ZAINAB https://whatsapp.com/channel/0029Vb7ASdiJ3jv1qnuWHH3U PAGE NA 1 DANA 2 SHA'AWANATU FARUK DIGGI MARUBUCIYA Zamu fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, Allah ya sa yadda na fara wannan littafin Allah ya nuna min gama shi lafiya, Allah ka yafe min kuskure da ke cikin shi. Banyi wannan littafin dan cin zarafin wata/wani ba ko cin fuska. Inayin ko masoya na kuma ina godiya da haɗin kain da kuke bani Allah ya sa ka da alkairi 🙏🙏. 1&2 Wata budurwa ce ke tafiya a natse bata kallon komai face in da take sanya kafafunta, tayi nisa acikin tafiyarta kenan ta tsinkayi muryar wata budurwa na kwala kiran Abuh! Abuh! da jin wannan murya ta budurwar dake kwala kiran Sunan Abuh ko ba,a fada mata ba tasan Halima ce tsayuwar ta da minti uku sai ga Halima ta iso in da take a tsaye. "Haba Abuh yanzun tafiyar ki kika yi bayan kin san ina jiran ki, wallahi ba ki da mutunci kuma ga shi bakida lafiya kuma kice sai kinje school." har ta ga ma mitar ta kyakkyawar budurwar nan da aka kira da Zainab bata tanka mata ba.. Da ga ni dai yarinyar miskila ce😄 chan bayan kamar minti biyu haka ta cigaba da tafiyar ta kamar ba ta ji abunda Halima ke fada ba duk da kuwa tana jinta rass. Da Halima ta ga alamar ba tsayawa za ta yi ba ta ga alamar yan miskillancin sun motsa dole haka ta bita suka cigaba da tafiya a tare har suka iso makarantar . Dukan latti suka tarar a nayi aiko ido ya raina fata dan Zainab akwai tsoron duka. "Assalamualaikum" Malam Rabi'u ne ke dukan latti Zainab rage tsawo . cikin Dan yin ƙasa da kai ta furta acikin zazzakar muryar kamar ana busa sarewa, ko algaitu ga ta da sanyi Wanda in tana magana zakaji har tsikar jikin ka natashi, dan Allah malam ka yi hakuri, da ta furta ne yasanya ni dawo wa da ga sumar tsayen danayi tun lokacin da ta buda baki ta yi sallama. "Zainab kullum ma kara kike yi kuma kinfi kowa tsoron duka." "Wallahi malam da wuri muka fito sai dai muna da nisa ne kamin mu iso." "Toh ba sai ki riƙa hawa machin ba amma kullum sai kin zowa mutum da uzuri, jiya ma haka kika yi nayi miki uzuri toh yau kam sai na ɗiba na ga shi wallahi." Malam dan Allah ka yi hakuri in sha Allah gobe ba zan sake latti ba. "Ashe kina magana ƴar iska ina miki magana kina sharewa dani, ai duka yasaki magana." "Ta romin hanunki ko ki kwanta." Malam ya faɗa Hannunta ba shi bulala goma ya yi mata amma ko a jikinta amma fa taji zafin dukan sosai dan hannunta har kumbura ya yi. Goma ya yiwa Halima tana ihu tana ƙari har aka gama mata. Shigowar wata baƙar mota wulik cikin makarantar shine yaja hankalin mafi yawan ɗaliban. Motar tatsaya daidai wata bishiyar dalbejiya, A yanzu kallo ya koma ne akan Wanda zai fito daga cikin wannan mota mai kyau da ɗaukar hankali. Ƙafarsa yafara zirowa ƙasa maisanye da sauciki na farin takalmi, yakuma zuro ɗayar itama, saikuma yafito gaba ɗayansa. Ajiyar zuciya Halima ta sauke tareda faɗin ya salam!. Ita Zainab batasan wainar da ake toya ba saboda zafin dukan har yanzun bai bar jikinta ba. Kallon Halima ta yi dake kallon wani wajen kamar ta samu T V . "Ke Halima lafiya kike kallon waje ɗaya ko kin samu matsala ne da dukan da malam ya yi miki ne?." Hannu Halima ta yiwa Zainab nuna da abin da take kallo. Kallon can Zainab ta yi wani mutum ta gani a tsaye wajen mota amma bataga komai ba. Jijjigar Halima ta yi sannan Halima ta nuna mata wanda ke tsaye a wajen mota. Farine sosai dogo kuma dankuwa yanada tsayi sosai, kallo ɗaya zaka masa kagane ƙaƙƙarfane saidai bashida ƙiba, ma sha Allahu akwai ƙyawun fuska, gashi kuma ya ƙawata fuskar tasa da saje baƙi siɗik, ya kwanta sai walƙiya yakeyi, sanyake da farar shadda wando da Riga ɗinkin zamani, kayan sun masa ƙyau.... "Mene ne abin kallo a nan aikin banza kawai kin ji haushi dai wallahi." "Ai ke zancewa kinji takaici saboda ni macece dole zan yi magana idan naga abin maganar, bale wannan gaye ɗin Allah ya sa shine Sabon malamin mu." "Ba ameen ba." Aji kowa ya shiga sakamakon ringing da aka yi na shiga Aji. S s one ƴan mata ne sai tsokanar juna suke yi amma mutum ɗaya ce ba ruwan ta da kowa sai karatun ta take yi. "Malam ne ya shigo suka ce good morning Sir?." "How are you students sit down." "I am your new English teacher, God willing, Everyone should take out their book so that we can continue, God willing." Kowa sai kallon shi yake komai yake nufi oho ma sa. "Why are you (all) just looking at me mtsww?." "Sir, please forgive me, I just want to talk (or meet) with you, please.” Sai sannan hankalin shi ya kai kanta. "Where did you stop?." Faɗa ma sa tayi sannan ya ci gaba da aikin shi, har ya gama sai ya tambayi wanda bai gane ba, kowa ya ce bai gane ba harara ya banga masu sannan ya yi tafiyar shi. "Chapp yanzun idan bake ba wallahi ba mai iya ba shi amsa." "Kefa kika ce Allah ya sa yazama malamin ku kuma ga shi nan amma kika yi shiru." "Ai wallahi ni kam kallon shi kawai nake yi, saboda malamin akwai kyau ga sajen nan baƙi, ga hancin nan na shi, wayyo Allah, Allah ya sa ni ce matar shi ko ke." "Ba ameen dan Allah ki barni haka kirki sakamin ciwon kai." Wani malami ne ya shigo daga ganin shi ba malamin kirki bane sai kallon ƴan mata yake yi Musamman Zainab. Ta shi suka yi dan gaida shi amma ya ce su zauna kawai. In da Zainab yazo yana faɗin wannan anyi halitta anan ba Zainab ba har sauran matan sun tsorata da malamin. Halima suman zaune ta yi saboda tsoro sai kallon su yake yana lasan baki sai kace maye. "Malam dan Allah ka yi mana abin da yakawo ka, saboda banga abin kallon mu kana lasan baki ba." Idon da Halima zata ɗaga sai ganin Sir baƙo ta yi yana kallon malamin. "Ke kinfi kowa baki ne harni za ki kalla kina gaya min abin da zanyi." "Zoki yi kama kunnen ki a gaban allu." "Malam ai gaskiya na faɗa kuma wallahi a makarantar nan ba a saka mata kamun kunne." "What is happening here?" Kowa taga ya kalla har shi malamin saboda ba wanda ya ganshi sai halima sai waɗan yake kan tagar su. Shiru ya yi sai daga baya yake cewa "Karatu ne nake masu shine yarinyar nan ke raina min da hankali." "I don’t understand Hausa., speak to me in English." Shiru malamin ya yi ba amsa. Ajin ya shigo ya kalli Zainab yana faɗin "What is your name?." "My name is Zainab Hassan." Faɗa ma sa komai ta yi har kallon ta yake mata da lashe lashen da yake. ZAINAB PAGE 📄 📃 Na Sha'awa marubuciya diggi WhatsApp number 08080304152 3&4 Ringing ɗin cin abinci aka yi dan haka ga baki ɗaya suka fita dan zuwa cin abinci. Zainab.. Zainab dan Allah ki tsaya kiji Please my friend. Tsayawa ta yi amma bata yi magana ba kuma bata juyo ba sai ci gaba da tafiyar ta da ta yi. "Zainab wai me ya sa ba kyada tsoro ne ni wallahi ina tsoron abin da malamin zai miki." "Uhmm komai zai yi bai daman ba kuma Allah yana tare dani." "Wallahi nima Naja'atu shinake tunani dan da gani malamin ɗan iska ne wallahi." Wajen wata dalbejiya suka zauna sai buga zance suke. Shiko yana cikin motar shi yana kallon ɗaliban sai wucewa suke yi. "Zainab ki riƙa saka tsoro a ranki saboda kina da rauni fa, ke macece ba namiji ina jin tsoron ranar da wani zai cutar da ke." "hmmm karki damu da rayuwata saboda bata da amfani, ki damu da rayuwarki kawai, kuma duk abin da Allah bai nufeni da shi ba toh ba wanda ya isa ya sakar min shi." "Haka ne Allah ya sa mu dace ." "Ameen." Duk abin da suke faɗa duk a kunnen shi sosai Zainab ta birge shi saboda jajircewar ta. Ta shi suka yi zuwa Class bin bayan su da kallo ya yi sai da suka ɓacewa ganin shi, sannan ya fito zuwa office. Zainab sai karatu take yi saboda haka duk ta watsar da su Halima da Naja'atu. Wani yazo yana yamutsan fuska shi ala dole mai kuɗi . Gai da shi suka yi sannan kowa ya zauna ya cigaba da abin da zai yi, sai kallon matan ajin yake yi. Haka kawai ya cika allo kuma bai yi bayani ba kawai ya yi tafiyar shi. "Dariya ƴan ajin suka fara yi, su na faɗin waye zai mana bayani. Wani ɗan ajinne ya tashi yana faɗin, "Ke Zainab tashi ki yi mana bayani." "Hahaha rufamin asiri dan Allah ai wannan sai kai ke iya bayanin shi." "Haba Abuh karki ba dani mana, idan ba za ta yi ba ke Halima yi mana bayani ." Toh shi ke nan fita ta yi tana dariya tana faɗin. "Kowa ya fitar da littafin shi test zamu yi dan naga kuna raina min hankali." Wani daga cikin mazan ne ke faɗin. "Hahaha wallahi kin iya maganar shi sosai." "When everyone has published their book, we'll take the test —it's not that you wanted it, right." Aiko kowa kallon window yake yi saboda basu san da mutum a nan ba. "Sorry Sir wallahi bamu shiryawa test Yanzun ba," wani ɗaya daga cikin su ya faɗa. "Okay, please tell me, Sir, when are we going to do it?" "Yi hakuri malam." Ƴan ajin ga baki ɗaya Kowa littafin shi ya fitar a gaban aji suka raga daga su sai takardar su "Zainab, Halima, Naja'atu, da sauran ƴan ajin duk sun tsorata da test ɗinnan da ba shiri Haka kuwa kowa ya yi test ɗinnan amma hannu a gaba dan basu san ko ya yi daidai ba. Ƙarbawa ya fara yi yana kawowa in da Zainab sai da ya ƙalli sunan ta sannan ya haɗe ta da sauran. Tafiya ya yi sai office ɗin shi marks ya fara yi sosai ya yi mamakin ganin Zainab kawai taci 66/70 hakan ya sa ya ce leka a window yaga wata ƴar S S 3 ya ce ta kira ma sa Zainab Hassan S S one. Toh ta faɗa amma ranta na mata ƙuna akan mi zai aiki kiran jiniyar ta tana siniya. Shiga ajin ta yi ta ce "Zainab Hassan ki je in ji Malam Aliyu." Ta ce "waye malam Aliyu?." Uwarki ce ƴar iska daga zuwan malam har kin maƙale ma sa mayya kawai. Sai lokacin ta gane waye Sir Aliyu. Banza ta yi mata kamar ba da ita take yi ba. Ta shi ta yi zowa in da ake kiran nata. "Assalamualaikum" "Waalaikimussalam" Sir na shigo Sai da ya ɗau lokaci sannan ya furta cewa "Eh." Shiga ta yi amma sai ta yi tsaye a bakin ƙofar kuma ta yi shiru sai daga baya ta faɗi "Sir gani ance kana nema na." Shima shirun ya yi ma ta sai da yaɗau lokaci mai tsawo dan har ta fara gajiya. Sannan ya ce "Eh" Shiga ta yi ta yi tsaye tana kallon shi cikin ranta ta ce ma sha Allah, Allah ya yi halitta a nan "Kallona kike tsayawa ko neman kiran da aka yi miki." Saurin faɗan "A a Wallahi." Kujera ya nuna ma ta ya miƙa ma ta ta karda yana faɗin "ki sake rubuta test ɗin ki dan ban yarda da wannan ba." Mamaki take wai dama Sir ya yi Hausa amma yake musu turanci. Zama ta yi tana mamakin me ya sa zata sake rubuta test ɗin. Takardar ta ɗauka ta fara rubutawa. Ido ya zuba ma ta yana kallo Zainab farace sosai dan tafi shi haske, ba doguwa bace sosai amma tana da tsayi, hanci siriri sai kace bairo, tana da tattawar Allah ya gefen bakinta labɓanta jajaje kamar ta yi kwalliya, tana da dimpul ko bata yi dariya,. "Ma sha Allah", ya faɗa bai san ya fito ba. Jin ya yi magana ya sa ta ɗaga kanta dan ta ga me yake yi ta ji yana faɗan ma sha Allah. Kamin ta kalloshi har ya janye idanunsa, sai ta kalle shi bata yi magana ba sai kawai ta ci gaba da rubutun ta. "Malam nagama." Kallon ta ya yi sai ya sake kallon takardar, ya yi mamaki sosai da ganin lallai ba copy ta yi ba. Hmmm kawai ya ce sannan ya ɗauki paper's ya miƙa mata. "Idan kika je ki bawa monintar ɗinku." Ita ko har yanzun mamaki take yi sosai dan bata yi tunanin yana jin hausa har haka ba. "Toh" kawai ta ce. Fita ta yi daga office ɗin wani lafiyayyen ajiyar zuciya ta sauƙe sannan ta tafi ajin su. Shiko yana kallon ta window 🪟 amma haka kawai ya tsinci kanshi da murmushi. Zainab na shiga ajin Naja'atu da Halima suka sakar mata tambaya "Zainab mekikawa Sir ne?, da aiko a kira ki kuma kin jima sosai." "Ba komai fah." "Wallahi bamu yarda ba." "Toh sai kuje ku tambaye shi mana." "Ke dai muke tambaya ba shi ba malama." "Shi ke nan toh." Ringing ta shi daga makaranta a ka yi dan haka suka tashi dan zuwa gida. A hanyar su ta zuwa gida gaban sai bugawa yake yi saboda abin da zata tarar a gida Haba dai Abuh meke damunki ne haka kinyi shiru ki yi hakuri wata rana sai labari . "Ke ni kam ba abin da nake tunani kawai naga ji da surutun ne." Hmmm Amma fa badan sun yarda ba. "Kin san idan Sir baƙo ya ce yana sona wallahi da gudu zan amshi soyayyar shi, malamin akwai kyau ga kuɗi ga jida kai, ilimin boko ilimin addini duk ya haɗe, ni Allah ya sa idan ban zama matar sa ba, ina fatan zainab ta zama matar sa, saboda ina ganin hankalin shi sosai." "Mtsww gaskiya Halima kin cika min kunne da surutu, toh ni ina ruwana da shi ke dai mai son shi Allah yasa ya zama mijinki." Zainab ta faɗa cikin son gajiya da surutun. "Ne dai gaskiya ina son shi wai anya Zainab ke cikakkiyar mace ce, duk mace na son rayuwa da namiji, shima namiji yana son rayuwa da mace, sannan ke kizo kina mana hauka akai." Naja'atu ta faɗa suna taɓawa da Halima. ZAINAB Marubuciya Sha'awa Faruk diggi ✍️ WhatsApp number 080808304152 PAGE NA 5&6 Yamutsa fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce "Eh ni ba mace bace dutse ne, ke ni na faɗa miki ban tashi aure ba yanzun, sai na gama school ko zan maida hankali na kan samari." "Kan ki ake ji kar ma ki yi aure ki zauna haka nan." Rabuwa suka yi saboda gidajen su, suna kallon juna ne, hakan yasa suka rabu. Tana shiga gida ta tarar da wata matashiyar mata zaune wajen murhun wuta sai gumi take yi. "Assalamualaikum" "Waalaikimussalam" "Mama ina wuni ya gida?." "Lafiya ƙalau Abu Mama, ya karatun?." "Lafiya ƙalau Alhamdulillahi." "Toh yau kam baki makara ba ko?." "Tabb wallahi Mama nasha bulala sosai ji hannuna fa", ta faɗa tana nunawa Mamarta ta hannun ta. "Ayya Abuna yi hakuri je ki cire kayan jikinki ki huta." "Mama ai Abba ba zai barni ba." "Je ki kawai ki cire kayan jikinki ki kwanta, idan kika ji sauƙi sai ki fito kamin yadawo." "Toh shi ke nan Mamata, na gode Allah da ya bani ke a matsayin Uwa, Allah ya kare min ke ya ƙara tsaremin ke Mamata." Dariya Mama ke yi saboda ƴarta na bata dariya sosai. "Toh ameen Abuna kema Allah ya tsare min ke da kullimin musulmin Allah gaba ɗaya." "Ameen Mamata." "Allah ya nuna min ranar bikin ki yarinyata." Dariya Zainab ta yi sannan ta shige ɗaki. Kayan jikin ta ta cire tasa kayan zaman gida falle da t shirt ruwa ta ɗiba a bokiti ta shiga bayan gidan. Wanka ta yi sannan ta yi alwala, ɗakin ta shiga ta gabar da Sallar, kwanciya ta yi sai bacci. "Wai har yanzun wannan ƴar iskar yarinyar bata dawo gidan nan ba, kuma na faɗa miki ta daina zuwa wannan karatun dan ba amfanin da zai yi mata." "Haba Abban Abu yanzun da kan ka zaka shigo cikin gida ba tare da ka yi sallama ba, idan yaranka suka gani kuma fa suka ɗauka mai zaka ce musu?." "Wallahi Zara'u ki fita idona ya rufe ko yanzun naci mutuncin ki anan, ta fito idan ta dawo ko naje har makarantar na dauko ta." "Dan Allah ka bar yarinyar ta huta haba dan Allah, yarinyar ka ce dai ko baka so wallahi." Zainab surutun ta ji ya yi yawa hakan ya sa ta fito dan jin meke faruwa ganin Abban ta ne ya sa ta ganewa abin da ke faruwa hakan ya sa ta ce "Abba ina wuni ya kasuwa?." "Idan ban wuni ba za ki ganni anan ne, dan uwarki wace ki ɗebo ruwa kizo ki a jiye min kayan gwari na a titi." "Toh Abba Amma islamiyya fa da ƙarfe huɗu ake zuwa." "Kinci ƙaniyarki wuce ki je ɗebo ruwan, kuma wallahi idan kika gama baki je in da nace ba sai kin bar gidan nan." "Yi hakuri Abba zanje yanzun." Harara kawai ya watsa mata ya yi tafiyar shi waje. "Kenan yau ba zuwa islamiyya ko?." "Toh Mama kin ji abin da Abba ya ce dole zanyi hakuri da zuwa islamiyyar." "Shi ke nan Allah ya yi miki albarka Abuna." "Ameen ya rabbin alamina." Tashi ta ɗauki bokiti dan zuwa ɗiban ruwan . Tana tafiya tana hawaye ga yunwar da take ji kuma ga rashin zuwa islamiyya, sannan ga shi tanajin zazzaɓi sakamakon dukan ɗazun. Acikin tafiyar ta ji ana kiran "Abur Mama dan Allah tsaya ki ji." Tsawa ta yi dan ganin mai kiranta wani mutum ne baƙi ne sosai ga ƙaton ciki, shima kanshi ƙato ne. "Haba Abu mama tun ɗazun na ke kiranki fa amma kin share ni." "Ayya yi hakuri ban ji bane meke tafe da kai sauri nake zanje ɗebo ruwane." "Ah toh muje na rakaki ko?." "A a a na gode sosai ba na buƙatar hakan." "Saboda mi kika ce haka babyna nifa wallahi son ki na ke da gaske idan kin yarda dan Allah karki ce min a a." "Nima ina sonka amma irin soyayyar ɗan uwa musulmi." "Ta masoya fa?" Ya tambaya. "Gaskiya ka yi hakuri amma ni ban tashi yin aure yanzun ba." "Toh shi ke nan zan jira ki har lokacin da kika tashi." "No bazan yi aure ba nake nufi." "Saboda mi a haka za ki zauna ba aure." "Eh", ta faɗa cikin gajiya da surutun nasa. "Amma... Bata bari yaƙara sa maganar ba da dakatar da shi. "Ka yi hakuri ruwa zan ɗebo sai anjima. Tafiya ta yi sai rafi wani ƙayatacce wuri ne, ruwan farare tas sai wasu tsirrai ƙanana, ƙanana gwanin kyau, sai ma ka ganshi. Tsayawa ta yi na wasu lokuta sannan ta ɗebo ruwan ta bar rafin . A hanyar ta zuwa gida ta ga wasu ƴan mata su biyu . Tsayar da Zainab suka yi su na faɗan . "Dan Allah ke yar wani unguwa ne?." "Ga gidan mu nan." "Ayya kice muna ku sa kenan." "Dayar ta ce "Ga gidan mu muma "Toh." "Za ki biyo mu mu je gidan mu cewar", ƙaramar cikin ƴan matan nan biyu. "A a yanzun ruwa nake jida sai na gama in sha Allah zan zo." "Toh ba damuwa." "Amma baki faɗa min sunan ki ba." "Ayya na manta ban faɗa miki, sunana Khadijah wannan yayata ce, sunan ta Hafsat, saura ke ki faɗa mana sunan ki." "Sunana Zainab." Ta faɗa . "Toh jeki kar na tsaida ki amma anjima zan zo muyi fira." "Toh shi ke nan sai kin zo." Zainab sai da taga ma jidan ruwan sannan taje fitar da kayan gwarin Abba. Tana nan har a ka kira sallar magarib, gida taje ta yi sallah sannan ta dawo, ba ita ta tafi gida ba sai isha'i kamin ta koma gida. Khadijah taje gidan su Zainab sai ƙarfe goma sannan Zainab ta rakata har gida, da yake gida biyu ne tsakanin su. Washe gari Zainab ce ta yi shirin zuwa makaranta tsayawa shan koko ta yi hakan ya sa su Halima suka ri gata fita, "Haba Abu mama yanzun baki shirya ba kike nufi." "So take sai Malam Rabi'u ya sake zane mu." "Gaskiya baki kyauta mana Wallahi kullum sai mun jiraki." "Kai dan Allah ku yi mini shiru ai nima wata rana zan jiraku." "Assalamualaikum." "Waalaikimussalam" "Ina kwana Mama antashi lapiya?." "Lafiya ƙalau wallahi." "Ke yanzun makarantar mu ɗaya kenan." "Eh wallahi Best." "Toh shi ke nan ga ƙawaye na." "Allah sarki ƙawayen mu dai ko? Ya sunan su." "Wacce sunanta Halima wannan kuma Naja'atu." "Allah sarki toh sannun ku." "Kema sannun ki yakike ya gida?." "Lafiya ƙalau Halima." "Toh mu je amma Best ai ba Class ɗinmu ɗaya ba ko?." "Wallahi ban sani amma ni s s one zan shiga." "Laaaa wallahi ajinmu ɗaya dake." "Da gaske kike Halima." "Eh mana." Haka suka ƙarasa makarantar suka tarar da dukan latti. Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, Zainab ta faɗa tana hawaye. "Kai kuzo nan au har na kunsamu cikon ta uku ko?, ku zo nan wai me ya sa kullum sai kun makara ne, ke dai naga kamar ke sabuwa ce a makarantar wuce abin kawai ." "A a malam ba in da zanje na bar Best na sai dai ka dake mu gabaki ɗaya." Suna cikin maganar sai wata mota farace sosai mai shegen kyau. Parking ya yi daidai wajen dalbejiya, ƙafar shi ya fara fitarwa sannan ya fito gaba ɗayan shi, wow Ma sha Allah, sanye yake da riga da wando ɗinkin zamani saddace fara sosai kamar motar shi. Kallon makarantar ya fara yi ko mai yake kallo oho, can ya hango ana dukan mutanen wajen ya dusa, zama ya yi akan kujerar malam Rabi'u, yana kallon ƴan mata da ake duka. "Ke saura ke kawo min hannun ki." "Malam dan Allah ka yi hakuri wallahi bana da lafiya ne, yanzun haka hannuna ciwo yake sakamakon dukan jiya, dan Allah ka yi hakuri." Da ido Aliyu ya bita sai kallon ta yake. "Idan nayiwa wata layin ki ya sake daga ƙasa, kuma wallahi sai na miki bulala sha biyar." Wasu ƴan mata ne su biyu suka shigo su na wani yanga kamar hawainiya wuce wa suka so sai jin magana suka yi. "Kai kuzo nan kunfi ƙarfin kai da mutane, kum "Kai kuzo nan kunfi ƙarfin kai da mutane, kuma kuzo ku tarar da dukan latti amma sai ku tafi." Yana maganar yana duban wani wajen kamar ba ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️ WhatsApp number 0808304152. PAGE NA 7&8 Hankali malam ya kalli ɗaliban, yana ɗan murmushi, amma idonsa na nuna wata irin damuwa da kuma fatan alheri a gare su. Ku sani, ya ci gaba da cewa, "ilimi ba kawai karatu da rubutu ba ne, ilimi haske ne, amma tarbiyya ita ce fitilar da ke kare wancan hasken daga shuɗewa, idan kana da ilimi ba tare da tarbiyya ba, kamar kana da wuta ne a cikin iska; duk da hasken ta, sai ta ɓace." Wani ɗalibi daga baya ya ɗan ɗaga hannu, cikin nutsuwa "Sir in ji shi, amma me yasa wasu masu ilimi suke yin abubuwan da ba su dace ba?." Sir ya ɗan yi shiru na ɗan lokaci, yana kallon ɗalibin da murmushi mai cike da tausayi. Domin sun manta da rabin hanya, ya ce. "Sun dauka ilimi kaɗai zai ishe su, suka bar tarbiyya a baya, amma babu nasara sai an haɗa biyun, kamar yadda na ce: ILIMI + TARBIYYA = NASARA. Ya juya zuwa allo ya rubuta wannan " jimla da manyan haruffa, sannan ya ce: "Wannan ba kawai magana ba ce "Wannan hanya ce ta rayuwa, duk wanda yake son a girmama shi, ya fara da girmama kansa, iyayensa, malamansa, da gaskiya, domin girmamawa tana komawa ga wanda yake bayar da ita." Sai aka sake samun shiru a cikin aji, Amma wannan karon, ba shiru na nadama kawai ba ne, shiru ne na canji a zuciyun wasu, an fara sake tunani, a zuciyar wasu kuma, an fara sabon alƙawari. Daga wannan rana, kalmar “ILIMI + TARBIYYA = NASARA" ta zama tamkar tambari a cikin zuciyoyin su, kalmar da za ta jagorance su har zuwa gobe. Tun daga ranar da Sir ya faɗi kalmar ILIMI + TARBIYYA = NASARA, a cikin zuciyar Sagir, wani sabon abu ya taso. Ba ya gane shi sosai, amma yana jin kamar an kunna wata ƙaramar fitila a cikin zuciyarsa, fitila mai sanyi, amma cike da ƙarfi. Sagir ɗalibi ne mai wayo, amma ya saba yin wasa da malamai, yana da saurin ba’a, yana yin dariya da ƙasƙantar da waɗanda ba su iya kamar shi, Sai dai tun ranar, kowanne lokaci da zai yi irin waɗannan abubuwan, sai maganar malam ta dawo masa a kunne: Duk wanda yake son a girmama shi gobe, ya koyi girmama kansa da malaminsa yau..." Ranar Juma’a bayan sallah, ya tsaya a bakin ɗakin karatu, Malam Haruna yana share tebur, yana shirin rufewa Sagir ya tsaya gefe, yana kallon shi cikin shiru. A da, da ya gan shi haka, sai ya yi wasa da shi, ko ya yi dariya da muryarsa, amma wannan karon, sai kawai ya ce da nutsuwa: "Malam ina iya taimaka maka?." Malam Haruna ya ɗaga kai cikin mamaki. "Ka taimake ni?, in ji shi da murmushi. toh Sagir ka ban mamaki ne yau." Sagir ya yi dariya kaɗan, yana shafa kai "A’a malam kawai… ina so in koyi yadda ake girmama, da farko zan fara da kai." Malam Haruna ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ɗan dafa kafaɗarsa "Ka fara hanya, Sagir idan ka ci gaba da haka, ka riga ka zama abin koyi." Daga wannan rana, Sagir ya canza Ya fara zuwa makaranta da wuri, yana gaishe da malamai da ladabi, yana taimaka wa ƙanana. A hankali, sauran ɗalibai suka fara lura da shi. Wasu suna mamaki, wasu suna dariya, amma daga baya, wasu suka fara koyi da shi. Malam Haruna kuwa, a kowane lokaci da yake kallon Sagir, sai yake murmushi, murmushin wanda yake ganin amsar addu’arsa a zahiri. Zainab ta ƙara natsuwa sosai, dama can ma tana da hankali da miskilanci, yanzu kam wannan halin nata ya ƙara fitowa fili, idan tana cikin mutane, bata yin yawan magana sai dai idan ta ga ya zama dole, amma duk lokacin da ta buɗe baki, mutane sai su tsaya suna sauraro, saboda kalamanta na cike da hikima da hankali. A makaranta, malamai sun fara ɗaukar ta a matsayin abin koyi ga sauran ɗalibai, ko da wani abu ya faru da zai sa wasu su rikice, Zainab takan tsaya da kwanciyar hankali ta yi magana da natsuwa har kowa ya nutsu. Abokanta kuwa suna son zama da ita saboda tana ba su kwarin gwiwa, amma kuma suna jin wani irin girman hali a tare da ita ba girman kai ba, amma irin wanda ke nuna cewa tana da tarbiyya da wayewa. Wata rana a lokacin da ake shirin gasar ilimi ta makaranta, malamai suka zaɓi Zainab ta wakilci aji, duk da cewa ta yi mamaki, ta karɓa cikin tawali’u, tana jin tsoro a ranta, amma ta ce a zuciyarta: "Idan na yi natsuwa, zan iya Allah zai taimake ni." A ranar gasar, duk makarantu sun hallara, Zainab ta tsaya a gaban mutane da kwanciyar hankali, tana amsa tambayoyi cikin hikima da karimci, mutane suka yi mamakin yadda yarinya mai natsuwa haka take da basira sosai. Bayan gasar, sir ne malamanta ya ce: "Zainab natsuwarki ita ce makamin nasararki." Ta saki murmushi, tana mai jin daɗin kalaman malaminta, ta ji kamar kalmarsa ta buɗe wani sabon shafi a rayuwarta, tun daga wannan rana, ta ɗauki kalmar a zuciyarta kamar alamar tunawa duk lokacin da ta fuskanci wata ƙalubale, sai ta tuna da ita: "Natsuwarki ita ce makamin nasararki." A kwanaki masu zuwa, makarantar su ta cika da labarin yadda Zainab ta yi fice a gasar, wasu dalibai suka fara neman shawarar ta, wasu kuma suka fara kallonta da sabon girmamawa amma ba ta bari wannan ya girgiza ta ba, har yanzu tana tafiya a hankali, tana yin komai da tunani da nutsuwa. Wata rana, ana shirin gasar jihohi, malaminta ya kira ta ofis dinsa, "Zainab," in ji shi, yana dubanta da murmushi mai cike da alfahari, "muna son ki wakilci makarantar mu a gasar jihohi, na san ba zai zama sauƙi ba, amma na yarda da ke." Zainab ta ɗaga kai cikin ladabi. "In sha Allah, malam zan yi ƙoƙari ba don in burge kowa ba, sai don in nuna cewa ilimi da natsuwa suna da ƙima." Malam ya gyada kai. "Haka nake so in ji, kada ki manta, nasara