BAQEER      NA AYUSHER MUHD             DA UMM ASGHAR DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊAYA *RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.* *TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA* *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 [1] Tafe yake a gefen titi hannunshi na dama na riƙe da waya wacce ke saitin kunenshi, yanayin shi kaɗai zaka kalla kasan yana cikin ɓacin rai wanda ke nuni da abinda ake faɗa a cikin wayar ba abu ne mai daɗi ba. Magana yake yi a nutse sai dai kuma ranshi a ɓace yake matuƙa saboda rainin hankalin da mutumin yazo mishi dashi, taya zai sa yayi mishi aiki akan bayan kwana biyu zai biya shi kuɗin aikin shi amma gashi har yanzu da ake neman yin watanni biyar bai gama biyanshi kuɗin shi ba? Sai ma tsitsinka mishi kuɗin da yayi ta yadda babu wani ƙwaƙƙwaran abu da zai iya yi da kuɗin tunda ba a dunƙule ya bashi ba. Cike da takaicin abinda yake ji ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin yin magana, abinda yaji ne yasa ya kasa tantance a wace duniyar yake, wani abu yaji yayi sama dashi, idanunshi ne suka sauka akan sararin samaniya yaji kwakwalwarshi ta ɗauke dif na wucin gadi, sam ya kasa gane abinda ke faruwa dashi, kafin yai auni ya dawo da kwakwalwarshi tai wani aiki yaji ya faɗo kan wani abu, kanshi ne ya ji ya bugi gaban mota sannan ya sulale ya faɗi ƙasa, dishi-dishi ya shiga gani a hankali yake ƙoƙarin buɗe idanunshi yana son sanin meke faruwa dashi, sai dai idanunshi mai makon su buɗe sai ma kullewa da suke, karar kiɗa kawai yake ji a kunuwanshi, nan idanunshi suka rufe wanda daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba. Daga cikin motar kuwa wani saurayi ne wanda kallo ɗaya zaka yi mishi kasan ɗan gayu ne wanda ke ji da kanshi. "Goddamn it! This bastard is gonna make me late." Matuƙin motar ya faɗa haɗe da dukan stearing wheel na motar da ɗan ƙarfi, burki ya taka sannan ya rage sautin kiɗan dake tashi cikin motarshi, bai ko kashe motar ba ya fito a fusace yana duba gaban motar, ganin da yayi babu abinda ya sameta yasa shi komawa cikin motar yayi reverse ya kaucewa saurayin dake yashe a ƙasa wanda kana ganinshi zaka ga babu alamun rai a tattare dashi, yaja motarshi da wani irin mugun gudu ya bar wurin yana mitar 'duk Daddy ne ya janyo musu ya rasa unguwar da zai yi gini sai cikin talakawa wai shi a dole yana protecting political image ɗin shi, gashi nan abinda ya janyo musu mingling da ƴaƴan matsiyata da basu san komai ba sai gidadanci.' Majalisar samari ce zaune a kan kujerar dake ƙarƙashin bishiyar darbejiya, daga gefensu kuma mai shago ne yana ta saye da sayarwar shi, idan ka kalli can nesa dasu kuma zaka ga gungu-gungu ne na yara suna wasanni kowanne na daidai shekarun su. Idan ka buɗe ido ka kalli yanayin gidajen unguwar sosai zaka gane cewa kowa ta haɗa wato daga masu hannu da shuni har zuwa matsakaita masu rufin asiri bakin gwargwado da kuma talakawa, a taƙaice dai unguwa ce ta kowa da kowa. Musu ne ya kaure a wannan majalisar inda samarin unguwa ke taruwa su zauna yawanci da yamma bayan sun taso daga wuraren sana'o'in su ko makaranta. Musu ne akan siyasar ƙasar nan don haka wurin ya kaure da hayaniya har wani baya jin abinda ɗan uwanshi yake cewa, wani daga cikin samarin ne idanunsa suka kai kan abinda ya faru daga gaba dasu kaɗan, ihu ya saki da ƙarfi wanda ya sakasu kallon wurin suma, hankali a tashe suka rugo inda saurayin nan yake a yashe. Suna ƙarasowa hankalinsu ya sake tashi ganin halin da yake ciki. A guje Bello ɗaya daga cikinsu ya ƙarasa wurin hankalinshi a mugun tashe, jiki na rawa ya kai hannu saitin hancin saurayin dake kwance akasa dan ya tabbatar yana numfashi, wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauƙe jin yana numfashi a hankali, kafin ya nemi taimakon sauran jama'ar da ke wurin akan su taimaka akai shi asibiti. Cicciɓarshi aka yi za'a saka shi cikin motar ɗaya daga cikin mutanen da suka taru a wurin, hankalinsu ya sake tashi ne ganin jini ta bayan inda aka ɗaga shi, haka su Bello da wani daga cikin abokansu suka sakashi a mota, duba wayarshi Bello yayi sai dai sam babu alamar ta, ya sani sarai a cikin mutanen wurin ne wani har ya sace dan yanzu in aka yi hatsari wasu sata ce kawai a gabansu ba wai ceton rai ba. Accident and emergency (A&E) na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano suka isa dashi, a gaggauce aka karɓeshi aka yi ciki dashi domin kuwa ba ƙaramin jigata yayi ba, kuma har yanzu bai san inda kanshi yake ba, sai numfashi da yake fitarwa shima a hankali. Nurse ce ta kawo musu takarda akan su cike sannan tace "Ya sunanshi?" Bello cikin sanyin jiki yace "Muhammad Baqeer!" "Kai ne guardian ɗinshi?" Kalaman da yaji nurse ɗin tayi mishi kenan, kafin yayi magana tace "In kasan ba kai bane please ka ƙira su yanzu dan muna son su saka hannu cikin gaggawa." Tana kaiwa nan ta juya ciki da alama sauri take yi, Bello idanunshi duk sun yi jaaa, wayarshi ya ɗauko yana ƙoƙarin ƙiran mahaifin Baqeer, mamaki ne ya kamashi ganin ƙiran wayar mahaifin nashi, nan ya daure ya ɗauka "Aka ce Baqeer yayi hatsari?" Kalaman da yaji ya dake shi da ita kenan, cikin rawar murya yace "Eh muna asibitin Aminu Kano!" "Ni nasan wannan abotar taku ba abinda zata jawo mana sai ɓacin rai, don na sha faɗa maka ka daina zuwa kana kiranshi in yana aiki amma da yake kai ba mai jin magana bane kai kenan da ziryar janshi ku tafi majalisa." A hankali Bello yace "Wallahi yau Baba bama ni na ƙirashi ba sannan yana zuwa ko zama bai yi ba ya tafi." Jin alamun an kashe wayar yasa ya shafi saman goshinshi yana sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya. Baba daga can ɓangaren ranshi ne ya sake tunzura a fusace ya fara ƙoƙarin fitowa daga gidan, hannu tasa ta rikeshi tace "Kai ma Alhaji ka kwantar da hankalinka, na tabbatar ba sosai bane da sukace yaji ciwo sosai, kasan zancen yara su dama sun iya zuzuta abu." Hannunshi ya fincike daga hannun matar dake tausasar sa da kalaman nan, yana ji kamar zuciyarshi zata fito, yana fitowa daga ɗakin yaga Fatima wacce itace mahaifiya ga Baqeer ɗin, tana ƙoƙarin shiga da kwanukan da ta wanke cikin ɗakin ta, fita kawai yayi ranshi na sake ɓaci, da gudu kanin Baqeer wanda saurayi ne bai wuce shekaru 24 ba shine ya fito daga ciki gidan ya biyoshi tare da buɗe ƙofar mota ya shiga gefenshi ya zauna. Baba bai musa ba ya ja motar don ko magana baya son yi. Tuƙi kawai yake yi amma gabaki ɗaya ya rasa nutsuwarshi, hukuncin Allah ne kawai ya kai su asibitin lafiya amma ba don yayi nutsatsen tuƙi ba. Suna shiga accident and emergency Bello wanda dukkanin nutsuwarahi tana wajen ƙofar da aka shiga dashi ya taso ya taresu. Durƙusawa yayi yana gaida mahaifin Baqeer sai dai bai iya ya amsa shi ba saboda halin da yake ciki sai ma tambayar shi da yake yi yanayin jikin na Baqeer ɗin "Tunda muka zo aka shiga dashi ciki basu fito ba sai dai an buƙaci sa hannu wanda ganin baku zo ba yasa nayi, sun bukaci za'a ƙara mishi jini nida Salim daya kawo mu mun je an gwada namu ko yazo ɗaya da nashi sai dai anyi rashin sa'a basu yi matching ba, to bayan nan dai har yanzu basu ƙara fitowa ba sai dai ko muje mu tuntuɓi waɗancan nurses ɗin muji yadda ake ciki." Hannu Baba ya ɗaga mishi alamun ya kyaleshi sannan ya nufi wurin Nurses ɗin, Salim dake fitowa yana gaisheshi ko amsa wa baiba saboda hankalinshi baya jikinshi, Nurses ɗin har sun fara tafiya sai ga ɗaya daga cikin likitocin da suka karɓe shi nan ya fito hakan yasa Bello dake biye dasu a baya ya nunawa Baban Dr ɗin yace "Yauwa gama likitan dake duba shi nan ya fito" Baba yi yayi kamar bai jishi ba har suka ƙarasa wurin shi. "Sannu likita." "Yauwa sannu Baba," yace yana mai gyara tsayuwarshi. "Yarona ne aka kawo mota ta buge shi ance ku kuka dubashi, ya jikin nashi dai? Ina fatan babu wata matsala?" "Hmm.." kawai kanin Baqeer yace yana taɓe baki don a ganinshi da ace ɗaya daga cikin shi ko ƴan uwanshi ne hakan ta faru dasu ba lallai ne ya nuna damuwarshi har haka ba amma da yake ɗan gwal ne baya da lafiya duk yabi ya ruɗe tun ma bai ga a halin da yake ciki ba,"Allah yasa ma kada ya tashi" ya samu kanshi da yiwa ɗan uwan nashi mummunar addu'a babu tausayin halin da ya samu kanshi a ciki. Ɗan kallon shi likitan yayi yana tunanin ta yadda zai fara faɗa mishi halin da ɗan nashi yake ciki ganin yadda hankalinshi yake a tashe "A yanzu dai ba zance komai ba, sai abinda gwaje-gwajen da aka yi mishi suka nuna, mun dai yi ƙoƙarin tsayar da zubar jinin da yake yi sai dai muna buƙatar wanda za'a ƙara mishi ina fata kun zo da wanda zai bashi jinin, sannan akwai karaya a hannunshi na dama da ƙafarshi ta hagu". "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Allahumma ajirni fi musibati wa akhlif li khairan minha" Kawai Baba ke nanatawa. Cikin wata irin kasalalliyar murya irinta wanda abun duniya ya taru yayi wa yawa yace "Ko nawa jinin za'a iya ɗiba matukar jininmu ɗaya ai, Allah ya sauƙaƙa mishi ya tashi kafaɗunshi.” Ya ƙarasa maganar cikin murya mai karkarwa. Dukkansu suka amsa da 'Ameen' banda kaninshi da yake tsaye a gefe sai faman cika yake yi yana batsewa shi a dole bai so zuwa asibitin ba ya biyoshi ne kawai dan mahaifiyarshi ta turo shi akan yazo yaga meke faruwa ya kai mata labari. Jikin Baba a mugun sanyaye ya shiga cikin ɗakin, ja yayi ya tsaya yana jin kafafuwanshi nayi mishi nauyi ganin ɗan lelen ɗan nashi a kwance wanda duk wani mai imani in ya ganshi sai ya zubar mishi da ƙwalla saboda gaba ɗaya kamanninshi sun sauya don ba ƙaramin buguwa yayi ba, Bello da Salim a gefe suka tsaya kawai dukansu hawaye sukeyi shi da Salim, don abun akwai ban tausayi ace awa biyu baya kana cikin koshin lafiya yanzu banda numfashi ba abinda kakeyi, hancinsa ɗauke yake da na’urar taimakawa gun yin numfashi na oxygen, a hankali Baba ya ƙarasa wurin har a lokacin bai dawo hayacinsa ba ya kalli Bello cike da tausayin ɗan nashi yace “Garin yaya hakan ta kasance?” Jiki a sanyaye Bello yake faɗa mishi iya abinda ya sani sannan yaran daya mai motar a yanda ya musu kwatance suna zargin yaran gidan Alhaji Sunusi Karaye ne shine wanda ya bugeshi, da yadda yaja motarshi ya bar wurin ba tare da yabi takan Baqeer ɗin ba wanda hakan yasa basu gane ko tabbas shi ɗin bane. Nan da nan Baba ya sake fusata, yana ji ranshi na sake soyuwa, tabbas zai je har gida ya samu ubanshi don ba zai yarda da ganganci a cutar mishi da yaro ba. Baba ne ya fito aka gwada jininshi ganin girma ya kamashi suka bukaci a gwada na kanin nashi, kallan Bashir yayi yace “Wuce a gwadaka.” Ji yayi kamar zai yi ihu haka ya wuce dan tabbas suna tsoron mahaifinsu sosai, dawowa yayi ɗakin yana jin kwalla na sake taso ma idanunsa, zubawa Baqeer ido yayi kaf cikin ƴaƴanshi yafi ji da Baqeer sannan ya kwallafa rai a kank Baqeer ɗin ne zai samu abinda shi bai samu ba. Hannunsa yasa ya riƙo hannunshi yana sake bin fuskarshi da jikinshi da kallo zuciyarsa na sake karyewa, ya daɗe riƙe dashi kafin yace “Allah ka dubeni ka tashi kafaɗn yaran nan, Allah ka dube ni da idan rahama….” nurse ce ta shigo ta ƙara sa mishi wani jinin wanda aka ɗebe daga jikin Bashir. Baba kallon Salim yayi shida Bello da suke tsaye carlo-carko a gefe yace “Please ku tafi mun gode da kulawa.” Jiki a sanyaye suka juya, Baba ya saƙe riƙe Baqeer bayan fitarsu kawai hawaye ne yaji sun zubo mishi, tabbas in har wani abu ya samu Baqeer ba zai yafema Alhaji Sunusi Karaye ba, idanunshi ne suka sauka kan bandage ɗin da ke naɗe a wutsiyar hannunshi na dama, hankali a tashe ya ƙarasa ɓangaren daman ya ɗan ɗaga hannun, nan danan ya fito cikin sauri yana neman nurse ɗin data fito daga ɗakin, a gaban wani ɗakin ya hangota cikin sauri ya ƙarasa yace “Nurse me ya samu hannun daman yarona?” Kallonshi tayi sannan tace “Muje na duba.” Tare suka shigo ta nufi ɓangaren dama tana dubawa ta kalleshi tace “Karaya ce a wurin…….” “Karaya? Kinsan me yake yi da hanun da zaku ce karaya?” Cike da rashin fahimta tace “An mai ɗori insha Allahu zai warke.” Cike da faɗa yace “Kina tunanin dan kun mai ɗori hanunshi zai dawo yanda yake ne? In ya kasa amfani da hannun fa ko ya kasa yin aikin painting ɗin da ya saba? Gasar da zai shiga ta zane da za ayi a karshen watan nan fa?” Bashir ne ya ƙara so da sauri dan ance ma ya kwanta ya huta yace a’a ahi gida zaije, nan ya wa nurse alamar ta tafi, tana fita ya zabgawa Bashir wani kallo yace “Baka da hankali ne? Ko ka ɗauka ban ganka bane?” “Baba ita me nene laifinta? Kula dashi fa kawai suka yi? Sannan shi me yasa kowa na zaune agida amma shi yana yawo a titi da majalisa?” “Kana sake magana zaka ga ɓacin raina, shashashan banza kawai.” Bashir bakinshi yaja yayi shiru, Baba kallon hannun yayi yana ji ya zai yi idan yaron nan bai warke ba? Shikenan rayuwarshi ta shiga garari, duk wani buri nashi ya tarwatse. Hmmmm... #Baqeer #Shalele # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕 Duk guda ɗaya 1k KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.* *TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA* *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 *2* Yau tunda ta tashi take jin jikinta babu daɗi gabaki ɗaya yayi mata nauyi ga wani irin ƙunci da ya lulluɓe kirjinta lokaci zuwa lokaci sai taji gabanta ya faɗi, komai take yi tana yin shi ne cikin rashin karsashi tunda tasan ba rashin lafiya take yi ba sai dai yanayin data samu kanta a ciki sam baya yi mata daɗi. A kasalance ta yunƙura daga inda take kwance a tsakar ɗakinta ta tashi, tsakar gidansu ta fito ta hau tattare wajen da suke yin girki don itace da girkin ranar, haka nan cikin dauriya ta samu ta haɗa wutar ta ɗora tukunya, aikin take yi salalaf-salalaf kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki don sam jikinta baya da wani ƙwari. Tana lura da abokan zamanta da suke ƴan maganganu ƙasa-ƙasa a gefe da sun ganta sai suyi shiru suna zunɗenta da baki abinda yasa ta ƙara tunanin tabbas akwai abinda ya faru da suke ɓoye mata duk kuwa da ba yau ne karon farko da suka taɓa yi mata irin hakan ba sai dai na yau ɗin yayi tsanani ga kuma yanayin data tashi dashi tun safe yasa tayi tunanin tabbas ba lafiya ba, gashi ma maigidan tunda ya fita bai dawo ba haka nan Baqeer yau yayi nisan kiwo abinda ba halin shi ba ya fice waje yayi zamanshi in har ba wani muhimmin uzuri ne ya riƙe shi ba ba tare da ya leƙo yaga a halin da take ciki ba don duk inda ya tafi hankalinshi yana kanta sanin irin zaman da take yi a cikin gidansu yasa baya son yin nesa yana barin gidan don kaɗan da aikin mutanen gidan suyi mata wani abun na cutarwa ita kuma ba iya kare kanta take yi ba. Har ta gama girkin ta raba kamar dai yadda suka saba Baqeer bai shigo gidan ba abinda ya ƙara ɗaga hankalinta don baya taɓa kaiwa magriba a waje duk inda yaje yana ƙoƙarin dawowa gida kafin ayi sallar magriba idan kuma ya zama lallai sai ya daɗe a wajen to tabbas zai kirata a waya ya faɗa mata. Sai da ta kawar da komai ta tsaftace wurin kafin ta tashi ta koma ɗakinta, wayarta ta ƙara ɗauka ta kira number Baqeer sai dai har yanzu a kashe ake ce mata, juya akalar kiran tayi zuwa ga wayar maigidan sai dai har ta ƙari ɓurarinta ta gama bai ɗauka ba, ƙara kiran wayar tayi amma har yanzu bai ɗaga ba. Tunani tayi watakila sallah yake yi don haka ta ajiye wayar da zummar ta sake kiranshi in anjima, tashi tayi ta fita don ta ɗauro alwalar ita ma tayi sallah sai dai abinda taji a tsakar gidan yasa ta sakin butar dake hannunta ta faɗi sauran ruwan dake cikin butar ya tsiyaye akan simintin tsakar gidan nasu. Kamar wacce aka jeho sai ganinta suka yi a gabansu tana cewa "Me ya samu Baqeer ɗin kuke ɓoye mini? Ni dama nasan shirun nan nashi bana lafiya bane tabbas akwai abinda ya faru dashi, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta ƙare da ɗora hannayenta bibbiyu a kanta tana kuka. "Ke dallah kada ki cikawa mutane kunne da kwakwazo a cikin gida, wani abu kika ji ance ya samu Baqeer ɗin da zaki cika mu da iface-ifacen kuka," Uwargidansu Jamila tayi maganar cikin yi mata tsawa. Duk da faɗan da ta rufeta dashi bata saduda ba sai da ta ƙara cewa "Amma sai naji kamar kun ce Baqeer yana asibiti, dan Allah ku taimake ni ku faɗa mini ba hakan bane ko hankalina ya kwanta, yau tunda Baqeer ya fita bai dawo ba bayan hakan ba sabon shi bane." ta ƙare maganar cikin rawar muryar da tashin hankali ya gama kassarawa. Har Jamila ta buɗe baki zata cigaba da zazzaga mata masifa sai Abu ɗaya kishiyar tasu ta ɗaga mata hannu alamar tayi shiru don haka Jamilar taja bakinta ta tsuke sai dai ranta fal ƙuna taso Abu ta ƙyaleta yau ta zazzaga mata rashin arziƙi saboda yadda tafi jin haushinta da kishinta akan Abu ganin yadda mai gidan ya ɗauki dukkanin wata soyayya ya ɗora akanta da tilon ɗanta sai kace fin nasu ƴaƴan yayi. Muryar tausayi Abu tayi ta wani kwakkwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "Ashe baki ji ba ai da baza mu fara yin maganar nan har taje kunnenki ba amma tunda kin riga kin ji babu amfanin ɓoye miki," ta ɗan yi jim kamar tana juya ta yadda zata fara faɗa mata wannan mummunan labarin bare yadda taga duk ta matsu taji a wane hali ɗan nata yake ciki. Sai data gyara tsayuwarta sannan tace "Baqeer ne Allah ya aikowa da tsautsayi mota ta buge shi, yanzu haka su Alhaji na can asibitin Mallam Aminu Kano inda aka kai shi shi da Bashir, sai fatan Allah ya kiyaye gaba dai amma ga yadda nake ji kamar ance bai ma san a inda kanshi yake ba." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta ƙara ambata tana mai fashewa da wani irin kuka duk da tunda Abu ta fara maganar take tsiyayar da ruwan hawaye dama "Yanzu Baqeer ɗin yana asibiti tun ɗazu aka rasa mai faɗa mini? Wayyo ni Allah ka tashi kafaɗun yarona alfarmar Annabi da Alqur'ani" ta ƙare maganar tana nufar hanyar waje da nufin tafiya asibitin taje taga halin da ɗan nata yake ciki, tsabar ruɗewa tama mance da ko mayafi babu a jikinta bare kuɗin motar da zata hau ta kaita asibitin. Abu ce tayi hanzarin janyota ta dawo da ita tsakar gidan tace "Malama ina zaki? Yanzu da daren nan daga faɗa miki magana? Salon Alhaji yace waya faɗa miki kice mune bayan ya hanemu da yin hakan?" Kallon Abu tayi da kumburarriyar fuskarta data koɗe saboda kuka tace "Wallahi bazan iya zama ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba idan har ba zuwa nayi naga a wane hali yake ciki ba, don Allah kuyi haƙuri ku barni na tafi wallahi bazan faɗawa Alhaji a wajenku naji ba." Sai sannan Jamila ta saka musu baki don duk abinda suke yi kallonsu kawai take yi tunda Abu ta haneta da yin magana, cewa tayi "Idan dai kin tabbatar da baza ki faɗa mishi mu muka gaya miki ba sai kiyi tafiyarki don ko nice hakan ta faru da yarona nasan hankalina ba zai taɓa kwanciya ba idan ba zuwa nayi naje naga a halin da yake ciki ba, sai dai kuma kada ki manta ko mayafi babu a jikinki bare kuɗin mota ko kina tunanin akwai wanda zai yi miki kallon hankali a hakan da kike". Sai sannan ma ta tuna ai ko sallar magriba bata yi ba ashe fa alwala ta fito zata yi taci karo da wannan mummunan labarin da yayi fatali da dukkanin wata nutsuwarta. Ɗakinta ta shiga ta fara zarya kafin ta ɗau ki hijab, zurawa kawai tayi ta tada sallah sai dai sam ba ka jiyo karatunta sai sautin kukanta, da tazo sujjadar karshe kuwa kasa miƙewa tayi kawai ta cigaba da kuka tana neman Allah ya tausaya musu ya tsagaita wahalar Baqeer. Da ƙyar ta iya sallame sallah, ko hijab ɗin bata cire ba ta jawo jakarta ta nufi hanyar waje kai tsaye, ba komai take ganewa ba, hakan yasa ta zura takalmin da take aiki dashi a tsakar gida kawai ta fita titi. Abu da Jamila suna hangota ta tagar window ɗin dakunansu, a tare suka saki wata dariya ta jin dadi dan tabbas sun san yau akwai kura a gidan nan, su dai iya kacinsu su buɗe ido su kwashi kallo. Mai adaidaita ta tare sannan ta shiga ciki tana tafe tana lazimi, har saida yace gasu a Aminu Kano. Idanunta ta sauƙe kan asibitin tana jin gabanta na faɗuwa, haka ta fito ta kira Bashir akan ya sanar da ita inda aka kwantar da Baqeer ɗin, a lokacin yana kwance dan ba'a daɗe da gama ɗaukar jininshi ba, hakan yasa yace ta kira Bello shima bai sani ba ya kashe wayar tare da jan wani tsaki haka kawai shi ba da hatsari ba an kwashe mishi jinin jikinshi, shi yasa sam baya kaunar Baqeer saboda a komai sai Baban ya nuna fifiko a kanshi. Bello ta kira cikin sauri, nan ya sanar mata zai zo ya ɗauketa daga inda take kasancewar asibitin da girma yake, sannan Baba ya hanashi komawa cikin ɗakin. **** Zaune Baba yake gaban Baqeer wanda kallo ɗaya za kayi wa fuskarshi ka fahimci tsantsar damuwar dake ɗauke da ita, idanunshi na kan Baqeer yana kallon yadda yake kwance kawai baya ko motsi, numfashi kawai yake yi, hannayenshi ya riƙo zuciyarshi na sake karyewa yake magana “Baqeer ka taimakeni ka tashi, ka sani kai kaɗai ne burina, da kai kaɗai nake taƙama a duniyar nan, kaine wanda in na gani nake jin sanyi a raina nake kuma kyautata zaton nayi abin arziki na kawoka duniya da nayi, ka taimakeni ka farka kafin wannan taron naku, kada ka bari abinda muka daɗe muna shiryawa ni da kai ya tafi a banza……” Maganarshi ce ta maƙale jin sako ya shigo cikin wayarshi, duba wayar yai yaga sakon secretary na Gomna ne wanda yake sanar dashi sun turawa Baqeer kuɗi akan yayi siyayyar abinda zai buƙata in yaje Abuja yin gasar. Wayar ya maida aljihu ya sake damke hannun Baqeer yana ji kamar ranshi zai fito. Ƙofar da yaji an buɗe ne yasa ya kalli ƙofar tare da sakin hannun Baqeer, nan da nan idanunshi suka canza fuskarshi ta murtuke, rai a ɓace yake kallinta, sai dai ko bi takan shi ba tayi ba ta ƙarasa shigowa ciki da gudu tana cewa “Na shiga uku, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Baqeer?” Cike da tsawa Baba yace “Fatima ashe baki da hankali?” Cak ta tsaya daga inda take tana kallonshi a tsorace “Banda hauka da rashin tunani uban wa ya baki izinin zuwa asibitin nan?” Hawaye ne suka gangaro mata tace “Haba Alhaji, yanzu ta ina kake tunanin zan iya zama bayan naji ɗana yayi hatsari? Sannan kalli yadda aka nannaɗeshi da bandage wanda kana gani kasan……”Kuka ne ya kwace mata wanda ya hanata ci gaba da magana, nan ta ƙarasa jikin gadon tana wani irin kuka mai taɓa zuciya, Baba yana tsaye yana saurarenta na wasu mintina kafin yace “Kin ganshi ai ko? To tattara ki koma ni bana son shirmen banza, ɗana ba abinda zai sameshi kuma bana so wasu mutane su sani balle a mana hassada da baƙin cikin da aka saba, kuma wallahi karna sake ganin ƙafarki anan in har ba ni nace miki kizo ba.” Ɗago jajjayen idanunta tayi ta kalleshi cike da tausayi tace “Alhaji kar kayi min haka na rokeka da Allah ka barni na zauna kusa da ɗana dan Allah ka dubi wannan mahaifiyar.” Hannu ya ɗaga mata alamar tayi mishi shiru dan Baba kowa ya sanshi akwai zafi, sam bashi da sakin fuska shi yasa yaranshi da matanshi kowa ke shakkarsa, “Wallahi kika bari na sake magana sai ranki ya ɓaci ni bana san shirmen banza, ce miki aka yi Baqeer rago ne irinki da zaki zauna kina kuka yana saurara? To ni bana son shirme ki koma can gida kiyi ta kukanki kina sharewa, yarona da izinin Allah ba abinda zai sameshi ki koma na miki alƙawari yana farkawa zan sa a kawoki.” Hawaye kawai take yi kamar wanda ake zuba mata ruwa a cikin idanuwanta saboda yawan hawaye, da ƙyar take jan ƙafafunta ta fito daga ɗakin. Bashir wanda ya taso dan ya ga mai zai faru yana jikin ƙofa yana kunshe dariyarshi, jin alamun ana toshe baki yasa Fatima ta juya ta kalli Bashir, cike da raini ya nuna mata hannunshi yace “Jinina aka ɗauka aka sakawaa ɗanki.” Hannun ta kalla ta juya ta kalli ɗakin inda jinin ke shiga jikin Baqeer, tace “Nagode Allah ya kara haɗa kanku.” Juyawa tayi suka fara tafiya da Bello. Baba kuwa a ɗaki zirya ya shiga yi don a  yanzu abin yafi ɗaga mishi hankali, “Kai Bashir shigo.” Bashir dake waje abinda yaji Baban nashi ya faɗa kenan, da sauri ya shiga ciki yana sosa bayan ƙeyarshi. “Ka zauna da Baqeer duk wani abu daya faru kayi mini waya ka sanar dani dole zanje gidan Sulaiman Karaye bazan taɓa yadda da wannan iskancin ba, ni muna nan asibiti shi yana kwance a gida hankali kwance.” Yana kaiwa nan ya juya bai ma tsaya ya jira mai Bashir zai ce ba, da sauri ya fito daga waje ya hango Fatima, nan ya ƙarasa inda take jiran adaidaita a mota ya tsaya kusa da ita. Ganinshi yasa ta buɗe gaban motar tana share kwalla ta zauna zuciyarta duk babu daɗi, “Kema yanzu kin fara daina jin magana ta ko? A wani dalili da zaki fito bada izinina ba?” Ta share kwalla tace “haba Alhaji kayi mini adalci mana, wacce uwa ce zata zauna a gida bayan taji halin da ɗanta yake ciki ba tare da taje ta ganshi ba? Sannan ka duba yadda Baqeer yake kamar wanda bashi da rai?” Hawaye kawai take yi tana jin zuciyarta na wani irin zafi, ya fahimceta sarai amma ɓacin rai da halin da yake ciki bazai barshi ya sauƙa daga fushin da yake ba. A ƙofar gidansu yai parking nan ta fita bai ko ce mata komai ba, tana sauka yaja mota ya nufi gidan Sulaiman Karaye. ***** Katon gida ne wanda a unguwar yana daga cikin manyan gidajen masu kuɗi, tun daga waje zaka gane kyan gidan saboda fitulu da aka saka suke haska layin gidan, ba wai kato bane gidan wanda baza’a iya kwatantawa ba, ba kuma cinye rabin layin yayi ba, gida ne dai babba daidai misali wanda za’a iya gina gida uku ko hudu na mai ƙaramin ƙarfi, kasancewar gidan sabo ne yasa yake sake ɗaukan ido. Alhaji Sulaiman Karaye ba wai bakon mutum bane don sun san juna shekaru masu yawa a baya. A gaban gidan yayi parking tare da sanar da mai gadi yana son magana da mai gidan. Kamar mai gadin zai musa sai ya fasa dan Alhaji Sulaiman ya sha sanar dashi duk wani dattijon dake son ganinshi to fa a sanar mishi kome yake yi zai bari ya saurareshi tunda bai san uzurin dake tafe dashi ba. Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻 0020428430 Ishaq Fatima A GTBank KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k #BAQEER #AYUSHERMUHD #UMMASGHAR BAQEER      NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD PAID BOOK ƊANƊANO DAGA TAGWAYE SHAFI NA UKU KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O? INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA. Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 {3} Kishingiɗe yake akan kujera fuskarshi sanye da glasses yana karanta jarida, jefi-jefi yana ɗan kallon tv ɗin dake kunne a cikin falan, shigowar da tayi cikin parlourn ne yasa ya kalleta, sanye take da wani haɗaɗɗen lace wanda yabi jikinta ya zauna ɗas, baka ce daidai misali sannan tana da tsayi wanda hakan yasa ba'a ganin kibarta sosai, mace ce mai fara'a wanda fuskarta kullum a sake, murmushi ta sakar mishi tace "Diatinguished Senate ana sallama da kai." Rufe jaridar yayi yana dariya yace "Wai har kin bani matsayin?" Ta zauna a gefenshi tana cewa "Me za'a fasa? Ai kujera ka hau ta ka gama, sai da kai uban  Zainab da Kabir." Kai ya girgiza yana wani irin murmushin jin daɗi yace "Ke dai Halimah wallahi baki da dama." Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye daga kan kujerar "Bari na leƙa naga wanene?" "Yana waje nace mai gadi yace ya shigo falon baƙi yace a'a." Waigowa yai ya kalleta yace "To me yasa?" Ta ɗan girgiza kai tace "Wallahi ban sani ba, ƙila kunya yake ji ko sauri yake." Bai ce komai ba ya ke kallanta, ta sake murmushi tace "Ai sai naga wajen ma kamar yafi ko?" Yanda ta kalleshi ne yasa ya saki fara'a yace "Wannan matar baki da dama, nafahimta kuma sosai yafi, bari na wuce." Nan ya fito yana sake tabbatar da fitilun waje da fatan a kunne suke, sannan ya taɓa aljihunshi ya tabbatar yana da wadatacen kuɗi, gate ya buɗe ya kalli mutumin dake tsaye a waje ya ɗan juya baya. Daga bakin gate ɗin yace "Assallamu Alaikum." Da sauri Baba ya juya suka kalli juna ido cikin ido, wani kallo suke yiwa junansu na wasu dakiku kafin Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya dake ya kauda kai yace "A'a Alhaji Badaru? Wai kaine dama?" Baba ya sake tamke fuska yace "Kira min yaronka kace ya gaggauta dawowa dan daga nan wurin ƴan sanda zan yi dashi." Nan da nan fuskar Alhaji Sulaiman Ƙaraye ta canza, yayi mishi wani kallo sosai yace "Wai kai har yanzu baka girma da wannan shirmen bane? Sai yaushe zaka girma ka daina magana kamar mara tunani? Ni yanzu kaf garin nan kana tunanin akwai wanda ya isa ya kama min ɗana?" Cike da masifa shima yace "Kai kana ganin nima kaf garin nan akwai wanda ya isa ya nemi halaka ɗana inyi shiru? Ka gaggauta sawa a ƙira shi ko kuma in tattaro dattijan unguwar nan in sanar dasu abinda yayi." Nan da nan gaban Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya hau faɗuwa mai kuma yaron nan ya sake jawo mishi? Waya ya ɗauko ya ƙira Hajiya Halima wacce har yanzu tana nan a zaune a falon tana jiran dawowarshi, ringing biyu ta ɗauka, tana ɗagawa tace "Senate kun shigo ne?" Yasa ƙiran a speaker sannan yace "Ina yaran nan yake?" Cike da mamakin yadda yayi maganar yasa tace "Yana ɗaki a kwance, tun safe yake ɗan fama da zazzabi shi yasa ko abincin dare bai ci ba." Kashe wayar yayi sannan ya kalli Baba yace "To ka dai ji yana gida, menene kake faɗa akai haka?" "Tunda yana gida komai yayi daidai, sai ka sa ya fito ya sanar dani a wani matsayi ya ɗauki ɗan adam da har zai buge ɗana a mota sannan dan rashin imani yaja motarshi ya tafi? Wallahi kai kafi kowa sani akan Baqeer ba abinda bazan iya aikatawa ba sannan duk wani abinda ya sameshi wallahi bazan yarda ba, hukunci kuma dole ne ya fuskanceshi daga hukuma." Da sauri Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya ɗaga mishi hannu yace "Ya isheni haka nan Malam! Kai banda ma saukin kaina har ka isa kazo ƙofar gidana kace zaka yi mini zancen banza? Sannan yaron nan ance maka yana gida tun ɗazu ko kana nufin karya muka yi maka? In zaka je ka nemi wanda ya buge maka ɗan ka kaje ka nema amma ba Kabir ba." Bai jira Baba yace komai ba ya sake cewa "Sannan kana tunanin hukumar ta isa ta kama yaran da bai da laifi ne tace zata hukuntashi?" Ya kalli mai gadi yace "Kabiru ya fita yau?" Da sauri yace "Ni rabona dashi tun jiya daya shiga yau ko masallacin daya saba zuwa bai fito ba" yayi maganar kanshi a ƙasa don kuwa yasan ƙarya ce ya shirga shi Kabir ɗin da kanshi ne ya gargaɗe shi akan kada ya kuskura yace yau ya ganshi bare har aje ga batun fita. Alhaji Sulaiman Ƙaraye ya kalli Baba ya ƙira wayar Kabiru itama yasa a speaker yace "Kana ina?" Cikin sanyin murya yace "Dad ina ɗaki inzo ne?" "A'a naji ance ka fita ne ɗazu." Ɗan nishi yayi yace "Ina zan je ni kam bayan tun dare nake kwance ina fama da zazzaɓi?" Kashe wayar yayi ya kalli Baba da duk jikinshi yayi sanyi, ba dai yaran nan basu ma gama tabbatar da wanda yai hatsarin ba? Hannu Alhaji Sulaiman Ƙaraye yasa a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mai yace "Tunda akan su kazo yiwa yarona sharri gashi ni mai iya baka ne kyauta abinda ya faru a tsakanin mu da ya riga ya wuce." Ganin Baba ya kasa ko motsi yasa ya saka mishi a aljihu ya juya ya koma ciki. Baba Badaru shiru yayi ya dafa kanshi yana da na sanin zuwa ƙofar gidan mutumin da tun asali basa ga maciji dashi, ganin zai shige cikin gidanshi ne yasa shi hanzarin bin bayanshi ya watsa mishi kuɗin daya saka mishi a aljihu yace "Kai dai kasan har abada ba zaka taɓa yin kuɗin da zan zo wurinka maula ba, me jiya ma tayi bare yau?" yayi wani matsiyacin tsaki ya juya ya bar wurin ya ƙarasa motarshi ranshi yana wani irin ƙuna da ɓacin rai, kanshi ya kwantar a kan sityarin motar yana sake tuno hannun Baqeer dake mane da bandage, fuskarshi ya shafa cikin tsananin tashin hankali, ya zai yi in har wani abu ya samu Baqeer? Kenan duk burin daya daɗe yana shiryawa zai tashi a banza? Kenan duk yadda ya sadaukar da komai akan Baqeer ɗin komai zai zo ya wargaje? Nan da nan ya shiga wani irin yanayin da yaji gaba ɗaya komai yayi mishi zafi, wayarshi ce tayi ƙara wanda yasa shi ɗauka. "Alhaji kana ina ne? Meya samu Fatima ne ta shiga ɗaki sai kuka take yi." Abu tai maganar cike da damuwa ita a dole bata san meya samu Baqeer ba. Tsaki yaja yace "Bana son shirmen banza, ita yarinyace da in tana kuka za'a nemeni a waya? Ko kuwa salon raini ne wannan?" Cike da dana sani na makirci tace "Kayi haƙuri Alhaji nayi kuskure." Kashe wayar yayi ya sakata a gefen mota tare da duba agoggon hannunshi ƙarfe sha ɗaya da rabi (11:30) na dare, asibiti ya koma zuciyarshi na sake ɗaukar zafi. Kai tsaye reception yaje ya cire kuɗi daga cikin wanda gomnati ta bashi dan shirye-shiryen gasar da Baqeer zai tafi ya biya kuɗaɗen da ake bukata sannan ya nufi ɗakin da aka kwantar da Baqeer, mamaki ne ya kamashi ganin Bashir baya ɗakin kenan da yace ya zauna yawonshi ya tafi? Alwala yayi tare da yin sallar isha'i a ɗakin sannan ya samun kanshi da dagewa da yiwa Baqeer addu'a akan Allah ya tashi kafaɗunshi a yau ɗin nan dan su cigaba da shirye-shiryensu tunda tafiyar nan dai matsowa take yi, ya daɗe yana addu'a kafin ya dawo inda Baqeer ɗin yake, shiru yayi yana tunanin yadda rana ɗaya rayuwa take neman juya musu baya, yadda komai yake neman rugujewa bayan ya daɗe ya kuma ɗauki shekaru masu yawa yana faman shirya ma zuwan wannan lokacin, yatsun hannunshi ne yaji alamun sun motsa, a zabure ya saki hannun ya kalli Baqeer dake kwance fuskarnan tayi fayau yace "Baqeer? Ka farka? Ni dama nasan bazaka bani kunya ba, na sani kai kaɗai ne wanda baka wasa da farin ciki na, Baqeer buɗe idonka ka ganni kaji ɗan albarka." Motsi yaji yatsun nashi sun ƙara yi sai kuma idanunshi dake fafarniya alamun son ya buɗe su sai dai ya kasa saboda nauyi da yaji kanshi yayi mishi. Acan nesa yake jin ƙiran da mahaifin nashi yake yi mishi sai dai ya kasa tantance muryar waye yake ji, ƙoƙarin motsa ƙafafun shi yayi sai yaji ya kasa gashi dukkanin jikinshi yayi mishi nauyi tamkar wanda aka saka igiya aka ɗaɗɗaure shi kyakkyawan ɗauri irin wanda ake yiwa huhun goro. "Baqeer kana jina kuwa? Daure ka buɗe idanunka ka kalleni nine nan mahaifinka ko na samu nutsuwa nasan cewa wani mummunan abu bai sameka ba" Baban yayi magana muryarshi na rawa don hankalin shi sam ba'a kwance yake ba, fatanshi a yanzu kawai yaga Baqeer ɗin ya miƙe ya samu tabbacin cewa babu wani abu da ya samu ɗan nashi da ya ɗauki dukkanin wani burinshi na rayuwa ya ɗora a kanshi. Kamar mai koyon yadda ake buɗe idon haka ya buɗesu a hankali yana jin kanshi yana sara mishi da matsanancin ciwo, hannunshi na dama ya ɗaga da niyyar dafe kan ko ya samu raɗaɗin da yake yi mishi ya ragu sai dai yaji shi a ɗaɗɗaure ko motsa shi ya kasa yi, a hankali ya juyar da kanshi ya kalli hannun sai ya ganshi a naɗe a cikin cast alamun anyi mishi aiki a hannun shi yasa ya kasa motsa shi abinda yasa shi wurga idanu yana ƙarewa ɗakin da yake kallo yana tabbatar da akan gadon asibiti yake, juyawa yayi ɗaya ɓangaren ya kalli hannunshi na hagu yaga babu abinda ya sameshi sai ya ɗaga hannun ya dafe kan nashi daya matsanta mishi da azabar ciwo. "Sannu Baqeer" Baba dake tsaye a kanshi yana kallon duk abinda yake yi ya faɗa. A hankali ya ɗaga mishi kai alamun amsawa don baya jin zai iya buɗe baki yayi magana. "Ciwo kan yake yi maka?" Baban ya tambayeshi ganin tunda ya farfaɗo yake riƙe da kan abinda ke alamta matsanancin ciwon da yake yi mishi. Ƙara ɗaga mishi kan yayi don ko ƙwaƙƙwaran motsi baya son yayi idan ba ya zame mishi dole ba. "Bayan kan sai ina kuma yake yi maka ciwo?" Ya ƙara tambayarshi ba tare daya lura da yanayinshi ba da sam baya son yawan magana, shi dai burinshi ya tabbatar babu wani mummunan ciwo a jikin Baqeer ɗin ko ya samu a sallamesu da wuri ya koma gida ya fara shirin tafiya gasar da zai je. Da ido yayi mishi nuni da hannunshi mai karayar da shima ya matsanta mishi da ciwo. "Sannu, Allah ya baka lafiya" yace tare da komawa kan kujerar dake gaban gadon ya zauna. Ji yayi gaba ɗaya ya takura da kwanciyar don sam bata yi mishi daɗi, ƙoƙari yayi ya gyara kafafuwan shi ko yaji daɗin kwanciyar sai yaji ya kasa motsa su, yayi-yayi ya motsa kafar yaji ya kasa, a hankali ya ɗaga kanshi ya kalli ƙafafun nashi sai yaga ƙafar shi ta hagu a ɗaure take alamun akwai ciwo a jikinta itama sai dai kuma sam baya jin tana yi mishi ciwo kamar yadda hannunshi ya matsanta mishi da ciwo. Cikin dauriya ya sake ƙoƙarin motsa ƙafar sai yaji ai kwata-kwata ma baya jinta tamkar ba'a jikinshi suke ba don sam baya jin wani feeling a ƙafafuwan nashi. Gabanshi ne ya faɗi saboda yadda ya kasa motsa ƙafafun alhali gasu nan a jikin shi yana kallon su. Cikin rawar muryar data shaƙe saboda daɗewar da yayi bai yi magana ba yace "Baba wani abu ya samu ƙafafuna ne? Gaba ɗaya bana jin su na kasa motsa koda ɗan yatsana ne sai nake ji tamkar ba a jikina suke ba". Tasowa Baban yayi a ruɗe yace "kamar yaya baka jin su tamkar ba'a jikinka suke ba? Kada dai kace mini wani iftila'in ne yake neman faɗo mata bayan na karayar daka samu a hannunka hannun ma na dama wanda dashi kake amfani kana yin zane dasu". A gigice ya fice daga ɗakin ba tare daya ƙara kallon Baqeer ba dake kwance cikin tashin hankali don sosai ya tsorata da yadda Baban yayi magana. "Likita, likita" ya hau ƙwala kiran likita tamkar dai ya manta cewa a cikin asibiti yake kuma marasa lafiya ne a kwance a wajen da basa buƙatar wata hayaniya bare tashin hankali, har ya ƙarasa nurses station bai bar ƙwala kiran likita ba. "Babu likita ne a kusa, don Allah kuzo ku duba mini yarona ya kasa motsa ƙafafun shi," yayi maganar a ruɗe abinda yasa nurse ɗin da tayi niyyar balbaleshi da masifa saboda hayaniyar da yake yi musu ta fasa don ta lura kamar ma ba'a cikin hayyacin shi yake ba. "Muje na gani" tace tana yin gaba ya bita a baya har suka ƙarasa ɗakin da Baqeer ɗin yake kwance. Har gaban gadon ta ƙarasa kafin tace "sannu ko, ina ne yake yi maka ciwo yanzun?" Da hannu ya nuna mata kan shi sai kuma hannunshi mai karayar. "Ƙafar fa ko ita bata yi maka ciwon?" Ta ƙara tambayar shi. A hankali yace mata "Na kasa motsa kafafun nawa duka biyun kuma bana jin feeling ko kaɗan tamkar ba a jikina suke ba har mai ciwon, hatta ƴan yatsun kafata na kasa motsasu." Hannu tasa ta dafa shi tace "Yanzu fa? Ka ji saukar hannuna akan kafar taka?" Girgiza kai yayi alamun a'a. Da ɗan karfi ta matsa kafar ta ƙara tambayarshi "Yanzu fa?" nan ma yace mata bai ji komai ba. "Ina fata dai ba wata matsalar bace ko nurse?" Baban yace gabaki ɗaya hankalinshi ya kai ƙololuwa wajen tashi don bai san ta yadda zai ƙarbi wannan ƙaddarar dake tunkaro rayuwarsu ta ƙarfin tsiya ba. Ɗan girgiza kanta tayi tace "A gaskiya dai bana ce ba amma bari naje na sanar da Dr duk abinda kenan zai sanar da kai, sannu Allah ya baka lafiya, ta cewa Baqeer sannan ta juya ta fita daga ɗakin cikin tausayawa yanayin da Baqeer ɗin ya tsinci kanshi a ciki. Bata jima da fita ba likitan ya shigo shima, a zabure Baba ya miƙe yace "Yauwa likita don Allah zo ka duba mini yaron nan yace baya jin ƙafafun shi tamkar ba'a jikinshi suke ba kuma ya kasa motsa su,"?yayi maganar cikin raunanniyar murya tamkar ya fashe da kuka. Ƙarasawa yayi gaban gadon yace mishi sannu sannan ya hau taɓa ƙafarshi mai lafiyar yana jujjuyata tare da tambayar Baqeer ko yana jin feelings ɗin a yanzu yana girgiza kai alamun a'a. Ya jima yanavmatsa ƙafar yana jujjuyata waje-waje amma Baqeer yace shi baya jin komai. Juyawa yayi ya kalli Baba yace "Dole sai anyi mishi CT scan da MRI kafin mu faɗi wani abu akan rashin iya motsa ƙafafuwan nashi dama rashin jin alamun ƙafafun a jikin shi gaba ɗaya, In Sha Allah ba wani abun damuwa bane sai dai idan an yin zamu tabbatar daga inda matsalar take." "To likita nagode" Baba yace wata irin zufar tashin hankali tana yanko mishi don a yanzu tunaninshi yafi karkata ga yawan kuɗaɗen da za'a kashe don ya tabbata wannan ƙaddarar data afko musu sai ta lashe maƙudan kuɗi kafin a samu akai gaci gashi kwanakin tafiyar su Baqeer ɗin sai matsowa suke yi shi yana kwance a gadon asibiti babu alamun zai warke bare har ya iya taɓuka wani abun arziƙi. #Baqeer #Shalele #Asiya # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD Domin biyan ƙudin littafin nan 500 Naira only Zaki biya ta wannan account ɗin👇🏻 0020428430 Ishaq Fatima A GTBank Ki tura shaida ta +234 809 845 6130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k BAQEER      NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HUƊU KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O? INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA. Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI  - MAGANIN NONO MAGANIN HIPS - MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA - GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO - MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB - MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA - MATSI MAGANIN NI'IMA - MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU.....Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 4 Yau tsawon kwana huɗu kenan bata ji daga Baqeer ba duk kuwa da ya kamata ace tun kwanaki huɗun da suka wuce yazo wurinta don bai taɓa saɓa ranar zuwa wurinta hira ba a tsawon shekarun da sukai tare sai wannan karon, haka nan tayi fushinta na kwana biyu ta huce ganin ko a waya bai ƙirata ba bare ya bata haƙurin rashin zuwanshi wurinta. Ganin da tayi har kwana biyu bai nemeta ba yasa ta bawa kanta hakuri ita ta ƙira shi don a yanzu kam ta tabbatar ba lafiya ba don Baqeer bai taɓa ƙin ƙiran ta a waya na yini guda bama bare har na kwana biyu ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba sai dai kuma koda ta ƙira wayar tashi sai taji ta a kashe hakan yasa hankalinta ya ƙara tashi, haka tayi ta gwada kiranshi amma bata samu ba gashi yau har anyi wasu kwanakin biyu bata ji daga gareshi ba. Gabaki ɗaya ta tashi hankalinta don bata sani ba ko wata ce ta ɗauke mishi hankali yake nema ya juya mata baya, da kuwa ya cutar da ita cuta mafi muni kuwa don sai da ya bari ta zurfafa a cikin soyayyarshi sannan zai yi mata halin mazan zamani da yaudara da rashin cika alƙawari, da yin wannan tunanin sai taji wata irin zufa ta yanko mata gabaki ɗaya jikinta ya ɗauki rawa tana tunanin ta yadda zata iya rayuwa babu Baqeer a cikinta. "Asiya, ke Asiya!" taji ƙiran mahaifiyarta daga tsakar gida. A sanyaye ta amsa sannan ta tashi jikinta babu karsashi ta fito, daga bakin ƙofa ta tsaya tace "Gani Inna." Ɗagowa tayi ta kalleta tace "Dan iskanci kuma daga nan zaki tsaya ba zaki karaso ba?" Cikin sanyin jiki ta ƙarasa kusa da mahaifiyar tata ta samu bakin turmi ta zauna ba tare da cewa komai ba. Kallon tsaf Innar tayi mata kafin tace "Ƙalau kike kuwa kwana biyun nan nake ganinki sukuku kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki?" Hawaye ne taji ya sulmiyo mata daga cikin idanunta tayi sauri tasa ɗan ya tsantsa manuniya ta ɗauke don kada Innar ta gani tace "Babu komai Innarmu, kawai dai kwana biyun ne bana jin daɗi." "Kuma shine zaki zauna da ciwo ba zaki faɗa ba a sama miki magani, shirun zai yi miki magani ne banda shiririta da shirme irin naki? Ga tuwonku nan ki ɗaukar muku sai kizo ki karɓi panadol idan kin gama idan jikin bai warware ba zuwa gobe sai Habi ta rakaki asibiti kiga likita don kin san bana son zama da ciwo." Kwanukan abincin ta ɗauka ta koma ɗakinsu ta dangwarar dasu a gaban Habi ta koma kan katifarsu ta kwanta. Kallonta Habin tayi cikin mamakin yadda take cika tana batsewa, in banda ita ɗin mai haƙuri ce tana kai zuciya nesa da ba ƙaramin haurawa zasu yi ba. "Ba zaki ci bane kika dire mini kwanukan a gabana?" Ta tambayeta sai cewa tayi "Kici kawai ni na koshi." Daga haka bata ƙara yi mata magana ba ta buɗe kwanon tuwon ta hau zuba loma, sai da ta kusa cinyewa sannan ta ƙara ɗaga kai ta kalleta tace "Wai shin don Allah meke damunki gaba ɗaya kin rasa walwalarki kin koma wata sukuku dake, ko duk rashin samun Baqeer ɗin ne a waya duk ya sururutar dake haka?" Ajiye wayar hannunta tayi da mamaki ta kalleta tace "Ya aka yi kika san nayi ta nemanshi bana samunshi, wallahi gaba ɗaya na damu tunda bai saba yi mini hakan ba duk sai na damu nake tunanin ko wata ce ta ɗauke mishi hankali daga kaina yake nema ya gujeni." Tasowa Habi tayi ta dawo kusa da ita ta zauna ta kamo hannunta ta riƙe a cikin nata mai kyaun tace "Haba Asiya kada ki yiwa Baqeer gurguwar fahimta mana tunda dai kin san yaudara bata daga cikin halayenshi, tabbas akwai abinda ya faru daya hana mishi nemanki ko a waya ne ke kuma rashin nutsuwar da kike ciki ya hana miki tunanin neman wani daga cikin abokanshi kibi ba'asin rashin ji daga gareshi sai kika zauna kina ta zullumi da saƙe-saƙen abinda ba gaskiya ba." Gaba ɗaya ta juyo ta rungume Habi cikin murna take furta "Nagode Habi da shawararki wallahi sam tunani na bai kai can ba, bari na kira Salim na tambayeshi nasan In Sha Allahu ba zai ɓoye mini komai ba." Wayarta ƙirar samsung galaxy s20 wacce Baqeer ya saya mata ta ɗauka ta nemo number Salim tayi dialing, ringing biyu sai gashi ya ɗauka da sallama suka gaisa a mutunce sannan ta tambayeshi abokinshi fa ta kwana biyu bata ji daga gareshi ba tana fatan dai lafiya. "Don Allah kiyi haƙuri wallahi laifina ne da ban sanar dake Baqeer na asibiti yayi accident ba, kuma a wajen aka ɗauke mishi a waya shi yasa ko kin ƙira ba kya samunshi." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" tace haɗe da fashewa da kuka "Garin yaya? Tun yaushe yayi accident ɗin? ina fata dai da sauƙi?" Ta jero mishi tambayoyin a jere ba tare da ta jira ya amsa mata ba. "Eh to da sauƙi Alhamdulillah, ya samu karaya a ƙafarshi ta hagu da hannunshi na dama sai kuma ɗan buguwa da yayi." "Kai Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, yana gida ko yana asibiti?" Ta ƙara tambayarshi har yanzu kukan da take yi bai tsaya ba. "Yana asibitin Aminu Kano a male surgical ward." "Allah ya sauƙaƙa mishi ya bashi lafiya, In Sha Allah zan je na duba shi" daga haka suka yi sallama a wayar tana yi mishi godiya. Bayan ta ajiye wayar ta yiwa ƴar uwarta bayani duk kuwa da cewa a gabanta tayi wayar ta kuma ji duk abinda Salim ɗin yace "Ko zaki faɗawa Innarmu ta tambayar mana Babanmu sai muje mu dubashi gobe?" Ta lanƙwasar da kai tana roƙon Habi don tasan ita ɗin ce kawai zata faɗawa Innar ta yarda ta tambayar musu Baban sabida ta iya tsari tsaf zata kalallame Innar har ta yarda. Washegari ƙarfe 9 ta shirya zama tai akan gado ta matse hannayenta biyu tana addu'ar Allah yasa a barta ta fita dan itakam in bata gano halin da Baqeer yake ciki ba hankalinta bazai taɓa kwanciya ba. Habi ce ta buɗe labulen ɗakin nasu, tana ganinta ta miƙe da sauri tace "Ya ya?" Hannu ta miƙa mata tace "Kawo ɗari biyar." Harararta Asiya tai sannan ta ciro a jakarta tace "Gashi, an barni?" Kai ta ɗaga tace "Amma ance karmu daɗe saboda akwai aikin waina da Inna zatai anjima na biki da zamu tayata." Fitowa sukai tare da yiwa Inna sallama suka yi waje. Adaidaita suka hau Habi na tsokanar ta wai ta kusa ganin Baqeer hankalinta ya kwanta. ***** Physiotherapist ne tsaye gaban Baqeer ya dan ɗaga ƙafar tasa kaɗan, yace "Yanzu fa?" Wasu zafaffan hawaye ne suka sake zubowa daga idanun Baqeer, a hankali ya girgiza kai alamar a'a yana kallan Baba dake tsaye ya harɗe hanaye, wanda kana kallansa kasan yana cikin tsananin tashin hankali, da ɓacin ran abinda ke faruwa. Baqeer cike da kuka yace "Baca najin ƙafata gaba ɗaya,a jikina daga nan banajin komai zuwa ƙasa," ya ƙarasa maganar ya na nuna cinyarsa, sake kallan juna sukai da Doctor da Physio ɗin nan wanda ya sake duba takardun dake hannunsa dake ɗauke da result ɗin da ya fito, ya miƙa wa Doctor sannan ya ɗan ja gefe Dr Sajjad yace "Am sorry to say amma muna zargin kafafunsa sun kamu da cutar nan ta paraplegia." Wani kallo Baba yamai dake ɗauke da rashin fahimta. Dr Sajjad ya ɗan yi ajiyar zuciya ya cigaba "Paraplegia ciwo ne wanda yake bangaren paralysis, sai dai shi kasan mutum yake taɓawa daga cinyoyin sa zuwa ƙasa, wanda a dalilinshi mutum bazai iya tafiya ba, Ciwon yana faruwa ne sakamskon ciwo ko hatsari, to shi nashi hakan ya faru ne sakamakon buguwar da yai wanda wanda kashin bayansa ko kwakwalwarsa wani daga cikinsu ya daina aika sako zuwa jijiyoyin da suke kula da ƙasansa, da mun ɗauka ƙafa ɗaya ya taɓa sai dai yanzu da muka sake dubawa munada 95% tabbatarwa akan shine, idan ka duba wannan hoton na X-ray za kaga........" Da ƙarfi Baba yace "Dan Allah Dr dakata, bazan kalla ba kuma ba zai yiwu ba badai Baqeer ɗina ba, duk wannan bayanan naka ni bawai ya dameni bane, dan babu wannan a tattare da yarona, ku dai kuje ku sake duba result ɗin, babu tantama wannan ba nashi bane, sai ku sake duba na waye ya fito shi ma ku nemo mai nashi, kai Baqeer sauko mu wuce gida bansan shirmen banza." Ya ƙarasa maganar yana nufar inda Baqeer ɗin yake. Jikin Baqeer ne ya fara karkarwa, nan danan ya shiga wani yanayi saboda duk yanda yake sake kokarin jan ƙafafunsa ya kasa, ya shiga girgiza kai yana wasu irin zazzafan hawayen wanda duk wanda ya ganshi zai tausaya mai, pillow ɗin bayansa ya cillar ƙasa da ƙarfi ya fara jan jikinshi ta wajen kafaɗar sa, ƙoƙarin sauƙowa daga kan gadan yake amma sam ya kasa banda wajen kafadar tasa da yake iya ja kafafunsa suna nan a tsaye cak, Bashir dake tsaye ne ya riƙe shi yace "Me kakeyi?" Fizge hannunsa yai da ɗan ƙarfi ya sa hannun hagu ya fara ɗago kafarsa ɗaya, jiyai ƙafafun sunyi nauyi ga hannunsa na dama wanda aka mai ɗori saboda karaya wanda hakan yasa bazai iya sa hannu biyu ba, wani irin ihu ya saka ya fara kuka mai sauti sosai, nan ya shiga dukan kafafunsa da hannunsa na hagu, duka yake iya ƙarfin sa wanda gaba ɗaya tausayinsa yasa kowa na cikin ɗakin yai shiru, jan jiki ya sake cigaba dayi da sauri Physio ɗin ya rikishi ya maidashi kan gadan, hannun damansa yaje ɗagawa nan wata azaba ta sake shigarmai, Baqeer hannun hangunsa yasa kawai a saman kansa ya fara dukan kan da karfi yanaji lalai rayuwarsa ta gama zuwa karshe. A fusace Baba ya kalli Dr yace "Bazai yiwu ba, ba abinda ya samu ƙafar yarona kuma babu abinda zai sameta nan gaba, me kuke san cewa? Kuna nufin bazai sake tafiya ba kenan? Yaran da zai zama abin kwatance nan gaba? Yaran da za'a ɗin ga nuna shi ana yabawa basirarsa? Sannan kucemin ya zama gurgu? Nakashashe? To baku isa ba wallahi." Baqeer ne ya sa hannunsa na hagu ya fara jan hannun Bashir dake tsaye kusa dashi, da sauri yace "Menene?" "Bashir taimaka ka daki kafata na tabbatar in wani ne ya daki kafa zanji, ka san ance in kai ne kai abu baka fiya ji ba, dan Allah...." Yai maganar cikin wani irin rauni wanda kanaji kasan shi kaɗai yasan abinda yakeji a ransa, lokaci ɗaya rayuwarsa ta zama wani abu da ko a mafarki bai taba kawowa ba. Bashir ne ya kalli Doctor ɗin wanda gaba ɗaya tausayin Baqeer ya hanashi magana tabbas Baqeer abin tausayi ne domin kuwa saurayi ne matashi ga buri dayawa a kanshi. Physio ɗin ne ya matso ya zare hannun Baqeer daga hannun Bashir yace "Baqeer furzar da iskar dake bakinka." Baqeer bai tankashi ba cikin ɗaga murya yace "Bashir ka taimaka ka daki kafaya dan Allah." Matsowa yai ya ɗan bugi ƙafar yana kallan Baba, Baqeer cikin ihu yace "Da ƙarfi Bashir ka taimaka kamin da ƙarfi banajin komai banaji! banaji!" Asiya ce ta saki ledar dake hannunta wacce ta siyo yoghurt zata kawowa Baqeer, idanunta ne suka ciko taf da kwalla dan tun dazu abinda ake a kan idanunsu akai, Habi ce ta kalleta cike da tausayi. Idanun Baqeer ne ya sauƙa akan Asiya dake tsaye, idanunsa sunyi wani irin jaa suna zubar da wasu zafaffan hawaye, kai ta shiga girgizawa tana jan kafafunta baya-baya, ta sake yin wani taku ɗaya baya tana sake girgiza kai. Habi ta fara ƙoƙarin riƙo hannunta sai dai Asiya ta juya a guje tana hawaye. Baqeer yana kallanta lokacin sai dai yanzu bata ita yake ba ta rayuwarsa yake dan tabbas tsoron abinda ke faruwa yakeyi. Baba ne tsoro ya matsar da Bashir gaba ɗaya yanzu hankalinshi ya gama tashi ya tabbatar kafafun nan sun samu matsala, ya kalli Doctor yace "Yanzu in shine menene magani? Ai dai asibiti babu maganin da baku dashi, nidai karkuce ba magani." Ajiyar zuciya Doctor yai yace " Wannan result din MRI ne wannan ma X-Ray sannan wannan na CT Scan ne sannan munmai test na electromyography wanda ya sake tabbatar mana kafansa baya aiki." "Warkewa? Ita fa?" Baba ya katseshi. Hannu yasa ya ɗan cire abu daga idanunsa yace "Babu magani, sai dai yanda Allah ya bashi iko sai kuma shi da zai dage ya amshi kaddararsa ya fara rayuwa a haka." Baba ne ya shiga girgiza kai yace "Bazai yiwu ba, inalilahi wa ina ilaihi raji'un Allah bazai jarabeshi da hakan ba." Baqeer ji yai komai ya tsaya mai cak hawayen ma yanzu sun kafe nama yajin alamunsu, wani irin yanayi ya fara ji, kanshi na mishi wani irin zafi, hannun hagu yasa kawai ya cigaba da dukan kafarsa iya karfinsa, Physio ɗin ne ya sake riƙeshi yace "Baqeer fara addu'a." Kasa magana yai kawai idanunshi sun yi wani iri kamar wanda baya hayyacinsa, ƙafar kawai yake neman sake kaiwa duka. Baba hawaye kawai yakeyi, Bashir duk yanda bai damu da Baqeer ɗin ba sai daya samu kansa da kwalla, Baba ya kamo hannun Doctor ɗin yana hawaye yace "Zanyi duk abinda kukace amma dan Allah karkuce ba wata hanyar? Ta ina zai iya rayuwa a haka? Kasan yanda na ɗau ra duka burina akanshi? Doctor menai? Menene laifina? Dan Allah na rokeka da Allah ka taimaka mana. Ajiyar zuciya Dr yai cikin wani yanayi yake kallan Baba, jiki a sanyaye Baba ya matso ya rungume Baqeer su kaɗai sukasan abinda suke ji, zuciyarsu na sake wani irin zafi. Bayanshi Baba ya shiga shafawa a hankali, alamun lalashi, Baqeer wanda ko mutuwa akai baka ganin hawayensa saboda dauriyarsa yau shine yake kuka haka, shikanshi Baba bai taɓa ganin kukan Baqeer ba tunda ya mallaki hankalin kansa sai yau, yanzu kuma ga kukan ma ya kafe wanda yake ganin gwara kukan da wannan abin da yakeyi. Baba ne ya kalli Doctor yace "Hannunsa fa? Yaushe kake ganin zai warke?" "Ya danganta da yanayin saurin warkewar jikinsa, kawai dai karku tursasashi akan yai amfani da hannun yanzu ku bari hannun ya warke da kanshi tukun." A fusace Baba ya miƙe yace "To yanzu na gama gane bakin ciki kuke mana, Kai Bashir zo ka goya yayanka ko ka samu kujera mu turashi mu kaishi wani asibitin." Baba yai maganar cikin matukar ɓacin rai. Ku kasance tare da Baqeer da yanda zai fuskanci canji mai karfi a rayuwarsa. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 BAQEER      NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA BIYAR KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O'O? INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?" KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA. Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI  - MAGANIN NONO MAGANIN HIPS - MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA - GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO - MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB - MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA - MATSI MAGANIN NI'IMA - MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU.....Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 5 Da ƙyar likitocin nan suka samu suka lallaɓa Baba har ya haƙura da ɗauke Baqeer ya mayar dashi wani asibitin da yake son yi bayan sun yi mishi doguwar nasiha da bayani kan cewa duk inda ma suka je abu ɗaya ne za'a faɗa musu ga kuma ƙarin kashe kuɗi tunda duk waɗannan tests ɗin sai an sake yi kuma mawuyacin abu ne results ɗin su fito ba irin na nan ba. Haka nan dai ya haƙura ba don yana so ba sai don tunanin irin kuɗaɗen da ya kashe tunda Baqeer ɗin ya kwanta a asibiti gashi har ɗan abinda gwamnati ta basu na shirin tafiyar Baqeer ɗin wajen gasar ya tasarma ƙarewa buƙata bata biya ba sai ma nakashewa da yayi, wannan abu yana yi mishi ciwo idan ya tuna yadda ya sadaukar da komai nashi don ganin Baqeer ɗin ya kai matakin da shi ya kasa cimmawa a rayuwa yanzu ga abinda ya faru yana ji yana gani mafarkin shi na neman tsayawa a mafarkin kawai ba tare daya cika burin shi ba. Wannan takaicin yasa shi barin asibitin ba tare daya ƙara bi takan Baqeer ba da har wannan lokacin yake kukan baƙin cikin ƙaddarar data afko mishi don a ganinshi duk laifin Baqeer ɗin ne da baya iya zama a cikin gidansu yayi abinda zai fishe shi sai ya tafi yawon majalisa gashi nan yanzu asarar da ya janyo musu. Yana tafe a hanya yana ƴan mitocin shi kamar yana yi da wani har dai ya ƙarasa gidan, tun daga soro yake ƙwala kiran sunan Fatima hankali a tashe. A gigice ta fito daga ɗakin a tunaninta ko Allah yayi wa Baqeer ɗin rasuwa ne saboda irin wannan mahaukacin kiran da yake ƙwala mata gashi ya hanata zuwa asibitin ta zauna dashi sai dai idan lokacin ziyara yayi taje ta ganshi ta dawo shima kuma ba kullum ba. Murya a shaƙe tace mishi "gani Mallam, ya wajen Baqeer ɗin? ina fatan dai lafiya?" Jikinta gaba ɗaya ya saki dama kuma tunda Baqeer ya gamu da tsautsayin nan ta ƙara yin sanyi fiye da da duk abinda ake yi a cikin gidan bata iya saka musu baki saboda hankalinta ba a kwance yake ba. Harara ya watsa mata kafin ya bata amsa murya a ɗage "ina fa lafiya bayan duk abinda na kashewa ɗanki duk don na inganta rayuwarshi yaje yayi sanadin da yanzu duk abinda na kashe ya tashi a banza, gashi can likitoci na maganar gurguncewa, kamar ni ace a gidana an samu nakasashe salon maƙiya su samu abun yi mini dariya akai". Kamar a mafarki taji maganar wai Baqeer ɗinta ya zama gurgu ba zai tashi ba, rigijib ta zube a ƙasa dafe da kirji saboda wani irin tsinkewa da zuciyarta tayi. Tama kasa buɗe baki tayi magana tsabar ruɗewa da tayi sai rawa da bakinta yake yi amma ta kasa cewa komai. Haka ya rufe ido yayi ta zazzaga mata ruwan masifa ba tare da la'akari da yanayin firgicin da take ciki ba, har yayi ya gama ya shige ɗakinshi tana nan zube a ƙofar ɗakinta ta kasa motsawa. Abu ce ta kamata ta shigar da ita ɗaki ta kwantar da ita akan gado, su kansu kishiyoyin nata jikinsu yayi sanyi da jin irin ƙaddarar data afkowa Baqeer ɗin don haka aka rasa me magana a cikinsu haka kowacce ta koma ɗakinta suna juyayin wannan al'amari. Tashi tayi zaune jin da tayi ba zata iya zama ba alhalin tasan Baqeer ɗin nacan a wani hali saboda afkowar ƙaddarar nan a rayuwarshi a daidai wannan lokacin ba ƙaramin al'amari bane da dole yana buƙatar lallashi da tausayawa daga wurin makusantan shi gashi uban nashi da zai tsaya ya lallashe shi ya baro asibitin cikin fushi. Hijabin sallarta ta ɗauka ta saka ta ɗauki ƴar purse ɗinta da take ajiyar kuɗi ta fice, kamar tayi wucewarta ba tare da ta sanarwa Mallam ɗin ba ganin irin tijarar da yayi mata a tsakar gida kamar Baqeer ɗin ne ya ɗorawa kanshi larurar sai dai kuma ba zata iya yin hakan ba don ba sabonta bane fita bada izininshi ba bare ma da yake cikin gidan a zaune ba wai baya nan ba. Daga bakin ƙofa taja ta tsaya ta ɗaga labulen ƙofar ɗakin tace mishi "zan tafi asibitin na zauna dashi tunda kai ka dawo". Da yake shima a ƙullace yake da ita ko musu bai yi mata ba sai ma ɗaga kanshi da yayi alamun amsawa, ganin hakan itama tasa kai tayi ficewarta zuciyarta cike da tausayin yaronta da mummunar ƙaddara irin wannan ta afko mishi da kuruciyarshi, tana tafe tana ɗauke hawaye da bakin hijabinta har ta samu adaidata sahu ta tara ta shige ba tare data tsaya sun yi dogon ciniki ba. Lokacin data isa asibitin ta samu babu kowa a wajen shi sai shi kaɗai yana kwance yayi lamo abin duniya ya taru yayi mishi yawa, ya kasa gaskata wai shine ake cewa ba zai sake iya taka ƙafarshi ba, shikenan ana nufin ya zama nakasashe ya tashi daga mai lafiya ya zama gurgu. Yana kawowa nan a tunanin wasu hawaye masu tsananin zafi suka sulmiyo daga idanunshi, hannu tasa tana share mishi hawayen sai dai ita kuma ta kasa tsayar da zubar nata hawayen ganin tun ba ayi wata tafiya mai nisa ba mahaifin Baqeer ɗin daya kamata ace shine na farko wajen ƙarfafa mishi ya ƙarbi ƙaddarar data sameshi ya juya mishi baya. Abun nan yayi mata ciwo ba ɗan kaɗan ba. Sai da suka yi kukansu ya ishesu sannan ta tambayeshi ina Bashir yaje tunda tazo bata ganshi ba bayan kuma shi ne yake zaune a wurin shi yana jinyar shi. "Tun bayan tafiyar Baba shima ya fita bai ce mini ga inda zai je ba" ya amsa mata da shaƙaƙƙiyar muryar data sha kuka ta ƙoshi. Zama tayi akan kujera daga gaban gadon ta riƙo hannunshi mai lafiyar tace "kayi haƙuri Baqeer, kowanne bawa da kake gani yana tafiya ne akan ɓigire na zanen ƙaddararshi, muhimmin abu a wajen mumini shine karɓar ƙaddarar a duk yanda tazo mishi, tunda kaga hakan ta faru da kai to haka nan Allah yake so ya ganka don haka nake horarka da yin haƙuri ka ƙarɓi ƙaddararka a yadda tazo maka In Sha Allah ba zaka taɓe ba. Allah yayi maka albarka ya tashi kafaɗunka.” Baqeer ji yayi ya kasa cewa Ameen a fili, jugum-jugum suka yi a ɗakin gaba ɗaya kowa da abinda yake sakawa a ranshi, wayar tace tayi kara da kamar ba zata duba ba sai kuma ta ɗauko taga ƙanwar Baqeer ce mai bi mishi ke kiran, tayi aure tun shekaru biyar da suka wuce, tana ganin itace ta kalli Baqeer wanda ya ɗan kalli wayar shima, nan da nan wani abu ya sake taso mishi, kanshi kawai ya sake kwantarwa, cike da tausayi ta kashe wayar tace “Ka tashi kaci abinci, na siyoma alale mutumin ka.” Kai ya girgiza a hankali alamar a’a kawai dan baya ji bakinshi ma zai iya tauna abinci. Ta sani sarai ba zai iya cin abincin ba amma dole ne ta karfafa mishi gwiwa, wannan wacce irin muguwar kaddara ce ta samesu? **** Duk yadda Habi take yiwa Asiya magana ta kasa tankata, cike da takaicin abinda take aikatawa Habi ta fizgota tace “Asiya menene hakan? Ya zamu zo asibiti dubiya amma ki gudu? Bayan kin san yana bukatar wanda zai lallasheshi a wannan lokacin?” Fizge jikinta Asiya tayi tace “kinga Malama karki kuma tado mini maganar dubiya, hauka nake kina tunanin zan cigaba da soyayya da Baqeer? Ko baki ji me likita yace bane? Akan ba zai warke ba? Aure zanyi ko kula da gurgu?” Baki Habi ta saki mamaki ya sake rufeta tace “Asiya kina nufin yanzu daga yin wannan abin shine har kwakwalwarki ta tafi lissafin haka? Kin manta wanene Baqeer a gareki? Ko kin manta karatunki ma ba dan shi ba da baki karasa ba? Sannan shekara nawa yayi yana kula dake da duk wasu bukatunki?” “To saka shi nayi? Ko tilasta mishi nayi?” Ta faɗa tana cigaba da tafiyarta, gaba ɗaya Habi kasa motsawa tayi saboda mamaki, tana nan tsaye har Asiya ta shiga adaidaita ta ɗan ɗaga murya tace “Zaki zo mu tafi ko na tafi na barki?” Kasancewar tasan za’a mata faɗa a gida yasa ta ƙaraso ta shiga adaidaitar suka fara tafiya, sam Asiya bata ba ta fuskar magana ba hakan yasa ta yin shiru kawai suka cigaba da tafiya, suna sauƙa Habi tace “Lallai na yarda ɗan adam butulu ne, yanzu duk soyayyar da kike magana iya kacinta kenan?” Tsaki tayi tace “Da nace miki bana son shi ne? Ko kinji na faɗi haka da bakina? Sai dai ni ba auren jinya zanyi ba, kinfi kowa sanin kaf gidan mu babu wanda ya kai ni kyau da diri mai tsari ga karatu na nayi daidai gwargwado, ta ya ina planning na future ɗina magana ta sauya zuwa raino? Bana ɗaukan lokaci akan ajiye duk wani abu da zai kawo mini cikas a rayuwata, ba zanyi aure irin na gidan mu ba da za’ace babu dan haka karki sake yi mini maganar Baqeer.” Tana kaiwa nan bata jira amsar Habi ba ta shiga ciki ranta a matukar ɓace. Gaba ɗaya Habi mamaki ne ke sake rufeta yarinyar da a saninta ko wayar Baqeer ne bata ji ba hankalinta tashi yake yi? Haka ta shiga gida jikinta duk a sanyaye, Inna ta gani zaune tana ɗaura tandar waina, da sauri ta ƙarasa ta gaisheta sannan ta cire mayafinta tana neman amsar aikin. “Waya taɓa Yayarki naga ta shigo rai a ɓace." “Shareta Inna kin san halinta ai ita wannan.” Habi ta faɗa tana neman zama. “A wanke hannu kafin a fara.” Dariya tayi ta miƙe tsaye tana nufar wajen famfo don ta wanke hannun. ******* Umma ce ta kalli agoggo ganin har azahar ta wuce ba Bashir gashi tun ɗazu Baqeer ke nemanshi ya taimaka mishi yaje banɗaki, ita dai wannan abu ya zasu yi da wannan sauyin? Baqeer ne ya kalleta muryarshi a karye yace “Umma dan Allah nemo wani ya taimakeni….” Ya kasa karasawa saboda yanayin da yake ji a ƙasan ranshi, tana buɗe ƙofa tayi kicibis da Salim, wata muguwar ajiyar zuciya ta sauke tace “Salim mun gode, dan Allah taimaki abokinka ka shigar dashi banɗaki.” Gaisheta yayi sannan ya shiga ciki hankali a tashe, ganin Baqeer yayi ya dafa saman goshinshi da hannu, cike da tsokana yace “Wato an farka shine ka dawo da mulkin naka ko?” Kallonshi kawai Baqeer yayi yama rasa abinda zaice gashi a ɗan matse yake, jiki a sanyaye yace “Please Salim ga wheelchair can taimakeni naje toilet.” Bai kawo komai ba ya ƙarasa da wheelchair ɗin yaja ya tsaya yana jiran Baqeer ya hau, sai dai ina duk yanda ya motsa ya kasa, mamaki ne ya kama Salim yace “Wai buguwar haka ta wahalar da kai?” Kai ya girgiza kawai yana ji yana magana to tabbas kuka zai yi, wai yau shine ya koma haka? Jikin Salim rawa ya fara ganin duk yanda yaso daga Baqeer ya kasa ɗaga ƙafar shi, Umma ta shigo ta taimaka da kyar suka sakashi akan kujera, babu abinda kowa ke yi sai hawaye sun kasa ko magana, haka Salim yaja shi banɗaki zuciyarshi na zafi sosai. Suna shigewa Umma ta sake fashewa da kuka a hankali ta ɗauki waya ta ƙira Baba, kamar ba zai ɗauka ba sai kuma taji ya ɗauka, bayan sun gaisa tace “Mallam dan Allah ko zaka kira Bashir yazo babu kowa a gun Baqeer sai yanzu da Salim yazo kasan yana bukatar namiji kusa dashi.” “Wannan kuma ya dame ni ne? Ko kina son ce mini Bashir mai jinya zai koma? To ni bazan tilastawa yarona ba in yaso yaje ya zauna in bai so ba ra’ayinshi ne, ke a matsayinki na mahaifiyarshi kisan yadda zaki yi.” Jin kalamanshi tayi kamar an watsa mata ruwan zafi tace “Mallam ka manta wanene? Baqeer ne fa?” Tsaki yayi yace “Da can bai san shi wanene a gareni ba sai yanzu? Sanda nake mishi faɗa kina ina? Sannan ki gagauta sanar dashi ya tabbatar ya fara rike pencil dan akan shi bazan sadaukar da burina ba, in bashi da ƙafa ai yana da hannun da zai yi zane, lokacin ni da kaina zan kai shi Abuja a keken guragun muje muyi komai tare, wannan shi kaɗai ne uzurin da zan sake yi mishi, kina zaune kin bar yaron nan ya lahanta kanshi kun cuceni daga ke har shi wallahi, sai dai bazan bari ku salwantar da abinda na dade ina fata nake addu’a akai ba shekara da shekaru.” Yana kaiwa nan taji ya kashe wayarshi, daga banɗaki taji ihun Salim, da gudu ta tashi ta ƙarasa tace “Salim lafiya?” A tsorace ya buɗe ƙofar yace “Umma.” Idanu ta zaro ganin Baqeer a yashe a ƙasan banɗaki….. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*       *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SHIDA* *Assalamu Alaikum* *Hajiyata kinada labarin kayan Egypt da muke kawowa kuwa to in baki saniba matso kusa kiji Ainam stockpile mun kawo muku kaya na gani na fada na gayu wainda sai wance da wance ake gani dasu ba kano made bane kunsan a koda yaushe burinmu mu kawo muku unique abu.Available ne ba jira zakiyi akawo ba muna bada sari muna kuma aikawa koina,duk abinda kike bukata hajiyata ki latsoni kawai* *wa.me/2348146766440* *Ko baki siyaba yanzu kiyi saving number ta murika ganin status din juna* *Nagode* "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, garin yaya ya faɗi?" Tayi maganar tana mai durƙushewa a gabanshi, hannu tasa tana ƙoƙarin juyo dashi don ta fuska ya kife sai dai ta kasa saboda jikin girma gashi kuma ƙarfi ba ɗaya ba. Ɗagowa tayi ta kalli Salim tace "ko zaka fita ka nemo masu taimaka mana a ɗagashi don zai yi wuya mu iya tashin shi daga ni sai kai kawai?" Yana fita ya samu wasu bayin Allah ya roƙesu da su taimaka zasu ɗaga mara lafiya ne ya faɗi. Haka Umma tayi ta musu godiya tana share hawayen tausayin Baqeer da yadda lokaci guda Allah ya juya halittarshi ya tashi daga mai lafiya zuwa nakasashe. Sai a sannan Salim yasan ƙaddarar data afkawa Baqeer ɗin, zama yayi shima yana share hawayen saboda tsananin tausayin Baqeer ɗin daya kamashi. Wai yau Baqeer ne a kwance a haka, mutum mai ji da lafiya da ƙarfi shine ƙaddara ta juyar da rayuwarshi haka. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum babu mai iya magana daga shi har Umman Baqeer ɗin bare kuma shi Baqeer da tunda ƙaddarar nan ta afka mishi ya daina iya magana idan har ba ta zama dole ba, komai aka yi nashi idanu ne saboda shi kaɗai yasan irin ƙuncin da yake ji tattare da zuciyarshi. ***** A gidansu Baqeer kuwa Jamila ce ta fito tsakar gida tana ta surfa ruwan bala'i akan Umma ta fice tun rana ta bar gidan bata dawo ta ɗora sanwar dare ba gashi har rana na neman faɗuwa dama kuma ba wani abincin kirki ta dafa musu da rana ba saboda tana sauri ta fice ta tafi asibiti wajen ɗan da aka fifita fiye da kowanne ɗa a cikin gidan. Abu tana daga gefe tana yi mata famfo murya ƙasa-ƙasa dama kuma zai yi wuya kaji ana irin wannan faɗan da Abu, ta dai fi kauri wajen haɗa husumar ta koma gefe tana zuga amma ba dai kaji muryarta ba don ga wanda bai san halinta bama ba zai ce da sakun hannunta cikin faɗan da Jamilar take yi ba, dama kuma mafi yawanci ingiza mai kantu ruwa take yi mata, tare zasu kitsa abunsu amma sai ta koma gefe tayi shiru abunta tamkar ba da ita ake yi ba koma ta kama wata sabgar ta daban ita kuma Jamila har yau ta kasa gane halin Abu bare ta daina ɗaukar zugarta. Fitowar Baban daga ɗaki bai sa Jamila ta sassauta murya daga faɗan da take yi ba don a cewarta ta gaji da rainin wayon da Umman Baqeer ɗin take yi musu, tun wuri gara ya ɗauki mataki don baza su yarda ta dinga fakewa da jinya tana ficewa tana barinsu da yunwa ba alhalin su ranakun girkinsu ba haka suke yi ba, ko kuwa dai baƙin ciki ne don tasan sune masu ƙananun ƴaƴa a gidan. Haka dai tayi ta faɗa tana sakin maganganu marasa daɗi akan Ummar Baqeer ɗin. Ai kuwa ya cika yayi fam don dama mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki don daga Fatimar har ɗan nata haushinsu yake ji, gani yake yi kamar shirinsu ne yasa aka ce mishi Baqeer ɗin ya zama gurgu alhalin ya mance ita ɗin uwa ce babu ta yadda za'a yi taso ɗanta da nakasa ko miye dalili kuwa. A fusace ya danna kiran number Umman, tana ɗagawa ko amsa sallamar da tayi mishi bai yi ba ya hau cewa "Da kika tafi kika yi zamanki wani kika ajiye da zai yi miki girkin, ko kuwa shikenan don danki baya da lafiya mutanen gida ba zasu ci abinci ba?" Murya a sanyaye duk kuwa da ranta ya ɓaci da hargagin da yake ta kira yana yi mata tun ɗazu tace "A'a Mallam zan dawo mana sai dai fa har yanzu babu kowa a wurinshi, haka zan taho na barshi shi kaɗai alhalin babu mai kula dashi bayan kuma kasan komai sai anyi mishi tunda ba iya tashi zai yi ba". "To sai miye idan ba zai iya tashi ba, haka zai dawwama ba zai koyi yiwa kanshi hidima ba kenan tunda gaki uwar son ƴaƴa kin saki hidimar komai da kowa kin kama tashi, wallahi idan magariba ta rufa baki dawo ba Fatima ranki ne zai yi mummunan ɓaci idan kika yi wasa ma sai na hanaki zuwa asibitin gaba ɗaya naga ta tsiya" daga haka ya kashe wayarshi sai faman fitar da huci yake yi. "Zuwa zan yi asibitin nasa a sallameshi, gara yazo ya fara shirin tafiya wajen gasar nan don wallahi bazan yarda daɗaɗɗen burina ya tashi a banza ba, rashin ƙafa ai ba rashin hannu bane bare ace ba zai iya zane ba" yayi maganar cikin ranshi haɗe da yin ƙwafa don sosai yake jin ciwon nakashewar Baqeer ɗin, a ganinshi mai lafiya ma yaya ya ƙare a irin waɗannan wuraren bare kuma gurgu. Acan asibiti kuwa a sanyaye Umma ta sauke wayar daga kunnenta tana tunanin yadda za'a yi ta tafi ta bar Baqeer a cikin wannan halin bayan babu wani a wurinshi da zai zauna ya kula da shi, Bashir ɗin dake zama yana jinyarshi ita tunda tazo ma bata ganshi ba. Gefen hijabinta tasa ta ɗauke hawayen daya sulmiyo daga cikin idanunta don bata son yin kuka a gaban Baqeer sai dai abun nema yake yi yafi ƙarfinta, ga dukkan alamu ubanshi nema yake yi ya cire hannu daga al'amuranshi babu tausayi ba tausasawa kamar ba ɗan shi mafi soyuwa a wurinshi ba, ashe duk mutanen duniya halinsu ɗaya sai kana da amfanin da zaka yi musu suke yi da kai daga inda ka rasa wannan damar sai su juya maka baya. Ɗagowa tayi ta kalli Salim dake tare dasu tun ɗazu tace "don Allah kana nan naje gida na dawo, kaga yanayin larurarshi ai ba a barshi shi kaɗai ba" "To Umma, sai dai kuma da kin haƙura da dawowar tunda magriba ta kawo jiki dare ne zai yi jinyar namiji kuwa sai namiji, In Sha Allah zan kula dashi". "To kuma ayi haka daga zuwa dubiya sai ka ɓuge da zaman jinya, idan kana da wani uzurin fa kaga ai zaman ya zama takura a wurinka" cikin ranta tana jin babu daɗi don bata so ta takura mishi da abinda bai zame mishi dole ba. "Babu wata takura Umma, ni da Baqeer ai abu ɗaya ne, nasan ko nine kwance a wurin nan sai inda ƙarfinshi ya ƙare wajen kulawa dani to don me yasa ni bazan yi mishi hakan ba, kiyi tafiyarki Umma In Sha Allah zan kula dashi kamar kina wajen in yaso goben kya dawo". Wani daɗi ne ya lulluɓeta ganin Allah ya rufa mata asiri ya kawo mai tallafa mata ya tayata jinyar Baqeer abinda tasan ita ba zata iya ba sai dai ƙarfin hali tunda ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba ga kuma girma daya fara cimmata abubuwan da take iya yi a da yanzu nema suke yi sufi ƙarfinta. Tashi tayi ta matsa gaban gadon na Baqeer da ya samu bacci saboda allurai da magungunan da ake bashi masu sakashi yawan bacci ta dafa kanshi tana karanto mishi addu'o'in neman waraka tana tofa mishi, sai da ta gama sannan ta juyo ta kalli Salim tace "Ga amanar ɗan uwanka nan na bari a hannunka Salim don Allah ka kular mini dashi ka kuma yi haƙuri dashi saboda yanayin larurarshi yanzu dole sai ana yi mishi uzuri. Allah yayi muku albarka". Cikin sanyin jiki ta juya ta fice daga ɗakin tana ji kamar idan ta tafi wani abu ne zai samu Baqeer ɗin. A hankali Baqeer dake kwance ya buɗe idanunshi da suka kaɗa suka yi jaa, wasu zafafan hawaye ne suka taru a cikin idanun a kwance kawai yake yayi kamar mai bacci amma idanunshi biyu dan baya ji ma bacci zai iya ɗaukan shi a halin da yake ciki yanzu, a hankali ya ƙara maida idanunshi ya rufe yana sake duba abubuwan dake faruwa dashi wanda ko a mafarki bai taɓa tunaninsu ba. Kalaman Salim ne suka katse mishi tunani da yaji yana cewa “Hello Asiya? Kin samu ganin Baqeer ɗin kuwa?” Shiru yayi dan ya saurari me Asiyan zata ce sai dai bai ji komai ba sai muryar Salim daya sake cewa “Asiya? Hello? Hello?” Sai kuma yace “Hala ba network ne dan bata ji.” Baqeer ya sake maida ido ya lumshe yana hango idanun Asiya a ɗazu ya tabbatar ta shiga cikin damuwa dan shi kaɗai yasan yadda take kaunarshi, ya ƙannenshi zasu yi in suka ji abinda ya sameshi? Wannan tunanin ne yasa ya dan damtse idanunshi yana addu’a a cikin ranshi. ****** Ƙarfe shida da wasu Umma ta sauka daga adaidaita ta shiga cikin gidan, babu kowa a tsakar gidan wanda hakan yasa tayi tunanin ko sallah suke yi, sai data haɗa murhu tasa ruwa a tukunya sannan ta shiga ciki tayi alwala tayi sallah, a sujjadarta ta karshe addu’a kawai take yiwa Baqeer wanda ko miƙewa ta kasa yi, ta daɗe a haka sosai kafin ta dago ta ƙarasa sallar, ta cire hijab ɗinta sannan ta fito waje hannunta ɗauke da robar da zata yi amfani dashi gun yin talge, cak ta tsaya ganin ruwan nata babu alamun zafi bayan ta tabbatar yaci ace ya tafasa a lokacin, da mamaki ta ke kallon tukunyar. “Umma ni na juye ruwan wanka zan yi, kin dai san tun jiya ina asibiti wurin Baqeer.” Da sauri ta kalli Bashir cike da jin daɗin ganinshi tace “Bashir mun gode sosai Allah ya ƙara haɗa kanku, dan Allah gobe zaka iya komawa wurinshi? Yau Salim yace zai kwana.” Jamila ce ta fito kamar wacce dama take jiran kiris tana tafa hannu kafin tafe “Tab! Yau naga abinda ya hanani sukuni. Ɗan lelen nawa ne kike maganar ya zama mai jinyar Baqeer? Ko kin manta yadda kuka dinga nuna mana mu bamu isa ba a gidan nan? Ko kin manta yadda Malam yasa ɗanki makarantar masu kuɗi ya maka namu a ta gomnati? Sannan duk abin nan kina kallo shine yanzu yaran nawa kun ganshi da lafiyarshi jinin da aka yashe mishi bai isa ba sai an haɗa ga gangar jikinshi?” Sakato Fatima tayi kafin ta koma ta zauna kawai ta janyo garin tuwo dan tasan halinsu yanzu tana tankawa zasu maida gaba ɗaya laifin abinda ke faruwa kanta, wani banzan kallo Jamila ta mata sannan tayi wa Bashir alamar ya wuce yaje yayi wankanshi. ******* A hankali ta kwankwasa ƙofar ɗakin sannan ta buɗe zaune yake akan gado hannunshi ɗauke da controller na game, yana ganinta yayi dariya yana yin game ɗin yana cewa “Mummy ni kam pretending ɗin rashin lafiyar nan ya isheni, I just wanna go out and chill.” Zama tayi daga gefen gadon ta ɗan harareshi tace “Kasan da haka wa yace ka aikata abinda kayi?” Cak ya tsaya sannan ya kalleta narai-narai da ido yace “Har kin gano?” Hannu ta kai saitin kunnenshi da sauri ya rufe kunnen yace “Allah Mom I didn’t do it on purpose yaron ne kawai ya taho yayi jumping a gabana, ke kin san yadda nake tu(i da hankali, sannan tsoron ruining reputation na Dad yasa ban tsaya a wurin ba.” Harararshi ta sake yi tace “Yanzu me kake tunanin zai faru in akwai wanda ya ganka? Sannan kama sa ɗan gidan waye?” Da mamaki yake kallonta yace “Do I have to know?” “Ɗan gidan Badaru…..” Cikin ɓacin rai yaja tsaki yace “I just hate that guy wallahi tun muna yara, wai dama shine? Matslarshi ce sannan da nasan shine ma bayan na bige shin sai na takashi da mota zan wuce.” “Kai dai baka ji ba kuma zaka daina ba ko? Yanzu da ban ɓoye akan kana gida ba me kake tunanin zai biyo baya?” Kallonta yayi ya kwantar da kanshi a kafaɗarta (Wai su a dole turawa) yace “Sorry Mummy! Zan kiyaye.” Ta dan shafi sumar kanshi tace “Yauwa please ka kula, sannan Zainab ta kusa dawowa ɗazu mu kayi waya da ita.” Baki ya taɓe yace “I don’t care, kin san yadda yarinyar nan ta rainani, tana ganin yanda Nabila take girmamani ita da take Aunt ɗina ma.” Murmushi kawai Mummy tayi don in da sabo sun saba, ta fito daga ɗakin ta nufi part ɗin mai gidan nata. ****** Baba ne ya kalli Dr yace “Ni dai koma menene ina so ku sallameshi gobe zan zo da safe mu tafi, yana da abubuwa da yawa a gabanshi wanda bazan iya barinshi a asibiti ba, sannan kuma bana ji kuna da wani abinda zaku iya yi mishi kuma, gwara ni in na dage zan koya mishi ya dawo yanda yake da.” Da mamakin kalamanshi Dr yace “Wai Alhaji ni kam kasan risk na abinda kake magana akai kuwa? Taya za kai pushing ɗin shi bayan kasan wannan ciwon ba wai abin wasa bane? Magana fa nake yi maka akan ba zai iya komai da kafafun ba.” Hannu ya ɗaga mishi yace “Ɗana ne kuma ni ke da iko dashi, yana da gasar da zai yi wanda ni bazan bari ku salwantar mishi da shi ba, zan zo gobe.” Yana kawai nan ya fito daga office ɗin kicibus suka yi da Bello wanda gabanshi ke faduwa na jin kalaman Dr dan ya zo duba Baqeer ya hango Baba shine ya zo yayi mishi ya mai jiki ya tsaya a waje akan su gama magana daga nan kunnuwanshi suka juyo mishi waɗannan kalamai. Wani mugun kallo Baba yayi mishi yace “Nasan dama kana da ƙarancin tarbiyya amma ban san abin naka ya kai har ka dinga laɓe ba.” Da sauri Bello yace “Baba ba haka bane nazo duba Baqeer ne na ganka shine nazo na gaisheka.” “Kaine ka kira Baqeer akan yaje majalisa ranar da abin nan ya sameshi?” A tsorace Bello ya kalleshi ya fara neman tattaro amsa, juyawa kawai Baba yayi ya wuce ya barshi anan wajen a tsaye. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 Umm Asghar Ce Da Ayusher Muhd BAQEER      NA AYUSHER MUHD       DA UMM ASGHAR RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA BAKWAI Kai kawai Baqeer ya kauda daga inda Salim yake zaune yana ƙoƙarin kai mishi abinci bakinshi, hannu yasa ya amshi cokalin da hanunshi na dama, faɗuwa cokalin yayi saboda karayar dake hannun, sake ɗauka yayi nan ma spoon ɗin ya faɗi, gaba ɗaya Baqeer tsoron abinda ke faruwa dashi ne ya sake kamashi, nan da nan yasa hannun hagunshi ya ɗauki cokalin yana jin wani irin zafi da raɗaɗi na sake dabaibaye mishi zuciya, shi kanshi Salim tausayinshi ne duk ya rufeshi, nan Baqeer yayi spoon ɗaya wanda yake jin abincin ya koma mishi tamkar maɗaci saboda ɗaci, da ƙyar ya haɗiye na bakinshi sannan ya maida cokalin ya ajiye kafin ya rufe ido. Addu'a kawai ya samu kanshi dayi akan Allah yasa duka waɗannan abubuwan dake faruwa dashi su kasance mafarki ne ba gaskiya ba. Sallamar Bello ce tasa ya sake runtse idanunshi, yana ji Bello na yiwa Salim magana akan halin da Baqeer ɗin ke ciki yace "Salim ashe abinda ke faruwa kenan? Ni ina can Kaduna ban san aminina na cikin wannan halin ba? Wallahi ranar da muka kawoshi asibiti washegari na tafi Kaduna akan akwai wani aikin zane da wani yake so za ayi wai na decoration ne za'a saka a hotel din daya buɗe, Baqeer ne ya haɗani da mutumin saboda shi ya fara nema shi kuma sunata shirin tafiya Baba baya so yayi nesa da gida, sam zuciyata bata kawo abin ya kai girman haka ba." Cike da jimami Salim yace "Ayya!" "Amma dai ba da gaske bane kafafun Baqeer sun samu matsala ko?” Bello yayi tambayar cike da tsoro, Salim gaba ɗaya kasa amsa mishi yayi sai dai kawai ya girgiza mishi kai alamun babu magana “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Kawai Bello yake faɗa gaba ɗaya ya kasa iya cewa komai, meke faruwa da aminin nashi haka? Mutumin da future ɗinshi a shirye take taya wannan mummunar ƙaddarar zata afka mishi? Da ƙyar ya jinginar da kanshi jikin bango yana maida ajiyar zuciya, ya daɗe a haka kafin yace “Amma dai babu abinda ya samu hannunshi ko?” Salim ya sake girgiza kai yace “Wannan karaya ce kawai sai dai matsalar warkewar ba yanzu ba.” Hankali a tashe Bello ya matso kusa da Baqeer cike da wani irin mugun tausayi, zuciyarshi na wani irin harbawa na tsantar tausayin abinda ke faruwa da abokin nashi. A hankali Baqeer ya buɗe ido ya zubawa Bello dake tsugune kusa dashi, idanunshi sun yi jaa sosai, da ƙyar ya iya ƙaƙalo wani wahalallen murmushi wanda iyakacin sa leɓensahi cike da jimami yace “Baqeer wannan wani ibtila’i ne ya samemu?” Kai kawai Baqeer ya girgiza dan baya jin ma bakinshi zai iya furta wani abun. Bello ya cigaba “Ɗazu Yallaɓai ya kirani ina hanya akan yana ta nemanka bai sameka ba idan ya kira Baba kuma sai yace mishi baka gida, wai yana sin ku haɗu gobe akan maganar tafiyarka, yanzu ya zamu yi da wannan ƙaddarar?” Idanun Baqeer ne suka cigaba da kara kaɗawa suna yin jaa sosai, babu shakka shidai kam rayuwarshi ta ƙare, da ace babu karayar hannun nan ma da watakila abun yazo mishi da sauƙi, ina zai kai burin daya ɗauka akan gasar nan? Auren da zai yi fa? Ƙannenshi daya yiwa alƙawari zai taimakawa su samu jarinsu mai ƙarfi fa? Mahaifinshi da yake jira ya faranta mishi da kyautar daya samu fa? Nan da nan ya shiga jin wani abu na harbawa a saman ƙirjinshi, nan ya fara fitarda numfashi da ɗan sauri da sauri, da sauri Bello ya riƙeshi yace “Baqeer ya isa haka nan, dan Allah ka rufa mana asiri kar wani abu ya sake samunka.” “Allah gani nan a hanunka, ka ɗauki raina kowa ma ya huta da wannan wahalar da nake shirin ɗaura musu, ni ban faranta musu na sauƙaƙa musu ba gashi ina ƙoƙarin sanyasu cikin uƙuba.” Abinda Baqeer kawai ke faɗa a cikin ranshi kenan, cike da tausayi Bello ya ajiye ledar dake hannunshi ya kalli Salim yace “Bazan iya zama anan ba zuciyata sai ta buga saboda tausayin Baqeer inda wani abin ka taimaka ka kıranı ka sanar min zan dawo gobe In Allah ya kaimu.” Yana kaiwa nan ya fita da sauri bai tsaya ba sai a cikin motarshi, shiru yayi yana nazari dan ko motar ya kasa kunnawa, can ya ɗauki waya ya kira Asiya. A lokacin tana kwance akan gado ranta duk a ɓace, Habi na zaune a ɗakin tana gugar kayansu da suka bushe dan tun sassafe tayi wanki, Asiya sam bata wankin kayanta in har Habi na gida a ganinta ita babbar yarinyace mai karatun degree wacce tasan ƴan dabarun daɗin bakin da take tasa Habi tayi mata komai. Habi ce ta kalleta tace “Asiya kin kira kinji ya jikin Baqeer ɗin kuwa?” Tsaki tayi tace “Habi dan Allah ki bar maganar nan, kema kin san bazan kira ba kin san taurin kaina.” Ajiyar zuciya tayi dan tasan halin yayar tata, wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka ganin Bello ne bata san me zai ce mata ba saboda har yanzu a ƙasan ranta tana skn Baqeer. Tana ɗauka suka gaisa yace “Asiya kin je duba Baqeer kuwa?” “Naje amma ban shiga ba.” Ta faɗa tana kauda kai, cike da zargi yace “Me yasa? Ko tausayi?” “Umm” kawai tace tana ƙoƙarin kauda maganar da cewa “Kaje Kadunan?” Daɗi ne ya kamashi ganin yau ta tambayeshi abinda ya shafeshi yace “Naje, kuma Alhamdulillah na samu kuɗi sosai sannan sun ce zasu sake kirana saboda sunji da ɗinaikin da nayi musu.” Kai ta jinjina tace “Congrats Allah ya ƙara buɗi ni zan kwanta.” Da sauri yace “Baqeer har da hannunshi suka karye fa?” Cikin sanyin murya tace “Na sani, sai da safe.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar, Bello ne ya dafa kanshi yana jin wasu tunanuwa na ɗarsar mai a zuciya, waya ce ta shigo wayarshi, ganin sunan Yallabai yasa yayi ajiyar zuciya ya ɗauka cikin fara’a suka gaisa sosai Yallabai ne yace “Wai ku haka ake abu? Taya zan yita neman amininka wayarshi a kashe? Ko wayarce ta lalace ai zai iya kirana ta wurinka ko ta wurin Babanshi, menene kuke yi haka ne? Bayan kun san jibi zamu je ganin Deputy Gomna akan tafiyar mu.” Bello yayi ajiyar zuciya ya kasa magana, ran Yallabai a ɓace yace “Bana son iskanci fa, wani abun kuke ɓoye mini ne?” Bello ya sake ajiyar zuciya yace “Yallabai ka kira Baba ka tambayeshi ni tsoron yin magana nake yi.” A fusace yace “Kenan dai wani abun ya faru? Da kaina zan je gidan gobe.” Bello yace “To Yallabai in dai da taimakon da kuke buƙata ku sanarmin.” Kashe wayar yayi ya fara wani tunani kafin ya tada motar ya bar wurin. ****** Washegari da safe Baba da kanshi yazo yace sai an sallami Baqeer, duk yanda ake lallaɓashi akan yayi haƙuri ya barsji ya ƙara samun sauƙin bai yarda ba, haka nan suka sakashi a keken guragun da Baban ya siyo suka turashi zuwa mota shi kuma ya tsaya ya amshi magungunan da aka rubutawa Baqeer ɗin ya fito don shi dai ba zai bari su ruguza mishi shirin da suka daɗe suna yi ba. Da ƙyar Bashir da Salim suka cicciɓeshi sakashi a cikin motar. Salim ya kalli Baba yana son yace zai bisu amma yasan halin faɗan Baba da rashin son yaga Baqeer da abokai. Baba har yaje zai shiga mota sai yace “Kai da mota kazo?” Da sauri yace “A’a adaidaita na shigo.” Ya sani sarai magana Baban ya faɗa mishi tunda shi dai ba motar nan ce dashi ba, alamu Baba yayi mishi da kanshi akan ya shiga baya kusa da Baqeer, hakan yasa Salim shiga, duk wannan abinda ake yi Baqeer na zaune idanunshi na kallon window yana hango satin daya gabata fa yazo duba Auntyn Asiya asibitin nan ta haihu suka zo tare suna tafe suna ƴar soyayyarsu, cike da farin ciki da annashuwa, wai yau gashi sai dai ya kalli waje ta window amma babu damar ma ya taka? Yana jin Salim ya shigo har suka fara tafiya babu mai magana a cikin motar, can Baba ya kalli Bashir yace “Kai kuma yaushe zaku koma makaranta?” Da mamaki Bashir ɗin ya kalli Baban dan tun wancan wata aka koma ya sanar da mahaifin nasu amma yace bashi da kudi ya jira in an biyasu kuɗin tafiyar Baqeer zai bashi yayi registeration ɗin, da aka turo kuɗin ya sake yi mishi magana sai Baban cewa yayi ya jinkirta yaga nawa Baqeer ɗin zai bukata sai ya duba ragowar in zai isa a bashi yayi registration, shima tun daga nan bai sake bin Baban da maganar makarantarshi ba, a rayuwa har mamakin Baba suke yanda bai damu da kowa ba a cikinsu banda Baqeer din, bai damu da rayuwar da suke yi ba sai ta Baqeer wanda hakan yasa kiyayyar Baqeer ta gama shiga zuciyoyinsu kaf ɗin su babu mai sonshi har kuma wannan lokacin babu mai tausaya mishi, su ganin hakan ma suke yi da Allah ne yayi musu sakayya. Yawun bakinshi ya haɗiya yace “Baba ka manta nayi maka maganar tun kwanaki?” “Ka shirya gobe ka sake yi mini magana sai kaje ka biya, dan naga kai har yanzu ba hankali kayi ba baka san abinda ya kamata ba, karatun nan shine gatanka.” “Toh” kawai ya iya cewa don bai ma san me zaice ba kuma, a ƙofar gida suka sauka, haka suka kinkimeshi da ƙyar aka saka shi a keke sannan suka turashi ciki. **** Suna zaune a tsakar gida, Abu dake sana’ar maganin mata tanata dafa tsumin ta a gefe, tana zaune akan kujera irin ƴar tsugunno ɗin nan, ita kuma Jamila tana gefe tana tsince shinkafar da zata yi girkin rana dashi dan yau itace da girki, suna yi suna gulma da habaicin Fatima wacce ke zaune a cikin ɗakin ta tasa carbi a gaba tana addu’a, ita dai kawai addu’a take Allah ya sassauta musu, ta sani jarabawa ce daga Allah sai dai tana fatan Allah ya basu ikon cinye jarabawar. Kamar daga sama taji muryar Abu tana tafa hannu tana salati, Jamila hankali a tashe ta riƙe haɓa tace “Yau me zan gani? Duwawo ya mutu ya bar zani? Baqeeru? Ya ka fita da ƴan ƙafafunka zaka dawo mana a kujerar guragu? Yau ni naga abinda zai kasheni? Wai abin nan dai da gaske ne ashe?” Abu ce ta ɗaura da salati tana ajiye ludayin da take tuka tsumin dashi tana cewa “Baqeeru? Wannan wani ibtila’in ne ya samemu?” Baba ne ya kauda kai yace “Ku shiga dashi ɗakin shi.” Salim dake tura keken ne ya cigaba da turawa suna shiga Fatima ta taho da gudu ta zubawa Baqeer ido wanda ke zaune akan kujera kai baka ce yana magana ba, kallon komai na wurin kawai yake yi, idanunshi ne suka sauka gun Umma dake jikin ƙofa tana ganin yadda aka dawo dashi gida bayan bai ko gama warkewa ba. “To sannunku ku fita.” Baba yayi maganar yana kallon Salim, fita yayi jiki a sanyaye, Fatima tana ƙoƙarin shiga ɗakin Baba ya ɗaga mata hannu sannan ya maida ƙofar ɗakin ya rufe, cak ta tsaya a bakin ƙofar cikin tashin hankali dan ita kam tasan ba ƙalau ba. Baba ne ya maida idanunshi kan Baqeer wanda ke zaune akan kujera, turashi Baba yayi zuwa gaban table ɗin da yake zane, da mamaki Baqeer ke kallonshi, Baba ya cire takardar kai yasa sabuwa, ya saitashi yadda ya kamata, pencil ɗin da yake amfani dasu ya ɗauko ya miƙa mishi yace “Bismillah!” Daga waje kuwa Abu ce ta kalli Fatima tace “Me kike yi a tsaye a bakin ƙofar ki shiga mana?” Fatima ta kalli ƙofar ba dai abinda take tunani bane yake faruwa a ciki? Nan da nan zuciyarta ta shiga bugawa, ya zata yi? Ga tsoron Malam take balle ta kwankwasa ƙofar ɗakin. Jamila ce tace “Ba dai yaron da aka kawo daga asibiti bane za’a sashi aikin da aka saba?” Abu ta sake tafa hanu tace “Ai shine ma, yo dama daga sun shiga ɗaki sun kulle ai kowa yasan kwanan zancen.” Nan da nan Fatima ta ƙara jin hankalinta ya tashi, Baqeer ne yasa hannun hagu yana neman amsa, a fusace Baba yace “Dama zaka saka, ko ka taɓa yin zane da hannun hagu ne?” Baqeer ya kai hannun damanshi sai dai yana kaiwa ya amshi pencil ɗin yaji yatsun hanunshi sun kasa riƙewa sai jin pencil ɗin kike a ƙasa, Baba rai a ɓace ya tsuguna ya ɗauko ya sa hannu a saman kafadarshi yace “Ka manta kai wanene a gareni Baqeer? Ka manta abubuwan dana sadaukar saboda kai? Ko kuwa ka manta duk wani burina a duniyar nan akanka yake? Naji ka rasa ƙafa zan iya hakura da hakan amma banda hannu, dole ka cikamin burin nan nawa, kai kaɗai ne wanda nake ganin abinda ban yishi ba zaka yi mini shi, kafi kowa sanin hakan, saboda kai har mantawa nake yi ina da wasu ƴaƴan, saboda kai mahaifiyarka ta samu girma da daraja a gurina, idan har ba so kake yi duk abubuwan nan su ruguje ba ka ɗaga hannu kayi abinda na saka ka, dan har yanzu mutane nayi mini kallon shashasha saboda na dage akan zanen da kake yi ina nuna musu shima sana’a ce ana ganin rashin sanin ciwo kai na da nuna ban san me ke faruwa ba, na dage har kazo ka kai wannan matsayin da zaka wakilci garin mu sannan muna sa ran ka wakilci ƙasa shine zaka ce wai karaya ta hanaka amfani da hannu? Kai har ka isa ma? Baqeer hannunshi na rawa idanunshi sun cika taf da kwalla ya kai hannu cike da dauriya wanda bai taɓa sanin ma yanada ita ba, sai dai me? Yatsunshi ne suka sake yarda pencil ɗin. A tsorace ya kalli Baba wanda yanayinshi kaɗai zai sa kasan yana cikin tsananin ɓacin rai. Fatima dake waje tana jiyo kalamanshi sama-sama hawaye kawai take yi, ita kam tasan ko kowa zai amshi kaddarar abinda ya faru tasan banda Malam, yanzu ya zasu yi? (To wannan lamari mu kanmu kallon juna muka yi dan tuni tausayin abinda ke faruwa ya gama mamaye mu, me kuke ganin zai faru?) *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 Umm Asghar Ce Da Ayusher Muhd BAQEER NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAKWAS {8} Yanda ya da ka mishi tsawar itace ce ta ƙara gigita shi yace "Ɗauki mana, ka tsaya kana yin wani abu salalo-salalo kamar mara jini a jiki, kana ganin idan baka dage ba zamu kai ga cimma nasara ne? Maza ɗauki pencil ɗinnan ka fara tun raina bai gama ɓaci ba, kuma so nake yi ka ƙure basira wajen yin zane mai kyau mai ma'ana." Hannunshi yana rawa ya ƙara ɗaukar pencil ɗin ya riƙe da ɗan ƙarfi wai don ya samu ya zauna a hannun sai dai wata irin azaba da yaji ta ratsa shi har tsakar kanshi ya sakashi sakin pencil ɗin jiki na rawa, wasu hawaye ne masu ciwo suka sulmiyo daga idanunshi, ɗaga kai yayi ya kalli Baban daya kirne fuska ya sha kunu tamkar ba shine wannan Baban mai yawan so da tattalin shi ba, kwata-kwata yanzu babu tausayi a cikin ranshi sai fatan cikar burinshi kawai da yasa a gaba. Da ƙyar ya iya buɗe baki yace "Wallahi Baba ba zan iya ba, hannuna bai gama warkewa ba ko yaya nayi ƙwaƙƙwaran motsi dashi ba ƙaramar azaba nake sha ba." Babu zato yaji Baba ya sauke mishi wani irin gigitacen marin daya gigita shi har ya kusa faɗowa daga kan wheel chair ɗin cikin taimakon Allah yasa hannunshi mai lafiya ya riƙe hannun kujerar wanda ya taimakeshi bai kai ga faɗowa ba. Cikin hargagi da masifar da Baqeer ya saba jin shi yana yiwa ƴan uwanshi da iyayensu mata sai dai bai taɓa katarin an sauke mishi shi ba ya nuna shi da yatsa yace "Wallahi ba zaka so ganin kalar ɓacin raina ba idan har baka ɗauki pencil ɗin nan kayi zanen nan ba, kana nufin duk uban kuɗin dana kashe da lokacina dana ɓata a kanka sun tashi a banza kenan? Baƙin ciki kake yi min ne Baqeer? Ganin ina daf da cika burina na shekara da shekaru, inace akwai ƴar baƙin ciki a tsakaninmu dama?" ya karashe maganar yana ji kamar ya saki kuka ko yaji sauƙin damuwar data cunkushe a zuciyarshi, ta yaya sai da yake daf da ganin cikar burinshi Baqeer zai nemi ya watsa mishi mafarki da burin da ya ɗauka gaba ɗayan rayuwarshi yana ginawa. Hawaye kawai Baqeer yake yi don yafi Baba jin baƙin cikin wannan ƙaddarar data sameshi sai dai baya da yadda zai yi don a yanzu dai a irin ciwon da yake ji a duk lokacin da ya motsa hannunshi yasan babu abinda zai iya ko yana son yin zanen bare ma baya cikin nutsuwar da zai iya yin wani zane a yanzu, ƙunci da damuwar dake danƙare a cikin zuciyarshi baza su bari ya iya yin komai ba. A fusace ya fito daga ɗakin ya buga ƙofar da ƙarfin da sai da ya girgiza ginin ɗakin, wani irin wulaƙantaccen kallo ya watsawa Fatima data kasa matsawa daga ƙofar ɗakin tun bayan da Baba ya korosu waje ya rufe ƙofar ɗakin da Baqeer a ciki, yana wucewa tayi wuf ta faɗa ɗakin sai dai halin da taga ɗan nata a ciki ya ƙara sanyayar mata da gwiwa, kuka yake yi irin mai cin zuciyar nan wanda baka jin sautinshi sai dai kaga zubar hawayen kawai, tunda take bata taɓa ganin Baqeer cikin wannan yanayin ba, itama bata san lokacin da kukan ya suɓuce mata ba sai dai tayi saurin saka hannu ta toshe bakinta tana ƙoƙarin hana kanta yin kukan sai dai tausayinshi da take ji ba zai bari ba don duk sadda ta kalleshi sai taji wani irin rauni ya lulluɓeta. A haka taja jiki ta ƙarasa gabanshi ta tsugunna, hannayenta tasa ta kamo hannunshi mai lafiyar ta riƙe a cikin nata duka biyun, wani irin rauni ne ya lulluɓeshi ganin da yayi wa mahaifiyarshi a tsugunne a gabanshi, tausayinsu gaba ɗaya ya kamashi har bai san lokacin da ya fashe da kuka ba "Umma" kawai yake ambata muryarshi na rawa. Sai da suka yi kukansu ya ishe su sannan ta haƙurƙurtar da zuciyarta tasa hannu tana share mishi hawayen tace "Kayi haƙuri Baqeer da duk abinda zaka gani a yanzu, dole sai ka koyawa zuciyarka haƙuri ka koyi ɗauke kai daga al'amuran mutane ka koyi haƙurin zama dasu a yadda suka zo maka don ba kowa ne yake baƙin ciki da ƙaddarar data sameka ba, wasu har cikin ransu murna suke yi da abinda ya sameka ba dai zasu fito su nuna bane kawai, Allah ya baka lafiya ya ƙara maka haƙuri da danganar karɓar sabuwar ƙaddarar data shigo rayuwarka a yanzu." An ɗauki lokacin tana yi mishi nasiha akan falalar haƙuri da karɓar ƙaddara a duk yadda ta zowa bawa har ya samu ƴar nutsuwa ya daina kukan da yake yi. "Umma Baba fa, ya zan yi dashi bayan ya kasa gane a yanzu babu abinda zan iya yi da hannuna, gani yake yi kamar da gangan naƙi yin abinda ya sakani?" Yayi maganar idanunshi akan hannunshi na dama yana jujjuyasu a hankali, yana ayyana ko sai yaushe zai fara amfani dashi wajen yin zane kamar da. "Shima haƙurin zaka yi dashi har ya fahimci ba yin kanka bane ƙaddararka ce tazo a hakan ya sauko, kasan yadda ya ɗora dukkanin wani buri nashi a kanka lokaci guda hakan tazo ta faru dole abun ya dakeshi to amma ya zamu yi bayan muyi haƙuri mu fawwalawa Allah dukkanin al'amuranmu In Sha Allah yana sane damu ba kuma zai ƙyale mu a haka ba zai kawo mana mafita ta inda bamu yi tsammani ba, kayi haƙuri kaji ka cire komai daga cikin zuciyarka sai kaga Allah ya dafa maka." Miƙewa tayi zata fita sai kuma ta dakata tace "Ko akwai abinda kake so nayi maka kafin na fita, ba dai wani daɗewa zan yi ba wanki kawai zan je in ƙarasa yanzu zan dawo, dazu na fara na ajiye." Girgiza kanshi yayi yace "Babu wani abu Umma har kin gama ki dawo ina nan ai ba wani wuri zan iya zuwa ba." Sai taji tausayinshi ya ƙara kamata, wai yau Baqeer ɗinta ne ya dawo haka, Ya 'Allah ka sauƙaƙa mishi ka bashi ikon ɗaukar wannan ƙaddarar daka sukar mishi' ta samu kanta dayi mishi addu'ar a cikin zuciyarta. '"Ko dai zaka kwanta kafin na dawo don naga kamar ba wani jin daɗin zama akan kujerar kake ji ba?" "A'a Umma barni a zaune kawai don na gaji da kwanciyar nan ciwon jiki take sakani." "To ai shikenan, bari naje nayi maza na gama na dawo, don Allah ka cire komai daga cikin ranka kaji? Kada ka zauna kana tunane-tunanen da baza su ƙare ka da komai ba sai yawan damuwa." "To" kawai yace mata cikin ranshi yana cewa tunani kam ai ya zama dole a wurinshi a yanzu tunda baya da wani abun yi da zai ɗauke mishi hankali daga halin daya samu kanshi a ciki. ***** Baba kuwa yana fita ɗakinshi ya shige ya fara shirin fita kasuwar da duk kwanakin nan bai samu yaje ba don ma Allah yasa yana da yara masu kular mishi da harkokin kasuwancin nashi ai da ba ƙaramar asara ya tafka a cikin kwanakin nan da yayi ta sintiri a asibiti bai je ba gashi alamu sun nuna ba lallai ne ya samu abinda yayi sadaukarwar domin shi ba tunda Baqeer nema yake yi ya watsa mishi ƙasa a ido abinda bai taka kara ya karya ba na neman gagararshi, yayi fatali da dukkan wani ƙoƙarin shi da jajircewarshi wajen ganin sun cimma nasara ya cika burinshi. Har ya gama shiri ya bar gidan zuciyarshi bata daina tafasa ba hakan yasa ko sallam bai yiwa matan gidan ba yasa kai yayi ficewarshi. Koda yaje haka yayi tayi wa yaran nashi masifa, abu ƙalilan zasu yi mishi sai ya rufe su da faɗa, gaba ɗaya ya rasa nutsuwarshi tunanin ta yadda zai takura Baqeer yayi zane kawai yake yi, har tunani yayi to ko wani zai nema da ya iya zanen su tafi wajen gasar tare yayi zanen a madadin Baqeer idan yaso shi sai ya biyashi, tunane-tunane dai iri-iri babu wanda bai yi ba na neman mafita amma kasa samun matsaya guda ɗaya da zai kama. Dole ne ma Baqeer ya dage ya ƙarfafi zuciyarshi ya cigaba da zanen idan ba haka ba kuwa sai dai shi da uwarshi su biyashi duk abinda ya kashe akan harkar zanen Baqeer ɗin. Yana cikin waɗannan tunanin ne aka kirashi a waya, sai da gabanshi ya faɗi daya duba yaga Yallaɓai ne ke kiranshi. Ido kawai ya zuba yana kallon screen ɗin wayar tana ta ƙara ya kasa amsawa saboda dai bai san kuma me zai faɗawa Yallaɓai ɗin ba, sai da ta kusa katsewa sannan ya amsa wayar cikin sallama. Ko gaisawa Yallaɓai bai bari sun yi ba yace "Haba Mallam Badaru, ta yaya zan yi ta nemanku a waya kuna raina mini hankali bayan kasan tafiyar nan ta matso, idan Baqeer ɗin ba zai iya ba tun wuri ba sai ka faɗa mini ba a nemi wani sai kayi ta yi mini yawo da hankali". A ladabce kamar yana gabanshi don har ɗan russunawa yake yi yace "Kayi haƙuri Yallaɓai wallahi wata ƴar matsala aka samu shi yasa kaji har yanzu ban nemeka ba, amma ya za'a yi mu raina maka hankali". "Yanzu ina Baqeer ɗin? Ina fata dai ya gama shiryawa don kasan gobe ne zamu je wajen deputy gwamna a game da batun tafiyar." ya katse shi ba tare da ya bari ya gama jin me zai ce ba. Shiru Mallam Badaru yayi yana juya ta inda zai fara faɗa mishi abinda ya samu Baqeer ɗin. A ɗan tsawace yace "Wai wani abu ya faru ne Mallam Badaru da kake ɓoye mini?" "Wallahi Yallaɓai tsautsayi ne ya afku da Baqeer, yau sati guda kenan da mota ta kaɗeshi ya karye a ƙafa da hannu, zancen nan da nake yi maka ma dai ya zama gurgu don ance ƙafafun nashi sun tashi daga aiki," yayi maganar yana jin baƙin cikin halin da Baqeer ya sakasu a ciki, daya zauna a gida bai fita shegen yawonshi na tsiya ba ai duk da haka bata faru ba gashi nan yanzu suna nema suga samu suga rashi. Cikin wani irin fushi Yallaɓai yace "What? Karaya? Kana nufin karaya dai? Kuma shine kayi shiru da bakinka kaƙi faɗa mini na nemi wani, wai me yasa mutane sam baku san ku rama alkhairi da alkhairi bane, ka barni anan sake da baki zamu je wajen taron nan da ɗanka ashe shi ya zama useless ni ban sani ba, sai kayi gaggawar dawo da kuɗin tallafin da kuka karɓa daga hannun gwamnati don kasan dai ba bar muku za'a yi ba tunda ba zuwa zai yi ba." Shi dai haƙuri kawai yake bayarwa kamar ya ari baki, haka Yallaɓai ya kashe wayarshi yana ta masifa yana mamakin halin mutanen wannan zamanin da basu san komai ba sai son kansu da yayi musu yawa. Wayar Bello ya ƙira, Bello yana ganin Yallaɓai ne ya amsa da hanzari don yasan ba zai wuce yaji abinda ya samu Baqeer ba shine yake kiranshi. Cike da ladabi ya amsa yana gaisheshi, sai bayan sun gama gaisawa sannan Yallaɓai yace "Ni zaku maida karamin mutum? Ashe abinda ya samu abokinka kenan shine kuke ta ɓoye-ɓoye kuka kasa faɗa mini na nemi wani gashi gobe zamu je wajen deputy gwamna? Ƙaramin mutum kuke san maidani?" "Wallahi kuwa Yallaɓai, accident yayi sai kuma abu yazo da tsautsayi ya rasa ƙafafun shi gaba ɗaya." "Mts... Allah dai ya bashi lafiya amma ni damuwata ta yadda zan nemi wani contestant ɗin a tsakanin yau da gobe wanda zai maye gurbunshi kawai tunda ko be karye a hannu ba ƙafafunshi sun tashi daga aiki, taya zai shiga taro irin wannan akan keken guragu, wallahi Mallam Badaru ya ɓata mini rai don daya faɗa mini da wuri da tuni nasan abun yi, gashi mun riga mun aika sunanshi." Ya ƙarasa maganar rai a ɓace. Dukkansu shiru suka yi kowa da abinda yake tunani a cikin zuciyarshi, Bello ne yayi ƙundunbalar cewa "Yallaɓai idan babu damuwa nace ko ni ba sai na wakilcemu? Tunda dai nima na iya zanen nan, asali ma abinda ya haɗa abotarmu da Baqeer ɗin kenan." Wata nannauyar ajiyar zuciya Yallaɓai ya sauke kafin yace "Kuma fa haka ne Bello, ni ba na manta ba ashe kaima duk harkarku ɗaya, matsalar da za'a samu kawai wajen canja suna ne tunda mun riga mun miƙa sunan Baqeer a matsayin wanda zai wakilcemu, shi yasa ma abun ya dameni don sai da lokaci ya ƙure sannan aka samu wannan canjin amma In Sha Allah zan yi ƙoƙarin ganin an gyara komai ya koma da sunanka, kai dai ka zama cikin shiri don koyaushe zan iya nemanka, fatana kar canza sunan ya zama matsala. "To Yallaɓai nagode Allah ya ƙara girma" yace cikin tsantsar farin ciki irin wanda bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba "Yallaɓai in kana ganin sunan zai jawo matsala ina ganin ba matsala bane tunda ai dama da initials ake amfani to nima kuma sunana Bello Bala kaga Muhammad ɗin kawai za'a ƙara mini daga gaban sunan, kuma duk wani namiji ai Muhammad ne, ko ba haka ba?" Wata irin dariyar farin ciki Yallaɓai ya saki ganin ya samu mafita yanzu-yanzu kamar ba shine ke tunanin neman replacement na wanda zai maye gurbin Baqeer ɗin da ke neman kassara shi ba. (Wani abokin dai sai Allah, ga dai Bello ba kunya ba tsoron Allah, ga kuma mahaifin da ya kasa duba halin da danshi yake ciki.) Baqeer #Shalele #Asiya # RayuwadaKaddara #Hawayena *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 - Uku 1200 - Biyu 1000 - Ɗaya 500 - VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k Promo zai kare zuwa wani satin, garzaya kisai naki🙌🏻💃🏻 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 BAQEER🦼      NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TARA Dandano...... {9} Yallaɓai yana kashe waya Bello ya daka wani irin tsalle tare da yin ƙaramin ihu, lalai ba shakka rayuwa zata fara masa da ɗi yanzu, masu mai gani-gani su shirya ganin abinda zai zama yanzu. Sako ne ya shigo wayarshi na Yallabai akan wai ya tura samples na zanen dayai ya gani dan ya sake tabbatarwa akan ba matsala. Ajiye wayar yai ya durkusa ƙasan gado yana jawo zanukan da yai, wanda kusan kowane ya ɗaga sai yaga Baqeer ne ya tayashi ko kuma Baqeer ne ya nunamai yanda zaiyi, tsaki yai yace "Nuna min yai ai ba shiya zana min ba." Kallan initial na sunanshi da ya saba amfani dashi yake wato BB da sauri yasa pencil ya ƙara M a gaba nan danan da ɗi ya ƙara rufeshi ba shakka Allah ne ke sanshi da rahama, shafar zanen yai yanajin wata nutsuwa na sake zuwa mai, yau ina mutanen dake ganin zane ba inda zata kaishi? Wanda ciki harda mahaifinshi? Dole ya shayar dasu mamaki dan bazai sanar dasu ba sai yaje ya ciyo gasar da za'ai a Abuja nan ne fa zai nuna ma duniya shi ɗin wanene. Haka ya ɗau hotuna kala-kala ya tura nan da nan Yallabai yamai reply akan komai yayi sai sun haɗu gobe. ****** Kallan ɗakin tai cike da jin daɗi a hankali ta ke sake takawa ciki, wani sanyi na sake ratsata, ta baya taji an dafata, ba tare da ta juyo ba ta saki murmushi tace "Senate Allah yayi autata zata dawo." Kai ya girgiza yace "Ke dai wallahi san yaran nan ya miki yawa, ina fitowa da naga ban ganki ba dama nasan kina nan, ba last year tazo hutu ba?" Waigowa tai tace "Hutun wata ɗaya ne fa kacal? Yanzu kuwa fa? Kaga dai wannan karan inta dawo shikenan ba komawa." Kai ya girgiza yana kallan yanda tasa aka canza komai na ɗakin, kallanta yai yace "Nabeela ce zataje airport ɗin?" "Eh nace taje dan kasan halinta in taga ka tura yaran nan shi kaɗai bamusan me zata aikata ba." Yana ɗan jinjina kai yana cewa "Sam bansan meke damun yarinyar nan ba, ace wai ita ba'a isa a hadata da wani ta kulashi ba? Tunda kike da ita kin taɓa ji tace tanasan wani? Ita bata kawo ba sai taurin kan tsiya." Hannunta ta saƙala cikin nashi tace "Calm down please my Senate, kasan Zeey abubuwa ne suke mata yawa, ita bawai auren bane bataso kawai....." Hannu ya ɗan daga mata alamar tai shiru yace "Nidai Allah tana dawowa ki sanar da ita ko ta kula wannan ko karta kulashi a shekarar nan zan aurar da ita, sam banasan yarinya mace ta min girma haka a cikin gida, tun yaushe nake san aurar da ita amma abu yaki yiwuwa?" Sanin halinshi yasa ta nemi janye maganar da cewa "Yau ne zakuyi meeting ɗin da kace?" Fara tafiya yai yana fita daga ɗakin yana cewa "Yau ne, nidai ki faɗawa Nabeela taja mata kunne kindai san wannan ɗan wanene bansan shirme." Zatai magana yace "Da zatai rabin hankalin Nabeela da ba haka ba." Daga nan bai jira tace wani abu ba ya wuce, itadai sam batasan ya zatai ta nusar dashi akan ya rage tsauwalawa Zeey ba. *** Baqeer tunda Mama ta fita ta barshi a ɗaki yake zaune a gun, banda ƙoƙarin riƙe pencil dayake tayi babu abinda yakeyi, ganin yafi awa ɗaya yana abu ɗaya yasa ya runtse ido, yanajin wani irin kunci a zuciyarshi wanda kawai yacigaba da samun kansa da addu'ar Allah ya ɗau ranshi ya huta da wannan bakin cikin, Fatima ce ta shigo jiki a sanyaye tace "Baqeer bari na roki Bashir ya taimaka ya kaika bandaƙi kai alwala azahar tayi." Kamar wanda aka daɓa masa wuka a zuciya haka yaji kalamanta, shikenan shi yanzu komai sai an taimaka mai yayi kenan? Kasa magana yai har sai da ta fita ya ciji kasan leɓensa yana sake runtse idanuwansa. "Bashir baya nan, sannan banaji sanda na haifi ɗan akwai gadan zaki sashi wahalar nakashashen ɗanki." Kalaman da Jamila tace kenan wanda yasa Fatima hadiyar yawo a ranta tace "Inama yanada kani namiji?" Abu ta kalla tace "Abu dan Allah naga kamar Kamalu ya shigo ko zaki mai magana?" Baki Abu ta buɗe tace "Kamalun saninshi ne bakiyi ba? Sai kije da kanki ai kinsan ɗakin shi." Kamalu shine mai bin Baqeer a gun mahaifinsu, sam ba jituwa tsakaninsu, tunda yaga Baban yanasan Baqeer sosai sai ya kangare ba wanda ya isa ya sashi balle ya hanashi, har zargin shaye-shaye akemai sai dai tsoronshi yasa inba Baba ba bamai masa magana. Wani tunani ne yazo mata wanda yasata juyawa ta koma ɗakin tana murmushi tace "Baqeer bama sanan amma na ƙira Salim yace dama gashi nan zuwa." Kai kawai ya ɗaga dan yasan akwai abinda ya faru faɗane kawai batai ba, hanyar fita tai ya daure yace "Umma dan Allah aran wayarki." Cikin sauri ta miƙa mai, ya fara ƙoƙarin sa hannu dama zai amsa, da sauri ta ɗau ra mai akan cinyarsa ta fita ɗakin zuciyarta na sake karyewa, gaba ɗaya intaga Baqeer a haka sai taji hawaye, Baqeer ɗinta wanda a koda yaushe yake cikin ji da ita wai shine a wheelchair. Wayar ya ɗauka da hannun hagu ya sa number Asiya ya ƙira, tana zaune suna cin abincin rana itada Habi, ganin ƙiran da number da bata sani ba yasa ta ɗaga, tace "Hello!" Baqeer ya haɗiyi wani abin yace "My love!" Dam gabanta ya faɗi dan kuwa tasan waye, cak ta kame ta kasa magana, Baqeer ya daure ya sake cewa "My love am so so......" Kashe wayar tai da sauri tana maida hakki ta maida kallanta kan Habi wacce take cewa "Wenene? Ko Baqeer ne?" Abincin ta cigaba da ci tace "In ma shine sai me? Kinga ni dan Allah ki kyaleni ke in hakan ta faru dake ki tabbatar baki bar mutum ba." Habi cike da takaici ta tsame hannunta tace "Butulci dai babu kyau." Wata muguwar harara Asiya ta zabga mata ta ɗauke kanta. **** Baqeer kuma kasa sauƙe wayar yai daga kunnenshi mamaki gaba ɗaya ya kasa barinshi, kodai Asiya tausayinshi ne yasata shiga wani hali? Ba shakka abinda ya faru dashi ta gani yasan tana cikin wani hali. Salim bai daɗe ba sai gashi nan ya taimaka mai yai alwala yai sallah sannan Fatima ta kawo musu abinci, da kyar yai loma uku yace ya koshi. Suna zaune a ɗakin Baqeer yace "Salim dan Allah tunda kuma shiri da Habi ko zaka taimaka ka fita dani waje kasa Habi ta ƙira mana Asiya in mata magana? Na tabbatar tana bukatar wanda zai taushasheta, in har ta ganni nasan zata yarda da kaddarar data samemu." Salim yace "To shikenan." Anan ya ƙira Habi yace bayan magriba sai su haɗu kusa da shagon Sidi. ****** Zainab ce tai wata irin miƙa sannan ta cire abinda ke rufe da idanta na sleeping mask, tunda ta shiga jirgi take bacci sai dataji an tsaya ta farka, kallan waje tai sannan ta ɗan saki murmushi, ta ɗauko madubi tana kallan fuskarta wacce ta dan gyara da zaman ɗan kwallinta. Macece baka sai dai ba mai duhu can sosai ba, kana ganinta zakaga tsayinta irin tsaka-tsakin nan ne, batada jiki sai dai tana da shape ɗinta, sanye take da english wears na riga doguwa maroon colour har gwiwa sai wando datasa na jeans ta ɗau ra dankwali shima maroon, sai yanzu ta ɗauko wani karamin mayafin baki ta sa a saman kanta, wayarta ta zaro a gefen jakarta ta kunna, fitowa tai janye da suitcase ɗinta fara, airpod ne a kunnenta tana waya, cike da sakalci tace "Mum na iso Allah duk na gaji." Tai maganar tana tsayawa jikin wani shop dake gun inda tasai juice na gwangwani, ƙoƙarin buɗe wa take ga kuma wayarta dake riƙe, ga jakar hannunta da kuma wanda take jaa. Mum ce tace "Kinga wanda muka turo ɗin? Mundai tura miki hotonsa tun jiya.” Da mamaki sai ta hangoshi yana nufo inda take, alama tamai da hannu akan ya ƙara so da sauri, aifa guy ɗin ya kara hanzari yana tafiyar niggas irinta samarin dake ji da kansu, kayan da yake sanye dashi da trainers ɗinshi kaɗai zaisa kasan ɗan masu kuɗi ne dan kuma riga t Tommy Hilfiger ne ga takamin Adidas. Tace "Mum gashi ma ya iso." Cike da jin daɗi tace "Please Zeety wannan karan karki wulakantashi yaran babban mutum ne Babanshi yana ganin mutumcin Dad ɗinki.” Zeey ce ta katse ta jin tana cewa "Please ja jakar, inata jiranka kana tafiya kamar bakai breakfast ba." Da mamaki guy ɗin yake kallanta sai dai ya amsa baisan ya nuna gazawarshi, juice ɗin ta miƙa mai tace "Ɗan Buɗe min hannuna." Baki ya ɗan buɗe cike da mamaki ya amsa ya buɗe ta amsa daga hannunshi tana sipping tace "Yauwa Mum kikace me?" Acan kuwa Mum ta runtse ido tace "Zeey please ya isa haka." Sai tace "Okay sai mun iso." Kallanshi tai wanda da alama kunya yake a ganshi yana binta a baya, dan ta kula sai saurin matsowa daf da ita yake dan su jera, kallanshi tai tace "Yauwa yama sunanka? Jamil? Jamal?" Takaici ya sake kamashi yace "No ni sunana Najib." Ta jinjina kai tace "Ohh! Yaushe Dad ya daukeka aiki? Hope dai personal driver ɗina ne kai dan inada abubuwan yi." Cak ya tsaya yace "What? Driver? Na miki kama da driver?" Waigowa tai tace "Then?" A kufule yace "Ba'a turo miki hoto na bane?" "Ooops! Anturomin, wai kaine dama?" Hanci ya fara hurawa ta fara kunshe dariya tace "Sorry! Sorry! Amma kamar filter kasa a hoton ko? I’m not trying to be rude amma you look different.” Jakarta ya tura mata daga inda yake yace "Mene?" Wuyanta ta ɗan shafa tace "Kamin kama da driver ne da Dad ya min magana akan zai ɗaukar min kafin na dawo." Nabeela wacce ke makale a gefe tana kallansu ta ɗan daki goshinta kaɗan tana girgiza kai tare da furzar da iska, dariya ta fara tana ƙara sowa ta dafata tana matsa kafaɗarta cikin magana kasa ƙasa tace "Ya isa yi shiru kafin ki ƙarasa lalata komai." Zeey da ƙarfi tace "Ouch! Me nai? Jamal ranka ya ɓaci?" "Najib nace miki sunana." Yai maganar cikin ɗaga murya, nan kawai ya juya ya fara tafiya da sauri Nabeela ta bishi tace "Dan Allah kayi hakuri bata ganeka bane, bawai wulakanci tama ba." Ai bai kulata ba yai gaba yana huci kamar shi? Kamar shi babban yaro a maidashi wani gaja? Waigowa tai ta zabgawa Zeey harara wacce ta ɗan ɗaga kafaɗa alamar oho. Haka suka fito Zeey tana dariya ita ko a jikinta, a hanya Nabeela tace "Zeey wai haryanzu bazaki daina wulakanta samari ba? Sai yaushe ne zaki bar abin nan?" "Sai sanda zuciyata ta aminta da abinda nake so, Aunty Nabs please mu bar maganar, to ya gida? Ina Nan?" Ajiyar zuciya Nabeela tai tace "Da kin ɗauken a matsayin Auntyn da kinji magana ta ai." Dariya tai tana danna waya tace "Ke fa dariya kike bani, nafa girmeki da 8month." "Ko dai kin girmeni dai ni kanwar Mumyn ki ce." Dariya sukai a tare haka suka cigaba da tafiya suna hirarakinsu sam Zeey bata tauna magana take faɗa kuma kanta tsaye sai dai kai maganar ta ɓata ma rai amma ita ko a jikinta. Zeey ta kalli Nabeela bayan sun shigo unguwarsu tace "Please kaini shago a layin nan na sai abu." Da mamaki tace "Meyasa baki faɗa da wuri ba? Da munje store." "No bana san can, simple abu zan siya." Tace "to" **** Baqeer sun samu sun fito shi da Salim kamar yanda suka tsara sukacewa Umma wai iska zaisha a waje, sunyi sa'a Baba bai dawo ba. Asiya kuwa ta fito ita da Habi wacce tace zasuje shagon Sidi su siyowa innarsu abu wai tsoron fita take ita kaɗai suna tafe Asiya na masifa akan ta sakata ta fito ba tare da ta yi niyya ba, suna isa turus tai ganin Baqeer daga lungun shagon, kallan Habi tai wacce tai saurin fara tafiya. Neman juwaya tai Baqeer da sauri yace "Asiya please!" Dawowa tai ganin inba tayi da gaske ba bazai kyaleta ba. Daga kusa dashi ta tsaya ta ɗan kauda kai yace "My luv nasan halin dana shiga ne ya jefaki cikin wani hali sai dai mu sani haka Allah ya kaddara mana ba yanda....." Katseshi tai da sauri tace "Ya kaddara ma dai! Baqeer kalleni hanna yena da kafafuna garau suke, ko ina zan iya zuwa da kaina kuma ko me nake so zan iya zama indai nasa kaina, mena cema akan ka nemi wani aikin ka ajiye shirmen zanen nan? Cemin kai zane ma sana'a ce, to yanzu ga hannunka ya samu matsala taya zaka cigaba? Ga kuma kafarka wacce har abada a keke zaka kare kaga kuwa kaine ke dauke da kaddara ba ni ba." Mamakin kalamanta ne suka hanashi cewa komai da kyar yace "Me kike nufi?" Tace "Abinda  kake tunani kaga please ka daina ƙirana kaje kaji da yanda zaka amshi kaddararka bani ba, aurenka zanyi ko jinyarka?” Tana kaiwa nan ta fara tafiya, cikin sauri ya fara tura keken nashi da hannun hagu dan Salim ya ɗan basu guri yana tsaye a shago yana jiransu. Da sauri ya tsaya ganin mutum a gabanshi, Zeey bata san sanda ta fara kunshe dariya ba tana girgiza kai, ashe ta fito a shago taga abinda ke faruwa ita kuma da san abin dariya kawai ta tsaya tana kallansu. Baya tai ta kaucemai tana sake kunshe dariyarta, Baqeer ne ya sauke idanunshi da sukai jaa a kanta, da sauri ta ware hannu tace "Oops sorry!" Ta fara tafiya tana magana ƙasa-ƙasa "Maza sai ka rasa irin kwakwalwarsu, clearly kasan ba sanka ake ba ta kuma nuna ma tunda kai gurgu ne batayi, amma inaa kan nan ba komai.." Karaf a kunnen Baqeer a fusace yace "Me kikace?" Yai maganar cikin daka mata ɗan tsawa. Ƙofar mota ta buɗe tace "Sorry no time." Ayusher Ce 🏌🏻‍♀️ Da Ummu Asgar Baqeer #Shalele #Asiya # RayuwadaKaddara #Hawayena *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 - Uku 1200 - Biyu 1000 - Ɗaya 500 - VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k Promo zai kare zuwa wani satin, garzaya kisai naki🙌🏻💃🏻 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 BAQEER🦼      NA UMM ASGHAR DA AYUSHER MUHD DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA Kallon inda Asiya ta fara tafiya kawai yake yi baki a sake, jikinshi na wata irin rawa da tsuma ta tsananin tashin hankalin daya tsinci kanshi a ciki yanzun nan, shi maganar yarinyar can ma bata ɗaga mishi hankali ba irin maganar da Asiya tayi. Cikin rawar murya yace "Me kike nufi kenan Asiya? Saboda Allah ya aiko mini da ƙaddara kike nema ki gujeni? Ina alƙawarin da muka yiwa juna na duk rintsi duk wuya muna tare babu abinda zai iya rabamu, shine yanzu zaki janye maganar saboda kinga Allah ya mayar dani haka?" Yai maganar wani siririn hawaye mai ɗumi ya biyo gefen idonshi ya silalo kan kumatun shi, yana jin wani irin ciwo mai zafi na damƙa a cikin ƙirjinshi har ma fiye da yadda yaji lokacin da aka sanar mishi da ƙaddarar data same shi, dan tunda yake rayuwa bai taɓa tunanin akwai abinda zai sashi rabuwa da Asiya ba, komai na rayuwar shi da ita yake ginawa, dame akeso yaji? Cak ta tsaya sannan ta waigo tare da sake takowa inda yake, wani wulaƙantaccen kallo ta watsa mishi tayi tsaki "Kai nan a tunaninka zan iya cigaba da yin soyayya da kai, a hakan? Kalle ka fa ka kalleni kai ma kasan ajina yafi gaban na zama matar gurgu, never wallahi har abada" Ta ƙarasa maganar tare da tofar da yawu kamar taga wani abun ƙyama. Juyawa tayi ta fara tafiya sai kuma ta juyo ta kalleshi irin kallon tsaf ɗinnan kafin tace "Ina fata zaka cireni daga cikin ranka ka manta ka taɓa sanin wata mace mai suna Asiya, ka ɗauka duk soyayyar da muka yi a cikin mafarki ta gudana ba gaske bane don ni tuni na cireka daga cikin zuciyata daga lokacin da nasan ka zama nakasashe gurgu nasa a raina ban taɓa saninka ba don haka nake haɗa ka da Allah kada ka ƙara nemana ko a waya ko kace zaka zo gidanmu don idan kazo ma bazan fito ba." Daga haka ta juya tayi tafiyarta ta barshi yana ƙwala ƙiran sunanta yana cewa "Please Asiya kada kiyi mini haka, kada ki juya mini baya don kinga larura da ta sameni, idan kika barni a cikin wannan halin dana tsinci rayuwata ban san inda zan waiwaya ba naji daɗi kuma." Ko waiwayowa bata yi ba har ta ƙurewa ganinshi kuwa, haka ya sunkuyar da kai yana zubar da hawaye mai ciwo yana jin wai yau shi Baqeer, Asiya take faɗawa waɗannan maganganun saboda taga yadda Allah yayi dashi, har Salim ya dawo kanshi yana ƙasa ya kasa ɗagowa, sai da ya dafa kafaɗarshi sannan yasan ya dawo don dama matsawa yayi ya basu wuri. Salim gani yayi fuskar Baqeer tayi jawur gashi tayi caɓa-caɓa da hawaye. "Lafiya kuwa Baqeer? Wani abu Asiyan tace maka naga duk ka firgice ka fita daga hayyacinka?" Girgiza kai kawai yayi don bai ji zai iya buɗe baki yayi magana a daidai wannan lokacin ba, maganganun da Asiya ta yaɓa mishi sosai suka dakeshi duka bana wasa ba don ko kusa bai taɓa tsammanin tana daga cikin butaulallun mutane ba masu saurin manta alheri, bai ɗauka a cikin ɗan taƙaitaccen lokaci Asiya zata juyawa soyayyarshi baya ba sai kuma gashi ta ƙaryata tunaninahi ta nuna mishi rashin amana irin na mutanen wannan lokacin. ***** A kwance Habi ta shigo ta tarar da ita akan katifarsu tana danne-danne a cikin waya. Kallon tsaf tayi mata taga babu abinda ya dameta da abunda tayi sai ma wani ɗan murmushi da take saki idanunta manne da allon wayar. Ninke hijabin ɗin data fita dashi tayi ta ajiye akan jakar kayanta kafin ta zauna daga bakin katifar wajen ƙafafun Asiya zuciyarta duk babu daɗi. "Ke kuwa Asiya me yasa zaki yi haka saboda Allah, ko ba kya son Baqeer bai kamata kiyi mishi irin wannan cin fuskar ba babu tausayin halin daya samu kanshi a ciki a haka ya taso don ya ganki yana ganin ko da ya rasa komai a rayuwa kasancewarshi tare dake zai sauƙaƙa mishi abubuwa ashe ke ɗin mayaudariya ce mai saka alkhairi da sharri, me manta girman soyayya da sanin darajar masoyi." A harzuƙe ta tashi zaune tayi wurgi da wayar can gefe ta hau nuna Habi da yatsa tana cewa "Kinga Habi ki kiyaye ni ki fita daga idona na rufe, akan gurgun kike cewa na manta alkhairi, gurgun? To idan na aureshi bara zai yi ya ciyar dani ko kuwa ni zan turashi a keken guragun mu tafi yawon barar, wallahi nafi karfin auren nakasashe Allah ya tsareni da auren wahala, to me na sama yaci bare ya bawa na ƙasa? Idan ban rabu dashi tun yanzu ba sai yaushe? Ko kin fiso nayi ta bashi false hope ina yaudararshi alhalin ba aurenshi zan yi ba? To ni ba haka nake ba tun farko da nasan gurguncewa zai yi ma bazan fara kula shi ba bare har ki samu bakin faɗa mini baƙar magana, aikin banza kawai bayan ko kece babu yadda za ayi ki yarda ki aureshi shine ni zaki cikani da baƙin munafurci da iyayi  har da wani wai abinda nayi ban kyauta ba, mtsew" Ta ɗauki wayarta ta koma ta kwanta tana cigaba da chatting ɗin da take yi kafin shigowar Habi tayi mata ruining mood ɗin ta. Murmushin takaici Habi tayi tace "Gaskiya ce ba kya so ni kuma bazan daina faɗa miki ba idan kin so ki ɗauka kiyi aiki da ita idan kin so kiyi watsi da ita kamar yadda kike yi da duk wata gaskiya da zan faɗa miki, kada dai ki manta ramin ƙarya ƙurarre ne kuma ƙarya fure take yi bata ƴaƴa kuma duk wanda ya hau motar kwaɗayi zata sauke shi a tashar dana sani, ni sai yanzu ma na fahimci tun asali dama ba son Baqeer ɗin kike yi ba hidimar da yake yi miki kike kwaɗayi yanzu daya rasa duk wata dama tashi shine kike nema ki guje shi." "An guje shi ɗin, idan kin ji haushi ke ki aureshi mana, ha'an kin fa isheni Habi wallahi ki fita idona in rufe, tom," tayi wata irin ƙwafa alamun dai ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, daga baya ma tashi tayi ta fice ta bar mata ɗakin. Bin bayanta Habi tayi da kallo tana jin takaicin halin ƴar uwarta tana jiye mata aikin dana sani don tasan komai daren daɗewa sai tayi dana sanin yaudarar da ta yiwa Baqeer ta gujeshi kawai don Allah ya jarabce shi da larura. Asiya ta gyara kwanciyarta dan dole ta yakice komai a ranta, duk da a can kasan ranta tana tausayinsa sannan tasan bata kyautamai ba, sai dak hakan shine daidai dan tabbas a yanda tasan Baqeer na santa in har tamai lagwa-lagwa to fa bazai taɓa rabuwa da ita ba, ita kuma a yanzu tasan wutsiyar rakumi tayi nesa da ƙasa shiyasa bama tasan abinda zai ja rabuwarsu ta ɗau lokaci gwara yaji zafin kalamanta ya kyaleta. ***** Suna tafe shiru babu mai iya cewa ɗan uwanshi komai, shi dai Salim tausayin Baqeer ne fal a ranshi don lokacin da yaga budurwar nan tana magana ya taho ya ɗauka wani abin ne, ganin sun ja mota sun tafi yasa yai kamar zai koma cikin shagon, sai yaji kalaman Baqeer wanda ya sashi tsayawa gefe hakan yasa yaji duk abinda Asiya take cewa, sosai ya cika da tsoron Allah yana mamakin halin mutanen yau. A yadda yasan soyayyar Baqeer da Asiya bai taɓa zaton zata guje shi cikin lokaci ƙanƙani ba don kawai Allah ya jarabce shi da wata larurar da bashi ya ɗorawa kanshi ba. Suna tafe yana tura Baqeer a keken guragun shi sai dai ya kasa ce mishi komai don yana jin yadda yake sauke ajiyar zuciya akai-akai, fatanshi Allah yasa kada ya ɗauki damuwar Asiya ya ɗora a ranshi alhalin dama ba wai ya warware daga damuwar ƙaddarar da ta sameshi bane. Har suka ƙarasa gidansu Baqeer babu mai magana, dama dai tunda abun nan ya faru Baqeer bai cika yawan magana ba idan ba ya zame mishi dole ba, Salim ɗin ne mai yawan maganar ko ba zai amsa ba yasan yana jin shi to shima yau damuwar abinda Asiya ta yiwa abokin nashi ta hanashi sukuni. A ƙofar gida suka tarar da Baba dake ta faman kaiwa yana kawowa tunda ya dawo gida ya tambayi ina Baqeer Umma tace mishi baya nan sun fita da Salim sai dai bai faɗa mata inda zasu je ba hankalin shi ya tashi, sam baya so mutanen unguwa su san halin da Baqeer ɗin ya samu kanshi a ciki don a ganinshi kamar zai zama abin zunɗe da dariya ganin yadda ya ɗaukake shi a cikin dukkanin ƴaƴan shi ya fifitashi ya fifita uwarshi akan baiwar zanen da kowa yake ganin ɓata lokacin shi yake yi akai don basu ɗauke shi wani sana'ar kirki ba kamar yadda shi ya ɗauka, har nasiha an sha zuwa har gida ayi mishi akan bai kamata yake fifita Baqeer ɗin da ƴan uwan shi ba sai yace ai dole ya fifita Baqeer don kuwa shi ɗin ɗa ɗaya ne tamkar da ɗa goma, shine zai share mishi hawaye ya cika mishi daɗaɗɗen burinshi na rayuwa suma idan suna so ya gatantasu kamar Baqeer suje su koyi yadda ake zane zasu ga yadda zai ji dasu ya ɗaukaka su a cikin ƴaƴa. A duk sanda ya faɗi haka kallan mara tunani mutane ke mai, zane fa? Ya rasa abinda zaiyi alfahari dashi sai zane? Dan mu kasarmu sam bamu ɗau ki zane da sunan sana'a ko abin alfahari da mutum zaiyi dashi ba. Wani wulaƙantaccen kallo ya watsawa Salim daya durƙusa yana gaishe shi, bai amsa ba sai masifa daya balbaleshi da ita akan don me yazo ya fita da Baqeer yawo, wato gurgunta shin da yayi bai isa ba shine yake zuwa har gida yana fita dashi salan wani abun ya ƙara samun shi. Shi dai haƙuri kawai yake bashi don idan da sabo yaci ace ya saba da halin Baban abokin nashi, shi Baqeer ɗin ne yake bashi tausayi shi yasa baya kula duk wani baƙin hali na Baban yake zuwa yana taimakawa Baqeer ɗin da wasu abubuwan amma in banda haka ai da tuni yayi zuciya ya fita daga rayuwar ɗan shi tunda dai dashi ne baya son ganin shi. Shi ya tura wheelchair ɗin zuwa cikin gida yana ƙwalawa Umma ƙira tun daga soro. Tuni su Abu da Jamila suka fito daga ɗakunansu tun ma kafin Umman ta fito don son jin gulma sun san tunda ya shigo da hayaniyar nan tabbas tijara zai yi mata. A nutse ta fito daga ɗakin duk kuwa da yadda gabanta yake faɗuwa tunda taji mahaukacin kiran da yake ƙwala mata. Daga bakin ƙofar ɗakinta ta tsaya tace "Gani Mallam, barka da shigowa." Da wani irin kallon takaici ya bita kafin yace "Kina cikin gidan nan don shashanci zaki dinga bari wancan lalataccen yaron yana zuwa yana ficewa dashi yawo salon mutanen unguwa su ganshi a keken guragu suyi min dariya, owo zane ne ba zai iya ba idan anyi magana kuce bai warke ba har yanzu hannunshi nayi mishi ciwo amma ya iya ficewa yawo har sai an nemeshi kafin ya dawo gida, ni dama nasan baƙin ciki kike yi mini shi yasa kika ƙi yarda ya koma aikinshi na zane, to ai ba ni kaɗai na rasa ba harda ke uwarshi tunda kafin yayi mini maganin naira goma ai yayi miki na ɗari, kuma na faɗa miki kada ki ƙara bari wancan yaron ya shigo mini cikin gida ya fita dashi yawo, tunda dai ba zai yi zane ba sai yayi ta zama a cikin gida amma na yanke hulɗa a tsakanin shi da shi." Murmushi tayi mai ciwo ganin yadda maigidan nata ya ware murya yana yi musu tijara a tsakar gida kamar ba shine wannan uban dake ji da Baqeer yana lallaɓashi ba amma yanzu saboda ƙaddara ta sameshi shine na farko wajen juya mishi baya babu tausayi bare tausayawa halin da yake ciki shi dai damuwarshi kawai burinshi ne da ba zai cika ba. Sai da ta gyara tsayuwarta sannan tace "Amma Mallam idan ka hana Salim shigowa wajen Baqeer waye zai tallafa mishi wajen yin buƙatun da dole yana buƙatar mataimaki, kasan dai ni mace ce akwai larurar da dole sai namiji ɗan uwanshi ne zai taimaka mishi da ita kuma shi Salim ɗin da baka son ganinsu tare shi kaɗai ne yake tallafa mishi a irin waɗannan lokutan kaga kuwa ko don wannan ai baka rabasu ba tunda dai mu muke amfana dashi ba shi yake ƙaruwa damu ba." Tsaki yayi cikin ranshi yana ganin kuma fa haka ne dole Baqeer ɗin yana buƙatar mataimaki gara ya bar Salim ɗin yaci gaba da kula dashi tunda dai yaji ya gani shi yasa kanshi ba wani ya saka shi ba don haka yace mata "Shikenan yana iya zuwa ko don kula dashi ɗin amma sai a kula da fita dashi waje don bana so." Sai a sannan Baqeer ya ɗago kai ya kalli mahaifinshi yana tunanin dama haka yake ko kuwa wannan ƙaddarar data sameshi ce ta mayar dashi hakan, a tunaninshi ko kowa ya juya mishi baya banda mahaifin shi mi ji dashi mai tsanani so da ƙaunar farin cikin shi, sai dai kash mutanen duniya ba'a ci musu alwashi don baka sanin asalin kalarsu sai idan wata ƙaddara ta afka maka sannan suke bayyanar maka da asalin ɓoyayyiyar fuskarsu. ***** #Baqeer🦼 #RayuwadaKaddara #Hawayena #Samudarashi #UmmuAsgar #Ayushermuhd *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 Umm Asghar Ce Da Ayusher Muhd *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *ƊANƊANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA* Da taimakon Umma Baqeer ya koma ɗakinshi. Abincin shi ta fita ta ɗauko sai dai ko kusa ya ƙi yarda ya sanya ko loma ɗaya a bakinshi don halin da ya tsinci kanshi a ciki yafi gaban ya iya sakawa cikin shi wani abu, haka tayi ta lallaɓa shi da ban haƙuri da nasiha akan ya daure yaci ko kaɗan ne amma ya kasa, haka nan ta haƙura ta ƙyaleshi ganin duk yadda tayi dashi ya ƙi karɓar abincin da take kaiwa bakinshi, sai da ta tabbatar baya buƙatar komai kafin tayi mishi sallama ta fita daga ɗakin taja mishi ƙofar ta rufe. Tana fita hawayen da yake ta riƙewa suka samu sararin zubowa, idanu ya kai kan ƙafafun shi da ko kaɗan baya jin alamun su a jikinshi, shi kenan shi yanzu haka zai yi ta zama ya nakasa ya zama musaki ba zai iya ƙara amfanawa kanshi komai ba sai dai ayi mishi. Sai ƙoƙarin ɗaga ƙafafuwan yake yi amma ya kasa, yayi-yayi ya motsa su ko yaya ne abu yaci tura. Hannunshi mai lafiyan yasa yayi ta dukan ƙafafun ko zai ji wani feeling nan ma babu abinda yake ji. Wani irin ihu yasa yana cewa "Nooo..." haɗe da dukan ƙafafun da yake jin su tamkar ba a jikin shi suke ba da ƙarfi. Duk mutanen gidan babu wanda bai ji ihun da yake yi ba don haka duk suka firfito daga ɗakunansu suna kallon ƙofar ɗakin Baqeer ɗin sai dai babu wanda ya iya ƙarasawa ya duba halin da yake ciki. Kamalu ne yaja tsaki yace "Wannan hala bayan gurguncewar harda matsalar ƙwaƙwalwa ya samu ba'a sani ba, shine aka kawo mana mahaukaci cikin gida aka ajiye" babu wanda yayi magana sai ma kallonshi da suka yi suna gasgata hasashen da yayi a cikin ransu. Umma ce ta fito daga ɗakinta sanye da hijabi don duk abinda ake yi tana jin su hankalinta kuma yana wajen ɗanta sai dai ba zai yiwu ta katse sallar da take yi ta fito ba. Suna ganin ta Kamalu ya saki wani ɗan iskan fito cikin magana irinta ƙauraye yace "Yauwa da Allah in kin shiga sai ki faɗawa mahaukcin  ɗanki bashi kaɗai bane a gidan ya ɗan sassauta murya haka nan ko don muna so mu kwanta muyi barci, ah to." Ko kallonshi bata tsaya tayi ba ta faɗa ɗakin Baqeer a gaggauce tana cewa "Baqeer lafiya kake kuwa? Ko wani wajen ne yake yi maka ciwo?" Ta ƙarasa kan katifar ta zauna sannan ta rungumo kanshi a jikinta tana shafawa kamar mai lallashin ƙaramin yaro. Jin shi a jikin Ummanshi yasa ya fashe da kuka mai tsanani, kuka irin wanda tunda ƙaddarar rasa ƙafafunshi ta afko mishi bai samu yayi kamar shi ba. Kuka yake yi yana shesheƙa abun tausayi kamar ba saurayin nan ɗan kwalisa mai ji da kyau da iya ado ba, matashi mai tsayuwa da ƙafafun shi ya nemi na kanshi abun alfaharin kowanne iyaye. Ita kanta Umma kukan take yi don tasan yanzu ne Baqeer zai san mecece rayuwa, yanzu ne zai san asalin masoyanshi na gaskiya da masu yi mishi soyayyar bogi don ba kowa ne zai karɓi ƙaddararshi a yadda tazo musu ba, tasan da yawan mutane yanzu gudunshi zasu yi shi yasa take ƙara tausaya mishi tasan ɗaukar dangana ba abu ne mai sauƙi ba a wajen shi yanzu. Sosai yayi kuka mai yawa kafin ya tsagaita da kukan ya ɗago kai ya kalleta suka haɗa ido sai yaga ashe itama hawayen take yi, hannu yasa ya goge mata hawayen yace "Shikenan ni yanzu bani da wani amfani Umma kowa guduna yake yi saboda na zama gurgu, har Baba da ya kasance mahaifina ba zai tausaya mini ba da ƙaddarar data sameni? Yanzu tsakani na dashi sai kyara da hantara kamar ba shine wannan Baban mai yawan nuna mini soyayya da tattalin farin cikina, ashe mutanen duniya sai kana da wani amfani da zaka yi musu suke sonka daga inda ka rasa duk wata dama taka sai kowa ya juya maka baya," sai ya ƙara fashewa da kuka don wani irin ciwo yake ji a cikin zuciyarshi, ji yake yi da zai iya babu abinda zai hanashi fincikota ya jefar ko ya huta da azabar raɗaɗin da take yi mishi. Kanshi ta dafa cikin sigar lallashi tace "Kayi haƙuri Baqeer kowa da kake gani da yadda ƙaddara take zuwa mishi ba kuma ka taɓa sanin asalin masu ƙaunarka sai idan wata ƙaddara ta same ka, mahaifinka ba gudunka yake yi ba ya dai kasa karɓar ƙaddarar data same ka yayi haƙuri ya gane cewa komai daya faru nufin Allah ne, babu wani daya isa ya tsara maka rayuwa face abinda Allah ya hukunta zai sameka don haka nake jan hankalinka daka cire damuwar komai daga ranka ka sanya dangana a cikin ranka, nakasa ba kasawa bace jarrabawar rayuwa ce." Haka nan dai tayi ta mishi nasiha har ta samu ya daina kukan ya koma sauke ajiyar zuciya kawai cikin hukuncin Allah kuma sai bacci mai nauyi ya ɗauke shi, ganin da tayi ya samu bacci sai ta gyara mishi kwanciyar shi ta mayar mishi da kanshi akan pillow ta janyo abun rufar shi ta rufe shi, sai da ta tofe shi da addu'a sannan ta tashi ta kashe mishi fitila ta fita. Tana fitowa suka haɗa ido da Baba dake tsaye a ƙofar ɗakinshi ya kalmashe hannu a ƙirji yana watsa mata wani irin wulaƙantaccen kallo, ashe duk abinda ke faruwa yana ji bai dai yi niyyar fitowa bane sai da yaga lokaci yaja Fatima dake da girkin ranar bata je ɗakin shi ba sannan ya fito. "Saboda nakasashe musakin ɗanki kika bar ni ina jira har yanzu?" Ya watso mata tambayar cikin faɗa tamkar ya mance dare ne yanzun komai ƙanƙantar sauti ɗauka yake yi. A sanyaye ta ƙaraso daf dashi sannan tace a taƙaice "kayi haƙuri" don bata son jan magana mai tsawo a tsakaninsu, tasan halinshi sarai ba haƙuri ne dashi ba don ya kwana yana yi mata tijara ba damunshi yayi ba ita kuwa yanzu bata da lokacin biye mishi suyi tashin hankali damuwar halin da ɗanta yake ciki ne a gabanta. Har ta wuce shi ta shige ɗakin nashi ta karkaɗe gado ta hau ta kwanta bai shigo ba, sai zuwa can kuma har bacci ya fara ɗaukarta taji motsin shigowar shi ɗakin. ***** A guje Mummy ta rungume Zeey cikin tsananin murna itama ta ƙanƙame ta, Nabeela dake gefe tana kallonsu ta girgiza kai tace "Aunty na ɗauka kunnenta zaki ja? Kinga abinda ta yiwa guy ɗin nan kuwa?" Hararar Nabeela tayi tace "To kanwa uwar haɗi, har wani abu ma nayi mishi?" Mummy zata yi magana suka ji ana kwallawa Zeey kira cikin magana mai sauti, Kabir ne shiyasa basu wani ɗagawa kansu hankali ba har ya ƙaraso, kallonta yayi cike da masifa yace "Kina nufin abokina kika yiwa kallon driver? Kika wulakantashi a gaban mutane? Kalli..." Yayi maganar yana nuna mata wayarshi inda da alama wasu ne suka ɗauki video ɗin abinda ya faru suka watsa a social media. "Calm down bro, meye kake exaggerating ɗin abun haka wai? Chill out!" Takaici ne ya sake rufeshi yace "Kinsan Allah zan zabga miki mari, ina miki faɗa kina cemin wani chill out?" "To chill in shikenan?" Kallon Mummy yayi yana ji kamar ya shaƙota ya zabga mata mari, Mummy ta ɗan murmusa tace "Ya haƙuri Kabir am sure ba da saninta tayi ba, kayi haƙuri kaji? Kema bashi haƙuri." Huci Zeey ta saki kafin  tace "S" Kabir ji yai kamar yayi hauka don takaici, a fusace ya bar parlourn yasan shi kenan yanzu zaman gidan zai fara bashi haushi don sam yarinyar nan ta gama rainashi. Harararta Mummy tayi tace "Me kika yii haka?" Tace "Ban fa sani ba, na ɗauka driver ne." Daga waje suka jiyo shigowar motar Dad cike da jin daɗin dawowar Zeey. A ɓangaren Bello kuwa tunda ya samu aka kirashi zuwa wajen deputy gwamna gashi har an mayar da sunanshi a madadin na Baqeer a matsayin wanda zai wakilci Jihar Kano a wajen gasar da za'a yi yake murna. Shi dai kam yasan kakarshi ta yanke saƙa, ya taki sa'a irin wacce bai taɓa zaton zai samu ba a rayuwa, wannan accident ɗin na Baqeer ai shi aka yiwa don a komai Baqeer ɗin na gabanshi gashi yanzu cikin ruwan sanyi ya samu abinda ya daɗe yana mafarkin samu. Fifikon da Baqeer yayi mishi na matuƙar baƙanta mishi zuciya ganin dai harkar zanen duk ita suke yi hasali ma ita ce ta fara haɗa su abota sai dai kafin a ambace shi a waje sai an fara kiran Baqeer kafin a ambace shi sau ɗaya an ambaci Baqeer sau babu adadi, duk wani alheri daya tunkarosu to wajen Baqeer yake fara zuwa kafin su, a komai sai dai ya samu sauran Baqeer, abinda yake baƙanta zuciyarshi don a ganinshi Baqeer bai fi shi da komai ba sai tsantsar sa'a da tsayayyen uban dake tayashi wajen faɗi tashin ganin ya cimma burinshi. Shirye-shiryen tafiyarshi Abuja kawai yake yi inda anan ne za'a yi gasar da za'a zaɓi waɗanda suka yi nasara a ɗauki nauyin faɗaɗa karatunsu a harkar zane a ƙasashen ƙetare. Yana ta shirin shi ba tare da ya bari wani daga cikin abokansu yasan shi zai tafi a madadin Baqeer ba don baya ma so kowa ya sani har sai yaje yayi abinda ya kaishi ya dawo inda yake fatan nasara ta zama tashi, a lokacin ne zai nunawa duk masu cewa Baqeer yafi shi da masu cewa baya iya yin zane sai da taimakon Baqeer ko shi waye, a lokacin zasu yi dana sanin wulaƙanci da cin fuskar da suka yi tayi mishi suna nuna mishi iyakarshi suna ganin shi ba kowa bane. ***** Har aka kwana biyu Baqeer na ƙunshe a ɗaki baya fitowa ko tsakar gida bare ya fita waje dama kuma yana da banɗakin shi a cikin ɗaki don haka ya ƙara takure kanshi da zaman ɗakin don sosai yasa maganar Baba a ranshi ta kada ya ƙara ganinshi a waje don kada mutane su ganshi ayi mishi dariya. Inda Allah ya taimaka ma kullum Salim ke zuwa safe, rana da dare yana taimaka mishi wajen turashi zuwa banɗaki ya taimaka mishi yayi wanka da duk wasu ƴan buƙatocin shi dai amma haka Salim zai zo ya ƙari maganarshi Baqeer ba zai ɗaga kai ya kalleshi ba bare ya tanka mishi sai dai ko kusa hakan bai taɓa damunshi ba sosai yake yi mishi uzuri tunda yasan da can ba haka yake ba yanayi ne kawai ya mayar dashi hakan. Yau Umma na wankin kayanta dana Baqeer da suka yi datti, wankin da a baya ta manta yadda ake yi don kayanta na yin datti Baqeer zai haɗa ya fita dasu sai dai ya kawo mata a wanke a goge iyakaci ta shirya a cikin wardrobe amma gashi yau kuɗin sabulun da zata yi wankin ma da ƙyar ta samu Baba ya bata bayan ya gama sauke mata kwandon tijara akan shi fa ba zai iya da tsirfarta ba idan ma zata nemi abun yi gara ta nema don bai ɗaukewa sauran matan shi sabulun wanki dana wanka ba ba zai fara a kanta ba. "Umma yau da kanki kike wankin da tsakar ranar nan? Ina Yaya Baqeer ɗin bai samu ya fita dasu ba?" Jin maganar yasa ta ɗaga kai tace "Hadiza? Yau kece da safen nan?" Shigowa tayi tana sallama Hadiza, ƴarta ta biyu ce  wacce ke bin Baqeer, tana shigowa tana cewa "Umman mu abin ne ya bani dariya kece da wanki?" "Da kaina nake yi Hadiza, ku shiga daga ciki yanzu zan ƙarasa na shigo nima." Bata shiga cikin ba sai ma saka hannunta da tayi a bokitin wankin tana cewa "Kawo na ƙarasa miki Umma ki zauna ki huta kema." "To kuma daga zuwanki ko zama baki yi kin huta ba sai ki kama wanki?" "Idan ban yi miki ba Umma wa zan yiwa, don Allah ki bari na ƙarasa, gashi naga ma ƙarashe ne wankin naki." Haka nan ta sakar mata kayan ta ɗauki jakarta da ƙaramar ƴarta data yaye suka shige ɗaki, sauran abincinta na safe ta ɗaukowa yarinyar ta zauna tana bata a baki kamar tasan da zuwansu dama. Ai kuwa yarinyar ta ware ciki tana cin abinci sai kace kuncen yunwa, tas ta cinye abincin duk kuwa da yana da ɗan yawa, ita kanta Umman tayi mamakin yadda yarinyar ta cinye abincin tas ga alama daɗaɗɗiyar yunwa ce a jikinta, ganin ta fara gyangyaɗi yasa ta miƙe ta ɗebo ruwa ta bata ta sha sannan tasa zani ta goyata, kafin wani lokaci har bacci ya ɗauketa. A daidai wannan lokacin Hadiza ta shigo, ganin ƴarta a baya yasa tace "Wannan ƙatuwar yarinyar kika goya Umma salon ta saka miki ciwon baya?" Harararta tayi tace "Ina abun girma a wannan ƴar yarinyar da bata haura shekara biyu ba banda dai lalaci da yayi muku yawa ba kwa son goyo." Zama tayi akan doguwar kujera ƙwaya ɗaya dake ɗakin Umman wacce Baqeer ne yasa aka yi mata ita tana dariya. "Umma ina yini? "Lafiya lau Alhamdulillah, duk ƙalau kuke? Ya yaran?" "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, kwana biyu bamu gaisa ba gashi ni wayar tawa akwai da babu sunanta ina ta roƙon ya bar ni nazo ya hana sai yau Allah ya nufa ya barni nazo a hakan ma wai kada na kai yamma, Allah yasa dai Yaya Baqeer na nan don ina son ganinshi." Kallo ɗaya zaka mata kasan cikin damuwa take, gaban Umma ne ya ɗan faɗi, Allah dai yasa ba wani abin bane mai girma itama tazo dashi? *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #Shalele # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD Umm Asghar Ce Da Ayusher Muhd *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR* *DADANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BIYU* Yadda Umma ke kallonta ne yasa gaba ɗaya jikin Hadiza yin sanyi cike da kulawa take bin Umma da kallo tace "Ba dai har lokacin tafiyar tasu Abuja yayi ba?" Umma zata yi magana suka jiyo salatin Bashir yana haɗawa da sunan Baqeer, cikin hanzari Umma ta miƙe ta fito ita ma Hadiza tabi bayanta, kafin su iso har Abu da Jamila sun fito, gaba dayansu ɗakin Baqeer suka nufa, a ƙasa suka ganshi ruwa duk ya malale a ƙasan, cikin sauri Umma ta ƙarasa kuda dashi tana cewa "Baqeer meya faru? Menene?" Kasa magana yayi sai hawaye kawai dake cigaba da taruwa a idanunshi, Bashir ta kalla tace "Me ya faru?" Yace "Ni ban sani ba na shigo zan ɗauki aron laptop ɗinshi na ganshi a ƙasa da alama ma ya daɗe da faduwa". Nan da nan Umma taji hankalinta ya tashi, Abu ta kalli Jamila kafin tace "To Fatima wannan fa ina ga sai dai ki sakashi kusa dake inba haka ba wani abun zai iya samunshi ba'a sani ba." Takaici ne ya kamata don tasan wulakancinsu ne ya tashi idan ba haka ba taya zasu ce ta mayar da Baqeer dakinta? Bata ko kulasu ba suka juya suna ƴan ƙananun maganganu, Bashir ne ya taimaka mata suka mayar dashi kan katifa sannan ya fita, Hadiza kam a ƙame take ƙam tana jin zuciyarta kamar zata fashe, me take gani haka? Meke faruwa? Gaba ɗaya ƙwaƙwalwarta ta kasa gasgata mata abinda take gani, idanun Baqeer ne ya sauka kanta, sai a lokacin hawayenshi suka zubo ganin yadda take hawaye wani na bin wani, jan ƙafafunta ta shiga yi zuwa inda yake ta kama ƙafafuwan shi kawai tasa wani irin kuka, ganin haka yasa Umma ta miƙe ta bar musu ɗakin tana share ƙwalla, ta sani Baqeer kamar uba yake a wurin su ta daɗe tana tunanin yadda zasu ɗauki wannan abun, tafi minti goma tana kuka don har ƙarfinta na kukan ya fara raguwa kafin ta ɗago, kallonshi tayi kai kawai ya kauda tare da runtse ido, ta dawo inda yake tace "Yaya ba zai yiwu ba ka tashi kayi tafiya dan Allah! Na rokeka da Allah ka tashi kayi tafiya." Hannunta da tasa tana jan hannunshi ya kalla ya kai hannunshi na dama sai riketa yaji wani uban zafi ya maida hannun wanda hakan yasa ta kalleshi da sauri sai a lokacin ta kula da yanda aka naɗe hannun, a rikice ta sakeshi ta fashe da kuka tana cewa "Na shiga ukuna Yaya menene haka? Laifin me muka yi da Allah zai jarabce......" Hannu yayi saurin sawa ya rufe bakinta yana girgiza mata kai, hannu tasa ta goge hawayen idanunta tace "Meya faru Yaya? Yayan mu dan Allah ka tashi." Yawun bakinshi ya haɗiya don ko magana yanzu baya son yi, Baba da Asiya sun sake tabbatar mishi abinda yake tsoro. Bakinshi ya sake motsawa kafin yace "Mijinki fa? Babu dai wani abun ko?" Nan fa hawayenta suka ƙaru tace "Yaya wa ke tani kana cikin wannan halin? Yaya duk abinda nake ciki bai kai kwatan naka ba, na shiga uku." "Kin tabbatar ba wani abun?" Ji take yi kamar tayi ihu, wannan wani irin abu ne take fuskanta? Da gudu ta tashi ta bar ɗakin tana shiga ɓangaren Umma ta wuce ɗaki ta faɗa kan gado, shikenan su kuma sun zama marayu don dama Allah ne gatansu Baqeer gatansu, duk su biyun rayuwar auransu kowane na cike da kalubale amma babu wanda ya sani a gidan sai Baqeer saboda shi kaɗai ke saita musu komai ba tare da manya sun shiga cikin maganar ba, yanzu ya zasu yi? Kuka take sosai har ƙarar kukanta ya tashi yarinyarta Aydah dake kwance daga bacci. Umma ta shigo ta ɗauketa ta fita da ita don tasan dole Hadiza tayi kuka, samun Baqeer yasa su kwanciyar hankali wanda a koda yaushe take alfahari da yadda yake kula dasu. ******* Asiya ce kishingiɗe akan gado tana jin Inna da Habi nata aikin waina a waje amma tana kwance a ɗaki don ita sam bata son aiki ba kuma ta son girki especially da murhu, shi yasa tace gidanta inba gas cooker ba sai dai a siyo takeaway amma ba zata iya aikin hayaƙi ba. Waya take yi cike da fara'a, Habi ce ta shigo ɗakin sai gumi take yi na hayaki idanunta sunyi jaa ta shigo ɗaukan radion Inna ne data ara jiya da daddare, ganin Asiya tana waya yasa tace "Waye? Baqeer ne?" Asiya ta kauda kai alamun a'a sannan tace "Yanzu kana Abujan?" Daga jin haka yasa Habi ta matsa tasa kunnenta gefen wayar tana son jin abinda ke faruwa, Asiya tace "To shikenan Bello Allah ya bada sa'a sai ka dawo." Miƙewa Habi tayi tana wa Asiya kallon tuhuma harta kashe wayar, cike da mamaki tace "Bello kuma? Yaushe kuka fara waya akai-akai haka? Don jiya ma naji sanda ya kira yace miki kiyi mishi addu'a wai zai yi tafiya." Tsaki Asiya tayi tace "Koma yaushe muka fara menene damuwarki a ciki? Kawai kirana yayi yace in sakashi a addu'a akwai abinda yaje yi Abuja yana so Allah ya bashi nasara shikenan sai nace bazan yi ba?" "Ji wani munafurci, addu'ar iyayenshi bata isheshi ba sai ya haɗa da taki? Ko sanda Baqeer yake nemanki a waya kin ɗaga ne? Wallahi dai kunji asara daga ke har shi in ma wani abun kuke tunani, aikin banza kawai." Tana kaiwa nan ta juya ta ɗauki radio ɗin ta fita a fusace ranta a mugun ɓace, baki kawai Asiya ta taɓe don ita ƙarfin halin Habi har mamaki yake bata. ******* Da ƙyar Hadiza ta saki ranta, jin shirunta yasa Umma ta shiga ɗakin ta zauna kusa da ita ta sanar da ita duk abinda ke faruwa, ta kalleta a rikice tace "Yanzu suna nufin shikenan ya rasa ƙafafuwan shi?" Kai Umma ta ɗaga tace "Addu'a ce tamu amma haka suka ce." Ta goge hawayenta wanda idanunta har sun ƙanƙance saboda kuka tace "Umma ɗazu fa da alama ruwa yaje sha ya faɗo dan ga jug na ruwa nan a ƙasa, kina nufin haka zai dinga rayuwa?" "Wanda kuma Allah ya halicce shi a haka fa? Wanda kuma Allah ya jarabceshi da rashin ƙafa? Hannu da ido fa? Ko kuwa wanda Allah ya jarabceshi da ciwon da baisan inda yake ba fa? Ba haka suke cigaba da rayuwa ba?" Hadiza tayi ƙasa da kai don ita kam bata san me zata ce ba "To ya zamu yi? Mun isa jaa da hukuncin Ubangiji ne?" "Bamu isa ba sai dai ina ganin mu samu wani ya dinga kula dashi bazai iya zama shi kaɗai babu mai taimaka mishi ba." Hadiza tayi maganar cike da jin tausayin ɗan uwan nata. "To Hadiza in mun samu wani waye zai dinga biyanshi?" Umma tayi maganar tana kallonta, nan ta dago tana jin zuciyarta na zafi ace duk abinda yayansu yayi musu yanzu su lokacin rama mishi yayi amma babu hali? Ita mijinta ba mai babban karfi bane gashi kullum cikin rigima suke dashi saboda ba ita kaɗai bace a wurinshi gashi baya son haihuwa tunda suka yi aure bata dade da samun ƴan biyunta ba ya fara ito mata da halayenshi sai gashi kuma babu daɗewa ta ƙara samun cikin Aydah anan ne yace sai dai taje asibiti a zubar ita kuma tace sam, haka suka yi ta rigima data so yin yajin Baqeer ya daidaita su, sai autar Umma Maryam ita kuma mijinta dan kasuwa ne yana da kuɗi kuma yana kyautata mata bakin gwargwado sai dai matsalar uban miji wanda ya addabeta ya hana samun zaman lafiya da mijinta, gaba ɗaya zaman aurenta bata sati ɗaya ko biyu sai Baqeer yaje yayi sulhu akan saɓanin da uban mijin ke haddasawa a tsakanin su. Jin kalaman Umma yasa Hadiza tayi shiru, shikenan su babu yadda zasu yi? Miƙewa tayi ta koma wajen Baqeer ta gyara ƙasan ɗakin ta dawo ɗakin Umma ta ɗauki drawer ɗinta ta gefen gado ta kai ɗakin tasa kusa da inda katifarshi take tasa aka siyo ruwan pure water tasa a saman drawer ɗin, sannan tasa spoons da plate da wasu ruwan a cikin drawer ɗin, ta ɗauko papers da pencils tasa a na ƙasa nan ta fara kale-kale tana neman wasu abubuwan da zai buƙata, duk abinda Hadiza take yi idanun Baqeer na kanta, kallonta kawai yake yi don kwanan nan sam baya jin magana mutuwa kawai yake jira tazo ta ɗauke shi, ɗazu ma daya faɗi shi yasa ko ƙira bai yi ba azo a taimaka mishi, jira yake yana daga kwancen nan rai yayi halinshi, sai gashi nan garau sai ma wani tashin hankalin daya sake shiga. Wayarta ta ɗauko kawai ta cire sim ɗinta na mtn ta bar airtel a ciki ta ajiye kusa dashi tace "Yaya ga wayata sim ɗin bana amfani dashi data kawai nake siya idan na samu dama, Umma tace an sace maka waya dama kaine ka saya mini ita kaga yanzu sai ta dawo wurinka, ina zaka iya rayuwa babu waya babu aikin daka saba babu komai a ɗaki? Sannan anjima Salim zaizo sai mu turaka tsakar gida ka dinga samun iska kana shaƙa ba wai kullum kana ƙunshe a ɗaki ba." Wayarta ya miƙa mata kawai ya girgiza kai alamun a'a cikin dakewa ta girgiza kai tace "Don Allah Yayah ka rufa mana asiri kaine gatan mu, wannan rashin maganar Yaya baza mu iya ɗauka ba ka taimakemu ka dawo yanda kake kar baƙin ciki yayi maka illa don Allah!" Murmushi yayi na yaƙe, ta sake miƙa mishi wayar sannan ta fito, kallon wayar yayi yana ji kamar ya kira Asiya sai dai inaa bazai iya ba don shi yanada zuciya baya zama inda ba'a sonshi, balle yanzu da yake neman komawa ga Allah, hakan yasa ya ajiye mata wayar a gefe. Hadiza tana fitowa ta ɗauki wayar Umma ta kira Maryam tace Inda hali tazo gida in ta dawo daga ɗauko Areef daga makaranta. Ba tare da wata damuwa ba tace to zata biyo. ***** A hankali Zainab ke buɗe ido tana rufewa, kallon agoggo tayi ganin azahar har tayi yasa ta yin miƙa sannan ta mike, wayarta ta duba ganin missed calls tayi kusan guda goma, tsaki tayi sannan ta duba text ganin saƙo ne daga number ta duba, da alama yaron jiya ne dan bakaken maganganu yake faɗa mata akan ta zubar mishi da mutunci tasa yanzu ana yi mishi dariya. Baki ta taɓe sannan ta kira number, bugu ɗaya ya ɗauka tana jiyo alamun mutane daga gefe ana cewa "Yess karka barta." Nabeela ce ta shigo ɗakin ɗauke da kayan da aka aiketa ta siyowa Zeey na lotions ɗinta wai ta manta da nata acan, Zeey tana kallon Nabeela tace "Yes Jamal inaji!" "Najib!" "Oh Alhaji Najib!" "Ki bani haƙurin abinda kika yi mini sannan ki faɗawa friends ɗina wasa muke yi bawai da gaske muke ba." "Wai dama shine dalilin kiran? Okay! Friends hope kunji? Sannan please Jamal next time in zaka wurin budurwa dress properly, I mean dress like a real guy please." Tana kaiwa nan ta kashe wayar tare da blocking number ɗinshi. Nabeela ta girgiza kai tana ajiye kayan kan dressing mirror tace "Zeey please ki bar wulakanta mutane." "Wai gaskiya ce ban isa na faɗa ba? Ni ban wulakantashi ba abinda ke raina kawai na faɗa bana ji kuma laifi ne don nayi hakan" Shiru kawai Nabeela tayi don tasan ba'a cin Zeey a magana, miƙewa tayi tace "fita zan yi idan nayi sallah, bani car key ɗinki please bana so Dad yasan bana nan ba dadewa zan yi ba." Kamar zata musa sai kuma ta bata, da sauri ta shiga toilet bata dade ba ta fito ta shirya cikin English wears riga doguwa har gwiwa da wando, tayi sallah sannan ta miƙe tace "Ki zauna a ɗakin please kafin a nemeni in kika ga zata kwaɓe ki faɗawa Mum da wuri, bye." Bata ko jira taji amsarta ba ta fice. Saman kanta kawai Nabeela ta shafa. ita kam tasan watan maida ita baiwa yayi don Zeey maidata take kamar wata ƴar aikinta bayan ita kanwar mahaifiyarta ce kawai dai Zeey ɗin ta girmeta ne da wata shida. Zeey tana fara tafiya suka yi kiciɓis da wata mota, kallin juna suka yi cike da mamaki wanda hakan yasa kowa yaja gefe yayi parking, da sauri Zeey ta fito ta ƙara so jikin motar ɗayar, itama ta fito suka rungume juna cikin jin daɗi cike da mamaki tace "Wai ya aka yi kika ganeni? Ashe rai kanga rai?" Zeey tana dariya tace "Maryama Daso tawa, da gaske dai kece ni kuwa in ban ganeki ba a duniya ai duka za ayi mini, daga ina kike?" Tayi maganar tana kallon bayan motar ganin yaro a ciki yasa ta buɗe baki tace "What?" Maryam tasa dariya tace "Ehen ke fa?" "Inalillahi yaushe kika yi aure har dasu haihuwa?" Dariya tayi tace "Kinsan last mun haɗu dake sanda naje graduation na brother ɗina a Buk to lokacin ban ƙara 1year ba nayi aure." "Inalillahi I just can't believe it, how?" "How kamar ya? Ke fa? Kina nan kina neman maganar taki da kika saba?" Zee zata yi magana suka ji horn daga bayansu sai a lokacin suka kula da yanda Zeey tayi parking, dariya suka yi Zeey tace "I just hate naga mutane ba haƙuri, ya ɗan jira kaɗan mana." "Madam kin san uzurinshi ne? Halinki na nan dai ashe." "Hmm share kawai kin ji, Umma fa? Ina Umman mu?" "Tana nan bayan sam kin manta da ita tunda kuka tashi ko leƙota bakya yi." Fuska ta tsuke tana juyawa alamar zata tafi tace "Kin dai san dalili ai daga nan kuma ban san ya akayi ba zumunci ya watse." Dariya sosai Maryam tayi tace "Wai har yanzu baki manta ba? To kizo muje am sure Ya Baqeer na gida ku gaisa shi ya manta." Tsaki taja tace "Allah ya sauwake ni yaushe rabon dana ganshi ai ko a lahira kowa ya kama gabanshi, nifa banda yayanki ne da ɗan Umma wallahi da...." Sai kuma tayi shiru tana cewa "Zan aika a amsomin numberki wurin Umma tunda muna kan hanya." Kai Maryam ta gyada nan ta tuno abubuwan da suka faru shekarun baya wanda yasa ta murmushi da girgiza kai kafin ta shiga mota. Areef ne cikin gwaranci yace "Mamy itama ƙawar kice?" Ta ɗaga kai tana dariya tace "ƙawata ce sai dai ƙawancen da bai yi nisa ba." Ta ƙarasa tana tada mota cike da mamakin yadda aka yi Zainab ta ganeta da wuri haka wasu abubuwa na sake dawo mata waɗanda ta tabbatar nisantar junansu shine abinda ya kamata. Nan ta ƙarasa gidansu.... *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer 🦼 #MBB #Asiya #Rayuwa da Kaddara #Nakasa #Hawayen rayuwa Na Ummu Asgar Da Ayusher Muhd *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*            *DA* *UMM ASGHAR* *ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA UKU* https://www.tiktok.com/@maims_kiddies "Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta. https://Wa.me//08101378616 Maryam sai data kusa isa gida ta duba jakarta, takaici ne ya kamata ganin naira ɗari biyar ce kaɗai a ciki, ajiyar zuciya kawai tayi tare da yin parking sannan ta fito da Areef suka nufi cikin gidan, tun daga soro zaka jiyo hayaniyar Baba yana magana cikin faɗa, da yake tasan halin Baba sai bata yi wani mamaki ba, ta tabbatar Kamalu ne ko Bashir ko kuma Salihu wani a cikinsu ne ya taɓoshi tunda yara matan gidan daga wanda yayi aure sai wanda suke boarding school. Ta ƙara yin taku ɗaya taji Baba ya ambaci sunan Baqeer, cike da mamaki ta shiga cikin gidan, Hadiza ta hango jikin bango banda hawaye babu abinda take yi, Abu da Jamila suna tsaye daga jikin ƙofar ɗakunan su suna kallon abinda ke faruwa, Umma ce a gaban Baba wanda hakan ya tabbatar mata da Umma ake faɗan, mamaki ne ƙarara ya bayyana a fuskarta jin Baba yace “Kin san Allah Fatima ki fita idona, idan har kika bari na sake magana to tabbas zaki tsinci kayanki dana ɗanki a waje, ni zaku maida soko? Kuna nufin ni da gidana ban isa inyi hukunci ba? To ni nace Baqeer ya tattara ya koma ɗakin Kamalu ya zauna shi kuma Bashir da Salihu su dawo nan, hakan ba adalci bane?” Fatima ta share kwallarta tace “Bance ba adalci bane amma sai yanzu Malam? Ka manta sanda kasa aka gina ɗakin nan da kaina nace ka haɗa mazan nan bibiyu wuri ɗaya me kace min? Cewa fa kayi Baqeer ba zai haɗa ɗaki ɗaya da kowa ba, kai baka son a dinga ɗauke mishi hankali da shirme gwara yayi zamanshi shi kaɗai zai fi maida hankali akan zanen shi, ko ka manta tsakar gidan mu ka rage ka gina ɗakin saboda shi shi kaɗai? Kayi mishi ban ɗakin shi a ciki?” “To nace yanzu na janye? Ko ke kika bani kuɗin dana yi ginin? Tunda har yaron nan ya tozartani ya wulakantani kema ai kinsan dole ku kwashi kayanku a hannu ko?” Zata sake magana ya ɗaga mata hannu yace “Na dai faɗa miki, kima barni naji da yanda zanyi na maidawa Yallabai kuɗin shi da muka cinye, sannan ki barni da dana sanin yanda na sadaukar da rayuwata kan yaron da ba wata rana da zai yi mini.” Cike da mamakin kalaman da Maryam keji take shigowa cikin gidan tace “Baba? Ya Baqeer ne fa?” Wani mugun kallo yayi mata ya maida kallonshi kan Umma da banda hawaye babu abinda take yi ya cigaba da cewa “Ki kuma sanar da yaranki wallahi duk wacce tayi gigin dawo mini gida da sunan yaji ko mutuwar aure sai dai ta shiga duniya ba dai ta zauna a gidana ba, sannan kafin naje na dawo ku tabbatar kun ɗauke shi daga ɗakin.” Yana kaiwa nan ya juya ya fita yana balbala masifa, ranshi gaba ɗaya yau a ɓace yake tunda ya kunna radio yaji ana maganar gasar da za’ayi gobe a Abuja da yanda masu gasar suka hallara suna masaukinsu. Ji yake yi zuciyarshi kamar zata fito saboda ɓacin rai, shekara guda kenan da turawan suka shigo da maganar gasar kuma shekara guda kenan yana shirin gasar nan amma gashi da ranshi da lafiyarshi abu ya gagara. Maryam kam da kyar ta iya jan kafafunta zuwa inda Umma take kame tace “Umma menene ke faruwa?” Areef ta kalla tace yaje ciki gun Aydah, Hadiza ce ta taho inda take da sauri ta rungumeta kawai tana kuka sosai, haka kawai Maryam ta samu kanta da hawaye a haka ta jata zuwa ɗakin Baqeer, yana zaune akan katifa kanshi kawai ya jinginar a jikin bango duk abinda ke faruwa akan kunnenshi ne, a zaune kawai yake idanunshi yake buɗe wa kawai yana rufewa, Maryam ganin hanunshi a naɗe yasa tace “Na shiga Ya Hadiza meya samu Yaya a hannu?” Hadiza ta fito da ita suka koma ɗakin Umma sannan ta sanar da ita abinda ya faru, tasha kuka itama ta gode Allah sai dai babu yadda zasu yi ƙaddara ce Allah ya jarabcesu da ita, haka suka fito dukansu suka tattare kayan Baqeer suka shiga dashi ɗakin Kamalu, wanda dama tare yake dasu Bashir, ɗakin kaca-kaca kai kace ba mutane ke kwana a ciki ba, haka suka gyara ɗakin sannan suka saka mishi kayan zanenshi a gefe, sunyi sa’a Salim ya zo don dama yace yana dawowa daga aiki zai zo, nan aka maida Baqeer gefe a cikin ɗakin suka jera mishi komai nashi, duk abin nan da suke yi ba wanda yake iya magana banda kwalla kawai da suke sharewa gashi Baqeer kallo ɗaya zaka yi mishi kasan shi kaɗai yasan meke faruwa akanshi dan idanunshi duk sun shanye kawai kallon kowa yake yi babu alamun mamaki ko magana, sai da suka gama sannan Maryam ta zauna a gabanshi tace “Kome zai faru Yaya muna tare da kai, Allah kuma na tare da kai, don Allah kayi ta addu’a kada ka bari ƙwaƙwalwar ka ta gushe maka tare da kowa.” Ido kawai ya lumshe mata ya buɗe alamun to, ya ɗauki wayar Hadiza ya miƙa mata, ta girgiza kai tace “Ka dinga saka karatun Alqur'ani kana saurara, ni zan bata ɗayar wayata tunda biyu gareni.” Baya son magana shi yasa kawai ya maida kanshi kan pillow ya kwanta, karatu ta kunna mishi sannan ta fito daga ɗakin, Salim kuma ya zauna a wurinshi. “To ni wannan lamari, lokaci ɗaya yarima ya zama bawa? Ina aka taɓa wannan abu? Banda dai shi Malam bashi da hakuri?” Abu ta faɗa tana kallon Fatima dake gyara kayan shanyarta data zuge a labule saboda a wuce da kayan Baqeer. Jamila ce ta sauke ajiyar zuciya tace “To ai abin ne kin san in aka koroka daga sama yafi ciwo, kin san kuwa yanzu haka har Bashir yaje yayi registration? Yau fa da kanshi Baban nasu ya kai shi makaranta.” “Yaron nan kin san ba zai faɗa mini ba don baya so nakasheshen mu ya shiga damuwa.” “To nima ai Salihu ne ya kawo mini gulma, kin san Bashir ɗan albarka ne.” Jamila ta ƙarasa tana zunɗen Fatima. “To sai aka yi me? Ai Bashir da Salihu da Baqeer duk daya suke sannan ƙaddarar data sameshi bata wuce kan kowa ba, kuma menene ma sabon abu dan mahaifi ya kai ɗan shi makaranta? Banda dai……” “Maryam!” Umma ta faɗa cikin kakkausar murya wanda hakan ya sakata yin shiru don ita dama bakinta baya shiru, don Daso ma suke ce mata a gidan saboda tsiwarta, sam bata ɗaukan raini kuma bata jiran ta kwana, su kansu Abu da Jamila sun san halinta. Abu ta zabga mata harara tace “Sai tsabar rainin tsiya ko waye sa’anki anan ni ban sani ba, mu ba’a matsayin iyayenki muke ba? Ko kinji munce wani abu ne mai zafi da zaki faɗa mana magana?” Jamila ta cafe tana cewa “Yara sai raini da rashin tarbiyya, to mu kunji munce wani abu ne? Ba jimami muke akan abinda ya faru ba?” Maryam zata yi magana Umma tace “Maryam wuce ciki kizo ki koma gidanki.” Jita yi kamar zata yi kuka don ɓacin rai, to amma ya zata yi? Haka dole ta wuce ɗaki tana shiga ta rungume Hadiza dake zaune akan kujera banda hawaye babu abinda suke yi, Umma tana gamawa ta shigo ta kallesu tace “Ku tashi ku koma gidajenku tun kafin ku sake samun saɓani da mahaifinku tunda mai kare mana gaba ɗaya kunga yadda Allah yayi mana dashi.” Maryam ji take yi kamar zata yi hauka, babban baƙin cikinta duk kudin mijinta ace babu abinda zata iya yiwa ɗan uwanta? Ita yanzu account ɗinta ko dubu biyar babu tasan kuma tana yin magana uban mijinta zai fara zancen shima yana buƙatar ganin likita, kuma in tace a ɗauki mai kula dashi tasan kai tsaye ma zasu ce babu kuɗi, haka suka yi mishi sallama suka tafi don ko tanka musu bai yi ba yana kallonsu dai har suka bar ɗakin. Baqeer har Salim ya bar gidan bayan ya gama yi mishi duk wani abinda yasan zai bukata bai ce ko kalma ɗaya ba, sai da Salim yazo yi mishi sallama ne ya kalleshi yace “Salim nagode!” Cike da tausayi ya jinjina kai yace “Bello yazo?” Kai kawai ya girgiza alamun a’a, jiki a sanyaye Salim yace “Naji ance baya nan kenan da gaske ne abinda naji.” Kallonshi yayi alamun tambaya nan Salim yace “Ban san ina yaje ba na dai ji Habi na maganar ne da muka yi waya.” Kai ya ɗaga nan ya sake yi mishi sallama ya fita, Baqeer na nan a zaune yana kallon Kamalu ya shigo yana ƴan waƙe-waƙenshi, ko kallon inda Baqeer yake bai yi ba ya gama abinda yake yi ya ciro doya da kwai daya siyo da juice ya shanye sannan yayi miƙa a kan katifa, shiru ne ya ratsa ɗakin don Baqeer ya ɗauka ma Kamalu yayi bacci ne sai ji yayi yace “Yanzu ya kake ji? Gashi dai kai ne ɗan gata ga kuma halin daka tsinci kanka a ciki, ko banza ni ina da kafafuna, ko da ba’a barni nayi karatu saboda kai ba ina da lafiyata wanda kai yanzu baka da ita.” Idon Baqeer na kanshi sai dai bai tanka mishi ba, zama Kamalu ya miƙe yayi yace “Ka cigaba da zama kamar kurma a ɗakin nan dan in har kana son zaman lafiya da ni to tabbas ka bini yadda nake so don wallahi haushinka da nake ji na shekara da shekaru wannan ciwon naka ba zai saka ya goge ba balle ya hanani tafka maka rashin mutunci.” “To ka fita dani daga ɗakin mana kowa ya huta? Zaka iya kaini waje ka yasar ai.” Baqeer ya samu kanshi da faɗan haka. Da mamaki Kamalu ya kalleshi don ko sanda Baba yake ji dashi bai iya mayar mishi da magana sai dai kawai ya tafi ba tare da ya kulashi ba. “Ni kake faɗawa haka?” Baqeer bai tanka shi ba ya ɗan harɗe hannunsa a kirji kawai ya lumshe ido, shi da Kamalun ma zai fita dashi ƙila da hakan yafi mishi sauƙi don rayuwar ta isheshi. Kamalu dama da fitarshi ya ɗan sha ƙwayar da suka saba sha, nan da nan idanunshi suka yi jaa ya miƙe ya janyo keken Baqeer ya fara neman saka shi akai, yana tunanin Baqeer zai bashi hakuri yaga ko kulashi bai yi ba, Kamalu na haki haka ya saka shi a kan wheelchair hankalin Baqeer a kwance yake babu alamun dana sani ko bada hakuri. Da yake a soro suke kai tsaye ya fita dashi waje ya fara turashi a keke cikin ƙarfi yana cewa “Ka nemi yafiyar abubuwan daka aikata mana ni da ƙanne na.” Sam Baqeer bai da ma niyyar yin magana, takaici ne ya rufe Kamalu kawai ya ajiye keken nashi daga can gefe tare da ja baya yana cewa “Kasan Allah yau zan nuna maka ni mahaukaci ne in dai baka bani haƙurin abubuwan da aka yita yi mini a gida saboda kai ba, Baqeer bai ko kalleshi ba sai addu’a kawai da yake yi a cikin ranshi. Wani irin birki da aka taka da ƙarfi ne yasa hankalinsu ya tashi, Baqeer abinda ya faru dashi ne ya dawo mishi nan da nan zufa ta shiga keto mishi ta wanke mishi jiki, shi kanshi Kamalu tsoro ne ya rufeshi don gabanshi sai dukan uku-uku yake yi. Zainab dake cikin mota tana ta sauri saboda wayar gaggawa da Nabeela tayi mata itace ta ɗago kanta daga sityarin motar cikin wani irin ɓacin rai ta fito, kan Kamalu tayi wanda yake kallonta hankali a mugun tashe, bai yi auni ba yaji ta zabga mishi wani irin mari. A fusace yana haki yake kallonta yace “Ke? Baki da hankali ne?” Cikin faɗa take kallonshi ita ma kafin ta kalli mutumin dake kan wheelchair, ba dai yaron jiya bane? Kauda tunanin tayi daga ranta sannan ta matsa inda yake ta janyeshi daga kan titi ta ajiyeshi a gefe cikin ɗan duhun farkon dare take kallonshi tace “Me yasa kai baka rabo da haɗuwa da mutanen banza? In kasan wanda kake tare dasu basu da hankali me yasa ba zaka zauna a gida ba? Ko kana tunanin kai ba mutum bane dan baka da ƙafa? Ko kuwa kana tunanin kai kaɗai ne ke cikin mummunar ƙaddara da har kake yarda ana juyaka duk yadda aka so? Rannan ba kai bane mai bin mace tana wulaƙanta ka? Sannan yau ka ɗauko wanda yake son yin ajalinka ma gaba ɗaya? To ka sani in har ka bari rayuwarka ta salwanta ko ka mutu ba lallai irin waɗannan mutanen suyi maka addu’a ba, in ma zaka buɗe ido ka buɗe akwai mutanen dake cikin wani hali sama da kai.” Bata ko jira amsarshi ba ta fara ƙoƙarin shiga mota, a fusace Kamalu ya nufota yana shirin fizgota, waigowa tayi cikin tsananin ɓacin rai ta nunashi da yatsa tace “Don’t you dare! Wallahi ni ba sa’arka bace sannan daga ganinka ma ba a hayyacinka kake ba, useless kawai.” Ta shige mota tana jan wani tsaki. Kamalu ji yayi ya kasa motsi don motar kaɗai daya gani yasan ba sa’ar yinshi bace, haka yaja Baqeer sam babu wanda ya sake cewa uffan har suka koma gida. Duk yadda Baqeer yaso ya cire kalaman yarinyar daga cikin ranshi ya kasa, duk wani motsi da zai yi kalamanta ne suke sake taso mishi, tabbas gaskiya ce tsagwaronta ta faɗa mishi, bazai yiwu ya maida kanshi nakasashe ba don kawai Allah ya ɗauke wani sashi na jikinshi don ya jarabce shi, in har bazai warke ba to fa dole ne ya koyi rayuwa da ƙaddarar data same shi….. Me kuke tunanin zai faru? Ga dai Zeey ta tafi gida ana mata kiran gaggawa, ga kuma Baqeer ya fara tunanin canza rayuwarshi, Bello fa? Kuna ganin zaiyi nasara? *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #Shalele #Zeey #MBB # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SHA HUƊU* https://www.tiktok.com/@maims_kiddies "Lallai Dr irin wannan kyau haka tamkar kunzo daga ƙasar UK? Gaskiya kayan jikin su Hanan sunyi matukar kyau, amma dai ba'a ƙasar nan kuka siya ba?" Cikin dariya Dr Aisha tace. "A ƙasar nan muka siya, sai dai kamar yadda kika ce ɗin haka ne, duk wannan kayan da kika gani a jikin yaran nan na ƙasar UK ne da *@Maims_kiddie* take sai da su a cikin Nigeria, muma a wajanta muka siya kuma ba tare da munje inda take ba, kayan na gani a Instagram account ɗin ta na *KIDS THRIFTY/OKRIKA STORE.