[04/12 09:41] Meela Adeel: 1⃣ ° *ZUMUNCINMU A YAU* ° By Aysha Ya'u Kurah *FIKRAH WRITERS ASSOCIATION* '''BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM''' Sadaukarwa ga mahaifi na kwarai *LATE ALHAJI YA'U KURAH* Allah SWT ya jikanka ya kai rahama kabarinka.. *SHIMFIDA* "Assalamu alaikum" Ta faďi karo na uku cikin siririyar muryarta, cikin ďaga murya taji ance, "Wai wacece ta ke ta kwaďa mana sallama ne haka?!" A hankali jikinta na rawa ta amsa. " Ni ce." "Tooo!! Sannu NI CE, me ya kawoki?" Cikin rawar murya ta ce "Mamma ce ta aikoni in kawo muku abinci." Daga cikin ďakin ta jiyo muryar dattijon wanda ya bata tabbacin shima yana ciki. "Toh ki ce an gode, je ki ďauki naira ashirin a saman tagar ďakina kiyi gaba." A hankali ta sauke ďankwalin da aka ďaure kayan a ciki ta kwance ta fito da sababbin samirun tuwo da miya ta cire ďankwalinta tace "Nagode BAFFA, Allah ya saka da alkhairi." Ta ďauki ashirin ďin ta fita cikin k'unan rai. A hanyar da zata sada ta da kofar gida taci karo da su Husna rik'e da manyan kuloli suna tafe suna nishi da kyar, rab'ewa tayi ta basu guri dan su wuce, suna karasowa dab da ita suka kwashe da dariya haďe da faďin "Nadiya roba-roba." Badariyya ta ajiye kular hannunta ta shafi kayan jikin Nadiya tace "Kaiii!! Wannan ba roba bace rai fess ce." Suka sake tintsirawa cikin shakiyanci suka ce "Su Nadiya bana an samu canji, daga atamfar roba zuwa shaddar roba." Cikin sanyin jiki tayi gaba tana jiyo ihunsu har suka shige cikin gidan. Tana fita tayi tafiyar minti biyar sannan ta isa titin da zata roki masu mota su ďauketa da naira ashirin ďin da aka bata, dan in tace zata tafi gida a kafa sai ta kai yamma saboda nisa, zuciyarta cike take da mamakin yadda zumuncin zamani ya koma, tun tana karama ta ga mahaifiyarta na fuskantar irin waďannan wulakancin saboda kasantuwarsu talakawa, sau tari takan tambayi mahaifiyarta anya Baffa ne ya haifeta kuwa? Acikin gidan kuwa, su Husna na shiga babu ko sallama suka faďa ďakin, zabura Baffa yayi ya sakko daga kan gado yana faďin. "Lale da matana, lale-lale." Badariyya ta faďa jikinshi tana faďin "Kakus, ina barka da Sallah na?" Cikin rawar jiki yasa hannu a aljihu ya ciro yan ďari biyar-biyar sababbi ya k'irga goma ya bata, yatsina fuska ta yi tace "Haba kakus, dubu biyar fa ka bani, ni gaskiya sunyi min kaďan Pizza kaďai zanci da su." Washe baki ya yi yace "To yar lele, an gama." Ya karo mata wasu biyar ďin ta mike a jikinshi babu ko godiya sai ma faďin "Ko kaifa, ai da na sake ka yanzun nan,,, Husna ta matsa kusa dashi tace " Saura ni kakus." Dubu goman itama ya bata saboda yasan sakon barka da sallan shi na tafe don tun safe y'arshi mafi soyuwa a gareshi ta kirashi tace zata aiko MUSADDIQ da sak'o, yasan sakon bai wuce na kuďi. "Ina yayanku? Ko ba tare kuka zo ba?" Baffa ya tambaya yana gyara aljihu. Badariyya tace "Ka ji kakus a kofar gidannan fa muka sameshi, yana fita muna shigowa dan ya riga Nadiya fita ma." Kallon mamaki yayi musu yace "Aiko bai shigo ba." Goggo ta rufe kular da ta bude ta ce "Kasani ko ya manta da wani abu ne?" "Hakane kuma." Ya faďi tare da basar da maganar. Nan suka hau hira da ciye ciye, sun ma manta da samirun tuwon da Nadiya ta kawo saboda sunsan babu wani abun arziki a ciki. Zaune take tayi tagumi tana jiran shigowar Nadiya dan tasan in Allah Ya yarda zata samu ko ďari biyar ce a gurin su Baffa na barka da sallah, Zainab ce ta taso rike da robar abinci tace "Mamma zan kara abinci." Janyota ta yi jikinta tace "Yi hakuri auta, yanzu Anti zata dawo har madara ma sai kisha in kinaso kinji?" Gyaďa kanta tayi cikin murna ta kurawa kofar gidan ido tana jiran b'ullowar yayarta. A gajiye ta shigo gidan ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi, da sauri Zainab ta mike ta ďauko mata ruwa, karb'ar ruwan tayi haďe da janyota jikinta tace " Kin ci abinci?" D'aga mata kai tayi, "Eh naci amma ban koshi ba. Mamma ta ce zaki kawo kuďi a siyo min madara." A hankali ta ďago jajayen idanuwanta ta sauke kan mahaifiyarta, kallon tausawa juna sukayi sannan suka kau da kawunansu, cikin sark'ak'ak'k'iyar murya Nadiya tace "Mamma na kai musu, Baffa ya bani naira ashirin, ki tayani yi mishi godiya dan ya taimakamin, da a kafa zan dawo gida." Cikin b'oye b'acin rai Mamma tace "Kai madallah!! Allah ya biyashi da aljanna, gaskiya naji daďi, tashi maza kije kiyi sallah." Tana kokarin mikewa taji anyi sallama, juyowa tayi haďe da amsa sallamar, suna haďa ido tayi saurin kau da kanta, Mamma ta mike cike da murna tace "Maraba da Musaddiq, yanzu kake tafe?" "Eh Mamma ina wuni." "Haba dai daga tsaye?" Ta faďi haďe da shimfiďa dadduma. Zama yayi yana sosa k'eya suka gaisa sosai, kuďi ya zaro a aljihunshi kusan dubu dari biyu yace; "gashi inji mummy tace a kawo muku" bai jira jin me zata ce ba ya ajiye kuďin ya fice daga gidan da sauri dan yasan in ya daďe a gidan to asirinshi zai tonu.. Kasa tab'a kuďin tayi saboda firgici Kai anya Musaddiq yaji inda aka aikeshi da kyau kuwa? Wannan kyautar tayi yawa dan tsakanin ta da yar uwarta bai wuce kyautar dubu biyar, "Nadiya mik'o min wayar can" tace tana mai nuna ma nadiya wayar, da sauri ta ďauko ta mik'a mata. Hannu na rawa ta fara neman lambar yar uwarta, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ďaga cikin isa da tak'ama, murya na rawa Mamma tace "ina yini Hajiya" "lafiya" kadai tace murya can k'asa, bata damu da amsawar ba dan in da sabo ta Saba, sai ta cigaba "yanzu Musaddiq Ya kawo min sak'o shine nace bar..." Dakatar da ita tayi ta hanyar cewa "ina da abin yi Suwaiba nasan godiya kika kira kiyi, bakomai yiwa kai ne" tayi saurin kashe wayar, cikin mamaki ta ajiye wayar tana duban kuďin zuciyarta cike da farin cikin yar uwarta ta fara sanin muhimmancin zumunci.... Musaddiq na fita ya nufi motarshi ya kashe wayoyinshi ya ta da motar yayi gaba yana nazarin yadda zaiyi ya fahimtar da mahaifiyarshi da kakanninshi muhimmancin zumunci, A kullum yana mamakin yadda zumuncin zamanin yanzu ya zama sai in kana da kuďi, yana takaici matuka saboda irin wulak'ancin da Mamma suwaiba da ya'yanta ke fuskanta saboda kawai basu dashi, bashi da wani burin da ya wuce yaga kan zuri'arsu ya haďu, Mai shi ya taimaki mara shi, amma kullum abun k'ara lalacewa yakeyi saboda masu shi ďin basa taimakawa na jikinsu saidai na neman suna.. Mrs Tijjani Shattima... [04/12 09:42] Meela Adeel: 2⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° BY Aysha Ya'u Kurah                "Nadiya amshi maza kira min yayanku, cike da murna ta karbi wayar ta latso number, Yana zaune ya kifa kanshi a wheel barrow yana tunanin ta inda zai fara, 'Dan kudin dakon da ya samu na Sallah shi ya had'a yayi ma kannenshi kayan sallah, ragowar ya ba mahaifiyarshi tayi abincin sallah, karar da wayarshi keyi ne ya dawo dashi cikin duniyar tunanin da ya tafi, hannu ya zira cikin aljihunshi ba tare da ya d'ago ba ya danna ya Kara a kunnenshi, Assalamu alai-- "hello Ya Hafiz ta katse shi cikin kaguwa, dago kanshi yayi  cikin firgici yace "Nadiya Lafiya,? fizge wayar mamma tayi tace "Hafizu kana Ina ne, duk abunda kakeyi ka barshi ka dawo gida, mikewa yayi da sauri ya Sanya silifas dinshi, ya kalli abokin aikinshi yace "Haladu dan Allah ka Mik'a min baron nan gidan oga lukman in har ban dawo da wuri ba,  Haladu yace "lafiya dai ko, "walhy ban sani ba mamma ke kira na, ya karasa fadi yana tafiya da sauri , "Allah yasa lafiya haladu ya fadi da karfi dan Hafiz ya kusa karya kwana, zuciyarshi cike take da fargabar abinda zai je ya tarar a gida... Hello Baffah, an yini lafiya, baki har kunne baffah "yace lafiya lau ya sallar, "sallah alhamdulillah, "Dan Allah Baffa kace ma su Husnah su biyo MUSADDIQ na aiki Haruna driver, to bakomai daga ya karaso zansa su taho saboda dare, "kana nufin har yanzu bai zo ba baffah, baffah yace "eh to sunce min sun ganshi d'azu amma ni har yanzu bansa shi a idona ba, ikon Allah ta fadi hade da gyara zama, ya rigasu fita gida fa, kuma saida na mishi kashedi akan yawo, Yanzu haka yana can gurin abokan banza, amma dai ya basu sak'onka ko? , "ko kusa bai basu ba, baffah ya fadi had'e da yak'e wanda yafi kuka ciwo dan ya kosa yaji makwafin kudin da ya ba jikokinshi da Karin wasu a aljihunshi, "karka damu baffah bari in kirashi inji inda ya tsaya, "too bakomai Kar dai ki matsa mishi kin San yaran yanzu saida lallami, haka ne baffah nagode a gaida Goggo,"to zata ji Nima na gode,.... Kiran Musaddiq ta shiga yi, abin ya d'aure mata kai da taji wayoyin shi a kashe, lallai yau zan bala'in sab'a ma Yaron nan, duk fadan da na mishi akan shirman partyn nan baiji ba ko, Allah ya kawo shi gida wallhy Mai rabani dashi sai Allah ta wurga wayar cikin jaka ta d'auki gyale da mukullin mota ta fita... "ji nake kamar a mafarki mamma, shafar kudin ya sake yi yace "ban taba tunanin zan rike irin wadannan kudin ba a rayuwata, Mamma da farin ciki ya mantar da ita damuwa da yunwa tace "kaidai bari, Allah kenan maji rokon bawa, duk yadda mutum ya kasance cikin kunci da bakin ciki to in ya dogara da Allah sai ya samar mishi mafita,, Hafiz yace "haka ne mamma, to yanzu ya zamuyi da kudinnan, "shi nake tunani hafizu, mu jira babanku ya dawo sai musan abin yi dashi,   dubu biyu ta ciro cikin kudin tace je kayo mana cefane da wannan muyi abinci kafin ya dawo, Zainab da ke kwance Kan cinyar Nadiya tace "anty Madara ta, Nadiya tayi dariya tace "kiyi hakuri yanzu za'ayi abinci muci, mamma na jinsu tayi kamar bata ji ba tace, "au Hafizu na manta ka siyo ma auta Madara kaji, Nadiya tayi murmushi tace kamar kinsan maganar da takeyi kenan, Mamma tace au haba, taho auta ta kinsan ni namiki alkawari kuma bazan manta ba,,                    haka suka kasance cikin farin ciki a ranar, ji sukeyi kamar babu kamar su a doron duniyar Allah SWT,                     Allah sarki, kud'in da bai wuce kudin naman wani gida ba shi ya Sanya bayin Allahn nan murna har suke Jin babu kamarsu...... Mrs Tijjani Shattima... [04/12 09:42] Meela Adeel: 3⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° BY Aysha Ya'u Kurah *******10:56pm****** Zaune yake cikin motarshi kafafunshi duk biyun na waje yana latsa wayarshi da ko minti uku baiyi da kunnata ba, text din mummy ya karanta yayi d'an murmushi had'e da shafa kwantaccen sajenshi, rufe wayar yayi ya sake duba agogo,… gyara zamanshi yayi ya rufe motar yace "na tabbata yanzu mummy ta isa k'asar Singapore ita da k'awanta cikin mafarki, tada motar yayi ya karaso kofar gida, kiran mai gadin su yayi a waya dan ya bud'e mishi gate,  yana tsoron latsa hon ya dawo da mummy cikin kasar Nigeria, da sauri Mai gadin ya bud'e mishi,  ya shiga yayi parking a gurin da aka tanada dan ajiye Motoci, Kiran waya ya shiga yi kafin ya karasa kofar parlon.. Badariyya na zaune tana buga game taji land line din dakinsu na Kara, pause ta danna ta Mik'e tana tsaki, "hello.. ta fadi cikin muryarta Mai cike da izza da isgili, "hey Badar zo ki bude min kofa kuma kiyi a hankali Kar mummy ta jiki kin gane ko, katse wayar tayi ba tare da ta amsa shi ba ta juya ta fita daga d'akin,  d'akin mummy ta nufa, bud'e kofar tayi ta shiga ba tare da tayi sallama ba, dan a ganin Badariyya sallama ta talakawa ce,, hasken da ya gauraye d'akin ne ya farkar da mummy daga bacci, Mikewa tayi hade da mik'a tace "BADAR lafiya, yaya Musaddiq ne ya kira ni wai in bud'e mishi kofa.... Bawan Allah yana waje yana jiran Badariyya ta bud'e mishi kofa, ganin da yayi har minti 5 ta wuce bata bude ba ya fara mita cikin zuciyarshi, d'aga wayar yayi da niyyar sake kira yaji ana tab'a kofar, tura wayar yayi cikin aljihu ya k'arasa kusa da kofar fuskarshi d'auke da murmushi, "ina kika tsaya ne haka, har hakuri na ya fa---- maganar ta makale mishi a mak'oshi sakamakon ido hud'u da sukayi da mummy, zaro ido yayi ya had'iye wani mugun miyau, dariya ya fara yi yana fad'in mummy baki kwanta ba, tun d'azu Ina nan k'ofar gida a zaune ni da Tinau Mai gadi yana bani Labarin k'auye, sannan malam--- juyawa tayi ta barshi a tsaye, shigowa yayi ya rufe kofar ya bi bayanta da gudu, can gefe ya hango Badariyya tsaye tana mishi kallon raini, harara ya jefe ta dashi yace "tun kina yar ficiciya kin iya munafurci da makirci Ina ga in kin girma, wallhy kinji haushin rayuwar ki idiot,, tsaki taja ta wuce d'akinsu,, Kofar dakin mummy ya karasa, a hankali ya murd'a kofar ya shiga had'e da sallama, kusa da ita yaje yayi kneel down ya kamo hannunta yace "kiyi hakuri mummy, wallahi ba party na je ba, ina gidan su Mahmud tun da na fita daga gida, sai dare na bar gidansu na dawo kofar gida na zauna, Dan Allah kiyi hakuri banason wannan fushin please ya karashe a shagwabe,, bata tanka mishi ba ta zame hannunta cikin nashi tace "bani,, zuciyarshi na dukan uku uku yace "me zan baki?, K'ara tamke fuskarta tayi tace kud'in Baffa da na aike ka dashi, dakewa yayi yace "ni gidan mama suwaiba kika aikeni saidai ko driver kika aika gidan Baffa, "karka raina min hankali Musaddiq, kalleni da kyau banyi girman da zan fara mantuwa ba, dubu biyar na baka ka kaima "SUWAIBA" dubu d'ari biyu na Baffa, sai dubu Hamsin na k'anwar k'awata "Hajiya Nafeesa dake layin su suwaiba, bud'e baki yayi yace "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, mummy ai banji duk lissafin da kika min ba, ni dai sunan mama suwaiba kad'ai naji, na bata dubu dari biyu da biyar, ga dubu hamsin nan a aljihuna na manta inda kika aikeni dashi, karki damu gobe in shaa Allah da wuri zan kai mata, kika ce gidanta na kusa da gidan mama suwaiba ko? Wani mugun kallo ta bishi dashi had'e da taune leb'enta, matsawa baya ya fara yi dan yasan in mummy ta fara taune leb'e to abin da zai biyo baya bazaiyi kyau ba, dai dai kofa ya tsaya kamar zaiyi kuka "yace mummy kiyi hakuri dan Allah, cike da takaici tace "Musaddiq Anya rayuwar da ka daukarwa kanka Mai b'illewa ce, ka zama almubazzari Wanda baisan darajar kudi ba, in ba iskanci ba me suwaiba zatayi da dubu dari biyu harda d'oriya, wallhy tun muna mu biyu da kai gobe kafin goma na safe kaje ka amso min kudi na, kuma ka tabbatar ka kaima Hadiza kanwar Hajiya Nafeesa kana ji na ko, gyad'a kanshi yayi fuskarshi da bata cika nuna fushi ba ta canza launi saboda tsananin b'acin rai, Takalmin kafarshi ya cire ya kwanta yayi ruf da ciki yana tunanin yadda zaiyi ya samu dubu d'ari biyu gobe ba tare da yaje gidan mama suwaiba ba, Sai karfe daya ya yanke shawarar Kiran yayyenshi mata ya fad'a musu komai yasan a cikinsu bazai rasa Mai bashi ba..... Mrs Tijjani shattima.... [04/12 09:43] Meela Adeel: 4⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah Kamar a mafarki yaji ana bugun kofar dakinshi, mikewa yayi akan dardumar da bacci ya dauke shi bayan sallar asuba, mik'a ya fara yi hade da addu'ar tashi daga bacci, kara buga kofar da akayi ne ya sashi kallon agogo, goma saura kwata ya fadi da karfi yana mai karasawa kofar dakin, murda kofar yayi a hankali  ya ja da baya hade da runtse idanuwanshi saboda tsoron irin kallon da zaiyi Karo dashi...    *HAPPY 17TH BIRTHDAY BROO* Muryoyin su ya daki dodon kunnenshi, bude idonshi yayi da sauri ya bisu da kallo daya bayan daya, wani murmushi ya saki mai matukar kyau, take ya manta da damuwar da ta hanashi bacci ya fara rungumarsu yana fadin "thank u so much sweeries,, " Happy womb escape uncle"  ya jiyo cikin siririyar murya, ''omg HINAD!! ya fadi da karfi, murmushi tayi mishi hade da yi mishi nuni da hanyar shigowa dakinshi da idanuwanta,, Ta madubin console din dake kallon dakinshi ya hangota tsaye cikin shigar jallabiya ta alfarma kanta yane da jan mayafi ta nade hannayenta a kirjinta tana murmushi, ihu ya saki hade da kwasawa a guje ya nufi gurinta, bude hannuwanta tayi ya fada kirjinta, "Best birthday gift eva luvly sis, I love u so much, dago fuskarshi tayi ta cire farin glass din Idonta tace ''Happy birthday little Diku nah, love you more,, karasowa suka yi cike da mamaki suka ce ''saukar yaushe ANTY REEMA, ''yanzun nan!, ko gida banje ba, ta fadi tana maida glass dinta,   waigawa musaddiq yayi gurin Hinad ya lakace hancinta yace ''cutie pie ina handsome? yamutsa fuska tayi tace yana mota wai bazai shigo ba, dalili? Musaddiq ya tambaya yana kallon Anty Reema, ''don't ask me kasan halin d'an naka, kallon Sauran kannenta tayi tace mummy fa?, RADIYA ce ta fara magana, ''muma zuwan mu gidan kenan, ina ga bata tashi ba, hannun RAUDHA ta kama tace ''ina kika baro WALEED,? ''yana gidan Anty RALLY can yayi sallah, nasan suna hanya yanzu,, Raudha ta bata amsa cike da girmamawa, falo suka koma dukkansu banda musaddiq da tuni ya fita gurin HILAL.... Maganata ta karshe kenan babu wanda ya isa ya sake dawo da ita farko, bazan mishi party ba wannan shekarar FAKAT!!! mummy ta karashe fadi tana hararar musaddiq dake zaune kanshi a sunkuye, but mummy why,?  RALIYA da shigowarta kenan ta tambaya tana karasowa parlon, tsaki mummy taja ta tashi ta wuce kitchen, Radiya da Raudha kuwa mamaki ne ya hanasu magana dan a iya rayuwarsu sunsan babu abin da mahaifiyarsu ke so sai bidi'a, haka nan ma kirkirar party takeyi in kudi yayi mata yawa, babu d'a, ko jikan da shekara ta taba wucewa ba ayi mishi kwarya kwarya ba, barin ma danta d'aya namiji tilo wanda partynshi ke banbanta da na kowa, shiyasa sukayi sammako dan ayi komai dasu,  ''wow MIRACLE ya sakko kenan, yau mummy ce da kanta take cewa bazata yi ma little birthday ba, iko sai Allah Anty Reemah ta fadi tana mai mikewa, Raliya tace ''kedai bari anty na Kasa ajiye jaka saboda mamaki,, '''Ba abun mamaki bane laifi yayi ma mummy''' waigowa sukayi suna kallon ta inda maganar ta fito, karasowa tayi rike da cup a hannunta tace ''kwarai kuwa, almubazzaranci yayi da kudin mummy, ta aikeshi ya kaiwa Baffa shine ya kai gidansu Nadiya Roba Roba, kuma kudin da yawa  har 200k, mikewa musaddiq yayi a fusace yayi kanta, rikeshi Anty Reemah tayi da sauri ta girgiza mishi kai alamar ya kyaleta, Badariyya ta rike kugu tace da kin kyaleshi anty, karya akayi maka, mtswww wanda bais----''shut up'' Anty Reemah ta katseta da karfi,, ''yaushe yarinyar nan ta fitsare haka, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, duka nawa kike Badar?, Musaddiq sa'an ki, ''Ba sa'a na bane amma abin da zaiyi ni bazanyi ba, dan Sam bashi da hanka----- wucewar walkiya da tsayuwar ji na wucin gadi ne ya hanata karasa maganar, rike kuncinta tayi ta Sanya kara mai firgitarwa, cike da firgici su Radiya suka karaso gurin, kallo anty Reemah ta bishi dashi yana huci hade da zazzaro ido, cikin zafi yace ''I usually give people more chances dan dey deserve, but once am done am done,! waye sa'an ki anan, tun dazu kina ta zuba rashin kunya an kyaleki shine kike kokarin wuce limit dinki, ya kalli musaddiq cikin kunan rai yace ''kanwar kanwarka ta tsaya tana fada maka magana kai kuma kana tsaye kamar gunki, u'r pathetic wallhi mtswwwwwwwww, yaja tsaki hade da daukar wayarshi yace ''wannan dalilin ya hanani shigowa gidan nan, kallon Anty Reemah yayi yace  ''plss lets go Mum,, faduwa kasa Badariyya tayi tana ihu tana shureshure tana fadin ''Allah ya isa mugu azzalumi, wayyo Allah na mummy ya tsinka min kunne, da gudu mummy ta karaso ciki dan duk budurin da akeyi bata sani ba tana can bayan kitchen tana duba masu yi mata hidima..... Mrs Tijjani Shattima.... [04/12 09:43] Meela Adeel: 5⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah Ya ya, me yake faruwa? kukan wa nakeji kamar Badar, da gudu ta ruga jikin mummy, Hilal ya bita a guje ya daga hannu zai kai mata duka mummy ta daka mishi tsawa, ''kulll karka sake ka taba ta, rasa kunya berar danga, ko girgiza baiyi ba bare ya saurari abinda ta ce ya sauke hannunshi a bayanta, wani ihun Badar ta sake saki kamar wacce ake yankawa, kallon gurin da suke mummy tayi cikin bacin rai tace' ''Reemah dan iskanci kina tsaye danki zai raunata min 'ya, babu Wanda yayi yunkurin hanashi, kuma saboda rashin ta ido ya iya Zuwa har gabana ya narka mata gudumar hannunshi a baya, to wallhy bazan dauka ba, ko ki rama mata ko kuma ni in rama mata da kaina, Raliya tace ' ''haba mummy, ya za'ayi mu shiga fadan yara, Badar ce fa bata da gaskiya, rashin kunyarta kullum dad'a k'aburi yakeyi, babu Wanda ya isa ya fada mata taji, daga fitowarta babu ko gaisuwa ta fara magana cikin isa da rashin kunya, thank God akwai Hilal a nan,  da dukan da zan mata wallahi sai yafi haka, mummy ta saki baki cikin mamaki tace me tayi ne waiii, Husna ta kwashe duk abinda ya faru ta fada mata, mtswwwwwwwww mummy taja tsaki tace ''to karya ta fada, duk Wanda yaga musaddiq yasan baida cikakken hankalin zaman duniya,, Sam baisan inda yake mishi ciwo ba, bai San darajar kudi ba saboda baya nemosu, kashesu kadai ya iya yi, da yasan darajar kudi bazai daukesu ya kaisu muhallin suwaiba ba saboda bata da bukatarsu, bata ma San me zatayi da su ba, bai San su kudi ana kaisu inda in suka shiga zasu fito da mafiyinsu ba, a'a kawai shi ga mai tausayin banza ya dauki zunzurutun kudi ya kaiwa suwaiba, K'ara kaurara murya tayi tace "wallhy tun muna Shaida juna ka fita kaje ka karbo kudin nan, kafin wani azal ya afka musu, ka bar mata dubu biyar din da na saba bata kuma ka tabbatar ka kaima kanwar Hajiya Nafeesa kana Jina ko,? kasa dago kanshi  yayi saboda kwallar da ta taru a idonshi, wani karamin tsaki Hilal yaja yayi waje cikin kunan rai, Kiyi hakuri mummy, Anty Reemah ta fadi cikin taushin murya, hakuri daya zanyi inji kudi na a hannuna, Radiya da Raudha suka kalli musaddiq suka ja tsaki, Radiya tace ''haba little dubu dari biyu fa, kaima kasan kayi rashin hankali, mutanen da duk iya rayuwarsu basu taba rike dubu goma ta kansu ba, "Raudha miko min wayata maza in kira mama suwaiba dan Kar ma ganin kudin ya sa su kirkiri amfani da shi, dan su kudi kana ganin su amfaninsu ke zuwa ko ba budget, gara ko man Mota mu Sha dasu Kinga sunyi mana amfani, dauko wayar Raudha tayi ta fara latsawa, ''ba sai kin kira ba Raudha ga kudin nan nazo dasu ta fada cikin sanyinta had'e da karasa shigowa cikin parlon, ajiye zainab tayi ta tsuguna har kasa ta gaida mummy, ta ciro kudin cikin jaka ta mik'a mata tana murmurshi, tun bayan tafiyar musaddiq ban yarda aiko shi kikayi ba, nasa a raina ko mantuwa yayi shiyasa na biyo baya, da na kiraki kika tabbatar min kin aikoshi sai na ajiye har Malam ya dawo shine yace in dai kawo in tambaya da kaina, tunda na doso naji maganganu sai na tabbatar mantuwa yayi ya kawo, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, ameeeen!!! mummy tace hade da karbar kudin, Matsananciyar kunya ce ta lullube Reemah da Raliya, Musaddiq kuwa daki ya wuce ba tare da ya dago kanshi ba hawaye sai ambaliya suke a idonshi ,, dambun kifi mama suwaiba ta dauko a Jakarta ta ajiye a Kasa kusa da mummy tace ''gashi ba yawa da fatan kunyi sallah lafiya, ''kalau suwaiba,! to alhamdulillah Allah ya Maimaita mana, "ameen ya Allah" mummy ta fadi ta wuce daki rike da kudinta a hannu, waigowa mama suwaiba tayi fuskar nan dauke da murmushi tace duk Ina kwananku, da sauri anty reemah ta karasa gabanta tace Ina kwana mamma, lafiya lau Ant--Dan Allah ki daina cemin anty mamma, Reemah ta katseta da sauri, murmurshi tayi tace to na daina, yaushe kuka zo,? hannun zainab ta kama tace "dazu muka zo ina su Nadiya da Hafiz, Hafizu ya tafi gurin aiki Nadiya kuma tana gida, yau bata zo mana yawon sallah ba, Raliya ta fadi tana karasowa gurinsu, har mun shirya tace Wai kanta na ciwo shine nace tayi zamanta a gida, nan suka shiga taba hirar yaushe gamo da anty Reemah da bakin ciki da kunya sukayi mata katutu a zuciya, kallon fuskar mamma takeyi wacce kyawu da fara'a suke boye ainihin bacin ranta, Mama suwaiba jarumar mace ce mai tsananin kawaici da boye bacin rai, kullum fuskar nan cikin murmurshi take...... Kad'an daga cikin abubuwan dake faruwa cikin zuri'ar mu kenan anty, laifin duk na su Baffa ne, su suke nuna fifiko saboda abin duniya, soyayyar abin duniya ta rufe musu ido sun mance taimakon Yan uwansu na jini sai dai bare na neman suna,, har ga Allah nayi niyyar kaiwa Baffa kudin dan na je har gidanshi, abin da naga sun ma Nadiya shi ya karya min zuciya har zuciyar ta rinjaye ni da aikata hakan, bansan abin zai kwabe haka ba, da ban kai ba, da na jira dawowar Daddy sai in karba in kai musu, yanzu nasan "ransu bazai musu dadi ba" ya karashe cikin shashshekar kuka, share mishi hawaye tayi tace "Ya Allah ka karfafa min raguwar zuciyar Diku nah, har yanzu kana nan da halinka na kuka, lokaci ya canza Little, yanzu ka fara girma u are not a child anymore,, tashi kaje kayi wanka muje gida, akwai wani surprise din da na shirya maka, cikin sanyin jiki ya tashi ya shiga bayi,,  Tagumi Reemah tayi tana tunanin hanyar da zata bi ta wanke zukatan bayin Allahn nan, Allah ya sani bata da masaniyar halin kuncin da suke ciki, ita dai tasan suna da wadatar zucin da zaisa kullum ka gansu cikin farin ciki... Mrs Tijjani Shattima.... [04/12 09:44] Meela Adeel: 6⃣ Ayi min Afuwa pls wasu hidimdimu ne suka rike ni, Ina Mai baku hakurin jiran da kukayi nagode matuka da kauna, Ina kaunarku har cikin raina Yan uwana... In shaa Allah zaku jini kullum yanzu °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah Ashe gaskiyar babanku ne da yace kila mantawa Musaddiq yayi, hakan ce kuwa ta faru, dan kudin na Baffa ne, tayi tayi ma in amsa nace mata a'a kudin sunyi yawa, mamma ce ke maganar cikin sakayawa tana kallon ya'yanta, Nadiya dake kulla kankarar kuka, tace "nima dai mamma jiki na ya bani ba namu bane, dan dai naga kin kirata ne shiyasa na dauka da gaske ne,   Alwala Hafiz ya karashe hade da addu'a yace "mun gode Allah ma da yasa ba muyi amfani dasu ba, wannan din ma da ta bamu Allah yasa musu albarka, "Ameen mamma tace hade da mikewa ta nufi cikin daki, babu wanda a cikin su ya karanci ainihin bacin ranta saboda fuskarta dake dauke da murmushi... ****** Hey handsome duk wannan cika da batsewar na menene? Come on chill my guy, yau fa is my day banason kowa yayi fushi a cikin ta, Kara tamke fuska yayi hade da jan dan karamin tsaki ya mike yace   "bansan me ke damun zuciyarka ba, bana cika mu'amula da masu irinta saboda wata rana haushin su zai sa inyi musu tsana marar misaltuwa, u'r my uncle nd friend as well bana son abun da zaisa inji haushin ka, nowadays masu irin zuciyarka basa samun nasara a komai saboda sanyinsu, "sanyinka yasa kana namiji kai kadai a gidanku amma kowa ya rainaka harda BADAR for dat matter, yaushe aka haife su?, dey are just 9! if am nt mistaken, kuma ka tsaya a gabansu kana wani kuka, gaskiya ka bata min rai, just go nd have fun Kar in bata maka naka ran, Hilal ya karashe fadi yana nuna mishi kofar fita da hannu, "sannu ubanshi, Anty Reemah ta fadi tana karasa shigowa dakin, Hilal ka fita idona walhy, bana son iskanci, kasan inda zaka dinga nuna wannan bakar zuciyar taka, kai a kullum duk inda kaje sai Kasa mutane sun tafi da kai a baki, meye amfanin rashin hakuri, abin da hakuri bai baka ba wallahi rashin shi bazai taba baka ba, duka nawa kake kaima da kake barin zuciya tafi karfinka, wallahi kayi gaggawar sauke bakar zuciyarka har mu bar kasar nan in ba kanaso inyi mummunan saba maka ba, sakarai kawai, "haba anty sorry mana,  ba fa wani abu yace min ba, musaddiq ya fadi cikin tausasawa hade da kama hannunta, kallonshi tayi cike da son halinshi tace ko baice maka komai ba meye amfanin abun da yayi a gida, "mum nifa babu abin da nayi, kawai dai gaskiya ce bakwa so, shiyasa Sam bana son shiga gidanku saboda ni ba na gani in kyale kuma in nayi kuce nayi rashin kunya, Allah ma yasan akan gaskiya na-- rufe min baki anty reemah ta fadi hade da bige bakin a hankali, Janta musaddiq yayi suka bar dakin tanata masifar da Sam bata karbeta dan ba sabawa tayi ba, kullum cikin bakin cikin halin danta takeyi wanda Sam bai biyo halinta dana ubanshi ba, da ya tashi sai ya dauko halin mamanta har ya damata ya shanye saidai shi Sam bashi da neman suna kuma komai zaiyi sai yanada hujja... Ruwa musaddiq ya bata tasha yace "kiyi hakuri anty kin so ki bata ranki ne, kinsan halin Hilal, babu mai iya canza shi sai Allah, kuma kin San duk abin da zaiyi akan gaskiya yakeyi he is open, baya barin abu a ranshi, dole ya koyi barin abu a ranshi musaddiq, Reema ta fadi tana mai ajiye kofin da ta sha ruwa,! meye amfanin duk abun da akayi ma mutum yace sai ya rama, wani lokacin ma ba dashi akeyi ba sai ya sako kanshi saboda shi baya gudun bakin duni-- kwanciyar da taji anyi a bayanta ne ya hanata karasawa, kamshin turaren da taji ne ya sanar da ita ko waye, Kara tamke fuskarta tayi hade da Jan tsaki, cikin muryarshi ta yan gayun yaran hutu yace "ki daina gudun bakin duniya Momma na, in dai duniya muke son mu burge to lallai munada aiki babba a gaban mu, "chapter closed", am so sorry for hurting you mum, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta hade da kara kaunar dan nata, duk iya inda yakai da zuciyarshi ya tsani bacin ranta, baya daukar mintina sai yasan hanyar da yabi ya wanke zuciyarta, dariyar farin ciki musaddiq yayi "yace komai ya wuce ''aunty momma!! , murmushi tayi hade jan kunnuwansu, zama sukayi suka sata a tsakiya suna mata hira kamar babu wani abu na bacin rai daya gifta a tsakanin su,, karar da wayarta tayi ne ya katse musu hirar, zaro ido tayi ta mike tana fadin ya ilahi hade da daukar wayar, sorry Rally shaff na mance da ku, daga dayan bangaren Rally tace ai na Lura da hakan, gashi har mun gama komai, cikin farin ciki Anty reema tace kinyi komai simple dai ko, kinsan komai namu very simple muke yinshi, saima kin gani anty, abin sai ya burge ki ta fadi tana gyara balloons din da sukayi kasa kasa, ok thank u babe, gamu nan Zuwa, juyowa tayi tace kuje ku shirya ku raka ni wani guri, Hilal da ya riga ya harbo su yace ni a shirye nake mum, bata kalleshi ba ta kamo hannun Musaddiq sukayi daki, a cikin sababbin kayan da ta siyo mishi ta zaba mishi tace ya saka ta fita ta bashi guri, saida ya dau minti goma yana shiryawa, jar riga ya saka mai matukar kyau da deep blue wando, ya taje kwantaccen gashin shi, kyawun  bakar fatarshi mai sanyi ya kara bayyana, hatta madubin da ya kalla yasan babu karya shi din mai kyau ne matuka,, fitowa yayi cikin takunshi na nima na fara girma, kallon kauna anty reema ta bishi dashi tana fadin wowwww kanina, babu kamarka a wannan zamanin, gaskiya kayan nan sun karbe ka, sajenshi ta shafa tace "Allah ya nuna min aurenka dole in zauna da matar saboda kar ta cutar min da kai, Hilal ya ajiye cup din coffee yana dariya yace saboda kinsan uncle din nawa is nt brave ko, zanci ub-- toshe mata baki yayi da sauri hade da rungumeta yana dariya harda kyakyatawa, tureshi tayi tace "wallahi yaron nan ya rainani sosai, zanyi maganin ka, dariya suka saki Hilal ya dauko keyn mota Kan centre table yace oya mu wuce, Anty reema ta kalleshi Sama da kasa tace da wannan wandon zaka fita,,, pls mum karki fara muje kawai ya fadi yana wani narkewa, hmmm kawai tace ta kama hannun musaddiq suka fita Zuwa gurin Mota..... Mrs Tijjani Shattima.....! [04/12 09:44] Meela Adeel: 7⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah Mamma duba min kiga kwabin yayi haka, mamma dake kashingide ta dan mike ta kalli kwanon madarar da Nadiya ta kwaba, hannu tasa ta dan taba ta gutsuri kadan tasa a bakinta, "mmmm gaskiya yayi dadi kuma yayi danko ta fadi tana lumshe ido alamar santi duk dan ta kara ma diyarta kwarin gwiwa, murmushin Jindadi Nadiya tayi ta ajiye a kan tabarma ta shiga kitchen ta dauko leda da kwalbar da zata murza madarar, Cikin nutsuwa take murzawa tana yanka su kanana tana sawa cikin wata tsaftatacciyar robar sweet da ta amso a shagon Tasi makocinsu, hira sukeyi cikin jindadi mamma na taya ta kirga wadanda ta yanka, saida suka gama tsaf, Nadiya ta kalli mamma tace "Mamma in rokeki wani abu, mamma ta karashe rufe robar tuwon madara tace fadi kanki tsaye yar albarka, Dan Allah Mamma kiyi hakuri ki daina yin "wankau" ban taba Jin zafin masu yi min gorin kina wankau ba sai yau da Nafi'un Baba Atika yayi min a shagon Tasi, wai masu wanke daudar wasu bazasu taba yin arziki ba, Dan Allah mamma ki daina, in shaa Allahu wannan karamar sana'ar da muka fara zata dinga rufa mana asiri da dan abun da baba da yaya hafiz zasu samo, tunda ta fara maganar idon mamma ya ciko da kwalla, kauda kanta tayi ta dan share da gefen zani tace "Nadiya wanki baya kawo talauci duk canfin hausawa ne, saidai zan daina saboda in karfafa gwiwar ki tunda hakan kika bukata, sannan zamu hada da ruwan kankara saboda yayi karanci a unguwar nan, wani farin ciki ne ya lullube Nadiya tace "alhamdulillah" nagode mamma, bari inje in kaiwa Tasi dan yace ina gamawa in kawo mishi, gyada kai mamma tayi tace "a kai da bismilla Allah yasa mishi albarka, Ameen Nadiya tace tana kiciniyar sa hijab dinta, karo tayi da samari biyu suna kutso kansu gidan hade da sallama, da sauri taja da baya ta kame jikin bango saboda irin kallon da Hilal yake yi mata, tsaki yaja hade da kakkabe kayan jikinshi ya wuce, kanta a kasa ta gaida musaddiq ta raba ta gefenshi ta wuce, binta yayi da kallo zuciyarshi a karye, Allah kadai yasan irin tausaya musun da yakeyi, yarinya karama tasan wahalhalun rayuwa, muryar Anty Reemah ya jiyo tana tambayarta inda zata, sunne kai tayi tace "zanje shago ne in kai tuwon Madara, Hinad ta kalli hannunta tace "wow dan sammin, budewa ta fara kokarin yi Anty Reemah tace "kyaleta kinji na nawa ne duka, cike da Jin kunya tace "na dari takwas da hamsin ne, sai na dari ribar Mai shago, Anty Reemah tayi murmushi tace duka dari tara da hamsin kenan ko, girgiza kai Nadiya tayi tace ki bani dari takwas kawai, dubu daya ta zaro a Jakarta tace to gashi ki dauki dari takwas na tuwon Madara canjin ki siyo takalmi ki cire wannan hadi da Bautan kinji yar kasuwa, rufe fuskarta tayi tana dariya tace nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Ameen anty Reemah tace ta mikewa Hinad tuwon madarar suka karasa cikin gidan tare da Musaddiq,, Hilal suka tarar a tsaye mamma na mishi hira yana fadin umm in na a'a ne yace um um, mamma na ganin su ta karaso tana musu oyoyo, a dadduma suka zauna ta kawo musu ruwa, duk ta rasa inda zata sa ranta saboda dadin yau nata yazo inda take, me za'a dafa muku tayi ta fada kamar zata fado kansu saboda murna, Anty Reemah tace wallhy a koshe muke mamma daga gurin partyn Musaddiq muke nace bari mu biyo mu gaisheki mu kuma yi miki sallama dan inaga jibi zan koma, Ayya mamma ta fadi tana Mai zaunawa kusa da ita, har zaki koma Antyn Yara, Reemah tace eh zamu koma tare da musaddiq na sama mishi makaranta a can,, Allah sarki musaddiq zaka bamu kewa ashe, to Allah yasa ka je ka fara a sa'a, Ameen musaddiq yace yana Sosa keya, da sauri ta dawo gidan da sabon silifas a kafarta da ledar madara da suga, ajiyewa tayi a kofar kitchen tace sannunku, mamma ta kalleta kallon tuhuma tace a Ina kika samo sabon takalmi? , canji ta ciro a cikin aljihunta ta mika ma mamma tace Anty ce ta siye duka ta kuma bani kudin takalmi, shine dan sakarci baki shigo kin fada min ba mamma ta fadi rai a bace, Anty Reemah tace "kiyi hakuri mamma ni nace tayi sauri ta siyo takalmi, mamma tayi murmushi tace to mun gode fa Allah ya saka da alkhairi, Ameen anty Reemah tace tana kallon Nadiya da ke rabe tana wasa da hijabinta, ni ko mamma wace makaranta Nadiya ke Zuwa?   Mamma ta yi murmushi tace ta zana jarabawar aji shida zata cigaba da makarantar gaba in shaa Allah, to ai mamma naga har an kusa gama third term wace makaranta kuke neman mata? , mamma ta kalli gefen da Nadiya take tace makarantar kwana ta Queen Amina dake kakuri, to har yanzu bata samu bane? Reemah ta tambaya cike da damuwa, muna ta kokarin har hada abin da zata tafi dashi ne mamma ta fadi cike da Jin kunya, Anty Reemah tayi ajiyar zuciya tace mamma karatun diya mace nada matukar amfani, Dan Allah Kar ayi wasa da ita first term din nan da za mu shiga, ki bar batun queen Amina, zan ma abban Hilal magana zai sa a bata admission a fgc malali in shaa Allah, sannan ki turo min hafiz inason ganinshi gobe kafin muje gidan Baffa, Kasa rufe baki mamma tayi saboda murna, share hawayen farin ciki ta shiga yi tana kallon Nadiya dake ta dariya, kai gaskiya nagode Antyn yara, Allah ya biyaki da aljanna, nagode sosai, anty Reemah ta mike  tana fadin haba mamma me akayi ai duk daya ne, Dan Allah ki daina min godiya, Godiya ta zama dole Reemah mamma ta fadi tana rike baki, kedai kawai Allah shine zai saka miki, Ameen anty Reemah tace ta fito da dubu biyar a jaka ta bawa Nadiya tace wannan na auta ne in ta tashi kice mata gashi inji ni kinji, Nadiya ta karba ta shiga godiya hade da bayyana kyawawan hakoranta, har gurin Mota suka raka su suna ta godiya kamar bakin su zai tsinke, musaddiq mamma ta kalla tace "me kake so in kawo maka ka tafi dashi? , murmushi yayi yace koma meye mamma nagode, mamma tace to an gama dan albarka..  Hon Hilal yayi yace muje ko mum, bata bashi amsa ba sai ma harara da ta bishi dashi, mamma tayi dariya tace Hilal Allah ya kiyaye hanya ka gaida abbanka kaji, zaiji kawai Hilal yace ya tada motar sukayi gaba..... Mrs Tijjani Shattima...... [04/12 09:45] Meela Adeel: 8⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah Washe gari karfe 8 a gidan Anty Reemah tayi wa Hafiz, a kitchen ya sameta tare da Yan aikinta suna ta aikin abun karyawa, da fara'arta ta tarbeshi tasa ya wuce parlor, sai da ta kammala komai tasa shi ya karya sannan ta dawo gurinshi, Wace sana'a kakeyi? Tambayar da ta fara yi mishi kenan, kanshi a kasa yace "dako nakeyi da wheelbarrow, wheelbarrown naka ne? Ta sake jefo mishi tambaya, a'a ya fadi yana mai girgiza kanshi, haya nake daukowa duk yini dari uku nake bashi, Good anty Reemah tace tana gyara zamanta, Hafiz ka saurare ni da kyau kanaji ko, gyada kanshi yayi yace inajinki anty, da farko dai zanso insan sana'ar da kake sha'awar yi, ka ture batun dako, dan banga amfanin sa ba, sunne kai yayi yace walhy anty bani da wani idean sana'a yanzu sai dai in kika bani shawara bazanki dauka ba, ajiyar zuciya tayi tace "to akwai mijin kawata a railway station yana sana'ar fruits, zan mishi magana in hadashi da kai sannan zan baka jarin da zaka tsaya da kafafunka ka rike mahaifanka da yan uwanka, basu da kowa a duniya sai kai Hafiz, hakkinka ne ka kula dasu da ilimin su, nasan kana nema, rashin Jari ne ya taushe ka amma inada yakinin in na baka zaka kula da hakkinsu, Dan Allah Hafiz karka bari suyi kuka da kai ko ba dade ko ba jima na rokeka da Wanda bama gani amma shi yana ganin mu, mikewa daga zaunen da yake yayi ya durkusa yace wallhy zan rike amanar su in ban rike amanarsu ba tawa zan rike, nagode sosai anty Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen anty Reemah ta fadi ta dauki wayarta ta kira Hajiya Maryam, sun dade suna magana sannan sukayi sallama, tace "gobe in shaa Allah zaka fara Zuwa ka koyi yanda sana'ar take, zan turo maka kudin a account dinka, in baka dashi ka bude dan gara in baka su a hannunka, Allah yasa ka fara a sa'a, Ameen ya Allah nagode kwarai Allah ya kara daukaka, Ameen ameen Hafiz ban kuma ce ka fadawa kowa ba, ka rike shi sirri a tsakanin mu, angama anty babu wanda zaiji in shaa Allah, nan suka dan taba hira har kusan goma yayi mata sallama ya tafi cike da farin ciki.... Duk nuku nukunki sai kinje Nadiya, Baffa mahaifina ne duk abin da yake min badan baya sona bane tunda shi ya kawoni duniya, Nadiya da bata da mafita tace "zanje mamma rigar ce taki shigana, zama ta shige ki ne matso in zage miki zip, matsawa tayi badan ranta yaso ba mamma taja mata rigar ta shige tsaf kamar a jikinta aka dinka, gashi ya shige maza daura dankwali muje, dankwalin ta daura ta yafa gyale duk ranta a jagule, ta tsani wulakancin su Badariyya, tasan Sam haduwarsu ba Mai dadi bace kullum suka hadu sai sun tozarta ta kuma babu Mai hanasu, daukar zainab tayi ta bi bayan mamma suka fita hade da rufe gidan... Gidan cike yake da 'yayan kawayen mummy da iyayensu da ita kanta, suna can ciki anata wasa da ciye ciye, iyayen kuma suna hira hade da Shewa, can gefe kuwa su Reemah ne ita kannenta sunata hira babu Wanda ya lura da zuwansu, hakan ya ba Nadiya daman zama can nesa dasu tana kallon yaran dake dakin 'ya'yan hutu kawayen su badariyya, zainab da hankalinta ya gama tashi da tulin kayan wasan yara sa'aninta ta mike a jikin Nadiya tace anty zanyi wasa, Nadiya ta zaunar da ita tace ki bari su gama kema sai kiyi kinji, gyada kanta tayi tanata binsu da ido suna wasa babu kakkautawa, Mamma kuwa tana can gurin su goggo da mummy da kawayenta sunata hira, tunda ta gaishesu ta nemi guri ta zauna a kasa itama, babu Wanda yace musu ga abinci haka in za'a ba yara barka da sallah babu wanda ke kallonsu, sallah kadai ke tada iyayen Sannan su dawo su cigaba da hira, "Suwaiba tashi ki tattara gidan nan tunda baki San abinda ya kamata ba sai an fada, muryar goggo ta dakin kunnen daukacin mutanen dake cikin parlorn, da sauri mamma ta mike tana murmushi ta fara tattare kwanukan da suka ci abinci, kwala Kiran Nadiya tayi tace taho ki fitar min da kwanukan nan, zaunar da zainab tayi ta mike sum sum ta karbi kwanukan hannun mamma tayi waje dasu, Badariyya dake kwance tana game a iPad dinta ta bita da ido cike da rainin wayau, tsaki taja ta cigaba da danna iPad dinta, ta rasa dalilin dayasa ta tsani Nadiya, bata jin ko digon kwayar Santa a cikin zuciyarta, tasan tafi Nadiya dukkan gatan rayuwa, haka kyau karyarta ta nuna mata, can kasan zuciyarta ta jiyo yayi amsar kuwwar "KYAWUN JIKIN FA" tsaki taja tace saidai jikin Shima dan bamu gama girma bane amma Nadiya babu abin da ta fini dashi, Husna da Laila yar kawar mummy suka bita da kallon mamaki sukace to waye ya ce Nadiya tafi ki wani abu, gimtse fuska tayi hade da runtsa ido dan bata San maganar zuci ta fito fili ba, A ranar babu wani abu da ya shiga tsakaninta da badariyya saboda Hilal da yayi kaka gida a parlorn, Kasa katabus tayi saboda tsoron Kar ya sake marin kyakykyawar fuskarta, ta tsani abin da zai taba fatarta koda kuwa kuda ne,, Yaji mamma tayi ma Reemah da yawa na tafiya sannan tayi ma musaddiq dambun kifi da nama, murna sosai sukayi sunata godiya, sai bayan Isha mamma ta fara shirin tafiya, dakin Baffa ta shiga Wanda yake cike da 'ya'yan mummy da ita kanta suna meeting ana ciye ciye, durkusawa tayi tace Baffa mu zamu tafi sai da safe, to madalla sai da safe suwaiba, yaki taho zainabu ki karbi kudin mota, nokewa zainab tayi saboda rashin Sabo, mamma tayi murmushi tace "quiwa gareta, , toooo... to ta rike kanta ta cinye, sai Allah ya tashe mu ki gaida Adamun, to zaiji Baffa, ta waiga tace masu sai da safenku, to sai da safe duk sukace suna masu kai nama bakinsu.. Reemah dai kai kawai take girgizawa cike da takaici, yafito Hilal tayi da hannu tace maza yaje ya sauke su a gida, kunkuni ya fara yi yana buga kafa, musaddiq ya mike yace bani mukullin, da sauri ya wurga masa ya koma ya zauna ya cigaba da latsa wayarshi, a can bakin gate ya tarar dasu suna kokarin fita, Mota ya bude yayi musu hon yaja ya isa gaban su, bude musu yayi yace mamma muje in kaiku,, ayi haka.... mamma ta fadi tana rike baki, bakomai ku shiga muje, baya suka shiga ya ja motar suka wuce.... ******** Tun daren suka gama shirye shiryen komai na tafiya, ba kananan kudade daddyn shi ya turo na siyayyar tafiyarshi ba, mummy da kanta ta shirya mishi kaya suna ta hira cikin farin ciki, Yaya wata nawa zakayi? Husna ta tambayeshi tana bude ledar dambun naman da mamma tayi mishi, mummy tayi dariya tace shekara nawa dai, ai sai kin ganshi kawai, Husna tace "tabdi har shekara anya mummy zai iya zama kuwa, shi da baya ko iya kwana a wani gari, shafa kanshi mummy tayi tace "can ma ai gida ne ko little? , gyada kai yayi ya kwanta kan cinyarta yace but I will miss you so much mummy, i will miss u more my baby, ka kwantar da hankalinka zan dinga zuwa ganin ka a kai kai kaji, um kawai yace yana kallon Badariyya dake mishi kallon shi din baida wayau, tsaki yaja ya mike ya nufi dakinshi, rainin Badariyya a gareshi yayi yawa, lallai taga gadon barcinshi amma babu komai with time Shima zai zama jajirtacce marar daukar raini in shaa Allah ya fadi yana mai karfafa zuciyarshi..... Mrs Tijjani Shattima.... [04/12 09:46] Meela Adeel: 9⃣ °ZUMUNCINMU A YAU ° By Aysha Ya'u Kurah HAPPY NEW YEAR, Allah yasa mun shigeta a sa'a AMEEN.... 2017 is unforgettable... Allah yayi Maka Rahama Babana... "Kilode sis"... Husna ta fadi tana zungurar Badariyya da tayi tagumi tana kallon Kasa, tsaki Badar ta ja tace "nothing bacci kawai nake ji, Husna ta tabe baki hade da kwanciya tace "to ai sai ki kwanta, Badar ta dan kashingida ta runtse ido kamar mai bacci, har cikin ranta bata son tafiyar Musaddiq, duk da yawan samun sabanin da sukeyi tafi son kasancewarshi kullum a gida tana mishi koda kallon raini da wulakancin da ta saba ne, to in ya tafi wa zata dinga gani, Husna tayi mata kadan a cewarta, duk da sa'oin juna ne amma a koda yaushe Badar gani takeyi ta girme ma Husna nesa ba kusa ba saboda tsantsar sangarta da d'agawa, tunanin hanyar da zata bi ta hanashi tafiya ta shiga yi, ta dade tana tufka da warwara kafin daga karshe ta samo mafita,.. a hankali ta Mike ta murda kofa ta fita , dakin mummy ta nufa dan tasan bata ciki tana can gurin musaddiq, drawers ta fara janyowa ta shiga binciken visan musaddiq da aka kawo mishi jiya, da kyar ta gano inda take cikin wata karamar jaka, dariyar farin ciki ta shiga yi a ranta tace zanga yadda za'ayi ya tafi ba wannan, hannu tasa zata fara yagawa taji an Fisge visan  a hannunta, saurin waigawa tayi dan ganin ko waye, Husna ta gani tsaye tana kallonta cikin ido, "haba Badar yanzu muguntar taki har ta kai haka, meye amfanin yaga mishi visa,? tun fitar ki na biyo ki dan nasan ba fitar alkhairi kikayi ba, akwai abin da kike shirin kulawa da shurun da naga kinyi,, mtswwwwwwwww Badar taja dogon tsaki tace "dalla malama bani, ni nace miki yagawa zanyi, to me zakiyi dashi? husna ta tambaya fuskarta dauke da mamaki, ban sani ba Badar ta fadi tana mik'a hannu zata kwace, kaucewa husna tayi tace wallahi bazan baki ba, sai dai ki kwata ta karfin tsiya, nan suka fara kokawar da ya janyo hankalin su mummy, Kaiiii, kaiiii, lafiya menene haka, mummy ta fadi da karfi tana shiga tsakaninsu, Husna tasaki wahalalliyar ajiyar zuciya hade da haki tace mummy visar Yaya zata yaga, Visa kuma, to me yasa?? mummy ta tambaya cike da mamaki tana kallon Badar, Cike da shagwaba Badar tace "mummy karya fa takeyi wai dan taga na dauko na rike a hannuna ina karantawa shine tace wai zan yaga, akan me zan yaga mishi visa, me yaga war zai amfane ni dashi, kawai dai sharri zata min dan taga ba k----- mummy tayi saurin rufe mata baki ta rungumeta tana rarrashinta, yi hakuri Badar din mummy, nasan karyar husna ai, in mafadin magana wawa ne majiyinta bazai zama wawa ba, Husna ta fito da ido waje cike da mamaki tace Badar kiji tsoron Allah, tabdi!!!! ta kara fadi cike da kullewar Kai tana tsananin mamakin halin Badariyya a Yan Kananun shekarunsu, ajiye visar tayi a kan madubi ta raba ta gefen musaddiq da ya nade hannayenshi yana kallon ikon Allah ta wuce rai a bace, rufa ma Husna baya yayi hade da hararar Badar yana fadin Allah dai ya kyauta, "Ameen" mummy ta fadi a fusace tana sharewa Badar fuska tana kara bata hakurin abinda husna tayi mata, Sam bata son bacin ran Badariyya, wata iriyar kazamtaciyyar soyayya takeyi mata wanda bata da masaniyar wannan zurfaffan son zai mata illah marar misaltuwa anan gaba....... ******** "Babu sallama......" Ta ji an fadi a bayanta, da sauri ta waigo a firgice ta kalli motar, kwantar da sit yayi a gaggauce hade da karasa bude tint glass din,, nan da nan ta saki murmushi mai sanyin kyau, tace "ina kwananku, Hinad ta turo kanta daga baya tace "leko kiga mai magana Nadiya, Yaya Hilal ne yake bukatar yin sallama dake, Hilal ya chire hular da ya rufe kanshi dashi ya dago sosai ya hade girar Sama da kasa yace wallahi zan karya yarinyar nan, Hinad ta zaro ido ta kalli drivern mummy tace dan Allah mal---- bige bakinta yayi yace dan Allah Malam ja muje inda mum ta aike ka, Hinad ta turo baki tace "Nadiya bani milk candy pls Kinga yau zan tafi, Nadiya tayi saurin juyawa shagon tasi ta dauki robar da ko minti biyar batayi da bashi ba ta miko ma Hinad tace gashi ki tafi dashi duka, Allah ya kaiku lfy, ki gaida anty da Yaya Musaddiq,, ta cikin bakin glass Hilal yake satar kallonta, duk tunanin shi ba wanda ke ganinshi bai San drivern mummy idanshi kyar akanshi ta mudubin motar ba, sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa ya biyoshi kuma ya tursasa mishi biyowa ta layin dan ko kusa ba hanyar inda zasu bane, murmushin zuci yayi yace "yarinta hooo," in ba yarinta me wannan dan yaron ya sani akan mace, macen ma jaririya, ko da yake akwai Soyayyar  yarinta da kuma ta jini, muryar Hilal ce ta maido shi daga duniyar zancen zucin da ya tafi, da sauri ya tada motar suka fara tafiya, daga musu hannu Nadiya  ta shiga yi alamar bye bye, suna gab da kure layin ya sake kallon madubin gefenshi karo na barkatai ya hangota tana juyawa gurin mai shagon, kwantar da kanshi yayi kan sit hade da lumshe ido yana Nazarin abubuwa da dama.... LARNACA INTERNATIONAL AIRPORT CYPRUS 2:27am daidai,, agogon kasar Cyprus ya buga, daidai da karfe 1:27am na agogon kasarmu Nigeria,, Hayaniyar mutanen cikin jirgin ne ya farkar da musaddiq da bacci yayi can wata kasar dashi, mik'a yayi ya sake gyara seat belt dinshi, ya kalli Hilal  yace "har mun iso? , da kai Hilal ya bashi amsa, alamar eh,, Alhamdulillah Ala kulli halin musaddiq ya fadi yana mai gyara zamanshi kafin jirgin ya karasa tsayawa,,, "Welcome to the third largest nd third populous island in the Mediterranean uncle" Hinad ke maganar cikin kwarewa tana bude hannayenta hade da lumshe idanunwanta a Saman matattakalar benen jirgi, thank u my darling daughter, musaddiq ya fadi yana mai sunkuyawa dai dai kumatunta yayi mata peck, saukowa sukayi  kowa rike da Jaka suna ja, suna baza idanuwa,, daga can nesa suka hangoshi tsaye cikin ash jallabiya yana hamma hade da duba agogo, a guje Hinad ta ruga tana kwala kiranshi da karfi, "PAPA", bude hannayenshi yayi yana murmushi ta shige jikinshi ya dagata Sama yana juyata, " I  MISS U SO MUCH PAPA" misd u more more more angel, Hw waz ur trip? , boring ta fadi tana tabe baki,, ohhh why my dear?  Ya tambaya yana Jan kumatunta,----- for crying out loud PAPA abinda kazo yi nan kenan, anty reema ta fadi cikin katse musu hanzari, sauketa yayi yace come on my dear Reems u knw am here for u, kallon musaddiq yayi cike da murna yace welcome broo, ya hanyar? , "lafiya lau alhamdulillah, mun sameka LFY? musaddiq ya tambaya yana murmushi,, fine fine ka dai ganni sai dai dan wuya na rashin girkin yayarka ya fadi cikin zolaya, dariya musaddiq yayi yace I cee, Gud morning father, PAPA ya fadi yana mai tsugunawa HILAL dake ta faman latse latsen waya, ohh dad  neman magana ne kawai kasan zan gaisheka ai, just don't want to interrupt you, you knw i miss u,, gaisuwar mu dabanne, harara Papa ya bishi dashi ya karbi jakar hannun matarshi yace "oya lets go bacci nake ji sosai sosai, kama hannunshi Hinad tayi suka nufi hanyar waje.... Mrs Tijjani Shattima...... [04/12 09:46] Meela Adeel: °ZUMUNCINMU A YAU° By Aysha Ya'u Kurah 1⃣0⃣ Agios tychonas, limassol.. Estate ne gari guda na ma'aikata, da yawansu turawa ne yan kasashe daban daban, yan kasar turkiya sunfi kowa yawa a cikin estate din, sai tsirarrun bakaken fata yan Africa,, A katafaran parking space din harabar gidan sukayi parking motar, fitowa sukayi kowa na mik'a suka nufi cikin gidan, lift suka danna suka shiga, ya kaisu hawa na takwas, "AMB G KANGIWA 380" shine rubuce a Saman kofar part din, wani kati mai kauri yasa ya bude kofar, tsayawa fadin tsaruwar parlon ma bata lokaci ne, parlor ne na garari na kuma gani a fada a ko'ina, Daki kowannensu ya wuce sukayi wanka suka sauke da farali, kafin su fito parlon, kawar anty Reema matar abokin "amb GADDAFI KANGIWA" ta aiko da abinci kala kala, Babbar diyarsu "MEERAH "  wacce sa'ar Hilal ce ita ta kawo abincin ta shiryashi kan table, da murmushi anty reema ta karaso gurin tana fadin "oh Allah ita ko Ammi bata gajiya, irin wannan hidima haka, Meerah tayi murmushi tace "ina kwana mum, lafiya lau diyar albarka, har ke bakiyi bacci ba, ina su Adeel? , sunyi bacci, ina tsaye a balcony naga shigowarku ai,, Meerah ta fadi tana mai Jin kunya, ikon Allah anty Reema ta fadi tana shafa kanta, to kice mata mun gode sosai kinji, gyada kanta tayi tace "mum Hilal fa, Anty Reema ta kalli kofar dakin shi tace yana ciki tare da kanina, wata cooler ta dauka mai kyau ta yi hanyar dakin, Tarar gabanta hinad tayi tace "Hey smarty, ajiye cooler tayi ta rungumeta tace "my little smarty, tot kinyi bacci,? Hinad tace "banyi ba ni ina nawa? Ohh smart gal bansan zan ganki ba, ki bari gobe da safe zan miki duk abin da kike so, "naki Wayan, hinad ta fadi tana Noke wuya" wannan na coolr zanci ko nima in miki rowar abin da na kawo, dariya Meerah tayi tace "issoryt" muje sai kuci tare, No.. no.. no.. Hinad ta fadi tana girgiza kai, tsaya a nan in dauko plate, wannan acicin ne zai bari muci tare, Dariya ce ta gauraye parlon ciki harda musaddiq da suka fito tare da Hilal, wani miyau Hinad ta hadiye ta kwalolo ido saboda irin kallon da Hilal ke mata, baya ta fara ja a hankali tana kallonshi, a guje ya bita ta saki wata razananiyar kara ta nufi Sama tana fadin "wayyo Allah Papa zai kasheni,, cike da tsokana papa ya daka mishi tsawa yace, "karka taba min 'ya tunda ba karya tayi ba, duk rabin abincin gidan nan wake cinye wa,? Sanin ci irin naka ne yasa Meerah tayi Maka naka abincin daban, ko ba haka ba Merah?,   aaaahhh... Papa pls karka hada ni da Hilal meerah ta fadi fuskarta  dauke da murmushi, favourite dinshi na dafa mishi daban, Papa ya murtuke fuska yace nayi karya kenan? Meerah ta daura hannu a kai tace nooo baka yi ba,, Papa ya kalli Hilal yace "to kaji, zo kawai ka zauna Kaci abinci nasan kana jin yunwa, hade rai Hilal yayi yace "nakoshi"  yasa kai yayi hanyar daki, kiranshi anty reema ta shiga yi ko waigowa baiyi ba ya shige dakin ya bugo kofar da karfi,, kallo anty reema tabi Papa dashi ya dauke kanshi ya cigaba da cin abincinshi yana yan wake wake, Musaddiq ya mike zai bi Hilal Papa ya tsayar dashi yace dawo Kaci abincinka indai hilal ne yana zuciya da komai banda abinci, ka rubuta ka ajiye ko karfe nawa ne sai ya fito yaci abincin shi,   nan take Hinad ta saki dariyar da ta dade tana gimtsewa, Anty reemah ranta ya kara baci tace "walhy zanci mutuncinki yanzun nan, sa'anki ne? Gyada kai tayi tace "sorry mum, dalla yi kiyi ki tashi kije kiyi sallah ki kwanta, da wani katon bakinta Mai shegen surutun tsiya, Papa dai baice komai ba ya mike ya nufi gurin meerah dake tsaye yace "je ki kwanta Dota Allah yayi miki albarka, Ameen Papa,, ta kalli anty reemah tace "gud nyt mum, nyt sweet heart ki gaida Ammi.... ******* Kaduna.. Nigeria Rayuwa ta dan fara sauyawa su mamma suwaiba saboda yar sana'ar da sukeyi, ga hafiz dake harkar fruits, yanzu kullum sai ya samu dari biyar wata rana fiye da haka, ga kuma rarar fruits da yake samu ya taho dasu gida su Sha su kyautar da sauran, Yana matukar Jin dadin sana'ar saboda sana'a ce mai albarka, Saida yayi sati uku yana koyan harkar sannan anty reemah ta turo mishi da dubu dari biyar, a ranar saida yayi kukan murna dan ko a mafarki bai taba tunanin rike dubu hamsin tashi ta kanshi ba, bare dubu dari har guda biyar, Allah kenan in yace "ku fa ya kun" shikenan, (Allah ka datar damu).. Zama yayi da Mai gidanshi sukayi shawarar abunda zaiyi da kudin, d'aura shi yayi akan harkar sosai saboda yanada jarin shi na kanshi, babu inda basa Zuwa saro Kaya basu onitcha, enugu Lagos da sauran guraren sarin kayan fruits,, Cikin ikon Allah da taimakon Papa aka bawa Nadiya admission a fgc malali, Hafiz yayi kokari wajen yi mata komai na tafiya makaranta, haka babanta da Mamma suwaiba duk sunyi mata kokari, Sam bata San tafiya saboda tausayin mahaifanta, wani bangare na zuciyarta kuma ya bata shawarar, Ilimi shine gishirin zaman duniya, kuma ko ba komai zata kauracewa ganin Badariyya, da wannan tunanin ta samu karfin gwiwar tafiya makarantar kwana.... ***** Frederick University.. Gudu yake shararawa cikin motarshi kirar KIA karama ruwan goro, wakar "Rockabye" ta "Anne-marie ya Kure volume yake saurare yana bi a hankali, hon ya latsa da karfi yana sauke glass din motar hade da kallo inda take.. mikewa tayi ta isa gurinshi ta bude kofar gaba zata shiga yayi saurin dakatar da ita, "baya zaki zauna ko kin manta bani kadai bane, rufewa tayi bata ce kala ba ta bude baya ta shiga, ko kallonta baiyi ba ya tada motar ya wuce "faculty of engineering" a kofar dept din ya hango shi zaune yana duba wasu littafai, kashe motar yayi ya fito ya karaso gurinshi yace "heyyy guru" shall we, musaddiq ya mike yana kakkabe jikinshi yace eh mu tafi, waya Hilal ya mik'a mishi yace "call ur mama ta kirani Wai wayarka a kashe,   Musaddiq ya dan ja tsaki yace "barta zan kira in naje gida na gaji Sosai, mayar da wayar aljihu yayi ya bude kofar motar ya shiga,, gaisawa musaddiq sukayi da meerah dake baya tana shafa hoda a fuska,. kallonta Hilal yayi ta mudubi yace "madam makeup"  an fara, banza tayi mishi ta cigaba da kwalliyarta, jan motar yayi yana murmushin ko a jikina yarinya... Mrs Tijjani Shattima... [04/12 09:46] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣1⃣ Shekaru sun dan jaaa, cikin farin ciki da akasin shi saboda halin rayuwa na yau zuma gobe madaci, "Nadiya Adam" muje mu rage Miki hanya mana, yamutsa fuska Nadiya tayi cikin damuwa tace bari kawai Rukky, zan samu napep in tafi, Kallonta rukky tayi cike da mamaki dan dai tasan bata da ko Naira biyar a jikinta, hannu tasa ta fara daukar kayanta tace zan kai miki kayan, ki taho a mashin ma wannan ke ta dama, bin ta Nadiya tayi da kallo tace "Haske dan Allah ki barshi kar in matsa muku Kinga hanyar mu ba daya bace,   "ke kika rokeni? Rukayya ta fadi fuska a hade,, Girgiza kai Nadiya tayi tace "a'a amma--- amma me Haske tayi saurin katse ta, tace "zo mu tafi dan Allah, kwashe sauran kayan tayi ta bi bayan Rukayya Haske ranta duk a jagule, A gatance ta fara makaranta, tun daga shigarta har Zuwa ss1 third term, tunda ta dawo first term din nan ko sau daya babu wanda ya ziyarce ta, zuciyarta cike take da fargabar abin da yake faruwa da Yan gidansu, number yaya Hafiz Sam bata shiga haka ta mamma, tunda ta shiga motar take addu'ar Allah yasa kowa na nan lafiya, dai dai kofar gida suka sauketa suka wuce cike da kewar makaranta, Jakarta ta dauka ta fara tafiya domin karasawa cikin gidan, A can bakin murhu ta hangi mahaifiyarta idonta yayi jawur hanci duk ruwa saboda wahalar hura wuta, ajiye Jakarta tayi ta karasa kusa da ita, idonta cike da kwalla take kallon mahaifiyarta dake mata murmushi, hannunta Nadiya ta kama zata fara magana suka jiyo tari me karfi babu kakkauci daga cikin dakin, da gudu mamma ta nufi dakin tana fadin subhanallah!! sannu, bin bayanta Nadiya tayi da sauri, ta tarar da abin da ya daga hankalinta matuka, mahaifinta ne kwance cikin bargo kamar jaririn goye, ya rame ainun, idanuwanshi sun zurma sai tari yakeyi hade da kakin jini, kuka mai karfi Nadiya ta saki tana fadin meya sameka Baba?, mamma me ya sameshi,? mamma dake tare jinin da wata tsumma tayi kokarin boye idonta da ya ciko tace "bashi da lafiya ne amma da sauki, wani irin sauki mamma, Ina saukin yake anan?, dan Allah ki kira yaya Hafiz mu kaishi asibiti, nan kukan da mamma ke boyewa ya bayyana, Take Nadiya ta rikice, dan ita dai tun tasowarta bata taba ganin bacin ran mahaifiyarta ba bare har takai ga zubar ruwan hawaye, Durkushewa Nadiya tayi tace "mamma me nayi,? Dan Allah kiyi hakuri, Wai me yake faruwa ne? kuka mamma takeyi iya karfinta gunin ban tausayi, kallonta Malam Adamu keyi hawaye na zuba ta gefen idonshi a ranshi yana mai Jin dadin kukanta domin ko ba komai zata samu saukin nauyin dake cikin ranta, sai da tayi mai isarta ta share hawayenta, ta kalli Nadiya dake kuka tana share hawayen idon mahaifinta tace "tashi maza kije kiyi wanka kiyi sallah, bari in nemo miki abin da zaki ci, Nadiya ta share hawayenta tace "ki barshi kawai, bari nayi wanka in daura mana, zauna ki kula da baba, Gyada kai mamma tayi kawai, dan bata son tasan abinda ke faruwa, Nadiya na shiga bayi mamma ta fita shagon Tasi da ya kara cika ba kamar da ba, Indomie da Kwai ta ce ya bata, dakyar ya bata dan yana bin ta bashin kusan dubu daya da dari hudu, da sauri tayi cikin gidan, ta hado yayi, ta sauke ruwan dumin da ta daura ma mijinta, ta iza wutar ta daura Indomien cikin karamar tukunya.. Wanka da sallah Nadiya tayi, ta saka doguwar rigar deep blue material mai gajeren hannu ta shan iska,, ko mai bata shafa ba ta daura jar hula a kanta, kyawu mai sirri da cikar budurci suka bayyana a tare da ita, wani irin kyau Nadiya ke dashi marar hayaniya, wanda ya kara fitowa saboda dan hutu da kuma rufin asirin da suka samu,, kusa da Mamma ta tsaya tace "sannu da aiki mamma, ina Zainab? "Tana  islamiyya,, mamma ta bata amsa tana tura leda cikin murhun, Tambayoyi ne cure cikin zuciyar Nadiya, ta rasa wanda zata tambaya ya bata amsarsu, ko zata mutu tana tambayar mamma bazata amsa koda tambaya daya cikin tambayoyin da take dasu ba,, Daki ta shige gurin mahaifinta da ya fara bacci numfashin shi na fita dakyar, Kure shi tayi da ido tana addu'a tana tofa mishi, Mamma na kwashe Indomien zainab ta shigo gida da gudu jikinta yayi futu futu, "mamma yunwa nake ji, zainab ta fadi murya a sarke saboda tsabar gajiya.. kallon Indomien mamma tayi tace to bari kiyi wanka ko? , noke wuya tayi kamar zatayi kuka tace cikina na murda min, je ki wanke hannu kizo muci, Nadiya ta fadi tana fitowa daga daki, rungumeta zainab tayi tace "yaushe kika dawo anty? Dazu kina islamiyya, da fatan kina karatu a makaranta, Nadiya ta tambayeta tana shafa kanta,, gyada kai zainab tayi tace Sosai ma, kin kawo min chocolates, Kumatunta Nadiya taja tace "eh yana jaka ta, maza wanko hannu muje muci abinci.. Mamma kinci abincin ne? Nadiya ta tambaya idonta kyar akan mahaifiyarta, mamma dake kofar daki tace "eh munci sosai, bansan zaki dawo ba da na ajiye miki, zainab da ta kai Loma kamar zata shake tace "mamma yaushe kika ci abinci?, bayan tafiya ta makaranta, shine kika cinye baki ajiye min ba, mamma ta saci kallon Nadiya, tayi saurin maida kallonta gurin zainab tace ba gashi kina ci ba, maza kici karki kware, Nadiya dai hannu kawai take juyawa cikin abincin har zainab ta kai karshen shi harda sid'e kwanon, meya ke faruwa mamma??? Tambayar ta fito a bakin Nadiya cikin rashin sanin fitowarta, me kika gani? Mamma ta amsa ta cike da fargaba, rarrafowa Nadiya tayi ta dafa cinyarta tace "mamma boyemin abin da ke damunki bashi da amfani, nasan bani da maganin shi amma atleast zaki ji sauki in kin fada min.....     ********** Ohh ni!!! "wacce iriyar rayuwa ce wannan? d'aki kaca kaca sai kace ba na mata ba, mummy ke mitar tana tafe tana tsintar kayayyaki a kasa da takalma, Husna dake kwance tana duba littafi tace "kema kin San ko aikin waye mummy, "ni gaskiya na gaji wallhy, canza min daki za'ayi, bazan iya wannan rayuwar ba, kwance take cikin matsatstsiyar jar riga da yellow mini skirt, Gashinta Parke a tsakiya da yellow ribon, kunnenta dauke da earpiece alamun bata ma San me sukeyi ba, kada kanta kawai takeyi tana bin wakar hade mutstsuka santala santalan kyawawan kafafuwan ta, kafarta mummy taja a hankali, juyowa tayi tana cire earpiece din kunnenta cike da rashin da'a tace "ya akayi ne mum"   mummy ta ajiye kayan makarantar ta a gefen gado tace "babu komai baby na, kinci abinci dai ko? gyada kai Badar tayi alamar eh sannan ta juya ta mayar da kanta kan pilo tana cigaba da jin waka hade da chatting,, "hmmmm" kawai Husna tace ta sakko daga kan gado tace "mummy zanje gidan Anty Raudha, "me akeyi?? mummy ta tambaya tana gyara ma Badar skirt dinta, "birthday din Amal diyar Anty Laura, Husna ta bata amsa, gyada kai mummy tayi tace "too jira Badar ta shirya ku tafi tare, hanyar bayi husna ta nufa tace "bata San me muke fadi ba sai ki fada mata dan gaskiya ina shiryawa zan tafi, Badar da ke saurarensu da kunne daya tace "kifi ruwa gudu, ke kika damu da local partys, duk inda kika ji sha'ani jiki na rawa kin tafi, 'anyways baki yar a kasa ba, maida earpiece dinta tayi ba tare da ta kalli mummy ba ta cigaba da danne dannen waya, Husna kuwa bayi ta shige cike da bacin ran irin rainin da Badar ke ma mummy, abin da ke kara bata ranta bai wuce yadda mummyn ko a jikinta ba, duk rainin da badar ke mata sai dai tace "yarinta ke damun ta, ita kuwa komin kankantar abu in tayi mummy ta dinga masifa kenan kamar zata ari baki, watsa ruwa tayi cike da takaici da tunani iri iri.... Mrs Tijjani Shattima... [04/12 09:47] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣2⃣ A hankali take maimaita kalmar "innalillahi wa Inna ilaihir rajiun" ruwan hawaye na tsere akan kumatunta, kirjinshi take dannawa tana share kumfar jinin dake fita a bakinshi, nishi yakeyi Sama Sama yana kakari da karfi, magana yake fisgowa daga can kasan makoshinshi, muryarshi ta kara karfi tamkar amsa kuwwar loud speaker, "kiyi Hakuri suwaiba! , kiyi Hakuri da rayuwa, nasani ban jiyar dake dadin duniya ba saboda talauci na, gashi zan tafi in barki cikin rayuwar talaucin da babu mataimaki, kiyi hakuri suwaiba, Allah kadai yasan tanadin da yayi mana a lahira, ki cigaba da hakuri da duk yadda kika tsinci kanki, nasani kin iya kanki, ki rike yaran nan,, basu da kowa a duniya sai ke, ki fadawa Hafizu in ya dawo na yafe mishi,! na yafe mishi,! na yafe mishi,!!! Idonshi da yake lumshewa ya daga Sama, ga azabar zafin fitar rai ga kuma radadin barin iyalanshi cikin yanayi na rashin garkuwa, Ya Allah! ka iya ma zuri'ata abin da bazasu iya yi ma kansu ba, LA' ILAHAILLALLAH----- kukan mamma ya karu saboda tsabar firgici, A gigice Nadiya ta farka daga gajeren baccin da ya dauketa saboda jiyo kukan mahaifiyarta, fitowa tayi daga daki da sauri har tana turgude kafa ta karasa dakin baban su, kasa shiga tayi saboda hangoshi da tayi  damke da karfen gadon dakin hade da hannun mamma, yana haki da sauri sauri. Juyawa tayi ta fita a gigice,  "wake ta takalmi ko mayafi a wannan lokacin", gudu takeyi da iya karfinta, ita dai tasan jefa kafafuwan ta kawai takeyi, bata ma San akan abinda suke sauka ba, hanyar gidan Baffa ta dauka, duk nisan dake tsakanin su bata gani ba, ita dai burinta a taimakesu a ceci rayuwar mahaifinsu, Da dutse take bugun gate din gidan da iya kurewar karfinta, Ya salam!! Baffa ya fadi yana mai mikewa, yanzu duk samarin dake kofar gida basu ji bugun gate dinnan ba, mtsww... ya ja tsaki ya dauki torch ya bude kofa, Wayeeee ne? Baffa ya tambaya cikin muryar bacci, Nice, Nadiya ce, Dan Allah ka bude Baffa, Tsaki ya kara ja yace ohh ya Allah, Ya bude gate din ya kalleta Sama da kasa yace "lafiya da wannan daren? "Baffa--- baba zai mutu, dan Allah kazo muje ka kaishi asibiti, Dan Allah baffa, harararta yayi yace "kece kike daukar rayuwa da kikasan zai mutu, waya ya ciro a aljihunshi yace bari in kira Antyn ku sai kije ta bada driver sai ya kaiku, dadi taji cikin ranta dan ko ba komai ya kula, sau uku ya kirata bata dauka ba, kudi ya ciro a aljihunshi Naira dari biyu, bai duba duhun dare ba yace "maza ki samu Mota kije gidan ki buga musu kamar yadda kika buga min, kinga babu kowa a gidan nan bare ince su kaiki, tsugunawa tayi ta karba tayi godiya ta juya da sauri ta tafi, duk motar da ta tara kin tsayawa tayi, gudun ta sake yi har Allah yasa ta samu machine, ta hau ya kaita har kofar gidan, Tura kofar tayi ta shiga, Mai gadin gidan ta hango a can kofar bayi, da gudu ta shige ciki, kofar parlon ta fara bugawa da karfi, Badariyya dake daki ta jiyo bugun kofa, bugun zuciyarta ya tsananta, ta fara gyara jikinta, wannan Karan doguwar riga ce a jikinta silk material, Tayi kyau ainun, tafiyarta mai kyau takeyi har ta isa kofar, Bacin rai ne ya ziyarci zuciyarta ganin Nadiya a tsaye, waje ta leko a hankali taga babu kowa, dogon tsaki taja a ranta tace "duk gyaran nan da nayi na wannan banzar ne, "Badar Ina mummy? Nadiya ta katse mata zancen zucin da takeyi, Kallon banza badariyya tayi mata tace " ta tafi koyo sallama, Badar plss is very important in ga mummy, Dan Allah tana ina, kofa Badar ta kama zata turo Nadiya tayi saurin riketa tace, "plss Bad---- don't u dare, Badar ta katse ta hade da bige hannunta, dis nyt is very important for me as well, banason abin da zai bata min shi kin gane ko, ki bar gidannan kafin ki hadu da wulakanci marar iyaka, da karfi ta turo kofar ta jingina a jikinta tana maida numfashi, i hate her, wayyo Allah na, ta fadi hade da dafe goshinta, ganinta a daren nan ya kara darsa hassadarta a cikin ranta, me ya kawota gidan nan cikin daren nan? , daren da ta kosa da zuwan shi shekaru da dama, tun bata gama sanin kanta ba, , daren da take mafarkin zuwanshi a cikin yan kwanakin nan, ta window ta leko ta hango Nadiya na tafe tana kuka hade da shashsheka, zuciyarta ko digon tausayi babu dan a tunaninta wani abun ne ya kawo ta wanda ya danganci taimakon kudin abinci, parlor ta karasa ta zauna tana saka yadda zata ganshi a zahiri, tun tafiyarshi basu taba ko da waya ba, Bayan tafiyarshi ne ta fahimci ya zamo wani bangare na rayuwar ta, a karancin shekarunta ta fahimci lallai shi din wani sashe ne a cikin labarin rayuwar ta, hotunanshi da ke kan IG  ta bude ta fara dubawa, "kyawun gaske" jajayen labbanta suka furta cikin taushi.. Hoton da yayi posting last a jirgi shi tayi zooming, lumshe idonta tayi tana hango yadda zatayi mishi in ya shigo gida.... A gajiya yake saukowa daga matattakalar jirgin, akwatin shi yake ja yana tafe cikin kasaitarshi da ta kara karuwa saboda gogewa da Ilimi, Salam alaikum Malam, Kamar "Little Diku ko"? kyakykyawan saurayin ya tsaida shi yana tambayarshi, daga kai Musaddiq yayi alamun nazari sannan ya sauke ya kalleshi yace "noop wannan "ENG MUSADDIQ M KYARI"  ne duba cikin Sauran mutane may be ka ganshi, akwatin shi ya cigaba da ja, saurayin ya biyo shi ya rike akwatin yace "so sorry guy, kamaninku sun baci, saidai ni Diku na ba haka yake ba, okk den, je ka nemoshi sauri nakeyi, abokina na jirana a waje musaddiq ya fadi fuskar nan a tamke kamar da gaske, kallonshi saurayin yayi Sama da Kasa ya juyo shi sosai sannan ya d'aka mishi duka  hade da rungumeshi sosai, "I miss so much friend, "missed u more Mahmud, musaddiq ya fadi yana dariya, kaga yadda ka zama kuwa, omg, KYARI ya zama big guy, Allah yasa ZUCIYAR ma ta girma, Mahmud ya fadi cike da zolaya,, daure fuska Musaddiq yayi yace bansan iskanci, dama abin da yasa kace kai zaka zo daukata kenan, dariya sosai Mahmud yayi ya dauki jakarshi yaja hannunshi yace "sorry abokina, kasan a gida nace musu sai gobe zaka dawo jirgin ku ya tsaya, BADAR ce kadai tasan yau zaka dawo, yanzu ma ta kirani, "kace ni yau da yunwa zan kwana, musaddiq ya fadi yana Murmushi, Mota Mahmud ya bude yace "why? , nasan Badar ta shirya zuwanka tunda tare muka hada plan din nan, bude motar kawai yayi yace lallai kam, Badariyya da kanta, ni tunda na tafi ko sau daya bamuyi waya ba, tada mota Mahmud yayi yace "haba dai, "am serious musaddiq ya fadi yana zare takalmin kafarshi..   Hirar yaushe gamo suka shiga yi cike da nishadi wanda ya mantar da musaddiq gajiyar da ya kwaso,, Karar wayarshi ce ta katse hirar, da fara'ar shi ya daga yace "my chocolaty bakiyi bacci ba, daga dayan bangaren tace "ohhh haba uncle wani irin bacci, bamuji ko kun isa lafiya ba, Ga mum can sai gyangyadi takeyi ka barmu da jira, auuchhh,  so sorry, kinsan ko na kira bazai je ba, jira nakeyi inje gida in kiraku, ina take bani ita? gaisawa sukayi da anty reema da papa,, sannan suka cigaba da hira shi da Hinad, INA ON ELEPHANT ,? (KANGIWA) dariya sosai Hinad tayi ta kalli gefen da Hilal yake zaune cike taff da tarin takaddu a gaba, a hankali tace "gashi can as usual rai a bace,, dariya Musaddiq yayi yace "Me kuma akayi mishi? Su ADEEL nd dere rashin ji, suka jika mishi sketching dinshi da water gun dinsu, kaga yadda yayi musu duka, ko kunyar idon MEERAH baiji ba, kai mishi wayar in mishi magana, kin sanshi da son sktcn dinshi, ko ni da muke tare ban taba ganin su ba duk tsawon shekarun nan, su ya akayi suka gani? oho fa Hinad ta fadi tana karasawa gurin Hilal, mik'a mishi wayar tayi tace "uncle yace in baka, kamar bazai karba ba sai kuma ya karba ya kara a kunnenshi.... Kiiiiiiiiiiiiiiiiiiii!!! ya taka burkin da karfi hade da fadin Inna lillahi wa inna ilaihir, Tsayar da wayar musaddiq yayi a kunnenshi kamar wanda aka dasa, zufa ta shiga karyo mishi, kirjinshi kamar zai fado saboda tsabar firgici, Da sauri Mahmud ya fita cike da masifa ya fara surfa mata zagi jiki na rawa, dago kanta yayi daidai da hasko fitilar da musaddiq yayi alamun kiran Mahmud dan yazo su tafi tunda ba abun da ya faru, tsayar da wutar yayi chak a Kan fuskarta da ta kumbura ta jike sharkaf da hawaye, girman da ta kara bazai sa ya manta fuskarta ba domin ita din jininshi ce, wacce tausayinsu ke karya dukkan sassa na jijiyoyin jikinshi, Cike da tashin hankali ya furta sunan NADEEYAH!!! ,, Tunda ya kara wayar a kunnenshi bai ce uffan ba, tana nan makale a kunnen yanajin duk abin da sukeyi bai tanka ba, bai kuma damu da sanin abinda ke faruwa ba, sunan da musaddiq ya fadi ne ya sanyashi kallon takardun dake gabanshi ya maimaita sunan Nadeeyah? "Me ya Samu Nadiya ya fadi da karfi kamar zai tsaga wayar..... Mrs Tijjani Shattima.... [04/12 09:48] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣3⃣ WOHN IS 3 TODAY ALHAMDULILLAH WOHN FAMILY I LOVE YOU FISABILILLAH... A firgice Hinad ta saki kofin da ta Kai ruwa bakinta ta nufi gurinshi, ihunshi ba ita kadai Ya firgita ba har papa da fitsari ya farkar dashi, palon ya nufa da sauri. tsaye Ya samesu Hinad tana rike dashi tana tambayarshi, wayar dake kunnenshi papa ya amsa Ya Kara a kunne, Shuru yaji Ya cireta ya duba, kallon Hilal yayi yace "lafiya dai?, Kai da wa cikin daren nan,? Kai komai naka baka yinshi cikin hankali, dafa papa hinad tayi tace "shi da uncle ne papa ba fada bane, Wani abu ke faruwa a can gida naji Ya kira Sunan NADIYA, ajiye wayar yayi kan stool Ya Kalli hilal da idanuwanshi da farar fuskarshi sukayi jawur Saboda bacin ran rashin amsashin da musaddiq yayi, burinshi a wannan lokacin ya ganshi a Nigeria, cikin taushi papa yace "wacece nadiya? Inajin Nadiyar mamma suwaiba, Hinad ta bashi amsa,, dafashi papa yayi yace "me Ya sameta? Kamar jira yake "yace Nima bansani ba papa, Musaddiq Yaki fadamin, kamar accident ne! subhanallahi papa ya fadi Yana mai daukar wayar da niyyar sake kiran musaddiq, Ya kira Yafi sau shurin masaki babu amsa, A bangaren musaddiq kuwa tunda Ya saki wayar a kasa Ko takalmin da Ya cire bai sa ba ya fita Ya nufi inda suke, masifa Mahmoud ke mata kamar zai duketa, kuka sosai takeyi tana bashi hakuri, Nadiya!!! Ya kira sunanta a can karkashin makoshi, dago kanta tayi ta kalleshi, bata gane muryarshi ba Kuma bata ganinshi Saboda duhun dake gurin! a kufule Mahmoud yace ka Santa ne? Hannunta Ya kamo ya fara tafiya ba tare da Ya ba Mahmoud amsa ba, kuka mai karfi Nadiya ta saki tana fadin Dan Allah kuyi hakuri wallahi ban san--- shhhh Musaddiq ya katseta hade da daura lallausan hannunshi kan labbanta, hasken motar da ta gifta Su ne Ya bayyana mata fuskarshi, langwabar da kanta tayi hade da sakin doguwar ajiyar zuciya mai hade da shashsheka, hawayen dake fitowa a idanunta Ya shiga share mata da yatsun hannunshi, daga ina kike?? Ya tambayeta Yana mai bude bayan motar, cikin kuka tace "Baba, Baba--bashi da lafiya dan Allah yaya Musaddiq ka taimakemu kar Ya mutu, ba musaddiq ba har Mahmoud dake kufule sai da Ya tausaya mata, shiga ciki muje da sauri Musaddiq ya fadi yana gyara hannun kofar, a gaggauce ta shiga, Gudu Mahmoud keyi kamar zai tashi sama, a dai dai kofar gidan yayi parking, A tare suka shiga gidan da sauri, dakin da yake suka nufa, inda ta barshi a nan ta sameshi, sai dai wannan karan idanuwanshi a rufe suke kamar me bacci, murmushi tayi tace "Alhamdullilah kun ga ya samu bacci, kusa da mamma ta matsa wacce ke jingine jikin gadon kamar mutum mutumi, "ya samu bacci ko Mamma? Na tsorata sosai na fita babu Ko takalmi, a hanya na hadu da Su yaya musaddiq, gasu nan ku gaisa sai ki tashi Baba mu kaishi asibiti, "He is no more fa KYARI, Mahmoud yayi mishi rada a kunne.. Rawa jikin musaddiq ya fara yi Yayi saurin matsawa kusa dasu Nadiya, dafa Mamma yayi hannu na rawa Saboda firgici da tausayin rai, suuuu suka ga ta fadi kasa babu alamar numfashi, Innalillahi Wa Inna ilaihir rajiun Mahmoud ke maimatawa Saboda tsananin tashin hankali, Wani irin kuka Nadiya da musaddiq suka saki a tare, jijjigata Nadiya keyi tana kiran sunanta, komawa jikin Babansu tayi tana tashinshi, Baba ka tashi kaga Mamma, me Ya sameta, waje musaddiq ya fita da gudu Yana kuka kamar ba namiji ba, Mahmoud ne yayi karfin halin dagata Yana mata nasiha, fisgewa tayi ta kwanta kan mamma tana ihun kuka mai Sosa zuciya, "nasiha bata da muhalli a wannan lokacin, (Allah da Kuma Wanda abun Ya faru dashi ne kadai suka San irin halin radadin da mutum yake ciki a wannan lokacin).. zubar da ruwan hawayenta keyi a fuskar mamma Ya fara farfado da ita daga doguwar sumar shock din da shiga, motsin da nadiya taji ne Ya sata mikewa da sauri tana kallonta, dagota tayi tana kiran sunanta da karfi tana dariyar farin ciki, tsugunawa Mahmoud yayi ya rike kanta yace "jeki maza ki debo ruwa, a guje ta fita ta nufi ma'ajiyar ruwan Su ta dibo cikin kwanon sha, tare suka dawo da Musaddiq da idanuwanshi sukayi jawur saboda kuka, a hankali Mahmoud Ya debi ruwan a hannunshi ya shafa mata a fuskarta hade da tofa mata adduo'i,  ajiyar zuciya ta saki Mai karfi ta fara binsu da idanu, tana sauke idonta kan Nadiya ta fashe da kuka Marar sauti, kukan da idan ka ga mai yinshi sai dukkan gabban jikinka sun saki saboda tsabar tausayi, rungumeta Nadiya tayi suka cigaba da kukan tare, Mahmoud ne kadai yayi karfin halin tashi ya rufe Baba da zani sannan Ya dawo Ya dafa Musaddiq yace "Tashi muje mu sanar da mutane a gaggauta Yi mishi sutura kafin safiya, Mikewa yayi yana share idonshi da bayan hannunshi kamar karamin yaro sukayi waje suna jiyo kukan Nadeeyah kamar ranta zai fita... Nayi tarayya da mutane da dama tun tasowa ta har kawo wannan lokacin, na hadu da mutane masu hali na Kwarai haka na hadu da marasa kirki Kwarai dagaske, a cikin yawon da nayi kasashen duniya da cikin kasarmu ta Nigeria ban taba haduwa da mutum Marar imani da kirki Wanda babu abinda ya sani Sai kansa ba irinki ki! dole ne yau in fitar da abin da yake raina, BAKI DA IMANI Badariyya, ki guji bakin duniya, ke ko babu baki ki guji rayuwar ita kanta, ganinki kikayi a inuwata shiyasa kike yin San ran-------- Tabdijam lahaulu Wa la quwwata, Alhaji!!! Ashe da raina zanji batun gori Ya shiga tsakaninka da jinina, Gori kuma??? Daddy ya furta yana kallon mummy da ta rike hab'a tana mishi kallon raini, kuka Badariyya ta fashe da shi tayi hanyar da mummy ta fito ta rungumeta, shafa bayanta ta shiga Yi tace "Gori mana Alhaji, har nawa Badariyya take da zaka kira ta da Marar imani? Har kana furta tana zaune a karkashin inuwarka, wallhy ko a mafarki ban taba kawo zakayi tunanin goranta ma Badariyya ba, Sai gashi yau a zahiri naga wannan bakar rana, mtswwwwwww... Daddy yaja dogon tsaki yace "Na goranta mata, indai Badariyya bazata canza halinta ba wallahi ba gori ba wata rana Kiri Kiri zan nuna ba n------ katse Maganar yayi dan baiga amfanin furta ta ba, Ya cigaba da fadin Kinsan abinda tayi ne, in har kikaji abinda tayi ko ke sai kin kirata da fin kalmar Marar imani, nan ya kwashe duk yadda ya ji sunyi da Nadiya ya fada mata, ya cigaba da fadin kafin in sako riga in fito Yarinyar nan ta Koreta Koda na fita banga Hanyar da ta bi ba, Abin da yafi bani tsananin takaici nayi Allah wadai da ZUMUNCIN ZAMANI bai wuce rashin sanin gidan su Suwaiba ba, kaii Innalillahi Wa inna ilaihir, Allah Ya rangwanta musu daddy ya karashe hannunsa duk biyu dafe a kanshi, duk rashin imanin Mummy saida jikinta yayi sanyi saboda Jini ba wasa bane, sakin Badariyya tayi tace "Baki kyauta ba Badar, Dan Allah Karki sake kinji rashin lafiya yafi gaban wasa kinji, gyada Kai Badariyya tayi tana turo baki, shafa kanta tayi ta nufi Daddy tace tashi muje in rakaka gidan Sai mu kaishi asibiti, SAI DAI KU KAISHI MAQABARTA, GIDA, KUMA DAKINSHI NA GASKIYA, DAKIN DA DUK MAI RAI SAI YA SHIGE SHI.... Muryar da basu tsammace ta a daren ba suka jiyo daga bakin kofa.... In shaa Allah koda 700words ne a rana zaku dinga samu, in banyi ba to ayi min uzuri, yau da gobe Sai Allah... Ina matukar kaunarku Sosai Sosai fa.. Allah Ya hadamu a aljanna firdaus... My world of hausa novel 1/2 (wohn)  I just can't do without you... Mrs Tijjani Shattima...... [04/12 09:48] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u kurah 1⃣4⃣ A tare suka waigo da sauri, murmushin farin ciki da shaukin murnar jiyo muryar sanyin idanuwansu ya dauke  saboda ganin yanayinshi,, mummy ce ta fara isa gareshi ta amshi rigar daya daura a kafada tace "daga ina kake? Yaushe ka shigo kasar? Kaga yadda ka zama kuwa!! ta karashe tana mai tallabo fuskarshi, Hannuwanta Ya cire a fuskarshi Ya fara jan kafarshi a hankali har ya isa gurin mahaifin shi.. "Daddy dan Allah ka taimaka ka dauki liman muje ayi ma Mijin mama Suwaiba sutura.. hannu Daddy yasa Ya share hawaye dake kwance kan fuskar Musaddiq yace "basai ka roke ni ba little yanzu kuwa zamu tafi, Kai dai calm yourself kaje kayi Wanka ka huta Kaji, girgiza kanshi yayi yace "muje tare daddy bazan iya zama a gida ba daren zaiyi min tsawo,, Lallausan hannu yaji cikin hannunshi murya can kasa ta marairaice tace "Haba yaya little, dawowarka kenan fa Ya kamata ka huta Kaci abinci sauran abubuwa Sai su biyo baya, kaga Daddy zai tafi Kuma kaima daga can kake,, yar kara ta saki saboda yadda yayi wurgi da hannunta gefe,   a da yana tunanin halin Badariyya yarinta ne, yanzu kam ya tabbatar wa da kanshi Sam Badariyya bata da zuciyar mutane, babu abinda zai iya canza ta, bata da halin gara a cikin halayenta, tsaki Ya saki Mai karfi hade da galla mata hararar Kyama sannan Ya maida kanshi gurin Daddy yace "muje Daddy, mukullin mota daddy zai dauka Musaddiq yace "Mahmoud na waje tare muke dashi muje a motarshi,  fita sukayi mummy ta Yi Saurin shiga daki ta dauko hijab tabi bayansu... Limamin massalacin gidanshi suka dauko wanda ya fito da likkafanin da baya rabo dashi, da kuma abin gwajin tsaho.. Koda suka isa babu Kowa a kofar gidan, a ciki ne suka ga mata hudu makotansu da mazajensu wadanda kukan Nadeeyah ya   iske kunnuwansu  a hanyarsu ta dawowa daga majalisar dare, Nan take liman yayi gwaje gwajen da zaiyi, Ya baiwa Mahmoud Ya tafi ya kai gurin tela, malam Sada tela yayi Saurin karbar likkafanin da gwajin yace "bari inyi Saurin dinkawa tunda nan kusa muke, Cikin awa daya aka Yi ma 'Malam Adamu' sutura aka feshe shi da turaren Musaddiq dake cikin kayanshi na motar Mahmoud, Adduo'i suka shiga jero mishi na neman yafiyar ubangiji da samun rahama, Sai da suka idar sannan suka Yi ma mamma gaisuwa da sallama hade da fadin sai zuwa safiya zasu dawo a kaishi,, gyada Kai Kawai takeyi idanuwanta na ambaliyar hawaye,  waje suka fita dukkaninsu Mazan, suna fadin halin Kwarai irin na malam Adamu, da irin hakurin da yayi na rayuwar talauci, Mummy da Musaddiq kadai aka bari a cikin gidan, duk yadda mummy takai ga kyankyamin talaucin yar uwarta Sai da ta tausaya mata saboda yadda rai yake da alfarma,   A zuciyarta fadi Kawai takeyi "INA MA NA TAIMAKI ADAMU LOKACIN DA YAKE DA RAI" dana sani Marar amfani mummy ta dingayi wanda hakan yake ga Kowa lokacin da zafin mutuwa ke ratsasu... ( MU TAIMAKI YAN UWAN MU KAR MU BARI SU TAFI SU BARMU DA DANA SANIN DA BAZAI AMFANE MU BA, MU KYAUTATA MU'AMALAR MU DA MAKUSANTANMU KAR MU YARDA MU RASA SU MUNA MASU DANA SANI, MUTUWA BATA BADA NOTICE BARE MUCE ZAMU JIRA LOKACI YAYI MU KYAUTATAWA JAMA'A). Ana idar da sallar asuba Baffa da Goggo suka iso, tun daren mummy keta neman numbersu a kashe, tare suka iso da su mummy da suka koma gida tun dare, A inda mummy ta tafi tabar mamma da Nadiya nan ta samesu, Nadiya ta tura kanta cikin cinyoyinta hawaye Ya jika rigar jikinta har yana diga, kuka Baffa ya fashe dashi a can cikin zuciyarsa yana jin tsanar kanshi na rashin taimaka musun da baiyi ba, cikin muryar kuka yace "Wayyo Adamu ashe mutuwa zakayi, ina ma jiyan da Nadiya tazo na biyota mun kaika asibitin, walhi bani da masaniyar ciwon yayi zafi haka, shiyasa na turota gidanku dan Nasan can akwai direbobi komi dare, wani sabon kukan takaici ne Ya kufce ma Nadiya, Musaddiq da Daddy kuwa waje suka fita saboda takaici, anan ne Musaddiq ya kwashe duk yadda Zumuncin nasu Ya kasance wanda sani tun tasowarsa Ya fada wa daddy, cike da mamaki daddy yace "yanzu duk kudin zakkar da nake bawa Mahaifiyar ku ta bawa Suwaiba bata bata,  Musaddiq yace "wallahi ba'a bata, na dai San ana bata dubu biyar duk shekara, Ya Kara da bashi Labarin abinda ya faru kafin Ya tafi Cyprus, girgiza Kai daddy ya shiga Yi cike da takaicin halin dangin matarshi... Ohhh Ho Ho!! wai waye ne keta damunka da wannan sanyin safiyar, Tsaki taja ta daga kanta a kan kirjinshi ta mika hannu ta miko mishi wayar,  Sai da ta dauka saboda ganin bakuwar number a zatonta mace ce,  jin muryar Namiji yasa ta mika mishi wayar ta Mike ta nufi toilet dan yin wanka, karawa yayi a kunne cikin magagin bacci yace "Waye ne, Hafizu ni ne, 'Garba kero' ne,   Allah yayi ma mahaifinka rasuwa cikin dare, Nima yanzu labari Ya iske ni, A gigice Hafiz ya Mike daga luntsumamman gadon da yake kwance, "kero bansan iskanci kana jina,! in dai so kukeyi kusan inda nake to kuzo ina nan a AYALLA HOTEL Area 11 Abuja, Kazo yau zan baka kudin da ka tambayeni, amma ka daina Yi min wasan mutuwa akan iyaye na, Tsaki kero yayi hade da hadiye yawun bakin shi yace "in kaga dama  daga nan ka wuce ROCK VIEW, damuwarka ce, bana bukatar kudinka yanzu, saboda ina neman na kaina Kuma ina tafe da albarkar iyaye, Kuma kasan, Ni ba mahaukaci bane da zanyi maka karyar rasuwa, mahaifinka Allah Ya karbi abinshi, kana iya zuwa in kaga dama, in kuma babu dama to kana iya tura mishi da addua dan dama zuwanka bazai maido shi ba, yaja tsaki ya kashe wayar cike da takaicin halin son kai irin na Hafeez, (Dama Halin mutum na Kwarai ko kirki baya bayyana Sai yayi arziki).... Jiki na rawa Hafeez ya Mike, Ya dauki riga Ya sawa jikinshi, ko jiran farkarshi baiyi ba yayi waje yana jiyo muryarta tana kwala ihun kiranshi, inaaa bai ko waigo ba bare yayi tunanin komawa dakin Ya sallameta, Motarshi Henesy ya shiga ya tayar Ya fara gudun fitar hankali, hanyar Kaduna Ya dauka yana tafe yana kukan dana sani.... Takwas da rabi ya iso gidan lokacin ana kici kicin daukar gawar Malam Adamu, kuka ya fashe dashi da ya hada ido da mamma, Kure shi tayi da ido cike da mamaki da takaici, durkushewa yayi a gabanta yana kuka Mai Sosa zuciya, ganin da yayi za'a fitar da gawar ne Ya sanya shi mikewa da sauri ya nufi gawar, ya sa hannu zai karbi makarar a hannun Musaddiq yaji wata gigitacciyar tsawa a bayanshi, " IDAN KA KUSKURA TA TABA MAKARAR NAN BAZAN TABA YAFE MAKA BA,, Chakkk ya tsaida hannunshi ya waigo ya Kalli cikin idonta, kau da kanshi yayi da sauri saboda abun da ya gani a kwayar idon, soyayya mai dishi dishin kiyayyar bacin rai ya gani, "Kiyi Hakuri Suwaiba, mahaifinshi ne Ya zame mishi dole yayi rakiyar gawarshi, Sailuba matar malam Sada ta fadi tana share hawaye, "Ban hanashi rakiya ba, amma kar kazamin hannunshi ya kuskura ya taba min gawar miji, ta karashe hade da mai da kanta jikin bango tana gunshekar kuka, fitar da gawar akayi nan gidan ya sake gawraye da kukan mutane musamman makusantan gawar..... Mrs Tijjani Shattima [04/12 09:49] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣5⃣ Ranar murna, mun cinye gasar BBC, proudly fikrians💃🏻💃🏻💃🏻 Safiyya ciyaledi i ❤ u bebi..... FIKRAH WRITERS Bamu fi kowa ba, Amma da wuya ka samu irinmu, komai namu daban yake... Yin na Allah ne ba namu ba ALHAMDILILLAH..... "Ita Rayuwar nan da kake ganin ta Hafeezu kamar gari ne kaje wanda ba naka ba, kaga komai daren dadewa, komin dadin zaman garin nan dole ka barshi, saboda ba garin ka bane, bakunta ne ya kaika... TALAUCI jarrabawa ce babba wacce cinyeta yana da matukar wahala, duk karfin imaninka dole wata rana zuciyarka ta raurawa saboda zafin wannan jarabawar, Haka shima *ARZIKI* Jarabawa ce mai wuya kuma mai sauki ga wanda ya fi karfin zuciyarshi, ina mai baka shawara da kayi yaki da zuciyarka, ka tafiyar da arzikin da ya fara ziyartar hannunka ta hanyar da ya dace, domin akwai ranar da zakayi bayanin hanyar da ka kashe su, nayi maka farin ciki matuka na samun abin yi Allah ya sanya wannan arzikin ya zama sanadiyyar shigarka aljanna, Allah ya baka ikon sauke hakkinmu kafin mu bar duniyar nan domin Allah shi kadai yasan gawar fari..........  **** Durkushewa Hafeez yayi idonshi na hango murmushin fuskar mahaifinshi yayin da yake mishi wannan Nasihar, Wayyo Allah na, wayyo Baba, kaico na, kaicon rayuwata, ya Allah ka dauki raina nima in huta da wannan bakin cikin, wayyyyo baba..., dakyar mazan gurin suka iya dagashi saboda yadda ya cije yana buga kanshi a kasa, ku sakeni Dan Allah rayuwata bata da sauran amfani, dan Allah ku barni in mutu, Tsawa mai karfi Daddy ya daka mishi hade da ma mutanen alamu da su sake shi, hannu yasa a bakinshi yace "wallahi zan bata maka rai idan kayi yunkurin sake koda nishi kwakwkwara a gurin nan,   in har so kakeyi ka nuna mana ka fita a musulunci to kaje daga wajen makabartar nan akwai rijiya ka fada, domin wannan duk haukan banza kakeyi,   Nutsuwar da daddy yaga ta bayyana jikin Hafeez ne yasa shi ya sakko ya dafa shi yace "zai fi kyautuwa ka tsuguna kayi mishi addu'a domin a wannan gabar ita kadai yafi bukata a gurinka ba kuka ba, Hannun Daddy Hafeez ya kama yana kuka sosai, yace "in na rokeshi gafara zai ji ni ya yafe min, idon Daddy ya ciko da kwallar tausayi domin yana auno shine mahaifinshi ya mutu yana fushi dashi, rungumeshi yayi yace "nasan ya yafe maka Hafeez kai dai ka dage mishi da addu'a da sadaka su kadai zasu nuna zallar soyayyarka a gareshi.... limamin da ya jagoranci sallar gawar ne yayi addu'oi hade da nasihohi, sannan duk suka juya suka bar makabartar suna masu yi ma mamacin fatan dacewa...... CYPRUS Tsaye yake jikin wagegen bud'ad'd'en windon dakinshi, iska na kada labulen windon yana taba gefen fuskarshi, hannunshi rike da daya daga cikin zanen, ya kura mishi jajayen idanuwanshi, zuciyarshi a karye take a wannan lokacin, wayarshi ya dauko ya sake kiran Musaddiq, wannan karan ma bai daga ba, wurgi yayi da wayar hade da dafe kanshi yana mai jin radadi a cikin zuciyarshi, komawa gado yayi ya kwanta ruf da ciki, shi kanshi a yawancin lokuta yana mamakin yadda Nadeeyah ke makale a cikin dukkan kewayen zuciyarshi, tun baisan kalmar So ba yake jinta a ranshi, tun ganin da yayi mata lokacin da ita kanta bata san kanta ba, yana mamakin da a kullum bashi da zanen da ya wuce nata, kullum kara auno fuskarta yake da yanayin girmanta, gyara kwanciya yayi yanata juye juye, a kunnenshi akayi kiran sallar asuba, mikewa yayi jiki ba kwari yayi alwala ya fito dan zuwa masallaci, Anty Reemah da Papa ya hango zaune a parlon kasa sunyi jugum jugum cike da damuwa, da sauri ya sakko daga sama har yana bige kafarshi a matakalar karshe, baibi takai ba ya karasa gurinsu, Mum, Papa, "meya faru na ganku haka? Ya tambaya yana mai tsugunawa kusa da mahaifiyarshi, uhhmm Anty Reemah tace, sannan ta cigaba da cewa, "mijin Mama Suwaiba ne ya rasu cikin dare, yanzu Raliya ta kirani ta fadamin, "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kalmar da Hilal keta maimatawa kenan a cikin zuciyarshi, tunanin shi ya tafi gun sanin halin da Nadeeyah take ciki, zungurinshi Anty Reemah tayi tace "bakaji an tada Sallah bane, mikewa yayi a firgice ya bi bayan Papa da yake kokarin fita daga kofar palon..... Kuka sosai Badar takeyi hannunta rike da kanta tana shashsheka, saboda tsabar kuncin da take ciki bata san gari har ya waye ba, rana ce ta kyallaro ta jikin dan tsagin labulen ta kashe mata ido, a daidai lokacin ta mike da niyyar wucewa daki tayi tozali da madubin parlon, wani irin kamanni ta gani a tattare da ita mai wuyar fassaruwa, fuskar nan tayi jawur hancin yayi suntum saboda kukan da tasha, wani kukan ta sake fashewa dashi hade da rugawa cikin daki, cikin kunan rai ta fada bayi ta kunna pampo tana watsa ruwa a fuskarta tana magana cikin kuka, "Nadeeyah bazan taba kyaleki ba, kamar yadda kikayi min ruining wannan ranar sai nayi ruining life dinki gaba dayanta, bazan taba iya tuna rabon da na zubda hawaye ba, amma yau na zubar sanadiyar ki,  na tsaneki, na tsaneki Nadeeyah!! ta karashe hade da kifa kanta jikin bangon bayin........ Mrs tijjani shattima..... [04/12 09:49] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣6⃣ A yau ne malam Adamu ya cika kwana bakwai da mutuwa, in kaga Nadeeyah da mamanta a wannan lokacin sai ka matukar tausaya musu, duk da irin wadatar abincin da suke samu baisa su walwala ba bare har su kai ga cinshi cikin jin dadi, A cikin kwanakin Mummy tayi bajinta matuka, ta manta duk wani girman kai nata, sai ma tsananin tausayin yar uwarta, A wannan lokacin ne Daddy da Musaddiq da duk wasu makusantansu suka san lallai jini daya ya wuce wasa, yaran mummy ma sunyi bajinta matuka daga su har mazajensu, sam mummy bata ba kowa kofar da zaiyi complain ba.. A cikin kwanakin kullum ta koma gida a tsorace take, Jikinta na bata kamar  zata iya rasa wani makusancinta lokaci daya, ( Nidai nace Allah yasa wannan canjin ya daure).. Bayan an watse adduar bakwai kowa na shirin tafiya gida, mummy ce ta shigo daki ta zauna gefen gadon da mama suwaiba take, cikin Nasiha tace "suwaiba ki kwantar da Hankalinki, kiyi tawakkali, Allah ya fiki san Adamu, kuma ya karbi abinshi, dan Allah kar kiyi abin da zai sa ya'yanki su cutu, domin yanzu ke kadai kika rage musu, dan Allah suwaiba ki rage tunani, ga kayan abinci nan na hadesu guri daya, na bawa Nadeeyah mukullin, gyada kai mamma tayi idon nan yayi ciki ciki, tace "Mun gode mummy Allah ya bada lada, Allah ya biyaku da gidan aljann----- bata karashe ba kuka mai karfi ya kwace mata, Hakuri su mummy da sauran matan dakin suka shiga bata suna tayata sharar kwalla, nan fa kuka ya rikide ya zama tari mai karfi, tun tana tarin da sauran karfinta har takai ga ta fara tarin jini, a gigice mummy ta fito tana kiran sunan Hafeez.. Hafeez na kofar gida yana sallamar baki shi da musaddiq suka jiyo ihun mummy, suka ruga cikin gidan a guje, a rude mummy tace "maza ka fito da mota Hafeezu mu tafi asibiti Suwaiba Aman jini takeyi, fito da ido waje Hafeez yayi cikin firgici yace "aman jini? eh mummy ta fadi tana turashi cikin dakin, Daukota yayi cakk ya fito da ita waje yana fadin dan Allah mamma kiyi hakuri, karki tafi ki barmu, gurin motarshi ya nufa da ita musaddiq ya bude baya aka shimfideta, gefe Nadeeyah ta shiga idon nan a kafe babu ko digon hawaye, zafin da kirjinta yakeyi ba mai kwatantuwa bane a wannan lokacin, motar Hafeez yaja da karfi suka nufi Asibiti mafi kusa. Da isarsu Hafeez ya sauka ko key bai cire ba ya fara kiran nurses, gadon emergency aka gunguro aka shimfideta a kai, gungurashi ciki suka fara yi da sauri sauri, da kyar kalmar salati ke fita a bakin mamma, babu wani sauran karfi a tattare da ita, komai nata ya riga ya gama sakewa, da karfi ta cakumo hannun Nadeeyah wacce take tayata salati ta hada da na Hafeez, idanuwan nan nata dakyar take iya budesu, "Ka rike min su Amana Hafeez, dan Allah ka rikesu, nasani kai me rauni ne Hafizu, abu kadan ke juya kwakwalwarka, na rokeka kar ka barsu suyi kukan rashin mu, na yafe maka, kuma mahaifinka ma ya yafe maka, ta juyo da kallanta gurin Nadeeyah da idonta ya kada sosai tace "Nasani Zainab nada nagartacciyar uwa, basai nace komai ba! Allah ya albarkaci rayuwarki, kiyi Hakuri da rayuwa Nadeeyah, ina matukar alfahari dake tun daga haihuwarki har kawo yau, Allah ya cigaba da taimakonki a duk halin da kika tsinci kanki, hannu Nadeeya tasa ta rufe mata baki tace "mamma babu abin da zai sameki in shaa Allah.. Dakin emergency aka shiga da ita aka ce su jira a nan likita zai shiga ya duba ta, kuka sosai Hafeez da Musaddiq keyi, Nadeeyah ce kadai tayi karfin halin yin addu'a, minti talatin da shigar doctor su mummy suka shigo, kafin su karaso doctor ya fito fuskar nan cike da damuwa, Kallon Hafeez yayi nan take zuciyarshi ta karye yace "am sorry, she is no more!! zuciyarta ta kai awa daya da yin collapse, yanzu ta daina aiki kwata kwata.. wani irin ihu Mummy ta saka wanda ya razanar da daukacin mutanen asibitin... Juyayi kwakwalwar Nadeeya ta shiga yi, a can cikin kanta take jin kalmar "she is no more, baya ta fara ja tana ganin mutane biyu biyu, kukansu sai juya kwakwalwarta yakeyi, batayi aune ba sai jinta tayi jikinta ya saki bata da wani sauran karfin da jikinta zai dauketa, sulalewa tayi saura kadan ta kai kasa, Cikin zafin nama ya karaso gurin ya riketa, babu wanda hankalinshi yake kanta, kowa kuka yakeyi babu kakkautawa, suma shigowarsu gurin kenan don daga airport asibitin suka wuto saboda Raliya ta fada musu halin da ake ciki.. Sunan Doctor HILAL ya fara kira da karfi hade da dagata ya rike a jikinshi, nan take hankalin masu kukan ya dawo kansu, wani daki aka shigar da Nadeeyah aka kwantar da ita a kan gado, hannunta Hilal ya rike yana murzashi da karfi yana kiran sunanta, koda doctor ya shigo Hilal na zaune a gefen gadon yanata bubbuga hannun, magana doctor yayi mishi yace ya tashi ya dubata, mikewa Hilal yayi ya koma kusa da su Papa ya harde hannunshi hade da jingine kanshi a bango, zuciyarshi ta karye matuka, da ya iya yi ma damuwa kuka da irin kukan da zaiyi ba mai misaltuwa bane, sai dai shi sam kuka baya daga cikin jerin abinda ya dauka me yaye damuwa, dan in yaga mutum na kuka har mamaki abun yake bashi. Minti kalilan doctor yayi a kan Nadeeyah ya fita bayan ya sanar musu shock ne yasa ta faduwa, amma in shaa Allah nan da awa daya zuwa biyu zata farka... Dakin gawar suka koma, kuka ya dawo musu sabo,    Zuwan Daddy ne ya sanyasu cikin hankalinsu da nasihar da yayi musu, sannan yasa aka dauki gawar a ambulance suka wuce dan yi mata sutura.... ( *ALLAHU AKBAAR*    Haka rayuwar ta gada, mutuwa na daya daga cikin abubuwan da muka debo na daga rayuwarmu, akwai masu rasa biyar lokaci daya, kuma badan Allah baya sansu bane, sai dai dan musan mutuwa ta zama dole, dukkanmu zamu dandanata komin daren dadewa, Allah ya kara mana hakurin rashin da mukayi dukkaninmu, kuma yasa mu cika da kyau da imani) Ameen ya Allah Mrs Tijjani shattima... [04/12 09:50] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU By Aysha Ya'u Kurah 1⃣7⃣ Ba gidan mutuwar ba, har unguwar su Nadeeyah sai da ta sake hargitsewa da koke koke, duk rashin imanin mutum sai ya zubar da hawaye saboda tausayin rai... ana sauke gawar, kofar gidan ya sake dinkewa da mutane.. A sanyaye Zainab ta shigo gidan, dama dakyar taje islamiyya a ranar, Hafeezu da kanshi ya kaita saboda tirjiyar da tayi, sai da ya sai mata sweets sanan ta yarda suka tafi.. mummy ta tarar a zaune tana kuka kamar ranta zai fita, duk sauran yaran na kanta suma suna sharar kwalla, dakin mamma tazo shiga da sauri, bin bayanta Husna tayi dan ta hana ta shiga, kafin Husna ta karasa zainab ta isa cikin dakin, kwance ta samu Mamma a rufe cikin likkafani, a gigice ta karasa jikinta, girgizata ta shiga yi tana fadin Mamma me ya sameki? meyasa naga suna ta kuka a waje, duk da karancin shekarunta tasan menene mutuwa domin tun rasuwar mahaifinta tasan mecece kalmar, kuma ta fahimci in mutum ya mutu to fa bazai dawo ba, kuma taga yadda akayi wa babanta haka akama mamanta, domin kafin a fitar da gawarshi saida aka kaita kanshi, wani irin kuka ta saki hade dayin wurgi da sweets din da Hafeez ya sai mata bata sha su a makaranta ba, Mamma ki tashi, dan Allah ki tashi, wallahi bazamu sake barinki kiyi kuka ba, ga yaya Hafeez ma zance kar ya sake tafiya ya barmu, dan Allah ki tashi, hannun wacce tayi mata wanka ta kamo tace "dan Allah ki tasheta, kice tayi hakuri karta tafi yanda Baba ya tafi, wallahi muna santa ni da Anty Nadeeyah, kowa baya santa, tasani mu kadai ne muke santa, rungumeta Husnah tayi hawaye na bin idanuwanta, ta dauketa ta fitar da ita a dakin dakyar,, babu wanda bai zubda hawaye a gidan ba.. Bayan an gama shiryata kowa yayi mata addu'ar samun dacewa da rahama.. Baffa na zaune a kofar gida, idon nan nashi kamar gauta, jikinshi babu inda baya rawa, dakyar aka dagashi ya shiga dan yiwa diyarshi addu'a, ki yafe min suwaiba, ki yafe min, ubangiji Allah yayi ma abin da kika bari albarka, na cutar dake matuka, tun kuruciyarki har kawo yau, kuka sosai yakeyi kamar karamin yaro, tabbas mutuwa tayi mishi gaggawa, ina hankalinshi yake lokacin da yake azabtar da marainiyar Allah, babu abin da yasani nata tun tasowarta, bashi da masaniyar damuwarta, duk rashi irin nata bata taba gajiyawa gurin kyautata musu shi da matarshi ba, wani irin kunci yakeji a cikin ranshi da ya tuno bai taba barinta ta samu abinda take so ba, kallon gefenshi yayi ya hango Daddy tsaye shima hawayen ne ke zubar mishi babu kakkautawa, dukkansu biyun abubuwa masu zafi suke tunowa da faruwarsu shekaru da dama da suka shude, share hawaye Daddy yayi ya fita daga dakin zuciyarshi a karye... ************ ****Kalli sararin samaniya ki fada min abun da kika gani, sauke idonta tayi bayan ta kalla, tace "Naga abubuwa da yawa, wasu taurari masu kayatar da duhun daren samaniya, saidai Mamma, ga wani tauraro can, yafi kowanne haske, ga kuma wasu masu haskawa biyu a kewaye dashi, sannan ga wasu can sun disashe su biyu ba'a ko iya hangosu, murmushi Mamma tayi ta dafa Nadeeyah tace "Tauraron da yafi ko wanne haske 'Kece Nadeeyah', sannan biyun dake kewaye dake bani da masaniyarsu, amma tabbas alkhairai ne masu karfi da yalwa a kewaye dake, sannan sai biyun da suka disashe----- sai tayi shuru tana kara kallon sama, tace "bar batun biyun nan Nadeeyah Allah kadai ya barwa kanshi sani, saidai a gefen tauraronki baki hangen wani wanda yake turo kai karfi da yaji yana san doke hasken naki, da sauri Nadeeyah ta kalli sama, a firgice ta maida kanta kasa tace "waiii Mamma wannan hasken mai cutarwa ne, bazan iya jurar kallanshi ba.. Jajircewa zakiyi Nadeeyah, daurewa zakiyi ki fuskance shi domin bashi kadai bane, hango wani yana fasowa a dayan gefen, duk sun kewaye taurarin dake kewaye dake da haskensu, waigawa tayi cike da zumudi da murnar jin maganar mahaifinta, Baba dama baka mutu ba? kaga yadda kayi kyau kuwa, hannuwanta ya kama yace "Tafiya ce ta kamani ta gaggawa, kinga mahaifiyarki bata iya jure zaman, ta biyoni, saidai dawowar mu ba mai yiwuwa bace, domin tafiyar ta din din ce, lokacin da zakiyi wannan tafiyar baiyi ba, yanzu lokaci ne na hakuri da jajircewa, in kina son nasara sai kin jure, in kina san zuciyarki tayi haske sai kinyi hakuri, "Amma fa ba hakurin da zai cutar dake ba, cewar mamma tana murmushi tana shigewa jikin mijinta, akwai hakuri me cutarwa ne Suwaiba, murmushi tayi tace "akwai mana, hakurin da kana ji kana gani a taka ka a wuce, wannan hakurin ka iya fasa zuciya, manzon Allah s.a.w yace "in bazaka iya hakurin abun da akayi maka ba ka rama daidai yadda akayi maka,, "kwarai haka yake, Baba ya fadi sannan ya cigaba cewa "ke din me nasara ce, zaki daukaka fiye da tunanin mai tunani, saidai kinsan dukkan ma'abocin daukaka yana tare da kalubale, amma ki sani kuma kisa a ranki, a ko yaushe Allah swt yana tare dake, karki yada Addu'a domin ita din garkuwa ce ga mu'imini... lokacin tafiyarmu yayi, ki kula da dukkan rayuwarki da ta yar uwarki, sannan kiyi hakuri da dan uwanki, domin shi din mai rauni ne, Nadeeyah tayi saurin cewa "zan biku Mamma, murmushi mai sanyin kyau sukayi mata, suka hade baki cikin murya me kamar amsa kuwwa, sukace "wannan tafiyar ta musamman ce, lokacin yinta a gareki baiyi ba Nadeeyah, Tafiya suka fara yi Nadeeyah na binsu tana kuka tana fadin karku tafi ku barni, tun tana hangensu har haske ya kara kewaye gurin, tsayawa tayi hade da runtse ido tana kiran sunayensu hade da shashshekar kuka... Hannun da taji kan kuncinta mai sanyin kamshi ne ya soma farkar da ita, a hankali ta bude idonta ta saukesu kan Hinad da itama kukan takeyi.. "Sorry Nadeeyah, kiyita karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun, i know it hurts but bamu da yadda zamuyi, addu'a itace tafi dacewa dasu a wannan lokacin, Allahn da ya halicce su ya fimu sansu..  kawar da kai Nadeeyah tayi tana tunano hirarsu ta cikin mafarkinta, "kunyi tafiya mai nisa Mamma, tafiya mai dadi a gareku in shaa Allah, sannan mai radadi a garemu, hawayen idonta bai bar ambaliya ba ta cigaba da maganar zucin da takeyi, yanzu yaya rayuwarmu zata kasance, shikenan bamu da wani sauran gata... "Gatan kowa Allah ne Kanwata, babu wani gata mai daraja, dadi, da dadadawa irin na ubangiji, in Allah ya baiwa bawa gata, to babu wanda ya isa ya tauye ko ya kwace mishi, mika lamarinki gurin ubangiji, kuma kiyi tawakkali kisan shi ne kadai maiyi... saida ya kai aya Nadeeyah ta dago ta kalli gefen da yake, tabbas zancen da takeyi a zuci ne ya fito har ya iske kunnuwanshi, shi din ma tsaye yake idon nan nashi yayi jawur kamar gauta, wani hawayen ya share sannan ya karaso jikin gadon da take, zama yayi gefenta yace "ya jikin naki, runtse ido tayi ta amsa da sauki, Allah ya baki lafiya da hakuri hade da juriya, "Ameen yaya Musaddiq,  Hinad fadi tana share mata sauran hawayen dake gefen kunnenta.. Ina Zainab take yaya Musaddiq? Kafin Musaddiq yayi magana sukaji an murda kofar, Hafeezu ne ya fara shigowa sai su Anty Reemah, Hilal ne karshen shigowa shi da zainab, hannunta rike da ledojin kayan kwalama, fuskar nan tata tayi jawur, tana ganin Nadeeyah ta saki ledar ta karasa ta fada jikinta tana kuka, mikewa Nadeeyah tayi a hankali sannan ta janye daga kusa da  musaddiq, ta dago kan zainab tace "menene, me aka miki? Anti Nadeeyah mamma ma ta mutu, ta tafi gurin baba, sun dauketa sun fita da ita, shikenan bazamu sake ganinta ba, dariya Nadeeyah tayi tace "inji wa yace miki, mamma bata mutu ba, kinsan tace miki zata je Agadaz rannan ko? Eh zainab tace tana me kallon Nadeeyah, to can ta tafi, kina gani sun shiryata ta hau jirgi tana jin dadinta ke kuma kina nan kina kuka, oya share hawayenki ki ji abin da mamma tace in fada miki dazu kafin ta tafi, da sauri ta share hawayenta ta matso da kunnenta kusa da bakin Nadeeyah, rada tayi mata a kunne wanda Allah kadai yasan me tace mata, sai ko Zainab ta kyalkyace da dariya hade da rungume Nadeeyah, tace "dagaske kikeyi Anti?  