ba kawai samun lambar yabo ba ce, nasara ita ce yadda mutum yake tafiya da kima har zuwa ƙarshe." Daga wannan lokaci, Zainab ta fara shirye-shiryen gasar jihohi da ƙwazo, ta rika tashi da safe, tana nazari, tana karatu da kulawa duk da cewa wasu lokuta tana gajiya, amma kullum kalmar malaminta tana maimaituwa a zuciyarta. "Natsuwarki ita ce makamin nasararki." Ta ci gaba da tashi da wuri kowace safiya, tana tsara jadawalin karatunta da kyau, duk da gajiyar da take ji a wasu lokuta, zuciyarta ta kasance cike da kwarin gwiwa, kalmar malaminta, "Natsuwarki ita ce makamin nasararki,” tana ta buga a zuciyarta kamar wani ƙararrawa, tana tunatar da ita cewa duk wani ƙoƙari da za ta yi cikin nutsuwa da hankali zai kai ta ga burinta. Rana ta zo da gasar jihohi ta fara, Zainab ta shiga cikin ɗakin gasar da fuska mai nutsuwa da tsari yayin da ake rabon takardu da tambayoyi, duk wani sautin damuwa ya kau daga zuciyarta; ta mayar da hankali ga kowace tambaya, tana amfani da ilimin da ta tara da kuma dabarun da ta koya wajen tsara amsoshi cikin hankali. Bayan wasu mintuna da suka yi tsawo, lokacin amsa tambayoyi ya wuce, Zainab ta fita daga ɗakin da zuciyarta tana ta bugawa da jin dadi, ba tare da sanin sakamakon ba, amma tana da tabbacin cewa ta yi iya ƙoƙarinta, abokanta sun lura da bambanci a gareta kwanciyar hankali da tsari sun bayyana a dukkan matakan da ta ɗauka. Da safe na gaba, lokacin da sakamakon ya fito, sun bayyana cewa Zainab ta yi fice a gasar, ta samu matsayi mai girma a tsakanin ɗaliban jihohi, amma mafi muhimmanci ga Zainab, ba wai nasara ce kawai ba, har ma da yadda ta koyi muhimmancin natsuwa, jajircewa, da tsarin rayuwa ta fahimci cewa nasara ba ta tsaya kawai a ga sakamako ba, amma a cikin yadda mutum ya shirya kansa da yadda yake tunkarar kalubale cikin nutsuwa. Daga wannan rana, Zainab ta ƙara ƙwazo wajen ilimi, amma yanzu ta fahimci cewa natsuwa ita ce ainihin makamin da zai jagorance ta ga duk wani buri da take so ta cimma. Tun daga wannan rana, Zainab ta fara tsara rayuwarta cikin tsari da hankali, Kowace rana, tana ware lokaci don karatu, nazari, da kuma tunani mai zurfi ta fahimci cewa ba kawai ƙwazo kadai yake kawo nasara ba, har ma da hakuri da daidaito a cikin dukkan ayyukanta. A lokacin da take fuskantar ƙalubale, maimakon ta yi saurin firgita ko jin haushi, sai ta ɗauki lokaci tana nazarin yadda zata magance matsalar da hikima, wannan sabon fahimta ya sa ta fara samun sakamako mai kyau a makaranta, har ma wasu malamanta suka fara lura da bambancinta. Zainab ta kuma gane cewa natsuwa ba wai kawai tana taimaka mata wajen cimma burinta bane, har ma tana kawo mata kwanciyar hankali a zuciyarta duk lokacin da ta ji damuwa ko fargaba, sai ta ɗauki numfashi a hankali, ta tuna cewa komai yana da lokacin sa, kuma duk abin da ta sanya a ranka da zuciya mai tsabta zai kai ta ga nasara. A hankali, rayuwarta ta fara canzawa daga tsoro da rashin tabbas zuwa kwarin gwiwa da kwanciyar hankali. Kuma a cikin wannan sabon yanayi, Zainab ta fara ganin burinta na dogon lokaci a matsayin abu mai yiwuwa, wanda kawai natsuwa da jajircewa zasu iya kai ta wurin. Bayan wasu watanni na aiki tukuru da natsuwa, Zainab ta samu damar shiga gasar ƙasa-ƙasa ta ilimi wadda za ta tantance ilimi da basira a tsakanin ɗalibai masu hazaka daga ko’ina, a lokacin da ta fara shirye-shiryen gasar, zuciyarta ta ɗan firgita tun tana da ra’ayin cewa wannan gasar zata zama babban gwaji na ƙarfin zuciya da hankalinta. Amma yanzu, tare da fahimtar cewa natsuwa ita ce makamin da zai jagorance ta, Zainab ta fara tsara shirin ta cikin hankali a raba karatun ta zuwa ka shi-ka shi, tana nazarin kowanne fanni cikin zurfi, amma kuma tana ɗaukar lokaci don hutu da tunani mai zurfi, ta koya yadda za ta sarrafa damuwa yayin gasa, da yadda za ta mayar da hankali a lokacin da matsaloli suka taso. Ranar gasar ta zo, kuma Zainab ta shiga dakin gasa da zuciya mai kwanciyar hankali, duk da cewa wasu ‘yan takara sun yi saurin firgita, Zainab ta tsaya a kan dabarunta: natsuwa, tsari, da tunani mai zurfi, lokacin da aka fara tambayoyi masu wahala, ta yi amfani da duk abin da ta koya, tana mai da hankali kan kowanne bayani. A ƙarshe, sakamakon gasar ya bayyana: Zainab ta yi fice sosai, har ta lashe kyautar farko a fannin da ta fi kwarewa. Amma abin da ya fi muhimmanci ga ita shi ne: ta gane cewa nasara ba kawai sakamakon ƙwazo bane, har ma sakamakon natsuwa, hakuri, da daidaito a cikin kowanne mataki na rayuwa. Kuyi hakuri zakuga na juye Sir a matsayin malam ai duk ɗaya ne kun sani. ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️ WhatsApp number 08080304152 PAGE NA 9&10 Bayan gasar, Zainab ta zauna a bakin taga tana kallon yadda rana ke faduwa a hankali. Iskar sanyi ta taso tana kadawa cikin gashin kanta, tana tunanin duk abin da ya faru, ba don kyautar ba take farin ciki sosai, sai don yadda ta samu nutsuwa da kwarin gwiwa a kanta. A baya, ta kan ji tsoro idan aka ambaci kalmar gasa tsoron kuskure, tsoron faduwa, da tsoron a raina abin da take yi. Amma yanzu ta gane cewa tsoro ba abokin gaba bane, sai dai jarabawa ce da ke nuna irin ƙarfin zuciya da mutum yake da shi. Washegari a makaranta, Malam Sir ya kirata zuwa ofishinsa. Da fara’a a fuskarsa, ya dubeta yace: "Zainab, na san cewa wannan nasarar taki ba ta zo ne kawai saboda kin yi karatu sosai ba, amma saboda yadda kika sarrafa lokacinki da tunaninki, wannan ita ce hanyar da ake gina shugabanni.” Zainab ta sunkuyar da kai cikin kunya amma zuciyarta cike take da godiya, "Na gode Malam," ta ce cikin nutsuwa. "Abin da kuka koya mana game da natsuwa da gaskiya shi ne ya taimake ni. Malam Sir ya murmusa, ya daga hannu kamar yana son ya nuna mata wani abu mai muhimmanci. "Ki tuna wannan, Zainab: nasara tana fara ne daga cikin zuciya, Idan zuciyarki ta yarda da abin da kike yi, duniya za ta yarda da ke." A lokacin ne Zainab ta yanke shawara wannan nasarar ba ta ƙarshe ba ce, ita ce farkon sabon babi a rayuwarta, za ta ci gaba da ƙoƙari, ba don kyauta ko yabo ba, amma don ta zama mafi kyawun sigar kanta. Bayan nasarar gasar ta wuce, makaranta ta ci gaba da tafiya kamar yadda aka saba, amma rayuwar Zainab ta fara ɗaukar sabon salo, Mutane da yawa suna kallonta da wani sabon kallo wasu suna yaba mata, wasu kuma suna ganin tana jin kai. A cikin ajin su, akwai wata sabuwar daliba da aka canja daga wata makaranta, sunanta Maryam, Maryam tana da hazaka, mai magana, kuma tana da halin da ke sa mutane son zama tare da ita. La, kowa yana son ta, har ma da malamai, A hankali, mutane suka fara daina ambaton Zainab sosai sun fara kallon Maryam a matsayin "sabuwar tauraruwa." A farkon makonni, Zainab ta yi kamar ba ta damu ba, amma daga baya ta fara jin wani sanyi a zuciyarta. "Ko dai suna mantawa da ni ne?” ta kan tambayi kanta a lokacin da take zaune ita kaɗai bayan ajin. Rana guda, Malam Sir ya shigo ajin yana sanar da wani sabon shiri: "Za mu shirya wata gasa ta hadin kai kungiyoyi biyu za su hada kai su tsara wani aikin kimiyya, Kowane rukuni zai zabi shugaba." Da zarar aka raba rukuni-rukuni, Zainab da Maryam suka fada cikin rukuni guda, dukan su biyu an fi ganin su da cancantar jagoranci, kowa yana jira ganin wace za a zaba shugaba. Sai ɗaliban suka fara tattaunawa wasu suna cewa Zainab ta cancanta saboda ta riga ta nuna bajinta, wasu kuma suna cewa Maryam ta fi iya magana da jawo mutane. Zainab ta zauna shiru, tana jin maganganun a zuciyarta kamar iska mai sanyi, Amma a wannan lokacin, ta tuna da abin da Malam Sir ya faɗa mata: "Nasara tana fara ne daga cikin zuciya." Ta numfasa a hankali, sannan ta miƙe ta ce da tawagarsu: "Ba lallai ne ni in zama shugaba ba, Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu haɗa kai mu yi abin da zai burge duniya." Maryam ta kalleta, ta ɗan yi mamaki, a karon farko, ta ga irin natsuwar da ke cikin Zainab ba ta fito daga girman kai ba, sai gaskiya. Daga wannan rana, suka fara aiki tare kuma duk da bambancin halayensu, suka fara fahimtar juna, a hankali, soyayya ta abota ta fara girma tsakanin su. Wai ina Halima da Naja'atu ne kubibiye ni dan jin sona ina ne. "Hali me kin san meke damuna a yanzun?." "A a sai kin faɗa." "Abba yasaka ni a gaba wai aure zai min da wani yaron abokin shi, amma ni kam yaron bai min gaskiya, kuma bana son shi." "Ki yi hakuri, ki yiwa iyayen ki biyayya karki saɓa ma sa, ki barshi ya yi duk yanda zai yi da ke kin ji Abu mama." "Wallahi hali ba ki fahimci ni ba ne ina son yin karatu sosai amma ina ga kamar ba zai yiwu ba." "Karki sare Abu Mama in sha Allah za ki yi karatu sosai." "Ke Naja, ba za ki ce komai ba ne, kin bar mu sai zuba muke kina kallon bakin mu." Zainab ta faɗa tana kai mata duka. "Yi hakuri Abu Mama wallahi abin ne ke bani mamaki sai ka ce ba shi ya haife ki ba." Abu Mama ta kalli Naja, da idanu cike da mamaki. "Zainab! Me ya sa za ki faɗi haka? Kin san kalmar da kika faɗa kuwa?" Naja ta ja bakinta, ta yi kamar za ta ce wani abu amma ta kasa, Sai ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. Halima kuwa ta tsaya tana kallon su biyu, zuciyarta na bugawa da ƙarfi, "Sai ka ce ba shi ya haife ki ba... ” kalmar Zainab tana maimaituwa a cikin kunnuwanta kamar amo. Halima ta share hancinta da ɗan ragi, ta ja numfashi, “Ku daina wannan maganar, Kowa ya ta shi muje Class ni ban so fitina a wannan makarantar." Tafiya ta fara yi, da ƙafafunta da suka yi nauyi, Naja ta bi bayanta da ido, sai ta ɗago kai ta dubi Zainab, wadda har yanzu ke tsaye tana murza hannayenta. "Naja, me kike nufi da maganar da kika faɗa?" ta tambaya a hankali, muryarta na rawa. Naja ta ɗaga kai, ta dubeta kai tsaye, "Ni ma ban sani ba Zainab, na ji ne kawai ana cewa... ai ke ba ‘yar Abba bace, amma ban san gaskiyar maganar ba, wallahi." Zuciyar Zainab ta yi wani irin tsalle, Tuni ta ji wani abu ya tsaya a maƙogwaro, "Waye ya faɗa miki haka?" ta tambaya, murya na rawa sosai. Naja ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce, “Na ji Baba Lawan yana faɗawa uwata da dare. Amma suka ce kar in faɗa miki." Zainab ta ji kamar ƙasa ta buɗe ta shige, Idanuwanta suka cika da hawaye, amma ta daure, ta miƙe, ta ɗauki jakarta ta tafi Class cikin sauri. Naja ta bita da ido, ta furta a hankali, "Allah ya kyauta..." A waje, iska tana kadawa, rana ta dushe, Zainab ta tsaya a bakin ƙofar gida, ta kalli sama. "Allah ka nuna min gaskiya, ko ni ce ba ‘yar gidan nan ba, ka bani ikon sanin wacece ni." Ta share hawaye, ta nufi in da ta san zata samu amsar tambayoyinta gidan tsohuwa Hajiya Lantana, uwa ga mahaifin da ake kira Abba. Ita ce kawai mai riƙe da sirrin da babu wanda ke iya faɗa. Tafiyarta daga wannan rana ta buɗe mata ƙofa zuwa wani ɓangare na rayuwa da bata taɓa tsammani ba ɓangaren da zai nuna mata wacece ita a gaske, da kuma dalilin da yasa ake son a rufe gaskiyar. Yamma ta yi, rana ta fāɗi, Iskar ƙasar Arewa tana kadawa a hankali, tana ɗauke da ƙanshin ƙasa bayan ruwa, Zainab ta yi tafiya cikin nutsuwa tana nufar gidan tsohuwa Hajiya Lantana. Gidan tsohuwar yana bakin unguwa, tsohon gida ne da katanga mai tsawo da ƙofar ƙarfe wadda ake buɗewa da ƙara, Ta turo ƙofar a hankali, tana cewa: "Assalamu alaikum..." Muryar tsohuwa ta ji daga ciki, mai rauni amma cike da nutsuwa, "Wa alaikumus salam, ke ce Zainab? Zo ciki "yata." Ta shiga, ta tarar da tsohuwa tana zaune a tabarma, tana ɗinke wani zani, fuskar Hajiya Lantana ta cika da annuri amma akwai wani abu a idanunta, kamar sirrin da ke neman ɓoye gaskiya. Zainab ta durƙusa, ta gaisheta da ladabi. Bayan gaisuwa, ta ce da ƙasa-ƙasa: "Hajiya, akwai magana da nake son tambayarki, amma don Allah ki faɗa min gaskiya, na yi alƙawari ba zan faɗa wa kowa ba." Tsohuwa ta tsaya cak, allura ta faɗi daga hannunta, "Magana kuma? Wacce iri ce, Zainab? Naja ta ja numfashi mai nauyi, "Hajiya... gaskiya ne ni ba ƴar Abba bace?" Hajiya Lantana ta ɗago kai a hankali, ta kalleta da ido mai zurfi, a cikin idonta akwai rudani, tsoro, da alhini, "Waye ya faɗa miki haka?" "Naja ce ta faɗa, Ta ce ta ji ana magana da dare..." Hajiya ta sauke numfashi, ta jingina da bango, tsawon lokaci babu wanda ya ce komai, sai ƙarar ƙudan zuma daga waje, Daga baya ta furta da muryar da ta yi rauni sosai: "Zainab... gaskiya tana da nauyi, kuma ba kowa ne yake iya ɗauka ba." Zainab ta matsa kusa da ita. "Don Allah ki faɗa min, Hajiya Zan iya jure komai." Tsohuwa ta rufe fuskarta da tafin hannunta, hawaye suka fara fita a hankali. "Kin tabbata kina son ji?" "Eh, Hajiya zan jure." Hajiya ta ɗago kai, ta ce da murya mai sanyi: "Abbanki... ba shi ne mahaifinki ba, amma ba laifinsa bane, Ki sani, ya yi miki alheri da kauna fiye da yadda mahaifinki