewa, "Alex baka kwanta ba, I think kayi bacci" girgiza kai Alex yayi yana cewa, "ina so muyi magana ne" gabaki daya sultan maida hankali yayi kan Alex dake zaune saman sofa yace, "sultan ina so na shiga addini ka..! ina so nima na zama Muslim brother's me zanyi na zama" sultan dake zaune saman gado wani irin murmushi ya saki yana cewa, "are you serious? "yeah am serious na dade ina nazari kan adini ka har da kyawawan dabi'un ka suka ja ra'ayi na" wata irin runguma sultan ya kai ma Alex yana cewa, "amma wannan maganar taka tafi kowa ce magana dadi dana saurara yau Alex" nan sultan yayi kalma shahada Alex na bi har ya zama cikakyan Musilmin sannan suka shiga toilet dan dauro alwala kara harbi da suka ji ne ya sasu juyowa a razane suna kallan juna zuciyar sultan lugude ta fara a hankali Alex yace, "ka ji abinda naji kuwa? daga kai sultan yayi yana cewa, "oh my god an biyo mu nama a kashe ni ne yaushe ne zan samu peace of mind ne" a hankali Alex ya bude kofar toilet ya ciro bindigar shi dake makale a kugun shi suka fito tare da sultan daga cikin toilet lallabawa sukayi bakin kofa dakin bindiga sultan ya ciro a bedside drewar bude kofar dakin Alex yayi suka nufo parlour abinda suka ganine ya sasu shan ruwan jini jikin su, kusan an kashe duka security's din dake parlour jikin sultan rawa ya dauka yana kallan gawawakin dake parlour zube Alex ma sakin baki yayi kara harbin da suka kuma jine ya sasu lafewa jikin bango mutanene suka shigo parlour sun kai su biyar nan suka far aikawa su sultan harbi suma suna aika masu a haka suka kashe mutum biyar din suka boye suna maida numfashi, wanine ya shigo cikin makisan daga ganishi shine babba ya shigo da wasu yaran sun kai su biyar fuskar shi na rufe daga bindiga yayi cikin harshan turanci yace, "ku fito ku aje bindigun hannu ku" lamo sultan yayi bayan kujera yana kallan Alex dake bayan kofa zuciyar shi na kara tsinkewa ya san kawai mutuwar su ce ta zo gashi bullet din cikin bindiga shi saura daya, takowa sukayi a hankali daya daga cikin sune ya sha gaban sultan dauke shi yayi da harbi kafin ya harbe shi lumshe ido yayi yana juya bindiga hannu shi, kafin yayi wani yunkuri an zagaye shi da bindigu daga hannu yayi sama fisgo shi Frank yayi ya watso shi tsakiyar parlour ya tafi taga-taga ze fadi, cikin zafi nama Alex ya fito ze dauke Frank da harbi seta juna su sukayi tsaka ni Frank da Alex sultan na rike yana kokarin kwace kan shi harba bindiga Alex yayi Amma se dai me bullet ya kare dariya frank ya saki yana nuna Alex yace, "so funy, ku kama min shi" duk yadda Alex ya so ya kwace ya kasa rike shi akayi gam se fisge-fisge yake yana huci, wani kyakyawan mari Frank ya dauke sultan da shi ji kake tas, tas, har se daya kifa jini yana bin gefan bakin shi kafin ya dago Frank ya finciko shi yace, "nadad'e ina neman ka se yau Allah yayi zan kai ka" taka ma sultan kafa yayi da booth din kafar shi wata kara sultan ya saki idanuwan shi jawur Alex dake rike yana fisge-fisge yana cewa, "karku taba shi na fada maku duk wanda ya taba shi se na kashe shi da hannu na" Alex yana maganar cikin zafi rai wargi yayi da sultan ya fada saman kujera yana sauke wata irin ajiyar zuciya matse ma Alex baki Frank yayi yace, "shhhh..! yima mutane shuru a tunanin ka kai ma da rai zamu barka kayi kuskure ai tare zaku bakunci kiyama, ina fatan ka gane," wukar da aka ci Apple aka bari a sama stool sultan ya fakaici idanuwan su ya dauka ya cakawa wanda ya tsare shi a wuya ihu ya saki dafe da wuya juyowa Frank yayi a fusace daukar bindiga yayi ze dauke sultan kwacewa Alex yayi daga rukwan da yaran frank suka mashi jikake daram..! Alex ya ture sultan an dauke shi da harbi a ciki, tafe ciki Alex yayi jini na zubuwa dukewa yayi yana sauke numfashin kara sultan ya saki yana cewa, "no..! no..! Alex..!.! da sauri ya kara so gaban Alex da jini ke zubo mashi yana kallan sultan daga bindiga Frank ya kuma yi ture sultan Alex yayi da kyar ya mike dafe da ciki yana gani biyu uku dauke shi da rabi Frank yayi a kafada tafiya Alex yayi taga-taga numfashin shi na daukewa yana dawowa hawaye na zubo mashi sulalewa kasa yayi yana wani irin numfashin kuka sultan ya saki yana jijiga Alex yana cewa, "no no Alex karka mutu ka barni Alex please" gabaki daya jikin shi rawa yake da bakin shi, Alex yayi laushi yana rike da hannu sultan magana yake sanyi amma ya kasa, fisgo sultan Frank yayi ya gurza kanshi saman dining gabaki daya kayan dining suka watse Alex na kallo ba abinda ze iya yana jin duk abinda ke faruwa, bindiga Frank ya zaro a aljihun daya daga cikin yaran shi ya seta zuciyar sultan daya galabai ta yana wani irin nishi na wahala ba abinda ya fada mashi a rai se Nihal daya tuna yadda ta damu kan tafiyar Ashe jikin ta ya bata tunda akayi kokarin kashe shi yasan Nihal ma bata tsira ba tunda Alex be tsira ba, wani irin karfi ne ya zo ma sultan murd'e hannu Frank yayi nan suka fara artabu daya daga cikin yaran Frank dauke sultan yayi da harbi ji kake daram..! zaro ido sultan yayi da kyar ya iya kallan kafar shi dake zubar ji tasha harsha shi fisgo shi Frank yayi wukar dake makale a kugun shi ya ciro ya lumama sultan a ciki wani irin numfashin sultan ya ja hawayan wahala na bin fuskar shi yana kallan Frank, Alex dake kwance shi da gawa ba maraba kuka yake, dukewa sultan yayi hawayan wahala na bin kuncin shi yana motsa ba.... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/22, 8:52 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_fan's ina mai baku hakurin jina kwana biyu shuru hidimomi ne sukayi min yawwa, masu kira na da masu yimin text duk na gode wannan page naku ne kyau ta, kuyi yadda kuke so, ina ganin comment yadda ya kamata hakan na karamin gwarin gwiwa_* *Page: 113_114* Dago sultan Frank yayi daniyar ya kara luma mashi wuka jiniyar motar yan'sanda ce ta katsewa frank hanzari zaro ido yayi yana kallan yaran shi da sauri ya saki sultan ya fadi kasa, da sauri suka shiga guduwa ko da yan sanda suka shigo sun sha mamaki irin ta'adancin da aka aikata kafin su iso, kafin ka ce mi ambulance ta zo wasu cikin su sun mutu wasu da sauran su sultan da har a lokacin yana jin motsin mutane sama-sama aka sa shi cikin ambulance. Kaitsaye asibiti aka wuce da su dan basu taimakwan gagawa shugaban kasar Moscow yasha mamakin irin wannan ta'adaci da aka tafka abin takaicin ma ko mutun daya ba a kama ba, kuma duk yawan security's basu tabuka komai ba, ko dayake daga gani ba kananan makisa aka samu ba amma yace a tsana ta bincike har se an gano su tunda yan kasar ne babu idan zasu, sannan ya hana shige ta fice har ma da masu yunkurin barin kwasar yace karsu barta, har sai an gano makisan. Likitoci suna iya bakin kokarin su a kan Alex dan ganin cewa sun ceto rayuwar shi dan ba karamar galabai ta yayi ba, dan ba suyi tunanin yana da rai ba da farko, dan har an sashi cikin matatun hannun shi ya fara motsawa, cikin ikwan Allah an cire mashi bullet's din dake jikin shi amma har a lokacin yana como, bangaran sultan ma an cire mashi bullet daya na kafar shi ayi mashi dressing an kai shi waiting room har a lokacin be tashi ba. ******* Yau dai kam Nihal suku-suku ta tashi gaban ta ban da faduwa ba abinda yake haka dai tayi wanka ta shirya cikin uniform din ta, wayar ta ta janyo ganin bata ga miss call din sultan ko daya ba, wata zuciyar tace ta kira shi toh ko ta kira shi yanzu a can dare ne kilama yana bacci hakan ya hana Nihal kiran sultan sannan ta wuce main parlour dan yin break, lokacin su Ammi suna zaune suna break gaishe da su tayi a takaice ta zauna Ammi ce ta kalle ta tace, "Nihal yana ganki suku-suku ko tun yau kin fara missing mijin naki? Cike da kunya Nihal tace, "a'a Ammi bana jin dadi ne shiyasa" "sannu kin ji, kuma shine kikayi shirin zuwa makaranta? ki zauna gida ki huta, idan kin samu sauki se ki je," "zan iya zuwa makaranta tunda ciwan ba wani rufe ni yayi ba, kuma kin ga jiya ban je ba, be kamata na rinka fashi ba daga fara zuwa na" "haka kuma toh kafin ki fita ki tabata kin sha magani" daga kai Nihal tayi tana break haka nan dai ta tsakuri abincin sannan ta wuce parking space lokacin driver na zaman jiran ta. Koda Nihal taje makaranta bata daina jin faduwar gaba ba, Nana ce ta ta lura da yanayin da Nihal ke ciki ne tace, "Nihal mike damun ki ne baki daya yau kinyi sanyi kamar wani abu na damun kin, ko dazu da uncle ya shigo hankalin ki baya kan karatun kwata-kwata" numfasawa Nihal tayi tace, "Nima Nana ban san me ke damuna ba bana jin dadi jiki na gabaki daya" "Allah ya sauwake ki yawai ta addu'a ita ce makamin mumini, idan an tashi break se muje ki sha magani," 'bana jin zan iya shan magani na san dana koma gida komai ze zama normal" "Allah yasa" "Amin" shigowar Malami ne ya katse Masu zance suka cigaba da daukar darasi a haka har lokacin tashi yayi Nihal ta dawo gida. Koda ta dawo part nasu ta wuce tayi wanka ta shirya cikin wata blue doguwar riga, rigar ta mata kyau ta kama jikin ta sosai, sai dai fuskar nan tata ba walwala tayi fayau da ita kamar ta kwana biyu tana ciwo, wayar ta dake ciki drewar ta ciro har yanzu ba kiran sultan ba alama da kanta ta shiga kiran layin amma wayar kashe dan kwata-kwata bata shiga lamarin har ya fara daure mata kai amma se ta share ta wuce part din Basmal dauke da sallama a bakin ta ta shiga Basmal dake zaune a parlour tana kallo ta amsa cikin fara'a tace, "Aunty Nihal yanzu nake cewa zan shigo cikin gida na tanbaye ki gabaki daya yinin yau wayar yayana bata shiga, hankali na duk ya tashi," zaunawa Nihal tayi tana cewa, "Nima na kira amma wayar bata shiga, ina tunanin aiki ne ya mashi yawa," "kuma fa tana iya yuyuwa saboda na san yayana baze kashe wayar shi haka nan ba, ko dan ke ze barta kune, amma kuma yayana be saba kashe waya ba idan yayi tafiya kina ganni lafiya kuwa? Shigowar Ammar ne ya katsewa Basmal zance da sauri Basmal ta karasa tayi hugging nashi tare da sakar mashi pack a kumatu ta amshi briefcase din hannun shi cikin sigar shagwaba tace, "my love sannu da zuwa" "yauwa abar kauna ta, yana ga fuskar ki na dauke da tsantsar damuwa waya taba min ke? "Ban wanda ya taba ni lamarin yaya ne ya fara bani tsoro," "Me ya faru da shi abar kauna ta? "babu komai, kunyi waya da yayana duk yinin yau? "a'a bamuyi ba na kira wayar bata shiga amma nasan aiki ne ze rike shi, ki daina damun kanki abar kauna ta, har kin sa hankali na ya tashi" "Kayi hakuri my love, Aunty Nihal ma duk ta damu da jin yayana shuru, tana kewar yayana da baya kusa da ita, dama tare suka tafi se sunfi samun sakewa" "uhm kuma kinyi gaskiya musanman yadda suke love bird" Ammar ya ida zancan cikin sigar tsokana Nihal dake zaune dan darawa tayi tare da gaishe da Ammar ya amsa cikin fara'a yana cewa, "karki wani damu Nihal na san aiki ne ya rike shi daya kunna waya ke ze fara kira, karki bari wanna matar ta ruda ki" Murmusawa Nihal tayi tace, "nima nayi tunani haka" sannan Ammar ya wuce bedroom Basmal tace, "bari na bishi ciki" "Toh shikenan" Nihal ta ida zancan tana mikewa, "Aunty Nihal ina zaki? "Cikin gida yanzu na tuna da Assignment nawa da banyi ba" "Toh shikenan Aunty Nihal ki gaishe min da Ammi da mom kafin na shigo" "Za su ji" sannan Nihal ta fice, Kaitsaye part din Ammi ta wuce koda ta shiga se da ta tanbaye ta ko sunyi waya da sultan tace a'a sannan ta kwantar Ammi da hankali ta ganin hankalin ta duk ya tashi, maimartaba ma ya kira sultan yafi a kirga musanman da mom take gwada mashi tsantsar damuwar ta rashin jin shi tun jiya yanke shawara maimartaba yayi mindin sultan be kira gobe ba dole su bi lafiyar dan su tafiya Moscow ta kama su sannan ya cigaba da lallashin mom kanta kwantar da hankali ta. ***** Bangaran sultan kuwa har yanzu basu farka ba, dan basu san duniyar da suke ba se dai ana basu kyakyawar kulawa dan shugaban kasar Moscow yasa tsaro sosai a asibiti tare da tsana ta bincike, har sai an ganu mashi wayanda suka aikata wannan katobara yan'sanda kuwa suna iya bakin kokarin su wajan ganin cewa sun gano su musanman kowa burin shi be wuce ace ya gano ba, shugaban kasa ya kara mashi matsayi a wajan aiki ba, hakan ya sasu jajircewa da dagewa wajan kokarin gano su frank dan tunda abin ya faru an hana shige da fice, tare da tsana ta bincike da na'ururi computer. ********* "Gabaki daya hankali na ya kasa kwanciya har yanzu frank be kira ni ba, ban ji labari wani jirgi daya taso daga Moscow zuwa Nigeria ba, komai ya kule min brain nawa tayi zafi, Gashi ba labarin cewa sultan ya mutu ko dana kuna news a CNN ban ji wani labari daya shafi sultan ba, idan ya mutu ya kamata ayi maganar a gida jan labarai saboda shugaban likito cin Africa ne, amma na kira wayar shi kashe hakan na nufin sun kashe shi ne an kamasu ko me, ko kuma ya ji rauni yana asibiti hakan ba zeyu ba," Ashad ya ida zancan yana watsi da kayan dining, Gimbiya jalila tace, "na rasa gane wannan ragwan a zancin naka gabaki daya ka tadawa kanka hankali ka tadamin, dubi yadda kake bari da kaya saboda Allah son, ya kamata ka kwantar da hankalin ka babu abinda ze faru Mara dadi mutuwa ce dai yanzu nasan sultan ya riga dayama mutu tunda ka kira wayar shi kashe" fadawa saman kujera Ashad yayi yana cewa, "baza ki gane bane Momi jiki na yana bani akwai matsala..! "ka kwantar da hankali ka ba wata matsala my son" haka Gimbiya jalila ta rika kwantar Ashad da hankali da nuna mashi cewa sunyi nasara wannan karan. Da daddare bayan Nihal ta gama shirin bacci ta kamar kullun part din Ammi ta wuce dan kwata-kwata part din nasu ba dadi ga kewar sultan da ta taru tayi mata yawa gashi ta kira wayar shi yafi a kirga kashe, da wannan tunanin ta wuce bedroom din ta na part din Ammi ta kwanta ta dade bacci be dauke ta ba, tana juyi da kyar ta samu bacci ya dauke. "Nasan cewa duk halin da ake ciki yanzu na san kowa ya kwanta ina so a aiwatar da abinda na uwarce ko dai-dai, bana so a samu matsala" "Ran ki yadade baza'a samu wata matsala ba, sai ma dinbin sara Gimbiya" "Da kyau kina iya tafiya, idan kun gama aiki kudin ku na jiran ku" Nazili na gama fadin haka Aziza ta fice, Nazili ta cigaba da zancan zuci, "yau zan nuna maki wacece Nazili ba dai fuskar nan taki yake kallo ba, har baya gani kyan tawa fuskar baya gani na saboda kyanki ya rufe mashi ido, ya kusa daina marmarin ganin ta, Allah sarki *Sultan salim* zaka sha mamaki idan ka dawo ka ga fuskar hayaty se ka razana, daga lokaci ni kuma tawa tutar zata daga zan zama cikakiyar Gimbiya, sultan nawa ne ni kadai..! ya zama dole a kira ni da Gimbiya ma'ana matar sarki ba matar matsiyaci ba dan tallaka" dariya Nazili ta saki ta haye bed tana cewa, "gida ya kusa gwarayewa da ihu da kuka saura kiris zuciya ta ta cika fal da farin ciki" Nihal dake kwance tayi nisan bacci cikin bacci ta fara jin motsi kamar a bisa kanta kafi tayi wani yunkuri an manna mata handkerchief a hanci sai mutsu-mutsu take ta kasa kwace kanta har se da ta daina motsi, Aziza tayi ma fadawan dake kusa da ita alama da ido daukar Nihal cak sukayi suka fitar da ita daga cikin daki, wani daki suka kaita na cikin gidan, wanda ko ba'a fada maka ba kasan ya dade dakin dan ba komai cikinsa se komutsai da yanar gizo-gizo, a hankali Nihal ta bude ido tana bin dakin da kallo tace, "ina ne nan, mi ya kawo ni nan,? turo kofar da akayi ne yasa Nihal mikewa cikin kidima da rudewa tana kallan bayi mata guda biyu da suka shigo fuskar su rufe cikin wani yaddi idan ka kura masu ido zaka iya gane su nufo Nihal sukayi bakin ta na rawa tace, "Mi nayi maku ku fitar dani daga nan dan Allah, karku matso kusa dani" duk abinda Nihal ta rarumo sai ta jefa masu su kau ce tana ja da baya fisgo mata gashi sukayi daya ta dauke ta da mari ji kake tas, tas, ririke Nihal sukayi tana kokarin kwance kanta suka manna ta a bango suka matse ta jikin bango ta yadda bata iya kwace kanta, Aziza ce ta shigo ta dangwalo wuta a icce fuskar ta a rufe ta nufo Nihal girgiza kai Nihal take tana cewa, "karku cutar dani dan Allah..! Dariya Aziza ta saki tana nufo fuskar Nihal da wuta zafi daya ziyarci Nihal da radadi ne yasa Nihal daga murya tace, Sultan...! Da karfi Gabaki daya gidan sai daya gauraye da ihu da Nihal ta saki, ta fadi sumama da sauri su Aziza suka shige dakin dake kusa da dakin da Nihal take suka kule, kafin kace mi gidan ya gauraye da ihu Nihal mom dake part din maimartaba kwance mikewa zaune tayi tana cewa, "Nihal..! A tare suka mike da maimartaba sleep robe din ta kwai ta daura saman rigar bacci ta suka fito a tare sinbul da tunda ya ji ihun ya nufi inda ya ji ihu kofar dakin bude ya same ta wuta na ci kama baki sinbul yayi yana cewa, "ya sallam..! can yashe ya hango Nihal cikin wuta sume da sauri ya karasa gaban ta ganin fuskar ta kone tayi shawur da ita jikin shi ya dau rawar da kyar ya iya daukar ta ya fito da ita gabaki daya yan gida na compound har da Adda da waziri suna kokarin nufo daki Sinbul ya fito da ita da sauri mom ta karasa ita da Adda suna cewa, "Mi ya same ta? Abinda suka ganine ya sasu ja da baya rike da baki mom tace, "innalillahi wa'inna'ilai raju'un "me nake gani haka me ya sami fuskar ta, waya aikata mata haka Abba sultan? mom ta fada tana sakin kuka Ammi da jiri ya fara dibar ta luuu ta tafi Ammar ya taro ta yana cewa "Ammi..! Ammi..! Daukar ta yayi cak ya shige da ita ciki Basmal ta bi bayan shi da Adda Sinbul shima ciki yayi da Nihal gidan gabaki daya ya rud'e sai kuka dake tashi Nazili na gefe tana murmushi tana zancan zuci ai konewar da fuskar tayi hakan be mata ba tunda ba konewa kurumus tayi ba, doctor Amir maimartaba ya kira ya duba Nihal ko a wuce da ita asibiti Ammar kuma na duba Ammi Gimbiya jalila ko abin dariya yaso bata dan basu ji komai ba saura su ji mutuwar sultan se gidan ya kara cakudewa a cigaba da kuka na tsawan kwana uku, Ashad dake gefe mamaki ne ya lullube shi lallai gidan nan akwai mugaye basu kadai bane akwai wasu kenan shi daya ke tunanin sultan na mutuwa ya lallaba ya aure Nihal din shine se aka samu munafukin daya kona mata fuska, ya san bame aikata haka ze Nazili yariyar nan itama A ce wallahi. Amir dressing yayi ma Nihal ya rufe mata fuska gabaki daya idanuwan tane kawai bud'e ya daura mata drip shi kan shi abinda ya gani ya girgiza shi, ya sultan ze ji idan ya dawo ko ya ji labari wai shi me yasa komai nashi se an bata mashi Allah ya kare shi ya tsare yana fitowa daga daki maimartaba da mom suka ce, "ya jikin nata? "da sauki amma zatayi kwana biyu da dressing a fuskar ta ranar Monday zan zo na cire mata dan abin ya zo da sauki turirin wutar ne ya taba ta, inda wutar tataba ta bashi da wani yawa a fuskar se dai turirin wutar yayi mata ila, idan har magani dana shafa mata beyi ba se an fidda ta waje kuyi fatan Allah yasa kunar bata taba cikin fatar ta ba," kuka mom ta saki tana cewa, "wannan wace irin rayuwa ce dubi yadda yariyar mutane ta koma saboda sultan, wai yaushe ne d'a na ze samu natsuwa? na gaji da wannan cutarwar da ake mashi daga shi har matar shi ba'a kyale ba har yau ba'a taba kama ko mutun daya ba dake da sahannu a cikin abubuwan dake farwa ba daya baya daya, na gaji da wannan rayuwar dan inayin shuru shiyasa har yau aka kasa gano masu laifi Abba sultan, tun yana karamin yaro yake shan wahala kana tunanin hakan namin dadi ne kowa ce uwa zata so ace d'an ta na da natsuwa da kwanciyar hankali amma ban da nawa d'an toh hakan ya fara isa ta kar asa na fara zargi cikin gidan nan ake so a ga baya d'a na da matar sa, to wannan karan bazan dauka ba" kokarin janyo ta jikin shi maimartaba yake mom ta kwace tana cewa, "bazan kara saurara ka ba sai ka ganu min wayanda ke kokarin rabani da dana da suruka ta, ida ba haka ba zaka fara ganin dayan hukunci dan allura zata tonu galma" Mom ta ida zancan tana kallan Gimbiya jalila tare da ficewa fuuu, ruwan jini jikin ta Gimbiya jalila tasha me wannan matar take nufi kar ace fa ta san makircin su, amma hakan be hana ta sakin malallacin murmushi ba sannan ta juyo kan maimartaba dake kokarin bin mom ta tari numfashin shi da kar ya bita ta burbusa mashi wani labari musanman da ran ta ke bace tace, "karka bi ta tashin hankali ne ya mata yawwa, nasan bata bukatar kowa kusa da ita, tana bukatar samun space zuwan ka ba abinda ze haifar se wani zafin" Gimbiya jalila ta ida zancan tana rungume maimartaba ta cigaba da cewa, "wannan abu dake faruwa ba ita kadai ya shafa ba har muma ya shafa muna jin zafin shi" Gimbiya jalila ta ida zancan cike da munafirci har da kwalla maimartaba na lallashin ta fitowar Ammar daga dakin Ammi ne ya sasu dunguma suka shiga dan duba ta Adda da waziri kuwa sai tausaya Masu suke musanman Adda da Nihal tayi mata tsaye a zuciya wannan wani irin mugun abu ne, wannan dalilin ne ya hana kowa na gidan rintsewa Nazili da Aziza ne kawai sukayi bacci se Gimbiya jalila, Ashad kuwa ya kasa rintsawa saboda tunanin wani hali su frank ke ciki bunu-bunu ya duba wayar shi. ***** A hankali sultan ya bude ido yana bin dakin da kallo yana ganin biji-biji maida ido yayi ya lumshe Nihal ce ta fado mashi a rai da sauri ya bud'e ido herry dake zaune yana jinyar sultan ne ya mike cike da farin cikin ganin sultan ya bud'e ido yana yunkurin ta shi da sauri ya fita dan kira doctor ya zo duba shi, sultan kuwa yana tashi zaune kokarin cire drip din Hannun shi yake dan Nigeria yake so ya koma dan gabaki daya zuciyar shi na tunani wani hali Nihal zata shiga, har ya cire drip din ze taka wata yar kara ya saki saboda fama kafar shi dayayi dan kwata-kwata ya manta da Harbin da yasha a kafa komawa yayi ya zauna yana maida numfashin lokaci yayi dai-dai da shigowar doctor da sauri ya karaso yana cewa, "sultan what are you doing like that" maida shi herry da doctor sukayi saman gado suka maida mashi drip din cikin sanyi murya sultan yace, "I can't stay here anymore..! I have to leave, please let me leave i need to go back Nigeria let me be doctor, am fine just leave me alone" sultan ya ida zancan yana kokarin kara banbare drip doctor yace, "sultan you are not feeling much better you have to stay here" a haka ya lallaba yayi ma sultan allura bacci a hankali bacci ya fara dauke sultan yana surutai furzar da isa me zafi doctor yayi yana kallan herry yace, "mr President must no abut this issue, you have to call him before sultan wake up," "I will doctor" sannan doctor ya fita be zame ko ina ba se dakin Alex wanda har yanzu a Como yake injinane kawai ke aiki a jikin shi babu abinda ke motsi a jikin shi sai kayan aiki da suke nuna alamar yana da rai, Haka doctor ya gama dube-dube shi sannan yayi mashi allura a jijiya. ******* Washe gari da safe kamar yadda Dr Amir ya fada ya dawo ya duba Nihal har a lokacin bata farfadu ba Basmal dake bakin gado tana rike da hannu Nihal se matsar kwalla take Ammar ne yace, "abar kauna ta kukan da kike ya isa haka, ko break ba kiyi ba addu'a zaki mata Allah yasa ta samu lafiya," juyowa Basmal tayi tana goge hawayan idanuwan tace, "my love tana bani tausayi ne, me tayi har za'ayi mata wannan mugun abun kona ta fa akayi, kuma a fuska baka tunanin fuskar ta ta lallace ban san wani hali zata shiga ba, ta wayi gari fuskar ta, ta samu matsala, koma waye ya aikata haka ba karamin azalumi bane" Basmal ta ida zancan tana jan majina janyo Basmal Ammar yayi jikin shi yana shafa kanta shima ji yake kamar ya zubarwa Nihal da hawaye cikin sigar lallashi yace, "insha Allah ba abinda ze samu fuskar, in Allah ya yarda kunar bazata shiga cikin fuskar ta ba, addu'ar mu take bukata kin ji abar kauna ta, muje nayi feeding naki abinci na lura yau kina so ki wahala min da baby" ya ida zancan yana shafa cikin ta shigewa jikin Ammar Basmal tayi tana dariya tace, "Waya ce ma akwai baby a ciki na, ba wani baby" ja mata hanci Ammar yayi yana cewa, "zaki ganine da idanuwan ki soon" haka dai Ammar ya lallaba Basmal dan ta ci wani abu. ********** Wanna karan da sultan ya tashi bayan allura bacci ta sake shi da sauri ya mike zaune drip din hannu shi ya banbare, a hankali ya sako daga saman gadan yana dingishi dan ya daukar wa kanshi alwashin yau ze koma Nigeria dan ya ga wani hali Nihal take ciki saboda hankali shi ya kasa kwanciya Alex ne ya fado mashi a rai, murda kofar da akayi ne ya sasa waigowa da sauri herry ne ya shigo yana rike da handle din kofa yana bin sultan da kallo tunda sultan ya dage se ya bar kasar se fa ya bari kara kawai a fadawa Mr President ya sanar da shi gaskiya magana kara kawai ya sani ko kallan herry sultan beyi ba yace, "I need some cloth" "sultan you need to get much better before you leave, oh my goodness sultan why can't you see your self sultan, you are serious sick" herry...! Sultan ya ida zancan rai had'e fita herry yayi ya dawo rike da suit da waya hannun shi ya mikawa sultan yace, "mr president..! jim kadan sultan yayi sannan ya amshi wayar ya kara a kunne Mr president ne keta magana wanda bame jin me yake cewa hakan ne ya haifarwa sultan zama saboda jirin dake dibar shi har wayar Hannun shi ta subuce ta fadi, bugun zuciyar shi na karuwa kamar zuciyar shi zata fasa kirjin shi ta fito, saboda abinda Mr president ya fada mashi hawaye ne kawai ke bin kumatun shi, jikin shin ya mutu murus haka sultan ya shirya cikin suit na shi yana kuka shi kadai ya san zafi daya ke ji ya zama dole ya koma Nigeria, sai daya fara biyawa dakin Alex kwance yake har yanzu a Como sultan be san sanda kuka ya kubuce mashi ba saboda tausayi Alex ganin saboda shi ya shiga wanna halin Allah sarki Alex, lallai Alex ya fi dan'uwa a gare shi yayi abinda dan'uwan shi baze iya ba, kuka sultan ya kuma saki zuciyar shi na kara zafi da takaicin abinda kunna shi ya ji da kunyar abinda kunnuwan shi suka ji mashi yau, cikin zuciyar kuwa cewa yake Allah ya kare mashi Nihal din shi saboda abinda ya ji yafi ko mai daga mashi hankali Nihal ba komai ba ce sultan ya kara sakin kuka da kyar ya samu ya tsagaita kukan da yake, ya dade yana kallan Alex shigowar herry ne yasa sultan fitowa, kaitsaye gidan Mr president suka wuce duk yadda Mr president ya so sultan ya tsaya ya warke amma fir yaki dole tasa Mr president bada umarni akai sultan airport, kaitsaye airport suka wuce haka sultan ya fito yana ingishi dan kafar ba warkewa tayi ba ga wani kuna da zuciyar shi ke mashi hawaye na zubo mashi a haka jirgin su ya tashi zuwa na Nigeria. ********* Da yamma Amir ya dawo ya duba Nihal yana kokarin cire mata dressing din da yayi mata yana cire mata hawaye na sulalo mata gabaki daya mutanan gidan na dakin Nihal ban da Nazili da Aziza mom ko addu'a take Allah yasa kunar bata shiga cikin fuskar ta ba Dr Amir yana gama cirewa ya mikawa Nihal mirror, jikin ta na rawa ta amsa a hankali ta kara mirror din a fuskar ta wurgi Nihal tayi da mirror din hannu ta ji kake taratsatsa..! glass din na tarwatsewa cikin daki wani irin kuka Nihal ta saki da karfi ta furta, "ya Allah wannan wace irin cutar wace..! da gudu Nihal da dankara... ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/23, 10:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 115_116* Da gudu Nihal ta dankara zata fice daga dakin Ammar ya tsafko ta wani irin marayan kuka Nihal ta saki tana kokarin kwace kanta daga rukwan da Ammar ya mata duk wanda ke dakin sai da zubar da kwalla, kokarin kwance kanta kawai Nihal take alama Ammar yayi Basmal da ido ta miko mashi allura bacci a hankali ya yayi mata allura lukus Nihal tayi tana kuka mara sauti a hankali bacci ya dauke ta Ammar ya shifid'e ta saman bed, Ammi kuwa kuka takeyi kamar me Adda tace, "na rasa dalilin bibinin rayuwar yaran nan da ake kiri-kiri ana so a maida yarinya karama mahauciya, Allah ya toni asirri koma suwaye" gabaki daya dakin aka dauka da Amin, Nazili dake gefe Hannun ta nad'e a kirji cikin zuciyar tace ba Amin ba kiran sallah magrib ne ya tashi kowa dan zuwa gabatar da sallah Nazili na fitowa taci karo da Aziza fisgo Hannun ta tayi suka shige cikin daki. suna shiga ta sake mata hannu tana cewa, "ni fa wannan aikin be mun ba fuskar bata kone yadda ya kamata ba, ya kamata ace tafi haka lallacewa," "ran ki yadad'e har da ihu da tasa ya firgita mu, kuma kinga da sinbul be je da wuri ba har ita kan sai ta kone ba fuskar ta kad'ai ba," "kuma fa amma dai wannan sinbul ya watsa min aiki i wish dukan ta ta kone, zan so ace sultan ya dawo na kusa ya ga fuskar abar kauna shi yadda ta zama, se yasha mamaki, bari na baki kudin ku kuje ko raba amma next idan na saku aiki bana san shirme..,! drewar Nazili ta bude ta ciro badil din 1k har hudu ta mikawa Aziza ta amsa tana godiya ta fice. Misalin karfe 7:00pm flight din sultan ya sauka Nigeria a hankali yake takowa daga stairs din jirgi har ya sako gabaki daya taxt ya tara driver taxt din ne yace, "yallabai dama irin ku na shiga motar haya? kamar na so na san ka a gidan TV ana fira da kai ba kai bane Dr sultan dan sarki kano" murmusawa sultan yayi yace, "nine" ya ida zancan tare da shigewa motar yana cewa, "dan ina Dr sultan ba shi ze hanani shiga motar haya ba dani daku duk daya muke a wajan Allah" "haka ne yallabai har dakuma kai din na daban ne cikin alumma, amma sai na ganka kamar baka da lafiya dan naga kamar da rauni a kafar ka, ko mu wuce asibiti ayima dressing," "Ah na gode ba sai mun je ba idan naje gida zan duba da kai" "toh shikanan yallabai Allah ya karo sauki" "Amin" suna tafiya driver motar na jan motar yana jan sultan da hira sama-sama sai dai sultan ya bi shi da eh a'a a haka har suka karaso gida da kan shi driver taxt ya budewa sultan kofar motar har sultan na cewa, "ya bari baya san irin haka" shi kuma yana cewa dan yaga kafar shi da raunine sai da sultan ya fito sannan yace, "sai dai ban san suna ka ba? "Au suna na yallabai suna na mudi..! "malam mudi gashi ban fito da kudi a jiki ba yanzu haka daga ni sai kayan jiki na, na iso kasar nan amma gobe ka dawo zan baka kudin ka" "yallabai daka barshi kawai kayi ma tallakawa abinda yafi haka ko motar nan daka gani cikin ta cikin motocin da karabawa matasa ne kwanaki," "A'a baza'ayi haka ba komai ga nayi inayin shi dan Allah kuma hakkin ka ne kamar yarda nace ma gobe to goben ka dawo" "toh yallabai na gode Allah ya kara ma lafiya da daukaka" sultan yace amin sannan ya shige gida fadawan dake bakin geta suka fara sakin baki suna bin sultan da kallo zubewa sukayi suna gaishe shi, daga masu hannu sultan kawai yayi kaitsaye part din Ammi ya wuce. Tun daga baki kofa yake cewa, "Hayaty..! Hayaty..! Ko lura da muta nan dake parlour beyi ba ya cigaba da cewa, "hayaty..! mikewa gabaki daya yan parlour sukayi zuciyar su na lugude dan basu so dawowar sultan yau ba ya ga halin da Nihal ke ciki ba, Gimbiya jalila wutar jikin ta daukewa tayi tana bin sultan da kallo fuskar shi had'e ba kamar yadda suka saboda gani shi ba tayi jawur jijiyoyi duk sun taso mashi yana cigaba da kira Nihal, Nazili da fitowar ta daga daki kenan sakwamakwan suna Nihal da sultan ke ta kwadawa nad'e hannuwan ta a kirji tayi tana murmushi cikin zuciyar ta tana cewa, "yanzu drama ta zata fara aiki yau zaka ga abinda hayaty ta zama Nazili na zancan zuci tana malallacin murmushi, da sauri Ammar ya karasa gaban sultan yana cewa, "Sultan me ya sami kafar ka mike damun ka na ganka cikin wani yanayi,? ka zauna ka huta first" zame hannu Ammar sultan yayi yana cewa, "ina Nihal? Sultan ya ida zancan yana tsare Ammar da ido zuciyar shi na lugude musanman daya ga kusan mutanan gidan a parlour har wani jiri yake gani dan tsoro yake kar ace mashi ba Nihal da karfi ya kara kira suna Nihal. Nihal dake kwance a daki tana bacci ciki bacci ta fara ji kamar ana kiran ta a hankali ta bude ido murya sultan ce ta ziyar ci kunna ta a hankali ta furta, "love..! da sauri ta mike ta cire drip din dake hannu ta har ta iso bakin kofa taci birki, tana shafa fuskar ta rintse ido Nihal tayi siraran hawaye na sulalo mata tana kokarin komawa ta kwanta Dara dake bayan ta tace, "ya kamata ki je koma me ya same ki, be kamata ki gujewa kiran mijin ki ba Gimbiya" hayawa dake bin fuskar ta Nihal ta goge wani dankwali ta janyo ta rufe fuskar ta idanuwan tane kawai ke bude da sauri Nihal ta fice, sultan dake baki kofa ganin Nihal ya sasa saki murmushi da sauri ya ingiso ya ture Ammar dake gefan shi Ammar ko saki baki yayi yana kallan sultan dan kamar baya gani har da maimartaba da waziri a parlour, Nihal da fitowar kenan ita kanta bata lura da muta nan dake parlour ba, takowa take tana kallan