* Kayane masu kyau da kwari daki bari kenan malam Khadija dan tun da na fara siyan kayan yara a wajanta shikenan na dena ganin kyawun na ko'ina. Kema/kuma zaku iya nemanta a Instagram link ɗin dake sama. Za kuma ku iya samunta a WhatsApp ta wannan link ɗin dake ƙasa. Ko lambar wayarta. https://Wa.me//08101378616 {14} Wani irin ihu Kamalu ya saki tare da durowa daga kan gadonshi wanda hakan yasa Baqeer kallan inda yake, cike da mamaki yake yi mishi kallon zararre. Kamalu ya sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu gefen fuskarshi ya ƙara faɗawa kan gado a fili yace "Dole na nemoki Roshni ɗi ta ai bansan soyayyar lokaci ɗaya tana yiwuwa ba amma gaba ɗaya kin gigitani, nasan marin nan ke kanki yayi miki zafi." Yasa hannu ya finciko pillow ya ƙanƙame yana juyi, kai kawai Baqeer ya girgiza don shi abinda ke gabanshi yafi shirmen nan. Wayar da Hadiza ta bashi ya ɗauka ya saka number Asiya kawai yana kallo, wani abu ne yaji ya taso mishi hakan yasa ya mayar da wayar ya ajiye tare da runtse idanunshi, Bello yake jira yazo ya faɗa mishi abinda Asiya tayi mishi don har yanzu ƙwaƙwalwarshi ta kasa ɗaukar abinda ke faruwa. Yana kallan Kamalu na ta ƙara kankame pillow yana mannawa pillow kiss lalai yau ya tabbatar kanshi ba ɗaya ba, takaici ne ya rufeshi kawai ya juya kai gefe. ***** Tun daga bakin gate Zainab tana parking ta hango Nabeela, tana tsayawa da motar ta ƙaraso da sauri tace "Zeey ya muka yi dake?" Maimakon ta tanka mata key ɗin motar kawai ta bata tace "Whatever! Ni raina a ɓace yake please." Da kallo Nabeela ta bita harta shiga ciki bata iya bin bayanta ba, A ƙofar shiga taga Mummy, kusa da ita kawai taje ta rungumeta tace "Mummy ni kam me yasa mutane basu da kirki ne?" "Ki ajiye batun mutane kin san yau me kika nemi ja mana a gidan nan kuwa? Tunda Dad ɗinki ya dawo yake faɗa, me nace miki akan in zaki fita? Ba nace ki tabbatar kin sanar min ba?" "Oh yeah! Na tuna amma inda naje yana da muhimmanci ba wai yawon banza naje ba Mummy kin dai sanni." Ajiyar zuciya tayi tace "Shi yasa nace ki dinga sanar mini ɗin ai tunda kin san Babanki ba yarda zai yi ba." Zata yi magana taji an daka mata tsawa "Uban wa ya baki izinin fita ba tare da sanina ba? Sannan tun kafin ki dawo ba na sanar dake ba ke babu fita ke kadai ba? Ko kina tunanin wasa nake yi?" Idanunta ne suka yi raurau tace "Dad nasan nayi laifi amma......" "Amma me? Ke wato ba'a isa a faɗa miki magana kiji ba ko? Daga dawowarki ko jira baza kiyi ma mu gama murnar zuwanki ba zaki dawo da halin naki ko?" Hawayenta ta share don tasan inta tambaya ma ko zata mutu ba barinta zai yi taje ba shi yasa ta sulale ta fita ta ɗauka zata dawo da wuri kafin ya dawo amma babban uzuri ya hanata, cike da faɗa yace "Wuce ciki kuma wallahi kika sake gigin fita ba da izinina ba kin san sauran don shirmen da kika yi a baya a unguwar nan da maganar da kika janyo mini a yanzu bazan sake ɗaukanshi ba.” Idanunta ne suka ciko da kwalla tayi ɗakinta da gudu kawai ta faɗa kan gado, Mummy ce tabi bayanta tana shiga itama ta shiga ɗakin, kusa da ita ta zauna tasa hannu kawai tana shafa bayanta alamar lallashi, cike da takaicin abinda ya faru ta ɗago tana hawaye tace “Mummy nasan nayi laifi amma aƙalla a tambayi ina naje ko? Sannan asan dalilin daya sa na fita, ban san me yasa Daddy yake yi mini haka ba….” Hannu tasa a saman bakinta tace “Dalilin kenan, Zeey bakinki ba zai yi shiru ba? In mahaifinki na magana ba zaki yi shiru kice ayi hakuri ba? Kin bari ɗabi’ar turawa ta shiga kanki kin manta da wacce muka baki?” Kallan Mu8my tayi tana share hawayenta tace “Mummy kema kin san ba haka bane tun kafin na tafi karatu muke samun saɓani da Dad sam baya yi mini uzuri.” Ajiyar zuciya tayi tace “Taurin kanki ne baya so, in har kika saukar dashi zaku zauna lafiya, sannan bakinki, ki taimaka ki daina faɗar duk abinda ya fito daga cikinshi.” Kallon Mummy kawai take yi tama kasa magana sai hawaye kawai da take zubarwa, share mata tayi tace “Yanzu in kinaso ku shirya gobe Najib zai zo don sunyi magana da mahaifinshi ki tabbatar kin bashi hakuri kun daidaita, Zee dan Allah kar ki ƙara jawo mana matsala.” Tana kaiwa nan ta miƙe ta fita ta bar Zeey a zaune kawai tana hawaye. ***** Abu ce ta shige cikin ɗakin ta yau kwanan Jamila ne tasan kuma yanzun nan zata lalaɓo ta fara ce mata ta bata kayan mata ita kuma yanzu babu abinda zata iya bata tunda dai kambun Fatima ya rushe dole ne ta ƙwace Malam ya dawo gareta. Daga waje take jiyo kiran da Jamila ke mata cikin magana irinta raɗa “Abu! Taimaka ki miƙo mini saƙon da Hajiyar Sokoto ta aiko miki.” Kwafa tayi tasa hannu ta ɗauko gutsiran tuwon alkama da sukai, tasa a ƴar farar leda ta shiga murza tuwon sai da ya fashe sannan ta ɗauko zuma ta zuba a ciki ta sake murzawa kafin ta ƙulle ledar, fitowa tayi tana dariya tace “Ke ina can ina nemo miki maƙal-maƙal kina nan kina nemana.” Washe baki Jamila tayi ta amshi ledar tace “Kai Abu Allah dai ya bar mini ke ya raya mana Kamalu mu sha biki.” “Ameen gashi nan kisa da audiga kin dai sani abu shar kayan mu ba wasa.” “Heee! Ai har wani tsuma nake dole mu dawo da Malam hanunmu.” Tana faɗa tana fita waje cike da jin daɗin abinda ke faruwa “To kar dai muji ihun Malam yana sambatu.” Jamila sheke da dariya jin kalaman Abu tace “Ke dai wlh baki ji kisa audiga a kunnenki.” Ta ƙarasa maganar tana fita. Abu ta ja tsaki da harara tace “Banda rainin wayau ɗakin Baqeer kin ƙwace kin bawa ƴaƴan ki kin haɗa Kamalu na da shi yanzu kuma mijin kike son ƙwacewa, wannan kuma kin yi kaɗan wallahi.” Ta juya tana cigaba da masifa a ranta. ***** A rikice Baba ya shigo cikin ɗakin lokacin Baqeer na zaune ya sa karatun Al-Qur’ani a waya kawai yana sauraro yana yi yana kallon Kamalu wanda har lokacin yake kwance yana bacci har Salim yazo ya taimaka mishi yayi wanka yaci abinci yayi sallah a zaune amma bai tashi ba,  jin yadda Baba ya shigo a rikice ne yasa gabanshi ya shiga faɗuwa, ba dai wani wurin za’a ƙara kai shi ba ko? “Waye wannan kamar Bello?” Kalaman Baba daya juyo kenan a kunnuwanshi yana maganar yana miƙa mishi wayarshi, hannayenshi biyu ya miƙa duk da yasan bazai iya amsa da hannun daman ba. A guje Kamalu ya tashi ya afka banɗaki don yasan yanzu Baba zai ci mutuncinshi. Da mamaki yake kallon hoton dake jikin allon wayar “Ba Bello bane ko kuwa idona me ke yi mini gizo?” Kallon Baba yayi sannan ya sake kallon rubutun ƙasa da aka rubuta wanda yaci gasar zanen da akayi a yanzu haka a garin Abuja. Da sauri ya kalli Baba wanda ya ke kallanshi cike da takaici yace “Duba da kyau me aka rubuta a kasa?” “MBB?” Kallan Baba ya sake yi da sauri wanda ya fizge wayarshi yace “Ya maka kyau! Gashi dai abokinka ne yayi amfani da sunanka ya maye gurbinka kuma alamun da ya bayyana a fuskarka ya tabbatar mini baka sani ba, sanda nake hanaka nuna mishi sirrinka kaji magana ta? Allah ya kara yanzu gashinan ai duniya ta juya ma baya.” Yawun bakinshi Baqeer ya haɗiya yana jin wani abu mai ɗaci na sake taso mishi “Yanzu ga ka nan a kwance shi kuma fa? Gashi can ya maye gurbinka, ka fake da wata karaya ka kasa taɓuka komai, sai kayi ta zama a nakashe baƙin cikin da ka sakani baka fara ganin komai ba, malalaci kawai.” Yana kawi nan ya juya ya fita, hannu Baqeer yasa a sumar kanshi yana jin wani irin zafi na taso mishi, ya maida hannun saman ƙirjinshi dake yi mishi wani irin raɗaɗi, idan Bello ya faɗa mishi zai maye gurbinshi yasan ba zai hana ba tunda idan ma bai je ba wani dai za'a tura to amma me yasa ya ɓoye mishi cewa shi zai je gasar a madadin shi? Ba dai shima gudunshi yake yi ba saboda abinda ya faru? Ko kuwa abinda Baba ke yawan faɗa mishi ne ya tabbata akan ya daina yarda da abokai? Iska ya shiga furzarwa da sauri cikin ƙarfi sakamakon jin da yayi numfashinshi na neman ɗauke wa. Umma ce ta shigo da sauri don tunda taji kiran da Baba ke yi mishi tasan ba lafiya ba, karshe ma jinshi tayi a tsakar gida yana sababi akan ai dama shi yasan hakan zai faru, gashi nan kuma abinda yake tsoro ya afku, cikin sauri ta nufi ɗakin ganin halin da yake ciki yasa ta ɗauki littafi da sauri ta fara fifita mishi fuska wanda da ƙyar ya samu numfashinshi ya daidaita, kallonta yayi idanunshi sunyi jaaa yace “Umma na!” Ta goge kwallarta tace “Baqeer dole kasa dauriya a zuciyarka, abubuwan dake faruwa da kai yanzu ka fara ganin su in har baka ɗauki dangana ba baza ka taɓa samun salama ba.” Kai ya ɗaga mata yace “In sha Allahu Umma, tun jiya na fara sawa kaina wannan tunani amma Umma kina ganin Bello ma munafurtata yayi?” Ajiyar zuciya tayi tace “In ma yayi kanshi ya yiwa, rayuwar nan nawa take? Ni ban damu da wani abu ba Baqeer ɗina nake so naga ya dawo daidai.” Kallonta kawai yayi don bai san me zai ce ba.kuma, ta miƙe ta fita don bata son daɗewa a cikin ɗakin sanin Kamalu a ɗakin yake. Tana fita kuwa sai gashi ya fito daga wanka yana fito, kallonshi yayi ya kwashe da dariya yace “Shalele yaya? Abubuwan sun ƙi daidaituwa ne?” Baqeer bai tanka shi ba ya ɗan matso yace “Yarinyar jiya ka santa ne?” Da mamaki ya kalleshi yace “Kamar ya?” “Naga ta shigar maka faɗa ne har da yi mini shafar soyayya shine nake son tabbatarwa ko ƙanwar abokinka ce.” Kai Baqeer ya kawar cike da takaici, Kamalu yaja tsaki yace “Kai sai faɗin ran tsiya kace baka sani ba ne bazaka iya faɗa ba? Wallahi na dai faɗa maka in har kana son kwanciyar hankali ka tabbatar ka bani girma stupid kawai nakasashe.” Ya ƙarasa maganar yana zura kaya, sallar asuba da azahar ya haɗa sannan ya ɗauki wayarshi ya fita, dole ne ma ya shiga neman yarinyar nan lungu da saƙo don banda tunaninta babu abinda yake yi tunda ya haɗu da ita. Takaici ne ya kamashi daya fito yaga Bashir yana ƙoƙarin shiga motar Baba wato shi sam yaran gidan nan sun rainashi, shi kenan da hawa babur, cikin tsawa yace “Kai Bashir bani key ɗin nan ka hau babur.” Da yake duk sun san halinshi yasa bai yi mishi musu ba haka ya miƙa mishi makullin motar ya amshi na babur ɗin, fuskarshi ya sake shafa inda Zeey ta mareshi dole ne yaje ya nemota ya tabbatar inta ganshi a mota shima zata kulashi. ***** Baqeer a cikin ɗaki yayi shiru, Hadiza da Maryam duk sun kirashi sunji yanayin jikinshi, Salim ya kira a waya wanda ringing biyu ya ɗauka yace “Baqeer akwai abinda kake so ne?” Wani abu ne ya ɗarsu a ranshi, Salim abokinshi ne tun na yarinta sai dai zuwan Bello unguwar da kuma yanayin karatunsu na Art yasa shaƙuwarsu tafi ƙarfi tun daga nan ya tattara Salim ya ajiye, in har ka ganshi da Salim to sai dai haɗuwar masallaci ko kuma a hanya su gaisa ya wuce. Jiki a sanyaye yace “A’a dama tambayarka zan yi kaji labarin Bello kuwa?” Ajiyar zuciya yayi da alama bai so yin maganar ba kafin yace “Kayi hakuri Baqeer kasan na faɗa maka Habi taji suna waya da Asiya akan tafiyarshi, ashe gasa yaje ɗazu Habi ta kirani take sanar dani abinda ke faruwa da link ɗin BBC inda suka ɗaura labaran, abinda ya bamu mamaki me yasa yayi amfani da initials ɗinka kamar yadda kake yi a matsayin sunanka? Sannan yaushe sunanshi ya zama Muhammad Bello?” Hannunshi dake riƙe da waya ya ɗan matse kaɗan zuciyarshi nayi mishi zafi, yace “Komai ta wurin Asiya ake ji kenan?” “To ni Habi bansan meya faru ba amma…..” Sai kuma yayi shiru, Baqeer yace “Amma me?” “Babu komai kawai dai ban san meke damun Bello ba.” “Wayar da Asiya take yi da Bello akwai alamar tambaya ne?” Tambayar da Baqeer ya daki Salim da ita kenan, haka kawai yaji ƙwaƙwalwarshi tana ayyana mishi abu, in har Asiya ta rabu dashi ta bar ɗaukan wayarshi taya zata cigaba da hulɗa da abokinshi wanda ta dalilinshi ta sanshi? Sannan ace duk wani abu daga wurinta ake fara ji? Salim yayi wata ƙaramar shaƙuwa yace “Ni dai wallahi ban sani ba kawai Habi ce dai bata son wayar da suke yi.” Kashe wayar kawai Baqeer yayi don bai san me ma zaice ba, zuciyarshi na sake ayyano mishi abubuwa da dama. ******** Duk wani kayan ciye-ciye an jerashi a parlourn, Mummy ta shigo ta tabbatar Zeey tayi shigar daya dace, Nabeela na zaune akan gado tana murmushi don tasan Zeey in har ta leƙa wuein Najib to tabbas sai ta kwafsa, kallonta Zeey tayi tace “Aunty Beela ina fa kallon yadda kike kallona tun ɗazu.” Dariya tayi tana kallon Mummy tace “Ni dai bance komai ba kawai dai ina jiyewa ne garin gyara a ƙara ruguza abu.” “To ke kuma da baza kiyi fatan alkairi ba sai kiyi shiru.” Mummy ta faɗa tana hararar Nabeela. Mai aiki ce tayi knocking ta sanar da su zuwan Najib sannan tace suna falo tare da Kabir. Koya kuke ganin zata kasance da Baqeer akan Bello? Ga dai Kamalu an tafi neman Zeey, ga kuma Najib yazo ganin Zeey. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #Shalele #Zeey #Kamalu # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD https://www.arewabooks.com/chapter?id=656d9ccf22d5844413e4fa27 *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*            *ƘARSHEN ƊANDANO DAGA RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BIYAR* MUMMY ce ta sake riƙe hannunta tace “Kin san ina bayanki a koda yaushe ko?” Cike da sanyin jiki ta kalli mahaifiyar tata kafin ta rungumeta tace “Mummy dole ne sai Daddy ya aurar dani ga wanda yake so?” “Sai haƙuri kin san shi ɗan siyasa ne shi yasa yake son aurar dake ga wanda yasan zai taimaka mishi a harkar siyasar shi.” Ajiyar zuciya Zee ta sauƙe tace “Am sorry Mummy amma bazan taɓa auren wanda bana so ba.” Daga haka ta zare jikinta ta bar cikin ɗakin, jiki a sanyaye Mummy ta kalli Nabeela tace “Nabeela please banda ke akan me bazaki dinga ƙarfafa mata gwiwa ba? Ya kuke so tayi ne? In har bazaku fahimceta ba?” Wani murmushin takaici Nabeela tayi tace “Yaya wannan abin da kuke wallahi ba so bane, nasan kinsha wahala kafin ki sameta amma wannan bai kai dalilin da zai sa ku sangartata ba, ku dinga barinta tana fitsarar data ga dama ba.” Nan da nan fuskar Mummy ta canza tace “In ke kina kanwata kin faɗi haka na waje suce me?” Kai kawai ta kauda gefe zuciyarta na takaicin yadda idanunsu suka rufe saboda son yarinyar nan suka manta sam da abinda ya kamata suyi, hatta Daddy da ake ganin yana da zafi a kanta sam ita bata gani tunda zafinshi baya wani ɗaukan lokaci, tasan suna son Zeey amma a kalla….. “Ki wuce falon yanda in kinga zata faɗi ba daidai ba ki taimaka ki daidaita.” Kalaman Mummy ne suka katse mata tunaninta, mayafinta kawai tasa ta fita daga ɗakin. **** Ƙafa ɗaya kan ɗaya Najib ya ɗaura yana girgizawa shi a dole ta ƙona mishi rai yana jira ta bashi hakuri. Zeey ce ta shigo hannunta ɗauke da tray na drinks da fruits da aka yanka mishi, taga mai aiki zata kawo ta amsa tace zata miƙa da kanta. Mummy data fito daga ɗaki ganin haka yasa taji wani daɗi ta kalli Nabeela tace “Ɗan basu minti goma su biyu.” Zeey da murmushi a fuskarta ta shiga sai dai tana sauke labulan ɗakin ta canza yanayin fuskarta, kallonshi tayi tace “J?” Wani kallo ya zabga mata tayi mishi alama da kai tare da nuna mishi tiren hannunta, sake watsa mata wani kallo yayi sai dai ya rasa me yasa yake sake kallonta, kyaunta yake ƙara gani sama da na jiya da alama kayan dake jikinta ne ya sake fito da kyaun nata don sanye take da lace an mata ɗinkin doguwar riga irin straight gown ɗin nan tayi kyau sosai a cik,i ba tayi kwalliya ba don mai kawai ta shafa sai ƴar powder data goga a fuskarta amma sosai tayi kyau kamar wata ƴar tsana. Yanda ta kalleshi ne yasa yaji kamar an sakashi dole sai gashi ya miƙe yazo inda take ya amshi tiren, ta nuna mishi table ɗin dake tsakiyar parlourn tace “Ajiye acan.” Ajiyewar yayi sannan ya koma ya zauna ya ɗaure fuska tamau, bata ko bi ta kanshi ba ta ɗauki remote kawai yaga ta kunna tv tana kallo, sun fi kusan minti biyar ba wanda yake magana sai ita kawai da take kallon drama na Turkey a tv tana murmushi, Najib ya cika ya cika har bai san ɓacin ran dake damunshi ba don takaicinshi ma ko kallon inda yake bata kuma yi ba tunda ya zauna. A kufule yace “Zainab wai ba hakuri aka ce ki bani mu daidaita kan mu ba?” Waigowa tayi ta kalleshi tace “Ince me kenan?” “Kice kayi hakuri nayi kuskure amma bazan ƙara ba.” Kai ta jinjina tace “Perfect gashi nan ka faɗa ai ko akwai sauran abinda kake son ji?” Wani huci yayi yace “Gashi nan na faɗa?” Ta ɗaga kai tace “Ka faɗa mana ko bayan haka da ƙari?” A wannan lokacin Najib ya gama kaiwa bango, ya miƙe a zuciye yana sakar mata wani mummunan kallo, kallonshi ta sake yi jin alamun ana kallonta tace “Oh! Ba dai har zaka wuce ba?” Kasa magana yayi kawai yana kallonta, ƴan mata nawa ne suke binshi yana wulakantasu? Ƴan mata nawa ne yake disgasu saboda yanda suke rububin shi? Kamar shi Najib Guy ace mace tana neman maidashi shashasha?” A fusace yayi hanyar ƙofa, Nabeela ce ta turo ƙofar jiki a sanyaye ta kalleshi, zata yi magana ya ɗaga mata hannu, Kabeer ne ya taho don dama yana ɗaki haka kawai jikinshi ke bashi rainin hankalin Zainab babu abinda baza tayi ba. Cikin sauri ya ƙarasa wurinshi yace “Najib menene?” Rasa abin faɗa yayi don a ganinshi  ƙasƙanci ne ma ya faɗi abinda tayi mishi kamar ya zubarwa da kanshi aji ne, a fusace yace “Ka tambayi ƙanwarka sannan bazan sake dawowa ba taje can ta nemi wanda yayi mata.” Nabeela tace “Kayi hakuri Najeeb ba wai har ranta tayi ba……” Bai jira amsa ba ya wuce, Kabeer ne ya bishi a baya da sauri, ita kuma Nabeela ta shiga ciki. Tana shiga ta ganta tana shan fruits ɗin da aka yankawa Najib tana kallo yanda kasan ba ma da ita ake abin ba, kasa magana tayi kawai ta juya tabar parlourn. ***** Baqeer ne duk hankalinshi yaƙi nutsuwa, baya son ya cika zargi amma dole ne yayi, wayar nan ya ɗauka ya kira Salim, ringing biyu ya ɗauka jiki a sanyaye yace “Salim don Allah gobe idan Bello ya dawo ka taimaka kazo ka kaini inje in ganshi in dai har shi bai zo ba, ina sin sanin amsoshin tambayoyin dake kaina.” Yace “Shikenan nima anjima zan zo dama na gyara ka.” Daga haka suka yi sallama ya maida kanshi kan katifa kawai yana addu’oin samun nutsuwa don zuciyarshi tuni take ƙissima mishi wasu abubuwan da bai dace ba. Kamalu ne ya shigo gidan ranshi a matuƙar ɓace, bokitin dake tsakiyar tsakar gidan yayi fatali dashi wanda hakan yasa Abu fitowa da sauri, don ta ƙule cikin ɗakin ne tana hada sirrin matsi na ‘tif da taya’ wai in dai mace tayi amfani dashi da yamma suka sadu da miji to fa shikenan sun zama gamgam, bata so Jamila ta gani balle ta fara mata surutan banza “Kamalu?” Ta faɗa tana yi mishi alama da yazo don dama nemanshi take yi, shiga yayi sai kumbura fuska yake cikin ƙunar rai yake cewa “Kinga Mama karki ɓatan lokaci don sauri nake yi ina so in ɗauki chager na wayata ne zan koma waje.” Ƙofar ta mayar ta rufe bayan ta tabbatar babu wanda ya ganshi tace “Kamalu haka zaka zauna yanzu Bashir ya kwace fadar mahaifinku bayan Baqeer?” Cikin kakkausar murya ta irin fitinanun mazan nan yace “Wannan ya rage nasu ni abinda ya dameni daban, suje can da yawarsu.” Iska ta furzar tace “Kai matsalarka kenan sam ba’a faɗa  maka kaji, ko so kake wulakancin daka sha shekarun baya ya sake faruwa?” “Kinga Mama ba wulakanci ba suyi abinda ya fishi ma ni bai dameni ba, wannan ina zaune ya lalata ƙafa dan da ina da dama ma ni da kaina zan karya ƙafar da hannun to amma tunda wani ya rigani kinga na huta amma wannan mahaukacin ya rainani wallahi zaki jishi a maƙabarta.” Yayi maganar a fusace tare da buɗe ƙofar ɗakin zai fita, ji yayi tace “Kamalu magana nake yi maka fa?” Kallonta yayi kawai ya fice tare da bugo ƙofar da ƙarfi, babu abinda ya tsana irin a dinga haɗa shi da mutane shi kenan daga a haɗa shi da wannan sai a haɗa shi da wancan to wallahi ba zai yiwu ba. Ɗakin shi ya nufa rai a ɓace. Baqeer yana zaune bayan Salim yazo ne da zai tafi yace ya sakashi akan kujerar dake gefen table ɗin zanen shi, pencil yayi ta ƙoƙarin riƙewa sai dai hannunshi na gocewa, sam ya kasa taɓuka komai, kanshi ya dafa yana tunani, shi ba wani abin ya sani ba balle yace zai gwada wani abin, zanen nan kawai ya iya da kuma shi ya dogara, yanzu ya zai yi da rayuwarshi? Ajiyar zuciya yayi gashi an ɗauke mishi waya bai samu ya kira mutanen da suka amshi aikinshi ba tare da sun biya ba, da wanda suka amshi aikinsu suka fara biya basu gama ba, ya zai yi? Banko kofar da Kamalu yayi ne yasa ya kalleshi, a fusace Kamalu ya shigo yace “Uban me kake kallo?” Baqeer ya kawar da kai dan baya son tanka mishi sam, hankaɗe table ɗin gaban Baqeer yayi yace “Wawa kawai in ma zaka farka daga shirmen mafarkin da kake to kayi ka farka don anyi gaba an wuceka, sannan daga yanzu na maka iyaka a cikin ɗakin nan kada ka kuskura ka wuce nan zagayen din nan ɓangarena ne.” Ya ƙarasa maganar yana nuna mishi sashin da yake nufi, kallonshi kawai Baqeer yayi ya kauda kai wanda hakan ya sake tunzuro shi yace “Ni kake kawarwa da kai?” Bai tanka mishi ba sai ajiyar zuciya da yake don shi yanzu komai na rayuwar nan mamaki kawai suke bashi, yanzu yadda zai yi ya samu kudi ya sayi magungunan da aka rubuta mishi yake nema, don a gabanshi aka bawa Baba takardar magungunan daya kamata a saya mishi amma har yau babu abinda aka bashi sai paracetamol da Umma tasa aka sayo mishi sanda ya dinga fama da yawan ciwon kai. Takaici ne ya ƙara rufe Kamalu ya ɗauki charger wayarshi ya fito yana zazzaga masifa dama ranshi a matukar ɓace yake sakamakon tun safe yake yawon neman Zeey babu ita babu labarinta, duk wanda ya yiwa kwatancen yar masu kudi baƙa kyakkyawa sai dai a hankada shi wani gidan, akwai gidan da yaje ma kare ya biyoshi tun daga nan ranshi yake a ɓace gani yake ta leko ta koma Zee tayi mishi. ******* Ɗakinta ta kulle tana ji Kabir nata bubbugawa har sai da Mummy tayi mishi magana sannan ya ƙyaleta, gashi dama Dad baya nan yaje Gombe taron jam’iyarsu. Ko da Daddy yayi waya Mummy ce mishi tayi basu daidaita ba amma sun sulhunta tana saka ran inya sake zuwa su daidaita. Takaici ya kama Kabir yace “Mummy wai ba zaki bari na farfasawa yarinyar nan baki ba? Haka zamu zauna tana mayar da mutane kamar wasu yaranta?” Fuska sosai Mummy ta ɗaure wanda hakan yasashi tashi yabar parlourn. ****** Washegari……. Daf da magriba Bello ya sauka a Kano ta jirgin sama wanda murna da yake ciki ba zata misaltu ba, mahaifinshi da kanshi yazo ɗaukan shi a airport. Yallabai ya sake yi musu godiya da sanar dasu akan za’a kirasu wanda suka ci na ɗaya zuwa na uku a sake karramasu kafin a tallafa musu akan karatunsu zuwa kasashen ƙetare. Nan suka shiga motar mahaifin Bello, basu fita daga airport ba yace “Bello meke faruwa? Baka sanar dani akan tafiyar nan ba? Sannan a iya sanina ba Baqeer bane mai zuwan?” Ajiyar zuciya yayi yace “Baba nima ba’a son raina hakan ya faru ba, Baqeer yayi hatsari wanda ƙafarshi da hannunshi suka samu matsala, shine ya tursasani akan sai naje a madadin shi nima banyi niyyar zuwa ba ganin kamar hakan bai dace ba sai dai ya matsa don haka na tafi kawai.” Jin kalaman Bello yasa hankalinshi ya ɗan kwanta, da sauri Bello yace “Shi yasa na kasa sanar daku don ni kaina kunya nake ji gani nake yi kamar ban kyauta ba.” Cike da jin daɗi yace “Masha Allah wannan abotar taku tana sanyaya zuciyata Allah ya ƙara kareku, da hankalina ya tashi amma yanzu na fahimci MBB ma da kayi amfani dashi hala saboda asan shine kai?” Bello yayi murmushi yace “Sosai Baba shine dalilina, don Allah ko zaka bari in sauka don ina son na fara nuna mishi sakamakon abinda ya mayar dani.” Baba ya ƙarasa gida sannan yaba Bello key ɗin motar yace “Amma karka dade Goggonka na jiranka.” Cike da jin dadi ya ja mota ya bar wurin. Salim ne zaune shi da Baqeee sun kira Bello a waya har sun gaji bai ɗauka ba, Salim ya kira Baban Bello inda ya sanar dashi ai yana nan hanyar tahowa wurinsu. Mamaki ne ya kama Baqeer ya kalli Salim tare da ƙara kiran Bello sai dai yanzu ji suka yi ma wayar wai a kashe. Habi ce ta kira Salim wanda ya ɗauka don sanar da ita tayi hakuri zai kira ta daga baya. Sai dai me? Yana ɗagawa ta sanar dashi wai Bello yana ƙofar gidan su. Kallon Baqeer yayi wanda bai san me ake cewa ba sai dai yanayinshi kaɗai zaka kalla kasan akwai zargin da yake yi, Salim na kashewa ya kalleshi, jinjina kai Baqeer yayi yace “Salim zaka iya kaini gidan su Asiya?” Dafa hannunshi Salim yayi yace “Baqeer ka share kawai.” “Please! Ganinsu ne kaɗai zai tabbatar da abinda nake tunani kuma shine zai ɗauke kokonton da nake yi akan su.” Shiru yayi sai dai shi kanshi zuciyarshi ta kasa nutsuwa, Umma na murjin taliyar hausa da take yi in ta samu masu auna, so take ta samu kuɗi ta taimakawa Baqeer ya samu mai taimaka mishi da safe don bazai yiwu su cigaba da takurawa Salim ba. Da mamaki ta kallesu tace “Sai ina?” Salim ne yace “Zamu ɗan fita shan iska ne tunda duhu ya ɗan kawo kai.” Kamar ta musa sai dai tace “Sai kun dawo.” Haka suka yi ɗan tafiya kaɗan kafin su isa kwanar su Asiya duk cikinsu babu wanda ya iya tanka wa wani. Tun daga nesa Baqeer yake kallon motar mahaifin Bello don kuwa rabin hawa motar sune suke yi, Salim ne yace “Baqeer don Allah mu juya.” “Please Salim!” Yayi magana cikin wata karyayyiyar murya, suna tafe yana tuno rayuwar da suka yi da Asiya mai tsafta, harta gama boarding school shi ke mata shopping a ɓoye don iyayenta ba wani abun kirki suke iya saya mata ba to shi ke saya mata abubuwa da yawa, da yadda take tsananin ƙaunarshi, a rana in bai kirata sau biyar ba ta dinga tambayarshi ko lafiya? Balle rayuwarsu da Bello wanda ke cike da farin ciki, yawanci zancen da yake zuwa ma dashi yake zuwa. Cak ya tsaya daga gefen gidan dake gaba da nasu kaɗan gidan mai kyau ne sosai dan fitilun gidan ne suka haske inda Asiya da Bello ke tsaye, daidai lokacin Bello ya matso tare da ciro award ɗinshi ya miƙa mata, wani irin murmushi ta saki ta ɗan jingina da gaban motar cikin farin ciki take yi mishi wani kallo, kafin daga bisani ya ɗauko waya ya fara ɗaukan ta hotuna tana tsaye rike da award din kai daga ka gansu kasan love ake sha. Baqeer kanshi ne yaji yayi mishi wani irin nauyi, shekara kusan guda kenan yana ayyana wannan ranar yana cikawa Bello baki akan duk ranar da ya amshi award ita zata fara gani ya sakata a gaba yayi mata hoto, ashe ba shi bane hakan zai faru dashi Bello ne? Idanunshi ne suka canza launi sosai da sosai yana jin zuciyarshi nayi mishi wani irin zafi, ya zai yi da rayuwarshi? Ina zai saka kanshi yaji daɗi? Asiya ya hango ta miƙawa Bello award ɗin ga mamakinshi hannunta ya riƙe ita kuma tana murmushin ta dake sanyaya mishi rai a baya wanda yake gani shi kaɗai take yiwa…… Tsaye take a jikin balcony na gidansu wanda daga gefe take hango mutanen biyu wanda ta gansu kwanaki ta kuma ga na keken shekaran jiya, hannayenta a harɗe a kirjinta duk abinda ke faruwa akan idanunta, yanda taga yana kallon gaba kaɗan da inda yake ne yasa ta kalli wurin, dan hasken fitilun gidan su ya haska layin, idanunta ne ya sauka akan yarinyar da ta wulakanta gurgun kwanaki, kana kallonta kasan soyayya suke yi da wanda ke tsaye kusa da ita, wani murmushin takaici tayi tare da girgiza kai, ta rasa me yasa maza sam wasu basubsan me ya dace dasu ba, kalaman wanda ke kusa da gurgun ne ya katse ta yana cewa “Please ka furzar da iskar dake bakinka, ka taimaka kayi magana.” Nan da nan takaici ya sake rufeta ta rasa me yasa ita bata ganin abu ta ƙyale, wayarta kawai ta ɗauka ta fito daga gidan, kusa dasu kaɗan ta tsaya tana yi kamar mai yin waya tana cewa “Some people are just helpless, sai su dinga zuwa inda ba’a nemansu, in kasan ba’ayi da kai you just need to move on, amma wasu kamar basu da zuciya, sannan gani suke kamar in Allah ya jarabcesu rayuwarsu ta riga ta tsaya kenan.” Waigawa Baqeer yayi don kalamanta kaf cikin kunnuwanshi kuma tabbas muryar nan dai ita ce wacce tayi mishi magana sau biyu. Kafin yayi ƙoƙarin yin magana tayi gaba….. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #Shalele #Asiya #Zeey # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *PAID BOOK* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA SHIDA* *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 {16} Kallon Salim yayi bayan ya ɗauke kanshi daga kallon inda yarinyar ta suce, muryarshi cikin sanyi yace "Salim taimaka mu koma gida." Babu musu Salim ya fara turashi, bai sake iya waiwayen su Bello ba don wani irin zafi da ƙuna yake ji a zuciyarshi, tabbas Asiya da Bello sun yi mishi abinda bai taɓa tunanin wani mahaluki zai yi mishi ba, yana gani ana cin amana amma bai taɓa kawowa zai zo kanshi ba. A ƙofar gida suka tsaya ganin ƴar ƙofar shiga gidan a kulle, da mamaki suka kalli juna don ba'a kulle gidan sai ƙarfe sha ɗaya na dare, ya zaro wayar dake aljihun gaban rigarshi yaga tara da rabi, nan yasa hannu ya ɗan buga kofar gidan, basu jima ba aka zo aka buɗe, hankali a tashe suke kallon Baba dake tsaye a ƙofar, bai yi wani auni ba kawai ya tsinke Salim da wani irin mari, a razane Baqeer yace "Baba?" Ai bai tsaya saurarenshi ba yace "Kasan Allah in har na sake yi maka magana ka take umarnina gidana hana ka shiga zan yi, kai a duniyar Allah ba'a koya maka bin maganar manya bane? Nasan ka taso ba mahaifi ina yi maka uzuri tunda mahaifiyarka da tayi aure ajiyeka tayi gun iyayenta wanda dama kowa yasan tsofafi ba tarbiyar da zasu iya badawa, amma naga alama uzurin da nake baka sam baya shiga cikin kunnenka, to wallahi ka fita idona na rufe kaji na faɗa maka." Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Salim ya kalli Baqeer da kunyar duniya ta rufe shi yace "Baqeer kayi hakuri amma ba zaka sake ganin na tako ƙafata gidan ku ba." Daga haka yayi gaba yana share kwalla, an daɗe ana ci mishi mutunci amma bai taɓa jin zafi ba kamar wanda mahaifin Baqeer yayi mishi duba da yadda yake tunani iya ƙoƙarin yana yiwa ɗan shi, to menene laifinshi? Banda yana tausayin Baqeer dama da tuni sun raba abota. Juyawa Baba yayi ya barshi a zaune akan kujera a ƙofar gida, Umma na ta safa da marwa a tsakar gida, Jamila na daga gefe tana kallonta, ita kuwa Abu yau banda shirin tarbar mai gida babu abinda take yi. Baba yana shiga kai tsaye ɗakin Abu ya wuce ba tare da ya tanka musu ba. Da sauri Fatima ta zura hijab ta leƙa waje, yana zaune yadda kasan ba mai rai ba ko motsi baya yi, tunani kawai yake yi ina ne zai je ya zauna yayi rayuwarshi bayan nan gidan? Ina yake dashi da zai tattara ya tafi ya zauna shi kaɗai? Ganin Umma ne yasa zuciyarshi ta ƙara karaya kawai ya damtse hannu yana jin wani abu na sake tokare mishi zuciya. Haka ta turashi cikin ɗakin, Kamalu na zaune yana kallon ball a wayarshi, ta kalleshi cikin sanyin murya tace "Kamalu din Allah taimaka mishi ya kwanta." Wani kallo ya watsa mata yace "Ya kwana a kujerar in dai ni ne zan taimaka mishi." Wani kallo Baqeer yayi mishi zuciyarshi na takaicin yadda yake yiwa mahaifiyarshi magana sam babh respect, sai dai me zai ce? Bayan a dalilinshi ne ake faɗa mata magana? Kallonshi tayi tace "Kana gani zaka iya in na taimaka maka?" Zuciyarshi ce ke sake rauni tausayinta na ƙara kamashi a hankali ya ɗaga kai, haka ya dinga ƙoƙarin akan kar ya sakar mata nauyinshi gaba ɗaya wanda dalilin hakan yasa sai kifawa yayi, nan ya shiga jan jikin shi iya karfinsa, ganin yadda yake yi yasa bata ƙara takurawa akan sai ta taimaka mishi ba. Haka ya kwanta kawai yayi shiru don yasan bacci kam yau ko barawo ne ba zai ɗauke shi ba. ****** Iska Zeey ta furzar iya karfinta cikin tsananin ɓacin rai ta fara fifita da hannunta tana dafa ? ɗin apple dake table ɗin ɗakin “Wai Zeey baza ki faɗa mini menene ya ɓata miki rai ba? Nasan dai ba shakkar gobe Daddy zai dawo kike yi ba? Balle nace kina tsoron abinda Najib zai je yace ne ya dawo kanki.” Zama tayi a bakin gado tace “Aunty N please ki duba mun wannan abun, wani ne……” Sai kuma tayi shiru ta fasa maganar, to ita tace me? Wani wa? Baya kawai tayi da kanta kan katifa cikin ɓacin rai don tasan bakin Nabeela baya shiru in har tayi magana to yanzu zata ji maganar wurin Kabir azo ana tambayarta menene nata na shiga abinda bai dameta ba, wa zata faɗawa ko zata huce? Tsaki tayi da takaicin rashin amsar number Maryam da tayi dole gobe ta duba gidansu taje ta gaida Umma ta amso tun kafin Daddy ya dawo ya hanata fita. Da wannan tunanin ta kwanta sai dai har tayi bacci takaicin saurayin ya isheta, ita a rayuwarta ta tsani taga ana wulakanta mutum yana mannewa a wuri. ****** A kafadar Mummy tasa kanta tace “Mummy please kinga ba dadewa zan yi ba.” “Kuje ke da Nabeela ai tafiyar biyu dai tafi ko?” “Please Mummy ni kaɗai nake son zuwa sannan ko 30minutes bazan yi ba zan dawo, i promise.” Zeey tayi maganar tana kallonta don tasan in har taji ina zata je tofa ko zata mutu ne ba barinta za ayi ta fita ba. Cikin kokonto Mummy tace “Baby don Allah karki dade yau Daddynki zai dawo in har ya dawo ba kya nan bansan me zance mishi ba.” Kiss ta manna mata a kunci tace “Max 1hr.” Tana kawai nan ta fito da sauri hannunta riƙe da key na motar Nabeela don Daddy ya hanata fita, balle in aka san inda zata je ko mutuwa zata yi babu mai barinta taje, sam itama ba son zuwa gidan take yi ba number Maryam kawai take son ta amso ta kuma gaishe da Umma daga nan kuma In Sha Allahu bazata sake komawa. Da sauri ta fito ta faɗa mota sannan ta fita daga gidan, ta ina zata fara duba gidan? Don rabonta da gidan har ta manta, gaban yaron dake sayar da rake akan titi ta tsaya tace “Don Allah kasan gidan su Maryam?” Da mamaki yace “Maryam wacce?” Tace “Kanwar Hadiza?” Nan ma yace “Bangane ba.” Ƙasan leɓenta ta ciza sunan dai da bata son ambata a dole ta kula sai tayi. “Maryam ɗin Baqeer.” Nan fa yaro yace “Oh na gane.” Ya shiga yi mata kwatance da hannu, tayi godiya tare da bashi 1k sannan ta ja mota ta tafi shi kam sai godiya yake zubawa. A nesa da gefen gidan ta tsaya tana tunanin ta yadda zata taka kafafunta zuwa cikin gidan, gidan da sam tasa a ranta ba zata ƙara zuwanshi ba, sai dai darajar Umma da Maryam fa? Abinda yazo mata kenan wanda yasa ta shafar fuskarta, ta tabbatar Baqeer ba zai ganeta ba, kuma ƙila harta shiga ta fito ma bai san tana nan ba. ***** Kamalu ne ya diro daga kan gadonshi cike da jin daɗin wayar da aka yi mishi cigiyar Zeey daya bada aka ce an gano gidansu, ba zai iya jira ya watsa ruwa ba hakan yasa ya shiga fesa body spray sai daya kusa ƙarar da shi ya cillar anan tsakar ɗakin sannan ya zura wando da riga yana yi yana taka rawa, kallon Baqeer yayi dake zaune yana karatun Qur’ani yace “In an kawo abincina a ajiye mini zance zani.” Ko kallonshi Baqeer bai yi ba balle yasa ran zai amsa mishi, a kufule ya naushi iska da ƙafa saitin inda Baqeer yake yace “Gurgu kawai.” Fitowa yayi bai kula da motar dake gefen gidan ba ya hau babur ɗinshi yayi gaba. ***** Abu a tsakar gida sai girki take tana zabga nishadi din tabbas jiya Malam ya tsunduma a tarkonta jinta take yi kamar wata yarinya ƴar shekara ashirin da biyar, yo dama ina zata yarda ace wai don ta girma shikenan baza ta ɗana sakalci ba? Jiya ta tabbatar da kalmar da ake cewa maza basa girma. Jamila sai kallonta take yi tana binta da harara don yau sai 12 na rana Malam ya fito daga ɗakin Abu wanda kuma baya yi musu hakan ko a lokacin da Fatima take ƴar gaban goshinshi, ta tabbatar wani makircin ta sake yi ta barta a gefe. Fatima ce ta fito daga ɗaki ganin Salim har rana babu shi babu labarinshi, ta tabbatar Baqeer na neman taimako don da asuba da ƙyar ta lallaɓa su Bashir suka taimaka mishi yaje banɗaki, Abu ta kalla tace “Abu dan Allah ko zaki yiwa Kamalu magana ya taimakawa……” “Aye yare aye nayi yara ye iya aye yare munga idon wasu yara ye iye, wasu gasu can ba ƙafa yara ye iye, sai bi suke a taimaka yara ye iya to in kunsan da haka? Yara ye iye meya sa baku yi biyayya ba tun farko?” Waƙar da Abu take yi ne yasa Fatima kasa ƙarasa maganar da take yi, Jamila ta sheƙe da dariya suka tafa tace “Kai Abu yaushe kika zama mara kirki haka?” Fatima ta share ƙwallarta ta zura hijab ta leƙo waje, Zeey dake tsaye bakin mota tana saƙar shiga da warwarewa akan ta koma gida ta hangota, kallo ɗaya tayi mata ta tuna Umman nan ce dai mai ƙaunarta, murmushi ta saki tana jin sanyi a ranta, da sauri ta fara takowa wurin daidai nan wani yaron almajiri yazo wucewa Umma tana cewa “Dan Allah bawan Allah ka taimaka ka dubo mini Salim a gidan can. Ko kuma in akwai almajirin daya fika girma ka kirashi kace zamu biya ya taimaka mana.” Yaron na juyawa idanunta ya kai kan Zeey, sam bata ganeta ba hakan yasa ta nemi juyawa da sauri Zeey tace “Umman mu?” Da mamaki ta kalleta, nan idanuwanta suka fara mata alamun kallon sani, Zeey ce ta rungumeta tace “Nice Zainab fa? Zainabun ki.” Da mamaki ta ɗan zareta tace “Zainab? Kece?” Kai ta ɗaga tare da sake rungume Umma, cike da jin dadi suka shiga cikin gidan, Jamila ce ta watsawa Zeey kallo ganin shigar dake jikinta tace “Ha’a ba dai ita ce wacce Baqeer ke zancen zai aura ba? Ta shigo mana ganɗarɗar haka?” Umma tace “Ba ita bace wannan….” Hannun Umma ta riƙe da sauri tare da girgiza mata kai alamar a’a, Umma tasan dalili hakan yasa tace “ƙawar Maryam ce.” “Oh na ɗauka ai budurwarshi kika ɗauko don ta taimaka mishi.” Kalaman ta sun konawa Umma rai sai dai bata da damar amsawa. Abu dake zuba maganin mata a jarkoki tace “Wai ma kin dubashi ko? Kin san zai iya gangarawa ba tare da an sani ba tunda ba kafafun guduwa.” Gaban Umma ne ya faɗi wanda yasa tayi hanyar ɗakin da sauri tana tafe tana addu’a. Bin bayanta Zeey tayi don da alama ba lafiya ba, bata tsaya maida ƙofar ba ta tura ɗakin da sauri zuciyarta cike da tsoro. Baqeer ta samu a zaune ya rufe idanunsa gam hannunshi na hagu ya cukwikuye takardar zane da ita, ƙasan ɗakin duk pencils ne a zube an watsar. Da sauri Umma ta ƙarasa ta riƙo shi tace “Baqeer menene? Meya faru?” Zeey jin Umma ta ambaci sunan Baqeer yasa ta nemi juyawa da sauri, idanuwanta ne suka hango mata keken guragun dake gefen katifar shi, gabanta ne yayi wani irin faduwa nan da nan jikinta ya fara rawa, kalaman Umma ne suka sake rikitata “Baqeer kayi hakuri ban san ina Salim yake ba, na aika dai yanzu a kira shi zai zo ya taimaka maka, wannan bala’in da muka shiga Allah ya fitar damu Baqeer rashin ƙafar nan taka na daga mini hankali, sai yaushe zanga ka dawo Baqeer mai yawan fara’a? Zee bata san sanda tayi karo da bango ba, Baqeer? Umma ce ta waigo ta kalleta tace “Zainab kin tsorata ko? Ƙaddara ce ta afka mishi.” Zeey tana kallonshi tana girgiza kai, Baqeer? Baqeer data sani wanda kwarjininshi yasa take tsananin shakkarshi? Wanda kusan kullum sai ya sakata kuka ba tare da ya damu ba? Wanda akan baƙar maganar da yake yi mata har zazzabi take yi? Wanda a dalilinshi abotarta da Maryam ta yanke? Ina Baqeer ɗin data sani da har zai bari mace ta wulaƙantashi? A nemi illatashi a titi? Meke faruwa? Ƙwaƙwalwar ta sam ta kasa gasgata abinda ke faruwa cikin wata murya tace “Umma meya faru haka?” Muryarta daya ji ne yasa shi buɗe idanunshi da suke rufe gam a hankali ya saukesu a kanta, wacece wannan dake bibiyarshi? Yanzu kuma har gida? Ya aka yi ma tasan Ummanshi? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #Shalele #Zeey # RayuwadaKaddara #Hawayena #UMMASGHAR #AYUSHERMUHD *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *PAID BOOK* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI* *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 {17} Taku biyu tayi baya, tsabar rudanin data shiga yasa ta fice daga cikin gidan a gaggauce ba tare data tsaya jiran fitowar Umma ba, jikinta gaba ɗaya rawa yake yi ta rasa takamaimai abu ɗaya da zata kama. Haka nan dai taja jikinta da yayi wani irin sanyi ta ƙarasa wajen data ajiye motarta ta buɗe ta shiga ciki ta zauna, ta daɗe zaune a cikin motar da ƙyar ta iya saka makulli ta tashi motar ta bar wurin, har ta ƙarasa gida zuciyarta nata kai kawo akan abinda ta gani yanzun nan, kasa fita tayi daga cikin motar sai ma kifa kanta da tayi a jikin stearing wheel tana tunanin to me ya faru dashi haka? Ita dai tasan lafiyayyen mutum ne mai ji da ƙarfi to garin yaya ya zama gurgun da sai an turashi akan wheel chair? Kai Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, abun duniya ya dameta duk ƙoƙarin da take yi na kawar da tunanin shi daga ranta ganin tun da can babu wani shiri a tsakaninsu bare damuwar halin da yake ciki ta dameta ta kasa sai ma ƙara kutse da tunaninshi yake yi cikin zuciyarta. Tsaki tayi cikin ranta tana cewa "to wai ni miye ma damuwata ne da daga ganin mutum zan bi na rasa sukuni?" Tunanin hakan yasa ta ficewa daga cikin motar ta shiga gida sai dai duk da hakan ta kasa yakice ganin da ta yiwa Baqeer akan keken guragu a zaune daga ranta. Da murna Mummy ta tareta ganin yau ɗaya dai Zeey taji maganarta ta dawo gida da wuri don tun fitarta take zullumin kada Daddy ya dawo bai tarar da ita ba bayan ya hanata fita ko ina, tasan da ba ƙaramin ɓacin rai hakan zai janyo mata ba sai kuma ta taimaketa ta dawo kafin Daddyn. Akan doguwar kujera ta zube ta kwanta ba tare da ko takalman ƙafarta ta cire ba, kallon tsaf Mummy tayi mata ta lura kamar da akwai abinda ke damunta sai dai ba tayi magana ba sai ma tayin abinci da tayi mata ganin har ta fita bata yi lunch ba. Ga mamakinta ko musu Zainab bata yi mata ba ta tashi ta nufi wajen da suke cin abincin taja kujera ta zauna, Mummyn ce tayi serving ɗinta don dama ita ta sabar mata da komai take so sai anyi mata gashi yanzu har girmanta bata iya tsinanawa kanta komai. Juya cokali kawai take yi a cikin abincin ta kasa kai ko loma ɗaya bakinta, haka nan sai ganin abinda ya faru tsakaninshi da buduwarshi take yi da kuma lokacin da wannan marar kan gadon ya ajiye shi akan titi. Wane irin canji ne ya samu rayuwarshi haka a ɗan taƙaitaccen lokacin data ɗauka bata sanya shi a ido ba? Tunanikan sun kasa barin zuciyarta har ma ta kasa cin abincin duk kuwa da tarin yunwar da take ji tun ma kafin ta fita ta bar gidan, tashi kawai tayi ta bar abincin ba tare da ko ɗanɗanawa tayi ba. Kallonta Mummy tayi ta kalli plate ɗin da yake cike taf da abinci yadda ta zuba haka Zeey ta bar mata shi. "Meke damunki ne Zeey? Tun dawowarki na lura kamar akwai abinda ke damunki, ba dai wani mummuna abu aka yi miki a inda kika je ba ko?" Kallon Mummyn tayi ta girgiza kai alamun babu komai sai kuma tace "Babu komai Mummy kawai dai na gaji ne.” "Allah ya kyauta," kawai Mummy tace ba don ta yarda da amsar da Zeey ɗin ta bata ba sai don bata fiye son matsanta mata ba amma a yadda take da surutu da rawar kai tasan tabbas akwai abinda take ɓoye mata don haka nan Zeey bata iya shiru in dai har tana wuri to sai ta addabi kowa da karaɗinta. Juyawa tayi zata bar wurin ta koma ɗakinta Daddy ya shigo, yana ganinta kuwa ya fara faɗa ko sannu da zuwan da take yi mishi bai amsa ba. "Wato Zainab har abada ke ba za'a faɗa miki magana ki ji ba ko, shine don ki nuna ban isa dake ba kika sake wulaƙanta yaron nan Najib bayan cewa da nayi ki bashi haƙuri?” Faɗa kawai yake yi irin wanda bai taɓa sakata a gaba yayi mata ba sai dai ko kusa hankalinta baya wajenshi bare ta tanka mishi irin yadda a mafi yawan lokuta take yi idan yana yi mata faɗa tana ƙoƙarin defending kanta, a yau zuciyarta tayi nisan kiwo ba saurarenshi take yi ba, tunaninta na wajen Baqeer da alhinin abinda ya sameshi, to wai ma shin yaushe ne yaji ciwon da ya nakastashi haka? Mummy ce tace "Zainab" da ɗan ƙarfi lura da tayi sam hankalinta baya wajen, sai cewa tayi "Eh naji" kawai alhalin bata ma san maganar da ake yi ba. A halinta na rashin barin abinda ke cikinta sai ta samu kanta da kasa furtawa kowa damuwar halin da taga Baqeer ɗin, tana mamakin wai dama wannan gurgun da take yawan gani a mabanbanta lokuta Baqeer ne. ***** Mamaki ne ya kama Umma data fito bata ga Zainab ba, leƙawa tayi ƙofar gida ko zata ganta sai dai ko alamunta bata gani ba, haka ta juyo tana cewa "Kenan tafiya tayi?” Komawa tayi ta kama aikin taliyar da maƙwabtansu suka kawo mata, tana yi tana share ƙwallar tausayin Baqeer. Wai kenan haka zasu cigaba da rayuwa baya da mataimaki? Salim ɗin da suka dogara a kanshi Mallam yayi sanadin da yayi fushi ya daina zuwa alhalin shi ba tausaya mishi zai yi ba bare ya tallafe shi. Dole ta tashi tsaye ta kama sana'a ta yadda zata samu ta ɗaukar wa Baqeer mataimaki ko almajiri ne da zai ke taimaka mishi tana biyanshi. Ta gama aikin taliyar ta shanya akan igiyar data ɗaura a kusa da ɗakinta, tattare wajen da tayi aikin ta hau yi tana kawar da kayayyakin data ɓata. Abu dake zaune a ƙofar ɗakinta tana zuzzuba garin dakan da take sayarwa a ƙananun robobi ta kalleta ta taɓe baki kafin ta saki shewa tace "Ahayye nanaye, duniya rawar ƴan mata na gaba ya koma baya, yau ga uwar shalele, mowa a cikin ƴaƴa na sana'ar hannu, ai na ɗauka neman kuɗi sai mu irin ku sun girmi sana'a sai dai ƴaƴan ku su fita su nemo su kawo muku kuna daga kwance, ashe dai duk abun bogi ne,” ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya har da kama hanci ta saki guɗa. Har Jamila dake aikin abincin rana na tayata tace "Yo ba dole ta tashi ta nema ba tunda mai kawowar ya zama gurgu, zaman gida kuma ya aureshi? Kin manta sanda ɗan kanzagi ya ɗauke injin taliyarta ya ajiye wai ta huta?” Dariya suka sheke dashi duka su biyun wannan abu na basu dariya. Ran nan na Abu fari ƙal da farin ciki don a yanzu ji take yi tamkar tafi kowa, ƙiris ya rage gida ya dawo hannunta tunda ma gashi ta fara samun Mallam a hannu. A wulaƙance ta kalli Umma da ko ɗaga kai bata yi ta kallesu ba duk kuwa da yadda zuciyarta ke tafarfasa da wannan cin kashin da suke yi mata tace "Dama sakin wannan aikin taliyar kika yi kika tura shi bakin titi kuka yi bara sai kiga kun samo kuɗi fiye ma da abinda yake samu a harkar zanen don yanzu almajirai ai sune da kuɗi tunda su kullum cikin karɓa suke basu san su bayar ba.” Sai wannan lokacin Umma ta kalleta har zata yi magana sai kuma ta fasa ta shige ɗakinta ta barsu anan suna cigaba da sakin baƙaƙen maganganu duk dai akan fifikon da Baba ya dinga nunawa Baqeer akan ƴaƴan su. Zama tayi a bakin gado tana kukan tausayin kansu daga ita har Baqeer ɗin ganin yadda aka mayar da larurarshi abun gori har ana cewa ta turashi su fita bara kamar shi ya ɗorawa kan shi. Yana daga ɗakinsu yana jiyo duk abinda ke faruwa a cikin gidan da duk gore-goren da suke yiwa Umman. Wani irin ƙunci da baƙin ciki yake ji a cikin ranshi, yadda kowa ya juya mishi baya nayi mishi ciwo. Kallon ƙafafun shi yayi da ko kaɗan baya jin alamun su a jikin shi, ya kalli hannunshi dake naɗe a cikin bandage yace "Shikenan yanzu ni a haka zan yi ta zama ba zan morawa kaina komai ba?” Ƙoƙarin motsa ƙafafun yayi tayi yaga ko zai iya tashi ya kasa, haka nan ya haƙura ya buɗe drawer dake ajiye a gefen katifarshi ya ciro takarda da pencil ya hau ƙoƙarin yin zane sai dai hannunshi baya da ƙwarin da zai iya riƙe pencil dole ya haƙura yayi watsi da kayan a tsakar ɗakin yana sakin huci kamar wanda yayi tseren gudu. Gabaki ɗaya rayuwar bata yi mishi daɗi ji yake yi ina ma ya mutu ya huta, duk ya juya ya kalli ƙafafun shi naɗe a waje ɗaya basa iya ko motsi ya ɗaga hannunshi ya ganshi a naɗe a cikin bandage sai yaji to shi miye amfaninshi ma tunda ba zai iya amfanar kanshi da komai ba. Ƙarfin imani ne kawai ke hanashi ɗaukar mummunar shawarar da zuciyarshi take kitsa mishi don wasu lokutan sai yaji kamar ya datse rayuwarshi ya huta gaba ɗaya da waɗannan matsaltsalun da suka dabaibaye rayuwarshi. ***** Kamalu kuwa yana fita ya burga babur ɗin shi yabi kwatance tiryan-tiryan kamar yadda aka yi mishi sai gashi a ƙofar gidan su Zeey. Kallon ƙatuwar katangar gidan yayi yana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarshi, yau dai gashi a ƙofar gidansu Roshni ɗin shi fatanshi dai tayi na'am dashi ta amshi tayin soyayyar shi, kallon rigarshi yayi yana ƙara kakkaɗeta yana tabbatar da shigarshi tayi ko gaban gwamna zai iya zuwa a haka. Sauka yayi ya ajiye babur ɗin a gefe ya ƙarasa gaban gate ɗin gidan yasa hannu ya ƙwanƙwasa. Daga ciki mai gadi ya taso ya buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ya leƙo da kanshi waje. "Sannu dai" Kamalu yace yana ɗaga mishi hannu. "Yauwa sannu" maigadin yace bayan ya fito waje ya janyo ƙofar ya rufe yana ƙarewa Kamalun kallo. "Lafiya dai ko? Wa kake nema?" Wani kallo Kamalu ya jefa mishi irin na kada ka raina mini wayo kafin cikin maganarshi irinta gagararrun ƴaƴa yace "ka gane ba wato akwai Roshini ɗita wata ƴar black beauty nan haka tana jan wata jar Honda Accord ance nan ne gidansu, da Allah ita zaka yiwa magana kace mata Kamel ne yake sallama" yana yi yana gyara zaman rigarshi irin a dole shi ga gayu ɗinnan. Wani irin kallon banza maigadin ya watsa mishi yace "Kai kama kalli kanka a madubi kuwa kafin ka fito? Anan gidan ne kake da wata Rashida take ko wa? Don Allah ɓace mini da gani tun kafin kayi mini sanadin aikina, in banda sakarci ma irin naka ta yaya kamar kai guntun ƙwaya da wiwi zaka ce kazo wajen wata ƴa a cikin gidan nan, ni wallahi da farko na ɗauka wajen Alhaji kazo irin ƴan bangar siyasar nan ne ashe wai kai wajen Rashida kazo, to babu Rashida a gidan nan sai ka ƙara gaba ko zaka yi dace da samunta a wani wurin.”Ya juya zai bar wurin Kamalu ya damƙo wuyanshi yana cewa "Kai kasan koni waye da har kake faɗa mini maganar banza? Kai matsiyaci ma maigadi har ka isa ka hanani ganin Roshni? Tun Roshnin bata fito ba har kana da bakin kore mata NI, to wallahi baka isa ba, ko ka shiga ciki ka kira mini ita ko nayi maka rotse a wajen nan.” Ya hankaɗa shi jikin gate ɗin yana sakin huci. Shi kuwa maigadi yana jin an sake shi ya shaƙi iska ya kwasa a guje yayi cikin gidan ya datse ƙofar gate yana mayar da numfashin wahala don ba ƙaramar shaƙa yayi mishi ba. Leƙa gate ɗin Kamalu yayi ta tsakankani, motoci ya gani yace “Ai Roshni ina auranki wancan zan amsa don babu shakka ita ta dace dani.” Ya sheƙe da dariya yana tuno wata ragwargwajajiyar motar Baba wanda ake faɗa akanta a gidansu, kafin yaja tsaki yace “Ni yanzu nafi karfin shiga Golf ɗin ku sai kuje can ku karata.” Ya ɗan daka tsalle tare da sake kallon mai gadin yana ji kamar ya zabga mishi mari. Horn suka ji daga cikin gidan da sauri Mai Gadi ya nufi wurin shi kuma Kamalu ya maƙale a lungu yana leƙe, ganin an fito da ɗaya daga cikin motocin nan yasa yabi wanda ke cikin motar da kallo, namiji ne da bai fi sa’anshi ba, huci ya furzar yana jin ina ma shine a cikin motar nan? Ko da yake an kusa ai. An kusa me Kamalu? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #MBB #Zeey #Hawayen zuci #Kaddara #Kamalu KB #AYUSHERMUHD #UMMASGHAR *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *PAID BOOK* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS* *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 {18} Tun jiya da dare take dakon shigowar mai gidan nasu sai dai har lokacin barci yayi ta shiga ɗaki ta kwanta bata ji ɗuriyarshi ba, hakan yasa yau tun sassafe ta fito tsakar gidan ta zauna sanin halinshi ba wai ya kula da bin ɗakunan matanshi ya duba lafiyarsu idan gari ya waye ba, haka nan idan bada wani ƙwaƙƙwaran dalili ba baya taɓa shiga ɗakunan baccinsu sai dai su haɗu a tsakar gida idan kuma kece da girki ki iskeshi a ɗakinshi, ko wacce irin magana gareki sai dai ki faɗeta a tsakar gidan gaban kowa don bai yarda da bin bayanki don kuyi sirri ba, ita ce ma take da wannan alfarmar ada lokacin da ɗanta yake da mamora ba yanzu ba da ya gama yi mishi amfani yayi watsin ruwan tsarki da al'amarin da duk ya shafe su. Tana nan zaune Jamila ta fito ta hau kici-kicin ɗora abun karyawa. "Ina kwana" tace mata ganin bata lura da zamanta a wajen ba. Waiwayowa tayi ta kalleta sai kuma ta taɓe baki tace "ke kuma lafiyarki kika fitowa mutane tsakar gida da duku-dukun safiya, ko kuwa dai wani sabon salon munafurcin ne kika ɓullo dashi". Bata tanka mata ba jin bata amsa gaisuwar da tayi mata ba sai ma wasu ƙananun magangnu data bita dasu. Jamila na aikinta tana sakin maganganu ita dai tana jan carbinta don tun zamanta dama abinda take yi kenan shi yasa ma zaman wajen bai gundureta ba. Har Jamila ta gama ɗumamen tuwo ta dama koko ta zubawa kowa nashi, sai sannan ta tashi ta ɗauke nata dana Baqeer ta kai ɗaki ta ajiye ta dawo ta cigaba da zama a ƙofar ɗakinta tana dakon fitowar Mallam ɗin. Bai fito ba sai can da rana ta take ya fito da shirin shi na fita kasuwa. "Ina kwana Mallam" ta gaishe shi a ladabce cikin muryarta mai sanyi. Juyowa yayi ya kalleta ya watsa mata wani banzan kallo kafin ya juya yana miƙawa Jamila kuɗin cefanen su na ranar, ganin ya nufi hanyar fita yasa ta ɗan ɗaga murya tace "Mallam magana ce dani don Allah". A fusace ya juyo yace "sai aka yi yaya idan kina da magana? Ko kuwa saboda maganarki sai na fasa fita kasuwa, banda kinibibi da kutinguila sai da kika ga na gama shiri zan fita sannan zaki tsayar dani salon ki sakani makara, ko kuwa yau nake cikin gidan da baki samu lokacin magana ba sai da na fito zan fita". "Kayi haƙuri" tace kanta a ƙasa. "Tun jiya nake tsumayen dawowarka har bacci ya ɗaukeni baka dawo ba, dama maganar komawar Baqeer asibiti ne da aka ce bayan sati shida a koma don a kunce ɗaurin da aka yi mishi zan yi maka ganin yau har an ƙara kwana uku akan sati shidan da aka bamu ban ji kace komai ba". A fusace cikin masifa da tijara irin tashi ya hau nunata da yatsa yana cewa "kinga Fatima ki kiyayeni, na lura raini kike neman kawo mini a cikin gidan nan, au bayan kin gama zuge ɗan naki yayi fatali da dukkan sadaukarwata a kanshi yaƙi yin abinda na sakashi shine yanzu zaki kwaso jiki ki tareni da batun mayar dashi asibiti? Don bance ku biyani kuɗaɗen da yasa nayi asara a kanshi ba shi yasa kike tunanin zan mayar miki dashi asibiti a kunce ɗauri, to ya dauwama a haka mana ina ruwana tunda dai babu wani amfani da zai yi mini na ƙare kashe kuɗina a kanshi a banza ba tare dana amfana da gina shin da nayi tayi ba sai ma nakasa da yayi yana nema ya ɗora mini wahala, to ba zan yi ba idan kinga zaki kai shi asibiti ban hanaki ba amma sisina ba zai ƙara yin ciwon kai a kanshi ba, sai ku gode abincina ma da yake ci a kullum ba tare da yayi wata wahalar nemowa ba, mtsew" ya saki wani dogon tsaki ya juya ya fice daga gidan yana huci kamar kububuwa. Yana fita suka yi kaciɓis da makwabcin shi Mallam Nuhu, ɗauke kai yayi ya wuce kamar bai ganshi ba. Yana ƙoƙarin saka makulli ya buɗe motar yaji muryarshi daga bayan shi yana cewa "Mallam Badaru barka da asuba, an tashi lafiya?" Juyowa yayi irin kamar sai yanzu ya ganshi ya bashi hannu suka gaisa. "Kwana biyu bamu gaisa ba, ina taso na leƙo ma nayi maka jaje ashe tsautsayin da ya afkawa Baqeer kenan ban samu dama ba, wallahi Mallam Badaru sam bani da labari sai shekaranjiyan nan dana hange shi ana tura shi a keken guragu ake ce mini ai mota ce ta buge shi sanadin hakan har ya rasa ƙafafu gashi hannun nashi ma ya karye don haka ko gasar masu zane da zai je bai samu zuwa ba sai abokin shi ne ɗan wajen Alhaji Bala yaje a madadin shi. Allah ya kiyaye gaba ya mayar kaffara". Tunda Mallam Nuhu ya fara magana Baba ya ƙara ɗaure fuskar nan tamau kamar bai taɓa dariya ba yana jifanshi da wani irin kallon wulaƙanci. Tsaki yaja yace "Ai sai ka kauce ka bani wuri tunda dai ka gama abinda ya kawo ka, in banda gulma da tsugudidi da can baka san Baqeer ɗin yayi hatsari ba sai yanzu zaka tareni da wasu zancen banza?” Ya buɗe motarshi ya shige ya jata a guje ya bar wurin yana baɗe Mallam Nuhu da ya bishi da kallon mamaki da ƙura, abun arziƙi ya taɓa zama na tsiya ne dama? Har ya ƙarasa kasuwa zuciyarshi baƙi ƙirin yake jinta, ya rasa inda zai saka kanshi yaji daɗi, duk ya tuna wai Bello yaron da jajircewar Baqeer a kanshi ce tasa ya ƙware a harkar zane ne wanda ya tafi a madadin Baqeer har ma ya karɓo award sai yaji kamar ya kwanta a ƙasa yayi ta burgima ko ya samu yaji sauƙin raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyar tashi, gashi mutane da gulma da kinibibi yayi wa yawa sai faman tararshi suke yi suna tambayar ba'asin yadda aka yi Baqeer bai tafi gasar ba sai dai abokin shi ne yaje a madadin shi, har rasa amsar bayarwa yake yi don ashe wai duk ɓoye-ɓoyenshi na kada asan halin da suke ciki da Baqeer ɗin mutane sun sani, har wani gugar zana ake yi mishi ana cewa yaron daya fifita fiye da sauran ƴaƴan shi gashi kuma inda rayuwa ta kaisu bai zama abinda yake kuri da cika bakin zai zama ba a harkar zane. Yaran shagon shi kansu sun san yau zuciyarshi a wuya take, ɗan kuskure ƙalilan zasu yi sai dai ya rufe su da faɗa don haka suke takatsantsan dashi don sun daɗe da sanin halinshi dama shi yasa suke haƙuri da tijarar shi idan ya fara sai dai suyi ta bashi haƙuri. Yana zaune a cikin shagon shi inda yake sayar da kayayyakin sawar mata kama daga su atamfa, leshi, shadda, material da voiles yana kallon shige da ficen mutane masu shigowa yin sayyaya ɗaya daga cikin yaran shagon yazo ya russuna yace mishi yayi baƙo. Ɗan tsaki yaja irin na an takura shi ɗinnan ya cewa yaron ya cewa baƙon ya shigo daga ciki. Ƙara tsuke fuska yayi ganin mahaifin Bello Alhaji Bala ya shigo da fara'arshi. Hannu ya miƙa mishi haɗe da yi mishi sallama sai dai da ƙyar ya buɗe baki ya amsa sallamar ba tare daya bashi hannu sun gaisa ba. Sai ajiye hannunshi Alhaji Bala yayi ganin Mallam Badarun baya da niyyar mayar mishi. Bai fasa abinda ya kawo shi  ba duk kuwa da yaga irin karɓar da yayi mishi. Da farko tambayarshi ya fara yi yanayin jikin Baqeer sai dai Mallam Badaru yayi kicin-kicin da fuska yaƙi amsa mishi don haka ya bar wannan maganar ganin kamar baya sonta ya fito da envelope daga aljihun shi ya miƙa mishi yana cewa "Dama zuwa nayi mu gaisa na kuma kawo maka ɗan wani abu daga abinda Bello ya samo a wajen gasar da yaje ganin komai ya zama Baqeer ne sila nace ai ba'a yi tuya a manta da albasa ba tunda ma banda Allah ya aikowa da Baqeer wannan tsautsayin kujerar ai tashi ce to kana naka ne Allah yana nashi ta Allah kuma ita ce daidai, dama can Allah ya nufa Bello ne mai zuwa wannan wurin shi yasa nace bari na kawo maka wannan kasa albarka, shi kuma Baqeer Allah ya bashi lafiya ya tashi kafaɗunshi ya bashi ikon cinye jarrabawar da yayi mishi.” Da ace Alhaji Bala ya lura da yadda maganarshi ta fusata Mallam Badaru yana ƙara hawa kamar farashin mai a Najeriya da tuni yayi shiru sai dai da yake shi da zuciya ɗaya da kuma kyakkyawar manufa yazo wurin shi yasa bai lura da yadda yanayin shi ya canja ba har sai da ya daka mishi tsawa yace "Dallah Mallam yi mini shiru munafukin banza munafukin wofi, har ni zaka kawowa munafurci kazo da wani kuturun wulaƙanci kana ce mini haka Allah yayi ba Baqeer bane mai zuwa wajen gasa Bello ne? Ni dama na daɗe da sanin abotar Baqeer da ɗanka babu inda zata kai shi sai a ajin dana sani, shine bai sani ba har ya janyo Bello a jikinshi ya nuna mishi yadda ake zane ya baje mishi dukkanin wasu sirrikan samun nasararshi gashi nan yanzu yayi mishi halin ƴan adam ya munafurce shi ya tafi wajen gasar a madadin shi bayan yasan Baqeer baya da wani buri a rayuwa face zuwa wannan wuri, da Allah tattara gayyar tsiyarka ka fice mini daga shago idan ba haka ba nasa yara suyi maka dukan mutuwa wallahi.” Baki buɗe Alhaji Bala ke kallonshi yace “Dama abun arziƙi ya taɓa zama na tsiya? Daga zuwa nayi maka alheri ganin komai Bello ya zama ɗanka ne sanadi shine zaka bini da baƙaƙen maganganu kana nema ka zageni?” A harzuƙe ya tashi tsaye shima yana nuna shi da ɗan yatsa yace "An zageka ɗin, nace maka an zageka ɗin, kai ɗin har wata tsiya ce da ba za'a zageka ba, munafukai masu saka alheri da sharri, duk alherin da Baqeer yayi wa Bello bai yi mishi baƙin ciki ba ya nuna mishi kan sana'ar shi amma ya rasa da abun da zai saka mishi sai wannan?” Haka dai suka yi ta cacar baki da ƙyar aka samu aka fitar da mahaifin Bello daga shagon don sosai ranshi ya ɓaci da tijarar da Mallam Badaru yayi mishi daga abun arziƙi. Har ya bar kasuwar zuciyarshi nayi mishi zafi, dama takaicin maƙwabcin shi daya tare shi da gulma wai yanayi mishi jaje sai kace ance mishi yana buƙatar jajenshi, a yanzu shi abu ɗaya ne zai wanke mishi zuciya yaga Baqeer ya dawo daidai ya koma harkokinshi kamar da. ***** Tunda ta kwanta sai faman juye-juye take yi akan makaɗeɗen gadonta da yaji shimfiɗa ta alfarma. Koda wasa ta kasa runtsawa data rufe idanunta shi kawai take gani yana yi mata gizo, ta kasa yardar wa ranta cewa wai wannan gurgun da take yawan gani ana tura shi a wheel chair Baqeer ne wanda ta sani tun suna yara, yayan ƙawarta Maryam mai yawan tsokanarta yana sakata kuka har ya janyo ta daina shiga gidansu saboda yawan tsokanarta da yake yi. Juye-juye kawai take yi tana saƙa da warwara maganar na cinta a rai ta kasa furtawa kowa ko don bata saba barin abu a ranta ba yasa wannan ɗin ta dameta ganin ta kasa faɗawa kowa yadda ganin Baqeer ɗin a keken guragu ya ɗaga hankalinta. Yaye duvet ɗin data lulluɓe rabin jikinta tayi ta sauko daga kan gadon a nutse ta saka bedroom slippers ta fita zuwa ɗakin Nabila dake daura da nata. Cikin sanɗa ta tura ƙofar ɗakin ta zura kanta a hankali, switch ɗin fitila ta danna haske ya gauraye ɗakin. A naɗe akan gado taga Nabila tana bacci hankalinta kwance alamun babu abinda yake damunta, ƙarasawa tayi gaban gadon tasa hannu zata yaye duvet ɗin data rufe ilahirin jikinta dashi sai kuma ta fasa, yanzu idan ta tasheta tace me ya hanata bacci, ita dai tasan ko kusa ba zata iya fitowa tace mata ga abinda yake damunta har ya hana mata bacci ba don haka ta juya ta kashe mata fitilar ta bar ɗakin. Ɗakinta ta koma ta hau kan gado ta kwanta sai dai cikin ranta ta ƙudurce gobe zata koma gidansu ko don ta ƙara tabbatarwa da kanta cewa Baqeer ne dai data sani wannan gurgun. Da ƙyar ta samu bacci ya ɗauketa koda ta tashi sai ta tashi da ciwon kai saboda rashin samun isashen bacci da bata yi ba. Haka ta fio idanunta a kumbure, Mummy na ganinta ta tashi ta tarota cikin tsantsar kulawa take cewa "Kinga yadda fuskarki ta kumbura kuwa Zeey? Ba dai wani abu ne ya sameki ba ko? Dan tun jiya na kasa gane kanki.” Tana yi tana taɓa jikinta sai dai babu alamun zazzaɓi don haka ta ɗan kwantar da hankalinta sai dai Zeey ɗin nace mata headache ne take fama dashi ta ƙara rikicewa har sai da Nabila tayi magana tace "Haba Sis, headache ɗin ne zai ruɗar dake kamar baki san Zeey da raba dare tana kallo ba, yanzu haka kwana tayi tana kallo bata kwanta da wuri ba shi yasa kanta yake ciwo amma daga taci abinci ta sha magani zai warware.” Kallonta Mummyn tayi tace "Wai haka ne My Zeey?" Ɗaga mata kai kawai tayi don yau sam bata jin son yin magana, zama tayi akan kujerar dining table. Da kanta Mummy ta taso ta haɗa mata tea sannan ta ɗauki plate ta haɗa mata breakfast duk ta tura a gabanta tana cewa "daure kici kin ji baby sai ki sha magani kije ki kwanta ki huta". Da kai ta amsa mata sannan ta fara cakalar abincin kamar mai cin maɗaci, haka dai ta caccakala ta tashi ta koma ɗakinta bayan ta sha paracetamol tayi wanka sannan ta hau gado ta kwanta. La'asar nayi ta tashi ta shirya cikin wata free English gown beige color sai ta yafa farin jersey veil a kanta, bata yi wata kwalliya ba sai perfume da ta fesa. Ɗakin Mummy ta shiga tace mata "Mummy don Allah zan ɗan fita yanzu zan dawo ba zan daɗe ba". Kallonta Mummy tayi tace "har kan naki ya daina ciwo da zaki fita? Wai shin ina ma kike yawan zuwa kwanannan da kullum sai kin ƙirƙiri fita bayan kin sani sarai Daddynki ba son yawan fitarki yake yi ba". "Kiyi haƙuri Mummy wallahi ba zan daɗe ba yanzu zan dawo.” "Ni dai don Allah kada ki daɗe bana so Daddynku ya dawo bai sameki ba". "Thank you Mum" tace haɗe da hugging ɗinta, fita tayi tana ɗokantuwa da son sake saka Baqeer a idanunta. Zuciyarta sam ta kasa nutsuwa, wai Baqeer dai Baqeer? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *PAID BOOK* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA  GOMA SHA TARA* *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 {19} Tana shiga soron gidan ta ganshi daga bakin ƙofa ya ƙurawa ƙofar shigowa gidan ido sai dai idan ka lura sosai zaka gane hankalinshi ba'a wajen yake ba yayi nisa sosai wajen tafiya duniyar tunani. Tsayawa tayi tana kallonshi ta ƙara tabbatarwa da kanta lallai fa shine dai Baqeer ɗin data sani ba wani daban ba, kafin taja jiki ta shige cikin gidan tana jin wani irin tausayin shi yana ratsa ta. A tsakar gidan ta tsaya tana sallama, Umma da ɗakinta ke a kusa da ƙofar shigowa ta fito tana amsa sallamar. Ganinta a tsaye yasa ta washe baki tana cewa "Ah ah Zainab kece? Lale lale sannu da zuwa, shigo daga ciki.” Bin bayanta tayi itama tana murmushin, kujera ta nuna mata ta zauna ita kuma ta koma bakin gado. Ɗan russunawa Zeey tayi ta gaisheta, da fara'arta ta amsa mata tace "Jiya kuma sai kika tafi ba tare da kin jirani ba, har waje na leƙa ban ganki ba.” Sai ta samu kanta da jin kunyar Umman kada tayi tunanin ko guduwa tayi saboda ganin halin da Baqeer ɗin yake ciki. Kanta a ƙasa tace "Kiyi haƙuri Umma wai fa zuwa nayi na gaisheki na kuma ƙarbi number wayar Maryam ranar mun haɗu har muka rabu kuma ban samu na ƙarba ba, sai dai ruɗewar da nayi da yadda naga Yaya Baqeer ya koma yasa na fice ba tare da ko sallama na tsaya yi miki ba.” Ta ɗan ja numfashi kaɗan tana murza tafin hannunta a saman cinyarta, kafin ta cigaba “Umma ni kam meya faru dashi haka na ganshi a wani hali daban saɓanin yadda na sanshi ada?”Hawaye ne ya sulmiyo daga idanunta tasa gefen rigarta ta share. "Kin dai ga yadda Allah ya mayar da Baqeer, ƙaddara ce ta afko mishi wacce bawa bai isa ya kauce mata ba tunda haka Allah ya hukunta, wani ne ya kaɗeshi da mota sanadin hakan ya rasa ƙafafunshi likitocin sun ce sun tashi daga aiki baza su ƙara moruwa ba,” ta ƙarashe maganar kukan da take riƙewa a cikin ranta na ƙwace mata, damuwar data yini a ciki ce ta taso mata lokaci guda har ta kasa riƙe kanta a gaban Zainab ɗin. Duk sai Zainab taji babu daɗi ganin yadda Umman ke kuka kashirɓan gaba ɗaya tausayinta ya lulluɓeta, tashi tayi ta koma kusa da ita ta zauna ta kamo hannayenta ta riƙe cikin tausasa murya tace "kiyi haƙuri Umma, ƙaddararshi ce tazo a hakan kamar yadda kika ce kuma bawa bai isa ya kauce mata ba, Allah ya sauƙaƙa mishi ya bashi ikon cinye jarrabawar da yayi mishi". Da ƙyar ta iya tsayar da kukan tana jin kunyar yadda ta tasa yarinya a gaba tana yi mata kuka sai dai kuma damuwar dake danƙare a cikin ranta ce ta taso mata lokaci guda tafi ƙarfinta, a halin da ake ciki yanzu bata san ya zata yi ta kai Baqeer asibiti ba gashi ita bata ajiye ba bata bawa wani ajiya ba bare ta samu abinda zata yi hidimar kula dashi, dama shine ya ɗauke mata dukkanin wasu buƙatunta to ga kuma ajin da rayuwa ta kai shi shima a yanzu neman mai taimaka mishi yake yi. Sun jima shiru babu wanda ya ƙara magana sai zuwa can Zainab tace "Umma zan tafi Mummy tace kada na daɗe". "To Zainab nagode kin ji, Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.” "Ameen Umma" tace tana nufar ƙofar ɗakin sai kuma Umma tace “Yau ma zaki tafi baki karɓi lambar Maryam ɗin ba?” Juyowa tayi tana dariya tace "Wallahi na sha'afa bayan kuma abinda ya fito dani kenan.” Dariya itama Umman tayi ta ɗauko wayarta ta lalubo number Maryam sannan ta miƙa mata wayar ta kwafa. A daidai wannan lokacin Mallam Badaru daya kasa zaman kasuwa saboda ɓacin rai ya shigo yana ƙwalawa Umma kiran da duk wanda yaji yasan bana lafiya bane. A take jikinta ya hau ɓari ta fita daga ɗakin jiki na rawa har zanin jikinta yana kuncewa tsabar ruɗewar da tayi. Tana fita tsakar gidan taga ya janyo Baqeer ya dangwarar da keken nashi a tsakar gidan, komawa yayi ɗakin yana watsi da duk wani kaya da yasan na Baqeer ɗin ne. Sai daya gama fitowa dasu tas sannan ya fito, nunata ya hau yi da ɗan yatsa yana cewa "Wallahi na gaji, na gaji da zaman nakasashen ɗan nan naki a gidana, na gaji da zunɗena da nunani da mutane suke yi duk lokacin dana fita waje ana yi mini dariya saboda kawai naso ɗanki na fifita shi a cikin ƴaƴa gashi yanzu da abinda yazo ya saka mini, duk wani ƙoƙarina na ganin ci gabanshi a rayuwa ya tashi a banza, to bazan iya ba gashi nan ki fitar mini shi daga gidana don na tsani na buɗe ido na ganshi, yaje can yayi rayuwarshi inda bazan dinga ganinshi ba bare ya saka mini cutar hawan jini.” Zainab da tun fara faɗan Mallam Badaru ta kasa zaune ta kasa tsaye mamakin jin tijarar da yake yiwa Umma da Baqeer a tsakar gida cikin mutane kawai take yi kamar ba shine wannan mai ji da Baqeer ɗin ba da baya iya ɓoye soyayyar da yake yi mishi a gaban kowa ma nuna mishi so yake yana alfahari dashi, wai shine yanzu don wani iftila'in rayuwa ya saukar mishi yake neman ya juya mishi baya, ji take yi kamar ta fito ta faffaɗa mishi baƙaƙen maganganu ko ranta yayi sanyi ita dai tasan ko me zai sameta a rayuwa Daddynta ba zai taɓa barinta ba amma shi wannan sai gashi shine ma kan gaba wajen nunawa ɗan nashi ƙiyayya. Kasa haƙurin jure jin waɗannan maganganun tayi ta fito ta fice fuu a fusace ta bar gidan, da kallo ya bita yana tunanin ita kuma wannan wacece, idanunta kan Baqeer suka sauka wanda daidai nan shima ya ɗago ya kalleta, yanayin kallo tayi mishi wanda ya sakashi sake kallonta sai da ta ƙurewa ganinshi sannan kalaman Baba suka dawo dashi daga kallon wurin, me idanunta ke son ce mishi? Meya kawota gidansu yau ma? Baba yaji  ya cigaba da zazzagawa Umma tijara tana tsaye tana zubar da hawaye, shi kuwa Baqeer baƙin cikin yadda Baban yake nuna mishi ne ya cika fal cikin zuciyarshi sai wani irin kallo da yake bin Baban dashi yana tunanin wai dama can haka yake ko kuwa yanzu ne dai ya canja halinshi ganin babu wani amfani da zai iya yi mishi. Ajiyar zuciya yayi wanda Baban yace “Kai Baqeer ina fada kana sauke mini ajiyar zuciya?” Kai ya kauda kafin ya samu kanshi da cewa “In ka gaji dani ka sallamani mana, wannan wace irin rayuwa ce?” Baki buɗe Baba ya kalleshi a fusace yayi kanshi yana neman ya dakeshi cike da hargagi yake cewa “Ni kakewa magana haka?” Umma ce tayi saurin shan gabanshi tace “Mallam na rokeka da Allah ka bari, wannan wace irin rayuwa ce? Dame ake so yaron nan yaji?” Kallon Baqeer yayi yanda ko kallonshi baya yi, nan ya sake fusata yace “Ni Baqeer zai yiwa haka? Duk yadda na kula dashi a rayuwa? Sannan ina faɗa ki dinga cemin wace irin rayuwa ce wannan to wallahi yattara kayanshi ya bar min gidana, kuje can kusan abun yi.” Abu ce tace “Mallam ayi haka? Ba dai almajiranta kake so su fara janshi ba ko? Gurgu ina zai je in ya rasa wurin zama?” Jamila ce tayi saurin cafewa tace “To ai yanzu barar ma sana’a ce kawai dai yaron Mallam ya girmi sana’ar barar ne.” Ai kamar sun sake ingizoshi sai cewa yayi “Yaje yayi abinda yafi bara ma ya dameni ne? Na dai faɗa muku wallahi kafin nan zuwa magriba kusan inda kuka kai shi, har ni zai faɗawa magana? Duk ya gama tallata kanshi a titi wato azo aga Baqeer babu ƙafa ko? To kai ma ka ɗana kaji ya zaka yi rayuwa in ba gida.” Yana kaiwa nan ya juya cikin ƙunar rai yayi waje. Umma ce ta kalli Baqeer wanda take tunanin zata ga yana hawaye da mamaki ganinshi tayi garau, kallonta yayi sannan ya ɗan murmusa gefen leɓenshi kaɗan yasa hannu yana tura keken zuwa ɗakin shi. Jikin window yaje ya zubawa waje ido abubuwa da yawa na sake yawo a cikin ranshi, rayuwa kenan, ada ko a mafarki aka ce Babanshi zai yi mishi haka ba zai yarda ba, mutumin da ko dukanshi aka yi a islamiyya da kanshi yake zuwa yaci ma malaman mutunci, wai yau shine ke faɗar ya bar mishi gida. A hankali ya runtse idanunshi idanuwan yarinyar ne suka sake giftawa ta idanunshi, wai wacece dake neman shigowa rayuwarshi ƙarfi da yaji? Wayarshi ce tayi kara a hankali yasa hannu ya ɗauka sai yaga Salim ne, hakan yasa bai ɗauka ba, ba wai don yayi fushi ba sai dai ba zai bari Baba ya dinga cin zarafin shi ba daga taimako, ya sani abinda Baba yayi mishi tabbas ya taɓa ranshi sosai tunda yasan yadda yake ji in wani yayi mishi gori, kuma shi yanzu dake gaf da tafiya lahira baya ji zai bar Salim ya shiga wani halin saboda shi, saƙo Salim yayi mishi ‘Baqeer ya jikin? Kayi hakuri tun daga ranar nan ban sake zuwa wurinka ba.’ Kamar kada ya mayar mishi saƙon sai kuma dai ya rubuta mishi ‘Salim ina godiya har abada bazan manta da hallacinka gareni ba, haƙiƙa kai aboki na gari ne.’ Yana kaiwa nan ya tura tare da kashe wayar gaba ɗaya. Sake maida idanunshi yayi ya rufe yana son sanin wani irin kallo yarinyar nan tayi mishi, na tausayi ne ko na jin ƙai? Me take son cewa wanda idanunta suka nuna mishi? Kanshi kawai ya kwantar yana sake yawo da abun a ranshi. **** Abu ce tace “Tab din jam! Fatima yanzu ya zaku yi? Ba dai da gaske barar zaku fara ba?” “In ma barar zamu fara ina dai ba Kamalu bane ɗan jagora?” Umma ta faɗa tana komawa ciki ranta a matukar ɓace, Jamila ce ta sheke da dariya tace “Abu kema dai da neman magana kike.” Wani mugun kallo Abu ta watsa mata ta koma ciki, Jamila ta taɓe baki ta koma nata ɗakin ita ma, haɗin da Abu ta bata rannan ta ɗauko tabbas wannan haɗin ba abin arziki aka bata ba dan gashi sai cusawa take yi bata ga wani canji daga Mallam ba iya kace ma kwanciyar da ƙyar take samu suke gamawa. Ƙwafa tayi tace “Muguwa wato ni zaki cuta ko? To nima zaki ga wulakanci, ai ina da mutane a Sokoto, mu saka ƙafar  wando ni dake. Umma kuwa tana shiga ɗaki ta ɗauki waya ta kira Maryam da Hadiza ta sanar dasu suzo gida akwai gagarumar matsala. ***** Da ƙarfi ta daki steering wheel na motar tana sauke wani huci tare da furzar da iskar dake bakinta, ji take yu zuciyarta na wani irin azalzala, da ƙyar ta kai kanta gida tana shiga ta maida ƙofar motar cikin ƙarfi ta nufi ciki da sauri, Mummy na kitchen ana ta shiryawa Daddy abinci don yau akwai baƙin daya gayyata zasu zo. Zeey na shiga ta ƙarasa wurinta da gudu ta rungumeta. Bayanta ta shiga shafawa tana cewa “Ya isa haka nan, ni kam meke damunki ne gaba ɗaya kin canza? Kin san maganarki nawa kuwa daga jiya zuwa yau?” Zeey ta ɗago ga mamakin Mummy hawaye ta gani a fuskarta, hankalinta ne yayi mugun tashi ta kamata suka yi ɗaki a bakin gado ta zaunar da ita ta kwantar da kanta saman cinyarta tana shafa saman kanta tana cewa “Zainab menene? Menene yake damar mini ke haka?” Kallon Mummy tayi ta share hawayenta tace “Mummy nima ban san meke damuna ba, takaici ne kawai yake damuna na rasa yadda zanyi nayi magana.” “Kamar ya kenan?” Yawun bakinta ta haɗiya tace “Mummy ashe iyaye ba zasu iya yarda da ƙaddara ba in Allah ya jarabci ɗan su? Ashe iyaye zasu iya manta soyayyar da suke yiwa ɗa saboda ya samu wani giɓi a rayuwar shi? Mummy ta yaya hakan zata kasance?” Murmushi ta ɗan yi kaɗan tace “Ba lallai sun manta da soyayyar bane watakila dai abinda ya samu ɗan nasu ne ke damunsu sosai wanda yasa suke huce takaici a baibai.” Kai ta girgiza tace “A’a wannan ba haka bane.” Ta sake shafar kanta tace “Kin san Allah yayi mu daban-daban dole wasu halayensu zai banbanta, amma ke menene naki na damuwa? Ko wanda aka yiwa hakan kin sanshi ne?” Kallon Mummy tayi da sauri, Mummyn tace “Namiji ne?” A zabure Zeey ta miƙe tace “A’a mace ce sannan ba wai saninta nayi ba Mummy a hanya na gani shine abun ya dameni.” Kai ta jinjina cike da gamsuwa don tasan Zeey da tausayi, shi yasa abin bai wani bata mamaki ba. ****** Maryam da Hadiza sun sha kuka jin abinda ke faruwa, jiki a sanyaye Maryam tace “Ni matsalata uban miji, da zai bari da sai na kaishi BQ na gidana ya zauna, amma kun san halinshi dai yana gani na tafi dashi gidan sai hakan ya zama abun magana har ma ya nemi haɗa fitina a tsakanina da Baban Aareef.” Umma ta girgiza kai tace “Kema kin san ba bari zai yi ba don haka kar ma ki fara.” Hadiza tace “wurin Dada ne kawai ya rage mana amma ta tsufa Umma ita kanta tana buƙatar mai kula da ita.” Maryam tace “Ya zamu yi? Haka nan zamu kaishi sai mu nemi mai aiki ko a layin ne ta dinga zuwa tana gyara gidan da safe.” Shiru suka yi don tabbas sunsan basu da wata mafita data wuce wannan. Cikin takaici Maryam tace “Gwara ma ya bar gidan don zamanshi anan ba abinda zai jawo mishi sai depression, ace gidan iyayenka sam baka da kwanciyar hankali?” Hadiza ta girgiza kai tace “Wallahi abin nan na cimin rai dole mu tashi mu nemi kuɗi mu taimakawa Ya Baqeer wahalar da yayi damu shekara da shekaru muma mu nuna mishi yana da ƴan uwa masu ƙaunarshi.” Umma ta share kwalla tabbas itama tana ganin gwara ya bar gidan don ko kalmar bara dasu Abu ke ambata inta tuna ranta ɓaci yake yi. Haka su Maryam suka kwashe kayanshi aka saka a motarta, nan suka jawo kekenshi, wani babban almajiri ya taimaka aka sakashi a mota ko sallama basu yiwa su Abu ba suka yi gaba. Abu na ciki ta fito da sauri jin ƴar hayaniya kaɗan, Jamila ma ta fito da sauri suka kalli Umma dake tattare kaya a tsakar gida suka kalli juna, Abu tace “Na ɗauka ma baƙi aka yi?” Umma ko tankasu bata yi ba ta cigaba da aikinta, tunanin saida injin taliyarta ne ya faɗo mata akan ta sayar ta aikawa Dada da kuɗin su fara amfani dashi kafin ta samu abun yi. Baqeer kuwa har suka isa gidan baice komai ba don shi kanshi bai son zama a gidan su kuma yanzu ya tattara rayuwar ya ajiyeta, me zai yi a cikin duniyar nan? Baba ya juya mishi baya, zanenshi ya tafi, Asiya daya gina rayuwa da ita ta juya mishi baya, Bello amininshi, sannan Salim dake rage mishi radadi an rabasu to me yayi saura? 😪 Wannan lamari *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* "DA* *AYUSHER MUHD* *PAID BOOK* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN* *KIN TABBATA KIN CIKA MACE? BABBAR MACE DAKE JI DA KANTA? KINA CIKIN MATAN DA SUKA SAN KANSU? WANDA SUKA SAN MUTUNCI DA DARAJAR KANSU? KO KUWA KEMA KINA CIKI SAHUN SU O’O?* *INA KUKE MANYAN MATA? WAƊANDA SUKA SHIRYA DAN GYARA JIKINSU? AURANSU? DA KUMA FARINCIKINSU?” *KUYI MAZA KU GARZAYA GUN FITACIYGA KUMA INGANTACIYAR MAI MAGANIN MATA DA MAZA DAN AMSAR NAKU KU GYARA DA KANKU WATO MEERAH HERBS WACCE TAI FICE GUN KAWO MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA BA TARE DA ALGUS BA.* Mun gwada mun gani 💯 Mun gani mun shaida 💯 Anyi mun gani 💯 MAGANIN SANYI MAGANIN NONO MAGANIN HIPS MAGANIN SLIMMING MAGANIN NANKARWA GYARAN AMARE GYARAN MAIJEGO MALLAKAR MIJI KO MATA SUBULU DA SCRUB MAYUKA NA GYARAN JIKI TURAREN WUTA MATSI MAGANIN NI'IMA MAGANIN TSUMI INFECTION FLUSHER DA DAI SAURANSU…..Uwar gida, Amarya, Budurwa, Saurayi, Ango, Mai gida? Duk mai kuke jira? Kuyi maza ku garzaya Meerah herbs maganin dake ingantace 💯 08142800199 07068558096 {20} Dada a garin Mariri take wanda ɗan gefe ne kaɗan da cikin garin Kano, tana zaune a waje tana tsince ragowar shinkafar da take dashi zata ɗan dafa, mace ce mai yawan kyauta wacce duk sanda kaje gidanta zaka taddata bata rabuwa da yan matan dake shigowa suna tayata aiki tana basu dan wani abin, hakan yasa kayan abincinta basa daɗewa, sai dai bata kuma rasa kayan abinci, yayyen Umma maza suna ƙoƙarin haɗa mata kayan abinci bakin gwargwado yadda zai isheta, tunda ta fahimci matan su ba so suke su zauna da ita ba shi yasa tace su barta a gidanta, to da yake suma duk maza ne Umma ce kawai mace sai suka ɗauka kayan abincin kawai da suke bata ya isheta, gashi dama dukkansu babu wanda yayi aure a Kano. Kamar daga sama ta jiyo muryar Hadiza hakan yasa ta miƙe a hankali tana cewa “Yau kuma Dijangala ce a gidan namu?” A tsaye ta ganta da gudu Hadiza ta taho ta rungumeta, bayanta ta shiga shafawa tace “Meya faru? Ko mijin naki ne har yanzu abun bai daidaita ba?” Ta girgiza kai tana share kwalla tace “Dada ya zamu yi?” Da mamaki take kallonta tace “Name kenan?” Ta ƙarasa maganar tana leƙa waje kaɗan, a cikin mota ta hango Baqeer a zaune yana kallon ƙofar gidan, tace “Da Baqeer kuke tafe?” Kafin Hadiza ta samu damar ba ta amsa taga Maryam na buɗe keken guragu, da mamaki take kallonta sai dai haka kawai taji jikinta yayi sanyi, don Baqeer ba zai taɓa ganinta a tsaye ba tare da ya fito da sauri ya gaisheta ba, balle yadda ya kalleta kallo ne na wanda kamar baya cikin ma hayyacinshi, kallo ne na wanda damuwa da takaicin rayuwa suka ma yawa. Maryam tasa keken daf da gefen inda zai fito tare da buɗe ƙofa, bai ko tanka ba Hadiza da Maryam suka taimaka mishi ya hau kan keken, da sauri Dada tayi baya tana girgiza kai, wannan wace ƙaddara ce ta samesu haka? Kasa motsi tayi har suka ƙaraso dashi cikin gidan, Dada da sauri ta rungume Baqeer ta sa wani kukan tausayi wanda hakan ya ƙara saka Baqeer cikin wani kunci shi kenan kai daga an ganka sai kowa ya hau kuka? Wannan wace irin rayuwa yake ciki? Hannu yasa ya toshe kunnenshi kawai ya fara sakin wani irin kara wanda yasa hankalinsu duka ya tashi, da sauri Dada ta sake riƙeshi tace “Baqeer menene haka? Meya sameka wai?” Jikinshi ne kawai yake rawa yana sake toshe kunnuwanshi, ganin haka yasa tace akai shi ɗaki, suna hawaye haka Maryam ta tura keken zuwa ɗakin suka fito cike da tausayi, a nan tsakar gida suka zauna a tabarma suka sanar da Dada duk abinda ke faruwa, hankalinta yayi mugun tashi sai dai takaicin Badaru yafi komai damunta, sam dama kowa yasan rashin mutunci da wulakancinshi amma bata taɓa tunanin zai yiwa Baqeer haka ba. Tace su barshi anan ita batada matsalar mai gyara mata gida don yaran layin har rububin zuwa gyara mata gida suke yi. Maryam ta buɗe jakarta ta ciro dubu biyun da mai gidanta ya bata tayi cefane ta miƙawa Dada tace “gashi ku sayi wasu abubuwan kafin muga yadda hali zai yi.” Nan ta amsa suka fito bayan sun mata sallama don tace kada su leƙa ɗakin Baqeer don da alama hankalinshi tashi yake yi in yaga an damu da halin da yake ciki. ***** Maryam a gidan Hadiza ta ajiyeta sannan ta wuce ta makarantarsu Aareef ta ɗaukeshu, ta san tayi lattin zuwa ɗaukarshi shi yasa take ta sauri, tana isa makarantar aka sanar da ita ai mahaifinshi ya ɗaukeshi, ajiyar zuciya tayi sannan ta fito daga ciki ta shiga mota ta koma gida fuskarta sam babu walwala don tasan tabbas yau akwai ɓacin rai, tana shiga ta hango surukinta a zaune a harabar gidan yana karanta jarida, parking tayi sannan ta ƙaraso ta gaisheshi da gida tana cewa “Baffa shan iska kake yi ne?” Kallonta yayi yace “Kin dawo?” Ta miƙe tana cewa “Abban Areef fa? Naga banga motarshi ba.” “To ke da mijinki ni ina zan san inda yake?” Yayi maganar tare da cigaba da karatunshi, miƙewa tayi ta koma ciki, a kitchen ta tsaya ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin yadda zata yi girki ba nama tunda dai kuɗin ta ɗauka ta bawa Dada, da sauri ta fara dafa shinkafa da wake, ta yanka kayan miyan da take dashi ta ɗauko kifin gwangwani na mackerels tasa tana yi tana addu’ar Allah yasa kada yayi maganar nama. Daga waje ta jiyo ƙarar buɗe gate ta gyara da sauri tare da ɗan jingina da kofar kitchen tana murmushi, Areef ne ya shigo da gudu ya rungumeta yace “Ummy yau ina kika je baki zo da wuri kin ɗaukeni ba?” Ta shafi kanshi tace “Ka manta Uncle ba lafiya? Naje na dubashi ne, a  ina kuka tsaya naga baku dawo da wuri ba?” Kafin yayi magana mahaifinshi ya shigo tana murmushi tace “Gwaskana sannu da dawowa.” Babu alamun zai tanka ta a fuskarshi kawai ɗaki ya wuce, bin bayanshi tayi tana tsokanarshi “Yau ka tashi da wuri nayi mamaki da akace ka ɗauki Areef daga school.” “Don me na saya miki mota?” Kalmar da taji ya faɗa kenan, jikinta ne yayi sanyi tace “Kai Areef makaranta da ɗauko shi.” “To akan me baza ayi abinda aka siya domin ta ba? Yanzu da Baffa bai kirani ya sanar dani kin fita ba da bazan taɓa tunanin ɗauko yarona daga makaranta ba, tunda dai  ke wayarki bata shiga, sam ni na kasa gane wannan halin naki.” Zata yi magana taga ya shige toilet, kitchen ta dawo idanunta na neman cikowa da ƙwalla, babu shakka tasan tayi laifi da bata sanar dashi ba amma ya zata yi? Yanayin data shiga ne ya hanata ga wayarta ba charge. ****** Tunda su Daddy suka shigo da abokansa tana ɗaki a kwance, tanaji su Nabeela nata zaryar kai kayan abinci da tarar baki, kamar daga sama taji muryar Kabir yana kwalla mata ƙira daga bakin ƙofar ɗakin, taba daga kwance tace "Menene?" "Dalla malama ki taso Dady yace kizo ku gaisa da bakin." Baki ta turo sannan ta zura abaya a saman vest da short ɗin dake jikinta, Mumy ce ta ganta ta saki murmushi tace "Saki ranki mana auta." Kabir ne ya cukume fuska yace "Karma ta saki ran ni ba sai na farfasawa mutum baki ba." "Bro please chill kai meyasa kake abu kamar gangster?" Ai kamar ta taboshi ya fusata yace "What? Wallahi yau sai na karya yarinyar nan." Kai ta girgiza irin na takaicin halayensa ɗin nan, wannan abu ya tunzurashi sosai sai dai ba yanda zaiyi ya wuce ciki rai a ɓace. Zeey shiga tai ta tsuguna ta gaishesu, bata wani kallesu ba dan ba kasafai take san kallan mutanen da bata sani ba. Kamar daga sama taji wani yace "Ai wannan haɗin yayi daidai kaga ita dama bata saba da nan ba shima haka sai su saba tare." Dady yai dariya yace "Sosai! Na tabbatar hallayarsu zata zo ɗaya in har ya dawo." Wani ne yace "Wani satin ne ai insha Allahu." Itadai kanta na ƙasa ta kuma tabbatar abinda take zargi shi suke yi, Dady ne ya sake cewa "Wai Zainab baki ganeshi ba? Mahaifin Junaid ne fa." Taɗan saki fuska kaɗan tana sake gaisheshi ya amsa yana cewa "Kuna waya kuwa?" Kai ta girgiza tace "Mun kwana biyu wlh tunda na zama busy shima haka muka daina." "Masha Allah." Mikewa tai dan zaman ya isheta, kalaman mahaifin Baqeer duk sun hanata sukuni, burinta kawai taji yanda ake ciki dashi, ba yanda zatai ta fita yanzu dole sai dai gobe, haka ko falo bata fito ba takaicin halin data shiga duk ya isheta, wai akan me ta damu da Baqeer? Kamar ta manta wani Baqeer ɗin ne? Wanda ko hanya ta taho ya taho ta gwammace ta koma? Duvets ɗin data luluɓa dashi taja ta rufe kanta tana ɗan bubuga ƙafa cikin takaici. ******* Baba tun daga waje yana packing Bashir ya taho da sauri ya sanar dashi Baqeer baya gidan, kai tsaye ɗakin su Baqeer ɗin ya nufa ya buɗe ƙofar ya shiga, ganin baya nan yasa ya kara shiga ciki yana bin ɗakin da kallo, babu komai na Baqeer agun sai kayan zanenshi, wanda hakan ya sake tunzuroshi ya jijiga kai tare da yin ƙwafa, ya fito ya nufi ciki, mai makon ya shiga ɗakin Fatima sai ya nufi ɗakin Abu duk da kuwa kwanan na Fatima ne, tana jinshi sanda ya shiga ta kauda kai dan ita yanzu ba wannan bane a gabanta, tunanin yanda zata samo kuɗi ta aikawa Baqeer takeyi, dan yana bukatar komawa asibiti, ta sani Baqeer nada kuɗi sai dai kaf kuɗin shi a hannun mahaifinshi suke, wanda yake ajiyewar kuma duk ya musu hidima dashi ita da kanenshi, idanunta ne suka sauka akan injin taliyar nan ba ɓata lokaci ta ƙira wata kawarta mai saida kayayyaki ta sanar da ita zata saida injin taliyarta amma tana san kuɗi hannu, dubu biyar tace zata siya haka Umma tace to tunda tasan ba yanda zatai. Jamila kam an shaka an shaka lalai Abu banu munafuka irinta, maganin data bata ta ɗauko rai a ɓace ta sa a bin hanzu zargi ma take kila ma asiri ta bata na rabata da Mallan ita kuma ta dinga cusawa. ***** A bangaren Baqeer kuwa, tunda ya shiga ɗaki yake jin komai na duniya ya sake fita a kanshi, Dada ta shigo tai ta magana bai iya ko furta kalma ɗaya ba, daga baya ma ta fara tunanin kamar baima san me take cewa bane, haka ta ajiye abinci ta fito, tagumi kawai tai tana mamakin yanda rayuwa ta juyawa Baqeer baya, yaran da ganinshi kaɗai ke sata farin ciki yau shine haka? Tun yana saurayi ya mata alkawari shi zai kaita Hajj ashe haka Allah ya shiryawa rayuwarsa? Tana gani ya turo keken ya nufi bandakinsu dake waje, yanzu kam bai nemi taimakon kuwa ba haka ya dage ya matsa jikin toilet seat yai fitsari yai tsarki sannan yai alwala ya sake tura keken ya koma ɗakin, baisan kallanta dan ya tabbatar zuciyarta a karye take saboda shi, sallah yai daga zaune bayan ya gama ya fara rokar Allah yai gaggawar datse rayuwarshi ko ya samu sassaucin raɗaɗɗin da yake damunsa, bai ko kalli abincin ba balle yaci sai ruwa kawai dayasha. Yana zaune yana juyo Dada da yara a waje suna ƴar hira wanda ya tabbatar shigowa sukai, yau wayar ma airplane ya sakata kawai ya kunna karatun Qur'ani. ***** Wajen azahar aka aikowa Fatima da kuɗi ita kuma ta bada injin taliyar a boye dan kar asan meke faruwa. Sunyi waya da Dada ta sanar da ita halin da Baqeer yake ciki, Umma abin duniya ya sake taruwa ya mata yawa tana juyo Abu na shewa wai yau da gaza zatai girki, Jamila ce ta fito tana mata kallan sama da ƙasa tace "To kiyi da agwagwa ma mana meya damemu." Abu ta dan wurga mata wani kallo tace "Ke kawata kar muyi haka dake ai ke cinya ma zakici." Takaici ya kama Jamila tace "Hala a ɗakin da kuka shige ciki ranar kwanan Fatima baku tuna da hakkin wata kuke ci ba?" "Ke bansan iskanci har yaushe kika fara maganar hakki? Kedai na kula da bala'i yau kika tashi ni zuciyata tas take yau shiyasa bana san husuma da kowa." Tsaki Jamila tai ta wuce ciki ranta a matukar ɓace, Abu ta taɓe baki tace "Wannan kuma damuwarki ne." Fatima kai kawai ta girgiza dan ita duk wannan abun ba shine a gabanta ba, addu'a kawai take Allah ya kawo wanda zata aikawa da kudin nan. ******** Zeey ce tsaye jikin shagon da Nabeela ke siyayya, takaici tsayuwar duk ya isheta ta kalleta tace "Kinga na kula baki shirya gama siyayyar nan ba, in kin gama ki kira driver ya maida ke gida zan ɗan je wani guri na dawo." Mamaki ne fal ya rufe Nabeela tace "Ina zaki?" Card ɗinta na atm ta mika mata tace "Gashi sai na dawo." Bata jira amsarta ba ta juya da sauri ta shiga mota tai gaba, gidansu Baqeer tai parking shiru tai a cikin motar tana tunanin inta shiga tace me ya kawota? Dabara ce ta faɗo mata akan zataje tace ai number jiya batai saving ba ashe, har zata fito sai kuma ta sake komawa ta zauna tana maida ajiyar zuciya kafin ta sake daurewa ta fito, da sauri ta shiga dan bataso Baqeer dake soron gidan ya hangota. Abu na ta fige kaza sanda ta shigo ko kallo bata isheta ba balle tai mata magana. "Nikam ke wacece wai? Dan jiya ma naga fitarki daga gidan nan." Zeey kamar batasan da ita takewa magana ba tai sallama ƙofar ɗakin Umma, wata hamdallah Umma tai ganin Zainab, bayan sun gaisa ta amshi number Maryam ne Umma ta mika mata kudin tare da rokon taba Salim ya taimaka yakai Baqeer asibiti. Da mamaki tace "Baya gidan ne?" Jin Umma na cewa dama ta rasa wanda zaije inda Baqeer yake. "Yana gidan Dada a Mariri." Cike da mamaki take kallan Umma sai dai bazata iya tambayarta komai ba, nan Umma ta bata number Salim kamar tace Umma tabar 5000 ɗin zata bada amma tasan halinta tabbas ta faɗa yanzu za'a juyo faɗan ta, a cikin mota ta zauna tai shiru tana kallan kuɗin ko dai ta kara musu ne ba tare da sun sani ba? Amma in Umma taji kuma tace ba ita bace ba fa? Shafar fuskarta tai kafin ta ƙira Salim a waya ta sanar dashi sako ne Umma ta bada zata bashi. Nan yace gashinan zuwa, taɗan gangara cikin layin tai parking sannan ya fito. Kamalu dake ta sauri a babur ɗinsa zasuje kallan kwallio ɗakin wani abokinsu, kamar a mafarki yaga Roshni ɗinsa ta fito ta tsaya kusa da Salim, baiyi auni ba yaji yabar kan titi saura kadan ya kifo daga kan mashin ɗin, da sauri ya tsaya yana waiwayensu, ganin murmushi yai a fuskar Roshni nan fa kishi ya turnuko shi lallai Salim dama ya tsaneshi ya aka yi ma yasan Roshni ɗin shi? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR* *PAID BOOK* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA* {21} Cike da sauri Kamalu ya fara ƙoƙarin tsallaka titi ganin Salim na neman shiga motar, ganin da gaske babur ɗin babu dama yayi kwana dashi yasa ya jingineshi a titi ya tsallaka da gudu yana neman zuwa inda suke. Zeey ce ta kalli Salim bayan ta mika mishi 10k wanda ta ƙara 5k akai tare da fatan kada Allah yasa Umma ta gane, ta kalleshi tace "Gidan Maryam ɗin kusa ne?" Ya sauke wayar da suka gama da ita akan kai Baqeer asibiti, sannan yace "Eh ba nisa sosai zan hau mashin naje na amshi motar na kai shi sai na maida mata motar gida." Kai ta jinjina kafin tace "Muje nayi dropping ɗinka tunda in ka tafi da motorcycle ɗin ma dole ka ajiye." Daɗi ne ya kamashi don dama ba wani man kirki gareshi a ciki ba hakan yasa ya shiga gaban mota ita ma ta shiga, ta kunna mota suka fara tafiya. Kamalu sai haki yake yi wurin gudu sai dai kafin yazo yana gani suka yi gaba, iska ya nausa cikin matuƙar ƙunar rai yace "Wallahi Salim sai na fasa maka baki sai kasan motar Roshni ɗi ta ka shiga shegen yaro da shishigin tsiya." Juyawa yayi yana tafe yana zage-zage da masifa, turus yayi a gefen titi ya fara waige-waige yana neman inda ya ajiye babur ɗin shi, mamaki ne duk ya gama rufeshi ya rikice a wurin yana waige-waige sai dai babu babur babu alamarshi, hankali a tashe ya nufi wani mai saida yalo yace "Yayana don Allah kaga babur ɗina?" Yaron ya kalleshi yace "Yaushe na zama yayanka? Sannan wani babur kake magana?" Kamalu zufa ce ta fara keto mishi yace "A daidai nan na ajiye don Allah yi tunani kaga wani ya ɗauke?" "Wa zai ɗauke maka babur in har key ɗin na hannunka?" Nan ya laluba aljihunshi ashe ko key bai cire ba? Yaron ya kalleshi yace "To Allah ya kiyaye." Gaba ɗaya Kamalu kanshi ne ya ɗauki zafi ya fara bin hanya yana neman babur sai dai babu shi babu alamarshi. Haka nan ya haƙura ya nufi gida kamar wanda aka yiwa dukan tsiya. ****** Maryam ce ta kalli mai gidan nata dake zaune a ɗaki tana yi mishi tausa cike da sanyin murya tace "D don Allah kaji? Ba dadewa zai yi ba yana kai shi zai dawo." Kallonta yayi takaicin yadda take fifita ƴan uwanta sama dashi na damunshi don jiya ko bata faɗa ba yasan kuɗin cefanen daya bata su taje ta kashewa, sai dai ya zai yi? Yana sonta iya so shi yasa yake haƙuri da waɗannan abubuwan nata. Zare ƙafar shi yayi yace "To shi kenan ni bari na fita." Sumbatarshi tayi a saman leɓe tare da tsotsan kasan leɓen nashi kaɗan tace "Love you." Murmushi ya sakar mata sannan ya fito, ta rakashi har mota sannan ta dawo ɗaki, kayan da bai saka ba wanda ta ciro mishi ta mayar cikin drawer. Waya suka sake yi da Salim akan yana waje zai turo mai gadi ya amsar mishi key ɗin motar. Tace to tare da fitowa falo dan ɗauka me zata gani? Babu key ɗin motar a wurin, cike da mamaki ta hau dubawa sai dai babu shi babu alamarshi, ganin haka yasa ta kira mai gidan nata din tana tunanin faɗan da suka yi jiya watakila yasa ya manta ya ajiye  a wani wurin. Bayan ya ɗauka take sanar dashi bata ga key ɗin motar ba, buɗar bakinshi sai ce mata yayi Baffanshi ya amsa zai je wani wuri daga nan zai taho da Areef. Gaba ɗaya mamaki ne ya rufeta tace "D me kake cewa? Na ɗauka mun yi magana da kai akan zan bawa Salim ya kai Ya Baqeer asibiti?" "Ohh haka ne fa ki cewa Salim ya nemi adaidaita sai ki bashi 1k duk da nasan ba zai wuce 500 ba kinga ai babu laifi, kin dai san ba zai yiwu Baffa ya hau adaidaita ba bayan ga mota a gida, sannan don motarshi na wurin gyara bazan ce mishi kada ya fita da motar dana sayawa jikanshi ba." Kasa magana tayi saboda tsananin mamakin kalamanshi, duk da ba yau suka saba guma mata takaici ba amma na yau yayi mata zafi fiye da ƙima, yanzu duk soyayyar da suka sha daren jiya har ya manta ya koma gidan jiya? Kasa magana tayi sam bata ma san shi ya kashe wayarshi ba sai ringing taji a kunnenta, kallon wayar tayi Salim ne ta ɗauka cikin dakushashiyar murya taji yace "Nayi mishi magana zai zo ya amsa nima yanzu na iso, ƙawarki ce ma ta ajiyeni." Hawaye taji sun gangaro mata, ta sharesu tana cewa "Wacece?" "Zainab dai Zeeyn Baqeer, nayi mamakin ganinta wallahi data cemin Zeey ce nayi ta mamaki har muka iso mamaki bai bar kaina ba." Murmushin yaƙe tayi tace "Don Allah taimaka ka bata." Shi kanshi yadda ta amsa yasan da wani abun sai dai bai tambaya ba ya miƙawa Zainab, ta kara wayar tana cewa "Umma ce ta bani saƙo wurin Salim ashe ma wurinki zaizo, ban yi plan da shigowa gidanki ba shi yasa bazan leƙo ba." Maimakon taji ta bata amsar maganar data yi sai ji tayi tace "Zeey don Allah ki taimaka ki bada motarki akai Baqeer asibiti na rasa ya zan yi....." ta ƙarasa maganar cikin rawar murya "Okay, amma kin tabbatar babu wani abu?" Ta sauke ajiyar zuciya tace "Nagode sosai babu komai wannan ma da kika yi mana kin biya mana, Allah ya saka miki da alkhairi." Kashe wayar Zeey tayi don daga yanayin maganar Maryam tasan babu lafiya gashi bata so taga mutum cikin damuwar da ba zata iya tallafa mishi ba. Da murmushi ta kalli Salim ta miƙa mishi key ɗin motar tace "Kaje da tawa ashe ta manta akwai abinda zata yi kuma uzurin na dole ne." Ya amsa tare da godiya, kallonta yayi yace "In ajiyeki kafin na wuce?" Tunowa data yi in har tsautsayi yasa aka ganta akwai tashin hankali hakan yasa tace "No kawai kaje inka gama ka kirani na fito nazo inda kake na amsa." Da mamakin kalamanta yake kallonta to taya zata koma gida? Ƴar gayu kamar ta? Sai dai yasan a yanayin yanda Zeey take magana da isa bai isa ya sake tambayarta ba, bata ko tanka shi ba ta fito yana kallonta ta tari adaidaita kai daga gani kasan bata san ya ake tarar su bama, ta sanar dashi inda zataje yace 700 ga mamakinshi yaga ta shiga bayan shi jan magana yayi ya tsuga mata kuɗi, zaune take a ciki tana kallon yadda ake gwajab-gwajab da ita a hanya gaba ɗaya mamakin kanta ya isheta wai anya itace dai Zainab? Zainab Sulaiman Karaye? Anya kuwa a cikin hankalinta take abubuwa? Tun ɗazu take kallon kiran da Nabeela keyi mata amma taƙi ɗauka, kanta kawai ta shafa tana mamakin yadda ta manta abubuwan da suka faru a baya tsakaninta dashi sannan har ta ke manta kanta wurin ganin ta taimaka mishi. Gefen titi ta kalla daidai nan mai adaidaita ya sake jijiga tace "Ai ba don shi nake yi ba don su Umma nake yi."  Ta ƙarasa maganar tana sauke ajiyar zuciya. A gefen gidansu ta sauka ta bashi 1k tana neman wucewa, daga nesa ta hango yarinyar nan tsaye da saurayin rannan da alama kyauta ma ya kawo mata don ga abu nan a hannunta sai smiling take yi, shi kuma yana jingine a jikin mota, wani kallo tayi musu na takaici kawai ta shiga gida, shi kam mai adaidaita daɗi ne ya kamashi don ya kula bama tasan nawa ta bashi ba saboda hankalinta baya wurin, cikin sauri yaja adaidaitarshi yayi gaba don ma kada ta dawo tace ya biyata, mamaki ne ya rufe mai gadi daya buɗe mata ƙofa ta shiga, kai tsaye ɗakinta tayi ta faɗa kan gado tayi ruf da ciki tana ƙullawa da kwancewa. ***** Bello dake tsaye kusa da Asiya wata irin gigitaciyar soyayya ce take taso mishi, ji yake yi kamar yafi kowa dace a duniyar nan, ya mata alama data shiga cikin mota ta buɗe gift din, shiga tayi shima ya shiga ya zauna ta buɗe jakar sannan ta dauko box din dake ciki, kwalin jaka ne set ɗinshi da takalmi, wani sanyayyen murmushi ta sakar mishi tace "Bae ka bar sakaltani da yawa fa, kullum ne sai an kawo mun gift?" Hannunta ya riko yace "My love kin dai san kin fi ƙarfin komai a wurina, nayi miki alkawari zan jiyar dake soyayyar da ko sunan Baqeer baza ki tuna ba nan gaba." Murmushi ta sakar mishi tace "Yanzun ma kana yi" "Tukunna ki jira na samu fita ƙaro karatun don ƙafata ƙafar ki gwara muyi aure na tafi dake." Wani sanyi ne ya ratsata tabbas Bello zai cika mata burinta, har yanzu ba wai tana sonshi bane amma future ɗinta ta tabbatar a wadace take in har ta aureshi. ******* A bangaren Baqeer kuwa Dada ta sakashi ya fito falo yana zaune yana kallonta tana ta ƙoƙarin bashi labarin tasowar Umma duk don taga ya saki jikinshi sai dai kawai kallon gefe yake yi babu alamar hankalinshi na inda take, jiki a sanyaye take kallonshi ita kam Baqeer ɗin daa take son gani, sallamar Salim suka jiyo, ta amsa ba tare da tasan wanene ba, sai daya shigo ta ganshi, cike da fara'a ta amsa tace "Salim yau kai ne a gidan?" Ya shiga yana dariya yace "Tunda kin gujeni kuma me zaki ce mun?" "To kai in banda abinka in na aureka ai sai dai a binne ni da kai don tabbas baka isa ka rabu dani ba sannan ko aure baka isa kayi ba ko na mutu." Dariya sosai yasa yace "Wai abun haka ne dama? To ai ana auren ɓoye." "Ahaf kai na mutu'a ma kagani." Sun dade suna tsokanar juna sai dai Baqeer ko kallon inda suke bai yi ba, jiki a sanyaye Salim ya mika mishi hannu yace "Baqeer don Allah kayi hakuri kaji?" Bai kalleshi ba har yanzu idanunshi na gefe, yana murmushi yasa hannu a aljihu ya ciro kudi yace "Umma ce ta bada zamu je muga likita yanzu." Da kallo yabi kuɗin nan da nan yaji kanshi na wani irin sarawa, ina Umma ta samo kuɗi haka? Kanshi kawai ya shiga girgizawa yana neman tunano inda ta samu wannan kuɗin, ya tabbatar injin taliyarta ta sayar kila ma har da kayayakin ta. Hannu yasa kawai ya hau dukan ƙafarshi da hannun hagu yana wani irin numfashi, A zabure Salim ya taso yana ƙoƙarin janyeshi sai dai Baqeer cikin sauri ya tura kekenshi ya fara tafiya, binshi Salim ya nemi yi Dada ta girgiza mishi kai, har Baqeer yayi ciki ya banko ƙofar da karfi kai kace ɓallata yake son yi. Suna daga waje suna jiyo yadda yake ihu da alama kafar yake ci gaba da duka, dukkansu basu san sanda hawaye ya gangaro musu ba, Salim yana hawaye yace "Dada ya zamu yi da Baqeer?" Ido kawai ta runtse tace "Addu'a babu yanda zamu yi dashi sannan wannan halin da yake ciki shine zai maidashi jajirtacce, dole yasan rayuwarshi ta daa da kuma ta yanzu ba ɗaya bace, sannan dole ya miƙe ya nemarwa kanshi mafita ni da kai da ita Fatiman duk babu abinda zamu iya yi mishi in har shi bai shirya canzawa ba." Ya daɗe a cikin wannan yanayin kafin ya samu nustuwa, me za ayi da rayuwarshi? Ya tabbatar iyayenshi da zai faɗi ya mutu yanzu hankalinsu sai yafi kwanciya. Jin shiru yasa Dada ta buɗe ƙofar tace "Kazo kuje asibiti lokaci na ƙurewa, magana ce bai son yi sai dai yaja ya turje, ta kalleshi tace "Kasan dai ni kakar kace ko? To in har na isa da kai ka wuce ku tafi." Kallonta yayi yana son sanar da ita kuɗin injin taliyar Umma ne fa sai dai ba zai iya ba ji yake yi baya son ko furta kalma ɗaya har ajalinshi yazo. Haka Salim ya jashi suka shiga mota, wani kamshi ne yaji wanda yasa yaji zuciyarshi ta samu wata nutsuwa da shi kanshi bai san daga ina ta fito ba, idanunshi ya maida ya kulle yana ɗan maida numfashi sama-sama, har suka isa asibitin bai yi magana ba, suka shiga ciki Doctor ya musu magana akan tun last week ya kamata suzo amma basu zo ba, nan Salim ya bada hakuri aka kwance naɗin karayar da aka yi mishi ya sake duba Baqeer sannan ya rubuta musu magunguna, dubu takwas Salim ya siyo magungunan, suka koma mota, har yanzu kamshin motar ɗazu yana nan, ya sake kwantar da kai jiki a sanyaye ya cewa Salim "Salim don Allah ka ji da kasuwancinka kada ka damu dani wannan yawon da kake zai iya dakushe maka kasuwarka." "Baqeer mu dai fatan mu ka cire wannan damuwar dake ranka kana dai ji Dr yana cewa depression ne yake damunka don Allah ka....." Kanshi ya kawar gefe wanda hakan yasa Salim yin shiru, sun dade babu wanda yayi magana sai can yace "Motar waye wannan?" Kallonshi Salim yayi, anya yace mishi ta Zainab ce? Bayan kaf unguwarsu shekarun baya sun san cases ɗin daya shiga tsakanin mutanen biyu? Wanda a dalilinshi su Zeey suka tashi daga unguwar? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR* *PAID BOOK* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA ƊAYA* {22} "Ta wani abokina ne da muke mutunci sosai na aro tunda kasan ba zai yiwu mu ɗauki motar haya a wannan marrar da ake ciki ba ga nisan wuri ga tsadar mai". Jinjina mishi kai kawai yayi ya juyar da fuskarshi yana kallon waje. Har suka ƙarasa gidan Dada babu wanda ya ƙara magana don tun Salim na takalarshi da zance har ya haƙura yayi shiru ganin ba kulashi zai yi ba. Da taimakon wasu almajirai da suke yawan zama a ƙofar gidan Dada Salim ya samu suka fitar da Baqeer daga cikin mota suka ɗaurashi akan keken. Godiya yayi musu sannan ya turashi suka shiga cikin gidan. Sai da yayi wa Dada bayanin duka magungunan da aka rubuto mishi ta tabbatar mishi zata kula da bashi akan lokaci sannan ya sallame su ya tafi. Yana shiga unguwarsu yayi kiran Zeey a waya yace mata ya dawo ya za'a yi ya kawo mata motar, sai cewa tayi yayi parking ɗan nesa kaɗan da gidansu zata fito ta karɓa. Hakan kuwa aka yi don bai wani daɗe da tsayawa ba sai gata ta fito, yana ganin fitowarta ya buɗe motar ya fito shima yana murmushi. Miƙa mata mukullin motar yayi yana ta godiya don sosai ta taimaka musu da basu aron motar da tayi in banda hakan da sai dai ya ɗauki drop ɗin taxi ya kuma san kuɗi ne za'a kashe ba ƴan kaɗan ba. Karɓa tayi tace mishi "haba dai ai babu komai yiwa kai ne, ni nasan irin taimakon da zaku yi mini ne a gaba, fatanmu dai Allah yasa an dace da abinda kuka je yi asibitin". "Ah Alhamdulillah don an kunce ɗaurin ma kuma likitan yace gyaran yayi kyau sosai sai fatan Allah ya ƙara mishi lafiya". "Masha Allah, ni bari na wuce sai mun ƙara haɗuwa kenan". Yace mata "to Zainab nagode ƙwarai Allah ya bar zumunci". "Ameen Ya Rabbi" kawai tace ta shige motarta taja ta ƙarasa da ita gidansu, sai da tayi horn maigadi ya taso ya buɗe mata gate har ta shige ciki sannan Salim ya juya zai bar wurin. Yana juyowa suka kusa yin karo da Kamalu da tun ɗazu yake dakon dawowar Salim ɗin don haka akan idonshi Salim yazo ya wuce da motar Roshni ɗin tashi, har tsayuwarshi da duk maganganun da suka yi shi da Roshni ɗin akan idonshi suka yi sai dai baya jin me suke cewa, shi satar babur ɗin da aka yi mishi ma bata dameshi ba kamar tsayuwar Roshni da wancan tsageran yaron da yake jin kanshi kamar yafi kowa saboda kawai yana abota da wancan gurgun. Ƙwafa yayi cikin ranshi yana jaddada dole ma yaci uban yaron nan Salim don yaga alamun yana so ya kawo mishi raini tunda har yake zuwa wurin Roshni masoyiyar zuciyarshi. Kallonshi Salim yayi yace "Mallam lafiya zaka tare mini hanya?". Wani irin kallo yayi mishi irin na sama da ƙasa ɗinnan kafin cikin fusata yana nuna shi da ɗan yatsa yace "zuwa nayi naja maka kunne ba naga kanka yana rawa ba ka fita daga hanyar Roshni ɗita ita ɗin ba sa'ar yinka bace idan kuma kaƙi ji wallahi kaji na rantse jikinka ne zai gaya maka". Wata irin dariya ce ma ta zowa Salim ganin yadda ya dage yana zuba masifa har kamar ya kai mishi duka, kasa riƙe dariyar yayi sai da yayi abarshi sannan ya tsagaita ya kalli Kamalun da irin kallon da yake yi mishi yace "wacece kuma hakan? Kai kaga nayi maka kama da wanda zai tsaya yana kula irin tarkacen ƴammatan da kake kulawa marasa nutsuwa da kamun kai? Da Allah Mallam kauce mini daga hanya ni na wuce don ina da abun yi ba irinka bane zauna gari banza marasa aikin yi sai dai yawo daga wannan inuwar zuwa waccan kuna jiran ƴan Allah ya baku mu samu". Ai kuwa ba ƙaramin kunna Kamalu yayi ba don haka yasa hannu ya janyo rigarshi yace "don ubanka kai har ka isa ma ka buɗe baki ka zagi Roshni bayan ta gama yi maka rana har tana ɗaukar motarta ta baka aro shine kake kiranta mara kamun kai? Kai har ka isa ma kace zaka faɗi wata maganar banza akan Roshni ɗita na ƙyaleka" don ganin nan fa da yayi wa Salim a cikin motar Roshni gashi kuma wai har ta bashi aro ya tuƙa ba ƙaramin zafi yayi mishi a rai ba don gani ma yake yi kawai shima Salim ɗin son Roshni yake yi shi yasa ma har ta ɗauki motarta ta bashi ita ta dawo a napep. Sai lokacin Salim yasan akan wacce yake magana don haka ya ƙara kwashewa da dariya, cikin dariyar yace "au wai dama Zainab ce Roshni ɗin da kake magana akai, lallai kuwa na yarda abar da kasha tayi maka karo har tana faɗa maka ƙarya tunda gashi ka hau kai ka zauna". Kaucewa yayi ya wuce ya bar Kamalu a wurin yana nanata suna ZAINAB, ashe sunan Roshni ɗin shi kenan Zainab suna mai daɗi sai kuma aka yi dace irin sunan Innarshi gareta wato Abu. Ji yayi kamar ya ƙarasa ƙofar gidan yasa ayi mishi sallama da ita tunda dai yau Allah ya taimake shi yasan sunanta sai kuma ya kalli kayan jikinshi yaji ina ai basu dace da zuwa zance wajen Roshni ba don haka ya juya ya koma gida da nufin canjo kaya sannan ya dawo wurin Zainab ɗin. ***** Tunda dai ta samu tabbaci daga Salim cewa ya kaiwa Baqeer kuɗaɗen har ma sun je asibiti an kunce ɗaurin sai taji hankalinta ya kwanta, godiya tayi ta mishi tana saka mishi albarka don tasan ba don shi ba da bata san yadda za'a yi saƙonta ya iske Baqeer ɗin ba bare da aka ƙara samun tazara mai yawa a tsakaninsu. Tashi tayi ta koma ɗakinta tana ƙarewa ɗakin kallo ko ta samu wani abu mai muhimmanci da zata ɗaga ta sayar ko ta samu taja jari don zama haka bai ganta ba ita da take da ɗa mai larura ga Hadiza da take da wani irin mugun miji da yake ƙyashin abincin da zai basu suci ma bare sauran buƙatu na rayuwa, dama Baqeer ɗin ne mai taimaka mata to shima yanzu ga yadda Allah yayi dashi. Kallon tsaf ta ƙarewa ɗakin ta rasa abu guda ɗaya mai daraja da zata ɗaga ta sayar idan dai kuma ba kujerunta zata saka a kasuwa ba, zama tayi akan doguwar kujerar tana shafata tare da tuna lokacin da Baqeer yayi mata su sababbi fil a leda haka aka shigo dasu ɗakinta aka jera, a waccan ranar taga tashin hankali don muraran su Jamila suka kasa ɓoye hassada da baƙin cikinsu don a cewarsu ma Mallam ne yayi mata aka fake da wai Baqeer ne yayi duk don a raina musu hankali, to ina ma yaga kuɗin da zai iya yin waɗannan kujerun masu daraja banda dai ana so a raina musu wayo, a cewar Abu kenan data kasa ɓoye hassadarta a wannan ranar saboda ita tafi Jamila wayo ba komai take fitowa ta nuna ba sai dai tayi ta mata ingiza mai kantu ruwa ana ganin laifinta. Zuciyarta babu daɗi saboda duk ta kalli kujerun ta tuna Bqeer ne ya saya mata ba ƙaramin daɗi take ji ba gashi yanzu halin rayuwa yasa dole zata ciresu ta sayar tayi jari ko ta samu abinda zata rufawa kanta da iyalinta asiri. Wayarta ta ɗauko ta kira makwabciyarsu da suke hulɗar arziƙi sosai da ita tace mata ko zata taimaka ta samo mata masu sayen kujerunta, ba tare da bin ba'asi ba tace ai ko itama sai ta saya don kujerunta nata babu abinda suka yi. Haka dai suka ajiye akan zata shigo ta ƙara ganinsu sai suyi ciniki. ***** Tana shigowa cikin gidan ɗakinta kawai ta wuce ta kwanta, sai ma tayi sa'a bata haɗu da kowa ba don bata so Mummy tayi mata magana akan tafiya da tayi ta bar Nabila a kantin da suka je da sai keke napep ta hau ta dawo gida don bata san wani uzurin zata bayar ba kuma duk kuwa da tasan Mummy bata cika yawan matsanta mata ba to amma fa bata so tana yawan ɓata mata rai. Tana shiga ta sakawa ƙofar ɗakinta makulli ta rufe don bata so kowa yazo ya dameta, tana jin lokacin da Nabila tazo tana buga ƙofar ɗakin amma tayi shiru ta rabu da ita kamar bata jinta, a haka har bacci ya ɗauke ta inda bata farka ba sai ana wajen ƙarfe biyu da rabi, tana tashi bathroom ta faɗa tayi alwala tazo ta tada sallah, sai data idar sannan ta tashi ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta fita. Akan dining table ta tarar dasu Mummy suna cin abinci. Mummy na ganinta tace "baby har kin tashi?" A shagwaɓe ta ƙaraso wajen tana ɗagawa Mummyn kai ba tare data buɗe baki ta amsa ba. Kujera kusa da Mummyn taja ta zauna, da kanta Mummyn tayi serving ɗinta su dai Kabir da Nabila suna kallonsu sai ma taɓe baki da Kabir yayi yace "wallahi Mummy ke kike daɗa shagwaɓa yarinyar nan shi yasa take tsula iskancinta son ranta don tasan babu abinda za'a yi mata". Harararshi Mummy tayi haɗe da cewa "to ina ruwanka? Ko kuwa dai sa ido". Gwalo Zeey tayi mishi tana dariya ƙasa-ƙasa. Ƙwafa Kabir yayi yace "wallahi idan na damƙeki sai kin gane ke ƙaramar mara kunya ce, na lahira sai yafi ki jin daɗi". "Mummy kin ganshi ko" tayi maganar kamar zata saki kuka. "Mummy kin ganshi ko" shima ya kwaikwayeta da irin muryarta. Anan suka hau cacar baki kamar wasu ƙananun yara, dama kuma sabon su ne don babu yadda za'a yi su zauna a waje ɗaya basu takali junansu sun yi faɗa ba. Sai da Mummy ta tsawatar musu sannan suka bari sai dai suna ta hararar junansu ƙasa-ƙasa ba tare da sun bari Mummyn ta gani ba. Sai da suka gama cin abincin har ma ta tashi zata bar wurin Mummy ta kira sunanta tare da bata umarnin ta koma ta zauna magana zasu yi. Zama tayi gabanta yana faɗuwa don tasan akan abinda ta aikatawa Nabila ne Mummy zata yi maganar. Ai kuwa dai tana zama Mummyn ta fara magana cikin tausasawa kamar mai gudun ɓacin ran Zeey ɗin tace "wai ni kuwa Zeey meke damun ki ne kwana biyun nan duk kin canja idan kuma an tambayeki sai kice babu komai?" Shiru Zeey tayi ba tare data amsa mata ba. Kallonta Mummyn ke yi tana jiran jin amsa daga bakinta sai dai har wucewar wasu mintuna Zeey bata ce komai ba don haka Mummy tace "baki da lafiya ne?" Girgiza kai tayi alamar a'a. "To meke damunki?" Mummyn ta ƙara tambayarta nan ma tayi shiru. "Shikenan to tunda ba zaki amsa ba amma ina kike yawan zuwa da kullum sai kin fita bayan kin san Daddynku ba cika son yawan fitarki yayi ba, kuma ina kika je yau da kika bar Nabila a inda kuka je kika tafi da motar sannan kuma kika dawo a napep kamar yadda maigadi yace sai daga baya kika fita kika amso motar kika shigo da ita? Wama kika bawa aron motar ke kika hayo napep Zeey ba kya gudun wani abu ya faru dake a hanya?" Kawai sai ta sakawa Mummy kuka abinda ya dakatar da Mummy daga jerin tambayoyin da take yi mata kenan. Tuni hankalin Mummy ya tashi ta koma lallashinta, su Kabir da Nabila dai takaici kamar ya kashe su, su dama sun sani Mummy ba zata iya yiwa Zeey faɗa ba don a wurinta komai Zeey tayi daidai ne sai tace ai yarinta ce tasa wata rana ko ance tayi ba zata yi ba. Tashi suka yi suka bar musu wurin, sai da Zeey tayi kukanta ya isheta Mummy nata aikin lallashi sannan ta iya cewa "kiyi haƙuri Mummy wallahi ni kaina na rasa meke damuna, abun haushi abun takaici kuma na kasa cire abun daga raina". Ajiyar zuciya Mummy tayi tace "ke kuwa wane irin abu ne wannan daya dameki haka kuma baza ki iya buɗe baki ki faɗa ba ko kya ji daɗi, fatana dai ba akan saurayi bane don kin san fa akwai wanda Daddynku yake son haɗaki dashi, don Allah kada kije kiyi abinda zaki janyo mana ɓacin rai daga ni har ke". Sai da gabanta ya faɗi da jin wai za'a haɗata da wani duk kuwa data tsinci zancen a parlourn Daddyn ranar da yayi baƙi amma bata wani ɗauke shi da muhimmanci ba. "Ba akan saurayi bane Mummy, ke dai ki tayani da addu'a Allah ya yaye mini damuwar dake raina" kawai ta iya cewa Mummyn ta tashi ta koma ɗakinta, binta Mummy tayi da kallo tana tunanin to me yake damun yarinyar nan ne wai? Gaba ɗaya ta canja kamar ba Zeey ɗinnan ba ƴar hayaniya don in dai tana wuri baka taɓa jin shi tsit. ***** Sai da ya nufi gidansu da zumuɗin son ya shirya ya koma wajen Roshni ɗin shi sannan ya tuna ashe fa an samu wani ɗan shegiyar ya ɗauke mishi babur ɗin shi, kamar shi kuwa ai yawa ne ya tafi zance wajen Roshni a ƙafa don haka ya fasa shiga ɗakin shi yayi shirin tafiya wajen Roshni ɗin sai ya shiga cikin gida wajen Abu yasan dai ba zai rasa na sayen wani babur ɗin ba a wajenta don a yadda take da zafin neman nan ko mota yace ta saya mishi yasan tsaf zata saya. Tana zaune a tsakar ɗakinta tana ɗura tsumi a jarkoki saboda masu zuwa saye. Zama yayi daga bakin gadonta yana cika yana batsewa. Kallonshi tayi ta mayar da kofin da take ɗibar tsumin cikin robar tsumin ta ajiye. "Kai kuma lafiyarka ka shigo sai faman kumburi kake yi? Ko kuwa dai wani abu aka yi maka a wajen ka shigo ka huce a kaina?" Sai da yaci serious irin maganar da zai yi mai matuƙar muhimmanci ce kafin yace mata "babur ɗina fa aka sace". "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta hau cewa tana tafa hannaye, "kai kuwa garin yaya aka yi haka?" Kasa faɗa mata yadda aka yi yayi sai ce mata yayi wai ya ajiye shi ya shiga shago sayen abu kafin ya fito har anyi gaba dashi. "Yanzu dai Inna ɗan wani abu zaki bani naje na sayi wani don wallahi yadda na saba da babur ɗinnan bazan iya komawa yawo a ƙafa ba". Dariya ta saki haɗe da shewa tace "to kai in banda abinka baga motar Mallam nan ba don me kaima baza ka riƙa karɓa kana tuƙawa ba". "Hmm Inna kenan, Baban ne zai yarda ya bani motarshi?" Da sauri tace "yo me zai hana bayan a yanzu gida ya dawo hannunmu, dama ai saboda wancan gurgun yasa yaƙi kowa amma yanzu da idanunshi suka buɗe ya gane ashe shayi ruwa ne ai dole ya dawo wajenmu mu ɗin dai daya watsar, kada ka samu wata damuwa duk lokacin da kake da buƙatar motar ka faɗa mini kawai ni nasan yadda zan bi dashi na karɓar maka makullin daga haka wata rana ma har sai kaga ya bar maka motar gaba ɗaya in yaso shi ya sayi wata", Suka saka shewa harda tafawa kamar wasu abokai, Kamalu dai daɗi fal ranshi don yana ganin kamar Roshni taso shi an gama ne in dai har yayi dace da samun motar nan.... *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*       *Da* *Umm Asghar* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA UKU* {23} Zeey tana jin isowar mahaifinsu ta fito daga ɗaki suna gaisawa bata jira wani abu ba tace "Daddy don Allah gobe ina son zuwa Ɗambatta." Ai kafin ta ƙarasa maganarta ya tsuke fuska tamau kai kace saƙon mutuwa aka kawo mishi, fuskar nan babu alamar wargi yace "Kina sake yi mini maganar Ɗambatta wallahi ranki in yayi dubu sai ya ɓaci." Sosai itama ta canza yanayin fuskarta tace "Daddy wai haka ake rayuwa?" "Haka ake rayuwa? Ni kike yiwa magana haka?" Yayi maganar cikin ɗaga murya da tsawa, da sauri Mummy ta ajiye abinda take yi a kitchen ta taho wurinsu tace “Senate ya isa haka nan don Allah, ke kuma wuce ɗaki.” A fusace yace “Bata isa ta tashi ba sai ta faɗa mini dalilin da yasa ba’a isa ayi mata magana ba sai ta mayar da martani, akwai sa’anta anan ne ko kuwa don mun kashe kuɗi mun kaita waje karatu shine take neman juye mana abubuwan banzan data koyo a can?” Kasa tayi da kanta ranta na sake ɓaci, daga maganar Ɗambatta sai ya hau faɗa? Menene laifinta anan saboda Allah? Mummy ce ta dafashi tace “Senate please ya isa haka kasan yarinya ce ba komai take ganewa ba.” “Yarinya ce amma ta iya zabgawa Najib rashin mutunci ko? To wallahi wannan karon in har kika kori Junaid ki shirya auren duk wanda naga dama don kuwa baza ki janyo mini magana ba.” Murmushi tayi ta kalleshi tace “Daddy in dai maganar Ɗambatta ne na daina amma please kai ma ka bar maganar Junaid, yaron nan fa sa’a nane kuma hatta ƴan matan da yayi da na sani.” “Wannan damuwarki ce ko cewa aka yi don kin san ƴan matanshi shi kenan bazaki iya aurenshi ba?” Fahimta da tayi ran Daddy ya gama ɓaci yasa ta ɗan dafa kanta kawai sai gani suka yi tayi baya ta kwanta, a rikice Mummy ta taso Daddy ma haka duk ya rikice don Zeey ce sanyin idaniyarahi dauriya kawai yake yi yana yi mata faɗa don ya lura rashin tsawatar mata na nema yasa ta kangare, ɗagota Mummy tayi tana kiran sunanta cikin ƙarfi, a hankali ta fara buɗe idanunta tana lumshesu tace “Mummy ki bawa Daddy haƙuri….”ta sake maida idanunta ta rufe, hankali a tashe ya ƙaraso suka hau ƙoƙarin maidata kan kujera, Mummy ta kwallawa Kabir da Nabeela kira. A kusan tare suka shigo falon, Kabir daga gefe yaja ya tsaya ranshi na sake ɓaci yace “Wallahi in baki tashi ba zaneki zan yi da belt ɗin jikina.” Shareshi tayi tana ji Mummy nayi mishi faɗa ai kuwa Kabir ya nufota yana ɗan ware belt ɗin shi, ido ta buɗe kaɗan ganin yadda ya nufota yasa tayi saurin miƙewa ta ɓoye a bayan Daddy wanda mamaki duk yasa sun kasa magana, hararar Kabir tayi tace “Bro wallahi ka canza rayuwa.” Ta kalli Daddy tace “Sorry Dad just joking.” Tana kaiwa nan ta ruga tayi ciki tana dariya. Takaici ne yasa su dariya wanda Kabir yace “Daddy ka gani ko? Shi yasa nace ka barni da ita na gyara mata zama. Zainab kuwa kwanciya tayi akan gado  har yanzu dariya take yi, can ta tsaya da dariyar tunowa da halin da Baqeer yake ciki da tayi. Ko ya yake yanzu? ***** Washegari…….   Umma tana kallon Baba yadda ko kallon ɓangarenta bai yi ba yake ƙoƙarin fita daga gidan, gaisuwar ma da take yi mishi bai amsa ba, cike da dauriya tace “Mallam nace nasa kujeru na a kasuwa saboda magungunan Baqeer tun jiya nake so na sanar da kai.” Cak ya tsaya sannan ya waigo ya zabga mata wani kallo yace “Ya aka yi baki haɗa dake kanki ba?” Yayi maganar tare da ƙarasawa waje, ajiyar zuciya tayi sai kuwa ji tayi Abu na guda, fitowa tayi tana taku ɗaɗai ta wani turo ɗaurin ɗankwali gaba tana tauna chewing gum, Jamila ce ta fito sa sauri tace “Abu lafiya?” Girgiza jiki ta ɗanyi tana wani yauƙi tace “Wallahi Mallam ne da wasan shiririta jiya goyani yayi a ɗaki shine yanzu nayi mishi maganar ya arawa Kamalu mota ya bani key babu ko musu.” Jamila nan da nan ta ɗaure fuska tamau tace “Bayan Bashir ne zai shiga da motar makaranta yau kuma jiya ya faɗa mishi sai ya bawa Kamalu?” Ta ɗan murmusa tace “To kinga ai bashi da laifi abinka da wanda so yake ɗawainiya dashi, mantawa yake yi da wasu abubuwan balle abu in ya shafi wanda suke zaune kara zube…..” ai kafin ta karasa magana Jamila ta cakumota rai a mugun ɓace, Abu tayi murmushi tace “To kin dai san hannunki in ya kai jikina za’a iya sallamarki.” Jamila ta hankadata baya a fusace ta koma ɗaki, Fatima dake wanke-wanke ko kallonsu bata yi ba bare susa ran zasu ji ta tanka musu. Abu ta sake yin dariya tace “To borori asha aikin gida da kyau. ***** Yau Zainab ta gama sawa ranta dole taje taga Baqeer ta kuma sa a ranta wannan shine zuwa na karshe da zata yii, shima zuwan zata yi ne don kawai taga ya jikin nashi yake bayan jiya ya dawo daga ganin likita. Da wannan tunanin ta yiwa Mummy k6arya akan zata je amso saƙo a wurin wata ƙawarta. Kamar zata hanata sai kuma ta barta don bata son damuwar nan da take gani a fuskarta. Ɗaki ta koma ta janyo riga da wando zata saka sai kuma ta maidasu runa wurin wanda zata je, kallon atamfa tayi tana tuno wasu kalamanshi na can baya shekaru masu ɗan yawa, daga ya ganta da kayan turawa zai ce ko kyau babu, tsaki tayi a fili tace “Damuwar ka ai dama ba don kai zan saka ba.” Mai makon tasa kayan turawan sai kuma tasa atamfa, doguwar riga ce tayi mata kyau sosai, kasancewar ba sawa take yi ba sai ta fito daban kamar ba ita ba. Bata ɗaura ɗan kwali ba don bata ma iya ba kawai mayafi tasa a sama ta fito, da mamaki Mummy ke kallonta sai dai ganin wajen ƙawarta tace zata yasa tayi shiru, Nabeela bata nan don tun safe taje gidansu inda mahaifiyar su take. Sai data hau kan titi sannan ta fara tunanin wanda zata kira ta tambayi address ɗin don dama ita ba wurinshi zata je ba kawai dai jikinshi zata je gani daga nan kuma tasan ba zata ƙara ganinshi ba. Har zata kira Maryam ta tambayeta kwatancen gidan sai ta fasa ta kira Salim, bayan sun gaisa ne tace “Salim dama naga wani kwalin magani ne a mota nake son na baka to kuma na fita nima nace ko kawai zaka faɗa mini gidan Dada sai na ajiye mata na wuce?” Mamaki ne ya kamashi don ya tabbatar ya fita da duk magungunan sai dai zai iya yiwuwa bai kula da lokacin da wani ya faɗi ba. Nan yayi mata kwatance ta kashe sannan ta shafi fuskarta, me yasa ta koyi ƙarya saboda Baqeer ne? Iska ta furzar sannan ta cigaba da tuƙi, bata sha wahala sosai ba don tana shiga layin ta tambaya aka nuna mata. Tafi minti biyar a waje tana kokwanton shiga kafin ta daure ta fito, har ta kai ƙofa ta girgiza kai lallai ajinta zubewa yake nema yayi, ta ya ma zata shiga gidan tace me ya kawota? Neman juyawa tayi sai taɗan ji sautin maganar Dada da ɗan ƙarfi tana kiran Baqeer, da alama ƙofa take bugawa, sam ta manta ta fasa shiga gidan sai kawai ta tura ta shiga hankali a tashe, Dada ce ta kalleta da mamaki don bata ganeta ba. Zee sai a lokacin tasan ta kwafsa, to meya kawota ma ne? Murmushin yaƙe tayi ta gaisheta, nan ta amsa tare da cewa “Wacece?” Yawun bakinta ta hadiya tace “ƙawar Maryam ce magani suka manta a mota nazo kawo mishi.” Nan da nan ta saki fuska tace “Ayya Masha Allah! Mun gode kuwa.” Zeey ta ciro paracetamol a jaka ta miƙa mata, Dada ta amsa sannan tace “Na rasa yadda zan yi da yaron nan tunda ya shiga ɗaki tun jiya har yanzu bai ko leƙo ba, ga baici abinci ba balle ya samu yasha maganinshi.” Dada ce ta sake buga ƙofa tace “Baqeer wai din Allah wace rayuwa ce wannan?” Zeey ce ta kalleta tace “Dada bari na wuce.” Tayi saurin riƙeta tace “Ai kam dai ba kyazo ki tafi ba ko ruwa ban baki ba, zo ki zauna mu gaisa kici abinci.” Baqeer da ƙamshin turaren da yaji jiya a motar nan ne ya shigo ɗakinshi yasa ya tura keken shi da hannunshi zuwa bakin ƙofa, jingina bayan keken yayi da ƙofar don son sanin wacece? Muryarta kaɗai da yaji ya gane ta. Akan me take bibiyar rayuwarshi ne wai? Shiru yayi yana tunanin turaren nan da yaji jiya ba dai jiya har motar abokin Salim ta shiga ba? “Dada Allah babu komai, amma ya zaki yi in bai buɗe ƙofar ba?” Kalamanta ne suka doki kunnuwanshi, “Ni kaina ban sani ba wallahi sam na kasa gane me ke damunshi, ƙaddarar nan Allah ya riga ya aiko mana ita dole ne mu amsheta.” Tunowa tayi da yadda taga mahaifinshi na magana jiya ta tabbatar waɗannan abubuwan sune suke damunshi, murmushin da ya tsaya iya leɓe tayi kafin tace “Sai mutum ya halaka kanshi saboda ƙaddarar da Allah ya ɗaura mishi? Dada ashe mu baza mu godewa Allah ba mu san iskar kaɗai da muke shaƙa a duniya kyauta bace daga Allah zuwa garemu?” Kallon ƙofar yayi saboda kalamanta da yaji, Dada ce tace “Abin ne duk na rasa kanshi wallahi ni kaina jiya ban yi bacci ba.” Tayi maganar cike da jimami, fitowa tayi Zeey ta kalli ƙofar, alamun motsi taji daf da ƙofar wanda Baqeer ke neman barin bakin ƙofar. “Haka zaka cigaba da rayuwa?” Abinda ta faɗa kenan wanda ya sakashi tsayawa da tura keken, “Baka duba mutanen da ke tare da kai waɗanda suka damu da kai? Sai wasu ƙalilan da basu damu da kai ba?” Yawun bakinshi ya haɗiya tare da kallon ƙofar, “In har kana son ƴan uwanka to ka cire rashin ƙafar ka a matsayin nakasa ka maidata challenges na rayuwa da Allah ya ƙaddara maka, baka san me Allah ya shiryawa rayuwarka ba da ya jarabceka da hakan. Please ka sha magani ka kuma ci abinci.” Tana kaiwa nan ta fito waje, Baqeer ji yayi wani abu ya tokare mishi zuciya, wacece wannan? Wani abu yake ji wanda shi kanshi bai san menene ba. Zeey a waje taga Dada da alama so take yi ta kawo mata abu, kallon yadda take juye abincin daga robobin biyu tana ƙoƙarin maidasu ɗaya take, shinkafa da wake ne, da alama ma babu yaji don gwangwanin take ta ɗan bugawa a ƙasa tana tashin wanda ya danƙare daga ƙasa, idanun Zeey ne ya nemi cicikowa, da sauri ta maidasu tace “Dada ni nama tuna ana nemana bari  nayi sauri naje zan samu lokaci nazo naci abincinki.” Tana kaiwa nan ta fito da sauri ta faɗa motarta, janta tayi ta bar wurin tausayin Dada sai damunta yake yi, bata yi auni ba sai gata a gaban babban shagon unguwar, ajiyar zuciya tayi ta duba account dinta wanda take da kudi sama da naira duba ɗari takwas, amma gashi can abincin dubu ɗaya yana neman gagararsu. Ya zata yi ta taimaka ba tare da an san ita bace? Salim ne ya faɗo mata ai zata iya siya ta bashi ya kai a matsayin aikenshi aka yi ko? Haka ta cigaba da tafiya tana nazarin abinda ya kamata. ***** Kamalu yana fitowa daga ɗakin Abu kawai ya daka tsalle tare da dukan bokitin robar dake tsakar gidan da kafarshi, ji yake wai yau shine zai tuka motar Baba da Baqeer, kallon kayanshi yayi babu laifi gwanjo ne amma masu kyau, comb yasa ya taje kanshi sannan ya fesa turare ya shiga mota ya ƙure kiɗa cikin ƙwambo ya fara tuki, unguwar su Zeey ya nufa, yana shiga layin yaje gidan mai gadi ya ce bata nan yana yi mishi kallon mara hankali, cike da takaici ya juyo yana tunanin ba dai wurin Salim taje ba? Kwafa yayi don wallahi yana tausayawa Salim duk ranar daya damƙeshi, kamar a mafarki ya hango motarta, ai cikin hanzari ya jaa motar yasha gabanta, wanda saura kaɗan ta buge shi, burki ta taka da sauri tana maida ajiyar zuciya, Allah ya taimaketa kan layi ne ba titi ba, da mamaki ta ɗago ta kalli motar, Kamalu ne ya sakar mata wani murmushi tare da ɗaga mata gira, bata ganeshi ba hakan yasa ta tsaya tana kallonshi har ya fito daga motar da yake yazo inda take, glass din da take ciki ya ɗan buga yana mata alama data fito tare da kashe mata ido. Mamaki ya sake rufeta ta sauke glasses ɗin motar tace “Yaro ya haka?” “Yaro?” Ya maimaita kalmar tare da nuna kanshi, tace “Eh, saboda halin yarinta kake yi, menene hakan?” Yawun bakinshi ya hadiya yace “Roshni plz magana nake so muyi ina ta zuwa gidanku ba’a barina na ganki.” Kallon mamaki kawai take yi mishi tace “Roshni?” Dariya yayi yana haɗe leɓenshi yace “oh Zainab mantawa nayi.” Takaici ne ya isheta kawai ta zuge glass tana neman yin reverse da sauri ya tsaya bayan motar tare da tare hanyar da zata yi reverse ɗin, mamakinta ne ya sake ƙaruwa hakan yasa ta fito don sam bata da hakuri yanzun ma damuwar Baqeer ne yasa take kokarin haƙuri da shirmen yaron. Murmushi yayi ganin ta fito ya dawo yana tafiyar nigga ya tsaya kusa da ita yace “Roshni nine fa Sadaath ɗinki kin manta love at first sight.” Ya kanne mata ido yana shafa kuncinshi. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #Zeey #Kamalu #Sanyin Zuciya #Rayuwat *Na Umm Asghar*    *Da* *Ayusher Muhd*🏌🏻‍♀️ *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA HUƊU* {24} Wani irin wulaƙantaccen kallo tayi mishi tare da sakin tsaki, ita duk sai taji ranta ya ƙara ɓaci ma ajinta ya zube ƙasa warwas idan har wannan mahaukacin zai iya tararta ya buɗe baki yace yana sonta ba tare daya duba ɗumbin tazarar dake tsakaninsu ba. Cikin fusata tace "Dallah mallam bana son hauka, tun wuri gara ka kauce ka bani wuri na wuce ko kuwa kaga nayi maka da mai taɓin ƙwaƙwalwa irinka da zaka zo ka tareni a titi kana yi  mini soki burutsun zance mara kai bare ƙafafu?" Shi kuwa duk hargagin da take yi bai ma san tana yi ba sai ma kallonta  yake yi cikin shauƙi yana jin wata iriyar soyayyarta na ƙara ratsa dukkanin wasu sassa na jikinshi. Yau dai gashi ga Roshni a tsaye, sakarar zuciyarshi ma sai take ayyano mishi ai kallon soyayya take jifanshi dashi don haka yake ta washe mata haƙora shi a dole murmushi yake yi. Ganin ɓata lokacin ta kawai take ƙara yi da tsayuwa a wajen wannan mahaukacin yasa ta koma cikin motarta ta tasheta da nufin idan har bai matsa ba tabi ta kanshi kawai ta wuce sai dai duk abinda zai faru ya faru amma ba zata tsaya tana cigaba da jin zantukan bakin mara hankalin nan ba. Sai da yaga ta nufo kanshi gadan-gadan kamar zata bugeshi sannan ya matsa yana cewa "A’a Roshni ya zaki tafi kuma bayan muna hirarmu ta soyayya gwanin daɗi?" Bin bayan motarta yayi da kallo yana jin tamkar ta tafi da wani ɓangare na zuciyarshi, sai da ya daina ganinta sannan ya nufi motar Baba da Abu tasan ƙulunboton da tayi har ya bashi aro ya buɗe ya shiga yana jin kanshi on top don yau yayi dacen haɗuwa da Roshni don ma basu samu sun zanta sosai kamar yadda shi yaso ba amma dai babu damuwa zuwa anjima zai je gidansu ya sameta yadda zai ƙara kafa kanshi sosai. ***** Bayan wucewar Zainab ne Dada ta ƙara ɗauko abincin Baqeer data mayar kitchen ta ajiye ganin yaƙi buɗe ƙofa ya karɓa ta nufi ɗakin da yake. Ƙwanƙwasa ƙofar tayi tace "Yanzu saboda Allah Baqeeru ba zaka buɗe ƙofar nan ka fito ba? Ga abincinka nan tunda zafinshi nake bin kan ka kazo kaci gashi yanzu har ya huce, ayi rayuwa a haka ace bawa yayi ta zama da yunwa, shikenan don Allah ya jarabceka da wata ƙaddara sai ka shige ɗaki ka ƙuntata rayuwarka maimakon ka gode mishi bisa tarin ni'imomin da yayi maka sai kuma kake nema ka butulce mishi saboda ya jarabci rayuwarka don ya gwada imaninka, wannan wacce irin rayuwa ce da bawa ba zai karɓi ƙaddara a duk yadda tazo mishi ba?” Ga mamakinta sai gani tayi Baqeer yazo ya buɗe ƙofar ɗakin ya miƙo hannu ya karɓi kwanon abincin nashi da tuni ya huce. Miƙa mishi tayi ta juya tana cigaba da ƴan mitocinta akan rufe kanshi a ɗaki da yake yi. Shi kuwa maganganun yarinyar nan ne suka tsaye mishi a rai yake ta faman juyasu a cikin ranshi inda take cewa "Haka zaka cigaba da rayuwa baka duba mutanen dake rayuwa tare da kai suka damu da damuwarka? Sai maganar wasu ƙalilan da basu san ciwon ka ba basu damu da kai ba zaka ɗauka ka saka a rai?" Shi yasa yaji ba zai iya ƙyale Dada tana maganganunta ba shine kuma yasa shi buɗe ƙofar ba tare daya shirya wa hakan ba. Gara kekenshi yayi ya koma cikin ɗakin ya tasa abincin a gaba yana kallo, tun asali shi ba mai son cin kowanne irin abinci bane shi yasa ma Umma ke yi mishi girkin shi daban don baya iya cin girkin su Abu saboda daga ita har Jamila basa iya tsayawa su gyara girkinsu saboda maigidan ba wani kuɗin cefanen kirki yake bayarwa ba su kuwa kowacce na ƙyashin ta cire daga aljihunta ta ƙara yadda za'a yi wadataccen abinci mai kyau, dama Umma ce bata ƙyashin gyara girkinta bare kuma da Baqeer ɗin yake tsaye akan al'amuranta bata nemi komai ta rasa ba shi yasa yaran gidan har ɗokin zagayowar ranar girkinta suke yi don sun san zasu ci abinci mai daɗi ba kamar na iyayensu ba. Haka nan ya daure ya tuttura abincin gashi aka yi rashin sa'a wake da shinkafa ba cimar da yake so bane sai dai kuma a yanzu dole yayi haƙuri da duk abinda ya samu tunda dai bai kawo ya ajiye ba bare yayi zaɓen abinci. Ko rabi bai ci ba ya mayar da murfin ya rufe ya samu wuri ya ajiye kwanon, ƙishirwa yake ji sai dai duk ɗakinshi babu ruwa shi kuma yana jin ƙyuiyar ya buɗe baki yayi magana bare ya cewa Dada ta kawo mishi ruwan. Kallon tsakar gidan yayi ya hango randar ruwan Dada mai ɗan karen sanyi daga can hanyar fita daga gidan sai dai baya jin zai iya kai kanshi tsakar gidan bare ya ɗebi ruwa ya sha. Rufe idanunshi kawai yayi ya buɗe yana ƙara kallon wajen da randar take yana ƙara ganin nisan wurin daga nan inda yake zaune, kamar Dada tasan ruwan yake da buƙata sai gani yayi ta nufi wajen randar ta ɗebo ruwan ta kawo mishi. Karɓa yayi ya kafa kai ya sha bai ajiye ba sai da ya shanye ruwan nan tas dama ya daɗe yana son shan ruwan ya buɗe baki yayi magana ne yake ganin asara. Hannu yasa ya gara keken wajen katifar da yake kwanciya sannan yasa hannayenshi duka biyun ya daddafa ya sauka daga kan keken ya koma kan katifar ya kwanta yana murza hannunshi na dama inda ya samu karaya, duk da likita yace hannun ya warke zai iya yin komai dashi kamar da har yanzu yana jin ciwo a wurin bare daya kasance har aikin da ƙafarshi zata yi yanzu hannayen ne ke yi. ***** Tana ji tana gani haka ta cire kujerunta ta sayar, sauƙinta ma ƙawarta data saya ta sayesu da daraja. Tunani ta zauna tana yi to yanzu wacce sana'a ya kamata ta kama don fa ba zai yiwu ta saka kuɗi a gaba su cinye ba alhalin basu da mataimaki sai Allah, duk da ƴan uwanta na cikin wadata tasan zai yi wuya su tallafe ta don dukkansu daga su sai iyalin su sai ko Dada da suke yiwa aiken kayan abinci lokaci zuwa lokaci, tun can asalinta ma Allah bai yita mai kwaɗayin abun hannun wasu ba shi yasa bata taɓa nufar ƴan uwan nata da nufin su taimaka mata ba sai kuma tayi dace da samun ɗa ɗaya tamkar goma daya ɗauke mata dukkanin wasu larurorinta yake yi mata hidima bakin gwargwado daga ita har ƴan uwanshi basu nemi komai sun rasa ba sai fa yanzu da Allah ya jarrabce shi da larura duk da ma dai akwai kuɗaɗen shi a wurin Mallam don duk abinda ya samu shi yake karɓa yana juyawa don yace ba zai yiwu abar kuɗaɗen haka ba a juyasu ba, a yanzu kuwa tasan bata isa ta tambaye shi batun waɗannan kuɗaɗen ba don tasan dai ba bayarwa zai yi ba sai dai ma ranta da zai ɓaci a banza. Wayarta ta ɗauka da nufin kiran Hadiza suyi shawarar yadda za'a yi da kuɗin da irin sana'ar daya kamata ta fara sai kuma ta tuna ashe fa babu waya a hannun Hadizar tunda tata ce ta barwa Baqeer ba kuma lallai ne ta samu ta sayi wata ba tunda tasan halin matsin da take ciki gashi sanda Maryam taso bata daga komawa gida tasan mijin ne ya hana. Maryam ta kira a maimakon Hadizar sai taji muryarta tayi sanyi ƙasa-ƙasa kamar wacce ke cikin damuwa. Hankalinta ne taji ya tashi ta hau jerowa Maryam ɗin tambayoyin ko lafiya suke? Jin muryar mahaifiyarta kawai sai tasa kuka, yi take yi babu ƙaƙƙautawa Umma na jinta bata katseta ba sai dai yanayinta gaba ɗaya ya canja ta tsinci kanta cikin damuwar itama. Sai da tayi kukanta ya isheta sannan tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. "Ki cigaba da haƙuri Maryam komai mai wucewa ne watarana sai kiga kamar ba'a yi ba sai dai a labari, kin ji?” tayi mata maganar cikin tausasawa ba tare data buƙaci jin abinda yasa ta kukan ba tunda dai tsakanin harshe da haƙori ma ana saɓawa tasan ba zai wuce tsakaninta da maigidanta bane. Ajiyar zuciya ta sauke tana share hawaye tace "Umma zaman gidan nan ya isheni, ana samun matsala da uwar miji ni uban miji ne matsalata, babu dama ya ƙyalla ido yaga muna zaman lafiya da Baban Aareef sai yasan yadda yayi ya wargaza zaman lafiyar nan, ko wani alheri Baban Aareef yayi niyyar yi mini sai ya hana yanzu motar da aka saya mini saboda kai Aareef makaranta da ɗaukoshi yasa ya karɓe saboda wai idan yasa ƙafa ya fita yawona nake ficewa nima bana zama ko Aareef ɗin ma bana zuwa na ɗauko saboda kawai rannan nazo na ɗauki Yaya Baqeer na kai shi wajen Dada kuma wallahi Umma daya dawo sai da nayi mishi bayanin abinda ya faru amma mutumin nan ya juyar da magana ya zuge ɗanshi ya karɓe makullin motar daga hannuna, da nace mishi to Aareef ɗin fa ya za'a yi da kai shi makaranta da ɗaukoshi sai cewa yayi wai ai makarantar bata da wani nisa sai na dinga zuwa a ƙafa ina kai shi ina ɗaukoshi don nace ni dai gaskiya ba zan iya ba sai dai ko ya ɗaukar mishi mai napep shine yace ai gidanmu ma dai yaga ba motar ce damu ba da har zai ce ga yadda za'a yi zan yi mishi gardama saboda na samu wuri.” Sauraren Maryam kawai Umma take yi tana girgiza kai, dama tana yawan ji Maryam ɗin na kuka da uban mijin nata sai dai bata taɓa zama ta bayyana mata halin da suke ciki ba sai dai taji suna maganar yawanci ita da Baqeer ita kuwa bata saka musu baki. Hannu tasa ta ɗauke ƙwallar da suka taru a cikin idonta tace "Kiyi haƙuri Maryam, kowanne aure da kike gani da irin ƙalubalen da ma'auaratan ke fuskanta ba kuma zai yiwu kowane lokaci ace akan mahaifinshi kuke samun saɓani ba, ai shi ubanshi ne kuma dolen shi ne yayi mishi biyayya. Saboda Allah ta yaya ubanshi zai ce ga yadda za'a yi ke kuma kice ba haka ba ya yarda, kenan sai ya ɗauki maganarki sama data ubanshi saboda kawai baya son ɓacin ranki, ai ba haka ake zaman duniya ba abinda haƙuri bai baka ba kuma rashin shi ba zai taɓa baka ba. Kici gaba da haƙuri don Allah duk abinda kika san yana janyo matsala a tsakaninku ki dinga ƙoƙarin kiyayewa, ni ranar dana san baki faɗa mishi zaki zo ba ai da ban bari kin ɗauki Baqeer kin kai shi har mariri ba da sai nasa a nemo motar haya na tafi na kai shi duk ba wani abun damuwa bane.” Haka dai tayi ta mata nasiha tana tausar zuciyarta kafin suka yi sallama ta ajiye wayar tana jin ƙarin damuwa akan wacce take ciki. Gaba ɗaya ƴaƴanta babu wacce ke jin daɗin zaman gidan miji, dama Baqeer ne tsaye akan al'amuransu to shima ga yadda rayuwarshi ta koma dole yana buƙatar matallafi kafin suga yadda rayuwa zata yi dashi, watakila idan hannunshi ya warke ya koma kan harkokin zanen shi komai zai warware musu tunda ai dama rashin yin zanen ne ya saka su a cikin halin da suke ciki, rashin yin zanen ne yasa Mallam ya juya mishi baya ya fitar da hannunshi daga al'amuranshi, tasan daga ranar da ya warke ya komawa harkokinshi komai zai gyaru, daga wannan ranar Mallam zai janye korar da yayi mishi daga gidanshi don zai ga nakasar data sameshi bata hanashi cigaba da al'amuran rayuwarshi kamar da ba, sai dai kuma yaushe ne zasu ga zuwan wannan ranar? Dole ta tashi ta tsaya da ƙafafunta har zuwa lokacin da Baqeer zai samu lafiya ya koma kan harkokin nashi, kafin nan dole ne ta zama jaruma jajirtacciyar mace mai tsayawa ta nemi na kanta ba tare data jira sai wani yayi mata ba. Zata tashi ta kama sana'a komai runtsi komai wahala don ta tallafi rayuwarta data iyalinta. ***** Zainab na ƙoƙarin shiga gida ta hango samari tsaye a gate din gidansu, da mamaki ta karasa wurin, mai gadi ne ke ta mata alama da karta ƙaraso sarai ta gane sai dai bata bi ta kanshi ba ta nufo gadan-gadan zata shiga. Jikin motarta suka nufo hakan yasa ta gane Najib dake ɗaya daga cikinsu. Kai ta girgiza tare da furzar da iskar bakinta, wato dai yau mutane neman kaita bango suke yi da shirmensu na sunan soyayya? Knocking din glass ɗinta yayi, ta zuge tana yi mishi wani irin kallo na takaici, ya ɗan jingina da ƙofar motar yace “My Zeey mun zo wurin Kb ne zamu fita su kuma abokaina ganinki suke son yi.” Kallansu tayi tace “Hi!” tana ɗaga ƴan yatsunta guda biyu. Matsowa suka yi suna murmushi, tana kallon Najib tace “Babu laifi ai, hope ka faɗa musu mun yi north-west?” Kallonshi suka yi tana ɗan murmushi tace “Kada ku damu ya samu wata ne, so ba wani issue bane, J bye sai munzo biki.” Tana kaiwa nan ta shiga cikin gida zuciyarta na sake tafasa don sam ba wannan shirmen bane a gabanta, ita tunanin yadda zata taimaki Baqeer kawai take yi, ko yaci abincin? Fuskarta ta shafa tare da takaicin halin da ta shiga. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #Zeey #Kamalu #Sanyin Zuciya #Rayuwata *Na Umm Asghar* *Da*   *Ayusher Muhd🏌🏻‍♀️ *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR* {25}   Nabeela ce ta kalli Kabir wanda ke ta watso da kaya ƙasa a cikin ɗakin shi cike da kulawa tace “Ya Kabir me kale nema ne?” Kallonta yayi yace “Please ki fita, ko me nake nema ba ɗaki na bane?” Jikinta ne yayi sanyi ta fara neman barin ɗakin sai kuma yasa hannu ya riƙo rigarta yace “Sorry raina ne a ɓace ba wai wulaƙanci bane takardu na shigo dasu jiya kuma ban gansu ba.” Ajiyar zuciya tayi cike da damuwa tace “Takardun menene? Akwai dai wanda Zainab ta kai ɗakinta jiya amma su na mota ne.” Sakinta yayi ya fito daga ɗakin cikin sauri ya shiga ɗakin Zeey, akan dressing mirror ya gansu, ƙwafa yayi ya sake dubawa ganin komai yadda ya ajiye yasa ya ɗauka ya fito fuskarshi sam babu alamar walwala. Zeey ce ta shigo ranta duk a ɓace ama barta da damuwar Baqeer wannan mahaukacin da wannan yaron na neman ƙona mata rai, takardun ya nuna mata bayan ya tare ƙofar shiga yace “Uban wa yace ki ɗaukar mini takardun motar nan?” Kallon takardun tayi a wulaƙance sannan ta kalleshi tace “Kaga don Allah banda lokacin wasu takardun motarka, na shiga ɗakinka na gansu na ɗauka motar da aka ce za’a saya mini ne ka shigo da takardun, shine na ɗauka don na duba.” “Kawai daga ganin abu a ɗakina sai ki ɗauka ko kin tambayeni ne?” Saman goshinta ta shafa tace “Please! Ya isa haka ba gashi ka ɗauka ba sai ka sakasu a abinci kaci…….” Cikin ɗaga murya yace “Malama ni kike yiwa magana haka?” Mummy ce ta fito da sauri da alama ma sallah take yi don sanye take da hijab, kallonsu taiy tace “Zaku fara ko?” Zeey ce ta fara neman wucewa ciki don bata da lokacin Kabir balle shirmen da yake yi. Kallon Mumy yayi yace “Wallahi wata rana sai na fasawa yarinyar nan baki in dai ni zata dinga yiwa magana a haka.” Zeey ko kulashi bata yi ba ta wuce cikin falo, tana jiyoshi ya fita wurin abokanshi tare da bugo ƙofar da ƙarfi. Kallon Nabeela tayi tace “Meya faru?” Nan ta sanar da ita abinda ya faru cike da ɓacin rai tace “To ke menene naki na sanar dashi? Sai ki zo ki faɗa mini gashi nan yanzu a dalilinki kin janyo musu sun samu matsala?” Zeey dake falo tana jiyosu ta dawo tace “Mummy menene laifinta a ciki? Gaskiya ta faɗa ni fa bani da lokacin Ya Kabir neman faɗa kawai yake ji, sannan idan ya dawo ki sanar dashi kada ya ƙara janyo ruɓaɓɓun abokanshi gidan nan su tare mutum suna yi mishi shirme inba haka ba wata rana sai na faɗa musu magana.” Yadda Mummy take kallonta ne yasa ta shagwaɓewa ta shiga ɗaki cikin jin haushin kanta yanda takaici da damuwat halin da Baqeer ke ciki yasa duk hankalinta yaƙi kwanciya. Nabeela ta sake kalla fuskarta a ɗaure tamau tace “Kin dai san nace a’a ko? To wallahi bana son hauka in ba haka ba ki tattara ki koma gida.” Wani abu ne ya tokare mata maƙoshinta sai dai bata iya cewa komai ba sai juyawa data yi idanuwanta na sake ciccikowa da ƙwalla ta bar wurin. ****** Kamalu daya biyo Zee a mota ashe yana ganin sanda Najib ya jingina da mota wanda hakan ya sake tunzuro shi, nan da nan kishi ya turnuƙeshi, Roshni ɗin tashi wani soko zai tare? Bayan shi ya gama shirya rayuwar love da ita? Ko kallon ƙauna data yi mishi ɗazu kaɗai ya tabbatar mishi ta gama amsar soyayyarshi. Tsayawa yayi a gefe har saida yaga sun shiga mota sannan shima yabi bayansu, a wani restaurant suka yi parking da motocinsu uku suna shiga ciki ya fito da ƙusoshi ya jera a ƙasan tayoyin yana yi yana waige-waige wai kada a ganshi, daya gama yayi wani murmushin jin daɗi ya shige motarshi yayi tafiyarshi ko banza dai ai ya rama. Haka ya dinga yawo a gari yana nunawa abokanshi motar babanshi wai shima yau gashi nan an bashi, wani wurin ma nuna musu yake yi kamar motarshi ce. Su Kabir da Najib suna fitowa suka yi reverse suka bar wurin wanda shirmen ƙusoshin da Kamalu yasa bai yi musu komai ba. **** Umma yau haka ta wuni sukuku saboda tunanin halin da Maryam take ciki a gidan mijinta, ita kaɗai ke da mata biyu dake zaune anan garin, ƴaƴan Abu mata da suka yi aure su biyu ba’a Kano suke ba, daga Hadiza har Maryam babu wacce tayi dace a gidan aurenta, wannan abu na bala’in ɗaga mata hankali, tana nan a kishingiɗe hankalinta duk ya tafi kan tunanin ƴaƴanta sam bata kula da shigowar Baba ɗakin ba kawai sai ji tayi ance “Kefa yanzu gaba ɗaya kin zama mara mutunci ko? Har kin isa na shigo gidan baki ko ɗago kai kin kalleni ba bare nasa rai da gaisuwa?” Da sauri ta miƙe zaune tace “Mallam sam ban ji shigowarka ba wallahi.” Kallon ɗakin yayi ranshi na sake ɓaci yace “Au na ɗauka ai kin bi titi kema.” Kallon mamaki tayi mishi don bata gama gane me inda kalamanshi suka nufa ba.” Ya zabga mata wata muguwar harara yace “Bani.” “Me zan baka?” “Kuɗin kujerun ko da ke a naki haukar bar miki kuɗina zan yi? Ko ba da kuɗina kika sayi kujerun ba?” Mamaki ya gama rufeta tace “Mallam kujerun nan fa Baqeer ne ya saya mini kuma kuɗin shi zan samu na tallafawa dasu.” “Inyee? Fatima ni kike yiwa magana haka? Ni kike cewa Baqeer ne ya saya miki kujeru? To wallahi na saka ƙafar wando ɗaya dake a gidan nan, zanga in gurgun ɗan naki zai iya tallafa miki, ni zuciyata fari tas tunda ba shi kaɗai gareni ba sannan ina da lafiyayun ƴaƴa zan kuma nuna muku dukkanku a tafin hannuna kuke.” Idanunta ne taji sun cicciko duk haƙurinta sai data ji ta kasa jurewa don haka tace “To Mallam tunda haka ka zaɓa mu bamu da ikon hanaka, sai dai shima ƙaddarace ta faɗo mishi ba yin kanshi bane.” Ƙwafa yayi ya fice daga ɗakin ranshi a mugun ɓace, Jamila wacce dama take gadi a ƙofar ta sam bata so ya wuce bata tare shi ba tayi saurin fitowa tana lanƙwasa jiki da yanga tace “Mallam ashe ka dawo?” Wani kallo yayi mata yace “Ke kuma meye hakan kike yi kamar wata mai ciwon haƙarƙari?” Abu ce ta kwashe da dariya wacce fitowarta kenan tace “Kai Mallam yanga fa ake yi maka irin ta jan hankali.” Tsaki yayi yace “Yanga ko hauka, ni bani wuri na wuce don Allah.” Yayi maganar yana tureta ya wuce bangaren Abu, nan da nan zuciyar Jamila ta sake zafi ta dinga ji kamar zata yi hauka, kai tsaye ɗakin Fatima tayi wacce ke zaune tana tunanin yadda Mallam ya juya mata baya kamar ba ita ce ƴar lelenshin nan ba. Tana shiga tace “Fatima wai haka zamu zauna Abu ta mallake Mallam muna kallo ba zamu ɗauki wani mataki ba?” Ko kallonta bata yi ba tace “Ku mallaka ta dama ni dai don Allah kuje can ku karata.” Jamila nan da nan takaici ya ƙara rufeta a fusace ta banko mata ƙofa ta fito, har ga Allah ita bazata taɓa yarda Abu ta ƙwace musu miji tana ji tana gani ba. ***** Dada tayi mamaki da Baqeer bai musa ba data kawo mishi abincin dare, kuma banɗaki da kanshi yake gungura kekenshi yake zuwa, hakan ya sake tabbatar mata zuwan yarinyar nan ne yayi tasiri sosai a tare dashi, to wacece ita? Dole ta tambayi Maryam alakarsu don bata san me tace mishi ba amma tabbas tun bayan tafiyarta ya canza, washegari haka kawai ya samu kanshi da tunanin ko zata zo sai dai babu ita ba labarinta, murmushin takaicin kanshi yayi, iyayenshi ma suka gujeshi bare yarinyar da har yanzu ko sunanta bai sani ba, yarinyar da kawai ganinta yayi amma wai har wani sashi na zuciyarshi ke kwaɗaita jin muryarta, wanda ya tabbatar ko a hanya ya ganta ba lallai ya iya ganeta ba, to wai wacece? Wannan tambayar ita ce ke sake ƙona mishi rai, wayarshi ya ɗauka abinda tunda ya fara ciwo bai taɓa yi ba, dubawa yayi yaga Maryam ta saka mishi kati kawai ya gwada siyan data na kwana ɗaya, facebook ya leƙa inda ya dinga ganin hotunan Bello na tayashi murna da ake yi da kyaututtukan da aka bashi, har ya canza sunanshi ma zuwa MBB, wani murmushin takaici yayi ya sake duba wani hoto inda yaga Bellon riƙe da hannun mace wanda ko ba’a faɗa ba yasan Asiya ce, nan yayi deleting account dinshi ya ajiye wayar kawai. ****** Zeey yau kwananta biyu kenan bata leƙa Baqeer ba sai dai yadda kasan mara lafiya haka take jinta, ko doguwar magana bata yi, Mumy har ɗaukan ta tayi suka je shopping amma sam taƙi dawowa daidai, suna hanyar komawa gida tace “Mummy don Allah ki barni naje gidan ƙawata akwai abinda zan amsa.” Kamar zata hanata sai kuma ta fasa tace “Please Zainab in har da wani abun ki sanar dani na tsani ganinki haka.” Rungumar Mummy tayi tace “Ni kaina ban san meke damuna ba Mummy shi yasa na kasa sanar dake.” Kanta ta shafa don Daddynsu har ya gaji da tambayarta ko wani abun ke damun Zeey. “Muje gida sai ki hau motata ki je, tunda har yanzu bai baki motarki ba, kin dai san kulawa ce tasa hakan ko?” Kai ta girgiza tace “So yake yasan duk inda nake zuwa Mummy kema fa kin sani.” Wani kallo tayi mata irin na son ta canza abinda ke ranta, Zeey kwantar da kanta tayi a saman kujera tace “Kema fa kin san haka ne.” Haka suka isa gida sannan ta hau motar Mummy bayan tayi mata kashedi akan kada ta daɗe, ta tsaya ta sayi kayan marmari sannan ta isa ƙofar gidan su Dada, kanta ta maida bayan kujera tana mamakin yadda wai sam ta kasa cire Baqeer daga ranta, rayuwar da suka yi dashi a baya ta tuna hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya bayan ta tuno yadda mahaifinta sam ya hanata kallon gidansu Baqeer, ya zai ji idan yaji ita take bibiyarshi? Yaro ta samu ya shiga da ledojin cikin gida. Dada na zaune tana tsinke zogale yaron ya shigo ta tambayeshi inji waye yace “Watace a mota a waje.” Da sauri ta miƙe tare da leƙowa nan ta hango Zeey tayi reverse tana neman wucewa, da sauri tace “Ƴar nan ina zaki?” Karaf a kunnenta hakan yasa tayi parking tana murmushi tace “Dada sai da kika fito?” Harara ta zabga mata tace “Ina nan ina ta addu’ar na ganki kuma zaki zo naga kin tafi baki shigo ba?” Fitowa tayi tazo kusa da ita tana dariya tace “Gani nayi ban sanar daku zanzo ba…..” Ai bata ƙarasa ba taja hannunta ciki tace “Ni kullum in zaki zo daɗi zanji, wannan kayan duk na menene?” “Ke na kawowa kici kiyi ƙiba da lafiya.” “Ni ko shi?” Ido  Zeey ta zaro tace “Ke dai, rabani da wannan zancen Dada.” Dariya suka yi tare da shiga ciki sosai. Baqeer na zaune a ɗakin shi bai rufe ƙofar duka ba, kallon ƙofar yayi jin kamar muryar data kasa barin cikin kunnenshi, muryar da kullum ke yi mishi yawo a zuciya. Zeey ce ta kalli ƙofar gabanta na wani irin faduwa haka kawai take jin faɗuwar gaban taƙi tafiya, idanunsu ne suka haɗu da juna nan ta ɗan lumshe ido sannan ta sake buɗewa, ta sake saukesu kanshi sannan suka wuce ciki ita da Dada. Zama tayi har yanzu bata daina ji gabanta na faduwa ba, ta sani tausayin Baqeer ne ke damunta amma faɗuwar gaban ta menene? Shakkar shi da kike yi tun da ko kin manta? Da wannan tunani ta gama tabbatar wa hakan ne. Baqeer na jiyosu daga ɗaki Dada na cewa “Wai da tafiya zaki yi da ban jawo ki ba?” Zeey tayi murmushi tace “To Dada mai zan shigo nayi? Wancan karon ma Maryam ce ta aiko ni.” Ta ƙarasa maganar tana ɗan kallon ƙofar ta gefen ido. Haka kawai yaji kalamanta sun yi mishi zafi, to da yace tazo ne? Dada ce kawai yaji ta ƙwalla mishi kira tace “Baqeer ka fito mana ku gaisa.” Ko amsawa ma bai yi ba don ji yayi kamar Dada ta gama tozartashi wato har ta gane abinda yake tunani shi yasa take magana da karfi haka? Miƙewa tayi tazo ta wangale ƙofar tana cewa “Kazo ku gaisa mana.” Kai ya girgizawa Dada alamar baya son zuwa don baya son ma yin magana balle taji ta ɗauka son ganinta yake yi. Mikewa Zeey tayi tace “Dada kin dai san ba fitowa zai yi ba ko kin manta ya gama yanke alaƙa da duniya?” Nan da nan ran Baqeer ya kai bango, me take nufi? Zeey ta cigaba “Ai Dada kawai ki barshi yayi ta zamanshi a ɗaki tunda har yanzu bai fahimci abinda ya dace yayi ba.” Dada dariya tasa a gaban Baqeer tace “To ka dai ji namiji  da bai san me ya dace ba kuwa ai gani nake akwai matsala ko Muhammadu?” Fuskarshi ya tamke sosai don shi saboda tsabar baya son raini shi yasa ko wasan tsokana baya yi, Zeey da yake tasan halinshi tace “Dada ya gama azumin ne ko yasha ruwa?” Dada ta sake kwashewa da dariya wanda hakan ya sake ƙular da Baqeer matuƙa, ya gurguro kekenshi cikin ɓacin rai ya nufi ƙofa, tana jingine a jikin ƙofar tana murmushi, cak ya tsaya yana kallonta itama kallonshi tayi wanda ta sake sakar mishi murmushi tace “Dada bari na wuce kafin na ganni a waje.” Tayi maganar idanuwanta a kanshi, a ina yasan fuskar nan? Tambayar da ta sake zuwa mishi kenan, baya son ta gane kallonta yake sosai hakan yasa ya ɗan kauda kai, zai rufe ƙofar Dada ta riƙe ƙofar tace “A’a ni kar a rufe dani a barni naje mu sha hira da ƙawata, tunda kai dai ka kulle kanka sai kasha zamanka lafiya.” Wani murmushi tayi mishi wanda ya kasa gane wani iri ne tana kallonshi shima yana kallonta tace “Toh Dada in ma mutum zai farka ya nemi abin da zai debe mishi kewa ya farka in ba haka ba yana zaune mutanen da ya daɗe yana kula dasu zasu ƙarasa rayuwarsu cikin baƙin ciki.” Tana kaiwa nan ta koma inda Dada ta saka musu tabarma ta zauna, Baqeer wani irin yanayi ya tsinci kanshi dashi wanda yaji yama kasa rufe ƙofar, Dada ce ta fito don tabbas tasan kalaman Zeey sun shigeshi dole ta roƙi Zeey ta dinga zuwa don ta tabbatar Baqeer na neman mai fada mishi gaskiya gwara ya san abun yi. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer #Zeey #Kamalu #Sanyin Zuciya #Rayuwata *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd*🏌🏻‍♀️ *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA* {26} Maida ƙofar Baqeer yayi kawai ya juya kekenshi tare da jinginar dashi a jikin ƙofar, kunnenshi sosai ya kasa a waje yana son sanin me suke tattaunawa. Dada ce tasa dariya tace “Ahh yau naga babban, haka kawai an turkeni can a lungun ɗaki ana neman rufeni da raina.” Zeey ce ta buɗe baki cike da mamakin kalamanta tace “Dada ni dai ba ni bace kin san wanene.” Harararta tayi tace “Amma ai kina kallo ana neman rufeni baki taro ni ba.” Dariya Zeey tayi don tana son zolaya takaicinta ɗaya gidansu komai da gaske ake ɗaukan shi tace “Ke dai Allah Dada har da neman magana, ni ina bakin ƙofa ina ni ina shiga ciki kinkimo ki?” “To ai da baki kinkimoni ba na kinkimo kaina, ke ni ba wannan ba wai kin tabbatar babu komai tsakaninki da Baqeeru?” Ido ta zaro da sauri tace “Babu komai kamar ya?” “A’a to naga ne kuna wasan kallon-kallo nan don kar a ganni a tsofe a ɗauka ban san komai ba.” Mikewa Zeey tayi da sauri tace “Kinga Dada ki rabani da wannan zancen, ni kinga ma wucewa ta.” Riƙo hannunta tayi tana miƙewa suka fito waje tana sake godiyar fruits data kawo musu Zeey ce tace “Dada kar kice wa Ya Baqeer nice na kawo in ba so kike yayi faɗa ba.” Dariya tayi tace “Don Allah ni dai in da hali ki cigaba da zuwa lokaci zuwa lokaci Baqeer na buƙatar wanda zai dinga faɗa mishi gaskiya, kuma na kula ke kaɗai ke iya faɗa mishi gaskiyar kai tsaye.” Kallon Dada tayi jiki a sanyaye kafin ta ɗaga kai kawai alamar to, haka ta shiga mota idanuwanta na sake hango mata kallon da Baqeer yayi mata, ta tabbatar yaji zafin kalaman data faɗa mishi kawai don baya da niyyar kulata ne yayi shiru, amma tasan da yasan itace Zainab ɗin daya sani ta faɗa mishi magana haka babu shakka da tuni yaci mutuncinta. Har ta isa unguwarsu zuciyarta na saƙawa da kwancewa, akan layinsu da zata shiga motar Bello ita kuma tazo fita, kallo ɗaya tayi mishi ta ganeshi ga Asiya nan zaune a gefen mota sai hira suke ana wani rirriƙe hannu cike da so da ƙauna, nan da nan takaici ya turnuƙeta, babu shakka mutanen nan basu da kunya don ranar da suka je gidan Maryam da Salim yake bata labarin wai Bello abokin Baqeer ne, ranar tayi mamaki har ta gaji ace wai abokinka shine zai ci amanarka irin haka, da saninta ta ɗan bugi gefen motarsu kaɗan wanda hakan yasa Asiya da Bello suka yi ɗan gaba kaɗan sannan suka yi baya, da sauri ya ɗago tare da riƙo gefen fuskarta yace “Sweetheart are you okay?” Kukan shagwaɓa tasa tana nuna wuyanta wai ta buge da kujera, a fusace Bello ya fito ya nufi motar Zeey, wacce ke jiran fitowarshi dama, sun glasses tasa kafin ya ƙaraso ta ɗauki waya ta fara daddannawa. Knocking glass ɗin motar yayi saitin inda take, Zeey ta zare glasses ɗin fuskarta kaɗan wanda ya bashi damar haɗa ido da ita sannan taja motarta tayi gaba ta barshi tsaye cike da mamaki, ganin gidan data nufa yasa ya kasa ƙarasawa  don duk sun san gidan Suleiman Karaye ne wanda kaf unguwar babu wanda ya kai shi kuɗi bare yafi shi, bai san meye haɗinta da gidan ba amma yasan tunda yaga ta shiga to akwai dangantaka mai ƙarfi a tsakaninta dasu, Asiya har tutiya take yi akan layinsu ɗaya. Dawowa mota yayi yana saka hannu a aljihu, ta kalleshi cikin sakalci tace “My heart me tace? Don na hango mace ce.” Ya zauna yana dariya yace “Ta bada hakuri ashe bata kula bane.” Turo baki tayi tace “Ni ya kamata kace ta bawa hakuri ai don ni ta buge, amma ƴar wacece na ganta a katuwar mota haka?” Don kada ta rainashi yayi saurin cewa “Da alama wucewa tazo yi.” Motar ya tada yana ɗan murmushi, ita ma murmushin tayi don restaurant zai kaisu cin abinci tace Habi tazo suje wai bata zuwa gayyar mayaudara. ***** Gida ta shiga tana ɗan kaɗa key ɗin hannunta ko banza ta ɗan huce takaici don da ta fito sunyi magana lallai da sai taci zarafinshi. Ɗakin Nabeela ta shiga taga ba ta nan, fitowa tayi ta nufi bangaren Mummy, nan ma bata nan, hakan yasa ta nufi kitchen, ma’aikatan gidan ne ke girki tana kallon banbar cikinsu tace “Iyani ina Mummy?” Murmushi tayi tace “Tana nan a ciki don bata leƙo mu ba.” Cike da mamaki ta sake komawa ciki tana mamakin inda take, don gidan tsit babu alamun mutum, ɗakinta ta nufa ga mamakinta Mummy ce kwance akan gadonta da alama bacci take yi, kai ta girgiza tare da sakin murmushi, tana mamakin yadda Mummy ke ji da ita, shi yasa a koda yaushe take tabbatar da ita ɗin ƴar gata ce, don sau da dama Mummy nace mata haihuwarta ce ta ceci rayuwarta wanda zuwa yanzu ta tabbatar da hakan, alwala tayi sannan tayi sallah haka nan take jin nutsuwa na sake ratsa zuciyarta, tazo kusa da Mummy ta kwanta itama nan bacci ya ɗauketa don kwanakin nan sam bata samun bacci mai daɗi. Cikin barcinta ne ta fara mafarkin Baqeer wai ga mahaifinshi nan yana neman turashi daga saman dutse, zabura tayi ta miƙe zaune tana addu’a, nan da nan Mummy ta tashi ta rungumeta tace “Menene?” Kai Zeey ta girgiza tana mamakin abinda ke damunta, anya kanta ƙalau kuwa? Anya baza taje ganin likita ba kuwa? Don wannan abinda take yi tabbas ba na masu cikakkiyar hankali bane. ***** A hankali Baqeer ke buɗe ido yana rufewa yanzu kam ya tabbatar kalaman yarinyar nan yake son ji, ya tabbatar ba ƙaramin tasiri kalamanta ke yi a zuciyarshi ba, hakan yasa ya gurgura kekenshi ya zubawa kaɗan daga cikin takardunshi da Umma ta bada aka kawo mishi ido, ajiyar zuciya yayi tare da rike pencil a hanunshi yana kallon takardar sai dai ya kasa ɗora pencil ɗin akai bare har ya gwada yin zanen, to shi yanzu ya zai yi? In ma yayi zanen waye zai siya? Ina zai nemo mutanen da zasu gani su siya? Bayan wayarshi dake ɗauke da duk wasu muhimman abubuwa nashi an sace? Sannan Baba dake tallafa mishi akan harkokin shi shima yayi watsi dashi? Wannan dalilin ne yasa ya ajiye takardun sannan ya maida idanuwanshi ya rufe kafin ya buɗe, yanzu haka zaka cigaba da rayuwa? In Allah yaja kwanakinka fa? Haka zaka zauna komai sai an miƙo maka ba zaka tashi da ƙafafunka ka nema ba? Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauke haɗe da ƙara ɗaukar pencil ɗin don ya gwada yin zanen sai dai kuma ina ya kasa don ƙwaƙwalwar shi ce yaji ta zama blank kamar bai taɓa sanin yadda ake riƙe pencil ba, hannunshi kuma ya hau rawa yaji tamkar an ɗauki wani abu mai nauyi an ɗora akan hannun har ma ya kasa riƙe pencil ɗin ya sake shi ya faɗi a ƙasa. Wani irin ihu ya saki yana ƙara haɗe da riƙe kan shi da hannu bibbiyu. A sukwane Dada ta faɗo ɗakin tana cewa "kai Baqeeru lafiyarka ƙalau kuwa?" Ja tayi ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda yayi watsi da takardun zanen nashi duk yabi pensiran ya kakkarya. "Yau ni nake ganin abinda ya girmi kakata Saude, su kuma takardun da kayi watsi dasu laifin me suka yi maka? Anya kuwa Baqeeru shikenan haka zaka cigaba da rayuwa ba zaka sanyawa ranka haƙuri da dangana ba ka karɓi ƙaddararka da haƙuri da ikhlasi? Kai kenan kullum cikin ƙunci da baƙin rai ka ƙuntata rayuwarka ka ƙuntata rayuwar makusantan ka yau gashi har takardun ma baka ƙyalesu ba. Haba wannan wacce irin rayuwa ce, shikenan shi bawa Allah ba zai jarabce shi ba sai yace don me? Har ina murna ka fara samuwa kwana biyu shine kake nema ka koma ruwa, idan ka kassara rayuwarka a tunaninka ubanka yana da asara ne, uwarka da ƴan uwanka su zaka yiwa don kuwa ubanka yana da wasu ƴaƴan a yanzu ma ai ka gani yadda yayi watsi da kai ya koreka daga gidanshi bayan a lokacin da kake da lafiya yafi kowa cin moriyarka, to tun wuri ma idan zaka yiwa kanka faɗa  ka ɗauki rayuwa a yadda tazo maka kasan cewa rayuwarka kai kaɗai zata amfana gara kayi.” Sunkuyawa tayi ta tattare kayan daya watsar ta killace su a gefe tana cigaba da yiwa Baqeer faɗa, shi dai yayi bakam kamar bai san tana yi ba sai dai duk abinda take cewa yana saurarenta yana kuma gaskata duk abinda ta faɗa sai dai ya kasa daina jin ciwon yadda rayuwa tayi dashi, ya kasa yardar wa ranshi cewa shine rayuwa ta mayar dashi haka, yau shi Baqeer da yake ji da lafiya da ƙuruciya ne a kanannaɗe a keken guragu ya zama musaki, gurgu wanda ba zai ƙara amfanuwa da ƙafafunshi ba. Ko yayi ƙoƙarin cire abun daga ranshi sai wani dalilin yasa shi tunowa sai yaji gaba ɗaya rayuwar ta fita daga ranshi, ƙuncin zuciyar da yake fama dashi ya daɗu, sai yaji baya son ganin kowa kaɗaici kawai yake buƙata. Hannu yasa ya ɗauke hawayen daya gangaro daga idanunshi ya biyo kuncin shi, shikenan shi yanzu haka zai cigaba da rayuwa baya da wata mamora, zanen daya ɗauki dukkanin burikanshi na rayuwa ya ɗora akai na neman ya gagareshi yi. Gangarawa yayi ya rufe ƙofar ɗakin sannan ya koma kan katifarshi ya kwanta yana jin ina ma Allah zai ɗauki rayuwarshi da yaji daɗi ya rabu da dukkanin wasu ƙalubalen rayuwa da abinda ke cikinta. ***** Zama Zeey tayi tana kallon Mummy dake haɗa wasu kaya a ɗakinta, miƙewa tayi ta sake nufar ɗakin Nabila, kwana biyu yanayin data samu kanta a ciki yasa ko zama basa yi suyi hira, ita komai ma daina yi mata daɗi yayi shi yasa ta gwammaci ta killace kanta wuri ɗaya inda ba za'a dameta da hayaniya ba. Shiga tayi tana ƙwala kiran small Aunt sai dai ta iske ɗakin wayam Nabila bata ciki yanzun ma, hankalinta ne ya kai yanda ɗakin ya ɗan ragu, gashi babu wasu daga cikin kayayyakinta a ɗakin kamar ma dai tayi tafiya ne. Fita tayi ta koma ɗakin Mummy tana tambayarta inda Nabilan taje. Taɓe baki tayi tace "Share ta fushi tayi akan nayi mata faɗa shine ta haɗa kayanta ta koma gida, kin dai santa ai bata so ana faɗa mata gaskiya ni kuwa tana zaune a gidana ba zan kawo ido na zuba mata sai abinda take so zata yi ba.” A shagwaɓe tace "Kai Mummy don Allah, wai me Aunty Nabila take yi miki ne da kullum sai kin yi mata faɗa, duk ƙoƙarinta nata burge ki ba kya gani? Yanzu har wani laifi ma take yi da za’a dinga yi mata faɗa?” "Au haka ma zaki ce bayan duk abinda nake yi saboda ke nake yi, har wani ƙoƙari take yi ta burgeni daga neman suna kawai, tana dai yi don ta burge waɗanda take son burgewa amma bani ba.” "Ni dai Mummy don Allah ki daina abinda kike yi mata wallahi bana jin daɗi kamar ba ƴar uwarki ba, kefa kike yi mana faɗa akan rashin jituwarmu da Kabir amma gashi ke kuma kina yiwa ƙanwarki hakan.” Kallon Zeey tayi baki buɗe tama kasa ce mata komai, da bata san halin Zeey ba da ta mata faɗar rashin kunya. Tashi tayi ta fita daga ɗakin tana cewa  "Ni gashi sam bana jin daɗin zaman gidan nan idan bata nan gashi yanzu kinsa tayi fushi tayi tafiyarta gidan Inna, dole ne ma naje nayi bikonta gaskiya ko kuma na bita can mu zauna tare amma bazan zauna wancan Kabir ɗin nayi mini jaye-jayen tarkacen abokanshi ba.” Tayi maganar a shagwaɓe tana fita daga ɗakin *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR*    *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI* {27} Zeey na shiga ɗaki ta kira wayar Nabeela sai dai harta katse bata ɗauka ba, takaici ya kamata ta cilla wayar gefe, mamakin kanta take yiwai har da jan faɗa akan faɗan da bai shafeta ba, so take ta samu yiwa wani magana amma bata san wa ba. Ƙofar ɗakinta aka buɗe hakan yasa ta kalli wurin don tasan Mummy ce. Shigowa tayi tana kallon ɗakin kamar ba yanzu da suka tashi tace ta ɗan gyara ba amma yafda ta tafi haka ta dawo ta sake samun ɗakin babu alamun gyaran, sai ma ƙara ɗan batashi data yi, Mummy ce ta kalleshi wanda gaba ɗaya hankalinshi baya maganar da take, cike da mamaki tace "Senate ni kam lafiya dai ko? Tunda ka shigo hankalinka ba a jikinka yake ba." Ƙaramar iska ya furzar daga bakinshi yace "Yau zamu yi taron manyan unguwar nan, zan ji ƙorafe-ƙorafensu na kuma taimaka musu tare da yardar su kuma zasu taimakeni har kar siyasa ta." Ajiyar zuciya tayi tace "Ah Alhamdulillah, ba dama abinda muka zo zama anan din kenan ba?" Kai ya jinjina yace "Haka ne amma ba kya tunanin mutumin can zai iya ruguza mana shirin mu?" Ajiyar zuciya tayi don ta gane Badaru yake magana tace "Da wannan kuma, amma shi don neman masifa shikenan taron ma ba zai bari ayi lafiya ba? In ba zai zo ba kawai ya zauna a gidanshi mana." “Taya zan hanashi zuwa bayan kina ganin yana daga cikin dattijan unguwa.” Kai ta girgiza tana riƙe hannunshi tare da cewa “Mantawa kayi wanene Badaru? Ai bana ji zai zo in har yasan taron naka ne, ko ka manta ko ganinka yayi a hanya canzata yake yi? Bayan kuma dama an riga anyi muku tsakani dashi.” Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke yace “Har kinsa naji hankalina ya kwanta, sam yanzu bana son abinda ya faru tsakaninmu shekarun baya ya sake faruwa.” Tana murmushi tana cewa “Ba zai faru ba in Sha Allah! Muna hawa kujerar zamu bar Kano mu koma Abuja daga nan kuma ka fara plans ɗin ka da cikar burinka na zama govenor.” Rungumeta yayi tabbas shi kam har mamaki yake yi yadda manyan mutane ke yawan complain akan matansu don shi dai kam sai hamdalla, kanshi ta shafa tace “Allah ya kare mini kai Senate.” Nan yace Ameen yana miƙewa daga kan gadon. ****** Baqeer ne ya turo kekenshi zuwa falo inda Dada take, wanka yake son yi amma bai san ta yadda zai yi yace mata yana son ruwan ɗumi ba, sam tausayi take bashi, sau da dama in zai yi wanka kafin ya nema ma zata ce ta kai mishi ruwan banɗaki amma yau zuwan baƙuwar nan yasa ta sha’afa, dariyarta ya jiyo ta bayanshi tana cewa “Ka huce ka gama fushin da takardar?” Fuskarshi sam babu fara’a ya ɗan kawar da kai kaɗan, plate ɗin hannunta ta miƙa mishi wanda ke ɗauke da yankakkun kayan marmarin da Zeey ta kawo. Bai amsa ba sai dai yanayin kallonshi da ya canza jiki a sanyaye yace “Dada daga ina kika samu fruits?” Murmushi tayi tace “Aiko mana aka yi.” Cike da kokwanton kalamanta yake kallonta ko me ya tuna sai kuma fuskarshi ta canza sosai yace “Ba dai yarinyar ɗazu bace ta kawo?” Dada tayi saurin waskewa tana cewa “Ruwan wanka kake so hala? Don dama ɗazu nake tunanin ɗora maka.” “Itace ko?” Ya ƙara jifanta da tambayar. Kallonshi tayi tace “Wai Baqeer ni kam fitinar me kake ji da ita ne? Nace aiko mun aka yi ba shikenan ba?” Ajiye plate ɗin yayi ya gara kekenshi zuwa ɗaki, rufewa yayi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, me kenan take yi haka? Yaji ta bada motar da bai san tata bace ko ta aro ce amma banda ta dinga kawo abu cikin gida, ba zai lamunci wannan ba tunda ba saninta suka yi ba. Waya ya ɗauka ya kira Salim, ringing uku ya ɗauka yace “Baqeer inzo ne?” Kai ya girgiza tare da yin shiru to wai ma taya zai ce a bashi number ta? Bayan ko sunanta bai san yadda zai yi ya tambaya ba? Sumar kanshi ya shafa yace “No babu komai kawai dai tambayarka zan yi ya kasuwa?” Cike da jin dadi Salim yace “Alhamdulillahi gashi nan muna fama.” “Don Allah ko zaka leka Umma kaga ya take? Mun yi waya amma hankalina ya kasa kwanciya.” Ba tare da wani dogon nazari ba yace yana tashi zai biya, shiru suka yi ya ɗan yi gyaran murya kaɗan yace “Ranar da muka je asibiti da motar wa ka kaini ne ni kam? Ina taso na tambayeka.” Salim yayi shiru yana nazarin abinda zai ce, Baqeer ne yayi saurin cewa “Kar kayi mini ƙarya Salim please, motar ƙawar Maryam ce ko?” Yawun bakinshi ya haɗiya yace “Eh! Am really sorry da ban sanar da kai ba, Maryam ce tace nayi using ɗinta tata bata ga key din ba.” Kai ya jinjina kenan har hancinshi yasan ƙamshin ta? Nan da nan yaji hankalinshi ya tashi, lallai Baqeer “Don Allah number fa? Kana da shi? Ina son nayi mata godiya.” Cikin jin daɗi Salim yace “Yanzu kuwa zan turo maka.” Nan suka yi sallama ya kashe wayar. Muryar Dada ya jiyo tana buga kofa tana yan mita “Ni kam hala dai halinka gaba ɗaya aka canza? Yanzu ko itan ce ta kawo sai kace ba zaka sha ba? Kyautatawa ce ai ba roko ba, maimakon ka amsa kayi godiya sai ka hau fushi kaƙi amsa?” Hannu biyu yasa ya shafi fuskarshi ba wai bai gode bane haka kawai yake ji wani sashin na zuciyarshi na tunanin rayuwar yanzu, mahaifinshi ma ya banzatar dashi taya wata da bashi da haɗi da ita zata dinga kula dashi kamar yadda take yi? Dole zai yi mata magana akan abinda tayi. ***** Zeey ce zaune a ɗaki ta shige cikin bargo tana kallon korean drama ‘Killing Vote’ mind dinta gaba ɗaya yana kan tv ɗin dake manne a bangon ɗakinta, wayarta ce tayi ƙara da takaici ta janyota, number ce hakan yasa ta kara a kunnenta ba tare da tayi magana ba, Baqeer shima kasa magana yayi sai sautin numfashinsu ne daya sauka a tare, Zeey cike da mamaki ta kalli wayar tata ta sake karawa a kunnenta haka kawai taƙi yin magana don rainin wayon ya isa a kira ka a waya a ƙi magana kuma. Baqeer kuwa ji yayi ya kasa cewa komai, to yace me? Mun gode karki sake? Ko kuwa karki sake zuwa? Bayan yasan in tace ta daina ba daɗi zai ji ba. Takaicin kanshi da rashin sanin abinda zai ce duk ya isheshi. Zeey ranta ya ƙara ɓaci don ta tabbatar wannan kuma rainin wayau ne, a speaker tasa wayar kawai ta ajiye a gefe ta cigaba da kallonta, Baqeer ganin kuɗin shi na tafiya ba tare da yasan me zai ce ba yasa ya kai hannu zai kashe wayar, mamaki ne ma ya kamashi da ya fara jiyo sautin kallo a cikin wayar, nan ya kashe tare da ajiye wayar akan katifarshi, haushin kanshi ya ƙara kamashi, haka zai zauna komai bai iya ba kamar wani yaron da aka haifa yanzu? Ƙofa ya buɗe Dada na ganinshi ta ɗauke kai ta cigaba da tsinke zogalen da take yi, kusa da murhu ya nufa ya sunkuyo taga yana neman haɗa wuta, duk yanda taso ta ƙunshe dariyarta kasawa tayi haka tana gani ya haɗa wuta yasa tukunya da ruwa, Dada abin sai ƙara bata dariya yake da yanda fuskarshi take a ɗinke babu alamun fara’a, yana gamawa ya koma ɗaki. A hankali ta girgiza kai lallai Baqeer babu shakka zuwan yarinyar nan da shawarar da take bashi yasa ya fara canzawa, murmushi ta saki ko ƴar gidan wacece? Tabbas zata tambayi Maryam in tazo. Zeey kuwa ganin an kashe wayar tayi tsaki tace “Ni dai kwanan nan ban san da wasu irin mutane nake haduwa ba.” Ta sake maida hankali kan kallon aka sake kiran ta, kanta ta cusa cikin bargo ta ɗan yaye bargon tana bubbuga ƙafafunta, cike da takaici ta janyo wayar gwara ta dauka in kudinsu ya ƙare sun daina damunta, tana ɗauka tasa a speaker ta ajiyeshi a gefenta “Don Allah a maidani kunne bana son a ajiyeni a gefe.” Kalaman da suka fito kenan daga cikin wayar wanda ya sata bin wayar da kallo, ganin number Junaid ya sata sakin murmushi sosai wanda har haƙoranta suka fito “To ya?” “Haka dai zaka cigaba da saka mini ido kamar mai CCTV ko?” Shima murmushin yayi yace “To ni dai ɗari bisa ɗari ina da yaƙinin babu wanda yasan ki sama dani.” “Shiyasa ka turo a ganni?” Dariya yasa yanzu kam tace “Kar ka wani wayance nasan kaine.” Ya ɗan yi juyi a kan gado yace “Wato dai kin gama sanina kema?” Kafaɗa ta ɗaga kamar a gabanshi take tace “Ai ƴar ƙure ne abun?” “Na sakar miki ƙotar don nasan tabbas aka fara tsab za’a ƙure ni.” Hira suka cigaba dayi sosai wanda kana ganinsu kasan sun saba da juna sosai, can tace “Ya aikin ba zaka dawo nan ka cigaba ba?” Ajiyar zuciya yayi yace “Dole na dawo tunda an ce na aureki.” Kai ta girgiza tace “Kasan dai bazan aureka ba, na sha faɗa maka abota ne kawai a tsakanin mu.” “Nima na sha faɗa miki abota tana komawa soyayya, kuma a kaina zaki amince.” Shiru ta yi jin wani abu yazo ranta, da sauri ta gyara zama tace “Junaid please serious magana when will you be back? Akwai wani brothern ƙawata da ya samu matsala a kafafunsa, an dai ce paraplegia ne  so nasan ku da yake aikin ku ne kun san ko akwai wani abu da mutum zai yi.” Cike da kulawa yace “Subhanallah, garin yaya?” Tace “Am not sure exactly nasan dai accident yayi.” Ya ɗan yi ajiyar zuciya yace “Lallai he needs us, kinga karatun da aikin da nake kenan na physiotherapist so ina saka ran nan da 4days zan dawo don abinda ma na kira na sanar dake kenan, idan na dawo zan fara aiki a asibitin Dad ɗina in yaso sai ki ma friend ɗin taki magana su kawoshi mu gani, ko bai warke ba at least zai iya controlling ɗin jikinshi.” Wani irin daɗi ne ya kamata wanda yasa shi cewa “Yana da aure ne?” Tace “A’a menene?” Shiru ya ɗan yi sai dai yasan Zee ba yanda za ayi taso gurgu yarinyar da manyan maza kyawawa masu kuɗi ma bata kulasu ba. Da wannan suka cigaba da hira kafin suyi sallama, wani nishaɗi ne kawai yake sake rufeta don Junaid har shaidar yabo an bashi saboda ƙwazonshi tana saka ran zai taimaki Baqeer sosai, ji take ba zata ba gobe saboda akwai inda zasu da Mummy amma jibi zata je ta sanar mishi. ****** Hadiza ce kawai ke share hawayenta ganin  ta rasa me zata dafa a cikin gidan, gidan babu komai balle ta lallaɓa ta dafa wani abun, gashi ko naira biyar bata da shi balle ta sa a siyo mata kuka, yarinyarta tasa a baya ta fito daga ɗaki, kishiyarta dake wanke tsakar gida ta kalla don ko abinci basa hadawa saboda ita tana ɗan aikinta na gwamnati tana samun ƴan kuɗaɗen ta. Gida ta nufa tana tafe tana hawayen tunanin Baqeer don tabbas wannan abu ita yafi shafa. A ƙafa taje tafiyar sama da minti ashirin, da Salim suka haɗu shima zai je gidan Umma, nan suka gaisa suka ƙarasa gidan sun ƴar hira, ta bayansu kawai suka ga an tallewa Salim ƙeya sai ji kake tass. Da sauri suka juya a tare, Kamalu ne anci riga da wandon gayu yana girgiza ƙafa, Bashir na gefenshi don ya kira shi zai aikeshi ne ya hango Salim ya taho da sauri shima yabi bayanshi. Da mamaki Salim yake kallonshi yace “Kamalu menene hakan?” Daƙuwa yayi mishi yace “Gidanku ne, uban me kazo yi gidan mu? Ko zuwa kayi kaja faɗa dani don na ƙwace Roshni ta dawo inda ya kamata?” Wani kallon mamaki yayi mishi yace “Yanzun ma zancen Roshnin ne?” A ƙufule Kamalu yace “Kasan Allah inma ni kake  nema da fitina daidai nake da kai, muje filin casu kaga hauka.” Tsaki Salim yayi yana neman shiga ciki Kamalu ya finciko shi yace “Wai ni ka yiwa tsaki? Kai dan gidanku ni sa’anka ne?” Salim na neman ƙwace jikinshi amma Kamalu sai hayagaga yake yi yana zage-zage wanda yasa Hadiza saurin shiga ciki don ya kira azo ayi mishi magana. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce*        *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA TAKWAS* {28} Bashir ne ya rirriƙe Kamal daga ƙoƙarin kaiwa Salim duka da yake yi shi dai Salim yayi tsaye kawai yana kallon shi da haukar da yake yi don baya saka Kamal a sawun mutane masu hankali. Umma ce ta fito daga cikin gidan tana cewa "Kamal lafiya kuwa?" Don ko da Hadiza ta shiga gida ta faɗawa Abu ko zata fito tayi mishi magana gashi can a ƙofar gida yana cakumar Salim da faɗa cewa tayi babu inda zata, ai haka nan Kamalu ba zai nemi rigima dashi ba sai idan shi ya fara tsokanarshi don haka a ƙyaleshi yaci ubanshi yadda gobe ko kallon banza bai isa yayi mishi ba tunda yasan idan yayi ma ba ƙyaleshi zai yi ba, sai Umma ce ta saka hijabinta ta fito jin da Salim ake faɗan tasan kuma wurinta yazo tunda dai Baqeer baya gidan yanzu bare tace ko wajenshi yazo. Wani banzan kallo yayi wa Umma yace "Malama ki rabu dani na koyawa wannan tsageran yaron hankali, kai har ka isa kayi mini tsaki a ƙofar gidanmu don ubanka?" Ya nuna Salim da yatsa yana ƙoƙarin kai mishi mari sai dai Bashir ya rirriƙe shi ya hanashi kaiwa ga Salim ɗin. "Umma ina yini" Salim ya durƙusa yana gaisheta kamar ba da shi Kamalu ke faɗan ba. "Lafiya lau Salim, me ya haɗa ka da Kamalu ne?" Murmushi ya saki yace "Wallahi Umma babu abinda nayi mishi kawai ina tafiya naji ya talle min ƙeya yana cewa zai koya mini hankali." Ita kanta Umma sai da tayi dariya jin wai ya talle mishi ƙeya kamar wasu ƙananan yara. Kallon Kamalu tayi tace "Kayi haƙuri kome yayi maka kaji Kamalu zan yi mishi faɗa In Sha Allahu ba zai ƙara tsokanarka ba". Ƙwace jikinshi yayi daga riƙon da Bashir yayi mishi ya saki wani dogon fito kafin ya kalli Salim da har lokacin yake durƙushe yace "zamu haɗu ne don kada ka ɗauka ka sha, sai ka raina kanka wallahi duk ranar daka sake ka shigo hannuna" ya wucesu anan yana tafiyar ƙwambo irinta nigogi. Gaba ɗaya suka bi bayanshi da kallo har sai da ya karya kwana sannan umma tace "Salim mu shiga daga ciki ko?" Har ya miƙe zai bi bayanta zuwa cikin gidan sai kuma ya tuna da Baba da tijarar da yayi mishi akan Baqeer to ina ga ace ya ganshi a cikin gidanshi ai duk abinda yayi mishi shi ya saya da kuɗin shi don haka yaja ya tsaya yace "a'a Umma ba sai na shiga ba, dama Baqeer ne yace nazo na duba mishi ke". Sai taji ƙwalla ta cika idanunta, Allah sarki Baqeer wato har a halin da yake ciki ma ita ce damuwarshi, yasan rashin shi a kusa da ita ba ƙaramin taɓa zuciyarta yake yi ba to amma ya zasu yi bayan suyi haƙuri su rungumi ƙaddarar data raba tsakaninsu tunda Baba yayi rantsuwar ya bar zama mishi a gida kenan ita ma kuma baza taso ya ƙara dawowa cikin gidan da zama ba gara ya koma gefe yayi rayuwarshi har Allah ya dubesu ya kawo musu ɗauki a cikin halin da suka tsinci kansu a ciki. Tayi murmushi "Baqeer kenan, abinda kullum sai ya kirani a waya mu daɗe muna hira shine kuma ya taso ka daga kan ayyukan ka don kazo ka duba mishi ni kawai, bai gamsu da cewar da nake yi ina lafiya ba kenan". "A'a Umma ba haka bane, kin san bai taɓa daɗewa irin haka bai ganki bane shi yasa duk yabi ya damu amma ba don bai yarda dake bane". "To ai shikenan tunda kareshi kake yi sai ka faɗa mishi lafiya ƙalau muke nima ina nan tafe naje na ganshi ai In Sha Allahu". Hannu yasa a aljihu ya fito da kuɗi naira dubu biyu ya miƙa mata "Umma gashi wannan babu yawa dai". Kallonshi tayi ta kalli kuɗin da yake miƙo mata tana girgiza kai tace "a'a Salim bazan karɓa ba, gaisheni da kazo yi ma ya wadatar, nagode ƙwarai Allah yayi muku albarka". Ƙara miƙa mata kuɗin yayi yace "na ɗauka ni da Baqeer ɗaya muke a wajenki, kenan ɗa zai yiwa mahaifiyarshi alheri ta maida". Hannu tasa ta karɓi kuɗin tana yi mishi godiya haɗe da jera mishi addu'o'i. Sosai yaji daɗin hakan kuwa shi yasa kuma yake son Umman Baqeer ɗin saboda yadda ta ɗauke su duka ƴaƴanta bata taɓa bambantasu ba a komai, yadda take zaunar dashi tayi mishi nasiha haka suma take yi musu bare shi da yayi maraicin iyaye tun yana ƙaramin shi. Tana shiga gidan ta miƙawa Hadiza kuɗin hannunta ba tare data ƙirga taga ko nawa bane. "Na miye wannan ɗin Umma?" Ta tambayeta. "Salim ne ya bani sai kije ki riƙe a hannunki don nasan ba lallai ne da akwai wani abu a hannunki ba". Kuka kawai ta fashe dashi cikin ranta tana ƙara jin ƙaunar mahaifiyar tasu mai yawan kyautayi da tausayawa a garesu. Sai da tayi kukanta ya isheta sannan ta share hawayenta tace "nagode ƙwarai Umma, Allah ya ƙara girma yaja mana da rayuwarki, wallahi kamar kin san fitowar nan da nayi rashin abincin da zamu ci ne dalili, yau na tashi ko ƙwaya bani da ita ga yara sun kusa tasowa daga makaranta dama kuma ba wani abu na basu ba da safe koko ne na saya musu da ɗan canjin da ya rage mini suka sha suka tafi makarantar. Yanzu shikenan a haka zamu yi ta zama cikin wahalar rayuwa Umma? Dama Yaya Baqeer ne yake taimaka mini yanzu shima ga yadda Allah yayi dashi shi kuwa Babansu Aydah ko zamu mutu da yunwa ba damuwa yayi ba". Da tausayi Umma ke kallonta tunda ta fara kukan, ita dama tunda ta ganta yanzu da ranar nan tasan ba zuwan daɗi tayi ba, miji ne ta gamu da wani irin mugun mutum da bai san ya sauke haƙƙoƙin su dake kanshi ba. Idan ma da ace yana basu abinci sauran haƙƙoƙin su ne baya saukewa da sauƙi to shi ko abincin ma ba basu yake yi ba ba don ba zai iya basu ba sai don bai ɗauki hakan a matsayin wani abu mai muhimmanci daya zame mishi dole ba. Haƙuri Umma tayi ta bata akan irin zaman da take yi a gidanta, tashi tayi ta ɗaga katifa ta ƙirgo wasu kuɗin ta dawo ta miƙa mata tace "Kuɗin kujeruna ne dana sayar dama nace zan shawarceku muga abinda ya kamata muyi dasu don zama a haka bai ganmu ba daga ni har ku don har gara ma Maryam bata nemi komai ta rasa ba a gidanta tunda mijinta na bakin ƙoƙarin shi a kanta, wacce sana'a kike ganin ya kamata muyi tunda dai kin san Allah ne gatanmu Baqeer ne gatanmu shi kuwa a yanzu sai dai ma a tallafa mishi tunda ga yadda rayuwa tayi dashi, dole ne ki dage ki nemi na kanki don ba zai yiwu ki cigaba da zama a haka ba abincin da zaki bawa ƴaƴanki yana gagararki.” Karɓar kuɗin tayi tana jujjuyasu tace "To ni Umma wacce sana'a zan yi bayan kin san mutumin nan idonshi idon kuɗi sai yasan yadda yayi ya rabani dasu, dama ace zan samu aiki nema ko na cleaner ne sai nayi amma a yanzu ina fara sana'a zai kafa mini ƙahon zuƙa sai yaga yadda yayi ya rabani da ita hankalinshi zai kwanta. "Ai kuwa dole ki tashi ki nemi na kanki ki kuma san yadda zaki yi ki tattala abunki ki bar bari yana sanin samunki tunda wanda yaji ya gani ya ɗauke miki larurorin gidanki yanzu baya dashi, ita kishiyarki da yake ta iya tattala kayanta ai kinga bata cikin wahalar dake kike ciki. Dole ne ki nemi wani abu ki dinga yi da zaki taimaki kanki ba kullum ba kina jira ayi miki ba.” "To Umma, In Sha Allah zan duba naga me ake buƙata a wajen namu sai na fara, dama Yaya Baqeer ne yace zai saya mini injin markaɗe idan yaje Abuja wajen gasar nan ya dawo to ashe ma baya da rabon zuwa wajen gasar tunda ga ƙaddarar data afko mishi," ta ƙarashe maganar tana share hawaye. Itama Umma hawayen ta share sai kuma tace "Nawa ne injin markaɗen? Idan wannan kuɗin zai saya ai gara a saya ki fara sana'ar akan dai kiyi ta zama a haka babu abun yi abincin da zaku ci yana gagararku idan yaso abinda ya ragu daga cikin kuɗin sai na sayi wani injin taliyar na auni fulawa na dawo da yin aikin taliyar dama kwana biyun nan sai shigowa ake yi nema sai dai nace babu.” Murmushi ta saki jin Umma zata saya mata injin markaɗen tace "Wallahi Umma ban san nawa bane sai dai na bincika naji duk yadda ake ciki zan kira na faɗa miki.” Tace "to shikenan kiyi hakan, Allah ya taimake mu ya dafa mana". "Ameen Umma, bari na tashi na koma kada yaran nan su dawo su tarar bana nan gashi ban bar musu komai da zasu ci ba.” ***** Kayanta ta haɗa cikin akwati kamar mai yin wata idan ta tafi ta janyo trolley ɗin ta nufi ɗakin Mummy, bata tarar da ita a ciki ba sai ta fita parlour nan ma bata ganta ba sai data shiga kitchen sannan ta ganta suna haɗa abinci ita da masu aikinta. Kallonta Mummy tayi ta kalli ƙatuwar akwatin da take ja tace "Ina zaki haka da akwati baby kamar mai gudun hijira?" Turo baki tayi gaba irin na shagwaɓaɓɓun yara abinda ya riga ya zame mata jiki har ma bata sanin lokacin da take yi tace "Nima gidan Inna zani tunda kin korar mini small Aunt gashi nan taƙi dawowa ko ɗaukar wayata ma bata yi nasan kuma duk laifinki ne ya shafeni." cikin ranta kuwa cewa take yi gara ta tafi gidan Inna yadda zata samu tana zuwa duba Baqeer akai-akai don tasan Inna ba hanata fita zata yi ba bare tabi ba'asin inda zata je. Baki Mummy ta taɓe tace "Da dai wata ce bake ba, ke ɗin ce kike iya zuwa wani wurin ki kwana?” Dire-dire ta hau yi tana cewa "Allah Mummy idan na tafi sai kin je kin yi bikona kafin na dawo, gara ma na matsa na baku wuri kinga ai sai ina nan Kabir zai samu wacce zai takurwa.” Har ta juya zata fita sai Mummy ta tsayar da ita tace "Da dai kin haƙura da tafiyar nan har Daddynku ya dawo ki faɗa mishi kin dai san halin shi bai cika son yawan zuwa wani wuri a kwana ba.” Dawowa tayi ta rungume Mummyn tace "Please mana Mummy idan ya dawo sai ki faɗa mishi, kin dai san yadda zaki lallaɓa shi kada yayi faɗa amma wallahi idan ni na tambayeshi ba bari na zai yi ba kina dai ji ranar nan daga cewa ina so naje Ɗambatta ya rufe ido yana zazzaga faɗa kamar cewa nayi idan naje bazan dawo ba.” Zeey ita ce weakness ɗin Mummy bata iya yi mata musu duk abinda tace tana so shi take yi mata don haka ta kasa hanata tafiya gidan Innar kamar yadda ta buƙata duk kuwa da tasan idan Daddy ya dawo ya tarar bata nan sai yayi faɗa. "Shikenan Zeey ki gaishe da Innar amma fa idan yace bai yarda da zamanki acan ba dole ki dawo don kin sanni ni dai bana son tashin hankali". "Thank you my Mummy, ba ma zai ce ba In Sha Allah, na tafi sai na dawo" taja akwatinta ta fice daga kitchen ɗin tana jin wani tsantsar farin ciki yana ratsa ta, ko babu komai ta samu hanyar zuwa taga Baqeer ba tare da ta yiwa Mummy ƙarya ba. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ASHIRIN DA TARA* {29} Zeey ɗaya daga cikin motar Mummy ta shiga wacce da ita take amfani saboda Daddy bai bata mota ba har yanzu, fuskarta ta daka da tafin hannunta ta tuno yanda ta dinga zuba atamfofinta cikin akwati dazu da tana haɗa kaya, yanzun ma sanye take da brown doguwar riga har ƙasa take sai wata tattara da aka yi a daidai ƙugunta da black colour, ta naɗa mayafi black a saman kanta, ba mai kwalliya bace amma fuskarta bata rabuwa da kwalli da kuma lipstick, ƙamshin turaren nan nata wanda ya gama bin jikinta wanda sau da dama ko bata sa ba baya barin jikinta na Dior Miss Dior, goshinta ta sake bugawa lallai kanta ba ƙalau ba, yau wai ita ce da karya don ta tafi gidan Inna saboda Baqeer? But why? Tambayar data zo kanta ta furzar da iskar bakinta tace “Whatever ni dai nasan abu ɗaya tausayinshi nake ina kuma so naga ya dawo yanda yake da.” And? Tambayar da zuciyarta tayi mata kenan tace “Hmm and ya nunawa Babanshi kuskurenshi na wofintar da rayuwarshi da yayi.” And? Zuciyarta ta sake tambayarta, ta ɗan kwantar da kanta jikin kujerar motar kafin tace “And? Shikenan?” Idanunta ta lumshe tana tuno wasu abubuwa da suka faru tsakaninsu a shekarun baya, yaƙe tayi kafin tayi wani murmushi sama-sama, nan ta ja motar ta bar gidan, zuciyarta na kwaɗaita mata dawowar Junaid don tasan tabbas Baqeer zai samu taimakon da yake buƙata. Mai makon tayi gidan Inna kamar yadda ta tsara gidan Dada ta fara yi duk da taso tsayawa ta siyan musu wani abu tasan bata isa ba, tunda tasan waye Baqeer tun kafin ma ya hanata zuwa gara ta shiga hankalinta. ***** Baqeer yau ya tashi duk zuciyarshi babu daɗi sakamakon mafarke-mafarken da yayi daren jiya na auren Asiya da Bello wai gasu nan a gabanshi yana bata abinci a baki, suna yi mishi dariya, ko kunu da ƙosan da Dada ta kawo mishi bai iya ci ba sai kunun daya kurɓa kaɗan wanda ɗacinshi ma yaji. Duniyar gaba ɗaya ta canza mishi babu wani abu da yake burgeshi a cikinta, kamar a mafarki yaji Dada na mata lale da zuwa, kekenshi ya tura da sauri zuwa saitin ƙofar ya jingina da ƙofar kamar yadda ya saba in yana son jin muryarta. Dariya ta6i tace “Dada faɗa mini gaskiya dama jirana kike yi ko?” Tace “Kamar kin sani wallahi har addu’a nake yu Allah ya kawo mini ke ki yiwa yaron can faɗa ko abincin safe bai ci ba ɗan kunun da ya sha ina ji bai fi cokali biyu ba.” Baki ta buɗe tace “Dada rufa mini asiri ina na isa?” Hannunta ta kama suka shiga ciki, Baqeer na jin almun tahowarsu ya burga kekenshi da sauri zuwa wajen window garin sauri har hannunshi ya buge da jikin bango ya ƙarasa yana ɗan murza hannun a jikin cinyarshi. Dada tana ƙwanƙwasawa kafin ma yayi magana har ta buɗe ƙofar, Zee daga bakin kofar ta tsaya tare da juya baya da sauri don ita kam bata san me zata ce ba “Tunda baka jin magana ta nace bari tazo tayi maka faɗa.” Kallon Dada yayi fuskarshi a tamke sosai yace “Dada me kike faɗa haka don Allah? Salon a samu damar rainani.” “Raini na nawa kuma? Tunda gaka nan kullum a ɗaki kamar munafukin miji.” Saman goshinshi ya shafa don lamarin Dada ya wuce misali, Zeey kuwa dariya ta bata ta juyo tana kallonshi tana ƙunshe dariyarta, Dada ta bar wurin tana cewa “To sai ka nuna mana ba hakan bane ai.” Zeey ce ta kalleshi fuskarshi sam babu annuri a ciki, tana nan tsaye ta jingina da ƙofar dakin, gyaran murya yayi yace “In ba wani abu ki maida mini ƙofar ki rufe.” “Ni?” Ta tambaya tana waigawa bayanta ko zata ga wani, takaici ne ya sake rufeshi don banda rainin wayau ba ita kaɗai bace a wurin? Baya tayi tace “Kofarka ce.” Bai tanka mata ba ya burgo keken shi zuwa ƙofar ranshi duk a ɓace don ya kula ta raina mishi wayau, sai da yazo daf da ƙofar tasa ƙafa ta jikin ƙofar ta ƙasa ta tare wanda ya hanashi rufewa inya ja kuma yasan bugewa zata yi. Kallonta yayi sai yaga itama kallonshi take yi tace “Dada tayi maka faɗa ba kace komai ba.” Kallon mamaki yayi mata mai cike da ayat tambaya, tayi mishi alamu da abinci da hannunta, shima alama yayi mata da ido na meye nata a ciki? Yawun bakinta ta hadiya tace “Ƴar aikenta.” Kallon kafarta yayi ta sake gyara ƙafar tace “Muje waje ka bata hakuri.” Da mamaki ya kalleta yaushe yarinya kamarta sa’ar Maryam bama Hadiza ba ta fara bashi umarni? Ta ɗaga mishi kai, duk yanda take shakkarshi da yanzu gani take yi dole ne ta canza. Baqeer mamakinta ne ya rufeshi kawai ya juya yana neman komawa ciki, hannu tasa ta rike hannun wheelchair ɗin, cike da mamaki Baqeer ya waigo ya kalleta, idanunshi ta kalla shima ya kalleta wanda tunda suke haduwa basu taba tsayawa kusa da juna haka ba sai yanzu, ji tayi gabanta na wani irin faduwa, tana shakkar Baqeer sosai shi kuma kallonta yake tabbas yasan kamaninta a wani wuri, amma a ina? Zeey ce ta daure tare da haɗiyar yawun bakinta tace “Dada ce keso ka fito abu take so ta nuna maka.” “Da shine baki faɗi gaskiya ba kika fara wani zancen?” Hannunta ta zare jikin wheelchair ɗin don yanda take ganinta daf dashi yasa ƙafafunta sun ɗan sage, baya taja wanda hakan yasa ta fitowa daga ɗakin, Baqeer ne ya tura keken ya fito shi kanshi mamakin kanshi yake yi. Sakin baki Dada tayi tana kallonshi har ya fito waje yaja ya tsaya a gefe yana wani kakkauda kai. “A’a Baqeeru? Da na ɗauka abu kake so ba dai fitowa kayi shan iska ba?” Kallon Zeey yahi da sauri wacce tayi saurin yin gyaran murya tace “Dada kin manta abinda zaki nuna mishi?” “Ni? Me zan nuna mishi ni kuwa?” Baqeer ya kalli Zeey sosai, lallai yarinyar nan, kekenshi ya fara neman turawa ya koma tana kallon Dada tace “Dada maganar fa da muka yi akan halin mutum, in ya zauna wa yake so ya kula da mahaifiyarshi?” Jaa Baqeer yayi ya tsaya ba tare da ya juyo ba, wani abu ne ya samu Ummanshi? Zeey tana wurin Dada tace “Dada kina dai ganin mutum shine gatan su Umma, kina kuma ganin yanda Baba ke abubuwanshi don haka mu dai shawarace namu mutum ya samu abun da zai yi don ya taimaki kanshi, akwai abubuwan yi kala-kala da ba sai da kafa ake yinsu ba, wanda basa gani ma suke sana’a bare.” Idanun Baqeer ne suka kaɗa suka yi jaa ya waigo yana kallonta, Dada kuwa cike da jin daɗin kalamanta tace “Hmm gashi ni kuma dai ba daɗewa zan yi a duniya ba, duk da ba wanda yasan gawar fari Baqeer dole ka ajiye wannan kuncinin ka san abun yi, in kuma ba so kake Fatima ta tattaro ta dawo nan ta kashe aurenta saboda kai ba.” Kallon Dada yayi wani abu na sake taso mishi, maimakon yayi ciki kawai saii ya fita waje yana tura keken, Dada har zata bi bayanshi Zeey ta riƙeta tare da yi mata murmushi tace “Mu barshi Dada dole ya dawo Baqeer ɗinshi nada sannan akwai wani da zai zo ya dubashi ko mu kai shi asibiti sai dai nasan ba yarda zai yi ba in yaji daga nine.” “Yayi miki faɗan kayan marmarin da kika kawo ne?” Dada ta tambayeta tana kallonta. Kai ta girgiza alamar a’a, “Hmm to shekaran jiya ko abu ɗaya bai sha ba saboda faɗa.” Raurau tayi da ido tace “An kusa hanani zuwa wurinki da alama.” “Shareshi wannan ne bai isa ba, in zaku je wurin mutumin sai ku tafi da Salim, in ma zuwan ne ya zama dashi ina ganin zai fi fahimta.” Kai ta ɗaga cike da gamsuwa. Baqeer kuwa keken shi ya burga gaba da gidan Dada kaɗan inda ya tsaya yana kallon mutane kowa nata hada-hadar kasuwanci, kowa dai harkar neman kudin shi yake yi. ******** Abu ce ta kalli yaron da aka aiko tace “Kai bana son iskanci wallahi wannan robar ko ba’a faɗa ba an ɗiba ruwa aka ƙaramin a cikin tsumin nan don haka ka koma kace bazan amsa ba.” “Don Allah ki amsa ki bata kuɗinta tace bata so.” Tsaki tayi tace “Wallahi ko kabar gidan nan ko nasa Kamalu yayi maka dukan tsiya.” Juyawa yaron yai a tsorace don kuwa sun san waye Kamalu, tsaf yanzun nan sai yaji mishi ciwo. Jamila ce ta fito tana ƴan harare-hararenta, Abu ko kallonta bata yi ba, zama tayi akan kujera sai kuwa ta fara kakarin amai, ji kake buiu, ta sake yi buuui. Dariya Abu ta kwashe dashi tace “Hala kinci ƙuda ne ko tsutsa shi yasa kike ƙoƙarin yin amai?” “Kin manta maciji naci ba tsutsa ba.” Abu ta sake fashewa da dariya tace “A’a to wai dai ba cewa zaki yi ɓatan watan kika yi ba ko?” Jamila tayi ƙwafa ta koma ciki ranta na sake ɓaci. Umma na daga ɗakinta tana jiyosu, kai kawai ta girgiza… ***** Baqeer ya ɗan jima kafin ya dawo, sai dai kafin ya dawo Zeey ta tafi don yana tsaye tazo ta wuce bai kula ba, sai ita data ganshi, ta dade a gefenshi daga baya sai da taga yana shirin tafiya sannan ita ma ta tada mota tayi gaba, zuciyarta duk ba daɗi. Gidan Inna ta wuce kai tsaye. Inna na ɗaki tana ƙirga kuɗi tana jin Zeey ta ɗaga katifa ta sakasu sannan ta kuna radio tana ji kamar ba a gidan ake sallamar ba. Zee ce ta shigo tace “Hajiya Inna tawa dama nasan kina ciki magana ce bakyajin yimin.” Fuskar nan tata a ɗaure babu alamun fara’a tace “Tunda ke bakinki bazaiyi shiru ba sai kin faɗa ai ba laifi.” Zama tai tace “Hmm Allah dai ya kawo randa zaki saki rai dani.” Wani kallo ta mata tace “Yau kuma me ya kawoki? Bayan ba san zuwa kike ba?” “Aunty Nabila fa? Batanan?” “Ba’a sani ba, wai mai aikin ku ce Nabilan da baza’a barta tazauna a gidansu ba? Bayan in taje gidan naku banda aiki ba abinda kuke sata?” Kai ta girgiza tace “Kedai Inna neman faɗa kike amma yaushe aka sakata aiki a gidan?” A fusace Inna tace “Ke ai ba’a isa ai magana ba sai kin bada amsa san ranki, wannan halin naki yasa sam bana sake miki an bi an sangartaki ace komai ya fito daga bakinki sai kin faɗa? Sannan Nabilan karya akai ko gadan da kika kwana na zakice ba ita ke gyarawa ba?” Mikewa Zeey tai tace “Bari na shiga ɗaki na huta in kin huce mayi maganar.” Tana kainan ta fita nan fa Inna tahau faɗa Zeey kam ko a jikinta ɗaki ma ta shiga ta baje a kan gado tana tunanin abinda ya faru tsakaninsu da Baqeer. ****** Bayan magriba ne Daddy ya halarci babban falon bakinshi inda ya gayyato dattijan unguwar, anyi abinci kala-kala yadda kowa zai ci ya ƙoshi, sosai yaji dadi da aka ce Zeey bata nan shi yasa ko faɗa bai yi ba a ƙalla babu abinda zai bashi matsala. Zama suka yi duk wuri ɗaya ana ci ana hira kowa na yaba miah da bashi tabbacin zai bashi gudunmawa ɗari bisa ɗari. Badaru ne ya sauka gaban mai bread zai sayi na karin safe. Mai bread ya kalleshi yace “Malam Badaru har kun gama taron ne?” Da mamaki yace “Taron me kuma? Don ni dai daga kasuwa ma nake.” Taro dai da za ayi a gidan Alhaji Suleiman Karaye ko da yake kai ai kowa yasan ba kwa shiri to na tabbatar shi ya hanaka zuwa.” Nan da nan Baba ya gimtse fuska tamm, ranshi ya ɓaci sosai yace “Yanzun taro ake yi a unguwar babu ni?” Yana kaiwa nan ya amshi bread ɗin shi ya nufi gida, a waje ya bawa almajiri ya miƙa mishi ciki sannan ya wuce gidan Suleiman Karaye, dole ne yaci zarafinshi don ba zai yarda da wannan iskancin ba, ai ko ba zaije ba sai a faɗa mishi yace baya son zuwa yafi yaji a titi. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Muhd Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR       *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN* {30} Almajirin da Baba ya bawa saƙo ne ya shiga cikin gidan yana sallama, Jamila ce kaɗai a tsakar gidan tana alwala, Abu da Umman Baqeer duk sun shige ɗakunansu suna sallar isha'i. Miƙa mata ledar yayi yace "Wai gashi aka ce na shigo dashi ciki". Karɓa tayi ta latsa ledar sai taji biredi ne, ajiyewa tayi a gefe tace mishi "To jeka angode." Sai da ta gama alwalar sannan ta ɗauke ledar ta shige da ita ɗakinta ta buɗe durowa ta ajiye tana cewa "Wannan biredin dai ya shigo kenan wallahi sai dai ka sayi wani baƙin munafuki, da haka zaka ɗauka ka kai mata ku cinye ba tare da mun san anyi ba." Hijabi ta ɗauka ta kabbara sallah ranta fal farin ciki don wallahi babu mai karɓar biredin nan a hannunta yau, suma sun samu na karyawa da safe ita da yaranta. Shi kuwa Mallam Badaru ya nufi gidan Alhaji Suleiman Ƙaraye yana ta zage-zage a hanya kamar wani sabon kamu. Tun daga gate maigadi ya tsayar dashi ya hana shi shiga nan ma ya rufe shi da masifa yana cewa "Da zaka hanani shiga ni ba dattijon unguwa bane? Ko kuwa ce maka aka yi kada ka barni na shiga wurin taron da ake yi? owoo wato kun san abinda kuka taka baku da gaskiya shi yasa kuke ƙoƙarin hanani shiga?" Mamaki ya rufe mai gadi ganin ba zai iya da jidalin Mallam Badaru ba yasa ya buɗe mishi ƙofa tunda yasan ana taron da yace mishi yazo a cikin gidan. Wucewa yayi ciki yana ayyana tabbas sai yayi wa Suleiman Ƙaraye rashin mutunci irin wanda bai taɓa zato ba, don cin fuska da rashin mutunci har ya shirya taron manyan unguwa a kasa sanar mishi saboda munafurci, haka ma fa kwanaki da yazo ya saka mishi kuɗi a aljihu irin ga ɗan maula yazo, sannan shi fa har yanzu ba wai ya yarda da cewar da yayi ba ɗanshi bane ya nakasta mishi yaronshi ba kawai dai yayi shiru ne ganin baya da tartibiyar shaidar da zai gabatar. Yana shiga parlourn da ake taron sai ya tarar da mutanen unguwar wanda yawancin su abokan hulɗar shi ne ana ta raha ana cin abinci babu wanda ya kula da shigowar shi wurin. A take yaji ranshi yayi wani irin ɓaci cikin fusata yace "Ehh yau na tabbatar da mutum mugun icce ne shine don munafurci za'a shirya taron manyan unguwa a kasa shaida mini saboda an mayar dani saniyar ware, ko kuwa kun cireni daga cikin dattijan unguwa?" Ya kalli makwabcin shi Mallam Nuhu dake ta yagar naman kaza yace "Au don munafurci har da kai ake cin dunduniyata, Mallam Hamza? Alhaji Kabiru? Ashe dukkan ku munafukai nake tare dasu ban sani ba, ai dai kun san ƴar tsamar dake tsakanina da wancan mutumin" yace yana nuna Suleiman Ƙaraye dake zaune akan doguwar kujera yana kallon duk abinda yake yi fuskarshi ƙunshe da murmushi kamar ba taro Mallam Badaru yazo ya ɓata mishi ba, ya cigaba "Amma shine don munafurci har da ku a halartar taron daya shirya? Eh wato gani ni ba kowan-kowa ba shi yasa aka shirya taro aka kasa sanar dani, ko?" Kowa dai yayi tsit sun zubawa Mallam Badaru ido yana ta zuba tijara sai mahaifin Bello ne ya taso yace "Haba Mallam Badaru ya kamata fa idan an girma a riƙa sanin an girma, ta yaya abinda ya faru tun da ƙuruciya zaka yita riƙe dashi har yanzu?" A take ya taso mishi da masifa kamar zai kai mishi duka yana cewa "Dalla gafara can yi mini shiru baƙin munafuki da wani munafukin gantalallen ɗanka maci amana. Waye kai da har zaka taso ka tareni kana faɗa mini maganar banza, in banda ma Baqeer daya janyo mini masifa da bala'i ya haɗa sabga da ɗanka kai ka isa ka kalli inda nake shine har zaka zo kana yi mini zancen banza, dalla matsa ka bani wuri, ko sanda aka yi abun ka sani ne? Sai shishigi kamar an aikeka." Sai a lokacin Suleiman Ƙaraye ya taso cikin lumana saboda ya kare mutuncin shi dana kujerar da yake nema yace "Haba Mallam Badaru ya kamata mu manta duk wani abu daya faru lokacin ƙuruciya a yafi juna haka nan, bai kamata ace har girman nan namu da muka fara ajiye jikoki ana jin kanmu akan ɗan abinda bai taka kara ya karya ba." Ai kuwa dai ranshi yayi mummunan ɓaci don yana ganin rainin wayo kawai Suleiman ɗin ke neman kawo mishi irin wanda ya saba yi mishi tun da can don haka yayi ta bala'i yana masifa har yana cewa in dai yana raye Suleiman Ƙaraye bai isa hawa kujerar senator ɗin da yake hari ba don sai ya tabbatar ya nunawa mutane asalin waye Suleiman Ƙaraye da ɓoyayyiyar manufarshi akan su. Da ƙyar dai aka samu aka fitar dashi daga cikin gidan yana ta zage-zage yana masifa, bayan fitarshi sai suka hau zancen ba'a san meke damun shi ba da sam baya so a zauna lafiya. Wani yace "Ai kun san tunda iftila'in nan ya faɗawa ɗan shi ya koma kamar wani zararre, watakila dan ganin burin da yaci akan ɗan ba zai cika ba ƙwaƙwalwar shi ta taɓu." Anan Alhaji Suleiman Ƙaraye ke jin abinda ya faru da Baqeer ɗin, sai yayi ta mamaki yana jinjina lallai kam dole  Badaru ya ƙara gigicewa tunda ɗan da yake ji dashi ya zama nakasashe. Haka dai taro ya tashi kowa ya tafi da abinda Mallam Badaru yayi a bakin shi sun kuma tabbatarwa da Alhaji Suleiman Ƙaraye da zasu taimaka mishi wajen yaɗa kyakkyawar manufarshi a wajen sauran mutanen unguwa don irin shi dama suke buƙata da tsayawa takarar siyasa waɗanda suka san su suka san buƙatunsu da zasu yi musu aiki tuƙuru wajen magance musu matsalolin su ba waɗanda ba'a ganinsu ba sai lokacin campaign yayi. Haka suka yi sallama yana jin daɗin yadda taron ya kasance don yana hangowa kanshi nasara a zaɓen da za'a gabatar duk da ma Badaru yaso ya watsa mishi taro amma da yake kowa yasan halin shi sai abun bai zama wata babbar matsala ba. Yana shiga gida yake faɗawa Mummy yadda taron ya kasance har ma da ƴar hatsaniyar da Mallam Badaru yaso tayarwa anan nema yake faɗa mata abinda ya samu Baqeer. A take ta nuna bata san zancen ba duk kuwa da ita ta taimakawa Kabir wajen ɓoye laifin shi a wajen mahaifin nashi, tasan tabbas in har ya sani tofa akwai matsala sai cewa tayi "Garin yaya kuwa?" Yace "Wallahi ban sani ba sai dai ban sani ba ko hatsarin da yazo yace yaron yayi kwanaki ne sanadi wanda har yace Kabir ne ya buge ɗan nashi." Sai ta taɓe baki tace "To waya sani ne kam, shi da ba'a rabashi da neman rigima, ai tun lokacin na faɗa maka sharri ne kawai yake so ya ƙullawa Kabir don ya samu abinda zai riƙe yace kayi mishi kaga in yayi haka ai ya zubar maka da mutuncin da yasan mutane na ganinka dashi." "Haka ne kuma fa, to Allah ya kyauta mishi ya ganar dashi hassada dai ba abu bace me kyau." "Ameen dai distinguished, In Sha Allah kujerar nan tamu ce tunda muka samu manyan unguwa a hannun mu." Wani murmushin jin daɗi ya saki yana hango kanshi akan kurerar senator don ji yake yi kamar ma har yaci ya gama sai dai a jira lokacin zaɓe kawai. ***** Tunda aka fitar dashi daga gidan maigadi ya mayar da gate ya rufe yake faman zazzaga masifa har mutane na tsayawa suna kallonshi sai dai babu wanda y tambayeshi dalilin faɗan shi domin kuwa kowa yasan hali Mallam Badaru mafaɗacin mutum ne, ba'a taɓo shi ba ma ya aka ƙare dashi bare an takaleshi. Sai da yaga dai an mayar dashi kamar mahaukacin shi kaɗai yake faɗan shi babu abokin tayi sannan fa ya kama hanyar gidan shi yana cigaba da zazzaga masifa, har ya isa gidanshi bai yi shiru ba sai da ya ganshi a tsakar gidanshi ko sallama bai yi ba tsabar bala'in dake cin zuciyarshi. Da yake Jamila tasan tsiyar data shuka mishi ko leƙowa tsakar gidan bata yi ba bare kuma Fatima da dama yanzu ba wani shiga sabgar shi take yi ba ganin shima ya tattara al'amarinta ya watsar don ko ranar girkinta idan bai ga dama ba ɗakin Abu yake shigewa ko kuma ya gaiyaceta nashi ɗakin, Jamila ce dai da aka san ba zata yarda a danne mata hakki ba basa yi mata wannan kama karyar amma yadda Abu ta sameshi a hannu sai abinda tace yanzu ake yi a gidan. Abu na fitowa yace mata "Ina biredi na dana bayar aka shigo mini dashi ɗazu?" "Biredi kuma? Gaskiya ba'a bani ba sai dai ko idan Jamila aka bawa. Amma waye ka bawa ya shigo dashi don ni dai ina ɗaki ban ji shigowar kowa ba". Ai tuni ya ƙara harzuƙa jin wai Abu bata san an shigo da biredi ba. "To wa aka bawa biredin nawa bayan ke nace a kawowa?" "Gaskiya Mallam ban sani ba don ni dai babu wanda ya kawo mini biredi". "Jamila. Jamila!" Ya hau ƙwala mata kira ita kuwa tana jin shi tayi luf kamar ba ita yake yiwa wannan kiran mafarautan ba, sai da taji ya nufo ɗakinta yana cigaba da ƙwala mata kira sannan ta fito tana cewa "Mallam lafiya, irin wannan kira haka kamar naci bashi ban biya ba". Hannu ya miƙa mata yace "bani nan". Yi tayi kamar bata san akan me yake magana ba tace "me zan baka?" Cikin tsawa yace "Kinga Jamila kada ki kawo mini rainin hankalin da kika saba, shiga ki ɗauko mini biredi na dana bayar a shigo mini dashi." Tsuke fuska tayi itama tace "Kuma ɗan aiken ni yace maka ya kawowa biredin naka? Ko kuwa dai tijarar taka ta fama zaka sauke a kaina, to wallahi sam ba zata saɓuba tun wuri gara ka nemi inda aka kai maka biredinka amma ba wajena ba, yo in banda neman fitina ma irin taka da kayanka kake bani da zaka zo wurina neman abunka ko kuwa ni kaɗai ce a gidan da don ka rasa abunka zaka tsallake kowa ka taho wajena nema? Me yasa baka tambayi Fatima ba yanzu haka ma ita aka bawa tana ji kana tuhumar mu tayi shiru a ɗaki." Ai kamar kada ta ambaci sunan Umma sai ya mayar da akalar kiran nashi a kanta, ita kuwa baiwar Allah tana zaune akan sallaya tana lazumi tunda ta idar da sallar isha'i bata tashi ba, duk hayaniyar da suke yi tana jiyo su sai dai ko kaɗan bata ji zata saka musu baki ba shi yasa har sai da ya dangana da ɗakinta sannan ta ɗaga kai tana kallonshi. "A ina kika ajiye mini biredin don wulaƙanci kina ji ina nema ba zaki fito ki bani ba?" Yana yi yana bincike ɗakin yana neman inda ta ajiye mishi biredin. Bata tanka mishi ba har ya gama bincike ɗakin tsaf bai ga inda ta ajiye biredin ba don haka ya zuba mata ido yana jin wani sabon ɓacin rai na taso mishi yace "ba dai har kin cinye biredin ba?" Sai sannan ta amsa mishi cikin tausasawa da "Wai wane biredi ne kake nema haka? Ni babu wanda ya bani biredin ka hasali ma tunda nayi alwalar sallar magriba ban ƙara fita tsakar gidan ba har yanzu sai dai ka tambayi su Abu ko Jamila." A harzuƙe yace "Basu na fara tambaya ba suka ce ba'a basu ba idan ba ke aka bawa ba to ina biredin yayi?" Ƙara tausasa muryarta tayi tace "Wallahi Mallam ba'a bani biredin ka ba, ni yaushe  rabon da wani abu naka ma ya shigo hannuna" ta ƙare maganar idanunta na ciccikowa da ƙwalla. Fita yayi yana bala'i wallahi duk inda biredin shi yake sai an fito mishi dashi, ita dai Abu sai rantsuwa take yi akan ita ba'a bata wani biredi ba shi kuma yace ai ita yace almajirin ya kawowa to don me yanzu zata ce bata san maganar ba. Jamila dai na daga gefe tana dariya a zuciyarta tana cewa "Ai yau ko kafi ƙuda naci sai dai ka haƙura da biredin nan don bazan bayar ba, Allah ne ya ƙwato mana haƙƙinmu da kake dannewa, ke kuma makira algunguma ko banza dai nayi miki sanadin ɓacin rai fiye ma da yadda kika yi ta sakani a kwanakin nan" daga baya ma sai tayi shigewarta ɗaki tana rausaya jikinta irin na duniya tayi mata daɗi ɗinnan. *ƳAN TAGWAYE BIYAR* KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce*         *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*🦼      *NA* *UMM ASGHAR* Da *AYUSHER MUHD*           *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ƊAYA* {31} Badaru haka ya kwanta ranshi duk a jagule ji yake yi zuciyarshi nayi mishi zafi kwanan nan, har rasa irin masifar shi yake yi, to shi yanzu ba mutuncin kowa yake gani ba tunda burinshi ya lalace jin zafin kowa da haushin kowa yake, duk yanda Abu taso taja ra'ayinshi bata samu fuska ba, da yake sun san kwanan nan bala'i yake ji tun bayan abinda ya samu Baqeer yasa itama bata nace ba ta kwanta tana ƴan mitocinta wanda suka tsaya iya zuciyarta. Dole gobe a cikin jarinta ta bada a siyo mishi kwai da bread yanda zata ƙara kamashi kafin ya canza mata ita ma. ***** Zeey ce ta ajiye littafin dake hannunta tare da yin miƙa tana ɗan bubbuga bayanta, fuskar Inna a tamke tace "Sai kace wani abu kike yi, bayan tun safe in kika tashi ko gadonki ba iya gyarawa kike ba, yarinya sam an sangartata kamar ba mace ba." Zeey tayi gyaran murya tana kwanciya akan kujera tace "Inna wallahi ni ban san me yasa kika takura mini ba, ni kenan komai nayi ba daidai ba." Kallon kazar da take figewa tayi tace "Taso ki tayani to, tunda ke ko kunya ba kya ji irin taimakon nan ma baki iya ba, ke wai a haka ma zaki yi auren?" Kallon kazar tayi kamar tace bazata iya ba sai dai yafda Inna ke kallonta yasa ta sauka tana cewa "Dama ni mijin da zan aura ai komai yi mini zai sa ayi, nifa ko kitchen ba shiga zan yi ba idan nayi aure, iyakaci na bakin ƙofa nace a dafa kaza." Tsaki Inna taja tana mikewa tace "Shirmen banza kenan, ita Nabeela dana koya mata komai kina nufin talaka zata aura?" Da mamaki ta kalleta tace "Inna me ya kawo zancen Nabeela daga hira?" Kai Inna ta girgiza tace "Sam ni mamakin tarbiyar da aka baki nake, manya na magana kina magana, sannan Nabeela ma kike kiranta?" Baki Zeey ta turo don dama in dai tazo gidan Inna an dinga ɓata mata rai kenan shi yasa ko awa biyu cikakke bata iya yi a gidan, anya zata iya zama a gidan nan saboda son ganin Baqeer kawai? Muryar Nabeela ta jiyo ta miƙe ba tare da ta kalli kazar ba, Inna ta girgiza kai kawai ta dawo ta cigaba da figar kazarta. "Seee ji mana." Zeey ta faɗa tare da yi mata murmushi, baki Nabeela ta buɗe ta tsaya tana kallonta cike da mamaki, a tare suka sa dariya kafin tace "Saukar yaushe?" "Ke kai yawon yaushe?" Kai ta girgiza cike da jin daɗi tace "Ke dai wallahi neman maganarki yayi yawa In....." Da sauri Zeey ta rufe mata baki kafin tace "So kike dai a fasa mini jiki a kuma koreni." Dada tana figar kazarta tace "Banda dai jikina babu ƙarfi ai da tuni na aikata." Nabeela ce ta shigo ciki sosai tace "Meke faruwa?" Kafaɗa ta ɗaga tace "Zuwa nayi daukarki." Ai kamar Inna aka taɓa sai cewa tayi "Ɗaukan ta zuwa ina? Inda ba'a ganin girmanta?" Kallon Inna suka yi ta gefen ido sannan suka yi ɗakin Nabeela, gida ne madaidaici wanda aka ƙawatashi, ɗaki huɗu ne a gidan sai dai uku suka gyara ɗayan a ajiye kawai yake Inna na tara shirgi, akan gadon Nabeela ta kwanta ta sauke nannauyar ajiyar zuciya yanayinta a hankali ya canza. Nabeela ce ta zauna kusa da ita, tana kallonta cike da mamaki kafin tace "Meke damunki ne?" Zeey ta miƙe tare da janyo pillow ɗin dake kan gadon ta ɗora akan cinyarta tace "Aunty Nabs." Ta kira sunanta cike da sakalci. "Tunda kika dawo kema kin shareni ga Mummy sai baƙaƙen maganganu take yaba mini son ranta, ni kam ba shiri na tattara na bar muku gidan ku." Ta sake maida kanta kan katifa tana kallon ƙwan wutar ɗakin tace "Ni kaina ban san meke damuna ba, ga abu ina son faɗa amma daga nazo yin maganar sai na rasa abin cewa." Kai Nabeela ta girgiza tace "Wai da a duniya kina rasa abin cewa? Ni ai na ɗauka wannan sai dai mu." Tashi tayi ta zauna da sauri tace "Ya guy ɗin nan yanzu ya san kina sonshi kuwa?" Iska ta furzar tace "Ko kaɗan tsabar ma bai sani ba ni yake tambaya shawara akan ƴan matan shi." "Ba kanta kuma sai ki bashi?" "To ya zanyi?" Kai ta girgiza tace "Ba dani ba nifa sai dai mu hakura da abotar kawai kowa yasha zamanshi amma bazan maida kaina ƙawar ƙarfi da yaji ba, shi yasa nifa har yanzu ban fahimci ya kuke wannan son ba, shi yasa kuma nace bazan yi aure ba sai nima na samu wanda nake yiwa irin wannan son da ake faɗa." Dariya Nabeela tayi tace "Hmm ai ke ko in Allah ya tashi kamaki akan so ko? Harda hakkin mutanen da kika wulaƙanta zai haɗa miki, mu ganki a cikin ɗaki kina kuka shaɓe-shaɓe......" ai bata ƙarasa ba Zeey ta je kai mata duka, a guje ta fita ita ma tabi bayanta, bayan Inna ta ɓoye tana cewa "Wasa nake asibiti zamu kai ki a ƙara miki ruwa." Inna ce ta kalli Zeey dake neman jawo Nabeela tace "Wai ni kam Zainab baki san kunyar idon uwa ba ko?" Tsayawa tayi tana kallonta, ta cigaba "Shin Nabeela ba Auntynki bace kike neman dukanta? A gabana mahaifiyarta?" Takaici ne ya kama Zeey kawai ta koma ɗaki ta kwanta, shiru tayi tana tuno yadda ta bar Baqeer ɗazu, ko ya koma gida yanzu? Me yayi daya daɗe a tsaye ɗazu? Ji tayi zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, nan da nan kuma taji hankalinta ya tashi, wayarta ta ɗauko ta dubo number Dada data amsa akan in mutumin ya iso zata kirata ta sanar da ita. Ringing uku ta ɗauka tace “Assallamu Alaikum wanene?” Zeey ce tayi murmushi tace “Hajiya Dada ba dai har kin kwanta ba? Naga dai ba’a daɗe da yin isha’i ba.” Jin muryar Zainab yasa ta fara magana a rikice “Zainabu na shiga uku, tun ɗazu nasa a nemo Baqeeru amma har yanzu ba’a ganshi ba.” A wani zabure ta mike tsaye tace “Kamar yaya ba'a ganshi ba?” “Wallahi tun fitar da yayi har yanzu bai dawo ba.” Ai bata gama jin wani abu ba ta zari key a guje ta fito daga gida, Inna ce ta kalleta tace “Dama kece zaki iya zaman nan? Ke da ko faɗa ba kya so?” Ta kalli Innan sannan ta kalli Nabeela tace “Aunty Nabs zan je na dawo ki faɗawa Inna ta taimaka ta maida wuƙar.” Tana kaiwa nan ta fita cikin hanzari. Da yake babu nisa tsakanin Ɗanladi nasidi zuwa Mariri inda Dada take yasa bata daɗe ba ta iso, maimakon tayi gidan inda ta ganshi ɗazu tayi sai dai babu shi babu alamar shi, hankali a tashe ta cigaba da nemanshi, tunanin zuwa wurin Dada tayi ganin tayi nisa cikin layin don har bata san inda ma take ba. Kamar a mafarki ta ganshi zaune gefen wasu yara kamar almajirai suna hira yana zaune yana kallonsu, can taga yana nuna musu abu kamar a takarda sai kuma suka sa ihu suna tafi. Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tana jin zuciyarta na sauka a hankali, lallai ba kanta ƙalau ba, to wai ma Baqeer yaro ne da zata rikice haka? Amma ba laifinta bane tunda yanzu duniyar ce ta koma haka. Miƙa musu takardun yayi sannan ya fara ƙoƙarin burga kekenshi wani ta gani yazo da sauri cikin yaran yana turashi, bata san me suke cewa ba amma tabbas fuskar Baqeer ta canza da alama ya samu nutsuwa zaman da yayi dasu. Motar taja a hankali tana binsu a baya, waigawa yayi gefe nan suka haɗa ido da ita, da sauri ta ɗauke idanunta kallon yaron da yake turashi yayi ya mishi alama daya bari sannan suka yi magana sai taga ya juya. Fitowa tayi daga motar ganin bashi da niyyar cigaba da tafiya, daga ɗan gefenshi kaɗan ta tsaya, sanye take da kayan ɗazu. Shiru suka yi sai kallon gari da suke, a hankali tace “Me kake yi anan? Hankalin Dada ya tashi.” Shiru yayi babu alamar amsa a tattare dashi, haka kawai taji duk takaicin kanta ya rufeta, tana mace mai aji me take yi haka ne wai? Ba tunani ba komai? Juyawa tayi sai dai bata yi taku ko ɗaya ba taji yace “Me iyayen yaran nan suke tunani da suka kawosu almajiranta?” Waigowa tayi ta kalleshi ba kallonta yake yi ba sai dai har yanzu idanunshi nakan gefe inda yaran suke, kallonsu tayi kafin tace “Neman ilimi, sannan da rage dawainiyar yaran da suke dashi.” Kai kawai ya jinjina ga mamakinta bai ce komai ba ya fara tura kekenshi, so take ta tura mishi amma baza ta iya ba, so take yi ta bishi nan ma bazata iya ba, Baqeer kuwa tunanuka kala-kala ne suka zo mishi a fitar nan da yayi, anan ne kuma ya gane tabbas Allah na sonshi da rahama da bai ɗauke mishi hannayenshi ba, yaga abubuwa da aiyuka kala-kala, tsofaffi haka suke famar aikin ƙarfi don su tallafi iyalansu, zuwanshi wurin almajiran nan hankalinshi ya tashi ganinsu babu abinci babu wata suturar kirki, babu wani abun yi amma basu karaya ba, sai bi suke yi suna neman abun yi don a biyasu ko naira ashirin ne su samu suci abinci, nan ya tsaya wurinsu yana gani suna hirar yanda mutane ke cutarsu in suka yi musu aiki su hanasu hakkinsu wanda hakan ba ƙaramin tada mishi hankali yayi ba, sai dai ga mamakinshi duk da hakan basu karaya ba gobe ma komawa suke yi, kusan sama da rabinsu babu ma mai takalmi, almajirin ne taga ya sake tahowa da gudu ya bi inda Baqeer yake ya riƙe keken, yana turashi, barinta zai yi anan babu ko magana? To wa ya kawoki Zeey? Abinda zuciyarta tace mata kenan wanda ba shiri ta shiga mota, kiran Dada tayi da sauri ta ɗauka tace “Zainabu? Kinga nama sa an siyo minu kati na kirashi wai fita kawai yayi yanzu zai dawo.” Tace “To Alhamdulillah, sai da safe.” Nan ta kashe wayar ta kwantar da kanta a kujerar motar, ko Dada hankalinta bai tashi ba sanda ta kirata amma ita kalleta harta rugo kamar ance mata mahaifinta aka rasa. Babu shiri taja mota ta wuce, yana kallon sanda motarta ta wuce, da kallo yabi motar tabbas ƴar gidan masu kuɗi ce kuma yanzu ya tabbatar ta ɗauke shi ne a matsayin irin mutanen da suka saba taimakawa don haka dole ya miƙe ya bambanta kanshi daga ragwayen maza. Tana komawa gidan Inna ɗaki ta wuce ta canza kaya tayi brushing ta kwanta, ko abincin ma bata jin ci sam ta kasa gane abinda ke yawo akanta sai dai yanayin Baqeer ya kasa fita a ranta, tabbas wani abu ya canza a tattare dashi amma bata san menene ba. ****** Bello ne ya kalli Babanshi yace “Baba maganar Asiya, kaga dai ance za’a sake kiranmu Abuja akan aikin da muka yi sannan tunda ni banci na ɗaya ba sun ce zamu je a bamu wasu ayyukan da zamu yi wanda za’a dinga tura musu suna siyarwa a ƙasar su ana dawo mana da kuɗin kafin lokacin tafiyarmu ƙaro karatun yayi, shi yasa nake ganin ba sana’ar data fi wannan a yanzu, don Allah aje gidansu Asiya ayi maganar aure.” Wani mugun kallo Baban yayi mishi yace “Wai ni kam Bello kanka ɗaya dai ko? Ina ce kai da kanka ka sanar dani Baqeer shine saurayin Asiya kwanakin baya da na ganku a ƙofar gidan kace kai rakiya kayi?” Bayan kanshi ya shafa yace “Eh shine amma yanzu sun rabu ai.” “Kai bana son shirme don Allah, kai da hankalinka yarinyar da ta rabu da saurayinta saboda ƙaddara ta afka mishi ita kake son aure? To ahir ɗinka ko ba don haka bama bazan bari ka auri budurwar abokinka ba, sannan Badaru kana gani yadda yake tijara tun bayan faruwar abun nan baza ka zo ka sake jaza min case dashi ba.” Yana kaiwa nan ya fita ranshi a ɓace, Goggo mahaifiyarshi ce ta kalleshi tace “Bello don Allah kada kaci amanar Baqeer yaron nan ya taimakemu a rayuwa kada kayi abinda alhakinshi zai sa komai da kake taƙama dashi ya tafi.” Ita ma tana kaiwa nan ta wuce, miƙewa yayi yace “Gobe wurin Baffa zan je ai dai kuna jin maganar shi dukanku idan ya sakaku baku isa kuce a'a ba.” ****** Dada ce ta harari Baqeer tace “Haka kawai zaka tada mini hankali.” “Dada nifa ba yaro bane, sannan kin san dai babu inda zanje kema, kawai abubuwa ne suka yi yawa a kaina na fita don na samu nutsuwa, kiyi haƙuri idan na tayar miki da hankali.” “Wayar tawa ce babu kati babu yadda zanyi na kira ka bare naji kana ina, gashi babu kuɗi  a hannuna a ƙarshe sai wurin Talatu na shiga na ari dari nasa aka siyo mini katin na kiraka.” Kallon tausayi yayi mata tabbas ba zai cigaba da zama haka ba. Kallon almajirin yayi wanda bai ma san mai zai bashi ba na godiya, Dada ce ta ɗauko fruits ɗin nan lemon da ayaba ta bawa yaron tana yi mishi godiya, shima godiya yayi ya amsa ya juya ya fita. ***** Baba yau a fusace ya kwana washegari ma ko abinci bai ci ba ya ɗauki motarshi ya fita, jikin Abu ne duk yayi sanyi ta fito tsakar gida tana daka garin maganin mata tana yi ranta na ɓaci, Kamalu ne ya shigo yace “Hajiya ya bani makullin mota zan ɗan je yawo.” “Kaima dai kasan Babanka ya fita da ita, baka ga bata ƙofar gida ba?” Bashir ne ya fito da alama makaranta zai je, Kamalu yace “Kai Bashir bani kuɗin hannunka.” Kallon mamaki yayi mishi ya kalli ɗari biyu  da Jamila ta bashi yace “Ai kam kayi hakuri amma bazan baka ba gaskiya babu dalilin da zai sa na baka kuɗin da zanyi amfani dasu na tafi makaranta.” “Kai don gidanku ni kake yiwa magana a haka?” A ƙufule Bashir yace “Kayi haƙuri amma bazan bada ba.” *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer🦼 #RayuwadaKaddara #Hawayena #Samudarashi #UmmuAsgar #Ayushermuhd *BAQEER*🦼      *NA* *UMM ASGHAR* Da *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA BIYU* {32} Cakuma ya kaiwa wuyan rigarshi ya shake shi yana cewa "Dan uwarka ba zaka bayar ba fa kace? Ni kake faɗawa ba zaka bayar ba don ka raina ni ko kuwa don kana ganin kayi tsawon ƙafa ka kere ni a tsawo? Idan da wancan nakasashen ne yace ka bashi kuɗin hannunka zaka faɗa mishi haka ne?" Da ƙyar ya iya ɓanɓare hannayen Kamalu daga wuyanshi domin kuwa ba ƙaramin shaƙa yayi mishi ba. A sakarce ya kalleshi yace "An hana ka ɗin sai dai kayi duk abinda zaka yi amma ba zan ɗauki kuɗina da zan tafi makaranta ba na baka alhalin ba wani abu zaka yi dasu ba watakila ma sigari zaka saya, kuma da kake cewa da Yaya Baqeer ne bashi zan yi ai shi Yaya Baqeer sai dai a ƙi shi don wani abu amma dai ba don halin shi ba don kuwa kowa a gidan nan ya sani abun hannunshi bai rufe mishi ido ba kuma babu ruwanshi da bambancin da Baba yake nunawa idan ya tashi alherin shi gaba daya yaran gidan nan yake hadawa yayi wa kowa shine har kake haɗa kanka dashi bayan kai baka taɓa iya morawa mutum da ko sisi sai dai ma kai ayi maka.” Ai kamar ya tunzura Kamalu ya kuwa hayayyaƙo mishi yana ƙoƙarin kai mishi duka yana cewa "Ni kake faɗawa wannan maganar don uban uwarka?" Cikin hanzari Jamila ta fito daga ɗakinta tana cewa "Rashin mutuncin naka har ya kai ka zagi ubana Kamalu? Akan ya hanaka kuɗin shi kake yi mana wannan ɗiban albarkar?" A fusace yace "Shi baki ji abinda ya faɗa mini ba sai ni don na rama zaki taso ki shigar mishi.” Ƙwafa tayi tace "To uban uwarka Abu ka zaga ba dai ubana ba ato.” Abu naji an haɗa da ubanta ta taso da tata masifar itama alhali da tana zaune a gefe tana kallon rashin mutuncin da Kamalun yake yi bata hanashi ba. "A'a fa Jamila wallahi banda tsikarin uwar miji da taɓarya, saboda me zaki sako da ubana ko kin ji na saka musu baki tunda suka fara abinsu da zaki sako dani?” "Au ashe babu daɗi, ba'a gabanki ɗanki ya zagi nawa uban ba kin hanashi ne? Ko kin yi mishi faɗa, to wallahi ba ubana ya zaga ba sai dai naki, haka kurum don yana ji da tijara sai ya huce akan yarona ko kuwa sai kada yaje makaranta tunda ɗan gwal wanda bai san daɗin ilimi ba ya buƙaci ya bashi kuɗin?” A take faɗa ya kaure a tsakaninsu har suna nema su kaiwa juna duka, sai Umma ce ta fito daga ɗakinta ta rabasu jin hayaniyar tayi yawa, da ƙyar suka haƙura kowacce ta koma ɗakinta suna faman zage-zage. Komawa Bashir yayi ɗakin Jamila yana bata haƙuri kafin ya fito ya tafi makarantar ranshi duk babu daɗi. ***** Yau ta tashi cikin farin ciki ganin tun jiya suke daɗi da maigidan nata. Sandwiches tayi musu sai ta dafa milk tea ta zuba a flask, a gefe ga farfesun kayan cikin rago da ta dafa tun jiya da dare yau kawai ɗumamawa tayi. Kwalliya tayi cikin wata riga da tabi jikinta ta lafe duk wasu curves na jikinta suka bayyana, rigar iya kacinta gwiwarta sannan siririn hannu gareta guda ɗaya ɗaya hannun babu komai don haka ko bra bata saka ba. Tunda ta fito yake binta da kallo domin kuwa shigar da tayi ta tafi dashi ba kaɗan ba, a ƙarshe ma kasa haƙuri yayi ya janyota ya zaunar da ita akan cinyarshi yana sunsunar sassanyan ƙamshin turaruka da tayi amfani dasu. Haka suka ci abincin a cikin nishaɗi yana saka mata a baki itama tana bashi, ɗagowar nan da zata yi kawai taga Baffa(surukinta) tsaye a kansu. Wata irin zabura tayi sai kuma ta koma ta cukuikuye a jikin Baban Aareef kamar mai ƙoƙarin komawa cikin shi. Shi kanshi sai da yaji babu daɗi da yadda Baffan yayi musu tsaye aka yana bin su da wani irin kallo. Murya a cunkushe yace "Baffa barka da asuba," har wannan lokacin Maryam na naɗe a jikinshi baƙin cikin duniya ya lulluɓeta saboda ganin da uban mijin nata yayi mata da shigar da ko nata uban bai kyautu ya ganta da ita ba. A ɗage ya amsa mishi "Barka kadai, kana nan mace ta sanya ka a gaba tana zuba maka karuwanci kai kuma sai faman yage baki kake yi kamar wani sakarai ina ta kiranka a waya kaƙi ɗagawa?” Murya a shaƙe yace "kayi haƙuri Baffa, amma don Allah ka fita daga waje sai na fito na sameka" ranshi idan yayi dubu ya ɓaci don ko shi yau abinda Baffan yayi ya ɓata mishi rai. Sai da ya watsa mata wani mugun kallo da bata ma san yana yi ba don ta ɓoye fuskarta akan ƙirjin mijinta bama ta son ta ɗago bare taci karo da fuskarshi sannan ya fita. Sai da ya tabbatar Baffan ya fita sannan ya ɗagata daga jikinshi yace "Ina zuwa please, bari naje naji me Baffa yake so.” Ko kulashi bata yi ba don haushi ganin kamar ma bai damu da yanayin da Baffan yazo ya samesu ba. Yana fita ta fashe da wani irin kukan baƙin ciki tana jin takaicin yadda uban mijinta baya kunyar faɗo musu ɗaki ko tunanin yanayin da zai iya riskarsu a ciki baya yi gashi kuma Baban Aareef baya kallon hakan a matsayin wani abun damuwa idan tayi magana ma har saɓani suke samu akan hakan. Har ya dawo ciki bata daina kukan ba, duk sai taji farin cikin da take ciki ya gushe takaici da baƙin ciki duk sun mamaye mata zuciya. Tsayawa yayi yana kallonta ganin tana kuka sai kuma ya taɓe baki yace "Shi kuma kukan da kike yi na menene? Ko kuwa dai jin daɗi?” Ko ɗaga kai bata yi ta kalleshi ba ta cigaba da kukanta shima sai yayi kamar bai fahimci dalilin kukanta ba yace "to ni zan fita nasan dai babu wata matsala tunda komai da za'a buƙata akwai, idan lokacin tashin Aareef yayi sai kije ki ɗauko shi" ya miƙa mata kuɗin napep. Kasa karɓar kuɗin daya miƙa mata tayi ta kuma kasa haƙuri sai da tace mishi "Saboda Allah haka zamu cigaba da rayuwa duk lokacin da Baffa yaso kawai sai dai mu ganshi tsaye akan mu ya shigo mana wuri babu tunanin a wane irin hali zai iya riskarmu kuma kai baza ka iya yi mishi magana ya daina ba, wannan wace irin rayuwa ce ace ni da gidana amma bani da wani sakewa a cikinshi, shikenan ni ban isa nayi wa mijina kwalliya ba saboda fargabar kada a shigo a tarar dani da shigar da bata dace ba. Gaskiya ni dai ya kamata a sake tsari ko dai ya daina shigo mini ciki ko kuma ka canja mini wurin zama amma ba zai yiwu ya dinga shigo mini ɗaki koyaushe ta raya mishi ba.” Wata uwar harara ya watsa mata yace "Duk waɗannan maganganun a Baffan kike yi? Mahaifin nawa? Shine kike iya buɗe baki kina faɗar duk maganar da tazo bakinki a kanshi, to da zaki ce ya daina shigo miki gida nan ɗin gidanki ne? Nace gidanki ne da zaki ce ba zai shigo ba, ina ce dai gidan ɗanshi ne ai ko kuma yadda yake da iko dani haka yake da iko da duk wani abu dana mallaka don haka ke baki isa ki kafa mishi doka ba a cikin gidan nan, idan kina ganin zamanki dashi akwai matsala zaki iya fita ki bar mishi gidan tunda zaman bai zame miki dole ba shi kuwa baya da wani wurin zuwan idan ba nan gidan ba.” Ya watsar da kuɗin a tsakiyar parlourn yayi ficewarshi ya barta anan babu wani tausasawa bare lallashi sai kace ba ita aka yiwa laifi ba. Sai da taji kanta ya fara ciwo saboda kukan da tayi ba kaɗan bane sannan ta bawa kanta haƙuri ta goge fuskarta ta tashi ta tattare kuɗin daya watsar mata a ƙasa ta adana sannan taje ta sakawa ƙofarta makulli duk dai da baya shigo mata wuri sai idan Baban Aareef na nan amma bata so ta sakankance tunda shi bai san ya kamata ba. Tattare kwanukan abincin da ta ɓata lokacin ta wajen shiryawa tayi ta mayar kitchen don gaba ɗaya sai taji abincin ma ya fita daga ranta halin ɓacin ran da ta samu kanta a ciki ya cika mata ciki. Haka nan ta yini sukuku zuciyarta duk babu daɗi komai take yi dauriya kawai take yi har lokacin ɗauko Aareef daga makaranta yayi ta fita ta ɗauko shi. A harabar gidan sai data tsaya ta ƙarewa motarta kallo wacce Baffan ne yasa aka karɓe daga hannunta kawai don ta fita tayi hidimar ɗan uwanta da ita gata nan yanzu an ajiye ta kawai tana busar iska ita kuma duk wani uzurinta sai dai ta fita ta hau napep duk da ma ba wani fita take yi ba kai Aareef makaranta da ɗauko shi ne kawai sai kuma uzurin zuwa gidansu idan ya kamata da take fita a motar taje ta dawo amma shine sai da yasa aka ƙwace kawai don dai ya nuna mata iyakarta bayan shi nashi ƴaƴan kowacce na warwasawa a gidan aurenta sai ita da yazo ya sakawa ido. ***** Haka nan ta tashi yau sukuku da ita zuciyarta fal tunanin Baqeer da duk mafarkanta na yau shine a ciki, ta rasa me yasa ta damu dashi har haka alhalin tun asali ma ba wai suna wani shiri bane bare tace ko yarintarsu take tunowa yasa yanayin da yake ciki a yanzu ya tsaye mata a rai. Ta dai fi bayarwa tausayin halin daya samu kanshi a ciki ne yasa take yawan tunawa dashi ta damu da dukkanin wasu al'amuranshi da har idan bata je taga halin da yake ciki ba bata samun nutsuwa. Tunda ta tashi tana kwance akan gadon bata tashi tayi komai ba sai dai ta juya nan ta juya can sai Nabila ce kawai take kaiwa tana kawowa tana ƙoƙarin tsaftace gidan. Ɗakin Inna ta shigo ta watsa mata harara tace "To sannu ƴar mai da ba'a koya mata komai ba sai sakalci da lalacin tsiya, kina nufin haka zaki yi ta kwanciya ba zaki tashi ki kamawa Nabila komai ba ita kaɗai zaki bari da aiki kina naɗe akan gado sai idan ta gama abinci kice zaki buɗe ciki kici. Ke dai wallahi baki ji daɗin halinki ba kuma ni dai idan kin san ba za'a amfana da zamanki ba gara tun wuri ki tattara ki koma gidanku inda ba'a sakaki ba'a hanaki amma ba zai yiwu kizo sai dai ki naɗe akan gado ba kice ba zaki yi aiki ba ah to.” Tashi zaune tayi tace "Haba don Allah Inna daga tashi na bacci kawai zaki rufeni da faɗan ki na fama da baya ƙarewa tun ban gama wartsakewa ba, shi yasa wallahi ban cika son zuwa wurinki ba don nasan takura mini kawai zaki yi da yawan faɗa kamar irin kina jin haushi na ɗinnan.” "Ungo naki nan ƴar ƙaniya mai bakin tsanya, wacce baka kasheta a zance" tayi mata daƙuwa da duka hannayenta bibbiyu. "Shikenan ke ba za'a yi miki faɗa ki saurara ba sai kin mayar da amsa saboda a gidanku ba'a yi miki tarbiyyar sanin darajar manya ba, to ni gidannan ba'a yi mini iya shega in ƙyale, idan kinga ba zaki iya zama ba ƙofa a buɗe take ki tattara ya naki ya naki ki bar mini gidana dama ai bani na gaiyaceki ba". Tagumi kawai Zeey tayi ta zubawa Inna ido tana ta faman zazzaga mata masifa sai dai sam yanayin da take samun kanta a ciki a ƴan kwanakin nan yasa bata ji zata iya tanka mata ba don haka har tayi ta gama bata ƙara ce mata komai ba, sai bayan data fita tayi mata gwalo tana cewa "Jarababbiyar tsohuwa kawai, haka kurum daga tashi na zata zo ta cika mini kunne da masifa kamar ance mata ina da energy ɗin ɗaukar jidalinta yanzu da sassafen nan”. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer🦼 #Zeey #RayuwadaKaddara #Hawayena #Samudarashi #UmmuAsgar #Ayushermuhd *BAQEER*🦼      *NA* *AYUSHER MUHD*          *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA UKU* {33} Yau Junaid ya sauka a garin Kano ya wuce gida inda ya huta yayi bacci, tashi yayi ya watsa ruwa sannan yasa riga t-shirt da wandon jeans ya fesa turare sannan ya fito, a falo yaga Mamy ta jera mishi abinci, murmushi yayi sannan ya zauna yana cewa “Mamy inyi maza-maza dai in kawo miki suruka kema ki huta.” Dariya tayi tace “Ah to ka dai ce kana dawowa zaka kawo mana Zainab.” Wayarshi ya kalla dake ƙara ya dagota tare da kallon Mamy yace “Gata ma ƴar halak.” Ya ƙarasa maganar yana saka wayar a kunnenshi. “J ya? Ka iso?” “Duk hankalinki dai da alama yana kaina, hope anyi mini shirye-shirye ne shi yasa kike jirana.” Dariya tayi kaɗan tace “Kada ka damu in muka je kaga mara lafiyan daga nan zan kai ka yawo.” Wani sanyi yaji a ranshi da alama ita ma ta fara cireshi daga bangaren aboki yace “Shikenan ki bani zuwa bayan la’asar In Sha Allahu.” “Shikenan zan zo sai mu wuce.” “Wai zuwan ma ɗauka na za ayi? Ki bari zan zo na ɗaukeki.” Ajiyar zuciya tayi tace “Kai da kasha hanya? Kai dai ka shirya zan zo.” Da yake yasan dagiyar Zeey yasa yace to kawai, Nabeela dake tsaye tana gyara drawer ce ta kalleta tace “Waye kuma J?” Zeey ta kwanta akan gado tana ɗan wasa da kafarta tace “Junaid.” Da mamaki tace “Junaid dai naki?” “Nawa ko nasu? Shi dai ya dawo yau.” Kallonta Nabeela tayi cike da zargi da sauri Zeey tace “Kada ma ki fara babh abinda ke tsakaninmu.” Dariya ta saki tace “Wannan karan kin bani mamaki kece yau kwananki biyu a gidan nan?” “Ni kaina mamaki nake bawa kaina, don ma yanzu mitar Inna ba wani bani haushi yake ba.” “Dama can bai kamata ya baki ba tunda kin san halinta.” Ajiyar zuciya tayi tace “Matsalar bana iya yi mata shiru ne.” “Dama ina zaki mini shiru kina kwance kowa yana aiki banda ke?” Suka jiyo muryar Inna data shigo ɗauke da kayan gugar da aka kawo, ta miƙawa Nabeela tana kallon Zeey dake kwance akan gado tana magana tana cin soyayyiyar cashew, ko a jikinta ma. Fita tayi hakan yasa Zeey ta miƙe tace “Bari nayi wanka fita zamu yi da Junaid.” Kai kawai Nabeela ta ɗaga ita kuma ta shiga toilet, ƙwalawa Nabeela kira tayi wai ta miƙo mata towel ta manta bata ɗauka ba, ɗauka tayi ta miƙa mata sannan ta cigaba da aikin, tana mamakin Zeey sam halinta na ko in kula abinda ke gabanta kawai shi take yi amma ragowar ba damuwarta bane, gadon ta gyara sannan ta ɗauko tsintsiya ta share ɗakin ta fito falo inda ta samu Inna zaune tana sauraren radio, kallonta tayi tace “Inna me za’a dafa?” Innan ta kalleta tace “Me kike gani? Ni ko menene ma bani da matsala.” “Ko muyi shinkafa da wake?” Kai ta ɗaga alamar 'eh' kafin tace “Allah yayi miki albarka ya kawo miki mijin da zaki aura wanda zaki ji daɗin shi." “Ameen Inna,” ta faɗa cikin jin daɗi. Inna tana zaune tana binta da ido har ta shiga kitchen, ajiyar zuciya tayi don tana tsananin tausayin Nabeela. Zeey kam kaya ta saka ta fara jawowa tana tunanin wanda zata saka, atamfa ta ciro doguwar riga irin buba ɗinnan, tasa ta ɗaura ɗankwali irin na Zarah Buhari, nan fa ta fito cass tasa turare, kallon kayan data cire tayi kamar baza ta kwashe ba sai kuma ta ɗauke tace “Kafin yanzu a hauni da masifa.” Jaka ta ɗauko ta ɗauki wayarta, falo ta zauna gefen Inna tace “Inna wai ni kam radio ɗinnan kunna shi kawai kike yi amma dai ba saurara kike ba ko?” “To ko ma dai menene ai kunnena ne ko?” Baki ta taɓe, wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka da sauri ta fashe da shagwaɓa tace “Mummy Allah Inna ta takura mini.” “Kin gani ko? Ki tattaro ki dawo don ni har yanzu mamakin zaman nan naki nake yi.” Tana kallon Inna dake harararta tace “Wasa nake yi wannan karon Inna lallaɓani take yi? Ko Inna?” “Ahaf ita tasan bazan lallaɓaki ba ai, tunda su sun gama sangartaki.” Dariya tayi tace “Mummy gaba ɗaya Inna fa bata gajiya da mita.” Mummy ta sauke ajiyar zuciya tace “Daddynki ma ya ƙosa ki dawo gidan babu daɗi da ba kya nan.” Tana murmushi tace “In Sha Allahu Mummy, kema kin san ina missing ɗinki, love you Mummy.” Nan suka yi sallama Inna tayi tsaki tace “In ma roba ne can ku kuka sani.” Zeey tasa dariya sosai tace “Love you ake cewa.” “Can muku nace kuce samira ko tangaran ma bai dameni ba.” Miƙewa tayi tana cigaba da dariya don Nabeela dake kitchen ma dariya take yi musu, Zeey ta fito ta shiga mota ta fita har lokacin ta kasa daina dariya. Inna ce ta bita da harara, Nabeela ce ta leƙo Inna tana kallonta tace “Ki tabbatar in zata koma kun koma tare, gwara kije can ki huta ni in Basira ta zo tayi mini abinci na ya isheni, sannan ki rage wannan saurin fushin naki.” Kai ta ɗaga sannan ta koma kitchen ta cigaba da girkin. ***** Gidan su Junaid ta nufa bayan sun yi waya bai dade ba sai gashi ya fito, tunda ya shiga mota ya zuba mata ido yana jin ƙaunarta na shiga mishi rai sosai, kallonshi tayi itama tace “J kallon ya isa haka nasan baka saba ganina da atamfa ba duk shine.” Ido ya lumshe sannan ya buɗe, a kyau bai kai Baqeer ba amma da yake ɗan gayu ne shi sosai mai kuɗi a haka sai kaga ya fishi, sai saje daya tara a fuskarshi dake ƙara mishi kyau, girman ido ya ɗan rage irin yanda yake jan hankalin mata yace “Zeey you just look different, sai nake jin kamar yau na soma saninki.” Ido ta ɗan juya kaɗan tace “Junaid please kada ka sakani dariya ba wani different kawai dai ka ganni ne bayan shekara of course dole kaga na canza.” Mota ta tada tana cewa “Ni dai Allah yasa baka ma Mamy magana ta ba.” “Guess?” Harararshi tayi tace “Ya Allah ban san ya zan yi da kai ba.” “Amincewa kawai zaki yi muyi aure shikenan komai yayi daidai.” Murmushi tayi tace “Me nace maka?” “Sai wanda in kika ganshi zuciyarki bata nutsuwa, sai kinji butterflies na yawo a cikinki in ya matso kusa dake bla-bla-bla ba dai har yanzu yarintar na nan ba?” Kafaɗa ta ɗaga tace “Call it whatever you want ni dai haka nake ra’ayi.” Idanunshi na kanta yace “Kin san in na matso kusa dake you will definitely feel it?” “Problem ɗin shine ni bazan bari ka matso ɗin ba sannan inka matso ma abotar ta ƙare daga yanzu.” Dariya yayi abinda yasa yake son Zeey kenan bata shakka ba kuma ta magana don kaji dadi abinda ke ranta kawai take faɗa. ***** Baqeer wannan karon shine karo na biyar daya duba agogon hannunshi, tun  jiya Dada ke cewa zata zo bai kulata ba gashi har huɗu da rabi babu ita ba labarinta, ba dai haushi taji ba akan rannan ya tafi ya nuna bai san nemanshi taje yi ba? To lokacin ai ba laifinshi bane tunda shi bai san me zai ce mata ba? Ko dai ta fahimci bata buƙatar su a rayuwa ne shi yasa ta cire su? To shi menene nashi? Sumar kanshi ya shafa yana tunani duk ya rasa me yasa hankalinshi da tunaninshi suke kan yarinyar, yana jiyo Dada tana hira da yaran dake yawan shigo mata shi sam wannan ba shine a gabanshi ba, rayuwarshi duk ta zama babu daɗi haka kawai ya fara jan kekenshi yana gyara ɗakin, kallon agogo ya sake yi biyar saura minti goma yanzu kam ya tabbatar ba zuwa zata yi ba hakan yasa ya ɗauki wayarshi kawai ya kunna karatun  Qur’ani yana saurare idanunshi a lumshe. Kamar daga mafarki yaji Dada tace “Lale lale tun ɗazu nake jiranki ashe kina tafe.” Sautin karatun ya rage sosai tare da nutsuwa don yaji ko itan ce tazo. Zeey ce ta rungume Dada tace “Hajiya Dada kwana biyu ne fa baki ganni ba amma duk kin yi rashina.” Kunnenta ta ɗan jaa kaɗan wanda yasa Zeey yin ƙara tace “Dole inje gidanku na roƙa a bar mini ke ko a bani ke na bawa jikana.” Ido Zeey ta buɗe tace “Wa? Ba dai ni ba?” “Akwai jikokina sai dai ba a Kano suke ba.” Dariya kawai tasa tace “Dada kin yi mishi maganar kuwa?’ “A’a yana ɗaki kin san halinshi ai tambayata zai yi wanene, kawai dai nace mishi zaki zo yau.” “Hmm shiru yayi ko?” Dada tana murmushi tace “Kin san hali ai.” Dada ce tayi gaba ta kamo hannun Zeey suka shiga ciki, ƙofar ɗakin ta ƙwanƙwasa sannan tace “Baqeeru?Idonka biyu?” Idanunshi ya sake runtsewa sannan ya buɗe yace “Umm!” Ƙofar Dada ta buɗe, Zeey tana jingine da bango ta juya baya, ƙamshin turarenta ne ya shiga hancinshi, kallonta yayi kaɗan yayi saurin mayar da kanshi gefe, Dada tace “Ko zaka ɗan fito akwai wanda yake son ganinka ne.” Kamar zai tambayi waye sai kuma yaji bai son yin magana saboda yadda take tsaye daga waje, Dada ta juya tana saka tabarma a tsakiyar falon dake ɗauke da kujeru biyu. Keken ya turo da kanshi har yazo inda Zeey ke tsaye, kasa cigaba da tafiyar yayi ita ma bata motsa ba, a hankali ta waigo shima ya ɗago suka kalli juna, da sauri suka ɗauke kai, Zeey tace “Yau baka je yawo ba?” “Dama kullum nake zuwa?” “Au ashe fa ba kullum kake zuwa ba.” Kallonta yayi itama ta kalleshi sai kuma yaga tayi murmushi ta wuce wurin Dada, Baqeer da kallo ya bita. Waya Zeey ta yiwa Junaid ta sanar dashi ya shigo, ta fito ta wuce Baqeer tayi waje, kallon Dada yayi da mamakin kafin yace “Dada waye zai zo?” Tace “Wallahi ban gama sani ba kai dai zai zo gani.” Da mamaki yake sake kallonta yace “Baki san wa zai zo ba har zaki barshi ya shigo?” Tace “To ba dai da Zainabu suke ba?” Kallonta yayi lallai Dada bata san zamani ba, waigawa yayi waje ya hangosu suna tafe a tare fuskarsu ɗauke da fara’a, kallonsu yayi yanda suka dace da juna nan da nan yaji takaici ya kamashi, kallonshi ya sake yi tun daga sama har ƙasa to kai Baqeer babh ƙafa ma me kake tunani? Menene ma naka a ciki? Wani abu ya haɗiya kamar zai koma sai yaji Dada tace “Baqeeru ina zaka? Bayan wurinka aka zo?” Haɗa ido suka yi da saurayin kafin suka ƙaraso ciki, Zeey ce tace “Physiotherapist ne zai duba ka ne kafin kuyi making appointment kaje asibiti ya sake ganin taimakon da zasu iya yi maka.” Hannu Junaid ya miƙawa Baqeer wanda shima ya miƙa mishi, dukkansu fuskarsu babu walwala, Junaid zuciyarshi cike take da son sanin wanene wannan da Zee duk ta damu dashi? Hannunsu na riƙe da juna Junaid ya kalleta yace “Kamar gaske in kina magana da serious voice.” Ta saki murmushi tace “Ban gane kamar gaske ba? Kai ma dai kasan in na canza yanda nake.” Dada ce ta kalleshi ganinta yasa ya saki hannun Baqeer sannan ya rusuna ya gaisheta ta amsa fuska a sake sosai, nan suka shiga ciki Baqeer ya tura keke suka shiga sosai,  kusa da Baqeer ya zauna sannan ya dan tsuguno yace “Sauƙe kafar daga kan keken muga.” Baqeer yasa hann ya ɗaga cinyarsa sannan ya sauke, kallonshi yayi yace “Well done! Bari muga.” Yayi maganar yana ɗan daga ƙafafunshi, Zeey da Dada dake tsaye suna kallonsu, ya ajiye ƙafar ya sake ɗaga ɗaya ƙafar, kallon Baqeer yayi yace “Zaka iya motsa yatsun ƙafafunka?” Baqeer duk yanda ya gwada abun bai yiwu ba ya girgiza kai zuciyarshi na wani irin zafi. Junaid yace “Babu komai dama dai gwadawa ne ai, ya sake momotsa ƙafafun yanayi yana nazari, yace “Takardun da aka baka na asibiti suna nan?” Yace “Dada takardun da Umma ta aiko dasu suna kusa?” Da sauri ta wuce don ta ɗauko, Junaid ne ya dawo inda Zeey take yace “Me kike tunani?” “Babu komai, ya kake gani?” “Haka kika yarda dani?” Murmushi tayi tace “Kaima ka sani ai.” Kalaman da suke yi duk Baqeer na jinsu, wani abu ne yake ji yana tokare mishi maƙoshi wanda bai san ko menene ba, yawun bakinshi ya haɗiya yana mamakin abinda yake ji. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 #Baqeer🦼 #Zeey #RayuwadaKaddara #Hawayena #Samudarashi #UmmuAsgar #Ayushermuhd *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA HUƊU* {34} Ya ɗauki wani lokaci yana duba takardun kafin ya ɗago kai ya kalli Baqeer yace "naga anan ance accident kayi shine cause na paraplegia ɗin ko?" Ɗaga kanshi kawai yayi alamun amsawa ba tare daya buɗe baki yayi magana ba don baka nan tsayuwar Zeey a kusa da saurayin ke saka mishi ɓacin ran da bai san dalili ba. Kallon Zainab Junaid yayi yana murmushi yace "In Sha Allah with proper care and treatment ko bai taka ba zai samu ya iya motsa ƙafafun da kanshi sai dai kuma kin san ciwo ke shiga farat ɗaya sauƙi sai hankali, ba wai daga fara session ɗin mu zai warke ba, it will take time before we can be able to see some changes". Daɗi ne ya kama Zeey jin cewa Baqeer ba zai dawwama a haka ba akwai yiwuwar ya warke, mutane su daina wulaƙanta shi saboda nakasar shi. "Thank you J, i really appreciate it" tace tana murmushi. Daɗi Junaid yaji yana ganin yayi wani abu daya faranta ran Zeey duk da bai san alaƙarta da patient ɗin ba, sanin wacece Zeey ɗin mai lafiya ma ba kowa take so ba bare nakasashe yasa yake danne abinda yaje ji yana mintsinin zuciyarshi akan Baqeer ɗin. Murmushin ya mayar mata shima yace "it's my pleasure". Kallon Dada tayi tana yi mata bayanin abinda Junaid yace, itama sosai farin ciki ya kamata jin akwai yiwuwar warkewar Baqeer ɗin, sai ga Dada na share hawayen farin ciki don sosai take jin tausayin Baqeer da yadda mahaifinshi ya juya mishi baya saboda ƙaddarar data sameshi. "Da kanka ma zaka iya yin exercises ɗin zan nuna maka yadda zaka yi kana daga zaune da hannayenka, In Sha Allah with time komai zai zama tarihi amma sai kayi haƙuri ka sakawa ranka juriya don irin wannan abun is very tiring" Junaid yace yana kallonshi. Ciki-ciki ya amsa mishi da "to" don yana lura da wani irin kallo da yake jifan Zeey dashi wanda yake ƙara saka mishi nauyin zuciya, haka nan yaƙi jinin yaga Zeey ɗin a tsaye a gefenshi, shi sai yaga ma kamar yau tafi koyaushe fara'a saboda tana tare da saurayinta. An ɗauki tsawon lokaci yana exercising mishi ƙafafun sannan ya nuna mishi yadda zai dinga mommotsa ƙafafun da hannayenshi yace "wannan exercise ɗin zai taimaka wajen tada jijoyoyin da suka mutu su koma aiki, Allah ya baka lafiya". Dada ce ta amsa da "Ameen" sai faman washe baki take yi tana saka mishi albarka daga shi har Zainab data kawo shi. Sun yi mata sallama suka tafi Zainab nace mata sai sun dawo ƙara dubashi don yace ba kullum zasu dinga yin treatment ɗin ba za'a na yin tsallaken kwana ɗaya idan anyi yau gobe ba za'a yi ba sai kuma jibi. Bayan fitarsu Dada ta kalleshi tace "Allah dai ya yanke maka wahala Baqeeru yasa a dace". A cikin zuciyarshi ya amsa da 'Ameen' don bai ji zai iya buɗe baki yayi mata magana ba saboda hatta ita haushinta yake ji ganin yadda take ta wani nan-nan da Junaid. ***** Yau ta tashi ɗakinta babu komai ko ƙwayar shinkafar da zata dafa babu, ƴan kuɗaɗen da ta samo wurin Umma tuni suka ƙare. Kallon ɗakinta tayi tana tunanin abinda zata ɗaga ta sayar ta samu ta saya musu abinci, ita yunwar cikinta ba damunta ma take yi ba don idan da sabo zata iya cewa har ta saba da ita to amma yaran fa ya zata yi dasu su da basu san babu ba. Fitowa tayi tsakar gida ta kalli uwargidanta dake tsugunne a gaban murhu tana girki. "Sannu da aiki Maman Aisha" ɗagowa tayi ta kalleta ta watsar don tasan wani abun zata tambayeta ganin yau tunda ta tashi bata ɗora sanwa ba tasan bata da komai ne ita kuwa kayan abincinta nata ne da ƴaƴanta ba zata iya ɗauka tayi neman suna ba alhalin itama nema take yi. Duk da taga kallon wulaƙancin da tayi mata sai tayi kamar bata gani ba tace "don Allah ko zan samu aron dubu ɗaya a wurinki? Wallahi yau na tashi bani da komai ga yara sun kusa dawowa daga makaranta bani da abinda zan basu". Mafici ta ɗauka ma ta hau fifita wutar girkin da take yi tayi kamar bata ji abinda Hadizan tace ba. Duk da taji haushin ƙyaletan da tayi bayan tasan sarai taji ta tsabar wulaƙancinta ne ya tashi amma sai ta haɗiye fushinta tunda tasan idan ba wurinta ba bata da inda zata je ta samu, idan ma tace ta tafi gida wajen Umma kafin ta ƙarasa ma yaran sun dawo gashi haka nan ta turasu makarantar ko ɗan kokon ma yau basu samu ba. Kwantar da murya tayi tace "don Allah Maman Aisha kiyi haƙuri ki bani aron wallahi ba zanyi miki wasa da kuɗinki ba zan baki". A fusace ta ɗago tana nunata da yatsa tace "bafa na son rainin da kike neman kawo mini Hadiza, da can ni nake baki abincin da zaki nemi ki takura mini ko kuwa ni na ajiye ki, ha'an haka kurum mace baki san ki tashi ki nemi na kanki ba sai dai a ɗauko kina daga kwance a baki idan ya ƙare ki nemi takura mini kamar nj na ajiye ki". Kamar tayi kuka haka take ji sai dai bata da yadda zata yi don haka ta ƙara cewa "kiyi haƙuri don Allah wallahi zan baki". Tsaki taja ta juya ta cigaba da aikin girkinta tana barta anan a tsaye tana jin takaicin rashin tashi ta nemi na kanta tun da gatanta sai kawai tayi kwance duk wata Ya Baqeer na ajiye mata kayan abinci don haka bata da wata damuwa a lokacin gashi yanzu tazo abincin da zasu ci ita da ƴaƴanta na neman yafi ƙarfinsu, shi dama maigidanta babu abinda ya dameshi idan yayi ficewarshi tun safe baya ƙara waiwayarsu sai lokacin kwanciya bacci yayi acan inda yake fita yake cin abinci don haka bai damu da ko suci ko kada suci ba. Ɗakinta ta koma tana share hawaye, tunaninta ɗaya yanzu idan yaran suka dawo daga makaranta me zata basu? Ɗakin kawai take bi da kallo tana tunanin ita yanzu ba wani abu gareta ba bare ta ɗaga ta sayar ta samu abinda zasu ci abinci, idanunta ne suka kai kan wata tshowar akwatin garwa ta maigidan da ta daɗe a ajiye a ɗakin nata, ba komai yake yi da ita ba sai haɗa ƙura don haka ta tashi ta janyota ta karkaɗe ƙurar kai tasa hijabinta ta sunkuci akwatin ta fice ta kaiwa ƴan gwangwan, ko ɗari biyar suka bata ai dai ta isheta ta samar musu da abinda zasu ji, da kallo kishiyarta ta bita tana ayyana lallai yau akwai bala'i a gidan don kuwa tasan ba ƙaramin ɓaci rayuka zasu yi ba akan wannan matacciyar akwatin. ***** Tunda suka bar gidan babu wanda yayi magana har sai da suka hau titi sosai suka yi nisa da unguwar ta mariri. "Who is he to you?" Ya tambayeta. Waiwayowa tayi ta kalleshi tace "na'am J, magana kake yi?" Ƙara maimaita tambayar yayi yace "Who is he to you? naga kin damu sosai da al'amuranshi". Shiru tayi ta kasa amsa mishi don sai ta samu kanta itama da yiwa kanta makamanciyar tambayar da yayi mata "waye shi a wajenta? Akwai wata dangantaka ne a tsakaninsu bayan kasancewar shi yaya ga ƙawarta Maryam?" Kasa bawa kanta amsa tayi don haka tayi shiru bata amsa Junaid ɗin ba, shima sai bai ƙara tambayarta ba jin tayi shiru sai dai yana jin fargaba akan abinda zuciyarshi ke neman saƙa mishi sai dai kuma idan ya tuna wacece Zeey ɗin da yadda take kallon maza ƴaƴan manya masu ji da kyau da class a ba komai ba sai ya samu ƴar nutsuwa kaɗan don yasan babu abinda zata yi da gurgu sai dai kuma tambayarshi anan itace waye shi a wajen Zeey ɗin data damu dashi da yawa har haka? Har suka ƙarasa gidansu babu wata hira a tsakaninsu kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarshi, sai da zai sauka nema tace mishi "nagode sosai J, please ka gaishe mini da Mami kace ina sauri ne shi yasa ban shigo na gaisheta ba amma takanas zan zo na gaisheta, sai kuma batun payment ɗinka ban ji kace komai ba". Harararta yayi yace "ai bakin ki ne payment ɗin" ya mayar da ƙofar motar ya rufe ya wuce ba tare da ko waiwayowa yayi ba. Bin bayanshi tayi da kallo har ya shige cikin gidansu sannan taja motarta ta bar wurin cikin ranta tana jin ina ma zata iya mayar mishi da martanin soyayyar da yake yi mata don tasan J yana sonta shi yasa yake ɗaukar duk wasu al'alarta sai dai kuma ba zata iya ba don ba wani girmarta yayi ba beside that bata jin shi har ƙasan ranta a matsayin wanda zata iya spending the rest of her life with. Girgiza kanta tayi kawai ta kawar da wannan tunanin daga ranta, haka nan ta samu kanta da yawatawa akan titi don bata ji tana son komawa gidan Inna ba taje suyi ta faɗa tana sakar mata baƙaƙen maganganu don ma dai tana kawarwa tana mayar da abun wasa amma abun yana yi mata ciwo yadda Inna take treating ɗinta sam baya yi mata daɗi. Sai can goshin magriba ta gaji da yawon a titi ta ɗauki hanyar da zata sadata da gidan Inna tana jin koma zuwa zata yi ta tattara kayanta ta koma gida ne. ***** Shi kuwa Bello ganin da yayi iyayen shi sun ƙi su goya mishi baya aje gidansu Asiya a nema mishi aurenta  daya ɗauki dukkanin buri ya ɗaura akai yasa shi niƙar gari ya tafi garin Rano inda Baffanshi babban yayan mahaifin shi yake da zama ya kai mishi ƙarar su Baban akan ya samu yarinya har sun daidaita kansu amma su Baba sun ce ba zai aureta ba. Nan fa Baffan ya rufe ido yayi ta faɗa yana cewa "don me yaro ya girma ya kai munzalin ajiye iyali zasu ce ba zai yi aure ba, to shi ba zai lamunci wannan ba dole aje a nema mishi auren tunda dai ya nuna buƙatar hakan kuma yana da abinda zai riƙe matar dashi". Haka nan Bello ya ɗauke shi a sabuwar motarshi daya saya don ba ƙaramin alheri ya samu ba a gasar nan da yaje suka tafi Kano. Duk yadda Baban Bello yaso yayi wa ɗan uwanshi bayanin dalilin da yasa suka ce Bello ba zai auri Asiya ba ya toshe kunne yaƙi karɓar uzurin su don kafin tahowarsu sai da Bello ya jiƙa shi da kuɗi don haka yace tunda dai yaji ya gani kuma yana da abinda zai riƙe matar to su ƙyale shi ya aureta, haka nan dai ba don su Baban sun so ba aka je gidansu Asiya aka nema mishi aurenta, shi kanshi Babanta da yaga iyayen Bello ne suka zo neman auren nata sai da yaji mamaki don yasan dai Bello abokin Baqeer ne asalin manemin auren ƴar tashi sai kuma yanzu iyayenshi suzo da wani zance na daban kuma don haka ya dakatar dasu sai da ya shiga gida ya kira Asiya ya tambayeta da saninta iyayen Bello suka zo neman aurenta? Babu kunya Asiya ta amsa mishi da eh, "to ina maganar Baqeer ta kwana da zaki sa abokinshi a nema mishi auren ki?" Sai cewa tayi "Baba Baqeer fa ya zama gurgu ta yaya za'a yi na aureshi?" Ɗan jim yayi kafin yace "ai shikenan tunda Bellon kika zaɓa, kin dai tabbatar kina son shi ko?" Ɗaga kai tayi alamun amsawa tana murmushin farin cikin ganin Baban bai bata wata matsala ba ya amince, sai Innarta ce tace "amma Mallam sai ka biye mata bayan kasan yaron nan Baqeer yayi wahala da ita ba kuma shi yace ya fasa ba sai ita da taƙi shi saboda kawai Allah ya jarabce shi da larura". Sai ce mata yayi "to in banda abunki shi da ya nakasa yanzu wane batun aure zai yi? Ai sai a bawa mai lafiya dama tunda kuma Allah ya kawo mijin ai ba zamu ƙi aurar da ita ba saboda wani dalili can". "Haka ne" kawai tace ba don ta gamsu da bayanin da yayin ba. Haka nan ya koma wajen iyayen Bello ya karɓi kuɗin aurensu nan dai aka tsayar da magana aka sa rana watanni uku masu zuwa. To sai muce Allah ya tabbatar da alkhairi.... *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce*        *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA BIYAR* {35} Da mamaki Zeey ke kallon motar da aka yi parking a harabar gidan, in har ba wai tayi kuskure ba motar Mummy ce, to yaushe tazo? Tambayar data faɗo mata cikin rai kenan, da sauri ta ƙarasa ciki fuskarta ɗauke da fara'a don tasan Mummy missing ɗinta ne yayi mata yawa,  harta shiga falon bata ga kowa ba, hakan yasa ta nufi ɗakin Inna kai tsaye don daga cikin falon tana iya jiyo magana na fitowa daga sama-sama don dama ta gaji da takurar Inna gwara ta bita su koma gida gashi kuma ta samu Junaid  zai dinga taimakawa Baqeer. Hannu tasa zata ƙwanƙwasa taji muryar Inna na cewa "Ke sam kamar ba uwa ba baki san me ya kamata ba? Wannan wace irin rayuwa kika ɗaukar wa kanki? Kenan ke baki san abinda ya kamata ba? Ko ce miki aka yi ita ba....." Ƙofar ta buɗe wanda hakan yasa su kallonta da sauri, ajiyar zuciya tayi zuciyarta na tafasa idanunta a kansu tace "Ni kam don Allah sai yaushe zaku daina faɗa a kaina? Wannan wace irin rayuwa ce?" Mummy ce ta taho tana neman riƙeta ta ɗaga mata hannu tace "Mummy please ki bari, ni yarinya ce? Ko kuwa shi kenan ni ban isa nace zanyi abu ba? Gidanku ne fa ba wai wani wurin naje ba amma sai kin nuna kamar ana wahalar dani?" Inna ce tayi tsaki tace "Ba sai tai tayi ba ni dai na faɗa ban gayyaceki ba don haka babu wanda zai zo ya ɓata mini rai a cikin gida don haka ki tattara ki bita." Takaici ne ya rufe Zeey kawai ta wuce ɗakin su da gudu, kan gado ta faɗa tana kallon Nabeela dake zaune tana karatu cike da shagwaɓa kamar mai shirin yin kuka tace "Aunty Nabs wai haka zamu zubawa Mummy da Inna ido? Shi kenan su daga sun haɗu sai faɗa, ba zaka taɓa ganinsu suna hirar arziƙi ba? Wannan wace irin rayuwa suka ɗaukarwa kansu? Ƴa da uwa kamar wasu maƙiyan juna? Kuma babban takaicina duk a kaina suke wannan abun?" Jiki a sanyaye Nabeela ke kallonta tace "To ya zamu yi dasu? Ni shi yasa muna gaisawa na bar musu falon don nasan dama raina ne kawai zai zo ɓaci." Kanta tasa a saman pillow cikin takaici tace "Ni wallahi na gaji da wannan abin nasu haba! Da zan bi Mummy mu koma gida amma yanzu Allah babu inda zani." Ta faɗa tana juya baya zuwa saitin Nabeela tana tunanin wannan rashin jituwa ta Mummy da Inna. Ita dai Nabeela kai kawai ta girgiza ta cigaba da karatunta don bata shiga wannan case ɗin. Mummy ce ta shigo ɗakin tana yiwa Nabeela alama da tayi shiru har ta ƙaraso ta zauna kusa da Zeey, hannu tasa ta ɗan mintsineta kaɗan, Zeey ta juyo da sauri rungumeta tayi tace “Mummy please!” Nabeela ce ta tashi ta bar musu ɗakin hakan yasa Mummy shafar bayan Zee tace “Naji ya isa am sorry shikenan?” Kallonta tayi tace “Bana son ku dinga faɗan nan, especially a kaina don Allah!” Jinjina kai tayi cike da fahimta tace “Naji to tashi mu wuce.” Ajiyar zuciya ta saki tace “Please Mummy ki bar ni zuwa jibi, abubuwa ne a kaina wallahi gaba ɗaya ni kaina ban san meke damuna ba, watakila faɗan Inna zai sa na dawo hayyacina.” Cike da mamaki take kallonta tace “Har akwai wani abu da zai hanaki sukuni a duniyar nan Zeey? Dad ɗinki yafi sonki a gida kema kin sani kaf duniya yafi ji dake sama da komai.” Fuska ta tsuke sosai tace “Kema kin san zolaya kike Mummy ni gaba ɗaya…….” Ta maida kanta kan cinyar Mummy cike da damuwa tace “Ban san ya zanyi ba sam haushin kaina da damuwar halin da nake ciki ya isheni.” Shafar kanta tayi tace “Koma menene kar ya dameki, a duniya mahaifinki ko me kike so zai tsaya miki ki samu, haka duk wani abu da bai fi ƙarfina ba kema kin san zan tabbatar kin samu abun nan, don haka ki sanar dani koma menene, na gaji da ganinki cikin wannan halin.” Tace me to? Bayan ita kanta bata san mazaunin da take ba? Mikewa tayi ta zauna a gaban Mummy ta lanƙwashe ƙafa a kan gado tace “Mummy mutum ne ya shiga raina, komai nake yi da tunaninshi nake yi bayan na kuma san bani da haɗi dashi to cut it short ma ni dashi enemies ne wanda am sure ko sunana yaji ya ganeni kallona ba zai sake yi ba, sai dai ban san meke damuna ba.” Da mamaki take kallonta tace “Son shi kike yi?” Kai ta girgiza da sauri tace “No of course not! Sannan ba ma lafiya gareshi ba kina ganin tausayi ne yasa nake jin hakan?” Shiru tayi tana nazari na wajen minti uku kafin tace “Ban san meke ranki ba Zeey sai dai nasan koma menene na baki damar kiyi abinda hankalinki ya kwanta dashi, a koda yaushe ina bayanki.” Rungumeta tayi tace “Mummy I love you so much, zan yi ƙoƙari nayi sorting tunanina kafin jibi in na dawo zan sanar dake komai.” Kai ta jinjina cike da gamsuwa sannan tace “Kuɗi fa kina bukata?” Kai ta girgiza tace “Har yanzu wanda Dad ya bani ban ma ci ko rabi ba.” “Bari na wuce.” Saukowa tayi daga kan gadon suka fito falo, har yanzu Inna bata fito ba da alama Nabeela na wurinta don suna iya jiyo dariyarsu ita da Nabeela daga falon, Zeey na mamakin wannan abu a koda yaushe Inna bata fushi da Nabeela amma baka taɓa ganin fara’arta da Mummy. Haka Mummy ta wuce ita kuma ta koma ɗaki, zuciyarta na tunanin ko Baqeer yana can yana exercise ɗin kuwa? Haka kawai sai taji murmushi ya kamata. ****** Washegari……. Umma tana gugar kayan Baqeer ragowar da aka bari a gidan tana so ta tattara ta samu taje ta ganshi, ita dai fatanta Allah yasa ya barta taje, tana mamakin yadda duk kwanakin da Baqeer yayi a gidan Dada har yau Badaru bai tambayi ina aka kai shi ba bai kuma tambayi lafiyarsh ba, ita sam dama bata damu da sai dole yazo ɗakinta ba amma a ƙalla soyayyar da yake nuna wa Baqeer bai ci ace ta gushe lokaci guda ba. Kamar daga sama taji ance “Hadiza? Uban me kike mini a gida har da ƴaƴanki da ƙatuwar jaka?” Garin razana da Umma tayi bata san sanda dutsen gugar ya ɗan shafeta ba, da sauri ta ajiye a gefe tunda na gawayi ne ta fito cikin sauri tana addu’ar Allah yasa ba Hadizanta bace yake magana akai. A tsugune taga Hadiza tana share ƙwalla tana gaida mahaifin nasu. A fusace ya nuna mata hanyar waje yace “Wallahi tun kan ranki ya ɓaci ki tashi ki bar mini gida, bana son haukar banza da wofi, bazan aurar da ƴara ba sannan su dawo mun gida da jaka don wannan jakar ko ban tambaya ba nasan ta yaji ce, ko ƙarya nayi?” Hawaye ta share tace “Baba don Allah ka tsaya ka saurareni wallahi auren nan sam……” “Kina sake magana zan sallami uwarki kuje can ku ƙarata, yau naga shirmen banza da wofi ni dama yanzu na cire rai da yaran Fatima amma babu ƙatuwar macen da zata dawo mini gida bayan ta cinye kayan gara da kayan ɗakin da na kashe kuɗi nayi mata.” “Ai dai gidan mahaifinta ne ko? To in ma komawar ne ba dai yau ba, don kuwa babu inda zata". Cike da dakiya Umma ctayi maganar duk kuwa da irin faɗuwar da gabanta yake yi. Salati Abu ta saka tana tafa hanu tace “Fatima? Wai Mallam kike yiwa magana haka gatsal? Ba tarbiyya babu biyayya? Tab lallai kin riƙa, wannan ai tarbiyar da take amfani da ita kenan shi yasa aka korota.” Nan da nan kuwa Badaru ya sake tunzura yace “Ki kwashi shirginki kibar mini gida kema, sai kuje can kuyi yawin tare tunda iskancin naku ya isa.” Umma bata tanka mishi ba tasa hannu taja Hadiza da ƴaƴanta suka shiga ɗaki tasa makulli ta rufe, suna jiyoshi yana zazzaga masifa amma babu wanda ya tanka a cikinsu sai Abu dake ta sake tunzurashi, Jamila mamaki duk ya rufeta wai yaushe Abu ta kile har haka? Bayan aurenta ne ta koya mata maida martani? Umma suna shiga ta kalli Hadiza dake ta kuka ga Aydah a bayanta itama kamar tasan me ake yi kawai kalle kake take yi ga ƴan biyu da alama bacvi ma suke ji, kuka sosai take yi Umma tayi shiru ita ma tana matsar ƙwalla a fakaice, wannan wani irin bala’i ne. ***** Kamalu dake ta shiri zai fita ya fito yaga Baba na zabgawa Hadiza faɗa shi abun dariya ma ya bashi yayi waje yana fito don abinda babu ruwanka daɗin kallo gareshi. Salim ya hango tsaye jikin mai baron sayar da yalo, kusa dashi ya ƙarasa yana tafiya yana cigaba da fito har yazo inda yake ya kalleshi yace “Kana dai da kuɗin yalon ko ba sata kazo yi ba?” Cike da takaici Salim ya kalleshi kawai ya kauda kai, Kamalu ne ya kalli mai yalon yace “Ka tabbatar ya baka kuɗin ka don ɓarayi ko a ina suke sai sun nuna halinsu.” “Wai ni kam Kamalu meye damuwarka dani?” “Damuwata ka fita hanyar Roshni yanzu ma can zani zance ko baka ga gayun da nayi bane? Irin babban yaro da babbar yarinya ba wai kai maloho ba, sannan ka sanar da abokinka yazo ya kwashe tsohuwar shi da ƙanwarshi dan tsoho ya sallamasu.” Gaban Salim ne ya faɗi hankali a tashe ya riƙoshi yace “Me kake nufi?” Fizge rigarshi yayi ya nunashi da yatsa yace “Wallahi kaji na faɗa maka ka shiga hankalinka dani inba haka ba na fasa ma baki.” Yana kaiwa nan ya ɗauki yalo ɗaya babu alamun zai biya kuɗin yayi gaba, haka Salim ya biya kuɗin haɗe da nashi, hankalinshi kasa kwanciya yayi tunda Baba na gida yasan bai isa yaje gidan ba don haka dole ya kira Baqeer ba don yaso ba. Baqeer na zaune a ɗaki yana ta gwada exercise ɗin da Junaid ya koya mishi, ajiyar zuciya yayi a fili yace “Kamar wani yace ta kawo mana saurayinta har gida.” Sai kuma yayi shiru tunda yasan taimakon shi aka zo yi, shi dai sam ya rasa me yasa zuciyarshi ke sake hango mishi Junaid da Zee tsaye kusa da juna, tsaki yayi ya cigaba da exercise ɗinshi, jin wayarshi na ƙara ya ɗaga da sauri ganin Salim ne. Tun daga yadda Salim ya amsa mishi sallamar yasan akwai matsala, jiki a sanyaye yace “Salim wani abu ya faru ne?” Kamar yace a’a sai dai yasan ba lokacin ƙarya bane in wani abun ya samu su Umma fa alhalin ya sani? Cike da sanyin jiki ya sanar dashi abinda Kamalu yace. Hankalin Baqeer ba ƙaramin tashi yayi ba nan da nan idanunshi suka canza kala sosai, wayar ya kashe a fusace ya fara tura kekenshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, har ya gama sanin meya faru in dai Hadiza ce tayi yaji “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” abinda zuciyarshi kawai ke faɗa kenan, matsalar nan dai ta kuɗi ce yanzu kam ko aikin ƙarfi ne tabbas zai yi in dai zai fitar da ƴan uwanshi daga halin da suke ciki, wani yanayi yake ciki mai wuyar fassarawa, sam bai ji kiran da Dada ke kwaɗa mishi ba ganin yana tura keke yayi hanyar waje, ita kuma ganin bai dawo ba yasa ta ɗauka fitar da yake yi kwanan nan ita ce yake son sake yi, hakan yasa ta koma ta cigaba da aikinta tana cewa “In zaka fita ai ka sanar mini banda dai Baqeer kai ma halinka sai kai.” Baqeer huci kawai yake yi, yau tana daga cikin rana mafi muni da wannan rashin ƙafar ta janyo mishi don gashi a titi amma bai san me zai yi ba.don duk hannun da yake ɗagawa babu mai adaidaitan daya tsaya mishi, waigawa kawai yake yi idanuwanshi na sake yin wani jaa, takaicin wannan rayuwar duk ta gama isarshi. A hankali motar ta tsaya a gabanshi, kallon motar kawai yayi yasan ta wacece don kuwa ya ganta a ciki kwanan nan, sauka daga titi tayi tare da yin parking idanuwanta kawai ta samu suna zubar da ƙwalla, ta fito zata kawo ma Dada irin abin motsa jiki data sayawa Baqeer a daren jiya kawai ta hangoshi a titi, ita da tayi niyyar bawa Dada ta koma ba tare da ta ganshi ba sai gashi a titi gwanin tausayi, share ƙwallarta tayi sannan ta fito daga motar, bata ce komai ba har tazo kusa dashi, hannun keken ta baya kawai ta riƙe ta fara turawa, yanzu kam ta tabbatar akwai abinda zuciyarta ke auna mata akan Baqeer don sam idanunta neman cigaba da zubar da ƙwalla suke yi sai ƙoƙarin maidasu kawai take. Shi kanshi Baqeer tunda ya ganta ya kasa magana, har wannan lokacin da take turashi kasa magana yayi, sai da suka bar kusa da titi yace “Zan iya.” Bata tanka shi ba ta cigaba da turawa har suka shiga wani kwana da zai sada su da gidan Dada. “Zan iya!” Baqeer ya faɗa cikin yanayi na jin haushin rayuwarshi, yanzu kam ya tabbatar yasan dalilin da yasa Asiya ta gujeshi. Tsayawa tayi a ta bayanshi tace “Meya faru?” Wani abu ya hadiya zuciyarshi na zafi yace “Ba komai.” Cikin wata kasalalliyar murya tace “Ya Baqeer haka zaka cigaba da rayuwa?” Damm gabanshi ya faɗi, Ya Baqeer? Yaji tasan sunanshi amma haɗashi da Yayan na menene? Don tana ƙawar Maryam? To amma damuwa dashi fa? Ko bai waiga ba muryarta cike take da tausayin shi. Zeey kuwa ji take yi ina ma zata san yanda zata yi taga ya miƙe? Bata son ganinshi cikin wannan halin, zuciyarta zafi take yi…… Waigowa yayi ya kalleta itama idanunta ta sauke cikin nashi, idanunsa sun yi jaaa ita kuma idanunta ciki suke taf da ƙwalla dake ƙoƙarin saukowa saman kuncinta, wani yanayin kallo suke yiwa junansu ko wane da abinda yake ayyanawa a cikin ranshi. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA SHIDA* {36} Shi ya fara kawar da kanshi yana ƙoƙarin danne abinda yake ji yana neman taso mishi. Cikin dabara tasa hannu ta ɗauke ƙwallar data taru a cikin idanunta tana kawar da fuskarta daga kanshi itama tana mai jin kunyar dogon kallon da suka yiwa juna, hannu tasa ta cigaba da turashi har suka isa gidan Dada kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyarshi. Sai da suka isa ƙofar shiga gidan sannan ta saki keken ta gewaye shi ta shige cikin gidan ta bar shi anan, bin bayanta yayi da kallo yana mamakin yadda take neman shiga cikin rayuwarshi ta ƙarfi don a yanzu in har bai ganta ba sam baya jin daɗi. Tana shiga Dada dake zaune ta tadda a waje tana gyaran waken da zata yi musu fate, tana ganinta ta fara yi mata lale maraba fuskarta ƙunshe da fara'a don tayi wani irin sabo da Zainab ɗin da idan ta kwana biyu bata zo ba zata yita cigiyarta tana jin kewarta. Itama murmushin ta saki duk kuwa da bata cikin yanayi mai daɗi ta soma gaisheta. Hannu tasa tana tayata gyaran waken tace "Yau gidan shiru Dada, sai ke kaɗai?" Kafin Dada ta buɗe baki ta bata amsa har ya gurguro kekenshi ya shigo gidan, bin bayanshi suka yi da kallo har ya shige ɗakinshi ba tare da ko kallonsu yayi ba, wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Zeey ta saki tana jin wannan baƙon yanayin yana sake ziyartar ta, taɓe baki Dada tayi tace "Ashe yawon naka ba mai tsawo bane, ai ni a yadda naga ka fice na ɗauka yau ma sai na ganka.”A surutu irin na Zeey a yau sai ta samu kanta da kasa amsawa Dada duk hirar da take yi mata har Dadan ta tambayeta "Lafiyarki ƙalau kuwa ƴar nan?" A ɗan firgice ta kalli Dada tace "Me kika gani?" Don duk a zatonta ko ta fahimci halin da ta samu kanta a ciki ne. Girgiza kai kawai Dada tayi tace "Ganinki nayi ba a yadda na saba ba shi yasa na tambaya ko ba kya jin daɗi ne?” Dariya tayi duk don ta kawar da tunanin Dadan tace "Da a yaya kike ganina?" "A yaya nake ganinki kuwa banda a yadda na sanki, sam ba'a raba fuskarki da walwala da fara'a gaki da yawan son barkwanci da hira yau kuwa duk kin yi wani sukuku dake tamkar ba ke ba shi yasa kika ji ina tambayar ko ƙalau kike.” Ƙoƙarin danne wani abu da taji yana neman taso mata tayi cikin muryar dake ɗan rawa tace "Lafiyata ƙalau Dada kawai dai ƴan maganar ne basa kusa ina jin shi yasa kika ganni a hakan.” "To Allah ya kyauta muku, kema kin koyi irin na Baqeeru kenan haka nan ana zaune dashi lafiya-lafiya gabaki ɗaya kuma sai kiga ya birkice sai kace wani mai jinnu.” Dariya ta saki tace "Kai Dada, Ya Baqeer ɗin ne mai jinnu, maza dai yaji ki wallahi babu ruwana.” Dariya ita ma Dada tayi tace "Yo sai me idan yaji ni, ko a gabanshi ma sai na faɗa tunda dai ba tsoron shi nake ji ba.” "To shikenan ni dai babu ruwana, ato.” Bata wani jima sosai ba ta tashi ta yiwa Dada sallama ta tafi, cikin zuciyarta ji tayi kamar ta leƙa ɗakin shi ta ƙara ganinshi sai dai kuma tayi wa kanta faɗa tace ki leƙa ɗakin shi kice mishi me? Don haka ta wuce ba tare da ko kallon ƙofar ɗakin tayi ba. Shi kuwa har ta bar gidan yana jikin ƙofa yana sauraren su duk da rabin hirar ba jinta yake yi ba sai dai jin tana dariya yasa yaji wata irin nutsuwa na saukar mishi. ***** Ƙyaleta tayi tasha kukanta ya isheta sai da tayi shiru don kanta sannan Umma tace "Sarai kin san halin mahaifinku Hadiza amma ba zaki yi haƙuri kamar yadda kowace mace take yi ki zauna a ɗakin ki ba, kun dai fi so kullum sai kun janyo mini ɓacin rai?” Wani hawayen Hadiza ta share cikin rawar murya alamun kowane lokaci zata iya cigaba da kukan tace "Umma ya zan yi? Wallahi duk haƙurina mutumin nan baya gani sannan kuma saboda Allah Umma a ina ake yin aure babu abinci, kullum fa haka yake ficewa ya bar mu da yunwa daga mu har yaran sai dai kowacce tasan yadda zata yi ta ciyar da ƴaƴanta ni kuma kin sani ba wani abu gareni ba, jiya na tashi ko ƙwaya bani da ita a ɗakina kuɗin da nazo kika bani ya ƙare a awon abincin da zamu ci da ƴan sauran buƙatu, jiya haka su Hassan suka tafi makaranta basu ci komai ba ni kuma ganin har lokacin tashin su ya kusa na rasa yadda zan yi yasa na ɗauki wata tsohuwar akwatin shi ta garwa na kaiwa ƴan gwangwan suka saya sannan na samu nayi mana abincin da muka samu muka ci, to wai akan ya dawo na sanar mishi da yadda aka yi na ɗauki akwatin da ba ma amfani yake yi da ita ba shikenan ya dinga surfa ruwan bala'i yana yi mini zagin tsame nama har yana cewa wallahi ba zai yarda ba sai na biyashi akwatin shi ko na bashi kuɗin da aka sayar ni kuma nace bazan bayar ba tunda ai hakkin shi ne ya ciyar damu amma ya fice ya bar mu babu abinda zamu ci don nayi ƴar dabara shine akan haka zai ci mutunci na, wallahi Umma har marina yayi da ace na tsaya ma nasan har dukana sai yayi ni kuma shi yasa na taho gida don wallahi na gaji da auren nan da babu abinda nake tsinta a cikinshi sai tarin damuwa da baƙin ciki," ta ƙarashe maganar tana sakin wani marayan kuka. Ita kanta Umma kasa riƙe hawayenta tayi tana jin tausayin irin rayuwar da suka tsinci kansu a ciki ita da ƴaƴanta kowanne akwai tarin ƙalubalen dake dabibaye da rayuwarsu sai dai kuma hakan ba shine zai sa ta goyawa Hadiza baya ta kaso aurenta ba alhalin zaman gidansu ma ba daɗi gare shi ba don haka cikin tausasawa tace "ai kuwa dai haka nan zaki koma ki cigaba da haƙuri, sanin kanki ne zaman gidan nan a yanzu yafi ƙarfinki tunda dai kina jin abinda mahaifinki yace ba zaki zauna mishi a gida ba ba tare ma da ya bari yaji abinda kika zo dashi ba, dole kije ki cigaba da haƙuri ko don ƴaƴanki ki kuma nemi abun yi da zai riƙe ku ke da ƴaƴanki tunda dai kin san halin mijinki ba mai ɗaukar nauyin gidan shi bane sai dai ku kuyi mishi.” Cigaba tayi da kuka jin Umma tace sai dai ta koma alhalin zaman gidan gaba ɗaya ya fice mata akai, idan ace akwai abinci ma sauran buƙatu ne ba'a ɗauke musu da da sauƙi sai taje tayi ta haƙuri amma saboda Allah ta ina zaman aure zai yiwu babu abinci don haka tace "Yanzu Umma haka ma zaki ce na koma bayan idan na koman ma ba canjawa zai yi ba?" "Haƙuri fa zaki yi Hadiza ki koma amma ba zai yiwu na barki ki zauna a gidan nan ba alhali mahaifinki yace sai dai mu haɗu mu bar mishi gidan gaba ɗaya, ni kuwa da girmana bazan je na zaune wa Dada ba bayan ga Baqeer can na kai mata tana riƙe dashi, sana'ar dai ita zaki nema dole don haka sai kiyi tunani anan unguwarku me kike ganin mutanen wajen sun fi buƙata ko kuma me nene ba kuda yawaitar masu shi kinga daga nan sai mu san wacce irin sana'a zaki yi tunda dai akwai kuɗin kujerun nan a wajena sai ayi amfani dasu ki kafa jarin.” Ajiyar zuciya kawai Hadiza take saukewa tana share hawaye, ita dai a sonta Umma ta barta ta zauna a gida sai dai kuma bata ga alamar Umman zata ƙyaleta ba, gara ma taje ta nemi na kanta yadda zata fi ƙarfin wulaƙanci har a wurin mijin ma don yadda yake yi mata cin kashi baya yiwa kishiyarta haka saboda ita tana da abun hannunta bata neman komai a wurin shi sai ma shi da yake lallaɓawa tana bashi rancen kuɗi. Tashi tayi ta ɗauke Aydah da tayi bacci a ƙasa ta gyarawa su Hassan da tun shigowar su suka kwanta bacci kwanciya sannan ta nemi wuri kusa da ƴaƴanta ta kwanta, tasan dai dole tayi tunanin abinda zai fisheta kafin gobe ta tattara ta koma can gidan. ***** Tunda ya shige ɗakin yake tunanin abinda ya kamata ya fara da zai taimake shi da mahaifiyar shi da ƴan uwanshi sai dai kuma duk sana'ar da tazo ranshi sai yaji anya kuwa zai iya irin wannan sana'ar alhalin shi ba ƙafa ce dashi ba a yanzu, matsalar da aka samu ita ce tun farko da zane ya buɗe ido kuma shine kaɗai abinda ya tsaya ya koya don yana tuna wani lokaci acan baya da yaso ya koyi sana'ar ɗinki Baba ya hanshi yace me zai yi da wani ɗinki shi da yake da sana'ar shi a hannu, yadda Allah ya bashi baiwar iya zane kuɗin da zai samu a harkar bai ninka abinda zai riƙa samu a ɗinki ba, yana ji yana gani ya haƙura da wannan burin nashi ya mayar da hankali akan zanen to yanzu gashi inda rayuwa ta kawo shi, bai iya komai ba sai wannan zanen da baya jin a yanzu zai iya ƙara riƙe pencil da sunan painting ko da za'a saka mishi bindiga a kanshi kuwa. Wajen kayan zanen shi ya nufa ya ciro takarda da pencil ya saita su yadda zai ji daɗin yin zane, pencil ɗin ya ɗora akan takarda ya rufe ido yana so yayi picturing abinda zai zana kamar dai yadda yake yi a baya sai dai jin ƙwaƙwalwar shi yayi ta zama blank kwata-kwata sai yaji tamkar bai taɓa sanin yadda ake yin zanen ba, yayi-yayi ya jarraba yin zanen nan amma ya kasa. Ji yayi gaba ɗaya zuciyarshi ta ƙuntata, ta yaya abun da tun yana yaro ƙarami ya ƙware akai yanzu tashi ɗaya lokaci guda zai gudu ya bar shi tamkar bai taɓa sanin yadda ake yi ba, gaba ɗaya sai ya zama frustrated yayi jifa da takardar ya watsar da pensiran yana sakin huci. Kanshi ya kama ya rirriƙe yana jin kamar yayi ta sakin ihu ko yaji wani sanyi ko yaya ne a cikin ƙirjinshi da yayi mishi wani irin nauyi yana yi mishi zafi. Ƙara janyo kayan da yayi watsi dasu yayi ya sake ɗaukar pencil wai ya ƙara gwada zana ko kaza ce amma duk yadda yayi tunanin ta yadda zai fara ya kasa, haka nan dai yayi ta ƙirƙirar abinda zai zana har ganye sai da yayi tunanin ya zana amma ya kasa, sai ya samu ƙwaƙwalwarshi kamar an shafe mishi sanin yadda ake yin zanen ne kawai, wata irin ƙara ya saki yana jin rashin amfanin kasancewar shi a raye tunda ba zai iya yiwa mahaifiyarshi da ƴan uwanshi maganin kukansu ba, shine babba kuma shine gatansu duk wata taƙamarsu dashi suke yi to yanzu gashi ba zai iya yi musu maganin komai ba shi yasa sam baya ganin amfanin rayuwar shi. Da hanzari Dada ta shigo ɗakin tana cewa "haba Baqeeru, ayi bawa shi dai ya kasa tawakkali kullum sai ka ɗaga mini hankali ka ɗagawa uwarka da bata da wani tunani sai naka, ai ko baka ɗauki dangana don kanka ba kayi don mahaifiyarka". Kallon tsakar ɗakin tayi taga yadda ya watsar da kayan zanenshi tace "Dole ne sai kayi zanen ne? Ba sai ka nemi wata sana'ar ba tunda dai Allah bai hana maka rai da lafiyar da zaka tashi ka nemi na kanka ba, haba. Banda dai ubanka ya kwaɗaita maka son zanen nan ni banga wani abu da mutum zai tsinta a cikin shi ba wai sai kaji an saka maƙudan kudaɗe an sayi takardar da wani ƙato ya taƙarƙare ya zana. Ai ina ga kwashe kayan zanen zan yi idan baka ganin su ai baka ce dole sai kayi ba alhalin duk ranar da ka gwada yin zanen bama zama lafiya, ƴar walwala da nutsuwar da ka samu duk sai subi su ruguje.” Tana sababi tana tattare kayan haka ta kwashe su ta mayar ɗakinta tayi musu kyakkyawan ɓoyo don bata jin zata ƙara barin Baqeer ya gansu ma bare yace zai ɗauka ya gwada yin zane bayan ta lura abinda ke ƙara dagula nutsuwa da kwanciyar hankalin shi kenan. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce*       *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA BAKWAI* {37}    Da kallo yabi Dada tabbas tsanar kanshi duk ta isheshi, babu shakka shi ba kowa bane in babu zane, wace irin rayuwa yayi da bai dogara da komai ba sai shi? Idanunshi ne suka yi jaa yana tuno lokacin da yana yaro ko wasa zai fita waje Baba hanashi fita yake yi akan dole ya koma ɗaki yayi practicing painting tun yana shekara huɗu yake yi haka zai yi ta yin shirme amma Baba na yaba mishi a hankali yazo daya ƙara wayau ya fara zane abubuwa kamar dabobi da yake Allah ya bashi baiwa ga kuma Baba dake sakashi yi a koda yaushe yasa tun yana ƙarami hannunshi ya ƙware da yin zane, da ya shiga school kuwa bama a competing dashi don kowa yasan zanenshi ya fita zarra, a kuma nan makarantar ne suka haɗu da Bello wanda basu san unguwarsu ɗaya ba, yanzu shi me zai yi? Me ya iya? Hawaye ne suka cika taf cikin idanuwanshi nan ya haɗiye wani abu daya makale mishi a maƙoshi, yana jin zuciyarshi na wani irin zafi. Idanuwanshi ya rufe, kalaman Zeey ne ke sake yi mishi yawo a ƙwaƙwalwa, dole yasan abun yi ba zai bar mahaifiyarshi da ƙannenshi cikin tashin hankali haka ba. Wayarshi ya ɗauka ya kira Umma. Ringing uku ta ɗauka ganin sunan Hadiza wanda ya tabbatar mata da Baqeer ne, jiki a sanyaye yayi sallama, ta amsa cike da jin daɗi, muryarta na rawa tace “Ya jikin?” Cikin dakewa yace “Da sauki Umma, komai lafiya?” Ta sake daurewa tace “Komai lafiya Baqeer kai ne abun ji ai.” Zuciyarshi ce ta sake karyewa yace “Kada ku damu dani komai lafiya, ya wurin su Hadiza da Maryam?” Umma tayi ajiyar zuciya tace “Suma duk lafiya ƙalau, Hadiza ma taso zuwa nace ta jinkirta don muzo tare.” Wani yanayi ya tsinci kanshi a ciki ganin Ummanshi na ƙoƙarin ɓoye abu saboda shi, ya zai yi? “Baba fa? Ya bar takura muku?” “Kar ka damu da wannan Baqeer shima yanzu ya daina, ya Dada?” Yace “Lafiya kalau.” Shiru suka yi kamar basu saba ba, jin alamun kukan Aydah yasa tayi saurin yi mishi sallama ta kashe wayar. Saman goshinta ta shafa don kanta wani irin ciwo yake yi wanda take jin har wajen idanunta yake tabawa. Haka ta kwanta sai dai har wajen ƙarfe uku bata yii bacci ba, tashi tayi kawai don tayi alwala ganin ya fiye mata kwanciya tana saƙe-saƙe. Zabura tayi a waje ganin mutum na ƙoƙarin rungumar bango, sai kuma ya girgiza kai yace “Sorry Roshni na tsaya ƙyam salute!” Ya dan buga ƙafa yana daidaita tsayuwarshi, kafin yayi hanyar shiga ɗakin Kamalu, Umma tsorata tayi ta fara neman son yin ƙara taji yace “Shhhhh! Malama nine.” Kallonshi tayi da mamaki tace “Kamalu? Me kake yi a waje a daren nan?” Cike da takaici ya ƙaraso yace “Wannan kuma ba damuwarki bace ke da kike waje yanzu me kike yi?” Mamaki me ya hanata magana don daga yanda yake magana ma ba wai kanshi ƙalau bane, ba dai zargin da ake yi mishi na yana shaye-shayen kayan maye da gaske ba ne? Tana ganinshi ya shiga ɗaki. Alawala tayi ta koma ɗaki, a iya saninta Baba da wuri yake rufe ƙofa to tabbas ta katanga ya sauko kenan, Innalillahi lallai Kamalu bashi da kai dole a dage da yi mishi addu’ar shiriya, tasan yanzu tana yin magana za ace din taga ɗanta ya rasa ƙafa ne take neman ƙaƙabawa Kamalu laifi. ***** Wayarta ta ɗauka tana jujuyata, jibi zasu je asibiti wurin Junaid sai dai tun yanzu tana ji zuciyarta baza ta iya haƙuri da rashinshi ba, ido ta runtse tare da jan bargo ta lulluɓe fuskarta, Nabeela ce ta girgiza kai tace “Allah Zeey akwai abinda ke yawo akan ki, anya kuwa.” Juyowa tayi dukanta tace “Aunty Nabs ya zaka yi ka cire mutumin da kake tausayi daga ranka?” Kallonta tayi tace “Ya zaka yi dai ka cire wanda kake so a ranka?” Tsaki tayi tace “Ke fa matsalarki kenan sam baki fahimta to mu bar maganar.” Sauka Nabeela tayi ta fito daga ɗakin hakan yasa Zeey sauke ajiyar zuciya, waya ta ɗauka ta kira Salim nan ta sanar dashi zuwan da zasu yi asibiti yace to zai zo da safe, tace “Yauwa bani number shi zan tura mishi text na abubuwan da zamu tafi dashi.” Salim yace “To shikenan.” Zata yi magana taji muryar mace tana cewa “Waya kake yi?” Zee cike da tsokana tace “Wacece?” “Habi ce ƙanwar Asiya saƙo na kawo mata.” Da mamaki tace “Asiya?” Gyaran murya yayi yace “Budurwar Baqeer tada.” Mamaki ya kama Zeey tace “Me kake yi tare da kanwarta?” “Saƙo kawai zan bata na juya, sannan ita babu ruwanta kinga duk abinda ya faru ma daga wurinta muka ji.” Murmushi tayi tace “Anya kuwa saƙo ne kawai?” Yasa dariya yace “A’ah fa ba komai tsakaninmu.” Nan suka yi sallama ya tura mata number Baqeer. Sa wayar tayi a ƙasan pillow ta daki saman goshinta tace “No babu abinda zan yi, Zeey calm down and take a deep breath.” Nan ta fara breathing in and out tana cewa “Ba komai a raina, tausayi ne, tausayi ne, da kuma zumuncin Maryam.” “Yaushe kika je gidan Maryam? Yaushe kika kirata ko a waya? Yaushe ma kika nemeta?” Kai ta girgiza ta fito daga ɗakin da sauri babu kowa a falon, baki ta taɓe sam Inna babu ruwanta da ita, ƙofar ɗakin Inna taje ta ƙwanƙwasa. Suna zaune ita da Nabeela suna hira suna dariya, kallon Inna tayi a shagwaɓe tace “Inna a dai dinga yi mini kara.” “To ai ko ban miki ba kina yiwa kanki.” Zama tayi kusa da ita tace “Hirar me kuke yi ni aka warenj?” “Ba ji zaki yi ba, ke ni kam me yasa kike da son jin abinda bai shafe ki ba.” Shiru tayi don tasan Inna dama baƙar magana zata faɗa mata, ga mamakinta shiru ɗakin ya koma, jiki a sanyaye ta miƙe ta bar musu ɗakin tunda babu amfanin zaman nata. Wayarta ta kalla ta kalli number Baqeer, taɓawa tayi nan da nan wani abu yazo mata hankali a tashe ta ɗauki wayar zata kashe, tana kai hannu zata kashe shi kuma ya kai hannu ya ɗauka, ido ta runtse da sauri ta kara wayar a kunnenta. Baqeer wanda ke zaune a ɗaki wayarshi ce tayi ƙara, kallon sunan da yayi saving number yayi ‘ƙawar Maryam’ kallon wayar ya sake yi yana mamakin ashe tana da numbershi? Kenan tasan lokacin da ya kirata? Nan ya ɗauka yana son tabbatar da itan ce ko a'a don in haka ne lallai yayi abun kunya. Zeey ganin ya ɗauka yasa ta zaro ido tare da sauke ajiyar zuciya, shiru yayi shima don bai san me zai ce mata ba. A hankali tayi gyaran murya tace “Hmm nace na kira Salim.” Yace “Toh!” Toh? Ta maimaita a ranta sannan tace “Na sanar dashi maganar zuwa asibitin shine nace zan kiraka don na faɗa maka ka taho da takardun da aka baka a Aminu Kano.” Ga mamakinta yanzun ma toh kawai yace, takaici ne ya kamata tace “Toh toh bye.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta kifa kanta akan pillow sai kuma ta ɗauki wayar tayi saving ɗin numbershi da ‘Toh’ Baqeer kuwa tana kashewa ya kalli wayar yace “Meye abun fushi to? Ba dai nace toh ba?” Ya ajiye wayar yana mamakin fushin na menene. ****** Washegari Umma ta bawa Hadiza dubu uku a cikin kuɗin nan sannan tace “Kije in muka yi magana da Maryam sai ki samu ko injin markaden ne ki siya ki fara sana’a don zamanki haka babbar illa ce.” Ita dai Hadiza taso ta sake kwana ɗaya amma babu halin yin hakan don ita kanta tsoron Baba take kada ya dawo yazo ya tarar da ita ga kuma karatun yara da babu yadda zata yi, takaicinta ɗaya ko waya bai yi ba balle ma ya nuna yayi dana sanin abinda yayi. Haka ta fito riƙe da yaranta idanunta fal da kwalla, Jamila ce ke shara a tsakar gida, ganin Hadiza yasa tace “Dije tafiyar zaki yi?” Kallonta tayi dao sam bata ma san me zata ce mata ba, Abu ce ta leƙo tace “Dije to kinga dai kafin ki maida ku zawarawa daga ke har uwar taki gwara ki lallaɓa ki riƙe aurenki da daraja, in kuma ba gidan Maryam zaki tare da zama ba ayi abun kunya.” Mamakin kalamanta ne yasa Hadiza kallonta tace “Dadinta dai kema kin taɓa yin yajin.” Baki Abu ta saki, ai kuwa kamar an tsungunota cike da masifa tace “Uban wa kike faɗawa haka? Ni? Eh lallai kam wuyanki ya isa yanka, lallai yarinyar nan, ba dai zugoki aka yi a ɗaki don kiyi mini rashin kunya ba ko?” Ita dai Umma tana jinsu bata san magana don maganar ma ƙara tada husuma zai yi, daga ciki tace “Hadiza bana son shirme fa ki wuce ki tafi gidanki.” Fita tayi ranta a matukar ɓace, ta tsani cin kashin da suke yi musu kwanan nan don kawai Ya Baqeer ya samu nakasa shikenan sai a maidasu kamar ba yaran gidan ba? Ita dai ko ina babu daɗi, wannan wace irin rayuwace? ****** Yau tun safe tayi wanka kai kace makaranta zata je, Zeey da aka sani da baccin safe amma yau ƙarfe bakwai tayi wanka, akwatinta ta buɗe bayan kanta ta shafa tana jin haushi bata wani kwaso kaya da yawa ba gashi tasan gobe dole ta koma don Daddy da kanshi ya kirata jiya yace ta dawo. Zazzage akwatin tayi ta fito da ragowar kaya kala uku da bata saka ba, ɗaya atamfa ce sai biyu laces, tunani tayi kamar Baqeer bai taɓa ganinta da lace ba hakan yasa ta maida atamfar ta fara duba ɗinkin laces ɗin, light brown riga da skirt ne sam bata son saka kayan da zai takura mata shi yasa bata sa kaya da skirt amma haka nan ta saka shi, turarenta ta fesa ta shafa mai da kwalli sannan ta ɗaura ɗankwali, cike da mamaki Nabeela dake kwance akan gado take kallonta, can ta kasa daurewa tace “Zeey ba dai wata ƙasar zaki babu labari ba?” Kallonta tayi tace “Wai kin tashi? Asibiti zani.” Kallonta take da mamaki tace “Asibiti? Kina nufin duk shirin nan na zuwa asibiti ne?” Kafaɗa ta ɗaga mata tace “Nawa ra’ayin kenan.” “Wai skirt ma kika sa? Kai kamar ma ɗinkin da Mummy tayi miki wanda taso kisa da taron da aka yi last year kika ce baza ki saka ba tunda skirt ne?” “To ko ma dai menene yau dai nasa zan tura mata da picture.” Zeey tayi maganar tana duba agoggo. Ita gani take yi ma lokacin baya sauri “Karfe nawa zaki fita?” Nabeela ta tambayeta itama tana duba agoggo. “11am ne appointment ɗin.” Nabeela bata san sanda ta miƙe zaune ba tace “11 shine kika shirya tun 8? Eh lalai wannan da alama dai zance zaku yi ke da likitan.” Murmushi tayi don ita kam bata san me zata ce ba kuma, da ƙyar ta haɗo tea ta sha don sun yi da Salim 10am zasu haɗu. ***** Shi kanshi Baqeer yau da wuri yayi wanka ya gunguro kekenshi ɗaki yasa kaya, farar shadda yasa mara nauyi irin mai shara-shara ɗin nan, jin Dada tana ta fama a waje yasa ya fito, ganinta yayi tana surfa wake, yanayin fuskarshi ne ya canza yana kallonta yace “Dada me kike yi hakan?” Dariya tayi tace “Baqeeru ka fito? Ranar naji Zainabu na maganar ƙosai shine…..” Ai bai san sanda ya katseta ba yace “Dada shekarunki nawa da zaki yi surfe? In tana so ki jira in tazo sai kuyi tare ko kuma in yara suka zo su tayaki, amma fisabillilahi menene hakan? Salon wani abun ya sameki kuma?” Ya ƙarasa maganar yana nufar inda take, amsar taɓaryar yayi yana kau da kai fuskarshi a ɗaure ya fara bugawa da yake ba iyawa yayi ba gashi a zaune sai turmin ke ta rawa, yanata dukan gefe, dariya tayi tace “Wai da gaske bari nayi inga ko zaka amsa ashe kuwa zaka amsan, ahh Baqeeru kaga shikenan matarka ta huta.” Bai bata amsa ba sai suka ji sallamar Salim, kallon Baqeer yayi cike da zolaya yace “Shi kenan zamu fara sanar da mutane ana surfe a gidan Dada.” Baqeer wanda idanunshi suka haɗu da Zeey dake shigowa kawai ya ɗan kau da kai, yanzu me Dada ta jawo musu wannan abun kunya har ina? Aga namiji babba kamarshi na surfe? Dada ce tasa dariya tace “Shi kenan ba kaga ni na huta ai, Zainabu wai ƙosai zan yi miki kafin ki dawo shine yake tayi, Baqeer ni kam an gama surfen ne? Naga ka tsaya.” Kallon Zeey yayi kamar ita tayi maganar kafin ya kalli Dada kawai ya ajiye taɓaryar. Dariya tasa ita da Salim, nan suka fito Dada na zolayar shi har suka shiga mota. Baya ta zauna shi da Salim suna gaba, Baqeer kallonta yake son sake yi sai dai babu dama don tabbas gani yayi kamar yau tafi ko wace rana yi mishi kyau, to wai shi meke damunshi? Kada dai ka manta ƙawar Maryam ce. A jikin wani shago suka tsaya na ɗinki Salim ne zai amshi sako, Baqeer  ne ya zubawa shagon ido yana kallon yadda suka yi kwalliya da ɗinkuna daga waje, sam hankalinshi ya tafi wurin kalin styles. Zeey idanunta na kanshi tana kallon yadda ya zubawa shagon ido cike da kokonto tace “Ya Baqeer naji ance zane kake yi, kana zanen kaya?” Waigowa yayi ya kalleta, idanuwansu ne suka haɗu da juna, idanun Zeey dake ɗauke da kwalli ya kalla, wani abu ne yake ratsa zukatansu wanda su kaɗai zasu iya kwatantawa a hankali yace “Haven’t tried it yet amma ina ga I can do it, meya faru?” Ta ɗan yi murmushi kafin tace “Yauwa! Akwai ɗin kin da nakeso ne ni duk masu ɗinkin dana kaiwa teloli da yawa sun kasa yi mini abinda nake so am sure in kai ka zana zai yi.” Zai yi maganar Salim ya buɗe ƙofar hakan yasa su yin shiru gaba ɗaya……… ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA TAKWAS* {38} Har suka ƙarasa asibitin babu wanda ya ƙara yin magana cikinsu sai Salim da jifa-jifa yake jefo musu hira ganin duk sun share shi yasa yaja bakin shi ya tsuke shima, cikin ranshi dai tunani yake to me ya faru a tsakanin su daga fitarshi da ya sakasu canjawa lokaci ɗaya har haka. Asibitin private physiotherapy clinic ne mai kyau da mahaifin Junaid ya buɗe mishi tun kafin dawowarshi ƙasar aka kuma zuba ma'aikata da kayan aiki masu kyau da inganci aka fara aiki tun Junaid ɗin bai dawo ba. Suna shiga cikin reception ta fito da wayarta daga cikin ƴar ƙaramar jakar hannunta tayi dialing number Junaid, tana fara ringing kamar wanda yake jiran kiranta ya ɗauka. "Hey babe, ya aka yi?" Ɗan yamutsa fuska tayi kamar yana ganinta jin ya ambace ta da babe, "Gamu mun ƙaraso muna reception.” "Ok, ku tambaya a nuna muku office ɗina sai ku shigo.” Kashe wayar tayi ta mayar cikin jaka sannan ta ƙarasa wajen receptionist tayi mata bayanin abinda Junaid ɗin yace. Tashi tayi ta rakasu har ƙofar office ɗin sannan ta juya tana mamakin su kuma waɗannan ɗin su waye da suka shiga wajen chairman direct, ga dukkanin alamu dai VIP ne don ba kowa yake yarda ya gani ba. Sun shiga office ɗin da sallama, ya taso ya tare su yana murmushi. Hannu ya miƙawa Salim suka gaisa sannan ya bawa Baqeer hannun shima yana tambayarshi yanayin jikin shi, kamar baya so ya amsa mishi da 'lafiya' don haka nan yake jin takaicin Junaid ɗin bare daya lura da wani irin narkakken kallo da yake bin Zainab dashi. Wajen zama ya nuna musu Zeey da Salim suka zauna shi kuwa Baqeer yana zaune akan wheelchair ɗin shi dama, kallon ƙaton office ɗin Salim yayi yana jinjina tsaruwarshi da yadda aka kashe kuɗi wajen zuba kayan aiki a ciki, ya tabbata ba don Zeey ba basu isa su samu ganin Junaid ba bare har ace shi da kanshi zai ke duba Baqeer, to ai ko asibitin baya jin zasu iya zuwa saboda daga gani da ido ma an san ba wajen zuwan mai ƙaramin ƙarfi bane don zai yi muguwar tsada ko daga yawan kayan aikin daya gani kawai. Kallon Salim yayi ya miƙa mishi wata takarda da yayi rubutu a jiki yace "Please abokina ko zaka je reception kayi musu magana a buɗe mishi file yanzu sai ka kawo min.” Tashi yayi ya karɓi takardar ya fita. Sai sannan yayi wa Zeey magana yace "Ga alama dai yau nayi laifi tunda Zeey ta shigo ko kallona bata yi ba,” yayi maganar yana sakar mata ƙayataccen murmushin shi mai tafiya da tunanin ƴammata. Harara ta watsa mishi haɗe da turo baki gaba ba tare data tanka mishi ba abinda ya ƙara ƙular da Baqeer don sai yaga shagwaɓa ce kawai Zeey ke yi mishi duk kuwa da bata buɗi baki tayi magana ba. Dariya ya saki yace "Hoo Zeey, wai don Allah da gaske fushi kike yi dani? To me nayi miki ne hum, faɗa min, kin san fa bana jurewa fushin ki please kiyi haƙuri ko ɗan murmushi ne kiyi min.” Sai sannan ta ɗaga dara-daran idanunta ta kalleshi sai kuma taji kunyar gwasaleshi tunda dai tasan babu abinda yayi mata kawai dai tana tauna tsakuwa ne don aya taji tsoro, ita tasan Junaid da gaske yake son ta sai dai ita kuma she can't give him anything more than friendship bare a yanzu da take ƙalubalantar kanta da sabon yanayin data tsinci kanta a ciki, ba zata so Junaid ɗin ya zura jiki a sonta ba alhalin she cannot reciprocate his feelings bayan haka ma bai wani girme mata ba ita kuma tun asali bata taɓa jin sha'awar yin soyayya da saurayin da bai bata wasu shekaru da yawa ba. Murmushi ta saki tace "laifin me zaka yi mini, kawai dai i'm not in the mood ne.” Tafa hannushi yayi yana dariya yace "Ashe kuwa yau za'a yi ruwa da ƙanƙara, dama akwai wani mood da zaki shiga ya hanaki surutu? Kece kuwa Zeey ɗin dana sani ko kuwa dai wata ce me kama da ita?” Ta buɗe baki zata bashi amsa kenan Salim ya turo ƙofar office ɗin ya shigo don haka ta mayar da bakin ta rufe. Sai da ya karɓi file ɗin sannan ya juya ya kalli Baqeer daya cika yayi fam yake ganin kamar da gayya Zeey ta kawo shi wajen saurayinta suna soyayya a gabanshi, yace mishi "Ina fatan dai kana yin exercises ɗin kamar yadda na nuna maka?" A cunkushe yace mishi "eh" yana jin kamar ya janyo shi ya tsokane idanun nan masu yawan kallon mata (mu kuma muka ce masu yawan kallon Zeey dai ko Mallam Baqeer). Sai da yayi ƴan rubuce-rubuce akan folder ɗin sannan ya tashi ya zagayo wajen Baqeer bayan ya fito da wasu machines ya ɗora akan table, da taimakon Salim suka ɗora shi akan gadon da yake duba marasa lafiya sannan yaja labule ya rufe wajen saboda samun privacy, ɗaya daga cikin machines ɗin ya ɗauka yana daddana mishi akan ƙafafun nashi tun daga gadon bayanshi, haka yayi ta amfani da machina kala-kala a jikin Baqeer idan ya gama da wannan sai ya ɗauki wannan kuma har aka ɗauki wani lokaci mai tsawo, kafin kace miye wannan kuwa Baqeer ya haɗa gumi kashirɓan a dukkanin gaɓɓan jikin shi. Shi da kanshi yaji daɗi a jikinshi daga yadda treatment ɗin nasu ya kasance. Fitowa yayi ya barshi a wurin yana mayar da kayanshi don kafin a fara treatment ɗin sai da ya rage kayan jikin shi ya zama daga shi sai boxer short, wajen sink ɗin dake gefe guda daga cikin office ɗin ya nufa ya wanke hannayenshi bayan ya cire handgloves din ya zuba a dustbin sannan ya dawo ya zauna. Har ya gama saka kayan yana tunanin ta yadda zai yi magana azo a taimaka mishi ya sauko daga kan gadon don yayi mishi tsawo ba zai iya daddafawa ya koma kan wheelchair ɗin tashi ba, jin shirun shi yayi yawa yasa Salim ya taso don yasan halin Baqeer ba zai taɓa cewa yana buƙatar taimako ba sai dai suyi ta zama a haka. Da taimakon Salim ɗin ya koma kan wheelchair ɗin Salim ya tura su zuwa gaban table ɗin Junaid a wannan lokacin kuwa hira suke yi da Zeey yana tsokanarta wai ba zai barta ta fita daga cikin asibitin ba sai yasa anyi mata allura don ya santa da tsoron allura tana kuka tun da can idan za'a yi mata sai anyi daga da ita, ita kuma tana cewa "Da kenan wallahi yanzu wuce nan na tsaya ina kuka akan allura" shi kuma yana cewa "A’a fa Zeey gara dai ki daina cika baki kada kizo kina jin kunya.” “Allah ya sauwaƙe wallahi,” tace tana murguɗa mishi baki. Wani abu Baqeer yaji ya tokare a makoshin shi, haka nan shi dai baya son ganin Zeey tana yiwa saurayin nan fara'a duk kuwa da bai san miye a tsakaninsu ba, bai san lokacin da ya saki siririn tsakin da a tunaninshi a cikin zuciyarshi yayi ba sai da yaga duk sun zuba mishi ido sannan yasan a fili yayi, kawar da kai yayi kamar bai lura da kallon da suke yi mishi ba ya kalli Salim da fuskar da babu ɗigo na fara'a ko kaɗan a ciki yace "Mu wuce ko?" Ɗaga kai kawai yayi alamun amsawa don haka nan yaji kamar Baqeer bai kyauta ba da yadda yake ta cika yana batsewa kamar wanda aka yiwa wani abu bayan duk ƙoƙarin da Zeey take yi na ganin ya samu lafiya abinda mahaifin da yake tutiyar yafi kowa son shi ya kasa yi mishi. Kallon Zeey Salim yayi sai ta miƙe tana cewa "Thank you J, ka dai ƙi muyi maganar nan amma In Sha Allah ina komawa gida zan kira ka, please kada kace a'a" ta ƙarashe maganar tana langaɓar da kai gefe, shi Junaid ya fahimci maganar payment da yaƙi suyi ranar take yi mishi don haka yayi murmushi kawai yace "Waiting for your call with pleasure," yayi winking mata idonshi ɗaya. Takaici ne Baqeer yaji ya lulluɓe shi matsawa yayi kusa dashi ya ajiye wayarshi yace “Sorry ba kuɗi a hannuna ka riƙe wannan In Sha Allahu in na samu kuɗi zan kawo maka.” Zeey ce tayi mishi alama wanda yasa Junaid yin murmushi yace “Kar ka damu, sabon asibiti ne sai muke trial na 30days, so after 30days in dai kazo you have to pay.” Da mamaki Baqeer ya kalleshi Junaid ya nuna mishi wani flyer dake wurin wanda ya bawa Baqeer amsa, ganin da gaske yake yasa yace “Thank you” ya gara kekenshi da sauri ya bar office ɗin yana jin kamar zuciyarshi zata buga tsabar kishin da yake ji wanda tunda yake bai taɓa jinshi akan wani ba, da sauri Salim yabi bayanshi bayan ya yiwa Junaid godiya, Zeey ma tabi bayanshi suka fita tana jaddada wa Junaid zata kirashi idan ta koma gida. Bayanta yabi da kallo har ta fice yana sakin wani malalacin murmushi, har cikin zuciyarshi yasan yana son Zeey sai dai ta kasa ɗaukar shi da muhimmanci ita kallon aboki kawai take yi mishi gashi yaga alama shima wannan gurgun kamar son ta yake yi don yana lura da yadda yake harararshi a fakaice, shi dariya ma abun ya bashi don dai yasan idan har da gaske shima son Zeey ɗin yake yi to haukarshi kawai yake yi don kuwa babu abinda zai haɗata da nakasashen mutum, maza masu lafiya masu ji da class da kuɗi ma basu isheta kallo ba bare wani gurgu sai dai kuma deep down yana jin shakku na yadda Zainab ta ɗauki al'amuranshi da girma don shi dai zai iya cewa bai taɓa ganin Zeey ta damu da wani mutum kamar yadda ta damu da Baqeer ba. ***** Kamar yadda suka zo haka suka koma babu mai yin magana a cikinsu har Salim da a zuwa yake jansu da hira jefi-jefi. Motar na tsayawa a ƙofar gidan ta buɗe mota ta fice ta barsu anan Salim na kicin-kicin taimakawa Baqeer ya zauna akan wheelchair ɗin shi. Da fara'a Dada ta tareta tana cewa "Har kun dawo?" Zama tayi akan tabarma kusa da Dada tace "Wallahi kuwa Dada, mun daɗe ko?" "Kun yi sauri dai" Dada ta amsa mata tana ajiye flask ɗin data zuba mata ƙosai a gabanta. Buɗe flask ɗin Zeey tayi tana cewa "Kai Dada amma wallahi yau kin biyani, har na manta yaushe rabon da naci ƙosai.” Ta ɗauki ɗaya ta dangwala yajin Dada mai ɗan karen daɗi ta kai bakinta tana lumshe ido. A daidai wannan lokacin Salim da Baqeer suka shigo, kallon flask ɗin gabanta yayi ya kawar da kai cikin ranshi dai yana tsegumin sai da Dada dai tayi mata ƙosan nan hankali ya kwanta. Gefe guda yayi da wheelchair ɗin shi a ƙarƙashin inuwar umbrella dake shigowa daga gidan maƙota. Salim ma wuri ya samu ya zauna yana cewa "Hajiya Zainab abun ƴar haka ce babu ko tayi?” Ƴar dariya tayi cikin jin kunya tace mishi "To Bismillah," Shima dariyar yayi yace "A’a ci kayanki ni bazan ci ƙosai yanzu da tsakar rana ba sai dai ban sani ba ko Baqeer zai ci.” Ɗaga kai tayi ta kalleshi sai aka yi dace shima kallonta yake yi a lokacin don haka a tare idanunsu suka shige cikin na juna. Wani irin kallo yake yi mata da ta rasa a wane aji zata fassara shi, ita ta fara janye idanunta ta mayar kan kwanon ƙosanta murya ƙasa-ƙasa tace "Idan zai ci gashi nan da yawa ai zai ishemu.” Shi dai bai saka musu baki ba har ta gama cin ƙosan ta tashi ta wanko hannunta ta dawo ta zauna, sai sannan tace mishi "Yauwa Ya Baqeer zaka zana mini style ɗin?" Yi yayi tamkar bai jita ba kawai sai ya fito da wayarshi daga aljihu yana daddannawa. Haushi ne ya kama Dada don tana ganin yadda mafi yawan lokuta yake yiwa Zainab alhalin bata nufin shi da komai sai alheri don haka cikin faɗa-faɗa tace mishi "Kai kuwa dai Baqeer ban san irinka ba wallahi, Allah ya wadaran halinka na baƙar zuciya mai manta alheri, haba yarinyar nan binka take yi tana tsaye akan komai naka abinda take yi maka wani ɗan uwan na jini ma ba lallai ne yayi maka irin shi ba amma baka da abar wulaƙantawa sai ita, wallahi ka sake halinka don dai ba halin mutanen kirki bane wannan, ah to" ta tashi tayi shigewarta ɗaki ta bar su anan. Duk sai yaji babu daɗi don shi ba da nufin wulaƙanci yake yi mata hakan ba kawai dai mafi yawan lokuta bata samunshi a lokacin da yake cikin yanayi mai daɗi ne. Ita kam Zainab bata daddara da sharetan da yayi ba cikin shagwaɓar da bata ma san tayi ba tace "Please mana Ya Baqeer" ta wani lanƙwasar da kai tana kallonshi fuska a kwaɓe kamar zata yi kuka. Sosai yaji shagwaɓar nan tata har cikin ranshi don haka ya kasa yi mata musu sai ma ce mata da yayi "Kayan suna wurin Dada," kamar baya so yayi maganar. "Yayyy" tace tana ɗan  tsallen murna daga zaune tace "Amma ai zaka yi mini ko? Um?" Tana ɗan turo baki gaba irin na shagwaɓaɓɓun yara, sai yaga ta ƙara yi mishi kyau a yadda take yi kamar wata yarinya wacce bata da wata damuwa a rayuwarta don haka bai san lokacin da ya saki murmushi ba har kumatunshi na lotsawa ciki ba. Dariya tasa tace "laaa Ya Baqeer yau kai ne kake yi mini murmushi?" Da sauri Salim ya kalleshi jin abinda Zeey tace, duk ƙoƙarin shi na ganin ya gimtse fuska sai ya samu kanshi da kasawa don haka kawai ya kawar da kai bayan ya gallawa Salim harara. Shi dariya ma ya bashi don haka ya ɗaga hannayenshi sama in surrender yace "nifa babu ruwana, ah to". Bin bayan Dada tayi ɗakinta ta karɓo kayan zanen da yace suna wurinta, miƙa mishi tayi ta zauna tana kwatanta mishi yanayin style ɗin da take so. Kallonta kawai yake yi yadda take kwatance kamar wata malama a gaban aji tana bayar da darasi. Idanunshi ya rufe ya ɗora pencil ɗin akan takardar, ga mamakinshi sai yaga yadda Zainab ta kwatanta mishi style ɗin tar a cikin kanshi, da sauri ya buɗe idon shi ya ɗauki paper ya fara yin zanen sauri-sauri. Tunda ya fara sketch ɗin bai ɗago ba sai da ya gana ya miƙa mata yace "duba ki gani haka yayi?" Wani ɗan ihu Zainab ta saki tana cewa "Wow! Ya Baqeer haka kake da talent dama? Don Allah duba yadda style ɗinnan ya fita kamar yadda na kwatanta mishi abinda teloli da yawa suka kasa yi shi a cikin ƴan mintuna yayi" ta miƙawa Salim takardar, karɓa yayi ya duba sai yayi murmushi don dai bai yi mamaki ba a irin baiwar da yasan Allah yayi wa Baqeer ɗin ta fitar da zane duk da ba zanen kaya yake yi ba. Fitowa Dada tayi daga ɗakinta tana cewa "Kai lafiya kuke yi mana ihu?" Itama sakin baki tayi tana kallon ikon Allah ganin yadda Baqeer yayi zanen ɗinki kamar dama can irin zanen da yake yi kenan. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar CE*             *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA TARA* {39} Zeey cike da zumudi tace "Dada kalla ki gani?" Amsa tayi cike da mamaki tace "Baqeeru yaushe ka iya zanen ɗinki haka?" Kallon Zeey yayi kaɗan ƙasan ranshi yana jin wata irin nutsuwa, ashe dai yana da amfani? Ya ɗan kawar da kai yace "Ita ta faɗi ya take so ayi." Dariya Zeey tayi tana kallon Dada tace "Dada don na faɗa ai mai zanawa shine mai ƙoƙarin ko?" "Dukkanku dai kun yi ƙoƙarin kai Masha Allahu." Tayi maganar tana komawa ciki zuciyarta na wani irin sanyi da nutsuwa. Zeey ce ta kalli Baqeer ta ɗan karkatar da kai tace "Tukuicin aiki fa?" Kallonta yayi fuskarshi sam babu alamun fara'a yace "Ki bawa saurayinki." Yana kaiwa nan ya fara tura keken yana jin wani irin yanayi da bai taɓa ji ba, me yasa take karkatar da kai a gabanshi gashi tana neman ja mishi ciwo a zuciyarshi da yadda take bugawa da ƙarfi. Har ya shiga ciki Zeey tana kallonshi murmushi ya kasa barin fuskarta, wai saurayi? To wa kenan? Da yake ba shine a gabanta ba hakan yasa bata kula ba, sallama ta yiwa Dada tana jiyota daga ciki ta fito, wata irin nutsuwa take ji wacce ita kanta bata san daga ina take saukar mata ba, anan ta bar Salim don yace shi ba yanzu zai tafi ba. Kai tsaye wurin tailor dinta ta wuce, ta kai mishi dinki tace ya sayi atamfar da zata yi kyau da ɗinkin, don ita yawanci kayanta sai dai ko Mummy ta ɗin ka mata amma sam bata iya zuwa shopping ta sayi kayan mu na hausa ta kai a ɗinka don ita a ganinta babu abinda ya kai hakan ɓata lokaci da wahala, yanayin sa ne ya canza ya sake kallon takardar sosai yace “Hajiya waye yayi wannan zanen?” “Menene?” “Ai tun kafin a ɗinka ma hankalina ya tafi kai na tabbatar in aka yi ɗinkin nan tabbas zai yi kyau sama da yadda kike tunani.” Murmushi tayi tace “Ka fara ɗinkawa sannan ni na kawo style ɗina ba kuma naso wasu su gani suce kayi musu irin shi, na dai yadda kayi tallan shagonka dashi amma ba ka ɗinka irinshi ba.” Kuɗi ta bashi sannan ta fita hankalinta ya ƙara kwanciya jin yaba ɗinkin daya yi in har masu abu sun yaba alamu ne na komai yayi yanda ya kamata. Wayar Mummy ce ta shigo wayarta wanda hakan yasa ta gangara gefen titi ta ɗauka cike da shagwaba tace “Mummy na!” Maimakon Mummy ta amsa sai tayi ajiyar zuciya wanda hakan yasa jikin Zeey yayi sanyi, kashe wayar tayi kai tsaye ta nufi gida maimakon ta koma gidan Inna. Kabir ta gani a falo yana cin abinci ta jefa jakarta kan kujera tana tambayarshi inda Mummy take, wani kallo ya watsa mata yace “Sai yanzu kika tuna da ita sai da kika gama yawon gantalinki?” Tsaki tayi tace “Matsalarka kenan kai maganar arziki ma baza ayi da kai ba, tayi ɗakin Mummy da sauri, a kwance ta ganta cikin bargo hakan yasa ta ƙarasa da sauri tana bin ɗakin da kallo wanda mai aiki ke ta faman gyarawa, kallonta tayi wani abu yazo mata tace “Ɗan bamu wuri.” Fita tayi hakan yasa ta ɗago Mummy, da sauri Mummy ta share ƙwallarta ta rungumeta tace “Baby kin dawo?” Idanun Zeey ne suka fara canzawa sosai nan da nan ƙwalla suka cika taf a cikin idon tace “wani yazo daga Ɗambatta ne?” Kai Mummy ta girgiza mata alamar a’a, Zeey baƙin ciki ne ya isheta ta goge ƙwalla tana sauke huci tace “Ba Daddy ya hanasu shigowa ba?” “In Daddy ya hana ni na isa na hana ne? Haka kuma rayuwar zata kasance?” Cikin takaici tace “Mummy please ki daina magana haka, sai yaushe ne zaki ƙwatarwa kanki ƴanci? Haka zaki zauna suna abinda suka ga dama? Kiyi hakuri Mummy tsautsayi ne yasa nima nace zanje wurinsu kwanaki na tuba bazan sake ba………” kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata karasa maganar, Kabir ne dake tsaye jikin ƙofa shima tun dazu ranshi a ɓace yake yace “Mummy daga yau kema kar ki sake bari a buɗe musu ko gate ne sannan har Ɗambattan zan je wallahi enough is enough bama son akuyanci.” “Akuyanci?” Mumy ta maimaita fuskarta a matukar ɓace, kai ya kauda kawai ya bar ɗakin don duk wanda zai taɓa Mummy to fa baza su yarda ba. Mummy ce tasa hannu ta ɗago Zeey ta rungumeta tace “Ya isa haka nan please ba gashi kun zo ba? Ni ku kaɗai kun isheni rayuwa.” Hawayenta itama ta goge tana kallonta cike da tausayi sam basa shiri da mahaifiyarta sannan ga mutanen can na Ɗambatta da suke kara takurawa rayuwarta, ya zata yi ta sanyaya ran mahaifiyarta? “Mummy in dawo gida?” Kai ta ɗaga da sauri tana riƙeta, murmushi tayi tace “Zan yiwa Aunty Nabs magana tazo in kuma bata zo ba bazan ƙara bin ta ba nima.” Cike da jin daɗi Mummy ta ɗaga kai tana sake rungume Zee rungumar da sai ka ɗauka wani ne zai ɗauke mata Zee ɗin. Waya ta yiwa Nabeela ta sanar da ita ta dawo gidan don Mummy bata jin daɗi, jin haka yasa tace zata zo itama, tana kashewa ta ƙira Daddy wanda yaje Abuja yau saboda wani taro. Yana ɗauka Mummy tayi saurin ƙwace wayar daga hannunta ta kashe tace “Zeey me kike yi haka?” “Sanar dashi zan yi yayi musu magana.” Ido Mummy ta zaro tace “Baki san yanzu akan haka tashin hankalin da zai sake faruwa yafi wanda ya faru ba? Bafa wani abun bane ya faru sosai.” Cikin ɓacin rai tace “Mummy please! Nifa bazan bar wani abu ya sameki ba yanzu kalli har kwalbar turaren wuta an fasa nan gaba in wani abun ya sameki fa?” “Babu abinda zai faru In Sha Allahu, ba dai gaki ga Kabir ba babu komai In Sha Allahu.” Rungume Mummyn tayi tausayi na sake shiga ranta, dole ta kula da Mummy don bazata bari a cigaba da sa musu ita kuka ba da girmanta. Nan ta kira mai aiki ta gyara wurin don Zee ko gyaran gadonta ba yi take ba sanda taje karatu sai dai in ɗakinta taga ya gaji da datti ta kira cleaner ta mata deep cleaning amma sam bata son aiki bare shiga kitchen, taɓ ai iya kacinta da kitchen to fa ruwan zafi zata dafa a kettle ko kuma abinci zata yi warming a microwave haka tayi rayuwa a school nan kuwa ruwan zafin ma sai dai tasa a dafa mata. Ɗaki ta wuce ta kwanta tana jin zuciyarta har yanzu tana zafi, waya ta ɗauka ta kira Baqeer, yana zaune haka kawai yake sake auno Zee yana sake yin wani zanen ɗinkin mamaki yake yi yadda idea ta ɗinkin ke sake floating cikin mind ɗin shi, yana gamawa yaji wata idea ɗin ta sake zuwa, nan ya sake ɗaukan pencil ya fara, wayar Zee ce ta katseshi ya kalli sunan da yasa mata a hankali yayi smirking sannan ya ɗauka. Shiru yayi itama shirun tayi kafin tace “Raina a ɓace yake.” “Why?” “Hmmm family issues.” “Umm!” Gyara kwanciyarta tayi tace “Shikenan abinda zaka ce?” “Umm!” Baki taɗan turo tace “Mutum ba kara, tambayata ya kamata kayi ko am alright?” “And then?” Ta ɗan yi jim kaɗan tace “Sai nace maka eh.” “And?” “Hmm sai ka tambayeni ina ina?” “And then?” “Sai ince ina gida.” “And?” Shiru ta ɗan yi kafin tace “Sai na tambayeka ni kuma, me kake yi?” “And?” Cike da shagwaba tace “And ɗin me? Allah ni har kasa ma naji bana son kalmar.” Shiru yayi tace “Ka tambayeni to.” “Ai kin bada amsa.” Shiru tayi can tace “Allah wayau akayi mini ban yarda ba a sako daga farko.” Bai yi magana ba hakan yasa tace “Kaji?” “No!” “Allah in nayi fushi baza ka ƙara ganina ba, in baka yi mini magana ba naiy counting 5 bazan sake nemanka ba nima.” Nan ta fara “5,4,3,2,1,1,1,1” Zata kashe yace “Okay!” Cike da takaici tace “Shiyasa ma budurwarka ta gudu ta barka.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar, kan gado ta cila ta don ita bata tauna magana ma take faɗa, haka Allah yayi ta komai ya fito bakinta faɗa take yi. Baqeer ne ya kalli wayar maimakon yayi fushi sai murmushi ya suɓuce mishi, idanu ya rufe yanayin yanda ta langwaɓar da kai dazu kawai yake hangowa, shi kam bai san meke kanshi ba. Zeey kuwa pillow ta cillar ƙasa tace “Allah nayi fushi.” ***** Nabeela sai dare ta samu ta iso, Zeey da kanta ta kaiwa Mummy abinci a ɗaki, tana jinsu suna waya da Daddy kamar babu wani abu da ya faru da ita da rana, itafa ko aure tayi gaskiya bazata ɓoyewa mijinta komai ba dole yasan duk abinda ke faruwa ya kuma sanar da ita itama don bata son sirri a aurenta. Jin muryar Nabeela yasa ta leko tace “Aunty Nabs ina wurin Mummy.” Shigowa tayi ta dubata sannan ta fito ta bar Zeey a ciki, ɗakin Kabiru ta nufa fuskarta ɗauke da murmushi, yana zaune yana game a PS5 ɗin shi da yake ɗakin shi nada girma sai akayi mishi sitting area daga gefe kaɗan, knocking tayi ya amsa sannan ta buɗe. A jikin kofa ta tsaya tace “Dama nayi tunanin game kake yi.” Bai kalleta ba yace “Kin dawo?” Kai ta ɗaga tace “Kayi tunanin abinda na faɗa maka kuwa?” Kallonta yayi kaɗan ya ɗauke kai yace “Ba sai nayi tunani ba don its a big NO.” “Ka tabbatar?” Yana kallonta yace “Yes!” Murmushi ta sakar mishi tace “Shall we make a bet?” Kallon mamaki yayi mata yace “Na me?” Tace “Na maganar mana, mu sake magana in 2months.” Tana kaiwa nan ta juya, ɗakin Zainab ta fara shiga ta gyara sannan ta koma nata ɗakin, exams ne da ita hakan yasa ta ciro books ɗinta ta fara karantawa. ****** Yau Maryam tun safe ta tashi ta fara shiri, babu shakka yau duk yadda zata yi sai ta lallaɓa Baban Areef ya barta taje duba Ya Baqeer, cike da salonta ta shirya tun yana kan gado ta kwanta ta shige jikinshi, a hankali ta gangara ta fara yi mishi wasu salon wasanni da suka janye hankalinshi gaba ɗaya, wani irin nishi kawai yake saukewa yana gurnani, wani irin salo ta shiga yi mishi daya rikitashi nan da nan ya fita daga hayyacinshi, nan suka shiga nunawa juna ƙauna. Tare suka yi wanka ya rungumeta yana sumbatarta. Saman fuskarshi ta shafa tace “Bae please inje wurin Dada?” Kai ya ɗaga mata yace “Kije zan sanar da Baffa kawai dai ki dawo daidai lokacin ɗauko Areef daga school.” Sumbatarshi ta sake yi tace “Haka zan je bazan riƙe musu komai ba?” “Fitowa yayi ya ɗauki wallet ɗin shi ya miƙa mata dubu biyar yace “Ki saya musu wani abu, nima zan samu lokaci naje na gaishe su.” Murmushi tayi sannan suka shirya suka fito, breakfast ta haɗa suka zauna dukansu akan dining table, bayan sun gama ya shiga gaida Baffa nan yake ce mishi yana son kuɗi da zai riƙe a hannun shi, ganin babu kuɗi ya shigo gidan sai ya fito yazo wurin Maryam ya kalleta yace “Kuɗin da na baki ko zaki bani na bawa Baffa ke sai na tura miki ta account?” Mamaki ne ya rufeta tace “Ko shi zaka turawa ta account ɗin ni kaga wurin masu fruit ba kowa ke amfani da POS ba.” “Bani please ai dubu uku ma yake so Baffa yace kema dubu biyu ta isheki.” Kamar zata yi magana ta fasa don tasan komai ta faɗa komawa zai yi ya sanarwa Baffan amma in banda haka dubu me zata yi mata, haka ta ciro ta  bada ita kuma ta riƙe dubu biyun, zuciyarta duk babu dadi haka ta ajiye Areef a makaranta sannan ta wuce gidan Dada bayan tasa yi kayan marmari ƴan kaɗan don ba zai yiwu taje musu gida hannu na dukan cinya babu wani ɗan alheri ba. +******* “Lale-lale maraba da Maryamu Daso, yau kece a gidanmu da safen nan?” Maryam ta gaisheta tare da ajiye ledojin hannunta tace “Dada ni kam har yanzu ana yin tsame?” “Ana yi mana a gidan Talatu ko dai Areef zai yi kanwa ne?” Murmushin yaƙe tayi don ita kanta cikin take so ta samu amma har yanzu shiru, nan ta bawa wata yarinya data shigo wurin Dada 200 ta siyo mata, suka shiga ciki. Ƙofar ɗakin Baqeer ta ƙwanƙwasa, ya buɗe yana kallonta, wani sanyi ne taji ya ratsata ganin nutsuwa a tattare da Baqeer tabbas bata taɓa zaton zata zo ta ganshi haka ba ta ɗauka in tazo zata ga ya rame sai gashi ta ganshi kamar da harma yafi da samun nutsuwa a fuskarshi. Haka suka fito falo suna hira da Dada shi kuma yana daga gefe sai jefi-jefi yake saka musu baki, anan aka kawo tsamen suna ci ana cigaba da hira. Shi dai duk hirarsu ba itace damuwarshi ba so yake ya tambayeta game da kawarta Zainab, wacece ita? A ina suka haɗu? To amma ta ya zai fara tambaya? Dada ce ya kamata tayi maganar amma yaga sam bata da alamar yin hakan sai wani zancen ma da suke yi wanda shi duk ba shine a gabanshi ba. Ya tambayeta ne? Ko kuwa dai yayi shiru? To in zai tambaya yace me? Menene haɗinshi da ita da ya damu da sai yaji ita wacece? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce*     *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD*             *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN {40} Har Maryam ta mike zata tafi Baqeer bai iya tambayarta komai ba game da Zainab. Haka suka fito Dada ta rakota sai da zata shiga mota Dada tace "Maryam nikam ki mana godiya gun kawarki." Da mamaki Maryam ta kalli Dada tana ƙoƙarin bata amsa waya ya shigo cikin wayarta hakan yasa ta ɗaga tare da ɗagawa Dada hannu. Nan ta shiga mota ta bar gun. ****** Ranar da Zainab taje ta karɓi ɗinkinta  ita da kanta tayi mamakin yadda style ɗin ya fita fiye ma da yadda tayi zato gashi kuma sosai ya dace da atampar da telan ya zaɓa mata, sai zuzuta haɗuwar kayan take yi tana jin daɗi. "Ai Hajiya idan kinga yawan mutanen da suka ce nayi musu irin ɗinkin nan wallahi zaki yi mamaki bare ma dana ɗora a shafin mu na IG da facebook baki ga yawan likes da comments ɗin da muka samu ba, sai dai haƙuri kawai nayi ta bawa mutane nace mai kayan tace bata son ganin irin style ɗinta a jikin kowa." Wata dariyar farin ciki ta saki tana jin daɗin yabon da kayan nata da ya samu, tana kuma daɗa jinjinawa Baqeer don shi ya fito da zanen style ɗin fiye ma da yadda ta kwatanta mishi, tana wannan tunanin ne taji telan ya ƙara cewa "Da zaki daure sai ki haɗani da wanda yayi miki wannan zanen Hajiya don naga ya iya tsara style ɗin ɗnkuna masu kyau dan kuwa nasan ba ƙaramin ciniki zamu samu ba." Kallonshi tayi tana jinjina abinda yace cikin ranta, tabbas idan Baqeer zai yarda yana daga zaune ya samu sana'ar yi tunda dama bai san wani abu ba bayan harkar zane watakila daga zanen kayan sai kaga ya koma wa harkar paintings ɗin shi cikin ƙanƙanin lokaci don haka ta cewa telan "Zan yi mishi maganar muji me zai ce amma fa kasan zaka yi mishi biya me kyau ne idan ya amince ko?" Ai tuni ya fara washe haƙora yana murna yace "Haba Hajiya me zai hana kuwa na biyashi idan har irin waɗannan styles ɗin yake zanawa da ba ko ina za'a iya ganin su ba, ai ko ace wasu sun kwafemu sun yi irin su to a wurin mu dai za'a fara gani kinga kuwa ko wannan ai riba ce a karan kanta bare kuma nasan zasu ƙara janyo mana customers." "Haka ne" tace tana mayar da kayan cikin ledar su. "To muyi maganar price tun yanzu yadda idan naje zan faɗa mishi, nawa zaka na biya akan kowane sketch?" Tsayuwar shi ya gyara yace "Eh to ina ganin zan dinga biyanshi kaso ɗaya cikin huɗu na abinda na samu."Wani irin kallo tayi mishi "You're not serious at all, to zaka biya shi akan kowanne ɗinki ko kuwa a guda ɗaya? Kenan idan kayi ɗinki akan dubu ashirin dubu biyar ne nashi, bari kaga tafiyata don naga alamar ba da gaske kake yi ba, ka dai san ba kai kaɗai bane telana zan iya neman wani telan muyi ciniki ba sai na tsaya kana raina mini wayo ba,” ta suri ledarta ta nufi ƙofar fita daga shagon. Da sauri ya dakatar da ita yana cewa "Haba Hajiya kada muyi haka dake mana, duka abun ai bana zafi bane, kawai tsayawa zaki yi mu daddale akan nawa zan dinga biya kinga idan na biya shi shikenan ni style ɗin ya zama nawa." Murmushi ta saki tace "To yanzu naji magana amma ina jin barin maganar price ɗinnan zamu yi har sai naje mun tattauna dashi don kasan fa harkar paintings yake yi zai fi kyau ma ya yanke kuɗin da kanshi don shi yasan a yadda yake sayar da kayanshi." "Amma Hajjaju style ɗin ɗinki daban painting daban ba zai yiwu ayi musu kuɗi iri ɗaya ba,” yace mata don baya so aje a tsuga mishi kuɗi da yawa tunda yasan paintings suna da tsada sosai." Harararshi tayi tace "Duk ba zane bane kuma ƙwaƙwalwa ke ƙirƙirarsu to don me kuɗin su zai bambanta? Kai dai kada ka samu damuwa I assure you sketches ɗin da zai yi maka har matan gwamnoni sai sun nemeka don ka zama telansu, ai dai ka gani wannan kaɗai daka ɗinka mini yadda mutane suka yaba dashi." "Haka ne kuma Hajjaju, to sai na jiki dai kenan ko?" Tace "In Sha Allahu, kada ka samu damuwa." Tana barin wajen tela, Mariri ta nufa don taje ta nunawa Baqeer yadda style ɗin da ya zana mata yayi da aka ɗinka, wani irin farin ciki take ji a cikin ranta don tana ganin kamar duk wasu matsaltsalun Baqeer ɗin sun zo ƙarshe idan har ya karɓi tayin tailor nan don ta lura kamar yawan damuwarshi ta ta'allaƙa ne ga zanen da ya daina yi yanzu bayan a baya shine komai na rayuwarshi. Haka ta ɗin ga zuba gudu a titi don ta matsu taga ya reaction ɗin fuskarshi zai zama idan yaga ɗinkin. Wani ƙayataccen murmushi ta saki don tasan dole ne ma ɗinkin ya burgeshi kamar dai yadda yayi mata. Tana tsayawa a ƙofar gidan Dada ta sunkuci ledar kayan ta fice tana ji kamar tasa gudu ko zata ganta gabanshi, sai da ta shiga soron gidan sannan ta daidaita nutauwarta ta koma yin takunta a hankali ta shiga tana yin sallama kamar bata so. Daga cikin ɗaki Dada ta amsa tana cewa "Muryar wa nake ji kamar Zainabu?" "Nice Dada" ta bata amsa tana nufar hanyar ɗakin. A zaune ta iske Dada tana shan kunun kanwa da aka aiko mata daga gidan maƙwabtan ta inda aka yi haihuwa. Zama tayi akan tabarma kusa da Dada tana gaisheta. Bayan sun gama gaisawa Dada ta tura mata kwanon kunun, girgiza kai Zeey tayi tace "Meye wannan ɗin Dada?" "Kunun kanwa ne aka kawo mini daga maƙwabta anyi haihuwa.” Ɗan yanutsa fuska tayi tace "Kunun gyaɗa kawai nake sha Dada ko kunun tsamiya bana so ko da azumi idan aka yi a gida sai dai na sha tea ko Mummy tasa ayi mini kunun gyaɗa." Mayar da kwanon kununta Dada tayi ta ajiye tace "Shima Baqeeru irin wannan tsirfar ce dashi komai aka yi sai yace baya so yanzu ne ma naga yana karɓar duk abinda na bashi ko baya so ya tsakuri kaɗan ya ajiye sauran." Murmushi Zeey tayi tace "Ina yake nema Dada? Wurinshi nazo daga wurin tela nake nace bazan koma gida ba sai na kawo mishi ɗinkin daya zana mini ya gani yadda style ɗin ya fita sosai," ta zazzage kayan a gabanta tana ɗagawa Dada ta gani. "La'ilahaillallahu" Dada tace tana tafa hannu, "Wannan ai irin ɗinkin da Baqeeru ya zana miki ne rannan sak kwabo da kwabo kamar hoton na takardar aka yi, amma ni ɗin kin ku ne sai naga kamar ƴar tsana za'a sawa." Dariya tayi tace "Ke kuma Dada wace ƴar tsana? Kedai kice yayi tsaf zan shige cike." Kai ta jinjina tace "Ni mamakin ma yanda yai ɗinki nake, ko ya akai ya iya zanashi haka?" "Wallahi kuwa Dada, ai ko lokacin da nake kwatanta mishi ɗinkin ban ɗauka haka zai fita ba sai da ya zana naga ya fita fiye ma da yadda ni nayi tsammani." Tashi Dada tayi da kayan a hannunta tace "Yana ɗakin shi yau tun safe bai leƙo waje ba ina ganin ƴan miskilancin ne suka motsa gama tunda ya gamu da larurar nan ya ɗauki miskilancin dole ya ƙaƙabawa kanshi, taso muje," ta cewa Zeey tana yin gaba. Tashi tayi tabi ta a baya sai dai suna zuwa ƙofar ɗakin taja ta tsaya a wurin taƙi ƙarasa wa ta shiga, sai Dada ce ta shiga ta sameshi a zaune da takardu a gabanshi yayi sketches na ɗinkuna da yawa tun daga kan riga da skirt har zuwa dogayen riguna. "Au ashe kace zane ka samu shi yasa yau naji ka shiru" Zeey ta jiyo Dada tana faɗa daga cikin ɗakin abinda yasa ta shiga ciki babu shiri don taga zanen da Dada ke cewa yayi, a karan farko kenan data taɓa shiga ɗakin. Tsayawa tayi tana bin sketches ɗin da yayi da kallo tana mamakin irin styles ɗin daya fitar. A mamakance tace "Ya Baqeer dama ka iya zana ɗinkuna ko kuwa dai yanzu ne ka fara?" Ta sunkuya ta ɗauki takarda ɗaya tana kallon style ɗin doguwar rigar daya zana. Ai dole ne ma ayi mata wannan ɗinkin don sosai ya tafi da ita. Kallonshi tayi tana murmushi sai aka yi dace shima ita yake kallo yana ganin yadda annurin farin ciki ke fita daga fuskarta kawai don tazo ta iskeshi yana zane sai kace wacce aka yiwa wata gagarumar kyauta. Ɗan turo baki tayi gaba tana ayyana yadda murmushi yake ƙara mishi kyau amma kullum ka ganshi fuska a gimtse kamar bai taɓa dariya ba. "Ba shiryawa mukai ba ɗinki na fa nazo na nuna maka yadda yayi kyau sai nazo kuma na tarar kayi sketching waɗanda suka fishi kyau ma." Sai sannan ya lura da kayan dake hannun Dada tana ɗaga mishi, sosai shima yaji mamakin yadda style ɗin ya fita. Yasan tun daa can yana da passion for ɗinki amma koda Zeey tace ya zana mata style ya dai jarraba ne kawai ba don ya ɗauka zai iya ba ganin ko normal zanenshi da yake yi ya jarraba yin su sau babu adadi amma kamar an share ƙwaƙwalwar shi ya kasaiyawa sai gashi a gwajin farko yayi zanen ɗinkin gashi kuma kamar an buɗe mishi ƙwaƙwalwa ne sai wasu zanen yake yi har ma ya fara tunanin jarraba zana ɗinkin maza. Hannu ya miƙawa Dada ta bashi kayan ya ɗaga yana kalla sai kuma ya waiwaya ya kalli Zeey da ita ma shi take kallo. "Good!" yace mata a daƙile kama baya so, ita dai murmushi kawai tayi sai kuma ta janyo kujerar roba guda ɗaya dake ɗakin ta zauna. Dada dai ficewarta tayi ta bar musu ɗakin don haka suka kasance shiru kamar ba zasu yi magana ba. Zeey ce ta fara kawar da shirun ta hanyar cewa "Ya Baqeer sketches ɗinnan naka sun yi kyau sosai wallahi ko dai ka taɓa yin sana'ar ɗinki ne shi yasa abun bai baka wahala ba lokacin da nace ka zana min style?" Bai amsata ba sai cigaba da yayi da jujjuya kayanta da har yanzu suke hannunshi. "Shi kan shi tailor fa baka ga yadda ya yaba da ɗinkin ba don ma sai da nayi warning ɗin shi akan bana so ya ɗinkawa kowa watakila da yanzu style ɗin ya zama uniform." Sai sannan yace mata "What's there in it don an yiwa wasu irin ɗinkin ki?" Taɓe baki tayi tace "Nop! Gaskiya ni dai bana so gara kowa yaje ya nemi style ɗin shi amma ba nawa ba." "Umhm" kawai yace ya hau tattare takardun shi daya barbaza don dama a zaune yake akan katifarshi yana zanen don yafi jin daɗin yi a haka akan idan yana zaune akan wheelchair ɗin. "Kasan wani abu Ya Baqeer" ɗagowa yayi ya kalleta sai ta cigaba da cewa "Tailor ɗin nema yace wai na haɗaku please ka ɗin ga yi mishi sketches ɗin yana biyanka to na dai ce mishi sai nayi magana da kai duk abinda ka yanke zan faɗa mishi amma ni sai nake ganin why not ka karɓi tayin shi tunda dama can sana'arka kenan yin paintings in a way wannan ɗin ma kamar yin painting ne tunda dai duk zane ne amma me kake gani?" Tun kafin ma yayi magana Dada ta shigo ɗakin tana cewa "Me zai hana kuwa yayi Zainabu tunda dama dai sana'arshi ce ai ki faɗa mishi kawai zai yi babu wani ja." Kallon Dada kawai yayi yana mamakinta yadda kawai ta yanke mishi hukunci ba tare data jira jin ta bakin shi ba. Ɗan waiwayawa yayi ya kalli Zeey sai yaga shi ta zubawa ido tana jiran jin amsar bakin shi. "I don't think if I will do it, mutanen yanzu basu da amana nafi so komai zan yi yanzu ya zamanto ban haɗa sabgata da kowa ba" yace yana ɗaga kafaɗa, tunanin Bello da abinda yayi mishi ne kawai ya faɗo a ranshi don haka yaji tayin da Zainab ɗin tayi mishi bai kwanta mishi ba. "Ba zaka yi ba fa kace Baqeeru? To idan baka yi wannan aikin ba me zaka yi tunda dai ba wata sana'a ka iya ba face zanen?" "Zan je na koyi ɗinkin da kaina sai nake yi." Salati Dada tasa tana sallallami tace "Da wace ƙafar zaka taka keken ɗinki ki akwai keken guragu ban sani ba Zainabu?" Ta juya tana kallon Zeey. Dariya ce taso suɓuce mata sai dai yadda taga Baqeer ya haɗe fuska yasa ta haɗiye kayarta bata yi ba. "Akwai keken ɗinkin mai aiki da wuta ai Dada wannan baya buƙatar a takashi da ƙafa, zai iya yin ɗinkin bawani abu bane don yana da lalurar ƙafa kawai dai ina ganin Ya Baqeer ko na wani ɗan lokaci ne kayi aiki dashi in yaso daga baya idan ka koyi ɗinkin ka ƙware sai ka koma aikinka da kanka amma dai ya ka gani?" Ɗan jim yayi yana tunani sai kuma yaga yanzu ko tailoring school ɗin zai shiga ai dole sai da kuɗi don haka yaga gara kawai yayi accepting tunda dai ma zanen kawai zai a saya a wurinshi ba wai tare zasu yi zanen ba kamar dai yadda suka yi da Bello don haka yace "Okay." "Yayyy" tace tana ɗan tsallen murna jin cewa yayi accepting. Kallonta kawai yayi yana mamakin yadda take yin abubuwanta kamar wacce bata da wata damuwa a rayuwarta. "In Sha Allah gobe zan ɗauko shi na kawo shi sai kuyi magana har ma ya ga sketches ɗin da aka yi,” tace bayan ta gama tsalle-tsallen murnar da take yi.... *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA ƊAYA* {41} Karfe goma sha ɗaya na safe Zeey ta gama shirinta tsaf ta fito cikin sabon ɗinkinta don haka nan taji kayan da take so ta saka kenan, tana so taga ya Baqeer zai yi idan yaga kayan a jikinta, ta dade a jikin madubi tana bin jikinta da ɗin kin da kallo, murmushi ta saki mai sanyi dan ta tabbatar wannan ɗin kin dan ita akai jiyake kamar ta samu guri mai mahimmanci a gun Baqeer. A ɗakin Mummy ta sameta tana shirya kayanta da aka kawo daga wajen wanki a cikin wardrobe. Kallonta Mummy tayi ta mata alama da tayi kyau sosai, murmushi tai tana ɗan juya mata ɗin kin, nan da ban Mumy kuma ta canza ganin alamar shirin fita tayi tace "Yau kuma sai ina? Kin dai koyi yawo Zeey, kusan kullum yanzu sai kin fita, wai shin ina kike yawan zuwa ne?" A ɗan shagwaɓe ta hau turo baki tana bin bango tace "Yawo kuma Mummy? Please ki bari kada wancan ɗan sa idon ya jiki yanzun nan sai yaje ya haɗani da Daddy ina zaman -zamana yasa a hanani fitar ma gaba ɗaya." Dariya Mummy tayi tace "To nayi shiru amma dai don Allah kada ki daɗe sannan kuma a rage yawan fitar nan haka nan please." Rungume Mummyn tayi tace "To Mummy ba zan daɗe ba ai I promise, sai na dawo." Tana fita shagon ɗinkin ta wuce don ko yau da safe sai da tailorn ya turo mata da saƙon text yana yi mata tuni wai kada ta manta yau ne zata kai shi wajen me zane. Koda ta isa bata fita ba sai ta tsaya a mota ta danna mishi horn kawai, shima da yake dama ita yake jira tun ɗazu yana ganin lokacin da tayi parking ɗin motar ya taso da hamzari ya fito. "Ranki ya daɗe sannu da zuwa" yace fuskarshi a sake cike da nishadi bayan daya ƙaraso wurin. Buɗe mishi gaban motar tayi sai dai ya mayar da murfin ya rufe yace mata "Ai ina ganin bari kawai na ɗauko babur ɗina sai na biyoki a baya ko?"Ɗaga mishi kai tayi alamun amsawa kawai dan dama kawai dan abun ya shafi Baqeer ne amna batasa mutane a motarta. Haka suka tafi tana gaba yana biye da ita a baya har suka ƙarasa gidan Dada. Fitowa tayi daga motar bayan ta rufe ne ta juyo ta kalleshi tace "Bari na fara shiga na sanar musu zan kiraka sai ka shigo." "To" kawai yace mata yana mai ɗokantuwa da son ganin mai zanen da kuma wasu style zanen da yayi don ko waɗanda Zeey ta nuna mishi jiya sosai suka tafi dashi. A tsakar taga Baqeer shida Dada, ita tana gefe tana sauraran radio shi kuma hana zaune yana zane suna hira sama-sama, sallamarta kawai waji yaji komai ya tsayamai dakewa yai bai dago ba sai dai bai iya cigaba da zanen ba. Dada ta fara lale lale, cike da fara'a dan tana kaunar Zainab sosai, kallan Baqeer tai tana kusa da Dada jnda take gaisheta tace "Sai a ganka ai kamar ba'a ganka ba." Dagowa yai suka haɗa ido, tace "Nida tailor ɗin ne." Dada tai caraf tace "In akai kamar ba'a ganki ba ai ni na ganki ko? Kinga share wannan dukum-dunkum ɗin, yi maza kice ya shigo." Kalmar da Dada ta haɗa Baqeer dashi ne yasa yai saurin kallanta, bata ko bi ta kanshi ba Zeey ta mike tana kunshe dariyar da ke neman kwace mata suna haɗa ido da Baqeer ta kira Sani a waya tace ya shigo. Da sallama a bakin shi ya shiga gidan sai ya tarar dasu zaune a tsakar gida sai Baqeer dake zaune akan wheel chair ɗin shi don ko da Zainab tazo ma anan ta iskesu da wasu sketches ɗin ajiye a gefenshi ga wani akan cinyarshi yana zanawa ita kuwa Dada tana ƴan kaye-kayenta a tsakar gidan. Sosai Sani tela ya kalleshi yana mamakin wai dama gurgu ne mai yin zanen? Gashi dai tabbas yaga zahiri tunda gashi nan ma wani zanen ne akan cinyarshi yana yi, Allah mai iko. Hannu ya miƙe mishi suka yi musabaha kafin yaja kujerar daya gani a gefe ya zauna yana gaishe da Dada. Kallon Baqeer Zeey tayi tace "Ya Baqeer ga tailorn da ya ɗinka mini kayan daka zana, tunda ya gani yace na haɗa shi da kai kamar dai yadda na faɗa maka na kuma faɗa mishi dama bazan yi maganar kuɗin aikinka daga ni sai shi ba sai dai yazo na kawo shi wurinka kuyi magana." Gyara zama Sani yayi yace "Yallaɓai ina faɗa maka tunda na ɗora kayan Hajjaju akan IG bayan an ɗinka mutane ke damuna gashi kuma tace bata son kayanta su zama uniform" ya ɗan yi dariya sai kuma ya cigaba da cewa "Na tabbata idan nayi amfani da designs ɗin wurinka kamar dai yadda Hajjaju ta nuna min wasu jiya ba ƙaramin alheri za'a samu ba shi yasa ma nake so mu haɗa hannu waje ɗaya ka dinga yi mini zanen tunda Allah yayi maka baiwa ta nan ɓangaren ni kuma ina ɗinkawa sai mu tsara yadda zan dinga biyanka." Sai sannan yayi shiru yana kallon Baqeer yana jiran yaji me zai ce. Bai ce mishi komai ba har sai da ya gama zana takardar dake gabanshi sannan ya haɗata da sauran waɗanda ya zana ya miƙa mishi. Karɓa yayi yana kallon styles na garari irin waɗanda bai taɓa mafarkin gani ba, tuni fuskarshi ta washe da fara'a yana jin tamkar yayi fice a harkar ɗinki ya gama idan har zai na ɗinka irin waɗannan styles ɗin. Kallonsu yake yi yana ƙarawa ya kasa daina kallon sketches ɗin , ita kuwa Zeey kallon shi kawai take yi tana murmushi sai kuma tace "Ai na faɗa maka idan kaga designs ɗin shi sai ka ruɗe." "Ai kuwa dai gashi nan na ruɗe don na rasa ma wanda zan fitar nace yafi saura kyau," yayi maganar yana ƙara ɗaɗɗaga takardun. Da ƙyar dai ya iya ajiye papers ɗin sannan ya kalli Baqeer yace "Yo yallaɓai akan nawa zaka bani?" Kallon inda Zeey take yayi sai yaga ita ma shi take kallo, gira ya ɗage mata irin ya dai sai ta taɓe baki ta kawar da kai tana jin haushin yadda take ɓarar da ajinta idan har tana zaune a gaban Baqeer bata iya kawar da kai bata kalleshi ba. Mayar da kallonshi yayi ga telan yace "Duk da ban taɓa sayar da zane na style ɗin kaya ba bana sayar da paintings ɗina at nothing less than 100k so nawa kake ganin zaka iya biya?" Baki Sani ya saki jin manyan kuɗin daya ambata, kallonshi yayi ya marairaice fuska yace "Haba Yallaɓai har dubu ɗari bai yi yawa ba, ina ma laifin dubu ashirin haka zuwa dubu talatin?" Wani miskilallen murmushi ya saki kafin yace "Anya kuwa ka shirya yin kasuwanci dani? Daga dubu ɗari ka dawo dubu ashirin, kaso ɗaya a cikin biyar na abinda nace fa kenan?" ya miƙa mishi hannu da nufin ya bashi sketches ɗin. Ƙara damƙe su Sani tela yayi yace "Haba Yallaɓai ai ba za'a yi haka ba, yanzu dai kayi mini ragi a yadda zan iya biya amma dubu ɗari tayi yawa akan kowanne zane tunda ba guda ɗaya zan karɓa ba." Kallon Zeey yayi yana so tasa baki Baqeer yayi mishi ragi sai dai yaga ita ko a jikinta kawar da kai gefe ma tana yin game a wayarta don a ganinta wannan ba maganarta bace tunda bata da wani sani akan harkar zane da yadda ake sayar dasu shi yasa bata saka musu baki ba ta ƙyalesu suyi cinikin a tsakaninsu. Ƙara marairaice fuska yayi yace "To nawa zan biya yallaɓai?" Jin da yayi Baqeer bai ce komai ba. Shima kallon Zeey yayi sai yaga hankalinta ma baya wajensu don haka ya cewa Sani "To ka kawo 50k each take it or leave it daga haka ba zan ƙara yi maka ragi ba" ya haɗe fuskarnan kamar wanda bai taɓa dariya ba don shi sam baya so a nemi raina mishi wayo akan sana'arshi. Ko da ba irin waɗannan zanen yayi ba a baya ai yasan nawa yake sayar dasu don haka yanzu ma babu dalilin da zai sa ya sayar da zanen shi a kuɗi ƙalilan, sannan mutane sau da dama sun iya tayin wulakaanci da nuna bakasan darajar abu ba, kowa kanshi ya sani ada farkon fara zanenshi haka mutane sukai ta maidashi wawa sai dai bayan yasan darajarsa ya canza. "To Yallaɓai nagode, yanzu bari na zaɓi kaɗan idan yaso daga baya sai na ƙara. Hajjaju ko zaki taya ni zaɓe ne don ni nama rasa wanda zan ɗauka kowanne ba baya ba wajen tsaruwa,”ya ƙarashe maganar yana kallon Zeey. Karɓa tayi tana dubawa sai kuma tace mishi guda nawa kake so?" "A yanzu dai guda huɗu nake so idan yaso daga baya sai na ƙara zuwa na karɓi wasu tunda ma naga wuri."Guda huɗu da suka fi yi mata kyau ta ware ta miƙa mishi, hannu biyu yasa ya karɓa yana ƙara kallon waɗanda ta zaɓa din. Tabbas waɗannan styles ɗin idan yayi su zasu janyo mishi customers sosai yasan kuma In Sha Allah zai samu alkhairi a ciki. Godiya yayi wa Baqeer ɗin kafin yace "Yanzu dubu ɗari ce a jikina cash da zan kai banki ko zaka karɓa in yaso idan na koma shago sai na ciro maka sauran?" "Hakan yayi" Zeey tace "Amma me zai hana ka saka mishi sauran ta account ai kamar zai fi ko?" Ta kalli Baqeer don son jin me zai ce. Ɗaga mata kai yayi alamun amsawa don haka Sani ya fito da kuɗi cash dubu ɗari daga aljihun shi ya miƙa mishi. Karɓa yayi ya ƙirga yaga sun cika cif, account number ya bashi a take a wurin ya tura mishi sauran kuɗin sai gashi da dubu ɗari biyu cif nashi na kanshi. Wani irin daɗi Baqeer yaji ya mamaye zuciyarshi, a tunaninshi tunda larurar nan ta sameshi ya tashi a aiki kenan ashe dai yana da sauran amfanin da zai yi da rayuwarshi. Sallamar su Sani tela yayi ya tashi ya tafi. Yana fita Baqeer ya miƙawa Zeey kuɗaɗen gaba ɗaya. Tsayawa kawai tayi tana kallonshi, "Amsa" yace mata shima idanunshi a cikin nata. "Me zan yi dasu ni da zaka bani, ba kuɗinka bane?" tace tana turo baki gaba abinda ya kula kamar ya zame mata jiki tsabar shagwaɓa. Ganin ba zata karɓa ba ya ƙirga dubu ashirin ya miƙa mata. Noƙe kafaɗa tayi taƙi karɓa sai ma tashi da tayi ta shige falo gun Dada ta bar shi anan wurin. Da kallo ya bita kafin kuma ya tattare sauran sketches ɗin shi ya gara keken nashi ya bita cikin falan. Tana kishingide akan kujerar ƙarfen Dada ita kuma Dada tana zaune akan tabarma suna hira. Gefen kujerar ya ƙarasa ya miƙa mata kuɗin, sai ma kawar da kai tayi kamar bata ganshi ba. Kallon Dada yayi yace mata "Dada yi magana."?Baki Dada tasa tace "Ke kuwa Zainabu ki karɓa mana, ai ba'a mayar da hannun kyauta baya." Tashi tayi zaune tace "Allah Dada ba zan karɓa ba, ya daga fara abu kawai zai ɗauki kuɗi ya bani ya bari a gaba na karɓa amma dai ba yanzu ba." Bai ƙara jan maganar ba sai ma ya miƙawa Dada kuɗin hannunshi. Karɓa tayi tace "Na miye wannan ɗin?" Sai da ya kawar da fuska sannan yace "Naki ne." "To daga farawa kai kuma Baqeeru sai ka cire iyayen kuɗi kamar wannan ka bani, da dai ka rage." Ƙin amsa yayi sai ma ya cire dubu goma a sauran kuɗin ya saka aljihun shi ya miƙawa Zainab sauran dubu saba'in ɗin yace "Please ki kaiwa Umma kice ta ɗauki 30k sauran ta bawa Hadiza da Maryam" karɓa tayi tasa a jakarta tana godiya kamar ita aka bawa. Dada ce tace "to kai kuma haka ake yi duk kabi ka rabar da kuɗaɗen naka?" "Saboda ku nake neman ai Dada" abinda yace kenan kawai yace ya gungura kekenshi zuwa ɗakin shi. ***** Bello da Asiya kuwa saboda tafiyar shi data matso kusa yasa aka dawo da bikinsu baya don a samu ayi bikin kafin lokacin tafiyar tashi yayi, shi zai fara tafiya daga baya sai Asiya ta bishi don aƙalla zai yi shekara uku zuwa huɗu acan ƙasar da aka turashi. Tsare-tsaren biki kawai suke yi Asiya ana ta iyayi da gwalli ita a dole ta zama big babe tunda zata fita ta bar ƙasar ƙawayenta na ƙara zugata suna fasa mata kai. Gida ma da Bello zai kama haya cewa tayi bata son mai tsakar gida sai dai ya nema mata gida me gate gashi duk inda suka je neman irin gidan da take so sai suji yayi tsada don kuɗinsu daga dubu ɗari takwas zuwa miliyan ɗaya ne har da inda aka ce musu miliyan ɗaya da rabi. Da ƙyar suka samu wani three bedroom flat a tarauni, gidan sama da ƙasa ne na saman suka samu. Sai da Bello ya jinjina yawan kuɗin gidan amma da ya tuna ba wani daɗewa zasu yi a ciki ba su tattara su bar ƙasar sai yaji ba wani abun damuwa bane don haka ya kama yana murna burinshi ya kusa cika. Events kala-kala ta tsara da zasu yi shi kuma yana biye mata idan Habi tayi magana tace ya kamata ta rage ƙaryar data ɗaukarwa ranta ta tuna ita ba ƴar kowa bace iyayenta basu ajiye ba basu bawa wani ajiya ba sai ta hayayyaƙo mata da masifa tace tana yi mata baƙin ciki don taga Allah ya ɗaga darajarta ya kusa rabata da ƙangin talauci. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA BIYU* {42}   Dada ce ta fita jin sallama daga waje, Zeey a hankali ta kalleshi sai kuma ta canza yanayin fuskarta ganin kallan da yake mata, takardun ta kwasa sannan ta miƙe ta koma jikin ƙofa tana sake kallansu, yana daga zaune yake binta da kallo, gyaran murya yai yana ɗan kauda kai. Ta kalleshi tace "Ya Baqeer karma ka fara." "Me?" Ya tambaya yana kallanta, tace "Wai karma ka canza magana kaga dai magana ɗaya kake yi." Bai san sanda ya ɗan murmusa kaɗan ba, kanta ta kwantar jikin bango tana kallanshi, ba shakka itadai yanzu kam ta tabbatar san Baqeer nada mahimmanci arayuwarta wanda murmushinshi kaɗai nutsuwa take saka mata. Yanda ta kalleshi ne yasa yace "Kallan na menene?" Kai ta girgiza alamar a'a tace "Hakuri na nake jira ka bani?" "Name kenan?" Ajiyar zuciya tai idanunta na kanshi tace "1?" "Zero ɗin fa ina aka kaishi?" Tasan halinshi sarai kwanan nan, yanzu har kalamansa sun daina bata haushi, kallan zanen ɗinkuna dake hannunta take tabbas Baqeer Allah ya bashi basirar zane taya mutumin da bai taɓa ɗin ki ba zai zane ɗin kuna haka? Kallansa tai shima daidai nan ya ɗago yana kallanta, ya zaiyi da abinda ke ransa? Wai yau shine ya wuni yana zanen kayan da Zeey zata ɗin ka tasa, haka kawai in ya ajiye sai yaji kwakwalwarshi na auno mai ita cikin wata shigar wasu kayan, idea na sake saukar mai wanda hakan zaisa ya zauna ya sake yin zanen, sannan abinda ke ɗaure mai kai yanda zanen kayanta ke sashi farinciki da nutsuwa a cikin ranshi. Yasa a ranshi ko keken electric ɗin bai fara amfani dashi ba zai fara yanka dan yanzu ji yake yana san ɗin ka mata abinda zata sa. "Zaka min sketch na maza?" Kallanta yai da mamaki sai kuma ya tuno Junaid badai so take tace ya zana mata saurayinta ba? Nan danan fuskarsa ta canza, ya kauda kai tace "Hmmm a tsayi bai fika ba, sannan a jiki ma haka, ashekaru ma ina ga bai fika ba." Fuskarshi ce ta murtuke sosai dan yanzu kam ya tabbatar da Junaid take duk da basu gwada tsayi ba amma yana tunanin kansu ɗaya sannan jiki ma da kadan Junaid ya fishi kenan ko kaya ne zasu iya sawa, mamaki ne ua kama Zee ganin yanda ya canza fuska lokaci ɗaya. Tace "Me kuma nai? Ko bazaka dinka ba?" "Eh!" Kalmar dayaji ta fito daga bakinshi kenan shi kanshi bai sani ba "Meyasa?" Nan ya fara tambayar kansa dan shi kanshi baisan amsar da zai bata ba, yana ƙoƙarin yin magana Dada ta dawo tana cewa "Baqeeru almajirincan ne Tanimu wai gaisheka yazo yi." Ja mishi ƙofa sukai suka bashi guri dan ya hau keken guragun, haka ya hau ya turo keken zuwa jikin ƙofa yana buɗe wa suka ƙara kallan juna, wani yanayi ne ke ratsa zuciyar ta da ita kanta batasan sanda ta canza yanayin kallan da take mai ba, wani abu ne ya tsayamai wanda yai saurin kauda kai yana cewa "Tanimu?" Da sauri yaran ya taso da bai wuce shekara 16 ba yana gaida Baqeer, tana daga ciki tana kallan yanda suke magana fuskar Baqeer a sake, hakan yasa ta kasa ɗauke idanunta daga kanshi. Mikewa tai ta ɗau dinkin ta sannan tawa Dada sallama. Yana kallan sanda ta fita ganin taki mai magana yasa ya rasa ta yanda zai mata magana harta kai bakin ƙofa idanshi na kanta, takardun hannunta ta ɗaga mai sama kaɗan, kai ya ɗaga mata alamar to tana murmushi tace “Zan kawoshi.” Nan ma kai ya ɗaga mata, ta kalli Taminu sannan tace “Bazan ƙira waya ba.” Yanzun ma kai ya ɗaga mata, fuska ta canza sannan ta fita waje, mota ga shiga tasa hannu saitin kirjinta tana fitar da wani irin numfashi sama-sama nutsuwa ce take saukar mata ta sake kallan sketch ɗin tana cewa “Duk ni zan fara ɗin kunan nan.” Baqeer kuwa samun kanshi yai kamar wanda bashi da damuwar komai, yana mamakin yanda ta shigo rayuwarshi har ta cire duk wani duhu dake baibaye dashi. Tanimu ya daɗe a gidan dan har gyaran ɗakin Baqeer, Dada tace ya jira yaci abinci yace a’a zaije kasuwa ne yin dako sannan ya tafi. ***** Bashir ne ya fito hannunshi ɗauke da kofin shayi ya ajiye sannan ya fita, Abu na zaune sai sake cika da batsewa yau tun safe ranta a ɓace yake sakamakon kwanan da Alhaji yai a gun Jamila, tana zaune tana jujuya kazar amarya da aka aiko mata ta dafa, Jamila ce ta fito sanye da atamfa tasha kwalliya kai kace wata yan mata, an dambara hoda da jambaki tana tauna chewing gum, kanta ta turo ɗaurin ture kaga tsiya zama tai a waje tana wani kale-kale da muzurai har Bashir ya gama ya fita, can ta dau waya ta kira tana cewa “Ah to mu namu kunsan ba irin nasu bane, mu har a nuna mana sanabe? Mutum ya girma wai shi a dole maida tsohuwa yarinya? Yo ta ina ka tsufa zakace zaka dawo yaro? Gane mun hanya abinka da wacce bata waye ba kinsan kan nan ba komai a ciki sai tunanin kayan mata, to ya girma yana san hutu an sha magani an hanashi bacci ba dole ya gudo ba?” Ai Abu dake saurarenta ta gama kaiwa bango a fusace ta matso inda take tana nunata da ludayin hannunta tana cewa “Jamila na rantse da Allah zaki jawo ai abin kunya dan wallahi banki na kwabe mu daky ba kiga waye tsohon.” Ajiye wayar tai dan dama wayar ma ta karya ce tace “Kinga ni bansan tashin hankali ke wai sai yaushe zakisan ni na finkarfin yin dambe? Yarana na aure a ganni ina dambe ai wallahi nafi karfin wannan, shayi ne dai an hana ku ke sanda kuke ci kuke cinyewa a ɗaki wani ne ya sa muku ido?” Fatima ce ta fito daga ɗaki buta ta ɗauka ta nufi bandaki kamar batasan sunayi ba, ta dawo tana kallansu duna cece kuce sai dataje wajen ɗakinta sannan tace “In kun tashi fadanku nan gaba ina ganin ku yishi in yana gidan matsalar kai abu ba’asan kanayi na kenan.” Tana kai nan ta wuce ciki dan ta kula rashin hankalinsu karuwa yake maimakon angirma asan an girma. ***** A bangaren Zeey kuwa kai tsaye gun mai ɗinki ta koma ganin yanda Baqeer yai zane yasa mamakinshi ya kara karuwa, kallanta yai yace “Hajiya dan Allah zan iya ganinshi gobe?” “Eh zan ƙira shi naji lokaci sai mu hadu dakai a gidan.” Daɗi ne ya kamashi yace “Kai nagode lalai inaji a jikina alkairi ne ya zo gareni.” Haka ta kwashe takardun tace “In kun gama yanke yanda zakuyi business ɗin na dawo maka dashi.” Ba yanda zaiyi haka yana gani ta tafi dasu, ji yake harya kosa gobe tai, nan ya dinga kallan shagonshi yana tunanin da alama dole ya ƙara fadada shagon tunda alkairi ne ya zo musu. A hanyarta ta komawa sau hudu tana ɗaukan wauarta tana ajiyewa tana kwaban kanta akan itama taɗan ja aji irin na mata, har mamakin kanta take yanda take da jan aji wai akan Baqeer sam bata iyawa, harta isa gida bata ƙira shi ba. Mumy ta tarar a kitchen tana bada umarnin girku, a shagwabe tace “Mumy ruwa.” Kallan ɗaya daga cikin masu aikin tai nan ta miko msta da sauri, Zeey ta amsa tai daki tana tafe kamar ba laka a jikinta duk zuciyarta nemab kin hakura da ƙiran Baqeer take. Binta Mumy tai tana shiga itama ta shigo tace “Suta lafiya?” Huci ta sauke sau uku sannan tace “Mumy waya nake san yi kuma bana san yi.” “Me kenan? Kinaso kuma bakyaso?” Ta ɗaga kai tace “Banaso ya rainani kuma na kasa hakura.” Kallan mamaki ta mata, tace “To ni bansan meke faruwa ba ina na isa bada shawara?” Jawo jakarta tai ta ciro takardun tace “Yauwa Mumy kalla?” Amsa tai tana kallo mamakin yanda Zeey ta koma farinciki take, sai sa ta gams dubawa sannan tace “This is incredible waye yai?” Amsa tai daga hannun Mumy tana dariya tace “Dan baiwa.” “Mai disability ɗin da kika ban labari?” Kai ta ɗaga a hankali tace “Mumy karki manta sirrin mu ne.” Kanta ya shafa tana cewa “Karki damu sannan karki manta na ce miki ina bayanki duk abinda kika zabarwa kanki ina tare dake.” Kai ta ɗaga a hankali taee da rungume Mumy wata nutsuwa ma saukar mata, Mumy na fita ta jawo wayarta, sako ta turamai ‘Ka kirani’ Shima maida mata yai yace ‘Why?’ ‘Kawai nidai ka ƙirani so nake naga ya receiving call ɗinka zai kasance.’ Kai ya girgiza kamar bazai kiraka ba har na wajen minti biyar, dan Zee har ta ajiye wayarta tare da jan tsaki tace “Na sani dama ai.” Karar wayarta ce yasa ta mike zaune da sauri ta jawo wayar tana jin wani sanyi cikin ranta, ringing biyu ga daure akan bazata dauka ba, tana jiran na ukun da zata dauka kawai taji ya kashe, wayar ta cilar kan hado sannan ta kwanta, cike da takaici ta ƙira yana daukar tace “Ringing uku ma baza’a bari yai ba?” “I thought bakyajin yin wayar ne.” “Bayan ni nace ka kirani?” “Then?” Baki ta turo kafin tace “Naje gun tailor ɗin, nan ta zayyane mai abinda ke faruwa, Baqeer da ɗi ne ya kamashi cikin kakkausar murya yace “Thank you!” Gyaran murya tai tace “Ni sam banji me kace ba me kace?” Mamaki yake yanda sam batada damuwa ko ɓacin rai bai taɓa gani ba a idanta, sai dai tai na wasa, shiru suka ɗan yi kowa da abinda yake sakawa a ransa kafin yace “Bye!” Tace “Bye.” Kace wayar yai tabi wayar da kallo tare sa jan bargo ta rufe fuska, kafafunta tadan bubuga sannan ta ɓoye takardun cikin drawer, alwa tai ganin la’asar tayi sannan tai sallah, rabin addu’arta Baqeer takewa akan Allah ya kara mai lfy yasa taga ranar da zai taka da kafafunsa, Allah ya bashi ikon fara yin sana’arnan lfy.” ***** Fatima yau kunnenta na waje dan tun jiya wayarta ta mutu taki tashi gaskiya Baqeer takesan dubawa dan haka hankalinta na kan shigowar Malam. Cikin faɗa yake magana “Wallahi Abu kinji na faɗa miki in bakiwa Kamal magana ba zan tattarashi shima na koreshi, gıdana ne nan ba uban daya isa ya jamin ɓacin rai, yanzu na gama da takaicin Baqeer har zan fita wani banza ya tareni yana wai ban shawara akan insa ido a kan Kamal? Wuya zansa ba ido ba kindai ji na faɗa miki, a kalla su Bashir makaranta ne kawai basa zuwa amma yanzu tunda na musu magana sunji shifa? Shi ba karatun ba sai ja min magana? To ni ba uban da zai samun hawan jini kinji na faɗa miki.” Ajiyar zuciya Fatima tai dan tasan tana tambayarshi cikin wannan halin ma wani tashin hankali zata jawa kanta dan dama a san samunta ma ba cemai zatai gun Baqeer ba, cewa zatai zata barka ko biki.” Haka ta koma ta zauna ranta na sake ɓaci, cike da mamaki taga an buɗe labule, Mallam? A bangarenta? Mamaki ne ya kamata ta mike tace “Mallam kaine? Sannu da dawowa.” “Ba ni bane aljanina ne, ke wai nikam meke damunki? Dama lekowa nai na amshi kuɗin da nake binki.” Kallansa tai tace “Wane kenan?” “Wanda nasa na sai kujeru kika haɗa kika cinye, same mace ace Allah ya yiki ba imani?” Kai ta kauda tace “Mallam na ɗauka mun yi maganwf kujeru kuma ka fahimceni?” Zagaye ya fara a ɗakin wanda hakan ya tabbatar mata dama ba zancen kudin yazo ba bincike yazo mata, yana tafe yana cewa “Na fahimceki kamar ya? Ke ai na dade da daina fahimtarki daga ke har ƴaƴanki, Maryam ma dana aurar gidan dauka na ɗauka za’a samu a amfana ashe fankan fayau ce.” Yaja tsaki sannan yabar ɗakin, ba ta da niyyar kuka dan yanzu ba shine a gabanta ba, tunda sukai magana da Baqeer taji muryarshi wasai ta tabbatar komai lfy kawai dai ganinshi take san yi sai dai in haka zai sake jawo matsala gwara ta jinkirta. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Muhd Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA UKU* {43} A duk sanda Habi taga Asiya na wannan zumudin kasa ɓoye mamakinta take, yanzu ma tana kwance bayan sallar asuba take juyo kunkunin Asiya, farkawa tai ta ɗan juyo tana cewa "Yau kuma menene da sassafan nan ke da bakya rabo da neman magana?" Asiya tsaki tai tace "Ni dasu Inna ne wallahi badai ni za'awa kayan ɗakin dubu dari biyar ba kamar wacce wace ba tada gata? Ai ko miliyan biyar ni yamin kaɗan a jeran gidana." Sake baki Habi tai tana kallanta tace "Miliyan biyar? Asiya kanki kalau dai ko?" Wani mugun kallo ta mata tace "Banasan iskanci ke in bikinki yazo kice kin yafe kayan ɗaki ku zauna a tabarma, aikin kawai tun yaushe ma aka daina kayan ɗakin 700k? Na tabbatar ko mutanen kauye yanzu suma sun waye." Daga waje Habi ta juyo Inna tana ƙoƙarin haɗa murhu, ta mike tana gyara inda ta kwanta tana cewa "Su masu miliyan biyar ɗin rainan gas ne ke kuwa rainan itace ce ko gawayi sai ai sati ba'ai amfani dashi ba a gidan da kika taso.” Ai da sauri ta mike tana neman jawo Habi, ganin haka yasa ta ruga waje da gudu tana ma Asiya gwalo wanda ba karamin ɓata mata rai yai ba. Kwafa tai tace "Zaki dawo wlh." Habi kuwa tana fita tai tsaki tace "Auren cin amana akewa zumudi haka, mutum sai karya kamar ɗan wani? Kawayenta har yau ba wanda ta taɓa bari yazo gidansu amma dan san a sani harta bisu ta sanar dasu zatai tafiya." Muryar Inna ce ta katseta "Habi shine ke baki ɗan kwanta ba zaki fito da safen nan?" "Ke kika fito bare ni Inna?" Ta faɗa tana ƙarasa was tare da ɗaukan abin tatar koko. **** Zeey a ƙofar gidan Umma tai parking, kallan kanta tai a madubi wai yau itace take bin namiji? Itadai sam tasan wannan rayuwar ba tata bace, gabanta ne ya ɗan faɗi kadan ya Baqeer zaiyi in yasan itace Zainab? Wani yanayi ne ya bayyana a fuskarta ta daure ta buɗe ƙofar mota ta fito. Jamila na waje ta shimfida tabarma tana yanke farcen kafarta, yau sau ƴan harare-harare sukeyi uta da Abu dake busar da aya zatai sana'ar data saba. Zainab ce ta shigo ko kallan inda suke batayi ba ta fara neman wucewa bangaren Umma. Abu a kufule tace "Ke cokal? Kin wani cokalo takalmi mai tsini kinzo mana gida kina neman shigewa ciki? Hala dangin mijin Maryam ce? Dan nasan kaf zuri'arsu Fatima ba wanda zai sa atamfar jikinki." Duk yanda sukeji da faɗa ita da Jamila sai ji mukai Jamila tasa dariya tace "Yoo wannan ma dangin nata da su ai da babu duk daya, uwar ma bakiga ba ganinta zuke zuwa yi ba." Zainab ce ta waigo tana murmushi tace "Dama aiko ni akai naga yawanku dan shugaban mu yace zai fitar da zakka amma da akama mace ɗaya ce a gidan." Jamila ce tai zuruf tace "Shareta ƴar nan wannan fa dama haka take duk wani kursusun gulma daga gunta yake fitowa nace wanene shugaban?" Abu ce tai tsaki tace "Andaiji jiki wlh mutum ya nemi sana'a yaki sai yaji za'a raba ɗari biyar ya hau bin layi." Zeey kam ganin suna masufarsu yasa ta shiga ciki ta barsu, Umma na ɗaki tun safe take jin kanta babu daɗi ga wayarta ta kunnu amma tana tsoron ƙiran Baqeer kar ya gane halin da take ciki daga muryarta. Sallamar Zainab ce yasa ta miƙe tana amsawa, ganin Zainab yasa fara'arta ta ƙara faɗa da tace "Zainab kece?" Zama tai ta gaisheta sannan tace "Daga ina haka?" "Dama nakaiwa Dada sako ne Ya Baqeer ya aikoni gunki." "Baqeer? Ya yake? Ya jikin naashi? Ya yake rayuwa?" Umma tai tambayar a jere idanunta na cikowa da kwalla, murmushi Zeey tai tace "Umma yanzu komai ya daidaita?" Kai ta jinjina tana murmushin yake tace "Indai har su yaran suna zaune lafiya ni ko ma menene bakomai." Tausayin Umma ya kamata dole ta taimaki Baqeer ko dan ya ƙara tsayawa da kafarsa, hannu tasa cikin jakarta ta ciru kuɗin ta ajiye gabanta, Umma da mamaki ta zaro ido kafin ta tamke fuska tace "Kindai san bazan karbi kuɗin iyayenki ba, ban rikeki ba abaya ban kuma......" Da sauri Zeey ta katseta tace "Inji Ya Baqeer sakon ne." Mamaki ne ya hana Umma magana tace "Baqeer?" Kai ta ɗaga zatai magana wayar Nabeela ta shigo kamar bazata ɗauka ba saboda tunanin kar a gane inda take sai kuma ta daure ta ɗaga. Nabeela tanaji ta ɗaga tace "Zeey kina ina? Dady ya kusa isowa, yana Kano." Da sauri ta mike tace "Okay, nagode Aunty Nabs." Kashewa tai sannan ta kalli Umma ta mata bayanin yanda Baqeer yace a kasafta kudin sannan tace "Zan wuce Umma ana nemana." Harta fita Umma na riƙe da kuɗi mamaki ya gama rufeta, ina Baqeer ya samu kuɗi? Kuɗin ma har haka? Wayarta ta ɗauko tadan bubuga bayan sannan ta tashi, ƙiran Baqeer tai ta ɗau kudin ta shiga dashi ɗaki ta zauna a bakin gado, karin mamakinta ma ya akai Baqeer yaba Zee sako? Zeey cikin sauri ta fito tana ji su Jamila na gulmarta itada Abu itakam ko ta kansu batai ba tai waje, dan tasan in Dady ya san yawo take tabbas hanata fita ma zai gaba ɗaya ita kuwa yanzu aka hanata ganin Baqeer to fa an mata giɓi sannan batajin zuciyarta zata iya dauka. Kamalu ne ya sauka akan babur da mamaki yaga wata kamar Roshni ta shiga mota, cikin sauri ya ke tahowa yana hadawa da ɗan gudu-gudu, sai dai kafin ya iso taja motarta ta tafi, motar da take hawa ne sai dai bayaji Roshni zatazo gidansu, gida ya shiga ya nufi gun Abu wacce ganinshi yasa tace "Kamalu? Hala yunwa ta koroka?" "Roshini ce ta shigo gidan nan?" Da mamaki tace "Rasheeda? Au wai sunanta kenan? Yo ai ni ban sani ba." Da takaici cikin dan ɗaga murya yace "Wace wata Rashida? In ma Rabi ce ni bai damenba." A fusave Jamila tace "Karka sake kiran sunan mahaifiyata in zakai zagi ko magana ku kare can tsakaninku. Tsaki yai yana kumboro baki kawai ya fita daga gidan, ya banko ƙofar gida kai kace ɓalata zaiyi. Da gudu ta shiga ciki, saura kiris ta buge Kabir da ya nufi hanyar waje, tace "Oops! Sry." Kai ya girgiza ya bita da harara sam yarinyarnan ta rainashi wato ko dawowa ma ya bata hakuri baiyi ba? Duk an bari ta rainashi saboda bin bayanta da kowa yakeyi. Muryar Nabeela ce ta katse shi tana cewa "Are you alright?" Kallanta yai ta sakar mai murmushi, kai ya girgiza kawai ya fita dole ma yaje gun abokansa suje club, waya ya ɗauko bayan ya shiga mota ya ƙira Mumy. Ta dauka tana cewa "Abu kake so?" "No Mumy please fita nakesan yi zanje gun wani friend dina ne in Dady ya dawo kice ina bacci, ba dadewa zan ba.” Kafin tai magana ya kashe wayar ya shiga motar ya bar gidan. A ɗaki ta ajiye jakarta sannan ta cire mayafi ta fito gun Mumy inda take shiryawa Dady abinci. ***** Baqeer ne ya ɗaga ƙiran Umma, bayan sun gaisa tace “Baqeer meke faruwa? Ka barni riƙe da kuɗi ina kokonto.” “Umma badai so kike kice baki yarda da ɗan ki ba wanda kika haifa kika kuma raina, kindai san bazan yi abin banza ba.” Ajiyar zuciya tai tace “Bawai abin banza ba kawai tsoro abin yaban.” Jiki a sanyaye yace “Umma insha Allahu Allah bazai wulakanta mu ba, Allah zainzama gatan mu, kedai ki cigaba da mana addu’a.” A hankali tace “Allah ya dafa mana Baqeer sai dai nayi mamaki sannan yaushe kuka……” sai kuma tai shiru a matsayinya na mahaifiya da dama batasan wannan gabar tun shekarun baya me zai sa ta tambayeshi har ta kara taso da abin? Haka sukai sallama yana Dada wayar. Dada fitowa tai waje dan ta bata labari ta kuma san yanzu Baqeer zai kwafsawa hirarsu. Umma ce ta katseta da cewa “Dada nikam Baqeee yasan Zainab ne?” Dariya tasa tace “Sani kai ai duk wannan abin da taimakonta ya tabbata.” Mamaki ya kama Umma sai dai Alhamdulila da Baqeer ya cire wannan mumunan abin a ransa ya saki jiki suke gaisawa da Zainab, sai dai kasan zuciyarta na tsoro kar abinda ya faru baya irinshi ko shigenshi ya ƙara faruwa. Kai ta girgiza sannan tace “Dada dan Allah kar wanda yasan sana’ar da Baqeer yakeyi yanzu, mu barshi a matsayin sirri ina tsoro kar tsautsayi yasa mahaifinshi yaji labari. Kai Dada ta jinjina alamar hakan yayi nan suka ɗan yi hira kaɗan da Dada sukai sallama. Ba shiri Umma ta fito tai alwala ta koma ɗaki tai sallah tanawa Allah godiya akan abinda ya faru lalai babu shakka Allah shine maj bayarwa kuma shine mai hanawa. ******* Plate kowa yaja yasa abinci a falo da Dady, kallan Zeey yai yace “Ƙira Kabiru mana.” Kallansa tai tace “Anya ma yana gidan kuwa bari dai na duba.” Mumy ce tai saurin rikota tana cewa “Baya ɗan jin dadi shine nace ya kwanta.” Da mamaki tace “Yanzu fa na ganshi da zan….” Sai kuma tai shiru kar ya gane yanzu ta dawo ta wayance tace “Allah Mumy ba wani bacci kawai gulma ce.” Rikota Mumy tai tana cewa “Bari ni na duba.” Bata musa ba ta koma ta zauna ta kalli Dady tace “Dady bari na ƙira Nabeela.” Hannu ya mata alamar ta dakata sannan yace “Magana nakeso muyi shiyasa bance tazo ba, mahaifin Junaid yace kun haɗu ko?” Nan danan yanayin fuskarta ya canza tace “Eh amma Dady kasan ba wani abu tsakanin mu.” Kai ya jinjina yace “First step ne so babu matsala, Mumy fa? Da na tafi batajin dadi ne naga duk tayi sanyi.” Kai tsaye ta buɗe baki tace “Mutanen Dambatta ne……” Cikin hanzari Mumy wacce ta taho tace “Zee zo kiyi maza ki dubamin Nabeela.” Kallan Mumy tai da mamaki sai dai ganin yanayinta yasa ta tashi da sauri, tana zuwa inda take ta ja ta sukai falan ciki tace “Zeey kin manta nace mu bar maganar nan?” Baki ta turo tace “To gashi nan abin yana damunki har Dady ya gane.”- “Please Zeey ya isa nima na ware banasan na zama sillar mai raba alakar da Allah ya haɗa .” Jiki a sanyaye ta kalleta sannan tace “Shikenan na bari Mumy.” Haka suka koma Mumy tace Kabir ma wanka, sukaci abinci ta koma ɗaki tai salla sannan ta faɗa gado. Kwanciya tai zuciyarta na tuno mata yanayin Baqeer nan ta ɗau waya tamai text tace ‘Me kakeyi?’ Baqeer dake zaune yana addu’oi sai daya shafa sannan ya ɗau wayar maida mata yai da ‘?’ Baki ta taɓe tace “Oh ni!” Zata ajiye wayar wani sakon ya shigo ‘Thank you’ kallan sakon tai zuciyarta na ji kamar tafi kowa farin ciki, rungume wayar tai a ƙirjinta taɗan yi juyi tana lumshe ido. Zata mai reply kenan Nabeela ta shigo da sauri ta rufe wayar tace “Aunty Nabs.” Karasowa ciki tai ta zauna tana cewa “Ɗazu kinwa Kabir laifi ne?” Ido taɗan juya kaɗan tace “Allah ni na ɗauka ma wani abin ne, kinga Allah ki kyale shi yai abinda yaga dama nifa a iya sanina ba abinda namai kawai kinsanshi sam baya rasa abin cewa.” Jiki a sanyaye tace “Kinsan dai kaf duniya baki da kamar shi dan Allah Zee ki daina ɓata mai rai.” “Wai ke kullum a bayanshi kike bakya taɓa ganin laifinshi?” “Ke kuma kullum su Mumy da Dady a bayanki suke ai.” Kallan Nabeela tai cike da zargi tace “Bayan gaskiya dai ke kanki dan dai kina san biye mai ne amma kema kinsan neman faɗa yakeji dani ko da yaushe.” Kawar da maganar tai da cewa “Abinci fa? Kinci?” “Umm!” Kawai tace dan tabbas tana jin ba da ɗi, mikewa tai da sauri Zee ta ɗago ta kalleta har tabar ɗakin. Dakinta ta koma ta kwanta zauna tana tunani, ya zatai da abinda ke ranta? Bayan tasan ba laifi bane amma ba wanda zai yadda da ita? Hannu biyu tasa ta shafi fuskarta. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA HUƊU* {44} Da sassafe ya tashi ya shirya don baya so Salim yazo ya samu bai gama shiryawa ba, tun jiya dama ya faɗa mishi yazo yau da safe zai yi mishi rakiya wani wuri, Salim ɗin bai bi ba'asin inda zai raka Baqeer ɗin ba sai ma daɗi da yaji na ganin ya fara warewa ya fara dawowa da walwalarshi, rayuwarshi ta fara hawa kan saiti kamar yadda take a daa ba kamar yadda ya ƙuntata rayuwarshi tun bayan da ya gamu da larurar nan ba. Ita dai Dada tana kallonshi ƙanzil bata ce mishi ba, tana kallon lokacin da ya haɗa wuta sannan ya ɗebo ruwa a randa ya zuba a tukunya ya ɗora ruwan wanka, bayan yayi zafi da kanshi ya sauke ya juye a bokiti sannan yaja boktin a hankali ya kaishi har wajen randar ya surka, a hankali ya dinga tura bokitin yana kan wheelchair ɗin shi har ya kai banɗakin, bai nemi taimakon Dada ba ita ma bata ce zata taimaka mishi ba kamar yadda take yi a mafi yawan lokuta da idan taga yaje zai yiwa kanshi wani abu zata tashi ta karɓa tayi mishi ko bai ce ba. Haka yayi tara-tara da dabara ya kai ruwan wankanshi da kanshi ya tuɓe yayi wankan bayan ya gama ya fito ya shirya cikin wasu kayanshi wankakku sai dai babu guga. Kallon kanshi yayi yana tunanin wai shine Baqeer wannan ɗan ƙwalisan saurayin da komai nashi ya fita daban dana matasa ƴan uwanshi gashi yau ko ɗan turaren da zai fesa a jikinshi baya dashi, shine yau yake saka sutura babu guga, tabbas dole ya saita rayuwarshi ta koma daidai ya tsaya da ƙafafunshi ya nemi abinda zai rufawa kanshi asiri ba zai yiwu ya cigaba da zama a haka ba yana ƙuncin zuciya kawai don Allah ya jarabce shi da wata larura ya mayar da kanshi mara amfani ba, bai ma ƙara tabbatar da nakasa ba kasawa bace sai da yake ɗan fita waje a yanzu yana ganin yadda mutane suka tashi tsaye da neman na kansu, akwai wani makaho anan inda yake yawan zama yake ganinshi yana sana'ar gyaran takalma har yana mamakin ta yadda yake iya yin gyaran alhalin baya gani, ranar daya fara ganinshi sosai abun ya tsaya mishi a rai don yaga dai ga wanda yafi shi zama nakasashe tunda shi ko ganin ma baya yi amma bai zauna ya dogara da kowa ba ya fito yana neman na kanshi to ahi kuwa don me yasa don ya gamu da larurar ƙafa kawai zai koma ya zauna yana jiran komai sai anyi mishi. Salim bai zo ba sai can wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe. Yana jin muryarshi suna gaisawa da Dada yayi zuruf ya fito yana maka mishi harara. "To ko dai na koma don naga kamar baka yi maraba da zuwana ba, daga ganina kawai sai ka riƙa aiko mini da harara?”Hararar tashi ya ƙarayi yace "Tun ƙarfe nawa nace maka kazo shine baka tashi zuwa ba sai yanzu?” Shima hararar tashi yayi yace "Anƙi azo da wurin Mallam daga zuwana zaka wani tareni da faɗa ko tambayar abinda ya tsayar dani baka yi ba?” “Au haka ma zaka ce?" "Eh ɗin" Ita dai Dada tana jin cacar bakin da suke yi tana dariya sai da suka gaji suka bari don kansu sannan suka yiwa Dada sallama suka fita. Sai da suka fita waje Salim ke tambayarshi inda zasu je, sai sannan yayi mishi bayanin zanen da yayi wa Zeey ranar nan bayan ta kaiwa telan ya ɗinka mata ya nemi da yayi mishi wasu ya saya da duk yadda aka yi dai har ma da kuɗin daya samu shine yake so ya rakashi kanti ya sayi ƴan abubuwan buƙata. Jinjina kai Salim yayi kafin yace "Kai amma nayi maka murna abokina, wallahi sosai nayi farin ciki, don baka san yadda zamanka a haka yake damuna ba don nasan har da hakan yake ƙara maka yawan damuwa tunda ba sabawa kayi da irin wannan zaman ba, tun baka gama mallakar hankalinka ba kasan neman na kanka to yanzu kazo baka iya yin komai kaga kuwa ai dole ka shiga damuwa amma yanzu Alhamdulillah da Allah ya kawo maka wani abun yin cikin sauƙi, Allah ya sanya alkhairi yasa wannan shine silar warwarewar duk wasu matsaltsalunka.” "Ameen Ya Rabb, nagode Salim. Ka tabbata aminin ƙwarai, kai kaɗai ne baka gujeni ba tun bayan da iftila'in nan ya afko mini, da yawa daga cikin abokanmu ma ko dubani basu zo sun yi ba bare su tausayawa halin da nake ciki, kai kaɗai ne ka tsaya tare dani ka kula dani da jikinka da aljihunka, nagode ƙwarai Allah yayi maka mafificin sakamako da aljannarshi da yayi tanadinta wa masu yin abota domin shi" haka nan yaji ƙwalla na taruwa a idanunshi, ƙoƙari yayi ya mayar da ita bai barta ta zuba ba. Shi kanshi Salim sai da jikinshi yayi sanyi da abunda Baqeer ɗin yace don shi shaida ne yadda abokansu duk suka juya mishi baya shi kuwa Bello ma sai ya haɗa da cin amana mafi muni bayan duk a cikinsu tasu tafi zuwa ɗaya shi da Baqeer saboda ra'ayinsu da yazo ɗaya na yin zane. Mai adaidata sahu Salim ya tarar musu ya faɗa mishi inda zai kai su, da taimakon mai adaidaitan suka saka Baqeer a ciki ya zauna sannan Salim ya naɗe wheelchair ɗin ya shigar da ita shima ya shiga ciki ya zauna. Suna tafe suna ƴan hirarrakinsu har suka ƙarasa wani store anan kan titin hotoro. Salim na tura wheelchair ɗin suka shiga cikin kantin bayan sun biya mai adaidata kuɗin shi. Kayan amfanin shi ya saya irinsu sabulun wanka, toothpaste da brush, man shafawa, hair cream sannan suka ƙarasa ɓangaren turare. Kallon wajen yayi idanunshi suka kai kan turaren intense oud (Gucci) da yake amfani dashi tunda ya fara riƙe kuɗi na ƙashin kanshi sai dai yanzu yasan bai isa ya iya saye ba tukuna, ɗauke kanshi yayi ya cigaba da duba turarukan mata yana so ya sayawa Zainab. Yana son saya mata turare mai tsada sai dai kuma yana jinjina kuɗaɗen su gashi shi ba wani kuɗi bane dashi masu yawa, dubu ɗarin da akatura mishi ce a account jiya, haƙuri yayi ya ɗaukar mata turaren da bai haura dubu ashirin ba ya nemi wanda bai gaza dubu biyar ba ya ɗaukarwa kanshi. Yanzu ba lokacin sayen abubuwa masu tsada bane lokaci ne da zai yi ƙoƙari ya gina kanshi in yaso komai yake son yi yayi daga baya. Kallon Salim yayi yace shima ya ɗauki turaren sai yace a'a ya saya mishi wata rana amma ba yau ba. Harara ya watsa mishi sai ya ɗaukar mishi irin wanda ya ɗauka yace "Gashinan sai muyi anko.” Dariya kawai Salim yayi sai dai bai ce mishi komai ba, har sun juya zasu bar wurin idanunshi suka sauka akan wata rose flower me kyau an sakata a cikin wata garai-garai ɗin roba. Tsayawa yayi yana kallon rose ɗin yana tunanin ya dace ya haɗa mata da ita to show his appreciation. Salim dai na kallonshi bai ce mishi komai ba sai da yaga baya da niyyar barin wurin yace "Malam idan saya zaka yi ai gara ka ɗauka mu tafi mu bar ɓata lokaci rana tana ƙara yi idan kuma ba saya zaka yi ba to mu tafi don ina so naje kasuwa bayan na mayar da kai gida.” Kallon Salim yayi ya haɗe fuska don baya so ya kawo wani abin a ranshi sannan ya ɗauko flower ya saka a cikin basket ɗin suka bar wurin. Dariya ce ma taso kama Salim ganin yadda ya ɓata rai wai shi a dole kada ya kawo mishi wasa sai kace idan yayi niyyar tsokanarshi shan ƙamshin shi zai hanashi ne, ai ba wannan ne lokacin tsokanarshi ba don yasan yanzu yana buɗe baki yace zai yi magana fasa sayen flower ɗin zai yi shi kuma ba zai so ya fasa abinda yayi niyya saboda shi ba, shi yasa yayi shiru ya ƙyaleshi. Haka suka je wajen cashier aka buga musu kuɗi ya fito da atm card ya biya. Sai da suka fita har sun hau adaidaitan da zai mayar dasu gida sannan ya cewa Salim "Dan Allah idan ka samu lokaci kazo ka rakani banki nayi updating account ɗina kasan tunda na rasa wayata ban yi welcome back na layina ba don haka bana ganin alerts idan anyi min.” “To sai nazo wajen jibi In Sha Allah" sai kuma ya kalleshi yana ƴar dariya ƙasa-ƙasa yace "Shi turaren da rise flower wa ni aka sayawa?" Harararshi yayi ya ɗauke kai bai amsa mishi ba, shi dama yasan ba ƙyaleshi Salim zai yi ba sai yayi ta tsokanarshi akan wannan flower ɗin da yaga ya saya. “Ah to nidai na mata na gani kuma ni namiji ne amma ba matsala zan iya amsa na kaiwa crush dina.” Wani kallo Baqeer yamai yace “Hala Habi ce crush ɗin?” Salim yai gyaran murya yace “Nidai ban ce ba, kaine ma za’a tambaya tunda kai ka siya.” Gefe ya kalla baice komai ba dan dama sun saba haka da Salim indai cacar baki da zolaya ne. ***** Tunda ta samu Umma ta bata kuɗi ta sayi injin markaɗe shikenan aka daina jin kansu da maigidanta don yanzu ta daina damunshi da bani-bani akan abinda zasu ci. Har wani ƴar daɗi suke yi bare idan yazo yaga ta shirya mishi abincin da bai san yadda tayi ta samu ta girka ba, haka zai zauna yaci yana washe baki yayi tayi mata kame-kamen zancen abinda bai shafeta ba. A yanzu bata da wata damuwa don tana samu tayi duk wasu ƴan hidingimunta a cikin ɗan abinda take samu duk da har yanzu cinikin bai zauna ba soaai saboda ba kowa yasan tana markaɗen ba duk da lokacin data fara ta tura ƴan biyu makwabtansu na kurkusa duk sun sanar cewa ta fara yin markaɗw na kuɗi idan suna buƙata, to amma ko a haka babu abinda zata ce sai gidiyar Allah domin kuwa sun daina zama da yunwa tunda duk tsiya bata rasa abinda zata girka musu abincin da zasu ci kullum har ma ta samu na sayen sabulun wanka da omon wanki. Wai kuma sai da kishiyarta taga ta samu canjin rayuwa tunda ta fara markaɗen sai ta tsiro da tsurfar wai ƙarar injin tana damunsu tana hanasu walwala a cikin gida markaɗen da ba kowane lokaci take yi ba amma shine ganin tana samun na rufin asiri take neman rabata dashi, sosai suka yi rigima har sai da maigidan ya saka baki sannan ta haƙura ta ƙyaleta ta cigaba da yi anan soron gidan nasu don da cewa tayi sai dai ta fitar dashi ƙofar gida don haka nan ba za'a kashe musu kunne da ƙarar inji ba. ***** Kabir bai shigo gida ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya na dare bayan kowa ya tafi ya kwanta, tun Daddy na tambayar ina yake Mummy na kakkarewa har ya haƙura yayi ahiru ya daina tambayar. Cikin sanɗa yazo zai shige ɗakinshi don baya so aji motsin shigowarshi har Daddyn da baya son yasan bai yini a gida ba ya fito ya ganshi a yanayin da yake ciki. Ya kai tsakiyar parlourn kenan yaji ansa hannu an riƙo shi, sai da gabanshi ya faɗi don baya son ganin kowa a wannan lokacin. Ƴar nutsuwa ya samu da yaji kaurin hannun alamun na mace ne. Fitilar wayarshi ya kunna yana fatan ace ba waccan ƴar sa idon bace ta zauna zaman jiranshi don yasan idan har ita ce to asirinshi ya gama tonuwa. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke da yaga Nabila a zaune tana yi mishi wani narkakken kallo. Ƙwace hannunshi yayi ya haɗe rai don kada ma tace zata kawo mishi raini yace mata "Me kike yi har yanzu baki je kin kwanta ba?" Narkar da fuskarta tayi tace "Taya zan iya bacci alhalin baka dawo gida ba har wannan lokacin, wai shin ina kaje nema Kabir tun rana fa Daddy yake tambayarka.”Tsaki yayi yace "Koma ina ne ina ruwanki da inda naje, kin san sarai dai bana son yawan sa ido.” Yayi wucewarshi ya barta a wurin, yasan dai ba zata faɗawa kowa ba amma ya lura sai ya taka mata burki don yaga alama nema take yi ta takura rayuwarshi akan abinda daga shi har ita sun san ba mai yiwuwa bane. Sai da ya shige ɗakinshi ya mayar da ƙofar ya rufe sannan ta tashi ta bar wurin zuwa ɗakinta tana share hawaye. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER*      *NA* *UMM ASGHAR*          *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA BIYAR* {45} Yau kwana biyu kenan Zee bata zo ba gashi ko waya taƙi yi mishi, sam komai yaji ya fita daga kanshi, haka kawai inya kalli turaren da rose flower ɗin daya siya sai yaji ranshi ya ɓaci, Dada tana lura da duk wani ɓacin ran da yake ji dashi kwanan biyu, don ko waje baya fitowa sai in abu yake so, zanen ma da yake na ɗinki ya ajiye tunda yana jiran a gama sayar da wancan kafin ya sake wani. Yanzu shine karo na takwas daya ɗauki wayarshi yana ajiyewa, tsaki yayi ya cilla wayar kan gado, sallama yaji daga ciki hakan yasa ya ɗan gunguro kekenshi zuwa jikin ƙofar ɗakin shi. “Talatu kece?” Abinda ya jiyo Dada tana faɗa kenan hakan yasa ya maida kekenshi ciki takaici duk ya ƙara kamashi, exercise na kafarshi ya shiga yi sannan ya ɗauki wani littafi yana karantawa na fashion and design, “Me zai dameshi bayan mahaifinshi ma tunda ya koreshi ko waya bai taɓa yi ba yaji ya yake? Ai duk da bai san inda yake ba ya tabbatar daya tambayi Umma zata sanar mishi.” Rufe idanuwanshi yayi yana tunanin meke damunshi akan Zainab? Me yasa yake ji kwana biyun nan kamar wata guda? Wayarshi ya janyo ya rubuta ‘Hope kina lafiya?’ Gogewa yayi ya sake rubuta ‘Zaki zo?’ Ido ya zaro yace zamana take yi ashe? Nan ya goge ya rubuta ‘Nace ba?’ Nan ma ya goge cike da takaici ya rufe wayar yana jin haushin kanshi. A haka yayi sallar azahar, ko da Dada ta bashi abinci ma tsakura yayi ya ajiye yace ya ƙoshi, ita dai bata kulashi ba  ta shirya ta fita gidan mai jego inda aka yi haihuwa kusa dasu. Haka yayi sallar la’asar ya fito waje yana neman fita waje wurin wannan makahon haka kawai yake ji yana son bashi ko dubu biyar ne a cikin kuɗin shi, turus ya tsaya jin ƙamshin turarenta, baya yayi da keken ya koma tsakar gida yana ɗan gyaggyara zaman rigarshi, sallama tayi ya amsa ciki-ciki, da mamaki ta shiga tsakar gidan yi tayi kamar bata ganeshi ba tace “Dada fa?” Mamakin kalamanta ne ya sakashi waigowa, kallonta yayi sanye take da doguwar rigar abaya sabon yayi, a saman abayar aka yi hula sai ta ɗaura ɗankwali tasa hular a sama, tayi kyau sosai sai yaga ma kyaunta kamar ƙaruwa yayi, kai ta ɗan karkatar tace “Tana ciki?” “Ban sani ba.” Amsar daya bata kenan ba tare da yasan ya furta ba. Ga mamakinshi sai gani yayi zata juya ta fita da sauri yace “Ina zaki?” Waigowa tayi tace “Gida.” “Gida?” Ya tambaya fuskarshi a tamke tace “Eh, ko da wani abun ne?” Kasa magana yayi sai kallonta da yake tace “Meye amfanin zuwa inda in aka ji kwana biyu kayi shiru ba za’a yi maka waya ko a tambayi lafiya ba ina ganin ba amfanin zuwa.” Kallon juna suka yi, juyawa tayi zata wuce sai ga Dada ta shigo, dariya suka saki ta gaisheta tana cewa “Haba duk kwana biyu gidan babu daɗi ba kya nan shi kuma o’o sai ƙuncini da cin magani.” Ta gefen ido ta kalleshi shi dai duk bai jin daɗi yaso yayi mata magana kuma sai ga Dada ta shigo, da alama ma bata ji daɗi bane, duk sai yake jinshi babu dadi. Wayar Zee ce tayi ƙara kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗaga haka kawai taji zuciyarta na ingizata yin abu, tace “J haba ai ni nayi fushi.” Kalmar J data furta ne ya sakashi kallonta, nan da nan takaici ya kamashi Junaid fa kenan, shine basu tashi yin wayarsu ba sai da tazo nan gidan? Junaid yace “A’a fa nine zan yi fushi, sau nawa ina kira baki ɗauka ba.” “Wai ka kira sam ban kula ba ban ɗan ji daɗi bane kayi hakuri.” Kallon Baqeer tayi shima kallonta yake yi sai yaji ranshi duk babu daɗi, to wai shi menene nashi? Yasan bai kyauta ba amma wayar da take yi da Junaid haka ji yake yi kamar ya kwace wayar ya hanata magana. “Allah a’a kaima kasan ba haka bane.” Shagwaɓar da yaji tana yiwa Junaid kenan, wani abu yaji ya sake tokareshi nan ya kauda kai. “Okay to shikenan zan sanar mishi sai muzo kasan ni na ɗauka kaine zaka bamu appointment ai.” Sallama suka yi ta kashe wayar sannan ta kalleshi tace “J yace ya kamata ka koma.” “Na dauka Junaid sunanshi?” “Eh amma J nake ce mishi.” Wani kallo ya maka mata ta kauda kai tana cin magani. Bata jira me zai ce ba tace “Yaushe zamu je?” “Zamu je da Salim.” Wani kallo tayi mishi ranta ya ƙara ɓaci sai dai shi haka kawai baya son ya dinga sakata wahalar yawon nan sannan baya son ma ya dinga haduwa da Junaid. Dada ce ta sake dawowa tace “Zo mu shiga ciki kin ji waje akwai ɗan sanyi.” Zeey wucewa ciki tayi suka barshi a waje takaici duk ya isheshi, shigowa yayi ya kalli jakar turaren daya siyo mata sannan yasa hannu ya ɗauka, fitowa yayi yaga Dada tana waje da alama banɗaki ta shiga, Zeey na zaune tana daddanna waya, kusa da ita ya nufa ya miƙa mata gift bag ɗin, ɗagowa tayi ta kalleshi tace “Na menene?” “Ki amsa.” Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta amsa tana kallonshi, shagwaɓewa tayi tace “Allah fushi nake yi.” Wani irin yanayi ya shiga ya ɗan dake yace “Zazzaɓi?” Kai ta girgiza alamar a’a yace “Ciwon ciki?” Nan ma kai ta girgiza yace “Me ya sameki?” “Kawai.” Maimaita kalmar yayi yana kallonta, ta turo baki kaɗan tace “Kawai babu abinda ke mini daɗi ne.” Wani murmushi ne yazo mishi wanda shi kanshi bai san yayi ba, kallonshi tayi tace “Allah da gaske nake yi.” Kai ya ɗaga alamar eh sannan yace “Sai kije saurayinki yayi miki allura.” Yana faɗar haka ya fara tura keken, kallonshi tayi sannan ta buɗe jakar, flower ɗin data gani da turare ne yasa ta miƙe da sauri tace “Ka san mai bada rose flower dai yake nufi ko?” Kallonta yayi daidai ƙofar shiga ɗaki yace “Me yake nufi?” Kafaɗa ta ɗaga tace “Ka bani baka san ma’anarshi ba?” Kai ya kauda yace “Ni dai ban fassara ba.” Zai rufe ƙofar ɗakin tayi saurin cewa “Thank you!” Kallonta yayi yace “Nima.” “Ban ji ba Allah me kace?” Gyaran murya yayi tace “Yauwa me kake gani in muka nemi wasu masu ɗinkin suma kana musu zanen?” Kallonta yayi yace “Hmm idea ce mai kyau, zan…..” Da sauri ta katseshi tana cewa “Zan je na kai ɗinki kamar yadda muka yi wannan am sure zasu zo da kansu gwara suzo da kansu da ace mu muke nemansu.” Murmushi ya saki yana jin daɗin yadda komai take faɗarshi duk da wani sa’in ya kula bata iya magana ba amma a ƙalla abinda ke ranta take faɗa. Itama murmushi tayi tace “Ya Baqeer yaushe zamu duba school ɗin ɗinkin?” “Kada ki damu zan duba zan faɗa miki yadda ake ciki.” “Hmmm sai kayi mini alƙawarin in ka jini shiru zaka dinga kirana Allah bana son a shareni sai naga kamar ba’a damu dani ba.” A ranshi yace ke kuwa aka damu dake amma a fili murya kawai ya gyara. Dada ce ta shigo hakan yasa ya rufe ƙofar ɗakin, wayarshi ya tadda tana ƙara ya ɗauka da sauri ganin Umma ce, tambayarshi tayi jiki nan yake sanar da ita makarantar da yake son shiga, tayi farinciki sosai sai dai tunda makaranta mai tsada ce sannan kafin ya gama ya buɗe shago tasan zai ji jiki nan suka ɗan yi hira sannan ta kashe. *****   A fusace Badaru ya fara kiran sunan Kamalu kana ji kasan ranshi a ɓace yake, Abu ce ta fito da sauri har zaninta na neman kwancewa, tace “Malam me yayi?” Yatsa ya nuna mata yace “Wallahi in ba so kike yi nasa a kulle ɗanki ba kice kada ya kuskura ya ƙara zuwa mini shago ya ɗauki abu, don asara da rashin hankali satar ma a shagona zai yi? To daga ke har shi zan iya sallamaku ke kin san ba damuwa ta bane.” Jiki a sanyaye tace “Mallam anya kuwa shine zai ɗauka  duk fa fitinarshi baya halin ɓera kasan wannan Bashir ke yi.” Salati Jamila tasa tace “Bashir? Ahir ɗinki ko tsinke bai taɓa dauka ba tare da izinin mahaifinshi ba ehe.” Badaru cike da takaici yace “Ni dai banyi sa’ar ƴaƴa ba kaf cikinsu kowa da ɓacin ran da yake ƙunzuga mini, to wallahi ni daidai nake da kowani ɗan iska kun ji na faɗa muku.” Ɗakin Fatima ya shiga yana sababi, haushi ne ya ƙara rufeshi da yaga babu kujeru ya wuce ɗakinta ya kwanta akan gado. Jamila ce ta kalli Abu tace “Kin dai yi asara wallahi a gidan uban wa Bashir ya taɓa sata? Amma Kamalu fa? Sai dai kar ki faɗa amma kowa yasan yana ɗauke ɗauke.” Harararta Abu tayi ta shiga ciki tana masifa itama. Ita dai Fatima tana kallonshi don yanzu tunanin yadda zata tunkare shi ya bada filin Baqeer take yi, gani take in aka sayar da filin tabbas zai ishi Baqeer biyan kuɗin makaranta ya kuma buɗe shago sai dai taya zata amshi takardun fili a wurinun Badaru? Sannan inya tambayeta wace ƙaryar zata yi? ****** Zeey da tsantsar farin ciki ta shigo gida, parking tayi mai gadi ya taho da sauri ya miƙa mata leda yace “Hajiya gashi wai inji Sadaath wai ku hadu ko a menene din soyayya?” Wani banzan kallo ta yiwa ledar tace “Waye hakan?” Yace “Wannan dai yaron da yake zuwa nemanki.” “Ban san shi ba ban kuma san daga ina yake ba, ka ajiye in ya dawo ka maida mishi bana son hauka please.” Tana kaiwa nan tayi ciki, ɗakin Mummy tayi tana ganinta ta rungumeta ƙam tana cewa “Mummy na kalli.” Amsa tayi ta buɗe jakar, nan ta zaro ido tace “Inji wa?” Shigewa jikinta tayi tace “Wanda ya sakani jin duniyar babu daɗi kwana biyu.” Dariya tayi tace “Wai harda rose? ashe kun fara dating?” Kai ta girgiza tare da sauke ajiyar zuciya tace “Wannan clueless man ɗin kawai siya yayi ba da wata manufa ba, Mummy kina ganin so ne ke damuna ko?” Kuncinta ta ɗan jaa tace “ɗari bisa ɗari kawai dai tsorona mahaifinki, kinga Junaid yake son baki bana son ku samu matsala.” Baki ta taɓe tace “Nifa kin san babu mai takura mini nayi abinda bana so, sannan Daddy fa don siyasarshi yake son aurar dani ga Junaid kema kin sani.” Riƙo hanunta tayi tace “Kada ki damu kisa a ranki ni ina bayanki a koda yaushe.” Kai ta ɗaga cikin jin daɗi tace “Shi yasa nake sonki Mummy na.” “An dai girma ba’a san an girma ba.” Nabeela ta faɗa tana daga tsaye jikin ƙofar, Zeey ta ƙara ƙanƙameta tace “Ke dai Aunty Nabs ko kishi kike? Ko muje ki rungumi Inna hankalinki ya kwanta.” Maimakon ta bata amsa kawai juyawa tayi, abincin Kabir ta ɗauka tayi ɗakin shi, bata ko ƙwanƙwasa ba ta shiga, ya fito daga wanka kenan da towel a ƙasan shi sai kuma ƙarami yana goge kanshi, a zabure ya kalleta yasa hannu ya rufe ƙirjinshi yace “Meye hakan?” Juya baya tayi da sauri tace “Sorry KB ban kula ba.” Riga yayi sauri ya zura yace “To ba sai ki fita ba me kike yi anan?” Waigowa tayi ta tako har inda yake tana murmushi tace “Plz Kabir ka canza tunaninka, wallahi it's not a big deal.” Matsawa yayi ya juya mata baya, da sauri ta saƙalo hannunta ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi, gabanshi ne ya shiga faduwa don duk rigimar Kabiru baya harkar mata ba kuma ya shaye-shaye tace “Baka so na kasance kusa dakai?” Waigowa yayi yace “Nabeela please!” Yayi maganar yana janye jikinshi, idanunta ne ya cicciko tace “Allah ne ya ƙaddara mini nima ba ni nasa wa kaina ba.” “Please enough don Allah! Ke wai me yasa kike yin abu babu tunani? Don Allah kada ki sake yi mini haka, ya isheni haka nan bana son shirme please.” Yana kaiwa nan ya fita ma ya bar mata ɗakin, hawayenta ta share ta fito, Mummy ce ta ganta tana shiga ɗakinta ita ma ta shiga tace “Me nace miki? Wai uban me kike zuwa yi ɗakin Kabir?” Kai ta kawar tana ƙoƙarin zama tace “Abinci na kai mishi.” “Yaushe kika zama mai kai mishi abinci? Ha’a wallahi zaki tattara ki koma gida wannan shine last warning da zan miki tana kaiwa nan ta fito. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*         *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR*        *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA SHIDA* {46} Tun da suka rabu da Zainab yake tunanin ta yadda zai yi ya faɗaɗa sana'arshi, ba zai yiwu ace yana daga zaune komai sai tayi mishi ba. Ta dai yi mishi hanyar yadda zai kafa tubalin business ɗin shi amma dole yayi komai da hannunshi, dole yasan yadda zai yi ya nemi customers da kanshi kafin ya nemi tailoring school ya shiga don a yanzu yaji babu abinda yake da bukatar yi irin sana'ar ɗinki, dama can yana da passion for ɗinkin harkar zanen nan ce ta ɗauke mishi hankali da kuma Baba da ya hana mishi damar da zai koyi ɗinkin don a cewarshi babu abinda zai yi dashi bayan yana da sana'ar da tafi ɗinkin da yake so daraja da kawo kudi. Wayarshi ya ɗauka ya kira Salim yace idan ya samu dama yazo yana nemanshi, dole yana da buƙatar mataimaki a yanzu kuma da Salim kaɗai ya yarda shi yasa ma zai janyo shi suyi harkar tare. Kafin gari ya waye yayi duk wasu tsare-tsare na yadda zai faɗaɗa kasuwancin nashi akan takarda, zuwan Salim kawai yake jira ya nuna mishi abinda ya tsara zasu yi. Da wuri kuwa Salim yazo don tun da yaga kiran wayar Baqeer jiya bayan har ya kwanta yasan cewa abu mai muhimmanci yasa yake neman shi. Tare suka karya sai da suka gama sannan Baqeer ya ɗauko takardar nan ya nuna mishi. "Yanzu dai dole mu nemi masu sayen sketches ɗin idan anyi don ba zai yiwu muce yarinyar can ce zata samo mana masu saya ba, ta dai kafa mini tubalin kasuwancin and I really appreciate her for that amma ya kamata ace na karɓi komai ya dawo hannuna ba wai ina daga zaune komai sai anyi mini ba, tana da rayuwarta kaga bai kamata mu dogara da ita ba, sannan tana mace bai ma kamata ta dinga bin mutane saboda mu ba.” Salim ya jinjina kai yace "Wannan shawara ce mai kyau Baqeer its high time dama ka tashi ka gyara rayuwarka ka sani cewa babu mai taimakonka sai har idan kai ka taimaki kanka, babu wani dalili da don Allah ya jarabce ka da disability shikenan kace rayuwarka ta kare bayan yayi hakan ne don ya jarrabi imaninka. wannan tsarin da ka kawo mai kyau ne kuma In Sha Allah zan tuntubi wasu tailors dana sani akan sayen sketches din namu duk da dai ba directly zamu nemesu da su sayi kayanmu bane zamu ɓullo musu ta yadda Zainab ta yiwa wancan telan sai mu haɗa dasu Maryam idan zasu yi dinki a basu sketch din su kai daga haka idan har suna buqata su zasu kawo kansu da kansu ba sai mun bisu ba, sai kuma sabon page da zamu bude a ig da zamu dinga ɗora hotunan sketches din idan anyi sai kuma mu ƙirƙiri sunan da za'a sakawa business ɗin sai kuma muyi logo da zamu dinga ɗorawa a jikin sketches ɗin saboda masu satar fasaha". Haka dai suka zauna suka yi ta tsare-tsare har wani lokaci, basu tashi ba sai da Dada ta gabatar musu da abincin rana sannan suka yi akwala suka fita masallaci suka yi sallah sai da suka dawo ne suka ci abincin. Da Salim zai tafi ya karbi wasu daga cikin sketches ɗin akan zai kaiwa Maryam ta kaiwa telanta ya ɗinka yasan zai yi wuya shima bai biyosu ba kamar dai yadda wancan telan yayi. Akan haka suka rabu Baqeer ya koma ya kwanta yana jin wata irin nutsuwa na sauka a cikin zuciyarshi, dama can har da  rashin abun yi yasa damuwarshi ta yawaita amma yanzu ya samu nutsuwa tunda ya samu wani abun yin da ko bai sayarwa da wani ba zai iya yi da kanshi don a yanzu nema yake ƙara jin son koyon ɗinki fiye da shekarun baya da sha'awa kawai yake bashi. ***** Lokaci zuwa lokaci Zeey ke sakin murmuahi idan ta tuno da kyautar da Baqeer yayi mata, duk da turaren bai kai tsadar wanda take amfani dashi ba amma sosai taji daɗin kyautar kuma take jin son turaren cikin ranta bare idan ta tuna da rose flower ɗin daya haɗa mata dashi sai tace anya kuwa shima baya jin irin yadda take ji a kanshi a kanta? Idan ta tuna da cewar da yayi kuma wai taje wajen saurayinta yayi mata allura sai taji wata dariya ta kamata. "Is he jealous?" ta samu kanta da yiwa kanta wannan tambayar sai kuma tace kai a'a zai yi wuya ace kishi yake yi bayan ko damuwa bai yi da ita ba idan har ba ita ta nemeshi ba shi sam baya nemanta, gaskiya bata zaton yana jin irin abinda take ji a kanshi tunda gashi ita bata iya yin dogon fushi dashi ko tayi ma da kanta take bawa kanta haƙuri ta huce amma shi yana iya shareta idan har bata nemeshi ba baya iya nemanta. Bedside drawer dake gefenta ta janyo ta fito da rose flower ɗin ta shinshina tana lumshe ido tana jin wani shauƙi da farin ciki na kamata duk ta tuna wannan kyautar daga hannun Baqeer ta fito, wani ƙwayar mutum guda ɗaya da a yanzu take jin dukkanin wani farin cikinta ya ta'allaƙa ne da kasancewarshi cikin farin ciki da walwala, har mamakin yadda ta damu dashi da yawa har haka take yi bayan tasan a daa can babu wani shiri a tsakaninsu, koda yake tafi danganta rashin jituwar tasu ta wancan lokacin da yarinta. ***** Tun safe yau gidan babu kowa, Abu ta fice kasuwa sayen kayan magungunanta ita kuma Jamila ƴar ƙanwarta ce ta haihu yau suna don haka ta fita da sassafe. Ita kaɗai ce a gidan tana zaune tana hutawa bayan gama dukkan wasu ƴan hidindimunta, Baqeer ne ya faɗo a ranta tana jin daɗin yadda rayuwarshi ta fara samun saiti, duk wannan ƙuncin da rashin walwalar ya tafi duk kuwa da bata je ta ganshi ba har yau tun bayan barinshi gidan amma tasan daga yanayin yadda take jin muryarshi a waya al'amuranshi sun fara daidaita. Tunaninta ne ya ƙara komawa kan takardun filinshi da suke hannun Mallam da tasan ko sama da ƙasa zata haɗe ba bayarwa zai yi ba, idan tace zata tambayeshi ma tasan ranta ne kawai zai ɓaci ya kuma zo bai bata ba. Kallon ƙofar ɗakinshi tayi sai taga ɗakin a buɗe ga alama mantawa yayi ya fita bai rufe ba don ba sabonshi bane barin ƙofar a buɗe saboda rashin yarda. Wani tunani ne ya ɗarsu a cikin ranta ai kuwa zuruf ta miƙe ta nufi ɗakin, tura ƙofar tayi ta shiga ta janyo akwatin data san yana ajiye dukkanin wasu muhimman abubuwa nashi. Buɗe akwatin tayi ta fara fitar da kayan ciki tana duba duk wata takarda da hannunta zai kai akai, cikin sauri take komai don bata so wani ya dawo ya isketa a ɗakin so take yi tayi abinda zata yi ta fita ba tare da wani mahaluki ya ganta ba. Sai da ta kusa gama fitar da kayan cikin akwatin Allah ya bata sa'a taga takardar da take nema. Hannunta har rawa yake yi data warware takardar taga itace dai wadda take nema, haka ta ajiye ta a gefe sannan ta mayar da sauran kayan data fitar cikin akwatin har ta gama ta ɗauke ta mayar dashi inda yake kamar bata yi komai ba ta fita ta janyo ƙofar ta rufe kamar dai yadda ta ganta, tana shiga ɗakinta ta samu wuri tayi mata kyakkyawan ɓoyo sai ranar da zata je ganin Baqeer zata tafi mishi da ita ta bashi tasan idan ya sayar da filin ba ƙaramin taimako kuɗin zai yi mishi ba, sai sannan ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciyar da bata san tana riƙe da ita ba don fa har ta shiga ɗakin Badaru ta fito zuciyarta na bugawa don tsoro kasada kawai tayi ta shiga ɗakinshi ta ɗauko takardar nan amma tunda Allah yasa har tayi ta gama babu wanda ya ganta ta godewa Allah. Da yake yau ita ce da girki sai ta tashi ta cigaba da ƴan kujiba-kujibarta, ta ɗora sanwar abincin rana har ta gama babu wacce ta dawo. Har yaran ma yau babu wanda ya shigo, haka ta gama ta rarraba ta ajiyewa kowa nashi sannan ta gyara wurin, Fatima ba dai tsafta ba, duk cikin matan Mallam Badaru ita kaɗai ce bata barin wuri da datti ko tace sai tayi aikin yamma zata haɗa ta gyara, tana gama girki zaku samu ta gyare wurin tsaf kamar ba a nan aka yi aiki ba. Sai wuraren la'asar sannan Abu ta dawo niƙi-niƙi da buhun kayayyakin da take haɗa magunguna dasu, anan tsakar gidan ta dire buhun ta zauna tana sauke numfashi don sosai ta kwaso gajiya. Sannu da zuwa Fatima tayi mata, kai kawai ta iya ɗagawa sai faman haki take yi. Ita dai Fatima bata ƙara bi ta kanta ba sai ma cigaba tayi da aikin girkinta, dama can babu wani sakewa a tsakaninsu saboda haɗe mata kan da suka yi suka wareta a cikinsu shi yasa itama ta fita sabgarsu ta kama ƴaƴanta kawai take hidimarta dasu. Sai da ta gama hutawa sannan ta tashi ta shiga kitchen ɗin ta ɗauko kwanon abincinta na rana. Anan tsakar gidan ta zauna taci sai da ta ƙoshi tayi hani'an sannan ta kora da ruwa ta tashi tayi alwala ta shige ɗakinta don ko sallar azahar bata yi ba tana can tana bulayi wajen masu haɗa mata maganin mata. ***** Baqeer yayi nasarar ɗora sketches ɗin shi akan sabon page ɗin daya buɗe akan IG da facebook har ma da tiktok da twitter. Cikin hukuncin Allah cikin kwanaki biyu da ɗorawa akan shafukan nashi sai gashi yaci karo da saƙonnin mutane  masu son designs ɗin nashi, godiya yayi wa Allah domin kuwa ba iyawarshi bace ko dabararshi tasa mutane suka nuna sha'awarsu ga kayan nashi. Tuni ya fara neman makarantar koyon ɗinki mai kyau inda yake so ya fara cikin ƙanƙanin lokaci. Da taimakon Salim ya nemi makarantar har ya sayi form ya cike ya mayar, a yanzu matsalarahi kawai kuɗin makaranta da zai biya, yana da kuɗaɗe a account ɗin shi amma ba wasu masu yawa bane ga baya son ya faɗawa Umma tunda yasan ba shi gareta ba kawai zai ɗaga mata hankali ne, gaba ɗaya ya damu don bai san yadda zai yi ya samu kuɗin ba, dama ya saka rai ne da samun kuɗi saboda wasu da suka ce suna son zai yi musu designing wasu kaya amma su zasu bayar da description na kayan sai ya zana to ya basu address ɗin gidan Dada akan zasu zo tun kwanaki biyu da suka wuce har yanzu shiru kake ji kuma basu ƙara nemanshi ba. Shigowar Dada ce ta katse shi daga tunanin da yake yi tace "Tanimu yazo fa tun ɗazu kai yake jira.” Ajiyar zuciya ya sauke ya gunguro wheelchair ɗin tashi ya fito, anan tsakar gidan yaga Tanimun ya tambayeahi ko ya samo musu mai adaidata sahu? Yace "eh" Sallama yayi wa Dada suka fice daga gidan Tanimu yana tura shi. A ƙofar gida mai adaidaitan ya tsaya Baqeer ya faɗa mishi inda zai kai su ya kuwa yanka musu kuɗi, babu wani jaa Baqeer ya amince suka taimaka mishi ya shiga ciki sannan Tanimu ya naɗe wheelchair ɗin ya shiga suka tafi. Suna tafe Tanimu nayi mishi hira yawanci labarin garinsu ne da Innarshi sai ƙannenshi mata guda huɗu, mahaifin shi ya rasu shine wan uban ya kawo shi almajiranta wai a rage mishi nauyi. Jefi-jefi yake amsawa don hankalinshi ya kasu kashi biyu, ɗaya yana tunanin yadda zai yi mutane su san shi da sabuwar sana'arshi ɗayan kuma yana wajen tunanin Zeey da a ƴan kwanakin nan ta koyi shariya don ko gidan tazo sai tayi ta wani sha mishi ƙamshi tana basar dashi sosai hakan ke damunshi kawai dai yana dannewa ne kada ya nuna mata don bai cika son ya zura jiki ba kada yaje yayi nisan da zai kasa dawowa alhalin tafi ƙarfinshi ba iya samunta zai yi ba. Har cikin asibitin mai adaidaitan ya shigar dasu, da taimakon Tanimu ya zauna akan wheelchair, sai da ya sallami mai adaidaitan sannan suka shiga cikin asibitin. A reception ya faɗi number folder shi da kuma wurin wanda suka zo. "I know" kawai tace don tasan duk zuwan da suke yi Junaid ɗin suke gani. Sai da ta miƙa mishi folder sannan ta basu izinin shiga. Shi kuwa Junaid yana ganin folder Baqeer wani farin ciki ya lulluɓeshi nan ya fara gyara zaman rigarshi yana murmushi don ya kwana biyu bai ga Zeey ba kuma ko a waya ba sosai suke magana ba sai dai suna shiga sai yaga wani saurayin yaro ne ya rakoshi babu ma abokinshi da suka saba zuwa bare Zeey da ita yake sa ran fara gani. Fara'ar fuskarshi ce ta ɗan ragu yace "ina kuma Zeey ɗin yau baku zo da ita ba?" Wani malalacin murmushi Baqeer ya saki don haka yaji daɗi da Junaid ya zama disappointed da rashin ganin Zeey. Yaga murmushin da yayi sai kawai ya basar cikin ranshi yace "Wannan gurgun fa na lura har wani gani-gani yake yi mini akan Zeey sai dai kuma duk abun shi bai isa na bar mishi ita ba ko yana da lafiya kuwa bare a yadda yake da disability.” Haka dai aka yi session ɗin ranar zuciyar Junaid a cunkushe shi kuwa Baqeer sai daɗi yake ji, har da haka yasa ya hana Zeey yi mishi rakiya kamar yadda taso ta cigaba da kawo shi. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR*         *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TALATIN DA ARBA'IN DA BAKWAI* {47}   Suna fita Junaid ya cillar da file ɗin Baqeer ƙasa, yau yaci burin ganin Zeey da soyayyar da zasu ci amma sai gashi komai bai tafi daidai ba, secretary ɗinshi ce ta shigo tace “In kawo tea ɗin?” Rai a ɓace yace “Mai tea ɗin zaki kawo.” Yayi maganar tare da cigaba da aikinshi a computer cike da ɓacin rai, fitowa tayi tai shiru tana tunanin ina zata ga mai tea, da sauri ta fito bakin gate ta sanar da mai gadin rehab centre ɗin nasu akan ya kira mai shayin dake ƙasan layinsu tana tunanin ko yunwa yake ji yana son a bashi wani abun. Babu dadewa kuwa sai ga mai shayi nan tace ya biyota, office ɗin Junaid suka nufa, yana zaune yana rubuce-rubuce, izini ya bata ta shiga shi kuma yabi bayanta, wani kallo Junaid yayi mishi yace “Waye?” Hankali a kwance tace “Mai shayin ne don bansan me kake so ba.” “Shayin me kuma?” Ya tambaya cike da mamaki, ta ɗan kalli mutumin dake tsaye sannan tace “Ɗazu kace in kira mai shayin?” Wani kallo yayi mata yace “Nafisa ni kam hausa ce ba kya ganewa?” Da yake yoruba ce zaman Kano ne yasa ta iya hausa yasa tace “Ba haka kake nufi ba?” Kai kawai ya girgiza ya sallamesu ya cigaba da aikinshi. ******* Bello tare suka je Abuja da Asiya wurin visa ɗinshi, a jirgi suka je zasu yi a ranar su dawo, tunda suka je Abuja suke yawon restaurant bayan an gama application ɗin babu abinda take yi sai ɗaukan pictures tana ɗaurawa a IG ɗinta, suka sayi zobe iri daya suka saka sannan tayi caption a ƙasa wai ‘His wife!’ Nan fa kan Bello ya ƙara fasuwa don tabbas yana son Asiya, bayan sun dawo sun je gidan da zata zauna ƙaton apartment ne, don su mahaifiyarta da Habi da suka zo ganin gida sai baki suka sake, Habi tace “Asiya ina Bello yaga kuɗin biyan wannan ƙaton gidan?” Wani mugun kallo ta zabga mata tace “Bana jin wannan damuwarki ce ke dai kiji da naki ruɓaɓɓun samarin in kuma kishi kike yi to.” Dariya Habi tayi tace “Akan me zan yi kishi ni kuwa? Bayan banga abin kishin ba?” Fusata Asiya tayi tace “Ke in baki gani ba ni na gani.” Ran Habi ne ya ƙara ɓaci tace “Ko banza dai Baqeer yafi shi komai wallahi kuma dai a dinga tsoron Allah.” Tana kaiwa nan ta fito cike da ɓacin rai, ita ma Asiya takaicin Habi ne ya hanata binta, kwanan nan sam basa jituwa, to dole ne? Tace bata yi da Baqeer in ita ta damu taje ta aureshi mana. Nan tayi tsaki ta sanarwa iyayensu akan wai taje wani wurin, su kansu mamakin gidan ya ishesu Baban Asiya yace “Gaskiya ba zai iya gyara ɗaki uku ba shi ko biyu ma ba zai iya ba don haka ɗaki dayan nan da falo kawai zai gyara in su suna da hali nan gaba sayi amma ba zai kwashe komai yayi mata kayan ɗaki alhalin Habi na tasowa ita ma. Kalmar nan ta ƙonawa Asiya rai tace “To ita a kwashe ayi mata in yaso in auran Habi yazo ita zata sa Bello yayi mata.” Shi dai yace a’a babu ruwanshi da wannan gangancin, da haka suka fito ta rufe gidan ranta duk ya gama ɓaci don ita gaskiya kayan ɗakin da take so masu tsada ne tafi so a zo biki kowa ya koma da mamakinta a ranshi, dole tasa Bello yayi mata wani jeren amma ba za’a zubar mata da class ba haka kawai. ****** Baqeer kam har ya isa gida ƙasan ranshi wasai ko banza ya san Junaid yau yaji a salansa, haka yayi ta duba wayarshi amma babu message akan designs ɗin daya ɗaura, sake gyara profile dinshi yayi akan duk hotunan da ya saka basu zai bada ba sai dai duk da haka shiru har ya kwanta yayi bacci. Kallon rose ɗin dake hannunta Zee tayi ta saki murmushi tace “Muje muga Dad ɗinki?” Tayi maganar tana rufe fuska sai kuma ta saki huci tace “Me kike tunani?” Cikin ranta tace “Yanzu kamar ni one sided love nake yi?” Tasa mayafi a kanta tasa rose ɗin a cikin jakarta, kan gadonta ta kalla yau Nabeela bata shigo ba, ta fito tana kiran mai aiki akan ta gyara mata, Mummy ce ta fito daga ɗaki ita ma da alama fita zata yi don ta shirya cikin lace tsadadde, rungumeta Zee tayi Mummy ta shafi bayanta tace “Baby ni kam kwanan nan lafiya kike? Kullum sai dai na ganki da kayan mu na gida?” Murmushi tayi tace “Ya zanyi Mummy? Ni kaina ban san ya aka yi na koma haka ba.” Kuncinta taja tace “Yafi son kayan gida ne?” Cike da kunya ta shige jikin Mummy tace “Hmm duk da ban san yanzu ko ya canza ba.” Kallon mamaki tayi mata tace “Kin san shine da?” Laɓɓanta ta haɗe tace “Labari ya banu.” Tayi maganar tana juya kai, Mummy tace “Nima zan fita ne akwai abinda zan siyo Daddynki matar abokinshi ta haihu zan je barka.” Kai ta ɗaga alamar to sannan tace “Aunty Nabs fa?” “Wallahi ban sani ba, bari naje kafin nayi yamma.” Nan ta fito ita kuma ta leƙa Nabeela, tana kwance cikin bargo tana daddanna waya, Zeey ta buɗe tana kallonta tace “Aunty Nabs? Meke faruwa?” Kai ta girgiza alamar babu komai kafin tace “Kawai bana jin tashi ne yanzu.” Maimakon tace wani abu kawai ta maida ƙofar ta rufe ta fito ta shiga mota, a hanyar fita mai gadi ke bata labarin yaron nan ya sake dawowa ya bashi kayan amma yace ba zai amsa ba. Shiru tayi tana tunanin me zata yi mishi, don duk ranar da Daddy yasan ana biyota har gida lallai ranta ne zai ɓaci. “Yaushe yazo?” “Mai gadi ya ɗan kalli waje yace ai bai ma dade ba don in na fita a guje ma zan ganshi.” “Zaka tuna kayan da yasa?” Ya ɗan yi dariya yace “Shadda ce taji jiki daga ruwan sararin samaniya ta koma wata kalar daban.” Ta kula neman magana mai gadin yake ji dashi hakan yasa tace “Bani kayan.” Da sauri ya miƙa mata tasa a gefe sannan ta fita, da ɗan sauri take tafiya, a gefen wani saurayi tayi parking, kallon motar yaiy garin mamaki saura ƙiris ya faɗi ƙasa, da sauri ya riƙe gefen motar yana haɗiyar yawu yace “Roshni?” “Kana da sana’a ne?” Sumar kanshi ya fara shafawa yana ɗan gyara tsayuwa yace “Eh mai gidan mu nada shago.” “Hmm da alama, hope ba satowa kayi ba?” Tayi tambayar tana nuna mishi ledar, yayi ɗan yi yaƙe yace “Roshni ya kike haka?” Fuska ta tamke sosai sannan ta miƙa mishi. Kamalu kamar zai yi kuka yasa hannu ya amsa, sannan ta kalleshi tace “Sata dai sata ce sai a canza hali.” Tana kaiwa nan ta mayar da glass na motar tayi gaba, da kallo yabi bayan motar sam kasa motsi yayi, da ƙyar ya iya jan ƙafarshi zuwa gida, sam ya manta ledar dake hannunshi ya shiga. Abu ta leƙo waje don ta zubar da shara ta ganshi, sam bai ji maganar da take yi mishi ba yana tafe kamar ba shi ba, mamaki ne ya rufe shi tasa hannu ta riƙo ledar tana cewa “Kamalu lafiya kake ina magana ba ka ji?” Tayi maganar tana riƙe da ledar,  jan jikin da zai yi sai ledar ta yage, atamfa ce ta faɗo, ido ta zaro da sauri tace “Kamalu ina ka samo ta? Ba dai a shagon Babanka ka ɗauko ba?” Sai a lokacin ya kalleta ya kalli atamfar, Abu da sauri ta ɗauka ta ɓoye tayi ɗaki da ita ta samu wuri ta ɓoye a ƙasan gado, tabbas tun kafin ta janyo wa kanta da yaranta magana gwara ta ɓoye a inda ba za’a gani ba. ******* Yana zaune a ɗaki ya zuba wa wayarshi ido anya kuwa za’a dace? Kai ya girgiza da sauri ai komai haƙuri ake yi dashi ba zai yiwu abu kwana biyu ba jikinshi ya karaya, idanun ya ɗan runtse, Zee ya gano tana yi mishi smiling, shima murmushin yayi a bayyane nan ya ɗauko takarda ya fara zanen ɗinki, yana cikin yi yaji Dada tana lale lale da yar albarka. Kofar ya ɗan kalla yace “Da kullum sai tazo yanzu kuwa sai bayan kwana bibbiyu.” Bai motsa daga inda yake ba sai dai hankalinshi gaba ɗaya yana waje, mamaki ne ya kamashi ganin tafi minti goma da zuwa amma har yanzu ko Dada bata ƙwanƙwasa mishi ƙofa ba, gani yayi haƙurinshi ya ƙare yasa ya wawwaiga ɗakin, kwanon da yaci abinci ya ɗauko ya gunguro kekenshi ya fito “Dada kina ina?” Abinda ya fara cewa kenan. Ido suka haɗa da Zee dake zaune akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ta zuba mishi ido, gyaran murya yayi yace “Dada fa?” “Kawai?” Turo keken yayi zuwa cikin falon yana kallonta yace “Yaushe kika zo?” “Yaushe jikinka ya baka?” Kai ya kauda tasan tunda yayi haka ba zai amsa ba, tana murmushi tace “Faɗa mini Ya Baqeer in banzo ba kana damuwa?” Kallonta yayi nan da nan idanuwansu suka ɗan sarke da juna yana mamakin yadda mace bata kunyar magana haka. Kai ta karkatar tace “Baka yi?” Nan ma bai ce komai ba sai dai yanzu ya ɗan canza yanayin kallon da yake yi mata, neman juyawa yayi da sauri ta rike handle ɗin keken, hakan yasa ya tsaya, juyo da keken tayi inda zai ganta sosai tace “Baka bani labari ba kaje wurin J ɗin?” Kallon da yayi mata ne yasa ta gane me yake nufi tace “Ya plan ɗin school din?” Waya ya ɗauko ya buɗe mata page ɗinshi na IG mai ɗauke da sunan ‘MOHBAQ’ da yanda ya tallata abun, daɗi ne ya kamata da sauri tayi following ɗin shi, tace “Ko nasa kayan da aka ɗinka mini sai nayi pic daga wuya ne kasa sample?” Wani mugun kallo yayi mata, ita ma dama tayi ne don ta gwadashi, tace “Inyi?” Yanda yake mata kallo ne yasa ta shagwaɓe tace “Me kuma nayi? Ni sarkin laifi?” Kai ya kauda ranshi ya ƙara ɓaci wai tama san me take cewa kuwa? Langaɓar da kai tayi tace “In baka so ba gwara kace a’a ba da kayi shiru, menene a ciki?” Waigowa yayi yace “Na saki?” “Wai so nake yi ka sakani.” Jan keken ya fara ƙoƙarin yi tayi sauri ta ƙara riƙewa tace “Naji na haƙura, shikenan? Amma fushin na menene daga tambaya?” Shima tambayar kanshi yayi fushin na menene? Anya Baqeer? Yayi soyayya da Asiya amma bai taɓa jin abinda yake ji akan Zeey ba bayan ya daɗe da ita ya kuma so ta kowa ya sani. Dada ce ta shigo falon hakan yasa ya juya, Zeey da kallo ta bishi tana murmushi. ****** Umma ce a ɗaki ta kalli takardun filin, zata kira Maryam ko Hadiza ta basu takardun su kaiwa Baqeer a samu a saidashi ya fara harkar sana’ar, ai hakkinshi ne tunda aiki yayi a masarautar garin Gombe aka basu kuɗi masu kauri wanda Badaru ya sayi mota dashi, ya ƙara faɗaɗa shagonshi shine da tayi mishi magana ya saya mishi fili 50 by 50, ta tabbatar filin darajarshi ta ƙaru, tasan zai isheshi yayi wani abun dashi, tunani ne yazo mata ai ko itace tace zata je wurin Dada ba zai kawo komai ba tunda bai san a inda Baqeer ɗin yake ba balle ya kawo tana can. Da wannan shawarar taji hankalinta ya kwanta, turaren wuta ta fito ta hura ta koma ɗaki tana tunanin Allah yasa har sai ta kaiwa Baqeer an saida filin sannan hankalinshi zai kai wurin. ***** Nabeela ganin babu kowa a gidan sai ita yasa ta fito ta wuce ɗakin Kabir, shima baya nan kwanciya tayi akan gadon ta jaa bargonshi tana shinshinar ƙamshin shi har bacci ya ɗauketa, sanye take daga ita sai rigar bacci shara-shara. Kabir ne ya shigo ɗaukan abu da mamaki ya hango mutum akan gadonshi, ƙarasawa yayi ya ɗan ɗaga blanket ɗin. A tsorace yake kallonta, me take yi anan? Nan da nan hankalinshi ya tashi, juyawa yaje zai yi ta riƙo hannunshi tace “KB na!” Zare hanunshi yayi yace “Meye hakan kike yi? A ɗakina? Baki da hankali ne?” Tashi tayi hakan yasa jikinta ya bayyana cikin kayan baccin, ta dawo gabanshi a tsorace yace “Me kike yi hakan?” “Kabir plz ka maidani halalinka, I really need you.” Fita yayi daga ɗakin ranshi a matukar ɓace, fitowa tayi idanuwanta sunyi jaa suna neman zubar da kwalla. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 “ *Ayusher Ce*        *Da* * *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR*        *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA TAKWAS* {48} Fitowa tayi daga ɗakin tana share hawaye suka kusan yin karo ita da Mummy sai sannan ta dawo cikin nutsuwarta sam bata san Mumy ta dawo ba. Ganin Mummy tsaye tana yi mata wani irin kallo yasa gabanta faɗuwa sai dai ta dake ta ƙaƙaro murmushi tace "Mummy har kin dawo?" Wata uwar harara Mummy ta doka mata tace "Uban me kika je yi ɗakin Kabir a haka da wannan shigar? Wallahi Nabila ki kiyayeni, zaki tattara ki bar min gidana ki koma wajen Inna don ba zaki ɗaukar min magana ina zaman lafiya ba, ai dai kin san nace miki a'a amma da yake ba jin maganata kike yi ba shine kullum sai kin kai ƙafa ɗakinshi ko?” Cikin jin haushin Mummyn tace "To ni me nayi? Komai nayi sai kin yi min faɗa kamar ba ƴar uwarki ba?” Da mamaki Mummy take kallonta tace "Ni kike yiwa magana a haka Nabila sai kace wata sa'arki, to wallahi tafiya zaki yi bazan iya ba, haka kurum ba zaki janyo min magana ba tunda ke baki san abinda ya kamata ba.” Fuuu Nabila ta wuceta a tsaye a wurin tana faɗa ta shige ɗakinta, da kallo Mummy ta bita tana mamakin wai ita yau Nabila ke yiwa rashin kunya haka kamar wata sa'arta akan ta faɗa mata gaskiya. Ƙwafa tayi ta wuce ɗakinta tana jaddada dole ne ma Nabila tazo ta bar mata gidanta idan ba haka ba zata ɓallo musu ruwa tayi musu sanadin abun kunyar da basu isa su warware ba. ***** Da sassafe ta shirya yau gidan Dada zata je ta yini, da ƙyar Mallam Badaru ya barta ma taje don da cewa yayi me zata je tayi? Sai da tace mishi "Dada ce fa nace maka zan je na gani mahifiyata ba wata can daban ba" sannan ya amince. A cikin kuɗin da Baqeer ya aiko mata ne tayi cefane tayi musu soyayyiyar miya da zata jima bata lalace ba, sauran abinda ya rage kuma ta saya musu kayan shayi dasu sabulun wanka dana wanki sai omon wanke-wanke, dama ta saba yiwa Dada irin wannan sayayyar miyar ta kai mata duk lokacin da zata je ta duba ta don ma ba kasafai Badaru ya cika barinta taje ba sai kuma ya sameta ba mai yawan son tashin hankali bace don haka take haƙuri duk da ba daɗin hakan take ji ba ace suna gari ɗaya da mahaifiyarta amma sai ta ɗauki wani tsawon lokaci kafin taje ta gaisheta. Sai data duba jakarta ta tabbatar takardar filin na nan a inda ta ajiyeta kafin ta ɗauki ledar kayanta ta fice. Sallama tayi wa su Abu da Jamila wanda ke ta gulma ganin gana soyayyar miya, da sun san Baqeer ke bata kuɗi yanzu kuwa sun tabbatar kuɗin kujerunta tasa a gaba take miya, ita dai ta fita tana jin ɗokin son sake saka tilon ɗanta a idanunta bayan wani lokaci da suka ɗauka ba suga juna ba sai dai suyi magana ta waya abinda bai taɓa faruwa ba kenan a tarihin rayuwarsu tun daga haihuwarshi har zuwa girmanshi sai fa yanzu da tijarar Mallam Badaru ta raba su. Ƴar tafiya kaɗan tayi ta samu adaidata sahun daya ɗauketa har ƙofar gidan Dada. Da sallama ta shiga gidan fuskarta ƙunshe da fara'a ta tsantsar farin cikin daya kasa ɓoyuwa. Daga cikin ɗaki Dada tace "Muryar wa nake ji kamar ta Fatima?" "Nice Dada" ta amsa tana nufar ƙofar ɗakin. Cikin barci yaji kamar muryar Ummanshi suna gaisawa da Dada, ai kuwa zumbur yayi ya miƙe zaune yana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyarshi. Wheelchair ɗin shi ya janyo ya daddafa ya hau kai ya zauna yana garata, wai kuma sai da yaje baƙin ƙofar ɗakinshi sai yaji ba zai iya fita ba, haka nan yaji tausayin kansu shi da Umman ya kamashi, yasan wannan tsawon lokacin da suka ɗauka a mabanbanta wuri ba ƙaramin dauriya da haƙuri tayi ba. Kasa fita yayi ya tsaya daga nan yana jin sautin muryar Umman da yayi kewa iya kewa. Ita kuwa Umma suna gaisawa da Dada hankalinta na wajen ɗanta kara da kawaici ne kawai yasa ta kasa tambayar inda yake sai kallon ƙofa take yi a kaikaice tana zuba idon ganin ta inda zai ɓullo. "Yana ɗaki watakila bacci yake yi tunda kika ga bai fito ba" Dada tace mata don tana lura da yadda take satar kallon hanya tasan Baqeer idanunta ke kwaɗayin gani. Kunya ce ta kama Umma ta sunkuyar da kanta ƙasa ganin Dada har ta fahimci ɗokin son ganin Baqeer da take yi. Sai ta kasa cewa komai sai da Dada tace "Ki shiga ki ganshi mana ai ya samu sauƙi fiye da lokacin da ya dawo nan, ko daga walwalar da ya samu ma bare da yarinyar nan Zainabu ta haɗashi da likitan ƙashi yana zuwa can asibitinsu yana dubashi.” Kallon Dada Umma tayi tace "Zainab ɗin na yawan zuwa nan ne?" Tace "Ai bata kwana biyu bata zo ba yarinyar kirki mai yawan barkwanci da sanin darajar mutane, da badan ita ba Baqeer da har yanzu banajin zai dawo daidai.” Jinjina kai Umma tayi har yanzu ta kasa daina mamakin jin wai Zainab ce take yawan kawo musu ziyara har ma da taimakon da ta yiwa Baqeer bayan tasan ƴar tsamar dake tsakaninsu wanda abu har iyaye ya haɗa, wanda tashin hankalin da akai a shekarun baya, sai dai ganin yanzu sun girma kila shi yasa suka zubar da duk wasu abubuwa na yarinta. Tashi tayi ta shiga ɗakin nashi sai ta ganshi daga bakin ƙofa, haka nan taji wani irin rauni ya saukar mata kawai sai ta fara hawaye, tana son Baqeer a cikin ƴaƴanta tana kuma tausaya mishi saboda dattijon yaro ne da bai ɗauki rayuwa da girma ba, mai mayar da damuwar wasu tashi shi yasa ya zame musu bango abun jinginarsu daga ita har ƴan uwanshi, ya ɗauki dukkanin wasu damuwoyin su ya mayar dasu nashi, bai taɓa bari sun yi kukan rashin wani abu ba bakin gwargwado yana kyautata musu. Tsugunnawa tayi a gabanshi ta riƙo hannayenshi a cikin nata tace "Ya jikin naka?" Ɗaga mata kanshi yayi alamun amsawa don haka nan yaji bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa furta ko kalma ɗaya. Cikin rawar murya tace "Ina can ina ta fama da kewarka kai kana nan kana cigaba da rayuwarka cikin kwanciyar hankali.” Hannu yasa ya share mata hawayen dake ta faman zuba daga idanunta sun kasa tsayawa tunda ta ganshi. "Nima ina cikin kewarki Umma nayi kukan rashinki a kusa dani sau babu adadi, sai dai nasan in na cigaba da zama cikin damuwa sai kin fini damuwa.” Tausayinshi ne ya ƙara kamata ta ɗan yi murmushi na ban tausayi. Zama tayi suna hirar sai tambayarta lafiyarta yake yi tana ce mishi tana nan ƙalau sai dai ya kasa yarda don sai yaga gaba ɗaya ta canja mishi, sai yaga kamar walwalarta ta ragu shi idan ba idon shi nema ke faɗa mishi ƙarya ba da sai yace har ramewa yaga tayi. Sun jima a ɗakin kafin ta turashi su koma wajen Dada da bata katse musu hira ba ta ƙyalesu su ga na sosai don tasan sun yi kewar juna. Yau yini suka yi cikin farin ciki da annashuwa bare da Umma ta dafa musu shinkafa suka ci da miyar data kawo musu sai Baqeer yaji kamar lokutan baya da suke tare a gidansu da sam baya iya cin girkin kowa idan ba na Ummanshi ba shi yasa ko ba ita bace da girki kullum ne sai ta girka mishi nashi abincin daban don a cewarshi su Abu basu iya girki ba baya iya sakewa yaci abinci ya ƙoshi idan su suka dafa. Takan daɗe bata je taga Dada ba amma duk ranar da taje bata barin gidan sai tayi mata kwalema ta share kowane lungu da saƙo na gidan ta goge na gogewa ta wanke na wankewa, kyakkyawan gyara take yi mata irin wanda za'a kwana biyu gidan bai haɗa datti ba. Sai data gama duka waɗannan aikace-aikacen don har wankin kayan sakawar Dada sai da tayi sannan ta fito da takardar filin ta miƙawa Baqeer. Karɓa yayi yace "Takardar miye wannan ɗin Umma?" "Kai dai ka buɗe ka gani mana" tace mishi. Sai da ya buɗe sai yaga takardar filinshi ce dake wajen Baba. Ɗan yamutsa fuska yayi yana kallonta yace "Ki mayar mishi da ita Umma don bana buƙata.” Kallonshi take yi itama ta kuwa ɓata rai tace "Bazan mayar mishi ba domin kuwa fili dai naka ne sunanka ne a rubuce a jikin takardar ba nashi ba, sannan da kuɗin ka aka saya bashi ya saya maka ba to na miye kana da buƙatar kuɗin don ka gina rayuwarka sai kace baza kayi amfani da kadararka ba bayan amfanin ajiye kadarar kenan.”Juyawa tayi ta kalli Dada sai tace "Takardar filin shi ce daya saya na kawo mishi a saka a kasuwa idan Allah yasa aka dace da samun masu saye ba sai yayi amfani da kuɗin ya biya kuɗin makarantar koyon ɗinkin da yake son shiga ba ga sayen keken ɗinkin tunda yace dole sai dai yayi amfani da mai aiki da wuta wanda baya buƙatar sai ya takura ƙafafunshi wajen taka keken da dai sauran ƴan matsaltsalun daka suka mishi.” Dada tace "Haka ne,” tana jijjiga kai "Ai daɗin sayen kadarar a ajiye kenan dama.” Yana jin su sai dai ya kasa yin musu dasu duk kuwa da yadda baya son karɓar filin, shi duk wani abu daya danganci Baba ma ba son shi yake yi ba shi yasa bai yi wani farin ciki da ganin takardar filin nashi ba dashi a mance ma ya manta yana da wani fili don tun lokacin da aka saya takardun na wurin Baba ba kuma su ƙara yin maganar fiin dashi ba. Dada ya miƙawa takardar filin yace ta ajiye a wurinta don shi ko ganinta ma baya son yi, haka Umma ta ƙara gyara gidan tasa turaren wuta. Sai can da yamma sannan tayi musu sallama zata tafi, sai yaji sam baya son rabuwa da ita da da hali da ya bita sai dai yasan a yanzu zaman gidan baba yafi ƙarfinshi tunda dai shi da kanshi ya kore shi yace ya bar mishi gidanshi saboda ƙaddarar rayuwa ta afko mishi, abinda yafi yi mishi ciwo kenan a duk abinda ya sameshi yadda Baba ya juya mishi baya tamkar bai taɓa sanin shi ba kawai saboda ya gama yi mishi amfani, har da wannan yasa ya ƙuduri aniyar in har ya cigaba da rayuwa da izinin Allah sai Baba yaga yadda Allah zai yi dashi, akanshi zai san cewa nakasa ba kasawa bace, sai yayi alfahari da abinda zai zama don ba zai taɓa zama komai sai anyi mishi ba alhalin Allah ya barshi da ranshi da lafiyar da zai iya tashi ya nemi na kanshi. Har bakin titi ya rakata sai da ya tare mata adaidata sahu ta shiga har ma ya biya kuɗin a cikin sauran kuɗaɗen zanen shi da suka yi ragowa sannan suka yi sallama, bai bar wurin ba sai da adaidaitan tayi mishi nisa ya daina ganinta sannan ya sauke ajiyar zuciya ya koma gida yana jin kewar Umman ta sake kamashi, fatanshi dai Allah yayi mishi arziƙin da zai ɗauke Umma ya mayar da ita kusa dashi don yana da burin rabata da zaman gidansu wanda bata tsintar komai a ciki sai kayan ɓacin rai. ***** Da Asiya ta kafa naci sai da Bello ya ware wasu kuɗi daga cikin kuɗaɗen daya ajiye a bankin saboda sayen fili ya fara gini tunda gashi Allah yasa zai fara ajiye iyali dole ne yayi planning yadda rayuwarsu zata kasance. A cikin kuɗin ne ya cire wani abu yayi mata sauran kayan gadon da iyayenta suka kasa yi mata saboda takurar da tayi mishi ta hanashi sakat wayar safe daban ta yamma daban ta dare daban duk dai akan ya daure ya sayi sauran kayan ɗakin don kamarsu bai dace ace an shigo gidansu aga ɗaki ɗaya kawai suka iya shiryawa ba. To da yake shima ɗan ƙaryar ne irinta da tayi mishi bayani sai yaga fa eh lallai haka ne shine ya cire kuɗin aka sayi sauran kayan gadon da za'a saka a ɗakunan biyu da suka rage, haka shi ya sayi gas cooker dasu fridge da freezer har da washing machine aka zuba a gidan. Ai kuwa kan Asiya sai ya ƙara girma ta dinga iyayi tana fi'ili ita a dole ta kerewa sa'a ta shiga sahun manya a yanzu. Haka zata kalli Habi ƙanwarta ta sheƙe da dariya tace "ke kam ina ga ai sai dai kiyi amfani da gawayi don banga alamar wanda kike kulawa zai iya yi miki hidimar arziƙi irin wannan ba.” Ita dai Habi ko kulata ma bata yi don tace ɓata lokaci ne tsayawa ta biyewa Asiyar suna rigima akan abinda tasan ba lallai ne ya ɗore ba. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 “ Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR*        *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ARBA'IN DA TARA* {49} Tunda Umma ta tafi yake zaune yana lissafi, wayarshi ya janyo jiki a sanyaye tunda har yanzu babu wanda yayi mishi magana, ga mutumin daya amshi zanen nan ya biyashi har yanzu bai sake yi mishi magana ba shima. Saƙo ya gani ta shigo ta direct message ɗinshi buɗe wa yayi don yana da tabbacin Salim ne. Business account ɗin daya gani ne yasa ya buɗe cike da mamaki don daga yanayin dp ɗin ba masu ɗinki bane, yaso shiga cikin profile ɗin su yaga me suke yi sai dai idanuwanshi ne suka gane mishi saƙo ana tambayarshi akan sketch na ɗinki, iska ya furzar sannan ya danna reply akan guda nawa suke so, waya ce ta shigo ta IG ɗin ganin daga su ne yasa ya ɗauka, namiji ne mai maganar nan ya sanar dashi a Abuja suke amma suna da branch anan Kano, zasu turo representative ɗin su yaga inda yake saboda gudun kada su sayi abinda ya watsa gari dole su tabbatar ba zai cucesu ba sannan ba zai bawa wasu zanen da yayi musu ba, don haka suke son sai yayi signing contract sannan su dinga siya. Kai tsaye yace babu matsala shima baya son yin business da mutanen da bai sani ba, mutumin yace “Sai dai mu muna neman ragi gaskiya akan zamu dinga siyan ko wane ɗaya akan naira dubu talatin, saboda yanzu abubuwan ba sauƙi garesu ba, suna kuma son su dinga fito da styles kala-kala wanda zai ƙara inganta business ɗin su.” Baqeer yayi ɗan jim kafin yace “No, gaskiya sketching is not that easy sannan ku idan na sai da muku ya zama naku ya tashi daga nawa.” “Mun sani amma muna so kasan mu business ɗin gaske muke son yi da kai, muna da branches a kusan garuruwa goma, sannan mu ba ƙananun mutane bane contract zamu yi duk wata zaka dinga bamu kuma duk wata zamu dinga biyanka, in muka yi requesting sketch 20 a watan nan zamu biya ka naira dubu ɗari shida.” “In kuma baku yi ba fa?” Baqeer yayi tambayar jin ana neman dauke mishi hankali da abinda ya kamata ya sani, “Well in har bamu yi ba still zamu baka dubu hamsin sai mu ƙara a cikin contracts, ka duba business account ɗin da nayi maka magana dashi.” Nan Baqeer ya buɗe ganin yadda suke da mabiya sosai da yadda abinsu ya bunƙasa. Ya sani sarai babu yadda zai yi tunda bai iya yanka da ɗinki da kanshi ba, zai amince dasu sai dai baya da tabbas akan zai dogara dasu. “Okay, sanda zaku turo wani sai muyi arranging inda zamu haɗu.” Nan suka yi sallama ya kashe, shiru Baqeer yayi yana bin account ɗin su da kallo sam zuciyarshi bata gama yarda dasu ba kawai dai babu yadda zai yi shi yasa ya amince da hakan. Har zai kifa wayar sai kuma ya dubo sunan Zainab, so yake yi yaji ya take sai dai bai san me zai ce ba, shiru yayi yana tunani, tunowa yayi da ƙofarin da tayi mishi ne yasa yayi mata text, “All good?” Ya tura tare da kallon wayar yana tunanin zai ga reply sai dai shiru babu komai. **** Zainab ce ta kalli Nabeela tace “Haka Mummy tace?” Nabeela dake share ƙwalla ta ɗaga kai alamar to, da sauri ta fita daga ɗakin ta nufi falo. Mummy na zaune suna hira da Daddy ta zauna a gefen ta tace “Mummy don Allah ki yiwa Aunty Nabs magana tace ke kika ce ta tafi?” Fuska sosai ta tamke tace “Auta ƙyaleta gwara taje ta zauna kusa da Inna tana buƙatar taimako.” Daddy ne ya kalleta yace “In ba don Nabeela ba a gidan nan kina tunanin komai zai tafi daidai? Kika jure wannan sai Nabeela ce kullum ke laifi?” Zeey ce ta turo baki tace “Ni dai kullum nice mai hali mara kyau.” “Yanzu amsa min ɗin da kika yi a haka shima daidai ne kenan? Nabeela kuwa ko da wasa baza tayi magana haka ba ko da bare ne ya mata magana kuwa bare.” Mummy ce tayi saurin cewa “Don Allah ka bari Senate, ita dai bata isa tayi magana ba sai an ce maganar ma bata yi daidai ba?” Kai ya kawar ya ɗauki jarida bai tanka musu ba, yana murmushi don shi kam yasan lamarinsu sai a hankali sam Mummy bata taɓa ganin laifin Zeey, kafaɗarshi ta dafa tace “Ranka ya daɗe ba dai fushi kayi ba? Kai ya girgiza yana kallon Zeey yace “Sai kuyi tayi, sannan a halayen ta kuma bata tunanin bin umarnina ta auri namijin da nasan zai jure halayyarta.” Tana jin haka tayi maza ta tashi tace “Daddy na manta ina da abun yi a ɗaki.” Ta fara tafiya da sauri sai data kai ƙofar fita daga falon ta waigo tace “Mummy sorry amma bazan barta ta koma ba gaskiya, Daddy sai da safe.” Ta waiga da sauri, Kabir ta gani a tsaye da alama ma tsayawa yayi don yaji me suke cewa, wani banzan kallo yayi mata yace “Akan me bazata koma ba? Ko ke ce kika haifeta?” “Kaga don Allah ka bari, kai wai a duniya ba zamu zauna lafiya ba? Neman faɗa har da wanda bai shafeka ba?” Ranshi ne ya ɓaci ganin shi Nabeela ke takurawa a gidan nan don yanzu saboda ita zaman gidan ma ba sosai yake san yin shi ba yayi ƙwafa sannan ya juya, kallonshi tayi ta harari bayanshi sannan ta bishi a baya tana cewa “Yaya K please kasan masu ɗinki irin professionals ɗin nan na mata?” Cak ya tsaya sannan ya kalleta yace “Ɗinki ina wanda yake yi miki na wurin Mummy?” Ta ɗan yi kif da ido sannan tace “Ba ni zanyi ba sannan bata son na Mummy wani take son gwadawa.” Jim ya ɗanyi sannan yace “Akwai amma sai na yiwa Najib……..” ai kafin ma ya ƙarasa tace “No, kada ka damu nama tuna.” Ta shiga ɗaki tana cewa “Rabani da abokinka yanzu in Baqeer ya sani am sure..” sai kuma tayi shiru kafin tayi ajiyar zuciya a fili tace “Always getting ahead of yourself, a wani waje Baqeer ya ajiyeki?” Kan gado ta faɗa ta ɗauko wayarta, nan da nan ta zaro ido tana ganin tambayar da yayi mata, bata san sanda ta saki wani irin ƙara ba tana bubbuga ƙafa kai kace wani kyauta aka bata. Ta fito daga ɗakin da gudu ta nufi ɗakin Nabeela wacce ke zaune ta saka akwati a gaba, janye akwatin tayi ta riƙo hannunta tace “Aunty Nabs yau shi ya fara nemana.” Da mamaki take kallonta tace “Wa?” Kai ta girgiza tana daidaita nutsuwarta tace “Mu bar wannan maganar, don Allah me yake nufi idan namiji ya miki text yace All good?” Ɗan yatsuna fuska Nabeela tayi tace “All good? Har wani kalma ne mai ma’ana daban?” Saketa tayi tace “Share baza ki gane ba,” tayi maganar tana fita, kan gado ta faɗa tayi rub da ciki sannan ta kira Baqeer, a lokacin shi kam har ya gaji da jin haushin kanshi da saƙon daya tura yana ganin gashi nan ya janyowa kanshi rashin reply ai, wanda a ganinshi bada kanshi ya gama yi. Ɗauka yayi ba tare da yace komai ba, ita ma bata ce komai ba har kusan sakan bakwai sannan yayi ɗan gyaran murya ita ma gyaran muryar tayi suka sake ɗan shiru kafin ta sake gyaran murya, “Mura kike yi?” Ya tambaya ganin abun nata ba irin nashi bane.” “Matsalar a zauna kusa da masu mura kenan sai su sa maka before you know it.” “Wa ke mura?” Ta dan rage murya tace “Kai mana Ya Baqeer ka manta kai ka fara gyaran murya?” “Don nayi gyaran murya sai akace kuma mura nake yi?” Ta ɗan kwantar da kanta akan pillow tace “Kuma fa haka ne to ba mura nake yi ba ciwon GM nake.” Yanayinshi ne ya canza zuwa na damuwa yace “GM? Me kenan?” Ta dan yi jim sannan tace “G for gyara, M for murya?” Duk yadda Baqeer yaso ya daure kasawa yayi kawai yaji dariya tazo mishi, wani irin shauƙi ne ya dinga ratsa sassan jikinta babu shakka ƙaunar da take yiwa Baqeer ta riga ta gama bin jini da jijiyarta. Yatsa yasa ya sosa kunnenshi ya daidaita kanshi sannan yace “Umma tazo yau.” Tace “Haba? Kai masha Allah kace yau cikin farin ciki kake.” Yace “Uhmm!” Ta dan ja bargo wani tunani na shiga ranta tace “In tambayeka?” Yace “Eh!” Ta ɗan sake yin shiru kafin tace “Ka yarda dani?” Da mamakin kalamanta yace “Kamar ya?” Kai ta girgiza tace “Kawai tambaya ce.” Shiru yayi bai amsa ba, jin haka yasa tace “Ina Dada ta?” “Ta kwanta,” ya faɗa yana kallon wayarshi, so yake ya sanar da ita zancen contracts amma yana tunani gwara ya bari yayi signing tukunna don ya kula tafi kowa farin ciki in taga abun alkairi ya sameshi to gwara ya jinkirta sanar da ita har sai ya tabbatar da contracts ɗin . Sun ɗan yi shiru kafin yace “Yace sai da safe.” Har zai kashe tayi saurin cewa “Ya Baqeer?” Tsayawa yayi sai dai yanda ta kira shi yasa yaji dim ta ɗan rage murya sosai, cikin wani yanayi tace “Baka ji amsar tambayar da kayi mini ba.” Kasa amsata yayi saboda yanayin daya shiga jin yadda tayi maganar, nan ta cigaba “All good, sannan thank you for asking.” Wani abu ne ya ɗan tokareshi da sauri ya kashe wayar yana mamakin abinda ke faruwa dashi, Zeey kuwa iska ta furzar da karfi tana shafa sumar kanta. **** Umma tana dawowa ta tarar da Jamila da Abu a zaune yau yan haɗin kan nasu ya tashi dan suna zaune tare suna hira, tasa key zata buɗe ƙofar ɗakinta sai taji ƙofar a buɗe, da mamaki ta kallesu gani tayi sun kawar da kai, ta ciki aka buɗe ƙofar da ƙarfi wanda ya sata tsorata kaɗan ta ɗan yi baya. Badaru ne ya banƙare kofar ya fito yana kallonta sheƙeƙe yace “Eh dama ni nasan ba mutunci ne dake ba kwanan nan, yanzu ko kunya da imani baki ji ba kika yi miya kika juye tas kika kaiwa tsohuwa ni da yake baki ɗauke ni da daraja ba baki ajiye mini ba? Bayan ke kin san Jamila ba lafiya ne da ita ba bazata iya girki yau ba?” Mamakin kalamanshi ne suka rufeta, ba yau ta saba yin miyar nan ba menene suke neman maida abun wani zance daban? Sannan yaushe Jamila ta fara ciwo? Kafin ta gama tunani sai ji tayi Abu na cewa “Sannu Jamila, Allah dai ya baki lafiya.” Mallam kayi hakuri ni wallahi naso yin girki  kuɗi ne sam babu a hannuna.” Kallonta ya sake yi yace “Allah wadan naka ya lalace wannan mugun halin naki shi yaranki suke kwaikwaya shi yasa rayuwar auransu ba daɗi kuma wallahi ni da siyan kujeru ke da saidawa sannan ke da cinye kuɗin.” Rai a ɓace ya wuceta ya shiga ɓangaren Jamila, Fatima ciki kawai tayi don ita ta ɗauka ma zancen fili zai yi to in dai wannan ne ita kam ko a jikinta yaje can su ƙarata, da can da take miyar ai bai taɓa sa ido ba sai yanzu, ita fa duk wani abinshi yanzu ya daina hata haushi. **** Yau Dada haka kawai ta tashi da ciwon ƙafa da take fama dashi da kuma ciwon hakarkari wanda yawanci ciwonta ne tana fama dasu dama lokaci-lokaci balle in sanyi yazo to fa dama sai tayi su kamar sau biyu ko uku, tun dare ta fara ji tasha magani amma bai tafi ba, kwance tayi a ɗaki sai dai hankalinta ne ya kai kan Baqeer tana ganin ya kamata fa yaci abinci, haka ta miƙe da ƙyar ta fito ta nufi ɗakin shi yana zaune yana zana riga da skirt na mace ɗinkin zuwa mishi yayi bayan yayi sallar asuba to baya son ya gudu daga kanshi ne yasa ya ɗauko don ya zana, shigowa tayi sai dai jiri ta fara ji yana neman kamata, a rikice ya taimaka mata ta zauna yana tambayar meke faruwa, Dada kam ido kawai take lumshewa da alama wannan karon bayan ciwukanta har da wani yanayi take ji a zuciyarta. Baqeer idanunshi ne ya cicciko da yaga ya kasa bata wani gudunmawa daya kamata, asibiti ya kamata ayi da ita amma taya zai iya? Cikin sauri ya kira Salim sai dai wayarshi ma a kashe take, ya sake kira nan ma haka, ganin yadda Dada ke sake bin katifa yasa hankalinshi ƙara tashi yanzu in ya kira Umma ya tabbatar ba lallai ma Baba ya barta tazo ba, number Zeey ya kira sam ba tare da wani dogon nazari ba. Zeey kuwa a lokacin Mummy bata daɗe da barinta a ɗaki tana bacci ba don akwai inda zasu je amma tace bacci take yi, wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka cikin bacci tana neman maida ita silent don yanzu ma tsautsayi ne yasa tabar wayarta a ringing. Wayar ta kalla sosai ganin sunan dake jiki, da sauri ta ɗaga ganin zata katse. Baqeer hankali a tashe yace “Please in kina available ki taimaka mu kai Dada asibiti! Am really sorry.” Ai bata tsaya nazari ba tace “Ganinan zuwa.” Dirowa tayi daga kan gado duk ta rikice hankalinta gaba daya baya jikinta, kayan barcin bata canza ba ta saka dogon hijabin sallarta wanda yake har ƙasa kawai ta fito, ko Mummy bata tambaya ba tayi waje ta shiga mota zuciyarta da tunaninta sam basa jikinta. Meya samu Dada? Meya faru? Tambayar da take mata yawo kawai akai kenan. Baqeer kuwa kusa da Dada yayi, cikin nishi take ce mishi “Baqeer babu komai kar ka damu zai daidaita.” *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR*        *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN* {50} Hankali a tashe Zainab ta ƙaraso gidan, ita ta taimakawa Dada ta sakata a mota Baqeer na biye dasu akan wheelchair ɗin shi sai sannu take zubawa Dada. Wani private clinic ta kai su don tasan idan suka tafi asibitin gwamnati sai sun bi dogon layi, zasu daɗe sosai kafin su samu ganin likita ita kuma a yadda take ganin yanayin jikin na Dada sai take jin ba zata iya kaita inda zata kusa yini bata samu ganin likita ba. Duk wani kai kawon buɗe folder da kama Dada su shiga ɗakin ganin likita duk Zainab ce tayi shi Baqeer nashi kawai ya bayar da kuɗin da aka nema shima don yaƙi yarda Zainab ta kashe musu ko sisinta yace ɗauko su da tayi ma ya wadatar. Sai sintiri take yi ta kasa zama wuri ɗaya don ganin an bawa Dada kulawar data dace. Bayan fitowarsu daga wajen likita ma ita ta tafi da takardar da aka rubutawa Dada magani taje ta sayo a pharmacy, duk inda tayi yana binta da kallo yana tunanin matsayin data taka a zuciyarshi, yana mamakin irin muhimmancin da ya bata don bayan Umma da ƴan uwanshi itace mace ta farko da zai iya neman wata alfarma a wurinta idan buƙatar hakan ta taso don yasan kome take yi zata ajiye tazo inda yake. Anan ya ƙara tabbatar da lallai ta samu babban matsayi a cikin zuciyarshi da bai san lokacin da hakan ya faru ba, babu wani abu da zai yi ya biyata ɗawainiyar da take yi dashi. Tana ta wannan kai kawon a cikin asibitin ashe Mummy nata kiranta a waya ta saka wayar a silent bata sani ba. Sai da aka gama komai har magunguna sun karɓa sannan suka bar asibitin lokacin wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe, a hanyarsu ta komawa sun zo daidai kan traffic ɗin kwanar sabo ta kalli masu sayar da fruits daga gefe sai ta juya ta kalleshi tace "Am Ya Baqeer." Juyowa yayi ya kalleta sai yaga ita ma shi take kallo wani irin kallo mai ƙoƙarin fallasa asirin dake binne a cikin zuciya, idanunshi ya zuba a cikin nata yana yi mata kallo kwatankwacin wanda take yi mishi, zuciyarshi har bugawa take yi fat-fat kamar zata faso ƙirjinshi ta fito. Wani ƙayataccen murmushin daya saka Zeey jinta tana yawo tamkar akan gajimare don daɗi ya sakar mata kafin ya janye idanunshi daga kanta yana ƙoƙarin danne abinda yake ji yana taso mishi a kanta. Sai da yayi gyaran murya don daidaita muryarshi kada ta gane halin da zuciyarshi take a ciki yace "Wani abu kike so?" A daidai lokacin kuma motar dake bayansu ta danna wani uban horn da yasa Zeey ta firgita, sai lokacin ta lura ashe har an basu hannu motocin gabanta duk sun wuce bata sani ba. Jan motar tayi suka bar wurin sannan tace "Na'am." Ita ma tace tana basarwa kamar bata fahimci tambayar da yake yi ba, girgiza kanshi kawai yayi ya basar don yasan da gangan ta amsa shi a hakan. Lokaci bayan lokaci suke satar kallon juna suna jifan junansu da murmushi mai ratsa zuciya. Ita dai Zeey ta gama haƙiƙancewa ranta son shi take yi da gaske ba da wasa ba shine dai har yanzu take tantamar anya kuwa ta samu zuciyarshi kamar yadda yayi kaka gida a tata. Ita dai Dada tana kwance a bayan mota bata san wainar da suke toyawa ba har suka ƙaraso gida. Da taimakon Zainab Dada ta shiga cikin gida, bata zauna ba tayi mata sallama ta tafi sai data fita sai taga har lokacin yana cikin motar ashe. Fitowa tayi da wheelchair ɗin daga boot ta buɗe ta ajiye a gabanshi daidai yadda zai iya hawa. Da kulawa take kallonshi tace "Zaka iya kuwa, ko na samo wanda zai taimaka maka ka hau?" Girgiza kanshi kawai yayi sannan ya daddafa da ƙyar ya koma kan wheelchair ɗin, ita kuwa sai faman jera mishi sannu take yi kamar mai ciwo, sai taji gaba ɗaya ya bata tausayi kamar ta ɗauke larurar ta mayar jikinta haka take ji. Kasa tafiya tayi har sai da taga shigar shi cikin gida sannan taja motarta ta bar wurin tana jinjina yadda ta ɗauki al'amuranshi da girma haka, sam bata iya sukuni idan har ya buƙaci wani abu bata yi mishi ba. ***** A hankali Nabeela ta tura ƙofar ɗakin ta shiga cikin sanɗa kamar mai gudun kada wani ya ganta. Bata ganshi akan gado ba don haka ta hau jujjuyawa tana ƙarewa ɗakin kallo, motsin da taji daga banɗaki ne ya bata tabbacin yana ciki sai ta shige can cikin ƙuryar ɗakin inda kayan gadonshi suke ta kishingiɗe akan gadon tana danne-danne a wayarta. Bata daɗe da kwanciya ba sai gashi ya fito da towel ɗaure a ƙugunshi sai wani ɗan ƙarami a hannunshi da yake goge ruwan jikinshi dashi. Tana kallon duk abinda yake yi daga nan inda take sai dai ko motsi bata yi ba bare yasan da wanzuwarta a cikin ɗakin har ya gama shiryawa cikin wandon faded jeans baƙi da polo shirt kalar maroon. Sai sannan ta taso cikin rangwaɗa ta nufi gaban madubi inda yake duba tarin turarukanshi yana zaɓar wanda zai fesa. Yana ganinta ya haɗe rai tamkar bai taɓa dariya ba sai dai ko a jikinta ɓacin ranshi bai hanata nufarshi ba kamar yadda tayi niyya sai ma ɗaukar ɗaya daga cikin turarukan tayi ba tare data duba ko wanne bane ta rangwaɗar da kai gefe guda cikin wani irin salo na jan hankali tace "May I?" Bata jira jin ta bakinshi ba kawai sai ta hau fesa mishi turaren a dukkanin jikinshi, takaici ne ma yasa ya tsaya ƙiƙam kawai yana kallonta yana mamakin ƙarfin hali irin nata da bata jin duk jan kunnen da yake yi mata akan shigo mishi ɗaki. Kwalabar ta ajiye ta ɗora hannunta akan kirjinta tana yi mishi wata irin shafa da tasa ya kusa rasa nutsuwarshi, bai yi aune ba kawai sai jin saukar leɓunanta yayi akan nashi cikin wani tattausan kiss, duk rashin jin Kabir baya kule-kulen mata, barshi dai da son harkar chilling da clubbing amma sam babu ruwanshi da shiga sabgar mata shi yasa abun yazo mishi a bazata. Bai san lokacin da ya fara mayar mata da martanin kiss ɗin ba sai can kamar wanda aka yiwa raɗa cikin kanshi ya tuna wacece ita da matsayinta a wurinshi, da sauri ya hankaɗeta yayi baya ya bayar da tazara mai yawa a tsakaninsu ranshi a matuƙar ɓace da wannan rashin hankalin da tayi mishi. A fusace yana nunata da yatsa yace "Bana son iskanci fa Nabila wallahi idan baki fita sabgata ba zan yi miki rashin mutunci irin wanda baki taɓa tsammani ba, haba wannan wacce irin jaraba ce? Ana so dole ne ko an gaya miki kowa ma jaki ne dabba wanda baya aiki da tunani da zaki yi tunanin wani abu makamancin wannan zai taɓa shiga tsakaninmu, ko kin manta ke wacece a wurina da zaki dinga damuna da abin da kika san ba zai taɓa yiwuwa ba, to wallahi ki fita a hanyata kada ki ƙara shigo mini ɗaki idan ba haka ba duk wulaƙancin da nayi miki ke kika saya da kuɗin ki." Yayi tsaki kawai ya fice ya bar mata ɗakin don bama zai iya tsayawa ya jirata ta fita ba. Haka kawai shi da ɗakinshi da gidansu amma tana nema ta takura mishi, yanzu gaba ɗaya baya iya sakewa a cikin gidan don yana tsoron yadda take yawan shigar mishi ɗaki ba tare daya sani ba. ***** Tana komawa gida ɗakinta ta wuce tayi sauri ta shiga wanka ta shirya a gurguje don sai bayan dawowarta sannan ta tuna ashe fa akwai inda zasu je ita da Mummy shaf ta manta saboda hankalinta daya bar jikinta tunda ta amsa ƙiran Baqeer tunaninta gaba ɗaya ya koma wajenshi, bata tashi tunawa ba sai data ɗaga wayarta don ta duba lokaci taci karo da tarin missed calls ɗin Mummy. Sassauƙar shiga tayi cikin pencil trouser da kaftan top data kai mata har wajen gwiwa, medium veil tayi rolling  a kanta ta ɗauki turaren wurin Baqeer tayi amfani dashi da tunda ya bata ta daina amfani da kowane turare idan bashi ba har gashi ma ya kusa ƙarewa. Sai data gama shirinta tsaf sannan ta fita zuwa ɗakin Mummy. Tana shiga Mummy tace mata "Ina kika shiga yau tun safe bayan kin san zamu fita kuma shine nayi ta kiranki a waya baki ɗauka ba?" Langaɓar da kanta tayi gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace "Ayya, i’m sorry Mum wallahi wani ɗan uzuri ne ya fitar dani kuma wayar tawa a silent take ban tashi ganin missed calls ɗinki ba sai da na kusa ƙarasowa gida, i'm sorry please bazan ƙara ba," ta ƙarashe maganar tana kama kunnuwanta duk cikin ban haƙurin. Girgiza kai kawai Mummyn tayi tace "Idan ban haƙura ba ya zanyi dake Zeey, most a times nafi ganin laifin kaina don ni na sakar miki da yawa har haka shi yasa kike abubuwan ki babu shakkar abinda zai je yazo amma in banda haka bayan kin san Daddynku yana gari shine kika saka ƙafa kika fita tun safe ba tare da sanin kowa ba salon idan ya tambayi ina kike na rasa amsar bashi ko." "Please mana Mum tunda nace kiyi haƙuri ba sai ki haƙura ba abar maganar, yanzu dai gani na shirya ko mun fasa fitar ne na tafi naje na kwanta?" Ta ƙarashe da tambayarta. "Hmm" kawai Mummy tace tana jin rashin daɗin yadda Zainab tayi mata magana sai dai kuma baza ta iya tsawatar mata ba don tana ganin ai har yanzu Zeey ɗin yarinya ce shi yasa bata tauna magana kafin ta faɗeta tasan data ƙara girma zata daina duk irin waɗannan abubuwan da bata so ɗin. ***** Tun da ya samu aikin contract ɗinnan sai yake ganin bama lallai ne sai ya sayar da filinshi ba yana ganin a cikin abinda zasu bashi ya isa yayi amfani da kuɗin ya biya tailoring school ɗin da yake son shiga sai dai kuma har wasu kwanaki mutanen basu ƙara tuntuɓarshi ba don haka ma yake ganin kamar dama dai wasa da hankalinshi kawai suke son yi, gashi ƴan kuɗaɗen da suka rage mishi a account ma har sun ƙare shima Sani telan bai ƙara nemanshi ba duk da tabbacin daya samu daga wurin Zeey na yayi styles ɗin ɗinkunan daya karɓa a wurinshi har ma yayi wa wasu da yawa irinsu kenan dai yayi ciniki sosai da styles ɗin, yayi mamaki da har yanzu bai dawo ba don shi kanshi sai da ya leƙa shafin shi na IG ɗin yaga yadda yayi ɗinkunan sosai da yawan likes da comments ɗin daya samu na masu son yayi musu irin wannan ɗinkin. Har tsawon sati biyu mutanen nan basu ƙara nemanshi ba don haka yaga baya fa da wata dabara baya ga ya saka filinshi a kasuwa duk kuwa da a farko burinshi ya gina wurin ne, daya samu contract ɗinnan har ya fara murna don yana ganin ba lallai ne sai ya sayar da filin ba amma yanzu idan har yana son shiga tailoring school ɗinnan tofa lallai ne sai ya haƙura da filin nan duk kuwa da yadda yake son gina wurin saboda yadda tsarin wurin yayi mishi, unguwa ce da babu hayaniya tsarin wurin yafi kama da tsari irin na GRA shi yasa ma ya zaɓi sayen fili a wurin saboda irin waɗannan unguwannin na burgeshi yadda basu da cinkoso da hayaniya rayuwar babu ruwan wani da wani bare aje ana saka maka ido a al'amuran rayuwarka. Waya ya ɗauka ya kira Salim ya faɗa mishi abinda ke faruwa da abinda yake so yazo suyi saboda a yanzu shine kamar manager ɗin shi baya komai sai da shawarar shi, da shi kaɗai ya yarda a halin yanzu don shine mutum ɗaya tilo da bai juya mishi baya ba bayan Ummanshi da ƙannenshi guda biyu Maryam da Hadiza sai ko Zainab da duk abinda ya zama a yanzu yake ganin ita ce sila, he will forever be indebted to her don tayi mishi abinda wani makusancin bai yi mishi ba a rayuwa... *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR*        *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA ƊAYA* {51}    Sun saka filin a kasuwa dan haryau dai mutanen basu ce komai game da contract ɗin Baqeer ba shima kuma yana tunanin in ya nemesu zasu ga kamar a matse yake, haka Salim yazo aka sa fili a kasuwa, Umma har sadaka tayi akan Allah yasa komai ya tafi daidai ya bawa Baqeer sa’a don ita kam kwanan nan rayuwa kawai take yi amma babu abinda ke faranta mata rai, a koda yaushe tunaninta yadda zata taimakawa Baqeer har yau tana mamakin yadda ko da wasa Badaru bai taɓa tambayarta Baqeer ba illa harkarshi kawai da yake yi, wannan abu na daure mata kai, wai mahaifi? Yau tana zaune tana fanken sadaka, Abu ta fito da ƙatuwar leda ta ajiye a waje tana kiran Jamila, Umma ko kallonsu bata yi ba balle ta so sanin menene a ciki, Jamila ta fito tana kallonta tace “Saƙon Nusaiban ne?” Abu ta ɗan kalli Umma ta gefen ido tace “Wallahi shine ai dai babu abinda yafi komai daɗi irin Allah ya baka ɗan da zai fitar da kai kunya, yanzu ke kiga abinda ta aiko mun, da ana yi mata kallon wacce bata dashi sai gashi yanzu tafi wacce tayi auran daɗi taimakon iyayenta.” Dafata Jamila tayi tace “Yoo wai ba ita ce naji ana zargin uban miji na sintiri ba? Yayi shima ɗa yayi?” Tsabar tashin hankalin da Umma ta shiga taje jefa fanke cikin mai sai ji tayi man ya ƙonata ashe hannunta ta kai kai, cike da tsoro ta kalli Jamila tace “Jamila ni kam kin san harshe yana daga cikin babban abinda ke kai bawa wuta ko?” Kallon Umma tayi tace “To ni dai ba dake nake ba balle kiyi mini wannan mumunan zaton, zance ne nake yi akan labarin da naji a radio, bana son sharri ban kuma san ayi mini ƙazafi.” Abu tayi saurin fito da kaya tana cewa “Meye abun tsarguwa in har kun san kuna da gaskiya?“ Umma komawa tayi ta zauna tasa ruwan sanyi ta cigaba da suyar ta idanunta sunyi jaa, tabbas sai Allah ya yiwa Maryam sakayya, dama ya za'ayi uban miji ya zauna a cikin gida? Tasan ko ba daɗe ko ba jima wani sai ya faɗa musu baƙar magana akan hakan, da ƙyar ta gama suyar ta zuba musu ta ajiye sannan ta bada aka fita dashi. Tana shiga ɗaki Jamila tayi tsaki tace “Wai kuɗin kujerun ne har yanzu bata cinye ba?” Abu ta ɗauke kai tana duba atamfar da aka kawo mata, sai yanzu ma data kula taga mai arhace haushi duk ya isheta ta maida ita leda tana cewa “Inba su ba ina taga kuɗin kashewa? Bayan yanzu ficika Mallam baya bata?” Nan dai suka cigaba da gulmace gulmacensu na hassada suna yi suna cin fanken. ***** Yau Baqeer cikin farin ciki suka tashi don an samu mai siyan fili, an turo rabin kuɗin suka je shida Salim ya cike form akan zai fara zuwa, sun yi mamakin ganin gurgu da zuwa koyon ɗinki amma jin yace da keken electric zai yi yasa suka amince, sun yaba sosai da yanda duk da rashin ƙafarshi bai hanashi neman abinda zai taimaki kanshi dashi ba, Baqeer nada kyau sannan yana da cikar zati hakan yasa ko a baya mata ke sonshi, a yanzun ma in ba ganinshi aka yi akan wheelchair ba ba’a kawowa yana da nakasa, sun fito bayan sun yi registeration, ajiyar zuciya yayi ya kalli Salim wanda shima kallonshi yake yi kafin a hankali suka yi murmushi yace “Yanzu gobe zaka fara zuwa?” Kai ya ɗaga alamar eh yace “Zamu dinga zuwa da Tanimu kai dai ka cigaba da zuwa kasuwarka kafin na gama In Sha Allahu.” Cike da gamsuwa ya jinjina kai yace “Hakan yayi amma ragowar kudin filin fa? Zan turoma yanzu.” Kai Baqeer ya girgiza alamar a’a yace “ In har da hali yanzu muje bank mu buɗe wani account na saka a ciki ya zama na sana’a ne, bana son mu saka kuɗin a gaba kuma in na gama koyan muzo babu halin buɗe shagon.” Kallonshi yayi yace “Hakan yayi, mu je?” Nan suka hau adaidaita sukaje bank na GT suka buɗe account aka tura ragowar kuɗin ciki sannan suka koma, a hanya ya turawa Umma, Hadiza da Maryam kuɗi daga cikin na fili, sannan ya turawa Salim, suka ɗan ƙaro abubuwan gida sannan suka dawo a gajiye gashi gobe zai fara zuwa school. Sun shiga gida yana shiga tsakar gidan idonshi ya sauka kan Zee dake tsaye rike da ludayi, kallon mamaki yayi mata sannan ya kalli ludayin hannunta yayi mata sign da gira akan me take yi? Cike da sakalci tace “Oho, nima Dada tace na tuka mata wai tuwo.” Ya kalli ludayin miyar dake hannunta sannan yace “Da wannan?” Ludayin tayi saurin ajiyewa tace “Ahh na manta bari na amsa waya tuntuni ake kirana, tayi maganar tana guduwa daga wurin, Dada ce daga ciki take cewa “Zainabu? Kin tuka?” Ta ƙarasa maganar tana fitowa daga ɗan store ɗin da suke ajiyar kayayyakin su na buƙata, ganin Baqeer tayi a zaune yana kallonta shima ta ɗan waiga tace “Tana ina?” Alama yayi mata da ciki yace “Yaushe tazo?” Ta ɗauki muciya tana cewa “Dazu, kun cike fam ɗin?” Ya ɗaga kai yana shiga ciki, Zeey kuwa data samu ta gudu tana zama a kujera ta sauke ajiyar zuciya lallai tasha da ƙyar wai, me yafi wannan abun kunya in Baqeer yasan bata iya komai ba? Shigowa yayi ya ɗan tsaya gefen ɗakin shi yana kallonta, ita ma kallonshi tayi zuciyarshi na sake jin wani daɗin ganinta da yayi, kwantar da kanta tayi saman kujera tace “Shine ka tafi babu ni?” Wani kallo ya mata tayi saurin cewa “Bafa da wani abu ba amma da mun je tare, ko nima na shiga makarantar mu dinga zu……” kallon da yayi mata ne yasa ta turo baki ta sake maida kanta tace “Na haƙura to,” tayi maganar tana kallonshi. Ɗan murmushi yayi kaɗan wanda ya sata zuba mishi ido ita kam ya zata yi da son Baqeer? Ya dago yace “Sai kuma kice zaki shiga makarantar koyon ɗinki saboda me?” Har yanzu kanta na kan bayan hannunta akan hannun kujerar tace “Kawai!” Ya maimaita kalmar tare da cewa “Ban saki ba, kema ki duba abinda kike so kiyi.” Ji tayi cikin ranta tace “Kai ne ai.” Kallonta yayi jin kamar yaji alamun maganar ta amma bai ji komai ba yace “Me kika ce?” Da sauri ta zauna tace “Ban ce komai ba.” Kai ya jinjina zai yi magana sai ga Dada ta shigo tana cewa “Abu ashe kina ciki?” Tace “Waya aka yi mini daga nan kuma na zauna, au bari na tuƙa miki tuwon.” Tayi maganar cikin ɗan dauriya, nan tace “A’a yi zamanki ma don ni kam na riga na tuƙa ai, kada ki damu.” Ta kalli Baqeer tace “Kayan da Salim yasa a shigo dasu duk namu ne?” Kai ya ɗaga yana cewa “Eh.” Ta koma ta shigo da leda tana cewa “Wannan naga kayan shafe-shafe ne? Anya nawa ne ba na Zainabu ba?” Ɗagowar da zai yi sai yaga idon Zeey a kanshi da sauri yace “Naki ne mana Dada.” Ta kalleshi tana cewa “A’a fa ban yarda ba ina ni ina shafa irin wannan man? Zainabu ba irin shi bane wanda kika taɓa shafa mini wani mai kalar manshanu?” Dariya suka yi, Zeey tana kallonta tace “Mugani.” Miƙa mata tayi Zeey tana buɗewa taga brand na man da take shafawa, hand lotion ɗin irinshi ne sak wanda take sawa a jakarta, da mamaki ta kalli Baqeer wanda yayi saurin shafar bayan kanshi kawai ya gurgura kekenshi yayi ɗaki, sam ya manta lokacin da suka siyo bai ɗauke shi ba daga cikin kayan, yanzu gashinan Dada ta gama bashi kunya don shi kam bai isa magana ba. Zeey kuwa murmushi tayi don ta tabbatar nata ne, sai ga Dada ta sake shigowa da wata ledar tace “Ahaf ni nasan wannan naki ne, kinga mai gurguwa gashinan nawa.” Murmushi tayi tana cewa “Kila dai wannan ɗin ma ke ya sayawa.” Baki ta taɓe tace “Ni dai kam na bar miki in ma ni ɗin ce don ban isa  ba.” Har Zeey ta fito daga gidan Baqeer bai leƙo ba. ****** Badaru ne ya dawo daga kasuwa duk yana jinshi a gajiye, ganin abokanshi yayi a zaune suna hira da alama wani abun ne ke shirin faruwa, wajen yaje yana cewa “Ahh Malam Iro kune?” Ga mamakinshi ɗif suka yi kamar ba sune ke hirar nan ana dariya ba, nan fa ranshi yayi mugun ɓaci ganin sun fara watsewa ɗaya bayan ɗaya, nan fa ya sake kaiwa bango ya kalli Malam Iro yace “Wai har da kai? Wani irin cin zarafi kuke neman yi mini ne?” Malam Iro yayi gyaran murya yace “Kai matsalarka kenan faɗa da kuma zargi, zancen Bello muke yi da zai tafi ƙasar waje bayan auransu da kwana biyu to mun san halinka shi yasa muka yi shiru.” Ai kuwa kamar an taɓoshi ya fara cewa “Ya tafi sararin samaniya ma ba ƙasar waje ba, yo dama munafiki har ya isa a daraja shi? To sai me? Sai me in yaje? Ko banza dai da ba don ɗana ba bai isa ya zama wani ba, banzaye kawai munafukai.” Ya juya yana cigaba da zazzaga masifarshi, yana shiga gida kai tsaye ɗakin Fatima ya shiga, a lokacin tana waya da Baqeer tana yi mishi faɗa akan don me zai turo musu kuɗi bayan yana da abubuwan yi masu muhimmanci a gabanshi, ai tana jin muryar Badaru ta kashe wayar da sauri, sai kuwa gashi ya shigo rai a ɓace yace “Allah ya isa cutata da kuka yi, kun munafurceni yaron nan don baƙin hali ya hanani jin daɗin rayuwa wallahi sai kun san kun yi dani.” Umma cike da takaicin kalamanshi tace “Mallam yanzu ya dace ka riƙa yin magana akan ɗanka haka?” Yatsa ya nuna mata yace “Kafin na zabga miki mari kiyi mini shiru, kece ai baƙar munafukar.” Ya juya rai a ɓace ya bar ɗakin, wayarta taje ɗauka me zata gani? Ashe bata kashe wayar ba, hankali a tashe tasa wayar a kunne tace “Baqeer?” Kasa magana yayi kawai ya kashe wayar yana jin wani abu ya tokare mishi maƙoshi yana neman hanashi numfashi. A hankali ya shiga neman jawo numfashinshi yana sauke ajiyar zuciya, wayarshi ce tayi ƙara ya ɗauka Umma ce sai yaga Zeey ce, saƙo ta turo mai ‘In nawa ne thanks in ma ba nawa bane thanks’. Kallon sunan ta yayi yana tunanin yanda ta shigo rayuwarshi daidai lokacin da yake neman wanda zai fahimci halin da yake ciki, ta shigo rayuwarshi daidai sanda yake neman wanda zai nuna mishi hanya. Saƙo ta sake turowa ‘Me kace?’ Maimakon ya amsa mata sai ya kira Umma saboda ƙaramar nutsuwar da tazo mishi din yasan tana cikin wani hali yace “Umma karki damu, bansa abinshi a raina ba ina fata kema bazaki saka ba.” Bayan sun yi sallama ne taji hankalinta ya ƙara kwanciya Allah dai ya raya mata Baqeer ya kare mata shi. ***** Zeey kuwa fitowa tayi daga ɗaki ganin Baqeer bai mata reply ba, kitchen ta shiga ta kalli masu aikinsu tace “Babba ni kam ya kuke tuƙa tuwo?” Da mamaki Mummy dake tsaye tace “Ke kuma me ya haɗaki da tuƙa tuwo?” Kallon Mummy tayi sai kuma ta ƙarasa wurinta ta rungume ta tace “Haka kawai naji curiosity na son in sani nasan naga suna yi amma ban taɓa gwadawa ba.” Shafar kanta tayi tace “Kada ki wani damu da harkar kitchen ke ƴar gata ce duk mai aurenki ma sai ya amince da mai aiki sannan ni da kaina zan nemo mai aikin ke dai ki zauna cikin farin ciki kici kisha.” Nabeela ce ta girgiza kai cike da takaici tace “In kuma mijinta yace sai tayi mishi girki fa?” Wani kallo Mummy tayi mata tace “Wannan kuma ba damuwarki bane, sannan in tayi auren in baya son me aiki sai na dinga aika mata abinci daga gidan nan, Nabeela wai ni kam menene matsalarki?” Kai kawai ta sake girgizawa ta juya, Zeey tabi bayanta da kallo. Hanyar ƙofar ɗakin Kabir tayi bata san Mummy ta biyota ba sai ji tayi tace “Uban me zaki yi anan?” Waigowa tayi da sauri ta ɗan kalleta a tsorace kafin tace “Babu komai kawai airpod ɗinshi zan ara.” Wani kallo ta sake yi mata tace “Wuce kafin ranki yayi mugun ɓaci, wallahi kin sani nace a’a bana son hauka bana son rashin hankali da tunani.” A fusace tayi ɗakinta tana tunani ai zata tafi ta kwanta don haka dole ne taga Kabir babu mai hanata. Zeey kuwa ɗaki ta shiga ta duba wayarta saƙon Baqeer ta gani yace ‘Me kika ce?’ Murmushi tayi tace “Inyi godiya?” Shima reply yayi mata “An yafe miki shi.” Bargo ta shige ta sauke ajiyar zuciya tana jin ƙaunar Baqeer na sake ratsata, gaskiya tana buƙatar hoton Baqeer a wayarta, especially in tayi missing ɗinshi. A hankali ya shigo gidan don ya tabbatar sun yi bacci, tun sanda Nabeela tayi mishi kiss yake jin wata irin sha’awa na taso mishi, gudun ɓarna yasa yaƙi zaman gidan, hannunshi yaji an riƙo, dayake duk fitilun gidan a kashe suke yasa yace “Waye?” Jan hannunshi tayi zuwa ɗakinta, yana shiga dim light ɗin dakin yasa ya ganeta, ajiyar zuciya yayi yace “Nabee……” Sumbatar da ta kai mishi ne yasa ya kasa ƙarasawa…. 