na gaskiya zai iya yi." Zainab ta ji jikinta ya yi sanyi. "To... waye mahaifina, Hajiya?" Hajiya ta girgiza kai, tana share hawaye. "Wannan labari ne mai tsawo, Zainab amma zan faɗa miki a hankali... Mahaifinki yana da alaƙa da sirrin da iyayenki suka daɗe suna ɓoyewa,Kuma akwai wanda zai iya yin komai don wannan gaskiyar ta ƙara ɓoye." Zainab ta durƙusa gaba ɗaya, zuciyarta na tsalle. "Don Allah Hajiya, kar ki ɓoye min, Ina so in san wacece ni a gaske." Tsohuwa ta kalleta, sannan ta furta suna da ya ɗauki hankalin Zainab gaba ɗaya... "Sunan mahaifinki... Malam Faruk Abdulrahman." Zainab ta ɗaga kai da mamaki. "Faruk? Wane Faruk?" Tsohuwa ta ɗauki hoton da ke gefenta hoton saurayi cikin farin kaya, yana murmushi ta mika mata. "Wannan ne... shi ne wanda duniya ta ɗauka ya mutu shekaru goma da suka wuce." Ta ɗauki hoton da hannunta ke rawa. "Mutuwa?" Tsohuwa ta gyada kai. "Amma gaskiyar ba haka ba ne, Ya ɓace ne saboda wani abu da Abbanki da wasu mutane suka ɓoye." Shikenan. A nan labarin ya fara shiga cikin asirin gaskiya wanda zai bayyana dangantaka mai rikitarwa tsakanin Abba, Faruk, da Zainab. I'm "Ni ba na jin tsoro," Zainab ta faɗi da murya mai ƙarfi, ko da kuwa zuciyarta na dukan kamar ƙarar gangar yaƙi, "Na daɗe ina gudu daga tambayoyi, amma yanzu... yanzu zan fuskance su." Tsohuwa ta miƙa mata wata ƙaramar akwatin katako. "Ki buɗe wannan kawai idan kin kai garin Ruwa Uku, a can ne za ki fara samun amsoshin da kike nema." "Garin Ruwa Uku?" Zainab ta maimaita, tana jin sunan yana ɗauke da wani nauyi, "Ba wanda ke zuwa can.” "Eh," tsohuwar ta ce, tana mai ɗaukar numfashi mai nauyi, "Saboda ba kowa ke dawowa ba." Zainab ta ji sanyi ya ratsa jikinta, amma ta karɓi akwatin da hannuwanta masu rawa, tana ji a ranta cewa tafiyar nan ba ta komai bane face farawa, farawa na gaskiyar da za ta girgiza duk abin da ta taɓa yi imani da shi. Da daddare, tana cikin ɗakin otal ɗin ƙauyen, ta zauna tana kallon hoton Faruk. Fuskar nan mai cike da sirri, da idanun da ke kamar suna kallonta daga wani wuri mai nisa. "Faruk," ta faɗi a hankali, "me yasa ka ɓoye gaskiya daga gare ni?" Sai dai abin mamaki, kamar daga cikin duhun ɗakin, wata murya mai rauni ta amsa ba daga kunne ba, amma daga cikin zuciyarta: "Saboda gaskiyar tana da farashi, Zainab... kuma ni na biya rabin nasa." Zainab ta zabura, ta dubi ko akwai wani a ɗakin, amma babu kowa sai iska mai sanyi da ta shigo daga taga, tana kaɗa hoton da ke kan tebur. A lokacin ne ta lura da wani abu a bayan hoton, akwai rubutu da ba ta taɓa gani ba a baya: "Garin Ruwa Uku in da komai ya fara, kuma in da zai ƙare." Zainab ta zauna cak a bakin gadon, tana kallon rubutun da hannunta ke rawa. "In da komai ya fara, kuma in da zai ƙare…" Ta ji kalmomin suna echo a cikin zuciyarta, kamar ana karantawa daga wani nesa, wani sanyi ya ratsa ta daga ƙafafunta zuwa wuya, sai ta ɗaga kanta da sauri ta duba madubin da ke gefen ɗakin. A cikin madubin — kamar wani ɗan lokaci ta ga wani inuwa a bayanta, mai siffar mutum, amma kafin ta juya, inuwa ta shuɗe kamar hayaƙi. Ta tsaya, ta dafa kirjinta. "Zuciyata ce kawai," ta faɗa a hankali. "Babu komai." Amma daga gefe, akwatin katakon da tsohuwa ta ba ta ya fara yin ƙara ƙarar ƙaramar murya, kamar ana murmurɗa makulli daga ciki. Zainab ta matsa kusa, tana jin bugun zuciyarta yana ƙaruwa. "Ba yanzu ba," ta tuna da gargadin tsohuwa, "Ki buɗe kawai idan kin kai garin Ruwa Uku." Sai dai wani abu a cikin zuciyarta ya motsa, wata ƙwaƙwalwa ko sha’awa ta haramun. Ta ɗauki akwatin, ta girgiza shi a hankali. Sautin ƙaramin abu ya buga daga ciki kamar zobba biyu suna haɗuwa, ko ƙaramar ƙwallon tagulla. Ta ɗauko makullin ƙaramin siriri da ta saba ratayawa a wuyanta — mallakin Faruk tun kafin ya ɓace ta gwada buɗe akwatin. Klik. Akwatin ya buɗe da sauti mai laushi, a ciki akwai ƙaramar takarda, da wani zobba da ba ta taɓa gani ba, a cikin takardar, akwai kalmomi guda uku kawai, da rubutun da ta gane nan take rubutun Faruk: "Ki daina nema na.” Zainab ta saki takardar ta faɗi kasa, Idanunta suka cika da hawaye, ba saboda tsoro ba amma saboda wannan saƙon ya tabbatar da abu ɗaya: Faruk yana raye. Amma me yasa yake so ta daina nemanshi? "Me yake boyewa? Kuma me ke da alaka da wannan garin ruwa uku?" Haka ta ci gaba da tambayoyin da ba mai amsa mata. Ta rufe akwatin da sauri, ta ɗauki jakar tafiya, zuciyarta cike da tambayoyi, a lokacin da ta fita daga ɗakin, wata iska mai kauri ta biyo bayanta tana ɗauke da murya mai sanyi wacce ba ta san daga ina take ba: "Gaskiyar ba ta so a binciketa, Zainab... amma kin riga kin fara." Tafiyar ta fara da safe, lokacin da hasken rana bai gama wayewa ba. gajimare ya lullube hanya, kamar sararin samaniya ma bai yarda da tafiyar Zainab ba. Motar su Khadijah da yake ta saba tuƙa motar wani maƙo cin su, tana tuki cikin shiru, ta bi hanyar ƙauyuka da ke shiru fiye da yadda ta taɓa gani, lokaci zuwa lokaci, sai ta hangi tsofaffin alamu na hanyoyi da aka bar su shekaru da dama alamun da suka dusashe kamar tarihin da ake ƙoƙarin manta da shi. Wayarta babu sadarwa. GPS ya kasa gano hanyar. Sai kawai titin da yake ta ja a gaba, kamar yana jagorantar ta zuwa in da bai kamata ta je ba. Bayan awanni biyu, ta iso wani wuri da ake rubuce a jikin wata tsohuwar farar duwatsu: "Ruwa Uku ku Shigo da nutsuwa." Amma babu nutsuwa a ranta. a ƙofar garin, ta ga wani mutum ɗaya tsaye dattijo mai ɗan gajeren hula, yana sanye da riga mai ɗan duhu, Idonsa yana bin ta da wani irin kallon da ke haɗa mamaki da tausayi. "Assalamu alaikum," Zainab ta faɗi, ta sauka daga mota. Dattijon ya ɗaga kai a hankali. "Wa alaikumus salam… kin shigo?" Ta ɗan yi murmushi. "Eh. Ina neman wani mutum... sunansa Faruk." Mutumin ya tsaya, yana kallonta kamar ya ji sunan da bai kamata a ambata ba. "Faruk?" ya maimaita, kamar suna ne da ke da nauyi. "Kin tabbata za ki iya ɗaukar abin da ke biye da wannan suna?" Zainab ta ɗauki numfashi mai zurfi. "Ba zan dawo baya ba." Dattijon ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya juya ya nuna mata wata hanya mai cike da bishiyoyi. "Ki bi hanyar nan," ya ce da murya mai rauni. "Za ki ga tsohuwar masallaci, a can ne ki tambayi Hajiya Kubra, ita ce ta san in da komai ya fara." Ta gode, ta shiga cikin garin" amma yayin da take tafiya, ta lura da abu mai ban mamaki garin ya yi kamar baya cikin lokaci guda. Mutane suna motsi a hankali, kamar hotuna masu rai da ba su san suna rayuwa ba. Wani yaro ya tsaya yana kallonta, idonsa a buɗe, amma ba ya magana. Kamar duk wanda ke garin yana jiran wani abu... ko wata. Lokacin da ta ƙarasa bakin masallaci, ta ga wata mata zaune a ƙarƙashin bishiya, tana saka tabarma da hannunta mai rawar sanyi. "Ina neman Hajiya Kubra," Zainab ta ce. Matar ta ɗaga kai, idonta suka haɗu kuma Zainab ta ji sanyi mai kaifi ya ratsa ta. "Ni ce," matar ta ce a hankali. "Ke ce ƴar’uwarsa… ko?" Ƴar’uwarsa?" Zainab ta tambaya. "Na Faruk?" Hajiya Kubra ta ɗan murmusa, amma murmushin ba shi da daɗi. "Eh. Amma Faruk ba ya nan, a gaskiya, bai taɓa barin garin nan ba." Zainab ta ɗauki numfashi a hankali, zuciyarta ta bugawa. "Ba kin ce yana ɓoye ba… amma kina nufin" "Kin makara, Zainab," Hajiya Kubra ta katse ta, tana dubanta da ido mai cike da alhini. "Gaskiyar da kike nema, tana ƙarƙashin ruwa. Kuma Faruk… shi ne ruwan nan." "Faruk… shi ne ruwan nan?" Zainab ta maimaita tambayar, kamar kalmomin sun fito daga wani mafarki, Hajiya Kubra ta dubeta na dogon lokaci kafin ta tashi a hankali, ta yi nuni da tafkin da ke bayan masallaci. "Ki bi ni," ta ce kawai. Sun yi tafiya cikin shiru har suka iso bakin tafki mai zurfi, ruwa mai sanyi yana motsi a hankali, yana ɗauke da wani ƙamshi da ba na ruwa ba kamar ƙamshin turaren mutum da ya ɓace shekaru da dama amma har yanzu yana da tasiri. "Garin ruwa uku," Hajiya Kubra ta fara bayani, "ana kiransa haka ne saboda akwai tafkuna uku a nan ruwa na Farko, na biyu, da na uku, amma wannan na uku… ba ruwa bane kawai. Wannan wurin yana rike da rai da kuma ajali." Zainab ta kasa magana. Idonta ya makale kan tafkin. "Me kike nufi?" ta tambaya a hankali. "Faruk," Hajiya Kubra ta ce, tana kallonta kai tsaye, ya yi ƙoƙarin yin abin da ba a taɓa yi ba ya nemi ya mayar da rai da ya ɓace, Ya shiga cikin ruwa nan shekaru huɗu da suka wuce... kuma bai sake fitowa ba." "Amma na ji muryarsa!" Zainab ta faɗa cikin firgici. "Na ji yana magana da ni! ya bar min saƙo, da rubutu" Hajiya Kubra ta girgiza kai. "Eh saboda ransa bai bar duniya gaba ɗaya ba, ruwan nan yana riƙe da shi. duk wanda yake da alaƙa da shi zai ji shi, zai gan shi a mafarki, zai ji numfashinsa a iska, amma ka da ki kuskura ki kira sunansa da niyyar neman amsa… domin zai amsa." Iska ta fara kaɗawa ruwa ya fara motsawa da ƙara, kamar ana jefa duwatsu a ciki. Zainab ta ja baya. "Me yake nufi da gaskiyar tana da farashi? Me yasa yake hana ni neman shi? Hajiya Kubra ta matso kusa da ita, ta kama hannunta da sanyi mai ban mamaki. "Domin idan kika nemi Faruk gaba ɗaya," ta ce da murya mai laushi, "ruwan zai buƙaci maye gurbin da ya ɓace, kuma wannan maye gurbin… ke ce." Zainab ta ji numfashinta ya tsaya. a lokacin ne ruwa ya yi wani ƙara kamar ana kiran sunanta daga zurfin ƙasa. "Zainab…" Ta zabura, ta waigo, amma babu kowa, Sai tafkin, da iska, da sautin muryar da ta fi kowacce daɗewa a zuciyarta. "Na gaya miki… ki daina nemana." Sai ruwa ya fara ɗaukar hoto a saman sa fuskar Faruk, mai cike da ciwo da gajiya. "Faruk!" Zainab ta kira, hawaye na zubo da hawaye. "Ka dawo! Zan taimaka maka!" Hajiya Kubra ta yi ƙoƙarin riƙe ta, amma Zainab ta sulale daga hannunta ta nufi bakin tafkin. "Zainab, ki tsaya!" Amma lokaci ya makara. Ta saka ƙafarta cikin ruwan, kuma a lokacin da ta yi hakan, duk garin ya yi shiru, wani sanyi ya ratsa duniya, kuma hasken rana ya shuɗe. Tafkin ya fara janyo ta a hankali, kamar yana maraba da ita gida. "Gaskiya tana da farashi…" Muryar Faruk ta sake maimaituwa daga cikin ruwa. kuma yanzu, ke ce za ki biya rabin da ya rage." Da zarar ƙafarta ta nutse cikin tafkin, Zainab ta ji kamar ana janye ta daga duniya. Iska ta tsaya. Ƙarar tsuntsaye ta ɓace. sai shiru mai nauyi mirin shiru da ke cike da murya. Ruwan bai yi sanyi kamar yadda ta zata ba. A maimakon haka, yana da ɗan dumi, kamar jinin da ke gudana cikin mutum, ta ji yana zagaye da ita, yana rufe kunnuwanta, hancinta, idanunta sannan komai ya shuɗe. Da ta buɗe ido, ba cikin ruwa take ba, amma a wani wuri mai launin toka sarari mai yalwa, ba sama, ba ƙasa. Tana tsaye a kan abin da ya yi kama da ruwa amma ba ya motsi. A can nesa, ta hango wani mutum tsaye cikin farin kaya, yana kallonta da idanun da ta sani fiye da kowanne: Faruk. "Faruk…" ta faɗi da rawar murya. ya yi murmushi mai raɗaɗi. "na ce miki kar ki zo, Zainab." Ta yi tafiya zuwa gare shi, amma kowane mataki da ta ɗauka, wurin yana nisa. "Me ya faru da kai? me yasa kake nan?" "Na nemi gaskiya," ya ce, muryarsa tana ƙara yin ƙasa kamar ana haɗa ta da iska. "Na nemi abin da bai kamata ɗan adam ya nema ba, na so in dawo da wanda muka rasa… amma ruwan nan bai ba da rai kyauta, Sai da ya karɓa., "Ya karɓa me?" Faruk ya dubeta, ya ɗan ɗaga hannunsa, a cikin tafin hannunsa, ta ga wani haske mai launin zinariya, yana ƙonewa a hankali zuciyarta. "Ya karɓi rabin raina, kuma yanzu, idan kin zo nemana ni, zai karɓi rabin naki." Zainab ta girgiza kai, hawaye suna zuba. "Ban damu ba! Zan zauna tare da kai, ko a nan, ko a wancan wuri!." Faruk ya matso kusa da ita a hankali. "Kin manta me tsohuwa ta faɗa?" ya tambaya. "Gaskiya tana da fuska biyu, na farko soyayya ce, Nn biyu... hadiya ce." Iska ta motsa, wurin ya fara dusashewa. Wani murya daga can ƙasa ta soma kiran sunanta "Zainab! Ki dawo! Kar ki bari ruwa ya rufe ki!" Muryar Hajiya Kubra ce. Faruk ya kama hannunta, hannunsa sanyi amma mai daɗin taɓawa. "Zabi ɗaya ne ke nan, Zainab, Ki tafi, ki rayu da labarina, ko ki zauna nan da ni a tsakanin gaskiya da mafarki." Zainab ta kalli hannunsa, sannan ta kalli sama in da wani haske mai launin fari ke haskowa daga nesa. "Faruk," ta faɗi cikin kuka, "ban iya rasa ka sau biyu ba." Sai ta matso kusa ta rungume shi. A lokacin, ruwa ya sake yin ƙarar girgiza, kamar ana rushe duniya, haske ya cika komai, sannan shiru. Da ta buɗe ido, tana kwance a bakin tafki. Hajiya Kubra tana kan kanta, tana kuka. "Alhamdulillah... kin dawo, Zainab." Amma Zainab ba ta ce komai ba. Sai ta ɗauki akwatin katakon daga gefenta, ta buɗe a ciki babu takarda, babu zobba, sai ƙaramar ƙwallar haske, mai launin zinariya kamar wacce ta gani a hannun Faruk. Ta murmusa a hankali, idonta ya cika da hawaye. "Faruk bai ɓace ba," ta ce da ƙasa. Yana tare da ni