sultan a hankali ta sauke idanuwan ta a kafar shi dayake ingisawa hawaye suka kara zobo mata da gudu ta karasa ta rungume shi tare da sakin marayan kuka mai tsuma zuciyar mai saurare shafa bayan ta sultan yake yana cewa, cikin muryar shi kamar me rada, "is okey hayaty am here, kuka ya isa haka hayaty, shhh..! yana maganar yana shafa bayan ta Nihal ko tayi lamo tana sauke ajiyar zuciya a hankali ya dago da Nihal dankwali daya gani ta rufe fuska da shi ya kama ze cire rike Hannun shi Nihal tayi hawayan na bin kumatun ta zame hannu ta sultan yayi a hankali ya cire dankwali abinda ya ganine ya sashi shock idanuwan shi suka kara rinewa zuwa ja, yana rike da dankwali yana bin fuskar Nihal da kallo dama ya san haka se ta biyo baya wani marayan kuka Nihal ta saki tana cewa, "love ka ga abinda fuska ta ta zama an kona min fuska" Nihal ta ida zancan tana sakin kuka talabo da fuskar ta sultan yayi yana cewa, "hayaty ki daina zubar min da hawayan ki, I love you for who you're not your beauty" a hankali sultan ya shiga shafa fuskar ta hada baki su yayi waje daya yana kissing Nihal tamkar ba gaban mutane suke ba, Nazili kuwa kamar ta hadiye zuciya ta mutu tana kallan sultan dake shafa fuskar Nihal yana kissing nata kota ko ina yana cewa, "ina san ki mata na komi kika zama ina tare dake Nihal..! Sultan ya ida zancan yana taloba da fuskar ta daukar Nihal yayi cak Ammi ce kad'ai ta samu damar magana saboda kowa bakin shi ya mutu mudus tace, "sultan..! kunya ce ta lullube Nihal lokaci daya tamkar ta bare kasa ta shige, gogan nata kuwa ko a jikin shi yace, "babu abinda za'a fada min na bar matata amana na dawo na iske ta ba yarda na bar ta, sannan kuke tunanin zan saurare ku never," maimartaba dake yunkurin yin magana waziri ya mashi alama yayi shuru kallan Gimbiya jalila Sultan yayi ya aika mata da mugun kallo ya fice da Nihal. part din su ya wuce da ita yana shiga saman bed ya sauke Nihal se bin shi take da ido ga kunya data baibaye ta, drewar sultan ya bud'e ya ciro zuma ya juye a cikin dan boll yayi addu'a ya shiga shafa ma Nihal a fuskar ta se da ya shafa mata a ko ina yana kokarin mikewa Nihal ta rika Hannun shi tace, "love mi ya sami kafar ka,? "hayaty bigewa nayi wajan sauri na dawo gida na ganki" murmushi yake Nihal tayi duk da bata yadda da abinda sultan ya fada ba aje boll din hannu shi yayi saman bedside drewar ya janyo Nihal jikin shi ya rungume yana shafa bayan ta a haka bacci ya dauke ta, zame jiki shi sultan yayi ya kwantar da Nihal tare da kiss forehead din ta, kayan dressing ya dauka ya shige toilet sai daya fara sakarwa kan shi shower yana yin kwankan yana zubar da hawaye masu zafi a haka ya gama wanka yayi ma kafar shi dressing sannan ya shirya cikin fara jallabiya drewar ya bud'e ya ciro bindiga yana jujuya ta ya tura cikin aljihun shi ya fice daga dakin. Gimbiya jalila ce ke zagaye daki ban da tsuma ba abinda take tace, "yakumbo kin ga fuskar yaran nan kuwa wani kallo daya watsamin sai da hantar ciki na ta katsa," Ashad yace, "dama tunda naji shuru na fada maki akwai matsala, hankali na be kwanta ba hakan na nufi ya gane da sahannu mu, ban san da wani ido zan kalle shi ba gobe zan hada kaya na, na barka kasar nan da ba zan zauna ba har Abba ya ji labarin abubuwan dana aikata tare da sa hannu ki momi" Ashad ya ida zancan tare da ficewa part na shi ya shiga ya bud'e drewar ya fara loda kaya cikin trolley maganar data doki dodan kunna shi ce ta sashi dagowa a razane yana kallan sultan "ina zaka je a tsohan daran nan? bakin shi na rawa yace, "uhm, uhm, yaya da yaushe ka dawo? "yau na dawo," "am....! "Zuwa nayi mu sha coffee mun dade bamu gana ba" sultan ya ida zancan yana jan hannu Ashad daya sankare suka fito parlour se zare ido Ashad yake yana hadiye-hadiye sultan ya zauna da shi ya shiga hada masu coffee Ashad na bin shi da ido zuciyar shi na lugude dan bakin shi ya mutu mudus, sugar sultan yasa yana juya coffee ya juyawa Ashad baya idanuwan shi cike da kwalla ya mikawa Ashad cup ba tare da ya bari sun hada ido ba, jikin Ashad na rawa ya amsa yana rike da cup din ya kasa shan coffee din yace, "yaya..! "sha mana ko kana jin tsoro kar na kashe ka ne kanina..! amsar cup din sultan yayi ya shaye coffee din hawaye na bin kuncin shi yace, "Ashad me na tsare maka a duniya? Me kake nema a duniya wanda sai ka kashe ni zaka samu, ko duniya zata taru tana bani labari wani yayi ma dan uwan shi abinda kamin ba zan yarda ba, amma sai gashi dan uwana yamin, ban taba tunanin kiyayar da kake nuna min a idanuwan ka ba takai haka ba Ashad, kayi kokarin kashe ni yafi a kirga me kake nema a duniya wanda har se ka kashe ni" sultan ya ida zancan yana jijiga Ashad hawaye ne suka zabowa Ashad ganin yadda sultan ke kuka yana jijiga shi ya cigaba da cewa, "ina san ka kanina bani da dan uwar sama da kai Ashad, amma kai baka da babban makiyi sama dani, ka riga ka zamar min da uwar rigar kaya na cire ka nayi yawo tsirara na saka ka cutar dani, ka cutar dani yafi a kirgi duk wani farin ciki na kai ke bi kana rusa shi ban taba tunanin haka kake ba, Ashe kai ke bibiyar rayuwata ba kowa ba yanzu kuma ka dawo kan matata wanda nake matukar so zan iya yafe maka komai amma ban da cutar da Nihal, idan har mutuwa tace farin cikin rayuwar ka" bindigar dake ciki aljihun shi sultan ya ciro ya kama hannu Ashad ya daura mashi yace, "ka harbe ni ka huta Ashad ka kashe ni da kanka amma ka fara fadi min laifin dana aikata maka kake aikata min haka sai na nemi yafiyar ka..! jikin Ashad ban da rawa ba abinda yake sai hawaye dake zubo mashi yana kallan bindigar da sultan ya daura mashi a hannu sultan ya cigaba da cewa, "idan baza ka iya kashe ni da bindigar ba ga poising ka samin cikin tea din nan ka duramin shi har se na shanye, tsawan kwana uku zan dauka kafin poising din ya fara aiki kaga ba wanda ze gane kai ka kashe ni, idan har hakan shi ze samama farin cikin har karshan rayuwar ka, na taba cutar da kai ne Ashad? ka fadin min idan na taba, ka jefe rayuwar mutane dawo cikin hadari saboda kana san ganin bayan yayan ka sultan..! kasan mutane nawa ka kashe saboda ni,? I can't still believe cewa my on blood brother do such a thing like that not even in my dream" kuka Ashad ya saki yana cewa, "ya ishe ni haka dan ka gane ina san kashe ka sai me? naji nike yunkuri kashe ka wace rana ko wani yini, kan san dalili..! saboda mi za'a fifita ka a kai na, kan wani dalili komai za ace kai ne, ba a taba cewa ni..! duk wani abu mai kyau na kane ni kuma fa? ba me taba jin sunana na tashi sai na ka, me yasa ba zanyi yunkurin kashe ka ba saboda nima a rinka kiran suna na kamar yarda ake kira ka, hata kanena ka kwace sun zama naka kai kad'ai kakar ta mu ma ta zama taka kai kad'ai sai kace kai kad'ai ne jika sannan ta zaba maka mata mai kyau, ni ban isa auran bane ko ban dace a samamin matar bane? gurin aiki karkashin ka nake aiki bayan karatu daya mukayi kwallin da kake takama da shi nima shi gare ni, kana tunanin duk haka na min dadi se na zuba ido ina kallan ka? ba tare da na nemar wa kai na mafita ba, ko ban kashe ka ba bakin cikin ka ze iya kashe ni to kafin haka ta faru kara na kashe ka..! Ashad ya ida zancan yana kuka sultan ma kuka yake yana cewa, "idan ba'a kira babba a gida ba karamin za'a kira Ashad? wanna dalilin yasa kake so ka kashe dan uwan ka Ashad" Sultan ya ida zancan yana kama hannun Ashad ya daura bindigar a kirjin shi yace, "harbe ni ka huta kashe ni Ashad," kuka Ashad ya saki tare da ture sultan ya fada saman kujera jikin shi na rawa ya koma gefe guda yana kuka rike da bindiga gabaki dayan su kuka suke bame lallashin wani a cikin su Sultan yace, "idan har kashe ni shi ne ze samama duk abubuwan daka fadi Ashad ka kashe ni, amma ka yafe min Ashad bani na kwance maka kanne ba, kai ne baka jan su a jiki gurin aiki bani na hana ka jajircewa ka kai matsayi na ba, bani na hana ka zuwa wajan Ammi ba, kan me yasa zaka zauna kana ganin laifi na Ashad har kana yunkuri kashe ni" sultan ya ida zancan tare da mikewa kafar shi Ashad ya rike yana sakin kuka bakin shi na rawa yace, yaya..! Tsayawa sultan yayi cak yana jin san kanin nashi tunda hannu ka baya rubewa ka yanke, cikin dakewa sultan yace, "Ashad tunda ka rantse sai ka kashe ni zaka samu kwanciyar hankali ka kashe ni, koda wani lokaci ina zaman jiran ka" sultan ya ida zancan tare da ficewa Ashad na kallan shi har ya fice ya bar part din kuka Ashad ya kuma saki. Bangaran sultan part na su ya nufa yana tunanin kalaman da Ashad ya fadi wani abun har da laifin su dama idan har a family za'a nunawa wani launi fata ana iya dasa mashi bakin ciki wani me karamin kwakwalwar har ya aika abinda ba shi bane, Allah ya tsare mana imani mu da wannan tunanin sultan ya janyo Nihal jikin shi ya lumshe ido ba wai dan yana jin baccin ba. Kiran sallah Asuba ne ya tashe su bayan sun idar da sallah Nihal ta koma bacci, ta bar sultan yana lazumi saman prayer mat. Misalin karfe 9:00am Nihal ta tashi a hankali ta sauke idanuwan ta kan sultan dake hada kaya cikin trolley murmushi ya sakar mata, cikin sanyi murya Nihal tace, "love ina zaka je naga kana hada kaya cikin jaka? Nihal ta ida zancan a shagwabe aje rigar Hannun shi sultan yayi ya tako gaban ta yace, "hayaty tafiya zamuyi" "ina zamu? Nihal ta fada tana turo dan karamin baki ta figer din shi sultan yasa yana zagaye lips din ta yace, "yawo ko baki so? da sauri Nihal ta duro daga saman gado tana cewa, "zani mana, dama bana fita kullun ina cikin gida, to amma haka zan bika fuska ta a kone" rungume ta sultan yayi ta baya ya daura kanshi a kafadar ta suna kallan juna ta cikin mirror ba laifi kunar ta dan ragu saboda zumar da sultan ya shafa mata a hankali sultan ya sakar mata pack a kumatu yace, "Ni ke nake so ba cute face din ki ba hayaty, kuma nima baki ga na zama gurguba ki je kiyi wanka saura 30 minutes flight din mu ya tashi" makale kafa Nihal tayi tana cewa, "love ka daina cewa mijina gurgu..! Cikin wata murya mai cike da shagwaba data kara mata kyau cikin rada sultan yace, "ko na maki wankan ne? sultan ya fada yana kashe mata ido zaro ido Nihal tayi tace, "laaa..! ta ture shi ta shige toilet da gudu dariya sultan ya saki yana cewa, "kin manta baki dauki towel ba" ya ida zan yana daukar towel ya karasa bakin toilet din ya mika mata har sai da yayi kokarin fisgo ta Nihal ta sakar mashi kara dariya yayi ya barbaza sumar kan shi ya ida shirya kayan cikin trolley ya fita dan mikawa sinbul. Koda Nihal ta fito daga wanka bata sami sultan a dakin ba sai wata orange gown da ta gani saman bed murmushi Nihal ta saki ta dauki rigar, shafe jikin ta tayi da lotion ta fashe jikin ta turare Masu kamshi sanyi dadi sannan ta saka rigar tana kokarin zuge zip sultan ya shigo lokacin har ya shirya cikin black suit yayi kyau har ya gaji takowa yayi ya zuge mata zip din rigar Nihal na kallan shi ta cikin mirror san shi da kaunar shi na karuwa a zuciyar ta, sannan suka fito. main parlour suka wuce lokacin kowa ya halara ban Ashad da Gimbiya jalila da Nazili maimartaba ne yace, "har kun fito" daga kai sultan yayi yana cewa, "Eh..! "Amma zakuyi break kafin ku wuce" "A'a ba se munyi break ba idan mun isa za muyi ko a cikin jirgi ne saboda flight din ya kusa tashi" sultan ya ida zancan yana kallan Nihal da kunya duk ta rufe ta dan tun abinda ya faru jiya bata daina jin kunyar su mom ba rungume ta mom tayi tare da turo mata wani abu cikin jaka tace, "ki kula min da kanki nasa maki wata ajiya cikin jaka idan kun isa zan kira ki nayi maki bayani" "toh mom" pack Ammi ta sakar ma Nihal tace, "Allah ya kara maki lafiya ya kai ku lafiya ya maido ku lafiya, sultan ka kula da Nihal" murmushi sultan ya saki yace, "Ammi karki damu zan kula da ita" haka suka rako su compound bandil din 1k sultan ya ciro daga mota ya mikawa sinbul yace, "wani bako ze zo nemana mudi idan ya zo ka dauki kudin nan ka bashi" "toh" sinbul yace Nihal data ji an ce mudi sai da gaban ta ya fadi a hankali ta maimaita mudi cikin zuciyar ta sannan suka shige mota driver ya ja su zuwa airport. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/25, 4:16 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_wannan shafin naki ne kyauta daddy's mom kiyi yadda kike so da shi na gode da kaunar da kike nuna min ni da littafin na da duk wani me bibbiyar wannan littafi ina kaunar ku Allah ya bar kauna_* *Page: 117_118* Bayan sun shiga jirgi sun zauna Nihal sai raraba ido take kasancewa bata taba shiga jirgi ba, kuma hakan be hana ta gane first class suka shiga ba sultan sai kallan ta yake saboda komai Nihal tayi kara birge shi take, murmushi Nihal ta saki me cike da kunya musanman yarda take kauyanci announcing din daura sit belt aka fara sultan da kanshi ya daura mata belt sannan ya daura wa kan shi sannan aka fara announcing jirgi ze ta shi jin yadda jirgi yake kokarin tashi Nihal dake zaune jin take kamar yan hanjin ta zasu fito ya sata saki ihu ta kankame sultan ta rintse ido, dariya sultan ya saki yana magana kamar me rada yace, "yau fa yar kauye ta shigo jirgi" dagowa Nihal tayi daga saman fafadan kirjin shi tana bin yan cikin jirgin da kallo ganin ba me kallan ta ya sata sauke ajiyar zuciya ta bala ma sultan harara tana cewa, "baka ji yarda yan hanji na ke jijigawa bane da yan ciki na hata kai na sai daya jijiga dama haka jirgin yake" dariya sultan ya saki mara sauti ya kara janyo ta jikin shi yana cewa, "dan baki saba bane hayaty" ita dai Nihal lamo tayi a fafadan kirjin shi, a haka jirgin ya tashi zuwa *ENGLAND* Misalin karfe 4:00pm jirgi su ya sauka England a babban birni *MANCHETER* Nihal na makale da sultan suka fito daga cikin jirgi Hannun shi daya na jaye da trolley motocin dake fake a gefe suka nufa Nihal sai mamaki take wato shi sultan har a kasar waje me kudi ne, security din dake tsaye sultan ya mikawa trolley din hannu shi ya saka a booth daya kuma ya bude Masu murfi mota sannan driver ya ja su zuwa masauki. A wani hadad'an gida suka nufa da motocin iya kar haduwa gidan ya hadu geta man ne ya bude masu geta aka shige da motocin, gidan sama da kasa ne kasancewar snow ake compound din gidan duk kankara lallacewa Nihal tayi tana kallan ikwan Allah ko a mafarki bata taba tunanin zata keta hazo ba, bare har akai da ta zo wannan gida mai kyau yau sai gata ga snow kamar a cikin mafarki ko a film, kama hannu ta da sultan yayi ne yasa Nihal juyowa tana kallan shi murmushi ya sakar mata yace, "muje ko" sake da baki Nihal ta bi sultan suka shiga cikin gida a tsakiyar parlour Nihal ta tsaya tana bin parlour da kallo parlour ba karamin haduwa yayi ba komai na cikin parlour sky blue and white, hakan sai ya karawa parlour kyau jikin bango Nihal ta sauke idanuwan ta tangameman hotan sultan ne manne yana sanye cikin suit din shi ya saki murmushi har dimple din shi ya loma, gefe kuma na duka yan gidan su kara juyawa Nihal tayi ta sauke idanuwan ta saman hotan da suka dauka da bikin su Ammar murmushi Nihal ta saki ta dago tana kallan sultan dake hayewa stairs jaye da trolley tace, "love da yaushe wannan hotan ya zo nan? dan tsayawa sultan yayi yace, "tun san da akayi shi" "uhm yayi kyau sosai gidan nan yana da kyau love, dubi yadda nake ganin abubuwa kamar a cikin dream" dawowa gaban ta sultan yayi yana mata cakulkuli har ta fada kujera ya bita tana dariya hada kan su yayi guri guda yana cewa, "yanzu kin gane ba dream kike ba" murmushi Nihal ta saki tana bin sultan da kallo tana shafa gefan fuskar shi, daukar ta yayi cak Nihal na mashi magana tana cewa, "love kafar ka ba lafiya amma kana dauka na so kake na fama ma ciwan kafar ka" "Bazaki fama min ba ai baki da nauyi" zagaye hannu ta Nihal tayi a wuyan sultan tana ta zuba mashi surutu yana cewa eh a'a a haka ya haye sama da ita bedroom ya nufa da ita, suna shiga bedroom din Nihal ta kara sankarewa tana kallan dakin saboda haduwar shi har sultan ya shifide ta saman tangameman gadan dakin Nihal na bin dakin da kallo sultan na kokarin mikewa Nihal ta ruko hannun shi cike da kauyanci da santin gidan tace, "A gaskiya gidan nan yana da kyau ban taba tunanin zan zo irin wannan gidan ba ko a mafarki ba sai gashi yau na zo," Nihal ta ida zancan idanuwan ta cike ta kwalla ta cigaba da cewa, "akwai abinda nake so na fada maka wanda na dade ina boye maka game dani tsawan lokaci, yanzu lokaci yayi daya kamata kasan ko ni wacece tunda muna san juna mu yanzu a ganina babu wani boye-boye a tsakanimu bana so kaji labari daga baya kayi fushi dani" tsayawa Nihal tayi tana kallan sultan daya tsare ta da sexy eye's ball din shi yana kallan ta maida gashin kanta baya Nihal tayi ta kama hannu sultan tace, "A gaskiya ni ba almajira bace gudowa nayi daga kauyan mun saboda..! Daura finger din shi sultan yayi saman lips din ta yace, "Shhh..! duk abinda zaki fadi min na sani hayaty guduwar ki alheri ce da baki gudu ba da ban san wace rayuwa zaki tsinci kanki ba, sana diyar guduwar ki tasa kin had'e da mai kaunar ki wanda ze baki kulawa har karshan rayuwar shi zan sama maki SAUYIN RAYUWA daga nan har bayan rai na bana so kina tuna abubuwan da zasu daga maki hankali" a hankali yasa hannu yana goge mata hawayan idanuwan ta murmushi Nihal ta saki tana makale da hannu sultan tace, "nima bada san rai na nayi maku karya ba, nayi ne saboda gudun abinda ze je ya dawo, amma ya akayi kasan ko ni wacece? "Hayaty muje mu rama salolin dake kan mu kin ga duhu nayi" "ya kamata ka fadi min," "zan fada maki amma ba yanzu ba, na fara jin yunwa" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "wayau kake so ka min" a haka suka shige toilet suka dauro alwala sannan suka fito sultan ya ja su sallah bayan sun idar da sallah sultan ya juyo yana facing Nihal yana sakar mata murmushi a hankali ya kama kanta yana mata addu'a knocking din kofar da akeyi ne yasa sultan cewa, "bari naje na dawo na san abincin da nayi ordering ne ya iso," murmushi Nihal ta saki tana bin sultan da kallo har ya fice. ****** Iya kar takaici Nazili ta kwasa har ji take tamkar zuciyar ta zata fito saboda bacin rai yinin ranar ko abinci ta kasa ci tana kwance tana kuka saboda tsabar kuka zazzabi me zafi ya rufe ta, Ammi ta tausaya mata tayi mata tanbaya duniyar nan meke damun ta sai dai tace ba komai, Ammar ta kira ya dubata ya bata magunguna sannan ya tafi da kyar Ammi ta tilas ta mata taci abinci tana ci tana tunani wace hanya zata bulowa Nihal dan ta rabata da sultan. Bangaran Ashad kuwa yinin yau zungur yana daki ya kasa fitowa koda parlour ne jin shi shurun da Gimbiya jalila tayi ne ya sata biyo sawun d'an na ta a daki kwance ta same shi idanuwan shi jawur kallo daya zaka mashi kasan ya sha kuka fuskar shi na dauke da nadama da takaicin abinda ya aikata, cikin kidima Gimbiya jalila ta shiga tanbayar shi lafiya, nan ya kwashe duk abinda ya faru ya fada mata wani irin tsaki Gimbiya jalila ta saki tace, "to sai me dan ya sani shine sai ka zauna kana kuka? ka hana kan ka walwala inda nice a lokacin da yake min maganar zan aika shi lahira zancan banza kai..! I wish ni na samu damar daka samu da sai na aika shi in ya so na fitar da gawar waje," sakin baki Ashad yayi na kallan Gimbiya jalila yace, "Momi dan Allah mu daina wannan maganar ni yanzu na gane kuskure ne duk abinda na aikata nayi danasani yinsu, saboda kalaman da yaya ya fadamin sun sosa min zuciya nayi takaici abinda na dade ina shuka mashi karkashin kasa, inda wanine ba ze nuna min ya sani ba sai dai ya kashe ni, kuma duk abubuwan nan dana mashi ya iya bud'e baki shi yace yana so yana ji na har yanzu a matsayin kani shi, tir da wannan hali nawa da yaya ze kashe ba zan ji komai ba, da duka na yayi ba zan ji zafi ba amma kin san me ke sani jin zafi kalaman da ya fada min suke sosamin zuciya saboda san da yake min dan kar na shiga Hannun hukuma ya watsar da maganar kuma beyi kokarin tona mana asirri gaban kowa ba, ina takaici wannan hali nawa kuma ba kowa ya kara tunzura ni ba sai ke momi, na rukeki mubar wannan abun tunda har asirrin mu ya tonu kuma yaya baya nufin mu da shari, mu godewa Allah ba'a fadda ya falasa maganar nan ba da ba abinda ze hana Abba daukar mumuna hukunci a kan mu, kuma alkawari ya dauka idan kin manta ni ban manta ba kuma kin san hukunci gidan sarauta barin gidan nan ya zamar mana dole ko da ba'a hada mu da hukuma ba an riga da an tsamemu a gida kenan, ina san zama ciki family dina momi, please mu SAUYA RAYUWAR MU..! wani irin kallo Gimbiya jalila ke watsawa Ashad da mamakin SAUYIN RAYUWAR shi lokaci daya Allah kad'ai ya san wace uwar sultan ya fada mashi, takaici ma hana ta magana yayi a fusace ta bar mashi dakin. Bayan mudi ya gama cinikin shi na ranar tsaf ya biya gidan maimartaba kamar yadda sukayi da sultan kasancewa sinbul ya san da zuwan nashi yana zuwa ya dau kudin da sultan ya bashi cas ya mika mashi, haka ya rinka zuba godiya har ya nemi ya ga sultan dan ya kara mashi wata godiyar aka ce mashi be kasar cike da murna ya juyo gida, a cewar shi ze dawo idan sultan ya dawo dan nuna mashi jin dadi kyautar daya mashi. ****** Rike da Leda da plate sultan ya dawo daki lokacin Nihal na zaune saman sofa idanuwan ta lumshe dan ba karamar gajiya tayi ba taso ace sai da ta fara wanka sannan tayi sallah, hura mata iskar bakin shi sultan yayi me sanyi a hankali ta bud'e lumsasun idanuwan ta ta sauke su kan sultan cikin honey voice din shi yace, "bacci? girgiza mashi kai Nihal tayi yace, "gajiya..! daga mashi kai Nihal tayi a shagwaba tace, "jiki na ciwo yake na gaji" "sorry ta so muci abinci kin ji hayaty se ki kwanta ki huta" ya fada yana binta da kallo mai cike da so sakowa kasa Nihal tayi ta zauna ringing din wayar sultan ne ya katse masu tunani mika hannu yayi saman drewar ya dauki wayar suna maimartaba da ya ganine ya sashi sakin murmushi ya dauka ya kara a kunne dauke da sallama daga dayan bangaran maimartaba yace, "kun isa lafiya? "Lafiya lau Abba yanzu haka muna gida da niya ta da mun gama cin abinci na kira ku" "Masha Allah tunda kun isa lafiya, bari na baka mom din ka" Sultan yace mom ce ta amshi wayar tace, "son kun isa lafiya? "Lafiya lau habibty" "Masha Allah bani daughter naji muryar ta tun yau na fara missing nata" "Mom ni fa bakiyi missing nawa ba" "Banyi ba ai kai yanzu ba Dana bane ita ce yata" cikin sigar shagwaba sultan yace, "shikenan mom ni za'a nunawa launi fata, ai na san Abba na tare dani" dariya mom ta saki tace, "mika mata ka cika ni da surutu" mikawa Nihal waya sultan yayi yana cewa, "mom..! Amsar wayar Nihal tayi cike da murna ta kara a kunne suka gaisa da mom tace, " kin ga sakwan dana saka maki cikin jaka girgiza kai Nihal tayi kamar mom na gaban ta tace, "ban duba ba" "OK turarukan wuta ne a ciki har dana wanka akwai wani garin na nan ki sashi da fresh mlik kafin ki kwanta" toh Nihal tace tana yima mom godiya ta datse kiran murmushi Nihal ta saki tana mikawa sultan wayar tace, "mom tace ka siyo min fresh mlik" "Akwai a fresh" "Toh Nihal tace, tana kallan sultan cikin plate ya juye checken and chips wraps gefe guda kuma fresh orange juice ne, janyo Nihal jikin shi sultan yayi yana feeding nata yana feeding kan shi, shagwabe fuska Nihal tayi tace "Na koshi" "hayaty baki ci da yawa ba ki dan kara kadan mana" turo dan karamin bakin ta Nihal tayi tace, "na koshi so kake ciki na ya fashe," dariya sultan ya saki yana cewa, "cikin ki ba ze fashe ba" sultan ya ida zancan yana bata fresh orange juice da kyar Nihal ta amsa ta sha dan wani irin bacci take ji mikewa sultan yayi yace, bani 5 minutes na hada maki ruwan wanka daga mashi kai Nihal tayi idanuwan ta a lumshe, toilet sultan ya shige, da kan shi ya had'ewa Nihal ruwan wanka be wani dau lokaci ba ya fito dakin lokaci har bacci ya fara kokarin dauke Nihal yace, "hayaty tashi ki je kiyi wanka na hada maki ruwan" daga kai Nihal tayi sannan sultan ya tatare plate din da suka ci abinci ya fita Nihal ta shige toilet ta dade tana wanka sannan ta fito daure da towel d'aya kuma ta nad'e kanta da shi, koda ta fito lokacin sultan baya dakin rigar bacci ta gani saman gado murmushi ta saki, shafe jikin ta tayi da lotion sannan ta bude handbag din ta sakwan da mom ta aje mata ta gani turarukane kala-kala Masu kamshi shafe jikin tayi da turare ta ko ina sannan ta bude karamin frigde din dake dakin ta dauki cup ta hada garin da fresh milk ta shanye har da lashe baki Nihal tayi tace, "da dadi fa wallahi ko minene" juyowa Nihal tayi ta dauki rigar dake saman gado daga rigar tayi zaro ido tayi tace, "love ya za'ayi na iya sa wannan rigar duk ta barke ita da babu duk daya" wurga ta saman gado tayi ta zauna zaman jiran sultan dan baza ta iya sa rigar ba, jin shuru sultan be shigo ba yasa Nihal daukar rigar tana juyawa gani akwai yar sama ya sata sakin a jiyar zuciya tace, yanzu naji magana" a hankali ta saka ta farko tana kokarin sa yar saman sultan ya turo kofar dakin, zaman yan burin Nihal tayi tana kallan sultan dake sanye cikin dark blue sleeping robe din shi binta yake da wani irin kallo a hankali ya sauke idanuwan shi saman mulamulallun jajayen cinyoyin ta ya kara sauke ido kan na fulanin ta a hankali sultan ya tako gaban ta ya dago da Nihal da idanuwan ta ke rintse yana bin fuskar ta da kallo kamar me neman wani abu ga wani kamshi ta daya mamaye mashi hanci lokaci daya Nihal ta riki ta shi yar saman ya dauka ya saka mata yana shinshi na wuyan ta cikin salo a hankali ya furta "hayaty..! A hankali Nihal ta bude lumsasun idanuwan ta ta sauke su kan sultan gabaki daya jikin ta ban da rawa ba abinda yake, ko kafar ta da kyar take daukar gangar jikin ta, daukar ta yayi cak har a lokacin Nihal na bin shi da ido ga wani irin yanayi da take jin kanta sauke ta yayi saman bed shi kan shi sultan wani bakwan yanayi yake ji hada bakin su waje daya sultan yayi yana kissing Nihal kissing din juna suke without second thought, with an immerge feeling da dukan su suke da shi, a hankali sultan ya lallubo haskyan dakin ya gashe (Ni dana ke makale ina daukar rahoto sulalewa nayi na fice)🤪 ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [1/27, 9:01 AM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_masoya SAUYIN RAYUWA ina mai baku hakuri da rashin ganin posting dina jiya am to busy shiyasa, sannan gobe bazan samu damar typing ba saboda azumin da nake Monday and Thursday_* *Page: 119_120* Nihal dai ta jiga ta saboda sultan bana wasa bane, ya rungume ta yana lallashin ta ita kuwa sai kuka take mashi, yana sa mata albarka rike masa amanar kanta da tayi. Daukar ta yayi cak ya kaita toilet ya sata ciki ruwan mai zafi, ya da dawo daki ya dauke bedsheets din kan gadan yasa wani bayan Nihal taji dadin jikin ta ne sultan ya dauko ta ya dawo da ita daki ya aje ta saman bed, har a lokacin Nihal na kuka shagwaba har wani cewa take saboda haka ya kawo ta, wata kasa yarda ba wanda ze kawo mata dauki, sultan kuwa ya zage sai ban baki yake yana wani riritata kamar jariraya yana tarairayarta ya rungume ta yana cewa, "hayaty kin sa zuciya ta nishadin da farin cikin wanda ba zan iya fadar su duka ba, saboda ba zai kwatantu ba, Allah yayi maki albarka yasa ki gama da duniya lafiya" Nihal kuwa tayi luf a fafadan kirjin sultan tana jin dadi kalaman sa, haka sultan ya cigaba da riritata tamkar ya maida ta cikin sa saboda tsabar so da tatali yana kara aika mata da wasu sabin salan nashi masu rikitata, Nihal da ta fahimci inda sultan ya dosa narai-narai tayi da ido tace, "love kayi hakuri karka kashe ni, ka bari na warke" shiko sultan be ma san tanayi ba cikin wata kasalaliyar murya shi yace, "kiyi hakuri hayaty, ba zan iya kyale ki ba, kuma duk wanda kika gani a gidan ta da haka ta fara kuma bata mutu ba, ki barni na samu natsuwa a tare dake ki taimaka please" sultan ya ida zancan cikin sigar tausayi. Duk da zafin da Nihal ta ke ji ta danne ta hakura ta jure haka sultan yayi kidan shi yayi rawar shi sai da Asuba ya saurara mata shi kan shi ya tausaya mata, da kansa ya kuma hada mata ruwan zafi da dettlo ya sata a kwamin wanka ya fice luf Nihal tayi har wani dan bacci ta fara yi, saboda dadin ruwan zafin, dawowa toilet sultan yayi ya taimaka mata tayi wanka sannan yayi mata na sabulu tayi alwala suka fito a tare ya jasu sallah da kyar Nihal ta iya yin sallah saboda duk jikin ta ciwo ya keyi mata, bayan sun idar da sallah sultan ya juyo yana sakar mata murmushi mai sanyi ya jawota jikin shi yana cewa, "am sorry hayaty, na wahalar da ke ko? ita dai Nihal a tsorace take da sultan dan kar ya kuma, dan ja mata hanci sultan yayi yace, "tsoro na kike ma ji ko hayaty? am sorry ba karawa zanyi ba naga duk kin firgice tausayin ki nake ji hayaty, jiya dai an sha kuka..! sultan ya fada cikin sigar tsokana cikin jin kunya Nihal ta kawo wa sultan duka a kirji ya goce yana mata dariya daukar ta yayi ya shinfid'e saman bed tare da janyo ta jikin shi yana cewa, "ayi min a fuwa hayaty na kasa control din kai nane har sai dana mance wace duniya nake, Allah na gode maka daka bani Nihal a matsayin matata hakika ke ce sirrin na abin alfahari na, hayaty ki daure ki so ni ko kwanta wanda nake maki ne please" "Love kenan naka san kawai ka sani nima ina kaunar ka, bani da wanda nake so a rayuwa ta bayan kai, kai ne gata na kai ne iyaye, bani da kowa sai kai" Nihal ta ida zancan tana kara shigewa jikin sultan sauke ajiyar zuciya sultan yayi yace, "Alhamdulillah..! a hankali ya sakar ma Nihal kiss a forehead din ta yana shafa bayan ta har bacci ya dauke su. Sai da gari yayi haske sannan Nihal ta tashi a hankali ta sauke idanuwan ta saman agogan dake manne jikin bangwan dakin kusan karfe 10:30am koda ta tashi bata sami sultan a dakin ba, gyara dakin tayi tsaf sannan ta shige toilet ta watsa ruwa tayi brush ta fito, sanye da dan karamin towel ta shafe jikin ta da lotion tabi jikin da turare masu kamshi da sanyi dadi, drewar ta bude dan ciro kayan da zata saka ta sauke idanuwan ta saman blue shirt din sultan daya aje a hankali ta kai hannu ta taba murmushi ta saki sannan ta dau rigar ta saka tare da nanad'e gashin kanta kamar ganmo ta gaba ya dan zubo kamar taliya rigar kuwa ko gwiwa bata kai mata ba, hakan sai ya bayana santala-santalan kafafuwan ta da cinyar ta duk da ba wata kwalliya tayi ba tayi masifar kyau kuma kunar fuskar ta ta ragu nesa ba kusa ba, fitowa Nihal tayi daga bedroom a hankali take taka stairs komai na jikin ta na amsawa cikin siririyar murya ta mai dadi ta shiga cewa "love..! Love..! Sultan dake cikin kitchen yace, "Na'am hayaty..! ya ida zancan tare da fitowa hannu rike da abin tsame dankalin murmushi ya saki yana kallan ta tun daga kasa har sama a hankali ya karaso ya zagane hannuwan shi a waist din ta ita kuma ta zagaye hannuwan ta a wuyan shi, cikin muryar ta mai dadi tace, "morning love" light kiss sultan ya sakar mata a lips yace, "morning hayaty rigar nan ta maki kyau" fari da ido Nihal tayi tana sakin murmushi, tana wasa da bottle din rigar sultan sun tsare juna da ido kaurin da Nihal fara ji ne ya sata cewa, "love me ke kauri? baka ji wani kauri ba" "Ah na manta breakfast din mu kan wuta gabaki daya kin rikita ni har zan bar abinci ya kone," dariya Nihal take tana cewa, "ba ruwa na..! a tare suka shiga kitchen, dankalin da sultan ya daura kuwa ya kone sai da ya daura wani kusan a tare sukayi aikin kitchen din duk da sultan na hana Nihal yana cewa bata da lafiya, bayan sun kamala a tare suka fito suna jerawa a dining bayan sun gama jerawa sultan ya daura Nihal a cinyar shi yana feeding nata abinci itama tana feeding nashi. Bayan sun gama cin abinci sultan na zaune saman kujera kan Nihal na bisa cinyar shi yana wasa da gashin kanta suna kallo yace, "hayaty ki shirya mu fita waje ki ga gari," mikewa zaune Nihal tayi tace, "da fuska ta a kone zamu fita, so kake a maka dariya" bata fuska sultan yayi kamar be taba dariya ba yace, "hayaty bana san irin haka ni na gani na ce ina so ba ruwan wani dani," ya ida zancan yana kara had'e rai ganin haka yasa jikin Nihal yin sanyi ta shiga bashi hakuri har da yar kwallan ta ganin haka yasa sultan hakuri yayi kissing goshin ta yace, "kar ta kuma ce ma fuskar shi konana," a tare suka mike dan su shirya bedroom Nihal ta wuce ta shirya cikin jean and black shirt ta kama jikin ta sosai tayi kyau sannan ta saka boot black tare da daukar brow suwaita ta daura saman kayan ta sannan ta yafa white veil ba karamin kyau Nihal ta zubaba sannan ta feshe jikin da turare, turo kofar da akayi ne ya sata juyowa sultan ne ya shigo cikin jean and white t-shirt sai black suwaita dake jikin shi murmushi ya sakar ma Nihal har dimple din shi na lomawa yace, "muje ko..! a tare suka fice daga gidan sai da suka fara biyawa babban asibitin fata suka ga doctor yayi masu bayani cewa kunar bata shiga fatar ta ba sana ya basu magani sha dana shafawa, daga nan wuraran shakatawa suka nufa Nihal sai mud'e ido take tana kallan gari suna ta picture's, wajan hauwa doki suka je da sultan ya daura Nihal a gaba yana bayan ta, sai dariya take faranran hakoran ta na bayana duk wani motsin ta na kan idanuwan sultan yana zuba mata soyayya, sakin linzamin dokin sultan yayi rintse ido Nihal tayi a tsorace tare da sakin kara, dariya sultan ya saki ya kankame ta, juyo da ita yayi suna facing juna murguda mashi baki Nihal tayi, a haka suka gama wasa da doki, sannan suka sauko wajan wasa da kankara suka je sosai sultan ke wasan cikin kwarewa Nihal na mashi video tana murmushi, wucewa sultan ya zoyi da gangan ya saki abin wasan ya fadawa Nihal sukayi kasa gabaki daya yana mata cakulkuli tana dariya da kyar take maida numfashin zamewa tayi daga jikin shi, kankara ta debo tana watsa mashi yana binta da gudu tana dariya tana mashi gwalo, har ya cin mata daga ta sama sultan yayi yana juya ta tana dariya sauke ta yayi suna facing juna hada hanci su sultan yayi suna maida numfashin rungume shi Nihal tayi san mijin ta na karuwa a zuciyar ta rungume ta tsam sultan shi ma yayi, gabaki daya yan su tunanin SAUYIN RAYUWA da suka samu suke, tabas rayuwa ta sauya masu mai cike da so da kauna, da wannan tunanin suka biya restaurant kasancewar dare ya fara yi a plate daya aka zubo masu abincin carrot rice and stew with cabbage and tomatoes and fresh juice, Nihal ce ke feeding sultan yana ci bud'e baki yayi kauda spoon din Nihal tayi ta kai bakin ta tana mashi gwalo, dariya sultan yayi har dimple din shi na lomawa yana cewa, "zan rama..! kara debo abincin tayi ta kai mashi baki janye spoon din tayi tana dariya tayi sama da spoon din da sauri ta tura spoon din bakin ta, batayi auni ba taji baki sultan cikin nata zaro ido tayi tana kwada mashi akwai mutane, amma ko a jikin shi sai dan kan shi ya sake ta yana ja mata hanci dukan kirjin shi Nihal tayi cike da shagwaba ta kwantar da kanta tana murmushi welter sultan ya kira ya bashi kudin abincin suka bar wajan, sun zagaye gari sosai sunyi pictures. A gajiye likis suka dawo gida Sultan na dauke da Nihal tana ta zuba mashi shagwaba bata gaji da yawo ba, a haka ya haye sama da ita ba dakin da suka kwana jiya ya kai ta ba, wani daki ya nufa da ita dakin ya sha gyara da red flowers yayi kyau har ya gaji bangwan dakin duk picture's din sune, sakin baki Nihal tayi tana kallan sultan dake kallan ta, tama kasa cewa komai tana kallan dakin cike da surprise, rungume ta tabaya sultan yayi a hankali ya furta, "I love you hayaty" ya ida zancan yana juyo da ita suna facing juna a hankali ya zame veil din dake kanta Nihal ko bakin ta ya mutu mudus, saboda mamaki da irin gata da tattali da sultan ke nuna mata matsar da gashin ta gefe sultan yayi yana shinshina wuyan ta a haka ya samu nasara cire mata suwaitar jikin ta, a hankali ya shiga cire mata bottle din rigar ta lumshe ido Nihal tayi daukar ta sultan yayi idanuwan Nihal na lumshe tana shakar dadad'an kamshi turaran jikin shi jin ta cikin ruwan dimi ne ya sata bude lumsasun idanuwan tana kallan sultan dake mata murmushi yana watsa mata ruwan a jiki dariya Nihal take itama tana watsa mashi, a takaice a tare sukayi wanka kunya kuwa duk ta rufe Nihal ko ido ta kasa bud'ewa, sannan suka fito sanye da bethrobe sultan na dauke da ita da kan shi ya shafa mata magani kunar a fuska tana bin shi dana mujiya har ya gama yayi drying gashin kanta, sannan yasa mata night dress pink rigar dai-dai gwiwa ya mika mata magani da ruwa ta sha, sannan shima ya shirya cikin white sleeping robe din shi ya sungume ta ya shinfid'e saman gado tare da janyo ta jikin shi suna jin bugun zuciyar juna su. Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru ciki har da farwarewar da fuskar Nihal tayi ta murje ta kara fresh sultan ma kafar shi ta warke, tsakanin sultan da Nihal ba'a magana saboda tsantsar shakuwa da soyayya da suke zubawa juna su kowa burin shi ya faranta ma dan uwan shi, suna waya da muta nan gida sosai Ammar kuwa ya kira sultan ya mashi tsiya har cewa yake dare yabi yabi duhu ya dauke Nihal ya gudu to ya kamata ya dawo aiki nan na zaman jiran shi, soyayyar ta isa haka sai dai sultan yayi dariya yace ai shi yanzu ya bar naija yana nan tare da hayaty aje aikin shi zeyi ya dawo nan kasar da aiki, inda ba yan sa ido kamar su Ammar dariya Ammar yayi yace, "sai na biyo ka, me a cikin kullun sukayi waya sai Ammar ya mashi tsiya wani lokacin har yace basabanba, Nihal kuwa na waya da Basmal sosai suna kara shakuwa dan yanzu haka Basmal nada dan karamin ciki wata 3, Ammi ma na kiran su, su dade suna fira da ita a waya. Yauma kamar kullun Nihal na kitchen tana soya miya tana sanye da yar karamar riga ko cibiyar ta bata rufe ba white sai wani zare data daure rigar da shi, tana sanye da wando ko gwiwa bai kai mata light brown, tayi parking gashin kanta tayi wani irin kyau har wata yar kiba ta dan kara, kallo daya zaka mata kasan tana cikin kwanciyar hankali da kulawa aikin ta kawai take, sultan na bedroom yana bacci shine ta lallabo dan ta daura masu wani abu. Hannu ta ji an shafi cibiyar ta a razane Nihal ta juyo ganin sultan ya sata murmushi ta cigaba da aikin ta tana murmushi, "sannu da aiki hayaty shine baki tashe ni ba na taya ki, bana so kina aiki dayawa," yana maganar yana shinshinar wuyan ta Nihal tace, "yauwa love naga baccin yama dadi ne shiyasa ban tashe ka ba na barka ka samu bacci," "idan na hana ki na dare fa..! aje spoon din hannu ta Nihal tayi ta juyo tana facing sultan ta langwabe kai ta zagaye hannuwan ta a wuyan shi tace, "Na san love baze hanani bacci ba ni da kai na zan sa kayi bacci," murmushi yayi, ya manna bakin shi saman lips din ta wannan dabi'a ce ta sultan ya riga ya sabawa Nihal da shi, tun tana jurewa da irin sakwanin da sultan yake aika mata har ta nemi zubewa kissing nata kawai yake talabo ta sultan yayi yana magana can kasan makoshi me cike da kasala yace, "zo muje daki ki ga wani abu" zamewa Nihal tayi daga jikin sultan tana cewa, "miya ta zata kone" murmushi sultan ya saki yana cewa, "Na lura baki so mu koma gida da tsaraba" sultan ya ida zancan yana dauke mata abinda ta bata yana kai mata zing yana wankewa, dariya Nihal tayi tana cigaba da juya miyar ta kunsan tare sukayi aikin kitchen din a tare suka fito suka jera komai a dining sannan suka wuce bedroom a tare sukayi wanka suka fito sultan na dauke da ita shi ya shirya ta da kan shi cikin wata yellow gown tayi kyau sosai itama da kanta ta fido mashi kayan da ze saka, jean and red t-shirt yayi kyau da shi ya kara samun natsuwa sannan suka wuce dining. Suna cin abinci sultan yace, "hayaty gobe zamu je Moscow duba Alex jiya doctor ke fadi min an fito da shi daga como ina so muje mu duba shi" murmushi Nihal tayi tace, "Allah ya kai mu.. ```Taku har kullun salma mas'ud Nadabo```[1/31, 9:12 AM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 121_122* Washe gari da safe shiryawa sultan yayi cikin ash suit din shi yayi wani irin kyau har ya gaji Nihal na sanye da after dress sai black suwaita kasancewar garin an tashi da snow, trolley sultan ya janyo Nihal na makale a gefan shi suka fito, security ya mikawa trolley yasa cikin booth sannan suka shige mota driver ya ja kaitsaye airport ya wuce da su. Bayan sun shiga jirgi suna makale da juna murmushi sultan ya sakar mata yace, "hayaty...! Lamo Nihal tayi a kirjin shi tana cewa, "uhm love..! "this time around baza ayi mana ihu ba" ya fada yana kashe mata ido dariya Nihal ta saki tana jama Sultan kumatu tace, "yanzu na saba" ta fada tana kara shigewa jikin shi murmushi yayi tare da daukar newspaper yana karantawa jirgi ya tashi zuwa MOSCOW. Misalin karfe 3:00pm jirgin su ya isa Moscow kasancewa Mr president ya san da zuwan su yasa aka tarbe su a airport, murmushi herry yake ta saki daga nesa ganin sultan, har sultan ya karaso ya mika mashi hannu sukayi hugging din juna kallan Nihal yake da surprise saboda be san sultan yayi aure ba murmushi sultan ya saki yace, "my wife..! washe baki herry yayi yana cewa, "oh godness when have you got married sultan" smile sultan yayi yace, "long story" murmushi herry ya kuma saki yace, "hey Mrs sultan..! Nice to meet you Sultana" Nihal dake gefe tace, "Nice to meet you to" sannan suka shige mota kaitsaye asibiti suka wuce dan sultan ya matsu ya ga Alex. Dakin da aka kwantar da Alex herry ya gwadawa sultan da murmushi sultan ya murd'a handle din kofar hannu shi daya na makale dana Nihal, Alex dake zaune saman gado jingine hannu shi daya na daure, daya hannu shi na rike da Qur'ani yana kara bita karatun da aka koya mashi, murmushi ya saki yace, "sultan..! tare da aje Qur'ani sama bedside drewar da sauri sultan ya karasa wajan shi ya kai mashi hug yana cewa, "I miss you dude ya jiki? jiya na samun labari ka fito daga como" "kwana na biyu da fitowa jin kana tare da Gimbiya ne, na hana a fadama ka, amma na kira Ammar na fada mashi yauma ya bar kasar nan muna tare da shi" murmushi sultan ya saki Nihal dake gefe tace, "ya jiki..! "da sauki ran ki ya dade..! zama Nihal tayi saman kujera sultan na saman gado yana cewa, "wannan jinyar haske ta karama Alex har wata kiba kayi" Sultan ya fada cikin sigar zolaya dariya Alex yayi yana cewa, "ba dole nake yin haske ba tunda na bar duhu na dawo haske, Allah na gode maka daka ganar dani, ban fada maka ba, na zancan suna yanzu na tashi daga Alex na koma Ahmad" "oh my godness am happy to her that Alex oh Ahmad..! Lalai Allah abin godiya ne Allah yasa mu cika da imani" "Amin..! murmushi Sultan ya saki yana nuna jin dadin shi yace, "Amma na ji dadi sosai da SAUYIN RAYUWA daka samu Ahmad, har wani gemun sunna ka aje kana ta karatu, na lura sai ma ka fimu zama malami" dariya Ahmad ya saki yana cewa, "No.! No..! ina ni ina kama kafar ku, am just trying naga na iya karatun da Ammar ya koya min" murmushi sultan ya saki nurse ce ta shigo rike da tray din abinci Sultan ya mike ya amsa yana cewa, "yau ni zanyi feeding dude tunda na zo" murmushi Ahmad ya saki da kan shi sultan ya taimakawa Ahmad ya ci abinci Nihal na gefe tana kallan su shi dai sultan yana da hali mai kyau sai ka zauna da shi zaka gane hakan ko yarda yakeyi da friends na shi ze nuna maka mutumin kirki ne, bayan ya gama bashi abincin ya aje tray din yace, "Ahmad bari mu je masaukin mu ko can bamu je ba daga airport direct nan muka zo" "Eyya sultan ka bar Gimbiya da yunwa ko abinci baku tsaya kun ci ba kun huta," "bana iyawa kullun da tunanin ka nake kwana shiyasa ina jin labari na taho" "Na gode da kulawar da kake nuna" harara sultan ya bala mashi yace, "bana san haka kuma ka sani, after all wannan abun daya faru saboda dani ya faru" "OK, ok naji bazan kara ba ni da kai ai duk daya ne, kai ma bana so kana fadin, saboda kai something like that..! na matsu na warke na dawo Nigeria jina nake duk a takure" "Sai ka warware sosai zaka koma" sultan ya fada yana cewa, "hayaty muje ko" mikewa Nihal tayi Ahmad ya bisu da ido ba wace ta fado mashi a rai sai Nazili sanda ya dauke ta garden iska mai zafi ya furzar ya lumshe ido zuciyar shi na wasu tunane-tunane. Gidan Mr president suka sauka part na musanman aka basu cikin gidan 2 bedroom da parlour sannan Mr president yace idan sun gama abinda suke so fito ayi dinner da su, to kawai sultan yace matar Mr president sai yaba kyan Nihal take har tana cewa sultan be kyau taba da bai fada masu yayi aure ba ashe ma ya dade da yin aure hakuri kawai sultan ya basu sannan suka wuce masaukin su. Nihal ce tsaye gaban dressing mirror tana kokarin cire dan kunna dake kunna ta rungume ta sultan yayi tabaya yace, "hayaty..! cikin honey voice din shi yana kallan ta ta cikin mirror murmushi Nihal ta saki tana cewa, "kallan fa? na canza maka ne love,? kumatun Nihal sultan ya ja yana cewa, "bana gajiya da kallan ki hayaty, kullun burin na be wuce na jini makale dake ba kina shayar dani soyayyar ki da kaunar ki" murmushi Nihal ta saki ta juyo suna facing juna hannu tasa tana cire mashi necktie tana cewa, "shiyasa nafi kowa ce mace sa'ar miji, Allah ya barmu tare love" "Amin..! sultan yace tare da sakar mata light kiss a goshi Knocking din kofar da akayi ne yasa sultan zamewa daga jikin Nihal ya karasa bakin kofa Nani ce rike da wasu kaya a hannu ta, amsa sultan yayi ya shigo da su lokacin har Nihal ta shige toilet kara ruwa ne ya tabatarwa sultan wanka take murmushi ya saki tare da ficewa. Koda Nihal ta fito daga toilet bata sami sultan a dakin ba murmushi ta saki ganin kayan dake saman bed wata dark blue gwon daga rigar Nihal tayi tana jona ta a jikin ta a fili tace, "love baya gajiya da yimin hidima, dubi rigar nan me kyau..! shiryawa tayi cikin dark blue rigar tayi mata masifar kyau rigar ta fito da shape din ta sosai daga kasa an tsaga rigar, zaunawa Nihal tayi ta tsantsara make up bakin ta yasha maroon jan baki sai shining yake gashin ta tatare ta maida shi gafe ta saka sarkar ta mai tsadar gaske wanda akayi da zala diamond, ita kan ta Nihal data kalli kanta a mirror ta sheda kyan data zuba, murda kofar da akayi ne yasa Nihal juyowa karfa suka hada ido da sultan, yana shirye cikin Ash suit din shi ta kama jikin shi yayi kyau har ya gaji sajan shi ya kwanta luf-luf cike da kallan so sultan ke bin Nihal da kallo dan ba karamin kyau ta zuba mashi ba, a hankali ya tako yana kara bin ta da fitinan kallan shi mai kashe mata jiki murmushi kawai Nihal ke saki tayi kasa da kanta, cikin murya shi me dadin saurare sultan yace, "wow hayaty kinyi kyau sosai" "Na gode love kai ma kayi kyau sosai" murmushi sultan ya saki tare ciro wayar shi yana daukar su hoto ringing din wayar shine ya katse mashi tunani ganin suna Mr president, "oh har an fara kira na muje hayaty" kallan Nihal sultan yayi lokaci daya kishi ya rufe shi yama za'ayi Nihal ta fita haka suyi dinner haka kawai turawa su gane mashi mata idan ko haka zata fita kara a fasa dinner, trolley ya bude Nihal dai bin shi da kallo kawai take blue veil ya ciro ya tako gaban ta Nihal dai na bin shi dana mujiya hannu yasa ya nanad'e mata gashin ta yayi ganmo da shi ya yafa mata veil din a kai yayi sannan ya dan ja baya yana kallan ta murmushi ya saki a fili yace, "hakan ya fi" murmushi Nihal ta mashi sannan suka fice a tare. Fadin tsaruwar wajan bata lokaci ne haduwar wajan takai haduwa wani kayatacan dinner Mr president ya hadawa sultan, wanda shi kan shi be san da ita ba acewar shi wannan ce kad'ai gudumuwar da ze bawa sultan tunda yayi aure, manya-manya masu kudi na kasar sun halara da likitoci sultan da Nihal suna nufo wajan dinner wani tartsatsi me kyalkyali ne ya shiga watsowa har abin ya so ya firgita Nihal jawota jikin shi sultan yayi yana saki murmushi yanayin yarda suka shigo wajan sai ya bada salo na daban, mikewa muta nan wajan sukayi suna tafi wajan ya dauka flowers na zubowa su Nihal ta ko ina Nihal kuwa lallacewa tayi tana kallan tsaruwar wajan ko ba'a fada mata ba ta san kudi yayi kuka, kowa da zaka gani a wajan yana makale da matar shi har suka karaso wajan da aka tanadar masu na musanman Sultan sai murmushi yake yana kara makale Nihal a jiki shi Nihal ma haka murmushi take daga sama wani hadadan cake yake saukowa yana ta kyalkyal mamakin duniya kuwa ya ishi Nihal tana kallan ikwan Allah har cake din ya tsaya saitin su wuka Mr president ya mikawa sultan, murmushi sultan yayi ya amsa, kama hannu Nihal yayi suka yanka cake din a hankali ya gutsuro ya bata a baki, itama ta bashi tafi wajan ya dauka raf, raf camera sai haska su take duk inda suka juya camera na biye da su, sai da Mr president yayi jawabi sannan sultan shima yayi tare da nuna godiya shi a kan dinner da Mr president ya hada masu, abokan arzikin da suka halari dinner mikawa Sultan hannu suke da Nihal suna cewa congratulation suna mika masu gift, sannan aka fara cin abincin kid'a mai taushi yana tashi har a lokacin Nihal bata daina amsar kyauta ba tana mikawa security's dake take masu baya suna ajewa, bayan kowa ya gama bada gift din shi, mawaki na musanman ne ya shiga raira waka mai sanyi ta masoya, kowa mikawa matarshi hannu yayi suka shige fili Nihal sai murmushi take tana kallan rawar turawa a kunne sultan ya rada mata, "hayaty ko kema zakiyi rawar..! murmusawa Nihal tayi tace, "love ban iya ba" "zan koya maki..! Girgiza mashi kai Nihal tayi duk yadda Nihal tayi da sultan ya kyale ta amma yaki dole ta mika mashi hannu ta ya kama suka shiga fili suka fara a hankali sultan ya daura hannu shi saman waist din ta ya daura nata saman kafadar shi ya kama daya hannu ta a hankali suka shiga rawar duk abinda sultan yayi Nihal nayi wani irin juya ta sultan yayi cikin salo Nihal ta dawo saman kirjin shi gabaki daya kallo ya koma kan su, kunya kuwa ta rufe Nihal tafi kawai ake masu saboda birge muta ne da salan su ayin ciye-ciye da lashe-lashe taro ya watse cike da murna sannan sultan da Nihal suka wuce masaukin su a gajiye likis koda suka koma sauya kaya sukayi suka bi lafiya gado. Washe gari suna tashi wanka suka sheka Nihal ta shirya cikin light brown gwon ta kama jikin ta tayi kyau sultan kuma ciki light brown shirt da jean dark brown Nihal na sanye da veil brown, lafiyayan breakfast suka farayi daga nan suka wuce asibiti duba Ahmad jikin shi ya warware sosai sun dade asibiti suna fira da sultan har yana cewa gobe za'a cire mashi daurin hannu shi sultan yayi murna da jin haka sai da sukayi sallah la'asar da Ahmad a asibiti sannan Nihal da sultan suka bar asibiti zuwa yawo cikin gari. Duk wanda yayi nasara samun Nihal da sultan a irin wannan yanayin zai fahimci masoya ne masu tsantsar san juna su, haka kuma baza ka taba tunanin sun san wani abu damuwa ba, yanayi yadda iskar wajan ke kadawa da sanyi da yarda ruwan bitch din ke korowa yana dawowa Nihal a kafarta wadda ko takalma babu idanuwan ta a lumshe, sultan na bayan ta ya wani rungume ta tamkar ya maida ta ciki, yana kora orange juice a glass cup, yana bama Nihal chocolate a baki cikin muryar mai dadi Nihal tace, "love..! "uhm hayaty..! "Yanayin wajan nan yamin dadi sosai musanman yadda ruwan nan ke tafiya yana dawowa" "Saboda haka na kawo ki hayaty na san wajan ze birge ki sosai" sultan ya ida zancan yana daura lips din shi saman na Nihal yayi kissing nata tare da zamewa murmushi Nihal ta saki tana shafa gefan fuskar sultan tana bin shi da idanuwan ta masu kashe mashi jiki tace, "love you, i will be always there for you, always remember that..! love" cakulkuli sultan ya shiga yima Nihal har ta fadi kasa tana dariya yana cewa, "I now hayaty I love you more" zamewa Nihal tayi tana dariya ruwan bitch Nihal ta fara watsawa sultan yana dariya rugawa da gudu Nihal tayi, zagaye wajan suka shigayi sultan na bin ta tana dariya tana mashi gwalo har yayi nasara kamata gabaki daya kasa sukayi suna dariya sauke numfashin Nihal take tana kallan sultan da shima yake sauke ajiyar zuciya yace, "hayaty kin iya gudu sosai da kyar na iya kama ki" sultan ya ida zancan yana lalacewa Nihal hanci. Kwana uku suka kwashe a MOSCOW suka dawo ENGLAND suka cigaba da gudanar da rayuwar mai ke da tsantsar so da kauna tare da nunawa juna tsantsar soyayya. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [2/1, 11:37 AM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 123_124* Yauma kamar kullun bayan Nihal ta gama duk wani aikace-aikacan gidan tabi ko ina da turaran wuta sai kamshi gidan yake zubawa, breakfast din data kamala ta jera a dining area, duk wannan aiki da Nihal keyi ba wai dan ba ma'aikata bane sai dan kawai tafi so tayi komai da kanta a ganin ta nan take da damar nunawa mijin ta tsantsar kulawa, stairs ta haya dan tado sultan daga bacci tunda yayi sallah Asuba ya koma itama lallabowa tayi batare da sani shi ba idan ta shine ko kara ba zai bari ta dauka ba. Kwance saman makeken gado ta hango shi ya wani kudindine daga gani bacci nayi mashi dadi, har kuma da yanayin garin kasancewar tun jiya ake snow labilan dakin ta zuge gabaki daya wanda yasa haske ya gware dakin juyawa sultan yayi tare cigaba da bacci murmushi Nihal tayi a hankali ta hayo saman bed din tana shafa sumar kanshi dai-dai saitin kunna shi tana hura mashi iskar bakin ta mai sanyi sultan da idanuwan shi ke lumshe cikin muryar bacci yace, "hayaty yau na lura da rigima kika tashi, ban gaji da bacci ba" jawota yayi yana cewa, "kwanta..! mikewa zaune Nihal tayi tana cewa, "love ka tashi rana tayi" lumsasun idanuwan shi sultan ya bude ya zuba wa Nihal cike da shagwaba yana kallan ta yace, "hayaty gani na tashi fadi min abinda zaki fadi min na koma" zaro ido Nihal tayi tana cewa, "love baccin ya isa haka muje kayi wanka ka zo muyi break..! bata ida kai ayaba sultan ya jawo blanket har da ita ya lullube su mutsu-mutsu Nihal take cikin blanket tana dariya tana cewa, "love ka bari mana please" har sai da Nihal tasa mashi kukan shagwaba ya bude blanket din yana dariya Nihal kuma sai turo baki take tana gyara zaman rigar ta sai da sultan ya nufi toilet yana cewa, "duk san da kika tashe ne daga bacci..! sai ya kashe mata ido pillow Nihal ta janyo ta wurga mashi da sauri sultan ya shige toilet yana dariya Nihal ko tana cewa, "zaka fito ka same ni" daga toilet sultan yace, "ki shigo daga ciki sai komai yafi bada light" yar kara Nihal ta saki mai cike da shagwaba sannan ta fidowa sultan kayan da ze sa. Zaune suke a dining Nihal na serving sultan sai wani hada rai take ita ala dole fushi take da shi, hannu ta sultan ya kama ya kafe ta da sexy eye's ball din shi cikin muryar shi me dadi yace "hayaty fushi kike dani am sorry" sultan ya fada yana kama kunnuwan shi kauda kai Nihal tayi tana cigaba da serving nashi langwabe kai sultan yayi yace, "nine fa ko kin manta" turo dan karamin bakin ta Nihal tayi tana cewa, "ba kai bane uhm,uhm" dariya sultan ya saki yana toshe bakin shi ya jawo Nihal saman cinyar shi yana bata hakuri tana kara narke mashi shi da kan shi yayi feeding nata itama tana feeding nashi. ****** Yau Ahmad ya iso Nigeria misalin karfe 3:30pm koda ya iso gida an fara kiraye-kirayan sallah la'asar kayan shi kawai ya aje a daki yayi alwala ya wuce masallaci cikin gida fadawa dake kokarin shiga masallaci sakin baki da hanci sukayi suna bin (Alex) Ahmad da kallo lallai wannan mutumin bari muga iya gudun ruwan shi baki sake suma suka shige masallaci suna kuskus, har aka gama sallah da shi yana kokarin fitowa suka had'e da maimartaba da waziri kasancewar da Ammar ya dawo ya basu wannan dadadan labari gaisawa sukayi da maimartaba da waziri har suke ce mashi ya jiki suna cewa sun so su zo duba shi a asibiti Allah be nufa ba sai gashi ya dawo yau har maimartaba yace ya zo ya same shi a fadda, sannan maimartaba da waziri suka wuce suna tattaunawa. Ahmad dake kokarin shigewa part nashi, Ashad ya tare shi da mugun kallo Ahmad ke bin shi dan yasan abinda yayi sarai kwata-kwata Ashad be damu da irin kallan da Ahmad ke mashi ba saboda ya cancanci abinda yafi haka, mikawa Ahmad hannu Ashad yayi kauda kai Ahmad yayi ze bud'e kofa ya shige bedroom Ashad yace, "na taya ka murnar zama daya daga cikin Muslim brother's" murmusawa Ahmad yayi yace, "shine yasa ka tare min hanya? "A'a akwai tanbaya da zan maka please" "Bani da wannan lokacin malam" "Haba Ahmad ka saurare ni mana yanzu na canza daga Ashad din daka sani a baya" "I can see matsamin na wuce" "Ka saurare ni mana please" "Na lura so kake na maka rashin mutuncin ina daga maka kafa ne saboda sultan ba saboda kowa ba if not da tuni nama rashin mutunci" Ahmad ya ida zancan ze shige daki, Ashad ya ruko hannu shi a fusace Ahmad ya juyo ya dauke Ashad da lafiyayan mari ji kake tas..! tas..! har sai daya kifa jini na bi mashi gefan baki gabaki daya wajan sai daya dauka fadawan dake wajan ne suka nufo su Ashad ya daga masu hannu ya mike yana shafa gefan bakin shi, nuna shi da yatsa Ahmad yayi yace, "bana jin zan kara daukar wani nonsense game da kai karka kara gigin taba ni malam idan kayi ma sultan ka kwana lafiya ni baza ka min ba" Ahmad ya murda handle din kofa maganar Ashad ce ta sashi juyowa ba shiri, "Wai me yasa baza ka saurare ni bane ko Allah munayi mashi laifi ya yafe mana na zo ne kawai na tanbaye ka yaushe yaya ze dawo..! wata uwar harara Ahmad ya maka mashi yace, "yau she ze dawo..! ka aika shi lahira, tana kuma ka bulo da wannan salan ka dawo tunda asirrin ka ya tonu ko, to ban sani ba so kake ya dawo ka karasa shi ko to aniyar ka ta bika an fadama bamu san kowaye ya aika mana muta nan da suke neman rayuwar mu ido rufe ba ne, amma dai baka da kunya a tunanin ka ban san irin munafircin ka ba, da makircin ka I wish kai kanina ne am gonna kill you with my hand I swear...! ka bani kunya Ashad ban taba tunani zaka iya aikatawa dan uwan ka haka ba, dama ni jiki na ya dade yana bani kai ke aikatawa, gudun kar nace kai ne na shiga tsakanin yan'uwa shiyasa na ja baki na nayi shuru, a ganina laifin daka aikata hukuncin kisa ya dace a maka dan dai kawai sultan ya kashe wutar nan da ba abinda ze Hanani hura ta I tell you, do you what bana san ganin ka malam ka bani guri" Ahmad ya ida zancan cikin tsawa, "Me yasa baza ka kalle ni ba ka ga sauyin dana samu ba ni kaina na zauna na gane abinda na aikata a baya ba dai-dai bane sharin shedan ne da hasada ya jefa ni a halaka, Ahmad yanzu na tashi daga Ashad din da ka sani a baya mara tausayi mara imani na gane kura-kuran dana aikata a baya neman yaya nake ido rufe na bashi hakuri duk da nasan mawuyacin abune ya iya yafe min laifukan dana aikata," Ashad ya ida zancan yana kuka ya cigaba da cewa, "kai kanka Ahmad na san na cuta maka dan Allah ka yafe min Ahmad na san na cutar daku kai da yaya ka daure ka yafe min" Ashad ya duka har kasa hannuwan shi hade hawaye na sulalo mashi jim kadan Ahmad yayi yana nazarin fuskar Ashad wanda ke cike da dunbin nadama can kasan makoshi yace, "Na yafe maka Allah ya yafe mana gabaki daya murmushi jin dadi ne ya subucewa Ashad ya rungume Ahmad yana cewa, "Na gode Ahmad" sannan ya sake shi ya bar wajan. Nazili ce kishingide tana sanye da bathrobe white tana latsa wayar ta Aziza na mata massage mikewa tayi a zabure tana kallan screen din wayar ta hatta Aziza sai da ta razana saboda harbata da Nazili tayi, ba komai ya haifarwa Nazili haka ba sai pictures din sultan da Nihal data gani a media wanda sukayi a ranar dinner, cikin zafin rai tace "amma dai Allah ya tsinewa wannan yarinyar, na lura muta nan basu da niyar dawowa bana fata matsiyaciyar yarinya nan ta samu ciki amma naga alamar hakan ta kusa faruwa, ya kamata naje England ziyara, dan na tarwatsa farin cikin da suke ciki" Nazili ta ida zancan tana murmushi mugun ta Aziza dake zaune tace, "ran ki ya dade ki bar tada hankali ki, ko cikin gare ta ai sai mu bara da mugu cikin sauki, bama na tunanin tana wani abu haihu duk ta kare juyace...! duka yaushe akayi auran Gimbiya Basmal amma yanzu haka ciki gare ta na wata 3 ita ko fa shekara daya da aure amma shuru ba amo ba labari ko batan wata bata tabayi ba sai dai aci ayi kashi, idan ko bata haihuwar kin ga dole sultan ya karo aure dan magajin gari ba ze zauna ba d'a ba jika ba," numfasawa Nazili tayi tace, "maganar ki taso ta zama gaskiya, zanyi tunani akan maganar, kin ga maganar bin su England be tashi ba zama zanyi na jira su dawo, daga lokacin kowa zai fara gajiya da rashin haihuwar tata har shi sultan din lokacin ni kuma zanyi anfani da damata, ya kika gani, hada min ruwan wanka ina da meeting after isha da manya-manya yan kasuwa," Aziza ta mike zuwa toilet. Nazili ce ta fito shirye cikin brown gown ta kama jikin ta sosai ta zubo da gashin ta har gadan baya ta fito daga bedroom din ta, tana kokarin fita, Ammi tace, "abar kauna ta ina zaki je da wannan daran? birki Nazili taci tana cewa, "bana fada maki ina da meeting ba yau, kan business dina yau nake sa ran shugaban kasa ze sa hannu a takadun company nina daga nan zan zama shaharariyar yar kasuwa zai zamana babu mai shigo da wasu kaya daga wata kasa sai dai na company nina, Mr president zeyi alfahari dani," "Na taya ki murna abar kauna ta sosai Allah ya tabatar da alheri, amma abar kauna ta sai a rasa lokacin yin meeting sai da dare ke fa macece ba namiji ba wai mi yasa kike abubuwan tamkar namiji ne? neman kudin da kike yayi yawa, baki rasa ci ba baki rasa sha ba yanzu saboda Allah wanna rayuwa ce dubi shigar da kikayi kamar ba diyar musulmi ba, gashin kan ki bude ji yarda rigar ta kama maki jiki gabaki daya suraki na waje wannan shigar a gida ta dace kiyi ta, maza wuce ki canza kuma ki yafa veil" galala Nazili tayi tana kallan Ammi sannan tace, "Ammi kisan ba ma zan iya canza wasu kaya ba kisan kayan nan daga ina nayi ordering nasu kuwa? saboda meeting din nan na siya su, kuma ni gaskiya bana iya sa wani abu wai shi veil ba ban saba ba kuma bazan fara yau ba haba dan Allah duk anbi an sami ido na gaji da wannan rayuwar" Nazili ta ida zancan zata fice Ammi tace, "shikenan abar kauna ta ina tunanin kowa naba wannan dokar da oda zata bi amma ke da kanki keke watsamin kasa a ido Allah ya ji kan mahaifin ki da yana raye baze bari ki fita haka ba ai, har da laifi na da bana fadawa maimartaba abinda kike" Ammi ta ida zancan tana matsar kwalla, tsayawa Nazili tayi tana cewa, "oh Ammi yanzu kuma da iyaye na kabari zaki hadani da maimartaba fine naji zan sa," Aziza Nazili ta shiga kwallawa kira ta kawo mata ash veil tayi rolling din shi a kanta tace, "daga haka bazan kuma canzawa ba" murmushi Ammi ta saki tace "ko ke fa Allah ya baki miji na gari, amma dan Allah ki min alfarma daya abar kauna ta ki bari driver ya kai ki tun da dare yayi driving din mace ba dadi da daddare why not tunda Alex na gida yayi dropping naki, ba driving kad'ai ba har lafiyar ki sai ya kare" "oh my god Ammi am getting tied of you, you are trying to make me sick" kuka Ammi ta saki tana cewa, "A dawo lafiya Nazili tunda ban isa dake ba, tunda bani na haife ki ba, dole ki rinka gaya min magana san ranki" Ammi ta ida zancan tana dafe kujera saboda jirin dake dibar ta, tab'e baki Nazili tayi tace, "gabaki daya baki nemana da alheri cikin daran nan sai a kira shi yayi dropping nawa kin ji dadi ko sai ki daina dafa kujera kar ace nina ke neman karasa saki" kwata-kwata Ammi bata damu da abinda Nazili keyi ba ta shiga kiran wayar Ahmad cikin dan kankanin lokaci ya zo Ammi ta mashi bayani yace ba komai Nazili harara kawai take maka mashi Ammi tace tayi promise bazata cire veil din kanta ba tace tayi ta fice. tana isa bakin motar ta ta zare veil din kanta tana kokarin turawa cikin jaka, maganar Ahmad ta sauka a kunna ta "mi yasa zaki cire? juyowa Nazili tayi a fusace har gashin kanta na shafa fuskar Ahmad ta tsare shi da ido irin ina ruwan ka cikin gadara tace, "ina ruwan ka ni wai me ka dauki kanka ne hum fadi min naji, baka wuce guard ba amma shinshingin ka yafi karfin ka driving nawa aka ce kayi ba tanbaya ta abinda ya shafe ni ba" Nazili ta ida zancan tana aikawa Ahmad muguwar harara girgiza kai Ahmad yayi yace, "promise kikayiwa Ammi baza ki cire ba, amma kuma sai gashi daga fitowar ki tun kafin kije ko ina kin cire, kin san girman alkawari kuwa? dan siririn tsaki Nazili ta saki tace, "ka rinka gyara kalaman ka da Gimbiya kake magana i hope you get me right, mind your business malam kana bata min lokaci..! Nazili ta ida zancan tare da wurga mashi car key din ta, "ni kuma bazan kai ki ba sai kin maida veil din ki, if not sai dai kiyi driving kanki ni ba dan aikin ki bane, ko kuma na koma na fadawa maimartaba yarda kike fita waje daga nan kin ga maganar company ta kare" Ahmad ya ida zancan yana kokarin wucewa fadda, da sauri Nazili tasha gaban shi tana sauke ajiyar zuciya ran ta had'e iya kar kuluwa Nazili takai har tana tunanin me Alex yake takama da shi har yake gaya mata magana san ran shi, ba yarda ta iya taji ance maimartaba kuma taga da gaske Alex yake a hankali ta ciro veil din tayi rolling din kanta da shi tana harara shi tayi gama ta shige mota ta zauna a back sit, had'e rai Ahmad yayi yace, "dawo gaba ni ba driver ban ki bane, ko fita zanyi da sultan mota daya muke shiga bale ke karan-kada miya" nan ma haka ya kara kuleta har tana ji tamkar ta shake shi ya shuru, koda yake ba laifin shi bane da ta auri sultan be isa ya fada mata magana san ran shi ba. ****** England Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru ciki har da shirye-shiryen dawowa Nigeria da Nihal da sultan suke Yauma bayan Nihal tayi wanka tayi gayun ta cikin jean and pink t-shirt and black jacket kamar yadda ta saba sultan ya kwashe ta zuwa wani babba shopping mall dan tayi ma yan gida tsaraba, sun kwashi kaya sosai abun har mamaki yake ba Nihal yarda sultan baya jin kudin shi ko kad'a, duk abinda Nihal ta dauko sai dai sultan ya kara, hatta Basmal dake da ciki Nihal bata manta da ciki ba haka ta rinka lodo mata kayan baby's sultan kuwa ya zage sai tsokanar ta yake yana cewa idan zata dauka ta dau biyu saboda itama tayi tsaraba sai dai Nihal tayi murmushi, Minal da nawwara ma sai da ta kawas masu tsaraba acewar ta idan sun je masu visiting ta basu, har da nana ma daukarwawa bayan sun gama shopping suka wuce park sun dad'e can suna ta zuba soyayya su haka Nihal ta hau lilo mai juyawa tana dariya sultan nata daukar ta pictures har funy face take maida fuskar ta sultan nata dariya, for sure sunyi spending honeymoon din su a England yau saura kwana daya su dawo Nigeria. A gajiye likis suka dawo gida saman kujera Nihal ta fada tana cewa, "wash am tied" Nihal ta ida zancan tana lumshe ido zaunawa sultan yayi ya dauka kamar Nihal a cinyar shi ya fara mata massage duk yadda ta so ta hana shi yaki bari dole ta hakura yana yi mata massage har bacci ya fara dauke ta, Sanye da bathrobe suka fito Nihal sai shagwaba take zubawa sultan lotion ya dauko ya shafa mata tare da bata night dress ta saka, haka suka gama shiryawa sannan sultan ya dauko wayar shi ya kira mom da maimartaba ya sheda masu gobe zasu dawo Nigeria mom tayi murna da jin haka sosai tace, "Allah ya kiyaye hanya ya maido su lafiya" dan ba karamin kewar su take ba, suna gama wayar ya kira Ammi ya fada mata Ammi sai murna take tana cewa tayi missing nasu Allah ya maido su lafiya. Washe gari da daddare jirgin su sultan ya tashi zuwa Nigeria sai dai muce Allah ya kai su lafiya. