KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 1* *FREE BOOK* Duƙe take a gaban murhun tana hura shi da iskar bakinta, daga idanunta har zuwa hancin ta da suka yi jajazir kasancewar ta fara tas zubar ruwa suke na hayaƙin da ya turnuke sararin wurin sbd kasancewar iccen ɗanya, hannunta da yayi baƙi sandiyar hura wutan ta sanya ta kamo ɗan kwalin kanta irin me yauki na da ɗin nan ta sa ta share hawayen idanunta kan ta mike a hankali tana gyara zanin da yake tsab tsab saboda tsananin tsabtarta sede a koɗe yake yayi fari fat.. Katon cikin dake jikinta na fallasa kanshi, a hankali take tafiya zuwa bakin rariyar su ta duka ta ɗauki buta tare da fyace hancin ta sossai, Seda ta wanke hannunta dake baƙi sbd hura itace kan ta wanke hancinta zuwa fuskanta ta sa sabulu guntu da ta tsinta wurin wanke wanken ta wanke hannayenta da kyau kan ta sake wanke fuskanta.. Wata yarinya dake gefen ta da suke matukar kama da bata wuce shekara 6 bane ta ce "Mama wutan ya ki kamawa ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tana kara kikkimta mawankin tace "Aisha ya zan yi, ya ki kamawa tsabar fifita kin ga yadda hannuna ya zama" Yarinyar ta matso tana ɗaukan maficin ta cigaba da fifitawa tace "mama ko in koma in sami baba me faskare ya tsanmmana rairayi da sauran faskare mu zo mu sa, yunwa nake ji kinga yaya manu ma dake rashin lafiya tun safe be ci komai ba" Lumshe idanunta tayi da suke kyawawa har mamakin ganinta a irin wannan yanayi na rayuwa Ya rufe ni,(sede ba'a mamaki da ikon me duka) a hankali cikin muryarta dake fallasa rashin son Magana da hayaniyar ta ta ce "Aisha baze gaji damu bane? Kullum muna kan yawo wurin shi neman faskare bayan ba saya muke ba?" Dakuna fuska yarinyar tayi hawaye na zubo mata. Matsowa matar tayi ta zauna a kujeran tsuguno dake wurin tare da karɓan maficin ta ce "kar kiyi kuka bari na cigaba da fifitawa samu ruwan ya tafasa in dama kunun ki sha, kiyi hakuri" Dukda ita karan kanta ba wani karfi ne da ita ba tsabar yunwa tun jiya da rana da ta sha kunun da ya zame musu jiki na garin masara da tsamiya bata kara saka wani abun a bakinta ba bayan ruwa har yanzu da ake neman karfe sha ɗaya na rana ban da Juyawa babu abinda yaron cikinta ke yi cigaba da fifita wutan tayi da kyar ta samu ruwan ya tafasa dama tun tuni Aishan ta dama musu garin masaran da ruwan tsamiya sbd rashin abun sarrafa shi kawai ta juye a ciki tana Juyawa har ya nuna. Saukewa tayi Aisha ta je ɗan karamin kitchen ɗinsu dake zagaye da zink da yayi baƙi kirin ta ɗauko wasu kofuna marasa hannun arziki ta kawo guda uku, ba tare da sugar ba sbd basu dashi basu da dalili ta zuzzuba, ta Mikawa Aisha nata ta rufe nata a gefe tare da ɗaukan Ɗayan ta karasa kan yaloluwar taburma dake shimfiɗe cikin varender ɗin sun da rabi a fashe rabi da siminti, farin yaron da kammaninsu yake sak kaman Aisha da shima ba ze wuce 10yrs ba ta ɗago ta taimaka mishi ya zauna, jikinshi banda tururin zafi babu abinda yake fitarwa. Cikin yanayin muryanta ta ce "Usmanu tashi ka sa wani abu a cikinka ka ji? Sannu.. Daure babana" Da kyar ya iya yin kurɓi biyu se amai, ya fara kelawa ruwa banza sanadiyar rashin komai a cikin nashi daga karshe ma banda kakari babu abunda yake yi, hawaye masu zafi ne suka kwararo mata, banda fatan Allah ya jefo mata Yusuf babu abunda take yi a ranta, zata tambaye shi zata roke shi ya taimaka kar yaron su ya rasa ranshi kwance a gida ko da ze zage ta har zagin ya Mannu a jikin ta ne bata damu ba. Allah ya amsa mata Adu'ar ta kuwa sbd banko kofar kyauren da aka yi tare da kamshi irin na turarukan da Yusuf ɗin ke anfani dasu da ya bule gidan ne ya shaida mata da shi ɗinne ya shigo, kwantar da Usman tayi tare da zubawa Aisha da ta taso da gudu ta dawo bayanta ta makale idanu, shi karan kanshi Usman ɗin dake kwance rawan jikin shi ya karu, zuwan Abbansu ba alkhairi bane gare su har ma ga mahaifiyarsu wani irin tsoro suke mishi da na tabbatar ko mala'ikan ɗaukan rai ne suka ji motsin shi se haka. Tsab fuskar shi ya bayyana fari sol tsiririn bafulatani Sam bashi da ƙiba sede yana da kyau iya kyau kaman shi ya halicci kan shi, takowa yake yana kwaɓe fuska kaman wadda ke bin cikin kashi Dukda tsakar gidan banda shatin tsintsiya na shara ko tsinke babu, komai a kimtse yake a gyare cike da tsabta irin ta matar gidan, har ya karaso varender da suke ya ɗago ya watsa musu wata muguwar harara cike da neman magana. Babu wadda ya iya ɗaga ido ya kalle shi a cikin su se yaran ne baki na rawa suka ce "san...sannu da zuwa Abba" Tsaki me karfi ya ja yace "kuma sannun in da daaɗi... Ke Hidayat ke kin fi karfin marabtata ko in na dawo cikin gidan nan? Zaki gayamin zaman uban da kike in ba nawa ba da har zan shigo cikin gidan nan ki kasa ɗaga ido ki mini sannu da dawowa, To wallahi ubanki zan ci in baki kiyaye ni ba, wannan iskancin bazan ɗauka ba wallahi..." Sababi ya ci gaba da yi ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, kaman wacce ta aikata wani babban laifi, kanta na ƙasa bata ɗago ba, ba se rashin bashi haƙurin ya kara ɓular da shi ba ya shiga zagin ta zagin cin mutunci ba ita kaɗai ba har da iyayenta da zuri'arta gabaɗaya, bayan ya gama wanke ta son ranshi ya karasa wani kyakyawar kofa dake daga gefe gini ne na zamani da fentin shi Milk da pink ba kaman wadda suke zaune a gabanshi ba me single room da varender banda plaster ko arzikin penti be samu ba.. Key ya sa ya buɗe tsararriyar kofar ya tusa kanshi cikin parlorn, tare da kunna wuta nan haske tar ya bayyana haɗuwar parlorn me ɗauke da milk and gold royal set na kujeru da dining tsararre a gefe kayan kallo da home theaters se fridge da labulaye ruwan gold me adon milk har Ac akwai a parlorn, cikin ɗaya daga cikin kujerun ya je ya zauna yana fiddo Wayanshi kirar iPhone 12 ya fara operating cikin kwarewa kan ya sa a kunnen shi ya fara magana daidai lokacin da ta turo kofan a hankali tare da sassanyiyar sallama nan daga bakin kofan parlorn ta duke don nan ɗinne kawai take da izinin takawa a muhallin nashi idan ba shara da goge goge bane ya shigo da ita. Wayanshi ya cigaba da yi cikin narkakkiyar murya yana zuba kalamai kaman ba shine ya gama tijaresu ba yanzu a tsakar gida, Seda ya shafe a kalla kusan awa kan ya kashe wayan nan ma be kula ta ba ya ɗauki remote ya kara muryar TV abin shi. Kafafunta da suka fara tsami sbd tsuguno ne yasa a hankali ta ce "Hamma Yusuf wurinka na zo, Dan Allah ka aramin mintuna biyu cikin lokacin ka magana nake so mu yi" Seda ya bushi iska kan ya ce yana kuma haɗe gabas da yamma "se yanzu kike da bakin magana da ni alhali kin min laifi ina faɗa a gaban waennan tsinannun yaran naki masu busashun ido irin ki baki iya bani hakuri ba?" Lumshe idanunta da zuwa yanzu ta tabbatar baza'a samu hawaye ciki ba sbd kila sun kare tayi, 'Yarana zasu yi albarka in shaa Allah' ta faɗa a ranta a fili kuwa ta furta a hankali. "Dan darajar Allah kayi hakuri, na san nayi kuskure kayi hakuri" Ta riga ta saba ko da bata da laifi dolen ta ne ta bashi hakuri a duk sadda ze zage ta ko ya ci mutuncinta. Share ta yayi, ta tattaro duk wani dauriyanta ta haɗiye miyau da da kyar take iya haɗe su a bakinta sbd azabar yunwa da ciwo da take fama dashi tana daurewa ta ce "hamma..! Usman bashi da lafiya yau kwana biyu kenan kullum gaba gaba jikin yake yi, dan Allah ka taimaka ko chemist ne a kaishi yana jin jiki... Sannan bamu da ko kwayar hatsi a gidan nan garin masara kalilan da ta saura da shi na mana kunu da rana" Wani mugun kallo ya watsa mata, tare da jan tsuki ya ce "ai dama ta inda kuka fi kauri kenan kuɗi da abinci ba, ba kince kin ji kin gani daga an taɓaki se ciki a ce ki zubar bazaki zubar ba ba? Toh wallahi ba ruwana da ciwon yaron ki hakanan ba ruwana da cin su ko shan su, ke ɗin da kika zama dole na auna miki masarar da na san a cimar cikin ki ze miki wata guda churrr yanzu tsakiyar wata ki wani zo da baki kaman shadda ki ce min abinci ya kare? Toh wallahi bazan iya ba bazata saɓu ba wai bindiga a ruwa, kin tashi kin ɓace min da gani ne ko se na take ki hanjin cikinki da wannan abunda kika kuntson sun yo waje? Gantalalliya uwar fi'ili" Duk yadda tayi kokarin haɗiye wani abu da ya tsaya mata a kirji ya tokare ta kasawa tayi, duk iya kokarin ta na ganin hawaye sun zubo mata ko da kalilan ne kasawa tayi, sun riga sun kafe sbd cin mutuncin Yusuf, se wani haki da ta fara wadda duk shekarun nan take fama dashi idan ta fara bata san denawa ba, daga kirjinta har kanta kaman zasu fice fit su bar jikinta don tsananin azaba... Da kyar ta iya fusgo maganan dake bakinta.. "Kaji tsoron Allah hamma, ka sani da ni da yaran nan zamu tsaya gaban ubangiji yayi mana hisabi, me ka tanada don kare kanka a wurin mahallicinka? Allah be hana ka ba karka tauyemu Dan Allah, Ka taimakeni Dan Allah kar in rasa ɗana zan iya jurar komai Amma Dan Allah banda su.." Se a lokacin wasu irin hawaye masu tsananin zafi da ɗacin da take ji har ranta suka ɓalle mata. Zuba mata idanu yayi kaman me jin tausayinta kan ya taɓe baki yana jan tsaki, hannu ya sa a aljihu ya ciro 1k sabuwa dall ya jefa mata yana cewa "kin ci sa'ar yau baby ta hanani ɓacin rai da se na nuna miki true color na munafuka, dubu Ɗayan nan kuma har nan da wata guda in ji kin tambaye kuɗi ki ga yadda zan saɓa miki kamanni dangin Mayu kawai" Rarrafawa tayi ta ɗauki dubu gudan, tare da mishi godiya saboda ta tabbatar in bata yin ba dubu Ɗayan se ya karɓe kuma ko kukan jini zata yi baze bata a yau ba kam gashi babban damuwanta Usman ne. Mikewa tayi da kyar ta fice, banda ciki da idanu se karan hanci babu abunda zaka hango a jikinta gabaɗaya ta rame ta lalace, ɗaki ta shiga ta ɗauko ash himar ɗin ta da shima yayi fari sol ta saka, ta fito ta dubi Aisha dake tsugune gaban ɗan uwan nata tana share hawaye itama sanye take da doguwar rigar atampha da ya ɗangale mata sossai se milk hijab ƙarami da duk ya yage har ana ganin jan gashin ta a waje cikin yanayin sanyin ta tace "Aisha kama min shi mu kaishi chemist ɗin Dr Musa" Aishan ta dube ta cikin yanayi na manyancenta ta ce "mama baki ci komai ba, Dan Allah ki sha kunun kafin mu tafi in kema kika fara rashin lafiya ban san yadda zan yi ba" Yarinyar bata jira Cewar uwar ba ta karasa gaban murhun su ta ɗauko kunun masarar ta zo ta Mikawa maman, zama tayi ta kurɓe Dukda wani irin murɗawa da ɗan cikinta yayi a sadda abincin ya sauka gare shi, wani irin tausayinshi ne ya lulluɓe ta hannunta ta daura kan cikin ta ce "kayi hakuri" Bayan ta gama sha ta mike, Aisha ta taimaka mata suka dafe Usman suka fice daga gidan bayan ta sa mishi rigar wani kodaɗɗen jumfa da gefe da gefe suka yayyage, fitowa suka yi idanu ta ɗan zubawa motar Yusuf ɗin kirar Vibe sabuwa dal baƙa me ɗaukan idanu kan ta ɗauke kai suka zagaye shi suka wuce chemist... **** Tou fa mutanena, ga Gureenjoh da wata sabuwa su waye wannan ahali wani irin zama ne wannan? Shin Hidayat bata da en uwa ne? Bata da dangi ne? Shin Ba auren soyayya bane suka yi tsakanin ta da Yusuf? Ko kuwa auren dangantaka ne tunda tana alakan ta shi da hamma...? Shin yaran ba yaranshi bane da yake alakanta su da tsinuwa? Me suka yi da zafi haka? Duk ku biyo Ƴar mutan Gurin na jihar Adamawa don warware wannan zare da Abawar wannan littafi kyauta ce... A sha karatu lafiya. #Vote #share #Comment 🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 2* *FREE BOOK* "Maman Usman yaron nan ai ba chemist ya kamata ki kawo shi ba asibiti ya kamata ki kaishi yana jin jiki sossai.." Share hawayen ta tayi sbd mammatsa cikin Usman da malam Musa ke yi yana ƙara cikin azaba se taji ina ma zata iya cire mishi ciwon ya dawo jikinta Allah sarki uwa kenan. Cikin damuwa tace "babu halin ne Dr da akwai da na kaishi, in na tafi asibiti da dubu guda babu me saurara ta, ka taimaka ka bashi ko na rage zafi ne kan in je in nema Dan Allah" cike da tausayinsu Dr Musa ya Haɗa musu magani kuma be karɓi kuɗin ba yace "ku je ku gwada Allah ya bashi lafiya" Ta mika mishi kuɗin "gashi se ka cire" "A'a maman Usman ke de Allah ya bashi lafiya" Godiya sossai tayi mishi kan ta kamashi Aisha ta taya ta suka dawo gida, ruwa ta samu ta bashi ya sha ya kwanta bacci ya samu ya ɗauke shi. Zugum ta zauna tana Tunanin yadda zata bi da dubu gudan nan har ya kai musu karshen wata, kaman yadda Hamma Yusuf ya faɗa ko da mutuwa take idan har watan nan be kare ba ba basu kuɗin nan ze yi ba, dafata da Aisha tayi yasa ta buɗe idanunta da suka yi laushi da gajiya, yunwa, damuwa da ciwo ta zube su kan yarinyar. "Mama Tunanin me kike?" Aisha na da wayo ko ta ƙi faɗa mata haka zata yi ta naci tayi ta naci se ta sani. "Ina Tunanin yadda kuɗin nan ze kaimu wata ne Aisha" Ta faɗa mata ne kawai ba don wai da tunanin samun mafita daga yarinyar ba, ita ma rashin abun cewa ya sa tayi shiru kawai ta zubawa wuri guda ido.. Kaman saukar aradu haka taji a sadda kunnuwanta suka jiyo mata sallamar wasu mata da suka shigo su hudu, akallah ba akasara ba babu wacce zata haura 28 cikinsu, se matashiya da zatayi sa'a da Hidayat kaman yadda naji Hamma Yusuf ya faɗa sunan. A maimakon farin cikin da kowa yake yi idan yayi baƙi saɓanin Hidayat tashin hankali ne ya bayyana karara a fuskanta tana shirin magana ɗaya daga cikinsu tace "Shafaffiya da mai yau ko arzikin sannu da zuwan ba zamu samu ba kenan ana baƙin ciki da lafiyarmu" Baƙar tace "Eh to Salamatu ba dole tayi baƙin ciki da lafiyanmu ba tunda da shine muka tako muka zo har gidanta" Matashiyar tace "A'a Aunty kausi gidan ɗan uwan mu dae... Ni wlh in banda ya Yusuf banga abun ɗauka a wanna ƙashi da ran ba se fari kaman aljana" Na karshen tace "ke kuwa Surayya baki da labarin ita ce ta shiga ta fita sbd ta sha a nono tayi yadda tayi ta sa shi Yusuf ɗin ya fara son ta har Abba ya Haɗa auren, to da aka zo ba'a samu yadda ake so ba kuma an kasa bari an manne kaman dangin maita" Na farko wacce aka kira Salamatu tace "To wa ya sani Abu a duhu.." Budurwar Surayya tace "a kuma cikin baƙar Leda" Suka kwashe da dariya... Aunty kausi tace "wai kuma dan bala'i Da aka tashi auren aka Haɗa da nawa Abba har da yiwa wannan munafukar annamimiya kayan da suka fi nawa har yau in na tuna kaman in mutu" Dariya duk suka yi Salamatu tace "ki bar ɓata ranki yanzu duk suna ina?" "Gidan Boka" Cewar Fahariyya itace ta karshen.. Suka kwashe da dariya tare da tafawa.. Wucewa sukayi har Surayya na bangajeta Seda suka shiga ɗakinta kaman yadda suka saba suka yi filla filla da ɗan tarkacen ta suka gama kan suka nufi parlorn Yayan su suna masu ci gaba da ci mata mutunci daki daki. Idan dutse ya tanka to fa Hidayat ta tanka, se kara jan Aisha da ta lafe jikinta tayi tana me mayar da idanunta ta lumshe, ta riga ta saba da duk wasu maganganunsu da muguntarsu tunda a ciki ta tashi, a ciki tayi wayau a kuma ciki aka raine ta har tayi aure, dukkansu babu wacce bata saba da bautar ta da kuma duka da zagin ta ba, tun tana damuwa har abun ya zo ya bi jikinta.. Tana nan zaune Yusuf ya fito shi da Surayya suka fice bata buɗe idanunta ba kaman yadda basu kalli inda take ba, bata san mintunan da ta ɗauka haka ba kawai ji tayi saukar ledoji a jikinta da kuma karfi, a razane ta furta "A'zubillahi minasshaiɗanir rajeem" "sede in kece sheɗaniyar ko kuma uwarki" Cewar Surayya. Yusuf yace "oya maza tashi sun zo suna jin yunwa, sannan ba su kaɗai ba ina da baƙi biyu anjima tashi ki ɗaura musu sanwa yanzun nan" Aisha take shirin kwantar wa ta mike don ta san rashin mikewa da wurin ma ka iya zama laifi sede bata kai ga zame ta ba ya daka mata tsawar da ta kaɗa har abunda ke cikinta Aisha dake bacci ta farka a firgice. "kin tashi ko se na taushe ki???? Ana magana kina wa mutane abu lagwai lagwai kaman lagwani" Kallon babanta take har Mamanta ta mike ta tattare ledojin da har wasu abubuwa sun watse a ciki ta nufi inda take hura wuta. "Ga min ƴar banzar yarinya ke don uwarki kin dena kallona da waennan Mayun idanun naki ko se na tsole miki su kin makance?" Hawaye ne suka zubo mata cikin rawar murya tace "Abba mama fa bata da la..." Marin da ya ɗauke ta dashi yasa ta hantsila maganan bakinta ya yanke, duka ya rufe ta dashi tana ta ihu babu wadda ya iya fitowa a cikin goggoninta ya amsheta, Hidayat dake duke bakin murhu da yaro matashi ya shigo da itace busasshu ya zube da Alamu aikan Yusuf ne ko ɗago kai bata yi ba. Seda ya gaji ya kyale ƴar yarinyar yayi wucewarshi inda ƴan uwanshi dake shewa suna kallo a parlorn shi, da gudu Aisha ta mike ta zo ta faɗa jikin uwarta tana me sakin sabon kuka wadda Seda ya sa Hidayat hawaye.. "Mama me yasa Abban mu baya son mu kaman sauran Abban kawaye na? Ko shi ba shine Ab..." Hannu Hidayat ta sa ta toshe mata baki. "Kar na kara jin hakan daga bakinki mamana, shima yana son ku kiyi ta mishi Adu'a in shaa Allah watarana se labari" Da taimakon Aisha take aikin Dukda ba wani abun Arziki ta iya ba har ta Haɗa jollof rice me kaza a ciki. Fagen girki Hidayat ba baya ba sbd ta horu dashi tun bata iya ba ake sakata tayi in be ciyu ba ace se ta cinye in bata iya cinyewa ba wani sa'in a mata ɗure da amai da komai wani sa'in kuma ta daku iya dakuwa... Lumshe idanunta tayi tana tambayar kanta amsan da ta ba Aisha 'ko se yaushe wataranan ze zo?' da wannan tunanin ta gama girkin ta tsabtace wuraren tas, Haɗawa tayi ta kai kofan parlorn tare da knocking basu amsa ba suna ta shewarsu gajiya da tayi da tsayuwa yasa ta tura da sallama a bakinta ta ajiye musu daga bakin kofa zata wuce Aunty kausi tace "Eh ga mayunwata in yunwa ta kusa halakamu se mu rarrafa mu ɗiba ko?" Yusuf dake wani faffaɗi cikin jin shi ya isa da gidan shi yace "ke ɗauko ki kawo nan, ki shiga kitchen ɗina ki haɗo musu duk abun bukata ki kuma zo kiyi serving ɗinsu, Allah ya Taimakeki kwarzane baki yi min jikin warmers ba.. Hmm" Seda ta sake duba warmers ɗin na hannunta da kyau gudun matsala kan ta karasa gangansu ta ajiye tana ɗagowa surrayya na toshe hanci wai wari, bata ce komai ba ta je kitchen ta haɗo plates da spoons da cups ta zo, bazata iya dukawa a duƙe ta sa musu ba hakan yasa ta tafi kan gwiwowinta hannunta dafe da mararta da yayi mugun kullewa, a haka ta sassaka kan ta lallaɓa ta miƙe ta ajiyewa kowa a gabanshi.. Babu godi bare na gode haka ta fito, ɗan wadda ta rage a ƙasan tukunya ta zubawa Usman da Aisha, a chan ɗaki ta kular dasu sbd idan har uban su ze gansu suna ci babu abunda ze hana shi kikkifa mata mari da kiranta da suna ɓarauniya, ita ta dinga lallaɓa Usman da kyar ta samu ya ci kaɗan ya sha magani, sauran ta rufe ma yaran akan se anjima ita kuwa ta fito ta kankare tukunyar ta ci ta sha ruwa. Tana rayuwa ne kawai ba don tana jin daaɗin shi ba, in har zata zauna ita kaɗai damuwa da Tunanin rayuwarta kan jefa ta wani yanayi me matuƙar wahala, sallama da ta ji ana dokawa ne yasa ta ɗago kai da sauri tana ɗan murmushi tace "Ummi sannu da zuwa, yau ke ce a gidan namu?" Wacce ta kira da ummi na jefanta da kallo me cike da tausayi tace "ni ce hidayat" "maraba Lale, karaso ciki" Ɗakinta suka shiga don bata son masifar su Aunty kausi ya bi kan ƙawarta Dukda ba haƙuri ne da ita ba sede su kwasa in dae ummi ce. Da sauri ta karasa kan Usman da ta gani kwance tana taɓa shi tace "hidayat Usman ɗin ba lafiya ne?" Kai ta gyaɗa mata tana cewa "da sauki ma ai, ɗazu muka samo magani daga chemist" Cike da wani yanayi ummi tace "hidayat har se yaushe? Uhm! Har se yaushe zaki hutashe kanki da wannan azababban rayuwar?" Manyan idanunta da suka rame se haske ta zuba mata kan tace "ummi in na Rabu da hamma Yusuf ina zanje? Gidan su fa zan koma, a da da nake buduruwa ma basu riƙeni da zuciya ɗaya ba se yanzu ga yara? Kin dae san halin umma tun muna makaranta ba ma ita kaɗai ba ina kike so na kai jidalin su Surayya?" Girgiza kai Ummi tayi cike da dumbin tausayin hidayat kwarai da tana da taimakon da zata mata wurin neman dangin ta ko na uwa ko na uba da ta yi, wannan wahalar har ina? "Ina namesake ɗita?" Hidayat na murmushi tace "yanzu ta tafi islamiyya, ya su Maami?" "Suna nan lafiya" Mikewa Hidayat tayi da kyar ummi na mata sannu taje ta ɗibowa ummin ɗan sauran shinkafar da ta rage ma yaran na dare da ruwa a cup, ta zo zata ajiye ummi tayi saurin mikewa ta karɓa tace "da na san tashin nan nawa ne da ban bari kin miƙe ba" Murmushi kawai hidayat tayi ta zauna, ummin bata ci abincin ba ta barshi a rufen shi, ba kuma wai don kyama ko reni ba, ta san a tsabta babu na biyun hidayat tun suna school daga primary har suka kai ss1 hidayat ce ke samun prize duk speech and price giving day Inde best in neatness ne, duk da kuwa irin kangin rayuwar da take ciki. Hira suka ci gaba da yi suna dariya, sossai ummi ke deɓewa hidayat kewa take kuma bata shawarwari, ummin ƙawarta ce sun yi school tare har zuwa ss1 kan kaddararta ya yanke karatun sbd babban bangon ta da ya faɗi ciwo wadda har kawo yanzu be tashi ba. Duk yadda tayi da ummi taci abinci ƙi tayi akan ta ci kenan ta fito Dukda ba daga ma gida take ba, kawai bata son ci ne sbd ta tabbatar iya abinda hidayat ɗin ke dashi kenan ta bata, Allah yayi hidayat me son kyauta da karamci ita ko last kobo ɗinta ne ko da zata takuru ne zata ba ka, ta sha bata transport da kuɗin break ɗinta idan ta yar da nata, ummi gidansu basu kai inda Hidayat ta tashi hali ba hakan yasa ba'a zuwa ɗaukan su daga gida da mota sede a basu transport saɓanin su hidayat. Sun sha hira ko tafiyar su fahariyya basu ji ba, se dab magrib ummi ta mata sallama zata tafi a nan ta ajiye mata 2k Dukda yadda hidayat ta nuna ba se ta shiga ɗawainiya ba, harara ummi ta zabga mata wadda ya sa ta dariya tace "to godiya nake, Dan Allah ki gaida min maami da su Noor" Har ummi ta fice daga gidan bata sake waiwayawa ba, rayuwar hidayat na sakata kuka da tana da halin bata abunda yafi haka zata bata, ita yanzu take university wani lokacin se taji da ma hidayat ce ta samu wannan dama yadda kowa ya Santa da son karatu ga kwazo sede dubi inda rayuwarta ya ƙare. hidayat na shirin Juyawa kenan daga rakiyar da ta yiwa ummi ta ga shigowar ta, kan ta kauce ta bangajeta a razane tayi baya tana me zare idanu saboda tabbatarwa da tayi babu abunda ze hanata faɗuwa... #like #share #comment                      🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 3* *FREE BOOK* Tunaninta ya yanke ne a sadda taji ta dafe kyauren gidan tana sauke ajiyar zuciya da godiya ga Allah da be bari ta kai ƙasa ba, da kallo ta bi budurwar da ko waiwaye bata yi ba har ta shige sashen Yusuf, girgiza kai tayi duk cikin ƴan matanshi da yake kawowa gidan babu marar mutunci kaman firdous, in har ta zo ta dinga wahala kenan. A ganin firdaus hakan ne ze rage mata kishin Hidayat tunda Yusuf ya ki sakinta, bata da masaniyar da tana da inda zata da bazata taɓa zama da wannan kadararren auren ba. Tsaki tayi ita tun kawo ƴan matanshi na damunta har ya zo ya dena damunta kwata kwata, ɗaki ta shige ta kishingiɗa jefi jefi su kan yi magana da Usman Aisha ta tafi islamiyya, anan ne ma ta yanke shawarar ta fara sana'ar gawayi. "Mama in na girma bazaki sake yin wahala ba, zan gina miki babban gida da mota in zuba miki masu aiki irin na gidan Alhj mudan" Murmushi ta saki tana kallon Usman ɗin da tsakaninsu da Aisha kwata kwata shekara ɗaya da rabi kenan don yanzu yana cikin shekara na 6 da ƴan watanni, tace "in shaa Allahu babana, Allah ya bamu yawan rai" Cike da jin daaɗin ganin murmushinta yace "Ameen". Ta miƙe tana saka hijab tace "bari in shiga nan maƙota in nemi yaron da zan aika ya saro min gawayi a chan hanyar hadeija yafi kyau" Yace "Mama gawayi zaki fara sayarwa?" Tace "eh Usman, ka ga unguwan nan babu masu sayar da shi sossai kuma ana amfani dashi, dayawa se sun je layi na gaba suke samowa kaga zamu yi ciniki in shaa Allah" Gyaɗa kai yayi yace "Allah yasa kar su maman zubair su hana ki, kaman yadda suka zo nan suka hana ki sayar da kayan miya" Murmushi kawai tayi tare da girgiza kai, yaran yanzu se a hankali komai sun sani, tana tafiya tana Tunanin yadda mutanen unguwan suka haɗe mata kai sbd ɗan cinikin da take yi a kayan miyan da take sayarwa karfi da yaji suka sa ta dena sana'ar su suka cigaba se a lokacin ta san eh lallai duk kankantar samunka wani baƙin ciki yake da kai, baƙin cikinta da sana'ar take samun na biyawa yaran nan ɗan kuɗin PTA da na islamiyya se kuma ɗan abunda zasu saka bakin salati Dukda shima ba na arziki bane, suturu kam ba'a magana. Har ta isa gidan tana Tunanin duniya, da sallama ta shiga daga tsaye suka gaisa da matar gidan da ta kira da Asabe, kan ta ɗaura da "Dan Allah ko a cikin yaran akwai wadda ke kusa aike ne nake ɗan so in yi" Habiba dake kofan ɗakinta tayi Charab tace "se kuma ki rasa yaran aike se na gidan nan?" Bata kalleta ba idanunta na kan Asabe da Seda ta jira karshen maganan habiba kan tace "kin ga kuwa wlh duk basa nan kiyi hakuri in sun dawo ko zuwa gobe se in turomiki ɗaya daga cikinsu" Lantana dake zaune kofar ta tana tankaɗe tace "munafunci da iyayin banza, in an ga dama a karɓa kawai a je yanzu ba se an jira yara ba karshen soyayya da tausayi kenan" Habiba da Zulai da itama ta ɗaga labule tana jin Abunda suke faɗa suka kwashe da dariya. Fita Hidayat kawai tayi ba tare da tace musu komai ba, bata san me ta tare musu ba ita rayuwar da take ciki ma kaɗai ya ishe ta, yadda suke mata ko tsakaninsu da suka Haɗa miji basa yi se da ita. Asabe ta kallesu tace "wlh bakwa kyautawa abunda kuke yi, baiwar Allahn nan tana fama da lalura ga wahalar rayuwa Dukda haka bata fasa baku girmanku na maƙota kuma ƴan uwa a musulunci ba, amma kun kafa mata karan zuƙa..." Katse ta Zulai tayi wacce ita ce uwargidan su tace "mu ji duka kan mu san kina yi Asabe" Habiba tace "Ah to!" Daga haka bata sake magana ba ta cigaba da abunda take yi, waye be san irin rayuwar da hidayat ke yi a gidanta ba! Waye be san irin kaddararen miji da Allah ya Haɗata dashi ba! Ko basu tausaya mata don komai ba sa tausaya mata sbd cikin dake jikinta da kuma kankantan shekarunta cikin Kab matan da suke layin. Hidayat kam na fita bata tsaya sake shawara ba ta taka zuwa bakin titi ta tsare machine suka yi ciniki ta hau se hadeija road, anan ta saro gawayinta se sauri take sbd magrib da ya karato gashi yaranta na gida su kaɗai, rokan me machine ɗin tayi ya kawo ta har kofan Gida Albarkar abun cikinta ya amince, anan ya dire mata buhun gawayin hannunta rike da leda wadda cikinshi ledoji yellow masu zanen baƙi ne ciki na kulla gawayin. Almajirai ta nema suka shigar mata ciki ta basu hamsin, da gudu Aisha ta zo ta karɓi ledan tana mata sannu da zuwa. Usman da ya samu karfin jiki ya kawo mata ruwa, murmushi tayi ta karɓa tana godiya duk halin da take ciki idan har zata zauna ko da na seconds da yaran nan nata se taji zuciyarta yayi haske, kaunar da suke mata ya samo asali ne daga tsananin tausayinta da suke ji, duk kankantar shekarunsu sun san duk abubuwan dake wakana a rayuwarsu, ita kuma burinta shine rayuwar su ta inganta, bata son ganin sun yi kukan wani abu bata taɓa Barinsu da damuwa ko da kuwa ita cikin ranta dankare yake da damuwar. Hakin dake yawan damunta tai tayi Dukda ruwan da ta sha sede be dena ba, da kyar ta samu ya lafa ta kalli Aisha tace "shatu! Ki shiga Gidajen maƙotan mun nan ki faffaɗa musu muna saida gawayi kin ji? Kar fa kiyi nisa iyakacin layin nan kinga magrib ya gabato" Kai Aisha ta gyaɗa kan ta fice da gudu. Seda aka fara kiraye kirayen sallah kan ta dawo tana bata labarin waenda suka yaɓa mata magana da waenda suka amshe ta suka ce se sun zo saya da waenda ko kallon arziki ba'a mata ba da waenda masu gadi suka koro ta daga kofar gidan. Tana ta murmushi kawai tana matse kafafunta da suka kumbura, Seda suka saki kan ta mike tayi alwala suka gabatar da sallarsu a tare, anan suka zauna suka yi azkar don duk rintsi bata barin su su kwanta ba tare da sun yi azkar ba haka bayan sallar asuba, karatu suka ɗan yi na Qur'ani kan ta basu abincin da ta rage musu, yaran na da tsananin wayau hakan yasa basu ce mata komai ba sede fa duk wadda yayi loma ɗaya ze sa mata ɗaya idanunta cike da hawaye take karɓa har suka gama suka sha ruwa suka zo suka kwanta sbd basa fita ko ina daga magrib yayi, in sun yi isha kuma haka zasu kwanta suna hira tsakaninsu har bacci ya sace su hakan yasa yaran nata ke da tsananin kulafucinta wani irin shaƙuwa da kusanci ke tsakanin su. *** Alhamdulillah Hidayat ta fara sana'ar gawayi kuma daidai gwargwado tana samun ciniki sbd kafin sati buhun ya ƙare ta samu napep ta je ta sayo buhu biyu ta cigaba da sana'ar ta sbd ita tun daga washegarin ranar da ta fara sana'ar gawayi bata sake saka Yusuf a ido ba tun kuma 1k da ya wurga mata. Usman ya warke garas yanzu ya koma makarantarshi boko da Islamiyya, ita kanta ba yaran ba hankalinsu a kwance yake na rashin saka Yusuf ɗin a idanu sbd a sake suke komai ba tsoro da kaffa kaffa. Da ɗan cinikin ta ta fara tara wasu abubuwan da suke dole wurin haihuwa sbd tana da tabbacin ko yau ko gobe zata iya tashi da naƙuda don har ta ma wuce Edd ɗinta. Yau haka kawai ta tashi da son ganin Abba, hakan yasa ta ajiye duk wani fargabarta da tsoron ta ta shirya cikin kodaddun kayan ta da hijab ɗinta da yayi fari fat sbd koɗewa ta fita ta hau achaɓa, cikin sanyin murya ta faɗa mishi unguwar da ze kaita cikin mintuna kasa da talatin suka isa ta sallameshi gabanta na faɗuwa ta shiga gate ɗin gidan. Allah ya taimake ta bata gamu da kowa a wakeken tsakar gidan ba har ta isa sashen Abba, da sallama ta shiga uwar ɗakin se suka Haɗa idanu da dattijon a take ta saki murmushi shima fuskanshi a take ta washe baya iya magana amma a cikin idanunshi ta karancin murnar ganinta da yayi, babu abunda ya raba shi da Yusuf se tsufa da ze nuna mishi. Da sauri ta karasa gabanshi ta duƙa tace "sannu Abbana!" Kallon cikinta yake yi, hakan yasa ta miƙe tana fahimtar so yake ya hanata duƙawar sbd cikinta tana murmushi tace "ya jiki Abba? Allah ubangiji ya baka lafiya yasa kaffara ne wannan ciwon" Idanu ya lumshe, yana me kallonta tace "Abba su Aisha na gaisheka duk suna lafiya sun je islamiyya ne yasa ban taho dasu ba" Sake lumshe ido yayi ya buɗe tace "Abba ka sha maganin ranar ka kuwa? Abba ya kake zaune kai kaɗai?" Bata jira Cewarshi ba ta gyara ƙimar ɗinta ta taimaka mishi ya zauna da taimakon Allah ta mayar dashi kan kujerar shi na turawa wato wheel chair sbd ganin rashin tsabtar ɗakin da take, ta turo shi varender inda yake shan iska, komawa tayi ciki ta fara da wanke bayi, ta gyara bedroom ɗin zuwa parlorn Kal Kal ta saka room fresheners dake ɗakin ta ɗan kara Ac sbd zafin da garin ya ɗauka yanayi ne da damina ke dab da sauka hakan yasa a kullum zafin ke kara yawaita. Bayan ta gama ta miƙe da kyar sbd bayanta da ya kage ta koma ta turo shi suka dawo, kunun da ta samu a flask ta tsiyaya ta bashi da spoon dukda rabi ke shiga rabi na zuba haka ta bashi ta goge inda ya ɓaci a jikinshi, nan ta zauna kasan kafan shi ta miƙe kafa tana ta bashi labarai tana murmushi. Hidayat is a strong girl/woman he has ever seen a rayuwarshi, lumshe ido yake yana me mata Adu'a a zuciyarshi Allah ya gani ya bata Yusuf ne da tunanin ze riƙeta amana ya kula da maraicinta be san ganganci yayi ba seda lokaci ya kure, ba yadda ze yi ne yake ganinta cikin wannan kangi na rayuwa, a kullum ya kan roki Allah lafiya ne sbd ya samu ya kwatar mata hakkinta. Yarinya ce da ta tashi cikin wahala ta Rayu cikin wahala tayi aure cikin wahala, she deserves a better life, natsuwa, hankali, ilimi da kyau Duka tana dashi why life choose to be so rude to her? She's so jovial faram faram ce da matukar wuya ka fahimci damuwarta. Duba yanzu kaman ba shi ya haifi iyalin da suke gasa mata aya a tafin hannu ba, duk ranar da ta zo wurinshi ya kan tsinci kanshi cikin farin ciki sbd yadda zata zage ta bashi kulawa tayi making time ɗin lively da hirarrakinta ta tsabtace mishi muhalli wadda matar da yake aure kuma uwar Yayanshi bata mishi ba, duk cikin yaranshi babu me tsayawa yi mishi wannan hidima se me aiki, be taɓa sanin wani lokacin kuɗi kan zama masifa da bala'i ba seda wannan kaddarar ta same shi, da shi ɗin talaka ne, da lokacin neman kuɗinshi be shiga lokacin iyalinshi ba da ya dasa shakuwa da tausayi a zuƙatarsu, ya kan ga laifukanshi a kaso mafi yawa cikin abubuwan da suka faru da rayuwarshi kuma yana ɗaukan darasi in ya mutu falillahil hamd idan kuma yana da rabon lafiya ze yi iya kokarinshi wurin ganin ya gyara. "ABBA..!" Hidayat ta kirashi tana waving hannunta fuskanta cike da shagwaɓa wadda ya fidda asalin ainihin kananun shekarunta tace "ko Hirar bata maka daaɗi ne naga idanunka sun sauya kala?" Idanun ya zuba mata se ya lumshe su alamun a'a, tace "in cigaba?" Ya sake lumshe mata idanu, idanunta ne suka sauka kan agogo ta wara ido yaran suna gab da dawowa bazata so su dawo su tarar bata nan ba, mikewa tayi tace "Abba zan tafi zaka kwanta?" Ya lumshe mata idanu sau biyu alamun a'a sbd ya gaji da kwanciyar, hannunshi yake ta motsawa wadda yatsu biyu ke iya ɗaguwa hakan yasa ta fahimci magana yake son mata, kallon inda yake kallo da kokarin pointing tayi taga bedside drawer ɗinshi ne ta kalleshi tace "A'a Abba ina da kuɗin machine" Haɗe fuska yayi yaki kallonta hakan yasa ta fahimci fushi yayi, se ta taka zuwa wurin ta buɗe tare da sa hannunta akan kuɗin zata zare 1k kenan aka turo kofan, karab idanunsu suka haɗe wadda ya haddasa mata mummunar faɗuwar gaba da sauri ta miƙe sbd Kab duniya babu wacce take kallonta taji hanjin cikinta ya kaɗa irin umma, ta gana mata azabar da ko sunan umma taji an kira se gabanta ya faɗi. "La'ila ha'illallahu Muhammadur rasu lillahi salla lahu alaihi wa sallama... Sata? Hidaya abunda kika koma Kenan? Ɓarauniya..!" #like #share #comment                    🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 4* *FREE BOOK* Cikin rawar murya tace "A'a umma don Allah kiyi haƙuri wlh Abba ne ya matsa na ɗauki kuɗin machine shine zan zari dubu ɗaya.." Wasu Zafafan maruka hagu da dama ta ɗauke ta dashi wadda Seda ta saka ta kaiwa kasa tana ji kaman amsa kuwwan maganan umma tana cewa "Munafuka! Algunguma sharri zaki yiwa Alhajin? Ina ya ga bakin magana da har ze matsa ki ɗauki kuɗi? Idan ba salon sata ba me yasa da kika shigo baki shiga cikin Gida ba kika sulale nan? Eyee wato da mudi me gadi bai ce min kina nan ba sede mu zo mu samu an wawushe Alhaji? No wonder kullum kwanan duniya ake samun kuɗi ya ɓata.." Hawaye ne masu zafi suka zubo mata, ta sa hannu ta goge har lokacin bata ji daidai sbd umma ba bahaushiya bace irin kabilan kudun nan ce da suka ginu da tuwo da wahala hakan yasa hannunta na daga cikin hannun da in ta sauke maka se ka rasa natsuwa da ji na tsawon lokaci, cikin rawar murya tace "Wallahi ban taɓa ɗaukan abin wani ba umma kuma ke sheda ce, da ina sata da tun kan nayi aure da kin sani Allah ya gani b..." Gwaɓe mata baki tayi wadda Seda ya fashe umma tayi. "Rashin kunya kuma zaki min? Eh lallai dole.. Karki ga kaman kin haihu biyu ko kina da tsohon ciki wlh baki sauya a idanu na ba, be dame ni ba yanzu in lakaɗa miki na jaki in ga uban da ya tsaya miki a garin Kano, banza ƴar Zina...." Faɗuwar mutum da suka ji yasa duk suka juya, Jijjiga Abba ya fara wadda har yana sulmiyowa daga cikin kujeran ba tare da sun kula ba seda ya faɗi. Da gudu suka yi kanshi suna kiran sunanshi, umma na shikenan ta kashe min shi ta huta. Kaman daga sama se ga Yusuf da kaninshi mus'ab da gudu suka ɗauki Abba suka fito zuwa mota. Hidayat bata tsaya ba ta shiga motan tare da kafe shi da idanu tana zub da kwallar takaici da baƙin ciki, babu wadda ya kula sbd tashin hankali suka ja suka yi asibiti umma ta biyo su da motan ta, suna parking a harabar kumfa ya fara fita daga bakin Abba hankali tashe Hidayat ke share mishi da hijab ɗinta. Buɗe idanu yayi ya kafe ta da shi, wani natsuwa da karfin gwiwa ta samu a take ta fara karanta Kalmar shahada abu da ikon Allah mutumin da ya shekara ɗai ɗai har shekaru bakwai da watanni a yanayi na jinya da rashin magana da tsananin ciwo ya buɗe baki kalmomin na fita a rarrabe ya fara cewa "Kiyi haƙuri da rayuwa, ki yafe min hidaya!" Sune suka fito kaman an fusgo su daga bakinshi, kalaman da suka yi sanadiyar karasa ruɗata tsabar hawayen dake kwaranya har bata iya gani da kyau tana girgiza kai tace "baka min komai ba Abba..! Baka min komai ba..!!" Murmushi yayi se ya fara karanta Kalmar shahada daga karshe numfashinshi ya tsaya Chakk. Daidai lokacin da Yusuf ya fisgota waje ba tare da yayi la'akari da cikin jikinta ba, isowarsu kenan da gadon marasa lafiya don a ɗauki Abba sede likitan na lekawa yace "Innalillahi wainna ilahi rajiun! Sede haƙuri Allah ya riga ya amshi abun shi" Ihu umma ta kwala, yayinda hidaya da ta riga da ta san da mutuwar sede bata yardar ma zuciyarta ba seda taji daga bakin likitan, chaak duniyar ta tsaya mata Sam bata san me suke yi ba. Idanunta sun yi ja ga hawaye masu zafi suna gangarowa, ji tayi kirjinta ya mata nauyi ga wani zafi da yake aikin yi mata kaman ze kama da wuta ko ya riga ya kama, Ko sunanta zaka tambaya a lokacin tana da tabbacin bata san daga wata kalma ta fara ba tsabar tashin hankali, shikenan ita kuma alqiyamarta ta tsaya, bangon ta, jigon ta ya rushe ya zube! Shikenan fah bata da kowa da ya saura mata a duniya shikenan! Wani irin jiri ya ɗibe ta ta duƙe bisa gwiwowinta ta fashe da wani irin kuka da dukkan zuciyarta kaman wacce aka lodawa gabaɗaya damuwan duniya a kirji. 17 YEARS EARLIER Yarinya ce ƴar kimanin shekaru biyar tsaye jikin rariya Dukda Duhu da sanyi irin na asuba da ya mamaye garin ita tsaye take tunbur babu ko ɗan kamfai a jikinta, banda rawar sanyi babu abinda take yi hawaye kuma wani na bin wani a idanunta sbd jikinta dake raɗaɗin duka da taci da asubahin Allahn. "Tsaye kika yi baki watsa ruwan nan kin zo kin fitar da kayan nan kin wanke ba?" Da sauri ta ɗauki bocket ɗin ruwan ta kwarawa jikinta bayan ta ɗauke numfashi saboda azaban sanyin shi musamman umma ke ajiye shi ya kwana buɗe yadda ze yi sanyin da se ya kusa daskarar da gudun jininta. Bayan ta gama ta taka a hankali zuwa cikin ɗakin ta ɗauki rigar ta da ya koɗe wadda kuncen Surayya ne ta saka, dukda ba wai ta girma bane ga rashin girman jiki da ya mayar da ita ƴar pirut ta ɗauko ledan pitsarin da zanin ta koma chan baya ta wanke ta shanya a saman soak away sbd tsawon ta da baya kaiwa igiya. Har ta dawo ɗakin dukkansu yaran gidan na kwance suna bacci, tsabar kwarewar umma a mugunta Dukda akwai masu shara sede ita ɗin de ita zata yi a Cewar ta bata kai matsayin ƴan gida ba kuma dole ta dinga tunawa da ita ɗin Ɗiyar Riƙo ce, haka ta daddage tayi ta shara in be fita ba ta koma ta sake sbd a haka ta saba, se a lokacin yaran gidan suka tashi, manyan suna wanka da kansu yayinda yaran se de ayi musu har Surayya kuwa dake sa'ar ta, bayan sun gama aka shiryawa kowa breakfast ɗinshi wadda dankalin turawa ne da shayi me madara. Raƙubewa tayi jikin dining ɗin tana jiran su gama ta bi plates wadda suka rage ta ci, hakan kuwa aka yi bayan sun koma parlor kowa na saka safa ta tashi ta bibbi plates ɗin ta cicci wadda suka rage ta tattare ta kai kitchen, ta dawo da sauri ta je ta saka uniform ɗinta sbd sun fara ficewa in kuwa ta ɓata musu lokaci ba karamin duka zata ci ba. Bayan ta saka bata tsaya sa safa ba ta riƙoshi a hannu da jakanta ta fito da sauri, a gaban Abba ta same su da shima ya fito ze tafi wurin aiki, tun daga nesa ta sakar mishi murmushi shima yana murmushi har ta ƙaraso hannunshi ta riƙe tace "Abba ina kwana?" Yace "lafiya ƙalau hidayat, an shirya kenan?" Kai kawai ta gyaɗa sbd bata da yawan magana, hannu ya sa a aljihu ya ciro hundred hundred Naira ya ba kowaccen su, godiya suka yi kan suka yi mota a lokacin Yusuf na Level one a university. Khausar da suke cewa Aunty kausi tana js2 se Mus'ab dake primary 6, se Salamatu dake pri 5, fahariyya tana Primary 4, se ita da Surayya dake primary 2, babu wacce ta mata kallon arziki a cikinsu sbd bata takale su ba inda ta saba duƙawa a ƙasan motar wurin ajiye kafafu ta duƙa don bata da darajar zama a seat har suka isa makarantar, kaman yadda ta saba seda ta kwashe jakkukkunansu ta kaiwa kowacce class ɗinta kan ta ɗauki nata dana surayya ta kai musu class, a seat ɗinta ta ajiye mata kan ta wuce nata ta zauna kusa da ummi. Kaman ka'ida ana tashi ta bi ta tattare jakukkunan ta kai musu mota kan ta tsuguna a mazauninta suka kama hanyar gida, ko da suka isa gida ma a nan parlor suka dinga cillar da abubuwansu tana tattarewa tana kaiwa inda suke tara kayan na wanki, a ɗakin nasu chan lungu aka shimfiɗe mata taburma da zanin gadon da bata san shekarun shi ba alhali kowacce a cikinsu da gadonta na katako a wakeken ɗakin. Anan ta cire uniform ta sauya na islamiyya ta fito, lokacin sun yi nisa da lunch inda ta saba zama ta zauna, minti minti wannan ze aike ta wanchan zata aike ta har suka gama, ta tashi ta bi plates ɗinsu ta ci abinci kan ta tattare ta kai kitchen, ganin babu wacce ke da niyyar zuwa Islamiyya cikinsu yasa ta fice. Wuraren karfe biyar ta taso daidai kofan gate suka haɗu da Abba wadda driver ya dawo dashi daga office, bayan ya shiga be shige sashen shi ba se ya jirata har ta karaso ta gaida shi cike da kulawa ya amsa yace "hidayat ina ƴan uwanki? Me yasa baku taho tare ba duka kuke tafiya daban daban?" Cike da yaranta tace "Abba ai basu je ba, ni kaɗai na je" Ya jefa mata tambayar "ko me yasa?" Da sauri. Tace "nima ban sani ba Abba" Hannunta ya kama suka wuce sashen umma, a parlor ya same su baje, masu kallo na yi masu danna waya na yi be yi wata wata ba ya zare cable ɗin TV Seda ya ba kowacce biyar biyar kan ya ja musu kunne akan ko da wasa ya sake samun su ran islamiyya basu je ba sun zauna suna shashanci yana kai nan ya fice. Tunda aka fara dukar taji kaman fitsari na shirin kubce mata don ta san yau yankata ne umma ba zata yi ba, yadda take ƙaunar yaranta ko kuda bata so ya taɓa su, tunda Abba ya fice ta zube bisa guiwowinta cikin shesheka take cewa "Wallahi ba ni na faɗa mishi ba, umma wlh ban faɗa ba.." Mikewa umma tayi ta nufota, yarfe hannu kawai take tana wayyo Allah, ko da umma ta iso ɗankwalinta ta cire ta cusa mata a baki tare da fusge hijab ɗin kanta ta ɗaure bakin yadda ihunta baze fita ba ta fara jibga kaman me faɗa da sa'ar ta. Zata iya cewa ta suma a lokacin sbd azaba ga ba halin ihu bare roƙo, Seda umma taga tana shirin kashe rai kan ta sauka ta wuce ba tare da tace uffan ba ta karkaɗa kan yaranta zuwa ɗakinta, dab kofa ta waigo ga hidayat dake yashe ko motsin kirki bata yi ba tace "saura in ga gilmawarki da sunan neman abincin dare wlh wannan kaɗan na miki" Tana kai nan suka shige. Me aikinsu dake tsananin tausayin hidayat ɗin ce ta zo da gudu ta sunce mata bakin tare da ɗago ta ta bata ruwa tana share hawaye, wani irin rashin imani da tausayi ne wannan? Seda ta sha sossai kan ta taimaka mata zuwa makwancinta sauri sauri take komai don in umma ta ganta akwai matsala, bayan ta kwanta ta fice ta kwaso kayan fitsarin ta ta zo ta mata shimfiɗa ta taimaka mata ta kwanta. Hidaya bata sake motsi ba sbd azaba da  ciwo har Seda taji zuban ruwan sanyi a jikinta, a razane ta miƙe ganin yau bata yi fitsari ba yasa umma jan tsaki ta fice tayi niyyar yau tana kwaran ruwan sanyi tana shwaɗe ta ne se Allah ya taimake ta. Da zazzaɓin tayi shara ta shirya makaranta inda suka saba haɗuwa da Abba ya basu kuɗin break suka haɗu yana kallonta yace "me ya sameki hidayat?" Tace "Abba kaina ne yake ciwo" Yace "sannu kin sha magani?" Kai ta gyaɗa don gudun fitina, yace "Ina lunchbox ɗin ki?" Tace "yana mota" alhali bata da shi don ba'a taɓa sa mata abinci a foodflask ba. Sallamanta yayi tare da Adu'a, har suka tashi school hidayat na fama, daga karshe tayi ta kuka a islamiyya Seda wani malami ya kaita chemist aka bata magunguna. Rayuwar hidayat a haka ya saba tafiya kuma a haka yake tafiya, inda take samun sauƙi ɗaya, Abba! Shi kuma ba me sa ido bane kan iyalinshi rayuwa ake na Turai, sede ko makaho ya shafa ya san hidayat na cikin Matsin rayuwa. Saboda azaban umma ta dena fitsarin kwance, tana da shekaru bakwai ta fara girki a gidan da dolen dole, gishiri yayi yawa ta daku, Maggi be ji ba ta kirɓu, yayi ɗanye a kusa yankata haka bautar su Aunty khausi kullum tana cikinta. Yau tunda aka tashi school bata jin daaɗi amma haka da ta dawo Seda tayi duk wani aiki da yake nata, an kara mata wanke wanke sbd umma tace bazata zauna tana ci da ita da tufatar da ita a banza ba, girkin dama Friday, Saturday and Sunday ne take yi. Bayan ta gama wanke wanke ta tattare ɗakin da suka hautsina da gangan ta fito ta bibbi plates ɗinsu ta ɗan ci abinci kan ta shirya islamiyya ko kan a tashi zazabi ne sossai ya rufe ta, da suka dawo da kyar tayi magrib da isha bata fita neman abinci ba haka tayi bacci, washegari a school ta samu health prefect ta bata paracetamol, karfe 11:10 na yi malamin basic science nasu ya shigo. Nan ya fara karɓan assignment, Surrayya ta miƙe ta zo gaban Hidayat tace "ke ina assignment ɗina?" Da sauri hidayat ta ɗago gabanta na faɗuwa tace "banda lafiya ban yi ba" Wani irin ashar ta lailayo ta zuba mata, kafin ta ɗaura ummi tayi saurin cewa "Auzubillah, ke Surayya me na zuwa mana desk kina wannan ashariyar ke hannunki me yake yi da ba ze yi assignment ɗin ba?" Bata jira cewar Surayya ba ta juya ga hidayat tace "kema wlh ban ga dalilin da ze sa kullum in dinga yi mata assignment ba haka kawai, ba aji ɗaya muke ba kuma malami ɗaya duk ke koyar da mu ba?" Hidayat zata yi magana sbd irin kallon da Surayya ke mata kenan malamin ya iso desk ɗinsu, ummi ta Haɗa da nata da na Hidayat ta bayar sbd ta karɓi littafin don ta kwafi note sbd bata zo makaranta ba shekaranjiya shiyasa tayi musu assignment ɗin duka. Ai ko malami kam ya fidda waenda basu yi ba ya basu biyar biyar, tun ana dukan Hidayat ke kuka tana yarfe hannu zuciyarta kaman ya fito don bugawa yau umma zata kashe ta, ta bari an daki yarinyarta shikenan. Surayya ta dinga kuka har aka tashi makaranta duk idanunta suka kumbura, a lokacin aka nemi Hidayat aka rasa babu inda basu zaga ba basu ganta ba, haka suka dawo gida drivern da kanshi yayi sallama ya faɗawa Abba an tashi hidayat bata makaranta... #like #share #comment                      🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 5* *FREE BOOK* Ba ƙaramin tashi hankalin Abba yayi ba, nema har police station ta ya ze fara cewa Allah ya kasa riƙe alkawarin da ya ɗauka na riƙon marainiyar nan har karshen rayuwarta? Cikin haka ya ga call da sabon layi kaman ba ze ɗaga ba se kuma ya ɗauka. "Alhaji kana magana ne da mahaifin Ummi kawar ƴar wajenka Hidayat ce kawai muka gansu bayan an tashi gashi har yanzu ta ƙi yarda a maida ta gida" Ajiyar zuciya ya sauke kan ya tambayi kwatancen gidan, nan ya faɗa mishi unguwan da kyar ya iya cewa drivern "mu je dorayi malam isa" Bayan sun isa mahaifin Ummi ya musu iso zuwa cikin gidan, karamin gida ne na masu rufin asirin Allah machine ɗinshi na Parke daga gefe, har parlor suka shiga ya saka ummansu ummi ta kira mishi su, hidayat na ganin Abba ta fara hawaye, itama ummi na tayata riƙe hannunta tayi tace "bana so a dakeki Hidayat amma ya zan yi?" Haka suna gani Abba ya janye ta suka tafi, a mota cikin karaya da ganin yadda take hawaye yace "Hidayat! Tunda kika fara wayau Na taɓa tauye miki wani hakki na uba akan ƴarsa?" Kai ta girgiza cikin sanyi yace "to menene? Gayamin yanzu me yasa bakya son komawa gida?" Cikin kuka tace "Abba Umma zata kasheni in na faɗa maka" Idanu ya kura mata na lokaci kaɗan kan yace "in shaa Allahu babu abunda zata miki, ba zan bari ba gayamin kin ji?" Kai ta gyaɗa kan tace "Abba bani jin daaɗi ban yiwa Surayya assignment nata ba nima ummi ce ta min sbd takardar a wurinta ya kwana, teacher ɗin beat for the assignment na san in na koma umma ma dukana zata yi" Driver ya girgiza kai, yace "kayi hakuri Alhj amma zan bada sheda don akwai ranar ma da bata yi mata assignment ba aka dake ta a gabana hajiya ta zane yarinyar nan hidayat, wani abu dake ci min tuwo a ƙwarya shine yadda suke hana yarinyar nan zama a kujera gashi bani da halin magana, nayi sau ɗaya hajiya tace in tsaya matsayi na ko in rasa aiki na" Abba cikin wani yanayi yace "menene shi da yake ci maka tuwo a ƙwarya?" Driver yace "Alhj Hidayat bata isa ta zauna akan seat na kujeran ba, a inda kafafun ka suke ɗin nan wurin tsugununta kenan a kullum sannan bata da kulan makaranta" Da sauri Abba ya kalli inda kafafunshi suke ya juya ya kalli hidayat hawaye ya cika idanunshi yace "hidayat me kuma take miki? Ki gayamin kinji?" Abubuwan da ake mata ta bashi labarin wasu, he was totally speechless har suka isa gida be iya ya ce komai ba, sashenshi yayi da Hidayat abincin da aka yi don shi ya bata ta ci ya dinga saka mata namomin har ta cinye, shi yaje har ɗakin su ya ɗauko mata kaya ya saka ta tayi wanka a toilet ɗinshi ta sauya, shi ya wanke mata uniform ɗinta Kal ya shanya. A lokacin daya dawo ya samu tayi bacci nan kasa ya ɗaga ta ya maida ta kan gado haka ya zuba mata idanu yana kallo, yanzu har yarinyar nan tayi girman da za'a iya zalunta? Umma bata tsoron wani abu ya samu wannan ƴar batalikar Allahn? Fisabilillahi this loving soul kyakyawar yarinya na nunawa sa'a. Babu irin Tunanin da be yi ba akan matakin da ze ɗauka, har Tunanin ƙara aure Seda yayi daga karshe ya yanke hukuncin da zuciyarshi ta fi bashi ita ce daidai. Chan ɗakin shi ya bar hidayat a time ɗin karfe wurin tara na dare ya tura kofan ɗakin umma ya shiga, tana tsaye jikin wardrobe tana duba abu ganin yanayin fuskanshi yasa ta rufe wardrobe ɗin ta bashi hankalinta yace "Amina ashe ba kya tsoron haɗuwar ki da ubangiji? Amina ina abun cuta a jikin Hidayat? Me ta sani nan duniya? Me ta yi miki da zaki dinga zaluntarta? Mahaifiyarta ranta ba'a hannunta yake ba da a hannunta yake na tabbatar bazata taɓa zaɓan tafiya ta bar yarinyar ba, kema kuma haka naki ran ba'a hannun ki yake ba ko yanzu Allah ze iya ɗaukewa idan aka yiwa naki abunda kike yiwa ɗan wani zaki ji daaɗi? Kiji tsoron Allah ki Sani Allah baya zalunci kuma baya barin me yi..." Dakatar dashi tayi tace "yanzu ita hidayat ɗin ce ta ce maka ina zaluntarta da har zaka zo ka cika ni da wa'azi? Allah na tuba ai idan zan mutu in bar yarana ma ba zan bar su a titi da kokonton ko ƴaƴan sunnah suke ba ko ƴaƴan zina, dangi gaba da baya Alhamdulillah, ita fa? Wa ya san daga inda uwarta ta yayumo ciki ta kawo kai kuma me tausayi da imani ba dangin iya ba na Baba ka ɗauka ka rike ta mutu ta barmu babu wani hujja ko haske, yarinya kyau kaman ita tayi kanta, wa ma ya sani ko kai ne ka yayumo mata cikin aka korota daga garin su ta zo ka saka ni riƙeta har ta mutu ta bar ƴar Zi...." Marin da ya sauke mata ne ya hanata karasawa, a zafafe yake kallonta yace "dama abunda ke zuciyarki kenan shine se yau kika amayar? Ina me baƙin cikin Haɗa zuri'a dake Amina baki da zuciyar imani da tausayi, wa ma ya sani irin wahalar da baiwar Allahn nan ta sha hannunki? Ki tattara kayan ki ki koma gidanku idan aka karanta miki karatun da ya kamata se ki dawo ki gyara rayuwarki karki ɓata min rayuwar yara da wannan halin kafurcin" Yana kai nan ya juya ze fita da gudu ta sha gabanshi tace "ni ka mara akan wanchan ƴar shegiya..?" Kara zabga mata mari yayi yace "idan har zaki cigaba da kiran hidayat da irin sunayen nan hannuna ba ze gaji da hukunta ki ba" Ihu ta kurma tace "Wallahi ba zan tafi ba se da hujjah, ba zan bar gidan nan ba har se ka ban hujjar tafiya" Yace "hujja kike so? OK ki je na sake ki saki ɗaya" Hannu ta sa a kai ta kurma ihu "akan ts...." Fasa faɗar tsinanniyar tayi ganin ya sake ɗaga hannu tayi saurin cewa "yanzu akan hidayat ka sakeni Abubakar? Akan wannan yarinyar?" Yace "ba saki kaɗai ba, zan auro wacce zata kula da ita tunda ina da damar hakan" Me umma zata yi! kuka wiwi kaman yarinya Alhj ya ce ze yi aure, a haka ya fita ya barta, a kofar ɗakin ya samu sauran yaran be kula su ba ya fice abun shi, suna ji suna gani umma ta Haɗa akwati ta fice. A ranan a sashen Abba hidayat ta kwana bayan tafiyan umma ma fita yayi ya sayo musu gasashen kaji da su ice cream ya biya super market ya sayi sabon lunch box hadadde, Washegari a sashenshi ta ci abincinta suka fito mota a tare, yaran basu ɗauko mata lunch box ba ya kalli khausar bayan sun gaishe shi yace "koma ki ɗauko wa hidayat basket ɗinta" Juyawa tayi bakin ciki kaman ya kashe ta, haka ta je ta ɗauko ta kawo musab dake zaune a gaba ya kalla yace "mus'ab koma baya" Fita yayi ya koma baya da kanshi ya saka hidayat a gaba yace "as from today wurin zamanta kenan Habibu driver duk ranar da ka kuskura muka haɗu ko daga nesa ne ban hange ta ɗaga gaba ba a bakin aikin ka, sannan duk ranar da ta sake fita ba lunch box baka gayamin ba shima a bakin aikin ka" Yana kai nan yayi musu waving bayan ya ba kowa kuɗin break ɗinshi suka fice. A mota sun yi shiru ne sbd sun san ko an koma habu ya faɗawa Abba in ya tashi dukansu babu umma me karɓansu, a school ne suka Taran mata suka mata kacha kacha Aunty khausi har niyyar dukanta tayi aka raba su. Wasa wasa satin umma uku Abba kaman be san da zaman ta a gidansu ba, gidansu irin gidan hayan nan ne masu ɗakuna dayawa, magana har ya soma yi mata yawa ga takura gashi bata samun sakewa kaman tana gidanta, tasha alwashi Kala kala akan Hidayat, tun tana Tunanin Abba ze zo ya ɗauke ta har ta sadakar ta fara kama kafafu da manyanshi bayan sati daya aka samu suka zauna. Ya gindaya mata sharuɗa akan hidayat ta ji ta amince ta bashi hakuri sossai kan ya amince ta dawo, a lokacin har wani fari da kumatu hidayat ta kara irin kulawar da Abba ke bata ko yaranshi be baiwa ba, ya mata sayayya ba na wasa ba Dukda ya kan Haɗa da su khausar sede nata fa na daban ne. Tunda umma ta dawo bata shiga sabgar hidaya ba haka itama, shakkan umma da take yasa bata bari ma su haɗu, bayan dawowanta da sati biyu aka tura Abba wani aiki a France ya tattara ya tafi tare da kara jadaddawa umma kula da Hidayat ya kuma tabbatar mata ko tsawa me karfi umma tayi mata ta gayamishi in ya dawo. Umma ce zaune tana Tunanin abunda zata yiwa hidayat don Wlh abunda ta mata ba ze taɓa tafiya a banza ba, wasa ma ake ace ta hakura komai ya wuce, hidayat ɗin ita wacece? Hmm Bayan ta gama nazari ta tashi tayi kitchen, ruwan ta me kankara ta samo ta fito tayi gaban TV ta samu cable su Surayya na kallonta, tayi ɗakin su a kwance ta samu hidayat bisa shimfiɗarta tunda Abba ya fice take a haka a ɗarare ta san umma kaman yunwar cikinta, tana cikin tunani kawai taji ruwan sanyi a jikinta bata gama dawowa daidai ba ta fara jin saukan cable, ihu ta kwala ta fara kokarin gudu sede umma ta fi karfinta haka ta rike ta Tsam ta hau jibganta kaman Allah ya aiko ta, Seda tayi mata laga laga kan ta janyota parlor. "Fahariyya kawo min wuƙa" Wani irin zaro idanu hidayat tayi anan ta fara "Umma Don Allah kiyi hakuri, umma karki kashe ni wallahi ba zan sake ba, umma kiyi hakuri.." Idanunta rufe take ta baiwa umma hakuri ta ruɗe ta gigice, bata kara sarewa ba seda fahariyya ta kawo wuƙa umma ta saka khausar kama mata kafafu, fahariyya ta kama hannayenta suka Mikar da ita Salamatu da Surayya suka danne ta da kyau, kaman zata shiɗe take rokon umma kar ta yanka ta. "Zaki sake ko da ambatan sunana a gaban Abba?" Da sauri ta girgiza kai tana cewa "A'a a'a umma ba zan sake ba" "A'a zaki sake gwara in yanke ki tsab in birne ya dawo in ce kin gudu" "Ki rufa mun asiri umma ki taimakeni karki kasheni, Wayyoooo..!" Umma ta gyara wuyanta ta saka wukan nan, kokawa hidayat ta fara yi da numfashinta don tsoro, a take fitsari ya kufce mata, umma kuwa ko ajikinta ta didara mata wukan nan a take ya shiga wadda yayi daidai da sumewar hidayat. Yusuf da ya turo kofa ya shigo kenan daga Maiduguri ganin abunda suke shirin yi yasa yayi sauri ya karɓeta, ɗaukanta yayi zuwa asibiti suka watse da dariya umma harda hawaye, su Surayya na kwatanta yadda hidayat ɗin take yi. Daga wannan rana da aka yiwa hidayat ɗinki a wuya ko muryar umma taji se jikinta yayi reacting, wani irin tsoron ta take ji kaman rai, su kuma suka samu abun yi. Yusuf shi de baya hana su Idan ba ya ga dukanta da gaske gasken zasu yi ba, sannan shi baya mata Dukda yana da zafin zuciya sossai. Ko da Abba ya dawo ko ya tambaye ta ana mata wani abu da gudu take cewa a'a, a haka hidayat tayi rayuwa, tana da shekara goma ta fara musu girki. Idan be yi daaɗi ba zata daku kuma ta cinye, ko zata amayo hanjinta se ta ci, a hankali a hankali suka sallami me aikinsu gabaɗaya, zata yi breakfast a ci tayi shara, su tafi school su dawo kan islamiyya tayi musu abincin rana tayi wanken wanken safe, kullum se an dake ta a islamiyya sbd letti, tana dawowa zata yi na dare tayi wanke wanken rana, ta wanke musu uniform duka. Bata da maraba da baiwa a gidan, abunda har yau ta kasa ganewa shine a idanun Abba yusuf kaman ya maida ta ciki amma a bayan idanunshi babu ruwanshi da ita Dukda baya duka ko zaginta, sbd yawan damuwa da yawan kukanta yasa har mutanen layi kan gane tana cikin damuwa. Bayan wani lokaci! tana da shekara goma sha huɗu a lokacin Dukda khausar ta gama secondary har an sanya mata rana ma amma har a lokacin hidayat ce ke bautar gidan, wanke wanke take da sauri sbd ta riga tayi letti a islamiyya, tsautsayi ya saka ta fasawa umma cup na tangaran kirjinta da suke a cike Dukda yarantanta ta dafe a fili ta furta "innalillahi wainna ilahi rajiun" Bata rufe baki ba umma ta shigo kitchen ɗin, mari ta saukar mata hagu da dama nan ta hauta da wani irin faɗa, kasa bata hakuri tayi ai ko umma tace dawa Allah ya Haɗata ai dama ta lura kwanan nan hidayat ɗin ta fara kwaso halayen rashin kunya zata yi maganinta ta fitar mata dashi a kanta, duka ta yi mata kaman zata kashe ta. Bayan ta gama wanke wanken da kyar ta fito, ta sanya uniform sbd in ta zauna a gidan ma ba natsuwa zata samu ba, tana tafiya kaman iska ze yarda ita lokaci lokaci ta kan share hawaye, banda raɗaɗi babu abunda fatar jikinta ke yi. Bata hankara ba taji an sha gabanta. "Baiwar Allah! Hawayenki ko kogi ne ina Tunanin yana gab da yankewa" Baya ta matsa tana kallon shi don bata san shi ba. Yayi murmushi yace "is ok don't be afraid, sunana hamza I'm a military officer kullum idan har zan tsaya anan a irin wannan lokaci na kan tsinkayi wucewarki cikin zub da hawaye hakan ya kwaɗaita min jin matsalar ki Ko Allah ze sa in iya taimakonki" Kallonshi kawai take, this is the first time wani yake mata magana cikin kamala da tsantsar kulawa, in aka cire Abba da ummi ƙawarta, tabbas tana bukatar comfort kuma daga gani Ɗayan nan ta aminta dashi sede labarin ta na da tsai. "Labarina bashi da wani armashin saurara babu abunda ze kara maka banda damuwa da tunani, so ka ga babu amfanin ji" Kallonta yake da mamaki yace "amma tukuna shekarunki nawa?" Tace "sha huɗu" Kara wara idanu yayi wadda har ya sakata murmushi yace "amma shine kika iya zaro zance haka?" Tana murmushi ta kauda idanunta daga kanshi tare da harɗe hannu tace "lokuta da dama ba mu muke iya abubuwa dayawa a gashin kanmu ba se abunda rayuwa ta koya maka kake iyawa, rayuwata ba irin ta kowa bace hakan yasa bana sa'a da sa'anni na a fannin komai na rayuwa" "wow please what's ur name?" Tace "HIDAYAT" #like #share #comment                    🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 6* *FREE BOOK* "Hidayat! Ni kuwa zan so sanin wannan labari ko zan amfana da wani darasi na zamantekwar rayuwa" Zata yi magana suka Haɗa idanu da Yusuf dake bautar ƙasa yanzu, irin kallon da yake aika mata yasa tayi saurin wucewa Dukda be taɓa dukanta ba sede ta san yana da manufa me girman gaske a kanta. Hamza na ta aikin kiranta sede ko waiwaye bata yi ba, Yusuf ya kalla na seconds kan ya juya ya tafi. Bayan ta dawo daga islamiyya tana shirin shiga gida Kenan taji an fisgo hannunta, a tsorace take Kallonshi har ya isa sashesu da ita a jikin gini ya bugata har Seda ta runtse idanu, manneta yayi sossai ba tare da ya damu da haramcin hakan ba yace "ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurareni, ya zuwa yanzu kalar muguntar Umma da su khausar kawai kika sani baki san ni ba, amma idan kina so ki fara sani in kara ganinki da kowanni kalar namiji ki gani!" Kai ta gyaɗa banda hawaye babu abunda ke zuba daga fuskanta sbd yana maganan ne yana tattaɓa jikinta, bayan ya saketa ta fice da gudu cikin kuka Abba be yi dacen mata da ƴaƴa ba, taya mutum me karamci irin shi ze samu ƴaƴa da mata irin umma da su Yusuf? Ko da ta shiga gida bata dawo daidai ba khausar da duk suka ajiye islamiyya tunda Abba yayi tafiya tace ta yi mata custard a babban jug sbd shi suke son sha yanzu yanzu, ko jaka bata ajiye ba ta shiga kitchen har lokacin jikinta rawa yake na abunda Yusuf yayi mata hawaye kuwa wani na bin wani a fuskanta, ta gwammaci abunda su khausar ke mata sau dubu da abunda yusuf yayi mata yau ta ja Allah ya isa ya fi abinda ya fi a ranta. Saboda yadda take a ruɗe garin dama custard abu kam yayi gudaje, Sam bata ma kula ba ta ɗauko ta kawo musu dayake haɗewa take da madara da sugar da garin, tana kawowa ta ajiye ta juya har ta ɗaura hannu kan handle na kofansu taji Fahariyya ta saki ashariya, a razane ta juyo gabanta na dukan uku uku. "Aunty khausi kina ganin irin Gudajen dake cikin custard ɗin nan!" Aunty khausi da Surayya har rige rigen karɓan cokalin suke, suna gani kuwa suka kirata ta dawo. "Ɗauka ki shanye!" Wara idanu tayi a duniya babu abunda bata iya sha irin custard, amai yake sakata hakuri take shirin basu, Khausar ta tsinka mata mari tace "dauka nace!" Dauka tayi sede ta kasa kaiwa baki, mikewa suka yi suka danneta suka ɗura mata shi cikin tsantsar mugunta, Surayya bata saki hancinta ba seda custard nan ya kare tas, mikewa tayi zata fice da gudu umma dake zaune tun ɗazu bata ce komai ba se yanzu tace "dawo ki zauna, kika kuskura kika amayar min da madara da sugar na wlh se na lahira ya ciki jin daaɗi tunda ba guminki bane" Zama tayi sede bata da wani iko da amanta, duk yadda tayi son dannewa kasawa tayi ta yunkura zata mike Salamatu ta saka mata ƙafa anan ta faɗi a kan hannunta, aman da take dannewa ya kwace mata ta sake shi anan. Duk mikewa suka yi suna zazzare idanu sbd tas a jikin mus'ab ta kwararo shi, yana mikewa ya sake mata wani bahagon mari da Seda jini ya balle a hancinta, kasa magana yayi ya juya ya fice. Umma bata barta ba seda ta kwashe aman tas ta wanke wurin da omo ta saka turaren wuta da room freshener kan ta samu ta shiga kitchen ta dinga zuba ruwan sanyi a kanta har haɓon ya tsaya, hannunta da take ji kaman ya samu matsala ta tallafe tana zub da hawaye, a haka ta ɗaura musu abincin dare cikin taka tsantsan don in tayi kuskure kashin ta ya gama bushewa. Haka ta kwana kan safiya hannun yayi tsami amma babu wadda ya ɗaga mata ƙafa Seda tayi aikace aikace da duk take bata yi fashin school ba don idan bata je Bama se ta ci uban ta hannun umma. A yammacin ranar ta fito don zuwa Islamiyya har ta kusa isa taji Muryarsa cikin sanyi yace "Hidayat!" Tayi saurin juyowa tana kirkirar murmushi tace "ya hamza ina yini?" Yace "lafiya ƙalau ya school?" Tace "Alhamdulillah" Kanta ta mayar kan hannunta dake kumbure tana Tunanin ta yadda zata dakatar dashi da shiga harkarta ba don komai ba se don bazata iya da tashin hankalin da Yusuf ke shirin kawowa rayuwarta ba. Idanunshi ya saukar inda take kallo a matukar mamakance yace "Subhanallah! Hidayat me a hannun ki haka?" Tace "faɗuwa ne nayi da sauki ma ai" Yace "please drop it! Wani irin da sauki ina ganin in ba gurɗewa kika yi ba to tsagewar kashi ne muje a duba miki" Zata yi musu ya zare mata idanu kwarjininshi ya hanata, haka ta taka ta shiga motar shi da ya buɗe mata, haka kawai ta yarda dashi, gidan wani malami wadda ya kira da kakanshi ya kaita daga gani irin abubuwan da yake yi kenan. Yana gani kuwa yace gocewar ƙashi ce gyara yayi mata tana ta zub da hawaye sede bata yi ihu ba hakanan babu wadda ya riƙe ta, umarni ya mata ta shiga gidan tace shi ya aiko ta, mikewa tayi ta shige. Mutumin ya kallo hamza yace "Ina ka samo yarinyar nan mazan fama? Ka kuwa san ban taɓa ganin yarinya me matuƙar dauriya irin ta ba? Gocewar ƙashi da za'a same shi yanzu ma wani babban se an tara gayya kan a gyara amma natan nan fa har tsami yayi amma hawaye kawai ta zubar" Hamza ya gyara zama yace "Rayuwar yarinyar akwai tausayi kaka daga kallo ɗaya zaka fahimci hakan, ni karan kaina na rasa takamaimen abunda ke damunta sede zan bincika in shaa Allah" Kakan yace "Allah sarki! Allah ya yaye mata" Suka amsa da Ameen, se gata ta fito rike da Leda ƙarami. Godiya ta mishi kan suka fice, a mota hamza ya matsa mata har Seda ta bashi labarinta da irin abunda take fuskanta, bata boye mishi har abunda yusuf yayi mata jiya ba. Yana da wani kalar zafin zuciya hakan yasa aikinshi na soja ya karɓe shi. Wani kalar tafasa jininshi ke yi yana ambaton "innalillahi wainna ilahi rajiun" Da kyar ya samu yayi controlling kanshi, ita kuwa se hawaye kawai take sharewa, har Suka isa unguwan su be iya cewa komai ba, zata sauka yace "Hidayat!" Da sauri ta kalleshi sbd irin muryar da yayi anfani dashi bata taɓa ji daga gareshi ba yace "I want to help you! Tunda na fara ganinki na san akwai dalilin da Allah ya sa ya Haɗa mu, zaki Aure ni?" Wani kalar zare idanu tayi kan ta fice da gudu, murmushi ya saki tunda ta gama bashi labarin yake Tunanin ta hanyar da ze iya taimakon ta, hanya mafi sauki kuma shine aure, yana da tabbacin tunda me gidan ya san irin rayuwar da take yi a gidan Dukda ya musu faɗa da barazana sede yana da tabbacin ba bari zasu yi ba So aure ne kadai ze tsallakar da ita wannan siradi, shi kuma yayi alkawarin aurenta ya inganta mata rayuwa. Wasa wasa hamza ya sabar mata da soyayyar shi me sanyi, Yusuf ya kamata sau biyu ya kikkifa mata maruka sede ba shi ze hana gobe ta saurari hamza ba. Ranar da Abba ya dawo washegari da yamma suna tsaye da hamza a hanyar ta ta islamiyya se ga Yusuf yana zuwa ya ɗaga hannu ya kifa mata mari yace "ke tsintacciya marar galihu ashe gargaɗina be shige k...." Wasu tagwayen maruka da ya saka shi faɗuwa hamza ya sakar mishi kan ya hau naushinshi kaman ya samu jaki, ihu ta kurma tana rokon shi ya kyale shi in ba haka ba ta shiga uku a rikice tana kuka, hamza be barshi ba seda ya karya hannun da yake taɓa ta dashi ɗin. Da kyar aka kwace shi, kuka kawai take tana 'Na shiga uku!' Hamza ze yi magana Wayanshi na wurin aiki ya ɗauki ringing da sauri ya saisaita nunfashinshi kan ya ɗaga umarnin tafiya zuwa Zaria aka bashi, ba son barin ta yake ba amma bashi da yadda ze yi, yana kallonta yace "zan je zaria three weeks work Ina dawowa zan turo su Abba na" Bata iya ta ce mishi komai ba har ya tafi, kuka take tayi mutane suka kama Yusuf zuwa gida Abba na ganinshi basu zauna ba aka yi asibiti dashi cikin tashin hankali, kwanan shi biyar aka sallamoshi a parlornshi duka ya tara su yana kallon Yusuf yace "Yusuf me ya faru da kai haka? Kai da wa har ya maka irin wannan raunin?" Kanshi a ƙasa cikin ladabin kule yace "Abba kayi hakuri wacce nayi hakan don ita ban burge ta ba babu anfanin tone tone" Abba yace. "Tambayarka nayi kuma bana son wani kwana kwana amsa zaka bani" Ya kara yin kasa da kai yace "Abba sanadiyar Hidayat wannan abunda ya same ni ya faru, wallahi Abba ina son hidayat ina son mata alkhairi da rayuwa me kyau sede ban san meyasa ta fara biye biyen da ba shine ba, tana da wani saurayi Hamza tun ranar da na fara ganinsu tare na kirata nace mata a matsayina na wanta ina bata shawarar idan sonta yake ya turo magabatanshi ne a yi magana ba kullum ya dinga tareta a hanya yana hure mata kunne ba don ko islamiyya ta dena zuwa, ranar ma har daukarta yayi a mota suka fita se dab magrib ya dawo da ita" Su umma suka saki salati, Abba kuwa kallon Yusuf kawai yake, cikin damuwar karya ya cigaba. "Five days back ina dawowa daga aiki kawai na sake ganinsu don naje in hukuntata a matsayin yaya gareta yarinyar nan ta hau min rashin kunya harda cewa ina ruwana da rayuwarta bamu Haɗa komai ba bare in ce zan mata wa'azi, hannu na sa zan janyota mu taho gida kawai saurayin ya rufeni da duka saboda shi Soja ne" Hawayen da ya gangaro mishi ya share yace "Abba na san ina son hidayat so na tsakani da Allah, ba zan so ta auri wadda bata da tabbaci a kanshi ba sede ni me iya hakura ne in bar mishi ita, in har shine farin cikinta na bar mishi ita ya aureta" Abba yace "Over my dead body Yusuf! Ko shine kaɗai namiji da ya saura a duniya wlh wallahi ba zan bashi auren hidayat ba, hidayat bata da miji se kai" Ihu ta kurma zata yi magana umma ta gwabe mata baki se kuka da take yi kaman ranta ze fita, kasa shiru tayi tace "Abba dan Allah karka aura min ya Yusuf wallahi bana son shi" Abba na kallonta da mamaki yace "se wa kike so?" Tace "Abba hamza yace ze turo iyayenshi in ya dawo daga tafiya don Allah Abba karka aura min yaya Yusuf" Cikin tsantsar yarinyata take zancen, Abba yace "Eh lallai wannan ko waye ne ya ɓata min hidayat, aurenki kuwa har Abada ya haramta a gareshi wallahi billahi" Duk yadda hidayat taso fahimtar da Abba be fahimta ba saboda Yusuf ya riga ya sharewa kanshi Fage, Abba ya riga yayi amanna Yusuf na kaunar ta kuma ba ze cutar da ita ba. Ganin zata iya birkicewa yasa Abban ma ya yanke za'ayi bukin da na Khausar da saura wata guda in ya so ta karasa secondary ɗin a ɗakinta. Hmmm a wata gudan nan mutuwa ne kawai bata yi ba, hidimar gidan babu abunda basu sakar mata ba, ga cin zali, ga muguntar Yusuf, ga auren dake ta matsowa duk duniya kuwa babu wadda ta tsana irin Yusuf. Hamza ya dawo ya zo gidan sede Abba ya ja mishi federal warning a kanta be hakura ba musamman da yaji wadda Abban ya zaɓa mata, haka ya dinga turo mutane Abba ya ki sauraran su karshe iyayenshi suka ce ko ita ce autar mata ba zasu kara komawa gidan neman mishi aurenta ba. Rana bata karya ranar Juma'a aka sheda daurin aurenta da Yusuf wadda ya sakata doguwar suma, Seda ta sha jini har Leda biyu sanadiyar bukin nan, se a lokacin kuma Abba ya bar fushin da ya ɗauka da ita me tsanani da be taɓa yi ba. Kwatanta irin zamanta da Yusuf ɓata lokaci ne, Tsananin azabar Rayuwa, yunwa, matsi, mugunta, musgunawa babu abunda bata fuskanta, ga zina da a kullum take Rokon Allah kar ya sakawa yaran mutane a kan nata yaran, tun tana damuwa har ta dena, kayan ɗakinta da ya fi na khausar kullum suna hanyar gidan da ɗauki ɗaiɗai suka karar da komai na gidan nata. Ita bata san wani amarci ba se baƙar azabar sex irin na Yusuf, bata yi wata biyar ba ciki ya bayyana nan Yusuf yace bata isa ba shi baya son yara. Duk yadda ya so ta zubar ki tayi se azabanta ya karu, duka kam har bata san sau nawa ta sha a hannunshi ba, ze daki cikinta har se ya so kashe ta Amma da Allah yayi Usman me zuwa duniya ne Seda ya zo, kan haihuwar Usman Abba ya haɗu da kaddarar hatsari inda ya kwanta ciwon da shine yayi ajalinshi, da sana'o'in da take ta samu ta hada mishi abunda ya kamata ita tayi mishi huduba da suna Usman. Usman na da shekara da watannin da basu wuce uku zuwa biyar ba ta sake samun wani cikin, Yusuf be farga ba seda cikin ya shiga wata biyar, irin dukan da ya mata Seda tayi ta bleeding kaman bazata haife ta ba, da taimakon Allah itama ta haifeta ita ma itace duk wahalar yarinyar uban be san dasu ba, ya kuma yi rantsuwar abincinshi basu da rabo ita kaɗai yake ciyarwa banda yaran. Wallahi ko makiyinta bata mishi fatan rayuwa irin tata. Tunda ta haifi Aisha be sake kusantarta ba se wata rana da ya sha abubuwan shaye shayenshi lokacin Aisha na shekara biyar ya faɗo mata inda kaddarar wannan cikin ya samu, zaginta a kullum yake daga an taɓa ta se ciki.. KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 7* *FREE BOOK* Abba yayi nadamar hukuncin shi gareta yafi abunda ya fi a kullum se ya zub da hawaye in ya ganta, rashin kula da rashin suturu duk sun haɗu sun maidata tsohuwar da bata kai ba, yayi nadamar rashin sauraren ta kuma a kullum in har zata je gareshi ta kan karanci irin rokon gafararta da yake da idanu, shine kaɗai take kalla tayi farin ciki ta kuma buga kirji tana da wani a duniya shima yanzu ya tafi, bango mafi girma a rayuwarta ya zube tas bata da karfin fara wani tubalin bare ta sake gina makamancinshi a rayuwarta... DAWOWA LABARI Cikin wani irin yanayi take kukan, kuka ne wadda duk wadda ze kalleta ze san akwai abu mafi girma da ya sameta na rayuwa ganin yadda ko la'akari da jama'ar dake kai kawo bata yi, wata mata ce ta matso ta tare da dafata tace "baiwar Allah kiyi hakuri! Duk tsanani yana tare da sauki ki duba condition naki it's not good for you da irin wannan kukan da kike" Kallon matar take da idanun rayuwa daaɗi yake miki ni tawa rayuwar bata da sauran anfani banda na yarana, ba tare da tacewa matar kala ba ta mike ta nufi gate tana tafiya kaman iska ze ɗauke ta, da Kallo matar ta bita cikin tausayawa duk yadda akayi matarchan tana cikin depression me girma. Har ta isa gida bata dena zub da hawaye masu zafi ba, a kofar gida ta ga Usman da Aisha zaune da gudu suka zo suka mata oyoyo, tana share hawaye wani na bin wani ta rungumesu itama, cikin sanyin murya tace "Usman me yasa baku shiga ko wurin Asabe bane kuka zauna a kofar gida tun yamma?" Aisha tace "ba mun je ba su Lantana suka koremu wai tunda bamu da gado mu bar musu gida" Bata sake cewa komai ba, hannunta na rawa ta fiddo key sede ta kasa buɗewa se Usman ne ya karɓa ya buɗe suka shiga, akwai wutar nepa alwala tayo suma duk suka yi cikin karfin hali a zaune haka ta miƙa sallar magrib da isha da ake ta kira. Bayan sun idar tana jin yaran na azkar sede ita bakinta be iya yayi ba se a zuciya take binsu, bayan sun gama Usman yace "Mama baki da lafiya ne?" Aisha ma tace "Mama kina ta kuka Ko Abba ya biki ya bugeki ne a unguwar da kika je?" Rungume Aisha tayi ta saki sabon kuka, duk yaran ma se suka soma kuka, da kyar ta dakatar da kanta tace "Usman, Aisha ina kun san Abbana na gidan umma?" Aisha tace "Umman Abbanmu wacce itama take dukanki?" Lumshe idanu tayi tace "Aisha ba na hana ki cewa ana dukana ba?" Shiru yarinyar tayi, se Usman yace "Abba da be da lafiya mama?" Kai ta gyaɗa tace "shine yau ya rasu, ya tafi ya barni ƴaƴana bani da kowa se ku se kuma Allah...." Ta fashe da wani irin kuka. Aisha tana shafa bayanta Usman na share mata hawaye, sun jima a haka Kan Aisha tace "Mama malam yace haramun ne in mutum ya mutu a yi mishi kuka ko Ya Usman?" Usman yace "Eh Mama, muma ya ce mana duk hawaye da ze diga daga fuskanka kaman azabar wuta kake karawa wadda ya mutun" Gyaɗa kai tayi tace "Na dena! Na dena kunji?" Kai suka gyaɗa mata tace "daga yau in kun yi sallah karku manta saka Abbana a Adu'a kun ji?" Kai suka sake gyaɗawa, Usman ya je ya ɗauko musu abincin da seda ta girka musu kan ta tafi wurin Abban nata, shi ya zuba musu Aisha ta ɗauko cokali sede duk yadda suka yi da Maman tasu ta kasa ci ko kaɗan. Ita kadai ta san irin azabar da take ciki na nakuda, yadda cikinta ke yi kaman ze barka fata ya fito, gumi kawai take Haɗawa cikin dauriya irin na wadda ya Rayu cikin azaba ya girma cikin azaba tayi ta zama har suka gama cin abincin tana ta Kallonsu. Bayan sun gama ta kalli Usman tace "Usman je ka kiramin Asabe don Allah" Fita yayi yaje gidan ya dawo ya samu abu kam fa kara tsanani yake don ko buɗe idanu se tayi da gaske suke buɗuwa, yace "Mama Su Habiba sun koreni" Lip ɗin ta dake cikin haƙorinta ta saki da kyar tace "ka ce su taimakeni nakuda nake yi" Aisha na rike da Hannunta tana kuka ya fice, Seda ya jima kan ya dawo yana zub da hawayen halin da ya zo ya tarar da maman sun yace "Mama kowa ya ki zuwa ya taimaka mana, duk korata suka yi Zulai har da cewa ki mutu ma in kin ga dama, Mama ai ba zaki mutu ba ko?" Kai ta gyaɗa cikin dauriya tace "In shaa Allah, ka fita....ka samo napep don Allah ka kula Abban mama" Ficewa yayi da gudu, Aisha ta kalla tace "ɗauko jakan baby da na Haɗa" Ɗaukowa tayi jakan gwanjo ne ta sayo ta Haɗa ƴan abunda baza'a rasa ba, a ciki akwai dubu uku uwar kudin jarinta kenan da dama gawayin zata sake sayowa, ko da Usman ya dawo kan ta samu ta mike Seda tayi da gaske kafafunta sun kasa motsi, da kyar da taimakon Allah da dafa bango ta samu ta fito suka shiga adaidaitan bayan ta saka Usman rufe gidan cikin karfin hali. Me adaidaitan se Kallonsu yake cikin tausayawa yace "ko a unguwa babu wadda ze iya raka ki asibiti kan ƴan uwanki su zo? Yaran nan ai sun yi kananan kai ki haihuwa" Hawayen da ya zubo mata ta kai hannunta  da shima nauyi yake mata ta share tace "Bani da kowa se Su se Allah" Shiru yayi ya ja machine ɗin, har suka isa asibitin da anan ne take awo babu wadda ya ce komai, sun sauka yaki karbar kudin haka ya tafi, da taimakon yaran nata suka shiga asibitin sede abun takaici babu wani wadda yayi attempting attending ɗinta tunda ba masu kudi bane, tunda ba wasu suka sani ba bare a san su. Ko da suka samu ta zauna Aisha ce tayi gudu ta rike hannun wata senior nurse da bata kula dasu ba tace "Aunty mamana zata mutu don Allah ki cire mata babyn nan" Da sauri ta kalli maman nata ta sake kallon Aishan ganin yadda take zub da hawaye gata kaman almajira yasa ta juya ta nufi Hidayat, "sannu baiwar Allah, ina katinki?" Jakar ta kalla cikin karfin hali, buɗewa nurse ɗin tayi ta fiddo shi tare da Juyawa seda ta kwashe mintuna masu yawa kan ta dawo ta kama hidayat suka nufi wani daki, mata sun yi goma a ɗakin gashi banda karni babu abunda yake yi na haihuwa, sossai tsabtan yayi karanci. Fitar dasu Aisha tayi tace su zauna a kan bench ɗin, ita kuma ta koma ta duba Cm na Hidayat sede fa haihuwa ba nan kusa ba, kallon hidayat tayi tace "Daurewa zaki yi baiwar Allah yadda kika jikkatan nan idan haihuwar ta zo kuma se yaya?" Kallonta kawai hidayat take yi ita kadai ta san me take ji, in banda abun ya fi karfinta daga Usman har Aisha a gida ta haifi kayan ta babu me kaita asibiti in banda taimakon zuwa awo da ko yanke cibiyar Usman bata san ta yadda zata yi ba ga kananun shekaru. Hijab ɗinta ta cire sbd sauro da taga suke yawo kaman kuda ta Mikawa nurse ɗin tace da kyar "Don Allah ki bawa yarana su lulluɓa" Kallonta matar tayi kan ta karɓa, ita kuma Hidayat ta ja zanin gadon ta kwanta a kan gayar ledan gadon. Usman na Zaune Aisha na kwance bisa cinyar shi a haka bacci ya kwashe su bayan sun sha kuka, Hidayat kam bata iya ta rintsa ba, tun kan asuba ta fara wani kalar jijjiga tana taune harshe da haƙorinta idanunta na kakkafewa. Nurses ɗin ne suka ruga suka kira likita, yana zuwa ya fara faɗan rashin kiranshi tun kan hakan ya faru, dukufa suka yi a kanta da kyar suka samu ta dena jijjigan sede tana cikin mummunan hali, fitowa yayi lokacin ana kiran sallah yace "Ina waenda suka kawo ta?" Wata nurse tace "Naji dae senior nurse kan ta bar shift tace yaran chan ne suka kawota" Dayake government hospital ne sun saba ganin irin haka yaje ya samu Usman ya bubbuga shi yace "Ina babanku?" Usman yace "ban san inda yake ba" Likitan yace "Toh maman ku na bukatan aiki cikin gaggawa idan har ta kai awa shidda a haka ko ta haukace ko ta mutu" Kuka suka fara, wani ya kalli likitan yace "be kamata ka faɗawa yara irin wannan maganan ba bawan Allah kaman ba likita ba?" Likitan be ce komai ba banda taɓe baki ya juya ya fice. Aisha ta kalli Usman da fuskanta da yayi jaga jaga da busashun hawaye da majina tana sakin sabon kuka, hawayenta ya share mata yace "Ki dena kuka zan je in nemi Abba ya zo ya biya kar ta mutu ko ta haukace" Kai ta gyaɗa mishi, ya tashi ya fita. Ita kuma an musu clock a basic science kuma mamansu ta koya musu yadda ake reading na clock saboda shine a ɗakinta. Agogon ta kurawa ido tana kallo tana kirga awanni shida da ya bayar, wasa wasa saura awa ɗaya lokacin da ya bayar ya cika, fitowa tayi ta tsaya a bakin ward ɗin yadda tana kallon gate kuma tana kallon agogo a lokaci ɗaya tana kuka. Bata yi mintuna sha biyar da tsayuwa ba aka wangale mashigar asibitin, wasu rantsatstsun motoci Prado bakake siɗik guda biyar suka shigo a jere banda ɗaukar eyes babu abunda suke sbd sabunta da kyalli, parking suka yi Seda aka dauki seconds kan kofofi takwas na biyu daga cikin motocin wadda suka saka ɗaya a tsakiya suka buɗu, wasu manyan bouncers majiya karfi sanye