Gyada kai Nadeeya tayi tace "eh, hawayen da ta boye ne ya fara bin idanuwanta, ta kankame zainab tana zubar dasu ba tare da ta bari ta gansu ba, wayyo mutuwa.....! @ Mrs Tijjani Shattima....! [07/03 6:31 AM] fareedah: ●ZUMUNCINMU A YAU● 1⃣9⃣ By Aysha Ya'u Kurah Had'a kayayyakinsu cikin jaka Nadeeyah keyi, idanuwan nan nata sai ambaliyar ruwa suke, Hafeez ke tayata had'a kayan yana labarta mata abubuwan da suka gifta tsakaninshi da iyayensu a yan watannin da suka shude, jan numfashi yayi kamar karamin yaro, daga zuciya har idaniyar shi zubar ruwan hawaye sukeyi, "yan kudaden da suka fara shigowa hannuna su suka ruda ni, na canza abokai, kullum bani wancan club bani wancan, ban tsaya nan ba har sai da na koma harkar mata, tun ina boyewa, su Baba basu sani ba har takai ga mata har gida suke biyoni, bazan taba manta daren da zan bar gida ba, Baba ya fito zai tafi Sallar asuba ya jiyo muryata da SAILUBA yar gidan Hinde mai tuwo, ranar a daki na ta kwana, Koda Baba ya bude kofar, Sailuba na kwance a jikina, duk yadda na kai ga tureta in suturta jikina ta kafe ta danneni, na kasa tabuka komai, saida Baba ya juya, nayi karfin halin turata na mike nasa jallabiya nabi bayanshi, Kuka na tarar dashi yana yi a tsakar gida, a tare muka iso inda yake ni da Mamma, ajiye butar hannunta tayi ta fara tambayarshi dalilin zubar hawayenshi, bai kai ga yin magana ba Sailuba ta fito da daurin kirji da kayanta a hannu tana sawa tana fadin "Zo ka sallameni Hafeezu in tafi kar a nemeni a gida, wani irin juwa Mamma ta ji a tsakiyar kanta, bakinta da kyar yake iya furta innalillahi wa inna ilaihir rajiun, daki Baba ya jata ba tare da ya dubi inda na ke ba, koda na biyosu ciki da sauri Baba ya dakatar dani yace "fitar min a daki da kazantar dake jikinka, tafi kaje ka sallameta, ka wadata ta da duk wani nau'i na jin dadi tunda kaima ta jiyar da kai dadin, ubangiji Allah ya shiryar dakai Ameen, Har na iso kofar dakina ina jiyo sautin kukan mamma, Baba yana ta bata hakuri.. Da kudin da ni kaina bansan yawansu ba na sallami Sailuba, sai na wuce nayi wanka nayi sallah, shaidan ya dinga raya min in bar gidanmu in tafi can inda babu wanda yasanni, tunda ina da kudina inje in ci karena babu babbaka, a haka nabi umurnin zuciyata na shirya kayana tsaff na sasu a mota, Zainab na gani a kofar shagon Tasi, na bata dubu biyar ta kaiwa Mamma, nace ta fada musu nayi tafiya, tun kafin ta shiga gidan na shige mota nayi gaba, a tunanina duniyata zatayi kyau tunda babu mai samin ido, ashe tafiyar da zata kashemin zuciya ta barni da dana sani har karshen rayuwata nayi... ya karashe maganar cikin matsanancin kuka... Takalman Zainab Nadeeyah ta tura cikin ledar dake hannunta, wacce tun fara bata labarin ta budeta da niyyar zuba takalman, ledar ta jike sharkaff saboda hawayen da ke sauka a kanta, kallon Hafeez tayi tace "Yaya Allah yayi mana jarabawa mai zafin gaske, rayuwa ce yanzu zamu fara ta wacce bamu san inda zata kaimu ba, ka godewa Allah da yasa suka yafe maka, sannan kaji tsoron Allah, ka nisanci duk wani aikin alfasha, kasani duk abinda zakayi yanzu za'a tada su Mamma ace su tashi suga dansu, shin irin wannan tarbiyar suka baka, kasani yanzu babu wani wanda zai fada maka gaskiya, rayuwa ce zakayi ta ta rashin mafadi, kai da kanka zaka zama mafad'in kanka, ni da zainab kuma duk inda zamuje na tabbatar bazamu rasa mai kwaba mana ba, kaga mummy yanzu ta canza, matsalata daya itace "Bad----- shigowar Hinad cikin dakin ya katseta, ta kallesu tace "Nadeeyah Mummy tace kuyi sauri, hawaye ta share ta dauki karamar jakar, Hafeez ya dauki babbar suka fito sukayi waje, loda kayan sukayi a motar Hafeez, sannan kowa ya shiga mota, Hinad da Nadeeyah motar Hafeez suka shiga, makota suka kewaye su Nadeeya anata musu fatan alkhairi, Tasi ya leko ta windon motar, ya miko mata ledar lolli pop idonshi cike da kwalla yace "ki ajiyewa Zainab, Allah ya hadaku da alkhairi Nadeeyah, Wani kukan ta fashe dashi na tuno memories dinsu na lokacin da dukkan iyayenta suna da rai, da irin kara kainin da sukayi tsakanin gida da shagon Tasi, Tasi ya bada gudunmuwa mai karfi a rayuwarsu, bai taba kazawa gurin tallafa musu da bashi da kuma kyauta ba, kallonshi tayi yana share hawaye tace "mun gode Tasi Allah ya saka maka da gidan aljanna.... Islamiyyar su Zainab suka biya dan daukota, motar Mahmoud suka tarar a kofar makarantar, kafin suyi parking suka hango Musaddiq rike da hannunta sun fito daga ciki, baya ya bude mata suka shige, Mahmoud yaja motar suka wuce, Bayansu Hafeez yabi, zuciyarshi ta dan rage zafi da fargaba saboda yasan in shaa Allahu Musaddiq da mahaifinshi bazasu bar kannenshi cikin garari ba..... A katafaran gidan "Alhaji Mukhtar Kyari dukka motocin sukayi parking, Ta window Badariyya take lekensu daya bayan daya, Husna da dawowarta daga saloon kenan ta fito daga bayi tana kallon Badariyya a jikin Window tana leke, murmushi tayi ta zira Hijab dinta ta fito tsakar gidan tana ma mummy barka da dawowa, dan ita ba gidan rasuwar take kwana ba, gidan Anty Raudha take bin ta su kwana, yau ne kadai bata je gidan rasuwar ba taje saloon dan wanke kanta, Anty Radiya da Anty Raudha suka kalleta cike da shakiyanci suka ce "Amarsu ta ango, cikin rashin fahimta ta waiga bayanta taga babu kowa tace "wacece haka? Dariya suka kwashe da ita suka ce ke mana! Zatayi Magana Anty Reemah tace "wani irin sakarci ne wannan, ku dan matsa daga can mu wuce sai ku cigaba da shakiyancin tunda sa'arku ce Husnan, darewa sukayi ta wuce ita da Anty Raliya, harara Raudha tabi Raliya dashi tayi tsaki tana kunkuni a ranta, "su in an barsu mutanen kirki, Radiya tace "manta dasu dallah, taja Husna sukayi ciki, mummy tayi kamar bata jinsu tace ma Nadeeyah su kamo kayan su shigo, A d'arare ta dauki jakar ta fara tafiya, kama gefen jakar Hinad tayi suka karasa cikin parlon, wani irin faduwar gaba Nadeeyah taji, idanuwanta suka ciko da kwalla, tuno abubuwa mabanbanta da suka faru da mahaifiyarta na rashin dadi ta dingayi, wani lungu ta zauna inda suka saba zama da mahaifiyarta in sunzo gidan..... Labulen windon Badariyya ta saki kirjinta kamar zai fado saboda bakin ciki, bata hango Nadeeyah ba, amma ganin Zainab a gurin Musaddiq suna magana yana dariya ya tabbatar mata da lallai su Nadeeyah sun dawo gidansu da zama, bata karasa tunaninta ba taji an shigo dakin ana dariya, Cikin kaguwa Husnah tace "Anty Raudha tell me, waye amaryar plss, Radiya ta ajiye yaronta Fadeel a kan gadon tayi hanyar bayi tace "ke mana, kece amaryar Hafeez, wata dariyar suka sake kecewa da ita sannan Radiya ta shige bayi, Husnah ta turnube fuska tace "wani Hafeez din, Anty Raudha tace "Hafeez din mama Suwaiba mana, kaff ta kwashe labarin abinda ya faru ta fadawa Husna suka karashe da dariya dukkaninsu, Badariyya tayi tsaki mai karfi tace "da an hadasu din, da zaifi mana alkhairi walhy, domin zuwansu nan din gaskiya akwai matsala, bama mai yiwuwa bane zamansu anan!! ta karasa fadi a gadarance, "Saboda kece mai gidan ko, Raliya da shigowarta kenan ta fadi tana harararta, Raudha tayi tsaki tace "nima zamansu anan din walhy bana sanshi, ni fa Allah ya sani na tsani talaka, ko sunan talauci banasan ji, Radiya daga bayi ta dago murya tace "ai talauci masifa ne, ni na rasa laifin me talaka yayiwa Allah, subhanallahi!!! Raliya tayi saurin cewa, ya salam, ku kuwa kuji tsoron Allah, talaucin nan fa wadanda suke cikinsa basu suka sawa kansu ba, kuma basu isa su cireshi ba sai Allah yaso, haka zalika arzikin da kuke ciki baku kuka bawa kanku ba, babu banbanci tsakaninmu, tunda duk abinda da talaka zaiyi mai kudi ma zaiyi, wadatar zuci tafi komai a rayuwa, suma Allah bai mance dasu ba, kuyi fatan kar Allah ya jarbceku da dandana rayuwar talauc----- "" eeeeeeh eeeh wait hang it, Radiya tayi saurin katseta, " har abada bazamu taba dandanawa ba "idiotic being, saboda muna sharhi kan talauci shine zaki rabashi jikinmu, to we reject it walhy, sakarai kawai,, uhmmm kawai Raliya tace ta fita tana mamakinsu, har ta kure dakin bata daina jiyo muryoyinsu ba.... Har karfe biyar na yamma Nadeeyah na zaune a inda take, da himilin kayansu, anan taci abincin da me aikinsu ta zubo mata, tana kallon dukkan ahalin mummy a cikin parlon ana hira, Anty Reemah ce kawai bata cikinsu, dan ita tun zuwansu suka wuce can gidansu ita dasu Hinad, ba yadda Hinad batayi tazo su tafi ba taki, kwanciyar hankalinta daya zainab ta bisu shiyasa ma zaman bai gundureta ba, gyangyadi ta farayi a zaune ta jiyo muryar Badariyya tana zuba rashin kunya tana fadin "wallahi mummy indai yarinyar can zata zauna a gidan nan ni bazan zauna ba, saidai ku zabi daya, janyota mummy tayi jikinta tace "haba baby, kiyi hakuri mana, dalili ne yasa zata zauna, kiyi hakuri pls na lokaci ne, kuma kinga makaranta zata koma, ba ganinta zaki dinga yi kullum ba, Keyn mota Raliya ta dauka a kan center table, ta dauki danta tace "Mummy sai anjimanku, tayi hanyar waje ba tare da ta jira amsarsu ba, badan a karkashin wani take ba, wallhy babu abinda zai hanata tafiya da Nadeeyah, mutuwa mai tonan asiri, duk talaucinsu basa zuwa gurinsu maula, rikon na Nadeeyah nawa yake? abinci ne fa kadai sai gurin kwanciya, sai dan kyautatawar yau da kullum, share kwallar idonta tayi ta shiga motar tana fadin, "ya Allah ka raya mu cikin ya'yanmu.... Dakyar mummy ta shawo kan Badar ta yarda, da sharadin a dakin mai aikinsu Nadeeyah zata zauna, dan ita sam bazata iya hada daki da Nadeeyah ba, dan a samu kwanciyar hankali mummy ta yarda amma can cikin ranta badan taso ba, Husna ma abin ya mata zafi sosai, Raudha da Radiya kuwa tsaff suka goyi bayan Badar... Dakin mai aikin nasu ma da d'an kyanshi, kayanta kawai ta shigar ciki ta fada bayi, sai da tayi kuka mai isarta sannan tayi wanka ta daura alwala ta fito... A inda ta idar da sallar ishaa bacci yayi gaba da ita, sai ajiyar zuciya take cikin baccinta, mai aikin nasu yar dattijuwa ce, taji tausayinta matuka, ta kuma yi tirr da hali irin nasu mummy, masu yin watsi da jininsu saboda talauci, tashinta tayi ta maida ita kan gado taja mata abun rufa...... Mrs Tijjani Shattima........! [07/03 6:31 AM] fareedah: ●ZUMUNCINMU A YAU● 1⃣8⃣ By Aysha Ya'u Kurah Tsakurar abincin dake gabanta takeyi tana juya cokalin, ta rasa menene asalin abinda take ji cikin ranta, farin cikin sanin halin da Nadeeyah ke ciki na rashin iyayenta takeyi ko kuwa bakin cikin tarewar da kowa yayi a gidansu Nadeeyan, Mutuwar mamma na iskarta tayi murmushin farin ciki, tasan Nadeeyah na can cikin radadin da ta sanya ta, saidai takaicinta daya musaddiq sam baya yarda su hadu, duk wata kafa da zata sadasu ya tosheta, dan sam baya son jin ko muryarta, wani irin tsanarta yakeji a zuciyarshi na rashin imaninta, babu wanda bai ziyarci gidan mutuwar ba sai ita, kullum tana zaune a gida daga kallo sai cin abinci sai game, babu yadda mummy batayi ba akan tazo gidan mutuwar tun farkon yin ta, amma sam taki zuwa, gashi wata mutuwar ta sake bullo kai... Tura abincin gefe tayi ta mike ta wuce daki dan ta watsa ruwa, ita kadai ta kwana a gidan, sai daddy da taji tashin motarshi da asuba tasan shima a gidan ya kwana, ko gezau bata ji ba a zuciyarta bare ta karaya ta shirya zuwa gidan su Nadeeyan, ita sam bata san zafin mutuwa ba, a ganinta kuncin da Nadeeyah ta sanyata yafi zafi akan radadin mutuwa, tsaki taja hade da wurgi da kayan jikinta ta fada bayi...... *********** Bayan doguwar addu'ar da aka gabatar a kofar gidan malam Adamu na sadakar ukun mamma Suwaiba, sadakar abinci akayi sosai, duk wanda yake gurin saida ya wadatu da abinci saboda yawanshi, cikin kankanin lokaci jama'a suka watse ya rage saura makusanta kawai, Baffa da shock din mutuwar bai sakeshi ba har lokacin ya mike kamar ba laka a jikinshi ya shige cikin gidan, Saida ya zauna yana maida numfashi sannan ya dubi gurin da mummy da Goggo ke magana, fada mummy keyi akan rashin zuwan Badariyya, ita kuwa goggo goyon bayan Badariyya take hade da fadin "kinsan yarinya ce kuma bata san hayaniya, duk mu da muka zauna a gidan har kwana uku bamu wakilceta ba, Baffa dai kallonsu yakeyi zuciyarshi na tafasa amma bakinshi yayi nauyi ya gaza furta koda kalma daya ce, Hinad dake zaune can gefe kusa da Nadeeyah ya yafito da hannu alamar tazo, da sauri ta karaso gabanshi tace gani Baffa, cikin murya mai rauni yace, taje ta kira Hafeezu da Daddy a waje, sai a sannan mummy tasan da shigowarshi, karasowa tayi ta zauna kusa dashi tace "Baffa yaushe ka shigo, murmushin yake yayi yace "yanzun nan, tafi ki kirawo min dukkan ya'yanki akwai maganar da nake so muyi daku, kai ta gyada tace "to Baffa, ta mike ta fita tsakar gidan, Zama Goggo tayi tana matsa mishi hannu hade da cewa duk kwana ukun nan baka da wani kuzari, mutuwar nan fa ba a kanta aka fara yi maka ba, ka rasa uwa, uba, mata, da ya'ya, saidai wannan mutuwar na lura tafi razana ka, wanda ni bansan dalili ba, mutuwa daya ce, in mutum yayi ta baya dawowa, inda ana dawowa sai ince ka cigaba da damuwar, watakil damuwar taka na iya dawo da ita, ya kamata ka sanya wa kanka nutsuwa kayi tawakkali, Hawayen da ya zubo a gefen idonshi ya share zuciyarshi na rawa yace "Asama'u! duk mutuwar da akemin ta Suwaiba tafi tsaya min, kinfi kowa sanin hal---- da sauri ya dauke idonshi cikin nata, ya kauda kanshi ya canza maganar da cewa "ina matukar tausayin halin da yaran nan zasu shiga ne, waye zai rike su? Ina zasu je? Goggo tayi saurin cewa "ai Nadeeya ta mallaki hankalin kanta, sannan ga Hafeezu shi zai fito da mata yayi aure sai ya hada ya rikesu gaba daya, in suka zauna anan shine hankalinsu zaifi kwanciya, d'an abun da baza'a rasa ba ma dinga taimaka musu, ai su yan gata ne, tunda akwai Hafeezu, kuma su uku ne zasu dinga ganin junansu, kama kwantar da hankalinka akan maganarsu babu abinda zai samesu, ake mutuwa abar jariri ma bare su da suka mallaki hankalin kansu, Daddy dake tsaye cike da al'ajabin kalaman Goggo ya kasa motsawa bare yayi magana, jiran ta bakin Baffa kadai yake in hukuncin da zai yanke mai yiwuwa ne, A d'arare Baffa yace "eh kuma haka ne kema kin kawo shawara, rabasu din baida amfani gara Hafeezu yayi aure ya rike kannanshi tunda yanzu da dan jari a hannunshi, yanzu bari Hafizun yazo sai mu ce mishi ya fito da matar da zai aura cikin gaggawa, kuma ya gyara gidannan ya zauna da matarshi ta rike mishi kannenshi... Sallama Daddy yayi ya karaso gurinsu cikin kunan rai, zuciyarshi nata juya kalamansu, lallai ya yarjewa kanshi duk zumuncin da ake samun tsaiko ko rashin jituwa a cikinshi daga tushe abin ke farawa, duniya ina zaki damu, wannan shi ake kira da Zumuncin zamani, tun ranar farko da ya fara ziyartar gidan da niyyar neman aure yasan akwai matsala a cikin zuri'ar, ko gurin bashi auren yasan cewa suwaiba bata da galihu, da tana da galihu da----- bismillah zauna mana Alhaji, "Goggo ta katse mishi zancen zucin da ya tafi na tunanin abubuwan da suka faru shekaru da dama, zama yayi fuskar nan babu yabo ba fallasa, a lokacin duk sauran yan yaran suka karaso, Dakin ya musu kadan, amma haka suka rab'a suka zazzauna, hankalinsu suka mayar gurin Baffa dan jin abin da yasa ya tarasu, Da bismilla ya fara, kowa ya shiga nutsuwarshi dan duk tunaninsu maganar da zai fada ta dattaku ce, sai da ya fara jajantawa su Nadeeyah akan zazzafar rashin da sukayi, sannan ya cigaba da cewa wannan mutuwar duk ta shafemu kuma ta taba mu fiye da tunanin me tunani, Abun da yasa na taraku anan ba komai bane sai dan in fada muku na yanke shawarar yadda zamuyi da Nadeeyah da Zainab, Kallon gefen da Hafeezu yake yayi yace "kai Hafeezu, kana da yarinyar da kake so? Girgiza kai Hafeez yayi cikin rashin fahimta, Baffa ya cigaba da cewa "to na baka nan da wata daya ka nemo yarinyar da zaka aura domin ta zo ta rike maka kannenka, wani irin kallo mummy ta yi ma Baffa, a lokacin in ranta yayi dubu to duk sun baci saboda a tunaninta Baffa ne zai rikesu Nadeeyah saboda sune suka fi cancanta da rikesu din, maganar da Baffa ya cigaba dayi ne ta katse ta, "abinda yasa nace haka, saboda kaga rabaku zai iya zama matsala, duk inda kuka je bazaku ji dadin zama ba saboda kun saba da junanku, ku kadai kun isa ku debewa kanku kewar rashin iyayenku, Goggo ta amshe da cewa kwarai kuwa, kuma kai Hafeezu hankalinka zai fi kwanciya in kasan kannenka na gurin ka, fatanmu dai Allah yasa a samu mace ta gari, Duk cikar gurin babu wanda maganarsu tayi mishi dadi, har shi Baffa din bayan gama maganar saida yayi ajiyar zuciya sannan ya cigaba da zubda hawayen zuciya, Anty Reemah ta bude baki zatayi magana Daddy ya rigata, "kwarai kuwa Goggo shawararki tayi kuma na gamsu da ita dari bisa dari, Musaddiq da Hilal na jin furucin Daddy wanda ya zama shine na karshe da ya rage suji me zaice, zuciyoyinsu suka tsinke a tare, nan take kwalla ta taru a idon musaddiq da ya kalli gefen Nadeeyah da Hafeez yaga dukkaninsu kukan rashin gata sukeyi, kallon bakin Daddy yayi da ya cigaba da cewa "ba sai Hafeezu ya fita neman aure ba, ni nan zan bashi mata wacce nasan bazata cutar da kannenshi ba, Ya kalli Baffa da yayi kasake yana sauraronshi yace "ina son hada auren HAFEEZU da HUSNA..... Kamar saukar aradu haka Goggo taji zancen, zaro ido tayi cike da firgici tace wace Husnan, " *Husnah Mukhtar Kyari*, Daddy ya fadi da gadara saboda yasan shi kadai keda iko da ita,, Nawa Husnan take muntari, Goggo ta fadi tana share gumin daya fara tsatsasafowa a goshinta, Daddy yace "Ita da Nadeeyah shekarunsu daya, in har zamu iya barin Nadeeya ta rike kanta da zainab me zai hana mu hada auren da Husna sai su zauna su rike kansu gaba daya, jinin ai daya ne, babu wani bare ko Baffa, wani irin murmushi Hilal yayi da karfi yace "You are the best grandpa.. Anty Reemah da ta harbo jirgin mahaifinta tayi saurin amsheshi da fadin "hakan shine daidai Daddy, kaga basai ma an shigo da bare ba, kuma Husna ma ai ba yarinya bace, muma muna kamarta aka daura mana aure, Allah ubangiji ya inganta wannan hadin... sai dai ya inganta uwarki Goggo ta fadi ba tare da tasan ta danno ashar ba, Kowa a gurin ya gimtse dariyarshi saboda sunsan yadda Goggo ke son Husna da Badariyya, barin Husna ma son ta na musamman ne a ranta, kullum hango Husna take cikin villar rahamaniya, bazai yiwu ta bari rayuwar Husna ta kare a gurin wadannan masu kashin mindirikin ba, Haukar gangan ta fara yi musu harda kuka wai Daddy yayi mata Gadara da diyarshi, cikin sanyin murya Daddy yace "Goggo ba gadara bane, ai naga duk jikokin ne, tsatso daya suka fito, basu da wani banbanci, cikin ficewar hayyaci tace "Allah ya kyauta wadannan masu kashin tsiyan su fito a tsatson---- da sauri mummy ta mike ta rufe mata baki tayi mata ihun da bata san ta mata shi ba, itama a nata bangaren ko sama da kasa zasu hade bazata bar autarta ta auri Hafeez ba, dan ta kawo karshen rigimar tayi kasa da murya mai alamar kuka tana matso hawaye tace "Rike su Nadeeyah bazai taba zame min matsala ba, basu da kowa sai ni, nice uwa kuma ubansu, dangin mahaifinsu suna nesa damu "Aagadaz" ba nan kusa bane bare muce zamu tura wani nashi yazo, durkusawa tayi gaban Daddy tace "dan Allah in bazaka damu ba zan rike yaran nan a gidanka, ajiyar zuciya Daddy yayi cike da farin ciki yace "Babu wani matsala ai d'a duk na kowa ne, bare kuma yaran nan jininki ne, Baffa farin ciki cike fal a zuciyarshi yace "Nagode nagode Alhaji Allah ya saka da alkhairi, "babu komai Daddy ya fadi yana kallon Goggo dake zabga mishi harara, zuciyarta cike take famm saboda bata san jinin suwaiba ya rabi kowa nata, bata ankara ba taji muryar Anty Reemah na cewa "Mummy dan Allah ku bani daya daga cikinsu in tafi da ita, nima in samu ladan rikon maraya,, Goggo ta kara hassala ta figi hijabinta a kan gado tace "ki je cikin kabari ki fito da Suwaiba da *ATIKA* ki hada duk ki tafi dasu..... Banda Mummy da Baffa da suka san wacece Atika, babu wanda a cikinsu yasan wacece Atika?? Sunan Atika ya shiga yawo a kunnuwan dukkan yaran dake gurin.......WACECE ATIKA???? Shine tambayar da zuciyoyin mazauna gurin ke yi.......! Mrs Tijjani Shattima...... [07/03 6:31 AM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣2⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* Share zufa Goggo tayi cike da tashin hankali tace "To Allah ya kaimu, sai kunzo, Ajiyar zuciya Mummy tayi tace "to Goggo, amma bakya ganin fadin sirrin zai iya kawo karshen zama na da Muntari, "Ko kusa, Goggo ta fadi cike da dakiya tace "in ya rabu dake ina zai kai yaran da kika haifa mishi, ai zancen rabuwa babu shi, domin kuwa yanzu girma ya kamaku, ki kwantar da hankalinki ni nasan abun da zanyi..... Ajiye wayar Goggo tayi ta shiga safa da marwa a cikin dakinta, Gumin dake tsatstsafowa a fuskarta bai tsaya ba duk ko da irin sanyin fankar dake kad'awa a dakin, jiki na rawa ta haye can saman gadonta mai rumfa dakyar tana numfarfashi, ta mika hannu tayi ta dauko wani akushi, bude cikin shi tayi ta zuraa mishi idonuwanta duk jikinta a sanyaye kamar wacce aka tsinkewa lakka, nan take tunaninta ya tafi can shekaru da dama da suka wuce... Shekarun da Allah subhanahu wa ta'ala ya arawa Goggo su, Shekaru masu cike da abubuwan al'ajabi wadanda aka shafe tunaninsu a doron kasa... "sau tari Allah na arawa mutane lokaci ko zasu samu su gyara abubuwan da sukeyi marasa kyau, amma ita Goggo a gareta gani takeyi cancantarta ne yasa har yanzu Allah bai mata komai ba, saboda yasan irin gwagwarmayar da tasha .... *********TARABA 1969********* Kauyen *GEMBU* dake Karkashin karamar hukumar *SARDAUNA* a cikin jahar TARABA, Babban kauye ne wanda yake cike da fulani arna da kuma tsirarun musulmai, Irin arnan da babu abinda sukeyi a rayuwarsu sai kiwo da noma, mazan su da matansu, Hatta abin da zasu ci ma su suke noma shi da kansu, Kauye ne inda babu wanda ya damu da addini bare har sukai ga assasa shi, "walau Addinin kirista ko na musulunci" kowa harkar gabanshi yakeyi, da yawansu saboda rashin addini basu dauki kowacce irin mugunta a bakin komai ba, komai suke aikatawa a garin su a ganinsu dai dai ne...... Ihun shanaye ne kawai ke fitowa daga cikin wagegen bukkar gidan JAURO, Samarin dake zaune a kofar gidan kowa ya fara gyara zaman jarkarshi dan sun san yanzu za'a fara kiran layi.. Cike da gadara ya ajiye jarkarshi a gaban ta kowa, ya koma jikin gidan yana sakuce hakorinshi.. Shuru sauran mutanen sukayi saboda tsoronshi da sukeji, Cike da damuwa saurayin da ke zaune tun safe a gaba ya daga jarkarshi a kasa, ya kuma ga in yayi shuru to fa za'a cuce shi, Mikewa yayi cikin sanyi ya fara magana da gurbatacciyar hausarshi ta kabilun fulani "Tun asuba nake nan, kayi hakuri can tsauni zan kai madara kaga da nisa banasan dare yayi mana, bude idoo saurayin yayi cike da gatsali yace "amma kai bako ne anan ko? gyada kai saurayin yayi yace "eh a can tsaunin Mambila nake, nazo siyan madara ne akwai bakin da suka zo daga Cameroon zasu tafi anjima da maraice kuma suna son madara irin ta gidan jauro, shine nazo siya, kayi hakuri a bamu, tare muke da yar su gata can a zaune duk ta gaji, Dago kai saurayin me suna SHAHO yayi ya kalli gurin bishiyar da saurayin ya nuna mishi, kyakyawar budurwa ya hango zaune a gefen bishiyar fuskarta da alamun gajiya, da ganinta kasan ba yar nigeria bace, jikinta rufe yake ruff da bakar riga har kanta, sandar dake hannunshi ya ajiye yace "a zuba maka in ma jarkar da ka kawo sun kai goma, kanshi ya fara kakkabewa ya fara nufar inda budurwar take, Da sauri saurayin ya taro shi yace "ina zaka je? Yarinyar nan bata jin hausa haka fulatanci, larabci kadai take ji, kayi hakuri muyi abinda ya kawo mu, mu tafi mu bar muku garinku, wani irin kallo Shaho yayi mishi, baice dashi kala ba ya bi ta gefenshi ya karasa kusa da yarinyar, gyara rigarshi yayi zai zauna saurayin ya tureshi ya tare gurin zaman, "Na fada maka, yarinyar nan bakuwa ce, alama yayi mata da hannu yace ",ga motar da muka zo can je ki shiga ki jirani, gurin kwarababbiyar motar shanun ta nufa ta haye tana ta kalle kalle jikinta duk a mace, wani irin ihu Shaho yayi har saida matan dake gefen bukkar suka tsaya da tatsar madara saboda firgici, saurayin dai bai girgiza ba sai ma kara komawa jikin motar da yayi ya tsaya, sauran mutanen gurin suna kallonshi cike da mamaki suna tsoron irin hukuncin da Shaho zaima saurayin, tunkarar motar shaho yayi gadan gadan, cikin harshen larabci saurayin yayi wa budurwar magana, a firgice tabi umarnin shi ta kwanta kan kujerar hade da runtse idonta, yana isowa gurin ya dunkule hannu ya kai wa saurayin naushi, gocewa yayi ya daki karfen motar har saida ta girgiza, kafin ya kai mishi wani naushin saurayin ya kai mishi a baya, nan fa suka fara kokawa sosai, ganin da shaho yayi saurayin yafi karfinshi yasa shi zaro wata sharbebiyar wuka ya zabtari naman gefen kanshi, Nan fa jini yayi tsalle ya fallatsa har fuskar budurwar, wani irin ihu ta saki tana fadin "Ya subhanallah, Ya Hayyu ya kayyum bhi rahmatika astagithu" cikin zafin nama saurayin ya sake yin kan shaho, kafin ya karaso kusa dashi ya sake luma mishi wukar a ciki, ihu mutanen gurin suka shiga yi, wasu na tausayin saurayin wasu na kuranta shaho, kaca kaca shaho yayi wa saurayin da wuka sannan yayi wani ihun murnar ganin ya samu galaba akan saurayin, bakin motar yayi yana maida numfashi, "wayam" ya gani babu kowa a ciki, dube dube ya fara yi yana fadin ina ta shiga, ina yarinyar nan ta shiga, babu wanda ya lura da sanda yarinyar ta bacewa gurin, nan Shaho ya hargitsa gurin da nemanta... Da sassarfa ya isa gida ya turo kofar gidan gam harda kara sanya wani karfe, "Ma'u, Ma'u am, da sauri ta fito daga sakarkari hannunta rike da yar jinjira, lafiya dai irin wannan kiran me muka samu ne, sauke budurwar yayi a bayanshi ya kwantar da ita akan wata tabarma, ajiye jinjirar ma'u tayi cikin daki kusa da wata yar yarinya da bata wuce shekara 8 ba, da sauri ta fito tana mai zumudin sanin inda mijinta ya samo yar MAKKA, dan su duk wani balarabe a gurinsu dan Makka ne, " kawo di yam ma'u, ya fadi yana mata firfita hade da share jinin fuskarta, ruwa ta debo cike da koko ta mika mishi ta zauna a kusa dashi, a hankali ya fara shafa mata ruwan a fuskarta da hannunta, Ajiyar zuciya tayi mai karfi hade da fashewa da kuka tana kiran sunan "HABEEB" toshe mata baki yayi da sauri saboda jiyo ihun su shaho a bayan gidanshi, cikin harshen filatanci yacewa ma'u tayi saurin shigewa daki da ita, kama hannunta tayi suka shige can kuryar daki ta turata cikin wani yayi ta daura mata kaya a kanta, kafin su kai ga taba kofar bukkar mai gidan ya fito daga gidan yana mika, tsayawa su shaho sukayi yace "Kai Baffan Bingel da Boddo kaga wata yarinya Makka da bakin kaya, hamma ya kakaro yace a ina zan ganta ni da na tashi daga bacci yanzu, wucewa sukayi suna ta maganganu cikin fushin rashin ganinta, muryar shaho ya jiyo daga can yana fadin "babu abinda zai hanashi kasheta in ya ganta, da yaso ya sameta yayi yadda yake so da ita amma yanzu kasheta zaiyi dan in ya barta zata iya zama barazana ga rayuwarshi, jin haka yasa Baffa cikin tashin hankali yayi saurin komawa cikin gidan, A kofar sakarkari ya samu ma'u zaune tana damun fura da nono, ganin da tayi ya shigo a firgice yasa ta mikewa ta nufo shi, "lafiya?, ta tambaya tana kallon yadda jikinshi yake rawa, daki ya jata yace "ina bakuwar balarabiyar nan, maza fito da ita mu nemi wani gurin mu korata dan walhy rayuwarmu tana cikin hatsari, ya kwashe duk abin da yaji shaho ya fadi ya gaya mata, cikin dakiya irin tata da jarumta tace babu inda zaka kaita in ba iyayenta ne suka zo neman ta ba, ya zama dole a samu me tsawatarwa shaho, abubuwan da yakeyi a cikin garin nan ya isa haka, kallonta yayi galala yace "wa kike ganin zai tsawatar mishi?, ki fada min wake da wannan zarrar? kwaryar damunta ta dauko tace "nidai na fada maka babu inda zata, ta wuce daki tana tsuma tana fadin babu wanda ya isa ya taba makka, "sunan da ta rada mata kenan tun kafin taji sunanta, ita zuciyarta ta tafi can tunanin in iyayenta suka zo to fa zasu musu alherin ganin sun taimaki yarsu, kuma zata kafa tarihin ita ta fara taba jikin balarabiya a duk fadin tsirarun musulman da suka musulunta a kauyen, cire kayan tayi ta dago yayin ta fito da ita tace "sannu hai yar budurwa, fito muje ki sha fura sai kiyi wanka, raba dara daran idanuwanta ta fara yi dan ko kalma daya bata dauka cikin kalaman ma'u ba, hannunta ta riko suka fito waje ta shimfida mata sabuwar tabarma ta nuna mata tace "zauna, bata fahimta ba haka ta kuma kama hannunta ta zaunar da ita, furar ta mika mata ta dauka ta fara sha hawaye na zirarowa daga cikin idanuwanta, tunanin kaninta takeyi dan shekara 6 a duniya wanda ta zamo gata a gareshi gaba da baya, ko a wani hali yake yanzu Allah masani, ludayi uku tayi ta miko ma ma'u.. Amsar kwaryar tayi tana fadin "hai har kin koshi, da kin kara kadan ta fadi tana miko mata, Girgiza kai tayi saboda ta fahimci nufinta tace "Alhamdillah, Jazakumullah khairan" yashe hakori Ma'u tayi tana dariya har can cikinta tana kyakyato shi, dariyar murnan jin yaren larabci, da kuma ganin ita kanta balarabiyar makkan a gidanta takeyi, saida ta gama dariyarta tace "hai Baffan Boddo an je gidan kawu suwidi in fadowa su inna wuro munyi bakuwa mai tsarki yar Makkah, takalmin robarta ta janyo me ruwan bula tasa a kafarta, ta yayo dankwalin saka ta rufe kanta ta fara tafiya, ta kusa taba kofar Baffa yayi saurin tareta yace "A wala hakkilo na" ("baki da hankali ne?) Kinsan irin halin da zaki samu a ciki in kika gayyato mana mutanen gidan Kawu Suwidi?, kince bazata bar gidan nan ba na hakura ta zauna amma ki sani babu me shigo min gida bare ya ganta ya jaza min masifa, tana nan zaune nasan za'a zo cigiyarta a lokacin sai in mikata gurin iyayenta,, kalonshi ma'u tayi fuskar nan cike da gamsuwa tayi kamar ta yarda din da gaske, yaye dankwalin kanta tayi tace "Haka ne, na manta ne ina ta zumudin kai rahoto dan kawai in burge su inna wuro, yanzu bari inje in sata tayi wanka sai ta canza kaya a wanke na jikinta, gyada kai Baffa yayi cikin jin dadi ya koma daki kusa da yaranshi ya zauna yana shafa kan karamar dake kokarin tashi.. Murdaddiyar sarkar murjanin gwal din da ta cire kafin ta shiga wanka ma'u tayi ta juyawa a hannunta tana dariyar farin ciki, "Aiya Ya Allahn Hard'ejo, (sunan yayan mijinta kenan malamin da ya fara kawo musu musulunci kauyen), ji wani "kuje ndade' (sarka) kamar ba hannun mutum bane ya kerashi, sashi tayi a wuyanta tace "wannan ko matar Ardo Laminu bata da irinshi, kaii ya zame min dole in je gidan su inna wuro dan bazan bar wannan daddadan labari ya wuce ban basu shi ba, ai ni ko da wannan maka wuyar aka barni na tsira, daki tayi da sauri tana magana kamar zararra, kayanta dake cikin wani akwatin katako ta dauko sababbi na fulani tace " Baffa zan bata wannan kayan nawa tasa saboda a wanke wadancan, gyada mata kai kawai yayi dan mamakinta bai barshi ya bude baki yayi magana ba, ma'u da ko dankwalinta bata iya bawa wani aro shine har ta dauko kayanta da bata taba sasu ba zata bawa wata tasa, lallai yar makkah ta ciri tuta.. Sosai kayan fulanin suka mata kyau a jiki saboda tsabar kyawunta, lallausan gashinta ma'u ta shiga kitsashi da kyar tana yi yana warwarewa, haka dai tayi mata irin nasu na fulani ta dauko mata su sarka da abun hannu duk dan ta mantar da ita sarkar gwal dinta... Mrs Tijjani Shattima... [07/03 6:31 AM] fareedah: •• ZUMUNCINMU A YAU •• 2⃣1⃣ By Aysha Ya'u Kurah Hanyar sama Badariyya tayi da gudu tana shashshekar kuka kamar ranta zai fita, kofar dakin Daddy ta shiga bugawa kamar zata ballata, da gudu mummy ta fito daga bayi jiki na rawa ta bude kofar, Daddy kuwa zaune yayi yana jiran ganin me mishi irin wannan bugun kofar da safiyyar nan, jikin mummy Badar ta fado ta sake kecewa da wani kukan, waigawa tayi ta kalli Daddy da ya rike kanshi yana tsaki, waje ta jata ta rufo mishi kofar, ta kama hannunta sukayi dakin ta, zaunar da ita tayi a kan gado ta shiga rarrashinta, saida ta tabbatar ta fara samun nutusuwa sannan ta tambayeta abinda ya faru, karya ta shiga rerowa mummy cikin wani sabon kukan, "Ya Hilal ne yayi min dukan tsiya, wai saboda Nadeeyah taje tana wanke wanke kunama ta harbeta, shine yaje ya taso ni ina bacci wai tace mishi ni nasa ta, kuma tace mishi wai na hana a bata abinci jiya har tayi bacci, sannan a gabana Ya Musaddiq ya dauketa ya sata a mota suka kaita asibiti wai kafin su dawo in tabbatar na gama wanke wanken da ya rage------- , Wani irin kunci da tukuki mummy taji a ranta, "Hilal din ne ya dake ki? gyada kai Badar tayi wasu zafafan hawaye na sake bin kuncin ta, 'irin kallon da Musaddiq ke ma Nadeeyah shi ya fi komai taba zuciyarta, kwanciya tayi jikin mummy ta runtse idanuwanta saboda ganin hanun Musaddiq da takeyi cikin na Nadeeyah, "Hello Reemah, daga daya bangaren Anty Reemah ta bude idonta hankali tashe cikin muryar bacci tace "Na'am, ina kwana Mummy, ''lfy kadai mummý tace, ta cigaba, "kizo gida yanzu ina nemanki, bata jira amsarta ba ta kashe wayar.. Mikewa Anty Reemah tayi jiki a sanyaye, tasan akan matsalar Hilal akayi kiranta da safen nan, cikin zafi tace "wai wannan wani irin yaro ne da yakeson kashe ni tun lokaci na baiyi ba, wallhy yau, ko gobe zamu bar kasar nan kar ya jaza min bala'i, ina kokarin gamawa da mahaifiyata lafiya yana neman janyo min tsinuwa, Papa tashi plss ka fara mana shirye shiryen tafiya bari inje gida in dawo, Ajiyar zuciya kawai Papa yayi ya juya ya kara jan bargo, samm bayason abinda zai matsawa matarshi da ta zamo jigo kuma garkuwa cikin rayuwarshi, "Papa kara rufe kanka kayi? ta fadi kamar zatayi kuka, yayewa yayi da sauri yana murmushi yace "its too early my omri, kije ki dawo sai muyi shirye shiryen tare, gyada kanta tayi tasa hijab har kasa ta dauki mukullin mota ta fita... ******** "Waye ya sa ki aiki da wannan safiyar? Tambayar da Hilal ya jefo mata kenan idonshi na kallon titi, Tana zaune a kaikaice a baya, saboda kar ta bata musu mota, cike da jin tsoronshi tace "babu kowa, naga kayan sunyi datti ne, Are u an au pair girl?? Musaddiq ya kara jefo mata wata tambayar, shuru tayi idonta yayi narai narai zai fara zubar hawaye, juyowa baya yayi ya kalli yadda ta zauna yace "to ruwa ruwa, zauna dakyau sai kiji dadin yin kukan, kara kaikaicewa tayi ta kife kanta jikin sit din da yake zaune, "hey wasa nake miki zauna yadda kike so, ya fadi hade da maida fuskarshi gaba, Daidai wani babban shago dake bakin layin Hilal yayi parking, kallonshi Musaddiq yayi yace "me zaka siya, hannu Hilal yasa a aljihunshi yaji ba kudi, bai amsa musaddiq ba yace "akwai kudi a jikinka, taba aljihunshi yayi yace i don't think akwai, ko akwai ma basu da yawa, dauko wallet dinshi da ya bari cikin motar yayi ya cire atm din da PAPA ya bashi ya shige shagon, "Kunada pos? ya tambayi wani yaron shagon, eh akwai sir, yaron ya amsa shi cikin girmamawa, wucewa ciki yayi ya dauko "pad" guda uku, "Tunda suka isa Asibiti ya lura ta kasa zama har aka gama yi mata allurori, kuma yaga alamar digon jini a jikin rigarta, babu inda bai karewa kallo a jikinta ba, hatta yatsun kafarta wadanda suka fi tafiya da imanin zuciyarshi, siyayya yayi mata na turaruka da mayuka da sabulai masu kyau da dan tsada, yadda ya barta haka ya fito ya sameta, Hira musaddiq ke janta dashi tana amsa wasu, wasu kuma tayi shuru tana murmushi ba tare da ta dago kanta ba, gefen da take zaune Hilal ya bude, a tsorace ta dago saboda ta kusa fadi dan ta jingina da kofar, Ganin Hilal ne ya sanya ta gyara zama ta nutsu sosai, wani sanyayyen kallo yayi wa nutsuwar da tayi, sannan ya mika mata kayan ya rufe kofar ya shiga suka wuce.. Rike kayan tayi a darare, ta gefen idonta ta hango pad, gabanta ne ya yanke ya fadi a zuciyarta tace Allah yasa ba staining tayi ba, tsoro da kunya duk suka kara dagula lissafinta a cikin motar, suna isa cikin gidan tayi saurin bude motar ta fita ba tare da ta dauki kayan ba, kashe motar yayi ya bita da shagalallen kallo har ta kusa shiga cikin gidan, "yarinyar nan bata dauki kayan nan ba, musaddiq ya fadi hade da bude baya ya dauko su, motar Anty Reemah ya gani yace "ur momma is here, kallonshi Hilal yayi yace "a haba, ina take? "Tayarta na gani ba ita ba ya karashe yana murmushi hade da nuna mishi motar, fitowa yayi suka karasa cikin gidan a tare... "Ga munafukar nan ma ta shigo, Mummy ta fadi a kausashe tana kallon Nadeeyah, tsayawa Nadeeyah tayi a bakin kofar ta kasa daga kafarta, nan take jikinta ya fara rawa, karaso ciki algunguma, daga zuwanki jiya zaki yi min setting gida on fire da farar safiya, to walhy bazan dauka ba, Nadeeyah saboda tsoro hakoranta suka fara kara kainin haduwa da junansu, har lokacin bata iya karasowa ba dan kafarta ta gaza dagawa, ba dake nake magana ba? Mummy ta kara fadi cikin daga murya, kuka mai karfi ne ya kufce ma Nadeeyah, "laaaa ha ila ha illahu!! uban me aka miki zaki tsaya a bakin kofa ki sake ma mutane kuka, kaii nikam na bani, na dauko makirar yarinya da hannuna na kawo cikin gida na, Mikewa Badariyya tayi ta kamo hannunta out of anger, ta fara janta tana fadin zo ki wuce munafuka dangin tsiya, yau sai kin bar gidannan tunda ba gidan ubanki bane, tayi wurgi da ita a tsakiyar parlon tana maida numfashi kamar bakin kumurci, zuciyarta mugun zafi take yi na ganin Musaddiq na petting Nadeeyah kuma harda rike hannunta.. Antyn Reemah dai bata ce uffan tana zaune idonta yayi jawur saboda irin tashin hankalin da mummy ta sata na furucinta a kanta, tana tsoron sake magana kar ta kara harzuka mummy, Hannu Badar tasa zata fisge karamin hijab din jikin Nadeeyah, Hilal ya rike hannun ya dauketa da mari kwarara guda biyu, ke din gidan ubanki ne? Nace gidan ubanki ne? Yanda kike a gidan nan haka take! Ihunta ne ya gauraye gidan ta shiga zaginshi tana fadin Allah ya isa mugu azzalumi kawai, wani dukan zai sake kai mata Anty Reemah ta rike hannunshi ta kwada mishi mari, wani irin kallo yayi mata na mamaki yace "Mum------ shut up ta katseshi rai a bace, kana hauka ne, wace irin zuciya gareka da zata dinga saka dukan mace, ko ka sami jakar ka ne? tun safe kake jibgarta, Koma me tayi maka ai da sai ka fadawa mummy ba wai kai ka yanke hukunci da kanka ba, beside ma ina ruwanka dan tasa Nadeeyah wanke wanke, meye naka a ciki, kullum ni kenan in nazo gida bani da kwanciyar hankali saboda kai, duk sona da yin zumunci haka nake hakura saboda bakar zuciya irin taka, yanzu rashin kunyar taka akan mahaifiyata ya kai har ka kusa zaginta, saboda dai ka nuna wa duniya mu bamu baka tarbiyar girmama na gaba da kai ba, To bari kaji, yadda na haifeka itama haka ta haifeni, walhy duk ranar da ka yarda tayi min baki akanka babu ni babu k------- da sauri Musaddiq ya rufe mata baki, subhanallah!!! Anty me ya kawo wadannan magangannun? Me yayi zafi haka? Kallonshi Anty Reemah tayi tace "barni da yaron nan little, so yake yi ya kashe ni, baya san zaman lafiya ko kadan, tun jiya da daddare mummy ta fada min irin rashin kunyar da yayi mata, sannan yau da safe ya sauke dukkan fushinshi kan Badariyya, me tayi mishi har takai ga duka sai kace " *SHAGON MADA* " in ma da gaske Badar tasa Nadeeyah wanke wanke wat is the big deal in it? ai mace ce, kuma kowace mace da aikin gida aka santa, most he sai ya nuna karfinshi jikin 'ya mace sai kace ya samu jaka, Rage sautin kuka Badariyya tayi saboda taji asirinta na gab da tonuwa, zatayi magana Musaddiq yayi saurin cewa waitt Anty, waye ya fada miki Hilal ya daki Badariyya? Hararshi Mummy tayi tace "Nice! Ko karya nayi, bai daketa din bane, fada mishi da bakinki Badar, ya daketa saboda wannan munafukar ta hada tuggu da karya saboda kawai ta shiga tsakanin ya'yana suyi ta fada kamar karnunka, to ta Allah ba taki ba walhy. . Ni fa ban gane ba? Musaddiq ya fadi hade da kai idonshi kan Badariyya dake rike da kuncinta, Me Nadeeyah tace game da ke, kuma da yaushe Hilal ya dake ki? "Uhmmm uhmm--- uhmn--- ka fita lokacin yace in-- in ya dawo zai min dukan tsiya, ina tsoron kar ya dake ni shiyasa na fadi ma mummy ya dake ni dan ayi wa tufkar hanci, kallon Mummy Musaddiq yayi yace "kinji abinda tace ko in maimaita miki? A kunyace mummy tace "to meye nashi na mata barazana, ai dole in gasgata saboda nasan bashi da aiki sai duka da zagin na kasa dashi, Anty Reemah kuwa idonta na kan Hilal dake rike da kunci har lokacin, shi din ma ita yake kallo idonshi jajur, karyar da kanta tayi zata mishi magana yayi hanyar dakin Musaddiq da sauri, ajiyar zuciya tayi ta kalli Musaddiq dake ta ma Mummy magana cikin fada, "Nadeeyah da kika kira munafuka babu abinda tace game da kowa, hasali ma wannan bakar dagar bata san meke faruwa ba har saida muka zo kaita asibiti, ita ce ma tayi ma Hilal rashin kunya ina jinta bai tanka ba, walhy in dai baki daina biyewa yarinyar nan ba wata rana sai kinyi dana sani marar amfani, haba dan Allah ya karashe rai a bace hade da gallawa Badar harara, Durkusawa yayi kusa da Nadeeyah dake kuka yace "tashi kije daki kisha magani ki kwanta, mikewa tayi tana share hawaye ta fara tafiya, kayan da Hilal ya sai mata ya dauko ya bi bayanta, Dakin Delu yaga tana kokarin shiga yace "ba nan bane dakin gashi nan, ya nuna dakin su Badar, Husnah da tun ihun Badar ta farka, tayi hamma tace "a dakin Delu ta kwana kayanta na can, jinginar da kanshi yayi jigin bango yace "Hasbunallah, dakin ya bita ya mika mata kayan ya fito da sauri yayi hanyar Sama, A tsaye yaga Daddy yayi folding arms dinshi fuskar nan tashi a murtuke, asalin Kanuri ya bayyana a tare dashi, "Daddy kana gan----- naga komai *Saaaaaadiq* " haka yake kiranshi har sai yaja sunan! kasa ya sauko ya kalli Mummy da duk ta sukurkurce yace "bana san jin komai, anjima karfe biyu na rana bayan jumm'a duk mu hallara a gidan Baffa, "i want to clear all my mystifications, dole ne ku fitar dani cikin duhu, dan alamu sun nuna min ba Goggo bace ta haifi SUWAIBA, sannan ba talaucin su bane ya sanya ku tsanarsu a matsayinsu na jininku, akwai dai wani abun a kasa, *WALLAHI* Daddy ya fadi da muryar da ta ba Mummy tsoro, "in har baku fitar dani cikin wannan duhun ba aurenmu dake zai kare, saboda na gaji sosai da irin halinku da ya shafi zuri'ata, bazan dauka ba..! ya mike a zafafe ya haye sama.. Jikin Mummy babu inda bai rawa, ta mike ta haye saman ita ma ta bar Musaddiq da Reemah da Husnah a falon sunyi jugum jugum.....!!!! Mrs Tijjani Shattima..... [07/03 6:31 AM] fareedah: ••ZUMUNCINMU A YAU•• 2⃣0⃣ By Aysha Ya'u kurah "Wai ina zaku tafi ne? bakwa ganin dare yayi! hannunta ta nuna saitin agogo ta cigaba da fadin pass 10 fa, bansan yawon banza ku koma dakinku, Ja da baya Musaddiq yayi yace "wallahi Anty Reemah haka na fada mishi wai shi yau a gidan mummy zai kwana, bansan sanda ya fara shiri da compound din gidan ba, ni da ya kyaleni ma bacci nake ji, Harara Hilal ya watsawa Musaddiq hade da tsaki, yace "plss mum, air con din dakina ba gas and u knw dat, Kuma tun isowarmu na fadawa Papa, ajiye kopin coffee Papa yayi ya kalli Hilal yace "wane Papan?   "kai mana, Hilal ya fadi hade karyar da kanshi a shagwabe yace "plss papa don't prolong dis issue, dare na dada yi, mukullin motar papa ya dauka yaja hannun Musaddiq yace "Gud nyt Honey stars, girgiza kai Anty Reemah tayi tace "Allah ya shirya, Ameen!! Papa yace hade janyota jikinshi, hab'arta ya dago ya kalli kwayar idonta wacce ya hango damuwa sosai a cikin ta, me akayi ma first lady? Wa ya taba min ke? tun dawowarki na lura da yanayin ki, sannan kiran da Raliya tayi miki naga ya kara sanya ki cikin damuwa, fada min matsalarki ko tafi karfina inyi kokarin magance miki ita, Ajiyar zuciya tayi tace "as usual Papa, sai matsala ta dauko kamar zata warware sai ta kara dagulewa, nasan duk family ana samun crisis, amma sai inga namu na daban ne, san zuciya shine ke haddasa komai cikin gurbacewar zumuncin zuriarmu, labarin abin da ya faru a gidan su Nadeeyah ta bashi ta daura da abin da Raliya ta fada mata a waya, sannan ta cigaba da cewa "tun ina karama in naga yadda suke treating mama suwaiba sai inyi ta tunanin anya kuwa Goggo ce ta haifeta, abin da Goggo kema Mummy da Anty Leemah sam yasha banban da wanda take ma mama Suwaiba, a kuruciyata sai nayi tunanin ko dan ta auri talaka ne, furucin Goggo na yau ya sanyani cikin tunani sosai na son sanin wacece ATIKA, meye alakarmu da ita..... Tambayar da Anty Reemah keyi wa zuciyarta a wannan lokacin ita Daddy keyi a zaune a balcony din dakinshi, Isowar mummy gurin ne ya katse tunaninshi, cikin taushin murya tace "in kawo maka ruwan zafin? black or green tea? Wanne zan kawo, Mikewa yayi yace "ko wanne ki kawo, da fatan yaran nan sun kwanta, kuma babu wata matsala,? gyada kai mummy tayi tace "eh Nadeeyah ma tayi bacci ita kuma zainab tana gidan Reemah, Good Daddy yace hade da cewa ki ja ma Badariyya kunne, bana son fitina, suyi zamansu guri daya tunda duk sa'anni ne, zama cikin nasu shine zai kara musu dankon zumunci, dan Allah ki kula sosai dan duk ya'yanki ne banason nuna banbanci, murmushin yake mummy tayi tace "ba sai ka tuna min ba, na riga na fada musu, kuma in shaa Allah komai zai tafi normal, kafin yayi magana yaji Hon din mota ya cika gidan, gate din ya kallo daga sama dan ganin mai shigowa a wannan daren, hasken dake gidan ne ya haska cikin motar, ganin Musaddiq kadai yakan sanya Alhj Mukhtar manta duk wata damuwa, Ajiyar zuciya yayi yace "su kuma daga ina, cike da jin dadin yadda fuskar Daddy ta canza mummy tace "Gidan Reemah, ni duk tunanina a can zai kwana, tafiya ya fara yi yana fadin "gara dai ya dawo gida, tunda ya dawo ma bamu zauna ba, bare mu tattauna akan sakamakon makarantarshi, Sakkowarshi kasa tayi daidai da shigowar su Musaddiq cikin parlon, Remote Daddy ya dauka fuskarshi cike da annashuwar ganin zaratan mazan familyn shi, kuma ababen kaunarshi yace "ABOKI KANGIWA, kai ne a daren nan? yau anan zaka kwana kenan, kusa dashi Hilal yaje ya rungumeshi yace "yes ABOKI DADDY, a dakinka ma zan kwana, mu raba dare muna hira, mun dade bamu hadu ba, dariya Daddy yayi ya zauna yana kallon Musaddiq dake tsaye yana murmushi, "zo ka zauna auta na, kar kafarka ta sage, AUTA fa Daddy?  To in shi auta ne ni kuma fa? Husna da ta fito daga kitchen rike da plate din indomie ta fadi tana turo baki, Dariya Daddy yayi yace "haka ne my baby,  na manta ne, ba auta bane, kafi auta ne, kece auta,, Kumbura baki tayi tace "ni ce duka biyun, dariya sukayi dukkansu, mummy ta mika ma Daddy kofin tea, shan kunu Hilal yayi yace "ni fa, ina nawa tea din,? hararar shi mummy tayi tace "kai asu wa? a mijinki Hilal ya fadi yana gyara zama,   ko bakya auren? Tuni na sake ka, ka riga ka gama rainani, na barwa "Yalwan Kangiwa" kuje can ku karata, dariya Hilal yayi ya mike ya dauko kopi ya zauna a kasa ya tsiyayi ruwan zafin, "Zo ki zauna muci tare auta, Musaddiq ya cewa Husna da ke kokarin shigewa dakinsu, "wayyo Yaya tare da Badar zamuci! Husnah ta bashi amsa tana kallonshi cike da damuwar taga yana san abu ba halin bashi,, "Muje muci dukkan mu mana, ai zai ishemu,, cewar Badariyya da tun shigowar Su musaddiq take tsaye a jikin kofar dakinsu, jin da tayi zaici abincinsu ya bata damar murda kofar dan a ganinta ta samu damar da zata sanyashi a idonta,  gefe ya juyar da kanshi ya dauki kopin da ya rage ya tsiyayi ruwan zafin, kallon shi mummy tayi zuciyarta ba dadi, tasan yana fushi da Badar, amma batayi tunanin fushin har ya kai haka ba, "My little yau kuma kai da kanka zaka sha Lipton, i knw u are nt a fan of it, in indomie kakeso kaje kuci da yan uwanka ko kuma Badariyya ta dafa maka wata, mikewa yayi yace "mummy ba Lipton zan sha ba, hot chocolate zan hada, wasa nake ma Husnah, its too late for me in ci indomie, gara dai ruwan zafin, kafin ya kai gurin dinning har Badar ta dauko gwangwanin "Cadbury hot chocolate, Ya ilahi!! ya fadi hade da dafe kanshi, juyawa yayi dan komawa ya zauna, tayi saurin cewa, am sorry gashi!, bai saurareta ba ya koma ya zauna, kallonshi Mummy tayi ranta ya fara baci da irin tsanar da yake nunawa Badariyya, "miko min nan in hada mishi! cike da tsanar kanta taja kafarta ta mikawa mummy gwangwanin ta wuce daki da sauri, Soyayyar Musaddiq ita ce weak point dinta, wen it comes to Musaddiq zuciyarta mai taushi ce matuka, shi kadai take iya daukar wulakancin shi, soyayyarshi tayi ma zuciyarta illa tun bata san mecece kalmar so ba, *****Tun tana yar yarinyarta ba ta yarda kowa ya rabe shi, koda kuwa Husnah ce, ko da yaushe tana tare dashi, sunyi matukar shakuwa da juna, shi a nashi bangaren tausayinta yake ji na rashin iyaye tun tana jarinta, yawanci rainonta shi yayi, in yana gida bata taba barinshi sukuni, Tun da ta shiga school shakuwar tasu ta fara raguwa saboda halayyarta, tun tana nursery take ma yan ajinsu mugunta musamman in taga yarinya ta fita kyau ko gashi, ko kuma ta ga wanda ya fita a komai, ( zamu iya sanya Badariyya a cikin jerin irin halittun dake da hassada, wadanda basa san kowa ya fisu).. Musaddiq kullum in yazo class dinsu sai ya tarar da ita tana duka da jan gashin yara, karfi da yaji ta zama boss a class, kowani yaro tsoronta yake ji, haka a gida in suna wasa da Husnah ta dinga kyararta kenan tana sata kuka, wannan halin shi ya farraqa shakuwar Musaddiq da Badariyya, shareta da yake yi da sanyin hali irin nashi yasa ta rainashi sosai, kullum sai ta tsokaneshi hankalinta yake kwanciya, dariyarshi da bacin ranshi duk suna da ma'anoninsu a zuciyarta.. Hey Badar, "baza kici abincin bane, tun dazu nake miki magana kina jina, sai cika kikeyi kina batsewa, plss zo muci kinga 11 ta wuce, tashi muje pls, Husnah ta karashe hade da kamo hannunta, kwacewa Badar tayi ta maida kanta jikin gado tace "na koshi, je ki cinye, Husnah ta bata fuska tace "haba nw sis, karki sauke fushink---- plsss Ma'u lv me alone, ko dole ne sai naci, Badar ta katseta a kausashe, fita tayi a dakin tana kunkuni a ranta, da kinsan bazaki ci ba da baki wahalar dani ba, kuma da baki barta ta fara sanyi ba, da mitar ta karasa parlor ta zauna a kasa kusa da Musaddiq da Mummy ta mikawa kofin tea ya karba ya ajiye, Fada ta fara mishi sosai iya karfin ta, tun Daddy na kawaicin saurarenta har hakurinshi ya kusa karewa, kallon da yayi wa Musaddiq yaga idonshi ya ciko da kwalla ne ya karar da hakurinshi, kafin yayi magana Hilal ya rigashi, "Haba Mummy, irin wannan fadan sai kace yayi wani mugun laifi, haba dan Allah, is not fair walhy, shiyasa yaran nan duk suka raina shi, Duka mummy ta kaiwa Hilal ya goce, cike da masifa tace "wallahi Hilal ka fita idona, bana son rashin kunya, dan uwarka ina ruwanka, walhy zanyi mugun bata maka rai in ka sake shiga sabgata, tunda ni ba sa'arka bace, "ai gaskiya na fada, akan wannan fitsararriyar yarin----- daga hannu tayi ta kwada mishi mari, Daddy baice komai ba idonshi na kan tv., zuciyarshi sai kai kawo takeyi, ranshi in yayi dubu ya baci, muryar mummy ce ta kara cika kunnenshi, "zo ka fitar min a gida, wallahi zanyi mugun sabawa uwarka in har bata ja maka kunne a kaina ba, yaro sam baya ganin girmana, Hilal cikin zafin zuciya zaiyi magana Musaddiq yayi saurin janshi sukayi daki, Kitchen Husnah ta kai abincin da ta kasa ci, ta rasa dalilin da yasa mummy da Hilal sam basa jituwa, ita a ganinta Hilal bashi da mutunci, kuma sam bashi da kunya, baya ganin kowa da gashi, zata iya kirga maganar da suka taba yi da Hilal tun tasowarta har kawo yanzu, kullum kallon mai bakar zuciya take mishi.... Sai da Daddy ya gama saisaita zuciyarshi, ya kalli mummy dake zaune tana zuba ruwan masifa a waya, gyaran murya yayi yace "kashe wayar nan in kin gama kai karar jikanki gurin diyarki, a hassale mummy tace "kana ganin abin da yaron nan yake min, ba tun yau ba, walhy bazan dauka ba, dole uwarshi ta ganar dashi muhimmaci na, "Uhmm Daddy yace, ya cigaba da fadin "yanzu kin kirata ne ta zaba ko ke, ko shi, ko kuwa kin kirata ne tayi fushi dashi, kin san meye matsalarki!? baki da hakuri in dai akan Badariyya ne, da ke, da Hilal halinku daya, kinsan ance magaji mafiyi, saidai shi akan gaskiyarshi yake yi, sabanin ke da keyin naki bisa son zuciya, babu ranar da Allah zai hadaku da Hilal baku raba hali ba, ke ba hakuri shima hakan yake, shin sa'anki ne? Duka nawa Hilal yake da zaki tsaya maida magana dashi, kara kaurara murya yayi yace "wannan ya zama na karshe a gidannan, na daina daukar irin wannan abun, yaron nan saboda ke sam baya son zuwa nan gidan in suna kasar nan, ke ba abun alfaharinki bane zuciyarshi ta fara muradin gidan, tunda ya shigo yake janki da wasa, saboda yasan halinku ya sabarwa juna, amma kikayi biris dashi, Connection dinshi da Musaddiq kin sani tun suna yara, babu wanda ya isa ya taba Musaddiq a gaban Hilal, ko da kuwa ke da kika haifeshi, bakya ganin kina kara karyar da zuciyar da bata karfi, kin sani sarai rashin son fada shi ya sanya musaddiq yake kaffa kaffa da duk wani abun da zai bata ma kowa rai, zuciyarshi raguwar zuciya ce kin sani, meyasa kike son kara raunana ta, Sau tari akan Badariyya  kina sa yaron nan zubar da hawaye, ke a ganinki baya sonta, wani irin so kikeso yayi mata, kowa nada labarin irin shakuwarsu kafin ta fara girma bakin Halinta ya raba su, ki dinga yaki da zuciyarki, sannan ki tauna abu kafin ki fadeshi, ni kaina yau badan na kai zuciyata nesa ba da walhy sai munyi abun kunya a gaban yara, sai Allah ya taimakeni akwai tsageran da ya fini son d'ana,, ya karashe cike da zolaya, sosai Daddy yayi mata nasiha akan yadda take tafiyar da yaranta, da kuma nuna banbancin da takeyi a tsakaninsu.......! ••••••••••• Kiran sallar farko a kunnen Nadeeyah akayi shi, mikewa tayi hade da mik'a idanuwa da kanta sun mata nauyi sosai, da kyar ta iya jan kafarta ta shiga bayi da niyyar dauro alwala, bako ta riska a tattare da ita, tashin hankali sosai ta shiga na rashin audugar da zatayi amfani dashi, tsumma sam baya tare ta, bata ma san yadda zatayi amfani dashi ba, saboda duk zata koma makaranta sai an sai mata guda uku, ragowar ta dawo dasu gida tayi amfani dasu, kayan jikinta ta cire tayi wanka da ruwan zafin dake zuba a pampo, gasa gefen kanta dake mata nauyi tayi da dukkan jikinta, sai da taji dadi sannan ta fito, pant dinta ta dauko da wani karamin dankwalin Zainab, tayi dabara ta sanya a jikinta, shiryawa tayi tsab cikin doguwar riga kimono jaa, dinkin yayi mata cib a jikinta, duka kayan basu wuce dubu biyu ba, amma yadda suka karbeta kamar kayan dubunnai, blue baby hijab tasa a wuyanta ta fara gyara kayansu, tana gamawa ta hau gyaran dakin, tsintsiya ta fara dubawa bata gani ba ta tabbatar tana parlor, ko kitchen, fitowa tayi ta fara dube dube, can ta hango tsintsiyar a bakin kofa, daukowa tayi ta sharo dakin sannan ta dawo parlor ta fara gyara shi, sai da ta gyareshi tsaff, tayi mopping kamar ba'a taba taka kasan tiles din ba, kitchen ta wuce shima ta gyareshi tass, ta hada kayan wanke wanke ta fara yi... Da hira suka shigo parlon kowa da farar jallabiya a jikinshi, sama Daddy ya wuce dan baccin bai isheshi ba, badan sallar asuba ba babu abinda zai fitar dashi,, Kallo sukeyi suna hira hade da dariya, hamma Musaddiq ya fara yi hade da tsaki, "wai kai yau baka jin baccin safe ne, zo muje mu kwanta mana, gyara zama Hilal yayi yace "Baccin safe asara ne my guy, kullum sai mum ta fada mana, hararashi Musaddiq yayi yace "really!!! yau ne kasan da wannan, dalla tashi muje mu kwanta, kafin Hilal ya bashi amsa suka jiyo ihu a kitchen, Hanyar sama Musaddiq yayi a tsorace dan shi a tunanin shi wani mugun abun ne, dan yasan a gidan babu mai shiga kitchen a wannan lokacin, Hilal kuwa mikewa yayi ya tsaya kyam cike da jarumta yace "Hasbunallahu wa ni'imal wakil, "wayyo Allah hannuna, wayyo Allah na, abin da suka jiyo cikin ihun kukan kenan, da sauri Hilal yayi kitchen din saboda ya gane mamallakiyar muryar, dawowa musaddiq yayi ya bi bayan Hilal shima da sauri, A durkushe Hilal ya sameta rike da hannun sosai tana kuka kamar ranta zai fita, mugun radadi takeji har tsakiyar kanta, karasowa yayi a gaggauce ya dagota, hannun ya fara kokarin kamawa ta kara tamkeshi saboda azaba, "me ya sameki?, and me kikeyi a kitchen at dis hour, saitin windon ta nuna mishi hade da runtse idon ta, katuwar KUNAMA ya hango tana tafiya a hankali, hannun ya saka da sauri ya dauko takalmi, mugun duka ya kai mata har saida net din windon ya tsage, duk wani bacin ranshi ya tattaro ya sauke a kan kunaman, saida yayi mata pieces sannan yayi wurgi da takalmin, waigowa yayi da niyyar fita da Nadeeyah yaga wayam babu kowa, da sauri ya fito parlon yaganta zaune a kan dining, kusa da ita Musaddiq ne yayi kneeldown rike da hannun yana hurawa, yana fadin sorry, zafin yana raguwa ko?, girgiza kai tayi saboda zafin kamar dado shi akeyi, tsaki Hilal yayi yace "who told u zafin harbin kunama na ragewa haka nan, bari in dauko key mu kaita hospital, gyada kai Musaddiq yayi yace "kayi sauri plss, Hawayen fuskarta ya fara share mata yana fadin "stop crying, it won't help sai dai ya kara miki ciwon kai, kiyita addu'a, kinji!, uhm ta fadi tana gyada kai, Badariyya da tun ihun farko ta farka, tana zaune a inda take tana tsaki, a ranta tana fadin "Allah yasa ciwon mutuwa Nadeeyah keyi ta mutu kowa ya huta, mikewa tayi ba tare da tunanin yin sallah ba ta bude kofar dakinsu dan surutai da shashshekar kukan da takeji sun fara damun kunnenta, Mummunan gamo tayi wa idanunwanta, wani abu taji a kirjinta kamar saukar aradu, tashin hankali marar misaltuwa ya ziyarci zuciya da ilahirin jininta, bata karasa gama shiga cikin kogin bacin rai ba taji muryar Hilal na fadin "ke miko mata babban hijab cikin kayanta, a firgice kamar me farfadowa daga suma tace "Hijab din wa? Wa kika gani anan? Ko ina sa Hijab ne? Hilal ya fadi yana harararta Cike da ficewar hayyaci da rashin kunya tace "sai kuma kaga nayi kama da yar aikenta ko, sai kaje can dakin da ta sauka ka dakko da kanka dan kasan bata isa muyi sharing daki da ita ba, a hasale ya nufeta, Musaddiq yayi saurin cewa rabu da ita Kangiwa, muje mu kaita a haka, ciwon k'aruwa yake yi,, dagota musaddiq yayi ya riketa sosai suka nufi hanyar waje, "zamu hadu in na dawo Hilal ya cewa Badar hade da nunata da hannu, wani irin kuka ta saki hade da fadin ka kasheni in ka dawo, karka sake ka barni da rai, bai tsaya biye mata ba yayi waje dan ba ta tata yake yi ba, burinshi yaga Nadeeyah ta daina kukan nan da takeyi, sannan yasan wani daki aka sauketa a gidan, kuma yasan musababbin shigarta kitchen a wannan safiyar kamar baiwa.. A iya saninshi a sama, dakin mummy da Daddy ne kadai, a kasa kuwa na musaddiq ne sai nasu Badariyya da na masu aiki, ko BQ mummy ta kaita ita kadai? kauda tunanin yayi ya shiga motar ya tada ta suka wuce.....!!!! Mrs Tijjani Shattima.. ... *** [01/03 12:08 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣3⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* Sallamanku!! A razane Ma'u ta juyo dan jiyo sallamar tayi bagatatan hade da shigowar me sallamar, "wa sallama" ta fadi tana kokarin kare fuskar bakuwar, "Ayya Haire am kece tafe da maraicen nan, "Aaa nice, mon be sare! Haire tace tana kallon kafar wacce Ma'u ke karewa, dad'a kareta tayi tace "Yauwa sannu Haire, tayi saurin cigaba da cewa "babu fura! yau tun safe ta kare saboda masu shigowa siyan nono, Haire ta kara matsowa tana leken idon bakuwar tace "Ni ba fura nazo siya ba, labari nazo in baki, yau ko nonon bamu samu ba, bare ayi zancen siyan fura! Cike da kaguwar san jin labari Ma'u tace "Baku samu nono ba? Ba'a tatsi madarar nonon bane? Haire tace "Hmmm, yau ai anyi rigima a kofar gidan jauro, har Shaho ya kashe rai, kisa,,, ma'u tace gabanta na dukan uku uku kamar bata san komai ba, wa aka kashe? Ke ko Ma'u baki bani gurin zama, duk irin gajiyar nan da na kwaso ki barni a tsaye, Tsaff ma'u ta gano manufarta, taja hannunta tayi hanyar sakarkari da ita, saboda tsaho irin na ma'u tsaff ta hana haire damar waigowa, Labarin abin da ya faru ta fada mata hade da cewa "yanzu Hardejo yasa a dauke gawar yaron ayi mata sallah, dan ance saurayin musulmi ne, kuma ya wakilta wani yaje can tsaunin ya nemo inda yan uwanshi suke a fada musu, cike da damuwa Haire tace "ni yanzu yar buduwar nake tausayi, dan shaho na can ya tashi hankalin gari, kuma yace duk wanda ya dauketa ya boyeta in dai ya samu labari sai ya hallaka shi, kinsan shaho, a wala hore na,, duk dakiya irin ta ma'u saida cikinta ya dauki kugi saboda yadda take jin labarin shi tun zuwanta garin da aure ya kawota,, magana ta fara yi jiki a sanyaye tace "Haire am kinsan babu abinda zan boye miki, gyada kai Haire tayi tace "nasani ma'u, yauwa tace tana mai gyara tsayuwa, ta kwashe yadda akayi Baffa ya kawo yar makka gidan da kuma amfanin da take ganin yar makkan zata yi mata, ta karashe da fadin duk irin kokarin da zanyi in ga na samu wani abu a gurin iyayenta da ita zanyi, sannan kema bazan barki a baya ba, rabawa zamuyi daidai in kin yarda zaki rufa mana asiri, Ajiye kwarya Haire tayi ta zauna tana washe baki tace "wannan ai karuwar mu ce duka, ke ni har na fara hango ni a kasa mai tsarki, yadda su Hardejo suke fadin kasar ace muma gamu a cikinta, shewa sukayi dukkansu Ma'u tace "ai kaff kauyen nan sai sun dawo yi mana bauta, ke dai ki bani hadin kai mu samu abinda muke so, yanzu bari kiga sarkar da na dauke mata na hadata da tarkacen tawa, "aiko dakko ta mu gani, kin gani, ashe dai dama gaskiyar Hardejo da yace musulunci dadi gareshi, gashi nan cikin kwanaki kadan da karbarshi mun sami damin arziki, dariyar murna ma'u tayi ta wuce daki inda take jiyo kukan boddo, rashin ganin Baffa a dakin baisa ta kawo komai a ranta ba, ta dauki Boddo Halima ta duba gurin da ta ajiye sarkar taga wayam ba komai, dube dube ta farayi a gefen da tayi ajiyar, nan ma bata ga komai ba, a kidime ta fito da sauri tana kiran sunan Baffa, Rashin ganin bakuwar a inda ta barta ne ya kara daga hankalinta matuka, bayin gidan ta duba ko tana ciki, nan ma taga wayam babu kowa, gurin Haire ta koma jiki a sanyaye tace "Baffa ya dauketa a gidannan, dama yace zai koreta na hanashi, shine ya faki idona ya aiwatar, shi tsoro gareshi, daya barni da shaho ni nasan yadda zanyi inyi maganinshi, yanzu gashi ya janyo min asarar sarkar gwal da kyautar da iyayenta zasu mana in sunzo daukarta, Cike da kunan rai Haire da ta gama hango kanta a wata duniyar tace "amma Baffan Bingel bai kyauta mana ba, badan sunan annabin Hardejo gareshi ba da sai inyi kokwanton amsar musuluncin shi, tunda ai addinin Hardejo yace mu sowa dan uwanmu abin da muke sowa kanmu, jugum dai ma'u tayi tana bawa Boddo nono, tunanin ko ina mijinta zai kai yar Makkah ne ya cikata ya hanata magana..... Shi kuwa Baffa jin hirar da sukeyi da Haire ne ya sashi dauko sarkar da rigarta ya rufe mata fuska hade da kamo hanunta suka fita a gidan, Hanyar gidan yayanshi Hardejo yayi, duk wanda ya gansu a hanya sai yayi tunanin Ma'u ce, wasu a ganinsu wani abu ne ya faru ta rufe fuskarta take kuka, babu wanda ya ganeta kasancewar ma'u ma fara ce sosai, saidai farin nasu ba iri daya bane.. A kofar gida ya samu Hardejo yana koyar da samari karatun Allo, can ciki ya shige gurin matan shi, aiki ya samesu sunayi dukkan su a tsakar gidan, dakin uwar gidan ya shige kai tsaye tare da ita, ganin su a haka ya sa uwar gidan cire hannu a aikin ta wankesu tabi bayansu dan jin ko lafiya taga Ma'u haka, A tsaye ta sameshi yana safa da marwah a cikin dakin, yana ganinta yace "yauwa me babban suna, dama ke nake jira, taimakona nazo kiyi, zama tayi kusa da budurwar da take tunanin ma'u ce, tace "me ya sameki ma'u? Zama yayi daidai kafarta ya bude fuskar budurwar yace ba ma'u bace, bakuwa ce wacce rayuwarta ke cikin hatsari, labarin abinda ya faru kaff ya kwashe ya fada mata har dalilin da yasa ya kawota gurinsu, ya cigaba da fadin "nasan Shaho bashi da karfin da zaizo gidan nan yace zai dauke ta ko ya mata illah, gata nan zan bar miki ita, domin Allahn Hardejo ki kula da ita har iyayenta suzo daukarta,,, A tsorace Aisha (mai babban suna) ta kalli budurwar tace "a wani gari take? Inafa zan san daga inda take, Baffa ya fadi cike da zullumi, gyara zama tayi tace "to babu matsala, na samu labarin abinda ya faru sama sama dazu, Kuma naji ance malam ya tura aje a dauko gawarshi mutanen shaho sun hana sun zauna jiran dawowar budurwar ko wanda zai dauki gawar, cike da tausayawa ta kalli budurwar tace "ya sunanki, Baffa yayi dariya yace "ai bata jin komai, larabcin kadai na lura take ji, da yake Aisha ta dade cikin musulunci, babanta babban malami ne a jalingo, kuma sanadiyyarsu Hardejo ya musulunta har aka bashi aure, tace "maa ismuki ya ukhtee... cike da jin dadi budurwar tace "ATIKA " *ATIKA SHEIK SAHEEB SAIFUDDEEN* Juya sunan Baffa yayi tayi yace "kai ilimi akwai dadi, yanzu kinga sai musan labarinta ta dalilinki mai babban suna.... Mikewa Aisha tayi tace "bari in kawo mata abinci taci sai tayi sallah, kaga magariba ta kusa.... Bayan sallar isha'i kowa ya nutsu a gida, kuka da karai kainin shanaye kadai ke tashi a cikin gidan, matasa da yaran gidan duk suna zaure suna daukar karatun dare, yayin da wasu daga cikin malaman hardejo suka wanke gawar Habeeb da suka samu daukowa da kyar, hade da suturceta kamar yadda hardejo ya koya musu... Zaune yake cike da damuwa ya zurawa abincin gabanshi ido, "mutanen kauyen nan har yanzu imani bai gama ratsasu ba, duk irin fatawar nan da ake badawa bazai sa su hankalta su saduda ba, Hannu yasa a sama yace " *YA ALLAH DUK WANDA ZUCIYARSHI TAKE A KESASHE BATA DA NIYYAR RUSSUNAWA KUMA BA MAI SHIRYUWA BACE YA ALLAH KAYI MANA MAGANINSU DA GAGGAWA* AMEEN suka amsa dashi dukkansu, Adduoi yayi sosai akan duk abinda zai zamto barazana akan alummar musulmi Allah ya kauda shi.... ****** Cikin Harshen larabci take bawa Aisha da Hardejo labarinta... Sheik Saheeb Saifuddeen shine sunan mahaifina, dan asalin kasar cairo ne, babban malami ne kuma dan kasuwa wanda ake ji dashi a