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [2/2, 6:31 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Umman Khalil wannan shafin naki ne ke kad'ai kiyi yarda kike so da shi Allah ya raya mana khadija a tafarki na addini muslunci Allah yasa mata albarka ta zama mahadaciyar Al Qur'ani_* *Page: 125_126* Bayine ke ta kai kawo da gyara-gyaran tabar sultan da Nihal dan Ammi tace yarda suka kwana biyu basa gida dole ayi abinda ze kayatar da su duk wani kayan ciye-ciye da lashe-lashe Ammi tasa anyi musu mom ma ba a barta a baya ba, dan sawa tayi aka canzawa su Nihal kayan part nasu gabaki daya, kowa ka kalla murnar dawowar su ya keyi karma ace fadawa da sultan yake masu augo duk sanda zai fita. Nazili ce ta fito daga dakin ta tana sanye da gown brown mai kamar bubu hannu ta daya na rike da cup na coffee yau zuciyar ta fes take ganin cewa kasuwan cin ta na tafiya yarda ya kamata kudi na shigo mata kowani lokaci, turus tayi ta ja ta tsaya tana kallan bayin dake kai kawo a parlour Ammi, ko ba'a fada mata ba alama ta nuna baki zasuyi, zama Nazili tayi saman one star tana shan coffee din ta ta cewa Ammi dake zaune Dara na mata tausa "hala baki zamuyi masu muhimmanci? Murmusawa Ammi tayi tace, "abar kauna ta baki da labarin cewa yau dan gaban koshi zai dawo shi da sultana, shiyasa na bada umarni ayi duk abinda zai birge su," tab'e baki Nazili tayi tace, "kuna kokarin ganin kun birge su, to su me sukayi dan su ga cewa su birge ku? matar da har yau kusan shekara daya ko bari bata tabayi ba, ko ba komai maimartaba zai su yaga jikan shi jini shi amma yayi shuru saboda karya bata maki rai, Ammi gabaki daya kin rintse ido ba kyan ganin aibun yarinyar nan, mu ka mu muna so muga jini sultan a cikin gidan nan da tana haihuwa da yanzu da jikan maimartaba zasu dawo yana yawo cikin gida yana wasan ni shi lokacin ke kuma zaki bada uwarni ayi abinda ze birge shi ba su ba," Nazili ida zancan tana kallan Ammi wanda hankali ta bai taba kai ta nan ba sai yau da Nazili ta fada mata jikin tane yayi sanyi idan bata manta ba yau shekara daya da auran su da yan watani amma ko bari Nihal bata tabayi ba, ganin yadda Ammi tayi suku-suku yasa Nazili murmushi mugun ta tace, "Ammi kinyi shuru," "ba komai abar kauna ta" "Ammi ya kamata ki zaunar da sultan ki ji tafiyar matar shi, ga Basmal nan yanzu ciki gare ta na kusan wata 3 dayake ita din me tushe ce ba yawo ta gama a titi ba aka daura ma wani ita ba kilama ta gama..! "Nazili..! ya isa haka" Ammi ta ida zancan tare da barin parlour dan kalaman Nazili sun sosa mata zuciya, Nazili kuwa dadi ne ya lullube ta dan ganin cewa Ammi zata saurare ta ko ba yau ba har sai ta cusa mata tsanar Nihal sai ta nunawa muta nan gidan cewa Nihal din ce bata haihuwa saura ta samu mom ta daura ta a kan layi, shumin murmushi Nazili ta saki tana fatan samun nasara. Gimbiya jalila ce ta tasa Ashad gaba tana kunfan baki "yanzu saboda Allah son rayuwar daka zabawa kanka kenan ka gwanmace ka watsawa mahaifiyar kasa a ido, ka ni san ta kan ka dani ko part nawa baka zuwa, ai da ba haka kake ba yanzu saboda ka maida kankan mara anfani shine sai ka zauna katan kafiri ya dauke ka da mari kana tsaye baka ce komai ba, har ya fasa ma baki..! Wallahi ka bani kunya son duk abubuwan da nake dan samama farin ciki baka gani lokacin daya ka watsa min kasa a ido muna nan da kai zaka zo ka neme ni indai nice, yau sultan ze dawo idan kaga irin tarbar da za'a mashi zaka sha mamaki, zaka iya fadamin ranar da kayi tafiya ka dawo aka tarbe ka aka gyara gida saboda zaka dawo? "Momi please ki daina wannan maganar to minene dan a tarbe shi yayana ne ze dawo kuma magajin gari, kuma Alex din nan da kika ta maganar shi kina ce mashi kafiri ya riga daya muslunta ki daina kiran shi da kafiri, marin da Ahmad ya min na cancanci amin abinda yafi haka" galala Gimbiya jalila ke kallan Ashad tace, "ai baza ka taba gane abinda nake fada maka ba tunda ka riga ka canza ka tashi daga Ashad din dana sani," "Canjin da nayi shi yafi dai-dai a rayuwa ta and I love my new self momi, idan kina so mu shirya ki dauke idanuwan ki kan yaya..! takaici ne ya hana Gimbiya jalila magana ta fice daga part din Ashad jiki mace. Misalin karfe 2:00pm jirgi su Nihal ya sauka Nigeria kaitsaye motocin dake fake zaman jiran su suka nufa suka shige mota dan zuwa gida. A harabar gida motocin sultan suka faka a hankali suka fito yana makale da hannu Nihal murmushi Nihal ta saki tana kallan gidan bayin dake compound zubewa sukayi suna ta kwasar gaisuwa kirari fadawa suka shiga zubawa sultan, wanda zai sheda ma yan'gida sultan ya dawo da Gimbiyar shi, Ammi dake parlour sai washe baki take cikin murna da jin dadi Ammi da mom suka fito suka rungume su suna nuna masu tsantsar murna su pack sultan ya sakar wa mom a kumatu tare da Ammi Basmal da cikin ta ya fara fitowa da gudu ta rugu ta rungume Nihal su ta murnar ganin juna yaushe gamo Ammar kuwa saitin kuna Basmal ya matso yace, "honey ki bi a hankali karki wahala min da baby" turo dan karamin bakin ta Basmal tayi ta ja hannu Nihal gabaki daya suka dunguma ciki. Part na su suka wuce dan watsa ruwa kafin su fito main parlour lallacewa Nihal tayi tana kallan sauyin da part nasu yayi komai na part din an canza ba kara min kyau part din ya kara mata ba, bayan sunyi wanka sun shirya suka wuce main parlour lokacin da suka isa kowa ya halara nan suka ci abinci cikin jin dadi mom sai nan take da Nihal har sultan na cewa mom batayi missing nashi ba Abba ne kawai yayi missing nashi Gimbiya jalila kuwa sai faman tabe baki take Bayan sun ci sun koshi Nihal ta bude tsaraba tana ba kowa nashi tsarabar Basmal taso tafi ta kowa saboda har baby clothes data siya mata godiya sosai Basmal tayi mata da nuna jin dadin ta kowa ta ba tsaraba shi sai ya nuna mata jin dadin shi har su Adda da waziri tayi ma tsaraba, hatta maimartaba sai da ta mashi tsaraba kuma ya ji dadin kyautar sosai har yasa mata albarka, wata jaka Nihal ta dauka ta shopping ko ba'a fada ba kasan kyautar ce ta musanman tabawa Nazili kerere Nazili tayi tana kallan Nihal ganin idanuwan mutane na kanta yasa Nazili amsa tana yak'e. Sultan ne zaune a garden saman resting chair shi da Ammar da Ahmad suna ta shan fira yaushe gamo, sai ga Ashad ya zo wajan kai sunkuye dan bema san ta ina zai fara rukwan sultan ya yafe mashi ba, ganin haka yasa Ammar da Ahmad basu guri dan su tattauna da d'an uwan nashi tunda sun san kwana zancan, Ashad yace, "yaya..! Cikin murya mai rauni, nuna mashi guri zama sultan yayi ya zauna Ashad ya cigaba da cewa, "yaya na san ni mai laifi ne, ba lallai ka sake yarda dani ba a matsayin kanin ka ba, na aikata maka laifin da zeyi wuya ka yafemin kwata-kwata ba kayi sa'ar samun dan uwa kamata ba na rokeka ka yafe min yaya" "Bana so kana fadin irin wad'an nan kalaman abinda ya faru ya riga daya faru kuma ya wuce, ko ubangiji muna mashi laifi ya yafe mana, na riga dana yafe maka tun ba yau ba Allah ya yafe mana gabaki daya, ni dama fata na Allah ya kara hada kan mu ya tsare mu daga sharin shed'an ya shirya min kai kamar carbi," Sultan ya ida zancan cikin zolaya wani irin farin ciki ne ya lullube Ashad ya rungume sultan tare da sakin kuka yana cewa, "Allah na gode maka daka bani dan uwar mai saka shari da alheri Allah na tuba na aikata maka abubu..! Toshe mashi baki sultan yayi yana girgiza mashi kai murmushi suka sakarwa juna su, haka sultan ya rinka jan Ashad da fira dan ya saki jiki shi ya maida komai ba komai bane komai ya gira ya wuce. Nazili na shiga bedroom zagaye daki take rai bace bud'e jakar hannu ta tayi ta ciro kwallin dake cikin jakar, wata hadadan gown ta gani mai shagen tsada da fost, ciki masifa Nazili tace "Amma dai wannan yarinyar ta rainani har ni zata sa kudi ta siyawa kaya sai ka ce matsiyaciya" wata takada ta ganni makale jikin kwallin dauka tayi ta karanta dunkule takardar Nazili tayi cikin bacin rai tace, "zan gwada maki ko ni wacece Nihal..! almakashi Nazili tace Aziza ta bata ta zauna tayima rigar gutsin-gutsin ta maid rigar cikin kwallin data ciro ta, ta maida fost din Aziza dai bace kala ba tana tsaye gafe tana takaici yaga rigar da Gimbiya tayi dama ita tabawawa ta rage zafi dan ba karamar riga ta wulakanta ba sannan ta fice daga dakin. Nihal ce ke takowa tare da bayin ta barira da Yasmin A dai-dai corridor din da ze sada Nihal da part nasu taji muryar Nazili na cewa Nihal..! Tsayawa Nihal tayi cak tare dayima bayin ta alama da hannu su ja gefe karasowa Nazili tayi tace, "Naga abinda kika rubuta min dalilin ne ya kawo ni nan dan na gwada maki na isa..! Gyara tsayawa Nihal tayi tana saurara ta "An fada maki kowa matsiyaci ne irin ki how dare you zaki kwaso wata kazamar rigar ki ki bani, ce maki akayi ban da sutura da zaki siya min riga? ke ce ke bukatar riga bani ba, ko ina amsar tsaraba bana amsar ta matsiyata irin ki megare ki mezaki bani, karki manta karka shin wani kike kuma kudin shi kike ci bana naki ba bana uban ki ba..!sai abinda sultan yaci ya rage yake baki sannan ki zo kiyi tunkaho da shi..! har kiyi kokarin dauka ki ba almajirai irin ki marasa galibi bani ba Gimbiya Nazili..! idan na so yau sai amin kalar rigar da kika bani sau dubu ba tare da kudi na sunyi ciwo ba..! saboda cikin kudi na tashi na girma ba cikin tsiya da talauci ba kamar ke Nihal yar gidan matsiya ta..! duk maganar da Nazili keyi Nihal na saurara ta zuciyar ta na suya tana kara mata kwarin gwiwa a kan abinda tayi niyar aikatawa dan hakan yafi dacewa da Nazili dan su goge rai nin dake tsakanin su, kwallin rigar Nazili ta bude ta juyewa Nihal a jiki ta tare da taka fost din da kafar ta tace, "Na fi karfin ki ko ta ko ina gabaki daya dangin kakaf zan iya ciyar da su da kudi na har duniya ta tashi, saboda taran matsiya ta aka tara ko uwar ki bata isa ta bani abu na amsa ba to megare ta da zata bani babu shi ba ayi shi ba, kwancan kaya na na dauka na ba uwar ki sai ta amsa bale kuma sabo bloody fool kawai...! Fisgo Nazili Nihal tayi ta dauke ta da mari jikake tas..! tas..! ta hagu ta dama Nazili ta kife kasa Nihal da idanuwan ta sun rine zuwa ja saboda bacin rai dafe kumatu Nazili tayi tana kallan Nihal fisgo ta mata gashi Nihal tayi ta kara dauke ta da wani marin, da kyar Nazili ta kwace kanta daga rukwan da Nihal ta mata kokowa ne ya shiga tsakanin Nihal da Nazili har Nihal ta samu nasara kada Nazili kasa ta bita ta zaune mata ruwan ciki, cikin bacin rai Nihal tace, "how dare you bitch zaki zagi iyaye na na kyale ki...! dukan ta Nihal kawai take kamar wadda imani ya fita daga jikin ta marin fuskar Nazili kawai take tana cewa, "dama ko baki zo ba ina sane da ke an fada maki ban san ke kika kona min fuska ba, I wish ranar dana fita Ammar ya barni da ranar kema sai na kona taki fuskar na lallata ta" takalmin kafar ta Nihal cire ta rinka kwadawa Nazili a fuska tun tana ihu har muryar ta ta dashe gashi ba motsin kowa bare a kawo mata dauki, Aziza da ta biyo sahun Nazili jin ta shuru, abinda ta ganine ya sata zaro ido zata zunduma ihu, Yasmin dake bayan ta toshe mata baki gam sai zare ido take tana mutsu-mutsu alama da ido Nihal tayi ma su Yasmin daukar Aziza sukayi cak suka shige wani daki da ita sai mutsu-mutsu take mikewa Nihal tayi tana sauke numfashin tayi kwallo da Nazili wanda ta dade da sumewa fuskar ta tayi kaca-kaca da jini Nihal bata damu ba, dakin daka shige ta Aziza ta nufa wuta ta cinno a icce tasa aka toshewa Aziza baki da tsumma Yasmin da Barira suka ririke ta gam nufo ta da icce Nihal take ko a jikin ta saboda alkawari ta daukar wa kanta sai ta rama ko ba yau ba, ta bankawa fuskar Aziza wuta wani ihu ta saki amma saboda bakin ta na toshe bame jin ta alama Nihal tayi masu da ido su fice ta wurgar da iccen cikin daki suka fice, har sun fito Nihal cikin muliki da isa tace, "ku dau ke Nazili ku fitar da ita waje ba tare da sani kuwa ba" sannan Nihal ta wuce part nata. Kaitsaye toilet Nihal ta shige ta sakarwa kanta shower, sai da tayi wanka hankali ta ya dawo jikin ta ita kanta mamakin rashin imani data tafka take zama tayi zaman sofa ko lotion ta kasa shafawa jikin ta sai rawa yake yanzu idan Nazili ta mutu fa me yasa tasa aka fidda ta waje yanzu idan ba'a ganta ba fa idanuwan Nihal sunyi jawur sai kuka take jikin ta na tsana ta rawa, murda kofar da akayi ne yasa Nihal mikewa a zabura sultan ne ya shigo Nihal kuwa sai zazare ido take tana bin bayan shi da kallo tsare ta ido sultan yayi yace, "hayaty ya..! kafi sultan yayi wata magana ta hada bakin su waje daya tana kissing sultan ta ko ina, wasani suka shigayi tsakanin su har suka zube saman bed (nima na sulale na fice) Nihal ce rungume da sultan tana yawa da hannu ta saman chest din shi har a lokacin Nihal bata dai tsuma ba sultan yace, "hayaty yana ji bugun zuciyar ki na gudu da sauri da sauri ga jikin ki yayi zafi mike damun ki hayaty ko baki lafiya ne? Sultan duk ya rud'e yana tanbayar Nihal, idanuwan Nihal da suka ciko da kwalla ita kanta tsoran kanta take ringing din wayar sultan ne ya katse masu tunani Ammi ce ta kira shi daukar wayar yayi abinda Ammi ta fada mashi ne ya sashi mikewa a zabure yana cewa, "yanzu tana ina..! duk da Nihal bata jin abinda Ammi ke cewa ba ta san maganar Nazili ake da Aziza katse wayar sultan yayi Nihal dake kwance tace, "love mike faruwa? cikin sanyin murya yace, "Nazili ce ba lafiya, an tsice ta a waje an mata duka da alama yan fashine suka tare ta, ita kuma Aziza rabin jikin ta ya kone" sultan ya ida zancan yana saka jallabiya Nihal kuwa sauke ajiyar zuciya tayi tasa duguwar rigar ta suka fice tare. Labari har yaje kunna maimartaba gabaki daya muta nan gidan suna part din Ammi, Ammi sai kuka take mom na bata hakuri Aziza kuwa asibiti aka wuce da ita Nazili kuwa fuskar ta ta kunbura kallo daya zakiyi wa fuskar kaji baka marmarin sakewa bakin ta ya kunbura suntun kamar yaja ruwa saboda tsabar duka daya sha a hannu Nihal, idan ka kalli bakin har dariya sai ta nemi ta kwace maka, Ammar ne ya bata taimakwan gagawa yasa mata drip, Aziza kuwa asibiti aka wuce da ita dan na ta matsala yafi karfin kula a gida, koda suka je asibiti sai da akayi wa Aziza theater Nihal kuwa ta jinjina rashin imani data tafka daga ita sai su Yasmin suka san tsiyar da suka shuka. Washe gari da safe kasancewar yau ta kama Monday bayan Nihal ta shirya cikin uniform din ta ita da sultan suka wuce main parlour sukayi break a gwagwace kasancewar sun makara har sun fito company Nihal tace, "love ban duba Nazili da jiki ba bari na je na duba ta" kallan agogan dake makale a hannun shi yayi yace, "hayaty mun makara fa kiyi sauri ki fito" to Nihal tace, ta koma cikin gida kasancewar Nazili a dakin ta take jinya Nihal ta shiga ta maida kofar ta kule da key Nazili dake bude kunburarun idanuwan ta ta sauke kan Nihal, ganin Nihal ya sata ranaza tana kallan ta dan yanzu tsoro Nihal take bata takowa gaban ta Nihal tayi ta ciro wuka a schoolbag din ta tana kyali tayi kamar zata cakawa Nazili rintse ido nazili tayi hawaye na wanke mata fuska ko magana bata iyawa bare tayi ihu dariya Nihal ta tintsire da ita a hankali Nazili ta bud'e ido Nihal na zaune gefan gado tana kallan Nazili tana girgiza kai tana dariya can kuma ta daure tace, "somin tabi na maki idan har zaki cigaba da bibiyar rayuwa ta zaki ga abinda yafi haka muni idan kunne ya ji jiki ya tsira hope you get me right sannan Nihal ta fice. Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi sosai Nihal ke maida hankali kan karatun ta, tsakanin Nana da Nihal kuwa sun kara kulewa dan yanzu haka Nihal bata da kawa sama da Nana itama Nana haka, har cewa ake suna kama saboda tsabar abota, idan Nana ta koma gida bata da wani labari sai na Nihal haka zata wuni tana ba mama labarin Nihal kawar ta mama kuwa har so take taga Nihal, ba komai ke sata jin haka ba sai tuna Nihal din yaya hansatu Allah sarki Nihal din ta wanda yanzu ta zama tarihi babu irin neman da basuyi mata ba, har aunty Aisha ta sare ta mika lamuran ta ga Allah. So biyu Nana tana zuwa gidan sarki wajan Nihal a nan Ashad ya Kyala ido yaga Nana tunda ya ganta ya rasa suku ni tun yana karya ta abinda yake ji game da ita har ya yarda da cewa ya kamu da san Nana so mai tsatsani, haka ya samu sultan ya fada mashi kan yayi ma Nihal magana kan Nana tunda kawar ta ce sosai sultan ya ji dadi hakan dama Nana akwai natsuwa da hankali. duk abinda Gimbiya jalila tayi yunkuri aikatawa Ashad sai ya hana ta har gwada mata cewa yayi duk abinda ya sami sultan ta rubuta ta a je kamar ya same shi ne, hakan yasa Gimbiya jalila ta zubar da makaman ta badan ta so ba sai dan farin cikin Ashad. Nazili kuwa ta rage shiga sha'ani Nihal dan ba karamin razana tayi da barazanar kashe ta da Nihal keyi ba, gashi duk wani abinda ta aikata mata Nihal ta gwada mata ta sani kuma itama zata iya aikata mata mafi muni shi zaman su lafiya shine ta cire sultan a zuciyar ta ko kuma tabi dare ta kashe ta ko kuma ta tona mata asirri da irin wannan barazanar Nihal ta ci galaba a kan Nazili ga wani mulki da take shinfidawa cikin gidan. Yauma kamar kullun bayan ta dawo daga makaranta part din Ammi ta wuce saboda tun a makaranta kanta ke mata wani irin ciwo komai ta kasa ci sai ruwa, duk abinda ta kai baki sai taji kamar za tayi aman shi ga wata kasala da take fama da ita tun ba yau ba ko part nasu bata san shiga tafi gane ma ta zauna a dakin ta na part din ammi, ko kayan jikin ta ji take bata san su sai wata yar shirt din sultan blue data saka, a parlour ta same Ammi tana shan fruit ciki fara'a Ammi tace, "har an dawo kenan? murmushi Nihal tayi tace, "Eh Ammi na dawo" kallan rigar dake jikin ta Ammi tayi tace, "Ah lallai soyayya ruwan zuma yau kuma rigar tashi aka dauko aka saka tunda baya gida" dariya Nihal ta saki duk kunya Ammi ta rufe ta daki ta shige Ammi na cewa, "dawo na ja'iri idan tayi tsami zamu ji ne," dariya Ammi tayi tana girgiza kai, Nihal na shiga daki ta kishingida saman sofa turo kofar da kayi ne ya sata mikewa zaune Dara ce ta shigo dauke da plate din danbu wanda Nihal tace ma mom ta naso idan ta dawo makaranta ta ci da kanta mom tayi mata danbun jin ta shuru yasa mom cewa Dara ta biyo ta da shi murmushi Dara tayi tace, "Gimbiya ga danbun nan da zafin shi sauko na baki" turo baki Nihal tayi tace, "umma wai yaushe zaki daina ce min Gimbiya ni fa bana so tamkar uwa na daukeke" Dara kanta dake sunkuye tace, "insha Allah zan daina cewa tun da ba ki so" murmushi Nihal ta saki ta sako kasa ta zauna Dara na bata danbu cike da zakuwa Nihal tace, "bari ma na gwada maki hotan umma da Abba tunda yau na samu dama" murmushi Dara ta saki tana cewa, "ki bari ki gama cin abincin na lura sam baki san cin abinci yan kwana kin na" bata fuska Nihal tayi Dara tace, "dako min na gani yau dai Allah yayi zan gan su kwanaki kiran da Gimbiya ta maki ne ya hanani gani" drewar Nihal ta bude ta ciro hotan umma da Abba tace, "gashi Umma..!Hannun Dara tasa ta amsa tana ta murmushi abinda ta ganine ya sata daskarewa hannun ta na rawa kwakwalwar ta na wani irin juyawa jirin na din barta nuna hotan take da yatsa tace, "ya Ha..! sulalewa tayi kasa sumamiya da karfi Nihal tace Dara....!! ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [2/3, 6:30 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 127_128* Jijiga Dara Nihal take amma ko motsi da gudu ta fito parlour jikin ta na rawa tace, "Ammi! Ammi..! Ammi dake zaune mikewa tayi tana cewa, "lafiya kuwa Nihal? nuna daki Nihal take tana cewa "umma.! Umma.! "Me ya sami umma? nuna daki Nihal take tana kuka dunguma sukayi gabaki daya har da bayin dake parlour suka rufawa Nihal baya, koda suka shiga dakin Dara na kwance ko motsi batayi Ammi ce ta kalli Nihal tace, "garin ya haka ta faru ko dama bata da lafiya ne amma yini yau lafiyar ta lau ko ciwan kai bata ce min tanayi ba" ciki kuka Nihal tace, "daga na gwada mata hotan umma da Abba shine kawai naji tana wasu maganganu ta sume..! "Maza kawo ruwa na yayafa mata, sannan ki kira sultan ya zo ya duba ta" ruwa Nihal ta debo ta yayafawa Dara amma shuru ko motsawa batayi ba, da sauri Nihal ta wuce zuwa part nasu dan dauko wayar ta, layin sultan ta shiga kira sultan dake duba patient ganin kiran Nihal ya sashi matsawa gefe ya bar patient da nurse, da kyar Nihal ta sai ta kanta amma hakan baya hana a gane taci kuka tace, love.! "Hayaty meke faruwa naji muryar ki wani irin, jikin naki ne? cikin jan majina Nihal tace, "A'a love umma ce ka dawo gida we need your help Umma ce ba lafiya" Nihal ta ida zancan tana kuka sultan na jin haka yace gashi nan zuwa ta daina kuka everything will be okay datse kiran sultan yayi da sauri ya bar asibiti zuwa gida. Koda sultan ya dawo gida da sauri Nihal ta tare shi tace, "umma na bedroom dina duk laifi nane love nina janyo mata haka please ka duba ta bana so wani abu ya same ta saboda ni" duk Nihal ta rud'e talabo da fuskar ta sultan yayi yana kalla wadda tayi jawur yace, "calm down hayaty zata samu lafiya insha Allah kin ji" hura mata iskar bakin sultan yake a fuska yace ta rinka jan numfashi tana saukewa a haka Nihal ta samu natsuwa suka wuce bedroom din Nihal. Duk wani taimako daya dace a ba jakadiya sultan yayi amma abu ya faskara gashi tana numfashi amma bata motsi, hankalin mom ba karamin tashi yayi ba da taga halin da jakadiya take ciki, hatta bayin dake karkashin Dara kuka suke saboda Dara mutuniyar kirki ce. Asibiti aka wuce da Dara saboda ciwan ya wuce gida isar su asibiti aka shiga da Dara emergency dan bata taimakwan gagawa alamarin Dara ya faskara test sultan yasa aka mata, ba abinda ke damun ta result ya nuna, duk wata na'ura da ake duba cuta da ita ansawa Dara amma still lafiyar ta lau yake gwadawa, har sai da takai an tara meeting saboda ciwan Dara daga karshe bincike ya nuna ciwan Dara bana asibiti bane asirri ne. Koda suka dawo gida daki aka kwantar da Dara sultan nayi mata karatun Al Qur'ani kafin malamin cikin gidan ya zo kusan duka gidan dauka yayi da karatu gabaki daya a ranar sai da akayiwa Dara sauka, Nihal dake ta sharbar kuka aje Al Qur'ani hannun ta tayi saman bedside drewar ta cigaba da kuka jawota jikin shi sultan yayi yana kissing forehead din ta sauke ajiyar zuciya Nihal take tace, "love duk nina ja mata shiga wanna yanayin, daga nuna mata hotan umma da Abba ta suma har yanzu bata farka ba, idan ina ganinta cikin wannan halin ina tunawa da umma na lokacin da ciwan ta ya same ta daga irin haka bata kara mikewa ba har ta rasu," sauke ajiyar zuciya Nihal take shafa bayan ta sultan yake yana cewa, "is okay hayaty ba insha Dara zata samu sauki..! Shigowar maimartaba da malam ne ya katsewa sultan zancan guri suka ba malam Nihal ta koma cikin su Ammi ta daura kanta saman kafadar mom. Ruwa a cup aka ba malam ya dade yana addu'a cikin cup din ya tofa ya shafawa Dara a fuska, cikin kira ashi mai dadi ya fara yiwa Dara rokiya ana fara rukiya Dara ta fara juya kai kamar mai mafarkin ban tsoro zufa sai keto mata take kamar tayi tsere har sai da malam ya gama karatu sannan ta daina juya kai, magunguna malam ya bada na karya samu yace, "insha Allah akayi mata anfani da wannan magani cikin kwana uku zata mike da yarda Allah abinda yasa ma yanzu bata mike ba, ba karamin asirri aka mata akala asirri zai fi shekara daya a jikin ta, kuma asirrin anyi shine yarda zata manta kowa nata da ita kanta sannan aka kara mata da kurciya makarin asirrin shi ne duk sanda tayi tozali da wani nata ze kare to abinda ta gani jiya shi yayi yunkuri karya asirrin, insha Allah gobe zan dawo dan cigaba dayi mata magani" sallati su Gimbiya jalila suka dauka asirri kuma to waya mata suka shiga kallan-kallo har kusan fiye da shekara cike da gulma Gimbiya jalila tace, "na ga abinda ta gani ya sata shiga wanna hali..! dan har yau bata daina halin ta na tsegumi ba shiga safgar sultan ne kawai ta daina, Nihal jikin ta na rawa ta mikawa Gimbiya jalila hotan hannu ta, kallan hotan Gimbiya jalila tayi ta mikawa yakumbo, yakumbo ta mikawa mom haka suka rinka kallan hotan suna alajabi, maimartaba kuwa godiya yayi ma malam sosai sannan malam ya tafi, Nazili ce ta katse shurun da cewa, "hala na jikin hotan ne suka mata asirrin" wani irin kallo Nihal ta watsawa Nazili ta mike a hasale doke bakin Nazili tace, "iyayan nawa ne ke asirri" rike baki Nazili tayi ta kaiwa Nihal duka ta goce takalmin kafar Nihal ta core tana kokarin kaudawa Nazili, rike Nihal sultan yayi Ammi ta rike Nazili saboda kokowar dake neman balewa tsakanin su, Ammi tace, "baki gani bata lafiya idan baki iya bakin ki ba sai kin bawa kanki wulakanci" bama Nihal kunne sultan yayi yace, "hayaty 2days din nan kin fara zama mafadaciya wallahi" murguda mashi baki tayi tana aikawa Nazili harara Da daddare bayan kowa ya koma part na shi sultan da Nihal suka wuce part nasu suna shiga, zuciyar Nihal ta fara tashi dan kwata-kwata bata san shiga part din toilet ta nufa da sauri tabar sultan a parlour, kwarara amai kawai take kamar zatayi aman yan cikin ta, wanke baki tayi ta kora ruwa a zing aman ya wuce shirt din sultan daya cire yau daya dawo daga office ta gani cikin basket din kayan wanki ta dauka tana shinshin nawa ta wani lumshe ido, sultan dake parlour yana kallan news jin Nihal shuru yasa ya bita bedroom kara ruwan daya jine ya sasa nufar toilet tsaye gaban zing ya hango Nihal ruwan famfo sai zuba yake ita kuma rike da riga shi a hannu har sultan ya kashe famfo zing din idanuwan Nihal na lumshe sultan yace, "hayaty na lura yau cikin good mood kike me sirrin" lumsasun idanuwan ta Nihal ta bud'e tana murmushi shafa kumatun ta sultan yayi yace, "hayaty mikike da wannan rigar me dati ce fa" amshe rigar sultan yayi yasa cikin basket din wanki, didira kafa Nihal take tana cewa, " ka bani abu ai na sani, kamshi rigar kemin dadi" ta ida zancan tana dauko rigar bata fuska sultan yayi yace, "hayaty rigar dati ce fa Allah kadai yasan germs din da kike shaka baki gani dana dawo gida nake canza kaya saboda warin asibiti, ki aje rigar muje mu kwanta kin ji" langwabe kai Nihal tayi tace, "please love ka kyale ni na kwanta da ita duk abinda na shaka ban jin dadin shi sai rigar da ita zan kwanta," "Ke kuma da wannan rigima ya zo maki muje mu kwanta na lura rigima baby na yake saki, oya muje" Nihal na gaba sultan na bayan ta suna fitowa bedroom ta koma toilet da gudu tana kara kwarara amai sultan ya rude sosai gani yarda Nihal ke kwarara amai da kan shi ya gyara wajan ya wanke mata fuska saman abin kwamin wanka Nihal ta zauna tana shinshi na riga shi cikin shagwaba tace, "love bazan kara zuwa bedroom ba bana jin dadi kamshi dakin, bazan kwana a part din nan ba" "Hayaty idan bamu kwana ana ba ina zamu kwana" cike da shagwaba Nihal tace mu kwana ko ina amma banda part din nan," Nihal ta ida zancan tana kukan shagwabe, to sultan yace ya hada mata ruwan wanka yace, "ki fara yin wanka first kafi ki fito na gama tunanin inda zamu kwana tunda baki san nan din" daga mashi kai Nihal tayi sannan ya fice. Koda Nihal ta gama wanka sultan ya mika mata pink night dress din ta ta saka sannan ta fito rike da rigar shi a hannu dogwan hijab sultan ya mika mata ya dauki car key yace, "muje..! har a lokacin rigar sultan na hannu ta sultan yace, "hayaty ki aje rigar nan mana" makale kafada Nihal tayi, amshe rigar yayi ya aje kuka Nihal ta saka mashi ganin kukan take da gaske yasa sultan mika mata da sauri Nihal ta bar part din. suna fitowa parking space suka nufa Nihal tace, "love ina zamu je? "Zamu je inda zaki samu bacci ke da baby na" dan karamin bakin ta Nihal ta turo tace, "baby kuma a ina" jawota jikin shi sultan yayi yana shafa cikin ta pack ya sakar mata a goshi yace, "thank you hayaty, Allah na gode maka daka azurta ni da babba kyauta," ita dai bin sultan dana mujiya Nihal take tana surprise wai ita keda ciki murmushi take saki tana bin fuskar sultan da kallo a hankali ta daura hannu ta saman na sultan wanda yake saman cikin ta tace, "Da gaske ni ina da ciki eeeh" Nihal ta fada tana washe baki ja mata hanci sultan yayi yace, "Eh mana.! Bude mata hannu sultan yayi ta shige jikin shi kamar ya maida ta ciki dan murna ya kusa zama daddy. mota suka shige sultan ya ja suka bar harabar gidan asibitin shi ya fara zuwa, ya dauko allurai da magunguna da Nihal zata bukata musanman daya lura cikin me sata laulayi ne, cikin mota ya dawo ya sami Nihal ta dan kwanta jikin seat goshin ta sultan ya taba zafi rau tausayin tane ya lullube shi lumsasun idanuwan Nihal ta bude tana sakin smile, "sorry hayaty me zaki ci? cike da shagwaba Nihal tace, "tuwan dawa miyar kuka" yar dariya sultan ya saki yace, "ina zan samu tuwan dawa cikin daran nan,? na lura baby na da rigima ya zo" mota sultan ya ja, haka sultan ya rinka zagaye garin kano yana neman tuwo duk restaurant din da suka je ya kare da kyar ya samu akayi mashi kwatancan gidan jummala mai tuwo a nan ya samu tuwan shima na karshe. Kaitsaye hotel suka wuce dama sultan yayi bucking daki kafin su iso room key din kawai ya amsa suka shige Nihal na shiga ta zauna sultan ya zuba mata tuwan ta zauna tana ci tana lumshe ido sultan na kallan ta yana latsa wayar shi yace, "uhm wanna baby dan kauye ne, har ya fara maida min mata yar kauye" murguda mashi baki Nihal tayi ta cigaba da cin tuwan ta sai da ta gama cin tuwan tas sannan ta fara jin tashin zuciya da sauri ta mike sultan yace, "ya dai aman ne,.! da gudu ta shige toilet ta kwarara amai sai dai ba wani mai yawa bane, wanke mata fuska sultan yayi ya dauke ta cak ya maido daki ya kwatar da ita saman bed ya ja mata blanket ya koma toilet ya gyara wajan ko daya fito Nihal na kwance cikin blanket tana rawar dari, gwalbar magani ya dauka yasa sirinji ya zuko allura a hankali yace, "tashi na maki allura kin ji I now how you feel ki daure ki tashi" kuka Nihal ta sa mashi tace, "bana san allura ni dai ka bani magani kawai na sha" "Sorry na san baki so bazan maki da zafi ba, a hankali zan maki" kuka Nihal ta saki tana cewa, "ni dai bana so" numfasawa sultan yayi yana shafa kumatun ta rike da allura yace, "inna baki magani yanzu aman shi zakiyi na sani, dana maki allura zaki samu sauki fever dake damun ki zata sauka aman da kike ze tsaya ko bakya so ki warke, "Ina so na warke" "Good girl ba zan maki da zafi ba kin ji, a kwance ma zan maki" daga kai Nihal tayi takoma ta kwanta ta rintse ido, a hankali sultan ya mata allura amma saboda tsabar rigima ta Nihal har da mashi kukan shagwaba jikin ta kuwa yayi rau a haka bacci ya dauke ta, sultan na ganin haka ya debo ruwa a boll da towel yana dadana mata a ko ina na jikin ta *Washe gari* Kamar yarda malam ya fada washe gari ya dawo ya karayyi ma jakadiya rukiya sai dai ta rinka zufa tana girgiza kai yana mata addu'oi. yau ce rana ta uku da malam ya dawo sanyawa yayi aka dauki Dara aka fito da ita parlour aka jinginar da ita jikin kujera, yana kwararo mata karatun Al Qur'ani sannan ya bata ruwan addu'a tasha ya shafe mata jikin ta da sauran ruwan, wata irin atinshawa Dara ta saki har sau uku a hankali ta bude idanuwan ta, tana bin muta nan parlour da kallo daya bayan daya kasancewar kowa na gidan na parlour a hankali ta sauke idanuwan ta kan Nihal dake rab'e jikin mom hawaye suka sulalowa Haulatu ganin tsantsar kamar Nihal da Hansatu sai dai kawai Nihal ta gwadawa hansatu fari da murjewa kasancewar ita abirni take ko ba'a fada mata ba wannan jini tace jini yaya Habu ce, yanzu ta gane Nihal dawa take mata kama alama jakadiya tayiwa Nihal da hannu ta matso kusa da ita kallan-kallo aka fara a parlour Nihal da jikin ta ya dau rawa idanuwan ta sunyi raurau da hawaye, alama sultan ya mata taje jiki a mace ta mike ta karasa gaban jakadiya shafa kumatun Nihal take tare da fashewa da kuka tana cewa, "yarinyar dana bari a gida tana da shakara 4 itace ta zama haka Nihal..! rungume Nihal jakadiya tayi ta fashe da kuka itama Nihal din kuka take tana cewa, "Ashe ina da raban saki a idanuwa na aunty Haulatu, munyi kewar ki aunty Ashe ina da saura farin cikin a rayuwa ta" dago da fuskar ta jakadiya tayi tana murmushi a hankali ta sakarwa Nihal pack a goshin ta tana goge hawayan idanuwan Nihal kara rungume juna sukayi cikin murna jakadiya take cewa, "Ashe akwai ranar da zan tuna baya ashe akwai ranar da zan iya tuna ko ni wacece Allah na gode maka daga nuna min wannan rana tabas munga SAUYIN RAYUWA a cikin zuri'a mu munga iftila'i mara karewa..! kuka Dara ta saki tace, "Allah sarki rayuwa ina inna, baffa, yaya Habu, yaya Tanimu karki ce mun babu su suna sun bi su yaya hassan kwakwalwa ta baza ta dauki rashin yan'uwa na ba kuka Dara take sosai Nihal na girgiza mata kai cikin kuka tace Abba da umma rushewa tayi da wani irin kuka mutuwar su umma ta dawo mata zabuwa har wani shidewa take jawota sultan yayi ya rungume tsam dan baya fatan abinda ze samu Nihal da abinda ke cikin ta dan kukan ba karamar ila ze iyayi ma abinda ke cikin ta ba lallashin shin ta kawai yake be damu da mutane nan dake parlour Kuka sosai Dara take cikin kuka tace, "A daran daurin aure ne na bar gidan mu cikin dare wanda a lokaci jina nake tamkar a kaya babu abinda na dauka daga ni sai kayan jiki na, hatta garin a lokacin bakin shi nake gani bana fata na kara waiwayar garin koda na fito daga gida jeji na yanka dan karma a neme a tasha saboda bana fatan waiwayowa gida, tafiya kawai nake ni kaina ban san ina zani ba daga wannan lokaci na manta kuni wacece, a haka nake tafiya ina wuce kauyi ka idan dare yamin na kwana a gona ki tunda Asuba na mike na cigaba da tafiya ko abinda zan ci be dame ni ba ni dai burin na na bar yankin...! ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [2/5, 1:51 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 129_130* "haka na rinka yanka jeji ina tafiya idan naji kishin ruwa na tsaya na sha na rafi ko na makiyaya bani na iso garin kano ba sai dare, a lokacin Gimbiya da maimartaba sun je ran gadi suna dawowa saboda tsabar galabaitar da nayi yasa ko gabana bana gani har na haura kan titi motar fadawa ta banke ni wannan dalilin yasa suka taimake ni suka kaini asibiti, bayan naji sauki na waware suka min tanbayar duniyar nan ko ni wacece na kasa furta ko da kalma daya saboda na manta kai na bana iya tuna komai ko suna na bana iya cewa gashi, ganin haka yasa Gimbiya Nadiya ta tausayamin ta dauke ni muka dawo gida ta mikani hannu Ammi na cigaba da yi mata aiki kamar yarda sauran bayi keyi duk sanda nayi yunkurin tunani mai zurfi game dani sai na wuni ina fa da ciwan kai wannan dalilin yasa bana yunkurin tuna ko ni wacece..! Dara ta idan zancan tana kuka maitsuma zuciya gabaki daya muta nan parlour tsit sukayi, Nihal da Dara nata sheka kuka Dara ta numfasa tace, "ina baffa ina inna yaya Habu yaya tanimu? ko baki fada min ba na san mutuwa ta cigaba dayi mana dauki dai daya kamar fari" kuka Nihal ta saki tana kara sauke ajiyar zuciya idanuwan ta sun kunbura tace, "Allah abin godiya duk da bani da wayau a lokacin da kika bar gida ina yawan jin labarin ki, a bakin umma na" nisawa Nihal tayi tace, "yau ce ranar data dace na falasa kuni wacece bayan miji na da ya Ammar babu wanda ya san kuni wacece, ku yafemi a kan karyar danayi maku a farko ba komai ya janyo nayi karyar ba sai dan gudun abinda zeje ya dawo da kuma fargabar komawa kauye" nan Nihal ta shiga bama Dara labarin irin bakar wahala data sha hannun gwoggo da Baffa har sanadiyar guduwar ta zuwa birni ta ida zancan tana cewa, "umma a gaban idanuwa na Abba ya rasu mutuwa mai firgitarwa wanda har yau na kasa daina tuna irin mutuwar da Abba yayi duk sanda na tuna sai na zubar da hawaye duk da bani da wayau a lokacin amma na dade ina razana tunda Abba ya rasu RAYUWA ta sauya daga ni har umma mun azabtu a hannu gwoggo sai da muka zama marasa gata ko abinda zamu ci gagara mu yake kullun nice yawan talla, ta safe daban ta rana daban haka ta yamma har umma ta rasu cikin kunci da bakin cikin RAYUWA" Nihal ta ida zancan tana marayan kuka kowa na parlour ya zubar da hawaye jawo ta sultan yayi jikin shi yana lallashin ta. Nazili kuwa duk rigima da suke da Nihal sai data tausaya mata jikin ta yayi mugun sanyi tana jinjina bakar wahala da Nihal ta sha, numfasawa Dara tayi tace, "Allah ya ji kan magaba tan mu ya ji kan yaya da umma Allah ya gafar ta masu ya kai haske kabarin su, idan tamu ta zo Allah yasa mu cika da imani" gabaki daya aka amsa da amin Dara ta cigaba da cewa, "Amma dai yaya Tanimu ya cika mugun butulu mai saka alkairi da shari, baiyi amana ba yaci amanar yaya Habu ya tozarta mashi iyali bai kyauta ba ya tafka babban kuskure...! malam ne ya nisa yace, "Alhamdulillahi ala kulli hali lafiya ta samu, Allah mun gode maka da ka kawo karshan wannan matsala, Ah malama bai kamata kina jifar dan'uwan ki da wad'an na kalamai ba, bai kamata aga laifin shi ba tunda idan na fahimci bayani ku akwai rikitacan alamari game da labarin da kuke badawa mai rudani da alamar sahannu a cikin alamarin ku, tana iya yuyuwa musibar data fada maki ita ce ta fada mashi tana iya yuyuwa shima samu akayi mashi, kina iya ganin farak'u aka mashi da iyalan dan uwan nashi" maimartaba yace, "wannan gaskiya ne baza a yanke hukunci lokaci daya ba" waziri yace "tabbas..! malam yace, "yanzu yarda za'ayi ya kamata muje kauyan na su suyi magana ta fahimtar juna su sasanta kan su, idan har alamarin ya hada da junu sai muyi mashi magani dan samun waraka ko ya kace ran ka ya dade? nisawa maimartaba yayi yace, "duk yarda kace malam haka za'ayi ni dai fata na Nihal ta kasan ce da yan'uwan ta matsala dake tsakani su ta warware ta samu SAUYIN RAYUWA kamar kowa ni d'a mai gata, idan Allah ya kai mu sai mu shirya muje shanonon gabaki daya" kowa yayi na'am da zancan maimartaba sannan taro ya watse mazan suka wuce masallaci mata suka wuce bedroom dan dauro alwala. Wuni yau zungur Nihal na makale da Dara kafar Dara kafar Nihal sai tsiya ake mata kan yarda duk tabi ta likewa jakadiya tamkar za'a kwace mata ita daga ita har jakadiya baka gane mai kwakwar wani saboda nunawa juna su tsantsar fari ciki da kokarin faran ta wa juna su. Da daddare Nihal ce kwance ta daura kanta saman cinyar Dara tana cin fruit tana zuba mata shagwaba dan wanna cikin nata har da shagwaba yake sata da fada na karfi da yaji, sultan ne ya shigo dakin cikin fara'a ya zauna cikin ladabi Dara tayi yunkuri gaishe shi yace, "haba haba umma ko a da can baya ina hana ki bale kuma yanzu da kika zama surukata" murmusawa Dara tayi tana jin dadi irin girmamawar da sultan ke nuna mata tun ba yau ashe da raban wata rana zai zama surikin ta, bata da abinda zata iya cewa su maimartaba saboda halacin da suka mata ya kai, kallan Nihal sultan yayi yace, "hayaty gabaki daya yau kin manta dani ko dadi umma, ko magani ki na dare baki sha ba" sunne kai Nihal tayi tana kallan sultan ta kasan ido da yake ta faman aika mata da kallo mai cike da tsantsar kauna, Dara ce tace, "Dare ma ya riga da yayi ya kamata ku wuce shashan ku sai ta samu ta sha magani yanzu nan ma na gama yi mata bita kan rashin san ci abinci da takeyi, gobe da safe ma cigaba da hira d'iya ta" turo baki Nihal tayi tana kallan sultan kamar karamar yarinya tace, "Ni kam yau tare zamu kwana da Umma," dan zaro ido sultan yayi yana kallan Nihal da tayi mursisi umma tace, "ba za'ayi haka ba ki lallaba ki bi mijin ki, in dai nice kullun ina cikin gidan nan ba guduwa zanyi ba, kuma yarda kike fama da laulayin na ai sai likita bokwan turai" sai da sultan ya fakaici idanuwan Dara yayi ma Nihal gwalo yana cewa, "fada mata dai umma" Nihal kuwa tayi kincin-kincin da rai ba yarda ta iya haka ta mike tabi sultan tana turo baki. suna fitowa parlour sultan yace, "fushi ake dani dan na hana a kwana da Umma saki ran ki magani zan baki sai ki koma kin ji hayaty" sultan ya ida zancan yana kashe mata ido cike da zolaya didira kafa Nihal take tana dukan kirjin sultan cikin sigar shagwaba tace, "ai kasan umma baza ta bari ba shiyasa ka ce haka" Nihal ta ida zancan tana ja ma sultan kumatu hannu ta ya kama ya sakar mata pack cikin tafin hannu ta yace, "ina san ki mata na, nayi sa'ar samun ki a matsayin matata..! murmushi Nihal ta saki tana wasa da bottle din rigar sultan tace, "nafi kowa sa'ar mijin ina matukar sanka love" a hankali sultan ya daura labban shi sama lips din Nihal ya sakar mata kiss tare da daukar ta cak suka wuce part nasu Nihal nata zuba mashi shagwaba. Washe gari da safe bayan kowa ya shirya cikin shigar shi ta alfarma gabaki daya kowa na sanye da alkyabar shi mai tsadar gaske sai dai duk ta maimartaba tafi ta kowa tsada daga ta shi sai ta sultan, bayan sun gama breakfast suka dunguma gabaki daya suka wuce parking space Dara da Nazili mota daya suka shiga sai mom da Gimbiya jalila mota guda Ammi da Adda mota daya maimartaba da waziri mota guda Ammar da Basmal na mota daya sai Ashad da malam ciki mota daya sauran motar ta fadawa sultan da abar kaunar shi cikin mota suna makale da juna a gidan baya duk da har a lokacin zuciyar Nihal bata daina tsinkewa ba ganin haka yasa sultan daura kan Nihal sama fafadan kirjin shi a haka motocin suka tashi zuwa shanono. Nihal dake kwance saman fafadan kirjin sultan hayaniyar mutana kauye ne ya tashe ta daga baccin daya dauke ta, a hankali ta mike tana bin garin da kallo ta cikin window tunda suka iso jikin ta yayi sanyi tana tuna abubuwan da suka faru a da, kama Hannun ta sultan yayi ya sakar mata kiss murmushi yake Nihal ta sakar mashi tana kara kallan window mai agwaluma data ta hango ne yasa Nihal juyowa tana cewa, "love please a tsaya a siya min agwaluma ina san sha" ja mata hanci sultan yayi yana cewa, "wannan cikin naki ya fiye janye-janye hayaty yanzu kuma daga zuwan mu gari sai mu fara siyan agwaluma, ko kyankyami bakiyi" bata fuska Nihal tayi ganin haka yasa sultan cewa, "bala driver tsayar da mota ka karasa wajan me agwaluma can ka siyawa hayaty" to bala yace tare da cin birki ya faka mota gefe Nihal sai washe baki take, 1k sultan ya ciro a walad din shi ya mikawa bala sannan bala ya fice iska mai sanyin Nihal ta furzar tana cigaba da kallan window wata almajira ce tayi tsaye bakin window tana bara, kasancewar glass din motar tinted ne na waje baya ganin na ciki kwakwasa window tayi tana cewa, "sadaka sabo da Allah ku taimaka kuma Allah ya kara maku arziki" tirtsetan cikin ta kawai Nihal take gani sai muryar ta dake rawa tana cewa, "tun daran jiya rabo na da abinci ku taimaka, ko dan abinda ke ciki na," tausayin tane ya kama Nihal fost din ta Nihal ta bud ta zaro dubu daya ta zame window ta mika lallausan hannu ta, ta window tace, "gashi..! rankwafowa almajira tayi da niyar amsa abinda Nihal ta ganine yasa hannun ta daukar rawa tana kallan almajira bakin ta na rawa idanuwan ta cike da kwalla tace, "_Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un_..! sultan dake zaune ne ya mike ganin Nihal ta bude murfin mota da sauri ta fice shima ya bude ya bita jada baya Sara tayi a razane, hannun Nihal na rawa hawaye na bi mata kunci tana bin tirtsetan cikin Sara da kallo wanda haihuwa yau ko gobe Sara ma daskarewa tayi tana kallan zukekiyar Gimbiyar data fito dan kwata-kwata bata gane Nihal ba saboda Nihal ta tashi daga Nihal din da ta sani a baya kodada wadda yunwar duniya ta ishe ta, motocin dake bayan su ne suka faka lokaci guda suka bale murfin motocin ganin Nihal daskare dan yatsan ta na nuna Sara hawaye na mata anbaliya zagoyawa sultan yayi ya kama Nihal ya juyo da ita suna facing juna yace, "hayaty mi ta maki me hadaki da wanna almajira muje kin ji" sultan ya ida zancan yana jan hannu ta yana makawa Sara mugun kallo duk a tunanin sultan maya ce dan tafi kama da su, mutuwar tsaye Nihal tayi tana kallan Sara da tsoro ya kamata lokaci daya ganin fadawa na nufo ta ya sata cewa, "baiwar Allah daga bani sadaka sai ki fito kina kuka wallahi babu abinda na mata ran ka ya dad'e, ka ja matar ka ku tafi bana neman massifa, masifar data dame ni ma tamin yawa abinda zanci nake nema idan har bara danayi ya haifar mata da haka, ku yafe ni ran ka ya dad'e" Sara ta ida zancan zata juya Nihal tace, "Sara..! me ya same ki na ganni a cikin wannan halin ina gwoggo da Baffa da ya mudi kika fito cikin rana da tsohun ciki kina bara..! juyowa Sara tayi a razane tana kallan Nihal tana kara tantance muryar ta daskarewa tayi hawaye na bi mata kunci bakin ta na rawa tace, Nihal..! Karki ce min ke ce kika koma haka yar gayu yar huta yar mulki da sarauta..! kuka ne ya kwacewa Sara rike da kwana ta na bara da hakuran ta sun mata yellow tace, "kinga yar da Allah ya maidani Nihal, kin ga yarda sakayar Allah ta sauka a kai na duk abinda gwoggo ta lusafa zai same ki a rayuwa ni ya sama, naga SAUYIN RAYUWA dubi yarda na koma kalli abinda ke jiki na" numfasawa Sara tayi tace, "ke dake talla safe da rana baki kwaso abin kunya ba sai ni, ke dake talla baki wulakanta a duniya ba sai ni" durkoshewa Sara tayi duk da cikin dake rinjayar ta ta hada hannuwan biyu tace, "na rokeki Nihal ki yafe mana abinda muka aikata maki idan kikaga yarda rayuwa ta lallace mana saboda tozar taki da mukayi ke da umma, zaki tausaya mana idan kika ga halin da muke ciki" Nihal dake kuka da sauri ta karasa ta daga Sara yan kauye na gefe sunyi cirko-cirko suna kallan su haka su maimartaba cikin kuka Nihal tace, "bana fata ko makiyi na na ganshi a cikin wannan hali Sara na yafemaki koda can ban rike ki a rai na ba" Nihal ta ida zancan tana rungume Sara duk da tsami da warin da take zubawa Nihal bata damu ba Dara ma fitowa tayi tana kallan Sara nan Nihal tayi ma Sara bayani Dara washe baki Sara tayi tana share hawayan fuskar ta, ta gaishe da Dara cikin sakin fuska Dara ta amsa, amshe robar hannu Sara Nihal tayi tace, "muje gida ko" Nihal na maganar tana smile, motar su Nihal Sara ta shiga ta zauna gaban mota sannan driver ya ja mota warin Sara nata kunbura mashi ciki sultan kuwa daura kanshi yayi saman kafadar Nihal yana shakar kamshi ta. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 131_132* Tunda suka doso harabar gidan Nihal ke kallan gidan yarda ya lallace a da ba gidan daya kai nasu kyau da tsaruwa, Amma a yanzu babu gidan daya kai shi lallacewa murfi mota suka bale gabaki daya suka fito Sara tayi masu jagora shiga ciki. Gwoggo dake kokarin fitowa daga kurya tana yafa zani kodadiyar atamfar ta saboda labari ya zo mata cewa, Sara tayima maimartaba ba dai-dai ba daga zuwan shi rangani da iyalan shi, sallama Sara ce ta katsewa gwoggo hanzari da sauri ta fito daga daki tayi hanyar zaure muta nan data ganine tare da Sara yasa gwoggo makalewa tsaye tana bin su da kallo baki sake, da karkatacan bakin ta kaya a kode sun sha ruwa sunyi daud'a hannu rike da zani, Sara ce ta katse mata tunanin da cewa, "gwoggo kalli ki gani Nihal ce fa ta zo tare da su maimartaba sarkin kano kin ga yarda Nihal ta zama duk abinda muka mata hakan be hana ta neman mu ba Gwoggo" Sara ta ida zancan idanuwan ta taf da hawaye, Baffa dake kwance a tsakar gida yana juyo murya Sara tana fadin wannan zancan hawaye ne suka sulalo mashi. Kallo daya zakayiwa Baffa kaji baka marmarin sake wa saboda yarda jikin shi ya koma tamkar yayi gobara ya kone ya lallace yayi baki ga wani ruwa mai wari dake fita daga jikin shi, bakin shine kawai ke motsawa shima da kyar amma duka jikin shi ya lallace. Dafe kirji gwoggo tayi tana nuna Nihal da yatsa tana girgiza kai tana ja da baya tana cewa, "inaaaaa bazeyu ba Nihal ce ta koma haka tana yawo da manyan mutane wayanda sai a TV kake ganin su, jini Habu ce ta koma haka inaaaaa, inaaaaa wallahi da sake" dariya ta tintsire da ita tana cewa, "ah bazeyu ba duk abinda muka aikata ni da malam dan gani cewa basu ci gababa shi ne yanzu take tare da sarki inaaa hahha," hauka gwoggo take tuburan cirko-cirko su maimartaba sukayi da Nihal din ita kanta ganin yarda gwoggo ke hauka tana dariri ku, kuka Sara ta saki tana cewa, "innalillahi wa'inna ilaihi raju'un me haka kike gwoggo me nake gani haka" Sara ta ida zancan tana kama gwoggo dake kokarin yage kayan jikin ta ta dankara a guje, da kyar aka kama gwoggo tana shure-shure aka tura ta daki aka kule da kwado amma har a lokacin tana dukan kofar dakin almarin su Nihal karasawa yayi jikin su maimartaba yin sanyi. Warin da gidan keyi kad'ai ya isa ya hana ka hadiye yawu Nazili sai yan yatsine-yatsine take hancin ta dode haka suma sauran maimartaba da waziri ne da Nihal da sultan kawai suke mazewa amma suma warin na damun su ganin halin da Baffa yake ciki ne yasa Nihal da Dara karasawa da sauri suka hada baki wajan cewa, "me ke damun ka Baffa, me a jikin ka haka Baffa wanna wani irin ciwo ne yaya? Dara ta fada tana sakin kuka haka Nihal cikin shashekar kuka tace, "love ka taimaka mu kai Baffa asibiti a duba lafiyar shi dan Allah" cikin shakakiyar muryar shi Tanimu yana wani irin tari ga kudaje nayi mashi rangadi yace, "murya wa nake ji kamar haule? Baffa ya fadi cikin yanayi na mamaki, Dara dake gefen Baffa tace, "ni ce yaya Tanimu nice na dawo gare ka yaya..! numfasawa Baffa yayi yana cewa, "Haulatu.!! Nihal..! Ashe ina da raban gani ku kafin wa'adina ya cika," kara matsowa su Dara sukayi gaban Baffa suna cewa, "baza ka mutu ba Baffa zaka samu lafiya insha Allah daga kanka an gama irin wannan zalinci Baffa" wani irin nishi Baffa yayi ya cigaba da cewa, "rayuwa kenan shiyasa aka ce duk wanda zai gina ramin mugun ta ya gina shi dai-dai da shi idan ka gina shi da zurfi har da kai za'a fada" wani irin tari Baffa yayi wanda yake jin wata irin azaba idan yayi yace, "Haulatu ki yafe ni bani da bakin da zan iya budewa wajan neman gafara ku, ko kun yafe min ba lallai Allah ya yafe min ba dan ba ku kad'ai nayiwa laifi ba harda ubangiji na" Dara ce ta katse Tanimu da cewa, "yaya wace irin magana ce kakeyi haka mara dadi ji, ko dai zafin ciwo ne ke damun ka," nisawa Tanimu yayi yace, "haule kenan ba ko daya baki san komai ba ne haka kema Nihal abubuwa ne kawai ke faruwa ba tare da sani kowa ba, daga ni sai Allah sai indo muka san abinda muka shuka a karkashin kasa wanda shine ke bibiyar mu a halin yanzu, abinda muka shukane muke girbewa..! gabaki daya mutanan wajan sunyi tsit baka jin komai sai sautin kukan Dara dana Nihal da Sara wani irin tari Baffa yayi yace, "wannan bakin nawa ma dake bude Allah ya bar min shine saboda wannan rana wato ranar tuna siriri kun ga hasada bakin ciki gani kyashi ba karamin annoba bace ni Tanimu ita ta kai ni ta baro a doran duniya, duk abinda nayi dan shi yanzu babu ya kare," numfashi Baffa ya kara ja ga kudaje nata yi mashi rangadi sai kayi dauriyar gaske zaka iya tsayawa ka kalle shi bayan Nihal da Dara babu wanda ya iya karasawa gaban shi, Ashad da Gimbiya jalila da Nazili jikin su yayi mugun sanyi tunda Baffa ya fara zanyanu zance musanman Ashad Baffa ya cigaba da cewa, "haulatu Nihal ku yafe ni ba kamar ke Nihal kunga mutuwar Usaini kunga mutuwar Hassan kunga mutuwar Habu nad'ewar Hansatu sanadiyar barin ki gida Haule" Baffa da kuka yaci karfin shi da kyar ya iya furta cewa, "nine sanadi nina aikata..! kowa na wajan kallan-kallo aka shiga Nihal kuwa zaro ido take tana girgiza kai nan da nan Baffa ya shiga zayano masu duk katobara daya aikata ya ida zancan yana kuka yace, "ku yafe ni...! Dara kuwa wani irin marayan kuka take tana jera ajiyar zuciya tana cewa, "ka cuce mu yaya Tanimu ka tafka babban kuskure mara gyaruwa..! mikewa Nihal tayi dafe da kunne tana ja da baya saboda bakin ta ya mutu mudus bakin ciki ma ya hana ta cigaba da kuka wani abu yayi mata tsaye a zuciya tana tuna irin halacin da Abba yayi wa Baffa amma ya cuce su haka, ya cuci yan uwan shi haka jini Abban shi ganin yadda Nihal keyi kamar sabuwar kamu sultan ya nufe ta da sauri ya jawota ta jikin shi, rungume shi Nihal tayi gam tare da sakin wani irin marayan kuka mai tsuma zuciya mai saurare tana cewa, "ka cuce mu Baffa ka rabani da farin ciki na ka mai dani mara gata ka jefa rayuwar mutane da yawa cikin bakin ciki saboda farin cikin ka, ka cuce mu Baffa ka maida Abba na mahaukaci hakan be ishe ka ba har sai da yayi mutuwar wulakanci, ka nad'e umma ka kashe kawu Hassan Usaini bakin cikin abinda ke faruwa ya kashe kaka da inna saboda farin cikin ka Allah ba ze taba barin ka haka ba sai ka dangwama cikin masifa da bala'i har duniya ta tashi..! insha Allah rahamar ubangiji ta yanke maka daga nan har kiyama, ban taba jin natsani wani mahaluki a duniya ba kamar ka, bana tunanin ko cikin magagin bacci zan iya furta na yafe maka". Baffa dake kwance shame-shame sautin kuka shi kawai ke ta shi sai ihu gwoggo dake daki tana hauka tuburan yana cewa, "na rokeki Nihal" cikin dakewa Nihal tace, "masifa da bala'in duniya sune ajalin ka, na tsane ka na tsani gani ka tir da halin ka" gabaki daya muta nan wajan ras-ras suke jin kalaman Nihal idanuwan su waje suna kallan ta suna kallan Baffa, da gudu Nihal ta fice sultan ya bita a baya Dara ma mikewa tayi tana aikawa Baffa mugun kallo tace, "Allah ya isa tsakani mu da kai Tanimu..! gabaki daya muta nan wajan sun tsume waje daya sunyi cirko-cirko wani irin tausayi da imani ya shige su musanman Gimbiya jalila da Nazili. Sara kuwa ban da kuka ba abinda take bata taba tunanin muguntar su Baffa da rashin imani su ya kai haka ba mikewa Sara tayi da kyar tana cewa, "me yasa kayi haka Baffa me yasa hudubar shedan ta zauna maka kai da gwoggo, kun cuce mu ban taba tunanin muguntar ku da rashin imani ku ya kai haka ba, kunyi sanadiyar rasa rai d'aidaya har bakwai a duni..! abinda ta fara jine ya sata cijewa tana dafe bango tana kuka mai cin rai ba komai bane sai nakuda durkushewa Sara tayi dafe da ciki tana wash ciki na tana wani irin kuka da sauri Ammi da Adda suka rufa ma Sara haka itama Dara nakuda sosai Sara take dan haihuwa ce ta zo mata gadan-gadan ko kafin a kai ta asibiti ta haihu alkyabar jikin su Dara suka cire suka mata runfa dan amsar haihuwar ta. Nihal na fitowa waje durkushewa tayi cikin dashashiyar muryar ta tace, "ya Allah wannan wace irin cutarwa ce Baffa ka cuce mu ka ci amanar zuminci" ta ida zancan tana wani irin kuka har da marin kanta take ko mafarki take kalaman data ji saboda sunyiwa kunna ta nauyi sai sanbatu take jikin ta sai rawa yake Sultan da Basmal a tare suka danno a guje zuwa wajan Nihal Ammar na biye da su a baya rukota sultan yayi ya juyo da ita suna facing juna cikin muryar shi mai sanyi yace, "hayaty dan Allah ki natsu ki dawo hankali ki dan Allah..! Sultan ya ida zancan yana rungume ta tsam a jikin shi yana mai cigaba da cewa, "dan Allah ki dawo dai-dai ba zan juri ganin ki cikin wannan halin ba, ni kadai nasan yarda nake ji, kina kokarin gefa kanki cikin wani hali ke da abinda ke cikin ki, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un zaki rinka furtawa itace makamin mumini kin ji matana" sultan ya ida zancan yana hura mata iskar bakin shi mai sanyi a wuyan ta a hankali ya talabo da fuskar Nihal yasa harshanshi yana goge mata hawayan fuskar ta tas, maida ta kirjin shi yayi ya rungume ta tsam tayi lamo tana sauke ajiyar zuciya jefi-jefe yana shafa bayan ta, zuciyar tace ta fara tashi zamewa tayi daga jiki sultan ta koma gefe tana wani irin amai ruwa Basmal ta mikawa sultan ya wanke mata fuska ta kuskure bakin ta sultan ya talabo ta wani irin jiri Nihal kawai take gani a hankali take lumshe ido tana budewa, murfi mota sultan ya bud'e ya sata cikin mota ya kule murfin motar Ammar ne yace, "dude ya kamata ku wuce gida kafin mu karaso tana bukatar huta" "Abinda nake kokarin yi kenan Ammar" sultan ya ida zancan a raunane "Toh shikenan ka kula everything will be okay" daga kai sultan yayi ya zagaya ya shige mota driver ya ja. Ajiyar zuciya Basmal ta sauke tare da shigewa jikin Ammar tana cewa, "wannan wani irin rashin imani ne aunty Nihal ta bani tausayi" Basmal ta ida zancan tana matsar kwalla Ammar yace, "ko zamu bisu ne dan bana san abinda ze taba min ke da" Ammar ya ida zancan yana shafa cikin Basmal wanda ya fito amma ba sosai ba a hankali Basmal ta daura hannu ta saman na Ammar suna jin motsin baby murmushi Ammar ya saki yana cewa, "baby yana so ya gaisa da daddy" duka Basmal ta kai mashi Ammar ya goce yana dariya ya bud'e mata murfi mota suka shige driver ya ja. Nihal dake kwance saman fafadan kirjin sultan tana sauke ajiyar zuciya jefi-jefi gidan da taga sun nufo ne ya sata mikewa zaune tana bin gidan da kallo ba abinda ya fado mata a rai sai lokacin da take zuwa da bokitin kokwan ta Ammar na mata juye, tunawa tayi da lokacin da gwoggo tayi mata bugun mutuwa da kyar ta iya karasowa da jan jiki toshe baki Nihal tayi tana sakin marayan kuka tare da fadawa jikin sultan ta kankame shi tana gunjin kuka, lumshe ido sultan yayi siraran hawaye na mashi zarya parking din driver ne yasa sultan goge hawayan shi da sauri dagowar da zeyi ta cikin mirror ya hango bala driver na matsar kwalla saboda duk abinda ya faru yaji a kunna shi tausayi da imani ya shige shi da takaicin hali irin na Baffa daukar Nihal sultan yayi cak suka shige ciki. Kasancewar ansan da zuwan nasu komai na gidan tsaf Nihal kuwa tayi lamo a jikin sultan tana sauke ajiyar zuciya up stairs sultan ya haye da Nihal bedroom ya shige da ita, ya shinfid'e ta saman bed rage kayan jikin shi yayi ya cire alkyabar jikin shi da babba riga da links din hannun rigar shi ya nanad'e hannu rigar, toilet ya shiga ya hadawa Nihal ruwan wanka masu dan dumi-dumi ya fito daga toilet ko daya fito har a lokacin kuka take jin motsin shine ya sata goge hawayan fuskar ta da sauri takowa sultan yayi gaban ta a hankali yake magana cikin lallashin yace, "please hayaty ki daina kukan nan, bana so ina gani kina zubar da hawayan ki, damuwar da kike sawa kanki ba ke kadai take shafa ba da ni dake da abinda ke cikin ki take shafa please ki daina, ko dan abinda ke cikin ki karya samu matsala please" sultan ya ida zancan yana rage mata kayan jikin ta ya dauke ta cak suka shige toilet. Iyakar galabaita Sara ta galabaitu ga yunwa ga nakuda sai nishi take tana kuka dan ta riga da ta fara sadakarwa da zata rayu, hankali su Ammi da Adda ya tashi sosai sai addu'a suke Allah yasa ta iya haihuwa da kanta sai nishi take ganin sun Ammi sun kasa, yasa Ashad ya fita ya shiga cikin mota ya dauko kayan aikin da baza a rasa ba a mota ya dawo cikin gidan da taimakwan Ashad Sara ta haihu tare da saki wani irin nishi ta sume da sauri Dara ta dauke baby tana buga bayan ta amma sai dai me rai yayi halin shi, Dara ta rasa mi take dadi mutuwar baby take ji ko bakin ciki duk abinda Tanimu ya shuka hakan be sa taji tsanar ya'yan shi ba. Bayan sultan ya gama ma Nihal wanka yana kokarin daukar ta nad'e ciki towel ya fara jin knocking ya dan basar jin wayar shi na ringing ne, yasa ya aje Nihal yana cewa, "hayaty bari naje na dawo ki fara yin alwala, zan aje maki komai da zaki bukata nayin sallah sai ki rama salollin ki, nima Dana dawo zanyi fresh up nayi sallah" to Nihal tace mashi cikin sanyi murya sannan ya fito bedroom ganin number Ammar ya sashi ficewa dan bude masu kofa, Nihal kuwa alwala ta dauro dan gabatar da sallah ko da ta fito sultan ya aje mata After dress da milk hijab babba ya shinfid'a mata prayer mat shiryawa tayi tsaf ta kabara sallah tun cikin sallah cikin ta ke juyawa daurewa kawai take ga wani irin jiri dake dibar ta har ta idar da sallah mikewar da zatayi jiri ya debe ta ba tayi masauki ko ina ba sai saman fafadan kirjin sultan a sume talabo sultan yayi a firgice yana cewa, "hayaty..! Hayaty..! Nihal..! yana jijiga ta iya kar rudewa sultan ya rude dan wannan karan kuka yake sosai tamkar karamin yaro ya rasa yarda ma zeyi da ita dan ya manta shi din likita ne, murya shi ne da su Ammar suka juyo a rikice ne ya sasu haurawa sama shi da Basmal hali da suka tsinci sultan a ciki da Nihal ya matukar razana su da kyar Ammar ya karaso gaban sultan dake kuka rike da Nihal a rikice Ammar yace, "sultan me ya same ta? kuka sultan yake yana cewa, "bata motsi zata mutu ta barni Ammar, help me Ammar" ganin yarda hankali sultan ya tashi yasa Ammar sasauta muryar shi dan ya kwantarwa sultan da hankali yace, "asibiti zamu kai ta yanzu-yanzu kaji" sultan da ya zama tamkar saban kamu d'agowa yayi da jajayan idanuwan shi yace, "bata mutu ba baza ta mutu ba ko Ammar eh zamu kai ta asibiti..! yana maganar yana shafa kumatun Nihal Basmal kuwa kuka ta saki Ammar da idanuwan shi sun cika da kwalla yace, "toh dauke ta muje kaji" kamar karamin yaro sultan ya dauki Nihal da sauri suka fice daga gidan cikin mota suka sa Nihal sultan na makale da ita Ammar ya ja mota da gudu zuwa asibitin kauyan. Suna zuwa asibiti da sauri nurses suka fito amsar Nihal har a lokacin sultan na kuka wasu kuwa sakin baki sukayi babban likitin da suke gani a TV yau gashi cikin asibitin garin su da Ammar aka shiga da Nihal dan bata taimakwan gagawa, zama sultan yayi yana ta kuka a hankali Basmal ta rungume shi tsam a jikin ta tana shafa bayan shi tana cewa, "kukan ya isa haka yayana insha Allah Nihal zata samu sauki, ban san ka da rashin juriya ba Allah yana tare da kai yayana" jan numfashi sultan yayi yana cewa, "insha Allah hayaty tana tare da ni idan na rasa hayaty binta zanyi na fada maki bazan iya rayuwa babu Nihal ba am gonna die if I loose her" "Calm down..! Basmal take cewa tana shafa bayan sultan cikin sigar lallashi fitowar su Ammar ne ya katse masu hanzari mikewa sukayi a tare suka nufi Ammar jiki a mace suna cewa, "ya jikin nata? shuru Ammar yayi yana kallan sultan da zuciyar shi ke kara tsinkewa murmushi ya saki yana yace, "da sauki yanzu haka tana waiting room" dariya sultan ya saki mai had'e ta kuka da sauri ya kaiwa Ammar hug yana dariya ya zame jikin shi da sauri ya karasa dakin yana murda kofar ya hango Nihal kwance murmushi yake ta saki har dimple din shi na lomawa. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_Assalamu alaikum masoya SAUYIN RAYUWA ba zan gaji da baku hakuri a kan jina shuru ba network ne ke bani problem shiyasa, ko message basa shigo min sai a hankali ina ganin messages naku fan's ba damar reply ko nayi baya zuwa ina yin ku irin sosai din nan_* *Page: 133_134* A hankali sultan ya karaso gaban gadan da Nihal ke kwance har a lokacin yana sakin murmushi siraran hawaye na bi mashi kumatu, kama hannu Nihal yayi wanda ke makale da drip ya sakar mata kiss dayan hannu shi yana shafa cikin ta da shi, kneel down sultan yayi yana shafa kanta, a hankali Nihal dake kwance take bud'e lumsasun idanuwan ta ta sauke su kan sultan kallan shi take hawaye na gangaro mata, girgiza mata kai sultan yayi alamar ta daina kuka tare da sa hannu yana goge mata hawayan fuskar ta, nuna idanu Nihal sultan yayi da finger din shi yana cewa, "me nake gani kamar..! Sultan ya fada a dan razane a rud'e Nihal take kokarin taba kumatun ta dariya sultan ya saki har dimple din shi na lomawa ya hada hanci su waje daya dariya Nihal take cikin sanyin murya tace, "ka bani tsoro love na dauka wani abu ya sami fuska ta" ta ida zancan tana shafa gefan fuskar sultan murmushi ya saki ya daura hannu shi saman nata yana cewa, "ke din ce kinki daina kuka bana so kina kuka hayaty ina jin kukan har cikin zuciya ta hayaty a duk lokacin da kike zubar da hawayan ki zuciya ta kona take tana tafarfasa" shuru Nihal tayi tana bin sultan da idanuwan ta a hankali ya daura labban sa saman lips din Nihal yana kissing nata, gyaran murya da akayi ne yasa Nihal rintse ido cike da kunya shima din yaji kunya yar dariya Ammar ya saki yana cewa, "lafiya ta samu sai a basu takadar sallama ko habibty? sun bar mu waje jiki a mace ashe su suna nan suna shan soyayya," dariya Basmal ta saki tana cewa, "masha Allah tunda lafiya ta samu dama fatan mu kenan ko sweetheart" Nihal kuwa tayi shuru sai sultan dake ta wasa ta yatsun hannun ta yana ta smile, Ammar ne ya ce, "dude bari naje nayi sallah ko sallah ban samu damar yi ba tunda muka iso garin nan," "Nima banyi ba muje muyi" sultan ya ida zancan yana sakarwa Nihal pack a kumatu ya ce, "me zaki ci? na taho maki da shi" lallausan murmushi ta saki tana kallan sultan tace, "komai..! "are you sure" "Yes" sannan sultan ya fice, yar dariya Basmal ta saki tare da sa hannu ta a fuskar Nihal tana cewa, "ya tafi kallan kofar ya isa haka sai a maido hankali waje na" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "to yar sa ido wallahi sa idan ki ya fiye yawa" far da ido Basmal tayi tace, "daga fadin gaskiya sai ace sa ido to a daina yi a gaba na sai na daina gani" "Tab di jam sai dai ki rintse ido kuwa" dariya mai sauti Basmal ta saki tare da ciro wayar ta dake cikin handbag ta kira su mom ta sheda masu suna asibiti Nihal ba lafiya hankali su ya tashi sosai amma Basmal ta kwantar masu da hankali da cewa da sauki su kwantar da hankali su. Bangaran su Dara bayan Sara ta sauka lafiya sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba wanka akayiwa jaririyar aka mata sutura aka sata cikin kwali liman da su maimartaba suka mata sallah aka wuce da ita makabarta da tsirarin muta nan kauyan kowa na tofa albarkacin bakin shi. lokacin da Sara ta farfado daga doguwar sumar da tayi koda taji labarin mutuwar baby tayi kuka wanda bata iya gane na bakin cikin ne kona farin cikin, wani bangaran na zuciyar ta kuwa ce mata yake kara da baby ta mutu saboda kyara da zata sha cikin al'umma ma kad'ai ya ishe ta, Dara nata lallashin ta da su Ammi sannan Dara ta tashi ta share gidan kwal da daki da Sara zata zauna wankan jego sannan suka shige gabaki daya su, Sara dai na zaune har a lokacin tana matsar kwalla su Ammi nata ban baki Nazili kuwa zaman duk ya ishe ta haka nan take daurewa duk ta matsu su tafi, kayan haihuwar Dara ta wanke tas, ta shanya ta hura wuta ta daura ruwan wanka, mom ce ta fita ta shedawa bafade ya samu masu ganyan bedi sai da suka gyara gidan tsaf ko ta kan su Baffa da gwoggo basu biba, sannan mom tace bari su je asibiti duba lafiyar Nihal Sara dake kwance ji take tamkar ta bi su taga lafiyar Nihal din, da sauri Nazili ta mike tayi gaba ga wayar ta dake ta faman ringing ta rasa wake kiran ta da new number yana takura mata cikin wanakin nan, suna fitowa waje suka sami Ashad yana waya da Nana sai zuba mata soyayya yake har yana cewa da sun dawo ze turo manya cike da shagwaba tana ce mashi ya bari sai tayi candy Ashad na cewa baze iya jira ba har nan da shekara daya ganin su Ammi ya sashi katse wayar yana smile, sannan suka shige mota gabaki daya dan zuwa asibiti aka bar Dara da Adda a gida suna kula da Sara. Nihal ce zaune sultan na feeding nata abinci hankali kwance sai shagwaba take zuba mashi sai ya zo bata abinci sai ya kauda spoon din yana dariya tana bin hannu shi tana turo baki, Ammar dake zaune Basmal ta daura kanta saman fafadan kirjin shi yana game da waya sai dariya suke masu suna cewa, "wallahi lafiya ta samu ya kamata su bar asibitin haka kafin yan kauye su ce an kawo masu yan iskan patients asibiti dama dazu da wata nurse ta shigo sai kallan su take tana zaro ido" dan shari na Basmal cewa tayi sultan ne ya mata" turo baki Nihal tayi tana cewa, "wallahi ya Ammar ta gani dama ta lura tunda ta shigo ya Ammar ke bin ta dana mujiya" dariya sultan yake yana kokarin cirewa Nihal drip din hannun ta ya ce, "to kin ji darling mijin ki ne ke kallan ta" zaro ido tayi tana kallan Ammar tace, "wai da gaske? Ammar zaro ido shima yayi yana cewa, "daga taya ku jinya sai a fara a hadi da matata tashi mu tafi mu kyale su tunda abin nasu har da sheri" dariya Nihal take har da hawaye musanman yarda Ammar yake magana a susuce dariya sultan yake tare da cewa, "hayaty kin hada mata da miji kina dariya ko, sai na ci je ki" sultan ya ida zancan yana dan ji ne mata kunnu ne yar kara ta saki mai cike da shagwaba, lakace mata hanci sultan yayi yana kissing din ta ko ta ko ina tana dariya, Ammar yace, "wallahi sultan baka da kunya na rasa ina ka aje kunyar ka" ya ida zancan yana wurga mashi bedsheets dake kusa da su dariya yayi yana cewa, "ai tana samun rest zan dauke abita mu cala ko hayaty? daga mashi kai Nihal tayi tana rike da hannu sultan sallama su maimartaba ce ta katse masu tunanin da sauri Ammi ta karaso bakin bed din tana cewa, "ya jiki Nihal sai muka ji ba kya jin dadi," Nihal da kanta ke sunkuye tace, "da sauki sosai," "masha Allah" nan mom da Gimbiya jalila suka matso suna mata sannu har da Nazili Ashad ma ya mata ya jiki na suka zauna suna ta nan da Nihal ko motsi tayi kad'an a tanbaye ta lafiya ko tana jin wani abu musanman mom dake tatalin cikin Nihal, haka Nazili ta saki jikin ta sosai wannan karan ba wani girman kai da nuna isa cikin su ta shiga anata zuba hira kiran sallah magrib ne ya tashi mazan zuwa masallaci matan ma suka fara haramar dauro alwala. Kwana biyu Nihal ta kwashe a asibiti saboda bed rest da aka bata suka dawo masaukin su bayan sun dawo ne Gimbiya jalila ke bama Nihal labarin cewa, Sara ta haihu abinda ta haifa be zo da rai ba Nihal bata jin dadin hakan ba, amma ta wani fanni taji dadi hakan dan tana bakin cikin a nuna yar uwar ta tayi cikin shege bare kuma ace ga diyar na raye mutuwar shine jin dadi su su duka duk da ba lalai fentin ya goge a zuri'ar su ba, amma bata jin zata iya zuwa gidan duba ta saboda har yau bata daina jin suyar abinda Baffa ya aikata ba Gimbiya jalila kuwa dama gulma ce ta ciwo ta, ta fesawa Nihal ganin ba'a da niyar fada mata shiko sultan bari yayi ta samu natsuwa sosai sai ya fada mata. Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru ciki har da shirye-shirye komawa kano da suke amma Dara shanono za'a barta har sai Sara tayi arba'in zata dawo, cewan Baffa kuwa ya kara tsanani, gwoggo kuwa hauka ba kama hannu yaro. Yau dai kam Sara ta gwadawa Dara tana san zuwa taga Nihal kodan ta kara neman gafara ta, tayi mata bankwana tunda gobe zasu wuce kano duk yarda Dara ta so ta hana ta sai ta gama wanka zata fara fita, amma Sara ta gwada tana san zuwa kodan tafiyar da zasuyi, ganin haduwar ta su nada mahimmanci yasa Dara cewa "to idan bala driver ya zo kawo min kaya na sai ki bishi ku je," cike da murna ta shirya cikin kodadiyar atamfar ta da hijab din ta tasha ruwa ta gaji bala driver yana zuwa kawo wa Dara kaya Sara ta bishi. Kasancewar gidan ba kowa sun fita zuwa gona daga nan su zagaye gari da maimartaba daga Nihal sai sultan ke gida Nihal na hada masu kaya cikin trolley a cewar su idan sun gama abinda suke zasu biyo su, kasancewar gobe suke sa ran komawa gida sultan na zaune saman bed yana dana system yana shan coffee Nihal dake kokarin wuce shi rike da shirt din shi zata saka cikin trolley, fisgo ta sultan yayi ta fada saman kirjin shi far da ido Nihal ta mashi tana cewa, "rigima ko ka bari na gama hada kaya nan kaji love idan na biye maka sai mu kai gobe bamu hada komai ba tun jiya kake min haka dana fara hada kaya sai ka hanani" binta da idanuwa sultan yake, ya amshe rigar hannun ta yace, "hayaty ki zauna ki huta zan cigaba da hada kayan bana so kina zarya kina wahala min da baby" yar dariya mai sauti Nihal ta saki tana zagaye hannu ta a wuyan shi tace, "love hada kaya ba wani aiki bane yanzu zan gama sai mu fita mu zaga gari ko mu bi su Ammi" Nihal ta ida zancan tana kashe mashi ido ta rarafa zata sauka daga saman bed jawota sultan yayi yana mata cakulkuli dariya Nihal take tana cewa, "na lura baka so na hada kaya" kwace kanta Nihal tayi tana daukar pillow tana tilawa sultan yana biyo ta yana dariya suna zagaye dakin tana mashi gwalo da gudu Nihal ta fice daga daki tana gudu tana sakowa daga stairs sultan na binta har suka iso main parlour a nan sultan ya samu nasara daukar ta cak yana juya ta tana dariya, knocking din kofar da akeyi ne yasa su natsuwa suna kallan juna cikin muryar mai dadi Nihal tace, "sauke ni na bud'e kofa ina tunani su mom sun dawo" makale kafada sultan yayi yana nufar kofar Nihal na cewa, "love ka sauke ni mana ka sani ko bakin kunya ne tana maganar," tana zaro ido kara matse ta sultan yayi yana cewa, "to minene matata ce na dauka" ya ida zancan yana kashewa Nihal ido ya murda kofar yana murdawa Nihal ta rintse ido turus sultan yayi yana bin Sara da kallo ita ma sakin baki tayi da hanci tana kallan shi tana kallan Nihal kamar ba yan kasa ba tana jinjina gata da Nihal ta samu da tatali, waro ido Nihal tayi ganin Sara ya sata durowa daga rukwan da sultan ya mata tana murmushi tana maida gashin ta baya cike da kunya tana kallan sultan tace, "Sara shigo mana kin tsaya bakin kofa" Nihal ta ida zancan tana murmushi pack sultan ya sakar mata a kumatu yace, "bari naje na dawo" toh Nihal tace, har a lokacin Sara na rab'e da kyar ta iya gaishe da sultan da ze wuce ta sannan ta ida shigowa tana bin parlour da kallo hannu ta Nihal ta kama ta ce, "shigo mana sai wani bin bango kike sai ka ce bakuwa" murmushi Sara ta saki ta shigo ta zauna saman kujera Nihal na dauke pillow din kujera da suka watsar sannan ta bud'e fridge ta ciro mata dirks masu sanyi da kayan marmari sannan Nihal ta zauna tana cewa, "ya muka ji da hakuri Sara? "an gode Allah" "Allah ya ji kanta" murmusawa Sara tayi tace, "Amin," Nihal tace, "ki ci mana ko ruwa naga kin kasa sha, ya umma" "Umma na nan Lafiya lau tana ma gaishe ki" zamowa Sara tayi daga saman kujera ta kama hannun Nihal dake zaune tana cewa, "bani da bakin da zan rukeki gafara abinda iyaye na suka maki Nihal na rokeki ki yafewa iyaye na ko zasu zamu sasaucin azabar da suke sha" hawaye ne suka gangarowa Nihal ta kauda kai tare da zame hannu ta dake cikin na Sara cikin sanyi murya tace, "idan dai ke ce Sara na yafemaki amma maganar su Baffa mu daina ta please karki yanke mana farin cikin da muke ciki yanzu" Nihal ta ida zancan hawaye na gangaro mata shuru Sara tayi hawaye na wanke mata fuska bakin ta na rawa tace, "Nihal..! daga mata hannu Nihal tayi tace, "bana san irin wannan maganar idan har kin san ita zaki min kofa bude take kina iya tafiya idan kuma ba ita bace ki zauna mu cigaba da hira mu cikin jin dadi" Nihal ta idan zancan tana murmushi yake shuru Sara tayi tana bin Nihal dana mujiya, ba yarda Sara ta iya haka ta ja baki tayi shuru ko jan ta a jiki da Nihal ta keyi tayi kokari ba kadan ba nan Sara ta saki ciki tana cin kayan marmarin da Nihal ta kawo mata tana ci Nihal na jan ta da fira sama-sama har ta gama ci kiran sallah la'asar ne ya tashe su tare suka gabatar da sallah bayan sun idar Nihal ta ja Sara bedroom trolley din ta Nihal ta bud'e tana murmushi ta cire kayan sultan dake ciki, ta fara zaro nata tana gwadawa a jikin Sara tana murmushi ganin yarda kayan suka mata kyau yasa Nihal jawo Sara gaba dressing mirror tana murmushi Sara ma murmushi ta saki mai had'e da hawaye tana jinjina alkairi irin na Nihal cikin muryar ta mai dadi tace, "shiga toilet ki gwada" haka Sara ta shige toilet ta gwada kayan ta fito tana bin bango washe baki Nihal tayi tana cewa, "masha Allah kayan sun maki kyau" jawo hannu Sara tayi tana juya ta tana murmushi tace, "kayan sunyi maki kyau sosai" murmushi Sara ta saki tace, "na gode Nihal bani da bakin da zan gode maki" Sara ta ida zancan tana sakin kuka bata fuska Nihal tayi ta ce, "bana san irin haka Sara" ta ida zancan tana rungume ta haka Nihal ta ta kwashe kayan sultan dake cikin trolley din ta gabaki daya kayan ta taba ma Sara har da trolley din, kala biyar kawai ta bari suma saboda ta samu na canza wa anjima sai kuma kayan da zata sa gobe su tafi godiya Sara ta rinka zubawa Nihal tana hana ta har su Ammi suka dawo gida Sara nan sai kusan yamma likis Nihal tasa driver ya sauke Sara gida. Tunda driver ya aje Sara ta fara ganin yan unguwar tsaye a kofar gidan su sunyi cirko-cirko da alama gulma ake, gaban tane ya yanke ya fadi, da gudu ta karasa ciki abinda ta ganine ya sata shock Baffa ne mace a tsakar gida Dara na gefe tana rokwan liman ya taimaka ayiwa tanimu sutura kowa ya kasa daukar gawarshi saboda yarda yake wari naman jikin shi na zagwayowa, wasu irin hawaye ne suka wanke ma Sara fuska daga daki ana juyo ihu gwoggo na hauka gefe guda kuma yan unguwa na zagin su har suna cewa dama irin wannan mutuwar ta dace da tanimu kowa na fadin albarka cin bakin. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo```[3/6, 2:18 PM] Sister: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUW* 🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *page: 135_136* Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un Sara ke anbata ta rushe da kuka tana kallan Dara dake faman rokwan liman ya amshi gawar Baffa gefe gudu yan unguwa na fadin albarkancin bakin su marasa dadi, Dara kuwa kuka take sosai har cikin zuciyar ta take jin ta yafewa Tanimu duniya da lahira domin Allah yayi kuncin tun a nan gidan duniya, duk yarda Dara taso liman ya amshi gawar Baffa ayi mashi sutura fir yaki haka liman ya fita Sara ta bi shi a baya bakin kofa ta duke tana gunjin kuka Dara dake gefe tace, "ni yanzu ya zamuyi da gawar yaya" Sara da dake gunjin kuka tace, "koma me ya faru Baffa shi ya ja mana, tun a nan gidan duniya gawar shi ta fara wulakanta" "Kul karna kuma jin irin wannan furucin a bakin ki addu'a akewa mamaci ba fadin maganganu mara sa dadin jin ba, ko duniya zata fadi magana mara dadi ke mahaifin ki ne addu'ar ki yake bukata, Allah ya ji kan yaya ya gafar ta mashi" Sara dake kuka tace, "Amin" ganin ba sarki sai Allah yasa Sara fita da gudu zuwa masaukin su Nihal, kafar ta ko takalma babu har ciwo taji a kafar ta amma bata damu ba burin ta ta isa masaukin su Nihal tana gudu yan gari na nuna ta da baki. Gabaki dayan su zaune suke a parlour anata raha kallo daya zaka masu kasan suna cikin farin cikin wasu na fira wasu na shan coffee kowa cikin fari ciki yake maimartaba da waziri suna gefe suna hira, sultan kuwa yana makale da Nihal sai alama take mashi da ido saboda rashin kunyar dayake zubawa dan shi ko a jikin shi kamar ba su mom a wajan yarda yake mata sai kace ita kadai ce mai miji, har d'an bige shi take tana ture shi idan ya kawo mata hannu duk abinda ke hannu ta sai ya kai bakin shi ya cinye sai dariya su Ashad suke mata yarda sultan ke mata sangarta sai ka ce karamin yaro, bango kofar da kayine ya sasu juyowa lokaci daya suna kallan Sara dake bakin kofa tana kuka da sauri Nihal ta aje cup din dake hannu ta ta karasa gaban Sara, kuka Sara ta saki ta fada jikin Nihal a rikice Nihal tace, "me ya faru kike irin wannan kukan Sara, wani abu ya same ki bayan tafiyar ki gida? Nihal ta ida zancan tana kallan kofa ta talabo da fuskar Sara da tayi shabe-shabe da hawaye cikin sarkewar harshe Sara tace, "ban taba ganin wulakanci da cin mutunci irin na yau ba, ban taba tunanin akwai rana irin ta yau ba" Sara ta ida zancan tana tsana ta kuka Nihal da ta rude itama ji take kamar tayi kuka saboda duk wanda yaci mutucin Sara tamkar yaci nata ne, cikin kuka Sara ta ce, "Allah yayiwa Baffa rasuwa amma gawar shi ta kasa samun arzikin sutura, kowa tir yake da gawas Baffa da tofin alatsine a kanta" Sara ta ida zancan tana kuka durkushewa Sara tayi gaban Nihal tace, "tun a duniya Allah ya fara hukunta Baffa dai-dai da laifin shi amma na rokeki ki yafewa Baffa ko ya samu sasauci ki daure ki yafewa Baffa ko nauyin muta nan daya zalunta zai ragu a kan shi..! Nihal da hawaye ke gangaro mata da gudu ta bar wajan kuka Sara ta saki tana cewa, "yanzu Nihal baza ki yafewa Baffa ba, karki manta hannu ka baya rubewa ka yanke Nihal..! Da sauri Sara ta rarafa wanjan maimartaba tace, "na rokeka ran ka ya dad'e a taimaka ayiwa Baffa sutura wallahi muta nan gari sun ki amsar gawar Baffa dan Allah a taimaka ayiwa Baffa sutura" tausayin Sara lullube maimartaba yayi sosai mom ce ta daga Sara tana lallashin ta sannan su maimartaba suka fice dan zuwa yimawa Baffa sutura a kai shi makwancin shi. Nihal na shiga daki saman bed ta fada wani irin kuka ya kwance mata tana jin da kamar wuya ta iya yafewa Baffa shi da gwoggo, dan iya kar cutarwa sun mata sun rabata da Abba da umma anya kuwa zata iya furta kalmar ta yafewa daya daga cikin su, kuka Nihal ta kuma saki wani bari na zuciyar ta na cewa da Abba na da rai da tuni ya manta ya yafewa Baffa saboda dan uwan ka dan uwan ka ne, kuma hannu ka baya rubewa ka yanke duk abinda Baffa yayi ma Abba ya tsaya anyiwa Abba sutura da umma, kamar an mintsine ta mikewa Nihal tayi ta jawo hijab din ta ta saka tana kokarin fitowa taci karo da sultan zai shigo wani irin dadi ya ji ganin Nihal din ta fito bude mata hannu yayi ta shige jikin shi tana sauke a jiyar zuciya a hankali sultan ya furta "Allah yayi maki Allah albarka, Allah yana san masu yawai ta yafiya ki daure ki kasance a cikin muta nan da Allah ke so ki manta duk abinda yafaru ki yafewa Baffa" Nihal da tayi lamo a fafadan kirjin sultan tana jin kalaman shi, dai tace komai ba sannan suka fice a tare. Ganin maimartaba yasa yan gari fitowa suma ba duka ba tsili-tsili liman ya zo yana ta yan kame-kame haka akayiwa Baffa sutura aka mashi sallah aka wuce da shi makwancin shi Nihal kuwa ganin gawar Baffa ta girgiza Nihal tabbas Baffa yayi wulakantaciyar mutuwa har cikin zuciyar ta take ji ta yafe mashi duniya da lahira haka aka cigaba da zaman makoki. Bayan sadakar uku su Nihal suka koma kano har da Dara aka bar Sara na kula da gwoggo kullun haukar gwoggo kara tsanine ta ke ba alamar sauki, haka Sara ke daurewa tana kula da ita dan ba karamar fama dake da gwoggo ba hauka take tuburan, saukin ta daya kama daga kan abinci har zuwa na sha ba abinda Sara ta nema ta rasa ta kara natsuwa da hankali tana mai cigaba da kulla da gwoggo. Rayuwa ta cigaba da tafiya da dadi ba dadi wasu na fari cikin wasu akasin haka, Nihal kuwa sosai take samu kulawa da tatali wajan mijin ta yanzu haka cikin ta nada wata uku na Basmal wata shida tare suke renan cikin su, cikin gata da kulawa Nihal kuwa ta rasa wayafi wani nuna mata gata kama daga kan maimartaba har Gimbiya jalila wadda yanzu ta zubar da makaman ta musanman yarda taga darasi a kan Baffa wannan dalilin yasa ta natsu ta shiryu, Nazili kuwa tuni ta nemi gafara Nihal sun shirya, sai dai har yanzu ba ruwan ta da samari da kyar ta iya yaki da zuciyar ta ta cire san sultan a zuciyar ta acewar ta lokaci ne da Nihal zata samu gata da farin cikin, ba wace tafi dacewa da sultan sama da Nihal dama ba komai kake nema a duniya ka samu ba ta maida hankali ta kan kasuwancin ta dan ko zama batayi a kasar. Bangaran karatun Nihal kuwa na tafiya yarda ya kamata yanzu haka shirye-shiryen zana wessce suke karatu suke ba kama hannu yaro dan ganin cewa sunci paper. Nihal ce zaune saman three star a part din Ammi tana shan ice cream da alama tana jin dadi ice cream din musanman yarda take kad'a kai Ammi tana cewa, "bari dai sultan ya dawo ya same ki kina shan ice cream din nan yanzu ya fara fada," turo dan karamin bakin ta Nihal tayi tana cewa, "yanzu zan shanye kafin ya shigo ki dinga kallan min kofa Ammi," "ni ba ruwa na" sallama Ashad ne ya katsewa Ammi zancan gaishe da Ammi Ashad yayi tare da zama saman one star Ammi tace "yau ka dawo da wuri kenan? eh Ashad yace yana kallan Nihal yace, "big aunty dadi ake ta sha kenan? washe baki Nihal tayi tana kallan robar ice cream din dariya Ashad ya saki ya ce, "bari yaya ya dawo sai na tona kina shan sanyi bayan ya hana ki" zaro ido Nihal tayi can kuma ta saki dariya tana cewa, "kana tonawa nima gobe Monday ina zuwa makaranta zan bata maka wasa" Nihal ta ida zancan tana daga gira, zaro ido Ashad yayi yana cewa, "kar muyi haka aunty wasa nake maki kema kin san ba tonawa zanyi ba" "na dauka da gaske" Nihal na magana tana dariya Ammi tace, "idan tayi tsami zamu ji na rasa mi ya aje a makarantar nan taki kullun sai ya zo nan gulma, yana maki ladabin yan kunama" dariya Ashad yayi Basmal da shigowar ta kenan ta ce, "ba kowa ke sashi ladabi ba sai..! da sauri Ashad ya toshe mata baki yana cewa, "to kazalaha me ya kawo ki nan part din ma for the first place," zame hannun ta Ashad Basmal tayi tana turo baki da tirtsetsan cikin ta tace, "toh kai me ya kawo ka? Basmal ta fada tana daga gira, "gaishe da Ammi ke kuma gulma ta kawo ki" dariya Basmal ta saki tana cewa, "ni ba shi ya kawo ni ba yaya dama chocolate cake nayi kuma nasan kana so shine na kawo ma naje part din ka baka nan na tanbayi momi tace min ka nan" Basmal ta ida zancan tana bud'e kwalin cake din washe baki Ashad yayi ya sa hannu ze ci Basmal ta balo ta bashi a baki yana ci har yana lumshe ido ya ce, "Darling kin kyauta kamar kin san na dade ban ci ba," murmushi Basmal tayi da cake din Basmal ta nufo Nihal da shi tana cewa, "kema ga naki" "ki aje min sai na gama shan ice cream zan ci" sultan ne ya shigo part din Ammi direct Nihal ya nufa Basmal sai alama take ma Nihal amma bata gani ba, rungume ta ta baya sultan yayi, har sai da Nihal ta razana saboda robar ice cream din dake Hannun ta, robar ice cream din da sultan ya ganine ya sashi hade rai tamkar bai ta ba dariya ba, amshe robar ice cream din yayi yana cewa, "wato na hana ki shan sanyi baza ki daina ba ko," shuru Nihal tayi tana raba ido a hankali tace, "am sorry bazan sake ba," sultan be ce komai ba ya kad'a kai tare da nufar Ammi yana cewa, "matar ya dai 2days naga sai wani fresh kike me sirrin far da ido Ammi tayi tace, "naki yin fresh tunda na sake miji, ni fa tuni na sake ku kai da Ammar saki uku uku na kama Ashad" dariya sultan ya saki yana cewa, "kin saki rashe kin kama ganye" dariya parlour aka dauka, Ashad na cewa, "kai yaya banda hadi mikake fadawa ammi wallahi bishiyar gabaki daya ta kama ba ganye ba" dariya kawai suke zubawa cikin fara'a amma har a lokacin sultan yaki kallan Nihal dan fushi yake da ita kan sanyin da take dirkawa kanta, salan ta samama baby su ciwan sanyi Nihal na lura da yanayi sultan duk sai taji bata kyauta ba tunda ya hanata ya kamata ta bari amma cikin nata ne yana masifar san sanyi, ita kanta tana mamakin yarda take ba sanyin mahimmaci yanzu ko bacci zasuyi sai ta kura AC koda sultan ya rage cikin dare sai ta lallaba ta kara. Da daddare Nihal ce tsaye gaban dressing mirror ta shirya cikin pink rigar baccin ta dai-dai gwiwa tana shafe jikin ta da humra, turo kofar da akayi ne ya sata juyowa sultan ne ya shigo cikin shirin shi na bacci ya haye saman bed, Nihal na kallan shi ta san har yanzu ba daina fushi yayi da ita ba saman bed din Nihal ta hau cikin sanyi murya tace, "love am sorry bazan sake ba" sultan dake jin ta yayi banza da ita tamkar ba magana Nihal take ba kuka shagwaba Nihal ta saki tana cewa, "am sorry love bazan sake ba ka ji please ka daina fushi dani, ashe zaka iya fushi dani haka" yarda Nihal ke kuka yasa sultan mikewa yana kallan ta rai had'e yace, "hold your sorry na lura baki san lafiyar ki da abinda ke cikin ki kuma ai ban ce maki komai ba amma sai ki hau kuka, bacci nake ji just leave me alone tunda baki san lafiyar ki na sha fada maki ki daina shan to much of sanyi but you refuse to stop" "Bazan sake ba love please ka daina fushi dani kar mala'iku su tsinemun daga yau ba zan kara shan sanyi ba" murmushi sultan yayi ya bude hannuwan shi yace, "oya come here" murmushi Nihal ta saki tana goge hawayan ta da sauri ta rarafa ta shige jikin shi yana cewa, "hayaty ki daina shan sanyi bana so kina shan sanyi, duk abinda kike so zan siya maki amma ban da abinda zai cutar da lafiyar ki, please ki rage shan to much of sanyi zai taba lafiyar baby mu" Sultan ya ida zancan yana shafa cikin ta "to bama zan sake ba" "good girl" kissing nata sultan ya shigayi ko ta ko ina yanayi mata salan shi mai rikitata itama Nihal biye mashi tayi suka Lula duniyar ma'aurata. Washe gari da safe bayan Nihal ta shirya cikin uniform din ta da taimakwan sultan ta shirya tana zuba mashi shagwaba, sannan suka wuce main parlour lokacin kowa ya halara sukayi break sannan suka wuce parking space sultan ne yayi dropping Nihal da kanshi a school duk sai da ya gama jagwalgwala ta san rashi sannan ya kyale ta, dan sam baya gajiya da ita har mamaki take yarda sam sultan baya gajiya da ita, sai da motar shi ta bar harabar makarantar sannan Nihal ta shige class. Zaune saman seat ta sami Nana da sharifa itama ta zauna suna gaisawa da sharifa suka gaisawa da Nana sama-sama yau dai kam Nana sai shan kamshi take Nihal na lura da yarda Nana ke ta hada rai yau ko magana kirki ta kasa, Nihal tace, "kawas yau kuma waya bata maki rai har laifin ya shafe ni tunda na shigo school yau kike ta hada rai ko Ashad ne ya maki laifi" tabe baki Nana tayi tace, "Ni fushi nake dake baki da kirki Nihal har yau kin kasa zuwa gidan mu amma ni naje yafi a kirga tun mama na tanbaya ta yau she zaki zo har ta daina kunya ma nake ji yarda muke ace wai har yau kin kasa zuwa gidan mu zuwa na gidan ku nawa ko dai sultan ne ke hana ki zuwa,? "laaa kawas ko daya wallahi ranar da zanzo ranar muka tafi shanono kuma ai na fada maki," "da kuka dawo me ya hana ki zuwa? zuwan Ashad nawa gidan mu wanda saboda ke na san shi," yar dariya Nihal ta saki tace, "ai shi nema yake dole ya zo kafin kwado ya mashi kafa," "na lura kin dau maganar nan wasa kin ga tafiya ta" Nana ta fada kasancewar an tashi break rike mata hannu Nihal tayi tana cewa, "haba kawas haba insha Allah zan zo kafin mu fara exam, karki bari su o'o su ji kan mu ayi mana dariya," sharifa dake gefe tace, "gaskiya Nihal baki kyauta ba ace duk abotar baki taba zuwa gidan su ba, har muna shirin gama makaratar gabaki daya ya kamata ki je gaskiya, ke kuma Nana kullun kina bin ta kamar jela ashe ko gidan ku bata taba zuwa ba" sharifa ta ida zancan tana dariya tsaki Nana ta saki tace, "to uwar hada gurmin in dai ni da kawas ne bame shiga tsakanin mu" dariya Nihal tayi tana shafa wa sharifa kai tana cewa, "anji ta idan an santa" dariya suka saki su duka sannan suka wuce break. Akwana a tashi ba wuya wajan Allah yau su Nihal suka fara exam, har lokacin Nana na mata bitar taki zuwa gidan su, ko magana ta daina yima Nihal dan fushi take da ita. Nihal ce da Dara a kitchen Nihal na yanka vegetable Dara na cewa da "kin je kinyi zaman ki Nihal kina bukatar hutu tunda dai gashi kin gama hada komai na cigaba da kula da sauran," "umma ki bari nayi komai da kai na bana san zama bana wani abu" "matsala ta dake daya ce idan kika fara aiki bakya gajiya kuma sai ki ce komai sai kinyi bayan ga ma'aikata yanzu vegetable din nan yaran dake kitchen din nan ya kamata ki ba su yanka, amma ke kin amshe kina tayi kuma kin san yarda sultan bai so ko kara kina dauka musanman da cikin ki ya fito" murmusawa Nihal tayi tana juye kayan miya a tukunya tace, "Allah umma na biyewa love ba abinda zanyi sai kwanciya, ko wajan awo ana cewa mu motsa jiki kuma fa ya sani" "Ai irin wannan aikin ne be so kina yi yafi so idan ya dawo ko zagaye gida ku motsa jiki.. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo ``` [3/6, 2:18 PM] Sister: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUW* 🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 137_138* Shigowar sultan kitchen ne yasa Dara sakin murmushi zatayi magana yayi mata alama tayi shuru, bayin dake kitchen fara ficewa daya bayan daya sukayi Nihal kuwa ko lura ba tayi da shi ba, tana faman juya miyar kwai da take, Dara ficewa tayi ba tare da Nihal din ta lura ba rufe mata idanu sultan yayi ta baya a razane Nihal take bin hannu sultan tana shafawa dadad'an kamshi turaran shine ya sheda mata masoyin na tane tana murmushi ta ce, "love na gane ka fa" zame hannun shi sultan yayi yana cewa, "uhm hayaty na dawo ba sannu da zuwa ba komai kina nan kina wahala min da kanki" hannu ta sultan ya kama suna juya miyar tare sannan ya rage gas din ya juyo da Nihal suna facing juna ya ce, "hayaty me yasa kike so ki dinga wahala min da kanki ne,? akwai fa masu yin aiki nan hayaty" Langwabe kai Nihal tayi cike da shagwaba ta zagaye hannuwan ta a wuyan sultan tace, "ina so na faran ta wa miji nane ko nayi laifi,? aiki da dake ba wani aiki bane love kuma bana so kana cin abincin ma'aikata" murmushi sultan yayi ya manna baki shi saman lips din ta, dan ture shi Nihal tayi tana dariya tace, "love a kitchen fa muke kowa na iya shigowa" Nihal ta ida zancan tana juyawa daura kanshi sultan yayi a kafadar Nihal yana shakar kamshin ta mai dadi yana shafa cikin ta wanda ya fito yace, "to minene hayaty idan an ganmu ba tare da matata aka ganni ba" sultan ya ida zancan yana shinshina wuyan ta. Yadda sultan yake mata ne yasa hannu ta kama rawa ta saki spoon din hannu ta tace, "love a kitchen fa muke please ka daina kana so miya na ta kone ko" Nihal ta ida zancan tana turo baki, lakace mata hanci sultan yayi yace, "na bari, bana so wannan dadad'an abincin ya kone ba" murmushi Nihal tayi kusan tare sukayi aikin kitchen din bayi kuwa na waje suna tsegumi, India sabo ya kamata su saba amma had yau sun kasa sabawa. Yau dai kam Nihal ta gaji da korafin da Nana ke mata kan bata zuwa gidan su, yau dai ta kira ta ta sheda mata zata zo murna wajan Nana ba a cewa komai, haka ta shedawa mama sannan tasa larai mai aiki tayiwa Nihal tuwan shinkafa miyar taushe, kasancewar favorite din Nihal ce tunda ta samu ciki bata da abinci sama da tuwan shinkafa miyar taushe. shiryawa Nihal take cikin less din ta brown mai ratsin flowers dark brown wanda akayiwa dinkin bubu dikin ya matukar amsar ta ya mata kyau sosai, tsantsara kwalliya Nihal tayi sosai tayi dauri mai kyau ya zauna a kanta das ta yafa veil din ta dark brown tasa flat shoe din ta black da handbag, murda kofar da akayi ne ya sata juyowa tana sakin murmushi tana kallan sultan dake tsaye bakin kofa ya shirya cikin brown shada shi tasha aiki da dark brown zare dinki ya kama jikin shi yayi kyau har ya gaji kan shi na sanye cikin hula dark brown da ratsin light, kusan colours din kayan su iri daya hakan sai ya kara fitowa da zalan kyan su, duk wanda yaci nasara ganin su wannan lokaci ya san masoya ne masu tsantsar san juna su musanman yarda sultan ya kafe Nihal da idanu shi masu rikita mata lisafi yana mata smile karasowa sultan yayi gaban ta yana cewa, "muje ko kar yamma tayi Nana tayi tunanin kin fasa zuwa" murmushi Nihal tayi tana cewa, "yanzu kuwa ta gama kira na tana cewa kar na shuka ta" tare suka fito gwanin ban sha'awa sultan da kan shi ya ja motar suka bar harabar gidan. Sai da suka fara biyawa shoprite sukayiwa su mama siyaya acewar sultan basa je hannu biyu ba, daga nan suka wuce jan bulo unguwar su Nana basu wani sha wahala gane gidan ba saboda sunyi anfani da location horn sultan yayi mai gadi ya wangale masu geta sultan ya shige da motar shi yayi parking motar a parking space dan murmushi Nihal tayi tana cewa, "yau dai mun zo, kora fi ya kare" su shukura dake wasa a compound suna ganin Nihal suka gane ita ce da gudu suka nufo motar suna cewa, "aunty Nihal oyoyo" bale murfin motar Nihal tayi tana cewa, "love bari na shiga amma ka jira ku gaisa da mama kafin ka wuce" ta ida zancan tana kokarin fita jawota sultan yayi yana nuna mata kumatun shi murmush Nihal ta saki ta sakar mashi pack a cheeks din shi, lips din shi ya nuna mata makale kafada Nihal tayi tana kokarin fita daga motar fisgo ta sultan yayi ta fada saman fafadan kirjin shi ya sakar mata kiss a lips din ta murmushi Nihal ta saki tare da ficewa, su shukara suka karaso suka rungume Nihal sai murna suke sannan ta bud'e back seat ta ciro siyayar da ta masu ta mika masu da gudu suka shige gida suna kwalawa Nana kira. Nana dake zaune tana kallo a parlour ta jiyo ihu su shukara suna cewa, "aunty Nana ki zo Aunty Nihal ta zo" da sauri Nana ta mike tana cewa, "oyoyo kawas kai amma naji dadi" da sauri Nana ta ruga ta rungume Nihal tana cewa, "kin cika alkawari wallahi da na dauka baza ki zo ba dana ga har four ta wuce" "na isa na ce zan zo na fasa na hadu da bitar ki, yanzu dai ina mama? "ai fa ko zama ba kiyi ba na cika ki da surutu" "mun cika juna dai" "mama na bedroom yanzu nan ta shiga wanka zauna" kitchen Nana ta shiga ta kwaso wa Nihal kayan motsa baki ta cika tray da su ta dawo parlour ta aje mata sannan ta koma kitchen ta dawo dauke da tray din abinci ta aje tana cewa, "bari na kira mamar nasan yanzu ta fito daga wanka" "to Nana amma duk wannan kayan da kika jibge min a gaba ni da wa,? harara Nana ta maka mata "bari na dawo sai ki fadi min baki ci kaitsaye kiga yarda zanyi dake" dan murmushi Nihal tayi Nana ta haye sama dan kirawo mama su gaisa. Aunty Aisha ce tsaye gaban dressing mirror tana murza hoda sanye take ciki tsadadan atamfar ta wanda ta amshi jikin ta Nana ta shigo daki tana cewa, "mama Nihal ta zo tana parlour tunda ta zo take tanbayar ki tana so ku gaisa" "toh ki ce mata gani nan zuwa naga d'iyar tawa" to Nana tace tare da ficewa ta koma parlour tana cewa, "ina babba yaya tare da shi kuka zo kuwa? "eh mana tare muka zo" "shine sai ki bar shi waje? ki ce mashi ya shigo mana" "dadi na dake sauri ki bari mama ta fito mu gaisa ai, shima sai ya shigo su gaisa" "haba kawas kin bar shi waje ko ba komai yayan miji nane" dariya Nihal ta sheke da ita tana cewa, "to uwar azarbabi ki bar a daure tukun" duka Nana ta kaiwa Nihal tana dariya gocewa Nihal tayi tana cewa, "sai na fadawa love kin dake ni" ganin Nana ta matsa kan bai kamata ta bar sultan waje ba yasa Nihal mikewa cike da raha ta fice ta sami sultan a waje ya biyewa su shuraka suna ta zuba mashi surutu, murmushi Nihal ta saki mai kara mata kyau tace, "love mu shiga ciki ku gaisa da mama" to sultan yace tare da kama Hannun shukara suka bi bayan Nihal. Koda mama ta fito Nana ta samu a parlour tace, "ina daughter tawa? "Taje ta shigo da sultan tare suka zo ta bar shi waje shi ne na ce bai kamata ta bar shi waje ba" murmusawa mama tayi tace "kin kyauta kuwa a bar mutum waje ko parlour baki ai ya zauna" Abinda ta ganine yasa Nihal daskarewa tsaye, tana bin Aunty Aisha da kallo idanu ta cike da kwalla, anya da gaske aunty Aisha ta gani ba mafarki take ba kuwa, Aunty Aisha ma ganin Nihal ne ya katse mata zance a zabure ta mike zuciyar ta na lugude tana kallan fuskar Nihal duk da Nihal ta goge tayi fresh hakan be sa ta mance kamanin ta ba, tsayawa cak Nihal tayi ta kasa gaba ta kasa baya sai idanu ta dake waje cike da kwalla tana kallan Aunty Aisha, sultan dake bayan ta ganin yarda ta tsaya cak yanayin ta ya sauya alamar ba lafiya juyo da ita sultan yayi har a lokacin idanu ta waje jijiga ta sultan yayi yana tanbayar ta lafiya, bakin ta na rawa tace, "Da gaske aunty Aisha nake gani kanwar umma love da gaske ita nake gani ba mafarki nake ba," kallan Aunty Aisha sultan yake itama ta daskare waje daya hawaye na wanke mata fuska tace, "ba mafarki kike ba daughter da gaske ni ce kika gani" ragowar hawayan dake makale a idanu Nihal ne suka gangaro tana cewa, "ita ce aunty Aisha da nake fada ma saboda ita na zo birni" murmushi ne ya subucewa sultan yana gogewa Nihal hawayan ta yana cewa, "ba kuka ya kamata kiyi ba godewa Allah zakiyi da ya hada ku" murmushi take wasu hawayan na kara biyu kumatun ta, aunty Aisha da hawaye ke mata anbaliya tace, "Ashe ina da raban sake ganin ki a idanuwa na Nihal ashe labarin diya ta Nihal na dade ina ji" Nana dake gefe mamaki ya lullube ta ta kalli Nihal ta kalli mama, da sauri Nihal ta nufo aunty Aisha haka aunty Aisha rungume juna sukayi tare da saki kuka a tare dago da fuskar ta mama tayi tana kissing kumatun ta tana kallan Nihal tace, "Ashe kina raye Nihal babu irin neman da bamuyi maki ba dan ganin cewa kin dawo gare mu" mama tana maganar siraran hawaye na mata zarya a hankali Nihal ta daura hannu ta saman na aunty Aisha tana cewa, "ba mafarki nake ba ashe na dade ina tare da yar uwa ta ban sani ba ashe akwai ranar da zan saku a idanuwa na" share mata hawaye Aunty Aisha tayi ta zaunar da ita suna facing juna murmushi ne ya subuce masu lokaci daya aunty Aisha na makale da hannu Nihal tace, "Allah mai iko Allah na gode maka daka amshi addu'a ta," kallan sultan mama tayi dake tsaye tana murmushi tace "zo ka zauna d'a na" kasa da kai sultan yayi yana sosa keya ya duka har kasa cikin ladabi ya gaishe da mama, mama da bakin ta ya kasa rufuwa ta amsa da wani shauki tace, "ina zuwa ya kamata Abban Nana ya ji wannan dadadan labarin da su yaya sani" mama ta ida zancan tana ciro wayar ta. Nana kuwa mamaki ya hana ta magana da kyar ta iya furta, "dama ke ce yar uwar tawa da su mama suke nema ido rufe" wani irin murmushi Nihal ta saki tana daga mata kai da sauri Nana ta karasa gaban ta ta rungume ta cike da murna. Dawowa aunty Aisha tayi ta zauna tana smile tace, "yaya sani na kan hanyar zuwa ya zo yaga wannan albishir Nihal ta dawo gare mu, saki jikin ki daughter haka kai ma son ko ruwa baku sha ba" murmushi kawai su Nihal ke zubawa musanman Nihal da farin ciki ya mamaye zuciyar ta. Koda su yaya sani suka zo sukayi tozali da Nihal zo ku ga murna Nihal kuwa taga gata wajan su baba sani har da baba khabir wanda duk abinda ya faru baya kasar dan jiya ya dawo kasar, dama sunyi maganar Nihal da aunty Aisha kan zasu cigaba da bincike har Allah yasa a gano ta koda gawar ta ce, sai gashi yau Allah ya bayana ta gare su, bayan komai ya nitsa Nihal ta kwashe duk abinda ya faru da ita ta shedawa su mama sai dai ba tayi gigin fada masu auran dole akayi mata da sultan ba, sun tausaya mata sosai tare da ganin namijin kokarin sultan daya aure ta da su kan su iyayan nashi, Nihal taga soyayya da gata kowa nan yake da ita hatta sultan yaga so sai zuba mashi godiya suke kan rike masu daughter da yayi amana ya bata kyakyawar kulawa kunya kuwa ta hana sultan cewa komai, sallah magrib ne ya tashe su zuwa masallaci su Aunty Aisha suka wuce bedroom dan dauro alwala. Bayan sun idar da sallah mama na kokarin cire hijab din dake jiki ta tace, "amma dai tanimu ba shi da imani ko kadan shiyasa san da yaya sani ke so a saurara mashi naki yarda saboda kwata-kwata hankali na be kwanta da shi ba Allah dai ya sauwake" Amin Hajiya farida tace da Nana mama ta cigaba da cewa, "shi kuma wannan yaro ya matukar kyautawa bamu da abinda zamu iya cewa family din shi sai Allah ya saka masu da alkairi" gabaki daya suka amsa da Amin sannan suka baje suna ta fira har aka kira isha suka gabatar da sallah. Nihal kuwa taga tatali da gata dan kuwa sun rasa ina zasu tsoma ta saboda tsabar murna, aunty Aisha kuwa cewa tayi sultan ya bari su kwana gobe da safe sai su tafi gabaki dayan su gidan dan su kara mika godiyar su wajan maimartaba da Ammi dan ba karamin halaci suka masu ba, hakan yasa sultan cewa to sannan ya kira su mom da maimartaba ya shide masu sosai sun taya Nihal murna. Daran yau kuwa hira kawai suka sha da aunty Aisha tana kara jinjina kokarin irin na su maimartaba da halaci da sukayiwa diyar tata, Nihal kuwa dakin mama ta kwana su uku sultan kuma da Abban Nana ya kwana cike da kewar Nihal din shi, haka itama Nihal din duk hira da ake cikin nishadi hakan be hanata kewar sultan ba musanman yarda ta sama kwana saman fafadan kirjin shi. Washe gari da safe bayan Nihal tayi wanka ta cancada ado cikin wata black after dress din da mama ta bata mai kyan gaske, kayan breakfast mama ta mika mata a tray ta kai wa sultan bedroom dan ta lura kunyar su yake ji tun jiya, cike da kunya Nihal ta amshi tray din ta nufi dakin. Dauke da sallama Nihal ta shigo dakin sultan dake tsaye gaban dressing mirror yana shiryawa ciki wata white jallabiya yana kokari makala agogo a tsintsiyar hannu shi, murmushi mai kara mata kyau Nihal tayi tace, "ina kwana love" "lafiya lau hayaty" sultan ya ida zancan yana amshe tray din hannu Nihal ya aje saman stool sultan ya jawota jikin shi ya ce, "wato ke dadi yan uwa yasa gabaki daya kin manta dani daran jiya na kasa bacci saboda missing na ki" dan murmushi Nihal tayi tana hada mashi tea tace, "nima nayi missing naka love" "ba wani kinyi missing nawa na kira ki yafi a kirga baki dauka ba ko good night baki min ba" "Love ni kai na ban san ina na aje wayar ba ina tunanin a parlour na barta" Nihal ta ida zancan a shagwabe "toh shikenan muna nan dake zan kwace su mama su zama nawa di kad'ai" dan karamin bakin Nihal ta turo cike da shagwaba mintsine mata baki Sultan yayi yar kara Nihal ta saki mai cike da shagwaba hada bakin su sultan yayi yana kissing nata sannan ya sake ta dan kan shi yana cewa, "yanzu ya daina zafi ko" daga kai Nihal tayi tana feeding sultan breakfast. Bayan sun gama karyawa gabaki daya muta nan gidan suka dunguma zuwa gidan maimartaba, cikin mutunci da mutuntawa maimartaba ya tarbe su haka su mom su baba sani sunyi godiya sosai nan maimartaba ya kara gwada masu ba komai duk yima kaine, Ashad kuwa kan shi kato ya karayi dan gani yake tamkar ya malaki Nana a matsayin mata wunin ranar zungur cikin nishadi da jin dadi sukayi shi musanman Nihal tafi kowa murna wannan rana. Bayan kwana biyu rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi inda su Nihal suka kamala jarabawar su ta SSCE Nihal ta amshi kyaututu ka sosai ranar speech and prizes giving day Amal da nawwara ma sun dawo gida, gidan sai ya kara dadi ya kara kacamewa. Bayan kamala jarabar su Nihal da wata biyu Basmal ta haifi baby boy din ta ranar suna ya ci suna waziri ana kiran shi da khalifa, murna wajan wannan family ba'a cewa komai Nihal kullun tana part Adda kasancewar a nan Basmal ke wanka, Sara ma ta zo suna a ranar suna ta hadu da wani abokin Ammar wanda matar shi ta rasu ta barshi da ya'ya hudu tunda ya kyala ido yaga Sara hankali shi ya kwanta da ita. Washe garin suna koda zata koma shanono shi ya kaita har yana cewa shi bada wasa ya zo ba, so yake ayi bikin su bada jimawa ba tunda shi ba saurayi bane, Sara kuwa ce mashi tayi zatayi tunani a kai, dan tana jin tsoran sake mashi kar yan kauye su falasa abin kunyar data aikata ko shanono daya kawo ta bada san ranta bane, su Nihal ne suka matsa mata suna nuna mata Sunusi yayi ita kanta ta san yayi dan sunusi ba ajin ta bane kwata-kwata dan dai so ba yarda baya zuwa. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo`[3/10, 2:14 PM] salma😝: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 139_140* Bayan suna da kwana biyu Gimbiya jalila ta sami maimartaba kan maganar Nana sosai maimartaba ya ji dadin zancan, dama Sultan ya zo mashi kan maganar Sunusi dake neman Sara sai a had'e bikin ayi lokaci daya, Gimbiya jalila ta dan jima a part din maimartaba suna tattaunawa da maimartaba kasancewar ranar girkin ta ne. Nazili ce tsaye a bedroom nata da alama yanzu ta dawo daga wajan aiki wayar ta dake cikin handbag ce ta fara ruri, inda sabo ya kamata ta saba da wannan kira da ake mata da bakuwar number, ko ta dauka ba a magana d'an siririn tsaki ta ja tana kokari wurgi da wayar, turo kofar da akayi ne ya katse mata hanzari, Aziza ce ta shigo kai sunkuye ta ce, "ran ki ya dade maimartaba yace ki same shi a fadda" jim kadan Nazili tayi tana mamakin wannan kira da maimartaba ke mata a hankali ta furta, "gani nan zuwa" jiki a mace ta canza kaya zuwa duguwar riga blue har kasa ta saka silver alkyaba ta wuce fadda. Zaune saman kujera mulki ta sami maimartaba zaune, ciki ladabi Nazili ta gaishe da maimartaba dake zaune, har sai da yayi mata nuni da mazauni ta zauna har a lokaci gaban ta na tsana ta faduwa ya ce, "Nazili..! Nazili...! yanayin yarda maimartaba ya kira suna ta yasa jikin ta mutuwa mudus dan maimartaba bai fiye kiranta da suna ta ba, kara kiran suna ta yayi karo na uku dagowa Nazili tayi ta maida hankalin ta kan maimartaba tana wasa da yatsun hannu ta ya ce, "sau nawa na kira suna ki? "sau uku Abba" "Ina fatan abinda zan fada maki zai zauna a kunna ki, tun ba yau ba nake maki magana kan ki fito da miji kiyi aure amma kin rintse ido ke a'a, har Ammi tayi magana ta gaji har ta zuba maki ido haka ni ma saboda bana san takura maki na matsawa d'iyar da tafi soyuwa cikin ya'ya na koda mahaifin ki na raye ba zai zuba maki ido haka ba, na sha baki lokaci dumin ki fido da wanda ya kwanta maki a rai kuka dai-dai ta kan ku amma naga alamar baki da niyar yin aure kin fi ganewa ki dinga fita zuwa kasashe kasuwanci kina neman kudi tamkar namiji..! abubuwan da kike sam ba al'adamu bace, ba tsarin mu bane na gidan saurata da mulki, anfi sannan ya'ya mu da zama gida da kamun kai duk abinda kike ina sane zuba maki ido nayi, naga yaushe zaki natsu amma naga ba rana to bazan lamunci hakan ba, na riga dana yanke hukunci zan hada ki da wanda hankali na ya kwanta da shi yanzu haka mun gama magana da magabatan shi....! tare za'a hada bikin ki dana Ashad" a razane Nazili ta dago tana kallan maimartaba wanda ba alamar wasa a fuskar shi idanuwan ta cike ta kwalla, kasa tayi da kanta maganar maimartaba ce ta kara katse mata tunani da cewa, "kina iya tafiya ki fara shirye-shiryen biki" Nazili da jikin ta ya mutu murus idanuwan ta cike da kwalla ta ce, "Abba yanzu wanda ban sani ba za'a aura min Dan Allah a karamin lokaci," "Zaki san shi kafin biki ni dai fata na kimin biyaya na yaba da hankali shi kuma ya cancanci abinda ya fi haka awaje na" zata kara magana maimartaba ya katse mata hanzari da cewa, "kin san dai bazan zaba maki abinda zai cutar dake ba dan haka na gama magana" Nazili da gwiwa a sage ta mike jiki a sabule cikin ladabi ta fice, hawaye na mata anbali tana jin tsanar wanda yayi wannan katobara na cewa ita yake so, aiko zai aurawa kan shi masifa da bala'i, kuka take sosai tana mamakin yarda rayuwa ta sauya mata daga farin ciki zuwa akasin haka, tir da irin wannan SAUYIN RAYUWA yanzu haka ma ko za'a tsare ta da wuka zaman da ake yanzu bata da wani saurayi sai dai friends da abokan kasuwancin ta, yaushe ma ta tsaya tayi soyayya ta riga da ta daurawa zuciyar ta san Sultan hakan yasa idanuwan ta suka rufe bata ganin samari a wata tsiya, gashi yau ta kare mata har ita za'ayiwa auran dole ko wani irin matsiyaci za'a aura mata da wannan tunanin Nazili ta wuce garden tana kuka fad'awa tayi saman resting chair ta zauna tana kuka tana cewa, "why me why Abba mai yasa ake so a rusamin farin ciki na," surutai Nazili kawai take, bata lura da wanda ke wajan zaune ba, ba kowa bane sai Ahmad dake shan iska hannu shi rike da cup da alama coffee yake sha sanye yake cikin shirt blue da wanda suit yayi kyau har ya gaji, ya kara haske ya fito zalan baturan shi kasancewar bai dade da dawowa naija ba, dan shirye-shiryan komawa US yake gabaki daya saboda kasar shi na bukatar shi kan wani aiki na kula da Mr President. Tunda Nazili ta zauna ya lallace yana kallan ta jin kukan ta yake har cikin ran shi ji yake tamkar ya jawo ta jikin shi ya lallashe ta lumshe ido yayi ko bata fada mashi ba a yarda take maganar ya gane ina ta dosa, jim kad'an yayi yana wani tunani can kuma ya saki smile handkerchief ya ciro cikin alhijun shi yana jujuyawa cikin murya shi mai dadi saurare ya ce, "mai yasa Gimbiya take asara hawayan ta masu tsada kwata-kwata kuka ba yayiwa kyawawa kamar gimbiya kyau" dagowa Nazili tayi tana kallan Ahmad daya tsare ta da blue eye's ball din shi ta kasa cewa komai handkerchief ya mika mata ya ce, "take this" da kamar baza ta amsa ba ta amsa tana goge hawayan idanu ta Ahmad ne ya katse mata tunani da cewa, "good kin ga yarda kika kara kyau da kika goge hawayan fuskar ki," galala Nazili ta tsaya tana kallan Ahmad, wani kyau na daban ya kara mata da haske a zuciyar ta ta ce, dama haka Alex yake da kyau da kwar jini sai dai sam bata san Alex ya muslunta ba, bata san cewa haskyan muslunci bane ya haskaka mata shi ya kara fito da zalan kyan shi da kwar jinin shi, Ahmad ne ya katse mata tunani da cewa, "kafar ki.! A zabure Nazili ta mike tana ihu tana cewa, "mi ka gani" gabaki daya ta rude taga-taga ta tafi zata fadi Ahmad ya tarota wani yanayi na daban suka tsinci kan su da sauri Nazili ta janye jikin ta tana cewa, "me ka gani a kafa ta? dan murmushi Ahmad yayi ya ce "na fadi hakan ne kawai dan ki daina kuka, kuka ba yayi ma kyakyawar fuskar ki kyau, me yasa duk san da zan ganki kina kuka wake bata maki rai? ki fadi min komawa waye yanzu mu je na rama maki" yarda Ahmad yayi maganar sai da yasa Nazili darawa duk da bacin ran dake cin ta kallan ta Ahmad yake ta wani kara mashi kyau yarda yake kallan ta ne yasa Nazili daga gira tana kallan shi ta ce, "why are you looking at me like you never see me before," murmushi yayi yana kallan ta ya ce, "komai kikayi yana maki kyau i can't stop looking at your natural beauty face" shuru Nazili tayi tana jin dadi kalaman da Ahmad ke fada mata dan ya faran ta mata rai murmushi Nazili tayi a hankali ta furta, "thanks" tana gama fadar haka ta mike da niyar barin garden Ahmad ya ce, "why not mu zama friends ko dan na dinga zane mai saki kuka" jim kad'an Nazili tayi tana kallan shi, shima din kallan ta yake yana tunanin watsin da zata mashi duk da ya ga sauyi da yawwa a tattare da ita murmushi Nazili tayi ta ce ce, "why not" tare da mika mashi hannu murmushi ya saki ya kama lallausan hannu ta gabaki daya su wani shock suka ji lokaci daya Nazili ce ta janye hannu ta har ta fara takawa. Ahamd ya ce, "me yasa baki san wanda Abba ya zaba maki a matsayin miji? Maganar ce tasa Nazili tsayawa cak Ahmad ya kara jefo mata wata tanbayar da cewa, "kina da wanda kike so ne? Jim kad'an Nazili tayi cikin mulki ta ce, "the truth is by know love doesn't exist in my dictionary since I loose the man I love so much and after all by know aure baya gaba na, I just wanna leave like that no love no tension," kallan ta Ahmad yake ido cikin ido a hankali ya furta, "ki daure kiyawa iyayan ki biyaya zaki ci ribar hakan tunda baki da wani tsayaye, kuma nasan zai rike ki amana cike da so da kauna tunda yana san ki" murmusawa Nazili tayi tana kallan Ahmad tace, "I don't think so zai iya rike ni" tana gama fadar haka ta bar wajan shuru Ahmad yayi yana nazarin kalaman ta murmushi ne ya kubucewa Ahmad a hankali ya furta, "everything will be ok soon zan koya maki so na I do love so much dear. Jiki a mace Nazili ta wuce part din Ammi zaune a parlour ta same su su duka suna zuba hira cikin jin dadi har da Nihal dake faman cin danbun shinkafa wanda mom ta dafa mata ya ji vegetables da tircecan cikin ta gaba, wanda haihuwa yau ko gobe murmushi yak'e Nazili ta saki tare da shafa kan Khalifa dake hannu Basmal sannan ta shige bedroom nata yanayi da Ammi taga Nazili ne yasa ta bin bayan ta da sauri zuwa daki, sai dai sam batayi tunani Nazili zatayiwa sarki biyaya cikin sauki ba sai gashi ta bata mamaki, ta nuna ba komai amma takaici na cin ta a zuciya haka Ammi ta rinka ban baki da nuna mata anfanin biyaya da irin riba da ake samu duk da cewa Nazili bata nuna komai ba sai dai kalaman Ahmad sun tsaya mata a rai. Tsame hannu ta Nihal tayi daga cikin plate din danbun shinkafa Minal dake gefe tace, "har kin koshi aunty? Daga kai Nihal tayi tana cewa, "har na koshi bari na lallaba na wuce part namu nasan love na kan hanyar dawowa gida" shewa su Nawwara suka saki suna cewa, "love bird har yau soyayya su aunty Nihal taki tsufa, wallahi kuna birge mu yarda kuke zuba love muma dai Allah ya bamu masu yimana" far da ido Nihal tayi tace, "har tsufan mu soyayya zamuyi, Allah ya baku masu yi maku" Amin su Minal suka ce Ammi da fitowar ta daga bedroom kenan ta ce, "haka dai kullun" dariya parlour ya dauka har ta fice daga part din suna tsokanar ta. Nihal ce tsaye gaban dressing mirror bayan ta fito daga wanka ta shirya cikin gown din ta maroon daga sama an jera mata Stone's cikin ta ya fito das da shi, sarka take kokari sakawa, turo kofar da akayi ne ya sata waigowa tana sanki sanyayan murmushi, Sultan dake bakin kofa ya jingina yana bin ta da kallo dan ba karamin kyau ta zuba mashi ba, ya nad'e hannu shi saman kirjin shi sanye yake cikin jeans and shirt white bottle din rigar bud'e gashin kanshi sai shining yake yana bin Nihal da kallo mai cike da so a hankali ya tako gaban ta, gashin ta ya maida gefe ya amshi sarkar yana sa mata ta cikin mirror ya tsare ta da ido itama haka har ya gama sa mata sarkar a hankali ya sakar mata kiss a wuyan ta yana shafa cikin ta cikin muryar rada yace, "kinyi kyau hayaty" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "thanks love" ta ida zancan tana cewa, "na gama shiryawa kai nake jira" ja mata hanci sultan yayi yana cewa, "um shine kikayi wankan ki baki jira ni munyi tare ba ko kin kyauta, kin so ki jira ni shiyasa baki jira munyi wankan tare ba" Sultan ya ida zancan yana kokari kissing lips din ta dan ture shi Nihal tayi tana dariya tace "baza ka bata min kwalliya ba kai mai wayau ko" barbaza gashin kan shi Sultan yayi yana cije lips ya shige toilet. Iska mai sanyi Nihal ta furzar tana murmushi ta bud'e drawer dan cirowa Sultan kayan da zai saka, bai wani dade ba ya fito da taimakwan Nihal ya shirya duk da yana hana ta, amma bata ji cikin black yadi ya shirya wanda ya sha aiki da gold zare babba riga kayan sun zauna a jikin das, kan shin na sanye da hula sajan shi ya kwanta luf-luf hakan sai ya kara fitowa da zalan haskyan shi yayi kyau, maroon veil din ta Nihal tayi rolling kanta da shi tana kallan kan ta, ta ciki mirror turo baki tayi tana kallan tircecan cikin ta kamar tayi kuka rungume ta sultan yayi ta baya yana cewa, "what hayaty naga kamar mood din ki ya canza me ya faru hayaty? kwabe fuska tayi idanuwan ta cike da kwalla tace, "ji fa yarda baby ka yasa ciki na kato yanzu haka zan fita ko kyau banyi ba" Nihal ta ida zancan a shagwabe tana turo baki juyo da ita sultan yayi yana cewa, "waya ce bakiyi kyau ba hayaty kinyi kyau sosai" turo baki Nihal tayi cike da shagwaba tanayiwa sultan rigima haka ya lallaba suka fice tana bitar yarda cikin ya maida ta. Direct Gidan baba Sani suka fara zuwa a compound suka sami baba Sani yana kokari wuce wa masallaci cikin ladabi suka gaishe shi cikin fara'a ya amsa yana cewa, "a'a ha sultan ashe kune tafe? "mune Abban," "to madalla sannu ku da zuwa," kallan Nihal baba Sani yayi cike da fara'a ya ce, "masha Allah daughter jiki yayi nauyi kenan Allah ya raba lafiya, Amin" Nihal tace, a kunya ce baba Sani yace, "ku karasa daga ciki masallaci zan wuce idan na dawo ma gaisa da kyau" sultan da kan shi ke sunkuye yace, "nima banyi sallah ba da yake muna kan hanya akayi kira" "to, to bari na kawo ma ruwa sai akayi alwala mu wuce tare ko" ciki baba Sani ya koma Nihal na biye da shi a baya cike da murna hajiya farida ta tarbi Nihal da su Naja dake zaune itama zuwan ta gidan kenan da yan ya'ya ta biyu. Da ruwa a buta baba Sani ya dawo ya mikawa sultan ya daura alwala suka wuce masallaci, bayan sun idar da sallah suka dawo gida a tare suna tattaunawa sam baba Sani ba shi da wata matsala musanman yarda ya ga sultan nada natsuwa yarda suke fira tamkar sa'anni juna sun dan jima sosai a can daga nan suka wuce gidan Aunty Aisha a nan ne fa suka baje suna fira kasancewar weekend ne Abban Nana na gida suna tare da sultan a company suna fira, Nihal kuwa na cikin gida tana zuba sangarta Aunty Aisha na biye mata rike da plate din pepper soup din yan cikin aunty Aisha ta fito daga kitchen tana cewa, "yauwa daughter zo ga pepper soup din ya sauka" washe baki Nihal tayi tana lumshe ido ta amshe plate din tana cewa, "na gode mama tun yana kan wuta miyau na ke tsinkewa tun kafin na ci," murmusawa mama tayi ta ce, "ai yanzu ya sauka sai aita ci" Nana dake zaune gefe tace, "na lura yanzu an fi ji da Nihal ta kwace min gwabnati" dariya Nihal ta saki tana mata gwalo murguda mata baki Nana tayi tana kokari sa hannu cikin plate din pepper soup din mama tace, "kul naga kin kara kai hannu cikin plate din nan tsame hannu ki, ki wanke wannan na daughter ne, dan ita nayi shi idan kina so ki shiga kitchen ki dafa da kanki" turo baki Nana tayi Nihal na mata dariya tana mata kwalele. Bayan Nihal ta cinye pepper soup din ta tas, suka baje a bedroom din Nana suna wata sabuwar hira, sai ku san bayan sallah isha suka dawo gida gajiye likis dan Nihal tun a mota ta fara jin bacci, a parking space drive yayi baki sultan ya bale murfin mota tare da daukar Nihal kamar baby suka wuce part na su. A bakin kofa ya aje ta tare da daure mata ido da veil din ta, Nihal na murmushi Sultan ya ja hannu ta tana bin shi kamar rakumi da akala, wani bedroom suka nufa dake cikin part nasu wanda duk zaman Nihal bata san akwai shi ba, bud'e kofar dakin Sultan yayi suka shige dakin tare iya kar tsaruwa dakin ya tsaru kayan baby's ne birjik komai na dakin pink and white, ga kayan wasa na mure rayuwa gefe guda kuma drawer ce wanda kayan baby ke ciki kala-kala, a hankali Sultan ya cire mata veil din dake idanu ta kallan dakin Nihal take da surprise tana murmushi dan ko bakin magana ta rasa juyowa tayi tana facing Sultan tana murmushi rungume shi tayi tana cewa "thank you love bani da bakin da zan maka godiya" haka Nihal ta gama zagaye dakin tana murna. Bayan kwana biyu abubuwa da yawa sun faru ciki harda shirye-shiryan bikin da ake ba kama hannu yaro tsakanin Nazili da Ahmad kullun shakuwa suke karawa sai dai sam Nazili bata san shine mijin da zata aura ba, d'an zaman da suke tare yasa sun shaku sosai, har takai ga Nazili ta fara jin wani abu game da shi musanman data ganu shi din musulmi ne yanzu, yau ma kamar kullun bayan ta dawo daga office wayar ta ta hau ruri ganin sunan Ahmad ya sata kai hannu da sauri ta dau wayar sun dade suna fira a waya har yace mata weekend yana so su fita su sha iska tare sannan idan bazata damu ba yana garden yana jiran ta, to Nazili tace mashi cike da murna sannan ta katse wayar tana smile cikin sauri ta shirya cikin kayan da suka amshi jikin ta, Ammi kuwa dadi ne ke lullube ta ganin yarda taga Nazili ta saki jiki ta da Ahmad. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [3/10, 6:30 PM] salma😝: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page: 141_142* Tunda biki ya rage saura wata uku Sara ta dawo kano tana shan gyara wajan Dara tayi fresh ta murje ta kara kyau ta bar gwoggo da wata datijuwa na kulla da ita, ana biyan ta duk wata tunda Sara ba shanono zata zauna da mijin ta ba. Kamar yarda Ahmad ya bukaci su fita da Nazili weekend hakan yasa Nazili ke shiryawa ciki wata light brown gown din ta, ta kama jikin ta tamkar dan ita akayi ta tayi make up sosai tayi rolling kanta da cream veil tayi kyau, kafar ta na sanye da takalmi mai tsini, ringing din da wayar ta keyi ne ya katse mata hanzari, ganin sunan Ahmad a scream din wayar ya sata sakin murmushi tare da ficewa daga bedroom din zuwa compound A compound ta sami Ahmad sanye yake cikin armini royal blue suit da white inner tie din sa kala suit din, ta kama jikin shi yayi kyau smile Nazili ta saki tana kallan Ahmad da shima din kallan ta yake dan ba karamin kyau ta mashi ba, a hankali ya bud'e mata murfin mota ta shige. Park suka wuce kaitsaye a wasu madaidaitan kujeri suka zauna masu dauke da table suna shan ice cream suna fira, yanayin wajan yayi ma Nazili matukar kyau musanman yarda iska ke kad'a wajan da green flowers din dake kad'awa lumshe ido tayi tare da ware su ta sauke idanu ta kan Ahmad da tun isowar su ya kafe ta da idanuwan shi, a hankali ya daura hannu shi zaman Nazili wanda a halin yanzu jikin ta ya mutu mudus san Ahmad da kaunar shi kawai ke azalzalata haka shima nashi bangaran cike da gwarin gwiwa ya fadawa Nazili cewa shine mijin da zata aura yana mai cigaba cewa, "na san cewa ni mai lafiya ne na nemi auran ki ba tare da amincewar ki ba, ki amince dani Nazili zan nuna maki so da kauna a rayuwar auran mu wallahi Nazili ina san ki ina maki so wanda ni kai na ban san adadinn shi ba, san ki ya dade da mamaye duk wani lungu da sako na zuciya ta, ki daure ki so ni koda kwatan wanda nake maki ne duk da zuciyar ki na tare da wanda kike so, please Nazili ki bani dama na nuna maki san da nake maki, Dan Allah kada ki ce ba kya so na" numfasawa Ahmad yayi yana kallan Nazili wanda idanu ta ke kasa tana wasa da yatsun hannu ta wani irin farin ciki ne ya lullube ta ya kara mamaye zuciyar ta, ita kanta bata san da ta fara godewa Allah daya bata Ahmad a matsayin miji da zata aura, ji take tamkar an cire mata k'aya lokaci daya taji wata irin iska mai dadi da sanyi na shiga kofofin jikin ta san Ahmad da kaunar shi na kara narkewa a zuciyar ta, ita kanta tanbayar kanta take yaushe ta afka tarkon kaunar Ahmad, yanzu ta fara so yanzu ne ta san menene so wanda a rana daya Allah ya dasa mata san Ahmad a zuciyar ta yabi lungu da sako na sansan jikin ta da ruhin ta, shuru da tayi ne yasa Ahmad dan matse hannu ta yace "ki ce wani abu please" kayatancan murmushi Nazili ta saki wanda ita kanta bata san tayi shi ba, ta zubuwa Ahmad idanu ta wanda ko bata fada mashi sirrin zuciyar ta ba ya hango tsantsar san shi a kwayar idanu ta yanayin kallan da take mashi ne ya saukar mai da kasala lokaci guda ya shagala da kallan ta a hankali ta furta, "nima ina san ka Ahmad..! a da ba so nake ba a yanzu na fara so a kanka na san me so, ni dai fata na ka rike ni amana" katuwar ajiyar zuciya Ahmad ya saki wani irin dadi ne ya lullube Ahmad ya rasa ina zai sa kan shi saboda murna Nazili kuwa taga rawar kafa dan gabaki daya Ahmad ya rasa ina zai tsomata, a haka suka cigaba da nunawa juna so da kauna. Baki dayan su zaune suke parlour a part din Nihal suna fira sai tafka musu ake tsakanin Nawwara da Minal parlour ya kacame da hayaniyar su, har da Nasim da Ashad ake hirar daga nan aka fada hirar program's din da za'a tsara Nihal dake zaune hannu ta rike da Khalifa baby dan wata uku sai wasa take mashi ta zakalkale ana tsara dinner da za'ayi tayi uwa tayi makarbiya Nazili na gefe itama kasancewar yanzu itama tana shigowa cikin su a dama da ita, har da ita ake tsara abubuwan da za'ayi, hayaniya kawai suke sai ka rantse da Allah an fara bikin yarda suka kacame parlour ana fira, shigowar sultan ne ya katse surutun dake tashi da kallo yake bin su daya bayan daya yana kallan yarda suka maida parlour, kamar yara ko gidan sha'ani a hankali suka fara tattare komatsan su suna cewa, "yaya sannu da zuwa" yauwa ya ce masu a takaice yana bin Nihal da kallo dake zaune da Khalifa ga tulelan cikin ta aje briefcase din shi yayi yana aika mata smile kamar yarda take aika mashi mai cike da tsantsar kauna ya amshi khalifa yana cewa, "amma dai Darling baki da kirki yanzu saboda Allah sai ki sakarwa hayaty wannan dirkekya d'an naki kamar dan shekara nauyin shi sai yasa ta haihu ba shiri," Nihal dake gefe tana murmushi tace, "ba ruwan darling nina matsa mata ta bani shi ba yarda ba tayi da niba na mikawa mai kula da shi ba naki," cike da zolaya Sultan ya ja ma Nihal kunne yana cewa, "oh dama keke wahala min da baby ko" yar kara Nihal ta saki mai cike da shagwaba tana dire-dire tamkar ba cikin jikin ta zaro ido Sultan yayi yana cewa, "ki bada himma ki samama baby na problem da kanki kiga yarda zamu kwashe a gidan nan" dariya Basmal tayi ta mika hannu ta amshe khalifa gabaki dayan su suka fice, Nihal kuma ta dauki briefcase din sultan ta bi shi bedroom kasancewar yayi gaba. Washe gari da safe tunda Nihal ta tashi sallah asuba bata koma ba saboda Sultan yace mata yau zai je abuja kan taran kiwan lafiya da zasuyi a birnin taraya, bayan ma'aikata sun gama gyara part na su kamar kullun, ta wuce kitchen ta umarci su Yasmin su fere mata dankali, bayan sun fere ta daura dankali kan wuta tana soyawa gefe guda tana pepper soup din yan'ciki cikin