a cikin ruwana." Tafkin ya yi wani ɗan motsi, kamar yana amsa mata. Zainab ta dawo cikin garin ruwa uku, amma komai bai kama da yadda ta bar shi ba, hasken rana ya fito, amma ya yi laushi kamar bai cika duniya ba. Mutane suna motsi kamar daidai, amma idanun su sun ɗauki wani sanyi mai zurfi, kamar sun san wani abu da ba kowa ya sani ba. A cikin jakarta, ƙwallar zinariya da Faruk ya bar mata tana haskakawa a hankali, ta sanya hannunta a kai, kuma ta ji dumin zuciyarta yana hade da dumin Faruk kamar yana nan, amma a wani wuri daban. Hajiya Kubra ta tsaya a gefenta. "Kin tsira, Zainab, amma kin biya farashi, ruwan nan bai bari ba tare da karɓar wani abu daga zuciya ba, Kin rasa nutsuwarki, amma kin samu gaskiya." Zainab ta kalli ruwa, wanda yanzu ya yi shiru. "Ni yanzu… ina da shi a kaina," ta ce cikin murmushi mai raɗaɗi. "Faruk, koda bau tare da gani ba, yana tare da ni, kuma gaskiya… tana nan, amma ba a bayyane ba kamar yadda na zata." Tun daga wannan rana, Zainab ta fara tafiya cikin duniya da sabon hangen nesa, kowa da kowa yana ganin ƴar matashiyar da ta dawo daga garin ruwa uku, amma ba wanda ya sani abin da ta gani a cikin ruwan nan. A duk lokacin da rana ke faduwa, idan ta kalli ƙwallar zinariya a hannunta, za ta ji muryar Faruk: "Zuciya ta kasance tare da ki, kuma yanzu ke ce mai riƙe da gaskiya." Zainab ta rufe idanunta, ta ɗan murmusa, sannan ta matso gaba. Rayuwarta ta cigaba, amma a cikin kowane zuciya da ta hadu da shi, a cikin kowane zabi da ta yi, akwai wani sirri mai ƙarfi: gaskiya tana da farashi, amma ba a rasa dukkan haske ba. Ruwan ruwa uku ya tsaya a cikin ƙwaƙwalwa, kamar labari mai ƙarfi wanda ba a taɓa mantawa da shi ba. Kuma Zainab, yanzu mai wayewa da ƙarfin zuciya, ta san cewa duk abin da ta rasa a waje, ta samu a ciki. Hasken rana ya shuɗe a hankali, amma zuciyarta kamar tafkin nan tana cike da ƙarfi, soyayya, da gaskiya. Shekaru biyu bayan tafiyar Zainab zuwa garin ruwa uku, ta koma birni mai cike da hayaniya, mutane suna ganin ta, amma ba su taɓa sanin abin da ta gani a cikin tafkin nan ba" Har yanzu tana ɗauke da ƙwallar zinariya a cikin jaka, mai haskakawa a hankali a kowane dare. Amma akwai wani abu da ya canza a cikinta, a duk lokacin da ta kalli rana na faduwa, ko iska mai sanyi ta busa ta fuskarta, ta ji muryar Faruk a hankali ba kamar mafarki ba, amma kamar wani abu yana magana daga wani wuri a cikin duniya. "Zainab…" Ta yi ƙoƙarin juyawa, amma babu kowa a bayanta, kamar duk wani tunani, sautin yana da gaskiya, amma babu tushensa. A lokacin da ta shiga gidanta, ta lura da wani abu a cikin madubi inuwa mai siffar Faruk, amma yana motsi daban-daban daga yadda take tsammani, ba ta tsorata ba, amma zuciyarta ta buga da sauri. Sai wani sauti ya cika gidan: "Ruwa na nan… kuma ni nan ne, a kowane zabi da ki yi." Zainab ta fahimci cewa garin ruwa uku bai bar ta ba, Faruk bai bar ta ba, ko da a zahiri ta dawo, wani ɓangare na ruwan nan da sirrin da suka haɗa shi da Faruk, yana cikin rayuwarta har abada. Ta sanya hannunta a ƙwallar zinariya, wani sanyi mai ɗumi ya ratsa hannunta, kamar ƙoƙarin tunatar da ita: "Gaskiya ba ta barin duk wanda ya nemeta… amma wanda ya karɓa, yana rike da iko." Ji mata da laushi, kamar yana cewa: "Zainab… yanzu ke ce mai rike da gaskiya da ruwan nan, kuma babu wanda zai taba ɗaukar abin da ke cikin zuciyarki." Shiru ya mamaye gidan, amma Zainab ta san, sirrin ba ya barin mutum, kuma babu wanda zai taɓa iya mantawa da shi. ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️✍️ WhatsApp number 08080304152 PAGE NA 13&14 Zainab ta buɗe idanunta a hankali, hasken ƙwallar zinariya yana ci gaba da haskakawa cikin dakin, yana jefa inuwa mai laushi a bangon da ke cike da tsoffin hotuna, iskar dare ta shigo ta taga, tana ɗauke da ƙamshin ruwa da wani sanyi mai nutsar da rai. Sai zuciyarta ta fara bugawa da sauri domin ta ji shi. Muryar da ta fi kowace irin murya ta sani. "Zainab…" Muryar Faruk ce, amma ba kamar yadda ta saba ji ba, wannan karon, muryar tana fitowa ne daga cikin ruwa ba daga nesa ba, kamu ba daga mafarki ba daga cikin ƙwallar zinariya kanta. Ta tsaya cak, hannunta na rawa. "Faruk?" ta furta da rauni. Sai ƙwallar ta ɗan yi wani motsi, kamar kumfa ta tashi a cikinta, sannan haske mai shuɗi ya bayyana, a cikin wannan haske, ta hango fuskar Faruk, sai dai idanunsa sun cika da wani launin ruwa, kamar yana kallonta daga ƙarƙashin teku. "Ba ki kamata ki kunna ta yau ba," ya faɗi, muryarsa mai taushi amma cike da damuwa. "Ruwan nan bai gama shirye ba, zai ji ƙamshin zuciyarki, Zainab kuma idan ya ji, zai nemi abin da kike ɓoyewa." Zainab ta matso da ƙwallar kusa da kirjinta. "Ban iya jira ba, Faruk Ina jin kamar sirrin nan yana canzawa a kowace rana, kamar yana kiran wani wanda ba mu sani ba." Shiru ya sake mamaye dakin, sai daga baya Faruk ya ce: "Wannan sirri ba na mu kadai ba ne yanzu, ruwan nan ya fara tashi daga garuruwan uku… kuma duk in da yake, ana jin muryarki, ana kiran sunanki." Wani ƙanƙanin sanyi ya ratsa ta. "Me kake nufi?" Faruk ya dubeta daga cikin haske Faruk ya dubeta daga cikin haske, idonsa na ɗauke da wata irin natsuwa mai haɗe da tsoro. "Ina nufin," ya ce a hankali, "ba mu da iko da abin da muka fara. Ruwan nan yana ɗauke da tarihin da ba mu rubuta ba kuma yana tunawa da duk wanda ya taba shi." Zainab ta girgiza kai, murya na rawa. "Amma ni dai ban yi ma sa komai ba, na dai kunna shi, kamar yadda kake koyar da ni." Faruk ya janyo numfashi mai nauyi. "Kin kunna shi da zuciya mai tambaya. Kin shiga da fargaba, kuma ruwan nan yana jin fargaba kamar yadda yake jin ƙauna, a yanzu… yana neman amsa daga gare ki." Kafin ta samu ta amsa, ƙarar ruwa mai laushi ta cika dakin ba daga injin ba, amma daga cikin ƙwallar da ke hannunta, ta fara haskawa da launin shuɗi mai sanyi, kamar hancin iska a cikin dare. Zainab ta matso da ita, numfashinta na daskarewa. "Faruk… yana motsi." "Ki ajiye ta!" ya yi ƙara, amma kafin ta iya, hasken ya bazu ya mamaye dakin, yana cike da murya murya guda ɗaya da aka haɗa da nata. "Zainab," muryar ta faɗa daga cikin ruwa, "kin dawo." Ruwan ya tsaya, hasken ya ragu, amma a yanzu, babu shakka ba ta cikin ɗaki kawai, tana cikin wani wuri da ya san sunanta tun kafin ta haifuwa. Ruwan ya ɗauke ta ba tare da an motsa jikinta ba, idanunta a buɗe suke, amma duk abin da take gani ya koma kamar mafarki, inuwa, launuka, da muryoyi ma su jituwa da zuciya. Ba ta cikin daki, kuma ba ta cikin duniya kamar yadda ta sani, wurin da take yanzu yana cike da haske mai laushi, yana ɗauke da ƙamshin ruwa da ƙasa mai sabo. Ta ji muryar Faruk a hankali, daga nesa kamar ana kiransa daga ƙarƙashin kogin lokaci. "Zainab… kada ki yarda da komai da kika gani, ki tuna da bugun zuciyarki shi ne jagoranki." Ta lumshe ido, amma a lokacin da ta buɗe su, ta ga wata mata tana tsaye a gabanta. Matar na sanye da farin zani mai launin ƙyalli, gashinta yana tafiya kamar ruwa, a fuskarta akwai nutsuwa, amma idanunta — suna da wani irin hasken da ƙwallar Zainab take yi. "Ke ce?" Zainab ta tambaya, muryarta tana girgiza. Matar ta yi murmushi. "Ni ce abin da kika boye, ni ce ƙwaƙwalwar da aka ɗaure a cikin ruwa saboda ki rayu ba tare da nauyin asali ba." Zainab ta matsa baya. "Ban gane ba ni fa ba ruhi ba ce mutum ce." "Mutum?" ta ce cikin dariyar da ta yi kamar amo daga nesa. "Eh, amma kin zo ne daga ruwa. Lokacin da aka haife ki, an ɗebo ki daga ruwan nan da hannun mahaifiyarki, an rufe asirinki domin kada kowa ya san yadda kike da alaƙa da shi." Zainab ta lumshe ido, hawaye suna taruwa. "Me yasa yanzu? Me yasa yanzu yake kirana?" Matar ta ɗaga hannunta ta taɓa goshinta. "Saboda lokaci ya kusa, garuruwan uku da ruwan nan ke bin su suna dushewa, Idan ba ki dawo ba, zasu shuɗe, kuma muryar ki muryar mu zata ɓace har abada." Zainab ta ji zuciyarta tana bugawa da karfi. "To me kuke so in yi?" "Ki dawo ki haɗa ruwan da jinin ki, ki tuna da kalmar farko da kika taɓa ji kafin ki iya magana." A wannan lokacin, hasken ya sake raguwa. Faruk ya bayyana a gefe amma fuskarsa cike da duhu, kamar yana daga tsakanin duniya biyu. "Zainab, ki tsaya! Kada ki saurari ta wannan ba ita bace!" Matar ta kalli shi da murmushi mai sanyi. "Shi ba zai iya fahimtar menene dawo ba, amma ke, Zainab… ke za ki iya dawo da mu duka." A nan ne ruwan ya fara juyawa, yana ɗauke da su biyu cikin ƙara mai kama da gurnanin duniya da take buɗewa dgurnanin duniya da take buɗewa daga ciki. Ruwan yana juyawa kamar guguwa mai sanyi, yana ɗauke da su cikin sararin da ba shi da sama ko ƙasa, Zainab ta kasa bambance in da rana take ko dare. Kowane haske yana zama inuwa, kuma kowace inuwa tana magana da muryarta. Faruk yana ƙoƙarin kusantarta, amma kowane motsinsa yana narkewa cikin ruwa. "Zainab!" ya kira, muryarsa tana yi mata kama da ƙarar ƙarfe a karkashin teku. "Ki saurare ni wannan matar ba ta fito daga gare ki ba, ita ce ke ta biyu, wadda aka ɓoye domin kar ta mallake ki gaba ɗaya!" Matar cikin ruwa ta yi murmushi mai nutsuwa, ta ɗaga hannunta, ruwan da ke kewaye da su ya daina motsi, kamar yana jiran umarni daga gare ta. Faruk yana tsoro, ta ce. "Tsoron gaskiya, ya san idan kika gane wacece ke gaske, ba zai sake iya kiran sunanki da wannan natsuwar ba." Zainab ta ji zuciyarta tana bugawa sosai. A lokacin da ta dubi Faruk, idonta ya ga abin da ba ta taɓa gani ba wani zobe mai haske a wuyansa, kamar alamar da ta saba gani a cikin mafarkinta. "Faruk…" ta furta cikin rawar murya. "Wane ne kai a cikin wannan?" Ya tsaya, numfashinsa yana fita da sauri. "Ni ne mai tsaron sirrinki, na rantse da ruwanki tun kafin ki zo duniya, cewa ba zan bari ruwan nan ya sake ɗaukarki ba, amma yanzu… yana kiran ki da sunan da ban taɓa faɗi ba." Matar cikin ruwa ta yi gaba, ta ɗora hannunta a kirjinta. "Sunanki na gaskiya," ta faɗa cikin sanyi, "ba Zainab ba ne" Zahara, wacce ke rayuwa tsakanin ruwa da iska, ki kira sunanki, kuma za ki tuna da komai." Zainab ta rufe idonta, a zuciyarta, ta ji kamar ana ja da jikinta biyu daban ɗaya yana neman komawa cikin ruwa, ɗaya kuma yana neman tsayawa da Faruk. Ruwan ya fara ɗaukar launin ja mai laushi. "Zainab!" Faruk ya sake kira. “Ki tuna abin da kika ji lokacin da kika fara ganin ƙwallar ki tuna da bugun zuciyarki, ba da muryarta ba!" Amma muryar matar ta ratsa zuciyarta, mai taushi, mai nutsuwa, mai ɗauke da wani irin tabbaci. "Zahara… lokaci ya yi." A cikin wannan ɗan lokaci, duniya ta tsaya, ruwan ya tsaya, hasken ya tsaya, numfashi ya tsaya. Zainab ko Zahara ta buɗe ido. "Idan zan zabi," ta ce cikin murya mai cike da ƙarfi, “zan zabi gaskiya, komai take nufi." Ruwan ya fashe da haske. Haske mai tsanani ya mamaye komai, yana cike da sautin bugun zuciya ɗaya, biyu, uku sannan komai ya shuɗe. Faruk ya farka da ƙarar iska mai sanyi. Ƙwallar na hannunsa tana haskawa da launin zinariya, amma yanzu tana da zafi kamar tana numfashi. Dakin da yake ya canza ba dakin da suka yi gwaji ba ne, wannan wurin ya yi kama da tsohon haikalin ruwa, bango da aka goge da shekaru, ƙasa mai laushi, da wasu zane-zane da ke motsi a hankali kamar suna numfashi. Ya tsaya a hankali, yana sauraron sautin da ke fitowa daga cikin ƙwallar. Muryarta ce, muryar Zainab, amma mai zurfi, kamar tana magana daga can karkashin teku. "Faruk… ka bi hasken, amma kar ka yi saurin shiga, kogin Kariya ba ya gafarta kuskure." Ya ƙara riƙe ƙwallar, zuciyarsa na bugawa. "Zainab ko Zahara, duk wacece ke zan same ki." Ya fara tafiya cikin hasken da ke fitowa daga ƙwallar, wanda ke nuna ma sa hanya ta cikin duhu, a kowane mataki, yana jin kamar ruwa yana magana a ƙasa kamar yana tambaya. "Shin kai mai gaskiya ne?" A gaban sa, wani ƙofa mai ɗauke da ruwa ya bayyana, ba ta ƙasa ko sama ba, amma tana raye, tana karkarwa da numfashi, a saman ta, akwai rubutu da ya ɓata da tsufa, amma har yanzu ana iya karantawa. "Wanda ya shige ba tare da gaskiya ba zai manta da sunansa." Faruk ya tsaya, ya san wannan ƙofa ce da masu ruwa ke bi don shiga cikin asalin su, amma shi fa mutum ne, mai tsoron irin waɗannan wurare, duk da haka, zuciyarsa ta ce masa Zainab tana ciki. Ya ɗaga ƙwallar, hasken ya ƙara ƙarfi har ya cika wurin, sai muryarta ta sake fitowa: "Ka tuna abin da na koya maka lokacin farko, Faruk ruwa ba ya cinye wanda zuciyarsa ta tsaya a kan gaskiya." Ya lumshe ido, ya shige cikin ƙofar. Da zarar ya tsallaka, ba ruwa ba ne ya same shi haske ne, hasken nan ya ɗauke shi kamar guguwa mai sanyi, yana ɗauke shi cikin sarari in da babu ƙasa, babu sama, sai ƙarar zuciyoyi da suka dade suna jira. A tsakiyar wannan haske, ya ganta Zahara tana tsaye a kan tabarma ta haske, gashinta yana yawo kamar ruwan teku, idanunta cike da ƙarfi da