da bakaken kaya suka diddirko suka zagaye motar dake tsakiyan.. Mutane da suka san dama cikin lokaci irin wannan ne Allah ke jefo musu wannan bawan Allahn suka shiga zagaye motocin daga nesa. Seda suka yi mintuna biyu da yiwa kansu matsaya kan ɗaya ya karasa ya sa hannu ya buɗe bayan motar, a hankali na ciki ya sako wani irin haɗaɗɗen kafanshi waje, Seda ya kwashe wasu seconds ɗin kan ya fito gabaɗaya, Wow.. Wani kalar gallant man ne a tsaye a wurin, dogo tsayayyen namiji sanye da wasu hadaddun jersey navy blue me tambarin kwallon kafan nan na Paris saint German wato (PSG) kafafunshi sanye da cover irin na ƴan kwallo na kamfanin PUMA, bazaka kirashi fari ba sede Sam baya cikin jerin bakake yana da wani kalar lafiyayyen fata ne wadda ya haɗu da zama Kasar ketare ya bada wani kala me daukar hankali, kanshi wata kalar aski ce irin ta ƴan kwallo an kwashe gefe da gefe tsakiyar aka yi mata wani kalar gyara se kuma ya rina ta zuwa kalar brown daga sama, gashin yana lilo har bisa kyakyawar goshinshi, kunnenshi na hagu sanye da wata tsadaddiyar Dan kunnen Diamond. Dukda sanye yake da facemask me matukar kyau kana iya zayyano kalar kyaun da Allah ya mishi, yana da wasu irin idanu masu fusgan hankali haka ma hancinshi dogo ne me kyaun gaske, daga gwiwanshi har idon sawunshi dake waje zuwa hannayenshi da suke waje duka akwai wasu kyawawan gashi a kwance bakake sidik. Murɗaɗɗun damatsanshi da suka yi kaman zasu yage hannun jersey ɗin zuwa faffadar kirjinshi kaɗai zaka kalla ka san eh lallai wannan ma'abocin motsa jiki ne bana wasa ba juya baya da yayi Zuwa cikin motar ne ya bani Daman kallon rubutun dake bayan Rigan inda aka rubuta "MOH RAED" da kalar ruwan gold se katon number 7 daga tsakiya. Tattausan hannunshi masu dauke da wasu irin dogayen yatsu zuwa faratunshi dake tsabtace ya Mika cikin motar bayan ya sauka se ga wani karamin hannu an sanya cikin nashi, gimtsewa yayi, tare da taimakonshi kyakyawar yarinyar da bata wuce 5/6 yrs ba ta sauko. Masha Allah, itama kyakyawa ce sossai sanye da track suit pink masu layin fari fari na kamfanin Nike ne sanye a jikinta, bata sa hulan ba se gashinta da ya sha gyara zube har kafadunta katon pink headphone ne a kunnenta kafafunta sanye da Fararen boot suma na Nike. Hannun babanta ta rike suka fara tafiya cikin tsantsar kasaita da ji da kai da kuma kuɗi. "Allah me hallita! Lallai Allah shi ya san abunda ya ajiye anan mene!" Wani ya faɗa cikin mamaki, wani matashi a gefen yayi dariya yace "amma da alama baka kallon kwallo ko?" Mutumin yace "ana ta kai wa ke ta kaya?" Wani daga gefe yace "Dukda haka dae na san bazaka rasa jin sunan MOH RAED a Nijeriya ba" Zaro idanu dattijon yayi yace "Wai shine wannan? Allah sarki bawan Allah ai ko in har kai mazaunin nan Kano ne dole ka san sunan ko baka san shi a fuska ba, mutum me tausayin talaka da tsantsar taimako ashe yana zuwa irin wuraren nan?" Wani chan yace "Aiko in kana son ganinshi ta sauki ma se a irin wuraren nan ya kan taimaki asibitoci sossai" Wani yace "Amma fa an ce rayuwarshi akwai sarkakiya me karfin gaske hakan yasa kwata kwata a fuska bashi da fara'a idan ba yana tare da yaran nan nashi guda uku ba, sannan da chan da "R MAI NAGGE" yake anfani daga baya aka ga ya sauya zuwa wannan sunan" A tare suka fara mishi Adu'ar Allah ya yaye mishi suna kallon ɗaya motar da wasu suka fiffito da jakukkuna masu girma girma suma duk sanye da kayan bouncers suka fara binshi a baya duk inda ya wuce za'a Mika maka envelope ɗaya. Har ya Gota ta kaɗan se ya sake dawowa baya ya zuba mata kawatattun idanunshi, yarinya ce karama da bazata wuce sa'ar Farah ƴarshi karama dake rike da hannunshi ba, yadda take kuka yake kallo se kawai ya tsinci kanshi da karasowa gareta zata gudu yayi saurin rike hannunta yace cikin taushin muryarshi me sanyi da zaka ji daga makogoro yace "hey! Calm down baby, what's ur problem? Where is u mama?" Wow daga accent ɗinshi zaka san wannan ba kalar turancin da ake jin irin su a Nijeriya bane harshen shi a lankwashe yake wadda ko hausan yake in ba kunne ka sa ba ba lallai ka fahimta ba, wannan turancin nashi ko ni ba fahimta nayi ba seda na zura da gudu na nemo Ameeratuh(ƴar gayu ƴar Abuja) ta fassaramin me yace. Farah ta ɓata fuska tana kallon majina da hawayen Aisha tace "Dad please let's go, she's disgusting 'Donc je ne la'ime pas'" Wara idanu nayi jin harda Faransanci tana nufin tayi kazanta dayawa shiyasa bata son ta. A ko yaushe maganan yaranshi shine gabanshi duk abunda suke so shi yake yi musu yanzu ma baze fara kin sauraran ta sbd wannan ba, mikewa yayi daga kyakyawar durkuso da yayi suka nufi ciki. #like #comment #share                       🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 8* *FREE BOOK* Taku biyu ya qara ya waiwayo ya kalli Farah yace "baby let's help her she's really in need of that OK?" Yamutsa fuska tayi kan ta sake mishi hannu ta koma gefe tayi folding hands nata kaman wata babba, girgiza kai yayi ya san fushi tayi sede jininshi ya kasa kyale shi yin biris da wanchan yarinyar, Aisha ya nufa yace "uhm Gayamin! menene?" Seda ta kalleshi kaɗan kan tace "likita yace mamana zata haukace ko ta mutu in aka wuce awa shidda ba'a mata aiki ba gashi yanzu saura awa d'aya.." Ta karashe da kuka, kallonta yake in disbelief yace "likita yace haka? Ina babanki?" "Yayana yaje ya nemo shi kuma na san ko ya same shi baze biya ba sede ya doke shi ya kore shi" Lumshe kyawawan idanunshi yayi da suka ɗan sauya kaɗan ya mike daga kyakyawar durkuso da yayi a gabanta yace "muje let's see the doctor" Hannunta ya kama suka nufi ciki Farah na binsu daga baya baya sbd kyamar Aisha da take, office ɗin likitan ya shiga wadda yayi saurin mikewa daga ganin Moh Raed washe 32 ɗinshi yayi yana Mika mishi hannu sede Raed fuskewa yayi yace "menene matsalar maman wannan?" Bayani ya mishi akan an kawo ta an barta da yara gashi tana shirin zauce musu sbd jijjiga da take tayi, yayan yarinyar ma be yi goma ba amma yanzu ya tafi nemo uban su, lumshe idanu yayi da kaman ɗabi'ar shi ce kan ya ware su akan likitan, Seda ya ja iska kan ya tambayi kuɗin aikin. A lokacin da likitan ya faɗa mishi wani takaici ne ya zo mishi wuya abunda ko dubu ɗari be yi ba, ba tare da ya zauna ba yayi call, se ga ɗaya daga cikin bounchers dake rike da folder ya zo, kudade masu yawa yayi dropping ma likitan yace "prepare for the operation now!" Ya juya kenan se kuma ya sake Juyowa, "make sure after the operation you change her to the Amenity ward give her all the care she needs, am very sure this will be morethan enough" Ya karashe yana nuna kuɗin da yayi dropping ɗin. Kai likitan yake ta gyaɗawa yana cewa "in Shaa Allah" Ficewa yayi yana me kallon agogon Gucci dake daure a hannunshi jirginsu to Paris is in a jiffy gashi he will like to help this little girl more, but he didn't have any other option. Yana tsaye aka turo Hidayat, Aisha yake ta kokarin consoling sede ganin an fito da mamanta yasa ta sake jakar kayan haihuwar dake hannunta tayi wurin gadon da gudu, kallon Gadon yayi for seconds kan ya ɗauke kai, baze iya cewa ga kamannin maman ba he only saw her coily hair dake zube bisa pillow, her arched eyebrows a slim nose  nd her cherrie lips da suka yi jajazir a bushe alamun yunwa da rashin abinci me kyau Ba tare da ya sake kallon gadon ba ya Riko Aisha yana rarrashinta, Farah dae bata ce musu komai ba don ba duka abunda suke faɗa take ji ba, hausa na musu wahala sossai gwara ma ita da ƴan uwanta dake chan gida Paris, dayake ita purse na dad ne duk inda zasu tare suke zuwa yasa ko wani shekara take shigowa Nigeria, yau daddyn ta is talking to stranger a gabanta har mantawa ma yayi da ita yau akwai daru, shima da ya san kayanshi in ya kalleta sede ya sakar mata soft smile, a tare ya Riko hannayensu zuwa mota lokacin har mutanen shi sun gama abunda ya shigo dasu asibitin, Manyan snacks ɗin Farah ya ɗiba dayawa ya zuba mata cikin wani fancy Leda ya Mika mata. Murmushi tayi me kyau tace "Thank you..." Se ta rasa sunan da zata kirashi shima murmushi yayi mata for the first time yace "call me Daddy" Tace "thank you Daddy, idan mama ta tashi Allah yasa kar tayi faɗa na kula stranger" Yana murmushin wayon yarinyar a ranshi yana kwaɗaita mata samun Ingantacciyar ilimi yace "bazata yi ba idan kika ce mata Daddy Muhammad ne tell her masu sunan basa cuta bare cutarwa" Godiya tayi mishi, ya ɗaga Farah dake ta fushi ya saka a mota kan ya shiga, Seda yaga shigar Aisha cikin ward ɗin kan yayiwa drivern umarni da su wuce. Dayawa suna ganinshi Miskilin gaske marar fara'a da sakewa sede yana wasa da yaranshi sossai a ganinshi idan be musu ba wa ze musu? Shi kaɗai suke da a duniya matsayin uwa da uba da dangi, be taɓa Tunanin za'a samu worst uba irin nashi uban ba seda yanzu yaga Aisha ya tabbatar uban ta ma irin nashi ne, hakan yasa ta tsaya mishi a rai. Daidai last flyover da zasu ɗauka zuwa hanyar Airport idanunshi ya faɗa kanshi, ko ba'a faɗa ba wannan shine Yayan Aisha, da sauri yacewa drivern "wait!" Parking suka yi, ya sauke glass yana kallon Usman dake bin mutane yana roko kaman almajiri, wani irin tausayin su ne ya sake mishi dabaibayi, ɗaya daga cikin masu tsaron shi da ya sauko don jin Abunda ogan nasu ke bukata ya kalla yace "call that boy" Da sauri yaje ya kira Usman Dukda a tsorace yake sede haka ya biyo shi yana share hawaye akai akai, ganin Raed yasa ya karasa yace "Dan Allah ka taimaka min mamana bata da lafiya tana asibiti karta mutu ko ta haukace" Dauke kai Raed yayi yana shafa hancinshi da bayan hannunshi, da kyar ya iya controlling kanshi kan ya juyo ga Usman dake ta kallonshi yace "a ina ne asibitin? Ina babanku?" Usman yace "nima ban sani ba duka, na kasa gane hanyar gida kuma nima ban san sunan asibitin da mamana take ba" Yanzu da be ga yaron nan ba da wannan uwar ta rasa shi kenan har Abada, eh har Abada mana baze gane gida ba ba kuma ze gane asibiti ba, idan uwar ta mutu ba taimako shikenan Aisha ma zata gantale, idan kuwa ta warke ta ina zata fara neman yaronta a birnin Kano? "What a worthless father nd a heartless husband!" Yayi exclaiming kan ya sake kallon Usman yace "ur mom zata samu lafiya ok? just follow him he will get u back to her" Yace "ka san mamana?" Raed ya ɗan yi murmushi yace "yeah harda Aisha also" Washe baki Usman yayi yace "ka biya ma mamana kuɗin?" Kai kawai Raed ya gyaɗa don be cika dogon surutu ba ko da yaran Nashi ma, wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskan Usman yace "Allah ya biya ka da gidan Aljanna ya sa a mizani haka mama tace a gayawa duk mutumin kirkin da yayi mana abun alkhairi" Murmushi kawai Raed yayi, Usman ya bi wadda aka Haɗa shi dashi zuwa motan karshe suka juya dashi zuwa asibiti yayinda Moh Raed yayi Airport. A asibiti kuwa gaban ɗakin da Hidayat take Aisha ta tsuguna rungume da jakan maman, lokaci lokaci take murmushin jin daaɗin mamanta zata Samu lafiya, taɓata taji an yi da sauri ta ɗago se taga senior nurse na jiyan nan ce, ta mike tana kallonta se kuma tace "Ina yini?" Matar tayi murmushi tace "Maman ki zata samu lafiya ko" Tace "haka Daddy yace in shaa Allah" Matar tace "masha Allah" a zaton ta ma daddyn baban su take nufi don ita bata ga Raed ba. Tace "mu je in miki wanka ki sauya kayan nan, na kawo miki na ƴata ina yayanki?" Murna Aisha ta fara kan tace "Na gode, yayana kuma ya tafi wurin Abba" Janta senior nurse tayi zuwa toilet nasu na nurses ta mata wanka ta sauya mata kayan da na yaran nata da ta kawowa har Usman, ba karamin tausayi suka bata ba rashin sutura babban matsala ce. Suna fitowa se ga Usman, da gudu taje ta rungume shi suna murnan ganin juna, ba karamin so da shakuwa bane ke tsakaninsu, shima wanka senior nurse ɗin ta mishi ta sauya mishi kaya. Godiya suka mata tana ta murmushi cike da yabon irin tarbiyar da yaran suke samu. Bayan sun dawo sun samu an fito da Hidayat, ɗakin Amenity aka kaita itama Senior nurse ɗin nan ta kaisu taburma ta samo ta shimfiɗa tace su zauna anan kar su damu mamansu da surutu kuma kar su fita ko ina, ɗakin Amenityn harda bayi ta nuna musu yadda zasu yi fitsari in suna ji. Tana fita Usman ya ja Aisha suka je suka yi alwala suka zo suka yi sallah Dukda basu san ma nawa zasu yi ba don lokacin la'asar ne kuma tun asuba basu yi sallan ba amma dayake yara ne ina ruwansu, ledan da Daddy ya bata ta janyo suka ci Samosa da doughnuts daddaya ba karamin daaɗi abun ya musu ba ba sabon ba, a bayi suka sha ruwa suka dawo suka kwanta akan taburman se bacci. Wuraren 8 na dare ta fara motsi alamun alluran ya fara saketa, a hankali ta buɗe idanunta da suka kara faɗawa saboda ciwo ta kurawa ceiling Seda ta kwashe kusan mintuna talatin a haka Kan kwakwalwanta ya iya fara aiki, idan ta lissafa daidai kwana tayi ba'a hayyacinta ba ta kuma yini ba'a hayyacinta ba, ina yaranta? Me suka ci? Wannan Tunanin yasa ta fara kokarin mikewa zaune, daidai lokacin wata nurse ta shigo duba ta, da sauri ta zo ta taimaka mata ta ɗan jingina da pillow cikin karfin hali tace "Nurse ina yarana?" Nurse ɗin ta kalli su Aisha tace "ba su ne waennan ba?" Da sauri Hidayat ta kalli wurin su se ta sauke wani irin ajiyar zuciya, nurse ɗin na dariya tace "amma baki tambayi na ciki da kika kwanta dashi ba fa?" Murmushi Hidayat ta ɗan yi wadda be ko yi mata kyau ba sbd yaƙe ne tace "su na sani kafin shi dole in fara damuwa dasu tukuna shi ya biyo baya" Nurse ɗin tace "yana nursery shima be da cikakken lafiya" Kai hidayat ta gyaɗa tace "Allah ya bashi lafiya" Nurse ɗin ta sake cewa "ga ruwan zafi da kayan tea Aunty jamila tace kiyi anfani dasu" Kallon kayan tayi Dukda bata fahimci wacece hakan ba ta gyaɗa kai, dukda tana da tambayoyi fal a ranta sede daga bakin su Usman take so taji komai. Nurse ɗin ta juya ta fice, Hidayat ta kalli ɗakin ta sake kallo ta san Amenity sbd Abba irin wuraren yake kwanciya kuma ta san yana da tsada don harda frigde da TV da kuma Ac to wa ze biya mata nan? Kallon Su Aisha tayi se ta fara kiran sunayen su, a tare suka farka ai suna ganinta zaune suka zo da gudu, ɗaya ya zagaya ta ɓangaren dama Aisha ta zo ta hagu  ta kuwa rungumesu a kirjinta hannayenta a kawunansu, Aisha tace "Mama kin tashi?" Kai ta gyaɗa, Usman yace "Mama muna ta damuwa karki mutu ko ki haukace" Tace "in na mutu wa ze kular min Daku babana? Ai in shaa Allah tare zamu Rayu har zuwa mutuwarmu" Aisha tace "mu girma mu yi kuɗi mu sayi irin motan Daddy, mu dinga kamshi kaman shi ko?" Shiru hidayat tayi chan ta ɗago su da sauri tace "Aisha waye Daddy? Waye ya biya kudin aiki na da kuɗin ɗakin nan? Wa ya muku wanka ya sa muku kayan nan? Wa ya baku abinci?" Waro idanu duk suka yi suna kallonta, se ta gane tambayar sun yi musu yawa kwakwalwansu ya kasa dauka, Tace "me ya faru da bani da lafiya? Kun san na hana karya ko? Kuma me karya Allah na ƙona shi so bana son karya" Aisha tace "Ya Usman ya tafi neman Abba, be dawo ba na fita ina ta kuka se ga Daddy shine ya biya likita, ya bani wannan" Taje ta ɗauko snacks da ya saura dayawa ta kawowa hidayat karɓa tayi ta buɗe tace "na shiga uku! Waye kuma Daddy?" Aisha tace "cewa fa yayi sunanshi Daddy Muhammad kuma yace in kin tambaya in ce miki me sunan baya cuta baya cutarwa" Kallon Aisha kawai take, Usman yace "nima na je neman Abba ban ganshi ba, Naga kuma ana samun kudi idan aka roka shine nima nake ta roko in tara in kawo se na ganshi, shine ya saka aka dawo dani a mota me sanyi" Hidayat dae ta kalli wannan ta kalli wanchan, karshe ta lumshe idanu kan tace a zuciyarta "Allah na gode maka da ka turo mana wannan mutumin Aljannan ya taimaka mana Allah Kaine abun godiya ya Allah" Se ta buɗe idanu tace "Usman me yasa kayi roko ban hana roko ba?" Se ya fara hawaye yace "Mama bana so ki mutu ne" Tace "ya isa, karka sake ka ji?" Kai ya gyaɗa ta sa hannu ta share mishi hawaye yunwar da take ji yasa ta kalli kayan tea ɗin se ta kalli su Aisha tace "waye kuma Aunty jamila?" Nan suka bata labarinta se ta fahimci senior nurse ce, Usman ta sa ya kawo mata abu ta kurkure bakinta don ba brush, da taimakon su ta hada tea ta samu ta sha da Samosa a zuciyarta banda Adu'a da fatan alkhairi babu abunda take yiwa wannan Muhammad ɗin kwarai ya ci sunan nashi, kuma in shaa Allahu har Abada bazata taɓa mantawa da shi ba. Jaka ta saka Aisha ta miko mata, buɗewan da zata yi se tayi tozali da wani farin envelope, a hankali ta buɗe a firgice tayi watsi dashi kaman wacce ta taɓa wuta kan ta furta "innalillahi wainna ilahi rajiun" #like #share #comment                    🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 9* *FREE BOOK* "Aisha..! Mutum ne ya baki duka wannan? Ya aka yi kika karɓa? Me wannan..!" A tsorace dukansu uku suka zubawa kuɗin idanu, bunch ɗaya na 1000 kenan har dubu ɗari, Kuka Aisha ta fara tana rantsewa wallahi ita bata ma san ya saka ba. Ta yarda da ita sede tsoron kuɗin take in ya dawo yace yana son wani abu daga garesu fa? Usman ne ya kwaso suka mayar cikin envelope ta mayar cikin jakar ta ajiye, da taimakon yaran ta rama sallolin dake kanta ta basu sauran tea ɗin da spring roll suka ci, har yaran suka sake bacci bata yi ba Tunanin wannan mutumi ya rufe ta, wanene wannan mutumin? Me manufarshi na taimakonsu?.. Banda magungunanta da allurar da be saketa gabaɗaya ba da ta san ita da bacci a daren nan se Allah, tana lallaɓa talaucinta bata shirya cin mutuncin Yusuf ba Sam. Washegari da safe da Aunty jamila ta zo hidayat ta tambaye ta akan wani Muhammad da ya taimake su, tace "Raed ne nima se da na bar wurin yaran nan nake jin ya shigo, karki damu mutumin kirki ne sannan kyauta ce fisabilillahi ba da manufa biyu ba Inde shine duk shekara yana shigowa asibitin nan taimakon bayin Allah" Ajiyar zuciya ta sauke kan ta mata godiya sossai bisa kirkin da tayiwa yaranta da ita kanta, bayan Abba da Muhammad itace mutum na uku da bazata manta da ita ba, da taimakon Aunty jamila tayi wanka, da snacks ɗin nan suka sake karyawa babu yadda bata yi da Aunty jamila ba ta ci snacks ɗin ta ƙi, ta so taje gidan na Hidayat ta samo mata kaya sede hidayat ta ƙi a Cewar ta hidimar ze mata yawa amma a baɗini bata son zuwa ne taga sirrin su. Se da rana ya ɗaga sossai kan aka kawo mata yaron, lulluɓe cikin zanin ta da bismillah ta karɓeshi tana rungumeshi cikin jikinta ƙaunar yaron na shiga har jininta, leƙa fuskanshi tayi masha Allah babu abunda ya bar mata, hawaye ne ya zuba mata Aisha ta sa hannu ta share tace "Mama yayi kyau dayawa ko?" Murmushi tayi tace "hawayen farin ciki ne da godiya ga Allah da ya bani wannan kyakyawar halittar a matsayin kyauta wadda babu mahalukin da ya isa ya baka shi banda Allah" Kafin ta haihu sunan Abba ne yake mata kai kawo a zuciya ta kudiri aniyar idan har ta haifi namiji to Abubakar ne sede yanzu zuciyarta ya chanza, kiran sallah tayi mishi hagu da dama kan ta kira shi da suna 'Muhammad Raed' Aisha tace "Mama ya sunan shi?" Usman dake ta kallonshi ta kalla tayi murmushi tace "Sunan Daddy ya ci, Allah ubangiji ya raya shi yasa yayi halin me sunan" Murna a Wurin Aisha ba'a magana an saka sunan Daddy haka kawai take ƙaunar Daddy Muhammad, ita kuwa Hidayat idanu ta zubawa yaron bayan ta sa mishi nono a baki ya kama da sauri yana sha, a zuciyarta take raya... ''Me sunanka is our life savior, shi ɗin kaman wani mala'ika ne da Allah ya aiko mana cikin tsanani, a ranar da be zo asibitin nan ba da kila na mutu tare da kai a ciki, da kila Usman ya ɓata kenan ya shiga gararin rayuwa walau ya zama ɗan daba, walau ya kare a almajiranci da wahala, da kila Aisha rayuwarta ya gama lalacewa a matsayinta na ƴa mace me kankantan shekaru babu wadda ta sani babu wadda ya Santa'' Hawayen da ya ɗiga a kumatun yaron ne yasa ya fara mirmir da idanu alamun son buɗewa, murmushi tayi tana share mishi ɗigon hawayen. Satin su biyu a asibitin, da Aunty jamila ta gaji da ganin hidayat da kaya guda ita ta kawo mata kala biyu, yayinda yaron hidayat ta bata kuɗi ta karo mishi kala uku, kayan su Aisha kuwa in sun sa sau biyu se ta wanke asalin nasu su saka na kwana biyu ta sake wanke na Wurin Aunty jamilan, abinci safe rana dare saya suke a bakin asibiti, sati biyu da suka yi a asibitin har wani kiba suka yi na zama wuri ɗaya da hutu. Ranar da aka sallamesu napep suka samo ya kwashe musu kayansu har gida bayan tayi ta yiwa Aunty jamila godiya ta kuma rubuta lambar wayanta a paper.. Ko da suka isa gidan sun samu kwaɗon gidan a ɓalle, ta san aikin yusuf ne suka fiffatar da ƴan kayansu suka shiga gida, a kan shimfiɗarta ta kwantar da yaron ta hau tattare gidan Dukda yadda take jin kiɗa na tashi daga sashen Yusuf alamun yana gidan, Usman ta ba kuɗi yaje ya sayo icce ta zo ta hura wuta ta ɗaura ruwa. Tana tsaka da sharar tsakar gidan kenan taji sallamar Asabe, ɗagowa tayi fuskanta a washe tana mata sannu da zuwa Asabe tace "Hidayat kin tsoratamu, ina kika shiga sama da sati biyu kullum se na leko tunda naji dawowan baban su Aisha sede shiru ba ki ba yara? A'ah haihuwa kika yi ne?" Murmushi hidayat tayi tace "eh wallahi ranar da abun ze faru na tura su Aisha su kiramin ke sede bakya nan" Tace "la shakka ranar na dawo su habiba ke cewa kina ta aikowa na saɓa hijabi na zo na samu gidan a garkame" Hidayat tace "ranar ne aka yi min aiki, kuma a ranar Abbana ya rasu" Salati Asabe ta saki tana mata gaisuwa, ita ta karbi Sharan ta karasa, a varender ɗinsu ta shimfiɗa taburma Nan Asabe ta fita chan se gata da daidaikun matan unguwan masu yi mata ta'aziyya na yi masu yi mata murnar karuwa na yi. Zulai da ta shigo tace "yanzu kenan kun yi suna a asibitin kenan?" Hidayat na murmushi tace "eh sunanshi Muhammad Raed" Habiba tace "Raed..! Me kuma hakan?" Hidayat na murmushi tace "Sunan larabci ne kuma yana cikin ma'anonin sunan Muhammad wato Shugaba ko jagora" Baki Zulai ta taɓe, sauran matan na masha Allah. Wata A'i daga gefe tace "to yanzu baza'a mishi yanka ba kenan?" Hidayat a zuciyarta tace dole kuwa in mishi yanka in shaa Allah, a fili tayi murmushi tace "Ina gayyatarku duka in shaa Allah jibi za'a yi sunanshi" Aah masha Allah! Kawai suke ta cewa. Bayan dayawa sun watse ta ari wayan Asabe ta tura Usman ya saya mata credit ta zo ta saka ta kira Ummi. Ummi na ɗagawa Hidayat ta fashe da kuka, ummi ta rikice duk yadda ta lallashi hidayat kasa shiru tayi tace tana zuwa yanzu yanzu. Ba'a yi awa guda ba se ga ummi har lokacin kuka hidayat take, tana ganin ummi ta tashi ta rungume ta, she really needs a shoulder to cry abubuwan sun mata yawa da shekaruntan nan, kwarai ba don Muhammad ba da rayuwarta ta gama nakasa, baabinta maybe da an jima da rufewa, ummi tace "Hidayat kina ruɗa ni, menene? Me ya faru kike kuka haka?" "Na Rasa Abba ummi, Abba ya tafi ya barni" Salati ummi ta saki ta sallame, zama suka yi tayi ta rarrashin hidayat har tayi shiru ta yi mata ta'aziyyan Abban, nan hidayat ta ɗauko yaron ta mika mata, cikin sanyinta ta mata bayanin duk abunda ya faru, Albarka tayi ta sawa wannan Muhammad ɗin da duk basu san shi ba in ka cire Aisha da Usman. Asabe ce tayi mishi wanka, yayinda hidayat ta zare dubu hamsin cikin dubu saba'in da ya saura a hannun su tace ta je tayi duk abunda ya kamata, ummi na fita gidansu tayi ta sanar wa mamanta tare da diban kaya akan bazata dawo ba se bayan suna, suma ƴan gidansu sun yi alkawarin zuwa mata sunan da gaisuwan Abba don duk wadda ya san ummi se ya san ƙawarta hidayat. Kasuwa ummi taje ta samo tunkiya ƴar dubu ashirin da biyar, tayi sayayyan kayan abinci har na dubu goma, akan zata ɗibi wadda zata yi abincin suna sauran ta ajiyewa hidayat ɗin su dinga amfani dashi kan suyi Tunanin sana'ar da zata fara kuma. Dubu goma ta sake fitarwa ta sayi atmpha kala biyu da yadi me saukin kuɗi kala biyu, ta bada ɗinkin turamen za'a yiwa hidayat da Aisha tunda duk ba jiki ne dasu ba zasu iya shearing turmi, yadukan ta bayar aka dinkawa Usman se ta sayi kayan jariri da showel na karamin kudi wadda ze saka a sunan. Haka ta dawo da kaya niki niki, aka daure rago kayan abincin suka shigar ciki, ta samu Asabe har tayi musu tuwo miya ne Seda ta dawo suka yi anfani da ƴar naman da ta sayo aka yi romon daddawa me jego aka zubawa sossai ta ci, Su Aisha se daaɗi suke ji, da wayon su dae ba'a taɓa ɗaura irin wannan sanwar don su a gidan ba sede baban su ya bayar kuma naman shi a kirge yake sede su sude bojuwa. Se Dare Yusuf ya fito ya gansu, a kanta ya tsaya da yaron ya gama kare musu kallo kan yace "Ashe kina da liver da kuma guts ɗin sake dawowa min gida bayan kin kashe mana uba?" Kanta ta duƙar ƙasa tace cikin rawar murya "A'a! Taya zan fara kashe Abba?" Hannu ya sa ya buge mata baki ko damuwa da Ummi dake zaune a wurin be yi ba yace "Umma zata miki karya kenan, ban yi tunanin kina da idon da zaki sake kallonmu ba bare har ki dawo garemu, Toh bari kiji ni na gaji da ɗawainiya dake da yaranki gaki kullum ke a haihuwa kaman Akuya, tunda har zaki iya mana ajalin uba muma kenan ɗaya bayan ɗaya zaki yi namu to baze saɓu ba, bari na turo miki Umman duk yadda kuwa tace ayi dake haka za'a yi Gayyar tsiya." Ummi tace "Haba Yusuf, kai kam wani irin miji ne? Wani irin uba ne kai? A gaban yaranta kake mata irin wannan cin zarafin? Sati har biyu baka ga matarka ba ta dawo bazaka iya tambayar lafiyar ta da na yaranta ba se ma ka sakata kuka? Baka ganin jarirink...." "Ke dakata rufe min baki! Me ya kawo ki gidana? Sa ido da shiga sharo ba shanu? To ki kiyaye ni wacce ta kawo ki ma tayi kaɗan bare ke ina ruwanki da rayuwar gidana?" Harara ta zabga mishi tace "gida! Gida fa kace ai ni anan ban ga gida ba kurkuku na gani me cike da baƙin duhu da azaba! Wallahi ka guji duniya don tafi bagaruwa iya jima ni de na gayamaka" Hidayat da ta mike ta kama ummi tace "Ki rufamin asiri ummi kiyi shiru don Allah" "ke dakata dallah! Wallahi a gabana wannan azzalumi matsiyacin ba ze ci mutuncinki in kyale ba, da me yake taƙama?" Kuka ta fara hakan yasa Ummi yin shiru ta zabga mishi harara ta wuce ciki, shi kuwa Hidayat ya kalla kan yayi kwafa irin da ni kike zancen ya fice daga gidan yana ball da tukunya har Seda ya buge tunkiyar dake ɗaure. "Ummi kin san irin bala'in da kika ja mini?" Ummi tace cikin zafi "se kiyi shiru ai kina Kallonsu suna cin zarafinki tun yaranki basu san zafin hakan ba har su zo su sani, har se yaushe zaki cigaba da haƙurin nan! Karshe zuciyarki ya fashe da hakuri ki mutu a banza? Toh wlh idan kika mutu duk a cikinsu babu me asara, yaranki sune da asara kuma suma ba tsira zasu yi a hannun su ba gwara tun wuri ki fara shirin kwatarwa kanki ƴanci" Ummi bazata gane bane, hakan yasa bata kara magana ba se Raed junior da ta zubawa idanu, kan Aisha ummi ta cigaba da shafawa har tayi bacci. Ranar suna tun asuba Ummi ta hau aiki ita da Asabe se wata makociyarsu maman Abba, kan karfe goma sun gama duk wani aiki na sunan daidai talaka mutane kuwa sun fara cika gidan, an yanka rago har ana suya, me jego tayi wanka ta saka kayan da ummi ta dinko musu haka ma Aisha da Usman se daaɗi suke ji. Taron suna yayi kyau daidai gwargwado kuma an ci an sha albarkacin Muhammad, masu kawo kaya sun kawo wasu sun kawo sabulu da omo wasu pampams, ummi Atampha ƴar dubu biyar da Kayan jariri tayiwa Hidayat, mamanta ma Atampha da kayan jariri, har Aunty jamila da Hidayat ta kira da layin ummi itama ta zo showel me kyau da kayan sanyi ta kawowa jaririn. Se yamma Lis gidan ya fara raguwa da mutane ana ta mamaki don duk taron sunanta batayi goshi irin na wannan yaro ba, kowa se cewa yake yaro ya zo da albarka. Wuraren biyar Umma da yaranta suka diro gidan, matukar tashi hankalin Hidayat yayi ta zo ta zube kasa tana gaida umman ba tare da ta amsa ba ta hambareta da kafa tace "da ban yini ba zaki ganni! Salon munafunci da tsugudidi... wallahi hidayat yau se kin bar gidan nan, bazaki kashe uban me gida kuma ki cigaba da cin moriyar gida ba" Khausar tace "Umma kiga wai harda taron suna" Fahariyya tace "Ai dole tunda ta gama yashe mana uba ta tara ba dole tayi taron suna ba, in ba ta yashe mana uba ba a ina zata samu kudin taron suna harda yanka rago" Surayya tace "a dadironta mana kin manta Ya Yusuf yace shi be yarda ma ɗan da aka haifan nashi ne ba.." A matukar gigice Hidayat ta ɗago daidai lokacin da ummi ta karaso ta sauke ma Surraya wani bahagon mari... Ihu ta kurma ƴan uwanta suka yi kan Ummi itama nata ƴan uwan da ta gayyata suka yi kansu a take gida ya kachame. #like #share #comment 🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 10* *FREE BOOK* Dama Sila ummi ke nema kuma ta samu, Seda ta tabbatar tayiwa Surayya mugun duka kan ta kira police waenda basu da nisa dasu aka zo aka kwashe kowa aka yi police station, banda kuka babu abunda hidayat take cikin tashin hankali don umma ma Seda aka fitar mata da jini. A police station ɗin ma ba'a natsu ba kace nace gabaɗaya ya cika wurin, Seda Dpo ya fito da kanshi don jin ba'asin abunda ke faruwa, umma ce tayi Charab tace "Yallaɓai mijina, marikinta kuma surikinta ta kama da maita, shekaran shi bakwai ana neman na takwas yanzu yana jinya kan daga zuwan yarinyar nan sati biyu da suka wuce ya ce ga garinku, ni kuma alkawari nayi jininshi ba ze tafi a banza ba" Dpo hidayat kawai ya kurawa ido kaman yana so ya ga ta inda maita ya bayyana a suffanta, ummi tace "Wallahi karya take! matarnan azzaluma ce, marar tsoron Allah ranka ya daɗe tun hidayat na tsummar goyo take hannunta, banda azabatarwa da bauta babu abunda ta sani na farin ciki a rayuwarta, tare muka yi karatu har zuwa matakin secondary kan kaddarar auren ɗan wannan azzalumar ya hau kanta, shima a gidan bata yi sukuni ko farin ciki na ko da second guda ba, daga mijin har dangin shi sun hanata sakat a rayuwa ai ko me tayi musu abun yayi yawa..! Bare babu abunda ta musu, laifinta ne don bata fito cikin gata ba? Laifinta ne don bata da dangi? Laifinta ne zaɓan wannan rayuwa da take ciki? Ai babu ɗan Adam da ze so zaɓarwa kanshi rayuwa cikin kakani kayi irin na Hidayat..." Kuka ne ya ci karfinta tayi shiru tana shesheka, kowa a wurin jikinshi yayi sanyi, Asabe tace "kwarai kuwa yallaɓai tun da muka san hidayat a matsayin makociya bata da wani banzan hali ko mugunta, yarinya ce me cike da kalubalen rayuwa bata jin daaɗi wurin ko ɗaya daga cikin zuri'ar dake kewaye da ita, daga miji har danginshi har ma wasu daga cikin maƙota, wannan matar" Ta Nuna umma "ita da yaranta basa sati guda chur basu zo sun musgunawa rayuwar baiwar Allahn nan ba, yanzu ba don Allah yasa akwai jama'a a gidan suka zo da wannan babban maganan ba da kila sede wan labarin ba wannan ba, wallahi duk abunda suke hidayat ko iya ɗaga kai ta kallesu bata yi abun takaicin ma dube ta nan faɗa har police station kuma wai da takaba a kanta" Dpo da ya tausayawa hidayat sossai sede bashi da wani hurumi a kan aurenta sede ze sama mata sauki ta wani ɓangaren, su Umma ya sa aka saka a cell yace Gobe da yamma hidayat ta dawo a karasa shari'ar don yana so kan gobe suma su ɗandana kaɗan daga cikin halin da suka jefa hidayat. Kowa tafiya yayi, ummi kaman ta daki hidayat don kuka take tana rokon DPO ɗin akan kar a saka su umma a cell be saurare ta ba har Seda aka cika umarnin shi. Jiki a sanyaye hidayat ta dawo ita kaɗai take hango masifar da ummi da su Asabe suka sakata, da sun bar umman ta buge ta ta huce ba se abun ya kai ga hukuma ba tunda dae duka baya kisa, ko da ta kawowa ummi maganan ummi cewa tayi "se kiyi, ina nan a gidan nan har se na ji hukuncin da DPO ze yanke gobe wallahi babu me taɓaki, karki manta ɗinki ne a jikinki ɗanye sharaf sannan taya zasu yi accusing ɗinki da kashe Abba alhali su da wannan banzar hallayar nasu su suKayi sanadin shi, wallahi su kiyayi sakayya da kuma hakki don baƙin cikinsu shine ya kashe Abba" Da dare a haukace Yusuf ya shigo gidan yana me hargowan ina ta kai su umma? Ummi ce ta amsa mishi da "inda ya dace a kaisu mana tun farko" Ze yi kanta ta shata mai layi tare da zaro numbern DPO tace "Wallahi kana taɓa ni tare zaka kwana da ƴan uwanka a cell, karka ji da wai ba iya nan abun ze tsaya ba wallahi se mun je kotu, kotun ma na addinin musulunci se ka gayamin wani addini ne ya baka lasisin zina, wani kuma addinin ne ya baka lasisin musgunawa matar aurenka da yaran ka" Baya ya koma yana kallonta, tabbas daga kallon idanunta zata aikata kwafa yayi yace "Zaku gani!" Ummi tayi Charab tace "Alkhairi ba! Se Alkhairi in shaa Allah" Juyawa yayi ya fice, hidiyat dae haka ta kwana cikin zullumi da sanyin jiki ummi kam ko a jikinta se hira suke tayi da su Aisha tana basu labarai kala kala suna dariya. Washegari bayan la'asar suka yiwa police station tsinke, a nan suka tarar da Yusuf da ba yadda be yi ba a bada belinsu sede DPO ko bari ya ganshi be yi ba se da time ɗin da ya dibar musu yayi yasa aka fiddo su zuwa office nashi hidayat dae banda faɗuwa babu abunda gabanta yake musamman da ta ga yadda su umma suka firgice sukayi zuru zuru da alamu sun ci duka duk a kwana ɗaya. Gyaran murya yayi kan yace "kun riga kun amsa laifin ku so Bama bukatar wani sake maida magana, yanzu doka zan kafa muku wadda duk kuka tsallake da human rights zan Haɗa ku tunda ita ba dabba bace kai ko ita dabba ce akwai animal right so ku buɗe kunnuwanku da kyau ku jini" Yayi maganan yana Kallonsu ɗaya bayan ɗaya kan ya cigaba "Wallahi ko me kama daku aka ce min an sake ganin gilamawarta a unguwan nan wlh ba zamu yi ta daaɗi ba, ba zan hana danku zuwa gare ku ba sede ita na haramta muku zuwa kusanta, please idan kuna Tunanin wasa nake just try me and see fileing ɗin ku zanyi as attempt murderer, ke kuma uwa ce kaman yadda aka haifeta haka kika haihu babu wadda ya san inda Rana zata faɗa in banda jalihci da ƙarancin addini taya zaki fara fitowa kawai don tashin hankali da takabar mijinki? Allah yayi gaskiya da yace mafi koluluwar jin daaɗin namiji a duniya shine mata ta gari, hakanan annabi ya horemu da samawa ƴaƴayenmu iyaye nagartattu amma ke kam baki daga cikin ko guda Allah ya shirye ki in na shiriya ne" Kuɗin beli ya fadawa Yusuf, jiki na rawa ya cire ya biya yace ya sallame su, shi kuma kar ya bari su haɗu. Godiya ummi tayi ta mishi shi kuwa hidiyat yayi consoling yace karta damu babu abunda ze sake faruwa she's safe. Ko da suka dawo shawarwari ummi ta bata ganin har lokacin hankalinta be kwanta ba yasa Ummi sake kwana, anan suka yanke shawarar sana'ar da zatayi da dubu ashirin din nan. Kaman da wasa aka saukewa Hidayat Gawayin dubu goma da kuma icce na dubu goma nan take ta fara sana'arta ba kama hannu yaro tana kula da yaranta cikin rufin asirin Allah da ikonsa, babu abunda ya gagaresu na daidai talaka Yusuf ya kan shigo sede kallo kawai yake hadasu baya ce mata ci kanki in ta gaishe shi ba amsawa yake ba. Raed junior na wata biyu ta sayi freezer ƙarami ta kara sana'ar Kankarar zobo da na nono da su kankarar tsamiya at dsame time tana icce da gawayin ta. A lokacin kuma ta fara lura da Yusuf da ya kan shigo kullum a birkice, sannan yanzu da kafa take ganinshi ƴan matan ma ya dena kawowa, bata dae dena gaishe shi ba Dukda baya amsawa haka yaran ta kan yi musu dole su gaida uban nasu Dukda tsoron shi da ya riga ya rikide zuwa tsanar shi da suke suma don tun tana iya kare shi har ta dawo shiru, yaran yanzu ne da ake haifar su da wayaun su. Yau tana zaune tana lissafin kuɗin da zata ware uwar kudin ta sake sayan kayan sana'a sannan ribar kuwa ta je kasuwa ta sayo musu abun bukata zuwa Abinci kaman an jefo shi haka ya faɗo ɗakin, idanunshi kan hannunta kuwa yayi saurin zuwa ya fusge a razane ta mike sede ko sake kallonta be yi ba ya juya ya fice. Sauke idanunta da suka kara kyau yanzu sbd hankalinta dake kwance tayi se suka hada idanu da Aisha dake kwance zazzaɓi ya dame ta bata je islamiyya ba, maida kwallar da ya cika mata idanu tayi saboda yarinyar ta zauna kawai tana me ɗaukan Raed da su Aisha ke ce mai Junior ta hau bashi Nono. Abu kaman kar ya fara nan fa ya kulla mata, daga ta ɗan yi ciniki kaɗan ze zo ya kwace wani lokacin ko ta ɓoye haka ze wargaza ɗakin kab ya bincike se ya samo haka zasu rakube da yaranta in ya gama ya fice su tashi su gyara ɗakin. Tun ɗan sauran da yake barin mata yana juyuwa har ya kare aka koma square one1 freezer ɗin ta sayar ta sake fara gawayi sede shima ba'a je ko ina ba ya sake kwacewa. Wani Ranar Alhamis da misalin karfe biyu suna zaune da yaran suna cin abincin da shine kaɗai ya saura musu a hatsi wadda suka dafe yau, a fujajan ya shigo kaman ba Yusuf ɗan wankan nan ba ita dae hidaya se mamakin abunda ke faruwa dashi take a baɗini ta san ba lafiya ba sede tunda bata da hurumi nata ido. A kansu ya tsaya yace "Ke! Bani kuɗi" Duk idanu suka zuba mishi se da ya daka mata wani tsawa a firgice junior ya tsala kara, yayyun shi suka haɗe kansu cikin rawan murya tace "ba..babu" Hannu ya ɗaga ze Mareta Usman yayi saurin cewa "Abba ta fa ce maka babu" Juyo idanu yayi kan shi yace "kai don ubanka har ka kai ina magana kana sa min baki? Irin banzan tarbiyar da uwar taku ta koya muku kenan?" Da sauri tace "kayi hakuri! Wallahi babu ko Naira biyar hannuna yanzu" Kafa ya sa ya harɓe ta yace "Bani kudi nace! Na san akwai kin boye ne.. Ai dama an fada min kece duk farar kafanki ce ta sa na zuba duka kudadenmu na gadon Abbah a hannun ƴan damfara wallahi se kin fito min da kuɗina!" Dukanta ya fara, hakan yasa Usman tashi da gudu yaje ya faɗi a jikinta yana cewa "Abba! Abba ka dena dukanta tace babu, bamu da komai duk ka karɓe" Yaron ya ɗaga yayi wurgi dashi wadda ya saka Hidayat runtse idanu tana kiran sunan Allah da karfi, Aisha dake rungume da junior duk suna kuka ta kara kankame shi tare da rufe idanu tana cewa "Abba kayi hakuri! Abba ka dena dukan su basu yi komai ba Abba! Mama ki bashi kuɗin ya dena dukanku, mama kan Ya Usman na jini..." Da gudu Hidayat ta miƙe tayi kan Usman da tunda kanshi yayi mugun gwaruwa da pillar ɗin varender ɗinsu be kara motsi ba, ɗago shi tayi tana furta.. "Innalillahi wainna ilahi rajiun Usman! Usman..! Usman tashi, buɗe idanunka ka gani kaji? Ka buɗe ka gani wallahi ya dena dukana ba kuma ze sake ba, don Allah ka buɗe idanunka..!" Kuka take yi me gunji da matukar ciwo, wani irin baƙin duhu ne ya mamaye ilahirin zuciyarta, da sauri ta ɗago Usman wadda yanzu ya fi karfinta a dauka haka ta saka shi a bayanta, daga ita se doguwar rigar sunan junior ta ɗaura ɗankwalin a kanta haka ta fice cikin tashin hankali don Yusuf ya jima da ficewa Abun shi. Gudu gudu sauri sauri haka take tafiya dashi a bayanta hawayen dake zuba mata yasa ko ganin gabanta bata yi, damuwanta kawai ta samu asibiti kusa inda za'a duba mata Usman, she can't take it! Bazata iya jure rayuwa babu su ba, wani irin ƙara ne ya ziyarci kunnuwanta, wadda babu tantama na birki ne sbd yadda taji mutane sun saki salati, se a lokacin ta lura da hancin motar dake dab kafafunta.. Kan ta ɗaga kai taji wani tsawa a kanta wadda ya kara sakata birkicewa har Usman ya silmiyo daga bayanta saboda jikinshi dake sake. "Hey! Are you out of your senses da zaki ke tafiya a hanya kamar animal? What nonsense for Goodness sake!" Sam bata bi ta kanshi ba se Usman da take sake kokarin ɗagowa ta sa a bayan ta sede haki da take ya hanata, a haukace take a birkice. Idanunshi da suke zube a kanta ya janye tare da mayarwa kan yaron within a second ya shaida shi, this is Usman Aisha's brother. Da sauri ya karaso ya sa hannu ya ɗaga shi yana aikawa hidayat wani irin kallon takaici, what sort of parents does this children have! Yayi exclaiming a ranshi kan ya saka Usman a mota. Da gudu ta zo ta shiga tana sake rukunkumeshi tana hakki da kuka at same time tana maganan da ita kanta bata san me take cewa ba. Da wani kalar speed ya ja motar Dukda nashi matsalar da ta sha kanshi sede he can't leave them like that without help not for the sake of the mother or father but bcs of the loving children. Wani asibitin kuɗi dake kusa yayi parking a take aka yi rushing Usman to Emergency, a jikin gini ya jingina tare da harɗe kafafu ya zubawa wuri guda idanu yana jin Hidayat dake going thou and fro tana gunjin kuka lokaci lokaci tana cewa "Usman! Allah na banda su ya rabb" Sun kusa one hour a haka ita bata zauna ba haka shima kaman be san da halittar mutum dake je ka ka dawo ba a wurin, ɗakin da aka shiga dashi ne ya buɗu likitan ya fito yana share gumi yace "am sorry we cannot save him Jini yayi forcing kanshi to his brain wadda yayi ajalinshi, Allah ya gafarta masa ya baku ha..." "Us..us..man ɗinaaa? A'aaaa A'aaaa ba shi ba dae! Ba shine bane! Dan Allah baze mutu yanzu ba..! Wayyoooo I can't, I cannot loose him! Yarona...." Wani irin kukan da bata taɓa yi ba na tashin hankali take, he's just a little child yanzu ya fara rayuwa! Sulalewa tayi kasa a sume, a take itama aka yi emergency da ita. Moh Raed da ya runtse idanu tun jin rasuwar ya buɗe tare da bin gadon da aka wuce da ita da kallo, he's so heartbroken yana tuna sadda Usman yake ce mishi fuska cike da farin ciki cikin Salon maganan yara.. "Allah ya biya ka da gidan Aljanna yasa a mizani haka mama tace a cewa duk mutumin kirkin da yayi maka alkhairi.!" Sake runtse idanu yayi yana tuna murmushin yaron, he can't imagine himself losing one of his child Norah or Farah. Shi yayi komai har aka fiddo gawar Usman zuwa motan Ambulance, hidayat da wata nurse ta taimakawa ta fito ko tsayuwa bata iya yi ya kalla gabaɗaya ta firgice, kaman robot haka take tafiya. Wayanshi da ya dauki ringing akallah na kusan shidda kenan ya kallah kan ya ɗaga a lokaci ɗaya ya lumshe kyawawan idanunshi yana sauraran faɗan da ake na mintuna kan ya saukar da wayan ba tare da ya ce komai ba, a Ambulance din hidayat ta zauna ya je motanshi ya dawo a kan cinyar ta ya ajiye envelope hakan ya sakata ɗago idanu. Sarkewa idanunsu yayi cikin na juna a hankali ta sauke nata cikin muryar nan tashi me nauyi da be fita sossai yace "May his gentle soul rest in Peace, he will be in a good place in shaa Allah" Yana kai nan ya juya ya wuce, shi karan kanshi da sau ɗaya ya taɓa ganin Usman he felt the death bare mahaifiyarshi but, she's really too young for this. Seda Ambulance ɗin ta fice a asibitin for some minutes kan ya iya tada motar shi ya fice da mugun gudu... *am in full tears😭😭😭🤧 kuyi hakuri gobe ba tabbacin Zaku samu sbd ina da abubuwan yi dayawa amma in na samu chance in shaa Allah Zaku jini* #like #share #comment                     🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 11* *FREE BOOK* **Ameeratuh kin hana ni baccin safe🤧 ga shinan kan ki zo min a mafarki🚶‍♀️🚶‍♀️** "Hidayat haba mana kar imaninki yayi ƙaranci ki dinga furta kalmomin da zaki je kiyi saɓo, Usman kwanan shi ya riga ya ƙare shine dalilin mutuwar shi Sam baki yi Sila ba sbd be yi gaggawa ba mu ma kuma ba jinkiri mu kayi ba, yau kwana bakwai kenan bakya ci bakya sha, sbd kuka dubi idanunki yadda suka koma ki kalla ki ga Aisha yadda take a firgice tun rasuwar nan shi karan kanshi junior  bakya bashi kulawar da ta dace idan ke kika Gaza su kuma fa?" Idanunta da suke a sussuntume tun rasuwar ta ɗaga ta kalli ummi tace cikin wani irin murya "haka ne! Na gode ummi yanzu ina ga lokaci yayi da zan yi abunda ya dace, ba zan yi faɗa da YUSUF yanzu ba amma ba shi yake nufin ya sha a banza ba, yanzu ne na fara koyo daga karatun da duniya take koyar dani, zan yi bita in hardace a duk sadda na tashi amsa jarabawar baze yiwa kowa daaɗi ba saboda da 100/100 zan fita, yanzu zan iya yin duk abunda ya dace saboda yarana biyun nan da kuma fansar jinin Usman... YUSUF! hmmm" Dukda ummi bata fahimci maganan ta ba, ita dae tunda tayi magana yau da sauki, abinci wadda ummi na shigowa gidan hidayat ta mika mata envelope da Moh Raed ya ajiye mata Dukda bata san waye shi ba ya taimaka mata har aka gama gaisuwar usman ba'a rasa abinci da ruwa ba. A gabanta ta ajiye Seda ta kalli abincin na seconds kan mutumin ya faɗo mata a rai, Allah kaɗai ya san daga ina yake ya tsaya ya taimakesu ba tare da neman komai a wurinsu ba, ko ma dae menene she's so much indebted to him. A ranan ummi ta koma gidansu ganin Hidayat ta dena koke koken ta natsu, kan Ummi ta tafi babu abunda bata mata ba har abinci ta sake girka wani ta sa a food flask ta ajiye mata, yamma Lis tana yiwa Junior wanka Aisha da yanzu babu yawan maganan tan nan na zaune gefe tayi tagumi kaman wata babba. Kaman an jefo shi haka ya faɗo gidan tun daga dukan da yayi musu ita da Usman bata sake ganinshi ba se a yau Usman na kwana na bakwai zuwa takwas a rami, yadda ya shigo yasa Aisha firgita ta tashi da gudu taje ta faɗa jikin hidayat tana kankameta kaman zata shide take cewa "Abba! Abba kayi hakuri don Allah karka dakemu... Ya Usman ya mutu nima karka kasheni karka rabani da mamana!" Hawaye ne ya sulmiyowa hidayat ta ɗago rinannun idanunta ta zube a fuskanshi, haɗe rai yayi kaman wani mala'ikan ɗaukan rai yace "ke ya ma sunanki? Wallahi kika kuskura na rike ki se na lahira ya fi ki jin daaɗi" Hidayat bata sake Kallonshi ba ta ɗago ta tana share mata hawayen dake zuba tace "karki sake kuka Aishana ai yanzu kuma me dukanki se ruwan sama shi ɗin ma se in na bari, ki dena kukan nan bana so" Har ya wuce ya dawo yace "me kike cewa?" Mikewa tayi tare da ajiyewa Aisha junior a cinyar ta ta kalleshi cikin idanu tace "nace me taɓa ta kai har ma ni a yanzu kam se ruwan sama!" "kina nufin ban isa taɓaku be kenan?" Da mamaki yake maganan ganin ko ɗar babu a fuskanta se wani irin shakkar ta ya rufe shi da a da ne ze iya kai mata hannu zuwa yanzu. "Yadda kunnuwanka suka ji" "Ah lallai kan mage ya waye, karki manta a gidana kike kuma har yanzu ni mijinki ne, ita kuma wannan ƴata ce don haka ina da ikon yin yadda na ga dama a lokacin da na ga dama.." Wani irin dariyar rainin hankali hidayat ta saki kan ta juya manyan idanunta tana kallon gidan tace "Gida fa kace? Ai ni ban ga gida ba banda kasungumin daji me cike da namun dabba masu hatsari da ban tsoro, jikin hidayat kuwa daga kwana bakwai baya ka datse duk wani alakarka da ita, datsewa ta har Abada kuwa... Ashe se yau ka san Aisha ƴar ka ce? To kaji da kyau Aisha da Muhammad Raed ƴaƴan hidayat shine sunansu, basu san wanene yusuf ba kuma ba za su san shi ba. har Abada sunansu ya tashi daga Aisha Yusuf zuwa Aisha hidayat Abubakar, ni nice uban su kuma ni ce uwar su don haka ka kiyaye alakanta kanka dasu" Gabaɗaya idanunshi a waje suke yana mamakin wannan sabuwar hidayat da be taɓa gani ba, kwarjininta da yadda take kallon shi cikin idanu babu tsoro se ma hango wani wutar bala'i dake tashi a cikin idanunta yasa yaji wani sanyi sanyi na kokarin lulluɓe shi. Cikin karfin hali yace "kin san a yau na sake ki zan iya auren mata huɗu rus? Kuma a yau na sake ki baki da wurin zuwa so dole ki dawo nan ɗin ki tsuguna a gabana ki roki gafara a lokacin kuma ina ga lokaci ya riga ya kure miki..." Hannunta ta harɗe tace "babu macen da zata iya zama Da Mugun Miji irin ka Yusuf idan ba hidayat ba har Abada ba'a yi macen da zata iya shigowa wannan kurkukun kaddarar ba, kuma ka ji da kyau idan har na saka kafafuna na fita daga gidan nan wallahi wallahi ko mutuwa zan yi a waje na gama taka harabar gidan nan kenan  gwara in mutu da in sake alakanta kaina da kai... Azzalumi, Fasiki, makashi..." Tayi maganan hawaye na gangaro mata sede fa ba shi ya nuna gazawarta ba, hawayen na wutar bala'in dake cin ƙasar zuciyarta ne.. "Ni kike kira da waennan sunayen? Kije na sake ki saki BIYU" Wani dariya tayi tare da haɗe hannunta ya bada sautin clap tace "tafi nono fari, ko baka sakeni ba dama bani da ra'ayin ci gaba da zama da kai.." Har ya fara tafiya tace "Baka ji ba!" Waiwayowa yayi tana murmushi tace "Karka yi tunanin Idan hidayat ta tafi ta tafi kenan fa, Hidayat zata dawo idan har ta Rayu zata dawo ta zama WUTAR DAJIN da babu zato babu tsammani se de kawai a ganta ta mamaye dajin, se ta tabbatar ta yagalgala rayuwarka ta yadda baka yi zato ba, nayi alkawari ni hidayat daga yau a gareka kadangariyar bakin tulu ce a bar ni na ɓata ruwa a tabani kuwa a fashe tulun... Daga rana irin ta yau jinin Usman ba ze barka ba har se ka je inda ka tura shi.... Kuskurenka ɗaya Yusuf! Shine na taɓa wutsiyar damisar dake bacci cikin yunwar kwana da kwanaki.. Ka ga ko me kwatarka se Allah.." Gabanshi ta karaso ta Haɗa yatsunta biyu suka bada wani sautin ɗas har sau uku kan tace "put this at the back of your thick lunatic skull!! Zan dawo.. Hidayat zata dawo" Tana kai nan ta juya ta ɗauki junior tare da kama hannun Aisha suka shige ɗaki, sabbin kayansu na suna ta fitar musu tare da shirya su a wani jaka ta Haɗa na Junior ma daban, wani Waist bag wadda daga gani ya ji jiki ta dauka ta ɗaura a kwankwasonta kan ta goya junior ta dauki hijab ta sakawa Aisha ta dauki nata ta saka suka fito.. Tunda ta kama tafiya ko waiwayen gidan bata sake ba, tana fita kuwa taji wani sabon iskar ƴanci ya lulluɓe ta, tafiyar kafa suka yi sossai in Aisha ta gaji su huta, ruwa kuwa in sun ga masallaci se su je randar wurin su sha. Dab magrib suka isa gidan Abba, tana da yakinin baza su karɓe ta ba sede bata da wurin zuwa da ya wuce nan, bata da ko sisi a jikinta. Da sallama ta shiga parlorn ganin umma da Surayya tayi zaune suna kallo Dukda chanje chanje da ta gani na ja baya a garesu hakan be hana ta duƙawa ba tace "Umma ina yini?" Wani taɓe baki umma dake aika mata da kallon uku saura kwata tayi tace "da ban wuni ba kya ganni?" Tayi maganan tana dauke kai, Surraya ta maka mata harara don har yau takaicin dukan da taci take yi tace "me ya kawoki wurin mu? Ina da kafafunki kika je police station kika sa suka mana tsakani? Me kika zo nema yanzu kuma" "Daga gida nake!" Ta faɗa kanta kasa.. "Eh na san daga gida kike tunda gidan Yusuf ɗin ba daji bane, shine kika kamo hanya kika zo mana da magariban nan?" Cewar umma. "Ya sakeni" Wani irin dariya umma da Surayya suka yi kan Surayya tace "to mu ina ruwan mu don ya sakeki, shine zaki zo mana nan? Kinga ki je chan ki san yadda zaki yi" Umma tace "nan gidanku ne? Ko kina da gado a gidan nan ne? Me gidan nan kin kashe shi kuma a iya sanina bakya daga cikin ƴaƴansa" Kanta kasa tace "Don Allah kuyi hakuri bani da kowa a duniyan nan se ku, in kuka gujeni ban san inda zan yi ba" Umma na mikewa tsaye tace "au kin san da hakan kika kaso aurenki kika zo mana? Bama ki da kunya wallahi..." Surayya tace "kinga babu abunda ya hadamu dake, babu abunda ya Haɗa ƴar tsintuwa da ƴaƴan halak ki je chan ki san nayi" Hawaye masu zafi ne suka zubo mata, laifin iyayenta ne ba nata ba, kowa ana haifanshi cikin gata da kauna amma sun tauye mata wannan farin cikin, a hankali tace "don Allah karku min haka, ku taimakeni bani da wani gida a duniyan nan se nan" Umma tace "ke kinga tsinto ki aka yi, kuma wadda ya tsinto kin nan ya mutu don haka baki da wani alaka da gidan nan don gida namu ne in har mu ke da iko dashi kuwa baki da matsuguni ko na kwayar zarra a cikin gidan nan" Hawayenta gudu suka kara, a Tunaninta umma zasu karɓeta ko da bauta zata ke musu bazata rasa na baiwa Aisha ba, cikin zub da hawaye tace "don Allah umma kiyi hakuri, ni amana ce a hannun ku bani da wani gata a duniyan nan se naku, ku kaɗai ne gata na" Surayya tace "mu ba gatan ki bane! Mu Ba gatan ki bane kije chan ki nemi gatan ki, ah to" Umma tace "se yanzu kika san mu gatan ki ne? Shafaffiya da mai, ina har korata kika sa aka yi a cikin gidan nan? Ko kin manta ne In tuna miki, ina ce wata biyu baya kika sa aka yi mana tsakani dake bayan kin sa an fitar mana da jini? Tun da wuri ki san Inda dare ya miki da inda gari zata waye miki" Dole ta sake jarrabawa saboda yaranta tana tsoron su faɗa mummunan hali idan har ta bar gidan Abba, da ita kaɗai ce zata iya ficewa sede Su Junior.. Cikin rawar murya tace "Umma kuyi hakuri bani da Inda zan je, ku rufamin asiri ko saboda Aisha da Junior ku barni in zauna Anan in muka tafi a wannan lokacin komai ze iya faruwa damu" "babu ruwan mu da abunda ze sameku, duk abunda ze sameku sede ya sameku kinga tashi ki fitar min daga gida.." Umma tayi maganan tana nuna kofa.. Mikewa hidayat tayi daga ita har Aisha hawaye kawai suke yi, zuciyarta yayi nauyi matuka, a hankali wani irin tsanar ahalin da ta taso a ciki na mamayeta, ficewa suka yi daga gidan suka kama tafiya ba tare da sun san inda zasu ba. Har magrib yayi suna yawo, gida ta gani ta shiga da sallama sede sallamar duniyan nan sun ƙi amsa mata Dukda suna zazzaune ne suna kallonta tana Kallonsu, bata ga laifin su ba sanin yadda duniya ta zama se ta fice, a haka ta jera Gidaje kusan biyar don ta samu tayi sallah sede sun ƙi amsa mata sallama ma bare ta roke su. Masallaci ta samu lokacin ana kiran isha anan sukayi magrib da isha, suna nan zaune cikin wani irin hali junior na bayanta Aisha na cikin jikinta har wurin karfe goma me gadin masallacin ya zo yace "baiwar Allah ku kara gaba lokacin rufe masallacin yayi" Rokon shi ta fara akan ya bari su kwana na yau kaɗai Sam ya ƙi haka suka mike suka fito. Tafiya suke tayi ba tare da sanin inda zasu ba, ko kula da inda suke zuwan bata yi tunani ya ci karfinta, damuwa yayi mata yawa, garin yayi shiru banda hasken farin wata babu abunda yake sararin na duniya kowa na cikin gidanshi a killace banda ita da yaranta. "Kai baba..! Wanchan yarinyar tayi Sak yadda honor ya tsara mana wacce yake bukata" Maganan da ya shiga kunnenta kenan ya sakata tsayuwa Chakk ta kalli hagu da damanta ko ɗan tsuntsu babu.. Wadda aka kira da baban ne yace "wai wannan gansamemiya taya tayi kama da kiyasin shi? Ka manta yarinya yace wacce bata kai goma ba?" Na farkon yace "kai dallah chan kalli hannun matar" "kai kai kai wallahi da gaskiyarka wannan ma ai har ta wuce yadda ya kiyasta mana, kaga mu je mu kwaceta mu kaita kila a yau ma zasu yi abunda zasu yi da ita don zaɓe ya riga ya gama karatowa" Basu gama maganan ba Hidayat ta damke hannun Aisha tace "Aisha zamu fara gudu, kiyi gudu da iyakar karfin ki in ba haka ba zamu rasa juna..." A take suka runtuma da gudu mutanen suka biyo bayansu suma da mugun gudu..... #like #share #comment                      🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 12* *FREE BOOK* *Afuwan Na ji na shiru da kuka yi jiya🙏* Cikin tsananin tsoro da fargaban abunda ze iya faruwa da su ta fara ambaton Allah.. "Allah gani gareka ya Allah, da kai na dogara Allah kuma a gareka kaɗai nake bukatar taimako, ya Allah ka karemu da zuri'a ta ya Allah....." Kaman daga sama suka hango mota na zuwa da mugun speed, gabanshi ta shiga ba tare ma da ta sani ba, wani wawan birki aka taka a daidai lokacin mutanen suka iso su. Zaune yake yana ƙarewa situation ɗin kallo cikin son fahimtan abunda ke faruwa, abu irin haka baya gaggawa sbd yanayin shi na famous mutum celebrity, ana iya tricking ɗinshi cikin sauƙi Dukda babu mahalukin da ya san ma yana Nigeria banda yaranshi se wanchan tsohuwar da ta sashi zuwa, tuna haka kaɗai ƙona mai rai yake. "Dan Allah karku cutar damu babu abunda muka muku!" Hidayat ta faɗi tana Haɗa hannunta wuri guda cikin roko. "Muma don Allah kiyi hakuri babu yadda kika iya hanyar samun mu kenan!" Ɗayan ya faɗa. Kara kankame Aisha hidayat tayi a hannunta tana girgiza kai tana cewa.. "Ba zan taɓa Bari ku taɓamin yarinya ba, ba zan bari ba sede in kasheni Zaku yi ku ɗauke ta.." "Hakan ma se ayi ai! Abunda muka sani yau se mun ɗauki yarinyar nan!" Buɗe kofar motan akayi wadda duk ya saka su maida hankali kai, Seda ya shafe seconds kan ya sako kafafunshi ƙasa ya sauko cikin wani salo na burgewa. Sanye yake da track suit riga da wando na Fendi me tsananin taushi da tsada, dark Ash ya saka hulan a kanshi yadda ya rufe giranshi da rabin idanunshi hancinshi sanye da facemask as usual cikin dakakkiyar muryarnan tashi yace "Says who?" Duk Kallonshi suke kan na farko yace "kaman ya says who? Mu muka ce haka kuma dole mu ɗauke ta malam ka kama gabanka ba ruwanka... Baba kamo ta mu wuce.." Hannu wadda aka kira da baban ya miƙa da nufin kamota se Charab yaji an riƙe hannun, wani wawan juyi yayi ya murɗe hannun tare da sauke mishi naushi da kafa ɗaya a fuska, ihu ya kwala yana zubewa sauran suka yo kanshi laga laga yayi musu su huɗu kan suka mike suka gudu. Duk wannan dukan da ya musu ko hulan kanshi be faɗi ba bare Hidayat da ta kara rukunkume Aisha ta ga fuskanshi, hakanan yana dukan ne kaman irin wadda baya so hannunshi yayi datti ɗinnan. Hannaye yasa a aljihu ya tsaya yana Kallonsu, so yake yayi magana sede ranshi a ɓace yake da abubuwa dayawa, tsaki me karfi ya ja ganin Hidayat ta fara jan Aisha zasu tafi a tsakar daren nan. "Shiga mota!" Ya faɗi maganan cikin dakakkiyar muryar salon bada umarni. Chakk hidayat ta tsaya gabanta na dukan tara tara muryarshi kaɗai ya haifar mata da wani kalar faɗuwar gaba bare umarnin da ya Bayar, shi kuma da wanne ya zo? Watsar dashi tayi ta sake jan Aisha tana jijjiga Junior da yake ta kuka. "I said enter the damn fucking carrr!!" Kawai se ta fashe da kuka me karfi saboda tsoratar da tayi hakan yasa Aisha ma fara sabon kuka. Wani tsakin ya kuma ja kaman ya wuce yayi tafiyar shi sede tunda ya gane Aisha daga cikin mota yaji ba ze iya tafiya ya kyale su ba hakan ne ma ya saka shi fitowa taimakonsu but look at what her mother is doing...! Be san wasu irin mutane ne a Nijeriya ba har yanzu mamakin waennan da suka zo satar Aisha kiri kiri yake, haka ƙasar mu ta lalace? Kallon Area ɗin yayi Gidaje ne manya manya na masu hannu da shunin garin Kano, ko wani gida ka kalla zaka san ba ƙaramin kudade aka kashe wurin ƙerawa ba, sede rabi da kwata Gidajen empty ne duk ana Abuja ko Lagos ko ma kasashen waje, wurin yayi shiru dayawa da za'a iya kashe mutum a binne ba tare da kowa ya sani ba ko da kuwa da rana ne bare dare. Hulan ya sauƙe, gyararren ponk ɗinshi rinanne ya bayyana, hannu ya sa ya shafa kan tare da zare facemask ɗin yana zuƙar iska tar kyakyawar fuskanshi ta bayyana, diamond ear ring ɗinshi na shining.. Aisha dake Kallonshi kaman yadda hidayat ke Kallonshi ta fusge ta ruga da gudu taje ta faɗa jikinshi tana cewa "Daddy!" wara hannu yayi ya chaɓe ta se ta fashe da kuka. "Shhh! Shhh Shhh it's OK you are safe honey.." Se a lokacin hidayat dake Kallonsu ta dukar da kai tana ɗigar da hawaye.. Shine Daddy? Shine wannan mutumin da ya taimaka mata a sharafan mutuwa, shine wannan wadda ta sanadiyar shi take numfashi har kawo yanzu, shine ya taimaki Usman a sadda ya ɓata garin nema mata taimako, shine wadda ya taimaka mata zuwa kai Usman Asibiti ya biya bill ya kuma biya Ambulance da ya maida su har gida, shine ya ciyar da mutane daga aljihunshi har mutane suka ci suka sha zuwa ƙarewar makokin Usman, sannan shine ya taimaka musu a yanzu da ake kokarin cutar dasu... Lallai Tarihin hidayat baze cika ba idan ba'a kira sunan wannan bawan Allahn ba, shi ɗin kaman mala'ika ne a wurinta da Allah ke turo mata a duk sadda take buƙatar taimako ita yanzu baiwa take a gareshi saboda ya mata abunda babu wadda ya mata a duniya... Hannun Aisha ya saki yana shirin wucewa tunda mahaifiyarta bata bukatarshi da sauri Aisha ta sake rike hannunshi tana kuka tace "Daddy karka tafi ka barmu, bamu da inda zamu je, Abba wai ya saki mama mun je gida umma ta koremu ni tsoro nake ji.. Karka tafi Daddy..!" Ɗago ido yayi ya kalli hidayat dake Kallonsu se tayi saurin duƙar da kai ba tare da ta bari sun Haɗa idanu ba, hannun Aisha ya riƙe ya zagaye ta ya je ya buɗe gaban motanshi ya ɗaga Aisha ya ajiyeta ya rufe kofan tare da xagayewa yaje ya shiga mazaunin driver, gwiwa a sage hidayat ta buɗe baya ta shiga sanyi da fitinannen kamshin motar na dukanta, kunce junior da har ya gaji da kukan yayi shiru tayi tare da saka shi a kirjinta, jakukunan kayansu duk sun zubar garin gudu gashi bazata iya ce mishi su je su duba ba ta ya ma zata fara?.. Se a lokacin ta lura da unguwan da suka kawo kansu, wasu irin mahaukatan Gidaje da bata taɓa gani ba take gani har suka isa wani golden Gate me kyau sossai daga motar ta ga ya ɗauki wani abu ya danna se gate ɗin ta zuge da kanta.. Kutsa kan motar yayi ya Parker a tsakankanin wasu mahaukatan range Rovers, fitowa yayi ya zagayo ya buɗewa Aisha tare da riƙe hannunta suka dan yi gaba, se hidayat ma ta sauko cikin mamakin irin kalar shi shi kuma kaman kurma? Cikin takunshi na xaratan maza yake tafiya hakan yasa hidayat kara sauri har suka isa kofan shiga gidan, kofan karan kanshi abun kallo ne, daga kasa taga ya danna kofar ta kawo wuta ya saka wasu numbers waenda suka bayyana a flat screen na lock ɗin se kofar tayi magana tare da buɗuwa, karasa turawa yayi ya shige hidayat ta bisu a baya. Wani kalar haduwar da parlorn ke dashi ya sakata dakatawa gabanta na dukan tara tara, da wa Allah ya Haɗata? Anan parlorn ya saki Aisha yace "seat" Yana nuna mata kujera da idanu, kafaɗa ta make tana sake rike hannunshi gani take kaman ze gudu ya bar su, hidayat ta matso tace "Aisha me haka?" Hannu kawai ya ɗan ɗaga mata ya sake rike hannun Aishan suka yi wani kofa... Mintuna biyar suka fito suka haye sama da kallo ta bisu har suka ɓace ta sake dawo da idanunta ta golden color staircase ɗin har ƙasa tana cewa Abba na da kuɗi ashe shi kam ba kuɗi yake dashi ba.. Maganan da aka yi ne ya dawo da ita hankalinta Dukda dai hankalinta rabi na kan Aisha da ya haura da, bata san waye shi ba Dukda tayi trusting ɗinshi sede fa a tsorace take dashi Allah ya gani. "Madam Oga said I should show u a room" Juyawa tayi ta kalli me maganan namiji ne, binshi a baya tayi zuwa wani ɗaki a nan ƙasa ɗakin babu abunda babu har TV kuma tsare yake a tsabtace. A ƙasa kan center rug ta zauna se ga mutumin ya sake dawowa da kayan cook ya ajiye mata tray da varieties of Food wadda ba Nigerian dishes ba yace mata "this is only what we have if u can't eat then I should cook u something different ma" Kallon tray ɗin tayi abinci har kala biyar Dukda ba yawa yawa sede yace bazata iya ci ba? Wacece ita? Uhmm girgiza kai tayi tace "is ok I will have this" "thank you ma." Yace kan ya juya ya fice. Cin abincin tayi sossai saboda yunwa da dama take ji kaman mene, tana gamawa ta sake zama ta shayar da Junior cikin tausayin rayuwarsu. Tana nan zaune har wuraren ɗaya taji knock a hankali, miƙewa tayi taje ta buɗe se idanunsu suka sarƙe wuri guda, sassanyar kamshinshi ya daketa, sanye yake da silk riga da wando na bacci cream color sede ba karamin kyau yayi ba, bata san me zata ce ba se ta nemi duburcewa Aisha dake ɗauke a kafaɗanshi ya nuna mata da hannu yace a ƙasaitance "can I put her on bed?" Miƙa hannu tayi zata karɓe ta ya mata kallon uku saura kwata ya wuce ta ya nufi gadon ya shimfiɗe ta, ya zo ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba.. Se da ya fita ya ja kofan kan ta sauke numfashin da take rike dashi mene? Gani yake bazata iya ɗaukan Aisha ba ko me? Amma lallai mutumin nan ya raina ta.. Taɓe baki tayi ta shige zuwa gadon tana kallon kayan bacci masu taushi da Aishan ke sanye dasu ba karamin kyau ya mata ba, shi kuwa Allah andi inda ya samo shi. Bayi ta shiga shima tana mamakin kyaun shi, duk abubuwan anfanin ciki bata taɓa gani ba tunda ita ba kallo take ba, kuma gidansu akwai na zamanin sede fa ba irin wannan ba, da ɗan dube dube da taɓe taɓe ta samu ta yi tsarki tare da alwala bata san gabas ba amma ta so tayi shafa'i da wutiri kafin ta kwanta haka dae ta kwantar da Junior akan gadon ta kashe Acn da wutan kan ta kwanta, tunani ta faɗa na yadda zasu yi rayuwa, tana so ta rayu ko don daukar fansar Usman tana so ta zama wani abu ko don su umma, sede ta ina zata fara shine bata sani ba. A wannan dare bacci ɓarawo ne kawai ya ɗauke ta ba wai don tayi niyyar yi ɗin ba. Da asuba ma se hasashenta tayi tayi sallah, tana nan zaune tana azkar har gari yayi haske, Aisha ta tayar ta kaita bayi tayo fitsari da alwala, kayan ta na jiya bata dawo dasu ba babu ko hijab haka hidayat ta cire nata ta bata ta saka tayi nata sallar. "Aisha wani hali kuma Kika ɗauko wadda ban koyar dake ba? Kin san shi a ina da zaki maƙale mishi? Sannan wannan bakin ban hana shi zuba zance anyhow ba?" Da faɗa take maganan hakan yasa Aisha fara hawaye. Tsaki hidayat tayi kan tace "magana fa nake miki!" Baya ta ja tace "Mama Daddy ne fa..!" "Daddyn gidanku? Kin....." Shiru tayi sbd knock da aka yi, mikewa tayi ta sanya hijab ɗinta ta je ta buɗe cook na jiya ne da abinci a tray, ajiyewa yayi da muryarshi na yarbawa yace "Good morning ma, Ma Oga said I should call Aisha for him" Tun kan ya rufe baki Aisha tayi waje da gudu, gyaɗa kai hidayat tayi tace zaki dawo ki sameni, amsa mishi gaisuwar tayi ya juya ya fita.. Oat ne se bread da kuma omelet, madaran oat ɗin a wani karamin jug me garai garai se suger cubes suma a bowl daban, ga fork da spoon da kuma tissue.. Bismillah tayi ta karya, sossai ta koshi kuma taji daaɗin karin junior ta ɗauko ta bashi Nono, tana nan zaune cikin saƙa da warwara ta ji maganan Aisha daga parlor Dukda bata ji nashi ba amma yadda Aishan ke magana ta san dashi take maganan. Mikewa tayi ta maida waist bag ɗinta ta ɗaura a kwankwaso ta saka Junior a baya, tare da sanya hijab ɗinta suka fito.. Zaune yake yayi relaxing bisa kujera sanye da kananun kaya three quarter da armless black cotton shirt hankalinshi na kan system da yake operating yayinda Aisha dake rike da pop corn tana zaune daga gefenshi tana surutu sede ya gyaɗa kai ko yayi murmushi, daidai fitowanta Wayanshi ya dauki ringing. Ɗagawa yayi ya kara a kunne yace "what again?" Bata ji me aka ce ba ya wani ɓata fuska yace "wait.. Daadida you kept me at this country for long... Ba zan iya zuwa wani wuri ba kuma yanzu after all I didn't fucking care abt his health or well being..." Daga inda ta ɗan duƙa tana jin tsawar da aka mishi wadda ya saka shi lumshe idanu se kawai ya zare wayan ya kashe gabaɗaya.. A kausashe yace "I see no reason da zan bi abunda kike so woman... He hates me nd I fucking hate him more" Yana maganan yana danna wayan da sauri ya kara a kunne.. "Buy me a ticket of any available flight to Paris now!" Ba tare da ya jira amsa ba ya kashe tare da wurga wayan kan kujera yana ji ana ta kira sede be sake kallon ko ta ɓangaren ba. Ita dae hidayat a tsorace take da mutumin nan wani irin mafadaci ne wannan Allah na? Ta ayyana a ranta tsoron mishi magana ma take, in ka kula da kyau zaka ga yadda jikinta ke rawa.. Da kyar ta iya cewa "Ina kwana!" Be amsa ba se ta dauka baya jin hausa jin yadda yake turanci, sannan ko yayi hausar ma ba fita take da kyau ba ta sake cewa "good morning!" Se a lokacin ya ɗago se idanunsu suka faɗa cikin na juna, janye nata tayi tana jin kaifin idanun nashi a jikinta kwarjininshi duk ya cika parlorn.. murya chan ƙasa yace "morning!" Tace "Dama.. Ina so ne in maka godiya bisa taimakon da kayi mana, ubangiji ya raya zuri'a, Allah ya saka da alkhairi ya sa a mizani." Lumshe idanunshi yayi yana tuna Usman, lokaci daya yana mamakin yadda ta iya turanci don da turanci tayi maganan, akwai abubuwan da suka ɗaure mishi kai a kansu sede bashi da lokacin saurara ko bincike tunda be shafe shi ba. Kai ya gyaɗa mata kawai, wasa da fingers ɗinta ta cigaba da yi feeling uncomfortable kan tace "mu zamu tafi.. Allah ya biya da gidan Aljanna" Aisha da bata san ya aka mata wanka ba sanye da hoodie na kamfanin Nike purple color tayi rau rau da idanunta.. Harara Hidayat ta zabga mata wadda ya sakata mikewa ta nufi Hidayat ɗin hannunta ta kama tace "se anjima" Suka nufi kofa abun su... #share #like #comment 🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 13 *FREE BOOK* *Adda Haneefa and herlieymertouh this page is for you😍🥰❤️* "Ina zaki je with this 2 little kids? Wai ni kam are you in ur right senses? How can you be so reckless abt ur kids well being? Do u really want them death as Usman?" Maganan ya mugun dakarta, hakan ya sakata tsayawa Chak... Me yake nufi? Zuciyarta yayi matukar zafi, ashe wani ze iya ganin laifinta akan yaranta? Yana ɗauka sakacinta ya saka kullum take cikin matsala? Bata ga laifin shi ba don ba shine a shoes ɗin hidayat ba, bata ga laifin shi ba saboda be san wacece hidayat ba.. Hawayen da take zubarwa ta sa hannu ta share, ba tare da ta juyo ba tace "I never wish anything bad to them, na yarda akwai sakacina wurin rasa Usman sede ya zanyi? Ina zanje? Wurin wa zan je? Duk ban sani ba, bani da kowa bani da komai taya zan fara duk ban sani ba...! Don Allah ka gayamin ta ina zan fara???" Ta karashe tana zubewa kan gwiwowinta tare da fashewa da kuka me tsananin cin rai, idan ta tuna sanadiyar kare mata duka Usman ya tafi se taji kaman ta kashe kanta ta huta sbd dacin zuciya... "Who are you?" Ya watso mata tambayar yana kallonta fuskanshi da little bit tausayinta da ya fara kama zuciyarshi daga ganin yadda take kuka she's terrified, and restless. Kasa magana tayi se kuka, Aisha na duke a gabanta tana goge mata duk hawayen da suka zuba, hakan se ya motsa zuciyarshi... Ganin kaman bata da niyyar amsa mishi tambayar yasa yace cikin cool voice "I just wanna help, nd I cannot trust you with the work am gonna give you in har baki gayamin wacece ke ba!" Yayi maganan yana maida idanunshi kan system ɗinshi, zafi zafi yake operating system ɗin a hankali yaji maganan ta cikin sanyi da karaya ta fara bashi labarinta tun daga farko yadda ta tashi ta ganta har zuwa kawo yanzu.. Tun yana yin typing ɗin sauri sauri har ya dawo a hankali a hankali daga karshe hannayenshi ne kawai zube bisa keyboard ɗin, ya lumshe idanunshi be taɓa jin labari makamancin wannan ba, yana Tunanin nashi labarin shine mafi munin labari ashe ba haka bane..! Ashe nashi azabar kaɗan ne shi namiji ne for that matter gashi yayi building career ɗinshi yayi kuɗi fiye da uban nashi.. Ashe akwai mutane haka? What a world are we living in.. Ya rabb. Duk wannan Tunanin a zuciyarshi yake saboda kukan da take yi jin tsikar jikinshi yake a matukar tashe, har rawa zuciyar shi yake... Yarinya karama ce sossai wacce sa'anninta suna nan suna building career ɗinsu but nata is already shattered.. "How... How can I help you?" Fuskanta da ya kumbura ta share, tace "I want revenge!" Da sauri ya ɗago ya kalleta jin yadda tayi maganan daga muryarta zata san har cikin zuciyarta abunda take nufi kenan.. "Da kaina nake so in bi ma Usman hakkin shi... Usman died bcs of me! Usman ya tafi saboda kare min duka how can I forget that?" Kallonta ya cigaba da yi ba tare da ta kalleshi ba ta sake cewa "Ina so in nemi aikin yi ko wani iri ne wadda za'a dinga biyana da wahalana, I want to study I want to be a barrister ta yadda zan dawo rayuwarsu kaman dirar mikiya!" Lumshe idanunshi yayi, yana nazari he can trust her with his kids sede su Norah fa? Ya san su sarai they don't want people from Nigeria.. But bari ya bata chance he loves her kids sbd wayaun su da tarbiyar su... "Can you nanny my kids? As a job?" Kanta ƙasa sbd idan har ze kalleta ita bazata iya Kallonshi ba, kai ta gyaɗa tace "in shaa Allah, zaka sameni yadda kake so wurin baiwa yaranka kular da ta dace!" Kaman ya ce mata they are not regular kids, rayuwarsu irin na Turai ne sbd ko wata babu wacce ta taɓa yi a Nigeria a cikinsu sede yayi shiru, she says she can then let's see... Waya ya janyo yayi kira... "Patric I wanna see u now" Ba'a yi mintuna talatin ba se ga Patric, already hidayat ta koma ciki cook ɗinshi ya aika ya kirata. Kuɗi ya zubewa Patric yace "take them to super market, they should buy anything like komai na bukata she will be Norah nd Farrah nanny so please guide her u knew their taste... From there u take her to immigration office for international passport and start processing her visa we r leaving together" "Yes sir!" Patrick ya amsa.. Tare da cewa "shall we go ma'am?" Kai ta gyaɗa suka fice ta so ta ce mishi ko ta gode ne sede fuskanshi tsoro yake bata, rashin sakewar fuskan tayi yawa gashi da I don't care attitude don har suka fita ko Patrick ɗin be sake ɗaga kai ya kalleshi ba.. Da ɗaya daga cikin Zafafan motocin shi suka fita, ita dae a muzance take jinta Dukda hijab ɗinta ba abunda ya same shi sede fa ta san rayuwar nan da ta shigo ya fi karfinta, nanny..! Allah andi yaran har nawa ne.. Rayuwar ƙasar waje kuma ya ze kasance mata? Sayayya na fitan hankali Patrick ya sa matar tayi mata, suna da spa a wurin ya sa suka mata facial and body scrub, dayake ta cewa matar duk dressing da za'a hada mata ba ta son me bayyana tsiraici se matar tayi mata haɗi masu kyau, har da su suits sede ba me kama jiki ba sannan da baby hijabs ko veils, har veils ɗin seda ta koya mata different design na yafa su sbd Patric ya gayamata yaran zasu iya mata mugun raini idan ta je a yadda ta je and they can deny her as nanny baban su kuwa be taɓa turning against their decision ba.. Kayan da taje da su Patrick yasa aka watsar, har junior sayayya shi daban, ita akwati medium da kit ɗinshi ash na zamani, na Aisha medium na yara pink me hoton frozen, se Junior wani jaka ne me kyau har da carriage na yara wadda ake daure su a gaban nan ya sa aka saka musu sbd ya san turawa basa goyo kaman yadda mu muke yi, man shafa, turaruka duk na matsakaitan kuɗi ya sa aka sa mata.. Fitowa suka yi hidayat sanye da peach English gown da yayi mata kyau sossai me dogon hannu, gyalen tayi mishi yafin ƴan kasan Oman sanye da Junior cikin carriage ta gabanta, hannunta rike da Aisha da bata chanza daga kayan Farah da Raed ya saka mata ba.. In ka kallesu zaka ɗauka asalin su masu kuɗin ne kyaunta yayi mugun bayyana Dukda ramar da tayi da kuma fatan ta da yayi duhu kaɗan.. Immigration office suka je aka yi mata passport abun ka da kuɗi awanni biyar aka basu zasu karɓa, Patrick ya maida su gida da sayayyarsu yayiwa Raed bayani a waya don ya riga ya bar parlorn.. Hidayat na ɗaki sede har washegari ko kofa bata leƙa ba, abunda yayi keeping ɗinta busy kuwa shine System da Raed ya aiko cook dashi da takarda da biro abubuwan da yaranshi suke so ne da waenda basa so, yadda suke yin breakfast, lunch, dinner.. School ɗinsu da komai dama duk.nanny ɗinsu da zata bar aiki zata yi documenting komai ta tura mishi yadda next nanny zata ɗaura daga nan, tun yamma take abu ɗaya har washegari nan ta fara sarewa, daga gani yaran nan ba kananun ƴan gata bane irin su kuma ta tabbatar they would be rude.. Sede zata yi hakuri da komai saboda cikar burinta.. Abunda bazata riƙe ba se ta rubuta a cikin hardcover da ya haɗo ta dashi, shi ya san yaranshi in bata musu ba se su hautsina mishi lissafi, and yana tausayinta apart from the nanny be san me zata musu na kuɗi da ze iya biyanta ba.. A cikin 3days komai nata ya kamalla, kuma har kwana ukun nan bata sake sanya shi a ido ba, Aisha dae tana mata wanka zata fice se dare cook ke dawo da ita wani lokacin kuma ta dawo da kanta kan magrib, farkon abunda ya fara ɗaga mata hankali shine idan Aisha ta dawo ta tambaye ta. "Kin yi sallah?" Se yarinyar tace "A'a" Hidayat tace "me yasa kina ji ana kiran sallah bazaki tashi kiyi ba? Ko bakya ganin daddyn nayi ne da zaki zauna bazaki yi sallah ba Aisha fa." Se yarinyar tace "Mama ai shima be tashi yayi ba..!" Hidayat bata kara magana sbd tsoro da fargaba da take shiga, Aisha bazata yi karya ba amma me yake hana shi yin sallah? Ko de ba musulmi bane? Toh ya akayi sunanshi Muhammad kuma..! Kwakwalwanta a sarƙe yake har ranar da zasu tafi, Adu'a kawai take Allah ya sa wannan rayuwar ya zame mata mafi alkhairi kar ya zama wani baabin mummunar kaddarar kuma daga cikin shafuskanta na rayuwa.. Sanye take da shirt nylon tare da palazzo trouser me faɗi se ta saka kimono marar nauyi wadda be gama kaiwa ƙasa ba aka yi wani style daga kasan ba karamin kyau tayi ba dake mayukan da take anfani dasu masu kyau din ne ga cima me kyau da take samu, ta shirya Junior cikin kananun kaya farare da ya amshe shi sossai yaron ba de kyau ba.. Aisha a wurinshi ta shirya cikin kananun riga da wando kanta ba ɗan kwali tana shigowa hidayat ta kama ta ta saka mata after dress saman kayan tare da sa mata baby hijab se tayi wani kyau abunta.. Fitowa suka yi suka tsaya daga bakin kofa, ba'a yi minti biyar  da tsayuwar su ba fitinannen kamshinshi ya fara musu sallama kan tsayayyen figure ɗinshi ya bayyana tafiya yake cike da ginshira da wani kalar ƙasaita hannayenshi sanye cikin aljihu.. Sanye yake da crazy Jean blue me kyaun gaske ya ɗan kama shi se wani silk shirt me zanen art emerald green me guntun hannu, kafafunshi sanye cikin emerald green combus daga gani ka san ba na karamin kuɗi bane, kanshi sanye da same color face cap ya saka baƙin sunglasses da facemask sbd ɓadda kama, ɗan kunnenshi se walkiya yake hakanan zoben azurfa dake hannunshi.. Agogonshi na Fendi dake ɗaure a hannunshi na hagu ya kalla it's almost time ba tare da ya kalli ko ɓangaren dining da cook ɗin shi ya shirya mishi abinci ba ya riƙe hannun Aisha da taje wurinshi da gudu suka nufi waje yana kallon dressing ɗin ta da ya mishi kyau, ko inanta a rufe se ɗan karamin baby face ɗinta, dab da ze fita hidayat da ta biyo bayansu tace "Good morning sir" Yace "morning" Suna karasa fita, Patrick ne ya buɗe bayan zazzafar Porsche ɗinshi suka shiga, yayinda hidayat ta shiga gaba ya ja suka fice daga gidan dama tun ɗazu ya saka kayayyakin su a booth sanin ogan shi ba tafiya da kaya yake ba.. Saboda shigan dake jikinshi babu wadda ya gane shi a Airport ɗin ma har suka shiga VVIP, ita dae hidayat banda bat bat bat babu abunda zuciyarta ke yi, bata taɓa ganin jirgi ido da ido ba se gata yau ita ce zata shige shi, daga ganin inda suka shigo ma ta san cewa ba wurin regular mutane bane zama yayi kaman a parlornshi briefcase da Patrick ya rako shi dashi har seat ɗinshi ya janyo ya ciro system ɗinshi ya hau operating yayinda Aisha ke zaune kujeran dake facing nashi tana mishi tambayoyi yana amsawa a takaice  anan hidayat ke gane wasu abubuwan.. Har za'a tashi ya ɗan kalleta bata ɗaura seat belt ba and a labarin da ta bashi he's quit sure bata taɓa hawa jirgi ba abunda ya fara kwantar mishi da hankali a tafiya da ita shine bata da hayaniya, button na gefen shi ya danna se ga one of the cabin crew ta shigo.. "How can I help you sir!" Tayi tambayar cikin tsananin girmamawa da taka tsantsan, kallon hidayat yayi yace "give her the safety guide" Da sauri tace "ok sir" Wucewa tayi wani cabinet ta ɗauko ta zo ta baiwa hidayat cikin girmamawa, karantawa hidayat ta fara se taji ma ana maimaitawa ta loudspeaker ɗin jirgin, da sauri tayi yadda aka ce da belt ɗin tare da gyara junior ta rufe idanunta har jirgin ya ɗaga sararin samaniya, shi da kanshi ya riƙe Aisha har aka daidaita ya tashi ya maidata Ɗayan kujeran ya gyara mata don already sun kashe wutan jirgin nasu.. A Lagos suka tsaya for about an hours Dukda basu sauka ba su bata dae san sauran mutanen jirgin ba kan suka sake ɗagawa sun tafi sun tafi har taji ta gaji, ga ciwon kai ga jiri da take ji, shi kam ko don ya saba ne aikinshi kawai yake abun shi, ita kuma Aisha tayi bacci, chan cabin crew ta zo ta tambayeshi me yake so ya faɗa, se ta matso ta tambayi hidayat rasa me zata ce tayi se tace ta kawo mata anything Nijerian dish.. Abincinshi ne ya fara zuwa har ya gama tsakura ya fara kurɓan coffee, junior da ya gaji ze fara rikici ne ta ɗaga tana ɗan mishi rawa da waka se yaron ya bangala dasori yana dariya, a hankali ya sauke idanunshi kan yaron, dariyarshi gwanin kyau, farar ɗaya yaji ƙaunar yaron fiye da yadda yake ƙaunar Aisha, yana so yace ta kawo shi sede bakinshi yayi nauyi, yadda take mishi wasan ya kalla hakwaranta dake jere farare tas a waje hakan ya ba dimples ɗinta duka biyu Daman loɓawa.. Ɗauke kai yayi ya cigaba da kallon Junior cike da sha'awa daidai lokacin aka kawo mata abinci, ajiye mata aka yi sede junior baze barta ta ci ba don ya iya janye janye gashi se son sauka yake yana ta tsalle yaron is full of energetic.. "Can't u give the child to his father so that u can eat peacefully?" Cabin crew ɗin tayi maganan, rikicewa hidayat ta so yi ta fara kame kame. Tsam Raed ya miƙe ya zo ya saka hannu ya karɓe shi yana chilla shi sama yaro kam ba se ya bangala dariya ba shima murmushi yayi yace mata "his name?" Tace "junior" Baki ya taɓe ya nufi kujerar shi dashi wasa yake ta mishi, har ta gama cin abinci aka kwashe abubuwan ta kishingiɗa a take bacci ya sureta, yaron ya gyara a kirjinshi suka kwanta a haka idanunshi a lumshe.. Tafiyar 6 hours ten minutes ya kawo su Paris sun gaji tilis, barin ma hidayat da Aisha da basu saba tafiye tafiye ba, a hankali suke saukowa idanun hidayat na buɗuwa da tsananin kyaun Airport ɗin na Charles de Gaulle(CDG) Aéroport de Paris.. Wasu rantsatsun baƙaƙen GLS 460 4matic baƙaƙen sidik ne suka yi parking gabansu guda biyu bayan sun fito daga terminal ɗin masu ɗaukan trolleys ture da chart ɗin dake ɗauke da kayan su Hidayat, kofofi biyu daga ciki suka buɗu wata kyakyawar matashiya da zata yi 14yrs ce ta fara fitowa sanye da leggings da shirt pink kafafunta combus ne pink se gashinta da ya sha gyara kan karama wacce bazata wuce Aisha ba ta fito itama irin dressing ɗin yayarta ne jikinta rige rige suke yi sede turus suka dakata ganin Daddyn nasu riƙe da wani yaro da basu sani ba.. A tare suka ce "Daaaaad!" Da wani expression a fuskansu.. Hannunshi ɗaya ya wara musu Farah taje ta shige yayinda Norah ta ja gefe tana kallon Hidayat da kuma Aisha ta sake kallon junior da baban su ke rike da shi tace "daad Qui est-ce?