egypt.. Ummuna ta rasu shekara shida da suka wuce gurin haihuwar kanina, ummuna mahaifinta dan cameroon ne, mahaifiyarta ce yar cairo, kasancewata babba gurin mahaifina yasa yake ji dani fiye da kowa,, Tun bayan rasuwar mahaifiyata aka aura mishi kanwarta Ummul khair saboda ta kula da kanina, tun daga lokacin rayuwa ta fara sauya mana zuwa yanayi na ban mamaki da tsoro, abin ya faro ne saboda ganin da ummulkhair tayi Abbuna ya dauki dukkan kulawarshi ya bamu ni da kanina *ATEEK* kiyayya iri iri babu wacce Ummul bata nuna ma Ateek, kiyayyarta a garemu batayi karfi sosai ba har saida ta haihu, a lokacin ne ta nuna wa Ateek karara ba ita ta haifeshi ba, in na tafi makaranta na barshi kafin in dawo gida ya jigata da yunwa, gaba daya Ummul ta shafe idonta ta manta da zumunci saboda kasa ta rufe idon ummuna wacce ta zamto yar uwarta ta jini, burinta a kullum Abbuna ya kula da ita da yaranta guda uku " Haidar, Affan, da Farouk," saboda rashin zaman Abbunmu shiyasa bai taba sanin halin da muke ciki ba, bai kuma kula ya duba ba, saboda a ganin shi kamar da ummunmu muke tare, bai taba kawo ummul zata taba koda yi mana kallon banza ba, bare har ta kai ga cuzguna mana, Kakarmu ita kadai ce gatanmu, gurinta hankalinmu ke kwanciya, wannan zuwan da mukayi ma ta'aziyar rasuwarta muka zo, daga can muka taho nan mambila inda kanwar kakanmu (wanda ya haifi ummunmu) take domin gaisheta.. gidan sam baya min dadi saboda duk yan uwa basa kulawa da lamarin mu saboda rashin idon uwa, kuma suna ganin Ummul ce mai rike damu sannan ga kudi tana musu facaka dashi shiyasa duk suka dauke idonsu akan mu, rashin jin dadin zaman gidan yasa da na ga Habeeb ya fito zai taho siyan madara na biyoshi dan in zaga inga gari hankalina ya kwanta, ashe kaddararmu ce anan ni da shi, tunanina daya *Ateek* da na tafi na barshi yana bacci, yaya rayuwarshi zata kasance in har babu wanda ya biyo sahun duba ni, yaya rayuwar Ateek zata kasance, ta karashe cikin kuka mai ratsa zuciya,,,,, Share hawayen tausayi Hardejo yayi yace "zasu zo su sameki, nasan zasu zo dan na tura a nemo inda iyayen yaron suke, ko basu zo ba ni zan je har mambilan in kaiki gobe, cikin kuka tace jirgin su a daren yau zai tashi ya koma cairo, kuma kasani ba'a samun jirgi akai akai, Kwantar mata da hankali Hardejo yayi yace "Gobe tun da asuba zan tafi in kaiki, ki kwantar da hankalinki, " "Abin da Hardejo bai sani ba shine labarin mutuwar Habeeb ya karade ko ina a tsaunin mambila, kuma an hade harda ita Atikar ance an kasheta, saboda firgicin labarin kuma ance musu limamin garin yasa an dauke gawar an suturce yasa gaba daya yan uwanta suka shirya komawa Cameroon a daren, harda ita kanwar kakar tasu wacce dama Habeeb din ne karfinta a garin.... Suna idar da sallar asuba sukayi janaizar gawar Habeebu, bayan an binneshi kamar yadda Hardejo ya karanta sukayi mishi adduoi sosai sannan kowa ya wuce gidanshi, ko abincin safe bai ci ba ya shirya ya tarar da Atika tana shan fura, tana gamawa ta mike suka dauki hanyar tafiya tun kafin garin ya gama yin haske, sai da sukayi tafiyar awa daya sannan suka samu motar awaki ta karasa dasu, A garkame suka samu gidan da ya kasance daki biyu tall, cike da tashin hankali malam Hardejo yabi makotan gurin yana tambayarsu, sukace ai kuwa tun daren jiya suka tafi saboda firgicin mutuwar su Habeebu, zamani na babu waya bare ace za'ayi kiransu su dawo, Takalmin Ateek ta gani a kofar gidan kafa daya, dauko takalmin tayi ta zauna dabas taci kuka ma ishi hade da rungumar takalmin tana sumbata, "Allah yasa ina da rabon sake ganinka Ateek, ya Allah ya hadamu da kai da alkhairi,, Hardejo saboda tausayi baiyi yunkurin hanata ba, saida tayi kukanta sosai sannan ta tashi suka koma can kauyen su Hardejo,, kauyen da rayuwa tayi dadi hade da wuya ga Atika, kauyen da ya maida yar gata baiwa, kauyen da Atika tayi rayuwa mai cike da ban tausayi.... Ya Allah kai ka zama gatan mara gata, Allah ka sanyani na zama uba kuma gatan Atika dan alfarmar annabi da hasken alkurani... addu'ar da Hardejo yayi tayi kenan har suka isa gida...... Mrs Tijjani shattima.... [01/03 12:08 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU*•• 2⃣4⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* Satin Atika hudu ta fara sakin jiki da yaran gidan duk da bata gane yarensu, karatun qurani da littattafai take yawan koyar da yan matan da yan yaran gidan, sai addu'oi na azkar wadanda ta koya daga gurin mahaifinta... Shaho kuwa tunda ya fahimci tana gidan Malam Hardejo hankalinshi ya tashi, duk iskancin shaho yana tsoron Malamin saboda kwarjinin da yawaitar ambaton Allah ya haifar masa, kullum in yayi niyyar zuwa gidan sai yaga gidan ya zame mishi bakikkirin,, gashi kullum bashi da nutsuwa saboda yawan mafarkin Habeeb da yakeyi, bacci sam ya daina daukarshi dan daga ya rufe ido zaiga fatalwar Habeeb.. kwance yake yayi firgai firgai zuciyarshi cike da kunci da radadi wanda baisan daga inda suke ba, hatta da abinci ya daina samun lokacin ci saboda yanayin rayuwar da ya tsinci kanshi,, rashin ilimin addini ya sa ya kasa gane jinin mu'muni da kuma adduar malami irin na zamanin da wanda baya iya yin komai na sabon Allah ne ke dawainiya dashi ba, iyayenshi sun kasance masu kudin kauyen sosai, shiyasa yake yin abin da yaga dama, ganin halin da ya shiga ba karamin daga hankalin mahaifiyarshi yayi ba, duk irin sangartar da yakeyi ita sam bata ganin laifinshi, ko da aka kawo mata labarin abinda yayi murna tayi tace "sai ku jerasu cikin sauran mutanen da ya kashe, ai ba yau ya fara ba, ita a kullum alfahari takeyi da halayyarshi saboda jahilci.... Halin da taga danta a ciki ne ya sanya ta dangata halin da son bakuwar gidan Hardejo, alkawari ta mishi na a cikin satin nan zata aura mishi ita koda kuwa duk abin da take dashi zasu kare..... ******-------******** Jin inuwar mutum a kansu ne ya sanya su dagowa daga duba littafin dake hannunsu, Maryam yar Hardejo ta mike tsaye jiki na rawa tace "ina yini, bata amsata ba tace "kira min Mai babban suna, da sauri ta shiga daki ta kira mahaifiyarta, kafin su fito maman shaho ta karewa Atika kallo sosai, a zuciyarta taji dadi da danta zai samu wannan zukekiyar yarinyar a matsayin mata.., "Gambo kece tafe, Aisha ta fadi tana shimfida tabarmar kara, ba zama nazo yi ba mai babban suna, nazo ne in fada miki Shaho yana son bakuwar gidanku, in Hardejo ya dawo kice mishi yazo ya sami Barde (mahaifin shaho) sai su shirya ayi musu aure yadda addinin Hardejo ya tsara, "galala Aisha tayi a zuciyarta tace "yau isar har ta kawo kansu, kafin tayi magana Baffa ya shigo gidan tare da ma'u, duk abin da ta fadi akan kunnensu, "ko bakiji abin da nace bane mai babban suna? Gambo ta tambaya tana huro hanci, karap Ma'u tayi tace "yo ko taji amsar me zata baki, yanzu ke d'anki har wani d'a ne da zakizo kina hurawa mutane hanci kina nuna iko akan yar mutane, to walle duk wani iskancinku yazo kurewa, dan ko sama da kasa zasu hade yarinyar nan bazata auri azzalumi irin shaho ba, ba Aisha da matan gidan dake tsaye a tsorace ba, har Baffa da yake namiji saida ya kusa sakin fitsari, dan yasan ahalin shaho gaba dayansu babu imani a tare dasu, bai bari maman shaho tayi magana ba yace "kiyi Hakuri dan Allahn Hardejo, kinsan Ma'u bata da hankali, Da hankali na!! Nace da Hankali na, in sun isa su kas--- toshe mata baki Baffa yayi ya jata dakin Aisha, hakuri Aisha ta bata hade da tabbatar mata da Hardejo zaizo har gida ya sami Barde, Har kofar gida matan gidan suka rakata suna tausarta... Cike da fargabar rashin son tashin hankali Hardejo yace   "Ya zama dole in yi wani abu akan yarinyar nan, buri na in samu kudin da zan kaita gaban iyayenta har can  egypt, to a halin da muke ciki ko daya cikin kwatan kudin babu, ga sarkar ta da nake tunanin saidawa an nemeta ko sama ko kasa an rasa, dafe kanshi yayi yace "ya Allah ka nuna min hanyar da zanbi in ceci yarinyar nan daga sharrinsu Shaho... Sallama dai... dago kai Hardejo yayi cike da bacin rai yace "sau nawa zan maka magana akan cika sallama Muhammadu, cike da girmamawa yace "Ayi hakuri, sai a hankali komai zai zauna min, neman guri yayi ya raba ya zauna, zuwa gidan yanzu duk dare ya zamewa Baffa jiki saboda zuwan Atika, kallon Hardejo yayi yace "yanzu me ka yanke akan maganar Atika, shin zaka aurar da ita ga shaho ne tunda bamu da kudin kaita gida, girgiza kai Hardejo yayi zaiyi magana ya kalli fuskar Muhammadu, wani irin Hasken annuri yaga ya gifta a fuskarshi, murmushi yayi yace "tabbas zan aurar da ita, amma ga kai muhammadu, kai zaka aureta saboda mu tseratar da rayuwarta daga azzaluman nan, saida ya tsugune saboda tsoro, ni kuma? A'a inaa, sam bazan iya hada kaina da tashin hankali ba, yo ta ina zan fara ma ma'u bayani, sannan ni kake so ka bari da bala'in Shaho da iyayensa, dariya Aisha tayi tace "matsoraci bashi zama gwani Baffan yara, to dama ni nace miki ina son zama gwani ne? Ya fadi a harzuke, dariya sosai sukayi, Hardejo yace "yanzu dai fada min cikin biyu, wanne kake tsoro? Ma'u, wallahi bazan iya yi ma ma'u kishiya ba, ka tuna fa rabo ta nayi daga can garin su na kawota nan ba uwa ba uba, sannan yanzu inci amanarta, haba malam, kaifa kace addinin ka ya hana cin Amana, kwarai ya hana cin amana muhammadu, amma kuma shi addinin ya halasta auren mace hudu, ko baka lura da matan dake gidana ba? Kirne fusķa Baffa yayi yace "kai ai ka girma, ni fa? duka yarana nawa, biyu kadai sai ince zanyi aure, ganin da hardejo yayi samm Baffa bazai fahimta ba yasa shi cewa "gobe zanje gurin Barde kawai a daura mata aure da shaho, a kasalance Baffa yace "Haba malam!! yanzu babu wata mafita sai wannan, mafitar kenan, kuma kaki bamu hadin kai, cike da Hikima irin ta mai ilimi Aisha tace "to me zai hana ya aureta har lokacin da zaka samu kudin da za'a kaita gida sai ya saketa, ta tafi, yauwa mai babban suna kin kawo shawara Baffa ya fadi yana gyara zama, yanzu kinga sai kije kima ma'u bayani gobe, cike da mamakin irin tsoron da yakewa ma'u tace "babu matsala, in ka amince wannan duk mai sauki ne, da wannan suka tsaida shawarar yadda zasuyi su taimaki marainiyar Allah daga sharrin ahalin shaho, sam basu da masaniyar halin da zata shiga yafi wanda shaho zai sanyata, wannan shine mafarin shigar baiwar Allah Atika cikin cakwakiyar rayuwar da zatayi sanadiyyar rayuwarta..... A dimauce tayi wurgi da Boddo akan gado tace "samm bazai yiwu ba, in har so yakeyi ya taimaketa ya saki wata a cikin matanshi ya aura, in yaso sai ya maida ita bayan ya samu kudin kaita, kuka ta saki da karfi tace "yanzu duk halaccin da nayi maka da wannan zaku saka min? ashe ni dazu fadan da nayi da Gambo kaina na jawa, ashe abin a kaina zai kare.. dakyar ya nutsar da ita hade da yi mata alkawarin bazai taba kusantar Atika ba, sannan yayi mata nuni da irin alherin da zasu samu da Atika, "nasan kece kika dauki sarkarta! to in kinason sarkar ta zama taki har abada, kuma kinason ki samu mafiyansu in muka kaita gida ki bani hadin kai mu ceto rayuwarta, alkawarin da nayi miki bazan taba canza shi ba... ki yarda dani..... (wannan kalmar nada matukar tasirin ruguza rayuwar macen da ke da saurin yadda).. Allah ka tsaftace mana zukatanmu, dan in mutum nada gurbatacciyar zuciyar da bata yadda da kaddara, to tabbas wannan kalmar ta sama zata sanya mutum cikin hadari in har aka samu akasin dagawar kalmar zuwa ga wani muhallin na daban... Allah ka taushi zuciyar dukkan matan musulmi su yarda da kaddara in tazo garesu..... Washe gari tun karfe goma na safe Hardejo ya daura Auren Atika da Muhammadu a sadaki nairah bakwai da sule biyar, cikin kudin da ya fara tarin tafiyar ya cire ya biya dan yasan Baffa bazai biya ba, bayan shaidu sun shaida daurin auren, Hardejo yayi adduo'i sosai na neman tsari a garesu da samun zuri'a a tsakaninsu.. dan shi kam yana hango ma kaninshi alherin kasancewarshi da Atika, zuwanta garin ma kaddara ce rubutacciya,, (Abinka da adduar mutanen da, masu tsantseni da tsananin tsoron Allah, malamai masu tsaftatacciyar zuciya wadanda basu san meye sabon Allah ba, malaman da Allah ke amsa adduarsu cikin gaggawa saboda tsantseninsu.)...... Juyi yakeyi sosai yana rike da kirjinshi da yake jinshi kamar ya fitar dashi ya yar ya huta, ba ciwo yakeji ba, amma abin da yakeji yafi ciwo zafi, Muryar mahaifiyarshi yaji tana shararo Ashar tana fadin yau lahira zatayi baki, Da karfi shaho ya kwala kiran sunanta, gurinshi ta nufa da sauri tana fadin kaji Hardejo ya aurar da matar da naci burin aura maka, dan tsaki yayi yace "Gambo ke kike ta aure, bakya ganin halin da nake ciki, ko bacci bana iya yi, daga na runtsa fuskar saurayin da na kashe nake gani yana matsowa kusa dani zai illata ni, mafitar halin da nake ciki zaki nema, ba wai maganar aure ba, cike da alajabi tace "yau ka fara kashe mutum? a kiyasin da nayi ka kashe ya kai talatin banda dabbobi, meyasa zaka sa wannan a ranka, Katseta yayi yace "wannan na daban ne Gambo, duk sauran kisan da nayi musu akwai kwakwkwarar hujjar yin hakan ya karashe ido yayi mishi jajur, kasa daure damuwarta tayi tace "tashi muje gurin Hardejo, tashi maza, bazan juri rashinka ba Shaho, mikewa yayi jiki babu kwari suka kama hanyar gidan Hardejo.... Allah gafurur rahim, lallai "Bala Shaho" Allah yana sanka da rahama, wannan abin da kakeji Allah ne ya fara nuna maka illolin abinda da kake aikatawa, lallai jinin Habibu jini ne na mu'imini, Adduoin da iyaye da yan uwanshi sukeyi akanka bazai taba barinka kayi sukuni ba, A farkon zuwan musulunci kauyen nan, naso mu rugumeshi cikin tsaftatacciyar hanya, amma sam kuka ki, kuka amsheshi sama sama, ku ka dinga aikata sabo saboda ance muku ko an aikata Allah na yafewa, cike da kunan zuci shaho yace "maleee, (sunan da suke ce mishi kenan cikin isgili) yanzu ka fada min abinda zanyi in daina jin wadannan abubuwan da nake ji, gyara zama malam yayi ya mishi bayanin addinin Allah da duk abinda Allah bayaso, sannan ya daura mishi da cewa "ta yiwu Allah ya yafe maka saboda kayi abubuwan da kayi a baya cikin rashin sani, kasan Allah baya kama mutum da laifin da baida masaniya akai, sannan sharadin tuba, sai ka tabbatar in ka daina ji da ganin abin da kake gani bazaka sake komawa cikin aikata sabo ba, '""Bazan sake ba malee"" ya fadi da sauri, ni kadai nasan irin wahalar da nasha, to Alhamdulillah Hardejo ya fadi yana murmushi, sannan ya fara koyar dashi kalmar shahada da kuma istigfari, ya horeshi da yin istigfari kafa dubu a kullum saboda yana kankare zunubai, sun dade tare yana koya mishi abubuwa zuciyarshi na samun nutsuwa, ita dai Gambo zama tayi kamar gunki tana kallon sabon mutum a gurin danta, da yake ita din mace ce mai son danta, da duk abin da yake so nan take itama tayi mubaya'a, malam Hardejo ya cigaba da fadakar dasu akan abubuwan da Allah keso da wanda baya so..... Rayuwar Atika a gidan Baffa, Rayuwace da ta fara yinta kadaran kadaham, sam ma'u bata kishi da ita saboda sanin yanayin da sukayi auren, da fari ta fara bijirowa da cewa tunda yanzu Shaho yayi nadama ya shiryu mai zai hana Baffa ya saketa ta koma ta auri shahon, a lokacin taga ainihin Fillo Hardejo, dan saida yayi mata wuzu wuzu sannan ta maida hankalinta, da yaga ta nutsu ne yasa shi ya koma lallashi, ya cemata ta sani ko tuban muzuru Shaho yayi, irinsu ba'a gane tubansu har sai an musu gwaji mai karfin gaske, cikin hikima ya kwantar mata da hankali, samm baya ko kaunar hango rabuwar Atika da Muhammadu saboda yasan ko babu rayuwarshi Atika zata zame ma dan uwanshi alkhairi..... **** Ashe dai ma'u baki da hankali ban sani ba kuma ban gama tabbatarwa ba sai yau, yanzu har wannan tsaleliyar budurwar Baffa zaice baze kusanceta ba kuma ki yarda, naman zomon da ta gasa takai bakinta tace " Haire am niko nake da hankali, an fada miki hakanan na sakankance, ai ba sakarai nake ba, nasan yadda Baffa yake da sakarcin nan akan mace wata rana zai iya kusantarta a bayan ido na, shiyasa na aika can garinmu gurin "Iyan gida" ta amso min gadalin mu na ukari, sannan ta hada da duk wata mallakar maida mace namiji a idon Baffa, yaushe zanyi wannan wawancin a barni in zama yar kallo, ai dole na mike tsaye ko dan yadda Hardejo ke nuna min ita din kamar yarshi take ta jini, shewaaa sosai sukayi hade da tafawa, dariya Bingel tasanya itama ganin mahaifiyarta na dariyar babu kakkautawa, dariyar tata ta sake sasu wata dariyar hade da kai naman zomon na karshe cikin bakinsu.... Kallonsu Atika tayi itama tayi murmushin saboda bata san abun da suke fadi ba, kara gyara goyon boddo tayi tana jijjigata tana mata wakensu na larabawa, tunanin Ateek ta tafi wanda ya zame mata tamkar shan ruwa dan kullum, Ya Allah ka dubamin Ateek.. kalmar kadai take ta maimatawa cikin harshenta na larabci...... Mrs Tijjani Shattima...... [02/03 9:59 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣5⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* *RUBUTACCEN AL'AMARI* Sauri sauri yake yi dan samun sahun gaba a cikin masallacin kofar gidan Hardejo wanda Barde da Gambo iyayen shaho suka gama gininshi, dabe ne na kasa suka bada kudi aka hada karfi da karfe aka ginashi cikin gaggawa, Shaho ne tsaye a kofar shiga yana sallama ga duk wanda yazo shiga, sanin muhimmacin Sallama da yayi, da kuma irin ladan da ake samu ya sanyashi a koda yaushe fara yin ta ga duk wanda yayi tozali dashi.. Bayan idar da Sallah Malam Hardejo ya zauna a tsakiyarsu ya fara janyo musu wa'azi mai kashe jiki, kowa a cikin massalacin saida ya nutsu, zuciyoyinsu suka narke matuka da tsoron Allah, a cikin wa'azin ya sako musu muhimmacin aure da kuma hakkin da mace take dashi akan mijinta, "Hakkin duk wani namiji ne ya ciyar da matar shi, Hakkinshi ne ya tufatar da ita, sannan Hakkinshi ne ya sauke duk wata bukata tata, lissafo bukatun yayi cikin hikima, sannan ya tunatar dasu azabar da mutum zaisha a gurin ubangiji in bai sauke wannan hakkin ba, wa'azi sosai yayi mai cike da tausayi da al'ajabi... jikin kowa a sanyaye suka tashi suka fita daga masallacin, matsowa Bala (shaho) yayi kusa da malam yace "Assalamu Alaikum, a sanyaye Malam ya miko mishi hannu suka gaisa hade da yiwa juna murmushi, kayi hakuri Bala, yau jikina baya min dadi, bazamu samu damar yin karatu ba, murmushi Bala yayi yace "Babu matsala Malam, Allahn Hardejo ya kare ka da lafiya, dariya malam yayi yace "Allahn mu gaba daya, gatan mu, kuma gatan zuri'armu.... ●●●●●●●●●● A hankali ya tura kofar gidan ya shiga, wa'azin Hardejo keta kai komo cikin kwakwalwarshi, zama yayi a tsakar gidan kan wani dakali, tunani ya dingayi na yadda zai sauke hakkin marainiyar Allah akanshi, ga kuma alkawarin da yayi wa ma'u shima kuma Allah baya son mai saba shi, yana cikin wannan tunanin ne ruwa ya kece a kanshi, mikewa yayi da niyyar wucewa daki sukayi karo da Atika ta fito ta kwashe kayan da ta wanke a kan duwatsun shanyar gidan, matsawa baya yayi da sauri yana mayar da numfashi, rab'awa tayi ta wuce ta kwaso kayan, kafin ta gama kwashe kayan gaba daya ta jike sharkaff, kallonta Baffa ya tsaya yi shima ruwan ya jikashi sosai, saida ta gama kwashewa tazo wucewa yaji ta dan gogeshi da kaya sannan yayi firgigit ya gane ta wuce, yasan ma'u bata gidan, tana can gidan inna wuro tare da yara, da jan kafa ya bita dakin, cikin kudurar ubangiji ya fara jin wani abu na fusgarshi game da ita, shaukin da bai taba jin irinshi ba ya shiga, a hankali ya kusanceta ya taimaka mata ta rabu da jikakun kayan jikinta, tuni labarin ya canza zuwa wani sabon babi na shafin labarin.... Mikewa yayi jiki a sanyaye zuciyarshi kamar an sauke nauyin da yakai girman dutsen mambila, ita kuwa azaba ta hanata yin kuka, dakyar ta iya tashi, abinka da mutumin "da" shi ficewa yayi yaje bayi ya wanke jikinshi ya barta a cikin dakin, A daddafe ta fito tsakar gidan, tunanin yadda zatayi ta rabu da wannan azabar da take ji take yi, dakyar ta iya ďiban ruwa ta wuce bayi, tsugunon ma zame mata aiki yayi amma haka ta daure dan dai kawai ta daina jin zafin gurin, tana watsa ruwan sanyin tayi wani irin ihun azaba, tsakar gidan ta fito tanata safa da marwa tana zubar da hawaye tana kiran sunan Allah, Azaba kam iya azaba Atika tasha ta a wannan ranar domin ko abincin kirki babu a gidan gashi babu abin da zata iza wuta ta sa ruwan zafi, A haka tayi tsaye tanata kuka a gurin har dare ya farayi, surutun Ma'u ta fara ji sama sama a kofar gidan, nan hankalinta ya fara kwanciya, tasan zata samu ko dan abinci ne taci, sallamaa dai Amarya, hannu tasa ta karbi Boddo dake kuka jikinta jike da fitsari, saboda duhun dake tsakar gidan Ma'u bata lura da yanayin tafiyar Atika ba, daki ta shiga ta yayo yayi ta fito ta dauko dutsen kyasta wuta, kyasta shi tayi cikin yayi nan take haske ya bayyana, bata kara bi takan Atika ba ta wuce daki ta dauko ragowar Tuwon da sukaci da rana, saka iya wanda zai ishesu tayi a tukunyar kasa dan ta dumama, ta zubawa Atika mai sanyin a cikin roba ta tura mata, dakyar ta iya dukawa ta mika mata Boddo, sannan ta dauki tuwon, can baya taje ta zauna dakyar tanajin radadin a can kasanta, tsabar yunwar da takeji yasa bataji sanyin abincin ba ta dinga turashi tana zubar da hawaye, muryar Bingel taji akanta tana share mata hawaye tana bata hakuri, wani sabon kukan ne ya kufce mata hade da rungume Bingel wacce itama kukan takeyi.... 11:34pm●●●● Tsugune take tana wanke geron safe tana gyangyadawa hade da shashshekar kuka, sanyin dake shigarta ta sama da kasa shi ya haifar mata da rawar sanyi sosai, jingina tayi jikin kwaryar ta fara kiran sunan Allah a cikin ranta, nutsuwace ta fara ratsata kaďan kaďan har bacci ya soma ďaukarta, ko mintina biyar batayi ba taji muryar Baffa da ya lallabo ya fito yazo inda take, murya kasa kasa yace "Atika, Atika, tashi muje ki kwanta, Kuka sosai ta fashe mishi dashi cikin yarenta na larabci wanda bayaji tace "Dan Allah ka kaini gurin "ummi Aisha", sunan Aishan da yaji ta kira ne yasa shi cewa "Mai babban suna? Gyada kanta tayi jikinta na rawar sanyi, Yace "to me mai babban suna tayi? Ganin da tayi bai gane abun da tace bane yasa ta mike ta fara tafiya dakyar, wani tausayinta ne ya ratsashi ya tuna abin da ya mata dazu kuma bai samu damar tsayawa ya taimaka mata ba saboda kar ma'u ta dawo, takawa yayi da dan sauri ya isa gareta ya kamo hannunta ya zaunar da akan dakali, dan ihu ta saki ta mike tsaye saboda zafi, "yi hakuri ya fadi jiki a sanyaye tsoro duk ya cikashi, yaayi ya debo da yawa ya iza wuta ya daura ruwa, saida ya tabbatar ruwan yayi zafi sannan ya juye mata cikin kwarya yayi mata nuni da ruwan, da sauri ta matso kusa da ruwan bata damu da tsayuwar da yayi a gurin ba, ta cire kaya ta tsugunna ta fara tsarki tana kuka sosai saboda azaba, saida ta tabbatar daga zafi ta fara jin dadi sannan ta watsa sauran ruwan a jikinta, kayanta ta dauka tasa ta wuce dakin da take kwana ta runtse idonta ko baccin da ta fara zaizo ya dauketa, saidai fa bacci yace ki nemani inda kika ajiye ni, mikewa tayi tana adduo'i tana rokon Allah abin da yafi zama mata alkairi koda kuwa ace mutuwa ce, ta tabbatar da yanzu bata da ragowar gata daga Allah sai Hardejo, shi kuma Hardejo sam bashi da masaniyar halin da take ciki, da wannan tunanin ta fara gyangyadi har bacci mai cike da mafarkai yayi gaba da ita..... Watanni uku sun shude, watanni masu cike da tsananin wuya ga Atika, duk wani aikin gidan na karfi ita take yinsu, kama da wanki, surfe, da sauransu, a cikin watannin an samu sauyi na cigaba sosai a kauye, cigaba daga bangarori da dama, sannan ci baya ga Baffa, kullum kwanan duniya sai shanayen da aka bar musu da wadanda ya siyo da kudinshi sun kasa, saidai ya yanka ya kaisu kauyuka domin a saya, a haka ne ya zamto mahaucin karfi da yaji, bai kara marmarin bi takan Atika ba saboda kar tsautsayi yasa har ma'u ta gane, a cikin wannan halin Ma'u ta dage da sana'oi kala domin ta yi hidimar gidanta da ya'yanta, Atika itace karfin sana'oin domin ita ke yinsu amma ko dankwali Ma'u bata taba tunanin siyan mata ba... Yammacin ranar asabar Ma'u na tsugune tana gasa naman gafiya, nan take kamshi mai hade da kauri ya gaurayen gidan, sannu a hankalin kamshin ke ziyartar hancin Atika dake tsugune tana goga gero a jikin dutse, tun tana daure jin kamshin har ya gagareta tayi saurin mikewa baki cike da amai ta dinga kwaro shi, saida ta amayar da komai na cikinta, ta zaune a gurin tana maida numfashi bayan ta dauraye bakinta, Bingel wacce ta zamo kawar hirarta ita ta matso da sauri tana shafa mata kai, ita kuwa ma'u sam bata kawo komai a ranta ba sai ma cigaba da gashi da tayi, duk tunaninta shawara ce ke damunta, tana gama gashin ta kalli Atika shekeke tayi mata nuni da geron, a hankali ta mike ta koma bakin aikinta, tana kallon ma'u ta kasafta naman ita da ya'yanta, dama naman bai bata sha'awa ba samm, aikinta ta cigaba dayi, in kaga yadda take aikin sai ka dauka baiwa ce..., Jin nama tayi a saitin bakinta, da sauri ta dago taga Bingel a tsaye tana mata murmushi, a kasonta ta cire mata da yawa dan taga ba'a bata ba, wani aman taji ya kara tahowa gadan gadan, wannan karan a gurin ta sakeshi, wata irin Ashar Ma'u ta saki tace "A kan gari na kikayi min amai, bata karasa maganar ba taji ta kara kwararo Aman har akan dutsen, "A'a wannan ba lafiya ba, Ma'u ta fadi tana matsowa kusa da ita, hannunta ta finciko ta duba, jiki na kyarma ta daga mata riga, ganin da tayi nonuwanta sun ciko kansu yayi bakikkirin ya sata sakin wata yar kara hade kiran sunan Allah, ciki gareki? Ciki gareki Atika? Babu mayafi haka ta fita ta nufi gidan Haire dan taga Atikar zata bata mata lokaci, a tsakar gida ta samu Haire da maryam yar Hardejo tana koya musu karatu, "Haireeeeee ta fadi da karfin gaske, a kidime Haire tace "lafiya Ma'u? Kuka ne ya kufce mata tace "Haire Atika ciki gareta, mikewa Haire tayi tace "ci me? Ciki Ma'u ta fadi cikin rawar murya, Gaba daya idonsu ya rufe sun manta akwai Maryam da yar Hairen kawar maryam a gurin, "anya ma'u ciki ne, ba kince Baffa bai taba kusantarta ba, to waye ya mata cikin? Ma'u tace "nima tunanin da nakeyi kenan, mayafi Haire ta dauko tace "muje gidan, Suna fita maryam tace ma Laraba "bari inje gida bayan la'asar zan dawo, Laraba tace "to sai kin dawo, kinga zanyi aiki da na raka ki, "babu komai maryam tace sannan ta kwashe yan littafanta tayi gida... Da gaske kike Maryama? Wallahi ummi (sunan da Atika ta radawa mai babban suna kenan) dagaske nake, Aisha batayi kasa a gwiwa ba tasa yaro yayi mata magana da Hardejo, kwashe komai tayi ta fada mishi sannan tace "Dama Laminjo tasha fada min halin da Atika take ciki a gidan, bana kamawa ne saboda kowa yasan Laminjo yawancin maganganunta karya ne, rai a bace Hardejo yace "ki shirya zansa Bala ya rakaki sai kuje ku taho min da ita, tunda Muhammadu ya fara tafiye tafiyen nan nasan lallai rayuwar Atika na cikin garari.. cikin gida Aisha ta shiga ta shirya tsaff da mawafi, Bala shaho wanda a yanzu ya zamto shakikin gidan Malam Harďejo shi yayi mata rakiya har gidan.. A tsakiya suka sata suna ta jero mata tambayoyi irin na kurame, da haushi ya ishi ma'u ta tashi ta dauko sandar shaďi ta fara narkarta dashi, bata taba raba dayan biyu Baffa ne yayi cikin nan, dukanta takeyi sosai Haire na tarewa tana faďin karki kashe musu 'ya Ma'u, ki bi komai a hankali, wani irin hankali zan bishi shi amm, ni Baffa zai ciwa amana? Ni zai ha'inta? kuka sosai takeyi tana dada narkar baiwar Allah da sanda, kwace sandar Haire tayi tace "shiyasa nace baki da wayau Ma'u, in ba rashin dabara ba kya fara jibgarta, maimakon ki bari mu yi komai cikin hikima, ga magunguna nan da zaisa cikin ya fita cikin makwarara.... Saidai kiga bin makwarara a gidanki da yardar Allah Aisha ta fadi tana karasa shigowa cikin gidan rai a baceee..... Mrs Tijjani Shattima..... [03/03 9:47 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣6⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* *Rabon Ajali* Da gudu Bingel ta rungume Aisha tana kuka tana fada mata irin dukan da mamanta tayi ma Atika, share mata hawaye tayi tace "Allah ya turo mai cetonta Zainabu, in da take tsugune suka karaso Aisha ta dagata tace "muje can gida, in shaa Allahu daga yau kin bar zaman wahala, cikin nan kuma sai kin haifeshi koda kuwa dukkan kauyen nan zasu taru akanki, kuma dole ya amsa sunan Muhammadu a matsayin uba, wani irin kululun bakin ciki ne ya ziyarci Ma'u, bata dubi girma da darajar da Aisha kedashi a kauyen ba ta fara zaginta, ta inda take shiga bata nan take fita ba, Aisha dai bata waigo ta kalleta ba tace "sai dai ki mutu da bakin ciki dan cikin nan babu abin da zai hanashi zuwa duniya, wani sabon faifan zagin ta bude idanuwanta sukayi jajur, asalinta na arniyar ukari marar imani ya bayyana a jikinta, da sauri Haire ta toshe mata baki tace "mai babban suna kike zagi Ma'u?, kinason Allahn Hardejo yayi fushi da dukka yan kauyen nan ne?, idan hankali ya gushe nemo shi akeyi, cike da masifa ta ture Haire tace "wallee sai kunga abinda zai sameku, dukkanku, badai ni *NANKWAT MANASIR* kukayi wa haka ba,(sunanta kenan kafin haduwarsu da Baffa) walle duk sai kun gani, ta finciko hannun Bingel hade da daukar Boddo ta fice a gidan, hakuri Haire ta bita tana bata, sam bata saurareta ba ta wuce da yaran, Bingel na kuka taki ko kallonta bare ta kula da abinda take so, Alkhairi!!! in shaa Allah Aisha ta fadi tana kallon ma'u da tayi nisa da gidan, gida suka wuce suma Haire na biye dasu tana fadin "Dan Allahn Hardejo kiyi hakuri mai babban suna, walle ko taba jikinta banyi baa, katseta Aisha tayi tace "Babu komai Haire, kowa yayi nagari dan kansa... Suna isa yaran gidan suka rugo suna ihu hade rungumeta, dama sunyi kewarta matuka dan ma'u bata yarda suzo gidansu, Matan Hardejo ma suka fito suna musu barka da zuwa hade da jajantawa Atika, Ďaki Aisha ta wuce da ita, tasa maryam ta iza wuta tasa ruwan wanka, kafin ruwan yayi zafi ta dama mata fura da nono, sannan tasa aka karbo mata kwadon zogale a gurin Laure matar Hardejo ta biyu, zogalen kadai ta iya ci, tasha ruwa, ta dan kwanta a inda take zaune, bacci ne mai karfi da dadi yayi gaba da ita, gyara mata kwanciya Aisha tayi cike da tausayawa, kyakykyawar fuskarta ta kalla ta sa hannu ta share mata hawayen dake gangarowa ta gefen idonta, a zuciyarta tana Hailala ga ubangijin da yake da ikon mayar da mai gata bawa, Allah ka ďaura mana jarabawa mai sauki wacce zamu iya daukarta, da waďannan adduoin mai babban suna ta tashi ta fita tsakar gidan dan samowa Atika naman da zata gasa mata, kicibus tayi da yaro ya shigo da zabuwa an yanka ta, dariya tayi tace "ko baka fada ba nasan Bala ne ya aiko ka, gyada kai yaron yayi ya fita da gudu, albarka ta shiga shi mishi saboda kullum sai ya kawo musu halastacciyar dabba gidan sunci, maryam ta mikawa zabon tace "maza tayi amfani da ruwan zafin ta gyara shi, amsa tayi cikin ladabi ta gyara shi hade da bankareshi yadda zaiyi kyaun gashi, kafin Mamanta ta fito har ta fara gasashi cike da kwarewa, saida ta gama tass sannan ta sa a karamin bangaji ta wuce ta kaima Aisha.... Saboda dadewa bata huta ba, da kuma karancin bacci da take samu yasata ta kai har bayan isha'i bata tashi ba, babu wanda ya tasheta saboda yanayin da take ciki, saida tayi bacci mai isarta sannan ta tashi tana mika hade da salati, ganin duhun dakin ya sanyata mikewa zubur ta fara lulube, dan hasken dake tsakar gidan ta hango ta tsagin tagar dakin, ajiyar zuciya tayi ta dauki mayafinta ta rufe kanta sannan ta fito waje, kamar jiranta yaran sukeyi ta fito suka kewaya ta suna kallonta, magana Aisha tayi mata tace "kije kiyi alwala kiyi salloli sai kici abinci kiyi wanka.. Tana idar da sallah suka kewaye ta da abinci da fura da kuma gasashshen zabo, tuwon taci sosai tana hamdalla a zuciyarta, rabon ta da taci irinshi tunda kaddara ta kaita auren Baffa, saida taci tayi katt sannan ta kora da ruwa, naman ne kadai bata ci ba saboda sam batason jin kamshin gashi, Ba karamin horata Ma'u tayi ba da gashinta na kullum, wanka tayi da ruwan zafi mai dadi sannan ta dawo inda suke ta zauna, rokon Allah ta shiga yi da ya barta a cikin su har Allah ya kawo sanadiyyar da zai hadata da Abbunta da kaninta Ateek, kallon irin zaman da sukeyi takeyi mai cike da tsafta da kaunar juna, yaran gidan duk suna kaunar junansu haka basa yi ma wacce ba uwarsu ba rashin kunya, matan kuwa kullum cikin hira suke da karatun al kur'ani, wani lokacin kuma mai babban suna ta tarasu dukkansu harda makota ta basu tarihin Annabawan Allah da iyalensu, da irin gwagwarmayar da suka sha, shiyasa a ko da yaushe gidan yake a cike da mata da maza, koda yaushe gidan baya rabo da abin ci da kuma sha saboda yawan sadaukarwar da sukeyi..... Shigowa gidan yayi fuska dauke da murmushi ya kalli ahalin gidanshi ya kara samun nutsuwa a cikin ranshi, a kullum kara godewa Allah yakeyi da ya hada shi da Aisha da kuma sauran matanshi masu fahimta da lura, Zama yayi a tsakiyarsu ya kalli Atika yace "Barka da zuwa cikin Ahali na, nayi matukar farin cikin jin zamu samu jininki a cikin zuri'ata, ina miki fatan Allah ya sauke ki lafiya, daga nan sai mu tafi can kasarku da dan da zaki haifa.. Ameen matan shi suka ce cike da farin cikin addu'ar, kallon Maryam yayi yace "Malama Maryama ku koma can gefe ke da kannenki zamuyi magana da iyayenki, mikewa sukayi cike da ladabi suka koma wata tabarmar a kusurwar dakin Saude matar Hardejo ta uku, Aisha ya kalla yace "mun kusa samun siriki, cike da farin ciki laure tace " Alhamdulillah, wanene ke son Maryama? Bala, Bala ne ke sonta, dazu ya turo mahaifinshi, na kuma ce na bashi, cike da farin ciki dukka matan suka ce mashaa Allahu, Allah yasa alkhairi, Allah ya basu zuri'a dayyaba, Ameen Hardejo ya fadi ya kalli Aisha da taki amsawa saidai murmushi kawai takeyi, ita a dole kunyar diyar fari, nan fa suka shiga tsokanarta cike da nishadi kamar ba kishiyoyi ba..... *BAYAN WATA BIYAR* ●●●●●● *Mummunar Kaddara* Har lokacin Baffa bai waiwayi gida ba, yana can yana neman kudi saboda ya tsira mutuncinsa da na iyalinsa, kullum cikin tunaninsu yake, ciki harda Atika da sam bashi da masaniyar tana dauke da cikinshi, cikin kudirar ubangiji neman da yakeyi Allah na sa mishi albarka a cikinsa dan har ya samu ya siya dan gida mai daki uku ginin siminti na jaka biyar da rabi a cikin jalingo, a wannan lokacin ne ya yi niyyar zuwa gida dan ya tattaro iyalinshi ya fara sabon zama dasu mai cike da jin dadi.. A cikin watanin da suka shude aka daura auren Maryam Da Bala Shaho, murna a gurin shaho ba'a cewa komai saboda yadda ya dauki malam da ahalinsa, bauta ce kadai bazai iya masa ba, domin kuwa ya taimaka mishi gurin samun rayuwa mai inganci da tsafta... Atika ma tayi bul bul, cikinta yayi girma sosai har yayi mata nauyi, gaf take da shiga lokacin haihuwarta, kula ta musamman take samu a gurin Hardejo da matanshi, ba irin kayan da basu sak'a ma jaririn ba tun kafin Zuwanshi duniya, a wannan lokacin Atika ta dan fara jin fillanci kadan kadan, dan in aka mata magana zata ji amma mayarwa ke mata wahala.... Ita kuwa Ma'u tun da ta tafi can garinsu ukari bata dawo ba sai dai aiken mugun abu da take ta yo wa Atika da cikin jikinta, haka duk juma'a sai ta bi motar katako taje garin dan taga ko mijinta abin kaunar ta ya dawo sannan ta shiga gurin Haire ta bata sakon magungunan da take kaiwa Atika dan cikin ya zube, bata san Haire watsi takeyi da maganin ba, domin ita mace ce mai tsananin tsoro, tunda ta amshi musulunci ta daina duk wani aikin sabon Allah, dama wani lokaci ma'u ke zugata suyi tare, yanzu ko da ba ta nan, kullum tana gidan Hardejo daukar karatu... Yau ma kamar kowace jumma'a ta gama shirye shiryenta na mugun kullinta, ta dauko su Bingel ta shiryasu dan yau in ta tafi bazata dawo ba, tasan da tana garin babu abin da zai hana ta kashe dan dake cikin Atika, yanzu kuwa ta dauki alwashin kashe har Atikan saboda in ta barta to fa Hardejo sai yasan yadda yayi ya sake sata cikin rayuwarsu, gara kawai ta kashesu gaba daya.. A daidai kwanar da zata sadasu da hanyar kauyen suka hango cincirindon yan ta'adda, babu kaya a jikinsu sai wukake rataye a kafadunsu da kugunsu, tsayar da motar sukayi suna ta wasa wuka a kasa, fitsari Bingel ta saki ta fara ihu tana kuka, sakko dasu mutanen sukayi suna mazurai, cikin wani irin yare suke tambayarsu ko su musulmai ne, drivern da yake yana yawon safara, Kuma yasan musulmai sun fara yawa yace "eh shi musulmi ne, nan take suka farďeshi sukayi wurgi da gawar, Ma'u jiki na rawa tace "Dama kai musulmi ne ka dauko mu? Ta fara tambayar karen motar, girgiza kai karen motar yayi yace ni cikakken mabiyin Addinin sarki *HAWAIZU NA UKARI* ne, Dariyar keta mutanen sukayi suka ce "ina za ku? Ma'u da ta gama samun mafita tace "Gembu, kauyen da Malam Hardejo ya cika shi da musulmai, zamuje ne domin yi musu magana akan abin da sukeyi mara kyau, sun yarda bautar iyaye da kakanni sun dauki wani addini da Hardejo ya kawo, cike da farin cikin samun Nama ogan yace "dama mun dade muna son kai farmaki kauyen, mai girma *SADUN* ya dade yana bamu labari akan malamin da yayi wa kauyen kawanya da musulmai, ku shiga mota ku jagorance mu dan mu aikata abin kirkin da za'a dade ana tunamu dashi har duniya ta dade..... A kofar Gidan jauro Ma'u ta sauka da ya'yanta, tayi musu nuni da gidan Hardejo, tace musu zata dubo dayan malamin ko yana nan zata zo ta samesu, wucewa sukayi; ita ma ta kama ya'yanta ta ruga da gudu ta shige gidanta ta turo, babban fatanta shine su fara yin layyarsu da Atika, can kuryar daki ta shige ta kwantar da ya'yanta hade da tsoratar dasu dan kar su tashi suce zasu fita, saida ta tabbatar bacci ya daukesu sannan ta fito ta tsaya a tsakar gida tana kasa kunne, ita dai in bukatarta zata biya Kowa ma ya mutu, yanda taci alwashi a kauyensu na cewar Baffa bai isa ya mata kishiya ba, kuma kawai sai gashi banda kishiyar har 'yan uba gare ya'yanta, inaa sam in ta bari hakan ya faru to bata cika jinin *MANASIR* ba.... Kamar yadda suka saba taruwa a kofar gidan ranar jumma'a maza da mata yau ma hakan ne ta kasance, Kamar daga sama sukaji tsayuwar motar katako a kansu, babu wanda yayi yunkurin katse sallar saboda a iya saninsu kauyen nasu lafiya lau yake domin musulmai sun danyi rinjaye a garin yanzu, tun ba ma komawar shaho cikin musulunci tsundum ba, a sujjadar karshe suke sukaji an fara kai musu farmaki, basu sallame ba har lokacin saida suka gama zaman tahiyar karshe, suna sallemawa kowa ya fara neman hanyar tsira, kewaye su yan ta'addan sukayi suka dinga sarar jikinsu, "Allahu Akbar Malam Hardejo ya fadi nan take gurin ya dauka, a nan fa Shaho da mutanenshi suka tuno da dabanci suka tube kaya suna fadin Allahu Akbaar, suka nufi yan daban, Rashin makamai ne ya cucesu shiyasa duk fadan da sukeyi aka sassari su shaho, cike da karfi Shaho yayi kokarin fusge katuwar wukar jikin ogan, nan fa yasa ihu ya fara sararsu iya karfinshi, a take samarin garin suka shiga gidajen kusa suka dauko makamai, ciki harda Barde mahaifin shaho, shi kuwa Hardejo sallah ya koma ya cigaba dayi yana rokon Allah ya kareshi da dukkan jama'ar musulmi, (idan Ajali yazo) babu makawa sai an tafi, babu addu'ar dake dauke ajali a jikin mutum, kamar hadin baki arnan kauyen suma suka fito da makamansu, "in ka san farkon rigima to fa baka san karshenta ba, Rigimar da Ma'u ta hada saboda san zuciyarta ya haifar mutuwar rayuka da dama, Ma'u bala'i ce a cikin alummar musulmi.... Shaho ya jigata iya jigata, shi kadai ne mai karfin dake yakarsu, sauran arnan garin abin da yasa sukaci galaba akansu saboda daga cikin gidan suka fara gurin matan, saida suka karkashe matansu da ya'yansu sannan suka fito suka hada hannu akan mazan, dama ba karamar tsana sukayi wa Hardejo ba, wani a cikinsu mai siyar da barasa yayi kan Hardejo da gatari saboda shi tuni yake hakonshi dan hani da yayi da shanta ga daukacin musulman kauyen yasa shi ya daina ciniki, Shaho na ganin haka yayi saurin tareshi hade da kai mishi wuka kirjinshi, ta baya wani ya lallabo ya sari gefen kafadun Hardejo, sannan ya sake luma mishi wukar, salatin da ya fara yi ne ya dawo da hankalin shaho kanshi, tuni jikinshi ya mutu ya saki wukar hannunshi ya durkushe a gurin yana rusa kuka, Ya Allah ga hardejonka nan, Ya Allah me yasa baka turo mana da kariya ba a lokacin da muke da bukata, Ni kadai bazan iya ba ya Allah, gawarwakin mutanen ya kalla harda na babanshi ya sake rusa kuka, cikin sanďa wani sumameshi ya luma mishi wuk'a a bayanshi saitin da zuciya take, nan take ruwa mai karfi ya kece a cikin kauyen, wani irin ihun murna arnan suka fara yi dan duk sunbi musulman sun musu kisan gilla, harda matansu da ya'yansu, cikin murna suka nufi cikin gidan suka fara kwaso shanaye suna bi takan gawarwakin.... Ma'u kuwa tun tana jiyo ihu har ta daina ji, anan ne jikinta ya bata an gama komai,, cike da murna ta fito gida da niyyar zuwa gidan Haire, a kofar gidan taci karo da Baffa da kaya niki niki a hannu, karbar kayan tayi ta fara murna suka shiga cikin gidan, a tsakar gida ya baje kayan yana bata labarin irin abubuwan alkhairin da ya samo, "Ta ina ka shigo garin nan? Ta jefo mishi tambayar tana kallonshi hade jiran amsa, " Ta bayan gari, saboda bana sann kowa ya rigani fada muku isowa ta, yanzu wanka zanyi in wuce gidan Malam, naga garin ma ba kowa nasan duk suna can maza da mata ana sallar juma'a da wa'azin Hardejo, cike da kissa tace "nima ko sai muje dan bacci ne ya daukeni ban samu zuwa ba, dube dube taga ya fara yi tasan tabbas Atika yake nema, murmushi tayi tace "Amarya tana can gidan Hardejo, ka tafi kabar amarya da nauyinka, nace su Baffa ba'a cika min alkawari ba, cikin rashin fahimta yace "me kike nufi? murmushi tayi a ranta na mugunta ne amma a fili ta nuna na soyayya ne tace "matarka dai ciki gareta, tama kusa haihuwa, a daburce yace "ma'u ban karya miki alk---- katseshi tayi da sauri tace "babu komai ai matarka ce, ni fatana ma mu samu dan namiji tunda naga dukkanku baku da namiji, kaga sai mu samu magaji, murmushin farin ciki Baffa yayi ya mike yace "dauko mayafi mu tafi, zunde tayi mishi ta baya sannan tace " har ka fara zumudi, nima bakaga yadda na kosa ba, komai a gidan nan bana barinta tayi, ganin cikin nema yasa hankalina ya kwanta dan ina tunanin namiji zata haifa mana, rungumeta Baffa yayi cikin farin ciki yace "Ma'u shiyasa nake kara kaunarki, tun farkon haduwar mu kike min halacci har kawo yanzu, nagode nagode, gwalo tayi ma bayanshi tace "Ai mun zama Daya Baffa.... Tun a bakin gidan jauro suke karo da gawa har suka isa kwanar gidan Hardejo, wani irin ihu Baffa ya saka da yaga Hardejo kwance cikin jini ruwan da akayi ya dama gurin, girgizashi ya fara yi ya dinga rusar ihu yana fadin waye ya aikata haka a gareka, waye ni, wayyo ni Allahn Hardejo, Dafa shi wani dattijo yayi a cikin wadanda suka gudu yace "Tashi Muhammadu, yanzu ba lokacin wannan bane muyi gaggawar haka rami a cikin gidan hardejo mu tattarasu duka musasu a ciki domin kuwa yanzu makasan sun tafi hada walimar murna kafin su dawo su mamaye gidajen, kuma kaima muna gamawa ina umartarka da ka gudu da kai da iyalinka, mikewa Baffa yayi a tsorace yana kuka suka shige gidan su biyar da wasu samari, a cikin gidan ma ya daburce ya dinga kuka yana kiraye kirayen suna, ita kuwa Ma'u rashin ganin Atika cikin gawar wakin ne ya fi daga mata hankali, kar dai ta samu ta tsere, dube dube ta fara yi har ta kai ga bayin gefen dakin saudatu, Atika ta gani tana kuka tana nishin nakuda, da sauri ta tufe bayin ta koma gurin su Baffa, duk wanda a cikinsu taga zaiyi gurin sai tayi maza ta hanashi, hak'a rami sukayi mai zurfin gaske da tsaho, suka fara dibo gawarwakin suna turawa a ciki, saida suka gama tsaff ta Hardejo ta zama ta karshen sawa, fuskarnan tashi dauke da murmushi, wani kukan Baffa ya saki yana zuba kasa a kanshi yana rusa kuka, saida suka gama komai sannan hankalinshi ya dawo kan Atika da bai ganta ba, Ma'u in dai ba idona bane yake min gizo banga Atika ba,, kafin Ma'u ta bashi amsa sukaji kukan jariri da karfin gaske, runtse ido Ma'u tayi tace shikenan yazo duniyar, da sauri Baffa yabi ta inda yake jin kukan, kofar bayin ya tura da karfi, a durkushe ya sameta tana dada dafe cikin alamun akwai wani a ciki, daukar jinjirar yayi sannan ya taimaketa ta fito suka wuce dakin Aisha, bin su Ma'u tayi tace bari in taimaka mata, Kamar zautacciya ta dinga maimata yan biyu kyautar Allahn Hardejo, tsaye yayi akansu ya rufe ma jinjirar hannunshi jiki da zanin mai babban suna, saida ta kara awa daya sannan ta haifo Danta kato namiji, cike da yake Ma'u tace "tafi ka nemo abin da zamu yanke cibi, wani abu mai kaifi Atika ta sanya a hannun Ma'u, harararta tayi ta yanke cibiyar, kallon jinjirar hannunshi tayi tace "dame aka daure cibiyar, zanin jikinta ne ta yaga ta daure dashi, kallon ta ma'u tayi a zuciyarta tace duk a ina ta koyo wadannan abubuwan, wani tsumman ta kuma yaga ta katsewa ma'u tunanin da takeyi, amsa tayi ta daureshi sama sama, ta kuma dukunkuneshi ta hana Baffa ya daukeshi, saboda rashin imani Ma'u na ganin jini na ambaliyar fitowa daga jikin yaron tayi banza da alamarin, kuka sosai yaron keyi amma saboda kawaici Baffa yaki yunkurin karbarshi, a ganinshi ma'u ma uwa ce a gareshi, kuka Atika ta fara yi ta yafito Baffa da hannunta, tsugunawa yayi a gefenta shima cikin kuka yace "bana gane abinda kike cewa, cikin yaren fulani wanda ta fara fahimta kadan kadan tace " *SUWAIBA* Shine sunanta,, sunan ummuna,,, shi kuma *SAIFULLAH* in har ya kasance cikin rayayyu, Ka kularmin dasu, Amanarka ne su, Dan Allah ka Nemi *Ateek* da Abbuna dan Allah.. kuka Baffa ya cigaba da yi sosai yana fadin bazaki mutu ba, ki yafemin dan Allah, share mishi hawaye tayi tace "Inda zan tafi ya fiye min nan, son samu ma in tafi da 'yarana, Allah yayi bazan rayu dasu ba, Muryar samarin sukaji a waje suna fadin ku fito mu tafi Muhammadu gasu nan dawowa, da sauri ya mikawa ma'u jaririyar ya dauki Atika a kafadunshi suka bar gidan da sauri... Tun a hanya ma'u ta gane namijin ya cika, nan fa hankalinta ya kwanta sosai, suna shiga gidan yayi saurin shimfidar da Atika ya dauko ruwa yana shafa mata, salati ta farayi idonta ya fara kafewa, ta kara cigaba da kiran sunan Allah, ga jini har lokacin zuba yakeyi kamar famfo, cikin tashin hankali yace ma Ma'u ta taimaka ta kawo maganin da take sha idan ta haihu, kwantar da yaran tayi taje ta dauko MANDA mai tsinka jini ta jikata da yawa ta kawo mata, dago kanta tayi tasa a bakinta ta dure mata shi tasss, wani jinin ne ya kuma tsinkewa shaaaaaa, nan da nan ganin Atika ya dauke, hannuwanta suka saki gaba daya, babu abin da kake iya jiyowa sai sautin kukan jinjirar da maganar Atika, *SUWAIBA* Sunan da take ta maimaitawa kenan hade da kalmar shahada..... Mrs Tijjani Shattima..... [04/03 11:57 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣7⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* *KADDARA* _Ba wanda ke shigowa cikin rayuwarmu ba tare da wani dalili ba, tun daga ranar da aka haifemu har izuwa ranar mutuwar mu, da kowa muka hadu a wannan rayuwar, akwai wani zare da ya hadamu wanda bama gani,shi wannan zare da bama gani shi ake kira da *KADDARA*_ A gaban kabarin da ya binne Atika da Saif ya tsuguna yana kuka kamar ranshi zai fita, Bingel ce zaune a gabanshi tana share mishi hawaye itama tana tayashi kukan, "Baffa kayi hakuri, kaga ka rufeta tana bacci, ta huta da wahala da duka, sannan ga yarinya ta haifa mana mai kyau sosai, ka daina kuka ka barta ta huta, "Duka? Wanene yake dukanta Zainabu, kafin Bingel tayi magana Ma'u ta fito tace "shirmen ta ne, wai dan ina mata tausa in kafarta ta kumbura shine take dauka dukanta nakeyi, kallon Ma'u yayi yana son karyata maganarta, ya gasgata ta yarshi, nan take wata zuciyar ta kwabe shi da cewar Ma'u ba muguwa bace.. Saida ta gama tattaro kayanta gaba daya da na ya'yanta, daga lungun gadonta ta dauko akushin dake dauke da sarkar Atika, majina ta fara ja ta fito gurin Baffa cikin kukan munafurci tace "Allah sarki, ga sarkar Atika, yanzu sai na ajiye wa yarta, dan nasan yanzu mallakinta ce, share hawayenshi yayi yace "nagode Ma'u, nasan *Suwaiba* baza tayi maraicin uwa ba, nagode sosai ya karashe cikin kuka hade da rungume jinjirar...... *MARAICI* Tafi awa daya a zaune a kan pou, ga zafin rana, ga kuda sun baibayeta,, tun tana kuka ana jinta har ya daina fita, Ma'u na can zaune a daki tana shan rake ita da Boddo da a lokacin take shekara biyu ciff, dama pou din da kanta ta hau shi, dan tasan irin azabar da take sha a karancin shekarunta in tayi kashin a kasa.. Kamar an tsikareta ta mike a islamiyya cikin kawayenta tace zata je gida tasha ruwa, Nafisa makociyarsu ce tace jirani in karasa rubutu a allon nan sai mu tafi, zama tayi ta jirata har ta gama sannan suka wuce, a kofar gida suka rabu kowa ya shige gidansu, tana shiga tayi karo da suwaiba fuska kaca kaca da zufa da hawaye, gyangyadawa takeyi, in tayi kamar zata fadi sai ta bude idonta ta cigaba da kukan, cikin kunan rai Bingel ta isa gurinta ta dagata sukayi gurin rijiya, ta janyo ruwa ta wanke mata dukka jikinta, tana yi tana kunkuni dan kar Ma'u taji, tana gama wanke mata jiki ta goyata ta shiga daki ta samu Ma'u na kankarewa Boddo kai tana bacci, Haba Goggo (sunan da yaran makota ke kiranta dashi) yanzu kina ganin yarinyar nan tafi awa zaune a kan pou baki wanke mata ba, wallahi kiji tsoron Allah, kullum a islamiyya ana fada mana muhimmancin rikon maraya, nawa Suwaiba take da ta cancanci wannan azabar, bakya t---- katseta tayi ta hanyar bige bakinta, sai kizo ki dukeni, nace kizo ki dukeni uwata, sauke ta a bayanki dan ubanki, fita Bingel tayi ta dauki hijab dinta ta koma islamiyya da suwaiba a bayanta tana share hawaye, ta rasa irin wannan tsanar da take nunawa Suwaiba in suna kebe su hudu, amma a gaban mutane da Baffansu bata da yar lele kamar suwaiba.. A kullum nunawa Baffa takeyi ita fa Suwaiba ta fiye mata ya'yanta, kuma koda wasa bata san kowa yasan ba ita ta haifeta ba, shiyasa Baffa ke tafiya neman kudinshi a duk fadin nigeria hankali kwance, ko ya dawo gidan baya samun damar daukarta saboda yadda Goggo ke makale ta a bayanta, saidai daddare in suna kwance ya shafa mata kanta yayi yar kwallar tausayin maraicinta da tunanin uwarta.... ●●●●●●●● Shekaru masu yawa sun shude cikin dadi ga masu sa'ar samun dadin, sannan cikin radadin azaba ga marasa galihun rayuwa, cikin wadannan shekarun Baffa ya samu cigaba sosai a rayuwarshi, dan sana'arshi ta maidashi Kaduna inda yake tsara atamfofi a kamfanin yar masaka, a lokacin yakan kasance da iyalinshi duk dare, a nan ne ya dan fara dan fahimtar zaman da Ma'u ke yi da suwaiba, a ko yaushe in ya fara wannan tunanin sai ya kauda shi saboda baisan sanya wasi wasi a zamanshi da Ma'u, in ya ga suwaiba tayi shuru sai yayita kallonta ya rasa bakin da zai tambayeta, wani lokaci in Ma'u ta lura da hakan sai ta sameshi ta fashe mishi da kuka tace "yarinyar nan bansan meyasa take yawon zama shuru ba, ni kaina inason a koda yaushe ta sake kamar yadda Halima take yi, na rasa me ke damunta, Baffa yakan yi murmushi yace "yanayinta kenan, haka Allah yayi ta shuru shuru, mu bamu isa mu canzata ba... *HADUWAR ALKHAIRI* _Muna Haduwa da mutane ta hanyoyi daban daban, to kenan ta yaya muke haduwa da waďanda zamu gudanar da rayuwarmu tare dasu ma'ana *MASOYA*_ "Leemah Muhammad", meye position dinki?, harararsu tayi tace "meye naku a ciki, kowa yaji da kanshi, dariya suka kece mata dashi hade da cewa bench warmer, daga ke babu wani, Suwaiba dake tahowa da Akwatinsu na gwangwaro tace "Haba Amina Sa'ad, babu kyau fa, ilimi Allah ne ke bada shi kuma yayi hani da gori akanshi, basu fasa dariyar ba suka ce barmu mu ci ma yar rainin wayan nan mutunci, ita a ganinta tafi kowa, sai anzo jarabawa ido ya raina fata ta fito da ziro me katon kanta, Wasu gungun mata dake bayansu a karkashin bishiya suma suka kece da dariya hade da cewa su Leemah gayu ba brain, sai ki dawo first term da juniors dinki, muko ay sai candy, kukan takaici ta fashe dashi ta ruga bakin gate din makarantar, bin bayanta Suwaiba tayi da kayan niki niki masu masifar nauyi, hakuri ta fara bata tace "karki damu, kisa ma ranki zaki iya next term din, dan an miki repeating ba yana nufin bazaki iya bane, zan tayaki addu--- katseta tayi cikin kuka tace "rike nasihar ki da adduar ki, ba na ja miki kunne akan babu ruwanki dani ba?, wai ma ban hanaki jerawa tare dani ba, ni sa'arki ce da zaki dinga jerawa dani har kiji abinda ake cewa a kaina, wallahi bari muje gida, sai na miki dukan tsiya, yar iska matsiyaciya kawai, Ajiye kayan suwaiba tayi tace "kiyi hakuri dan Allah, wallahi bazan kara ba, kinga in zaki min hukunci kiyi min anan, amma dan Allah karki bari Goggo taji, tsaki taja mata tayi gaba a zuciyarta tace "wallahi bazan sake dawowa makarantar nan ba, tunda karatun ba dole bane... Abokina!! irin wannan kallo haka, ai sai kasa ta fadi, ji yadda ka kafeta da ido, in dai wadancan biyun ne, to sun saba, kullum leemah cikin masifa take ita kuma suwaiba tayi ta tausarta, i think immediate ne, dan uwa daya uba daya suke, dalili kenan da yasa na daina sa musu baki, karka shiga fadan yan uwa, and kasan me ke yawan sasu fada, ita waccen,, ya nuna suwaiba, tana da masifar kokari, ita kuma dayar in kana neman dakiki ajin farko in ka sameta to ka rufe kofa, ja motar muje na dauko takardun, tada motar yayi har lokacin idonshi nakan Suwaiba, yana isowa saitin da take ya kashe motar ya fito, kallonshi abokin wanda ya kasance malamin makarantar yayi yace "Lafiya ina zaka, bai saurare shi ba ya zagaya gurin Suwaiba dake tsaye a gurin kamar an kafeta, tana tunanin irin hukuncin da zasu yanke mata a gida, addua takeyi a zuciyarta na Allah yasa yayarta na gidan, ita kadaice zata iya taimkonta daga ukubar da zasu mata, kamar daga sama ta jiyo sallamarshi, kallonshi tayi ta kauda kai tace "Ameen wa alaikum salam, ina yini, wani sanyi ne yaji ya ratsashi na jin daddadar muryarta, Amsawa yayi yace "lafiya kalau malama Suwaiba, dago kai tayi cike da mamaki tace "laaa sunana, a ina ka san sunana?, daga kanshi sama yayi yace "wahayi akayi min da sunan, kuma aka ce inzo nan in sameki, rike baki tayi ta daga kai sama tace "a can sararin samaniya? Gyada kai yayi yana murmushi yace "kwarai kuwa, ko kina tantama ne, cike da nutsuwa tace "kwarai ba tantama nakeyi ba, yarda ce banyi ba saboda na karanta a littafi, manzanni kadai ake wa wahayi, kuma nasan a cikin duniyar nan da azzalumai sukayi yawa babu tabbacin samun wani annabi, kuma ai annabin Allah shine karshen annabawa, dan Allah in ma gatse kakeyi to ka daina domin ina tsoron wani ya samu zunubi ko yayi shirka domin ni, "Ya ilahi ya fadi a zuciyarshi ya kalli Abokinshi dake cikin mota yace "kaji Kalamai daga bakin fasihiyya ko Abbakar, kallon motar tayi tace "laa uncle Abu ina wuni, fitowa yayi a motar yana dariya yace "lafiya kalau Suwaiba, anyi hutu ana jin dadi za'a koma gida ko, murmushi kawai tayi a zuciyarta tace wani hutu, ita da za'a barta ta kare rayuwarta a makaranta ai da taji dadi, katse mata tunani Abbakar yayi yace "wannan abokina ne, sunanshi *MUKHTAR KYARI* ganin irin masifar da yar uwarki take miki ne yasa shi tsayawa ya baki shawarar ki dage ki dinga ramawa, kyawawan mata da tsiwa aka sansu, ke kuma hakurin naki yayi yawa, kallonshi Mukhtar yayi yace "to sannu koma mota, nagode da ka tayani fada, dariya sosai Abbakar yayi ya wuce cikin mota yana fadin 5mins na baka, kasan we have alot to dzoo, a gaugauce ya tambayeta ko zai iya sauke su a gida daga nan sai yaga gidan nasu, kallon Leemah tayi da ta waigo tana hararar su tace "bari in tambayi yar uwata, ajiye akwatin tayi a kasa yayi saurin daukarsu ya zuba a boot, ya shiga motar yace "abokina kai zaka musu magana su shiga dan dakyar waccan masifaffiyar ta yarda su bimu, magana daya Uncle Abu yayi musu suka shiga motar, a kofar gidansu yayi parking, da sauri Leemah ta bude motar ta shige gida gudu, jiki na rawa Suwaiba ta bude motar tace "ina akwatinan mu? Bude boot din yayi ya fito da akwatinan yace "muje in rakaki, nauyinsu yayi yawa, a'a tayi saurin cewa, hade da mika hannu, Dan Allah ka rufa min asiri, fada za'a min a gida, "let her go kyari, bakasan condition din da take ciki ba, sakin akwatinan yayi tayi saurin dauka ta ruga cikin gidan da gudu, bin ta yayi da ido har ta kure cikin gidan sannan ya shiga motar ya tada suka wuce.... Mrs Tijjani Shattima..... [04/03 12:44 PM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣8⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* Tun daga zauren gidan take jiyo masifar Ma'u hade da kukan Leemah, sharri kala kala tayi mata sannan tace "ta hadu da saurayi tanata shige mishi har ta rokeshi ya kawo su gida, innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai suwaiba ke furtawa a cikin ranta, da sallama ta shigo gidan ta ajiye akwatinnan ta tsuguna har kasa ta gaida Ma'u, matsowa kusa da ita tayi ta daga hannu ta kwada mata mari, Halima sa'arki ce da zaku hadu da kawayenki kuyi ta cin mutuncinta, ke dan uwarki ke kika bawa kanki kokarin, au dan na yarda kun shiga makaranta daya, shine zaki nuna zakewa ki nuna kinfi ta iya komai, bulala Leemah ta miko ma Goggo tace "ga yaren da tafi ganewa nan Goggo, karbar bulalar tayi ta fara zuba mata tana cewa uban waye ya saukeku a kofar gida, yanzu dan rashin kunya kina ganin yayunki basuyi aure ba ke har kina da tsaurin idon tsayawa da saurayi, to wallhi in na kara ji da ganin kin tsaya da saurayi tun yanzu sai na miki illah, banason rashin ido a gurin y'a mace wallahi, bulalar da zata kai mata na karshe ne ya sauka a jikin yaya zainab (Bingel) da ta shigo gidan a lokacin, dago suwaiba tayi tana share mata hawaye itama hawayen take tace "haba Goggo, kowa ba rabonshi yake samu ba, yanzu wannan abun da kikeyi shine Allah zaisa mu samu miji ko me, ki duba kiga yadda na girma na rika a gida babu mashinshini, haka Halima babu wanda ya taba furta mata kalmar so duk ko da irin kyan da muke dashi, a cikin mu Allah ya sanya suwaiba nada farin jinin da duk ta fita sai ta samu mai cewa yana sonta, ai sai mu godewa Allah, wani kukan ne ya kufce mata na tuno saurayin da tayi arangama dashi a bikin Nafisa jiya mai cike da barkwanci da halin kirki, a zuciyarta tana takaicin yadda yayi mata nisa ta ko wani irin bangare saboda matsayin shi, daki taja suwaiba suka shige ta bar Goggo nata banbamin bala'inta, itama tana takaicin bakin jinin da yaranta suke dashi, babu irin maganin da batayi musu ba dan su samu mashin shini amma a banza, to ita kuwa ta yaya zata yarda ta bar suwaiba ta kula samari alhali yaranta duk ba mashin shini, masifar ta cigaba dayi kamar zautacciya zuciyarta na mata zafin balbalin wuta..... Albishirinki Ma'u!!! Kai yau cikin farin ciki nake wallahi, Goro ta fadi tana zuba mishi ruwa a kofi, baibi takan ruwan ba ya kwala kiran suwaiba, da sauri ta fito yace "akwai bako a waje kira Yayarki kuje ta rakaki, kuma kar ku dade, cike da faduwar gaba Ma'u tace "baka ce min komai ba kuma kace yara su fita, yanzu sai aga yara sun fita zance kai ba abin kunyar ka bane, "shiyasa nace Zainabu ta raka ta ai, saboda idon mutane, zuciyar ma'u kamar zata fito tace "to meye albishir din, gyara zama yayi yace "kinajin labarin Alhaji Garba Kyari mai fata ko?, gyada kai Ma'u tayi kirjinta na tsananta bugawa, yace "to danshi ne yaga suwaiba yake so, kuma da aure, nace yaje ya turo magabatanshi mu tsayar da maganar aure, wallahi Ma'u bakiji dadin da nakeji ba, ko ba komai zan fara aurar wa, mutanen unguwa zasu bar zundena, yake ma'u ta shiga yi tana fadin madallah Allah ya sanya alheri, Ameen.. Baffa yace ya mike ya wuce daki zuciyarshi wasai bai ko lura da yanayin ma'u ba, shidai a yadda yakeji a ranshi, yasan suwaiba ta gama samun gatan duniya saidai kuma ta roki lahira.... Tun da suka fito Bingel tayi tozali da Mukhtar cikin kayanshi riga da wando fela, gashin nan Afro ya tajeshi ya mike sosai, hankalinta yayi kololuwar tashi, shine, shine wanda ta ganshi a gidan Nafisa, karasowa yayi gurin kafin su iso yace "barka da fitowa sahibar ruhina, ya ilahi, suwaiba kamar zata nutse ta damki hannun yayarta hade da rufe fuskarta cikin hijab, no, no, no, wannan kunyar cutar dani zatayi, kiyi hakuri ki dago kanki ki kalleni, sakin hannun Bingel tayi ta ruga cikin gida da gudu ta barsu a waje da Bingel da tayi tsaye tana kallonshi kamar mutum mutumi, Hannu yasa yayi kasss a fuskarta yace "ina wuni yar uwarmu, firgigit tayi tace "ni ya kamata in fara gaisar dakai, murmushi yayi yace "kuma sai kika barta ta gudu baki rike ta ba, dariya tayi tace "kasan yarinya ce, kunya gareta, amma bari in tayata tadin, cikin nutsuwa ta dinga tambayarshi halayarshi da abubuwan daya kamata ta sani, sun dade suna hira yana fada mata yadda yake ji a cikin rashi game da kanwarta, da zai tafi ya bukaci ta kira mishi ita su yi sallama, sallama tayi mishi ta wuce gida ta iske suwaiba a zaure tace "jeki kiyi sallama dashi, ko so kikeyi yayi fushi, dakyar ta fito ta tsaya nesa dashi tace "ina wuni, jingina yayi jikin stalet dinshi yace "bazan amsa ba, ashe ma dai ni dodo ne ban sani ba, rufe fuskarta ta sakeyi tace a'a kayi hakuri, murmushi yayi yace to nayi, ya bude gaban motar ya dauko leda yace "gashi inji mamanki tace wai a kawo wa yarta, dakyar ta karbi ledar ta ruga cikin gida da gudu, murmushin shaukin samun farar mace kamila yayi sannan ya shiga mota ya tada ya wuce.... Bayan zuwan magabatan Mukhtar aka saka ranar aure sati biyu, babu irin hidimar da baya ma Baffa saboda so da kaunar da yake yi ma suwaiba, ita kuwa Bingel ramewa ta soma yi saboda tunanin mukhtar da ta sanya kanta ciki, bangaren Ma'u kuma sai hada tuggunta takeyi wanda zai hana auren, gori kuwa babu wanda bata sha daga makota, da abun ya isheta ta zauna wani dare ta dinga rusar kuka, Halima da itama kishin suwaiba ya dameta ta zauna tana tayata kukan, a haka suwaiba da ta dawo gurin mukhtar ta samesu, kudin da ya bata ta fito dashi ta mikawa Ma'u tace "Goggo gashi yace in kawo miki kudin walima, amsa tayi ta ajiye a gefe, cike da fargaba tace "Goggo me ya sameki, rungumar munafurci Ma'u tayi mata tace "Suwaiba ya zanyi da raina, ya zanyi da gorin mutane, yanzu kina karamar kanwar yayarki ace kinyi aure ita bata yi ba, kinsan dole abun ya dameni, dole ne in shiga cikin kunci da takaici saboda nasan babu wanda zai aureta yanzu, matso da ita ta kuma yi tace "kinsan dai ni na haifeku dukkanku ko? Gyada kai Suwaiba tayi tace "eh, to yar albarka ina umurtarki da ki janye auren nan akanki ki barwa yayarki, nasan Allah zai dubi abin alherin da kikayi ya baki wanda ya fishi, jiki na rawa suwaiba tace "Goggo, dan Allah kiyi hakuri, wallahi ina sonshi, kuma shim--- ya isheni, yanzu duk halaccin da Bingel tayi miki tun kina yarinya har kawo yanzu baki gani ba, duk irin kaunar da ta nuna miki bazaki dubashi ki sadaukar mata da mijin da zaki aura ba, kuka ne ya kufcewa suwaiba tace "hakkinta ne Goggo, Hakkinta ne a matsayinta na yayata ta kula dani kuma ta sadaukar da komai nata a gareni, wallahi da zan iya da na rabu dashi na bar mata shi amma bazan iya---- wani wawan mari Ma'u ta kai mata, tace "lallai rashin kunyarki ta tumbatsa, a gabana kike cewa kina son namiji, lallai ďan da baka haifa ba dole ya nuna shi ba naka bane, dammmmm.... suwaiba taji a kirjinta, kalaman Goggo suka sa zuciyarta ta fara yawo a cikin ma'ajiyinta........ Mrs Tijjani Shattima [05/03 11:10 PM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* 2⃣9⃣ By *Aysha Ya'u Kurah* *_Duniya kurkukun mu'imuni, kuma Aljannar kafiri, akwai mutanen da Allah swt yake Halittarsu a cikin duniyar nan ba domin suji dadi ba, sai dai domin rayuwakansu su zamto izina ga wadanda sukazo domin zamanta na din din, mai hankali shi kadai yasan duniya ba gurin jin dadi bane, lahira itace matabbata, sannan akwai tarin tanadi da Allah yayi wa bayinshi masu hakuri, tanadin Allah shine tanadi Allah ya sa mu dace,_* *RABUWA DA MASOYI* Mikewa tayi ta isa gabanta tace "Goggo, dan Allah karki ce bake kika haifeni ba, Kukan Munafurci Ma'u ta saki tace "Suwaiba yau kin sani na fada miki abinda ban taba tunanin fadin shi ba, yau kin kaini makura har na fito miki da *SIRRIN BOYE* kuka ne ya kufce ma Suwaiba tace "wacece mahaifiyata? , a ina take?, nan take shaukin son taga mahaifiyarta yazo cikin zuciyarta, rungemeta Ma'u tayi sosai tace "Tambayar bata da amfani tunda bata raye, ni nan ni na raine ki tun kina jarinta da taimakon yayarki, munsha gwargwarmayar rayuwa gurin baki tarbiyya, musamman yayar taki da kike yunkurin k'in sadaukar mata da soyayyarki, cikin kuka suwaiba tace "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kara kankameta Ma'u tayi tace "duk abin da kika ga na miki a baya bawai dan bana sanki bane, nayi shi ne dan samar miki tarbiyya mai kyau da amfani, kiyi hakuri, kiyi hakuri ki bar mata, "labarin karya ta shirya mata akan mahaifiyarta sannan ta karashe da fadin irin kular da zainab din tayi mata, kukan bai fasa zubowa a idonta ba tace "Allah ya jikan mahaifiyata Goggo, Ameen Ma'u ta fadi sannan tace "nasan zaki bar ma yar uwarki mijin da zaki aura ko? Nasan zuciyar zinari gareki, girgiza kai Suwaiba tayi tace a'a Goggo, yaudara ce wannan, bazan iya hakuri da shi ba, domin kuwa Allah sai ya tambayeni, yasa rai da aurena kuma kawai sai in ce mishi ya auri yayata, hakan bazai yiwu ba, tana karashe fadi hade da tashi ta fita zuciyarta na tariyo mata irin ukubar da tasha a hannun Goggo, ba tun yau take tunanin cewa ba Goggo bace ta haifeta, gashi yau sanadiyyar Mukhtar an warware mata komai, hawayen idonta ta share dan tasan in shaa Allahu ta kusa daina zubda su, tasan Mukhtar zai zame mata komai da ta rasa a rayuwa.. Dakinsu ta shiga jiki a sanyaye, a zaune ta tarar da zainab da ta gama sauraron duk abinda suke cewa, tafarfasa zuciyarta takeyi saboda yadda ta dauka Suwaiba zata iya barin mata komai take bukata a rayuwa, lallai a yanzu ne ta fahimci cewa uwa daya ya wuce wasa, tayi imanin da Leemah ce zata yarda ta barta Mukhtar dan kar ta kunyata, wata irin tsanar Suwaiba ce ta darsu a zuciyar zainab wacce dama ta dade ana mata aikenta, sai yanzu shaidan ya samar mata mazauni a zuciyarta, barka da hutawa yaya, suwaiba ta fadi tana cire hijab dinta, uhmmm!! kawai taji tace sannan ta mike kafarta a kan gado, gabanta ne ya fadi dan bata saba ganin hakan a gurin yar uwarta ba, gefen gadon taje ta tsuguna tace "yaya ko na miki wani abu ne, juya mata baya tayi tace "karki dameni suwaiba, kaina ke ciwo, nan take idonta ya ciko da kwalla ta mike ta fita kofar dakin, kuka sosai ta zauna tana yi, zuciyarta sai kai kawo takeyi akan maganar da Goggo tayi mata, sam bata damu da sanin cewa ba ita ta haifeta ba, dan ta dade da sanin uwar da ta haifeka baza tayi maka irin wannan tsanar ba, abin kawai da ya daga hankalinta shine rashin sanin uwarta da kuma rashin adduar da bata samu daga gareta a matsayin sadaka a kabarinta.. yanzu kuma babban tashin hankalinta bai wuce na rashin walwalar da ta gani a gurin yar uwarta mai kaunarta ba, tana wannan tunanin taji Ma'u tazo ta wuce cikin dakin... Yanzu dai kinga halin wacce kika fifita akan yar uwarki, kindai gani da idonki, kuka zainab ta fashe dashi tace "Wallahi Goggo ina mutuwar kaunar muntari, na dauka zan iya hakuri in bar mata shi, amma yanzu da naga aski yazo gaban goshi walhy bazan iya hakura ba, duk abinda da kika ga ya dace kiyi Goggo, nima ko meye zan yi walhy, murmushi Goggo tayi a zuciyarta tace "wuya makarantar kare, waya fada miki borno a gabas take, kwantar mata da hankali tayi tace gobe zatayi komai da tasan zatayi ta rabasu,,, wani sabon kuka ne ya kufcewa Suwaiba da ta gama sauraren kalaman Goggo, mikewa tayi ta je bakin pampo tayi alwala ta dawo dakin, a zaune ta samu Leemah da yaya zainab suna magana kuskus, darduma ta dauka ta fito waje tayi raka'a biyu ta zauna a gurin tana kai kukanta gurin ubangiji.... Baffa na fasa auren muntari! Wata iriyar faduwar gaba Baffa yaji wacce zata iya sanya zuciyar bawa tsayuwa, hade rai yayi kamar bai taba dariya ba yace "wace irin magana ce kin fasa aure?, dama yardar aurenki da rashinshi duk a hannunki suke,? dama ke kike da ikon zabawa kanki miji bani ba, dan Allah ya kawo miki miji shine har kike da bakin butulce mishi, lallai suwaiba ban taba tunanin baki da hankali ba sai yau, idan kika sake furta min wannan kalmar walhi sai na lahira yafi ki jin dadi, tashi ki bani guri sakarya kawai.. tashi tayi ta fita tana kuka a ranta tana fadin nima ba asan raina bane Baffa, ina gudun a sabauta rayuwata da ta muntari ne, ya zanyi in fahimtar dakai akwai matsalar dake shirin bullowa, ya zanyi ka fahimci matarka wacce na dauka uwa marar kaunata Guba ce a cikin rayuwarka, da wadannan tunanin ta isa zauren gidansu ta zauna akan dakali ta cigaba da kuka, saida ta dauki kamar minti talatin a gurin sannan ta tashi ta wuce makaranta... A dimauce ya dago kai ya kalleta sosai yace "maimaita abin da kika fadi, cike da dakiya tace "kayi hakuri dan Allah ka janye batun auren mu da kai, wallahi zuciyata ta kasa aminta da yin rayuwar aure dakai, share zufar da ta keto mishi yayi yace "karyane! Wadannan kalaman ba naki bane, ko kina da ciwon aljanu ne ban sani ba? Hawaye ne ya fara zuba a idonta tace "Gaskiyar magana nake fada maka daga cikin zuciyat---- karya kikeyi! Ya daka mata tsawar da sake sanya ruwan idonta ambaliya, sauke muryarshi yayi yace " baki da lafiya suwaiba, kin gane ko, jeki gida ki kwanta, "lafiyata kalau ta fadi murya na rawa, ka fahimceni, rayuwar aure bazata yiwu da zuciyoyin da basu gama yarda da junansu ba, nayi duk iya kokarin da zanyi in tusa sonka a raina na kasa, kallonta yakeyi da manyan idanuwanshi da suka rine zuwa jajaye, "me yasa kike kuka? Karki damu share hawayenki, share hawaye tayi da sauri, yauwa ya fadi hade da cewa kar in sake ganin kukan nan kinji ko? Gyada mishi kai tayi tace "na daina, "kin min alkawari? Eh "Nayi! Yauwa matar Muntari, kin gane ko, dama ni bana son ki soni, son da nake miki ya isa, ni fa ina sonki ne badan ki soni ba, so karki damu zanyi maneji, ko ba komai in na dawo gidana nasan da abin da nake so zan fara tozali, gyara tsayuwa yayi yace "baki san ke din sarauniyata bace, in kina gurina a killace to bani da wata damuwa, dan haka bana san jin komai je ki gida ni zan tafi, ko kina son wani abu? Wani kukan take kokarin sake yi yace "mutum dai yasan hukuncin mai saba alkawari! Nidai ba ruwana, kamun Allah bana mutum bane, share hawayen tayi da sauri ta ruga gida.. Kwantar da kanshi yayi akan sitiyarin motar zuciyarshi na azalzala da kalamanta, ya zaiyi in da gaske ya rasa Suwaiba, da wace mace zai iya rayuwa in ba ita ba, sake kallon kofar gidan yayi sannan ya tada motarshi ya wuce gida jikinshi duk a sanyaye.... Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, Suwaiba ta daina fita gurin Mukhtar, ko yazo saidai ya karaci tsayuwarshi saboda rashin baffa a gari, Ana jibi daurin aure ne ta fito ta sameshi, a wannan ranar saida ya nuna mata irin nashi bacin ran kafin ya tafi ranshi a bace, yana mata uzurin yarinta da kuma bata san meye kalmar so ba, gidan su Abbakar ya wuce direct, cikin bacin rai yake magana yana fada mishi yadda al'amura suka sauya cikin kankanin lokacin, "Abbakar kai kadai zaka mata magana, wallhi ina shiga cikin matsanancin hali in naji tace "bazata aureni ba, yarintar ta bata gaya mata gaskiya, in ba haka ba sai ka kalli mutun kace baka kaunarshi, Shiryawa Abbakar yayi suka wuce gidan su suwaiba, dakyar ta sake fitowa, har saida ma'u tace ta fita, ita duk tunaninta asirinta ne ya kama Suwaiba, bata san kauna ce ta sanyata hakura dashi ba, tasani tunda sukayi alwashi zasu iya rabasu kuma ta zauna a gidan su gasa mata aya a hannu, gara ta hakura dashi ya auri yar uwarta ko zasu samu maslaha da ita, dan a yan kwanakin nan ta jigata da rashin kulawar da Zainab take bata.. "Abokina yayi laifi ko? Rufe fuskarta tayi murya na rawa tace "A'a, to meya faru?, fada min a matsayina na uncle dinki, kuka ta fara yi kamar yarinya karama tace "nidai kawai bana sanshi ne, kuma yaki ya taimakeni yace ma Baffa bazai aureni ba, runtse ido Mukhtar yayi kirjinshi kamar zai fado kasa, matsowa kusa da ita yayi kamar zaiyi kuka yace "nasan bakya sona, kiyi hakuri ki bani amanar rayuwarki, nayi alkawarin koya miki sona, wani abu taji tun daga kanta har tafin kafarta, "meyasa Ya Allah, meyasa na samu gatan da zaisa in zama lele kuma yanzu gatan zai subuce min, meyasa, wannan shi ake kira da Dandani haukaci, a fili kuma kukan dai ta cigaba dayi tace "ni bazan iya jure zama dakai bane, uncle Abu dan Allah kace yayi hakuri ya nemi wata, "bazanyi hakurin ba, Abbakar yarinyar nan bata da hankali, rabu da ita kazo mu tafi, in an daura auren ta mutu, kafadunshi Abbakar ya dafa yace "calm down kyari, hannun ya ture kafadun shi yace "dan taga ina lallaba ta ne, wallahi abinda zai hanani aurenki saidai mutuwa, ko kuma dama bani da rabon zama dake har mu samu 'ya'ya, amma in har inada jini a jikinki sai kin aureni (Rabon yayi muku wannan farraqun), yana kaiwa nan ya fita yana huci kamar zaki, Duk irin lallashin da uncle Abu yayi mata ta kafe akan ita bata sanshi, har yaji haushi sukayi sallama, kafin yakai kofar fita yaji ta rushe da kuka mai ratsa zuciya, tsayawa yayi yana kallonta a ranshi yace tabbas akwai matsala, haka nan bazata ce bata son kyari ba, koma menene Allah ya kawo mata mafita.... *RANAR AURE* Tun da suka idar da asuba Suwaiba ta wuce islamiyyarsu ta zauna can wani lungu da babu mai zuwa gurin, kuka takeyi sosai hade da karatun qurani, tasan in har ba'a ganta ba to tabbas baza'a daura mata auren ba... Zufa Baffa ke sharewa yana fadin "ina tace miki zata, kukan munafurci Ma'u ta kirkiro tace "bata fada min ba, nidai naji Leemah na cewa Suwaiba tace "in aka mata aure saita kashe kanta, salati Baffa ya saki yana fadin yarinyar nan so takeyi ta kunyata ni, duk irin mutanen da muka tara a kofar gidannan so takeyi lallai sai na kunyata, Matsowa kusa dashi ma'u tayi tace "tunda tace bata sanshi a hakura mana, Wani kallo baffa yayi mata yace "so kikeyi in zama karamin mutum, kinsan adadin manyan masu kudin dake zaune a kofar gidannan suna jiran a daura auren nan, kawai kuma sai inje ince musu amarya ta gudu, Sake matsowa tayi tace "to ya zakayi, saidai ko dan mu fita kunya a hada auren da Zainabu, kaga shikenan asirinka a rufe, ita kuma tunda rayuwar da ta zabarwa kanta kenan shikenan sai taje can tayi, dan taga tana da farin jinin ne, in kayi tafiya itace wannan saurayi itace wancan, cike da bacin rai Baffa ya hau kan zancen Ma'u ya zauna, ya fita yanata sababi cikin zuciyarshi.. bai nemi shawarar mukhtar ba dan baisan samm ya rasa shi a matsayin siriki saboda tarin hidimar da yakeyi mishi, gurin daurin auren yaje ya zauna aka fara gudanar da auren kamar yadda addini ya tanada, saida aka daura aure akayi komai sannan maroki ya fara fadin, "Tuwon girma miyarsa nama, yau naga auren da ban taba ganin irinsa ba, jama'a ku shaida an daura auren *ZAINAB* DA *MUNTARI* akan sadaki naira na gugan naira har naira Dubu Uku.... Ba Mukhtar bane kadai ya girgiza, hatta Mahaifinshi saida ya tafi tunanin Zainab ko Suwaiba...... Mrs Tijjani Shattima..... [07/03 2:02 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣0⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Alhaji ku yafe ni!, na yanke hukunci ba tare da neman yardarku ba, dan Allah ku gafarce ni, nayi hakan ne dan in fitar damu daga kunyar jama'ar da muka gayyata, Baffa ne ke jero musu bayanan ban baki lokacin da suka kebe da Alhaji Garba yayi mishi tambayar dalilin sauya akalar daurin auren, share hawaye yayi ya cigaba da cewa, "yarinyar nan taso ta wulakanta ni, sai Allah yasa ina da 'ya'ya matan da basuyi aure ba, kuma bana son mutum kamili kamar Muntari ya subuce min, da zainab da Suwaiba duk daya ne, uwa daya uba daya suke, dan haka kaga wanda yazo daukar suwaiba kuma ya samu zainab ai duk daya ne tunda tsatso daya suka fito, kasa Magana Mukhtar da zuciyarshi ta kai kololuwa gurin bacin rai yayi, har lokacin baiji ko daya daga kwatan son da yake ma Suwaiba ya fita a ranshi ba, da yaji Babanshi na kokarin amincewa da batun yayi saurin cewa "Abba, dan Allah kuyi hakuri, ni suwaiba kadai nakeso, in aka daura mana aure da ita nasan zata hakura ta zauna dani! "Naso yin hakan,amma abin yaci tura saboda guduwa tayi tabar gidan, Baffa ya karashe cike da damuwa, wani abu Muntarin yaji ya soki kahon zuciyarshi, har kiyayyar ta kai haka, ta ina ya gaza da ya samu macen da ta nuna mishi irin wannan kiyayyar, me ya rasa, babu abinda bai mallaka ba na daga dangin kyau, ilimi, gayu, uwa uba arziki na jama'a da kuma na dukiya, me yasa Suwaiba zata rusa tanadin da yayi wa rayuwarsu, yanzu kenan dukkan mafarkinshi zai zamto cikakken mafarki, kenan babu ko daya a cikin mafarkinshi da zai zamto gaskiya, baisan Hawaye ya fito a cikin idanuwanshi ba saida yaji duminsu a kuncinshi, mikewa yayi ya fita zauren hade da share hawayen fuskarshi, motar da suka zo shi da abokanshi ya shiga hade rufe fuskarsa dan hawayen sunki daina zuba, Allah ya sani ba karamin so yake yi ma Suwaiba ba.... Godiya sosai Baffa yayi wa Baban muntari saboda fahimtarshi da yayi,da Kuma alkawarin da yayi mishi na yarshi bazata wulakanta a cikin zuri'arshi ba, ko yana so ko baya so dole ya karbeta hannu bibbiyu a matsayin matarshi, dan zuri'armu kaff babu me wulakanta mace... Sai dare suwaiba ta dawo gida lokacin Ma'u na buduri da makota ana shirin kai Zainab dakin miji, kallo ne ya dawo kanta, daga mai yi mata habaici, sai mai yi mata kallon marar hankali, dakin Baffa ta shige a darare, zaune ta sameshi yayi tagumi yana tunanin ta inda zai fara neman suwaiba, jin muryarta ne ya sanyashi waigowa da sauri, sanyi yaji a zuciyarshi da ya ganta lafiya kalau, a fili kuwa fada ya rufeta dashi, saida yayi mata cin mutunci sannan a karshe yace "Wallahi, wallahi, kinga rantsuwar nan, bata da kaffara, bazaki kara daga kafarki kije makaranta ba, kina cikin gidannan har sai na samu wanda zan bawa ke sadaka, ke ba takamarki kinada farin jinin samari ba, kin daukesu kamar rigar canji, to ki sani kin jawa kanki a gurina, fita ko nan da kofar gida ne ban yarda kiyi ta ba, sai ki zauna a gidan tunda kin zabi butulcewa Allah da ni'imar da yayi miki, tashi ki fita ki bani guri mutuniyar banza mutuniyar hofi, tashi tayi ta fita da gudu tana rusa kuka, a kofar dakin tayi karo da masu kai Amarya ana wakar "Ayye mama", ta gefensu tabi ta shige dakinsu ta kara bude wani sabon babin kukan.... (oyoyo talauci inji Meela) Rayuwar auren Zainab da Muntari kadaran kadaham, sam baya wulakanta ta saboda ya karanci hakkin mace akan miji, kuma mahaifinshi ya sake tunasar dashi, Da fari ta dan samu matsala da mahaifiyarshi domin sam bata san zainab, gani takeyi an lika mishi ita ne dan a cuceshi, saida "Abba" yayi mata nasihar cewa matar mutum kabarinsa, kuma wata bata auren mijin wata, sannan ne ta dan sakko, amma duk da haka bata cika bata muhimmanci ba, biyayyar da zainab ke mishi ne ya sanya shi sake sakewa da ita, wani lokaci yakan tuna suwaiba wani shashin zuciyarshi yaji yayi mugun tsanarta, wani shashin kuma yaji ta ciki a killece, ya sha in zai ambaci sunan zainab yace suwaiba, in ko yayi tafiya to fa sai ya cirewa suwaiba tsaraba, kome zaiyi da ita yake hadawa yayi, wannan abu shi ya kara dungunzuma zuciyar Zainab taji gaba daya Suwaiba ta fice a ranta, kullum cikin kulli Goggo take dan dai kawai kar auren yarta ya mutu, a irin zaman da sukeyi Zainab ta samu ciki har ta haihu, haihuwarta ita ta kara daraja ta a idon iyayenshi da shi kanshi, sannu sannu ya fara fitar da Suwaiba a cikin ranshi, saboda samun zuri'a da ya farayi. Saida Zainab ta jera mishi 'ya'ya Mata uku a karancin tsakani (gwarne ) cikin shekara hudun aurensu, Reemah ce Babba, sai Radiya Sai Raudha, a lokacin da take da cikin na hudu ne Muntari ya saduda ya mika mata ragamar rayuwarshi, domin yasan yanzu indai za'a kirashi to itace ta biyun da za'a kira a rayuwarshi.... Ita kuwa suwaiba baiwar Allah ta zama baiwa ta gidi, komai na gidan ita takeyi, babu makarantar islamiyya, babu fita cikin gari, iyakarta shagon buzu Adamu mai gadin jikin gidansu, duk irin kyawun da ta ke dashi ya disashe, rayuwar dai yinta kawai takeyi saboda Allah a hakan yaso ya ganta, kullum saidai tayita yi mishi Godiya da bai daura mata ciwo ba.... Leemah kuwa ta zama yar gayu sosai, university take zuwa Abu zaria, babu abinda zatace tana dauka a makaranta, ita dai kawai ta shiga gayu, yau ta tsaya da wannan gobe wancen, Baffa daga yayi niyyar yi mata magana Ma'u zata hanashi, takan ce in ba'a barta taje makaranta ba ina zata samu mijin aure, dole badan yaso ba ya barta tayi abin da taga dama.. "Bani omo malam Ado, ! dauko mata kullin bulan omo biyar yayi yace "jeki kiyi amfani dashi, na bar miki kudin ki siya silifas naga naki ya tsinke, murmushi tayi tace "nagode Adamu, "ba komai suwaiba kedai ki daina yawo ba takalmi, gyada mishi kai tayi ta wuce cikin gida, kallo ya bita dashi hade da girgiza kai cike da tausayawa, duk wannan abun da sukayi a idon Baffa wanda yazo shiga da mota gida, wani abu ya darsu a ranshi ya shiga gida yayi parking... "Kanason 'yata Suwaiba? Daburcewa Adamu yayi da yaji tambayar yace "a'a Alhaji, ai tafi karfina, in ba cutarwa ba ta yaya zan auri mace cikin gata alhali ni din ba kowa bane, dariya Baffa yayi yace "in dai kanajin zaka iya zama da ita to zan aura maka ita, washe baki Adamu yayi yace "suwaiba mace ce mai kawaici da hakuri Alhaji, waye zai kita a matsayin mata, bana tunanin akwaishi, murmushin farin ciki Baffa yayi yace "kaje ka shirya, rana ita yau zan daura muku aure, godiya sosai Adamu ya tsuguna yayi ma Baffa sannan ya wuce cikin gidan da yake gadi dan sanar dasu.... Koda ya fada ma Suwaiba nan take ta amince saboda a ganinta gara taje tayi bauta mai dalili, domin ta gaji da aikin jakin da takeyi.... Ranar da aka daura auren duk wani masoyin Suwaiba saida yayi mata bakin cikin karewa da kaskantaccen mutum irin Adamu mai gadi, shi kuwa Muntari gani yakeyi Hakkinshi ne ke bibiyarta shiyasa ta dade batayi auren ba a karshe ta auri mai gadi... Rayuwa mai cike da jin dadi da rufin asiri daidai gwargwado sukeyi, gidan da ya dade yana tari ya siya mai dauke da daki biyu da kitchen nan aka kaita, sosai take jin dadin zama dashi dan dama sun saba, shekararsu biyar da aure ta samu cikin Hafeez bayan ta fidda rai, lokacin Zainab Mummy ta haifi yarta Raudha, dakatar da haihuwar tayi ta hanyar allura saboda ita a ganinta in dai zata cigaba da haihuwa tofa tabbas mata zata haifa, wannan jinin zuri'ar mahaifinta ne kamar yadda suka canfa, a lokacin da aka haifi Hafeez ba karamin girgiza mummy tayi ba, ta dinga tambayar suwaiba yadda akayi ta samu namiji a haihuwar farko wanda saidai tajishi a gari ba'a zuri'arsu ba, ko da ta tambayeta saidai tayi murmushi tace "daga Allah ne, tun daga haihuwar Hafeez abubuwa suka fara dan ja baya saboda mai gidan da Adamu ke gadi ya bar garin, jikin gidanshi ya manna shagonshi da babu isassun kaya a ciki, dama da albashin shi yake cika shagon yayi hidimar gida, babu wanda a cikin yan uwanta yake taimaka musu, a ganinta basai ta fito ta fada ba sun san bata dashi... Shekarar Reemah 15 ta tafi karatun gaba da secondary sokoto, hazakar ta tasa aka dinga promoting dinta har Allah ya kaita jami'a, anan ne ta hadu da Gaddafi dan 400l, sanadiyar haduwarsu saboda ya kasance hazikin da ake ji dashi a engineering department, ko wani irin science course ya iya, kuma yana koya musu dan su biyashi ya samu na siyan hand out, zuwan Reemah ne yasa suka shaku, itace siyan hand out da komai nashi, shiyasa baya kasa a gwiwa gurin kowa mata karatu, ko da ya gama makaranta ya fito da first class babu wanda ya lura dashi bare yayi yunkurin bashi aiki, ajiye takardunshi yayi ya dawo cikin school yana hada tutorial dan a dinga biyanshi, tausayinshi yasa Reemah tayi ma Daddy magana har ya amshi takardunshi ya samar mishi babban aiki a lagos, tun daga lokacin kauna mai karfi ta kullu a tsakaninsu har ta kaisu ga aure... A shekarar Farko Allah ya azurta ta da ciki,, lokacin Mummy ta fidda rai da haihuwa saboda dadewar da tayi, bata san akwai dan makale a tare da ita ba, Tsirar Haihuwar su kwana tara ne, domin Reemah ta haihu da kwana tara Mummy ma ta haihu, wannan abun ga mutanen "Da", bawani abun kunya bane, murnar Samun Musaddiq ba a gurin mummy bane kadai, har da kakanninshi da babanshi da ya dauki dukkan so ya daura mishi, gata babu irin wacce (Mukhtar) Hilal da Musaddiq basu gani ba, babu tafiyar da Daddy zaiyi ba tare dasu ba.. Kamar yan biyu haka suka taso, kansu daya, kayansu iri daya, kamanni ne kadai suka banbanta shi Hilal fari ne musaddiq kuma Baki ne irin bakin barebari, gasu da jikin girma Masha Allah, komawar su Reema Cypros ne ya raba su, amma kafin nan koda yaushe suna yare..... Bangaren Halima kuwa tunda tayi karyar makaranta sun tura ta china karatu shikenan su Goggo suka hau suka zauna ba tare da bincike ba, yawon barikinta ta tafi yi da kuma neman kudi, saida ta zama hamshakiyar kanta sannan ta waiwayi gida bayan shudaddun shekaru, ko da ta dawo saida ta gyara gidansu dan acewarta bazata iya zama a irin gidan ba, Sana'arta ta business ta cigaba dayi tunda dai yanzu ta gama rikewa tasan babu wanda zaizo yace zai aureta, abu daya gareta wanda za'a yabeta dashi shine duk irin duniyancin ta bata yarda da karunwanci ba saboda shegen kyankyami gareta, shekaru da dama bayan dawowarta ta hadu da wani mayaudarin yaro mai tsantsar *SIHRUL KALAM* a take ya baibayeta ta fada tarkon kaunarshi, bata tsaya dogon bincike ba ta yarda ya aureta, hatta sadaki ita ta biya mishi saboda shaukin samun wanda ya furta mata kalmar so... Sai bayan auren ne ta gane yaudararta yayi, yazo ne kawai dan ya kwashi dukiyarta yayi gaba, ko da ta fahimci haka bata dauki zafi ba dan ita mai bashi dukiyarta ne, abin da ya tsiro dashi na shigowa da mata gidane yafi tunzurata har ta kai ga aikata kisa a gareshi cikin rashin sani, A kotu ne aka fahimci cewar tana dauke da cikinshi na wata hudu, koda ta fahimci hakan saida taci kukan dana sanin zuciyarta marar kyau, Kotu bata yanke mata hukunci ba har sai ta haifi dan dake cikin ta ta yaye, haka kuwa akayi har cikinta ya isa watan haihuwa, kamar hadin baki dukka ukun ya'yan Baffa cikin garesu, Husna aka fara haifa, washe gari Nadiya ta biyo baya, haihuwar Badariyya tayi gardama saida aka yanka Leemah, ba karamar wuya Badariyya ta ba mahaifiyarta ba, bayan awanni da yi mata aikin aka fahimci jikin nata babu dadi, cike da kwarewa doctors ke aikinsu amma ina abin yaci tura, aikin mala'ika da na mutun ba daya bane, Ashe leemah ajalinta ta auro har ta haifo mishi 'ya, ba karamin tashin hankali duk suka shiga ba na rashin yar uwarsu, musamman Goggo da tayi karamar hauka... mummy ce ta dauki Badariyya ta hada da Husna ta shayar dasu cike da kulawa... Tun a karancin shekarun 'yayan suwaiba suka fahimci zumuncin zuri'arsu sai in kana da kumbar susa, marasa wulakantasu aciki kadan ne.... Rayuwa Badariyya tun tana karama ta tashi a sangarce, bata ganin mutunci ko jin kunyar kowa, Hilal shine wanda tun fil'azal basa shiri, a gurinshi tasan ba mummy bace ta haifeta, ranar yaci dukan tsiya a gurin mummy, Tana gama dukanshi ya fita dan ko a jikinshi dama so yakeyi ya nuna mata ita fa ba yar gidansu bace ta daina kusu fi'ili...... Da wannan labarin zumunci ya faro, sila itace mace, uwa, wacce take da daraja, wacce Allah swt ya bata ragamar tafiyar da zuri'a, lallai Macce ta gari itace ginshikin alumma, domin gyara rayuwae ya mace kamar gyara alumma ne, mu dage tun yanzu gurin yi ma 'yayanmu maza adduar mace ta gari domin wayau ko dabara bazai basu ba, sukuma yayanmu matan ka sanya su zamto Mar'atus saliha ga mazansu..... Mrs Tijjani Shattimah.... [08/03 12:28 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣1⃣ By *Aysha Ya'u kurah* _HAKKI, HAKKI BABBAN ABU NE YAN UWA, KOMIN KANKANTARSHI MU GUJI DAUKARSHI DAN KANANAN ZUNUBBAI SUNFI MANYA ILLAH, DAN ALLAH MU KIYAYE HAKKIN JUNA_ *Cigaban Labari* Jiki a sanyaye ta dauko sarkar dake cikin akushin tayita juya ta a hannunta, tasan Baffa ya dade da mantawa da zaman sarkar shiyasa tayi mata muguwar ajiya, ko da wasa bata taba yunkurin sata ba, tun da taje ta tambayi kudin sarkar taji kudi ne masu tarin yawa ya sanyata kara yi mata kyakykyawan ajiye, ajiye sarkar tayi hade da tagumi. ya zame mata dole ta nuna musu gaskiyarta, shiyasa ta fito da sarkar dan bawa su Nadeeyah gadonsu, tasan wannan ita ce kadai mafita a gareta da diyarta, tasan in tayi hakan Muntari bazai yi mata zargin muguwar uwa ba, zaiyi mata kallon mai amanar da ta iya rike abu mai daraja saboda soyayyar uwarsu, wannan hanyar ita kadai ce abin da zai samar mata mafita... Rufe akushin tayi bayan ta dauko wasu magunguna a ciki, inda ta daukoshi nan ta maidashi ta fito parlor ta dauko leda mai kyau ta zuba sarkar a ciki, sannan ta shiga yin amfanin da magungunan domin rufewa su Daddy da sauran baki.... *1:51pm* Motaci uku ne suka shigo cikin harabar gidan Baffa, Motar Anty Reemah ce ta fara shigowa, sannan sauran kannenta suka rufa mata baya, Raliya ce zaune a gaban motar Anty Reemah, sai Zainab (kanwar Nadeeyah) da Hinad, a motar Radiya aka tara taron marasa mutunci, Raudha da Badar, Cikin kunci Badar take saboda Nadeeyah da Husnah sun shiga motar Hilal, duk yadda taso taja Husna suzo a mota daya taki saboda farin cikin tayin da Hilal yayi mata na shiga motarshi, ko kallon motarsu batayi ba ta wuce cikin gidan tana huci, a zaune ta samu Goggo hannu rike da carbi tana ja, Allah kadai yasan abin da take furtawa domin janshi kawai takeyi, babban tashin hankalinta bai wuce kar Baffa ya fada musu komai na labarin Atika ba, burinta su sameta ita kadai ta hada musu kirkirarren labari ta fada musu saboda tseratar da auren yarta, jikin ta Badar ta fada ta fara zuba mata shagwaba, gyaran murya Goggo tayi ta mata nuni da carbi alamar ja takeyi, sauka tayi ta daura kanta a kan cinyarta, damuwar da Goggo take ciki ta hana ta fahimtar damuwar dake kan fuskar yar lelenta... Sallamar su Anty Reema ne ya sanya Goggo sakin Murmushi hade da tattara hannu guri daya tana musu gaisuwa dan su gane carbin take ja bata son a katseta, neman guri sukayi suka zauna suka bude flow din hirarsu ta kasuwanci, shigowar su Nadeeya ne ya katse musu hirar saboda yadda Goggo ta yafito su da hannu ita da Zainab, a darare Nadeeyah ta sauke zainab suka matsa kusa da ita suka durkusa zasu gaisar da ita tayi saurin durowa daga kan kujerar ta hadesu ta rungumesu hade da kuka mai karfi, "Allah sarki Suwaiba, ganin jininki ya tuno min ke, inama ni mutuwa ta dauke ta barki cikin 'yayanki, inama zan juyo da hannun agogo baya da na nuna miki irin muhimmacin da kike dashi a cikin rayuwata, cike da mamaki daukacin mutanen parlon ke kallon Goggo, Ciki kuwa harda Baffa da ya sanyo kanshi cikin parlon ya tarar da abun da idanuwanshi basu taba tozali dashi ba, yaran da ko cikin parlon basa samun albarkacin shiga bare har su samu darajar runguma, wani dadi ne ya ziyarci zuciyarshi yayi tunanin mutuwar Suwaibar ce ta kadata haka, da sallama ya katse shurun mamakin yace "yau gidan nawa cike yake da matana kenan, sai wacce na zaba, Murmushi dukkansu sukayi suka gaida shi hade da cewa ai dukkan mu zaka hada, Badariyya ya kalla da ta rike kanta saboda bugeta da Goggo tayi gurin sakkowa daga kujera, "a'a Amaryata me akayi miki naga kin rike kai? sakin kan tayi ta turo baki tace "ba Goggo bace ta bigeni, kallonta Goggo tayi tace "yi hakuri Badariyya ban kula bane, hankalina nakan marayun Allah, babu uwa babu uba, kai wannan rayuwa abar tsoro ce, Anty Reemah da abun ya bar bata mamaki tace "dama haka ne Goggo, Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, ta yiwu mutuwar ita kadai Allah ya ga zata zamto hutu a garesu, shiyasa yayi gaggawar daukesu, Allah sarki Mama Suwaiba,, wani kukan Goggo ta kuma kecewa dashi tana dada kankame zainab, kallon tsoro zainab din take mata shiyasa ta saki kuka ta fisge kanta ta koma jikin Nadeeya, share ma juna hawaye sukeyi gunin tausayi, shigowar su Mummy dakin ne yasa duk suka mike domin bawa Daddy gurin zama, bayan yan gaishe gaishe Baffa yace " yau gida yayi albarka, dariya Daddy yayi ya tsuguna ya gaishesu, bayan yan hirarraki Daddy ya gabatarwa da Baffa dalilin zuwansu, ya kuma kara da cewa "kayi hakuri Baffa nayi maka shishigi a cikin alamarin gidanka, inason sanin dalilin kiyayyar ne saboda yana neman zama min matsala a cikin Zuri'ata... Kuka Goggo ta saki tace "Babu kiyayya cikin zuri'ata da na gina ta shekara da shekaru, kasan zumunci yanzu ya zama na yan zamani, amma ni a gurina kowa daya yake, bana banbanta su,, gyara zama Daddy yayi yace "nasan bakya banbanta su, domin dukkansu 'yayanki ne babu bare a ciki, amma ya kamata ku tsawatar akan yadda akayi ma zumunci rikon sakainar kashi, bana san yadda abubuwa suka kasance a nan gidan su kasance a cikin 'ya'yana, bazan dauka ba, inason 'yayana su fahimci muhimmancin mai shi da marar shi, banason dattin duniya ya zamana sillar yankewar zumuncin 'ya'yana, shiyasa nazo a warware min komai kuma ayi ma tufkar hanci, Gyaran Murya Baffa yayi zai fara Magana Anty Reemah tayi saurin cewa "yi hakuri Baffa zan katseka, dan Allah so nakeyi ka fada mana wacece *ATIKA* a duburce Goggo ta waigo ta harareta ba tare da sun hada ido ba, a zuciyarta tace "kaji shegiyar yarinya, ana neman kai magana karshe ba tare da an bullo da maganar Atika ba ta sako zancen ciki, kara gyara zaman carbinta tayi tana kallon Baffa dake shirin basu labarin Atika.... Kuka sosai Nadeeyah da Hafeez sukayi najin ba Goggo bace ta haifi mahaifiyarsu, ashe dalilin kiyayyar kenan, sun sani tabbas in har uwa daya suke dasu Mummy bazasu taba wulakanta mahaifiyarsu ba ko da kuwa mijinta yafi *KAMAYE* talauci Shi kuwa Daddy banda daurewar kai zuciyarshi ce ta tafi tunanin lokutan da ta dinga mishi magiya akan ya janye maganar aurenta, kalaman Abbakar ya shiga dawo mishi " *Kyari, yarinyar nan tana cikin matsala, anya kuwa mutanen gidannan su suka haifeta? "Ko a makaranta bata hutawa saboda hidimar yar uwarta, yadda kasan baiwa haka suka maida ta, ina tunanin yar riko ce, ka bita a hankali ka lallabata zaka fahimci daga inda matsalar take, walhi ta bani tausayi matuka saboda yadda naji tana kuka kamar ana yankan naman jikinta* dana sani marar amfani ne yayi mishi dirar mikiya cikin zuciyarshi, muryar Goggo ce ta katse tunaninshi, cikin kuka ta fito da sarkar da ta zame mata mafitar karshe da zaisa ta fita a zargi ta damkawa Hafeez a hannu, tace "wannan sarkar Kakarku ce da mahaifiyarku ta gada, nayi nayi suwaiba ta karba taki, yanzu gashi bata raye dole in sauke nauyin magada a kaina, kallon sarkar Baffa yayi ya share hawayenshi yace "Samun mace mai rikon Amana irinki sai an tona Ma'u, nagode da rike min Amana da kikayi, Anty Reemah dai kallonsu kawai takeyi hawaye yaki tsaya mata, tuno irin ukubar da mama Suwaiba tasha takeyi, babu abinda bata sani ba na daga halayyar da kakarsu kewa mama suwaiba da ahalinta, wannan shine dalilin da sanyata take matukar kauna da tausayinsu... Labarin halin kirkin Suwaiba Goggo ta dinga fadi saboda dai ta wanke kanta a idon Daddy, shi kuwa ya gama fahimtar komai tun da yaji cewar ba ita ta haifeta ba, sai Gab da la'asar suka fara shirin tafiya, kallon Aljihun Hafeez Goggo ke tayi tana tsine mishi a ranta, wato ma bazai ce mata ta ajiye musu sarkar ba, taso hada baki da Mummy su karbe sarkar taga mummy ta kanta takeyi, burinta kar Daddy ya canza mata... ko da ta fito waje ya riga ya shiga mota har ya tada ta yana kokarin tafiya, da sauri ta karasa ta shiga ciki tana mishi kallon tsoro da mamaki.... *GOMBE* Uncle Abdallah.. Kawu Abdallah... Sweet Papy Abdallah Ajiye takardun hannunshi yayi yace "Ruwaidah problem, ta dawo makaranta yanzu fa babu wanda zai huta, kafin ya ankara yaji ta fado jikinshi, nishi yayi da karfi yace "Ruwaida ai sai ki karya ni, baki san yanzu kinfi *OBENIZA* girma ba, dagashi tayi hade da bude baki tace "Papy Obe what? Hancinta ya ja da karfi yace "OBENIZA, bata rai tayi ta fara daga hannun rigarta tace "yanzu Papy har girmana ya kai na Obeniza ben? Wallahi sai na hadaka da *Anni* ! nan ta bar jakar islamiyyarta ta ruga cikin gida da gudunta tana kiran Mamy nd Anni da iya karfinta, Jamal ne ya fito daga daki hannunshi rike da Game yace "problem child is back again, tana zuwa zata gifta dakinshi tace "Yaya Jay, wai dagaske nakai girman obeniza ben? Kallonta yayi sama da kasa yace "to ai an cuci obeniza ma da ake hadaku, kinfi shi girma sau goma, hannunta ya kamo hade da rike kunnenta yace" warning na fito in miki, yau sunday, wallahi in kika kuskura kika dameni a gidan nan sai na kusa maida ke jaka dan duka, salin alin kije kiyi baccin rana kafin a kira la'asar, da fatan kinjini da kyau? Wani irin karaaa ta saki mai karfi tana bubbuga kafarta a kasa, Da gudu Mamy ta fito daga dakin Anni tace "waye? lafiya, motsin kofar Jamal ta gani ya tabbatar mata da shine ya taba ta, "bude kofar nan Jay, ta window ya leko yace "Mamy babu abin da na mata fa, kawai dan nace mata Anni bata da lafiya yau karta damu mutane shine fa ta fara kuka, daukarta mamy tayi tace "Sorry my love, Anni will get well soon in shaa Allah kinji, muje ki ganta, gefen Anni ta zauna tana fadin Anni wanene ya saki ciwo, hannunta Anni ta rike tace "bana ciwo takwara, lafiyata kalau, tashi kije kici abinci kizo kiyi min fira kinji, mikewa tayi tabi bayan mamy hade da cewa "to Anni na ni kadai banda Wicked yaya Jay... Suna fita Alh Abdallah ya shigo dakin ya zauna a kusa da ita, Anni likita yace "idan baki daina tunani ba zamu iya rasaki, zuciyarki ta kusa shiga matakin Karshe, me kike so wanda Allah bai miki ba, duk irin tsanar da akayi miki a gida saboda ni yanzu bai zame miki alkhairi ba, babu abinda na rasa Anni, dukiya, mace, 'yaya, ga kuma ke da kika zamo jigo a rayuwata, kece mafarin komai Anni, hawayen da ya zubo a idonta ta share tace "Uba" Abdallah, ka rasa uba, tun kana ciki ake min kallon fasika, har fitowarka duniya ban huta ba saboda kiranka shege da akeyi, nasani kayi min kawaici na rashin ganin laifina akan rashin sanin inda ubanka yake, A yau ma abun da na saba fada maka shi zan fada maka, wallahi tallahi Abdallah kai dan Aure ne, sunnar manzon Allah ita ta samar dakai, amma babban abin takaicin shine har yanzu bazan ce ga inda mahaifinka yake ba.... ta karashe da kuka mai hade da tari...... (Twist) karku rude ku biyoni da muje komai zai warware.... Daddy nayi magana da papa akan ina so a bani daya daga cikin yaran mama suwaiba mu rike, yardarshi tasa nace bari in tambayeka ko za'a bani, ajiye cup din hannunshi yayi yace "banajin ki Reemah, na yarje miki ki dauki zainab domin itace karama, ita take bukatar uwa irinki, ita kuwa Nadeeya yanzu ta girma gara ta zauna anan ta cigaba da makarantarta, Allah yayi miki albarka, ya kara miki soyayyar yan uwanki a cikin zuciyarki, Ameen Anty Reemah tace hade da janyo abin cire farce ta cire mishi wata kumba da ta dago a kafarshi.. yaushe zaku koma ne? Daddy ya tambayeta yana taba gurin da ta cire farce,, jibi in shaa Allahu Daddy, to Allah ya kaimu.... ta amsa da Ameen sannan suka cigaba da hirar ya da mahaifi... Mrs Tijjani shattima [09/03 6:50 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣2⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Karar da wayarshi keyi ne ya sanya shi jan tsaki hade da mik'a hannu ya dauka, kara ta yayi a kunnen shi, "uhmm *Meerah* Hw u, ya fadi kamar mai cin magani, daga daya bangaren tace "nt good kangiwa! Cire wayar yayi a kunnenshi ya kalli screen din yayi tsaki a hankali hade da mikawa Musaddiq, deal with her pls, inada abun yi, murmushi Musaddiq yayi ya karbi wayar cike da barkwanci yace "Meeran Kangiwa, kin ma manta da Allah yayi ruwan Musaddiq a doron duniya ko, bude baki tayi tace "laaaa small uncle kayi hakuri, kana raina kullum, in na kira kangiwa bai cika picking ba, kuma bani da contact dinka, am so sorry plss, "a'a haba bakomai, ba gashi yanzu mun gaisa ba, just pulling ur legs ne dama, ya karashe cike da zolaya, So ya gida nd su Adeel? Lafiyarsu kalau we missed u alot ta fadi murya cike da farin ciki, ummm really ya fadi hade da cewa "i missed u guys more more, barin ma su Adeel, plss my regards to them, "zasuji in shaa Allah Small uncle, Hira sosai suka cigaba dayi, duk ta gaji tana son tambayarshi Hilal, da ya fahimci haka yace "sorry fa, bari in baki mutumin, duk na cika ki da surutu, murmushi tayi tace "ba komai naji dadin hirar ai, mikawa Hilal wayar yayi hade da dauke kai saboda irin hararar da yake watso mishi, kara wayar yayi a karo na biyu, bai barta tayi magana ba yace " sorry Meerah, will call if am chance, bai bata damar sake yin magana ba ya katse wayar... "Bakyau, wannan wulakanci ne, ba kai ka kirata ba kuma ta kira sai ka kashe mata waya, is nt fair wallahi, Musaddiq ne ke magana rai a bace, Meerah na matukar bashi tausayi yadda take bin Hilal shi kuma yana wulakanta ta, "Na taba rokonta nace ta dinga kirana Mr Soft? Hilal ya jefo mishi tambayar yana mishi kallon jiran amsa, Tsaki Musaddiq yayi yace "its pointless talking to u, bazaka gane ba sai ka tsinci kanka a shoes dinta, Da sauri Hilal yace "i pray not to in shaa Allah, ka gane ne ko, mace da kamun kai aka santa, ya zata dinga kiran namiji every nw nd then, haba, ita bata ko jin kunya, nawa nake da mace zata fara min kwainanen soyayya, komai yana da lokaci, lokacin da zan sa kaina a cikin soyayya yana nan zuwa, runtse idonshi yayi yana siffanto Nadeeya ya cigaba da cewa, Soyayyar ma wacce babu irinta a fadin duniya... banza dashi musaddiq yayi ya ja takalmanshi yasa ya fita, Dariya Hilal yayi hade da daukar jakar laptop dinshi yabi bayan Musaddiq... A zaune suka samu Mummy tayi tagumi tana tunani, gefenta Musaddiq ya zauna ya cire mata tagumin yace "Mummy na menene? Kallonshi tayi zuciyarta duk ba dadi tace "babu komai Diku, har kun tashi?, ina Hilal? Kafin Musaddiq ya bata amsa Hilal ya zauna kusa da ita yace "an tashi lafiya Hajiya, shafa kanshi tayi tace "lafiya kalau, har ka shirya, naji ance gobe zaku tafi, cike da mamakinta Hilal yace "eh Mum ta fada min, mikewa tayi tace "bari in hado muku break fast, gyada kai sukayi hade da binta da kallo suna mamakin sabon canjin da suka gani tare da ita, gab da zata shiga kitchen suka kusa karo da Nadeeyah, da sauri taja baya ta tsuguna har kasa ta gaisheta, murmushi tayi ta dago ta tace "Lafiya kalau Nadeeyah, har kin tashi, gyada kai tayi tace "eh na tashi, hannunta Mummy ta kama suka wuce dakin mai aikinsu tace "ina kayanki suka, can lungu ta janyo jakar kayanta tace "gasu nan, kiran mai aikin mummy tayi tace ta dauko kayan ta biyosu dashi, da sauri ta dauki kayan ta bi bayansu, dakin su Badar Mummy ta bude suka shiga ciki, bacci ta samesu sunayi dukkansu, basa ko motsi kamar matattu, kallon Nadeeyah mummy tayi tace "nan ne dakin da zaki dawo, ga drawer nan, akwai wacce babu kaya a ciki, sai ki saka kayanki, a darare tace "Mummy dan Allah ki barni a can dakin, shima yayi sosai,, kafadunta mummy ta dafa tace "dake da su Husna duk daya ne a gurina, in har zan barki a dakin masu aiki, to tabbas zan bar su Husna ma a can, ki saki jikinki nan ma gida ne kinji ko, share kwalla tayi tace "Eh mummy, nagode sosai, kara share mata hawayen tayi tace "babu godiya tsakanin 'ya da uwa, jeki maza ki fara shirya kayanki kizo mu karya, saida Mummy ta fita tafara jan jakarta jiki a sanyaye, bude drawers din tayi tagansu cike da tsala tsalan kayan su Badar, drawer can karshe ta bude, babu komai a ciki sai zanin gado da towels, fito dasu tayi ta maidasu kasa, sannan ta fara fito da kayanta tana jerasu a ciki, tana gab da gamawa taji an saki ashar mai wuyar fadi a bayanta, juyowa tayi taga Badariyya tsaye rike da kugu, "keeee, uban waye yasa ki shigo mana daki har ki bude drawer ki zuba wadannan tsummokaran naki? Nadeeyah bata kula ta ba ta juya ta cigaba da fito da kodaddun kayanta tana cigaba da jerawa, a harzuke Badar ta fincikota tayi wurgi da ita, "ke har kin isa ina miki magana kiyi banza dani, leda ta dauko tasa a hannunta ta fara fito da kayan tana fadin "bazan iya taba dirty kayan nan da hannuna ba, ke in banda ma shegen tsaurin ido har kina da confidence din shigo mana daki ki fara jera kayanki, baki ma da hankali tunda har baki iya bijirewa kice dakin yafi karfinki ba, rufe drawer tayi bayan ta gama fito da kayan tace "oya oya maza hada tsummar roba robarki ki kara gaba, nan dakin yafi karfin kazamai irinki, Nadeeyah bata amsata ba ta tattara kayanta cikin jaka ta sa a can wani lungu ta yi hanya fita parlor, da karfi Badar ta janyo mata hijab har yana shaketa, harararta tayi tace "uban wa kika barwa kayanki? dalla wuce ki dauke mana su ko dakin mu zai samu saukin wari, cikin sanyin Murya Nadeeya tace "Badariyya sake min Hijab kin kama min wuya, "bazan sake ki ba, Badar ta fadi tana girgiza jiki, Kwacewa Nadeeyah tayi da kyar, ta dauko jakarta ta bude kofar palon, dankwalinta da ya fado kasa Badar ta dauko tayi saurin binta dashi ta wurga mata tace "dauki kayan war---- bata karasa fadi ba saboda hada ido da tayi dasu Hilal da Mummy a palon, sakin kofar tayi ta koma ciki ta fada bayi da sauri, a yanayin da taga Hilal tasan zai iya yi ma jikinta lahani, tsaki tayi tace "shigowar yarinyar nan rayuwata babbar matsala ce wallahi, hankalina bazai taba kwanciya ba har sai ta bar gidan nan, tunowa da tayi an kusa komawa school yasa ta sakin murmushi tasan in ta tafi school zasu dan sarara.... A tare Musaddiq da Hilal suka mike suka isa gurin Nadeeya, jakar Musaddiq ya karba Hilal ya bude dakin yana kwala ma Badariyya kira, farkawa Husnah tayi a tsorace tace "ya Hilal lafiya, "ina Badariyya?, ya tambaya yana huci, bargonta Husna taja tace "anan take kwance sai dai ko in tana toilet, hanyar toilet din yayi mummy tayi saurin tare shi, tace "kwantar da hankalinka, barni da ita, Nadeeyah dauki kayan ki sa a drawer, jin muryar mummy yasa Badariyya fitowa a bayin tana kukan da ba hawaye, "Mummy fa ba wani abu na mata ba, cewa nayi kayan sunyi datti kuma sun kode ta fitar mana dasu kar ta kawo mana kudin cizo, kuma mummy ki kalli gadon yayi mana kadan mu uku, dan Allah ki barta ta koma dakin da ta sauka, Dunkule hannu Hilal yayi zuciyarshi na tafasa, baya son kai mata duka saboda kunyar idon mummy da suka fara dasawa yau, jiran hukuncin da zata yanke yakeyi, in baiyi mishi yaje ya roki Papa kawai a hada Nadeeyah da zainab su tafi tare, Murya a kausashe Mummy tace " Nadeeyah a dakin nan zata zauna cikin yan uwanta, dukkanku 'ya'ya na ne, babu wanda yake bare a cikinku, ya zama dole ku koyi zama tare saboda zumuncinku yayi karfi, kallon Husna tayi tace "maza matso ki tayata ku jera kayan, ke kuma Badar, bana son tashin hankali, Nadeeyah yar uwarki ce, kaddara ce ta sanya kukayi nesa da juna, yanzu kuma Allah ya hada ku, kuma kinsan baki da yadda zakiyi da hadin Allah... Ajiyar zuciya Hilal yayi a ranshi yace "Allah yasa Mummy ta daure a haka, yanzu ne zai tafi hankalinshi a kwance, yafi son yayi nesa da ita ta samu damar yin karatunta ta zama cikakkiyar mace, yasan in har yana ganinta kullum bazai iya controlling kanshi ba, dole yayi abin da zata gane halin da yake ciki, shi kuma ba yanzu yake son furta mata ba, yana matukar tattalin kalmar har sai ta cimma lokacin ta..... Karfe 5pm suka dawo gida hannunsu rike da ledoji, kalolin jallabiya guda shida Hilal ya siyo ma Nadeeyah, sai flat shoes guda biyu milk nd brown, dayar ledar kuma jallabiya ce guda biyu, kwala kiran Husna yayi, da sauri ta fito daga kitchen tana tsane hannunta tace "ya Hilal gani, "ledar ya mika mata yace "wannan naki ne, kinsan yanzu mun fara dasawa, tsalle tayi tana ihu tace "Thank u *bro Son* , bai damu da sunan da ta kirashi ba yace "wannan ki kaima Nadeeyah, kinga kayanta duk sun kode, zan ma Anty Rally magana sai kuje kasuwa a samo mata yan atamfofi, karbar ledar tayi tace "ummm ya Hilal ashe dai kana da kirki, gaskiya thank u, kamar kasan in tasa kaya abin na dan taba ni, wasu ma sun mata kadan, Murmushi jin dadi yayi yace "yauwa gaskiya i love u, u will be my personal person daga yanzu, dariya tayi tace "godiya nake, gashi gobe zaka tafi, gaskiya zanyi missing dinka, bari naje na kai mata, nasan zata ji dadi.... Bude kayan Husna tayi ta dinga yaba kyawunsu tana gwadawa a jikinta, tana cikin gwada wata ja a cikin na Nadeeyah Badar ta shigo dakin, zama tayi a gefen gado ta dauki daya a ciki tace "waye ya kawo mana jallabiya, shine har kika fara zaba baki jirani ba ko ta fadi a gadarance, kwacewa Husna tayi tace "to Mummy kiyi hakuri, ya Hilal ne siyan ma Nadeeyah, ta dauko nata tace 'kinga nawa nima, wayyo, ai kamar Husna ta watsa mata ruwan zafi haka taji, dama duk yau cikin kunci ta wuni saboda yadda Mummy tayi wata wuzu wuzu akan Nadeeyah, mikewa tayi idonta ya ciko da kwalla zata bar dakin, tausayi taba Husnah tace "sis zo wasa nake miki, guda biyu ya kawo mana ni da ke fa, sauran ne na Nadeeyah saboda bata a kaya, bata saurareta ba ta fita daga dakin dan tasan Hilal bazai taba yi mata kyauta ba, ninke kayan Husna tayi ta maidasu cikin ledar ta wuce kitchen ta kira Nadeeya, A tsorace Nadeeya ke daga kayan tace "duka nawa ne? gyada mata kai Husna tayi tace "u are very lucky, yaya Hilal bai taba kyautar ko da naira dari biyar ba, yaushe ma kaga fuska a gurinshi bare ya baka, sai gashi yau har ni ya hada, dark blue din ta dauko a ciki tace "gwada wannan nasan zata miki kyau, bayi taje ta sa a jikinta, fadin rigar yayi mata cibb saboda tana da dan jiki, sai dai tsawon ya so yayi mata yawa, madubin bayin ta kalla hade da gyara gashin da ya kwanto a goshinta, ita kanta ta yarda a zuciyarta rigar ta mata kyau, dakyar ta iya fitowa daga bayin saboda kunyar Husna, wooooww.. Husnah ta fadi a fili, a cikin ranta kuma tace "see beauty, oh Gosh, Allah baya bawa mai wuka nama, "kinga yadda yayi miki kyau kuwa, kunya ce ta ishi Nadeeyah tace " nagode, bari inje in cire, tareta Husna tayi tace "godiya dai zamu je kiyi ma "ya Hilal, daburcewa Nadeeyah tayi tace "a'a dan Allah bari in canza kaya sai muje, dagewa Husna tayi tace lallai sai dai suje a haka, dakyar ta yarda ta yafa gyalen a kanta, murda kofar dakin suka ji anyi, a tare suka waigo, daburcewa Nadeeyah tayi ganin Musaddiq da Hilal tsaye a bakin kofar, karasowa ciki Musaddiq yayi cikin zolaya yace "a'a iyye, kaga kanwata, ashe dai kina da kyau haka, to juyo ki nuna mana kwalliyar mana, janyo hijab tayi ta cukwikwiye kanta tace "ba kwalliya nayi ba, Husna ce tace in gwada ko zai min daidai, dariya yayi yace "kuma ya miki kyau, ashe dai mun iya zabe, to babu ko yar godiya, kara rufe fuskarta tayi tace "yanzu dama zamu je muyi, kuyi hakuri, Nagode Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen Ameen, muma mun gode da addu'ar da muka roka, gurin Hilal Husna ta matsa tace "ya Hilal kaga yadda kayan suka karbemu, thank u once again, murmushi yayi yace "never mind, kinga mukullin motata cikin kayan nan, zazzage kayan ta koma tayi, babu komai a cikin su, dago kai tayi tace "baya ciki, ko ka barshi a jikin motar? Tunani ya fara yi yace "eh to bari inje in duba, ta gefen ido yake satar kallonta tun shigowarshi dakin, sai da zai fita ne ya kalli yadda ta matse kanta, murmushin shauki yayi ya fita zuciyarshi wasai saboda yadda yaga ta fara samun sakewa a gidan..... Jirgin karfe shida na yamma zasu bi, tun safe Hinad da Zainab suka tafi saloon suka wanke kansu akayi musu kitso, daga can gidan Mummy aka wuce dasu, nan suka yini har bayan la'asar sannan suka soma shirin tafiya, har bakin mota ta rakasu tana dada yi ma zainab nasiha, saida taga sun shiga motar sun zauna ta kalli Zainab da idonta ya ciko da kwalla tace "kuka kuma zakiyi, to bari in tafi in barki tunda kuka zakiyi, hannunta Zainab ta rike tace "Adda zan tafi in barki a gidan mummy su dinga saki kuka, meyasa bazaki zo mu tafi ba, share mata hawaye Nadeeyah tayi cikin dakiya tace "inji wa yace miki zasu sani kuka, bana nuna miki kayana da mummy ta kawo min ba, yau ma tace zata kuma kawo min wani, kar kiyi kuka kinji dukkan mu zamuji dadi, gyada kai Zainab tayi tace "Haka mumyn Hinad tace min, sake matse hannunta tayi tace "banda rashin ji kinji, in kikayi rashin ji zasu fada min, ni kuma sai inyi ta kuka anan, kinaso inyi kuka, girgiza kai tayi da sauri tace "a'a bana so, bazan kuma yi rashin ji ba, kumatunta Nadeeyah taja tace "good girl, hira suka cigaba dayi suna jiran drivern yazo suka hango motar Hafeez ta shigo gidan, da murna Nadeeyah taje gurin shi tana mishi barka da zuwa, rungumeta yayi suka wuce gurin su Zainab, ta window zainab ta fito ta dane wuyanshi tana murna, komawa mota yayi ya dauko katuwar leda yace "wannan sweets dinku ne ke da Hinad, kuma saura inji labarin kin mayar da shi abincinki, kara kankameshi tayi tace mun gode yaya, amma zaka dinga zuwa gurina ko? "Kullum zaki ganni, kedai kiyi karatu, banda rashin ji, banda takurawa mutane akan abin da babu kina ji na ko, gyada kai tayi tace "duk na sani Adda Nadeeya ta fada min, motar ya mayar da ita yace "to Allah ya kiyaye hanya, Hinad ki gaida Anty Reemah kinji, "in shaa Allah zan fada mata, ta fadi tana murmushi, hannu suka dinga dagawa juna har motar ta fita, kallon Nadeeya yayi yace "kina nan dai lafiya ko? Amsa mishi tayi da "lafiya lau yaya, labarin canjin da mummy tayi ta bashi sannan ta kara da hidimar dasu Hilal suka mata, hira sosai sukayi kafin ya shiga ya gaida mummy, bayan sun gama gaisawa yace ma mummy zai koma Gombe, akwai makarantar da yayi applying, sun mishi email ya samu shine zaije ya fara registration, addu'oi ta jero mishi na fatan alkhairi sannan ta tambayeshi in da ya ajiye sarkar da Goggo ta basu,. damun da Goggo tayi mata akan sarkar ba kadan bace, nuna mishi tayi bata san sarkar ta salwanta, Murmushi Hafeez yayi yace "tun ranar da aka bani Daddy ya karba, bata kwana a gurina ba, murmushin yake mummy tayi tace "yauwa ai kaga tana gurin Babba ya fi, Allah yayi muku albarka, amsawa dukkansu sukayi sannan Hafeez ya tashi ya tafi cike da kewar yan uwanshi...... Mrs Tijjani Shattima.... [09/03 9:57 PM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣3⃣ By *Aysha Ya'u kurah* A makare suka isa airport din, sauri sauri suka shiga inda ake layin shigewa gurin da jirgin yake, kallon Musaddiq Hilal yayi yana son mishi magana amma bakin shi yayi nauyi ya gaza furta komai, to me zai ce mishi, in yace ya kula da Nadeeyah, ya zai dauki kalmar a cikin zuciyarshi, saida layi yazo kansu sannan yayi musu sallama cike da kewa ya juya ya koma gurin motarshi,, Yana shiga kafin ya tada yaga wayarshi na fitar da haske alamar kira, "har ka fara missing dina? Musaddiq ya fadi yana dariya, daga daya bangaren Hilal yace "come on wani missing, hutawa ma zanyi da matsalolinka Mr soft, dariyar Musaddiq ya sakeyi yace "to why did u call, admit kawai *Head of elephant* , dariya sukayi dukkansu sannan Hilal yace "Zee ce tace in kiraka, and tace in