nutsuwa. "Faruk," ta ce a hankali, "ka zo, amma ka bar sunanka a baya." Ya dubeta da murmushi mai ɗaci. "Idan hakan ne farashin ganin ki, to ina bayar da shi." Sai ruwan ya rufe su, hasken ya narke kuma daga nesa, an ji ƙarar zuciyoyi biyu da suka yi daidai bugun lokaci ɗaya. Faruk ya buɗe idonsa cikin haske mai sanyi, amma wannan ba hasken duniya ba ne hasken nan yana da launi na rai, mai kama da kukan rana a ƙarƙashin teku. A gefensa, Zahara na tsaye ba kamar yadda yake ganinta a duniya ba, wannan karon, jikinta yana ɗauke da alamar ruwa a fatar sa, kamar ta kunshi teku a cikin zuciyarta. "Ka tsallaka, Faruk," ta ce, muryarta tana ratsa cikin iska kamar sautin ƙaho mai nisa. "Amma yanzu kai ba mutum kawai ba ne, ka shiga cikin jinin masu ruwa kuma hakan yana nufin kai ɗaya daga cikin su ne." Faruk ya kalli hannayensa haske yana fitowa daga jijiyoyinsa kamar ruwa mai motsi. "Ba zan fahimci wannan ba," ya ce cikin murya mai sanyi. "Me yasa ni? me yasa ke? me yasa ruwan nan yake kiranmu?" Zahara ta yi shiru na ɗan lokaci, sai ta juya ta nuna wani haske a cikin sarari. Hasken ya bayyana a matsayin tsohuwar murya, wacce take magana kamar daga cikin ƙarni da suka wuce. "Lokacin da duniya ta rabu da ruwa, an bar mana wasu guda bakwai masu riƙe da murya da zuciya, daga cikin su, Zahara ce ta biyu, amma lokacin ta ƙi bin hanyar da aka ware mata, ta zaɓi mutum mai suna Faruk ta yi ma sa alkawarin ba zata dawo cikin ruwa ba." Faruk ya ji jikinsa ya tsaya. "Kin… zaɓi ni?" Zahara ta ɗan yi murmushi, idanunta cike da wani irin ƙauna mai haɗe da nadama. "Na zaɓi ka lokacin da bai kamata ba, kuma don haka ne aka ɗaure ruhina cikin ƙwallar, ruwan bai yarda da ƙauna mai karya dokarsa ba." "Saboda haka," ta ci gaba, "lokacin da ka kunna ƙwallar, ruwan ya gane murya ta ya tashi daga barci, ya kira ni, amma ya Zahara ta kalle shi da idanu masu cike da labarai kamar kowace ƙwayar ido ɗaya na ɗauke da duniyar da ta wuce, da wata da ba ta zo ba, ta motsa hannunta, haske mai launin shuɗi ya fito daga yatsunta ya zagaye Faruk, kamar yana tantance shi, yana karanta shi daga ciki. "Ke yi tafiya mai nisa, Zainab," ta ce da murya mai laushi amma mai nauyi kamar ana karanta ƙa’ida daga littafin da aka manta, "Kogin Kariya bai karɓi mutum ba tun shekaru ɗari biyu da suka wuce, me ya sa ke.? Faruk ya yi shiru na ɗan lokaci, hasken da ke kewaye da shi yana motsawa kamar yana numfashi tare da ita, a ƙarshe ya ce: "Saboda kai da ita na san akwai abin da ke haɗa ku biyu, Zahara da Zainab, ban zo don in kwace ba, na zo don in gane." Zahara ta yi murmushi, ba irin murmushin farin ciki ba, amma irin wanda ke ɓoye gaskiya mai raɗaɗi. "Idan ka san abin da ke haɗa mu, to kai ma za ka zama ɗaya daga cikinmu, amma idan har zuciyarka ba ta shirya ba, hasken da ke riƙe da kai zai koma duhu." Sai ta miƙa hannunta, hasken ya koma kamar kogi yana gudana tsakanin su, a cikin kogin, Faruk ya ga hotuna ƙananan tunaninsa da rayuwarsa, lokacin da yake ƙarami, lokacin da margaji ta koyar da shi yadda ake sauraron ruwa, lokacin da ta ɓace, da lokacin da ya yi rantsuwa zai same ta ko da ya shiga duniya ta biyu. "Na shirya," ya faɗa da murya mai raɗaɗi, "ba zan sake gudu ba." Da wannan kalmar, Zahara ta matsa kusa, haske ya haɗa su, ya juye su cikin juna kamar ruwa biyu da suka zama ɗaya, sai zuciyar Faruk ta ji kamar ana kwance wani kulle da ya daɗe yana riƙe da shi. Daga nesa, muryar Faruk ta sake fitowa, wannan karon tana da annuri: "Zainab ki gane yanzu? ruwan gaskiya ba ya raba, sai dai yana haɗa waɗanda suka tsaya akan kalmarsu." A lokacin, Zahara ta yi shiru, hasken ya fara canzawa zuwa duhu mai sanyi, a cikin wannan duhun, Zainab ta gane cewa ba Zahara ba ce kawai ke gaban ta amma Faruk ma tana cikin ta, wata halitta guda ce, ruwan da ya rabu ka shi biyu don a gwada ta. Ya ce cikin nutsuwa: "Zahara... Zainab... kun kasance ɗaya tun farko." Ta ɗaga kai, ta ce da murya mai cike da ƙauna da nauyi: "Kuma kai, Faruk, ka zama maɗaukakin ruwa, gaskiyarka ce gadonmu yanzu." Da wannan kalmar, kogin haske ya buɗe a ƙafafunsa, yana gayyatar shi ya zaɓi ya tsaya da su cikin wannan duniya ta haske ko ya koma duniya ta mutane da zuciyar da ta gane sirrin ruwa. Zainab ta kalli hasken, ta kuma kalli duhun da ke cike da murya mai sanyi, sai ta ce a hankali: "Na ga haske, amma duniya tana bukatar shi fiye da nan." Sai hasken ya kwashe ta kamar iska, ya koma cikin ƙwallar da yake riƙe tun farko. A farkon rana, a bakin wani rafin da ke jikin tsauni, Zainab ta buɗe idonta. Ruwa yana gudana a gefe, kuma muryar Faruk tana yawo cikin iska mai nisa, amma yana murmushi. "Ka dawo, mai gaskiya." Faruk ya zauna a bakin rafi, hannunsa yana shafar ƙasan ƙwallar da yanzu ba ta haskaka kamar da ba, amma har yanzu tana da dumi, ruwa yana gudana cikin natsuwa, amma duk da shiru, tana jin kamar akwai kalmomi a cikin motsinsa kamar ana magana da shi, a hankali, cikin yaren da ba na mutane ba. Ta sunkuya, ta sanya yatsunya cikin ruwa. Nan take, yanayin ya canza. , ruwan ya daina gudu kamar yadda aka saba sai ta tsaya, tana motsawa kamar yana numfashi. Wani ƙara ya taso daga ƙasan rafi, ba ƙarar iska ba, ba kuma murya ta mutum ba, sai dai murya ce ta ƙasa da ruwa, mai cike da hikima da gargaɗi. "Mai dawowa daga hasken, kai ne ɗan farin ruwa, ka ɗauko gaskiyar da ba ta da tushe, amma har yanzu kina ƴan duniya." Zainab ta ɗaga kai cikin mamaki. "Ni ce nake magana da ku?" ta tambaya. "Ba da baki ba, amma da niyya,” ruwan ya amsa, “Mun saurari murya irin taka shekaru aru-aru, tun lokacin da mutane suka daina jinmu." Ruwan ya fara yin kwarara a hankali yana ɗaukar siffar fuska ba ta mutum ba, amma irin wadda zuciya ke gane ta: fuskarta Faruk, amma yanzu yana da nutsuwar Zahara, da hasken da bai da iyaka. "Na dawo, kamar yadda kika ce,” Faruk ya faɗa da muryar da ta shaɗe da tausayin tunawa. “Amma yanzu fa, me nake nufi da wannan hasken? Me yasa kuke bani wani abu da ba ku ga mutane da shi ba?” Murya ta ce cikin zurfi, tana haɗuwa da ƙarar ruwan da ke kwarara: "Domin ke ki saurara, mutane sun manta yadda ake jin magana ta halitta. Sun daina sauraron koguna, iska, da ƙasa, ke ce wanda gaskiyarka ta buɗe ƙofa, amma buɗe ƙofa yana nufin nauyi." Zainab ta lumshe ido. "Wane nauyi?" "Za ki zama mai ji, wacce zata ɗauki muryar abubuwan da ba su da baki, ya bayyana su ga duniya, amma ki sani, ba kowa zai yarda ba, wani zai kira ki mahaukaciya, wani kuma zai nemi karfin da ke tare da ke." A lokacin, ƙwallar ta fara ɗan haskawa, ta buga da zuciyar Zainab sai wani kallo ya shigo ma ta birane da suka lalace da fari, ruwan da ya mutu, koguna da suka dushe, mutane suna faɗa da ƙasa saboda rashin albarkarta. Zuciyarsa ta yi nauyi. "Na gane," ya ce cikin raɗa. “Ba don ni kadai bace, don duniya ne." Ruwan ya yi dariya mai sanyi, irin dariyar da take da hikima. "To, ki fara jin magana ta farko. "Ruwa ba ya bacewa sai dai ya canza hanya, ki koya hakan, kuma duniya za ta ji ta." Rafi ya koma gudu kamar da, sai Zainab ta ji iskar safe ta doke ta da sanyi mai daɗi. Ta ɗaga ƙwallar sama, haske mai launin ruwa ya dudduba cikin iska ya narke cikin rana. A wannan rana, a ƙarƙashin rana ta farko bayan dawowarta, Zainab ta zama mai jin ruwan duniya. Mutumin da zai sa halittu su sake magana da mutum. ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️✍️ WhatsApp number 08080304152 PAGE NA 15&16 Da dare ta sauka, kogin da ta taɓa yin shiru yanzu tana rera waƙa kamar tsohon aboki, Zainab ta zauna a bakin ruwan, tana sauraron sautin da ke fitowa daga zurfin da ba ido ke gani ba, sai zuciya. "Ki dawo," wata murya ta fito daga cikin iska, kamar ta haɗu da ƙamshin ganyen tsamiya da ɗanɗanon ruwan gishiri. Zainab ta runtse idanu, bata ji tsoro ba, tsoron ta bar shi tun lokacin da ta gane cewa ruwa ba ya bace sai dai ya canza hanya. "Na dawo," ta amsa cikin sanyi. "Amma ban dawo ni kaɗai ba, na dawo da murya." A lokacin, ƙasa ta yi ɗan karkarwa. Ganyayyaki suka yi kara, kamar suna dariya, wani ɗan ƙaramin ƙwaro ya hau kan yatsunta, ruwan da ke jikinya yana kyalli kamar madubi. "Muryar halittu ta sake buɗewa," murya ya ce. "Zai zama da wahala, Zainab Mutane sun manta yadda ake sauraro." Zainab ta miƙe, ta kalli kogin da ke yawo da hasken wata a saman sa. "Idan sun manta, zan koya musu, saboda duniya ba ta yi shiru ba mutum ne ya daina sauraro." Wata iska mai ɗauke da ƙamshin ruwan sama ta buso, ta nannade ta kamar tsohon alƙawari, a cikin kunnenta, ta ji kalmar da ta tabbata kamar alama: "Duniya za ta ji ta, idan mai ruwa ya yi magana." Zainab ta ɗaga hannunta cikin iska. Ruwan kogin ya motsa, ya zana alamu a saman ruwa kamar haruffa da aka rubuta da haske, kuma daga nesa, wata yarinya ta fito daga inuwa, tana kallonsa da mamaki. "Wace ce ke?" ta tambaya. Zainab ta yi murmushi mai nauyin asiri. "Ni ne wacce ruwa ke kira, amma mutane ba su gane ba tukuna." Yarinyar ta tsaya a bakin kogin, idanuwanta suna kyalli kamar taurari da aka nutse cikin ruwa, sunan ta Amina, amma ta ji kamar ruwan ya riga ya san ta fiye da kanta. "Ni… ban taba ganin irin wannan ba," ta ce, tana matse hannayenta. “Ruwa… yana magana?" Zainab ta yi murmushi, amma ba ta yi magana da sauri ba, tana jin ruwan yana motsawa a gefenta, tana fassara ma ta yadda zai amsa: "Ee, amma ba kowanne zai iya jin ta ba. "Ruwan yana neman wanda zai saurare shi da zuciya, ba kawai da kunne ba." Amina ta matso kusa da ruwan, ta yi ƙoƙarin jin abin da take cewa, sai a nan ta ji kalmomi masu laushi, kamar tsuntsaye da ke tsalle-tsalle a saman ruwa: "Kin zama mai sauraro, ki fahimci, ki ba da… saboda idan ki tsaya, duniya za ta fara sake magana." Zuciyarta ta yi sanyi, kamar wata alƙawari mai ɗorewa ta shige cikin ranta, ta kalli , Zainab tana tambaya cikin shiru: "Zan iya koya? Zan iya sauraron sa kamar ke?" Zainab ta yi ta murmushi mai nauyi: "Idan ka bar zuciyarka ta buɗe, ko da abin da ka ji ya kasance ƙaramar magana, za ka iya fara, amma ka sani, Amina… ba koyon jin ruwa kawai ba ne, zai koya maka yadda za ka saurari duniya baki ɗaya." Ruwan ya yi wani tsalle mai laushi, ya busa ƙamshin tsire-tsire da ƙanƙara mai sanyi a kan fuskar su. Amina ta ji kamar an haɗa ta da dukan kogin, dukan ruwan da ya taɓa gudana a wannan duniya, har ma da asirin tsuntsaye da kowane ganye mai rawaya a wuri mai nisa. A cikin zuciyarta ta fara samun wani wuri na sirri, wani wurin da kawai ruwa zai iya magana, kuma kawai masu sauraro za su iya fahimtar ta. Zainab ta ɗaga hannu, tana nuna hanyar da kogin take tafiya zuwa cikin daji mai cike da haske: "Za mu fara tafiya, duniya tana jiran masu sauraro, kuma lokacin da muka isa wurin farko… za kia gane abin da ruwa yake nufi da ‘sake magana’.” Amina ta miƙe tsaye, ta ɗaga kai, idanuwanta suna kyalli da irin na wanda ya fara fahimtar wani sirri mai zurfi, ruwan kogin ya yi wata rawa, ya yi kamar yana amincewa da zaben ta. Sai suka fara tafiya, ƙasa da rana suna yi wa ruwa busa mai laushi, kuma cikin zuciyarsu, sun ji cewa wannan tafiya ba ƙarshen ta ba ce amma farkon wani abu mai ban mamaki. Sun bi hanyar kogin, daji ya yi duhu amma akwai haske mai laushi daga ganye da ke motsi kamar suna numfashi, ruwan kogin ya yi ta busa cikin iska, yana ƙirƙirar sautukan da suke kama da kalmomi. Zainab ya kalli Amina: "Ke ji?” ta tambaya. "Na ji… amma ban gane ba," Amina ta amsa cikin shiru. Zainab ta yi murmushi: "Ba kowanne mutum ne zai iya fahimtar ki kai tsaye ba, Ki fara jin, amma ki koya yadda za ki fassara." A nan, daga cikin ƙasa, wani tsuntsu mai launi mai ban mamaki ya tashi, amma ba ya ƙara fida baki, ruwan ya yi wani tsalle mai santsi, kamar yana fadin: "Wannan tsuntsu ya daina magana saboda mutane sun daina sauraro." Amina ta yi shiru, ta fahimci cewa kogin ba kawai ruwa ba ne, amma mai magana da dukkan halittu da aka manta da su, Zainab ta nuna wata hanya da ke cikin daji: "Za mu kai su wurin su, wurin da ruwan ke tarawa, anan ne za mu iya sauraron halittu su fara magana da mutane idan kin shirya." Ta hanyar daji, sun ga ƙananan halittu da ba a taɓa ganin su ba, wasu suna kallon su da idanuwa masu ɗaukar haske, wasu suna motsi a hankali, kamar suna jiran wani abu, ruwan kogin ya yi tsalle cikin iska, ya busa fuskar Amina: "Ki sani, kowanne daga cikin su yana da labari, amma sun daina magana saboda mutum bai saurara ba, idan kin saurare su, za ku fara gane yadda duniya ke magana." Amina ta ji wani zafi mai laushi a cikin zuciyarta, kamar zuciyarta ce take bayyana, ta ɗaga hannu, ta matsa kusa da ƙanaan halittun, suna fara motsi da murmushi. Zainab ta yi murmushi: Yanzu kin fara, Amina, wannan shi ne farkon abin da za ki koya, ba wai jin ruwa kawai ba, amma jin dukan abin da duniya ke ƙoƙarin faɗi." Ruwan kogin ya yi tsalle mai ƙarfi, ya bayyana wata hanya ta haske a cikin duhun daji, wannan hanya ce za ta kai su zuwa wurin babban sirrin kogin, in da za su iya farfado da halittu da suka daina magana shekaru aru-aru. Amina ta kalli Zainab, idanuwanta cike da sha’awa da tsoro. "Shin… mun shirya?" ta tambaya. Zainab ta yi murmushi mai nauyi, amma cike da haske: "Mun riga mun fara, amma abin da za mu gani zai canza yadda ka ke kallon duniya… har abada." Ruwan kogin ya yi ƙarshe mai laushi kamar yana kiran su su ci gaba, a cikin zuciyarta, Amina ta ji alƙawari mai ɗorewa, zuciyarta za ta zama murya ga waɗanda suka daina magana. ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️ WhatsApp number 08080304152 PAGE NA 17&18 Ruwan da ke cikin kwandon gilashi a gefen tagar ya yi wani irin motsi kamar iska ta shafi saman sa, sai Zainab ta kalli wajen da ido cike da mamaki, hasken rana da ke shiga ta cikin labulen rawaya ya kwanta a kan fuskar ta, yana bayyana ƙuruciyar da lokaci bai shafe ba amma zuciya ta gaji. Ta zauna a ƙasa, ta jingina da bango, ta rufe idonta kamar tana sauraron wani murya daga nesa. "Ruwa na nan… kuma ni nan ne." Muryar Faruk tana dawowa a hankali cikin kwakwalwarta kamar ƙamshi daga wani tsohon wuri, ta murmusa, amma murmushin ya ƙunshi zafi da salo guda. "Me yasa rayuwa ke barin mu da abubuwan da ba za mu iya mantawa da su ba?" ta furta a hankali, kamar tana tambayar kanta. A lokacin, ƙwallar zinariyar da take rataye a wuyanta ta fara ɗan haske, kamar tana amsa tambayarta, wani ƙara mai laushi ya fito daga cikinta ba sauti bane, amma jininsa ya isa kai tsaye zuciyarta. Saboda gaskiya tana rayuwa ne a cikin mai ɗaukar ta." Zainab ta buɗe idonta da sauri, wani yanayi ya cika ɗakin iska da ɗan ɗumi, kuma ƙanshin ruwa mai ɗanɗanon ruwan sama ya fara bazuwa. Ta tashi, ta kalli madubin da ke gefe, a ciki ta ga fuskar ta, amma a bayan hoton nata akwai inuwa inuwa mai siffar mutum, tana kallonta da murmushi. "Faruk?" ta furta cikin tsoro da bege. Sai muryar ta dawo da wani laushi da ke sa zuciyarta bugawa da natsuwa lokaci guda: "Zainab, ruwan nan bai ƙare ba, gaskiya tana buƙatar wanda zai rike ta da tsoro da kauna tare." Ta durƙusa, tana riƙe ƙwallar zinariyar, hawaye na sauka a fuskarta. "Idan haka ne," ta ce cikin murya mai sanyi, "To bari na zama ruwa… bari na zama gaskiyar da ba ta gushewa." Ruwan a cikin kwandon ya yi ƙara, sannan haske ya lullube ɗakin gaba ɗaya. A lokacin da komai ya lafa, Zainab ta tsaya da nutsuwa, amma ba ita ɗaya ba akwai wani salo, wani natsuwa, da wani haske a idanunta da ke nuna cewa ta gane: Ba wai ruwan nan ne kawai ya bar alama ba, ita ma ta zama wani ɓangare na labarinsa. Ranar ta yi duhu kafin rana ta fadi. Wata iska mai ɗauke da ƙanshin ƙasa da ruwa ta ratsa ƙofar gidan, Zainab ta tsaya a tsakar gida tana kallon sararin sama da ke kumbura da girgije. A ƙasan zuciyarta,ta san akwai wani abu da zai faru, a duk lokacin da ruwan nan yake motsi, wani ɓangare na rayuwarta yana kira gare ta. Ta riƙe ƙwallar zinariya a wuyanta, ta runtse idonta, cikin wannan duhun, ta ji kamar tana cikin wani wuri dabam wuri mai annuri amma cike da nutsuwa. "Zainab…" Muryar ta sake dawo da sanyi, kamar tana fitowa daga zurfin ruwa. "Lokaci ya yi da za ki san asalin ruwan nan, ba a halitta shi kawai domin soyayya ba, amma domin gaskiya, gaskiyar da ta haɗa rayuka biyu kafin lokaci." Ta ji hawaye sun taru a idonta. "Wace gaskiya, Faruk? Me yasa ni?" Sai haske ya bayyana a gaban ta, yana canzawa zuwa hoton wani tsohon wuri kogi mai nisa, cikin daji, in da rana ke haskakawa ta cikin bishiyoyi, wani saurayi da mace suna tsaye a bakin ruwan, hannayensu a hade. "Kin gane su?" Zainab ta kalli su sosai zuciyarta ta fara dukan da ba ta iya fassara ba, sai ta gane fuskar matar… fuskar wata ce, Kuma fuskar saurayin Faruk. Ta ja baya da mamaki. "Amma wannan, wannan aii Mama ta ce, wannan kafin ku haifeni ne." Muryar ta dawo cikin sanyi, tana cika kunnenta: "Rayuka suna haɗuwa fiye da lokaci, ruwan gaskiya shi ne hanyar da Allah ya sa don tunatar da waɗanda suka manta abin da suka yi alkawari tun kafin duniya ta fara." Zainab ta durƙusa, ta riƙe ƙwallar zinariya tana jin zafi da sanyi lokaci guda, a lokacin, hasken ya zame mata hawaye, hawaye suka zubo cikin hannunta, suka koma ƙwayar ruwa ɗaya tsantsar haske. "Yanzu kin fahimta," muryar ta ci gaba, "Ba a ba ki ruwan nan don soyayya kawai ba, an ba ki shi domin ki riƙe gaskiya domin ki tuna cewa komai da ke cikin rayuwa yana da asali, kuma gaskiya ba ta mutuwa." Zainab ta buɗe idonta, ruwan sama ya fara sauka a zahiri, yana dukan saman rufin da ƙara mai laushi, amma wannan karon, ba ta ji sanyi ba, ta ji kamar ruwan yana shigowa zuciyarta, yana wanke komai da ta riƙe tsawon shekaru. Ta tashi, ta ɗaga kai sama cikin ruwan sama, ta ce: "Faruk… na gane, kuma zan kare gaskiyar nan, har abada." A cikin nisan sararin sama, wata annuri ta haska, kamar murmushi daga wani wuri dabam. Washegari kafin alfijir, Zainab ta tashi da wata nutsuwa mai nauyi kamar mafarki, amma zuciyarta ta san wannan ba mafarki ba ne kira ne, Ruwan sama da ya zuba daren jiya ya bar ƙasa cikin danshi, ƙamshin sabuwar rana yana cike da iska. Ta ɗauki ƙwallar zinariya ta saka a wuyanta, sannan ta rufe ƙofar gidan a hankali kamar tana barin wani ɓangaren kanta a baya. Babu in da ta nufa sai gabas in da hasken rana ke fitowa, kuma in da kogin da ta gani cikin hangen jiya yake. Da ta isa bakin ƙauyen ƙarshe, wani tsoho ya tsayar da ita, fuskar sa cike da layukan shekaru, amma idanunsa suna da wani haske mai zurfi. "Ƴar nan," ya ce cikin murya mai sanyi, "kina nufin Dajin Asali ne?” Zainab ta kalle shi da mamaki, "Ya ya ka san haka?” Tsohon ya yi murmushi mai kama da sanin da ta rasa: "Dajin ba ya kira kowa sai wanda ruwan gaskiya ya zaɓa, an riga an faɗi zuwanki tun kafin ki zo duniya." Ta ji jikinta ya yi sanyi. "Me yake cikin dajin?" ta tambaya da rawar murya. Tsohon ya kalli sararin sama, ya ce: "Gaskiyar da ta ɓoye shekaru dari da dama, amma ki sani, duk wanda ya nemi gaskiya, dole ya shirya da fansarta." Sai ya ba ta ƙaramin kwalba mai cikewa da ruwa mai santsi. "Wannan ruwan ne daga tushen kogin farko, idan kin shiga dajin, kar ki sha shi sai lokacin da zuciyarki ta kasa fassara abin da idonki ya gani." Zainab ta karɓa da girmamawa, sannan ta yi masa godiya. Ta ci gaba da tafiya. Lokacin da ta shiga cikin dajin, hasken rana ya fara dusashewa, amma ba saboda dare ba bishiyoyi masu tsawo suna rufe sama da ganyayyaki masu sheƙi. Iska ta cika da ƙanshin ruwa da ƙamshin ganye, kowane motsi yana da ma’ana, kamar dajin yana numfashi. Ta ji muryar Faruk ba daga waje ba, daga cikin zuciyarta: "A nan ne komai ya fara, Zainab, ki bi ruwan… kada ki ji tsoro." Ta bi ƙarar ruwa, har ta iso bakin wani rafi mai haske kamar azurfa. A tsakiyar rafin akwai dutse, kuma a saman dutsen ƙwallar zinariya iri ɗaya da wadda take wuyanta, tana walƙiya da haske mai launin shuɗi. Zainab ta tsaya, zuciyarta na bugawa. "To me ya sa akwai biyu?" Sai ƙwallar da ke wuyanta ta fara ɗan motsi da zafi, kamar tana amsawa. Ta ɗaga kai, ta ga wani haske yana fitowa daga cikin ruwa sannu a hankali, siffar mutum ta bayyana. Faruk ne. Amma ba irin yadda ta saba gani ba hasken jikinsa yana walƙiya kamar rana ta nutse a cikin sa. "Zainab" ya ce, muryarsa kamar iska mai magana, "Na dawo ne saboda wannan rana, dukkanmu mun kasance ruwan gaskiya ne, amma an raba mu shekaru da yawa don mu koyi ma’anar gaskiya daban-daban." Zainab ta ji hawaye a idonta. "Me zan yi yanzu?" Faruk ya miƙa hannu zuwa gare ta. "Haɗa ruwan nan biyu ki haɗa su da zuciya ɗaya, idan kika yi haka, gaskiya za ta bayyana gaba ɗaya." Ta ɗauki ƙwallar zinariyar daga wuyanta, ta kusantar da ita ga wadda ke kan dutse. Da zarar suka taɓa juna, haske mai ƙarfi ya lullube dajin, bishiyoyi suka yi tsit, ruwa ya tsaya, iska ta tsaya kamar lokaci ya tsaya. A cikin hasken, ta ji muryar da ba ta san tawa ce ko ta Faruk ba tana faɗin: "Gaskiya ba ta ɓoyewa, tana jiran wanda ya shirya ya ɗauke ta." Lokacin da hasken ya lafa, ta ga kanta tsaye a bakin rafi, amma yanzu kogin yana da sabon launi shuɗi mai kama da gilashi. A hannunta, ƙwallar zinariya ɗaya ce kawai amma tana da walƙiya mai rai. Ta murmusa, ta ɗaga kai sama: "Na gane, ba ni da ruwan gaskiya kawai ni ce ruwan gaskiya." Zainab ta tashi daga bakin rafin cikin shiru, wani sanyi mai taushi ya ratsa jikinta, amma ba irin sanyi na ruwa ba sanyi na natsuwa. Babu Faruk, babu hasken dajin da ya cika zuciyarta da mamaki, sai shiru mai ɗauke da nutsuwa, kamar duniya ta tsaya tana sauraron abin da zai biyo baya. Ta kalli hannunta ƙwallar zinariyar da ke cikinsa ta zama tamkar ƙaramin zuciya mai walƙiya da haske, a cikinta, tana iya ganin zaren ruwa yana yawo kamar rai. "Wannan gaskiyar… tana da rai," ta furta cikin rawar murya. Ko da babu wanda ya gani, tana saurare. Ta juya ta bar dajin. Kowane mataki da ta ɗauka, ƙasa tana amsawa da laushi, kamar tana godiya. Iska ta busa a gefenta, tana ɗauke da ƙamshin Faruk ƙamshin ruwa da ƙamshin soyayyar mahaifi. A lokacin da ta fita daga dajin, rana ta fito, duniya ta dawo kamar yadda ta saba, amma zuciyarta ba ta daɗe da zama iri ɗaya. Tana jin kamar duk in da ta kalli ruwa a rijiya, a tabki, ko a cikin idon mutum akwai wani ɓangare na labarinta a ciki. Da ta koma ƙauyensu, mutane suka lura da canji. Zainab ta yi shiru sosai, amma idan ta kalli mutum, kamar tana karanta zuciyarsa. Ranar farko da ta shiga kasuwa, wata tsohuwa ta tsayar da ita. "Ƴata" tsohuwar ta ce, "Me kika gani cikin dajin?" Zainab ta yi murmushi mai sanyi, ta ce: "Na ga cewa gaskiya ba ruwa ba ce kawai, ita ce abin da ke tafiya daga zuciya zuwa zuciya, ba tare da ta tsaya ba." Mutanen suka fara kiran ta "Zainab mai Ruwan Gaskiya." Wasu suna zuwa domin shawara, wasu domin neman waraka, wasu kuma kawai domin kallon idanunta da ke da hasken da ba na duniya ba. Amma a duk lokacin da ta zauna cikin shiru da daddare, ta kan ji muryar Faruk tana cikin zuciyarta: "Na gaya miki, ruwa ba ya barin wanda ya karɓe shi, kuma gaskiya tana raye cikin ke." Ta kan murmusa, ta ce cikin zuciyarta: "Faruk, ba zan bar ruwan nan ba. Amma yanzu na fahimci abin da ba na ganewa da farko, gaskiya ba ta nemi mutum ɗaya ba tana so ta haskaka duniya." Sai ta ɗaga ƙwallar zinariyar da ke wuyanta, ta riƙe ta a hankali. A ciki, haske ya yi walƙiya, sannan ya koma sanyi, kamar zuciya mai bugawa cikin natsuwa. A wancan dare, ruwan sama ya sake sauka, amma wannan karon, ba kamar da ba saboda kowanne digo da ya faɗo, yana ɗauke da haske. Mutanen ƙauye suka fito suna kallo, suna tambaya cikin mamaki: "Wane irin ruwa ne wannan?" Zainab ta kalli sama, tana murmushi cikin hawaye. "Ruwan gaskiya ne," ta ce cikin sanyi. "Ya dawo gida." Zuwa nan, ruwan gaskiya ya cika zagayensa daga sirri zuwa gaskiya, daga zuciya ɗaya zuwa duniya. Amma labarin bai ƙare ba domin gaskiya tana tafiya kamar ruwa, tana neman sabon tafarki. Shekaru sun ja bayan dawowar Zainab daga dajin asali. Ƙauyen ya canza mutane sun koyi natsuwa, sun koyi magana cikin gaskiya, sun daina ɓoye zuciya kamar da. Ruwan da suke sha daga rijiyoyin gari yana da ɗanɗano mai daɗi, kuma a duk lokacin da aka yi ruwan sama, ƙasa tana sheƙi kamar zinariya. A cikin wannan canji, Zainab ta ci gaba da zama cikin natsuwa, ba tare da neman yabo ko daukaka ba. Yara kan zauna kusa da ita suna sauraron labarai, mata su nemi shawara, maza su tambayi mafita. Amma duk lokacin da suke tambayarta yadda ta samu wannan hikima, sai ta ce da murmushi: "Ni ba ta ruwan gaskiya ba ce, ni dai na zama hanyarsa." Da dare ɗaya, ta zauna a bakin rijiya tana kallon taurari. Iska ta busa cikin laushi, sannan ta ji muryar da ta daɗe ba ta ji ba: "Zainab…" Ta runtse idonta, murmushi ya bayyana a fuskarta. "Na san za ka dawo, Faruk." "Ba domin ni ba ne, Zainab," muryar ta ce cikin annuri, amma domin ruwan nan, lokaci ya yi da zai ci gaba da tafiyarsa. Ta kalli ƙwallar zinariyar a wuyanta yanzu hasken ta ya fara raguwa, amma a maimakon duhu, tana zamewa kamar ruwa mai haske. "Ina nufin tafiyarsa ta ƙarshe?" ta tambaya. "A’a" muryar ta ce, "Tafiyarsa ta gaba, gaskiya ba ta ƙarewa tana komawa wurin da ake buƙatarta." Zainab ta ɗaga ƙwallar da hannunta biyu, ta ɗaga sama. A lokacin, wata annuri mai sanyi ta rufe ta gaba ɗaya, ta bayyana a cikin hasken wata, sannan ƙwallar ta narke ta zama ruwan haske mai fita kamar zuma. Ruwan ya tashi sama, ya watse cikin iska, yana yin ƙarar kamar waka mai taushi. Yaran ƙauye da ke barci suka ji iska mai sanyi ta ratsa su. Mutanen