(Who are they?" Ba tare da ya kalleta ba yace "ur new nanny nd her family" A tare suka ce "Whattt?" Ɗan ɓata fuska yayi yace "manners girls and parlez lentement, s'il vous plaít"(speak slowly please) Ya faɗa yana shiga motar da aka buɗe mai, duk a tare suka kalli Aisha da Hidayat da suke ji sun muzanta don kirkiri yaran suka nuna basu musu ba, hidayat bata san sadda ta wara idanu ba jin sun ce "Disgusting...!" A tare suka yarfa hannu suka shige motan da baban su ya shiga... #like #comment #share                     🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 14* *FREE BOOK* *Afuwan today I wasn't myself abubuwa sun cunkushe min ayi hakuri da wannan* No.1.3 Le Marais 4th Arrondissements, Saint Thomas d'Aquin. Shine sunan home Address da taga sun yi horn daga bakin hadaddiyar gate ɗin, gabaɗaya layin gidajen ba kananun Gidaje bane, Gidaje ne da suka haɗu suka kuma gaji da haɗuwa daga nan inda suke suna kallon Effile tower dab dab dasu kaima ka san me zama kusa da Effile tower ba karamin abun duniya ya tara ba.. Harabar gidan kaɗai abun kallo ne, riƙe da hannun Aisha suka sauko kaman yadda aka buɗewa Moh Raed ya sauko rungume da Junior, ma'aikatan gidan ne a jere cike da tsantsan girmamawa suke mishi welcome.. Hannu kawai ya ɗaga musu ya juya ga wata farar baturiyar mata yace "Miss Mary this is the new nanny, show her around..!" Cike da girmamawa tace "Noted sir..!" Daga haka ya miƙa mata junior ta zo ta karɓe shi cikin taka tsantsan, Juyawa yayi ya wuce rike da hannayen girls ɗin nashi kowacce na zuba shagwabanta da complain ɗinta.. "You welcome, am miss Mary I am the house keeper, can I please show you around Miss...." Hidayat tayi murmushi tace "Hidayat.. Thank you nice meeting you" Miss Mary ta sake cewa "Wlcm miss hidayat" Daga haka suka nufi ciki bayan ɗaya daga cikin mazan da bata san aikinshi ba ya turo musu akwatunansu, babban parlor ne wadda ya haɗu iya haduwa komai na more rayuwa akwai a cikinshi banda sanyin Ac da kamshin freshener babu abunda yake tashi. Daga gefe suka hau wani steps zuwa sama shima again wani parlorn ne different design da wadda suka bari shima a kyau kam karshe ne har kasa tantance wanne yafi kyau hidayat tayi.. Aisha dake rike da Ɗayan hannunta jikinta yayi sanyi wadda hidayat ta san musababbin ganin su Farrah da basu yi welcoming nasu bane, sbd yarinyar haka take idan ka nuna mata baka sonta tana iya yinta wurin ganin ta kaurace maka duk zakwaɗinta kuwa.. Babban ɗaki ne me ɗauke da gado da wardrobe, coffee table da haɗaddun kujerun su, white curtains da beddings ne se sanyin Ac ke tashi har da TV akwai a ɗakin. Miss Mary tace "this is ur room Miss Hidayat freshen up nd I will show u to d kitchen nd the girls rooms" "thank you!" Abunda hidayat tace kenan, bayan Miss Mary ta fita hidayat ta fara yiwa Junior wanka kan tayiwa Aisha, itama tayi suka sauya kaya suka yi sallah nan ma fa se guessing gabbas tayi sbd bata ga dae musulmin da zata tambaya ba kab gidan.. Suna nan zaune Aisha na wasa da kumatun Junior aka yi knocking hidayat ta mike ta je ta buɗe wata mata ce daban ta mata murmushi tare da mika mata tray ɗin dake rike a hannunta na abinci.. French fries ne da chicken se ketchup da ruwa, karɓa tayi tare da godiya. Bayan sun gama cin abincin miss mary ta dawo tace sir yana son ganinta.. Mikewa tayi tare da gyara gyalen kanta ta ɗauki Junior Aisha ta biyo bayanta suka fito, relaxed suka same shi a parlorn na saman hannunshi news paper ne yana dubawa ya sauya kaya zuwa three quarter da armless shirt, kanta ƙasa ta zauna a kan center rug ɗin tace "weldone sir.." Ɗagowa yayi se yaga Aisha zaune a gefenta cikin sakin fuska yace "hey! Are u avoiding Daddy today? Oya zo nan" Mikewa tayi ta je wurinshi tana kallon yadda Farrah ke mata wani kallo, yace "as from today kinga wurin zamanki in ina gida, this is ur sister Farrah..!" Ya juya ga Farrah yace "Farrah say Salute(hello)to your sister Aisha" Cikin low voice tace "hello" Kallon hidayat yayi ya nuna babban ƴarshi yace "Miss hidayat this is Norah and this Farrah, I hope u will give ur best in d job" "Farrah, Norah this is Miss hidayat ur new nanny as u knew the old one is gonna leave today" Hidayat tace "in shaa Allah zan yi iya kokarina" Norah tace "what is she speaking?" Farrah tace "that Nigerian language I think..!" Kallon da yake musu ne yasa Norah tace "hey miss hidayat" Farrah tace "hello" tana yatsina fuska. Ya kalli hidayat da kanta ke kasa tana wasa da ƙasan veil nata yace "I hope kin nazarci document da na baki?" Tace "yes sir!" Yace "ok ur work will start tomorrow morning Philip will take u to a nearby street to get phone nd iPad" Godiya ta mishi, ba tare da ya sake kallonta ba miss Mary ta zo suka wuce, Seda ta nuna mata rooms ɗin yaran da kowanne da kalar haduwarshi ta kuma nuna mata na baban su dake wani corridor incase Dukda basu shiga ciki ba, kitchen ta kaita da store taga komai, har Gym ɗinshi na saman sun shiga kuma ta ce mata akwai wani a parlorn ƙasa, daga nan suka fito waje.. Mutumin da ya haura mata da kayan wadda shine Philip ɗin ya ɗauke ta zuwa shago shike kula da shefenen gidan kuma shi yake kai yaran school, already akwai Atm na Moh Raed dake hannunshi dashi yayi anfani ya saya mata waya Samsung da kuma IPad na Apple a wurin aka yi mata setting komai da Sim na Paris.. Ko da suka dawo bacci tayi sbd a gajiya take Lis, da dare ta shiga kitchen ta fara duba Time table na yaran kowacce da abunda take ci kuma da abunda take tafiya dashi school, waenda bata iya ba ta fiffitar ta koma wurin miss Mary ta nuna mata yadda zata yi Googling recipes, Seda ta koyi anfani da Google da kuma YouTube ta dawo ɗaki ta hau bincike don sossai take son yin aikin, she really needs a bright future for herself nd for the kids.. searching a Google tayi yadda ake duba compass sbd kallon gabas kuma Allah ya taimaka akwai a iPad ɗin ta duba kuma taga da yardar Allah ashe daidai take yi, da asuban fari ta farka Dukda ba masallaci kusa sede sabo da tashi, sauƙa daga gadon tayi tana Adu'a kan ta mike tayo alwala ta zo ta fara nafilfili, Seda ta duba time na lokacin sallah taga lokaci yayi kan ta mike ta tada Aisha ta tura ta toilet A hankali ta buɗe kofan na ɗakinta ta fito, ɗakin Norah ta fara turawa ta sameta tana bacci rungume da teddy bear ɗinta, gefen gadon ta je ta zauna tare da sa hannu ta ɗan shafa kanta tace cikin sanyin muryarta "Norah..! Norah wake up it's time for prayer" Wani wawan tsaki Norah ta ja tare da Juyawa cigaba da tashinta tayi sede fir ta ki tashi daga karshe ma ihu ta mata da swear wadda ya saka Hidayat fita daga ɗakin, ɗakin Farrah ta shiga itama same abunda Norah tayi tayi mata ganin zata makara yasa ta kyale su ta shiga ɗaki tayi sallah, ita da Aisha suka shiga kitchen ta fara Haɗa musu wadda zasu karya.. Na Norah Tea ne da sandwich se na Farrah fried indomie and egg, hannunta ya riga ya faɗa da girki sossai hakan yasa ko yaya tayi girki yana daaɗi, dukda this is her first time she's very sure ze ciyu.. A dining ta je ta ajiye musu daidai lokacin wani alerm me karfi ya fara kaɗa duka gidan wadda dad ɗinsu ne yayi setting in ba haka ba suna bawa nanny's ɗinsu tought time wurin tashi, aiko alerm ɗin be bar ringing ba seda suka fito dukkansu biyu bakin kofofinsu cike da bacci suka Haɗa baki wurin kiran "Daaaaad" Tsit alerm ɗin yayi, tsaki Norah ta ja ta juya yayinda Farrah ta tsaya tana kallon Aisha dake gyara dining ɗin, lallai ma does this nanny mean they r eating what this little kid cook?. Hidayat ce ta fito ganinta tsaye yasa tace "hey Farrah good morning..!" Ciki ciki tace "morning." Hidayat ta ajiye abun hannunta tace "let's go nd shower u r getting late to school" Juyawa tayi ta shige hidayat ta shiga, da taimakonta tayi wanka Dukda da gangan Farrah ta ringa jika hidayat ɗin da ruwa har seda Fararen pjams ɗinta riga da wando masu faɗi suka jike, bata damu ba ta fito ta shirya ta cikin uniform ɗinta, wadda ko hula babu a matsayinta na ƴar musulma... Hidayat tace cikin harshen turanci (Kuyi hakuri da turancin kaman yadda novel din ya zo amma zan ta yin hausa instead of turanci ku de saka a zuciyarku yaran da uban su ba wani jin hausa suke ba har gwara uban ma) "Farrah ya kamata kiyi sallah, kinga ba kyau rashin yin sallah Allah na ƙona duk wadda baya sallah" Kallon hidayat kawai tayi ba tare da ta fahimta ba ta fice abunta.. A dining suka tarar da Norah sanye da shorts uniform ɗinta itama da yayi mugun karabarta sbd yaran kyawawane kaman babanta yayi khaki ya tofar, daidai lokacin babansu ya fito sanye da jersey alamun suna da wani abun yi da sassafen nan don har takalmi da socks na Club ɗinsu duk sanye a jikinshi kamshi kawai yake zubawa.. Baya Hidayat ta matsa tana kame jikinta dake jiƙe shakab ya wuce ta ba tare da ya kalleta ba, cikin sanyin muryarta tace "Good morning Sir" Yace "Morning Miss hidayat" Lumshe idanu tayi sbd yadda jikinta yayi wani iri da yadda ya kira sunan, bata taɓa jin wadda ya iya ambaton sunan nata irin shi ba, ta gwammaci ya cigaba da amsa mata da morning kaɗai da ya Haɗa da sunanta. Zama yayi daidai lokacin Farrah ta kai abincin bakinta da sauri ta dawo dashi tana tari, a ruɗe Raed yayi kanta yana bata ruwa tare da shafa bayanta yana cewa "sorry dear..!" Tace "WTF is this..!" Lumshe idanu hidayat tayi jin yadda yarinyar karama ke magana wadda be dace ba Sam, yace "menene?" Tace "Daad Indomie ɗin half done I can't eat this" Kallon Norah da itama ta ajiye tea ɗin yayi itama tana ɓata fuska tace "too sugary" Hidayat da jikinta yayi mugun sanyi ya ɗaga idanu ya kalla se ta rikice gabaɗaya ta ruɗe ta fara cewa "am sorry.. Wlh nayi iyakar kokarina ban taɓa girki half done ba nd ban wani cika sugar ba" Norah ta jefar da spoon ɗinta har yayi kara tace "did u mean we r lying?" Girgiza kai hidayat tayi a rikice ganin har lokacin kallonta Raed yake da idanunshi da suke kara rikitata tace "No! No am sorry please! Ba zan sake ba" Ajiyar zuciya ya sauke ya kauda kanshi tare da Kallonsu yace "girls let's eat outside, will drop u at d school myself " Norah tace "amma Daddy kayi warning ɗinta, haka fa da asuba ta zo tana wani tashina tana disturbing peace ɗina I don't like that" Ya juya yana ɗaga Farrah suka fice, Aisha dake tsaye bakin kitchen ta zo ta kama hannun mamanta, kallon yarinyar tayi se ta sauke ajiyar zuciya tana maida hawayen da ya cika mata idanu.. Da sauri taje kitchen ɗin ta ɗauko lunch box ɗinsu tayi waje, yana kokarin tada mota ta karasa tare da knocking glass ɗin hakan ya sa shi saukewa, cikin sanyin muryarta ba tare da ta kalleshi ba tace "Sir their lunch box" Kaman ba ze ce komai ba se yace "sa a baya" Buɗe back seat tayi ta saka tana Kallonsu har suka fice, ciki ta dawo ta samu Miss Mary na aikinta na shara da goge goge, sannu ta mata ta haura a nan suka karya da abunda yaran suka bari, wanka suka shiga sukayi tare da sauya kaya ta zauna ta sake fara karanto abubuwa da yaran suke so da wadda basa so.. Ta Tabbatar se tayi da gaske kafin yaran suyi blending da ita har wani shakuwa ya shiga tsakaninsu, yaran suna bukatar uwa tsayayya in ba haka ba rayuwarsu akwai matsala babba.. Ɗakin su ta gyara musu tsab kan ta fara duba abunda zata ɗaura musu na lunch Seda tayi ta kallo tana maimaitawa kan ta zo ta fara cikin taka tsantsan, wuraren ɗaya ta gama ta shirya a dining, tana gyara kitchen ɗin taji shigowar su babu ko sallama, fitowa tayi tace "girls annabi yace idan zaka shiga wuri dole Kayi sallama ga ahalin wurin kuma amsawa dole ce ga dukkan musulmi da yake wurin, kunga sallama na da kyau kenan hakanan In kayi sallama kana da lada me yawa kunga wadda kuma ya tara lada ne kaɗai ke shiga aljanna" Duk kallonta suke baki hangame kan Nora tayi tsaki ta wuce, Farrah kuwa dake jin yunwa dining tayi, abincin hidayat ta zuba mata ta diba zata kai baki hidayat tace "pray first" Se ta lumshe idanu hidayat bata ji abunda tace ba banda in Jesus name daga karshe, wara idanu tayi tana rike spoon ɗin da sauri a fili tace "Na shiga uku!" A tsorace Farrah ke kallonta tace "Farrah please say bismillah, u r a muslimah so be acting like one wannan ɗabi'ar ba namu bane" Seda ta kalli hidayat ɗin kaɗan kan tace "bismillah!" Ta fara cin abincin, ajiyar zuciya hidayat ta sauke tana dafe kanta ba karamin aiki ne a gabanta, haka suka yi da Norah ma da ta fito cin abinci amma ita bayan tayi bismillahn se jikinta ya ɗan yi sanyi wadda hidayat bata san na menene ba.. Da dare ma kusan yadda aka yi da safe suka yi don Seda babansu ya fita dasu amma yanzu harda Aisha ya kira suka fita, bayan sun dawo a gajiya suka kwanta bacci landline ɗin ɗakinta ne yayi ƙara da sauri ta ɗauka yace yana son ganinta.. Gabanta na faɗuwa haka ta ɗauki hijab ɗin ta ta saka, hanyar waje tayi tana jin sanyi sanyi na neman rufe ta bata son ɓata mishi rai har yayi mata faɗa gashi daga fara aiki yau har tayi laifi, bata ganshi a parlor ba hakan ya ƙara faɗuwar gabanta.. Kofan dakin shi tayi ta tsaya daga bakin kofa tayi knocking mintuna biyu yace "Come in" cikin hadaddiyar voice ɗinshi me kaurin nan, hannunta har rawa yake ta sa a handle tare da murdawa ta sanya kai kamshin da ya buge ta da sanyi Seda ya sakata lumshe idanu... #like #share #comment                     🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 15* *FREE BOOK* Abunda idanunta ya faɗa kai ne yasa tayi hanzarin ɗaukewa tana runtse idanu, mace a kan jikinshi? Daga gani ma ba musulma ba? Innalillahi wainna ilahi rajiun.. Wani irin rayuwa suke yi a gidan nan?.. Tayiwa kanta tambayar tana iya kokarinta wurin hana jikinta  ɗaukar rawar da ya fara, zaune yake bisa couch na ɗakin me taushi sanye da pants/boxers wadda be kai gwiwa ba kana iya ganin murɗaɗɗiyar jikinshi gabaɗaya, wadda gargasa yake nan kwance lublublub, a kan faffaɗar kirjinshi wata kyakyawar yarinya ce daga ganinta bata san me wani talauci ba, ta ci gayu ga nails an yi fixing dressing rabi jiki a waje kwata a rufe.. Daga idanunshi yayi ya sauke a kanta se ya ɗan tsaya yana nazartarta ganin yadda tayi wuri wuri, jikinta na rawa idanunta a runtse, magana yake shirin yi Wayanshi ya sake daukar kara.. "Handsome pls pick this phone samu mu huta da ringing.." Dauka yayi cikin yanga ba wai don Kimorah tayi magana bane yasa yake so ya ɗauka no kawai ya ga ya kamata ya ɗaukan ne ya ɗaga.. "Daadida please.. Don't spoil my mood yanzun nan, I don't really know what's ur problem mutumin nan tun farko fari yace baya so na, yace he hates me nd hates everything abt me and I also fucking hates him..! You lied to me akan baki da lafiya u made me went to Nigeria but at last u saw what happened... I promise idan baki dena min maganan mutumin nan ba zan yanke duk wata alaka da zaki sameni ta waya am damn tired with ur stress..." Shiru yayi yana sauke numfashin masifar da yake yana jin muryar matar na Kuka cikin kunnuwanshi wadda yake ji har tsikar jikinshi na tashi, yana son ta har ranshi itace mace guda da yake jinta har tsakiyar zuciyarshi kuma ita ce kadai ta rage mishi bayan yaranshi sede abunda take so daga gareshi shine yake kara nesanta su, be taɓa ganin macen da bata zuciya akan abu ba se akan Daadida she spent years tana abu guda bayan babu haske.. Zata yi magana yace "I have to pray, good night" Daga haka ya yanke wayan. Mikewa yayi ya wuce toilet, Kimorah da take ta kallon Hidayat tun fara Wayanshi tace "ke! Wacece ke?" Cikin harshen turanci don baturiya ce.. "New nanny!" Tsaki ta ja tana kallon irin kyaun fuska da na sura da Hidayat ɗin ke dashi Dukda a cikin hijab take, wani abu ne ya tsaya mata a wuya, haka kawai hankalinta be kwanta da nannyn ba. "Go to Paul ki ce mishi ya baki food ɗin ki kawo min am starving" Fita tayi Paul shine cook ɗin masu aikin gidan kuma shine yake yiwa Oga abinci, ƙasa ta sauka a kitchen na kasan ta same shi tace ga abunda wata dake ɗakin oga ta ce.. Yana murmushi yace "Kimorah.. Is her name she's the only fiancee of oga, ita kaɗai ta ciri tuta a cikin dubban matan da suke crushing a kanshi from different part of the world" Kai kawai ta gyaɗa, banda faɗuwa babu abunda gabanta yake.. Zuciyarta ke tirsasata shiga hurumin da ba nata ba sede fa idan ta tuna da tarihin nan na mutanen annabi Musa waenda aka hana su kama kifi ranar Asabar se ranan Lahadi da kuma sauran ranakun se su je su ajiye abun kamun kifin ranar Juma'a se ranar Lahadi da safe se su zo su ɗauka wai su zasu yiwa Allah dabara.. A cikin mutanen sun kasu ne kashi uku, kashi ɗaya sune masu kamawar, kashi na biyu su ne waenda suka gani ana yi sun kuma san ba kyau se suka ce Babu ruwan mu, kashi na karshen kuma sune waenda suka gani suka kuma yi magana.. Da Allah ya tashi se ya hukunta masu yi ɗin da waenda suka gani suka ce babu ruwan mu, a musulunci babu maganan ba ruwanka idan kaga ɗan uwanka na abunda ba shine ba ka faɗa mishi karka yi fushi ka cigaba da faɗa mishi har Allah yasa ya gyara Allah shi kadai ya san sakamakonka a ranar gobe.. Karɓar tray ɗin tayi ta koma sama, a gefe ta ganshi sanye da wata jallabiya me kyau da daukar idanu navy blue kirar Kasar Qatar ba karamin kyau ya mishi ba barin ma da ya saka hulan nan na taɓani kaji hadisi.. Sede abunda ya girgizata har ya so sakata sake tray ɗin shine yadda yake gabatar da sallar cikin rashin natsuwa da kuma watsar da ka'idoji masu yawa na sallar.. Innalillahi wainna ilahi rajiun ta dinga maimaitawa ba karamin abun tashin hankali bane gareta ganin namiji har namiji ga kuɗi har kuɗi ga kyau sede babu addini, yana mutuwa yau wuta fa za shi... Hawaye ne ya fara kwaranya a fuskanta cike da tsoron Allah lallai in ka tsinci kanka a wani jarabawar ka gode Allah sbd naka me sauƙi ne.. Da alama la'asar, magrib da isha ya hada don har ta gaji da tsayuwa ta duƙa a ƙasa, bayan ya idar ya kira sunanta wadda ya sa gabanta wani irin dokawa. "Miss hidayat!" "Na'am sir" Yace "Na tashi ban san wani farin ciki ba har Seda na samu yaran nan nawa guda biyu na san wani abu wai shi farin ciki, they are all I've got a duniya, ɓata musu kaman ɓata min ne, ina tausayin ki hakan yasa kika kai har yanzu a gidana kiyi kokari kiyi blending da yaran nan within a short period of time in ba haka ba you will loose this job" Kanta kasa ta sa hannu ta share hawayen da ya zuba mata, kan tace "in shaa Allah zan yi iya kokarina kayi hakuri pls" Kuka na daga cikin abunda Sam baya so, ganin yadda hawayen wani ke bin wani yasa ya kau da kai yana lumshe idanunshi masu yanayi da me jin bacci, yace "tomorrow ki shirya Aisha they will be going together with Farrah na yi mata komai, interview zasu mata su bata uniform and rest" Bata san sadda murmushi ya subuce mata ba har dimples ɗinta na bayyana ga kuma hawaye a idanunta, sossai taji daaɗi ta dinga mishi godiya.. Sake dauke kai yayi yace. "U can go" Ta mike ta fito.. Ɗakin Farrah tayi ta samu tayi bacci, gyara mata kwanciya tayi ta kashe wutan ta fito ta shiga ɗakin Norah.. Zaune ta sameta tana kallo, a hankali ta zauna bakin bedside ɗinta tace "Norah..! Please ki bani mintuna biyu cikin lokacinki ina so zamu yi magana" Seda ta ɗan kalleta kan ta ɗauke kai kaman bazata bada hankalin nata ba se kuma ta tsayar da kallon tace "am all ears" Hidayat tace "Norah kin san wanene Allah?" "Almighty God?" Ta tambaya, tana wara idanunta.. Kai hidayat ta gyaɗa, Norah tace "the creature of everything I guess" Hidayat ta kaɗa kai tace "Subhanallah..! Norah karki ce haka ba'a jingina mahallici da irin waennan kalmomi za kiyi saɓo.." Norah cikin mamaki tace "To waye Allah?" "Allah shi ne makaɗaici.." Da turanci take mata maganan sbd ba fahimtar hausa take ba.. Tace "to a ina yake?" Norah ta sake jefa mata tambayar "Allah yana sama, kuma shi kaɗai ne ake Nufin sa da buƙata" Hidayat tayi maganan tana jin daaɗin yadda yarinyar ta fara nuna interest, abun ku da karatun Turai yaransu idan suka sa interest akan abu se sunga karshen shi.. "To wayene ya haife shi?" Hidayat ta girgiza kai tace "Astagfirullah..! Be haifa ba kuma ba'a haife shi ba, kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gareshi... Yana da aljanna da yake sa masu aiki na kwarai kuma yana da wuta wadda yake saka masu saɓa mishi.." Shiru yarinyar tayi cikin tunani, Tace "ya wutan yake? Irin wadda ake cooking?" Hidayat tace "uhm uhm.. That fire is more than that, Seda aka wanke wutar Jahannama sau dubu saba'in kan aka jefo mana ita duniya muke anfani da ita" Tsorata yarinyar tayi tace "and nima Ina saɓawa Allah?" Hidayat tace "kwarai kuwa Norah, babban saɓawa ubangiji shine Haɗa shi da waninsa, abunda ke saurin kai mutum wuta kuwa shine rashin yin sallah duk wadda baya sallah baya shiga aljanna..." Mikewa tayi ta dawo wurin hidayat kawai ta rungumeta ta fara kuka.. "Please I don't want to be burn Miss hidayat" Shafa kanta hidayat take yi tace "bazaki shiga wuta ba in shaa Allah, am here and I will guide you ok?" Kasa kwanciya ɗakinta Norah tayi saboda tsoro haka ta bi hidayat suka kwana a ɗakinta.. Ko da asuba da Hidayat ta tashe ta ta ki tashi se tace mata.. "wutar gayyah shine makomar me jinkirta sallah ko marar yinta" Da sauri ta miƙe "menene wutar gayyah miss hidayat?" Hidayat tace "yana daya daga cikin kofofin wuta guda bakwai.. Up kar mu makara" Toilet suka shiga alwalar ma Seda hidayat tayi hawaye wani irin ɓakar ɓacacciyar rayuwa suke yi? Da taimakonta Norah tayi alwala, suka zo sallar ma se bin hidayat kawai tayi.. Tare suka je kitchen da Hidayat Da Aisha, Norah tace "Miss hidayat I want to learn qur'an that u r reciting" Hidayat tace "I will teach u, as from today da yamma babu bacci zamu ringa yin karatu so that wutar Allah ba ze ci ki ba" Da gudu ta fice taje tana tada Farrah wai kar Allah ya kona ta.. Har hidayat ta gama musu girki kan suka dawo, ga mamakin hidayat Norah tayiwa Farrah wanka, ganin kallon da take musu ne yasa Norah tayi murmushi tace "Ina so muyi sauri muje mu dawo ki cigaba da faɗamin waye Allah" Hidayat daaɗi ne ya kamata, abincin ta shirya musu se ga babansu ya fito, a dining suka zauna lokacin shima Paul ya kawo mishi nashi abincin.. "Miss hidayat u said Allah na da Annabawa da manzonni right?" Kai ta gyaɗa mata tace "sossai Norah, Allah ya ambaci annabawa guda ashirin da biyar a Alqur'ani, nd lemme tell you there stories are superb..." Norah tace "Wow it's getting interesting, can't wait.." Tayi maganan tana tsalle fuskar ta fall murmushi. Cikin tsantsan mamaki Raed ke Kallonsu wow, ya jinjinawa Hidayat har Norah ta fara sakewa da ita haka? Sam hankalinshi be kai kan Hirar da suke ba, babban abun dama yaran su sake da ita ne kuma tunda sun fara ai shikenan.. Farrah ce dai har yanzu bata wani sake ba, zasu tafi Hidayat ta dauko baby hijab ta sawa Aisha ta ce mata ko an bata uniform she shouldn't remove the hijab duk wadda ya tambaye ta tace she is a Muslim, kai ta gyaɗa suka fice.. Ita dae hidayat na Kallonsu barin ma Norah da ta fara girma ta kusa balaga sede gashi a sake da mini skirt haka suka fice, a hankali in shaa Allah zata gyara duka waennan.. Cikin farin ciki ba kaman jiya ba ta hau ayyukan da ya kamata bayan ta gama musu abincin rana lokacin suna gab da dawowa ta ɗauko iPad ɗinta ta fara searching wa'azuzzukan turanci irin na su Ahmad deedat, Bin uthman, yasir Khalid, zakir naik da dae sauransu tana ta downloading saboda yaran.. Eib Grenelle international school.. Dab ake da tashi fitowansu daga jolly phonics class kenan suna dawowa normal class ɗinsu, ita da friends ɗinta ne suke tafiya, ɗaya daga cikin tace cikin harshen turanci.. "Farrah wannan new Comer ɗin I saw her talking to u did u knew each other?" Cikin manyancenta na yaran da suke ido a buɗe Tace "she's a daughter to our nanny and I hate her" Ɗaya daga gefe tace "why?" Farrah tace "my dad started to share my space with her, I'm jealous abt that" Tana magana har ranta fuskanta kaman zata yi kuka.. Wacce ta fara maganan tace "she's also cute and talented, and her name is sweet Aisha..!" Farrah tace "Ina so su bar gidanmu I don't really know what to do gashi Sis Norah started to get close to them" Na gefe ne tace mata ta kawo kunnenta taji, raɗa tayi mata wadda ya saka su kwashewa da dariya suka tafa, class tayi cikin jin daaɗi... Kingsworth international school. Norah ce zaune suna ta manyance akan samari da sauransu da ƴan class ɗinsu, fitsari ne ya matse ta ta kallo friends ɗinta guda biyu tace su zo su je su yi fitsari, mikewa suka yi suka nufi toilets ɗinsu suna cigaba da hiransu, suna zuwa Stephen tace bata ji so se ta tsaya daga bakin kofan da Norah ta shiga cikinshi yayinda faith ta shiga d'aya toilet ɗin... "Oh no!" Ta ambata daga ciki.. Stephen tace "what?" Ta sake cewa "oh please oh no..!" Stephen tace "Norah..! Open the Door just let me in.." Kuka Norah ta fashe dashi da karfi tana maimaita "oh my God. Oh pleaseee" Da gudu Stephen ta je office na mistress ɗinsu ta kirata se gata da wasu officials na makarantar yin duniya Norah ta ƙi buɗe kofan se kuka take cikin tashin hankali wadda basu san me ya sameta ba.. Se kuma ta fara cewa "mom..! Mom oh my God" Hankali a tashe mistrees ɗinsu ta koma office ta ɗauki waya ta fara kiran residence na Norah, Seda ya kusa katsewa Hidayat ta ɗauka itama hankalinta tashi yayi jin yadda suke exaggerating ɗin abun, da sauri ta nemi gyale ta yafa tare da saukowa lokacin kuma Miss Mary ma ta fito don itama ta ɗaga landline ɗin kuma Seda ta kira Raed kan ta fito.. Makarantar suka yi gabaɗayansu, Hidayat ce ta tsaya daga bakin kofan tace "Norah!" Cikin kuka tace "Miss hidayat..oh please help me! Please help me!!" Hidayat tace "the door is locked Norah, I can't get in you have to unlock sweetheart, open up and tell me what's wrong with you?" Kuka kawai take tana shesheka ta ma kasa magana, lallashinta hidayat take cikin dabara, da kyar ta samu ta yarda zata buɗe kofan amma se kowa ya tafi, girgiza kai hidayat tayi tana Tunanin rayuwar Turai ji yadda ta ɗagawa kowa hankali amma maybe ba wani abun arziki bane ya same ta, waje duk suka fita kan kofan ya buɗu.... #Vote #share #comment                    🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 16* *FREE BOOK* ***Kun jini shiru, am sorry ear infection ke damuna wlh kuma dae in har ka san ciwon kunne ka san bashi da sauƙi*** Da sauri hidayat ta shiga tana rike hannayenta tace "it's ok calm down and tell me menene?" A hankali tayi mata whispering "blood" Murmushi hidayat tayi tana girgiza kai, komai fa na yan gata daban ne ita da ta fara period banda ita da ubangiji babu wadda ya sani yanzu ji wannan kwarmaton, fitowa tayi ta cewa miss Mary please ta dubo musu sanitary napkins a dispenser ɗin jikin makarantar. Kan ta kawo ta koma wurin Norah tace "it's fine, kowacce mace nayi yanzu girma ne ya kama ki Norah, dole ki dage mu koyi abubuwa dayawa in ba haka ba kina cikin hatsari sbd a musulunci duk wacce ta fara al'ada ta balaga kenan, kuma duk balagagge kaman an buɗe masa sabon file ne babu abunda ze yi na motsi ko magana ba tare da an rubuta ba kuma dashi ake anfani a yi hisabi" Hawayen ta ta share tace "am now a woman?" Dariya hidaya tayi ta gyaɗa mata kai, cikin mintuna talatin ta gama nuna mata yadda zatayi using har ta saka ta fito tana ta aikin sussune kai for the first time da take jin kunyar mutane har haka a rayuwarta don su basa kunyar komai. Daidai nan babanta ya karaso, a ruɗe yake sbd yadda miss Mary ta kirashi sanye yake da kananun kaya as usual kaman yadda kuka san ɗan ball da kaunar shorts, ko face cap babu a kanshi haka ma be saka face mask ba fuskanshi banda walki babu abunda take sbd reflection na rana ga shi kaman yana anfani da skin care don kyaun fata, yana da skin color me matukar tsada da fusgan hankali. Da sauri ya karaso ba tare da ya lura da hannun hidayat dake cikin nata ba kai ko ma ya lura su a wurin su ba komai bane ya sanya hannunshi ya kama nasu duka biyu yana kallon Norah from head to toes.. "Baby..! Are you alright? Me ya same ki?" Ya jefa mata tambayar da ta saka ta dukar da kai kawai, ya sake matse hannayensu yace "talk to me, kina da wata matsala ne da zan kasa kau dashi? Are you been bullied? Baki son environment ɗin ne? Should we change SC...." "Daaad" ta kira sunanshi cikin kunya, yace "yes darling menene?" Kasa magana tayi se ta kalli hidayat dake tsaye a wurin kaman statue, shima shanyayyun idanunshi ya juya ya watsa mata.. Tun daga sadda Tattausan fatar hannunshi ta sauka bisa nata ta daskare a wurin, wuta ne ya ɗauke mata gabaɗaya ko maganan da suke a wurin ba ji take ba, tsammm haka take jin wani abu na yawo a jikinta wadda bata taɓa ji ba, yaaa salam! Ta faɗi a zuciyarta a sadda taji saukar kaifaffun idanunshi bisa kanta, ji tayi kaman ɗaure ta akai... Norah ce ta zame hannunta wadda yayi sanadiyar saukar nata ya zame daga nashi hannun, tana kiran sunanta "Miss hidayat" Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tana  dawowa daidai ta amsa a daburce, be bi ta kanta ba don wani lokacin gani yake kaman ba daidai take ba abu kaɗan ke gigitata.. Daga wurin miss Mary ya ji abunda ke faruwa, se ya juya yana kallon Norah da kaman ta shige ƙasa daga ita har Hidayat ɗin, murmushi yayi yana rungume ta yace "my Lil girl is now a grown up woman" Itama murmushin tayi, suka dunguma sukayi gida Norah a motar babanta yayinda hidayat da miss Mary suka tafi a motar da suka zo na gida, sun samu su Aisha sun dawo har ma sun ci abinci, Seda hidayat ta fara taimakawa Farrah da wanka kan ta zo tayiwa Aisha, Norah ta shigo itama tayi wankanta ta zauna wurin hidayat tana sauraran darasussuka akan period wadda ita bata taɓa sani ba.. Hidayat sossai ta tsoratata da hulda da maza, ta nuna mata hadarinshi ba ga lafiyar ta ba har ma ga addininta, kuma sossai Norah ke ɗauka, kiran landline ne ya katse musu Hirar tasu Norah taje ta ɗauka dad ne yace ta kawo mishi Junior.. Ɗaukan shi tayi ta fito ta bar hidayat ɗin da Tunanin sabuwar yanayin da take tsintar kanta a ciki wadda bata taɓa ji ba.. A tsararriyar bedroom ɗinshi ta same su, Aisha na yin homework yayinda Farrah ke yin game a iPad kunnenta headphone ne tana jin wakar da game ɗin ke yi, haushin kasancewar su tare da Aishan take, karbar junior yayi yana mishi wasa yaron na bangala dariya.. Kwarai yake yabawa da tsabtar maman yaran sbd yadda a duk sadda ze ɗauki Junior kamshi na musamman ne ke tashi a jikinshi goyon ta Sam ba kazanta, a hankali ya tuna ranar da aka samu yaron da abunda ya faru, shi dae kwana biyu da suka yi da Hidayat kai tsaye ze iya cewa bata cikin mutane masu fitina ko rashin kunya, to meyasa babansu ze zaɓi wulakantata ta wannan hanya kawai don bata da kowa? Da fa shima macece hakan za'a yi mishi, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Wayanshi da ya ɗauki ringing ganin sunan Godfather yasa ya ɗauka facetime ne, hakan yasa wani kasurgumin pastor ya bayyana sanye da kayansu na father, hannunshi rike da Bible kaman yadda bayanshi ke nuna a church yake.. "Hey my son!" Raed na murmushi yace "father good af, trust you are doing great?" Da gudu Norah da Farrah suka zo fuskan wayar tashi suna leke ganin da gaske father ne yasa suka fara mishi surutu "hello grandpa ka ce zaka zo har yau baka zo ba, we are really mad at you" Murmushi yake yana cewa "am so sorry my queen nd my princess, by God grace I will be with you guys in a jiffy, ayyuka ne suka min yawa a nan muna ta bada word of God, mutane na karbar almasihu" Norah tace "u r always talking abt this almasihu but Miss hidayat said he is also a Prophet sent by Almighty Allah, bcs Allah doesn't have a wife nor a son" A take fuskar mutumin ta sauya yace "who is miss hidayat?" Farrah tace "our new nanny from Nigeria grandpa I don't like her" Raed na kallon Aisha yace "hey Farrah be nice ok?" Mikewa tayi ta fice wai tayi zuciya, girgiza kai yayi yana jin amsan da father yake baiwa Norah a lallai lallai se ta amince da faɗar cewa Almasihu is a son of God, ita kuma hankalinta ya fi kama na miss hidayat, daga karshe kyale ta yayi suka maida call ɗin phone call da Raed.. Kai tsaye ya nuna be son sabuwar nanny ɗinsu ze turo wata daga Amsterdam garin da yake a yanzu yana yaɗa addinin kiristanci ta cigaba da kula dasu, Raed be ce komai ba har suka gama wayan ya kashe.. Da Junior ya cigaba da wasa Aisha da Norah na mishi hira jefi jefi kaman daga sama ya jiyo ihun Farrah, da sauri ya miƙe ya nufi waje cikin Tunanin abunda ya same ta, a ɗakin hidayat ya ji kukanta shi da Norah da Aisha ne suka shiga ɗakin.. Tsaye suka ganta tana kuka sossai riƙe da kumatunta yayinda hidayat ke tsaye idanunta duk a waje zuciyarta kuwa banda skipping babu abunda yake.. "Farrah what is it? Me ya same ki?" Raed ya watsa mata tambayar yana kokarin cire hannunta da ta saka a kumatunta cikin kuka tace "she hit me" Tana maganan tana nuna hidayat. A razane hidayat take kallon yar yarinyar kaman yadda shima yake kallonta cikin ɓacin ran da be san ya bijiro mishi ba, cikin wata kalar murya yace "how dare you hit my dota?" A ruɗe tace "Wallahi wallahi ban taɓa ta ba, taya zan fara dukanta? She came here tace tana son custard na ce mata ina zuwa bara nayi sallar asr da lokacin ke shirin fita se in je in Haɗa mata se kawai gani nayi ta saki ihu tana rike kumatunta but ban taɓa ta..." "Enough please..!" Ya faɗa har lokacin da ɓacin rai sossai a fuskanshi. Hannun Farrah ya sauke daga fuskanta wurin kuwa yayi ja, Junior dake bacci ya ajiye bisa kan gadonta ya ɗauki Farrah zasu fita Hidayat ta sake kokarin kare kanta sbd bata taɓa jin zafin a jingina ta da abunda bata yi ba irin yau, sossai abun ya mata zafi wadda ta rasa dalili haka kawai take jin kaman zata yi hauka idan har ya fita da wannan fushin da kuma Tunanin ta taɓa mishi yarinya.. "Sir..! Please believe me wlh ban taɓa ta ba.." A tsawace yace "then why her chin shows that? Kalli kumatunta.. I can take anything but not hitting my child ni karan kaina ban taɓa saka musu hannu ba so ba zan yarda common nanny like you ta dakesu ba, If you can't do the job then you should please silently leave tun baki Harzukani ba" Yana kai nan ya juya ya fice, kuka hidayat ta fashe dashi tana jin ba daaɗi har kasan ranta, idan kuwa bata faranta mishi sbd taimakon da ya mata ba ba zata ɓata ranshi ba, Norah da Aisha ne suka zo wurinta suna share mata hawaye. Norah tace "I belive you miss hidayat you can't hit Farrah she's probably lying bcs she doesn't like you" Zama tayi kawai tana rufe fuskanta da tafukan hannunta tana cigaba da kuka, this is a minor thing a rayuwarta sede ya fi kona mata zuciya fiye da abubuwan Yusuf menene hakan? Aisha ficewa tayi ta je ta same shi yana ta rarrashin Farrah, a hankali tace "Daddy mama will never hit Farrah bcs ko mu bata taɓa dukanmu ba, she always says hitting someone is never a solution and will not ever be, gashi yanzu tana ta kuka har Ya Norah ma started to" Se yaji wani iri, dukda be san Hidayat ba sede Aisha bazata mishi karya ba, idan har bata taɓa dukansu su yaranta ba taya zata fara dukan Farrah, ya san irin yadda ta tashi sbd ya fuskanci abu makamacin hakan shiyasa shima be taɓa dukan yaranshi ba, idan har ze daga hannu da nufin dukan wani se Tunanin mugun mahaifin shi ya darsu a ranshi hakan yasa kwata kwata baya so yaji ko maganan duka ne.. Farrah ya kalla yace "Baby u knew na faɗa muku lying is a very bad habit right?" Kai ta gyaɗa, yace "then tell Me the truth did miss hidayat Hurt you?" Shiru tayi yace "I won't be mad ok? Tell me.." Se tace "bata dukeni ba, I just don't like her shine friends ɗina gave me idea yadda suka gani a wani film da yarinyar bata son stepmom ɗinta da tayi hakan her dad divorce the stepmom shine nima nayi" He's so shock da abun, taya yarinya kaman Farrah zata yi acting so fine kaman da gaske hidayat ɗin ta Mareta? Se yaji be ji daaɗi ba sede sbd yarinyar tayi kuka kuma baya so ya sake sakata wani kukan se kawai yace mata "don't repeat that again is a bad habit kin ji?" Kai ta gyaɗa ya juya ya kalli Aisha yace "tell miss hidayat am sorry" Daga haka ya miƙe ya shige toilet ɗinshi.. Fita Aisha tayi ta koma wurin hidayat da ta samu tana sallah, Norah na zaune daga gefen gadonta, alwala Aisha ma taje tayi ta dawo suka yi sallar tare, bayan sun sallame Aisha tace "Mama Farrah is lying dad ya gano hakan and he said I should tell you sorry" Dukda haka zancen be sakata farin ciki ba sbd sanin ranshi dae ya riga ya ɓaci sbd ita, aika Norah tayi ta kirawo Farrah se ta dawo tace mata tana bacci.. Qur'ani ta sa suka buɗe a iPad na Norah don babu a gidan gabaɗaya suka fara karatu seda ta karawa Aisha kan ta fara koyawa Norah daga Fatiha sbd sallah.. Ba karamin farin ciki Norah ke yi da sabbin abubuwan da take koyo ba, kan kwana bakwai ya zagayo da zata gama al'adar ta hidayat ta koya mata wankan tsarki ta kuma tabbatar da ta iya Fatiha fluently da qulhuwa, falaki da nasi. Ita kanta hidayat na jin daaɗin yadda Norahn ke koyo sbd abunda ya kamata ta koya yanzu kenan, dukda a gefe guda tana fuskantar wasu halayya irin na turawa Farrah ke dashi sede bata taɓa maida hankali ba, kwanakin da ya biyo baya tun daga ranar da Farrah ta Haɗata da Mahaifinsu bata sake sanya shi a idanu ba. Sede ya kan aiko Norah ta dauka mishi junior da yanzu suka fara sabo sossai da yaron, haka Aisha tana karatun ta hankali kwance Dukda abunda take ɗan fuskanta na kyara daga wurin Farrah.. Yau Asabar wankin da Hidayat ɗin tayi a washing machine ta sauka kasa don son shanyawa, bata taɓa ma zuwa ta ɓangaren igiyoyin nasu ba se yau, bayan banda shuke shuke da katuwar Mikano ɗinsu se ƴar lilon dake kada kanshi da kanshi cikin kyakyawar field dake shimfiɗe da grass carpet se wasu kujeru haka na shan iska babu abunda yake wurin. A natse take shanyar har Farrah ta zo ta wuce ta gefenta bata tanka ta ba, chan bayan inverter ɗin ta tafi se gata da wani katoton police dog brown color me baƙin baki banda dilalar da miyau babu Abunda bakinshi yake. Wani irin faɗi gaban Hidayat yayi gashi su kaɗai, yadda Farrah bata ƙaunartan nan tana da tabbacin in ta gane tana tsoron kare zata sakar mata shi wannan karen kuwa yadda yaken nan se ya cinye ta tsab.. Ganin da gaske nufota suke yasa ta fara ambaton Allah, jikinta na daukar rewa suna isowa wurin kuwa karen ya fara zuwa wurinta yana shunshuna ta, duk yadda take kokari wurin ganin bata firgice ba hakan be yiwu ba, wani ƙara ta saki tana kiran Sunan Allah a take karen yayi kanta bata tsaya ba ta saka gudu wadda ya sa Farrah tuntsirewa da dariya.. A gigice hidayat ke zagaye wurin karen na bin ta, kokarin barin wurin take se ta harɗe ta nufi faɗuwa wadda yayi daidai da isowar Raed wurin sbd tun ihun farko ya ji kuma ya ji haushin kare ya kuma san Bingo ba sanin hidayat yayi ba idan kuwa hakane cizonta ze yi.. Cikin hanzari ya sanya hannayenshi biyu ya riƙe mata kafadu don hanata faɗuwa sede dayake a gigice take bayanta take kokarin Juyawa taga ko karen ya iso ta aiko ganin gashi ga ita yasa ta sake sakin ihu tana runtse idanu hawaye wani na bin wani duk ta ruɗe shima se ta ruɗa shi, da sauri ya janye ta ya maidata bayanshi ta kama Rigan shi ta riƙe kamkam kam.. "Bingo!" Ya kira sunan karen ganin shima kokarin bin hidayat ɗin yake, sarkar wuyan shi ya kama yace "is ok, she's not a bad person oya back to your cage" Juyawa karen yayi ya fara gudu yana karkada bindi, hakan ya saka Raed kokarin juyowa sede Hidayat ta ki sake Rigan shi har lokacin idanunta a runtse hawaye wani na Bin wani, daga yadda suke tsaye yana jin bugun zuciyarta.. Idanunshi ya kai kan yadda ta riƙe mishi riga kamkam hakan ya saka shi sakin murmushi.. "Ya tafi fa!" Yayi whispering yana sake kallon ɗan karamin farin hannunta dake rike da riganshi, da sauri ta saki tana matsawa baya.. Juyowa yayi ya kalli fuskanta yadda yayi kaca kaca da hawaye ɗan karamin bakinta red se motsi yake alamar Adu'a take, hakan ya sa be san sadda wani murmushin me yanayi da dariya ya sake subuce mishi ba a fili yace "duk wannan tsoro ne?" Da sauri ta juya ta nufi ficewa daga wurin don abubuwa dayawa ne suka haɗu mata, ga tsoro dake barazanar sumar da ita ga kusancinsu dake haifar mata da wani yanayi marar misaltuwa ga kunyan yadda yaga take kuka sbd kare ga kuma wani dariyar da yayi da bata taɓa ji ko gani daga gareshi ba sbd shi mutum ne me ƙarancin fara'a.. Shi kuwa Juyawa yayi har lokacin yana murmushi ganin wai kuma kunya taji, faɗa ya fara yiwa Farrah don ya san ita ta fito dashi se ta kama kuka wai yana fififita nanny sama da ita daga karshe rarrashi ya koma sbd yana son yaranshi fiye da misali.. A daren ranar tana kitchen tana tattare abubuwan da tayi anfani dasu na abincin dare ya shigo, ƙasa ta soke kanta tare da cewa "Barka da shigowa sir, akwai abunda kake bukata ne?" Girgiza kai yayi ba tare da ya kalleta ba yace "no cigaba da aikinki" Fridge yaje ya ɗauki ruwa sbd na parlor ya kare ya kuma kira Paul akan a kawo, har ya kai kofa yace "ehen when u r done meet me at my room" Kai ta gyaɗa, har ya fice bayan ta gama ta wanke hannayenta tare da nufan ɗakin shi da take jin hayaniyar junior da su Norah, a kan couch ta same shi yana duba system da ya ajiye akan center table yaran kuwa suna kan carpet suna wasa da Junior yayinda Farrah ke kallon cartoon a TV ɗin ɗakin... A ƙasa ta zauna ɗan nesa dashi kanta kasa sbd daga shi se shorts jikinshi ba riga kaman yadda ta ga yake kaunar zama haka, banda murdaddun muscles ɗinshi da shafafen cikinshi har kwantacciyar gashin dake jikinshi babu abunda take iya kallo.. Wasu takarda ya Mika hannu ya ɗauka tare da mika mata, a ladabce ta karɓa yace "it's for ur studies, kin samu gurbin karatu a Paris science et lettres" Wani irin sanyin daaɗin da bata taɓa ji bane ya rufe ta, cikin tsananin farin ciki ta fara mishi godiya, murmushi kawai yayi ta juya tana nunawa su Norah da Aisha suma murna suka taya ta.. Haka Hidayat ta kwana yiwa wannan bayan Allahn Adu'a, wasa wasa abu kam ya zama gaske se ga hidayat a one of the best universities na duniya, karatunta be hana ta kula dasu Farrah yadda ya dace ba.. Tun kan asuba zata fara Haɗa musu breakfast ta saka musu na makaranta ta zo tayi wanka ta gabatar da sallar asuba ta je tayiwa Farrah wanka ta zo tayiwa Aisha da Junior duk su shirya, a sadda zasu fita tafiya makaranta kuwa a sannan itama zata fita tafiya school, bus take hawa kuma Alhamdulillah ba karamin fahimtar karatunta take ba.. Da yamma take yiwa su Norah karatun Qur'ani da ƴan tarihin annabawa, wadda Farrah bata cika maida hankali ba amma Norah na matukar so, Junior kuwa har ya fara buɗe baki a ƴan watannin nan da suka yi yanzu watanshi takwas da sati biyu, da Daddy ya fara buɗe baki wadda yake gani kaman shine Mahaifinshi.. A ɓangaren career ɗin Raed banda cigaba babu abunda yake gani, don sede idan baya cikin wasa za'a kira musu faɗuwa, ji dashi ake sossai a PSG har wasu clubs ɗin na fafutukar sayanshi... Kwatsam wani ranar Laraba Raed da kanshi ya fita dasu da yamma sbd rikicin da Junior ke yi yasa yace duka su zo su je su sha iska kadan, Norah ce ta saka Hidayat dole suka fito.. Sanye take da red palazzo trouser se white shiffon shirt me dogon hannun ta yafa red mayafi se ta saka white Shoe, duk cikin irin sayayyar da in har ya fita da yaran tare suke fita se ya ce itama ta ɗauka.. Yaran duka suna zaune cikin wata kyakyawar runfa bayan sun yi ordering ice cream flavor ɗin da kowa yake so, bayan an kawo se Farrah ta ɓarar wa Aisha da nata wadda ya so sakasu faɗa shine Hidayat ta bata hakuri ta mike ta fice don samo mata wani.. Ta fito kenan riƙe da ice cream ɗin shi kuma ze shiga wani karo suka ci ba tare da duk sun ankara da juna ba.. "Subhanallahi..!" Shine abunda ya fito daga bakinta wadda ya saka shi saurin kallonta don be tsammaci jin sunan Allahn a irin wurin ba.. Karab idanunsu ya faɗa cikin na juna. #like #share #comment                   🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 17* *FREE BOOK* "Ya Hamza..!" Ta faɗa tana wara dukkan idanunta da ta saka musu kwalli waje, duk da yadda ya kara girma da jiki ya tara kasumba gwanin burgewa hakan be hanata shaida shi ba a kallo ɗaya sbd shine mutum na farko da ya fara nuna mata ƙauna a duniya bayan Abba kuma kullum yana ranta.. Shi kuwa kokarin ce mata sorry yake amma ganin ta kira sunanshi yasa ya ɗan dakata tare da sanya mata idanu na seconds se kuma ya waro su gabaɗaya yace "Hidayat!" Dariya suka saki a tare yace "what a coincidence! Hidayat me kike yi a Paris? Taya kika zo?" Tana murmushi tace "labari ne mai tsawo" Yace "then mu je mu zauna se in ji da kyau, aurenki fa?" Kanta ta ɗan dukar tace "ya mutu" Wani sihirtaccen murmushi ya saki tare da Juyawa ta bi bayanshi Sam ta mance ma da Aisha jiran ta take da ice cream ɗin da ya ɓare again, wurin wasu kujeru guda biyu suka je suka zauna yana tsokanarta akan ta ƙara girma tayi kyau tana ta dariya.. Daga inda yake zaune sanye da designers Riga da wando na kamfanin Versace idanunshi sanye da designer shade na Swarovski ba karamin kyau yayi ba barin ma sabon diamond ear ring da ya sauya dake ta kyalli, tun da ta mike ya tsinci idanunshi a kanta har ta shige be dauke ba, daidai fitowanta da karon da suka yi duk a kan idanunshi.. Ganin suna dariya da magana alamu sun san juna yasa ya ɗauke kai yana jan tsiririn tsaki, agogonshi ya kalla se ya ɗauke kai again, Aisha dake zaune ya sake kallo ya ɗaga kai ya kalli sun nemi wuri sun zauna suna ci gaba da dariya, wani irin ɓacin rai ne ya bijiro mishi da be san na menene ba, miƙewa yayi kaman ze nufi inda suke se ya fasa ya shiga shagon ya sayo wani ice cream ɗin ya zo ya ba Aisha duk yana kokarin hana idanunshi kallon ɓarayin da suke.. Ita kuwa Shap ta ma mance dasu, a hankali take ba Hamza labarin abubuwan da suka faru tun tana dauriya har ta fara kuka tana zuwa wurin rasuwar Abba ta dakata tana hawaye sossai, handkerchief hamza ya ciro ya mika mata ta saka hannu zata karɓa se suka Haɗa idanu.. Idanunshi sun sauya sossai wadda kallon cikinsu ya haddasa mata wani mummunar faɗuwar gaba, a table ɗin ya zo ya zube hannayenshi ya ɗan duƙa kaɗan yana kallonta ba tare da ya kalli hamza ba yace "can u please get up mu tafi? U can't keep me waiting for u miss hidayat don't forget am ur boss" Mikewa tayi da sauri tace "Sorry sir..!" Tsaki ya ja ba tare da ya kalli inda Hamza yake ba ya juya ya wuce. Hamza yace "who is he?" A sanyaye tace "my boss as he says, bari na tafi we continue in muka haɗu gobe" Yace "ur digits pls" Ta karɓi phone nashi ta saka mishi tana kallon motan Raed da har ya tayar, da sauri ta karasa ta buɗe baya ta shiga bata gama rufe motar ba ya fisga da gudu ya bar wurin.. Har suka isa gida yana cin rai ko yaran babu wadda ya cewa kala, Kimorah da ya samu ce ta ɗan rage mishi damuwar da yake shirin bijiro mishi wadda ya mance ya kalar damuwar take tun da ya sa kafa ya bar gidan uban shi.. Washegari bayan ta gama duk abunda ya zama aikinta ta basu breakfast suna yi ita kuma ta shiga ta shirya, ta fito sanye da straight skirt brown da kuma blouse riga brown nd white se ta ɗaura kimono shara shara a kai ta saka gyale light Brown idanunta sanye da kwallin dake kara mata wani sirrin kyau yake kara musu haske da daukar idanu se lip balm da ta saka a baki.. Tana fitowa wayanta na kira, ɗagawa tayi tana nufan dining ɗin tace "Good morning ya hamza" Yace "morning heedayaah" Yadda ya kira sunan se da ya sakata murmushi yace "kin fito ne?" Tace "nop yanzu dae nake shirin fita" Yace "ai ko ni kam zumudi ya hanani zama in yi abunda ya kamata yanzu haka ina cikin school ɗin ku ko zaki bani address dinku na zo na dauke ki?" Girgiza kai tayi da sauri kaman yana gabanta tace "noo karka damu zan fito yanzu kawai ka bani mintuna" Yace "as u says my queen" Dariya tayi tana sauke wayan, Satan kallon shi tayi se suka Haɗa idanu.. A hankali tace "good morning sir" Be amsa ba, se yaran ya kalla yace "Horry up girls I wanna drop u guys today" Da sauri suka miƙe suna tattare jakukunansu da lunch box ɗinsu suka fice suna ce mata "bye Miss hidayat" Aisha ma tace "bye mama" Daga haka suka fice. Mikewa yayi ya kwashi phones ɗinshi, idanunta ta ɗan ɗago daidai zuwa hannunshi na hagu da ya ɗan tara farce fari sol, ganganta ya zo har tana jin kamshinshi na hawa kanta da sauri ta fara wasa da fingers ɗinta kaman zata karye su.. Idanunshi ya ɗan zuba mata kaman ze yi magana se kuma ya fasa, stairs ya nufa har ya ɗaura hannu a kai yace cikin harshen turanci "rayuwa ba baƙon abu bane a gareki, ya riga ya koya miki darasin da zaki hankalta.. Idan kin dauka ruwanki idan kuma kika sake wani kuskuren a karo na biyu shima matsalar ki ce, I just want to remind you cewa aiki kike min, and I'm using ur salary to sponsor you ba zan lamunci wasa a aiki ba bcs akwai dayawa masu nema na ɗauka na baki, idan tara samari shine abunda zaki fara then I have no any other option than to dismiss you.. Be careful miss hidayat" Tun da ya fara magana gabanta ke faɗuwa, zuciyarta har wani rawa rawa yake me yake nufi? Tara samari! Da sauri ta ɗago zata mishi bayani waye hamza se ta ga wayam baya wurin, ajiyar zuciya ta sauke ta fice ba tare da ta bi ta kan Breakfast ba dama junior wurin miss Mary take barin shi. Har ta isa makaranta juya maganganun na Raed take tana so ta fahimci inda ya dosa sede ta kasa, da suka haɗu da hamza kuwa ta ma mance da wani Raed ta cigaba da bashi labari.. Ya tausaya mata kwarai, tace "kai fa? Kayi aure?" Yace "uhmm last 3 months mahaifiyata ta sa aka ɗaura min aure da wata cousin ɗina they thought asiri kika yi min saboda ban san ina son ki dayawa ba seda aka ɗaura miki aure da Yusuf, karamin zaucewa nayi wadda sanadiyar shi har na bar aikin soja, yanzu ina maintaining company ɗin dad ɗina ne yanzu ma wani business deal ne ya kawo ni Paris, ashe Allah ya san abunda ya tanadar min anan" Murmushi ta saki kawai tace "Allah ya baku zaman lafiya" Yace "Ameen, but don't bother hakan ba shine ze hanani aurenki ba, I promised to marry you in shaa Allah I will stick to my promise bcs I still love you" Lumshe idanunta tayi tare da ware su bisa gefen hanya tana kallon ɗaiɗaikun mutanen da suke wucewa ta jikin car ɗin.. "I'm sorry to say yanzu babu aure kusa a tsarin rayuwata, ba zan yi aure ba har se na gama karatu na ɗauki fansar ran Usman I cannot just forget abt that, kuma bana son wani cikas da ze dakatar dani daga wannan kudiri kayi hakuri ya hamza!" Kallonta kawai yake she's now a grown up woman ba kaman sadda ya Santa ba, tana magana da hankali da kuma natsuwa, Sam maganan ta be dame shi ba yace "na sani and I will help u with all my strength idan bukatar hakan ta taso har ki cimma Burin ki, I just want ur love nd care Hidayat..!" Ya kira sunan a hankali, ajiyar zuciya ta sauke tace "zan yi shawara akan hakan na gode" Kai ya gyaɗa yace "I would like to see Junior and Aisha gashi flight ɗin yamma zan bi na koma Nigeria" Ko karen hauka ne ya cije ta bazata kaishi gidan Raed ba, a hankali tace "eyyaa next time in shaa Allah" Murmushi kawai yayi sun ɗan taɓa hira suka yi sallama, kuɗi ya bata ta ƙi karɓa se da yayi da gaske kan ta amsa ta Mishi godiya ta shige school.. Bayan ta dawo ta hau ayyukan ta kan yaran su dawo, tana cikin kitchen take ta jin ringing na landline ɗinsu wanke hannayenta tayi ta fito ta zo ta ɗauka ta saka a kunne se tace "Assalamu Alaikum warahmatullah" Shiru aka ɗan yi kan taji muryar wata dattijuwa tace "Wa'alaikumussalam warahmatullah yau sallama ake min daga gidan Raed?" Muryar wata dattijuwa ya ratsa kunnuwanta, a natse tace "Ina yini hajiya!" Matar na hawaye har muryarta ya bayyana hakan tace "lafiya ƙalau Alhamdulillah ƴan nan wacece ke?" Hidaya na mamakin halin da matar ta shiga kawai daga jin hausa da kuma sallama a gidan na Raed tace "Sunana hidayat, ni ce sabuwar nanny ɗin su Norah" Kuka kawai matar ta saki sossai tana cewa "Alhamdulillah adu'ata da na jima ina yi ne Allah ya amsa mini, ke ɗin kaman haske ce don Allah Don Annabi ki taimaki rayuwar waennan bayin na Allah, rayuwar su ya gama tabarbarewa bani da yadda zan yi ne nake Kallonsu a haka... Hidayat ki min alkawari zaki cecesu ki fitar dasu daga cikin baƙin duhun da suke ciki" Hidayat tace "kiyi hakuri hajiya ki dena kukan nan, in Shaa Allah zan yi miki duk abunda kike bukata in har be fita a musulunci ba" Godiya tayi ta mata kaman zata fito ta wayan ta duƙa mata, hakan ya taɓa zuciyar hidayat sossai a hankali matar tace "sunana Hafsah amma ƴaƴana da jikokina suna kirana Daadida" Kwarai ta taɓa jin sunan na Daadida eh ta taɓa ji wurin Raed, itace kullum yake yiwa masifa cikin waya.. "Nice na haifi mahaifin Raed" Shiru hidayat tayi tana sauraran ta, ashe suna da dangi da ƴan uwa kuma musulmai shine suke rayuwa cikin ɓata? "Rayuwar Raed abun a tausayawa ne kwarai da gaske, sbd be taso cikin farin ciki kaman kowanni yaro ba, ya rasa mahaifiyarshi tun yana shekara uku banda azaba da baƙar rayuwa be san komai ba a wurin yadikkonanshi da Mahaifinshi karan kanshi... Labarin Raed labari ne me tsawo da ba ze yiwu a waya ba sede abunda na sani baƙar Gaaba ce me tsanani tsakanin shi da Mahaifinshi hakanan be san komai ba game da addini, gashi yayi auren wuri da yara suma mahaifiyarsu ba musulma bace ƴar marikinshi ne ya aura kuma ta mutu ta bar mishi yaran babu addini.." Tayi shiru tana fyace majina tace "Kiyi mini alkawari za kiyi wannan aikin jihadin? Wlh Allah ne kaɗai ya san sakamakonki in kika taimaki rayuwar waennan Bayin Allahn" Ajiyar zuciya me karfi hidayat ta sauke, no wonder rayuwarsu yake a haka, ashe akwai binnannen abu a ƙasa cikin sanyin murya tace "in shaa Allahu zan yi iya kokarina wurin ganin na taimakesu saboda Allah" Godiya sossai Daadida ta mata suka yi sallama akan zata ke kiranta irin wannan lokacin a landline ɗin gidan.. Kitchen ta koma ta cigaba da aiki cike da tunanuka iri iri, tana cikin shirya dining yaran suka shigo Norah da Aisha suka mata sannu yayinda Farrah ta shige ɗakinta ba tare da ta kula ta ba, Norah da yanzu ta kan ɗan taimaka mata da wani abu ne ta shiga ta taya Farrah wanka yayinda Aisha tayi da kanta suka zo suka fara cin abinci.. Ita dae hidayat Tunanin ta yadda zata fara shiga rayuwar Raed har ta sauya shi take, mutumin da idan tana ganganshi jininta kaman tsinkewa yake, idan taji muryarshi gabanta har faɗuwa yake idan kuwa ya tsura mata waennan idanun nashi masu yanayi da na snake se taji kaman fitsari ze kufce mata shine tayi alkawarin sauyawa! Ta ina zata fara kuma ta yaya? Bayan sun gama cin abincin ta tattare ta saka Aisha da Norah Alwala suka zo suka yi sallah, bacci suka yi se bayan la'asar suka fara lessons nasu na Qur'ani da ta saba musu. Bayan sun gama suna zaune a parlorn na sama ya shigo babu sallama, a gajiya yake tilis har layi yake sbd zazzafar wasar da suka yi yau ya haɗu kuma da ƴar damuwar da yake dankare chan kasan ranshi wadda ya kasa cisgewa, da ita suka fara Haɗa idanu Norah tace "laaaaa dad u didn't say salam" Ɗan kallon yarinyar yayi cikin rashin fahimta, tana kallon hidayat tace "Miss hidayat ina kin ce dole ne musulmi yayiwa ɗan uwanshi musulmi sallama idan ze shiga wuri kuma na ciki ma dole ne su amsa?" Hidayat ba tare da ta kalleshi ba tace "kwarai kuwa Norah kuma akwai lada a cikin sallama" Aisha tace "eh ai kuma idan baka da lada dayawa bazaka shiga aljanna ba" Norah ta gyaɗa kai, duk be kallesu ba se ita ne ya zubewa gajiyayyun idanunshi yace "idan mutum ya mance fa?" Husky musculine Muryarshi ya dake ta, a hankali ta ɗaura idanunta a kanshi cikin kankan da murya tace "se ya koma da baya yayo in an amsa se ya shigo" Juyawa yayi ya fice se ya dawo yace "Assalamu Alaikum" Duka suka amsa Mishi suna murmurshi.. Norah da Aisha suka ce "welcome daad" Kai ya gyaɗa kawai ya shige room ɗinshi, ajiyar zuciya me karfi hidayat ta sauke bata taɓa zaton ze koma ya sake sallama ba, idan ko hakane zata yi anfani da yaran sossai wurin ganin ta sauya shi.. Tana cikin Tunaninta Farrah da ta bishi ɗakin ta fito da gudu tace "Daadddy is throwing up" Dukkansu mikewa suka yi Norah tace "is he sick?" Hidayat da tunda ta kalleshi take Tunanin wani abun na damunshi ta wuce ɗakin ba tare da Tunanin komai ba. Duƙe yake gaban washing hand base se amai yake kwararawa a wahalace, a gefen shi ta tsaya tace "sannu!" Kai ya gyaɗa mata har ya gama, ruwa ta saka mishi a hannu ya wanke fuskanshi da bakinshi yace "I wanna take shower" Fita tayi gabaɗaya a ɗakin taje wurin miss Mary ta sakata kiran family doctor ɗinsu don daga gani dauriya kawai yake, ko da ta dawo a tsaye ta samu Su Norah duk suna cikin damuwa, Norah ta tura ta duba ko ya gama shiryawa ta dawo tace mata ya kwanta ya rufe da blanket yana ta rawar ɗari.. Cikin mintuna likitan ya zo ya hau dubashi nan ya hada allura ya mishi ya ba Paul takarda ya sayo magani, bayan ya fito ya cewa hidayat a tabbatar ya sha tea kan ya hadiye maganin don da yunwa a tare dashi.. Bayan Paul ya dawo ya bata maganin, kitchen ta shiga gabanta na faɗuwa ta Haɗa tea ɗin ta ɗauko ta nufi ɗakin, da sallama ta tura kofan ɗakin... #Vote #share #comment                       🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 18* *FREE BOOK* **Assalamu Alaikum warahmatullah gaisuwa irin ta addinin musulunci, fatan duk kuna cikin koshin lafiya? Kuyi haƙurin jina shiru jiyan kaman yadda Zaku sake jina shiru daga wannan se ranar Friday in Allah ya kai rai.... Bautar ƙasa nake gamawa jibi Thursday kenan, tunda Monday ya shigo bamu da zama yini muke wurin abubuwan gamawan da ciwon kai, bacci da gajiya nake dawowa bani da natsuwar typing Sam, fatan Zaku min uzurin hakan. Na gode*** Da sallama ta tura kofan ta shiga, yana lulluɓe cikin bargo daga kafafunshi har kanshi a natse ta karasa gefen bed side ɗin ta ajiye tray ɗin, bata bi bugun zuciyarta ba ta gyara murya kaɗan tace "Sir ur tea is ready" Be motsa ba seda ta sake maimaitawa ya kai zara zaran yatsunshi ya janye bargon fuskanshi ya bayyana, gajiyayyun idanunshi ya buɗe a kanta hakan ya sakata saurin rausayar da nata don bazata iya jurar kallon cikin idanunshin ba.. Mikewa yayi ya zauna tare da jingina bayanshi da jikin gadon yana sake kallon fuskanta dake nuna taradaddin rashin lafiyan nashi. Ganin ya zauna yasa ta ɗauko ta mika mishi karamin tumbler ɗin ya sa hannu garin karɓa hannunsa ya ɗan gogi nata kaman wacce ta sa hannu a cikin wuta ta wani zare da hanzari tare da saurin zaro idanunta kuma tana kallon tea ɗin da ya kusa barewa jikinshi. Da sauri ya riƙe da kyau yana kallonta itama idanun nata ta ɗago ta kalli fuskanshi se ta duburce, wani malalacin murmushi ya saki yana janye idanunshi ba karamin dariya ta bashi ba, ita kuwa mutuwar tsaye tayi tana kallon kyaun halittar da Allah ya mishi, ba karamin kyau murmushin ya mishi ba. Ganin ze kara kallonta yasa ta ja baya ta fice da sauri, tean shi ya cigaba da sha yana murmushi lokaci lokaci bayan ya gama ya koma ya kwanta yana me sake rufe jikinshi, cike da Tunanin dalilin ciwon shi yana da wani abu guda idan har abu ya dameshi to se fa ya kwanta ciwo wadda kaman ya zame mishi jiki a daaa chan sede yanzu da ya mance menene damuwa hakan ya zama wani sabon abu a gareshi, so yake ya tantance wasu wasin da zuciyarshi ke yi ya tsayar da ita a matsaya ɗaya sede kwakwalwarshi ta kasa yardar mishi da amsa guda ɗaya tak dake amsa kuwwa daga cikin kanshi har zuciyarshi.. Tana komawa ɗaki ta samu Hamza na kiranta, ɗauka tayi sbd ya kusa yankewa suka fara waya yana mitar bata neme shi ba, daga karshe Aisha ya nema ta Haɗa su suka yi ta surutu, har junior ta makalawa yana ta kiran Daddy suna ta dariya ita dae idanu kawai ta zuba musu, hamza na matukar kaunar yaran nata Dukda be kai Raed ba sede she appreciate.. *** Juyi kawai yake yi from this side of the bed zuwa other side, numfashi da karfi yake ja sede kaman wadda aka shake mishi wuya numfashin baya wucewa zuwa cikin cikinshi hakan yasa yake ta kokawa da numfashin kaman me tashin asthma, zuciyarshi wani irin kuna take kaman an aje garwashin wuta, be saba ambaton Allah ba bare ya ambata yaji sauki, gashi dakakkiyar zuciyarshi bazata bari yayi kuka ba.. Cikin tsanani haka yayi ta juyi se daga baya Allah ya taimake shi ya janyo numfashin da karfi yana mikewa zaune lokaci ɗaya, saitin kirjinshi ya dafe yana haki kan daga karshe ya Haɗa kanshi da gwiwa idanunshi sun rine sun yi jajazir, ya jima be samu attack na panic ɗin nan ba se yau, ya kuma haɗu da wani mummunan mafarki da yayi.. Da sauri ya sauka daga gadon ya nufi frigde ɗinshi na ɗaki ya buɗe cike da son shan ruwa sede babu, haka ya juya ya nufi parlor da sauri.. Daidai lokacin ta fito don daukowa junior ruwan da ta manta bata dauko ba, karo suka ci da hanzari ta koma baya tana ambaton Allah, hannunta dake rawa ta laluba ta kunna switch.. Hard broad chest ɗinshi da ba riga ta ci karo da kan ta kai idanunta kan fuskarsa, wani irin zufa yake Haɗawa kaman ma a firgice yake, zata yi magana ta ga ya sulale ya zauna tare da haɗe kanshi da gwiwa kaman me tsoron mutane kaman kuma me tsoron ta ganshi a halin da yake ciki, da sauri itama ta durkusa tace "Sir! Me kake bukata? Jikin ne?" Cikin rawar murya yace "waaa...ter" Da gudu taje fridge ta ɗauko ruwan ta dawo ta buɗe murfin ta mika mishi ya karɓa ya kurbi kaɗan ya watsa sauran a fuskanshi zuwa kanshi yana karkada gashin shi wadda feshin ruwan har fuskanta lumshe idanunta tayi, Seda ruwan ya kare tsab kan ya jefar da goran ya sake maida kanshi cikin kafafunshi yana sauke numfashi.. "Mugun mafarki kayi?" Kaman yaro ya tsinci kanshi da gyaɗa mata kai.. Tace cikin sassanyar muryarta "ka ja numfashi a hankali sir, mafarki ne ba zahiri ba. Ana so idan mutum yayi mummunan mafarki a duk sadda ya farka ze ce 'Auzu bi kalimatillahi tammat min qablihi wa iqabihi wa sharri ibadihi wa min hamazaatis shayadini wa an yahduruun' Adu'ar na nan cikin hisnul Muslim" Gajiyayyun idanunshi ya ɗago ya zuba mata yana so ya ce ta sake don be sani ba se yanzu kuma ba ze iya maimaitawa ba, kanta ta mayar kasa ta sake farawa yana bi har suka kai karshe.. Seda ya ɗan natsu kan ya miƙe cikin kasalalliyar murya yace "thank you" Jurewa kallon idanunshi dake gigitata tayi cikin natsuwar murya tace "u welcome, kayi Adu'a karka sake yin irin mafarkin kuma" Har ya juya ya sake juyowa yace "ban iya ba" Runtse idanunta tayi sbd hawayen dake son zubo mata, shi kuwa wani irin rayuwa ne wannan da yayi! Tace "baka yin ko wani irin Adu'a?" Kallonta kawai yake, se taji kaman maganan yayi mishi rashin daaɗi zata ce yayi hakuri se taji ya ce "me zan roka?" A tsorace ta kalleshi tace "Subhanallah! Sir ai Adu'a dole ce ga dukkanin musulmi ko ka samu duniya ba shine ze sa ka kasa neman lahirarka ba, mahaifiyarka dake kwance cikin kabari itama tana bukatar Adu'ar ka don Adu'an ƴaƴa na daga cikin manyan sadakatul jariya  zaka nemi tsari da azabar kabari da na wuta, kuma ka nemi gamawa da duniya lafiya.." Bakinta dake ta motsi kawai yake kallo idanunshi sun sake rinewa don ambatar sunan mahaifiyar shi kaɗai ya Tono mishi wani miki da ya jima da binnewa, me ke faruwa ne? Meyasa bayan ya manta komai nightmere ɗin Mahaifinshi ke dawo mishi kaman yanzu? Muryarshi na ɗan rawa yace "ban san hakan ba..!" Hawayen tausayin shi ne ya zubo mata ta sa hannu ta share tare da Kallonshi tace "ai ka iya ayatul kursiyu, qulhuwa, Falaq da nasi?" Kai ya gyaɗa mata tace "ka karantasu kafa uku uku se ka shafa in Shaa Allah bazaka sake mafarkin ba" Kaman ze yi magana se kuma ya fasa ya juya ya wuce, da kallo ta bishi har ya shige room ɗinshi se ta samu kujera ta zauna hawaye na sake silalo mata, Matukar tausayin rayuwarshi na lulluɓe ta. Ta jima a wurin kan ta ɗauki ruwan ta koma ɗaki zuciyarta fal sake sake.. Washegari Seda likita ya sake dawowa ya sa mishi drip sbd jikin dae ba daaɗi, ba jikin kaɗai ba har zuciyarshi likitan ya tsorata ganin ciwon da suka samu suka raba shi dashi karfi da yaji ne ke shirin sake dawowa, idan kuwa hakan ta kasance har career ɗinshi se yayi affecting.. Yana fita ya kira Father ya sanar dashi, a rikice yace ze bi available flight yau ya zo Paris ɗin. Norah da Farrah jikinsu duk yayi sanyi kaman sune ba lafiyan har Aisha da kyar ta lallaɓa su suka tafi school, ita ta girka mishi abu marar nauyi da kanta ta kai mishi.. Cikin karfin hali ya mike yayi brush da ta ɗauko mishi har nan ta ajiye mishi abincin, kaɗan yaci yace ya koshi, maganin shi ta ballo ta bashi ya sha da coffee ɗin da ta hada mishi. Tattare wurin tayi ta fice, da kallo ya bi ta har ta rufo kofan ya koma ya kwanta. Da rana ma haka ta sake kawo mishi cikin muryarshi yace "baki je school ba?" Kanta kasa tace "eh, idan na tafi babu me kulawa da kai" Motsi me karfi yaji zuciyarshi tayi da Seda ya runtse idanu, a hankali ya buɗe yace "thanks" Kai ta gyaɗa, tace "ko zaka yi wanka sir?" Kai ya gyaɗa mata kawai, ta shiga toilet ta hada mishi ruwa me dumi ita dae taga turarukan wanka kala kala a bayin sede bata san wanne yake anfani dashi ba hakan yasa bata saka ba ta fito, ya miƙe yana dafe gini ya wuce nan ma jarumta kawai yake da karfin hali amma shi kaɗai ya san me yake ji.. Yana shiga ta hau gyara ɗakin, fes ta gyare cikin lokaci kankani, bata bari ya fito ya sameta ba ta fice daga ɗakin.. Abincin ƴan makaranta ta hau yi bata gama ba taji motsin shigowa, kuma bata ji hayaniyar yaran ba.. Da sauri ta ajiye abun hannunta ta leƙa se suka Haɗa idanu da kakkarfar mutumin sanye da wando da riga me yanayi da dogon riga baƙi da fari, se wani abu kaman mayafi da ya ɗaura saman rigar igiyar har wurin gwiwar shi, katuwar sarkar cross sanye a wuyan shi se Bible rungume a hannunshi na dama Ɗayan hannun kuma brief case. Fitowa tayi a ladabce don bata san wanene ba tace "u r welcome sir" Kallonta yayi sama da kasa wannan ce kenan da Raed ke faɗa itace sabon nannyn yaran, aiko se ta bar gidan daga gani ma itace sanadiyar ciwon shi da ya tashi tunda a farkon barowansu Nigeria a duk sadda ya ga baƙin fata se ya shiga panic attack, ya zo da wata baturiya daga Amsterdam na Kasar Netherland da dama yawancin zaman shi a chan ne don hakan sallamar wannan dole. Ba tare da ya amsa ta ba ya wuce zuwa room ɗin Raed, Seda yayi knocking kan ya buɗe yana shiga idanunshi suka faɗa bisa kanshi, da sauri ya karasa yana cewa "Son!" Tare da riƙe hannayenshi yana zama bakin gadon, 3 quarter ne a jikinshi da ya zazzage daga sama ya fitar da boxers ɗinshi fari Kal jikinshi ba riga yana jingine da gado yana duba phone ɗin shi ɗakin banda sassanyar kamshinshi me cike da wani ni'ima da sanyaya zuciya na musamman babu abunda yake ga sanyin Ac. Murmushi ya saki yace "father finally ciwona ya sa ka zo, Princesses will be happy today" Yace "drop that son! Me ya faru? What brings this illness back? Na tabbatar wannan baƙar fatar ce da ka ɗauko" Kai ya girgiza yana tuna damuwarta da ciwon nashi wadda a rayuwarshi baze ce ya taba ganin makamancin tausayinshi a fuskan wani ba bayan nata, ya karanci ba karamin jimami take ba shi kuwa be san tsoronta na in ya mutu a tsukukin nan yana cikin babban hatsari bane, taimakonta da yayi kuma wadda bazata taɓa mancewa ba yasa ta ci alwashi me girma a kanshi.. "She is not father, I just had a dream abt my past!" Yace "then seeing her is the essence, na yi hiring nanny from Amsterdam a well reserved person ita zata cigaba da kula min da jikokina u should fire this one, and that's final.." Da sauri ya ɗago ya kalleshi.. *** Ita kuwa ganin ya wuce kai tsaye yasa ta saka a ranta maybe dan uwansu ne, komawa kitchen ɗin tayi ta karasa duk wasu ayyukanta kan ta fito ta koma ɗaki. Kasa bacci tayi a jiya da Tunanin wani irin rayuwa Raed yayi. Shi kuwa menene tarihin rayuwarshi haka? Wanene shi? Kasa hakura tayi ta lalubi inda ta rubuta landline number ɗin Daadida ta saka kira.. Ringing na karshe aka ɗaga "Assalamu Alaikum jikata..!" Ɗan murmushi hidayat tayi tace "Wa'alaikumussalam warahmatullah ina yini daadida?" Daadida tace "mu a wurin mu har yanzu kwana ne, Awa ɗaya da ƴan mintuna ya rage mu shiga yinin" Murmushi hidayat ta sake tsohuwar akwai barkwanci tace "to ina kwana" Tace "lafiya ƙalau Alhamdulillah ya kuke duka? Ya wannan sarkin miskilancin? Wai fushi yake dani, in kira in kira ya ƙi dauka ja'iri kuma wallahi ba zan fasa gayamai gaskiya ba ko mutuwa ze yi" Hidayat ta ɗan yi murmushi tace "yana kwance bashi da lafiya" Daadida tayi salati ta sallame tace "Allah sarki, Allah ubangiji ya bashi lafiya ya sa kaffara ne" Hidayat ta amsa da "Ameen" Se ta ɗan yi shiru cikin shirya kalaman da zata yi akan tsari tace "Daadida kin roke ni a kan tallafar rayuwar uban gidana kuma na ɗau alkawari, sede duk inda na duba babu wata mafita har se in na san wanene Muhammad Raed, yaya rayuwar shi take wani giɓi ne ya samu yake buƙatar plaster se na san ta inda kuskuren ya faro kan in yi tunanin hanyar bi wurin gyara" Daadida ta sauke numfashi me nauyi tace "Hidayat shi ba giɓi bane a rayuwarshi, tubali ne bashi dashi kinga toshewa da plaster ba ze taɓa yiwuwa ba in har ana so yayi karƙo se an rushe an sake sabon dakakkiyar tubali, ina nan ina muku Adu'a, ina sadaka ina saukar Alqur'ani da yardar Allah mafarkin da na jima ina yi a kanki nake saka ran tabbatarsa don haka zan faɗa miki wanene Muhammad Raed...." #Vote #share #comment                  🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 19* *FREE BOOK* *Wannan shafi naku ne ɗaukacin masoyana da kuka tayani murnan kamalla bautar kasa ta lafiya, especially Gureenjo Novels group bazaku kirgu ba da na kirgo ku one by one sede in har kina karanta wannan just know that am really grateful and I sincerely appreciate...na gode sossai matsayinku a raina bazata kirgu ba kuma na ji daaɗi kwarai.. Allah ubangiji ya bar ƙauna😍🥰* 18/03/1986 Zaune take dabas a ƙasa saboda bazata iya jumrewa tsugunon ba hawaye ne wani ke bin wani a fuskanta tana sa hannu ta share lokaci zuwa lokaci, yayinda wani farin bafulatani tsayayyen namiji tsaye a kanta yana zabga masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba ko damuwa da a gaban mahaifiyar shi yake be yi ba. "Ke kin san Allah wallahi na gaji, na gaji da wannan jarabbaben jinya naki, ke kullu yaumin ciki, a yayin cikin in sha wahala in kashe kuɗi ki ishe mutane da laulayi kika tashi haihuwa ki haifo mace, nan ma suyi ta jinya suna karya tattalin arziki na har su zo su mutu to wallahi Allah ba ze yiwu ba wannan cikin zubda shi za'ayi a juye mahaifar" Dattijuwar dake zaune daga kan kujerar tsuguno ta zabga tagumi tana aikin kallon shi tace "Bukar kayi hakuri ka bari tunda tana son kayanta ta haihu baka san ko shine me tsayuwa ba.." Katse ta yayi da sauri "A'a mama dama tun farko kece kike ɗaure mata gindi shiyasa take jin daadi kuma take abunda ta ga dama" Shiru matar tayi saboda ita karan kanta shakkar yaron na cikinta take yi, har ya juya ze fita ta kalli Mairamu dake kuka kaman ranta ze fita ta ɗaga ta kalle shi tace "Bukar!" Da mamaki ya waiwayo saboda ya sani idan yayi magana ya zauna kenan ba me juya ta har uwar da ta haifeshi amma yanzu tana kokarin fara shiga sabgar gidanshi da iyalinshi kenan suma su ma su samu Daman raina shi kenan, fuskanshi a tamke ya amsa. Tace "Don Allah kayi haƙuri akan wannan kaɗai mun yarda idan be tsaya ba tun kan ta samu wani cikin se a juya mahaifar" Shiru yayi na mintuna kan yace "Tunda kin matsa ai shikenan sede fa ni ba ruwana ba kobo na da ze yi ciwo a akan cikin nan kuma hidimar aurena yadda take yi haka zata yi.." Kallonshi kawai Daadida ke yi har ya fice, duk sauran da suke tsatsaye har ita  wacce aka kira da Maryam dake durkushe nannauyar ajiyar zuciya suka sauke, ɗaya rike da karfe varender ɗinta tace "ke ma in banda jaraba tunda an ƙi samun namijin mama a hakura Haba!" Na biyun tace "Toh ina bakin ciki ze bari ke kuwa ba'a samu magajiya ko magaji ba" Na ukun tace "ni ba don ma haihuwar da take yi suna komawa ba da se ince wannan anya ba juya ba! To ko ni da nake Amarya yaushe na zo gidan nan har ina da biyu.." Daadida tace "ya isheni haka, babu ruwanku wannan tsakanin Maryam da mijinta ne.." Baki suka taɓe kan kowacce ta juya ta shiga ɗakinta dake dauke da parlor da ciki ɗaya Miƙewa Daadida tayi ta zo ta kama Mairamu ta mikar da ita da taimakonta suka koma ɗaki don haka laulayinta suke ba karamin wahala take sha ba.. Kaman yadda bukar ya faɗa hakan kuwa ta kasance, bukar mutum ne me tsananin zafi, Haɗa rai da rashin mutunci kwata kwata akan dukiyar shi bashi da mutunci, haka matanshi su su huɗu rass babu wacce ke ganin hakwaranshi da sunan dariya, ba mutan gidan ba har na waje shakkar shi suke, mahaifiyar da ta haife shi ma bata tsira ba Dukda ba ze zage ta ba sede itama yana shimfiɗa mata doka, amma matan suna shan bauta da aiki. Mairamu ce ta farko wacce tunda ya aureta in ta samu ciki baya zama in ya zauna kuma ta haihu ƴaƴan basa zama se su sha ciwo na watanni kaɗan su koma, a haka ya auro na biyu badi'ah yaranta huɗu mata. Se Naja'atu itama yaranta uku mata se Amaryar zarah yaranta biyu suma mata ne, suna tsananin kishi da Maryam saboda yadda daga mijin har surkar suke nuna sun fi kauna da sonta Dukda shi Bukar ba gane mishi suke ba sede kam zasu iya cewa hakan saboda ganin bayan Daadida ita ce kaɗai kan ɗan tankwara shi kaɗan amma sauran ko gwadawa basu isa yi ba. A gidan ko wani karshen wata ana kawo hatsi buhu guda, idan har Rogo ya jingine musu su zasu yi wahalar maida shi gari sede ya dinga turo abun miya sun dinga cin rogon kenan har se buhun ya kare se ya sake jingine wani hatsin, yana jingine shinkafa gumi, Gero, dawa, masara duk abunda yayi niyya amma fa guda ɗaya idan sun gama aikin se su raba ko wacce ran girkin ta ta san yadda zata sarrafashi kowa ya ci, ko Maggi ne zaka sa a miya se ka jira ya shigo kan ya kirga ya baka, haka in nama ne a kirge yake wai don kar a mishi Almubazzaranci. Sannan wankin shi shima in ya taru matan yake jibge ma wa haka zasu raba su dirza, sannan aikin wurin dabbobbinshi da tsabar yawansu aka mishi lakabi da MAI NAGGE wato me shanu, yadda in har ka shigo garin mambila kace Gidan Bukar mai nagge kowa ya sani, tsabar zafin shi har dabbobin su kan san da shigowar shi, in kana so kuyi rashin M ka raina shi ko ka mishi wasa da dukiya. Mairamu ta raini cikin nan nata cikin tsanani da azaba saboda laulayi me zafi take yi, hakanan ga ayyukan gidan tunda tunkunyar gidan lamba goma ce, daga shara har wanke wanke bata iya sede Daadida ta karɓa mata wadda da kyar take barin ta yi don ta dinga rokonta kenan akan ta bari ba se tayi ba se in ta nace ne zata sakar mata Ranan girkin ta haka zata tashi tun da duhu ta fara shara ta gama ta ɗaura koko na kari bayan nan tayi wanke wanke ta zo ta ɗaura abincin rana, tana saukewa za'a maida ruwan na dare, gashi wani lokacin se ana tsaka da yi za'a shigo da buhun hatsi saboda baya so a mishi asara ko kwari su shiga hakan ya sa baya bari hatsi ya kwana yana shigowa ya gani kin shiga uku da sababi. Kaman yau cikinta na cikin wata na hudu har ya fara fitowa, zaune take tana wanke wanke hannunta na rawa saboda cimar cikinta ya ƙi shi, Jan masara ne kuma tunda aka kawo banda koko da safiya bata iya cin komai saboda cikin ya ƙi jan masara. Shigowa yayi da gyaran murya wadda ya sa duka sauran matan gyara zama suna shiga taitauyinsu, kallon kwatar buhun  gero da ya ajiye musu  yayi ya sake haɗe rai yace "wannan kuma kason waye ne don wulakanci zata bar min dukiya a gantale?" Badi'ah tace "ka ganta chan uwar laulayin duk duniya" Ɗagowa Maryam tayi tace "kayi hkuri ba wai na ƙi yi bane ayyuka ne suka min yawa ga rashin karfi saboda bana iya cin jan masaran nan" Yace "ke kika jiyo ni de abunda na sani in ga hatsina a gyare tass" Yana kai nan ya juya ya fice. Hawaye take tana aikin da wahala, daga karshe kaman kullum se Daadida ce ta fito ta taimaka mata da dare kuma ta shirya ta tafi turaka.. A kullum Adu'ar Daadida be wuce Allah ya sauya mata hallayyarshi ba sbd baƙin bafulatani ne ba a fuska ba a zuciya saboda yana da arzikin da ze iya fidda kunci a gidanshi sede hannun shi a dunkule yake, yana da halin daukar masu aiki sede ba ze yi ba, yana da ilimin Addini amma ta rasa meyasa baya aiki dashi shi kuma haka Allah ya halicce shi yaranshi in sun ganshi kaman sun ga mala'ika, baya son yara mata iyakacinsu dashi cimarsu bayan nan duk wata hidamar ƴarki ki san yadda zaki yi. Wahalar da ta sha a cikin ba ƙarami ba gashi bata da kowa banda mijin saboda Fulanin tashi ne en uwanta kuma sun tafi bata san inda suka yi ba, da shi ta dogara wannan yasa yake anfani da rashin kowan yake mata yadda yake so, har dukanta ya taɓa yi da cikin saboda ɗan hatsaniya da suka samu da Zarah ta lauye maganan. Cikinta yana wata tara amma har lokacin babu hidimar da ya ɗauke mata, idan taje garken na dabbobinshi shara sede ta saka gwiwowinta a cikin kashi take iya sharar gabaɗaya jikinta se ya samu kashin dabobbin kan ta gama tun tana amai kaman zata amaye hanjin cikinta har ta koma daure dankwali a hanci da bakinta kan ta iya sharewa. Uban wankin shi ne jibge take tiƙa Dukda bayanta dake a sage cikinta kuma na juya banda idanu da hanci babu abunda zaka gani a jikinta se fari kaman aljana in ji faɗar Kishoyoyinta da ta rasa me ta tsare musu suka sako ta a gaba bayan ita ce uwargida ma. "Mairamu ki aje wankin nan ki zo ki huta hakanan ko ba ɗazu kika ce baki jin daaɗi ba?" Cewar daadida cikin tausaya mata Tace "Daadida bari na gama kin san in ya shigo ya samu ma magana ne" Zarah dake surfe ta taɓe baki ta fara wake waken habaice sbd haushin yadda surkuwar tasu ta fi damuwa da Mairamu suke ji ba kaɗan ba. Badi'ah tace "mu da muke ba ƴaƴa ba aikin ya kashe mu ba" Naja tace "Ai karshen alawa dae ƙasa Allah kuma ya sa shi ɗan ba me jin maganan na gaba da shi bane da tuni an sa ya kora mu waje" Mairamu ta miƙe tsaye tana rike baya tace "amma dae ya kamata ku dinga sanin maganan da Zaku ke faɗawa Daadida ko bata haife ku ba ta haifi uban ƴaƴayenku bare ma a haihuwa duk ta haife ku.." Zarah da ta fi raina ta akan kowa tace "don ta haifeshi se me? Shi ɗin ya ɗauke ta uwa ne? Ta je ta fama da damuwar ta ba ta zo ta tare a gidan surakai ba mana taga in mun bita mun faɗa mata magana ko ba haka ba?" Tayi maganan tana kallon Su Naja a tare suka ce "kwarai kuwa" Maryam zata sake magana Daadida ta hanata tace ta je ta zauna zata karasa wankin. Duk abubuwan da Bukar ke yi babu abunda yafi komai ƙona ranta irin yadda yake da mahaifiyarshi, mace ta dauki cikin ka ta Rena ta haife ka girma kana mata yadda ka ga dama? Anya yana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ai iyaye ba abun wasa bane. Karshe dai Daadidan ce ta mishi wankin ta shanya, cikin dare Mairamu dake dakinshi nakuda ya tasar mata, duk yadda tayi dashi da ya taimaka ya kira mata ko Daadida ne yace in ya fita a ɗakin wutar Allah ta ci shi. Da kyar ta iya mikewa cikin azaba ta fito ruwa har yana bin kafafunta ta fara bubbugawa Daadida wadda yayi sanadiyar farkawar matan suka fito suna kallo har Daadida ta shiga da