fada maka kasa mata ido akan yayarta, gata nan kwance duk ta damu, canzawa wayar kunne yayi ya rage sauti yace "Plss Kyari ka kula da yarinyar nan, kasan bata da kowa, nd Daddy bai cika zama ba, kai ne mazaunin gidan for nw kafin ka samu aiki, dan Allah ba sai ta tambayi wani abu ba, u shud knw abinda mace ke bukata every nw nd then, kawai tausayi suke bani, at der early age sun rasa iyaye duka, plss try kyari kaima ka zama jajirtaccen namiji ya karashe cikin shakiyanci, gerraut Musaddiq ya fadi yana dariya, dama ni ai jajirtacce ne, kawai dai.... bari ma dai meyasa nake fada maka, and karka damu tana bani tausayi as well, in shaa Allahu bazan bari tayi lacking komai ba, kuma zansa ido akanta, "yayyy dats my Good Boy, shiyasa nake sonka kanina, kuma kasan sosai fa nake sonka,Hilal ya fadi yana dariyar tsokana. "And i hate u ni kuma Musaddiq ya fadi murya a kausashe, dariya sosai Hilal yayi yace "chill kanina zamu shiga jirgi, take care plss, bai jira amsarshi ba ya kashe wayar ya isa gurin jirgin cike da annashuwa..... Satittika sun zo sun wuce, zaman gidan mummy a gurin Nadeeyah ya zama babu yabo babu fallasa, kula sosai Musaddiq yake bata duk da bata cika sakin jiki dashi ba, ita ma Husnah duk da tana shakkar Badar takan zauna suyi hira jefi jefi da Nadeeyah, kyawun Nadeeyar da yanayin jikinta ke matukar burge Husna, ita haka Allah yayita tanason ganin farar mace, uwa uba farin ya hada duk ingredients na dangin kyau, Matsalarta Nadeeyah 'Badar ce kadai, shima sai sunzo bacci, ta dinga zaginta kenan tana fadin saidai ta kwana a kasa, wani lokaci in Husna tasa baki fadan ya dawo kanta, haka dai Nadeeya ta maida gurin kwananta kasa kan bargo dan dai hankalin kowa ya kwanta, saboda mugunta irinta Badar sai ta kure a.c. ta kuma dukunkune a cikin bargo, in sanyin yayi yawa cikin dare sai Husna ta tashi ta rage ko ta kashe gaba daya ba tare da Badar ta sani ba, saidai in safiya tayi kaji hayagagar ta tana masifar dalilin da zaisa a dinga kashe mata a.c., kullum haka sukeyi har Husna ta gaji da kashewa, in taga sanyin yayi yawa sai ta tashi Nadeeyah ta matsa mata su kwanta, da yake tana rigasu tashi shiyasa Badar bata ganewa.... Zaune suke a tsakarsu gidan ta can baya, Badar na gyara kumbar ta, ita kuma Husna na tsifa, dayake kalaba ne shiyasa take tsefewa da hannu, kallon Nadeeyah tayi wacce take zaune tana taya mai aikunsu gyaran cabbage, "Nadeeyah yaushe zaki koma school? Barin yankan Nadeeyah tayi tace "15th, bude baki Husna tayi tace "jiya kenan, gyada kai Nadeeyah tayi tace eh amma zan iya komawa next week, "tabe baki Husna tayi tace "kuma kinajin dadin boarding? Kai ni ai bazan iya rayuwar wani guri, in ba gida ba, dariya Nadeeyah tayi tace "kuma akwai dadi, mutum na koyan abubuwa da dama na daga halin mutane, mabanbantan mutane kake haduwa dasu masu halaye kala kala, comb Husna ta dauka tace "ni fa koma meye bazan iya ba, kema da zaki yi ma Mummy magana a canza miki makaranta ki dawo day da yafi miki,, sai a sannan Badar tasa musu baki, "miss I too knw, madam over sabi, ai sai ki canza mata, tsaki taja da karfi ta mike hade da cewa "wallahi shegen iyayinki ya fiki karfinki, ita tasan public school ne daidai ita, in kuma kina da kudin canza mata sai ki bada himma tasa kai ta shige kitchen tana hararar Nadeeyah, tsaki Husnah tayi tace "gama muje ki rakani saloon ayi min kitso, kema sai ayi miki kiji dadin kanki, gurin famfon tsakar gidan Nadeeyah ta kai cabbage din ta kunna ta wanke shi tass ta tsane, tace ma Husna "na gama! muyi sallah sai mu wuce, da to Husna ta amsata suka wuce ciki, abubuwan Badariyya sam basu dameta ba tunda tana samun sassauci a gurin Husna... Yana gama nunawa plumber gurin dake zubar ruwa daga sama ya biyo ta kitchen dan duba ko akwai inda ke toshe a makwarar, tsaff yagama saurarar maganganunsu, maganar Badariyya ta tsaya mishi a rai, "wai yarinyar nan me ta dauki kanta ne, danne bacin ranshi yayi yakoma ya shiga ta parlonshi, a gurin dining ya samu Mummy tana hada plates din da suka ci abinci shi da bakinshi, gyaran murya yayi yace "Zainab wani class Nadeeyah take? Tunani Mummy ta farayi tace "mate din su Husna ce nasan class dinsu daya, zama yayi akan kujera yace "ki fada mata gobe su shirya tare da su Husna zan kaita makarantarsu ta karasa acan, duk da taji ba dadin yadda yakeson hada Nadeeya da ya'yanta baisa ta nuna mishi ba saboda yadda take taka tsantsan da zamansu, amsa mishi tayi da "to Allah ya saka da alkhairi, bai amsa mata ba ya cigaba da kallon tv.... Shiryawa tayi cikin wata koriyar atamfa mai ratsin ja, dinkin zamani riga da straight skirt mai tsagu, rigar kuma matsatstsa mai budadden hannu, tayi kyau sosai, Husnah ce ta bata a cikin kayanta da suka dan kamata dan tafi Nadeeya fadi kadan, dankwali ta daura ta kunshe kanta ta dauko hijab zata sa, fisgewa Husna tayi tace "u are a joker, wa zaki bi da wannan hijab din, gyale ta miko mata tace "dankwalin ma cireshi zakiyi, kallon Husna tayi tace "da wannan matsatsun kayan zan fita babu hijab? gyada mata kai tayi tace "hango kanki har kin fita ma, zatayi magana Husnah ta kwacee dan dankwali ta turasu cikin drawer ta rufe, shiryawa tayi tana waka tana rawa tana ma Nadeeyah gwalo, ita abin dariya ma ya bata ta sake kallon kanta a jikin madubi, babu ta inda kayan nan basu bayyana surorin ta ba, marairecewa tayi tace "kiyi hakuri Husna ko dankwali ne in daura, bata saurereta ba ta fara shafa mata powder tana fadin "ki cigaba da butulcewa Allah, dan dai So ba samu bane, wallahi da nice tsirara ne kadai bazanyi yawo ba, lallausan gashinta ta taje mata tayi mata parking da katon ribon, light janbaki ja ta bata tace "ki dan sa kadan kiga yadda zakiyi, amsa tayi tadan goga a bakinta, gurin madubin Husna ta jata tace "dan Allah kalla, kamar a bakinki aka halicceshi, mtsww taja tsaki hade da cije lips tana hango inama akai Nadeeyah school dinsu tayi ma gayu iskanci, ta nunawa *SABRINAH BILAL* ba ita kadai aka halitto da kyau da sura ba, gyale ta daura ma Nadeeyah a kanta irin yadda tayi tace "muje ko, a kunyace Nadeeyah ta bi bayanta tana tunanin yadda zata fita da kayan nan ba hijab, Fitowarsu tayi daidai da mikewar Badariyya, hade da fitowar mummy daga parlon Daddy, fassara yadda idon Badar ke nuna tsantsan tsana da kishin Nadeeyah mai wuyar fadi ne a alkalami, bata ankara ba taji Mummy ta sake furto maganar da taji ta kamar saukar Aradu, "yawwa Nadeeyah gobe ki shirya da wuri zaku je makaranta tare dasu Husnah, wani irin tsalle Husna tayi tace "so quick Ya Allah, lallai luck is on her side today, kallon Badariyya Mummy tayi tace "ke bazaki kitson bane? dauke kanta tayi tace "umm bazanje school ba gobe, tana kaiwa nan tayi hanyar daki, dakatar da ita Mummy tayi tace "saboda me? Kafin ta bata amsa Musaddiq ya shigo parlon yana hamma, tsayawa yayi daga nesa yana kallon Nadeeyah daga sama har kasa.. Karasowa yayi ya kewayeta yana kallon fuskarta da ta sunkuyar kasa, murmushi yayi yace "tsarki ya tabbata ga ubangijin da halicci kyawawan mata a cikin gidan mu, ina zaku je da irin wannan kwalliyar, Kusa dashi Husna ta matso tace "saloon, ko zaka kaimu ne? bata fuska yayi yace "na kwaso rana, bacci nakeji amma bazan iya refusing daukar kyawawan kannena a mota ba, kallonshi Mummy tayi tace "kyalesu su tafi Diku, jeka ka huta abinka, girgiza kanshi yayi yace "bari in kaisu Mummy, zanyi aski nima, jin haka ya sa Badariyya sakin ranta tace "Mummy su jirani nima zanje kitson, bata rai Husna tayi tace "wallahi Mummy Badar bata mana lokaci zatayi, harara mummy ta sakar mata tace "in ma zata kai la'asar sai kun jirata, turo baki Husnah tayi suka dawo parlon suka zauna, Wayarshi kirar iPhone x max ya ciro a aljihu ya kalli Husnah yace "meye zai bata ran autarmu, tashi muje waje inyi miki hoto da portrait camera, sanin halinta nasan hoto yasa shi fadin haka dan ya kwantar mata da hankali, da sauri ta bi bayanshi tana kiran Nadeeyah da tazo suyi tare, kin fitowa Nadeeya tayi saboda yadda mummy ta kafa mata ido, kyawunta da ta gani na yau da yafi na ko yaushe shi ya daga hankalinta, bata so samm Musaddiq ya fada tarkon kyawun nan, taci buri akan nema mishi 'yayan abokan Daddy ministoci dan samun karin girma a idon kawayenta, dole ta san abin yi akan irin wannan kwalliyar da Nadeeya ta fara yi, dawowa Husna tayi taja hannunta suka fita dan yin hoton.. Hotuna sukayi masu matukar kyau kamar an wankesu, wanda sukayi su biyu shi yafi komai yi mishi kyau, suna gama hotunan ya gyarasu ya daurasu akan status dinshi da instagram, bai rage ko daya cikin goman da suka dauka ba, yana gama daurasu ya sauka dan ganin fitowar Badariyya, gaba Badariyya ta bude da sauri ta shiga ta zauna, kallonta yayi ya kasa cewa komai yashiga ya waigo ya kalli su Husna a baya, tada motar yayi suka wuce, ta gefen ido Badar ke satar kallonshi, shi kuwa hankalinshi na kan titi yana tambayar inda zasu, cikin doki Husnah tace *MEENA'S TOUCH* Sabon saloon din da Anty Amina ta bude, ta madubi ya harereta yace "inada Allahn misirun sanin shagon kenan, kafin Husnah ta bashi amsa Badar tayi saurin cewa " *Kura plaza* bai sake magana ba ya dauki hanyar Yakubu gawon way.. Yana saukesu ya bawa Husna dubu shidda yace "bani da enough ku kara, kinsan nima sammin akeyi babu aikin yi, dariya tayi tace aiki kam zaka samu yaya, kaima kasani, lokaci ne, dariya yayi ya wuce yana dagawa Nadeeyah hannu... Wayarshi ya dauko a inda ya ajiyeta, yana bude ta kiran *Haidar Galadanci* ya shigo.. Dauka yayi yana dariya yace "Head Boy how far, ya kake, daga daya bangaren Haidar yace "fine kyari, kana ina ne? Taka birki yayi da karfi saboda mai mashin din da shigo mishi, tsakii yaja yace "ina gurin Leventis zanje waff road any probs? Kwantar da murya yayi yace "Kyari naga bebs din story dinka, plss farar fa, kanwarka ce?, nasan Husna, ban dai gane farar bane, dariya sosai Musaddiq yayi yace "kanwata ce Galadanci, kafin ya karashe maganar yaji kiran Hilal ya shigo wayarshi a karo na uku, hakuri ya bashi ya katse wayar dan ya dauki ta Hilal, kafin ya dauka ma ta katse, duba missed calls yayi sunfi hamsin, Hilal kadai talatin da uku yayi mishi, sai sauran daga abokanshi, kafin ya kira Hilal wayarshi ta shigo, bai jira jin kalmar Hello ba saboda baya cikin nutsuwa da hankalinshi yace "dis is madness Kyari, in banda rashin hankali ya zaka sanya hoton yarinyar nan a ig, a story is understandable, but ig is very bad, duk inda ka zaga su arewa cuties nd co hotonta ne ke trending, ya zakayi exposing dinta haka, wat is the need of all dis, kuma baka ma duba kayan jikinta ba kawai ka tashi ka sata a social media, idon mazan duniya su gama ganeta, am very angry with u wallahi, tunda ya fara masifar musaddiq yayi parking, saida ya gama zazzaga masifar yace "ka gama? Tsaki Hilal yayi yace "ban gama ba, ka hau kaga banzayen comments din da akeyi maka, na rokeka ka hau ka cire hotunan nan, cikin fada musaddiq yace "Bazan cire ba, nace bazan cire ba, hoton ta ita kadai nasaka, au su sauran matan da suke saka hotonsu ba mata bane, a fusace Hilal yace "ba irin su bace kyari, ka kasa fahimtar ba irin matan da za'a dinga exposing bace, yawo kalmar ta dingayi cikin kwakwalwar musaddiq yace "wat do u mean, kana nufin bata kai matsayin da zata hau instagram ba, ko kuwa tana da makusar da--- katse shi Hilal yayi yana share zufar da ta addabashi tun ganin hotunan da comments din abokan musaddiq yace "bazaka gane ba Kyari, taushi yayi da muryarshi ya cigaba da cewa "rayuwarta zaka duba, marainiya ce, a yanzu gatanta shine ilimi, wannan gayun ba nata bane, ilimin shine zai zamo gatanta gaba da baya, yanzu wannan hoton baka san abubuwan da zai janyo mata ba, samari zasu fara kawo mata hari, daga nan shikenan zasu zo su--- runtse idonshi yayi kafin ya furta kalman *aureta*, at end of the day kuma rayuwarta zata kare a bauta, wasu kuma will come su yaudareta, wasu su lalata ta, plss Musaddiq ka cire hoton nan, cike da gamsuwa Musaddiq yace "very true, kamar kasan yanzu *Galadanci* ya kirani akanta and lots more, gara da ka fahimtar dani, bari inyi maza in cire... Safa da marwah ya dinga yi a cikin dakinshi, pencil din da yake zane dashi yayi dagaga a bakinshi saboda tauna, hoton ya sake kallo kashi na ba adadi yace "ya Allah ka cire idon duk wani namiji akan hoton nan, yana cikin haka yaji karar notification din story a ig, *Husnah_kyari is live on instagram* da sauri ya hau, yana budewa ya zauna dabass, *what is dis, ya ilahi!! Ya fadi yana rike kanshi, video Husna tayi musu da kai a bude, gashin Nadeeyah ya sakko har baya, a juye take tana parking din kanta, bata san Husna na mata video ba, tsaki yaja sannan ya lalubi number wayarta, a zuciyarshi yace "kasheshi suke so suyi, "My Personal person ta fadi da karfi, bai amsa ba yace "tarbiyyar musulmi ne daura video babu dankwali, come on je ki cire shi, dariya tayi tace "done my PP, yanzu zan cire, ajiyar zuciya yayi yace "hope kuna nan lafiya, amsawa tayi da cewa lafiya kalau kowa yake, "Good yace hade da cewa ku kula sosai fa, kunsan samarin yanzu basu da kirki, is hardly su soku tsakani da Allah, ku kama kanku ku daina kwalliya kuyi focusing akan karatunku kinji, gyada kai tayi tace "in shaa Allah my pp, murmushin jindadi yayi yace "bani Nadeeyah, saida yaji kunya da ya fada, cire wayar yayi a kunnenshi ya kalleta hade da jin haushin kanshi, to me zaice mata? , sansanyar muryata yaji tana fadin "Assalamu alaikum, "kara wayar yayi a kunnenshi yace "Alaiki salam, ya kk , lafiya lau ina wuni ta fadi darare, lafiya lau, kinada abubuwa a gabanki kike kwalliya harda wani possing ayi hoto ko?, murya na rawa tace "a'a yau ne kawai, kuma munje saloon ne, dadi yaji har cikin ranshi yace "to ya zama na karshe, karatunki yanzu shi kadai zaki sa a gaba, ko powder ki daina shafawa, u are very ok a haka, ki daure kiyi karatu sosai ki zama independent woman kinji ko? Gyada kanta tayi kamar tana gabanshi tace "in shaa Allah zan kiyaye, "yauwa kanwata take care ya fadi hade da kashe wayar ba tare da ya barta ta bashi amsa ba....... Tun dare Daddy ya kira principal din makarantar, da yake suna ganin girmanshi shiyasa basuyi rejecting ba suka ce gobe a zo da ita a mata interview, godiya yayi mishi sukayi sallama, a waya ya kira Musaddiq yace gobe ya shirya ya kaisu school yayi mata registration, amsawa yayi yace "Allah ya kaimu Daddy... Kallo ne ya koma kan su Husna lokacin da suka fito a cikin motar, jar jallabiya Husna ta zabowa Nadeeya tace ta saka, saboda tayi bagu a makaranta, ai kuwa sun kawo kallo, har a registrar office duk staff din da ya shigo sai ya kalli Nadeeyah, bayan an gama mata komai suka mata interview, dakyar ta wuce saboda karatunsu yayi mata tsauri, Ss3 Art 1 suka kaita saboda Art take a makarantar da ta baro.. Sallama Musaddiq yayi musu ya wuce yana jaddada musu muhimmacin karatu, commerce class Husna take, saida taja ta suka je class dinsu kafin teacher ya shigo, zagayesu akayi ana tambayar Husna sunan sistern ta, murmushi tayi kanta yayi girma tace "She is my cousin, Nadeeyah Adam, wow nice name suka hada baki suka fadi, *Jameelah Aja* ce tace "a sit dina zata zauna, nan fa class din ya kaure kowa na a gurinshi zata zauna harda mazan class din, Dariya sosai Husna tayi tace "to a Art take, tsaki sukayi sukace 1 or 2, one ofcourse Salmah Habeeb ta fadi hade da cewa "wai halan uncle Kamal zabar kyawawa yakeyi ya kaisu art da kanshi badan suna so ba, dariya duka class din suka kece dashi suka ce very true, duk taron kyawawa ne a art, halan gani yayi duk sunfi dacewa da art gidan da babu Maths, Hango Economics teachernsu sukayi kowa ya nemi gurin zama ya nutsu, hannunta Husna taja suka hau sama inda class dinsu yake, daukar excuse tayi gurin Uncle Tahir literature teacher tace "new comer ce sir, uncle Kamal yace a kawota nan class din, kuma yace a bata special treatment, hararta yayi cikin slangs turancin shi yace go to your class, da sauri ta fita tana dariya, kallon Nadeeyah yayi yace "welcome, what is your Name? Gyara baki tayi cike da kunyar kallon da yan ajin suke mata tace "Nadeeyah Adam from Fgc malali, "Good ya fadi yana kare mata kallo, seat din Sabrinah ya kalla yaga ita kadaice bata barin kowa ya zauna, nuni yayi mata da sit din yace "go and sit down der, bata rai Sabrinah tayi fuska da alamar shagwaba tace "sir, Hararta yayi ya cigaba da abin da yakeyi, tana zama tace "sannu, ko kallonta Sabrinah bata yi ba tace ciwo nakeyi? Nadeeyah bata sake kulata ba ta maida hankalinta kan allo... *Gombe state university* 9:34am Monday 17th july, Assalamu alaikum.. Waigowa gungun samarin sukayi suka amsa da "wa alaikum salam hade da mika mashi hannu suka gaisa, dan Allah ina ne Acadamic planning? Hafeez ya tambaya yana gyara jakarshi, kwatance suka mishi yayi musu godiya ya koma motarshi, hanyar da suka nuna mishi yabi, yana zuwa gurin yaga sunan a manne, fitowa yayi da takardunshi ya karasa kofar shiga, layin students ya gani suna turereniya suna mika takardu, wani ya samu a gurin yace "dan Allah ina ne office din Director academic planing, nuna mishi office din yayi ya juya ya kutsa cikin layin, Da sallama ya shiga ya tarar da secertary dinshi, bayan sun gaisa ya tambayeshi ko lafiya, takardu ya mika mishi yace "nazo registration din D.E ne, karbar takardun yayi ya duba yace "kaje waje daga lungu zaka ga wani office ka tambayi ina Hajiya farida, ka bata, amsan takardun yayi hade da yi mishi godiya, yana kokarin fita daga office din yaji an murda kofar wani office dake kusa da kofar fita, dan saurayi ne ya fito fari kyakykyawa, kallonshi yayi ya miko mishi hannu suka gaisa, kallon sani Hafeez yayi mishi, tunanin inda ya sanshi ya shiga yi, "Kai Jamal, ka dauki key din motar ne, waigowa sukayi tare da Hafeez yace "yes Papy, kai fa ka miko min, a wannan karan ba kallan sani Hafeez yayi wa dattijon ba, kallon kamannin da yayi da mukusancin shi yayi mishi, Allah mai halitta, tabbas badan wannan fari bane tass babu abinda zai hanashi cewa shi bane...... Mrs Tijjani Shattimah...... [11/03 4:41 PM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣4⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Har kasa Hafiz ya tsuguna ya gaida dattijon, bai kalli inda yake ba ya amsa yana magana secretary dinshi, Mikewa Hafeez yayi har lokacin idonshi nakan dattijon, waigowar da zaiyi idanuwansu suka sarkafu cikin na juna, nan take wani abu ya tsarga a jikin dattijon, bai dauke idonshi akan Hafeez ba ya karaso kusa dashi yace "your face looks familiar, wani level kake?, cikin girmamawa Hafeez yace "yau na fara zuwa, nazo registration ne, "Good, ya sunanka and wane course? dattijon ya tambaya har lokacin bai fasa kallon Hafeez yana nazarin inda yasanshi ba, "sunana Hafeez Adam, daga kaduna, computer science ne sir! kauda tunanin inda yasanshi yayi dan ya kasa tunowa, shi dai yasan yaron ya shiga ranshi daga ganin farko, kuma a dan fisge idonshi na yanayi da Jamal, kafadunshi ya dafa yace "All the best, Allah yasa ka fara a sa'a, Ameen.. Hafeez ya fadi ya bishi da kallo har ya fita daga office din.... Rashin nutsuwar da bai samu ba saboda registration shiyasa bai koma gurin directorn ba, saida yayi sati uku ya samu nutsuwa har ya fara shiga lectures, a sannan ne ya fara tunanin konawa gurin mutumin dan jin ko yana da wani dan uwa, kamannin sunyi matukar yawa, badan tsufa da haske ba, babu abinda zai hanashi cewa su ba yan biyu bane, saidai wannan ya fishi yarinta, da haske da kuma ilimi... Yana gama cin abinci a cafeteria ya wuce masallaci yayi sallah, yana idarwa ya kama hanyar Academic planing, meeting ya samu suna yi sai ya fita harabar gurin dan ya jirasu, saida yayi jiran awa 3 basu gama ba sannan ne ya hakura ya tafi gida, zuwa academic planing ya zamewa Hafeez kullum, wata rana har yaje sau biyu duk ba sa'a, ko ace suna meeting ko kuma ace yana office din VC.. Ranar friday karfe 11 suke da lectures din Maths method, tun tara na safe ya shiga school ya wuce office din, zama yayi a gurin yana jiran ganin ta inda zai bullo, daga can nesa ya hangoshi yana tafiya sauri sauri secretary dinshi yana binshi a baya da jaka, mikewa Hafeez yayi ya iso gurinshi ya tsugana ya gaishe shi, dafa kanshi yayi hade da mishi alama da ya dago, sannan ya amsa, yace "malam Hafeez har ka gama settling ko? Cike da mamakin rike sunanshi da yayi yace "eh ranka ya dade, kullum sai nazo bana cika samun ganinka, tafiya ya fara yi yace "Allah sarki, schedules din nawa ne are very tight, muje in baka card dina kazo gida ka sameni...... *Kaduna* Cikin ikon Allah Nadeeyah ta fara sabawa da yan ajinsu mata, bata saki jiki dasu a farko ba saboda gudun wulakancin masu kudi, da taga kowa na shige mata sai ta fara sakin jiki dasu musamman *Haifa* da *Amal* su biyun nan su suka zama kawayenta, tun da suka fahimci Sabrinah na jin haushin shigowar Nadeeyah cikinsu sai suka dauke Nadeeya a sit dinta suka maida ita gabansu, duk jan ajin Sabrinah saboda ganin tana da kyau ta saukeshi saboda ganin yanzu duk yan ajin sun raja'a akan Nadeeyah.... " *Badariyyah Kyari* sisternki tana da kyau sosai, Rukky Mama ta cabe da cewar bari kedai Aliya, in muna tsaye a assembly kallonta kawai nakeyi, na rasa cikin jinsin da ta fito, fatarta kadai abar kallo ce, uwa uba yatsun hannu, kamar sun sokawa Badariyya Mashi tayi saurin cewa "ba sister na bace dalla, she is an orphan, kawota gidanmu akayi dan ta dinga tayamu aiki, u knw Daddy is very generous, kawai yaga tunda mate dinmu ce why nt ya sata a school tunda dama ss3 zata, she is our helper kun gane ko!! Kallonta Rukky tayi tace "kaii amma tayi sa'a, ga kyau, gashi ta dace gidan ruko, wallahi in tana wucewa gaban staff room malamai har leke sukeyi, uncle Tahir ne kadai bai wannan saboda class dinshi, shi duk yadda ake koda sabrinah bata gabanshi, shiyasa wannan ma bata d'ad'ashi ba, gajiya Badar tayi da jin maganganu akan Nadeeyah tayi saurin mikewa ta wuce hade da ja musu tsaki... bayanta suka bi da sauri saboda duk yan koranta ne..... Tsaye yake gaban class yana kallonsu daya bayan daya, cikin harcen turanci yace "Ba tambayarku nakeyi ba, kun shirya ma presentation and drama?, groups biyu suka mike suka ce sun shirya, sauran kuwa sukayi kwala kwala da ido, group 3 and group 6 meye topics dinku, ya tambaya fuska a murtuke, "*PLAGIARISM* "Khalifa ya fadi hade da mika mishi printed papers din da suka hada, kallon dayan group din yayi yace and you? Cike da rawar jiki Sabrinah tace *DRAMA, FICTION AND IMITATION*, hannu ya mika ya karbi nasu takardar sannan ya kalli sauran yan class din yace "Kowa yasan dis is your first CA test, to yanzu saboda kun nuna you are not serious na maida shi first nd second and is over 40 no attendance marks, yana kaiwa nan yace duk class din su tafi school Hall su jirashi yazo su fara presenting, cike da tsoro sauran suka fara ihu suna fadin sorry sir, wasu a cikinsu kuma suka tafi cafe dan shirya nasu ko baiyi yawan na sauran ba.... Karfe goma daidai group 3 suka fara presenting nasu, cike da kwarewar turancinsu mai dadi na butters suka gabatar dashi, saida suka gama tsaff kowa ya tafa musu harda observers, Shirye shiryen na dramar group 6 suka fara, saida suka kammala komai sannan suka fara presenting, definition din drama sukayi sai dan short fiction story of Beggars da illolin da irin wulakancin da mabarata ke fuskanta, a karshen labarin ne suka ce "Yanzu zamu yi muku drama akan labarin da muka gabatar... Nan jikin Nadeeyah ya fara rawa saboda tsoron turancinta ba irin nasu bane, Sabrinah da Ishaq sune masu kudi, sai Nadeeyah, Haifa, da Abdulhameed sune maroka, Nadeeyah itace Makauniya tana rike da sanda, sai Haifah kurmah, Abdulhameed kuma gurgu, cike da burgewa suka fara dramar akan stage, da fari Nadeeya taji tsoro, sai da Haifa tayi mata wuzuwuzu ta tunasar da ita marks din da zasu samu sannan ta saki jikinta, da sanda take shafa kasa tana fadin "a taimaki almajira saboda Allah da Annabi, cikin harshen turanci take magana ta karasa daidai inda Sabrinah da Ishaq suke zaune kan dadduma suna shan fruits ta tsaya, "Hajiya a taimaka min da sadaka saboda Allah.. tsaki sabrinah tayi hade da daukar ayaba tace "Mabaratan nan sunyi yawa a kasar nan honey, kuma mostly hausawa, kallon Nadeeyah tayi hade da watsa mata bawon ayaba ta cigaba da cewa "ku ko kunya ma bakwaji, da wannan barar da kukeyi ba gara kuje ku zauna a gida ku jira ranar mutuwarku ba tunda baku da amfani, katseta Ishaq yayi yana murmushi ya daga malunmalun ya fito da dari biyar yace "sweetie, in ba irinsu ta yaya zamu samu kudin, Allah na bamu kudin ne dan ya turo su suzo su amsa, yana mika mata kudin Abdulhameed da Haifa suka fito daga mabanbantan guri suna kokawar kwacewa, ana haka har suka tura Nadeeyah jikin Sabrinah kamar yadda suka tsara a labarin, Sabrinah na ganin haka ta mike hade da manta drama sukeyi ta tura Nadeeyah da iya karfinta, ihu Nadeeya ta saki saboda kafarta daya ta sauka akan stage ta rinjayi dayar, ga tsakanin stage da kasa akwai yar tazara, runtse idonta tayi ta sadakar ko kafarta ta karye ko kuma ta samu mummunan rauni, Bude idonta tayi da sauri saboda jinta hannun mutum da kuma jin bugun zuciyarshi alamar tsoro, kallonshi tayi ta hango manyan idanuwanshi cikin farin glass sunki daukewa a kanta, ajiyar zuciya tayi ta fara kokarin raba jikinta da nashi, sai a sannan ya sauketa ya koma gurin da yake tsaye har lokacin zuciyarshi bugawa takeyi, Husnah da Haifa ne sukayi saurin isowa gurinta suna mata sannu hade da hawa kan stage din inda Abdulhameed da Ishaq suke ta ma Sabrinah masifa, itama jikinta yayi sanyi dan bata taba tunanin Nadeeyah zata fadi kasa ba, hakuri Nadeeyah tabawa su Ishaq tace "mistake aka samu kun sani, kuma faduwar is part of the drama dan a nuna yadda mabaraci ke wulakanta, in Allah yayi muna da rabon marks zamu samu koda 30 ne, kalaman Nadeeyah sunyi matukar yin tasiri a zuciyar sabrinah, nan take taji ta shiga ranta, a zuciyarta tana auno da ita akayi wa haka da sai ta kusa yi ma mutum illa, nan dai sauran groups din suka fara presenting nasu.. Kallonsu kawai yakeyi ba tare da yasan me suke cewa ba, duk kakalen shi na lura da yadda suke fadin words a wannan lokacin bai bi ta kai ba, hankalinshi kacokan ya tafi can wani guri na daban, "Sir here is our presentation, Amal ta fadi hade da mika mishi papers din, glass din idonshi ya cire ya share zufar fuskarshi yace "ku je ku kara shiryawa zuwa next week, ki fada ma sauran groups din, wani tsalle Amal tayi ta wuce da gudu tana announcing, nan Hall din ya kaure da ihun maza da mata, da ganin haka observers suka miko mishi takardu hade da mishi sallama suka fita... "Uncle dafatan munci 40/40, dago kanshi yayi da jin muryar Sabrinah, papers ya fara hadawa yace "ko 20 baku kai ba bare kusa ran 30, Nadeeyah da Haifah dake can nesa dashi gabansu ya fadi, nan Haifa ta taho gurinshi da sauri tace "plss sir karka mana haka, plsss ta karashe kamar zatayi kuka, gurin da Nadeeyah take tsaye ya kalla ya kula da yanayinta yace "minus 5, hada baki sukayi suka ce "wayyo uncle, "minus 2 ya sake fadi har lokacin idonshi na kan Nadeeyah, a hankali ta fita daga Hall din dan kar ta cigaba da jin kayan takaici, tasan kaddararsu ce haka, in ba dagewa sukayi a exams ba dakyar zasu samu C, ganin ta fita yasa shi fara tafiya yana fadin ko A kuka kara cewa sai nayi minusing, yanzu dai kuna da 15/40, gum sukayi suna binshi a baya fuska dauke da kukan shagwaba, Bai ko kallesu har suka fita yayi hanyar office dinshi, jin zuciyarshi yake ta mishi nauyi, duk inda ya wuce yan mata sai sun gaishe shi cike da yanga, ko kallansu bayayi bare ya amsa, shiyasa suka mishi lakabi da mai girman kai.... Kallon kwallon sukeyi Ruwaida na ihu tana fadin "wayyyo zata fita waje, bin kwallon tayi da gudu tana nishin murna ganin ta sakko kasa, tana karasowa gurin taga kwallon a hannun Hafeez, gurinshi ta iso cikin command tace "bani abuna! Dariya yayi ya mika mata, har ta fara tafiya ta waigo tace "gurin Yaya Jamal kazo ko, to bayanan, kaje can farm house ka sameshi, yau dai bai zauna a gida ba bare ku hadu ku hanani mosti a gidanmu, tana karashewa ta murguda mishi baki ta wuce, bayanta ya bi yana dariya har taa kai inda Papy da mami suke zaune, tun daga nesa Papy ya hangoshi suka sakarwa juna murmushi, har kasa Hafeez ya tsuguna ya gaishesu, cikin sakin fuska Mami ta amsa sannan ta mike dan bude musu parlon baki... Hafeez ya ga karamci a gidan Alh Abdallah, saida suka gama yar hira yaje ya gaida Anni sannan suka dawo parlon, kallonshi Alh Abdallah yayi yace "Dafatan dai lafiya, naji kace kullum sai kazo office, sosa keya Hafeez yayi yace "lafy kalau sir, kawai dama dan in gaisheka ne, dadi Alhj Abdallah yaji yace "gaskiya ka kyauta, nima tun ranar da fara ganinka naji kamar akwai bond da ya hadamu, saidai kuma ni---- katse maganar yayi hade da cewa Allah ne kadai ya hada jinina da naka, dafatan zaka dunga zuwa kana gaishemu, in shaa Allah Hafeez ya fadi bakinshi dake dauke da maganar da tayi mishi nauyin tambaya, "a ina ka sauka ne? Papy ya kara jefo mishi tambaya, cikin girmamawa Hafeez yace "ina hotel nan kusa da school, har yanzu ban samu daki ba, wadanda aka samu nesa da school ne sai kuma 2 bedroom ni kuma yayi min tsada da girma, amma ana cigaba da dubawa in an samu zan koma can, gyara zama Alhj Abdallah yayi yace "zama a hotel ai kashe kudi ne, in zaka yarda kuma zaka iya ka dawo nan gida akwai dakuna sai ka zauna har ka gama karatu, cike da farin cikin karamcinsu yace "Nagode sosai sir, Allah ya kara daukaka, Ameen papy yace yana kokarin mikewa, tabe baki Ruwaida tayi tace Papy ka fada mishi ni ce princess a gidan nan, in yana son ya dawo sai ya yarda da bazai dinga min fada ba, kuma zai dinga kaini yawo kullum, dariya sukayi Papy yace "ai shima ya sani, karki damu ranki ya dade, sallama yayi ma su Mamy sannan ya wuce cike da farin ciki, yasan yanzu ya zama kusa dasu zai samu cikakken labarinsu, dan shi al'amarin kamannin suna rikita kwakwalwrshi, ace kamanni har a cikin 'ya'ya, abun yayi yawa..... Mrs Tijjani Shattima.... [13/03 9:18 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣5⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Watanni biyar kenan ina dakon soyayyar dalibata, dalibar da a kullum take kuka dani saboda tsauri na a gareta, juyi yayi akan kujerar da yake zaune bayan ya gama furta wadannan kalaman, agogon office dinshi ya kalla yaga sam baya mishi gudu, ya kosa goma tayi yaje ajinsu, A da zuwa aji yana mishi wuya saboda samm teaching ba layin shi bane, matsa mishi mahaifiyarshi tayi akan lallai sai ya kula da makarantar, ganin ya raina turancin malaman yasa shi daukar literature dan yara su samu ingantaccen turanci da kuma sannin yadda zasu kirkiri wani abu kamar labari domin dogaro da kansu, goma saura minti biyar ya cire medicated glass dinshi ya goge shi sosai, ya maida idonshi, kwantaccen sajenshi ya shafa da hannu hade da gyara zaman hularshi, danyen voile ne a jikinshi baki wanda ya amshi farar kyakykyawar fatarshi, fuskar nan tashi sai kyalli takeyi, Allah ya bashi wani irin sirrin kyau da ido mai narkar da zuciyar mata, duk wanda ya ganshi zai iya sanyashi a jerin yan 30's saboda jikinshi yayi daidai da shekarunshi, har ya kusa fita ya juyo ya dauki script dinsu na second term c.a test, arranging dinsu yayi, yasa nata ya zama na karshe, da gangan yayi failing dinta a script domin yaga yadda zatayi, amma a record dinta ya bata full marks din da taci,  yana dosar class dinsu  hanyoyin sadarwa na jikinshi suka fara charge, ganin fuskarta kadai kan sanyashi manta ko shi wanene, wani irin so yake mata marar fasaltuwa, tun daga nesa Sabrinah ta hangoshi ta fito da sauri ta karbi takardun hannunshi, gaisheshi tayi cike da kwarkwasa tana shishshige mishi, dan sauri ya kara yi yana amsata cike da basarwa, Bayan ya amsa gaisuwar yan ajin idonshi ya sauka gurin sit dinta, ba yadda ya saba ganin ta ya ganta ba, nan zuciyarshi ta shiga damuwa, yaso ta'allaka yanayinta da lokacin sanyi ne ya sanyata labta mai a fuska, ta kuma kunshe kanta kamar mara lafiya, a gurguje ya dan yi musu bayani akan topic din da yazo musu dashi, yana gamawa ya fito da script din ya fara rabawa, wasu suyi murna wasu su kunshe abin su, saida ya gama da kowa sannan ya kira sunan Nadeeyah, kamar mai tausayin kasa ta fito ta karba, tana budewa taga 10 duk sauran zeros, kallon shi tayi idonta ya fada cikin nashi saboda tunda ya bata bai dauke idonshi a kanta ba, kauda idonta da yayi narai narai tayi, nan take kwalla suka ciko su, kafin ta karasa gurin zamanta ta fashe da kuka marar sauti, har lokacin idonshi na kanta, ganin hawayenta ne ya sanyashi daburcewa, A dan ya fara magana yana yabawa da kokarinsu, sannan yace duk wanda yaga ba'a mishi marking daidai ba ya sameshi a office, yana cikin class din aka buga karrawar break, permission ya basu na kowa ya je yai break, takardu ya fara hadawa yana kallon su ta cikin glass dinshi, Amal na karbar script din tana fisgewa, fita yayi a ajin yasan dole in ta duba ta sameshi a office.. Babu yadda su Amal basuyi da ita akan taje ta nuna mishi baiyi mata marking wasu guri ba tak'i, tace musu babu mamaki shi din yaga banyi daidai bane shiyasa, zan dage a exams, cike da masifa Haifa ta fisge takardar tace "ni bari in kai mishi, sai shegen hakuri kamar damo, an fada miki ana hakuri da marks ne, bayanta Amal tabi tace " muje wallahi, sai ya gyara mata, kwala musu kira Sabrinah tayi da karfi, tana haki ta karaso gurinsu da yoghurt da bons a hannunta, karbar script din tayi tace "ku koma class in kai mishi, may be marking ya mishi yawa ne bai gani ba, da kamar su karba sai suka ga itace class rep dinsu suka bar mata hade da nuna mata gurin da tayi daidai.. Excuse sir.., bai dago kanshi daga kasa ba yace yes come in, da sauri ta shiga ta tsaya a gaban table dinshi, tsaki yayi a hankali da yayi gamo da Sabrinah, "lafiya, ya tambaya hade da mikewa kamar yana neman abu, makale murya tayi tace "Sir akwai script din da bakayi marking daidai ba, yarinyar tana can tana ta kuka, kuma ta san ta amsa daidai, murtuke fuska yayi yace "script dinki ne? Girgiza kai tayi tace "nooo na Nadeeyah Adam ne, zama yayi yace "ajiye takardar anan kije ki kirata tunda she is sure of wat she wrote, ajiyewa Sabrinah tayi ta fita tana girgiza ko ina na jikinta, ita dai Allah ya daura mata son Tahir, kasancewarsu makota yasa tare suke zuwa makaranta, komawa ne ba tare ba saboda baya tashi da wuri, ya dade da harbo jirginta shiyasa ya kama kanshi dan samm baya san macce mara kamun kai a cikin maza, ita kuwa Sabrinah ko wani namiji a school din yasanta saboda tsananin kyawunta da rawar kanta.... Tirjewa Nadeeyah tayi tace ita Allah ya kashe ta baza taje ba, zata dage a exams, bazata iya zuwa office dinshi yana kallonta dayday yana wulakantar da ita ba, ga turancinshi ya mata tsauri bama ta gane abin da ya ke cewa, haka nan su Haifa suka hakura sukayi banza da ita su a dole sunyi fushi, har aka tashi a gida basu kalleta ba, kamar bakinsu na ciwo suka ce "Nadeeyah sai gobe Allah ya kara sauki, share majinar hancinta tayi tace "kuyi hakuri ku fahimceni, basu ko tsaya saurararta ba suka fita, school bag dinta ta rataya ta fito itama, a gurin sauka kasa ta hadu da Husna, riko hannunta tayi tace "ya muran kin dan ji saukinta, gyada kai Nadeeya tayi tace "da sauki, muje mu jira malam Ali ya dawo daga kai Badar, walhi yau muna zuwa gida zan fadawa mummy duk abin da Badar ke miki, yanzu ki dubi yadda sanyi yayi miki mugun kamu, saboda tsabar bakin hali duk ta jike bargon da kike rufa, ni na rasa irin halinta, yanzu dole saboda mugunta kullum sai mun jira an kaita a dawo a dauke mu, ko tausayin malam Ali batayi, murmushi Nadeeyah tayi tace "kiyi hakuri karki fada, wata rana sai labari, babu abin da bai wucewa a rayuwa, muje school shop in samu tom tom insha, suna isa Husna ta siyan mata tom tom ta hada mata da biscuit da maltina mara sanyi, nasan baki fita break ba, muje mu zauna a can in kin gama sai mu koma gate... Tun yana kallon kofar shigowa har ya gaji ya dubi agogo yaga lokacin tashi yayi, tsaki yaja ya mike ya kashe komai na office dinshi, yasan bazata zo ba, a ganinshi tafi karfin tazo tayi rokon cewa tayi daidai ne, rai a bace ya dauki mukullin mota hade da rataya jakar laptop dinshi ya fita daga office din, jiki a sanyaye ya tada motar ya fara tafiya a hankali, yarinyar nan tane neman zame ma zuciyarshi damuwa, yana gab da fita gate din ya hangosu, atishawa take yi a jere masu zafi, nan idonta ya kada yayi jajur hade da fitar ruwa, daidai inda suke yayi parking, sauke glass yayi yana jiyo Husna na fadin "wani irin lalacewa kuma malam Ali, haba dan Allah, kasan Nadeeyah ba lafiya gareta ba, ga rana gashi babu motar haya, dan Allah ka koma gida ka karbi mukullin motar Mummy, rai a bace ta kashe wayar tana ma Nadeeyah sannu,, baisan sunan Husna ba saboda bai daukarsu komai, yadai san Badar saboda rashin mutuncinta ga dalibai ana yawan kawo kararta, kuma yasan gidansu daya, "Hey Kyari, babu wanda baisan muryarshi ba kaf cikin makarantar, da sauri ta iso gurinshi tace "Yes sir, Good afternoon! "Hw u ya fadi yana unlocking motar hade da cewa "baku wuce gida ba? yamutsa fuska tayi tace "driver yaje kai Badar on his way back motar ta lalace, yanzu dole mu jira shi ya koma gida ya dauko wata, and my sister is very sick, saida takai aya sannan ya dauke idonshi a kan Nadeeyah yace "ayya sorry, Allah ya bata lafiya, kuzo muje in kaiku gida, cike da murna Husna ta janyo Nadeeyah, zasu shiga motar Nadeeya taja Hannun Husna, tace "in wani guri zashi fa, ki kyaleshi mu jira malam Ali, fisgewa Husnah tayi tace dalla shiga muje, anan zaki zauna ciwon ya karu, baya ta bude ta shiga hade da cewa "ina yini, bai amsata ba yayi saurin rage A.cn motar hade da tada ta, sunan unguwar ya tambaya, Husnah ta fada mishi harda adress, duk yadda Nadeeyah ta kai ga matse atishawa abin yaci tura, a jere ta dunga sakinsu, ta mudubin gefe yaketa kallon yadda idonta yayi, A lokacin in hankalinshi yayi dubu to duk sun tashi, hanyar dialogue pharmacy ya dauka, suna zuwa ya kalli Husna yace "ku jirani in siyo magani, bai jira amsa ba ya fita, magunguna ya siyo na mura kala kala kamar zai bude shagon su, bayan ya biya kudin ne ya dubi yawan maganin, sai a sannan ya fahimci yawansu, murmushi yayi yace "cire min wadanda suka fi kyau, emergency, karba yaron yayi ya cire mishi masu kyau hade da rubuta yadda za'a sha su, barin mishi sauran kudin yayi ya fito ya shiga motar, Mikama Husnah maganin yayi, kafin yayi magana wayarshi ta fara ringing, tada motar yayi ya daga wayar, "Sweet heart, kunya ce ta kama Nadeeyah tayi saurin kunshe bakinta, hirarshi ya dinga yi yana fada mata yadda yayi missing dinta, cike da shagwaba kamar bashi bane mai mugun tsare gida yace "yaushe zaki dawo, gidan is empty witout u darling, basu jin abinda ake cewa a daya bangaren sai ji sukayi yace "Noo i won't accept that from u, in baki dawo ba this week zan bar school ba kowa in biyo ki, ita dai Husna burgeta yayi sosai na yadda yake kula da wacce ta kyautata zaton budurwarshi ce ko matarshi, kallon ledar tayi taga magungunan mura, murmushi tayi ta kalleshi bayan ya gama wayar tace "Sir kaima mura kakeyi, bai kalleta ba yace "ni lafiyata kalau, na siyo miki ne in mura ta kamaki kisha, murmushi tayi dan ta gane Nadeeyah ya siyo mawa tace "bana fatan Mura, saidai nagode sosai zan bawa yar uwata ita murar ta kamata, gyada kanshi yayi yace "kin kyauta, daganan bai kara magana ba har ya kai kofar gidan da ta nuna mishi, godiya Husnah tayi mishi ya amsa yana dan mata murmushi, cikin sanyin murya Nadeeyah tace "Mun gode Allah ya saka da alkhairi, Ameen yace a cikin zuciyarshi, a fili kuma murya can kasa yace "baki da matsala in kinyi failing test ko? It's well, na lura ai karatun bai dameki ba, yadda yayi maganar ba tare da ya kalleta ba ya dan bata mata rai, murda kofar tayi ta dauki school bag dinta tace "nasan bazakayi failing dina ba, ni nayi failing, shiyasa zan duba mistakes dina in gyara a exams, tana kaiwa nan ta rufe kofar ta fara tafiya, murmushi Husna tayi tace "haka take sir, ko cutarta akayi zata dauki kaddara tace haka Allah ya rubuta, mun gode sosai, itama ta bude kofar ta fita, kallo yabi Nadeeyah dashi, ji yayi kara samar mata special guri a cikin zuciyarshi, zai tada motar kenan yaga sun tsaya jikin motar da tazo shiga gidansu, dariyarta mai kyau ya hango, nan ya shagala da kallonta, bai kula da maganin da Husna ta manta dashi ba saida ya tada motar, yana gani yayi saurin kashewa ya fito da maganin yayi hanyar shiga gidan, da yake gate din a bude yake ya hangosu tsaye da wanda ya shiga da motar, sanye yake da uniform din Nysc, akwatinshi Nadeeyah ta dauka yayi saurin matsowa kusa da ita yace "bani yayi miki nauyi, kin bashi tayi tace "a'a yaya Musaddiq babu wani nauyi, kama gefen yayi yace "to mu kama, ni kaina yayi min nauyi bare ke, har sun kusa shigewa parlon mai gadin ya kwala ma Husna kira, a tare suka waigo suka ga Uncle Tahir a tsaye a wajen gate, ledar ya mikawa mai gadin yace ya ba Husna ya juya ya tafi gurin motarshi, haka kawai yaji zuciyarshi ta rike Musaddiq, ya rasa dalilin da yaki alakanta mu'amalarsu a matsayin yaya da kanwa, shiga motar yayi ya fara tukata a hankali kamar baya san barin layin..... Mrs Tijjani Shattima..... [13/03 9:58 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣6⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Magungunan Musaddiq ya karba yace "waye baida lafiya, "Nadeeyah ce yaya, Husnah ta fada tana tura kanta cikin parlon, kallon Nadeeyah yayi yace "yaushe kika fara ciwo, cikin muryar mura tace "jiya, akwatin ya kwace a hannunta yace "shan ruwan sanyi da kuma A.c, sam bakwa kula da lafiyarku, ga hancinki nan duk ya zuge yayi ja, Husna da ta ji me yace tace "walhy yaya laifin Badar ne, kasan a kasa Nadeeyah take kwana, kuma Badar ta kure a.c, bargon da take rufa kuma ta jikashi, da ta gane ina matsa ma Nadeeyah ta kwanta sai ta fara kwanciya tana cike gurin ta barmin guri kadan, kasan ko school zamu bata hada mota damu, saidai aje akaita a dawo a dauke mu, cike da mamaki Musaddiq yace "kuma Mummy ta sani, a'a bata san tana kwana a kasa ba, amma tasan ba tare muke zuwa school ba, ajiye akwatin yayi a kasa fuskarshi ta bayyanar da bacin ranshi, kallonshi Nadeeyah tayi tace "dan Allah kar kayi ma mummy magana, zaman lafiya yafi komai, wata rana zaka ga kamar ba'ayi ba, tausayi ta bashi matuka na yadda take magana, maganin ya mika mata yace "je ki ci abinci kisha maganin sai ki kwanta, sorry kinji, gyada kai tayi ta wuce dakinsu, tun daga kofa tayi karo da takalmin Badariyya, tattaresu tayi ta ajiyesu a mazauninsu, sannan ta dauke jakar makarantar itama ta ajiyeta a gurin zamanta, tana cire kaya ta hada da na Badar ta zuba a washing machine, sannan ta fito ta karbi na Husna, bayin Husnah ta bita ta tayata zuba ruwa da sabulu ta murda tace "suje suci abinci, duk abinda sukeyi Badar na kallonsu tana game a waya, tsaki taja tayi juyi ta cigaba da abin da takeyi, sam bata da masaniyar dawowar Musaddiq, duk zatonta motar malam Ali ce ta shigo, shiyasa bata fito parlon ba, Abinci suka zuba suka ci sannan tasha magani, a parlon suka kwanta Husna ta kunna tv, tun suna hira sama sama har bacci yayi gaba da Nadeeyah.. Yana gama shiryawa shima ya fito parlon, bai nemi abinci ba saboda baya jin yunwa, zama yayi kusa da Husnah yana tambayarta abubuwan da suka faru bayan tafiyarshi service, labarai ta dinga bashi na yadda Badar da su Anty Raudha suka sa Nadeeyah a gaba, ba kamar ma idan Anty Radiya tazo, ta dinga kakalo aiki kenan tana sata kuma mummy tayi ta kallonsu bata cewa komai, Allah yaya abin da akeyi ba'a kyautawa, abin haushin ma shine in mukaje gidan Goggo, in kaga yadda suke mata sai kayi mata kuka, sai fa in Daddy na nan ne take samun sauki, Anty Rally ce kadai in tazo zata fita yawo damu ta siyan mana abu iri daya da Nadeeyah, yawancin kayan sawanta ma Anty Rally ke dinka mata, jinjina kanshi yayi yace "ashe dai har yanzu wannan zumununcin namu bai daidaita ba, ashe har yanzu bamu zama daya ba, kallon Nadeeyah yayi cikin tausayawa yace "Ya Allah ka kawo ranar sauyi cikin rayuwar wannan baiwar taka, taga jarabawa iri iri kuma duk ta dangana, ya Allah ka rangwanta mata... Suna zaune a gurin har aka kira la'asar, kin tashinta sukayi saboda kar kanta yayi ciwo, masallaci ya fita dan zuwa yayi sallah, ita kuma Husnah ta wuce dakinsu, tana shiga Badar ta fito parlon, jin kamshin turarenshi ya tabbatar mata da dawowarshi, shekeke ta kalli Nadeeyah tana baccinta hankali kwance, kitchen ta shiga ta dauko swan mai sanyin gaske a fridge, ko dar bata ji a zuciyarta ba ta bude ruwan taje saitin kunnen Nadeeyah ta kwarara iya karfinta, wani irin ihu ta saki wanda ya janyo hankalin Musaddiq dake dawowa daukar wayarshi da ya manta, da sauri ya karaso parlon ya tadda Badariyya tsaye a kanta, tana ganin shi ta ajiye gorar ta fara cewa "ni bansan tana gurin ba, ruwa nake sha ya zubar mata a fuska, karasowa kusa da ita yayi yaga fuskar Nadeeyan a jike tana ta murza kunnenta ruwan ciki ya fito, bai tsaya tambayarta ba ya dago kanshi hade da daga hannu zai mari Badariyya, da sauri Nadeeyah ta shiga tsakiya hade da rike hannunshi tace "kayi hakuri dan Allah, bata san ta zuba min ba, wani irin kishi ne ya tokare wuyan Badariyya ganin hannun Nadeeyah a jikin Musaddiq din da ta ke kira da nata ita kadai, cikin bacin rai ta cire hannunta a jikin shi tace "karki sake taba shi, ina ruwanki, ke zai mara da zaki wani rike mishi hannu, turata tayi tace "dalla fita a tsakanin mu, dankwalinta ta dauka zata wuce daki Musaddiq yaja tsaki yabi bayanta yace "in ruwan ya shiga kunnenki muje kiga yadda zakiyi, murmushi tayi tace "bai shiga ba, ina goge gefen ne, bata san ta nuna mishi ya shiga dan kar ta kara janyo matsala a tsakaninsu, daki ta shiga ta tarar da Husnah na sallah, bayi ta wuce ta bude pampo ta zuba ruwa cikin kunnen ta karkata, nan take duk suka biyo sauran ruwan suka fito, alwala ta dauro itama ta fito dan yin Sallah... A parlor kuwa bin bayan Musaddiq Badar tayi tana cewa "nifa ba da gangan na zuba mata ruwa ba, kasan sharri irin na matsi--- katseta yayi ta hanyar nunata da hannu, yace "wallhi zagi daya kikayi ma Nadeeyah sai nayi miki dukan da ban taba yi ma wani irinshi ba, Sosai ta tsorata da yanayinshi, dan bata taba ganin bacin ranshi ba sai sanyinshi, baya taja tana kallonshi har ya karasa gurin motarshi, wani irin sonshi takeji yana ratsa dukkan sassan jikinta, kaff fadin duniya ita har yanzu bata ci karo da namijin da yayi mata 100% ba irin Musaddiq, ganin yanayinshi na yau ya kara dasa mata soyayyarshi a jinin jikinta, ko wani yanayi yana da shi kenan, sanyi da zafi, saidai sanyin yafi yawa dan sam baya da saurin fushi, zai dade yana tara laifi yana ma mutum uzuri, amma duk ranar da ka kureshi shima yanada nashi zafin, bai taba gano hakan a tare dashi ba saida ya hadu da wasu yan rainin wayau a gurin service..... Kasancewar lahadi ranar hutu ce ya sanya su shiryawa zuwa gidan Anty Rally, dama tun friday ta nemi suzo domin su tayata aikin kwalema, basu wani yi kwalliya ba suka sanya dogayen riguna kimono da gyalensu kalar kayan, babu yadda Mummy batayi da Badar ba taki binsu dan sam basa shiri da Anty Rally, sallama sukayi ma Mummy suka fita gurin Malam Ali da kafin su fito ya juyar da kan motar, shiga sukayi ya jasu suka wuce.. A tsaye suka samu Anty Rally a kitchen tana hade haden girki, tana ganinsu taji dadi sosai tace "yauwa maza ku zo ku karasa, turo baki Husnah tayi tace "ai sai ki bari mu huta, "iyyyeee Anty Rally tace tana kallonta, Dariya Nadeeyah tayi ta daura gyalen a kanta ta cigaba da aikin, cike da jin dadin yadda take komai tsaf tsaf yasa Anty Rally cewa "kai Allah yayi miki albarka, Allah ya kaiki gidan hutu inda zaki huta babu wanda zai sa miki ido, Ameen Husnah tace hade da cewa tare dani, rankwashinta Anty Rally tayi tace "Dalla can zo ki hada kayan cikin wancen basket din, ki jerasu tsaff bari in dauko hijab, jerasu ta fara yi tace "ina zamu, liquid anty Rally ta tsiyaya a hannunta ta wanke hannunta tace "gidan Anty Saude, jiya da daddare ta dawo daga Holland, shine zan shiga gaisheta, wacce Anty sauden, Anty sauden Legacy? Husnah ta tambaya, Eh ita, matar akwai kirki, tana daraja makotaka, Anty Rally ta bata amsa hade da wucewa daki ta dauko Hijab, kayan suka dauka Nadeeyah ta rike jug din kunnun Aya suka fito suka wuce gidan dake jikin na Anty Rally, Gida ne kayatacce wanda za'a iya sanyashi cikin jerin 1st 5 din gidajen masu kudin layin, kafin ka karasa cikin main house din ma sai kayi tafiyar 5mins, babu abin da kake ji sai motsin flowers da karan water fountain din dake tsakar gidan, suna karasawa kofar palon Anty Rally ta tura suka shiga ciki, wani irin kurda kurda suka shiga yi suna hawa sama suna sakkowa cikin wani under ground, sanyin A.c da daddadan kamshi ne ya tabbar musu da isowarsu parlon, cire takalmansu sukayi suka shiga ciki hade da Sallama, kyakykyawar mace wacce a kiyasi zatayi shekara Hamsin da biyar ta amsa musu, murmushi ta saki tace "Raliya ce a gidan namu, kusa da ita Anty Rally ta matsa ta sauke Fadil tace "ina wuni Anty, daukar fadeel tayi tace "lafiya kalau Raliya, Fadeel dina yayi wayau, ina babanshi,? murmushi Anty Raly tayi tace "yana nan lafiya, Hada baki Nadeeyah da Husnah sukayi suka gaisheta, kallonsu tayi tana murmushi tace "lafiya kalau, ina kika samo kyawawan yara haka, nuna Husna tayi tace nasan waccen bayan kamannin da kukeyi nasan tana zuwa Legacy, waccen fa ta nuna Nadeeyah da idonta yaki daukewa a kanta, itama kanwata ce Anty, cousin sis dina, ayya, mashaa Allah, tabarkallah dasu, ta fadi har lokacin bata dauke idonta a kan Nadeeyah ba, zatayi magana kenan ta jiyo muryarshi daga can cikin daki, "Momma nifa wahala kike bani, ban ganshi ba, dafe kanta tayi ohh gosh *TEE* a cikin blue trolly fa nace, cikin shagwaba yace "shi fa na duba babu, "anya Tee glasses dinka basuyi expire ba ta tambaya cike da tsokana, rufe akwatin yayi ya fito yace "ni fa yanzu ko babu su ina gani, bai kula da su anty Raly ba ya kwanto ta bayanta yace "kin gani sweetheart, babu su ko yanzu a idona, dariya tayi tace "gaskiya ne babyna, hannu tasa ta dauki glass din tasa mishi a ido tace "to yanzu koma may be ka iya ganinsu, dagowar da zaiyi yayi tozali da wacce ya kira da damuwar zuciyarshi, da sauri ya gyara glass din ya sake kallon inda take ko gizo take mishi, ita din ce zaune tare da Husna, kallon Fadeel yayi yace "Boy ina Mummy, dariya Anty Raly tayi tace "gani kusa da kai, gaskiyar Anty ne sai ka koma an duba idon nan, daukar Fadeel yayi yace "zan baku mamaki, yau ma ba glass zanyi driving, on a serious nt Anty saude tace "in ma wasa kakeyi kayi saurin daina shi, koda wasa ban yarda ka fita babu su a idonka ba, kana ji na ko? Dariya yayi sosai dan dama tsokanarta yayi ya wuce da Fadeel dakinshi... ganin Nadeeyah a gidanshi, a mahaifarshi ya sanya shi zama on top yau, jinshi yakeyi kamar sabon mutum, ashe yanzu in shaa Allah samunta bazai mishi wuya ba, rungume fadeel yayi yace "knwing ur mother is a blessing to me... Yafi minti talatin rike da fadeel yana mishi wasa, karar wayarshi yaji yasa hannu ya dauko a aljihu, "ka kawoshi zasu tafi ne, da sauri kafin ta kashe yace momma kice su tafi zan kawo shi, cike da mamakinshi ta kashe wayar tace "zai miko shi inaga yayi bacci ne, nagode sosai Raliya, a'a haba Anty babu godiya a tsakaninmu anty Raly ta fadi tana murmushi, sallama su Nadeeyah sukayi mata ta amsa cike da fara'a, bayan Nadeeyah tabi da kallo tana Nazarin wasu abubuwa, har saida ta kurewa ganinta sannan tayi ajiyar zuciya ta fara bude kulolin abincin.... Mrs Tijjani Shattima [15/03 12:04 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣7⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *JIGON RAYUWA* Kallon Mamaki Anty Saude ta bishi dashi, kayan da ya shiga dasu sanye a jikinshi ba dasu ya fito ba, wannan karan Ash Shadda ce a jikinshi, yayi kyaun da shi kanshi ya yaba, babu ta inda Taheer bai hadu ba, ya hada komai da duk namiji zai yi tunkaho dashi, matsalarshi daya ido, ciwon idon da ya samo asali tun yana yaro gurin wasansu na yara, babu inda ba'a kaishi dan duba idon ba, saidai ya dan samu sauki amma bazai bar ciwon duka ba, a karshe har iyayenshi suka hakura suka dawo asibitocin ido na nigeria, a nan ne suka daurashi kan magunguna har idon yayi kyawu sosai, da taimakon Allah da taimakon glasses dinshi da suka kara fito da ainihin kyawunshi yake ganin abun da ke nesa.. Zaunar da Fadeel yayi akan kujera ya dauki nama daya cikin soyayyun naman da Anty Raly ta kawo, zama yayi kusa da Anty saude ya kai naman bakinshi yace "Momma zan fita, "Ina zuwa kuma? ta tambaya hade da ajiye plate din hannunta, Murmushi yayi mai matukar kyau yace "zan mika Fadeel gida, sannan zan je aiken da zuciyata take ta min kullum, "Hannunshi ta kama da sauri tace "Fara isar min da aiken TEE, fada min sakon in taya zuciyar taka adduar samun karbuwar sakon, nata hannun ya rike shima zuciyarshi na kai kawo, farin ciki ne cike a cikinta na ganin tana gab da samun abin da take so, lumshe idonshi yayi , kana hango yanda gashin idon ya kwanta ta cikin glass yace "i'm in love Momma, wani irin numfashi ta saki wanda zai tabbatarwa da mai kallonta tana cikin matsanancin farin ciki, "wacece Taheer? wacece wannan? ya Allah kayi mata albarka, share hawayen da ya zubo mata tayi, tace "bani labarin ta Tee, "murmushi yayi dan dama yasan yadda zatayi reacting kenan, yace "calm down Momma, with time zaki santa, kuma nasan zaki sota, ni dai addua'arki nake bukata, ina son ki dage da addu'ar samun nasara, inason zuciyata ta kasance da ita a duk bugun numfashina, tun ranar da fara ganinta har zuwa yau kaunarta ce ke kara tasiri a cikin ruhina, "rungumeshi tayi sosai tana fadin Alhamdulillah a jere har sau uku, jin kukan da takeyi yana neman yayi yawa ya sashi saurin raba jikinshi da nata, hannu yasa yana share mata hawayen hade da girgiza mata kai, a shagwabe yace "kina so in bata kwalliyata ne, sai ma na fasa in bawa zuciyata hakuri tunda aikenta nasa min ke kuka, dan mari takai ma fuskarshi tana dariya tace "tashi maza ka tafi, Allah ya baka dukkan sa'a my boy, daukar Fadeel yayi yace "Ameen Momma, kallon farin ciki ta bishi dashi hade da mikewa ta isa gaban hoton mahaifinshi, rau rau idonta yayi tayi saurin maida hawayen hade da fadin "tun bayan rasuwarka Taheer dinka bai sake yin farin ciki ba, yau!! a karo na biyu a rayuwarshi na ganshi cikin farin ciki, kasa controlling hawayenta tayi tace "we missed u alot Abba, Allah yayi maka rahama, adduoi ta shiga jerowa mijinta da danta, saida ta gama ta share hawayenta ta kira Abida mai mata hidima dan ta tattara parlon.... Sau biyu ya taba shiga gidan Anty Raly tun zuwanta unguwar, motar da ya dauko daga gida ma ta musamman ce kai kace garin zai bari ba kusa da gida ba, sai da yayi zaman minti uku a ciki sannan ya kashe ya dauki Fadeel, mai gadin na ganinshi ya tsuguna har kasa ya gaisheshi dan babu wanda baisan dan gidan Hajiya Saude ba a unguwar, bude mishi kofa yayi ya shiga, Baya yaja zai tsaya ya hango Husnah ta fito ta nufo gate din, tana ganinshi ta kara sauri tana fadin "uncle da kanka ka kawo shi, mika hannu tayi ta dauki Fadeel hade da ce mishi tana zuwa, mai gadin ta kira tace "ina lawalli, kace yaje ya siyowa Anty Gas, cikin girmamawa ya amsa ya fita da niyyar zuwa kiran lawali driver, Dawowa gurin Taheer tayi ta sake gaisheshi, tambayoyi ta fara jefo mishi, "uncle dama kai dan Anty saude ne? ai na santa, bansan kai danta ba, kasan last year ka fara teaching a school shiyasa bamu san kai danta bane, she is very nice, kasan akwai lo--- katseta yayi yana dariya yace "ashe haka kike da surutu, to tunda bazaki bani gurin zama ba bari in tafi, da sauri tace "laaa sorry uncle muje dan Allah, bai bata lokaci ba ya bita hade da addu'ar Allah ya bashi karfin gwiwar sanar da ita, parlon Baban Fadeel ta bude mishi tayi mishi iso har ciki ya zauna, har zata zauna sai tayi saurin mikewa tace "bari in kawo maka ruwa, murmushi yayi yace "na dauka zama zakiyi da sai ince ashe baki iya tarbar baki ba, dariya tayi ta wuce kitchen, Suna shiga kitchen Fadeel ya saki Kashin da ya fito daga pampers har rigar Husnah, wani irin ihu ta saki wanda ya sanya Nadeeyah da Anty Raly zuwa kitchen din, dariya Raliya tayi na yadda Husnah ta bata baki hade da tale riga da kafarta, da sauri ta dauki Fadeel da ya fara bata mata kitchen da kashi tayi daki dashi, kallon Nadeeyah Husna tayi tace "dan Allah ki kai mishi juice parlor, bata tsaya yi mata bayani ba ta wuce daki tana ware kafa, dariya Nadeeyah tayi ta shirya juice a tray, duk tunaninta Baban Fadeel aka shiryawa abinci a parlon kafin ya dawo, bata damu da yadda gashinta yake a bude ba saboda tasan bai dawo ba, gyara wanda ya dan zubo ta gefen idonta tayi ta wuce parlon, sam bata kula dashi ba saboda kujerar da yake zaune tana baya, duk wanda ya shigo parlon in ba ya lura dakyau ba bai kula da na zaune a kujerar, ganin babu abinci a parlon yasa ta dube dube, sai da ta razana saboda ganin bazata da tayi mishi, da sauri ta ajiye tray din jiki na rawa hade da bugawar kirji tace "ina wuni uncle, bai amsata ba ya tako har inda take tsaye shima kirjin nashi bugawa yake yi sosai, "murya can kasa yace "bakina ya kamata ya fara furta wannan, an yini lafiya *Umm Nadeeyah* Wani abun taji ya tsarga