😒Umm Asghar ne da Ayusher suka kalli juna suka ce "to meke faruwa ne"❓ *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BIYU* {52} Bai san lokacin da ya fara mayar mata da martani ba domin kuwa ta tayar mishi da wani tsumi ne da bai san dashi ba, tun da ta mamaye shi tayi mishi kiss ɗinnan shikenan ya shiga cikin wani hali, dauriya kawai yake yi amma sai yaji babu abinda yake da buƙata face son kasancewa tare da ita hakan yasa ya kasa tanƙwara zuciyarshi har yaga rashin dacewar abinda suke yi sai kawai ya biye mata suka cigaba da aikawa da juna zafafan saƙonnin da suka sake fitar dasu daga hayyacinsu, kafin wani lokaci har sun dire akan gadonta sai da tafiya tayi tafiya tukunna Kabir ya dawo cikin hayyacinshi ya tuna wacece Nabila a wurinshi da abinda suke shirin aikatawa. Hankaɗeta yayi daga jikinshi ya tashi ya mayar da suturar shi da tuni suka yi watsi dasu suka yi nasu wuri, ko kallonta baya son yi don baya son ganinta a yanayin da take ciki, shi ya rasa wace irin jaraba ce wannan duk yadda yake kakkauce mata sai da tayi nasarar ribatarshi, in banda Allah ya kiyaye yasan da ƙyar idan basu aikata ɓarna ba. Yana gama saka kayanshi ya fice daga ɗakin yana sauke ajiyar zuciya ranshi fal takaicin Nabila. Yana fita tabi ƙofar ɗakin da kallo tana jin takaicin haƙanta da bai cimma ruwa ba don ita a tunaninta idan har ta ribace shi wani abu ya shiga tsakaninsu dole Mummy ta haƙura ta ƙyalesu suyi aure don a ganinta Mummyn ce babbar matsalarta ba wai Kabir ɗin ba. Tashi tayi ta faɗa banɗaki ta kimtsa jikinta sannan ta fito tayi shirin kwanciya bacci ta haye gadonta tana tariyo abinda ya faru a tsakaninsu bada jimawa ba tana jin wani irin daɗi da shauƙi yana ɗibarta. Shi kuwa Kabir yana shiga ɗakin shi ya dannawa ƙofar key don baya so Nabila ta ƙara mamayar shi ta shigo mishi ɗaki bai sani ba, yanzu in banda Allah ya kiyaye da bai san a wane hali zata saka shi ba gashi nan yanzu ta tayar mishi da abinda daa can kwata-kwata bai san  dashi ba. Haka ya kasance cikin wani hali har ya dinga ji ko dai ya tashi ya buɗe ƙofar ɗakin ne watakila ta biyoshi sai dai kuma yana kwaɓar zuciyarshi akan wai me yake tunanin aikatawa, shin yana da tabbacin idan ta shigo ɗakin nashi zai iya controlling kanshi kamar yadda yayi a baya? Bai san lokacin da bacci ya ɗaukeshi ba ya dai saka a ranshi cewa dole ne ma ya taka mata burki idan ba haka ba taja shi ga aikata dana sani, shi kuma abinda baya fata kenan a rayuwa. ***** Baqeer ya samu ya fara zuwa tailoring school ɗin, kullum da safe Tanimu yake zuwa ya turashi zuwa bakin titi inda zai tarar musu adaidaita su tafi Makarantar, daga baya ma sai ya nemi wani mai adaidaitan ɗan nan unguwar suka yi ciniki kullum shi yake zuwa ya ɗauke su ya kai su can makarantar idan lokacin tashi yayi yaje ya ɗaukosu ya dawo dasu gida. Sosai Baqeer ya mayar da hankali akan koyon ɗinkin, matsala ɗaya da yaci karo da ita shine da aka ce dole sai sun koyi ɗinki akan normal keke kafin su fara akan mai aiki da wutar kasancewar shi me matsalar ƙafa duk da a yanzu ya fara iya motsata kaɗan-kaɗan saboda physiotherapy session da suke yi da Junaid ga kuma exercises ɗin da koyaushe yake yi a gida, a hankali a hankali ya fara iya motsa ƙafar saɓanin da da baya jin alamun ta ma a jikinshi, a yanzu ya fara jin feelings a wurin sai dai ba zai iya sarrafata yayi kowane irin amfani da ita ba. Duk da wannan matsalar daya samu ta rashin iya taka keke da kanshi duk da buƙatar hakan da ake yi wajen koyon ɗinkin ya mayar da hankalinshi ƙwarai wajen iya sarrafa almakashi don sosai ya ƙware a iya yanka ya kuma iya fitar da designs masu kyau, ɗinkin ma yana gwadawa akan electric machine ɗin tunda ba zai yiwu yayi akan manual keken ba. Wani abun burgewa  da yayi shine daya saka Tanimu a makarantar koyon ɗinkin tunda ya nuna sha'awarshi ga ɗinkin sai ya biya mishi duk kuwa da tsadar kuɗin makarantar tunda dama tare suke zuwa yana taimaka mishi da ƴan ƙananun abubuwa irin su taimaka mishi ya hau kan kujerar wheelchair ɗin shi da turashi zuwa duk wani wuri da zai je haka a cikin makarantar ko zuwa mishi aiken sayen wani abu na daga kayan ɗinki haka. Duk da har yanzu mutanen can basu ƙara waiwayarshi da batun contract ba da ɗan abinda yake samu daga zanen da yake yiwa Sani tela ya ɗauke nauyin duk wasu buƙatun shi dana mahaifiyarshi da ƴan uwanshi, da yake yanzu akai-akai Sanin yake zuwa yana sayen zane a wurinshi. Har yanzu dai Sanin ne kawai wanda yake yiwa zane yana biyanshi amma dai Alhamdulillah yana samu bakin gwargwado tunda bai nemi komai ya rasa ba, duk wani abu da yasan zasu buƙata yana ƙoƙarin ganin ya ajiye musu shi, haka nan Umma kullum cikin yi mata aiken kuɗi yake ita da ƴan uwanshi Hadiza da Maryam. To itama Hadizar ga yadda yake ji tana samun rufin asiri da injin markaɗenta don haka ya ƙara samun kwanciyar hankali tunda yasan a yanzu basu da wata gagarumar matsala a rayuwarsu. ***** Yau tun safe suke zuba lissafi suna tusawa, ya rasa inda kuɗaɗen shi suke tafiya kullum a maimakon ya cigaba sai baya yake ci ga wasu ƙananun sata da ya rasa wanda yake yi mishi a cikin yaran kantin nashi, duk wasu matakan tsaro daya sani ya zuba musu amma har yau ya kasa dacen kama ɓarawon da yake yi mishi sata. Akwai ranar ma da har an gama ciniki da wata mata da tazo sayen atampopi sai da aka zo saka mata a leda guda ɗaya tace ɗaukeni. Haka aka yi ta nema ba'a gani ba sai wata aka ɗauko aka bawa matar shi kuma yana ji yana gani ya ɗauki asara don kowa yace bashi bane ya kuma rasa ta yadda zai yi ya fitar da ɓarawon daga cikin yaran shagon nashi. Haka nan dai ya haƙura aka gama lissafin ya ware kuɗin da za'a zuba wasu kayan, sai yaga ɗan abinda ya rage mishi bai taka kara ya karya ba gashi kuma dole ya biya ma'aikatan shi hakkinsu. Haka nan ba don yaso ba ya biyasu albashin su ya tattare ɗan abinda ya rage ya tafi gida yana huci kamar yana fatan wani ya shiga gonarshi ya huce takaicin shi a kanshi. Tun daga ƙofar gida yake surfa ruwan bala'i akan tumakin maƙwabta da suka yi mishi kashi a ƙofar gida, yana shigowa tsakar gidan yaci karo da bokitin ƙarfen Jamila a tsakar gidan, ƙafa yasa yayi ball dashi yana masifa akan don me za'a ajiye bokiti akan hanya salon yayi tuntuɓe ya faɗi idan yaji ciwo basu da asara. Daga Jamila har Abu tsayawa suka yi suna kallonshi babu wacce tasa mishi baki, a yadda suka ga ya shigo ɗinnan sun san idan suka ce zasu yi magana idan ransu yayi dubu sai ya ɓaci don sun daɗe basu ganshi cikin tashin hankali irin na yau ba sun san dole akwai abinda ya ɓata mishi rai a waje sun san cewa idan suka saka mishi naki a kansu zai huce su kuwa babu wacce ta shiryawa tijarar shi ta fama da idan ya fara baya jin yi haƙuri idan aka bashi haƙuri shi kamar ana turashi ya ƙara ruwan tijarar da yake yi. Fatima ce me girkin ranar tana jin shi yana faman tijararshi bata fito ba sai da taji shigarshi ɗaki sannan  ta fita ta haɗa kayan abincin shi ta ɗauka ta nufi ɗakin nashi dasu. Da sallama ta shiga ɗakin cikin nutsuwarta data zame mata jiki. "Sannu da dawowa Mallam," tace tana ajiye tiren abincin a gabanshi. Wani irin kallo yayi mata idonshi cike da fitina yasa hannu ya buɗe kwanukan abincin nashi sai yaga tuwon masara ne da miyar kuka. Watsi yayi da kwanukan ƙiris bai sameta ba tayi sauri ta kauce kwanukan suka watse anan tsakar ɗakin. "Mallam lafiya kuwa?" Tace tana kallon ɓarnar da yayi a tsakar ɗakin tana jin takaicin wannan wulaƙanci na Badaru, yanzu abincin da wasu suke can suna nema basu samu ba shine shi ya samu don wulaƙanci ya zubar. Nuna abincin yayi da yatsa yace "Miye wannan?" Yana bin miyar data kwanta a tsakar ɗakin da wani irin mummunan kallo kamar wanda yaga kashi. Kallon miyar itama tayi yadda ta kwanta a ƙasan ɗakin sannan ta ɗago ta kalleshi sai dai bata ce mishi komai ba tsabar takaici. "Ke dai Fatima wallahi kin yi asara, baki ji daɗin rayuwarki ba wallahi sam uwar baƙin ciki da mugun hali, abincin ma don mugun hali kin daina tsayawa ki girka mai kyau sai dai ki kwaɓa mana shi duk yadda ta raya miki." Hannu tasa ta tattare kwanukan ta haɗasu wuri ɗaya kafin tace "abinda ka kawo ai shi zaka gani, da ɗin ma da nake yin irin wanda kake so ai ba da cefanenka nake yi ba ka sani Baqeer ne ya ɗauki nauyin yin cefane yanzu kuwa daka koreshi kaga dole ayi da iya abinda ka kawo kawai tunda mai kawowar baya nan." A fusace yace "Yauwa ga maganata nan ta fito, kawai dama kice kina baƙin ciki don nace nakasashen ɗanki ya fita ya bar mini gidana shine kike nuna mugun halinki a abinci ba kya tsayawa kiyi shi da kyau kamar da, to sai dai mugun halinki ya ƙare a kanki, ɗanki ne dai ya bar gidan nan har abada kuma ban yafe dukiyata da lokacina dana ɓata a kanshi ba wallahi in dai baza ku biyani abinda na kashe ba." A razane ta ɗago kai ta kalleshi tace "Baqeer ɗin kake yiwa Allah ya isa kamar ba ɗanka ba Mallam? Wannan wacce irin rayuwa ce da bawa bai san ya karɓi ƙaddara ba, shi ya ɗorawa kanshi ne ba Allah ne ya ɗora mishi ba." "Oho dai wannan kuma ke kika sani, ni dai a biyani kuɗina idan ana son zaman lafiya dani ato." Tashi tayi kawai ta kwashe kwanukan tace "Allah ya ganar da kai Mallam amma In Sha Allahu sai kayi alfahari da haihuwar Baqeer." Tsaki yayi yace “Wa? Nakasashen ne zan yi alfahari dashi?” Bata ƙara kulashi ba ta fice ta bar ɗakin, ajiye kwanukan tayi a wajen wanke-wanke ta shige ɗakinta tana jinjina rashin tawakkali irin na Badaru da har yau ya kasa yarda da ƙaddarar data samu Baqeer. ***** Tunda satin bikin ya kama Asiya ta kasa zaune ta kasa tsaye don kuwa biki ne suke shiryawa na ƙarya irin wanda za'a daɗe ana labari. Events ma wajen kala biyar suka tsara za'a yi kuma duk Bello ne ya ɗauki nauyi koda yake ina iyayenta suka ga kuɗin da zasu yi mata irin wannan bikin na ƙarya. Duk wani ɗan abinda Bello ya mallaka ya shige a cikin sabgar bikin nan sai dai bai wani damu ba ganin ya kusa barin ƙasar yasan daga inda yaje ya fara aikin paintings ɗin shi shikenan zai mayar da fiye da abinda ya salwantar a wajen harkar bikin. Bayan kayan lefe da yayi mata duk wasu kaya da zata saka na fitar biki shi ya ɗinka mata tsadaddu don tace ai abun kunya ne a ga tayi kwalliyar biki da kayan lefenta sai ma ƙawayenta su raina ajinta a cewarta. Da bridal shower aka fara taron bikin inda Bello ya kama mata wani restaurant anan kusa da unguwarsu, duk wani abinci da aka ci a wurin taron restaurants ɗin ne suka basu. Haka event ɗinnan yayi ta yawo a social media, abinda ke ƙara sawa Asiya taji kamar kanta zai fashe don girma, tana ganin itama yanzu ta faso gari lokacinta ne yayi da zata shana tayi rayuwar ƴanci rayuwa irinta ƴaƴan masu kuɗi kamar yadda take da buri. Haka duk wani event da aka yi a bikin yayi ta yawo a social media har aka yi ɗaurin aure. A irin hotunan ne Baqeer yaci karo da hoton ɗaurin auren inda aka ɗauke su Bello ya rungumo kafaɗarta suna fara'a, duk da yanzu ya ajiyesu a gefe ya daina saka damuwarsu a ranshi sai da yaji wani abu ya mintsine shi a zuciya, a tunanin shi ko kowa zai yi mishi butulci bai kamata ace har da Bello ba bayan irin taimakon da yayi mishi a rayuwa. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD* Da *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA HAMSIN DA UKU* {53}    Yau ta fito zasuje wani guri ita da Nabila taga layinsu cike da mutane, baki ta taɓe tace "Bai wuce aure ake." Nabila ce ta kalli gun tace "Kamar fa yarinyar nan ƴar iyayin nan ake aure dan naga pictures ɗinta a IG da farko ma ban gane ta ba sai da naga kanwarta na gane itace ta layin nan." Dayake Zeey batasan sunan Asiya ba sai cewa tai "Ban santa ba, kinsan ni ba rike mutane gareni ba." Nabila ta hau kan titi tana cewa "Ni ma ba magana muke ba, sanda bakya nan dai ina ganinta, itace kamar akace saurayin ta yaci gasar zane kamar ko?" Kamewa a zaune Zeey tai da jin Nabila nan da nan hankalinta ya tafi kan budurwar Baqeer da aka yaura, badai ita bace? In itace ya Baqeer ke cike? Nan danan taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci ta dau wayarta tana cewa "Meye handle ɗinta?" Ba tare da dogon nazari ba tace "Cutie_Siya" da sauri ta duba ganin fuskar Asiya duk da ba wani dogon sani ta mata ba yasa bankalinta kara tashi, sam hankalinta ya tafi har Nabila ta gaji da magana tace "Wai menene?" Kallanta Zeey tai tace "Aunty Nabs bana jin yawon nan, plz saukeni kije ke kaɗai." Mamaki ne ya kamata tace "Zeey inje ni kaɗai kamar ya? Bayan mungama planning dake akan tare zamu?" Saman goshinta ta shafa tace "Banajin zuwa plz samu guri kiyi parking na fita." Takaici ne ya kama Nabila, tai parking ga mamakinta mai makon ma Zeey ta maida hankali kan ɓacin ranta gani tai ta fita kawai ta tari adaidaita sahu ta shiga hankalinta a kwance babu alamun ma ta damu. Hannayenta biyu tasa ta shafi fuskarta tana mamakin hali irin na Zeey da sam in tunanin ta yai wani gun bata bi ta kan komai, itama maimokon ta cigaba da tafiyar kawai gida ta koma, tana parkıng motar ta shiga ciki ranta duk ba da ɗi, tana ƙoƙarin yin hanyar dakinta ta hangoshi ya fito sanye da jeans da light brown ɗin riga da alama fita zaiyi dan yana rike da key a hannunsa yana kadawa, idanunsu na haduwa ya fara neman juyawa tai saurin cewa "Kabir in baka zo ba Allah zan ƙira sunanka da ƙarfi Mumy ta fito." Waigowa yai ya kalleta sannan ya tamke fuska sosai ya cigaba da tafiyarsa, har yazo kusa da ita bata matsa ba, yana yin taku biyu gaba da ita yaji ta sa hannu ta zagayo dashi gefen cikinsa, gabanshi ne yai wani irin faduwa hakan yasashi kasa ko motsawa, ya fara sauke numfashi cikin wani yanayi, kanta ta kwantar a bayanshi ta rikeshi sosai tace "My love dan Allah ka barni naji duminka ko na minti talatin ne." Kasa motsi yai saboda wani abu da yake ratsa mai gangar jiki, yawun bakinsa ya hadiya yace "Nabila abinda muke aikatawa ba daidai bane ke fa kanwar Mumy ce wannan wani kwamacala ne?" "Na sani Kabir shiyasa nake ƙoƙarin jure abinda ke raina, ba zina na nemi mu aikata ba, ban kuma ce sai ka soni dole ba dan Allah nidai ka dinga barina ina rungumarka, duminka na ragemin radadin zuciyata, numfashinka ya ragemin kewa da kaunar ka, a haka inaji a jikina san da nake ma zai ragu." Waigowa yai ya kalleta yace "Taya sona zai ragu a zuciyarki ta haka?" Idanunta ne ya ciciko da kwalla tace "Allah zaiyi dan Allah karka hanani tabaka," ta ƙarasa maganar wani kwalla na gangarowa saman kuncinta, janue jikinshi yai ya fita nan ta bishi da kallo tana share kwallarta, wannan wani irin bala'i ne? Tana san abu amma ace wai bazai yiwu ba? Ita alaka ta dameta ne? Indai za'a barta da Kabir koma menene a faɗa ba damunta zaiyi ba. Waigowar nan da zatai taga Mumy ta nufota, da sauri ta fara share kwalla tana neman daidaita kanta, Mumy kuwa tana ƙara sowa ta sharara mata mari ba tare da ta ce mata komai ba, nan da nan gabanta ya faɗi badai taji abinda tace ba? Da hannu Mumy ta nunata tace "Wallahi ki fita ido na, uban me kike cemai da kika tsare shi kina kwalla? Wai nikam Nabila anya bakida aljanu?" Fuska ta tamke sosai ita ma rai a ɓace tace "Bishiyar kuka ne a kaina, ni ban isa nai abu ba sai kin takuramin? Gaisawa ma kenan bazanyi dashi ba sai a hau zargina?" Baki Mumy ta saki, cike da mamaki da tsoron kalamanta, tana nan a tsaye har ta shiga ɗaki lalai dole tasan abinyi akan Nabila tab! ***** Baqeer yanzu abubuwa sun kankama, dan yankan ɗinki inya maka sai ka riƙe baki, sai dai baya dinkawa sai dai Tanimi ya haɗe mai, shi kuma in da na wuta ne yake yi, kafafunsa Alhamdulila yana jin canji sosai a tattare dasu, duk bayan sati biyu yake zuwa asibitin Junaid, wanda tunda yaga ya daina zuwa da Zainab ya haɗa shi da wani physiotherapist ɗin dan sama shi saboda Zee ya nace da zuwan Baqeer ɗin. Shi kuwa Baqeer ko a jikinshi hakan ma da ɗi yamai ko banza dai yanzu baya ganin Zee. Kamar yanda suka saba yau haka sukaje makaranta sun gama kenan suka shiga adaidaita suka dawo gida, a hanya Baqeer ya tsaya ya saiwa Dada lemo da ayaba, yana tafe yana kallan gari da yanda kowa ke ta hada-hada, har suka isa gida nan Tanimu ya fito da keken shi kuma ya hau yana mai godiya, hannu yakai zai fara turawa sai yaji an fara turashi, da mamaki yace "Tanimu karka...." Sai kuma yaga Tanimu a gabanshi, sai a lokacin yajuyo kamshin turaren da yake sai mata wanda yanzu ta daina ma kamshin turarenta ta koma na wanda yake sai mata, baice komai ba itama batace komai ba ta tura keken suka shiga soron gidan shi kuma Tanimu yai musu sallama ya tafi, a soron ta tsaya ta kalleshi tace "Are you okay?" Sai a lokacin ya kalleta, idanuwansu ne suka haɗu da juna wanda a wannan lokacin sukejin kaunar da sukewa juna ta wuce duk tunanin mutum sai dai ita bazata fara cewa tana sanshi ba alhalin bata san matsayinta a cikin ranshi ba, shi kuma bazai iya cewa yana santa ba saboda ajinta ya wuce ace tayi soyayya ko ya auri gurgu, ya tabbatar tausayi ne kawai take mai shima da kunya ya dubeta yace yanaso. "Da me kenan?" Yai tambayar idanunsa cikin nata, kallan shigarta yai riga ce ta ɗan wuce mazaunanta kaɗan sai pencil jeans sai kuma kanta datai rolling da mayafi, yanayinsa ne ya canza nan danan kishi ya turnikeshi taya zata fita a haka? Zee kuwa sam ta manta da shigar da tazo dan hankalinta sam ya tafi da jin auren Asiya. Katse mai tunani tai da cewa "Your Ex itace tai aure ko?" Kallanta yai yace "Oh I thought wani abin ne, yeah na gani." Ta ɗan mai wani kallo tace "Na ɗauka zan ganka kana zazzabin aureta da akai." "In akwai so da matsayi kenan a zuciyar mutum ko?" Kai ta jinjina tace "Yanzu babu?" Tai tambayar cike da san jin amsarsa, wani shanyayen kallo ya mata wanda yasa taji duk komai na jikinta ya sage yace "A haka kike yawo?" Kallan jikinta tai nan taji shakuwa tazo mata, mai makon ta amsa mai tai saurin shigewa ciki tana ƙiran sunan Dada. Dada kuwa tana jinta ta fito tace "Lale da Abu na ai saura kaɗan na sa cigiyarki gidan radio nidai bana iya jure rashin zuwanki dayawa." Rungume Dada tai tace "Allah sarki Dada ta bana san zuwa ne akai-akai kar wasu su fara tunanin gunsu nake sintiri." Tai maganar tana kallan Baqeer, wanda ke zaune ya harɗe hannu yana kallansu, Dada ta kalleshi itama tace "Tab to ba sai suyi tunaninsu su gama ba ni dai nasan guna kike zuwa dan kuwa bazaki zo gun Baqeeru ba yo wannan ma me zai kawoki gunshi? Yaran da magana ma sai ya dinga shan kamshi kafin yai?" Kallansa tai tana guntse dariya ta tace "Ah to Dada kema kinsani ai," cike da zolaya take maganar, lemon ya ajiye yai hanyar ɗakin shi sai dayazo daf dasu yace "Da ɗinta ma nasan ba guna ake zuwan ba." Dada tai caraf tace "Yadai fi maka, ah to tun kafin ka hanamin ita zuwa gwara da ka sani." Har ya shiga ɗaki tana satar kallanshi shima sai dayaje ƙofa ya waigo, da sauri ta ɗauke kai tace "Dada wallahi aikena akai na gudo ganinki bari naje zan dawo." "Kai nidai bangaji da ganinki ba amma bakomai ki taimaka ki dawo." To tace sannan ta juya, Baqeer kasa shiga ɗaki yai har sai da ta bar gidan, idanu ya lumshe inama ba a kujerar guragu yake ba ya sanar da ita abinda ke ranshi? Ya zaiyi da wannan san dake cika mai zuciya? Zeey kuwa gun aiken da Mumy ta musu ta nufa ga mamakinta Nabila bata nan, waya ta mata sai jitai wai tana gida batajin da ɗi, kai Zeey ta girgiza a fili tace "Itadai Aunty Nabs batasan zuwa gun in ba dani ba, na rasa wace irin kunya gareta." Nan ta nufi gida tana mamakin kunya da kara irinta Nabila sam bata hayaniya ko faɗa bakaji tanayi, itafa sam bazata iya irin wannan abubuwan ba dan ko yanda bata iya faɗar abu in ranta ya ɓaci mamaki take bata. **** Asiya Amarya da Bello an tare an kuma sha roman soyayya, ya kashe kudi dan duk kudin da aka bashi na tafiya ya juyesu a bikin nan, Abuja sukaje ya kama musu hotel sukai kwana biyu sannan ya wuce ƙasar Germany inda anan zasuyi jarabawar shiga, duk wanda suka ɗauka zasu ɗau ki nauyin iyalinshi da karatunshi har na tsawon shekara biyar. Asiya haka suka zo airport babu abinda take sai ɗaukan selfie tana sawa a IG kwanan nan da ɗi takeji, ji take kamar tafi kowace mace gata, shiyasa yanzu ba kowa ma take kulawa ba, Habi ma in tana mata magana kamar wata ƴar aikinta haka take mata, shima Bello duniya tai da ɗi matsalarshi ɗaya mahaifansa da suke neman takura mai, shiyasa yanzu yakejin da ɗi zasu bar kasar ma su huta, sunyi akan in yaje yai wata ɗaya zaizo ya ɗau keta dan itama tay applying visa, haka ya wuce ita kuma ta hau jirgi ta dawo Kano tawa Habi waya akan tazo su zauna saboda batasan zama ita kaɗai, taso kin zuwa sai dai mahaifinsu ya sata taje a ganinshi bai dace a barta ita kaɗai ba. **** Wace irin shakuwa ce mai ƙarfi ke ƙara shiga tsakanin Baqeer da Zainab, a koda yaushe yana bata mahimmanci a ranshi saboda yanaji Allah ne ya kawota cikin rayuwarshi dan ta daidai ta mai ita, a yanzu yafi da farinciki duk kuwa da bashi da ƙafa  a kalla yasan me yakeso yasan yai abinda zai kwantar mai da hankali, ba kamar da wanda Badaru ke kula da duk wani motsinshi ba, komai nashi sai da izinin Badaru gashi yai ta wulakanta ragowar kanensa saboda shi, wannan abu ya dade yana damunshi. Yau Baqeer ne zaune yana yanka shadar da ya siya zai dinkawa Hassan da Husaini da kuma Areef, yanajin da ɗin yanda a yanzu baya taɓa rasa kuɗi kuma haryanzu kuɗin filinshi bai cinye ba, ya tanada ragowar ne dan siyan keken wuta na electric da kuma shirin buɗe shago da yake san yi, wayarsa ce ta fara ƙara alamar an mai waya, kallanta yai ganin wata number yasashi jinkiri kafin ya ɗaga bayan sun gaisa ne mutumin yake sanar dashi akan shine wanda watanin baya ya nemeshi akan zanen da zai dinga musu. Baqeer ranshi ne ya ɓaci ganin sunzo da rainin wayau, taya tun nemenshi da sukai a baya basu sake nemanshi ba sai yanzu? Yanzun ma yasan daga wayar ba wani abu dazai faru. Katse mai tunani yai da cewa "Kayi hakuri matata tace Allah ya mata rasuwa sai abubuwan duk suka tsaya min komai ya fita daga kaina." Nan danan kuma sai jikin Baqeer yai sanyi yace "Allah ya mata rahama." Ya amsa da ameen sannan yace "Na shigo Kano inaso mu haɗu in ba damuwa gobe." Ya jinjina kai yace "Allah ya kaimu, ka turomin lokacin sai nazo." Nan suka tsara inda zasu hadu sukai sallama, sai dai haryanzu baije farinciki ko doki ba aganinsa sai yaga komai ya tabbata zai kwantar da hankalinsa, sam bai yadda da mutane ba yanzu. ***** Kamalu kam duniya tamai zafi shiyasa yanzu in ba ɗau ki dadai da yake a shagon Baba ba babu abinda ke rage mai zafi, gani yake gwara ya ɗauka ya fara tara lefe a dabarance, ya tabbatar Roshini intaga akwatinan laifi goma sha biyu to fa tabbas yasan zata sara ma kaunar da yake mata, za kuma tasan lalai shi ɗin saurayi ne da a ke yayi ake kuma sha'awar aura. ***** A zabure Kabir ya ture Nabila ganin aika-aikar da sukai, nan da nan kanshi yaji yayi wani irin sarawa, me ya aikata? Abinda ya faru daren jiya ne ya fara dawo mai.......... (😑😑Gaba daya Umm Asghar kasa motsi tai, Kabir da Nabila, Ayusher ce ta kalleta jikinsu gaba daya ya kame .) *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *BAQEER*      *NA* *AYUSHER MUHD* DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAKWAYE SHAFI NA HAMSIN DA HUƊU {54} Yaye bargon yai ya ganshi daga shi sai gajeran wando, kanshi ne yai wani irin sarawa ya sa hannu ya rike kan yana sake tariyo abinda ya faru, dawowarshi kenan daga yawonshi na abokai ya shiga ɗakin shi, kayan jikinshi ya fara cirewa dan bacci yakeji ko ganin su Mumy ba baisa ranyi ba dan kuwa yasan sun kwanta, ya cire kaya ya rage daga shi sai gajeran wando zai sa kayan bacci ta turo ƙofar, kallanta yai nan danan hankalinshi ya tashi, da sauri yasa hannu ya rufe saman kirjinsa yana cewa "Dan Allah fita, akan me zaki ɗinga shigowa ɗakin mutane ba tare da kin kwankwasa ba?" Mai makon tai abinda ya sakata sai ƙara takowa datai zuwa inda yake, nunata yai da yatsa fuskarsa a ɗaure yace "Wai ba magana nake miki ba? Karki kuskura ki ƙara so," nan ma bata kulashi ba sai ƙara takowa da take, tana isowa inda take ta rungumeshi, yawun bakinsa ya hadiya ya fara ƙoƙarin tureta, sake kankameshi tai tace "KB plz ka bari ba zina zamuyi ba, balle kace zunubi muke ɗauka." Da mamaki ya kalleta yace "Wai Nabila kinsan me muke yi kuwa? Me zai faru in wani ya shigo ya ganmu a haka? Dan Allah......" kiss ɗin data fara mai ne yasashi kasa cewa komai, tun yana neman janyeta tana rikoshi harya kasa, nan ya shiga maida mata martani, kan gado ya jata ya cigaba da sumbatarta, saman wuyanta ya gangara gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, Nabila kuwa gani take hakan shine daidai dan wannan ne kadai abinda zai hana Mumy rabata da Kabir dan indai aka hanata auran Kabir to fa har abada bazatai aure ba sai dai ta karashi rayuwarta haka, ko duniya zasu zageta in dai akanshi ne to fa bata damu ba. Kabir cak taji ya tsaya sanda ya fara zuge zip ɗin bayanta, hakan yasa ya saketa sai kuma ya kwanta rigingine yasa hannu ya shafi fuskarsa yace “bazan iya ba, am sorry.” Hawaye ne ya zubo saman kuncinta ta kankameshi tace “Naji amma dan Allah ka soni.” Hannunta yaje janyewa ta sake kankameshi wanda hakan yasa ya kyaleta, yana ji tana hawaye amma ya kasa hanata, a haka bacci ya ɗauke su wanda bai farka ba sai yanzu. Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauke jin komai ya dawo cikin kanshi, Alhamdulila da bai tafka kuskure ba dole yasan abinyi ya kuma kare kanshi daga aikata zina, haryau yaran da ya buge a mota yana zuwa mai cikin rai ya kuma san hakki na nan na binshi dan haka bazai bari ya sake aikata wani babban aikin dazai ƙara mikashi wuta ba. Yanda taja bargo ne yasa shi tsorata ya kalleta hankali a tashe yace “Menene kuma?” Kuka ta fashe dashi tana cewa “Kabir sai fa dana ce maka kar mu gangara,” ta ƙarasa maganar tana kuka, mamaki ne ya rufeshi yace “To ai bamu gangara ba.” Ta girgiza kai tana sake shashekar kuka tace “Da alama ba’a hayyacinka kake ba nikam na shiga uku na, wallahi ban ɗauka zakamin karfi ba.” Jiyai kanshi ya ɗaure nan ciwon kanshi ya ƙara tsanan ta yace “Me kike san cewa? Bayan na tuna komai kuma ba abinda ya faru?” Ta sake sa kuka tace “Iya abinda ka tuna dai kenan amma bayan na kwanta bacci kawai naji ka yayemin bargo ka hau cire mun kaya kamin ta ƙarfi……….” Ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani irin kuka, hannu yasa ya toshe mata baki da sauri yace “Bangane nasa miki ƙarfi ba bayan ko taɓa ki banba. Yaye zanin kaɗan tai sai gata ba pant, sai jini a matse-matsin kafafunta, idanu ya zaro jikinshi ne ya hau rawa, yama kasa gane meke faruwa dan shi dai a iya saninsa bai ko ta ɓata ba, to menene wannan? Hawaye ta share tace “Shikenan ka cuceni, shiyasa nake ta cema na zina ba, dan kaga ina sanka shiyasa kai min ƙarfi, na shiga uku nikam shikenan rayuwata tazo ƙarshe.” Kabir gaba ɗaya ya kasa tunani, jikinshi ne kawai yake rawa dan hanayensa ma sai rikesu yai saboda rawar da sukeyi, da sauri ya mike ya nufi hanyar toilet, cikin sauri tace “Ka ƙira min Mumy tsoro nakeji….” Tai maganar cikin rawar murya, dawowa yai da sauri yace “Na kira miki Mumy kamar ya?” Hannunshi ta kamo tace “Bazan iya tashi ba, nan dina zugi yakeyi.” Tai maganar tana nuna gun da hannu, gaba ɗaya zufa ke keto mai wannan masifa da bala’i da me yai kama yaushe ya kusanceta? Shi ba shayeshaye ba taya zaiyi abu baisan yayi ba? Shikenan rayuwarshi ta kare ace kamar shi fyade yakewa mata? Matqn mq kanwar Mumy? Inalilahi, kalaman Nabeela ne suka dakatar da tunaninsa datace “Kabir ka ketan haddi ka maidani budurbazar shikenan gwara na mutu na huta.” Kallanta yai yace “Nidai kome zai faru karki sanar da kowa abinda ya faru, bansan sanda nai ba haryanzu na kasa gasgata zuciyata, taya zanyi abu bansani ba?” “Hmmm! Dama ance haka maza suke sai suyi abu su maidashi tsautsayi ko suce basu san me hakan yake nufi ba, bari na ƙira Mumy ta maidani gun Inna,” tai maganar tana ɗaukan wayarta, da sauri ya amshe wayar yace “Ki bari mu samo mafita yanzu ki tashi ki wanke jiki ki fita zan fitar da bedsheet ɗin.” Man ta fara ƙoƙarin mikewa ya taimaka mata ta shiga banɗaki shi kuma ya fito da bedsheet kamar munafiki yasa a bayan motarshi sannan ya dawo, yai sa’a daya dawo bata ɗakin, kasa bacci yai kawai ya zauna ya dafa saman goshinsa, meke faruwa? ******* Maryam ce ta kalli Baban Areef idanunta sun ciciko tace “Yanzu haka zamu cigaba da rayuwa shikenan mu bamuda sirrin kanmu? Ni kenan komai zakamin sai abinda aka tsara ma?” Fuska ya tamke sosai yace “Kiyi hakuri kyaje nan gaba.” Idanuwanta ne suka ciciko da kwalla tace “Wannan wani irin aurene ace sam ban da ikon kaina bare insa ran samun ƴanci na? Ace kullum sai yanda akai dani, komai muka tsara sai ka kwashe ka sanar mai? Bamu isa muyi sirri ba?” Hannu ya ɗaga mata alamar ta dakata sannan yace “Kul wallahi na faɗa miki duk wani abu daya shafi Abbana dole ki darajashi kin kuma san sauran in baki bi ba.” Yana kai nan ya mike ya fita, hawayenta ta share ya dade yana cewa zata cigaba da karatu yana ki amma yanzu da ya amince ta sa ran amincewar ta gaske ne saboda har takardunta ya amsa kawai sai gashi an dawo mata dasu wai Baba yace kula da yara zatai ko karatu? *** Washe gari kamar wasa mutanen nan suka ce yaje Aroma cafe, nan yai shigarshi cikin hadadiyar shadda wanda ta sa kyansa kara fitowa, hula ya saka ya sa agoggo da takalmi, nan fa ya fito Muhammad Baqeer dinsa, Salim cikin atamfa ya shirya kasancewar ba mota a hannunsu yasa Salim yace zai tambayi Zainab, sai dai Baqeer kai tsaye ya hanashi yace gwara su nema ko suyi haya amma ba gunta ba, dariya Salim yai yace “Naga fa alama ƴar kunya kukeyi yanzu fisabillahi da mu samu motar bati gwara a sa mu biya?” Gefe Baqeer ya kalla yace “Kuma ko kunya mu kuma sai mu tabe da aran motarta, to Allah a’a ko kuɗin iya kacinsu kenan gwara mu bada.” Baki Salim ya buɗe yace “Hmmm ai sai muyi kallo daga gefe tunda kunfi kusa.” Baqeer sam bai maida hankali kan me yace ba sai da wasu dakiku suka wuce sannan ya fahimta da sauri yai gyaran murya yace “Munfi kusa a ina kenan?” Waya Salim ya ɗauka ya fito yana cewa “Wai a duba a gani ko?” Yana kaiwa nan yai waje, Baqeer yai dan tsaki yace “Shidai kullum in baiyi zolaya ba baijin dadi,” sai kuma yai jimm da gaske sunfi kusa kamar yanda Salim yace? Baisan sanda ya dan motsa leɓensa ba, Salim bai da de sosai ba ya dawo nan sukawa Dada sallama suka fita dan ita kanta bai faɗa mata inda zasuje ba. Sunje cafe ɗin suka tarar bai zo ba, minti biyar sukai Baqeer jiki a sanyaye yace “Salim mu tafi dan Allah.” Kallanshi yai yace “Ko mu ɗan jira?” Kai ya girgiza yace “Ba amfani dama can ban yarda zasuzo ba ko ka manta me ya faru?” Salim jiki a sanyaye ya kalleshi zaiyi magana sai ji sukai ance “Muhammad?” Kallansu yai dan haka yake amfani a IG saboda baisan a ganeshi, matashin saurayin ya ƙara so ya mika mai hannu suka gaisa yace “Sunana Nasir, wanda mukai magana.” Zama yai suka ƙara gaisawa sannan Salim ya gabatar da kanshi akan shine manager na Baqeer, haka suka zauna akai reviewing contracts ɗin, Baqeer yace a canza wasu abubuwan nan shima Nasir ya ƙara gyara abinda suke so, a ƙarshe Baqeer yace sai sunsa contracts din na shekara ɗaya sannan in za’a sake renewing dole sai dai in su duka bangarorin biyu sun yadda za’ai, nan suka amince aka sa hannu, Nasir sosai ya ƙara gamsuwa da Baqeer dan yanda yake magana kaɗai zakasan yanada talent sosai, anan ya fito da wayarshi ya sake nuna musu wasu zanuka da yai aka ɗin ka, sannan yace dan yana basu zane bazai hana wasu ba, suka amince akan sai dai kar ya bawa wasu irin nasu, cike da jin daɗin handa komai ke tafiya daidai Salim ke kallansu sai hamdallah yake a cikin ranshi, a kuma nan suka biya Baqeer 50k ɗinshi na duk wata sannan suna jiran zane guda goma, zasu bashi rabi in yai zana 5 sannan su bashi ragowar kudin in ya zana ragowar, nan sukai order na drinks suka sha sannan sukai sallama kowa hankalinshi a kwance. Salim yana ajiyeshi ya juya dan yabar shago a kule, Baqeer ne ya kalli Dada sannan ya sanar da ita abinda ke faruwa, guda ta shiga yi ji take kamar ba wanda yakaisu farinciki tace “Baqeer lalai idan Allah ya tsara bawa zaiyi arziki ko mutane zasu haɗu su hanashi sai Allah ya tada shi.” Murmushi yai yace “Dada ba komai kaddara ce sai dai a yanzu na gane kaddarar nan itace tasa na gane kaina, na gane mutanen dake tare da ni sannan na tashi na nemi abu da kaina bawai da taimakon Baba ba, ada na ɗauka yafi sona akan kowa na duniyar nan, wanda har nake shakkar san da yake min yayi yawa yana rufemai ido da bai ganin laifina sai dai yanzu na gane.” Tausayin Baqeer ne ya kamata tana gani ya wuce ɗaki, laptop ɗin daya siya ya buɗe irin ta zane mai pencil a jiki, bai ma da de da siyanta ba, har zai fara sai kuma ya ciro wayarsa, number Zee ya kurawa ido haka kawai yakeji yana san sanar da ita abinda ya faru, shiru yai yana tunanin ta yanda zai fara sai ya mata text ‘A dawon da abuna da aka ɗauka." A lokacin Zeey na kwance kan cinyar Mumy suna kallo ita kuma tana daddana waya, Nabeela na zaune daga gefe tayi shiru tana tunani. Ganin sakon Baqeer yasa ta mike zaune da sauri ta karanta, murmushi tai ta rubuta “Nace sai an ban hakuri.” “To ai laifin hakurin ne ban san nayi ba.” Ɗaki ta shige ta faɗa kan gado tace “Ka ƙira na faɗa ma mai kai.” Kallan wayar yai ta turo “Allah ka ƙira!” Yanzun ma kallan wayar yai kai ya girgiza sannan yace “Reason?” Smiley’s ta turo na rike baki tace “Haka kace? Shikenan.” Kiranshi tai ya girgiza kai yana murmushin da shi kanshi bai sani ba ya ɗaga “Inalilahi!” Kawai abinda tace kenan ta kashe, hankalin Baqeer ne ya tashi cikin sauri ya ƙirata, tana ɗagawa yace “Lafiya? Meya faru?murmushi tai tace “Hmm haka ake so.” Sai a lokacin ya gane me yake nufi kamar zai yi magana sai ya fasa “Me ya sani a kanta? Shi komai nashi ta sani shifa? Ko cikaken sunanta bai sani ba, kawai jiyai bai kamata ya faɗa mata ba, cikin wata murya yace “Ke kaɗai ce a gida?” Hankali a kwance tace “A’a yayana baya nan, to ni da Mumy na ne sai sister ɗinta, Dady ma bai nan.” Kai ya jinjina yace “Ku biyu ne kenan?” Nan ma tace eh daga ni sai shi, Mumy tace mun isa. Shiru suka ɗan yi tana mamakin tambayar datazo kai tsaye, zatai magana taji yace “Maryam fa? A makaranta kuka haɗu?” Gabanta ne yai wani irin faduwa me Ya Baqeer yake tambaya? Me yake san tace? Kalamansa ne suka sake katse ta dayace “Secondary ko FCE?” Muryarta ce ta ɗan sarke……… Umm Asgar Ce Da Ayusher Muhd *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BIYAR* {55} Ta buɗe baki ta rufe ta sake buɗewa ta rufe ta rasa ma amsar daya dace ta bashi, to ita a yanzu tace mishi a ina tasan Maryam bayan har yau bai gane wacece ita ba. Kasa bashi amsa tayi sai cewa tayi "kun yi waya da Umma?" Tana lafiya dai ko?" Ɗan murmushi yayi yana jin wata irin nutsuwa tana ratsa zuciyarshi, yadda Zeey ta damu da Umma abun yana yi mishi daɗi. A shagwaɓe tace "Ya Baqeer," sai da yaji ƙiran sunan nan har tsakar kanshi. Gyaran murya yayi yace "tana nan lafiya, baki je kin ganta ba?" "Na kwana biyu ban je ba amma In Sha Allah zan samu time naje na dubata, kasan fa yanzu mune idanunka dole mu dinga kai ƙafa akai-akai tunda mun san yadda Umma take a wurinka," ta ƙarashe maganar cikin kwantar da murya kamar tana gabanshi. Haka nan take jin wani farin ciki yana ratsa zuciyarta, ta rasa lokacin da hakan ya faru amma a yanzu ta tabbata ba zata iya rayuwar da babu Baqeer a cikinta ba. Sun daɗe suna hira wacce fiye da rabinta tsokana ce suke yiwa junansu. Bayan sun gama wayar Zainab ta kwanta rigingine tana kallon ceiling tana sakin wani ƙayataccen murmushi, so kawai take yi ta ganta a gaban Baqeer sai dai bata cika so tana yawan zuwa wurinshi ba a yanzu kada ya zamanto kullum ita take kai ƙafa ya kamata ace ko yaya ne shima yana kawo mata ziyara idan fa har suna son taking relationship din su to another level. Kaji Zainab dai wai relay, dama kuna relationship ne? Tayi wa kanta tambayar data kasa bawa kanta amsa tunda dai tasan Baqeer bai taɓa furta yana sonta ba yanayinshi ne yasa take ganin kamar shima yana sonta kamar yadda take son shi. ***** Yau tun safe ta tashi da aikin taliya da aka kawo mata daga nan maƙwabtansu za'a yi musu ta gara, da yake tun bayan data sayawa Hadiza injin markaɗe da kuɗin kujerunta data sayar sauran ƙudin daya rafe sai ta sake sayen injin taliya ta koma kan sana'arta tunda dama ana ta zuwa nema. Yanzu ta ɗauke hankalinta daga kan mutanen gidan data lura babu abinda suke so da gani irin kasawarta ita da ƴaƴanta. Tana kallon Jamila dake girkin ranar sai kaiwa da kawowa take yi kamar me neman wani abu ita dai ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba, da fai ta lura ba kulata Umma zata yi ba sai ta matso kusa da ita cikin murya ƙasa-ƙasa kamar wacce bata so aji me zata ce tace mata "kin san nan Mallam yazo yana faɗa akan ana yi mishi sata ko?" Bata jira Umma ta amsa ba ta cigaba da cewa "to ashe dai Kamalu ne yake zuwa yana kwashe mishi kayan shago yana kawowa uwar ta ɓoye wai kayan lefe yake tarawa aure zai yi, ko wane sakarkarun iyayen ne zasu ɗauki ƴa su bashi bayan sun san ba nutsuwa gareshi ba, ai dai zamu sha kallo duk ranar da Mallam yasan su suke ɗaukar mishi kaya." Kallonta kawai Umma tayi ta mayar da kai akan aikin taliyarta don ita dama ba shiga irin waɗannan gulmace-gulmacen nasu take yi ba shi yasa suke jin haushinta don duk yadda ka kai da iya tsegumi bata taɓa tofa nata a ciki sai dai ta bisu da Allah ya kyauta kawai. Wucewa Jamila tayi tana cewa "Ai ke matsalarki kenan, babu dama a kawo miki ƴar magana ana so a ɗan tattauna dake sai kiyi wani girim kamar ba kya magana." Murmushi kawai tayi ta cigaba da aikinta, Jamila kenan. Ita yanzu har ta manta da yadda suke haɗe mata kai ita da Abu kowaccen su sai ta ɗauko gulmar ƴar uwarta ta rasa da wanda zata yi sannan suke sanin da zamanta, ko ance musu mahaukaciya ce ita da zata biye musu bayan tasan irin zaman da suke yi da ita. Tana gama aikinta ta tattare wurin ta gyara sannan tayi shigewarta ɗaki ta bar Jamila a wurin ta bita da harara, tana jin takaicin yadda Fatima ke yi musu sam bata shiga sabgar su duk abinda zasu yi mata bata magana sai in sun ƙureta sannan take maida martani ɗaya-biyu tayi shigewarta ɗaki ta barsu ta ciwon zuciya. ***** Tunda Bello ya tafi Germany ta saka ƴan kuɗaɗen daya bar mata a gaba tana sayi banza sayj wofi ko abincin da Habi take girka musu bata ci sai dai tayi order a kawo mata Habi ta fita ta karɓo, babu abinda take yi daga kwanciya sai kwanciya sai dai tayi wanka taci gayu ta naɗe akan kujera tana yawo akan social media, ita ce ig ita ce tiktok don whatsapp ma ba sosai take hawa ba sai idan zasu yi video call da Bello. Duk wani aikin gidan Habi ce ke yi dama can Asiya malalaciya ce bata son moruwa sam shi yasa ta sakarwa Habi aikin gidan nata gaba ɗaya duk da ba wani aikin kuzo mu gani bane tunda ba yaran da zasu ɓata wuri gareta ba. Idan Habi taga yadda take kashe kuɗi tayi magana sai ta rufeta da faɗa tace tana yi mata baƙin ciki don daga Allah ya ɗagata ta samu rayuwar hutu shine sai ta nuna ƙyashi da hassadarta to ta dai kusa tafiya ma ta bar mata ƙasar idan ta daina ganinta sai kuma taga da wanda zata yi, don haka Habi ta daina yi mata magana duk abinda tayi sai ta kawo idanu ta zuba mata. ***** A yanzu Baqeer ya samu nutsuwa ya samu kwanciyar hankali, har wata ƴar ƙiba yayi sanoda kwanciyar hankalin daya samu. Baya da matsalar komai saboda dai Alhamdulillah yana samun kuɗi da contract ɗin da yayi signing gashi kuma kamar kada yayi signing contract ɗin sai mutane suke ta nemanshi da son yayi musu designing ɗinkuna, ga mahaifiyarshi da yake yiwa aiken kuɗi akai-akai haka ƴan uwanshi ya cigaba da taimakonsu kamar da tun ma ba Hadiza ba da dama shine yake ɗauke da nauyin gidanta. Anan ɗin ma ya wadata Dada da dukkanin abun buƙata don baya jira sai ƴaƴanta sun kawo mata duk abinda yasa zata buƙata yana ƙoƙarin ganin ya ajiye mata, tun daga kan kayan abinci, kayan masarufi, fruits ne da duk dai wasu abubuwa da ya kamata, gashi lokaci zuwa lokaci yake turawa Umma kuɗi tayi mata miya ta bawa Salim ya kawo mata duk don ya rage mata ɗawainiyar da take yi dasu. Sosai yake tausaya mata ganin girma ya kamata gashi kuma komai na hidimar gidanta ita take yi ba mataimaki gareta ba sai yaran maƙwabta idan sun shigo waɗanda baka raba gidanta dasu. Har ɗan ƙaramin gas ya saya mata duk don ya sauƙaƙa mata ya rabata da hura wuta da itace. Kullum kuwa ta buɗi baki albarka take saka mishi tana addu'ar Allah ya yalwata arziƙinshi yasa albarka a cikin nemanshi ganin yayi mata abinda ƴaƴan data haifa basu yi mata ba. Yau yini yayi yana sketches daya gaji ne ya fito waje don yasha iska. Leƙawa yayi ɗakin Dada zai ce mata ya fita don kada tazo tana nemanshi bata ganshi ba sai ya ganta a zaune akan sallaya ta jingina da bango tana gyangyaɗi. "Dada" ya kira sunanta bata s bs da ya ɗan ɗaga murya ya ƙara kiranta sannan ta buɗe ido tace "na'am Baqeeru, wani abu kake so?" tana gyara zamanta. "Fita dama zan yi nace kada kizo kina nemana sai na tarar kina bacci, ai gara ki kwanta kada jikinki yayi ciwo kina bacci daga zaune". Girgiza kai tayi tace "ai yanzu na zan tashi na ɗora girki da yake ma ba wani aiki bane mai wahala tunda ka sayo wancan abun shi yasa ma har ka iskeni ina bacci, sai dai ka tsaya ka kunna mini murhun kafin ka fita kasan har yanzu ba sanin yadda zan kunna nayi ba". Ƴar dariya yayi yace "Ke dai kawai kice tsoro kike ji kada ki ƙone shi yasa ba kya iya kunnawa da kanki bayan na nuna miki yadda ake yi ba wani wahala ne da kunnawar ba." Tashi tayi ta bishi a baya tana cewa "naji ɗin ni dai kada ka fita baka kunna mini ba." Sai da ya kunna mata gas ɗin ya nuna mata yadda zata yi ta kashe idan ta gama koda zai daɗe bai dawo ba kafin lokacin sannan yayi mata sallama ya fita. A ƙofar gida ya haɗu da Tanimu zai shiga gidan hannunshi riƙe da babbar leda. Yana ganinshi yace "kai kuma daga ina? Duk yau ban ganka ba saboda babu zuwa makaranta ko." Dariya Tanimun yayi yana sosa kai alamun jin kunya don duk yau bai leƙo Baqeer ɗin ba yace "Wallahi yau a shagon su Nuhu na yini ina tayasu aiki shine ma na karɓo wasu kaya nake so ka yanka mini sai naje na haɗa." Juya keken yayi suka koma cikin gidan yana cewa "ya kamata dai ka dage ka koyi yankan nan da kanka gashi kana son hawa keke amma ka kasa mayar da hankali ka tsaya ka koyi yanka sosai." Dada na ganin shigowarshi tace "Har ka dawo ko fasa fitar kayi?" Tsayawa yayi ya mata bayanin abinda ya shigo dashi sannan suka shiga ɗakinshi. Karɓar kayan yayi Tanimu yayi mishi bayanin abinda yake so yayi, da taimakon shi Tanimu ya yanka kayan don yace ba zai yanka mishi ba sai dai ya nuna mishi yadda zai yi tunda dukkansu koyo suke yi idan bai tsaya ya iya tun yanzu ba sai yaushe zai iya. Yana kallon yadda Tanimu yake yankan yana tunanin ya kamata ya sayi kekuna ko guda biyu ne ɗaya manual ɗaya na wuta su gyara shagon ƙofar gida su zuba su fara aikin anan kafin ya samu ya buɗe babban shago yadda yake da buri, don wuri babba yake so ya buɗe inda zasu dinga ɗinki har da ready made ba wai sai mutum ya kawo kayanshi ba to amma yasan irin wannan wurin sai a hankali zai buɗu ba wai lokaci ɗaya zai cimma wannan manufar ba shi yasa yake so su fara da ƙaramin shagon a gefe guda kuma yana cigaba da sayar da sketches ɗin shi ga kuma contract ɗin da yayi signing ana biyanshi albashi duk wata banda kuɗin da suke biyanshi duk lokacin da yayi musu designing kaya, yasan a hankali da abinda yake samu cikin lokaci ƙanƙani zai buɗe babban shagon kamar yadda yake buri amma yafi so ya fara da ƙaramin wurin hannunshi ya goge a ɗinkin kafin ya buɗe wancan ɗin. ***** "Abu, Jamila." Ya shigo yana ƙwala musu kira tun daga soron ƙofar gida har ya shigo tsakar gidan bai daina ƙwala musu kira ba. Kowaccen su ta fito daga ɗaki, Abu tace "haba Mallam wannan wane irin kira ne haka tun daga ƙofar gida mutane na ji, ai ko miye ma sai ka bari har ka shigo gida." Wata uwar harara ya jefa mata kafin yace "anƙi a bari a shigo gidan, wallahi Abu ki kiyayeni kada fa kiga ina sakar miki fuska kice zaki kawo mini raini sai naci mutuncin ki wallahi. Ina ƴaƴan naku suke? Wallahi yau sai an fitar mini da ɓarawon da yake zuwa yana yi mini sata a shago don ba yarda zan yi ba, haka kurum kuna nema ku karyani bayan baku san da yadda nayi na samu kuɗi na kafa jarina ba sai yanzu da kuka haifi lalatattun ƴaƴa zaku dinga turasu kasuwa suna yi mini ɗauki ɗai ɗaya tun ana yi da kaɗan-kaɗan ina shiru gashi yanzu har an fara ɗibar masu yawa." Gyara tsayuwarta Jamila tayi tace "sai kaje can ka nemi masu yi maka sata amma dai ba ƴaƴana ba tunda kai kanka kasan karatu suke yi basu da lokacin kansu bare har suje kasuwa suna yi maka sata, ahto. Sata kam ai sai zauna gari banza marasa aikin yi waɗanda basu ajiye komai ba sai yawo daga wannan inuwar zuwa waccan inuwar amma ba ƴan makaranta ba masu abun yi." Abu da bata saka baki tayi tsalan jin abinda Jamila tace don tasan Kamalu take yiwa gugar zana tace "to wa kike nufin yana yi mishi satar? Ba dai Kamalu kike so kice ba ko? Don wallahi ɗana yafi ƙarfin yayi sata sai dai kaje can ku nemi ɓarawon kayanka amma ba a ɗakina ba. Sannan ai ba mu kaɗai bane masu ƴaƴa ita Fatima me yasa baka kirata ba sai mu kaɗai saboda mu ka rainawa wayo." Gaba ɗaya sai suka kalli ƙofar ɗakin Umma da duk abinda suke yi tana jin su bata saka musu baki ba ganin ba'a saka da ita ba, ko yansu ma da Abu ta ambaci sunanta bata nuna taji su ba bare ta fito tace wani abu sai ma ta gyara kwanciyar ta tana cigaba da jan carbinta kamar bata ji meke faruwa a tsakar gidan ba. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA SHIDA* {56} Ana cikin haka sai ga Kamalu ya shigo ai kuwa Badaru na ganin shi ya damƙi hannunshi yaja shi har ɗakinsu yana cewa "Wallahi bazan yarda ba sai ka fito min da kayana da kake zuwa kana sacewa a kasuwa, nasan babu mai yi min wannan aikin sai kai tunda duk cikin ƴaƴana kai ne gagararre, haihuwa asara." Abu da tun lokacin da ya fara jan Kamalu ta biyo bayansu tayi caraf tace "A'a wallahi Mallam kada ka ƙara kiran ɗana da haihuwar asara haka kuma ban haifi ɗan iska ba, haba ace yanzu duk cikin yaran gidan nan Kamalu kaɗai zaka tsame kace shi yayi maka sata saboda shi an tsane shi ba'a son shi. Idan da gaskiya ai sai kayi bincike idan ka kamashi da laifi sannan ka iya cewa komai ba yanzu da kake lalube cikin duhu ba." Duk da hararar da yake jifanta dashi bai sa tayi shiru ba sai da ta dasa aya tukuna, shi kuwa Kamalu fito ma yake yi da baki yana kallon su ɗai-ɗaya kamar bai fahimci akan me suke hatsaniyar ba. A fusace Badaru yana nunata da yatsa ya fara faɗin "Duk wa ya lalatashi idan ba ke ba shine har zaki zo kina cewa an tsane shi za'a yi mishi ƙazafi, to ba lalataccen bane haihuwar asara wanda bai iya tsinananwa kanshi da komai ba sai dai ayi mishi. Wallahi tun muna shaida juna ka fito min da kayana idan ba haka ba kotu ce zata rabani da kai," ya ƙarashe maganar yana kallon Kamalu da sam hankalinshi baya wajenshi, kaya ne dai yaci kuma ba zai bayar ba sai dai ya ɗauki duk matakin da yake ganin ya dace, dolene ya saci kaya ya hada lefe ehe! Kallon Badaru yayi a wani shagiɗe cikin magana irin tasu ta gagararrun ƴaƴa yace "Don baka so na ba shine zai sa ka ƙala mini sharri ba, haka kurum kowacce shara ka ɗebo sai ka watsa ta a kaina, to idan baka so na ka kai ni bolar ƴaƴa ka jefar mana." Baki buɗe Badaru yaje kallonshi, da ƙyar ya iya cewa "Ni kake faɗawa maganar banza irin wannan Kamalu? To wallahi zaka fita ka bar min gida kaima tunda ba da uwarka muka haɗa kuɗi muka yi ginin ba ah to, na kori Baqeer ma babu abinda ya dameni bare kai gayyar tsiya haihuwar asara." "Kafa daina aibata mini ɗa Mallam bana so, kaje can ka nemi ɓarawon kayanka amma ba Kamalu ba. Taho mu tafi kaji," ta cewa Kamalu, suka fice suka bar Badaru a ɗakin yana cigaba da bambamin masifa don fa ba yarda zai yi ba sai an fito mishi da kayanshi, haka kurum yana ji yana gani ba za'a yita saka shi asara ba. ***** Tun daga waccan ranar Kabir ya ƙara janyewa daga Nabila tunda ya fahimci babu alkhairi a tattare da taraiyar su, gaba ɗaya ya ƙauracewa zaman gidan idan ya fita tun safe baya dawowa sai dare ya tsala sannan kuma ya daina barin ƙofar ɗakin shi a buɗe ko shiga kawai zai ya fita kuwa. Duk wata hanya da Nabila zata ganshi ta ƙara cusa kanta a wajenshi yayi ƙoƙari ya tosheta to itama ta ɗan ja baya dashi tunda wancan al'amarin ya ratsa tsakaninsu. Yanzu ba kasafai ta fiye nemanshi ba saɓanin da da ko bata ganshi ba ta dinga damunshi da waya kenan tana tambayar yaushe zai dawo gida yau tunda ta tashi bata sanya shi a idonta ba, irin waɗannan abubuwan dai da take amfani dasu tana manipulating ɗin shi don shi sam babu sonta a cikin zuciyarshi, to ta yaya ma hakan zai kasance bayan ga matsayinta a wurinshi, gashi yanzu duk yadda ya kai da kauce mata sai da ta janyo suka aikata abinda tun farko yayi ta guje musu afkuwarshi. ***** Tunda Badaru ya shige ɗaki abun duniya ya taru yayi mishi yawa, ya rasa inda zai tsoma rayuwarshi yaji daɗi. Yana ji yana gani duk wani buri nashi na rayuwa ya wargaje, dama akan Baqeer yake da hope to gashi shima abinda yayi mishi yayi watsi da duk wasu sadaukarwa nashi yayi fatali da burinshi ya watsa mishi ƙasa a ido yana ji yana gani yayi bankwana da tsohon burin daya gina rayuwarahi akai. Tashi yayi yana zagayen ɗakin ya kai gwauro ya kai mari ya rasa abinda ke yi mishi daɗi, yadda al'amuranshi suke ta cakalkalewa shi yafi damunshi gashi yanzu kasuwar ma sai asara kawai yake tafkawa, ya rasa ta inda kuɗaɗenshi suke ƙarewa sai kaɗar da dukiyarshi yake yi yana ƙara jari amma da ƙyar yake iya haɗa uwar kuɗin bare a fitar da riba. To ko dai filin Baqeer zai saka a kasuwa ya ƙara jarin tunda ma ai shi yayi ta wahala da Baqeer ɗin har ya zama abinda ya zama da yayi mishi sanadin mallakar filin, wani murmushi ya saki da yin wannan tunanin don yasan idan har aka sayi filin da daraja ba ƙaramin alkhairi zai samu a ciki ba in yaso sai ya ƙara jarin ya tashi kasuwancin shi abinda yayi ragowa kuma sai ya buɗe shago a ƙofar gida ya zuba kayan masarufi. Tashi yayi ya janyo jakar da yake ajiye duk wasu muhimman abubuwa nashi, zama yayi dirshan a ƙasan ɗakin ya buɗe jakar yana yi mata filla-filla yana neman takardar filin da yasan ba nashi bane. Hankalinshi ne ya fara tashi da yaga har ya kusa gama fitar da kayan cikin jakar bai ga takardar ba. Jiki na rawa ya cigaba da dubawa amma har ya gama bai ganta ba, zazzage jakar yayi a ƙasa ya fitar da komai amma bai ganta ba. Ai tuni hankalinshi ya tashi ya dinga bin takardun nan ɗaya bayan ɗaya yana ƙara dubasu amma bai ga takarda mai kama da wacce yake nema ba. A sukwane ya tashi ya fita daga ɗakin har yana tuntuɓe da dokin ƙofa ya fita yana ƙwalawa Kamalu kira. Ai ba Kamalu da ake yiwa kiran mafarauta ba kowa a gidan sai da ya fito idan ka cire Umma da bata shiga sabgarsu idan har ba an saka da ita ba. Gaba ɗaya suka tsaya cirko-cirko suna kallonshi, yana ganin Kamalu yaje ya cakumi wuyan rigarshi yana cewa "Wallahi ƙaryarka tasha ƙarya, duk inda ka kai mini takardar filin nan sai ka fito da ita don wallahi bazan ɗauki asara ba." Kici-kicin ƙwace wuyan rigarshi yake yi amma ya kasa don ba ƙaramin ruƙo Badaru yayi mishi ba, sai da Abu taga yana neman halakar mata da yaro ta taso ta ɓamɓare hannunshi da ƙyar tana cewa "Haba Mallam kashe shi zaka yi ne?" "Ki rabu dani na kashe ɗan iskan yaron nan wanda babu abunda ya sani sai shaye-shayen banza da wofi, wallahi Kamalu ka fito min da takardun filina idan ba haka ba kotu zan maka ka don bazan kamunta ba ka kasheni tun kwanana bai ƙare ba," Da ƙarfi Kamalu ya ture Badaru jin shakar dayamai yasa numfashinsa ya fara sarƙewa, Badaru baya yai sai kuwa ya bugi bango, ihu ya kwalla jin wani uban zafi ya ziyarce shi a kugunshi, Kamalu a tsorace ya kalleshi yana sauke numfashi, su Abu da Jamila kuwa sunyi kanshi, Jamila ce ta saki salati cike da ƙara tace "Wannan ɗa lalai anyi haihuwaf asara, kashe shi kake sanyi? Inalilahi yau naga abinda yafi ƙarfina Malam, sannu." Badaru da kyar ta taimaka mai ya miƙe yana rike da kwankwaso, Kamalu da sauri yai waje dan Abu ce tamai alama da yai maza ya fita daga gidan, gaba ɗaya Badaru dakyar yake tafiya ji yake kamar ya gurɗe kugunshi, magana kuwa ya kasa yinta saboda uban azabar dake ratsashi, ɗaki Jamila ta kaishi ya kwanta tana mai tausa, wai yau kamar shi danshi zai hankaɗe? Lalai gobe in ya warke dole ya sallami Abu ta koma kauye, matsala ɗaya ƴar uwarsa ce yanzu tana tafiya mutanen kauye zasu isheshi da zirga zirga sai dai dole ta tafi daga ita har ɗanta, Fatima kam tunda ta fito taga abinda ya faru ta koma ciki, ita yanzu zaman gidan kawai yinshi take dan ba yanda zatai dan babu wani abu dake burgeta a ciki. Ranar duk yanda yai bai samu bacci ya daukeshi ba, filinshi kawai yake tunani, ga azabar ciwo da yake ji, wajen asuba ma da gyangyadi ya daukeshi yai mafarkin wai Kamalu ya saida filin ya cinye kuɗin firgigit yai ya farka, hankali a tashe ya yai dafa kirjinshi dake mai nauyi, lalai Kamalu dole ya bar mai gida dan ya tabbatar wannan tsaf zai nakasa shi. ******    Baqeer kam komai Alhamdulila dan ya turawa mutanen nan zane nan kai tsaye sukace komai yayi akan zasu turo mai kuɗi, sunyi mamakin kwarewarshi dan shi kanshi yanzu yasan kwarewarshi tafi ta da saboda karatun da yake yi yanzu, yanka kuwa inya maka shi lalai sai ka dauka wanda ya shekara biyar yana ɗinki ne, haryanzu dai matsalarshi ɗaya itace ta taka keken ɗinki wanda Tanimu ke taimaka mai suma makarantar basu damu ba saboda su kansu mamakin kwarewarshi a yanka da fitar da styles suke, yau suna tasowa yai tunanin wucewa asibitin Junaid dan yanada appointment da physio ɗin dake taimaka mai, da yamma wajen hudu suka isa anan unguwar sukai sallah sannan suka ƙarasa shi da Tanimu suna tafe ba wanda yakewa wani magana dan Baqeer ba kasafai yake zance ba shi kuma Tanimu bai fiya san damunshi da hira ba, wannan dalilin ne yasa zamansu ya ƙara kwari, a bakin gate ɗin suna shiga ya canza yanayin fuskarsa sakamakon motar Zee daya gani, bayan yau kwana biyu kenan bai sata a idanshi ba amma shine zai ganta gun saurayinta? Fuskarnan tasa ta sake murtukewa da yaso ma yace su juya ya fasa dole ma ya shiga ya nuna ya ganta. Kasan ranshi ne ya tambayeshi to in ka ganta sai akai me? Auranka ne akanta ko kuwa soyayya kuke? Bai gama tunani ba yaji Tanimu na cemai "Ya Baqeer mukaje wancan satin zamu?" Kallanshi yai wani abu na sake tasomai yana bin office din Junaid da kallo, kawai ya fara tura kekenshi zuwa office ɗin Junaid sai daya kusa isa aka budo ƙofar office ɗin da sauri ya fara neman shan kwana, ganin haka yasa Tanimu ya taimaka mai, dariyar Zee ya fara juyowa tana cewa "Kai dai wallahi baka rabuwa da neman magana, nidai Allah na faɗa ma kasan yanda zakai ka dai san halina ba mai tilastamin in banyi niyyar abu ba," ta ƙarasa maganar tana kallan Tanimu, kai taɗan karkatar Junaid ne yace "Hmm ina mamakin yanda bakya tunanin halin da zan shiga kike faɗar abinda ke ranki, ki koma mu gama magana please bansan saurin me kike ba." Ganin yanayinta yasa yasan batama san me yake cewa ba, hakan yasa ya tsaya gurum yana kallanta, Baqeer jin kalaman Junaid yasa ya cigaba da tura kekensa, Tanimu na biye dashi, itama Zeey bayansu tabi tana tafe tana murmushi, Tanimu ne ya kalleta cike da jin daɗi ya gaisheta, tana murmushi ta amsa tace "Kanin Ya Baqeer ashe kuna hanya?" Tai maganar tana kallan bayan Baqeer, tsayawa da tura keken yai yanajin yana san ganinta amma kishi ya hanashi, Junaid kuwa cike da takaici ya biyota dan shi ya tsani yaga tanaba gurgun nan mahimmanci, ganin Baqeer baice komai ba ya cigaba da tafiyarsa itama yasa ta kalli Tanimu tace "Daga makaranta?" Kai ya ɗaga sannan yace "Ko gida bamu koma ba." Ta jinjina kai tana cewa "Shi kuma yayan naka yau bayajin yin magana ne?" Junaid yai saurin cewa "Malam Baqeer ashe kana tafe, muje yau ni zan dubaka ma." Kallanshi Baqeer yai sai a lokacin idanunsa suka haɗu dana Zainab, da sauri ya ɗauke idanshi, mamaki ya ƙara kamata ganin ko jiya sunyi waya menene hakan? Me kuma ya faru? Haka sukabi Junaid nan ya dinga sashi yin exercises kala, kala yana ɗan taimaka mai, suna gamawa ya kalli Zeey yace "Paper towel please kiga harna haɗa gumi." Daukowa tai ta mikamai, idanunta nakan Baqeer da ko kallanta yakiyi, wato shi bataga gumin da yakeyi ba shima? Saurayinta kawai ta sani? Kallan Junaid yai yace "Mungode sosai!" "No karka damu, Allah ya kara sauki it seems like kana abubuwan daya kamata am sure we will get there." Kai ya jinjina kawai ya tura kekensa, Zee ta mike zata bishi yaji Junaid yace "Zeey yauwa tunda kin dawo bari ma na nuna miki abu, da na ɗauka sauri kike ashe baki gaji da ganina ba." Waigowa Baqeer yai idanunsa na kanta, kishi yake? San gwadashi taji tanayi tace "J kaima kasan anything for you, nunamin." Idanun Baqeer ne sukai jaa wani abu yaji ya tokareshi, kallan Tanimu yai yamai alama kawai su fita, da kallo ta bishi suna fita ta kalli Junaid tace "Bye." Hannu yasa ya riko hannunta da sauri yace "Zeey wai meke damunki? Menene tsakaninki da gurguncan? Kedai nasan kinfi ƙarfin gurgu shiyasa nake ta ƙoƙarin ganin na cire shirman tunanin nan a raina but yanda kike be having akanshi yana tsoratani." Hannunta daya rike ta kalla wanda hakan ya sashi sakinta tace "J karka sa alaka ta zumincin dake tsakanina dakai ta kare, sannan kalamanka duka ka jira amsar da zan baka a kansu for now banda lokacin ka." Tana kai nan ta juya ta fita, ranta a ɓace tana jin kalaman daya Baqeer ma sunfi wanda ya mata ɓata mata rai. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA BAKWAI* {57} A waje ta gansu suna neman tarar adaidaita, gabansu ta tsaya tace "Mu wuce Ya Baqeer?" Kai ya kauda yana dube-duben abin hawa, mamaki ya ƙara kamata gani take ko kishi ne ai bai kamata ya ɗin ga banza da ita haka ba, Zee kamar ke ana binki kina wulakanta mutane yau kece kike bi ana wulakantaki? Ido ta kafamai, haka kawai ya juyo yaji zuciyarsa nasan ganinta, kallan juna sukai nan danan idanuwanta suka ciciko kallanta yai shima sai kuma hankalinshi ya tashi, meya mata? Ya ɗauka barinta da saurayinta shine daidai? Jan motar tai kawai ba tare da tace komai ba tai gaba, jiki a sanyaye yabi motar da kallo, wata iska ya furzar yanajin haushin kansa, to menene laifinta? Ai tun farko yadai san Junaid saurayinta ne to jin haushin na menene? Meya sameshi? Haushin kanshi ne ya isheshi har suka isa gida baice komai ba, Dada tana zaune a waje tana jin radio yau lale na dungurmi irin na tsofafi yarinyar makota tazo ta mata tace ta bari sai dare amma yarinyar ta nace akan sai ta mata yanzu, hakan yasa ta kyaleta, ganinsu Baqeer yasa ta saki fuska ta ɗan rage sautin radio ɗin tana cewa "A'a Malam cunkumi an dawo?" "Sannu da gida Dada, amma cunkumin na menene?" "Yo fuska ce kamar an aiko ma da sakon mutuwa me kake so a kiraka dashi?" "Babu." Abinda yace kenan yai cikin ɗaki, Tanimu ne ya kalleta yana gaisheta ta girgiza kai tace "Hala an taboshi ne?" Ya girgiza kai yana cewa "Wallahi ban sani ba Dada." Baki ta taɓe tace "Bakinku ɗaya ai can ku kuka sani." Ta cigaba da sauraran radio ɗinta tana cewa "Ga abincinka can Tanimu." Ɗaukan na Baqeer yai ya fara kai mai sannan ya ɗau nashi yai godiya ya fita. Takaici duk ya gama isar Baqeer me take nufi da kallan datamai da kuma hawayen dake idanunta? Bayan ita kullum cikin fara'a take? Sam zuciyarshi ta kasa nutsuwa ji yake kamar yaje ya sameta yaji meke faruwa. **** Zeey kuwa gida ta wuce kai tsaye, tana shiga ta ruga ciki tai falan Mumy, Nabeela na falansu tana ganinta ta girgiza kai sai kuma ta canza yanayin fuskarta sannan ta mike tana cewa "Zeey lafiya? Menene?" Bata ko kulata ba sai ɗakin Mumy datai, a tsaye ta ganta tana ninke sallaya da alama lokacin tai sallar la'asar, rungumeta kawai tai tasa kuka, mamaki ne ya kama Mumy ta kalli Nabeela dake bakin ƙofa ta mata alama data tafi, hakan yasa ta juya tana taɓe baki, kallanta Mumy tai bayan sun zauna a bakin gado ta ɗag fuskarta tace "Menene Baby na? Waye ya taɓamin ke?" Kara kankameta tai wanda hakan yasa Mumy tace "Babu wanda ya isa ya samin ke kuka in kyaleshi, Junaid ɗin da kikace zaki je kija mai kune ne wani abin ya faru?" Cike da shagwaba tace "J har isa ya sani kuka Mumy kema kinsan bai kai ba, sannan kunne fa naje jamai akan ya dakatar da iyayensa dan ni bazan aureshi ba." "To meya faru kuma? Nifa kukan ne bazan ɗauka ba." Kwantawa tai luf tana cewa "Mumy ni kawai haushin kaina nakeji, inyi ta bada kaina amma yana wulakantani, haka zan cigaba da rayuwa?" "To ki rabu dashi mana dole ne? Nifa bamga wanda ya isa ya cigaba da samin ke kuma ina kyaleshi ba." Dagowa tai tace "Shine bazan iya ba Mumy yanzun ma ganin yanda ya kalleni ne yasa naji ina neman yin hawaye, anya Mumy kaina kalau kuwa? Bayan ko kalmar so bai taɓa furtamin ba?" Shafar kanta tai tace "Zeey ya kikeso nai dake? Haka kikeso na cigaba da sa miki ido kina wannan san haukan? To shi bama ki da tabbas yana sanki kenan?" Kallan Mumy tai idanunta yai raurau tace "Inadai ganin alama." "Alama shine ya barmin ke ki taho gida kina kuka? Bani numbershi." Nan danan ta zaro ido tace "A'a Mumy abinfa baikai haka ba, kawai dai haushin yanda bai kulani bane yasa naji zafi amma zamu shirya." "Zeey kinsan dai ko kowa a duniya zai gujeki ina bayanki ko? Banasan ki dinga kaskantar da kanki dan Allah ki cigaba da zama Zainab dana sani wace bata barin abu ya dameta." Kai ta ɗaga ta rungumeta tace "Insha Allahu Mumy na, thank you." Ya dade a ƙofa yana san shigowa amma baisan Nabila ta ganshi ba dan takardun abokinsa daya manta ba tabbas da bazai dawo ba, sam taki tashi daga falan, ganin Zeey ta shigo da mota yasa ya ɓoye da sauri, yana kallo ta shiga Nabila ta bita yasa yai saurin lalaɓowa ya shigo, ɗakin sa yai ya ɗauko takardun sai dai yana buɗe ƙofa yaga Nabila a tsaye ta rike kugu, turashi tai cikin ɗakin sannan ta shiga tasa key, kallanshi tai tace "Ya Kabir badai gudu na kakeyi ba?" Matsar da ita yai tare da yin hanyar ƙofa yana cewa "In gudun naki nake ma ai ba laifi tunda kina neman zama abin gudu." Yana kai nan yai saurin yin waje sam yana mamakin Nabila, tana daga cikin mutane masu hankali daya sani a mata amma baisan me ya sameta ba tunda ta fara nuna tana sanshi yake ganin wasu halaye nata da ke tsoratashi a kullum ana haɗata da Zeey sai dai ko kaffara bazaiyi ba Zeey ko tanasan mutum bazata bada kanta ba, dan tasha yin samari abokansa sai dai ba wanda ma taba fuskar soyayya bare akai ga yin waya, haka zasu karashi binta su hakura, a haka kuma Inna kullum mitarta Zeey batada tarbiyya Nabila ce mai tarbiyya shima kuma Dady kullum maganar kenan. ******** Badaru da tsamin jiki ya tashi dan ko sallah a gida yai, sai wani nishi yake yana wash-wash, Abu kam tun dare take nazari dan tasan Badaru bazai taɓa kyalesu ba daga ita har Kamalu, gashi kuma tunda ya fita jiya haryanzu bai dawo ba balle ta zaunar dashi suyi magana a samu mafita, ƙofa taji an buɗe wajen karfe shiga na safe da sauri ta leka wajen Kamalu ne ya shigo cikin sanda, lekowa tai tamai alama daya shigo ɗakinta hakan yasa ya shigo suka shige kuryar ɗaki, kallansa tai tace "Kamalu ina kake kai kayayyakin Malam da kake ɗauka kadai san bazai barmu ba balle abinda kamai ɗazu." Kallanta yai yace "Amma kina kallo shekani barzaho yaso yi?" "Na sani amma kai dai kasan halinshi, laifinka kawai zai gani ba nashi ba." Taja numfashi ta cigaba "Ina kayayakin daka ɗauka suke? Wai ma nikam Kamalu me kake da atamfofi da lasuka kamar mai tara lefe?" Kai ya kauda ya zauna a bakin gaso yace "Lefe nake tarawa sannan wai me yake min ma da zaice yamin a matsayinsa na uba?" Baki ta saki tace "Lalai Kamalu, lefe kake tarawa? Lefen uban wa kake tarawa da kudin sata?" Cike da ɓacin rai yace "Kinga Umma karki kuskura ki ƙara zaginta, ta wuce duk yanda kike tunani, Roshini dinace, sannan ba abinda zan dawo dashi wallahi sai dai yai abinda zaiyi." Yana kai nan ya mike ya fita daga ɗakin ya barta da baki a buɗe. Jamila ce tai sallama a ƙofar ɗakin Fatima, ta bata izinin shiga, zama tai tana kallan Fatima nata faman tsinke zogale tace "Fatima kinsan yarancan ya jawo Malam ciwo? Shine na zo in akwai ƴan canji a gunki ki bani na siyo mai magani dan jikinshi yayi tsami." Kallanta Umma tai tace "Dama garin neman faɗa da yara ake jawo raini, mutum sai masifa sam ba hakuri ba yadda da kaddara?" "To yanzu dai mu bar maganar ki bani kuɗi dan Malam yana warkewa sai ya hukunta Kamalu dole kuma musha kallo da guda." Wani kallan takaici Umma ta mata tace "Ke kina tunanin kin tsira kenan? Hmm kema kiyi a hankali daga ke har yaranki ba tsira kukai ba, sannan ni banida kuɗi ɗari biyar ce gata nan ki sai mai magani ita kenan gareni." Amsa Jamila tai ta fito tana cewa "Ko gidan ubanwa take samun kuɗi dan dai baza'ace kuɗin kujeru ne haryanzu take dashi ba." Magani ta siyowa Badaru ta bashi yasha tana cewa "Sai hakuri Malam, mata da yarane baka tara na kwarai ba banda ni na damu dakai da haka nan zasu kyaleka kudin magani wannan ba wanda ya iya taimakon mu dashi, yooo sannu wannan a cikinsu wanene yama?" Shi dai Badaru banda takaici ba abinda ke damunsa gashi ya kasa mikewa, a cike yake fam da kowa jira yake ya samu sauki duk sai yaci zarafinsu. ***** Wannan shine karo na ba adadi da Baqeer ya ɗau wayarsa ya duba sannan ya ajiye, ganin da gaske ya kasa bacci gashi har karfe sha biyu da rabi yasa kawai ya danna ƙiran Zee, ya gashi da duba sunanta yana rufewa, kallan wayar yai ganin da gaske katsewa zatai ba ta ɗauka ba? Ji yai an ɗauka hakan yasa ya kara wayar a kunensa, ga mamakinsa kin magana tai, shima yai ɗan shiru ganin bazatai magana ba yasa yace "Ɗazu naga yanayinki ya canza wani abin ne?" Cike da mamakin kalamansa tace "Nima dazu naga yanayinka ya canza wani abin ne?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ni ba komai." "Nima!" Da sauri yace "No ke akwai abinda ya sameki." Shiru taɗan yi kaɗan kafin tace "Ya akai ka san abinda ya dameni? Bayan ba damuwa kai da yanayin da zan shiga ba?" Kalamanta ne yaji sun dakeshi, me take nufi bayan shi kanshi tsoron matsayin data samu a zuciyarshi yake? "Nasan kinje gun saurayinki so bansan ko abinda yafaru tsakaninku bane ya saki ɓacin rai." Sam baisan sanda kalmar saurayin ta fito daga bakinsa ba, kamar tace mai ba saurayinta bane kawai sai taji batasan faɗa tunda itama batasan menene matsayinta a gunshi ba hakan yasa tace "Wai J? Ni ko kaɗan ba shi ya ɓatan rai ba, ni bana ji ma ya taɓa min abinda zai sani ɓacin rai kawai bana san naga inama magana kana shareni ne, ɗazu abinda kamin ka kyauta? Kamar wanda mukai faɗa ko bamu san juna ba?" Kenan saboda shi ne? Tambayar datazo mai kenan hakan yasa yace "Kenan akai na ne?" Cike da shagwaba tace "Nifa banasan naga ina magana ana disgani gashi kuma a gaban Tanimu ka dinga wulakantani kallo na ma kin yi kai." Shiru yai saboda jin gaɓobin jikinshi sunyi laushi jin yanda take magana kamar mai shirin kuka. Sannan ta cigaba "Allah a faɗan me nai ko aban hakuri." Shidai bazai iya faɗar kishi yake ba, dan tabbas yanzu kam ya shaida kishi ne, kuma hakurin ma bai san badawa tunda yana gani ai an mai ba daidai bane yai, hakan yasa yace "Me kikeyi yanzu?" Tace "A kwance nake." Yace "Hmm akwai pen kusa dake?" Ɗan mikewa tai ta kulla side bed lamp dake gefen gado ta ɗauko da paper tana cewa "Zane za'a koyamin?" Yace "A'a rubutu." Da mamaki ta maimaita kalmar tana cewa "To na shirya." "Yauwa rubuta A" ta rubuta yace "Rubuta S," nan ma ta rubuta yace "Sai ki rubuta F" ta rubuta tana cewa "Sai me?" Yace "Shikenan" kallan abin tak tace "Asf? Me kenan?" Ka faɗa ya ɗaga yace "Ki bincika, ni zan kwanta." Kallan takardar ta sake yi tace "Hakurin fa Allah ba'a bani ba." "In kin san amsar ki dawo ki sanar dani zan baki." "To naji, amma Ya Baqeer please karka sake disgani cikin mutane kaki kulani." "Kema ki daina......." Sai kuma yai shiru ya kashe wayar da sauri, Baqeer me kake tunani? Badai kana gurgu kake neman jawo soyayyar wace ko a haka ka ganta kasan ƴar wani bace? Zee kuwa ta dade tana kallan takardar kafin ta kwanta, zuciyarta fess kamar ba itace sukai faɗa da Baqeer ba. ***** Kwance take a ɗaki Zeey ta shigo tace "Aunty Nabs tashi ki fadamin menene ma'anar kalmar nan?" Kasa magana tai sai sake lumshe ido take, Zeey tace "Nikam kalau kike?" Nabila ta sauke huci tace "Banajin daɗi Zeey ki duba google mana." Cike da kulawa tace "Me ya sameki?" Kai ya girgiza tare da cewa "Ban sani ba haka nan nake jina ba da ɗi." Da sauri Zeey ta kamo hanunta tace "Kila ma yunwa kike ji, muje Mumy na jiran mu muyi breakfast." Kamar bazata mike ba sai kuma ta tashi ta suka fito, zama tai Mumy ko kallanta batai ba sai Dady dake tsokanarta wai ina ta shige kwana biyu? Murmushi kawai tai suka fara cin abinci, Dady sai yaban Nabila yake Zeey kam baki ta taɓe tace "Bakomai Dady tunda nasan gun Mumy I'm the best." "Oho dai kuyi ta yi nidai na fadawa iyayen Junaid suzo muyi magana." Tunda ga haka bata sake magana ba harya gama ya tashi yai ɗaki, Zeey ta bishi akan zata mai magana. Mumy ce ta kalli Nabila da ta kasa cin abinci sai wani jujuyashi take tace "Wai meke damunki?" Ta buɗe baki zatai magana sai ta fara yunkurin amai, cike da mamaki Mumy tace "Meye hakan?" Nan ma zatai magana ta fara yunkurin amai, da sauri ta miƙe tai ɗaki tana sake yunkurowa, Mumy kasa ko motsawa tai sai kuma ta tashi da sauri har tana harɗewa tai ɗaki hankalinta a mugun tashe. (Hmmm wai inji me ciwon baki.) *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA TAKWAS* {58} Hankali a tashe Mummy ta bita cikin ɗakin sai ta jiyo kakarin Nabila daga cikin toilet, cikin sassarfa ta faɗa banɗakin a take taji wani mugun rashin hankali da bata taɓa tsintar kanta a ciki ba ya rufto mata lokaci guda ganin Nabila durƙushe a gaban toilet bowl tana kelaya amai. Muryarta na rawa tace "Ke Nabila baki da lafiya amma baki faɗa mini ba? Me ya same ki?" Ita dai Nabila babu baki don sosai ta galabaita da aman da take yi, kusa da ita Mummy ta matsa ta dafa kanta tana yi mata sannu sai dai a ƙarƙashin zuciyarta tana jin wani irin tsoro, tana tsoron kada tarihi ya maimaita kanshi akan Nabila. Da sauri ta kawar da wannan tunanin ta taimakawa Nabila bayan ta gama aman ta kuskure bakinta, tana riƙe da ita har sai da ta kwantar da ita akan gado sannan ta ƙara kallonta, sai taga tayi mata wani irin fayau fuskar nan ta ɗashe tayi fari tas duk kuwa da Nabila ba fara bace, kalar fatarta chocolate color ce. Sannu ta ƙara yi mata sannan tace "Me ke damunki kuma tun yaushe ne baki da lafiya baki yi magana an kai ki asibiti ba sai ki zauna da ciwo. Ki tashi ki shirya na kai ki asibiti a dubaki, hankalina ba zai kwanta ba idan ba kai ki nayi aka duba mini lafiyarki ba." Gaba ɗaya jikinta yayi yaushi don haka ko magana bata son yi, da ƙyar ta iya buɗe baki tace wa Mummy "ai na samu sauƙi ba sai mun je asibiti ba, dama cikina ne yake ɗan murɗata amma tunda na samu nayi aman sosai naji relief, kawai dai hutawa nake son yi nasan daga na samu bacci na tashi gaba ɗaya nauyin jikin zai sakeni." Wani irin kallon tsaf Mummy tayi mata sai dai bata ce komai ba ta haɗiye abinda take ji a cikin ranta ta kaɗa kanta ta fita daga ɗakin bayan ta faɗawa Nabila lallai taci abincin da zata bayar a kawo mata kafin ta kwanta don bata son zama da yunwa. Tana barin ɗakin Nabila ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya data ke riƙe da ita tun shigowar Mummy ɗakin, gyara kwanciyarta tayi ta janyo wayarta tana kiran layin Kabir sai dai har ta ƙara i rurinta bai ɗaga ba, sake kiranshi tayi amma har ta katse bai ɗauka ba, ajiye wayar tayi akan bedside drawer, dama tasan zai yi wuya Kabir ya amsa kiranta a yanzu da yake ƙoƙarin yakiceta daga jikinshi ta kowane hali sai dai ita kuma babu niyyar barin shi a tare da ita, bata fara don ta daina ba don haka sai dai yayi kauce-kaucen shi ya gama amma dole ya dawo wajenta don bata shirya haƙura dashi ba. ***** Sai da Badaru yayi kwana biyu yana jinyar jikinshi kafin ya warware, Jamila ce tayi fama da jinyar a gefe guda kuma tana ƙara yi mishi famfo tana nuna kamar duk gidan babu wanda ya damu dashi idan ba ita da ƴaƴanta ba. Yana samun kanshi ya tada tijara ko Kamalu ya fito mishi da takardun filinshi ko su fice su bar mishi gida daga shi har Abu data take ɗaure mishi yana yi mishi sata, sai dai fa daga nesa yake duk wata tijara tashi ko kusa da Abu bai je ba bare Kamalu don yana tairon kada ya taɓa ita kanta Abun Kamalu yayi mishi ƙamshin mutuwa don yaga alamar babu imani a tattare dashi tunda har zai iya saka hannu yana neman lahanta shi in banda Allah ya kiyaye. Yana daga ƙofar ɗakinshi yace "Kinga Abu tun muna shaida juna ki faɗawa ɗanki ya fito mini da takardun fili na idan ba haka ba alƙali ne zai rabani daku don wallahi bazan yarda na ɗauki asara ba, haka kurum don rashin tausayi tun yana yi mini ɗauki ɗaiɗaya a shago har ya fara biyo ƴan kadarorina yana kaɗarwa, to bazan lamunta ba tunda dai bada uban kowa na haɗa na nemi kuɗina ba ah to." "Ba dai ubana kake neman ka zaga ba dai ko Mallam?" Tayi maganar cikin ɗaga murya don Kamaku yana ɗakinshi a kwance tana fatan ya jiyota ko ya fito Mallam ya ganshi tunda ta lura kamar yanzu tsoron Kamalun yake ji. Kamar yasan abinda take shirya mishi ya waiwaya ya kalli hanyar soron gidan inda ɗakin na Kamalu yake, murya ƙasa-ƙasa kamar ba shine yake hayagagar nan ba yace "ke fa da neman magana kike, Kawun nawa zan zaga don baki da hankali to na zagi Kawu nace na zagi wa. Ni dai ki lallaɓa ɗanki don Allah ku fito mini da takardun nan ko na samu na ƙara jari idan ba haka ba wata rana abincin da zamu ci ma sai ya gagare mu don kullum kasuwar tawa ƙara ƙasa take yi." Sai data murguɗa baki gefe sannan tace "Wai har yanzu kana nan akan bakanka na Kamalu ne ya ɗauke maka takardun fili? Haba Mallam to Kamalu ya sace maka takardun fili yayi me dasu? Gaskiya ka nemi ɓarawon filinka a wani wuri amma ba Kamalu ba don ni dai babu ɓarawo a ɗakina." Takaici ne yasa Badaru kasa sake cewa komai amma ba don ya haƙura ba don ya lura kamar da haɗin bakin Abu Kamalu yake yi mishi sata shi yasa bata so ana faɗa amma wallahi akan takardun filin nan tsaf zai ture zumuncinsu a gefe ya shigar da ƙararsu har ita Abun a wajen alƙali har sai sun fito mishi da takardun shi don kuwa dai ba yarda zai yi ba. Duk abinda suke yi Umma na daga ɗakinta tana jin su, da har zata faɗawa Badaru gaskiya ita ta ɗaukarwa Baqeer takardun filinshi ta kai mishi kuma har ya sayar yayi amfanin da zai yi da kuɗin don ya daina ƙalawa mutane sata sai dai ta rabu dashi don ba yanzu take son yasan ita ta ɗauka ta bawa Baqeer ba don a yadda ya manta yana da ɗa mai wannan sunan ba taso ya tuna dashi har sai a gaba zuwa lokacin da zai yi dana sanin da baza tayi mishi amfani ba. Tashi tayi ta karo ƙofar ɗakinta ta rufe don bama taso ta dinga jin tashin muryarsu daga nan inda take, zama tayi ta ɗauki radio ɗinta ta kunna tana sauraren shirye-shiryen da ake gabatarwa a lokacin. ***** Tun ɗazu take dakon dawowarshi har kusan ƙarfe sha ɗay da rabi na dare sannan taji ƙarar buɗe gate, sai taji tsayuwar mitarshi har ma da fitarshi daga cikin motar ya rufe sannan ta tashi cikin sanɗa ta fita ta samu wuri daidai ƙofar ɗakin shi ta inda ba zai ganeta ba saboda duhu gashi fitilun wajen duk a kashe suke. Ta gabanta ya wuce sai dai sam bai lura da ita ba har yasa makulli ya buɗe ƙofar ɗakinshi ya shige da sauri kamar mai gudun kada wani ya ganshi sai dai abinda bai sani ba shine wacce yake gujewa na biye da shi a baya, ya turo ƙofar zai rufe tayi sauri tasa hannu ta tare, gabanshi ne ya faɗi daya ganta a daidai wannan lokacin. Sakar mata ƙofar yayi kawai ya koma cikin ɗakin don har ya gaji da yawan yin jayayya da ita tunda yayi-yayi da ita ta fahimci  babu wani alfanu a cikun taraiyarshi da ita ta kasa ganewa. Uffan bai ce mata ba ya ɗebi kayan baccin shi ya shige banɗaki ya rufe ƙofar haɗe da saka mata key don yasan a yadda Nabila ta mayar da kanta ƙadan da aikinta ne yaga ta shigo mishi banɗaki alhalin tasan wanka yake yi. A cikin banɗakin yayi wanka ya shirya sannan ya buɗe ya fito, bai yi mamaki ba da yaga har wannan lokacin Nabila na zaune a cikin ɗakinshi bata da alamun tashi ta fita. Sai da ya gama dukkan wasu al'adun ahi na kwanciya sannan yazo ya zauna a bakin gadon yace "Ya aka yi?" Yana ɗage mata gira da sigar tambaya. Kallinshi tayi taga yadda yake kawar da kai baya so ko ido su haɗa saboda yadda ta takura rayuwarshi tace "tun safe nake jiran dawowarka saboda ina da wata muhimmiyar magana da nake so muyi har kiranka nayi a waya don naji lokacin da zaka dawo amma baka ɗauka ba." A kaikaice ya kalleta yaga yadda ta mayar da hankalinta gaba ɗaya a kanshi ya kawar da kai sannan yace "wacce irin magana kenan? Wai don Allah Nabila me yasa ba zaki sama mini lafiya bane? Nace miki ba zai yiwu mu gina wata alaƙa a tsakaninmu ba bayan mun san dangantakar dake tsakaninmu saboda Allah me yasa ba zaki fahimta bane?" Wani malalacin murmushi ta saki irin na takaici, sai da tasa hannu ta ɗauke wasu sirararan hawaye da suka biyo kuncinta sannan ta juyo ta kalleshi muryarta na rawa tace "ni na daɗe da sanin baka ɗaukeni a yadda ni na ɗauke ka ba Kb to amma ya zanyi? Bani na ɗaurawa kaina ba Allah ne ya ɗaura mini sai dai ni ba abinda ya kawoni wajenka ba kenan abinda ya kawoni daban da wanda kake tunani." Kallonshi tayi sosai taga hankalinshi ya dawo kanta kafin tace "banga period ɗina ba wannan watan abinda yasa nake zaton ciki ne dani." Wani irin sanyi ne Kabir yaji yana ratsa shi kamar wanda aka yiwa wanka da ruwan ƙanƙara, me Nabila take so ta faɗa mishi? Anya kuwa ba mafarki yake yi ba don shi dai ba zai iya tuna wani abu ya shiga tsakaninsu ba duk da dai ita ta musanta amma ta yaya za'a yi ace yayi abu ba tare da yasan yayi ba, shi ko a cikin bacci bai ji alamar yayi abu makamancin wanda ita tace sun yi ba to ta yaya zata yi ciki bayan shi bai ji wani alamu na wani abu ya faru tsakaninsu ba. Wani kakkauran yawu ya haɗiya da ƙyar ya iya ƙwato muryarshi yace "Kin kuwa san abinda kike faɗa? Wane irin ciki kuma Nabila? Kin ma tabbatar lokacin period ɗin naki yayi? Nifa har yau ban yarda wani abu makamancin wanda kike faɗa ya faru a tsakaninmu ba don har yau ban iya tuna lokacin da hakan ya faru ba to ta yaya zaki ce wai kina da ciki alhalin ni dai nasan babu wani abu daya shiga tsakaninmu." Bata san lokacin da ta saki kukan da take riƙewa ba duk yau, kuka tayi mai yawa tana jin wani irin ƙunci a cikin zuciyarta. Sai da tayi kukanta ya isheta sannan ta ɗago idanun da suka rike suka yi jawur dasu kamar an ɗiga musu barkono tace "Kana nufin ƙarya zan yi maka kenan ko me?" Murya na rawa don hankalinshi idan yayi dubu ya tashi yace "Nifa ban ce ƙarya kike yi ba kawai dai na kasa tuna lokacin da hakan ya faru a tsakaninmu gashi kuma kina cewa wai ciki ne dake." "Wai ne ma?" Ta tambayeshi idanunta na ƙara tara ruwan hawaye, hannu tasa ta ɗauke hawayen kafin tace "kasan dai ko ina ƙarya bazan yi irin wannan ba wacce zata janyo mini zubewar mutunci da ƙimata ta ɗiya mace, bana jin daɗi Kb yanzu kwata-kwata ko abinci bana iya ci ba tare dana amayar dashi ba gashi yanzu har Mummy ta fara gane halin da nake ciki, yanzu ya zan yi idan aka gane ciki ne dani Kabir?" Ta ƙarashe maganar tana mai fashewa da wani irin kuka da yake fitowa daga ƙarƙashin zuciyarta. Ita dai soyayya bata yi mata adalci domin kuwa gashi ta kaita ta baro, bata tsinci komai a cikinta ba sai dana sani. Shi kanshi Kabir ji yayi gaba ɗaya hankalinshi ya tashi, gajiyar daya kwaso ma tuni ya nemeta ya rasa don wannan tashin hankalin yafi gaban gajiyar da yake ji a jikinshi. Komawa yayi ya zauna akan gadonshi suna facing juna, ya rasa wacce irin shawara ya kamata su yanke, tabbas bai kamata su bari wannan maganar ta fito ba don ba mutuncinsu ne kaɗai zai zube ba har da na iyayensu, yasan yanzu idan maganar nan ta fasu a gari haka za'a yi ta yawo dasu a social media bare idan aka ji dangantakar dake tsakaninsu. Sun jima a zaune shiru kowanne da abinda yake saƙawa a cikin ranshi sun kasa ko ƙwaƙƙwaran motsi bare su tsara wacce zata fishe su. Agogon ɗakin ne ya buga ƙararraar dake alamta ƙarfe ɗayan dare tayi abinda ya dawo da hankulansu jikinsu. Kallon Nabila Kabir yayi yace "to ko zuwa zamu yi a zubar don kin san dai bai kamata mu bari wannan maganar ta fita ba ko?" Tashi tayi tsaye dafe da ƙirji tace "a zubar kuma? Bayan ance mutuwa ake yi idan anje zubarwa." Shima miƙewar yayi yana jin takaicinta na neman kamashi ganin ita ta janyo musu shiga cikin wannan halin sannan kuma ya samo musu mafitar da yake ganin ita ce daidai tana neman ta kawo mishi tangarɗa. Ɗan ɗaga muryarshi yayi duk kuwa da cewa dare ne baya raina sauti yace "to me kike son ayi yanzu idan ba'a zubar ba?" A sanyaye tace "ka yiwa Daddy maganar aurenmu tun kafin...." "What?" Ya katseta a fusace jin maganar da take yi mai kama da a cikin tatsuniya ake yinta..... *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA HAMSIN DA TARA* {59} Hannunshi ta kamo tace “KB tsoro nake yi wallahi, don Allah kazo muje mu yiwa Daddy magana shi zai fahimci soyayya ce ta saka mu….” Fincike hannunshi yayi ranshi na ƙara ɓaci ya shiga jinjina kai yana cewa “Eh lallai na tabbatar kanki ba ƙalau ba, nama gama lura so kike yi mutane su fara nuna mu, sannan kina nufin Daddy shine zai bi bayanki? Shaye-shaye kike yi? To wallahi ki shirya gobe muje asibiti ki zubar da cikin nan, kin ji na faɗa miki, ni ba mahaukaci bane in ke baki da hankali.” Yana kaiwa nan yasa hannu ya jata ya turata waje ya kulle ƙofar shi, hawaye ne suka gangaro kan saman kuncinta a hankali tasa hannu ta share, tana juyawa zata wuce suka yi ido biyu da Zeey wacce ta tashi daga bacci ta nemi charger ɗin wayarta ta rasa, shine tayi tunanin duba ɗakin Nabila, tayi mamaki data shiga taga bata ɗakin don har toilet ɗin ɗakin a buɗe yake bare tayi tunanin ko tana ciki, haka ta fito cike da mamakin inda taje kawai taga Kabir ya buɗe ƙofa kafin tayi wani tunani taga ya turo Nabila, mamaki ne ya ƙara rufeta bayan sun haɗa ido, ta ɗan harɗe hannu tace “Aunty Nabs me kike yi a ɗakin Yaya a daren nan?” Gaban Nabila ne yake wani irin faɗuwa don ko Mummy bata shakkar ta ganta sama da Zeey don tasan bakinta ba shiru yake yi ba. Murmushin yaƙe tayi ta matso inda take da sauri cike da maganar raɗa tace “KB ina ji ya sha wani abu ne a waje ya shigo ciki ba a hayyacinshi ba shine ni kuma na tashi fitsari naji motsi na taimaka na kaishi ɗaki,” ta ƙarasa maganar tana ɗan kauda kai, mamaki ne ya kama Zeey tace “Are you serious? Shaye-shaye ya koma?” Bata jira Nabila ta bata amsa ba ta fara neman yin ɗakin Kabir cikin ɓacin rai, da sauri tasa hannu ta riƙo ta tace “Ina zaki? Bafa nufina shan wani abu na shaye-shaye ba wani abu ya sha shine cikinshi ke yi mishi ciwo.” Tsaki Zeey tayi tace “Karfa ki maidani wata mara wayau please, in naje na tambayeshi zan ji me ke faruwa.” Hankalin Nabila ne ya tashi ganin da gaske Zee ɗakin zata je, kuma tasan tabbas Kabir yaji harda sharri take yi mishi to fa ita dashi tasan sun ƙara yin hannun riga, ƙafarta ta riƙe da sauri tace “Zeey ƙafata,” kasancewar dare ne yasa tayi maganar a hankali, da sauri Zeey ta dawo ta ɗagota tana cewa “Bigewa kika yi?” Ta ɗaga kai tana alamun shishitu don kar a jiyo su, tare suka koma ɗaki ta kwanta a kan gado tana cewa “Wasa fa nake miki ɗazu dama so nake naga yanda zaki yi ne, saƙo aka bani shine na bashi.” Wata nannauyiyar ajiyar zuciya Zeey ta sauke tace “Allah har hankalina ya tashi, kin san dai na tsani shaye-shaye bare mai yi in har Yayana ya fara hankalina tashi zai yi.” Murmushi tayi tace “Kema kin san ba zai fara ba balle Daddy ne zai barshi?” Wani kallo Zeey ta mata sai suka yi murmushi a tare, fitowa Zeey tayi ta koma ɗaki, idanu ta rufe a hankali tana hango fuskar Baqeer, wayarta ta ɗauka ta zubawa sunanshi ido, ya ɓata mata rai shi yasa ba zata je ta ganshi ba duk da sun shirya gwara ta nuna mishi ita ma tana fushi, amma me ASF take nufi? Abinda yazo mata kenan kawai ta shiga goggle ta dinga searching ana bata wasu ma’anoni da duk ta kasa ganewa, haka ta kwanta duk ranta a ɓace na son tasan me Baqeer yake nufi, juyi tayi sai kuma ta ɗauki waya taga karfe 1 na dare, saƙo ta tura mishi “Ya Baqeer menene *ASF*? Nifa ka sanyani a duhu Allah zan yi kuka.” Tana kaiwa nan ta kifa wayar bayan ta jonata a charge don tasan bacci yake yi. ****** Bayan yayi sallar asuba ya daɗe yana addu’oi tare da godewa Allah da al'amuranshi suke sake daidaituwa, ji yake yi sai yanzu ne ma ya cika namiji tunda da kanshi yake neman kuɗi ba wai Baba ne yake tsaye akanshi ba, yayi karatun Alkur'ani sannan ya ɗan yi exercise na ƙafar shi, yanzu sosai yana jin ƙafar a jikinshi dkn har yatsun ƙafar shi ya fara iya motsawa, bayan ya gama komai ya dubi agoggo karfe bakwai da rabi gashi yau babu makaranta hakan yasa ya kwanta akan gado, wayarshi ya sake janyowa don tun kafin ya tashi yaga sakonta yace sai ya gama abinda yake zai yi mata reply. Fuskarshi ɗauke da murmushin da shi kanshi bai san yana yi ba ya rubuta “In kina so ki sani kizo wurin Dada ta sanar dake!” Ya kifa wayar tare da sa hannunshi a bayan kanshi, mamaki yake yi wai shine yake murmushi haka kawai inya tuno Zeey? To shi ya san tafi ƙarfinshi ya kuma san bai cancanci mace kamarta ba yana gurgu sannan ita me yayi mata? Ita kuwa abubuwan data mishi har ba zai iya ƙirgawa ba, a hankali yake lumshe ido yana buɗewa a haka bacci yayi gaba dashi. Can cikin baccinshi yake jiyo muryar Maryam ita da Hadiza, mamaki ne ya kamashi hakan yasa ya miƙe tare da duba agoggo karfe sha ɗaya na safe, haka ya tashi ya shirya sannan ya ɗauki wayarshi saƙonta ya gani akan in tazo kyautar me za’a mata? Ba tare da dogon tunani ba ya maida mata “Ƙawarki tazo kizo ku gaisa!” Yana kaiwa nan ya fita wurinsu Maryam wanda ganinshi yasa duk suka saki fara’a, wani irin jin daɗi ne ya kamasu don Maryam karyar ma tayi akan zata je wani taro a makarantarsu Areef ta samu ta gudo ganin Baqeer, har ga Allah bazata iya cigaba da daɗewa haka ba tare da ta ganshi ba, ita kuwa Hadiza dama ba hanata zai yi ba in dai yaji ba shi zai biya kuɗin adaidaita ba, haka suka shiga ɗakin Dada suka gyara shi tsaf sannan suka gyara na Baqeer suna tsokanarshi akan yanzu ya zama tailor don haka ɗinkin su na sallah na wuyanshi, murmushi kawai yayi yace “Ai ku kuma yanzu shikenan kun samu pass ku shirya har na mazajenku ma sai ai muku,” ya ƙarasa maganar yana duba agoggon jikin wayarshi ya kamata Zeey tazo gashi ya ce mata Maryam na nan amma shiru, zuciyarshi tana so taga yanayin yanda zasu yi magana ita da Maryam har ya samu yaji ya alaƙarsu take daga nan ya bugi cikin Maryam akan me ta sani akan Zeey. A bangaren Zee kuwa tunda taji labarin Maryam na nan ta san babu ita ba zuwa don tabbas in taje tasan shikenan Baqeer zai san ita wacece daga nan kuma alaƙarsu tasan tazo ƙarshe, gashi tana son ganin Baqeer, tsoro ne ya shiga yawo a zuciyarta kenan a haka zasu cigaba da alaƙa a sirrance? To alaƙar mecece tsakaninsu? Kanta ta kwantar saman pillow don bata san amsar da zuciyarta ke nema ba, Mummy ce ta turo ƙofar kallonta tayi bayan ta zauna kusa da ita tace “Ni kam yiwa yaron nan waya kice yazo ina son ganinshi don tabbas bazan taɓa yarda ya maida mini auta ta haka ba.” Zeey ce ta dago tana kallonta aranta tace “Kema in kin san wanene ba barina zaki yi ba.” Amma a fili sai cewa tayi “Mummy ban taɓa shakkar abu ba irin alaƙata tsakanina dashi, ban san matsayina a wueinshi ba, ban san ya zata kasance ba in har ya san ko ni wacece, Mummy shikenan rabuwa zai yi dani ko?” Da mamaki tace “In yasan ke wacece kamar ya? Akwai wata alaƙa ne tsakaninki dashi?” Kai ta kauda da sauri sannan tace “Ba haka nake nufi ba kawai dai kinga bai san komai nawa ba.” Kai Mummy ta jinjina tace “Taso muje falo so nake muyi magana akan matar Kabir ina ga is time yayi settling Daddynki yana tunanin Zinnira ɗiyar oganshi.” Saman goshinta ta ɗan daka tace “No wonder ashe neman auren dole kuke yi mishi shi yasa jiya ya dawo cikin wani yanayi, Mummy please ku ƙyaleshi ya zaɓi matar da yake so da kanshi.” “Cikin wani yanayi kamar ya?” Tayi tambayar tana kallonta, baki ta taɓe tace “Aunty Nabs dai ta kareshi amma ni ban yarda ba am sure wani abun yayi ashe kune.” Mummy bata ko tsaya jin ƙarashen maganar ba ta miƙe don dama maganar auren da take cewa yayi saboda Nabila ne tabbas bazata yarda da wannan haukan ba. Ƙofar ɗakin ta buɗe da karfi, akan kujera ta ganta a kishingiɗe tana danna waya, duk fuskarta ma taga ta sake ɗashewa, a fusace tace “Uban me ya haɗaki da Kabir har Zainab ta ganki?” Ta sani sarai bakin Zeey bazai yi shiru ba hakan yasa ta miƙe zaune tace “Bafa komai abu kawai na…….” Yunƙurin amai ta fara yi, nan da nan Mummy hankalinta ya ƙara tashi, a fusace ta kalleta tace “Wuce muje asibiti wallahi bazaki ja mini abin kunyar da za’a dinga nuna ni ba sannan Kabir aure zan yi mishi don haka ki tattara ki bar gidan nan, na dai faɗa miki.” Tana kaiwa nan ta juya, ga mamakinta Nabila biyota tayi waje tana dafa bango alamar jiri take ji, Mummy ce ta kalleta tace “Meye hakan kike yi? Ki koma ki kwashe kayanki yau zan maida ke da kaina ma….” Ƙarar data saki ne yasa Mummy tsayawa ta saki baki tana kallonta, Zeey ce ta fito da gudu tazo inda take, Nabila na ganin Zeey ta sulale a ƙasa tana riƙe ciki, hankali a tashe Zeey ta ƙaraso ta ɗagota tana cewa “Menene Aunty Nabs?” Hawaye ne ya zubo mata tace “Zeey ni kam tsintata akayi a titi hala? Wannan wace irin ƙiyayya ce ke tsakanin ya da ƙanwa? Ki taimaka ki kaini gidan Inna shi yasa sam bana son zuwa gidan nan, Mummynki ke kaɗai take son gani a gidan nan na gaji da gidan mu ayi ta wulakantani Zeey…” Fashewa tayi da wani irin kuka, Zee ta kalli Mummy cike da rashin jin daɗi tace “Wai don Allah Mummy me yasa kike haka? Sai kace bare? Ƙanwarki uwa ɗaya uba ɗaya tilo amma kin kasa kyautata mata?” Takaici ne ya rufe Mummy ganin yanda Nabila ke kuka wiwi, muryar Daddy suka ji yace “Ke Nabila tashi ki koma ciki ke kuma ki zo ina son magana dake.” Bin bayanshi tayi don takaici ma ya hanata magana amma duk abinda za ayi sai dai ayi dole Nabila ta bar mata gida. Haka Daddy ya sata a gaba yana faɗa, jinshi kawai take yi don shi a duniya duk abinda zaka ce akan Nabila baya gani shi a kullum gani yake yi ma ba kowa ne ya kaita tarbiyya ba, yana gamawa ya fito ya shiga mota ya bar gidan zuciyarshi duk babu daɗi. Da ƙarfi driver ɗinshi ya ja birki ganin motar data kawo kai, wanda har saida Sulaiman Karaye ya ɗan bigi kujera kaɗan, driver ya juya yana bashi hakuri sannan ya kalli motar, kafin driver ɗin ya fita har shi mai ɗaya motar ya fito yana tafe yana riƙe ƙugu, glass ɗin ya ƙwanƙwasa hakan yasa drivern ya fita waje yana cewa “Yallaɓai kayi haƙuri ban kula ka taho bane.” Wani kallo yayi mishi sannan yace “Eh da kasheni kayi ma kenan haƙuri zaka bawa iyalina? Ko?” Zai ƙara magana idanuwanshi suka kai kan Sulaiman dake zaune, wani mugun tamke fuska yayi yace “Da walaki ai tunda ka ɗauko ɓarawo ai dole dama idanunka ba zasu kula da hanya ba, aikin banza wallahi da kun bigeni da sai na kai ku ƙara wurin ƴan sanda, munafikai kawai.” Sulaiman ne ya zuge glass yace “Ka tabbatar kaje asibiti an baka gado dkn da alama ƙusumbi ne ya fito a bayanka, kai Mamman mu tafi don Allah.” Badaru takaici ya rufeshi yace “Kasan Allah ka shiga hankalinka dani, kafi kowa sanin tsaf zan ma tijara ni ba kunya gareni ba.” “Tunda tsufa yayi gardama dama kai kam menene ma baza kayi ba?” Mamman ne ya shiga suka ja mota suka bar Badaru yana ta masifa da zage-zage, kwankwason shi ne yayi ƴar ƙara ya ja tsaki yace “Wallahi Kamalu sai kasan kayi dani.” ***** Zeey kam da ƙyar ta samu ta lallashi Nabila ta daina kuka hakan yasa ta koma ɗaki takaici yasa ta ɗau key kawai tabar gidan tana ganin kiran Mummy amma taƙi ɗauka, Baqeer kawai take skn gani amma tsoron haɗuwarsu da Maryam take, ganin yamma ce yasa ta ɗauki waya tayi mishi text tace “Wani abu ya riƙeni kaɗan amma zanzo, suna nan dai ko?” Reply ya mata akan sun tafi, wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta sauke tare da yin hamdallah sannan taja mota tayi gidan idanunta taf da ƙwalla, sam bata son wannan hatsaniyar dake faruwa tsakanin Mummy da Nabila, ace ƙanwarka amma kullum cikin faɗa? Waya ta ɗauka ta kira Nabila akan taji ya take ciki sai dai me? Nabila na dauka ta cigaba da kuka tana cewa “Zeey na shiga uku ina ji ciki ne dani kuma cikin…..”ɗif kuma sai komai ya tsaya kamar an ƙwace wayar, gaban Zeey ne yayi wani irin faduwa da sauri taja gefen titi ta tsaya tare da dafa saman goshinta, ciki? Ciki? Ciki kamar ya? Jikinta ne kawai yake rawa sam ta kasa samun nutsuwa, wayarta ce ta fara ƙara ganin sunan Baqeer yasa ta ɗauka da sauri tana sauƙe ajiyar zuciya “Dama Dada ke cigiyarki tana son jin ko zaki zo?” Numfashi kawai yaji tana saukewa wanda nan da nan hankalinshi yayi mugun tashi yace “Zainab! Menene?” Kawai ji tayi ta kasa magana, nan fa hankalinshi yayi mugun tashi yace “Kina ina?” Hawayenta ta share tana son yin magana ta kasa, “Yi mini text ɗin inda kike.” Yana kaiwa nan ya kashe wayar, ajiye takardun da yake zane yayi ya fara tura kekenshi cikin sauri, Dada na zaune tana cin abincin da su Hadiza suka dafa musu tuwo miyar zogale tana ci tana jin radio gefenta yarinyar maƙota ce da ta shigo tayata wanke-wanke itama an zuba mata tuwon tana ci, da mamaki take kallonshi tana cewa “Kai kuma sai ina?” Yanda taga yana tura keken da sauri ne ya bata mamaki yana tafiya yana cewa “Ina zuwa Dada.” Da kallo ta bishi tana fatan Allah dai yasa lafiya…. Baqeer adaidaita ya tara yana jin gaba ɗaya hankalinshi ya tashi, meya sameta? Bayan yarinya ce da kullum fuskarta ke ɗauke da farin ciki da walwala? Ba dai Junaid bane? Haka ya isa inda ta kwatanta mishi ta text duk zuciyarshi babu daɗi, gaban motarta yace a ajiyeshi, kallon juna suka yi shi da ita dake cikin adaidaita ita tana mota, hawaye ne taji sun gangaro mata, da sauri ta fito ba tare da tace komai ba ta fito da wheelchair ɗin haka ya fito ya shiga ta turashi jikin mota sannan ya shiga ta sake nade wheelchair ɗin tasa a bayan mota sannan ta dawo ta zauna seat ɗin driver, kallon juna su kayi ga mamakinta kawai ta rasa abin cewa sai rauni da zuciyarta ke yi, anya bata da matsayi a zuciyar Baqeer kuwa, in ba haka ba taya zaizo daga sanar dashi? Kallonta yake yi kafin yace “Me ya sameki?” Hawaye ne suka zubo mata wanda tana ganin damuwa ƙiri-ƙiri cikin zuciyarshi yace “Menene? Junaid ne?” Wani kallo tayi mishi ta girgiza kai, yace “To wanene?” Kanta ta kwantar jikin kujera tana kallonshi tace “Ya Baqeer ban san ya zan yi ba, bana so naga Mummy na samun matsala da ƙanwarta sai na dinga ji kamar komai dalili na ne, don Inna tasha faɗa mini cewa nice na rabasu.” Bai san kan zancen da take yi ba sai dai ya fahimci abin daga gida ne ya kuma gane inda matsalar take, yace “In ƙanwarta ce ko sun yi faɗa zasu shirya, Umma ma tana samun saɓani da ƴan uwanta amma suna shiryawa.” Hawaye ta goge tace “Matsalar ina ga ta yanzu ba mai shiryuwa bace, sannan in Daddy yasan abinda ƙanwarta tayi Mummy ban san yadda zata yi ba…..” ta ƙarasa maganar tana hawaye, idanunta tasa cikin nashi wanda suka cika taf da ƙwalla kana kallonshi kaga damuwarta tsantsa a ranshi, yace “Meya haɗa laifin ƙanwarta da nata? Sannan in har laifin babba ne ku samu kakanni ko magabata suyi magana kafin abun ya girma Wani abu ta haɗiya tana kallonshi yaji tace “Ba ita ta haifemu ba ni da yayana, shi yasa danginta basa sonmu.” Daga Umm Asghar har Ayusher kallonta suka yi ,yau me muke ji? Mai karatu kai fa? Ka taɓa kawo haka? Ku biyo mu wasa farin girki🙌🏻 *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Muhd Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD*                 *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN* {60} Cike da mamaki Baqeer yake kallonta ga kuma wani tausayi da take ƙara bashi ganin yau ce rana ta farko da yake ganin hawaye a fuskarta haka, zuciyarshi ce ke ingizashi akan yasa hannu ya share mata amma inaa ba zai iya ba, tissue ɗin dake ajiye tsakanin inda take da inda yake yasa hannu ya ɗauka, miƙa mata yayi ta ɗauki biyu ta goge fuskarta tana murmushin yaƙe tana cewa "Ya Baqeer am sorry....." Katseta yayi da cewa "Ki koma gida kiji me ke faruwa tukunna and then make a decision." Cike da rauni ta kalleshi sannan ta ɗaga mishi kai alamar to, shiru suka ɗan yi sai dai shi zuciyarshi cike take da tambayoyi amma baya son ya juye mata su yanzu saboda abinda ke damunta, cikin sanyin jiki yace "Birth mother ɗin ku fa?" Kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace "Tana raye sai dai ta sake wani auren a garinsu, ta sake haihuwar yara mata biyu." Ta ɗago tana kallonshi idanunta taf da ƙwalla tace "Amma na daɗe ban ganta ba kuma itama ba wai ta damu da mu bane." Shima idanuwanshi na cikin nata yace "Ita ta faɗa miki bata damu daku ba?" Yanayin kallonta ne ya canza ta maida idanunta ƙasa tana goge fuskarta tana cewa "Akwai abinda ba sai an faɗa ba kake ganewa, sannan ina da Mummy na har cikin raina a matsayin wacce ta haifeni nake ɗaukan ta don ƙaunar da take yi mana ta dabance a kanmu ta haƙura da neman haihuwa tace mu kaɗai mun isheta rayuwa ba sai ta nemi wasu ba.” Ta ƙara kallonshi sannan tasa kanta a jikin stearing motar wani shauƙin ƙaunarshi na ƙara ratsata tace “Kana ganin duk da haka sai na dinga bibiyar wacce bata damu dani ba?” Ga mamakinta gani tayi ya ɗaga mata kai alamar eh, mamaki ne ya kamata tace “Why?” “Saboda ita ta haifeki, baki san uzurin ta ba baki san me yasa bata zuwa ba, sannan don tayi aure ta haihu ba shi zai sa ta daina sonku ba.” Baki ta ɗan taɓe tace “Hmm baka san ta bane shi yasa, matar da ko waya bata yi mana taji ya muke? Ya Baqeer mu bar maganarta please, ni yanzu tsorona kada Mummy ta shiga wani hali a dalilin Nabila.” Kallonta yake kawai bai ce komai ba, sai ma gani tayi ya maida hankalishi waje, baki ta turo tana neman sake zubo da ƙwalla, daidai nan ya waigo da sauri yace “Please kukan nan ya isa haka nan, bari na sauka kamar yadda nace ki koma gida kiji menene ya faru tukun.” Baki ta turo tace “Bari na kai ka gida sai naje.” “No kar ki damu zan hau adaidaita.” Ido ta zuba mishi wanda har ya kalli waje ya sake kallonta yace “Me?” Kallo take mishi na sakalci da harara tace “Allah a’a ba saboda ni ka fito ba? Ni naga saurin zuwanka ma Ya Baqeer faɗa mini gaskiya a ruɗe ka iso ko?” Gyaran murya yayi yana ɗan gyara kwalar rigarshi cikin son ya waske yace “Dama ina waje sannan ni bana son harkar kuka.” “Waje a ina kenan?” Kallonta yayi yace “Ba sai kinji ba uzuri na ne.” A shagwaɓe tace “Ya Baqeer please ka bari na saukeka Allah it's not easy shiga adaidaita da wheelchair,” ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya alamar lallashi, kai ya ɗaga alamar to, murmushi ta saki shima bai san sanda ya saki murmushi ba yana ɓoyewa don kar ta gani, motar ta kunna sannan suka fara tafiya, shiru suka ɗan yi kaɗan, baya son damunta da tambaya amma yana son yasan me yake faruwa a rayuwarta, ashe itama tana da nata matsalolin kawai dai bata nunawa ne, katse mishi tunani tayi da cewa “Baka fada minu me *ASF* ɗin yake nufi ba.” “Dama an taɓa bada assignment a faɗi amsa ba tare da an gwada ba?” Ɗan kallonshi tayi tana dariya kaɗan tace “To ai haka ake yi in aka bada assignment a school ko baka san answer ba za’a sanar da kai sannan ba kace zaka fada mini ba?” “Yaushe kenan?” “Kai lallai ma Ya Baqeer Allah wayau zaka yi mini.” Hannunshi yasa a aljihu bai ce komai ba, wata nutsuwa yake ji na ganin ta saki ranta. ***** Mummy dake tsaye jikin ƙofar toilet tana jiyo wayar da Nabila ta yiwa Zainab, banda ƙoƙarin buɗe ƙofar babu abinda take yi ranta a matuƙar ɓace take cewa “Wallahi Nabila in baki fito ba jikinki ne zai faɗa miki.” Tana daga ciki tace “Mummy bafa zan fito ba sai Zainab ta dawo babu abinda zaki ce mini har sai ta dawo gidan nan koma menene kiyi a gabanta, in ke kince a’a ita ai tasan da aure tsakanina da yayanta.” Mamaki ya sake rufe Mummy, ɓacin ran dake fuskarta kuwa ba zai misaltu ba, ganin da gaske ba zata buɗe banɗakin ba yasa ta fita daga ɗakin kanta na wani irin sarawa, ɓangaren Kabir tayi don sam yanzu ya daina zaman gida, yanzun ma baya nan, anan falon ta zauna ta ɗauki waya ta kirashi, yana ɗauka tace “Kana ina?” Ina nan ƙasan layi akwai wani gidan abokina ina can.” “Ka dawo yanzun nan,” tana kaiwa nan ta kashe wayar tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta dafa saman kanta da take ji yana wani irin zafi kamar wuta, yanzu ita ya zata yi? Ta ina zata fara ɓullo wa abinda ke faruwa? Kalaman Nabila ne ke dawo mata, bayan ta sake mata magana akan ganin likita tace ba zata ba, har zata fita daga ɗakin ta sake kallonta tace “Nabila na roƙeki da Allah karki janyo mini abun kunya, don Allah kar kiyi abinda zai sa farin cikin gidana ya lalace, shi yasa tun farko naƙi sakar miki fuska ni nasanki fiye da yadda kika san kanki nasan wannan ladabin da kike yi a gidan nan wanda har kowa yake ganin baki da wani mugun hali ni nasan pretending ne, sai dai ban taɓa nuna miki na sani ba, fatana don Allah ki koma wurin Inna ki samu miji kiyi aure don Allah.” Nabila taji tasa dariya da mamaki take kallonta tsoro ita kanta ya bayyana a fuskarta, tana kallon Mummy tace “Kinga rashin faɗarki bai daɗa miki da komai ba, yanzu burinki ya cika? Wacce baki yarda da ita ba ta tabbatar miki da mugun halin ta?” Yanayin Mummy ne ya canza tace “Me kike nufi?” Ƙafaɗa ta ɗaga mata tace “Idan Kabir ya dawo ki tambayeshi ni ba zanyi komai ba sai Zainab tazo, zan gani in zaki iya korata bayan abinda ya aikata.” A tsorace Mummy take takowa tace “Tashi mu wuce gida wurin Inna….” Kafin ta ƙaraso shine ta shige toilet da wayarta, tana shiga tasa key daga nan shine ta kira Zeey. Ji take yi zuciyarta na wani irin zafi wanda ta tabbatar da za’a gwada jininta a lokacin tabbas da zai kai hawa 200/130 ga wani uban ciwon kai dake damunta, duk laifin Inna ne don ta dade tana nusar da ita zaman Nabila gabanta shine sam bata son yawan zaman nan da take saboda Kabir don tun tuni ta fahimci son Kabir take yi. Ya zata yi in da gaske take cikin ne kuma na Kabir ɗin ne? Ƙwaƙwalwar ta sam ta kasa yin wani dogon nazari don abubuwan da zasu faru a kan cikin nan Allah ne yasan yawansu, Daddy wanda ko da wasa baya son image ɗinshi ya ɓaci taya zai fuskanci abun nan? Ga Zainab wacce tasan ko me zai faru ba zata bari ace za’a tauye hakkin Nabila ba duk kuwa da yayanta ne mai laifi don haka take a kuma kan maganarta Daddy ya kaita ƙasar waje karatu saboda ya gaji da wannan halin nata. Kabir ne ya shigo tana nan a zaune, kallonshi tayi sai kawai taji hawaye sun zubo mata, nan da nan hankalinshi ya tashi yace “Mummy menene? Ƴan Ɗambatta sun zo ne?” Wasu hawayen ta sake yi tace “Ba gwara suzo kullum ba da abinda kake neman jawo mana Kabir meya shiga tsakaninka da Nabila?” Gabanshi ne ya8i mugun faduwa hankalinshi yayi wani irin tashi, jikinshi na rawa yace “Mummy wallahi nima ban sani ba.” Wani abu ta haɗiya kamar zatasa kuka tace “Kabir ka janyo mana yanzu ban san yadda zamu yi da senate ba.” Da sauri yasa gwiwowinshi a ƙasa ya riƙe ƙafarta yace “Mummy ki taimakeni a zubar wallahi ni bansan komai game da abinda take cewa ba, ni wallahi ban tuna komai ba, Mummy in Dady yaji ni nasan kasheni zai yi.” Kallonshi tayi tace “Ta riga ta faɗawa Zainab.” Idanu ya zaro yace “Kafin magana ta kai kunnen Daddy dkn Allah Mummy ki sakata a gaba muje a zubar ni wallahi ban san nayi ba.” “Tana ciki ka gwada yi mata magana.” Cikin sauri ya mufi ɗakin Nabilan ya ƙwanƙwasa tare da sanar da ita shine, da kamar ba zata buɗe ba sai kuma ta buɗe don bata son ɓacin ranshi, kallonta yayi yace “Nabila na roƙeki da Allah muje a zubar dashi, na ɗauka ke kanki baki tabbatar da ciki bane da?” Itama kallonshi tayi tare da riƙe cikinta tace “Na tabbatar ɗazu da safe, sai dai bazan iya zubar da ƙwan ka ba, ko da kuwa zan rasa raina.” Tayi saurin rungumeshi kam tana cewa “Don Allah Kabir kar ka biyewa Mummy, da aure tsakanina da kai kada ka bari zancenta ya rabamu, ita tana ji kamar ta haifeku ne sai dai mu sa a ran mu ƙila ma rabon auren mu da zuri’armu ne yasa tazo a matsayin kishiyar mahaifiyarku.” Janye jikinshi yayi yace “A wurun mu ita ce mahaifiyarmu kuma babu wanda zai nuna mata mu ba nata bane, bazan iya auren kanwar mahaifiyata ba na sanar dake a baya yanzu zan ƙara sanar dake, ko ba don Mummy ba babu soyayyarki a raina.” Idanuwanta ne suka yi ja da sauri ta nufi gaban madubi ta fara zubar da kayayyaki ƙasa tana fasa su turare, cikin kuka take cewa “Haka kace? Haka kace? To lallai zaka tsinci gawata don bazan iya rayuwa babu kai ba kuma babu wacce ta isa tayi rayuwa da kai ina kallo sai dai duk mu taru mu rasa.” Hannunta ya matso ya finciko ya matseta sosai ta yadda zata nutsu taji me yake cewa yace “Enough! Just listen to me, kin san kina sona kika sanar da Mummy kina da cikina? Kika sanar da Zainab? Haka ake so?” Cikin dauriya tace “Naga kai bazaka maida hankali wurin ƙwato ni ba shi yasa ni na furta don na raya soyayyar mu.” Wata dariyar takaici yayi yace “Wallahi in har kika sanar da Zainab nine mai cikin wallahi magana bazan sake yi miki ba balle akai ga Shirmen zancen da kike yi na aure, na dai faɗa miki.” Yana kaiwa nan ya fito tare da wucewa ɗakin shi. Yana fita ko minti biyar bai yi ba Zee ta buɗe ƙofar ɗakin Nabila tana haki da alama gudu tayi wajen shigowa ciki, kallonta tayi a zaune a ƙasa ga kayan kwalliya nan duk an zubar a ƙasa, wasu kwalaben turaren ma sun fashe da sauri ta ƙarasa ciki ta rungumeta, nan Nabila ta saki wani kuka, bayanta Zeey ta shiga shafawa hankali a tashe, da ƙyar ta samu ta daina kukan tace “Faɗa mini meke faruwa? Me naji kina cewa kamar wai ciki ne dake?” Kallonta tayi sai tayi murmushi tace “Ciki na ke min ciwo ji nake yi kamar bazan rayu ba.” Kallon zargi ta tsareta dashi wanda hakan ya sata cewa “Allah da gaske nake yi wai ke da me kika ɗauka.” Ajiyar zuciya Zeey ta sauke ta zauna a ƙasan tana cewa “Har hankalins ya kwanta dama na gama sanin in dai har kamar ke aka ce ciki gareki to tabbas wanda yayi cikin fyaɗe yayi miki don ko kusa da namiji ba kya zama bare har ta kai ki ga riƙe hannunshi to taya kenan zaki yi ciki, a hanya nasa a raina in dai shine to fyaɗe aka yi miki ko magani aka sa miki aka yi ba’a hayyacinki ba.” Ƙeyarta ta talle tace “Lallai na kusa daina barinki kallon dramas ɗin nan da kike yi wato har kin tafi wani senario ɗin ma na daban? To ni ta ina zanyi ciki ke kin san ba maza nake kulawa ba.” Yanayin Zeey ne ya canza ta sake bin ɗakin da kallo sannan ta tsare Nabila da ido sosai cikin kakkausar magana tace “No Aunty Nabila ɗazu ba haka kika ce mini ba, ce mini kika yi Zeey na shiga uku ciki ne dani kuma cikin…….” Sai wayar ta yanke. Nan da nan gaban Nabila ya shiga faɗuwa, kallon Zeey tayi wacce yanayinta ya canza sosai tace “Haka kika ce am 100% sure.” Yanayin Nabila ne ya canza gabanta ya shiga faduwa, kallonta sosai Zeey take yi itama yanayinta ne yake canzawa, meke faruwa? Aunty Nabila? How? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA ƊAYA* {61} "Me yake faruwa ne Aunty Nabs? Ni sai yanzu ma na lura da wasu changes a jikinki. Garin yaya hakan ta faru ke da ma ba wani yawan fita kike yi ba ba kuma wani kike kulawa ba da sunan soyayya, ta yaya hakan ta faru saboda Allah, kuma kada kice min ba haka ba ne ko wasa kike yi don ba irin wannan maganar bace ake wasa da ita.” Ta tsurawa Nabila ido tana jiran jin amsa daga bakinta, ita sai yanzu ma ta lura taga duk ta ɗashe jikinta ya saki alamun dai lafiya bata wadaceta ba, to ita kuwa tana ina har Nabilan ta shiga cikin wannan halin bata sani ba, to wai shin ma wanene yayi wa Nabila haka ya keta alfarmarta don ita dai ta tabbata idan har da gaske cikin ne da ita to sai dai idan raping ɗinta aka yi don a sanin data yiwa Nabila babu ta yadda za'a yi ta kai kanta har ta yarda a keta alfarmarta da gangan. Ƙara kallon Nabila tayi sai taga itama kallonta take yi, tausayinta ne taji ya kamata ganin yadda lokaci guda gaba ɗaya ta canja, kamanninta sun sauya duk jikinta ya yamushe kamar wacce tayi sati jikinta bai ga ruwa ba. Wani irin kallo Zainab take yi mata cikin ranta tana ayyana 'kada dai ace' sai kuma tayi maza ta kawar da wannan tunanin. Har ta buɗe baki zata sake yi mata magana sai kuma taji ba zata iya ba don tunanin da tayi ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, fita kawai tayi daga ɗakin tana girgiza kai cikin ranta tana fatan kada Allah ya tabbatar da abinda zuciyarta ta saƙa mata yanzun nan. ***** Duk wani abu da Bello ya bar mata sun tasarwa ƙarewa gashi shiru har ana neman wata biyu da tafiyarshi tata tafiyar bata samu ba, tun yana yi mata daɗin baki da alƙawura akan akwai wasu shirye-shirye da yake yi yana gamawa zai yi mata shirin tafiya ta iskeshi har yazo ya daina sai ma wayarta da ba koyaushe yake ɗauka ba sai tayi ta kiranshi bata samu idan kuma tayi dacen samun shi to ba lallai ne ta samu ya amsa ba. Yanzu ma wayarta ta ɗauka ta danna mishi kira don kayan abincinta sun tasarwa ƙarewa dama kuɗaɗen da ya bar mata tuni suka ƙare saboda sayi banza sayi wofi data riƙa yi dole ta haƙura take cin abincin da Habi take girka musu. Har wayar ta katse bai ɗauka ba sai data ƙara kira sannan ya ɗauka daf da zata katse murya a cunkushe. Tana jin muryarshi ta fara masifa akan don me tana ta kiranshi yaƙi ya ɗauka, yana lallashinta ma yana ƙoƙarin yi mata bayani taƙi tsayawa ta saurare shi har sai da yayi spark ya fara yi mata masifa abinda bai taɓa yi mata ba tunda suka fara soyayya don haka bata san lokacin da tayi shiru ba tana mamakin wai yau ita Bello yake yiwa tsawa “Enough haba wai ke uwata ce?” Abinda ya faɗa kenan wanda ya sakata jin ta kasa magana. Shi ɗin ma ganin tayi shiru sai kuma ya sassauto yana cigaba da lallashinta akan akwai abinda yake shiryawa very soon itama zata  biyoshi ta ƙara haƙuri kaɗan. A shagwaɓe tace "To ka turo mini wani abu mana kafin lokacin na faɗa maka kuɗaɗen hannuna fa duk sun ƙare.” Kwantar da murya yayi yana bata haƙuri akan har yanzu ba'a fara biyanshi ba shi yasa bai turo mata komai ba tunda ya tafi shine ma dalilin da yasa har yanzu bai samu ya kama musu gidan da zasu zauna ba amma ana biyanshi zai ƙarasa shirin tafiyarta taje ta iskeshi don sosai yake missing ɗinta. Murmushi kawai take saki tana sauraren yadda yake ƙara fasa mata kai yana bayyana mata yadda yake jinta a cikin ranshi, basu ajiye wayar ba sai da katinta ya ƙare. Yana sauke wayar daga kunnenshi ya saki wani dogon tsaki, yanzu har fargabar ganin kiran wayarta yake yi don yasan rigima kawai zasu yi shi yasa a mafi yawan lokuta yake ƙin amsa kiran nata don ƙarairayin da yake yi mata har sun fara ƙarewa ya fara rasa ƙaryar da zai yi mata akan dalilin daya hanata tafiya tuntuni bayan a yadda suka tsara bai fi yayi sati uku zuwa wata ɗaya ba zata bishi. Tunda yaje basu fara yin abinda ya kai su ba sai da aka yi musu wata test wacce da ita ne za'a tantance matakin da za'a ajiye kowanne daga cikinsu a lokacin basu fi sati ɗaya da tafiya ba, a wannan lokacin ya gane ba shi da wayo domin duk wasu zane da yake yi ada da taimakon Baqeer yake yi bai taɓa yin zane nashi na kanshi shi kaɗai ba tare da taimakon Baqeer ba don ko waɗanda yayi presenting a wurin gasar da tun asali Baqeer shi ne ya kamata yaje yayi munaƙisar da shi ya tafi a madadinshi da taimakon Baqeer ɗin ya zana su shi yasa har ya samu yin nasara a wajen gasar da tayi mishi sanadin tahowa bunƙasa ilimin shi a harkar zane sai dai tun ba'a je ko ina ba suka koreshi daga makarantar don sun ce baya da wata fasaha a harkar a taƙaice ma basu yarda takardun zanen da suka saka shi yin nasarar nashi ne ba, tun daga wannan lokacin yake gararanba yana buga-bugar neman yadda zai yi ya samu aikin da zai riƙe shi ko na taƙaitaccen lokaci ne ko ya tara abinda zai ishe shi ya dawo gida ya kama wata sana'ar don dai duk ɗan abinda ya tara ya tafi ne wajen shiryawa Asiya biki na garari na ƴan ƙarya irin wanda za'a daɗe ba'a daina zancen shi ba, to gashi tun ba'a je ko ina ba ya fara ganin iyakar shi don zanen daya dogara dashi yake ganin shine zai zama silar arziƙinshi ya gane ashe shi ba komai bane a harkar idan har babu Baqeer a cikinta, a yanzu kuwa yasan ko giyar wake ya sha bai isa ya tunkari Baqeer da wani zancen daya danganci harkar zane ba bayan cin amana mafi muni da yayi mishi, ture batun auren Asiya da yayi bayan a irin son da yake yi mata  da kuma tafiya wajen gasa a madadin shi tunda suka kai shi asibiti dama bai ƙara leƙa shi ba sai sau ɗaya shine kuma lokacin da yaji ƙaddarar data afka mishi yayi amfani da wannan damar ya tafi wajen gasar da yasan Baqeer ɗin yaci burin tafiya. A yadda abotarsu take da Baqeer yasan daya faɗa mishi cewar yana so yaje a maimakon shi tunda baya da lafiya wallahi ƙarfafa mishi gwiwa zai yi amma sai bai yi hakan ba ya zaɓi ya munafurce shi gashi abinda ya janyowa kanshi don yasan shi ba kowa bane idan har babu Baqeer. Baqeer ɗin da ya so shi da zuciya ɗaya ya aminta dashi ta inda bai ji ƙyashin koyar dashi duk wasu dabaru na sana'ar shi ta zane ba duk da ƙalubalen da yayi ta fuskanta daga wajen mahaifin shi akan baya son abotarsu amma ga da abinda ya saka mishi, tabbas bashi da kaico domin komai ya faru dashi shi ya janyowa kanshi. ***** Baqeer kuwa yana kwance akan katifarshi tunanin Zeey da halin damuwar data shiga a ɗazu ne suka tsaye mishi a ranshi, yasan ba ƙaramin abu ke damunta ba tunda har ta iya yin kuka a gabanshi bayan kasancewar ta very jovial mai yawan raha da son wasa da dariya. Wayarshi ya janyo ya tura mata text, "Are you okay?" Ya ajiye wayar a gefe ya lumshe idanunshi yana tunanin abubuwan da yake son yi idan ya gama makarantar koyon ɗinkin daya shiga, bai sani ba ko kuɗaɗen daya ajiye zasu ishe shi buɗe shago ya kuma zuba irin kekunan da yake so domin a tailoring school ɗinnan an koya musu amfani da kekunan yin designs kala-kala yana kuma son ya zuba su a shagon da yake son buɗewa sai dai matsalar kuɗi ce zata kawo mishi cikas. Ƙarar shigowar text ne ya katse mishi tunanin da yake yi. Cike da ɗoki ya janyo wayar yana doka murmushi tun bai ga abinda ta rubuto ba don dai ya tabbatar message ɗin daga wajen Zeey yake. "Am good" kawai ta rubuto. Ajiyar zuciya yayi sai dai har yanzu hankalinshi bai gama kwanciya ba da amsar data bashi. Kafin yayi typing reply wani message ɗin ya shigo. "Me kake yi har yanzu baka yi barci ba?" "Sketching?" Ta ƙara turo wani saƙon. "Nope" ya mayar mata. Sai kuma ya sake tura mata "Ke me kike yi har yanzu da baki kwanta ba?" "Tunanin assignment ɗin daka bani ne ya hanani barci." "Ya Baqeer ba zaka faɗa mini ma'anar assignment ɗin ba? Please👋." Murmushi kawai yayi, bai san lokacin da ya samu kanshi a halin da yake ciki ba amma dai ya sani a yanzu Zainab ita ce farin cikin shi, ba zai iya cigaba da rayuwar da babu ita a cikinta ba. Sai dai idan ya tuna ba lallai ne ta so shi a yadda yake ba ya zama gurgu, nakasashen mutum kamar yadda wasu suke kiranshi sai yaji hankalinshi ya tashi don ya tabbata tausayi ne kawai yasa ta shigo rayuwarshi bata jin abinda yake ji a kanta a cikin zuciyarshi. Emoji na dariya😆 ya tura mata kawai. Tana ganin abinda ya turo ta mayar mishi da emoji na fushi😠 ta ajiye wayarta tana murmushi. Kasancewarta tare da Baqeer na sakata cikin shauƙi yana bata nishaɗi shi yasa hankalinta bai kai kan abinda ke faruwa a cikin gidan nasu ba. Da yin wannan tunanin ta nemi duk wani farin ciki da ta samu kanta a ciki ƴan mintuna ƙalilan da suka wuce ta rasa. Bata so zuciyarta ta riƙa kaita wurin da bata so amma ta kasa yakice tunanin daya ginu a cikin zuciyarta sai dai abinda ta ganarwa idonta yasa ta kasa yakice hakan, bata so hasashen da tayi ya tabbata don tasan idan har ya tabbata hakan ne ba ƙaramin tashin hankali zasu shiga ba. Kai to su ta yaya ma zasu bari har hakan ya kasance? Tashi tayi ta fita zuwa ɗakin Kabir don suyi magana saboda gaba ɗaya hankalinta ya kasa kwanciya, gara taje taji daga bakinshi cewa tunaninta ba daidai bane ko ta samu kwanciyar hankali. Tana murɗa ƙofar ɗakinshi taji ta a kulle, knocking tayi ta haɗa da kiran sunanshi. Sai da ya tabbatar muryar Zeey yaji sannan ya taso ya buɗe ƙofar, murya a cunkushe yace mata "lafiya?" Ba tare daya bata hanya ta shiga cikin ɗakin ba. "To ka bani hanya na wuce mana ha'an, ni magana nazo muyi." Ta tureshi ta shige cikin ɗakin ta zauna akan sofa. Sai da ya leƙa yaga babu wanda ya biyota sannan ya koma cikin ɗakin ya mayar da ƙofar ya rufe da makulli. Zama yayi akan kujerar dake kallon wacce take kai yana kallon Zeey yana jiran yaji dame tazo ɗakin shi a wannan daren, itama kallon nashi take yi tana kokawa da zuciyarta akan ta tambayeshi ko kuwa dai ta ƙyale shi sai dai tasan ba zata samu nutsuwar zuciya ba idan har ba tabbatar da gaskiya tayi ba. Zamanta ta gyara ta ƙara nutsuwa saboda abinda take shirin faɗa mishi da tasan idan har zarginta ne kawai ba wai gaskiyar kenan ba sai sun samu gagarumin saɓanin da bata hango shiryawarsu kwana kusa ba. "Kai ke da alhakin yiwa Aunty Nabs ciki ko?" Kawai ta samu kanta da watsa mishi tambayar ba tare data shirya ba ko ta tsara ta yadda maganar zata fito ba. A firgice ya ɗago yana kallonta sai dai ya kasa buɗe baki ya amsa ko ya musanta zargin da tayi mishi. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" tace haɗe da tashi tsaye hankalinta a tashe tana nuna shi da ɗan yatsa. "Kenan da gaske kai ne kayi mata ciki Yaya Kabir?“ Da sauri yace “Zainab please! Ita ta faɗa miki? Sannan wai hauka nake yi da zan aikata hakan?” Wani irin kallo tayi mishi cike da tuhuma tace “Unfortunately I don’t trust you, muje wurin Daddy a sakaku a gaba aji meke faruwa.” Hankalinshi ne ya sake mugun tashi da sauri ya tsaya gabanta yace “Wai kece uwarta? Sannan nace ba ni bane a wani dalili zaki dage akan Shirmen tunaninki?” “In ma shirme ne in ma ba shirme bane muje gun Daddy kayi bayani.” Tsaki yaja ya koma kujera ya zauna yace “Kanku ake ji ke da Nabilan, ai dai ni nasan ba ni nayi ba so ya rage naku ita zaki zubarwa mutunci ba ni ba.” Yayi maganar cike da dauriya don kar ta gane halin da ya shiga. Saman goshinta ta shafa yanzu kam ta tabbatar akwai abinda ya shiga tsakaninsu, din a iya saninta in har Kabir bai san komai ba in ta faɗa abu na farko da zai tambaya shine ciki? Ciki ne da ita? How? Ta yaya? Tunda dukkansu sun san wacece Nabila sannan ya kamata ma ya ɗauki maganar tata a matsayin hauka amma ganin yadda hankalinshi ya tashi yasa ta gasgata tunaninta. Nan da nan taji hankalinta ya ƙara mugun tashi, tsoro ya ƙara kamata, cike da ɓoye tsoronta tace “Wallahi kai kasan bazan bar maganar nan ba, Ya Kabir kada dai kace mini fyade kayi mat…….” Rawar da muryarta keyi ne yasa ta kasa ƙarasawa, ganin yanayinta ya taso da sauri ya ƙara dawowa gabanta, wani mugun kallo tayi mishi kafin yayi wani tunani ta sharara mishi wani irin mari tana yi mishi wani kallon tsana da ƙyama…….. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BIYU* {62} Hanyar ƙofa tayi da sauri ya riƙo hannunta, kallonshi tayi kawai taji hawaye ya soma taruwa a idanunta, saman goshinta ta shafa sannan ta fizge hannunta tana cewa "Haba Yaya wannan wani irin son zuciya ne, taya zaka yiwa Mummy haka? How?" Kuka ne ya nemi k6wace mata kawai tasa hannu ta sake turashi baya, jikin ƙofa ya jingina ya sa hannu saman fuskarshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi, ya zai yi da rayuwar nan? Kallonta yayi kamar zai yi kuka shima yace "Zeey sam nima ban san meya faru ba, ban tuna ba sam akan abinda ya faru kin dai san ba shaye-shaye nake yi ba." Wani mugun kallo tayi mishi tace "Ranar da ta taimaka maka ka dawo ɗaki hope dai ba ranar bane?" Kallonta yayi cike da rashin fahimta yace "Yaushe kenan? Don ni dai ban taɓa rasa hanyar ɗakina ba tunda dai kin san ba shaye-shaye nake yi ba." Hannu ta ɗaga mishi tace "Ta ina zan sani tunda ba ganinka nake yi ba, sau nawa ake neman ka a gida ba'a ganinka? Sannan ranar am sure abinda ta fara ce mini kenan da yake bata son aga laifinka sai ta wayance." Yanayinshi ɗauke da mamaki yace "Ban dai san me ya faru ba amma ni dai ba dai ni ta kawo ba sannan da kike magana haka ke kin san ma wacece Nabila ne?" Tsaki tayi tace "Malam bani hanya na wuce don wallahi baka isa ka tozarta Mummy ina raye ba, kai ko tausayinta ma baka yi? Ko duba yadda ta riƙe mu da amana baka yi ba? Kana gani abubuwan da take fuskanta akan mu a dalilin mahaifiyar mu da danginta, sannan kana ganin yadda suke faɗa da Inna akan mu, wannan wani irin rashin imani ne......." Ta ƙarasa maganar cikin tsananin takaici wanda kana ganin takaici a idanunta, taya zai yi haka? Shi kanshi kalamanta sun saka yaji jikinshi ya ƙara sanyi shi yasa duk wani abu da zai yi yayi ƙoƙarin yi ganin ya janye jikinshi daga kanta, amma yanzu yasan ba mai ganewa babu wanda zai fahimceshi. Ƙofa ta kama tana neman buɗewa da sauri ya ƙara maida ƙofar ya rufe yace "Ni kaɗai ne ɗan uwanki a duniyar nan, ki taimaki rayuwata ki jira na samu nutsuwa ni da kaina zan sanar in kuma har na wuce kwana biyu ban sanar ba na baki dama ki sanar wa Daddy ɗin, kiyi mini wannan alfarmar don Allah," ya ƙarashe maganar yana haɗe hannayenshi bibbiyu alamar roƙo. Hawaye ne ya zubo mata tace "Kwana biyu kaɗai Yaya don ba zai yiwu mu mata ace kullum muke ɗaukan laifi ba." Tana kaiwa nan ta fita, kasa ko motsi yayi saboda takaicin abinda ya aikata, tsanar kanshi na sake ratsa ko ina na jikinshi, taya zai yiwa Mumy haka? Nabeela da tun jin motsin Zee ta biyota duk abinda ya faru a ɗakin tana waje tana saurarensu, jin kalmar Zee na karshe yasa tayi saurin barin wurin tayi ɗaki tana shiga ta shige bargo ta fara kuka har da shesheƙa yadda za'a iya jiyowa daga waje. Ita kuwa Zeey tana fitowa jikin ɗakin ta tsaya tana jiyo kukan Nabeela, tabbas ba zata iya haɗa ido da ita ba, haka ta koma ɗaki kawai ta kwanta ruf da ciki, takaici duk ya isheta sai take gani kamar ma abinda ya faru laifinta ne tunda da bata dage sai Nabila ta zauna anan ba tabbas da bai haiƙe mata ba. Waya ta ɗauko tana son yiwa Baqeer magana amma bata son ɗaga mishi hankali don ta tabbatar dazu ta sanya shi cikin damuwa. Duk yadda Zee take da dauriya akan abu amma yau ji tayi ta kasa bacci haka tayi ta juyi sai wajen asuba bacci ya ɗauketa. ***** Habi ce ta kalli Asiya tace "Kinga tashi zan yi na koma gidan mu ba zai yiwu ki dinga yi mini abu kamar wata uwata ba." Cike da gadara tayi tsaki tace "Aikin banza gidan naku menene a ciki banda kunu? Ƙosai wannan ba kullum ake samu ba, amma nan kin samu banza sai ki dafa indomie ki soya kwai da dankali gashi nan duk kin cinye kayan abincin da My love ya siyo." Baki kawai Habi ta saki kafin ta tuntsire da dariya tace "Malama tashi daga baccin da kike yi, ke ɗin ƴar wacece? Kema ai ƴar kunun ce da shi aka raineki da shi kika girma." Yatsa ta nunata dashi cike da ɓacin rai tace "Wallahi ki shiga hankalinki dani, wai ni sa'arki ce ko kuwa don kinga na ɗaukeki kamar kawa kike son ki mayar dani marainiyar wayonki?" Harara itama ta zabga mata tace "Kinga kafin ma ki sallameni gidan kunu zan koma, gidan shayi asha da madara lafiya." Tana kaiwa nan ta miƙe ta fara haɗa kayanta a cikin jaka, takaici yasa Asiya jan tsaki ta koma ɗakinta tana cewa "Kiyi ki gama nasan dawowa zaki yi don yadda kika saba da cin mai maiƙo ba iya zaman gidan naku zaki yi ba, ta kalli wayarta cike da takaici don wallahi sai ta yiwa Bello wulakanci in har bai turo mata kudi yau ba, gaba ɗaya account dinta dubu biyar kacal take dashi ga kayan abinci da yawa babu, ita dai yayi sauri yazo ya dauketa su tafi don ba zata iya wannan rayuwar ba, rayuwar talauci da jiran sai an bata. Gara itama ta tafi daga can ko ta wataya ta ƙara zama babbar yarinya. ****** Cike da jin daɗi Baqeer ya kalli wayarshi, dubu dari hudu cif aka turo mishi. Wasu zafafan ƙwalla ne suka zubo mishi yana jin wani yanayi a cikin zuciyarshi na nutsuwa da salama, ya zai yi da wannan jin dadin? Sujudush shukr yayi wa Allah na godiya tabbas Allah shine maji daɗin bawa, in har yaso ya tasheka babu mai durƙusar da kai, miƙewa yayi ya dinga exercise ɗin ƙafar shi kafin ya sake kallon wayarshi, sunan Zainab ya fara dubowa sai kuma ya saki murmushi ya kira number Salim nan ya sanar dashi an biya kuɗin sannan yace suzo da yamma suje a dubo shagon da suka ce zasu kama, sai suga abubuwan da suke buƙata tunda yana da ragowar naira miliyab ɗaya da rabi na kuɗin filinshi da aka sayar, cike da jin daɗi Salim yace ai gani nan ma zuwa wannan ai ba abun jira bane. Sallama suka yi cike da jin dadi dukkansu, anan ya turawa Umma dubu arba'in ya turawa Hadiza dubu ashirin ita da Maryam su raba sannan ya turo kekenshi ya fito falo wurin Dada. Tana ganinshi tace "A'a cukumi an fito?" Murmushi kawai yayi ya hau danna wayarshi, yana son kiran Zainab sai dai yafi so sai ya kama shagon har an zuba kekunan ɗinki kafin ya kaita taga wajen. Kallon Dada yayi yace "Dada menene bamu dashi a gidan nan yanzu Salim zai zo zamu fita sai mu sayo daga can." Ƙwalla ce taji ta taru a idonta, tunda Baqeer ya samu abun yi bai ƙara bari ta rasa wani abu ba a cikin gidan don kafin ƴaƴanta su kawo mata ya cire kuɗi ya sayo duk abinda yasan suna da buƙata, ita kuwa me zata cewa Baqeeru bayan ta cigaba da yi mishi addu'ar fatan alkhairi. "Shikenan daga tambaya sai kuka Dada, idan ba kya buƙatar komai ai sai ki faɗa ba wai ki zauna kina share hawaye ba." Maficin da take fifita dashi ta ɗauka ta jefa mishi sai dai yayi saurin kaucewa yana dariya, itama dariyar tayi tace "babu abinda muke buƙata Baqeeru, ka wadata mu da komai Alhamdulillah, Allah yayi maka albarka ya baka masu yi maka kaima." Murmushi yayi, sosai yaji daɗin addu'ar da tayi mishi har yana hango kanshi da Zainab a matsayin ma'aurata har ma ga ƴan ƴaƴansu data haifa mishi, wani irin farin ciki ne yaji ya kamashi cikin ranshi yana raya inama wata rana mafarkin shi ya tabbata ya zama gaskiya yana ganin da babu wanda zai kai shi farin ciki a duniya. A daidai wannan lokacin Salim ya shigo yana sallama, ganin Baqeer a zaune yana murmushi shi kaɗai don tuni Dada ta tashi ta bar shi a wurin. Zama yayi akan shimfiɗar Dada yace "mutumina irin wannan farin ciki haka, halan wasu kuɗaɗen aka sake turo maka." Tsaki yayi still murmushin bai bar fuskarshi ba yace "tun ɗazu nake zaune a wurin nan ina zaman jiranka, a ina ka tsaya?" "Kasan lokacin da ka kirani ina kasuwa to sai da na sallami wasu customers kafin na rufe shagon na taho. Ina dai ka shirya mu tafi?" Ɗaga mishi kai yayi kafin yace "eh, bari na ɗauko atm card ɗina. Sai dai a ina kake ganin ya dace mu nemi shagon? Da a tunanina ko nan unguwar sai kuma na duba naga nan ɗin yayi wajen gari da yawa ba kowa ne zai iya biyo mu nan ba shine nace bari dai na jira kazo sai muyi shawarar inda kake ganin yafi dacewa mu buɗe shagon, idan zai yiwu dai mu nemi wurin da yake center kasuwanci inda ko address muka bayar ba zai yi wahalar zuwa ba ba cikin lungu ko cikin unguwa ba, koya ka gani?" "Hakan shawara ce mai kyau, In Sha Allah ina barin nan zan yi mana survey zan kuma bada cigiya a wasu wuraren da nake ganin za'a samu wuri mai kyau, ko kuwa yanzu kake ganin zamu fita neman wurin?" "Eh akwai wasu shaguna da wani da muke koyin ɗinki tare ya faɗa mini su nake so muje mu gani daga nan zaka rakani shopping zan je nayi mana ƴan tsince-tsince." Komawa yayi ɗaki ya canja kaya sannan ya ɗauki atm card ɗin ya saka a aljihu ya fito, kallonshi kawai Salim ya tsaya yana yi domin sai yaga Baqeer ɗin gaba ɗaya ya canja mishi kamar wanda ake yiwa wankan inji, fatarshi sai sheƙi take yi tana glowing kamar ta jarirai ga wata ƴar ƙiba da yayi alamun ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali fiye da daa. Kantin da yake zuwa idan zai yi sayayya suka je, suna tafe suna ƴar hirar su duk akan yadda suke so shagon da zasu buɗe ya kasance. Sayayya yayi musu kamar yadda ya saba sai turaren Zeey da baya fashin saya mata duk lokacin da zai je sayayya irin wannan sai dai wannan karon ya haɗa mata da wata doguwar rigar abaya daya gani tayi mishi kyau, yasan idan ta saka a jikinta tabbas zata yi mata kyau shi yasa bai ji ƙyashin saya mata ba duk kuwa da cewa rigar tana da tsada don da yaga kuɗinta sai da ya jinjina kai amma Zainab is worth every penny he has, zai iya kashe mata ko nawa ne don yaga farin ciki a fuskarta. ***** Umma na zaune a tsakar gida wajen da suke yin girki tana ƴan aikace-aikacen ta, Abu da Jamila na zaune kowacce a ƙofar ɗakinta, ita dai Abu ƙulle-ƙullen magungunan matan da take sayarwa tana yi suna zunɗen Fatima dake ta kaiwa tana kawowa ba tare data kula da me suke yi ba, tana cikin aikin Hadiza ta kirata ta sanar mata da saƙon da Baqeer ya tura musu ta account ɗinta ita da Maryam, bata san lokacin da ta saki wani murmushin farin ciki ba tana godewa Allah daya kyautata rayuwar yaronta bai bar shi ya shiga garari ba bayan da iftila'in rayuwa ya afka mishi, faɗa mata tayi ai itama ya turo mata kuɗin, nan dai suka taya juna murna domun basu yi zaton rayuwar Baqeer ɗin zata inganta har haka ba a yadda suka ga ya cire rai da rayuwa a lokacin da ya samu accident sai gashi yanzu komai ya wuce ya fara zama tarihi. Murya ƙasa-ƙasa Jamila tace "ita kuma wannan lafiyarta ƙalau dai ko naga tana dariya ita kaɗai." Kallonta Abu tayi ta yatsina fuska sannan ta ɗaga murya don Fatima ta jiyota ba kamar yadda Jamila ta saukar da tata ba tace "kika sani ko albishir ta samu nakasashen ɗanta ya warke." Suka kwashe da dariya gaba ɗaya harda tafawa, kallonsu Umma tayi tace "Abu kenan, nakasa ai ba kasawa bace jarrabawar rayuwa ce kuma mun karɓeta a yadda tazo mana muna kuma fatan Allah yasa mun cinyeta sannan kuma fata nagari lamiri idan akwai rabon zai taka a gaba sai kuga ya warke tunda abun duk yin Allah ne amma ko a haka Alhamdulillah tunda ya tsira da ranshi da lafiyarshi. Ina kuma baki shawara ki rage yawan izgili don baki san me gobe zata haifar ba sai Allah tunda dukkanmu rayuwar ba a hannunmu take ba bare muce mun san yadda ƙarshenmu zai kasance." Miƙewa Abu tayi a fusace tace "aniyarki ta biki, wato tunda ɗanki ya zama nakasashe shine kike yi mana mugun fata to ta Allah ba taki ba." "Ameen Ya Rabbi, aniyar kowa ta bi shi," Umma ta mayar mata itama don taga alama matan nan na neman ƙure haƙurinta, duk kawaicin da take yi musu basa gani har sai sun sa ta tanka musu sannan hankalin su yake kwanciya. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA UKU* {63}   Badaru ne ya shigo gidan riƙe da kwankwaso don har yanzu bai gama warkewa ba, daidai Fatima zata shiga ɗaki kamar dama jiranta yake yi sai jita yi yace “Ai ba tun yanzu ba nasan dama kin rainani, in banda iskanci kina ganina shine ba zaki gaida ni ba zaki wuce? Fatima na kula fa kin gama rainani a gidan nan wallahi zaki kwashi kayanki ki bar mini gida.” Kallonshi tayi maimakon ta bashi hakuri sai ji yayi tace “Sannu da zuwa,” daga haka ta shige ciki, ƙwafa yayi yace “Munafuka kawai ai an yanka ta tashi yanzu kaf dinku kallon kowa nake yi.” Abu tana jin haka tayi sum-sum ta shige ɗakinta ta maida ƙofar ta rufe, ya nufi ɗakin Jamila yana cewa “Munafuka kema daga ke har ɗanki kun kusa ku bar mini gidana.” Jamila ta amshi ledar bread dake hannunshi tana sanabe tana cewa “Malam kai dai kada ka wahalar da kanka don Allah kaga dai ba dadi kake ji ba.” Ciki ya shiga yana cewa “Ai ko ba lafiya gareni ba daidai nake dasu dukansu." Fatima kuwa tana shiga dakin ta saki murmushin jin daɗi tare da yiwa Allah godiya, account dinta da Baqeer ke turo kudi ta kalla, dubu dari ne a ciki don idan ya turo mata ba wani kashewa take yi ba gani take in mutanen gidan suka ga tana kashe kuɗi tabbas zargin ta zasu fara yi, ɗaki ta shiga ta kira Baqeer suka gaisa sannan tayi mishi godiya. Cike da jin daɗin dake bayyane a fuskarshi yake bata labarin shagon da zai kama, Umma wasu zafafan ƙwalla ne suka zubo saman idanunta albarka kawai take saka mishi tace zata samu tayi miya sosai a aiko musu, nan shima yayi godiya suka yi sallama. Ƙwallar data tarun mata a ido tasa hannu ta share tare da yin hamdallah. Baqeer ne ya kalli Salim wanda ya saki baki yana kallon jakar gift bag da ya siya yasa abayar nan da turaren nan a  ciki, ɗauke jakar yayi yana ƴan wurƙila ido yana cewa “Ahh lallai abu yayi karfi, ina ce dai ba a ɗinkin mata zamu ƙare ba?” Wani mugun kallo yayi mishi yace “Ka gama neman maganar ka kayan maza ma nake tunanin maida hankali sosai akai akwai abinda nake son yi.” Dariya Salim yasa yace “Faɗa mini gaskiya ba dai so kake yi ka dinga yin na maza ba saboda baka son yiwa wasu matan ɗinki inba Zee ba?” Tsuke fuska yayi yace “A yaushe nace hakan? Sannan Zeey sai dai ka faɗawa saurayinta haka ai ba ni ba.” Kai ya kau da yana shafar haɓa yana cewa “Adai gama waske-wasken za’a dawo dai inda aka barmu in ma mutum na neman sauƙi gwara ya fito ya faɗi abinda ke ranshi.” Gyaran murya Baqeer y8ai yace “Yauwa muna magana akan sunan da za’a sa in nayi ɗinki.” Matsowa Salim yayi yace “Ko zaka yi amfani da MBB ɗin ka don sunan nayi mini daɗi." Kai Baqeer ya girgiza alamar a’a sannan yace “Na gama amfani da sunan har abada, na farko na barwa wanda ya saci sunan shine last gift dana mishi a duniya, na biyu kuma bana son Baba ya gane nine da wannan sunan.” Cike da fahimta Salim ya jinjina kai yace “Na Baba dai na fahimta amma banga dalilin barwa butulu irin Bello sunanka ba.” Murmushi kawai Baqeer yayi don bai san me zai ce ba sai can yace “Ya kake ganin Muhammad B?” Salim yace “Yayi shima amma sai dai mu maida sunan Mohd kaga zai yi tsayi.” Shiru Baqeer yayi alamun nazari kafin yace “MOHBAQ fa?” Tafi Salim ya fara yace “Perfect yayi sosai dama MBB ma kai kasa da kanka sai naga wannan ma yafi dadi Mohbaq Muhammad Baqeer kenan.” “To shugaban yan washi bar zuzutawa dai.” “To ko mu tambayi Zee am sure……” Jakar hannunshi ya kusa kwada mishi, dariya Salim yasa yana cewa “Ah to wai don ka tabbatar.” “Kai dai nasan yanzu bakinka ba shiru zai yi ba kana matsawa zaka kira Habi.” Yanayin fuskar Salim ne ya ɗan canza yace “Nifa kunsa mana ido babu abinda ke tsakanina da ita," kamar tasan abinda ke faruwa kawai sai ga kiran wayarta cikin wayarshi, kallon Baqeer yayi tare da saurin maida wayar aljihu wanda hakan yasa Baqeer cewa “Ya? Ta kira ne? Kuje kusha soyayyar ku ni babu ruwana.” Fita yayi daga shagon da sauri yana cewa “Ba ita bace customer ne.” Kallonshi yayi yana girgiza kai, kallon shagon yayi nan ya fara tura kekensa yana bin girman shagon da kallo don shaguna huɗu suka je gani sai wannan hankalinshi ya fi kwanciya dashi saboda girmanshi yana ganin in za ayi abu gwara ayi shi a wadace. Aunawa ya dinga yi abubuwan da ya kamata su siya na furnishing ɗin shagon, nutsuwa da kwanciyar hankali ke sake ratsashi, wayarshi ya kalla sai kuma yayi murmushi haka kawai yaji yana son jin ya take, text ya mata yace “Zafa a baki fail a exam ɗin .” Zeey lokacin tana zaune ɗakin Mummy sun yi shiru gaba ɗaya ta rasa me zata cewa Mummy, ita kam Mummy a kwance akan gado wani matsanancin ciwon kai take ji don gaba ɗaya jiya bata samu bacci ba, senate kuma da safe ya fita saboda wani taro da zai yi attending a Niger State, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kamo hannun Mummy ta riƙe gam cikin sanyin murya take cewa, “Mummy na bashi kwana biyu ya sanarwa Daddy da kanshi, sai dai yanzu an riga an shiga kwana ɗayan farko In Sha Allahu zamu samu mafita, sai dai an cuci Nabila ban san yadda zamu yi da baiwar Allahn nan ba.” Kai Mummy ta girgiza itama ta ƙara rike hannun Zee tana cewa “Aikin gama ya riga ya gama, sannan in da lefin Kabir ita ma da nata laifin, tsorona Allah tsorona Senate ko Inna wani yaji abinda ke faruwa,” ta ƙarasa maganar cike da damuwa, kallonta ta sake yi tace “Ya aka yi kika sani?” Wani abu ta haɗiya tace “Ta kirani jiya akan tana da ciki to da farko ban yarda ba amma da nazo na ganta sai na tabbatar, sannan ƙin faɗar wanene da kuma yadda nasan ba yawo take yi ba yasa na fara zargin Ya Kabir, naje wurinshi na bugi cikinshi sai kuma kalamanshi da actions ɗin shi suka tabbatar mini abinda nake zargi, Mummy taya Ya Kabir zai yi mana haka?” Wasu ƙwalla masu zafi ne suka taru a idonta. Mummy ta rungumeta tace “Babu komai Zeey mubi komai a sannu In Sha Allahu Allah zai kawo mafita.” Kallonta tayi tace “Allah zai kawo mafita amma bazan bari a cuceta ba kin dai sani, dole ne Daddy yasan abinda ake ciki sannan Inna ma ki sanar da ita ko ni na sanar da ita, babu yadda za ayi tace tana da ciki a bar abu har sai ya girma kafin asan abun yi.” Ajiyar zuciya Mummy tayi don tasan wacece Zeey akan faɗar gaskiya ko da mahaifinta ne sai tayi faɗa sannan in tana da ra’ayin abu babu mai canza mata shi akan wannan dalilin yasa sam bata da ƙawaye don bakinta baya shiru. Ganin Mummy zata lallaɓata yasa ta fito daga ɗakin ta shiga nata, kallon ɗakin tayi yayi kaca-kaca saboda Nabila bata gyara mata ba, fitowa tayi tasa mai aiki tazo ta gyara mata sannan ta amso abincin Mummy ta kai mata ta koma ta ɗauko na Nabeela ta kai mata, rungume juna kawai suka yi Nabeela na kuka tana shafar bayanta, sun daɗe a haka kafin tace “Ya isa Aunty Nabs In Sha Allahu komai zai tafi daidai.” Kai ta girgiza tana cewa “Ta yaya? Bayan babu wanda zai fahimceni? Nice da cikin kuma ni aka ƙwacewa virginity? Sannan ni za’a bari da zagi?” “Kinyi PT ya nuna positive ne?” Kai ta ɗaga alamar eh kafin tace sau hudu ina yi amma still positive," ido ta ɗan runtse, Nabila ta kalleta tana hawaye tace “Zeey don Allah ki taimakeni tsoro nake ji ke kinsan ni wacece babu yadda za ayi na kula wani inba ta ƙarfi aka nuna mun ba.” Hannu tasa a saman leɓenta tace “Na sani, ke dai kici abinci ki kwantar da hankalinki.” Tana kaiwa nan ta fito daga ɗakin, jita yi komai na gidan ma bata so hakan yasa kawai ta shirya ta ɗauki wayarta ta fito ta faɗa mota tayi gaba. ***** Da mamaki Kamalu yake kallon yaron shagon Baba yace “Kai dan gidanku nida shagon mu zaka hanani shiga?” Yaron ya sake danne ƙofar ta ciki yace “Don Allah Kamal kar ka janyo mini matsala ka ga Baba saura kaɗan ya koreni don Allah ka bari in yana shagon kazo.” Buga ƙofar ya fara kamar zai ɓalla ta hakan yasa mutane suka fara kallonshi, ƙwafa yayi ya juya yana masifa "yaron nan wallahi sai na tareshi a lungu nayi mishi dukan tsiya, sai ya san ni ya wulaƙanta ɗan banza ɓarawo kawai, ai kaine kake sata tunda ni kayan ubana gadona nake ci." Aljihunshi ya laluba yaga babu komai, ajiyar zuciya yayi ya hango wani mai babur wanda yake sak irin nashi, da gudu ya nufi mai babur ɗin dake cikin hold up, yana zuwa yace “Bawan Allah ɗan zo nan don Allah tambayarka zan yi.” Me babur ya zabga mishi wani kallon banza yace “Sauri nake yi.” Ya fara tuƙin shi, gudu Kamalu yasa yana bin babur ɗin sai dai duk yanda yake zabga gudu bai cimma shi ba haka ya dinga haki yana sauke ajiyar zuciya, haka ya ƙarasa gida da ƙafa saboda babu kuɗi a hannunshi ya gaji ya galabaita sosai ga wata azababiyar yunwa dake ƙara kamashi. ***** Zeey tana tada mota taga text ɗin Baqeer a hankali ta saki wani murmushi, a yanzu shi kaɗai take son gani, maimakon tayi mishi reply sai ta ajiye wayar ta nufi gidan Dada. Dada ta dawo daga maƙotansu kenan inda aka yi haihuwa kwanaki yau mai jego tayi arba’in zata koma gidan mijinta shine tazo gidan suka sha hira, tana ganin motar Zeey ta fara murna tana cewa “Lale da Zainabuwa ta.” Fitowa Zeey tayi tana murmushi tace “Dada ta daga ina haka?” “Naje makota ne mai jego tayi arba’in baki ga yaron ba yayi ɓulɓul abinshi.” Murmushi tayi tace “Dada kina son yara.” “Saura naki ɗan, Allah yasa nayi wa ɗanki wanka ke da Baqeer.” Ido ta zaro da sauri tace “Dada wani Baqeer ɗin?” “A’a Zainabuwa kwantar da hankalinki nufina da yaran ki da yaranshi ai ko tsugunawa yayi bazan bashi ke ba yadda kike ɗin nan sai namijin da yafi kowa mutunci zan bawa.” Dariya Zeey tasa tace “Dada tawa Allah dai ya bar mini ke.” Ciki suka shiga tana cewa “Mutumin baya nan ma sun fita shi da Salim….” Ganin takalminshi yasa tace “Ashe ma ya dawo, Baqeeru kana ciki ne?” Shafa addu’ar da yake yayi ya koma kan wheel chair yana cewa “Dada kin dawo?” Yayi maganar yana buɗe ƙofa, idanuwanshi ne suka sauka akan Zee, tana jingine da jikin bangon kusa da ɗakin, wani nutsuwa da farin ciki ne ya sauko mishi ya zuba mata ido yana cewa “Dada ban san kin shigo ba ai.” Itama murmushin tayi tace “Dada kin kulle ɗaki ne hala?” Daga ciki tace “Zainabu bari ina zuwa abu zan ɗauko.” Kallonta yayi yace “Ɗaki yafi dadi ai,” Yayi maganar idanunshi na kanta. Tana kallonshi itama tace “Bani.” Ido ya ɗan canza yace “Me?” “Mark ɗina," hannunshi yasa a aljihu ya ciro biro yazo daf da inda ta miƙo hannun ya fara mata zane, kallonshi kawai take yi tana murmushi, zanen ƙwarangwal yayi mata sama-sama, baki ta buɗe bayan ta kalla a shagwaɓe tace “Wato nice ma ƙwarangwal?” Biron yasa a gefen kuncinsa yace “Mark kika ce kuma baki ci komai ba.” Ta turo baki tace “Allah a faɗa mini, please menene.” Kiyi browsing ki gani, wayarta ta dauka ta rubuta ganin bata gane ba still yasa tace “Wani yare ne?” “Hmm arabic?” Nan ta sake rubutawa kurawa wayar ido tayi kawai sannan ta dago tana yi mishi wani kasalalken kallo wanda ya dinga ji komai na jikinshi na sagewa, tace “Wai da duk sorry ne aka dinga wahalar dani? Allah sai na rama an yi 1-0.” Shima murmushin yayi yace “Anya ba 5-0 aka yi ba?” Jakar gift ɗin daya saya mata ya kalla yana son ɗaukowa yaji muryar Dada tana cewa “Zainabu share wannan kizo in nuna miki wani abu,” Kallonshi tayi shima kallonta yayi sannan suka kalli Dada. Me zai gani? Album ne a hanunta da sauri yace “Dada wallahi a’a.” Dariya tayi tace “Dalla kai dai ka koma ɗakin ka ni hotona zan nuna mata ba wani abun ba.” Da sauri ya turo kekenshi, itama Zee ta nufo wurin tana dariya tana cewa “To Ya Baqeer ai dai hoton Dada aka ce ba naka ba.” *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar ce* *Da Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA HUƊU* {64} Zaman dirshan tayi ta baza hotunan a gabanta tana kallo tana dariya, yawanci hotunan Dada ne tana budurwa sai waɗanda suka ɗauka da mahaifin su Umma lokacin tana amarya. Haka Zeey ta sakata a gaba tana dariyar kwalliyarta harda ƙwalla. Tana cikin kallon hotunan ne taga hoton wani yaro an ɗaukeshi da kwanon fura a gabanshi fuskar nan tayi dagace-dagace da furar kamar wanda ya wanke fuska da furar. Ɗagowa tayi ta kalli Baqeer sai ta ƙara kallon hoton, can dai tace "Dada waye wannan?" Ta ɗaga hoton tana nuna mata. Dariya Dada ta saka kafin tace "Waye kuwa idan ba dunkum ba, kin san fa ci ne dashi yana ƙarami." Kallonshi Zeey tayi sai ta kwashe da dariya har da riƙe ciki tace "Wai Ya Baqeer ka ganka kuwa," hannu ya kai zai ƙwace hoton tayi sauri ta janye hoton tana cigaba da dariya. A gefe ta ajiye hoton ta cigaba da kallon hotunan sai dai duk da haka lokaci bayan lokaci sai ta juya ta kalleshi ta sake kwashewa da dariya. Har suka gama kallon hotunan bata daina dariyar wancan hoton na Baqeer ba, sai da ta tattare wa Dada hotunanta ta ɗaga wancan hoton tace "Dada ina son wannan, kin bani?" "Baki da dama Zainabu, duk hotunan nan ki rasa wanda zaki ɗauka sai wannan?" A shagwaɓe tace "Ni dai Dada shi nake so ki bani, kin ji?" Dariya tayi tace "Idan ma duka kike so ai zan baki bare wannan ƙwaya ɗaya." Juyawa tayi ta kalli Baqeer tayi mishi gwalo sai kuma tace "Ya Baqeer," shiru yayi ya rabu da ita. Tashi tayi ta koma kusa dashi tace "Ya Baqeer mana, please ka juyo ka kalleni magana zamu yi." Har cikin ɓargonshi sai da Baqeer yaji ƙiran nan da tayi mishi don tayi ƙasa sosai da muryarta sai tayi maganar cikin yanayinta na shagwaɓa abinda yasa yaji wani abu ya tsirga mishi tun daga tsakar kanshi har zuwa tafin ƙafarshi. Kallonta yayi sai yaga itama shi take kallo, hoton dake hannunta ta ɗaga mishi tana dariya ƙasa-ƙasa tace "Ka tuna?" Gira ya ɗaga mata da sigar tambaya sai kuma yace "Me?" "Wannan hoton ka tuna lokacin da aka ɗauka?" Girgiza kai yayi alamar a'a don anyi hoton lokacin bai fi shekara biyu ba, ba zai iya tuna sanda aka ɗauka ba. Hannu ya miƙa mata don ta bashi hoton har ta miƙa mishi sai ta tuna ba lallai ne ya dawo mata dashi ba don haka tayi saurin janye hannunta tana dariya tace "Naƙi wayon nasan idan na baka ya tafi kenan ba dawo mini dashi zaka yi ba." Shima dariyar yayi "Da gaske zan baki gani kawai zan yi." Maƙe kafaɗa tayi tace "Ni dai a'a gaskiya." Ɗan ɓata rai yayi kamar yayi fushi yaƙi magana, kallonshi tayi tace "Wai fushi kayi don nace bazan baka ba? To gashi," yi tayi kamar ta miƙo mishi sai da ya waiwayo yaga wayarta take miƙo mishi. Da mamaki ya kalleta yace " Me zan yi da ita?" "Oho," tace tana ɗaga kafaɗa, naga kamar kayi fushi ne shine na baka wayata a madadin hoton. Mayar mata da wayar yayi sai kuma yace "Ki ajiye wannan zan baki wani kinga wannan tsohon hoto ne." "Ni dai shi nake so sai dai idan zaka yarda na ɗauke ka wani a wayata sai na baka wannan." Girgiza kai yayi alamun a'a, cewa tayi "Shikenan ka huta sai ka bar min abuna tunda dama ba kai ka bani ba bare kace sai na dawo maka dashi." Cikin ranta kuwa cewa take yi 'me kike yi haka ne wai Zainab? Kada fa kiyi abinda zai fallasa asirin da kike ɓoyewa cikin zuciyarki'. Shiru suka yi na wasu ƴan mintuna, tashi tayi ta leƙa Dada a ɗaki tace "Zan tafi Dada sai an kwana biyu kuma," tashi tayi ta biyota tana cewa "Bari na taka miki." Koda suka fito daga ɗakin baya tsakar gidan, ƙofar ɗakinsni Zeey ta kalla tana tunanin daga tashinta shine har ya shige ɗaki, kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru, daga nan tsakar gidan suka yi sallama da Dada ta fita. Tsayawa tayi turus ganin shi a jikin motarta da gift bag a hannunshi, ƙarasawa tayi wurin tace "Kana nan ashe?" "Da ina kike tunanin zani?" Shima ya mayar mata da tambayar. Ɗaga kafaɗa tayi irin nima ban sani ba ɗinnan sai kuma tace "Ban sani ba ko ka shiga ɗaki ne." Miƙa mata gift bag ɗin yayi, bata karɓa ba sai cewa tayi "Me zan yi dashi?" "Karɓa mana, naki ne," hannu tasa ta karɓa sannan ta buɗe gift bag ɗin ta leƙa ciki sai taga kwalin turaren da yake yawan saya mata ne sai kuma fabric ɗin da bata san ko miye ba sai taje gida sannan ta duba ta gani. "Thank you," tace tana ɗan murmushi cikin jin daɗi, matsawa yayi daga jikin motar ya bata wuri ta shige. Har ta tayar da motar zata tafi sai kuma ta leƙo da kanta waje tace "Me yasa kake yawan yi min kyauta Ya Baqeer? Wacece ni a wurinka?" Bata tsaya ta saurari amsar da zai bata ba ta figi motar a guje ta bar wurin don gabanta faɗuwa kawai yake yi saboda kamar wacce aka matsi bakinta ta samu kanta da yi mishi wannan tambayar ba tare data shirya ba shi yasa tayi saurin barin wurin don bata son jin amsar da zata fito daga bakinshi ta zama akasin abinda take fata. ***** Har motar ta ɓacewa ganinshi bai daina bin hanyar da tayi da kallo ba. Wacece ita a wurin shi take tambayar shi, to wacce amsa zai bata? Zai fito ne ya faɗa mata gaskiyar matsayin da ya bata a cikin zuciyarshi ko kuwa zai ƙyaleta ne suci gaba da tafiya a yadda suke yi? Idan ya fallasa mata asirin zuciyarshi ba lallai ne ta amshi soyayyarshi ba don ido ba mudu ba yasan ƙima, ko ba'a faɗa mishi ba yasan daga babban gida ta fito, ko babu nakasa ita ɗin ba ajin shi ba ce to bare ga larurar dake tare dashi bayan haka bai manta da Junaid ba duk da taƙi amsa mishi shi yasan saurayinta, to ya isa yayi takara dashi a yadda yake ɗinnan? Yasan idan aka bata zaɓi tsakanin shi da Junaid dole shi zata zaɓa ta barshi saboda shine tsaran rayuwarta shine sa'an aurenta ba shi ɗan gidan Mallam Badaru da Umma Fatima ba. Kasa komawa cikin gidan yayi sai ya tafi can wajen da su Tanimu suke zama inda yake zuwa daa, bai samu Tanimu ba saboda yanzu akwai shagon da yake zuwa yana taya su ɗinki yace so yake yi hannunshi ya faɗa sosai kafin lokacin da Baqeer zai buɗe nashi shagon. Zama yayi cikin yaran da ya samu a wurin yana kallon duk abinda suke yi, tausayi yaran suke bashi don wasu a cikinsu basu fi shekaru biyar ba, yaran da basu wuce raino ba shine iyayensu suka tsige su daga jikinsu suka kawo su almajiranta babu ci babu sha kuma a haka suke iya bacci hankalinsu a kwance alhalin basu san a wane hali ƴaƴansu suke ciki ba, cikin ranshi yana ji inama shi wani mai faɗa aji ne da babu abinda zai hana bai daƙile kai yara garuruwa yawon almajiranta ba tunda in dai don karatu kowanne gari akwai makarantun allo me ya hana su barin yaran a kusa dasu idan har da gaske saboda karatun ake kai su ba don su yakice nauyin da Allah ya ɗora musu ba. Bai bar wurin ba sai da aka yi kiran sallar magriba, daga nan wurin masallaci ya wuce bai koma gida ba sai da ya sallaci sallar isha'i sannan ya koma. Yana shiga gida Dada ta tare shi da tambayar inda ya shiga tun ɗazu bai dawo ba. Ɗan murmushi yayi yace "Dada ni yaro ne da don na fita na daɗe ban dawo ba duk zaki bi ki damu, ina can wajen dasu Tanimu suke zama daga nan kuma na wuce masallaci kin san kuma ina tsayawa ɗaukar karatu duk bayan sallar magriba zuwa isha'i, abinda ya hanani dawowa da wuri kenan." Kwanukan abincin shi ta ajiye a gabanshi tace "Ni dai bana son daɗewar nan da kake yi a waje yadda rayuwar nan ta lalace babba ma ba tsira yayi ba bare yaro bare kai da ba lafiyar ƙafafu gareka ba." Jinjina kai yayi yace "To Dada In Sha Allah xan kiyaye," don yasan fa gaskiya ta faɗa mishi, yadda rayuwar nan ta lalace mutane ba abun yarda bane. ***** Sai da tayi nisa sosai da barin unguwar sannan ta samu wuri tayi parking ta ɗora hannunta akan ƙirjinta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi kamar wacce zata fasa ƙirjinta ta fito. Ita kuwa yau me ya shiga kanta ne? Me ya kaita furtawa Baqeer waɗannan kalmomin? Yanzu da wane ido zata ƙara kallonshi saboda Allah bayan wannan abun kunyar data tafka, wai wacece ita a wurin shi, inndai ba abinda take fatan ji daga gareshi zata ji ba me ya kaita yi mishi wannan tambayar. Idanunta ne suka kai kan gift bag ɗin daya bata ta janyo ta buɗe ta fito da kayan ciki, turaren Arden beauty (Elizabeth Arden) daya sabar mata da fesawa don tun daga ranar farko da yayi mata kyauta dashi ta bar turaren da take amfani dashi ta komawa wannan, ajiye shi tayi a gefe ta fito da abayar ai bata san lokacin da ta furta kalmar "wow" ba don sosai abayar nan ta tafi da ita, tayi mata kyau sosai kuma daga texture na fabric ɗin tasan ba ƙananun kuɗi ta kwasa ba. Irin waɗannan gestures ɗin na Baqeer ke sawa take ganin shima yana sonta kamar yadda zuciyarta ta afu a soyayyar shi, to amma idan da gaske yana sonta me ya hana shi furta mata duk tsawon lokacin nan da suka ɗauka tare, bai taɓa tambayar wani abu a kanta ba, bai taɓa nuna son yasan wacece ita ba duk da tana tsoron ranar da zai gano ita wacece amma tana ganin idan har akwai wannan son a tsakaninsu sanin asalin wacece ita ba zai zamo matsala ga tarayyarsu ba. Haɗa kayan tayi ta mayar cikin gift bag ɗin sannan ta ɗauki wayarta ta tura mishi saƙon sms. "I wanted to let you know how much I love the gift you gave me. Your thoughtfulness truly touched my heart. Thank you." Ajiye wayar tayi bayan ta tabbatar message ɗin yayi delivering sannan ta tashi motarta ta bar wurin, wani irin mixed feelings take ji a tattare da ita, ɓangare ɗaya tana jin takaicin kanta na yadda take kasa iya controlling emotions ɗinta akan Baqeer har sai tayi wani abu da daga baya zata zo tana dana sani a ɗaya ɓangaren kuma tana jin shauƙi da ƙaunarshi na daɗa ratsa dukkanin wasu sassa na jikinta, ta rasa me zata yi da Baqeer zai fahimci halin da take ciki, tana so duk ranar da Daddy ya ƙara yi mata maganar Junaid ace tana da makamar dafawa amma idan bata san a wane matsayi ya ajiyeta ba bata isa ta tunkari Daddy da zancen shi ba. Har ta ƙarasa gida bata da cikakkiyar nutsuwar zuciya, gabanta ne ya faɗi da taga motar Daddy fake a harabar gidan, yaushe ya dawo? Tayi wa kanta tambayar da bata da amsarta. Jiki a sanyaye ta fito daga cikin motar har ta ɗauki gift bag ɗin zata shiga da ita gida sai tayi wani tunani don haka ta mayar da ita mota ta ajiye, tasan yanzu tana shiga ciki za'a fara yi mata tambayar daga ina take tunda ba wai ta faɗawa Mummy zata fita bane, to a yadda ta fita ta bar gidan ma ai bata jin akwai wanda zai lura da rashinta a gidan yadda duka mutanen gidan basa cikin walwala. Har tayi hanyar ɗakinta don bata so kowa ya ganta bare asan dawowarta gidan sai ta fasa jin kamar hayaniya na tashi daga parlourn Daddy. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un," tace haɗe da ɗora hannu aka ganin yadda Daddy yake dukan Kabir da wata sharɓeɓiyar dorina, a gefe ga Nabila a tsugune tana kuka sai Mummy dake tsaye hankalinta a tashe idanunta na tsiyayar da hawaye, tama kasa ƙarasawa kusa da Daddyn bare ta hanashi dukan da yake yiwa Kabir ɗin. A rikice Zainab tace "Daddy......" *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD*         *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BIYAR* {65} Ta ƙarasa wurin da sauri tace “Daddy please!” Wani kallo ya watsa mata yace “Ban taɓa tunanin har dake za’a haɗu a tozartani ba, a cikin gidana? No way!” Ya sake maganar yana ƙara zubawa Kabir bulala, yana zaune duk uban azabar da yake ji na zafin dukan bai sa ya tashi ba don dama tunda Daddy yaji yasan abinda zai biyo baya sai ya wuce haka, kallon Nabila yayi wacce tayi ƙasa da kai tana share ƙwalla, tana cewa “Daddy don Allah kayi haƙuri na tabbatar shima yayi dana sani, don Allah Daddy…..” kuka ne yaci karfinta wanda ya hanata iya cigaba da abinda zata faɗa, ganin jini ta gefen wuyan Kabir yasa Mummy tace “Senate please ya isa haka.” Hannu ya ɗaga mata tare da cewa, “Tashi ki koma ɗaki wannafatan umarni ne na baki.” Mummy haka ta miƙe kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki tayi ɗaki, ya sake ɗaga bulalan zai doki Kabir, Zeey tayi saurin tsayawa a gabanshi zuciyarta baza ta iya bari a cigaba da fasawa Kabir jiki haka ba, kallon Daddy tayi hawaye suka zubo mata tace “Daddy kar ka illatashi a zauna asan solution ɗin da za’a nema tunda mai afkuwa ta riga ta afku.” “Kin matsa ko kema sai na zuba miki dukan a jiki? Ni zaku maida shashasha a gidana? To wallahi ba a gidan nan ba, babu wanda ya isa ya tozartani balle yaja mini mutane su fahimci gidana ma ban gyara ba balle in jagoranci mutane.” Matsawa yayi daga inda Zeey take ya sake zubawa Kabir wani bulalar, ido ya runtse don shi kaɗai yasan me yake ji, saukar bulalar yaji sai dai ba a jikinshi ba, hakan yasa ya buɗe ido, ganin Zeey yayi a tsaye a daidai inda Daddy ya kai dukan, ya sani duk faɗan da suke yi da ita tana sonshi don kaf duniya su biyu ne a wurin mahaifinsu, kallon juna suka yi idanunta sun cicciko da ƙwalla don rabon da a daketa har ta manta, shi kanshi Daddy ganin Zeey ya daka yasa jikinshi yayi sanyi, kallonshi tayi tace “Daddy na roƙeka da Allah ka bar wannan dukan, sannan bafa abinda ya faru kake shakka ba tsoron siyasarka kake kaga mafita itace.” Fuskarsa a tamke yace “Ba wani mafita shiryawa zata yi gobe ita da Mummy zasu je a cireshi, da hankalina babu wanda ya isa ya kawo min ɗan shege sannan ko an zubar bazan iya aura mata shi ba zan dai nemo mata wani ta aura, kai kuma wallahi in baka yi wasa ba gidan mari zan kaika aje can a rufe soko don wallahi baka isa ka lalatamin tafiyar nan ba.” Kai kawai Kabir ya saukar ƙasa yana jin wani irin ƙunci a zuciyarshi. “Daddy zubarwa kuma?” Zee tayi tambayar cike da shakkun kalamanshi, wani kallo yayi mata ya yarda bulalar yace “ƙwarai kuwa don ba dai ni za’a haifawa cikin shege ba.” Yana kaiwa nan yayi ciki yana sababi, wani kallo tayi wa Kabir wanda kana gani kasan na  bacin rai ne sannan ta kamo Nabila suka bar wurin. Tun a hanyar ɗaki Nabila ke kuka har suka shiga ɗaki ta kamo hannun Zeey tace “Zeey tsoro nake ji don Allah kar a zubar ba gwara muyi aure a huta ba?” Kallonta tayi cike da tausayi kafin tace “Kin san Daddy ba zai yarda ba, ki kwanta ki huta In Sha Allahu komai zai tafi daidai. Nabila tana riƙe da ciki tana cewa “Ni dai bazan zubar ba sai dai na shiga duniya, Zeey ki taimaka min don Allah, akwai aure tsakanina dashi me yasa kuke haramta auren bayan ya halarta?” Tausayinta ne ya ƙara kama Zeey hakan yasa tayi ɗakinta jiki a sanyaye tana shiga ta kwanta akan gado tana jin kanta na wani irin sarawa, ga bayanta inda aka daketa har yanzu zugi yake yi mata, tashi tayi ta kalli madubi ta yaye rigarta ta baya sai ga shatin duka har ya fara tashi, nan da nan taji zuciyarta ta karaya, waya ta ɗauka ta kira Baqeer don muryarshi kawai take son ji. Har sai data kusa katsewa don yanata yankan ɗinki sam bai ji kiran ba wayar tana silent, da sauri ya ɗauka sanda idanunshi suka kai kan sunanta na motsi a jikin wayar, karawa yayi a kunnenshi yace “Assalamu Alaikum!” Cikin sanyin murya tace “Wa’alaikasalam da na ɗauka baka kusa.” “Me ya sameki?” Tambayar daya jefeta dashi kenan, cike da mamaki tace  “Me ka gani?” “Yanayin muryarki ya canja, meya faru?” Kwanciyarta ta gyara taja bargon duvet da aka yi gyaran gadon dashi tace “Abubuwa da yawa, ɗazu ma ganinka dana yi abu ne ya faru yasa na bar gidan, sai dai na yanzu yafi na ɗazu.” Ɗan ajiyar zuciya ya sauke kaɗan yana cewa “Zancen ranan nan ne?” Tana ƙifta ido gun dauriya tace “Eh!” “Kenan solutions ɗin bai samu ba?” Ta kara cewa “Eh sannan yanzu abubuwan ma sunfi lalacewa zance ya ƙarasa kunnen Daddy.” “How?” Ya tambayeta yana ajiye scissors ɗin hannunshi, ita kanta tambayar data yiwa kanta kenan how? Taya aka yi ya sani bayan lokacin da ta fita baya gidan? Sannan ta tabbatar Kabir ba shi zai sanar dashi ba to meya faru? Muryar Baqeer ce ta katseta da cewa “Baki san ya aka yi ba?” Miƙewa zaune tayi tace “Ya Baqeer bye zan kiraka anjima.” Kai ya jinjina ga mamakinta ji tayi yace “Please ki kula da kanki.” Cak ta tsaya saboda kalamanshi sun shiga jikinta, shi kanshi jin abinda bakinshi ya furta yasa yayi saurin kashe wayar don tabbas abinda ke zuciyarshi ne ya fito fili ba tare da ya shiryawa hakan ba, shafar sumar kanshi yayi sannan ya ɗan maida hankali kan wayar yana cewa “Allah ya warware muku abinda ke faruwa.” **** Zee kuwa miƙewa tayi ta sauko daga kan gado ta zauna akan sofa ɗin ɗakin tana nazari, ya aka yi Daddy ya sani? Waya sanar dashi? Don dai kaf cikin wanda suka sani bata jin akwai wanda zai sanar dashi, fitowa tayi daga ɗakin kai tsaye ta nufi ɗakin Kabir, a kulle taji shi sai dai tasan dama da ƙyar in zai barshi a buɗe, hakan yasa ta nufi ɗakin Nabila saboda ta tabbatar ba Mummy bace wannan kam bama sai tayi tunani akai ba. Nabila har yanzu na nan kwance a inda ta barta, zama tayi a bakin gado fuskarta a tamke sosai babu alamun wasa take kallonta, kafin tace “Aunty Nabs ke kika sanar da Daddy?” Gaban Nabila ne yayi wani irin faɗuwa don sam bata tsammaci tambayar nan daga wurin Zee ba, zama tayi ta kalleta tana goge ƙwalla kafin tace “Ba….” “Kar ki ce ba ke bace don Ya Kabir ba zai taɓa sanar dashi ba balle Mummy duk da kema bansa a raina zaki yi ba sai dai nafi tunanin ke akan su, na farko Kabir yasan in Daddy yaji shine zai shiga tashin hankali sannan mun yi dashi akan kwana biyu kenan gobe ne lokacin dana bashi, wanda nasan goben ma sai mun kai ruwa rana zai yarda a sanar.” Cike da rawar murya tace “Nima ban sani ba mistakenly ne naje tura text ma Dr ashe Daddy na turawa ban kula ba, kin ga dukkansu D ne to ina kwance kaina na ciwo sam ban kula da wanda na turawa ba har sai da Daddy ya dawo ya kirani nan ya fara tambayata akan meya faru shine na sanar mishi, kema kin san wallahi a san raina bazan sanar dashi ba.” Kallon zargi Zee kawai take yi mata, mistake? Ganin bata gamsu ba yasa ta ɗauko wayarta da sauri ta nunawa Zee text ɗin wanda a ciki ma Dr ta rubuta akan ya zata yi da ciki ƙarami ba wanda ya sani a gidansu tana kuma tsoron aji. Miƙa mata wayar Zee tayi kafin tace “A ina kika san Dr ɗin da har zaki yarda ki sanar dashi irin wannan babban sirrin?” Nan ma wata faɗuwar gaban ce ta kamata, mamaki take yi yaushe Zee ta fara wayau haka? Don a iya saninta ta yarda da ita in har ta faɗa mata abu bata taɓa bincike take yarda, anya bata yi ganganci ba kuwa wurin tura saƙon nan? To amma kuskure ne ai ba laifinta bane, kallon Zee take cike da rauni tace “Na sanshi don sanda nayi BUK yana level 5 ina level 1 to muna shiri sosai, bayan ya fara aiki ma duk yawanci abubuwana wurinshi nake zuwa.” Kai Zeey ta jinjina alamun fahimta duk da ta rasa me yasa zuciyarta ke shakku akan abinda ke faruwa, miƙewa tayi ta nufi ƙofa ta waigo ta kalli Nabila sannan ta fita, ɗakin Mummy tayi, daga waje tana juyo sababin da Daddy yake yiwa Mummy yana cewa “Kina zaune a gidan nan har yaron nan yayi wa yarinyar nan fin ƙarfi? Ke kin san yadda na yarda dake na jingina amanar gidana a hannunki ashe da abinda zaki saka mini kenan? Tun yaushe nake sanar dake yaron nan sam ban yarda da wasu daga cikin dabi’un shi ba?” Mummy cike da tausayin Kabir tace “Senate ƙaddara ce fa Allah ya ɗauro mana wallahi ni nasan Kabir ba zai aikata abin nan da sanin shi ba, ka duba ka gani duk yawon da yake yi da ƴan matan da ke sonshi ka taɓa ji an kawo ƙararshi ance yana neman wasu? Ko kuwa duk matan dake sonshi za ace su basu kai Nabila bane? Allah shine shaidata ni nasan ba da saninshi bane sannan ita ma Nabilan ka daina bata gaskiya gaba ɗaya…….” “Ba wani kema kin san Nabila dai bazata taɓa kai kanta wurin Kabir ba, yanzu me kike so ayi in har Inna taji? Bayan kece shaida dama tana jin haushin yadda na sakar miki kula da yarana. Tana ganin kamar ni na hanaki haihuwa." Kamo hannunshi Mummy tayi tace "baza ma taji ba, in har babu wani abu ka bari suyi aure, ita kanta Inna baza tayi faɗa ba in taji aure suka yi kaga ko haihuwa tayi a ƙalla za ace ai ta haihu da wuri ne tunda cikin nan ƙarami ne, ina tsoron garin zubar da ciki wani abun ya faru ne, sannan in tsautsayi yasa Inna tasan abinda ya faru daga baya wallahi har ƙara zata iya kaimu kasan yadda take ji da Nabila.” Zama yayi a bakin gado ranshi na ƙara ɓaci shidai gaskiya ba dai aure ba, ba wai baya son Nabila bane sai dai gaskiya ba zai bari su ƙare a gidansu Inna ba, shi ya auri Mummy ne don babu yadda zai yi wanda daga baya ya maida ita class ɗin da yake so, amma banda Nabila don ɗan shi gaskiya sai dai ya auri yarinyar da zata taimaka mishi a siyasa, ba wai wacce ba’a sani ba. Kallon Mummy yayi don ba zai iya sanar da ita dalilinshi na ƙin auran ba sai cewa yayi “Ki shirya zan kira Dr Suhail kuje a zubar da cikin nan, salin alin ba tare da wani ya sani, kinga daga nan ta koma wurin Inna kawai ni zan nema mata miji na nunawa tsara ayi aurensu cikin rufin asiri.” Mummy ta jinjina kai tace “Shikenan!” Jin haka yasa Zee ta bar wurin, ɗakin Kabir ta ƙara komawa don zuciyarta ta kasa nutsuwa, in har ita bayanta ya fashe haka da shatin bulala ina ga shi? Ƙwanƙwasawa tayi tace “Ya Kabir buɗe.” Kamar bazai buɗe ba sai kuma ya buɗe bai jira ta shigo ba ya koma ciki ya zauna a bakin gado tare da haɗe hannayenshi waje guda, jingina tayi da jikin ƙofa tana kallonshi tace “Yanzu menene plans ɗin ka?” “Banda wani plan kema kin san sai abinda Daddy ya tsara.” Cike da takaici tace “Kai ma Yaya why? In mace kake so me yasa baza kayi aure ba? Yanzu fisabillilahi me ka jawo mana?” Idanunshi da suka yi jaa ya ɗago ya zuba mata yace “Nake son mace a ina? Ke kinsan da a matse nake da tun kan ki dawo nayi aure, kawai bani da ra’ayin ajiye iyali ne yanzu.” Ranta a ɓace da jin kalamanshi yasa tace “Ba kada niyyar ajiye iyali amma kana da niyyar yin fyade? Sannan a cikin gida? Ba kunya ba tsoron Allah,   abinda Aunty Nabs ke ji....” Cike da ɗaga murya yace “Wai kowa ni yake ɗaurawa laifi? Ita fa? Ko don ina namiji shi kenan nine mai yin komai? Kuna ina sanda take biyoni har ɗakin nan don na kulata? Kuna ina sanda take nuna soyayyarta a gareni ina rejecting ɗinta? Kuna ina sanda nake korarta daga ɗakina amma take ƙin fita? Ko don ni ban bayyana abubuwan da take yi mini ba shi kenan kuma sai laifi yayi ta zama nawa?” Hankali a tashe Zee ke kallon Kabir tana mamakin jin kalaman dake fita daga bakinshi, kanta take ji yana wani irin sara mata, me take ji yana faɗa? Nabila? No way…….. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA SHIDA* {66} Girgiza kai kawai take yi ta kasa gasgata abinda kunnenta ya ke jiye mata, ta yaya ma za'a yi ace wai Nabila ke bibiyarshi, Nabila dai data sani wannan mai yawan nutsuwar da kamun kai wacce kullum idan Daddy zai yi mata faɗa da ita yake yin kwatance yace tayi kwaikwayo da kyawawan halayenta ko yace bata ganin yadda Nabila take girmama manya ga son aiki saɓanin ita da bata iya komai ba sai son jiki ga rashin iya magana, kai ba zai taɓa yiwuwa ba ba dai Nabila. Wani irin kallo tayi mishi ta juya zata bar ɗakin sai jin muryarshi tayi yace "Kenan kin fi yarda da ita akan ni ɗan uwanki?" Juyowa tayi ta kalleshi ya ɗaga mata kai yace "Ribar me zan ci idan nayi mata sharri akan abinda bata yi ba, ki yarda dani Zainab wallahi ita ta riƙa bibiyata idan kin lura zaki ga na rage yawan zama a gida to wallahi duk saboda ita ne, ko ƙarfe nawa zan kai a waje idan na dawo gida zan tarar da ita tana jirana ko ta shiga ɗakina ta laɓe kuma duk a hakan ban taɓa gwada nemanta da wani abu ba saboda babu son ta a zuciyata don haka ban taɓa jin sha'awar kasancewa da ita ba, ita ta fara nemana da wannan rayuwar a cewarta romance kawai zamu yi, tun ina kaucewa har nazo na biye mata kuma wallahi ni ban yi mata fyaɗe ba tunda dai kin san bana shaye-shaye bare tace na sha wani abu daya fitar dani daga hankalina har na afka mata ban sani ba. Please Zainab ki yarda dani idan har da gaske cikin dake jikinta nawa ne ki yarda to ba fyaɗe nayi mata ba da yardarta da amincewarta komai ya faru." Gaba ɗaya fuskarshi ta koma kalar tausayi, lokaci guda duk ya rame yayi wani iri alamun yana cikin tashin hankali mai girma wanda sam bata kula da hakan ba sai yanzu. Ita tama rasa tunani guda ɗaya da zata yi, gaba ɗayansu daga Nabilan har Kabir ɗin kowa idan ya tara maka zance sai kaji shine mai gaskiya. Fita tayi taje ta ɗauko first aid kit ɗinsu ta dawo ɗakin sai ta samu ya cire rigar jikinshi ya kwanta akan cikinshi, gaba ɗaya bayanshi ya kwaye tsabar dukan da Daddy yayi mishi. Hankali a tashe ta ƙaraso cikin ɗakin tace "Me yasa ka tsaya yayi maka irin wannan dukan kamar ya samu jaki baka gudu ba?" Zama tayi akan gadon ta wanke mishi ciwukan tana yi tana mitar don me yasa zai tsaya Daddy yayi mishi irin wannan dukan gashi nan duk ya farfasa mishi jiki. Shi dai yana jinta halin damuwar da yake jin kanshi a ciki ne yasa ya kasa amsa mata. Haka ta wanke mishi duka ciwukan sannan ta tashi ta fita da first aid kit ɗin, kitchen ta shiga tasa masu aiki suka dama mishi oats ta ɗauka ta kai mishi, da ƙyar ta matsa mishi ya tashi ya sha sannan ta ɓalli paracetamol ta bashi yasha har jikinshi ya game da zazzaɓi me zafi sai rawar sanyi yake yi, rufe shi tayi da duvet ta fita ta rufe mishi ƙofar ganin alamun shi kamar bacci yake son yi. ***** Shi kuwa Daddy yana barin ɗakin Mummy ɗakinshi ya koma abun duniya ya taru yayi mishi yawa, shi yanzu ya zai da abun maganar da Kabir yake neman janyo mishi ace kamar shi ɗanshi yayi wa ƙanwar matarshi ciki. Tashi yayi ya hau zagaye a tsakar ɗakin shi yana neman mafita, gaba ɗaya yana cikin tashin hankali, tension yayi mishi yawa, ga yawon campaign daya sako shi a gaba ko zaman gidan baya samun yi soaaigashi Kabir yaje ya ɗauko mishi wata maganar. Tunani yayi tun kafin maganar cikin nan taje kunnen Inna tace dole sai Kabir ya auri Nabila gara ya nemo mishi mata yayi maza ya aurar dashi. Kai gaba ɗaya ma zai aurar dasu ya huta haka kurum ba zasu janyo mishi magana ba, dama uban Junaid ya daɗe yana so suzo a saka rana shine yake watsar da zancen saboda yafi son a samu fahimtar juna sosai tsakanin Zainab da Junaid ɗin amma yanzu tunda haka ne zai basu dama su fito a tsayar da rana kawai ayi bikin cikin ƙanƙanin lokaci, babu mai janyo mishi matsala a harkar siyasar da yake ganin akwai nasara a cikin tsayuwarshi takara. Wayarshi ya ɗauka ya ƙira mahaifin Junaid, bayan sun gama ƴan gaishe-gaishensu irin na tsofaffin abokai da suka aminta da juna yace mishi dama akan batun auren Junaid da Zainab ne idan sun shirya su fito a tsayar da rana don baya son abun ya ɗauki lokaci so yake yi ayi auren tare dana Kabir kafin lokacin zaɓe yayi. Sosai baban Junaid yaji daɗi don dama abinda suke ta fata kenan suga auren tilon ɗan nasu da matar da yake matuƙar so. Suna gama waya ya ƙira Junaid yayi mishi albishir, duk da maganar tazo mishi a bazata sosai yayi murna don bai taɓa tunanin Zeey zata sauko da wuri ta amince mishi aurenta ba ganin yadda ko wayarshi yanzu ba koyaushe take amsawa ba. Yana asibiti lokacin da Babanshi yayi mishi wayar haka ya sallami sauran patients ɗin shi akan ba zai iya dubasu a yau ba sai dai su dawo gobe ya tafi gida zuciyarshi cike da ɗokin son ganin Zeey. Fitowa Daddy yayi yana ƙwala ƙiran Zainab lokacin ta fito daga ɗakin Kabir kenan, sai da taji gabanta ya faɗi saboda irin ƙiran da yake yi mata. A parlourn shi ta tarar dashi a tsaye ya goya hannayenshi a baya sai kaiwa da kawowa yake yi, tashin hanakalin da ya samu kanshi a ciki yasa ya kasa zama a wuri ɗaya, idan ba gani yayi ba ya samu mafitar wannan badaƙalar da ƴaƴanshi ke neman sakashi a ciki ba hankalinshi ba kwanciya zai yi ba. Zainab na zuwa tace "Gani Daddy," bayan ta zauna akan kujera tana kallon yadda Daddyn ya kasa zama a wuri ɗaya sai fama zagaye yake yi a cikin parlourn kamar mai yin parade. Kallonta yayi ya nunata da yatsa yace "Ina fata kun gama daidaitawa da Junaid don mun gama magana da mahaifin shi zasu zo mu tsayar da ranar aurenku nan ba da jimawa ba." Shiru tayi ma ta kasa magana jin yadda maganar tazo mata a bazata, ana cikin wancan case ɗin me ya kawo wannan? "Tashi kije," taji muryar Daddy kamar daga nesa yana bata umarni. Sai sannan ta dawo cikin hayyacinta tace "Wani irin aure kuma Daddy bayan na faɗa maka bana son shi, ni dai gaskiya bazan aureshi ba." A fusace yace "Na dai faɗa miki aurar dake zan yi kuma banga uban da ya isa ya hanani ba, ruwanki ne ki koyawa kanki son shi ruwanki ne ki ƙi aure ne dai ke da Junaid babu fashi." Ya fice daga gidan a fusace ranshi yana tafasa. Tashi tayi a guje ta shige ɗakinta tana kuka. Mummy da fitowarta kenan daga nata ɗakin taga wucewar Zainab ɗakinta tana kuka ta bita ɗakin hankali a tashe tana fatan ba wata matsalar bace ta sake kunnowa kuma. Tana shiga ta ganta ta kifa kai akan gado sai gurshaƙen kuka take yi, tambayarta tayi abinda aka yi mata take irin wannan kukan. Ɗagowa tayi ta kalli Mummy fuskar nan tayi jawur idanunta sun yi kozai-kozai alamun taci kuka ya isheta tace "Wai Daddy ne yace sun gama magana da Baban Junaid zasu saka ranar aurenmu dashi bayan tun da farko na faɗa mishi ni bana son shi amma yaƙi yarda kuma ma Mummy ni ina da wanda nake so me yasa ba za'a barni na aureshi ba." Zama Mummy tayi a bakin gadon tasa hannu tana shafawa Zainab baya kamar mai lallashin wata ƙaramar yarinya tace "To me yasa baki faɗa mishi ba?" Sai cewa tayi "Bayan bai bari nayi magana ba ya fice yana masifa ni kuma wallahi babu mai yi min auren dole haka kurum." Shiru tayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin tace "Ai kin san ko kowa bai tsaya miki ba ni zan tsaya miki, ba Daddy ba koma waye babu mai yi miki auren dole idan har ina raye wanda kike so shi zaki aura, haba wane irin auren dole sai kace muna zamanin iyaye da kakanni." Kanta ta kwantar akan cinyar Mummy tana jin wata irin nutsuwa na ratsata don tasan ko kowa bai goya mata baya ba Mummy na tare da ita. A shgwaɓe tace "Mummy bai fa ce yana so na ba." Tsaki Mummyn tayi tace "Ke ba sai ki faɗa mishi ba tunda dai ba haramun bane ba kuma ace dole sai namiji ne zai fara furtawa mace soyayya ba, babu batun wani ɓoye-ɓoye yadda zamanin nan ya canja don kin faɗa mishi kina son shi ba laifi bane." Haka Mummy tayi ta ƙarfafarta tana nuna mata ta kwantar da hankalinta don ba zata taɓa bari ayi mata aure da mijin da bata so ba abinda yasa ta samu ƴar nutsuwa ke ab don tasan tunda Mummy tace haka ita tasan yadda zata yi tasa Daddy ya haƙura da batun aura mata Junaid. Tana kwance tana saƙa da warwara akan shawarar da Mummy ta bata na ta fara furtawa Baqeer cewa tana son shi sai dai kuma zuciyarta ta kasa nutsuwa da yin hakan tana ganin kamar bai dace ba a matsayinta na ɗiya mace da aka sani da kunya da kawaici ta fara bayyana mishi asirin zuciyarta, to sa ma ace tayi hakan idan shi baya jin irin abinda take ji akan shi ba fa kenan ta zubar da ƙimarta ta ɗiya mace ta fallasa mishi asirin zuciyarta yazo yace baya sonta bata san a wane hali zuciyarta zata kasance ba, tana jin watakila ma bugawa zata yi don bata ga ta inda zata iya rayuwar da babu Baqeer a cikinta ba. Mummy ce ta shigo ɗakinta tana faɗa mata Junaid na guest sitting room yana jiranta. A fusace ta tashi zaune tace "Mummy me yazo yi a wurina kuma? Please Mummy kice mishi ya tafi wallahi na tsane shi bana son ganinshi, shine bayan duk faɗa mishi da nayi tayi akan ni bazan aureshi ba a matsayin aboki kawai na ɗauke shi yaje ya turo Babanshi zasu sa ayi mini auren dole to wallahi bazan aureshi ba, idan shi maye ne sai dai ya cinye kanshi da kanshi amma ni nafi ƙarfin nacin shi wallahi." Hannayenta Mummy ta riƙo tace "Duk wannan faɗan da kike yi ai shi ya kamata kije ki yiwa ba wai ki zauna anan kina yi ba alhalin bai ma san kin yi ba, zuwa zaki yi kija mishi kunne kice ya fita sabgarki don ba aurenshi zaki yi ba tunda dai kin tabbatar ba kya son shi to gara ya kama gabanshi tun wuri yasan nayi don nasan harda yawan ganinshi yana zuwa wurinki da Daddy ke yi yasa ya bijiro da maganar aurenki da shi kamar wacce muke neman kai dake, ni an faɗa mishi idan zaki tabbata babu aure zan damu ne, a yadda nake jin ƙaunarki a cikin zuciyata ban ƙi muyi ta zaman mu a cikin gidan nan ba don bana son tuna akwai wata rana da dole zamu rabu kiyi aure." Tashi tayi tana jinjina kai, tabbas harda fuskar data sakarwa Junaid yasa kowa ke tunanin soyayya suke yi bayan tasha faɗa cewa ita ba zata aureahi ba saboda a aboki kawau take kallonshi ba wai masoyi ba. Haja ta fita fuska kozai-kozai ko ruwa bata sa ta wanketa ba Tana shiga sitting room ɗin babu wata gaisuwa babu komai kawai Zainab ta rufe shi da masifa tace "ai dai kasan ba sonka nake yi abotar ma kuma na fasa don haka tun wuri gara kaje ka samu su Daddy ka faɗa musu ba zaka aureni ba don wallahi idan ka yarda ka aureni ka aurar wa kanka tashin hankali, haba bana son naci wallahi. Ka dai san nasha faɗa maka ni bazan aureka ba amma ka nace akan magana ɗaya, to tun wuri kaje ka faɗa musu ka janye don ni dai bazan aure ka ba, to na auri sa'ana nace na auri wa ma?" Idan ka kalli Junaid a wannan lokacin sai ya baka tausayi gaba ɗaya ɗokin da yazo dashi ya gama gabanshi, ashe bada yardar Zeey iyayensu suka yanke musu wannan hukuncin ba. Ɗan zamowa yayi daga kan kujerar da yake zauna yace "haba Zainab don Allah kada ki bari son da nake yi miki ya tafi a haka, kema kin san ina son ki tun kafin iyayenmu suyi tunanin haɗamu, please ki bani dama na nuna miki irin son da nake yi miki, bana buƙatar sai kin soni son da nake yi miki kaɗai ya ishemu ba sai kin so ni ba har ƙarshen rayuwarmu," tsaki tayi ta mishi wani irin wulaƙantaccen kallo tace "Ai ni zama da wanda bana so ne ma ba zan iya ba kwata-kwata, shawara kuma ta rage ga mai shiga rijiya don ni dai na gama magana," daga haka ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi anan. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD*         *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA BAKWAI* {67} Tana fita daga falon ɗakinta ta nufa nan da nan kuma tausayin Junaid ya ziyarci zuciyarta, ta sani bata kyauta mishi ba sai dai babu yadda zata yi don kuwa babu abinda zai sa ta aureshi, duk wani abu da Daddy zai yi sai dai yayi amma ita dai babu mai tilasta mata aurenshi, Baqeer take so kuma yanzu ta sani shine jigo na rayuwarta ko da ba zata iya furta mishi ba zata jira lokacin daya shirya sanar da ita abinda ke ranshi akanta. “Kina tunanin yana sonki ne?” Tambayar data zo kanta kenan ji tayi abin duniya ya isheta, pillow ɗin dake kan gado ta ɗauka ta cillar ƙasa, wani irin takaici na ƙara kamata, sallar magriba tayi sannan ta zauna tana jin yunwa amma ɓacin rai ya hanata neman abinci. Junaid kuwa da ƙyar ya iya kwasar ƙafarshi ya bar gidan don ji yayi kamar an ɗebi ruwan sanyi an kwara mishi, mota ma da ƙyar ya iya shiga yayi zuru yana tunanin ta yadda zai yi ma ya kunna motar yaja ya tafi gida, yafi minti goma a ciki kafin ya daure yaja motar sai dai tafiya kawai yake yi babu wani laka a jikinshi. Mummy ce ta turo ƙofar ɗakin riƙe da tire na abinci, Zee tana ganinta ta sake jan bargo ta rufa, zama tayi kusa da ita tace “Auta tashi don Allah kin dai san bana son wannan halin ko?” Kallonta tayi cike da shagwaɓa tace “Allah Mummy ba wai naso wulaƙanta Junaid bane kawai dai nasan in ban faɗa mishi maganganu ba bazai ƙyaleni ba.” Kai Mummy ta jinjina tace “Hakan shine daidai in har kasan abu ba zai zama alheri ba to tabbas kar ma ka soma bawa mutum false hope, shi Daddynki muƙaminshi yake dubawa sai dai ni farin cikin ki nake dubawa, Nabila ta ruguza mana farin cikin gidan nan ba zan yarda ke ma a ruguza miki farin cikin rayuwarki ba.” Ƙanƙame Mumy tayi tace “Na sani duk duniya babu mai sona sama dake, ke kaɗai ce gatana shi yasa a koda yaushe nake alfahari da kasancewarki mahaifiyata.” Shafar saman kanta tayi tace “Nice zan yi alfahari Zeey baki san yadda nake farin cikin kasancewa tare da ke bane.” Ɗagowa tayi kaɗan tana kallonta tace “Wannan sakaliyar ƴar taki da bata iya komai ba?” Kuncinta taja tace “Sai me? Sannan menene zai sa ki koyi wani abu bayan muna da kuɗin da zamu yi providing ɗinki with everything you need? Burina kiji daɗin rayuwa bawai ki wahala ba, ko aure ki kayi na faɗa miki zan haɗaki da mai kula da komai naki babu abinda zaki yi sai hutawa.” Dariya taɗan yi kaɗan tace “Mummy ni kam tambaya, Aunty Nabila tana son Ya Kabir ne?” Yanayin Mummy ne ya canza ta ɗan janye kaɗan tana cewa “Bana son zancen yarinyar nan sam, sannan gobe da safe zamu je asibiti daga can wurin Inna zata koma.” Cike da rashin jin daɗin kalamanta Zee tace “Mummy me yasa ne sam ba kya tsayawa ki fahimci halin da take ciki? Yanzu tun bayan faruwar abun nan kin duba ta? Kinji ya take ciki? Kin tambayeta halin da take ciki?” Mummy ta kalleta jiki a sanyaye tace “Ba sai na tambayeta ba don kuwa bana son jin komai, ni zamanta a gidan nan ma ba so nake yi ba, balle yanzu da ta gama ja mini cin mutunci.” Mamaki gaba ɗaya sai sake rufe Zeey yake yi kawai ji tayi bazata iya magana ba, hakan yasa ta sake jan bargo ta rufa, Mummy ta yaye bargon tace “Tashi kema kici abinci, ai Zabba’u tace kin sa an yiwa Kabir abinda zai ci amma ke baki yi tunanin kice ayi miki ba.” “Aunty Nabila fa? Taci abincin ne?” Mummy ta tsuke fuska sosai tace “So kike muyi faɗa?” Shiru Zeey tayi kawai tana kallonta, ajiye mata abincin tayi sannan ta shafi gefen kanta ta fita, ga mamakinta Nabila ce tsaye a ƙofar ɗakin kamar dama jiranta take yi ta fito, yi tayi kamar bata ganta ba sai jita yi tace “Ki gama kauce-kaucen dole zaki dawo kibi bayana.” Wani kallo Mummy tayi mata tace “Ke yanzu laɓe ma ba abin kunya kika ɗauke shi ba naga alama, ki haɗa kayanki da safe daga asibiti gidan Inna zan kai ki.” Da sauri tace “Babu fa inda zani don ina nan har sai anyi aurena da Kabir.” Wani banzan kallo Mummy tayi mata tace “Waye zai yi miki auren?” Da mamaki tace “Wa kuwa in ba Daddy ba?” Tsaki Mummy taja tace “Na kula har yanzu hankalinki bai dawo jikinki ba, mutumin da yace a zubar da cikin jikinki shine kike tunanin zai aura miki ɗanshi? To ki buɗe kunnuwanki kiji da kyau in ma bacci kike yi ki farka Senate duk yadda yake yabon kyawawan halayenki a wurinshi baki kai ya aura miki ɗanshi ba,” tana kaiwa nan ta cigaba da tafiya cike da takaicin shirmen Nabila, shi yasa take ta nuna mata a’a amma ita sam ta kasa ganewa. Nabila kuwa kasa ko motsi tayi har Mummy ta ƙule bata iya cewa komai ba, ɗakinta ta nufa hankali a tashe ta fara cin babban farcenta na hagu jikinta har karkarwa yake yi saboda tsoro, ta shiga uku, yanzu ya zata yi? (Umm Asghar da Ayusher kam muka ce muma bamu sani ba🥴) ********   Baqeer kam da Zee ya kwana a ranshi yana tashi asuba bayan yayi sallah yayi addu’oi kiran wayarta yayi haka nan yaji zuciyarshi baza ta iya jira gari ya waye ba tare da yaji muryarta ba, Zeey ita ma tayi sallah kenan don ta ɗan makara kaɗan saboda tunanuka da suka yi mata yawa, ganin kiran Baqeer yasa tasa a ranta zata tambayeshi matsayinta da safen nan don ta samu ta yiwa Daddy bayani akwai wanda ma take so, ajiyar zuciya tayi sannan ta kishingiɗa akan gado ta ɗaga wayar. Shiru suka ɗan yi kaɗan kafin yace “Ba sallama?” Tace “Assalamu Alaikum!” Yace “Wa’alaikissalam kin ware yanzu?” Ta ƙara gyara kanta tace “Bayan baka damu dani ba baka kira da daddare kaji ya nake ba.” Da sauri yace “Inji wa?” Sai kuma yayi shiru, kallon wayar tayi cike da mamakin kalamanshi don ta tabbatar daga ƙasan ranshi ya fito tace “To ba haka bane?” “Umm!” Tace “Umm?” Yace “Eh to shikenan? Seriously na ɗauka kin kwanta ne.” Murmushi ta saki kamar yana ganinta tace “Guess what?” Yace “Me?” Tace “kayi guessing kai dai.” Ɗan nazari kaɗan yayi yace “Kun samo solution?” Ta girgiza kai tace “Nope! Abinda ya shafeni ne ni da kai.” Nazari ya sake yi yace “Menene?” Ta ɗan sake rage murya tace “Wasa nake yi.” Murmushi yayi sosai yace “Na manta wa nake waya da ita ashe.” Shiru suka ɗan yi kowa da abinda ke ranshi kafin yace “Is everything alright?” Ta ɗan yi shiru kafin tace “A’a komai ya sake wargajewa, sai dai ina fatan komai ya tafi daidai.” Jiki a sanyaye yace “In Sha Allahu komai zai tafi daidai.” “Jiya Junaid yazo,” ta faɗa cike da son jin me zai ce, Baqeer kuwa nan da nan ya haɗe rai, ai bai tambayeta zancen saurayinta ba bare tace amsa ta bashi tunda ya tambayeta, shiru yayi hakan yasa tace “Ya Baqeer kaji me nace?” Cikin dakakkiyar murya yace “Eh!” Shiru tayi don yadda ya amsa yasa ta rasa me zata ce, can tace “Akwai abinda nake son faɗa maka amma ba gobe ba sai dai ko jibi.” Cike da son jin menene yace “Kuma sai a bar ni da tunani har kwana biyu?” Kallon wayar tayi kafin tace “Ni wacece a wurinka wacce in nace zan faɗa maka magana baka so ta daɗe ban sanar maka ba?” Shiru yayi yana son cewa “Muradin zuciyata, wacce zuciyata ke bege a koda yaushe," sai dai ganinshi a keken guragu da irin ƙatuwar motar da take hawa da ƙatuwar mota da aikin Junaid yasa yaji ya kasa cewa komai, shi a wa? Jin shiru yasa Zee jikinta yin wani mugun sanyi, muryarta cikin sanyi tace “Kayi tunani jibi in mun haɗu ka faɗa mini in har baka san matsayina a wurinka ba to a gabanka zan goge number wayarka sannan ni da gidan Dada kuma shi kenan har abada don banga amfanin cigaba da tarayyarmu ba.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar, kifa kai tayi tana tunanin wannan shine mafitar data dace da ita, wai ita yarinyar da bata yarda da so ba ita ke zubar da ajinta akan ɗa namiji? Bayan tasan duk ranar da yasan ita wacece shikenan alaƙarsu ta ƙare? “Ya Allah!” Ta furta a fili tana jin wani yanayi a cikin zuciyarta. ***** Umma cikin baccinta taji kamar ana ƙwala mata kira, ita ba yara ƴan makaranta ba balle ta tashi da safen nan, ga sanyi da ake a gari, abin mamakin ma daga waje ake kiran nata ba ciki ba. Fitowa tayi da sauri tana cewa “Malam lafiya? Allah dai yasa ba wani abun ne ya faru ba?” Wani banzan kallo yayi mata yace “Yau wai ba girkinki bane?” Mamaki ya kamata wanda ya bayyana a fuskarta tace “Girki nane amma kiran na menene?” Da hannu ya nunata yace “Kinga bana son shirmen banza da wofi ki fito yanzu kisa a siyo wake da mai don ƙosai nake son ci da kunu.” Baki ta ɗan buɗe kaɗan tace “Malam haka kawai da safe kace ƙosai zaka ci da kunu? Ina ma masu shagon suka buɗe?” “Eh lallai wuyanki ya isa yanka, to a cikin kuɗina na kujeru da kika cinye ki ciro kisa a siyo wake da mai, sannan ayi mini kunu wallahi in lokacin fita ta yayi ba ayi ba za’a gamu da ɓacin rai na.” Kallonshi tayi jiki a sanyaye tace “Malam kaji tsoron Allah rabona da in ganka ma a ɗakina har na manta balle kuɗin cefane da zaka bani ranar girki na, kana son cewa har wannan lokacin kuɗin kujeru muke ci?” “To in ma ba na kujeru bane da alama kuɗin sata ko haram kike ci tunda ke dai ba kudi gareki ba ba kuma sana’ace dake ba, ni dai na faɗa miki in fito inga abincin da nake so,” yana kaiwa nan ya shiga ɗakin Jamila yana cewa “Zan koya miki hankali da kaina, ina zaune zaki ɗauki jakarki ki bar mini gida.” **** Ƙarfe bakwai Mummy ta haɗa breakfast a kan dining, Daddy ne ya fito fuskarshi sam babu walwala wanda kana gani kasan ba wani baccin kirki ya samu ba, zama yayi sannan ya kalleta yace “Bani wayata na kira Kabir.” Miƙa mishi tayi tana cewa “Senate ka saki ranka please kaga dai akwai important meeting da zaka yi yau.” Murmushi kawai yayi baice komai ba, sai kiran Kabir da yayi yana zama ya kira Zeey itama. Kallonsu yayi yana cin haɗin soyayyen dankali da kayan ciki wanda yasha attarugu da tattasai da albasa sai ƙamshi ke tashi, fuskar nan tashi babu walwala yake cin abincinshi, babu alamun zasu ci don dukkansu da alama cikin ɓacin rai suke, Daddy ne ya kalli Zeey yace “Jiya kin dai ji me nace miki ko?” Kanta tsaye tace “Naji amma ba abinda zai sa na aureshi bayan tun farko na faɗa maka ni bana son shi.” Wani kallo yayi mata sannan ya kalli Kabir yace “Ka shirya anjima kaje gidan Alhaji Nafi’u kaga yarinyarshi mun riga mun gama magana auren ku zan haɗa nayi ƙarshen wani watan kuma wallahi duk wanda yaƙi bin umarnina zai gamu dani.” “Daddy me kake cewa? Taya zan yi aure a cikin wannan yanayin? Ana wannan case ɗin?” Kallonshi yayi yace “Wani case kenan?” Da mamaki Zeey da Kabir suka kalleshi, ya cigaba da cin abincinshi yana cewa “Oh wai tsautsayin daya afka kan Nabila? Baiwar Allah ƙaddara ce ta afku mata amma da zarar yayarta ta fita da ita komai zai dawo daidai.” Zeey bata san sanda tayi wani murmushin takaici ba tace “Na ɗauka ma daka kira shi haƙurin dukan daka yi mishi ka farfasa mishi jiki zaka bashi sai ma kazo da wani zance? Taya ma zaka ce yayi aure? Ita kuma Nabila fa” Tamke fuska yayi sosai ya tashi yana kallon Kabir wanda shima kallonshi yake yi, babu tsoro yanzu ko shakkar Daddy da yake dashi a da, yace “Na dai faɗa maka,” yana kaiwa nan ya fita daga falon, shima Kabir fita yayi ya bar gidan ma gaba ɗaya. Mummy ce ta kalli Zeey wanda gaba ɗaya suma yanayinsu babu daɗi sai dai basu da ta cewa, haka ta fito ita da Nabila suka shiga mota suka bar gidan suma. A hanya Nabila tace “Saukeni.” Mummy ta kalleta tace “Kema kin san baki isa ba, tun kafin ki ja mana matsala gwara ki kwantar da hankalinki aje a cire cikin nan, kafin ma ki lalata rayuwarki don Kabir ma aure zai yi.” Gabanta ne yayi wani irin faduwa tace “Aure?” Mummy bata kulata ba sai cigaba da jan mota da take yi, Nabila ta fara sakin wani irin ihu tana jijiga ƙofa kai kace zararriya ce tana ihu tana cewa “Buɗe ni, buɗe ni ko wallahi na ce satoni kika yi.” Tsoron abinda Nabila ke yi yasa Mummy yin parking ai kafin ta gama daidaita motar ma Nabila ta fita, adaidaita ta shiga ta wuce gidan Inna tana tafe tana kuka kai kace wani ne ya mutu. Tana shiga gida tun a tsakar gida ta ƙara buɗe maƙogwaro tana zabga ihu, Inna daga ciki ta jiyo ihu cike da tsoro ta fito, mamaki ne ya kamata ganin Nabila nan ta rungumeta tace “Nabila? Menene?” Kuka sosai take yi kamar ranta zai fita a cikin kukan tace “Inna na shiga uku, Kabir yayi mini ciki ta ƙarfi sannan yanzu mahaifinshi yace aure zai yi mishi da wata bani ba.” Jikin Inna ne ya fara rawa da sauri tayi baya tana maimaita kalmar ciki? Ciki? Ina zan sa kaina da wannan abun kunya a karo na biyu? Baya tayi saboda jin wani duhu ya mamaye mata idanuwanta, jikinta har rawa yake yi take cewa “Kaini gidan wallahi ba zai yiwu ba, kaini gidan yanzun nan Nabila.” Da yake abinda take so kenan da sauri ta fito dama tace mai adaidaita ya jirata tunda tasan Inna dama dole taje gidan, haka suka juya gidan Inna sam ta kasa nutsuwa zuciyarta sai bugawa take yi da sauri da sauri, kanta na wani irin zafi. A falo suka samu Mummy don dama tunda Nabila ta gudu ta dawo gida, ta zauna a falo tana tunanin abun yi ko dai ta tashi taje wurin Inna ne tayi mata bayani? Ai kafin ma ta bawa zuciyarta amsa taji ance “Shashashar banza shashashar wofi wallahi kin yi asara ke dai kam baki ji daɗin halinki ba, ki sadaukar da komai naki kiƙi haihuwa dashi amma ƴarki ƙwaya ɗaya baza ki iya amsar mata hakkinta ba? Jininki guda ɗaya dake duniya shine ba zai iya kula miki da ita ba?” Mummy a zabure ta ɗago ta kalli Inna waigawa tayi da sauri tana fatan babu wanda ke wurin sai dai me? Daddy ta gani tsaye a bakin ƙofa don har yayi nisa ya tuna ya bar wasu takardu ya kuma kira number Mummy bata ɗauka ba, jikinta ne ya fara rawa, me zata gani Zeey na tsaye a jikin ƙofar ɗakinta don jin hayaniya yasa ta fito, wasu zafafan ƙwalla ne suka zubowa Mummy shikenan rayuwarta ta ƙare…….. (Baki a sake muka kalli juna, meke faruwa? Me Inna ke nufi da kalamanta? Tana son cewa Nabila ƴar Mummy ce ko kuwa dai kuskuren harshe ne tayi?) ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD*         *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA TAKWAS* {68} Gaba ɗaya parlourn ya ɗauki wani irin shiru na wasu ƴan mintuna, sai a sannan Inna ta ankara da ɓaramɓaramar da tayi. Hankali a tashe Mummy ke kallon Daddy, wani irin kallo yake yi mata daya ƙara sawa jikinta yin sanyi. Baki ta buɗe zata yi magana sai dai ta rasa ma me zata ce. Ƙarasa shigowa cikin parlourn Daddy yayi yace "Me nake ji Inna tana faɗa Halima?" Jikin Mummy ne ya ɗauki rawa sai girgiza kai take yi ta kasa cewa komai. "Da gaske ne Nabila ƴarki ce da kika haifa ta cikin ki ba ƙanwarki ba?" Ya sake jefa mata wata tambayar, Mummy dai babu baki sai ido. Wata irin gigitacciyar tsawa yayi mata yace "magana nake yi miki ki buɗe baki ki amsa mini shin Nabila ƴarki ce ko ƙanwarki?" Gaba ɗaya sai ta sake rikicewa don tunda take da Daddy bata taɓa ganin fushin shi irin wannan ba, in banda hawaye babu abinda ke kwarara daga idanunta. Wani irin kallo Daddy yake yi mata sai ya juya ya kalli Nabila dake tsaye a gefen Inna yana ganin kamanni na zahiri tsakanin Mummyn da Nabila kamannin da bai taɓa tsayawa ya lura dasu a tsakaninsu ba saboda duk lokacin nan a zaman ƙanwarta take a wajenshi. Hannu yasa ya tura hular daje kanshi baya ta faɗi a ƙasa. "Lahaula wala ƙuwwata illa billah,' kawai yaje ambatawa. Tuni ya manta da batun meeting ɗin da zashi da mantuwar da yayi ta dawo dashi gidan har yaji wannan mummunan zancen mai kama da almara. Ƙara kallonta yayi sai yaga gaba ɗaya baƙinta yake gani, cikin wata irin masifaffiyar murya da duk wanda aka yiwa amfani da ita sai ya ruɗe yace "duk tsawon shekarun da muka ɗauka tare baki yi tunanin akwai wata rana da zata zo ba da zan iya sanin cewa ita ɗin ƴarki ce shi yasa kika zaɓi ki ɓoye mini?" Cikin rawar murya tace "Senate," hannu ya ɗaga mata alamun baya son jin komai daga bakinta. Juyawa yayi ya kalli Inna yace "kun san cewa Nabila ba ƙanwarta bace ƴarta ce amma kuka rufeni baku taɓa sanar dani ba? Akwai wani abu da kuke ɓoyewa ne?" Gaba ɗayansu suka yi shiru ita kanta Inna a yadda taga Daddy ya birkice musu a yau wani irin mugun tsoronshi ne taji ya kamata. Wani tunani ne ya ɗarau a ranshi sai ya waiwaya ya ƙara kallon Mummy yace "kun ma je inda na turaku kuwa?" Ɗan shiru tayi tana tunanin to ina ya turasu, aka kuma ta tuna ashe fa asibiti yace suje a zubar da cikin jikin Nabila. Da kai ta amsa mishi don a yadda take jin bakinta yayi mata nauyi baza ta iya furta kowacce kalma ba. A fusace yace "baku je saboda kema kina son Kabir ya auri ƴarki?" Murya ba rawa tace "ba haka bane Senate, wallahi ba haka bane zan kaita." "Da dai ya fiye muku don na faɗa miki Kabir ba zai auri Nabila ba ba a gidana za'a yi wannan kwamacalar ba ace ɗana yana auren ƴar matata wacce kowa yake yiwa kallon ƙanwarta, mun riga mun gama magana da Alhaji don haka tun wuri gara ku san yadda zaku yi da cikin nan, ba kuma naso maganar ciki ta ɗara parlourn nan kin san idan ta fita ba ƙaramar illah zata yiwa kujerar da nake nema ba don haka ku kiyaye." Nabila na jin abinda Daddy yace ta zube a wurin tana birgima tana ihu akan ita dai a bar mata cikinta kada a zubar tsoro take ji. "Rufe mana baki mutuniyar banza, duk bake kika janyo mana ba da baki je kin bashi kanki ba hakan zai faru ne?" Inna tayi mata tsawa tana jin wani irin ɓacin rai na ƙara taso mata ɓacin ran da bata taɓa nuna tunanin zata ƙara jin kwatankwacin shi ba tun a shekarun baya da wani abu mai kama da wannan ya faru dasu. Rarrafawa Nabila tayi wajen Daddy tace "Don Allah Daddy kada kuce sai an cire cikin nan wallahi tsoro nake ji ance mutuwa ake yi a wajen zubar da cikin, ka aura mini Kabir ɗin yadda asirinmu zai ƙara rufuwa in yaso sai ka aura mishi waccan ɗin ni na amince." Wani irin kallo yayi nata yace "Zancen banza kenan ko ki amince ko kada ki amince Kabir aure zai yi, maganar aure a tsakaninku kuma na haramta shi, ki tashi kuje a zubar da cikin kamar yadda na ce, ni zan samo miki miji daidai ke amma ba Kabir ba." Haushin Nabila ne Inna taji ya kamata ganin yadda Daddy yake nanata ba zai aurawa ɗan shi ita ba ita kuma sai faman naci take yi kamar shi kaɗai ya rage autan maza. A fusace tace "Tunda yace ba zai aura miki ɗanshi ba ai sai ki haƙura muje a zubar da cikin don ba zan ƙara yin rainon shege ba, na dai yi ɗaya ba zan ƙara yin na biyu." Da wata irin ƙaƙƙarfar murya kamar ba tata ba Mummy tace "Inna!" Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta, wai ita yau me yake damunta ne da take ta faman fallasa asirin da suka binne cikin ransu shekara da shekaru, asirin daya rabo su da ƙasarsu ta haihuwa duk don su samu su lulluɓeshi ba tare da kowa ya san shi ba. "Don't tell me cikin shege kika yi kika haifeta Halima? No wonder itama tayi following footsteps ɗinki, tabbas barewa ba zata yi gudu ba ɗanta yayi rarrafe." Daddy yayi maganar ranshi na ƙara ɓaci sai dai kuma bai yi mamaki da jin cewa Nabila shegiya bace don yasan haka nan baza su ɓoye ita wacece ba inba don suna gudun asalinta ba. Zeey da tunda aka fara maganar nan take hawaye ta kalli Kabir fuskarta ƙunshe da mamakin abubuwan da suke taji yau ɗinnan. Ji tayi ba zata iya cigaba da tsayuwar ba don haka ta koma ɗakinta tana kuka, wannan wacce irin kwamacalar rayuwa suke ciki. Ace wai Nabila ƴar Mummy ce ta cikinta ba wai ƙanwarta ba kamar yadda kowa ya ɗauka. To ita kuwa Mummy me zai sa ta ɓoye musu irin wannan sirrin mai girma haka? A ganinta ai ko ta ɓoyewa kowa bai kamata ace su ta kasa faɗa musu ba tunda dai ai sun zama ɗaya yanzu tana ganin babu wani batun ɓoye-ɓoye kuma a tsakaninsu. To amma idan har Nabila ƴar Mummy ce me yasa take yawan kyararta tana yi mata faɗa alhalin ita ba haka take yi mata ba? Sam fa babu wata jituwa tsakanin Mummy da Nabila yadda take yi ma kamar haushinta take ji komai tayi sai tayi mata faɗa har ita tana mamakin yadda aka yi sam babu jituwa a tsakaninsu kamar ba ƴan uwa ba to ashe ma uwa ne da ƴarta sune basu sani ba. To ko dai haka duk iyaye mata suke idan ta duba taga yadda tasu mahaifiyar tayi watsi dasu tunda ta bar gidansu bata ƙara waiwayarsu ba sai ma ƴan uwanta dake yawan zuwa suna ɗagawa Mummy hankali duk don akan ta riƙesu kamar ƴaƴanta bayan ita data haifesu tayi watsi dasu ta manta ma tana da wasu ƴaƴa data fita ta bari. Kwanciya tayi tama rasa abun dake damunta, ta rasa tunani guda ɗaya da zata yi a cikin kanta. Har yanzu ganin abubuwan da suka faru take yi kamar almara ko a cikin shirin film. Wayarta ta ɗauka ta rubutawa Baqeer text. "Komai ya kwance min Ya Baqeer na rasa ya zan yi." Ko minti biyu bata yi da ajiye wayar ba reply ɗin shi ya shigo yace "Are you okay? Me ya faru?" Hawaye ne ya zubo mata don ganin reply ɗin shi ya sata jin wani irin rauni ya lulluɓeta. "Nothing was as it seems Ya Baqeer. Rayuwar nan gaba ɗaya ƙarya ce mutanen duniya mayaudara ne." Hankalinshi ne yaji ya tashi don haka yayi saurin kiranta, tana ganin shine ta ɗauka sai ta fashe mishi da kuka. Tashin hankalin shi ne ya ƙaru sai cewa yake yi "Zainab menene? What happened? Are you okay?" Ita kuma kuka kawai take yi don a yanzu tana buƙatar yin kuka a inda za'a rarrasheta, ga matsalar rashin sanin matsayinta a wajen Baqeer ga matsalar auren da Daddy yake son ya ƙaƙaba mata na dole gashi Mummyn data kasance mata abar jingina a duk lokacin da take cikin damuwa ta sameta da ɓoye musu sirri mafi girma a rayuwarta a yanzu bata san wane matsayi zata ajiye ta ba kuma. Sai data yi kukanta ya isheta sannan tayi shiru, shima tun yana rarrashinta har yayi ahiru ya ƙyaleta tayi kukan sosai don ya lura kamar akwai abinda yake damunta. Sai data tsagaita da kukan sannan yace "Are you okay?" Ɗaga mishi kai tayi alamun amsawa sai kuma ta tuna ashe fa baya ganinta don haka ta buɗe baki tace "Eh," cikin dakusashiyar murya. "Me ya faru kike irin wannan kukan Zainab?" Ya ƙara tambayarta. "Ashe mutanen duniya maƙaryata ne mayaudara Ya Baqeer? Ashe zaka iya zama da mutum na tsawon wani lokaci ba tare da kasan gaskiya guda ɗaya a kanshi ba?" "Me ya faru? Waye ya yaudareki? Is it Junaid" Ya ƙara tambayarta muryarshi a cunkushe yana jin wani ɗaci a cikin zuciyarshi, shi yasan dama Zainab tafi ƙarfinshi zai yi wuya ta iya son shi ko yana da lafiyar ƙafafu bare kuma a yadda yake ɗinnan. "No, its not him," tace tana girgiza kai sai kuma tace "Thank you for lending me your shoulders to cry on," ƙit ta kashe wayarta ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya. Duk da ta yarda dashi tana ganin kamar bai kamata ta kwashe abinda yake faruwa a cikin gidan su ta faɗa mishi ba, tana ganin kamar wannan wani sirrinsu ne da ba kowa ya kamata yaji ba, ***** Badaru na zaune a kasuwa wani abokin shi da suke harkar kasuwanci tare ya kawo mishi ziyara. Bayan sun gama gaisawa yace "Mallam Badaru ashe yaronka ya fara gina filinshi dake unguwarmu babu labari? Nace to Badaru mantawa yayi bai faɗa min za'a fara ginin ba bayan muna haɗuwa kusan kullum a kasuwa, ai irin wannan sai ka sanar dani yadda zan saka muku ido sosai a harkar ginin ba wai naga an fara ba bayan tare dani aka yi duk wasu shige da fice har Allah yasa aka sayi filin." Tunda ya fara magana Badaru yake kallonshi fuska ƙunshe da mamakin jin cewa wai an fara gini a filin Baqeer. To ta yaya ma za'a fara gini a wajen ba tare da an sanar dashi ba? Kada dai ace Kamalu sayar da filin nan yayi shine har aka fara gini bai sani ba. Ai da yin wannan tunanin ya miƙe zumbur ya zari makullin motarshi ya fice daga shagon ba tare daya tsaya yayi wa abokin nashi bayani ba duk kiran da yake ƙwala mishi kuwa bai sa ya tsaya ba sai ma sauri da yake ta faman zambaɗawa yana fatan yaje gida ya iske Kamalu yau babu me rabasu sai dai Allah. Kamar wanda zai tashi sama haka ya kwaso mota a guje, hukuncin Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya. Ko tsayawa ya daidata parking motar bai yi ba ya fita da sauri har yana cin tuntuɓe da wani dutse Allah dai ya kiyaye bai faɗi ba. Yana shiga cikin gidan da Abu ya fara cin karo ai kuwa ya kai mata damƙa yace "ina Kamalu yake? Ina yake nake tambayarki?" Jiki na rawa don ta tsorata da yanayin data ganshi a ciki fatanta dai Allah yasa ba shagonshi ya ƙara zuwa ya ɗebo mishi wasu kayan ba. "Mallam lafiya?" Wata uwar harara ya zabga mata yace "ina fa lafiya ɗan iskan yaron nan ya kassarani yaje ya sayar da filin nan har an fara gini a wurin." "Kamalun ne ya sayar maka da fili Mallam? To yayi me da kuɗin?" "Oho nima na sani zai wuce yawon iskancin shi zai tafi da kuɗin." "Gaskiya Mallam ka daina cewa shi ya sace maka fili tunda dai ba ganinshi kayi ya ɗauka ba, ko kuwa wani ya gaya maka ya ganshi lokacin da ya ɗauki takardun filin?" Tsaki yayi yace "Har sai wani ya faɗa mini, ki gaya mini duk gidan nan akwai wani ɗa daya gagara ne bayan shi? To wallahi ki faɗan gaskiya ko na tsine mai." Shiru tayi dan mamakinshi ya hanata magana, sai cewa yayi "Kin gani kema kin san gaskiya." Umma ce ta fito daga ɗakinta jin abu na neman kaiwa ga tsinuwa yasa ta fito tace "Takardun fili dai ni na ɗauka na kaiwa mai filin ya sayar yayi amfani da kuɗin." "Ke kika sace mini takardun filin fa kika ce Fatima?" Girgiza kai tayi tace " Haram, ni ban sace maka komai ba takardar filin Baqeer na ɗauka don nasan ko nace maka ka bani ba bayarwa zaka yi ba kuma mai filin yana da buƙatar kayanshi shi yasa ni kuma na ɗauka na kai mishi." Baki buɗe yake kallonta don ya rasa wane mataki ya kamata ya ɗauka a kanta. "Habawa ashe shiyasa kike da kuɗi? Kudin sata kike ce to wallahi Fatima ki karɓo min takardar filina in har ba barauniya kike san zama ba, idan kuma ba haka ba wallahi zan yi matuƙar saɓa miki akan takardun nan zaki iya bar min gidana." Murmushi tayi tace "Filinka ko na Baqeer kuma idan kace na bar maka gidanka sai me tunda ka iya korar ɗan cikinka bayan ka gama cin moruyarshi ma bare ni da ka sameni da girmana," daga haka tayi shigewarta ɗaki ta barshi anan da sakakken baki. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD*         *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SITTIN DA TARA* {69} Abu bata san sanda dariya ta ƙwace mata ba, ganin wani mugun kallo da Badaru ya watsa mata yasa tayi saurin cewa “Malam to yaya? Kamalu dai sai ka nemi yafiyarshi watakila ma atamfofin su ke sata ba’a sani ba.” Ai kuwa tana kaiwa nan ya hayayyaƙo mata don dama a wuya yake saboda kalaman Fatima, a fusace yace “Gurgun ne kike nufi zai je kasuwa yayi sata? Ko kuwa kina son cemin shi yaron shagon nawa bai san Kamalu ba? In Baqeer ɓarawo ne shima Kamalun ɓarawo ne aikin banza ka haifi yara taron ɓarayi a gida ni dai kam banji daɗin haihuwa ba.” Jin yanda ya rufeta da masifa yasa tayi sum-sum ta shige ɗaki, maimakon ya koma ciki sai ya nufi ɗakin Fatima yana masifa “Kina ina munafukar banza da wofi, ni Fatima har kin yi idon da zaki yi mini sata? Ni? Ni?” Tana daga cikin ɗaki ko motsi bata yi ba yi tayi ma kamar bata san me yake yi ba, ai kuwa ya ƙaraso cikin dakin yana hayagaga yana cewa “Eh lallai idanunki sun isa yanka, to tashi maza ki bar mini gida na.” Maimakon ma ta bashi amsa gani yayi ta janyo hijabi ta saka ta jawo akwatin ta a ƙasan gadonta na ƙarfe tana neman watsa kayanta ciki, wani tunani ne yazo mishi in har ta tafi shikenan bashi ba kuɗin filin nan don ya tabbatar kuɗin na hannunta ko Baqeer amma ko yaya in ya ajiye Fatima ai dai ko banza zai iya ƙwace kuɗin shi a hankali, wani kallo yayi mata kafin yace “Kina sa ƙafa kika bar gidan nan Allah ya isa.” Da mamaki wanda ya kasa ɓoyuwa a idanuwanta ta kalleshi, idanuwanshi sun yi jaa saboda tsabar masifa ya sake yi mata wani muzurai don ta ƙara shakkar shi sannan ya fita, kai ta girgiza don baƙin ciki ya isheta taso ta tarkata ta tafi duk da itama bata son tafiya har sai Baqeer ya zama abinda Badaru da kanshi zai yi ƙwallar da na sani, amma da zaran ta tattara ta koma wurin Dada tasan neman faɗanshi kaɗai sai ya sa ya bita har can, sannan wannan kishiyoyin nata masu gulma tasan bazasu barta ba haka zasu yi ta sawa ana musu leƙen asiri, amma da tuni itama tayi yaji don ba abinda yake zaune da ita a gidan. Badaru kam ɓacin ran da yake ciki ne yasa ya fito waje,  yana ƙoƙarin fita Kamalu na shigowa, daga ɗan gefe kawai ya raɓa yana neman wucewa ba tare da ya yiwa Badaru magana ba, kamar ya shaƙo wuyanshi ya kifa mai mari yake ji amma baƙin ciki ya hanashi gashi yana tunanin haukar yaron nan kar yasa ya ƙara bigeshi wanda ya tabbatar a rashin kanshi zai iya aikatawa, shi dai kam bai yi sa’ar yara maza ba, duk yanda yake kulafucinsu gashinan duk sun zo babu wanda yayi mishi rana. Tafiya kawai yake yi don bai masan inda yake saks ƙafarshi ba, yanzu filin nashi da gaske Fatima ta sace? Mai zai yi mata da zai ƙuntata mata? Don wallahi bataci bulus ba, dama ɗanta ya cireshi daga sahun yaranshi don shi kam babu abinda zai yi da Baqeer to yaranta mata ma aikin banza duk ba wani jin dadi suke yi ba, ƙwafa yayi yana waigawa suka haɗa ido da Suleiman Ƙaraye yana zaune a cikin mota a baya ya sauke glass yana sauke wani irin numfashi na ɓacin rai, don yau shi kaɗai yasan ɓacin ran da yake ciki wanda yake jin ƙwaƙwalwarshi ma ta kasa tunani mai kyau, wani kallon-kallo suka yiwa juna sannan yace wa driver ya hanzarta su tafi bai son tsayuwa a wurin. Badaru ya ƙara tamke fuska ya juya ya cigaba da tafiyarshi abun takaicin ma shine sai yake ganin kamar kowa yana cikin farin ciki ne banda shi. ******* Tsugunnawa Bello yayi ya haɗe hannayenshi alamun roƙo yana murza hannun yana cewa “Sir plz help me,” yayi maganar cikin roƙo, wani kallo suka yi mishi mutanen dake zaune a office ɗin, ɗayan wanda kana gani kasan bature ne, ya kalleshi yace “Am sorry but you have to go back to your country, we brought you here to sponsor you but unfortunately you couldn’t pass any test and at the end we realised everything you said was false.” Gabanshi ne ya ƙara faduwa, sam ya manta karatunsa da passport ɗinshi suna daban-daban ya saka, su sun yi visa da sunan Muhammad Bello Bala, sai dai bayan yazo ya faɗi gwaje-gwajen da suka yi mishi suka tausaya mishi akan to ya kawo karatun degree da yace yayi in yaso su nema mishi wani aikin, sai dai yana kawowa suka ga Bello Bala Jogana, wannan dalilin yasa suka ce sato takardun yayi, duk yadda yake fahimtar dasu bai sa sun fahimceshi ba, gashi maganarsu ta turanci da sauri suke yi shi kuma ba fahimtarsu yake yi sosai ba. Wani ne ya kalleshi yace ya shirya wai ƙarshen satin nan zasu maidashi gida in kuma ya cigaba da zama zasu lalata mishi permit ɗinshi na zama wanda ko aiki bai isa ya samu ba. Haka ya fito ya shiga masaukin da aka bashi da ƙyar kanshi na wani irin sarawa saboda ɓacin rai, zama yayi a bakin gado ya zuba tagumi yana tunanin abun yi, gaba ɗaya bai yi nisa da tunani ba sai ga wayar Asiya. Wani ƙululun baƙin ciki ne ya kamashi ya ɗaga fuskarshi a tamke, ba tare da yace komai ba. “My love baka turo mini kuɗin ba bayan mun yi magana rannan, sannan Habi ta tafi wai ta gaji so take ta koma wurin Inna, shine nake so in ka turo kuɗin zan ɗauki masu aiki biyu kafin ka zo ka ɗauke ni don sam zaman garin nan ya isheni wallahi,” ta ƙarasa maganar cikin kashe murya. Wata irin iska ya furzar yace “Ni kam Asiya hala baki san komai ba sai kisan kuɗi ko?” “Ba dai suma cewa zaka yi ba zaka bani ba?” Ranshi ne ya ƙara ɓaci don dama ƙoƙarin danne ɓacin ranshi yake yi, a fusace ya kashe wayar don yana ji kamar idan ya cigaba da yi mata magana to lallai zai iya furta kalmar sallama don shi dai ta gama kai shi bango tunda yake da ita bata taɓa tambayarshi ya yake ba? Yana da kuɗin da take so ko babu, amma a iya saninta da Baqeer lokacin suna soyayya kullum ta Allah in suka yi waya da safe sai ta tura mishi text na soyayya wanda a zamanshi da ita har suka yi aure bata taɓa yi mishi text ɗin soyayya ba, sai na godiya in yayi mata wata kyautar. ****** Baqeer shiru yayi yana tunani meke faruwa da Zee? Don da alama akwai abinda aka yi mata sosai sannan menene laifinshi? Kashe wayar data yi ya tsaya mishi a rai yana ganin kamar shima ya ɓata mata rai, tambayar data yi mishi na son sanin matsayinta shi ke sake dawo mishi, ko dai ya sanar da ita yana sonta ne? Iya kaci in bata sonshi tace a’a sai dai baya son ya zama sanadiyyar rabuwar zumuncin Dada da ita sannan Maryam da ita. Shafar sumar kanshi yayi sannan ya turo kekenshi zuwa waje Dada ya kalla dake saka maggi cikin ɗan wake yace “Dada yau kuma ɗan wake kika yi?” “Ina fa aiko mini aka yi daga maƙwabta, ga naka can kaima na ragema, yanda yayi daɗi nake ta tunani ina ma Zainabuwa zata zo.” Murmushi yayi yana ɗaukan kwanon yana cewa “To ai sai ki aika mata ni dai ci zan yi don ya bani sha'awa.” Wani kallo tayi mishi tace “Nikam Baqeeru son Zainab kake yi ko?” Gabanshi ne ya faɗi ya maida murfin kwanon ya rufe yana cewa “Dada me kike nufi? Wani irin so ana zaune ƙalau?” “In ba haka bane abar maganar amma ni haka kawai nake gani.” Sake buɗe kwanon yayi yana cewa “Ku dai tsofaffi da son zancen aure kuke,” yayi maganar yana kifkif da ido. ****** Mummy ce ta goge hawayenta, Inna na gefenta itama tayi shiru tana tunani, daurewa tayi tace “Aikin gama ya riga ya gama yanzu abun yi zaki yi tunani ai ke mai wayau ce sannan ba kya rasa mafita duk abinda ya shige miki duhu. Wani kallo ta yiwa Dada cikin magana mai ɗan sauti tace “Kin san da haka shine kika biye mata kuka zo kuka janyo mana tozarci? Sannan sanda kika yi magana sam babu alamun mamaki a fuskarta dama ta sani ne ko me?” Inna ta kalleta yanayinta ya ɗan canza tace “A’a banaji gaskiya.” Mummy ta girgiza kai tana tuno abubuwa da dama da Nabila take faɗa mata especially akan Zainab lallai ta sani kawai dai nunawa take yi kamar bata sani ba, Inna ce ta katseta da cewa “Bana ji gaskiya da ta sani da ta nuna.” Kai Mummy ta girgiza tace “Ta sani shi yasa ta ƙwallafa rai da Kabir so take yi ta tozartani.” Wani kallo Inna ta zabga mata tace “Kada ki kuskura ki yi mata wannan  ƙazafin, zan ɗauketa mu koma gida ke kin san me zaki yi ki shawo kan komai,” tayi maganar tana miƙewa, har ta kai ƙofa Mummy tace “Shi yasa nake cewa ki dinga sawa bakinki linzami yanzu don Allah me kika ja mana?” Tayi maganar tana bin Inna da kallo. Waigowa tayi ta kalleta sai bata ce komai ba kawai ta fita ta ja ƙofar. Mummy ta share ƙwalla tana murza bayan hannunta tana cewa “Duk abinda na gina shekara da shekaru rana ɗaya mahaifiyarka ta ruguza ma shi? Da wani ido zan kallesu? Da kuma wani ido zasu kalleni?” Saman kanta kawai ta riƙe tana jin takaicin abun nan. Daddy duk yadda yake ƙoƙarin ƙwaƙwalwarshi ta ɗauki abinda ke faruwa ya kasa, har ya tafi zai je guest house ɗinshi ya fahimci ba zai iya zama ba tare da an cire cikin nan a gabanshi ba. Nan yace driver ya sake maidashi gida don meeting dai an gama shi tuni dama guest house zashi, suna zuwa suka ga su Inna sun fito zasu tafi, cewa yayi su tsaya a gabansu bayan sun tsaya ne ya kalli Nabila yace “Shigo!” Kallon Inna tayi a tsorace Inna ta kalleshi tace “Alhaji kayi haƙuri don Allah.” Magana zamu yi da ita ke ki wuce gida zan ajiyeta in mun gama, haka ta shiga motar a tsorace don babu alamun wargi a fuskar Daddy balle ta bashi hakuri, gaba ta shiga kusa da driver ko sake kallon Inna bai yi ba balle ya sa a kaita gida, sai driver daya kalla yace “Muje asibitin Zahir” daga haka bai ce komai ba, gaban Nabeela ne ya faɗi ta waigo hankali a tashe zata yi mishi magana, wani mugun kallo yayi mata wanda ya sata maida kanta gaba, gabanta na wani irin faɗuwa wanda take jin kamar zuciyarta zata fasa ƙirjinta ta fito. Idanu kawai take ƙiƙƙiftawa akan titi, a hankali zufa ke ɗan karyo mata tana jin wani dummm bata gama fahimtar me ke faruwa da jikinta ba sai gani tayi an zo asibitin don dama ba wani nisa gareshi ba zuwa gidansu. Fitowa Daddy yayi sannan ya kalleta yace “Wuce gaba saboda bana son a ganeni kiyi gaba ina binki a baya, sannan wallahi kika kuskura kika yi wani abu ko magana da zata sa hankalin mutane yazo kan mu sai ranki ya ɓaci.” Bakinta na rawa ta ɗaga kai don tasan  bata isa tayi magana ba, haka suka wuce tana tafe ƙafafuwan ta na sake yin sanyi, nauyinsu na ƙara tafiya, kuzarinsu na ƙara raguwa. Waya yayi mishi ya sanar dashi ya iso hakan yasa ya turo secretary ɗinshi akan ta shiga dasu, sun shiga suka sake gaisawa, Nabila na takure gefe ɗaya kamar ƙuli, bayan sun gama magana ya sanar dashi ciki gareta yana so a cire mata, ƙanwar matarshi ce sai tsautsayi ya afka mata tayi ciki, ya ɗan jinjina abun sannan ya umarceta da tazo su shiga ɗan kewayen cikin office ɗin kaɗan don yayi scanning wanda zai bashi damar sanin taimakon da zai yi mata ba tare da matsala ta afku ba. Nabeela ta sake kallon Daddy wanda ya sake haɗe rai yace “Magana ake yi miki ko?” Ta ƙarasa wurin kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, idanunta kuwa nan da nan suks fara zubar da ƙwalla, keɓantaccen guri ne a cikin office ɗin ansa labule an kulle ta yadda na waje ba zai iya ganin meke faruwa ba, haka ta gyara zaman skirt ɗinta ta hau saman gadon da Dr ya umarceta ta hau, hawayenta ya kasa daina zuba, haka tana gani ya fara sa mata gel sannan yasa abun scanning akan cikinta, mamaki ne ya kamashi ganin duk inda ya duba a mahaifarta babu ciki babu alamunshi, da mamaki ya kalleta yace “Ya aka yi kikasan kina da ciki?” Gaban Nabila ne ya faɗi tace “Na'am?” “Kinyi pt ne?” Yawun bakinta ta haɗiya da ƙyar tace “Eh!” “Kuma positive ya nuna?” A tsorace ta ɗaga kai. Cike da mamaki ya sake yin scanning yace “Amma babu alamun ciki babu ma alamun mahaifarki ta taɓa ɗaukan ciki.” Daddy dake zaune mamakin kalaman Dr ya kamashi a fusace ya miƙe yace “Me kake nufi?” Dr yana scanning yana cewa “Gaskiya bata da ciki ban san ya aka yi kuka yi tunanin tana da ciki ba.” Tsoro ne ya rufe Nabila tayi saurin durowa daga kan gadon ta zube ƙasa tace “Dr ka duba sosai wallahi ciki gareni, don Allah kada kace babu, don sai dai in zubewa yayi ban sani ba……” A ƙufule Daddy ya yaye labulen ya kalleta yace “Kina son kice mini cikin da kika ce kina dashi minti goma sha biyar da suka wuce shine ya  zube ba tare da kin sani ba?” Dr ne ya kalli Daddy yace “Yallabai ka kwantar da hankalinka bari muyi bincike.” Yayi maganar yana fita daga office ɗin, wani gigitaccen mari taji an ɗauketa dashi wanda yasa ta ƙarasawa ƙasa riƙe da kuncinta……. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN* {70} Wani irin kallo Daddy yake yi mata da yake sake ruɗa mata ciki take jin kamar ta saki gudawa a wando. Ƙasa-ƙasa yayi magana cikin wata irin masifaffiyar murya data ƙara ruɗar da Nabila yace "Cikin ƙarya kika yi shine kika lanƙayawa ɗana kika yi breaking trust ɗin dake tsakaninmu don kiyi tarnishing image ɗina." Girgiza kai take yi ta kasa magana saboda tsabar tsoron da ya kamata, ita wa ya aiketa ne ma yin wannan kasassaɓar gashi allura tana nema ta tono garma. Zama Daddy yayi akan kujera ranshi idan yayi dubu ya ɓaci, ya rasa wane irin mataki ma ya kamata ya ɗauka. Tsakanin jiya zuwa yau hankalin shi a tashe yake fata kawai yake yi ya kashe wannan matsalar data kunno kai cikin gidanshi ba tare da ƴan adawa sun ji ba su samu abun kawo mishi suka amma ashe wai duk wannan tashin hankalin daya shiga ƙarya ce kawai babu wani ciki a jikin yarinyar nan, to ita kuwa ribar me zata ci da tayi hakan ta ɗaga musu hankali gaba ɗaya. Ita dai Nabila na zaune a gefe dafe da kunci don har yanzu tana jin zafin marin da Daddy yayi mata tana sharɓar kuka. A cikin haka ne Dr ɗin ya shigo da nurse ta ɗebi jinin Nabila yace ta kai lab a gwada mishi yana so yaji if she's pregnant don in dai har akwai ciki to blood test yana nunawa komai ƙanƙantar shi kuwa. Zama yayi akan kujerarshi ya dubi Daddy yace "kayi haƙuri Yallaɓai bari a kawo result ɗin mu gani idan har akwai cikin blood test ɗin zai nuna, kasan test ɗin ne wani lokacin yana bada false positive to watakila itama irin shi ta gani tayi zaton akwai cikin amma ina tantamar cikin nan don scan ɗin da aka yi ya nuna mahaifarta bata taɓa ɗaukar ciki ba." Tsaki Daddy yayi yace "Ai tunda kace babu cikin na yarda da kai Dr ita dai tasan dalilinta na yin ƙaryar cikin da idan abokan hamayya suka ji zasu iya amfani dashi suyi tarnishing image ɗina," ya wurgawa Nabila wata uwar harara, babu shiri ta sunkuyar da kanta ƙasa idanunta na zubar da hawaye. Suna zaune a wurin nurse ɗin ta dawo da result ɗin test ɗin da aka yi, karɓa Dr yayi ya duba sannan ya kalli Daddy yace "Kamar yadda na faɗa maka ne Yallaɓai babu ciki a tare da ita watakila dai false positive ta gani a wancan test ɗin da tayi a gida shi yasa tayi tunanin akwai cikin, Allah ya kiyaye gaba." "Ameen Dr nagode," Daddy yace bayan ya miƙa mishi hannu sun yi musabaha. "Sai ki tashi mu tafi ai, mutuniyar banza da wofi," ya daka mata tsawa sai dai cikin ranshi yana ji ya samu nutsuwar da tunda maganar cikin nan ta fito bai samu ba tun ba da tace Kabir ne ke da alhakin cikin ba, ko baccin kirki bai samu yayi ba jiya don yana ganin kamar duk wani motsin su a idon abokan adawa suke yin shi zai iya jin maganar ta fita ta inda bai taɓa zato ko tsammani ba. Har suka je gida Nabila na sharar hawaye, bata taɓa tunanin asirinta zai tonu da wurwuri haka ba, ta ɗauka Daddy zai yi maganar aure ne a tsakaninta da Kabir don a taru a rufawa juna asiri ashe shi a wajenshi ba haka bane bata kai matsayin da zai aura mata ɗanshi ba sai m wani ɓoyayyen sirrinsu daya bankaɗa. Suna zuwa gida Daddy ya fice daga motar a fusace ya shiga cikin gida, tun daga parlourn ƙasa yake ƙwalawa Mummy kira "Halima, Halima." Tana jin irin kiran da yake yi mata sai da gabanta ya yanke ya faɗi, ita yanzu gaba ɗaya Daddy ya zame mata abun tsoro daga taji muryarshi take shiga tsananin tashin hankali. Fitowa tayi jiki a sanyaye don bata san kiran me yake yi mata ba. Wani banzan kallo Daddy ya watsa mata yace "Dama kun haɗa baki ne da ƴarki (yadda ya ambaci kalmar ƴarki a kamar wanda yaga wani abun ƙyama) tayi ƙaryar ciki don kuyi tarnishing image ɗina ku kuma yi breaking trust ɗin dake tsakanina da ɗana?" Da sauri Zainab ta kalli Kabir don tunda Daddy ya fara yiwa Mummy ƙiran mafarauta duk suka fito daga ɗakunansu. "Ƙaryar ciki kuma?" Zeey tayi maganar ƙasa-ƙasa yadda babu mai iya jin ta. Cikin rawar murya Mummy tace "ƙaryar ciki kuma Senate? Kana nufin Nabila ba ciki ne da ita ba?" Sai da ya harareta yace "Koma menene ai da saninki yake faruwa tunda dai Nabila bata isa tayi abinda tayi ba idan har ba sakata aka yi ba." "Wallahi Senate babu ruwana," Mummy tayi saurin tarar numfashin shi. Nuna Nabila dake rakuɓe daga bakin ƙofa don ta kasa ƙarasa shigowa ciki ma yayi yace "to gata nan ashe ƙarya take yi babu wani ciki da take dashi, anyi mata scanninga ba'a ga komai ba har blood test aka yi duk sun nuna bata ɗauke da ciki." Da ƙarfi Kabir yace "I knew it, ni dama nasan babu wani abu daya shiga tsakanina dake don bazan iya tuna lokacin da abu makamancin wannan ya shiga tsakaninmu ba" ya ɗaga hannun shi sama in a fist. Dukkansu suka kalleshi, Daddy yace "Kasan da haka amma kayi shiru baka yi magana ba ka bari suke tayi mana yawo da hankali." Takowa yayi ya sauko daga matattakalar bene, sai da ya shigo parlourn sosai sannan yace "Ka bani damar da zan kare kaina ne? Ina ce kafi yarda da ita akan ni ɗanka na cikinka daka haifa don haka ka yarda da maganarta ba tare da kaji ta bakina ba kayi jumping into conclusion sai yanzu ne zaka zo kana cewa ban faɗa maka ba, to me zan faɗa maka bayan tun farko ka aminta da abinda ta faɗa maka?" Shiru Daddy yayi yana jin wani abu mai kama da dana sani na lulluɓeshi. Wani irin kallo Kabir ya jefawa Nabila yace "Kin sani tun farko ban taɓa nuna ina sonki ba, lokacin da kika zo mini da maganar soyayya na faɗa miki ba zai yiwu ba saboda ke ƙanwar Mummy ce ina yi miki kallon ƙanwar mahaifiyata saboda kallon da nake yiwa Mummy kenan don haka bazan iya aurenki ba, anyi haka ko ba'a yi ba." Bai jira jin ta amsa ba ya cigaba da cewa "Duk da haka baki haƙura ba kike biyoni har ɗakina duk wata ƴar dama da kika samu sai dai na ganki a cikin ɗakina har ta kai ga bana son zama a cikin gidan nan saboda takurar da kika yi mini duk da haka baki saduda ba daga baya ma sai kika ɓullo mini da wani abu mai girma duk da na nuna miki bazan iya ba baki haƙura ba sai da kika san yadda kika yi kika rinjayeni har na fara biye miki amma kin sani na sani wani abu makamancin wancan abun bai taɓa shiga tsakanina dake ba, ko a ranar da kika tuhumeni da yi miki fyaɗe ke kika kawo kanki har ɗakina kika yi ƙoƙarin tilasta ni akan sai na kusanceki naƙi a haka bacci ya ɗaukeni kawai sai farkawa nayi kika ce wai na gwada miki ƙarfi, duk yadda nayi ƙoƙarin son na tuna na kasa tunawa saboda babu abinda ya shiga tsakanina dake." Wani irin zazzafan huci ya sauke yace "Kije na barki da Allah ƙazafin da kika yi mini Nabila shi zai bi mini hakkina." Daga haka ya juya ya koma ɗakinsji yana share ƙwallar daya kasa tantance ta farin cikin jin cewa wani abu bai gifta tsakaninshi da Nabila bane ko kuwa ta takaicin sharrin data ƙulla mishi ne. Bin shi Zainab tayi sai ta sameshi zaune akan sofa ya dafe kanshi da hannayenshi yana sauke ajiyar zuciya. Zama tayi a kusa dashi ta dafa bayanshi tace "Kayi haƙuri Ya Kabir nasan akwai ciwo ayi maka sharri amma sai ka godewa Allah daya bayyana gaskiya tun ba'a je ko ina ba asirinta ya tonu, ni gaba ɗaya kwakwalwata ta kasa ɗaukan abubuwan dake faruwa, na rasa gane komai." "Hmm..." Kawai yace yana jin wani ɗaci a cikin zuciyarshi, Nabila ta cutar dashi don a cikin ƴan kwanakin nan data taso shi a gaba da tashin hankali ko baccin kirki baya iya yi daya samu bacci ya ɗaukeshi kamar wanda ake yiwa raɗa sai zancen cikin nan ya faɗo mishi a cikin ranshi shikenan kuma sai ya nemi baccin ya rasa haka zai yi ta juyi har safiya tayi yana saƙe-saƙen abinda ya kamata yayi. Zama suka yi shiru kowa na saƙe-saƙe a cikin rai, nisawa Zeey tayi tace "Ya Kabir kasan me yafi ɗaure min kai kuwa? Yadda Mummy bata taɓa nunawa Nabila ƴarta bace sai ma nesanta kanta da take yi da ita bayan mu kuma ta riƙemu kamar ƴaƴanta amma ga tata ƴar ta watsar da ita a gefe, ko me yasa tayi hakan abun yana ɗaure mini kai." Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta sai dai bai yi magana ba, shima sai yanzu yake tunanin to me yasa Mummyn tayi haka? Shi yasan da ace ta fito ta faɗawa Daddy zai riƙe mata ƴarta kamar shi ya haifeta sai ta zaɓi data ɓoye tace ƙanwarta ce alhalin ƴarta ce, ko ribar ne zata ci data yi hakan oho. ***** Mayar da kayan data fara zubawa cikin akwati tayi a wardrobe ta shirya, komawa tayi ta zauna akan tabarma tana jan carbi sai dai lokaci bayan lokaci tana tuna tijarara da Badaru yayi mata, kome yasa ya hanata tafiya kuma bayan shi da kanshi yace ta bar mishi gidanshi. Wayarta ta janyo ta kira Baqeer, lokacin da kiran ya shiga wayarshi yankan ɗinki yake yiwa Tanimu don shi har yanzu hannunshi bai gama faɗawa ba ya dai iya taka keke sosai ya haɗa kaya amma yanakwar na ɗan bashi wahala. Ajiye scissors ɗin hannunshi yayi akan kayan da yake yankawa ya ɗauki wayar, yana ganin sunan Umma ya saki wani murmushi. Da sallama ya amsa wayar sai bayan ta amsa sallamar da yayi mata sannan suka gaisa. Tambayarshi tayi yadda ake ciki da shagon da yake son ya buɗe ganin har ya kusa kammala makarantar koyon ɗinkin. Nutsuwa yayi yace "Ai na faɗa miki mun samu shagon har an biya rabin kuɗin hayar, In Sha Allah zuwa ƙarshen watan nan akwai waɗanda na yiwa sketches zasu biyani da kuɗaɗen da wasu dana ajiye a banki nake so na zuba kekunan, a yanzu dai ni da Tanimu ne zamu fara zama a wurin sai munga yadda kasuwar ke tafiya kafin mu nemi wasu ma'aikatan kuma." Tana sauraren shi har ya gama yi mata bayani sai gyaɗa kai take yi cikin nuna gamsuwa da abinda yake faɗa duk kuwa da ba ganinta yake yi ba. "Allah ya taimakeka ya bada sa'a ya saka maka albarka a cikin kasuwancin da zaka fara. Allah ya kareka daga sharrin maƙiya da mahassada ya kawar da dukkanin wasu abun ƙi ya yalwata arziƙinka." "Ameen Umma," kafin yake cewa yana jin wasu ƙwallar tausayinta sun cicciko mishi a ido. Ko ƴaƴa nawa ne irinshi da suka yi dacen samun uwa ta gari irin Umma mai mayar da damuwar ƴaƴanta damuwarta, mai sayar da farin cikinta don ƴaƴanta suyi dariya, mai yawan kyautayi da tausayin ƴaƴanta wacce cigaban ƴaƴanta shine nata, gaskiya basu da yawa don kafin a samu irin Umma a cikin al'umma sai an daɗe. Har suka yi sallama bata daina yi mishi addu'a ba abinda yake ƙara mishi ƙwarin gwiwa da karsashi akan son ya ƙara dagewa wajen ganin ya cimma burinshi ko don ya saka farin ciki a cikin zuciyar Umma. Tun lokacin da ya faɗa mata ƙudirinshi akan sana'ar ɗinki da yake so ya fara ta duƙufa wajen yi mishi addu'a babu dare babu rana tana roƙa mishi alherin Allah akan abinda yasa a gaba, ita a yanzu bata da wani buri data sanya a gaba sai fatan ganin cigaban Baqeer, tana so taga ya zama wani abu a rayuwa shi yasa take jure duk wani wulaƙanci da take gani a cikin gidan har ranar da Allah zai iyakance musu wannan zama ta tafi ta barwa Badaru gidanshi din daga ranar daya kori Baqeer daga cikin gidan taji a ranta itama bata da muhalli a cikin shi... *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* Da *AYUSHER MUHD*         *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA ƊAYA* {71} Mummy ce ta ja Nabila ɗaki ganin su kaɗai suka rage a cikin falon, suna shiga tasa key ta rufe ɗakin zuciyarta na wani irin zafi, ta kasa waigowa daga jikin ƙofar, Nabila kam zama tayi a ƙasan ɗakin tana share ƙwalla kafin tace “Mummy ni dai don Allah ko ma menene kiyi amma ki sa a aura mun Kabir…..” Wani irin waigowa tayi ta bita da mugun kallo kafin tace “Kabir? Ke yanzu kina ganin ko numfashin mutuwa kike yi Senate zai aura miki shi? Sau nawa ina ce miki ki bari? Ko kina tunanin ni ban san me nake yi bane?” Kai kawai ta sunkuyar ƙasa tana jin tsanar kowa na kamata, Mummy ce ta ɗan sauke ajiyar zuciya kafin tace “Ya aka yi kika san Inna ba ita ta haifeki ba?” A hankali ta ɗago ido kafin ta kauda kai gefe tana kallon wajen gado ba tare da tace komai ba, Mummy ta sake cewa “Ya aka yi kika sani? Don kaf garin nan babu wanda yasan sirrin nan, kuma saboda wannan sirrin tunda muka baro Nijer bamu sake komawa ba, ba neman ƴan uwan mu muka yi ba bare su san inda muka koma suzo, to ya aka yi kika ji?” Yanzu kam kanta ta dawo dashi wurin Mummy, ɗan nazari Mummy tayi don da Nabila na bala’in jin maganarta, sannan babu ruwanta kwana a gidan ma da ƙyar Zee da Inna ke sakata zuwa kafin shekaru huɗu baya da ta fara canza halaye, a gaban mutane ita mai tarbiyya ce amma in su biyu ne sai ta fara mata maganar raini. Da sauri ta kalleta tace “Ba dai sanda Inna tayi mini faɗa akan karatunki ba? Sanda Zeey bata daɗe da fara karatu a ƙasar waje ba akan insa Senate ya biya miki kema ki tafi?” Kanta ta sunkuyar. Mummy ji take yi kamar ta rufeta da duka, hakan yasa itama ta tsugunna a wurin da Nabilan take zauna ta sa hannu ta ɗago kafaɗarta ta riƙe da hannayenta biyu tana jijjigata tace “Yanzu hankalinki ya kwanta kin ɗauki fansar abinda kike so?” Wasu hawaye ne suka zubo mata, Mummy ta sake matsa kafaɗarta tace “Kin san baƙin cikin da kike sakani a ciki kuwa? Kin san halin da nake shiga a baya saboda ke? Amma na daure na nemar miki gata, ko kina tunanin da ban auri senate ba zaki yi school ɗin da kika yi? Zaki zauna gidan da kuke yanzu? Zaki samu mota da gatan da kike dashi yanzu?” Takaicin Nabila take ji wanda ji take yi baƙin cikinta duk ya gama nuƙurƙusarta. Sakinta tayi kawai ta miƙe tsaye ta fara ciro kayan Nabila tana zubosu ƙasa daga cikin akwati, Nabila da sauri ta sa gwiwoyinta a ƙasa tace “Mummy na tuba, na tuba wallahi kawai kishi nake yi yadda naga kina son su Zainab amma sam ba so nayi a tozartaki ba, sannan wallahi bansan abinda ya faru zai koma haka ba, don Allah ki yafe min.” Wani irin ɓacin rai Mummy ke ji sai data watso kayan duka sannan ta ce “Tashi ki haɗa kayanki ki bar mini gida, kin ji na faɗa miki.” Tana kaiwa nan ta fito daga ɗakin idanunta sunyi jaaa saboda ɓacin rai, abinda ta gina shekara da shekaru yarinyar nan ta lalata mata shi lokaci ɗaya yanzu ya zata yi, ta rasa wani tunanin zata yi kawai idanunta suka hango Zeey da Kabir sun fito daga ɗakin shi, baya tayi kawai sai ji tayi ta faɗi, da gudu Zeey ta taho inda take ta ɗagota tana tambayarta menene? Mummy a hankali take kallonta tana fitar da numfashi sama sama tana cewa “Jiri kawai nake ji, Auta abubuwan da ke faruwa ƙwaƙwalwata da zuciyata sun kasa ɗaukansu.” Kama mata tayi ta kaita ɗaki har Mummy ta riko hannunta, zare hannunta tayi daga cikin na Mummy ba tare da ta amsa mata ba sannan ta fito daga ɗakin. Kabir na tsaye inda suka barshi kai kawai ya girgiza ya koma ɗakin shi, Zeey ma ɗakinta tayi sai dai da yake ɗakinta kusa dana Nabila ne tana jiyo kukanta daga ciki, kuka take yi sosai wanda yasa Zeey take jin komai ba daɗi ita dai sam ba zata yafe mata ba sannan bata son ganinta a wannan lokacin, sai dai kukan na ƙara ɗaga mata hankali ga magriba ta kawo kai, hakan yasa ba zata iya fita ba, waya ta ɗauka ta kunna karatun Qur’ani kawai ta haɗe kanta da gwiwarta wuri ɗaya, ta rasa wani tunanin zata yi, sam yanzu tsoron mutane take. ***** Nabila kam ta dinga buɗe makogaro tana kuka saboda Zeey taji sai dai ganin tayi kusan awa biyu tana kukan ba tare da tazo ba yasa ta daina don ji tayi har muryarta na neman dusashewa, haka ta kwashe kayanta ta dinga leƙawa sai dai gidan babu kowa kamar anyi mutuwa, su kansu masu aiki da alama sun fahimci akwai abinda ke faruwa a gidan don suma aikin gidan a hankali suke yi, ɗakin Kabir taje sai dai ta jishi a kulle haka taja akwatin ta fita idanuwanta duk sun yi ƙanƙanta. Motarta ta shiga ta bar gidan tana jin komai yayi mata zafi, takaicin abinda ta aikata ya isheta. Gida ta wuce kai tsaye, tayi parking sannan ta janyo manyan akwatinanta guda biyu tayi ciki, tana tafe kamar zata faɗi saboda wata irin yunwa da take ji, don kaf ɗin su tun breakfast babu wanda ya ƙara cin abinci. A zaune taga Inna tayi shiru da alama tunani take yi, har ta shiga da akwatinan bata tanka mata ba, ganin haka yasa ta dawo tace “Inna.” Kallonta tayi cike da ɓacin rai kafin tace “Yanzu hankalinki ya kwanta? Kin ruguza farin cikin mahaifiyarki?” Zama tayi a ƙasa kusa da Inna tana maida ƙwallarta tace “To ni menene nawa Inna? Ta tsaneni ba tare da nayi mata laifin komai ba, ko abinci take ci idan nazo wuri haƙura take yi sannan daga baya naji wai bama Yayata bace mahaifiyata ce? Sannan ni da nake ƴarta bata damu dani ba sai su Zainab? Kina ganin yadda take yi musu bata iya ɓoye son da take yi musu.” Cikin faɗa Inna tace “Wannan dalilin bai kai kiyi abinda kika aikata ba, tunda Halima ta kira ni a kan cikin ƙaryane, ke kin san rayuwar data shiga a baya saboda cikin ki? Kin san yadda tasha wahala? Ko kuwa kin san abubuwan da tayi saboda ta canza tabon dake jikinta saboda nan gaba ke kar kisha irin wahalar data sha?” Nabila ɗagowa tayi sai taji kuka ya ƙwace mata tace “Inna na tuba, don Allah ku yafe min, kishin su Zainab ne da son Kabir ya sani aikata hakan.” Inna ba tace mata komai ba ta miƙe tayi ɗaki, nan ta ƙara durƙushewa tana rera wani kukan na tsananin dana sani. **** Zeey kam bayan sallar Isha’i tana kwance kan sallaya bacci yayi gaba da ita, bata farka ba sai asuba, haka ta tashi tayi sallah sannan ta zauna akan gado tana tunani, fitowa tayi ganin gari ya fara ɗan haske ta nufi ɗakin Daddy, sai dai da alama ma baya gidan, jikinta ne yayi sanyi hakan yasa ta juya, muryar Mummy taji tace “Auta bai dawo ba, da alama a guest house ɗinshi ya kwana.” Bata tanka wa Mummy ba kawai ta koma ɗaki har ta zauna ta tuna gift ɗin da Baqeer ya bata hakan yasa ta fito taje motarta ta ɗauko ta koma ɗaki, anan kan sofa ta zauna ta buɗe jakar, idanuwanta ne suka sauka kan fabric ɗin nan, ta fara janyoshi ta wareshi, nan da nan tayi wani murmushin jin daɗi, abayar tayi mata kyau har bata san yadda zata kwatanta ba, a fili ta furta “My Baqeer.” Ta ɗan rungume abayar, turaren ta ciro ta ajiye shi akan dressing mirror sannan ta ajiye abayar a bakin gado, agoggo ta kalla karfe takwas na safe gani take lokacin ma kamar baya sauri sam, saƙo ne ya shigo wayarta hakan yasa ta janyo wayar sai taga daga Baqeer ne, wani murmushi ta saki a fili tace “ɗan halak!” _Sending you good thoughts and hoping you believe in yourself just as much as I believe in you. Morning_ Sakon ta ƙurawa ido tana jin wani irin kewar Baqeer na shigar ta, dole zata bayyana mishi ƙaunar da take yi mishi don a wannan lokacin tana ji gwara tayi aure ta bar gidan don ganin Mummy ya fara mata wahala. Maimakon tayi mishi reply sai ta kwanta ta ɗaura wayar a saitin ƙirjinta ta rungume tana tunanin Baqeer a haka wani ɗan karamin bacci yayi awon gaba da ita. **** Baqeer kuwa bayan ya tura mata ne ya sake karantawa, goshinshi ya ɗan riƙe yace “Ko dai saƙon bai kamata bane?” Sai kuma ya girgiza kai yace “Abinda ke raina ne  sannan I think it’s time to let her know abinda nake ji a kanta, in har bata yi gwara na haƙura kafin na ruguza abinda ke tsakaninta dasu Dada.” Da wannan shawarar ya cigaba da exercise dinshi, gwada sauke ƙafar yayi yana ɗan neman yin amfani da ita ya tsaya tsaye, sai dai yaji ya kasa, ya sake nan ma ya kasa, dabara ce tazo mishi ya saukesu sannan ya riƙe head board na gadon ya ɗan sa ƙarfi gadon ya zame mishi kariya ya riƙe, yana tsayuwa ko second biyar bai yi ba ya faɗa kan gadon, samun kanshi yayi da dariya yace “Baqeeru da sauranka.” Wayarshi ya sake janyowa Zee har yanzu bata yi reply ba, IG ya shiga ya sake posting na wasu flyers da yasa aka musu na adverts sannan yai shiru yana tunanin wani yankan ɗinkin maza daya fara, wani unique designs ne wanda bai taɓa ganin anyi ba, ya tabbatar in aka gama ɗinkin nan zasu samu mutane In Sha Allahu. Sai wajen goma Tanimu yazo suka je makaranta suna dawowa ya leƙa shagonsu suka sake gyarawa su biyu sannan ya ƙarasa yankan da yake yi, yanayi yana nunawa Tanimu yadda zai yi ɗinkin, basu gama ba sai karfe sha biyu, wani murmushi ya saki ganin ɗinkin ya fita sosai yadda ya tsarashi, Tanimu kam sai dariya yake yi bakinshi yaƙi rufuwa. Baqeer yayi murmushi yace “Muna needing styles kamar biyar kafin mu buɗe shago, na mata muna da su kawai ɗinkawa zamu yi sannan ina so na sayi wasu manyan electric sewing machine idan aka samu kuɗi, ina ganin daga nan zamu iya buɗe shagon.” Tanimu yace “Allah ya ƙara daukaka ka, zuciyarka mai kyau ce shi yasa Allah ba zai barka haka ba.” Fitowa suka yi suka shiga adaidaita suka yi hanyar gida, suna parking ya hau kan kekenshi sai ga motar Zeey tayo kwanar, bai san sanda ya saki murmushi ba, ya kalli Tanimu yace “Ka wuce gida ni zan ƙarasa, juyawa yayi shi kuma ya tsaya har sai da ta kashe motar, kafafuwanta ta zuro idanuwanta na kanshi shima haka, kafin ta fito ta maida kofar ta rufe. Kasa ɗauke ido yayi daga kanta ganin abayar daya saya mata ce ta saka, bai ƙara ganin kyan abayar ba sai yanzu da ta saka, tayi kyau har ya rasa me zai ce. Ido ta ɗan lumshe tana murmushi kafin ta fara takowa inda yake, sai data zo kusa dashi tace “Na sani nayi kyau kar mutanen waje su gane ka kasa ɗauke ido daga kallona.” Tana kaiwa nan tayi ciki, a bakin ƙofa ta ɗan tsaya sannan ta waigo sannan tayi mishi murmushi tayi mai ƙaramin gwalo, sumar kanshi ya shafa yana jin wani yanayi wanda ba zai iya fassarawa ba, fuskarshi ya shafa sannan ya sake murmushi yabi bayanta. Dada ce take cewa “Zainabu na! Lale lale kai ina zaki haka kika sha kyau? Ba dai wurin saurayinki zaki ba?” Ta gefen ido ta kalli inda Baqeer ke tahowa tace “Ya riga ya ganni Dada yana gama ganina nazo kema ki ganni.” Nan da nan yanayin fuskarshi ya canza, ya tamke fuska sosai da kayanshi daya bata zata je Junaid ya ganta? Dada ce tace “Shiga falo ki zauna bari na ƙarasa abu.” “Dada kema ki dinga hutawa don Allah, ni kam na kai shekarunki bani ba girki.” Dariya tayi tace “To ai gwara na motsa jikina bana son zaman haka nan, sannan yawanci kinga abinda nake fa ba mai wahala bane.” Zeey ta nufi inda take har zata ce zata tayata ta tuna babu abinda fa ta iya hakan yasa tayi saurin yin kwana tayi falo, Baqeer ranshi a ɓace ya gungura yayi ciki yana kuncini, yana jin Dada na cewa “Wannan kai dai wallahi baka ji daɗi ba, matarka akwai aiki a gabanta.” Bai tanka mata ba ya shiga, Zeey ce ta kalleshi ya ɗauka tana ciki sai ya ganta daga gefen ƙofa kaɗan tace “A dinga sakin fuska dai Ya Baqeer.” Kallonta yayi duk da yana jin haushinta sai yaga kamar har ƴar ƙaramar rama tayi, jiki a sanyaye yace “Are you okay now?” Nan da nan yanayinta ya canza, ta girgiza kai alamar a’a  tace “I’m not.” Wani irin sanyi jikinshi yayi maimakon yayi ɗaki kamar yadda yayi niyya sai ya nufi cikin falo ya ja burki ya nuna mata kan kujera dake gefenshi kaɗan ya buga kaɗan alamar tazo ta zauna. Ƙarasawa tayi ta zauna ya kalleta yace “Meke faruwa?” Kallonshi tayi zuciyarta na zafi tace “Komai ma ya faru, komai da nake tunanin shine gaskiya ya koma ƙarya, yanzu ban san dame zan yarda ba.” “Kin yiwa yayanki magana akan mahaifiyarku?” Kallonshi tayi tace “Itan ce ba neman mu take yi ba.” “Kunji dalili daga wurinta? Ko ku kun taɓa nemanta?” Idanuwan ta ne suka sake yin raurau alamun son yin kuka tace “Ni naso zuwa wurin danginta amma abinda suke yiwa Mummy yasa naji bana so.” Maimakon ya bata amsa sai ya kafeta da ido, kai ta sunkuyar da sauri cike da shagwaɓa tace “Me nayi kuma?” Shi kawai mamaki yake yadda sam basu da mai basu shawara yace “Ki samu time kije da kanki kiji me yasa ita bata nemanku, a matsayinta na mahaifiyarku.” Kallon juna suka yi…… *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*         *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA BIYU* {72} Kallon juna suke yi kowa yana kokowa da abinda yake ji a cikin zuciyarshi, a wannan lokacin kowanensu ji yake yi kamar ya fallasa asirin dake cikin zukatansu ko sun samu suji sauƙi sai dai kowanne da tunanin da yake yi dake taka musu burki wajen amayar da abinda suke ɗauke dashi. Zainab ce ta fara kawar da kanta tana sakin ajiyar zuciya, murya ƙasa-ƙasa tace "Taya za'a yi mu nemeta Ya Baqeer bayan tunda ta tafi bata ƙara waiwayarmu ba tayi aure ta haifi wasu ƴaƴan da take so mu ta manta damu." Murmushi Baqeer yayi yace "Zainab kenan naga alama baki san wacece mahaifiya ba baki san girmanta ba shi yasa kike faɗar haka, idan ita bata nemeku ba kenan ku ba zaku taɓa nemeta ba? Bayan haka kuma kun ji ta bakinta ne kun ji dalilinta na ƙin nemanku da zaku yanke mata hukunci? Haka nan uwa ba zata saki ƴaƴanta ta watsar dasu ba sai da wani babban dalili don haka dolenku ne ku bata dama ta faɗa muku nata side of the story ba wai ku ɗauki fushi don tunda ta tafi bata ƙara waiwayarku ba. Komai na rayuwa ɗan uzuri ne, idan ta rabu daku ku sai ku nemeta kuje inda take tunda itama tana da hakki a kanku, bayan haka ma baku san a wane hali take ciki ba watakila akwai dalilinta na rashin waiwayarku da bata yi ba tun bayan barinta gidanku." Jikinta ne yayi sanyi da taji abinda yace, cikin ranta dai ta ƙudurce In Sha Allah zata yi amfani da shawarar shi tabbas lokaci yayi da zasu nemi mahaifiyarsu wacce rabonsu da ita tun suna ƙanana don ita bata jin zata ganeta ma saboda ta bar gidansu lokacin bata fi shekara huɗu zuwa biyar ba. Har ta koma gida tana auna abinda Baqeer yace a cikin ranta, tana ajiye motarta ɗakin Kabir ta wuce. Murɗa handle ɗin ƙofar tayi ga mamakinta sai ta sameta a buɗe saɓanin kwanaki da sai tayi knocking kafin ya taso ya buɗe. Samunshi tayi yana kwance akan gadon shi yana danne-danne a waya. Zama tayi a bakin gadon tana kallonshi, ita sai taga kamar daga jiya zuwa yau ma har ya ɗan cicciko daga ramar da yayi ta tashin hankalin daya samu kanshi a ciki kwana biyu. Tashi yayi ya zauna yace mata "Kwanan nan fa kin fara damuna bini-bini sai ki shigo mini ɗaki kamar wacce kika bani ajiya na cinye ban biyaki ba." Hararar shi tayi tace "Au haka ma zaka ce? Yanzu daka samu ka fita daga waccen matsalar shine har kake da bakin yi mini wulaƙanci ko, ai shikenan ni na nuna na damu da kai amma kayi da ƴa." Dariya yasa yace "Allah ke ɗin ce kin fiye damu." Tashi tayi tace "Ai dai ka tsaya kaji abinda ya shigo dani kafin ka fara wulaƙancin ka daga yau kuma bazan ƙara zuwa inda kake ba." Da sauri ya riƙo hannunta ganin kamar tayi fushi zata bar ɗakin yace "kefa daɗina dake baki san wasa ba sam, dawo ki zauna ni wasa nake yi miki." Komawa tayi ta zauna ta zuba ido tana kallonshi kamar mai tunanin ta yadda zata fara faɗa mishi shawarar data yanke, sai da taga kamar ya ƙosa da jiranta sannan tace "Ya Kabir nace baka ganin ya kamata ace mun nemi Ummi kuwa? Tunda ta bar gidan nan fa bamu ƙara sakata a idanunmu ba sai ƴan uwanta dake zuwa lokaci bayan lokaci suma ba'a taɓa katarin sun zo sun samemu a gida ba." Wani irin kallo yayi mata yace "Wace Ummin kenan?" Itama kallonshi tayi tace "Har Ummi nawa garemu, of course Ummi mahaifiyar mu nake magana akai." A fusace ya tashi yace "Amma dai baki da hankali ko, matar da tunda ta watsar damu muna yara bata ƙara waiwayarmu ba tsawon wannan lokacin shine kike cewa muje wajenta, to muje wajenta muyi mata me bayan mun girma mun mallaki hankalin kanmu? Tunda ta nuna bata da buƙatar mu a rayuwarta ba shikenan ba muma bama buƙatarta a rayuwarmu sai kowa yayi rayuwarshi yadda yake so babu ruwan wani da wani." "Ya Kabir mahaifiyarmu ce fa." Katseta yayi yace "Mahaifiyar tamu, ki fada mini abu guda ɗaya da tayi mana da zai yi nuni da ita ce ta haifemu? Tunda ta bar gidan nan bata ƙara waiwayarmu taga a wane hali muke rayuwa ba, ko halin dana tsinci kaina a ciki ai laifinta ne idan da bata watsar damu tayi tafiyarta ba duk haka da bata faru ba." Da mamaki Zainab ke kallonshi tace "Ya Kabir wane irin laifinta kuma? Ita tace Nabila ta ƙala maka sharri saboda Allah." "Idan ma bata ce ba ai dai rashin zamanta damu ne ya janyo don haka ni babu inda zan je kema da zan baki shawara ki ɗauka da nace kada kije don bana jin ko ganinki tayi zata tuna dake don alamu sun nuna ta daɗe da mantawa da ta haifi wasu ƴaƴa data fita ta bari." Tashi Zainab tayi tace "Ni dai gaskiya to zan je don ban san dalilinta na ƙin waiwayarmu ba tun bayan barinta gidan nan zan je naji ta bakinta kafin na yanke mata hukunci, bayan haka kuma ita ɗin mahaifiyarmu ce da bamu isa mu canjata ba duk kuwa da gatan da wata zata nuna mana ba zai sa ta amsa sunan mahaifiyarmu ba." Daga haka tai hanyar fita daga ɗakin har taje bakin ƙofa sai kuma ta tsaya tace "Kunyi magana da Mumy?" tana jin lallai zata je taga mahaifiyarta don sai a yanzu tasan tayi wauta da duk waɗannan shekarun bata taɓa tunanin ya kamata taje inda take taga a wane hali take ciki ba, ba zata iya tuna abinda yasa ta fita ta bar gidansu ba amma tana iya tuna wasu daga cikin moments ɗin su masu daɗi da tsayawa a rai. Takan tuna lokutan da take fita dasu yawon shaƙatawa a motarta ita da Kabir suyi ta faɗa akan wanda zai zauna a gaba, wasu lokutan sai ta hanasu zama gaba ɗaya tace duk su koma baya babu mai zana a kusa da ita tunda faɗa suke yi. Tana shiga ɗakinta ta hau haɗa kaya a cikin akwati don ta riga ta sawa ranta zuwa Ɗambatta a gobe bata jin akwai wani abu da zai hanata zuwa. Sai da ta gama haɗa kayan tsaf sannan ta ɗauki waya ta kira Daddy don tunda ya fita ya bar gidan jiya bai ƙara waiwayarshi ba. Bata daɗe tana ringing ba ya ɗauka, a shagwaɓe tace"Daddy ina ka tafi tun jiya ban ganka ba?" Da kulawa yace "Raina ke ɓaci idan ina cikin gidan Zainab shi yasa na kauce har sai na huce don kada na yanke hukunci a cikin fushi daga baya nazo ina dana sani." Ɗaga kanta tayi kamar yana ganinta tace "haka ne kuma, Daddy dama zan faɗa maka ne gobe ina so zan je Ɗambatta na kwana biyu." Shiru yayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin yace "Ɗambatta kuma? Lafiya dai ko?" "Lafiya lau Daddy kawai dai ina so naje ne don Allah kada kace a'a," tayi maganar cike da shagwaɓa. Samun kanshi yayi da kasa musa mata duk da ba son zuwanta Ɗambattan yake yi ba bare da mutanen suka nuna mishi ba mutanen kirki bane su amma ba zai yiwu ya cigaba da hanasu zuwa wurin dangin mahaifiyarsu ko gunta ba don haka yace mata sai ta dawo amma kada ta daɗe. Da murnarta ta ajiye wayar har da ɗan tsallenta don bata taɓa tunanin Daddy zai amsa mata da wurwurii haka ba ta ɗauka hanawa zai yi kamar yadda ya sha yi a baya idan ta nuna tana son zuwa wurin mahaifiyarta. Ƙara ɗaukar wayar tayi ta turawa Baqeer saƙo. "In Sha Allah gobe zan je Ɗambatta, nagode da tunatarwa." Ajiye wayar tayi ta tashi tana ƙara duba ɗakin ko da akwai abinda take buƙatar ɗauka kada ta manta. Mummy ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, kallo ɗaya Zeey tayi mata ta juya ta cigaba da abinda take yi. Jikinta ne yayi sanyi ganin irin kallon da Zeey tayi mata. Ƙarasa shigowa tayi cikin ɗakin ta zauna a bakin gado tana bin yadda Zeey ta barbaza kaya a cikin ɗakin da kallo. "Wani wuri zaki je ne auta?" Ta tambayeta tana ƙara bin ɗakin da kallo. Ɗan taɓe baki tayi tace "Um," kawai ta cigaba da abinda take yi. Kallon Zainab tayi tace "kema kina jin haushina kamar Daddy ko? Shi yasa kika daina kulani." Wani irin kallo Zainab tayi mata da itama bata san tayi ba har ta buɗe baki zata bata amsa sai kuma taji ba zata iya ba kawai tayi shiru, har yanzu ta kasa gane dalilin Mummy na ɓoye musu Nabila ƴarta ce bayan duk wannan tsawon lokacin da aka ɗauka, to da ace haka bata faru ba baza ta taɓa sanar musu ba kenan ko me? "Ki bani dama nayi miki bayani," katseta Zeey tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tace "Bani zaki yiwa bayani ba Mummy don ba zamana kike yi ba a gidan nan mijinki ya dace ki yiwa bayani bani ba." Daga haka bata ƙara bi takan Mummy ba har ta gaji da zaman ɗakin ganin da tayi Zeey ba zata kulata ba yasa ta tashi jiki a sanyaye ta bar ɗakin. ***** Kwanakin nan bata cikin nutsuwarta saboda ta daina samun Bello a waya ko zata kwana tana nemanshi wayarshi bata shiga, babbar damuwarta yadda kusan komai nata ya ƙare saboda dama ba wata sayayya suka yi mai yawa ba tunda dama a tsarinsu baza su daɗe a ƙasar ba shi yasa suka sayi kayan abinci na adadin kwanakin da suke saka ran zata yi anan kafin ta bishi to gashi kwanakin har sun haura ita bata bishi ba sannan kuma bai turo mata wasu kuɗaɗen da zata sayi wasu kayan buƙatun ba. Tana kwance a parlourn ta wurin yayi kaca-kaca don tun bayan barin Habi gidan bata ƙara saka tsintsiya da sunan shara ba, komai taci anan wurin take barin shi bata ɗaukewa don haka parlourn ya cika da ƙazanta. A gefe ga farantan da take cin abinci nan sun yi tsibi guda don ko su bata iya kawarwa sai dai idan tayi amfani da wani ta ɗora shi akan waɗanda ta tara, ga ledojin tarkacen kayan ciye-ciyenta nan da ribobin lemo da ruwan da take sha sun haɗa wata ƴar ƙaramar bola. Ita kanta idan aka kalleta ba za'a so sakewa ba don ga dukkanin alamu tayi kwanaki jikinta bai ga ruwa da sunan wanka ba, gaba ɗaya tayi biji-biji da ita duk ta fita daga hayyacinta. Tana kwance tana danne-danne a waya ga alama ita wannan bolar data haɗa bata damunta don chatting take yi da sababbin ƙawayen data yi tana murmushi don sai fasa mata kai suke yi suna cewa ai sun ɗauka da suka jita shiru kwana biyu ko har ta tafi ne babu labari. Turo ƙofar yayi ya shigo parlourn bakin shi ɗauke da sallama yana rataye da jakar matafiya a kafaɗar shi sai akwatin trolley da yake ja a ɗaya hannunshi. Sallamar da yayi ce ta maƙale mishi a maƙohgaro ganin parlourn kamar ba nasu ba, fita yayi ya duba yaga tabbas gidan ne dai ya shigo don haka ya koma ciki yana ƙarewa parlourn da alamu suka nuna kamar babu mutum ɗin dake rayuwa a ciki. A kwance akan doguwar kujera ya ganota. A fusace yace "Asiya miye haka?" Yana nuna tsakar parlourn da hannu. Wai sai a sannan tasan da shigowarshi cikin gidan don hankalinta gaba ɗaya ya ɗauku ga wayar da take dannawa ko kusa bata ji motsin shigowarshi ba. Miƙewa tayi tsaye fuskarta ƙunshe da mamakin ganinshi a daidai wannan lokacin da bata yi zato ba tace "Bello! Saukar yaushe?" Bin jikinta yayi da kallo sai yaji ranshi ya ƙara ɓaci, bsyan ƙazantar gidan har ma jikinta ba zata iya tsayawa ta gyara ba. Tsaki yayi kawai ya wuce ciki ya barta anan. Bin bayanshi tayi sai ta ganshi a tsaye yana ƙarewa ɗakin kallo. "Tafiya babu sanarwa Bello, hala kazo ka tafi dani ne. Kamar kasan dama na gaji da zaman ƙasar nan wallahi duk na matsu na bika ashe ma kai da kanka zaka zo mu tafi shi yasa bana samunka a waya." A fusace yace"Dallah Malama yi mini shiru, a hakan zan kwasheki na fita dake ƙasar waje kina zuba wannan uwar ƙazantar, kalli jikinka saboda Allah ki duba muhallinki kamar ba gidan amarya ba komai ya fita daga hayyacinshi tsabar ƙazanta." Kallon kanta tayi ta kalli ɗakin data manta yaushe rabon da a gyara a hakan ma wai shine mai ɗan dama don ba kasafai ta cika shigowa nan ɗin ba, cewa tayi "ya kake so nayi saboda Allah bayan nace maka zan nemo mai aiki saboda aikin yayi mini yawa bazan iya ba kaƙi amincewa." Ajiye kayan hannunshi yayi zai fita daga ɗakin tace "To yaushe zamu tafi don na fara shiri?" Wani wulaƙantaccen kallo ya wata mata yace "Ina? Ai babu inda zamu don nima na dawo kenan," kawai ya fice ya barta a ɗakin. Bin bayanshi Asiya tayi da kallo hankali a tashe tace "Iyyeee.......Bangane ba ba inda zamu je a ina? Ni kaga bari nazo na tattara kayanmu." Tsaki yai kawai ya cigaba da tafiya, kallan mamaki ta bishi dashi ai ko za'a mutu sai ya fitar da ita daga kasar nan, tab ai bataga yban daya isa ya hanata ba.... Mukam mukace to ga fili ga doki🥴 * *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA UKU* {73} Duk da Baqeer yasan zai yi missing ɗin Zee in ta tafi amma wata irin nutsuwa da jin daɗi yake ji, tabbas a matsayinta na mace tana buƙatar ta nemi mahaifiyarta sai dai in ita mahaifiyar ce ta nuna bata son zuwan nata, yau yana tashi ya tuna yau ne zata wuce, tun yanzu ya fara jin rashinta ya fara damunshi, wayarshi ya ɗauka ya tura mata text _Karfe nawa zaki wuce?_ Ba dadewa sai ga reply _11am In Sha Allah_ ajiyar zuciya yayi ya maida wayar, wani saƙon ne ya ƙara shigowa _In na dawo ina son jin amsar tambayar da nayi maka_ murmushi ne kawai ya bayyana a fuskarshi don shi kanshi amsar yake son bata, ganin bai yi reply ba yasa ta shiga wanka, tana fitowa ta shirya cikin atamfa anyi mata ɗinkin doguwar riga tasha kwalliya da stones tayi kyau sosai, bata son ɗaura ɗankwali hakan yasa tasa ƙaramin mayafi tayi rolling sannan tasa abaya buɗaɗɗiya a sama, fitowa tayi daga ɗakin, gidan yayi shiru kamar ba mutane a ciki,  ita kaɗai tayi breakfast shi yasa kawai taci toast bread da tea, ji take yi komai baya yi mata daɗi a gidan, ƙofar ɗakin Mummy taje tana tafe tana tuno irin tsananin ƙaunar da Mummy take nuna mata, ta tabbatar wannan abinda take yi mata dole in taga ta shareta abun ya dameta. Hannu tasa ta murɗa ƙofar ɗakin ta tura a hankali, a duƙunƙune ta ganta tana bacci da alama sanyi take ji, bargo ta janyo ta lulluɓa mata cike da tausayin halin da suka tsinci kansu sai dai bata ji zata iya yafe mata yanzu kila dai in taje wurin Ummi ta dawo. Juyawa tayi ta fita bayan ta sanar da masu aiki akan su kai mata abinci anjima sannan in bata ci ba su sanar da Kabir. Motarta ta shiga tana ganin saƙon Daddy wai zai turo driver ya kaita da sauri tayi mishi reply akan ita da kanta take son zuwa don Allah ya barta. Tayi sa'a daya ce mata Allah ya kaita lafiya ta tabbatar ta kira shi in ta isa. Haka ta fito daga gida tana tafe tana tunanin yadda zata yi magana da mahaifiyarta don kuwa ita ko gidan da take aure bata sani ba, shekarun baya sukan je Dambatta amma tunda dangin mahaifiyarta suka fara tsangwamar Mummy sai taji sun fita daga kanta gaba ɗaya, hakan yasa ta tattarasu ta watsar dasu.    Wayarta ta kalla wanda kiran Junaid ya shigo maimakon ta ɗauka sai ta kifa wayar ta cigaba da tuƙin ta, tana tausayawa Junaid sai dai ba zata sadaukar da kanta akan abinda tasan ba zai sanyashi farin ciki ba, ita mace ce da in har ba ta son abu to fa bata iya ɓoyewa, haka zalika in tana son abu kana iya gani a fuskarta, shi yasa har yanzu take mamakin yadda Baqeer ya kasa gane son da take yi mishi, ajiyar zuciya tayi ta cigaba da tuƙi ai ya dai yi ya gama in ta dawo zasu yita ta ƙare, bazata bari suyi ta tafiyar tatata haka ba. ***** Baqeer yau yana da appointment hakan yasa ya shirya da safe Tanimu yazo suka je, ga mamakinshi office ɗin Junaid aka kaisu, sunfi minti goma suna jira kafin yazo, nan yace Baqeer ya biyoshi, haka Baqeer ya gungura kekenshi suka nufi ciki, Junaid ya zauna yana sa Baqeer yayi gwaje-gwajen abinda ya umarceshi, kafin daga bisani shima ya zo da kanshi ya duddubashi, kallon Baqeer yayi bayan sun gama, fuskarshi sam babu walwala yace "Akwai wani abu ne tsakanin ka da Zainab?" Da mamaki Baqeer ya kalleshi, sai dai haka kawai yaji ya kasa bashi amsa a ganinshi wannan tambayar ba shi ya kamata yayi wa ba, Junaid ya ɗan kauda kai yace "Of course nasan ba kai bane kenan akwai wani?" Sake kallonshi yayi duk da zuciyarshi na son sanin me yake nufi da kalamanshi sai dai haka kawai yaji ba zai iya tambaya ba, Junaid ya sauke ajiyar zuciya yace "Baqeer please naga Zainab na ganin girmanka da kula da kai kamar yayanta me zai hana ka bincikomin wanda ke hure mata kunne yake neman hanata bin umarnin iyayenta?" Yanzu kam yanayin kallon da Baqeer yake yi mishi ya canza, kallo ne mai alamar tambaya wanda da alama Junaid ya fahimci kallon da yake mishi, ya ɗan miƙe tsaye yana sa hannu a aljihunsa yana cewa "Tana da gardama ne ban san ya zan yi ta fahimceni ba, wannan dalilin yasa nace yau a turoka wurina,” ya ƙarasa maganar jiki a sanyaye, yana ƙoƙarin matsawa daga wurin yaji ance “Babu komai a tsakaninku kenan ko me?” Da mamaki ya waigo suka yi wa juna kallon kallo shi da Baqeer, kallon da su biyun kaɗai suka san ma’anarshi sai dai gaba ɗaya Junaid ji yayi ya kasa bada amsa, sai kauda kai da yayi wanda hakan yasa Baqeer ya tabbatar da amsar da yake son sani, a hankali ya saki siririn murmushi wanda da alama bai san sanda ya fito daga ƙasan zuciyarshi ba. Ba tare da yace komai ba ya fara tura kekenshi zuwa ƙofar fita, ina ma Zee tana nan ya ruga ya sanar da ita ƙaunar da yake yi mata? Dariya ma kalmar Junaid ta bashi wato ya binciko kanshi kenan ko me? Don ya tabbatar in har Zeey ba Junaid take kulawa ba to tabbas akwai sonshi a ranta kamar yadda yake sonta, ya daɗe yana ganin sonshi a ƙwayar idanuwanta sai dai in ya tuna soyayyarsu da Junaid sai yayi tunanin tausayi ne, wani tausayi ne ake tambayar matsayi? Abinda yaji zuciyarshi ta tambayeshi kenan, wani murmushi ya karayi ji yake yi tun yanzu ya ƙosa ma ta dawo ya fallasa mata abinda ke ranshi don wannan maganar dole sai gashi gata. Kamar ya kirata a waya sai ya fasa tunowa da yayi tana hanya, nan suka wuce shago, sun kammala ɗinki na biyu suka sake jera kayyakin da Salim ya kawo musu, suna yi yana ɗan sakin murmushi wanda yasa Salim kasa jurewa yace “Wai hala Zainab tazo yau?” Da mamaki ya kalli Salim yace “Me kake nufi?” Cigaba yayi da aikin yana cewa “To Malam Baqeer ai in dai aka ganka kana murmushi kwanan nan to tabbas akan Zeey ne.” Nan da nan ya tamke fuska yace “Me kake nufi?” Dariya Salim yasa yace “Ah to ku za’a tambaya ai ba wani ba,” yayi maganar cike da zolaya. ****** Mumy kam bata tashi ba sai karfe sha biyu don dama sai wajen goma ta sake kwanciya, ganin bargo a jikinta yasa tayi saurin miƙewa tana tunanin Senate ne ya shigo tana bacci, sai dai tana shiga ɗakin shi ta tabbatar ba shi bane, jiki a sanyaye ta juyo ta nufi ɗakin Zee don babu shakka in dai ba shi bane to Zainab ce, shiga tayi sai dai babu alamar Zainab a ɗakin ga dai ɗakin nan an gyarashi tas wanda hakan yasa tasan mai aiki ce tayi, fitowa tayi ta nufi kitchen tana kiran Karima wacce tasan sun jitu da Zainab. Da sauri ta fito ashe itama wurin Mummyn zata je ta kai mata breakfast tunda taga ta farka ta shigo don ta tattara kayan abincin, Mummy ta kalleta tace “Ina Zainab?” Kai tsaye tace “Ta fita Mummy tun ɗazu.” Idanun Mummy na kanta tace “Ina?” Kai ta girgiza wanda hakan yasa Mummy juyawa don tasan dama ba zata san inda take ba, Kabir ta hango sanye da jeans da long sleeve shirt da key a hannunshi yana ɗan kaɗa su yadda ya saba, tayi saurin cewa “Kabir baka yi breakfast ba zaka fita.” Waigowa yayi ya kalleta don shi bai masan me zai ce mata ba, neman juyawa yake yi tace “In har Zainab bata fahimceni ba kai dai bana ji ya kamata ka ƙi fahimtata, Kabir ka manta abubuwa nawa na ɓoye sirrinka? Sai ni don na ɓoye nawa sirrin ƙwaya ɗaya shi kenan sai ka kasa yafe mini?” Cak ya tsaya sai kuma ya waigo, nan da nan jikinshi yayi sanyi, ganin haka yasa ta tako inda yake tace “Kai bai kamata kayi mini haka ba, Kabir ka sani bazan iya furta kalmar bane shi yasa na ɓoye bawai don inaso ba, nasan nayi laifi amma sai ku duba zaman amanar da muka yi ko?” Murya cikin sanyi yace “Mummy na sani sannan zan huce ki bani kwana biyu don Allah, nasan dama Nabila ba da izininki tayi abubuwan nan ba.” Kai ta jinjina alamar fahimta kafin tace “Zeey fa? Na duba bata nan.” Tsaki yayi yace “Dambatta taje.” Wayar Mummy dake hannunta ce taji tayi mata nauyin ɗauka wanda sai jinta suka yi a ƙasa, hannu yasa ya ɗauko ya miƙa mata sannan ya kalleta yace “Mummy?” Murmushin yaƙe tayi tace “Daddynku ya barta?” Ɗan wani motsi yayi da bakinshi yafin yace “It seems so, don ta tambayeni jiya nace ba zani ba.” Kai ta jinjina kawai ta juya tana tafiya ƙafafunta na ɗan neman kasa ɗaukan ta, ɗaki ta shiga ta kalli abincin da Karima ta ajiye, hannayenta tasa a matse-matsin cinyoyinta kamar mai jin sanyi tana matsasu, tama kasa yin tunanin komai, wayar Zee ta kira sai dai da alama babu network ko wayar a kashe take don taƙi shiga, ajiyewa tayi tare da sake matse hannayenta. ^**** Tunda ta shiga Dambatta gabanta ke faɗuwa, yaushe rabonta ma da ƴan uwan mamanta? Duk laifin da suke yiwa Mummy ya kamata ace sun yi musu magana ne ba wai su janye jikinsu ba, wayar babban yaron ƙanin mamanta ta kira don numbershi kaɗai take dashi shima don ya kirata ne kwanaki akan za ayi family meeting in da hali suzo, shine lokacin data tambayi Daddy akan zata zo ya hanata daga nan tayi saving ta kira tace baza su samu zuwa ba, har kiran ya katse bai ɗauka ba, hakan yasa ta sake kira, yanzun ma kamar zai katse sai kuma taji ance “Hello?” Ajiyar zuciya tayi tace “Ya Adam kana ina? Gani a Dambatta.” Duk da yayi mamakin zuwanta bai hanashi cewa “Dambatta? Ke ɗin? Sannan in kinzo menene nawa a ciki?” Hankali a kwance tace “Kaga don Allah kar mu tsaya shiririta kana ina? Sam na kasa gane garin gani dai kusa da wani shago, gefen tasha kazo sai muje gidan Hajiya Goggo daga nan ina so in ɗan yi ziyara.” Ga mamakinshi kafin ma yace mata zai zo sai ji yayi tace “Kayi sauri ina jiranka,” tana kaiwa nan ta kashe wayar tana kallon mutane nata hada-hada, murmushi tayi tana tunanin yanzu fa kowa da tashi rayuwar, kowa da matsalolinshi. Atm ta hango daga gefe ta gangara ta ciro kudi 100k tasa a jakarta, sannan ta sake dawowa, tana kokarin duba agoggo taji anyi knocking glass ɗinta, zugewa tayi ta kalleshi da yake shi ta sanshi har sanda tazo sallama zata tafi ƙasar waje shi yasa bata yi wani kokonto akanshi ba hakan yasa tace “Ya Adam shiga.” Shiga yayi ya tamke fuska shi a dole yana son ta bashi haƙuri, Zeey ta hau hanya tana cewa “Ina zamu yi?” Samun kanshi yayi da nuna mata sai dai fuskar nan har yanzu babu wargi, har suka isa gidan Hajiya Goggo, parking tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya tace “Muje?” Gaba yayi yana tafe yana muzurai, ita kam ko a jikinta. Daga waje yace “Hajiya Goggo ga Zainabu.” Tana daga ciki tace “Zainabun Malam Lawi?” Zeey tayi saurin cewa “Hajiya Goggo taku dai.” Mamaki ne ya kamata ta ɗan yaye labule don ganin wacece, Zeey ta sakar mata murmushi tace “Hajiya Goggo ina wuni?” Tamke fuska sosai Hajiya Goggo tayi wanda babu alamun wargi a tattare da ita, ta maida labulen tana cewa “Hala aurenki yazo ne kina tsoro kar azo biki aga babu dangin mahaifiyarki ko ɗaya.” Zeey ta sani sarai basu kyautaba ta taho jikin ƙofar ta tsaya tana cewa “Hajiya Goggo kishiruwa tunda  na taho bansha ruwa ba, sannan bikina bai zo ba da saura sosai.” Hajiya Goggo bata tanka mata ba sai kuma can ta leko kamar an tunzuro ta tace “Kun gama tozartamu shine yanzu zaku dawo neman mu? Ace duniya da gaskiya? Kwanaki Kawu yana kan gadon mutuwarshi amma burinshi ya sakaku ke da Kabir a idanunshi, nan na wanki ƙafa ni da Altine muka je har gidan ku amma aka hanamu shiga aka koro mu wai mahaifinku ya hana mutanen Ɗambatta shiga mishi gida, haka muka tura a sanar da matar gidanku dalilin zuwan mu amma fir aka hanamu shiga, muka gaji da zama a waje muka dawo.” Kalaman Hajiya Goggo ne taji sun ɗaure mata kai, mene? Ita dai a iya saninta sune suka je suka ciwa Mumy mutunci akan ta mallakesu, me suke nufi kuma yanzu? Adamu ne yayi saurin cewa “Allah in na tuna abun nan ji nake yi kamar naje har gidan dukanku nayi muku rashin mutunci don haka ki zo ki tattara ki bar mana gari.” Zee gaba ɗaya kanta taji ya kulle, bakinta na rawa tace “Anya ba ciki kuka shiga ba?” Tsaki Dada tayi tace “Yaushe rabon da ko harabar gidan ku a barmu mu shiga? Ni ban masan kun koma gidanku na da ba sai da muka je wancan aka ce kuna nan to Allah ya taimakemu mahaifiyarku akwai wata ƙawarta a unguwar ita tayi mana kwatance muka je.” Idanuwan Zee ne suka fara canza launi tsoro da fargabar abubuwan da take ji su zama gaskiya take, taya zata fuskanci abubuwan nan in har Mumy ƙarya tayi musu a karo na biyu? Hajiya Goggo ce ta katseta da cewa “Kuje can mu mun sallama ku ai ba ku kaɗai muke dasu a dangi ba.” Bakinta na rawa tace “Gidan Ummy a taimaka a kaini," ta ƙarasa maganar muryarta na wani irin rawa tana jin har cikin jikinta na rawa, yanayinta da suka gani ne yasa suma ta basu tausayi, ta juya da sauri tana kallan Adamu tace “Don Allah…..” *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD*         *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA HUƊU* {74} Bakinta na rawa tace "Gidan Ummy a taimaka a kaini," ta ƙarasa maganar muryarta na wani irin rawa tana jin har cikin jikinta na rawa, yanayinta da suka gani ne yasa suma ta basu tausayi, ta juya da sauri tana kallon Adamu tace "Don Allah," da wani irin desperation a muryarta. Hajiya Goggo jikinta ne yayi sanyi da ga yadda Zeey tayi tabbas bata san abinda ya faru ba, Zeey kamar zata yi kuka tace “Ya Adam Kawun fa? Ko wurinshi zan fara zuwa?” Ya kalleta shima jiki a sanyaye yace “Ya rasu sai dai mu yi mishi fatan rahama, yanzu watanshi biyu kenan da rasuwa.” Jikinta ne ya ƙara mutuwa nan da nan taji idanunta sun ciko da ƙwalla, muryar Hajiya Goggo ce ta katseta da cewa “Ɗauki jakar kayan naki ki shiga da ita ciki idan kin huta zuwa anjima sai a raka ki, yanzu bata dawo daga wurin aiki ba." Ba don ranta yaso ba ta tashi taja akwatin kayanta ta shiga ciki kamar yadda aka umarce ta, shiru tayi a cikin ɗakin tana tunanin rayuwa, ajiyar zuciya tayi ta sakawa ranta son ganin Ummy bata ɗauka zata kai wannan lokacin ba'a haɗata da ita ba, gashi bata son zama a nan kar ma ayi mata zancen abinda zuciyarta bata shirya ji ba. Tana shiga ɗakin ta samu wuri ta zauna sannan ta ɗauki wayarta ta kira Daddy kamar yadda ya umarceta tayi ta sanar mishi ta iso lafiya. "To, ki gaishe su," kawai yace ya kashe wayarshi. Sai taji bata ji daɗi ba da yadda Daddyn yayi a ƙalla dai ai ya tambayi lafiyar mutanen gidan ko ba zai ce a bawa Hajiya Goggo wayar ya gaisheta ba. Har ta mayar da wayar cikin jaka ta ajiye sai kuma tayi tunanin faɗawa Baqeer isowarta lafiya. Ɗan gajeren saƙon sms ta tura mishi ta mayar da wayar ta ajiye. Hajiya Goggo ce ta shigo ɗakin hannayenta ɗauke da kwanuka, ajiye kwanukan tayi a gaban Zeey tana kallonta, ta ɗauka zata tashi ta karɓar mata kwanukan sai taga har ta ajiye Zeey bata yi alamun zata taimaka mata ba. Zama tayi a bakin gadonta tace "Ke kaɗai kike tafe ina Kabirun ko shi bai yi niyyar zuwa ya gan mu ba?” Ɗan taɓe baki tayi tace "Yana gida." Daga haka suka yi shiru don babu wani sabo a tsakaninsu. "Ku kune kuke yada zumunci amma mu baza mu iya yadaku ba don mahaifiyarku mace ce ta gari mai son zumunci.” Shiru kawai Zeey tayi don bata san me ma zata ce mata ba, Hajiya Goggo tace “Sai kici abincin kafin Adamu ya dawo sai ya rakaki wajen Innar taki.” "Wacece kuma Inna nifa wurin Ummi nake so naje ba wata Inna ba," Zeey tayi maganar cikin rashin kulawa. Da mamaki Hajiya Goggo ke kallonta jin yadda tayi mata magana kamar wata sa'arta babu tausasawa bare ladabi. Tuni ta murtuke fuska tasha kunu don ita ba'a kawo mata wargi. "Uwarki nake nufi, ko sai ance Ummi zaki fi ganewa," ta mayar mata. "Au wai Ummin ce Inna sai kace wata tsohuwa," Zeey tace ba tare data lura da yadda Hajiya Goggon ta canja fuska ba.  Tashi tayi ta fita ta bar mata ɗakin don idan ta zauna watakila ta iya kaiwa Zainab ɗin hannu don taga alamar baza su shirya da ita ba sam. Buɗe kwanukan abincin tayi tana yatsina fuska, dambun shinkafa ne wanda yaji zogale da gyaɗa sai ƙamshin soyayyen man gyaɗa yake yi. Mayar da murfin tayi ta rufe don bata cika son cin irin wannan abincin ba. Kwanon sha ta buɗe sai taga damammiyar fura ce data ji nono tayi fari tas gwanin ban sha'awa. Sai furar tasha don ta manta yaushe rabon da tasha fura irin wannan don yanzu zamani yazo an canza mata dandanon ƙauye, har wani lumshe ido take yi saboda garɗin furar da yake ratsata. Tana gamawa ta haye gadon Hajiya Goggo ta kwanta don sai taji gaba ɗaya gajiyar data kwaso ta haɗu da baccin da bata samu tayi ba kwana biyu sun saukar mata da wata iriyar kasala bacci kawai take so tayi. Babu daɗewa kuwa baccin ya sure ta, koda Hajiya Goggo ta dawo ɗakin sai ta tarar baccinta yayi nisa, tattare kwanukan data kawowa Zainab abinci tayi ta fita dasu cikin ranta tana mitar yadda ta bar mata kwanukan a wurin ba tare data kawar mata dasu gefe ba. Sai daf da la'asar Zeey ta tashi daga baccin daya ɗauketa bata shirya ba, fita tayi tsakar gidan ta ɗauro alwala. A tsakar gidan taga Hajiya Goggo tana ta ƴan kaye-kayenta, sai taji ta tuna mata da Dada haka itama take sam bata iya zama waje ɗaya. "Hajiya Goggo wai ba kya gajiya ne?" Ɗagowa tayi ta kalleta fuskar nan a tamke tace "Gajiya da me?" Ƴar dariya Zeey tayi tace "Da aiki mana, na lura ku dai tsofaffi ba kwa son zama waje ɗaya wallahi," daga haka tayi shigewarta ɗaki ta bar Hajiya Goggo da bin bayanta da kallo, lallai wannan ƴa lamarin ta akwai gyara, Hafsatu na da aiki a gabanta don ga alama gaba ɗaya an gurɓatawa yarinyar tarbiyya. Sallar azahar ɗin da bata samu tayi ba lokacin da take bacci da la'asar duk ta haɗa tayi. Bayan ta idar ta dade tana yiwa Kawu addu’a sannan tayi shiru yanzu kam Ummy take son gani, ɗaukan wayarta tayi ta kira Adam, da kamar ba zai ɗauka ba sai kuma dai ya ɗauka yace "Ya aka yi?" A shagwaɓe tace "Please mana Ya Adam, kai fa nake jira kazo ka kaini wajen Ummy ɗin." "Gani nan," kawai yace ya kashe wayarshi. Ajiye wayar tayi ta kishingiɗa tana jiran shi, tashi tayi ta fita tsakar gida wajen Hajiya Goggo ta zauna, ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba sai ma cigaba da tayi da jan carbinta ita kuma Zeey tana danne-danne a wayarta, ita duk ta gaji da zaman ma wallahi don ita dai bata saba zaman shiru ba nan kuma ta lura kamar kakar tata ba mai yawan son surutu bace. Ƙasan zuciyarta kuwa kokowa take yi da ita akan manta abubuwan dake faruwa, ƙurawa gefe ido tayi tana tuno yadda Inna ta tsangwemeta har yasa take tunanin ko haushinta take ji saboda Mummy ta sadaukar da komai saboda su ashe bata sonta ne saboda tana ganin Mummy na kula dasu ta bar ƴar cikin ta, ajiyar zuciya tayi tana tausayawa rayuwarsu shi yasa take jin tayi daidai zuwa ganin mahaifiyarta da tayi. Hajiya Goggo tana kula da yanayinta wanda ya sake tabbatar mata akwai abubuwan dake faruwa da alama maganar ce ba ta son yi. Sallamar Adamu taji ai kuwa da sauri ta miƙe yana shigowa tace “Yauwa Ya Adam kwaso kayana mu wuce don Allah.” Hajiya Goggo tayi caraf tace “Ki kwaso kayanki dai." Bata musa ba ta shiga ta jawo jakar suka yi sallama akan zata dawo suka fita, iska ta furzar suna fita tare da dafa kirjinta ji take yi kamar akan ƙaya take, gani take yi duk wani motsi data yi Hajiya Goggo na kallonta. **** Wannan shine kira na bakwai da Asiya ta ke yiwa Bello amma yayi kunnen uwar shegu da ita, ganin da gaske bashi da niyyar amsa mata yasa tace “Kasan Allah Bello in har ba ka shirya karɓar tashin hankali mara misaltuwa ba ka sanar dani yaushe zamu bar garin nan, yau naji rainin hankalin da bazan iya ɗauka ba.” Sake gyara kwanciyarshi yayi wani irin baƙin ciki na kwasar shi, yanzu fisabillilahi hakan shine auren? Ya gama sadaukar da komai saboda ita amma bata ma damu da halin da yake ciki ba? Gidan daya kashewa kuɗi ta maidashi kamar bola? Cike da tsiwa ta kama kugu tace “Malam magana nake yi maka kar ka maidani ƴar iska fa.” Da alama shima yanzu ya kai bango don zama yayi ya kalleta sheƙeƙe yace “Kinga Allah in har baso kike yi mu samu babbar tangarɗa ba ki wuce ki gyara mini gida na, sannan nima da kika gani koroni aka yi a ƙasar dana je balle kisa ran zan kaiki don kin yi masifa, ki barni nima naji da abinda ke damuna ko kuma wallahi daga ni har ke muyi dana sani, don na kula sam baki da tunani,” yana kaiwa nan ya gyara kwanciyarshi yana ji shi dai wannan aure duk shi ya janyo mishi talauci da ya lallaɓa ƴan kuɗaɗen shi ya tabbatar da har yanzu yana da kuɗaɗenshi amma ya biyewa wannan shashashar tasa duk sun kwashe kuɗin yanzu gashi nan ba ƙasar wajen ba aiki babu kuma kuɗin, don inda yake aiki ma anan Nigeria ganin shi ya zama celebrity ya kori kanshi da kanshi wai shi a dole ya girmi aiki a wurinsu. ****** Baqeer sam yau bai zauna ba daga shi har su Salim da Tanimu don sai yamma suka kamalla komai, ƴar karamar miƙa yayi yana kallon Salim yana cewa “Ya maganar abinda za’a yi mana printing ɗin?” Salim yace “Wallahi ban koma ba, jiya har naje zan shiga naga ƙaninka a waje shi da gang ɗin shi kasan ba kai gareshi ba yanzu sai yayi mini hauka cikin mutane shi yasa kawai na bar wurin ba tare dana ƙarasa ba.” Kai Baqeer ya girgiza yace “Allah ya shirya Kamalu shi ko girma baya yi.” Baki Salim ya taɓe yace “Kaima akwai taka dashi shi yasa duk ranar da ya ganka kai da masoyiyarshi to ka tabbatar kana da abun kare kanka don kuwa akwai yaƙi.” Cike da rashin fahimta Baqeer yace “Masoyiyarshi? Ni me zai haɗani da budurwarshi?” Salim ya ɗan yi dariyar mugunta yace “Ai ba abinda ma bai hadaku ba, kai dai ka shirya kawai,” yayi maganar yana hango abubuwan haukar da Kamalu yayi mishi akan Roshni lallai akwai drama ranar da zai ganga da Baqeer. Waya Baqeer yayi da mutanen da yake yiwa zane akan wasu sketch da ake so yace zasu samu ƙarshen satin nan, don shi kanshi kuɗin yake buƙata su gama shirya shagon sai ya fara shirin da yake son yi don tabbas wannan ƙudirin nashi yana fatan aiwatar dashi. **** A hankali Zee take bin gidan da kallo don dai kam ko a cikin gari ba za’a kira gidan da sunan gidan talaka ba don gida ne na masu rufin asiri, nan da nan kuma sai taji jikinta ya kara wani irin sanyi, lallai basu yiwa kansu adalci ba ace mahaifiyarsu bama su san wanda take aure ba? Basu san ya take rayuwa ba? Balle su san ƙannensu da aka haifa musu? Adam har ya fita ya ciro kayanta a bayan motar bata da alamar fitowa, ganin haka yasa shi yin gaba tare da ƙwanƙwasa ƙofar gidan, daga ciki wani saurayi wanda bai fi shekara 14 ba ya fito ya buɗe ganin Adamu yasa shi sakin dariya yace “Ya Adamu kai ne?” Murmushi yayi yace “Nine, Ummy ta dawo? Don tayi baƙuwa.” Kallon motar yayi sannan ya kalleshi yace “Ta dawo tana ciki," tare suka shiga da Adamu, Zainab da ƙyar ta fito ta bisu a baya, ba dai yaron Ummy bane wannan? Waigowa yayi ya kalleta yace “Aunty ina wuni?” Bakinta cikin ɗan sarkewar murya tace “Lafiya ƙalau.” Tsayawa suka yi a waje ganin yaron yayi ciki, Adamu yace “Muje mana.” Ta girgiza kai tana cewa “Ka shiga zan shigo.” Bai musa ba yayi ciki don yasan dole haɗuwar zata zo musu daban, gefe taja tana sauke ajiyar zuciya tare da fitar da iskar dake bakinta. Wayarta taji tana ƙara da sauri ta cirota tana fatan Allah yasa Baqeer ne, ai tana ganin shine ta ɗauka da sauri cike da shagwaba tace “Allah nayi fushi yau kuka zan tayi maka.” Har cikin jikinshi sai da yaji shagwaɓar nan ya murmusa yana tuno kalaman Junaid yana cewa “Hmmm wata dai tana son yin kukan nan.” Baki ta turo tace “Ya Baqeer ina gidan Ummy na kasa shiga.” “Why?” Ta sauke wata ajiyar zuciya kafin tace “Wallahi ban sani ba kawai sai nake jin kamar ban shirya ba, me kake gani ya kamata nace mata in mun hadu? Ina wuni? Nice ƴarki ko……..” maganar tace ta katse jin kamar motsin mutum hakan yasa ta waigo, nan da nan taji zuciyarta ta karye da fuskar da baza ta iya kwatanta kamaninta ba, don Daddy ko hotunanta bai bar musu ba suma da yake basu damu da ita ba basu taɓa tambayarta ba, matar da ke tsaye jikin ƙofar falonta bata wuce shekara hamsin ba, tana da kyaun jiki amma kana ganinta kasan mahaifiyar Zainab ce don kamannin dake tsakaninsu ma ba’a magana, idanuwanta Zee ta kalla wanda take ganin tsantsar bege a ciki, Zeey wasu zafafan hawaye ne suka gangaro ta sulalo da hannunta ƙasa ba tare da ta katse wayar ba, kallon juna suke yi kafin Ummy ta haɗiye wani abu mai ciwo tace “Me kike yi a waje? Ki shigo mana.” Kasa jure yanayin da take ciki tayi ta ƙarasa wurinta da sauri kawai ta rungumeta, don tasan babu wata magana da zata iya yi yanzu kam bayan ganin Ummy da idonta, hawaye ne suka zubo kuncin Ummy ta ɗan runtse ido. Yarinyar data rugu da gudu ta rungume Ummy Zee ta kalla, ta ɗauka tafi kama da Ummy don Kabir da Daddy yake kama itace kamarta daban amma ganin yarinyar yasa tasan ta fita don komai nasu iri daya ne da Ummin. A hankali yarinyar tace “Aunty ina wuni? Meya samu Ummyna?” Kallonta Zee tayi yarinyar bata fi shekara bakwai ba, wannan wani irin son kai suka aikata? Taya suka aikata hakan? Gaskiya daga ita har Kabir har Daddy basu yiwa kansu adalci ba. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN BIYAR* {75} Ummy ce ta janye jikinta daga jikin Zee tana sake maida wani abu daya tsaya mata a maƙoshi, har ga Allah ta daɗe tana jiran wannan ranar sai dai yaran sun ƙi suyi hankali bare su waiwayeta, tayi kewarsu tayi tayi har ta haƙura, yarinyar ta kalla tace “Inaya me ake yi in aka ga baƙi?” Da sauri ta durƙusa ta gaida Zainab, rarrafowa inda take Zeey tayi tasa hannu ta rungumeta kawai tana hawaye, tari tayi tana cewa “Aunty ba nice Ummyn ba gata can.” Zeey ta ɗago ta shafi gefen fuskarta tace “Sunan wannan cutie ɗin Inaya?” Kai ta ɗaga alamar eh sannan tace “Na gaskiya fa?” Ga mamakin Zeey sai ji tayi tace “Little Zainab!” Kasa fahimtar me take nufi tayi da sauri ta kalli Ummy wacce ta kauda kai sannan ta maida kallonta kan yarinyar tace “Sunanki little Zainab? Zainab sunanki kenan?” Kai ta jinjina tace “Eh!” Duk yanda Zeey ke neman dakewa ji tayi ta kasa kawai ji tayi hawaye nayi mata gudu a fuska, sunanta Zainab dama tasan sunan mahaifiyar Ummy ne data daɗe da rasuwa aka saka mata shi kuma Kabir sunan mahaifin Daddy, da yake akwai ƙannen Daddy da suka saka sunan mahaifiyarsu yasa shi bai saka ba, lallai sun yi rashin hankali ita da Kabir don gani ɗaya data yiwa mahaifiyarsu tasan lallai tayi kewarsu, babu shakka basu yi mata adalci ba sannan basu kyauta mata ba. Ummy tana kula da yanayin Zeey sai dai zafin da take ji yafi na Zainab ɗin, dakewa tayi tace “Ku shiga ciki kin sa yarinya a gaba kina kuka.” Share hawayenta tayi suka shiga ciki, kallon cikin falon tayi wanda yake a gyare tas, ga hoton Ummy nan da saurayin nan na ɗazu da Inaya sai kuma mijin Ummyn, kallonshi tayi daga ganinshi yana da fara’a don a hoton ma yafi Ummyn sakin fuska. Zama tayi akan kujera, Adamu ya miƙe yace “Ni zan wuce, in kin shirya zan zo na kaiki ragowar gidajen yan uwa.” Kai ta ɗaga a hankali tace “Nagode.” Fita yayi, saurayin nan na dazu yace “Kece Aunty Zainab ta Kano?” Kallon mamaki tayi mishi, Inaya ma ta kalleta, yayi murmushi yace “Naga kamar ku ɗaya da Ummy shine na tambayi Adamu yake faɗa mini.” Kai ta jinjina tace “Kai fa? Ya sunanka.” Inaya da sauri tace “Ya Mubashir.” Zeey ta shafi saman kanta tace “School fa? Ka gama?” Ya ɗaga kai yana cewa “Na daiyi diploma yanzu zan tafi Uni,  BUK na samu admission.” Cike da jin daɗi tace “Sai kazo gida ka zauna kaga in zaka je sai na dinga saukeka ko nasa a kai ka, in kuma ka iya mota sai na baka tawa….” “A hostel zai zauna,” Ummy dake shigowa ta katseta, shiru tayi don bata ga alamar wargin da zata musa ba, kallonta Ummy tayi tace “Muje ɗaki.” Ba musu Zeey ta miƙe suka yi ɗakin Ummyn, bayan sun shiga ta maida ƙofar ta rufe sannan ta samu kujera ta zauna, shiru Ummy tayi kafin ta samu bakin gado ita ma ta zauna, Zeey kanta na ƙasa tana ɗan murza tafukan hannayenta, shiru suka yi don da alama babu wanda ya shirya fara magana, can Zeey ta daure ta ɗago tace “Ummy mun sameku lafiya?” Yawun bakinta ta haɗiya kafin tace “Lafiyan mu kalau, Allah ya bamu ikon kaiwa wannan lokacin.” Haka kawai Zeey taji kamar magana cikin magana Ummy tayi mata, miƙewa tayi tazo daidai kafafuwan Ummy ta zauna ta riƙe saman ƙafarta tare da kwantar da kanta daga gefe tace “Ummy mun yi laifi ki yafe mana.” Ido Ummy ta runtse tace “Kina mace? In har ba’a barki kinzo ba ko waya baza ki iya yi mana ba? Mahaifiya dama ba a bakin komai take ba?” Kai ta girgiza tace “A’a Ummy kiyi hakuri wallahi zuciyarmu ce ke bamu tunda kika tafi kika barmu baki damu damu bane sannan alama ce ta kema ba kya son mu nemeki.” “Bana son ku neme ni? Sannan tafiyar tawa ɗin yin kaina ne ko kuwa ba saki na aka yi ba? Kayan sallar da nake aika muku duk sallah kaɗai bai isa yasa kusan na damu daku ba? Ko kina tunanin har numberki data Kabir ban samu na kiraku bane?” Zeey kallon Ummy tayi jikinta ya shiga wani yanayi mai wuyar fassarawa, tana jin kamar an ɗauke ta an jefata cikin ruwa, ganin yanayinta kaɗai yasa Ummy tasan lallai ba’a taɓa ma basu kayan sallar ba kenan, dakewa tayi tace “Shi yayan naki yafi ƙarfin yazo ya gaida wacce ta kawoshi duniya kenan ko?” Bakinta taji ya fara rawa tace “Bai san na taho bane nan gaba in zan zo zamu zo tare.” “Hmm! Ki tashi kije kiyi sallah kici abinci mayi magana daga baya.” Kai ta ɗaga sannan ta tashi jikinta duk yayi wani mugun sanyi, daga ɗaki Ummy ta ƙwalawa Inaya kira sai gata da gudu tace “Rakata ɗaki sai kizo kiyi abinda na saki, sannan ki shirya ki tafi islamiya.” Hannun Zee ta kama suka bar ɗakin, tana fita Ummy ta share ƙwallar data cika taf cikin idanunta sannan ta sauke ajiyar zuciya, Alhaji Sulaiman bai kyauta mata ba bai kuma yi mata adalci ba, ita mace ce mara son magana da hayaniya shi yasa ta dinga kauda kai sannan ƴan uwanta kullum ganin suna baƙin ciki da mitar abun yasa ta ƙara yin shiru, tana sawa a ranta in dai Kabir da Zainab suka  girma tasan zasu nemeta bata san har zasu kai girma haka basu nemeta ba. Suna shiga ɗakin Zeey ta kwanta a kan gadon ɗakin ta kalli Inaya tace “Dakinki ne?” Tace “Eh amma bana kwana a ciki nafi kwana a wurin Ummy saboda Abbah ma baya nan a Abuja yake aiki.” Kai ta jinjina tace “Ummy ma ance tana aiki ko?” Inaya tace “Eh vice principal ce a school ɗin mu.” Cike da jin daɗi tace “Inyee wata taji daɗi, Inaya in aikeki ki siyo min paracetamol? Kaina ciwo yake yi.” “Ummy tace na share falo na shirya na tafi islamiya.” Kallon agoggo tayi tace “Uku kuke zuwa?” Kai ta ɗaga alamar eh, Zee tayi dariya tace “Jeki ki siyo mini zan yi miki sharar kinga kina dawowa sai dai kisa kaya.” Inaya tayi dariya tace “To shikenan, Ummy baza tayi mini faɗa ba?” “Ai yanzu zaki dawo bazata miki ba.” Ta ciro gudar dubu ɗaya ta bata tace “Ki siyo alawa daga nan.” Inaya hankali kwance ta fita, Zeey tayi miƙa ta fito, falon babu kowa hakan yasa ta kalli ƙasa, da alama abinci taci don ga shinkafa nan ta zubar, leƙe-leƙe tayi har taga kitchen ta shiga ta ɗauki tsintsiya tana mamakin yadda aka yi basu da mai aiki, falo ta dawo tayi ajiyar zuciya tana tunanin ma ta yadda zata yi sharar don ita kam bazata iya tuna ma sanda ta riƙe tsintsiya da hannunta ba bare tayi shara, ko a ƙasar waje da vaccum cleaner suke amfani. Falo ta dawo kawai ta fara sa tsintsiya maimakon ta tattare inda aka ci shinkafar ai sai ta baza wurin ma shinkafar tayi ɗaiɗai, tana sharowa suna sake yin wani wurin, tsaki tayi tace “Ai ma na gama.” Ta maida tsintsiyar har zata yi ɗaki taji Ummy na kiran Inaya, daga falon tace “Ummy na aiketa.” Ba tare da ta amsa ba ta fito, a bakin ƙofar ɗakin ta tsaya tace “Kin aiketa kamar ya?” Ummy fuskarta kam babu fara’a, Zeey jita yi shakkar Ummy ta kamata a shagwaɓe tace “Abu na aiketa ta siyo min.” “Ta fita bata sanar min ba?” Shiru Zeey tayi, kallon falon tayi wanda duk ya sake rikicewa bayan sanda ta shiga ɗakin kawai inda aka ci abinci ne yayi datti tace “Aikin dana sata bata yi ba shima?” Cike da zakwaɗi tace “Na riga nayi ai.” Kallon falon ta kuma yi tace “Me kika yi?” Da mamaki tace “Shara.” Ummy kallon falon tayi sai dai bata son nuna mamakinta da abinda idanunta suke gani ko dai gajiyace tasa ta kasa? Wannan amsar yasa ta tabbatarwa kanta shine dalili, Inaya ce ta shigo da gudu tana ganin Ummy tayi turus, Ummy ta tamke fuska tace “Wuce kiyi shara kisa kaya.” Zeey kamar ta sake cewa tayi sai kuma tayi shiru tana kallon Inayan, har ta ɗauko tsintsiya a gaban Zee ta share tas sai ga shinkafa ta haɗu, mamaki ne ya rufe Zee tayi sum-sum ta shige ɗaki, baki ta taɓe tace “Ba komai ai ni ba dole sai na koya ba, ko aure nayi da mai aikina zani.” ***** Yaye bargon da ya lulluɓa dashi tayi sai hura hanci take kai kace iskar gari take san shaƙewa, ta sa hannu a kwankwaso tana girgiza ƙugu tana cewa “Na rantse da Allah Malam baka isa ba ka tashi mu wuce ka sayi ticket mu tafi banga uban daya isa fa ya sani zama a ƙasar nan ba.” Kallonta yayi cike da mamakin yanda ta rainashi yace “Wai ba na sanar dake nima koro ni aka yi ba? To in ma tafi dake muje ina?” “Oho sai ka nemo inda zamu.” Miƙewa yayi yana ƙoƙarin fitowa daga ɗakin, caraf ta kamo bayan rigarshi yana ja tana ja yana ja tana ja, da ƙarfi ya fincike ai kuwa ya ƙarasa ɗaya ɗakin gudu-gudu sauri sauri yana shiga ya kulle yana haki wannan wani irin bala’i ne? To wallahi dole ya tsawatar mata ya nuna mata shi ba sa’an wasanta bane, kallon ɗakin yayi shima tayi kaca-kaca dashi, takaici da dana sani sun gama isarshi ace kai da gidanka baka da kwanciyar hankali, to shi yanzu kuɗin hayar gidan ma in ya ƙare bai san ya zai yi ba bare. ***** Mummy tun safe har dare ta kasa cin komai, gashi sai kiran Daddy take yaƙi ɗauka, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba jin Zainab na Dambatta. Ita kam bata san ya zata yi ba, wayar Inna ta kira don sam ta kasa samun nutsuwa. Inna ce ta ɗauka bayan sun gaisa tace “Inna na rasa ya zan yi Senate fa yaƙi dawowa gida.” Inna ta sauke ajiyar zuciya tace “Halima ina tunaninki yake? Kin manta komai na rayuwarmu kece kike tsara mana yanda zamu tafiyar dashi? Ya kike neman maida kanki mara wayau? In ya tafi ki bishi inda yake mana.” Ido Mummy ta runtse kafin tace “Zainab ma taje Dambatta, ina tsoron kada su faɗa mata wani abu in ta dawo ta sanar da babanta.” Yanzu kam hankalin Inna ya tashi tace “To kiyi maza ki yiwa tufkar hanci amma ke garin yaya kika barta ta tafi?” Shafar fuskarta tayi tace “Ban sani ba wallahi kin san fushi take dani, Inna kinga abinda kuka ja min ko? Shi yasa nake ce miki ki bar yarinyar nan a wurinki yanzu ga abinda ya faru.” Inna jiki a sanyaye tace “Kiyi hakuri Halima wallahi ni haushi nake ji ne in naga yaran can kun sadaukar da komai saboda su amma sam baki damu da Nabila ba.” Ƙasan leɓenta ta ciza tace “Kema Inna duk gatan da Nabila ta samu dole sai ta samu sama da hakan? Yanzu wa gari ya waya?” Shiru Inna tayi don bata san me zata ce ba, kashe wayar Mummy tayi cike da takaici don a ganinta duk da sun zauna gidansu sirrin nan ba zai taɓa fitowa ba har abada. Miƙewa tayi ta shirya sannan ta kira drivern Daddy ta tabbatar inda yake kafin ta fito, kai tsaye driver ɗinta gidan Daddy inda suka taso ya kaita, har ta shiga falo baya nan sannan ta wuce ɗaki, yana kishingide a kan gado yana waya, yana ganinta ya kauda kai ya cigaba da wayarshi wanda tana ji ma tasan da Deputy Governor ne daga yanda yake yi mishi magana, zama tayi a gefenshi tana ɗan matsa mishi kafa, bai ko kalleta ba ya cigaba da wayarshi sai da suka gama sannan ya kashe, kusa dashi ta dawo ta jawo hannunshi tana matsawa tace “Senate please!” Wani irin kallo yayi mata yace “Ni Halima? Ni zaki munafurta? Shekara ba ɗaya ba ba kuma biyu ba ashe ke a soko kike zaune dani, wallahi ke kin san da badon ban san career ta siyata ta sake gurguɗewa ba da kin tafi gidan ku, amma nayi saki ɗaya bana son sake wani.” Yatsa tasa da sauri ta rufe mishi leɓenshi, hawaye ne suka ciko mata tace “Senate kana tunanin a son raina na ɓoye maka? Wallahi a’a babu yanda zanyi ne, na daɗe ina son sanar da kai amma ban san ta ya zan fara ba, am so young sanda abin ya faru sannan ƙaddara ce ta afka min wanda har yanzu zuciyata ma tariyo mini abinda ya faru, in baka manta ba sanda Aunty ta fara barina ina shigowa gidan ku ba tausayi na bane ya kamata? Har nake zuwa ina tayata yan aikace aikace, ka tuna da kyau Senate a wani hali nake a lokacin?” Kallonta yayi don bazai iya tunawa ba amma yasan tabbas mahaifiyar Zainab ce ta jawota jikinta har wani sa’in take kwana a gidan saboda gidan da suke zaune ɗaki ɗaya ne shi yasa a lokacin da yace zai aureta aka dinga ganin wai cin amana zai yi wanda shi kuwa yasan so ne sannan da kyawawan halayenta da kuma guarantee da yake dashi na wanda zai kular mishi da family ɗin shi ya kuma ƙarfafa mishi gwiwa, abu mafi mahimmanci kalmar da ya fara girmama ta tsakaninsu sanda tace mai tana ji a jikinta zai zama governor nan gaba. (Hmmm mudai kam bamu da bakin magana🥴) *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA BAKWAI* {77} Zee tana shiga ɗaki akan gado ta faɗa ta kwanta, me yasa Ummi ke yi mata faɗa akan abinda tasan ba laifi bane, in ma ba haka ake yanka dankalin ba a matsayinta na uwa ai haƙuri zata yi tayi amfani da wanda ta ɓare amma sai ta hauta da faɗa? Mummy ce ta faɗo mata a rai don tasan tabbas da ita ce sai dai ma tace "Auta sannu, da fatan hannunki bai yi ciwo ba?" Kallon yatsunta tayi wanda har peeler ɗin ta ɗan karceta kaɗan amma gashi ita Ummi sam bata damu da tasan ma a wani hali ta fere dankalin ba, daga nan ɗaki take jiyo muryar Ummi da alama ita da Inaya ne don tana iya jiyo yanda suke magana cikin farin ciki, fitowa tayi da son sanin meke faruwa, nan ta taradda Inaya ce data dawo daga Tahfiz ta taho da kyauta taci na biyu, nan itama ta fara murna, sallama aka yi da gudu Inaya tayi waje tana kiran sunan Daada, Ummi ta kalli Zainab tace "Baban Inaya ne ki tashi ki sanyo mayafi." Tashi tayi tasa mayafi ta dawo, yana zaune a falo ya sa Inaya akan cinyarshi fuskarshi ɗauke da fara'a yana tsokanar Inaya, ganin Zainab yace "Ah ah ah ai ina ji ance Zainab tazo nace lallai dole na samu dama nazo wannan satin mu gaisa." Kanta ta sunkuyar kasa sannan ta rusuna ta gaisheshi tace "Ayi hakuri bamu zo mun yi gaisuwa da wuri ba." Har yanzu fuskarshi ɗauke da murmushi yace "Ah to kun dai san kun yi laifi, sai dai ita rayuwa wanda ya gane kuskurenshi yafe mishi ake yi." Ummi ce ta kira Inaya wacce ta ruga da gudu zuwa kitchen, ba daɗewa sai gata da tire da ruwa da cup a kai, ta ajiye sannan ta zuba ta miƙawa Daada tana cewa "Daada ka siyo min doll ɗin da kace? Mai gashi?" Gashin kanta ya ɗan ja kadan yace "To gashi ita kuma bata da gashi ina ga naki za'a gutsire a sa mata ko Ummin mu?" Shigowa tayi falon tana cewa "Kun fi kusa dai, baza kuji bakina ba." Bayan ya sha ruwan ya kalli Zee yace "Wai haka Yaya Babba?" Zee kanta tsaye tace "A'a kam bamu yarda ba." Ummy ce ta kalleta fuska a tamke, Zee a ranta tace "Me kuma na sake yi ni sarkin lefi." Kallon Ummi yayi ya ajiye cup ɗin hannunshi yana cewa "Daga ji dai girkin Yaya Babba zamu ci don wannan ƙamshin ma sai naji ya fita daban." Ita dai Zee tayi ƙasa da kai sai take ganin kamar ma magana ake faɗa mata, Inaya ce tayi saurin cewa "Daada, Aunty fa tace mun bata iya girki ba." Wani kallo Ummi tayi mata wato har ma fariya take bata iya girki ba? Daada yayi dariya yace "Wasa take kin taɓa ganin babba kamar ta da bai iya girki ba?" Ita dai Zee sum-sum tayi ta bar falon don ji tayi bazata iya zaman ba, rai a ɓace ta ɗauki wayarta kawai idanunta ya gane mata kiran Baqeer har sau biyu, da sauri ta kira shi ta kishingida akan gado, har ta katse bai ɗauka ba, tana ƙoƙarin ajiye wayar ya kira, har ta kai hannu zata ɗauka sai ita ma taƙi ɗauka tana kallon kiran ya katse sai ta kira tana murmushi tana hasaso fuskar Baqeer, ga mamakinta ƙin ɗauka yayi har ta katse sannan ya kira. Cike da shagwaɓa ta ɗaga kiran tana ɗan gyara kwanciyarta, yace "Ƴar Ummi ana can ana zuba shagwaɓa ne?" Sakalce mishi tayi tace "Allah ni ina ji gida zan koma gaba ɗaya an takura mun a gidan komai nayi ba daidai ba." Yayi ɗan shiru kafin yace "Hmmm kamar me da me kenan?" Tace "Allah ni kawai komai ma, ciki har da girki." Ajiyar zuciya yayi yace "Ba dai wata a haka take son tayi aure bata iya girki ba? Kice akwai case a gaba." "Case? Kamar na me? Nifa Mummy tace ba sai na koyi komai ba ko aure nayi da mai aiki na zata kai ni Allah ni bana son takurar da ake yi mini a gidan nan." Cike da mamakin jin abinda take cewa yace "Ita Mummy haka aka koya mata? Ko haka aka yi mata?" Tambayar tazo mata a ba zata hakan yasa tace "Name?" Yana riƙe da wayar yace "Na komai, ko ita bata iya komai ba?" Kai ta girgiza kamar tana gabanshi tace "Ta iya amma nice bata so na wahala." Ya jinjina kai yana cewa "In kika auri talaka fa irin su mu?" Yayi maganar cike da bugar ciki, ido ta lumshe tana hango fuskarshi cikin ƙwayar idanunta tace "Da mai aiki na ai." Ya ɗan murmusa yace "To kuma irin mu ina muka ga inda zamu saka mai aiki? Sai dai ke bana ji zaki auri talaka watakila shi yasa ba kya wannan tunanin." Da sauri tace "Allah a'a!" Shafar sumar kanshi ta baya yayi yace "A'a me?" Ta gyara kwanciya tace "Ban ce komai ba." "A dai faranta ran Ummi kinga dai shekaru kuka ɗiba ba kwa tare sannan abinda take nuna miki gata take yi miki don ko ni bazan yarda matata ta zauna bata komai ba," yayi maganar cike da son jin me zata ce, sai dai kawai ji yayi tace "Umm!" Jikinshi ne yayi sanyi da Umm ɗin da tace amma ya daure yace "Yaushe zaki dawo? Dada nata tambayarki da alama missing ɗinki take yi." "Ita kaɗai?" Tayi tambayar itama tana son jin me zai ce, da yake ya dawo gida yana zane sai ya tura kujerarshi baya yace "Kila?" Zee tace "Kila kenan babu tabbas?" Kallon sketch na material ɗinta da yake yi yayi yace "Ko a tambayar miki?" Tace "In dai sai an tambaya na yafe kaga kenan ba ayi." "A'a ai sai anji ta baki ake fahimta," yayi maganar cike da zolaya, Zee ta ɗan motsa baki kafin tace "A'a wannan daga zuciya ya kamata ya fito." Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta cilla ta gefe tare da binta da harara tace "Allah sai na fanshe, ni kam anya Ya Baqeer na so na?" Ta tambayi kanta idanuwanta na kan wayar kamar wayar take tambaya, sai dai kalaman Baqeer na sake dawo mata, to ita ya zata yi? Gaskiya ko zata koya gwara ta koya a gidan su ba dai nan ba bata son abinda zata yi ace ba tayi daidai ba. ****** Inna ce ta shigo ɗakin rai a ɓace ta yaye bargon da take lulluɓe dashi cikin takaici tace "Baza ki fito kici abinci ba?" Maida bargon tayi saman kanta tace "Bana ci." Takaici ne ya sake rufe Inna tace "Wai na ɗauka zaki amshi laifinki ki nemi yafiya ashe shirme zaki aikata?" Kamar dama jira take ta tashi ta zauna a bakin gadon tana magana mai kamar ta kuka tana cewa "Inna wai menene laifina? Akwai aure tsakanin mu da Kabir sannan babu wani abu daya haramta, abu na biyu magana ta bayyana kowa ya sani to a barni na aureshi mana." "Anƙi a barki ki aureshin, nace anƙi a barki, ja'irar yarinya, yanzu duk kyawawan halin ki dama akwai wani halayenki da kike ɓoyewa wai har kece zaki yiwa kanki sharrin ciki? Cikin ma na shege? Ke kinsan me cikin shege yake nufi?" Nabila kamta ta sunkuyar tace "Nifa saboda a haƙura a bar mu muyi aure na........" Inna ce ta katseta da cewa "Kina ƙarasa maganar nan zan tsinkeki da mari, aure a gidan uban wa? To ki sani Halima tace shi ko a jikinshi sannan wacce ake so ya aura ma yaje ya ganta, sai naga abinda zaki yi, sokuwa wato ke ko tausayin mahaifiyarki ba kya yi." Inna tana kaiwa nan tayi hanyar waje, Nabila jan bargo ta sake yi zuciyarta na tafasa, in dai haka ne to lallai ba wanda zai zauna lafiya in har ita ba'a barta ta zauna lafiya ba, haushin kanta ne ya kamata tunowa da tayi bata san saurayin da Zee take so ba tabbas da ta kira Daddy ta sanar mishi don ta tabbatar bai san da wanda take so ba. ***** Ɗaki Mummy ta shiga ta ɗan fara kaiwa da komowa, hankalinta sam baya jikinta don ta kasa nutsuwa gashi dai Senate ya dawo gida amma fa yanda suke yi kamar da ya daina, hira wannan ba sosai yake yi da ita ba, to yanzu matsalarta yanda zata jawo Zainab daga Ɗambatta wanda ta rasa ta wani hali zata aikata hakan, baya tayi saboda jirin da taji ya ɗebeta, a hankali ta janyo wayarta tana sauke numfashi ta kira Zee, sai dai har tayi ringing ta gaji bata ɗauka ba, kiran Kabir tayi akan yazo. Ba daɗewa sai gashi don dama yana gida, duk da shima bai gama sakewa da abinda ya faru ba amma shi yayi mata uzuri ya tabbatar fyaɗe aka yiwa Mummy kuma ba da saninta ta aikata hakan ba yana ma gani Inna ce hala ta tursasata. Yana shiga ya ganta a kwance a ƙasa hankali a tashe yace "Menene Mummy?" Kai ta girgiza tana lumshe ido tace "Kabir ƙirjina keyi mini wani irin nauyi nama kira Zainab bata ɗauka ba." Hankalinshi a tashe yace "Bari na kira Dr, ta girgiza kai tace "Kar ka damu kawai dai gani nake in na ganku zan samu nutsuwa ne, In Sha Allahu ba komai. Ran Kabir a ɓace ya kira Zainab, sai dai lokacin ita bata ma ɗaki tana falo a zaune, cike da tausayin halin da Mummy ke ciki yake yi mata sannu. ******* Zee dake zaune a falo ce ta miƙe ta nufi kitchen inda su Ummi suke don dama abinda ya fito da ita kenan daga ɗaki, tana son bin shawarar Baqeer hannayenta na baya yana ɗan motsi dasu tace “Ummy dame zan taya ku?” Kallonta Ummy tayi kafin ta ɗan sauke ajiyar zuciya tace “Me zaki iya daga abubuwan da muke yi?” Kallonsu tayi Ummy na yanka kayan miya, Inaya na tsinke zogale, cike da son jin bakinta Ummi tace “Ko zaki tayamu da wanke-wanke?” Ido ta zaro da sauri tace “A’a gwara abinda Inaya ke yi bansan taɓa kayan da aka ci abinci.” Mamaki me ya kama Ummi kawai ta girgiza kai don bata san ma me zata ce mata ba, zama tayi babu kunya suka tsinke zogale sai wani daɗi take ji tana so taji Ummi ta yabeta, ita kam Ummi kasa tanka mata tayi don bata san me ma zata ce ba saboda takaici. Inaya ce ta shiga banɗaki tana fitowa taji wayar Zee na ƙara hakan yasa ta fito mata dashi ta bata, kallon wayar tayi ganin Kabir yasa ta ɗauka da sauri don ta haɗa su da Ummi su gaisa, shi kam tana ɗauka yace “Wato kinci moriyar ganga ko? A wani dalilin Mummy zata yi ta nemanki ki dinga ƙin dauka? Naji tayi miki laifi amma ai sai ki yi mata uzuri kiji dalilinta ko? Ko ba haka ake so ƴaƴa su yiwa iyayensu uzuri ba?” Zee ta kalli Ummy da ita ma kallonta take yi sannan tayi ciki da sauri, ba tare da ta rufe kofa ba ta shiga ɗaki tace “Ya Kabir me kake yi hakan? Sannan ai kaima kasan abinda tayi mana bata kyauta ba ko?” Tsaki yayi yace “In ta mutu kya yafe mata tunda wacce kika tafi wurinta itace ta raineki har kika kai girman haka, wannan halayen naku na mata shi yasa mata suke tsoron riƙe yaro da zuciya ɗaya.” Hankalinta ne ya ɗan tashi tace “Bata da lafiya ne?” Cike da takaici yana haɗe fuska yace “Eh gata nan ana ƙoƙarin sa mata drip kada Allah yasa kizo kiga jikinta,” yana kaiwa nan ya kashe wayar, Zee tace “Yaya! Yaya! Yaya!” Sai dai ya riga ya kashe, fuskarta tasa da hannaye biyu ta shafa, kallon bakin ƙofa tayi inda Ummi ke tsaye da alama biyota tayi da son jin meke faruwa, idanunsu ne ya haɗu da juna, Ummi tayi murmushin yaƙe tace “Kije kafin wani abun ya faru, na ɗauka ta daina wannan ƙananan shirmen ashe har yanzu bata san ta girma ba.” Kalaman da taji Ummi ta furta kenan wanda yasa ta kallonta fuskarta cike da mamaki, ganin Ummi zata juya yasa ta saurin cewa “Me kike nufi da kalamanki Ummi? Kina nufin ƙarya Mummy take yi kenan ko me?” Waigowa tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace “Ki koma ki tambayeta, sannan ki haɗa da tambayar da nima nake son sanin amsarsu, me ƴan uwana take cewa sun yi kamar yanda kika ce shine dalilin hanasu zuwa da Babanku yayi? Dan a iya sanina babu wanda ya taɓa zuwa don neman taimako gidanku duk zuwan da wani zai yi to fa lallai babban dalili ne ya kai shi saboda dukansu sun san waye Sulaiman, kayan da nake ɗinka muku shekaru kusan ashirin suna ina? Sannan number wayar data aiko min da sunan wayoyin ku nasu waye? Ahh abu na ƙarshe me da me muka yi da har Sulaiman ya aiko har Ɗambatta akan kar ya ƙara ganin wani daga cikin mu a gidanshi, in har ta sanar dake duka ina so ki sanar dani don mu san dalili,” Ummi tana kaiwa nan tayi gaba zuciyarta na wani irin zafi don lallai abubuwan nan sun fara isarta shekaru nawa rabon data sa su a ido ace sati guda baza ta iya ƙyale mata ƴarta tayi mata ba? Zee kuwa ji tayi kamar an daskarar da ita kalaman Hajiya Goggo ke sake dawo mata, gabanta ne ya shiga faɗuwa ba dai yanzun ma ƙarya Mummy ta dinga yi musu ba duk yawan shekarun nan? Ji tayi kanta yayi mata wani nauyi nan da nan tasa hannu ta riƙe kanta tana sauke ajiyar zuciya. ****** Kamalu ne ya kalli yaron da yake bawa ajiyar kaya yace “Yauwa fito min da kayan nan inga ko sun haɗu.” Nan yaron ya fito mishi da tulin atamfofin daya sace a shagon Badaru, dariya yasa sai kuma ya tamke fuska kamar wani mai aljanu yace “Matsalar babu lace bare shadda. Maida kayan yayi ya fito yana tunanin zuwa kasuwa ya ɗan yi samfe, sam bai kula da Salim dake tahowa ba da alama shago yaje, sai da Salim yazo daf dashi ya ganshi, kauda kai yayi yana neman wucewa sai ji yayi yace “Kai soko baka ganni bane?” Salim ya kalleshi ya girgiza kai cike da takaici yana cigaba da tafiyarshi, dariya Kamalu yasa yace “Saurayi soko da alama an kasaka ne shi yasa tafiyar ma kake yinta ba cikin hayyacinka ba, to ya zaka yi? Manya sun ƙwace maka wacce kake so.” Duk yanda Salim yaso ya kauda kai sai da yaji dariya ta kwace mishi yace “Ah kace kai da Roshni abu ya kankama?” “Sosai, ba dai baƙin ciki kake yi ba?” Ya dan girgiza kai yace “Ni? Ai ban isa ba, na bar muku ai ku manya, yaushe ne bikin?” Kamalu ya maka mishi harara yace “Malam ba zuwa zaka yi ba, don mu ba kowane soko muke gayyata ba, kaje can in abokinka zai yi aure kaje.” Dariyarshi ya sake guntsewa yace “Tab gaskiya kam ai da alama abokina yafi guarantee gwara na tsaya a ɓangaren shi,” ya ƙarasa maganar yana tafiya, shi dai Kamalu ya bishi da harara yace “Wawa kawai.” **** *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA TAKWAS* {78} Tunda taji wannan maganar a bakin Ummi kanta ya ɗaure ta shiga tunani, kada dai ace duk tsawon shekarun nan Mummy ƙarya take yi musu take nuna dangin mahaifiyarsu na yin tattaki takanas suna zuwa har gidansu kawai don suci mutuncinta duk don tana riƙon su. Tukuna ma tsaya, wacce magana taji Ummi nayi akan duk shekara sai ta aika musu da kayan sallah abinda ita ko Kabir wani bai taɓa sani ba, tasan farkon zuwanta tayi magana makamancin haka amma bata gama fahimtar me take nufi ba, ya Mummy take yi da kayan da take aika musu ko kuwa dai ɗan aiken ne baya kaiwa sai ya dawo yace mata ya kai? Tana ganin hakan nema don babu ta yadda za'a yi Mummy ta ɓoye musu abu irin wannan, wani ɓari na zuciyarta taji yace Mummyn kuwa? Har kin manta da ɓoye muku da tayi akan Nabila ƴarta ce in banda Allah ya nufa sai kun ji Inna tayi suɓul da baka ta fallasa sirrin da suke ta ɓoyo kina tunanin da zaku sani ne? Girgiza kanta tayi tana kasa gasgata wai Mummy ce tayi musu duk waɗannan abubuwan tasa suka ƙullaci mahaifiyarsu da gangan alhakin tasan duk abubuwan da take zaunar dasu tana faɗa musu ƴan uwan Ummin sun yi mata duk ƙarya ne. Kai Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ita kuwa Mummy me yasa zata yi musu haka? Me zai sa ta hana ƴan uwan mahaifiyarsu kusantar inda suke? Laifin me suka yi mata da zata yi musu irin wannan cutarwa? Eh cutarwa mana tunda tasan duk abinda take faɗa musu ba gaskiya bane sai ma ƙara nesanta su da mahaifiyarsu da yake yi. Kawai sai taji hawaye yana zuba daga idanunta, tausayin Ummi ne taji ya kamata yadda suka rayu suna jin haushinta ashe babu laifinta ko ɗaya a cikin watsar dasu da suke zargin tayi. Tana zaune a wurin tana saƙa da warwara taji wayarta tayi ƙara, da kamar ba zata ɗauka ba sai kuma tayi tunanin ko Baqeer ne ya ƙirata duk da basu wani daɗe da gama waya ba abinda yasa ta janyo wayar don ta amsa kenan sai taga ashe Daddy ne yake ƙiran ta. Sai da gabanta ya faɗi cikin ranta tace Allah dai yasa ba wani abu ne ya samu Mummy ba. A sanyaye ta amsa wayar don bata cikin yanayi na jin daɗi, bayan sun gama gaisawa da Daddy yace mata ta shirya ta dawo gida gobe hutun ya isa haka nan. Murya na rawa tace "Amma Daddy..." Katseta yayi yace "Kiyi abinda nace Zainab, lallai gobe na dawo gida na iske ki bana son zamanki a wannan garin ya isa haka nan." A sanyaye tace mishi "to," tun yanzu tana jin kewar Ummi na lulluɓeta, ga kuma Inaya da suka yi wani irin sabo da yarinyar tasan idan ta tafi ba ƙaramin kewarta zata yi ba. Tashi tayi jikinta yayi wani irin sanyi ta nufi ɗakin Ummi, tana tsaye a gaban wardrobe ɗinta tana neman abu Zainab ta shigo ta zauna a bakin gado. Juyowa tayi ta kalleta sai taga tana share hawaye. Cike da kulawa tace "wani abu aka yi miki kike kuka?" Girgiza kanta tayi sai kuma tace "wai Daddy ne yace na koma gida gobe." Murmushin takaici tayi tace "ke kuma shine kike kuka? Gidan naku ne ba kya son ki koma ko ya aka yi?" Gaba ɗaya sai ta fashewa Ummin da kuka don bata gaji da ganinta ba, da ta ɗauka cewa bata da buƙatar Ummin a rayuwarta domin Mummy ta cike mata dukkanin wasu gurbi na uwa don haka nema bata damu da rashin Ummin a rayuwarta ba sai yanzu da ta zauna da ita na wasu ƴan kwanaki tasan ashe lallai babu wani giɓi da wani zai cike maka na mahaifiya kowacce irin kulawa yake yi maka kuwa, ashe ita uwa matsayinta daban ne, ganinta gata ga Ummin kaɗai wata irin nutsuwa da farin ciki yake sakata wacce duk tsawon rayuwarta bata taɓa tsintar kanta a ciki ba. Zama Ummi tayi a kusa da ita ta kamo hannayenta ta riƙe cike da tausasawa irin ta uwa tace "ai bamu rabu ba kenan Zainab, tunda kika zo kika ga wuri nasan idan kin tafi ma zaki sake dawowa. Kada ki saɓa umurnin mahaifinki ki shirya ki koma kamar yadda yace ga waya nan ai zamu dinga gaisawa kin ji?" Ɗaga kai tayi alamun amsawa sai dai har wannan lokacin bata daina kukan ba. Haka Ummi tayi ta lallashinta tana bata baki har ta samu ta sassauta kukan da take yi. "Tashi kije ki wanke fuskarki kada Inaya ta shigo ta tarar dake kina kuka," ɗan murmushi tayi sai ta tashi ta koma ɗakin Inaya inda aka sauketa tunda tazo anan suke kwana ita da Inaya. Da dare suna zaune a ɗakin Ummi tana haɗa mata kayanta tana yi tana mata ƴar nasiha ita dai Zainab tana saurarenta sai dai bata jin daɗin tafiyar da zata yi ta bar Ummin, bata gaji da zama da mahaifiyarta ba duk da ba wani sakewa take samu daga Ummin ba komai tayi sai tayi ta mata faɗa tace bata iya ba hakan bai sa taji zata gujewa zama da Ummin ba. Inaya na maƙale da ita tunda Zainab ɗin ta faɗa mata gobe baza ta dawo daga school ta isketa ba. "Aunty Zeey idan kin tafi yaushe zaki dawo?" Ta tambayeta. Ɗan shiru tayi tana kallon Inaya da duk tayi wani iri kamar tasa kuka, kawar da kanta tayi daga kallon Inayan tace "In Sha Allah bazan daɗe ba zan dawo kin ji," ɗaga mata kai tayi alamun amsawa. Ummi na kallon duk abinda suke yi ita kanta bata jin son tafiyar da Zainab ɗin zata yi saboda tana son zama da ƴarta ta koya mata hidimar kula da gida da ba'a koyar da ita ba to amma ya zata yi tunda ubanta yace lallai ne ta koma. ***** Maryam yau ta samu kanta cikin tsantsar farin ciki sakamakon ƙiran ta a waya da Baban Aareef yayi yace mata yana tafe da kyakkyawan albishir wanda ta daɗe tana jiran samuwarshi ta tanadar mishi tukuicin da zata bashi. Duk da ta kasa iya tuna menene wannan abu da ta daɗe tana fatan samuwarshi amma ta samu kanta cikin ɗoki da son sanin abinda ta samu da yasa maigidanta kasa jira ya dawo kafin ya faɗa mata, tasan dai ko menene abun alkhairi ne. Tashi tayi ta ƙara kimtsa gidan ta shiga kitchen ta shirya mishi kyakkyawan abinci, stir fried spaghetti tayi sai chicken salad da sharma milk (kunun shinkafa). Haka ta jere komai akan table sannan ta shiga tayi wanka tayi kwalliya cikin atampa julius holland da aka yi mata ɗinkin straight gown, sosai kwalliyarta tayi kyau kayan suka bi jikinta suka kwanta suka fitar da duk wasu curves na jikinta. Dawowa tayi parlour ta zauna, ƙamshin turaren wutan data saka ya haɗu dana jikinta da sanyin ac ya bada wani sassanyan ƙamshi mai kwantar da zuciya da sanya nutsuwa. Tana zaune taji shigowar motarshi don dama yace mata zai biya ta school ɗin su Aareef ya taho dashi shi yasa yau bata fita zuwa ɗaukarshi ba. Tashi tayi taje ta tsaya daga bakin ƙofa tana jiran shigowarshi. Da fara'arta ta taresu ta karɓi jakar hannunshi. "Sannu da zuwa Daddy," tace tana rausayar da kai gefe. Ɗan rungumota yayi a jikinshi cike da kulawa. Sai da ta cirewa Aareef uniform tayi mishi wanka ta bashi abinci sannan ta koma wajen Babanshi. Taimaka mishi tayi ya cire kayan jikinshi ya shiga wanka bayan ta haɗa mishi ruwan wankan. Fito mishi da kayan da zai saka tayi ta feshe su da turare ta ajiye akan gado sannan ta koma parlourn wajen Aareef don bata cika son barinshi ya zauna shi kaɗai ba sai yaje yayi mata wata ɓarnar bata sani ba. Bayan ya fito daga wankan ya shirya sannan ya fito parlourn, direct wajen dinning table ya nufa itama tashi tayi ta bishi, yana zama ta ɗauki plate tayi serving ɗin shi abinci ta ajiye a gabanshi, kujerar dake gefen damanshi taja ta zauna yana cin abincin shi suna ƴar hira har ya gama cin abincin ya tashi ya koma wajen kujeru ya zauna ita kuma ta tattare wurin ta mayar da kayan kitchen sannan ta dawo ta zauna a kusa dashi suna taya Aareef kallon tashar cartoon, duk ta ƙosa ya faɗa mata albishir ɗin shi kuma sai faman ja mata rai yake yi. Sia da ya gama wanata sannan yace ta ɗauko mishi jakar laptop ɗin shi a ɗaki, tashi tayi taje ta ɗauko ta kawo mishi ta koma wajen zamanta ta zauna. Buɗe jakar yayi ya fito da wata takarda ya miƙa mata, hannu biyu tasa ta karɓa tana karantawa. Ai tun bata gama karanta abinda ke jiki ba tasa ihu tana ɗan tsallen murna daga zaune, shi dai sai dariya yake yi yana jin daɗi cikin ranshi saboda farin ciki da ya yasa ta. Offer ce ta aiki daya daɗe yana nema mata sai yau Allah ya nufa ta samu. Sosai ta nuna farin cikinta da samun wannan aikin itama ta samu ta tallafawa Umma ba komai sai an jira Baqeer yayi ba ga kuma Hadiza a gefe da itama take buƙatar taimakonsu don ma yanzu Allah yasa albarka a cikin markaɗen da take yi bata rasa abinda zasu ci abinci ita da yaranta har ma tayi wasu ƴan buƙatun nata a ciki. Sai murna take yi ta kasa ɓoye farin cikinta, ƙasa yayi da murya don baya son Aareef dake kusa yaji ne zai ce yace mata "sai murna kike yi har yanzu baki bani goron albishir ɗin ba," wata ƴar dariya tayi cike da kissa tace "kai ma kasan goron albishir ɗin ka na nan na tanadar maka sai mun shiga daga ciki," ta amsa mishi tana lumshe ido. Haka suka zauna cikin farin ciki har lokacin sallar magriba yayi ya tashi ya fita masallaci, tashin Aareef tayi suka shiga ciki sai da tasa shi a gaba yayi alwala ya fara sallar sannan ta tafi ɗakinta tayi sallar itama. Tasan Baban Aareef baya dawowa sai yayi sallar isha'i tukunna, turaren quta ta ƙara kunnawa gidan tana jin daɗi cikin ranta don tuni ta cire rai da smaun aikin nan ganin an daɗe ana nema ba'a dace ba ashe rabonta ne a gaba shi yasa tuntuni bata samu ba sai yanzu. Tare suka fito daga masallaci shi da Baffa, suna tafe a hanya suna ƴar hira ta tsakanin ɗa da mahaifi anan ne yake faɗa mishi batun samun aikin da Maryam ɗin tayi. Wani kallo Baffan yayi mishi yace "Kai yanzu daka sama mata aiki ka gama yarda da ita ne?" "Ban gane ba," ya tambayi Baffan nashi da mamaki. "Eh ka gama yarda da ita ka tabbatar baza ta ci amanar ka ba ka amince ta fita aiki inda zata je tana cuɗanya da wasu mazan? Wai me yasa baka yin abu da tunani ne? Baka yi shawara ba babu komai kaje ka nemawa mace aiki matan nan da ba amana ce dasu ba kana zamanka lafiya lau aje a yayibo cuta a saka maka ko a kawo maka ɗan da ba naka ba cikin gida. Ka dai yi tunani wannan maganar aikin a barta gara ta zauna a cikin gida ta cigaba da kular maka da gidanka kai kuma ka fita ka nemo ka kawo mata tunda ai Alhamdulillah komai da take buƙata ka ɗauke mata shi to me take nema da har sai ta fita aiki zata samu." Shiru yayi yana jinjina maganar da Baffan ya faɗa, sai yaga kuma haka ne fa wasu matan basu da kamun kai suna fakewa da fita aiki suna yawon banzar su, duk da yasan Maryam yasan bata daga cikin irin waɗannan matan to amma maganin kada ayi kada a fara gara kawai a haƙura da aikin tunda Allah yasa bata fara ba. Sallama yayi wa Baffa bayan sun shigo harabar gidan ya nufi part ɗin shi shima ya shige nasu. Aareef yayi bacci har ta kai shi ɗaki ta kwantar dashi dama kuma da wuri yake kwanciya saboda school da yake zuwa. Tana parlour a zaune tana kallon wani korean series lokacin daya shigo, zama yayi shima suna cigaba da kallon tare. Kamar daga sama taji muryarshi yana cewa "Hmm ina ganin batun aikin nan a haƙura dashi don mun yi magana da Baffa ya nuna mini illar fitar mace aiki sai kuma naga haka ne don haka ki haƙura kawai tunda ma baki nemi komai kin rasa ba bare ace dole sai kin fita nema." Baki a buɗe take kallonshi tace "Ban gane a haƙura ba, aikin da kia kayi mini alƙawari kuma sai yanzu bayan na gama sa rai tunda ka kawo mini offer zaka ce a barshi?" "Eh haka nace a bar maganar fita aiki babu ita, kawia ki zauna ki cigaba da kula da gida," daga haka ya tashi ya shige ɗaki ya barta tana jin wani irin ƙunci ya mamaye zuciyarta, ita kenan komai zata yi sai da yardar uban miji idan bai amince ba duk yadda ta kai da son abu sai dai ta haƙura? **** *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA SABA'IN DA TARA* {79} Haka Maryam tasha kukanta ta gaji don tasan tunda suka riga suka tsara to fa babu canji babu kuma yanda zata yi, takaicinta ma data juya taga yana bacci kamar ma bai san halin da take ciki ba, haka ta kwanta tana share ƙwalla har bacci ya ɗauketa. Da safe ta fito kitchen don haɗawa Areef abun breakfast, Baffa ta hango a falo yana zaune yana karanta jarida, takaici da tsanar abinda yayi mata ya kasa barin fuskarta, a ɗan dakile ta gaisheshi, bai ko kalleta ba ya amsa yana cewa “Ina dai ba haka kike gaida naki mahaifin ba?” Kallonshi tayi kawai takaici yasa ta wuce kitchen don tasan ko ƙara ta kai laifin ma kanta zai koma, shi yasa abubuwa da yawa da ya shafeshi bata iya sanarwa. **** Da safe Zee ta shirya, Inaya sai binta take yi duk inda tayi, Daada mijin Ummi kanshi bai ji daɗin tafiyar nan ba, da kanshi yaje shago ya siyo shadda da atamfa da turare ya bata wai ita da Kabir, haka tayi godiya tana yi tana kallon Ummi wacce yanayinta kaɗai zai sa kasan tabbas dauriya kawai take yi, Zee ce ta maida ƙwallar dake neman zubo mata tace “Ummy na manta akwai saƙo da zan baki, don Allah muje ɗaki.” Bata tanka mata ba tabi bayanta zuwa ɗakin suna shiga Zee ta rungumeta tana hawaye tace “Ummi zan dawo ki yafe mana don Allah.” Jikin ta ne yayi wani irin mugun sanyi, ta ɗan shafi saman kanta kaɗan dln mace ce mai kawaici bata so Zainab ta gane halin da take ciki, ɗan zareta kaɗan tayi tace “Nasan ba son zama kike yi anan ba tunda ina saka ki aiki, sai dai Zainab ki sani a matsayin ki na mace ba rainon nan ya kamata ace anyi miki ba, duk gatan da kike dashi kina buƙatar kisan yanda zaki kula da kanki da mijinki idan kinyi aure.” Kai ta sunkuyar cikin ɗan sakalci tace “Zan gyara In Sha Allahu.” Kai Ummi ta ɗaga sannan tace “Sannan maganar Kabir,” sai kuma tayi shiru, tausayin Ummi ne ya ƙara kamata, babu shakka ta daɗe tana missing ɗinsu, tun daga jin sunan Inaya take dana sanin abinda suka aikata. Ummi ce ta katseta da yin murmushi kaɗan tace “Ba sai kin yi mishi magana ba, Allah ya bashi mace ta gari.” Kallonta tayi tana son bata labarin Nabila sai dai bata son ɗaga mata hankali, kai kawai ta jinjina tace “In Sha Allahu zai zo ma, amma Ummy me yasa…..”sai ga Inaya ta shigo hakan yasa ta kasa tambayar abinda ke bakinta, haka ta kamo Inaya suka fito har mota suka rakata taba Mubashir number ɗinta sannan ta bashi ragowar kuɗin hannunta, Ummi tasa hannu ta amsa ta cirar mai 3k ta bashi ta maida mata ragowar tana cewa “Banda sakalci ya ba aikin da yayi zai samu kudi da yawa haka kawai? Wannan yana daga cikin abinda yake lalata yara.” Ita dai Zee bata ce komai ba don bata san ma me zata ce ba. Haka ta kamo hanya zuciyarta duk ba daɗi don sai data dade tana share hawaye a hanya saboda yanda take jin takaicin halayensu, sai dai tana buƙatar ta koma don taji meke faruwa, me Mummy ke ɓoye mata sannan ta sanar da ita dalilinta na aikata abubuwan data aikata. Ajiyar zuciya tayi ita kam kwanan nan rayuwa take yi amma kamar ba rayuwa ba, ji take kamar mafarki take abubuwan dake faruwa da ita, ace komai na rayuwarsu ya canza lokaci ɗaya? Abinda suka daɗe suna ginawa su gane wai ashe duk ƙarya ne? Gefen kanta taji yana ɗan sara mata hakan yasa ta gangara gefen titi tare da ciro paracetamol ta haɗiyi guda biyu, kanta ta kwantar saman kujera tana sauke ajiyar zuciya, wayar Baqeer ta kira don haka kawai take jin muryarshi take son ji, sun dawo daga makaranta kenan don sun ma kusa gama makarantar, suna tafe yana tunanin abubuwan da ya kamata suyi dan ƙara bunƙasa shagonsu, yana ƙoƙarin shiga adaidaita sahu sai ga motar Badaru tazo wucewa, Bashir ne a ciki yana ƙoƙarin yin parking ya fito su kuma sun shiga adaidaita sun yi gaba, wayar Zee ce ta shigo hakan yasa ya ɗaga cikin ragaggiyar murya wanda ko kana kusa inba kunne ka kai kusa dashi ba baza kaji me yake cewa ba yayi sallama. Zee ta amsa a hankali tana lumshe ido, ji take yi ina ma dai ta ganshi a gabanta? Ji take missing dinshi na neman rikitata, murmushi yayi yace “Ya Ummin?” Tunani tayi akan tana son yi mishi surprise hakan yasa tace “Tana nan lafiya, mun fito siyan abu ne dasu ni ina mota.” Ya jinjina kai yace “Shine aka ɗan tuno mutumin nan?” Tana murmushi tace “Ba gwara ni na tuno mutumin ba? Shifa?” “Ke nan dai gori ake yiwa mutumin?” Tana murmushi tare da riƙe gefen kanta dake ciwo tace “Uhm hmm sai ya canza in zai iya.” Kai ya ɗan girgiza yace “Zan baki mamaki, sannan ki shirya kar kiyi mita akan na dameki da kira.” Cike da neman magana tace “Wa? Kai ɗin? Allah Ya Baqeer baza ka iya ba.” Da mamakin kalamanta yace “Dalili?” Ta dan wurƙila ido tace “Saboda ban san matsayina a wurinka ba, sannan a yanda kake bana ji in zaka iya aikata hakan.” Kallon Tanimu yayi bai son fallasa abinda ke ranshi a gabanshi da ya sanar da ita abinda ke ranshi, murmushi yayi yace “In kin dawo zan sanar dake, sannan get ready kema inji nawa amsar.” Wani irin energy taji yazo mata ta runtse ido tana jin wani shauƙi na ratsata, ji tayi baza ta iya cigaba da wayan ba don tabbas so take ta ganta kawai gaban Baqeer, hakan yasa tace “Su Ummi sun fito sai ka kirani.” Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta sha ruwa sannan ta cigaba da tuƙi, tana jin wata nutsuwa na ƙara saukar mata, ina ma tana da wanda zata sanar wa halin da take ciki, Nabila ce ta fado mata ta girgiza kai tana neman kauda ta daga ranta. A bangaren Baqeer kuwa murmushi yayi suna zuwa gida yaga Dada na ƙoƙarin fita yace “Dada ina zaki?” Tace “Dubiya zani wallahi ƙawata ce bata jin daɗi,” tayi maganar cike da kulawa, cike da ɗan jimami yace “Kuma wai Dada ƙawa kuke cewa da girmanku?” Gyara zaman mayafinta tayi tasa takalme yi tace “To in bamu ce ƙawa ba kuliya kake so muce? Ha’a yau ni naji abinda yafi karfina, ku dai baku isa mu faɗi abu ba sai ace mun girma da faɗar hakan.” Dariya yayi kaɗan yace “Hajiya Dada tamu ke dai yanzu sai kin dawo. Kallon mamaki tayi mishi da alama yana cikin farin ciki don wannan zolayar da biyu yake yin ta. Ɗaki ya shiga ya kalli shaddar daya ɗinka yana jiran ta dawo yayi expressing abinda ke ranshi, ƙasan leɓenshi ya ɗan ciza kaɗan ganin bai gama yi mata ɗinkin material ɗin ba, abinci kawai yaci ya fito ya tafi shagonsu. Zee kuwa da yake daga Dambatta zuwa cikin kano ba wani nisa gareshi ba yasa ta iso da wuri, kallon jikinta tayi atamfa ce doguwar riga sai mayafi da tayi rolling a saman kanta don bata sa ɗankwali ba, fuskarta babu komai sai mai da lip gloss, madubi ta ciro bayan ta shigo layin ta gyara fuskarta, wayarta ta kalla wanda kiran Mummy ke ta shigowa ga na Kabir, bata jin amsawa kuma ba mai sata amsawa, tana gama gyara fuskarta ta fito ta nufi gidan, ganin gidan a rufe yasa tasan basa nan don basa rufewa in dai har ba fita zasu yi ba, baki ta turo ta koma mota, text tayi mishi tace “Ya Baqeer ɗazu naji kamar kana hanya ka koma gida?” Sam bai kula ba don hankalinshi na kan kayanta da yake haɗawa, gashi electric yake amfani dashi to a wahale yake yi saboda kafarshi in ya daɗe yana amfani da ita sai yaji tana yi mishi ciwo, bai san kowa ya tayashi yi mata wannan ɗinkin don yana ji wannan shine ɗaya daga cikin hanyoyin da ya shirya don yin confession na soyayyarshi. Ganin bai yi mata reply ba yasa ta kai hannu zata kira shi sam bata kula da kiran Mummy daya shigo ba kawai sai ji tayi hanunta ya taɓa, ganin ta riga ta ɗaga yasa ta gaisheta, Mummy cikin muryar marasa lafiya tace “Zainab kina can? Hankalina yaƙi kwanciya don kuwa Daddynki yaje Abuja shi da mahaifin Junaid ina tsoron kar suje daɗin tafiya tare yasa suyi arrangement na auranki.” Hankali a tashi Zee tace “What? Mummy gani nan zuwa,” tayi maganar tare da shiga mota da sauri, wayar Junaid ta kira bai jima ba ya ɗauka tace “Junaid yanzu zan zo office ɗin ka don haka ka fito waje.” Tana fadar haka ta kashe wayar, ji take a wannan lokacin babu abinda ba zata iya ba, don zuciyarta ta gama shiryawa tsaf don amsar abinda Baqeer zai sanar mata wanda tasa a ranta in har yace ba soyayya yake sonta dashi ba to fa ita zata sanar dashi soyayyar take so. Bata wani jima ba ta isa, a waje ta ganshi yana tsaye sanye da suit yana duba agoggon hannunshi, da alama jiranta yake yi, a kusa dashi tayi parking, ta jikin kofar inda take ya tsaya ta zuge glass ta kalleshi, tausayinshi ne ya kamata don tabbas tasan ya dade yana binta da soyayyarshi, murmushi ta sakar mishi tace “J har ka fito?” Kai ya ɗaga mata alamar eh yana kashe mata ido yana cewa “Ya zan yi sanyin raina ta kirani?" Kai ta kauda tace “Kai dai wallahi ka fiya neman magana, J please bana son nayi hurting feelings ɗin ka shi yasa na fara tsayawa a nan inyu maks magana, kada kaji ba daɗi in kaji abinda zance don tabbas in har aka ƙara maganar auren mu zan bayyana abinda ke raina, wancan karon na faɗa maka maganganu wanda har yanzu ina jin ba daɗi .” Kallonta kawai yake yi yadda kai tsaye take rejecting ɗinshi ko da wasa bata taɓa tsayawa tayi reconsidering ƙaunar da yake yi mata ba, mota ta tada tayi mishi sallama, har zata zuge glass yasa hannu yace “Baqeer kike so?” Kallonshi tayi sai dai bata ce komai ba, mamaki ne ya kamashi, how? Zainab? No way, don yayi tambayar ne saboda abun na damunshi sai dai yanayinta yasa shi shan jinin jikinshi, hannayenshi ya zare kamar mara laka taja mota tayi gaba hankalinta a kwance. Gida ta nufa kanta na ƙara sara nata ga wani sanyi da ke ratsata, ciki ta shiga janye da akwati, tun daga falo take jiyo ƙamshin turaren wuta, kiciɓis suka yi da Mummy tana riƙe da kasko, kalaman Baqeer ne suka faɗo mata, ita Mummyn haka aka raineta? Yawun bakinta ta hadiya, Mummy cikin hanzari ta ajiye kaskon ta rungume Zainab, tana sauke ajiyar zuciya tana cewa “Auta nayi missing ɗinki, banda lafiya nace bari na tashi nayi wani abun saboda na samu sauƙi a raina, ji nake rashinki a gidan nan duk gidan ba daɗi, kallon Mummy kawai take kafin tace “Na ɗauka saboda kina son zama ke kaɗai a gidan kike hana ƴan uwan mahaifiyata zuwa?” Gaban Mummy ne yayi wani irin faɗuwa a tsorace ta kalleta tace “Me kike nufi?” Muryar Zee na rawa tace “Sun ce rabon da su shigo cikin gidan nan sunfi shekaru goma, iya kacinsu bakin gate, amma ni a sanina sau sama da biyar kina cewa sun shigo sun yi watsi da kaya akan sai kin basu wani abun saboda kwacemu da kika yi.” Mummy fuskarta ɗauke da mamaki tace “Haka suka ce? Wallahi sharri suke yi mini, Auta ba dai kin yarda dasu sama dani ba?” Idanuwan Zee ne suka yi jaa sosai tana kallon Mummy tace “Naji ace wannan ƙarya ne, kayan da mahaifiyarmu ke ɗinko mana shekara da shekaru fa? Mummy I just…..” ta kasa ƙarasa maganar saboda raunin da muryarta tayi. Mummy ta kamo hannunta da sauri tace “Wannan mahaifinku ne ya hana ba ni ba, sannan zancen farko sharri suke yi mini, ki tuna sau nawa kina zuwa kina ganin gidana a hargitse? Sannan mai gadi ba a gabanki a farko yace sun shigo ba?” Zee ce ta kalleta don ita kam bata son wannan abubuwan dake faruwa sai ma ta kasa gane mai gaskiya dame ƙarya, ga ciwon kanta dake ƙara ƙaruwa. Ganin jiri na neman ɗibanta yasa ta wuce ɗakinta da sauri tana shiga ta kulle ƙofa ta sulale jikin ƙofar ta zauna tana dafa kanta iduwanta a rufe. ***** Bashir kam yana zuwa gida ya fesawa Jamila yaga Baqeer zai hau adaidaita, dariya Jamila ta kwashe ta fito ta sanarwa Abu nan suka sake kwashewa da dariya, Abu tace “Ahaf ni dama nasan ko fili  suka sata ba abinda zai tsinana musu yoo nakasashe dama me zai iya yi? Na tabbatar kuɗin haya ya biya a ɗan dakin daya samu hala sai ragowar suka juye a asibiti.” Jamila tasa dariya tace “Ai jiya da naji Badaru na zazzagawa matar can rashin mutunci baki ga daɗin da naji ba.” Umma tana yanka alaiyahu a falo sai dai yanda suke magana da ƙarfi yasa tana jin duk abinda suke cewa, murmushi kawai tayi don sam bata son kula wannan shirmen nasu, so take yi ma gobe tayi miya ta kai musu. ***** Miƙa yayi ganin ya kammala ɗinkin ya gunguro ya kashe injin daya kunna saboda ɗinkin sannan ya sauke ajiyar zuciya yana kallon kayan, wanda kyansu sai wanda ya gani, gashi colour na material din da irin colour ɗin yayi aikin shadarshi sabon yayi. Wayarshi ya janyo yana son jin yaushe zata dawo don babu shakka ya ƙosa ya sanar da ita sirrin zuciyarshi. Ganin saƙonta yasa yayi saurin kira, da ƙyar Zee ta ɗauka saboda yadda take sauke numfashi, hankali a tashe Baqeer yace “Meke faruwa?” Ta lumshe ido ta buɗe tace “ɗazu nazo gida baka nan kai da Dada.” Da mamaki yace “Kin dawo? Meke faruwa?” Kai ta girgiza tace “Ba komai zan ware…..” yanda tayi maganar kana ji kasan dauriya kawai take yi, kashe wayar yayi da sauri ya kira Salim, yana ɗauka yace “Salim don Allah kasan gidan su Zainab? Yanzu ba wasa nake yi ba kamar yadda ka saba ɗauka, gidansu na gaskiya nake so please!” Gaban Salim ne ya faɗi, meke faruwa? Ta ina zai fara? Bayan bai shirya ganin masoyan biyu sun rabu ba? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* Da *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN* {80} Tunda ta dawo tana kwance a ɗaki zazzaɓi ya rufeta, da ƙyar ta daure ta kira Ummi a waya ta faɗa mata isowarta gida lafiya. Koda Ummin ta tambayeta lafiya taji muryarta tayi ƙasa sai ce mata tayi gajiya ce kawai da kuma bacci da take ji bata don yi saboda yamma tayi, nasiha Ummi tayi mata kafin suka yi sallama bayan Ummi ta bata Inaya sun gaisa. Komawa tayi ta kwanta kanta yana wani irin sara mata ga tunani da yayi mata yawa ta rasa menene gaskiyar duka abubuwan da taji a kwanakin nan, ta rasa maganar wa zata ɗauka ta mahaifiyarta ko kuwa ta Mummy da tayi musu riƙo na gaskiya tamkar ƴaƴanta shekara da shekaru. Tana kwance Kabir ya shigo ɗakin, shigowarshi kenan Mummy ta faɗa mishi dawowar Zeey shine ya shigo ɗakin don ya ganta. Ɗago kanta tayi taga Kabir a bakin ƙofa sai ta mayar ta kwanta. Ƙarasowa ciki yayi yace "Sai yau kika ga damar dawowa? Ai da kin sani kin yi zamanki acan  butulu kawai mai manta alkhairi, shine Mummy tayi ta kiranki kika ƙi ɗauka saboda kin tafi wajen matar da tayi abandoning ɗin mu, ko kuwa laifin Nabila nata ne?" Murmushin takaici kawai Zeey tayi ta lumshe ido sannan ta buɗe ta zubawa Kabir tana kallon yadda yake wani cika yana batsewa duk don ta taka ƙafa taje wajen mahaifiyarsu. A sanyaye saboda kanta dake damunta da ciwo tace "Ya Kabir kenan, kai yanzu laifina kake gani don naje wajen Ummi? Kada ka manta mahaifiyarmu ce dake da hakki a kanmu, wacce taci kashi da fitsarinmu, ta kula damu tun daga haihuwarmu har zuwa ranar da aka rabata damu. Ka taɓa tsayawa ka tambayi kanka dalilin da yasa tun bayan barinta gidan nan bata ƙara waiwayarmu ba? Kai baka taɓa son ka san dalilin da yasa ta watsar damu ba kamar yadda muke tunani? Kama san cewa tun tafiyarta duk shekara sai ta aiko mana da ɗinkunan sallah amma ba'a taɓa faɗa mana ba bare a nuna mana kayan ko baza mu yi amfani dasu ba. Kasan sau nawa ƴan uwanta suka zo aka hanasu shigowa su ganmu? Watanni biyu da suka wuce Kawu ya rasu, yana jinyar ajali burinshi guda ɗaya shine ya saka mu a idonshi takanas su Hajiya Goggo suka zo don su faɗa mana aka hanasu shigowa, to ka faɗa min a ciki waye mai laifi, su da aka hanawa ganinmu duk lokacin da suka buƙata ko Ummi da aka rabata da yaranta tun suna ƙanana?" Da mamaki yake kallonta yace "What are you trying to say? Aka hanasu shigowa ko suke zuwa suna yiwa Mummy rashin arziƙi." Girgiza kanta tayi tace "Duk abinda kaji na faɗa gaskiya ne, Ummi bata yi abandoning ɗin mu ba duk tsawon lokacin nan muna maƙale a cikin ranta, akwai saƙonka a cikin kayana sai na tashi zan baka yanzu kaina yana ciwo. Idan ka fita ka rufe mini ƙofar ɗakin," taja duvet ta rufe har kanta don bata son yawan magana tana jin kanta kamar zai ɓalle ya faɗi ƙasa saboda azaba. Tana jin lokacin da Kabir ya tashi ya fita sai dai bata ƙara yi mishi magana ba har bacci ya ɗauketa. ***** Yanzu abubuwa da yawa sun yiwa Hadiza sauƙi saboda sana'ar markaɗe data kama Allah kuma yasa mata albarka a ciki saboda anan kurkusa dasu babu masu sana'ar markaɗen don haka kusan kowa ita yake kawowa shi yasa yini take yi a tsaye tana aiki, ɗan abinda ta samu kuma dashi take yin duk wasu ƴan buƙatunta har ma a ciki ta yiwa Umma ɗan alheri. Shi kanshi maigidan yanzu sam ba'a jin kansu saboda dama dai shi kuɗinshi ne ba zai cire ya bayar ba yanzu kuwa data daina tambayarshi abunshi sai aka zauna lafiya, a haka kuma har shima ya nemi wani abu ta ɗauka ta bashi duk dai don a zauna lafiya. ***** Tunda yaji Zainab bata da lafiya hankalinshi ya tashi, lallai lokaci yayi daya kamata ya bayyanar mata da abinda ke zuciyarshi yana ganin batun ɓoye-ɓoye kuma ya ƙare lokaci yayi da zasu san matsayin juna idan yin yi idan barin bari amma ya gaji da raragefe zuciyarshi kullum bata da nutsuwa saboda bai san matsayinshi a wajenta ba. Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi yayi yaga lokaci ƙarfe bakwai saura kwata na yamma, in banda yanzu dare zai yi da babu abinda zai hanashi zuwa wajen Zainab a yanzu amma In Sha Allahu gobe ba zata wuce ba ba tare da yaje ya ga a halin da take ciki ba. Koda ya koma gida sai ya samu kanshi da sanarwa da Dada batun rashin lafiyar Zainab ɗin ya kuma faɗa mata gobe zai je ya dubata. Cikin alhinin rashin lafiyar Zainab ɗin tace "Da kuwa ka kyauta don Zainabu yarinya ce mai mutunci da bata ɗauki rayuwa da girma ba, hausawa ma suka ce gaida me gaishe yadda ta ɗauki al'amuranmu da girma ya dace aje a gaisheta da jiki, wannan zuwa dubiyar ma kamata yayi ace harda ni za'a je." Girgiza kanshi yayi yace "Zan dai faɗa mata kina gaisheta amma kiyi zamanki, kinga bamu taɓa zuwa gidansu ba bamu san irin karɓar da za'a yi mana ba bare da ganin Zainab kasan ba daga ƙaramin gida ta fito ba." Tace "haka ne, to ka gaisheta kace ina dubata da jiki." Ɗakinshi ya wuce zuciyarshi fal tunani sam baya da nutsuwa sai dai yana jin ɗoki da farin cikin kasancewar gobe zai bayyanawa Zainab abinda yake ji a kanta a cikin zuciyarshi. Wayarshi ya ɗauka ya kirata yana so ya ƙara jin yanayin jikinta. A lokacin da ƙiran ya shigo ta idar da sallah kenan don tun dawowarta tana kwance bata motsa ba, shigowar Mummy ɗakin uku tana tarar da ita a kwance duk a tunaninta bacci take yi bata san tana jinta ba bata son yin magana da ita ne kawai. A kasalance tace "Ya Baqeeer," muryarta na rawa. Sai da yaji wani abu ya ratsa tun daga tsakar kanshi har zuwa tafin ƙafarshi saboda yadda taja sunanshi. "Ya jikin naki? Hope yayi sauƙi yanzu," Ya tambayeta cike da kulawa. "Da sauƙi Alhamdulillah, ya Dada? Nayi kewarta yau naso na ganta sai kuma nayi rashin sa'a ban sameku a gida ba." Ɗan murmushi yayi, duk da bata da lafiya amma tana tambayar Dada. Waɗannan halayen nata na daga cikin abinda yasa ta shige zuciyarshi tayi kane-kane ba tare daya shiryawa hakan ba. "Tana nan lafiya tace na gaisheki da jiki." "Wai faɗa mata kayi?" Ta tambayeshi da mamakin hakan ƙunshe a muryarta. "Ina dawowa gida na faɗa mata baki da lafiya gobe zanje na dubaki sai tace itama zata je, da ƙyar dai na lallaɓata ta haƙura amma tace lallai nace tana gaisheki da jiki," ya ƙarashe maganar yana dariya. Cike da jin daɗi take murmushi saboda kulawar da yake bata ya tabbatar mata tanada matsayi a gunsa, ajiyar zuciya yai yace "Magani fa? Kinsha?" Ta ɗan sauke ajiyar zuciya tace "Nasha paracetamol." Kai ya jinjina yace "Zanzo naga ya jikin naki....." gabanta ne yai wani irin faduwa bata san sanda tace "A'a karka damu Ya Baqeer nasan gobe in na tashi zanji na ware." Mamaki yak da jin kalamanta sai dai ya alakanta hakan da kulawa ne tunda tasan halin da yake ciki, baisan batada lafiya ya ɗaga mata hankali kawai sai yace shikenan. Suna gama waya ya ƙira Salim yace dan Allah gobe yazo, Salim cike da zargi yace "Inzo? Badai maganar gidan su Zainab din bane?" Baqeer yace "Kai dai kazo ina jiranka." Kafin Salim yai magana ga kashe wayar. ***** Wannan karon shine karo na biyar daya ƙara kallon jikinshi, ɗinkin dake jikinshi kaɗai abin kallo ne, yayi kyau sosai da sosai. Wani sanyayyen murmushi yayi wanda ya ƙara sawa cikar zati da annurin fuskarshi ta bayyana "Ya Baqeer menene matsayina a wurinka?" Kalaman ta ne suka sake dawo mishi kamar a lokacin take faɗa mishi "Kasan rashin lafiyar me nake yi? Ko kuwa har yanzu zaka ce baka san komai ba?" Nan ma wasu bangare na cikin kalamanta suka sake zuwa mishi. "Yau zan sanar dake matsayin da kika taka a cikin zuciyata," yayi maganar yana sakin wani sanyayyen murmushi kamar ita ce a gabanshi. Salim ne ya saki baki ganin Baqeer yayi kyau caz kai kace wani ango ne yace "Wai ina zamu haka duk kabi ka dameni?" Kallonshi yayi yace "Gidansu Zeey zaka kai ni, bata jin daɗi ni kuma hankalina yaƙi kwanciya gashi akwai amsoshin da nake ganin baki da baki ya kamata na furta mata." Nan da nan tashin hankali ya bayyana a fuskar Salim hankali a tashe yace "Baqeer kayi mata waya mana tazo sai kuyi maganar, gani nake yi ba sai kaje ba." Wani kallo Baqeer ya yiwa Salim, me yasa a duk sanda yake son zuwa gidan su Zainab yake hanashi? Me yake ɓoye mishi ne da baya so yaje ya gani? Nan da nan ya tamke fuska sosai yace "Ko ka kaini ko na nemi wani ya kaini duk ɗaya amma dai yau nayi niyyar zuwa wajenta babu kuma abinda zai saka na fasa." Haka nan ba don Salim yaso ba suka shirya suka fita zuwa gidansu Zainab, adaidaita suka tara ga mamakin Baqeer sai yaji Salim ya ambaci sunan unguwarsu, wai dama Zeey ƴar unguwarsu ce amma shine bai taɓa saninta ba, gaskiya abun da mamaki duk da dai ba cika shiga sabgar mutane yayi ba watakila shine yasa bai santa ba tun da sai yanzu. Koda suka shiga unguwar kallonta kawai yake yi sai yake ganin duk ta canja mishi kamar wanda yayi shekaru bai shigo ba, kasa kallon layin gidansu yayi saboda wani ƙunci da yaji yana neman lulluɓeshi sai dai baya son yayi ruining musu wannan ranar shi da Zainab don haka yayi sauri ya kori duk wani tunani daga zuciyarshi sai na yadda gamuwarsu da Zainab zai kasance. Babu yadda Salim ya iya haka suka ƙarasa layin gidan, wani tunani yayi ganin ya kawoshi layin gidansu Asiya budurwar data yaudareshi bayan rasa ƙafafunshi, wacce ta juya mishi baya ita da amininshi, nan da nan kuma ya sake kallon layin yana tuno kalamanta data yi mishi farko-farkon haɗuwarsu a wannan layin. Ƙofar gidan da Salim yayi parking ya kalla, gabanshi ne ya fara dukan uku-uku yana jin wani tsoro da fargaba na yawo cikin ranshi, bakinshi ne ya fara rawa yace "Salim ba dai nan ne gidansu Zainab ba?" Ido Salim ya runtse don abinda yake ta gudu kenan tun farko shi yasa yaƙi kawoshi gidan, riƙoshi yaje yi da sauri ya ɗaga mishi hannu alamar kada ya taɓashi sannan yace "Please wheel chair!" Haka ya fito ya buɗe mishi ya hau kan kekenshi na guragu ya tura zuwa ƙofar gidan, duk wani turi ɗaya da zai yi sunan Zainab ne ke dawo mishi cikin ranshi, ba dai? Ba dai Zainab Sulaiman Karaye bace wacce ya sani? Ba dai itace Zeey ɗin da tayi kane-kane a cikin zuciyarshi ba? No No Zeey? Zainab? It can't be. A daidai jikin gate ya tsaya sakamakon kanshi da yaji yana wani irin juyawa, wani irin dum yake ji wanda yasa baya gani sosai, wayarshi ya ɗauka ya tura mata text akan yana waje, sannan ya kalli Mai Gadi yace "Don Allah ba nan ne gidan Sulaiman Karaye ba kuwa?" Hankali a kwance yace mishi "eh nan ne," tura kekenshi baya yayi jikinshi nayi mishi wani irin sanyi, zuciyarshi na bugawa akai-akai kamar zata fasa ƙirjinshi ta fito. "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, how? Ta yaya? Ta yaya Zainab ɗinshi take fitowa daga cikin wannan gidan? Kallonta yayi nan da nan kamanninta na yarinta suka fara dawo mishi tar a cikin kai, sai data bari sonta yayi tsamari yake jin duk wani bugun numfashin shi da ita yake yi sannan ya ganta a matsayin wacce ko a hanya baya fatan gamuwa da ita? Abubuwan da suka faru a baya a ta dalilin ta ne suka fara dawo mishi, kai kawai yake girgizawa yana tura kekenshi iya saurinshi. Ita kam tun sanda taga saƙonshi akan yana waje tasan shikenan komai ya ƙare, ita kam tasan rayuwarta ta ƙare. Baqeer shine jigon rayuwarta in dai har ya rabu da ita to tabbas rayuwarta tazo karshe. "Ya Baqeer!" Ta ƙira sunanshi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, da sauri ta sha gabanshi ta tsugunna suka yi kai ɗaya tana hawaye tana cewa "Why? Please ka tsaya." Idanunshi sun kaɗa sun yi jaa sosai, kenan ita tasan shi wanene amma ta raina mishi wayau? Ba dai fansa ta ɗauka akanshi ta hanyar sace zuciyarshi ba? Gagarumin case ɗin da aka yi shekarun baya ne wanda har yasa suka bar unguwar yake dawo mishi kamar a lokacin abun ke faruwa wanda a dalilinshi komai sai da ya kusa tarwatsewa, how? Taya zata yi mishi haka? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD*         *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA ƊAYA* {81} Da sauri Salim ya taho ya riƙe keken Baqeer da yake ta saurin turawa saboda yana son barin unguwar, kallon Salim yayi wanda shi kanshi kallon shi yake cike da dauriya yace “Baqeer ina zaka kake wannan saurin?” Kallonshi yayi cike da mamaki da takaici, sai a lokacin ya kalli Zainab dake tsaye a inda ya barta, kanshi ya kauda da sauri sannan ya cigaba da tura keken, Salim ne ya kalli ledar dake hannunshi wanda ake ta murna za’a bawa Zainab, shafa bayan kanshi yayi yana tunanin abun yi. Wurin Zainab ya koma dake tsaye kawai tana share ƙwalla, ledar ya miƙa mata, amsa tayi tana kallonshi, muryarta na rawa tace “Salim please ka kula dashi.” Kai ya ɗaga sannan yace “Ki koma ciki In Sha Allahu babu abinda zai faru.” Ta ɗaga kai alamar to sannan tace “Nagode,” tayi maganar tana juyawa, sai daya ga ta shige gida sannan yabi bayan Baqeer lokacin har ya kai ƙarshen layin, adaidaita ya tarar musu suka bar layin suna fatan babu wanda ya ganshi. Shi dai Baqeer tunda ya zauna bai ce komai ba, zuciyarshi ce kawai take tafasa, shi yasa ashe ko da wasa bata so tayi maganar data shafeta, hannayenshi ya dunƙule zuciyarshi na wani irin zafi, how? Taya zata mishi haka? Sai data bari ya gama mutuwa akan sonta? Shi a kanta zai iya rufe ido yace sai ita to amma me? Mahaifinta ya sani ko duniya za’a haɗu a bashi baki ba zai bashi aurenta ba, shi bai damu da yardar Badaru ba sai dai shi yasan da ƙafarshi ma mahaifinta ba yarda zai yi ba bare babu, kanshi kawai ya kawar yana kallon titi shi kuma haka ƙaddararshi take? Daga wannan sai wannan? Yanzu da yake sa ran komai yana tafiya daidai ashe yanzun ma wani abun zai ƙara ɓullo wa? Har suka isa gida babu wanda yayi magana, shi dai Baqeer kawai ya wuce ɗaki Dada tana jiyosu ta fito tana tambayar jikin Zainab, sai Salim ne ya tsaya ya bata amsa don Baqeer ɗakin shi kawai ya shiga ya kulle, jikin ƙofar kawai ya jinginar da kujerar shi ta wheelchair yana maida numfashi, komai ne yake sake dawo mishi kamar a yanzu ake yinsu, tashin hankalin da aka sakasu shida iyayenshi a dalilin ta ne yake sake dawo mishi, amma ya aka yii bai ganeta ba? A iya saninshi tana da ƙiba to yanzu ta zama siririya duk sai kamanninta suka canza, idanunshi ya runtse sai dai fuskarta ce tana mishi magana ɗazu kawai ke dawo mai. Wayarshi ce ta fara ƙara ɗagota yayi ya zubawa wayar ido wanda sunanta ne ke jikin allon wayar, ido ya rufe ya sake buɗewa yana kallo har ta katse, bata sake jira ba ta ƙara kira ji yayi zuciyarshi ta kasa jurewa, duk da yasan ba abu ne mai yiwuwa ba amma a ƙalla ya sanar da ita abinda ke ranshi, wayar ya ɗaga ya karata a kunnenshi sai dai ya kasa magana, ita ma a bangarenta da alama ta kasa magana don ajiyar zuciya kawai suka sauke a tare, ƙasan lebenta ta ciza da  har yanzu bata jin daɗi tace “Ya Baqeer!” Ido ya runtse gam don kiran data yi mishi har tsikar jikinshi sai da yaji ta tashi, yawun bakinshi ya haɗiya yace “Why?” Wasu hawaye ne suka gangaro saman kuncinta tace “I’m really sorry wallahi da farko ba wai ɓoye maka nayi a sanina ba, lokacin da muka yi ta haɗuwa da farko coincidence ne don ban ganeka ba sai sanda naje wurin Umma naga ashe kaine, at that time I feel so bad na ganin abinda ya sameka.” Wani murmushin takaici yayi yace “Kenan duk abinda ke faruwa ƙarya ne? Taya zaki bari sai da na gama kamuwa da sonki nake ji bazan iya rayuwa babu ke ba sai naji kece wacce ni nasan ko za ayi me mahaifinki ba zai taɓa amince wa ba.” Ji tayi komai na jikinta ya tsaya ta sauke wata ajiyar zuciya tace “Ya Baqeer me kace?” Sam abinda ke ranshi ya faɗa wanda hakan yasa bai gane me take son ya maimaita ba, Zee ta daure tace “Ya Baqeer please me kace? I’m sure kunnena jiyo mini yayi zancen soyayya.” Cike da takaici yace “Who cares Zainab? Ko kin manta ƙatuwar katangar dake tsakaninmu? Da so da rashinsa yanzu…..” Katseshi tayi da sauri da cewa “I care, sannan for me that’s all that matters, duk duniya babu wanda ya isa ya rabani da kai, kalmar so kawai nake jira naji daga bakinka kuma naji ba damuwa ta bane ko ma me zai faru.” Yasan halinta ba abinda baza ta iya aiwatarwa ba sai dai shi a dalilin so ba zai taɓa saka yan uwanshi cikin matsala ba, especially Umma hakan yasa yace “Mun gama magana, bye.” Ba tare da ya bari ta ƙara magana ba ya kashe wayar ma gaba ɗaya, yasan waye Alhaji Sulaiman ya kuma san akan ƴar lelen ƴar shi babu abinda ba zai aikata ba, shi kuma duk da yasan yana mugun sonta yana ji in har bai aureta ba ya haƙura da aure kenan, amma fa ba zai salwantar da rayuwar ƴan uwanshi saboda ita ba. Takaici ne ya kamashi kawai ya cillar da wayar kan gado yasa hannu biyu yana dafa kanshi yana jin zuciyarshi na wani irin zafi. Zee kuwa hawayenta ta share don tabbas babu mai rabata da Baqeer, ɗakin Mummy ta nufa lokacin tana zaune tana duba wasu takardu wanda da alama masu amfani ne, Zee na shigowa ta ɗan maidasu gefe kallo ɗaya tayi mata tasan akwai matsala, hakan yasa ta ware mata hannu ita kuma ta ƙara so ta shiga jikinta, duk kuwa da haushin Mummyn da take ji a yanzu neman me lallashinta take yi, kuka kawai ta saka tace “Mummy ki yiwa Daddy magana ni wallahi da wanda nake so sannan aurenshi nake son yi yanzu.” Mummy cike da mamaki ta ɗagota tace “Shine wanda kike bani labari?” Kai ta ɗaga tana sake goge ƙwalla tana cewa “Shi Mummy bana ji zan iya rayuwa babu shi, don Allah ku barni na aureshi ni a yanzu ma a shirye nake.” Dafata Mummy tayi tace “Shifa? Yace yana sonki?” Kai ta ɗaga cike da alfahari da hakan tace “Eh Mummy don haka ki sanar da Daddy.” Kai ta ɗaga sannan ta shafi fuskarta tana goge mata hawaye tace “Zazzabi kike yi ne? Naji jikinki da zafi.” Hannu tasa ta riƙe hannun Mummy tace “Ba shine a gabana ba Mummy ni dai ki mishi magana.” Shiru Mummy tayi kafin tace “Ko ma menene kiyi ina bayanki, abinda kike so as always nima shi nake so, sannan ko ya yake ina bayanki, kawai dai ina tsoron magana ne kin san har yanzu bai sauko da abinda ke faruwa ba.” Kallonta Zee tayi sai yanzu ma ta tuno da ashe itama fushi take yi da Mummyn tsabar ta matsu yasa tama manta. Neman miƙewa tayi da sauri Mummy ta riƙota tace “Zainab please ban da ke, ki tuna shaƙuwar dake tsakanin mu, nasan nayi muku laifi akan Nabila amma a matsayinki na mace ya kamata ki tausaya mini ki fahimceni.” Kallonta Zee tayi tace “Zamu yi magana daga baya, don maganata akan su Ummi ne,” tana kaiwa nan ta fito, ɗaki ta wuce tayi sallar la’asar sannan ta kwanta, tun ruwan tea babu abinda ta sha don bama ta jin shan komai balle taci wani abun, ledar da Salim ya kawo mata kaya ta bude tana kallon kayan da Baqeer ya ɗinka mata ta tabbatar yasha wuya kafin ya haɗa ɗinkin. Kuka ne kawai taji ya ƙwace mata don da alama abinda zuciyarta ke son yi kenan, ta zubar da ƙwallar har ta gaji, kuka take yi sosai tana rungume da material ɗin. Daddy wanda shigowarshi kenan yake jiyo kukan Zainab, hankalinshi a tashe ya nufi ɗakin don ya tabbatar dangin mamanta ne suka sakata wannan kukan, kuma tabbas ba zai ƙyalesu ba har Ɗambattan zai je duk sai ya ci mutuncinsu, dama shi yasa ko da wasa baya son taje yanzu gashinan abinda ta jawowa kanta, ƙofar ɗakinta ya ƙwanƙwasa bai jira ta amsa ba ya tura ƙofar don zuciyarshi har wani azalzala yake. Rai a ɓace yace “Da da nake hanaki zuwa ai baki yarda ba yanzu da alama kin san amfanin abinda nake yi miki tunda gashi kema da kike tasu sun gwada miki halinsu.” Kallonshi tayi ta ajiye kayan sannan tace “Ni ba saboda su nake kuka ba.” Da mamaki yace “Saboda wa kike kuka to? Ko akan waccan shashashar Nabilan ne?” Kai ta girgiza tace “Ba’a kanta bane sannan Dady kada dai ka manta ƴar Mummy ce kake kiran ta shashasha.” Tsaki yayi ta sauko ta tako gabanshi, kallonta yayi da son jin me ya faru don sai yaga gaba ɗaya ta canza, anya ma sun kular mishi da yarinyarshi kuwa? Tsugunawa tayi tace “Daddy surukinka nake so yazo ya gaisheka shine nake jira ka sanar dani lokacin da kake nan.” Wani wulaƙantaccen kallo yayi mata yace “Ina da wani suruki ne bayan Junaid? Kin dai san bana son shirme ko?” Ta dake tace “Junaid ba surukinka bane sai dai in wata ƴar kake dashi daban da zaka bashi.” Fuska a tamke yake kallonta, ɓacin ranshi ya fito bayyane a fuskarshi yace “Ke sam baki da kunya ko? Ni kike yiwa magana haka?” Dakewa tayi tace “Daddy yaushe kake gida? Zai zo ku gaisa?” Yatsa ya nuna ta dashi yace “Kin san Allah ranki kike so ya ɓaci, ki kawo mini wani ɗan iska gida ki gani.” Mummy ce ta katseshi da cewa “Senate please! Ka tambayeta wanene? Ko kuwa ka ganshi bai yi maka ba ne? Ka jira kaga wanene mana in bai maka ba sai ka sanar da ita ra’ayinka.” Tsaki yayi yace “Ke har kina tunanin zata kawo saurayin da zai kwanta mini? Har yaushe ma tasan mutane ta zauna dasu balle tasan abinda ya kamata?” Zee ce tace “Ban sani ba amma nasan abinda nake so, Daddy kasan bazan auri Junaid ba kuma babu wanda ya isa ya rabani da wanda nake so, abu mafi sauƙi shine ka amsheshi hannu bibi……” hannu ya ɗaga kamar zai kai mata mari, ko me ya tuna sai kuma ya fasa, ya dunƙule hannu tare da nunata yana fitar da iskar ɓacin rai yana cewa “ɗan gidan uban waye? Ko shima zaki ce baki sani ba?” Kai ta kauda tace “Na sani amma ba wannan bane a gabana.” Rigarshi kawai ya kaɗa yayi ciki, zuciyarshi na azalzala, Mummy ce ta kalleta sannan ta jinjina mata kai alamun tayi daidai ita kuma tabi bayan Daddy. Ɗaki ya shiga ya zauna tare da buɗe ƙafa yana huci kamar zakanya, zama tayi kusa dashi tana shafa gefen kafaɗarshi tana cewa “Senate calm down, yarinya ce bata san meke faruwa ba, sai dai inaga don Allah kayi haƙuri ka bari yazo kaga wanene, in har bai yi maka ba kace bai maka ba, itama a lokacin na tabbatar bata da uzurin da zata ce a’a.” Kallonta yayi yace “Sam ban san ya zanyi da yarinyar nan ba gaba ɗaya bata jin magana.” Ta kwantar da kanta akan kafaɗarshi tana cewa “Yarinya ce kayi mata uzuri don Allah.” Da ƙyar ya sauke wata ajiyar zuciya yace “Kice yazo kuma maganarta da Junaid yana nan har sai na gamsu da shirmenta na watsa mata ƙasa a ido, na tabbatar bata isa ta ƙara yi mini musu ba.” Mummy ta fito ta shiga wurin Zee ta sanar da ita saƙon Daddy, sai dai duk da haka babu walwala a fuskar Zee, kwanciya tayi kawai tana ji zazzabin na sake rufeta, ya zata yi? Ta san Baqeer ko da ƙafar shi ba zai taɓa yiwa Daddy ba, balle in yasan ɗan wanene, tasan duk kuɗinshi yana ji ance ɗan Badaru ne to fa an rabu kenan balle ga babu kudi ga kuma babu ƙafa, pillow kawai ta janyo ta kwantar da kanta tana tunanin abinda zata yi. ***** Baqeer yana jiyo Dada nata mita akan tunda ya shiga ɗaki alwala kawai taga ya fito yayi bata ƙara ganinshi ba, sannan ga abinci ta bashi yaƙi ci, shi kam yana jinta don ko magana baya son yi, takaicinshi ɗaya rashin ƙafafuwan nan, haka yasa ƙafar a gaba yana ta ƙoƙarin takawa, sai dai daga ya tsaya a kanta sai yaji ya faɗi, yanzun ma sake gwadawa yayi ya faɗi, kanshi ya jinginar a jikin gado yana haɗiyar wani takaici da ɓacin rai, shi yanzu ko zai daki kirji yace yana son Zainab yayi yaya da ita? Hannu kawai yasa yana dukan saman ƙirjinshi da yake ji kamar wani abu ya tsaya mishi a wurin yaƙi wucewa, can ya janyo wayarshi ya kunna, saƙon Zainab ne ya shigo _Daddy yace kazo gobe da yamma ya ganka_ sake maimaita saƙon yayi, lallai Zainab da gaske take yi, shi yanzu ta ina zai iya zuwa? Wai anya ta tuno abubuwan da suka faru a baya kuwa? A dalilinsu? Abinda yasa har ƴan sanda suka shiga maganar? Badaru kuwa a ranar yayi mata iyaka da shiga gidanshi? Shima aka yi mishi iyaka da ko ganinta yayi kar ya sake yi mata magana? Dama can akwai ƴar tsama tsakanin iyayensu sai dai case ɗin nan shine ya kawo ƙarshen gaisawar da ake yi don kuwa tun daga nan komai ya wargaje, ashe Maryam sun cigaba da ƙawancensu saboda makarantarsu ɗaya, abinda yake so ta sani shi zai iya bijirewa Badaru amma ita fa? Inta bijire me auransu zai tsinana? Aure babu albarkar iyaye? Wai ma ta ina da kujerar guragu zai nufi Alhaji Sulaiman? ****** Abu ce ta kalli Kamalu tace “Ban gane lefe ka haɗa ba?” Dariya yayi yana shan robar kunun ayan daya siyo yace “Ai ke na kula baki fahimceni bane, aure zan yi don komai ya kammala kayan kwalliya ne ban siya ba sai abayoyi da jaka da takalmi.” Katseshi tayi da cewa “Ba dai ka gama haɗawa ba dai zaka ce, wannan dogon lissafin da kayi ai yaci rabin kuɗin aikin.” Kamalu ya ajiye robar kunun ayan yace “Ni dai don Allah ki bani ajiyar nan taki na saida na ƙarasa haɗa lefe na, kin dai ga suruka zaki yi sannan wannan surukar manya ce don haka kar ki wani damu da yawan kuɗin da kika kashe.” Wani kallo tayi mishi tace “Ba dai wai zoben dana siya da gadon da aka raba mana kake cewa na baka ka saida ba?” Kai tsaye yace “Shi mana, to menene amfaninshi dama idan ba kadara ba?” Wani mugun kallo tayi mishi tace “Kaga bana son shirme, in zaka yi aure to fa ka haɗa komanka da kanka.” Tana kaiwa nan ta shige ciki tana mitar rainin wayon da yazo mata dashi. ***** Bello kam gidan duk yayi mishi zafi bai isa ko falo ya fito ba Asiya zata haushi da masifa, duk ya rame ya jeme, abun takaici ta ƙi bashi key ɗin motarshi daya bata kafin ya tafi, don ya bar mata ne akan tayi amfani dashi tunda baya nan to yayi yayi ta bashi taƙi, sannan shi kunyar ma fita waje yake ji mutane su ganshi ga gida kullum datti, abinci wannan sai kame-kame yake ci, kallon mutunci ma taƙi yi mishi, gashi irin masifaffun matan nan ne da idonsu rufewa yake yi in suna bala’i. Yau kam ya gama gajiya da rainin wayonta dole ne ya taka mata birki, fitowa yayi a fusace ya shiga ɗakinta…….. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA BIYU* {82} Yana shiga ɗakin ya ganta a kwance tana danne-danne a waya, ita ko damunta ƙazantar data haɗawa ɗakin bata yi, haushi ne yaji ya ƙara rufe shi, ayi mace bata san komai ba sai baƙar ƙazanta tun yanzu ma kenan da take ita kaɗai bata iya tashi ta tsaftace muhallinta ba ina ga idan ta fara tara yara kuma yana ganin wannan lokacin sai dai ya haƙura da zama gidan don yasan iska ba zata shaƙu a cikinshi ba. A fusace yace “Ya kuma isheki haka nan Asiya, na lallaɓaki iya lallaɓawa amma sam ba kya gani. To wallahi bazan ɗauka ba kuma ki fito mini da makullin motata tunda bada ubanki muka haɗa kuɗi muka saya ba." A fusacen itama ta tashi don dama irin haka take jira ranar da zai buɗe baki yayi magana ita kuma ta yagalgala shi son ranta. "Bello ubana kake zagi?"  "An zagi uban naki idan kin ji haushi ki fito min da makullin motata, haba ya daga abun arziƙi yana nema ya zama na tsiya. Tunda na dawo baki barni na sha ruwa ya tsirga mini ba, ance miki nima daɗin dawowar nake ji da zaki sakani a gaba da masifa da bala'i kawai don ban fita dake ba ko da kin san ko hanyar airport ne banda Allah ya haɗaki dani da zaki bi ki isheni da masifa saboda baki fita ƙasar waje ba kamar yadda kika ci buri, ni da naga samu naga rashi kuma fa nace me?" Murguɗa baki tayi tace "Wannan kuma damuwarka ce ni dai ai alƙawari kayi min kuma baka cika ba don haka ka dinga ganin tashin hankali kenan idan har baka ciki ba, haka kurum bayan duk nabi ƙawaye da ƴan uwana na gama yi musu kurin ba'a ƙasar zamu zauna ba sai ka dawo kace wani wai kai ma koroka aka yi?” Ƙwafa yayi yace "Au haka ma kika ce? Shikenan mu zuba ni dake shege ka fasa kuma wallahi ki fito min da makullin motata kin ji na faɗa miki." Wata uwar harara ta danƙara mishi ta saki tsaki tana girgiza jiki tace "Na ƙarfi ne idan kana dashi ka ƙwata," tayi shigewarta banɗaki ta banko ƙofar ta rufe. Duk bala'in da Bello yake ji sai da ya kasa magana don kullum mamakin rashin arziƙi irin na Asiya take yi. Juyawa yayi ya fita daga ɗakin yana jin wani irin dana sani yana kamashi, shi wai waya aikeshi ne ma gashi yanzu duk yabi ya cakalkala al'amuranshi da hannunshi. Shi sai yanzu ma ya gane ashe ba wani so yake yiwa Asiyar ba kawai don tana tare da Baqeer ne yasa yake ganin kamar shima sonta yake yi ashe ba haka bane burinshi na son mallakar duk wani abu daya kasance na Baqeer ne yasa yake tunanin sonta yake. ***** Baqeer kuwa tunda ya karanta saƙon da Zeey ta turo mishi yake saƙa da warwara, ta ina ta yaya zai fara tunkarar Alhaji Suleiman a matsayin manemin ƴarshi? Shi yasan ko yana da lafiya ko ace ya cigaba da harkarshi ta painting Suleiman Ƙaraye ba zai bashi ƴarshi ba bare kuma da yake gurgu a yanzu wanda ya damu wata tawaya a jikinshi ga sana'ar ma yanzu yake ƙoƙarin ginata yasan babu ta inda zai fara tunkararshi a matsayin wanda yake son Zainab. Da yaga yawan tunanin da yake yi na neman saka mishi ciwon kai sai ya ɗauki waya ya ƙira Salim, tana fara ringing Salim ɗin ya ɗauka. Baqeer na jin muryarshi ya sauke wata ajiyar zuciya yace "Zainab na neman saka min ciwon kai Salim, wai kasan bayan dawowarmu saƙo ta turo mini akan naje naga mahaifinta gobe." "Daidai kenan, idan har da gaske kuke son juna dama ai kasan dole sai iyaye sun shigo maganar." A ɗan tsawace yace "Ka kuwa ji abinda nace Salim?" Yace "Ƙwarai kuwa naji ka kuma san hakan shine daidai kaje ka samu mahifinta kuyi magana shine zai san da gaske kake kana son ya baka auren ƴarshi." Wani zazzafan huci ya furzar yace "Wai ka manta waye mahaifin nata hala, Alhaji Suleiman Ƙaraye ne fa mutumin da kasan ko ina da lafiyar ƙafafu ba zai taɓa ɗaukar ƴarshi ya bani ba bare yaga naje mishi akan wheelchair." "Why do you lack confidence in your self Baqeer? Wannan abun da kake yi is an act of cowardice, idan har da gaske kake son Zainab bai kamata kaji tsoron haɗuwa da mahaifinta ba tunda kasan in dai har auren nata zaka yi dole ne ku haɗu." "Tabbas ina sonta sai dai wannan ba dalili bane da zai sa na kai kaina inda za'a wulaƙantani ba," yayi maganar yana jin wani ƙunci yana ƙara lulluɓeshi. Me yasa Zainab ta ɓoye mishi kanta gashi nan yanzu abinda ta janyo musu sun faɗa halin da ba lallai su iya fita ba. Nisawa Salim yayi yace "Idan har zaka ji shawarata ka shirya kaje wajen mahaifin nata baka san me zai faru ba, sai kaga Allah ya juya al'amarin yazo da sauƙi ba kamar yadda kai kake tsammani ba. Ina ganin hakan kawai zaka yi ka nunawa Zainab tabbas kana ƙaunarta kana kuma tare da ita a cikin kowane hali." Ɗan shiru yayi yana jinjina abinda Salim ɗin ya faɗa kafin yace "Shikenan Salim zan yi amfani da shawararka amma dai kasan bani kaɗai zan je ba ko? Sai kazo ka ɗaukeni mu tafi Allah ya tabbatar mana da alkhairi amma ni dai ina jinjina haɗuwar mu da Alhaji Suleiman Ƙaraye nasan zai yi wahala ya karɓe mu a matsayin manema auren ƴarshi." Murmushi Salim yayi yace "Ko kai fa? You have to be brave idan har da gaske kake son Zainab dole ka fuskanci dukkanin wasu ƙalubale da zasu iya kawo muku cikas wajen cimma burinku na zama mallakin juna. Goben zan zo muje In Sha Allah, kamar ƙarfe nawa zamu je?" "Ban sani ba gaskiya amma dai zan tambayeta naji sai na sanar maka." Da haka suka yi sallama da Salim yana fatan Allah yasa Suleiman Ƙaraye yayi musu bazata ya amince mishi ba tre da wata tangarɗa ba, sai kuma yayi wata dariya ta takaici don yasan abu ne mai wahala hakan ta kasance sai dai bawa baya cire da abinda yake so yana fatan kada su samu ko wacce irin tangarɗa daga wajen shi. Wayarshi ya ɗauka ya turawa Zainab message. _What time Daddyn yake son ganin mu?_ Ajiye wayar yayi ya kwanta yayi rigingine yana kallon ceiling, gaba ɗaya zuciyarshi bata yi mishi daɗi, shi yasan mawuyacin abu ne taraiyarshi da Zainab ta cigaba don shi yasan waye mahaifinta ya kuma san irin burin da yaci akan ƴarshi, shi yasan ba irin shi ne mijin da yake yi mata fata ba to amma ya zai yi da soyayyarta da tayi mishi wani irin kamu, soyayyar da tasa yake jin ashe da can ba son Asiya yake yi ba don bai taɓa jin yadda yake ji akan Zainab akanta ba. Zumbur yayi ya tashi zaune jin ƙarar shigowar text a wayarshi. Ɗaukar wayar yayi ya duba. _Ƙarfe huɗu zuwa da rabi haka_ kawai ta rubuto. Ajiye wayar yayi haka nan yake jin gabanshi yana faɗuwa, sai yake jin kamar ranar rabuwarshi da Zainab ce tazo don shi dai ya kasa yardar wa ranshi wai Suleiman Ƙaraye zai bashi auren ƴarshi ko ace yana da lafiya kuwa abu ne mai matuƙar wahala bare yadda kowa yasan ƴar tsamar dake tsakaninsu shi da Badaru. ***** Umma na zaune a ƙofar ɗakinta tana gyaran kayan miyar da take so ta yiwa Dada da Baqeer miya Badaru ya shigo. Dama sallama ba al'adar shi bace don yace gidanshi ne daya gina da gumin shi babu sisin kwabon uban kowa don haka bai ga dalilin da zai sa don zai shiga ace sai yayi sallama ba. Ko ɗaga bata yi ta kalleshi ba tayi mishi sannu da zuwa tana cigaba da aikinta. Kallonta yayi sheƙeƙe ya taɓe baki yans lura da yadda ta bawa aikin da take yi muhimmanci kamar bata san da tsayuwarshi a wurin ba. "Wato Fatima ba zaki fito min da kuɗin filina ba ko?" Ɗagowa tayi ta kalleshi sai kuma ta sunkuye ta cigaba da cire hancin tattasai cikin sanyin muryarta tace "Ai na faɗa maka abinda aka yi da kuɗin filin tuntuni bana jin za'a samu saura." Wani irin takaici ne ya lulluɓeshi, shi ya rasa ne ya yiwa Fatima da tayi mishi irin wannan muguntar ta sace mishi takardar fili ta kaiwa nakasashen ɗanta idan ma shi ɗin ta kaiwa da gaske don ga labarin da Bashir ya bashi bai kamata ace zai hau adaidaita ba idan shi ta kaiwa takardar filin ai sai dai ya sayi mota ana jan shi. "Ke dai wallahi Fatima muguwa ce azzaluma, sai Allah ya bi min hakkina a kanki wallahi," ya ƙarashe maganar kamar zai fashe da kuka, yana jin baƙin cikin filin nan da Fatima ta rabashi dashi. Ita kuwa ko kallonshi bata kuma yi ba haka ya gaji da tsayuwa ya shige ɗaki yana kumfar bakin kotu ce zata rabashi da Fatima idan har bata dawo mishi da kuɗaɗen filin ba tunda dai yasan an sayar gashi an faɗa mishi har an fara gini a wurin. Babbar damuwarshi jarin shi da yayi ƙasa bai san ta inda zai farfaɗo dashi ba, dama akan filin ya dogara to ashe waccan muguwar matar ta rabashi dashi yana zaune da baki buɗe shine bai sani ba. ***** Tunda ya tashi da safe yake jin faɗuwar gabanshi na ƙaruwa. Haka ya yini sukuku ko abinci kasa ci yayi haka Dada tayi ta fama dashi akan yaci abincin har ta gaji ta watsar dashi ta cigaba da ƴan sabgoginta. Ita bata san yadda yake ji ba shi yasa ta dameshi da batun wani abinci ko ance mata yana da ntsuwar da zai iya zama yaci abinci ne. Tun bayan azahar ya tashi ya shirya a cikin wata dakakkiyar shadda kalar light brown sai aka yi mata aiki da zare kalar coffee a irin waɗanda ya ɗinka ne, sosai yayi kyau ya fito cikakken namiji tsaf gashi dama tubarkallah Allah yayi mishi siffa irinta cikakken ɗa namiji gashi da wani irin kyau, sai abun ya haɗu da iya gayu da tsafta. Turarukanshi ya ɗauka ya feshe jikinshi dasu, wayarshi ya ɗauka ya fita parlourn Dada yana zaman jiran isowar Salim don ya matsu su bar gidan ko sun je suyi abinda ke gabansu yasan matsayin soyayyarshi da Zainab. Bai daɗe da zama ba Salim ya iso shima cikin shiga irinta Baqeer. Dada na ganinshi tace "Hala gaisuwar surukai zaku shi yasa kuka yi gayu haka." Murmushi Salim yayi yace "Ashe bai faɗa miki ba, mahaifin Zainab zamu je mu gaisar," shi kuwa Baqeer cewa yayi "da bama kwalliya sai zamu wani wuri." Harararshi tayi tace "Idan nayi magana daga kai har Zainabu kuce ba haka ba ashe ni kuka ninke baibai, to Allah ya tabbatar mana da alkhairi wallahi naji daɗi." "Ameen," Salim yace. Ƙara kallonsu Dada tayi tace "Ai gara ku hanzarta ku tafi kada suyi ta jiranku, idan kun je ku cewa Zainabu ina gaisheta akwai kuma tamu ni da ita zata zo ta sameni har gida naji dalilin wannan ƙunbiya-ƙunbiyar." Dariya Salim yayi yace "zan kuwa faɗa mata Dada, sai mun dawo." Tunda suka fito babu wanda yayi magana, shi dai Salim ganin kamar Baqeer baya cikin nutsuwa yasa yayi shiru da bakinshi ya ƙyaleshi yaji da damuwar shi, shi kuwa Baqeer tunanin bai san abinda zasu je su riske ba ne yafi tsaye mishi a rai, yasan zai yi wahala su samu karɓuwa a wajen mahaifin Zainab. Anan cikin unguwar suka tsaya a masallaci suka yi sallar la'asar, haka Baqeer yayi ta gaisawa da mutane suna yi mishi jajen abinda ya faru. Bayan sun fito daga masallaci Salim na turashi suka ƙarasa gidan su Zeey. Ciro wayarshi yayi ya ƙirata, tana ɗauka yace mata "Gamu a ƙofar gida." "Okay bari nazo na shigo daku," kawai tace ta ajiye wayar. Basu wani daɗe suna jiran ba sai gata ta fito cikin material ɗin daya ɗinka mata. Kallon-kallo suka hau yi zuciyoyinsu cike da bege da ƙaunar juna. Sosai Baqeer yaga ta ƙara yi mishi kyau gashi kayan sun karɓeta kamar yadda yayi hasashe. Salim ne ya katse kallon-kallon da suke yiwa juna yace "Hajiya Zeey barka da yamma." A kunyace tace "barkanmu dai, ku shigo." Tayi gaba suka bita a baya. A parlourn karɓar baƙin Alhaji Suleiman ta sauke su, sai da ta zauna suka ƙara gaisawa da Salim sannan ta kalli Baqeer ta sakar mishi wani ƙayataccen murmushi tace "Ya Baqeer ina yini," cikin wani salon magana da ita kanta bata san ta iya ba kawai dai ta tsinci kanta dayi. Lumshe ido yayi ya mayar mata da murmushin kwatankwacin irin wanda tayi mishi yace "I'm fine and you?" Karkata kai tayi tana dariya tace "Lafiya lau, sai dai fa ban yi tunanin da gaske zaka zo ba." "Me yasa?" Ya tambayeta yana tsatsareta da ido. Ɗan kawar da kanta tayi daga kallonshi da yake neman kassara mata jiki tace "Saboda jiya ka nuna min ba zaka iya pursuing ɗina ba." Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ina sonki Zainab har ban san yadda zan kwatanta miki ba amma ina tantama idan mahaifinki zai amince ya bani aurenki, kin dai san komai ba sai na faɗa miki dalili ba." "Kasancewarka tare dani ne abu mafi muhimmanci da nafi buƙata, ni kai kaɗai nake so kai kaɗai kuma zan iya aure don haka kada kasa damuwar komai a ranka In Sha Allah bazan bari kowa ya rabamu ba." Sun daɗe suna musayar kalamai kafin ta tashi ta shiga cikin gida akan zata faɗawa Daddy zuwansu. Kitchen ta fara shiga ta bada umarnin akai kayan motsa baki guest sitting room ɗin Daddy sannan ta shiga ɗakin Mummy tace mata ta faɗawa Daddy ga baƙin sun zo. Ɗakinta ta shiga tana addu'ar Allah yasa kada Daddy ya basu matsala don ita dai baza ta yarda a rabata da Baqeer ba domin kuwa shine farin cikinta dashi kaɗai zata iya rayuwa. Tunda Mummy ta shiga ta faɗa mishi baƙin sun iso yake baƙin rai, ya daɗe bai tashi ya shirya ba don sai da ya ɓata fiye da mintuna talatin kafin ya tashi ya canja kaya ya fita. Fuska a murtke ya shiga sitting room ɗin, Salim dake zaune akan kujera yayi saurin zamowa ƙasa ya zauna yana gaishe shi. Wani irin kallo Daddy yake yi mishi don ya ɗauka shine manemin auren Zainab ɗin. Shima Baqeer ya shiga gaisheshi cikin girmamawa. Kallo ɗaya yayi mishi ya mayar da kanshi wajen Salim yace "Kai ne mai san ƴata?" Girgiza kai Salim yayi yace "A'a bani bane abokina ne Baqeer," yace yana nuna Baqeer dake zaune akan wheelchair ɗin shi. Daddy bai san lokacin da ya miƙe tsaye ba yace "What? Gurgun? Gurgun ne ke neman auren ƴata?" Yace yana nuna Baqeer da ya sandare a zaune da ɗan yatsa. Da gudu Mummy ta ƙaraso cikin parlourn don taga me yasa Daddy ihu irin haka. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *UmmAsghar Ce* *Da* *Ayushe Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA UKU* {83} Zee sam ta kasa zama sai zarya take yi zuciyarta ta kasa nutsuwa, Mummy ce ta riƙe hannayenta tace "Kar ki damu auta komai zai tafi daidai." A hankali ta jinjina kai alamar eh sannan tace "Matsalar nakasa da nace miki yana dashi ne bana so Daddy ya wulakantashi saboda wannan, nasan halinshi," ta ƙarasa maganar tana neman shiga falon, da sauri Mummy ta sake riƙota tace "Kar ki shiga shi kanshi Baqeer ɗin ba daɗi zai ji ba in ya ganki." Da mamaki ta kalli Mummy, ya aka yi tasan sunanshi? Don a iya saninta bata taɓa sanar da ita wanene wanda take so ba, baki ta buɗe zata yi magana suka jiyo muryar Dady daga falo yana cewa "Gurgu? Kai wannan wasa ne bana son shirmen banza da wofi, ni? Kamar ni gurgu mara ƙafa zai zo yace yana son ƴata? Uban waye ya tsaya maka da har ka rainani zaka tako kazo cikin gidana?" Baqeer kalaman Daddy sun kai shi maƙura sai dai wahalar da Zainab tayi dashi ne yake tunowa, hakan yasa ya daure don kalaman Alhaji Sulaiman ba ƙaramin ɓata mishi rai suka yi ba, gurgu ba mutum bane kenan ko me? Daddy yana hura hanci yace "Kai kaga mun yi maka kama da inda zaka zo da kekenka? Dalla fita ka bar min gida kafin nasa securities su fitar min da kai." Zee ce ta shigo ciki da sauri, daidai nan Baqeer ya saki wani murmushi yace "Ashe girma bai sa ka canza halayenka ba." Waigowa yayi ya zabgawa Baqeer wani mugun kallo yace "Me kace?" Kai kawai ya girgiza yana ɗagowa suka haɗa ido da Zainab, murmushin takaici da tausayawa kansu yayi, lallai daya sani da ya riƙe son da yake yi mata a zuciyarshi tabbas da yasan ƴarshi ce da ya gwammace ya nuna baya sonta a ƙalla zata auri wanda yake sonta wanda zai kula da ita kamar Junaid. Shi da budurwarshi ta gujeshi ma da wannan larurar ta sameshi ina ga Alhaji Sulaiman? "Me kace nace? Kai dalla ja keken guragunka ka bar min gida kaje can bakin titi nan ne ya dace da kai, ni ko mai gadin gidana gurgu bai kai yayi ba bare auren tilon ƴata," Yana kumfar baki yake maganar bai jira komai ba ya cigaba "In dai har Zainab zata kawoka a matsayin wanda take so to tabbas asiri kayi mata, wawan banza wawan wofi kai dai kayi asara wallahi....." Zee ce tace "Ni nake sonshi Daddy," tayi maganar idanuwanta na kan Baqeer, a fusace ya zabga mata wani kallo, fuskar nan tashi duk ta sake canzawa yana ƙara kumburota yace "Me kika ce?" Ta maida kallonta kan Daddy tace "Ni nace ina sonshi, laifi ne?" Baqeer ne ya katseta da cewa "Koma ciki." Kallonshi tayi kamar zata yi kuka, kai ya jinjina mata alamar babu komai, hannu tasa ta shafi fuskarta sannan ta juya, mamaki ya kama Daddy ganin duk gardama irinta Zee gashi tana abu babu musu, ai kamar an fusatashi yace "Waye ubanka? Sannan mema abokinka yace sunanka?" Baqeer ya haɗiyi wani yawu yace "Baqeer sunana." Yanayin Daddy ne ya canza zuwa mamaki yace "Baqeer?" Nan da nan ya tuno zuwan Badaru gidanshi akan ɗan shi yasa yaronshi hatsari, abinda ba zai iya tunawa ba yace ƙafar shi ta saku matsala ko bai faɗa ba? Don shi a trayuwarshi ma bai taɓa jin sunan Baqeer ba sai da Badaru ya sawa ɗan shi, bai mantawa sanda aka sa sunan har sai da yace menene ma'anar Baqeer? Kai ya girgiza don tabbas yasan ba dai ɗan Badaru ba. Cike da zargi Alhaji Sulaiman yace "Ba dai zaka ce min Alhaji Badaru ne mahaifinka ba?" Yanda Baqeer ya kalleshi ne yasa yayi baya ya zauna akan kujera, sai kuma ya miƙe yana haɗe yatsunshi yace "Wai yaron Badaru ne Baqeeru? Ka gaggauta fitar min daga gida ko sai nasa an kulleka, kai dan gidanku ni sa'anka ne? Ko nayi maka kama da wanda zaka zo ma kace kana son ƴa ta? Ba ma gurguntaka kaɗai ba yaron Badaru? Yaron Badarun ma ɗan iskan yaron da ka ja mana tashin hankalin da aka yi mana tsakani?" Cikin ihu yake maganar wanda yasa Zainab dawowa. Baqeer ne ya kalli Alhaji Sulaiman dake kumfar baki yace "Zan ƙara sanar da kaina, nine Muhammad Baqeer Badaru wanda yake son ƴarka Zainab......." Cikin hanzari Alhaji Sulaiman yayi kanshi a fusace don ranshi ya ƙara ɓaci yana ji zuciyarshi har wani tafasa take yi, Zainab har tayo ciki don ta tare sai taji Baqeer yace "Daddy!" Cak Alhaji Sulaiman ya tsaya, eh lallai Baqeer ya gama raina mishi hankali, yama rasa ta inda zai fara ci mishi zarafi, ya zai yi ya tozarta Baqeer yanda ya gama ci mishi mutunci, komawa yayi ya zauna ya kalli Baqeer kawai kafin yace "Daddy?" ya saki wani murmushin takaici sannan ya ɗauki waya ya danna, wani yake kira yace "Naga kasuwarku ɗaya da Badaru ko zaka kirashi kace yazo ya ɗauki nakasasshen ɗanshi da yazo bara gidana?" Yana kashe wayar ya kalli Baqeer yace “Daga Badaru har uwarka wannan karon sai na tozartaku mutanen banza mutanen wofi.” Baqeer kallon Daddy yayi don kalamanshi sun kai shi bango, ƙasan leɓenshi ya ciza don duk yadda yaso ya daure da ɓacin ranshi ya kasa, abubuwan da suka faru baya ke sake dawo mishi tun kafin Alhaji Sulaiman ya tara musu jama'a gwara su bar gidan, kallon Salim yayi wanda gaba ɗaya kana kallonshi zaka san cikin takaicin abinda yake faruwa yake, kai ya ɗaga mishi alamar su tafi, shi kanshi Salim baya ji zai iya cewa Baqeer ya cigaba da zama, Zee wacce Mummy tayi saurin riƙeta ya kalla, ya kauda kai kawai ya fara tura kekenshi, hankali a tashe tace “Ya Baqeer!” Ta kira sunanshi tana tahowa inda yake bayan ta ƙwace hannunta daga cikin na Mummy, hawaye ne fal cikin idanuwanta tana zuwa inda yake suka zubo ta ƙara cewa “Ya Baqeer!” Wani murmushi yayi mata wanda kana ganinshi kasan na menene sannan ya cigaba da tura kekenshi, tana neman binshi taji Daddy yace “Wallahi kina fita sai dai ki nemi wani uban ba ni ba.” Waigowa tayi da mamakin halayen shi ta zuba mishi ido tana tunanin ma me ya kamata tayi. Baqeer bai ko ƙara waiwayensu ba ya ja kekenshi kawai Salim ya turashi don ma suyi saurin fita. Zee hawaye tasa hannayenta ta share tana kallon Daddy da har yanzu bai gama masifar shi ba tace “Ka shirya ganina a cikin gidan nam har na mutu kuwa don Dady ka sanni ka kuma san kafiya ta, ban taɓa son wani ba sai Baqeer kuma shi kaɗai zan aura, in har kana son ganina nayi aure to ka taimaki kanka ka barni na aureshi.” Tana kaiwa nan ta ruga ciki da gudu don ba ƙaramin wulaƙanta ta Daddy yayi ba, ta sani shekarun baya tana yarinya aka yi abun kuma babban abinda ya janyo saɓanin laifin tane da tayi magana tasan da abun bai kai haka ba, in bata manta ba tun daga case ɗin ta fara canza halayenta, ko rai zai ɓaci to fa zata faɗi abinda ta sani abinda kuma ke ranta. Daddy wani takaici ne ya ƙara kamashi ji yake yi ko sanda yaji Nabila ƴar Mummy ce ranshi bai ɓaci ba irin yau, kamar shi? Kuma a rasa ma wa zai ce yana sonta sai Baqeer? Lallai bai taɓa fuskantar ɓacin rai irin wannan ba, ga siyasar shi na kawo kai za’a tantance wanda zai hau takarar wato primary election, shafar suman kanshi yayi yana jin wani ɓacin rai, Mummy ce ta zauna kusa dashi tana shafa gaɓɓan bayanshi tana cewa “Calm down Senate, tsautsayi ne ya afka amma yanzu komai zai warware ai insha Allah, bansan ya aka yi wannan abun ya faru ba.” Kallonta yayi idanunshi kaɗai sun isa kasan ɓacin ran da yake ciki yace “Kina ina har hakan ta kasance? Baqeer? Ni Zainab zata gayyatowa matsiyata cikin gida? Taya ma har ta ganshi har suka fara magana?” Kai Mummy ta girgiza alamun bata sani ba kafin tace “Ni kaina abun ya bani mamaki amma in ka duba laifin na yaron ne, taya zai so Auta? Ta yaya? Ai yasan haɗin ba ɗaya bane.” Tsaki yayi yace “Zancen banza zancen wofi ni ko da ƙafar shi ai wallahi bai kai na bashi ƴata ba bare,” ya ƙarasa maganar cike da ɓacin rai wanda yake ji kamar zuciyarshi zata fito, miƙewa yayi yace “Duk laifinki ne don kece kike barinta take fita, inba haka ba taya ma ta haɗu da shashashan can?” Yaja tsaki ya wuce ciki da ƙarfi ya rufo kofa. Mummy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe tayi ɗakin Zee zuciyarta duk ba daɗi, kuka Zee take yi sosai don abinda Daddy yayi ba shakka tasan shikenan Baqeer ya haƙura da ita don dama tasan tunda yasan wacece ita take tantama amma gashi ya daure yazo an tozartashi. Hawaye ta sake sharewa tana kallon wayarta, kiranshi take son yi amma bata san taya zata fara ba. Ƴar karamar ƙara ta saki daidai nan Mummy ta turo ƙofa. ***** Baqeer kuwa yana fitowa suka yi kiciɓis da Kabiru gabanshi ne yayi wani mugun faduwa, tunani yake ba dai shine wanda ya buge a mota ba? Don in bai manta ba ya bincika kuma ance mishi ƙafarshi ta samu matsala, kar dai shine ya zo kawo ƙara? Shi kuwa Baqeer kallonshi kawai yake yana tunanin Kabiru ne? Salim ne yace “Baqeer are you okay?” Kai ya ɗaga mishi alamar eh, wanda hakan yasa Kabir yaji sunan Baqeer gashi dama yasan yaron Badaru ya bige, innalillahi, yanda yaga Baqeer na mishi wani kallo ne yasa ya tabbatar abinda ya kawosu kenan? Bakinshi na rawa yace “Ba dai Dady kuka zo kawo wa ƙara ba?” Kallonshi Baqeer yayi cike da mamakin kalamanshi sai kuma yayi tunani kila ko yasan yana son Zainab ne hakan yasa yace “Eh, laifi ne?” Kabiru ya matso daf da Baqeer yace “Ka dai sani Daddy ba zai taɓa bani laifi ba sannan kai tsautsayi ne baka sani ba? Nasan nayi laifi amma kaima sanda kake tafiya me yasa baka duba inda kake takawa? Da sai ka fara samuna na baka hakuri in kuma kuɗi kazo nema na baka amma ba wai ka kawo karata ba,” yanda yake magana kaɗai zaka san a ruɗe yake, kalaman da yake yi ba sai Baqeer yayi tantama ba don abinda yake son cewa a bayyane yake, murmushi Baqeer yayi wanda yafi kuka ciwo sannan ya sake kallon motarshi, tabbas motar can ce ya gani sanda ya bugu, idanun Baqeer ne suka canza yanayi ya ciji leɓenshi na ƙasa yace “Sanda ka kaɗeni me yasa baka tsaya kaga halin da nake ciki ba?” Kabir ya haɗiyi yawun bakinshi yace “Ban san mutum bane sai daga baya, amma…” hannu kawai Baqeer ya ɗaga mishi ya kalli Salim yace “Mu tafi,” yayi maganar cike da raunin murya. Tafiya suke kawai zuciyar Baqeer na sake tafasa, sam ji yake kamar kanshi zai faɗo saboda tashin hankalin daya shiga, Salim kanshi ya kasa magana saboda mamakin abubuwan dake faruwa, lallai wannan soyayyar ta Zee da Baqeer kyanta shine kowa bai san kowa ba ayi a rabu a haka amma ina zasu kai wannan ɓacin ran da suka shiga da tashin hankali? ****** Zee kuwa Mummy ce ta rungume ta kawai kuka take yi tana cewa “Mummy yanzu Daddy yayi mini adalci? Yayi wa Baqeer adalci?” Shafa bayanta tayi tace “Kiyi hakuri Zee ni kaina bansan meke damun senate ba, sai dai ya kamata muyi mishi uzuri kin dai san yadda yake ji dake.” Kallon Mummy tayi Mummyn tace “Yadda yake ji dake ne yasa yake haka, kiyi haƙuri zan sake yi mishi magana sannan nasan zai fahimceki in kika nuna son da kike yi mishi.” Kallon Mummy tayi tace “Mummy kiyi mishi magana don Allah bazan auri kowa ba sai shi, in kuma ba haka ba Allah ya shirya zama dani har tsufana.” Kai ta jinjina tana riƙe da ita tace “Na sani, anjima kije ki ƙara sanar dashi ra’ayinki ni ina tare dake ba kuma zan yarda ayi miki auren dole ba, menene a ciki don bashi da ƙafa? Sannan shi faɗan da shikenan bazai wuce ba ko me?” Cike da gamsuwa da maganar Mummy tace “Mummy nagode da kika fahimceni.” Hannu tasa ta share mata hawayenta tace “In ban fahimceki ba wa zai fahimceki?” ****** Badaru cike da ɓacin rai ya sauke wayar da aka yi mishi wai yazo ya ɗauki nakasashen ɗan shi. Me ya kai Baqeer gidan Alhaji Sulaiman? Abu ɗaya ne yazo mishi tabbas Kabir ne ya buge Baqeer kila shine yaje ya nemi hakkinshi, ai kuwa in haka ne dole yaje yaci zarafin Alhaji Salaiman tunda dai saboda shi komai na rayuwarshi ya ruguje sannan yana neman inda zai sauke ɓacin ran da yake ƙunsa kwanan nan. Da wannan tunani ya baza rigarshi ya fito daga ɗakin Jamila. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA HUƊU* {84} Yana tafe fakam-fakam yana saƙar wasiƙar jaki yana ayyana abinda zai yi da kuɗaɗen da zai karɓa a wurin Suleiman Ƙaraye na fansar abinda ɗanshi yayi wa Baqeer. Har ya gama tsara yadda zai kasafta kuɗinshi don wallahi sai an biyashi asarar da aka janyo mishi tunda dai ya tabbata ɗan nashi ne ya kaɗe Baqeer da mota kaɗewar da itace sanadin halin daya tsinci kanshi a ciki yanzu. Yana zuwa gaban gate ɗin gidan ya hau bubbugawa da ƙarfi kamar zai ɓalla ƙofar gate ɗin. A fusace maigadi ya taso yana cewa "Kai da Allah ana zuwa, haba mutane sam babu hankali kazo gidan mutane kana buga ƙofa kamar qanda yazo yaƙi." Yana buɗe ƙaramar ƙofar suka haɗa ido da Badaru dake tsaye sai faman hura hanci yake yi. Yana ganin shine ya tare ƙofar ya hanashi wucewa. A wulaƙance ya kalleshi yace "lafiya?" Don yasan zuwan nan na Badaru ba alheri ne ya kawo shi ba tunda kuwa kowa yasan ƴar tsamar dake tsakaninsu da maigidan. Harararshi Badaru yayi yace "Kauce ka bani wuri na wuce, ni ba da kai zan yi ba da ubangidan ka zanyi don shine tsaran yina ba kai ba." Ƙin matsawa yayi ya bashi wurin kamar yadda ya buƙata sai ma cewa yayi "Tsaya dai anan naje na faɗa mishi kazo amma bazan baru ka shiga ciki ba alhalin wancan zuwan da kayi ka tayar da tarzoma ƙiris baka yi mini sanadin aikina ba." Jayayya ce ta ɓarke a tsakaninsu Badaru ya dage sai dai a barshi ya shiga shi kuma maigadi yace ba zai shiga ba sai dai ya jira yaje ya sanar da zuwanshi idan ance ya shigo sannan zai buɗe mishi ƙofa ya shiga. Hayaniyarsu ce ta fito da Alhaji Suleiman daga cikin gida, tun kafin ya ƙaraso wurin ya shaida muryar Badaru. Yana zuwa yace "lafiya? Me kazo yi a gidana? Idan kuma nakasashen ɗanka kazo ɗauka tuni ya tafi". Wannan kalami na Suleiman Ƙaraye sai ya ƙara tunzura Badaru, a masife yace "Waya nakasa min ɗan nawa idan ba ɗanka ba? Kuma ni zuwa nayi a biyani fansar nakasa ɗana da kuka yi tunda dai ya tabbata ɗanka ne ya kaɗeshi don nasan babu abinda zai kawo Baqeer gidanka sai don a biyashi diyyar ƙafarshi da ɗanka ya nakasta mishi. Waya sani ma ko da gayya kuka nakasta shi don kunga ya taso da basirar iya zane yana daf da tafiya gasar da zata ɗaukaka sunanshi a duniya kowa ya san shi." A sakarce Suleiman Ƙaraye ya kalleshi yace "Har wani ɗa gareka da za'a yiwa baƙin ciki, tun wuri gara kaje ka nemi wanda ya nakasta ɗanka amma ba Kabir ba. Kada kaga kwanaki kazo har gida kayi mini hauka na rabu da kai wallahi idan na sake ganinka a ƙofar gidana sai na ɗaure haka har igiya tayi rara kuma ka faɗawa gurgun ɗanka babu shi babu ƴata ko yana da lafiya shi bai isa na bashi auren ƴata ba bare yana gurgu nakasashe." Mallam Bala rufe mini gate ɗin gidana sannan daga yau idan ka kuma bari mahaukacin nan yazo mini gida a bakin aikinka." Ya shige cikin gida yana bambamin faɗa kamar shi in banda raini ta yaya za ace wai ɗan Badaru ne ke son ƴarshi. Yana shiga Mummy ta taso tace "Senate me ya faru? Tun daga waje nake jiyo faɗanka." Zama yayi akan kujera, tsaki yayi yace"Wancan wawan mutumin mana wai yazo karɓar diyyar nakasta ɗanshi da Kabir yayi." Zama tayi a kusa dasi tace "Badaru wai? Har yanzu bai bar batun Kabir ne ya kaɗe ɗanshi ba duk da an faɗa mishi a ranar da abun ya faru ma Kabir bai fita ba? Wai shin meke damun shi ne?" Tsaki yayi yace"Waya san mishi mana, koda yake duk laifin Zainab ne data rasa wanda zata ce tana so sai ɗan shi in banda haka shi ya isa yazo ƙofar gidana yace zai  kawo mini zancen banza." Dafa kafaɗarshi tayi tana shafawa a hankali zuwa bayanshi tace "Ka daina ganin laifin auta ni na tabbata yaron nan yaudararta yayi in ba haka ba ina shi ina Zainab ka kuma fa san mutane ba wani tsoron Allah suka cika yi ba yanzu haka ba haka nan ya barta ba shi yasa gaba ɗaya ta susuce akan shi don in dai ba aikin asiri ba ban ga ta yadda za'a yi auta ta so gurgu ba gurgun ma ɗan gidan Badaru." "Ni dai na faɗa ko mutuwa zata yi bazan aura mata ɗan Badaru ba, ah ti gara ma ki faɗa nata idan zata haƙura su daidata da Junaid tun wuri daya fiye mata." Tashi yayi ya bar parlourn ranshi yana ƙara ɓaci wai kamar shi ace gurgu ne masoyin ƴarshi gurgun ma ɗan Badaru, Badaru dai da tun asali babu wata jituwa a tsakaninsu. ***** Shi kuwa Badaru ganin an rufe mishi ƙofa ya juya ya kama hanyar gidanshi yana jin takaicin kai kanshi gidan Suleiman Ƙaraye da yayi, shi da yasan wata maganar Baqeer yaje ɗauko mishi me zai sa yaje wannan gidan ya jiyowa kanshi kayan takaici da baƙin ciki. Ace wai duk faɗin garin Kano Baqeer ya rasa ƴar da zai ce yana so sai ta Suleiman Ƙaraye. Tun daga soro yake ƙwala kiran Fatima har ya shiga ɗakinta, tana kwance tana jan carbi bacci ya kwasheta bata sani ba. Kamar a mafarki taji yana ƙwala mata kira, tana buɗe ido sai ta ganshi tsaye a kanta sai huci yake yi. Tashi tayi zaune tana gyara ɗaurin ɗankwalinta daya zame tana bacci. "Mallam sannu da zuwa," tace mishi duk kuwa da taga alamun zuwan nashi bana lafiya bane. Yana daga tsayen yace "Ki faɗawa nakasashen ɗanki ya kiyaye ni wallahi ya fita idona in rufe in ba haka ba sai na wulaƙanta rayuwarshi, in banda rashin mutunci ya rasa ƴar mutumin da zai so sai ta Suleiman Ƙaraye salon ya janyo mini ƙasƙanci da wulaƙanci a wajen shi." Mamaki ne ya kamata tace "Shi Baqeer ɗin ne yake son Zainab?" Tsaki yaja yace "Na dai faɗa miki ki gaya mishi babu shi babu ƴar wannan mara mutuncin mutumin. Haba ƴaƴa sun zama kamar ƴaƴan Allah bani bau guda ɗaya na kirki a ciki kowanne da irin baƙin cikin da yake cusa maka." Bayan fitar shi Umma na zaune tana jin mamakin wai Baqeer ne yake son Zainab, to a ina ma suka haɗu da har ya ganta yaji yana sonta? Ta yiwa kanta wannan tambayar sai kuma ta tuna ashe fa Dada tace mata Zainab ɗin tana zuwa a lokacin abun ya ɗaure mata kai sai dai bata zurfafa tunani ba ashe su soyayya suke yi ba'a sani ba. Shi kuwa Baqeer me ya kai shi bayan yasan akwai daɗaɗɗiyar rashin jituwa a tsakanin iyayensu, ture batun Badaru ma tunda ya kori Baqeer daga gidanshi amma Suleiman Ƙaraye fa ita tasan babu ta yadda za'a yi ya bashi auren ƴarshi alhalin yqna ɗan Badaru. Nisawa tayi ta ɗaga hannayenta sama a fili tace "Allah gamu gareka, idan har akwai alkhairi a taraiyarsu Allah ka tabbatar ka kawar da fitina." Wayarta ta janyo ta kira Baqeer sai dai ta kasa samunshi, haka tayi ta gwadawa bata sameshi ba har ta haƙura ta ajiye wayar akan ta ƙara gwadawa zuwa anjima. ***** Tunda suka bar ƙofar gidansu Zeey hankalinshi yake a tashe, daga shi har Salim an rasa me yiwa wani magana saboda kowa damuwa ce danƙare a cikin zuciyarshi. Shi Baqeer ma abubuwan ne suka taru suka yi mishi yawa ya rasa tunani ƙwaya ɗaya da zai kama. Tun lokacin da yayi accident bai ƙara tunanin wanda ya bugeshi ba don a ganinshi babu amfanin da sanin mutumin daya kaɗeshi zai yi mishi sai yanzu yake tuna yadda accident ɗin ya faru. Tabbas Kabir ne ya kaɗeshi ya janye motarshi ya tafi ya barshi a kwance a wurin, duk da bai ga fuskarshi ba amma ya gane motar tabbas ita ce motar da yake hawa yana baɗesu da ƙura idan yazo wucewa. A daidaita Salim ya tarar musu suka shiga ba tare da sun faɗa mishi inda zasu ba, sai da suka fara tafiya sannan Salim ya faɗa mishi mariri zai kai su ai kuwa ya yanka musu kuɗin da zasu biyashi, amsawa kawai Salim yayi don baya cikin yanayin da zai tsaya yin jayayya dashi. Lokaci zuwa lokaci Baqeer yake sauke wata ajiyar zuciya, ga wata irin rawa da yaji jikinshi ya ɗauka ga alama dai zazzaɓi ne yake neman kamashi. Tashin hankalin daya tsinci a ciki ba zai faɗu ba, a yadda Zainab ta shiga ranshi bai hango ta yadda zai iya rabuwa da ita ya zauna lafiya ba. Wannan wacce irin rayuwa ce? Ace akan abinda bai taka kara ya karya ba, saboda wani saɓani daya shiga tsakanin iyayensu a shekarun baya za'a hanasu samun farin cikin su. Kallon ƙafafuwan shi yayi sai kuma yayi wani murmushi mai ciwo cikin ranshi yace 'What do you expect? Kana tunanin kowa ne zai ganka akan wheelchair ya amince ya baka auren ƴarshi.' Shi yasan ko babu matsalar kasancewar Badaru mahaifi a gareshi to wannan nakasar kaɗai ta isa tasa a hanashi aure to bare kuma ga babban ƙalubalen Mallam Badaru daya kasance uba a wajenshi abokin adawar mahaifin Zainab kuma. Har suka isa gida Salim ya taimaka mishi ya fita daga cikin adaidaitan ya zauna akan wheelchair ɗin shi, hannu yasa ya gara tayoyin ya shige cikin gida bai tsaya jiran Salim dake sallamar mai adaidata ba. Yana shiga ya wuce Dada dake zaune a tsakar gida tana gyaran zogale zata yi musu kwaɗo in anjima. Kan katifarshi kawai ya faɗa ya kwanta a rigingine yana kallon rufin ɗakin, wasu ƙwalla ne suka taru a idanunshi sai dai ya hanasu zubowa. Cikin ranshi yana jin ciwo da nakasar shi ta kasance abu na farko da zai sa a hanashi aure kamar mutane sun manta ai da ba haka yake ba ƙaddara ce ta afko mishi kuma babu wanda ya wuce ta faɗa a kanshi shima. Salim ne ya shigo ya zauna a gefen katifar yana kallon Baqeer da lokaci guda duk ya zabge ya rame kamar wanda ya kwanta jinya. Tausayin shi ne yaji ya kamashi, a cikin lokaci ƙanƙani matsaltsalun rayuwa sun saka shi a gaba daga wannan sai wannan kamar baza su wuce ba sai dai yasan komai mai wucewa ne kamar yadda wancan ya wuce haka nan wannan ɗin ma zai wuce sai dai shi kanshi bai ji daɗin yadda mahaifin Zainab yayi musu ba kamar ya manta Allah ne mai tsarawa kuma shi ya ƙaddari baqeer ɗin da kasancewa haka da zai zaunar dasu yana faɗa musu maganganu na ɓatanci son ranshi. Kallon Baqeer ɗin yayi yace "Kayi haƙuri Baqeer nasan abinda mahaifin Zainab yayi mana da ciwo amma haƙuri zaka yi please kada kasa abun a ranka yayi ta damunka, a yadda nasan Zainab na sanka nasan ba zata taɓa yarda a rabaku ba." Bai cewa Salim komai ba don shi kaɗai yasan abinda yake ji a cikin eanshi, wani irin ƙuna yake ji da bai san ta yadda zai iya fasaltaw ba. Yasan ba Zainab ba kowacce mace yace zai nema wannan nakasar ita zata zame mishi cikas don ya san babu uban da zai ɗauki ƴarshi ya bawa gurgu. Idan yayi wannan tunanin ne hankalin shi yake ƙara tashi, shi kenan shi nakasashe ba mutum bane da za'a dinga gudun shi irin haka kamar wani annoba. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *UmmAsghar Ce* *Da* *Ayushe Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA BIYAR* {85} Kabir yana shigowa ɗaki ya shiga ya dinga zarya a cikin ɗakin, tsoro duk ya hanashi sukuni, daga cikin ɗakin yake jiyo fadan Daddy akan zuwan Badaru, hankalinshi ne ya ƙara tashi ya leko ya ɓoye a jikin ƙofa yana ji Mummy na kareshi, Daddy ranshi a ɓace ya shiga ɗaki bai daɗe ba sai gashi da key ya fito ko kula Mummy bai yi ba yayi waje, taya ƴar yafi so a rayuwarshi zata janyo mishi ɓacin rai haka? Dan ƙaunar da Daddy yake yiwa Zainab a bayyane take kawai baya son nunawa ne amma ita kanta Zee ɗin ta sani. Yana fita Kabir ya fito kana kallon yanayin fuskarshi zaka san lallai yana cikin tashin hankali don idanuwanshi duk sun jame, bakinshi na rawa yace “Mummy yaron nan zuwa yayi maganar bugeshi da nayi ko?” Kallonshi tayi tace “Muje ciki.” Tayi maganar tana kallon ɗakin Zee wanda taga alamun za’a buɗe, ɗakin Mummy suka yi yana shiga yace “Mummy meke faruwa? Zancen bugeshin da nayi ne?” Ajiyar zuciya tayi tana ɗan kallon ƙofa don basu rufe ba tace “Kabir ba wannan ya kawo shi ba sai dai yanzu in har aka san abinda kayi bayan abinda ya faru to lallai akwai gagarumar matsala.” Cike da rashin fahimta yace “Ba hakan bane?” Hannu tasa ta shafi fuskarta tace “Gaisuwar surukai yazo Zainab yake so.” Ido ya zaro hankali a tsananin tashe yace “What? Zainab? Bata da hankali ne zata ce tana son Baqeer? Gurgu ne fa? Sannan taya zata wulaƙanta mutane da yawa tace yaron nan take so?” Gaba ɗaya magana yake yi cikin ɗaga murya yana yi yana tafiya yana yarfe hannu don mamakin abun nan ya isheshi wai Zainab, Mummy ce ta kalleshi tace “A bar maganar Zee nasan shi yana sonta, yanzu me kake tunani zai faru in har tasan kai ka bugeshi, in har tasan kaine silar rasa ƙafar shi da yayi. Ƙofar da aka ƙarasa turawa itace tasa su waiwaya su kalli wurin, Zainab wacce jin fitar Daddy yasa ta fito don ta yiwa Mummy magana akan zata je ta bawa Baqeer hakurin wulaƙancin da Daddy yayi mishi kunnuwanta suka jiye mata wannan mummunan labarin, hawaye ne kawai suke gudu a saman kuncinta don kamar wanda ake korosu haka suke zubowa, Mummy da Kabir ma hankali a tashe suka kalleta, da sauri Mummy ta nufo inda take, hannu ta ɗaga mata alamun karta ƙaraso inda take sannan ta juya da sauri daga ita sai material ɗin ɗazu sai ɗankwalin kanta, ta fizgo mayafi da wayarta, kallon drawer ɗin gefen gado tayi ta ɗauki key ta fito da sauri, Mummy ce tace “Zainab!” Ko kallonta ba tayi ba tayi waje da gudu, mota kawai ta shiga mai gadi ya buɗe ta fita daga gidan da gudu, gudu kawai take don saura kaɗan ta buge wani mai yalo dake tura baro, birki ta taka da ƙarfi ta kifa kanta a sitiyari tana maida numfashin dake fita da sauri da sauri, da ƙyar ta iya buɗe ƙofa ta fito ta bawa mai yalo haƙuri sannan ta komo mota, tana tafe kuka kawai take yi. Ina zata kai son Baqeer da tausayinshi? Taya za’ace yayanta shine ya ja mishi abinda ya faru dashi? Hawaye kawai take yi tama rasa ta ina zata fara tunanin abun yi, tausayin Baqeer ne fal cikin ranta wanda take ji ya riga ya gama bin duk wasu gaɓoɓi dake jikinta. Bata san inda take jan mota ba don tuƙi kawai take yi, ga mamakinta sai ganin kanta tayi a ƙofar gidansu Dada, kanta kawai ta kwantar a kan kujerar ta runtse ido, to ita dama ina take dashi na wurin zuwa banda nan? Kasa fita tayi daga mota sai hawaye kawai da take yi, tafi minti sha biyar a haka sai kuma taji zuciyarta na son ganin Baqeer yanzu kam ta tabbatar babu ita babu shi don in har yasan Kabir ne ya ja mai nakasa to fa ita dashi kila har abada. Ciki ta shiga ta tsaya daga daidai ƙofar shiga tana goge fuskarta, sai dai idanuwanta kaɗai  zaka kalla kasan tasha kuka, tana shiga taji Dada na faɗa tana cewa “Mutum sai kace yaro, komai aka baka kace baza kaci ba, in har kaje gaisuwar surukai ba’a dace zuwan farko ba ai haƙuri ake yi sai a ƙara gwadawa, to ni dai ga abincinka nan in kaga dama sai ka buɗe ɗakin,” tana kaiwa nan ta ajiye kwanon a bakin ƙofa tana waigowa taga Zainab a bayanta, da sauri Zainab ta rungumeta kamar dama jira kukan da take so tayi yake kawai ta fashe da kuka. Kuka take yi wanda in kaji sai ka tausaya mata, shafa bayanta kawai Dada take yi cike da tausayin halin da suke ciki wanda ita aka barta a duhu bata san meke faruwa ba. Tun daga ciki yake jiyo kukan wanda ya ɗaga mishi hankali, saukowa yayi daga kan gado ya hau kekenshi zuciyarshi na wani irin zafi ji yake kamar yaje ya rungumeta ya bata haƙuri, turo keken yayi cikin sauri yazo daf da jikin ƙofa hannu yasa ya buɗe ƙofar din zuciyarshi ta kasa haƙuri da abinda yake ji, da yake tana rungume da Dada fuskarta tana kallon saitin ƙofar ɗakin, cike idanuwanta suke da ƙwalla take kallon ƙofar da aka buɗe sai dai bai leƙo ba. Dada ce jin shirunta yasa ta zareta daga jikinta tace “Ba komai In Sha Allahu zai yarda shima Baqeer ba laifi yayi ba Allah ya ƙaddaro mishi hakan,” tayi maganar tana kallon inda Zee ke kallo, ganin Baqeer ya buɗe ƙofa yasa tace “Asha na manta na bar abu a kitchen,” tayi maganar tana yin kitchen ɗinta dake waje. Zee a hankali take takawa har jikin bangon ɗakin tsugunawa tayi ta ɗauki kwanon abincin da Dada ta ajiye, ba tare da ta miƙe ba ta ɗago suka haɗa ido, idanunshi yayi ja sai dai ita idanunta cike suke da hawaye wanda suka sauko daidai sanda ya kalleta, sharewa tayi tana murmushi tace “Mantawa nayi ban tambayeka ya ka ganni ba bayan kaji wacece ni,” tayi maganar cikin hawayen da take ta ƙoƙarin tsaidawa, yanayin maganarta kaɗai zai sa kasan lallai tana cikin babban damuwa, murmushin yaƙe yayi yace “Shi yasa ban ganeki ba Abulele.” Ta jinjina kai tana goge fuskarta tare da yin wata dariya mai cike da ban tausayi tana cewa “Me na canza?” Shima murmushin yayi yace “Komai, sai dai da alama ba kya cin abinci ne yasa kika rame haka.” Ta ƙara yin ƴar ƙaramar dariya tana jan hanci tace “Randa na fara ganinka nima ban ganeka ba.” Kai ya jinjina don yana ji in har yayi magana zata fahimci rawar da muryarshi keyi, ta sadda kai tace “Da wannan, da kuma girma,” tasa hannunta kan hannun kujerar guragun, kai ya sake jinjinawa yana cewa “Umm!” Hannu biyu tasa tana maida kwallarta tare da goge ƙasan idanunta tace “Da alama bazan ƙara ganinka ba ko?” Kai ya ɗaga mata alamar eh, ta haɗiyi wani abu mai ɗaci tace “Hmm na sani, amma kayan da aka bani an bar mun ko?” Kai ya ɗaga mata alamar eh, gaba ɗaya tausayin kansu ya isheshi. Murmushi tayi ta miƙa mishi kwanon abincin da ɗaya hannunta na dama wanda tasa kwanon a saman cinyarta, hannu ya kai ya amsa yasa a jikinshi. Kallon juna suka yi ta miƙe tsaye tana haɗiyar wani abu mai ɗaci wanda ta rasa daga ina yake ziyartar makogwaronta, da sauri ta juya baya don ji take baza ta iya riƙe hawayenta ba, Ya Kabir bai kyautawa Baqeer ba, an san da tsautsayi, ya zata yi ta sanar da Baqeer akan Kabir ne ya janyo mishi zama gurgu? Dada dake kitchen duk jikinta yayi sanyi ita kam meke faruwa da har yayi zafi haka? Ta ɗauka kawai dai iyayenta ganin gurgu ne shi yasa suke jinkirin basu ita amma yanzu ta fara tunanin akwai abinda yafi haka. Zee ce ta waigo suka haɗa ido da Baqeer kowannensu abinda zuciyarshi ke aika mishi daban, saƙo ne mai zafi da ƙuna wanda muhimmancin junansu da ƙaunar da suke yiwa juna ya tarwatse lokaci ɗaya. Kasa jurewa tayi kawai ta juya da sauri ta fita, ƙofar kawai Baqeer ya maida ya rufe ya jingina da ƙofar tare da runtse ido, ta ina zai fara? Lallai babu inda soyayyarsu zata kai, laifin da ya aikata aka kulle Badaru a cell sai da yayi kwana ɗaya ana biyun aka sallameshi kaɗai ba zai bari a bashi aurenta ba. Abubuwan da suka faru a baya ne suke dawo mishi…….Itama Zainab tana shiga mota taja tana tafe abubuwan da suka faru ke dawo mata. Tuna Baya…… Asalin iyayen Alhaji Suleiman ƴan Ƙaraye ne sai dai zama daya dawo dasu cikin garin Kano. Mahaifinshi mai kuɗi ne don babban ɗan kasuwa ne a kasuwar kantin kwari. Shi kuwa asalinshi ɗan cikin birnin Kano ne, anan unguwar aka haifi iyayenshi da kakanninshi anan suka taso suka girma har suma suka yi nasu gidajen anan cikin unguwar, bai san wani wuri da zai kira da asalinshi ba bayan nan. A rayuwar Badaru babu abinda yake ƙauna irin karatun boko gashi Allah yayi mishi baiwa da iya zane, tun yana zane akan ƙasa ko ya samu gawayi ya zane sumuntin dakalin gidajen mutane har ya fara sayen pencir da littafi yana yin zanen akan takarda. Yaso mahaifin shi ya barshi yayi karatun boko inda zai faɗaɗa ilimin shi akan harkar zane mahaifin nashi yaƙi, babu irin roƙon da bai yi mishi ba amma sam yace ɗanshi ba zai je makarantar boko inda ake koyawa yara kafurci ba. Haka nan ya haƙura ba don ranshi yaso ba sai don babu yadda zai yi, sai dai duk da hakan bai rabu da yin zane ba yana yi yana ajiyewa a cikin kayanshi ba don zasu yi mishi wani amfani ba sai don zanen yana sanya shi nishaɗi shine abu guda ɗaya da yake ƙaunar yi a rayuwa. A farko farkon rayuwarsu Badaru da Suleiman Ƙaraye abokai ne saboda gidajen iyayensu dake maƙwabtaka da juna sai daga baya abotar tasu ta fara ja baya saboda shi Suleiman yana ganin Badaru bai yi karatu ba don haka bai kai yayi abota dashi, ba to shima Badaru da yake ya kasance mutum ne mai tsananin zuciya yasa ya janye jikin shi daga Suleiman don ba zai ɗauki ƙasƙanci da cin fuskar da yake yi mishi ba duk suka haɗu a hanya ko wani wuri dai haka. Haka dai suka sake abokai kowa yana yi da daidai shi ba kowane lokaci suke gaisawa ba sai ta ƙure. Ana cikin haka ne Badaru ya haɗu da wata yarinya daya mato a soyayyarta, son Uwani yake yi bil haqqi da gaskiya. Kullum sai yaje zance wurinta saboda baya iya yin kwana ya yini bai sanyata a idanunshi ba. Kusan kowa dake unguwar yasan da soyayyar Badaru da Uwani saboda ita ma anyi dace bata kula kowa sai shi, duk wanda zai je wurinta yace yana sonta a take zata sallamesu tace akwai wanda take so, tace dole ta taya Badaru kishin kanta saboda bai rageta da komai ba, komai ya samu nata ne, kafin ya yiwa kanshi hidima sau ɗaya yayi mata sau goma don haka take tattalin farin cikin shi take gudun abinda zai ɓata mishi rai. Ana haka har iyaye suka shiga maganar aka yi musu baiko. Tuni Badaru ya tayar da ginin gidanshi, yana ta shirin aurenshi da Uwani da aka saka rana har shekara biyu zuwa lokacin ya gama ginin da yake yi. Wata rana Suleiman na zaune a majalisar da suke zama shi da abokanshi Uwani tazo wucewa. Yana ganinta yaji ta kwanta mishi don haka ya nemi sanin gidansu a wajen abokanshi anan suke faɗa mishi ai budurwar Badaru ce don anyi musu baiko ma ranar auren kawai ake jira a ɗaura. "Ai dai baca riga an ɗaura ba ko?" Yace yana kallon abokinshi da yayi maganar. Da kai ya amsa mishi. "Ku zuba ido kuyi kallo ni na faɗa muku ba dai yarinyar can ta auri Badaru ba idan har ban sameta ba sai dai duk mu taru mu rasa gaba ɗaya.” Wannan alwashin da yaci ne yasa yana tashi daga wurin bai dire ko ina ba sai a ƙofar gidansu Uwani yasa aka yi mishi sallama da ita. Da farko ta ɗauka Badaru ne yazo duk kuwa daba lokacin zuwan shi bane sai data fito taga wani mutum da bata taɓa gani ba. Haka dai Suleiman yayi amfani da wayewarshi irin ta ƴan boko ya tsara Uwani, tun tana ƙin kulashi har tazo bata san lokacin da ta fara son shi ba. Haka tayi ta yiwa Badaru halaye har dai daga ƙarshe ta fito ta nuna mishi ita fa ba zata aureshi ba don ta samu miji ɗan boko daya ƙware a iya gayu da ƙwalisa. Hankali a tashe Badaru ya baza neman saurayin da ya hurewa Uwani kunne har take neman guje mishi, anan yake jin ai Suleiman ne saurayin da take cewa tayi ɗan boko, baƙin ciki kamar ya kashe Badaru don a rayuwa idan akwai wata da yake so to Uwani ce, shine Suleiman zai je ya hure mata kunne ya rabashi da ita. Itace ya ɗauka ya nufi majalisar dasu Suleiman ke zama, yana zuwa wurin ya ɗaga itace zai kwaɗa mishi aka tattare aka hanashi. Badaru ya ƙara harzuka yana masifa yaa cewa Wallahi yau ko shi ko Sulaiman dan sai sunyi kunar bakin wake. Hankalin Sulaiman ya tashi ganin da gaske Badaru yakeyi zai halaka su, nan fa aka fara bashi baki. Haka yayi ta ɗurawa Suleiman zagi yana cewa sai yaga bayanshi tunda ya rabashi da masoyiyarshi tace bata son shi bayan daf ake da ɗaura musu aure. Wannan abun da Suleiman yayi wa Badaru ne yasa suka ƙara ƙullatar juna ƴar gaisuwar da suke yi ma tuni suka daina. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA SHIDA* {86} Wani abun Allah shi kanshi Suleiman ɗin da yayi ƙwacen budurwa sai kuma yazo bai auri Uwanin ba duk da tsananin son daya samu kanshi yana yi mata don da farko da niyyar yaudara yaje mata bare da yaji ance ita ce wacce Badaru zai aura sai yaga ai kawai bari yaje ya tarwatsa abun amma tun tafiyar bata yi nisa ba ya afkawa sonta mai ƙarfi. Sai kuma Mahaifin shi yace ba zai aureta ba saboda ta fito daga ƙaramin gida ma'ana iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne shi kuma yana ganin ai ɗanshi yafi ƙarfin yayi aure a irin wannan gidan. A haka Uwani tayi ba wan ba ƙanin karatun ɗan kama. Ita bata auri Badaru ba da yaso ta da dukkan gaskiyarshi saboda ta samu Suleiman ɗan gayu ɗan boko da take ganin yafi Badaru komai yace yana sonta, a ganinta irin wannan damar sau ɗaya take zuwa a rayuwa idan tayi sake ta rasashi ba ƙaramar asara zata tafka ba. Sannan ita bata auri Suleiman ɗin ba don iyayenshi suna ganin yafi ƙarfinta. Sai kuma daga baya ta dawo wajen Badaru shi kuma yace taje ya barwa Suleiman. A Ɗambatta makarantar da aka turashi bautar ƙasa ya haɗu da Hafsatu a lokacin tana aji biyar na secondary shi kuma yana ɗaukarsu darasin English. Suleiman yana ganinta yaji ta kwnta mishi a rai, tun bayan rabuwarshi da Uwani bai sake gain macen data shiga ranshi farat ɗaya ba irin Hafsatu. Bai ɓata lokaci ba ya gabatar mata da kanshi ya miƙa mata ƙoƙon barar soyayyarta. Sai aka yi dace itama ya kwanta mata don haka bai sha wata wahala ba wajen yaɗa manufarshi. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fara soyayya, babu daɗewa iyayen Suleiman suka nema mishi auren Hafsatu don koda suke a ƙauye ta fito daga babban gida irin wanda mahaifin Suleiman ke so don haka aka saka rana bayan ta gama makaranta da sati biyu. Anan unguwarsu mahaifin shi yayi mishi gini mai kyau a jikin gidan shi, kasancewar Suleiman tilon ɗanshi yasa yake gatata shi fiye da ƙima. A wannan lokacin matan Badaru uku, Jamila ce uwargida sai Abu sannan ya auri Fatima daga baya saboda daga Jamila har Abu ƴaƴa mata suke ta haifa mishi shi kuma namiji yake so shi yasa ya kasa haƙuri yana ganin kamar su ɗin basu da cikin haihuwar ƴaƴa maza. Fatima na zuwa ta samu cikin Baqeer wanda tsiransu da Kamalu wata uku ne itama Abu ta haifi ɗa namiji. Tunda Fatima ta haihu Badaru ya ɗauki son duniya ya ɗorawa Baqeer komai ya samu Baqeer, tun bai fara cin abinci ba ake sayo mishi kayan ƙwalama ya hana asauran ƴaƴanshi idan Fatima tayi magana yace ba haka ba wani sa’in har burin Allah ya isa yake mata in dai tabawa wani abu. Wannan bambancin da yake nunawa ne yasa sauran matan suka tsani Fatima da ƴaƴanta don Badaru ya fifita su akan su da nasu ƴaƴan don ko da Abu ta haifi Kamalu bai nuna wani farin ciki ba sai ma cewa da yayi sai yanzu zata haifa mishi namijin bayan ya riga ya samu, ranar suna baiji kunyar yankawa Baqeer katan rago ba shi kuma Kamalu aka yanka dan akuya karama. Tunda Badaru ya ƙyalla ido yaga Baqeer yayi gadon baiwarshi wajen iya zane yayi ta murna yana alfahari dashi yana jin shine zai cika mishi burinshi da nashi mahaifin ya daƙile mishi tun bai yi nisa ba, hakan yasa ya hana Baqeer sakat yana koya mishi dabarun yin zane, ko wasa Baqeer bai isa ya fita ba sai Badaru yace bayan ya bashi aiki bai yi ba shine zai ce ya biyewa yaran banza suna shashanci. A komai sai ya nuna bambanci don komai na Baqeer daban yake a wajen Badaru. Makarantun daya saka su daban su suna zuwa ta yaku bayi shi kuwa mai tsada mai kyau, haka ko wajen sutura ba iri ɗaya yake ɗinka musu ba, komai na Baqeer yafi kyau da tsada. Wannan bambancin da yake nunawa ne yasa ƴan uwanshi suka tsaneshi idan ka cire Hadiza da Maryam babu mai san shi a cikin ƴan uwanshi kowa haushin shi yake ji. A gidan Suleiman kuwa Ummi ta kasance mace mai mai haƙuri da sanin ya kamata. Ƴaƴa biyu ta haifa daga Kabir sai Zainab wanda tsiran shekaru biyar ne a tsakaninsu. Zainab nada shekara huɗu wasu mutane suka tare a gidan dake jikin nasu. Mace ce da ƴaƴanta biyu budurwa sai ƴar ƙaramar da bata fi sa'ar Zainab ba. Kasancewar Ummi mace mai faram-faram da jama'a da saurin sabo yasa nan da nan suka saba da maƙwabtan nata tun ma ba budurwar ba mai suna Halima. Kullum zaka sameta a gidan tana taya Ummi ƴan aikace-aikace.!Da kaɗan da kaɗan sai Ummi ta sakar mata hidimar gidan ta gaba ɗaya komai su Zainab da Kabir suke so sai tace su tafi wurin Halima, ya zamanto dai ita bata tsinana komai a cikin gidanta sai dai Halima tayi. Tun Suleiman bai lura ba har yazo ya fahimci ai Hafsatu ta sakarwa Halima duk wasu hidindimu na gidanshi, ga wani irin kauna da Haliman ke wa yaran, abinda zai baka mamaki har takai ta kawo indai yaran na san abu to fa gun Halima zasuje ba gun Ummi ba, wanda ita ko damunta bayayi gani take saukin ta ne. Alhaji Sulaiman wannan abu na bala’in birgeshi dan yana san Kabir yai karatu sai gashi zaiga Halima tasa Kabir a gaba akan yai karatu, kusan duk sanda zai shigo gidan zai ganta tana karatu da Kabir, gashi yana san Zainab wanda ya kula Halima ma tafi Ummi kula mishi da Zainab. Wane tudu wane gangare sai ga Halima da Suleiman sun fara soyayya, cikin ƙanƙanin lokaci aka yi aurensu dan a lokacin ya gama yadda Halima ce wacce yake bukata, balle in suna hira tana karfafa mai gwiwa akan siyasar sa da yanda take ganin tabbas har matsayin Governor zai iya kaiwa tana ji a jikinta, duk Ummi bata sani ba saboda sun yi abun ne a ƙudundune basu bari kowa ya sani ba sai dai batun ɗaurin aure kawai mutane suka ji daga sama. Mai unguwa ne ya bada auren Halima don basu da kowa a garin a cewar Inna mahaifiyarta mahaifin su Halima ya rasu ƴan uwanshi suka danne gadonsu suka koreta shine ta tattaro ɗan abinda ya saura musu ta taho nan ta kama hayar gida tana sana'ar sayar da abinci a bakin kasuwa, amma a zahirin gaskiya cikin shege Halima tayi bayan har an saka mata ranar aure da wani ɗan aminin mahaifinta tace ita bata son shi, shi kuma mahaifinta yace ba zai bawa wanda ta kawo ba don bai yarda da tarbiyyarshi ba shine Halima ta tafi ɗakinshi don su gudu to basu gudun ba dai sai tsarabar ciki data koma gida dashi. Ciki na bayyana a jikinta mahaifinta yace sai ta fita ta bar mishi gida ita kuma Inna tace sai dai ya haɗa ya koresu gaba ɗaya don babu inda tilon ƴarta zata tafi ta barta, wannan ne sanadin baro ƙasarsu wato Niger suka shigo Nigeria bayan Halima ta haihu Inna ta ɗauki ƴar ta riƙe a matsayin ita ta haifeta suke kuma faɗin wancan labarin na ƙarya da suka ƙirƙira don su ɓoye sirrin daya rabosu da ƙasar su. A lokacin da Hafsatu ta samu labarin auren cin amanar da Suleiman da Halima suka yi sosai ta ɗaga hankalinta, tashin hankali aka yi sosai a inda har Suleiman yace ta fice ta bar mishi gidanshi ya saketa don a lokacin gani yake yi baya da buƙatarta tunda komai na hidimar gidan dama Halima ce ke yi. Koda ta tashi tafiya ta haɗa kan ƴaƴanta zata tafi dasu sai Suleiman ya ƙwace su ya bawa Halima, tana kuka tana roƙon shi akan ya bar mata ko Zainab ce ita da take mace idan yaso shi ya riƙe Kabir amma ya ƙeƙasa ƙasa yaƙi a ƙarshe ma sai yayi mata korar kare yace idan ya bar mata yaran da ba iya kulawa take yi dasu ba. Abinda ya baƙanta ranta kenan tayi fushi ta tafi sai dai tasan komai daren daɗewa ƴaƴanta zasu nemeta. Suleiman ya ɗebi yara ya bawa Halima ita kuma tasa hannu bibbiyu ta riƙe su kamar nata sai dai a haka ne ake ganin soyyayar da take yi musu anma a zahirin gaskiya yaran ba wani damuwa tayi da yaran ba kawai dai tasan idan bata yi musu riƙon kirki ba to ba lallai ta samu ubansu yadda take so ba shi yas take nuna musu soyayya take nuna musu kamar nan duniya babu mai son su kamar yadda take yi. Alhaji Sulaiman Karaye da Alhaji Badaru suna da ƙullalliya wanda kaf unguwar an san ƴar tsamar dake tsakaninsu, duk da ba faɗa suke yi ba sai dai basa jituwa, wanda a baya a lokacin ƙuruciyarsu an shaida abokan juna ne su biyu suka san me ya haɗa su sai ɗaiɗaikun mutanen unguwa da suka san abinda ya faru a wancan lokacin don su dai matansu haka nan suka taso suka ga basa shiri sai ƴar tsama, Zainab makarantar islamiyarsu ɗaya da Maryam wanda haka kawai jininsu ya haɗu, tana ƙarama yar duma-duma ce, duk lokacin islamiya shi kuma Baqeer a lokacin ya takurawa Zee duk sanda ya ganta sai yace “Abulele! Injin taliya” ba abinda ta tsana irin ya dinga tsokanarta da sunaye barkatai, ko wasa ake yi da yake shi dama Badaru baya barinshi yayi wasa yana daga zaune yana zane zaka ji yace “Karfa kusa Abuwa don kuna sakata zata lalata muku wasa.” Duk sanda ya faɗi haka ita kuma zata sa kuka ta kai ƙararshi wurin Umma, haka Umma zata yita yi mishi faɗa akan ya daina takurawa Zainab. Shi Kabir a lokacin sa’an Baqeer ne sai dai sam basa shiri don Badaru makarantar da aka sa Kabir nan ya kai Baqeer aka sakasu aji ɗaya, babban farin cikin Badaru shine yaga Baqeer yaci na ɗaya yayi ta yadawa Sulaiman habaici shi kuma hakan ke sa ya sake takura Kabir akan karatu, a lokacin Mummy ce matar Daddy don sun rabu da Ummy a lokacin shekarun su Kabir sha biyu ita kuma Zee shakarunsu bakwai ita da Maryam, Hadiza kuma shekararta tara. Haka kawai Allah ya haɗa kan Zee da Maryam bini bini tana gidan, duk kukan da Baqeer ke sakata bata fushi da zuwa gidan. In har aka hanata ma fita sai ta saci hanya tazo, Alhaji Sulaiman yayi faɗa har ya gaji, Mummy tana nuna mishi ai ba komai in tayi hankali sosai zata daina. Wani sa’in ko gidan zata shigo sai ta leƙa ta leƙo ta tabbatar Baqeer baya nan kafin ta shiga, sai dai tana shiga zata jishi ta ɗakin shi yana yi mata waka ‘Abuwale Abulele yar dumi-dumi ƴar duma-duma, ina zaki babu hanya.’ Takaici in ya kamata wani sa’in ta ɗebi ruwa a kofi ta watsa mishi ta window, haka Umma zata zo tayi rabiya, ita kuwa Abu mahaifiyar Kamalu daga taga ya fara zata ce eh dama dani kake shine kake wayancewa. Sai dai duk da haka baya dainawa, shi dai yana son ya takurawa Zee, Umma tayi fada har ta gaji, ita kam Zee tasha kuka don kusan duk sanda tazo sai ya sakata kuka hankalinshi ke kwanciya. Gashi abun na bashi dariya daga ya tsokaneta sai kuka, wani sa’in tana tafiya sai yazo bayanta kawai ya firgitata haka zata ruga a guje taje gida tana kuka, Mummy ta bata haƙuri tace ta daina zuwa, sai dai gobe da sun nemeta suka rasa sun san inda take. Ranar da abun ya faru ranar walimar su Baqeer ne na saukar Alqur’ani a islamiya shida Kabir, bayan an raba kyaututtuka anyi karatu sai Baqeer ya fito saboda yada maganganu da Badaru ke yi a wurin, wai a dole asan Baqeer ɗanshi ne, shi kuma sam baya son abinda Badarun yake yi, yana tafe yaji alamun ana binshi a baya, waigowa yayi yaga  Zainab alokacin yake ce mata Abu dumi me kike yi anan? Kallonshi tayi tace “Nifa Allah ka daina ce mini Abu dumi ai dai Allah ne yayi ni haka.” Dariya Baqeer yayi yace “Inyee yarinya kin girma.” Ta murguɗa mishi baki tana cewa “Oho dai, kuma ni ba binka nake yi ba abu zan siyo.” “Me zaki siyo bayan ga shago can a can?” Ta ɗan waiga tace “Ya Kabir zan saiwa kyauta kaga kudina,” ta nuna mishi ɗari biyu sannan ta cigaba “To shi kwallo yake so kuma Daddy ya hanashi shine zan je na siyo mishi.” Kallonta Baqeer yayi yace “Dumi kinsan inda ake saidawan ne?” Ta taɓe baki tace “Oho koma dai ina ne zan duba.” Tunani yayi ko dai ya tsokane ta ne? Da yake ba abokai gareshi ba yana jin daɗin tsokanar ta. Kwafa yayi a ransa yace “Dumi muje na kaiki?” Da mamaki ta kalleshi tace “Kai din?" Yayi dariya yece “Kina wasa ne?” Haka suka dinga tafiya inta tambaya anzo Baqeer yace ba’a zo ba, shi kanshi tun yana gane hanyar har yazo baya ganewa, gashi lokacin gidaje basu yawaita ba, in ka fiya tafiya sai daji, Zee tunda taga an zo inda babu gidaje hakalinta ya tashi nan da nan ta maƙalƙale ta bayanshi, matsar da ita yayi shi kanshi ya fara jin tsoro. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA BAKWAI* {87} Hankalinsu ne ya tashi ganin sun rasa hanya sai daji kawai suke gani, da shuke-shuke, nan da nan Zainab ta fashe da kuka. Kallonta Baqeer yayi cike da takaici taya suna cikin wannan hali zata fashe mishi da kuka, gaba yayi yana cewa in taga dama ta biyoshi da sauri in kuma ba haka ba zai yi tafiyarshi ya barta don ba zai je dare yayi musu a daji ba, ganin da gaske Baqeer tafiya zai yi yasa ta fara binshi a baya da gudu tana kuka, faɗuwa tai cikin kwacalin dake cikin dajin, nan ta ƙara saka kuka, shi kuma ya ɗauka kukan ɗazu ne dai take tayi har yanzu yasa bai tsaya ba yana tafe yana masifa yana cewa in ta gaji da kukan tayi shiru, ta barshi ma yasan yanda zai yi su bar dajin ba wai ta dameshi da kuka ba. Ya ɗan yi tafiya mai nisa kaɗan sai ya fahimci baya jin muryar kukan Zainab, da mamaki ya waigo sai dai bai ganta ba, hankalinshi ne ya ƙara tashi ya fara ƙwala mata kira sai dai babu ita babu muryarta, da gudu ya fara komawa sai dai da yake daji ne shi kanshi bai san ina yake yi ba, hawaye ya fara shima don hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba balle daya tuna laifin nashi ne. Zainab! Zainab! Kawai yake kira sai dai sam ya rasata, maimakon yaga inda zai ganta sai gashi ya hango titi, kuka ya saka ya fara tunanin zuwa ya nemo taimako wurin mutane. Sai dai shima titin ya gani amma bai gane unguwarsu ba, wurin wani mai shago yaje ya sanar dashi ƙanwarshi ta ɓata a cikin dajin nan, mamaki ya kama mai shagon yace kai yanzu me ya kawo ku daji? Sannan ka sani ita ko wani ya ɗauketa ta koma gida? Ka koma gida in kuka ga bata nan sai ku dawo a sake nemanta. Abunka da shima har yanzu yaro ne kuma yasan babu abinda zai iya, sai mai shagon nan ya taimaka mishi ya kai shi hanyar unguwarsu nan Baqeer yaga mutane carko-carko da alama anyi nemanshi har an gaji, da kuka ya kira sunan Badaru yace “Baba!” Hankali a tashe Badaru ya kalli inda yake a guje ya arto ya rungume Baqeer yana tambayarshi meya faru don kana kallon wandonshi duk kwacalin datti don kayan saukar tasu farare ne, kuka kawai Baqeer yake yi haka suka koma ciki, Kamalu ko kallonsu bai yi ba don shi har addu’a ma yayi akan Allah yasa a nemi Baqeer a rasa. Tunda suka shigo ciki Badaru ke bin ko ina na jikinshi da kallo sai daya tabbatar ba ciwo sannan hankalinshi ya kwanta, Umma ce ta kalleshi take ce mishi ance an gansu da Zainab don yayanta yazo tambaya ɗazu take cewa Baqeer baya nan. Hannun Badaru ya kamo yana cewa “Baba ka taimaka ku ɗauko Zainab ta ɓata a cikin dajin can.” Kallon mamaki Badaru yayi mishi yana tambayarshi dama tare suka fita? Ya ɗauka basa jituwa? Nan Baqeer ya sanar dasu abinda ya faru, hankalin Umma ne ya tashi ta ɗaga hannu zata zabgawa Baqeer mari da sauri Badaru yace kina marinshi ina rama mishi, laifinshi ne? Uban wa yace ta bishi? Sannan shima ba yaro bane?" Umma takaici ya rufeta tace “Kenan don yana yaro sai ya maida kanshi ɗan shekara biyar? Ba zai kama hannunta a matsayinshi na babba ba? Wannan ƙaton yaron ne za’a dinga mai dashi ɗan ƙarami? Wallahi wannan banzan hali ne kadai san Alhaji Sulaiman in har yaji ba bari zai yi ba.” A fusace Badaru ke cewa ba damuwarshi bane ai su suke barin ƴarsu na yawo. Ai bai gama rufe baki ba sai ga Bashir ya shigo da gudu yana sanar dashi ana sallama dashi a waje. Baqeer ya kalla yace ya tashi yaje yayi wanka yaci abinci yayi sallah sannan ya kalli Fatima yace wallahi ta dakeshi ta shirya ganin ɓacin ranshi. Yana fitowa yaga Alhaji Sulaiman, yana kumfar baki yake tambayarshi inda Baqeer yake don ance mishi sun fita da Zainab. Badaru ya murtuke fuska yana cewa kaje can bayan gari ku nemo ƴarku don Baqeer yace can ya ganta tayi don haka kar ku kuskura ku ɗaurawa yarona laifi." Baki kawai Alhaji Sulaiman ya saki ai zuciya ta kawoshi ya cakumo wuyan Badaru yana cewa “Ka fito da ɗanka yazo ya kaini inda yata take ko kuma wallahi ku fuskanci ɓacin raina.” Ko me ya tuna sai kuma ya sakeshi ya juya da sauri ya shiga motarshi yayi wurin ƴan sanda anan aka baza mutane daji neman Zainab sannan ya kai ƙarar a kama Badaru da Baqeer akan ƴarshi da suka ɓatar, da yake Baqeer yaro ne sai suka kama Badaru aka makashi a cell ya dinga masifa yana iface-iface shi kam Baqeer banda kuka babu abinda yake yi, su Abu da Jamila abun ma dariya ya basu, suka shige ɗaki suna dariya da fatan Allah yasa ma a haɗa da Fatima a rufe. Tashin hankali mara misaltuwa suka fuskanta don har zuwa dare babu Zainab ba labarinta, haka Alhaji Sulaiman yasa aka kama Umma ita ma, da har su Abu yace suka ce wallahi su basu da wani haɗi da Baqeer don haka babu inda zasu. Haka aka rufe su, cigiya har gidan radio, Mummy kam tasha kuka don har idanunta sun kumbura, a koda yaushe Daddy ya mata maganar haihuwa sai tace bata so ita wadannan biyun ma sun isheta, to yau ga shi ba Zee dole kowa ya shiga jajanta mata. Ranar basu taɓa ganin tashin hankali irinshi ba, duk wani bincike anyi amma babu Zainab, haka su Badaru da Umma suka kwana a cell shi kuwa Baqeer a gida Kamalu ganin ba kowa ya takale shi fada sai da yayi mishi duka ya huce haushin tsanar da yake mishi, su Abu na zaune suna kallonsu har sai da Kamalu ya fasawa Baqeer goshi sannan suka raba faɗan su Maryam da Hadiza sai kuka suke yi. Haka aka kwana cikin wannan tashin hankali wanda gidan biyu banda su Jamila da Abu babu wanda ya samu bacci, su kuwa bacci har da makara sallar asuba. Badaru kuwa a cell sai da Alhaji Sulaiman yasa officer yayi mishi duka wai akan interrogation ake mishi ya fito da inda yayi garkuwa da Zainab, don Alhaji Suleiman yace ramuwa yayi saboda ƴar tsamar dake tsakaninsu, haka aka yiwa Badaru jina jina, Umma kam hawaye kawai take yi tana addu’a akan Allah ya bayyana Zainab. Washe gari wani masallaci suka sanar da asuba akan an tsinci yarinya ta kwana a gidan liman jiya tsakar dare wajen sha ɗaya, nan wasu suka sanar akan sun ji cigiya a gidan radio, haka aka sanar da gidan radio nan suka sanar ma Alhaji Sulaiman, tare suka taho da Mummy suka ɗauko Zainab wacce ke kwance saboda zazzabin daya rufeta har lokacin ajiyar zuciya kawai take yi. Alhaji Sulaiman har kwalla sai da yayi saboda tausayin ƴar shi, baƙin cikin abinda ya faru yasa aka ƙara wahalar da Badaru akan sai ya fito da Zainab, sannan suka ƙara barinshi yayi kwana ɗaya sannan suka sakeshi, tare da gargaɗin babu shi babu gidan Alhaji Sulaiman sannan yaransu ma babu su babu su. Baƙin cikin wannan abu da tashin hankalin da suka shiga yasa Alhaji Sulaiman hana Zainab fita ko makaranta taje ɗauko ta ake yi, sai dai har lokacin bata haƙura da Maryam ba, Mummy ta sanar dashi akan har lokacin bata daina wasa da Maryam ba, wannan dalilin yasa su barin unguwar, sai dai tsautsayi da rashin sani sai gasu sun sake haɗuwa a unguwa ɗaya na secondary school, ita Zainab nayi private ita kuma Maryam na government school kasancewar makarantun ba nisa yasa duk sanda suka tashi suke haɗuwa, wani sa’in sai sun fara hira sai su hango Baqeer yazo ɗaukan Maryam hakan zai sa Zainab ta gudu ta ɓuya. Bayan sun gama secondary school basu sake haɗuwa da Maryam ba sai a graduation ɗin da suka haɗu daga nan kuma sai dawowar da tayi daga makaranta. Zainab nada kiba da sosai sai dai da ta girma ta sirance ta rame sai kyaunta ya ƙara fitowa. Wannan kenan…….. ***** Har Zainab ta isa gida kuka take yi, tana shiga tun a harabar gida ta hango motoci biyu ɗaya na Junaid ne ɗayan kuma bata san na wanene ba. Shafar fuskarta tayi ta wuce ciki tana fatan yanda take jin ɓacin ran nan Allah dai yasa ba zancen banza Junaid zai yi mata ba. A falonsu taga Kabir a zaune ya haɗe hannayenshi yana ganinta ya taso da sauri yace “Zainab wurin Baqeer kika je? Me kika ce mishi?” Wani banzan kallo tayi mishi kawai tayi hanyar ɗaki, gabanta yasha da sauri yace “Daddy yasa su Junaid da magabatanshi sun zo.” Yanayin kallonta ne ya canza tace “And?” Ya girgiza kai alamar rashin sani kafin yace “Kin dai san halinshi am sure aurenki zasu yi fixing.” Kai ta jinjina tace “Damuwar su kai ma damuwarka,” tana kaiwa nan tayi ciki ta banko ƙofar ɗakin, komai baya yi mata daɗi a duniyar nan, Nabila, Kabir, Mummy da Daddy, bata san ta ina zata samu nutsuwa ba in dai ba a wurin Baqeer ba to yanzu shima ya rabu da ita tasan shikenan ita da farin ciki kuma kila har abada, kayanta kawai ta shiga watsowa daga wardrobe ta zuge akwati ta shiga zubasu a haka. Tun daga abinda Nabila tayi musu take tunowa kawo yau, kawai kuka take yi tana haɗa kaya. Ƙofar ɗakin aka turo, Mummy ce cike da tausayi ta nufo zata rungumi Zainab, hannu ta nuna mata alamar ta dakata sannan tace “Enough Mummy please, a matsayin uwa kike a wurina kar ki bari raini ya shiga tsakanin mu.” Kallon mamaki Mummy tayi mata tace “Me kike nufi auta.” Wani murmushin takaici tayi tace “please Mummy zaki iya tuna cikakken halayenki?” Bata jira amsa ba ta cigaba “Tsabar fake smile am sure kin manta yaushe kika yi wanda ya kai har zuciyarki, hmm da alama dukan mu bamu da hankali shi yasa idon mu ya rufe muka kasa gane wacece ke, taya ɗanki zai buge mutum wanda da abu yazo da ajali zai iya mutuwa amma ki taya shi ɓoyewa ki koya mishi ƙaryar da zai yi kar a gane shi yayi? How?” Ta saki wani yaƙen takaici ta cigaba “Imagine? Baki tashi maganar ba sai da kika ga na taho? Ko ɗazu bamu haɗa ido dake ba kin kalli inda nake tsaye ta gefen ido don ni nasan naga sanda kika ganni ban farga ba sai da ina haɗa kayan nan nake dawo da komai, sannan ban taɓa sanar dake wanene wanda nake so ba ya aka yi kika san Baqeer ne? Abu ɗaya ne yazo min taya ba zaki sanshi ba bayan ke kin san Kabir ne ya gurguntashi? Sannan duk wani hint na riga na baki?” Ta ɗan yarfe hannu tace “Bayana? Auta ta? Kinsan yanda nake ji dake? Yan uwan mamanku? Mahaifiyarku?” Ta Ɗan sa dariyar takaici tace “Taya zamu zama wawaye haka? Sannan Nabila da kike nuna baki damu da ita ba magana ta gaskiya ba wanda ma kika damu dashi sama da ita, kin sata tayi karatun law abinda kika san burin Daddy kenan nayi, kin koya mata duk wani aikin da mace ya kamata ace ta iya, sannan duk wani haɗin aure da ake yi mini in bana so me kike cewa? In tura Nabila in bana so ni kuma na ɗauka so ne hakan sai na wulaƙantasu na tura ta, I haven’t realised miji mai kuɗi kike nema mata a fakaice.” Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Mummy wacce ke kallonta cikin yanayin da ba zaka taɓa ganewa ba, hannayenta ta haɗe alamar roƙo tace “Thank god basu yi min bane kuma ko ba Aunty Nabila ba zan iya tura koma wanene, sannan Baqeer da kike ta zugani a fakaice shi nake so, kuma ko duk duniya zasu haɗu shi ɗin dai shi nake so, ba kuɗi ne a gabana ba farin ciki ne a gabana da wanda zan zauna dashi cikin kwanciyar hankali, congratulations Mummy burinki ya cika, kin taimaka na mutu kan Baqeer kin kuma sanar dani Kabir ne ya buge shi, kin kuma zuga Daddy yaga Baqeer, menene next plan ɗinki?” Kasa ko magana Mummy tayi sai kallon Zee kawai da take yi, ƙofar ɗakin aka yi knocking nan da nan Mummy ta nufi ƙofa ta buɗe ganin Daddy yasa tace “Senate! Ya zamu yi? Zainab barin gida take son yi yanzu nake yi mata faɗa sai dai bana ji zata ji.” A fusace ya ƙarasa shigowa ciki, kawai Zee tasa wata dariya kamar mahaukaciya, tana yi hawaye na zubo mata tana bin Mummy da kallo. (😞🥺😟) *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA TAKWAS* {88} Tsayawa kawai Daddy yayi yana kallon Zeey ganin yadda take ta dariya kamar wata sabin kamun hauka. Sai da tayi dariyarta ta isheta sannan ta tsagaita, wato Mummy tunda ta gane ita wacece shine zata yiwa Daddy bariki a gabanta ko, ita dariya ma ta bata ganin yadda ta haƙiƙance tana nuna damuwarta a fili. Da ace da ne da idanunta basu buɗe tasan asalin wacece Mummyn ba da tayi mamakin yadda lokaci guda ta juya magana amma yanzu ta gama ganeta sarai sai abun bai wani bata mamaki ba, tasan fiye da hakan ma zata yi in dai Mummy ce. Wani kallo yayi mata yace "Gidan uban wa zaki da kike haɗa kaya?" Turo baki Zeey tayi idanunta ƙyar babu alamun tsoro tace "Wajen uwata zan koma tunda dai ba za'a aura min wanda nake so ba ni banga amfanin zamana anan ba." Hannu Daddy ya ɗaga zai kwaɗa mata mari sai Mummy tayi saurin riƙe hannunshi tace "Haba Senate ya zaka mareta bayan kasan auta yarinya ce har yanzu ba wani sanin daidai tayi ba, don Allah kayi haƙuri abi abun nan a hankali. Ke auta bashi haƙuri kullum ina faɗa miki ki daina yin musu da mahaifinki." Wani kallo Zeey ta watsa mata kawai ta cigaba da haɗa kayanta, a fusace Daddy yace "Ki tattare kayan nan ki mayar dasu cikin wardrobe don babu inda zaki je, kuma ki sani nasa ranar aurenki da Junaid sati huɗu masu zuwa don bazan yarda ki zubar min da mutunci da ƙimata ba.” Itama ƙara tamke fuska tayi tace "Ai na faɗa maka wallahi bazan aureshi ba sai dai nayi ta zama a haka babu aure in har ba zaka aura min Baqeer ba sai ka shirya ganina a cikin gidanka, ai tun farko na faɗa maka ni bana son Junaid bazan aureshi ba ka dage sai anyi to sai kasan yadda zaka yi dasu don ni dai bazan taɓa auren mijin da bana so ba." Ƙara yunƙurowa yayi zai kai mata duka Mummy ta sake tare shi ta hanashi kaiwa ga Zeey ɗin. Sosai ranshi ya ɓaci duk da yasan halin Zainab bata iya yin shiru idan anyi mata abu amma bai ɗauka zata tsaya a gabanshi yana faɗa tana faɗa ba. Juyawa yayi zai bar ɗakin don idan ya tsaya zai iya lahanta ta da duka sai ji yayi tace "Kuma na faɗa maka bazan zauna a gidan nan ba don kada ma kuje kuna yawon nemana ah to." Tsaki kawai yayi ya fice Mummy ma tabi bayanshi suka bar ɗakin. Cigaba tayi da zuba kayan a cikin akwatin, sai da ta tabbatar ta ɗauki duk wani abu da tasan zata rinka buƙata sannan taja akwatinta ta fice. A parlour suka kusa karo da Kabir. Kallonta yayi fuskarshi ɗauke da mamaki yace "Ke kuma ina zaki?" Wani irin kallo ta watsa mishi ta ratsa gefenshi ta wuce don shi kanshi haushin shi take ji, sai take ganin kamar shine sanadin wannan halin da take ciki don watakila da bai nakasta Baqeer ba da duk hakan bata faru ba. Bama zata ga ana wulaƙanta shi ba bare har tausayin shi ya ginu a zuciyarta, da kuma Badaru bai koreshi daga gidanshi ba. Watakila ma da yanzu sun yi aure shi da Asiya. Tana yin wannan tunanin taji wani abu mai nauyi ya sauko ya tokare a ƙirjinta, bugun zuciyarta ya ƙaru fiye da ƙima, numfashi ta dinga yi akai akai har ta samu bugun zuciyarta ya dawo daidai. Tana fita a harabar gidan taga Junaid ya nufo inda take yana murmushi. Ƙara tamke fuskarta tayi ta cigaba da tafiya zuwa wajen motarta, buɗe motar tayi ta jefa akwatin a baya sannan ta rufe. Daidai lokacin Junaid ya ƙaraso inda take. "Hajiya Zeey kin yi wuyar gani." Wani kallo tayi mishi ta saki tsaki ciki-ciki don bata so yaji saboda tana ganin mutuncin shi kawai dai halin shi na naci ne bata so tunda tace bata yi ba sai ya haƙura ba amma ya dage shi a dole sai ya aureta gashi tana ganin kima da darajarsa. Cigaba yayi da cewa "Kin ji abun farin cikin da yake tunkaromu ko? Su Daddy sun saka ranar aurenmu, In Sha Allah nan da four weeks kin zama mallakina." Yatsina fuska tayi tace "Idan ma mafarki kake yi gara ka farka don ba tun yau ba na faɗa maka ni bazan aureka ba to yau ma ina ƙara faɗa maka bazan aureka ba, idan har ban samu Muhammad wanda nake so ba sai dai na haƙura da aure don haka tun wuri ma gara kaje ka faɗawa waɗanda ke da alhakin sanya ranar auren nace bana yi su warware." Ta buɗe motarta ta shige ciki ba tare da ko kallon Junaid ta ƙara yi ba. Kamalu daya faki idon maigadi ya samu ya shigo gidan don ya faɗawa Roshni ɗin shi ya gama haɗa lefe ta faɗi ranar da za'a kawo don so yake yi ayi komai da komai lokaci guda ba sai anyi ta kai komo ana zuwa ana dawowa ba, ganin ta fito ya fito daga bayan motar daya laɓe, yana wani gyara kwalar riga, da sauri ya koma bayan motar ya sake laɓewa ganin saurayi ya nufi Zee ɗin, har ya fara auna cin zarafin da zai mai indai yace yanasan Roshini dan kuwa kowa yasan Roshini ta Saddarth ce, sai dai kalaman Zee sun sa ya zauna dabas a ƙasa. Sakin baki yayi yana kallon Zeey da saurayin da ta gama yagawa, tabɗijam idan har zata iya kallon idanun wannan tsalelen saurayin tace bata son shi to shi kuma a wa da zai yi tsammanin zata so shi. Lallai Roshni ta wuce da saninshi, sai dai duk da haka gara ya gwada sa'arshi don bai san inda za'a dace ba. Wa ya sani ma ko shine Muhammad din? Tunda dai kowa yasan Kamal ma ana cemusu Muhammad Kamal. Ƙarasawa yayi jikin motar yace "My Roshni!" Wani banzan kallo tayi mishi taja wani irin tsaki don sarai ta gane waye Kamalun ɗan uwan Baqeer ne, shi bai san duk haushin ƴan gidansu take ji ba saboda abinda ubansu ya yiwa Baqeer bare wannan mahaukacin da sam bata sakashi a layin masu hankali. Har zata shiga mota sai kuma ta kalleshi tace “Na ɗauka nace in neman taimako kake a bakin ƙofa zaaka tsaya ko?” Kallan kanshi yai da irin wankan dayai na gayu ya buɗe baki zai sake magana kawai yaga ta shiga motarta tayi reverse kafin ta danna wani mahaukacin horn, a guje maigadi ya taso ya buɗe mata gate ɗin taja motarta ta fice daga gidan a guje. Kallon wurin data bari Junaid yayi ya juya ya nufi motarshi don bai ga tsaiwar me yake yi ba a wurin kuma sai jin muryar Kamalu yayi yace "Ah to tun wuri gara ka kiyayi Roshni don ba sa'ar yinka bace." Ai juyowa bai yi ya kalleshi ba ya cigaba da tafiyarshi, duk da ranshi a cunkushe yake da maganganun da Zainab ta yaɓa mishi sai da yayi dariya din ya fahimci kamar shima wancan jakin son Zeey ɗin yake yi. Har sai daya zo kusa dashi a mota ya sake mai wani kallan takaici ya kalli kafafunsa da suka sha wani tsohon takalmi, kai ya girgiza, Kamalu ganin irin kallan daya mai yasa ya harsuko yana kumfar baki yana cewa “Dallah Malan ware ko banza wacce kake so bata sanka ni take so Muhammad Kamal ɗan gata sarkin iya soyayya.” Shidai Junaid wucewa yai kawai ya dinga jin dariya na zuwa mai, duk kuwa da bacin ran da yake ciki. ***** Tunda ya dawo wani abu bai shiga tsakaninshi da Asiya ba duk da a matse ya diro ƙasar amma annakiyar ƙazantar data haɗa tasa yaji sam baya son kusantar ta, to ita ma bata cikin yanayin daɗin rai tunda yace mata ba zasu koma ba shi yasa bata damu da rashin nemanta da bai yi ba. Yau sai ya tashi da tsananin buƙatuwa, haka nan ya daure ya shiga ɗakin Asiya ya tarar da ita a kwance tayi shame-shame sai shaƙar bacci take yi. Hannu yasa ya toshe hancin shi warin dake busowa daga toilet na hautsina mishi ciki. Kallonta yayi yaga yadda take bacci hankalinta kwance ga alama ita wannan warin daya cika ɗakin baya damunta. Ƙarasawa yayi jikin window ya bubbuɗe don iska ta shigo ko ya samu warin ya fita. Juyawa yayi ya kalli ƙofar banɗakin sai ya ganta a hangame, runtse idonshi yayi ya janyo ƙofar ya rufe banɗakin don baya son ma idanunshi suyi mummunan ganin da zai hana mishi zaman lafiya. Tsaki yaja yana jin takaicin shigowa ɗakin Asiya da yayi sai dai yanayin daya tsinci kanshi a ciki ne ba zai iya haƙuri dashi ba idan ba ya fitar da abinda ya taru a mararshi ba. Ƙarasawa yayi gaban gadon ya ɗan bubbuga pillown da take kwance akai, shi kanshi pillow case ɗin yayi baƙi ƙirin da dauɗa if he's not mistaken kamar tun wanda aka shimfiɗa ne da aka kawota gidan bata canja ba. Tashi tayi tana mutsitsika ido, ganin Bello tsaye a kanta yasa ta haɗe rai tace "Malan lafiya zaka tashe ni ina bacci?" Wani irin wari ne ya buso fuskarshi data buɗe baki tayi magana, ai tuni zuciyarshi ta tashi yaji cikinshi na wani irin hautsinawa ɗan abinda yaci yana neman dawo mishi. A sukwane ya fice daga ɗakin, yana shiga ɗakinshi ya faɗa toilet ya fara kelaya amai, tuni ɗan abincin da yaci ya fice sai kakarin kawai da yake yi. Daya tuna warin bakin Asiya sai yani wani aman ya yunƙuro mishi gashi cikin shi babu komai. Da ƙyar ya samu aman ha tsaya ya fito yana sauke numfashi, haba wannan masifa har ina? Shi yanzu da wanne zai ji fisabilillahi? Ga rashin aikin yi ga mata ƙazama Allah ya bashi, duk inda ya juya baya jin daɗi ya rasa inda zai saka ranshi yaji daɗi. Ƴar buƙatar data shigar dashi ɗakin Asiya ma tuni ta kama gabanta tayi nata wuri don a yanzu sai yaji ko ɗan yatsanta ba zai iya riƙewa bare har ya haɗa jiki da ita. Allah ya taimaki Baqeer da yanzu shi ake yiwa wannan ƙazantar shi da baya son ƙazanta ko misƙala zarrati. Koda yake hakki ne shima yake bibiyar shi hakkin abinda ya yiwa Baqeer gashinan yana ɗanɗana kuɗarshi a hannu. Dana sani iya dana sani Bello yayi ta akan abinda ya yiwa Baqeer gashi nan tun ba'a je ko ina ba yaga sakamakon abinda ya aikata. ***** Tunda ta hau titi take sharara gudu fatanta kawai ta ganta a gaban Ummi ta kwanta a kafaɗunta tayi kukan baƙin cikin da yake damunta, tayi kukan rabata da masoyinta da ake nema ayi, tayi kukan yaudararta da soyayyar bogi da Mummy tayi, tayi kukan tausayin abinda ɗan uwanta na jini ya jawa Baqeer, tayi kukan abubuwa da yawa data rasa a rayuwarta saboda riƙon taɓararru da Mummy tayi mata. Hannu tasa ta ɗauke hawayen daya zuba daga idanunta, duk ta tuna yadda Mummy ta dinga raina musu wayo tana ƙara nesanta su da mahaifiyarsu suna jin haushinta sai taji zuciyarta ta ƙuntata, ta rasa laifin me suka yi mata data yi musu irin wannan zaluncin ta shiga tsakaninsu da mahaifiyarsu tasa mahaifinsu ya hana su zuwa inda take ya kuma hana ƴan uwanta zuwa su gan su. Ribar me Mummy taci da duk tayi hakan bayan basu aikata mata laifin komai ba. Hukuncin Allah ne kawai ya kai Zainab Ɗambatta lafiya don bata da wata nutsuwa haka nan tayi tuƙin har Allah ya kaita garin lafiya. A wani wajen sayar da layin waya ta tsaya ta sayi sabon layin mtn aka yi mata register ta biya ta bar wurin. Dole ta canja layi idan har tana so ta nesanta kanta daga Baqeer, tana jin nauyinshi tana jin nauyin ƙara haɗa ido dashi sabida abinda Kabir yayi mishi, gashi Daddy yayi rantsuwa ba zai aura mata shi ba, ita kuwa baza ta iya aurenshi ba har sai Daddyn ya amince da batun auren da kanshi, a yanzu kuwa tasan abu ne mai wahala yayi hakan, bata so ta cigaba da jin muryarshi ko ta ganshi don tasan rabuwarsu zata yi musu matuƙar wahala. Tana yin parking motarta a ƙofar gidan Ummi, Inaya na dawowa daga makarantar islamiyya. Tana ganin motar Zeey ta tsaya a ƙofar gidansu ta rugo a guje tana murna. Sauri tayi ta goge hawayen fuskarta ta fito daga motar tana dariya, buɗe hannayenta tayi Inaya ta shige jikinta ta rungumeta. "Aunty Zeey ashe zaki dawo da wuri?" Ta tambayeta tana ɗaga ido ta kalli fuskarta, ɗan ɓata fuska tayi ganin yadda fuskar Zainab tayi jajawur da kumbura saboda kukan da tayi. Cike da kulawa tace "Aunty Zeey me aka yi miki? Kuka kika yi ko?" Girgiza kanta tayi tace "A’a abu ne ya faɗa min a ido shine yayi tayi min zafi amma yanzu ya fita." Ɗaga kai Inaya tayi alamun ta fahimta, suna riƙe da hannun juna suka shiga cikin gidan. Tun daga harabar gidan Inaya ke ƙwalawa Ummi kira tana ceqa "Ummi fito ki gani Aunty Zeey ta dawo," har suka ƙarasa cikin parlourn. A tsaye a bakin ƙofar kitchen suka tarar Ummi ta zubawa ƙofar parlourn ido tana so taga shin da gaske ne abinda taji Inaya na faɗa ko kuwa. Zeey na shigowa taga Ummi kawai sai ta ruga a guje ta rungumeta tana sakin wani irin kuka mai ciwo, hannu Ummi tasa tana bubbuga bayanta a hankali dan tabbas tasan wani abu ya sake faruwa. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* Da *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA TAMANIN DA TARA* {89} Ummi bayan ta kawai take shafawa har sai da ta gaji da kanta ta tsagaita da kukan, Inaya kam tana gefe tayi tsuru duk zuciyarta ba daɗi ganin Zee na kuka, ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta kamo hannunta tana cewa "Inaya ki je ki cire kayan islamiya ki watsa ruwa kizo kici abinci." Ba musu tayi ciki su kuma suka shiga ɗaki, da yake Zee ta saba shigewa jikin Mummy sai take jin yau ɗumin jikin tata mahaifiyar take so, kanta ta kwantar akan cinyar Ummi tana maida kukan dake neman ƙara tasowa, Ummi ce ta daure tace "Ki kwanta in kin ware anjima sai muyi magana," tayi maganar tana zare jikinta don ta kula Zee na buƙatar kaɗaicewa, da sauri Zee ta riƙota tana girgiza kai tana cewa "Ummy karki tafi don Allah, gaba ɗaya duniyar nan bata mini daɗi wurinki kaɗai nake sa ran samun sauƙin abinda ke damuna." Kallonta Ummi tayi ta dawo kusa da ita ta zauna ta kamo hannayenta tare da juyo da ita saitinta tace "In ɗan adam ya shiga damuwa me yake cewa?" Wasu hawaye ne suka zubo tace "Nayi addu'o'i Ummi kawai zuciyata ce nake ji kamar zata buga." Kallon da Ummi ke yi mata ne yasa tace "Allahumma inni a'udhu bika minal-hammi wal-Ḥuzni, wal-ajazi wal-kasli wal-bukhli wal-jubni wa ḍala'id-dayni wa ghalabatir-rijal." Lumshe ido tayi, Ummi ta saki murmushi kaɗan kafin tace "Ke da Halima ne?" Kai ta girgiza sai kuma hawaye ya sake zubowa tace "Ni da kowa ne ma Ummi wanda nake so an hanani aurenshi, Daddy ya takura sai dai na auri Junaid kuma ni bana sonshi," ta kalli Ummi tana jin wani zafi a ranta tace "Ummi don yana gurgu shikenan sai ya zama abun ƙyama?" Mamaki ne ya bayyana a idon Ummi tace "Gurgu ne?" Zee ta jinjina kai tana goge fuska tace "Kema nasan ba yadda zaki yi ba sai dai wanda ya ja mishi abun...." Sai kuma tayi shiru don bata son ta ɓata Kabir a wajen Ummi tun kafin ma su haɗu, ita dai Ummi baza tayi ƙarya ba amma tabbas ba zata yiwa yar ta fatan auren gurgu ba, Zee ta kalleta sai kuma tayi shiru kawai don bata son ta ɗagawa Ummi hankali daga zuwa, kai kawai ta girgiza alamun babu komai tana ciza ƙasan leɓenta. Ummi ta shafi saman kanta tace "Ki tashi kiyi sallah kici abinci naga babbar jaka kika zo da ita a hankali sai mu tattauna." Kai ta ɗaga alamar to, hakan yasa Ummi fita, tana maida ƙofar ta rufe ta bi ɗakin da kallo cike da tausayin Zee tabbas abubuwa da yawa sun faru sai dai da alama na saurayin yafi damunta, a hankali zata kula da yarta za kuma ta gina shaƙuwar da suka rasa, kuskuren da tayi a baya na barin Halima ta gaje mata yara ba zata sake makamancinshi ba yanzu. Zee kuwa a ɗakin alwala tayi bayan tayi sallah ta kwanta akan sallayar ta zubawa wayarta ido, number Baqeer take nema bayan ta goge komai dake cikin wayar ɗazu, wayar ta ɗaura akan kirjinta tana jin wani raɗaɗi na rashinshi na damunta, kalaman Badaru ne ke sake dawo mata, ashe yayanta ne duk ya janyo mishi wannan bala'in? Ta runtse idanuwanta wanda suka ƙanƙance saboda kukan da tasha. ***** Baqeer tunda Zee ta tafi ya turo ƙofa ya rufe ɗakin shi, abincin data bashi ya tura gefe don ko alamun yunwa ma baya ji, ko idanuwanshi ya runtse sai ya dinga ganin Zee tana yi mishi murmushi, hannu yasa ya ɗan matsa saman girarshi sannan ya janyo takarda ya fara sketch, yi kawai yake yi kamar wanda ake zubowa basirar, ji yayi hannunshi na ɗan zafi hakan yasa ya ajiye pen ɗin tare da dafa saman kanshi dake ciwo, maimakon ya daina sai ya janyo shaddar daya siyo kawai ya bajeta ya sauka daga kan kenenshi ya fara yankawa, sai daya gama fitar da komai sannan ya ajiye scissors ɗin tare da duba agoggo, magriba yaga tayi ya turo kekenshi ya fito. Dada tana ganinshi tace "Anga dama an fito? Banda shirme in kana sonta da gaske ai ba haƙura zaka yi ba, sannan ko kunya ka shige ɗaki ka barta ta tafi gida da kanta." Shi dai bai ce komai ba sai bandaki kawai daya wuce. Bayan yayi sallah ya ji zuciyarshi ta kasa nutsuwa sunan Zainab ya kalla cike da damuwa ya danna kira ai dai ko ba komai ta cancanci kulawar shi don yadda ta bar gidan nan yana tsoron wani abun ya sameta, da sauri ya kashe kafin wayar ta shiga ya kifa kan wayar tare da sake wani dogon numfashi, yadda yake jin zuciyarshi na zafi ko Asiya da suka dade tare bai ji rabin abinda yake ji akanta ba bayan sun rabu. Wayarshi ce yaji ta fara ƙara da sauri ya ɗauka yana fatan Allah yasa Zainab ce, ga mamakinshi Umma ce yanayinshi kaɗai zaka san ba haka yaso ba sai dai Umma ce ita kanta yana son jin muryarta. Ɗauka yayi bayan sun gaisa cike da kulawa tace "Baqeer dama Zainab sonta kake yi?" Yawun bakinshi ya haɗiya kafin yace "Ba dai Baba ya huce akan ki ba? Umma don Allah ki kwashe kayanki daga gidan nan zan zo na ɗaukeki," yayi maganar a ɗan hasale. Cikin sanyin murya tace "Ba maganar da muke yi kenan ba, taya zaka nemi janyowa kanka magana Baqeer? Kafi kowa sanin wanene Alhaji Sulaiman ka kuma san abinda zai yi akan yaran shi, ka sani ko da ƙafafunka ma ba baka Zainab zai yi ba." Baqeer ji yayi wani abu ya tokare mishi a maƙoshi, mikin da yake ƙoƙarin dannewa na neman tasowa, muryarshi ce ta ɗan sarƙe yace "Umma ban sani ba wallahi, sanda kuma nasan ita wacece nayi nisa da har nake jin zan iya gwada sa'a ta, duk wannan lokacin a matsayin ƙawar Maryam kawai na santa, ta canza kama sannan ban ma taɓa kawowa Zainab dana sani zata kula dani haka ba. Umma ita ce wacce a dalilinta nake zaune cikin kwanciyar hankali yanzu, na tabbatar Allah ne ya kawo min ita cikin rayuwata a lokacin da nake buƙatar wanda zai fahimceni, wanda zai nuna min hanya ya hanani faɗawa wani hali, Umma tunda nazo gidan Dada nake roƙon Allah ya ɗauki raina na huta sai dai ita ce ta nuna min kuskurena ta kuma sani fara sana'ar da nake yi yanzu, ni....ni!" Kasa cigaba da magana yayi kawai sai ya runtse ido yana haɗiyar wani abu mai ɗaci da yaji ya tokare mishi maƙoshinsa. Umma tausayin ɗan nata ya kamata, lallai da ta sani tun sanda tasan Zainab ce data tuntuɓeshi kila da lokacin bai mato a sonta kamar yanzu ba don kalamanshi kaɗai sunsa tasan yana sonta sosai. Murmushi yayi na yaƙe yace "Baba yayi halin nashi ko?" Cike da tausayin ɗan nata tace "Babu komai ni faɗanshi baya damuna, kai kuma In Sha Allahu Allah zai dubeka ya baka lafiya zai kuma baka wacce iyayenta zasu soka." Murmushi kawai yayi don Ameen ɗin ma ji yayi ya kasa cewa don in dai aure ne to da Zainab kawai yake son zama, ɗan shiru yayi kafin yace "Don Allah Umma karki sadaukar da farin cikin ki saboda ni, babban burina a duniyar nan na faranta miki shi yasa babu amfani na ganki cikin ɓacin rai, ki bar gidan kamar yadda yace miki kizo mu zauna, ni hankalina zai fi kwanciya in kina nan zan kuma fi maida hankalina wurin sana'a ta, sau da dama barin Dada ita kaɗai baya mini daɗi ta kawo girman da take buƙatar wani tare da ita," ya ƙarasa maganar yana rage murya zuwa rashin jin daɗi. Ta sani sarai duk abinda ya faɗa daidai ne hakan yasa tace "Shikenan zan yi tunani skai." Cike da jin daɗi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Number Zainab ya sake dubowa ya kwantar da kanshi a bayan wheelchair ɗin yana tunani, sai dai baya ji yana da ƙarfin iya kiran ta. **** Yau kwana huɗu kenan da tafiyar Zee Ɗambatta sosai suka ƙara shakuwa da Ummi da Inaya, shi kanshi Mubashir da bashi da yawan magana sosai sai da Zee tayi ƙoƙarin janshi a jiki, ko waya Abba yayi haka Inaya zata yi ta bashi labarin abubuwan da suka yi da Aunty wanda abun ba ƙaramin daɗi yake yi mishi ba, yana son Ummi sosai shi yasa yake jin daɗi ganin tana cikin farin ciki, yaso Ummi da farko sai dai bai sanar da ita ba saboda shi abokin yayanta ne, in yazo wurin abokinshi yana ganin Sulaiman yazo zance, wannan dalilin yasa bai sanar da kowa son Ummi da yake yi ba, yaja bakinshi yayi shiru har tayi aure shima yai aurdnshi, sai dai aurenshi bai daɗe ba matarshi ta rasu a wajen haihuwa ta koma ita da babyn da ta haifa, wannan dalilin yasa ya ajiye batun aure ya maida hankali wurin aikinshi, shekarar matarshi huɗu da rasuwa auren Ummi ya mutu, yazo Ɗambatta hutu ya ganta wannan dalili yasa ya sanar da yayan Ummi don baya son ya sake bari ya huce, bayan aurensu Ummi ta haifi Mubashir daga nan kuma sai ta dinga ɓari babu haihuwa, ƴan uwanshi suka fara canza mata saboda suna son yayi aure suna ganin aikin da take yi ne kila yasa ma cikin yaƙi zama. Ƴar uwarshi suka bashi akan ya aura yace fir ba zai aureta ba, sai dai Ummi ta nuna mishi rashin dacewar hakan, daga baya ya amince da auren sai da aka zo daf da auren suka gane ashe akwai wanda take so, auren shi kawai zata yi saboda yana da kuɗi amma ba wai don ta rabu da saurayinta ba. Ba ƙaramin ɓacin rai ya shiga ba yaci zarafinsu akan kar wanda ya kuskura ya ƙara yi mishi maganar ƙara aure matarshi ta isheshi baya buƙatar ƙari. Tun daga nan Ummi ta samu salama suka daina ƴan maganganu, daga baya Allah ya bata cikin Inaya, wanda ganin tasha wahala sosai wajen haihuwarta yasa yace to haihuwar ta isa haka su biyu sun isa, da kanshi ya zaɓawa Inaya sunan Zainab don ya san tsananin son da take yiwa ƴaƴanta kawai dai kawaici take yi take kauda kai. Shi yasa yanzu ya tabbatar Ummi na cikin farin ciki wanda hakan shi kuma ba ƙaramin daɗi yake yi mishi ba. Yau Ummi ce a kitchen ita da Zainab da Inaya, aikin girki ake taya Ummi, sai dai Zainab duk ta zama ƴar kallo tana tsaye tana ganin yadda Inaya ke taya Ummi yanke-yanke amma ita tana farawa Ummi tace ba haka ba. Baki ta turo tace "Ummi to wai ita wannan ƴar mitsilar ya aka yi take iya yin wannan yankan ƙanana?" "Kema haka nan zaki koya kuma ga naki nan kada na kuskura naga kinsa Inaya ta miki." Baki ta turo ta shiga daddagewa tana yankawa, ganin ta yanka daidai yasa ta daka wani tsalle ta kalli Ummi tace "Ummi Ummi kalla, wallahi ni nayi." Kai kawai ta girgiza ganin yadda take murna kamar wacce tayi wani abun kirki. Sosai Ummi ke ƙoƙarin janta a jiki da kauda mata tunanukan da take yi, sai dai duk sanda tazo kwanciya sai tayi kuka ta gaji saboda tunani da rashin Baqeer tana ji son Baqeer ya zama jinin jikinta, tunda tazo Daddy bai nemeta ba in ta kira kuma yana amsa gaisuwarta yake kashe wayar ko dama baya bata suyi magana, Mummy kuwa ko waya basu sake yi ba balle da Ummi ta bata labarin yadda ta shiga jikinta dasu har ta auri Daddy wannan dalili yasa ta ƙara tabbatar da makircin Mummy. **** Baqeer kuwa ya tattara komai ya sashi a gefe, duk da Zainab na cikin ranshi amma ya danne bai bari a gane, shagonsu sun kammala gyarashi da sanya kayan aiki, yin aiki da mutanen nan ba ƙaramin alheri yake samu ba, hakan yasa yace ko ya buɗe shagonshi zasu cigaba da aiki tare, wani idea ne yazo mishi na yanda yake fitar da ɗinkin maza, style ne wanda ba'a taɓa ganin irinshi ba, sai suka yi meeting akan yanda zasu ƙayata ɗinkin ya karɓu a wurin mutane, Salim ya bada shawara akan su haɗa shi kamar gift su dinga sayawa kayan huluna da takalmi suna ɗaurawa a social media, designs ɗin jikin hulunan su suke bayarwa ayi musu sai suyi wa kayan aiki irin shi, keken da zai yi aikin sun yi sa'a ba irin wanda zai taka bane, yana daga zaune zai yi dan shi kaɗai yasan yanda yake son style ɗin ya kasance, kuɗin siyan injin aikin suka maida hankali wurin haɗawa don kuwa yana da tsada sosai, gashi baya so su je wani wurin suyi aikin wani yaga idea ɗin ya sace, dole su zasu fara in suka fara tallanshi wasu suka kwafa a kalla kowa yasan sune dai asalin masu abun. **** Yau Bello tun cikin baccinshi yake ji ana buga ƙofa, miƙewa yayi don sam basa kwana ɗaki ɗaya da Asiya, ganin ƙazantar ta na neman illa tashi yasa ya nemo mai aiki take zuwa safe da yamma tana gyara gidan ta tafi, Asiya sam bata damu ba sai ma wani halin banza data tsuro mishi in taga an gyara gidan sai ta ɗauki abu ta saida ta gayyato ƙawayenta suzo ayi ta hira ana koɗa jin daɗin da take yi a makeken gidan nan. Tsaki yayi jin buga ƙofar tayi yawa, ya fito yana murza ido don dama yau zai sake fita neman aiki ko Allah zai sa a dace, kwanan nan kuɗin cefane ma mahaifinshi ke basu. Ƙofar shigowa ya buɗe don yasan Asiya nacan na baccin asara, idanunshi ne suka sauka kan mai gidan daya basu haya, gaban Bello ne yayi wani mugun faɗuwa, ba dai har sun cinye kuɗin hayar su ba? Tabbas tun wancan watan yake ganin kiran mutumin yana ignoring gani yake yi surutun banza zai yi mishi. Yanda mutumin ke kallonshi ne yasa jikin Bello ƙara yin sanyi. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *AYUSHER MUHD* *DA* *UMM ASGHAR* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN* {90} Murya na rawa yace mishi "Yallaɓai barka da asuba." A wulaƙance mutumin ya kalle shi yace "Kai ba wannan ya kawo ni ba," hannu ya miƙa mishi yace "Bani." Kallonshi yayi ya kalli hannun da yake miƙo mishi yace "Me zan baka?" Gabanshi yana dukan uku-uku don yasa yau dai ƙaryarshi ta ƙare. Wani irin kallo yayi mishi yace"Kuɗin hayata ko makullan gidana." Duk da yasan abinda ya kawo mutumin kenan sai da yaji wata irin faɗuwar gaba ta ziyarce shi, yanzu idan aka koreshi daga gidan nan ina zai je? Cikin ƙasƙantar da kai yace "don Allah kayi haƙuri zuwa..." Ɗaga mishi hannu mutumin yayi ya dakatar dashi daga abinda yake cewa yace "Tun wancan watan hayarka ta ƙare don rainin wayo ina ta kiranka a waya kayi banza ka rabu dani ko bin bayan ƙiran baka yi ba sai yanzu ne zaka wani karkace wuya zaka yi min ƴar murya, to bazan lamunta ba idan kana so ka cigaba da zama a gidana ka biya kuɗin haya idan ba haka ba kuwa ka tattara ya naka ya naka ka ƙara gaba ina da mutanen da zan sa a gidana." Karkata kai yayi ya hau bawa mutumin haƙuri don yasan idan yace ya fita ya bar mishi gidanshi baya da wurin kamawa, "Dan Allah kayi haƙuri Yallaɓai kayi min lamunin kwana biyu In Sha Allah zan kawo maka kuɗinka har gida." Haka nan dai yayi ta bawa mutumin haƙuri har ya samu ya haƙura akan idan kwana biyu ta cika bai biya shi kuɗin hayar gidanshi ba zai fita ya bar mishi gida. Mutumin na tafiya ya juya ya shige cikin gida yana tunanin abun yi, yanzu a ina zai je ya samo wannan iyayen kuɗaɗen a cikin kwana biyu shi ba aiki ba shi ba wata sana'a ba. Ɗakin shi ya shige ko wanka bai yi ba ya canja kaya ya ɗauki makullin motarshi wacce da ƙyar ya samu Asiya ta dawo mishi dashi hannunshi ya fice daga gidan yana tunanin inda ya kamata ya fara zuwa. Tunani yayi gara yaje ya samu mahaifin shi watakila akwai taimakon da zai iya yi mishi. Bai damu mahaifinshi a gida ba fon haka ya bi bayanshi zuwa kasuwa. Ya yiwa mahaifinshi bayanin abinda ke tafe dashi. Wani irin kallo yayi mishi yace "To yanzu ya kake so ayi?" Ɗan shiru yayi yana sunkuyar da kai don sai yanzu yaji takaicin zuwan shi gaban mahaifin nashi bayan ko lokacin da zai kama hayar gidan sai da ya hanashi amma yaƙi ji, to amma idan ba Baban ba wurin wa zai je ya faɗi damuwarshi? Kanshi a ƙasa yace "Kayi haƙuri ka yafe min Baba, ban kasance ɗa na ƙwarai a wajenka ba duk abinda ka haneni dayi shi nake yi, wallahi nayi nadamar abubuwan da nayi tayi, ka taimakeni na samu na biya kuɗin hayar In Sha Allah zan yi ƙoƙari na biyaka cikin lokaci." Tsaki Baban yayi yace "Dame zaka biyani idan na ɗauki iyayen kuɗi da yawa tsababa na baka kai da ba aiki kake yi ba ba sana'a ba?" Da sauri yace "Ai ina neman aiki In Sha Allah ina sa rai da zan samu da an fara biyana zan yi ƙoƙarin haɗa maka kuɗin ka." Kallon baka da hankali Baba yayi mishi sai kuma yace "To ita motar da kake yawo da ita miye amfaninta da baza ka sayar ka biya kuɗin hayar ba?" Ai bai san lokacin da ya ɗago ya kalli Baba ba, taya zai ce ya sayar da motarshi motar da ita kaɗai ta rage mishi, kai gaskiya a'a ba zai taɓa yiwuwa ba sam ya sayar da motarshi. "To idan ba zaka sayar ba sai ka tattara ka bar musu gidansu idan yaso ka dawo gida ku buɗe ɗakinka na da ku zauna a ciki." Tashi yayi jiki a saluɓe ya bar wajen Baba, zai dai yi ƙoƙari daga nan zuwa kwana biyu yaga ya haɗa kuɗin hayar ya biya idan kuma hakan bata samu ba dole Asiya tayi haƙuri su tattara su koma gidansu da zama idan yaso sai su sayar da kayan ɗakin da yayi mata yaja jari tunda gidan nasu ɗaki ɗaya ne babu inda za'a zuba duka waɗannan kayan a ciki. ***** *BAYAN SHEKARA GUDA* A cikin shekara guda data gabata Baqeer yayi nasarar buɗe shagon shi na ɗinki mai suna *MOHBAQ TAILORING SERVICES*, sosai Allah yasa mishi albarka a ciki ta yadda kullum cikin samun sababbin customers suke. Designs ɗin ɗinkunansu idan har suka yi maka baka taɓa ganin su a ko ina sai a jikin wanda suka yiwa irin shi. Saboda yadda suke tsara designs ɗin su yasa ba kowa ke iya kwafarsu ba masu gwadawar ma sai dai su kamanta amma ba dai suyi shi sak da sak irin yadda suke yin nasu ba. Sosai shagon shi ya samu karɓuwa saboda bayan kaya da mutum zai kawo su ɗinka mishi har da ready-made suna ɗinkawa daga kayan maza har na mata babu wanda basa ɗinkawa kuma duka styles ɗin da suke yi Baqeer ne ke ƙirƙirar designs ɗin su kuma yaran shagon sai su ɗinka yawanci ma shi yake yin yankan da kanshi ko shi ko Tanimu, ganin yana samun kuɗi sai ya zuba irin machines ɗin da yake buri, wasu irin machines ne da suke amfani da computer. Hoton designs ɗin da ake so kawai za'a saka shi zai ɗinka maka automatically don haka aikin yake zuwa musu da sauƙi, idan machines ɗin suka yi zanen surfanin da suke so su kuma sai su haɗe kayan. Bayan shi da Tanimu da ya kasance kamar manager a wurin ya ƙara samun wasu yaran da suke yi musu aiki saboda yadda suka samu karɓuwa ayyuka na yi musu yawa. A yanzu haka ƙoƙarin buɗe wani branch ɗin yake yi. Shi dai a rayuwa babu abinda zai ce sai Alhamdulillah, yasan da ace har yanzu yana gaban Badaru ba lallai ya tsaya da ƙafafun shi yadda yake a yanzu ba, watakila da har yanzu yana nan yana paintings ɗin da kaso saba'in cikin ɗari na abinda yake samu na Badaru ne, abinda yake bashi bai wani taka kara ya karya ba wanda a ciki yake yin duk wasu buƙatun shi har ma ya ɗauki nauyin Umma da kuma ƙannenshi. Abu ɗaya ya kasa mantawa a cikin shekara ɗayar nan data wuce shine Zainab da soyayyarta, har yau ya kasa cireta daga cikin ranshi gashi ko kiranta yayi a waya baya samunta, ba sau ɗaya ba dau biyu ba yaje har gidansu sai mai gadi yace mishi bata nan tayi tafiya idan kuma ya tambayeshi inda ta tafi sai yace shima bai sani ba sai dai har yau bai cire rai da sake dawowarta cikin rayuwarshi ba hakan nema yasa ya kasa bawa wasu matan damar shiga rayuwarshi don a yanzu da Allah ya azurtashi sai ya zamanto ko nakasar tashi ba'a kalla shi ɗin dai kawai matan suke kallo ko kuma yace ƴan canjin hannunshi suke kallo, sai dai kuma sun makaro domin babu wani sauran gurbin ƴa mace a cikin zuciyarshi gaba ɗaya Zeey ta kankane tayi kaka gida, babu wata ƴa mace da yake iya kallo da sunan soyayya. Ƙarfe huɗu yake tashi daga shagon yana tattare cinikin da suka yi a ranar saboda ya kai banki kafin ya wuce gida, duk da mafi yawancin customers ɗin sun fi yi musu transfer akwai waɗanda suke basu cash to baya son barin kuɗi a shago shi yasa duk yamma sai ya fara biyawa banki ya ajiye kuɗin kafin ya wuce gida shi da Tanimu da yake tuƙa Baqeer ɗin duk inda zai je a motar Baqeer ɗin, sai ya kai shi gida sannan ya koma shagon sai wajen ƙarfe tara sannan ya rufe gaba ɗaya a tashi daga aiki. Shi Baqeer baya zama ya kuşan dare idan ba aiki ne dasu da yawa ba saboda bai cika son yana yin nisa yana barin Dada ba saboda tsufa da take ƙara yi kullum abubuwa da yawa da take iya yin su a da yanzu bata iyawa. Baqeer ya gyara gidan Dada sosai ya ɗaukar mata mai aiki da take yi mata ƴan aikace-aikacen gida tana kuma zama da ita kada kaɗaici ya daneta bare da ba cika zama yayi a gidan ba. Haka nan ya wadata Umma da duk wani abu da zata buƙata sai dai gidan ne tunda ya bar shi ko layin gidan bai ƙara taka ƙafarshi yake ba, su Abu da Jamila suyi ta surutun a ina Umma take samun kuɗin da take kashewa bayan ita ba sana'a take yi ba, wani lokacin idan gulmar ta ciyo su sai suce suna ganin kuɗin filin da suka sayar ne har yanzu basu gama cinyewa ba suke ci da kaɗan-kaɗan shi yasa kullum bata rasa abun ɓatarwa. Ita dai tana jin su ko kallonsu bata yi domin bata da lokacin tsayawa biyewa shirmensu. Babu yadda Baqeer bai yi ba ta bar gidansu taƙi sai dai akwai plans ɗin da yake yi yana kammalawa zai je ya ɗauketa daga gidan dan yasan tun tasowarsu take haƙurin zama a ciki ba ga mai gidan ba ba ga abokanan zamanta ba kowa ba daɗinsu take ji ba. ***** Sosai Zainab take jin daɗin zama a wajen Ummi bare da Ummi take janta a jiki, duk wani aiki idan zata yi zata sakata a gaba suyi tare, tun tana kwaɓawa har da kaɗan-kaɗan tazo ta fara iyawa. Sabuwar tarbiyya Ummi ta yiwa Zeey duk da take da kyakkyawar zuciya tana da rashin tsoro da faɗin duk abinda yazo bakinta bata duba girma ko shekarun mutum duk yadda magana tazo bakinta haka zata kwaɓa mishi ita. Akan haka sai da Ummi tayi da gaske da yawan faɗa da nasiha kafin ta samu ta daina. A harkar kitchen ma babu laifi ta iya abubuwa da dama don a yanzu wai har Ummi ta fita ta bar mata girki tayi kuma ya ciyu babu wani gyara, haka nan ɓangaren kula da gida da tsaftarshi yanzu duk Zainab ta iya. Sai take jin rayuwarta wata daban da wacce take yi da, ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali komai tana yin shi cikin ɗa'a bata yin abu da graje kamar yadda take yi ada. Tunani ɗaya ne ya kasa barin ranta shine na Baqeer, duk tsawon wannan lokacin bata manta dashi ba haka yasa taƙi bawa duk manemanta dama, har a cikin cousins ɗinta da yawa sun ce suna sonta taƙi amincewa saboda ta riga ta ƙudurce a ranta idan har ba Baqeer ba bata ga wanda zata aura ba, akan hakan ne ma suke yawan samun saɓani da Ummi don a yanzu burinta taga auren Zainab ɗin ita kuma tace idan har ba za'a aura mata Baqeer ba ta haƙura da auren. Lokaci zuwa lokaci take ƙiran Daddy a waya amma daga gaisuwa babu abinda ke ƙara shiga tsakaninsu, ko ta neme shi da hira ma baya amsawa haka zata yita takale-takalen zancenta ta haƙura saboda baya amsa mata saboda haushin yadda ta kunyata shi a wajen mahaifin Junaid bayan sun gama magana tasa ƙafa ta bar gidan ta kuma cewa Junaid ɗin lallai yaje ya faɗawa Babanshi ya janye don baza ta aureshi ba, mahaifin nashi da kanshi ya kirashi yace abar maganar kasai tunda dai yarinya bata so. Shi kuwa Kabir kota ƙira shi ma baya amsawa saboda haushinta da yake ji na yadda ta zaɓi Ummi akan Mummy da tasha wahalarsu a faɗarshi, yadda Mummy take langwaɓe mishi tana nuna shi da Zainab ne farin cikinta don Allah kada ya guje mata kamar yadda Zeey ta gujeta hakan yasa yake ƙara jin haushin Zeey ɗin akan abinda tayi shi yasa ko ta ƙiranshi a waya tai baya amsawa. Zaune akan doguwar kujera a parlour tana danne-danne a waya, Instagram ta shiga tana kallon hotunan ɗinki da Baqeer ya ɗora a pg ɗin shi, bi take yi tana scrolling through wani farin ciki na ratsata idan ta kalli hotunan taga wai wannan aikin Baqeer ɗinta ne, Baqeer ɗin da ake yiwa kallon nakasashe wanda ba zai iya amfanar kanshi da komai ba yau gashi yayi setting up business ɗin da ba kowa ne zai iya ba. Wani alfahari take ji ganin yadda kullum ƙara haɓaka yake yi yana samun karɓuwa kamar shi kaɗai ne tela duk wani mai ji da kanshi a kuɗi da harkar gayu to kayan *MOHBAQ* ne abun tu'ammalin shi. Manyan mutane da yawa a wurin shi suke ɗinki, wannan kaɗai abun farin ciki ne a wurinta na ganin yadda rayuwarshi tayi changing for the better. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar* Da *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA ƊAYA* {91} Baqeer gaba ɗaya ya zama busy, yau suka yi cinikin gidan da ya siya ya kuma bada rabin kuɗi akan zai biya ragowar ƙarshen wata, gida ne mai masifar kyau sannan babba ne part biyu ne a gidan gate din shiga ne kawai a haɗe amma kowa bangarenshi daban, so yake ya dawo da Dada da Umma ɓangare ɗaya shi kuma ya zauna a ɗaya, Salim ma a gefenshi kaɗan ya sayi nashi gidan don yanzu soyayya ta kankama tsakaninshi da Habi, abun na bawa Baqeer dariya yanda in suna soyayya yana shigowa zai fara wayancewa, wani sa’in sai yace “Ai kawai hirar zumunci suke yi.” Baqeer in yaji haka sai yace “Ai na ɗauka ta koma ƙanwarka ne ai.” Tun farko Baqeer yasan da ita ne don Salim bashi da budurwa, wanda Baqeer ya tabbatar don yana son Habi ne ya hanashi yin wasu, shi kuma kunya yake ji a yanzu yace yana son Habi saboda abinda ya faru tsakanin Baqeer da Asiya, sai dai ko kaɗan wannan abun bai damu Baqeer ba don kuwa Asiya sam bata gabanshi ko tunota inba da dalili ba baya yi, shima lokaci-lokaci Salim ne ke maganarta wai Habi tace mai sun koma gidan su Bello da zama, kai kawai ya jinjina, kwanaki ma Salim ya kwashe da dariya yana bawa Baqeer labarin koro Bello da aka yi wai Asiya tayi yaji akan komawarsu gidan shine take faɗar dalilanta wanda anan suka ji, Babansu kuwa ya zuba mata ido sai gashi ko sati ba ayi ba taga gwara ta tattara ta koma gidansu Bellon a ƙalla can yafi gidansu. Ko da Baqeer yaji kai kawai ya girgiza bai taɓa musu fata mara kyau ba balle yayi murna da abinda ya samesu. Kallon gidan yayi yana tunanin abubuwan furnitures da zasu buƙata, wayarshi ce tayi ƙara ƙirar iphone 14pro max ya ɗauka tare da amsawa, wasu masu son kaya ne ready made  a US suke suke so ayi musu shipping, nan ya musu bayani ya ɗauki details na yanda suke so da sizes ɗin su sannan yace nan da 7days za’a kammala saboda suna son kayan da yawa, account number ya tura musu ko minti biyar bai yi ba suka turo mishi da zunzurutun kuɗin shi, maida wayar yayi ya ajiye ya runtse idonshi tare da ƙara maida kanshi bayan hadaddiyar electric wheelchair ɗin daya siya wacce take tuƙa kanta sai dai yayi controlling ɗinta kawai da remote, ƙafafunshi na samun sauƙi sai dai har yanzu baya iya takasu, yana dai iya tsayawa ya hau kujera amma baya iya tafiya a kansu, ya canza asibiti na ganin physiotherapist don jikinshi na bashi Zee auren Junaid zata yi shi yasa sam baya son zuwa balle yaji abinda zai tada mishi hankali, fitowa yayi daga gidan Tanimu na waje yana jiranshi a mota, Baqeer ya buɗe mishi baya wanda ya kunna abinda ya sauko don wheelchair ɗin ta shiga kai tsaye. Kallon Tanimu yayi yace “Malam Tanimu kai dai ka dage baza ka zauna a shago ba kullum dai sai dai muje guri tare kaƙi yarda a nemi driver.” Dariya yayi bayan ya shiga ya zauna yace “Ba komai ni hakan yafi min daɗi.” Baqeer na shiga ya maida kanshi jikin kujera ya lumshe ido kamar yanda yanzu ya saba wa kanshi tunanin Zee a kusan duk sanda ya kaɗai ce, idanuwanta yake hangowa a ranar da ya ganta na ƙarshe, buɗe ido yayi a hankali sannan ya kalli waje, ko tana ina? Ya kira wayarta har ya gaji, ranar Salim har kasa jurewa yayi yaje ya tambayar mishi ko ta dawo aka ce har yanzu bata dawo ba. Murmushi mai sanyi yayi ko sai yaushe zai cireta a ranshi? Sai dai haka kawai yake ji tunaninta shike taimaka mishi yake rayuwa cikin farin ciki don ko yaya in ya tunota sanyi yake ji a cikin ranshi. Wayarshi ce ta sake ƙara ya ɗauka ma abin business ne sai yaga kiran Hadiza, ɗauka yayi suka gaisa kafin ya rufe baki tace “Ya Baqeer don Allah kana ina? Kazo gida in da hali don Allah yanzu.” Cike da damuwa yace “Meke faruwa? Don yanayinta kaɗai yasa yasan ba lafiya ba, bare shi ko hanyar gidan ma rabonshi da ita ya manta bare mutanen gidan. Cikin muryar raɗa tace “Case ake yi akan kayan da Kamalu ya sato a shagon wani, to matsalar yanzu sun kawo police suna ƙoƙarin tafiya da su Umma da Baba sun ce mutanen gidan kaf sai sun yi bayani.” Mamakin kalamanta ne suka rufeshi yace “Ban gane ba? Shi Kamalun yana ina?” Ta girgiza kai tana ƙoƙarin yin kuka tace “Ban sani ba wallahi, nima Umma ce ta kirani bata so ka sani ni kuma naga ba abinda zan iya yi.” Tanimu ya kalla yace “Don Allah Tanimu kai ni wurin Umma.” Da yake yasan gidan saboda saƙon da wani sa’in yake kaiwa ko kuma in Umma tayi musu miya yazo ya amsa. Nan suka yi sallama da Hadiza hankalinshi duk ya gama tashi, dole bazai ƙara barin Umma ta zauna a wannan gidan ba don ba zai iya ɗaukar wannan ɓacin ran ba, amma yaushe Kamalu ya fara sata haka? **** Badaru a fusace yake kallon Abu yace “Ke dai wallahi aurenki bai daɗa mini komai ba sai ɓacin rai, ɓarawo a gidana? Wallahi yau sai kin bar min gida,” yayi maganar yana kallon kayan da aka fito dashi daga ɗakinta wani lace ya janyo yace “Wannan ba shine lace ɗin da aka kawo mana bara ba nazo nan gidan ina faɗan an min sata?” Bashir ya miƙawa ya kalla kafin yace “Shine.” Badaru yayi mata wani kallon takaici yace “Kema dai ɓarauniyar ce ashe, dama ni ina mamakin inda kike samun kuɗi ashe kuɗin sata kuka haɗu ke da ɗanki kuke ci? Yanzu kaf shagona in aka zazzage ba za'a samu rabin kayan da aka fito dashi daga ɗakin ki  ba,” cikin harzuƙa yake magana, har wani kumfar baki yake fitowa da ita saboda masifa. Jamila ce ta girgiza kai tace “Abu gaskiya ku canza hali wallahi me za ayi da hakin ɗan ɓera.” Wani mugun Kallo Abu tayi mata tace “Dallah Malama rufe min baki ai dai ni anga me nake yi kuma ke kanki kin san bani ke satar ba, sannan in ma kuɗin satar ne ai dake ake ci, ke waya san me ƴarki take yi a Saudia? Ko kina tunanin bamu san aurenta ya mutu ba yawon karuwanci take yi tana turo miki kuɗi?” Nan fa Jamila ta kawo bango ta nufo Abu da sauri zata cakumota, Badaru ya daka musu tsawa yace “Kun yi mini shiru ko sai ranku ya ɓaci, ƴan sandan dake waje ne suka shigo saboda hayaniyar da ake yi, Umma na tsaye a gefe tana kallonsu, police ɗin na shigowa yace “Dukansu zasu wuce dasu yanzun nan don satar da Kamalu yai babba ne bakuma zasu sakesu ba sai yazo.” Jamila ce tayi saurin cewa “Officer nifa babu ruwana daka ganni nan, bani da haɗi da ita don Allah ka tafi da ita amma banda ni da yarana.” Badaru ne ya kalleshi yace “Ka tafi da ita Yallaɓai mu wallahi bamu san me suke aikatawa ba sannan nima sun min sata ka ajiyesu a musu hukunci har da nawa.” Kallonsu yayi ya nunawa ragowar ma’aikatan akan su kamasu duka, Hadiza ce tace “Amma ita Umma menene laifinta?” Wani kallo yayi mata yace “Ita ma wannan kayan da aka ɗauko daga wurinta ina ta samesu? Na tambayeta taƙi faɗa kuma kowa yasan bata sana’a don mijinta ma ya shaida har satar fili tayi mishi wannan ma don ta sata ba wani abun bane.” Mamaki ne ya rufe Hadiza ta kalli Badaru tace “Baba baka ji kunyar bada shaida kan matarka ba?” Nunata yayi da yatsa yace “In ba so kike ranki ya ɓaci ba ki ɓacen da gani, ƙarya aka mata? Sannan ina take samun kuɗi in ba satar take yi ba?” Jamila tayi caraf tace “Satar ce ma don wallahi Malam har kuɗi dunƙulallu tana dasu ai dai baza ace har yanzu kuɗin fili take ci ba. Bashir ne yace “Ita kuma Hajiya ta fa?” Officer yace “Ita ma mai gidan ya bada shaida tana sa mai hannu cikin aljihu in har zata yi sata a aljihunshi kenan zata iya bawa Kamalu dama ta taimaka mishi yayi sata ita ma ta samu, sannan satar da yayi ba ƙarama bace bare musa ran zaku iya biya don haka dukkansu wucewa zamu yi dasu.” Waje suka fito ana ƙoƙarin watsasu cikin bayan motar ƴan sandan. “Sorry to say amma banda Uwata,” abinda suka jiyo kenan ta bayansu, gaba ɗayansu suka waiga don Jamila har da ture kafaɗar Badaru tana son ganin waye  yayi magana da kakkausar murya haka. “BAQEER?” Gabaki ɗayansu suka ambata baki a sake, Umma kallon Hadiza tayi wacce tayi saurin kawar da kanta, ƙarasa rufe ƙofar haɗaɗɗiyar motarsu Tanimu yayi wanda yasa gaba ɗayansu suka sake buɗe baki suna bin motar da Baqeer da kallo cike da mamaki, Baqeer ya tsaya da kekenshi don ko gidan bai son gani, kallon officer ɗin yayi tare da miƙa mishi hannu alamar su gaisa, ganin motar kaɗai da kayan jikinshi da yanayinshi kaɗai yasa yasan lallai akwai maiƙo a tare dashi, miƙa mishi hannu yayi da sauri yace “Kai kuma wanene Alhaji?” Baqeer ya zaro business card ɗinshi yace “Sunana Baqeer kamar yanda ka gani ina da business mai kyau da zan iya kula da mahaifiyata, kaya da kuɗi daka gani ni nake tura mata don haka baku da hujjar tafiya da ita.” Kai ya shiga jinjinawa yana cewa “Ai bata yi bayani bane shi yasa, amma yanzu kaga ai mun san babu ita a ciki.” Hannu yasa ya ciro kuɗi dubu hamsin ya miƙa mishi yace “Asa kati nagode.” Ɓoyewa yayi yasa aljihu yana cewa “Godiya muke, kai dai Malam baka kyauta ba tunda kasan ita ba ɓarauniyar bace miye na kiran sunanta.” Badaru kam kamar an ƙamar dashi don rabonshi da Baqeer har ya manta, Jamila ce tayi saurin nufar Baqeer har tana taka ƙafar Abu tace “Ɗan albarka Baqeerun mu, ina ka shiga? Sai tunanin ka nake yi ko jiya sai da nayi mafarkinka ina ta Allah Allah na bawa Fatima labari na manta.” Bai ko kalleta ba bare ya tanka mata sai kallon Ummanshi da yayi yace “Umma mu wuce?” Jamila ta kamo kafaɗun Umma tace “Allah sarki Fatima dama na faɗa miki Baqeer Allah yayi rabon arziƙinshi a duniya yanzu kinga maganata ta tabbata, to ai mu ba wanda ya kai mu farin ciki.” Abu ce ta taho da sauri tace “Baqeeru don Allah ka taimaka kasa a nemo Kamalu ni tsoro nake kar naje wani abun ne ya sameshi, naji zan je police station amma don Allah ka taimaka min wannan mahaifin naku babu abinda zai yi saima ya ƙara janyo mishi masifa, don Allah ka taimakeni.” Jamila ce ta ture ta gefe tace “Ahh lallai Abu ko kunya ma ba kya ji? Naga kece kika jawa Fatima har ana cewa za’a kulleta? To yanzu ba kunya shine ma kike so ɗanta ya taimaka miki? To ba dai Baqeerun mu ba.” Mamaki kawai ya hana Umma magana tana mamaki yanda ko kunya basa ji duka su biyun, Badaru ya ɗan kalla kaɗan wanda har yanzu kallon Baqeer yake yi jikinshi duk yayi sanyi kamar bashi da laka, yanda Badaru yake wai yau shine ko kalma ɗaya ya kasa furtawa. Hadiza kam jan hannun Umma tayi ta cusata cikin mota sannan ta koma ciki don ta kwaso kayanta, Baqeer ne ya kauda kai yana neman juyawa, Jamila ta saki ƙaramin ihu tana cewa “Baqeer kar kayi mana haka don Allah, ni kafi kowa sanin duk abinda nayi ba’a son raina nake yi ba, kaima kasan yanda nake ji da kai a rayuwar nan, ko ka manta sanda Bashir ya dinga taimakon ka? Ai ko ba don ni ba sai ka tuna shi, da wahalhun da yayi maka, wayyo ni Jamila.” Baqeer kallon Bashir yayi wanda ke tsaye yana share ƙwalla, tabbas ko ba komai Bashir ya taimakeshi, Umma ce ta fito daga motar ta kalleshi kallon da ba sai tayi mishi bayani ba yasan irin kallon. Waigowa yayi ya kalli Abu dake kuka sannan ya kalli officer yayi mishi alama daya matso gefe suyi maganaa, sunyi minti goma suna magana kafin ya amshi number mai shagon akan zasu nemo Kamalu sannan suka ja mota suka tafi. Jamila ce tace “Baqeeru Allah yayi maka albarka don Allah nima kar ka barni anan gidan ka tafi dani kaga a ƙalla Fatima ta samu abokiyar hira.” Hadiza data fito da jaka bata san sanda dariya ta kwashe mata ba ta girgiza kai tana mamakin yanda mutane basa kunyar nuna zalamarsu da rashin kunyarsu a fili. Abu ce tace “Nima don Allah a tafi dani.” Hadiza baki ta saki tace “A koma gidan miji ayi biyayya don Allah.” *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA BIYU* {92} Kallon cikin motar Umma take yi tana ƙara godewa Allah da irin baiwar da yayi wa ɗanta, da Badaru ya koreshi saboda yana ganin babu wani sauran amfani da zai yi mishi sai korar ta zame mishi alheri gashi yanzu sanadin hakan Allah yayi mishi arziƙin da ba lallai yayi ba idan a gaban Badaru yake. Shiru tayi a cikin motar ta kasa cewa komai sai Hadiza da Tanimu ne suke ta hirarsu sai jefi-jefi Baqeer ke saka musu baki har suka ƙarasa gidan Dada. Yanzu ya zama dole yayi ƙoƙari ya cikawa masu gidan can kuɗaɗen su don ya samu a shirya gidan cikin lokaci tunda gashi ya ɗauko Umma a lokacin da bai gama shiryawa ba, da farko da ya bari ne sai ya gama cika musu kuɗin gidan an zuba furniture kafin yaje ya ɗauko Umman to kuma sai wannan al'amarin ya faru da yasa dole ya rabota da gidan. Gaba ɗaya suka shiga gidan Dada da Baqeer yasa aka gyara aka mayar dashi na zamani sosai kamar ba gidan tsohuwa ba. Ganin suna shigowa da kayan Umma yasa tace "Ke kuma lafiya? Ina Badarun kika tattaro kika dawo gida?" Zama tayi akan tabarmar da Dadan ke zaune kafin tace wani abu Baqeer yace "Na rabota da wancan gidan ne Dada ba zata sake komawa ba." Kallon mamaki Dada tayi mishi duk da tasha jin shi yana zancen zai ɗauke Fatima ya rabata da zaman gidansu ba sau ɗaya ba sau biyu ba amma bata taɓa tunanin zai aiwatar ba, duk tunaninta yana dai faɗa ne saboda takaicin halin uban su ashe shi da gaske yake yi, murmushi tayi ta girgiza kai tace "In banda abinka Baqeeru ta yaya zaka rabo mace daga gidan aurenta mijinta bai saketa ba, a ina ake yin haka saboda Allah?" Yana tafiya ɗakin shi ya bata amsa da "Za’a fara akaina, ni dai na ɗauko ta kuma baza ta koma ba," yayi shigewarshi ɗakin shi. Hadiza ce tace "Allah Dada Baban ne baya da kirki, yanzu haka idan kin ji abinda yayi ba zaki sake ganin laifin Ya Baqeer ba." Harararta Dada tayi tace "Kome yayi ai dai uban ku ne har kike cewa baya da kirki." Ƴar dariya Hadiza tayi tace "Hhamm Dada kenan, wai fa zuwa nayi gidan na tarar an ɗebo musu ƴan sanda Kamalu yayi sata shine Baba yake bayar da shaida akan Umma wai ta sace mishi takardun filinshi a haɗa har da ita a tafi bayan takardun filin da yake magana akai na Ya Baqeer ne ba nashi bane." "Allah ya kyauta," kawai Dada tace ta juya tana amsa gaisuwar da Umma take yi mata. Tashi Hadiza tayi ta kwashe kayan Umma ta kai ɗakun Dada, sai da ta shirya kayan tsaf sannan ta fito tayi musu sallama zata tafi gida saboda yamma tayi ta baro yara a gida. Hadiza na fita Umma ta tashi ta shiga ɗaki, ta rasa tunani guda ɗaya da zata kama sai take ganin al'amarin kamar a mafarki sai dai idan ta ɗaga ido ta kalli Baqeer yau bayan wani tsawon lokaci Allah ya ƙara haɗa su zama a muhalli guda sai tasan cewa ba mafarki take yi ba. ***** Zaɓe yana ta matsowa saboda haka hankalin kowanne ɗan takara ya tashi, kowa burin shi ace yau shi yayi nasarar lashe kujerar daya fito nema. Primary Elections za'a yi a jam'iyyar su Daddy don haka hankalin shi ya kasa kwanciya domin abokin takarar shi na neman saye ƴan jam'iyyar da kuɗi duk da shima ba baya ba wajen yi musu ɓarin kuɗin duk don ya samu su zaɓe shi a matsayin ɗan takarar jam'iyyar tasu. Yau sun fita yawon campaign a wani ƙauye basu baro garin ba sai dare. Suna tafe a hanya motocin campaign ɗin sai zura uban gudu suke yi a titi suka yi wani mummunan accident. Haka mutane suka yi dafifi akan su ana ta fitar da mutane daga cikin motocin da hatsarin ya rutsa dasu, wasu sun rasu wasu sun ji munanan ciwo, a cikin waɗanda suka ji ciwo har da Daddy don wani ƙarfe ne ya coke shi a cinya ya ɓullo ta ɗaya ɓarin cinyar abun babu kyaun gani. Sai da ƴan road safety suka zo sannan aka fara zuba su a mota za'a bar wutin dasu don wurin da suka yi accident ɗin daji ne. Haka aka kwashe su aka yi asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano dasu a ɓangaren accident and emergency. Kabir na kwance har ya fara bacci yaji wayarshi na ringing, haka ya tashi yana tsaki ya ɗauki wayar sai yaga ashe Daddy ne ke ƙiran shi. Cikin muryar bacci yace "Hello Daddy," sai yaji wata murya da ba ta Daddyn ba ta amsa. Ai tuni yaji ya wartsake jin wayar ba'a hannun Daddy ba, da ƙyar ya nutsu suka gaisa da mutumin sannan mutumin ya faɗa mishi maƙasudin kiranshi da yayi. Tuni hankalinshi ya tashi yana tambayar mutumin "Yanzu ina Daddyn? Da fatan dai bai ji ciwo ba?" "Eh to, yana nan accident and emergency na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano idan kun zo zaku ganshi." Hankali a tashe ya zari makullin motarshi ya fita, har ya isa harabar gidan ya tuna bai sanar da Mummy ba don haka ya koma yayi knocking a ƙofar ɗakinta. Cikin bacci taji ana ƙwanƙwasa mata ƙofa, sai da ta ɗauki wayarta ta duba lokaci sannan tace "kai waye anan?" Saboda har lokacin ba'a daina buga ƙofar ba. "Mummy nine," jin muryar Kabir yasa ta duro daga gadon ta ɗauki hijabin sallarta ta saka sannan ta buɗe ƙofar tana cewa "Kabir lafiya kuwa yanzu da dare?" Idanunshi sun yi jawur saboda tashin hankalin yace "Yanzu aka kirani a waya wai an kai Daddy asibitin Aminu Kano sun yi accident a hanyarsu ta dawowa daga campaign, har na fita zan tafi na tuna ban faɗa miki ba shine na dawo." Tuni itama ta rikice tace "Subhanallahi nima gani nan zuwa bari na shirya." Juyawa yayi ya tafi da kamar ya tsaya jiranta ta shirya ɗin kamar yadda tace sai kuma yaji ba zai iya ba gaba ɗaya hankalin shi yayi gaba gara yaje yaga a wane hali Daddyn yake ciki idan yaso ta iske shi a asibitin. Gudu kawai yake yi akan titi bare da titin ya kasance babu kowa saboda dare da ya fara yi babu yawaitar motoci a titun. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ƙarasa asibitin, yana shiga cikin accident and emergency ɗin ya kira number Daddyn, mutumin na ɗauka yace mishi gashi yazo sai yana ɗan ɗaga hannu, daga nesa mutumin ya ganoshi yayi waving ɗin shi back. Da sauri Kabir ya ƙarasa wurinshi yana zuwa yace "Ya jikin Daddyn? Ina fata babu wata babbar matsala." Hannunshi mutumin ya kamo yaja shi wajen kujera suka zauna yace "Mu ɗan jira su anan likitocin na dubashi har yanzu," hannu Kabir yasa ya riƙe kanshi yana jin tashin hankalin shi na ƙaruwa, a yanzu burinshi kawai yayi ido biyu da Daddy watakila idan ya ga a halin da yake ciki ya samu ƴar nutsuwar zuciya. Dafa shi mutumin nan yayi yace "Ka kwantar da hankalin ka In Sha Allah zai samu lafiya, kai dai kayi tayi mishi addu'a Allah ya sauƙaƙa mishi ya tashi kafaɗunshi." Kasa ki amsawa Kabir yayi, suna zaune a wurin babu wanda ya fito wurin su har lokacin sallar asuba yayi suka tashi suka fita amsallacin cikin asibitin suka yi sallah suka dawo. Har wannan lokacin likitocin basu nemesu ba, gaba ɗaya Kabir ya ɗaga hankalinshi gani yake yi Daddyn ya mutu kawai faɗa mishi ne basa so suyi. Sai can wajen ƙarfe shida na safe sannan ɗaya daga cikin likitocin ya fito, mutumin na ganinshi ya gane shi don haka yayi wa Kabir magana suka tashi suka ƙarasa wurinshi. Yana ganin wannan mutumin daya kasance ɗaya daga cikin yaran Daddy na amana ya yafito su, kallon Kabir yayi yace "And who are you?" Mutumin ne ya amsa mishi da "Mahaifin shi ne mara lafiyan ai." "Oh okay, to ku biyo ni," yaja su zuwa wani office. Bayan sun zauna ya kalli Kabir "muna buƙatar kuyi signing akan wannan form ɗin don zamu shiga dashi surgery," ya miƙa mishi consent form. Karɓar takardar Kabir yayi yace "Ya jikin Daddyn? Meya sameshi da har sai anyi mishi aiki?" Ya tambayi likitan ba tare daya duba takardar ba. Ɗan kallonshi Doctor ɗin yayi yace "Mahaifinka is diabetic gashi kuma ƙarfe ya shige cinyarshi ya ratattaka ƙashin wurin da ba zai gyaru ba don haka dole zamu yi amputating ƙafar don idan aka barta ruɓewa zata don ƙashin wurin ya tashi a aiki babu ta yadda za'a iya gyarawa." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun," kawai Kabir ke ambata, dafe kanshi da yake jin yana wani irin sara mishi yayi. Ya ɗauki wasu ƴan mintuna yana cikin halin ruɗani kafin da ƙyar ya iya buɗe baki yace "Yanzu ina Daddyn yake? Zan iya ganinshi?" Cike da tausaywa suke kallonshi Doctor yace "Me zai hana, idan kun shirya muje ku ganshi sai kuyi ƙoƙarin biyan kuɗin aikin dan a samu a shiga dashi akan lokaci." Zubewa kawai Kabir yayi a ƙasa saboda yadda yaga Daddy ya koma wani iri kamar wanda aka canjawa halitta gaba ɗaya kamannin shi sun juye. Da ƙyar ya iya tashi ya ƙarasa gaban gadon murya na rawa yace "Daddy," duk da Daddyn ba jin shi yake yi ba saboda har yanzu bai dawo cikin hayyacinshi ba. Ya daɗe a tsaye a wurin yana kallon Daddy hawaye duk ya cika mishi ido saboda tsabar tausayi. Da ƙyar ya iya barin wurin ya fita don ya koma gida ya ɗauko atm card ɗin shi sannan ya dawo ya biya kuɗin aikin da za'a yiwa Daddyn bayan ya bar wato Mallam Nuhu mutumin da ya ƙira shi a wurin don ba zai yiwu abar Daddyn shi kaɗai ba duk da bai san inda kanshi yake ba. Sai wannan lokacin ma tunanin rashin ganin Mummy ya faɗo a ranshi bayan tace mishi gata nan zuwa tun lokacin da yaje ɗakinta ya faɗa mata Dady na asibiti yayi accident. Kallan time yayi a jikin wayarshi sai yaga har ƙarfe goma sha biyu da rabi tayi, rasa abinda ya kamata ya fara yi yayi. Tunani yayi ya kamata ya kira Zeey ya sanar da ita duk da fushin da yake yi da ita na barin su da tayi ta koma wajen Ummi. Zeey na kitchen tana girkin rana lokacin da ƙiran Kabir ya shigo wayarta, a lokacin wayar tana hannun Inaya tana yin game don haka bata lura da shigiwar kiran ba sai gani tayi ta danna ok. Ganin ta masa ne yasa ta kai wayar kunnenta tayi sallama haɗe da cewa "Ya Kabir Aunty Zeey bata kusa bari na kai mata," saboda yadda Zainab take zaunar da ita tana bata labarin Kabir yasa take ganin kamar tasan shi, shi yasa da taga shi ya kira kawai ta amsa. Shiru yayi yana tunanin wacece ita kuma wannan yarinyar? Ba dai? Kafin ya gama tunanin da yake yi yaji muryar Zeey tana cewa "Ya Kabir sai yau kaga damar nemana bayan duk ƙiran da nake yi maka baka ɗauka, ai wallahi ba don Inaya ta amsa ƙiran ba da nima sai naja maka class kafin na ɗauki wayarka." Cikin wata irin cunkusashiyar murya Kabir yace "Daddy ne Zeey, Daddy yayi accident yana asibiti ance za'a yanke mishi ƙafa." Da ƙarfi Zeey tace "What? Garin yaya? Yaushe hakan ta faru ban sani ba?" Ai tuni ta fara kuka jin wai za'a yankewa Daddynta ƙafa. Ihun da tayi ne yasa Ummi fitowa daga ɗaki da sauri don tasan tabbas ba lafiya ba. Tana shigowa taga Zeey na kuka ta e "lafiya? Meya faru?" Zuwa tayi ta rungume Ummin tana cigaba da kukan, cikin kukan take faɗa mata abinda Kabir ya faɗa mata. Itama ji tayi hankalinta ya tashi amma haka nan ta daure ta zaunar da Zainab tana rarrashinta har ta samu ƴar nutsuwa. Tashi tayi ta kalli Ummi da idanunta da suka yi kozai-kozai tace "Tafiya zan yi Ummi, zan je naga a halin da Daddy yake ciki." Ɗaga mata kai tayi alamun amsawa sai kuma tace "Bari na ƙira wo Mubashir ku tafi tare don bazan yarda kiyi driving a wannan halin da kike ciki ba. "To," kawai ta cewa Ummin don ba zata iya yi mata musu ba. Kabir kuwa suna gama yin magana da Zainab ya tashi motar shi ya tafi gida yana tunanin abinda ya hana Mummy zuwa asibitin har yanzu kuma ko a waya bata kurashi taji halin da ake ciki ba bayan tasan abinda ya faru tunda sai da yaje ɗakinta ya faɗa mata kafin ya bar gudan ya tafi asibitin. Daga wajen gate yayi parking don baya so ya ɓata lokaci ya shiga gudan, direct ɗakin shi ya wuce ya ɗauki atm cards ɗin shi da duk wani abinda zai buƙata. Har zai yi ficewarshi ya koma asibitin sai kuma yayi tunanin watakila fa Mummy ba lafiya ba tunda har ta kai yanzu bata nemeshi ba don haka ya juya ya koma ɗakinta don ya dubata sai dai abinda kunnuwanshi suka jiye mishi yana dosar ƙofar ɗakin yasa ya daskare a tsaye a wurin....Me kunuwansa suke jiyemai? Anya ba mafarki yake ba? *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*       *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA UKU* {93} Hannun ƙofar ya saki tare da zubawa ƙofar ido, kalaman Nabila ne suka dawo dashi daga hayyacinshi “Koma menene Kabir nake so, in har da gaske kina so na kamar yadda kika ce to kisan yanda kika yi na aureshi, shi nake so kuma shi nake son aura.” Mummy ce ta katseta a fusace tana cewa “Sanda nake ta ce miki a’a ki bari kin ji magana ta? Ko har yanzu baki san shirmenki bane ya samu cikin situation ɗin da muke ciki yanzu? Da kin barni ni nasan yadda zan yi ki aureshi tunda ba aure ne ya haramta tsakanin ku ba amma shirmenki da gaggawa yasa kika lalata komai, banda dai ni nasan takan komai da yadda zan gyara abu da tuni kin kashe mini aure, to sa’a ta ɗaya Alhaji Sulaiman a tafin hannuna yake, sai yanda nayi dashi daga shi har yaranshi, ba boka ba Malam amma duk a tafin hanuna suke, ita kanta wacce ta nemi yi mini gardama na rabata da mahaifinta,” tayi tsaki sannan ta cigaba “Amma da yake ke sam baki da haƙuri gashi nan kin rasa Kabir ɗin, da kin bi maganata sanda nace a’a da yanzu sai yanda kika yi dashi, ko kina tunanin lokacin da kike munafircin kyawawan halaye duk ba training nake yi miki a fakaice ba?” Nabila kallon Mummy kawai take yi cike da mamaki kafin tace “Ke ba son su kike yi ba ni kuwa Kabir son gaskiya nake yi mishi, kuma Allah in kina so hankalina ya kwanta ki san yadda kika yi na mallakeshi.” Tsaki Mummyn tayi tace “A yanzu ko zai aureki bazan baki shi ba don kuwa babu dalilin da zai sa ki aureshi, primary election ɗin ma har sun faɗa ya faɗi, gashi yana asibiti yayi accident na kira driver ɗinshi naji meke faruwa saboda bani da time na yawon asibiti yake sanar dani ƙafarshi kamar ta samu matsala, to faɗa min me yake dashi da zan bashi ke? Bayan rabin dukiyarshi tawa ce.” Kabir duk yadda yaso ya daure akan abubuwan da kunnenshi ke jiyo mishi kasawa yayi ji yayi ƙafafunshi na neman kayar dashi ƙasa, da sauri ya dafa bango sannan ya fara jan ƙafafunshi yana tafiya kamar wanda bashi da laka, zuciyarshi bazata iya tsayawa ya gama jin abinda kunnenshi ke jiye mishi ba, waje kawai yayi ya shiga mota, ko tankawa mai gadi dake tambayarshi har ya fito bai yi ba, da ƙyar ya iya sawa motar key sannan ya bar layin. Kalaman Mummy ne ke sake mishi rito a zuciya wanda yake ji kamar ana sake dawo mishi dasu cikin kunnuwanshi, da ƙyar ya isa asibiti sai dai ya kasa fita daga motar kawai ya zauna yana tunanin wannan rayuwa, taya zata riƙesu shekara da shekaru ta dinga irin wannan furucin? Ya daɗe a haka kafin wayar Zainab ta shigo wayarshi, da sauri ya ɗauka yace “Kin iso?” Hankalinta a tsananin tashe tace “Ya Kabir kuna ina? Gamu yanzu mun shigo.” Kwatancen inda zata sameshi yayi mata sannan suka yi sallama, basu fi minti uku ba sai gasu sun iso lokacin yana waje yana jiransu. Da sauri-sauri gudu-gudu ta ƙaraso idanunta taf da ƙwalla tace “Ya Kabir ina Daddy?” Wani abu ya haɗiya tare da kallon Mubashir sannan yace “Muje.” Nan suka shiga ciki, duk ta rikice kawai Daddy take son gani, Kabir ne yace “Zainab akwai ragowar payments da bamu yi ba wanda ni kuma babu ragowar kuɗi a wurina.” Mamakin kalamanshi ne yasa ta kalleshi sai dai bata da lokacin wannan hakan yasa ta miƙa mishi card ɗinta ta sanar dashi pin sannan tace “A ina Daddyn yake?” Nan ya sanar da ita ɗakin ita dai hankali a tashe take tafiya, Mubashir ne yabi bayanta. Kabir sai daya biya ragowar kuɗaɗen sannan ya dawo inda Daddy yake. Tunda Zainab taga halin da Daddy yake ciki take kuka, kuka kawai take yi, a hankali ya ɗan motsa hannayenshi sannan ya buɗe ido kamar mai jin bacci ya saukesu a kanta, wani murmushi yayi mata na tausayi sannan ya maida idon ya rufe da alama dai maganin da drip ɗin da aka saka mishi akwai na sa bacci, kallon Kabir tayi tana hawaye ta kalli ƙafar da aka naɗeta da bandage tace “Ya Kabir ya zamu yi?” Kai ya girgiza alamar rashin sani kafin ya share ƙwallar shi yace “Ina ji duk alhakina ne ya sauka akan Daddy, Zainab na shiga uku….” Ya ƙarasa maganar yana dafa bango don shi kaɗai yasan me zuciyarshi take ji a wannan lokacin. Fitowa tayi daga ɗakin tace “Ya Kabir zo.” Bai musa ba yabi bayanta har sun kai bakin ƙofa ta kalli Mubashir tace “ƙanina ɗan zauna anan kaɗan yanzu zan dawo.” Cewa ƙanina da tayi yasa Kabir ƙara kallon yaron, wani abu ya haɗiya don yanzu kam ya tabbatar yaron nada haɗi da Ummi ko ba ɗanta bane yasan yaron dai wani nata ne. Fitowa suka yi suka zauna daga gefe, kallonshi tayi tace “Ina Mummy?” Kalmar Mummy da tace yasa ya kalleta ji yayi wani abu ya tsaya mishi yace “Zainab ashe matar nan ba tsakani da Allah take son mu ba.” Yanayinta ne ya canza tace “Ba dai wani abun tayi maka ba?” Kai ya girgiza zuciyarshi na zafi ya sanar da ita abinda ke faruwa.” Hawaye Zee ta goge tace “Ya Kabir me yasa kaga na bar gida ban ƙara waiwaye ba? Na gane halayenta ne kuma kai da Daddy kun kasa bani dama na sanar daku wannan dalili yasa naƙi dawowa.” Nan ita ma ta kwashe komai ta sanar mishi, mamaki duk ya hana Kabir magana, sai hawaye kawai da yake ta zubo mishi saboda tashin hankalin da yake fuskanta wurin matar da yafi yarda da ita a duniya fiye da kowa. “Zainab na faɗa miki alhaki ne, na yar da Ummi gashi nan abinda ya sameni, ya zan yi? Wannan daya kawoki wanene?” Murmushi tayi tace "ƙaninka ne wanda baka sani ba.” Kai ya kauda yana maida kwallar dake neman zubowa yace “Wacce muka yi waya fa?” Tace “Ita ma.” Ido ya runtse, tausayinshi ya kamata tace “Ya Kabir ka girma yanzu don Allah, yanzu dai kana ganin yadda rayuwa ta zo mana, matar nan haka ta dinga zuga Daddy yana kwaso kuɗin da ba nashi ba na gomnati yanzu kaga ko zuwa ta dubashi bata yi ba.” Kwafa yayi yace “Rayuwa ce tayi abinda ranta ke so.” Haka suka koma ɗaki suna ji suna gani aka shiga da Daddy aiki, takaicinta ɗaya da bata dage wajen sanar da Daddy da Kabir halin Mummy ba har sai sanda aka zo lokacin da abu ya riga ya ƙure. Mubashir ne ya siyo musu ruwa ya miƙawa Kabir ɗaya, kallonshi yayi idanunshi sun ciko hannu ya miƙa mishii alamar musabaha, Mubashir shima ya miƙa mishi, ji yayi zuciyarshi na ƙara karyewa kawai sai ya rungumeshi. ***** A hankali Baqeer ya kai hannu saman goshinshi da yake ji kanshi nayi mishi ciwo, Tanimu ne ya kalleshi yace “Ya Baqeer ka koma gida ka huta don Allah, ni zan kula da ayyukan da ake yi anan.” Kallonshi yayi sannan ya kalli kayan mutanen da yake taso a gama haɗa musu don yana da buƙatar wasu kuɗin ya haɗa da na hannunshi ya biya ragowar kuɗin gidan, in yaso a hankali ayi funitures ɗin da ya kamata, zai sake magana Tanimu yace “Don Allah kaje ka huta.” Murmushi yayi yace “Kai ma ka iya magiyar Salim ko?” Kai ya sadda ƙasa yana shafa bayan kanshi, tare suka fito suka shiga mota akan in ya kai shi zai dawo shagon shi. Kanshi ya maida jikin window yana kallon mutane, motar data gifta ta gefensu ya kalla da kuma sauri ya kalli number motar, sai dai bai iya duba number sosai ba ta wuce, kai ya girgiza tunowa da yayi ba ita kaɗai bace mai irin motar, sannan in da sabo ya saba ganin irin motar yana duba plate number yaga ba nata bane, ido ya ɗan lumshe sannan ya buɗe yana tunanin anya bai fi son Zainab akan yadda take sonshi ba kuwa? A wani shagon Rufaida yoghurt ya tsaya ya ɗan yi siyayya sannan suka wuce, ya bawa Tanimu nashi shi kuma ya shiga gida. Hadiza tayi wankin ragowar kayan Umma wanda aka zubar a waje suka ɗan ɓaci, gaisawa suka yi yace “Maimakon ki bari in za’a kai wanki a haɗa?” Tace “A’a ba komai, dama ɗazu muka zo ni da Maryam to ita ta koma saboda nemanta da mai gidan yake yi shine nace bari na ƙarasa kafin na tafi.” Kai ya jinjina yace “Yanzu dai ba matsala ko?” Dariya tayi tace “Inafa matsala ai Ya Baqeer yanda kasan ba Baban su Husaini ba haka yake min, nan nan yake dani tunda yaga ina samun kuɗi sosai, sannan kaga saida atamfofi da nake online ɗin nan shima ba ƙaramin taimaka min yake ba, ni dai kam ba abinda zance maka sai fatan Allah ya kara lafiya ya kawo mace ta gari.” Bai amsa a fili ba sai dai yace Ameen a ranshi. Mayafi ta ɗauko ta yiwa su Umma sallama sannan ta tafi. Dada ce suna gaisawa tace “Ni kam Baqeer auren mahaifiyarka kashe mata shi kayi ko me? Ita ta biyeka kai kuma banga kana da niyyar maidata ɗakinta ba.” Kai ya kauda yace “Da wannan auren da babu shi duk daya ne.” Baki Dada ta saki kafin tace “Koma dai menene ka maida ta ai dai ɗakinta shine darajarta.” Kallonta yayi sosai yace “Dada bafa zata koma ba, ni gidan dana siya ma na kusa gama biyanshi maidaku can zan yi.” Kallon mamaki suka yi mishi, ya shige ɗaki ba tare da ya ƙara cewa komai ba, Dada ce tace “Fatima nima ba son zamanki da Badaru nake yi ba amma aure da ƴaƴa kun riga kun zama ɗaya.” Murmushi ta yiwa Dada tace “Ke kika san mun zama ɗaya Dada amma ba Badaru ba, ni ba kashe aurena zan yi don ɗana Allah ya azurtashi ba kawai dai bazan koma bane har sai yayi nadama ya canza hali.” Jin haka yasa Dada kallonta, tabbas Badaru bashi da imani ita kanta tana bada shawarar ne a matsayinta na uwa wacce tasan hakan bai dace ba, amma me za ayi da auren Badaru? *** Asiya ce ta kalli Mama da ta miƙo mata wake tace wai ta surfa ta wanke za’ayi alale, kamar ita? Ai ita ko a gidansu bata daka bare hannunta yayi kanta. Kauda kai tayi gana gyara kwanciya tana cewa “Mama bana jin daɗi kin sani don haka bazan iya surfe ba gaskiya,” ta ƙarasa maganar tana gyara kanta.  Ajiye mata waken tayi tace “Sai ki zaɓa ko aikin dana saka ki ko kuma ku tattara ku nemi gidanku.” Komawa tayi ta zauna don kuwa tasan bata da wurin zama banda nan ɗin don ko banza yafi gidan su, bata son tuna wahalar da tasha a komawarta wai kamar ita zasu yi ta bawa ɗumame shima sai dai ta ɗumama da kanta, gashi itace ne, da farko kayanta na lefe taso siyarwa sai dai ba dama don kuwa Bello ya taho dasu nan gidan, dole ta tattara ta taho ai ko banza nan ɗin ana ci asha kuma gidan yafi na iyayenta. Haka nan ta amsa kamar zata yi kuka tana daka tana ƙunƙuni. **** A hankali Daddy yake bin ɗakin da kallo, idanunshi ne suka sauka akan Zainab dake gefen gado ta kwantar da kanta a kusa da ƙafar shi, hannu ya kai yana son taɓata kawai yaga ta ɗago, da sauri ta dawo inda yake tace “Daddy ka farka? Ya kake jin ka? Wurin yana yi maka zafi? Akwai inda kake jin ciwo?” Murmushi yayi yace “One at a time Auta, slowly.” Hawaye ne suka zubo mata tace “Daddy kayi haƙuri na tafi na barka, gashi abinda ya sameka, ka sani?” Kai ya ɗaga mata alamar eh, tare da lumshe ido yace “Kina tunanin zasu min aiki babu izinina ne? Ni nayi signing lokacin Kabir yaje gida ya dawo.” Murmushin tausayin kansu yayi yana ƙoƙarin riƙota da sauri ta mika hannunta ta kamo nashi tasa kuka. Lallashinta yayi har ta tsagaita sannan yace “Rayuwar kenan, sannan laifina ne dana bari diabetes ya shigeni haka ba tare da sanina ba ban kuma duba canjin da nake ji a jikina ba saboda hankalina yana kan siyasa, sannan ko na sani ma me zan yi Zainab?” Hawaye ta share ta ƙara riƙe hannunshi tace “Am sorry Daddy.” “Me kike ci a Dambatta da naga kin canza haka?” Fuskarta ta shafa tace “Kai Daddy.” Gefe ya kalka ya ɗan dubi ƙofa, Zee jikinta ya bata Mummy yake nema hakan yasa tace “Tazo ɗazu komawa gida tayi ta huta,” tayi maganar cike da son janye tunaninshi. Maida kallonshi yayi kanta yace “Ba ita nake nema ba Kabir nake jira, da alama tunda na kwanta bata zo ba.” Da mamaki Zee ta kalleshi tace “Daddy me kake nufi?” Murmushi yayi yace “Tunda aka yi aikin ina farkawa lokaci-lokaci sai dai bana iya magana saboda ƙarfin allura, a iya tsawon farkawar da nayi ban ga wata mace ba bayan ke.” Jikin Zee ne yayi sanyi don bata son yi mishi ƙarya, gashi Kabir da Mubashir sunje gida jiya ma suka ga bata gidan. Bai yi magana ba hakan yasa ta juya don ta kira nurse., da kallo kawai ya bita. **** A shagon Baqeer da aka yi mishi kwatance Kabiru ya tsaya, ido ya runtse tare da sauke ajiyar zuciya, bai ga ta zama ba dole ne yazo ya nemi yafiyar Baqeer, yana ji kamar laifukanshi ne suka sauka kan Daddy, mamaki yake yi yadda aka yi shagon dashi kanshi yasa yi kaya kusan kala biyar a wajensu ashe shagon Baqeer ne, fitowa yayi daga mota ya tsaya a jikin ta inda kana gano cikin shagon, Baqeer yana zaune sanye da riga da wando yasa table a gaba yana yanka, wuyanshi ɗauke da tape sai gefen kunnenshi da yasa pencil, ɗagowa yayi ya kalli waje ta glass door ɗinsu, idanunshi ne suka sauka kan Kabir. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Umm Asghar Ce* *Da* *Ayusher Muhd* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA HUƊU* {94} Sosai ya kalleshi yana mamakin abinda ya kawoshi nan sai kuma ya juya ya cigaba da aikin shi cikin ranshi dai cewa yayi "To ina ruwana tunda dai nasan ba wurina yazo ba." Kabir ya daɗe a tsaye a wurin yana tunanin ta yadda zai fara fuskantar Baqeer bayan abinda yayi mishi, haka nan ya ƙarfafi kanshi ya daure ya tura ƙofar shagon ya shiga. Tanimu na ganinshi ya taso ya tare shi da fara'arshi yana welcoming ɗin shi don babu laifi suna da kyakkyawar mu'amala da customers ɗin su. Bayan sun gaisa da Tanimun ne yace mishi wurin Baqeer yazo. Raka shi yayi wajen da Baqeer yake aikin yanka ya ɗauko mishi kujera ya ajiye kafin yaje ya kawo mishi ruwa da drink duk ya ajiye mishi sannan ya tafi ya bar su. "Assalamu alaikum," Kabir yace don duk tsawon lokacin da ya ɗauka a wurin Baqeer bai yi alamar yasan da tsayuwarshi ba. "Ameen Wa'alaikassalm," shima ya amsa mishi ba tare daya ɗago ya bar abinda yake yi ba. Ɗan shiru Kabir yayi yana jinjina ta yadda zai fara faɗin abinda ya kawo shi duk da bai ga fuska a wajen Baqeer ɗin ba sai dai kuma bai ga laifin shi ba don tun dama can su ɗin ba abokai bane ga kuma abinda yazo yayi mishi bayan ya kaɗeshi da mota sannan ya gudu ya bar wurin ko fita bai yi yaga a halin da ya saka shi ba. Ɗan gyaran murya yayi dai kuma yace "Zuwa nayi na baka hakurin abinda nayi maka duk da dai babu abinda hakan zai canja, don Allah kayi haƙuri ka yafe min, bani da wani excuse akan abinda nayin don haka ma bazan kawo uzuri akan hakan ba. Fatana ka yafe min don Allah ba don ni ba nasan in har ba yafe mini kayi ba bazan taɓa ganin daidai a rayuwata ba." Saurarenshi kawai Baqeer yake yi yana jin ciwon abinda yayi mishi yana dawo mishi kamar a lokacin abun ya faru. Idan yace bai ji ciwon rasa ƙafafunshi da yayi ba kowa ma yasan ƙarya ne to amma idan ya duba yaga alherin da hakan ya janyo mishi a rayuwa sai ya gode Allah don ya tabbatar da hakan bata faru ba Badaru ba zai taɓa barinshi yayi pursuing dream ɗin shi na zama tailor ba, watakila da har yanzu yana can Badaru na juya rayuwarshi yadda yake so bai isa ya yankewa kanshi hukunci ba dile sai abinda yace zai ayi. Ɗagowa yayi ya kalleshi yace "Kada ka damu abinda ya riga ya wuce babu amfanin dawowa dashi baya, Allah ya yafemu gaba ɗaya." Farin ciki ne ya cika zuciyar Kabir don bai tsammaci samun afuwa daga Baqeer ɗin da wurwuri haka ba, godiya yayi tayi mishi har sai da yace ya isa haka nan sannan ya bari. Ƙara gyara zama yayi na wasu ƴan dukkansu kuma sai suka yi shiru don babu wani sabo a tsakaninsu, sai da ya tashi zai tafi sannan yace "You didn't ask me about her, ko har ka manta da ita?" Ya ƙarashe maganar da sigar tambaya. Da sauri Baqeer ya ɗago ya kalleshi jin ya taɓo mishi abinda ke ƙunshe cikin ranshi. Ɗan kawar da kai yayi ya basar kamar bai ji abinda Kabir ɗin yace ba. "Bai tsaya sauraren abinda zai ce ba ya sake cewa "Ta dawo fa although bata san zan zo nan, zan ce mata kana gaisheta," ya ƙarashe maganar da tsokana duk da babu wani sabo a tsakanin shi da Baqeer yana so wannan awkwardness ɗin ya rabu dasu. Ɗan murmushi kawai Baqeer yayi sai dai duk da haka bai yi magana ba sai ma ɗaukar scissors da yayi zai cigaba da yankan kayan da Kabir ya tarar dashi yana yi. Ƙara nutsuwa Kabir yayi yace "Nagode sosai I really appreciate it, baka duba kuskurena ba ka yafe min duk da na aikata maka ba daidai ba, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi." Hannu Baqeer ya miƙa mishi suka yi musabaha sannan yace "Kada ka wani damu ya riga ya wuce kuma ni dama ban taɓa riƙe ka a raina ba." Wayarshi ya miƙa mishi yace idan baza ka damu ba ka bani number ka ma riƙa gaisauwa." Karɓa Baqeer yayi ya saka mishi number sai shi kuma yayi flashing Baqeer yaga tashi number sannan suka yi sallama ya tafi yana ayyana wani abu cikin ranshi. Haka Kabir ya fita yana jin daɗi don sai yaji kamar an suke mishi wani gungumemen dutse daga kanshi, ashe haka hakki yake duk yabi ya dabaibaye rayuwarka ya hana ka samun cikakkiyar nutsuwa. Yana fita Baqeer yabi bayanshi da kallo cikin ranshi yana cewa "Ai ko don Zainab dole na yafe maka tunda ka kasance ɗan uwanta." Duk da haka yayi mamakin abinda ya faru daya canjawa Kabir ɗin tunani har ya nemeshi ya nemi yafiya a wurinshi. ***** Tunda Baqeer yazo ya ɗauke Fatima hankalin Badaru ya tashi, ya kasa gasgata abinda idanunshi suka gani wai Baqeer ne yazo gidan cikin kyakkyawar shiga ga ƙatuwar mota, kenan cigaba yayi da aikin zanen babu shi? Yanzu don rashin imani irin na ɗan yau shine da hannun nashi ya warke bai nemeshi sun cigaba da yin harkar tare ba shine don rashin amana ya tafi yake yin abun shi shi kaɗai ba tare da ya nemeshi ba, ya mance duk tarin alherin da yayi mishi ya fifita shi a cikin ƴaƴanshi amma yanzu da yayi kuɗi uwarshi kaɗai ya sani. Wannan baƙin cikin ne yasa abu kaɗan zaka yiwa Badaru sai ya hau faɗa yana zage-zage tun ba Abu ba don yake jin haushi gana satar da Kamalu yaje yayi banda Allah ya tufa asiri Baqeer ya hana a tafi dasu watakila da har yanzu suna police station ga kuma na tayashi ɓoye kayan da yake zuwa kasuwa yana sace mishi da tayi shi yasa ko gilmawarta ya gani ya dinga surfa mata zagi kenan, to itama da yake lallaɓawa take yi shi yasa bata biye mishi sun yi rigima ba kamar yadda suka saba yi da. Daga Abun har Jamila abun duniya ya taru yayi musu yawa, sun rasa ta yadda aka yi Baqeer ya zama wani babban mutum haka daga ganin shi anga wanda yake cikin wadata da kwanciyar hankali. Ta yaya za'a ce duk wani alheri da zai samu a cikin gidan sai dai Baqeer ya samu bayan suma sun da ƴaƴan nan, anya kuwa babu wani abu da Fatima tayi don ɗanta yafi nasu ɗaukaka da kuɗi kuwa? Kai gaskiya ma haka ne don in ba hakan ba sai kace shi kaɗai ne ɗa a cikin gidan, su miye sa nasu ƴaƴan basu zama wani abu ba har yanzu sai shi da ko shekara biyu bai yi da barin gidna ba zai dawo yayi irin wannan kuɗin, to ko dai sata yake yi? Wata zuciyar ta Jamila ta kitsa mata hakan sai dai ta kasa yardar wa kanta Baqeee zai yi sata watakila dai wata sana'ar ya kama da kuɗin filin shi da Fatima ta ɗauke ta kai mishi. Har kamar ta tashi taje ɗakin Abu su tattauna don tunda abun nan ya faru basu zauna wuri ɗaya sun yi maganar ba ga kuma tijarar da Mallam yake yi musu kullum tasa kowaccen su ta kama kanta ta tsaya a iya ɗakinta kawai. ***** Har Daddy ya ƙari zamanshi a asibiti ya fito Mummy bata je ta ganshi ba. Hidimar gabanta kawai take yi da dukiyar shi data dinga sawa yana canjawa zuwa sunanta a cewarta saboda siyasar shi ne kada ya samu matsala, ko bincike aka zo ba za'a ga ya tara wani abu da yawa ba bare hakan ya kawo mishi cikas. Ranar da aka sallame shi suka koma gida ma basu sameta a gidan ba, sai Zeey ce ta turashi zuwa ɗakin shi akan wheelchair daya koma amfani da ita yanzu, bayan nan ta shiga kitchen ta shirya mishi abinci. Faten acca tayi mishi da yaji hanta da ganyen ugu. Tana ƙara tsaftace wajen ne bayan ta gama girkin Kabir ya shigo kitchen ɗin, kallonta yayi yaga yadda take aikin cikin nutsuwa kamar ba Zeey ɗin daya sani ba, kai shi sai yace ma tunda ta dawo yaga wata irin nutsuwa a tare da ita wacce sam da bata da ita. Lallai Mummy ba ƙaramin cutar su taso yi ba banda Allah ya kiyaye watakila so tayi su lalace ta yadda baza su iya amfanar kansu da komai ba. Ita Ummi da yake uwa ce ai gashinan a zaman shekara guda kacal da Zainab tayi a wurinta ta koyar da ita duk wani abu daya kamata ace ƴa mace mai shekarunta ta iya ga kuma tarbiyya da tayi mata wacce sam ba'a basu irinta ba tsawon shekarun da suka ɗauk aa cikin gidansu, komai suka yi daidai ne idan laifi suka yi sai dai ma Mummy tayi ƙoƙarin taya su ɓoyewa kada Daddy ya sani, a wancan lokacin gani yake yi duk duniya babu mai ƙaunarsu irin Mummy shi yasa ko mahaifiyarsu basu wani damu da ita ba ashe ita tana da manufarta tayin hakan sune basu sani ba. Ƙarasawa yayi cikin kitchen ɗin yace "Har yau na kasa sabawa da ganinki kina aiki, sai nayi ta mamaki ina tambayar kaina wai shin da gaske wananan Zeey ɗin ce dana sani da ko ruwan zafi bata iya dafawa ba." Dariya tayi tace "Ai dai wallahi anso a cutar dani Allah ya kiyaye da haka zan tafi gidan miji ban iya komai ba. Baka san abun haushin bama sai idan Inaya tayi aikin dana kasa yi Ummi tayi ta min gori tana faɗa babu shiri na tashi na koyi hidimar gida sannan na huta da faɗan Ummi lokacin da taga na daina yi mata kwaɓa." Shima dariyar yayi yace "Ina so naje naga Ummi sai dai ina jin nauyinta sosai, sam bamu kyauta mata ba tun ma ba ni da nake da wayo sosai lokacin da ta bar gidan ifan ke baki tuna wasu abubuwan ba ni ya kamata ace na tuna." Ajiye duster dake hannunta tayi ta kamo hannunshi tace "Ya Kabir Ummi bata yi fushi da kai ba kullum tana zuba ido ganin ta inda zata ganka don haka ka ture duk wasu tunanukan da zasu iya hanaka zuwa wurinta kaje ta ganka, lokacin zaka san ba'a yi mata adalci ba da aka rabata damu sannan kuma aka hana mata ganin mu." Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace "In Sha Allah zan je bari dai Daddy ya ƙara samun sauƙi sai mu saka time ki rakani," ɗaga mishi kai tayi alamun amsawa sannan ta cigaba da aikin daya tarar da ita tana yi. Bayan ta gama ta ɗauki tray ɗin data haɗawa Daddy abinci ta nufi ɗakinshi. Sai da ta ƙwnƙwasa ya bata izinin shiga sannan ta tura ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, lokacin yana kwance akan gado gaba ɗaya duniyar nan bata mai daɗi sai dai a yanzu bamai bashi mamaki kamar Mumy, sai dai bai sa abin a ransa ba yana ganin da mutuwa yai fa? Ƙoƙarin miƙewa yake yi amma ya kasa don haka kawai ya koma ya kwanta, ajiye tray ɗin tayi akan bedside table sannan ta kamashi ta taimaka mishi ya zauna, pillow ta ɗauka tasa mishi a bayanshi tana yi mishi sannu. Abincin ta zuba mishi sannan ta miƙa mishi plate ɗin tace "Daddy gashi da kaina na dafa maka, ci kaji yayi daɗi." Karɓa yayi yana murmushi, sai da ya i abincin yaji taste ɗin shi sannan ya kalleta yace "Da gaske ke kika dafa wannan abincin?" Ɗaga kanta tayi tana dariya, girgiza kai yayi yace "gaskiya yayi daɗi, hala karatun chef Ummin taki tasa kika yi a Ɗambattan." Cikin jin daɗin yabon da Daddy yayi mata tace "Babu wata makaranta dana shiga Daddy Ummi ce ta koyar dani duk wasu ayyukan cikin gida har na iya." Jinjina kai yayi yace "Ta kyauta, kinga yanzu bani da haufi idan na aurar dake don nasan kin iya duk wani abu daya dace macen ƙearai ta iya." Sunkuyar da kanta tayi bata ce komai ba si yanayinta daya canja daga farin ciki zuwa damuwa. Sosai Daddy ya kalleta sai ya ajiye plate ɗin hannunshi ya riƙo hannayenta yace "Kiyi haƙuri Auta nasan ban kyauta miki ba kin kawo wanda kike so na koreshi na hanashi aurenki, a wancan lokacin gani nake yi abun kunya ne ace na ɗauki ƴata na bawa gurgu gashi kuma ɗan Badaru mutumin da tun tasowarmu babu wata jituwa a tsakaninmu sai gashi tun ba aje ko ina ba Allah ya nuna mini iyakata, idan rashin ƙafa ce tasa na hana Baqeer aurenki to gashi nima na gamu da larurar wacce tafi tashi ma don shi ai da ƙafafuwan shi takawar ce kawai baya iya yi ni kuwa an yanke ƙafar ma gaba ɗaya ta tafi kenan ba zata sake dawowa ba." Tunda Daddy ya fara maganar nan Zeey take kuka, sai taji wani irin rauni ya lulluɓeta gana tausayin Daddy gana tausayin kanta. Hannu Daddy yasa ya goge mata hawayen yace "ki daina kuka kin ji auta, idan kuna tare har yanzu ki faɗa mishi ya turo iyayenshi ayi maganar aurenku don a yanzu bani da wani buri bayan naga na aurra daku daga ke har Kabir, siyasar dana ƙwallafa rai akanta ma ina kwance anyi zaɓen primaries ganin ga larurar data sameni yasa ƴan ƙarƙashina duk suka koma wajen abokin takarata don haka duk shi suka zaɓa shi jam'iyya ta tsayar a matsayin ɗan takarar senator ɗin." Kanta a ƙasa tace "Bama tare dashi Daddy tun wancan lokacin ya rabu dani," tayi maganar muryarta na rawa alamun kowanne lokaci zata iya fara wani kukan. Dafata yayi yace "Kada ki damu kin ji idan har da gaske yake son ki to zai dawo barazanar da nayi mishi bata isa ta raba soyyyarku ba sai dai idan dama can ba sonki yake yi ba." Ɗagowa tayi ta kalli Daddy idanunta cike da hope akan abinda ya faɗa, ɗaga mata kai yayi yana bata tabbacin dawiwar Baqeer wajenta. Wani farin ciki ne taji ya kamata sai take ganin kamar ta samu Baqeer ta gama tunda Daddy yayi na'am da soyayyarsu. Shi kuwa Dady yanzu gani yake kamar babu komai cikin rayuwarshi banda yaranshi, saboda kaddarar data sameshi, sai yake ji gwara ya gyara kuskurensa tunda ga ishara nan ya fara gani tun yanzu. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA BIYAR* {95} Inna ce ta kalli Mummy cike da mamaki tace “Kina nufin hatsari yayi amma baki ma san halin da yake ciki ba? Sannan kizo kice min umara zaki? Wani irin ibada ne wannan Halima?” Murmushi tayi tana kallon Inna kai kace ba faɗa ake mata ba tace “Inna kenan, to ni in na zauna acan ma me zan yi mishi, gwara naje nayi mana addu'a kila Allah ya sassauta, ni ban san me yasa ba na gaji da murmushin ƙarya da nake yi sai nake ji yanzu komai ya isa bazan iya ba bare jinya.” Cike da takaici Inna ke mata wani kallo kafin ta ajiye kulun da take saƙa tace “To wallahi wannan karan ba dani ba, wani irin mugun hali ne wannan? Mutumin daya riƙe mu hannu bibbiyu kika rabashi da matarshi, kika sa ya dinga biya ma ƴar ki kudin makaranta ba tare da saninshi ba har ta zama abinda ta zama yanzu sannan kice baza ki iya jinyarshi ba?” Ganin yadda Inna take faɗa yasa tace “Inna don Allah kinga karki kawo min ƙabali da ba’adi, sanda nasa aka maida ke Hajiya ai baki ce mun haka ba.” Baki kawai Inna ta buɗe tana mamakin kalaman da Mummy ke furta mata, muryar Nabila ce ta katse mata tunani da cewa “Ai ba ita tace ki maidata Hajiyan ba, sannan in ma maidata Hajiyan ne ai da badon ita ba kema baki isa ki zama ba,” ta ƙarasa maganar cike da tsiwa da takaicin kalaman Mummy. Miƙewa Mummy tayi fuskarta a murtuke don har mayafin kafaɗarta na faɗuwa tace “Nabila how dare you?” Kanta tsaye tace “Ke da kike faɗawa Inna baki yi tunanin zata ji zafi ba? Ko kuwa mu muka saka kije kiyi yawon banza har ki same…….” Marin da Mummy ta zabga mata ne yasa ta yin shiru sai waigowa da tayi tana mata wani kallon raini, jikin Mummy har wani rawa yake yi saboda mamakin abinda take ji, Nabila? Yarinyar da akanta tayi komai saboda tana so ta bata rayuwa mai kyau? Duk da tsanar da tayi mata saboda tsautsayin daya faɗa mata a can ƙasan ranta tana son taga ta zama wani abun ba tare da gori ba. Bazata taɓa mantawa ba tana makarantar da tayi diploma ranar da suka yi graduation suna ta murnar gama makaranta, to saurayin da take so malamin makarantar ne, yace tazo suyi magana kafin ta tafi gida, haka ta sulale ta gudu wurin shi ba tare da ta sanar da su Inna da suka zo mata taron ba, lokacin tana ji da rawar kai, matan babansu biyu Inna da Dada, ita Dada tana da yara da yawa ita kuma Inna duk inta haihu sai ɗan ya koma sai data yi haihuwa shida sannan Allah ya bar mata Halima, shi yasa ta ɗauki son duniya ta ɗaura mata, ita kuma ta taso cike da rashin kunya don bata ganin kowa da gashi sai Innarta, gata ta iya yiwa maza wayau don su bata kuɗi bawai don tana sonsu ba, wani sa’in haka zata kira a rikice wai zata asibiti kai Babanta sai sun turo kuɗin ta cinye, to shi wannan Malamin da gaske take sonshi don akan shi tasha yin faɗa da class mates ɗinta tana ganin ita kaɗai ta dace dashi, yau kuwa tunda taji yace tazo ta lallaɓa ta gudu tana ganin yau dai zai furta mata kalmar ƙauna tunda dai ta gama school duk da tasan akwai maganar wani akanta don Babanta yayi alƙawarin bayar da aurenta ga ɗan abokin shi, da zuwanta ya shiga da ita ɗaki ya fara yi mata zance soyayya da yadda ya daɗe yana sonta, da kuma kunyar sanar da mutane yake saboda ita dalibarshi ce, jin haka yasa ta ƙara tabbatar da soyayyar shi, haka ya dinga mata daɗin baki har sai da ya keta mata budurcinta, bata damu ba don gani take yi ai aure zasu yi, haka ta dinga biye mishi suna shan shagalinsu sai dai har sama da wata bai je ko kofar gidansu ba, ita ke zuwa inya kirata bata auni ba sai da cikin jikinta yayi wata hudu sannan ta fahimci ma bata al’ada sam a lokacin fa hankalinta ya tashi nan ta rikice tayi gwaji pt sai ga ciki, Inna ce ta fara fahimta ta tsareta da tambayar haka ta sanar da ita tana kuka, sai dai me? Duk yanda aka yi Malam ya amsa yace bai san zance ba shi hasalima aurenshi saura sati biyu a lokacin, haka suna ji suna gani ya sawa idanunshi toka yace in suka yi misi sharri ma ƙara zai kai su, Inna kuwa tsoron mutane su san abun kunyar daya faru yasa ta yin shiru, nan fa Halima tsoro ya kamata tayi kuka har ta gaji, gashi Dada sai tayi ta binta da kallo tana son tasan ƙibar da tayi da yawan saka hijab da take yi na menene. A lokacin da mahaifin Halima ya frga da cikin jikinta ne yace sai dai ta fita ta bar mishi gida ita kuma Inna tace in dai ya kori Halima sai dai ya haɗa ya koresu gaba ɗaya don babu inda ƴarta budurwa zata tafi ta barta, shawara ta bawa Inna akan su je ƙauyen Innar in ta haihu sai su dawo sai dai bayan sun kama hanya ta kalli Inna a tsorace tace “Inna ina ga mu bar ƙasar in na haihu, yanzu muje inda ba’a san mu ba muce ni matar aure ce hijira muka yi bayan na haihu babyn ya ɗan tasa sai muje wani gari muce abinda na haifa naki ne in yaso in muka ga babyn ya girma ko shekara biyu ne sai mu dawo kinga ba wanda zai gane.” Da wannan shawarar suka shigo garin Kaduna suka kama haya da kuɗin gadon Inna na fili da suka saida bayan ta haihu, Nabila na shekara biyu suka dawo Kano don a lokacin zaman Nigeria ya fara yi musu daɗi suna ganin gwara ta ƙara ko shekara biyu ne, Inna sam auren ma sai taji bai dameta ba don Halima na fita ta samo kuɗi, bayan sun dawo Kano ne suka kama haya anan ne kuma ta ga rayuwar Ummi wanda ta fara kwaɗaituwa da inama ita ce? Ta sani sarai yara dasu ake cutarka shi yasa taja su Zainab a jiki ya zama kafin ma Ummi taji matsalar su sun sanar mata. Dawowa tayi daga ƙaramin tunanin data tafi tana kallon Nabila wacce har yanzu itama tana tsaye a kanta. Inna ce tace “Dukanku ya isa haka, wannan wani irin abin kunya ne?” Tayi maganar cikin raunanniyar murya, wani abu Mummy ta haɗiya ta fito daga gidan ba tare da tayi magana ba, Nabila kusa da Inna taje ta rungumeta kawai tasa kuka, Inna ma hawaye kawai take sharewa wannan wani irin rayuwa ne? Nabila tana kuka tace “Inna ki yafe min wallahi nasan ina son Kabir amma ƙaryar ciki da nayi kawai fansa nake son ɗauka akan Mummy ganin ta banzatar dani taje tana neman suna wurin yaran da ba nata ba, nayi dana sanin haka don daga ɗaukan fansa kan Mummy soyayyar Kabir ta mamayeni har na aikata abinda nayi, ki yafe min.” Kai kawai Inna ta girgiza don bata san me ma zata ce ba, wannan wani irin bala’i ne? Tashi kawai tayi ta koma ɗakinta ta kulle ta baza tagumi lallai son zuciyarta ne ya ja mata don a zamansu sun yi niyya ne in Halima ta haihu su koma yanzu gashinan ita rayuwar ma ba daɗi take yi mata ba, tsoronta ta mutu ƴan uwanta basu sani ba, bare mijinta da kila ma baya raye. ***** Kabir ne ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Salim kafin ya ɗau robar ruwa ya kwankwaɗa yace “Yanzu ba yanda zamu yi mu haɗa su? Ya kake gani in muka yi amfani da matsayin mu? Kai ka kira Baqeer ni na kira Zee muce mu haɗu anan?” Salim ya jinjina kai yana dariya yace “Haka  zamu yi am sure in dai sun haɗu tofa tsumar ƙauna zata tashi.” Hannu suka sake yin musabaha wai deal ya haɗu, Kabir yace “Karfa ka manta an jima ƙarfe biyar na yamma.” Salim ya jinjina kai alamar gamsuwa yace “Kai ma kar ka manta.” Da haka suka yi sallama duk sunaji sun ƙosa gobe tayi. Baqeer kuwa kallon mai gidan yayi bayan ya amshi takardun gidan yace “Nagode sosai,” ya dawo mota Tanimu ya tuƙa suka koma gida. Yana shiga gidan yaji muryar Umma na cewa “Koma dai menene kar ki yiwa Baqeer magana yanzu, don na kula yanzu a wuya yake sam bashi da haƙuri sai ya maida abun wani abu, aiki ai ba dole bane.” Dada ce ta cafe da cewa “Tunda ya rabu da Zainab ya zama mara fara’a ga saurin fushi, ni amma Maryama dole ne aikin nan? Ki zauna kiyi biyayya kamar yadda muka yi.” Kekenshi ya tura zuwa cikin gidan, Umma ce ta kalleshi a ranta tana fatan Allah yasa bai ji ba, kallon Maryam yayi wacce tayi saurin goge ƙwallarta tace “Ya Baqeer sannu da zuwa, ni yanzu nake shan labari wai da gaske Zainab budurwarka ce?” Wani abu ne ya taso mishi ya ɗan motsa baki zai yi magana Dada tayi caraf tace “Tsohuwar budurwa dai ko? Yo ni Baqeeru kama taɓa zuwa zance?” Ji yayi kalaman Dada kamar sun ƙara taso mishi da ƙaunar Zainab, murmushin yaƙe kawai yayi yace “Hajiya Dada kenan,” yayi maganar yana juyawa maimakon ya shiga ciki, Umma ce tace “Ina kuma zaka?” Yace “Abu zan amso Umma ba daɗewa zan yi ba," yayi maganar yana murmushi. Waya ya yiwa Tanimu akan ya taimaka ya kaishi wani guri, ba musu ya dawo don dama ba abinda zai yi a gida, gidan Maryam suka nufa don yana son yin magana da mijinta ya sani ba sai an faɗa ba mahaifin mijin ne ya hana aikin, don ya daɗe shi ke shirya su in sun yi faɗa lallai ya daina sakin fuska tunda har Maryam ta gwammace faɗawa Umma akan shi bayan bata yi,  wayar Salim  ce ta shigo ya ɗaga nan ya sanar dashi wai akwai wani mutumi da yazo yana son ganinshi a Gusto wai yazo daga Abuja ne zai wuce, ajiyar zuciya yayi sannan yace yana zuwa. Zainab kuwa tana riƙe da kaskon turaren wuta tana yi suna waya da Inaya, dariya kawai take yi saboda tambayar da Inaya ke mata, Mummy ce ta shigo tana matse ƙwalla tana kiran Kabir tana cewa “Kabir kana ina? Nikam ina Senate ɗina tun bayan kwanciyarshi nima zazzabi ya rufeni daga asibiti nake kwanana bakwai ana yi mini ƙarin ruwa…” ganin Zee ne yasata yin turus, Zee ta kalleta ta kawar da kai ta cigaba da wayarta kamar bata ganta ba, kai tsaye ɗakin Daddy ta nufa tana cigaba da matse ƙwalla. Ta kai hannu zata buɗe Zee ta riƙe handle ɗin, da mamaki ta kalli Zee tace “Auta oyoyo Allah yayi kin dawo ya jikin Senate? Har yanzu jiri nake ji.” Bayan wuyanta Zee ta shafa tare da waigawa sai kuma ta juyo tace “Wa zai mayar dake asibiti?” Tayi murmushi tace “Na warke ai.” Kai Zee ta girgiza tace “Ahh a hakan?” Da yake Mummy bata shirya barin gidan yanzu ba sai cewa tayi “Zainab please kar mu tsaya sa’in sa.” Hannu tasa ga mamakinta key ta ciro cikin aljihun wandonta, a gaban Mummy tasa key a kofar ɗakin sannan ta girgiza mata key ɗin tasa a aljihunta tace “A gaida Inna, kar ki manta ki kwashi kayanki,” tana kai nan ta maida waya kunnenta suka cigaba da hira da Inaya, a fusace Mummy ta fice ta bar gidan. Kabir ne ya fito daga ɗaki yana dariya ashe tunda ta shigo yazo fitowa ya jisu da Zainab yace bari ya ƙyalesu, kallonta yayi yace “Bani key ɗin zan zauna wurin Daddy please taimaka ki amso mini saƙo wurin wani abokina a Gusto yazo daga Abuja zai wuce ni kuma Daddy na buƙata ta kinga har text yayi min, kallon shi tayi kafin tace “Kai dai baka so na huta wallahi,” tayi maganar tana bashi key ɗin bata wani canza kayanta ba kawai abaya tasa baƙa a sama tayi rolling tare da sa sun glasses ta fito. Baqeer ne ya fara isa ya shiga sai dai bai ga inda mutumin yake ba, gashi waiters har sun bashi wurin zama, ruwa ya sha yana duba agogon hannunshi na apple watch, ganin har minti ashirin ga Salim yaƙi ɗaukan wayarshi yasa kawai ya yanke shawarar tafiya gida, turo electric wheelchair ɗinshi yayi yana zuwa jikin ƙofar fita ya ja ya tsaya saboda abinda idanunshi da zuciyarshi suke hango mishi, Zee ce tafe ɗauke da waya a kunnenta da alama Kabir take kira ganin bai ɗauka ba yasa taja tsaki tana waigawa idanunta ya sauka akan abinda zuciyarta ta daɗe tana muradin gani, nan da nan zuciyoyin mutanen biyu ta karye, kallon juna suke kamar yau suka fara ganin juna, wasu mutane ne suka zo shigowa ɗaya saura kaɗan ta buge Zee, Baqeer da sauri ya mata alama da hannunshi akan ta matsa, matsawa tayi tana waigawa sannan ta sake maida ido kanshi, wani abu ya haɗiya yana jin kamar yaje ya rungumeta sai dai ya sani wannan lokacin akwai saura. Takowa ta fara yi shima yana turo kekenshi har suka haɗu a tsakiya, hawaye ne suka gangaro saman kuncinta ta saki wani murmushi wanda kana gani kasan kuka ke neman ƙwace mata tace “Ya Baqeer?” Ji yayi sunan ya ratsashi don abinda ya dade yana begen ji kenan, murmushi ya sakar mata yace “Zainab!” Ido ta runtse ta sa bayan hannunta ta goge bayan idonta tace “Ka canza.” Ta nuna kekenshi tana dariyar dake ɗauke da gudun hawaye, kai ya daga mata yace “Hmm ba kya nan lokacin.” Kai ta sake jinjinawa tana share ƙwalla tace “Umm bana nan.” Kallon juna suka yi suka saki murmushin da su kansu sun san na missing ɗin juna ne. Kai ya nuna mata alamar su zauna, kai ta jinjina ba tare da ta musa ba suka wuce suka zauna. Menu aka kawo musu ya miƙa mata tare da ɗaga mata kai yace “Yi mana order.” Ta saki murmushi sai kuma tasa hannu biyu ta rufe fuskarta hawaye na zubo mata tace “Ya Baqeer kasan Daddy yayi hatsari?” Tausayinta ne ya rufeshi ya cire tissue ya miƙa mata yana cewa “Umm naji.” Amsa tayi tace “I am really scared in ya bar duniyar nan fa? Ya zanyi? Ina zani?” Ido ya zuba mata yana jin ƙauna da tausayita na dawo mishi sabo fil yace “Ko mu fita?” Kai ta ɗaga don ba abinci ne a gabanta ba ganinshi ya gama ƙosar da ita kuma tana son kaɗaicewa da Baqeer. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* [2/6, 08:44] Ayusher: *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA SHIDA* {96} A jikin motarta suka tsaya Baqeer nata kallonta, gaba ɗaya sai yaga ta canja mishi, ga wata irin nutsuwa da take da ita yanzun. Wani irin farin ciki ne yake ratsa zuciyarshi, yau dai gashi ga abar son shi a zahiri ba'a irin mafarkan da yake yawan yi ba sai idan ya farka yaga ashe mafarki yake yi. Ƙasaitaccen murmushi ya sakar mata yace "Kin dawo daga tafiyar kenan?" Itama murmushin ta sakar mishi kwatankwacin wanda yayi mata, haka nan take jin kunyar shi yau. Cikin wata irin murya tace "Umm na dawo, ya aka yi kasan bana nan?" Tace tana kallon fuskarshi sai dai ta kasa haɗa idanunta da nashi. "Matsoraciya ce ke ai ban sani ba." Yar hararar tsokana tamai tace "Allah a'a, sannan indai ansan bana nan kenan nemana akaje ba'a sameni ba?" Kai ya ɗan kauda yana murmushi mai sanyi yana cewa "Hmm maybe, kila naje bakya nan ance kinyi tafiya, maybe kila na ƙira wayar bata shiga ba." Da mamaki ta juyo tana kallon shi jin wai yayi ta zuwa yana nemanta, ita ai ta ɗauka ya rabu da ita kenan tun daga abinda Daddy yayi mishi ashe dai bai manta da ita Aaaba, sai taji wasu hawaye na neman cika idonta, ɗaga idonta sama tayi tana ƙoƙarin mayar dasu ciki don bata son tayi kuka a gabanshi. Sai da ta samu hawayen suka koma sannan tace "Ɗambatta na tafi wurin Ummi, wayata kuma na canja number ne." "Saboda ni kika canja number?" Yayi mata tambayar muryarshi tana ɗan rawa don yaji babu daɗi da yaji wai ta canja number ne, kenan don kada ya kira ya sameta a waya shi yasa ta canja layi. Da sauri tace "No ba haka bane Ya Baqeer nayi ne saboda hakan zai fi mana sauƙi wajen mantawa da juna don nasan mawuyacin abu ne iyayen mu su bari muyi aure a wancan lokacin sai dai hakan da nayi bai rage komai na daga yadda nake jinka a cikin zuciyata ba sai ma kewa da tunaninka da basu taɓa barina na huta ba." Wani daɗi yaji da jin yadda take jaddada soyayyarta a gareshi, kallonta yayi sai yaga kamar ta gaji da tsayuwar don haka yace ko zaki shiga daga cikin motar ki zauna naga kamar kin gaji," kallonshi tayi sai ta girgiza kai alamun a'a don bata son abinda zai shiga tsakaninsu a yau ɗinnan. Shiru suka yi kamar ba zasu sake magana ba sai kuma yace "Da kikaje can kin manta dani?" Waigowa tai ta kalleshi, idanuwansu suka haɗu da juna, idanunta na kanshi yace "Ba haka bane?" Kai ta girgiza haryanzu idanunsa na kanta, ya dan waiga kaɗan gefe yace "In nace ban taɓa son wata mace kamar yadda nake jin son ki a raina ba zaki yadda?" Wani abu ne taji ya sauka daga saman kanta har kafafunta, idanuwanta ta zuba mai wanda suke tara kwalla, hannunsa yasa cikin aljihu yana cewa "Maganganun Daddy basu ban tsoro ba sai ma ƙara min ƙarfin gwiwa da suka yi wajen son ganin na mallake ki, tafiyar da kika yi ce abinda yayi min cikas don ni ban ɗauki rashin jituwarsu da Baba abinda zai hanani aurenki ba zan aureki with or without his consent, bana jiran ya bani izinin aurenki don bashi zai zauna min dake ba, Daddy ne dama matsalar shima kuma na shirya ɗaukar duk wani ɓatanci da zai fito daga wurinshi idan har zai haƙura ya bani aurenki." Wani murmushin farin ciki ne ya suɓuce daga bakinta, cikin yanayi na jin kunya ta goge kwallarta tace "Shima Daddy ba matsala bane don a yanzu ya amince na kawo wanda nake so zai aura min ni kuma kasan kai ne..." sai tai shiru tana ta rufe fuskarta saboda kunyar yadda ta iya tsayawa a gabanshi tana fallasa mishi asirin zuciyarta. Ya kalleta yace "Faɗa min nine me?" Kai ta girgiza tace "Kaima kansani." Shima kai ya girgiza yace "Bansan komai ba, a faɗa min ko daga haɗuwa na fara rubuta bashin da aka fara bina." Kallanshi tai tace "Zaɓina, kai nake so da kai nake da burin kasancewa har ƙarshen rayuwata." Dariya yayi kunyarta na ɗaya daga cikin abubuwan dake burgeshi da ita, duk da Zainab take sakaltacciya tana da kunya sosai abinda yake ƙara mishi jin sonta don ya kasance yana son mace mai kunya, kuma yanasan mace wacce zata faɗi abinda ke ranta shiyasa santa yai kane-kane a ranshi. "Yanzu dai an bani go ahead naje naga Daddy kenan?" A kunyace ta ɗaga mishi kai alamar amsawa, "In Sha Allah zamu je, sai kuma a bani number da aka canja saboda ni," ya ƙarashe maganar da tsokana. Dariya tayi ta miƙa hqnnu ta karɓi wayar da yake miƙo mata, number ta daddana ta miƙa mishi yayi saving, sai da ya fara kiranta don taga tashi number sannan yayi saving number da *Sweetums*. Kallanshi tai tace "Allah ka canza," tai maganar cike da shagwaba, kallan daya mata ne yasa tai saurin cewa "Ya Baqeer ina Dada?" kewar Dada na daga abun da yafi damunta a zamanta a Ɗambatta, sai sannan tasan ashe ba ƙaramin sabo tayi da Dada ba. "Tana nan lafiya ƙalau, kullum sai tayi maganarki." "Allah sarki Dada sosai nayi kewarta wallahi, don Allah kace ina gaisheta." Ɗaga mata kai yayi alamun amsawa. Kamar kada su rabu haka suke ji sai dai kuwa hakan ya zame musu dole don magriba ta kawo kai, kallon agogon hannunshi yayi sai sabbab ya tuna ashe fa fitowa yayi da niyyar zuwa gidan Maryam suyi magana da mijinta sai dai yanzu lokaci ya ƙure ba zai yiwu yaje musu gida da fare ba sai dai kuma gobe. Haka suka yi dallama da Zeey ta shiga motarta yana kallonta har sai data bar wurin sannan shima ya shiga tashi motar Tanimu yaja shi suka koma gida, daga shi har ita sun manta da wasu mutane da suka zo gani tunda suka haɗu da junansu shikenan suka manta da komai. ***** Da farin ciki Zeey ta koma gida, tana yin parking lot Kabir ya fito daga cikin gidan zai tafi masallaci sallar magriba, sai sannan ta tuna ashe fa shi ya tura ta taje ta karɓo mishi saƙo ita shaf ta ma manta da abinda ya fitar da ita ganin Baqeer da tayi yasa ta mance da komai. Fitowa tayi daga motar shima yana ganinta ya nufo wurinta da sauri yace "To ya?" Harararshi tayi tace"Ka duba wayarka ka gani sau nawa na ƙira ka, kawai ka tura ni wuri baka bani number ba don haka kada kaga laifina da ban karɓo maka saƙon ka ba." Ɗan sosa kanshi yayi yace "Share wannan batun don Allah, kun dai haɗu ai ko?" Ɗaga gira tayi tana kallonshi sai kuma tace "Baka ji abinda nace ba, ni banga abokin naka ba don ban san shi ba kai kuma kaƙi ɗaukar wayarka shi yasa nayi tahowata gida." "Da Baqeer nake nufi Zeey, I mean kun haɗu da Baqeer a wurin?" Baki buɗe ta tsaya tana kallonshi mamaki ƙunshe a fuskarta, ya aka yi yasan ta haɗu da Baqeer? Kada dai ace? Dariya yasa yace "Yup, nine nan na haɗa ina fatan dai kun yi sorting out issues ɗin ku." Girgiza kanta kawai tayi sai dai bata jin haushin abinda yayi ba sai ma ƙara jin ƙaunarshi da tayi cikin ranta don yayi mata abinda ta kasa yiwa kanta wato neman Baqeer su daidaita duk da tun farko it ta datse alaƙar dake tsakaninsu. Anan wurin ta wuce ta barshi taƙi bashi amsar da yake son ji, itama sai ta wanashi kafin ta faɗa mishi. "Come on mana Zeey," yace yana ɗan bubbuga ƙafafun shi a ƙasa. "Kana nan wurin har a tayar da sallah baka tafi," tayi shigewarta cikin gida. Sai da ta fara leƙa ɗakin Daddy ta ganshi yana zaune akan wheelchair ɗin shi yana sallah sannan ta wuce ɗakinta ita ma tayi sallar. Yau wani irin farin ciki take jin kanta a ciki bata jin akwai wani abu kuma da zai ƙara ɓata mata rai, dama Baqeer ne damuwarta kuma Allah ya dawo mata dashi cikin rayuwarta tana kuma da tabbacin Daddy zai aura mata shi a wannan karon. Ta idar da sallar kenan tana naɗe abun sallar Kabir yayi knocking a ƙofar ɗakin, sai data bashi izinin shigowa sannan ya tura ƙofar ya shigo. Kamo hannunta yayi suka zauna akan gadon kafin yace "Please Zeey ki faɗa mini ya kuka yi dashi." Ƙwace hannayenta tayi tace "Sai ka faɗa mini yadda aka yi kasan zai je wurin daka turani, tukunna ma tsaya kenan babu wani abokin ka da zai bada saƙo tsarani kawai kayi fon naje wurin?" Gira ya ɗaga alamun amsawa. Girgiza kanta kawai tayi sai kuma tace "Haɗuwata dashi came to me as a surprise don ban tsammaci ganin shi a wannan wurin ba sam. Mun yi magana dashi ya nuna interest ɗin shi a kaina har yanzun despite abinda Daddy yayi mishi yace ma zai zo ya gaishe da Daddy, so abinda ya faru kenan." Jinjina kai Kabir yayi yace "Ni dama nasan zai dawo wuyarta baku haɗu ba an farfaɗo da tsohuwar soyayya shi yasa muka haɗa plan da abokin shi Salim muka tura ku Gusto shi akan zai ga customer ke kuma nace kije ki karɓo mini saƙo, gashi nan kuwa shirinmu ya tafi bisa tsari yanzu sauranmu shan biki, iyye waya ga Zeey amarya." Harararshi tayi sai dai kuma ta kasa ɓoye farin cikinta don haka dariya ta ƙwace mata duk yadda take so ta basar ta kasa. Haka Kabir yayi ta tsokanarta sai da taga zai dameta ta koreshi daga ɗakinta ta sawa ƙofar key ta rufe, kwanciya tayi akan gadonta tana tunanin Baqeer da taga gaba ɗaya ya canja mata ya zama babban mutum, kana ganinshi kaga wanda yake cikin wadata da walwalar rayuwa abinda ya ƙara saka mata nutsuwar zuciya duk d tasan yadda shagon shi ya zama so successful saboda tan bin su a duk kafafan sadarwa na social media tana ganin irin cigaban da suke samu kullum tana kuma alfahari da hakan, tun ma ba idan an ƙoda shi ba sai taji kanta ya fasu tana jin wia Baqeer ɗinta ne wannan Allah ya ɗaukaka shi haka. ***** Sai da Zeey ta bar wurin sannan ya shiga mota Tanimu yaja suma suka bar wurin, suna hawa titi Tanimu yace "Zamu je can inda kace zamu ne da farko kafin oga Salim ya kira ka?" Girgiza kai yayi yace "A'a mu tafi gida kawai dare yayi, mun je gobe." Jinginar da kanshi yayi a jikin kujera ya lumshe idanunshi, Zeey kawai yake gani da sassanyan kallon da take jifan shi dashi da kuma murmushin ta mai sa zuciyarshi ta narke cikin ƙaunarta. Wani tunani yayi da yasa shi buɗe idanunshi ya ɗauki wayarshi ya ƙira number Salim. Kamar wnda yake jiran kiran kuwa tana fara ringing ya ɗauka. Baqeer naji ya ɗauka yace "Kai dai wallahi anyi ɗan iska, dama kasan abinda ka shirya shi yasa nayi ta ƙiran wayarka kaƙi ɗauka." "Ban burge ka ba kenan?" Shima ya mayar mishi daga can ɓangaren. Tsaki Baqeer yayi yace "Ai dai kasan amsarka, amma ta yaya hakan ta faru? Ya aka yi kasan zata je wurin a daidai wannan lokacin?" Ƴar dariya Salim yayi yace "Ina zaune a majalisa yayanta yazo ya sameni akan yana don haɗaku kai da Zeey ya nake ganin za'a yi, to anan muka haɗa plan ɗin turaku wurin a daidai lokaci ɗaya, amma kafin na amince sai da yayi min rantsuwa akan bada wata manufa zai yi hakan ba kawai yana so  ya gyara kuskurenshi na baya, baka taɓa faɗa mini shi ya bugeka ba amma." Shiru Baqeer yayi yana jinjina wai Kabir ne ya tura Zeey wurin don su haɗu su daidaita tsakanin su, Kabir ɗin da babu wata jituwa a tsakaninsu tun suna ƙanana sai dai kuma ba abun mamaki bane duba da yadda yabi shi har shago don ya bashi haƙurin kaɗe shin da yayi. "Babu amfanin faɗan ne shi yasa kuma nima ban gama tabbatar da shi ɗin bane sai ranar da muka je gidansu Babanta yayi mana wulaƙancin nan." Lokacin da suka shiga unguwarsu har an shiga sallar magriba don haka ya cewa Tanimu ya tsaya a masallaci suyi sallah sai su ƙarasa gidan gaba ɗaya. Sai da suka yi har sallar isha kafin su tafi gida. A parlourn Dada ya tarar dasu it Dada Umma suna kallon tashar arewa 24 suna cin tuwo. Bayan sun gaisa yake tambayar Umma ina Maryam sai tace mishi ai yana fita itama ta tashi ta fita gida, ɗaga kanshi kawai yayi cikin ranshi dai ya ƙudurce gobe da safe suna fita gidanta zai fara zuwa kafin ya ƙarasa shago don dole a shiga maganar ta da uban mijinta idan har mijin nata yana son cigaba da zama da ita dole mahifinshi ya ɗauke idonshi daga sabgar gidanta don ɗan shi take aure ba shi ba da zai bi ya takura rayuwarta. Dada ce ta kalleshi tace "Kai kuma lafiyatka tunda ka shigo kake ta faman washe haƙora?" Kallonshi Umma tayi, ashe ba ita kaɗai ta lura da fara'ar daya shigo da ita gidan ba. Murmushi yayi yace "Wai ke Dada komai kika gani sai kin yi magana ne?" Taɓe baki tayi tace "Kai dai ka sani, idan tayi wari ai zamu ji ne. Zaka ci abincin ne a kawo maka ko ba yanzu," girgiza kanshi yayi yace "A ƙoshe nake bazan ci ba Dada," don farin cikin da yake ciki ya ƙosar dashi baya jin zai iya saka wani abu a bakin shi. Juyawa yayi zai bar parlourn sai da ya kai bakin ƙofa sannan yace mata Zainab na gaisheki. Yayi ficewarshi tun kafin ƙwaƙwalwarta ta gama processing wacce Zainab ɗin, yana fita ya jiyo muryarta tana tambayrshi "A ina kaga Zainabun? Shi yasa ka shigo babu wannan ɗaɗɗaurewar fuskar daka tsiri yi yanzu?" Shi dai yana jinta bai amsa mata ba har ya shiga ɗakin shi yana tunanin kiran Zeey a waya don bai gaji da ganinta ba ɗazu kawai don ya zama dole su rabu ne yasa ya ƙyaleta ta tafi. * *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* [2/6, 11:40] Fatima Eshak: *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA BAKWAI* {97} Zee duk yadda taso bacci ya ɗauketa ta kasa ji take yi kamar in ta kwanta zata tashi ace mata mafarki take yi, wayarta ce tayi ƙara alamun saƙo ya shigo wanda hakan yasa ta saurin janyowa, sunan da Baqeer ya rubutawa kanshi ne kawai yasata sakin wani murmushi sannan ta mirgina tare da yin ruf da ciki ta bude, “Hmmm ban ce komai ba kar a sa ran love text na turo.” Dariya ne yazo mata don har sai da haƙoranta suka fito, reply ta danna zata mishi sai ga wani saƙon, “Hmm kar ki damu an yafe miki yin reply dama dai nayi checking ne ko number na aiki ba’a canza wata ba.” Saman goshinta ta ɗan buga saboda dariyar da Baqeer ya saka ta, sai ga wani saƙon yace “Hmm bacci?” Ƙiran numbershi tayi ringing biyu ya ɗauka yace “Oh ashe layin na aiki.” Dariya tayi tace “Ya Baqeer Allah ka bari nifa saboda kaina na canza number.” Ajiyar zuciya suka ji sun yi a tare ga mamakinta sai ji tayi ance “I miss you!” Wayar da ke hannunta ne ta nemi suɓucewa saboda mamakin abinda taji, yawun bakinta ta haɗiya cikin wani shauƙi tace “Ya Baqeer Allah ka canza.” “To ke wane kike so? Wannan Baqeer ɗin ko wancan?” Kunya kalamanshi suka bata, lallai ta yarda da ake cewa maza in suna son mutum basa kunya, tace “Both ni ai kai ɗin nake so.” Gira ya ɗaga don shi dama yana da tabbacin son da take yi mishi wanda hakan ne yasa yake ji dole ya bayyana mata abinda ke ranshi don shi yana da tabbacin son da take yi mishii amma ita fa? Yana ganin bai nuna mata ba balle ta samu wannan tabbacin. Katse tunaninshi tayi da cewa “Yaushe za’a kaini MOHBAQ?” Da mamaki yace “Ya aka yi kika sani?” Kafaɗa ta ɗaga tace “Da alama duk da na canza number ban iya canza abinda ke raina ba.” Wani sanyi ne ya ratsashi lallai dole ya dawo da Zee kusa dashi don rashinta a rayuwarshi sai yaji komai ya canza mishi har tunani yake yaushe rabon da ya zauna yana surutu haka? Haka suka ɗan sake taɓa hira kafin suyi sallama, kowannensu zuciyarshi na cike da so da ƙauna da begen ɗan uwanshi. Bacci tayi bata tashi ba sai asuba, tayi alwala tayi nafiloli sannan tayi sallah, ɗaki ta fito tayi wurin Dady zama tayi ya idar da sallah sannan ta gaisheshi, ta ɗauko maganinshi ɗaya da aka ce ya dinga sha ƙarfe shida bayan ya sha ta kalleshi tace “Daddy akwai abinda kake so?” Kai ya girgiza sannan yace “Allah yayi miki albarka Zainab, kwanan nan ina ji rayuwata ba wani amfani da take dashi, duniyar nan sai sake bani tsoro take,” ya ƙarasa maganar cike da rauni wanda kana iya ganewa ta muryarshi, kanta ta kwantar akan ƙafarshi yasa hannu saman kanta tace “Rayuwar kenan Daddy ina ga waɗanda suka mutu? Sannan kai ƙafa ɗaya wanda zamu iya zuwa waje a sa maka artificial ƙafa naga ana yi kuma mutum yana samu yayi tafiya.” Kai ya girgiza alamar a’a yace “Menene amfanin haka Zainab? Ba inda zani, a yanzu ina ji nafi tsoron Allah da nadama akan ruɗin duniya da abinda ke cikinta, hakkin mutane ina zasu barni? Kuɗaɗen mutane da muka dinga ɗeba suna ina?” Ya haɗiyi wani abu daya tokare mishi yace “Gashi nan abinda na gama sata nasa sunan matar nan saboda amana ko ganinta ban yi ba balle nasa ran ko kuɗin asibitina ta biya.” Tausayinshi ne ya kama Zainab ta shafi fuskarta tace “Haka rayuwa take, itama sai ka barta da duniya da kuɗin dama kai ma ba gumin ka bane kaga kenan duk abinda zata yi da kuɗin taje tayi ƙofa a buɗe take, ta shiga hakkin mu ta rabamu da mahaifiyar mu wannan shi kaɗai ne abinda bazan taɓa yafe mata ba amma sauran taje can tsakaninta da wanda ya halliceta.” Kalaman Zee sosai suka saka mishi nutsuwa cikin ranshi ya ɗan yi murmushi yace “Allah yayi miki albarka, ya baki miji na gari.” Ameen tace sannan ta ɗora da cewa “Daddy?” Sai kuma tayi shiru kallonta yayi yace “Ya? Ba dai har kunyi faɗa da Baqeer ɗin ba?” Mamaki ne ya kamata tace “Ya aka yi ka san na ganshi?” Sai kuma ta girgiza kai tace “Oh ni Ya Kabir.” Murmushi yayi yace “In kun gama shiri kwa sanar damu yazo mu gaisa.” Kallonshi tayi cike da tausayi ta ina zata iya barin Daddy cikin wannan hali tayi aure? Murmushi yayi mata yace “Ba dai har shekara zaku kai kuna ƙalula ba?” Bata san sanda tace “Daddy shekara?” Rufe baki tayi da sauri sai kuma suka saki dariya a tare kafin yace “Nasan ni kike ji sai dai karki damu Kabir na nan sannan menene bana iya yi?” Murmushi tayi sannan ta ɗaga kai jiki a sanyaye. ***** Jamila duk abin duniya ya dameta ta kalli Bashir tace “Kaga ka shirya ka kira Fatima kace saƙo ne zaka kawo mata, ita nasan zata sanar da kai inda take, to in har kaje kar ka kuskura ka taho sai kasan inda Baqeer yake aiki yanda zaka nemi ya ɗaukeka kai ma aiki kana gani gashi ka gama karatun amma aiki ya gagara.” Kai ya jinjina don shi dai yanzu in dai zai samu aiki to fa lallai zai yi, sannan ai gwara wurin ɗan uwanshi ma da bare.” Gyaran muryar Badaru suka jiyo da sauri ya miƙe ita kuma ta fara neman waskewa tana cewa “To adai kula bana son shirme da bin abokan banza.” Sai da Badaru yazo bakin ƙofa yana waige-waige yana hura hanci ya ɗan kalli ɗakin yace “Kai Bashir in ka samo inda Yayanka yake ka faɗa min, don raini ina mahaifinshi ba zai zo ya sanar dani sana’ar da yake yi ba bayan ni nasha wahala a kanshi, dole yazo ya bani haƙuri don yasan yayi laifi.” Bashir shi dai ya samu ya fito don haka kawai ba zai samu aiki Baba ya kashe mishi ba, waje yayi shi kuma Badaru maimakon ya shiga ciki sai ya fito yana hararar ɗakin Umma kafin yayi ƙwafa ya yaye labulen Abu yace “Ke har yanzu baki tattara kin bar min gida ba?” Cigaba tayi da ƙullin maganinta tana cewa “Babu fa inda zani Malam na faɗa maka aurena da kai mutu ka raba in ma ka sakeni zan yi zaman yarana ai kai kasan ba inda zani shekarar mu nawa tare? Kamalu ne kaje can kun fi kusa dashi amma ba inda zani.” Kallon mamaki yayi mata kafin yayi ƙwafa ya fito waje don shi dai takaici duk ya gama isarshi burinshi kawai yasan ya aka yi Baqeer yayi kuɗi? Bayan yasan da filin shi da aka sata ne sannan da zanen daya koya mishi ne? Sam kwanan nan rayuwa bata yi mishi daɗi don shagon nashi ma yau yayi cinikin ragowar ƴan sauran abinda ke ciki ya sallami yaran shagon saboda ba komai gashi ba zai iya biyan kuɗin haya ba, in ya tuna Kamalu ne ya yasheshi gashi ko labarinshi babu, wannan abu na baƙanta mishi rai. *** Yau Baqeer daga shago gida ya dawo ga mamakinsu Umma wanka ya sake yi bayan wanda yayi da safe, Dada tana gefe suna hira tana ganinshi sai ta fara waƙar gaɗa da ake yi a ƙauye na ‘saurayi zai je zance ya kasa bacci’ Baqeer na jinta shi dai ya wuce ɗaki ya rufo a yanzu ba kunyar da zai ji akan son da yake yiwa Zainab, farin cikinshi ɗaya ya sayi gidan nan don haka dole ya gaggauta ayi aurensu ya ganta kusa dashi, yadin da yake ɗinkawa da style ɗinshi na daban da yake yi shi ya saka, dakakkiyar hula mai tsada ya saka ya kalli kanshi a madubi ya fito cas dashi, lallai da ace yana tafiya da sai gayun yafi fitowa, miƙewa tsaye sannan ya hau kan wheelchair ya zauna saboda baya iya taka ƙafar har yanzu. Wayarshi ya ɗauka ya kira number Zee fuskarshi ɗauke da murmushi, bata daɗe ba ta ɗauka tare da sallama, amsawa yayi sannan yace “Mu biyu zamu fita ko ana son third party?” Dariya ma abun ya bata tace “Muna buƙatar third party tun kafin wani ya ɗaura mun aure ba magabata.” Duk yadda Baqeer yaso ya daure sai da yayi dariya, murmushi tayi ita kanta kafin tace “Allah Ya Baqeer tsokanar ka tayi yawa, ka shirya na fito?” “Third party ɗin fa? Kin san fa zan iya kai ki masallaci a ɗaura.” Kai ta girgiza tace “Zan fito yanzu.” Kai ya ɗaga kafin yace “Babu sallamar love?” Kashe wayar tayi tana dafa fuskarta da murmushin daya kasa barinta, lallai Baqeer ɗinta rigimarshi ta ƙaru da yawa, kallon kanta tayi yadda tayi kyau sosai, sanye take cikin wani dakakken lace mai tsada wanda mijin Ummi ya ɗinka mata don ko sakashi ma bata yi ba, tayi kyau sosai kyanta ya ƙara fitowa, falo ta fito jin alamun hira yasa ta nufi falon Daddy, yana zaune shi da Kabir ganin wani a zaune yasa ta kalleshi, waigowa yayi suka haɗa ido, mamaki ne ya kamata tace “J?” Dariya yayi yace “Zee in da amana ai ni ya kamata ki fara kira da kaddarar nan ta samu Daddy.” Kallon Daddy tayi tace “Sorry wallahi everything was so hectic at that time shi yasa.” “Sai ina?” Yayi tambayar yana kallonta, murmushi tayi tace “Secret place, anyway thanks for coming.” Kabir ne yace “Kice yayanki yace kar kiyi dare, sannan ban yarda da yawo akai-akai ba.” Harararshi tayi tace “Allah Daddy kayi mishi faɗa tunda yasan sirrina yabi ya hanani nutsuwa.” A tare suka yi dariya, sai kuma tace “Ina Mubashir?” Kabir yace “Ya koma school da safe yace zai zo da weekends.” Ƙwafa tayi tace “Lallai wato kai ya faɗa ma ni ko sanar dani bai yi ba,” gwalo yayi mata ta fita fuskarta ɗauke da murmushi duk da ƙaddarar data samesu taji daɗin ganin yau ana dariya a gidan, mota ta shiga ta tsaya ta sayi fruits sannan tayi gidansu Baqeer saboda ba dama yayi tuƙi, waya tayi mishi bayan ta isa da niyyar shigowa, yana ɗauka sai aka yi rashin sa’a Umma na tsaye a ɗakin tana yi mishi maganar Maryam, jin sunan Umma yasa Zainab tayi saurin kashe wayar, fifita tayi da hannunta tare da sauke ajiyar zuciya tace “Allah ya soni ban shiga ba, wannan abun kunya har ina.” Baqeer kuwa wayar yabi da kallo ba sai an faɗa ba yasan me ya faru, yace “Umma shi kenan sai dai in nayi mishi magana ina ga zamu fi samun mafita.” Shiru tayi sai dai ba zata hana ba don harga Allah tana ganin yawan shiru yana cutar da mutane sosai. Daga waje ta hangoshi fitowa tayi ta ɗan jingina a jikin ƙofar tana jifanshi da wani kallo, alama yayi mata da ƙofa, kafaɗa ta maƙale alamar a’a kafin tace “Umma na nan ba yanzu ba.” Ƙarasowa yayi da wheelchair ɗinshi, yace “Kika zo ɗauke mata ɗa?” Tana kallonshi tace “Da sauƙi ma tunda ɗan nata dama so yake na ɗauke shi.” Baqeer ya jinjina kai yace “Eh lallai dole na tura magabatana kafin amin auren dole.” Dariya ce tazo mata tasa hannu tana kauda kai tace “Allah ni wannan ko aure muka yi takura mun zaka yi da tsokana.” Ƴar gira ya ɗaga mata yace “To ai matsalar a hakan kike so a shafa fatiha.” Zee ta buɗe mishi ƙofa yana shiga ta rufe don wheelchair din zama take kamar kujera, shi yasa ta ɗaga kujerar baya. Gyaran murya tayi tace “Alhaji ina zamu yi?” Shima gyaran murya yayi yace “Driver muyi Hotoro.” Harararshi tayi tace “Charges zaka fara biya ai.” “In mun yi aure zan biya duka ki fara rubutawa.” Kunyar kalamanshi ne ya kamata lallai Baqeer, shiru suka ɗan yi yana nuna mata hanya har saida suka zo, kallonta yayi yace “Thanks for waiting for me.” Kallonshi tayi tace “Same, ɗazu J yazo duba Daddy.” Fuska ya canza ya kalleta yace “Nima yau zani dubiyar.” Dama da saninta tace “Da wuri haka?” Yana kallonta yace “Ai yanzu ba maganar wasa in zan je ma a shirye zani mu tattauna.” Kallonshi tayi bayan ta tsaida motarta a daidai shagon, ta kalli shagon sannan ta kalleshi wani irin kallo suke yiwa juna na tausayin kansu da tsantsar ƙauna, cikin wata irin murya yace “Kina tunanin zan iya jinkirtawa?” Ido ya ɗan maida ƙasa yana kallon fuskarta yace “Kinyi kyau, tun ɗazu naso na faɗa ganinki yasa hankalina ya tafi wani wurin.” Idanunta ta ɗago ta zuba mishi tace “Kaima, you look different.” Kai ya karkatar yace “Do you fall harder than before?” Kwantar da kanta tayi a bayan kujera tafe “Maybe.” Murmushi suka sakarwa juna kafin su fito, tayi mamakin ganin shagon Baqeer don kuwa babba ne sosai nan yake faɗa mata ai tun kafin ta tafi ya kama amma daga baya ya ƙara girman shagon, farin ciki sosai ta nuna don tasan shi mutum ne mai ƙoƙari matuƙa, kuma wannan alama ce ta nakasa ba kasawa bace. Guminshi ne hakkinshi ba kamar Daddy daya rufe ido suka dinga taɓa kuɗin mutane ba, aka ciyar da ita aka tufatantar da ita da hakkin mutane, lallai ita auren Baqeer rahama ne a gareta a ƙalla yanzu zata tsaftace rayuwarta da halal. Shi kanshi yaga farin cikin ta a bayyane, nan ta barshi ta tafi ganin su Tanimu sun zo, shi kuma dama so yake la’asar tayi yaje ya samu mijin Maryam, gashi yana son yaje ya duba Daddy. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA TAKWAS* {98} Sababbin designs ɗin da yake aiki akai ya zauna ya fitar, sai da ya gama har yayi uploading ɗin su cikin computer da suke aiki da ita sannan ya kira Salim ya faɗa mishi zasu fita in anjima bayan sallar magrib, bai faɗa mishi inda zasu je ba yace idan sun je ya gani duk da ma dai Salim ɗin yasan ba zai wuce gidansu Zee zasu ba. Ana yin sallar la'asar ya tashi daga aiki, daga masallaci basu koma shagon ba yace da Tanimu su tafi gidan Maryam, so yake yi suje su gama da wuri don baya so ya ɓata lokacin shi na zuwa gidansu Zainab. Suna isa bakin gate ya ɗauki waya ya kira Maryam yace mata gashi a wajen gate tazo ta shigo dashi. Tashi tayi cikin farin cikin yau Ya Baqeer ne a gidanta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe daya tako ƙafarshi zuwa gidanta ba tasan dai tun kafin ya samu accident ne. Fitowa tayi daga ɗaki ta faɗawa Baban Aareef dake zaune a parlourn Ya Baqeer ne yazo ya fita ya shigo dashi ciki. Shima yayi mamakin da jin Baqeer ɗin yazo gidan saboda daɗewar da yayi bai zo ba sai kuma lokacin yaji yana kunyar haɗuwa da Baqeer ɗin don duk tsawon lokacin nan bai taɓa zuwa yaje ya duba shi ba har Allah yasa ya samu lafiya ya cigaba da harkokinshi. Haka nan dai ya tashi ya fita jikinshi a sanyaye don ba zai yiwu ya barshi yana jira ba, surukuta ce sosai a tsakanin shi da Baqeer ɗin, yana girmama shi yana ganin mutunci saboda yadda yake tsaye akan al'amuran ƙannen shi ya ɗauki girman da Allah ya bashi. Yana fita ya ganshi akan wheelchair ɗin shi don tuni ya fito daga cikin motar yana jiran Maryam tazo ta shiga dashi cikin gidan, tunda uban mijinta ya dawo gidan da zama ya daina shiga kanshi tsaye saboda kaucewa gutsuri tsomar ƙananun maganganu bare daya fahimci halin mahaifin Auwal ɗin. Yana wani sussunkuyar da kai ya miƙa mishi hannu suka gaisa shi kuwa Baqeer sai bai nuna ma yasan abinda yake yi ba. Zuwa yayi zai tura wheelchair ɗin Baqeer ya ɗaga mishi hannu ya nuna mishi remote control ɗinta yace "kada ka damu ba sai ka turani ba zata tura kanta." Ɗan murmushi yayi ya koma gefe, gaba yayi Baqeer na biye dashi a baya har suka shiga cikin gidan babu wanda yayi magana. Suna shiga Maryam ta tashi da fara'arta ta tareshi tana yi mishi sannu da zuwa, Aareef na zaune akan kujera yana kallon cartoon. Yana jin muryar Baqeer ya taso yana yi mishi oyoyo ganin shi zaune a wheelchair sai yasa yaron yayi turus yana kallon shi. Hannu ya miƙa mishi yace "zo mana Aareef, zo mu gaisa na daɗe ban ganka ba." Kasa zuwan yayi sai juyawa da yayi yana kallon Maryam, sai data ɗaga mishi kai sannan ya ƙarasa wurin Baqeer yana mamakin yadda ya ganshi haka har dai ya kasa yin shiru sai da ya tambayeshi. "Uncle Baqeer me ya sameka na ganka akan wheelchair?" Murmushi yayi yana shafa kan yaron yace "Accident nayi Aareef Mommynka bata faɗa maka ba?" Da kai ya amsa mishi yana kallon kujerar wheelchair ɗin with curiosity. "Zaka sauka ka bani na ɗana?" Dariya Baqeer yasa jin abinda yaron yace sai ya ɗaga mishi kai alamun amsawa, su kuwa iyayen sai girgiza kai suke yi Maryam ji tayi kamar ta makeshi don haushi. Korashi ciki tayi don tasan idan har yana wurin ba zai bari su gaisa da ɗan uwanta cikin nutsuwa ba wanda alamu suka nuna akwai abinda ya kawo shi, tafi bayarwa dai ko Umma ta faɗa mishi matsalarta ne shi yasa yazo. Kitchen ta shiga ta haɗo mishi ruwa da drinks ta ɗora akan tray haɗw da cups ta kawo, sai da tsiyaya mishi ruwa da kemon duka a kufuna ta ajiye a gabanshi sannan ta samu wuri ta zauna ta soma gaishe shi. Bayan nan suka cigaba da hira jefi-jefi shi da Baban Aareef, anan ne ma yake bashi haƙurin rashin zuwa dubashi da bai je yayi ba ya kawo uzurin abubuwa ne suka sha kanshi shi yasa bai samu yaje ba. "Ai babu komai," Baqeer yace don bai ga amfanin ɗago wannan maganar ba. Gyara zamanshi yayi akan wheelchair ɗin sannan ya kalli Auwal sosai yace "wurinka nazo akan maganar Maryam." Kallonshi yayi sosai, shi dama tunda ya ganshi yasna dole akwai abinda ya kawo shi don tun da can baya zuwa musu gida haka nan sai idan sun samu saɓani shi da Maryam ko shi ya kira shi ko ita idan ta kirashi amma yawanci ma shine yake kai ƙararta. Gyara zamanshi yayi yace "wani abu Maryam ɗin tace anyi?" Kallonta Baqeer yayi yace "maimaita abinda kika ce yayi miki." A nutse ta buɗe baki ta fara magana, duk wata matsala da take da ita a zamanta da Baban Aareef da mahaifin shi yau sai data faɗawa Baqeer harda shigo mata da yake yi ɓangarenta kanshi tsaye akan hakan yasa yanzu ta daina zaman parlour kwata-kwata, a ƙarshe tace "to yanzu aiki ne ya sama min tun kwanaki don ya daɗe da yin alƙawarin zai barni nayi aiki saboda na faɗa mishi ina da sha'awar yin aikin, har nan ya kawo mini offer ina ta murna sai da ya fita sallah ya dawo yace wai wannan maganar a barta saboda sun yi magana da Baffa, nace ya faɗa min wacce magana ce suka yi da zai sa a hanani aiki bayan ansa min rai yace wai maganarsu ce shi da mahaifinshi nace to ai nima ta shafeni tunda akai na aka yi. Haka nan dai na haƙura da aikin ba don naso ba, nace mishi to tunda ba zai barni nayi aikin ba ina so zan koma makaranta nayi masters nan ma yace a'a ni kuma zaman haka ya isheni idan suka fita daga gidan nan haka zan yini ni kaɗai har sai sun dawo don haka nace mishi ina so zan fara snacks na sayarwa tunda abu ne ina daga cikin gida zan yi yace babu damuwa hakan shawara ce mai kyau kawai yana fita sai dawowa yayi yace wai batun sana'ar nan a haƙura kawai don shi baya son mutane suyi ta shigo mishi gida suna fita yanzu kuwa ina fara sana'a za ayi ta sintirin shigo mishi ana gane mishi sirrin cikin gida ni kuwa nace ita ma sana'ar da zan yi Baffan ya hana to kuwa in dai ba za'a barni nayi sana'a ba sai a ƙyaleni na fita nayi aiki don ba zai yiwu komai nace ina so ba sai an kushe shine yace wai ina yiwa mahaifinshi rashin kunya ni kuma Ya Baqeer gani nayi ba Baffa nake aure ba don me yasa zai dinga shiga rayuwata sai mun gama tsara magana da mijina sai ya rushe kuma ace bazan yi magana ba alhalin ni ake cuta," ta ƙarashe maganar muryarta na karkarwa alamun kuka take ƙoƙarin dannewa. Tunda ta fara maganar duk suka yi shiru suna saurarenta har sai da tayi shiru sannan Baqeer ya kalli Auwal yace "haka aka yi?" Gyara zamanshi yayi yace "Eh Ya Baqeer sai dai kada ka manta Baffa mahaifina ne dole nayi mishi biyayya akan duk abinda yace ita kuma Maryam sai tace ba haka ba to tana nufin sai abinda take so zan bi na take ra'ayin mahaifina." Shiru Baqeer yayi yana auna maganganun da dukkansu suka yi, kallon Auwal yayi yace "Da farko dai wacce magana take yi akan mahaifinka yana shigo mata har nan da gaske ne?" Don duk cikin maganganun da Maryam tayi wannan ya fi ɓata mishi rai. Shiru yayi ya kasa amsawa. Sai ya cigaba da cewa "da gaske ne kenan tunda kayi shiru, to maganar gaskiya dole ka dakatar da mahaifinka daga shigo mata cikin gida tunda shi ɗin ba muharraminta bane kai ko muharraminta ne bai dace ya shigo mata ba tunda bai san a wane irin yananyi zai risketa ba bayan haka ita ɗin yanzu baliga ce babu dalilin da zai sa don tana aurenka mahaifinka ya dinga shigo mata ɗaki, idan kuma baza ka iya hanashi shigo mata cikin gida ba sai ka canja mata muhalli don aure take yi ba bauta ba, idan bata sake a cikin gidanta ba a ina ake son taje ta sake. Sannan kuma maganar sana'a da tayi ina ganin kayi haƙuri ka ƙyaleta tayi tunda dai baka son aikin kuma ta haƙura idan yaso sai ka gindaya mata sharuɗɗa akan yadda kake son ta tafiyar da kasuwancin nata." Sosai yaji ranshi ya ɓaci sai dai yayi shiru bai katse shi ba har ya gama magana, cikin ɗaurewar fuska yace "Ni bazan iya cewa Baffa ya daina shigowa cikin gidan nan ba don dani da abinda na mallaka duka mallakin shi ne baya da wani iyaka da duk abinda na mallaka ba kuma zan iya canja mishi gida ba bayan nasan ba wani da zai kula dashi gareshi ba tunda mahaifiyarmu ta rasu ba kuma wata matar gareshi ba." Rai a ɓace Baqeer ya mayar mishi da "Bashiv da iyaka da komai naka face Maryam don kuwa ba a garin gaɓa-gaɓa muke ba mu musulmai ne ba kara zube muke rayuwa ba, idan har ba zaka dakatar da mahaifinka daga shigo mata ɗaki ba to lallai kuwa zan tafi da ita gida don bazan barta ta cigaba da zama da kai bata da sakewa a cikin gidanta ba tana fargabar kowane hali take ciki za'a iya shigo mata. Ke Maryam ɗauko mayafinki mu tafi don ba zaki cigaba da zama a gidan nan ba." Da sauri Auwal ya tare shi ganin har Maryam ta miƙe zata tafi ɗaukar mayafin kamar yadda Baqeer yayi mata umarni. "Kayi haƙuri Ya Baqeer don Allah kada ka tafi da ita yanzu dai me kake so ayi nayi alƙawarin yi maka in har zaka bar mini Maryam." Kallon kada ka raina mini hankali Baqeer yayi mishi yace "zaɓi ai yana wurinka tunda na faɗa maka su, inma dai ka canja mata muhalli ko ka hana mahaifinka shigo mata wuri dai kuma batun sana'a daka hana lallai idan har baza tayi aiki ba dole ka barta ta nemi na kanta saboda halin rayuwa ba'a san me gaba zata haifar ba bayan haka kuma ita ma tana da iyaye tana da ƴanuwan da zata so tayi musu hidima da guminta ba sai ta jira abinda ka bata ba." Haka nan ya amince da duk abinda Baqeer yace ba don yana so ba sai don yasan ba kowacce mace bace zata ɗauki abinda Maryam ɗin ke ɗauka ba. Zama da Baffa ne bata so to zai gyara mishi tsohon gidansu ya koma idan yaso sai ya nemi wata matar yayi aure, su dama tun bayan rasuwar mahaifiyarsu ai auren suka so yayi shine yaƙi shine kuma dalilin da yasa ya dawo dashi nan saboda acan ɗin babu kowa ko wajen abinci babu mai bashi amma yanzu ya zama dole ya koma ko ba zai yarda yayi auren ba idan yaso sai su nemi wanda zai dinga zama dashi suna biyanshi abinci kuma ko daga nan ko gidajen ƴan uwanshi sai a dinga girkawa ana kai mishi. Haka Baqeer yayi musu sallama ya tafi bayan ya cika Maryam da kyautar kuɗaɗe ya kuma ce tayi tunanin sana'ar da take son yi shi zai bata jari ba sai ta tambayi Baban Aareef ba. ***** Bashir na fita daga gidan ya dannawa number Umma ƙira, abinda ba zai iya tuna ranar da yayi hakan ba don fa iyayen su sun koya musu rashin ganin girmanta tun suna yara shi yasa kusan dukkansu yaran gidan suka rainata don ma ba shiga shirginsu take yi ba shi yasa duk abinsu basa iya yi a gabanta. Bayan ta ɗauka ne ya gaisheta sai kuma yace "Umma dama gaininki nake son yi don Allah." Duk da tayi mamakin jin wai Bashir ke son ganinta hakan bai hanata cewa tana gidan Dada yaje can ya sameta ba, kwatancen gidan tayi mishi don ba taɓa zuwa yayi ba. A wurin ya tari adaidaita ya faɗa mishi inda zai kai shi cike da fatan dacewa da abinda zai je nema. A ƙofar gidan Dada mai adaidaitan ya ajiye shi kamar yadda Umma tayi mishi kwatance don dama gidan ba wani wahalar ganewa ne dashi ba. A ƙofar gidan ya tsaya ya kira Umma a waya yace mata gashi ya ƙaraso sai tace mishi ya shigo kawai. Suna zaune a tsakar gida ita da mai aikin Dada suna haɗa abincin rana don tunda Umma ta dawo gidan ta karɓi aikin girkin sai dai mai aikin ta tayata da ƴan wasu abubuwan. Zama yayi akan tabarmar da Umma ta shimfiɗa mishi ya shiga gaisheta cike da girmamawa abinda da sam basa yi mata. Da fara'arta ta amsa tana tambayarshi lafiyar mutanen gidan yace mata duk suna nan ƙalau Jamila ma tace a gaisheta. Murmushi tayi tace tana amsawa jin wai yau Jamila ce ke aiko mata da saƙon gaisuwa. Ɗan shiru yayi yana juya ta yadda zai fara faɗa mata abinda ya kawo shi sai da taga baya da alamun zai ce wani abu sannan tace "Wacce magana ce kace zamu yi? Kada kaji komai ka buɗe bakinka ka faɗa mini ni uwa ce a wurinka." Ɗan gyara zamanshi yayi yace"Dama Umma cewa yayi don Allah ko zaki yiwa Ya Baqeer magana ya bani aiki a shagon shi tunda na gama makaranta aiki ya gagara samu bare aiki a ƙasar nan da ya zama na masu hanya sai kuma mai tsananin rabo." "Haka ne,"Umma tace. "Baqeer ɗin baya nan yana shago amma In Sha Allah idan ya dawo zan faɗa mishi nasan ba zai rasa wajen da zai ajiye ka ba." Godiya yayi ta yiwa Umma don yasan tabbas Baqeer zai bashi aikin don baya taɓa tsallake umarnin Umma. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce*        *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA CASA'IN DA TARA* {99} Baqeer na komawa gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wani tsadadden men lace kalar sky blue da ya yiwa special ɗinkin shi da wa kanshi kaɗai yake yin designs ɗin. Dark blue ɗin hula ya saka sai baƙaƙen takalma ƙirar kamfanin baertozzi da ya saka. Turarukanshi ya fesa da ba'a iya tantance sunayensu saboda ba guda ɗaya yake amfani dashi ba a lokaci guda, ya kan fesa a ƙalla turare uku zuwa biyar don haka ba'a taɓa iya tantance wane kalar turare yake amfani dashi. Yana fitowa Dada ta sa ka guɗa tana tsokanarshi tace "Iye wannan wankan dai daga gani zance zaka," shi dai murmushi kawai yayi. Ta cigaba da cewa "to idan kaje kace ina gaisheta da kyau da kyau, na kuma gode da kayan marmari." Bai iya amsawa Dada ba ganin Umma zaune a wurin, ita kuwa Umma sai daɗi take ji don tasan macen ƙwarai ce kawai abinda Baqeer ɗin ya rasa a yanzu, fatanta da burinta bai wuce na ganin aurenshi da zuri'arshi ba sannan tunda taga sun koma tare alama ce ta Dady ya sauko kenan. Sallama yayi musu ya fita inda Tanimu yake jiranshi don ya faɗa mishi dama kada yayi nisa zasu sake fita bayan magriba. Buɗe mishi motar yayi ya shiga ya zauna sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba yaja su suka bar wurin. Sai da suka hau titi sannan yake tambayar inda suka nufa, "Unguwarsu Salim zamu je don nasan yanzu yana can yana jiranmu, ban ɗauka zamu daɗe sosai a gidan Maryam ba sai gashi mun kai kusan magriba acan." Suna shiga unguwar ƙiran Salim na shigowa wayarshi, yana ɗauka Salim ɗin yace "haba Baqeer taya zaka sani na zauna ina faman jiranka amma har yanzu baka ƙaraso ba." Ɗan tsaki Baqeer ɗin yayi yace "To Malan gamu nan mun shigo cikin unguwar, a ina zamu sameka?" "Ina majalisar su Audu, please kuyi sauri don ina da wurin zuwa nima tun kafin kuma kace wani abu ba zance zani ba." "Kaji da gulmarka,da ɗin ta dai unguwarsu ɗaya." Baqeer yace ya kashe wayar bai jira jin me Salim ɗin zai sake faɗa ba. A majalisar su Audu suka tsaya, sai da Baqeer ya gaisa da ƴan zaman majalisar da suka kasnace tsofffin abokanshi sannan Salim ya buɗe gaban motar ya shiga Tanimu yaja motar suka bar wurin. Basu tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su Zeey, horn ya danna maigadi ya taso ya buɗe gate don dama Zeey ta sanar dashi zuwansu tace kada yayi nisa su zo suna ta yin horn babu mai buɗe musu ƙofa don shima akwai ɗan banzan yawo idan yaso tun ma ba yanzu da Daddy yake kwance baya da lafiya ba. A harabar gidan Tanimu yayi parking motar, basu fito ba sai da Baqeer ya ƙira Zeey a waya ya sanar mata da isowarsu. Ƙara gyara fuskarta tayi sannan ta fita wajen Daddy da yake zaune a parlourn shi da Kabir, a shirye yake tsaf zuwan su Baqeer kawai yake jira don tun bayan da suka rabu ɗazu tana dawowa gida ta sanarwa Daddyn cewa zai zo ya gaishe shi shi yasa ana yin sllar magriba ya shirya ya fito parlourn ya zauna yana jiran zuwan nasu. Faɗa mishi tayi su Baqeer ɗin sun iso, Kabir ne ya tashi ya fita don ya shigo dasu ita kuma ta tura Daddyn zuwa sitting room ɗin shi inda yake amsar baƙin shi. Bata jira shigowarsu ba ta koma ciki don ta haɗo musu kayan motsa bakin data tanadar musu. Kabir na gaba suna biye dashi a baya a haka suka ƙarasa parlourn na Daddyn. Sanda suka samu labarin rashin lafiyar Daddyn basu ɗauka yayi sanadin daya rasa wani ɓari na jikinshi ba, sai duk jikinsu yayi sanyi da yanayin da suka sameshi a ciki. Zama Salim yayi a ƙasa shi kuma Baqeer na daga kan wheelchair ɗin shi sai dai russunawa da yayi ya gaishe da Daddyn alamun girmanawa. Bayan sun gaisa yana tayi musu ƴan tambayoyi duk don su saki jikinsu ya kuma wanke kanshi daga abinda yayi musu wancan zuwan da suka yi gidan. "Yanzu wacce sana'ar kake yi ko har yanzu paintings ɗin dai kake yi?" Ya tambayi Baqeer don fa duk son da Zainab take yi mishi ba zai ɗauketa ya bashi ba idan har baya da ƙwaƙwarar sana'a duk da ma dai yanayin shigar jikinshi bata yi kama dana mara aikin yi ba. Ya buɗe baki zai amsa mishi kenan Zainab ta shigo, wani kallo yayi mata ya sakar mata kyakkyawan murmushin da yasa ta kusa rasa nutsuwarta, ajiye tray ɗin data ɗora kayan tayi akan center table sannan ta juya zata bar parlourn sai dai kuma Daddy bai barta tayi hakan ba sai cewa da yayi ta dawo ta zauna. Daga ƙasa ta zauna a kusa da ƙafar Daddyn tana satar kallon Baqeer da shima ya kasa ɗauke idanunshi daga kanta. Gyaran murya Daddy yayi abinda ya tunatar dashi a inda yake tuni ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana jin kunyar Daddyn na yadda ya kasa ɗauke idanunshi daga kan Zeey. "A yanzu ɗinki nake yi ina da shagon ɗinki a Hotoro sannan muna shirin buɗe wasu barnches ɗin ɗaya a Zoo road ɗayan kuma a Gadon ƙaya," ya bawa Daddy amsar tambayarshi. Jinjina kai Daddyn yayi yace "yanzu a hakan kana iya ɗinki? I'm sorry fa kawai ina mamakin jin yadda kake iya yin ɗinki ne." Murmushi kawai yayi don bashi ne na farko daya fara yi mishi irin wannan tambayar ba, wanda ya ganshi akan wheelchair sai yayi mamakin ta yadda ake yake iya yin ɗinki. "Yawanci kekunan namu electric ne wasu ma are computerized don haka aikin yana zuwa mana da sauƙi, a yanzu kuma da nake da ma'aikata ban fiye hawa keke ba sai dai nayi designing na kuma yi yanka su kuma sai su haɗe kayan." "Masha Allah,” kawai Daddy yake cewa don he's really impressed da yadda Baqeer ɗin yayi mishi bayanin, lallai tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace babu nakasashe sai kasashe shi dai Baqeer gashi nan nakasa bata hana shi tashi ya nemi na kanshi ba abinda ya kamata ace mutane masu disability sun yi koyi dashi kenan su tashi su nemi na kansu sai a daina yi musu kallon ƙasƙantattun mutane. "Wanda ya kaɗeka fa ko har yanzu ba'a sameshi ba?" Zeey ce tace "Daddy bakasan...." da sauri ya kalleta ya girgiza mata kai alamar a’a sai akai dace itama kallonshi take yi don haka tayi shiru ba tare data ƙarasa faɗar abinda tayi niyyar faɗa ba, shima Daddyn yaga lokacin daya girgiza mata kan sai ya ɗauke kanshi kamar bai gani ba. "A'a ba'a sameshi ba, ni kam ma tuni na yafe mishi don tuni na karɓi ƙaddarata a yadda tazo min don haka ko tunawa ma bana yi." Ya bawa Daddyn amsar a nutse don a ganinshi babu wani amfanin faɗa mishi Kabir ne ya kaɗeshi bayan Kabir ɗin yayi nadamar abinda ya aikata har ma yaje ya nemi gafararshi sannan bayan tashin hankalin da suke ciki baisan ya ƙara musu wani, balle ko badan komai ba ko dan darajar Zainab ai da matsayinta a gunshi ya kamata a bar maganar. Shi dai Kabir har ya sha jinin jikinshi yayi kif da ido yanajin yanda abin zaizo, sai yaji shiru hakan yasa ya kalli Baqeer wanda kalamansa yasa ya ji zuciyarshi ta karye, girma da darajar Baqeer suka karu a idanshi, kai kawai ya sunkuyar bai iya cewa komai ba. Sun daɗe tare da Daddyn bayan ya gama yi mishi duk wasu ƴan tambayoyi da ya dace yayi mishi sai yace ya bashi auren Zainab duk lokacin da ya shirya sai ya turo magabatan shi a tsayar da magana. Anan parlourn Daddy da Kabir suka fita suka basu wuri sai sannan ya ware ya kalli Zeey, sosai kwalliyarta tayi mishi kyau. Ɗage mata gira yayi yace "Amarya to ya? Kina ji dai Daddy yace ya bani ke ko yanzu na shirya nazo na ɗauke ki na mayar dake wurin Umma." Rufe bakinta tayi tana dariya tace "la'ila, yaushe aka yi hakan ina zaune ban ji ba? Ko kuwa kai kaji Salim?" Girgiza kanshi yayi yace “Ahh kaga mutum? To nima dai ban ji ba watakila kuma a mafarki yaji hakan yayi tunanin da gaske haka Daddy yace." Harararshi Baqeer yayi yace "To ɗan baƙin ciki, tukunna ma waya sa da kai daka wani tsomo bakin ka, magana ake ta tsakanin miji da mata idan ka shiga ma kai zaka ji kunya." Baki buɗe Salim yake kallon shi, ƙwafa yayi yace "gobe ma rana ce, ina zaune zaka zo ka sameni da wata buƙatar lokacin zaka san ni ka yiwa rashin mutunci." "Ni ba akwai inda kace zaka ba? Don Allah tashi ka tafi zamu tattauna da Sweetums ɗita." “Kai Ya Baqeer," Zeey tace tana dariyar faɗansu. "Ai ki rabu dashi Zainab, nima zan rama ne ai." Da sauri Baqeer yace "sai dai ka rame," tashi Salim yayi zai bar wurin Baqeer yace "idan kaje kace ina gaida Habi don nasan duk baƙin ran nan da kake yi akan yau na hanaka zuwa wurinta ne." Da mamakin yadda aka yi ya sani Salim yake kallondhi, ɗan taɓe baki Salim ɗin yayi yace "Wai kai ka ɗauka duk abinda kake yi ban sani ba ne, ƙyaleka nayi ka gama ɓoye-ɓoyenka don dole dai akwai ranar da zaka sanar mini tunda ba'a ɓoye za'a yi auren ba." Kasa magana Salim yayi, da ƙyar ya iya cewa "Hmm taya za'a yi nace ina sonta bayan abinda ƴar uwarta tayi maka." Katseshi Baqeer yayi da cewa "to miye a ciki don kana sonta, Habi ai ba Asiya bace besides that ni na daɗe da mantawa da wata Asiya a rayuwata bayan Allah yayi mini mafi kyakkyawan sakamako da my Sweetums to kuma me zai dame ni." Wani murmushin farin ciki Zeey ta saki jin abinda ya cewa Salim, duk da tasan Baqeer yana sonta amma bata ɗauka son da yake yi mata ya kai girman haka ba. Girgiza kanshi kawai yayi ya fita ba tare daya ƙara cewa komai ba, ba zai yiwu yaje wurin Habi a yanzu ba don tara ta wuce sai dai ko gobe kawai dai ya basu wuri ne don su tattauna shi yasa ya tashi ya fito. Salim na fita Zeey ta kalli Baqeer a shagwaɓe tace "Ya Baqeer," sosai yaji ƙiran sunanshi da tayi ya ratsa shi. Ƙasa-ƙasa kawai ya kalleta ya girgiza kai don bata san yadda duk tayi mishi magana da wannan muryar tasirin da take yi a jikinshi ba. Cigaba tayi da cewa "Me yasa ka hana na faɗawa Daddy Ya Kabir ne ya kaɗeka?" Da mamaki yace "Ke yanzu idan aka ƙyaleki sai kije kina faɗa, abinda ya riga ya wuce ai ba'a dawo dashi baya don haka ko ba Daddy ba please kada kije kina faɗa don ni ko Umma ban taɓa faɗawa ga wanda ya buge ni ba ko Baba ma hasashe ne kawai yake yi amma baya da tabbacin Kabir ne ko bashi bane ni kuma ba faɗa mishi zan yi ba don haka please a rufe wannan maganar kada a ƙara dawo da ita don tuni na yafe mishi tun ma kafin nasan ɗan uwanki ne shi." Idanunta ne taji sun cika da ƙwalla, nauyin da ƙirjinta yayi tun ranar da tasan Kabir ne yayi sanadin gurguncewar Baqeer taji ya yaye tamkar an sauke mata wani gungumemen dutse da aka sa aka danne ƙirjinta dashi. Cikin rawar murya tace "Nagode Ya Baqeer." "No, thank you, for believing in me even when I didn't believe in myself, for loving me the way I am despite all my flaws. Thank you for being there for me when I needed it the most, I don't know what I would have done without you. I will forever be grateful for having you in my life. I love you so much Sweetums." Bata san lokacin data buɗi baki tace "I love You too Ya Baqeer, fatana har kullum Allah ya bar mu tare cikin aminci har ƙarshen rayuwarmu." "Ameen Habibty," ya amsa mata yana jin wani irin shauƙin sonta yana ratsa duk wata jijiya dake harba jini zuwa zuciyarshi. Bai dan wane irin do yake yiwa Zainab ba abu ɗaya ya sani rayuwarshi is incomplete without her. Sun daɗe suna tattauna suna tsara yadda suke so bikin su ya kasance, ita tace tana son yin events shi kuma yace a'a dinner kawai zasu yi, ba zai hanata yin wasu events ɗin ba idan tana so amma shi dai dinner kawai zai je. Da ƙyar ta lallaɓa shi ya amince zai je mata kamu amma daga shi yace ba zai je komai ba to itan ma ta yarda babu jayayya tunda dai ta samu ya amince zai je kamu da dinner ɗin ai shikenan. Da ƙyar suka iya rabuwa shima sai da Kabir ya leƙo yace mata Daddy yace ta shiga gida haka nan sannan suka haƙura suka yi sallama ya tafi bayan ta rakashi harabar gidan inda motarshi take, sai da taga fitarsu daga cikin gidan sannan ta koma ciki tana jinta kamar tana yawo akan gajimare don shauƙi. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI* {100} Mummy ce ta sauke ajiyar numfashi ta kalli yaron da bai wuce shekaru talatin ba da yake gabanta tace “Sultan ka tabbata kuɗin zai ninku?” Murmushi ya sakar mata yace “Haba Aunty ban san me yasa kike tantama ba a gabanki da kuma kanki kika tura 1m ko kwana biyu ba ayi ba aka turo miki 1.5m to imagine in kika saka 100m nawa za’a baki? 150m kenan.” Lissafi tayi tunda ta saida gidaje uku tanada 200m to zata juyesu kawai in yaso in aka ninko mata kuɗin sai ta haɗa ta tafi Dubai ta saro manyan kaya ta buɗe ƙaton shago a Abuja, daga Inna har Nabila tunda basu zaɓe ta ba suje can suyi rayuwarsu itama zata yi tata, wahalarsu da tasha da ta isa. Katse mata zance yayi da cewa “Ba dai tunani kike yi ba? Ni yanzu kalleni? Ko ba gidanki na siya da kuɗin da na samu ba?” Murmushi tayi mishi tace “Na yarda fa, kazo muje bank sai na tura musu kuɗin ka zama shaida.” Dariya yayi yace “Dadina dake kin san abinda kike so shi yasa bana so wannan garaɓasar ta wuceki, don daga mutane sun gano abinda ke faruwa to fa rubdugu za ayi daga nan kuma sai wanda Allah yaci da rabonshi, kin san turawa suna son suga suna taimakawa wanda yake nema.” Kai ta jinjina alamar gamsuwa tace “Muje?” Miƙewa yayi yana yi mata tafi yace “Sai babbar mace ai ku irinku ba’a ja daku, ga kyau ga aji ga kuɗi.” Ji tayi ya ƙara fasa mata kai, nan suka je bank babu wani jan lokaci ta tura kuɗin nan cas sannan suka yi sallama akan daga kudin sun shigo zata kirashi ta bashi la’ada. Hotel ɗin data kama ta wuce tana shiga ta kwanta akan gado tana sauke numfashi ta rasa me yasa kwanan nan sai tai ta yin haki ta tabbatar saboda bata wahala ne yanzu gashi kwanan nan sai fita take yi tana ta ƙoƙarin saida filayenta tun kafin Alhaji Sulaiman yazo mata da shirmen banza. *** Wata irin tsaftatacciyar soyayya ce ke ƙara shiga tsakanin Baqeer da Zeey, Baqeer yau yake so ya yiwa Umma magana akan sa ranarshi da Zee da kuma son zuwa Dambatta yaje ya gaida mahaifiyarta da ƴan uwanta, tunda yaji su a waje suna hira ya fito yana murmushi ganin yadda suke zaune suna hira gwanin sha’awa, Umma kana ganinta zaka san tana cikin kwanciyar hankali don har canzawa tayi ta murmure, ita kanta Dada dake mitar Umma ta koma ganin yadda ta ke murmurewa yasa ta ɗan yi shiru don ta fahimci lallai Umma zaman gidan Badaru haƙuri kawai take yi tasa a ranta gwara ta ɗan huta kaɗan sai ta sake maganar komawar, yana ƙarasowa ya gane maganar Maryam suke yi hakan yasa yace “Umma tazo ne?” Kallonshi tayi fuska a sake sosai tace “A’a magana muka yi a waya da safe, tace ta kira ka bata sameka ba wai Baban mijinta ne zai tashi akwai wani karamin gida da ya saya mishi zai koma can, kamar har aure ma suke son yi mishi.” Dariya Dada tayi tace “A’a to ni dai kar ma yace yana sona don ina da zawara na ehe.” Baqeer duk yadda yaso ya dake sai data sashi dariya yace “Ya taimaki kanshi, dama ni sam banga dalilin barin mahaifinshi a gidan da matarshi take ba, sam ba tsari.” “Kai dai ba gashi kaje ka sa an koreshi ba, sai hankalinka ya kwanta, sai maganar aiki tace ya bada takardunta.” Sosai abun ya yiwa Baqeer daɗi har hakan ya bayyana a fuskarshi yace “Umma kenan dai saura ni.” Dada ta riƙe haba tace “Ahaf ni dama nasan ba iya jira zaka yi ba, to ni kam Baqeeru ko dai kawai nazo ni kadai na wakilceku a ɗaura ne.” Hannu yasa ya shafi bayan kanshi yana cewa “ko zaku yiwa Kawu Halliru magana?” Kallon mamaki suka yi mishi, ganin wanda yake magana yayan Umma ne, fuskar ta ce ta canza ta gyara zama tace “Kana nufin ba Babanka bane da yan uwanshi zasu nema maka auren?” “Babana a ina? Ni bana buƙatar shi ma a wurin ɗaurin auren ya sha zamanshi.” Sosai Umma ta tamke fuska tace “Ba kuwa zai yiwu ba sai dai in ba son auren kake yi ba, babu mai nema maka aure sai mahaifinka, duk laifin Badaru mahaifi mahaifi ne, sannan a iya sanina dashi duk fitinarshi a cikin gida take sai kuwa abokin faɗanshi mahaifin Zainab amma banda mu bana ji akwai wanda yake samun matsala dashi ba tare da dalili ba, shima mahaifin nata shi ya fara tsoksnoshi kawai dai Badaru rashin haƙuri ne da faɗa da yayi mishi yawa shi yasa aka fi ganin laifin shi,” bata jira me zai ce ba ta cigaba “Dan haka dole kaje ka sanar dashi.” Baqeer kasa magana yayi din zuciyarshi har wani zafi take yi yana ji shi gaskiya babu abinda zai haɗa shi da Badaru, Dada ce ta katse mishi tunani da cewa “Baqeer uba fa uba ne sannan ka duba kyautatawa da kaunar da ya nuna maka kafin ka tuna rashin kirkin da yayi maka.” Har yanzu dai bai yi magana ba sannan kuma babu ma alamar zai yi, Umma ce tace “Sannan maganar Bashir ina ganin ka kira shi yazo ya fara aiki ko ya ya ne dai ƙaninka ne na jini in babu mu dole su kake dasu.” Kai ya ɗaga kawai ba tare da yace komai ba, tasan halin Baqeer hakan yasa tace “Kana da numbershi?” “Eh Umma zan kira.” Ga mamakinsa sai ji yayi tace “Kirashi.” Shi abun ma dariya ya bashi kamar wani yaro? Sai dai ya ya iya haka nan ya kira wayar ba tayi ringing biyu ba ya ɗauka cike da zumuɗi yana gaishe shi, amsawa yayi sannan yace “Zan turo maka address na shagon mu sai kazo da yamma.” Cike da jin daɗi yace to. Komawa ɗaki yayi sai yaji duk ranshi ma ya ɓaci kenan dole sai ya sanar da Badaru? Umma kuwa yana barin wurin ta kira Baffa wato yayan Badaru nan ta sanar dashi maganar auren Baqeer da kuma yarinyar Alhaji Sulaiman ce, shi kanshi Baffa sai da yayi mamaki don yasan ƴar tsamar dake tsakaninsu sai dai ya sanar da ita zai je da kanshi suyi magana. Nan yayi mata godiyar kayan abinci da Baqeer ya aiko musu, daɗi ne ya kamata kafin suyi sallama ta kashe wayar Dada na cewa “Kin yi daidai don Baqeer in aka biyeshi haka zasu yi ta zama da mahaifinshi kuma ita rayuwa ba’a ajiye iyaye. *** Baffa kuwa da rana yasa yaronshi ya kawoshi don ya girma ba sosai yake fita ba, ƙin shiga yayi yace Badaru ya zo suyi magana, ya dade yana yi mishi nasiha akan rayuwa da kuma haƙuri da ake da rayuwa sannan ya nuna mishi kuskuren fifita Baqeer fiye da ƴan uwanshi da yayi wanda gashi nan shine ya raba mishi kan iyalinshi da kuma babban abu na rashin yarda da ƙaddara da yayi, jikin Badaru ne yayi sanyi don kwanan nan sam rayuwar bata yi mishi daɗi jiya da yaje asibiti saboda ciwon kai da yake fama dashi aka gwada jininsa gani aka yi jininshi ya hau nan likita ya bashi magani ya dawo gida, ga kwankwasonshi tunda Kamalu ya hankaɗe shi har hau ciwo yake yi mishi lokaci-lokaci, sai da suka gama magana sannan ya sanar dashi maganar auren Baqeer da ƴar gidan Alhaji Sulaiman, a fusace Badaru ya miƙe yace “Kaga Yaya bafa zai yiwu ba kafa san meke tsakanina da mutumin nan don haka ba dai yarona ba.” Kallon takaici Baffa yayi mishi yace “Kenan duk abinda nake sanar da kai baka ji ba? To ita Uwanin da kuke faɗa akanta ma ta daɗe da barin duniya kuma ku da kuke raye kuma ba dawamma zaku yi ba.” Jikin Badaru ne yayi wani sanyi ya kalli Baffa kafin ya koma ya zauna, Baffa yace “In ma zaka gyara rayuwarka dats iyalanka ka gyara tun kafin wanin abun ya sameka ka rasa wanda zai tausaya maka a cikinsu.” Haka ya tafi ya bar Badaru da dogon tunani, ji yayi hawaye ya ciko idonshi lallai ya tafka babban kuskure shi yasa sam rayuwarshi baya ganin daidai, yanzu ga Kamalu an nemeshi an rasa, shi dai yanzu ya fara tsoro Allah dai yasa ba wani abun bane ya sameshi. Bashir ne ya fito da alama fita zai yi, Badaru ya kalleshi yace “wurin Baqeer ɗin zaka?” Kallonshi yayi yana neman wayancewa, “in kaje kace ina son yin magana dashi,” Badaru ya faɗa yana shiga cikI, ɗakin Fatima yaje ya zauna yana tunanin abubuwan daya aikata, lallai rayuwarshi gaba ɗaya bai tafi da ita akan hanya mai kyau ba. Haka ya fito sukuku yaje masallaci, agoggo kawai yake dubawa yana jiran isowar Baqeer, Abu yau ita ce da girki gashi gidan babu komai, ta rasa yadda za ayi tayi mishi magana saboda ko fuska bai bada ba, haka tayi tuwo tayi miyar kuka daga garin kuka sai ruwa da gishiri a ƙalla dai aci. Bashir yana shago yazo nan yace ya fahimci ya shagon yake in yaso sai yaga me zai fara koya, anan ne shi kuma ya sanar dashi kiran da Badaru yake yi mishi, kalaman Umma ya tuna wanda yasa yasan tabbas ba zai iya ƙin zuwa ba, da la’asar ya kira Tanimu suka je, tun a waje yaga mutum biyu da alama cikin fushi suke, ga Badaru a tsaye yana kallon su babu alamar ma yana da ƙarfin yin faɗa, Baqeer na ƙarasowa yaji yana cewa “Bani kuɗina haka kawai ba zai yiwu ka amshi kayan abinci da zummar bani kuɗi ba gashi har sati uku baka biya ba, nifa matsalata da matsiyata kenan basu san hallaci ba……” “Kai kuma a wani ɓangare za’a saka ka?” Baqeer yayi maganar yana ƙarasa turo kekenshi, kallonshi suka yi idanunshi na kan mutumin yace “Nawa ne kuɗin naka?” “Dubu biyu.” Takaici ya kama Baqeer wai akan dubu biyu ake ciwa mahaifinshi zarafi, miƙa mishi dubu biyar yayi ya amsa kuma ko kunya babu ya fara godiya kafin ya juya. Badaru kallon Baqeer yayi yana tuno cin zarafin daya dinga yi mishi, ji yayi ƙwalla ta sake ciko idonshi ya kauda kai yace “Mu shiga ciki.” Shima Baqeer bai musa ba suka yi ciki, Jamila kam tana ganinshi ta rikice tama manta ɗanta ne sai gani tayi ta rusuna tace “Sannu da zuwa ina wuni?” Mamaki ya kama Baqeer yace “Me kike yi hakan? Ɗanki ne fa ni.” Sai kuma ta hau matsa ƙafa tana cewa “Wai na daɗe a zaune ne naji kafata tana amsawa.” Abu ta fito ita ma tace “Sannu Baqeer, ya labarin Kamalu?” Kai ya girgiza kafin yace “Na dai basu kuɗin mutumin nan to amma shi ɗin ne har yanzu ba labari inda ya shiga In Sha Allahu zaku ji alkairi.” Tace “Mun gode mun gode.” Ɗakin Umma suka je ba komai a falon sai tabarma da pillow da bargo wanda bargon yake na Badaru kenan yana shiga ɗakin? Zama suka yi duk suka yi shiru kafin Baqeer ya gaisheshi ya amsa yana cewa “Kafarka fa har yanzu dai?” Kai ya jinjina kafin yace “Ina dai iya tsayawa akanta amma bana iya takata, da alama ba zata taku ba ko kuma ba yanzu ba.” Kai ya ɗaga sannan yace “Ashe Zainab kake so?” “Eh!” Ya faɗa kawai, Badaru jiki a sanyaye yace “Shi mahaifinta ya amince?” “Eh!” Yanzun ma ya faɗa kawai Iska ya ɗan sauke kafin yace “Nine dai mafaɗaci kenan? Tunda har ka nemi izininshi amma ni ka kasa neman nawa.” Hannayenshi Baqeer ya haɗe yace “A’a na ɗauka baka damu da yadda nake rayuwa bane.” Kallonshi yayi sannan yasa hannu ya shafi cinyarshi yace “Ka yafe mini Baqeer lallai nayi kuskure kuma ban kyauta ba.” Ba wani dogon nazari yace “Na yafe maka Allah ya yafe mana gaba ɗaya.” Yana cewa ameen Abu na shigowa da kwanon abinci, amsa Baqeer yayi duk da ba ci zai yi ba, mamaki ne ya kamashi ganin wata irin miya wacce kana gani kasan ɗaci ma zata yi, ajiyewa yayi sannan yace “Baba ko muje a sayi kayan abinci?” Badaru ji yayi kamar yayi kuka lallai bai kyautawa kanshi ba, yanzu gashi nan gurgun dai shine gatanshi, kasa magana yayi sai Baqeer da yace “Kamar gwara muje tare saboda a siyo abinda ya dace.” Haka suka fito Tanimu ya jasu a mota, a hanya Badaru ke tambayarshi me yake yi, ya sanar dashi, nan ya sake tambayarshi maganar auren da kuma sanda suke so aje gaisuwa, Baqeer yace susa rana zuwa wani satin sai suje. Haka suka siyo kayan abinci suka dawo, murna a wajen Abu da Jamila kuwa ba’a cewa komai, nan suka yi sallama da matan gidan suka fito, Badaru ne yace “Fatima fa? Yaushe zata dawo?” Shiru Baqeer yayi yana kallon Baban don bai san me zai ce ba. Ganin haka yasa yace “Shi kenan ta huta kafin ta dawo." Jikin Baqeer ne yayi sanyi ganin har ya gane me yake nufi, dama fa tun da haka suke da Babanshi kafin yayi magana yasan me zai ce saboda tsabar shaƙuwar da suka yi. **** Jikin Mummy ne ya fara rawa ganin sai kiran numbar Sultan take yi ba’a ɗauka ba, farcen hannunta ta fara ci hankalinta a mugun tashe, yanzu ya zata yi? Wa zata nema? Ina zata sa kanta? Har gidan data saida mishi taje wai ake ce mata shima ya saidawa wani gidan data tambayi nawa aka siya sai mai gidan yace 80m bayan ita a 30m ta sayar mishi, nan fa hankalinta ya tashi. *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 Ayusher Ce Da Umm Asghar *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI DA ƊAYA* {101} Tun Mummy tana gwada ƙiran wayar Sultan tana ringing har ma ta daina ringing ɗin gaba ɗaya. Hankalin Mummy fa ya tashi ta rasa inda zata sa kanta taji daɗi, tsoron ta ɗaya kada dai ace yaron nan cutarta yayi ya karɓe mata kuɗaɗenta da dabara. Cikin kwana biyu gaba ɗaya ta futa daga hayyacinta don ko abinci bata iya sawa cikinta, a ranar da aka cika kwana biyu ne aka yi evicting ɗinta daga hotel room ɗin data kama saboda kuɗin data biya sun ƙare kuma bata da alamar cigaba da biya. Haka nan ba don taso ba ta tattare ya nata ya nata ta bar gidan ta koma gidan Inna. Inna na ganinta tace "ke kuma daga ina?" Kawai ta fashewa Inna da kuka cewa take yi "Na shiga uku Inna, don Allah ku nemo Sultan yazo ya bani kuɗaɗena wallahi na fasa yin kasuwancin." Ita dai Inna sai kallonta take yi har tayi ya isheta sannan Inna tace "idan na fahimce ki daidai wani kika damƙawa dukiyar ya gudu da ita," kasa amsawa Inna tayi don haka Inna ta cigaba da cewa "ai daidai kenan Halima, dama wanda yaƙi ji ai baya ƙi gani ba, nan babu yadda ban yi dake akan ki koma gidanki ki kula da mijinki da larura ta sameshi ba kika toshe kunnuwanki kika ƙi ji sai yanzu da kika haɗu da mutanen duniya suka yi miki hankali ne zaki zo ki sakani a gaba kina kuka. Ai baki ga komai ba tunda kika ce ke butulu ce mai manta alheri. Duk irin yadda mutumin nan ya riƙemu amana ya ɗauke dukkan wasu nauyin mu baki duba ba kika rasa lokacin da zaki butulce mishi sai da ƙaddarar rayuwa ta afka mishi, wato yanzu ya gama yi miki amfani to bari ki ƙara gaba ki barshi." Ita dai Mummy sai kuka take yi tana jin baƙin cikin damfararta da Sultan yayi, yanzu shikenan duk abinda take taƙama dashi take ganin ita ma yanzu ta kai wani matakin rayuwa data daɗe tana yiwa kanta fatan kaiwa ya rushe lokaci vuda kamar ba'a yi ba. Kallon tausayi Inna take yi mata har sai data tsagaita da kukan sannan Inna tace "Sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidanki ki nemi yafiyar mijinki don baki da wani rufin asiri face ɗakin ki, da Allah yasa ma ba sakin ki yayi ba ke kika ga dama kika baro gidan don wallahi baza ki zauna min anan ba ke ba bazawara ba ke ba sakakkiya ba nayi ta faman ɗawainiyarki alhali kina da gidan mijinki." Share hawayenta tayi tace "yanzu Inna sai na koma bayan duk abinda nayi mishi?" Kallon tsaf Inna tayi mata sai daga duk ta rame ta lalace kamar ba ita, cike da tausayawa halin da ta jefa kanta a ciki Inna tace "Komawa kuwa ta zame miki dole kije ki nemi gafarar maigidanki don dai kin san baki kyauta mishi ba bayan duk alherin da yayi miki a rayuwa, baki da wani gata face ɗakin ki Halima haka zaki yi haƙuri ki tashi ki koma. Maza shiga ciki kiyi wanka ki gyara jikinki sai kizo ko tafi kin ji, Allah yayi miki albarka." Cikin zuciyarta ta amsa Ameen ɗin ta tashi ta shiga ɗakin Inna don tayi wanka kamar yadda ta umurceta. Babu kunya haka Mummy ta koma gidan tasa makulli ta buɗe ɗakinta ta shige, babu wanda yace mata ci kanki sai ma hidimarsu da suke yi, to itama kunyar abinda ta aikata yasa ta kasa sakewa a cikin gidan kullum tana ƙunshe a cikin ɗaki bata iya fitowa, gaba ɗaya a ɗarare take da mutanen gidan duk da ma babu wanda yake shiga sabgarta a cikin su. ***** Badaru da ƴan uwanshi sun je wajen Alhaji Suleiman Ƙaraye nemawa Baqeer auren Zainab, sosai Alhaji Suleiman da nashi ƴan uwan da suka zo daga Ƙaraye suka yi musu tarba da mutunci da girmamawa, abinda ya ƙara sanyayar da jikin Badaru. Cikin mutunci da mutuntawa duka gabatar da abinda ya kawo su, babu wani ja'in'ja ko ɓata lokaci aka tsayar da magana guda ɗaya har an yanke ranar auren watanni biyu masu zuwa nan gaba. Haka suka rabu ana raha ana wasa da dariya. Bayan sun fita Badaru ya ɗan dawo ya kalli Alhaji Sulaiman yace "Ya jikin naka?" Murmushi yai ya sake mika mai hannu yace "Allah ne ya haɗa mana yaran nan dan mu sassauta wa kan mu a lahira saboda wannan gabar batada amfani." Badaru ya jinjina kai nan ya bashi hakuri shima Alhaji Sulaiman ya bashi hakuri sannan ya fito. Sosai Baqeer yayi farin ciki da jin an bashi Zeey don ma ranar da aka saka ɗin tayi mishi tsawo a cewarshi shi bai ƙi ace daga zuwa neman auren an ɗaura ba. Itama Zeey ta samu kanta cikin farin ciki don abu ne da har ta cire rai da faruwarshi sai dai da yake komai yin Allah ne sai gashi cikin sauƙi iyayen nasu sun aminta da maganar gashi har an saka rana. Kowanne ɓangare shirin biki kawai suke yi, ga Baqeer dai gyare-gyare yake yiwa gidanshi duk da sabo ne ya siya amma akwai wuraren da yake so a canja musu fasali sai kuka painti da za'a yiwa duka gidan har part ɗin su Umma. Da kanshi ya haɗa lefenshi don a yanzu za'a iya cewa yafi su Maryam sanin manyan kaya saboda harkar ɗinki da yake yi, babu irin zanin da baya gani, ya dai ɗaukesu sun rakashi amma komai da kanshi ya zaɓa ai kuwa kaya yayi mata masu kyau da tsada sosai, bai dai yi kaya irin na ƙarya ba sai dai komai mai kyau ne da inganci. Akwatina ne set biyu kowanne mai uku da kit sai suttura guda talatin da biyar amma fa duka manya sai dangin su dogayen riguna, abaya, ƙananun kaya da sauransu. Duk wanda yaga kayan sai da ya yaba don kaya ne aka yi su babu ƙaranta babu kuma fariya a ciki. Ita kanta Umma data ga irin kayan da Baqeer yayi sai data yaba sosai ta kuma ƙara godewa Allah daya ɗaukaka ɗanta gashi yanzu kullum ƙara samun cigaba yake yi. Ba wasu mutane da yawa ne masu kai kayan ba don Baqeer yace baya son gayyar mutanen nan don haka aka tsara a gidansu daga Abu sai Jamila ne masu zuwa sai Hadiza a cikin ƴan uwanshi sai kuma daga cikin ƴan uwan Badaru mutum biyu sai matar wan Umma, su kenan mutum shida. A ɓangarensu Zeey ma sai shiri suke yi, kuɗaɗe masu yawa Daddy ya tura mata a account ɗinta yace suje da Ummi su sayi duk wasu sayayyar kayan kitchen don furniture wani interior decorations company ya bawa kwangilar zuwa su shirya mata gidan. Babu abinda ake saka Mummy a ciki, to ina ma suka ganta tunda ta mayar da ɗaki wajen zamanta. Ranar da za'a kawo lefen ma haka ƴan uwan Ummi dana Daddy suka cika gidan sai hidima ake yi, anan nema wata ƙanwar Ummi tayi magana akan bata ga Mummy ba shine aka ce mata tana ɗaki. Tashi tayi ta tafi ɗakin Mummyn, daga bakin ƙofa ta tsaya tayi knocking. Tasowa Mummy tayi ta buɗe jikinta a sanyaye don tunda taji hayaniya ta cika gidan ta sakawa ƙofarta key don tsoron haɗuwa take yi da ƴan uwan Ummi saboda wulaƙancin da tayi ta musu a yanzu kuwa da suka dawo cikin rayuwar su Zeey bata san abinda zasu yi mata ba shi yasa ta dannawa ƙofarta key. Murmushi Aunty Badi ta sakar mata don ta lura da yadda take a ɗarare, kaucewa tayi ta bata hanya ta shiga cikin ɗakin. Zama tayi akan resting chair ita kuma Mummy ta zauna a bakin gadon. Gaisheta Aunty Badi tayi sai kuka tace "mun zo tun ɗazu naga ban ganki ba shine nake tambayar ina kike aka ce kina ɗaki, sai dai kuma hakan bai dace ba a matsayinki na uwa a wajen Zainab ace ana hidimarta sai dai wasu daga waje ne zasu tsaya akai ke da kike cikin gidan kamar ba kya nan shi yasa na shigo nace kome Zainab tayi maki kiyi haƙuri zaki yi yaran ne ka haifesu baka haifi halinsu ba don haka kiyi haƙuri ki fita a tari baƙin nan dake idan yaso ko meye ma daga baya sai kuyi wannan siririn ku ne na cikin gida bai kamata wasu daga waje su sani ba". Godiya tayi mata saboda taji daɗin yadda ta mutunta ta duk da abubuwan da tayi musu a baya, tashi tayi ta shirya cikin wani rantsatsen lace ta fita suka gaisa da mutanen da suka zo sai dai duk da haka ta kasa sakin jikinta sai take ganin kamar kowa na wurin yasan abinda tayi. Har ƴan kawo kaya suka zo suka tafi da sha tara ta arziƙin da aka haɗa musu Mummy na cikin su don duk wani abu da za'a nema ita Aunty Badi take tambaya don haka tun tana ɗari-ɗari dasu har dai ta saki jikinta aka yi komai cikin mutunci, a lokacin ne kuma ta ƙuduri niyyar samun Daddy ta bashi haƙurin abinda tayi mishi don tun dawowarta bata yarda ya ganta ba, kunyar haɗa ido dashi take yi. Da yan uwan Ummi zasu tafi da kanta taje ta basu hakuri akan kuskuren raba su Zainab datai da sharrin data dinga musu tayi haka ne saboda tana tsoron kar yaran su barta, haka tai ta basu hakuri ganin sun saki jiki sun nuna mata ba komai yasa ta ƙara samun nustsuwa. A daren ranar ta sami Dady a ɗakin shi bayan kowa ya tafi ya kwanta, durƙusawa tayi a gaban gadon shi tana kuka tana bashi haƙurin abinda tayi mishi, to shima bai wani ja da nisa ba yace ya yafe mata don a shekarun nan nashi yana buƙatar companionship Zainab aure zata yi haka ma Kabir dole yana buƙatar abokin zama don haka ya yafe mata suci gaba da haƙurin zama da juna, sannan in ya duba wani bangaren lefin nan ba nata bane ita kaɗai shi ma yanadashi a matsayinsa na namiji sam baiyi aikinsa ba, nan ta sanar dashi damfarar da aka mata, nan ma bai nuna jin haushinsa ba yace dama dukiyar ba hakkinsu bace gwara ma da aka kwashe. Mumy tai alkawari akan bazata sake yin wani abin da bai dace ba wanda yasa hankalin Dady kara kwanciya. Zeey na zaune a parlour ita da Kabir, tsare-tsaren biki suke yi don fa Zeey ba wasu ƙawaye ne da ita ba, dama dai Nabila ce a yanzu kuwa ko son ganinta bata yi don haka Kabir ɗin dai shine abokinta. Ƙiran wayar Baqeer ne yasa ta ajiye littafin dake hannunta tana rubuta abubuwan da suke buƙata a hidinar bikin. Ɗauka tayi cikin yauƙi tace "Ya Baqeer." Daga can ɓangaren Baqeer sai da ya lumshe idonshi saboda yadda muryar ta ratsa shi. Gyaran murya yayi saboda yadda yaji ta shaƙe kamar wanda ya daɗe bai yi magana ba sannan yace "Ba kya jin magana Sweetums bayan na faɗa miki ɓarnar da wannan shagwaɓaɓɓiyar muryar taki ke yi min ki adanata a gefe sai mun je gidanmu sannan kiyi amma kin ƙi bari ko?" Fuskarta ta rufe cikin jin kunyar abinda yace kamar yana gabanta tace "Wallahi zan kashe wayata idan baza ka bar yi min irin wannan maganar ba." Shima cewa yayi " Nima ki bar yi min magana da wannan shagwaɓaɓɓiyar muryar taki bana so." Dariya tayi tace "to na bari, ya kake yasu Ummana da Dadata?" "Duk suna nan lafiya kullum Dada sai tayi zancen ki wai yanzu kin daina nemanta." Dariya kawai tayi tace "Dada kenan, zan je ne amma ba yanzu," murya ƙasa-ƙasa yace "sai yaushe zaki ko sai kin zama Mrs. Baqeer tukuna?" "Umm," kawai tace cikin jin kunya. Sai da suka gama soyayyarsu sannan yace mata ranar Saturday zasu je Ɗambatta da wa zata haɗa su da zai yi musu rakiya. Cewa tayi "tunda weekend ne sai na yiwa Mubashir magana yazo ya raka ku," Kabir na jin abinda tace ya girgiza mata kai, "kai zaka?" Ta tambayeshi, ɗaga kai yayi alamun amsawa sai ta cewa Baqeer "To kaji wai Ya Kabir ne zai raka ku sai kace ba jiyan nan ya dawo daga Ɗambattan ba, naga alama nema yake yi ya ƙwace mini Ummi don shagwaɓar da yake yi mata ko Inaya bata yi yayi ta bata kunya cikin mutane bayan ita tana yi mishi karar ƴan fari sam baya gani." Harararta Kabir yayi jin abinda tace, bata miye mishi ba ta cigaba da yin wayarta da Baqeer sai ma tashi da tayi zata shiga ɗakinta sai ga Mummy ta fito daga ɗakin Daddy, hannunta da karamar roba da towel da alama dundumamai gun ciwon tai, ɗauke kanta Zeey tayi ta shige ɗakinta tana ƙunƙuni. "Ke kuma ke da wa?" Baqeer ya tambayeta, tsaki tayi tace "Mummyn nan mana, ni wallahi ko ganinta bana son yi." Girgiza kanshi yayi yace "kada ki kasance daga cikin butulallun mutane mana Zainab, matar nan duk da abinda tayi muku nasan ba za'a rasa alkhairin da tayi muku ba tsawon zamanku da ita to ko don haka baki ga ya dace ki yafe mata ba, tayi laifi sannan tayi nadamar abinda tayi ke da bakin ki kike faɗa mini baki da fargabar tafiya ki bar Daddy yanzu saboda tana tare dashi tana kuma kula dashi to ai ko don wannan yaci ace an yafe mata ki manta da abinda ya faru tunda Allah yasa yanzu kuna tare da Ummi komai ya wuce don ina ganin wannan ne mafi girman laifin da tayi muku raba ku da mahaifiyarku da tayi ko?" Kamar bata so tace "umm," yace "to kin gani, don Allah ayi baƙuri a yafe mata, abinda ma kwana kaɗan ya rage miki ki bar mata gidan." Haka dai yayi ta lallashinta yana yi mata nasiha har taji abranta zata iya yafewa Mummy abinda tayi musu. Shiru tai ta kwanta akan gado tabbas duk muguntar da Mumy ta mata ta kula dasu, ta basu kulawar da ko mahaifiyarsu basuji suna nema ba. ***** *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* DA *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI DA BIYU* {102} Ranar asabar da wuri suka ɗauki hanyar Ɗambatta, Salim ke tuƙin motar sai Kabir a kusa dashi Baqeer kuma yana baya. Suna tafe suna hirarsu cikin raha da nishaɗi kamar waɗanda suka daɗe da sanin juna tun ma ba Salim da Kabir ba abota suke yi sosai yanzu. Ƙarfe sha ɗaya na safe a ƙofar gidan Ummi tayi musu, da yake Kabir ya sanarwa da Ummi batun zuwansu yasa Ummi ta tashi da hidimar tarar su. Tun daga bakin gate Mubashir da yazo gida weekend ya taro su, shi yayi musu jagora zuwa parlourn Babansu kafin yaje ya sanar da zuwan nasu, shi kuwa Kabir tuni ya shige cikin gida wajen Ummi don ƴan kwana biyun nan da bai ganta ba kewarta yake yi duk da ma kullum ne sai ya kirata a waya sun daɗe suna hira yana jaddada neman gafarar wofantar da ita da suka yi tun ma bashi da ya kasance babba ba. Tare Ummi da Daadan su Inaya suka shiga parlourn, gaba ɗaya sai suka ƙara nutsuwa Baqeer dake zaune akan wheelchair ma ƙoƙarin zamowa ƙasa yake yi don haka nan ya samu kanshi da jin matsananciyar kunyar Ummin. Daada ne ya hanashi sauka yace mishi babu komai yayi zamanshi ai sun san yana da larura. Cike da girmamawa suka gaishe su, Ummi dai a kaikaice take kallon Baqeer tana tasbihi ga Allah cikin ranta tana yabawa da zaɓin ƴarta, duk da taji wani iri lokacin da Zainab tace mata ai gurgu ne wanda take so don babu uwar da zata so ace yau ƴarta na auren gurgu amma data ganshi yanzu sai taji wata irin nutsuwa da zaɓin ƴar tata don tasan rashin ƙafar ce kawai tayi mishi cikas bayan haka kyakkyawa kuma nutsatsen mutum ne wanda tsantsar kamalar shi bata ɓuya ba. Tashi Ummi tayi ta basu wuri bayan sun gaisa sai Daada ne ya zauna yana yi musu ƴan tambayoyi irin wanda duk uba na ƙwarai yake yiwa manemin auren ƴarshi. Mubashir da Inaya ne suka yi ta shigar musu da kayan abincin da Ummi ta tanadar musu, tashi Daada yayi ya basu wuri don yasan ba zasu sake su ci abincin a gabanshi ba. Basu bar gidan Ummi ba sai da suka yi sallar azahar bayan sun ajiye musu tsarabar drinks da ruwa da suka ciko boot ɗin motar su dashi. Daga nan gidajen ƴan uwan Ummi aka raka su duk inda suka je aka nuna Baqeer a matsayin wanda Zainab zata aura sai anyi mamakin ganin shi gurgu sai dai kuma duk wanda ya kalleshi sai ya ƙara don sun san Zeey ɗin fa ta iya zaɓe rashin ƙafar ne kawai yayi mishi cikas baya ga haka baya da wata makusa a jikin shi. Duk gidan da suka je sai Baqeer yayi musu kyautar kuɗaɗe abinda ya ƙara toshe bakin ƴan ƙananan tsegunguman da suka fara tashi. ***** A hankali Mummy ta turo kofar ɗakin Zainab hannunta ɗauke da babbar leda, bayanta wata mata ce hakan yasa Zainab kallon Mumy ɗin, jiki a sanyaye tace "Zainab mai gyaran jiki ce, zata dinga zuwa daga nan har biki tana gyara ki." Kallon Mummy tayi ta ɗaga kai alamar to don tasan Mummy na sonta har cikin ranta da alama buri ne yayi mata yawa yasa take tunanin basu ne a gabanta ba. Yawun bakinta ta haɗiya har sai da Mummy ta kai bakin ƙofa zata fita sannan tace "An jima zan zo sai muyi maganar shirye-shirye sannan kice Nabila tazo bai kamata ayi biki tana can ba." Ƙwalla ce ta cikowa Mummy a ido, kai ta jinjina mata don ta kasa magana, da sauri ta juya ta shiga ɗakin Daddy rungumeshi tayi ta fashe da kuka tana ƙanƙame dashi, bayanta kawai yake shafawa don ya kula abubuwa ne suka yi mata yawa, ɗagowa tayi jiki a sanyaye tace "Senate ku yafe min don Allah wallahi na sani da sanina na ɓoye Nabila don kar ku gujeni sannan na ɓoye neman da yan uwan mahaifiyarsu ke musu saboda ina tsoron rasasu, amma wallahi har cikin raina ina sonsu, nayi kuskure ku yafe min, duk na ɗauka mugunta nake yi musu amma wallahi har cikin raina a matsayin ƴaƴana na ɗauke su don Allah ku yafe min," ta ƙarasa maganar tana kuka, shafa kanta yayi yace "Halima ya isa haka nan, son zuciya ba abinda bays janyowa na sani tsakani da Allah kike sonsu don akwai abubuwa da dama da kika yi wanda uwa ce kaɗai zata iya yiwa ɗanta." Kallonshi tayi tace "Maganar Kabir dana ɓoye akan Baqeer? Senate nayi laifi ka yafe min wallahi lokacin ni na bashi shawara akan mu ɓoye maka kada mu bari ka sani, ka yafe min, komai nice na tsarashi." Shiru yayi yana kallonta haka kawai yaji zuciyarshi na tsoron tambayar abinda ke faruwa, don tabbas ko bata ƙarasa ba ƙwaƙwalwarshi ta kai mishi abinda ke faruwa, fuskar Baqeer ce ta dawo mishi sanda ya ke girgizawa Zainab kai akan kar tayi magana ko wannan ya isa ya tabbatar da inda kalaman Mummy suka nufa. Wannan dalilin yasa yaji son Baqeer ya ƙaru mishi tare da tabbatarwa da lallai zai kular mishi da Zainab har bayan ranshi. *** Ana jibi ɗaurin aure Badaru yazo gidan Dada, don Umma tace baza su koma sabon gidan Baqeer ba gwara yasa matarshi su zauna ita zata koma wurin mijinta in yaso ɓangarensu ya barshi sanda suka je sa sauka su ko kwana ɗaya ko biyu tunda duk gari ɗaya ne, bai musa ba don ya fahimci Umma duk rigimar Badaru da alama tafi son zama dashi. Dada ta daɗe a zaune tana yi mishi nasiha tare da nuna mishi kuskuren abubuwan da yake aikatawa, ya kuma amshi laifinshi ya kuma bada haƙuri, bayan nan ta tashi ta bar musu falon shi da Umma. Shiru suka yi kafin yace "Zaki zo mu koma? Kinga ai ba'a yi biki uwar ango tana wani wurin ba." Kai ta jinjina tace "Shi kenan sai mu tafi nima nasan bai kamata ba." Kallon ta yayi cike da tausayinta yace "Fatima ina ga bayan biki ki koma gidan Baqeer da zama ni sai na dinga zuwa ran kwananki." Da sauri tace "A'a gwara mu zauna a gidan mu suma mu barsu suyi rayuwarsu," ta ƙarasa maganar tana kauda kai, murmushi yayi don ya fahimci me take son ce mishi nan ya juyo yace "Na sani ba zaki yarda dani ba don tunda hali nane ba fasawa zan yi ba, ni nasan ba komawa kike son yi ba burinki dai kiga kin bar Baqeer yayi rayuwarshi don kin san in dai ina zuwa zan iya komawa halina nada." Shiru tayi don maganar gaskiyar kenan ba wai bata yarda dashi bane amma fa hausawa sun ce mai hali baya fasa halinsa shi yasa ta kasa yarda dashi. Haka suka fito ya kwaso mata kaya da yake Hadiza tazo suka wuce tare anan zata kwana ita da yaranta, Maryam kuma tace da safe zata ƙaraso. **** Bahaushe yace rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. A ranar asabar sha bakwai ga watan April aka ɗaura auren Muhammad Baqeer Badaru da Zainab Suleiman Ƙaraye akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Bakin Baqeer a wannan ranar ya kasa rufuwa saboda tsananin farin cikin daya tsinci kanshi a ciki, haka yayi ta gaisawa da waɗanda suka zo don taya shi murnar auren rabin ran nashi da yayi. Kallon Salim yayi yace "Abokina kaga fa mu yanzu mun bar sahun gauraye sai kusan inda kuka nufa." Dariya yayi yace "Wai ya labarin Siddarth har yanzu ba'a ganshi ba?" Ajiyar zuciya yayi yace "Wa ke nan?" Haɓarshi Salin ya taɓa yana dariya yace "Kamalu mana kai dai ka gode Allah baya kusa aka yi bikin da ban san me zai faru ba." Cike da rashin fahimta Baqeer ya kalleshi sai kuma yace "Yana prison next week za'a sallameshi bana son faɗawa kowa ne shi yasa nayi shiru, satan wayoyi suka haɗa gang suna yi to gaba ɗayansu an kamasu aka kullesu ance sai sunyi zaman gyaran hali na wasu watanni wanda wani satin zai ƙare za'a sakesu." Kai Salim ya girgiza yace "Gaskiya ba'a yiwa Siddarth adalci ba Roshni tana nan tayi aure za'a sha romon soyayya yana amsa romon yunwa." Baqeer ganin bai gane me yake nufi ba yasa ya girgiza kai. Gidan su Zainab suka wuce don za ayi hotuna da yamma kuma za ayi dinner. Tunda suka iso yake ɗan kallon gefe da gefe yana neman matarshi, Nabila ce ta fito ta gaishesu tace tana zuwa. Sanye take da black lace anyi kwalliyar da golden shi kuma yana sanye da white shadda anyi kwalliya da golden kallon juna suka yi a hankali suka sakar ma juna murmushi, Inaya ce tace "Ya Baqeer baka ganni ba?" Kallonta yayi yana dariya yace "Little Zee kinyi kyau." Haka suka sha hotuna Baqeer yana ji kamar ya sungumi matarshi su tafi ai gaskiya da yana da ƙafa tabbas a mota zai sata ya tuƙa sai dai kowa ya haƙura da dinner ɗin. Habi anci kwalliya za'a dinner, don Salim har gida ya kawo mata kati uku yace ta bawa wasu in tana so, Asiya ce data zo gidan ta kalleta duk ta rame ta canza sai ƙaton ciki wanda da alama an kusa haifeshi, Habi sai sha'awa take bata don kayan sawarta yanzu kana gani kasan masu tsada ne, yawun bakinta ta haɗiya tace "Habi nima da ina da pass da na rakaki bikin ko banza kaci kasha." Kallonta tayi tace "In zaki ki shirya muje ina da pass." Da sauri ta kalleta tace "Da gaske? Bikin wanene?" Kai Habi ta girgiza tace "Ke dai me ya dameki in zaki kawai ki shirya." Daɗi ne ya kama Asiya atamfar jikinta ta bari kawai tayi ɗan gyare-gyare a fuskarta suka fito, mota ya turo ɗaya daga cikin yaran shagonsu na ɗinki yazo ya ɗauke su, sai murna take akan ko banza zata je taci abinci mai daɗi a hanya ta kira Bello sai data kira sau hudu ya ɗauka ta sanar dashi zata biki to kawai yace ya kashe, sam zaman aurensu baya yi mishi daɗi a dole yake zaune da ita, balle yanzu da zata haihu yana ji zamanta dashi kamar ya zama dole. Sun isa ganin Salim yasa Asiya tayi saurin samun wuri ta labe tana mamakin me ya kawo Salim, gani tayi Habi ta bishi suna hira suna dariya, jikinta ne yayi sanyi don da alama shine saurayin, wanda ta hango akan kujera ne yasa ta murza idanunta tabbas Baqeer ta gani, mamaki ya kamata, ya canza ya canza sosai ya ƙara kyau da fresh, ga wata haɗaɗɗiyar mace a kusa dashi, hawaye ne suka zubo mata, ji tayi baza ta iya zama ba ta fito ta tari adaidaita ta koma gida, sai data isa ma ta tuna ba kuɗin da zata bada, sai ta tuna da kuɗin da Habi ta bata nan ta biya ta shiga ciki. Baqeer a wurin dinner ya ɗan matso yace "Sweetums yaushe za'a gama ne? Nifa na gaji so nake mu wuce muhallin mu." Harararshi tayi tace "Bari na faɗawa Ummi saƙonka." Ido ya zaro yace "Bar shi kawai I can manage." Haka aka gama taro, ganin Habi yasa Baqeer ya sanar da Zee gafa Habin Salim, Kabir a wurin dinner yaga wata junior ɗin su Zainab wacce a take yaji ta kwanta mishi don haka bai sanya ba ya gabatar da kanshi inda yayi sa'a a take ta amsa tayin soyayyarshi, Nabila dake zaune akan kujera tana ganin duk motsinshi, tana kallo sanda yaje yana gabatar da kanshi wurin yarinyar, share ƙwallarta tayi don tasan duk son da take yiwa Kabir ba zai taɓa zama nata ba ta riga ta ɓata rawarta da tsalle, ji tayi zaman wurin ya isheta ganin yadda suke magana kamar sun daɗe da sanin juna, haka itama ta bar wajen tana share hawaye. An kai amarya kai tsaye Baqeer yace su Salim su tafi daga shi har Kabir wai sun gaji bacci zasu yi. Ɗaki ya shigo Zee tana jiran taji yan siyan baki sai taji shiru, kanta ta ɗago kaɗan tana son ganin me ke faruwa cikin ɗakin hannunta taji an kamo an ɗaurata akan cinya, kallonshi tayi tare da yin murmushi ta ɗan daki ƙirjinshi kaɗan tace "Allah ka lalace Ya Baqeer." Kafaɗa ya ɗaga yace "Wai matsalar ma baki ga komai ba tukun." Kallon shi tayi tace "Kamar...." Kawai sai jin bakinshi tayi cikin nata, wani irin yanayi ta shiga wanda bata taɓa ji ba wani abu ne yake tsirga mata har tsakiyar kanta, shi kanshi ji yayi zuciyarshi tana wani irin bugawa da sauri, sun fi minti biyar suna sumbatar juna kafin su haɗa goshinsu guri ɗaya, ya haɗiyi yawun bakinshi yace "Muyi sallah kici abinci ko?" Kai ta ɗaga don ta kasa magana sam, tana neman miƙewa ya maidata kan cinyarshi sannan ya fara tafiya da keken hanyar banɗaki har suka shiga sannan yace "Take responsibility." Tace "Da nayi me kenan?" Kunnenta ya matso yace "Na birkita min tunani da kika yi, wannan gurgun gaskiya ba zai yarda ba." Murmushi tayi tace "Allah kai ko?" Tayi maganar cikin shagwaba, idanu ya runtse yace "Sweetums please ayi mini haƙuri da shagwaɓar nan muyi sallah kici abinci tukun." Haka suka yi sallah ta buɗe kaza zata ci ya buɗe baki cike da kunya ta kalleshi. Gira ya ɗaga mata ta saka mishi a baki, ci tayi ta ɗauko zata kara mishi ya girgiza mata kai alamar a'a tana kaiwa bakinta ko sashi a ciki bata yi ba ya haɗe bakunansu biyu ya ɗauki naman daga cikin bakinta, ita kam Baqeer wai haka yake dama? Ko kuwa yanzu ne ya koyi wannan abubuwan? Don ita gaba ɗaya ya gama birkitata tun kafin ma ayi nisa...... Sai da suka ƙoshi sannan ya sake yi musu addu'a suka shafa. Kallonta yayi yace "Na gaji, mu kwanta?" Da sauri tace "Bari na shiga toilet ina zuwa." Bata jira amsarshi ba tayi toilet tana sauke ajiyar zuciya, turaren da Umminta ta bata ta ɗauko ta shafa a cinyoyinta sannan ta kalli madubi tana sauke ajiyar zuciya kafin ta fito, tsayawa tayi kawai tana kallonshi ganin ya cire rigar shaddar ya bar wando da vest,  kallonta yayi yace "Ƙaraso mana." Bata tanka ba ta tsaya tana kallonshi, murmushi yayi yace "Bacci zamu yi ni ba abinda zan yi miki matsoraciya kawai." Jin haka yasa ta ƙaraso tana cewa "Ni dai ba tsoro nake ba kawai kai ɗin ne ke bani mamaki." Kwanciya suka yi akan gado rigingine ya sauke ajiyar zuciya tare da janyota ya ɗaura kanta saman kafaɗarshi yace "Sweeetums thank you for always been there for me." Ɗago da fuskarta tayi ta kalleshi, idanuwansu na hade da juna yace "Ni me za'a ce min?" Murmushi tayi tana neman maida kanta ƙirjinshi yasa hannu ya ɗago haɓarta kallon juna suka sake yi a hankali ya kai bakinshi cikin nata, salo yake yi mata wanda ya birkita tunaninta itama tana iyakacin ƙoƙarin ta wajen maida mishi da martani.... *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar* *BAQEER* *NA* *UMM ASGHAR* *DA* *AYUSHER MUHD* *RUBUTUN TAGWAYE SHAFI NA ƊARI DA UKU* Last Page❤️ {103} Kuncinta yaja yana kallonta, cike da jin kunya ta shige jikinshi a hankali ya kai bakinshi saitin kunnenta yace "Madam a sake yi mini kiss ɗin nan please sai naga duk na zama alawar lollipop." Hannu tasa ta maƙalƙale shi ta sake shigewa jikinshi tace "Allah kai dai ba zaka bari ba ko?" "Ina fa zan bari gaba ɗaya an tashi kaina?" Yanayin maganar shi ne ya canza yace "Thank you Sweetums for marrying this disab....." hannu tasa ta rufe mishi bakinshi wani kallo take yi mishi mai cike da so da ƙauna, wani abu ne yaji ya tsirga mishi a hankali ya fito da harshen shi ya fara wasa dashi a saman tafin hannun data rufe bakin nashi dashi, wani yanayi ta fara ji wanda ya sata ƙoƙarin zare hannun, a hankali ya sako hannunshi ya riƙe ƙugunta wanda hakan ya hanata tashi daga kanshi, idanunta lumshe tana jin wani abu na ratsata, miƙewa yayi dsga kwanciyar da yake zuwa zama har yanzu hannunshi na riƙe da ita hakan yasa ta kasance a saman cinyarshi fuskarsu na fuskantar juna sai dai idanuwanta na ƙasa, juyawa tayi tana san barin kan cinyar tashi, hannu yasa ya zagayo dasu saman dukiyar fulanin ta a hankali yace "Please karki matsa mijin naki ba zai iya gudu ya kamoki ba!" Yayi maganar cikin dashashiyar murya, waigowa tayi saboda yanayin da take ji yasa duk jikinta ya mutu, cikin wani yanayi yana wasa da hannunshi yace "Kiss me please!" Yawun bakinta ta haɗiya sannan ta matsa tare da kai bakinta saman leɓenshi, wani irin sumbata yake mata wanda yake nuna tsantsar buƙatuwar shi gareta, yana sumbatarta ya sauke rigar da ke jikinta, wani irin numfashi yake fitarwa a hankali ya saukar da bakinshi saman dukiyar fulaninta, nan ta fara sauke wani irin nishi don wani yanayi ta tsinci kanta a ciki mai wuyar fassarawa, kwantar da ita yayi ya mirgina samanta yana sarrafata cikin yanayin da shi kanshi yasan bata cikin hayyacinta, ganin yadda ɗakin ya ɗauki nishin junansu yasa Umm Asghar da Ayusher lallaɓawa suka bar ɗakin wannan abu sirrinsu ne... Kunya ce ta kamata hakan yasa tayi saurin jan bargo ta rufe kanta, Baqeer dake kwance kusa da ita har yanzu yana maida numfashi ya sa kanshi kan wuyanta wanda yasa ta lumshe ido ya sumbata sannan ya rungumota, shigewa jikinshi tayi yasa hannu ya shafi saman kanta, so take ta miƙe ta shiga wanka amma kunya duk ta isheta, wash yace yana ɗan matse ido, hankali a tashe ta juyo tace “Menene? Ko ƙafarka ce?” Ta tambaya ganin abinda ya faru tasan zai iya yiwuwa ƙafar tayi ciwo, kai ya girgiza yana runtse ido, cike da kulawa tace “Menene don Allah?” Hannu yasa ya riƙo gefe da gefe na fuskarta kallonshi tayi yace “Sweetums kin wahalar dani.” Baki ta buɗe ganin gata nan da ƙyar take juyawa amma wai ita ta wahalar dashi bayan shi ya wahalar da ita, gira ya ɗaga mata yace “Ya? Ba haka bane?” Kai ta kauda tana murmushi, rungumota yayi yace “Murmushin me kika yi?” Har yanzu tana murmushi tace “Hango rayuwata da kai nake yi da alama komai sai an tsokaneni za’aji daɗi.” Ajiyar zuciya yayi yana wani canza yanayin fuska yace “Matsalar kenan, yanzu ya zamu yi? Gashi ni babban burina naga na tsokane ki.” Bakinshi ya kai ya sumbace ta yace “one year da nayi ina jiranki duk sai na fanshe barina da aka yi.” Ya zata yi da Ya Baqeer? Ita sam bata san yaushe ya lalace haka ba, kamar yasan me take cewa sai ji tayi yace “Ni kaina ban sani ba, shi yasa you have to take responsibility don ke ce nan kika maidani haka.” A tare suka saki murmushi yau dai kunyarshi take amma tabbas zata fanshe abinda yake yi mata, kasancewar ƙafarshi ba iya takata zai yi ba dole ita ta sakko da ƙyar don ma ya tafi da ita a hankali bata sha wuya sosai ba, bargon ta yaye ta rufe jikinta dashi, ta barshi anan ta shiga toilet, yana kallon yanayin tafiyarta wanda hakan yasa yaji tausayinta ya kamashi, saukowa yayi ya hau wheelchair ɗin shi, ya kalli bedsheets ɗin da suka ɓata, yaye shi yayi don har ga Allah bai taɓa tantama dama akan Zeey ba, nan yabi bayanta zuwa banɗakin, sam bata kula dashi ba saboda ƙarar ruwan da ke taruwa cikin bathtub, in ta tuna abinda ya faru ɗazu sai tayi murmushi, hannunta taji an janyo an juyo da ita, kallonshi tayi a kunyace tace “Da ka bari na gama.” Kai ya girgiza alamar a’a yace “bayan wahalar dake da nayi ni ya kamata nayi wannan.” Hannu yasa a cikin ruwan har sai da ya haɗu ya mata alama da ta shiga, kai ta girgiza tace “Ka fara shiga in ka gama zan zo.” Ido ya ƙifta ya nuna mata bath ɗin da idonshi, ita kunya take duk da sun zama ɗaya amma bata shirya wanka a gabanshi tun yanzu ba, baki ya buɗe yace “Ba dai har kin fara son round 2 ba?” Ido ta zaro da sauri tace “Allah ni ka daina yi mini haka.” Shima maimaita abinda tace yayi kafin ya ɗora “to in ba haka bane shiga.” Shiga tayi tana runtse ido saboda zafin ruwan da take ji yana ratsata, turo keken shi yayi daf da ita ya janyo shower gel yasa a loofah sannan ya kai hannu jikinta, haka ya dinga romancing ɗinta da kumfar wani irin yana yi take ji wanda bazata iya fassarawa ba, sun daɗe a toilet ɗin bayan ta gama tana neman fita sai cewa yayi wai ƙafarshi in ya shiga bath ba zai iya fitowa da kanshi ba, haka ya shigo yasa ta wanke shi sannan suka buɗe rariyar ruwan ya fita shower ɗin ta ciro ta miƙa mishi akan yayi wankan tsarki nan yace ita zata yi mishi ita dai haka tayi cike da jin kunya tana yi yana kissing ɗinta kafin nan suka fito. **** Wata irin tsaftatacciyar soyayya ce ke gudana tsakanin Zee da Baqeer don dama honeymoon ɗin sati uku ya ɗauka da wata ma yace Salim yace kai Malam sati biyu fa ake yi, yace to shi uku zai yi. Yau tana kitchen tana haɗa breakfast, tunani take yi da ace ada tayi aure lallai da zaman gidan Baqeer bai mata daɗi ba tunda lokacin babu abinda ta iya, potato omelette tayi da stir fry na beef, daga cikin ɗaki taji yana kiranta “Sweetums!” Yadda ya ke kiran ne yasa ta nufi ɗakin da sauri bayan ta rage gas ɗin, a zaune ta ganshi akan gado yana ganinta ya ɗaga mata gira yace “Ba morning breakfast?” “Yanzu nake yi wai na ɗauka bacci mafa kake yi?” Turo kekenshi yayi yazo inda take yace “Bafa wannan ba breakfast ɗin dana fi so.” Dariya ta ɗan yi tace “Ka fito ga Baba nan yazo ku gaisa.” Ido ya zaro yace “Da safen nan?” Tace “Eh shi yasa nake ta sauri nama ɗauka kaji zuwan nashi ne.” Yanayinshi ne ya canza, tayi mishi gwalo, ƙwafa yayi yace “Ai dai gobe ba zuwa zai yi ba.” Tace “Ina ka sani kila ma kaga Kabir ko Bashir.” Gira ya haɗe yace “Matsalar fa zama kusa da unguwar dangi kenan, gaskiya we need to move.” Tare suka fito ga mamakinshi ba kowa a falon, kallonta yayi ta kwashe da dariya tace “Baba ina kwana?” Fuska ya tamke sosai ta sake yi mishi gwalo tace “1-0.” Kai ya jinjina yace “Kai? Lallai dole na fanshe,” yayi maganar yana neman kamota, da gudu tayi kitchen yabi bayanta da kallo yana murmushi. ** Kamalu yau za’a sakeshi don haka ana yi mishi waya yace zai zo da kanshi, yafi son yaje da kanshi ya ɗauke shi ya kawoshi gidanshi yayi mishi faɗa sosai kafin ya maidashi gida, haka ya cewa Zainab zai fita zai dawo da baƙo, kafin ya fita shi ya ɗan tayata yanke-yanke sannan ya shirya Tanimu yazo suka fita. Kamalu duk ya canza ya rame fuskar nan duk ta motse saboda wahalar gidan yari, ganin Baqeer yasa ya fara sum sum da kai, nan Baqeer yace ya shiga mota su tafi, a mota basu yi magana ba don baya son ko Tanimu yaji abinda ke faruwa, Zee tana ɗaki sanda suka iso, tayi kwalliya cikin lace wanda aka yi mata ɗinkin buba, tayi kyau sosai bata yi wani kwalliya ba sai ɗan kwalli data sa a idonta ɗaurin Zarah Buhari tayi, tunda Kamalu ya shigo yake bin gidan da kallo, wai gidan Baqeer? Ina ma shine? Haka suka shiga gashi an zubawa Zee tsadaddun furnitures wanda suka ƙara gyara gidan, fitowa tayi bayan Baqeer ya kirata, idanun Kamalu ne suka sauka kan hotonsu dake manne a bangon falon idanunshi ne ko kuwa mai kama da ita ne yake gani? Matar da yake ta mafarkinta a gidan yari har duka yaci akanta ranar da ya fara mafarkin aurensu ashe wani gardi ne a kusa dashi ya fara ƙoƙarin manna mishi kiss ai kuwa ya zabga mishi mari ya rufeshi da duka, inaa mafarki yake yi, kalaman Baqeer ne ya katseshi jin yace “Sweetums da kanki? Ai kawai kice Habiby zo ka ɗauki tray ɗin nan.” Kamalu ne ya juya idanunshi suka sauka akan Roshini, ƙamewa yayi a zaune don ji yayi kamar an zare komai na jikinshi har tayi mishi magana ma bai ji ba sai da Baqeer yace “Kamalu?” Ido ya ƙifta ya haɗiyi yawu kawai ya miƙe da sauri yace “Baqeer bari naje gida.” Kallonshi yayi yace “Menene?” Zainab da yake ta san me yake sai ji yayi tace “Ka zauna mana ai gidan wanka ne.” Kallonta yayi yana ji kamar ya saki kuka, fitowa yayi cikin sauri don sam bai kula ma takalmi daban daban ya saka ba ɗaya nashi ɗaya na Baqeer haka ya fito ya nufi gida, kawai a hanya sai ji yayi hawaye ya zubo mishi, har ga Allah duk ƙaunar da yake yiwa Zee ashe amanarshi zata ci ta auri Baqeer? Abu tana ganinshi ta saki ihu duk ta rikice saboda murna, shi dai komai na rayuwa ya tsaya mishi. Baqeer da kanshi yazo gidan ya sashi a ɗaki yayi mishi faɗa sannan yace “Zai sake zuba kaya shagon Baba in yaso ya dinga zama, don Kamalu bai yi karatu ba sannan Baba kaɗai ne zai iya sa mishi ido akan lamarinshi. **** Kwanaki sun shude rayuwa ta canza abubuwa da dama sun sauya, ciki kuwa har da Mummy wacce yanzu ta canza gaba ɗaya, to babu ma yalwar arzikin da zai sa ta yin bushasha sai dai rufin asiri da suke dashi ko fita ba tayi in ba da dalili ba, Kabir yayi aure yasa matarshi anan gidan ɓangaren su shi da Zainab da Nabila ya kasance ɓangaren shi da matarshi yanzu, matar yar boko ce don likitace, ita tasa Kabir ya maida hankali ya koma makaranta yin masters ɗinshi don da wasa da son harkar chilling da abokai ya hanashi maida hankali ya cigaba. Aurenta yasa abubuwan Daddy sun sake zuwa musu da sauki don yawanci treatment ɗin da bashi da wuya a gida take yi mishi. Inna kuwa ta je ƙasarsu sai dai yawanci mutanen da suka bari sun rasu haka dai suka nemi yafiyar wanda suka samu sannan ta dawo, Nabila kuwa ta samu wani mai madaidaicin ƙarfi ta aura a cikin samarinta da taƙi kulawa saboda Kabir sai da taga da gaske fa Kabir ba aurenta zai yi ba sannan ta haƙura ta fitar da miji tayi aure, balle da taga matar da Kabir ɗin ya aura tasan lallai yayi mata nisa. Dada kuwa jikin tsufa yau lafiya gobe ciwo hakan yasa Zainab ta dawo da ita nan wurinsu wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Baqeer ba, Umma taso ta ɗauketa sai dai tasan zaman gidan ba zai yiwa Dada daɗi ba, shima yana ta ƙoƙari akan ƙafafunshi wanda yake fatan nan gaba zasu warke don har yanzu baya iya tafiya dasu da wheelchair yake amfani. Shago kuwa sai dai ace masha Allah don kuwa har sun buɗe wani branch a Kaduna inda Tanimu ya koma can da zama shi kuma Baqeer ya ɗauki driver in kuma da Zainab ne sai su fita tare, Baqeer yaso ta fara aiki don baya son tauye mata hakki sai dai ta nuna ba yanzu ba gani take yi bai kamata su bar Dada ba sannan tana ganin Baqeer na buƙatarta sosai ya zai yi in ya dawo gida bata nan? Wannan dalilin yasa shima bai matsa ba don haka sai ta fara business ɗin shigowa da unique fabrics masu kyau Baqeer na ɗinka ready made daga na mata har na maza, yawanci kayan matan tare suke zama su ƙirƙiri styles ɗin shi kuma sai yayi sketching, na mazan ma takan taya shi ƙirƙirar design ɗin a inda suka gano Zainab is very creative kawai dai bata iya zanen bane, daga haka suka fara designing kaya very unique da idan ba a wurinsu mutum ya saya ba bai isa yaga irin styles ɗin su ba. Watansu shida da aure sai ga Zeey da ciki, murna a wajen waɗannan ma'aurata abun ba'a magana, kusan kowa daya kamata yasan da batun cikin nan sun faɗa mishi don yadda suke ta ɗoki da murna, ita dai Umma sai dai ta kallesu ta girgiza kai idan taga yadda suke giringiɗishi da rawar kai akan cikin. Haka suka yi ta rainon cikin su cikin kwanciyar hankali kuma inda Allah ya taimaki Zeey bata yin wani laulayi sai ɗan abinda ba'a rasa ba. ***** Asiya da Bello na zaune a layin ganin likita sun kawo ɗansu da baya da lafiya. Kallon asibitin Bello yake yi yana jinjina ta yadda zai fara biyan kuɗin asibitin gashi tun ba'a je ko ina ba ɗan abinda ya riƙo ya tafi a wajen buɗe folder. Tsaki ya saki yana jin takaicin nurse ɗin data turo su wannan asibitin da kana gani kasan na masu hannu da shuni ne. Kallon Asiya yayi yace "wai shi likitan dole sai anan asibitin za'a iya ganinshi ba zai yiwu a ganshi a asibitin gwamnati ba? Nifa bani da kuɗi kin sani daga ganin wannan asibitin kuwa kin san za'a kashe kuɗi." A kaikaice ta kalle shi cikin ranta tana tir da wannan halin rashin babu na Bello, ace wai kuɗin asibitin ɗansu ma sai yayi mita akai kamar shi ya yanke wa talauci cibiya. A daƙile ta amsa mishi da "kana jin dai abinda nurse ɗin tace sai muyi ta zuwa wancan asibitin bamu samu ganin shi ba saboda shine babban likita a wannan ɓangaren in har muna son ganin shi dole dai nan ɗin zamu zo idan kuma kana ganin baka da kuɗi a barshi sai mu koma gida musa yaron a gaba muna kallo har Allah yayi ikon shi akan shi." Bai ƙara cewa komai ba sai wani tsakin daya kuma yi. Kamar ance ɗaga kanka ka gani kawai sai hango Baqeer yayi akan electric wheelchair ɗin shi Zeey na daga gefenshi hannayen su cikin na juna suna fitowa daga cikin asibitin sai murmushi suke yi kana ganin su kasan basu da wata damuwa a rayuwa. Hannu yasa ya mutsitsika idon shi sai dai tabbas Baqeer ne yake gani, gaba ɗaya ya canja ya zama babban mutum kana ganin shi kaga wanda hutu ya zauna a jikin shi, ga matarshi da nesa ba kusa ba ta kerewa Asiya a komai. Juyawa yayi ya kalleta sai yaga itama ashe su take kallo idanunta sun tara ƙwallar ɓakin ciki, kaico da dana sani dafa yanzu itace kusa dashi. Tabbas ba ƙaramar asara ta tafka ba da barin Baqeer data yi gashi tun ba'a je ko ina ba Allah yayi mishi sakayya, ita ta guje shi saboda ya gurgunce sai gashi ya samu matar data fita a komai, Bellon data komawa gashi nan yanzu baya da komai sai kame-kamen rayuwa suke yi, tasan a yanzu Baqeer yayi mata nisan da har abada bata isa ta kamoshi ba. Shima Bello a cikin ranshi yana jinjina yadda yau Allah ya mayar da Baqeer bayan duk abinda yayi mishi, yasan da ace bai butulcewa Baqeer ba da yanzu wannan arziƙin dashi za'a ci don duk wani alheri da Baqeer ya samu a rayuwa shine mutum na farko da yake fara janyowa ciki amma shine yayi mishi halin ƴan adam ya munafurce shi ya guje mishi a lokacin da yafi buƙatar kasancewar shi a tare dashi, yayi watsi da abotar shekara da shekaru son zuciya da kwaɗayi suka rinjaye shi ya aikata cin amana mafi muni ga abokin shi gashi nan yanzu inda rayuwa ta kawo shi, Asiyar da yake ganin kamar ita ce koma shi yayi mishi ƙwacenta ta zame mishi ƙarfen ƙafa don a yanzu dai da suka fara tara zuri'a bai isa yace zai yakice ta ba bayan haka ma wacce mace ce zata yi haƙurin zama dashi da wannan baƙin talaucin da yayi mishi katutu. Kiran sunan ɗansu da aka yi ne ya katse su daga tarin dana sanin da suka tafi suka tashi suka shiga ɗakin ganin likita, waiwayawa Asiya tayi ko zata sake ganinsu sai dai taga wayam babu su babu alamar su don tuni suka fice daga cikin asibitin ma. ***** Suna zaune a mota Zeey ce ke tuƙawa shi kuma hannayenshi sun kasa tsayawa waje ɗaya sai tsokano ta yake yi. "For the last time Ya Baqeer ka bari idan dai ba so kake yi na watsar damu ba, tom," tayi mishi maganar a shagwaɓe idanunta na kan titi don bata son abinda zai yi distracting ɗinta daga tuƙin da take yi. Ɗauke hannunshi yayi kamar yadda ta buƙata sai kuma yace "tunda yarinya taga sardeden saurayi ɗan kyakkaywa gaba ɗaya tabi ta sukurkuce ta rasa nutsuwa duk da yake gurgu sai data san yadda tayi ta janyo hankalinshi ya fara sonta sannan hankalinta ya kwanta." Rufe bakinta tayi tana dariya tace "yau kuma nan wurin ka tafi? Ai dai wallahi kasan wuce nan, abinda ma kai ka fara nuna min soyayya a fakaice daga ka ganni a gidan Dada sai ka gurguro kekenka ka wani ajiye mini gift bag har da su kyautar rose flower, sarai kuma kasan me kyautar rose take nufi don haka kai ne ka ganni ka fowler mini har sai da kayi yadda kayi na afka maka shine yanzu zaka zo kana wani zance." "Um um fa Sweetums faɗi gaskiya, tunda kika ga wannan ɗan gurgun kika rasa nutsuwa har sai da kika nemo gidansu sannan hankalinki ya kwanta." Girgiza kanta kawai tayi tace "Allah Ya Baqeer kai ko," "Ni ko gaskiya, ai dai kin san abinda kika yi har ban san lokacin dana fara son ki ba." Wani irin kallo tayi mishi tace "I Love You Ya Baqeer." "I Love You too my Sweetums, Allah ya bar mu tare har tsufan mu." "Ameen," ta amsa tana jin wani irin shauƙi yana ɗibarta. ** Cikin hukuncin Allah Zainab ta haifi ɗanta namiji kyakkywa mai kama da uban shi sak kamar yayi kaki ya ajiye. Murna a wajen ahalinsu abun ba'a magana, ranar suna yaro yaci sunan *SALIM* saboda Baqeer yana ganin hakan kawai zai yi ya nuna mishi tarin matsayin shi a gareshi don Salim ya wuce aboki, ya tashi daga amini sai dai a kira shi da ɗan uwa. Ai kuwa yayi farin ciki sosai har ma ya rasa da bakin da zai yiwa Baqeer godiya shi kuma Baqeer yace komai yayi mishi bai biya shi tarin alkhairin shi a gareshi ba. To muma dai mun ce Allah ya bar zumunci har Aljanna. Suna ta shirye shiyen bikin Salim da Habi, Umma ta samu taje Umara ita da Dada wacce girma ya ƙara kamata, don Hajj tayi tsada sai dai a hankali, Baqeer yace wata shekarar zai biyawa Baba su kuma Jamila da Abu sai a hankali wata rana zai biya musu, yayi ƙoƙari sosai ganin ya haɗe kan ƴan uwanshi wanda suke uba ɗaya, wacce ke takaru ma a Makka ya sata ta dawo gida, Bashir na aiki sosai a wurinshi don ɗinki yake yi, Kamalu kuma an dage da zaman shago duk rawar kan nan an daina, gashi Badaru ya hana a bashi ajiyar kuɗi duk abinda aka siya ɗayan yaron shagon ake bawa. Randa Umma ta dawo daga Umara Jamila da Abu haka suka mata yi girke-girke dukkanin su burinsu su faranta mata ko Baqeer ya fara kai su makka, Maryam kuwa aiki take yi sosai shi yasa yanzu ganinta ya ragu sai dai duk ƙarshen wata suna haɗuwa a wajen Umma, Hadiza ma sana’a sosai take yi na atamfofi da laces wanda  bazata ce komai ba sai hamdallah don rufin asiri kam na abinda zasu ci baya gagararsu. Badaru kam yayi sanyi don faɗa ma ba kasafai zaka ji yana yi ba dama girma yayi kawai dai rashin haƙuri ne da rashin tunani irin nashi a da, amma yanzu ya canza sosai. Baqeer har wannan lokacin ƙafar dai bata takuwa sai dai muna fatan wata rana ya taka ko da sanda ne, zaune suke a kan kujera shida Zainab, hannunshi ɗauke da Salim, ɗaga Salim yayi ya sumbaci goshinshi yace “Sweetums ya zaki yi da baki aureni ba?” Hular dake kanshi ta zare tasa a saman kanta tace “Baby Salim tambayar mana shi ya zai yi idan bai aureni ba?” Kuncinta yaja yace “Bari na tashi na koma.” Dariya tayi tace “Ka gani ko? Ban san ya zaka yi da baka aureni ba kana aiki ka gudo gida don ka ganni.” “Faɗa mini gaskiya addu’a kika yi mini ko?” Dariya sosai take yi yanayinta ne ya canza, wanda hakan yasa yace “What?” Yana ɗan ɗaga gira tace “Love you!” “Love you too!” Baqeer ya faɗa yana kallon Salim ta sani sarai so yake tayi magana murmushi tayi tana jin daɗin rayuwar nan tare da fatan Allah ya barsu tare. *TAMMAT BIHAMDULILLAH* _A nan muka kawo karshen wannan littafi namu mai suna BAQEER, muna roƙon Allah daya yafe mana kura-kuran da muka rubuta a cikinshi, ya kuma yafe muku wanda kuka karanta kuma ya bamu Ikon aiki da duka abubuwan alkhairin dake cikinshi_ _Saƙon gaisuwa na musamman da kuma godiya ga dukkanin waɗanda suka sayi littafinmu na ƴan tagwaye, mun yaba muku kuma mun jinjina muku Allah ya ƙara muku buɗi, lafiya da kuma ɗaukaka, mun gode. Allah ya haɗamu a wata tafiyar cikin aminci_ *ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU*. *BAQEER* Ayusher Muhd Umm Asghar *KURMAN ALLO* Asmy b Aliyu Jidda Aliyu *AKWAI SIRRI* Zee Bawa Hajja ce *MUTALLAB ASAD* Nana Diso Billy S Fari *KULUWA* Zee yabour Sadiya Dan Duka Biyar ɗin akan 2k Hudu 1600 Uku 1200 Biyu 800 Ɗaya 500 VIP💕🔥 Duk guda ɗaya 1k NORMAL GROUP 500 VIP 1000 ACCOUNT NUMBER 0020428430 Ishaq Fatima A. Gtb Or 8098456130 Fatima Ishaq Opay digital services Shaidar biya 08098456130 KATIN MTN Ta👇 07043079282 Shaidar biya ta 07065283730 Ko a tuntubi 08086207764 0816 114 6563 +234 704 040 2435 ‪+234 903 056 9336 *Ayusher Ce* *Da* *Umm Asghar*