ita, ta sha baƙar wahala kan ta haihu gab asuba kukan yaron ya karade ilahirin gidan. Fitowa Daadida tayi ta shiga ɗakinta ta kwaso abubuwan da zata bukata wurin karasa ayyukan badi'ah tace "ta juye kenan to Allah ya ji kan rai tun kan lokacin yayi" Har Daadida ta saka hannu a kofan ɗakinta wurin komawa ta juyo tace "Tabbas ta juye santalelen lafiyayyen ɗa namiji kuma in shaa Allah shine me jan ragamarku nan gaba shine kuma shugaban ƴaƴayenku, ranshi a Hannun Allah yake ba hannun ki ba bare ki fara mishi hasashen mutuwa ke ba Alanmusuru ba" Shiru duk suka yi suna kallonta saboda maganan ya dakesu, shiganta suka kalli juna Naja tace "kaman namiji fa tace?" Badi'ah tace "kwarai abunda tace kenan" Zarah tace "Ah bamu ga ta zama ba fa" A ruɗe kowacce tayi ɗakinta sbd kalmomin Daadida na zama magaji kuma shugaban gidan abun be musu daaɗi ba Sam ya kuma dake su. Ko da gari ya waye Daadida ta fito taje tayi sallama kofar ɗakin Bukar ya leko kai yace "Mama lafiya kuwa?" Tace "yarinyar nan ta sauka kuma tunda ta haihun nan bata wani jin daaɗi ya kamata ka kaita asibiti a duba ta" Yace "wa? Tabb ai abunda kuma ba zan iya ba kenan mama ba zan kashe kuɗina a banza ba" Tace "yaron ma fa bashi da cikakken lafiya Bukar Haba don Allah ka ji tausayinsu mana" Karkaɗa kunnenshi yayi yace "Me kika ce?" Tace "nace yaron bashi da cikakken lafiya" Wara idanunshi yayi yace "kina nufin namiji ta haifa?" Kai kawai ta gyaɗa mai ganin kaman ya ruɗe ai se ya sheke da dariya wadda ya saka badi'ah, zarah da najah Kallonshi cikin dumbin mamaki. Jiki na rawa yayi ɗakin Mairamu Daadida tayi musu wani kallo na ba kun gani ba kan ta bi bayanshi, aiko farar ɗaya yaron ya shiga ranshi matuka gaya. A take ya kaisu asibiti aka duba lafiya su aka rubuta magunguna ya sayo, har kaji biyu ya yanka mata Daadida ta sarrafa mata shi ta samu ta ɗan ci cikin mamakin sabon halayyar Bukar ɗin lallai ɗan ta ya zo da albarka. Hidima kam ya musu har ran sunan shi ya naɗama yaron suna Muhammad Daadida kuwa tace Raed za'a kira shi tunda dae ya tabbata shine shugaba in ba Bukar. Abunda ba'a taɓa yi ba aka yi a gidan hidimar suna da yanka rago se akan Raed, ba tare da sun san wani baƙin hassada da kyashi da kuma tsanar Muhammad ɗin da Mairamu Bukar da Daadida suka kara musu ba. Raed na wata biyu wata matsala ta fara kunno kai na ɗauki ɗaiɗai da ake yiwa dabbobinshi don kullum se ya kirge su tsab, ranan da ya kirga yaga ba rago ɗaya tashin duniya ne kawai ba'a yi a gidan ba don duk ya tarasu ya kwashewa duk wadda ya taɓa mishi dabba albarka se washegari aka sake zare akuya ɗaya. Horon abinci ya musu yace kar yaga an hura mishi wuta a gidanshi in dae har da iccenshi da kuma kayan abincinshi za'a yi anfani, gwara ma Mairamu albarkacin shayarwa ya turo mata biredi da shayi wadda ita kuma ta raba da Daadida don har ita hukuncin shi be tsallake ba. Bayan kwana biyu aka sake dibar kaji biyar, ranan tarasu yayi yayi rantsuwar idan ba'a fitar mishi da ɓarawo ba duk ze sake su su bar mai gida da yaran su duka. Badi'ah ce ta fara magana tace "to ni de ban son in yi magana ne ace na ce amma tsakani da Allah banda Mairamu da Daadida dake shiga wurin dabobbin nan cikin mu ba me shiga daga shara se shara" Zarah tace "Najah mu faɗa" Najah ta girgiza mata kai yace cikin tsawa "me Zaku faɗa ɗin maza a faɗa in Ji" Zarah ta fara in ina.. Tace "dama gab asubahin yau ne na tashi da nufin zuwa bayi shine na leƙa window Naga an buɗewa wani kofa ya fita rike da wani kwando a hannunshi kuma da aka dawo ɗakin Mairamu Naga an shiga Dukda ban kalli fuskar ko waye ba" Ta Yi shiru kan ta sake cewa "ranar da Akuya ta ɓata kuwa da ni da Naja muna zaune daga wurin shiga turken Mairamu ta zo ta wuce mu ta shiga kuma ta jima kan ta fito ko kan fitowanta diran abu muka ji kaman ta gini da kuma kukan awaki amma mun leƙa tace mana ta ɗan yi tuntube ne garin kwashe kayan Raed daga kan gini shine akuya suka razana don ta kusa faɗa musu ko Naja?" Najah ta gyaɗa kai tace "hakane wallahi" Badi'ah tace "in de kuwa haka ne to itace me alamar tambaya Kato kuwa a kanta" Wani kallo Bukar ya watsa mata yace "me zaki yi min da dabbobi? Me kika nema kika rasa da zaki fara min ɗauki ɗai ɗai da dabbobi to kiji da kyau wallahi wallahi dabba na ɗaya ya sake ɓata zaki yi mamakin mataki da zan ɗauka" Daga haka suka watse ko sauraran ta be yi ba, tayi kuka tayi kuka har taji ba daaɗi saboda kazafi komin kankantarshi akwai ciwo Daadida ce tayi ta lallashinta. Wasa wasa aka gane satar dabobbin bukar wadda Mairamu ke shan azabar hakan saboda yadda yake gana mata wahalhalu akan hakan har sakinta yayi tayi ta kuka tana bashi hakuri don bata da inda zata je karshe yace ta zauna sede ta nemi abunda zata ci da kuɗin dabobbin shi da take sacewa kuma ɗaya ya kara ɓata se ta bar gidan. Haka suke raba abincin Daadida don ita bata da sana'ar da take yi kaman sauran matan waye ma ze bata jari, ga damuwa da ya mata yawa ga wahalan aiki don duk ayyukan da suke rabawa ita kaɗai take yinsu. A hankali a hankali bukar ya fitar da Mairamu da Raed a ranshi saboda laifukan da take mishi da yake ganin cin fuska ne, dukanta yake ba ruwanshi in abu ya samu dabbobinshi sanadiyar ta don ita kuma ke hidimar su tsab. Raed na shekara uku har ya iya tafiya da magana sede be isa ya fita tsakar gida ba mugunta babu irin wadda matan gidan da ƴaƴayensu basu mishi, wani lokacin ma har da wuta ko ruwan zafi. Wani rana kaddara ya sa Mairamu shiga ɗakin Bukar don gyara mai, dama aikinta ne amma fa se in ya faɗa kamin nan sannan kuma yana kofan ɗaki yana jiran ta har ta gama to yana sauri wani cinikayya da ze yi se be rufe ɗakin ba ya fice, ita kuwa ta gama duk ayyukan ta tace to akan ya dawo kuma ya sakata bari kawai ta shiga tayi shine ta shiga tayi ba tare da ta san ajali ke dibar ta ba. Ta shiga ta gyara fes ta fito ta koma daki wurin Daadida, chan bayan la'asar Bukar ya shigo ya shiga ɗakin shi kusan mintuna biyar ya fito ya fara kwala kiran Matan gidan gabaɗaya a razane suka fito jin muryarshi a haukace. Yace "ina kudade ne?" A gigice yayi maganan. Duk a tsorace suka ce "wani kuɗi malam?" Yace "tambaya ta ma kuke yi? Ku fito min da kuɗina ko kuma wallahi dukkanku rayukanku ya ɓaci wallahi wallahi akan kudin nan babu abunda ba zan yi ba ku fito mun da kudade na" Duk rantse rantse suka fara ya daka tsawa yace "wa ya shigar min ɗaki a cikinku?" Dukkansu Mairamu suka nuna aiko kan tayi magana ya fara sauke mata maruka har Raed dake hannunta ya faɗi, a gigice ya kwala kara itama tana kuka take ce mishi wallahi bata ɗaukar mishi kudi ba shi kuwa yana cewa se ta fitar da kudadenshi har dubu ɗari uku wallahi se ta fitar. Duk yadda Daadida tayi kokarin hanashi dukanta kasawa tayi karshe itama tura ta yayi ta faɗi ta kuma kasa tashi saboda kwankwasonta da yayi mugun bugawa se ta saka kukan bakin ciki kawai. Haɗa Mairamun yayi da Raed ya ja su kaman kayan wanki zuwa kofar gida ya watsa su wadda dab titi ne kuma Raed ne ya sauka bisa titin, dukda azabar da Mairamu ke ciki a gigice tayi kanshi ta ɗauke shi sede ta kasa mikewa, horn me karfi take ji amma ba yadda zata iya sake tashi hakan ya sa ta cilla shi gefen titi ita kuma ta runtse idanu tana ambaton Allah. Me motan ya kasa riƙe Birkin shi don da full spead ya zo hakan ya sa ya mata mugun bugawa a take ta some, ya ɗauke ta da Raed zuwa asibiti tare da wani ɗan unguwa, sede suna isa ma aka tabbatar da ai ta cika sossai pastorn ya firgita da mutuwar gashi musulma hakan ya sa be koma gidan bukar ba seda yayi Involving police aka dawo da gawa inda aka nemi bukar. Aiko yace se an biya diyya, nan pastor David ya biya kusan 2mil kuma bukar ya amsa cikin jin daaɗi wannan abu ya sawa Daadida hawan jinin da seda ta fi wata biyu tana jinya, a wata biyun nan azabar da Raed ya sha wurin yaddikonanshi ba'a magana sun dena kiranshi da sunanshi sede ɗan ɓarauniya ko Duna (saboda baƙin fata ne dashi kalar na Daadida don iyayen shi duka biyu farare ne) Ko da Daadida ta samu sauki ita da Bukar idanu ne, tana kula da Raed sossai babu kuma irin cin kashin da su Najah basa mata sana'a ta fara sossai tana biyawa Raed duk wani bukatar shi don ba ruwan uban dashi. Raed na five yrs wani babban al'amari ya faru wadda yayi sanadiyar da har Daadida ta bar gidan wadda su Najah suka zuga Bukar akan kar ya barta ta tafi da danshi aiko ya hana tafiya da Raed, taurin zuciyarshi kuwa ya hana shi ganin laifin da ya aikata babba. Raed ya taso ne cikin tsananin ƙaunar kwallo yana son ball ta yadda ko a cikin gida yake zaka ga yana buge bugen ƴan ledojin da yake Haɗawa ya maida su kwallo, dama Daadida ce ke koya mishi karatu a gida wadda yayi nasi zuwa sabbi da kuma ayatul kursiyu sede tunda ta tafi kuma yaddikonanshi sun hana shi zuwa wurinta da sau ɗaya yaje suka mishi sharrin da ya sa Bukar kusa kashe shi shima be kara zuwa ba. A hankali ya mance sauran wadda ya iyan ma banda Falaq nasi da kuma qulhuwa se ayatul kursiyu da salatin annabi saboda ba'a sashi a Arabi ba bare boko su sauran yayyun shi mata da suke yi ma saboda iyayensu mata ne ke biya musu shi da bashi dashi se dae zaman gida da bauta. Ya bautu iya bautuwa Sanna ya azabtu ya kai ya kawo a turken awaki yake kwana saboda ɗakin mamanshi da ɗakin Daadida su Badi'ah rabewa yaransu suka yi be isa ya shiga ba. Wata rana baban ya kalleshi yana kwallo ya rufe shi da duka akan abun Yahudawa ze kawo mishi gida, kaca kaca ya mishi da kyar ya iya bacci, da safe da hidimar gidan ya tashi shi ke diban ruwa yayi shara, ya share ɗakin dabbobi ya wanke ya kuma ciyar dasu. Se ya gama diban ruwa ya zo ze huta se yaga sun yashe ruwan masu wanka sun yi masu zubarwa sun zubar haka ze sake komawa ya sake dibowa gashi da kadan kadan yake dibowa don bucket yafi karfinshi, kuma kullum se an yi abunda ze sa Bukar dukanshi kaman Allah ya aiko shi. Akwai wani rana da ya zo ya ajiye ruwan dabbobi ze fara saka su sha Badi'ah tayi kiranshi ya je ta bashi kudi akan ya je ya sayo mata cingam ya fice ko da ya dawo ya samu shanu ɗaya ya sha ruwan kuma se ya ganshi kwance. Yaje ya taɓa shanun don be saba gani suna bacci haka ba sede shanu kam be motsa ba, Najah ce ta shigo ta rabka salatin da ya saka Raed mikewa a razane, Bukar ya shigo wurin da shigowanshi kenan yaji salatin wani ashariya ya zabga ganin katuwar bijiminshi kwance ba rai. "Me ka sa a ruwan?" A razane cikin tsananin kaɗuwa da tsoron uban yace "ban saka komai ba...wallahi Baba ban sa komai ba!" Gigitaccen mari ya ɗauke shi dashi wadda ya saka ya dena ji na wucin gadi. "Zaka fara yi min irin muguntar da uwarka tayi min ko? To wallahi uban ka zan ci" Da gudu yaje ya ciro murɗaɗɗiyar igiya na ɗaure saniya ya fara jibgarshi ko damuwa da ɗan shekara Biyar zuwa shidda ne be yi ba, be yi la'akari da tun farko kula da dabbobin ba aikin da ze iya bane. Da kyar Raed ya samu ya gudu ya fita a gidan yana ta kuka ya samu wani lungu ya dukunkune kaman maraya yana kukan raɗaɗin da jikinshi ke mishi yana kiran Daadida da Mamah (maamanshi) *Kai Har 4 thousand words🤔 gaskiya na yi kokari😉* #like #share #comment                    🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 20* *FREE BOOK* Tun daga nesa yake hangar kaman yaron nan da ya taɓa kade mahaifiyarshi har ta mutu, suna matsowa kusa kuwa ya taɓa shi wadda ya saka Raed firgita ya tashi kaman ze gudu, pastor Philip yayi saurin rikeshi yana cewa "hey calm down we r not gonna harm u" Pastor David yace "Muhammad ya kake?" Kallonsu Kawai Raed yake ya kasa magana don shi be sheda su ba, ganin da gaske be gane shi bane yasa yace "Me kake yi anan haka Raed? Ji jikinka duk kashin shanu da ruwa? Me ya sameka a fuska haka?" Se yaron ya sa kuka, duk wani tausayinshi ne ya kama su, lallashinshi suka yi tayi har yayi shiru yayi musu bayanin abunda ke faruwa Seda Philip yayi kuka da David ke faɗa mishi abunda yace don shi ba ɗan Nigeria bane ya je Mambila yawon buɗe idanu da yada addininsu ne shine ya sauka wurin Pastor David. David ya ce cikin harshen turanci "Tun daga sadda na kade mahaifiyarshi yaron ya kasa fita a raina, na sha zuwa don son ganinshi baban yake ce min baya nan ko yana makaranta in bashi kuɗi akan a mishi sayayya amma dubi yaron nan, kaman a bola yake rayuwa ko almajiri ya fishi kyaun gani.." Yayi maganan yana share hawaye, Philip yace "matsalanku kenan a Nijeria had it been a ƙasar mu ne taya hukuma zata bari a yi ma yaron nan Haka" Bayan gama jimaminsu suka ce ya zo su je su yiwa baban nashi nasiha Sam ya ƙi ya san karshen shine a ciki, kyautar kuɗi suka bashi shima ya ƙi karɓa, A mota suka dauke shi zuwa gidan David suka bashi abinci ya hau ci hannu baka hannu ƙwarya, se kallon shi suke har ya gama suka saka shi yayi wanka Philip ya sa kayanshi a washing mashing bayan ya fita tas suka yi drying suka goge suka bashi ya maida jikinshi take yayi kyau. A parlor suka zauna ya zauna a ƙasa ya kurawa TV da ake buga kwallo idanu, tsabar kallon da yake yiwa ball ɗin ko idanunshi baya son kaudawa be san time ya tafi ba seda ya ji kiran sallah a masallacin dake kusa da gidan David ɗin, da sauri ya miƙe yace ze tafi. Seda suka bashi abinci ya sake ci kan suka maida shi inda suka ɗauko shi, a raɓe ya shiga gidan Badi'ah tace "ka ci gaba da raɓe raɓe duk aikin da ka tara zan ga uban da ze maka ai, kuma babanka ya ce baka da abinci a gidan nan har nan da kwana biyu sbd kashe mishi sa da kayi kuma ka kiyayi sake haɗuwarku Duna kawai" Kanshi kasa ya wuce ya ɗauko roban da yake diban ruwa ya fita ya fara jidowa Seda ya gama ya je ya kwanta a cikin dabobbin gwanin tausayi. Daga haka David ya gane taimaka mishi, Philip ya koma amma da Tunanin Raed makale a cikin ranshi, rayuwar gidansu kuwa banda tsanani babu abunda ya ragu a gareshi, kasancewar shi yaro kuma abun ya mishi yawa yasa yayi developing Panic Attack.. Wani irin tsoron mutane yake, baya yadda ya kalli idanun kowa kullum a raɓe yake a wuri, idan kuwa ya tsorata numfashin shi se yayi ta seizing kaman ze mutu da kyar yake samu ya samu sauki se ya Haɗa kai da gwiwa yayi ta kuka. A haka ya sake shekara biyu a gidan ya cika shekara bakwai, a lokacin ya san yana da wani abu guda ɗaya dake debe mishi kewa yake hana shi shiga damuwa wato ball, ze Haɗa ledojinshi ya sami wuri yayi ta bugawa to fa shine kaɗai zaka ga haƙorin shi yana murmushi se kuma in ya je wurin Daadida da ya kan Saci hanya yaje sama sama da kyar ze tsaya ta kulla mishi abinci a Leda ya tafi saboda kar a gane Babanshi ya kusa kashe shi. Yau ya tashi baya jin daaɗi hakan ya sa yace da ya tsaya zuwa jeji dibowa dabbobin abinci gwara ya korasu suje su ci tunda ya kan fitar dasu, fita dasu yayi zuwa chan wajen gari se ya kaɗa su ya samu wuri ya kwanta tun jiya da rana be ci komai ba yunwa yake ji ga zazzaɓi dake damunshi wadda damuwa da yake ciki ne ya haddasa mishi.. Mutanen gari sun maida shi wani soko,gaula wasu har kallon marar cikakken hankali suke mishi hakan yasa yake iya yinshi wurin gujewa mutane. Yannenshi ko kusa dasu be isa zuwa ba daga me hanbari se me duka, yadikkonanshi babu wacce ta taɓa faɗan abun arziki a kanshi duk bautar da yake musu haka nan uban da ya haifeshi be san zafinshi ba. Kuka yayi sossai a wurin yayi ta jan numfashi daga karshe ya tashi ya kaɗa shanayen suka koma gida, ba tare da ya san a kiwon da suka yi da wasu shanayen akwai wani ciwo dake jikin waenchan wadda suka sakawa nashi ba. Dare shanaye basu barshi ya rintsa ba kan safe wasu abubuwa kaman bulalai suka fiffito musu a kafafu nan take biyu suka cika, hmm misalta irin halin da ya shiga ɓata lokaci ne.. Duka shanayen suka kamu ko da hantsi yayi lokacin da Babanshi ya zo duba shanayen kaman yadda ya saba abunda ya gani ne ya kusa sumar dashi.. Kasa magana yayi yasa aka kira likitan su yazo yayiwa sauran shanayen Allura Sede ana gamawa uku suka sake mutuwa Wayyoooo zubewa kawai Bukar yayi a sume aka fita dashi.. Badi'ah dake kallon yadda Raed ke numfashi da kyar yana fusga ne tace "Wallahi ka shiga uku Raed idan babanka ya dawo ya sameka a gidan nan, ka ga yadda ka kashe shanayen nan haka ze kashe ka, dama jiya ya gama gayamin ya tsaneka tsanar da be taɓa yiwa kowa ba baka da anfani a gareshi, ko kallon ka baya son yi yanzu kaga se ya kashe ka da hujja..." A tsorace yake kallonta.. Suka yi dariya suka tafa da Naja.. Naja tace "yau fa shikenan kwanan wani ya kare kaman yadda mamanka ta tafi har Abada" Mikewa yayi a tsorace ya rabe su ya fice sbd magana shine abu na karshe da zaka ji daga gareshi.. Tunda ya fita yake ta tafiya in yaga mutane se ya raɓe ya wuce idan kuwa namiji ne se ya dauka Babanshi ne ya fara ihu yana cewa yayi haƙuri baze sake ba.. Mutane dayawa sede su ce Allah sarki Allah ya baka lafiya yaro. Gidan David ya tafi duk uban nisan dake tsakaninsu, ya same su da Philip sede ya kasa karasawa se kuka,idan sun matso se ya matsa gabaɗaya ya rikice barin ma in ya tuna yadda aka fita da Babanshi ai in ya warke ya dawo shi ba a sume za'a fita dashi ba sede a mace. Philip da ze wuce Kano ne yace "Pastor I think I will be going with this boy, can't u see he's depressed and he's seriously sick.. Daga ka ganshi zaka san panic attack na damunshi idan uban shi baya sonshi ni ina son shi I will take him with me" Duk yadda David ya so ƙi Philip ma nacewa yayi yace idan yaron ya girma ya dawo da kanshi amma yanzu ba ze bari ya koma ba. Sanadiyar fitan shi Mambila kenan suka tafi Kano sun ɗan kwana biyu Seda Visa ɗinshi da komai nashi ya fita kan suka wuce US anan Philip yake rayuwa da matarshi da kuma ƴarshi mace wadda shekara huɗu Raed ya bata. First jinya ya fara yi sbd yadda ko cikin dare numfashi se ya sarƙe mishi ga mafarke mafarke, ga yawan tsorata rashin son mutane in kuwa ya ga baƙin fata nan take se ya ruɗe. Yana jinyar yana samun sauki a hankali Philip ya sa shi school sede be son boko Sam, da kyar ya gama grade 5 yace shi kam ya gama karatu da Philip ya tambayeshi abunda yake so yace ball. Nan yayi enrolling ɗinshi ya samu trainee wani irin baiwar kwallo yake dashi, nan take ya fara fita wasanni in kana son farin cikinshi ka mishi hiran kwallo, abu guda ɗaya da be bari ba sallah, ya kan Haɗa salloli biyar da dare yayi Dukda be ga kowa nayi ba a gidan. Wani irin shakuwa ke shiga tsakaninsu da Rabecca don da ita kaɗai yake hira har yayi dariya, itace ƙawarshi a komai.. Wasa wasa be sake maganan Gidansu ba seda ya zama shahararren ɗan kwallo ba wadda be san 'R MAI NAGGE' ba se lokacin ya samu Pastor Philip yace yana so ya je gida. Be hana shi ba ya shirya ya tafi Gembu, gidan Daadida ya fara zuwa ya kuwa ci sa'a tana wurin har lokacin rungume shi tayi tayi ta kuka a jikinshi tana mamakin yadda ya wani girma ya zama namiji sede kana ganinshi ba addini ba komai rayuwar Turai kawai.. Da kyar yake iya Haɗa hausa ya tambayi Babanshi fa. Shiru ta ɗan yi kan tace "Babanka babu inda be shiga ba a garin nan don nemanka saboda ya ɗauki mataki a kanka don cutar da ta shigi shanayen nan sune sukayi sanadiyar karyewar arzikinshi duk dabbobbinshi sun mutu, abinci ma gagararsu yake a gidan shiyasa ya ɗauki laifin komai ya ɗaura maka ban san ko yanzu ya huce ba amma duk sadda ze shigo nan se yayi magana marar daaɗi game da kai" Shiru Raed yayi yana kallonta yace "kin yafe mai kenan" Tace "Raed ai ko me bukar yayi min ɗa na ne Dukda ya bakanta min sossai har yanzu kuma zuciyata kuna take in na tuna sede Bukar ko ban yi fushi dashi ba ko ban mishi baki ba Allah ba ze barshi ba ina ga in na mishi baki? Ina mishi tsoron fushin ubangiji Raed" Rumgumeta yayi yace "ban taɓa ganin mutum irin ki ba lallai uwa uwa ce Allah ya ji kan mama" Ta amsa da "Ameen zaka je wurin mahaifin naka ko?" Kai ya gyaɗa ya mike ya je ɗakin da ta sauke shi yayi wanka ya sake kaya, three quarter ne as usual da shirt lokacin Daada ce ma a kanshi a murɗe ya saka ɗan kunne ga sarka a wuyan shi kana ganin shi dae zaka danganta shi da arne. Haka ya fito duk Yadda Daadida ta so ya sauya ki yayi yace mata ma sune kayan shi gabaɗaya, ko da ya fita jama'a suka gane shi da kyar ya tsira ya samu ya je kofan gidansu. Da sallama ya shiga, da Badi'ah ya fara cin karo se kwakwalwanshi ta fara tuna mishi karshen maganganunta gareshi tayi wani kala kaman tsohuwar da ta shekara saba'in, Zarah na tsaye tana zaginta ko sallamar shi basu ji ba seda ya sake suka juyo suna hadiye masifar da suke yi da junansu, ihu suka kurma kowacce ta ruga ɗakinta Badi'ah na cewa "Malam! Malam!! Fito ka ga wani gardi kasurgumin kirista da ya shigo mana kai tsaye gida" Da sauri Bukar ya fito riƙe da sandarshi yace "kai me haka? Me ya shigo da kai cikin gidana?" Raed yace cikin hausar shi da ta bace "Baaba Raed ne baka gane ni ba?" Wani ashariya ya lailayo ya maka tare da sake kiran sunanshi da karfi, Raed ya amsa se ga su Badi'ah sun fito su ma suna maimaita Raed! Seda bukar ya tabbatar shine kan ya ɗaga sandar hannunshi ya lailaya ya muka shi, kara ya saki yana tarewa tare da cewa "Holy christ! What the Fuck" Aiko se bukar ya sake haukacewa "Ni kake zagi da yaren yahudanci? Yahudu ka koma Raed? Dama Alkawari nayi duk randa na ganka se na maka dukan karya ni da kayi Muhammadu Allah ya isa tsakanina da kai, wuta bal bal wallahi kuma ka fitar min daga gida" Badi'ah tace "Raed ashe ridda kayi? La'ilaha illallahu wannan yanzu malam se ya ambaci sunanshi ya Haɗa da naka? Ƴaƴayenmu da suke fama da Gidajen miji ai se auren nasu ya karasa lalacewa aka ji jininmu ya zama Kaɗo" Zarah da Naja ma suka tofa nasu albarkacin suna cewa "kaci amanar Mairamu wallahi da tana nan na san mutuwa ce kawai sakamakon wannan bakin cikin da zaka kunso mata" Bukar ya fashe da kuka yace "Allah sarki Mairamu, wallahi Muhammadu ka sake jingina sunanka da ni ban yafe ba, na tsaneka! Bana so na sake ganinka cikin gidana ko kuma wallahi in yi ajalinka..." Raed da tsabar bacin rai har jijiyoyin kanshi suka nuna ne ya kallesu daya bayan daya yace "ban san wani irin zuciyoyi ne a kirjinku ba, duk abubuwan da kuka min ba wai na manta bane sede anything deserve a second chance! Na yarda every disappointment is a blessing a sadda na ga sanadiyarku na samu daukaka na kuma cika burina na zama ɗan kwallo hakan ya sa ni dawowa gareku, amma ashe halinku be sauya ba.. As from today zan fita a rayuwarku kamar yadda bakwa son ganina I hate u guys so.. Fuck all of u..!" Ya faɗa da karfi kan ya juya ya fice.. Duk baki suka saki suna Kallonshi har ya tafi yana zuwa gidan Daadida ya fara hada kaya duk yadda tayi dashi ya tsaya ƙi yayi itama be barta ba ya ɗauko ta suka zo Kano tare. Ya so su tafi America sede ta ƙi se ya saya mata gida ya sa me aikin gidansu na chan ya sama mishi workers Hausawa ya zube mata daga driver, me girki, da me gadi. Gida ne babba me tsananin kyau don yana da kudade ba na wasa ba kuma ba abunda yake yi dasu banda saye saye, be bar gidan ba seda ya tabbatar ko ashana se sun shekara basu nema ba kan ya koma America..yana zuwa kuma yayi papers a court ya cire sunan Mahaifinshi a nashi ya koma 'MOH RAED' Bayan wani lokaci soyayya me karfi ta kullu tsakanin shi da Rabecca inda aka yi musu aure na church. Shekarar farko ta haifi Norah, tare da ita suka je Kano wurin Daadida taji daaɗin ganinsu Dukda bata jin daaɗin rayuwar da Raed yake sede ba yadda ta iya daga ta kawo mishi maganan yake ajiyewa gefe ya kamo wata. Kwanan su biyu da zuwa ranar Juma'a zata fita sadakar da ta saba ana yi mata masa na mutane ɗari da hamsin bayan sati bibbiyu se ta fita zuwa unguwan masu bukata ta raba musu da Adu'ar Allah ya shirya mata kan zuri'a ya kare su, ya kuma sa su gane daga Raed har bukar da su kan yi waya tana kiranshi tunda ta gayamishi Raed ya dawo da ita Kano ya saya mata gida yace shi da taka inda take har abada sede in ta zo mambila. Ita ta rasa wani irin zuri'a take da, hakan ya sa take dagewa wurin musu Adu'a duk yadda take so Raed ya sauko ya nemi Babanshi su sulhunta a matsayinshi na ɗa Me bukatar albarka iyaye ya ki Sam. Bin ta yayi wurin sadakar se hakan ya bashi sha'awa ya kalleta yace "Daadida shi kuma wannan me anfaninshi?" Tace "Raed Sadaka maganin masifa ce, tana daga cikin abunda Allah yake so me shi ya taimaki marar shi sadaka na da falala dayawa don in kana yi bazaka taɓa taɓe wa ba" Tun daga sannan ya gane shekara shekara yake zuwa Nijeria yayi sadaka, Norah na da 9yrs rabecca ta haifi Farrah yana son familyn shi kaman me, barin ma Yayanshi yana son kayanshi har baze misaltu ba duk abunda suke so shi ake yi, yana sallah sede be taɓa saka Norah yi ba, tare ma suke zuwa church da Rabecca da father... Bayan Farrah na da 3yrs rabecca ta sake ciki inda garin haihuwa ta rasu ita da abunda ke cikin nata, tashin hankalin da Raed ya shiga Seda Father ya ɗauko Daadida don ciwon shi sabo ya dawo ya taɓa career ɗinshi sossai don Seda ya shekara biyu be yi kwallo ba. Da kyar yayi tawakkali yake kula da yaranshi iya yinshi shine duk wani gata nasu, be jima ba da mahaifiyar rabecca ma ta mutu inda suka dawo Paris suke cigaba da rayuwa don tun bayan warkewarshi PSG suka saye shi. DAWOWA LABARI "Toh Hidayat kinji waye Muhammad Raed..." Kuka ya hana Hidayat magana kaman yadda Daadida ma take kukan haka suka katse wayan Haɗe kai da gwiwa tayi tana kuka sossai wani irin uba ne wannan? Wannan Anya ubane? To ko asiri ne? Amma kuma in da asirin ne ma Hali ya tarar.. Allah sarki Raed ashe ya fuskanci abunda ya fi nata me yasa labarin su yayi kamanceceniya? "Miss hidayat" Norah ta sake faɗa karo na uku tana jijjigata ɗagowa tayi tana zub da hawaye yaran karan kansu wani irin son su da tausayinsu ne ya karu a zuciyarta, ganin Norah ya sa ta kara sake wani kukan tana kallonta.. Norah tace "Miss hidayat why are u crying? Look at Aisha is also crying since bcs of u?" Se ta janyo Aishan kawai ta rungume tana cigaba da kukanta wannan labari ba karamin taɓa ta yayi ba. Farrah ficewa tayi da gudu zuwa dakin Mahaifinsu tana buɗewa tace "Dad miss hidayat have been crying since!".. Idanunshi ya zuba mata ganin kaman ta ɗan shiga damuwa don ko murnan ganin Father bata yi ba tukuna, se ma hannunshi da ta rike tace "Dad come nd see Aisha begins to cry also". Mikewa yayi yace "ok I will go nd check now stay with grandpa" Fita yayi daga ɗakin ba tare da ya damu ya sa riga ba cikin mamakin abunda ya sakata kuka, Seda yayi knocking kan ya buɗe ya shiga har tsakiyar ɗakin yacewa Norah "Norah u nd Aisha should go my room nd greet grandpa" Hannun Aisha ta ja suka fice daga ɗakin, wuri ya samu ya tsaya tare da zube hannayenshi cikin aljihu three quarter ɗin a sanyaye yace "Hidayat..!" Da sauri ta ɗago ganinshi kaɗai se taji kaman rewinding labarin shi ake mata, ji take kaman ta tashi taje ta faɗa jikinshi tayi mishi kukan irin halin da ya tsinci kanshi a ciki kila shi be samu yayi kukan enough ba. Kau da kanta tayi daga gareshi don in ta cigaba da kallon narkakkun idanunshi dake bisa kanta, in har ta cigaba da kallon natsatsiyar kyakyawar fuskanshi in har ta cigaba da kallon broad hard chest ɗinshi babu abunda ze hanata karasawa ta rungume shi, an zalunce shi sossai an cuci rayuwarshi cuta me girma.. Karasowa yayi haka kawai yake jin damuwar kukan nata har ƙasan ranshi se zuciyarshi ya bashi maybe ta tuna rayuwarta ne. Bata san wani rashin na iyaye ma rahama ne ba,(kaman yadda shi ya ɗauka) da gwiwa ɗaya ya tsuguna gabanta ya sake ambatan sunanta a tausashe ya ce "Hidayat! But can u please stop this crying? Can you take a deep breath and relax? What ever you are going through is going to be okay. You'll be Okey, you'll feel happy again. Please you have to take care of your self..." Wayyo Allah ji tayi kaman ta kurma ihu.... #like #share #comment                     🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 21* *FREE BOOK* "In shaa Allah we will all be happy again..!" Da kyar ta iya faɗan hakan tana share fuskanta tare da ƙin Kallonshi. Be fahimci me take nufi da we will da tace ba hakan yasa ya miƙe tsaye yana me ci gaba da kallonta ya kai babban yatsanshi ya sosa giranshi kan ya juya ya fice kawai. Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke tare da bin bayanshi da kallo har ya fita, mikewa tayi taje toilet ta wanke fuskanta Tare da fitowa ta sauka kasa ta ɗauko junior wurin Miss Mary, ta dawo ta karasa Haɗa musu table ɗin duk fuskanta ba wani fara'a tana jin hayaniyar su daga wani room kuma na gidan dake daura da na Dad ɗin nasu bata De leka ba ta koma ɗaki tare da shayar da Junior tana Tunanin mafita, ta yadda zata shiga rayuwarshi a hankali ta samu ta karkato da hankalinshi zuwa bautar Allah ɗaya. Har dare yaran basu dawo sun dame ta ba, ko da Aisha ta shigo ce mata tayi Daddy ne ya hana su zuwa kar su takura ta she need a space, murmushi kawai tayi ta shirya yarinyar ta kwanta. Norah ma ta shigo ta mata good night ta kalleta tace "Norah hope u prayed?" Kai Norah ta gyaɗa mata tace "we prayed with Aisha in my room" Murmushi tayi tace "ok kiyi adu'a kan ki kwanta" Tace "good night miss hidayat!" Ta juya ta fice. Kwanan Father biyar ya tafi duk yadda ya so ya sa Raed sallamar Hidayat kin amincewa yayi, dama kuma su abunda basu iya ba takurawa yara Dukda hidayat ta fahimci sarai baya kaunar ta sede tana mishi uzuri don ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar Raed ɗin kuma ta san duk me ƙin ta a bayan umma ne. Ta kan yi waya da ya hamza akai akai don shi da gaske yake son ta yake kuma yana so ya aureta anytime soon. Sanadiyar shakuwarsu da Farrah kuwa shine rashin lafiya da tayi, hidayat ta kula da ita sossai wadda ya kawo kusanci tsakaninsu har yarinyar ta fara son ta, ta kuma fahimci daga miss hidayat har Aisha basu da wani nakasu kawai dae dama kishin Aisha take. Zaune yake a parlor yana aiki a system ɗinshi yayinda yaran suke tare da Hidayat a ɗaki a irin wannan lokaci ne take musu tarihin annabawa, sanin yana parlor yasa ta fara first move ɗinta cikin danne fargabar da ya cika mata ciki tace "mu yi tarihin nan a parlor" Aiko da gudu suka fito itama ta fito, kallo ɗaya ya musu dukansu ya maida idanunshi kan abunda yake yi suka samu wuri suka zauna tare da saka ta a tsakiya. Ba tare da ta kalleshi ba ta fara musu da "yanzu bari mu fara yin tambayoyi akan darasin mu na baya, wa ze gaya min annabawa nawa Allah ya ambaci sunansu a Qur'ani?" Dukkansu uku suka ɗaga hannu ta nuna Farrah. Da sauri yarinyar tace "25" Hidayat tace "Attakbir" Suka ce "Allahu Akbar" "To wa ze kira min sunayensu ɗaya bayan ɗaya?" Norah ta ɗaga hannu ta mike ta fara lissafo su daga kan Annabi Adam (As) har zuwa kan Annabi Muhammad (SAW) zuwa lokacin hankalin Raed ya fara yowa kansu. Alama he started getting Interest akan abunda suke yi, tace "to a Tarihin wa muka tsaya ma?" Suka ɗaga hannu ta nuna Aisha. "Annabi Nuhu(As) inda yayi katoton jirgi saboda tseratar da kanshi da mutanenshi tare da dabbobi daga ruwan ɗufana" Itama takbir tasa aka mata, daga nan ta cigaba musu da tarihin cikin muryarta me sanyin daaɗi, gabaɗaya hankalinshi ya Mika musu yana jin tarihin kuma yana mamaki don be taɓa ji ba, tana yi har ta zo inda ɗan Annabi Nuhu (As) ya ƙi shiga jirgin yace ze hau saman tsauni ruwa baze same shi ba amma daga karshe shima ya mutu don yana daga cikin taɓaɓɓu. "Wani darasi kuka koya cikin wannan Tarihi?" Nora ta ɗaga hannu tace "Ba zaka ɓoyewa Allah ko ka guje mishi ba in de har ya tashi kama ka da laifukanka" Takbir ta sa aka mata tare da Satan Kallonshi se suka Haɗa idanu, fuskewa yayi ya maida kanshi kan system ya cigaba da aikinshi da ya ma manta me yake yi. Wa'azin Bin othman ta kunna musu a iPad ɗin ta inda yake magana akan sallah. Inda ya ɗauko ta da zafinta yake cewa "Allah madaukakin sarki cikin Suratul Maryam aya ta 59 yana cewa 'se waensu en baya suka zo a bayansu suka tozarta sallah kuma suka bi sha'awowinsu. To da sannu a hankali za'a jefa su cikin gayyah" Allah SWT ya kuma cewa 'sede wanda ya tuba, kuma yayi imani ya kuma aikata aiki na kwarai' shima cikin Suratul Maryam aya 60." Babban Sahabin nan ibn Abbas Allah ya qara masa yarda yace "ba wai sun wulakanta sallah bane ta hanyar barin ta ba a'a kawai sun kasance sun jinkirta yinta ne akan lokacin ta" Kunga kenan da wannan fassarar ta ibn Abbas zamu fahimci cewa lallai waenda suke jinkirta sallah akan lokacinta wato basu yinta se lokacin da suka ga dama wannan aya akan su take, waenda suke wulakanta sallah da sannu a hankali zasu afka cikin wutar gayyah bayan mutuwar su, lallai kuma zamu fahimci cewa wanchan ayan ba tana magana ne akan kafirai bane a'a tana magana ne akan waenda suke ikirarin su musulmai ne! Saed ibnul musayyib imamat-tabi'ina Allah yayi masa rahama yana cewa dangane da wanchan Ayar sai yace "sune waenda basu yin sallar azahar har se lokacin la'asar, basa yin la'asar har se lokacin magrib basa yin magrib har se lokacin isha kuma ku sani duk wadda ya mutu yana a cikin wanna hali be tuba ba lallai alkawarin Allah a tattare dashi ita ce wutar gayyah! Wato wani Kwari ne a cikin wutar Jahannama wadda yake da zurfi mai nisa  kuma zasu dinga cin wani mummunan abinci me wari da ɗaci da uquba" Lokacin magrib da yayi ne ya sakata tsayar da Wa'azin tana me satar kallon shi, tsikar jikinshi tayi wani irin tashi idanunshi sun sauya, saboda yadda bin Othman ɗin ke Wa'azin dole In kana cikin masu aikata irin laifin hankalinka ya tashi. Jin tana cewa yaran suje su yi Sallah ya saka shi ajiye system ɗin shima ya miƙe ya nufi ɗakin shi don yin sallar. Da kallo ta bishi har ya shige, he's so soft and gentle sannan zama da yayi da su Philip ya hana shi tabuka komai a addininshi wadda ba laifin kowa bane laifin Mahaifinshi ne, kuskuren shi shine da ya girma ya mallaki hankali me yasa be nema sani da kanshi ba? Allah ba ze karɓi hujja akan Babanshi ba sede a karan kanshi. Tana fata ya sauya a hankali. Yana shiga yayi alwala ya zo ya gabatar da sallar bayan ya idar ya zauna se ya rasa Adu'ar da ze yi, be san ta yadda ake tuban ba cikin wani irin ciwo da zafin zuciya ya ɗaura fuskanshi bisa tafukan hannunshi hawaye masu zafi suka gangaro mishi. Wasa wasa kullum tare dashi ake jin tarihin annabawa da kuma wa'azuzzuka, wani Wa'azin mufti menk da yayi akan girman uwa da kuma muhimmancin yi mata Adu'a idan ta rasu yasa ya kasa rike hawayen shi wadda a idanun Hidayat suka ganganro da sauri ta kauda kanta itama idanunta na cika da hawaye. Ita karan kanta in ta ji irin Wa'azin nan se tayi kuka, mahaifiyarta mutuwa tayi sede bata san ta yadda ta same ta ba har ta faɗa hannun Abba, bata taɓa Tunanin ta hanya me kyau aka sameta ba Dukda yadda Abba ke yabon halayyar mahaifiyarta kan rasuwar ta.. Tambayoyi ne Bila adadin a kwakwalwanta sede bata da me amsa mata. Magananshi ne ya katse mata Tunanin da ta tafi. "Miss hidayat! Ya ake Tuba?" Ta kalleshi da kyakyawan idanunta da suka cika da hawaye murmushi na wanzuwa a fuskanta tace "sharudan tuba guda uku ne, na farko yin nadama bisa abubuwan da ka gabatar na zunubanka.na biyu ɗaura niyyar cewa bazaka sake aikata irin waenan laifukan ba nan gaba a cikin rayuwar ka, abu na uku shine ka dena aikata aikin saɓon nan take ko da ka kasance kana chuɗanya da ita" Kai yake gyaɗawa cikin fahimta tace "idan da hali ka yawaita ambaton Allah in shaa Allah ze yafe maka duk wani zunubanka" A hankali yace "thank you! I want to learn from you" Da sauri ta kalleshi shima kallonta yake alamun tabbaci, ya sake cewa "ki faɗi ko nawa ne zan biya ina so na koyi abubuwan da kike koyawa yaran nan! I want to pray for my mom" Wani irin daaɗi ne ya rufe ta cikin murmushi da har yake nuna hakwaranta tace "bana son ko Naira daga gareka, zan yi saboda Allah.. Nima ba kwararriya ba ce koyo nake har yanzu" Ze yi magana wayanta ta ɗauki ƙara Aisha dake rike dashi tace "laaa Daddy hamza ne" Karɓar wayar tayi Dukda yadda take jin kaifin idanunshi kanta hakan be hana ta ɗauka ba tace "nayi fushi fa!" Daga ɓangaren shi yace "Afuwan gimbiya ai in kika yi fushi da ni se in kashe kaina...!" Dariya sossai tayi kaman gaske, yace "kina Tunanin wasa ne ko hmm, yanzu ma kasa hakura nayi da kewar ki dake addabata na taso na zo har Paris" Wara idanunta tayi tace "Da gaske don Allah?" Yace "sa wasa" Tana dariya ta mike ta shige ɗaki suna me cigaba da wayan inda ya tabbatar mata da gaske yana Paris yanzu fa rabon da ya ganta yayi 3months, kuma ita yake son kallo da yamman nan, da kyar ta yarda zasu fita da yaran gabaɗaya. Shiryawa tayi cikin doguwar Abaya black and red ta sa red shoe, tare da riƙe handbag red ta fito tace "gurls who's in for outing" Ihu duka suka yi kan suka miƙe da gudu kowa yaje ya fara shiri don ta koya musu saka mayafi duk nata ta babbasu tace su ke rufe kansu in zasu fita. Tunda ta shige ya jingina da kujera tare da lumshe idanunshi, yana jinsu suna hayaniyarsu har suka fito ta kalleshi tace "Daddy mun fita" A zuciyarshi ya maimaita wani daddy mun fita, kwafa yayi yace "in zaki fita ki tafi ke kaɗai don't involve my children" Da sauri duk suka kalleshi daga yadda yayi magana zaka san ranshi a mugun bace yake, a sanyaye ta sake hannun Farrah dake cikin nata har zuciyarta maganan be mata daaɗi ba se kace wacce zata je yin aikin zunubi? Kau da kanta tayi daga Kallonshi tace "ok Farrah, Norah u should sit at home" Ta kama hannun Aisha tana rike da Junior suka nufi gangarawa se Farrah ta saka kuka, Norah na Kallonshi da puppy face tace "Daddy pls, we want to go also na san Miss hidayat zata kula damu kuma bazata bari mu yi dare ba, look at how she's upset ga Farrah na kuka" Yatsunshi masu kyau da tsari ya cusa cikin gashin kanshi tare da hautsinawa yana me fitar da iska, fuskanta kaɗai da ya nuna rashin jin daaɗi yake gani a idanunshi yana jin wani irin sabon damuwa na bijiro mishi. Murya chan kasa yace "follow them bfr they leaves!" Da gudu suka ganganra ya koma jagwab ya jingina da kujera cikin tsananin mamakin abunda ya faru a yanzu, be taɓa jin hakan ba duk yadda ya so ya saka shi a mizanin hankali ya auna yaga dalilin jin haushin shi be gani ba. Har magrib yayi yana zaune doing nothing a wurin banda tunane tunane daga baya ya mike yaje yayi sallah, da laptop ɗinshi yayi searching karatuttukan malamai inda ya zaɓi na Sheik minshawi don ya fi mishi natsuwa ya saka yana saurare Dukda ba iyawa yayi ba sede ya samu natsuwa me yawa daga sauraran Alqur'anin. Awa guda chur ya kwashe a wurin yana ta searching wa'azuzzuka yana downloading, bayan ya gama ya tashi yayi isha daidai lokacin ya ji hayaniyar shigowansu. Dakinshi su Norah suka yo suna nuna mishi shopping da Daddy hamza yayi musu, kallon kayan kaɗai ɓata mishi rai yake gyaɗa kai kawai yayi yace suje su ajiye a ɗakin su suka juya suka fice. Mikewa yayi ya fito ya samu wuri ya zauna yana kallon cook ɗinshi dake jera mishi abinci a bisa dining sede ba taste ɗin abincin cook ɗin yake so ba, taste ɗin abincin da ta bashi a sadda bashi da lafiya yake kwaɗayin sake ji. Junior ne dake Tatata ya fara fitowa yana ganinshi ya fara miƙa mai hannu yana dariya, mikewa yayi yaje ya ɗauko shi yana cilla shi sama yaron na ta dariya, fitowa tayi da nufin kama junior don Aisha ce ta bar kofan buɗe har ya fito turus tayi saboda kusa faɗa mishi da tayi da sauri ta ja baya tana me kau da kanta. Gyaran murya yayi yana me kallon fuskanta yace "I'm sorry for earlier" Ɗan Kallonshi tayi ta ga still ita yake kallo cikin sanyin muryanta tace "ya wuce ai" Kai ya gyaɗa yace "in da gaske ya wuce i want to start my lessons now" Kai ta gyaɗa ta koma ɗaki ta ɗauko iPad ɗinta ta fito zaune ta same shi ya ɗaura junior kan kafanshi yana mishi wasa, a ƙasa ta zauna tare da tankwashe kafafu shima kasa ya komo yayi irin zaman da tayi, ɗan muskutawa tayi ta kalleshi ya ɗaga mata gira alamun what? Kau da kai tayi tace "daga ina zamu fara?" Yace yana buɗe system ɗinshi "we have to go for Qur'an and Islamic books shopping it's embarrassing bamu da ko guda a gidan" Kai ta gyaɗa cikin yarda da abunda yace. Ya sake cewa "See ni fa apart from these three surah ban iya komai ba kuma" Dariya ne ya kama ta jin yadda yake maganan da iyakar gaskiyar shi ko kunya baya ji murmushi tayi har haƙorinta ya bayyana, tace "zaka koya ne a hankali maybe u r a fast learner" "Uhmm to Allah yasa kar in baki kunya in ganki gobe da bulala" Sossai ta saka dariya ashe ya iya cracking jokes, shi kuwa he was lost da ganin dariyar a fuskanta hakan yasa ya cigaba da kallon ta yana kallon irin baiwar kyau da Allah yayi mata. Haɗa idanu suka yi tayi saurin hadiye dariyar tana muskutawa, bismillah tayi shima yayi ta fara mishi daga Suratul adiyat. Masha Allah muryanshi har tada mata tsikar jiki yake duk da yadda yake cracking na en koyo sede yana da murya me tsananin daaɗi da ratsa zuciya, aya biyar din duka suka yi. Bayan sun gama yayi mata godiya murmushi kawai tayi tana gujewa eye contact ɗinshi duk jikinta amsawa yake a duk sadda suka Haɗa idanu. "The girls basu yi having dinner ba kar su yi bacci" Ta girgiza kai tace "they slept already dama sun ci a waje" Kai ya gyaɗa, mikewa tayi zata ɗauki Junior da yayi bacci a kafafunshi ya ɗan sosa kai yace "am starving" Kallonshi tayi ta kalli dining area tace "in kawo maka abincin nan ne?" Girgiza kai yayi yace "i don't like that, please wani abu zaki min me sauƙi if possible" Yadda yayi da murya alamun roko ne ya so bata dariya se ta danne kayan ta tana mamakinshi Dukda kasancewar shi me kuɗi kuma oganta baya abu da gadara, ze iya bata umarni kawai ta cika amma ji yadda yake rokon ta. Kitchen ta nufa shi kuma ya zauna ya cigaba da koyon ayoyinshi Qur'ani na ratsa zuciya da ruhinshi be san akwai wata natsuwa ta musamman daga cikin Qur'ani ba se yanzu. Duba time yake yana da training gobe a stadium ɗinsu it's getting late, call ne ya shigo mishi ya duba yaga Kimorah shi har ya mance da ita ma, ɗagawa yayi yace "hey!" Nan ta fara Mishi shagwaban wai ya manta da ita daga tayi tafiya, a natse yake amsa mata kaman yadda tsarin shi yake cikin tsararriyar muryarshi dake kashe ta da son shi da kuma kishin shi. "Kinga bana son rigima, I have a training to attend as early as possible nd it's getting late we talk tomorrow" Daidai lokacin hidayat ta dawo riƙe da karamin tray, a kanshi bowl ne gefe tissue da spoon se ruwa me rangwamen sanyi. A gabanshi ta ajiye tana sauraran irin kalaman da Kimorah ke mishi sbd wayan a handsfree yake, haka kawai ta tsinci kanta da jin haushi ranta yayi baƙi nan take da ta rasa dalili, ba tare da ta kalleshi ba ta ɗauki junior ta juya tayi ɗakinta, lumshe idanunshi yayi sbd kamshin ta da ta bar mai me kashe jiki ya ware su bisa kanta har ta rufo kofan ba tare da ya san me kimorahn ke cewa ba. Daga karshe sallama suka yi ya janyo abincin ya fara ci, shi ɗan kwallo ne yana da ci sossai sbd training da suke yi yana saurin burning colories a jikinsu, da ɗan yawa tayi dankalin na turawa da ta sarrafa shi da kifi yaji kayan haɗi ga persely da yayi garnishing abincin kamshin kaɗai ze tsinka maka miyau, tas ya Cinye abincin ya sha ruwa kan ya mike ya kai tray ɗin kitchen ya dawo ya kashe komai ya wuce room ɗinshi duk abunda yake yin nan kuma yana sake biya karatun shi a ranshi. #like #share #comment                     🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 22* *FREE BOOK* "ASSalamu Alaikum pls can I sit here?" Ta faɗa tana kallon Hidayat. Murmushi tayi mata tace "Wa'alaikumussalam warahmatullah, bismillah..!" Zama kyakyawar matashiyar black beauty tayi tace "thank u, am rashida from Nigeria and you?" Tayi murmushi tace "masha Allah, nima sunana hidayat daga Nigeria" Wani irin zaro Idanu Rashida tayi tace "kaiii wai dama ke ƴar Nijeria ce? Wow kin san Allah kullum ina kallonki na ɗauka irin Larabawa lebenon ɗin nan ce, masha Allah sister u r so beautiful" Tayi magana tana kallon orange gyale da Hidayat ɗin tayi wrapping ya fito da fuskanta dake nan smooth gwanin kyau. Dariya ta ba hidayat wadda seda ta dara, tace "haihuwar Nijeriya girman Nigeria kuwa!" Ita dae Rashida na ta mamaki ga hausa radau bakin hidayat kam, tace "Ina karanta MBBS second semester 100lvl ke fa?" Tace "law, nima second semester 100lvl, ashe tare muka shiga" Rashida tace "ai ko na samu ƙawa dama tunda na zo ni kaɗai nake yawo kaman aljana" Hira suka cigaba da yi, rashida buduruwa ce kuma wayayyiya daga ganin ta kuma ƴar gidan manya ce gata da surutu, nan take suka saba da Hidayat, kan a tashi har sun shaku tare suka fito daidai lokacin da taji saƙo a wayanta.. Dubawa tayi taga an "at the entrance of ur school just passing-by nd I guess it's ur closing time, can I pick u up?" Duba sunan ta sake yi "Sir Raed" Tana shirin dauke idanu kenan kuma wayan ya fara ringing "ya hamza!" Ɗagawa tayi ta gaida shi ya amsa yace "Ina gate ɗin ku kin tashi ne?" Rikicewa tayi tace "am uhmm ai.. ai na wuce tuntuni" Shiru yayi kan yace "is ok, zamu haɗu anjima ko?" Kai ta gyaɗa tace "in Shaa Allah by the way it's Friday half day ne ai" Yace "ok see u later" "thanks" ta faɗi tana kashe wayan. Seda ta tsayar da Rashida na mintuna taga tafiyar hamza kan suka fito sallama suka yi da Rashida ta tafi ita kuma ta nufi motan cikin tafiyan ta na natsuwa, in ka ganta bazaka ce ta haihu har uku ba, yarinya ce wacce ko 25 bata rufa ba amma kaddara da rabo ya zaɓa mata wahalar rayuwa. A jikinta take ji kaman ana kallonta sede batayi kuskuren ɗaga kai ba har ta isa motar ta buɗe gaba ta shiga, sanyi da kamshin motar na dukanta. Sanye yake da kayan kwallo har takalmi da alama shima tun safe se yanzu yake shirin komawa gida, cikin muryarta me sanyi tace "Good Afternoon sir" Ba tare da ya kalleta ba Yace "Afternoon how's studies" Tace "Alhamdulillah!" Babu wanda ya sake magana a cikinsu banda qira'ar minshawi dake tashi se take jin wani sanyi sanyi na shiganta ga tausayinshi na rufe ta don da gaske yake shirin koyon Addininshi dole ya tsani Mahaifinshi yanzu ma Allah ne kaɗai ya san da irin damuwar da yake kwana. Ya gyara parking bayan sun shiga gidan zata sauka yayi gyaran murya hakan ya sakata dakatawa, dashboard ya buɗe ya fiddo wasu Fararen takarda ya miƙa mata "5 tickets ne to Merseille, taking off in 2hours we're going for our Islamic shoppings" Da sauri ta kalleshi se suka Haɗa idanu kawar da nata tayi fuskanta na nuna rashin jin daaɗin tafiyan saboda ta tabbatar hamza ba ze taɓa jin daaɗi ya tako kafa da kafa daga Nijeriya ya zo wurinta ita kuma ta kara gaba ba. A hankali tace "school fa? I nd the kids!" Yace "we r coming back on Sunday and today is Friday I guess" Ajiyar zuciya ta sauke ba ta yadda zata kaucewa tafiyan, sede bata san yadda zata yi da hamza ba. Da ma ta bari ya ganta yanzu amma kuma Raed ogan ta ne bazata iya ƙin karɓar taimako da yake son mata na rage mata hanya ta bi hamza ba by the way it's her pleasure, mata nawa a duniya suke da Burin ganin su kusa da wannan celebrityn.. Sauka yayi ba tare da ya ce mata komai ba ya shige cikin gidan, itama saukowa tayi rungume da jakan ta ta shige, tana shiga yana karasa haurawa stairs da Junior da ya ɗauka a parlorn a kafadanshi. Itama haurawa tayi ta shige ɗakin ta se taji text ta duba shine yace kar su ɗauki kaya ko guda. Kitchen ta shiga ta sama ma yaran abunda zasu ci bata da cikakken kuzari don bata san me zata cewa hamza ba, kan ta gama suka shigo Norah ta saka tayiwa Farrah wanka ita kuma tayiwa Aisha, take suka fito gwanin kyau kowacce ta rufe gashinta Dukda ba Atampha bane ko jallabiya ba. A dining suka zauna, daidai lokacin ya fito shima shirye cikin wasu designers Versace riga da wando da ya amshe shi sossai, ya chanza ɗan kunne daga wadda ta gani ɗazu a kunnenshi kafafunshi sanye da rufaffun takalma na kamfanin Fendi, hannunshi sanye da diamond Rolex watch kamshinshi duk ya cika wurin kaman babu wani kamshi se nashi, yana rungume da Junior. Shima dining ɗin ya zauna yana amsa gaisuwar yaran fuskanshi ɗauke da fara'a, kau da kanta tayi daga Kallonshi shima tayi serving ɗinshi ta kai gabanshi ta saka hannu ta karɓi junior cikin taka tsantsan idanunta akan gashin kanshi da ya sauko ta gefe har ƙasan idon shi na hagu ƙasan black saman ba ja ba ba kuma fari ba an kwashe gefe da gefe zuwa kan ɗan kunnen da yake ta kyalli. Ajiyar zuciya ta sauke ta ja baya rike da Junior, a hankali zasu zo kan waennan abubuwan dole ya san haramcinsu. Juyawa tayi ta bar su yana musu surprise na tafiyan su kuwa suna ta ihun murna, murmushi tayi kawai tana jin yadda Aisha take turanci yanzu masha Allah, yarinyar ta samu kyakyawar rayuwar da take musu fata Allah sarki Usman, tuna hakan kaɗai ya saka hawaye cika idanunta. Wanka tayiwa junior ta shirya shi kan itama tayi ta shirya cikin Jallabiya peach ta saka wani karamin baby hijab me stones baya da gaba ya ɗan fi tsawo akan gefe da gefe shima peach amma ya ɗan turu saɓanin Rigan, kwalli kawai ta saka a idanunta tare da lip gloss ta fito. Duk a parlor ta same su suna ganinta suka miƙe suka sauka, itama ta bi bayansu Seda yayi magana da su Miss Mary kan ya shiga bayan motan da Paul ya buɗe mai, mota biyu suka yi zuwa Train station sarai zasu iya tafiya a jirgi su isa cikin mintuna sede haka kawai yaji ya fi son su tafi a train ɗin which will take them 3hours da wasu mintuna. VVIP aka yi musu reserving, be sauka ba seda ya saka face mask da glasses saboda mutane, in ka gansu se ka sake kallo zaka ɗauka wani big happy family ne yana rike da Junior yayinda Hidayat ke rike da hannun Farrah, Norah Da Aisha suna tsakiyar su. Ita kam bata taɓa shiga train ba, ta dauka yadda ake kallon na India ɗin nan me cunkoso da mutane dayawa zata gani se taga sun shiga wani hadaddiyar room wadda bazaka ɗauka a cikin train yake ba in kana ciki. Lufas ne manya masu faɗi kuma zagaye da ɗakin harda fararen labule center table da TV, akwai kuma toilet. Zama suka yiyyi ta zauna daura dashi tare da ɗan yaye labule tana kallon waje, daidai jirgin ya tashi wayanta ya fara ringing.. Dubawa tayi taga Hamza, a sanyaye ta ɗaga suka gaisa ya tambaye ta meeting point, ƙasa tayi da murya sossai yadda baze ji ba Dukda tana jin idanunshi a kanta ta fara yiwa Hamza karya a zuciyar ta tana tuba, akan an basu wani group assignment wadda zasu yi a Mersellei ita bata san ma da tafiyar yau bane kawai kiranta aka yi aka bata ticket. Daga muryanshi ta san be ji daaɗi ba, for the first time ta mishi en kalamai masu kwantar da hankali har Seda yayi dariya cikin jin daaɗi yace kuma ze jirata, tace "matarka fa? And aikin ka fa?" Yace "duk zasu yi hakuri don ko na koma baza su gane min ba don hankalina da ruhina Duka zan bari a Paris" Dariya tayi har haƙorinta ya bayyana tace "shikenan we talk later" Yace "take good care of your self" Daga nan suka yi sallama, ɗaga idanu tayi ta kalleshi bayan ta sauke wayan se taga yana jingine idanunshi a lumshe. Yaran tuni sun fara bacci kuma duk wurin ya ishe su su kwanta har da blanket ɗin rufuwa, itama jingina tayi ta kunna wayanta ta hau temple run, ta jima a haka kan ta sake ɗaga kai ta kalleshi se taga shima ita yake kallo da idanunshi da suka ɗan birkice, kanta ta mayar ƙasa daidai Wayanshi yayi kara dubawa yayi bayan ya kusa tsinkewa ganin Daadida ne yasa be ɗaga ba seda ta ya katse ya kirata back. Gaisawa suka yi, ta tambayeshi lafiyan yara yace "Alhamdulillah" "Raed har yanzu dae akan maganan mahaifinka ne ko yaya yake uba ne, ina jiye maka fushin ubangiji..." Cikin sanyin murya yace "wanni fushin ubangiji ɗaya bayan wadda ya sa ni a ciki? Daadida he abandoned me ko kaina ban sani ba, you also left me after na fara just koyon some verses na Alqur'ani wadda da su nake salla, sallar ma na ganin dama without knowing me nake jefa kaina, ban koya ba bare in koyar da yarana suma gashi sanadiyar baƙin hali da zuciya irin na ubana suma na cutar dasu especially Norah wacce ta girma bata san wani mahalicci ba... I've made it clear to you Kaman yadda baya so na I don't fucking care and I also don't like him as well.." Yana kai nan ya sauke wayan, tare da cillata ta daki jikin train ɗin wannan haɗin kan da Daadida ke so ba ze taɓa wanzuwa ba, da zafin zuciya da kuma ƙuna yake kwana yake tashi tun daga sadda ya fara fayyace laifukan shi a wurin ubangiji, me za'a yi da uba irin nashi tabbas da ana chanzawa suna da ya jima da chanzawa.. A hankali ta miƙe ta dawo gefen shi da ɗan rata tsakaninsu ta sa hannu ta ɗauki Wayanshi ta maida mishi kusa dashi, da wayanta tayi anfani tasa qira'ar Maher cikin Suratul Isra'i, shiru duk suka yi banda bugun zuciyoyinsu da ƙaran karafunan jirgin ƙasan se sautin karatun dake tashi babu abunda kake ji, kamshinsu ya haɗu ya bada wani yanayi me wuyar fassara a temperature ɗin jirgin. Itama jingina tayi tare da lumshe idanu tana sauraran bugun zuciyarta cikin mamakin sauyawarshi, sun jima sossai a haka se ajiyar zuciya yake saukewa da shi kaɗai ne hawaye ze zubar har ya samu zuciyarshi tayi sanyi amma yanzu ba ze iya ba kuma karatun ya taimaka mishi.. Bayan ya ƙare se wurin yayi tsit, a hankali ya buɗe idanunshi ya zube su bisa fuskanta yana ƙare mata kallo. Tana da kyau ya ayyana a ranshi daga kan gashin dake kwance lublub daga gaban goshinta zuwa idanunta masu fusgan hankali, karan hancinta da ɗan karamin bakinta ya karewa kallo kan yace cikin ƙasa da murya "Malama!" Da sauri ta buɗe idanun ta zube su cikin nashi wadda seda ya ɗauke nashi saboda dokawar zuciya da ta riskeshi har yana ji kaman zata iya jin ƙaran bugun daga inda take. "Uhm" Yace "Ki kara min karatun" Tace "tohm amma zaka bani wadda na baka ko? Don in san ko ya zauna" Ya gyaɗa kai kan yayi bismillah ya fara karantowa lumshe idanunta tayi muryarshi akwai daaɗi haka kawai ma bare yana rero karatu me ratsa zuciya bayan ya gama ta kara mishi da next surah, abunda ya ɗauke hankalinsu kenan har suka isa. Motoci biyu na train ɗin yayi hiring ya kaisu best hotel na garin "hotel sofitel" wadda yake tsakiyar ruwa, garin shima ya ƙawatu iya ƙawatuwa don shine second biggest city na France kuma akwai Arabs France dayawa a garin don tana ganin masu hijabs gasu nan birjik.. Suits biyu yayi reserving manya tsararru, sauran yinin a hutawa suka karasa washegari Asabar suka fita around 10, wani tsararriyar shopping mall suka je babu abunda babu a wurin sayayya har Seda ta tsorata ganin irin uban abubuwan da ya saya ba Qur'anai da littatafai ba a'a har da Abayoyi tsararru qirar ƙasashe daban daban su huɗu ya kwasar musu kusan hamsin, shima ya sayi jallabiyoyi masu kyau da tsada. Changing room ya shiga ya cire Rigan jikinshi ya saka wata ox blood jallabiya qirar ƙasar Qatar an yi mata ado da surfani ta gefen kirjinshi ta hagu ba karamin kyau jallabiya tayi mishi ba barin ma da bata je ƙasa chan ba tana bayyana wandon jikinshi wadda designer ne. Ko da ya fito kasa ɗauke idanunta tayi a kanshi shi kuwa murmushi ya sakar mata tare da dage gira alamun ya ne? tayi saurin kau da kai tana murmushi Masha Allah, ya fita kaman irin Larabawa masu ɗan duhu duhun fatan nan, barin ma jajayen lips ɗinshi da ya ɗan saka a baki yana tsotsa. Yaran se complementing ɗinshi suke yace ai ko barin kayanshi ze yi, duk zaɓar musu yayi suka sauya, wani Emerald green Abaya me stones na asalin Larabawa ya ɗauko ya miƙa mata. Ta kalli Rigan kan ta sa hannu ta karɓa ta mike ta shiga change room. Ko da ta sauya ta juya ta kalli kanta seda ta sake kallo, ba karamin kyau tayi ba murmushi ta saki tana shafa kayan kan ta yafa gyalen da kyau, ta fito cike da jin kunya sbd adon Rigan yayi yawa dole ya fisgi hankali. Idanu kawai ya zuba mata tana tsaye tana wasa da fingers ɗinta, ihun yaran ne ya dawo dasu daga duniyar da suka tafi suka tattara yayi payment suka fita. Yawo sossai suka yi a garin suna buɗe ido, wani wurin har yabon su ake da nice family sede yayi murmushi, se chan dare suka dawo. Washegari ma haka suka tafi yawon se biyar suka yi airport da loggage da basu zo dashi ba. Karfe shidda na yamma a Orley Airport yayi musu su Paul suka zo suka dauke su zuwa gida, 2days ɗin a wurin su duka was among the best days of there life, duk sun tsinci wani farin ciki da har yanzu sun kasa fayyace ma menene. A parlorn sama suka yi turus suna kallo gabaɗaya an sauya tsarin parlorn an chanza kujeru an yi shelf me girma da katon wurin sallah da ya ƙawatu ga kyakyawar darduma milk da ash dake shimfiɗe wurin kuma hasken shi me duhu ne se ya bada wani kyaun burgewa. Bayan sun yi isha suka zo suka shirya Qur'anai da kananun hadisan da suka sassayo a shelf ɗin se ya karasa kawata parlorn. Se murmushi yake yana ji yanzu za'a iya kiranshi cikakken musulmi, Kallonshi tayi tace "thanks" Yace "for?" Yana narka idanunshi cikin nata. Ta fusge a sanyaye tace "the shoppings" Yace "ko duka kuɗaɗen da na tara a duniya zan baki ban biya ki ba, u r an angel in human form..." Sautin kiran wayanta ne yasa yayi shiru tare da Juyawa kawai ya wuce ɗakin shi. Duba wayan tayi se taga number, bata san waye ba kuma ba Rashida ba picking tayi cikin mamakin yadda wani ya samu layinta.... #like #share #comment                     🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 23* *FREE BOOK* "Na tabbatar ba se na nemi sani ba ina magana ne da Hidayat daga Paris kike ko ma ina ne... Ba na kira bane in ji muryanki ko maganan ki ba na kira ne in buga miki gargadi me karfi akan mijina... Wallahi wallahi in baki fita hanyar mijina ba se na zama ajalinki! In baki ji tausayina ba nima ba zan ji naki ba.. Kaman yadda ya tsallake ya bi ƙasa ƙasa ya tafi wurinki har wata uwa duniya be damu da ya barni da tsohon ciki ba haka nima zan tsallako in zo har inda kike in halakaki in baki kyalemin miji ba.. Daaɗin abun Kuma kema macece kaman yadda kika min Allah yasa a miki ninkin ba ninkin, bazawarar banza..!" Tsit aka kashe wayan, tsamm hidayat ta tsaya a tsaye kaman an dasa ta tana kallon fuskan wayan da dama a hansfree ta saka, daga bayanta ya ɗan leko fuskanta don ya saka hannu kenan a kofan ya fara jin muryar yayi niyyar shigewa sede jin yadda ko ma waye magana take a harzuke da bala'i yasa ya dawo da baya. Hannunshi ya saka yayi waving fuskanta se tayi firgigit ta dawo da sauri ta kalleshi tana fiki fiki da ido wadda ta saka shi dariya, duk yadda ya so ya danne seda sautin dariyar ya fito. Yace "Au wai dama bazawarin naki ma me mata ne?" Raurau tayi da idanu ya sake sakin yalwataccen murmushi tare da ɗaga duka hannunshi yana shrugging kafaɗa yace "I surrender! Ni ba ni na kar zomon ba" Bata san ta Harare shi ba seda ya zaro Idanu duka waje yana kallonta da sauri ta shige zuwa room ɗinta tana ɗan murmushi, bayan ta shiga a fili ta furta "nima na rama.." Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kallon fuskan wayanta, layin Nigeria ne kwarai kenan matar Hamza ce, baki ta taɓe ita bata san a gaske hakan na faruwa ba seda ya faru a kanta a yanzu, abunda ya daure mata kai shine yadda mata suke iya furta yin ajalin mace akan ɗa namiji, Hausawa suka ce maza ƴaƴan mamansu.. Lallai kam. Aisha da su Noor da suka shigo ne yasa ta mance Tunanin wata matar Hamza da ta kirata, da shirin kwanciyar su suka ce yau a ɗakinta zasu kwana. Gadon ta bar musu ta sauka kasa da blankets masu taushi, Seda ta tabbatar sun yi Adu'a kan suka kwanta. Wayanta ne yayi ringing ta duba taga hamza se matarshi ta faɗo mata, baki ta ɗan taɓe kan ta ɗauka suka gaisa yace "gobe kam in Allah ya kaimu zan ga hasken raina" Tace "uhmm hasken ranka kam na chan ka barota Nigeria.." Yace "ban gane ba!" Tace "manta kawai, ya Paris to?" "Babu daaɗi tunda baki a kusa dani" Tace "hope kana ji daga wurin Aunty na?" Dariya yayi sossai yace "Zainab ɗin ce Auntynki?" Tace "eh mana, itace first wife ai Allah ya riga ya bata girman" A ranta kuwa tace Ashe sunanta zainab! Sama sama suka ɗan ƙara hiran kan suka yi sallama ta kwanta itama. Washegari kaman yadda ta saba da wuri ta gama musu komai suka fice a tare shi kam har lokacin be baro ɗakin gym ɗinshi ba ma. Bayan sun gama lectures suka haɗu da Rash, hira suka sha seda taga call ɗin hamza kan ta kalleta tace "kina da wani class ne?" Tace "A'a am done for today ya akwai outing ne?" Tayi maganan tana dage gira, dariya hidayat tayi tace tana ɗaukan call ɗin "ke yayana ne" Daga bayansu suka ji an ce "ta faɗi ba daidai ba husband to be dae" Da sauri duk suka juya, dariya tayi tace "ya aka yi ka gano mu?" Yace yana me kallon irin fresh da tayi da wani kyaun da ta kara "taya ba zan gano ki ba ke fa tauraruwa ce a cikin taurarin ma Zara kinga ko ko da zaki ɓuya cikin gajimare hasken ki baze dusashe ba" Rash tace "uhm bari na matsa kar in kurumce" Dariya duk suka yi, Hidayat tayi musu introducing juna suka gaisa, fita suka yi daga school ɗin zuwa wani hadaddiyar wurin shakatawa, Seda suka ci abinci kan rash ta mike tace bari ta ɗan zagaya ta fice ta bar su tare. "Tsakani Da Allah hidayat hankali na ya kasa kwanciya da aikin kin nan a gidan wannan ɗan kwallon, kin san ana cewa sunan musulmi kawai yake amsawa amma yayi Ridda tun yana matashi lokacin da kuɗi ya fara ratsa shi.." Lumshe idanunta tayi tana jin ba daaɗi kan ta buɗe tace "ka ce Astagfirullah Ya Hamza! Wallahi wallahi kaman yadda muke sallah haka shima yake yi, kaman yadda muke karatun Alqur'ani haka shima yake.. Zan iya cewa ya fi dayawa daga cikin musulmanmu da suka tashi cikin tsantsar musuluncin ma kyaun zuciya da na ɗabi'u karka yi Shedar Zurr saboda zaka tashi dashi a gaban Allah ayi muku hisabi" Kallonta kawai yake, duk fara'ar dake fuskanta ya dusashe hakan ya nuna magananshi ya ɓata mata rai.. "Wait..! Hidayat me tsakanin ki dashi da har don na faɗi maganar da na ji a gari akan shi ranki ze ɓaci?" Ya faɗa shima wani irin kishi da zafin zuciya na bijiro mishi. "Raina be ɓaci ba ya hamza, kawai ina maka gyara ne sannan kai ji kayi ni kuma zaune nake dashi wuri guda" "I will never let you stay in that house har zuwa sadda zamu yi aure, that won't be possible! Hidayat ba de son shi kika fara ba?" Ya karashe da wani irin muryar da ya sakata saurin girgiza kai tace "karka manta fa ya hamza hidayat ɗin nan ce dai marainiya, ni ɗin ce dai wacce bani da galihu da gata, hidayat ɗin nan ce bazawara wacce ɗa namiji ya yagalgalawa rayuwa, taya kake Tunanin zan kai kaina matsayin sanannen ɗan kwallon duk duniya? Ka san mata masu mutunci da ƙima! ƴan mata daga kasashe na Larabawa da na baƙin fata dake ma mutuwa a kanshi? Ko a mafarki Raed yafi karfina bare a zahiri... Don Allah karka yi min mummunar fahimta don kawai na gyara maka kuskuren ka a musulunce.." Ajiyar zuciya ya sauke, se kuma yaji rashin daaɗin abubuwan da ta alakanta kanta dashi saboda maganan da shi ya kawo ta. "Kiyi hakuri, wlh da Tunanin kasancewar ku inuwa ɗaya nake kwana nake tashi ba zan iya jurar wani abunda ze kuma raba ni dake ba kuma.. Don Allah ki amince mu yi auren mu kusa ko hankalina ze kwanta" Tace "ya wuce ya hamza! Sede aure har yanzu ban shirya ba, sannan karka manta matarka fa ko shekara baku rufa ba da aure taya zaka fara bijiro da wani maganan auren kuma?" Yace "in dae hajiyata ta fahimce ni in Shaa Allah bani kuma da sauran damuwa" "mahaifinka fa?" Yace "ai Alhaji ya jima a kwance bashi da lafiya komai se an mishi" Tace "Allah sarki, Allah ya tashi kafadunshi" a lokaci ɗaya tana tuna Abbanta. Da Ameen ya amsa suka ɗan yi shiru kan tace "ya kamata ka koma gida haka nan ko don Aunty na da ka bari da tsohon ciki" Hmm kawai yace kan ya kara da "zan tafi ne ba se kin Koran ba" Dariya tayi tace "ni na isa in koreka ni da ba a kaina kake ba?" Dawowan rash ne ya katse musu hiran yace "Rashida kinji ƙawarki na korata" Rashida tace "ba de Hidayat ce zata koreka ba sede in an yi kira dae daga gida" Wara idanu yayi yace "haɗe min kai Zaku yi?" Se suka fashe da dariya, shima yana dariya yace "to shikenan Allah na ze saka min" Hiran se ya koma tare da Rash ita fa ba ruwan ta da wani kunya ko kauda kai... Mikewan hidayat ne ya saka su duk kallonta tace "my gurls are almost home bari naje na sama musu abunda zasu ci... Please ya hamza karka maida maganan mu wasa, kaga dae da tsohon ciki ka bar zainab baka mata adalci ba in ka cigaba da zama kwana da kwanaki, ya kamata ka koma.. Ko Rashida?" Rashida tace "kwarai kuwa, kar ya sa mana shakkun auren ma, muyi Tunanin anya kuwa ze yi adalci?" Hidayat tace "ko kuma mu ɗauka a sadda ze nemi ta uku muma hakan ze mana ba!" Dage hannayenshi yayi yace "don Allah karku kaini da nisa... In Shaa Allah zan nemi available flight to Nigeria in tafi" Hidayat tace "ko kai fa!" Ya zabga mata harara wacce ta sakata dariya. Sallama ya musu akwai inda za shi Dukda ya so sauketa a gida sede ana jiranshi.. Suna takowa zuwa inda zasu samu abun hawa  tace "kin san jiya matarshi ta kirani ta ci min mutunci?" Nan ta bata labarin duk abunda zainab ta faɗa mata. Rash tace "Kambuuu! Ke kuma me kika ce mata?" Dariya tayi tace "ni ko me zan ce mata? Ko 'a' ban ce ba har ta gama sauke min kwandunan masifan ta kashe wayan" Wani kalar harara ta zabga mata "Amma wallahi Hidayat baki haɗu ba, kan bala'i gaskiya zan kwana biyu da takaicin wannan rashin amsar da baki bata ba! Don Allah bani layinta, har ta isa ta kai ne mijinta ze kashe kuɗi ya baro ta a chan ya biyo ki har Paris? Waye ya tsaya mata kab Nigeria da zata furta Kalmar yin ajalinki?" Ita dae hidayat kallonta kawai take tana tuna ummi ƙawarta, Allah sarki tun da ta samu waya take kiran layin ummi dake kanta sede baya shiga Allah kaɗai ya san halin da ta shiga na ɓacewarsu lokaci guda. "Wai shiru kika yi kina ji na?". Rash ta faɗa a harzuke Dariya hidayat tayi tace "Wallahi best friend ɗina kika tuna min da masifan nan taki" Rash tace "hala wani abu ne ya sameta?" Girgiza kai hidayat tayi tace "na taho bamu yi sallama ba, tunda kuma na samu layin nan in na kirata bana samunta gashi ban riƙe numbern kowa ba kuma a gidansu da kai" Rash tace "Allah sarki amma fa tana fama dake wai dama haka kike?" Dariya sossai hidayat tayi tace "Rash kenan ai na fi haka, yanzu ne ma nake iya buɗan baki in yi magana ummi ce me karɓar min faɗa" Rash tace "lallai aiko wallahi Inde haka ne zaki cutu" Hidayat ta ce "cutuwa kuma na nawa? Ke de a dae yi sha'ani kawai sede fa an sha ni kuma na warke..!" Dukda rash bata gane maganan ba sede bata sake cewa komai ba don sun zo inda zasu Rabu, sallama sukayi Rashida na ce mata idan matan hamza ta sake kira bata gaya mata shuwaka ba zasu haɗu wallahi. Tana dariya ta ɗaga mata hannu. "Masha Allah" Shine Kalmar da ya fito bakinta a sadda ta hauro saman idanunta suka sauka bisa kansu a keɓantaccen wurin sallan su, yana gaba yana jan su su uku jere a bayanshi sun rufe jikinsu da kyau junior na ta up and down a kanshi. Ba ƙaramin burgeta sukayi ba ta fidda wayanta ta musu hoto, a lokacin junior ya ganta ya taso da gudu gudu har yana faɗuwa yana mata oyoyo, da sauri ta ɗaga shi tana cilla shi tare da ɗan Juyawa se ya kyalkyale da dariya itama dariya take kan ta maida kanta garesu se taga duk sun sallame ita suke kallo ta ɗan yi  murmushi tana kauda idanunta daga kanshi ta shige ɗaki. Itama ta gabatar da Alwala tayi sallanta a ɗaki tana idarwa suna shigowa suka bata takeaway ta karɓa yau bata dawo da wuri ba ashe shine suka je suka yi takeaway da baban bayan sun idar da sallah. Ajiyewa tayi don a ƙoshe take, bacci ma take ji hakan ya sa ta kishingiɗa bayan ta kora su, se la'asar Norah ta zo wai ta tashi suyi sallah in ji dad. Mikewa tayi ta shiga bayi tayo alwala ta zo ta ɗauki wayanta ta fito, sallah suka gabatar a jam'i masha Allah, bayan sun idar duk Qur'anai suka ɗauka suka zagaye ta har Baban wadda hakan ya bata dariya. Tana murmushi ta fara bawa yaran in ta ƙara maka se ka tashi ka koma gefe seda suka saura su biyu, kan su fara karatun ya kalleta murya chan ƙasa sbd yara yace "anya kina tuna kina da buri kuwa a rayuwa?" Kallon ban gane ba ta mishi. Ya sake cewa "na ɗauka da gaske kike da kika nuna zaki jajirce ki ɗaukar wa Usman fansa ta hanyar hukuma se gashi kuma wankin hula na shirin kai ki dare" Kanta ta dukar tace "kayi hakuri ba wai burina bane ya dusashe, kuma ba wai na manta bane da Usman har Abada ba ze bar kaina da zuciyata ba, kai tsaye ba zan iya cewa bana son hamza ba.." Lumshe idanunshi yayi yana jin wani mitsini marar daaɗi a zuciyarshi. "Saboda ya so ni tun ina kwaila ta, shine mutum na farko da ya fara nuna tausayi na da son taimaka na sede kaddara ta a rubuce take se na sha wahala a gidan Yusuf, ya hamza mutum ne me ƙima da ba zan iya wulakanta wa ba, na tabbatar shima yana Burin ganin an biwa Usman hakkinsa sannan na san ze taimakamin ko bayan na aurenshi wurin cikar burina.." **Team Raed! Wa ze iya hasko mana zuciyar ɗan kwallo a yanzu?