mata tun daga kwanyar kanta har tafin kafarta, yadda yayi kiran sunanta ta ya sake kashe mata jiki dan duk duniya banda Babanta babu mai kiranta da Umm Nadeeyah, bata amsa shi ba ta fara tafiya da niyyar barin parlon, *Nadeeyah* ya sake fadi a hankali yana kallonta, tsayawa tayi kamar zata saki fitsari saboda tsabar tsoron yanayin shi, bai karaso inda take ba yace "dawo ki zauna, akwai maganar da nake so muyi, bata motsa daga inda take ba tana tsaye har seconds sittin, Murmushi yayi ya kara takowa yazo har inda take, kamar me rada yace "matsayinki ya kai in biyoki inda kike, kamar zatayi kuka ta juyo tace "um um dan Allah uncle kayi hakuri, zan dauko dankwali na ne, "Ya riga ya gama fahimtar yanayinta na tsoro yayi murmushi mai kashe zuciya yace "naki wayan, hular kanshi ya cire ya mika mata yace "ki rufe kanki dashi, saurin maida hannunta baya tayi tace "Dan All-- "karki hada ni da Allah, yayi saurin katse ta a kasalance, hannu yasa ya dago habarta ya sanya idanuwanshi cikin nata, kokarin sauke idonta tayi jiki na rawa, yayi girgiza mata kai alamar a'a, karkatar da kanshi gefe yayi, gaba daya soyayyarta tana neman maidashi zautacce, ya mance matsayin malami yake a gareta, suffofinshi na shagwababben Momma suka bayyana, a hankali yace "plssss!!! bata bari yayi magana ba tayi saurin runtse idonta hade girgiza kai, bata taba shiga yanayin da yake kokarin sanya ta a ciki ba, rufe idonshi yayi shima yace "karki hana ni plss, akwai abun da ya ke kokarin karya duk wani lago nawa, *Soyayya* ita gayyaceni zuwa gareki ba tare da shirya ma zuwanta ba, tell me,!! kina son in barta ta sanya ni na rankwafa, bani da wani sauran sukuni tun ranar da na fara ganinki, kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga cikin jinin jikina, Shuru ne ya dan ratsa gurin na minti daya, bugun zuciyoyinsu kadai suke jiyowa sai numfashinsu dake gauraya da juna, A hankali ta bude idonta wanda ya zamo kamar hadin baki shima ya bude nashi, da sauri ta dauke kanta hade da rugawa ciki da gudu, saida ta isa daki sannan ta fara maida numfashi.. jin karar ruwa a bayi ne ya bata tabbacin Husnah na ciki tana wanke jikin ta har lokacin, a gefen gado ta zauna ta runtse idonta, ta kasa fassara yanayin da take ciki, wani abu ne yake ta mata yawo a cikin kwanyarta.. karar wayar Husna ta ji tayi saurin mikewa ta dauko ta a gaban madubi, sunan da ta gani ne ya sanyata dauka, tun kafin tayi magana yace "kina lafiya, bata amsa ba tace "ina wuni Ya Hilal ba ita ce, "i knw ya fadi yana dada jinjinawa zuciyarshi da take saurin daukar haske akan kusancinta da Nadeeyah, tana dauka jikinshi ya bashi ita ce, "ya school, hope kina kokari ko,? cikin nutsuwa tace "umm ina yi, lumshe ido yayi ya bude yana kallon kasan office din da yakewa aikin zane yace "Good, babu ruwanki da kowa kamar yadda nake fada miki kullum, karatunki shine gatanki, bana san wani abu ya shiga rayuwarki yanzu, i want u to be successful kin gane ko, gyada kai tayi kamar tana gabanshi tace "in shaa Allah, in yana waya da ita ya kan manta duk wata zuciyarshi da bata san raini, yakan manta ko shi waye duk da har yanzu bai taba nuna mata alamar soyayya ba, so yakeyi ta zama macen da ko ina a duniya za'ayi alfahari da ita, "Zeemarh na gaishe ki, yau dakyar taje makarantar islamiyya wai ni zata bi, murmushi Nadeeyah tayi tace "Allah kuna lalata ta ne, anjima zan kira Anty ince ta dinga zane ta, "u are on ur own ya fadi hade da cewa kema musa a zaneki kuwa, sai ayi 50-50, dariya sosai tayi wacce ta sanya Hilal nishadi, zatayi magana kenan taji Anty Raly na kwala mata kira, sallama tayi mishi ta kashe wayar ta fita da sauri, kallo ta bita dashi fuskarta dauke da Murmushi, tace "Nadeeyah daga hannu sama mu godewa Allah, da sauri ta daga dan bata san me zasuyi ma adduar ba, bayan sun gama adduar tace "Allah ya kawo miki taimako, yanzu Taheer ya fita a gidannan, kaii yau saboda farin ciki bansan yadda zanyi ba, kin gama dacewa duniya, lahira kadai zaki nema, Nadeeyarmu ce zata zama matar Taheer surukar Anty Saude, wannan dadin ina zan kaishi yau, rufe fuska Nadeeyah tayi ta kasa gane ainihin yanayin da take ciki, na farin ciki ne ko akasinshi, kalaman Hilal ke mata yawo a zuciyarta, wanda sabonsu ke bata mamaki duk da har yanzu tana shayin shi, ga kuma zazzafar kaunar da ta gani a idon Taheer, rungumota Anty Raly tayi tace "saura 3 to months ki gama school, lokacin ne zamu fasa maganar nan, wallahi dadi yau kamar zai kasheni, daki Nadeeyah ta wuce da sauri tana nazarin abubuwan da suka gifta tsakaninta da Tahir...... ********___******* Turjiya takeyi a kasa tana ihu tana fadin "indai yaya Jamal zaije itama sai taje, dariya Hafeez yayi yace "Haba autar mami, yaya jamal fa ba bin mu zaiyi ba, ni da Papy kawai zamu tafi, kiyi hakuri kinji, fitowa yayi yana gyara button din rigarshi yace "fada mata gaskiya mister, dani za'a, dan Allah kafin mu dawo ki mutu tunda ni sa'anki ne, wani ihun ta saka wanda ya sanya Anni da sauki ya samuwa fitowa tana fadin Jamal zan ci maka mutunci akan yarinyar nan, turo baki yayi yace "haba Anni, kina ganin yarinya ta rainani, da nayi aure da wuri da na dire wacce ta fita ya karashe hade da rankwashinta, jikinshi ta shige tana ihu tana yakushinshi tana fadin "babu inda zakaje walhy, ni sai dai mu tafi tare, tureta yayi yana dariya yace "zan gani yau, ji min rigima fa, fitowar Papy ne ya sanyata zuwa gurinshi tana kuka, daukarta yayi yace "haba mamana, kaduna fa zani ba nan kusa ba, zo kiji a kunne, mika mishi kunnen tayi yayi mata rada, dariya tayi ta kalli Jamal tana mishi gwallo, har suka shiga motar tana tsalle tana ma Jamal gwalo tana cewa "an mishi wayau wooo, dariya sukayi dukkansu a motar, ta window ya leko yayi mata nashi gwalon shima kamar yaro karami, janta Mami tayi suka wuce daki dan kar Jamal ya sake ballo mata august... Karfe Hudu da minti ashirin suka shiga garin Kaduna, tunda suka shigo cikin garin Papy yaji jikinshi ya mutu, shidai yasan meeting yazo yi a Kaduna state university, amma yanzu ji yakeyi kamar wani abu mai muhimmaci akasin haka ne ya shigo dashi, Hotel din da aka kama musu Hafeez ya kaisu sannan ya yi musu sallama ya wuce da niyyar dawowa da safe... Washe gari bayan sun gama komai karfe biyu Hafeez yazo ya daukeshi, suna Hira Hafeez yace "mishi daga gidan kakanshi yake, baiji dadi ba jiya kwana yayi yana gudawa, da gangan ya fadi haka dan hakar shi ta cimma ruwa, in ma suna da dangantaka to suna ganin juna a yau zasu gane su kuma warware mishi komai, gidan Baffa ya wuce direct kamar yadda Papy ya bukaci zuwa gaisheshi,, A daidai kofar gidan yayi parking, cike da girmamawa ya bude mishi kofa yayi mishi iso har cikin gidan, fuskar Ma'u ke fuskantar hanyar shigowa, kamar an manne ganinta a fuskar papy, kallon Baffa tayi ta dago ta kara kallon Papy, Da sallama ya shigo ciki ya karaso ya tsuguna ya gaida Goggo, motsi kawai bakinta keyi amma ta gaza furta ko kalma daya, kamar ance Baffa ya dago nan Allah yayi ma fuskokinsu gamo, ko wanne saida ya tsorata da ganin fuskarkokinsu cikin na juna..... Mrs Tijjani Shattimah...... [18/03 8:06 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣8⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Dammmm..... gaban Baffa yayi mummunar faduwa, karasa mikewa zaune yayi har lokacin bai dauke idanuwanshi kan Papy ba, shi din ma Papy hakan take gareshi, saboda tsananin faduwar gaba bakinshi ya gaza furta koda kalma daya ne, Hafeez dake bayansu ya tsuguna zuciyarshi wasai saboda a yau yana tunanin warwarewar SARK'AK'IYAR da ya shiga watanni bakwai da suka wuce, kallon Baffa yayi hade da dan taba kafadunshi yace "Baffa wannan shine Papy wanda nake zaune a gidanshi a Gombe, a razane Baffa ya dawo hayyacinshi yace "au to madallah, an gode fa, Papy bai amsa shi ba ya zauna sosai zuciyarshi sai kai kawo take, ko tantama bayayi wannan mahaifinshi ne da Anni ta dade tana fada mishi, kamannin sun wuce kamanni kawai, tabbas akwai jini mai karfi a tsakaninsu, gaishe da Baffa yayi hade da tambayar jikinshi, Goggo ce ta iya amsawa babu inda a cikin jikinta bai saki ba, saida sukayi kusan minti biyar a zaune babu wanda ya sake magana, kowa da abun da yake tunani a ranshi, karfin Hali Baffa yayi dan ya gama hange hangenshi a yan uwa yasan babu wanda ya rage mishi na kusa, sannan yasan dai bashi da wani ďa banda wanda ya binne da hannunshi, kuma yasan bai taba yin aure a wani guri ba bare har yayi tunanin ya barta da cikinshi, wannan abun al'ajabin kamanni sun yi yawa, bazai iya jure barin shi a ranshi ba, dole yana bukatar sanin daga inda halittar nan mai tsananin kama dashi ya fito, kallon Papy Yayi yace "dan nan idan bazaka damu ba ina so inyi maka tambaya, takalma da safa Baffa ya cire ya gyara zamanshi sosai a kan tabarmar, ganin yatsun kafarshi ya kara daga hankalin Ma'u, shin meke shirin faruwa ne?, magana Baffa zai fara-- tayi saurin katseshi tace "daga mutum yazo gaisheka sai ka tsareshi da magana, ka sani ko sauri yakeyi, Murmushi Papy yayi yace "babu komai karki damu, ko bai tsayar dani ba nima babu inda zani domin akwai wani al'amarin da yake shirin faruwa, wannan al'amarin zai fitar da rayuka da dama cikin tunanin da suka shekara da shekaru suna yinshi, bude baki tayi da niyyar sake yin magana Baffa ya rigata da cewa "nasan kaima kana cikin zullumin da nake ciki, duk wanda ya ganmu ni da kai yasan jini daya ne saboda kamanni, wasu ka iya cewa yan biyu ne saidai yanayin tsufan da jikin shine kadai ya banbanta, dan Allah ina son ka fada min wanene mahaifinka dan inason sanin ko inada wani sauran dan uwa wanda kaddara ta boye min shi, ina son sanin inda mahaifinka yake dan inje mu gana, in baya raye to dan Allah ka bani tarihin shi wanda zai iya warware min komai, Papy baiyi magana ba ya fito da wayarshi, dannata yayi hade da karata a kunnenshi, "Hello Maimunah, hadani da Anni a waya, Papy na...., Ruwaidah ta fadi murya a shake, "Mama na, kuka kike yi? Kukan ta sake fashewa dashi kamar zata tsaga wayar, rage murya yayi yace "wanene, daina kukan and tell me, M-a-mi ce ta fadi tana ajiyar zuciya, tsaki yayi a hankali, yasan abin da aka mata bai taka kara ya karya ba, "yi hakuri Mamanah, jeki kai mata inji dalilin saki kuka, da dan gudunta ta tashi taje kitchen inda Mami da mai aikinsu ke kwashe mangyadan da ta zubar, a darare tace "Maami Papy ya kiraki, kwafa tayi ta goge hannunta a jikin tsumma ta karbi wayar, yana jin sallamarta yayi saurin amsawa, ba tare da jin dalilin kukan Ruwaidah ba yace "ina Anni? tana bacci lafiya dai ko, mami ta tambaya cike da zullumi, ajiyar zuciya yayi yace "lafiya kalau Maimuna, gobe da safe ku shirya guraren tara zan kira Badamasi yazo ya taho daku kaduna, zama Mami tayi gabanta na tsananta faduwa tace "Dan Allah ka fada min abin da yake faruwa, ina JAMAL da HAFEEZ?, murmushi yayi cike da tsokana yace khairan in shaa Allah ruďaďďiya, ke dai ku shirya kinji, gyada kai tayi har lokacin  gabanta bai daina faduwa ba... Kallon Baffa yayi bayan ya ajiye wayar yace "Sanin abubuwan da ka tambayeni wannan sai maihaifiyata tazo, domin nima ban san kaina ba, tashi nayi na ganni a hannun mahaifiyata ba tare da uba da yan uwa ba, ni kadai na rayu a gabanta, tare muka sha wahalhalun rayuwa, na dai san a kullum tana fada min ina da uba, amma bata san inda yake ba, A lokacin da Ma'u na tsaye to tabbas da ta kai kasa, kokarin mikewa takeyi Papy yace "inna dawo ki zauna ayi komai a gabanki, yau da za'a bincika zuciyata a gani to tabbas da an gano tafi takarda haske, kallon shi Ma'u tayi tace "ďan nan ina ganin dai kamanni ne, dan mu nan bamu da da namiji ko daya, sannan duk wasu y'an uwa namu na kusa duk sun mutu, kasan Allah yana iya halittar mutane masu kama da juna, akwai su da dama sab--- katseta Hafeez yayi cikin girmamawa yace "Goggo wannan ya wuce kamanni kawai, akwai jini mai karfi, ki duba girman makarantarmu duk daliban dake ciki ace dani kadai ya shaku har ya kaini gidanshi cikin iyalinshi, sannan kuma idan kika ga Jamal da Ruwaidah a nan ne zaki tabbatar da su ďin jinin mu ne, Daka mishi tsawa Goggo tayi "kai dalla rufe mana baki, manya na magana kana yi saboda tsabar rashin kunya, tashi ka fita kaba mutane guri, mikewa Hafeez yayi yana fadin kiyi hakuri, harara ta bishi dashi har ya bacewa ganinta sannan ta dawo da kallonta kan Papy tace "to bawan Allah mun gode da ziyara, sai anjima, sake gyara zama Papy yayi yace "Inna, bazan boye miki ba, barin gidannan a guri na sai da daddare, sannan gobe da wuri zanzo domin kuwa ina hango cikar burina na sama da shekaru arbain da doriya zai tabbata, cike da faduwar gaba ta kalli Baffa da ya kasa dauke idonshi a kan Papy, yanayin maganarshi, da komai irin nashi ne, gayu, gogewa da yarinta ne kadai ya banbanta su, taba shi Goggo tayi tace "lokacin Sallah ya kusa tashi ka shiga kayi alwala, da sauri Papy ya kalli agogon hannunshi yace "uku da kwata ne yanzu Inna lokaci baiyi ba, tun Goggo na daurewa kar ta fara nuna mishi halinta, har saida ya kaita bango ta dakawa Baffa tsawa tace "ya tashi su wuce daki, wannan mutumin in ba aljani bane to maye ne, jiki a sanyaye Baffa ya tashi yace ma Papy "yaya Sunanka, da sauri papy yace "Abdallah" nan Baffa yayi ajiyar zuciya yace "ba SAIFU bane, Ma'u ba saifu bane, duk tunanina shine shiyasa na cika da tsoron ya za'ayi wanda ya mutu ya dawo, nasan ni na binneshi da hannuna, kallon Papy Goggo tayi tace "kaji ko, dan Allah tashi ka fitar mana a gida, kuma karka sake zuwa kaje can ka nemi ubanka.. Nan tsakar gida suka barshi zaune yana ta nazarin abubuwa, kodai da gaske bashi bane mahaifinshi, sai da yayi wasu yan mintuna sannan ya tashi hade da gamsar da zuciyarshi koma meye in Anni tazo zata warware mishi komai.... Ita kuwa Goggo safa da Marwah ta dinga yi a daki tana tunanin ta inda wannan mutumin ya fito, tasan a hannunta saifu ya cika, kuma a gabanta aka binne shi, anya ba aure Baffa yayi ba lokacin da yake tafiye tafiyenshi, katse mata tunani yayi yace "Ma'u wannan yaron ko dai dan Hardejo ne, kodai..... saurin katse shi tayi murya a kausashe tace "ko kuma naka ba, ni zaka ciwa Amana Muhammadu,? ashe dama kayi aure a boye ban sani ba, "Nan jikin Baffa ya fara rawa yace "wallahi banda Atika ban taba auren wata mace ba, daga ke sai ita, kwafa Goggo tayi cike da masifa tace "gaskiya zatayi halinta ai gobe, da bana son yaron nan ya dawo gidannan amma gobe da kaina zansa Hafeez ya kawo shi dan a warware min wannan kullin, ina ganin watan jin kunyarka ne ya tsaya, saboda sanin yana da gaskiya shiyasa yace "Allah ya kaimu, komawa yayi ya zaune a zuciyarshi yace "shi yaushe ma ya kalli wata mace a matsayin mace har ya aureta, har yanzu gani yakeyi duk duniya babu macen da ta kamo kafar ma'u a komai, sauran mata duk kallonsu yakeyi kamar gumaka, tsaki yayi yace "Ma'u batayi mishi adalci ba, tasan bazai taba cin amanarta ba, amma babu komai gobe gaskiya zatayi halinta... Haka suka kwana dukkansu zuciyoyinsu ba dadi, kowa da abun da yake sakawa a ranshi, har gari ya waye Baffa bai bar hango fuskar Abdallah ba..... **********●●●******* Karfe biyu da rabi suka iso kaduna, Hotel din da su Papy suka sauka can Badamasi ya wuce dasu, bayan sun huta a masauki suka ci abinci sannan ne Mami ta tambayi Papy dalilin zuwan nasu, bai amsa ta ba saboda yaga Anni ta dan kashingide tana son tayi bacci, Ruwaidah ya daura akan cinyarshi yace "me Mamana tayi miki jiya kika duketa, irin kukan nan da tayi nasan ba karamin duka kikayi mata ba, Harararta Mami tayi tace "ai badan Anni ba walhi da sai na balla hannunta sai ayi dauri, kaga daga nan ma huta da barna, turo baki Ruwaidah tayi hade da tura kanta cikin kirjin Papy, "ni kike turowa baki,? mami ta tambaya tana nuna kirjinta da yatsa, a ina ta turo miki baki, ki kyalemin uwata ta huta, shikenan dan bana nan bazatayi abin da takeso ba, Mikewa Mami tayi tace "ko kai da kana nan sai ka tayani, man gyada na zaune cikin jarkarshi ta dauko tukunyarta ta wasan yara wai zata soya dankali, tasan jarkar tafi karfinta haka tasa karfi ta yar da ita kasa, gaba daya kitchen da store babu inda bai samu albarkar mai ba, "tabbb... ai Mami kin ma mata da sauki, da kin cire hannun ne sai a sa mata na roba.. harara Papy ya jefa gefen da Jamal ke zaune yana latsa waya kamar bashi yayi maganan ba, "shikenan dan ta zubar da mai sai a duke ta, ba koyon girki takeyi ba, in bata koya ba waye zai dinga tayaki aiki, "Na yafe Mami tayi saurin fadi tayi hanyar bayi tace "ka cigaba da shagwaba yarinyar nan, ta riga ta maida mu kamar kakanninta, bayan Ruwaidah Papy ya shafa yace "rabu da Mami kinji, zan siyo miki kayan abincinki ki koya da kanki ki dinga dafa min inci kinji ko? Gyada kai tayi tace "kuma bazamu samma Yaya Jamal ba, dariya papy yayi yace "eh mana wama zai bashi, yaje can yaci jagwalgwalon Mamin shi, dariya sosai Jamal yayi yace "opposite, Kuma in na kara ganin kin taba ma Mami ko da gishiri ne sai na yanka hannun da wuka, murguda mishi baki tayi tace "ni da Papy zai siyomin nawa me zanyi da naku, ko kitchen din mami ma bazan kara shiga ba, "yauwa Good Girl, muna komawa zan yi miki cefanenki, karki kalli kayan Mami sun tsufa, mikewa Jamal yayi yana dariya yace "har abincin Mami ma kar ta kara ci papy, ta dafa nata da kanta, dakuwa Papy yayi mishi ya fita daga dakin yana dariya.... Suna idar da Sallar la'asar Papy yace su shirya zasu je wani guri, manufar shi nakin fadawa Anni shine kar ya fada mata suje bashi bane hankalinta ya kara tashi, gara in suka je yaga bata sanshi ba sai su tafi ba tare da ya daga mata hankali ba, tun yana shekara bakwai ya yankewa kanshi daina matsa mata akan maganar mahaifinshi, domin ya kan ganta cikin tsananin damuwa duk ranar da yayi mata maganar, a irin yadda ya taso yaga ta wahala akanshi shi yasa baya san ganinta cikin damuwa ko kadan... Biyar saura suka isa kofar gidan, motar Mummy Hafeez ya gani a cikin gidan, Addu'a ya fara yi zuciyarshi na Allah yasa kar su hadu su wulakanta bayin Allahn nan, gabanshi bai tsananta faduwa ba saida ya jiyo muryar Radiya, farin sani yayi mata akan rashin mutunci, dake wa yayi ya karasa ciki dasu, Sallama sukayi dukkansu suka shiga cikin gidan, daga cikin daki sukaji an amsa Sallamar, mikewa Goggo tayi ta fito dama zaman jiransu take, tana fitowa idanuwanta suka sauka kan Anni, baya taja kamar zata fadi bakinta na rawa tace, H-an-ne....... Mrs Tijjani Shattima..... [18/03 8:06 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣9⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Kallon rashin sani Anni tayi mata dan bata gane fuskarta ba, nan dai ta fadada murmushinta tace "Na'am barkanku da gida, dafatan mun sameku lafiya, Goggo dake tsaye jikinta na rawa kamar mazari tace "lafiya lau, matsawa tayi gefe tace ku shigo ciki, tabarmi Mummy ta fito dasu tace "a'a Goggo bari su zauna a waje yafi iska.. Bayan sun zazzauna an gaggaisa, Goggo ta kalli Hanne kirjinta na duka uku uku tace "baki ganeni ba ko Hanne?, gyada kai Anni tayi tace "ban ganeki ba, gyara zama Ma'u tayi kishi ya motso mata ta fara charge ta kalli Papy tace "wannan ce mahaifiyarka?? Eh!! Papy ya fada yana mai jin dadin an gane mahaifiyarshi a gidan, "TABDIJAM Goggo tace "tana kallon Anni, Wato Hanne ke kika haifeshi,? wannan karan mamaki yasanya Anni cewa kwarai ni na haifeshi, dana ne, lafiya?? Idon Goggo ya rufe ta manta da yara a gurin tace "wato dama cikin shegen da kika dinga yawo dashi a tsakanin jalingo da Gembu dama Mijina ne yayi miki shi, kenan lokacin da nake tausayin ki in su Harira suna tsangwamarki ashe kallon sakarya kike min mijina ne ya kunsa miki, kallon Radiya tayi tace "maza tafi shagon Gidado ki kira min Baffan ku, kafin Radiya ta mike Baffa ya shigo gidan da sallama, yana ganin wucewarsu ya mike a shagon Gidado hade da amso musu lemu, Goggo sam bata basu damar amsa sallamar ba tace "yauwa gara da Allah ya kawo ka, nuna Hanne tayi tace ka gane wannan,? kallonta yayi yaga samm shi bai taba ganinta ba, ita kuwa Anni kallo ta bishi dashi idonta ya ciko da kwalla tana fadin Alhamdulillah, Alhamdulillah, zama Baffa yayi yace "ban santa ba, wacece ita? Tafa hannu Goggo tayi tace "yau ni naga Bariki, Hannen ce baka sani ba? Hannen gidansu Inna wuro kanwar Harira, wacce ta kunso cikin shege aka korota daga garinsu ta dawo nan, ashe kai ka kunsa mata, gashi dai kamanni sun bayyana min komai, wallahi kaji kunya, ta karasa fadi tana haki.. "innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai Baffa da Papy ke fada, ganin shurun da Baffa yayi ya kara hassala Ma'u ta fara surfafa masifa da bala'i, babu inda baya rawa a jikinta, da dai Anni taga shuru bazai taimakesu ba tace. "Wallahi tallahi ban taba koda magana dashi ba... shuru Ma'u tayi tana hararar Hanne tana fadin rainin hankali, uban wa zaki rainawa hankali? "gyara zama Anni tayi ta kalli Baffa tace "in ka yarda dani ka bani dama inyi maka bayanin komai, idonta ta mayar kan Goggo tace "in kikaji labarin abinda ya faru, da kuma yadda ya faru ni nasan gode min zakiyi ba zargi da zagi ba, ni ko a yau Allah ya dauki raina walhy naji dadi saboda zan cika buri na, kullum bani da tunanin da ya wuce ta yaya zan wankewa Abdallah zuciyarshi, ta yaya zan hada shi da mahaifinshi, nasan duniya tana da fadi wata rana ina da yakinin Allah zai amsa min addu'ata, sai gashi ta dalilin Hafeezu adduar da na dade ina yi Allah ya amsa... Alheri danko ne... Kallon su Radiya dasu Hafeez tayi tace "dan Allah ko yaran nan zasu dan bamu guri, "babu inda zasu, Ma'u ta fadi tana tafa hannu, kallon Jamal Mami tayi tace "dauki Ruwaidah ku tafi mota, noke wuya tayi tace "um um, zare mata ido Mami tayi zatayi magana Anni ta dakatar da ita, "zo takwara, zo kuje ku siyo min Goro kinsan kin fishi wayau naki yafi kyau, Jiki na rawa ta mike zata wuce ta taka kafar Radiya, da karfi ta hankada ta cikin ihun azaba saboda tsinin takalmin tace "ke makauniya ce? baki ta bare ta fara kuka idonta kyar akan Radiya, da sauri Hafeez ya ja hannunta suka fita yana rarrashinta, Harara Mummy ta sakarma Radiya tace "sai kace kina yi da sa'arki, turo baki tayi tace "mummy zafi wallahi, "tashi ki bamu guri dalla,mummyn ta fadi a hassale, da sauri Goggo tace "babu fa inda zata, gyara zaman ki, abun kunya ce suka kwaso suji kunyar su kadai, Girgiza kai Anni tayi tace "babu komai ma, zauna! labarin an yishi ne, ba kirkirarre bane, kaddara ce.. Kamar yadda kika sani ni kanwar Harira ce, mahaifina asalinshi dan Gombe ne, mahaifiyata ce yar jalingo.. Allah ya jarabceni da soyayya da dan kanin babanmu, mun dade tare dashi, kullum in na fita tallan nono a gurin yake zama har ya kare, mu tafi gida.. wata rana nono na yayi kwantai, yakai ni dare, a hanyar mu ta dawowa gida kaddara ta afka mana, kaddarar da dan adam bai isa ya tsallake ta ba, kaddarar dake sanya rayuwar budurwa da iyayenta cikin mawuyacin hali... kaddarar da ta sanya Mahaifina rasa rayuwarshi... Bayan an fahimci ina dauke da ciki, saboda tsabar kunya irin ta fulanin "da" mahaifina ya kashe kanshi ta hanyar fadawa cikin teku, a cewarshi bazai iya fuskantar jama'a ba.. mahaifiyata da kishiyoyinta suka sani a gaba, bani da katabus cikin kauyenmu, ko kofi na taba babu wanda yake dauka, haka in na fita gari an dinga darewa kenan, shi kuma wanda yayi min cikin an nemeshi ko sama ko kasa an rasa, daga baya ne muka samu labarin mutuwarshi, nan fa na cire duk wani tsammani na samun mijin aure, saboda tsabar tsana da iyaye da yanuwana suka min na fita hayyacina na kare na lalace, mahaifiyata ma kunya ta sanyata ta rame, saida abin ya isheta tace "in shirya in tafi jalingo gurin mahaifiyarta, To acan ma hakan take domin kuwa saida na gwammaci zama a Gombe da zaman jalingo, duk ranar jumma'a sai Yakumbo kakata ta turani Gembu gidan Harira saboda gudun kunyar jumma'a, tana tsoron kar mutane su shigo su ganni, gaba daya yan uwa sun tsane ni ta ko ina, bani da gurin shan iska... wata ranar jumma'a mai cike da ban alajabi da tsoratarwa, Jumma'ar da manta ta ga yan uwan mutanen kauyen Gembu abu ne mai matukar wahala.. Tun cikin dare nake jin kaina kamar bani ba saboda yadda cikina ya dinga murda min, a hakan Yakumbo tace in fito in wuce Gembu, tun a hanya cikin ke murda min har al'amarin yaso fin karfina, cikin ikon Allah cikin ya lafa min har muka shiga cikin kauyen, a daddafe na karasa cikin kauyen nayi gamo da tashin hankalin da yasanya cikina kadawa har kafata ta gaza daukata, ina kallonka sanda ka dauko matarka da wata mace kuna gudu, da rarrafe na bi bayanku har nazo lungun shiga gidanku, nan gaba daya karfina ya kare, haihuwar ta taho min gadan gadan, Cikin ikon Allah na haifi 'yata mace, dankwalina na cire na nadeta dashi hade da mahaifar, koda na duba ta na dinga jijjigata na tabbatar bata raye, anan ne nayi kuka sosai har muryata ta dashe, ban kara sanin inda hankalina yake ba saboda zubar jinin da nakeyi.. Iska mai karfi ce ta taso a kauyen wacce kafin ruwa ya sauka saida ta dauke gidaje, wannan iskar ita ta farkar dani nayi saurin mikewa da gawar yata na fada cikin gidan ka, koda na shiga babu kowa a gidan sai kasar da ke tashi tana rufe ko ina na gidan, Daki na shige da sauri, har cikin dakin kasar ke shiga saboda iskar ba ta wasa akeyi ba, Iskar na lafawa ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya, A nan ne naji ihun jariri daga waje, da sauri na fito na iso gurin na hango dan Mala'ikan Allah cikin zani kwance a kirjin mahaifiyarshi, Share hawayen idonta tayi tace "Allah shi ke raya Matacce a lokacin da yaso, in ba Allah ba waye zai raya wanda kasa ta rufe idonshi, ko da na dagoshi jini ne ke fita daga cikin cibiyar da ba'ayi mata yanka da kyau ba, nan take nayi daki dashi na gyara yankan cibiyar na daureta da tsumma, ruwan bai tsagaita ba sai can gurin magriba, yana tsayawa na kunshe yata na mayar da ita cikin gawar da Allah ya nuna ikonsa akanta, A tare na rufesu da kyau saboda ko yadda aka zuba kasar wata rana ruwa ka iya dago gawar saboda sam kabarin baiyi zurfi ba.. A lokacin ne na fahimci wani abu guda daya game da cikin da nayi, wannan abu kuwa shine bak'in zare mai shara shara wanda babu mai ganinsa sai ubangiji, wannan zaren kuwa shine zaren kaddara! kaddarar rainon Abdallah ta nuna Baffa tace "danka, ita ta sani na dauki ciki har sanadiyar shi nazo har wannan kauyen.. Da fari a kullum ina tunanin ni kadai ce Allah baya so a duniyar nan da ya jarabceni da yin cikin shege a cewar bahaushe, haduwata da Abdallah na fahimci dama nazo duniya ne domin shi, koda na koma gida Yakumbo tayi tayi ta rabani dashi, a lokacin ne na nuna musu nima ina da hakki akan dana, tunda ni na haifeshi, babu wanda ya taba samun labarin bani na haifeshi ba, A lokacin da na bijirewa yakumbo sai ta koreni tace in tafi gurin uwata ita bazata iya da wannan abun kunyar ba, bani da kudi haka na goyashi saboda bashi da kayan sawa, ga rashin karfi nawa da nashi, Cikin ikon Allah muka samu motar zuwa Gombe, saida muka kwana uku a hanya muna tafiya, duk kauyen da muka tsaya anan zan roki ruwan zafi in mishi wanka, wata baiwar Allah ce ta hada min da wani maganin da nasha har na samu karfin jikina, sannan ta bani wanda na barbada ma cibiyarshi hade da gishiri, koda muka isa gida nan ma akayi min caaa ana Allah wadai dani, ban saurari kowa ba na shiga gurin mahaifiyata na roki gafararta, nace mata zan tafi neman abun da zan rike ďa na, Bata kalleni ba amma shashshekar kukanta shi ya tabbatar min da tana cikin tsananin damuwa, har na kai kofa ta kirani, dawowa nayi naga ta kwanto gefen zaninta ta fito da kudi masu yawa na furar da takeyi ta bani ba tare da ta kalleni ba, Murmushin farin ciki nayi na dauki wannan kudin a matsayin sa min albarka tayi, nan nayi mata sallama na fita, A tsakar gida sai zunde na sukeyi, babu wanda ya kula da halin da zamu shiga ni da dana, su dai burinsu in rabasu da abin kunyar da na dauko musu, cikin gari na wuce dan neman aikin da zanyi in ciyar da kaina, Da farko a wani kango muke kwana wanda ake gininshi kullum, kayan sawa na dasu nake dukunkuneshi saboda bashi da na sawa, da safe in masu ginin sun zo sai in goyashi in tayasu dan in samu wani abun rikewa a hannu, a haka har mukayi sati daya a cikin gurin, Ranar da muka cika kwana takwas Abdallah ya tashi da ciwo mai zafi kamar bazai yi ba, saboda rashin sanin abin yi na zauna na tasa shi a gaba nayi ta kuka, daya daga cikin masu kula da gidan ne ya tausaya min ya dauke mu a gurin ya kaimu wani shagon kwano yace mu dinga kwana a ciki, Sannan ya nemo min bedi da yawa da icce da tukunya yace in dafa mishi ya dan sha ruwan in mishi wanka, kafin inyi mishi godiya naga ya fita ya karbo wata kwarya, tuwon dawa ne a ciki da miyar kuka, nan na hau ci kamar karamar zakanyar da taga nama, A haka dai muka cigaba da rayuwa har na samu aikin shara a wani gurin gwamnati, saida na shekara biyu ina aiki a gurin, a lokacin Abdallah ya fara girma amma yau da lafiya gobe babu, kullum matsalar cibiya yake fama da ita, saida ya shekara bakwai sannan na kaishi asibiti, anan ne ake fada min tarin datti ne ya shiga cibiyar, jinjina tsawon rai irin nashi likitan yayi da na bashi labarin yadda na sameshi yace "lallai yaron nan Allah yana san saukar da rubutacciyar aya ta dalilinshi, anan dai likitan yayi mishi aiki, cikin lokaci kalilan ya samu lafiya muka dawo aikinmu, kullum tare muke zuwa yana tayani, A gefen gurin da nake shara akwai wata makaranta, da naga yana yawan zuwa gurin ya tsaya, kuma yana sha'awar karatun, sai na kaishi makarantar, islamiyya ma yana zuwa ta allo sannan ina koyar dashi a gida.. gwagwarmaya babu irin wacce bamu sha ba ni dashi, Lokacin da ya gama makaranta, ya fito da sakamako mai kyau, gwamnati ce ta dauki nauyin cigaban karatunshi saboda hazakar shi, A lokacin da yake karatun ne muka dan fara samun sauki saboda in aka bashi kudi a nan gida yake barin su, ya gwammaci in ya dawo gida muyi amfanin da kudin, *Nasara* ta Allah ce amma ni zan iya cewa ita ainihin kalmar ma'anarta shine Abdallah, shekarar da ya gama jami'a aka bashi aikin koyar da yan aji daya a makarantar, duk inda yaje a unguwarsu zakiji Ana fadin *Abdallah Hanne*, da sunan da yake amfani kenan ko a makaranta, ko kuma ace uncle Abdallah.. yaran unguwa yake tarawa yayi ta koya musu karatu.. jan majina tayi dan kuka na neman cin karfinta ta cigaba da cewa "tunda muke da Abdallah sau daya ya taba cemin "Ina Babana *ANNE* sunan da yake kirana kenan tun yana yaro, a ranar nayi kuka sosai wanda ya tayar da hankalinshi, tun daga ranar duk gorin da ake mishi bai damunshi, saboda yasan wani mai uban ma bazai nuna mishi jin dadi ba, A kullum saidai in dinga fada mishi kana da uba, kai ba dan shege bane, kai dan sunna, aure ne ya samar dakai, Kullum addu'ata Allah ya hadani da mahaifin Abdallah koda sau daya ne ya ji wannan farin cikin da yayi dakon su shekara da shekaru, bayan ta kai aya ta kalli Papy da ya fita hayyacinshi saboda tsabar kuka tace "shine mahaifinka Abdallah, wannan shine ya haifeka! Rungume Anni Papy yayi ya tsananta kukanshi yace "duk duniya babu na biyunki Anni, saboda ni kika bar gida, kika bata rayuwarki da lokacinki! saboda ni kika ki yin aure, saboda ki inganta rayuwata kika hana taki ta zama ingantacciya, why Anni, Why?? Ya karashe yana kuka sosai, Itama kukan takeyi tace "bani nayi ba Abdallah, Allah ne, yin Allah ne, in ba Allah ba waye zai rabaka da iyayenka, babu mamaki yayi haka ne domin ka zama nagartacce, ya rabaka da danginka ne dan ka zama gawurtaccen mutum, babu mamaki da kana gida duk wadannan abubuwan bazasu samu a gareka ba, dalilin da yasa Allah ya barka da rai bayan ka shiga karkashin kasa ba karamin dalili bane.. Maimuna ma ta taka rawar gani a cikin rayuwarka, tasoka a lokacin da kowa ke kiranka da dan gaba da fatiha, Duk kushe ka da akeyi a lokacin kamar ana zugata ne, ta tubure sai ta aureka, Maimuna ta nuna mana kauna lokacin da kowa ya kyamace mu, Cikin Kuka Mami tace "kinyi jarumtar da ko kwatanshi banyi ba Anni, hadasu yayi ya rungumesu yace "banyi regretting rashin tashi a cikin yan uwana ba, domin babu abin da ban samu ba a gareku, uwa, uba, mata, kawa, Aboki, ni ko me zancewa Allah, babu abin da zance sai tarin godiya a gareshi da ya hada ni daku.... Shuru ne ya dan ratsa gurin, sai ajiyar zuciyar kuka kawai ke tashi, kallon farin ciki Baffa yakewa Papy, fuskan nan tasu jike sharkaff da hawaye, Hannun shi ya kamo ya sake fashewa da kuka yana fadin *SAIFULLAH*, Ma'u dana ne, *SAIFULLAH*, jinina ne Ma'u...... Mrs Tijjani Shattima..... [19/03 8:17 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣0⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *Rayuwa takaitacciya ce. Kada ka cika ta da damuwa. Kada dogon Buri ya dauke hankalinka daga mutuwa. Aikata alheri a kowane lokaci watakila shi zai zamo mabudin Aljanna a gare ka*. Alkalamina bashi da karfin rubuta irin gigitar da Ma'u tayi, a zaune take amma jinta take tamkar a tsaka tsaki take, ita bata kai kasa ba haka bata kai sama ba, jinta take kamar wacce take lilo a tsakiyar iska, gaba daya hanyoyin sadarwa na jinin jikinta da kwakwalwarta sunyi balaguron wucin gadi.. Jin hannu da tayi cikin nata ya sanyata dawowa cikin hayyacinta a firgice, kallon hannun tayi hade da mamallakin hannun, ido cikin ido sukayi Anni tace "Da fatan kin gamsu da bayani na, da fatan kin tuno abubuwan da suka faru kamar yadda kika ji na fadesu, yanzu kin yarda da maganata na cewa ban taba magana da mijinki ba, na yafe miki zargin da kikayi min, domin a yau bana fatan abun da zai bata min rai, a cikin farin ciki nake matuka na ganin Abdallah na ya samu abinda yayi shekara da shekaru yana kawaicin tambayarsa duk da nasan babu ranar da zata fito ta fadi ba tare da yayi tunanin rashin mahaifi ba, kullum in na kalli murmushinsa nakan hango damuwa a bayan murmushin, wannan suna da ake kiranshi dashi na *ABDALLAH HANNE*, yana matukar yi min ciwo, ansha zuwa gabanshi a kirashi da dan mace, duk damuwar da Abdallah zaiyi bai taba yarda yayi ta a gabana ba, sakin Goggo tayi hade daga hannun sama tace "Alhamdulillah, Allah zan cika maka alkawarin da na dauka na yin azumi duk ranar da ka cika min buri na... Murmushin farin ciki Baffa yayi yace "Alhamdulillah, Allah mun gode maka da ka dawo mana da saifullahi, ina ma Allah zai dawo da Suwaiba ta dawo taga dan biyun ta, sai dai kashh Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, kallon Mamaki Anni tayi ma Baffa tace "kana nufin Abdallah yan biyu ne? Kwarai kuwa Baffa ya fadi yana gyara zama, Gaba daya ya manta da Ma'u da bai samun katabus in tana guri, ya cigaba da cewa "su biyu mahaifiyarsu ta haifa, kamar yadda kika sani shi mun dauka ya mutu, to ashe shi din ne rayayye ita kuwa Suwaiba tabi mahaifiyarsu, watanni kenan da mutuwarta, ta rasu ta bar 'ya'ya uku, HAFEEZ shine babba, sai Nadeeyah da Zainab, "_Hafeez_" Papy ya maimaita wasu hawayen masu zafi suka biyo bayan furucinshi, "Tabbas jini ba karya bane Anni ta fadi tana share nata hawayen, soyayyar da Abdallah ya nunawa Hafeez daga ganin farko ashe ba haka kawai bace, ashe Jini ne yayi aikin shi, dalilin zuwan Hafeez karatu Gombe ba karatun bane, wannan haduwar itace silar zuwanshi, duk inda alkhairi yake baya taba faduwa kasa banza ta karshe tana goge idonta da gefen hijab dinta, waya Papy ya dauko ya danna number Hafeez, "Kana ina ne?, ya tambaya murya a shake, "Muna kofar gida, mu zo ne? Hafeez ya amsa cike da girmamawa, "eh kawai papy yace ya kashe wayar, Hankali a tashe ya shigo gidan saboda yanayin da yaji muryar yasan babu lafiya, kusa dashi yaje ya tsuguna "Gani Papy, Wani irin kallo yayi mishi wanda yake nuna tsantsar soyayya ga mai yinshi, hannunshi ya rike hade da hada jikinshi da nashi da karfi, "kai jinina ne Hafeez, ashe kai dana ne, ina ma nasan wannan tun ranar farko, da kome zakayi tare zamuyi shi, da ban barka kayi wahalar komai da kanka ba, cikin rashin fahimta Hafeez ya da dago ya kalli idon Papy da yayi jajur, zaiyi magana Papy yayi saurin kada kanshi yace "kai jinina ne Hafeez, kai dan yar uwata ne, dan wacce muka kwanta a mahaifa daya ne, Wani irin kukan farin ciki ne ya kufcewa Hafeez, duk yadda yakai da hangenshi bai hararo kusancin nasu har ya kai haka ba, shidai yasan kamannin Baffa sosai yake gani a jikin Papy sai fari da ya banbanta su, sake rungumeshi Papy yayi yace "yau ranar farin ciki ce ba ta kuka ba, Mummy da karyayyar zuciyarta ta tsumu sosai tace "kukan ya zama dole, kuka ne na farin ciki, Shi yanzu nasan kukan tunowa da Suwaiba yakeyi, share hawayen tausayi tayi tace "ina ma Lokacin da suwaiba ta debo mai tsawo ne ta ga wannan ranar, kallonta Papy yayi yaga ita din ma tana dan yanayi dashi yace "kema yar---- cike da murna Baffa ya katseshi da cewa yayarka ce, ita ce Babba, nuna Ma'u yayi yace "wannan ita ce ta haifeta, su biyu ne, Allah yayi wa Halima rasuwa da dadewa, sai ita kadai ta rage mana, ashe wani farin cikin na tafe zuwa garemu, ashe ina da rabon ganin Magaji na kafin kasa ta rufe min ido, Wannan kalma ta *MAGAJI* ita sanya Goggo jin wani dumi tun daga kanta har cikinta, Ido ta zurawa Baffa da yake ta sambatu a gaban Papy da Anni, duk yadda taso su hada ido dashi sam yaki dan gaba daya ya manta Allah yayi halittar ta a gurin, Yasan dai tana makale cikin ranshi amma ganin Papy ya sanyashi mance duk wata soyayya in ba tashi ba, ji yakeyi ina ma ace da kuruciyarshi da sai yayi zagaye da Papy a bayanshi ba tare da ya gaji ba.. Wani irin kugin taji a cikinta tunda Anni ta fara basu labarin shi dawo mata, ganin yadda tun yanzu Baffa ya ki koda kallonta ya tabbatar mata da lallai akwai aiki a gaban ta, Mikewa tayi da niyyar tafiya bayi dan cikin nata jinshi takeyi kamar zata kasayar da ya'yan hanjinta, Tana mikewa taji kafarta tayi mata nauyi saboda yadda zawon ya taho mata gadan gadan, dakyar ta daga kafarta, tana dagawa zanin jikinta ya sabule ta feso shi ba tare da sanin inda zashi ba, Wani irin ihu Radiya ta saki tana fadin "I'm dead" wayyo Allah na, "Dariyar Ruwaida ce ta cika gurin tana yi tana fadin *nyan nyan nya* disgusting! Papy kagani da kace "in an min abu in dinga hakuri Allah zai saka min, yau gashi naga ni da idona, wayyo cikina, she deserve more old lady karo mata,, Janyota Mami tayi da karfi ta sake maida idonta cikin mayafinta kamar yadda kowa yayi a gurin, kunnenta taja tace "ke wace irin yarinya ce, in sake jin kince pim kiga abun da zan miki, Mummy ce ta tashi da sauri tana tare Goggo tana fadin Goggo lafiya, Hawayen takaicin da Goggo ke rikewa ya zubo a kuncinta, cike tsoron ganin hawaye a idon wacce babu abin da ke sata kuka Mummy ta ja hannunta sukayi bayi, shi kuwa Baffa maida kallonshi gurin Radiya dake kuka tana kyankyame jikinta yayi yace "je ki wanke jikinki mana, ko so kikeyi warin ya kashe mu, baki ganin muna cikin farin ciki ne, karaff kalamanshi a kunnen Goggo, wani Kukan ta sake fashewa dashi a zuciyarta tana tambayar kanta ta inda aka samo matsalar, Damuwa ce karara a fuskar Mummy dan iya rayuwarta bata taba ganin hawaye a idon Goggo ba, bayan ta gama kimtsa ta suna jiyo muryar Baffa yana basu Labarin Suwaiba da 'yayanta, ita kanta Radiya cike take da mamakin yadda yake basu labarin suwaiba da 'yayanta dan a da ko labarinsu baya son ji bare ya ba wani, Kallon Goggo Mummy tayi tace "kiyi ma Baffa uzuri, shekaru sama da arbain rabonshi da dan da ya cire rai da kasancewarsa a duniya, sannan kuma shi kadai ya zame mishi namiji, kinga dole yayi farin ciki, ni kaina cikin farin ciki nake, dan a yanzu na fita a sahun ni kadai, mun zama biyu, ďan uwa dadi gareshi Gog---- dogon tsaki taja wanda ya katse mummy da karasa maganar ta, "Ba tun yau na lura da cewa ke din bakya kishi na da kanki ba, inama Allah Halima ya bar min ya daukeki Goggo ta fadi cikin gushewar hankali, Zaro ido Mummy tayi zatayi magana ta jiyo muryar Baffa yana kwala kiranta, bai bari ta amsa ba cikin doki yace "fito muje gidanki suga Nadeeyah, ki kira muntari in yana gari shima ya dawo gidan sai su hadu, Jaka Mummy ta dauka tace ma Goggo "kiyi hakuri, gobe zan dawo, ko kallonta batayi ba, idonta na kan kofa tana jiran ganin Baffa ya shigo dan su hada ido ta samu dukkan madafun ikon hanashi zuwa, Anni da Mami ne kadai suka leko suka yi mata sannu da jiki, sannan suka wuce,, Shurun da taji a tsakar gidan ne ya bata damar lekowa, babu kowa a gidan sai Radiya dake tsaye daga ita sai undies, tana ganin Goggo taja mata tsaki tace "walhy kin cuceni, sam bazan iya cin abinci ba yau, gashi Mummy ta tafi ta barni, nidai gaskiya baki kyauta min ba, kuma ga kashin ki nan walhi bazan kwashe ba, Hadiye miyau mai daci Goggo tayi ta wuce daki tana saka abubuwa marasa kyau da zata aikata, saken da tayi na ganin cewa babu wanda zai shigo rayuwarta shi ya janyo mata wannan matsalar...... ♡♡♡♡♡♡! ♡♡♡♡♡♡♡♡! ♡♡♡♡♡♡♡♡♡! Nayi kyau Momma!! Kallonshi tayi sama da kasa, jan wando ne a jikinshi ya dan matse daga kasa sai green riga ta dafe a jikin tayi mishi kyau sosai.. Murmushi tayi ta gyara mishi kwalar rigar tace "First class kyau ma, kaima kasan u are excellent! Rungumeta yayi hade da yi mata peck yace "zan fita ur --- prayer is needed ta karashe hade da cewa "kana da bukatar tuna min ne, dariya yayi ya dauki keyn motarshi, har ya kai kofar fita daga dakin tace "baka fa fada min sunan diyar tawa ba, waigowa yayi yana dariya yace "tooo expensive, nawa zaki siya?, Dariya tayi sosai tace "abun da yafi komai tsada a gurina zan biya, *TEE NA* Murmushi yayi yace "luv yhu Momma, *Umm Nadeeyah* is the special one.. my Omri... Ya karashe hade da fita da dan gudu gudu, zama tayi tana maimaita sunan farin ciki na ratsa ko ina na jikinta..... A kofar gida yaga Raliya tsaye tana tsaki tana kallon drivernta yana duba mota, tsayawa yayi yace "Maman fadeel fita zakiyi? "Eh Taheer motar kuma ta samu matsala, Ayya, shigo muje in kaiki mana, Taheer ya fadi yana fitowa a mota, Girgiza kai tayi tace "bazan matsa maka ba, jeka kawai walhy, Babu wani matsi Allah, saidai in motar ta miki karama ya fadi cikin tsokana, Dariya sosai tayi ta bude ta shiga ta cema drivern ya kai motar gurin mechanic... Dadin da yaji baya misaltuwa na sanin gida zataje... kwatance ta fara mishi taga yana ta kai kanshi tun kafin ta fada mishi, murmushin jin dadi tayi ta kasa tsokanarshi saboda kar tasa yaji kunya.... ******* Tun karfe biyu ya sauka a airpot din Abuja, bai tsaya jiran wata wata ba ya dauki drop har kaduna, zuwan nashi na aike ne a ganin Anty Reemah, bata san shi zuwan nashi ya wuce aiken da tayi mishi ba, Musaddiq ne kadai yasan da zuwanshi dan shima ya matsa a kawo mishi wasu takardun makarantarshi, saboda go slow basu iso kaduna ba sai to 5, A daidai gonin gora Musaddiq ya tsaya ya daukoshi cike da farin cikin sake haduwarsu bayan watanni, hira sosai sukeyi a motar kamar wadanda suka shekara goma basu hadu ba, ko wanne a cikinsu yayi kyau sosai, musamman Hilal da ya fara practicing karatun da yayi ta hanyar yin zanen da ya doke na dubban mutane a cyprus, Ba kananan kudi yake rikewa ba, shiko Musaddiq bautar kasa yakeyi, shima yana samun kudi sosai tunda yana taya Daddy wasu yan ayyukan, saboda tsabar kaguwar da Hilal yayi ya sanyata a ido shi ya sanya shi ganin kamar Musaddiq baya gudu, tsayar dashi yayi hade da karbar tukin ya taka motar a 140.... Tsayawa yayi da ya sauke Anty Raly a kofar gidan, ganin da tayi bai tafi ba yasa ta dawo tana murmushi tace "ko in kira maka ita ne?, Murmushi ya sakar mata mai kyau wanda ya bata amsar manufarshi, shigewa ciki tayi tana adduar Allah yasa Daddy baya gida, dan tasan a gidan basa zance sai sun gama secondary school, ita kuma bazata iya hana Taheer ba domin nauyinshi take ji sosai... A parlor ta samesu zaune suna kallo, saboda akwai Badar a parlon shi ya sanya Nadeeyah zama daga lungun Husnah tana gyara kumbarta da tasha jan lallen da ya rinu sosai ya koma maroon, zama tayi ta kalli Nadeeyah da take ta mata murmushi, "ina wuni Anty, ta fadi hade da mikewa ta dauki Fadeel, hannunta ta kama tace "wow waye ya muku lalle, Nuno mata hannu Husna tayi tace "Sadiya, jiya tayi mana, shafawa Anty Raly tayi tace "kaii gaskiya yayi kyau, kwa kirata tamin in Abban Fadeel zai dawo, kallon Badar tayi tace "Rasa kunya ina wuni, bata kalli inda take ba ta mike tana fadin lfy lau ta wuce daki, girgiza kai tayi tace "Allah ya shirya, Nadeeyah jeki waje ki karbo min sako pls, ajiye Fadeel tayi ta dauko dark purple hijab din islamiyya har kasa tasa ta yi hanyar waje, tsayar da ita Anty Raly tayi ta taso tazo inda take, gyara mata Hijab din tayi dan ya karbeta sosai bata ga dalilin sata ta canza ba, "karki bani kunya kadai ta fadi hade da tura ta waje, Tafiya ta fara yi tana maimaita "karki bani kunya a cikin zuciyarta, sharewa tayi kawai ta fita dan ganin sakon da zata amso mata, Tana fita idanuwansu suka sarkafu cikin na juna, tsayawa tayi a bakin gate din ta kasa karasawa gurin da yake, Tunanin juyawa tayi sai ta tuno kalaman Anty Raly, Kamar zatayi kuka ta makale a jikin gate din gidan, karasowa yayi yana murmushi, yanayin tsoronta na matukar burgeshi, gab da ita ya tsaya yana kallon yadda take wasa da yatsun hannunta, Hankalinshi kacokan ya tattaro ya maida kan yatsun hannunta da kafa, ya ilahi ya fadi a cikin ranshi, "Son yarinyar nan dada narkar da zuciyarshi take, Saida suka dauki minti uku babu wanda yayi magana, ganin shurun yayi yawa yasa ta dago kai ta kalleshi, saida ta gwammaci da bata dago ba saboda wani irin mayataccen kallon da yake mata, maida kanta tayi da sauri murya na rawa tace "ina wuni, wai ka bani sako inji Anty! Dariya yayi hade da sauke ajiyar zuciya, "sakon zuciyata zan baki, ki taimakeni ki amsheta hannu biyu, kinsan ita zuciya sakarya ce akan abin da take so, Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari, duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe. Jin daɗi da walwala ba za su taɓa samuwa a tattare da ni ba matuƙar babu soyayyarki a cikin zuciyata. Ki taimaki wannan zuciyar da bata taba furta so ba sai akanki *Umm Nadeeyah*. Kalamanshi sunyi mata nauyi matuka, sun sanya ta rikirkicewa ta kasa tsayuwa, sun sanya dukkan jikinta mutuwa, ta rasa ainihin abin da take ji a cikin jinin jikinta, "Dan Allah zan shiga gida kafin wani yazo ya ganni a waje, yanayin yadda tayi maganar ya sanya duk wata kasala sauka a jikinshi, yarintarta mai cike da nutsuwa ita tafi komai tafiya da imaninshi, Rankwafowa yayi ta kasan fuskarta yana kokarin hada ido da nata, gigitaccen Hon din da sukaji ne yasanyata dagowa da sauri har tana gogar kwantaccen sajen Taheer......... Mrs Tijjani Shattima......@ [24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣1⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Hannu Musaddiq yasa ya toshe kunnuwanshi saboda karar horn din , da yaga Hilal baida niyyar cire hannunshi a kan horn din yayi saurin janye hannun yana fadin "Haba Malam, sai kace tashin hankali, nasan yaji horn din da kayi zai bude, ko kallon inda Musaddiq yake baiyi ba bare yasan me yake fadi, nan da nan fararen idanuwanshi suka rine zuwa jajaye, da ace wani zai rabi saitin kirjinshi da yaji mugun bugun da yakeyi kamar ana lugude, ido ya zubawa Taheer dake tsaye jikin kofar gate din har lokacin bai matsa ba shima kallon motar yakeyi, kokarin bude gate din Nadeeyah tayi taga yafi karfinta ta shiga kwala kiran mai gadin, jin bai amsa ba ya bata tabbacin baya kusa, hannu tasa da niyar sake gwadawa ko zata iya taji hannun Taheer akan nata, da sauri ta zame hannunta taja baya, murmushi yayi ya bude gate din yana jiran mai motar ya shigo ya rufe, shuru har minti biyu ba'a motsa motar ba, "Muje Mana, an bude gate kuma ka barmu a zaune, har lokacin bai kalli Musaddiq ba, ganin da Taheer yayi motar ba shigowa zatayi ba yasashi kokarin rufe gate din, da sauri ta tare gate din tace "shigowa zaiyi, inaga motar ta samu matsala ne, bari in tambayeshi, samm bata kawo Hilal na cikin motar ba, karasowa gefen drivern tayi ta buga windon hade da fadin "Yaya Musaddiq zaka shigo ne? Bude kofar taji anyi da karfi... na take ta maida Murmushin fuskarta tayi da sauri saboda ganin yanayinshi, wani mugun kallo yake mata wanda ya sanya hantar cikinta kadawa, cikin dacin rai yace "wanene wancan? Un-un-cle din mu ne na school, kamar ta watsa mishi wuta yaji, uncle? Karatu yake koya miki anan? "Um um ta fadi tana girgiza kanta, tare da Anty Raly suka zo, Ehen sai ke kuma kika fito kina mishi me, "in ina ta fara yi wanda ya tabbatar mishi da zarginshi, dakyar ya iya controlling yaja tsaki hade wucewa gurin Taheer, Zagayawo Musaddiq yayi yana tsokanarta ya shiga gefen driver ya shige cikin gida, Bayan motar tabi tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, bata kalli inda su Hilal suke ba ta wuce da niyyar shigewa cikin gidan, kallo Taheer ya bita dashi har ta kurewa ganinshi, maido da kallonshi yayi gurin Hilal da ya tsareshi da tambayoyi, Amsar wasu ya bashi ciki harda fada mishi dalilin zuwanshi, tambayar karshe da yayi mishi ita yake ta juyawa cikin kwakwalwarshi, " *Shin soyayya kuke koyarwa a makarantar*? Bai iya amsata ba dan yana mishi kallon kuruciya karara, hannu ya sake mika mishi a karo na biyu yace "zan tafi mutumina, dan Allah ka dan turo min ita akwai sakon da zan bata, wani irin mugun kallo ya watsa mishi yace "kaga malam yarinyar nan marainiya ce, soyayya ba tata bace yanzu, ilimi shine kadai zai zama gatanta, in ta gama school den she decide abun yi next, nd ko ta gama karatu ma tana da mijin aure, Musaddiq ya nuna mishi wanda bai ma san sunayi ba, wakarshi yake ji a earpiece yana kada kai yace "kaga wancan he is her cousin nd husband to be, so plss spare her, ka barta tayi concentrating pls, wani irin dumi Taheer yaji a cikin jininshi, kallon Musaddiq din yayi sannan ya dawo da dubanshi gurin Hilal da ya fara tafiya yace "Hey.... tsayawa Hilal yayi ba tare da ya waigo ba, gurin da yake Taheer ya karasa yace "as far as batayi aure ba, ta zama allura cikin ruwa, in rabona ce ko an sa mata rana da shi, sai na aureta, nd da kake cewa Marainiya ce, dama Marainiyar nake nema, wacce zamu zama gatan juna, karatu kuwa *Umm Nadeeyah* zata yi shi daga matakin farko har karshe, ina yi ma kaina fatan nasara domin ina kallon future dinmu tare... have a nyc day.. ya karashe fadi hade da taba kafadunshi,.. *umm Nadeeyah* Hilal ya maimata zuciyarshi na dabdalar bugawa, wato ma ta fada mishi yadda take son ya dinga kiranta, kasa dagawa yayi a gurin da yake, kalaman Taheer sun zame mishi kamar dagger a cikin zuciyarshi, Yana tsaye a gurin ya jiyo muryar Musaddiq yana tambayar *Idi* meye a hannunshi, "sako ne akace in kai ciki, "kawo nan Hilal ya fadi cikin dacin rai, gurin da yake tsaya ya karaso ya rankwafo ya miko mishi, kamshi ne ya daki hancinshi da ya karbi ledar, wasu cards ne a ciki wadanda suke bayyana irin tsantsar son da akeyiwa wanda aka mallakawa su, sai sabuwar waya mai masifar kyau da tsada, Yana gama dubasu ya kwala kiran  Idi yana fadin ina mutumin da ya baka wannan ledar "ya wuce yallabai, Idi ya fadi cike da girmamawa, a hasale ya wuce hanyar parlon, bugun kofar yayi da karfi wanda hakan ya firgita Anty Raly da Nadeeyah da suke tsaye Anty Raly na jero mata tambayoyi, wurgi yayi da kayan a kasan carpet yana yi musu wani irin kallo, murmushi Anty Raly tayi tace "a,a My son, yaushe ka shigo garin? Bai amsata ba ya isa gaban Nadeeyah dake tsaye a tsorace, "Aure kike so ko Umm Nadeeyah?yadda ya kira sunan kamar me ciwon baki saboda tsananin kishin dake cinshi.. Dago ido tayi a firgice tana girgiza kai, sunan da ya kirata dashi ya firgita ta saboda ba hakan ya saba kiranta ba, rai a bace yace "to me kike so? at ur early age kinsan ki dinga kawo samari gida har ki fita zance, kina gab dashi kamar zaki shiga cikinshi, bazaki ko iya hakurin ki gama secondary school ba, ko tausayin kanki bakya ji, in aure kike so ayi miki, sai ki fada a sashi ya turo kije can ki bata rayuwarki tunda karatun ne bakya so, shi kanshi baisan yana zubo wasu maganganun ba saboda tsananin bacin rai, kukan da takeyi shi ya sanya Musaddiq dafa shi yace "calm down mana, haba, zunubi tayi ne? Meye laifi dan ta tsaya da saurayi? karbewa Anty Raly tayi tace "kuma Taheer ma bashi da matsala sam, kusa da gidana suke,  shin ba gara tayi aurenta ba ma ta huta, "sai ki aurar da ita, ya fadi cikin ficewar hayyaci, gaba daya idanuwanshi sun rufe, saboda bacin rai da tsananin kishi ko kukan da takeyi bai kula dashi ba, ya nuna ta da yatsa yace "na rantse da Allah in na sake jin kin tsaya da wani ko kin bashi dama har ya iya zuwa ki tsaya kuna taďi dashi sai na masifar ci miki mutunci tunda naga alamar baki san ciwon kanki ba, Anty Raly da ranta ya gama baci tace "yau naga ikon Allah, kai zaka aureta da zaka hanata kula samari, cike da rashin kunyar da ko yana ma wasu ita baya mata yace "Bazan aureta, domin ba sa'ar aurena  bace, she is too young for my liking.. zan dai zame mata garkuwar da zata rike kanta a ko wani ta samu kanta, kalmar "sa'ar aurena bace ta bata ran Musaddiq da Anty Raly matuka, kallonshi Musaddiq yayi rai a bace yace "hey bata bukatar garkuwarka, live ur life nd let her live hers, Hannunta ya kama ya cigaba da cewa "ba sa'arka bace, kamar yadda kace, so ka barta tayi abun da takeso, ka nemi sa'oinka ka zame musu garkuwa, yana kaiwa nan yaja ta zuwa dakinsu, Hilal kamar zai mutu saboda takaicin zuciyarshi da furucinshi, To ya zaiyi, shi kanshi baisan ya fadi wasu abubuwan ba saboda tsananin kishin da ya nemi zautashi, Kalaman Taheer sun matukar hassala shi, ledar da yayi wurgi da ita ya dauka ya mikawa Anty Raly yace "ki mayar mishi da abunshi, babu wanda a gidannan waya ta gagareshi, wallahi in kika ce baza ki mayar ba yanzu zan kira Daddy in fada mishi yadda kike son lalata rayuwar marainyar Allah, Yana kaiwa nan ya fara tafiya zuwa dakin Musaddiq, "In ka fasa Hilal, in ka fasa ka fada ka raina kanka, bazan mayar da wayar ba dan Allah in kana iyawa kazo ka zaneni, mara kunyan banza da wofi, Bayan Hilal Husna tabi tana fadin "sorry my PP, rabu da Anty gobe zan mayar mishi da wayar school, wani irin miyau ya hadiye mai daci a hankali yace " laifi ne dan inason gyara rayuwarta, girgiza kai tayi tace "a'a ya Hilal, in akwai irinka cikin rayuwarmu bazamu taba tagayyara ba, amma pls ka dinga danne zuciyarka, in kayi fushi kai kanka tsoron kanka kakeji, bana son ganin fushin.. gyada mata kai yayi ya murda dakin ya shiga hade cewa ta tafi ta barshi shi kadai.... A can daki kuwa Musaddiq keta rarrashin Nadeeyah wacce keta kuka sosai harda shashsheka tana fadin "walhi ban taba mishi magana ba, kuma ni bance ina sonshi ba, nima buri na inyi karatu mai zurfi, dan Allah Ya Musaddiq ka bashi hakuri, wallahi bazan kara ba.. Zaunar da ita yayi a gefen gadonsu, ya tsuguna a gabanta ya sa hannu yana share mata hawaye yace "karki damu, ranshi ne ya baci, duk tausayinki ne yaja hakan, Yasha fada min in dinga sa ido a kanki saboda maraicinki, Hilal na matukar son kiyi karatun da zai sa ki dogara da kanki, A iya sanina ban taba ganin abun da Hilal ya damu dashi ba bayan iyayenshi, sai ni, sai ke yanzu da kike son kwace min mishi, nidai bazan yarda ba, kawai kinsa ya daina damuwa dani, ko waya mukeyi ya dinga tambayata ke kenan, Dariya tayi sosai, yadda yayi maganar a shagwabe ya sanya ta manta duk wani kuncin da ya tokare zuciyarta, Murmushi yayi shima ya mike yaja kumatunta yace "haka nake so kanwata, karki kara zubda hawaye kinji? kai ta gyada mishi ya kashe mata ido daya ya juya zai fita a dakin, Ganin Badariyya yayi tsaye a bayanshi tana huci, wani irin kallo yayi mata hade da cewa "lafiya? Bata iya bashi amsa ba sai hawaye ya ga suna sauka a idanuwanta, mtswwwww.... dogon tsaki yaja ya bi ta gefenta ya bude kofar dakin ya fita, wani kololon bakin ciki ne ya turnuke Badariyya tayi ma Nadeeyah wani irin kallo hawaye na cigaba da ambaliya a idonta, Mikewa Nadeeyah zata wuce Badar ta janyo ta ta hankada ta baya, "uban me kukeyi a dakin nan ta fadi murya kausashe, Husnah da shigowarta dakin kenan tace "me ko sukeyi, *Soyayya* mana, baki san suna soyayya ba dama? ta fadi hakan ne dan ta tunzura ta, dan ta gane take takenta da dadewa.... aiko ta tunzuru, dan hauka ta fara yi, ta cakumi wuyan Nadeeyah iya karfinta tana fadin "wallahi saina kasheki, shakar da tayi mata ita ta hana ta ihu mai karfi, sai hawayen azaba da take fitarwa, Da Husnah taga ta kasa kwace Nadeeyah a hannunta kuma tana ganin take taken zata iya kashetan da gaske tace "na shiga uku, wallahi karya nakeyi, ki saketa Badar, inaa kesashshiyar zuciyar Badariyya bata ji bata gani wen it comes to Musaddiq, Da sauri Husnah ta fita tana ihu tana fadin "Zata kasheta, wayyo Allah Anty Raly kizo zata kashe ta, Wa za'a kashe? Daddy da ya shigo a lokacin ya tambaya a gigice, Husnah da kuka ya kufce mata ta nuna dakinsu tace Badariyya zata kashe Nadee---- kafin ta karasa fadi Hilal ya murda kofar da karfi har yana cire handle din kofar, lokacin da ya shiga kiriss ya rage Nadeeyah ta suma, dan idonta da ya jike da hawaye ya fara lumshewa, ita kanta Badar din kukan takeyi, amma zuciyarta ta ki bari ta saketa, dama wannan damar take jira, tsanar da tayi ma Nadeeyah mara misaltuwa ce, gara ta kasheta kowa ya huta, tasan hukuncinta kadan ne tunda bata kai 18yrs ba "a karancin iliminta na addini", Iya karfinshi ya sa ya janye Badar, yayi wurgi da ita jikin drawer dakin har saida mudubin drawer ya fashe, da gudu Musaddiq yayi kan Nadeeyah da ta durkushe tana tari dakyar, rungumota yayi jikinshi yana jijjigata, yana kiran sunanta da karfi saboda