dan kankanin lokaci ta kamala ta jera komai a tray su Yasmin suka biyo ta da shi part nasu, kayan abincin suka jera a dining sannan ta wuce bedroom. Kwance saman bed ta sami Sultan har a lokacin yana sana'ar bacci ya kudindine cikin blanket shida ya ce mata tunda safe zai bar garin, amma gashi nan yana ta bacci ganin goma ta gota yasa Nihal hayewa saman bed din, a hankali dake hura mashi iskar bakin ta a kunne mai sanyi tana wasa da gashin kanshi a hankali Sultan ya bud'e lumsasun idanuwan shi yana binta da kallo mai cike da so cikin muryar ta mai dadi tace, "love ka tashi ka kusa makara ka ce min flight naka 11:00am zai tashi gashi har 10 tayi kana bacci" shuru sultan yayi yana kallan yarda take motsa lips din ta jawo ta yayi jikin shi ya kama lips nata ya tsotse su tas, sannan ya sake ta suna kallan juna yana aika mata da murmushin shi mai kashe mata jiki, a hankali ya daura hannu shi saman cikin ta yana wani shafa shi kamar kwai a hankali ya daura kan shi saman tulelan cikin Nihal yana jin motsin baby shafa kan shi Nihal take tana smile tace, "love time" dagowa Sultan yayi yana kallan Nihal tare da ja mata cheeks nata yana cewa, "dadi na da hayaty bata san African time, shi kuma Sultan baya san tafiya ya bar hayaty a gida sai ya zama dole" "Um nima ai haka bana so kayi nisa dani kawai-kawai dai" "Um..! cakulkuli Sultan ya Shiga yima Nihal tana dariya a tare sukayi wanka suka fito Sultan na dauke da Nihal tana zuba mashi rigima tana fadi mashi irin missing nashi da zatayi 2days har ya dire ta saman bed a tare suka shirya juna su suka fito parlour. Direct dining suka nufa zaunar da Nihal yayi a cinyar shi ya ciyar da ita da kan shi haka itama Nihal, bayan sun gama break a tare suka fito Sultan na rike da trolley Nihal na rike da briefcase din shi Barma ya mikawa trolley ya wuce da shi parking space yasa a boot, sannan suka wuce main parlour lokacin kowa na gidan na parlour sallama Sultan yayi da su suna mashi Allah ya kiyaye hanya a dawo lafiya, a tare suka fito da Nihal, Sultan na kokari bale murfin mota Sinbul ya karaso yana cewa, "ran ka ya dad'e akayi bako" "bako? Sultan yace cikin mamaki tare da kallan agogwan dake Makale a tsintsiyar hannun shi ya ce, "wani bako ne? jim kadan Sinbul yayi yana cewa, "mutumin da ka ce a ba kudi kwana ki biyu da suka wuce, sau biyu yana zuwa neman ka baka nan yau ma Allah yayi zaku had'u ne ya zo yanzu" jim kad'an sultan yayi can kuma ya ce, "ka ce mashi ya karaso" Nihal sai smile take aikawa sultan tana mashi shagwaba, shi kuma ya biye mata. Dauke da murmushi Sinbul ya dawo wajan mudi dake rakube gefe daya yana sanye cikin shada shi ash kanshi dauke da hula ba laifi cikin rufin asirrin shi washe baki Sinbul yayi yace, "yau dai ka taki sa'a yanzu yake kokari barin garin, da baka zo da wuri ba da kunyi sabani dan yanzu haka yana bakin mota" dan murmusawa mudi yayi Sinbul ya ce, "ka karasa yana wajan motocin can dake fake zagaye da security's" musaba sukayi da mudi ya ce, "na gode" "Ah ba komai" sannan mudi ya karasa. Sara da fitowar ta daga part din mom kenan rike da boll din danbun nama wanda mom tayiwa Nihal tace ta kai mata part na su tunda ta jita shuru bata dawo daga rakiyar ba, dan murmushi tayi ganin ashe har lokacin Sultan bai tafi ba suna tsaye a parking space suna soyewa ita dai soyayyar Sultan da Nihal na matukar birge ta musanman yarda suke kula da juna su, tana wannan tunanin ta ji ta bangaje mutum a razane Sara ta dago tana kokari ba da hakuri, abinda ta ganine yasa Sara waro ido tare da sakin boll din dake hannu ta ya fadi ji kake taratsatsa..! gabaki daya compound din ya dauka, su Ammi dake main parlour a tare suka fito da maimartaba da sauran dake parlour lokaci guda hankali yan gidan ya dawo kan Sara, Sara dake daskare tsaye tana bin mudi da ido hawaye na mata zarya da sauri Nihal da Sultan suka karasa ganin mudi ne yasa Nihal tsayawa cak ido waje tana kallan shi da mamaki dama mudi na raye, hada baki Nihal da Sara sukayi wajan cewa, "ya mudi..! shima mudi ya daskare tsaye yana mamaki mai ya kawo Sara gidan bai kara tsinkewa da lamarin ba sai da yaga Nihal da ciki wanda ba zai taba manta kamanin taba duk da hutu da kyau daya zauna a jikin ta, da kyar ya samu bakin magana ya furta Nihal..! Sara..! Kuka Sara ta saki da sauri mudi ya tako zai karasa gare ta, d'aga mashi hannu Sara tayi ciki tsawa ido waje tace, "karka matso kusa dani dan ni ba yar uwar ka ba ce..! ashe dama kana raye tsawan shekara uku kasa kafa ka gudu ka bar mu a gida, mun sha wahala mun ga SAUYIN RAYUWA har Baffa ya rasu baka waiwaye mu ba kana nan birni duniya na kai maka yarda kake so, ka manta da iyayan ka da yar kanwar ka Sara, baka damu da ya muka kwana ya muka tashi ba" bud'e baki mudi yayi zai magana Sara ta daga mashi hannu tana cewa, "ba abinda zaka fadi min, ina da yaya kamar ka har almajiran ci nayi saboda mu samu abinda zamu ci bayan kai ka nan kana jin dadi kana hutawa ko baka fadin min ba yanayin ka ya nuna irin jin dadi da kake samu abirni, ka kyauta da ka barmu tsawan shekaru ya mudi" Sara na ida zancan tayi ciki da gudu tana kuka shima mudi hawaye yake yana cewa, "ki tsaya ki saurare ni mana Sara" Nihal dake gefe hawaye take waiwayowa yayi inda Nihal ke tsaye ya durkusa gwiwowin shi kasa ya hada hannu biyu yana kokari bata hakuri maimartaba da waziri dake tsaye suka ce, "ya kamata mu shiga ciki wannan magana bata waje ba ce" Sultan dake makale da Nihal tare suka shige mudi na biye da su gwiwa sage.. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [3/11, 1:56 PM] salma😝: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *_wannan shafin naki ne kyauta namesake kiyi yarda kike so da shi, Allah ya bar kauna_* *Page:143_144* Main parlour yayi tsif ban da muryar mudi ba abinda ke tashi yana mai cigaba da cewa, "na cutar da rayuwar ki Nihal nine sanadin barin ki gida kika shiga uwa duniya saboda san zuciya irin nawa da rashin hangen nesa, na rokeki Nihal ki yafe mun tunda wannan abun ya faru na rasa kwancinyar hankali da nutsuwa tun daga lokacin na gane ba sha'awar ki kawai nake ba har da san ki ke d'awainiya dani," sultan kuwa kara matse Nihal yayi a jikin shi tamkar za'a kauce ta daga gare shi, wani kishi ya zo mashi lokaci daya wanda bai san yana da shi ba, jiyayi kamar ya bigewa mudi baki har sai ya zubar da jini a kan furucin da yayi game da Nihal, wani abu ya tokare mashi makoshi kamar ya kife shi da mari. Maganar mudi ce ta kara katse mashi tunani yana mai cigaba da cewa, "komai daina min dadi yayi na rasa sukuni na wannan dalilin yasa na gudu zuwa birni ina neman ki ido rufe, ko zan gan ki amma ina nayi nema har na gaji hatta kayan mayan da nake sha daina sha nayi dalilin tunanin ki yasa na watsar da duk wani shaye-sheye da kunyar abinda shaye-sheye ya sani, tun daga lokacin na tsani duk abinda ke sa maye, kullun cikin rokwan Allah nake ya nuna min ke wata ran a tasha nake kwana bani da cin yau bare na gobe, ni dai fata na na ganki na nemi yafiyar ki na maido ki gida duk da gidan ba wani dadin shi kike ji ba sai dai na daukar wa kai na bazan bari aci zarafin ki ba, har muta nan tasha nake tanbaya ko sun ganki sai su ce min bani da hankali ai birni fadi gare ta, a haka na hadu da wani driver mota ya taimake ni na zama kwandastan motar shi ina samun na ci, har Allah yasa na ji labarin za ayi wani taran matasa wanda miji kine jagoran shirin a nan ne aka rabawa matasa mota har nima na samu" nan mudi ya kwashe duk abinda ya faru da shi har zuwa ranar da suka hadu da Sultan ya kawo shi gida ya ce ya dawo, tunda ya dawo ya amshi kudin da ya bashi masu tsoka ya tafi da su gida, ya rinka tsara abinda zaiyi da kudin har ya bud'e shago a kasuwa, ya zuba kaya sannan ya bada motar shi ana haya da ita, wannan dalilin yasa Sara ta ganshi fes, numfasawa mudi yayi yana mai kara rokar Nihal gafara har da Sara, Nihal kuwa cewa, tayi ta dade da yafe mashi Allah ya yafe masu baki daya tare da godewa Allah da yasa mudin na raye, Sara kuwa hakuri ta bashi na rashin fahimtar daya shiga tsakanin su da godewa Allah daya bayana mudi ko ba komai yayanta nan zatayi aure, Dara kuwa farin ciki ne ya lullube ta baki har kunne ta cewa mudi ya matso gare ta. Bayan komai ya lafa Sara ce zaune da yaya mudi har Dara tana labar ta mashi irin mugun halin da su gwoggo suka aikata suka birne har da irin mutuwar wulakancin da Baffa yayi, duk da cewa Dara ba taso labarin ba sai dai ya zatayi da Sara tunda ta fara zuba, jikin mudi sanyi yayi sosai yana mamakin rashin imani irin na iyayan nashi, dama ashe su suka rusa masu family saboda san abin duniya tir da irin wannan hali inji mudi, Dara tace, "kul na kuma jin irin wannan maganar ta fito daga bakin ka, Allah ya ji kan yaya tanimu daya rigamu gidan gaskiya" suka amsa da Amin har auran da zatayi Sara ta fadawa mudi da abin kunyar da ta aikata sam bai ji dadi hakan ba har fada yayi mata kan watsar da tarbiyar ta da tayi, koda yake ta wani fannin bai ga laifin ta ba, sai na gwoggo kalaman da take fadawa Nihal ne suka tabata kan diyar cikin ta, bayan sun gama tattaunawa suka tsaida magana kan cewa gobe zasu wuce Shanono ya duba jiki Gwoggo, har yamma tayi mudi na gidan suna hira da Sara har Nihal ta zo suka dasa da ita cikin farin ciki ya kara mika godiyar shi a kan namijin kokari da tayi na kulla da Sara, duk da abinda su Baffa suka aikata mata murmusawa Nihal tayi ta gwada mashi ba komai ya wuce, kiran sallah magrab ne ya tashe su zuwa yin sallah farin ciki fal a zukatan su. Washe garin da safe Sara da mudi suka dau hayar shanono a cikin motar da Sunusi ya aiko wa Sara ta hidimar biki, tun a kan hanya datijuwar dake kula da gwoggo ta kira Sara tana kuka ta sheda mata cewa, duk yarda tayi da gwoggo ta kasa haka ta fella a guje tayi kan hanya, tifar dake zuwa kauye dibar icce zuwa birni tayi sama-sama da gwoggo ta take ta ta mutu har lahira, da kuka suka karaso shanono lokacin ana kokari kai gwoggo makwancin ta. Bayan komai ya nitsa Sara ta kira Dara ta sheda mata rasuwar gwoggo, jikin Dara sanyi yayi tana kara yima Sara gaisuwa, sannan ta katse wayar dama tana part din mom ta labar ta mata rasuwar gwoggo, jikin mom sanyi yayi tayi mata gaisuwa ita da Gimbiya jalila kasancewar itama tana part din suna tattaunawa kan sha'anin bikin dake karatowa. kasancewar mom keda girki data je turakar maimartaba ta sheda mashi rasuwar gwoggo, washe garin da safe maimartaba suka shirya zuwa gaisuwa kasancewar Nihal tayi nauyi tana zaune gida tare da yakumbo da sauran yara, yakumbo na bata kyakyawar kulawa, sai dai kiran Sara tayi ta mata gaisuwa ta waya tare da mudin, Nana ma ta zo gidan suna ta shan hira har Nazili ta dawo ta daga office itama ta zauna aka dasa sabuwar hira da ita kasancewar bata samu damar zuwa gaisuwar ba sai dai tayi ma Sara gaisuwa ta waya. Bayan sadakar uku mudi da Sara suka dawo kano ya cigaba da kasuwancin shi, yana samun rufin asirri shi jefi-jefi yana zuwa duba Sara, Sara kuwa tana ta shan gyara kafin lokacin biki, ga kyakyawar kulawa da take samu wajan yaya mudi ya mai data yar lele shi da Nihal har da Dara ta rasa wayafi ji da ita cikin su. Yau dai kam Nihal wuni tayi wani iri tana jin jikin ta da kyar ta samu tayi sallah azahar tana part din mom duk yinin yau, mom na lura da yanayin ta, da ta tanbaye ta sai tace ba komai can dai wurin 4:00pm ciwo ya kara tsanani Mara da bayan ta suka rike, kuka Nihal ta saki dafe da ciki tana fadin duk addu'ar da ta zo bakin ta tana kiran mom, fitowa mom tayi daga bedroom tana cewa, "daughter lafiya? Ganin yanayin da Nihal take ya sata karasawa a kidime Nihal dake nukurkusu tace, "mom ciki na baya na kugu na" "Sannu daughter haihuwa ce kin ji daure ki rinka addu'a" kama ta mom tayi da taimakwan Dara suka wuce da Nihal asibitin cikin gidan. Bangaran sultan kuwa tun daran jiya yake kiran layin hayaty ba a dauka ba, har yau da safe kafin su ida meeting ya fito dan ya rasa natsuwar shi hawo flight yayi zuwa kano. Yana zuwa gida aka fada mashi Nihal na asibitin cikin gida, Kaitsaye can ya nufa isar sa tayi dai-dai da shigar da Nihal labour room yana juyo yarda take kwalla mashi kira, duk addu'ar da tazo bakin shi kawai yake fadi duk ya kidime ya rude, da sauri mom ta tare shi yana kokari kunna kai labour room din a kidime, idanuwan shi jawur zame hannu mom yayi tana kokari magana, Gimbiya jalila ta mata alama ta kyale shi Ammi kuwa ban da zarya ba abinda take Nihal dake labour room da karfi take furta, "innalillah wa'inna ilaihi raju'un, ya sallam ya Allah...! Sultan.. Sultan ku kira min Sultan..! da sauri Sultan ya shige labour room din Nihal dake kwance tana nakuda gadan-gadan zuba na karyo mata tana kara kiran suna shi tana cewa, "Sultan..! da sauri ya karasa ya kama hannu ta yana goge mata zuba yana cewa, "ina tare da ke hayaty Allah ya sauke ki lafiya yi nishi hayaty kin ji kara" da karfi Nihal ta saki nishi can tayi lakwas tana cewa, "bazan iya ba mutuwa zanyi ya sallam ya Allah" tana maganar tana kara kankame hannu Sultan tana kuka, Sultan kuwa kuka yake kamar karamin yaro, saboda Nihal na cewa zata mutu a hankali yake mata addu'a a cikin kunna ta a hankali yana cewa, "zaki haihuwa lafiya mata na insha Allah" Nihal na rike da hannu shi gam wani irin nishi Nihal ta saki tare da furta *SULTAN SALIM* da karfin ta inda yayi dai-dai da fadowar baby boy tare da sakin kuka wata ajiyar zuciya Nihal ta saki hawaye na bin kuncin ta wani murmushi Sultan ya saki, yana shafa kan Nihal a hankali ya sakar mata pack a goshi yana kara godewa Allah daya sauki Nihal lafiya da abinda ke cikin ta, bayan nurse ta yankewa baby cibi jiki na rawa Sultan ya amshi baby yana kallo yana smile, yana kallan Nihal dake murmur da ido ganin ta sauka lafiya ya fita ya sheda wasu mom cike da murna suka rungume shi musanman Ammi sai pack take mashi a kumatu tana cewa masha Allah, Alhamdulillah. Ana cikin haka aka turo Nihal saman goda nurse na rike da baby da sauri Basmal ta karasa ta amshe baby tana smile, amsa baby mom tayi bakin washe tare da mikawa Ammi, Sultan kuwa ya kasa rufe baki saboda murna Ammar da Ashad rungume Sultan sukayi suna taya shi murna harda Ahmad bakin shi ya kasa rufuwa dimple din shi sai lomawa yake haka aka wuce da Nihal waiting room. Sai wajan isha Nihal ta tashi daga wahalalan baccin daya dauke ta, a hankali ta bud'e lumsasun idanuwan ta, ta sauke su kan Sultan dakewa baby huduba su Ammi duk suna dakin har da maimartaba, aje baby Sultan yayi a hankali ya jinginar da Nihal wadda duk kunya ta rufe ta saboda rawar kafar da Sultan yake mata tamkar ba gaban su maimartaba ba, baby ya dauka ya mikawa Nihal yana cewa, "bashi ya sha na san yana jin yunwa" Sultan ya ida zancan yana smile kallan baby Nihal take tana smile kamar shi daya da baban shi tamkar Sultan yana baby dagowa Nihal tayi karaf suka hada ido da sultan kashe mata ido yayi yana cewa, "bashi mana" Ammi dake gefe tace "to dasa kunya beran tanka sai ka ba manya ka waje, ko kunya baka ji gaban uban ka kana cewa ta ba yaro nono Allah ya kowa mu ni kuluwa, sai ka tashi ko, yar tahali kan nan ko abinci bata ci ba ka tasata da yaro kana cewa ta bashi nono ka bari ko tea ta kurba, matsa ka ban guri" sosa yake Sultan yayi ya mike Nawwara da Minal dake zaune dariya suke kasa-kasa kallan da Sultan ya watsa masu ne ya sasu hadiye dariyar, mom kuwa girgiza kai tayi tana maka mashi harara maimartaba kuwa murmushi yayi ya kama hannu shi suka fice tare da waziri, Adda dake zaune mikewa tayi tana murmusawa ta karasa gaban gadan da Nihal ke zaune tana ba baby nono. Kwana Nihal daya a cikin asibitin gida ta dawo cikin gida part din mom ta sauka kasancewar a nan zatayi wanka, Sultan kuwa kullun yana makale da hayaty da rigima da komai mom ke tasa keyar shi waje dan ta lura fama zatayi da shi, dan sam bai yarda da zaman ta part din mom ba, kullun sai yayi bitar mai ya sami part nasu har zaunawa yake yana tsara mom ai shi likita ne zaifi kowa bata kyakyawar kulawa, yana kai aya mom zata rarumo mabigi idan Gimbiya jalila na kusa ta tare tana dariya shi kuma ya fice da sauri, wata irin kula yake nunawa baby dan ko gajiya ba yayi da daukar shi, su Ammar su rinka mashi tsiya suna cewa sai ka ce kan shi aka fara haihuwa, Ahmad kuwa cewa yake a kyale shi yayi suma lokaci suke jira ya zo. Ranar suna yaro yaci suna maimartaba ana kiran shi da Amir, maimartaba kuwa farin ciki lullube shi yayi ganin ya samu takwara, har filli yabawa takwara da gona da doki da god'iya saboda tsabar murna yaba Sultan ya aje mashi idan ya girma ya bashi nashine halak malak, Sultan kuwa ban da godiya ba abinda yake ita kanta Nihal din ta sha kyauta hannun maimartaba mom kuwa sarkar diamond ta bata, Gimbiya jalila kuwa jigidar gold ta bata kit guda, Ammi kuwa trolley din alkyaba ta bata da kayan baby, Nihal ta amshi kayan sosai har na ban mamaki su Aunty Aisha ma ba'a barsu a baya ba taga gata anyi ciye-ciye da lashe-lashe kudi sunyi kuka anyi bidiri sosai. Haka Nihal ta cigaba da wankan ta sosai baby Amir ke samun kula ya kara wayau, gyara mom takewa Nihal sosai ta kara fresh da kyau kasancewar ta kusa cika 40days ta kuma part nata. Yau Nihal ta cika 40days tsaye take gaban dressing mirror da daddare Yasmin da bariri na bayan ta da Dara a hankali ta saki towel din dake jikin ta, ta mika hannu wata fitinana riga Dara ta saka mata white mai zare-zare daga kasa a tsatsage take gaban boobs din ta kamar zasu fasa kirjin ta su fito, ta murje tamkar bata taba haihuwa ba zama tayi aka tsantsara mata make up, gashin ta ya nanad'e kamar taliya ya baje a gadan bayan ta kanta na dauke da wasu flowers a sama, Alkyaba blue aka saka mata wadda ta sha aiki da gold zare kungun ta na sanye da jigidar gold, da hula alkyabar ta rufe fuskar ta Bariri na rike da baby cikin towel din sarauta na baby's ya sha kyau ya gaji sai kamshi suke zubawa haka suka fito daga bedroom, fresh milk mom ta bawa Nihal ta kafa kai ta shanye tas sannan suka fice daga part din zuwa nasu. Bangaran Sultan ma Sinbul da Barma ne ke shirya shi cikin sleeping robe din shi White yayi kyau har ya gaji, sajan shi ya kwanta luf-luf da shi sai smile yake saki yana fitar da sanyayan kamshi, dakin ya sha gyara da red flowers yana fitar da kamshi da sanyi AC, gefe ga bed din baby pink shima ya sha gyara karma ace bed nasu dake baje da red flowers haka suka gama shirya shi suka fice kai sunkuye, tsaye yake yana facing tangameman mirror yanayin yana kallan agogo. Murda kofar da akayi ne ya sasa lumshe ido yana juyo jigidar dake kugun Nihal yarda take amsawa, wani yar yaji lokaci daya a hankali juyo yana sakin smile Nihal na rike da baby kanta sunkuye tana smile mai tsada ga wani kamshi ta daya cika dakin, a hankali sultan ya tako gabanta a hankali ya dago da fuskar ta "masha Allah..! ya furta a hankali yana bin fuskar ta da kallo tamkar ya cinye ta, da shu'umin kallan shi mai kashe mata jiki yake bin ta, kukan da baby ya saki ne yasa gabaki dayan su daura idanu su kan Amir dake hannu Nihal yana shuru kafa yana kuka ganin suna kallan shi ya sashi yin shuru yana raba ido, dariya Nihal da Sultan suka saki suna ja mashi kumatu a tare suka sakar mashi pack a kumatu amsar Amir Sultan yayi yana mashi wasa har ya kwantar da shi saman bed din shi suna Lila shi yana dariya yana wasa a haka bacci ya dauke shi. Ajiyar zuciya Sultan ya saki tare da juyo da Nihal suna facing juna matso da ita yayi jikin shi sosai yana kissing nata yana cewa, "I miss you hayaty" ya dauke ta cak kamar baby bai dire ta ko ina ba sai saman bed yana romance din ta daga nan suka lula duniyar ma'aurata. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya hada-hada biki ake ba kama hannu yaro yau dinner zaune suke gabaki dayan su a parlour Ammi ana masu kunshi mai kyan gaske Basmal tace, "masha Allah kunshin nan yayi kyau aunty Nihal" murmusawa Nihal tayi tana cewa "na gode" Minal ce ta shigo tana cewa, "gaskiya anyi mana san kai kunshin ku yafi kyau kar ma ace na aunty Nihal yafi na kowa kyau" dariya Nihal ta saki tana mata gwalo tace, "je ki goge naki a maki wani" murmusawa Minal tayi tace "aike mai kyau ce aunty komai kikayi yana maki kyau shi yasa kunshi ya hau hannu yayi das" smile Nihal tayi tace, "thank you" "Ni ko ina Amir? Murmushi Nihal tayi tace, "yana hannu love tun dazu ya amshe shi yanzu haka na san duk inda suke ya fara rigima raban shi da abinci tun safe" har aka gama masu kunshi suna hira, part nasu Nihal ta wuce a bedroom ta sami Sultan dauke da Amir yana ta kuka yana lallashin shi dafe goshi Nihal tayi tana cewa, "oh Amir dama na san by now kanan kana rigima, am sorry prince umma ta tafi ta bar ka da yunwa umma bata kyauta ba" hannu ta kai ta amshe shi tana cewa, "shhh ya isa mana love ya hana ka zama ko sorry" d'an murmushi Sultan yayi ya zauna kusa da Nihal yace, "hayaty nayi missing naki sosai" ya ida zancan tare da jawo Nihal jikin shi dake ba Amir nono cikin muryar rad'a Nihal tace, "Nima haka love nayi missing naka ai yanzu muna tare har zuwa time din da zamu je dinner ko love" daga mata kai Sultan yayi yana kallan lallan dake hannun ta yace, "hayaty wannan lallan yayi kyau sosai waya maki shi? murmushi Nihal tayi tana juya hannu ta tace, "na gode" hannu Sultan ya kama yana kissing na shi ringing din wayar shine ya katse mashi hanzari ganin Ahmad manne a screen din wayar ya sashi cewa, "aifa baza su barni na huta ba, hayaty bari nayi sauri nayi fresh up kafin Ahmad ya biyo ni dan tun da nace zan maido Prince na dawo yake kira na" dan turo baki Nihal tayi cike da shagwaba tana cewa, um, um za tayi magana Sultan ya sakar mata light kiss a lips nata, ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin milk yadi yayi kyau sosai ya daura hula, da ido Nihal ta bishi saboda kyan da yayi mata murmushi Sultan ya saki ganin yarda Nihal ke kallan shi yasan ya mata kyau hura mata iskar bakin shi mai sanyi yayi yace, "kallan fa? "kayi kyau love" murmusawa Sultan yayi yace, "thank you hayaty" ya cigaba da cewa, "bari naje na dawo" ya ida zancan tare da sakar ma Nihal pack da baby. Da daddare yan'mata sunyi shiri ciki ashoben suna dinner can na hango Nihal sanye da fitted gown light purple ta kama jikin ta tayi kyau shape din ta ya fito das da shi, sai ka rantse budurwa ce bata taba aure ba saboda kyan da ta zuba masha Allah, kan ta na dauke da head dark purple tayi kyau sosai, Sultan na sanye cikin shada shi Ash tasha aiki irin na sarautar nan a haka suka shige mota zuwa dinner. ```Taku har kullun salma mas'ud nadabo``` [3/11, 5:56 PM] salma😝: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 *Story* *And* *Writing*✍🏾 *By* *Salma mas'ud nadabo*👑 🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄 (```We are the best among the rest```) *Page:145_146* Fadin tsaruwar wajan dinner bata lokaci ne amare sunyi kyau har sun gaji, kallo daya zaka masu kasan suna cikin tsantsar farin ciki, karasawa gaban Nana Nihal tayi tana smile dukawa tayi tana mata magana a kunne tana smile daga nan aka fara gudanar da shagulgulan bikin, an cashe anyi ciye-ciye da lashe-lashe naira tayi kuka haka taro ya watse cikin farin ciki. Washe garin aka daura auran angwaye da amare a babba masallacin maimartaba sarkin kano inda manya-manyan yan kasuwa da k'ososhin gwabnatin sun halari daurin auran Ashad da Nana Nazili da Ahmad Sara da Sunusi kan sadaki lakadan naira dubu hamsim, angwaye baki ya kasa rufuwa karma ace Ashad dake ta zuba rawar kai cikin su, gabaki daya su cikin fara shada babba riga da Alkyaba angwayan suka shirya gwanin ban sha'awa duk idan suka gilma sai an tanka saboda yarda suka bada, kan sun had'e Sultan Ammar Ashad Ahmad sai Sunusi, maroka sai bin su suke suna busa, algaita sai tashi take. Cikin gidan ma amare sunyi kyau har sun gaji gidan ya kacame da busa, a daran rana flight din amare da agwayan ya tashi zuwa US honeymoon Ahmad da Nazili kuma Dubai suka wuce, bayan kwana biyu su dawo US da zama. *_Bayan shekara biyar_* Yara ne maza guda biyu suna ta gudu a company da alamar bama Nigeria bace saboda yanayin tsarin wajan da yarda yaran ke sanye cikin kayan sanyi suna wasa da ball a cikin garden, Amir da khalifa ne suke ta wasa gefe guda kuma yara ne mata guda uku da namiji daya cikin su suna wasa da Teddy's, dan namijin cikin sune ya amshe baby dake hannu d'aya daga cikin matan ya bale mata kai kuka ta saki har da birgima ta ruga tana cewa, "Habibty..! Ciki muryar ta mai tsamin da yarin ta ganin yarda take kuka yasa, Akram bin Duha yana lallashin ta yana gyara mata baby ya mika mata washe baki tayi ta sakar mashi pack a kumatu ta ruga tana cewa, "ya Amir ya Khalifa zo ku ga baby na da ya Akram ya gyara min" murmushi suka saki gabaki dayan su sauran matan dake gefe suna wasa rugowa sukayi da gudu suka nufo su Amir suna bin su suna gudu suna zagaye compound suna dariya suna jefa masu snow din dake kasa, lallacewa iyayan sukayi suna kallan yaran nasu yarda kan su ke hade. Nihal dake zaune saman resting chair ta daura kanta saman chest din Sultan yana shafa kanta sai zuba rashin kunya suke, Ammar da Basmal dake zaune gefe Basmal ta daura kanta saman cinyar shi pillow ya dauka ya wurgawa Sultan yana cewa, "na lura baka jin kunyar mu wallahi, bari dai yaran nan su zagayo su gan ku haka, idan baka ji kunyar mu ba ka ji kunyar ya'yan ka" dariya Sultan yayi ya kashe mashi ido Ahmad da Nazili dake tsaye gaban abun gasa nama da tulelan cikin ta wanda haihuwa ta biyu ce sai zuba mashi shagwaba take yana lallashin ta yana feeding nata nama, gefe Ashad da Nana suna sunuka wani iri ihu ta saki ganin ta cinye shi tana dariya rugawa tayi da gudu ganin ya biyo ta tana dariya tana mashi dariya, ta shige cikin yaran suna gudu tana mashi gwalo. After sun gama duk abinda suke suka hada kan ya'ya su zuwa cikin gida bayan sunyi sallah isha suka had'e a dining area nan ma sabuwar hira suka bud'e sai pictures suke da video's cikin jin dadi da SAUYIN RAYUWA mai cike da annuri da farin cikin mai daurewa. *_Bayan wasu yan shekaru_* Gida ne ya cika makil da al'umma da alama nadin sarauta ake yarda gidan ya cika ba masaka cinke cikin nadin har da yan ketare, yan jarudu sun cika gidan makil ba kowa ake nadawa ba sai Sultan sarkin garin kano da Ammar wazari Sultan da idanuwan shi cike da kwalla haka shima Ammar al'umma sai taya su murna suke, ana gama nadi fadda ta dauka da "gyara kintsi da kyau..! gabaki dayan muta nan dake fadda sukayi sunkeye bazgaye fadawa dake zagaye da Sultan suna cewa, "angaishe ku, an gaishe ku..! algaita sai tashi take ana kirari haka taro ya watse. Gabaki daya su zaune suke a main parlour suna jiran maimartaba busar dake tashi da algaita zai shedama sarki ya shigo cikin gida alamar an gama nad'i Nihal dake zaune mikewa tayi tsaye sanye take cikin silver alkyaba an mata dinki da gold zare, tana sakin murmushi Sultan ne ya shigo da Ammar cikin shirin su na nad'i gabaki dayan muta nan parlour mikewa sukayi Basmal da mom da Gimbiya jalila wanda yanzu sun tsufa Ammi kuwa na zaune saman wheelchair jikokin sun zagaye ta suna mata kiriniya, har da koyangin dake part din gabaki daya zubewa sukayi har da Nihal sukayi sunkuye bazgaye da kallo Sultan ke bin su shi da Ammar suna smile, har sai da Sultan ya zauna saman doguwar kujera sannan gabaki dayan su suka dago Nihal sai sakin murmushi take shima Sultan yana aika mata, jawabi yayi na yan mintocin sannan suka jeru camera man ya dauke su kowa ne fuskar shi dauke da fara'a Nihal na makale da Sultan Basmal na makale Ammar Nazili na makale da Ahmad Nana na makale da Ashad sun wani saki murmushi lokaci daya camera ta haska su. Nihal ce sanye cikin alkybar ta black tayi wani irin kyau, ta kara haske da girma bayi mata na take mata baya tana tafiya cikin isa da mulki tana murmushi mai tsada mai kara mata kyau, Habibty da aka ce ne ya sata waigowa dauke da fara'a saurayi ne matashi wanda ba zai wuce 20years ba ya kira ta kamar su daya da Sultan tamkar antsaga kara sai dai wannan yaro ne kan Sultan, murmushi ta saki cikin surprise tana bin shi da kallo shi da kannan shi dake bayan shi guda hudu tana kara fadadan murmushi ta cike da farin ciki ta bud'e masu hannu suka karaso gare ta rungume ta sukayi suna dariya ja ma saurayin kumatu tayi tana cewa, "masha Allah my boy ka kara girma yaushe ka iso baka sanar da ni dawowar ka ba, me yasa kake haka son baka san sanar da mu dawowar ka Nigeria" murmushi yayi yana cewa, "na sanar da Abbi da kanne na ko" ya fada yana jan kumatun yar autar su, dan had'e rai Nihal tayi tace "wato abun yar launin fata ce" Nihal ta ida zancan tana yima d'an nata harara wasa kama kunna shi yayi yana cewa, "sorry habibty next time ke zan fadawawa kin ji" murmushi Nihal ta saki tana cewa, "good boy Allah ya maku albarka ya'ya na bari naje wajan Abbin ku Amir ka kula da su" yar karamar cikin su ciki tsamin muryar ta tace, "Habibty zan biki wajan Abbi please ki je dani," shafa kumatun ta Nihal tayi tace, "Mamana yi hakuri dare yayi gobe akwai school ki je wajan Yasmin ta baki chocolate ki kwanta kiyi dream mai dadi" turo baki tayi tana makale kafada daukar Hafsat Yasmin tayi tana mata wasa tana cewa, "ya hakuri Gimbiya muje na baki labari mai dadi har bacci ya dauke princess," washe baki Hafsat tayi tace, "mu je aunty Yasmin" pack Nihal ta sakar mata tana murmushi Amir ya ja sauran kannan nashi suka wuce part na su yana masu wasa. Murmushi Nihal ta saki idanuwan ta cike da kwalla a hankali take takawa tana zancan zuci tana cewa, nice Nihal din nan yar talla nasha yawo k'afa ba takalmi a kauyan mu na sha wahala rayuwa nayi kwana yunwa, lokaci daya Allah ya kawo min SAUYIN RAYUWA mai daurewa har karshan rayuwa ta insha Allah, Allah ya kawo min farin ciki mai daurewa ban taba mafarkin zan zama Gimbiya ba, sai gashi yau na zama matar Sultan yar gata a wajan mijina abin kauna ta farin ciki rayuwa ta ina san ka Sultan..! ka zamo haskyan rayuwa ta farin cikin ruhi na yar lele a cikin zuri'ar ka, ka bani ilimi wanda nake tunkaho da shi yanzu tunda na cika burina na zama shugaban likitocin Nigeria rayuwa kenan, Allah na gode maka daka bani Sultan a matsayin miji uban ya'ya na..! Nice Nihal mahaifiyar Amir da Akram da jamal da Khadija da Hafsat, nice NIHAL...! hawayan dake makale a idanuwan ta ne ke kokari zubuwa lokacin yayi dai-dai da isowar ta bakin kofar turakar Sultan wage mata kofar akayi, ajiyar zuciya ta sauke tana bin turakar da kallo a hankali ta zura kafafuwan ta, alama tayiwa bayin dake bayan ta su tsaya waje, sannan ta karasa ciki tsaye ta hango sultan hannu shi nad'e ta baya yana kallan tangameman hotan Abba dake manne a bangwan dakin sanye yake cikin milk shada shi babba riga an mata aiki da dark brown zare da alkyaba light brown tasha aiki da dark brown zare kafar shi na sanye cikin takalmin sarauta kanshi na dauke da rawani, sanyayan murmushi Nihal ta saki tana kallan shi ta baya a hankali tace, "Love..! waigowa Sultan yayi idanu shi manne da farin glass ya kara girma da kamala ya manyanta, murmushi ya saki yace, "hayaty..! tare da bud'ewa Nihal hannu da gudu-gudu sauri-sauri ta karasa gaban Sultan ta fada jikin shi ya rungume ta tsam yana shafa bayan ta yana murmushi a hankali ya furta, "I love you hayaty" "I love you more love..! Um love shine baka sanar dani Amir zai dawo yau ba ko, kun kyau daga kai har d'an naka" murmushi Sultan ya saki yana cewa, "ban so ki wahala min da kanki wajan yi mashi something special kuma kin san halin Amir da tsurfa" um Nihal tace tare da kara shigewa jikin Sultan, kissing forehead nata yayi a hankali ya lallubu lips din ta yana kissing nata ya dauke ta cak tana dariya tana cewa, "love sai yaushe zaka girma ne? mun tsufa fa, muna da saurayin d'a fa" dariya Sultan yayi ya ja ma Nihal hanci yana cewa, "ni ban girma da soyayya, so ba ruwa da girma na," ya ida zancan yana zame mata alkyabar dake jikin ta daga nan wasa ya fara canza zani ganin haka yasa na sulale na fice. *_ALHMDULILLAH A NAN NA KAWO KARSHAN WANNAN LABARI NAWA MAI SUNA (SAUYIN RAYUWA) INA NAN TARE DA KU MAKARANTA NA, MASOYA LITTAFI NA ALLAH YA BAR KAUNA_* *_ABUBUWAN DANA FADA DAI-DAI DA WANDA BA DAI-DAI BA ALLAH YA YAFE MANA KURAKURAN MU_* ```TAKU HAR KULLUN SALMA MAS'UD NADABO``` *_GAMAI BUKATAR LITTAFI NA GA NUMBER TA 07063683025_*