*** #like #share #comment                  🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 24* *FREE BOOK* **Readers! Wai kuwa kun san magic ɗin dake cikin comment? Bari in baku wani takaitaccen labari, na tashi yau da ciwon kunne wadda rabona da in taɓa wayana ma tun 8am, se da karfe bakwai na dare ya buga nace bari in ɗan leka online tunda kunnena yayi sauƙi wallahi ban da niyyar typing yau, but to my biggest surprise se in na shiga nan in ga doguwar muhawara, in na shiga chan in kalli ruwan comments nace kai I cannot disappoint u guys dole in daure in baku page...! Wannan page ɗin naku ne masoya littafin kowa ya ga zabuwa😍🥰 one love** Shanyayyun idanunsa masu cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata na ƴan sakanni. Se a sannan kuma ta fahimci irin katoɓarar da ta zabga sede Hausawa na cewa Magana zarar bunu... Kasa Kallonshi tayi tana jin yadda idanunshi ke ladabtar da ita yadda ya kamata. A maimakon karatun Tsam ya miƙe ya fice daga wurin cikin salon takunshi, da kallo ta bi bayanshi har ya maida kofar ɗakin shi ya rufe.. A zabure ta mike tsaye ta koma tsakar parlorn tana zirga zirga, damuwa ta hango shimfiɗe a fuskanshi wadda ita a nata Tunanin damuwar ya ta'allaka ne da barin rayuwarsu da zata yi bayan sun fara sabawa da ita especially yaranshi, gabaɗaya ta rasa Tunanin da zata yi, da gaske tana jin hamza a zuciyarta kuma tana jin zata iya aurenshi.. Tana kuma son auren nashi ne ko ze samu natsuwa wurin fuskantar rayuwa guda ya dena raba hankalinshi saboda soyayyar ta. Sede ita kanta in ta ɗaura Tunanin ya su Norah zasu yi se taji wani tashin hankali ya lallaɓo ya rufeta, kenan abunda ta fara ze zama a banza? Alkawarinta da Daadida ze zama ta karya shi kenan? Shi kuwa a nashi ɓangaren yana shiga ya zube bisa gado rigingine, da sauri sauri yake fitar da numfashi, ambaton Allah yayi tayi har ya soma jin zafin da zuciyarsa ke masa na raguwa,gabaɗaya iharin jikinsa ya mutu murus... Har abada baza'a taɓa jifan shi da kalamin da ya mishi zafi irin wannan ba kuma wadda ya rasa dalilin jin zafinta haka. A iya tunaninshi bashi da wani businesses da ita banda kula da yaranshi se a yanzu da ta zaɓi gyara rayuwarsu da taimakon ubangiji zuwa hanya madaidaiciya, amma Sam be gane ba kuma girma da matsayin da wani sashe na zuciyarshi kuma ya bata ba. Har lokacin magrib yana nan kwance a wurin kaman wadda aka sassara mishi gaɓoɓi, da sunan Allah ya miqe ya shiga toilet yayi alwala ya fito fuskanshi a dinke tsab, parlorn ya fita cikin I don't care manner ɗinshi na asali, duk sun yi alwala suna shirin sallah, ba tare da ya kalleta ba yayi gaba ya tada musu sallar. Itama sau ɗaya ta kalli fuskanshi da ya koma mata sak na ranar da suka fara haɗuwa, bayan sun idar da sallah ya buɗe Alqur'ani ya cigaba da muraja'ar na baya. Toh fah tun tana ɗaukan abun wasa se taga ya ɗau zafi sossai da ita kaman wacce aka ce ta zage shi ko wani abu, se kuma hakan ya sakata a damuwa rayuwarshi bata gama saituwar da tayi alkawari ba, har Hamza ya koma be sake gane mata ba. Ranar da ya koma ba karamin daru suka kwasa da zainab ba wadda har ta kaisu gaban mahaifiyarshi dake goggo a gareta. "Hamza Abunda zainab ta faɗa haka ne?" Ta faɗa tana Kallonshi. "Eh hajiya, amma don Allah ki fahimce ni ba wai don cutar da zainab nake son shigo da Hidayat rayuwata ba, son ta ya samo asali ne daga tausayinta in bazaki manta ba a shekaru da dama su Abba ƙarami sun je nema min aurenta har sau uku a wurin marikinta.." Ya faɗa yana kallon Hajiyar cikin son tunatar da ita hidayat. "Eh kwarai na gane, wacce ka ce tana zaune ne wurin marikinta kuma bata jin daaɗin rayuwar gidan, daga karshe kuma aka aura mata ɗan gidan ko?" Ta faɗa tana mishi wani kallo. Yace "eh hajiya!" Cikin tsananin masifa ta fara magana "ban gane eh ba? Kana nufin ita zaka sake tura mahaifanka a tozarta su kaman yadda aka yi a baya? Marar tushe da asalin? Wacce dama tun a wanchan lokacin karfin ikon me mazari ne(kakanshi na wurin uba) yasa na zuba muku ido, Ko kana so ka ce zainab bata wadace ka as mace ba da har bata shekara ba kake maganan yayibo wani aure?" "Hajiya uban goyon ta ya rasu, bata da kowa se Allah don Allah karki hanani aurenta" Ya faɗa cikin roƙo. "Dakata ma tukuna! Yanzu a Paris ɗin wurin wa take zaune?" "Hajiya tana aiki ne na kula da yara waenda suka rasa mahaifiyarsu shine baban ya ɗauke ta aiki kuma tana karatu" ya faɗa da iyakar gaskiyar shi. Wata doguwar salati hajiya ta ja ta sallame nan fa ta fara balbale shi da masifa akan wallahi ba'a zuri'ar ta ba, ƴar bariki dake zaman kanta Inaaa.. Duk yadda ya so ya fahimtar da ita ta kasa fahimta, Hajiya irin manyan matan nan ne en duniya waenda duniya kuma tayiwa daaɗi, bata da mutunci ko na sule biyar bata san wani abu wai shi kawaici ko kunya ba, bata da kirki in ka taɓa ta kaman yadda girman kai da izzarta ba ze bari ta rabi kowa ba barin ma idan talaka ne, shi kuwa yana jin ba ze iya rayuwa babu hidayat ba. Daga karshe korarshi tayi, ɗakin Abban shi ya nufa ya same shi kwance jiya e yau, rufe yake da blanket fari, hancinshi abun oxygen ne ba uhm ba um um kuma yayi shekaru da dama a haka, idan jikin yayi tsanani se an saka mishi oxygen da abun abinci ta baki amma idan da sauƙi ya kan yi numfashi. Hannunshi hamza ya riƙe ya ɗaura fuskanshi a kai se hawaye, yana son hidayat son da be sani ba seda hajiya ta fara nuna mishi turjiya akan aurenta, kaman fa baze iya rayuwa ba tare da Hidayat ba, kwarai in hajiya ta raba shi da ita kwananshi kirgaggu ne a duniya. **** Tafiya yake kaman sabon kamun hauka wurjanjan, riga daban wando daban na yaɗi kodadde wadda ake kira wanke kuɗin ka, kayan da da in ya gani jikin Usman yake kyarar shi saboda kyamkyami se gashi yau na Usman ma yafi nashi kyaun tsabta da sabunta. Daga kafaɗun a yayyage yayi baƙi gabaɗaya ya koɗe kaman ba Yusuf ɗan kwalisa ba, buhun karshe na dako da yake yanzu ya kai ya karɓi Naira ɗari ɗaya da aka bashi yana juyata.. Me ɗari zata mishi? Ba Wa shi kaɗai ba harda familyn shi da suke gida suke jiran ya kawo? Ba ga matarshi da yake ji kaman ya mata sujada ba, ba ga mahaifiyar shi da ƙannenshi ba. Hanyar gidan ya kamo a rikicenshi in ya ga yaro tsaran Usman se ya ruga da gudu ya kama shi "Usman! Usman!! Baka mutu ba ko? Yauwa zo muje gida ba zan kara dukan mamanka ba don Allah ka barni in sarara" Wani lokacin idan abun ya Motso se an yi da gaske ake kwace yaro a hannunshi se yace Sam Usman ne ze kaiwa Hidayat shi saboda ya dena zuwar mishi a mafarki da zahiri. Gida ne na laka cikin wata kwaraɓaɓɓiyar unguwa da kwata shine abu mafi rinjaye da yayiwa anguwan ƙawanya, kudaje kuma suka zama ma'abotan huldarsu, kutsa kai yayi ba tare da ya damu da yayi sallama ba. Zaune yaga Kausar wacce itama ta zama wata jagwal, tana Haɗa abubuwan da take anfani dashi wurin toya doyanta na yamma.. Harara ya zabga mata ba wata wata itama ta rama. "Ni kike Harara?" "An harare ka ɗin, in ban harare ka ba wa kake so na harara? Wallahi in na ganka wani baƙin ciki da takaici nake ji kaman in kashe kaina, in banda wawanci irin naka da daƙiƙanci taya da degreen ka za'a damfare ka kudadenmu? Gashi ka mana sanadiyar baƙin talaucin da babu ranar fita daga cikinta.." Yace yana harzukowa "eh ai gwara ni da degree na ke fa? A sadda ake neman kiyi karatun ƙi kiyayi kika ce aure gashi yanzu uwar miji ta sakoki ba Chas ba ass se tallar doya" "ahayyeee ai gwara ni ban zama malohuwa sokuwa ba, mace nake kuma ina amsa sunana wasu mazan da suka koma mata fa? Kai da kayi degreen da me ya anfana maka? Gaka nan marabinka da mahaukaci bin bola...!" Ta kare tana buga kafa kasa cike da masifa, tsabar rama da talauci kana iya ganin ƙura na tashi in tayi wani jijjigan "ni fa kun ishe ni Haba!" Surayya dake fitowa daga fallen ɗakin dake gidan bayan wani me ciki da parlor ta faɗa tana saɓan mayafinta a kan igiya.. Tayi gaba "yawon shashancin da aka saba, tsabar lalacewa ma wai a wurin masu shayi da layin ga ruwa ake ƙarewa" Cewar Kausar again. Surayya da har ta fita ta dawo tace "ai gwara ni ina da abunda zan bayar ɗin in wata ta isa tayi mana..." Harzukowa Kausar tayi sede tuni Surayya ta fice, Zasu cigaba daga inda suka tsaya da Yusuf umma ta fito sanye da wasu riga da zani da suka ji jiki ta kare kaman ba umma ba, zata yi magana wata sangamemiyar mata ta fito daga daki me ciki da parlorn tace "kai ya isheka hakanan! Ina cefenen da na ce karka dawo gidan nan babu shi?" Sosa kai yayi cikin wani irin ladabi yace "Wallahi wallahi ba aiki yau dako nayi kuma shima ɗari ɗaya kawai na samo" "kawo ka wuce ka koma...marar zuciya sususu" Zuwa yayi ya miƙa mata ya juya ya fice. Kallon tsakar gidan tayi tana kallon umma tace "ya aka yi kwata kwata wurin ba'a kimtse ba?" Umma tayi saurin cewa "eh..eh dama yanzu ne za'a kimtsa..." Fara tattare gidan tayi tana kallo Kausar ta gama Haɗa doyarta ta fita ko yanka ɗaya bata bar mata ba gashi tun safe babu abunda ya shiga cikinta. Tunanin rayuwa ta faɗa.. Ashe haka hidayat ke ji a sadda suke azabtar da rayuwarta? Wani irin sakayyah ce wannan me muni? Tun bayan da ƙasa ya rufe idanun Abba ibtila'i yake sauko musu abu na karshe da tayi nadama shine korar kare da tayiwa hidayat da ɗanyen jariri. Yadda hidayat ta sa kafa ta tsallake kaman ta tafi ne da duk wani sauran rayuwar da suke lallaɓawan, garin wawancin yusuf ya zube dukiyar su duka hannun rikakkun ƴan 419 Sun sayar da Motoci har biyu wurin bin polisawa ko za'a samu clue dukiyar su ta dawo sede a banza. Bayan tafiyan hidayat Yusuf ya haɗu da wata mata, tunda ta ganshi taji shi take so kuskuren shi daya shine zina da ya fara da ita wadda shine makasudin rayuwar da suke ciki yanzu, saboda ana rade raden cewa muddin  ka kusanceta to zata mallake ka ne da abunda ke kewaye da kai har se in ita ta tafi da kanta amma baka isa guje mata ba. A yadda yake a hauka hauka saboda kasa sukuni da mafarke mafarken Usman cikin mugun yanayi ta saka shi aurenta, ita ke tura shi ya sato abubuwa masu muhimmanci da su umma suna sayarwa kan umma ta farka wayam, kayan sawa ma be bari ba, karatun Surayya ya tsaya Chak hafiz ya ɓata ɓat kaman walkiya. Har ta kai ta kawo gidan Abban ya fi karfinsu saboda suna zaune ne kaman a kango tunda gashi a cikin babban gida sede ba abinci, dalilin sayarwan kenan suka dawo suka saya wannan me saukin kuɗi a cikin irin wannan anguwa da da ko wucewa babu ɗayansu da ze iya yi. Kausar ta gamu da sharrin uwar miji sanadiyar kaninshi da tayiwa ƙage akan ya neme ta wadda kashe ɗan uwanshi ne kawai mijintan be yi ba, daga nan uwar mijin ta sa mata karan zuƙa wata biyar tana gana mata kalolin matsaloli har asirin ta ya tonu kawai tana jin haushin cin arzikin ɗan uwanshi da yake yi ne, nan suka mata jina jina tayi tilis kan suka korota daga ita se kayan jikinta. Daga karshe taje ta kwashe kayan ta sede a hankali suma aka sayar da komai chanjin ne har yanzu take Juyawa shima da tsiya tsiya. Fahariyya kuwa mijinta aure yayi ya auro wacce ta maida ta bola, tana zaune ne kawai saboda tsoron irin rayuwar da ake a gidansu amma kwarai tana azabtuwa yadda ya kamata! Matar Yusuf ba ginin da za'a taka a hau bace hakan yasa komai na gidan su suke yi, sau daya Kausar ta gwada Haɗa  ƙashi da ita Seda aka mata ɗauri, har yusuf ɗin in ta ganshi yana kallon wata haka zata saka shi a gaba ta zane tsab! Har Seda ya fara dana sanin zina a rayuwar shi. Gabaɗaya rayuwarsu ta taɓarɓare wadda a shekarun baya ko a mafarki basu taɓa Tunanin kasancewa cikin irin wannan rayuwa ba. (Ni ko nace ai wadda ya ƙi Sharan masallaci dole ze yi na kasuwa!) PARIS Zaune take riƙe da waya a kunne "Daadida! Don Allah ki kwantar da hankalinki a bi komai a sannu, a gaskiya taɓon da Baba bukar yayiwa rayuwar yallaɓai me matukar girma ne wadda bana Tunanin ze gogu sede watakila idan addininshi yayi zurfi zuciyar musulunci tasa ya iya gyara alakarshi da Mahaifinshi, karki manta ba iyaye bane kaɗai ke da hakki a kan yara, ƴaƴa ma suna da hakki a kan iyaye.. Mu yi ta Adu'a Allah ya dubi lamarin se kiga komai ya zo ya wuce" Daadida ta share hawayen fuskanta tace "bana so in mutu in bar su haka Hidayat, kullum ƙara tsufa nake rayuwar bukar ta riga ta gama taɓarɓarewa saboda abunda ni na san hakki ne...! Ciki harda laifi mafi girma shine na saɓawa iyaye, A hakan ma kullum ina rokar mishi gafara sede Allah babu ruwanshi abunda kayi shi za'a maka... Jiya ya bar nan cikin tashin hankali saboda wani mummunar faɗa da Badi'ah da Zara suka yi wadda yayi sanadiyar jefa ƴaƴan su rijiya, ya ce kullum gidanshi kaman gidan kaji ko na ƴan dambe, ko allura ya ajiye za'a nema a rasa saboda sata gashi har yau bayan Raed be da wani ɗa namiji... Yara mata ne cikinsu babu abunda babu, har da ƴar daba wacce yace tayi ikirarin yanka wuyanshi ya sake ɗaga mata murya gidanshi kuma dole ta shiga... Hidayat abunda ya ɗaure min kai har yanzu be yarda hakki ne ke binshi ba ya kasa neman yafiyata ya nemi albarka... Ya kasa neman ɗan shi ya nemi ɗauki wani irin azabtar da kai ne wannan?" Hawaye hidayat ta share tace "Ki cigaba da Adu'a da sadaka Daadida in shaa Allah komai ze yi sauƙi... Watakila Allah ne ya ɓatar dashi ya kuma mantar dashi Tunanin da ya kamata yayi wurin gyaran kuskuren shi saboda ya girbi abunda ya shuka, muyi fata Allah ya tsayar dashi iya haka" Dukda hidayat bata taɓa ganin Daadida ba sede akwai wani shakuwa da ya shiga tsakaninsu ta waya, saboda matsaloli Raed Dukda har yanzu ba shiga harkar ta yake kaman da farko ba, iyakar su karatu wadda yana gamawa ze fice,  ya fi maida hankalinshi kan sana'arshi yana kuma azabtar da kanshi da motsa jiki a ko wani lokaci. Sallama suka yi da Daadida tana sauke wayan hamza na kira. Ɗagawa tayi yace "Hidayat da wa kike waya tun ɗazu layinki busy?" "Da grandmother ɗin boss ɗina muna tattauna wani batu ne da ya shafe shi..!" Ta faɗa kanta tsaye da iyakar gaskiyar ta. A zafafe yace "kina so ki kashe ni ne hidayat? Wallahi hangen kwanana nake kusa...! Rayuwata na shirin taɓarɓarewa na kiraki ko zan samu sanyi ta wurinki shine kike gayamin maganan wani boss?" Dafe goshinta tayi tace "ya ilahi! Ya Hamza wani furuci nayi da ze harzukaka haka? Tambaya ta kayi na kuma baka amsa.. Me ke faruwa ne?" Runtse idanunshi yayi yace "Hidayat hajiya ta ƙi tsayawa ta saurareni zainab ta rigani a wurinta, a sanina yadda hajiya ke so na a matsayin tilon ɗan ta komai nake so yi min take amma yanzu tana shirin juyamin baya" "ya hamza ka san me ya fara burgeni da kai?" Ba tare da ta jira amsar shi ba ta cigaba. "Kaifin basirarka da natsuwarka amma yanzu duk kana nema ka rasa, ni ba gudu zan yi ba ina nan ka bi komai a sannu har mu samu albarkarta kaji don Allah?" "Hidayat companies ɗin Abba na na rawa wadda sanadiyar abubuwan dake faruwa dasu na bar aikin soja na dawo don in kula dasu amma na kasa focusing don Allah in zo a ɗaura mana aure daga baya se mu nemi yafiyar hajiyar ko zan samu in mai da hankalina kan abu guda.." Kasake hidayat tayi, Wai me ke faruwa ne?.ta tambayi kanta.. Wani irin possession ne wannan? (Nima nace ku tayani gani) **Don Allah wa ya san wani magani na ciwon kunne? Wallahi nayi yawon Asibiti na gaji** #like #share #comment                   🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 25* *FREE BOOK* *Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Na gode matuka da adu'o'inku duk babu wadda ban gani ba... Allah ubangiji ya bar zumunci, baki yayi kaɗan ya furta irin godiya ta da kulawar ku... Wannan page ɗin naku ne masoyan Kowa yaga zabuwa🥰😍* "Sam ba zan iya baka gudummawa wurin saɓawa mahaifiyarka ba ya hamza, mu cigaba da Adu'a kaji? Sannan kayi hakuri komai ze zo ya wuce kaman ba'a yi ba" Ta faɗa a tausashe sbd yadda hamza ya fara bata tausayi da gaske yake sonta yake sossai. Ajiyar zuciya ya sauke ba wai don hankalinshi ya kwanta ba suka yi sallama, ta jima zaune a wurin cikin tunani kan ta miƙe ta fito wurin yaran, yau har suka yi magrib da isha be dawo ba saɓanin yadda ya saba yi a gida tare da yaran. Suna zaune a dining suna cin abincin dare ita kuma tana tsaye a kansu tana Haɗawa Junior custard ya shigo, sannu da zuwa suka mishi da kai ya amsa kawai ya wuce room ɗinshi. Ba'a yi awa da shigar shi ba se ga Kimorah ta shigo sanye da wasu irin kaya da daga ka gani ka san wannan a addininsun ma an wuce gona da iri, kallo ɗaya ta yiwa dining ɗin tace "Norah, baby Farrah hey!" Kan ta wuce ɗakin Raed ɗin, lumshe idanu Hidayat tayi tana me kau da kai.. Norah ma fuskanta be nuna ta ji daaɗin zuwan na buduruwar mahaifin nasu ba, se cin abincin ya zama wani iri haka suka gama suka tarkata suka wuce ɗakin hidayat ɗin, duk yadda yaran suka so su sanya ta cikin hiran su bata iya shiga ba haka suka kyale ta.. "Ma....ma u..wa" Junior ya fadi cikin harshen yara waenda basu iya magana ba, Norah na assignment ne Aisha kam har tayi bacci yayinda Farrah take riƙe dashi hakan yasa hidayat ɗin miƙewa tace "bari in kawo maka junior" Ficewa tayi Sam bata kula dasu ba seda ta zo tsakiyar parlorn, zaune yake a karkace system ɗaure a kafanshi yana kallon Umar series yayinda kwance daga jikinshi Kimorah ce tana ta mishi magana cikin kanƙan da murya. Da sauri hidayat ta kau da kai ganin sun Haɗa idanu a hankali ta musu sannu kan ta wuce kitchen, buɗe fridge tayi ta ɗauki ruwa me sanyi ta sha sossai tana jin ba daidai ba gabaɗaya a yanayinta, ta jima tsaye nan ba abunda take kan ta ɗauki ruwa marar sanyi ta fito, bata kalli inda suke ba ta wuce ɗaki.. "Why are u looking at her?" Maganan Kimorah yasa ya ɗauke kai daga kallon bayanta ya mayar system ba tare da yace komai ba. "Meyasa se in ta maka magana kana share ni ne? Tun fa kan na tafi na dena gane maka ɗan kulani da kake wadda shi kaɗai ma yake sawa inji na fi kowacce mace ɗin ma yanzu baka yi, yanzu ko kwanciya nayi jikinka ka dinga ture ni kenan idan ba na nace ba sede in hakura, please in wani abu nayi maka ka faɗamun" Tayi magana da harshen turanci cikin Raurau da idanu. Yace cikin gajiya da komai da ma kallon.. "Please kimorah let me be! Ki shiga spare room ɗin chan ki kwana ko kije one of the rooms down stairs am not in the mood" Zata yi magana ya ɗaga mata hannu tare da mikewa ya shige dakinshi, haka ya karasa duk abunda ze yi ya kwanta cike da wasu tunannuka.. Washegari tayi ayyukan ta fiye ma da yadda ta saba tashi don kan ace bakwai ta gama komai da komai tayi wanka, bata jira tafiyar yaran ba ta fice don Allah ya gani kwanan ta da wannan buduruwar tashi inuwa ɗaya ba karamin baƙanta ranta yayi ba, haka ta isa makarantar ma ajin bata wani fahimta sossai ba. Bayan ta gaji da kallon malamin kawai ta fito ta samu wani keɓantaccen wuri ta zauna, lokaci lokaci se ta share hawaye, rabon da tayi kuka tun daga ranar da aka bata labarinshi shima na tausayinshi ne amma kukan dake fita daga zuciyarta tun tana gidan Yusuf se gashi yau tana yi haiƙan. Kafaɗanta taji an dafa, da sauri ta ɗago tana share hawayen idanunta se suka Haɗa idanu da Rashida.. "Hidayat! Lafiya kike kuka?" Kai ta gyaɗa tace "lafiya ƙalau Rashida, ba kuma kuka Nake ba" "karƙi maida karuwa ƴar iska mana hidayat, ai ko makancewa nayi na shafa idanunkin nan na san kin sha kuka, ko de baki ɗauke ni yadda kika ɗauki ummi bane?" A hankali tace "Wallahi ba haka Bane, maganan ban san ta inda zan fara bane!" "Fara ta ko ma ina ne zan baki listening ear" Zata yi magana taji an ce "Maama!" Da sauri ta juya se taga, Norah da Farrah da Aisha tsaye amma Aishan ce tayi kiran.. Da sauri suka zo suka yi hugging nata.. Ɗago Aisha Rashida tayi tace "Hidayat wannan ƙanwarki ce ko? Kinga yadda kuka yi kama?" Dariya ne ya kama hidayat tace "wani irin ƙanwa baki ji tace mama ba?" Harara ta zabga mata tare da cewa Aisha da tace mata ina yini. "Lafiya, gayamin gaskiya waye mamanki?" Hannu ta ɗaga ta nuna hidayat tace "itace mamanmu da ni da Ya Usman da kuma Junior, ko mama?" Wara idanu Rashida tayi tace "har ku uku?" Kanta se ya kulle hidayat at her age har ta haifi yara uku? Sannan in ta haihu me yasa yanzu suke nema da hamza? Ya abun yake ne kam.. Maganan Norah ne ta katse ta. "Miss hidayat! Daad is waiting in the car and he hates that." Wara idanu tayi tace "Meyasa baki faɗa min tuntuni ba? Mu Je" Gaba suka yi se Rashida ta rike hannunta tace "amma kin san ba zan bari ki tafi cikin damuwa ba ko? Ina so muyi magana tunda babu ummi ina so please kiyi shearing problems ɗinki dani wallahi aminiya na dauke ki" Ajiyar zuciya ta Sauke tace "yanzu kinga ana jira na ko zaki biyoni muje gidan se muyi magana?" Kai Rashida ta gyaɗa suka fito a tare, ya ɗan sauke glass ɗin gefenshi fuskanshi a kame as usual. Lekawa Rashida tayi ta gaishe shi se suka Haɗa idanu, gabaɗaya idanunta ta fiddo waje.. "OMG! Moh Raed??" Wani ƙara ta saki tana sake Lekawa da kyau wallahi kuwa shine.. Murmushi ya saki ganinta da Hidayat ya san maybe ƙawarta ce, hidayat ce ta ja hannunta suka shiga motan tana sake kallon Raed, yau gata ga famous footballer da sede a kalla a TV ko a waya. Har suka isa gidan bata dena mamaki ba, no wonder Norah suke kama sossai ai ita babbar fan ɗinshi ce. Ko da suka isa gidan haka tayi ta kallon gidan kaman bata taɓa shiga gida irin shi ba kuma duk sbd dumbin mamakin yau gata a gidanshi har ciki ciki take yi. Ko da suka isa ɗaki hidayat ta mata masauki tace bari ta samu simple abu ta yiwa yaran se suyi magana. Norah ta turo ta kawo mata ruwa da snack, se ga Aisha da Junior sun shiga karɓan shi tayi tana mishi wasa. Da Norah da ta fara shiga kitchen suna ayyuka tare tayi girkin ta gama ta zuzzuba musu lokacin da ta kai ɗaki rike da wani madaidaicin haɗaɗɗen tray ɗauke da warmers masu kyau da daga gani zaka san ya ja kuɗi ta samu tana sallah Itama ruwa ta watsa tayi sallah, suka ci abinci kan hidayat ta fuskance ta. A hankali ta fara bata labarin rayuwarta tun daga farko har kawo yau, se ga Rashida na kuka kashirban wallahi ita ko a labari bata taɓa gamo da irin na Hidayat ba.. Seda ta nitsa kan tace "sannu hidayat lallai kinga rayuwa! Kuma daga hamza har Raed sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar ki sede ko kama kafan na Raed hamza be yi ba.." Kai ta gyaɗa tace "na sani, Raed shi ya sama min rayuwar da nake cikin yanzu cikin sukuni da salama shiyasa nake iya yi na wurin ganin na taimakesu da yaranshi yadda zasu samu aljanna suma ta sanadiyata" Rashida tace "Amma Allah ya tsinewa Yusuf!" Dariya maganan ya ba hidayat wadda se da ta dara ganin yadda Rashida tayi maganan kaman taga Yusuf a gabanta ta bindige. "Hidayat maganan gaskiya ina Tunanin ke da Raed kuna son juna..!" Gabaɗaya idanunta ta waro "Ki rufamin asiri don Allah karki faɗa wani ya ji... Me Irin Raed ze yi dani? He is my boss for goodness sake in don damuwar da na shiga ne ba wai sbd wani abu bane ina baƙin cikin kasancewar shi cikin masu aikata laifin zina ne ba komai ba.." Rashida dake sake da baki take kallonta tace "ni bance ki kare kanki ba, sede fa na san Raed kuwa shi ke da abunda ze yi dake, wai kina kallon madubi kuwa? Wallahi idan ba don na kalli Aisha da Junior kuma naji labarin ki ba ba zan taɓa yarda kin haifesu ba.. U are really every man's dream kaman yadda Raed yake every woman dream kinga kenan se ku haɗu ku bada kala..." Ajiyar zuciya ta sauke tace "ni yanzu ba wannan ba Rashida taya kike Tunanin zan yi facing nashi da maganan haramcin zina? Yarinyar nan don bata da kunya kwance fa dare dare na sameta jikinshi jiya haka ma rannan.." Dariya Rashida tayi kan tace "uhmm, kawai ki fuskance shi ki mishi magana ta hankali da basira..amma ni de na san kuna son juna gwara kun dena kauce kauce ke kin mishi maganan wani ya ɗau fushi ke kuma ya kawo buduruwarshi kin hau koke koke!" Duka take shirin daƙa mata ta ja baya tana dariya, ajiyar zuciya hidayat ta sauke tace "amma ni kam hamza nake tunani! Shine ya furta mini kalamar so tun ban san kaina ba, bayan na fito ya sake tara ta da Kalmar so ba zan iya watsa mishi ƙasa a idanu ba zan yi Adu'a idan Hamza Allah yace in aura se kiga an yi Dukda yanzu auren baya gabana.. Don ban tsinci komai cikinshi da ze sani sake marmarin koma mai da garaje ba" Ajiyar zuciya Rashida ta sauke itama tana duba hamza kam daga ganin yadda yake yiwa hidayat zaka san irin su ko kwanciya tace yayi tabi bayanshi ta wuce tsab ze kwanta. Tattaunawa suka sake yi kan, rashida ta mike da shirin tafiya. Har ƙasa ta raka ta kan ta koma, tana jin hayaniyar su Norah a ɗakin Farrah sede bata leƙa ba ta nufi kitchen daidai lokacin shi kuma ya fito riƙe da coffee a hannu, saura kaɗan suyi karo yayi saurin janyewa har coffeen na fantsalar mishi a hannu, runtse idanu yayi a ɗan razane tace "Subhanallah! Sannu don Allah ban san kana zuwa ba" Kai ya gyaɗa mata ze wuce tace "am..umm don Allah ina so ne muyi magana yallaɓai" Kallonta yayi se ya kalli parlor, ta gane ba son Magana yake ba hakan yasa ya nuna mata da idanu akan suje parlor. Seda ta bari ya je ya zauna kan ta zo ta zauna itama cikin lafazi me taushi ta fara magana na hankali. Ayoyi da hadisai waenda ta sani da suka yi magana akan zina da haramcinsu ta fara ja mishi tana yi idanunta na cika da hawaye tana sharewa tana iya tuna a farkon aurenta da Yusuf a sadda ta fara fahimtar irin banzar ɗabi'ar shi ta zauna ta mishi wannan nasihan sede dukan da ya mata a yanzu da ta tuna Seda taji a jikinta kaman yanzu abun ke faruwa take duk wani tsika na jikinta ya tashi. Tsam ya miƙe daga inda yake ya dawo kusa da ita yana shirin zama tayi saurin saka hannu tana kare fuskanta a razane tace "Don Allah kayi hakuri ya yusuf...!" Wani irin karyewa zuciyarshi tayi, after some months da ya kusa rufa shekara don yanzu wata ya saura ta cika one year da barin Nigeria, har yanzu akwai wannan taɓo ashe ƙasar zuciyarta? Tausayinta ne ya motsa a ƙasan ranshi wadda ya saka shi lumshe idanu a hankali yace "calm down hidayat ban taɓa dukan ko kare bane bare mutum..! A jinsin ma ba namiji ba Mace.. I can't!" Hawayen idanunta ne ya gangaro tayi saurin dawowa hayyacinta tace "kayi haƙuri please" Ya ɗan yi murmushi yace "kalma me sauƙi kenan a bakinki na fahimta" Gyara fuskanshi yayi yace "Hidayat." Da sauri ta ɗago Seda suka Haɗa idanu yace "ban taɓa aikata zina ba hidayat! Zina na daga cikin abunda na kyamata a duniya bayan shan kayan maye da tattoo... Ban sani bane ko Allah ya kare ni saboda watakila mahaifiyata ta taɓa yi min Adu'ar kariya daga sharrin su, ban sani bane ko Allah na so na da rahamar shi ne yasa ya kare ni all I know duk yadda mata suke rububin kawo kansu gareni a kyauta ma ban taɓa kallon wata da fuskan sha'awa ba." Se kunyar maganan da tayi ya kama ta, Allah sarki ta mishi mummunan fahimta sede duk wadda ze ga yadda kimorah ke shishige mishi da yadda suke kwana ɗaki daya kaman yadda take ji bakin su Norah Dukda ta kan kwaɓesu kan maganan yaje ko ina har yanzu ma sun bari, tsab zaka ce sun yi ɗin ashe shiyasa Allah ya haramta shedar zina anyhow... "Am sorry!" Yana kallon fuskanta dake nuna kunyar da taji se yaji ta burge shi, be taɓa ganin wata na kunya a gabanshi ba se yau ko don rayuwar turawa ba ruwansu da wani kunya ne oho.. "U don't have to! Se menene kuma be da kyau?" Yayi maganan da iyakar gaskiyar shi. A hankali ta ɗago ta kalleshi se suka Haɗa idanu sun ɗau seconds suna kallon juna kan ta kalli gashin kanshi da kana gani ka san ba kananun kuɗi ya ja a gyara da style ɗin ba, ta kuma kallon kunnenshi dake ɗauke da ɗan kunnen diamond ga dama ta samu sede tana tsoron kar ya ki amincewa saboda ta san yana mishi kyau ne ya saka. "Uhyimm...!" Ya faɗi kalamar daga ƙasan makoshi wadda seda ta ji har tsakiyar jininta. Tattaro kuzarinta tayi ta fara magana. "Akwai hadisin da annabi yayi magana akan maza masu shiga ta siffa irin ta mata sakamakon su wuta ne hakanan mata masu shiga ta sutura da kamanni irin ta maza su ma hakan ne" A hankali ya sa hannu ya cire ɗan kunnen kunnenshi se ya wara mata fari Kal ɗin tafin hannun dauke da ɗan kunnen yace "is it about this?" Kai ta gyaɗa. Yace "as from today an gama... Then?" Kallonshi ta sake yi cikin kokonto yadda yake yin komai ba musu ko tantama shi ya fi tafiya da ita. "See ina so na zama pure, a irin wa'azuzzukan da nake ji about jannah and hellfire I really want to be among alhul jannah... I badly want my relationship with my almighty to be good! U are an angel sent by him to us idan kika gani don't resitate kiyi mana gyara because maybe kan mu gani a Wa'azin ya jima.." Ajiyar zuciya ta sauke tabbas kalamanshi masu tasiri ne, hakanan tsantsar gaskiya ce a ciki kwarai da dalilin haduwar rayuwarsu, komai dama Allah yayi shi cikin qadr. "Wannan hairstyle.. Akwai hadisin da annabi yayi magana akai inda yayi hani da aske gashi rabi da rabi, wato a kwashe wani ya fi wani tsawo sede idan zaka aske ka aske gabaɗaya hakanan idan zaka tara ka tara gabaɗaya" Kai ya gyaɗa yace "I will change this hairstyle first thing in the morning... Thank you. Se me kuma?" Tace bayan ta maida kanta ƙasa "taɓa mace ko namijin da ba muharramarka ba ko da ba da sunan zina bane annabi yace da ka aikata hakan gwara an buga maka kusa inci tara a tsakiyar kanka" Idanu ya lumshe yace "Noted! Se mene?" Ta ɗago ta narke fuska wadda ya saka shi ganin ta koma baby Farrah ko junior tace "saboda nice sarauniyar kakale kakale ko? To ya kare" Dariya ta bashi wadda seda ya murmusa har sautin ta fito. "I thought akwai wani abu ne kuma and u don't want to say because of ur silly reansons da ban sani ba" Kai ta ɗan karkata kan tace "akwai na tuna" Ya bata hankalin shi yace "what's that?" "Am sorry boss! Don Allah kayi hakuri" Kallonta kawai yake irin kallon da ya sakata jin kaman ta narke, kaman ƙasa ya buɗe ta shige ko ta ɓace nan take su turawan nan basu san ruwan kunya ba. Wannan kallon ma ya kamata ta mishi nashi karatun don ya fita musulunci.. Ze yi magana kenan kimorah da ta shigo tuntuni tace "what the hell is going on here? So Raed that's the reason? This filthy nanny is the reason why you are giving me hard time?" Yadda take magana da masifa ne yasa duk suka zuba mata idanu. Da sauri tayi kanshi zata taɓa shi kaman wadda yaga wuta yayi sauri mikewa yana ja baya yace "don't! Don't you ever lay ur finger on me" Wani irin kukan kura tayi tayi kan Hidayat.... #Vote #share #comment                     🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 26* *FREE BOOK* Fisgota yayi da karfi kan ta ƙarasa kanta ya nuna ta da yatsa yace cikin harshen turanci "karki kuskura ki fara abunda bazaki iya ba... Now! Get out of my house...!" Idanunta gabaɗaya ta waro tace "what do you mean?" "I mean it's over between us.." Kuka ta fashe dashi a zuciye ta wuce room da ta kwana ta janyo kayan ta ta fito ta sauka da gudu tana kuka. Tsaki yaja yana ɗauke kai daga kallonta se suka Haɗa idanu wani irin numfashin tsoro take ta saukewa, kanta ta mayar kasa tare da cewa "Seda safe" Bata jira amsar shi ba ta wuce Washegari shi ya sauke ta a makaranta Dukda dae ba wani hira suka yi ba bayan gaisuwa sede fuskanshi a sake ba kaman sadda yake fushi ba kuma sossai taji daaɗin hakan. **** Roba me ɗauke da garin kunu kaɗan da kuma kullin tsamiya da gyaɗa ta dire mata. "Tashi ki yi min kunu karki yarda tsamiya yayi yawa kuma ya nuna kar yayi ruwa" Kallonta Surayya tayi zata yi magana suka Haɗa idanu da Umma ta girgiza mata kai alamun kar tayi. Miƙewa Surayya tayi ta ɗauki robar kunun ta yi bakin murhu tana mitan.. "Kece matsiyaciya da kike shan kunu in ba da yanzu rayuwa ya chanza ba ai ko sunan kunu ba'a kira mana gida daga custard se oat" Tak bata ce ba ta samu kujera ta zauna, a cike take da su dukkansu kuma kaɗan take jira kab ta saita musu zama, umma dake zaune cikin Asabar da Lahadi na kodaddiyar Atampha ta zabga tagumi tana Tunanin Abba A lokacin da yayi mutuwar son tayi karatu ko don bayan ranshi tayi amfani da aikinta wurin kula dasu sede Sam ta ƙi tana ganin yana dashi ko ya mutu ba zasu yi rashi ba, ya sha gayamata dukiyar gado iska ce tsab se ta iya bin me shi cikin lokaci ƙankani, ya sha gayamata rayuwa ba tabbas sede duk tayi watsi da hakan. Yau a yanzu wa gari ya waya? Da Kausar taƙi karatu ma ita ce ta bata goyon baya haka Abban ya hakura ita kuma fahiriyya a sadda zata auri mijinta da take aure ya shaida musu ba karatu a gidanshi Abba ya ƙi bada ita ba karamin bore suka yi ba haka ya hakura ya zuba musu idanu, ita Surayya da take ɗan karatun an kore ta saboda rashin kokari gatan da ta nuna mata na Hidayat take yi mata komai ciki har test da exams ya ja mata. Yusuf bashi da maraba da mahaukaci, wanchan kuma bata ma san duniyar da yake ba..! Wata ashariya da hafsatu ta saki ne ya katsewa Umman tunani. Mari ta gaure Surayya dashi tace "don uwarki wanchan dake zaune haka na baki umarnin dama min kunu?" Surayya tace "Wallahi ba de uwata b..." Kwashe ta da tayi ya hana maganan karasa fitowa, se ga Surayya a ƙasa wanwar dama gata kaman karan kaɗa miya, danne ta hafsatu tayi bata damu da zafin kunun ba ta fara ɗura mata tana cewa "yau se nayi maganin bakin rashin kunyar nan..! Zaki san ni kika yi kokarin zagi" Ga tsinkakken kunu, ga Shakura, ga tsami saboda tsamiyar da ta labta don mugunta ga rashin sugar da zafin kunun duka ya Haɗar mata shidewa take sede ko a jikin hafsatu, ba ta sake ta ba seda taga kunun na fitowa har ta hanci ga idanunta kaman garwashi ko da ta sake ta mikewa tayi ta fara kwara amai tana tari kaman zata mutu. Idanu kawai umma ta zuba mata hawaye na gangaro mata a idanu tana tuna sadda suka yiwa hidayat ɗuren custard, lallai annabi yayi gaskiya da yace yadda kayi haka za'a yi maka. Surayya bata gama tari da aman ba suka fara jin hayaniya a kofar gida, tsaye umma ta mike ganin an shigo da Yusuf ranga ranga jiki jina jina. "Lafiya me ya faru?" "Ki Ja wa wannan mahaukacin ɗan naki kunne ko kuma ku samu mari ku ɗaure shi yau duka kawai ya samu gobe kuma ina ga sede bindiga..." "Ban gane ba bawan Allah me yayi?" Wani daga cikin waenda suka shigo da shin yace "zaki gane ne a sadda aka shigo miki da gawarshi in ba mahaukaci ba daga ganin ɗan DPO rike da hannun Babanshi ya ruga ya chakwame yaro yana kiran sunan wani Usman, yaro ya firgice anyi anyi ya saki ɗan mutane ya ki ya kwankwame shi seda DPO yasa yaranshi suka lallasa shi kan ya saki yaron don azaba, to wlh gobe yayiwa soja haka harbe shi ze yi ba ruwanshi.." Yusuf din umma ke kallo har suka fita, ba karamin duka ya sha ba se hawaye ke zuba a idanunshi. Ta kalli Surayya da ta lallaɓa ta miƙe ta shige ɗaki, ta san matarshi na ji sede bazata fito ba ko in ta fiton ma sede ta kara mishi akan ciwon da nata tashin hankalin. Murhun da Surayya bata kashe ba taje ta ɗaura ruwan zafi ta zauna ta zabga tagumi har yayi ta surka kaɗan ta zo tana matse mishi yana ihu tana share hawaye cike da Tunanin mafita. ***** "ya hamza..!" Zainab ta kirashi. Firgigit ya dawo daga duniyar da ya shiga yace "uhm baby hidayah" Haɗe rai tayi ji wani salon iskanci, zata fara magana ya tuna barnar da yayi se yayi sauri cewa "Don Allah kiyi haƙuri! Faɗamin menene?" Harara ta zabga mishi ba don maganan da take son faɗa mai ba da ta bar wurin don yanzu zancen hidayat kaman ruwa yake a wurinshi, motsi kaɗan se ya ambace ta ta rasa wani kalar kyau hidayat ɗin ke dashi da ze susuce a kanta, ta rasa da wani irin Boka hidayat ke tsafi da zata kanainaye mata miji ta hanata zaman lafiya a gida, kab duniya in kace wa ta tsana to hidayat ce.. "Ina so in na haifi namiji a saka mishi sunan Abbana.. Idan kuma macece se ta ci sunan Hajiya ka yarda?" Kallonta yayi na mintuna kan yace "idan macece sunanta Hidayat.. zainab" "mene? Sunan wanchan karu...." Wani irin tsawa ya daka mata "karki kuskura ki sa in nuna miki ɗayar kala ta, wallahi a duk sadda kika sake yin kuskuren danganta hidayat da mummunan kalma se na lahira ya fi ki jin daaɗi in kina Tunanin wasa ne kuma ki gwada... Sannan ina so ki rubuta ki ajiye in har nine uban abunda  ke cikinki in har dae mace kika haifa babu fashi sunanta Hidayat..!" Ya faɗa cikin zafin ran da hajiya ke sa mishi tension ɗin kuma sanadiyar zainab shiyasa take matukar bashi haushi, ya tsani mutum me kai ƙara anyhow zainab kuma tambarin ta kenan. Be gama Tunanin ba Wayanshi ya fara kira dubawa yayi yaga hajiya, ya tabbatar zainab tayi aikin da ta saba, tsaki ya ja yana ƙara ji tana fitar mishi a rai, kaman ba ze ɗauka ba se kuma ya ɗaga "Sannu isasshe..! Wato dayake hidayat ɗin itace uwarka shine zaka tada wa matarka jijiyan wuya akan ɗan cikin da ita ta ɗauki rainon kayan ta kuma zata sha wahalar nakuda ko? Wallahi hamza ka kiyayi ɓacin raina. Wai da wani irin Boka wannan hidayat ɗin take takama ne?" Yace cikin muryar da ke nuna lallai ranshi a bace yake an taɓa hidayat. "Hajiya hidayat baiwar Allah ce don Allah ki dena danganta ta da Boka, kiyi hakuri kuma amma na riga nayi rantsuwa in dae har mace zainab ta haifa sunanta Hidayat." Kasa magana hajiya tayi daga karshe tace "na yarda asiri gaskiyar me shi, wato ni kake sa'in sa da yau ko? To ba matsala zan ga uban da ze yarje maka auren ita hidayat ɗin take ko wa.. Sannan in har  ni na haifeka ka tsallakeni ka sakawa ɗiyar ka sunan wata bazawara wallahi zaka gane baka da wayau, shashasha kawai" Kit ta kashe wayan. Takaici ya saka shi jin kaman ya sa hannu a kai yayi ta ihu, wallahi shi karan kanshi be san yaushe ya fara yiwa hidayat ɗin irin wannan son ba, gashi Allah ya ɗauki ran kakanshi wadda ya taɓa yi wa hidayat gyaran hannu da ya san kwarai ze shige mishi gaba wurin ganin ya mallake ta. Gidan ya tafi don in ba Wurin Abban shi yaje ba baze samu natsuwar da yake buƙata ba, in ka ganshi kaman ba hamza ɗan gayu ba, ya tara kasumba wadda ya saka ramarshi fita, da Tunanin kasancewar hidayat inuwa ɗaya da Raed yake kwana yake tashi, ko ball yaga ake yi da PSG in har ya kyalla ido ya ga Raed ya ga irin kyaun sura da baiwa da Allah ya mishi se yaji kaman yayi hauka. A gaban Abban ya zauna yana rike da hannun shi ya fara faɗa mishi abunda hajiya tace kaman Abban na ji. Har ya gama yayi shiru, shi ba me yawan abokai bane Dukda yana da su ɗin sede be da maganan da ze sa ya iya baza musu duk wani sirrin shi, yana matukar kaunar Abban shi kaman yadda yake tuna sadda yake ƙarami Abban ke matukar ƙaunar shi ya san shi ze fahimce shi, Hajiya don tana mace ne ta kasa fahimtar shi. Motsi Abban yayi wadda ya saka hamza waro dukkan idanunshi waje.. Kaman wadda aka Umarta a hankali yayi ta kokarin buɗe idanunshi wadda ya saka hamza Suman tsaye, wani irin sassanyar farin ciki ne ya lulluɓe shi yana mamaye dukkan ilahirin jikinshi. Da gudu ya fito yana kiran hajiya. "Wai menene? Ni kam na shiga uku na lalace hidayat ta haukata min ɗa. Me hakan?" "Hajiya Abba ya buɗe idanu, Alhamdulillah Abba ya farka hajiya.." Harara ta maka mishi tace "mutumin da ƙasar waje ma cewa suka yi mu sa hannu a karasa shi saboda babu ranar waraka shine zaka ce ya buɗe ido?" Hannunta kawai ya janyo don ba ze iya magana ba, suna shiga kuwa Abba da ya rufe idanun saboda haske da ya mishi yawa ya sake fara kokarin buɗewa ai murna a wurin su ba'a magana nan take suka fita dashi aka yi asibiti don ba zasu iya jiran doctor ba. **** Zaune yake shiru a ɗaki yana jin wani irin tone tone da matan nashi ke yi suna baje iskan hammata, a razane ya miƙe tsaye da yaji sadda zarah ke cewa "azzaluma me Haɗa husuma tsakanin uba da ɗa... Wato abunda kika yiwa Raed har yayi sanadiyar barin shi gidan nan nima shi kike kokarin yiwa ta wa ƴar to ahir ɗin ki me gida da mota dae se ta aura.. Ki ji da ƴan daba da karuwan yaran ki" Wani irin shewa Badi'ah tayi tace "ai gwara ni abunda nayi me sauƙi ne, ke fa? Tsabar tsanar da kika yiwa uwar Raed ina anan kika shiga kika sace kuɗin malam ya zo ya lakada mata duka wadda sanadin shi ta gamu da ajalin ta...? Gwara ni sau dubu muna da mashinshina Dukda ƴar daban ce, karuwancin na ki  su samu mana" Da wani irin gudun da be san akwai sauran karfin yinshi ba saboda cin rogo carbohydrate yayi yawa ya fito a hautsine yace "maimaita abubuwan da kuke cewa ban ji da kyau ba...!" Wiki wiki suka fara da idanu don tsabar masifa sun manta yana nan.. Da gudu yaje ya rufe kofar gidanshi ya dawo da arda da gora. "Ko ku min filla filla ko in kashe ku in ya so nima se a kasheni...!" **** "Rashida ba karamin mamaki yallaɓai ya bani ba...ban taɓa cin karo da namiji irin shi ba tabbas da a cikin musulunci tsantsa ya tashi da musulmai sun yi alfahari da samunshi" Rashida tace "kin zo se koɗa shi kike tuntuni ni baki gayamin ya kuka yi ba" Dariya hidayat tayi tace "Rashida Allah ya tseratar da bawan shi, ya min rantsuwar be taɓa aikata zina ba, abun mamaki shi da ƴan mata suke rububi a kanshi, ga kuɗi ga suna sede ya kiyaye jefawa zuri'ar shi bala'in zina saɓanin Yusuf da ko kafan takalmin Raed be kamo ba amma ya mai da zina ado a rayuwarshi" Rashida tace "hmm, ai shi Allah in ya so kare bawa ko tsirara mata zasu yi yawo gabanshi Allah ze kare shi, kuma kinga yayiwa kanshi babban kiyamul laili da baya shan komai" "ban taɓa Tunanin Yallaɓai ze biyu ta sauki ba, yanzu damuwana tsakanin shi da Mahaifinshi" "ke kin san wallahi ina Tunanin son ki da yake ne babban maƙamin da ya sa yake biyuwa ta sauƙi" Harara Hidayat ta zabga mata tace "ba so ba kin manta...!" Dariya Rashida ta kwashe dashi tace "gashi daga magana kin fara blushing" "Rashida tsakani da Allah tsoro nake ji" "Tsoron me?" Ta tambaye ta tana gyara zama. "Rashida aure! Ina yin karfin halin maganan aure ne amma in na tuna da zancen auren wlh gabana faɗuwa yake, tsoro se ya shige ni. Ko kin san har yau bana samun cikakken baccin da ya kamata bawa ya samu?" "Na sani Hidayat! Shiyasa nake so ki godewa Allah ki kuma godewa Raed, kina Tunanin ba don shi ba rayuwa zata miki saukin blending haka ne? Ko Kin san da a Nigeria kike da yanzu baki da maraba da mahaukaciya? Abunda yasa nace haka, a nan baki ganin violence hakan ya taimaka wurin baki cikakken natsuwa, da zaki ga ana faɗa se abunda baki yi tunani ba ya same ki, hakanan zama da yaran nan shima kwarai ya taimaka miki ai a likitance taɓon da Yusuf ya miki warkewarshi ba yanzu ba.." Kai ta gyaɗa tace "hakane, shiyasa bana iya kallon film Sam don yana sani tsorata.. Sau ɗaya na taɓa kallon Animation ɗin su Farrah, goigoi ne amma dayake ana duka da faɗa ciki seda na kwana ban runtsa ba haka jiya da buduruwarshi ta so tada husuma wlh baki ji yadda gabana yayi ta faɗuwa ba" Rashida ta riƙe hannunta tace "a hankali in shaa Allah komai ze daidaita, Raed ba irin Yusuf bane zaki rabauta da samunshi" Zata yi magana wayanta ya fara ringing ta duba taga hamza tace "Allah se na gayawa ya hamza karfi da yaji kike son danganta ni da abunda kin san ya fi karfina" Tana kai nan ta ɗauki wayan, suka gaisa ya faɗa mata farkawar dad ɗinshi, sossai ta taya shi murna ta ba Rashida ma ta mishi murna, suka ɗan kara magana kadan kan suka yi sallama. Yau ko da ta iso gida bata samu yaran ba, ko da ta tambayi miss Mary tace sun fita da babansu. A natse tayi sallah ta hau girkin rana. Seda ta gama ta fara jerawa suka shigo suna hayaniya ga ledoji a hannunsu. Farrah ta zo da gudu ta kama hannun ta tace "Miss hidayat! We are going for a trip yeeeeey" Hidayat na ajiye tray ɗin hannunta tace "easy Farrah, school ɗin fa?" Norah tace "we are on mid-term break, Dad na da wasa a Belgium and he want us to attend" Aisha ta miko mata ledojin hannunta tace. "Dad made this shopping for you saboda kina makaranta and we don't know what u like" Ɗago idanu tayi se suka Haɗa idanu yana riƙe da Junior, murmushi ya sakar mata itama ta mayar mishi ba tare da ta san tayi hakan ba, ta karɓi Ledar Hannun Aisha tace "thank you Daddy!" Dariya ta bashi sede be yi ba ya ɗan murmusa. Yace "the trip is with u.. Hope bazaki samu matsala da karatunki ba" Kallonshi tayi tace "I don't think I can make it bcs ina da assessment this week" Kwaɓe fuska duka su uku suka yi a tare suka ce "oh no!" Dariya sossai hidayat tayi tace "ba wani abu ai u will enjoy the trip I trust Daddy" Gira ɗaya ya dage yana zama a dining ɗin irin yeah ɗin nan, dukda be ji daaɗin rashin samun zuwan tan ba, ganin kuma yaran da gaske sun damu yasa ya chanza shawara yace "hey gurls! Calm down and eat ur food.. "Mommy" is going in shaa Allah" Ras haka gabanta ya doka a sadda ya ambaci mommy ɗin, sossai jikinta ya karɓi sakon nashi don da wani kalar murya yayi anfani, ya wani lakaba mata mommy ita sa yaranta ma mama suke cewa su Norah kuma miss hidayat, Yaran ina suka sani se murnan zata je suke yi. A hankali ta kalleshi, ya dage mata gira ɗaya alamun what? "Amma ma...." "Shiii....!!" Ya ja I ɗin yana ɗora dogon yatsanshi bisa saman tausasan lips ɗinshi da yake tauna abinci a hankali, lumshe idanunta tayi kawai tana kauda kai... #Vote #share #comment                   🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 27* *FREE BOOK* *Afuwan jiya kun jini shiru was very busy ne* Lip ɗin shi ya ɗan cija yana kau da kai daga kallonta, yaran ta zubawa abincin se ta zuba nata zata wuce ɗaki ya ce "Miss hidayat! Why can't u eat here?" Farrah tace "yes please you always don't like eating in the dining with us" Lumshe idanu tayi tana jin yadda bugun zuciyarta ke harbawa, dawowa tayi ta ajiye plate ɗin tare da ɗan jan kujera ta zauna, daga su har yaran babu wadda ya sake magana se junior don ta hana su magana yayinda suke cin abinci, Sam a takure take don lokaci lokaci tana iya jin kaifin idanunshi a jikinta alamun yana kallon ta, hakan yasa take cin abincin kaman baby jikinta na mutuwa a hankali kaman yadda nashi ma yake amsawa. A duk sadda ze ga lips ɗinta yadda take tauna abincin kaman wani jan aji ko yanga wadda ya san duk ba haka bane rashin sabo ne kawai da ci a haka ɗin tunda bata yi ɗin, se yaji tsikar jikinshi na neman tashi... Tsammm haka yake shagala da kallon nata, hannun abincin ta kuwa har mantar dashi inda yake yake yi, sun riga sun saba da cimar kasashe barin ma French dishes Amma yanzu da ya kan zauna yaci abin da ta girka se yake jin ba ze iya cigaba da cimar Paul ba. Ita kuwa askin da yayi ne yake ɗaukar hankalinta, a hankali take satar kallon kan nashi da lowcoat ya maidata se ya kara mishi wani irin kwarjini da haske, yanzu ne take Kallonshi as cikakken musulmi don in zaka ɗau lokaci kana Kallonshi kana iya hango taɓon sallah da ya fara yin baƙi daga goshin shi. A duk sadda idanunsu zasu haɗu se su wani basar kaman ba Satan kallon juna suke ba, haka dae aka gama cin abincin ta tattare wurin suka koma parlor anan suka cigaba da tarihin annabawa inda take basu na Annabi Musa da firauna, sossai nan kam ya sakar mata idanu yana kallo wadda wani lokacin har kakarewa take saboda yadda gabaɗaya ta rasa natsuwar ta take neman Rikicewa.. Fahimtar hakan ya saka shi sakin murmushi me sauti, tarihin da ba'a karasa ba kenan ta gudu don ya hanata sukuni da kaifaffun idanunshi. Kaman yadda yace ɗin kuwa haka ta shirya Dukda tana Tunanin CA ɗin ta kaman wasa ta duba group chat ɗinsu se taga an yi canceling hakan ya bata natsuwar tafiyar, washegari da yamma suka fito duk a shirye. Sanye yake da wasu designers shirt and trouser na kamfanin Dolce and Gabbana wadda daga kallon ido kaɗai zaka fahimci ba kananun kuɗi ne aka kashe wurin sayar su ba, kafafunshi as usual sanye da rufaffun takalma, facing cap baƙi da kuma face mask baki ne a fuskanshi, hannunshi ɗaure da Iwatch na kamfanin Samsung. Ba karamin kyau yayi ba barin ma yadda yake tafiya cike da mazantaka. Daga gefenshi yaran ne kusan dukkansu riga da wando ne jikinsu se suka daddaura after dress me shara shara da kananun designers half sunna da daga gani zaka san na asalin Larabawa ne banda duwatsu babu abunda ke walwali a jikinsu, Junior sanye da kananun kaya shima me kyau rike a hannun Norah, murmushi yake saki sa'i da lokaci idan yaga yaran a haka tare dashi se yake jin cikakken farin ciki me sanyi wadda be san dalili ba. Duk mota suka shiga bayan ya karɓi junior, agogo ya duba yana me mata uzuri dukda jira na daga cikin abunda ya tsana amma se ya lura Inde har itace ze jira baya jin ginshira da jiran, ya san shirya yaran nan ne ze hanata yin nata cikin natsuwa, kaman an ce ya ɗaga kai ya hango ta tana tahowa.. Idanunshi gabaɗaya ya sakar yana me kallonta a lokaci ɗaya zuciyarshi na wani irin harɓawa, sanye take da peach tummy trouser me faɗi se blouse white shirt me dogon hannu wadda yake da tattara daga karshe hannayen, peach gyale ta yane kanta dashi se hill peach dake kafafunta da handbag white, a yadda take saurin se tayi mugu mugun tafiya da duk wani imaninshi, idanunta masu haske da suka haɗu da hasken rana se suka bada wani sparkle me kyau, lips ɗinta ya ɗan kurawa idanu banda shining babu abunda suke, ɗauke kai yayi yana jan iska tare da hurowa se ya lumshe idanunshi daidai sadda ta shiga motan kamshin ta ya dake shi, komai nata me sanyi da fusgan hankali ne. Tafiyar ta, maganar ta, adonta, kai komai da ya dangance ta abu ne unique da be taɓa gani daga wurin kowa ba se ita, gaishe shi tayi hakan yasa ya ɗan buɗe idanu ya kalleta kan ya amsa cikin kulawa. Har suka isa Airport yanayin shi be daidaita ba, ko a cikin jirgin ma lokaci lokaci su kan kama juna suna Satan kallon juna, ko da suka isa resorts me tsananin tsada aka musu masauki a harabar wurin kuwa suka haɗu da sauran en wasan na kwallon kafa wadda kowa ya ɗauka ita ɗin matarsa ce, wayancewa tayi wadda hakan ya burgeshi matuka suna gaisuwa cikin mutunci da colleges ɗin nashi da matansu, rashin hayaniyar ta ke bayyana kamewarta wadda komai sa idonka bazaka taɓa gane cewa ita bakuwar irin rayuwar ne. Se yaji wani girma ya ƙaru mishi musamman da wasu ke tsokanarshi da dole ya dinga ɓoye matarshi yake hana kowa ganinta ashe ya san abunda ya ajiye, wasu kuwa yaran ke ɗauke hankalinsu barin ma junior da yake so energetic. A gajiye suka kwanta, shi kam dayake ba wuri ɗaya suke ba Bama su san sadda ya kwanta ba. Washegari da safe a tare dasu ya zo ya karya ya sake ficewa bayan ya tabbatar babu abunda zasu nema. Da yamma suka fito a shirye tsab zuwa stadium ɗin da zasu yi wasan, ita ball ba abun kallonta bane sede ta wuce ana kallo amma yau se ta tsinci kanta da zumuɗin kallon wasan, tunda ta san yana ciki. "King Boudouin Stadium" shine rubuce daga saman hadadden stadium ɗin, mutane ke ta shiga ta ko ina saboda zazzafar wasa ce barin ma an san PSG ne zasu buga, wadda ya kawo su ne yayi leading ɗinsu har kujerun da Raed yayi mishi umarni wadda suna daga gaba gaba. Suna nan zaune ba'a yi mintuna ashirin ba se ga en wasan sun fara shigowa da joggings suna shaking hands da yaran da suke jere suna musu maraba, Seda suka daidai ta a filin kan aka fara gudanar da wasan da yayi mugun tafiya da ita. A nan ta sake take mishi kallon da bata taɓa yiwa wani ɗa namiji ba, duk inda ze yi idanunta na manne dashi wani lokacin in an mishi mugunta ita se ta fishi jin zafin, yaran se surutu suke wadda Junior dake hannun su shi kuwa se son sulmuyewa yake ya sauka tsabar kiriniya, gaskiya ko! me kallon ball se me cikakken natsuwa in ba haka ba jininka a take se ya hau saboda suspense. Wasan yayi bala'in zafin da duka clubs ɗin kowanne gwanaye ne, hakan ya sa aka ja lokaci sede attempts amma babu maganan ci, Ana gab da tafiya hutun rabin lokaci Allah ya ba Raed sa'a ya cilla kwallo a raga zo kaji ihun mutane, har Hidayat seda ta mike don murna tana tafa hannaye, shi kuwa sujada yayi yayinda sauran en team ɗinsu suka zo da gudu suka rungume shi. Ba'a cigaba da wasan ba aka tafi hutun rabin lokaci inda suka koma gefe suka haɗe kai ana shawara, ko da suka dawo daga hutun chanza salo kowanni club suka yi, dayake in an dawo ana chanza raga hakan yasa yanzu nasu Raed ɗin ke kusa kusa da inda suke, Ko da suka fara wasan lokaci lokaci ya kan kalleta ita kuwa bata sanin tana sakar mishi murmushi, shima se ya mayar mata Dukda tazarar dake tsakaninsu. Ana cikin wasa Raed ya ɗauki ball kenan yana cikin gudu seda ya shiga 18 kan ɗan ɗaya team ɗin ya zo da niyyar kwace ball ɗin inda da gangan ya sa kafafun Raed tsakankanin nashi ya murɗe, ƙara ya saki yana faɗuwa ringine a take referee ya hura wristle, don ba irin ciwon tashi lokaci guda bane daga yadda ya sa hannayenshi ya rufe fuskanshi hakwaranshi a haɗe zaka san yaji zafi sossai. Da gudu first aid suka zo aka cire mishi takalmi ana rubbing ankle ɗin, se ga Hidaya da take jin kaman an zuba mata garwashi a kirji na hawaye cap cap, haka kawai an ji mishi ciwo, tana Tunanin zafin da taji a sadda abun ya faru shi be ji ba. Su Norah se maganan suke tayi bata iya ta tanka su ba, ga mamakin ta se gashi ya tashi Dukda an ba wanchan ɗin yellow card akwai kuma penalty, yana ɗan dingishi da wullan kafan ya sake fara ɗan gudu se ta ɓata fuska tana me Kallonshi da kyau, yanzu cigaba da wasan ze yi? Bata rufe baki ba kuwa ya seta ball ɗin yaje da gudu ya wulla da taimakon en team ɗinshi se ga ball har cikin raga, nan fa wuri ya kaure da ihu. Junior ne ya ishe ta da koke koke ta kuma san pampers ɗin jikinshi ne baya so maybe yayi fitsari ciki, miƙewa tayi tace Norah ta kula dasu Farrah bari ta zo, ta ɗauke shi suka fara ratsa mutane suka fito zuwa wuraren toilets akwai mutane a wurin ma Dukda daidaiku ne da kuma en jarida, toilet ta shiga ta chanja mishi pampers yana ta sakata magana. Suna fitowa ya fara tsalle akan ta sauke shi ya tafi da kafan shi, garin sauke shi ya fincike gyalen kanta ya kuma kwasa da gudu, gashin kanta da yake a gyare a tsabtace ya zubo har kafadunta a kufule kaman zata yi kuka tace "Muhammad Raeeed" idanunta na cika da hawaye tace "come back here pls! Ka ga fuskanka kaman na takwaranka in na kama ka I swear se kayi kuka.." Bata san maganan da take da muryar takaici ya fara jan hankalin mutane kanta ba kawai se gani tayi idanun sun mata yawa se ta karasa Rikicewa ta rasa inda zata sa kanta, daga bayanta taji an sauke mata abu me yauki bisa kan nata tare da tattare gashin cikin abun aka ɗaure mata, da sauri ta juyo tana matasawa baya sbd daga kamshin da yadda bugun zuciyarta ya sauya ta gama tabbatar da shine. Tana juyowa ta kara ɗan firgita da taci karo da broad chest ɗinshi packs ɗinshi gasu nan raɗa raɗa alamun rigan jikinshi ya cire ya saka mata a kanta, camera ya jima da yin aiki a kansu yayinda wani ya Riko mata Raed junior ya miƙa mata da gyalen se Moh ya sa hannu ya karɓa duka, gaba ya ɗan yi se ta bi bayanshi tace "gyalen fa!" Ya ɗan waiwayo yace "oh! Bayan kin gama zagar mana fuska se mu baki?" Duka idanunta ta waro tace "ni?? Yaushe?" Sun ɗan shiga lungun stadium ɗin se ya juyo gabaɗaya yace "ok, zamu baki but repeat that name u called" Tsakani da Allah be taɓa jin sunanshi ya mishi wani daaɗi ba seda yaji a bakinta har skipping heart ɗinshi yayi, se ya kalli junior yana kara jin kaunar yaron don be taɓa sanin sunanshi Muhammad Raed ba se yau, sunanshi ta sakawa ɗan ta.. Kanta ta mayar kasa tana shagwabe fuska ba tare da ta san tayi hakan ba cikin ƙasa da murya.. "Ba zan iya ba!" Idanu ya kura mata kan shima cikin irin muryar da tayi magana yace "why??" Da sauri ta juya mishi baya gudun kar ya ji sautin bugun zuciyarta da yake bugawa da komai nashi... Juyawa yayi ze tafi bayan ya ɗauke kai daga kallonta se tayi saurin juyowa. "Eyyaaa mana pleaass..!" Ta ja maganan, numfashi ya ja ya lumshe idanu ya sake warewa, yarinyar nan tana illata shi ba tare da ta sani ba. Illar da shi karan kanshi be sani ba, juyowa yayi ya miƙa mata gyalen ta saka hannu ta riƙe se be sake ba seda ta ɗago manyan idanunta suka shiga cikin lumsassun nashi, shagala suka yi da kallon juna har Seda junior yayi tsalle yana kiran sunanshi kan yayi saurin sake mata gyalen, ta juya ta yafa kan ta zame Rigan shi ta miƙo mai ya karɓa ba tare da ya saka ba ya juya ya shiga cikin filin rike da Junior saboda shi ya riga ya fita a wasan an chanza shi da wani sbd kafan shi da ya ɗan dameshi, a lokacin da ya duba be gansu bane ya fito duba su sbd sanin ba sanin ko ina tayi a garin ba. **** Zaune yake gaban ɗakin na Abba da ake kara duba lafiyanshi saboda har yanzu idanun ne yake buɗe se kuma da alama yana gane mutane, amma be yi magana ba kaman yadda be yi tafiya ba zaman ma se an saka pillow fiye da uku ya tattare shi. A hankali yake scrolling bisa Facebook ɗinshi kaman daga sama ya sauka kan wani hoton da ya saka shi dakatawa, Tarr fuskan hidayat ya bayyana sanye da wani ash Abaya me stones dayawa, kanta Rigan kwallon kafa na PSG ne yayinda Moh ke tsaye a bayanta daga shi se wandon jesi, takalmi da dogon socks murdadden jikinshi duk a waje.. caption ɗin shine "Love in the air❤️ the greatest footballer MOH RAED covers his wife as she lost her hijab mistakenly in public" Ras Ras haka zuciyarshi ke bugawa a take idanunshi suka chanza launi, wani irin tashin hankali ne ya lallaɓo ya rufe shi, post ɗin it's just 10mins amma comments har ya haura 300 kuma ci gaba ake da comment, a sadda ya shiga ya farawa dubawa banda yabawa da su awwn da ake babu komai, sake wayan yayi yana jin kaman ya sa hannu a kai yayi ta ihu... Babu me fahimtar dasu cewa ba matarsa bace? "Kai hamza lafiya kuwa? Ko jikin Alhaji ne?" Yana juyowa yaga Hajiya ce da Zainab se kawai yaji hawaye na shirin kubce mishi, da sauri ya zagaye su ya wuce, duk tsaye suka yi suna kallon shi se kuma ya dawo ya finciki wayan kaman shine ya mishi laifi ya fice fuuuuu... **Yau na shirirince🤣 muma mun ɗan taɓa love a zo a dannewa hamza kirji* #Vote #share #comment 🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 28* *FREE BOOK* **Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka, fatan duk muna cikin koshin lafiya, kwana biyu kun jini shiru lafiya ta ƙalau wallahi I was extra busy ne, I was occupied ta yadda ko online bana hawa se in ya kama so waenda suka min messages zan yi reply in na karasa natsawa kuyi hakuri! Waenda suka kirani kuma na gode🙏 Allah ya bar zumunci** "Nace ku min bayani dallah dallah!!" Ya daka musu tsawa a karo na babu adadi, gabaɗaya rayuwarshi be taɓa samun sukuni ko na miskala zarratin ba, komai yanzu baya mishi daaɗi, komai baya sa shi farin ciki, bakin cikin da yake kwasa da yaran cikinshi abu ne da baze faɗu ba. A tsorace suka fara bayani dallah dallah sace sace da ake ta mishi sune suke yi suke rabawa tsakaninsu, yadda zarah ta sace kudadenshi suka ɗaurawa Mairamu, yadda suka yi ta Haɗawa Raed tuggu yana ɗaukan munanan mataki a kanshi. A hankali wani irin sanyi ke rarrafowa yake lulluɓe shi kwarai laifi me girma ya aikatawa ubangiji da ya jarabceshi da waennan matayen, wacce ita ce jin daaɗin duniyar shi yayi silar mutuwar ta da hannayenshi, abunda yake taɓa mishi zuciya shine har karɓar diyya yayi amma yaronta ko biyar be amfane shi da kuɗin ba a Tunanin shi mamanshi shi take kashewa kudadenshi da suke ɓata. Yunkurawa yayi da nufin rufe su da dukan mutuwa sede jininshi da ya hau a take ya saka ya yanke jiki yayi wani irin faɗuwa, ihu suka kurma dukansu uku suka yo kanshi da gudu, ganin mummunan yanayin da yake ciki yasa suka fita suka nemi taimako aka zo aka yi asibiti dashi. Tashi ɗaya bayan dogon bincike likitoci suka tabbatar da irin faɗuwar da yayi da yadda jikinshi ya hau fiye da ƙima ya samu paralyze komai baze iya yi da kanshi ba. Sun sha kuka a lokacin kam, kwananshi goma a asibitin yana cin wuya don ko magana a karkace yake fitowa, su kuwa tun suna jinyar da ɗan daaɗin rai suka fara mishi kawai na dole, don suna yi suna mita, ko Daadida basu kira sun sanar da ita abunda ke faruwa ba har aka sallamo shi ya cigaba da cin baƙar wuya saboda rashin kula. **** Kira yake yana sakewa sede be same ta ba, haka baƙin ciki na cinshi ya dawo asibitin ya cigaba da kula da Abban shi zuciyarshi ba daaɗi, yana jin tsananin ciwo da idan har aka ce ya rasa hidayat babu abunda ze hana shi mutuwa, hawaye ke cika idanunshi yana maidawa shi karan kanshi be san wani irin soyayya bace wannan. "Ham....za!" Muryar Abba cikin Crack ya kira sunanshi saboda bacewa da yayi cikin tunani. Da sauri ya mike ya iso kusa shi tare da kama hannunshi se hawaye sharrrr "Abba yau Kaine ka kira sunana da bakinka? Ashe zan sake jin amon sautin muryar ka da kunnuwa na? Alhamdulillah ya Allah!" Shafa kanshi Abba yayi a hankali yace "menene? Yake damunka" A rarrabe maganar ke fitowa. Da kyar ya iya tsayar da hawayen shi yace "Abba hidayat ce take so ta kashe ni! Abba na rasa me ke damuna a kanta anya ba wani sakamako bane soyayyar nan? Abba wallahi ji nake kaman zan yi hauka..." Kuka ya ci karfin shi. "Kana... Kaiwa Allah kukan ka kuwa?" Girgiza kai yayi yace "Abba Bana samun natsuwar yin ibada yadda ya dace, Abba na san hakkin aure na kuma san ina tauyewa zainab hakokkinta saboda masifaffen soyayyar da nake yiwa Hidayat amma na kasa controlling kaina in ba kaina natsuwar da ta dace..." Rike hannunshi yayi da kyau yace a wahalarce. "Ka natsu! Ka tsaida hankalinka wuri guda kaji? Ka roki ubangiji ka kuma lazimci karatun Alqur'ani zaka samu natsuwa in shaa Allah" Kai ya gyaɗa Abban ze sake magana aka budo kofa ko ba'a faɗa mishi ba ya san wacece hakan yasa ya saki hannun Hamza tare da lumshe idanunshi. Da kallon rashin fahimta duk suka bishi sede ba wadda yace komai saboda ba'a so ana takura mai amma fa abun akwai alamar tambaya ita kanta hajiya ta kula da yadda yake share ta tunda ya farka ko kallon second biyu be taɓa mata ba. **** Kan a tashi wasan nan seda kowa ya san Raed junior don gefe wurin zaman en kwallon ya zauna dashi ya ajiye shi kan grass carpet, yaro kam ya ruga ya je ya fara tura ball dake zaune daga gefe incase in na ciki ya samu matsala a sauya shine dalilin ajiye shi, da kyar yake tura ball ɗin se hankalin players da suke waje ya koma kanshi suna ta murmushi in aka tambayi sunanshi kai tsaye yake cewa "Raed junior" cikin wani irin alfahari, wannan shine takwararsa na farko, lokaci lokaci se ya kalli inda take ya saki murmushi Dukda bata Kallonshi bare ta san yanayi kanta a ƙasa. A ɓangaren ta kuwa zurfi cikin tunani tayi, bata taɓa jin abu makamancin wadda taji ba a jikinta ɗazu, eye contact da suka Samu ya bata wani saƙo me girma ga duk sassan jikinta har yanzu a jikinta take jin wasu abubuwa da suka dinga shiga idanunta a sadda suke kallon junan suke ratsa jini da jijiyarta, menene hakan da har yanzu sukuninshi ya ƙi barin ta? Lumshe idanu tayi tuna yadda ya sake protecting dignity ɗinta cikin jama'a be bari an kalli gashinta ba wadda shima yake al'aura ne a gareta tunda musulma take. Wasa wasa wasu sabbin abubuwa ne suke shiga tsakaninsu a cikin ruwan sanyi, kan su bar Belgium Seda suka sha yawo da kalle kalle, cima kuwa babu abunda basu ci ba a garin se abunda Allah ya haramta. A duk lokacin da ta kalli kanta ta kuma kalli yaranta taji yadda junior ke tashi babu Kalmar hausa ko guda a bakinshi taji yadda Aisha take mance ta iya hausa wani zubin ko ita Hausar ya fara mata wahalan yi se tace ina Yusuf yazo yaga yadda rayuwa ta koma mata? Lokuta dayawa ta kan kalli Raed taji duk duniya shine namiji mafi girman ƙima a rayuwarta saboda ya mata abunda babu wadda ya mata a duniya, yana ƙaunar yaranta fiye da yadda uba ze kaunaci yaranshi.. Hakan yake bata kwarin gwiwar tsayuwa tsayin daka da jajircewa bisa ilimin addininsu kuma Alhamdulillah ba karamin kokari suke ba tunda Allah ya riga ya sa musu kaunar addinin. "Rash...!" Ta kira sunan cikin kosawa don tunda suka haɗu take ta maganan hotunan su da yaje viral ita kuwa a duk sadda taji maganan har tsikar jikinta take tuna moment ɗin. "Ke komai zaki ce Kice, kin san Allah you were the real definition of perfect couple, na rantse baki ga yadda kuka bada kala bane" Duk yadda ta so hana kanta blushing Seda tayi, ta kau da maganan da "kin san ya hamza yana ta fushi a kan hoton nan? Duk yadda na mishi bayani ya kasa fahimta, sincerely bana son irin yadda yake yi it's like rashin yarda.." Ajiyar zuciya Rash ta sauke tace "in dae har kin san zuciyarki na son Raed it's high time ki gayawa hamza yayi hakuri, a gaskiya bana so ki sake komawa rayuwar wahala da bakin ciki wadda kika yi a baya ma ya isa, Raed kanshi a waye yake, rayuwarshi duka irin na Turai ne sannan labarinku na kamanceceniya ina ga ko don wannan Zaku rungumi juna ku baiwa yaran ku kulawar da ta dace" Ajiyar zuciya ta sauke tace "wannan fa ke kike Tunanin nan Rashida shi Raed ɗin ya taɓa cewa yana so na ne da zan kori ya hamza? No, I Will pray idan hamza Allah ya zaɓa min zan zauna lafiya da family ɗinshi in shaa Allah" A wurin suka bar maganan suka shiga wata. A gajiye ta dawo gidan Allah ya taimake ta yau ma kaman tunda suka dawo a waje ya sayo musu abincin rana so bata yi girki ba, bayan sun gama karatun yamma wadda shi be samu yayi ba sbd meeting da ze yi attending suka zauna hira. "I almost forgot! Na san Dad ma wallahi ya mance Farrah tomorrow is ur birthday" Cewar Norah cikin mamakin yadda suka so sha'afa. "Wow.. Farrah is turning 7 tomorrow it's a call for celebration" Hidaya tayi maganan fuskanta cike da fara'a, nan fa Farrah ta fara tsalle wai ita ta girma, Aisha ce tace "nima mama ai I will be 7 soon ko?" Hidayat tace "yeah but Farrah ta baki almost 3months" A take rikici ya barke Farrah wai se Aisha ta dinga ce mata big sis tunda ta girme ta, hidayat da Norah de se dariyar su suke tayi. "What's so funny?" Yayi maganan bayan ya shigo don ko sallamar shi basu ji ba, tsagaita dariyar da take tayi, idanunta dake sparkling na ɗan ruwa da ya taru a ciki sbd dariya ta ɗaura a kanshi, ɗauke nashi yayi ya maida kan Norah da take bashi labarin abunda yake faruwa. Murmushi kawai yayi yace "nima I almost forget tomorrow is my little angel born day, I will think about how we celebrate" Se lokacin Hidayat tace "welcome sir" Yace "thank you" Daga haka ya saki hannayen Aisha da Farrah da yake rike da yana tambayar Junior, Norah tace yana bacci. Wucewa yayi ɗaki don yana so ya ɗan yi wani aiki kan magrib maybe da safe zasu yi team trip wadda a bus na players ne dayake ba nisa zasu yi ba. Aikin ya riƙe shi sossai magrib ya fito yayi ya sake komawa har ze shige tace "Sir! Do you need anything?" Kallonta ya ɗan yi yace "just coffee" Kai ta gyaɗa ya shige, ita kuma ta tashi tana instructing yaran da suyi karatu tana zuwa. Kitchen ta shiga tana jujjuya yadda zatayi approaching ɗinshi da maganan dake cin ta wadda shine abu na karshe da zata so taga ya gyaru a rayuwar shi, honey coffee tayi ba me sugar ba, tayi cup ɗin yayi looking so good daga ido ma bare in ka kai baki. A karamin tray ta ɗauka ta nufi ɗakin sanye da free bubu se karamin chantley vail ba hula kanta tubkakken gashinta ya taimaka wurin riƙe gyalen da kyau ya fito da fresh and smooth face ɗin ta da babu komai bisa kai. Da sallama ta shiga yana zaune yana duba abu lokaci lokaci kuma yana ɗan rubutu, she feel it's not the right time to bring this up but ya zama dole tayi maganan bcs she doesn't want it to be late for him, ajiyewa tayi ya ɗan ɗago ya bata quick glance tare da cewa "thanks" Ya maida kanshi kan aikin, se ta gyara tsayuwa ba tare da ta tafi ba, jin har lokacin tana tsaye ne yasa ya sake ɗagowa yace cikin husky musculine voice ɗinshin nan "akwai wani problem ne?" Kai ta gyaɗa, yace "sit" Tare da nuna mata bakin couch na ɗakin, zama tayi tana fuskantar shi kanta a ƙasa tana karatun kuda, kan ta Haɗa confidence tace "Amm Daadida called..." A take yanayin fuskanshi ya sauya yace "what?? Why? When did you knew each other?" Ya haɗo mata duka tambayoyin. "Am sorry we knew each other not so long after na fara aiki, the truth is Dukda tunda na zo na fuskanci irin kalar rayuwar da kuke na saka a zuciyata dole ku gyara kuma Zaku gyara sede before taking any action or measure,one respectful day Daadida ta kira and ba kowa a gida I picked with salam, shine abunda ya ja hankalin ta tayi murna sossai and made me take a promise na saita rayuwarku." Dakatawa tayi ganin yayi relaxing bayanshi jikin pillow tare da lumshe idanu Fresh kafanshi Kal Kal kaman wadda baya taka ƙasa a harɗe bisa gadon kaman yadda hannayenshi suke rungume a kirjinshi, ba tare da ta jira yayi magana ba ta cigaba "wasu abubuwan na ban tsoro ba wai na tsoratarwa ba, sede I was confused how can a muslim wadda yake amsa suna musulmi ba ze iya yin komai daidai a addinin shi ba? daga karshe to clear my doubts na nemi ta bani labarinka and..." Yadda ya buɗe idanunshi da suka rine a take ya zube bisa kanta ne yasa tayi shiru tana maida kanta ƙasa. "She gave u?" Ya watsa mata tambayar. Kai ta gyaɗa tana me satar Kallonshi, se ya maida idanun ya sake lumshe wa ranshi sossai ya sosu kawai he doesn't like the fact da za'a ke Kallonshi da idanun tausayi bisa past ɗinshi, yana ganin yanzu ya riga ya wuce wannan mataki baya Tunanin kuma ko da za'a Haɗa en gembu karankatakap babu wadda ya isa ya ɗaura ɗan yatsa a kanshi se idan shine ya bada dama bare ayi maganan su Badi'ah. He got billions of dollars ba ma Nairas ba shiyasa yake jingine baabin rayuwarshi na da kaman ba'ayi ba. "Am sorry!" Tayi exclaiming. "Did you helped saboda wanchan wicked mutumin?" Ya watso mata tambayar ba tare da ya kalleta ba, daga muryarshi zaka san ranshi yayi daci. "Please don't address him like that, he's ur fathe....." "Hold on!!! Just hang on there..!" Ya faɗa da ɗan faɗa faɗa Dukda yadda yake kokarin calming kanshi saboda ita ce, da wani ne yana da tabbacin da yanzu police da zasu raba su su kuma yi musu tsakani sun iso. "Am sorry!" Huci me karfi ya fesar tare da sa hannu ya shafa kanshi yana me dunkule hannun, cikin muryar da ta fara mishi wahala yace "answer me" Tace "no, I helped because of Allah(SWT) abunda kuma ya kara min hakuri da juriya is because u also helped me! u are my life savior so in one way or the other I have to find a way da zan maida ko da da kaɗan ne cikin dumbin alkhairinka gareni.." Bakinta dake motsi a hankali yake fidda kalmomi masu kama hankali da natsuwa kawai yake kallo, chan yace "thanks! But as from now bana so ki sake alakantani da wadda ya jima da yanke alaka dani for decades ago, u can leave" Yayi maganan tare da maida hankalinshi kan system ɗinshi Dukda idanunshi da suka nuna kwantaccen bacin rai me wuyar fassaruwa. Bata da wani option se na bin umarnin shi, ajiyar zuciya ta sauke bazata gaji ba kuma bazata karaya ba Dukda ko kadan bata ji daaɗin saka shi a mood da yake ciki yanzu ba sede dole zata cigaba da kawo mishi maganan har ta samu ta shawo kanshi. Tana fita ya sake nannauyar numfashi tare da ture system ɗin, ko yace ze cigaba da aikin karya yayi, coffee ɗin ya ɗauka ya kurba tare da lumshe idanu yana jin yadda daaɗin shi da gardinshi ke bi mishi ko ina ga sanyi da ya ɗauka. "Daadida!!!" Yayi exclaiming yana hautsina fuska se ya janyo Wayanshi ya danna mata kira. #Vote #share #comment                  🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 29* *FREE BOOK* "What do you think old lady?" Ya watsa mata tambayar bayan ta ɗauka ko sallamanta be amsa ba. "Assalamu Alaikum warahmatullah" Ta sake cewa, karamin kwafa yayi yace "Wa'alaikumussalam warahmatullah duk yadda kike so ki kauce maganan nan baze kaucu ba, what do you think? Karki manta fa hidayah is my worker, she's under me I see no reason da zaki yi involving ɗin ta cikin mess ɗin wanchan mutumin" Tace "Raed ina yini?" Haushi ne ya kama shi, ze kashe tace "Allah kana hanging call nan zan saɓa maka Raed, wai kana dauka baka da mafadi ne kab duniya? Don na faɗa mata labses ɗinka wani abu ne? Mahaifinka na kwance a chan rai a hannun Allah ko kudin kunun da ze sha babu kana zaune a matsayin multi billionier ba abun kunya bane a wurinka?" Dariyar rainin hankali yayi, yana tuna clearly a sadda yake gaban mahaifin nashi da bin mawanki yake samu yaci wani lokacin ma haka ze yini ya kwana be ci komai ba. "Kunya!! Wow hmmm, the last time I checked da bakinshi ya ce na kara Haɗa sunana da nashi be yafe ba so it's up to him.. I just call to tell you hidayah bata san mutumin nan ba, bana kuma so ta sanshi in one way or the other bcs he always end up hurting duk wadda ya mu'amalance shi da alkhairi, and am very sure a labarin da kika bata she end up shading tears I don't like that... Good night" Yana kai nan ya kashe Wayanshi. Washegari kusan ya fita da sassafe don bayan abunda zasu yi akwai Private jet da ya saya don ya gaji da bin public abubuwa alhali yana da kuɗin yin na kanshin, yana so ayi launching ɗinta a gaban shi Sam ya sake mantawa da birthday ɗin Farrah.. Suma da suka tashi school hidaya ta tarkata su suka tafi, bayan sun tafi ta kira Rashida dama tun jiya suka yi magana ta zo da masu Deco, they decorated parlorn saman so perfectly yayi matukar kyau, ita da Rash suka yi berbie cake sbd Farrah na kaunar berbie, shima kaman ka lashe don kyau da tsaruwar da yayi, snacks da Chinese rice mara yawa sukayi da kuma pepper chicken da kuɗin da hamza ya bata na Kasar suka yi anfani wurin sayo en abubuwa kaɗan da babu a gidan. Wanka suka yi suka sauya kaya, a cikin kayakin da yake sassayawa yaran ta zaɓarwa kowa kayan sawa, birthday girl kuma ta cire mata wani purple gown me kyau da crown, suna isowa kuwa Rashida ta tare su a ƙasa, a chan suka yi wanka kowa ya saka kaya, crown ɗin bata sauko dashi ba. Suna fitowa zasu haura se gashi nan ya shigo yana sauri don daga Airport ya tuna birthday ɗin, saɓanin ɗazu da kayan ball ne jikinshi yanzu Ash suit ne da red tie da ƴar ciki itama red, da gudu suka je suka mishi oyoyo, ya shafa kan Farrah dake tura baki yace "am so sorry my princess, happy birthday" Dukawa yayi yayi mata peck a goshi yace "I love you today and always" Murmushi ta saki yace "u look good... Lemme go and freshen up se ki zabi duk inda kike so muje se mu je right?" Kai ta gyaɗa, suka nufi sama don tuni Rashida ta haye. Dulum suka ga saman dama asali shi wutan shi romantic light ne da dinner light, dukda sun fi anfani da romantic one ɗin be da haske sossai, sede yanzu Dulum dukun. "Miss hidayat! Aunt Rash!" Norah tayi kiran sunan, bata rufe baki ba haske ya gauraye parlorn. Rashida da Hidayat suka fito suna tafa hannu suna yiwa Farrah "happy birthday to you...!" Suna sauke first verse Norah da Aisha da ma Raed suka karɓa suna mata tafi, idanunshi zube kan hidayat da tayi wani irin kyau cikin Ash gown da ta sanya, turtle neck ne hakan yasa hula turban red kawai ta sa a kanta se wani fancy earring ta ɗan yi light makeup da red hot lipstick kafafunta sanye da wasu flat takalma masu taushi red. Sossai tayi mishi kyau and it was like a coincidence shima Ash ne jikinshi and red, Farrah tayi farin ciki ba kadan ba, dukda home party ne su ya su sede yayi kyau matuka, hidayat ta ɗauko crown ta saka mata, sun sha hotuna a 15 pro Max ɗin Raed wadda ko sau daya be yarda hidayat ta fita daga ciki ba daga nan Farrah ta yanka cake ta fara ba hidayat tayi mata kyakyawar runguma tace "thank you miss hidayat.. I love you" Tana murmushi tayi hugging ɗinta back tace "love u more baby girl" Ta juya ta ba Raed shima haka ta mishi kan ta ba Norah da Aisha da Kuma junior da yake ta so ya rusa cake ɗin, sossai ya sakar mata idanunsa masu rikita lissafinta so yake ta kalleshi sede taki Sam don tana jin kwayar Mayun idanun nashi a kanta. A hankali yace "thank you!" Se ta ɗan ɗago ta kalleshi tare da sakar mishi murmushi wadda yayi sanadiyar lobawar duka dimples ɗinta so Masha Allah, kasa dauke idanu yayi daga kallonta, yarinyar nan ta mishi illah! Illar da baya Tunanin yana da magani. Abinci suka ci wadda kaɗan kaɗan ne amma different varieties da snacks, daga nan ya shige yaje yayi wanka, ya sauya da kananun kaya suka yi la'asar, ya so su fita sede Farrah tace miss hidayat party is ok. Shi kaɗai ya sake fita ya sayo gifts ya dawo wadda seda ya sayawa hidayat wani diamond necklace me shegen kyau, ita kuma birthday girl sabon laptop da headphone me kyau, Norah da Aisha ma duk ya saya musu abu. Ko da Rashida zata tafi kudi ya baiwa Norah ta kai mata wadda a kudin Nijeria sun kusa dubu ɗari shidda zuwa bakwai Don 500dollars ne. Miss Mary ce ta tattare parlorn yayinda Paul yayi wanke wanke, suna zaune a ɗakinta da Farrah da Junior yayinda Norah da Aisha suke ɗakin Norah suna abunda ya shafesu call ɗin hamza ya shigo mata.. A natse ta ɗaga suka gaisa jin yanayin muryarshi kaman be da lafiya yasa ta tambaya "ya hamza fatan kana lafiya? Naji voice ɗin ka is sounding somehow" Yace "eh hidayat! Bani da lafiya I was admitted ma" "Subhanallah! Meke damunka?" "Stress ne ya haifar min da fever but am getting much better" "amma meyasa kake stressing kanka dayawa har haka yaya?" Yace "Toh ya kike so in yi hidaya? Uhm? A duk sadda zan tuna kina gidan wannan ɗan kwallon se gabana ya faɗi ina tsoron rasaki, sannan a nan zainab bata barni na sha iska ba the moment haihuwar ta na ƙaratowa the moment take ɗaga min hankali akan sunan da na yiwa kaina alkawarin sawa" Shiru ta ɗan yi kan tace "amma yaya ai na gaya maka ka kwantar da hankalinka, be kamata kana pressurizing kanka akan waennan kananun magunganun ba, zainab kuwa ba sunan hajiya bane?" "No! Sunanki nake son saka wa" Wara idanu tayi a zuciyarta tace ai dole zainab ta ɗaga maka hankali, soyayya kaɗai ma da take ga muna yi ta hanani zaman lafiya da call bare kuma ka sakawa ɗiyar ta sunan wata buduruwarka. "Amm yaya hamza a nan gaskiya ban ga laifin zainab ba! It's unfair mana ina ga har yanzu baka san menene kishi ba a wurin mace, babu macen da zata yarda da wannan duk haƙurin ta kuwa kayi hakuri ka barta ta sa sunan da ya mata please!" Shiru yayi, tace "kaji? Please" Yace "Toh naji na amince, yanzu dae bar maganan zainab ya namu maganan?" "Yadda kace in Shaa Allah" "Toh na ce daga Abba ya samu sauki saboda 100% goyon bayanshi na tare damu, yana karasa warkewa in Sha Allah zaki zama matata" Murmushi ta saki tace "yanzu am engaged kenan?" Yace" Morethan that ma, ni a wurina kin riga kin zama tawa" Dariya ta ɗan yi tana kallon Farrah da ta tashi da gudu ta fice kaman wacce aka kore ta tace "Ohk ka gaida Abba" Yace "in shaa Allah! Thanks take care" Ta sauke wayan tana me kishingiɗa da pillow, hannunta ɗaure bisa kan shafaffen cikinta da bazaka taɓa cewa ƴaƴa har uku sun zauna ciki ba, hamza is something else ta rasa menene ke hana shi kwantar da hankalinshi in har dae abu da ya shafe ta ne, ba wai tana da niyyar yaudaranshi ko wani abu ba sede tana jiye mishi idan Allah be qaddareta a matsayin matarshi ba! Kwarai zata iya aurenshi ta zauna dashi da iyalan shi lafiya ta auri Yusuf ta zauna da Yusuf ma na kusan shekara goma da daaɗi ba daaɗi bare hamza da yake matukar son ta?. Da gudu ta shigo ɗakin bata damu da zaune yake yana aiki a system hannunshi ɗaya rike da waya yana call jingine da pillows ba ta haye gadon tare da jan hannunshi dake rike da system ɗin tace "Daddy! Daddy! Miss hidayat wants to leave us" Da sauri ya kalleta yace "what??" Yarinya kam se hawaye sharrrr, katse wayan yayi tare da sauke system ɗin ya kamo hannunta "Farrah explain why did you said she wants to leave us?" "Dad this guy we called Daddy hamza he want to take her away from us! She's promising to marry him ahhh I can't believe this" Ta karashe da zabga tagumi tana cigaba da hawayenta. Kallonta kawai yake ganin kaman be ɗauki maganan serious ba Dukda a nashi ɓangaren he's in Morethan shock yasa tace "Daddy this is a big problem, he wants to take her away from us!" Cikin wani yanayi yace "Ohk baby! U know what am gonna do? I will talk to her not to leave us ok?" System ɗin ta rufe tare da matsarwa ta fara jan hannunshi "dadd come with me and talk to her..." Da kyar ya samu ya lallaɓa ta ta kwanta anan bacci ya ɗauke ta, se ya mike ya fara safa da marwa a cikin ɗakin, be taɓa jin fargaba da tsoro irin wannan ba har rawa rawa zuciyarshi yake yi, a hankali ya kai hannunshi aljihun wandon jikinshi ya fiddo wani gidan zobe me tsananin kyau black, da babban yatsanshi yayi anfani ya buɗe wani diamond ring hadadde ya bayyana se kyalli yake, shafa kai yayi ya sake rufewa. Wannan dare haka ya kwana be iya runtsawa ba cikin Tunanin mafita, daga karshe kuma ya tsayar da mafita guda ɗaya.. Idan har be yi working out ba yana da Plan B baya Tunanin kuma ze faɗi.. gab asuba kuma aka kira su akwai wani training haka ya fice da wuri. Ko da ta shirya su suka tafi school ita yau ma bata je ba, kasancewar revision suke yi suna gab da fara exams, bayan ta gama ayyukan ta karatu ta zauna tayi ta dubawa daga karshe ta sake gwada layin Ummi kaman yadda kullum take yi sede bata same ta ba. Abincin rana ta ɗaura musu bayan ta sauke tana fitowa parlor taji Paul na magana, da sauri ta juya wurin kofa yake ce mata oga ya ce ta shirya ta zo ze kaita wani wuri. Tambayar yaran tayi yace lafiyansu ƙalau suna school, ɗaki ta shiga bata tsorata ba sbd ta san dae baze taɓa cutar da ita ba, don haka a natse ta shirya cikin wani riga da skirt na material me taushi da tsada wadda a dinke yazo, hannun dogo ne sede yana da tsagu zuwa gwiwan hannu, kayan ya zauna mata sossai, ta ɗaura dankwalin sossai ya haske fuskanta kasancewar kayan ruwan powder ne. Milk veil ta yafa da milk shoe se handbag shima milk bayan ta saka fashion dan kunne milk, se ta saka sarkar da ya saya mata jiya, fuskanta ba komai banda kwalli da pink lip balm me haske. A natse ta sauko tana duba agogon da ta ɗaura na Apple watch me gold hand, yaran suna da ɗan sauran lokaci kan su tashi don haka bata damu ba ta fito, Paul da kanshi ya buɗe mata bayan katuwar farar GLK ɗin ta shiga ya rufe tare da zagawa ya tayar suka bar kofan gidan... **** "Wai Alhj me nayi maka ne? Bayan Duka shekarun nan da ka kwashe a kwance ina fama da wahalar ka in ci kashinka in ci fitsarin ka da abunda zaka saka min kenan bayan farkawarka? Ai ko me nayi maka ban cancanci haka daga gareka ba Alhj bare ma babu abunda nayi maka" Ta karashe cikin masifa, idanu ya zuba mata yana kallo, chan yace.. "Kika ce babu abunda fa kika min? Toh ba dole kiyi ba tunda ke kika zaɓarwa kanki? Ko kin manta kece sanadiyar wannan ciwon nawa?" Wara idanu tayi tace "Wallahi ba de ni ba, kaima ka san sanadiyar ciwonka ba ni ba kam karka ɗaura min... Ah to" Tana kai nan ta juya fuuu ta fice, da kallo ya bita, Hajiya bazata taɓa chanzawa ba a duniyan nan, Allah ya bashi lafiya shine rokon shi don yana da babban Burin da yake son cimma a duk ranar da cikakken lafiya ta same shi, lumshe idanunshi yayi yana ambaton Allah.. #Vote #share #comment                    🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 30* *FREE BOOK* *Fav sis🥰❤️ wannan page ɗin naki ne I love you ok😘** **Allah in ga Ruwan comment in ba haka ba tohm ni de Zaku jini a salansa🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️** Garin yayi lublub kaman hadari Dukda ba hadarin bane sede tarin ni'ima da garin yake dashi shine ya ɓoye ranan a irin wannan lokacin, tana ta kallon hanya Dukda ba tafiya me nisa suka yi ba suka iso wani gaɓar ruwa me cike da tarin boats Parke a bakin gaɓar daga nan kana iya kallon effile tower Tarr sbd ginin da ya riƙe shin a kan ruwan yake. Buɗe mata kofan da Paul yayi shi ya yanke mata Tunanin abunda ta zo yi anan ɗin, bayan ta sauko ya nuna mata wata mata baturiya yace "she will guide u ma!" Tace "wait! Are you leaving?" Yace "yes ma! My work here is to just drop u and go back home" Kai ta gyaɗa ya shiga motan ya fice kan ta kalli matar dake gaisheta ta amsa, jagora ta mata zuwa wani tamfatsetsen jirgin ruwa me tsananin kyau fari Kal, wani keɓantaccen wuri daga nan sama da yake kawace da tables farare ta ajiye ta tace "enjoy the view of seine river ma" Sossai kyaun wurin ya tafi da ita, ko don girman jirgin ne ko kuma don kyaun shi ne yasa bata ji wani alaman tashin inji ba kan ta ankara dae taga jirgin yayi nisa da bakin gaɓar, mikewa tsaye tayi ta taka a hankali ta karasa wurin karafunan jirgin ta rike tana kallo, masha Allah.. Bata taɓa ganin kayatuwar wuri haka ba, waennan karafun na Paris da ake kira effile tower an kawata shi da wuta blue da ja se walwali yake yi, se ta jita a cikin wani ni'ima na musamman wurin yayi shiru hakan ya saka mata peace of mind, zuciyarta blank ba Tunanin komai se kyau da ni'imar kogin. Bata san iya adadin lokutan da ta dauka a haka ba wata mata daban da na farko ta zo tace "weldone ma! Oga said it's time for prayer and dressing" Kallon kayan jikinta tayi me ya faru zata chanza? Bata yi musu ba tabi bayan matar suka dan sauka cikin jirgin kan ta buɗe wani wuri suka shiga, wow ashe akwai wuri haka a jirgi bata taɓa sani ba se yau, parlor ne me ɗauke da ɗaki da kitchen da toilet, kuma komai akwai, tana ta aikin mamaki har ta nuna mata yadda zata yi anfani da bayin ta fice. Da tayi alwala se ta tsaya kallon madubin bayin tana kallon kanta, lokuta da dama ta kan bace a tunani in zata ɓata lokaci a gaban madubi se ta shiga kokonton itace wannan ko wata me kama da ita, gabaɗaya ta tashi daga wanchan hidayat ramamma me idanu kaman na Mayu ta koma wata classic chic, ita kanta tana son yadda take tafiyar da rayuwar ta da kuma tsarin dressing ɗinta a natse ba hayaniyar kaya se na tsantsar kyau. Fitowa tayi ta gabatar da sallahn la'asar ɗinta don ta samu sallaya a shimfiɗe da katuwar ƙimar jalbib a cikin ledan shi ta ɓare. Bayan ta idar matar ta dawo rike da wasu akwatuna guda biyu tace "permit me to dress you ma!" Kai ta gyaɗa mata tana kallon ikon Allah, ita fa duk bata san me wannan ɗin yake nufi ba kuma, haka dae ta daure ta yi yadda matar tace a take ta fara rangada mata light nude makeup da yayi mugu mugun blending da skin color ɗinta ya bata wani astonishing color me fusgan hankali. Red dress ta ciro mata, doguwar riga ce kaman me zuwa promp night haka dress ɗin ya amshe ta Dukda ba ta inda jikinta ya bayyana banda tsagu dake bariyin kafan ta na dama shima se idan ta buɗe kafar sossai ne ake iya kallon skin ɗinta daga cikin net ɗin rigar shima be kai rabin sharaɓarta ba. coler neck ne kaɗan ne kawai a buɗe se ta saka mata sarkar ta da ta zo dashi da wasu designers ɗan kunne da kyaun su kaɗai ya ishi bayyana tsadarsu suna dauke da back stones daga tsakiya, kanta se ta saka mata cikin wani silk black ɗan kwali da ya zauna sossai a kan nata se black shoes masu Tsai, harda wani black purse, duk wadda ze kalli hidayat a lokacin ze ɗauka irin international celebrity ɗin nan ce saboda kyaun da tayi. Ita kanta se kallon kanta take a lokacin da aka gama shirin, matar ta feshe ta da turaruka masu sanyin kamshi. Ta lura matar se duba time take, bata dae ce mata komai ba ta samu wuri ta zauna, se dab karfe biyar da rabi kan tace mata zasu iya fita. Mikewa tayi da bismillah sbd takalman kafan ta, ji take kaman zasu yarda ita sbd tsinin su hakan ya sauya mata salon tafiya kaman me tafiyar tarwaɗa, sake idanunta tayi tana kwasar kallo sbd yadda saman ya juya mata daga yadda ta shiga ta bari, wow masha Allah, abunda ta furta kenan tana kallon jajayen furrani masu fitanannun kamshi da aka kawata jirgin dashi an yi organizing table da ɗazu ta zauna babu komai kai da wasu varieties na abinci harda cupcakes masu candle iska na ɗan kadawa kaman ze mutu kaman kuma baze mutu ba. Abunda yafi ɗauke mata hankali kuma shine rana da yake ta kokarin faɗuwa yayi wani haske me kyaun gani bata taɓa sanin haka sunset yake ba, ta shagala da kallon sunset ɗin taji wani ƙara kaman na flying boat yana zuwa daga nesa, a hankali ta sauke idanunta saitin inda take jin ƙaran zuciyarta ne yayi wani kalar tsalle. The view of him a tsaye ba riga se wata three quarter black yana riding flying boat ɗin cike da tsantsar kwarewa gashi ya fito ta ɓangaren da hasken ranar ke shirin faɗuwa se ya bada wani kalar kyau da ɗaukar hankali, lumshe idanu tayi ta sake buɗewa tabbas shine builded body ɗinshi se wani haske yake, bata san ta ɗan yi gasping ba ta kuma kasa ɗauke idanunta a kanshi har ya iso jikin jirgin da take yayi tsalle ya haye tare da Juyawa ya ja flying boat ɗin ya sa a mazauninshi na cikin babban jirgin. Se ya juyo suka Haɗa idanu daga inda take tsaye, lumshe nashi yayi ya sake buɗewa she looks so breathtaking to him, kaman kawatacciyar flower dake samun ban ruwa ta fitar da Fure me tsananin kyau da ɗaukar hankali haka ta zama, ji yake kaman ya hadiye ta ko ze huta da bugawar da jijiyoyinshi suke da sunanta. Cikin tafiyarshi ta xaratan maza yake tunakaro ta hakan yasa tayi kokarin fusgan idanunta daga cikin kwayar nashi se kuma ta saukar a inda ya kusa sumar da ita, don sun sauka ne bisa shafaffen cikinshi wandon shi ya ɗan sauka har kana iya hango v line ɗinshi cikin azama ta sake daukewa se ta rasa takamammen mazaunin da idanunta suke sha'awar kallo bayan shi ɗin. Wani ash cotton shirt da ya sa aka ajiye mishi a linke a wurin ya ɗauka ya sa kan ya karaso gabanta ya tsaya ya sakar mata shanyayyun idanunshin nan yana yaba kyaun halittar Allah a wurin, ganin ta kasa Kallonshi se kafafunshi da suke kyalli sanadiyar ruwan da ya taɓa su gasu bearfooted take ta kallo yasa yayi anfani da wata kalar murya yace "diehard!" Wani irin amsawa kirjinta yayi, tsikar jikinta suka bada wani yaammmmm she started to get confuse bata ɗago ba seda taji ya sake maimaita "die hard!" Did he mean da ita yake? Cikin tsoro ta ɗaga manyan Fararen idanunta da suka ji liner ta zube bisa kanshi seda ya so yayi loosing balance ɗinshi, ya lumshe idanu ya sake budesu a kanta ze yi magana se wani cool music ya fara tashi a cikin jirgin inda ya haɗu da yadda suke ɗin ya tafi da bugun zuciyarsu ya bada wani romantic scene. A hankali yace "I know u have so many questions to ask but please do me a favor of keeping mute nd just follow my lead..!" Yadda yake maganan da sanyi da wani kulawa yasa bata san ta ɗaga kai ba, yayi mata leading to kujerun wurin table ɗin da aka musu ado da jan kyalle, da kanshi ya janyo mata ta zauna kan ya tsaya daga gefenta kaman bawan ta ya shiga serving ɗinta a natse. Se lumshe idanu take tana sauraren lyrics na wakan dake tashi a hankali zuciyarta ke skipping.. "It's you! Ur eyes Ur smile The way you walk! The way you talk! The way you laugh! I could stare at you forever I love everything about you! It's everything..." Har wani rawa rawa hannunta yake yi tsabar yadda zuciyarta ya matse ya shiga cikin wani wahalalliyar yanayi da ya so mantar da ita komai da kowa a duniya se wannan moment ɗin da shi shi kaɗai. "Eat die hard" Da hannunta da yayi sanyi ƙalau tayi anfani ta ɗauki spoon ɗin ta fara cin brown rice da daga yadda yayi serving ma dole ya baka sha'awa, da coconut milkshake. Tana sa abincin a bakinta ta lumshe idanu daaɗin shi ya haɗu da wakar da ya sauya bugu zuwa wani waka na daban wadda ya fi wanchan zama romantic nd cool inda ya fara daga kalmomi kamar haka "I don't know how you do what you do...I'm so in love with you..! It just keeps getting better.. I wanna spend the rest of my life with you by my sideee! Forver and ever! Every little thing that you do baby am amazed by you...!" A hankali take cin abincin kaman me tsoron taunawa. A natse a kuma tsorace ta ɗago idanunta dake fallasa asirin zuciyarta se suka Haɗa idanu yayi relaxing just watching at her giving him goosebumps from the sunlight reflection, how he wish she's already married to him! Har wani lumshewa idanunshi suke suna buɗewa da kansu. Da kyar ta iya mishi alaman shifa? Idanu ya ɗan kaɗa mata alamun nah he just want to keep staring at her amusingly.. Ba sakon kaɗai ya isar ba harda jinin jikinta Seda ya kaɗa, ɗauke idanun tayi ta maida kan abincin kaɗan ta kara feeling restless da irin kallon da yake aika mata, tissue ta ɗauka ta share bakinta daidai lokacin wakar ya sake chanzawa zuwa... For my hand na Burnaboy ft ed sheeran A hankali ya mike ya dawo ya ɗauke