gari suka farka suka fito suka ga abin mamaki taurari suna walƙiya fiye da yadda suka saba, kuma ruwan sama yana sauka cikin haske. A tsakiyar tsakar gari, in da rijiya take, suka tarar da Zainab tana zaune cikin nutsuwa, fuskarta cike da natsuwa da murmushi, idanunta rufe. A jikinta babu ƙwallar zinariya amma a ƙasan ƙafafunta, ƙaramin rafi ya fara fitowa, yana gudana da sanyi cikin ƙasa, yana tafiya zuwa kowanne gida. Tsohon da ya taɓa ba ta ruwan farko ya zo, ya tsaya yana kallo. Sai ya ce da murya mai rauni amma cike da girmamawa: "Ruwan gaskiya ya samo tushe. Zainab ta zama hanya." Tun daga wannan rana, ruwan da ke fitowa daga rijiyar nan bai taɓa ƙarewa ba. Ko da lokacin fari, ko da lokacin tsananin rani ruwan yana nan. Mutanen ƙauye sun kira shi ruwan Zainab, amma tsofaffi suna kiran sa da sunan da ya dace: Ruwan Gaskiya. Kuma a duk lokacin da ruwa ya zubo cikin ƙasa, ana jin wata murya mai laushi daga cikin iska tana cewa: "Gaskiya tana tafiya kamar ruwa tana zuwa in da ake buƙata." Ranar da ruwan haske ya watse cikin sama, duniya ta canza da shiru mai daɗi. Zainab ta ji jikinta ya yi sanyi, amma zuciyarta ta cika da natsuwa, ta san ba ita kadai ba ruwan gaskiya yana nan cikin kowanne digo da ke sauka daga sama. Ta rufe idonta, ta furta cikin sanyi: "Faruk… gaskiya ta koma in da ya kamata, amma zuciyata ba ta son duniya ba tare da kai ba." "Naso nadawo tare kai saboda ina son nasan daɗin mahaifi." A lokacin, iska ta motsa da wani irin sauti kamar bugun zuciyar ruwa. Kogin da ke gefen ƙauyen ya fara walƙiya da haske mai shuɗi, sai ruwan ya fara tashi sama, yana jujjuyawa kamar gajimare. Zainab ta miƙe, idonta cike da mamaki da hawaye. A tsakiyar ruwan, ta ga siffa tana bayyana siffar da ta fi kowacce ta sani, ta fi kowacce ta jira. Faruk. Ba cikin haske kawai ba, ba cikin ruwa kawai ba amma cikin jikinsa na gaskiya. Ya takowa cikin shiru, ruwan yana bin sawunsa kamar yana girmamawa. Idonsa ya haɗu da nata, sannan ya ce cikin muryar da ta daɗe tana mafarki da ita: "Na dawo, Zainab, domin gaskiya ta gama aikinta, kuma lokacin soyayya ya dawo cikin zahiri." Zainab ta kalli sama, hawaye suka zubo mata, sannan ta yi murmushi mai kama da fitar rai amma cike da farin ciki. "Na jira wannan rana fiye da duk wata rana." Ta gudu zuwa gare shi, ta faɗa ma sa a jiki, kuma lokacin da hannuwansu suka haɗu, ruwan da ke kewaye da su ya tsaya. Haske ya zubo daga ƙwallar zinariyar da ke gefenta amma wannan karon, ta rabu biyu, ta ɗaya ta rataye a wuyanta, ta ɗaya kuma a wuyan Faruk. "Yanzu gaskiya ta sami gida biyu," Faruk ya ce cikin murmushi. "Tana tsakanin mu." Mutanen ƙauye suka farka da safe suka ga abin ban mamaki, Zainab da wani saurayi mai annuri suna tsaye a bakin rijiya, suna kallon rana tana fito da walƙiya. Babu wanda ya tambaya ko daga ina ya fito saboda a idanunsu, sun ga amsar tambayoyin da ba su taɓa faɗa ba. Daga wannan rana, Zainab da Faruk suka ci gaba da rayuwa a ƙauyen, ba kamar mutane na yau ba, amma kamar ruwan da yake saman hanya. Suna kula da ruwa, suna koyar da mutane cewa gaskiya tana rayuwa ne idan ana raba ta cikin soyayya. Idan dare ya yi, sukan zauna kusa da juna a bakin rijiya, suna kallon taurari cikin shiru. A wani lokaci, Zainab za ta ce: "Ka tuna lokacin da na ce na zama ruwa?" Faruk ya murmusa ya amsa: "Eh amma yanzu mun zama kogin gaskiya tare da ƴata." Sannan iska ta busa cikin sanyi, ruwa ya yi ƙara mai daɗi, kamar duniya tana yi musu addu’a. Shekaru da yawa sun wuce. Ƙauyen ya girma, yara sun zama manya, manya sun zama labarai. Amma gidansu Zainab da Faruk yana nan a bakin rijiya mai haske da ba ta taɓa bushewa ba. Da yake Zainab tana tare da Faruk ne bata koma cikin gidan su ba. Kowane dare, haske mai launin shuɗi yana bayyana daga saman rijiya, yana walƙiya kamar tauraro da ke cikin ƙasa. Mutanen ƙauye sun saba da shi, suna kiran sa "Numfashin Ruwan Gaskiya." Ba wanda ya san ko Faruk ne saboda yana nan kamar saurayi. A wancan shekara, lokacin da ruwan sama ya fi daɗi, aka lura cewa Faruk da Zainab sun fara yin shiru sosai. Ba kamar da ba, babu maganganu da yawa, babu tafiya zuwa kasuwa. Suna zaune tare a gefen ruwa, hannunsu a haɗe, suna kallon kogin da ke tafiya cikin natsuwa. ZAINAB Sha'awa marubuciya diggi ✍️ ✍️ WhatsApp number 08080304152 PAGE NA 19&20 Da yamma ɗaya, lokacin da rana ke faɗuwa ta bar sararin sama cikin zinariya da shuɗi, suka zauna kamar yadda suka saba. Iska mai sanyi ta busa, ta ɗauke ƙamshin ruwa, da ƙamshin furanni. Zainab ta kalli Faruk ta ce: "Na ji ruwan yana kiran, yana son komawa in da ya fito." Faruk ya murmusa, idonsa yana cike da haske. "To mu koma tare, ba a raba ruwa da gaskiya." Suka miƙe, suka ƙarasa bakin rijiya, suka jingina da juna. Sannan suka kallon sama kamar rana da wata suka haɗu a wuri ɗaya. A lokacin, ƙasa ta yi shiru. Rijiya ta fara walƙiya da haske mai ƙarfi, ruwa ya motsa da ƙarar da ta yi kama da kida. Mutanen ƙauye da suka fito suka tsaya a nesa suka ga abin mamaki haske mai launin shuɗi yana lullube su biyun, sannan sannu a hankali suka zama ruwa. Babu faduwa, babu ƙara kawai ruwa ne da haske suka haɗu, suka nutse cikin rijiya mai walƙiya. A cikin wannan haske, an ji muryar su cikin iska: "Gaskiya ba ta mutuwa… tana tafiya cikin kowane ruwa, cikin kowane zuciya da ta taɓa gaskiya." Da hasken ya lafa, mutanen suka ga cewa rijiya ta zama tamkar madubi tana nuna fuskar mutum da ke kallonta, amma da walƙiya a idanunsa. Tun daga wannan rana, duk wanda ya sha daga wannan ruwa, sai ya ji sanyi mai taushi a zuciyarsa da ƙarfi na faɗar gaskiya, da natsuwar soyayya mai tsarki. Yara suka koya cewa idan suka yi magana da gaskiya, ruwa zai yi musu murmushi. Kuma a kowace shekara, a ranar da rana ta fadi da launin zinariya, ruwan rijiya yana walƙiya fiye da yadda aka saba. Mutanen ƙauye suna cewa: "Zainab da Faruk sun dawo suna ziyartar mu, domin gaskiya tana tafiya, amma ba ta barin gida." Bayan shekaru masu tsawo bayan ruwan gaskiya ya ɗauki Zainab da Faruk, ƙauyen ya canza zuwa gari mai cike da albarka. Ruwan da suka bari yana nan ba ya bushewa, ba ya dushewa. Mutane sun koyi rayuwa cikin gaskiya, suna yin addu’a duk lokacin da suka sha daga rijiya. Amma wata rana, a lokacin da ƙasa ke amsar ruwan farko na damina, aka haifi wata jaririya. Uwarta ta haifi ta a cikin gida kusa da rijiya, kuma lokacin da jaririyar ta fito duniya, aka ji ƙarar ruwa daga cikin rijiya kamar ta yi murna. Jaririyar na da idanu masu launin shuɗi mai zurfi kamar kogin da ke cikin rana, kuma lokacin da ta yi kuka, sautin ya yi kama da ruɗin ruwa. Malamai suka zo, suka ce: "Wannan yarinyar ta musamman ce, an haife ta da alamar ruwa." Sunan da aka ba ta shi ne Zainab, don girmama wadda ta kafa ruwan gaskiya tun farko. Shekaru suka wuce. Ƙaramar Zainab ta taso da halayen da suka banbanta da sauran yara, tana jin muryar ruwa, tana ganin haske a cikin madubi. Idan ta shiga kusa da rijiya, tana jin kamar ana kiranta da murya mai laushi da soyayya. Wata rana, yayin da take wasa a bakin rafi, ta ji murya daga bayan ta: "Ruwa na kiranki, Zainab." Ta juyo da mamaki. A gabanta, wani mutum tsaye cikin suturar fari, idonsa kamar kogin da ya san hanyar gida, fuskar sa cike da natsuwa, amma cikin idanunsa akwai wani abu mai zurfi kamar yana tuna wani abu da bai taɓa manta ba. "Ni kake nema?" ta tambaya cikin rawar murya. Mutumin ya yi murmushi, ya durƙusa, ya ce cikin sanni. "Ba ni ne nake nemanki ba, Zainab Ruhi na ne." Zainab ta kalle shi sosai, zuciyarta tana bugawa cikin nutsuwa. "Na san wannan murya…" Ya ce: "Da domin ruhinki ya taɓa kirana a da, ni ne ruwa da ya riƙe gaskiyarki, kuma yanzu, na dawo ba a matsayin saurayi ba, amma a matsayin wanda zai kare ki mahaifinki." Hawayen da ba ta san daga ina suka fito suka zubo a idonta. "Mahaifina?" Ya ɗaga kai, yana kallonta da murmushi mai taushi. Zamani ya juya, amma gaskiya ta dawo da mu cikin sabon jiki, a wannan lokaci, ba don soyayya irin ta masoya ba, amma don soyayya irin ta rai da asalinsa. Ruwan kogin ya fara motsi, yana yi musu kida mai laushi. A lokacin da ta kalli ruwan, ta ga hoton mace a cikin sa, fuskar da ta yi kama da tata, amma da shekaru da hikima. tsohuwar Zainab. Hoton ya yi murmushi, ya ce: "Zagaye ya cika, gaskiya ta dawo gida." Sabon Faruk ya ɗauki jarumar Zainab yanzu ƴarsa ya riƙe hannunta yana kallon ruwan da ke gudana. "Daga yau, za mu kare wannan ruwa tare, domin gaskiya ba ta ƙarewa, tana canzawa ne kawai." Rana ta fadi cikin hasken shuɗi da zinariya. Ruwan rijiya ya yi ƙara kamar murmushi, iska ta busa ta ɗauke ƙamshin soyayya da haihuwa, da sabon rai. A wannan rana, ƙauyen ya sake zama cikin albarka domin Faruk ya dawo gida, kuma Zainab ta dawo cikin sabon siffa. Rai da mahaifi ruhu guda biyu cikin jini da gaskiya ɗaya. Gaskiya ba ta mutuwa, tana sake dawowa cikin waɗanda suka amince da ita. Lokacin da ruwan gaskiya ya sake walƙiya a rijiya, mutane sun yi mamaki amma wannan karon, ba sihiri ba ne, ba haske ba ne kawai. A safiyar ranar, lokacin da rana ta fara fitowa, aka ga wani mutum tsaye a bakin rijiya. Faruk ne. Babu haske a jikinsa kamar da, amma idanunsa suna ɗauke da nutsuwa da hikima, kamar wanda ya ga duniya daga sama. Mutanen ƙauye suka taru, suka yi masa sannu da zuwa. "Na dawo," ya ce cikin murmushi, domin wannan gari ne na gaskiya, kuma akwai wanda na bari a nan." Zainab wadda yanzu ta girma, tana koyarwa a makarantar ƙauye, ta fito da sauri. Idonta ya sauka kansa lokaci ya tsaya. "Faruk…" Ya yi murmushi cikin natsuwa, ya ce: "Eh Zainab wannan karon ba don ruwa ba, amma don rayuwa, ruwan gaskiya ya nuna min cewa gaskiya ta fi kowane sihiri kuma gaskiya tana cikin neman ilimi, aiki, da kyautatawa. Hawayen farin ciki suka zubo mata. Ta ce cikin sanyi. "Na jira wannan rana, amma na yi alkawari ban tsaya ba na ci gaba da karatu, saboda na gane gaskiya tana cikin ilimi." Faruk ya kalli makarantar da ke gefe, in da yara ke karatu da dariya. "Wannan ne ruwan gaskiya na yanzu," ya ce. "Ruwa da ke tsarkake zukata ta hanyar ilimi." Daga wannan rana, Zainab ta ci gaba da karatunta, ta tafi jami’a a babban birni. Ta karanci kimiyyar ruwa da ruwa da muhalli, saboda ta san ruwan gaskiya bai zo don soyayya kawai ba, amma don ya faɗakar da mutane su kula da albarkar ruwa da gaskiya a duniya. Faruk kuwa, ya zauna a ƙauye, yana kula da rijiya da makaranta. Ya zama kamar uba ga yara yana koya musu yadda za su girmama ruwa, su riƙe gaskiya, da yin aiki da amana. Idan Zainab ta dawo hutu, sukan zauna tare a bakin rijiya da daddare. Ta kan ba shi labarin abubuwan da ta koya, shi kuma yana gaya mata hikimomin da ya samo daga ruhi da tafiyarsa. Wata rana, Zainab ta ce: "Na gane, Faruk, au na manta Babana ruwan gaskiya bai zo don ya sa mu ɓace cikin sihiri ba ya zo don ya koya mana mu zama mutane masu gaskiya." Faruk ya yi murmushi, ya ce: "Da gaske ne, gaskiya ita ce ilimi, Ilimi kuma shi ne hasken da ba ya ƙarewa." Mutanen ƙauye suka ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da nishaɗi. Ruwan rijiya bai bushe ba, makaranta ta faɗaɗa, yara suna karatu cikin farin ciki. A kowanne bangare, ana jin labarin Zainab da Faruk ba kamar tatsuniya ba, amma a matsayin darasi. Soyayya tana wucewa, gaskiya tana rayuwa, amma ilimi shi ne hanyar da gaskiya ke tafiya. A ƙarshen shekara, lokacin da Zainab ta kammala karatu, ta dawo gida ta buɗe makarantar ruwa, ta koyar da yara yadda ruwa ke rayar da ƙasa, yadda gaskiya ke rayar da zuciya. Mutanen ƙauye suka taru suka yi shagali. Faruk ya kalli Zainab ya ce cikin murmushi. "Kin ga, ruwan gaskiya ya dawo gida da gaske a cikin zuciyar ki, da a cikin ilimin ki." Zainab ta ce: "Ilimi shi ne ruwa, gaskiya ita ce tafarkinsa." Rana ta faɗi cikin walƙiya, yara suna dariya, ruwa yana gudana. Ba a ji sautin sihiri ba, amma an ji sautin farin ciki domin wannan karon, ruwan gaskiya ya zama ilimi da rayuwa. Ƙarshe: Gaskiya Ta Zama Ilimi Faruk ya dawo gida, Zainab ta ci gaba da karatu, ruwan gaskiya ya koma zuciyar mutane. Alhamdulillah Alhamdulillahi Alhamdulillahi Allah na gode maka da ka nuna min gama wannan littafin lafiya Duk mai son littafina ya yi min magana da wannan number 08080304152 Mai son kirana dan kulla alaƙa ya kira ni wannan number Amma dan Allah kar namiji ya kira ni saboda ina da jarumin jarumai Allah ya sa kun fahimta. 08084277827 Ina godiya sosai Allah barmu tare Nice taku har kullum sha'awa marubuciya diggi ✍️ ✍️ Kar wanda ya kirani idan yasan ba data zai turamin ko kati ko kyautar kuɗi zai ban ba atoh🤪🤪 Mu kasance a cikin littafin mu na gaba. Mai chakwakiya rikitarwa da ilmantar kai har da faɗa karwa Littafi mu nagaba shine AMRAAH in sha Allah.