plate ɗin ya matsar se ya ɗauko na cupcakes da aka musu heart-shapes kowanne da candile a kanshi yana kadawa daidai inda ake cewa.. "When ever am broken' u make me feel whole.. When ever am lonely' you're there for my soul...! Where ever you are girl that's where I call my home!... When ever you doubt it, I'll be letting you know whoaaa... Girl I want to be dancin' with you forever..! U see through the storm and take me as I am.. Baby it's magic anytime that we're together! I make I just love you and hold you for my hand! Hold you for my hand.. My hand!!!" Idanunshi ya sarkafe cikin nata ya ɗan zube hannayenshi bisa table ɗin sun ɓata bat a kallon juna kaman masu kallon kuda, har zuwa karshen lyrics ɗin kan ya lumshe nashi ya nuna mata cake ɗin da idanu, itama da idanu ta tambayeshi what's for? Se yayi mata alamun iska da bakinshi wadda ya feso mata sassanyar kamshin lemon mouth wash ɗinshi da ya saka zuciyarta yin tsammmmm A hankali ta juya ta hure juyowar da zata yi don ganin what's next se ta ga mutum bisa gwiwowinsa a durkushe a gabanta in a stylish way, hannunshi rike da wani gidan zobe me haske da kyau.. A daidai sadda ze yi magana yaji motsin ruwa ɗagowar da zasu yi se hasken camera click click click har guda uku a kansu, be motsa ba sanin spies ne.. Celebrity rayuwarshi be taɓa tafiya a sirri ba, he doesn't like anything da ze yi distracting wannan moment ɗin nasu hakan ya sa be motsa ba bare ya kira security ɗinshi.. Kamshin junansu dake ratsawa yake shiga kofofun hancinsu yana aika musu da wasu sakonnin na daban tare da ni'imar wurin ya haɗu ya bada wata sassanyar moment me natsuwa da amincin ruhi.. Cikin wata kalar murya ya fara magana.. "Hidayah! That first moment da na ɗaura idanuna bisa kanki daga sannan na san cewa ruhinmu are connected in one way or the other... Daga sadda kika bani labarin rayuwarki daga sannan kika kasa barin kwakwalwata, u r all over me, in my head! My thoughts! My dreams nd my eyes! I did my best to keep that feelings hidden but I can't any longer, believe me ban taɓa sanin menene so ba se a kanki, your tears make me restless, dariyarki me sanyaya zuciya, kalamanki masu kwantar da hankali... Everything about you is so charming and breathtaking...kin gyara rayuwarmu from bad path to good path u r Morethan an angel to me nd my children.." Kirjinta ne yake bugawa fiye da misali se ta hau rawan jiki kaɗan kaɗan tana raba ido, ta ɗan sauke kanta se kuma ta ɗago jin yadda muryarshi ya fara rawa rawa se ta daure ta bashi glance ɗin dake nufin ya cigaba... "Please hidayat help me and give me ur heart or share with me na miki alkawari I will never hurt nor leave you!" Lumshe idanunta da suka cika tabbb da kwalla tayi zata fara kuka sbd abun ya fi karfin Tunaninta da hankalinta, ta kasa tuna komai bare kowa... A hankali yace "pls baby don't cry for me! Na jima ina so na fallasa miki sirrin zuciyata amma ina tsoro, by Allah ina ƙaunar ki fiye da Tunaninki I love you with all my heart and soul hidayah... Ko bazaki so ni ba just know that the love I have for u is enough for both of us. Don Allah ki bani dama to be ur only husband...sirrin ki, farin cikin ki, ur man, ur true and last love I beg of you hidayah!" Se hawayen idanunshi suka zubo.. Wani irin siririn kuka me nauyi ta fashe dashi.... Ze haukatata.. Raed is making her go out her mind, be san kwakwalwarta ƙarami bane? Be san zuciyarta bakuwar soyayya bace...! #Vote #share #comment                     🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 31* *FREE BOOK* **Alhamdulillah jiki na da sauƙi, na gode da adu'o'inku Dukda ba wai na warke bane amma dae Alhamdulillah ku cigaba da sakani cikin Adu'o'inku Allah ubangiji ya raba dukkanin bawa da ciwo🤧*** Shanyayyun idanunshin nan ya sakar mata yana kallon yadda take kuka a hankali cikin rashin sanin makama, cikin wata karyayyiyar murya yace "ya isa haka! Pls stop crying yana damuna wallahi har tsakiyar kirjina nake jin digar kowanni hawaye naki, Idan kina bukatar lokaci to think I can understand..but please karki ce a'a don ban san ta yadda zan fara ba, all I know is that I promise to love you forever and ever.." Kai ta gyaɗa tana share hawayen da ta kasa tsayarwa tace "zan yi tunani" Jikinshi ya bayyana irin sanyin da yayi, sossai yaji rashin daaɗi maybe bata son shine sbd be da komai a addini, maybe bata sonshi ne saboda hamza, maybe bata son shi ne sbd rough past ɗin shi.. Ko ma menene all he knows shine he Is deeply hurt. The drive was so silent Har suka dawo gida babu wadda ya sake magana a cikinsu, kokarin fighting na feelings da take ji akan abunda tayi yanzun nan take, she doesn't really know what goes over her abunda ta sani kawai shine she's confuse and abun ya zo mata out of blue, bata taɓa experiencing something like that ba so dole ta rasa Tunanin da zata yi. "Welcome home dad..! Welcome miss hidayat" Dukda yadda damuwa ya bayyana karara a fuskanshi hakan be hana sakarwa Norah da Aisha murmushi ba yana ɗaukan junior yace "thank you gurls, ina Farrah?" Tana kokarin shiga ɗakinta bayan ta amsa musu sama sama taji Aisha na cewa "she's upset ko abinci bata ci ba tun break!" Cikin damuwa yace "what upset her haka?" "I think she is having a bad day bcs her friends said something about having a mother.." Norah tayi maganan itama jikinta na sanyi don ta rarrashi Farrahn har ta gaji. Da sauri Hidayat ta fasa shiga ɗakinta tayi ɗakin Farrahn, a hankali ya tako sede ganin ta shiga yasa ya tsaya yana jin babu daaɗi a ranshi. Kwance rub da ciki ta samu Farrah tana kuka, da sauri ta ɗago ta tana juyota tace "oh my baby me ya ɓata miki rai haka?" Rungume ta Farrah tayi tace a hankali "am just missing my mom" Ɗago habarta hidayat tayi tace "am always here, in shaa Allah zan maye miki gurbin mom naki ahhhh am already hurt tunda har kika zubar da hawaye sbd mahaifiya afterall gani a kusa dake" Puppy face Farrah tayi tace "am not moody just bcs of mom, am moody bcs u are also leaving us soon.. Miss hidayat please don't leave us I promise to be a good girl" Lumshe idanunta hidayat tayi tare da rungumeta tace "who says am leaving you?" "U were promising to marry Daddy hamza and duk sadda kika aureshi  I know u will be leaving..! Daddy promised to talk to u but he didn't please if u have to marry then marry dad and be our real mom" Da mamaki hidayat ke kallon yarinyar baki kaman kanari da zuba zance. Tace "wa ya gaya miki saka kunne a zancen wani abu me kyau ne? It's not a good habit kin ji? Don't do that again.. Oya let's go ki ci abinci" Hannun da ya ɗaura kan handle ɗin ya janye jin ta fuske magana na biyu da yarinyar tayi, Juyawa kawai yayi ya wuce room nashi yana ji Farrah na sake tambayar ta zata iya kiranta mom sbd mama is not for her yayi local, maganan ya so bashi dariya sede baya cikin mood ɗin yi ɗin har ya shige be kula su Norah da suke shiga zancen nasu ba don already sun fito parlor. Kasan shower ya shiga tare da dafe glass ɗin da ya zagaye standing shower ɗin ya lumshe idanunshi ruwan na zuba daga kanshi zuwa jikinshi, hidayat na so ta hura mishi wuta, he never expected what she did.. Ya jima sossai a haka kan yayi wanka ya fito, a gaban madubin toilet ɗin ya tsaya ya riƙe kwankwaso yana kallon kirar jikinshi da kyaun surarshi. Lallai Hidayat daban ce a cikin mata, baya tunanin a kab kasashen da suke duniya akwai inda ze shiga be samu masu sonshi ba, ba ɗaya ba ba biyu ba, ko da macen bata kallon ball ta kan yi social media kuma baza'a rasa shi a kullum a yanar gizo ba Dukda shi ba ma'abocin yin bane sede ayi ta buɗe accounts da handle ɗinshi, wadda yake dashi ma sakuna suna mishi yawa don se ya samu thousands of dms a kowanni flat form da yake, but to his biggest surprise hidayat turns him down. A kasalance ya shirya yayi sallahn magrib da isha tare da kwanciya don ko fita be sake sha'awar yi ba, ko da junior ma ya tashi daga baccin nashi a nan ɗakin ya bashi madara ya sha sossai yayi mishi wanka ya sa mishi pjmas don duk yaran basa rasa kaya a ɗakin shi, anan suka sake komawa kwanciya. Yadda yaga rana haka yaga dare yana ta juye juye cikin damuwar da Hidayat ta haddasa mishi, kaman yadda be yi bacci ba haka itama bata runtsa ba, sossai take jin ba daaɗi sede bata so tayi gaggawa wa rayuwarta Sam, chance ɗin yanzu ne kaman yadda ya faɗa kuma a duk iya Tunaninta da hangenta auren hamza shine babban kalubale da zata so fuskanta a yanzu sbd matsalolin family ɗinshi yayinda auren Raed kaman wani kofa ne na dawamammiyar natsuwa da kwanciyar hankali don ko ba komai shi kamilalle ne, yaranshi suna sonta haka ma kakarshi na son ta, sede ko ta ina in ta duba Sanannen mutum irin Raed yafi karfinta a ko wani ɓangare ita ba tsaranshi bace, da taga Tunanin babu inda ze kaita se ta mike ta gabatar da alwala ta zo ta hau nafilfili daga karshe tayi istikhara tana me neman zaɓin Allah.. **** Yau aka sallami Abba daga asibiti sbd komai ya dawo normal tafiya ce dae kam har yanzu se a hankali, a parlor suka yada zango gabaɗaya sbd mutanenshi da suke zuwa akai akai ana taya shi murnar samun cikakken lafiya. Kowa ya shigo zaka san ba karamin mutum bane don harda minista me ci a yanzu da su comissiononi, en majalisu duk dae wadda yake a tare da Abba a da sbd Abban mutum ne me jama'an gaske, hidima ya hana hamza natsuwar duba waya Seda bayan isha suna zaune a babban parlorn da hajiya da Zainab su biyu suke hiran su don Abba ya bace a duniyar tunani yayinda hamza ya fiddo Wayanshi ya fara dubawa. A Twitter ya fara cin karo da abunda ya kusa zauta shi, clear picture me tsananin kyau da ɗaukar hankali har ze wuce sbd be sheda macen ba se kuma sunan Footballer Raed ya ja hankalinshi ya sake komawa don dubawa. "Breaking: the girl with the greatest footballer MOH RAED in the last pictures that go viral wasn't actually his wife she's his girlfriend as he is proposing in a best romantic way ever #Sunset at Seine River❤️" Be taɓa zagin kanshi ba se yau, yayi Adu'a wani ya fito ya shedawa duniya cewa ba matarshi bace sede gashi a lokacin da Adu'ar shin ta karɓu se ta zama wani kifiya da ya zo ya cake shi a zuciya ya hana gudanar numfashin shi, a take wani mummunan tari ya sarƙe shi kuma ya kasa dena kallon background ɗin don ko a hoto zaka san ba karamin ƙawatuwa wurin yayi ba gata ta fito kaman international celebrity gashi yayi wani tsuguno a gabanta dukkanninsu kuma idanunsu na bisa camera. Da sauri zainab da hajiya suka yi kanshi, zainab na mika mishi ruwa hajiya na sake salati tana sallamewa. Be sha ruwan ba sakamakon tafin hannunshi da ya saukar daga bakinshi jini na biyowa baya, ihu hajiya ta kurma tana cewa "na shiga uku! Jini!! Hamza menene? Me ka gani haka? Wayyoooo Allah na! Hamza" Shine ɗa ɗaya tilo da take dashi a duniya tana son shi fiye da komai da ta mallaka wallahi bazata iya jurar ganinshi cikin wahala ko wani damuwa ba, Inaaa baze taɓa yiwuwa ba. Zainab ma kuka ta fara, da sauri ya mike yaje ya kuskure bakinshi a washing hand basin dake dining section ya dawo tare da shan ruwa yana zubewa bisa kujera ignoring duk maganganun da su hajiya suke yi na ya tashi su tafi asibiti zainab na me yake damunshi?. Abba ne fuska cikin damuwa yace "Son menene? Me ya sameka haka?" Idanunshi da suka gama rinewa ya buɗe yace "Abba hajiya ce take son kasheni! Hajiya ta ƙi aminta da na auri Hidayat gashi wani na kokarin kwace ta daga gareni in ma be kwace tan ba zuwa yanzu" Ya karashe hawaye na zuba mishi. Zainab dake Kallonshi cikin wani yanayi ta fashe da kuka me karfi tana mikewa se ta dawo ta zauna tana dafe marar ta tare da sakin kara alamun nakuda da sauri shi da hajiya suka yi kanta Dukda halin da yake ciki se ta buge hannunshi da yake shirin taɓa ta tana Kallonshi cikin kuka tace "enough! Na gaji kuma ya hamza baka taɓa dauka na da muhimmanci a rayuwarka ba a hakan ne kake Tunanin yin adalci tsakanina da zaɓin ranka? Na sani ni aura maka ni aka yi sbd ni nake sonka sede ban cancanci wannan cin fuska daga gareka ba ko ba don albarkacin aure ba ko don albarkacin cikin jikina zaka tausaya min, idan har kai namiji kishin Hidayat ya saka ka cikin kunci da bakin ciki na kuka har ya kai kana tarin jini ni kuma a matsayi na na mace me ciki me kake tunani? Allah ya saukeni lafiya in shaa Allah zan baku space ka aureta don na gaji.." Kuka take yi sossai wadda ya mugun taɓa mishi zuciya be san yana illata ta haka ba seda yaga bacin ranta na hakika akan abunda yake yi. Sam taki ya taimaka mata se hajiya ce ta kama ta suka fice, jagwab ya zube bisa kujera yana ɗaura hannu a kai. Abba ya kira sunanshi cikin kulawa se kawai ya fara hawaye masu yawa.. "Abba na san bana kyautawa! Na kuma san wallahi in na Haɗa wata macen da Hidayat ba zan yi mata adalci ba! Wallahi ko a sadda hidayat ta auri Yusuf halin da na shiga me sauƙi ne akan wannan, Abba zuciyata ta kumbura likita ya tabbatar min da hakan... Ya zan yi in yi adalci? Ya zan yi in rage yadda nake ji akan hidayat? Ya Allah ka ragwanta mini wannan kadararren Son" Hannu Abba ya sa ya kirashi ya mike yaje ya kwanta a kafaɗar Abban yana me cigaba da zub da hawaye, cikin tsananin tausayinshi Abba yayi ta shafa kanshi yana kwantar mai da hankali, wannan soyayya ko asiri sede haka tabbas Allah ne ya ɗaura mishi shi kuma tashi kaddarar kenan Allah ya ragwanta mishi. **** Ko da Rashida ta gani washegari Saturday har gida ta zo ta cika hidayat da ihu, tana son jin kwakwab sede hidayat dake cikin damuwa bata bata amsar da ya sakata farin ciki ba, haushi kaman ta daki hidayat sede a sadda taji silly reasons ɗinta tayi shiru kawai tana kallonta bata ce komai ba, daga karshe ma tattarawa tayi ta tafi. Akwai UcL da zasu buga so suna da training kuma ba anan Paris ba hakan yasa washegari ya Haɗa kayanshi kawai yayi musu sallama sama sama ya bar Paris. *** Hamza kashe Wayanshi yayi gabaɗaya, bayan Abba ya gama mishi nasiha ya wuce asibiti Dukda hajiya na cikin damuwar jini da taga yana fita a bakin shi hakan be hana ta Mishi faɗan yadda yake yiwa zainab ba, hakuri kawai ya bata. Zainab ta sauka inda ta haifi ɗa namiji (nace shikenan raba gardama aka samu) Kuma tun da ta haihun se ta kama kanta sossai akan hamzan hakan ya saka shi cikin sabuwar damuwa sbd itama yana sonta as his first wife, kuma uwar ɗan shi na fari a duniya, she deserves something good daga gareshi.. Satin suna ya zagayo ya saka ma yaron sunan mahaifinta Dukda ta ji daaɗi kwarai sede bata yi zumuɗi kaman yadda ya so ba. Fushi sossai yake yi da Hidayat hakan yasa yake iya maida hankali akan zainab ɗin, sbd ya gaji da jin silly reasons nata, ta mishi bayani har ta so ta fishi fushi a sadda incidence na Germany ya faru sede yanzu baya tunanin akwai bayanin da ze gamsar dashi Dukda in ya tuna cewa wani dama ya ba Raed na ya cusa kanshi gareta se yaji kaman yayi tsuntsu ya tafi Paris sede a haka yake ta kama kanshi Abba na bashi shawaran yin abunda ya dace. *** "mom!" Norah da yanzu itama ta bi bakin Farrah ta kirata for the first time, hakan yasa firgigit ta kalleta. "Norah!" Itama ta kirata tana kallon ta, dukda murmushi ta so saki sede hakan be yiwu ba, ta kula har Aisha ma karfi da yaji Farrah ta hanata kiran mama ta koma mom sede dayake bata cikin cikakken natsuwar ta hakan yasa bata taɓa shiga cikin irin zancen dasu ba. "Mom! Me yake damunki?" Norah ta sake faɗa tana kallon hidayat ɗin. "Nothing baby! Kawai stress na karatu ne u know exams is around d corner" Norah zata sake magana Farrah daga dakin hidayat ta fara kwala mata kira akan Daddy is on the phone tayi gudu, lumshe idanu hidayat tayi zuciyarta ya buga a lokaci guda, sati ɗaya da kwana uku da tafiyan shi basu taɓa waya ba don da taji ya kira zata gudu kuma bata taɓa jin ya tambaye ta a wurin yaran ba, tana cikin damuwa kwarai sbd hamza ma ta kikkirashi tunda taga yadda hoton su ya zama topic a media yaki ɗagawa. Raed kuma bata sani ba ko fushi yayi ko yana cikin damuwa, kwarai tana feeling guilty don zuciyarta na tuhumarta da rashin adalci wa Raed, ya fi karfin komai a wurinta ba zuciyarta ba har ranta idan yana so ita me iya bashi ce bcs she's indepted to him. Washegari ta dawo daga exams na farko da wuri, sbd jarrabawa ya hana su yin magana me kyau da Rashida Dukda itama tana nuna har yanzu haushin hidayat ɗin take ji na ƙin accepting proposal na Raed hakan yasa basu zauna sun tattauna da kyau ba. Aiki take sede rabin hankalinta na chan wani waje, ringing na landline ne ya sakata dawowa Tunaninta ta fito tana goge hannunta da Towel tare da ɗagawa tace "Hello..!" #Vote #share #comment                   🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 32* *FREE BOOK* "Assalamu Alaikum warahmatullah..!" Dakakkiyar muryarsa ta shiga kunnenta ta aika mata da wani sako me karfi har tsakiyar zuciyarta, bata san sadda ta zauna ba.. Muryarta na breaking tace "Wa'alaikumussalam warahmatullah....ina kwana?" Seda ya ɗau seconds kan yace "kuna lafiya?" Tana jan kasan dankwalin kanta dake bisa kirjinta tace "Alhamdulillah..! Yaran...su suna school" Lumshe idanunshi yayi yana kishingiɗa da kyau yace cikin kasalalliyar murya dake nuna gajiyawa. "I know! didn't call the kids, I called you die hard." Shiru duk suka yi na seconds kan yace a sanyaye "na kasa cigaba da jurewa, I cannot believe soyayyarki tayi min Illar da take son hana min daily activities ɗina, die hard for this 8days ni kaɗai na san irin halin da na shiga da na hora kaina da jin murya da kuma ganin ki, I gave you space ko zaki fahimci kema kina jin a little bit abunda nake ji but to no avail babu abunda ya chanza ko? You hate me ko?" Daga muryarshi take jin ɗacin zuciyarshi duk sbd ita, hawaye ne ya gangaro mata tana ta son yin magana muryarta na rawa.. "It's OK! Don't cry u don't have to, I understand. Take care" Har ze sauke wayan tayi saurin cewa "wait!" Lumshe idanunshi yayi yana sake rike wayan da kyau a kunnenshi kaman wani ne ze kwace.. "Am...am so sorry for hurting ur feelings, it was never intentionally, it's just hard to believe cewa ni hidayat nice Muhammad Raed ya zaɓa a matsayin Abokiyar rayuwa duk tarin mata masu aji, kyau, nasaba, dukiya da kyaun asali..." Hawayenta ta share da tafin hannunta kan ta cigaba a sanyaye.. "U pleaded with me to share my heart ko da ba zan baka duka ba, Raed zuciyar hidayat gabaɗayanta mallakinka ce, ni da kai kaman ruhi ɗaya ne dake rayuwa a mabanbantan jiki...! Ka rokeni na baka dama.. Na baka a yanzu Raed, na mallaka maka ragamar rayuwata please Raed be my only husband, sirrina, farin cikina, make me ur only woman bcs u are my true and last love, I love you every second of every day....we missed you beyond words pls come back home paapi" Tana kai nan ta sauke wayan kunya na rufe ta, da gudu ta tashi ta shige ɗaki kaman wata yarinya ta zube bisa gado tana rufe fuskanta ji take wasai ta sauke abunda ya tokare mata zuciya, ita kanta bata san tana son shi haka ba seda taji bakinta na amayar da zancen zuciyarta wadda ita kam bazata ce ga sadda ta tsara su ba. Sako ne ya shiga wayanta, da sauri ta janyo ta buɗe. "Thank you! Thank you so very much, you don't know how badly I wanted to hear you say that! U made me the most happiest person in the world, I love you for exactly who you are today and I will love you tomorrow and the day after very same day🥺😘" Murmushi ta saki tare da ɗaura wayan a saitin zuciyarta tana lumshe idanu, ƙaurin abincin ta yasa ta tashi da sauri ooh soyayya ya sa ta mance abu ta ɗaura da sauri tayi kitchen tana murmushin kanta. **** "Daadida she accepted me, ta bani dama a rayuwarta.." Yayi maganan muryarshi na bayyana irin farin cikin da zuciyarshi take ciki. Murmushi me sauti Daadida tayi tace "Alhamdulillah! Se ka ji tsoron Allah ka kula da ita saboda Allah, hidayat wata haske ce a rayuwarku wadda idan ka bari ta dusashe rayuwarku ma zata dusashe" Kai ya gyaɗa yace "Daadida I want you to cook for 200 people ayi sadaka wa almajirai Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Murmushi me kyau ta saki lallai rayuwar Raed akwai chanji me matukar girma, kalaman da da baya yin su wadda a musulunce suke kaman dole sbd sunna ne yanzu duk yana yi, da da ne sede ayi celebrating a kashewa abokai ayi kida amma yanzu almajirai yake so ya baiwa, da da ne ba ze ɗauki Kalmar tabbatuwar alkhairi da muhimmanci da har ze furta ba don be san menene Adu'ar ya kunsa ba se gashi yanzu ya sani. Har ze kashe tace "wani hanzari ba gudu ba! Raed hankalina baze taɓa kwanciya kasancewar ku yanzu a inuwa guda da soyayya babu aure ba, a duk lokacin da Zaku keɓe sheɗan ne ze zama na ukun ku, kaman yadda Allah ya faɗa a cikin Alqur'ani me girma, shi kuma bashi da wani buri illa na ya haddasa fitina a ban ƙasa, don haka zan shawarceka da ka natsu ka yanke hukuncin da zata ficceku tun kafin sheɗan yayi nasarar ratsa tunaninku don daga sannan kuma wannan soyayya zata samu cikas, rayuwar aurenku baze taɓa yin albarka ba don an kashe albarkar daga waje" "zan yi tunanin hanya mafi bullewa kan in koma Daadida bana son abunda ze kawo mana rashin albarkar aure kaman yadda kika faɗa, in shaa Allah I will call back in faɗa miki hukuncin da na zartar" Murmushi ta saki tace "Allah ya maka albarka" Ya amsa da Ameen kan ya kashe wayan, kuɗi masu yawa ya tura mata na sadakar da yake so ayi, kan yayi call akan a tura mishi numbern Farik Naik ze mishi tambaya.. Cikin mintuna talatin ya samu personal line ɗinshi sbd connections ya kira shi, bayan sun gaisa ya sanar dashi waye shi suka sake Gaisawa kan yayi mishi tambayar da yake so yayi mishi, gamsashiyar Amsa ya bashi wadda Alqur'ani da hadisi suka zo dashi, yayi mishi godiya suka yi sallama.. Hidayat ya sake kira, Aisha ce ta ɗaga suka fara mishi hayaniya, Seda duk ya gama jinsu wai next week zasu yi hutu, they want a holiday outside Paris. "Where is ur mom?" Ya tambayi Farrah, se ta fara kwala kiran hidayat "mom! Mom dad want to talk to you" Fitowa hidayat tayi tana sakin murmushi ta karɓi wayan tare da sallama... Seda ya lumshe idanu kan ya amsa yace "Die hard when are you finishing ur exams?" Tace "Amm ina Tunanin in 8dys time" Yace "ok, I will be bit busy to then don zamu yi final muma in 10dys....!" Tace "kaiii...! U mean zaka fi week kan ka dawo?" Ita kanta bata san sadda tayi maganan murya a karye ba. Murmushi yayi me sauti yace "someone is already missing me ko?" Murmushi kawai tayi, yace "I want us to go for a trip after ur examination" Cikin zumuɗi tace "where?" Yace "it will be surprise, ke de kiyi mana Adu'ar sa'a a wasanninmu masu zuwa don sun ɗauko zafi" Tace cikin murmushi "I trust you in shaa Allah ku Zaku yi nasara! Allah ya bada sa'a ku ɗauko mana UcL cup" Sossai yaji daaɗin Adu'ar ya amsa suka yi sallama. Daadida ya sake kira ya gaya mata hukuncin da ya tsayar taji daaɗi sossai tayi mishi Adu'ar nasara itama, ta so ta kawo mishi zancen Mahaifinshi sede bata so ta ɓata mishi mood na farin ciki da yake ciki, kudin da ya turo rabi ta kira Badi'ah ta tura musu akan a koma asibiti sbd ita yanzu bazata iya tafiya daga Kano zuwa gembu da mota ba, ko daga cikin jalingo zuwa gembu tafiya ne me nisa sossai dole se da jirgi kuma babu jirgin da ze iya kaita gembu in ba helicopter ko private jet ba. A chan ɓangaren su Badi'ah kuwa kuɗi na shiga Seda suka kusa dambe a rabo, yana kwance a ɗaki cikin kashi da fitsari yana jinsu hawaye wani na bin wani a idanunshi... Kwarai Son zuciya da taake faɗar Mahalicci be da sakamako se na bakin ciki da dana sani, idan da ya girmama mahaifiyarshi ya mutunta ta da Raed be mishi abunda ya mishi ba ko da kuwa naman shi yayi ta yanka yana ƙarami, Dama an ce abunda kayi shi za'a yi maka, ya watsar da mahaifiyarshi a lokacin da ta fi bukatar shi gashi shima nashi ɗan ya watsar dashi a irin wannan lokacin. Ya zalunci matarshi me kaunarshi sbd Allah da tausayinshi wacce tayi ta fafutukar ɗaura shi bisa hanyar bin mahaifiyarshi ba tare da ya san kanshi ya zalunta ba ya zaɓi ɓara gurbi irin su Badi'ah ya watsar da Mairamu, Daadida dae bata mishi baki ba, bata yi fushi ba sede Allah me cika alkawari ne a duk sadda ya ɗauka shiyasa yayi mana hani ga saɓawa iyaye ko min kankantarshi, yanzu duk wa gari ya waya.. Kuka me sauti ne ya kwace mishi a sadda ya tuna amanar Mahaifinshi da ya ci wadda shine sanadiyar barin Daadida gidanshi a baya.. Ta ina ze fara gyarawa? Yana kwance cikin tsananin jinya da ciwo? Babu abinci babu magani? In ya mutu a haka ze ga rahamar ubangiji kuwa? *** "Hamza! Wai ka ga yadda ka koma kuwa? Hamza akan mace kake shirin kashe kanka nima ka kashe ni? Kai fa kaɗai ne abunda na mallaka don Allah ka sassautawa kanka wannan wahalan, wallahi na yarda na amince in har dae Auren hidayat ɗin nan shine ze komar da kai kaman da na amince ka aureta..." Hajiya tayi maganan tana share hawayenta. Da sauri ya mike zaune daga kwancen da yake yace "Hajiya da gaske kin amince?" Kai ta gyaɗa tana kallon tsantsar farin cikin da ya bayyana a fuskanshi, yace "Hajiya zainab fa" Kiranta hajiya tayi a waya sbd tana gidansu wanka, kai tsaye tace itama ta amince idan har itace zata saka walwalanshi ya dawo kaman da. Mantawa yayi da yana fushi da Hidayat a take yayi unblocking layinta ya fara kira... *** "Rashida kiyi hakuri ki bar fushin nan haka kiji wani labari! Tun kwana biyar baya nake son sanar dake sede bamu samu zama ba" "me zaki gayamin bayan abun takaici da kunyar da kika aikata?" Dariya sossai hidayat tayi don kwanakin nan walwalanta na daban ne, bata taɓa jin sanyin farin ciki me tafiya da natsuwa me kwantar da hankali ba se a tsakankanin nan, kwarai Raed daban ne cikin maza, dukda baya tare da ita yana kashe ta da soyayyar da bata tunani ko a labari akwai wadda ya kusanto irin tashi. "Shi wadda kike taya fushin ya ma mance an yi abun yana cikin walwala da kwanciyar hankali ke kina nan kina cin magani" Da sauri Rashida ta kalleta tace "ban fahimce ki ba?" Wuri guda hidayat ta kurawa idanu tace "Rashida wallahi ban san sa'adda soyayyar Raed tayi mun mugun kamu ba, ban farga ba seda ya furta min, ban kuma tabbatar ba seda ya janye jikinshi daga gareni na kwanaki kusan takwas fasalta miki irin damuwar da na shiga a sannan ɓata lokaci ne, ban hakikance cewa idan babu shi rayuwata tana cikin hatsari ba seda ya fara dafa ni da zazzafar soyayyarsa me narkar da zuciya, Rashida ina me tabbatar miki ban taɓa son abu makamancin soyayyar da nake yiwa Raed a yanzu ba.." Ihu Rashida ta kurma tana rungumeta cikin farin ciki tace "kaji min matar nan! Shine kika barni ina nan ina ta fushina ku kuna nan kuna ƙonewa! Zan rama ne" Dariya kawai hidayat tayi, Rashida zata sake magana wayan hidayat ya ɗauki ƙara, duk idanu suka mayar kai se a lokacin Hidayat ta tuna da ya hamza ma ashe fushi yake da ita tun daga ranar da Raed yayi proposing mata. Kallon Rashida tayi da idanun ya zan yi dashi tayi, rashida tayi shrugging kafaɗa, bata dauka ba kaman yadda be hakura da jera mata kira ba. Seda ta dawo gida ta ɗauki call nashi.. "Hidayat! Kiyi hak'uri" Tace "no baka min komai ba" Yace "idan da ban yi miki komai ba da baki ƙi ɗaga wayana a ringing na farko ba, na san kuma kina gani" Shiru tayi mishi, yace "Hidayat ko wanene dole ne ya shiga damuwa makamancin wadda na shiga idan yaga ana mai barazana akan soyayyarsa, baƙin cikin da nake ciki ya hana in saurare ki, da gaske Raed proposing miki rannan yayi?" Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ya hamza ya zainab? Har yanzu bata sauka ba?" Lumshe idanu yayi ya buɗe yace "ta sauka, ta samu da namiji" Cikin farin ciki tace "Alhamdulillah! Allah ya raya mana ya dayyaba" Yace "Ameen! Hidaya Albishir" Tace "Goro fari Kal" "Hajiya ta amince da aurenmu! Zainab ma ta amince da kasancewarmu family guda" Ya faɗa cikin farin ciki. Rassss haka gaban hidayat ya faɗi, dankari! Yanzu ya zata yi? Me zata cewa ya hamza? Ta ina zata fara? Ya Allah, ta ambata tana lumshe idanunta. "Hidayat!" Ya kira sunanta don tabbatar da tana kan layin sede bata iya ta amsa ba.. A sanyaye ya ɗaga wayan daga kunnenshi ya kalla yaga yana reading ya sake mayarwa ya ambaci sunanta....! #Vote #share #comment                 🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 33* *FREE BOOK* **Aunty safeeya da maman sadiq😍😍 wannan page ɗin naku ne kuyi yadda kuke so dashi son so❤️** "Ya hamza don Allah ina so ka saurare ni da kunnen basira, karka fassarani da abunda yake ba tsarina bane tsarin Allah ne, Raed ya taimaka min a sadda bana cikin hayyacina ina kan gadon mutuwa ta da baƙin cikin rayuwa da kuma baƙin cikin ɗa namiji, da taimakon Allah da na Raed aka yi mini aiki cikin sa'a, a sannan yarana were stranded shi ya taimaka ya basu natsuwa da kwanciyar hankali, a sadda mahaifin Usman ya kashe min yaro na fito titi bani da maraba da mahaukaciya Raed shine ya zo ya taimaka min zuwa asibiti he did his best Amma kwanan Usman ya riga ya kare ya tafi, Raed shine ya ciyar a wannan wurin makoki har aka watse wadda uban da ya haifeshi be iya mishi ba bayan yayi ajalinshi, taimakon wannan bawan Allahn be tsaya iya nan ba, bayan Yusuf ya wulakanta ni iyayenshi sun koreni...mugaye suka so hallaka min yarinya su hallaka rayuwata Raed shine ya bayyana ya taimaka mana, ya dawo min da murmushi da farin cikina, ya bani dama me girma a rayuwarshi, ya maida ƴaƴana tamkar nashi ina zaune a gidan Raed ne da sunan aiki amma kudaden da yake kashewa ni da yarana yafi karfin albashina na shekara, please put yourself in my shoes kana tunanin akwai wani abunda wannan bawan Allahn ze nema daga gareni in kasa mishi?" Wani irin bakin miyau hamza ya hadiye, yana jin wani irin turirin zafi na ratsa jini da jijiyarshi, zuciyar shi tayi baƙi kirin.. Be iya magana ba ta cigaba. "Kayi hakuri da abunda zan faɗa yanzu, idan duk aka jingine sadaukarwar Raed ga rayuwata beside all that ina son shi, ba zan ce ga sadda na fara ba sede na san cewa a yanzu Raed shine farin cikina, kayi Hakuri ka cigaba da zama a matsayin yayana na riga na ba Raed ragamar rayuwata....." Katse ta yayi yana zub da hawaye yace "Hidayat ba se kin ce ban kai Raed kuɗi ba, ba se kin sanar dani Raed ya fini suna da tashe ba, ba se kin tabbatar min da cewa Soyayyar da kika fara nuna min tun a baya yaudara bace, ashe fakewa kawai kika yi da hajiya... Hidayat ba zan iya hakura dake ba, wlh ko duk abunda na mallaka zan iya baiwa Raed a matsayin sadaukarwar shi gareki ya bar mini ke, don Allah karki hukuntani da rabuwa don ba zan Jura ba" Hawayen da ya zubo mata ta share... "Mutum baya auran matar wani ya hamza, kana da ilimin addini ka sani komai ya faru already a rubuce yake, kar son zuciya ya sa ka fassarani a baibai, kuɗi kuma ba ze taɓa sayan sadaukarwar R....." Faɗuwar abu taji da karfi, se taji ihun Hajiya tana kiran sunan Hamza, ruɗewa tayi bata kashe wayan ba tana ji hajiya na ihu tana kiranshi da jijjiga shi, tana ji har sadda aka fita dashi asibiti kan ta kashe ta kife fuskanta bisa tafin hannunta tana zub da hawaye cikin damuwar halin da ta jefa hamzan ciki. Ta jima anan kan wayanta ya sake ɗaukar kara ta duba se taga layin zainab ne don tayi saving.. Ɗagawa tayi tare da sallama, zainab na kuka tace "Hidayat don Allah kiyi hakuri da abunda nayi miki, nayi shi ne out of bacewar tunani da hankali, na auri hamza ne ba don yana so na ba se don soyayyar da ni nake mishi, a farkon aurenmu ya duba kamata da cancantata ya fara bani kulawa har zuwa sadda na samu cikinshi hankalina a kwance yake, sede daga sadda kika bayyana cikin rayuwarmu na rasa gane kan Hamza, na san halin matan yanzu a yadda hamza ya gigice a soyayyar ki se nayi zaton aikin asiri ne hakan yasa na kira na miki barazana ga mamaki na har yau baki fadawa hamza ba, don a yadda yake sonki na san da kin faɗa mai da watakila zamana ya kare a gidanshi, wannan dalili yasa kunyar abunda na miki ya baibayeni har nake jin zan iya kiran ki in baki hakuri sede ban yi hakan ba don hankalina be kwanta ba se yanzu na samu dama, don Allah kiyi hakuri.." Hidayat tayi murmushi tana gyara zama Dukda murmushin ba wai ya kai ciki bane.. "Babu damuwa ni dama ban rike ki ba, kowacce mace akwai hanyar da take ganin ya fiye mata wajen bi don kare martabar aurenta, abunda kawai nake so in tunashe ki shine...A duk sadda hankali ya ɓata hankali ke nemo shi, ni karan kaina ina ta so na kiraki don ni na daukeki ne a matsayin matar yayana zan kuma iya baki shawara, ko gaba hakan ba daidai bane don yana zubar da ƙima, ba irin kishin da matan annabawa da sahabbai suka yi kenan ba, a masali wata ce a shoes ɗina zata kira ta gayawa Hamza ƙimar ki ze zube a idanunshi, hakanan tunda akwai gigin karin aure a kanshi ze iya kawo karshen zaman ku sbd a duk sadda namiji ze yi aure to fa se kin yi hakuri kin kau da kai, lokaci kalilan ne kina zaune komai ze zo ya wuce kaman ba'a yi ba, ina kuma so na shawarceki yawan kai kara na fitarwa miji soyayyar mace sbd a kullum ze zamana baku da abun hange se laifukan junanku.. Fatan ban yi miki shisshigi ba" Murmushi zainab Ta saki tace "ko ɗaya, Seda na zauna nayi maganan da mahaifiyata ta fitar dani haske yadda kika yi min kan na san nayi kuskure, shiyasa nake shirin gyara.. Ya hamza na cikin wani hali yanzu haka maganan da nake miki muna asibiti ne, likita yace zuciyarshi ya kumbura kuma idan yana cigaba da shiga damuwa ze iya fashewa mu rasa shi hakan yasa na kira in roki arziki, don Allah kiyi taimako ki amincewa aurenshi mu zo mu gina rayuwa me kyau, bana so ɗana ya tashi cikin maraicin uba yanzu ne ya fara rayuwa don Allah" Ajiyar zuciya me karfi hidayat ta sauke cikin damuwa tace "Zainab zuciyata bata yiwa hamza soyayyar aure, hasalima akwai wadda nake so barin shi kaman cutar wa ne a gareni da kuma shi karan kanshi da iyalan shi don suma suna bukata ta" Hajiya ce ta fusge wayan cikin kuka tace "Shi yayi hakuri Don Allah, hidayat wallahi duk abunda kike so zamu miki, gani zube bisa gwiwowina ina rokon alfarma don Allah ki ceci rayuwar ɗana...! Shi kaɗai gareni" Kuka hidayat ta saki, ba zata iya amincewa rokon hajiya ba, ba zata iya cutar da Raed ba, gwara hamza yana da uwa shi Raed in ta barshi waye ze roketa ta dawo gareshi? Ta Tabbatar cutuwar da Raed ze yi se yafi wadda hamza yake ciki... Ina she can't ba wai don ta tsani hamza ba se don Raed Allah ya zaɓar mata.. Kuka sossai take yi wadda yasa ta kashe wayan ba tare da tace komai ba, yau ita ce hajiya ta roka akan ta auri dan ta bayan duk tozarci da cin mutuncin da tayi mata, lallai Allah ba azzalumin bawa ba ashe tana da muhimmanci a rayuwarsu... Wani call da ya shigo mata ne yasa ta ɗago tana kallon fuskan wayan, Raed ne., Gyara muryar ta tayi kan ta ɗaga da sallama. Shiru yayi na seconds kan yace "me ya same ki kika yi kuka? Die hard kina da wani matsala ne?" Hawaye ne suke gangaro mata tana jin mixed emotion ga damuwar hamza ga soyayyar Raed, ta sani duniya idan akwai abunda Raed ya tsana to hawayenta ne, abunda a da Yusuf yake da Burin gani a koyaushe bisa fuskanta, rayuwa fa kenan. "Bani da damuwar komai paapi" Yace "karki yi min karya domin zuciyata ta riga ta sanar dani akwai abunda ke damunki, muryar ki kuma ya fallasa ki tabbas kin yi kuka... Plz karki fara ɓoye min natsalarki die hard" Ajiyar zuciya ta sauke, kan ta ayyana gaya mishi a ranta taji shi kuma nashi point ɗin.. A hankali ta zayyane mishi abunda ke faruwa, shiru yayi na mintuna kan ya sauke ajiyar zuciya yace "Bana so ki Soni sbd wani hidima da nayi miki a baya, na yi shi ne sbd Allah...hamza yana son ki kwarai hakanan nima Ina son ki sossai da sossai, ba zan taɓa son kaina ba kaman yadda kika yimin bitar wani hadisi na imanin dayanku baze cika ba har se ka sowa ɗan uwanka abunda kake sowa kanka, karki yi tunanin ɗaya daga cikin alkhairai na just focus on yourself hidayat, ki zaɓi abunda zuciyarki take so kuma take ganin dashi kaɗai zata iya rayuwa wallahi zan fahimceki...farin cikinki shine na Muhammad Raed kin ji?" Hawaye ta shiga zubarwa masu zafi, Raed mutum ne na gasken gaske, da ba don tauye mishi hakki da mahaifin shi yayi ba Allah kaɗai ya san irin abunda ya ajiye anan, a komai nashi akwai nagarta da hange.. Taya yake Tunanin zata iya zaban wani a kanshi...? "U r my only choice paapi, ban taɓa yiwa hamza son soyayya ba ko a da da na so shi ban san menene soyayya bane, ba wai don be da quality ko nagartar da zan so shi ba, ba wai don be taka rawar gani a rayuwata ba sede soyayya GAMON JINI(Gureenjo) ce, Kaine zaɓin raina babu wani bayan kai kaima ka sani" Murmushi me sauti yayi yace "na gode kwarai am impressed, mu yiwa hamza Adu'a Allah ya sassauta mishi kuma na amince ki cigaba da kwantar mai da hankali har ya fahimta, don in baki yi yanzu ba gaba kaɗan babu wannan Daman.." Tace "in shaa Allah, thank you for everything paapi" "where are ur kids?" Ta ɗan yi rolling eyes nata tace "suna school yau suke hutu" Sun ɗan yi hira kaɗan kan suka yi sallama tana ajiye wayan yaran ma na shigowa suka ishe ta da hayaniya. **** "Hajiya kiyi haƙuri, ba wai nayi disrespecting ɗinki bane, a lokacin da na so auren Ya hamza wlh da kin amince mana da na  sede yanzu lokaci ya riga ya kure... Zan taya shi da Adu'a Allah ubangiji ya bashi lafiya me anfani ya sassauta mishi" Katse ta hajiya tayi tace "ya isa! Ba damuwa Allah ne ya ɗaura mishi ba mutum ba, kuma in Allah ya yarda ze yaye mai tunda babu zuciyar tausayi a kirjinki, kwana biyar kenan hamza be san inda kanshi yake ba a kullum kuma se na kira ki na roki Alfarmarki hidayat ko dutse ce a kirjinki ya kamata ace tayi motsi... Ba don kaddarar soyayya ba kina Tunanin ke tsarar hamza ce?...." Hidayat bata bari ta sake magana ba tace "Se anjima, Allah ya bashi lafiya" ta kashe wayanta. Hajiyar hamza bazata taɓa chanzawa ba, magana take son gayamata a fakaice dama wadda dae ya furta baya sonka ba ze taɓa son ka ba, Allah ya gani tayi iya Kokarinta wurin fahimtar da su hujjarta don haka daga yau bazata sake ɗaukar wayan kowan su ba, Adu'a zata yiwa hamza kuma ze je mishi a ko ina yake... "Die hard!" Taji Dakakkiyar muryarshi tayi kiranta, da sauri ta ɗago tana Kallonshi.. Tsaye yake sanye da farar shirt, black jacket and Grey pants duk na Kelvin klien kafafunshi ɗaure cikin wasu kyawawan rufaffun takalma, hannayenshi zube cikin aljihunshi ya sakar mata shanyayyun idanunshin nan yana kallonta fuskanshi ɗauke da sassanyar murmushi. What a surprise! Rasa me zata yi tayi se kawai itama ta sakar mai murmushi tana me sauke kanta daga Kallonshi, a sati biyu kaman sauya shi aka yi, gashin kanshi ya tashi sai dai be taɓa ba hakan yasa ya fito a ainihin na Fulani a murɗe a murɗe kaman taliya yara, saisa-saisa be yi yawa ba shi ba kaɗan ba. "Sannu da zuwa...!" Ta faɗa tana sake Kallonshi fuskanta cike da murmushi. Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke kan yayi sallama ta amsa, yana takowa gareta yace "ya rabb! I can't wait to be ur husband die hard, right now I want to hug you tight and tell you that how much am missing you.." Kanta ta sunne tana jin kamshinshi yadda yake baza parlorn a hankali, zama yayi yana murmushi kunyar ta na daga cikin abunda yake burgeshi da ita, Tsam ta mike ta nufi kitchen ba tare da tace komai ba. Da Kallo ya bita sanye take da plain white English gown kanta sanye da turban fari da silver, ɗan kunnenta silver ne, tayi kyau kaman fairy.. Ruwa da energy drinks da taga ya fi sha ta Haɗa a tray ta ɗauko ta kawo gabanshi ta ajiye se ta duƙa da kyau tayi serving nashi ya karɓa ya sha tare da lumshe idanu.. "Thank you die hard" Tace "u are welcome! Zuwa ba sanarwa gashi ban ɗaura komai ba I just came back from school" Yace "am supposed to come back tomorrow but ba zan iya cigaba da zama a chan wata uwa duniya ba tare da iyalina ba, that's why na dawo yau, ni fa fushi ma nake" Yayi maganan yana ajiye cup ɗin hannunshi, wani kallo ta mishi wadda bata san tayi ba tare da tura baki tana kauda idanu tace "nima ai fushin nake!" Wara idanu yayi yana narkewa kallonta yace "me nayi ni kuma?" Tace "ka hukuntani da nesanta kanka da ni, nan gaba ka dena hana min ganinka sbd ina shan wahala" Murmushi yake sossai har kana kallon Fararen haƙorin shi, haɗe hannayenshi yayi yace "Afuwan gimbiya sarautar mata paapi tuba yake!" Itama tana murmushi tace "an karɓi tuban ka, ni kuma me nayi?" Tayi maganan tana karya wuya yace "mun ci cup amma baki sani ba sbd bakya kallon ball Dukda ina ciki" Sossai fuskanta ya nuna farin ciki tace "Alhamdulillah! Masha Allah I knew dama tunda kana ciki zance ya kare, am so proud paapi Allah yasa a fi haka.. And am so sorry wlh exams da damuwar da su hajiyar hamza ne ya hanamin natsuwa kwanan nan" Kallonta kawai yake yana zagaye yatsanshi guda a jikin glass cup ɗin ruwan dake hannunshi yace "Ameen to all the prayers and thank you! Laifi kuma an yafe gobe ne final exam ɗinki ko?" Kai ta gyaɗa mishi tana murmushi yace "then next tomorrow we will be leaving for our trip!" Tana miƙewa tsaye tace "ba ka ki faɗamin inda muka nufa ba? Lemme get you something to eat" Yana murmushi yace "kaman kin san am dying to taste ur magic marvelous foods" Dariya kawai tayi ta nufi kitchen, mikewa yayi ya shige room nashi dake a gyare tsab se kamshin freshener yake wanka yayi ya sauya zuwa kananun kayan da yafi sakawa, armless da 3quarter, lallausan silifas ya saka bayan ya gama feshe turarukanshi ya fice ya nufi kitchen ɗin. A island ya zauna yana mata hira tana girkin, bata taɓa sanin Raed haka yake ba se yanzu, be iya soyayya saisa saisa ba, yana so ne da dukkanin zuciyarshi, he's a free person hakan yasa itama take zama free around him, ganin aikin ya ɗan mata yawa yasa ya sauka ya saka mata hannu, in ta kalleshi se taji zuciyarta na motsawa se ta tuna Yusuf, tsayuwa haka a cikin kitchen na soyayya yana taya ta aiki yana kuma kashe ta da Hirar shi cikin kula da tattausan lafazi shine abu na karshe da Yusuf ze iya mata a rayuwa, amma ga wannan billionier na yi mata cikin kankan da kai, Adu'ar ta Allah ya tabbatar musu da wannan moments ɗin har bayan aurensu. Duk sadda zasu Haɗa idanu zasu sakarwa juna murmushi har suka kammalla suka shirya dining dae dae lokacin yaran suka dawo suka cika gidan da ihun murna shi kuwa yana biye musu. Tsayuwa kawai tayi tana Kallonsu tana murmushi har suka gama, ta kora su dakunansu don yin wanka, ihun su kuma shi ya tada junior ta ɗauko wa Babanshi shi ta ajiye mishi, shima sossai yayi murnan ganin daddyn, bayan sun gama sun fito suka ci abinci cikin kwanciyar hankali. A kwana ɗaya da suka kara a Paris fasalta irin yadda suke kashe juna da soyayyarsu ɓata lokaci ne, sede dukkansu sun fahimci ba karamin soyayya da shakuwa bane ya shiga tsakaninsu, Yaransu har sun fahimta kuma sossai suka yi murna, washegari suka shirya trip ɗinsu suka yi airport harda Rashida sbd ya nemi ta bi su daga nan se ta wuce Nigeria ga mamakin ta se taga pjet, yau Rashida xa'a hau private jet se farin ciki take su ya sun su se air hostess da captain suka ɗaga sararin samaniya yana rungume da Junior.... *I have been smiling like mumu🤧** #Vote #share Comment                  🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 34* *FREE BOOK* *My Meerah😍❤️ wannan page ɗin naki ne se yadda kike so za'a yi😘* Wannan tafiya shi ya zama silar chanzawar rayuwarta gabaɗaya, tafiyar da ya zama silar farin cikinta da samun dawamammiyar kwanciyar hankali, ingantacciya kuma nagartacciya, kwarai Allah ya riga ya mata zaɓi.. Jirgin su be sauƙa a ko ina ba se King Abdulaziz international Airport jeddah, ko a mafarki bata taɓa mafarkin zata ziyarci ɗakin Allah ba, se gata nan a ciki tsamo tsamo kusa da manzon Allah, hawaye ne ya zubo mata daidai sadda suka Haɗa idanu bayan ya gama sauka, da idanu yayi mata alamar hawayen na me? Girgiza kai kawai tayi, tare da kankame hannun Rashida. Motoci na musamman ne suka zo suka dibe su zuwa masaukinsu, hotel ne me zaman kanshi wadda daga tsaruwarshi da securities ɗinshi kama daga mutane da na'urori zaka san ya wuce na ya ku bayi, flat ne na musamman a inda suke ɗin parlor da ɗakuna huɗu, kuma kowanne self content komai da komai akwai a gyare yake tsab. Baccin gajiya duk suka yi kan su tashi ya musu order na abinci kala kala, nan suka baje a parlor suka ci daga nan suka fita don kallon garin jeddah kan su wuce, dayake Rashida ta san Saudia sossai hakan yasa ya kyale su ya tafi harkokinshi daga karshe seda ya dangana da Riyadh sbd wasu meetings don Saudia suna so su saye shi... Be dawo ba se washegari amma ko wani lokacin cin abinci za'a shigo musu dasu gasu nan se wadda kowa yayi ra'ayin ci, washegari da yamma ya dawo a daren ya kira wayanta yace mata yana so su ɗan fita amma su biyu kawai.. Shiryawa tayi cikin jallabiya peach and red kirar Kasar Oman ya ji ado kam, se bata yafa gyalen ba ta ɗauki Red gyale tayi wrapping ta sa red flat shoe, da Rashida suka bar yaran suka fito yana sanye da kananun kaya as usual riga da wando, da kanshi ya buɗe mata bayan motar ta shiga, shima ya zagaye ya shiga bayan kusa da ita motar ta bar harabar hotel ɗin. "Hidayah!" Ya kira sunan cikin husky masculine voice ɗin nan nashi wadda seda taji a jikinta rabon da ya kirata da Hidayat ya jima. "Na'am paapi!" Ya waiwayo gabadayanshi gareta yana kallonta yace "alfarma nake roko na san kaman nayi sauri sede ina ganin menene anfanin soyayya idan ba hakan ba, ina son ki kina so na mun fahimci juna bamu da kowa se kawunanmu da yaranmu, don Allah ki bani dama in sake shiga rayuwarki na dindindin" "paapi ka wuce duk wata alfarma ko roko a gareni, duk abunda ka yanke mana ko zaka yanke mana na tabbatar me kyau ne kuma baze cutar damu ba so na baka dama.." Ta faɗi itama tana kallon shi. Lumshe idanu yayi ya buɗe yana sakin murmushi yace "Gobe zamu wuce madina, kaman yadda kika sani a aikin Umura zuwa madina is optional duk wani aiki na Umura a Makkah ne kuma a Makkah ya kare, gobe in Allah ya kaimu idan mun isa masallacin manzon Allah za'a ɗaura mana aure don ina so ki isa ga ɗakin Allah da martabar Aure bisa kanki..!" Kallonshi kawai take se hawaye ya fara zubo mata, me yafi wannan? Anya akwai wadda ze sakata farin ciki a duniyan nan bayan Raed, ita hidayat ce za'a ɗaurawa aure a madina! Ya Allah ina Yusuf, ina umma da su Surayya su zo su ga yadda rayuwarta ya inganta, ta nagartu da samun cikakken masoyi wadda yafi maza dubu a gareta, ita kam me zata mishi ta saka mishi bayan tsabtatacciyar soyayya da kauna marar algus? "Die hard! Why are you shedding tears? Kin san bana son kukanki ko?" Hawayen ta share cikin wani murya dake nuna farin ciki, mamaki da kuma sallamawa tace "Hawayen farin ciki ne, lallai na zama mace mafi sa'a a duniya! ni ce annabi ze shaida aurena...." Kuka ne ya ci karfinta, tace "ko a haka ka barni kayi min komai a rayuwata paapi, na gode kwarai Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa ya kaimu gobe lafiya! Ina kaunarka sossai da sossai" Murmushi ya sakar mata, yace "ana Aidan uhibbuki hubban khasira(I love you more)" Murmushi suke sakarwa juna na kauna yana ji ina ma akwai aurenshi a kanta da yayi mata rarrashi yadda ya kamata, zata yi magana taga sun iso Airport kuma mutane suna ɗan fitowa hakan yasa ya fiddo face mask ɗinshi ya saka ya fita hannunshi ɗaya cikin aljihu ya zagaye ya buɗe mata ta sauko suka nufi ciki a tare, in ka gansu bazaka taɓa cewa suna da yara a gida ba, sun yi mugun dacewa barin ma da yake fuskan hidayat kaman gonar auduga sbd farin cikin da take ciki a yau... Ko da suka isa arrivals tsayawa suka yi yana ɗan mata magana, idanunta ne suka sauka kan wata dattijuwa bazaka kirata tsohuwa kai tsaye ba sbd daga shiganta zuwa yadda take tafiya zaka tabbatar da akwai cikakken hutu da natsuwa a tattare da ita, sanye da Atampha riga da zani da hijab ɗinta hannunta rike da sandarta tana tahowa, bayanta masu ɗaukan kaya ne ture da akwatinta, tsantsar kama da taga suna yi da Raed ne yasa ta kalleshi se taga yana yiwa matar murmushi kan ya kalli hidayat yace "finally! meet Daadida!" Fuskanta ne ya kara washewa da fara'a da sauri ta taka ta nufi Daadida, tana zuwa kawai ta rungumeta se ta fara hawaye, Daadida na murmushi ta ɗago ta tace "Hidayat! Yau dae Allah yayi na ga jikata, masha Allah tabarakallah!" "Sannu da hanya Daadida kin zo lafiya?" Cewar hidayat ɗin. Tace "Alhamdulillah hidayat, sannu kinji tabbas kin cika mun alkawari na, kuma mafarki na ya tabbata, kin zama fitila a gidan Raed Allah ya miki albarka" Da Ameen ta amsa tana murmushi, yace cikin yanayin shagwaba "ni kuma fa?" Dariya suka yi Daadida tace "kaima Allah yayi maka albarka" Ya saki murmushi yace "yanzu na ji zance" Wucewa suka yi zuwa motar da ta kawo su, aka sanya mata kayan ta a baya, hidayat ce ta buɗe mata kofa ta shiga shi ya shiga gaba hakan yasa hidayat ta koma ɗaya gefen inda ya zauna ɗazu ta zauna, suka bar Airport ɗin. Kwarai Daadida dattijuwar arziki ce, daga zuwan su gidan zuwa tayi wanka taci abinci ta huta duk kusan suna tare da Hidayat ko wani motsi tayi zata tambaye ta abunda take so, suna yi kuma suna hira cikin hikima Daadida ke wayar mata da kai take kuma nusar da ita menene aure, abunda ba'a mata ba a zaman ta da Yusuf, dukda wasu ta sani sbd islamiyya, wasu kuma ta sani sbd experience ɗinta na aure sede ba duka ba, wannan na nagartacciyar tsohuwa ne me cike da hikima da sanin makamar aure da na rike miji a gargajiyance. Yaran basu shaku da Daadida sossai ba, dukda haka sun yi mata maraba sun kuma gaida ta tana ta masifar da wanchan pastorn ne baban mamansu da tuni sun cike wurin da hayaniyar ganinshi amma Raed ji yaranshi a gabanta, Norah kam ma tun lokacin rasuwar mahaifiyarsu bata sake ganinta ba se yau don bata zuwa Nigeria. "Ai ya kamata daga nan Nijeria Zaku yi bari uban naku ya dawo ma" Dariya kawai Rashida da Hidayat suka yi ashe da gaske take bayan ya dawo ta tabbatar mishi daga nan duka tare zasu tafi da Hidayat akwai abubuwan da take son ayi mata, be Musa ba yace Allah ya kaimu. Washegari karfe ɗaya na rana a cikin garin madina ya musu, kusan irin hotel da suka zauna a jeddah anan ma haka suka zauna, garin madina gari ne me cike da tarin ni'ima da albarka, jinta take wasai gata ga manzon Allah, har hawaye Seda ta zubar zuciyarta a cike da farin ciki, rashida na taya ta da su Norah. Kaman yadda ya faɗa bayan sallar azahar al'ummar annabi suka shaida ɗaurin auren *HIDAYAT ABUBAKAR DA MUHAMMAD RAED* akan sadakin sisin ɗanyen gwal wadda idan za'a musanya kuɗin shi da Naira ba kananun kuɗi bane, kuka sossai tayi na farin ciki, Annabi ya shaida Aurenta kwance cikin kabari, zata isa ga ubangijinta da martaba da darajar aure a kanta ko a mafarki bata kawo kanta nan ba. Kwanansu biyu a madina suna ziyarce ziyarce, suna zuwa inda annabi ke kwance ta fara mishi sallama kan ta fara jero mishi salati tana zub da hawaye cikin tattausar murya sbd ba'a so ka ɗaga murya kaman yadda ya zo a Suratul Hujurat, dukda a kwance yake sede yana ji kuma yana amsawa. Daga nan suka garzaya Makkah, duk fa Daadida bata yarda hidayat ta keɓe da Raed ba, shima be matsa ba don tun bayan da aka ɗaura auren da ya dawo ya sanyata jikinshi yana zub da hawayen farin cikin mallakarta itama ta kankame shi tana mishi godiya Daadida ta janyeta suka yi ɗakinta daga ranar ko hannunta be kara tabatawa ba sbd Daadida da tayi uwa tayi makarbiya.. Dab miqat suka tsaya suka yi duk abunda ya dace suka yi nafila raka'a bibbiyu tare da ɗaura niyyar yin Umura, ko da suka isa masauki be bari ta kalli gaze na ka'aba ba don hotel ɗinsu daga window ɗin ɗakunan kana kallon ka'aba tarrrr. Seda suka ajiye loggage ɗinsu kan suka fito zuwa masallaci, tana sa kafafunta a harabar masallacin ta lumshe idanunta tana jin wani ni'ima da sanyi, a hankali ya karaso kusa da ita ya sanya hannunshi cikin nata yace cikin raɗa "lower ur gaze" Bin umarnin shi tayi bata ɗago ba seda suka iso mataf area inda anan ake dawafi, hannunta ya sake shigarwa cikin nashi yana massaging a hankali yace "are you ready?" Kai ta gyaɗa mishi yace "ok lift ur gaze to set sight on the beutific vision of the holy ka'aba!" Yayi maganan dab kunnenta.. A hankali ta fara ɗagowa har ta ɗago gabaɗaya idanunta suka sauka bisa ɗakin Allah, kuka take yi da sauri ta ɗaga hannunta with the utmost concentration and sincerity as nan ɗin waje ne da Adu'a ke karbuwa seda ta fara yiwa annabi salati sbd duk Adu'ar da zaka yi ze tsaya ne tsakanin sama da ƙasa idan har baka cike ta da salatin annabi ba hadisi ne ingantacce. Rashida da Daadida tare da yaran duk sun wuce sun kyale su su biyun su, a tare suka yi performing Umura ɗinsu matsayin mata da miji, wadda dumbin musulmai da mala'iku suka sheda, tunda ya zo a hadisi cewa ko wani rana mala'iku dubu saba'in suke sauka a Saudi don aiwatar da Umura, suna rike da hannun juna suka yi dawafi suka yi raka'a biyu a kusa da maqama Ibrahim, suka yi sa'i a safa da marwa abu na karshe suka rage gashin su ita inch ɗaya da karamar scizors, umurarsu ta cika. Gida suka koma suka huta gajiya inda se dare suka zo suka yi magrib da isha anan masallacin, tayi Adu'a sossai ta roki Allah ya bayyana mata zuri'arta karo na farko a rayuwarta, ta roki Allah ya ji kan Abba, ta roki Allah ya bata zaman lafiya da zuri'a dayyaba a gidan aurenta, ta roki Allah ya kare mata mijinta ya raba shi da sharrin mutum da aljan ya sada shi da halal ya nesanta shi da haram, ta roki ubangiji ya raya musu yaransu, da yakinin Allah ze amsa tunda shi ɗin maji rokon bayin sa ne.. Kwana biyu suka kara a Makkah sallar farillah ko ɗaya bata taɓa yarda tayi a ɗaki ba, kaman kar su bar Makkah sbd gari ne da zaka ji baka son nesa da ita, barin ma ɗakin Allah har tsakiyar ruhinta take jin aminta da natsuwa a duk sadda zata ɗaura hannunta bisa ɗakin na Allah, jeddah suka dawo da pjet ɗinshi suka yi Nigeria inda suka barshi a baya don ze karasa Riyadh ya gama signing contract ɗinshi. Se gata a Aminu Kano international Airport bayan shekara da watanni da barin ta Nijeria, ta tafi cikin zullumi da kokonto, ta tafi cikin rashin cikakken wayewa da shakku, ta tafi a matsayin ƴar aiki se gashi ta dawo a matsayin cikakkiyar matar aure, ta dawo zuciyarta cike da farin ciki da soyayya, ta dawo da ilimi, natsuwa, da kuma nagarta. numfashi me karfi ta ja ta sauke kan ta gyara zaman sun glasses ɗinta, Rashida bata bisu ba sbd an zo daukarta daga gidansu inda driver ɗin Daadida ya dibesu zuwa gidanta. Ɗaki na musamman Daadida ta sauke ta ita kaɗai, tayi kiran waya cikin awa biyu se ga wata mata ta zo da akwati jibgege, itama ta sauka a ɗakin na Hidayat daga ganinta kaga cikakkiyar shuwa Arab  amma half kanuri ce, a ranar aka fara yi mata gyara ingantacciya. Sam bata hau online ba tunda suka isa madina se yau, ga mamakin ta ɗaurin aurensu har yanzu yana wani irin trending a kafafun sadarwa duk inda ta shiga hoton Raed ne sanye da jallabiya fara sol da hirami ya mata dauri irin na Larabawa fuskanshi cike da tsantsar annashuwa yana Gaisawa da mutane, dukda security suna kare shi sbd gudun wani matsala, amma kusan duk wadda yake wurin kuma yake da Burin ko da Kallonshi ne seda yayiwa musabaha. Adu'o'i kam har Seda ta zub da hawaye, al'ummar musulmi sun masu fatan alkhairi, lallai Raed na da masoya a duniya inda ta ci albarkacin shi, Sam basu yi hoto a Makkah ba amma ga mamakin ta se ga wani hoton su ta gani a media, hannayensu cikin na juna yana sanye da Fararen ihram ita kuma sanye da baƙar Abaya magana yake mata ita kuma tana Kallonshi tana murmushi hakwaranta a waje, ba karamin kyau hoton yayi ba, shiga tayi tayi saving, da sauri ta kashe datar ta janyo ciccibi da ta dahu da itacuwa masu kyau da wani sirri ta fara ci sbd jin motsin mata me gyaran jikin. **** A hankali baƙar GLS tayi parking a kofar gidan, Seda aka dau mintuna kan driver ya sauko ya zagayo da gudu ya buɗe seat ɗin baya, a hankali ya sako kafafunshi waje rike da sanda wadda tafi yanayi da na sarauta, takawa yake a hankali zuwa kofar gidan. Drivern ya karaso yace "ko za'a yi mana iso tukuna?" Kai ya girgiza cikin kamilalliyar muryarshi yace "ka yi sallama matan su gyara" Wucewa isa yayi cikin minti biyu ya dawo yace su karasa. A hankali suka nufi cikin gidan, aka yi musu jagora zuwa ɗakin... Da mamaki ya sanya kanshi cikin ɗakin, se suka yi tozali da mutumin da ko a mafarki be taɓa kawo ze sake ganinshi ba bare a zahiri, Idanu suka zubawa juna suna kallon kallo...... #Vote #share #comment                  🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 35* *FREE BOOK* ***Alhamdulillah! Ina matukar godiya da irin kulawar ku a gareni waenda suka kirani, waenda suka min SMS, waenda suka min saƙo ta what'sapp da ma masu min fatan samun lafiya a cikin groups Na gode sossai ALLAH ubangiji ya saka muku da gidan Aljanna, Allah ya bar zumunci.. Waenda basu sani ba kuma har sukan tambaya Bani da lafiya ne har yanzu kuma ina kan samun sauƙi ne, akallah na sha 12 bags of drip. Ciwo yake zuwa farar ɗaya saukin se a hankali... Ku cigaba da sani cikin Adu'o'inku Allah ya bamu duka lafiya me anfani🥰🙏*** **Wannan shafin sadaukarwa ce gareku daukacin masoyana❤️❤️** %%%% Wani irin kakkarwa jikinshi ya ɗauka kaman ana buga mishi gangi a firgice a kuma razane yana kokarin miƙewa sede saɓanin hakan kifewa yayi yana me cigaba da son yin magana jikinshi babu inda baya rawa.. Da sauri mutumin ya durkusa gabanshi yace "calm down Yaya buba, nine dae Usman ba wani ba... Me ya sameka kake cikin wannan mawuyacin halin kai kaɗai? Ina Mama? Ina Aisha da abunda ke cikinta?" Ai kakkafewa idanun buba suka fara lallai lallai yana son yin magana sede ya kasa se hawaye sharrrr suke zubowa, da kyar ya iya fito da Kalmar "Ina Aisha?" Usman yace "ban gane ba yaya buba?" Badi'ah dake makale jikin kofa tace "Hmmm ai Alhaji bana manta irin cin kashin da buba yayiwa Aisha da abunda ke cikinta korar kare shekaru da dama, korar da yayi sanadiyar tsananin fushin mahaifiyarshi gareshi wadda ba tantama sanadiyar shiganshi wannan hali kenan muma gashi muna fama babu cin yau bare na gobe" Dabas haka Alhaji Usman ya zube gumi na tsatsafo mishi ko ta ina, idanunshi suka rine a take suka juye zuwa wani abu daban jikinshi har rawa rawa yake.... "Ya Buba! Innalillahi wainna ilahi rajiun..! Innalillahi wainna ilahi rajiun!! Ka kori Aisha da abunda ke cikinta??? Aishar tawa?? Aisha fa??" Abunda kawai yake iya maimaitawa kenan. Isa ne ya zo ya riƙe shi yace "Alhaji kayi haƙuri a bi komai a sannu kaga kaima ba isashiyar lafiya ne da kai ba gashi babu wadda ya san kayi wannan doguwar tafiyar kar wani abu ya zo ya sameka..." Hanky fari Kal dake tashin kamshi ya ciro ya share fuskanshi kan ya miƙe da taimakon Isa, ya kalli Badi'ah yace "Ina mama? Karki ce min ta rasu don Allah" Tace "tana nan tana jin daaɗin rayuwar duniya ina mutuwa yanzu" Isa yace a zuciyarshi 'ji jahilci' "Address ɗin ta zaki bani" Usman ya faɗa cikin wani irin mawuyacin hali. Tace "nima ban san wani Adara ba shi buba kaɗai ya san wurin" Tana kai nan ta juya ta wuce ta san yau Alhaji Usman se ya daure buba har igiya tayi saura.. Kallon kwantaccen buba dake ta kuka Alhj Usman yayi, cikin tausayawa Dukda ƙasan zuciyarshi akwai daci da raɗaɗin abunda Buban ya mishi wadda har Abada baze gogu ba idan ba Hasken idaniyarshi ya gani ba sede yace "Yaya Buba zaka iya bamu kwatancen gidan Mama?" Da hannun dake ɗan aiki ya iya pointing wani Rigan shi, isa ya karasa ya ciro ya duba aljihun akwai paper ɗauke da address ɗin. Yace "gashi yallaɓai, bamu da nisa ma ashe" Karɓa yayi ya duba kan ya sa a aljihu yace "Isa ba zan iya barin shi haka ba, zaka iya ɗaukar shi ka sa shi a mota?" Isa na dariya yace "ai yadda ya zama kuɗin guzurin nan ko Kano se in je dashi a ɗauke..." Girgiza kai Alhaji yayi yace "careful Isa" "sorry sir!" Isa ya saramai, dukda yadda yake jinshi cikin tashin hankali da damuwa hakan be hana shi murmushi ba, Isa drivernshi ne na tun hankali na kwance tun be yi makaranta ba har yayi diploma a karkashin shi sbd shi mutum ne da duk na kasan shi ke jin daadinshi, baya taɓa bambance talaka da mai kuɗi a tsarin rayuwarshi kowa nashi ne. Ciccibar Buba isa yayi zuwa mota, Alhj da kanshi ya buɗe mishi baya ya sanya shi, matan suna tsatsaye hannu a ka duk a zaton su ɗaure shi Alhj ze je yayi, Alhj Usman yace "Isa ba zamu tafi da mace ko ɗaya cikin matan ba?" Isa na nufan su suka runtuma da gudu suka koma cikin gida harda rige rige na karshe na banko kofa, dariya ya saka yace "wawayyu! Babu rabon cin arziki" Yana kai nan ya buɗewa Alhj gaban motan ya shiga, shima ya zagaye ya shiga driver seat ya tayar da bismillah suka Lula, ba tare da ko gargadar hanyar suna ji ba sbd lafiyar motar da tsadar ta. Shi dae Alhj in ka bincika ko gani me kyau ba yayi sbd damuwa, Ina matarshi? Ina abunda ke cikinta? Suna raye? Sun mutu Allah kaɗai ya sani... Ko da abunda ze mallaka ze kare a duniya ba ze huta ba har se ya samo Aisha da abunda ke cikinta.... Hawayen idanunshi ya ɗauke cikin zafi da kunar zuciya. **** "Hhhh zaka iya ne?" Tayi maganan cikin kasa sossai da murya tana murmushi yace cikin wara idanu. "Kina mamaki ne? Ai kece ciki ni ina na san wani kunya...! In kuma kina ganin ba zan iya ba Allah ya kaimu in sauka a Nigeria babe zaki yi bayani..!" Dariya take yi tana rufe bakinta sbd Daadida dake zaune a parlorn. Duk yadda ya so ta gayamishi wani magana me daaɗi ƙiyawa tayi wai Daadida na zaune kuma bazata iya tashi ta tafi ɗaki rike da waya ba, kwafa yayi yace "kin ci bashi am promising you! Ina my boy?" Tace chan ƙasa "gashi chan ya hana Daadida shan iska cikin lumana" "please put him on the phone I missed him" Baki ta tura tace "mu da bamu da me missing namu ai bamu mutu ba...! Junior! Junior!!" Murmushi kawai Raed yayi yana lumshe idanu, yana jin sabon drama da suka fara don junior ko ya juyo ya kalleta ma bare ya san tana kiranshi. "Ka ga min yaro! Toh Daddynka ne ke son Magana da kai in kuma shima bazaka juyo ba se in j....." Shiru tayi ganin shi a gabanta yana kiran "Daddy?" Yana zazzare idanu. Rankwashi marar zafi ta mishi kan ta saka mishi wayan a kunne ta koma ta kwanta tana murmushi, rayuwa ne ya kawo ta wannan matsayi, ashe akwai farin ciki irin haka a cikin wannan rayuwa bata taɓa sani ba se yanzu? Idan taga inda take rayuwa da yadda take rayuwa da yanayin yadda fatan jikinta da komai nata ya zama na rich pikins se tayi murmushi tace Alhamdulillah. "Daddy pls come back I missed you! No one is playing with me here.. And this old Granny is always mocking me" Ya karashe yana tura baki yana kallon Daadida. Dakuwa ta mishi tace "ungu nan kai da turancin naka na tsiya, na san sarai magana ta kayi shiyasa kake min wannan kallon to kai da uban naka duk kun yi kaɗan" Dariya hidayat ke tayi ita kaɗai idan taga yadda Raed junior ya maida fuska ga Daadida na ta masifa kuma babu me jin yaren juna se ta kara saka dariya, Ta tabbatar rarrashin shi daddyn shi ke yi har ya sake fuska yana cewa "Many balls yeayyyyy" Taɓe baki tayi be wuce tsaraba ya tambaya ba yace balls yaro da ball wannan ai ko uban dake ɗan kwallo se ya shafa mishi lafiya. Su Aisha ne suka shigo cikin shigan Atampha da ya musu kyau Dukda dogayen riguna ne amma kana ganin Su Norah zaka san sun takuru sossai haka dae suke lallaɓawa don Daadida tace shigan Turai ba'a gidanta ba. Sallaman me gadinta ne ya katse musu dariyar jan Da su Norah ke yiwa Daadida tana ta masifa. "Hajiya baƙo kika yi kuma yace lallai lallai yana son ganawa dake don Allah daga chan Gembu yake" Tace "Ah malam mudi shigo dashi parlorn baƙi na gani nan zuwa yanzu" Mikewa tayi ta Sabi gyale ta rataya tace "Ke Nuriyya ki cewa Tabawa ta kawo abun taɓa wa parlorn baƙi na" Baki Norah ta tura don ta tsani wani Nuriyya da Daadida ke kiranta ta wuce kitchen, chan ta dawo bayan Daadida ta fita tacewa Hidayat dake danna wayanta suna chatting da Rashida akan sauran ɗinkunan da ta bayar. "Mom, Tabawa fa Daadida ta aike ta kuma ta sake aika na wurinta again" Hidayat tace "maybe ta manta ne, bari na Haɗa na kai, ba abun na aike ki ba kila baƙin kunya ne ki baiwa er tsohuwa kunya" Ta miƙe ta shige kitchen Norah ta bita tana cewa zata iya Allah ai taga yadda suke yi a Nijeriya, hidayat bata ce komai ba ta Haɗa ruwa da snacks a tray ta dauka ta fito ta ajiye bisa dining kan ta shige ɗaki ta ɗauko hijab ɗinta ta fito. Tunda ta doshi parlorn gabanta ke wani irin faɗuwa haka dae ta daure ta karasa sede jin tashin sautin kukan Daadida ya sanya ta saka kai cikin parlorn a rikice, daga bakin kofa ta ajiye ruwan ta karasa hankalinta na kan Daadida dake kuka sossai ta rungumeta tana cewa "Subhanallah! Daadida menene? Me ya same ki haka? Yanzu fa lafiyanki ƙalau wani ne ya rasu?" Ba tare da ta jira amsar Daadida ba ta ɗago don ganin wadda yake parlorn, saura kaɗan ta kife ƙasa saboda Rikicewa da bugawar zuciya shima a take ya mike tsaye yana kallonta hannunshi na rawa ya nuna ta. Daadida dake kuka se ta nemi kuka ta rasa ta tsaya tana Kallonsu yadda duk suke kallon juna da wani yanayi me wuyar fassaruwa. "Alhj Usman! Ka Santa ne? Hidayat!" Ta kirata tana jijjiga ta da sauri ta dawo daidai sede jikinta na wani rawa da ta rasa dalili, shi kam be ce komai ba se matsowa da yake yi gangan ta idanunshi a fuskanta yace "Mama ba ga AISHA ba!" Daadida tace "wannan ai sunanta Hidayat Usman, rabona da Aisha tun korar kare da Buba yayi mata! A lokacin bani da yadda zan yi dashi....wallahi wallahi a kullum se nayi kuka cikin dana sanin Barin Aisha ta tafi da tsohon ciki cikin halin rashin cikakken hankali gashi bata kara waiwayonmu ba, nayi nema har na gaji!" Ta karashe cikin kuka. "Mama a jikina nake jin ina da alaqa da wannan yarinyar! Mama ina iyayenta?" Ya faɗa hawaye masu zafi na gangaro mishi, duk da natsuwar shi da cikar kamalarshi sossai rauni da damuwarshi suka bayyana. "Bani dasu!" Hidayat ta bashi amsa itama tana zubar da hawaye. "Mahaifiyata ce kaɗai itama ta ra....su bayan ta hai...feni" Kuka ne ya ci karfinta. Aisha da ta shigo da gudu riƙe da waya tace "Mom Dad ya kira he wants to talk to you..!" Turus tayi kan tayi kan hidayat tace "Mommy! Why are you crying?" Riƙeta hidayat tayi tana share hawayenta, a take hankalin Raed dake kan wayan ya tashi yana ta magana sede tuni Aisha ta ajiye wayan bisa stool dake gefen kujeran. "Mama karfin jini ya wuce wasa, ina jin karfin jinin dake tsakanina da yarinyar nan ko ma ita wacece.... In baki da iyaye ina danginki?" Se a lokacin Daadida ta sharce majina tace "wallahi ni karan kaina tun daga kallon farko nake jin ta a raina tamkar yadda nake Jin Raed na ɗauka ko don ta taimakawa rayuwar Raed ne, na ɗauka don ta zama silar cikar babban Burin raina ne...amma yanzu da kayi magana na fara jin sabon al'amari tattare da ita tabbas tana ɗiban yanayi da AISHA" Mikewa hidayat tayi ta dube su tace "Wacece Aisha? Ku fahimtar dani Don Allah?" Kamata Daadida tayi ta zaunar ta dubi Aisha dake kuka tace "yi shiru ba wani abu bane ya samu uwar taku iyayen son uwa! Ki je kuyi wasa kinji? Zata zo yanzu" Kallon hidayat tayi se ta gyaɗa mata kai nan ta juya ta fice ta ma manta da wayan dake kunne Raed kuma na kan layi hankalinshi a tashe, Hidayat fa ke zub da hawaye da aurenshi a kanta bayan alkawarin da yayi bayan kukan farin ciki har abada ta gama kukan wani damuwa, ji yake kaman yayi tsuntsu ya baro Riyadh kaman shima ze yi kukan yake sauraron su zuciyarshi na zafi yana jin haushin wadda ya sakata wannan kuka. "Aisha ƴata ce hidayat ita take bin buba su biyu kaɗai Allah ya mallakamin a duniya, ina matukar ƙaunar Aisha saboda saɓanin Buba Aisha yarinya ce me tsantsar haƙuri, shiga rai da iya lafazi, tana da sanyin hali wadda a kullum nake mata Adu'ar kar ayi anfani dashi wurin cutatar da ita, ta taso ne da matsin wanta buba idan har ba Mahaifinsu na nan ba ko motsin kirki bata isa tayi ba don ko ni ba bari Buba yayi ba. Aisha sun haɗu da Usman ne a lokacin ya je kauyen mu akan hannun Jarin da ya zuba mafi rinjaye a wani kamfanin lipton, tun daga sannan Usman be yi kasa a gwiwa ba ya samu mahaifinsu saboda sanin addininshi da natsuwa irin tashi be sameta da maganan ba seda ya samu Mahaifinsu, shi ya bashi lokaci kuma Seda Mahaifinsu yaje har Kano yayi bincike akan asalin Alhj Usman sbd matashi ne a lokacin me ji da kuɗi, kin san kuma yadda kuɗi yake abun tsoro, sede Alhamdulillah ashe Sanannen ɗan kasuwa ne da yayi shura a lokacin ma, kuma samun shi da duk wani nagarta da ake so ne yasa ya bashi izinin neman auren Aisha. An yi sa'a sun fahimci juna tana matukar sonshi se kuma buba yace shi be amince ba, an kai ruwa rana har yana cewa in ta aureshi shi babu ruwanshi da ita har duniya ta nade, Mahaifinsu yace tunda ba shi ya haifeta ba in ya ga dama hanyar Da Aisha ta bi kar ya kara bi, kaman wasa ko gaisuwarta baya amsawa bare na Usman yayiwa Usman cin kashi iri iri sede Usman dan uwan Aisha ne a hakuri Dukda yana da karfin ikon hukunta buba amma be taɓa ɗaga kai ya kalleshi ba. Na ji wa Aisha daaɗin samun mutum irin Usman saboda dabi'unshi kaɗai sun isa su fada maka mutumin kirki ne sede na ji mata tsoron zama da kishiya kwarai kwarai sbd a sannan yana da iyali, a haka aka yi auren Aisha da Usman. Duk karshen shekara Aisha kan zo gida tayi wata biyu, in ka ganta tana cikin kwanciyar hankali tayi kyau tayi kiba kowa sha'awar ta yake ana faɗin tayi dacen gidan miji sede mu ce Alhamdulillah! Amma fa haihuwa shiru, tun baya damunsu har ya shiga damunsu a lokacin Usman ya shiga sahun masu arzikin Nijeria inda suka yi yawo kasashe kasashe sede haihuwa shiru ba labari. Seda suka shekara kusan goma sha biyu da aure lokacin Mahaifinsu ya kwanta dama, ina ta fama da matsalolin Buba Dukda Aisha kan tura min kuɗi da sunan in yi sana'a sede babban sirrin da na ɓoye duk da kudaden Aisha Buba yayi nashi arzikin da har kariyarshi ya zama mishi tashin hankali. Sanadiyar Aisha ya samu duk abunda yake fariyar Raed ya raba shi dashi ba tare da kowa ya sani ba, sirri ne a matsayina na uwa na riƙe mishi da be jira kanshi ba akan wannan arziki ya rasa mace irin Mairamu. Bayan rasuwar Mairamu Aisha bata ƙasar tana chan wani kasa tana ta ganin likitoci akan case ɗin haihuwar ta sede ta turo min kuɗi masu kauri wadda dasu nayi ta amfani wurin kula da Raed da suturunshi seda Raed ya shekara biyar ban sake ji daga Aisha ba ina fushi sossai da Buba hakan yasa ko da na mai maganan yace kawai ze bincika. Be bincika min ba, kwatsam rana tsaka se ga Aisha kaman an jefo ta, tayi wani kalar rama se uwar ciki se haske da kyau, na tsorata sossai nayi kanta yin duniyan nan Aisha ta ƙi ce min komai ruwa na bata ganin yadda bakinta ya bushe kwankwataran ina kuka. Shimfiɗe ta nayi, na ɗau gyale naje na kira Buba don mu kaita asibiti sbd duk yadda aka yi bata da lafiya ne duk kamanninta kaman ba na Aisha na ba! Ko da Buba ya zo ga mamakina ya shafawa idanunshi Toka yace sede Aisha ta bar mishi gida ai tun kan Auren ya faɗa an ƙi a ji yanzu kuma ta dawo mishi da taɓin hankali hankali a wani ce yayi jinyarta. Na tsorata kwarai duk yadda na tuna mishi amanar Mahaifinshi da kuma kwanciyar hankalina shine zama da Aisha wallahi Buba ya ki, ya tara min matanshi babu abunda basu faɗa ba. Baƙin ciki yasa na kasa ko motsi banda kuka babu abunda nake yi, haka ya kama Aisha ya kai waje ya hankadata ta faɗi ta gefe, sede bata yi kuka ba banda idanu da take bin kowa dashi kaman bata gane komai, ni na ɗauka shock ɗin sakinta da Usman yayi ne ya sanyata wannan hali da take ciki. Kukan bakin ciki na sanya na mike na fara Haɗa kayana don nima in fitar mai daga gida, tsab na Haɗa na dauko da nufin samun Aisha a waje mu tafi sede neman duniyan nan na yiwa Aisha ban sameta ba, zuciyana yayi ciwo Usman, Hidayat nayi kuka kaman mahaukaciya sanadiyar Buba sede ban samu Aisha ba. Ko da na zo zan ɗauki Raed yace kar na ɗaukar mishi yaro haka na dauki kayana da kuɗi na karshe da Aisha ta turo min na fice na kama ɗaki ɗaya na cigaba da neman Aisha, har dare nake dawowa sede in ci abincin titi seda na shafe sati uku ina abu ɗaya ban samu Aisha ba, na fawallawa Allah na dawo na kama sana'a da ƴar sauran kuɗin da ya rage....Kunji labarin abunda na sani game da Aisha da ɓacewarta...!" Daga Daadida, Hidayat har Alhj Usman kuka suke yi babu wadda ya iya cewa komai. Mikewa Hidayat tayi tace cikin rawar murya "Ina zuwa!" Kan ta juya ta fice...... **Ku Daure kuyi comments samu in samu kwarin gwiwan cigaba da typing da wuri pls🙏🙏** *Ashe Buba kam an daɗe ana zalunci! Ba Raed kaɗai bane aka zalunta! Ai na Raed me sauki ne akan na Mahaifiyarshi da Aisha***                   🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 36* *FREE BOOK* A haukace ta shiga ɗakin ta janyo akwatinta da tayo tafiyan nan dashi ta fara watsar da kayan ciki idanunta har basu gani da kyau, Allah kaɗai ya san abunda ke going a cikin zuciyarta babu irin Tunanin da be zo mata a cikin kai ba, da kyar hannunta dake rawa ya kai kan wannan Waist bag ɗin (in baku manta ba kan ta bar gidan yusuf ta ɗaura shi bisa kwankwasonta bayan kuma taimakon da Raed yayi mata dashi kaɗai suka tsira sbd yana a waist ɗinta ne..laalita/ kasheni ka ɗauka duka sunanshi ne). Buɗewa tayi ta fiddo wani ƙaramin box wadda a idanu zaka san ya jima sede a da ɗin ma ba abu bane me arha, da gudu ta mike ta koma parlorn tana haki ta ɗago box ɗin tace "a cikinku waye ya san wannan...!" Muryarta a rarrabe yake fitar da maganan. A hankali Alhj Usman ya fara matsowa hannayenshi na rawa kana kallon rauninshi karara don hawaye ke zuba a fuskanshi muryarshi na rawa yace "kwarai na san wannan box ɗin, sarƙa ce a ciki ni na kawowa Aisha shi a wata tafiya na na karshe da nayi kan rabuwarmu....." Kuka me tsuma rai Hidayat take yi, lallai wannan shine mahaifinta, amma ta yaya? Buba da yake kawu kuma suruki a gareta ya cuce ta cuta mafi muni amma Duka nata mahaifin ne sila... Girgiza kai tayi tare da saurin ja baya a sadda ya sa hannu ze riƙeta gunjin kuka take tana cewa "Ashe ni ɗin ɗiyar sunna ce? Ashe ina da asali da tushe da kuma gata? Ashe ni ba ƴar zina bace kaman yadda aka lanƙaya mun har ya zama shine tambarina? Alhaji ka cutatar da rayuwana na Rayu cikin tsantsar baƙin ciki da jarrabawa duk a sanadiyar ku! Na rasa duk wani gata, nayi baƙin ciki nayi kuka! Sede ka san ban taɓa yi maka Adu'a ba? Kaman yadda uwar goyo na take faɗi kilan rashin sanin takamammen mahaifina ya sa iyayen mahaifiyata suka kore ta ta shiga duniya! I believed that and I live my whole life with that belief Taya zaka zo rana tsaka ka nuna min soyayya in yarda??? Me yayi sanadiyar rabuwarku ba tare da kun yi la'akari da ni ba? Me nayi muku da zafi haka? Al...." Kukan da yake yi da tari ya sa ta kasa cigaba da maganan se kuka, Daadida tace "Haba hidayat kar hankalinki ya gushe mana, na tabbatar babu dalili Usman ba ze taɓa wofintar da Aisha ba...!" "Kuma be tashi nemanta da abunda ke cikinta ba se after good 24 years? Haba Daadida! Ki duba tsabar coincidence har ɗana na sanyawa sunanshi ba tare da na san sunan shi ne ba! Daadida kin kuwa san yadda na Rayu? Kin san baƙin cikin dake ƙasan zuciyata? Kin san irin fansar dake raina? An zalunceni, an ha'inceni, an cuceni an ci mutuncina, an tozartani da mahaifiyata da bata san komai ba... Duk saboda mahaifina da ya zaɓi nesa damu Daadida na sha kwana cikin azabar yunwa, na sha kwana cikin azabar ciwo,  cikin talauci da yagaggun kaya, har roko na yi don sanyawa bakina abinci, nayi rayuwa ba tare da sanin menene farin ciki ba kuma yanzu in zo in bugi kirji in ce ubana attajiri ne? Bana so....! Bana so....!! Na yafe wallahi na yafe..!!!" Yadda duk ta haukace ta sauya gabaɗaya ya ɗaga musu hankali ba su kaɗai ba har Raed da ya gama bada umarni a shirya komai ze wuce Nigeria don ma 6hours ne daga jedda zuwa Kano, faɗuwar Alhaji Usman yasa ba su kaɗai dake parlorn ba har Raed ya nufi jirgin da sauri yana ambaton innalillahi wainna ilahi rajiun.. Da gudu Daadida ta fita ta kira su Mudi da Isa driver ɗinshi suka dauke shi suka sa a mota suka yi asibiti hidayat dae na zube bisa gwiwowinta a wurin bata motsa ba banda kuka da take me ciwo, hannunta rike da sarkar da bata taɓa rikewa da hannunta ba banda box ɗin se yau, yau da aka tabbatar mata ta hanyar aure aka sameta, yau da ta san mahaifiyarta ta shiga rayuwa makamanciyar tata, lallai mahaifin Raed ba mutum bane sbd bashi da zuciya cikin kirjinshi, duk bata ganin laifin su kaman na mahaifinta. Tana bukatar ummi a kusa da ita, tunda ta iso take son zuwa Raed be yi mata izini ba, Tsam ta mike ta fito ko gani da kyau bata yi ta je ta ɗauki kuɗi a jakanta, Junior ne ya rungumeta ta zame shi ta baiwa Norah tana kallon Tabawa tace "Ki kula dasu" Daga nan ta fice daga gidan tana ganin jiri, Seda tayi tafiya me nisa a kafa kan ta samu abun hawa ta shiga ta faɗa mishi sunan unguwan su ummi tare da jan hijab ɗinta ta rufe fuskanta tana cigaba da kukanta. **** "kai! Wallahi wannan kaman Hidayat don Allah mu ganta da kyau" Surayya tayi maganan tana sake leka wayan saurayin da suke tare. Yace "ke dallah! Ina zaki san wannan in ba karyar da kika saba ba, matar fa fitaccen ɗan kwallon duniya ne, ba'a ƙasar nan ma suke zaune ba wannan hoton ma a Saudia aka dauke shi" Saka kanta ta sake yi fuskan wayan Haba, ai ko a mafarki taga hidayat zata gane ta bare a zahirin gaskiya. "Wallahi wannan ƴar uwata ce, hidayat ce fa? Yaushe ta san irin wannan mutumin har ta aureshi to?" Yace "kika sake rainamin hankali wallahi zan bajar dake wato daga leke har kin karance sunanta kin riƙe daram a kwanyar ki! Ka ji wani sharfadina...!" Jikinta har yana tsuma tace "don Allah ka bani wayan nan yanzu zan kawo maka!" Bata jira Cewar shi ba ta fusge tayi cikin gida hankali a tashe cikin wani irin yanayi tana kwala kiran sunan umma, tsallake Yusuf dake zaune bisa taburma hannunshi ɗaya a wani irin kwarmaɗe da alamun wani abu ne ya same shi se kudaje ke bi yama yama tayi kan Umma.. "Umma....ummaaaa hidayat fa! Kalli ki gani wallahi hidayat ce! Wai ta auri babban ɗan kwallo ba'a ƙasar nan ma suke rayuwa ba yanzu ma suna Saudia a chan aka ɗaura musu aure..... Don Allah umma ki ce min ba ita ba ce..... Umma ki ce min rayuwarta tafi namu lalacewa.... Wayyoooo" Kuka Surayya ke yi kaman wacce uwarta ta mutu na hassada da baƙin ciki kiri kiri, umma jiki na mazari ta fisge wayan tana saka idanu aiko tayi baya zata hantsula da azama gayen da ya biyo bayan Surayya ya riƙe Wayanshi yace "ka ji min tsohuwa zata yi min tsalalar tsiya, babu a Hausee..!" Yadda ya kira house ɗin se ka sha dariya har cikin ka ya kulle, amma su kam suna cikin wani irin alhini wadda ya fi karfin dariya. Da sauri Yusuf ya miƙa hannu ya karɓi wayan, kwarai ya gane Hidayat don tarrr kyakyawar fuskanta ya fito cikin wani army green designer jalbab me matukar kyau. Lallai yana ganin hotunan wannan ɗan kwallon me kama da Larabawa, a ina hidayat ta samo shi? Taya aka yi rayuwarta ta samu wannan cigaba? Har gayen yayi gaba da Wayanshi babu wadda ya iya motsawa a cikinsu, Surayya kuka wiwi umma ta Daskare. "Yanzu yarinyar nan tayi wannan kuɗi ta manta da asalinta? Ashe haka amana yace?" Umma ta iya fusgo maganan da bata san ma me take nufi ba, kaman ba ita ce tayiwa hidayat kora me muni da ɗanyen goyo tace wadda ya Haɗa ya raba kuma babu gado bare a samu matsuguni ba. Surayya tace "Umma in ita bazata iya neman mu ba saboda babu Abba mu mu neme ta" Se a lokacin yusuf ya gyara rufan hannunshi yana kade kuda yace "ke kin san waye Moh'd Raed kuwa? Ta ina zamu fara ganin iyalinshi? Ni yarana ma da ban san a wani hali suke ba!" Surayya tace "kaman gaske yaran ka damu dasu kaima! Karka manta dae mu da kai kar ta san kar ne, ya Yusuf ko sunan ƙaramin baka sani ba... Kana nan fatalwar Usman na maka yawo har yayi sanadiyar mota tabi ta kan hannunka baka daddara ba...!" Hannu ya kai ze Mareta ta kauce, nan kowa yayi zurfi cikin Tunanin yadda zasu ga Hidayat. Har yanzu babu me kaunar hidayat a cikinsu sede ganinta da cigaba ya kwadaita musu kusantarta ko zasu fita daga wannan kangi da suke ciki sun manta a baya da suke da wadata gidansu bashi da maraba da Kangin bauta ga Hidayat.. Ita umma yafiyar ta take so su nema ko zasu ga da kyau rayuwarsu ta gama taɓarɓarewa ta tabbatar ko kuɗin ta basu ta Barsu dashi ba ze anfanesu ba in bata yafe musu ba barin ma ita da Yusuf. **** "Assalamu Alaikum" Hidayat ta shigo gidan da disashiyar muryarta. Mahaifiyar ummi dake zaune tana tatar kamu ta amsa tana kallonta, fuskanta a rufe yake rabi sede daga Fararen yatsunta zuwa kalar yadin hijab ɗinta da flat designers da suke kafafunta na Findi mahaifiyar ummi ta san ba irin baƙin su bane. "Baiwar Allah sannu da zuwa!" Da gudu hidayat ta karasa ta zube gwiwowinta kasa tare da ɗaura fuskanta kan cinyar mahaifiyar Ummin tana kuka tace "Mama!" Kamshin ta da ya daki maman ne ya ɗan sakata jan lokaci kan ta ɗago ta tana shirin magana suka Haɗa idanu, gabaɗaya idanunta ta waro waje.. "Hidayat!!! Ummmiii! Ummmiii zoooo hidayat! Ga Hidayat!!" Da gudu ummi ta fito daga parlornsu tana cewa "Mama hidayat kike kira kaman?" Ai suna hada idanu suka rukunkume juna suna kukan yaushe gamo, da kyar suka tsagaita kukan ummi ta ja hidayat parlor suka zauna ummi na cewa "Hidayat ina kika shiga haka a duniya? Nayi nema har na gaji nayi kuka har na gaji, nayi ta sadaka da Adu'ar duk inda kike Allah ubangiji ya dafa miki yayi riko da hannayen ki, hidayat misalta tashin hankalin da na shiga a tsawon lokacin nan da na rasa ki ba karamin abu bane" Hidayat ta ɗago ta buɗe baki zata yi magana kamshin mouth wash ɗinta Seda ya saka ummi lumshe idanu, hakwaranta farare Kal a jere ga wani na Makkah guda ɗaya dake kyalli, gabanta ne ya fadi se a lokacin ta lura da irin kyaun da Hidayat tayi, hannunta dake rike da na Hidayat ɗin ta motsa wani irin taushin hannun yasa tace.. "Na shiga uku ni ummi! Allah yasa su umma basu yi nasarar wargaza miki rayuwa ba! Hidayat don Allah ki yi min magana ko hankalina ze kwanta! Ina Aisha? Ina junior?" A rikice ummi take. Hidayat tace "Ki kwantar da hankalinki ummi, umma basu yi nasarar wargaza min rayuwa ba, ummi na dawo a gareki a yanzu da aure me ƙima da mutunci bisa kaina wadda aka ɗaura shi a cikin masallacin fiyayyen halitta shima kuma ya zama shaida... Na dawo a gareki a yanzu da auren ɗan uwana wadda muke ƴar goggo da ɗan kawu.... Ummi yanzu maganar da nake miki mahaifina uba a gareni na bari rai a hannun Allah na taho nan.... Ummi ki bani shawara mijina baya ƙasar ko izinin fitanshi ban nema ba na taho nan..! Ya zan yi?" Ummi tace "duk ban gane ba hidayat? Taya hakan ta kasance? Ya aka yi duk waennan abubuwan suka faru ga rayuwarki alhali kin bar gaban Yusuf ba cikin cikakken natsuwa ba? Hidayat me yasa baki zo nan ba a sadda Yusuf ya sake ki umma tayi miki korar kare? Duk na samu labari ne saboda na koma muka yi kaca kaca da Yusuf anan na san ya sake ki na je gidan umma ma ba kunya suka bani labarin cin kashin da suka miki! Da kika fita ina kika yi?" A hankali hidayat ta fara bata labarin abubuwan da suka faru, idan ta zo wurin Raed bata sanin sadda siririn murmushi kan subuce mata barin ma irin ƙauna da soyayyar da ya nuna mata na hakika, tana zuwa na yau ta fashe da kuka yayinda ummi ta rukunkumeta tana kukan farin ciki. "Amma hidayat ban san ke baki aiki da hankali ba se yau! Tashi oya muje na san duk inda suke hankalinsu a tashe yake! Hidayat ina hankalinki? Ki saurare mahaifinki mana ki ji uzurinshi kan ki yanke mai hukunci? Ko kin manta duk wannan abunda ya faru already a rubuce yake? Kaddarar ki ce a haka kuma dole ki karɓeta a haka ko baki so! Karki yi watsi da ni'imar ubangiji mana hidaya idan kika duba yadda rayuwarki ta koma yanzu, idan kika duba irin kalar mijin da Allah ya miki zaɓi, idan kika duba ƴaƴan da Allah ya maye miki gurbin Usman dasu ai se ki gode mishi da ni'imominshi... Ke fa kika ce kin yi Adu'ar bayyanar ahalinki a ɗakin Allah inda ba'a mai da Adu'ar bawa, me yasa da Allah ya amsa miki Adu'ar zaki juya baya a gareshi Kiki farin ciki?" Kai hidayat ke gyaɗawa hakane a ko yaushe ummi daban ce a rayuwarta, hannu ummi ta sa ta share mata hawayen dake zuba tace "a lokacin da na bar gidanki a hanya ta ta zuwa nan aka sace min waya a adaidaita ko da naje welcome back kuma sun ce ba ni nayi register Sim ɗin ba so ba ze yiwu ayi welcome back ba, ni duk a tunani kina chan gidanki se ranar weekend na shirya na je, a nan ne nake samun mummunar labari makotanki karan kansu sun shiga matukar damuwa da tashin hankalin wannan abu, ko da zanje wurin umma tare muka je da su uku sede duk hankali tashe rai ba daaɗi muka baro unguwar, na neme ki har a gidan redio sede shiru Baba yace in hakura in biki da Adu'a, ko wani juma'a sena yi sadakar in kina raye Allah ya bayyana min ke...! Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah na gode maka da wannan sauyin rayuwa naki" Tana kai nan ta sake rungumarta, Mama ce ta shigo tace "ya fa kamata ku tashi kuyi sallolin da suka wuce ku ku ci abinci haka nan" Duba time ummi tayi se taga almost 11 na dare, ita kanta hidayat se lokacin ta lura se hankalinta ya tashi ta tabbatar yaranta na chan hankalinsu a tashe basu ganta ba, tun biyar da wani abu ta shigo gidan. Mikewa tayi tace "Mama zan wuce ni kam" Mama tace "A'a hidayat, kika san kan ki isa wani abu ya same ki ba fata ba baki sauke hakkin Allah ba? Ko bazaki ci komai ba kiyi sallah kan ki ɗau hanya" Haka dole tayi alwala ta fara gabatar da sallah, da ta idar ma sha ɗaya da rabi na dare, Gashi baban su ummi yayi tafiya bare ya maidata a machine nashi, damuwanta yaran hankalinsu a tashe yake ta sani Daadida ma duk yadda aka yi yanzu tana cikin tashin hankalin rashin ganinta, tayi wauta ko waya bata Riko ba... Wayan ummi ta karɓa ta saka layinta na Nigeria ta danna kira, ringing na farko aka ɗaga wani mummunan faɗuwa gabanta yayi jin husky voice ɗinshi yace a hargitse... "WHERE ARE YHU??" #Vote #share #comment               🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 37* *FREE BOOK* Wasa kawai take da yatsun hannunta tana alwalar kuda wadda babu ruwa, motar ta ɗauki shiru banda sanyin Ac da fitinannen kamshin shi babu abunda ke tashi, yadda yake tuƙi kaman ba ze tafi ba tunda ya ɗauko ta yasa ta ɗan ɗago ta saci Kallonshi. Da suke Gaisawa da Ummi kaman ranshi ba'a ɓace ba amma kallo ɗaya ta mishi taji bata so ta sake Kallonshi cikin wannan ɓacin ran ko ba Sanadiyarta ba bare sanadin ta, a hankali tace "Paaapi!" Be amsa ba Dukda muryar da tayi anfani dashi ɗin ba karamin shigarshi yayi ba, Raurau tayi da idanu muryarta na rawa tace "am so sorry....! Na san ban kyauta ba amma..." Kukan da yake son kubce mata ne yasa tayi shiru, kaman ze share ta sede ba ze iya ba, parking yayi gefen titi ya zuki iska ya fesar a lokaci ɗaya ya sanya hannu ya yaye hijab ɗin jikinta ya cire kan ya mirginota zuwa cikin jikinshi ya rungume. Dukkansu idanu suka lumshe suna jin kewa, soyayya da kuma tausayin juna. Hawayenta ne yake diga mishi har cikin fatar kirjinshi, ƙara sanyata yayi jikinshi cikin taushin murya ya ɗago haɓarta yace "shhhh! Baby gurl you cried enough today pls don't start again now..." Hannunta ta ɗaura bisa rigar shi ta kara riƙe shi jin yadda yake sake mannata da jikinshi cikin salo. "My fatherrr....!" "Shhhh baby don't say anything about him, ba laifinshi bane now u know who that evi...." Da sauri ta saka tattausan hannunta ta rufe lips ɗinshi. "Duk munin halayyar iyaye babu inda aka mana umarni da mu ci mutuncinsu ko mu zage su, Paapi I love you and bana son fushin ubangiji ya hau kanka saboda Baba Buba, pls find a place in ur heart and forgive him ɗan Adam ajizi ne..." Kallon mamaki yake jifan ta dashi yace "after all he have done to you? And my aunt? I mean ur mother?" Kai ta gyaɗa tace "Besides ni na yafe mishi, please forget the past and focus on the future..! Kaga ba don shi ba kila we will end up as cousins not lovers, ba don shi ba kila da baka min taimakon da ze sa in ji duk duniya babu wadda bana so ko kuda ya taɓa ba kaman kai... Maybe I wouldn't have given birth to Usman, Aisha and Junior you! Ka ga every disappointment is always a blessing..! Had it been be maka abunda ya maka ba da pastor polycap be ɗauke ka ka zama the greatest footballer of our Era ba..." Yadda ta kare maganan da wink yasa ya saki wani malalacin murmushi, lip ɗinshi ya kai yayi pecking idanunta da ta lumshe, ya dawo yayi na hagu kan yayi kissing nose tip ɗinta daga karshe ya dira a lips ɗinta. Seda ya gaji don kanshi ya gyara mata kwanciya yana saka hannunshi na hagu ya tallabo chin ɗinta yana shafawa a hankali yace "Baby gurl you are a blessing indeed! I love you" Tace "nima haka yayana!" Fuska ya ɓata yana turo lips yace "what?? What's nima haka again? I said I love you" Dariya tayi har hakwaranta na fita tace "love you more..!" Kiran Wayanshi ne ya katse shi, a hankali ya saka hannu ya ɗauko ba tare da ya raba ta da jikinshi ba ya manna a kunne, mintuna biyu ya sauke ya kalleta yace "ur dad regain his consciousness and yana so ya ganki please die hard don't cry again for my sake..! Allah baki ji yadda na shigo Nigeria da rashin daaɗin zuciya ba when ever Tunanin kin yi kuka ko kina kai yayi crossing mind ɗina, and please don't ever go out again without my consent I was totally upset ɗazun nan!" Lakace mishi kumatu tayi har dimple ɗinshi ya Luɓa suka yi dariya a tare tace "I won't in shaa Allah, am sorry" Kai ya gyaɗa kan ya taimaka mata ta koma mazauninta seda suka saka hijab a tare kan ya tada motar suka yi tsadaddiyar Asibitin da dama chan aka saba kai Alhaji Usman kuma anan suka kawo Baba Buba. **** Da kwatancen Daadida suka iso Amenity room ɗin na VVIP wadda bashi da maraba da gida sbd haɗuwa da tsaruwarshi, hannunsu riƙe cikin na juna yayi knocking kan ya tura ita kuma tayi sallama.. "Hidayat!!!" Muryoyi biyu suka yi kiranta wadda ya sakata tsayawa chakkkkk kaman an dasa ta, da sauri ta kalli wadda ya kirata na biyun ta maida kanta ga na farkon wadda shine mahaifinta ta kara maida idanunta ga na biyun muryarta na rawa tace "Ya Hamza???? Me kake yi anan? Dama ka san wannan??" Ta Nuna Alhj Usman don har yanzu bata san da wani suna zata iya kiranshi ba. Yace "Hidayat..! Wannan ai mahaifina ne, me kike yi anan? Dama kece hidayat da yake ta kira tun farfaɗowarshi?" Hajiya tace "kai! Kai!! Kai ni fa kun kulle min kai... Kowa hidayat hidayat hidayat! Daga mijina har ɗana? Ke wai wacece ke ne nikam? What's the meaning of whole this??" Alhj Usman yace "Hidayat jini na ce! Hidayat ƴata ce ta cikina! Hidayat ɗiyarmu ce ni da AISHA! ita ce ribar soyayyar mu.." Duuuuummmm haka Hajiya da Hamza suka yi, shi kam tsabar kaduwa ne, hidayat da yake hauka da mutuwar so har yanzu yana kan kallon likita sbd aman jini da be dena ba da damuwa ita ce yanzu ake cewa uban su ɗaya? Kenan ko ba Raed sun haramtawa juna ko menene? Kwarai yana iya tuna ya taɓa jin sunan Aisha chan chan baya matsayin matar Mahaifinshi... Da sauri ya kalli hajiya da ta zabga wani ashariya tace "Wallahi baze yiwu ba! Alhaji me ki....ka..ke nufi? Wace Aishar??? A ina ka samo ta bare har ka san wannan me kama da sadaka yallar ɗiyar ta ce?" Daga hidayat, Raed har Daadida sede wannan ya kalli wannan suna rarraba idanu tsakanin hamza, Hajiya da kuma Alhaji. Murmushi yayi yace "kwarai da aniya wannan jinin Aisha ce da baki so gani ba a duniya Hajiya Balaraba, hamza! Hakuri zan baka ina kuma baka tabbacin cewa bad deeds ɗin mahaifiyarka ne Allah ya ramawa baiwar Allah ta hanyar jarabtarka da matukar soyayyar ƴar uwarka jini ɗaya, ita mahaifiyarka na faɗi tashi wurin ganin ka tsira yayinda a baya tayi faɗi tashi wurin ganin ta raba auren sunna ta raba uwa, uba da ƴar su sede dayake Allah ba azzalumin bawansa ba Kaine ka wahala Sanadiyarta don ko ba komai da a gabana hidayat ta tashi da baka mata wannan son mutuwar ba..." Dishi Dishi hamza ya fara gani, ya kalli hajiya ya kalli Abban shi se kuma ya kalli hidayat, idanunshi ya sauka bisa hannayensu dake sarkafe cikin na juna da Raed, runtse idanu yayi wasu zazafan hawaye suka zubo. Hidayat hajiya ta zubawa idanu jin kalaman da Abbanta yake faɗa game da ita, kenan itace silar komai? Kenan ita ce ta raba ta da farin ciki da jin daaɗi na rayuwar wannan duniya? Shigowar likita ne yasa duk suka kalli kofa, yace "ya kamata ku barshi ya huta hakanan duk abunda Zaku tattauna ku bari gobe da safe jininshi ya hau har ya wuce misali.." Daadida tace "hakane Dr, yanzu zamu tafi in shaa Allah zamu hakura da jin koma menene seda safe" Hamza mikewa yayi da niyar fita se ya yanke jiki ya faɗi, Hajiya ta kurma ihu tayi kanshi tana cewa "Hidayat ce! Wallahi Hidayat ce! Duk itace, ita ce fa wallahi itace...!" Yadda take maimaita kalma ɗaya zaka yi tunanin akwai matsala a kwakwalwanta, Dr kiran nurses yayi aka ɗauki hamza zuwa wani room ɗin don dama shima ba'a sallame shi a asibitin ba yana kan medication ne. Hannu hajiya ta sa a kai ta kurma ihu tana nuna hidayat tana cigaba da faɗin duk ita ce wallahi duk ita ce ta rusa mata gida.. Raed dae bayanshi ya maida hidayat yana mata wani irin disgusting look, gangan Alhj Usman suka koma ya ɗan duka ya gaida shi, ya amsa cikin kulawa yana murmushi. Daadida tace "Sannu da jiki Alhj Allah yasa kaffara ce" Ya amsa da "Ameen mama na gode! Amma don Allah kan ku wuce ku duba yaya Buba tare muka zo yana next room" Shiru Raed yayi Daadida ta fara share hawaye tace "Allah sarki! Duk abunda yayi maka baka duba ba ka nufe shi da alkhairi? Allah ya saka ya sa a mizani mun gode... Raed ka gani ko? Ka ga irin zuciyar mutanen kirki? Shi fa salwantar mai da iyali yayi a lokacin be ma sa ran sake ganinsu ba hakan be hana shi taimakon shi ba se kai da ya haifa ya kawo duniya zaka Gaza yafe mai laifukanshi gareka..!" Hannunshi dake cikin nata ta ɗan matse ya kalleta da idanunshi da suka rine da ido ta mishi alamar please! Ya kalli Daadida yace "na yafe mishi already albarkacin macen kirki Hidayat..! Kiyi hakuri yanzu zan je na duba shi" Rungume su duka tayi tana kuka en jikokinta da bata da Kamarsu a duniya. A hankali Raed ya saki hannunta ya kama na Daadida ya ja suka fito yana yiwa hidayat kallon be careful Dukda hajiya tayi gaba already tana kaɗa zani sbd birkicewar da tayi har lokacin bata dawo daidai ba. A hankali hidayat ta taka gaban gadon ta ja kujera ta zauna tana kaucewa kallon da Alhj Usman ke mata, muryarta na kakkarwa tace "Saan..nu Ab....ba " Lumshe idanunshi yayi yana jin sanyi na ratsa shi, tunda ya farfado se yanzu yake jin wani abu na farin ciki na shiga cikin zuciya da ruhinshi, dukda yayi babban rashi sede ya gode Allah da ya bar mishi hidayat ɗin ma. "Sannu princess!" Se ta kalleshi jin sunan da ya kirata dashi, a tare suka sakarwa juna murmushi. Yace "princess yau zaki zauna da Abba ko? I want to spend the night listening to ur stories Ina so every single thing na rayuwar da kika yi kar ya wuce ni..! I've missed a lot bana so in sake missing ko da second ne na rayuwarki.." Murmushi me tafe da ciwo tayi tace "Abba gwara kayi bacci ka huta in Allah ya kaimu gobe se in baka labarin don in har na baka yanzu bazaka iya bacci ba" Shiru yayi na mintuna kan yace "mahaifiyarki mutumiyar kirki ce, har Abada zan cigaba da kewar macen arziki mar'atussaliha irin ta..!" Murmushi kawai tayi a hankali yake bata labarin wacece mahaifiyarta se ta fahimci a halayyar su kaɗan ne kawai suka sha bambam amma kusan duka halayyar su iri ɗaya ne, yadda yake murmushi me ciwo zaka san kwarai ya so mahaifiyarta kuma yayi kewar ta. **** Kusan a tare da Daadida suka shiga ɗakin sede shi daga bakin kofa ya ja ya tsaya yana kallon Baba Buba, yadda ya zama bazaka taɓa cewa shine Buban chan ba, Buba me son tarin abin duniya, Buba marar mutunci duk ya kwanjame baki a karkace, rabin jikinshi a mokaɗe. "Buba!" Daadida ta kira sunanshi da tarin mamaki don bata taɓa zaton jikin ya kai haka ba. "Buba baka samun kulawa ne? Baka cin abinci ne? Innalillahi wainna ilahi rajiun" Ta faɗa hawaye na zubo mata, lokaci ɗaya shima ya fara zub da hawaye me ciwo idanunshi na kan Raed dake tsaye daga bakin kofa ya kau da kai sbd hana hawayen idanunshi zuba. Ko yayi magana ba ji za'a yi ba in ya nace kuma shi yake shan azabar ciwon. Hannu kawai ya sa ya kama na Daadida yana zub da hawaye. Raed da kafafunshi suka gaza ɗaukan shi ya juya ze fita se Buba yayi karfin hali fusgo sunanshi.. "Muhammad!" Chak ya tsaya se ya juyo yana kallon shi. Baki a karkace cikin taune harshe yake maimaita "ka yafe min don Allah! Ka yafemin!" Yana kuka sossai. Da sauri Raed ya zo ya riƙe hannunshi Ɗayan yana zub da hawaye yace "Na yafe maka baba, ka dena kukan nan ka samu lafiya ka ji?" Yace "ni kaɗai na san azabar da nake ciki Muhammad! Ni da lafiya kuma har Abada, na zalunceku na raba abunda Allah yafi so Wato zumunci na cuci kaina na cuci rayuwata...." Tarin da ya fara me yawa ne yasa Raed danna red button se ga Dr da nurses. Dr yace "am sorry please wani irin Nutrition kuka ɗaura shi a kai? His condition is very bad am sorry to say!" Yace "ban gane ba? Is it about the paralyze or something else?" Dr yace "I don't really know me aka bashi we are not sure but rabin hanjinshi ya ruɓa, a hoton da muka yi ya nuna mana an yi aiki an yanke sede ba'a yi replacing ba so he keep suffering yanzu dole se mun sake aiki! Please karku bashi ko ruwa ne har nan da 5 days muga yadda aikin ze kasance" "innalillahi wainna ilahi rajiun!!" Daadida ta faɗi tana dafe baki, tace "duk yaushe aka yi haka Buba? Ina kudaden da nake aika maka na abinci da magani? Me hakan ke nufi Buba? Innalillahi wainna ilahi rajiun" Raed ɗauke idanu yayi yana maida hawayen ciki, yace "I think we are leaving to another country" Dr yace "duk abu ɗaya ne sir, muna da duk wani kayan aikin da zaka same shi a kasashen waje haka likitocin mu zasu yi mishi aiki fiye da na Kasar waje kwanciyar hankalinku muke bukata da nashi, in shaa Allah ze samu lafiya sede yanzu yana jin jiki" Kai suka gyaɗa Raed dae was not convinced, asibitin kam ya amsa sunanshi sede hankalinshi be kwanta ba. Babu wadda ake bari ya kwana, wuraren karfe ɗaya Hidayat ta zo ta duba baba Buba itama Seda tayi kwalla, lallai kaji tsoron rayuwa. Yanzu wannan alhaki dake dawainiya da wannan bawan Allah in tace bata yafe mai Bama ai ba zuciya a kirjinta itama kaman shi a baya. Haka suka bar asibitin cikin alhini me girma, Raed bayan ya sauke su gidanshi ya wuce duk se ta damu don kallo ɗaya zaka mishi ka san ganin Baba Buba ya taɓa shi ko min lalacewar uba ubane tabbas. #Vote #share #comment                   🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 38* *FREE BOOK* Bata iya ta runtsa ba seda ta tabbatar da yayi bacci, ta kashe lokaci sossai tana kwantar mai da hankali a wayan har ta dena jin amsar shi, mikewa tayi ta watso ruwa ta zo tayi nafila tana me rokarwa mahaifinta lafiya tana kuma Rokon Allah yaji kan mahaifiyarta. Washegari da wuri ta tashi da kanta tayi breakfast ta Haɗawa Abbanta ma breakfast wadda ze ji daaɗin shi, bayan ta gama taje tayi wanka a lokacin su Norah ma sun yi wanka suna tambayar ta ina taje jiya har suka yi bacci bata dawo ba? Tace musu "Dad ɗina ne be da lafiya I have to be there through out" Aisha tace tana so ta ganshi, tace su shirya su je duka tare. Bayan sun fito ta shiga wurin Daadida suka gaisa kan ta Haɗa mata breakfast ɗinta nan kan dardumanta don bata iya zaman dining wai na yara ne gwiwowinta se su sage, Albarka ta sa mata kan ta miƙe ta fito, tana rufe kofan yana rufo na parlor. Idanunsu ne suka sarƙe cikin na juna, a tare suka sakarwa juna tattausan murmushi, kallonta yake daga sama zuwa ƙasa, sossai tayi kyau cikin Rigan lace da aka mishi ɗinkin manya, ya haɗu karshe ya kuma bi jikinta kasancewarshi milk da emerald green.. Ɗan kunnen kunnenta fashion marar girma ne emerald green se sarkan mamanta na gold dake wuyanta. Shi kam as usual sanye yake da kananun kaya designers wando da riga black and ash, hannayenshi zube cikin aljihu, a hankali ya ciro su tare da warawa yana kallon idanunta, zare cute eyes ɗinta tayi kan ta make kafaɗa tana kallon kofan daakin Daadida, baki ya taɓe kan ya fara takowa zuwa gareta yana sakin murmushi ganin yadda ta sunne kanta kasa, shi kam ko a jikinshi ya rungumeta suka sauke ajiyar zuciya a tare. Peck yayi mata a goshi yace "Good morning Die hard!" Tana motsa hannunta dake sanye cikin nashi tace "morning paapi, hope ka tashi lafiya?" Kai ya gyaɗa yana lumshe idanu sbd kamshinta dake aika mishi da saƙo yadda ya kamata, tace "mu je kayi breakfast" Ya kalli hannunta dake riƙe cikin nashi farare sol kyawawa a gyare tsab yace "u rejected my proposal yanzu hannunki yayi somehow without a ring" Murmushi tayi tana jan hannun nashi zuwa dining tace "wani proposal kuma bayan na zama matar aure gabaɗaya, but that ring yana da kyau sossai fa!" Yace "I changed it with another one in mun koma zaki gani, baby gurl we are leaving together today right?" Zata yi magana yaran da suka kalli baban nasu yanzu suka fara gaida shi, Junior har da saukowa ya zo wurinshi, ɗaga shi yayi ya cilla sama suna dariya suka zauna, da kanta tayi serving nashi ta Haɗa mai tea ta tura mishi gabanshi, itama ta zuba nata don already yaran sun yi nisa a ci. Yana yin loma ɗaya ya lumshe idanu yace "you cooked?" Murmushi kawai tayi, yace "kin san wani abu?" Ta girgiza kai tana Kallonshi, yace "from the first time I tasted ur cook taste ɗinshi be ƙara barina na huta ba, I always longed to eat ur cooking u r really a great Cooker! Thank God" Yadda ya karashe har yana ɗaga hannu sama ne ya sakata sakin dariya, ƙasa ƙasa yake maganan ko yaran ba jin abunda suke faɗa suke ba. Cigaba da cin abincinta tayi wani sashe na zuciyarta na tuna mata Yusuf, zata gama wahalar yi mishi girki da mutanenshi babu sannu bare na gode, bare kuma a zo maganan yabawa, ta zauna da monster ne kawai as a husband. Har suka gama ci suka tashi Tabawa ta zo ta tattare babu wadda ya sake magana. Abincin asibiti aka kai motanshi se ga Daadida ta fito a tare suka tarkata duka suka yi asibitin. Ɗakin da Abba yake suka fara shiga, yana kishingiɗe hannunshi rike da chasbi yana ja, gabanshi wani farin dattijo ne zaune suna magana, shigowansu ya fadada fara'arshi yana musu sannu da zuwa. Hidayat dake murmushi ta karasa ta ajiye basket ɗin hannunta kan ta duƙa ta gaida dattijon, ya amsa yana kallonta da murmushi ta juya ta gaida Abbanta da suka gama Gaisawa da Raed, shima ya amsa yana tambayar ta gajiyar jiya, murmushi kawai tayi "masha Allah, duka waennan jikoki nane?" Daadida na murmushi tace "wannan da wannan sune yaran wajen Hidayat babban ya rasu, su biyun nan kuma yaran Raed ne mahaifiyarsu ta rasu duk suna wurin Hidaya yanzu!" Yace "masha Allah tabarakallah! Ga mata kam sababbi fil a Leda se wadda na zaɓa, kai kam bana yi da kai..." Yayi maganan yana kallon Junior, se ya koma ya kama hannun Raed yana Kallonshi fuska a kwaɓe, duk dariya suka yi, Norah da Farrah suka gaida shi yayinda Aisha taje ta kama hannunshi tana Kallonshi tace "Mommy kin ce Abban ki! Wannan kuma ai ba Abbanki bane na gidan umma...ba kin ce ya tafi kenan ba ze dawo ba? Ko in an mutu ana dawowa? Yaya Usman ma ze dawo?" Duk ta jero tambayoyin tana kallon hidayat. Rasa amsar bata hidayat tayi se ta kau da kai hawaye na cika mata idanu, kwarai itama tana matukar kewar Usman da Abba sede ta kan musuAdu'a Allah ya gafarta musu yasa sun huta, Abba ne yace "Aisha da gaske ne duk wadda ya mutu baze dawo ba! Wanchan ma Abbanta ne kin san mommynki princess ce tana  da Abba's dayawa dayawa" Ya karashe yana shafa kan yarinyar, cikin mamakin yadda hidayat ta sawa ɗan ta na fari suna Usman don ya san bata san shi ba! Har gwara Aisha ma ze iya cewa zata san sunan mahaifiyarta ne. "Princess wannan ma Abbanki ne, shine babban amini na minister of finance na yanzu" Dukawa tayi ta kara gaida shi tana murmushi shima ya amsa cikin fara'a yana mata barka da haduwar su da mahaifinta, Abinci ta zuba musu dukkansu biyu don tana ji Abbanta na maganan tun bayan da ya fito sallar asuba yayo nan don tun jiyan be san yana asibiti ba. Raed da Daadida da kuma yaran suka wuce ɗakin Baba Buba, se bayan fitansu Abbanta yace "Yayanki hamza ma yana samun sauƙi ɗazu ya bar nan!" Tace "Abba bari na kai mishi abinci ko?" Yace "eh ya kamata! Don ban ga hajiyar shi ba banda tabbacin ta zo ko bata zo ba, matarshi kuma na jego" Kai ta gyaɗa kan ta ɗauki basket ɗin ta fice bayan ya gayamata room number, da sallama ta shiga ɗakin yana zaune kan gadon ya zubawa gini idanu, duk ya rame ya lalace kaman ba hamza ba. Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai, ta karasa ta zauna bisa kujera kan tace "Yaya ina kwana? Ya jiki?" Kallonta yayi kan yace "lafiya na gode!" "Ba dae fushi kake da hukuncin ubangiji ba yaya? Duk abunda fa kaga ya samu bawa muqaddari ne daga Allah kila taka jarabawar kenan, don Allah ka kwantar da hankalinka ka samu lafiya ko hankalin Abba ma ze kwanta! Yanzu ka fara rayuwa saboda yanzu ne ka fara tara iyali please be yourself for the sake of Allah, Abba and ur little child" Hawaye masu zafi ne suka zubo mishi yace "Meyasa se ni za'a hukunta da laifin mahaifiya....." "Shhhh Astagfirullah! Karka yi saɓo mana yaya! Ka jingine duk wata damuwa a gefe ka sa a zuciyarka ni haramiyarka ce, ko da Raed ko ba Raed babu aure a tsakaninmu ko da mu biyu kaɗai muka rage a aduniya, don Allah ka komawa Allah duk abunda ya sameka harda sakaci wurin neman zaɓin Allah" Ta karashe a tausashe. Kai ya gyaɗa mata, jakanta ta buɗe ta fiddo counter ta bashi, ya karɓa yayi mata godiya.. Abinci ta saka mishi tana zaune a gabanshi har ya ci mai yawa, bayan ya sha kunun gyaɗar ya gama yace "Amma me kike Tunanin hajiya tayiwa mahaifiyarki da zafi haka? Hajiya wasn't herself tun jiya kaman akwai abunda ya taɓa ta, she called asking for some huge amount of money daga account ɗin Abba ban bata ba na dae bata abunda zan iya daga nawa account ɗin, like she was desperate!" Ya faɗa wondering don abunda ya hana shi bacci kenan Tunanin me hajiya zata yi da makudan kudin da ta ambata tana so. Hidayat tace "Ka dena Tunanin duka wannan yaya! Ka fara samun lafiya tukuna ka ji?" Kai ya gyaɗa, se aka turo kofan da sallama ɗago kai tayi se suka Haɗa idanu da Zainab. Ganin hamza zaune yana danna counter yasa ta karaso tana kallon hidayat tace "Hidayat??" Dariya hidayat Tayi tace "ya aka yi kika gane ni haka da wuri Auntyna?" Murmushi zainab tayi tace "jikina ne kawai ya bani ke ce hidayat! Sannu da zuwa yaushe a gari?" Hidayat tana karɓar yaron na bayan zainab tace "Na kwana biyu amma se jiya na haɗu da yayana, masha Allah wannan yaron ai ni yayo yaya hamza kalli kaga don Allah bamu yi kama ba?" Murmushi yayi ya san so take tayi cheering ɗinshi ya manta komai ya ɗauke ta as sister, shima se ya daure yace "sossai ma yaro in be ɗauko goggonshi sakike ba wa ze biyo to!" Dariya suka yi har zainab, hidayat tace "Aunty zainab kin shiga wurin Abba kuwa?" Tace "eh Seda na gaishe shi na shigo nan" Hidayat tace "ko bakon ya tafi?" Tace "A'a yana nan" Hidayat ta miƙe rungume da yaron tana duba wayanta tace "OK, bari na shiga Da Rashida ta gaida shi, ummi ma tace tana hanya" Bata jira Cewar zainab ba ta fice.. Kallon Hamza Zainab tayi tace "kaina ya kulle! Yaushe hidayat ta San Abba haka da har zata gayyato mutane gaida shi daga zuwa dubiya itama? Like yadda take maganan kaman akwai sanayya ko wani abu" Murmushi me ciwo yayi yace "Hidayat is my half sister zainab, mahaifinmu ɗaya muma se jiya muka sani" **** Tana fitowa ta isa enterence na ward ɗin ta shigo da Rashida suna hira, ɗakin Abba direct suka yi suna shiga da sallama Abokin Abba yace "Rashida?" Wara idanu tayi tace "Daddy!" Se ta saka dariya tace "Daddy dama ka San Abban hidayat?" Yace "eh shine best friend ɗina da na kan baku labari baku taɓa zuwa duba shi bane sbd bakwa zaman Nijeria" Rashida tace "Daddy and hidayat is my friend mun haɗu a school a Paris, kaga Ikon Allah ko?" Abba yace "ai ba'a mamaki da ikon Allah" Gaishe shi Rashida tayi tana ajiye Ledar hannunta, ya amsa da kulawa yana tambayar ta school... Suna cikin gaisuwa se ga ummi itama ta zo room number hidayat ta faɗa mata ta karaso itama da karamci Abba ya tarbeta suka gaisa sossai har yake cewa shi ya samu lafiya ma yau gida ze karashe wuninshi. Duk suka yi murmushi, hidayat tace "Abba bari na karasa dasu su gaida Baba" Kai ya gyaɗa yace "na shiga da safe nake jin abunda likita ya faɗa, Allah dae ya bashi lafiya amma kam yana jin jiki" Amsawa suka yi da Ameen, kan suka fice zuwa ɗakin Baba Buba suna tafiya Hidayat na musu introducing juna. Da sallama suka shiga, yana kwance as usual cikin jin jiki, Raed na tsaye yana waya amma tunda suka shiga idanunshi ke manne bisa kanta, murmushi kawai ta sakar mai ta kauda kai, yaran na zaune bisa center carpet dake ɗakin sun saka ma Buba idanu suna kallo sbd yadda yake rattabo zantuka, Daadida na zaune bisa kujera. Gaisawa suka yi da Daadida kan suka gaida Raed suka kuma gaida Baba Buba, yaran suka gaida su. "Yaran nan kun ji ko? Wai ba zan sha ko ruwa bane har nan da sati biyu, ko kurɓi ɗaya fa... Wallahi yunwa nake ji, kishi nake ji!" Cikin tausayawa hidayat tace "Baba saboda lafiyanka ne in shaa Allah komai ze wuce" Yace "uhmm ƴan nan yunwa bai da daaɗi, ashe haka nayi ta azabtar da Muhammad da yunwa ban kyauta ba! Ban kyauta ba wallahi" Duk fa da kyar yake iya fusgo maganan. Rashida tace "baba save ur energy yawan maganan nan yana kara rage maka lafiya ne, ka dinga Ambaton Allah in shaa Allah komai ze zo da sauki" Kallon Daadida yayi yace "Mama kin ce akwai ƴar Aisha da ta zama matar Raed anan? Waccecce don Allah in nemi yafiyar ta ko zan samu sassauci?" Hidayat tace "ni ce baba! Kuma na riga da na yafe maka, Allah ya yafe mana baki ɗaya" Hawaye yake zubarwa da miyau yana cewa "Allah sarki Aisha!" Yini sur suka yi a asibitin da su Rashida, ummi da Rashida kaman sun shekara da sanin juna, anan take ganin wasu daga cikin en uwanta ta ɓangaren Abba, duk wadda ya zo Abba ze aika a kira ta ko wurin ya hamza ko wurin baba ko chan waje Inde suke zaune ta zo yayi musu introducing juna, ba laifi kuma kowa na maraba da ita cikin farin ciki. Yamma Lis aka sallami Abba, hamza ma da Hidayat bata barshi ba ta saka shi yayi ta karatun Alqur'ani da azkar jikinshi ya ɗan yi karfi yace sede a sallame shi, shima aka sallame shi. Duk wadda ze shiga duba Baba Buba se ya zub da hawaye sbd kowa ya shiga se ya faɗa mai yana jin yunwa, Raed ya mai alkawarin kaza da youghurt me sanyi duk randa likita yace ya ci abinci, abun nashi kaman iska yanzu ze yi ta magana anjima in ciwon ya buge shi se nishi, cikin da ya kumbura kaman balon balon likitocin suka yi mishi Mini-surgery suka saka wani roba ta gefen yana zub da ruwan dake taruwa a cikin banda wari babu abunda yake. Fitowanta kenan tayi sallar magrib ta idar aka fara kiran layin wayanta, dubawa tayi ta Mikawa Hidayat take cewa "duba min sunan wanene?" Hidayat tace "Daadida ai ba suna lamba ce" Daadida tace "kayya! Tun fa jiya ake kirana da lamba in na ba wannan farar baturiyar(Norah) se tace layi ne kawai bazan dauka ba in sun gaji swa barni na shaki iska Haba" Hidayat tayi picking ba tare da tacewa daadida komai ba ta kara a kunnenta... #Vote #share #comment                   🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 39* *FREE BOOK* "Assalamu Alaikum muna magana ne da Maman Buba?" Hidayat tace "Wa'alaikumussalam warahmatullah jikarta ce! Allah yasa lafiya kuke nemanta?" Mutumin cikin gurɓataccen hausan shi yace "Lafiya ba lau ba! Tafe muke da abu me muhimmanci kuma muna so mu ganta ne ido da ido!" Hidayat tace "Amma a ina kuka samu layinta? Sannan wani irin muhimmanci abun yake dashi da bazaku iya faɗa a waya ba?" Mutumin yace "hooo ɗiyar nan, mun samu layinta ne wurin matar Buba Badi'ah, da kyar ta bamu bayan mun biya ta dubu biyar mun sayi layin, abunda muke Tafe dashi kuma yafi karfin waya yarinya... Mu musulmi ne munshe la'ilaha illah lahu don haka bamu san me cutarwa ba!" Shiru hidayat tayi kan tace "Ina Zuwa!" Kashe wayan tayi ta kalli Daadida tace "Daadida ko kina da wasu en uwa ne a ruga ko wajen Nigeria?" Daadida tace "ko ɗaya! Halan shirme aka miki a wayan?" Hidayat tace "sun samu layinki ne a wurin Badi'ah bayan sun bata har dubu biyar, sun ce magana me matukar muhimmanci suke tafe da ita suna son ganin ki ido da ido" Shiru Daadida tayi cikin nazari kan tace "ke basu adireshi kawai in ma kidmashin(kidnapping) ne su zo, ni yanzu duk buruka na sun cika banda son da nake in ji me ya samu Aisha me kuma ya faru har Usman ya dau tsawon lokaci be neme ta ba da ko yanzu ma a shirye nake da mutuwa!" Me Rashida da ummi zasu yi In ba dariya ba, hidayat tace "kina fa da matsala, daga son ganinki se ki kawo mutuwa da kidnapping? Yanzu dae in basu address ko?" Tace "eh basu, amma ki basu na babanki don gobe gidanshi zan yini in ma sun zo su same ni a chan ina jin labarin Aishatu!" Hidayat tace "Yanzu Daadida gidan Abba da gaske zaki yini gobe? Ya fa ce ze zo da kanshi goben har gida...!" Tace ita kam faufau sede fa hidayat ta bada address ɗinshi, tace itama bata sani ba se Daadida tace to shikenan su hakura masu son ganintan, su kuma jin shiru yasa suka cigaba da danna kira har Seda hidayat ta kira ya hamza ya bata address ɗin gidansu kan ta tura musu a message bata kara bi ta kansu ba. Rashida da driver ya zo ɗauka suka tafi a tare da ummi don su sauke ta, yayinda hidayat da Daadida da kuma Raed se dare sossai suka koma Dukda shi ya fita ya sake dawowa ne don har wanka ya sake ya sauya kaya, yaran driver ya maida su tare da Tabawa da ta kawo musu abincin rana asibitin. Duk yadda ya so ta bishi gidanshi ƙiyawa tayi, tace ya bari hankali ya kwanta tukuna har fushi yayi amma kan tayi bacci seda ta san yadda tayi ta saukar dashi. Washegari basu tashi da wuri ba se around 11 ma suka karya sbd gajiya, baba Buba baya bukatar abinci don ance ko ruwa ne kar a ajiye inda ze gani har ya ji kwaɗayi kuma asibitin full kula suna samu, wanka suka yi suka shirya hidayat ta fita tayi kyau sossai cikin Atampha me ratsin ja ta kafa ɗaurin zara buhari da ya zauna mata da katon mayafi red, daga takalmi har jakanta red ne tana son colourn ko don ta san yadda yake mata wani irin kyau ne oho, wuraren azahar Raed da driver suka dauke su zuwa gidan Abba. Ga mamakin hidayat gidan a cike yake da en uwa da abokan arziki, don kaman ƙwarya ƙwaryar liyafa Abba ya Haɗa na welcoming ɗin princess ɗinshi home, dukda rashin karfin jikin hamza da rashin ganin hajiyar shi haka Abba ya saka shi daga daman shi suna taryar baƙi tare. Gidan ko wurin parking babu sbd rantsa rantsar Motoci dake cike da harabar gidan har zuwa waje, uncles ɗinta biyu suka rungume ta suna hawaye, sossai taji daaɗin ganin family ɗinta masu dumbin arziki ne, hakanan masu karamci ne, se a sannan take ba Abba labarin haduwar ta da kakanta, hamza yace kwarai har yana gayawa Abba da uncles ɗinta irin complement da Kakansu ya bayar akan hidayat ashe Allah yayi zasu ga juna Dukda basu san alakar dake tsakani ba. Hidayat fa taga gata, kowa Seda ya san ita ɗin fa ta dabance wurin mahaifinta, hakan yasa duk wadda ya tashi tafiya se ya ajiye mata kyauta sbd ya sanya Abbanta farin ciki, aiko duk wadda ya bata ko min kankantan abu yana ganin ainihin farin ciki daga fuskan Abba, ta tashi da cheques na kuɗi har suna bata tsoro har da kyautar mota da gida duka ta samu sbd mahaifinta da ba ƙaramin mutum ba. Hidima sossai aka yi se la'asar likis abokai da dangi na nesa suka watse bayan an yi exchanging contacts da Hidayat saboda zumunci ya ci gaba da daurewa. Masu aiki suna ta hidiman tsabtace gidan da rumfunan da aka yi taron na cikin tamfatsetsen garden na Abban, yayinda Hidayat, Abba, Raed da kuma hamza suka fito don shiga cikin gidan suna sake tattauna irin baƙin na yau, don har yanzu en uwa na kusa na ciki da uncles ɗinta, matansu da yaransu se maman Rashida da kuma Rashida, ga Daadida da yaranta duk suna daga parlor. Hidayat taji daaɗin ganin yadda Hamza yayi matukar kokari wurin sakewa don ko a fuska be kyamaci Raed ba bare ya ji haushinshi, dukda yadda dayawa suka nuna ainihin jin daaɗin ganin mutum irin Raed aka yi ta hotuna dashi ya zama kaman topic a taron sede ga mamakin shi er uwarshi yake taya murnar samun miji kaman Raed har ranshi. Da kanshi yayi introducing Raed as Mijin Hidayat ga mutane dayawa kuma as yayanta ta ɓangaren uwa, har en jarida sun taru a wurin don dayawa se a lokacin suke sanin shahararren attajirin nan Alhj Usman Tafida ya tashi bisa kafafunshi bayan jinyar da ya sha na shekaru da dama, kirkinshi da irin taimakon bayin Allah da yayi a rayuwa sadda yake da lafiya ya hana TAFIDA'S mutuwa daga kamfanunnukanshi na fata, na Motoci, na sarrafa kayan abinci, na wayoyi da manyan shares ɗinshi duk suna running har kawo yanzu da taimakon Allah. Shigowar wasu buzaye ya saka su dakata wa, masu gadi ke kokarin hana su shiga se Hamza yayi magana, ɗaya daga cikinsu ya zo da sauri yace "Alhj waennan ɗin kaman buzayen Nijar ne sun zo wai suna son ganin Mama akan ta basu adireshin da zasu ganta anan, to a gaskiya mu dae bamu san wata mama a gidan nan ba hakan yasa muka hana su shigowa" Hidayat tace "baƙin Daadida ne, Barsu su shigo muji me ke tafe dasu!" Shigowa suka yi buzaye ne da irin shigarsu ta asalin buzaye, mazajen biyu kayan nasu baƙaƙe yayinda mata biyu sanye da brown da kuma farin mayafi duk fuskokinsu rufe. Suka ce "sannunku!" Hidayat tace "ku ne muka yi waya jiya ko?" Wadda yayi magana da farko yace "kwarai kuwa ƴar nan" Tace "mu karasa ciki ko?" Sun juya zasu shiga kenan aka wangale gate, motar Hajiya ta kutso kai, ba'a gama daidaita parking ba ta fito tana gyara ɗaurin zaninta, tun kayan shekaran jiya ne jikinta a birkice take kaman kace kyat ta zura da gudu, wucesu ta zo zata yi a fujajan se suka Haɗa idanu da ɗaya daga cikin buzayen nan.. Chakk ta tsaya tana kallon ta, kai ta sosa ta sake sosawa tace "Ke AISHA! Me ya kawo ki? Me ya dawo dake??? Ba kin tafi har abada ba?? AISHA! Aisha kin kashe ni! Aisha ke azzaluma ce Aisha shikenan na haukace...! Na lalace wayyoooooooo" Ta zabga ihun da ya fito da duka mutanen gidan tana cisge ɗan kwalin kanta. Alhaji Usman da ya tsaya tuntuni yana kallon idanun buzuwar ya fara takawa zuwa gareta ba tare da ya damu da Hajiya dake kururuwa ba, hannunshi da jikinshi duk rawa suke daga yadda ta kasa kallon cikin idanunshi ya ji a jikinshi cewa Hajiya Balaraba ba haukanta bane ya motsa.... AISHA TA GANI. Hannu yasa ya sunce ɗaurin fuskan nata se ga fuskan ta tarrr ya bayyana, baya Daadida da Alhj Usman suka yi zasu zube se Hamza yayi saurin tare Daadida yayinda Raed dake kusa da Alhj Usman ya tare shi yana kallon Aisha. Me ya razana su haka da kallon fuskanta? Hawaye ne ke kwarara bisa kamilalliyar fuskar ta wadda bazaka kirata da dattijuwa ba saboda da matukar wuya ta haura 40, Kallo ɗaya zaka mata ka san fara ce amma ta disashe zuwa kalar duhu hakanan kallo ɗaya zaka mata kaga ramarta Dukda daga idanu zaka san wannan tana da garin jiki me kyau. Waje hajiya zata yi wannan buzu ya kama ta ya fara ambaton wasu Adu'o'i se gashi ta ɗan natsu tana soshe soshe sede bakinta be dena ambaton "Aisha! Me ya dawo dake??? Aisha kin kashe ni?? Shikenan na haukace?? Aisha ta haukatani" ba, ko kuma ta kira sunan Aisha se ta kwashe da dariya. Mutumin ne yace "Maganganun dake tafe damu ba ze yiwu mu yi shi a tsaye ba, kowa na bukatar wurin zama" Se a lokacin Abba ya fusgo numfashi yace "Aisha dama kina raye?" Daadida tace "Dama baki mutu ba Aisha na?? Kina duniya? Ya aka yi aka sanarwa hidayat cewa kin mutu? Wani irin baƙar kaddara ce wannan da ta saka jikata tashi a matsayin marainiya gaba da baya bayan da uwarta da uban ta? Ina kika shiga tsawon lokacin nan baki neme mu ba har ni mahaifiyarki?? Aisha me yasa da Buba ya kore ki kika zaɓi ki tafi ba tare da kin kara ko da second guda ba? Duk laifina ne..... Ni ce na bada kofa..." Kuka take sossai wadda yasa Aisha ɗauke idanunta daga kan Abba karon farko ta nufi mahaifiyarta, tana isa kawai ta faɗa jikinta ta fashe da wani tsumammen kuka! Kuka take daga ƙasar zuciyarta. Cikin muryar kuka tace "Maa...maaa na bar yarinya ta hannun wani bawan Allah....! Na dawo naje har gidanshi basa nan...! Mama na haihu lafiya sede ko fuskanta ban iya na gani ba! Ko sunanta ban iya sani ba mama! Wace irin uwa zata dauke ni??? Ta ina zan fara nemanta??? A ina zan ganta??? Allah na tuba ya Allah! Allah idan wani laifi na aikata da ban sani ba ya Allah ka gafarce ni ka taƙaita min wannan azabar rayuwar!!" Daadida tace cikin kuka tana kara rungume Aisha dake shiga jikinta tana kuka jikinta na rawa tace "Allah baya bacci, Allah ya fi mu sanin daidai da ya zaɓi raba wannan zuri'a har kawo yanzu da ya haɗe mu wuri guda, Aisha seda yarinyarki ta bayyana kan bayyanar ki! Ga ƴar ki chan na cikinki! Gata chan ta tashi cikin kewa da tsananin begenku gabaɗaya! Gata chan sunanta Hidayat.... Ki je gareta ta ji ɗumin jikinki kaman yadda kika zo kika ji nawa na tabbatar da cewa ba fatalwarki bace ko mafarki nake ba" Da sauri Aisha ta miƙe tsaye ta fara kallon direction da Daadida ke nuna mata, hidayat ce tsaye kaman mutum mutumi idanunta da suka rine zuwa jajazir duk a waje, da sauri Aisha ta mike tsaye tana me kallon hidayat, wani irin kallon kallo suke aikawa juna kan suka fara ɗaga kafafunsu a hankali kaman masu tsoron taka ƙasa suka nufi juna.. Kasa jurewa hidayat tayi ita kaɗai ta san me take ji a gabaɗaya ilahirin jikinta, yau mahaifiyarta ce gabanta bata mutu ba ashe, me yasa Abba ya ce mata ta mutu? Me yasa yayi mata karya abunda ba ɗabi'arshi ba? Taya aka yi ta barta a zani ta tafi bayan ta san zalunci irin na umma??? Me yasa komai ya faru a haka?? Kasa ɗaukarta kafafunta suka yi ta tafi suuu zata faɗi daidai lokacin Aisha ta isota ta taro ta suka yi ƙasa a tare suna masu kallon juna ido cikin ido, kaman an ce kyatt suka wani rungumar juna suna fashewa da kuka me tsananin cin rai da taɓa zuciya..... #Vote #share #comment                 🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 40* *FREE BOOK* Shiru parlorn ya ɗauka Aisha na riƙe da Hidayat har lokacin ta ɗaura kanta bisa cinyar ta tana shafawa, Allah kaɗai ya san me ke tafiya cikin ran Raed don gabaɗaya be taɓa sanin menene ainihin ciwo a zuciya ba seda yaga irin kalar kukan da Hidayat take yi, gabaɗaya he wasn't his self yana riƙe da Junior da ya fara rikici, hamza na zaune gefen Abba da yayi shiru kawai amma shi kaɗai ya san me ke tafiya a zuciyarshi. Daadida ma na zaune gefenta buzayen nan ne namijin yana riƙe da Hajiya da take ta so ta fisge, gyaran murya mahaifin Rashida yayi yace "Toh Alhamdulillah aka ce komai yayi farko zae yi ƙarshe, sannan duk nisan jifa ƙasa zata dawo, abubuwa da dama sun faru wadda kawunanmu duka suka kasance cikin duhu Dulum tunda ga wacce aka tabbatar da mutuwar ta zaune a gabanmu, sannan ga hajiya dake wasu maganganu kaman wacce ta samu taɓuwar kwakwalwa, na tabbatar kowa a nan yana son sanin me ya faru? Taya abubuwa suka kasance a haka? Yaya kowannenku yayi rayuwa?" Shiru ya ɗan yi kan ya cigaba "Aisha! An auro ki an raboki da iyaye da en uwanki aka tsallake gari ya gari aka kawo ki har garin Kano, aka kuma damka amanarki hannun Hajiya Balaraba, ta karɓa hannu bibbiyu wadda seda kowa yayi sha'awar zamanku ake yiwa Usman dacen samun maatan kwarai kwatsam se kuma abubuwa suka juye, shin me ya faru?" Ba tare da ta kalli hajiya balaraba ba tace hawayenta ya kasa tsayuwa "Kaman yadda duk kuka sani sunana Aisha haifaffiyar garin mambila na jahar Taraba, na taso nayi rayuwa da iyaye na kaɗai ba tare da wani ilimi akan zama da kishiya ko kishi ba, ko da aka kawo ni garin Kano wallahi da zuciya ɗaya na shiga gidan yaya balaraba, a yadda ta karɓeni ta riƙe ni kaman ƙanwarta kowa se yayi sha'awar zaman mu, da ita zamana lafiya amma da mijina gashinan.... Mun Rayu cikin wannan aure da daaɗi ba daaɗi, dukda son juna da muke, matsalar da muka fara fuskanta shine a duk sadda ranar kwana na ya zagayo jini ne ze balle min baze tafi ba har se ya bar wurina ya koma wurin balaraba, tun bamu damuwa har abun ya zo ya fara damun mu saboda ina neman shekara da aure babu abunda ya taɓa shiga tsakaninmu. Da farko iyayena na so samu da matsalar, don damuwar har ta saka ni fara rama Dukda Alhj be taɓa nuna damuwa ba yana hakuri yana kuma Adu'a nima yana kokarin kwantar min da hankali da cewa lafiya ta ƙalau Dukda kankatar shekaruna na san ba lafiya ba, ranan muna zaune da Yaya balaraba se take tambaya ta.. "Ni kam Aisha lafiyanki kuwa? Kwanan nan fa se rama kike tayi ko de mun kusa jin kukan jinjiri ne kike ɓoye min?" Nayi murmushi nace "wani irin kukan jinjiri bayan abunda ya dame mu ya damemu" Tace "ban gane ba?" Nan na faɗa mata duk abunda ke faruwa, ban san kowa a Kano ba, bani da ƙawa bayan mahaifiyata a lokacin kuma sede ziyara, basu da waya a gida bare in faɗa mata damuwata ta waya, na ɗauki dukkanin yarda da amana na baiwa yaya balaraba, tashin hankalin da ta shiga a sadda taji wannan labari ko Alhj se haka, tayi ta damuwa tana maimaita maganan bayan kwana biyu ta nemi mu je wurin wani malami ya duba matsalar kilan mutanen ɓoye ne. Ban yi mata musu ba na tambayi Alhj, ze nuna rashin amincewa na saka mishi rikici don a ganina ba shine a cikin matsalar ba, Allah kaɗai ya san irin azabar ciwon mara da nake sha a duk bayan kwana biyu, haka ya kyale mu muka tafi malamin nan ya tabbatarmin da matsalar sheɗanu ne ga abunda za'a kawo a fara jinya. Seda nayi jinyar wata ɗaya zuwa biyu kan jinin ya fara ɗaukewa, a sannan hankalina ya fara kwanciya don ko ze zo bayan kwana biyun baya ciwo kaman baya, a sadda na fara murnan samun sauƙi a sannan Alhj ya ƙaurace min, baya cin abincina, baya kwana ɗakina magana wannan in ze Haɗa mu sede ya faɗawa yaya ta faɗa min, ita na samu da wannan matsalar ma ina kuka nake gayamata ga abunda ke faruwa tsakanina da Alhj, da kanta ta ajiye mu don yi mana sulhu buɗan bakinshi se cewa yayi na zama ƙazamiya komai nawa yana wari shiyasa baya son zama kusa dani da mu'amalantata don ko abincina kyama yake bashi. Nayi kuka sossai na shiga damuwa, se in yi wanka sau biyar a rana, nayi ta yawon tambayar Yaya ko tana jin wari jikina se tace ita kam bata ji komai ba, a lokacin Hamza na ƙarami sossai dashi nake yini nake kwana yana debe min kewa gabaɗaya na barwa Yaya Alhj ina me cigaba da Adu'ar samun sauƙi wurin ubangiji ina kuma yin maganin wannan malami da yaya ta kaini wurinshi. A taƙaice wannan matsala seda ta kaimu kusan watanni takwas, matar abokin Alhaji ita ce mace na biyu da take kaman ƙawa a gareni a Kano ta girme mini don zata yi sa'a da balaraba hakan yasa bana iya buɗe mata cikina gabaɗaya, har na je gida na dawo babu wadda ya san ina cikin damuwa saboda ganin irin farin cikin ganina da su Mama suka yi yasa na kasa faɗa musu matsala ta kar na saka su cikin damuwa. Bayan na dawo ne na kai mata ziyarar wani ɓari da tayi, nan take tambaya ta ni kam shiru ba ciki ba labari? har ga Allah ban so fitar mata da sirrin aurena ba sede abun na damuna, nan na bata labarin komai, bani da maraba da naani a gidan Alhj Usman, don komai na hamza a wurina yake, haka girki daga nawa har na Yaya ni nake yi ita ta kwana da miji. Salati ta saki ta fara yi min faɗa akan kishiya ko ya take ka ji tsoronta, ban hanaki zama da kishiyarki lafiya kuma da zuciya ɗaya ba sede fa ki kiyaye ki zama me lura da hange, ni ba son raba zaman lafiyanku nake ba sede akwai Ayar tambaya me girma akan Hajiya Balaraba. Tashin farko na nuna mata ban yarda ba, don har ga Allah duk wadda ze zagi ko ya kushe yaya har raina haushinshi nake ji, duk yadda ta so fahimtar dani na kasa fahimta se ta koma ta bayan fage, mahaifinta malami ne ta mishi bayanin komai ya neme ya ganni, roko na ta dinga yi akan kar na faɗawa Yaya haka ban faɗa mata ba na fita muka je. Adu'o'i da tofi ya bani da wasu magunguna akan in na fara sati biyu kar in fita ko ina, hayaƙi kuma in yi tayi a ɗakina, sossai ruwan da ya bani na sha ya taimaka mini, inda na dawo gida nake magungunan, kaman kuwa an toshe min baki ban fadawa yayar ba se bayan da na gama maganin ranan da rana muna zaune a babban parlor se ga Alhj. Da sauri na tashi zan shige ɗaki don kusan haka zaman namu yake a sannan yayi saurin cewa "Aisha! Ina zaki daga shigowa ta?" Daga ni har yaya da mamaki muka tsaya muna Kallonshi. Yace "kawo min ruwa pls" Na wuce kitchen na Haɗo mishi ruwa na kawo ya karɓa yayi godiya yana me kallona, zan tafi yasa na zauna hira suke da yaya ya kan sako ni ciki Dukda shakkar amsa shi da nake ji don ban manta wahalar da na sha a watannin daga gareshi ba, ko hanya muka Haɗa bani da maraba da kashi a wurinshi. A ranar a tare muka ci abincin rana da yamma ya fita damu shopping, yana ta kokarin janyo ni jiki yayinda yaya take nan shiru kaman ruwa ya cinye ta. Bayan mun dawo a lokacin ma bayan isha'i se gani nayi Alhaji yayi ɗaki na, da lallami yasa na saki jiki yayi ta min rantsuwar be san meyasa yayi min abunda yayi ba, tsakanin miji da mata se Allah, se a ranar Allah ya nufi tabbatuwar aurenmu bayan kusan shekara biyu. Washegari da Yaya ta fahimta se ta ɗauke min wuta, gashi Alhj se riritani yake yana lallaɓani, in na mata magana se ta share ni na sameta har ɗaki nake tambayar ta lafiya? Tace "ban san me kika daukeni ba Aisha! Ni kam a matsayin ƙanwa na dauke ki ashe har zaki iya tsallakeni ki je wurin wata neman taimako? Yanzu kin bata aikin malaminmu na farko kuma ya ce akwai matsala don aljanun da ya raba ki dasu na farko zasu iya dawowa" Na tsorata nayi ta bata hakuri tace ba ruwanta sede mu koma wurin malamin, duk a zatona hajiya Adama(matar abokin Alhj) ita ta gayamata. Haka muka sake komawa wurinshi ya bani wasu magungunan, zamana da yaya babu matsala amma Alhj yau lafiya gobe babu, na sha wahala sossai nayi ta rashin lafiya don sau kusan biyar ina yin ɓari, bani da sirrin da yaya bata sani ba tsakanina da miji na, kwarai naji tsoron Allah na ji tsoron munafukin mutum me fuska biyu, don na bata yarda ta ci amana ta, tana da baiwar lafuzza wadda ko baka so idan ta kanainayeka se ta ji cikinka da salon munafurcinta. Mun je kasashe kusan biyar ganin likita akan yawan ɓarina sede ba chanji, wani cikin da nayi Seda ya shiga wata na bakwai nayi nakuda me matukar wuya na kusan sati, na fita hayyacina gabaɗaya saboda wahala a lokacin muna a Saudia, da taimakon Allah wani malami kuma likita ya taimaka mana inda na haifi kadangare, iya tsoro mun tsorata nan ya kwantar mana da hankali ya tabbatar mana aikin asiri ne akwai Mahaifinshi ze taimaka mana. Mutumin nan ya taimake mu tsawon wata shidda nayi jinya kan na dawo garau, tun yaya na mita har ta gaji ta kyale mu a Tunaninta zama kawai muke ko jinya nake ta hanani zaman lafiya, bamu baro Saudi ba seda na samu cikin hidayat na wata uku. Ko da muka dawo wurin Adama naje muka kara komawa wurin mahaifinta nan yayi ta min nasiha yace kuma in kiyaye kishiya ta shima kuma ze cigaba da bani taimako, anan na fara jin tsoron Yaya don tabbas na yarda fuska biyu gareta. Da ta fahimci hakan se ta fara nuna min ainihin halin ta a fili, munafurci da kirsa babu wadda ban gani ba wurin yaya, wani lokacin Alhj ya yarda wani lokacin kuma Allah ya taimake ni, duk burina akan cikina ne, nayi alkawarin bashi kariya da raina da numfashina, babu abunda zata bani inci tayi yin duniya ta gaji ta kyaleni, cikina na wata takwas wani rana ina kwance bayan nayi walaha se bacci ya ɗan sureni. Mummunan Mafarki nayi macizai na fito min daga jikin gini zasu marasa kyaun gani, bakunansu na zubar da bakin jini kuma suna kiran sunana cikin muryar amsa kuwwa, a firgice na farka se muka Haɗa idanu da yaya da sauri tace "Aisha!" Nace "Na'am yaushe kika shigo?" Wannan magana shine na karshe da nayi da wani a gidan Alhj, a take naji na tsani environment ɗin da gidan na tsani garin Kano gabaɗayanta, kaman tunzura ni ake ana turani akan in bar garin, da hijab a jikina jakana kawai na ɗauka na rataya na fice ba tare da na sake ko waiwaye ba. Tasha na iso ina ji na ba lafiya ba, kaman me maƙuwa haka nake ganin kaina bana gane duk wani magana da ake a gefena ko a kusa dani, da taimakon Allah na ambaci Taraba a tashar nan suka gane inda nake son zuwa kenan aka ce min rana yayi motocin jalingo sun tafi sede Gombe, haka na biya na Gombe. Kusan tafiyar awa takwas ta kawo mu Gombe Dukda tarin gajiya, yunwa da ƙishir ruwa da nake ji haka na sake neman tasha ba tare da na damu ba na biya kuɗi aka sake dauka ta zuwa Taraba(jalingo) nan ma wata tashar na nema na samu motar da za shi gembu, kafafuna sun kumbura sumtum in banda sunan garinmu ban yiwa kowa magana ba tun fitowa ta don kaman bebiya na zama duniyar tayi min shiru babu abunda nake so illa in yi nisa da Kano. Kwana nayi a hanya don ban isa gidanmu ba se wurin karfe goman washegari, jiri nake gani sbd yunwa ga tsohon ciki da kyar na iya na kawo kaina gida, amma se yaya Buba ya ƙi amsata bakin ciki da ciwon da nake ciki ya hanani iya furta ko wacce kalma don ko nace zan furta ɗin ma bani da tabbacin magana me anfani ne ze fito daga bakina don kwakwalwata ya riga ya juye gabaɗaya bana jin nice karan kaina. Yana wullo ni na samu na kare cikina, na mike ban tsaya ba don nan ɗin ma ji nayi na tsani kowa, na mike na naushi hanya nayi tafiyar kafa na kusan awa uku zuwa huɗu don bana gani da kyau kafafuna basu iya daukana, ashe na bar gari ma gabaɗaya na fara shiga tsaunuka, anan na faɗi. Na farka na tsinci kaina a wani gida cikin wasu mutane, da kyar na iya buɗe idanuna cike da son fahimtar nan ɗin ina ne, se na fahimci kaman gida ne na masu zaman kansu ko na haya, don wasu na zaune suna karta, wasu na shaye shaye, wasu na Cacar baki, wasu na wanki suna jin wakokin da daga ka ji zaka san ba na mutanen arziki bane, babu abunda babu a tsakar gidan en daudu, mata da maza. "Kin ganta nan riba biyu, ga na ɗan ciki ga na jikinta.. A nawa zaki saye ta?" Matar da tayi kama da tsohuwar kilaki tace "amma ai kaman bata da cikakken lafiya gaskiya Ba zan baka ya wuce dubu ɗari uku ba" Yace "kai Asabe! Kin san Allah duk gembu ba zan sama miki irin macen da kike so me kyau da diri kaman wannan ba, ina me rantse miki tana haihuwa shikenan zaki fara Moran ta yadda ya dace" Ina kwance kaman mutum mutumi ana ciniki na, daga karshe dubu dari biyar ta bashi, ta sa aka kama ni aka kaini wani ɗaki ina rungume da jakana da be bar jikina ba. Abinci aka kawo min saboda irin yunwar da nake ji jikina na rawa ainun na hau ci hannu baka hannu ƙwarya na gama na sha ruwa se bacci, ba zan tashi ba se idan lokacin sallah yayi wannan kam Allah be mantar dani ba zan tashi na gabatar na sake komawa bacci, bana tashi se yunwa. Idan suka hana ni baccin kuma to haka zan kwana in yini ina maganganu wadda suke alakantawa da hauka, don zan yi kuka, in yi dariya duka ni kaɗai. Seda nayi sati uku wannan gida ba tare da na san a ma wani gari bane, wata rana tsakar dare wuta ya tashi a gidan..... #Vote #share #comment                  🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 41* *FREE BOOK* *Sorry! Jiya bamu da wuta wayana ya mutu kan wuta ya dawo kuma na wuce Garinmu a bacci! Yauwa I want to talk about ghost readers, kun ganku? Babu na gode, babu comments se an kwana biyu ba'a ganka ba se kaga ana cewa "wacce kam shiru!" "Yau babu kowa yaga zabuwa" ko kuma masu cewa "continue" Abeg ku duba wahalar da mutum yake sha wurin wasa kwakwalwa, data, hannu da idanu wurin faranta muku ku faranta mishi kuma... Typing is not a joke I repeat ba wasa bane wlh! Allah yasa mu dace*** Wuta sossai ya tashi a gidan ba tare da na sani ba saboda baccina ba na lafiya ba, wata ce ta zo ta tada ni karfi da yaji ta Jani muka hau gudu muka fita daga gidan kaman yadda sauran jama'ar gidan kowa yayi ta kanshi yayinda wasu daga ciki suka ƙone kurmus ciki harda magajiya, dab asuba kowa ya kama gabanshi haka nima na nausa nayi ta tafiya ban damu da dubun dare ba banda jakana da nake rungume dashi ba dare ba rana ko takalmi babu kafafuna. Karnuka sede su min haushi su gaji su wuce amma ko ta kansu bana bi bare in tuna wani abu wai shi tsoro, jikin wani gida na samu na zube a wurin saboda gajiya da nayi ga bacci ina ji, pillow nayi da jakana na hau bacci a wurin Dukda uban sauro dake yawo a unguwar. "Baiwar Allah! Baiwar Allah!!" Wata murya ke ta ambaton hakan har Seda na fara buɗe idanuna ina lumshewa, ganin garin yayi shaaaa Dukda be zama haske tangararam ba hakan yasa nake iya kallon kamilalliyar fuskanshi yace. "Me kike yi anan haka da tsohon ciki? Na fita zan je masallaci na ganki har kuma na dawo baki tashi ba! Baki tsoron sauro ya illatar dake da abunda ke cikinki?" Ban amsa ba se Kallonshi kawai da nake, chan na iya buɗe baki kaman an fusgo maganan nace "ru....wa" Yace "tashi! Tashi mu shiga gida se in baki kisha" Da kyar na iya mikewa sbd nauyin jiki da ciwon kafafu, haka muka shiga gidan nashi tun fitowa ta shine mutum na farko da ya tausayamin har ya taimake ni ba tare da ya san ko ni wacece ko daga ina nake ba! Mutum ne me matsakaicin karfi don baza'a kirashi me kuɗi ba, gida ne daidai na rufin asiri, sallama yayi cikin babban sashen. Wata mata ta fito tana kallonmu ɗaya bayan daya, yace "Umman khausar ga bakuwa nan don Allah kaita extra room ɗin nan ki bata ruwa in akwai wani abu a gidan ki bata kan a gama abin kari!" Kallon tara saura kwata take mana daga ni har shi seda ta gama kare mana kallo kan tace "amma Abban Yusuf ka ma raina min wayau, haka kawai ka shigo min da mace da tsohon ciki rimi rimi ka wani ce in bata extra ɗaki da abinci? Ina ka samo ta da sassafen nan?" Yace "tsaya tukuna Amina gidanki ne nan kam ko gidana? Taya zan ce ga abunda za kiyi kice ba haka ba matar nan tana tsaye tana jin jiki?" Dariya tayi ta tafa hannu tace "Aaaa lallai ni dayake ba ciki ne jikina ba a kwance nake ina jin daaɗi, taya zaka fara fifita wata kaina? Kab zuri'arku ban san me kama da aljannu ba bare in ce daga dangi take.." Juyawa yayi ya kalleni yace "zo mu je baiwar Allah" Juyawa muka yi zamu bar wurin tayi wani tsalle ta sha gabanmu ko damuwa da cikinta da ya ɗan fara fitowa bata yi ba tace "Ina Zaku je? Wai me kake nufi ne?" Hannu ya sa ya matsar da ita yace "wuce baiwar Allah" Na wuce ya biyo ni zuwa karamin sashen dake daga gaban wannan ɗin, da sauri ta kuma shan gabanmu tace "ɗakin ka zaka kai ta?" Yace "eh tunda nan kam ba naki bane baki da hurumin hanani ko yi mini iko" Bori sossai tayi tayi wadda wasu ba zan iya tunawa ba akan kilan cikin ma nashi ne dangina suka koro ni na dawo mishi da abunshi in ba haka ba ina ze sameni da sassafen nan, babban damuwarta kankantar shekaru da kyau na Dukda sossai ya ɓuya sbd wahala. Daga karshe ganin da gaske sashen shi ze ajiyeni tace ta hakura in zauna sashen ta, haka muka koma ta bani extra room, be barni ba seda ya tabbatar na ci abinci nayi sallah, ina gabamawa nayi pillow da jakana as usual na hau bacci. Dukda kasancewar Amina mace ƴar uwata sede ko sau ɗaya bata taɓa jin tausayina ba a zamana da ita Dukda taga banda cikakken lafiya da hankali, bayin ta babu pampo se wurin wanke wanke, da safe zata saka ni diban ruwa in cika mata randunan bayi, in yi wanke wanke kan ta bani abin karyawa, abincin rana wani lokacin se yamma idan Alhj ya dawo mutum me tsananin mutumci da karamci ze ɗauki nashi ya bani Dukda barazana da matarshi ke mishi a kaina iri iri. Na zauna na tsawon sati uku a gidan bana yiwa Kowa magana tun ruwa da nace ina so ban sake cewa kowa tak ba, da dare Alhj ya kan zauna ya tambayi suna na, mijina, garin da na fito ko wasu en uwana amma babu abunda nake iya ce mishi ko nake tunawa. Wata rana na tashi da nakuda bayan na ɗibi ruwa ina a na karshe cikina da bayana suka riƙe sossai, ban iya karasawa ba bokitin ya faɗi nan tsakiyar parlor ya jike Mata ɗaki, wani irin bangaza tayi mini ta hau zagi na babu irin sunan cin mutuncin da bata kirani ba har marina Seda tayi akan se na gayamata gaskiya mijinta ne uban ciki na? Ina fama da wahalar nakuda hakan yasa duk abunda take yi ɗin ban ma san tana yi ba, ta saka ni na share mata ruwan da na zubar ina cije baki da komai a tsugune na yi aikin ban iya komawa ɗaki ba nan tsakar ranan na faɗi ina shan azaba, matar nan bata fito ba bare ta kulani na fi awa uku a wurin har jini da ruwa suka fara bin kafafuna ga rana ana yi na jike sharkaf da zufa, da taimakon Allah Allah ya turo Alhj Dukda yaranta na nan suna kai kawo sede kallo babu wacce tayi min. Hankali tashe ya kirata ta zo ta taimaka min mu tafi asibiti tace ba da ita ba, lokacin da aka yi abunda aka yi ba'a gayyace ta ba se yanzu, haka ya taimaka min sbd babu yadda ze yi muka je mota ya kaini asibiti, da kyar suka karɓe ni seda suka yi faɗa sossai akan rashin kulawa da sakaci da aka yi gashi ba wurinsu nake zuwa awo ba. Bayan baƙar wuyan da nasha na haifo yarinya mace, ina haifanta kuma na fara wani kalar bacci kaman wacce ta bugu, su suka mata komai har nono suka bata ba tare da na sani ba. Se washegari da yamma bayan sun gama bincikensu suka bani sallama, tunda na farka kuma se hauka na muraran ya bayyana, ba zan ce na riƙe yarinyar ba sbd Alhj tsoron bani ita yake kar na yarda ta. Muna dawowa Amina ta sake tada sabon bore, Seda suka kai ruwa rana kan na shiga ɗakin da suka saukeni, da farkon dare ya kawo min yarinyar yace "Baiwar Allah ya kamata kiyi magana ko sunanki ne mu sani! Babu daaɗi yadda Amina take adressing naki da sunaye marar kyau" Kallonshi nayi kaman zan ce wani abu se nace "Aisha! Aisha!!" Ina ta maimaitawa Seda ya gaji yace "sunanki Aisha?" Kai na gyaɗa yace "daga ina?" Ban yi magana ba se jaka na buɗe na fiddo box na miƙa mai nayi murmushi, karɓa yayi yana Juyawa kan ya ɗago nayi bacci fita da yarinyar da ko kukanta ni ba zan ce ga yadda yake ba yayi, madara ya sa aka sayo mai ya bata a tare suka kwana. Karfe Taran dare naji ana tashina, ɗago kai nayi na kalli Amina ta zaro min idanu tace "tashi tsohuwar munafuka ki fitar min daga gida.. Ai nayi kokari tunda kika yi sama da sati uku" Mikewa nayi a tsorace na rarumo jakana na rungume, fisgewa tayi tana cewa "uwar menene ciki da kike mammaƙeta haka?" Zazzagewa tayi zobuna na suka zubo waenda suke gwal ne masu kuɗi a lokacin guda biyu, ɗauka tayi tana Juyawa ta kalleni tace "kam bala'i!! Wato Alhj ya iya saya miki gwal kina karuwarsa ni matar gida be sayawa ba?" Girgiza kai nake ba tare da nace komai ba, mari ta sauke min tace in zo in fitar mata daga gida kan ta kulle idanu ta buɗe zobunan kuma wlh bazata bani ba tunda da kuɗin mijinta aka saya. Kuka nake son yi ta fincikoni tare da toshe min baki ta ja ni har wajen gate ta cilla ni na faɗi har Seda goshina ya fashe da dutse, raina ne ya ɓaci ban sani ba ko aljannun da aka Haɗa ni dasu ne ko yaya kawai ina mikewa na dau hanya ba tare da ko waiwaye ba. Seda nayi tafiyar da ban san na awa nawa ba gari dae yayi shiru kan na iso wani rumfa inda buzaye suke zube sun hura wuta, anan na shiga cikinsu na kwanta basu ganni ba seda safe, sun tsorata macen ta tashe ni, ina farkawa mijin yace kar kowa ya min magana, wasu Adu'a ya dinga yi min kan yace "Baiwar Allah!" Na kalleshi sede ban yi magana ba, yace "hoo innalillahi wainna ilahi rajiun duniya ina zaki damu jama'a? Laure wannan mata na shikin masifa tana matukar bukatar taimako" Matar tace "to me gida ba se ayi wani abu ba?" Yace "yo ai ba ze yiwu anan ba duk abubuwan suna chan gida gashi kudu muka nufa" Tana kallona cikin tausayawa tace "kayi hakuri mu koma Nijar me gida! Wannan baiwar Allah duk inda danginta suke na tabbatar suna shikin tashin hankali" Haka gamji da matarshi Laure suka fasa wannan tafiya suka tafi dani Nijar, na sha wahala sossai wurin adapting rayuwarsu, nayi jinya me yawa wadda har na kan yi wata ba tare da na san inda kaina yake ba, abun ya zo ya fi karfin Gamji Seda ya Haɗa da neman taimako a wasu nahiyar na Nijar. Tsawon shekarun ashirin ina fama da jinya don se haukan yayi kaman yayi sauƙi se kuma ya taso, na samu lafiya shekaru uku baya inda komai ban manta ba, na basu labarina gabaɗaya saboda sun zama kaman yayyina sun riƙe ni da amana matuka, basu taɓa saka lomar wani abu a bakinsu ba tare da na saka ba, ko da suka ji labarina wadda ina zuwa wurin barin jinjirata da ba zan iya tuna fuskanta ba se kuka da firgici su rufe ni, ta ina zan fara neman ta? Kuma ta yaya? Wlh ko sunan Wannan bawan Allah da ya taimakeni ban sani ba bare unguwar da yake a birnin Kano. Mun kara delay na shekara uku kan mu zo ne sbd tsananin rayuwa da gamji yake ciki ya sayar da duk dabobbin shi wasu yayi asarar su duk ta hanyar neman min lafiya don aljannun sun sha kashe mishi garke gabaɗaya sbd ni akan ana mishi gargadi ya Rabu da ni da rayuwata babu ruwanshi. Da muka samu kuɗin suka taru kuma fita ƙasar Nijar ya gagareni seda muka yi ta biyan wasu kudade kan muka iya fitowa, mun kwana Kano kan muka nausa Gembu seda muka samu kab labarin abunda yake faruwa gidan Buba kan muka nemi layin mama, matarshi Badi'ah ta bamu shine muka kira, ko da muka iso Kano da neman taimako muka samu me adaidaitan da ya ɗauko mu zuwa wannan gida don ko biyar bamu tsira dashi ba kuma..." Shiru tayi tana share hawayen fuskanta, tana me cigaba da shafa kan Hidayat da take ta kuka har da majina, Abbanta da ya hamza ma kuka suke yi duk dauriya irin ta maza, sossai jikkunansu yayi sanyi babu wadda ya iya magana se muryar Hajiya Balaraba suka ji ta fara cewa "Hahahahahhaha ba kin dawo ba! Dama ya faɗa kina dawowa se na haukace ai kaikayi koma kan mashekiya ne! Aisha ke azzaluma ce, ina zaman zamana da mijina tun kan yayi kuɗi har yayi arziki shine ya tsallake ya auro ƴar gembu waenda ba inda labarin kyaunsu be je ba! Yana so ni balaraba in zama bora ya sa kyakkyawa gaban mota Hahahahahhaha" Ta sosa kai ta sake gyara zama kan tace "ni ce nan na je wurin neman taimako aka taimaka min ake sakar miki da ciwon ciki me tsanani da kuma zuban jini duk kwananki...! Hahahahahhaha kin ɗauka ban sani bane har da bani labari.... Ai wannan malamin ma ba malami bane ruwan asiri na yayi ta baki as magani ke kuma wawuyar kika yi ta amfani dasu har asirin warin jaɓa ya shige ki..." Kallon maman Rashida tayi tana kwalalo idanu tace "ke Adama ke munafuka ce! Har abada a matsayin hoto na so Aisha ta zauna gaban Usman se kika min zamba cikin aminci kika karya mun magani ba tare da na ankare ba.... Boka na yace min tunda har wannan ya karye babu yadda na iya sede in fara Haɗawa da kissa irin ta mata su zasu na aiki har gunki ya basu nasara..." Hararan Aisha tayi kan ta kwashe da dariya se ta fara kuka tace "Munafuka! Algunguma kwai na guda ɗaya jal na gani gidan Usman amma ke! ke seda na zubar miki da ciki har bakwai na karshe da ya fara girma na baiwa Boka suka shanye mai jini suka musanya shi da kadangare sbd duk maza ne" Hahahahahhaha tayi dariya kan ta cigaba "kuka maida ni shahasha kuka koma inda ban isa in taɓa ku ba baku dawo min ba seda ciki, na harzuka naje wurin Boka me taimako na, maji roko na! Yace tabbas cikin nan haifaffe ne be kuma san mace bane ko namiji don basa iya gani...! Na ji haushi raina yayi baƙi nace ya kashe ki Aisha ko ya ɓatar min dake in dena ganinki a rayuwata" Sosa jikinta da ya fiddo wasu manyan kuraje tayi tace "kin san me yace min? Munafukar bazata mutu ba sede a ɓatar da ita, amma duk shekara za'a dinga zubdawa aljannu jini sbd su kasance cikin gaskiya a aikinta, million biyu" Ta Nuna da hannunta tace "ko wani farkon shekara se na kaiwa Boka million biyu ya zubarwa aljannu jini... Ni ban ma san ko na mutum bane ko na dabba Hahahahahhaha..... Sharadin shine duk ranar da kika dawo ko jininki ya dawo har yayi ido biyu da Alhaji kaikayi ze koma kan mashekiya, ya ce min baze bari ku haɗu ba sbd barbushe ya bashi sa'a...! Yace har ku mutu bazaku sake arba da Usman ba! Munafukar ɗiyarki ta fara dawowa... A fujajan na tafi Kwara wurin Boka sede na samu dajin da yake ya ƙone kurmus babu abunda ya saura shi karan kanshi ko ƙashinshi ba'a samu ba! Shikenan na haukace Aisha ta haukatani... Kaikayi fa ya koma kan mashekiya, wallahi ya koma hahahahaaaaaa" Cikin tsananin kuka hamza yace "Hajiya why????? Meyasa hajiya? Hajiya kin cuceni kin cutatar min da rayuwa innalillahi wainna ilahi rajiun.... Menene ribarki? Me yasa kika zama uwata a duniya????" Kuka yake sosai wadda seda zuciyar kowa ya tabu Dukda kowa na cikin shock da jimamin jin wannan mummunar labarin daga hajiya... Alhj Usman yana zub da hawaye yace "Allah a gode maka! Allah na gode maka da ka jarabceni da samun irin wannan mace a matsayin mata! Balaraba kin cucemu, kin cuci mata ta da ɗiyata da ni karan kaina sede na gode Allah da ya nuna miki iyakar ki ya maidani Hoto a gabanki ni da kike son mallakewar, me ribar ki??? Kin raba Aisha da ni don in zama naki ni kaɗai, a ranar da Aisha ta tafi a ranar na bi hanyar gembu cikin tashin hankali da talatainin dare na faɗi cikin tsaunuka wadda na shekara ashirin ban anfane ki da komai ba! Ban farka ba kuma Seda ana gab da dawowar Aisha da Hidayat gareni, kin ga ikon Allah ko? Wallahi wallahi ba zan taɓa yafe miki wannan zalunci ba Balaraba, Allah ya isa wahalar Aisha..." Kuka ne ya kubce mai kaman ba babban mutum ba, Daadida na zub da hawayen tausayi tace "Hidayat!" Idanunta da suka kumbura suntum ta ɗago ta kalli Daadida, Daadida tace "Aisha ta barki hannun Amina, A labarin Aisha Amina bata da mutunci bata san shi ba, shin ya rayuwa ya zame miki hannun ta da iyalinta?" Raed da idanunshi suka sauya ne sbd damuwa yace "A'a Daadida don Allah! Ku ji tausayinta mana, kukan nan ya isa haka zuciyata na gab da samun matsala in ta cigaba... I cannot take it anymore!" Da gaske zuciyarshi na beating fiye da yadda ya kamata ya buga, har daci yake ji a makogoronshi.... Kallonshi hidayat tayi tace "I'm fine..! It's OK" Yayi saurin cewa "no you are not fine, it's not ok please die hard not now, not today" Abban Rashida yace "Raed kayi Hakuri ka barta ta bayar ɗin sbd iyayenta na so su ji irin rayuwar da tayi! Ina Alhjn da ya taimaka ma mahaifiyarta yake a yanzu da take a matsayin matar ka bayan ta aureka ne as me aikin gidanka! Ba tare da dangi ko zuri'a ba..." Runtse jajayen idanunshi yayi ba tare da yace komai ba. A hankali hidayat ta fara bada labarinta.... #Vote #share #comment                 🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 42* *FREE BOOK* ***Masha Allah🥰 Naga comments Bila adadin and I soo much love ur review about this book, na tabbatar saƙon ciki na isa inda ya kamata...Allah ya raba mu da son zuciya yasa mufi karfin zuƙatanmu ya kuma raba mu da sharrin shaiɗan.... Son so❤️ masoya wannan littafi*** A sadda take bada labarin daki daki tana zub da hawaye masu zafi waenda suke fita daga ƙasan zuciyarta na ciwon irin abubuwan da aka yi mata a rayuwa seda dukkansu parlorn suka zubar mata da hawaye, da ta zo wurin rasuwar Usman da Abba kuwa seda ta so shidewa don kuka, mahaifiyarta ce ta dinga tausarta ba tare da tayi magana ba, lallai Amina bata da mutunci Amina bata san girman darajar da Allah yayiwa ɗan Adam ba... Duk shiru suka yi suna jinjina irin wannan baƙar zuciya, Alhaji Usman ya share fuskanshi yace "Duniya ta lalace kwarai da gaske, yanzu kowa nashi da kanshi kawai ya sani taya muke Tunanin samun rabauta bayan Bama anfani da hadisin nan da yace ka sowa ɗan uwanka abunda ka sowa kanka? Amina babu zuciya a kirjinta bata Tunanin makomanta, bata Tunanin Abinda kayi shi za'a maka! Ta mance cewa alkhairi fa Danko ne... Ta wulakanta ku ta tozarta ku daga ita har ɗan ta da be san darajar mace ba bare matar aurenshi, sun ɗauka a cikin masu arziki su sun gama hayewa basu san cewa a sadda 'Suka ga ZABUWA.. Da zanen ta suka ganta ba' Allah ubangiji yaji ƙan Usman ya gafarta mishi, shi kuma Yusuf se ya girbi abunda ya shuka don baze taɓa sha da kisan kai ba, lallai ne wadda ya kashe a kasheshi.. Ita kuma Amina Duniya ce tafi bagaruwa iya jima... Raed Na gode na gode maka kwarai da gaske a sadda ka tallafi rayuwar hidayat ka juya mata shi daga baƙi zuwa fari ba tare da ka san ita er uwarka ba ce kayi hakan da zuciya ɗaya Allah ya baka aljanna sanadiyar hakan bani da abunda zan saka maka dashi" Shiru yayi yana jin ɗaci a makogoronshi duk sanadiyar balaraba ne ko kallonta baya son yi har gaban Abada, a hankali ya cigaba "Ku kuma gamji da Laure Allah ya saka muku da alkhairi, na gode kwarai da irin sadaukarwar da kuka yiwa mata ta, halayyar ku da ta Raed ya nuna cewa lallai na Allah basa ƙarewa a duniya ko da an samu mugaye dubu irin Amina da Balaraba, ko duka dukiyan da na tara zan baku bazan saka muku ba sakamakon ku na wurin ubangiji sede bata ɓaci ba, in kun zaɓi zama damu na muku alkawarin farin ciki da wadata har karshen rayuwarku da izinin Allah, in kun zaɓi komawa na muku alkawarin ko wani dabba da kuke kiwo garke biyar biyar, kuna da kujerun Makka! Gida da kuma Motoci ina so a cikin jama'ar Garinku in za'a lissafa masu kuɗi Gamji ka shigo ciki da yardar Allah..... Hamza ka yi haƙuri ka gafarceni, ka sani bawa baya taɓa wuce kaddararsa hakanan abunda Allah ya rubuta wani be isa ya sauya shi ba se ya faru, kwarai Allah me yin yadda ya so ne a sadda ya so, ya fito da kyakkyawa daga cikin mummuna tunda na farfado ake min murnar samun ɗa irin ka me cikakken nagarta da kamala Dukda ga yadda mahaifiyarka take, ka ga kenan Allah babu ruwanshi da wacece mahaifiyarka so bana so ka sanya damuwa a ranka, bana so ka kasance cikin masu aibata ko saɓawa mahaifiyarka karka ce mata komai kuma karka yi fushi da ita ka kula da ita sbd ta kula da kai a sadda baka iya kula da kanka, sede ni ba zan iya cigaba da zama da ita ba na saketa saki biyu.... Zaka iya kaita duk wani wurin magani da kuɗina hakan be dameni ba, Allah ya riga ya nuna mata iyakar ta tunda ya Haɗa ka da wacce bata so gani ba a duniya, ya kuma ɗauke lafiya ta a sadda take farin cikin samuna wa kanta ita kaɗai, daidai lokacin da ya bani lafiyan kuma ya dawo da Aisha rayuwata ita kuma ya fitar da ita cikin hikimarsa da buwayarsa, kaga wannan babban darasi ne Allah ya sa muyi anfani da Ayar dake cikin wannan rayuwa tamu gabaɗaya" Da Ameen suka amsa, ya kalli hidayat yace "princess Allah ya miki albarka, Allah yasa iya wahalar kenan lallai kin kasance cikin masu hakuri da juriya, Allah yasa kin tsallake taki kaddarar rayuwar kenan farin ciki ya dawwama a rayuwarki har gaban Abada" Da Ameen suka sake amsawa, Aisha ta kalli hamza da gabaɗaya kamanninshi sun sauya sbd tashin hankalin da be taɓa Tunanin riskan kanshi ciki ba, kunya da nauyin mutanen parlorn duk ya rufeshi, kwarai maganan Mahaifinshi ya shige shi hajiya yanzu bata da wani gata se nashi, tunda har ta haifeshi shi kuma ita ce jarabawar shi... "Hamza! Bana so ka hukunta kanka da abunda ba kai ka aikata ba, ka daukeni a matsayin mahaifiya kaman yadda nima zan zame maka gurbin hajiyarka, don Allah ka fawallawa Allah lamuranka shi kuma ze jiɓancesu ya wanke maka zuciyarka kaji? I will be always and forever be there for u!" Sheshekar kuka ya fara ya kasa ɗaga idanu yana ji hajiyar shi na dariya wadda ze tabbatar maka da kanta fa ya kunce, ji waenda hajiyarshi ta zalunta masu kyaun zuciya da dabi'u, me yasa mahaifiyarshi bata fita kaman na Hidayat ba! Gabaɗaya tsoron rayuwa ya kama shi, kowa seda ya bashi baki a parlorn har hidayat hakan ya taimaka sossai wurin hana shi collapsing don dama ji yake kaman baze kara awa a wannan duniya ba. Aisha ta sake kallon Raed tace "Son! Kai kuma Allah ya saka maka da alkhairansa..." Murmushi me kyau yayi yace "ya riga ya saka min ma MAAMI tunda ya bani autar mata..." Yadda yayi maganan yana kallon hidayat duk parlorn seda suka murmusa ita kuma tayi saurin sadda kanta ƙasa tana masifa chan ƙasa 'kaiii rayuwar Turai ma bata yi ba, ji ko a jikinshi' amma sunan da ya kira mahaifiyarta yayi mata sossai itama hakan zata ke kiranta. "Lallai kam Naga alama, ya jikin yaya Buba mama?" Daadida tace "da sauƙi Dukda dai kam yana fama" Tace "Allah ya bashi lafiya" Hidayat tace "Maami!" Se Aisha ta kalleta tayi murmushi, hidayat ta cigaba "Don Allah Maami ki yafewa Baba Buba na san be kyauta ba, da a sadda Kika koma garesu da mugun ranunin hajiya da ya karɓe ki da ban yi irin rayuwar da nayi ba, da kuma kema baki sha wahalar da kika sha ba sede ɗan Adam ajizi ne kuma kinga ta sanadinshi Allah ya tsaga min farin ciki na, ya bani Norah da Farrah..." Maman Rashida tace "A'a daughter faɗi gaskiya dae, ya baki baban su Norah da Farrah kike son cewa kaman.." Duk dariya suka yi ita dae kunya ya kusa kashe ta, wani irin murmushi Raed yayi yana kallon kunyar ta dake matukar burge shi, Maami tayi murmushi tace "Hidayat dukkaninmu muna kuskure, dukkanninmu tara muke bamu cika goma ba babu wadda yafi karfin duk waennan abubuwan da suka faru ya faru dashi, wallahi ko don saboda kyaun zuciyar Raed na yafewa Yaya Buba, har Hajiya Balaraba na yafe mata saboda Hamza, Sauran abunda ta shuka wannan tsakanin ta da mahaliccinta ne, amma ba zan taɓa iya yafewa Amina cutar min dake da tayi ba don Allah Alhj a yau nake so a shigar da ƙarar Usman bisa Assault da kuma kisan kai da yayi.... Abinda ya miki ko a hikaya ban taɓa ji ba kuma kwarai yayi min mugun rauni a zuciyata basu chanchanci yafiya ba, don baka da gata se aka ce a wulakantaka a tozarta ka yadda aka ga dama?" A nan kam bacin ranta ya fita, don abun yayi mata ciwo sossai da sossai.. Yau ko ɗiyar kishiya hidayat take iyaka kenan bare babu hadi ko na sisin kobo, ta kara da "Na san Zaku yi tunanin me yasa basu ci darajar Abban su ba, Abban su mutumin kirki ne kwarai halinshi na gari ya bishi, shi sakayyarshi gudana nake so yayi har cikin kabarinshi so nake ya isar mishi har ya mishi sanadiyar shiga aljanna madaukakiya in har ina da rai da numfashi" Duk gyaɗa kai suka yi, kiran sallar magrib ne ya ɗaga su suka fice, ana dawowa kuma aka fara shigo da abinciccika da Mahaifin Rashida ya bada order a kawo, bayan an ci an sha ya karkace ya fiddo dubu ɗari biyar ya ajiye yana kallon Maami yace "Ga sadakinki again, yanzu da aka yi sallar magrib Alhj Usman ya sake biya aka maida aurenku" Duk murmushi suke yi ita kam ta kasa ɗagowa sbd kunya Dukda Daadida na ɗaki, Hidayat ce ta ɗauko tana Adu'ar alkhairi zuciyarta fal farin ciki. Se bayan isha Daadida ta fito da shirin tafiya, maman Rashida ta mata bayanin maida auren kuma tayi farin ciki ta zauna da Aisha sun sake tattaunawa inda tayi mata nasiha, Seda ta gama kan tace "Mama hidayat fa? A yadda nake ganin Raed Please ku bashi matarshi hakanan mana? Babu anfanin cigaba da zaman" Daadida tace "nima na ga dacewar hakan, na so a kaita ne kaman yadda ake yiwa kowacce mace ƴar gata, gyaranta kuma be kamallu ba ke na ma fa ga kokarin wannan me dabi'un turawan da be shafawa idanunshi toka ya ɗauke ta ba, da sede in shafa in ji wayam" Dariya Maami tayi tace "Ai Raed baze taɓa wulakanta hidayat ba tunda har ya ɗauke ta da mutunci tun be san alakar dake tsakaninsu me karfi bane, na tabbatar duk abunda ya mallaka nata ne, zuciyarshi bashi da maraba da na Mairamu Allah ya ji kanta ya gafarta mata" Daadida ta amsa da "Ameen ya rabbi" Maami ta cigaba da "sannan gyara tunda an yi me yawan ko daga baya a hankali za'a karasa sauran please ku tafi da ita daga asibiti da Zaku duba Baba Buba se ya ajiye ki gida su wuce" Mikewa Daadida tayi tana murmushi tace "wannan fa son kai kike nunawa karara! Yaron ki kawai kika sani" Dariya Maami tayi kan ta mike suka fito, tuni hamza ya ɗauki Hajiya sun fice tana ta maganganu, hidayat da Rashida suka samu a dining suna ta kuskus Daadida tace "to in gulmata ake ma gani na fito se a ɗaga murya" Dariya suka yi Rashida tace "Daadida muyi gulmarki akan wani dalili? Ke da ba kwace mana samari da miji zaki iya ba?" Itama dariya tayi harda tafi tace "sa wasa kina zaune sede kiji nayi wufff da saurayin karki ganni haka a yarantata seda na kasa samari na zaɓa na darje!" Duk dariya suka yi, Raed na shigowa wurin dining ɗin ya bar su Abba a parlor yace "what's funny?" Hidayat tace "Don Allah paapi a baka zaɓi ni ko Daadida?" Kallon Daadida yayi se ta gyara tsayuwa tana wani gyagyarawa wadda ya saka su kwashewa da dariya har Raed ɗin kan ya ɓata fuska yace "Haba baby gurl har se kin tambaya? ga ki fresh blood me zan yi da Daadida?" Wani dariyar suka sake saki, Daadida ta haɗe rai tace "Dankari! Ni zaka rainawa wayau? Dama yau nayi niyyar baka matarka ku wuce to na fasa.." Zaro idanu yayi yayi saurin zuwa ya rungumeta yana cewa "oh my! Am so sorry my love ai daga ke ba ƙari, ke kaɗai ce da gaske a birnin zuciyar Raed" Dariya sossai Maami ke yi su hidayat na taya ta ganin yadda Daadida ke ture shi irin ita tayi fushin nan. Daga karshe kuwa haka aka yi Maami ta tattare yaran har junior tace babu me tafiya dasu, shi kam Raed daaɗi yaji daga Daadida se Hidayat suka wuce. Rashida da iyayenta ma suka wuce, part musamman Abba ya warewa su Laure komai akwai yace su huta sossai, sashensu daga su se su Norah. Asibiti suka fara zuwa suka duba Baba Buba gashinan dae jikin jiya e yau duk tausayin yadda bakinshi ya zama a bushe ya rufe su, gashi kaunarshi ne ze sa su taya likitoci tsare dokar su don a samu ayi aikin ya samu lafiya daga nan suka wuce gidan Daadida ya sauke ta kan suka fice.. Suna fitowa ya miƙa hannunshi ya sanya ya riko nata tare da matsewa yana sauke ajiyar zuciya, itama ajiyar zuciyar ta saki tare da Kallonshi suka sakarwa juna murmushi, a hankali ta maida idanunta kan hanyar tana kallon daidai inda ya taimake su, anan ta fara sanin shine ya taimake ta a rayuwa, anan ya fara illatar mata da zuciya da ƙaunar shi ba tare da ta sani ba, kirkinshi da irin rawar da ya taka a rayuwarsu ya sa zuciyarta bashi wani matsayin na musamman a ganin farko, suna isa gidan ta lumshe idanunta tana ayyana this is where it all started, gashi ta sake dawowa gidan as matar gidan mammallakiyarta... LALLAI ALLAH ME GIRMA NE! #Vote #share #comment                   🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 43* *FREE BOOK* A hankali ya shigar da motan parking space suka fito, hannunshi ya sake mayarwa cikin nata suka nufi enterence ɗin gidan, pin ya fara sakawa kan yayi wasu danne danne sannan ya ɗaga hannunta dake cikin nashi yasa se kofan yayi magana yace "welcome home Mrs Muhammad Raed" Murmushi tayi tana saka ɗaya hannunta ta rufe bakinta cikin mamaki, yana murmushi ya tura kofan yana faɗa mata password ɗin watakil wataran finger print ɗinta be buɗe ba which is hardly, tace "ur date of birth?" Gira ya ɗaga mata yana murmushi, a tare suka hau staircase ɗin ɗaki na biyu from right ya tura suka shiga a tare, ɗakin ya tsaru iya tsaruwa komai na ciki light ash and gold ne sossai furnitures ɗin suka burgeta, curtains ɗin are white very tick and beautiful yace yana kallonta "Is the room ok for you?" Kai ta gyaɗa in excitement tace "yayi kyau sossai" Yace "kina bukatar wani abu? Like ko abinci or something?" Girgiza kai tayi tace "am OK" Dariya take bashi yadda take ɗari ɗari hakan yasa yace "ok freshen up akwai duk abunda zaki bukata a closet.." Kallonshi tayi da alamun yaushe kayan ta ya zo nan? Gira ya dage mata alamun say ur mind, se ta sake maida kanta ƙasa tana murmushi fita yayi bayan ya ɗan yi hugging nata ya bata peck a goshi. Da kallo ta bishi har ya fice kan ta saki murmushi ta karasa bayin, kayan ta ta cire tana kallon ƙawatuwar bayin da komai na ciki neat and clean, towel ta ɗaura ta isa wurin kayan wankan wasu body wash dake jere a wurin masu kyau da kamshi tayi amfani dasu wurin yin wankan tana jinjina irin kyaunsu don kamshin kaɗai ya isa faɗa maka tsadarshi har wani tsantsi jikinta ke yi a sadda ta fito, a gaban dressing mirror ta zauna tana kallon abubuwan kai waenda ita kam bata taɓa gani ba, designers turaruka ne masu tsananin kamshi, mayukan hannu, kafa, jiki, kai, fuska, jiki da komai na anfani an ajiye a wurin. Man da taga an rubuta body lotion wadda na kamfanin oriflame ne ta buɗe ta fara shafawa tana jinjina kamshinshi da yadda yake bin jikinta, bayan ta gama ta shafa roll on ta feshe jikinta da turaren faux semblant Givenchy da ta gani a wurin kamshin seda ya saka ta lumshe idanu, har zata wuce taga wani turaren wadda kwalban yayi mata kyau ta ɗauko tana duba sunan Poison girl Dior, a wuyan ta ta ɗan fesa gefe da gefe shima kam kamshinshi wane wane wurin daaɗi. Murmushi ta saki tana matukar son turaruka and waenda ta gani anan ko waye ya mishi recommending ɗinsu sun yi mata Hundred percent, bata iya ta wuce closet da take son zuwa ba ta fara duba sauran turarukan seda ta shafa kusan biyar wai tana jin kamshinsu fuskanta cike da fara'a, komawa tayi ta zauna tana karanta sunayensu ɗaya bayan ɗaya. A hankali ya turo kofan ya shigo idanunshi basu mishi masauki a ko ina ba se kyakyawar surar jikinta dake ɗaure da towel kaɗai, wadda da kaɗan ya wuce mazaunanta,gashinta da ba kitso a zube a kafaɗunta baƙi siɗik a gyare, a natse yake tahowa yayi tsai a bayanta hannunshi cikin pajamas trouser ɗinsa na Gucci masu tsananin taushi, Rigan yayi fitting ɗinshi Dukda inda biyu kawai ya saka, gabaɗaya ta fidda qirarsa na cikakken namiji. Murmushi ya ɗan saka sadda ta lumshe idanu ta sake zuƙar kamshin wani oil da ta ɗan goga bisa bayan tattausan hannunta, ji yake kaman ya ɗauke ta ya haɗiye ta, wani irin zazzafar so ne nata yake shigansa zuwa kowanni sashe na jikinsa, se ya cigaba da takawa sannu sannu har zuwa bayanta ya tsaya sannan ya miƙa hannunsa ta gefen kafaɗanta ya rankwafa faffaɗar kirjinsa yana gogar bayanta,ya sanya tafin hannunsa ta wurin cikinta ya kama hannun da take shinshinawan ya kai ya shaki kamshin turaren, iska ya zuƙa tare da lumshe idansa ya buɗe. Cak ta daskare a wurin wani irin mahaukacin kunya na lallaɓowa ya rufe ta, Sam ko shigowar shi bata ji ba da bata barshi ya ganta a haka ba, idanunsa ya kai ya kalli towel ɗin nata da ya ɗan sauƙa daga sama ya bayyana saman Fararen kirjinta se ya shanyesu ya ɗago idanun bisa fuskanta waenda har sun fara lumshewa, take idanunsu suka sarqe waje ɗaya,fuskokinsu gab da juna,numfashin su ya fara gauraya wuri guda, kusan lokaci guda kuma a tare suka lumshe idanunsu suka buɗe, be iya cewa komai ba sai ya sanya hannunsa ya zame kwalbar turare dake bisa ɗaya hannunta ya ajiye bisa kan dressing mirror chan baya. Sannan ya saka hannuwansa biyu ya ɗaga ta Cak ya ture chair ɗin dressing mirror ya ɗaura ta akan asalin dressing mirror ɗin, ya janyo kujeran again dab ita ya zauna bisa kai hannayenshi ya sa a kwankwasonta ya kuma matso da ita kaman ze shige cikinta, kafafunta ya kwashe gabaɗaya ya ɗaura bisa cinyoyinsa. Daga santala santalan cinyoyinta dake bayyane suna tsole mishi idanu yabi da kallo har zuwa yatsunta, farare sol dasu babu ɗigon komai akai.. Hannu ya sa ya ɗan yi mata tafiyar tsutsa bisa kafafu da sauri ta saki dariya tana kokarin janye kafan tace "ka bari pls..!" Idanunshi da suka sauya gabaɗaya a idanunta ya sakar mata yace "da kin faɗa min u were so tired to be this lazy ai da na tsaya nayi miki wankan na shirya ki, it's almost 12 and baki shirya ba!" Murmushi tayi tana dukar da kai tace "I wasn't that tired, perfumes ɗin nan su suka ɗauke hankali na" Yace "do you love them?" Kai ta gyaɗa murmushi jin daaɗin su na bayyana a fuskanta tace "they are superb" Hannunta ya kama ya sake shinshina yana lumshe idanu yace cikin wata kalar murya "I also love 'em gashi sun tafi da imanin hubs ɗinki.." Be jira Cewar ta ba a ɗan zafafe ya fusgo ta ta faɗo bisa jikinsa tayi masauki a cinyoyinsa, gabaɗaya kirjinta ya haɗu da faffaɗar kirjinsa, jikinsa ya haɗu da nata, lallausar fatarta ta sake bada gudummawa wurin fara saka shi birkice mata, hancinshi ya cusa a wuyan ta yana shakar kamshin ta, nannauyan numfashi da ya fito daga makogoronshi ya saki, hucinsu suka saka gabaɗaya tsikar jikinta tashi yammmm. Hannayenshi ya saka yana mata tafiyar tsutsa bisa damatsanta a hankali ya fara bata wasu neck line kisses da suka so zautar da ita, sbd yadda jikinta yayi wani amsawa yasa bata san sadda ta rike damatsanshi gamgam ba, da kisses ɗin da yake sakar mata a wuya a hankali ya karkata kanta, idanunta da suke bayyana tsoro da firgicinta wadda ze tabbatar maka da cewa she have never been in this kind of hot romance ta kara zarowa jin yadda yake sake numfashi akai akai,da sauri ta buɗe baki zata yi magana yayi hanzarin shutting nata down da wani hot mouth to mouth, Sam bata iya ba, ga firgici da ya sa ta kasa taɓuka komai but he's such a bad kisser nan da nan yasa ta fara mancewa da duk wasu problems ɗinta da ma kowa da komai, jikinta ne ya fara mutuwa liqis, wasu zafafan electric sparks ke bin jikinta a sadda hannayenshi suka sauka bisa kai. Tamkar wadda aka ƙadawa gangi haka ya fara tsuma,cikin zafi zafi ya fara aika mata da wasu saqonni masu nauyi waenda suka nauyaya bisa qirji da zuciyarta, tunda take bata taɓa tsintar kanta cikin duniyar da ya jefa ta ba, saqonninsa  sun rikita mata kwakwalwa sun kuma kashe mata gangar jiki gabaɗaya, da ta rasa abun yi kawai se ta sakar masa kuka, Sam baya son abunda ze kawo mishi cikas, se ya haɗe bakunansu yana me tashi da ita a cikin jikinsa zuwa kan gado. Duk yadda ya ruɗe ya kuma ruɗata da kuma yadda jikinsa ke matukar rawa hakan be sa ya kasa binta cikin laluma da salama ba, a sanyin zafi da kuma tausayawa yake binta seda ya tabbatar zata iya dashi kan ya fara karanta Adu'ar da musamman ya koya don baya son abunda ze kawo musu wani cikas a zaman su, yana yin Adu'ar tana kubcewa sbd yadda murayarsa gabaɗaya ke breaking, hawaye masu zafi ke fitar mishi a sadda yake jefa su cikin wata duniya me nisan gaske wadda duk su biyun babu wadda ya taɓa tsammanin akwai ta... Tana kwance bisa faffaɗar kirjinsa bayan kusan shudewar awanni biyu, har lokacin babu wadda ya iya furta wani kalma a cikinsu sede bugun zuciyoyinsu da kuma irin kusancin jikinsu ya isa faɗa maka waennan ɗin masoya ne da suka bugu da mayen giyar zazzafar ƙaunar juna. Motsi tayi wadda ya saka shi sake rukunkumeta yana furta "am sorry" da husky voice ɗinshi da har yanzu be iya dawowa daidai ba, taji wannan kalma har ta gaji daji daga gareshi tun bayan da ya samu kansa daga birkicewar da yayi mata. Ita ba budurwa bace amma tayi karya idan ta ce bata ji jiki a wannan gamon nasu ba, sede kam ya bata abunda har ta mutu bazata manta ba, daga yinin ranan har darensa wani irin tarihi ya bar mata da baze mantu a gareta ba. A hankali ya sanya hannu ya kunna wutar ɗakin jin tana son tashi, se tayi saurin komawa cikin jikinshi tana kara rufuwa da bargon tare da binne kanta a cikin kirjinsa, dariya me sauti ya ja yana ɗan sulmiyowa ya haɗe fuskokinsu cikin muryarshin nan yace "I cannot breathe when you are not near. I love you, die hard!" Yaye bargon yayi ya ɗaga ta chadak tana me sarqafe hannayenta bisa wuyan shi suka yi toilet, cikin tsantsar kulawa da soyayya me tsafta ya tsaftace ta da kansa kan yayi nashi suka fito a tare daure da towels, a kujerar dressing mirror ya ajiye ta yana murmushin tuna this is where it started, da kanshi ya shafa mata mai bata iya bude idanu ba seda taga yana kokarin sake haukacewa a kan jikinta kan ta wara idanu tana rike hannayensa, murmushi kawai ya saki yaje closet ya ɗauko wasu en iskan nighties ya saka mata. Saura kaɗan ta nitse don kunya, shi de se murmushi yake yi, wandon pajamas ɗinsa kawai ya mayar ya gyara gadon ya ɗago ta Chak suka koma, rungume a jikinshi yana fitar mata da duk wasu sirrika na kirjinsa wadda kusan duk ta ji su a sambatun da yayi ta saki mata wadda be san ma yayi ba, murmushi kawai take saki ko da ze maimaita mata  sau hamsin a kowanni rana bazata gaji da jin su ba in dae har daga bakinsa ze na fitowa. Wani irin kula ya bata har bacci ya sureta, ya jima yana aikin kallon baby face ɗinta kan ya sake rungume kayanshi shima bacci ya ɗaukeshi a haka, kwarai da ana tsaga kirjin mutum a ga iya adadin kauna, da bazata taɓa iya ganin karshen ƙaunan da yake mata ba. Da safe ita ta fara farkawa tana mamakin irin makarar da suka yi, so tayi ta tashi da sauri sede tana karo da kyakyawar fuskarsa ya so mantar da ita Komai, da idanu ta dinga bin lungu da saƙo na fuskan nashi tana yaba hallitar Allah, dole mata su ke mutuwa a kansa, sanyin kyaunsa na dabanne... A hankali ta sanya tafin hannunta bisa kumatunsa tana tuna irin duniyar da ya jefa ta a jiya se ta saki murmushi a hankali in a whisper tace "I love you paapi" Idanunsa dake cike da bacci ya buɗe ya sake lumshewa kan muryarsa me taushi ta furta "I love you more baby gurl!" Da sauri ta mike tana murmushi ta dira a kan gadon tayi toilet, da kallo ya bita har ta shige tana sake kunna shi da kayan baccin nan nata, kauda tunanin yayi ganin da gaske rana ya fito shima ya mike ya fice zuwa ɗakin shi, a chan yayi alwala yayi sallah yana me miƙa dumbin godiyarsa ga mahallicci da ya mallaka masa mace irin hidayat. Itama a nata bangaren godiya me tarin yawa take Mikawa Mahaliccinta da ya bata Raed a matsayin miji, tana mikewa beddings ta fara chanzawa sbd yadda wanchan ya chukwuikuye baze gyaru ya kwanta ba, a washing machine ta sanya ta dawo ta ɗan kikkimtsa ɗakin, dama tayi wanka kan tayi alwala se ta sanya doguwar riga bubu da hijab tayi sallah, hijab ɗin ta mayar ta fito sbd sanin cewa namiji ne cook ɗinsa, ga mamakin ta babu kowa a ƙasan. Kitchen ta shiga yana nan neat ba kowa, sauri sauri ta fara Haɗa masa breakfast liver sauce ne da dafaffen Irish tana cikin kwashewa a warmers taji an sanya hannu an rungumeta ta baya, dukkansu suka sauke numfashi a tare.... #Vote #share #comment                 🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 44* *FREE BOOK* "Good morning..!" Yayi whispering yana zare mata hijab ɗin na jikinta, murmushi ta saki me taushi tace "Good morning, hope an tashi lafiya?" Ƙara shigar da ita jikinshi yayi yace "in akwai abunda yafi lafiya ma yau na tashi dashi baby gurl, sannu da aiki" Ba tare da ta kalleshi ba tace "sannu! Ammm se Naga kaman akwai namiji dake shigowa nan ko? Shiyasa na saka hijab" Yace "Nah! Daga nan har Paris babu namijin dake da hurumin shiga min parlor bare kitchen baby gurl, that was before" Bata sake cewa komai ba ta ajiye kular da ta gama kwashe dafaffen Irish ɗin, se ta tsaya cikin kunyar ce mishi ya saketa ta gama Haɗa breakfast ɗin, Sam duka wannan bambarakwai take jin su wai namiji da suna Hajara, leƙa fuskanta yake yi daga wuyan ta yace "wait! Baby gurl are you avoiding my eyes?" Ya karashe da sautin smile, bata ce komai ba Yace "please don't! Kin fa riga kin zama rakumi ni kuma akalarki duk inda zaki je yanzu a tare dani zaki, so feel free around me we are already one and I love you ok?" Duk yadda ta so sunnewa haka ta hakura kaman yadda ya faɗa kuwa duk inda tayi tare suke yi, breakfast ɗin ma kusan plate ɗaya suka yi da tea cup guda, bayan sun gama suka sake kwanciya bacci ba su suka farka ba se wuraren azahar. Kitchen ta sake shiga bayan tayi wanka tayi sallah tayi pasta half wadda yaji vegetables, bata sa a kula ba sbd shima ya sauko yana tare da ita so a plate suka juye shi ya wuce dashi cikin parlor yayinda ita ta ɗibi drinks da cup, a tsakar parlorn suka zauna suka ci abincin cikin nishadi, bata taɓa Tunanin haka aure yake ba. Bayan sun gama yace su je su shirya su tafi asibiti, cikin doguwar rigar Abaya ta fito maroon wadda yayi mugun amsar ta, ta rufe kanta da gyalen, wayanta kawai ta ɗauka ta fito a parlor ta same shi suka fita a tare hannunshi cikin nata. Ko a motan ma hiran su suke yi na masoya fuskokinsu cike da nishadi wadda ze tabbatar maka hankalinsu a mugun kwance yake, a haka suka shiga asibitin riƙe da hannun juna, kunya ne ya rufe ta a sadda suka tarar da iyayenta a ɗakin da duka yaran tare da Daadida. Daadida ta kasa shiru tace "Aaa lallai se yanzu ake ganinku?" Basu amsa ba se murmushi, ya gaida Abba, sannan Maami duk cikin jin daaɗin ganin da suka musu suka amsa, suma daga ka gansu ka san ma'aurata ne masu cikakken natsuwa da kwanciyar hankali, ita dae hidayat na ta fama da Junior dake tambayar ta ina taje ta barshi. Baba Buba kallon su kawai yake yana hawaye tare da murmushin karfin hali, rayuwa fa kenan, lallai mahakurci mawadaci dubi yadda duk suke cike da walwala shi kuma gashi kwance yana girban abinda ya shuka. Duk waje suka fita inda suka shimfiɗa carpet aka zazzauna ana hirarraki kaman dae yadda kuka san asibiti, anan ne ma Daadida ta kawo maganan ko za'a ɗauko matanshi duk babu me kira cikinsu yaji halin da yake ciki, a lokacin da yake bukatar su a sannan suka yi watsi dashi, su da baya so a sadda yake da mamora sune ke taimakon shi a yanzu. Abba yace a kyale su da sun damu ai da sun zo, shi dae Raed ya fita wani taro da aka gayyace shi, planning tafiya Saudia da baba Buba kawai yake, ko ba komai in ya ɗan samu karfi su shiga yayi aikin hajj don ya ragewa kanshi zunubi. Tunda hamza ya bar gidan ɗauke da hajiyarshi kai tsaye gidan mahaifinta ya nufa, a hanya ya kikkira yayyunta da en uwa na kusa akan su haɗu a gida akwai matsala, bayan an zazzauna a ɗakin taro aka buɗe da Adu'a hamza be ɓoye musu komai ba cikin duk abubuwan da suka faru sbd labarinta izina ne ga en baya masu irin halin ta, ina mijin? Ina dukiyar? Ina lafiyan? Duk ta salwantar da hannunta ba na wani ba. Daga karshe ya rufe da "ba na baku labarin bane saboda in tona mata asiri, na faɗa muku ne saboda ya zama dole ku sani kar ku ga kaman Abbana butulci yayi nata a sadda shi ya samu lafiya, zan gyara mata ɗakin inna (mahaifiyarta) zan samu me kula da ita su zauna tare, ku yi mata fatan samun lafiya da fatan shiriya saboda babu wadda ya fi karfin wannan jarrabawar" Kwarai sun jinjinawa karfin zuciyar hamza, yayi kokari sossai wurin ganin ya hana kanshi tsanar mahaifiyar shi, dukda ya san ta riga ta ɓata mai rayuwa da na zuri'a, kaman yadda ya roka Dukda yadda hajiya balaraba take da nuna isa da son a san ita fa wata ce, haka dae a gaban hamza suka yi mata Adu'ar shiriya da samun lafiya sede babu wadda ya kara da ko Naira biyar bayan nan. Ɗakin mahaifiyarta da single room ne sbd gidan ba masu karfi bane sede rufin asiri ya shigar da ita, be san a yau ɗin wa ze kwana da ita ba haka ya zauna ya zabga tagumi yana kallonta, daga karshe kuka sossai yayi a haka suka kwana ɗakin ko ta fara bacci zata tashi a firgice tayi ta ihu cikin dare. Haka ze tashi shima ko yayi mata karatun Qur'ani ko yayi mata Adu'a, da asuba kaninta dake gidan ko gaisuwar hamzan be amsa ba sbd kaman yadda basu yi bacci ba haka shima da iyalan shi dake gidan. Se rufe ta a ɗaki yayi da safe ya fita, a sannan suka yi waya da Maami da wayan Abba take tambayarshi ko ze shigo ya karya? Yace ba ze samu shigowa ba ze yi a wurin zainab. Hakan kuwa aka yi gidansu yaje ba laifi zainab ta tausaya mishi tunda taji labarin wurin mahaifinta, ita ta bashi breakfast kuma ganinsu ya sa ya ɗan samu karfin gwiwa, ta mishi alkawarin neman me aikin da zata iya kula da hajiyar. Daga nan wanka yaje yayi ya ɗan runtsa, kan azahar ya tashi ya sayi abinci a restaurant ya koma gidan se ya samu ma zainab taje da girki ta taimakawa hajiyan tayi wanka ta bata abincin tana ci, sossai yaji daaɗi a ranshi wani damuwan ya sake raguwa, a nan suka zauna har me aikin da ta kira ta zo, taimakon Allah hajiyan bata duka sede ihu da firgici se surutai marasa kan gado. ** "Isa ka gane kwatancen kuwa?" Yace "ai Alhj sede idan ba cikin birnin Kano yake ba, na gane tsab yanzu zamu isa" Kai kawai Abba ya gyaɗa kan ya maida hankalinshi kan maganan da suke da Maami a bayan motan, Farrah ce zaune daga gaba. Daga motan isa se na Daadida ita da Norah ne da Aisha se driver ɗinta, daga karshe kuma Raed ne da kanshi yake driving zaune daga gefenshi hidayat ce, daga baya junior. Kallonta yayi yadda tayi shiru ta kurawa hanya idanu, hannunta dake kan cinyarta ya sa hannu ya riƙe tare da matsewa, ta kalleshi ta ɗan yi murmushi yace "please die hard ki daina sawa kanki damuwa akan waennan mutane da basu cancanci damuwarki ba, promise me bazaki yi kuka don tuna wani abu da suka miki a baya ba, yanzu rayuwarki is a better life abunda ko a mafarkinsu basu taɓa hange ba" Idanunta da suka sauya ta mayar ƙasa tace "paapi sun yi min illa a rayuwa, sun yi min sanadin mutane biyu masu muhimmanci a rayuwata! Komai aka yi musu ko menene hukuncin su bana ji zan ji sassauci a raina idan har na tuna, sede Alhamdulillah idan na kalli irin rayuwar da Allah ya sauya min se in jinjinawa karfin hukuncin ubangiji dake fitar da rayayye cikin matacce ya kuma fitar da matacce cikin rayayye.." Kiran wayanta ya hana shi magana ta ɗaga tana tambayar ta iso daidai wurin? Ummi ta amsa da eh, basu kara tafiyar mintuna uku ba suka hangeta suka tsaya suka ɗauke ta. A mutunce suka gaisa da Raed, kan suka gaisa da Hidayat.. Aiko ummi tace "Hidayat saura mu je ki zubar da hawaye a idanun waennan kaskantattun mutanen har su ga damarki ni da ke ne..!" Murmushi kawai Raed yayi yana kallon hidayat da ta juya take harararta, Daga yanayin kalar unguwar da suka fara shigowa ummi da Hidayat suka buɗe baki suna kallon ikon Allah, wai anan umma da su Yusuf ke rayuwa? Tunaninsu be gama kuncewa ba seda suka yi parking aka ce mota ba ze yi gaba ba sede a shiga a fiddo su. Raed fuskanshi kawai ka gani se ka yi dariya, be taɓa shiga irin wurin a duniyan nan ba, kudaje da kwatami sune flowers da furannin unguwan. Babu wadda ya fita a mota saboda Abba ma hana Maami fitowa yayi, se Soldiers guda biyu da polisawa guda uku cikin mota biyu da Mahaifin Rashida ya turo ne suka kutsa kai cikin unguwan a take mutane suka yi cirko cirko ana kallon su kaman ba'a kwaryar Kano suke ba, har da masu leke ta gini, ba'a yi minti talatin ba se ga umma, Surayya, Kausar, fahariyya da Yusuf an tuso keyarsu zuwa waje. Da kallo tsuru tsuru kaman an tare ɓera a lungu suke bin zuƙa zuƙan Motocin da ko da suke da kuɗin ma basu ga irin ta ba bare yanzu, duk akan gwiwowinsu aka saka su zubewa, hidayat tana ta Kallonsu ɗaya bayan ɗaya a zuciyarta tana jinjina ikon ubangiji, a kan Yusuf ta tsaida idanunta zuwa hannunshi da gabaɗaya ya sauya halitta kaman ma ya ruɓa don wani baƙi da yayi, yana zubar da wani farin ruwa, shi karan kanshi ya rame ya tsirance yayi baƙi kirin, kana ganinsu kaga masu cutar tsananin yunwa. Seda suka kwashe seconds a haka kan Raed y buɗe ya fito bayan ya saka facemask yana Kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kan ya sa hannu ya buɗewa hidayat kofa ya mika mata hannu ta sanya nata ya taimaka mata ta fito a hankali, duk idanu suka zuba musu kaman yadda sauran Jama'ar suke Kallonsu. A lokacin Abba da Maami ma sun fito, daadida ma ta fito amma yaran kam Raed duk ya hana su fita, ita Aisha tunda ta kalle su ta gane su sede bata yi ko motsi ba don bata kaunarsu kaman yadda basa kaunar ta da mommyn ta. "Hajiya don Allah kuyi hakuri wallahi bamu san laifin da muka aikata muku ba! Ku yafe mana wallahi bamu da abunda zamu iya baku bayan hakuri don ko abunda zamu sa a bakin salati ma gagararmu yake.. Ku tausaya mana bayin Allah!" Umma ke rokon hankali tashe, don sanin waennan ɗin ba kananun mutane bane daga motocin zuwa kalar suturunsu da kalar fatar jikinsu. Surayya da ta kurawa hidayat idanu ne tace "laaaaaaa wallahi hidayat ce umma! Hidayat ce fa! Hidayat...." Ta tashi da gudu zata yi kanta wani wawan kafa police ɗaya yayi mata se gata a ƙasa tana sakin ihu, Yusuf, umma, Kausar da Fahariyya a tare suka ce "HIDAYAT???" Tana aika musu da kallon da bata taɓa yi musu irin shi ba tace "Kwarai Hidayat ce ba kuskure idanunku ke gani ba Amina!" Duk zaro idanunsu suka yi, suna masu tsananin mamakin hidayat ɗin. Ummi da ta fito ne tayi dariya tace "Surayya ashe Zaku gane hidayat ɗin haka da sauri? Kun ɗauka da kuka koreta cikin wulakanci da kaskanci rayuwarta ya tagayyara ne? To Allah ba azzalumin bawansa ba! Hidayat ta samu rayuwa me kyau da nagarta gata nan ta dawo muku da mahaifiyarta da mahaifinta, kakarta da kuma mijinta wadda yake wa a gareta sakike!" Hidayat ta sake cewa "Amina kin ga uwata da ubana! Hidayat ba shegiya ba ce kaman yadda kuka raine ta da Kalmar shegantaka!" Maami Umma ta kurawa idanu muryanta na tsananin rawa tace "Aisha???" Maami tayi murmushi tace "kwarai baki yi kuskure ba ni ce dae Aisha da kika rabata da ƴarta a tsummar goyo saboda rashin imani da tausayi" Umma ta rarrafa ta riƙe kafafun Maami tace "Na tuba Aisha Don Allah ki gafarceni! Bani da hujjar kare kaina daga laifukana na sani na cancanci a kirani da kowanni suna... Na tuba ki yafe ni" Maami tace "zan iya yafe miki laifukan da kika min amma wadda kika aikatawa ƴata ba me yafuwa bane Amina! Me hidayat ta miki kika zalunce ta irin wannan mugun zaluncin?" Tana kuka sossai tace "Wallahi wallahi nayi nadama, son zuciya ne kawai da rashin sanin Allah! Don Allah ku gafarcemu yanzu ma abunda muka shuka muke girba, alhakkinku ne yake bibiyar rayuwarmu don Allah ku yafe mana!" Yusuf yana kuka ya fara magana "Hidayat ni kam bani da wani bakin da zan iya neman yafiyar ki don na san ban miki adalci a rayuwa ba, na zalunce ki ba tare da na san kaina na zalunta ba, hidayat ina Aisha da abunda kika haifa? Ina yarana....!" Wani mummunan kallo da bata taɓa sanin ta iya ba ta aika mishi, bazata iya Haɗa jikinta da nashi ba a yanzu haka bazata iya bari mijinta ya taɓa shi ba, da sauri ta kalli Sojan dake tsaye gefenta cikin harshen turanci ta bashi umarnin tana so ta ga jini a bakin Yusuf.... Wasu irin zafafan maruka da ya saka shi tumurmushewa cikin ƙasa ya sauke masa, a tare bakinshi ya fitar da jini a gigice a kuma ruɗe ya samu ya ɗago idanunshi da suka cika da ƙasa yake kallon ta, idanunta da suke rine take Kallonshi dasu tana kaɗa yatsa tace "Wannan shine ze yi ta zama hukuncinka a duk sadda ka sake alaƙanta min yara da kanka! Ko ka manta na maka gargadi kan tafiyata? Ka manta na yanke duk wani alaka dake tsakanin ku?" Kausar tace "amma ai kin san ko me kika yi jininshi ne ke yawo jikinsu so babu yadda kika iya don ba'a chanzawa tuw...." Kallon da tayiwa wannan Sojan ne ya saka shi sauke mata nata rabon da seda haƙorinta ɗaya ya fita. Raed hankalinshi duka yana kan hidayat da take neman birkicewa, Kallonsu kaɗai sosa mata abubuwa dayawa yake yi, tana Kallonsu ne kaman tana buɗe shafuka shafukan rayuwarta a idanunta da zuciyarta, aka ce me hakuri be iya fushi ba.... ****Menene ra'ayoyinku game da Yusuf da iyalan shi da kuma hidayat??? Shin kuna gani rayuwa kaɗai ya isa koyar dasu darasin abubuwan da suka aikata ko kuwa anan ma hidayat tayi anfani da zuciyar haƙurin ta wurin yafe musu ko barin su da halinsu??? Shin idan Kaine a kafafun hidayat wani irin abu zaka iya aiwatarwa a irin zuciyar ɗan Adam??? Sun chanchanci ƴanci kuwa? Karku manta Allah yace duk wadda be yi anfani da hukuncin da na saukar ba lallai shi ɗin kafiri ne.., fasiki ne.**** #Vote #share #comment                   🖤Gureenjo🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 45* *FREE BOOK* "Har yanzu da sauran ku a sanin rayuwa Kausar... Kai Yusuf har ka isa kayi claiming right akan yaran nan? Anya akwai zuciya a kirjinka? Ka manta yadda ka dinga dukana kana azabtar dani da yunwa duk don kawai saboda kar su zo duniya? Ka manta duk wannan? Ka manta yadda ka ɗaga Usman ka buga kanshi da pillar wadda ya zama ajalinshi? Kana Tunanin wannan rayuwa da kake ciki shine kaɗai alhakin ran Usman? Yusuf wallahi wallahi da za'a bani izinin kashe mutum kwara ɗaya rak a duniya babu wadda zan zaɓa in halaka se kai, ka sani baka ga komai ba... A da nayi niyyan in ɗau fansar Usman da hannuwa na sede a yanzu na fasa wannan kuduri, kar ka yi tunanin saboda Abba ne ko su Aisha a'a, don babu ruwan Allah da wani yaci albarkacin wani a ranan gobe, ranar da uwa zata guji ƴarta, ƴa ta guji uwarta dangi su guji dangin su.. Abunda duk ka aikata shi kaɗai kai kaɗai zaka girbe abunka.. Aisha!!" Ta kira Aisha dake cikin mota, saukowa yarinyar tayi ta tako ta zo kusa da Hidayat tace "mommy ga ni!" Inda Yusuf yake bata kalla ba, wasu irin hawaye masu ciwo ne ke fitar mishi, se a yanzu yake jin wani irin ƙaunar yaran da son su na shiganshi, kallon Aisha yake yana fata ko sau ɗaya ne ta kalleshi ta kira shi da suna 'Abba' abunda da a baya idan sun kira shi da hakan ji yake kaman sun jingina shi da mutuwa, Kallonshi hidayat tayi ta kalleta tace "Aisha ga Abbanki na magana..!" Aisha bata juya ba tace "Mommy ni shi ba Abba na bane, ga daddynmu nan..!" Ta Nuna Raed, rarrafowa Yusuf yayi yana shirin kai hannu Jikin Aishan don riƙeta wani irin ihu ta saki tana tsugunawa ta boye kanta cikin kafafunta "No! Please don't touch, karka taɓa ni Mommy kice kar ya taɓa ni mugu ne! Ze kasheni yadda ya kashe yaya Usman... Mommy don Allah mu tafi kar ya dake ki ba zan iya shigar miki kaman ya Usman ba...!" Gabaɗaya ta ruɗe, da sauri Raed ya ɗaga ta yana calming nata. Yusuf kife kanshi yayi a ƙasar wurin yana kuka sossai, hidayat tace cikin muryarta dake rawa sossai "ka gani ko? Yusuf ruwa cikin cokali ya ishi me hankali ya sha yayi wanka! A yanzu da nake da komai cikin harda duniya wato kuɗi ina da daman da zan sa a daureka ko a kasheka ba tare da kowa yace komai ba amma ba zan yi hakan ba! Ka zauna kayi tunanin laifukanka da hukuncin ubangiji kilan ka rage wasu abu daga cikin manyan zunubanka..." Juyawa tayi tana kallon Abba tace "Abba ni ma mutum ce kaman kowa, ina da zuciya a kirjina Abba sun min abunda ko kuɗi nake takawa basu cancanci taimakona ba, amma ba zan iya barin su hakanan ba! Abba ka basu wani abu su sake gina rayuwa albarkacin Abbana" Daga haka ta juya ta koma mota tana share hawayenta, duk da kallo suka bita har ta koma, sossai umma da Yusuf ke kuka lallai rayuwa, haka Mahaifinta ya rubuta cheque ya ba umma, duk suka koma mota wannan karon kam Aisha motar Raed ta shiga suka bar arean, Maami bata ce komai ba saboda ta san idan Yusuf me hankali ne kalaman Hidayat gareshi shagube ne, idan ya fahimta yayi aiki dashi ya yiwa kanshi idan kuma be yi ba duk kanshi aka ce 'A word is enough for the wise' Seda suka sauke Ummi gida kan suka koma asibiti, jikin Buba dae gashi ga yanayin shi, se dare duk suka watse.. Har suka koma gida mood ɗinta be dawo daidai ba Dukda yadda yake ta comforting ɗinta, bayan sun yi wanka suka kwanta nan ne ya mata ainihin rarrashin da ya kamata suka yi bacci hankali kwance.. Washegari aka kira shi wani meeting na Kano pillars Kaduna, kwana biyu ze yi don ze shiga Abuja sannan ya dawo, ya so tafiya da ita amma ta ƙi. Gidan Abbanta ta koma, Laure ta nemi Maami da ta bata wasu kudade ta shiga kasuwa don sun riga sun zama kaman dangi babu wani kunya ko nauyi tsakaninsu, aiko ta bata dayawa ba tare da ta tambayeta me zata yi dasu ba. Sayayya taje ta yi sossai ta fara gyaran hidayat, tun tana kunya har ta sake tana kwasan ilimi wurin Laure, har Maami bata take ta sha, kwana uku kaɗai suka yi gyaran ciki da waje seda hidayat ta sauya, a ranar da ze dawo da safe ummi ta zo ta ɗauke ta suka tafi saloon suka wanke kai daga nan suka je gidan kunshi inda aka zuba mata kunshi ja da baki wadda yayi mugun amsar ta, rabon ta da kunshi tun sunan Junior shima ba wani me kyau bane chan. Ta fito a Amaryar ta se shining take, azahar a gidanta ya mata Baaba Laure na ta tsokanarta ko a jikinta, Maami dae se dariya bata ce musu komai ba. Ita da ummi da Rashida suka raka ta gidanta, suka yi en goge goge tunda ba datti yayi ba suka Haɗa mishi abinci, tuwon semo miyan kubewa da yaji naman rago tayi, rashida tayi rice da vegetable sauce se chicken kebab, ummi kuwa zobo ta hada se ta ɗan taya su da ayyukan suka shirya dining dab magrib... Sallama suka mata dama da motan Rashida suka taho, rashidan ta sauke Ummi kan ta wuce gida. Bayan sallahn magrib ta shirya cikin Atampha riga da skirt da ya zauna ya fitar da shape ɗinta sossai, isha tayi kan tayi light make up ta ɗaura dankwalinta ɗas. Kallon kanta take tana murmushi lallai rayuwa wani abu ne me cike da darasi iri iri, a da ina ta san wani wankan jiran miji amma ji ta a yanzu rayuwa babu zagi, ba firgici, ba duka, ba yunwa ba rashin sutura, babu ya zan yi yau da rashin lafiyana da na yarana, rayuwa ta sauya mata zuwa kololuwar daraja cikin dangin ta da jin daaɗi. Sam bata ji shigowarshi ba sbd nisa da tayi cikin Tunanin se ganin mutum tayi tsaye bayan ta mirror, tsorota tayi zata kurma ihu yayi hanzarin zagaye ta ya rufe mata baki da tafin hannunsa yana dariya. "Matsoraciya ni ne fa!" Ajiyar zuciya me karfi ta sauke se ta sauke hannunshi tana tura baki a shagwabe tace "shine ka tsorata ni..!" Yace "Toh kin ɓace a Tunanin da ban san na menene ba har fa sallama nayi baki amsa ba" Juyowa tayi tana zagaye hannunta a kwankwasonshi ta ɗaga kai tana kallon shi sbd tsawo da ya ɗara ta tace "bani da wani tunani se naka paapi..! I missed you sossai" A goshi yayi mata peck yana fadada murmushinshi yace "missed you more baby gurl" Kan tayi wani magana ya riƙe bakinta cikin nashi, da kyar ta dakatar dashi duk suna sauke numfashi tace "mu je kayi wanka ka ci abinci" Kallon lips ɗinta kaɗai yake a shagwaɓe.. Dariya take mishi ganin abunda yake yi kaman wadda ta hana shi wani abinci me daaɗi, ƙara rungumota yayi ya sake fara kissing ɗinta yana murmuring "bari nayi maganin me mini dariya..." Janyewa tayi tana sake dariya, yana jefa mata rikitaccen kallon yace "Baby gurl I can't stop myself from kissing your lips...cause you are the reason why I turned so romantic" Jan shi tayi zuwa toilet tana blushing, "ni de ba ruwana! yi wanka abinci na jiranka" Yace "bazaki taya ni ba?" Kafaɗa ta make tace "so kake in ɓata wankan da ko nayi kyau baka kai ga cewa ba?" Wara idanu yayi ze yi magana tayi saurin rufe toilet ɗin tana dariya. Ɗakin shi ta koma ta ɗauko mai kananun kaya da armless abubuwan da yafi sakawa, ta feshe su da turarukan shi kan ta kai mai ɗakinta ta sauka ƙasa gabaɗaya ta zauna. Saukowanshi yasa ta ɗaga kai tana Kallonshi suka sakarwa juna murmushi, a nan tsakar parlorn ta shirya mai abinci don ita bata cika son zaman dining ba ko don bata saba chan bane oho, tana zuba abincin yana bin hannayenta da kallo seda ta gama kan ya riko hannayen yace "hannunki yayi kyau sossai baby gurl I love this..." Yayi maganan yana bin zanen lallen da yatsanshi wadda ke tada mata tsikar jiki, yace "zaki dinga yi min? Ban taɓa sanin suna da kyau haka ba" Kai ta gyaɗa tace "amma fa in mun koma Paris da wuya a samu wurin yi" Yace "and ur dressing ban san haka kayan Hausawa ke da kyau ba, u look so breathtaking die hard I love you..!" Murmushi kawai ta saki tace "ga wani abincin Hausawan ma I know bazaka iya tuna Last da ka ci ba I cooked it myself I promise you will love it" Yaukin kubewan yake kallo yana ɓata fuska, da kanta ta wanke hannu ta ke yankan tuwon tana bashi, ba karya yayi daaɗi sossai da kuma ya cinye Leda biyu se yaji ya koshi fiye da yadda yake koshi da abinciccikan turawa, zobo ta bashi ya sha yana lumshe idanu yace "amma fa Daadida na cuta na, bata taɓa min tayin irin abubuwan ba when ever I visited her" Yayi maganan yana tura baki, dariya take yi tana cewa se ta faɗa mata santi ya saka yana mata sharri kilan da ta bashi ya ƙi ci ne...yana ce mata yanzu ma ya baro ta asibiti se Wayanshi ya katse shi. Picking yayi da "hello!" Da sauri ya miƙe tsaye yana cewa "What???" ***** Tun da Hidayat suka Barsu anan sun jima sossai zaune suna Tunanin abubuwan da suka aikata a rayuwa, barinma umma da Yusuf in suka tuna abunda suka aikata se su ji kaman su kashe kawunansu, basu taɓa sanin rayuwa zata juye musu haka ba. Se yanzu Allah ya ɗaura mishi tsananin ƙaunan yaranshi sede kuma sun riga sun mishi nisa babu yadda ya iya, da kyar ya iya maida kanshi gida ya rufe kanshi a ɗakin matarshi da ta gudu ta Barsu bayan ta gama dasu. Hannunshi da yake ji kaman ana yagalgalawa don ciwo yake kallo yana maimaita kalaman Hidayat, yayi karatu ya san me hannunka me sanda yake nufi, shin me anfanin rayuwarshi a yanzu? Yayiwa Allah laifuka masu yawan gaske, yana neman sassauci wadda tuba yayi kaɗan, Allah ya riga ya yanke dukkanin hukuncin laifukan shi shin ze zauna ya cigaba da ganin iftila'i kala kala ko ze nemawa kanshi sassauci wurin karɓar hukuncin da ta dace? Kwana yayi be runtsa ba, da sassafe ya miƙe ya fice daga gidan ba tare da yacewa kowa komai ba. Ko da ya isa inda za shi seda yayi jiran awa biyu kan aka buɗe, ya miƙe ya shiga. "Don Allah alkali nake nema?" Mutumin ya kalleshi yace "ko lafiya kake nemanshi?" Yace "abu me matukar muhimmanci ne ya kawo ni" Yace "ka ɗan yi hakuri yanzu zaka ga ya shigo" Zama ya sake yi minti minti se su Haɗa idanu da secretary ɗin be damu ba, illa kawai zuciyarshi da baya jin daaɗin ta ko kaɗan. Chan se ga alkalin ya iso bayan wani ɗan lokaci yayi umarni da a shigar da Yusuf, bayan ya shiga ya zauna suka gaisa ya tambayeshi me ke tafe dashi? "Na kawo kaina ne a yanke min hukuncin laifukana bisa tsarin shari'ar musulunci ko zan samu rabauta ranar gobe, nayi abubuwa masu yawa wadda bana Tunanin a yanzu in na mutu zan ji ko da kamshin aljanna ne... Ka taimakeni yallaɓai" Girgiza kai alkalin yake yi kwarai Allah na son Yusuf da tuba da har yayi wannan tunani "ko zan so sanin menene ka aikata haka?" Cikin kuka yace "na aikata zina da matan da ba zan iya kirgawa ba, abu mafi girma da na aikata shine kisan kai! Na kashe ɗana na cikina da hannayena saboda ya karewa mahaifiyarshi dukan kawo wuƙa da nake mata!!" Salati alkalin nan ya saki ya sake sakewa, a hankali Yusuf ya dinga bashi tarihin rayuwarshi da Hidayat har karshe, Seda alkalin nan ya zub da hawaye, shiru ya kasa magana. "Ka zalunce wannan baiwar Allah, ka cutar da rayuwarta, lallai lallai kan kowani hukunci da za'a yanke maka ka fara neman yafiyanta, Allah kan yafe laifin dake tsakanin shi da bawa amma baya yafe laifin tsakanin mutum da mutum wannan tsakaninku ne" Yace "a yanzu babu inda zan iya ganin hidayat in nemi yafiyar ta, ina so a sadda za'a yanke min hukunci in yi video sakona ya isa zuwa gareta watakila bayan raina zata yafe min, ina kuma so labari na ya zama izina ga mutane, a lokacin da ka samu dama kayi aiki me kyau da ita kan ta kubce maka wallahi wallahi tsakani da Allah na fara son hidayat sede ganin bata da galihu bata da gata sheɗan yayi nasara a kaina na cutar da ita na san babu wadda take dashi a duniya da ze kwantar mata enci na manta Allahn da yayini me kuɗi da dangi itama shine yayi ta..." Ajiye shi aka yi, bayan dogon zama tsakanin manyan malamai aka yanke mishi hukuncin bulala na laifin zina se kisa ta hanyar rataya bisa kisan Usman da yayi, yayi kuka sossai a sadda ya ji hukuncin wadda aka bashi kwana biyu ya gyara tsakanin shi da Allah ya tuba iya yadda ze iya kan kwana biyu ya cika😭😭              DIDDIGAR ƘAYA         (Mai wuyar Tsincewa) Gureenjo🥰😍 Paid book 300 Tsokaci/Dandano Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta. "Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali... Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan ɗaurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke ɗin tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faɗa miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaɗan ki hana wannan aure!" Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa "Na yarda baba Alhj....a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina...! Ko yaya yake... Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni.." Ta karashe da kuka sossai har tana shiɗewa. Wani mugun kallo ya watsa mata yace "ko mutuwa zaki yi se an ɗaura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan ɗin ba son auren tantiyar ƴar iska irin ki yake ba..!" Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta ƴar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su Haɗa ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi. Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama'ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe "Ammi! Baba Alhj basa ƙauna ta Ammi, Ammi don Allah kiyi wani abu kar su kasheni tun kwana na be ƙare ba! Ammi wallahi na tsane sa Ammi bana sonsa bana ƙaunarsa, ki tausaya min Ammi..!" Shafa kanta Ammin take cikin baƙin cikin da yake daskare bisa zuciyarta, in akwai wadda ta tsana a rayuwar nan To mahaifiyar Faizan da Mahaifinshi me ze sa komai na rayuwarta da ahalinta se da umarnin su za'a aiwatar? Allah kaɗai ya san irin zaman da suke yanzu da mai gidanta duk saboda su, me yasa ne ita bata da ƴanci a nata gidan da mijinta? Me suka fi su? Kuɗi ko suna? Me yasa Sulaiman a ko yaushe umarnin Prof shine gaba da na kowa? Ina soyayyar da Jaddah ke ikirarin tana yiwa Fauziyya ɗin? "Fauziyya kiyi haƙuri, duk yadda zan yi wurin ganin na hana aiwatuwar wannan aure na yi sede babu nasara sakamakon hakan ma aurena rawa yake, ki daure zuciyarki ki bari ayi auren amma ba zan taɓa yi miki dole ki zauna ko kiyi biyayya ba... Wannan karo ma Aisha tayi nasara a kaina" Sakin Ammi tayi ta sake mikewa ta fice da gudu, idanunta a rufe suke mafita kawai take nema, sashen Jaddah ta shiga a gigice Sam bata lura da mutanen da suke wurin ba, ta fara cewa "Zan kashe kaina! Wallahi tallahi zan kashe kaina.... Duk ranar da aka yi Adu'ar aurena da Wannan azzalumin ina me rantsuwa zan mutu! Sede a kai gawata ɗakin sa.. Ku gafarceni Jaddah..." Natsatsiyar muryar da take bayyana fushi da wani irin ciwo ne ta ratsa kunnuwanta, muryar da ta tsana fiye da na kowa da komai a duniya, sautin da take jinshi kaman saukar aradu a kunnuwanta da ma gangar jikinta... "Ka ji ba Baba? Ban taɓa yi muku jayayya ba se a wannan karo, baba bana fatan Haɗa jini da fasiƙa...! Idan har aka ɗaura wannan aure an cutar da ni da iyalina..." Sauƙar gigitaccen mari ne ya hana shi ƙarasawa. Jajayen idanunshi ya ɗago ya zuba mata na mintuna kan ya miƙe a zuciye kaman kububuwa ya fice.... "Menene hujjar ki na ƙin wannan aure?" Jaddah ta jefa mata tambayar karon farko tana kallonta. Shiru tayi tana kuka sossai don Kalmar fasiƙa da ya jefe ta dashi har tsakiyar zuciyarta take jin zafi da raɗaɗin shi. "Baki da hujja? To fitar min daga ɗaki" Kallon ban yarda Jaddahta bace a zaune anan take jefa mata kan ta yi baya baya ta fice da sauri tana kuka. Dafe kai Jaddah tayi cikin jin ciwon wannan abubuwa da suke faruwa a cikin zuri'ar ta... ***Shin ya kuka gani? Menene hasashenku kan wannan sabon littafi? Su waye ne waennan ahali? Me yake faruwa a cikin wannan gida? Menene musababbin tsanar da suke yiwa juna? Meyasa kowa ya buɗe baki da kalmar fasiƙa yake jefan Fauxa? Wani irin zama zasu yi bayan Haɗa Wuta da Auduga inuwa guda? Akwai fa'ida a wannan aure ko babu? Za'a daura ko kuwa? Duk ku biyo ni a cikin wannan littafi nawa me suna DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Karku sake a baku labari.                 🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA... (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN. (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..* *PAGE 46* *FREE BOOK* *Aunty Safeeya kin ɗaure ni da jijiyoyin jikina, babu yadda na iya na bazama wattpad🤧🤧🤧In shaa Allah final page ze sauƙa gobe* Duk me ɗaukan duniya matabbata tabbas ya ɓata ɓat ba tare da sanin mecece duniyar karan kanta ba, Hausawa kan ce duniya budurwar wawa, kwarai duk wadda ya bi ruɗin duniya ya ɓata lahirarsa yana cikin tsaka mai wuya domin tabbas duniya ƙaryace, rayuwarta taƙaitacciya ce lahira kuwa ita ce daahir, a kusan lokaci ɗaya Baba Buba da Yusuf sun tafi gidan gaskiya. Sun tafi ne ta hanya mabanbanta inda tsananin tausayin da jama'a suka nunawa Yusuf da labarin shi yasa dayawa suka mishi Adu'ar samun rabauta ciki har da Hidayat, ta roki Allah ya yafe mishi ita kam ta yafe, ta roki ubangiji ya sanyaya makwancinshi albarkacin tuba na gaskiya da yayi. Yayinda Buba ya tafi cikin mawuyacin halin ƙishi da yunwa, ya tafi yana me kukan abubuwan da ya aikata ba tare da ya san makomanshi ba, dukkanin su an kaisu Gidajen su na gaskiya inda Zaka girbi abunda ka shuka. Allah ya sa mu fi karfin zuƙatanmu. BAYAN WATA GUDA Kwance yake hannunsa cikin nata, kanshi na a kan kirjinta hannunta ɗaya na cikin gashinsa da ya taru yayi baƙi siɗik yayi kyau, a tausashe tace "Paapi!" "Uhmm my love menene?" "Yaushe ne zamu koma? Kaga an buɗe school ba nawa kaɗai ba har da yara ko mun dawo kenan?" Dariya yayi ya ɗago yana shafa lips ɗinta yace "Ina jin daaɗin zaman mu anan saboda ke kaɗai nake gani 24/7, bani da matsalar komai bani da Tunanin kowa da komai, ni yanzu maraya ne ina bukatar kulawarki amma in mun koma zaki manta dani ki ke shareni shiyasa bana so mu koma" Murmushi sossai tayi tace "Allah ya kula da maraicinka mijina, nayi maka alkawarin kulawa ta har abada, ko da yara, karatu da kuma aiki, dukda kasancewata me uwa da uba ka zamar mini mijin marainiya to me yasa zan kasa kulawa da kai?" Peck yayi mata a lip yace "in shaa Allah next week zamu koma I wanted to tell you tun jiya ma just carried away da maganan zuwa gembu ɗin nan" Tace "yeah hakane, but please muna kan magananmu ko?" "Ba na ƙi shawararki bane, but bana son ɗibo yaran nan in kawo su su hana Daadida kwanciyar hankali, you know at her age tana bukatar natsuwa" Shagwaɓe fuska tayi tace "su huɗu ne fa kwata kwata suke gida, Maami ta ce a bata ɗaya, sannan su Baaba Laure zasu koma da ɗaya, biyun su zauna wurin Daadida I am very sure na wurin Baaba Laure da Maami baza'a samu matsala ba, su kuma na wurin Daadidan suna shakkarta don bata yi musu wasa, sannan ga ka nan akwai kuma security ba ta yadda zasu fita bare su yi wani abu marar kyau, su kuma na Gidajen mazajensu da suke fama se ka basu jari... Please kannenka ne Kaine matsayin uba yanzu a garesu karka duba halayen iyayensu mata, baka san ta inda Allah ze rama maka alkhairin ka garesu ba" Ajiyar zuciya ya sauke kan ya miƙe zaune yana janyo ta itama ta zauna tana gyara towel ɗin jikinta "since you insisted babu yadda za'a yi madame" Rungume shi tayi tana murmushi, Daadida Tayi maganan ya ƙi shine ta Haɗata da shi, dira yayi daga kan gadon ya saɓeta suka yi toilet, ta sakale hannayenta a kafaɗansa suna hiransu. Bayan sun fito suka shirya juna suka fice zuwa gidan su hajiyar hamza da suka yi alkawari, hannunsu cikin na juna suka shiga ɗakin yana zaune ganganta, zainab na riƙe da hajiyar yana bata abinci. Rabi ke shiga rabi na zuba, in ka ganta kaman irin me ciwon paralyze sede ba paralyze ɗin bane ta lalace gabaɗaya banda miyau babu abunda take dilalarwa ga rashin hankalin, sossai hamza da Zainab suke kula da ita bayan me aiki da take dashi sede Dukda haka tana fuskantar tsangwama da kyara daga wasu cikin dangin ta musamman waenda suke cikin gidan. Ita kanta zuwa yanzu ta gaji da rayuwar, bata iya bacci Sam saboda razani da firgici, abinci wannan baya iya shiga cikinta, babu hankali ta rasa komai banda wannan ɗa da Allah ya ba ta to me ya saura mata a duniya? Tana kan girban abunda ta shuka mutuwa take fata Dukda tana cikin matsanancin tsoron abunda zata tarar sede rayuwar kuma ta isheta ta gundureta cikin wannan hali, ashe in Allah ya baka lafiya ka gode masa... Gaisawa suka yi, Hidayat ke tambayar "ya hamza ya me jiki?" Yace "ga ta nan Dae jiya e yau, amma Alhamdulillah" Tace "Allah ubangiji ya bata lafiya" Suka amsa da Ameen, Raed yace cikin hausarsa da har yanzu ba wai nuna tayi ba "ya kamata ku Haɗa da Islamic, karka ce bazaku nemi magani ba kuyi ta zama haka..." "And please rokon Allah ayi ta sadaka da neman yafiya, Allah ya bata lafiya me anfani" Godiya hamza ya musu, dukda su kan haɗu sossai barin ma lokacin rasuwarnan sede har yanzu baya iya yin doguwar magana da Hidayat sede Raed, su kan jima suna hira ita kuma hidayat ita ke saka shi cikin magananta wadda haka dole ze amsa Dukda irin kunyarta da har yanzu yake dawainiya dashi. Kayan amfani suka ajiye musu irin su madara,milo da dae sauransu, hidayat na cewa zainab tayi fushi bata taɓa zuwa gidanta ba sede su haɗu Wurin Abba, da wannan Hirar suka musu rakiya zuwa mota suka tafi. Wani madaidaicin gida suka yi parking, suka sauko a tare suka shiga da sallama, umma ce ta fito tana musu maraba sanye da hijab har ƙasa. Madaidaicin parlorn ta yi musu iso suka shiga suka zauna, ruwa taje ta kawo musu tare da zama ƙasa hidayat tace "A'a umma, don Allah zauna saman kujera babu yadda za'a yi muna zaune sama ke kuma kina zaune ƙasa" Tace "hidayat barni kin ji, don Allah ina me kara rokon afuwarki da gafararki wallahi nayi nadama, nadama me girma ki yafemin..." Kuka ne ya ci karfinta, tun rasuwar Yusuf wani irin nadama ya shigesu kwarai abun ya girgiza su, maganganun hidayat sun musu tsayuwar ƙawara a zuƙatansu yadda suka hana su ko da kwakwaran motsi ba tare da sun tuno makomarsu ba, hidayat me rama cuta da alkhairi bayan kwana uku da rasuwar ta kasa hakuri ta koma garesu albarkacin Abba, gida ta fara saya musu cikin unguwar mutunci da kudadenta wadda ta samu lokacin da Abbanta yayi mata walima, ta nemawa su Surayya islamiyya ta ɗinka musu uniforms suka fara zuwa, fahariyya da rana tana zuwa learning center tana koyon ɗinki, yayinda khausar ke koyon abinciccuka Albarkacin wannan hidayat da basu taɓa dauka da muhimmanci ba a rayuwarsu se gashi ashe ita ce rufin asirinsu. Ta sayi katon freezer umma na sayar da kayan sanyi daga cikin gida, Raed shi ya cika musu store da kayan abinci, ya kuma basu shawaran adana kuɗin da Abba ya basu zuwa gaba, Sossai Abba da Maami suka musu nasiha da tunatar dasu girman uwa wadda a yanzu suke yiwa umma biyayya yadda ya dace Dukda tun farko laifinta ne da bata ɗaura su a hanya madaidaiciya ba. Abinci ta musu tayi suka ce a koshe suke ɗan hira suka yi, hidayat ta bata form da ta yankarwa Surayya na diploma da wasu kudade suka yi mata sallama suka fice. Daga nan gidan Abba suka yi, sun ɗan jima a chan suna kwasar hayaniyar ƴaƴansu kan suka wuce gidan Daadida daga nan se Airport a pjet ɗinshi suka ɗaga se Taraba state daga nan chopper suka hau zuwa gembu, Sossai iyalan Buba suka basu tausayi ko rasuwar ta waya Daadida ta gayamusu basu iya zuwa ba saboda babu halin zuwan, suna wani irin rayuwa cikin tsananin yunwa da talauci. Ko zama Raed be yi ba ya bawa su Badi'ah 100,100k akan su koma gidajen iyayensu su yi sana'a don gidan Buba sayarwa za'ayi a raba gado don baya so abar Buban da wani nauyi bayan wadda ya tafi dashi, inda ya saka en matan Haɗa kayayyakin su in kaga fuskanshi babu ko ɗigon fara'a, hakan yasa jiki na rawa suka fara. Ya sa aka kira mishi na gidanjen mazaje suka zo, faɗa sossai ya musu akan kar su kwantar da hankali su zauna lafiya ai duniya ce suna ganin karshen iyayensu yadda ya kare, dukda harshenshi yayi musu kaifi sede sun ɗauki nasiharshi, suma duk jari ya basu kuma ya karbi layukan mazajensu. Daga nan abunda za'a yi duk aka yi aka raba gadon wadda shi kam be iya karɓa ba se hidayat ce ta karɓa, tusa en matan yayi suka wuce dare dare suka sauka a Kano. A gidan Daadida kannenshin suka kwana, da safe ya je ya sake ja musu federal warning, malama mace suka nema wadda ze ke yiwa su biyun lesson da karatun addini a gida. Ya ɗauki biyun suka yi gidan Abba, ya samu su Laure har sun fito da shirin tafiya garin su, sun shirya cikin yaduka masu tsada ga jerin Motoci guda biyar da zasu tafi dashi cike da dumbin arziki, tuni Abba ya je har Nijar ya cika alkawarinshi cikin maradi ya samar musu fantsamemen gida me haɗe da gidan gona, dabbobi har na waje akwai tunda dae Gamji ya ce burinshi kiwo. Raed yayi alkawarin gina company a maradin wadda yake so ake sarrafa duk wasu kalar nau'in albarkar kowacce dabba, inda yace a hannun gamjin ze bar komai. Kaman wasa ya basu kanwarshi ɗaya suka wuce, an riga an zama en uwa da kyar aka Rabu kaman kar a rabun, Ya ajiyewa Maami ɗaya. Daga nan gidansu ummi yaje Sam hidayat bata sani ba ya saya musu wani gida a nan cikin unguwar su, kusa ma sossai da su, ya samawa babanta aiki me tsoka tunda dama da karatunshi, kannenta duk ya sauya musu makaranta a sadda suke mishi godiya yace "babu godiya a tsakaninmu ummi, a lokacin da Bama tare da Hidayat kin tsaya mata kin so ta saboda Allah, kin bata shoulder to cry kin kwatar mata ƴancinta wurin masu zaluntar ta, komai nayi miki wallahi yayi kaɗan, Allah kawai ze saka miki ina ma kowa ze samu ƙawa ko aboki irin ki a duniya? Zuciyarki me kyau ce Allah ya baki abokin zama na gari" Godiya tayi mishi kwarai, ka kasance me aikata alkhairi karka damu da Tunanin me zaka samu bayan hakan saboda gashinan, bata taɓa Tunanin arzikinsu na tafe sanadiyar hidayat ba, ta so ta da zuciya ɗaya kuma Allah ya dubi lamarin su, sune cikin unguwar girma cikin manyan masu kuɗi, mahaifinta ya daina hawa machine se mota wadda Abba guda uku ya ajiye musu a gidan. Yana da kujerar Makka da shi da mahaifiyarta daga hidayat to me ya saura musu kuma? Kaman yadda Suka tsayar sati na zagayo wa suka tarkata suka koma Paris, basu yi sati ba ya fara processing musu transfer To Riyadh saboda Saudi sun saye shi, ze koma Al-nasar club tare da famous ɗan wasan nan Cristiano Ronaldo. Tsaye take tana gama kimtsa kayan na Norah tana jin abunda take faɗa a gefe ɗaya. "Shine se da dare zasu shirya miki taron? Bana son fitan daren nan fa Norah" Shagwaɓe fuska tayi tace "Mommy in shaa Allah ba zan kai goma a waje ba I promise, mata ne kuma class mates dina ne kawai, they didn't knew that gobe ne zamu wuce da sun yi da rana ne wallahi" Ita da hankalinta be so ba, haka tace ta shirya ta je amma driver ze jira ya dawo da ita.. Da gudu taje ta shirya Dukda riga da wando ne sede decent, Rigan ya sauka zuwa gwiwa and akwai na ciki long sleeve tayi light makeup ta yafa jersey scarf ɗinta da ya zauna bisa gashin kanta. Fita tayi tana sallamar mahaifinta, fitowa hidayat tayi daga kitchen tana miƙa mishi  mug ɗin coffee ɗinshi tace "Dad is getting lazy these days abubuwa sun maka yawa baka fa ɗaukar karatun ka" Yace "I swear! Ke de bari, but in shaa Allah the moment we settle a Saudi zan baki mamaki bcs I promise ke ce malamata har in sauke" Murmushi tayi zata yi magana se Wayanshi yayi ringing, dubawa yayi ya ɗaga mintuna biyu ya sauke yana jan tsaki yace "it's Jacob wai saƙo ze bani kuma ba ze iya zuwa ba" Tace a shagwaɓe "shine ze fitar min da miji cikin daren nan?? Is it that important? Na ga baka da yawan friend cikin club members dinku" Yace "yeah, form ne na leaving da na yi singing the coach wasn't around and bana so in yi dare shine na bar musu akan in ya dawo ayi photocopying bayan ya sa nashi hannun su kawo min, daga karshe dae suka ba the most unserious person mtseww" Dariya kawai tayi tace "and you have to collect it bcs k san 6am ba ze same mu Paris ba" Yana mikewa yace "oh yes! Zo ki rakani baby gurl" Kallon jikinta tayi don ta san shi fita a haka a wurinshi normal ne daga shi se three quarter da armless, ita kam wando ne jikinta da wani shiffon orange short shirt wadda motsi tayi se ya ɗan nuna fari sol ɗin cikinta. Mikewa yayi ya je ya dauko mata After dress me kauri ta saka da kanshi ya yafa mata gyalen ya riƙe hannunta suka fice, yaran suna dakunansu sun ma kwanta don akwai su da baccin wuri barin ma yau da duk seda kowa yayi aiki duk sun gaji. Ko da suka isa hotel ɗin tsaye tayi daga jikin mota tana jiran shi, ya san irin ɗakunan en ball barin ma turawa baza'a rasa ƴan mata ko kayan maye ba shi kam ba ze iya barinta shiga ba, tana nan tsaye ta ga wasu teenagers zasu wuce dukkansu sanye da short gowns different colors and design gashin kansu duk waje da idanu take bin su tana mamakin yaran turawa, kaman an ce mata kalla da kyau ta hangi wata kaman Norah a cikinsu... Bin bayansu tayi tana sake Kallon ta da kyau, babu tantama idanunta Norah suke gane mata. Ƙara sauri tayi ganin sun shiga cikin hotel club ɗin, ko da shigarta en matan sun fara rawa yayinda Norah ke rakube tana ta kakkare jikinta kawai se ji tayi an fisgo hannunta, zata yi magana Hidayat ta daka mata mummunar tsawa "shut up ko in tsinka miki mari.... Norah yaushe kika yi girman zuwa Night club? Ashe kin zama maƙaryaciya ban sani ba?" Zata yi magana hidayat ta gwabe mata baki saboda haushi da ya kusa kashe ta ita zata yi fooling ta taho night club? Allah kaɗai ya san me yaran turawan nan suka koyamata. Zuwan Raed ne ya katse su ganin shigan jikin Norah da kuma yadda ran Hidayat ke ɓace ya san akwai matsala, kafadan Norah ya riƙe yake cewa "are you OK? Me yasa take kuka?" Ya jefawa Hidayat maganan yana sake kallon bakinta da har ya ɗan yi jini.             DIDDIGAR ƘAYA (Mai wuyar Tsincewa) Gureenjo🥰😍 Paid book 300 Tsokaci/Dandano Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta. "Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali... Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan ɗaurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke ɗin tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faɗa miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaɗan ki hana wannan aure!" Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa "Na yarda baba Alhj....a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina...! Ko yaya yake... Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni.." Ta karashe da kuka sossai har tana shiɗewa. Wani mugun kallo ya watsa mata yace "ko mutuwa zaki yi se an ɗaura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan ɗin ba son auren tantiyar ƴar iska irin ki yake ba..!" Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta ƴar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su Haɗa ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi. Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama'ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe "Ammi! Baba Alhj basa ƙauna ta Ammi, Ammi don Allah kiyi wani abu kar su kasheni tun kwana na be ƙare ba! Ammi wallahi na tsane sa Ammi bana sonsa bana ƙaunarsa, ki tausaya min Ammi..!" Shafa kanta Ammin take cikin baƙin cikin da yake daskare bisa zuciyarta, in akwai wadda ta tsana a rayuwar nan To mahaifiyar Faizan da Mahaifinshi me ze sa komai na rayuwarta da ahalinta se da umarnin su za'a aiwatar? Allah kaɗai ya san irin zaman da suke yanzu da mai gidanta duk saboda su, me yasa ne ita bata da ƴanci a nata gidan da mijinta? Me suka fi su? Kuɗi ko suna? Me yasa Sulaiman a ko yaushe umarnin Prof shine gaba da na kowa? Ina soyayyar da Jaddah ke ikirarin tana yiwa Fauziyya ɗin? "Fauziyya kiyi haƙuri, duk yadda zan yi wurin ganin na hana aiwatuwar wannan aure na yi sede babu nasara sakamakon hakan ma aurena rawa yake, ki daure zuciyarki ki bari ayi auren amma ba zan taɓa yi miki dole ki zauna ko kiyi biyayya ba... Wannan karo ma Aisha tayi nasara a kaina" Sakin Ammi tayi ta sake mikewa ta fice da gudu, idanunta a rufe suke mafita kawai take nema, sashen Jaddah ta shiga a gigice Sam bata lura da mutanen da suke wurin ba, ta fara cewa "Zan kashe kaina! Wallahi tallahi zan kashe kaina.... Duk ranar da aka yi Adu'ar aurena da Wannan azzalumin ina me rantsuwa zan mutu! Sede a kai gawata ɗakin sa.. Ku gafarceni Jaddah..." Natsatsiyar muryar da take bayyana fushi da wani irin ciwo ne ta ratsa kunnuwanta, muryar da ta tsana fiye da na kowa da komai a duniya, sautin da take jinshi kaman saukar aradu a kunnuwanta da ma gangar jikinta... "Ka ji ba Baba? Ban taɓa yi muku jayayya ba se a wannan karo, baba bana fatan Haɗa jini da fasiƙa...! Idan har aka ɗaura wannan aure an cutar da ni da iyalina..." Sauƙar gigitaccen mari ne ya hana shi ƙarasawa. Jajayen idanunshi ya ɗago ya zuba mata na mintuna kan ya miƙe a zuciye kaman kububuwa ya fice.... "Menene hujjar ki na ƙin wannan aure?" Jaddah ta jefa mata tambayar karon farko tana kallonta. Shiru tayi tana kuka sossai don Kalmar fasiƙa da ya jefe ta dashi har tsakiyar zuciyarta take jin zafi da raɗaɗin shi. "Baki da hujja? To fitar min daga ɗaki" Kallon ban yarda Jaddahta bace a zaune anan take jefa mata kan ta yi baya baya ta fice da sauri tana kuka. Dafe kai Jaddah tayi cikin jin ciwon wannan abubuwa da suke faruwa a cikin zuri'ar ta... ***Shin ya kuka gani? Menene hasashenku kan wannan sabon littafi? Su waye ne waennan ahali? Me yake faruwa a cikin wannan gida? Menene musababbin tsanar da suke yiwa juna? Meyasa kowa ya buɗe baki da kalmar fasiƙa yake jefan Fauxa? Wani irin zama zasu yi bayan Haɗa Wuta da Auduga inuwa guda? Akwai fa'ida a wannan aure ko babu? Za'a daura ko kuwa? Duk ku biyo ni a cikin wannan littafi nawa me suna DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300. Acc no. 0545475847 Acc name. Fatima Muhammad Gurin Bank name. Gt bank Karku sake a baku labari. 🖤Gureenjoh🖤 KOWA YA GA ZABUWA...    (DA ZANEN TA YA GANTA) بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN.                      (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763 AND ON AREWA BOOKS @gureenjo Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* And Now *Kowa Ya ga zabuwa..*                       *PAGE 47* LAST PAGE *FREE BOOK* "yarinyar nan wai har tayi girman fooling ɗina, ce min fa tayi zata get together ta kuma fita da decent dressing amma yanzu ji dress dake jikinta? Ya Subhanallah" A sanyaye yace "calm down die hard baki gani gabaɗaya hankalinta ya tashi? She's just a teenager for goodness sake" Norah ɗin ya riƙe yana goge mata bakin nata, duk fuskanshi ya bayyana damuwa, Kallonsu ta tsaya yi kerere lallai Raed be ɗauko hanyar tarbiyatar da yaranshi ba, Juyawa kawai tayi ta koma mota ta zauna da kallo ya bita har ta rufo kofar kan ya kamo hannun Norah ya sanyata bayan mota shima ya shiga ya ja suka bar wurin. Har suka yi nisa babu wadda ya iya magana, chan ya dube ta ganin yadda take fushi ita kaɗai.. "Baby gurl please you need to calm down, ba wani abu me muni kika samu yarinyar nan tana yi ba..." Katse shi tayi "ba abu me muni ba ka ce? OK shikenan! Nunamin kawai zaka yi ƴar ka ce baka so in hukunta ta bayan ka san laifin da ta aikata babba ne, taya zata yi irin wannan rayuwa tana ƴar musulma?" "Ya Subhanallah! Hidayah me ya kawo wannan magana?" Shiru tayi bata ce komai ba har suka isa gida, duk ta riga su fita ta haura ta shige ɗakinta, ko da suka hauro da Norah kuka take yi "am sorry dad na Haɗa ku faɗa da mommy I had no idea night club zasu ja ni naje, wlh I dressed like this saboda zuginsu ban taɓa ba, ka tayani ba mommy hakuri duk su suka faɗa min abunda zan faɗa mata ta barni na fita ba zan ƙara ba" Zaunar da ita yayi shima ya zauna yace "kin san mommynku is my first cousin sis ko?" Kai ta gyaɗa ya ce "yau ko bani da rai she have all the right da zata zauna daku ta hukuntaku idan kun yi ba dae dae ba, sannan karya bashi da kyau kin yi ƙarya saboda ki aikata saɓo in kin mutu me zaki cewa Allah?" Kuka take yi ta sake cewa "am sorry" Yace "Yafiyar Allah zaki nema sannan ki ba mommynku hakuri idan ta huce, Thank God we are leaving France 2morrow, je ki cire kayan nan ki kwanta ok?" Kai ta gyaɗa ta miƙe ta nufi ɗakinta, ɗakin hidayat ya kurawa idanu yana nazarin ɓacin ranta a saninshi tana da sanyin hali da ko laifi aka mata cikin natsuwa take hukunci, amma kuma kwarai be ji daaɗin kalmarta na wai ze nuna mata Norah ba ƴarta bace, mikewa shima yayi ya nufi ɗakin shi, tun da ta tare gidanshi basu taɓa raba wurin kwanciya ba se ranar. Babu wadda yayi baccin kirki a ranar asuba farko ta fita ta fara Haɗa musu break, bayan ta gama ta bi su ta tashesu suka fara yin sallah kan suka yi wanka suka hau shiri, Farrah ta aika ta tada Norah ta dawo, har gari ya ɗan yi shaa kan suka fito suka karya, ko da ya zauna a dining ma "Good morning" Kawai tace tare da saka mishi abinci ta tura mishi, kaɗan ya ci ya koma parlor da suka bar komai an dae rufe da Fararen kyalle, suna gamawa suma Paul ya gama fitar da akwatunasu suka bar gidan zuwa Airport anan suka samu Rashida suka yi sallama, har suka sauka Riyadh Motoci kusan biyar suka taryesu babu wadda ya cewa wani komai se yaran ke ta hayaniyar su. Katuwar Mansion ne, komai gold da fari harta paint ɗin, ba karamin kyau gidan yayi musu ba barin ma cikin gidan babu abunda ba'a saka ba na anfanin gida, ɗakuna biyar ne ƙasa biyar sama, parlor huɗu ga manyan kitchen gidan dae ka san ba karamin kudi ya ci ba a kallo guda kawai in ka mishi. Dakunan saman ya nunawa Norah nata ya nunawa Aisha da farrah da komai nasu bibbiyu ne nasu, miss Mary da Junior ya nuna mata ɗakin junior ya kuma kwatanta mata nata a ƙasa in tayiwa junior wanka ta sauka, golden door da taga ya nufa saɓanin sauran da suke white yasa ta bishi da kallo.. Be nuna mata ɗakinta ba, bayanshi ta bi janye da karamin loggage ɗinta, parlor ne tsararre me wasu mahaukatan coushines da suka tafi da ita, ɗakin da ta tabbatar nan ya shiga ta buɗe itama ta shiga.. Har ya zauna a wani kujera bayan ya fidda black German suit da ya saka da white shirt ɗinta daga shi se wandon suit ɗin, duk kakkarfar kirarsa a waje, akwatinta ta ajiye bayan sun haɗe idanu ya ɗauke kanshi, kwankwaso ta riƙe seda ta shiga ɗaki jiya ta san maganan da ta faɗa be dace ta faɗeshi ba ko ina za'a je a dawo ita ɗin uwa ce ga yaranshi. Toilet ɗin ta leƙa ita dae daga ɗakin har toilet ɗin bata ga wani wurin sa kaya ko ajiye kaya ba, gashi so take ta watsa ruwa ba laifi Akwai nisa tsakanin France zuwa Riyadh, direct white ɗinshi ta ɗauka ta shige toilet ɗin ya bita da kallo. Wanka tayo ta sanya rigar wadda ya sauka zuwa rabin cinyarta hannun yayi mata yawa yadda ya rufe duka hannayenta karamin towel da ta samo bayin take anfani dashi wurin tsane gashin kanta,dab da kujeran ta zauna daga bakin gado tana me cigaba da abunda take yi, kamshin shower gel da tayi anfani dashi da kuma ruwan gashinta da ta watsa mishi ya saka shi ɗagowa a hankali, idanunshi suka fara sauƙa kan ƙafafunta ya fara haurowa har zuwa santala santalan cinyoyinta dake waje, ya Sani hidayat is super hot ta kan fitar dashi hayyacinshi da kallo ɗaya kawai da ze mata, yana kaunar ta kuma be san ya ake yi take turning ɗinshi on a koyaushe baya iya gajiya da ita ba, motsa kafafun nata da yake kallo tayi wadda seda ya saka shi fidda iska daga bakinsa yana kokarin kwarewa da miyaun bakinshi da sauri ya kawar da kai. Chadak ta miƙe ta nufi gaban window tana gyara labulen da taga ya yaye mata sossai, tsawon ta be kaiwa hakan yasa take Haɗawa da tsalle, be san ya ajiye system ɗin hannunshi ba ya miƙe ya nufe ta yana kara kallonta tana shirin kashe shi da ranshi, daidai lokacin ta juyo tana gyaran wuyan Rigan da bata saka buttons na saman ba ana iya kallon rabin kirjinta, wani kalar runguma taji yayi mata yana sauke numfashi. A hankali itama ta sanya hannunta ta zagaye zuwa bayanshi da babu komai a tare suka sauke ajiyar zuciya, kan yayi magana tace "Am sorry paapi" Lumshe idanunshi yayi seda ya gama shigar da ita jikinshi ya gama jin duminta da yayi missing kan ya ɗago ta yana maida mata gashinta baya a lokaci ɗaya idanunshi na bisa fuskanta yana aika mata da wani rikitaccen kallo yace "ko na ce zan yi fushi dake I can't baby gurl, when we first started talking I didn't realize you would become this important to me, u are someone I don't want to go a day without talking to, please karki sake furta irin kalaman da kika furta a gareni jiya, Norah da Farrah yaranki ne and you are allowed ki yi musu duk hukuncin da kike so a sadda suka yi laifi just understand faɗa da duka baya gyara yaro" Idanunta ta Sauƙar daga kanshi itama bata ji daaɗin abunda tayin ba barin ma a gabanshi ta san yaranshi are the most valuable things to him tun a da kuma soyayyar su ba wai ya chanza ba, she should have treated Norah better. Sake rungumarshi tayi tace "am so sorry it won't happen again nima ban san sadda raina ya ɓaci haka ba, believe me you are all I got jiya ban iya nayi bacci ba, I realized cewa you are not just my man, you are my home, my rest, my heart and my safest place Kaine komai nawa.." Murmushi me sauti yayi yana squeezing shirt ɗin nashi dake jikinta buttons ɗin na ballewa ɗaya bayan ɗaya suna zuba ƙasa, yana bin neckline ɗin ta da mahaukatan wet kisses yace within his throat "then let's grow old together like this baby...! I have gone totally crazy for you.." Gabaɗaya ya haukace mata kaman yau ya fara sanin ta, in a romantic way ya ɗaga ta zuwa kan gado yana hautsina mata lissafi da duk sauran wata natsuwa da ta saura musu, idanunshi da suka sauya yake bin jikinta da kallo dasu, yayinda ta lumshe idanunta cikin haukar giyar soyayyarsa da yake shayar da ita.... Da kyar muryarshi ya iya furta "All my life baby.. I haven't seen anyone as beautiful as you by Allah I love you Morethan life..." **** Bayan shudewar awanni, tsaye take a kitchen tana Haɗa musu abincin dare saboda ya riga ya zama addicted to girkin ta baya iya cin abincin kowa yanzu, abincin hawa kanta yake yi babu yadda ta iya ne kawai take girkawa da siririn gyalen kanta tayi amfani wurin toshe hancin ta, tana Tunanin tana da ciki. Saboda duk wasu alamu sun bayyana, wannan ne cikinta na huɗu kuma duk cikin da tayi baya babu likitan da ya gayamata ita tayi noticing kayan ta, yawan zafin jiki da take fama dashi da kuma zaɓen abinci yasa ta fara zargin hakan se kuma saurin hasala ga yanzu kuma tashin zuciya. Fitowa tayi tayi rubutu bisa takarda ta bashi akan ya samo mata kan ta gama abinci, ficewa yayi ko da ya dawo ta gama ta shirya musu a babban parlorn saman, se lokacin Norah ta zo ta tsuguna kanta a ƙasa tace "am so sorry mommy about yesterday, I won't repeat that again please forgive me..." Muryarta rawa ya fara alamun zata yi kuka, hidayat bata kula ta ba ta karɓi sakonta wadda shi karan kanshi uban gayyan be san me aka aike shi ya siyo ba, zama yayi be sa musu baki ba. Abinci tayi serving ɗinshi kan tayiwa sauran yaran ta zuba nata ta fara ci ba tare da ta kula Norah ba se ta ɗan ɗago taga dukkansu huɗu sun yi fuskan tausayi suna kallonta, shi ta kalla shima yayi puppy face duka suka ce "Sorry mommy don Allah ki dena fushi da Adda Norah" Ajiyar Zuciya ta sauke kan ta kalli Norah tace "it's fine, amma karki sake kin ji? It's haram in our Deen" Kai ta gyaɗa tace "thank you mom" Abincin suka ci suka gama Norah, Aisha da farrah suka tattare kwanukan, anan ta barsu suna bitar karatun Qur'aninsu har Junior da yake Alhamdu, toilet ta shiga tana murmushi ta fara gwada PT strip ɗinta se gashi layi biyu ma'ana tana da ciki... Ribar soyayyarsu da Raed, ɗan da zata fara haifa zuciyarta cike fall da soyayyar ubansa, wanka tayi ta chanza cikin wasu fitinannun hot red kayan bacci ta saka harda red lipstick, ta gyara gashinta se ta ɗauki hijab har ƙasa ta saka ta fito, Seda ta tabbatar kowa yayi alwala yayi Adu'a ya kwanta kan ta bishi ɗaki da ta riga raka shi. Ya fito wanka ɗaure da towel, tana shiga ta zare hijabin daga ita se kayan baccin da wani irin kallo ya bita, a take ya sanya lip ɗinshi na ƙasa a baki ya ɗan ciza yana sakin murmushi yace "kina kashe ni Baby gurl!" Hannu ya miƙa mata da wani kalar tafiya da ya kasa haƙurin jiranta ya karasa ya haɗe gab din tsakaninsu yace "me sirrin ne? Son ki kullum kara karuwa yake a raina Die hard da ana gwada so ko da kullum se likitan nan yayi mamakin yadda naki ke linkuwa at each Second a nan" Ya karashe yana ɗaura hannunta setin zuciyarshi dake bugawa da karfi. Zajaye hannunta tayi jikinshi se tayi baya kaman me lilo tana murmushi me ɗauke hankali tace "Daddy...!" Yace "yes mommy" Se ta saki murmushi tace "are you sure you are ready to be called dad again?" Yana rolling eyes nashi yace "am always ready, wait what are you talking about?" Tana murmushi tace "am pregnant..!" Shiru yayi kaman be fahimta ba se kuma ya zaro dukkanin idanunshi waje yace "Oh my God! Baby you are what???" Ta sake cewa "pregnant..!" Bata rufe baki ba ya ɗaga ta Chadak ya fara zagaye da ita cikin hannunshi daga karshe suka yada zango kan gado, Rigan ta ya yaye ya hau kissing cikin hawayen farin ciki na zubar mishi "I can't believe baby, I love you Ina sonki ina sonki! You are the story that I never want to end" Ita ce wannan karon ta karɓi ragamarshi ganin irin susucewa da rikicewa da yayi. BAYAN SATI BIYU Zuwa yanzu sun gama settling a Riyadh yara sun fara zuwa Islamic school da suke boko da Arabic hadda ba'a magana Sam basu da wani lokaci, itama ta koma karatun ta a nan university wata hadaddiyar Jaguar (car) ya saya mata da yamma kullun suna fita koyan tuki cike da soyayyar juna, shima kuma ya cigaba da tafiyar da career ɗinshi cikin nasara da natsuwa. Tsaye take riƙe da waya tana dariyar faɗar Daadida da maaminta tace "ni kam se masifa kike kinki faɗamin abunda uwat tawa tayi miki da kike ta sollewa" Tace "ai gata gabana, duk ta bi ta ɗagawa bawan Allah hankali wai fa hidayat ba'a haihuwa za'a haifeta? Ciki ne da ita ta ce Sam sede a zubar wai abun kunya haihuwa da jikoki nace a'a tattaba kunne" Sossai hidayat tayi farin cikin jin wannan zance itama zata samu kani ko kanwa, sede ta boye murnan ta ta lallaɓa Daadida akan ta bita a hankali ne ba da faɗa ba. Da kyar ta jira Raed ya dawo ta fesa mai suka yi ta jin daaɗi. 8YEARS LATER Tsaye tayi hannu a kwankwaso tana kallonsu Norah da ta zama matashiyar kyakyawar buduruwa ta hautsina gabaɗaya parlorn wai tana neman Nose percel ɗinta da Junior ya ɓatar, Farrah da Norah kuwa wai suna gwada water gun ɗin Najwa da Maher katti dasu ƴan mata, shi kuwa bawan Allah Nawaf na zaune gaban TV yana kallon avengers yayinda Junior ke cin abinci. "Lallai ma Yaran nan wai me kuka maida ni? Ji parlorna kaman na mahaukata? Norah, Farrah, Aisha da girman ku?" Duk natsuwa suka yi don sun san halin mommyn tasu bata musu da wasa kaman Daad, kallonta suke yi sanye da decent suit da mayafi se after dress hannunta rike da brief case. "Sorry mommy" Harara ta watsa mishi tace "Acici ba, ai kai kam idan aka ce yau ba abinci duniya an bonu da kai Junior" Da sauri Nawaf ya tashi yace "mommy welcome" Tace "zo babana damo sarkin haƙuri" Rungumeshi tayi shine farkon ɗan da ta haifa da Raed, wadda yake shekara takwas yanzu tana matukar kaunar yaron saboda hakuri da sanyin halinshi kuma sunan mahaifinta sannan Usman ɗinta Raed ya mayar, tana kallon Norah dake final year medicine tace "Ina yarana?" Farrah tayi saurin cewa "suna bacci mommy" Bayan Usman(Nawaf) da four years ta sake haifan twins Mairamu da Abubakar sunan iyayenshi shiyasa suka musu inkiya da Najwa da Maher. Tace " Naji, ku tabbatar kun tattara min parlor tsab kan in shiga in fito in ba haka ba zan ga me Bi na final wasan Daddy" Da gudu suka hau tattare, ita kam ɗaki ta shige yau Raed yake wasan shi na karshe daga shi ritaya ze yi su koma Nigeria amma zasu bar Junior saboda shine ya ɗau kafan Raed kwallo yake so kaman hauka har yanzu ba'a ce mishi junior zallah se Raed junior, yana makarantar horas da yara en kwallo. Cikin awa biyu suka fito a haɗe kaman ka sace, hidayat ta saka wani blue palazo se rigar Al nassr Yellow da blue bayan rubuce da sunan jarumin ta,ta kama daidai cikinta da pin ta baya yadda ya zauna mata kaman dama chan haka aka yo shi, jersey scarf blue ta zagaye kanta dashi se wani hill silver, ta riƙe jakanta na kamfanin D&G blue idanunta sanye da sunglasses Sam bata tsufa kyaunta da kyaun halin ta a kullum shi kowa ke yabo, ga iya ɗaukar wanka. Tana yawan zuwa Nigeria ita kam sbd a chan tayi call to bar Sannan ta kan karɓi case musamman ta je Nigeria shiyasa kowa ke fatan mijinta yayi retire su dawo don za'a ga jajirtacciyar barrister me faɗa akan irin abubuwan da ake yiwa mata a Gidajen mazaje da ma kan hanya. Yaran kowa ya ci wanka cikin Al nassr jersey da kalolin wankansu, Motoci uku suka yi zuwa babban filin wasan, hidaya na jan nata, Norah ma na jan nata se driver na jan na karshe, a gaba gaba aka jera su har aka fara wasa da zafi zafi. Yana cin kwallon farko ya ɗago yana kallonta yayi mata alamun zuciya da hannunshi alamun ya sadaukar mata da kwallon, murmushi me kyau tayi ta mishi blowing kiss ya dafe zuciya yana murmushi kan ya cigaba da wasa, haka seda ya sha ball uku yana mata dedicating a haka wasa ya tashi. Saukowa suka yi filin aka fara hotuna ana taya shi murnar retire, karramawa da ya samu ba'a magana, yana cikin tarihin Kasar Saudia a harkar kwallo na har abada don babu irin nasarar da be samar musu ba, Seda aka kusa tashi se ga Abba, Maami da en biyunta dake da 8yrs suma Zayd da zayyad, da gudu su Maher suka je suka rungumesu suna kira uncles. Se ga Ummi da ta auri wani ambassador suna zama US ita da yaranta uku biyu mata ɗaya namiji, chan se ga Rashida ma da nata familyn tana auren babban hafsin soja na Nijeriya yaranta biyu. A take media ta ɗauka "Love❤️🫶Moh Raed dedicated his final goals and shows her his heart during his last match in history, later she and the children descended from the stands onto the field🥹🫶" Hotunan su se yawo yake platforms An sha hotuna an kuma sada zumunci, inda daga karshe suka wuce gida kwana biyu suka kara suka juyo Nijeria aka maida Junior hostel har kuka yayi gidansu na nan kaman na Paris don su kan je vacation. Mahaifin mamansu ya rasu Allah be yi ze karɓi musulunci ba, Hajiyar Hamza ma ta cika bayan ta shafe shekara bakwai tana fama da lalura karshe har cisgar naman jikinta tayi tayi kan ta tafi inda ake girban abinda aka shuka. Ko da suka dawo Nijeriya gabaɗaya an chanza tsarin gidansu zuwa wani na daban hadadde, su umma sun zo yi musu murna khausar na auren wani dattijo itace matarshi ta huɗu, se fahariyya dake auren wani police su biyu ne matan nashi se Surayya da ko shekara bata rufa da auren wani ma'aikaci redio suna sana'ar su har abada kuma suna godewa Hidayat suna sanya mata albarka. Kannen Raed ma duk sun yi aure, waenda suke gidan mazajensu ma be Barsu ba seda ya tabbatar a ko yaushe babu abunda suka nema suka rasa da taimakon sana'o'insu. Bayan sun natsu ya fara harkar business ɗinshi ka'in da na'in, ita kuma hidayat ta fantsama ta zama topic da kowani namiji azzalumi yake tsoro, sossai ta jajirce wurin zama mace me kamar maza. Bayan wasu watanni Raed ya gane dangin mahaifiyarshi, mahaifiyarta da kuma yannenta maza biyu se kanwar ta mace ɗaya sun dawo neman Mairamu aka kwatanta musu gidan Raed da taimakon sisters ɗinshi na nan gembu suka isa Kano. Sossai yayi farin ciki Daadida ta nace sede su zauna tare ba se an sake nemar musu wani gida ba, mazan ya saka su cikin business ɗinshi. Kwance take a kirjinshi tana bashi labarin wani mutumin da aka yanke mai hukuncin shekara biyar gidan yari da tara me yawa akan irin zaluntar matarshi da yayi cikin azabtar wa. Yana shafa bayanta yana sauraron ta yana murmushi yace "in dae da irin ku Hidayah maza ba zasu zalunci mata ba, su kan manta cewa macece ta haifesu ta kuma raine su har suka zama abunda suka zama, a ko yaushe mace abar tausayi da kulawa ce, Allah ya cigaba da dafa miki matata, kwarai ina kaunarki,zuciyarki tsarkakakkiya ce shiyasa Allah be taɓa bari kin taɓe ba, I love you hidayah today and always karki manta da hakan" Ɗagowa tayi tana shafa hancinshi tace "A da ban san kaina ba, kai ka tsince ni ka zamar dani mutum wacce kowa ke alfahari da ita, da kowani namiji irin ka ne da mata basu sha wahala ba a duniya you are not just my favorite person you are my everything Muhammad Raed, I cannot breathe when you are not near. I love you" Ta karashe tana kissing lips ɗinshi, ya juya ta ƙasanshi yace "wai me sirrin ne?" Yayi maganan yana dage mata gira da sauri ta rufe idanunta tana dariya sossai... TAMMAT BI HAMDILLAH ABUNDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH YA BANI LADAN ABUNDA KUMA NA YI KUSKURE INA ROKON ALLAH YA YAFE MIN, ALLAH YA KAWO MU KARSHEN WANNAN LITTAFI GODIYA ME DUMBIN YAWA A GAREKU DAUKACIN MASOYAN KOWA YA GA ZABUWA..... GODIYA NA MUSSAMMAN ZUWA GAREKU FAV SIS(HANEEFA MOHD GURIN) MAMA TANKO SHANONO AUNTY SAFEEYA UMMULKHAIRI MAMAN SADIQ MAMAN KHALIL MAMAN ALI SIS JIDDAH ADAM AUNTY FARIDA MOM MUNEEFA AMEERATUH SIS AISHA USMAN KUSHERKI MAMAN AYSHAT SIS SADIYA UMAR ADAM SIS KHADIJA QUEEN SIS FIRDAUS DA MA WAENDA BAN KIRA SUNA BA KU SANI WALLAHI NA JI DAAƊIN TAFIYAR NAN DAKU KUMA INA MATUKAR GODIYA BISA HAKURI DA KUKA YI DANI. ALLAH YA HADAMU A DIDDIGAR ƘAYA... 🥰😍❤️                  🖤Gureenjo🖤