firgici...... Mrs Tijjani Shattimah...... [24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣2⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Ganin yadda take lumshe ido ya sa Daddy cewa "kawo ruwa da sauri Husnah, rige rigen dauko ruwa sukayi ita da Anty Raly, A kidime Musaddiq ya bude bakinta yana hura mata iskar bakinshi saboda yadda jikinta ya fara saki, babu wanda a cikinsu ya ji, ko ya saurari irin dukan da Hilal yakewa Badariyya kamar Allah ya aikoshi, Tun tana ihu anaji har muryarta ta dashe, da gudu ta rarrafa ta rike kafar Daddy tace "dan Allah Daddy kace yayi hakuri bazan kara ba wallahi, finciko Hilal yayi yace "kin san Allah dama, belt din hannunshi har ya tattare saboda azabar duka, Badan tausayi ba, sai dan saboda muryarta ta ishi Daddy yasashi cewa "kyaleta Muktar! Badan yaso ba ya kyaleta yana yi mata kallon ban gama dake ba, a guje ta bar dakin tana ihun azabar haurin da yayi mata a baya, a kofar shigowa palon taci karo da Su Mummy, rungumarta tayi a tsorace tace "ke lafiya, meya faru? Kankameta Badar tayi tace "zasu kasheni Mummy, wayyo Allah bayana, kallon su Mami da Anni tayi tace "ku shigo ciki ku zauna, shigowa sukayi suka zauna, Mummy taja hannun Badar suka shiga dakin, Tsaye ta samesu dukkansu akan Nadeeyah da ta bude idonta tana maida numfashi, Belt din hannun Hilal ta kalla rai a bace tace "uban me tayi maka kayi mata dukan ficewar hayyaci, abin da ya kawoka gidan nan kenan, ya ilahi kayi min maganin yaron nan da duk in yazo gidana sai ya tayar min da husuma, wannan wace irin mas---- dakata min!! Daddy ya katseta fuskarshi a murtuke babu alamun wasa, Naji alamar zuwan baki, muje in samesu, da kaina zanyi maganin matsalar gidana, naji duk abin da ke faruwa tun zuwan Nadeeyah gidannan har kawo yau da idona ya gane min, "Nadeeyah, Mummy ta fadi a hankali, ta kalli Nadeeyar dake kwance har lokacin a jikin Musaddiq, Saida Daddy ya bar dakin ta tambayi Husnah abun da ya faru, yadda abin ya faru ta fada mata, ta sakaya mata ainihin abun da ya tunzura Badar, jiki a sanyaye ta fita a daki dan bata da mafita sai jiran hukuncin da Daddy zai yanke.... Ya Musaddiq.. Daddy yana kiranka, Husnah ta fadi tana ajiye wayar da Daddy yayi kiranta, maida kan Nadeeyah kan pillo yayi, ya sauka suka fita a dakin tare da Anty Raly domin kaiwa baki abin ci da sha... "Baki da karfi dama kika fara *Soyayya* dagowa tayi ta kalleshi, tsareta yayi da ido kamar bashi yayi maganar ba, "ni bana soyayya, ta fadi hade da rufe fuskarta da hijab dinta, faduwar gabanta ya karu sosai, nade belt din hannunshi yayi yace "in ma kinada niyyar farawa gara in tuna miki, kije ki koyi fada, dan in baki da karfi zaki cutu a soyayya, ko tsoron maza bakya ji kin wani tsaya gab dashi, to da bamu zo gurin ba me zai faru kenan? Shi--- runtse idonshi yayi maganar ta makale a makoshinshi, a zuciyarshi yana neman tsari da shedan dake kawata mishi abubuwa marasa kyau, canza maganar yayi da cewa "wuyan baya miki zafi, in yana miki zafi kiyi magana a kaiki asibiti, "Murya can kasan makoshi tace "zai daina in shaa Allah, yana yi kadan kadan, Dauko waya yayi a aljihunshi ya danna number Hinad, tayi ringing sau biyu, a na uku ta dauka, "ina Zee,? jin ya ambaci sunan Zainab yasa ta mikewa zaune, "bata nan ya Hilal, sun fita da *Anty Mee*, kashe wayar yayi ya kira Meerah taki dagawa, wayar na katsewa tata ta shigo, video call, tsaki yaja ya dauka, "Hi dear, ta fadi tana daga mishi hannu, "Hello Meerah kina lafiya? Kamar yadda ka gani am very ok, but am missing yha, ta fadi a shagwabe, kauda zancen yayi ta hanyar tambayarta "where is Zee? Juya wayar tayi zuwa gurin Su Adeel cikin muryarta mai dadi tace "say Hi to Ya Hilal, fitowa tayi a cikin motar wasan yara ta bude hannu hade da cewa "oyoyo! Murmushi yayi yace "yawo, kika fita yawo baki fada min ba, nt good baby, karbar wayar tayi ta bata fuska tace "wayau zaka min ko, dan kaga na hakura bana kuka har yanzu, ka gudu ka barni baka kaini gurin Adda na ba, Tun Nadeeyah na rike murnarta najin muryar gudan jininta, har ta kasa tayi saurin zuwa gurinshi zata karbi wayar, hada ido sukayi tayi saurin maida hannunta, dariyar da bata fito fili ba yayi, sannan ya mika mata wayar, da sauri ta karba sukayi ido da ido da abar kaunarta, safa da marwa ta shiga yi suna hira cikin farin ciki harda yar kwallarsu, murnar ganin yadda zainab ta koma ya hanata sukuni ta dinga yi mata tambayoyi, sun fi minti bakwai suna hira sannan tace "ga Anty Mee ku gaisa, tana kula damu sosai ni da Ya Hilal, kallon juna suka yi na seconds kafin Nadeeyah ta saki murmushi tace "ina wuni, amsawa tayi itama tana mata musayar murmushi, yadda take jin sunan Nadeeyah a bakin Hilal ya tabbatar mata da lallai ganin da tayi mata yafi jinta, domin duk kushen mai kushe bai isa ya nemo aibun Nadeeyah ba, kyawunta na musamman ne, gashin da yayi kwance a gefen farar fuskarta su sukara kara kawata kyawunta, gashi in tayi murmushi ko dariya gefen kumatunta daya ke lotsawa can ciki, haka nan Meerah taji wani abu ya darsu a cikin zuciyarta, ita kanta Nadeeyah da bata cika lura da abu ko sanyashi a ranta ba taji wani abu kadan game da Meerah, kallon farko da sukayi wa juna dukkansu suka fahimci jininsu yayi nisa gurin haduwa, shurun da sukayi suna kallon juna ya sanya Zainab karbar wayar suka cigaba da hira, Tunanin inda ta taba ganin Nadeeyah meerah ta shiga yi, dakyar ta iya tunano sketch din da yayi a school as assignment, duk da wancan da dan yarinta sosai amma ta gane ita ce, lokacin duk wanda ya tambayeshi sai ya amsa cikin shakiyanci yace "My dream girl, a mafarki na na hadu da ita shine kamanninta suka mannu a zuciyata, nan da nan kamannin Meerah suka canza, zufa ta fara karyo mata tace "Zee bani wayar nan, mika mata tayi ta zauna kusa da ita, "Bani Hilal pls, tace ma Nadeeyah fuskar ta babu yabo babu fallasa, sai a lokacin Nadeeyah ta waigo ta kalleshi dan ta manta ma yana dakin, juyar da wayar tayi inda ake iya ganinshi ba tare da ta sani ba ta sunkui da kanta kasa, wani irin kallo Meerah ta hangoshi yana yi ma Nadeeyah wanda bata taba sanin ya iyashi ba, lokacin da ta mika mishi wayar bai kalleta ba ya fara kokarin kasheta, da sauri Meerah tace "Kangiwa kana ji na? "Yes Meerah Turaki ina jinki, yadda ya kirata ya tabbatar mata yana cikin shauki, "ina kabar Musaddiq, ta fada tana jin wani mugun kishi a cikin zuciyarta, sai a lokacin ma ya tuna da Musaddiq yace "auchh yana daki may be, ko Daddy ya aikeshi, bari in dubo shi will call u, ya katse wayar kafin ma ta sake magana, Yana kashe wayar Husnah ta shigo dakin da gudu tana kiran Sunan Nadeeyah, Hijab ta mika mata tace "yi sauri kisa, kallon Hilal tayi tace "my PP, zo muje kaga wani abun al'ajabi, Maida wayarshi cikin aljihu yayi ya bi bayansu dan ganin abun da zata nuna mishi... Ga Nadeeyahn nan.... Daddy ya fadi yana murmushin jin dadi, Allah kadai yasan irin farin cikin da yake ciki, gani yakeyi kamar da ita kanta Suwaibar yake zaune, gefe Nadeeyah ta tsuguna tace "ina wuni, Hannu Papy ya bude mata alamar ta iso gareshi, kalle kalle ta shiga yi suka hada ido da Hafeez ya gyada mata kai yana murmushi, mikewa tayi ta isa gabanshi tana mai mamakin kamannin, tsugunawa tazo yi yayi saurin dagota ya rungumeta, kukan da yake kokarin boyewa yaki boyuwa saida ya zubda su, Damke Hannun Hilal dake yunkurin zuwa gurin Husnah tayi tace "Babanta ne fa, twins din Mama Suwaiba, cikin rashin fahimta yace "what, ba Baffa yace ya mutu ba, Baffa dake zaune ya jiyo Hilal yace "muma duk haka muka dauka Muntari, ashe yana nan da ranshi, kaddarar da ta boye mana shi ita ta sake hadamu dashi, kallon Nadeeyah da ta kasa sakin jiki har lokacin Baffa yayi yace "saki jikinki, wannan uwa yake a gurinki, haka uba, domin tare suka zo duniya da Mahaifiyarki, kallonshi tayi sosai dan ta gasgata maganarshi, tun daga hannayenshi har kafarshi saida ta kare musu kallon, kyawawan yatsun kafarshi da ya zamto irin na Mamma da nata shi ya tabbatar mata da maganar Baffa, wata irin runguma ta sake yi mishi tana kuka sosai a zuciyarta tana jero alhamdulillah, ta kusa minti uku a jikinshi tana tunano rayuwar da sukayi da Mamma, ji takeyi kamar dawo da ita Allah yayi cikin wata suffar, saukowa a jikin Mami Ruwaidah tayi ta kama hijab din Nadeeyah tace "let my Papy be, karki bata mishi kaya da hawayenki, Papy na baya son kuka, dagashi tayi ta fara shafa fuskar Ruwaidah hade da rungumeta, duk rashin son mutanen Ruwaidah ta kasa nuna shi ga Nadeeyah, sai ma ce mata da tayi, "ki daina kuka mana, na fada miki Papy baya son kuka, ko so kikeyi yasa Yaya Jamal ya daura ki a bayan *OBENIZA* Dariya Hafeez da Jamal suka saki dan sunsan ta da mugun tsoron obeniza, share hawaye Nadeeyah tayi tace "nayi shuru, hannu Ruwaida tasa a gefen kumatunta ta share mata wasu hawayen tace "you are very beautifull, Yaya Jamal batayi kama da *MALEEKA SAHEEB* ba, kaga har one dimple din, kallon ta yayi yaga tabbas akwai kamanni saidai Maleeka akwai wayewar larabawa yan drama sosai a tare da ita, kaunar da sukeyi wa films dinta ya sanya kowa a gidan saninta... Masallaci suka tafi dan yin sallar Magriba, matan kuma duk sukayi a cikin daki, Badar kuwa dakin mummy taje ta kwanta dan jikinta yayi tsami sosai, har lokacin zubar hawaye takeyi tana kara jin tsanar Nadeeyah wacce take jin kamar da tsanar aka haifeta.. fada sosai Mummy tayi mata dan ta tsorata sosai bata san hukuncin da Daddy zai yanke a kanta ba... Magana ce a bakin Papy amma kunya ta hanashi furta ta, a yadda yake ji yanzu baijin zai iya koda kwana daya baisa duk su ukun a ido ba, harda Zainab da ya ga hotonta tamkar shi ya haifeta dan babu inda ta barshi, kallon Daddy yayi yace "Alhaji mun gode fa, gaskiya samun mutum irinka a wannan zamanin sai an tona, ni inaga jibi zan koma Gombe, nace --- ko --am ko--- dariya sosai Daddy yayi dan ya gano manufarshi, kace ko zaka iya tafiya Nadeeyah ko? Cike da jin kunya Papy yayi dariya yace "kunya ta hana ni fadi, Daddy yayi saurin cewa "na lura da hakan, amma fa bazan baka ba ya fadi cike da zolaya, Dariya Papy yayi yace "ai yarka ce, ka fini iko da ita, amma dan Allah ina rokon alfarmar tazo mana hutun wata daya, cike da farin cikin girmamashi da akayi Daddy yace "watanni ma Proff, kar ka damu sun kusa zana jarabawar waec, daga ta zana zata zo tayi maka hutu har sai ka kaji da ita, "inaa bazamu gaji ba Anni ta fadi tana dariya, tace "Allah ya kaimu lokacin, Da sauri Hilal yace "Daddy ayi mata transfer kawai tayi waec din acan, gara ta dan zauna a can ta samu nutusuwar zana jarabawa, "Bata da nutsuwa ne anan? Baffa ya jeho mishi tambayar, "a'a ina nufin zata ji dadin ganin su, kuma zata fi yin karatu sosai acan, Anty Raly da harbo jirginshi tace "babu inda zata, bamu gaji da ganinta ba, tayi zamanta har sanda Daddy yace, badan Raliya ta girmeshi ba, da babu abinda zai hana bai zageta ba, murmushi tayi hade da mishi gwalon babu yadda zaiyi da ita, ba yadda zaiyi haka ya hakura, yasa ma ranshi zai tsoratar da ita sosai akan kula samari musamman Taheer da yayi mishi muguwar tsana a ganin farko... Sai gurin tara da rabi su Papy suka bar gidan, babu yadda ba'ayi Ruwaidah ta zauna ba taki, duk da dan zaman da sukayi ta fara sabawa da Nadeeyah da Husna... Nadeeyah ta kira wannan ranar da ranar farin ciki, tabbas ta yarda in alheri zai doso ka sai ka hadu da bacin rai mai tarin yawa, kwana tayi tana hamdala tana godewa Allah...... A daren Daddy ya yanke hukucin bazai cigaba da zama da Badariyya a gidanshi ba, domin kuwa zata bata mishi zuciyar ya', babu irin hakurin da Mummy bata bashi ba ya kekashe kasa yaki hakura kuma ya hada yi ma Badariyya gori sosai badan baya santa ba, sai dan ta hankalta ta dawo cikin hankalinta, Wannan gori na rashin asali da yayi ma Badariyya, ba karamin tsayawa a ran Mummy da Badar din yayi ba, Ranar da Nadeeyah tayi kwanan farin ciki, a ranar Badariyya kwana tayi kuka tana saka mugayen abubuwan da zatayi ma Nadeeyah...... Mrs Tijjani Shattima.... [24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣3⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Da sassafe Mummy ta sa Husnah da Nadeeyah suje su roki Daddy akan ya bar Badar ta zauna a gidan, ko da suka je dakin a bakin gado suka sameshi yana duba laptop dinshi, gaisheshi sukayi suka hada baki suka ce "Daddy dan Allah kayi hakuri ka kyale Badariyya, Nadeeyah tace "sharrin shaidan ne Daddy, baya wuce kan kowa, in shaa Allahu zata canza, kayi hakuri dan Allah, glass din idonshi ya cire yace "zanyi hakuri saboda darajar ki, ke aka batawa kuma ke kika bada hakuri, babu yadda zanyi tunda kin hakura ni ma dole in hakura, amma sai na karya rantsuwata, taje gidan Goggo tayi wata daya, Mikewa sukayi suna godiya suka fita daga dakin, Mummy da ta gama jinsu ta wuce dakin su Badar tace ta shirya zata kaita gidan Goggo tayi kwana biyu har Daddy ya huce, kwallar da ta ciko idonta tayi saurin mayarwa, ta mike sukuku ta fara fito da kayanta, fita Mummy tayi dan bazata iya Kallon kayan tausayin nan ba, karfe goma daidai bayan sun gama karyawa ta fito da akwatinta ta fitar waje, shi kanshi Daddy saida ya dan tausaya mata saboda ta zama kamar jininshi, halayyarta ce sam baya so tun tana karama, shiyasa ko kadan baya bi ta kanta, Har mota Husnah ta rakata itama tausayinta ya cika ta dan bata saba zaman ko ina ba sai gida, ko gidajen su Anty Radiya bata zuwa da kwana saidai da yini, bare gidan Goggo, ko toilet kadai ya ishi Badar.... A hanya Badar ta kalli mummy dake tuki tace "Mummy alfarma nake so kiyi min, "ina jinki, ta amsa idonta na kallon titi, juyowa tayi tana kallon Mummy sosai tace "Mummy aure nake son ayi min? Kirrrrrr..... Mummy ta taka birki ta kalleta tace "aure? Wani irin aure kuma,? kukan munafurci ta fara kirkirowa tace "Aure dai Mummy wanda akeyi, dan Allah kuyi min aure, sake tada motar Mummy tayi tace "to sai ki turo mijin da zaki aura tunda ke kika zabi hakan da kanki, Abun da take jira dama kenan tayi saurin cewa "ni bana tsayawa da saurayi, ke zaki samo min Mummy, dariya Mummy tayi tace "yarinta hoo, to karki damu bari in nutsu zan duba cikin ya'yan kawayena, cikin sauri ta tari hanzarinta tace "a'a Mummy, gara dai ki nemo min a family, kinga a gida ne kadai zanyi aure hankalin kowa ya kwanta, Tsayar dasu traffic yayi Mummy tace "to Badariyya ina muke da aukin maza a family, ko Hafeez kike so? Allah ya kyauta tayi saurin fadi tana tofar da miyau waje, to shi kadai ne sai Hilal da yake danki, sai kuma *MUSADDIQ* Badar ta karshe da sauri, Mummy ina son yaya Musaddiq, dan Allah ayi mana aure cikin gaggawa plsss, faduwar gabar da tashin hankalin da Mummy ta shiga ba mai misaltuwa bane, bata kara kallon Badar ba ta cigaba da tukinta, magiya sosai Badar takeyi mata amma Mummy ko kallonta batayi ba bare tasan tana yi, suna shiga gidan Mummy tasa Rilwanu daukar akwatin Badar.. Bayan Mummy tabi tana tambayarta dalilin da yasa bata san Musaddiq ya aureta, a daidai gurin da zai sadasu da tsakar gidan Mummy tace "kar in sake jin kin maimata maganar nan, bare har wani yaji!! Tana kaiwa nan tayi Sallama ta fada cikin gidan, Da gudu Badar tabi bayanta kamar zatayi kuka, Mummy ta san sarai Badariyya naci gareta, bata gama tunanin ba taji Badar na cewa pls Mummy, a harzuke Mummy ta juya ta kalleta tace "bani hankalinki nan, aure ya haramta tsakaninki da Musaddiq, Dariyar takaici Badar tayi tace "Haramta? Menene ya haramta shi, naga we are cousins saidai in baki son farin ciki na, Buge bakinta Mummy tayi da karfi hade da cewa "bance karki kara min maganar nan ba, Zafin buge bakin da zafin ganin zata rasa masoyinta yasata sakin wani irin Kuka, Inda take Goggo tayo tana tambayar dalilin kukanta, bata amsa ta ba ta cigaba da kukanta, Mummy ce ta tsuguna a gabanta zata fara rarrashi, kafin tayi magana ta katseta... "Cikin kuka mai cin rai tace menene ya haramta aurena da Yaya Musaddiq Mummy, menene shi, a iya sanina bake kika haifeni ba, nasan babu abin da zai haramta aurena dashi saidai in kema so kikeyi ki min gori akan asalina kamar yadda Daddy yayi m---- tassss.. mummy ta dauke ta da mari, itama kukan ne ya subuce mata ta rungumota tace "Allah ne ya haramta shi Badar, Asalinki bazai taba zame min abin gori ba saboda ke din makwafi biyu gareki a gurina, na diya da kuma kanwa, ke kadai ce jinin yar uwata wacce nake gani inji dadi, ban damu da ya kikazo duniya ba nidai nasan ina ganinki a matsayin LEEMAH, Cike da shashsheka Badar tace "to mummy ki yarda ya aureni, walhy in na rasa shi zan iya mutuwa, *Badariyya* *NONO* daya kuka sha da Musaddiq, babu aure a tsakaninku...... Wani irin zaman dirshan Badariyya tayi wanda ya tafi da duk wani ganinta na dan lokaci kadan, " *NONO DAYA KUKA SHA* Kalmar ke ta mata yawo a kwakwalwarta, duk da bata zuwa islamiyya sosai tasan haramcin auren, wasu zafafan Hawaye ne suka dinga ambaliyar fitowa a idonta, "NA MUTU, BANI DA SAURAN AMFANI, kalaman da ta dinga fada kenan kamar zautacciya, rungumeta Goggo tayi tace "bazaki mutu ba indai ina raye, Musaddiq ne ki kwantar da hankalinki zan san yadda zakiyi ki aureshi, anjima zanje gurin liman BADARU ya nemo wani hadisin da ya halasta aurenku, tashi kije maza ki wanke fuskarki, Tashi tayi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta wuce bayin Goggo, Tashin hankalin da ta tarar a ciki ya sanya ta fitowa da gudu tana haki, "lafiya Suka hada baki suka tambaya, ina fa Lafiya bayi yayi kaca kaca, haba Goggo, dan Allah bakya yin flushing ne? Tabe baki Goggo tayi ta mikawa Zulai mai tayata aikin gida farar shinkafar tuwo dan ta gyara, ta waigo ta kalli Badar tace "tunda kinzo sai ki gyara ai, da tsufa na zanyi ta hakilon wankin bayi, "ay da sai zulai ta wanke ta fadi kamar zatayi kuka, murmushi Goggo tayi tace "kin sani sarai Zulai bata shiga min dakin miji bare bayi, matse fitsarin mararta tayi tace "gaskiya Goggo bazan iya ba, bazan iya zama har wata daya a nan gidan ba, "to ya zakiyi, haka nan zaki hakura, kije can dakin zulai ta tayaki gyarawa dan duk yayi kura, gani tayi kamar laughing stock suka maida ita ta nemi guri ta zauna kamar zatayi kuka tace "Mummy dan Allah ki kaini gidan Aunty Raudha ko Anty Radiya, "Lagos zaki bi Raudha, Radiya kuma kinsan halinta, duk yadda kuke shiri bazata raga miki gurin hidimar gida ba, kiyi zamanki anan na lokaci ne, Mummy ta fadi tana mikewa zata koma gida, Sallama tayi ma Goggo wacce ke amsata da kyar saboda laifukan da tayi mata ciki harda korar Badariyya da mijinta Yayi... Da kyar Goggo ta yarda Zulai ta wanke mata bayi, sai a sannan Badar ta shiga a kyankyame tayi fitsari ta fito da sauri, kan gadon Goggo ta kwanta tana maida numfashi.... "Fito kici Abinci, Goggo ta fadi tana fiffita tuwon a cikin faranti, badan taso ba sai dan tana jin yunwa ta sakko a gado ta fito waje, yadda yaukin miyar ke bin hannun Goggo da zulai yasa komawa daki da sauri, da karfi tace "Tuwo da rana tsaka Goggo, kuma miyar yauki kamar majina ta karashe fadi kar zatayi amai, wannan wace irin jarabawa ce, kudi ta fito dashi a jakarta ta kira Rilwanu ya siyo mata Abinci a restaurant mai kyau.... ko kallonta Goggo batayi ba ta cigaba da kai lomar tuwonta... Tunanin Musaddiq kwanta takeyi, ta ya za'ace babu aure a tsakaninsu, dan kawai sun sa nono daya, Allah yasa Liman ya gano wani hadisin da ya halasta hakan, in ba haka ba walalhi daga ita har shi saidai su mutu ba aure, dan duk wacce yayi yunkurin aura sai ta kasheta..... ******** Danna wayarshi yayi ya kira layin wayar da ya ba Nadeeyah a karo na ba adadi, har lokacin ba'a kunna wayar ba, juyi kawai yakeyi a kan makeken gadonshi, gaba daya ya rasa abinda yake mishi dadi, tun dawowarshi daga gidan su Nadeeyah ya kasa sukuni, ko abinci kwakwkwara bai iya kaiwa bakinshi ba, bacci kuwa sai dai dan barawo ne ya saceshi bayan ya idar da Sallar asuba, Ya gama sawa ranshi sha biyu nayi in yaji ba'a kunna wayar ba zai koma gidan koma me zai faru ya faru, Soyayyar Nadeeyah na neman yi ma zuciyarshi illa, yama za'ayi ya iya rayuwa babu ita, kallon kofar da aka murda yayi yaga Momma ta shigo dauke da kayan break fast, "Gud morning my Tee, Morning Momma, kin tashi lafiya? Lafiya kalau nd u? Nt bad ya fadi hade da mikewa zauna, 'Tee me yake damunka, yau baka fito ba kwata kwata, sannan jiya ina lura dakai dakyar ka tsakuri abinci, yar hirar da muka saba ma baka zauna munyi ba, tell me, meye matsalarka, Bazai iya boye komai na daga dangin farin cikinshi ko akasin haka daga gareta ba, gyara zama yayi ya rike hannuwanta, raunanannun idanuwanshi suka tara ruwa yace "Zan rasa ta Momma, Nadeeyah zatayi ma rayuwata nisa, Zan rasa farin cikin da ya ziyarceni a lokacin da na fidda ran zuwanshi, Fuskarshi ta tallaba da hannayenta biyu cike da tausayin shi tace "bazaka rasa ta ba, baka taba neman abu ka rasa ba Tee baza'a fara akan wannan ba da yardar Allah, ka kwantar da hankalinka kaci abincinka kamar ka sameta ka gama, Anjima da yamma zan kira *Kawu Tidjani* in fada mishi ya taho muje nema maka aure, Murmushin farin ciki yayi yace thank u Momma, Allah yayi miki sakayya da aljanna firdaus, Ameen my Boy, tashi maza kayi wanka ka shirya ka tafi gym wannan tumbin da ka fara ajiyewa ka gyarashi kafin ranar aurenka, shafa tumbin yayi yana dariya yace "ina tumbi anan Momma, sai dai in so kikeyi ya shafe da bayana, dariya tayi hade da mikewa tace "in kayi wanka kazo zan aikeka, gyada kai yayi yace "to Momma bari in fara wankan sai inci abincin.... ******** _Agadaz_.... *DIYA MURADUN AHMEDOO TIDJANI YALLO PALACE* Karar busar algaitar dake fitowa daga katafaren gidan shi ya bawa mutanen gurin damar mimmikewa saboda alamu ne na fitowar sarki, kirari dogarai suka fara yi cikin farasanci ana kodashi kamar yadda akewa sarakuna, Cikin daya daga jerin motocin da aka jera mishi ya shiga, nan ma fadawa suka dinga masa kirari har saida sukaga kurewar motar.. Wani katafaren gida motocin suka shiga, da sauri aka bude mishi kofa ya fito suka taka mishi har kofar parlon, suka murda ya shiga sannan suka juya dan shiga cikin gidan na iyalan gidan ne kadai... Cikin kasaita ya taka ya isa can sama ya fada wani kayataccen parlor, Zaune ya sameta kan dadduma jakadiyarta na danna mata kafa, tana ganin shigowarshi ta tsuguna ta gaisheshi ta fita daga dakin, Rawanin kanshi ya zare ya zagayo ta bayanta ya shiga daddanna mata kafudunta hade da cewa "My Sheri, wannan damuwar har yanzu bazaki daina ta ba, shekara da shekaru kina tunanin abu daya, haihuwa Allah ke bada ita, kuma bai rubuto mu cikin wadanda suke da rabon samu ba, kuka ne mai karfi ya kufce mata tace "ina tsoron ranar da zamu wulakanta bayan ranka, Mulkin nan ficewa zaiyi daga gidan nan, kuma in ya fita babu irin wulakancin da bazamu gani ba, zama yayi sosai ya janyota jikinshi yace "SHARIFAH, mulki na Allah ne, shi ke bawa wanda yaso, A lokacin da mahaifinki ya rasu, kin taba tunanin Allah zaisa a bani mulki duk da ni ba danshi bane sai dan na kasance miji a gareki, gudan jininshi wacce kika zama tilo, Da Allah ya ga dama, da fitar da mulkin zaiyi tunda sarki bashi da magajin kujerarshi, to da yake Allah ya rubuto ni din nan ni zan zama sarki shi ya sanya ya hadamu aure, rashin bamu haihuwa kuma wannan shi kadai ya barwa kansa sanin dalilin hakan, ta yiwu yayi wa wani can wanda bamu sani ba tanadin gujerar, shiyasa ya hanamu samun magaji... Share hawayen fuskarta tayi cikin gamsuwa tace "Allah ya kawo mana taimako, A zuciyarta tana tunano rayuwar kuruciyarta wacce tasan tayi shi tare da wani wanda ya zamto jinin ta, cikin kankanin lokaci kuma ya bacewa ganinta da tunaninta, a yan kwanakin nan ne take tunano shi da suffofinshi da dalilinshi na barin gida... Bata iya fadawa mijinta ba saboda ta kasa sanin hakikanin kusancinsu, , ko da yaushe ta runtse ido sai ta ganshi cikin mafarkinta, tare da farin saurayi mai tsananin kama dashi, saidai idanuwan saurayin sun fi nashi kyawu da girma, karar Waya ce ta katse mata tunani, Tana kallon shi ya dauki wayar cike da farin ciki, "Kuna lahiya Saude,? "lafiya lau kawu, an wuni lafiya? "Kalau kalau ina Tahiru Yallo? Yana nan lafiya kawu, dama akan maganarshi na kiraka, ya samu macen da yake so, shine nace ka shirya kazo sai muje gidan iyayenta, fadada murmushinshi yayi yace "to masha Allah, tuzuru zai angwance, Dariya sosai Anty saude tayi tace "haba kawu, ai ko danye ne sharr, nan suka cigaba da hira kamar ba surukai ba, saida suka gama ya mikawa matarshi wacce ta zamto kawa kuma shakikiyar Anty saude, nan suka shiga hirar yaushe gamo, Anty saude tace "kizo fa tare da kawu, dan tare zamu fara shirye shirye, bazamu sa bikin da nisa ba, Dariyar kasaita "Sharifa" tayi tace "to wacece uwar in ba ni ba, komai dani za'ayi, gobe in shaa Allah zamu biyo jirgi mu iso....... Mrs Tijjani Shattima.... [25/03 10:07 PM] Safiyya Umm Ab: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣4⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Juyi Musaddiq yayi a karo na biyu yace "ka duba cikin aljihun wandona, plss ka barni inyi bacci, tsaki Hilal yaja ya dauki wandon zai duba ya hango keyn a saman windon dakin, jefa wandon yayi kan fuskar Musaddiq dan a cike yake dashi, yafi 20mints yana tashinshi yaki tashi, daukar keyn motar yayi yace "in kaga dama ka kai 4 kana bacci, idiotic being kawai, murda kofar dakin yayi yana mitar yawan baccin safen Musaddiq, wannan in ya fara aiki ya kenan, sam Mummy bata kula da tashin shi, shi kuwa saboda sabon da Papa yayi mishi tun asuba in ya tashi baya iya komawa bacci... Zama yayi a parlor yana jiran ganin ta inda zasu bullo dan yayi alkawarin da kanshi yau zai kaisu makaranta, yana son nunawa Taheer shi din mai babban matsayi ne a gurin ta... Farin tight din da suke sawa a ciki saboda gajartan skirt dinsu ta dinga dubawa bata gani ba, tayata dubawa Husna tayi har tsawon minti uku basu gani ba, black kuma in suka sa korarsu gida akeyi, da suka gaji da dubawa Husna tace "dan Allah zo mu tafi, kar muyi latti, kallon kanta tayi tace "nice zan fita a haka, "to sai me, nima bakiga bana sawa ba, dama iyayinki ne, Husnah ta fadi tana nuna kafarta, dauko school bag Nadeeyah tayi ta rataya, ta tura gashinta cikin hular makarantar da taki zama akanta saboda cikowar gashinta..... Gud morning my PP, Husnah ta fadi hade da zama kusa dashi, "morning small aunt, har kun shirya, "eh yanzu zamu wuce ta karashe tana mikewa, "ina kwana, Nadeeyah ta fadi tana boye kanta a bayan kujera, "Lfy kadai yace ya mike yana kallon Husna, muje in kaiku makaranta, zanje gida dauko ma Mum abu, "yeyy... Husnah tace ta fara tafiya ya bi bayanta, Yana gab da shiga motar ya dago kai ya kalli Nadeeyah da har lokacin tana gyara hular kanta, Rufe motar yayi yana mata wani irin kallo har ta karaso gurin motar, sam bai kula da skirt din Husnah da har yafi nata gajarta ba, wani irin kishi ne ya turnukeshi, nan da nan zuciyarshi ta tafi tunanin irin kallon da Taheer yake mata da wannan gajerun uniform din, kama hannun motar tayi zata bude yayi saurin cewa "wait, da wannan skirt din kuke zuwa makaranta?, daga cikin motar Husnah tace "ya Hilal ka manta ne, haka uniform din legacy yake, "yes amma ai ana sanya wando ko, ku ko kunya bakwaji makaranta ba ta mata zalla ba ku dinga tsilla tsilla da wannan skirt din, maza fito kuje ku sa wando ya fadi yana bude kofar motar, Agogo Husnah ta duba tace "ya Hilal munyi latti, kuma bamu da legens fari sai baki ba'a barin mu muje school dashi, "okay to sai ku fasa zuwa school din, A firgice suka kalleshi dukkansu dan zasuyi submitting project dinsu, marairaicewa Husnah tayi tace "plsss muje ka kaimu, kasan dai muna shekarar karshe ne, kullum cikin assignment ga project zamuyi submitting, key yasa ya rufe motar yace "ko kusa bakin ko kuma ku hakura da school yau, da sauri Husnah ta fito tace "muje Nadeeyah, Bayansu yabi da kallo yaja tsakin takaici, tunanin yadda zaiyi ya rabata da skirt yakeyi, a da uniform din school din na burgeshi, ba kamar lokacin suna yara in su Anty Raly sun saka, amma yanzu gaba daya ji yayi ya tsani makarantar ma ba uniform din ba, Bai ga fitowarsu ba sai jin taba motar da Husnah tayi, saida ya kalli kafafuwansu sannan ya shiga motar ba tare da ya samu gamsuwa sosai ba dan ba mage ba miyau..... ***** Ke Badariyya, Wai bazaki tashi bane, tashi kije kiyi wanka ko bazaki makarantar bane? Mikewa Badar tayi da mika hade da goge zufar wuyanta, tun da ta taso bata taba azababen bacci irin na yau ba, fanka ma kashewa Goggo tayi wai sanyi take ji, shi kuwa a.c tun goma na dare ta kasheshi wai bazata sankarar da ita ba, duk soyayyar da takewa Badar ashe ta nesa ce, saboda ba ita ke hidimarta ba, sannan kuma ita ma tana cikin nata kuncin dan Baffa bai dawo gidan ba sai 1 na dare suka dawo tare dasu Papy, anan ma hirar suka zauna yi har 1:30, ya nunawa Papy gurin da yake sa ran zai mishi gini in yazo ya dinga sauka, Tana jiyo su dan ta kasa rintsawa, tana jin Papy na cewa nan da shekara daya shima zai baro Gomben ya dawo nan kaduna cikin yan uwanshi, ganin irin farin cikin da Baffa yakeyi shi ya sake tunzura zuciyar Goggo ta dau alwashin aiwatar da abin da tayi niyya shekarun baya.... "Gaskiya bazan sha wannan kunun ba Goggo, walhi bazan karya da wadannan kazantar ba, haba common tea ma sai kice bazaki bani in sha ba, Badar ce ke maganar kamar zatayi kuka saboda takaicin karo da kunun da tayi, tabe baki Goggo tayi tace "Sai dai kar kisha, tun da na tashi nake jiran Rilwanu bai zo ba, ni kikeso in fita in siyo miki kayan shayin, Da tsufana me zanyi da shayi ni, in kinga dama kar k----  Assalamu Alaikum, sallamar da akayi ta katse Goggo daga karasa maganarta, kaya niki niki taga Jamal da Hafeez suna shigowa dashi, a bayansu kuma ta hango Anni da Mami, papy ne ya shigo a karshe sai Rilwanu da Garzali suma dauke da wasu kayan, fitowa Baffa yayi da sauri saboda jin muryar Papy, kallonshi Anni tayi cikin zolaya tace "Alhaji karka fadi, irin wannan sauri haka, shima saurin yazo ya ganka ne ya hanashi ya barmu sai anjima muzo, Dariya Baffa yayi yace "marabanku, ai sai ki bani kunya, yanzu dai bari in boye murnata, Dariya dukkansu sukayi Papy ya tsuguna ya gaida Baffa, bai amsa ba ya dauko tabarma ya shimfida musu, saida ya zauna sannan suka gaisa dukkansu cikin farin ciki, Hira sosai Baffa sukeyi da Anni tana bashi labarin yarintar Papy har zuwa girmanshi, da irin nasarorin da ya samu, gaba daya Baffa ya manta da Goggo dake tsaye kasake tana kallonsu, ko tafiyar Badariyya makaranta bata sani ba, Kallon Anni yayi yace "tun jiya nake ta tunanin abun da zan miki in saka miki abin da kikayi min, Na tattaro duk abinda na mallaka naga sun yi min kadan in baki a matsayin tukwicin abin alherin da kikayi mini na taimakon dana da kikayi har ya zama abun da ya zama, na kwana ina miki addu'ar Allah ya sanyaki cikin farin ciki duniya da lahira, Allah shi kadai zai biyaki da aljanna firdausi, nagode nagode sosai Hanne, Kafin Anni ta amsa Ruwaida tayi saurin cewa "Ameen mijin Anni, baban Papy, kaka na ni kadai banda yaya Jamal, garammmm Goggo taji maganar kamar saukar aradu, tsayuwace ta gagareta ta dawo cikinsu ta zauna saboda shurun da taji sunyi, kallon kallo suka shiga yi a gurin Mami tayi saurin cewa Jamal ya kai Ruwaidah gurin su Nadeeyah, "suna makaranta Hafeez ya fadi yana rike hannun sarkin katobara, yace muje ki rakani.. Suna fita Anni tace "yarinta hoo, ita a dole farin ciki takeyi taga babanta cikin yanayin da yafi na da, "Yarintarta Ruwaidah akwai hikima a cikinta Anni, Papy ya fadi yana gyara zama.. Kallon Baffa yayi yace "Baffa kana son sakawa Anni, baka da abun saka mata dashi, dan Allah ne kadai mai saka mata, "abu daya zakayi ka kwatanta kyautata mata shine ka aureta, Ta zamto matarka, makwafin mahaifiyata, wannan shine kadai zai sani farin ciki, Anni ta ki yin aure saboda ni, bata jure ganin kowa ya wulakanta ni, shiyasa ta hakura da aure domin taga auren wani mabudi ne na wulakanci a gareni, Dan Allah Baffa ka auri ANNI, kallon Goggo da ta kureshi da ido yayi yace "INNA dan Allah kisa baki, auren shi kadai ne abun da zamuyi mu saka mata...... Kafin Goggo ta gama tattaro amsar bayarwa Baffa yayi murmushi yace "yo har sai ka roka, ni da nake neman abun da zan bada tukwici, ai na karbi wannan karramawar, kuma in shaa Allahu zata ga karamci domin wannan din ma wani sabon karamcin ne da yake bukatar tukwici, Dariya Mami tayi ta kalli Anni dake share kwallar da ta gangaro mata, hannunta ta kama tace "Alhamdulillah Anni, dan Allah ki amince, kuka ne ya kufce mata tace "na Amince Maimuna, wannan ya wuce tukwici, domin kuwa zan shiga cikin jerin matan da nake fatan in mutu cikin sutura, zan shiga jerin matan da zasu mutu ana maraba dasu, hannu ta daga sama tace "Alhamdullillah ala kulli halin, Karkiyi saurin Hamdallah Goggo da ta gama charge ta fadi tana mikewa da kyar, kiyi gaggawar maida murnarki domin a haka zaki mutu babu aure1, Mijina bai min kishiya tun da jajayen sawunmu ba, sai yanzu da muke rai a bakin rami, in banda kwadayi ma me zakiyi da wannan tsohon, me ya rage mishi da zaki suďa, "Murmushin ilimi Anni tayi dan a ganinta kishi ne, tace "ko ban samu abin sudewa ba zan samu martabar zama matar aure, kwantar da Hankalinki bazan zo dan yin kishi dake ba, zanyi aure dan in samu cikar kamalar da na dade ina nema, "Aiko zaki mutu baki samu wannan kamalar ba in dai mijina zaki aura, bakin da ya furta miki cewa zai aureki shi zai dawo yace miki ya fasa, Shekeke Baffa ya kalli Goggo, dauke kanshi yayi da sauri da yaga suna kokarin hada ido dan idanuwanta kan sanyashi manta komai, yace "Aure babu fashi, sati ma in shaa Allahu, Kallon Papy yayi yace "ka daukesu ka maidasu gida sai ka dawo mu nemo magina su fara aikin ginin nan.. Sallama Papy yayiwa Ma'u dake tsaye galala masifarta ta makale saboda furucin Baffa, Bin su tayi da ido har suka bacewa ganinta sannan ta fada dakin da sauri, kofar bayin ta shiga bugawa tana masifa tana fadin "baka isa ba, walhy Muhammadu baka isa ba, alkawarin da kayi min kenan, ni zaka butulcewa duk irin halaccin da nayi maka,  to wallhi ka fito nan ina jiranka, saidai ka zaba koni ko ita, dan wallhi bazan zauna da kishiya ba.. Yana gama wanka ya bude kofar ya fito ba tare da ya kalleta ba, kaya ya dauko yasa yace "Ma'u halacci babu wanda ban miki ba, shekararmu sama da hamsin dake ban taba yunkurin yi miki kishiya ba da kaina ba, sai yanzu da nake son saka alkhairi da alkhairi, yanzu ke ba abun kunya bane ki ts---- ka kalli idona ka fadamin haka Muhammadu, ta katseshi da karfi tana juyo kafadunshi, juyar da kanshi yayi ya dauki turare ya fesa yace "kallon idonki na daina shi har in koma ga mahallincina, kallon cikin idanuwanki sun sanyani fita cikin hayyacina har na aikata ma diyar cikina abubuwan da har na mutu bazan yafewa kaina ba, ki rike idanuwanki in rike rayuwata da mu'amalata, yana kaiwa nan yasa kai ya fita ya bar Goggo da masifa kamar zata ari baki, kayan dake tsakar gidan yasa Rilwanu kwashewa yasa mishi a dakin waje.. crates din kwan Goggo ta farfasa su da tabarya, ta dinga bin kayan tana tsine musu, Dakyar Rilwanu ya kwashesu, yana gamawa yayi mata sallama yace "gobe zai koma garin su, mahaifinshi baida lafiya, bata bashi ansa ba ya cigaba da cewa "ina tunanin dawo dashi garin nan Goggo zan kaishi asibitin dutse a duba shi, dan jikin nashi yaki dadi, tabarya ta dago ta kundumo mishi ashar tace "Allah yasa ya mutu dan ubanka, shege matsiyaci, Fita yayi yana kunshe dariyarshi dan shi fushin nata ma dariya ya bashi..... Mrs Tijjani Shattimah....... [25/03 11:25 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣5⃣ By *Aysha Ya'u kurah* A tare suka iso makarantar da uncle Taheer, kallon gaban motarshi Hilal yayi ya hango Sabrinah a gaba tana ta zuba iyayi, Gyara parking dinshi yayi ya kalli Husnah yace "ina sakon da kike ce zaki maida yau, taba jakarta tayi tace "yana cikin nan, "okay take care my personal p, In shaa Allah ta fadi ta murda kofar fita, Tun da suka tsaya take ta kokarin bude kofar ta kasa, saida Husnah ta fita sannan ta matso dayan gefen dan ta bude, A zatonta lalacewa abun yayi.. "Ki kula da abun da ya kawoki makaranta, in kuma soyayya kika zaba to bismillah babu mai hanaki, its ur life afterall.. Cikin sanyinta tace "ba soyayya nakeyi dashi ba, yace yana sona kuma har yanzu ban bashi amsa ba *ALLAH*, sai a lokacin Hilal ya dan samu nutsuwa ya waigo ya kalleta, narkewa zuciyarshi tayi saboda yanayin da yaga fuskarta, Cikin muryar da bai san yana da ita ba yace "kin tanadi amsar bashi? "Um um, ta fadi tana girgiza kai, hannu tasa ta kara gyara hular kanta da ta kakarce dalilin girgiza kanta da tayi, Bakar hular sanyin dake ajiye a gefen motar ya mika yace "wannan nada dan girma ki sata, ki daina saka ta kanki tunda tayi miki kadan, sannan in kika dawo gida zan baki amsar da zaki fada mishi, Dafatan ba saina sake tuna miki dalilin zuwanki makaranta ba, Yadda yayi maganar cikin dakiya yasata kallonshi, ido ya daga mata alamar kin gane, Sanya hular tayi da sauri tace "Eh in shaa Allah, "Good ya fadi hade da cire lock din ya fito ya bude gefen da take, yana hango Taheer tsaye a gate da Husnah da wasu yara a gefe, tana fitowa a motar ya dakatar da ita ta hanyar gyara mata gashin da ya leko, "wai bakya kitsone?, ya fadi a saitin kunnenta, gyada kai tayi tace "ko yau nayi zai warware, "okay to sai a yankeshi kawai ya fadi yana kallon yadda zatayi, Dariya ce ta kubce mata tace "to in na dawo zan yanke, "akwai barber karki damu kina dawowa sai muje, Maza ki shiga school nd becareful, "In shaa Allah ta fadi tana mamakin yadda ya damu da ita a yan kwanakin nan, mutumin da ba kowa yake kulawa bare har kaga dariyarshi, ta ta'allaka abun da tausayinta yake ji da kuma shakuwarsu da zainab, Harde hannu yayi yana kallonta har ta karasa gate din, "Good morning sir, ta fadi hade da rankwafawa, duk yadda yaso danne abun da ya tokare wuyanshi ya kasa, bai amsata ba ya juya dan komawa office dinshi, Husnah da hankalinta ya gama tashi tace "pls sir plss kasa baki ya barmu, bai waigo ba dan a harzuke yake matuka, Ko Musaddiq da Hilal yace shine wanda zai aureta bai tsaneshi ba kamar yadda yake jin tsanar Hilal, Yana shiga office ya jingina jikinshi jikin kofar office din zuciyarshi sai tafasa takeyi, Allah kadai yasan adadin abubuwan da suka dahu a cikin zuciyarshi,   Yana tsaye a gurin yaji bugun kofar office din, dakyar ya iya matsawa hade da bude office din, Husnah ya gani tsaye tana mishi murmushi, "ehen what again? Shigowa tayi ta sauke jakar makarantarta tace "Sir dakyar uncle Kamal ya barmu muka shigo school kuma yace mu cire black legens din jikin mu, Ledar da ya kai gidansu ta ciro ta mika mishi tace "ance in dawo maka dashi, bai kalli ledar ba yace "Okay ajiye ki tafi, ajiyewa tayi tace "sorry sir, gidan mu ba'a tsayawa da saurayi sai an gama sec school, Kaga Daddy baisan ka kawo ba Yaya Hilal yace a maido maka, "nt bad jeki kawai... ya fadi yana gyara gujerar da zai zauna, Tana fita ya kifa kanshi a tebur, tunani kala kala babu wanda baiyi ba, Da sauri ya fatattaki tunaninshi na karshe na " *ka rabu da ita*, dan bama zai iya imagining ba, bare ya aiwatar, Mikewa yayi dan zuwa ajinsu duk da yau bazai musu darasi ba, sa'a yaci da ya shiga babu malami dukkansu suna zaune suna hira, Gaisheshi dukka ajin sukayi ya amsa hade da cewa su zauna, Rasa abin ce musu yayi dan ba darasi yazo basu ba, saida ya kusa 5mints sannan yayi tunanin neman wadanda zasu gyara mishi office, Dadi tunanin yaji a zuciyarshi ya kalli duka yan class din yaga kowa idonshi na kanshi ita kadai ce kai a sunkuye, "Hey u with black cap, " *kyari* sunan dake rubuce a jikin hular, tabo ta *Amal Mus'ab* tayi  tace "Nadeeyah ke yake kira, Mikewa tayi da sauri tace "yes sir, keyn office din ya bawa khalifa yace "mika mata taje ta gyara min, da sauri Sabrina ta mike tace "zanyi sir, "noo zauna ki huta, ya karashe yana fadin hv a nice day class, thank you sirrrr... A hanyar shigowa harabar clases din ta ci karo da Badariyya, Ja baya Nadeeyah tayi dan ta bata hanya, wani irin kallo Badar ta bita dashi from head to toe, tana zuwa daidai kanta taga hular wanda take kira da *Rayuwarta* *iyyye.....* Badar ta fadi tana kallonta shekeke, uban waya baki hular nan,  Taba hular Nadeeyah tayi taga babu amfanin bata amsa tayi saurin bi ta gefenta zata wuce, Janyota tayi ta zare mata hular tace "ke har kin isa ki hada jiki da shi, tattara gashinta da zubo har gadon bayanta tayi ba tare da ta amsa ta ba ta juya dan komawa dauko hularta, Hada ido sukayi yana tsaye duk abin da Badar tayi a idonshi, "zan dauko hula ta a class sir, karasowa gurin Badar yayi yace "Hular ki ce, girgirza kai tayi tace "ta mijin da zan aura ne, "ikon Allah ya fadi cike da mamaki, "ehen ita kuma wacece kenan a gurinshi, "ba komai bace sir, kawai dai tana zaune a gidan mu ne, mamanta da babanta sun mutu, talauci yasa yayansu bazai iya rikesu ba shine aka dawo dasu gidanmu, "Nan da nan alamun shi suka sauya yace "abin da na tambayeki kenan?, "Na baka amsar abin da ka tambayeni a farko na cike da karin bayan ta fadi tana turo baki, Hannu ya mika mata yace "bani hular nan, rai a bace kamar zata mutu tace "sir ya za'a yi tasa min hul--- give it here ya katseta cikin tsawa, Daura mishi a hannu tayi tana kunkuni, Mikama Nadeeyah Hular yayi ya wuce, ďan labarin ta da yaji ya sanya mishi kwadayin sanin cikakken labarinta..... "Alo Hajja Saude, kiyi  hakuri bazamu samu daman zuwa yau ba, zamu tafi morocco kai *ummu Ayyu* asibiti, jikin yaki, Gyara zaman wayar Anti saude tayi a kunnenta tace "Allah sarki, jikin har yanzu dai, to Allah ya bata lafiya, babu komai, karku damu ni zanje in fara gabatar dashi kafin ku dawo, Cikin jindadi aminan suka hau hira duk akan sarautarsu da kuma familynsu..... Hoton da ta gani a kan table din ta dauka tana kallo sosai, saida tayi mishi guga na musamman sannan ta ajiye, tana gama gyaran office din ta sake daukar hoton tana kallo, Hakanan taji mutumin cikin hoton ya shiga ranta, Sanye yake cikin babbar riga da hula, yayi kyau sosai, Tana kokarin ajiye hoton taji yace "my late Father " *Alhaji Haroun Yallo*, Ajiye hoton tayi da sauri tace sorry Sir, na gama yanzu zan wuce class, Bashi da niyyar matsa mata a makaranta sam, dan a yadda ya tsara a makaranta nuna mata rashin sani zaiyi kururu. amma ya zaiyi, soyayyarta ta hanashi katabus, Takowa yayi ya karaso inda take tsaye ya dauko hoton, "Wannan shine Mahaifina, rayuwar da mukayi dashi ba mai goguwa bace, kullum in ban tunashi a duk numfashin da nakeyi ba to tabbas zan tunashi a duk takun da zanyi a rayuwata, He is my best friend, Mutuwarshi ita ta kashe wasu sassa na farin cikin dake cikin zuciyata, mutuwa ce wacce yayi ta ba zato babu tsammani, Ajiye hoton yayi yace "Mutuwa wata abace wacce zafinta yafi dukkan zafin wutar dake cikin duniyar nan, zafin wuta na warkewa ya barka da tabo, amma mikin rashin makusanci kullum sabo yake zama, Mahaifina ya nuna min kauna har ranar da zaiyi tafiyar din din din, "A ranar da zai mutu ranar na dawo daga Canada, saboda kar ya daga hankalinmu shiyasa ya boye mana ciwonshi, ya dinga biye ma duk wata rigima tawa, Tare muka je aski, cikin rashin sanin yana ciwo nasa akayi mishi askin dukka kanshi dan ya zame min abin tsokana, haka nan badan yana so ba ya yarda akayi mishi, Daga gurin askim muka wuce yawo muna ta zaga gari muna ziyarar gidajen Abokanshi, Masallacin cikin gidan mu nan ne guri na karshe da muka tsaya, A daddafe ya idar da sallar magriba, jin irin numfashin da yake fitarwa ya sani tambayarshi ko baida lafiya ne, dariya ya kakaro hade da naushin cikina kamar yadda muka saba yace "in yana da ni ta ina ciwo zai samu muhalli a jikinshi, Nan take Muryar Taheer ta raunana, hawayen da suka cika idanuwanshi suka dinga tsere a tsakaninsu, ya cigaba da cewa "A sujjar karshe ta sallar isha'i karfin Abbana ya soma karewa, Gaba daya masallacin yayi shuru saboda jam'i da ake bi, numfarfashin Abbana kadai ake ji a ciki da wajen masallacin, gaggauta yin sallama liman yayi, kowa yayi kanshi saboda ganin har lokacin bai dago daga sujudi ba, kuma bai bar fitar da numfarfashi ba,  Ko da aka dago shi ya gama fita cikin hayyacinshi, A lokacin wanda ya taba dandanar mutuwa zai fahimci inda Abbana ya dosa, Dagoshi nayi da karfi ina fadin ya tashi muje asibiti, Girgiza kai ya shiga yi yana fadamin "ka barni anan Taheer, ka barni anan, asibiti, ko gida, a yau basu da amfani a gareni, Murmushi yakeyi mai dauke da kuka yana fadin Taheer kayi hakuri, kayi hakuri abokina, na boye maka ciwo na saboda nasan ba na tashi bane, Naso sai ka koma makaranta zanyi tafiyar nan amma inaa lokacina yayi, ban isa kara kwana daya ba koda kuwa ina son kara shi, "Kukan da Taheer yakeyi a lokacin mai sautine dan bai taba fitar da wannan labarin da yayi mishi karan tsaye cikin rayuwarsa ba sai yau da a karo na biyu yake shirin rasa wacce yake tunanin dawowar farin ciki cikin rayuwarshi, Ita din ma Nadeeyah kukan takeyi na tausaya mishi da tausayawa kanta, domin ita ma tayi rashin dukka iyayenta, "Ban taba kawo mishi mutuwa ba saboda ban yarda zai tafi ya barni a wannan lokacin ba, kin saurararshi nayi muka daukeshi dan kaishi asibiti, ina tuno sanda ya shafa fuskata muna gab da fita daga masallacin yace "Taheer kaki yarda ko? Dole ka yard---a d------a wann---- nan ya fara kakari har yafi karfin wadanda suka rikeshi, ka-- kula  da--- kanka da-- da-- mahaifiyarka, damke hannuna yayi har lokacin idonshi bai gama rufewa yana tayi min murmushin da ya saba, "A wannan ranar ne na ga abun da ake kira damuwa karara, a wannan bakar ranar naga kaddarar rabuwa da abin da kakeso,  a wannan daren mahaifina ya mutu tare da duk wani kuzari nawa.. Tun daga ranar na manta farin ciki da yadda akeyinshi, babu abin da ke burgeni a duniyar nan bare har yasani farin ciki, Rabuwa da Abbana.... ya ilahi!! nan da nan Nadeeyah ta rikice saboda yadda yake kuka kamar ana zare ranshi, kuka sosai yakeyi wanda bai samu damar yinshi ba ranar da ya rasa mahaifinshi, Abubuwan da suka cunkushe mishi ya fitar yau yake kokawa a kansu, shakuwar da yayi da mahaifinshi ta wuce ta ďa da uba, ta zamo shakuwar jini da hanta, a ko da yaushe ya rufe idonshi murmushinshi kadai yake gani, bai taba karo da bacin ranshi ba sai dai farin cikin shi, Gabanshi ta tsuguna itama kukan yaci karfinta tace "Uncle kayi hakuri, sau tari abubuwan da muke so basu cika kasancewa tare damu ba, jarabawar mu kenan, gara kai kana da wacce in ka juya zakaji dadi, ni fa babu uwa babu uba, babu yan uwan uba da zan kirasu nawa saidai na uwa, ka godewa Allah domin not all are fortunate, Duk abinda kaga Allah ya dauke maka to yana da dalilin yin hakan, ta yiwu in ya bar mana su wata rana saboda azabar ciwo mu gwammaci tafiyarsu akan tsayuwarsu cikin ciwon da mu kanmu bamu isa mu magance musu ba, nasan yadda kakeji domin nima ina jinshi ko ma ince fiye da naka, Dan Allah a duk lokacin da ka tunashi ka dinga fadin *innalillahi wa inna ilaihir rajiun* sannan kayi mishi addu'a domin yafi bukatarta a yanzu.... Wata irin nutsuwa ce ta saukar mishi wanda tun kafin rasuwar Abbanshi rabon da ya shiga irin ta, share hawayen idonshi yayi ya dago ya kalleta, Sai a lokacin yake tambayar kanshi dalilin dayasa har ya fada mata damuwar da ya dade yana dakonta, Tabbas zuciyarshi ta gamsu ita ce wacce zai samu nutsuwa da ita, kalamanta sunyi matukar sanyaya mishi zuciya, jin zuciyarshi yake wasai kamar an sauke mishi duk wani nauyin da zuciyarshi ke dauke da shi, Tsugunawa yayi kamar yadda tayi yace "is ok, kukan ya isa haka, ni nasa ki kuka, ni kuma na daina ke kin ki dainawa, sorry kinji, tashi ki zauna... Mikewa tayi tace "zan tafi class ne, kujera ya ja mata yace "kice wa ya saki kuka? Ajiyar zuciya tayi mai karfi sannan ta zauna, Ji yakeyi kamar ya rungumeta ya hanata wannan kukan da yasan irin ciwonshi, "nace ya isa ko nima so kikeyi in cigaba, kinsan in na fara nawa biyu zan hada, da na rashin mahaifi da kuma rashin farin cikin rayuwata, ya karashe fadi a raunane cikin damuwa, Share hawayenta tayi kamar me shagwaba tace "na daina, "Kina sona Umm Nadeeyah? Yadda ya jefo mata tambayar ta sanyata saurin dauke kanta daga kallonshi, "ummm bani amsa plss, nd "who is Musaddiq? Ya karashe yana janyo kujera... "Yaya Musaddiq? Ta fadi tana kallonshi, gyada kai yayi yace "yes waye shi, meye alakarku? "Babu komai, he is my cousin,  "nd husband to be, Taheer ya karashe yana kallon cikin idonta, A razane tace "whatt, ba gaskiya bane, kaga sister na wacce ta karbi hula dazu? Gyada kai yayi alamar eh, "to ko zaiyi aure nasan ita zai aura, wannan hularshi ce "ya Hilal ya bani shine ta dauka shi ya bani, "yaya Musaddiq is very nice, bashi da matsala, yadda ya dauki su Husnah haka ya daukeni, cike da gamsuwa ya dan samu nutsuwa yace "Hilal kuma ya kuke dashi? Murmushi tayi tace "dan yayata ne, He is like an angel to me sir, he wants the best for me, Bayan yaya Musaddiq da ya nuna tausayinshi ga iyayena, Yaya Hilal shi yake bani duk wata kulawa lokacin da na rasa iyayena, he luks after komai nawa, movements dina da komai, he wants me to be an independent lady and---- katseta yayi ta hanyar cewa yayarki ce ta haifeshi, i mean mamanku daya da mamanshi? "No Anty Reemah yayar Husnah ce, she is my cousin, "Okay kawai yace ya kauda maganar ta hanyar cewa bani amsar farko da na tambayeki, Ya zame mata dole ta fada mishi gaskiyar yanzu babu soyayya a gabanta, Danne tausayinshi tayi a can kasan ranta tace "Uncle, shhhh nt uncle, Taheer... ya fadi yana mata wani narkaken kallon da ya kashe duk wasu gabbai na jikinta, Call me TAHEER, ina son jin sunan daga bakinki plss, marairaicewa tayi tace "no sir i can't, sorry plss, "zaki koya with time, inajinki! "Kayi hakuri in abun da fada maka yayi maka ciwo, bance bana sonka ba, a yanzu ba soyayya bace a gabana, nasan in kana sona sosai kamar yadda kace zaka girmama ra'ayi na, Dan Allah sir mu ajiye maganar soyayya yanzu, kayi hakuri ka taimakeni in taka matakin nasara a rayuwata, in Allah ya rubuta kai din mijina ne, babu wanda ya isa ya rabamu saidai mutuwa, Dan Allah uncle kayi hakuri, mu yarda duk abin da Allah ya rubuta akan mu shine alkhairi, "Murmushi ya sakar mata mai kyau zuciyarshi ta samu nutsuwa da kalamanta, dole ya girmama ra'ayinta yayi nesa da ita ya tayata cika burinta, yasani kamar yadda ta fadi in har kasantuwarsu tare rubutacce ne a lauhil mahfuz, babu makawa duk inda taje dole ta dawo gareshi, A yanzu jin kanshi yakeyi kamar sabon mutum wanda ya yarda da duk abin da ya faru dashi kaddararshi ce tazo da haka, "Na amince da bukatarki, zan kuma girmama ra'ayinki saboda karatu nada matukar muhimmaci a rayuwar mace, musamman marainiya irinki, naci burin aurenki a cikin kwanakin nan, nasan inada karfin kaiki bangon duniya kiyi karatu in har anayi, to nima inaso ki samu abin da kike so, lokacin da kika mallaki hankalin kanki you decide who u want to settle with, i pray to Allah nine wanda zuciyarki zata amince dashi a lokacin, Zan kauracewa ganinki har kiyi achieving goals dinki, saboda ganinki zai dinga hanani sukuni har in kasa tayaki cika burinki, Wani zobe ya fito dashi a jakarshi ya mika mata yace "Aure nufi ne na Allah, in Allah yayi ni mijinki ne kamar yadda zanyi addu'a ba dare ba rana to babu makawa sai na aureki, ki rike wannan zoben a matsayin kariya daga gareni, "Take care of yourself please, u will always be my omri.. Hawayen da ke makale a idonta ne ya sauko ta kasa dauke idonta akanshi, hannu yasa a lallausan kuncinta ya share mata hawayen yace "bana son kuka Omri na, karki dinga kuka kinji, duk abin da zai dameki ki tuno *Taheer Haroun Yallo* yana tare dake kuma baya san ganin damuwarki, Mikewa tayi da sauri ta fita daga office din, bayan office din ta zauna ta dinga zubar da hawayen tausayin Taheer, shine mutumin da ya fara furta so a gareta, badan santa da karatu ba da babu abinda zai hanata amince mishi, zoben ta kalla ta kankameshi a kirjinta kamar zata maidashi cikinta.... A bangaren Taheer kuma daurewa yayi sosai ya iya yi mata wadannan alkawuran, ya sani sarai rashin ganin Nadeeyah babban masifa ce a rayuwarshi, ya zaiyi yana sonta dole yaso farin cikinta, Waya ya dauka ya kira *Captain Mus'ab* bayan sun gaisa yake ce mishi yasa a shirya mishi visa, nan da 5days yake son komawa Canada, "Har zaman nigeria ya isheka kenan *Mus'ab* ya fadi yana dariya, "Yes uncle Mus'ab, zan koma Phd, "to makarantar fa? wa zaka barwa ita, "Momma na nan, ya fadi a kasalance yana jajantawa kanshi, "Jiya Amal ke ce min project dinsu, Yanzu haka zaka bar mana yara ka tafi, kaga "Aman baya wani kokari yanzu, Allah science yafi karfinshi yanzu, yasa wasa, har Amal ta fishi kokari, Dariya Taheer yayi yace "karka ma hadasu, shi da yake science flexibilityn ma ba daya bane, Amal dake Art wasan yara kawai suke yi, Dariya Captain Mus'ab yayi yace "naji wannan nidai kasa a sake samin ido akanshi, sannan kazo office anjima sai muje in sa a fara shirya maka visa, yar Hira suka taba sannan sukayi sallama....  Tattara takardunshi masu muhimmaci yayi yasa cikin wata jaka, yana gamawa ya fito da jakar yasa a mota, Yana hango Amal da Aman daga nesa suna fada akan kudin break, Haifa na tsakiya tana rabasu, Abin da kullum sai sunyi ne, shiyasa ma bai bi takai ba ya shiga motarshi, Ta mudubin gefenshi ya hangota tana lekenshi tana kuka, nan shima zuciyarshi ta karye sosai, tada motar yayi da sauri ya bar gurin dan kar ya kasa jure ganin kukanta ya saba alkawarinshi tun kafin aje ko ina..... Mrs Tijjani Shattimah....... [27/03 8:42 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣6⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Ajiye motarshi yayi a gurin da aka tanada dan ajiyar motoci, saida ya kusan minti biyar yana tattara duk wasu abubuwa masu muhimmanci a cikin motar, sannan ya fito ya rufe hade da mikawa wani yaron gidan mai musu hidima kayan ya wuce ciki, jikinshi sam babu kuzari da walwala, Kauracewa abinda kake so dan farin cikinsa, ba karamin jarumta bane wanda samun masu yinsa sai an tona.... Koda ya shiga bayi domin watsa ruwa kasa tabuka komai yayi, yana tsaye a tsakiyar shower ruwa na ratsa dukkan sassan jikinshi, a maimakon yaji sanyin ruwan a zuciyarshi sai yaji wani irin zafin da ke kona duk wata kwayar halitta da aka halicceta domin soyayya a cikin ma'adanar ta, alwala ya dauro ya fito jikinshi sam ba karfi, karfe goma da rabi lokacin, brown jallabiya yasaka ya shimfida sallaya dan yin sallahr walaha (Duha).. Yafi minti talatin yana kai kukansa gurin rabbil izzati akan ya mallaka mishi Nadeeyah kuma ya sanyata farin ciki har karshen rayuwarta, "Tee lafiya ka dawo gida?, Momma da ta shigo dakin bayan ta fita taga motarshi a parke ta fadi hade da zama a kujerar dake fuskantarshi, Shafa addu'a yayi yace "Lafiya lau momma, dama yanzu nake shirin zuwa gurinki, Mikewa yayi ya nade daddumar ya dawo kusa da ita ya zauna, "Ina son komawa school Momma, munyi magana da Uncle Mus'ab nace su shirya min visa, ina son yin phd dina tun yanzu Momma, rike makaranta irin legacy sai da Phd, daga nan ma sai in kara gaba in shaa Allahu, ina son mu samu rassar makarantar a ko ina a cikin Nigeria, kinga dole in gogu cikin il--- "Ba gaskiya bane Taheer ta katseshi cikin sauri dan kar yayi zurfi cikin karyarsa, "Kalleni Tee, ni na haifeka, na raineka har kawo wannan lokacin, a kan murmushin fuskarka ina iya hangen damuwarka, "jiya ka gama cemin ka samu yarinyar da kake so da aure, yau kuma sai kazo min da zancen tafiya har Canada kuma ba wai kwana daya ba har shekaru, sannan kake tunanin in yarda baka da damuwa, "Fada min matsalarka maza maza, ka sani babu abin da yake cikin duniyar nan wanda bazan iya magance maka shi ba, koma me kake so ka fada min yanzun nan kaga aiki da cikawa, Hannunta ya rike a hankali yace "nasan zaki iya magance min komai Momma, amma ban da soyayyar Nadeeyah, bana son in a matsa mata ta zauna dani, nafi son ta zauna dani domin kanta, nafi son ta soni da kanta ba tare da an tursasata ba, nasan Allah swt zai kawo mana wannan ranar, Addu'a kawai zamu cigaba dayi, in shaa Allah zamu dace, Zan tafi ne dan in bata damar yin karatunta cikin kwanciyar hankali, in shaa Allahu lokacin da ta kammala karatunta nasan zata karbi bukatata, "Jiranta zakayi Taheer? Yadda tayi maganar cikin damuwa yasashi jin wani iri a jikinshi, yayi karfin halin cewa "kamar yau ne Momma, kuma kinga karatu zan tafi nima, lokaci gudu yakeyi, sai kiga kamar yau ne ta kammala, Shafa fuskarshi tayi tace "lokaci sakarai ne Taheer, wucewa yakeyi da abin da muke so, amma tunda ka bukaci haka kuma kana ganin itace wacce zuciyarka ta gamsu da ita shikenan, zan tayaka addu'ar samunta indai alkhairi ce a garemu, Sannan visar biyu za'ayi, me zan zauna inyi babu jigon gidana, murmushi yayi yace "nine gidan ma gaba daya, "ofcourse, yaushe zan zauna ni kadai a gida, ai sai zuciyata ta buga, School kuma zan barshi gurin Kamal da  Mr Kabeer, nasan zasu cigaba da rike mana Amana, cike da gamsuwa yace kwarai kuwa, ai ko yanzu ma su suke wasu abubuwan, zan koma school din anjima daga can sai in wuce office din *Captain Mus'ab*....... Dariya Hilal yayi ya kalli Baffa yace "me zan zana anan?, saidai in a rushe filin gidan kaf in zana full house a fara aiki malam, nan me za'a gina? Akurki! "Daidai ruwa daidai tsaki, Baffa ya fadi yana dariya hade da cewa nan din nakeso ka zana musu, kaga masu ginin suna son fara aiki, kallon Hafeez yayi yace "zo kayi mishi bayani dan Allah,   naga kamar akwai rikicin tsufa akanshi, Dariya Hafeez da Jamal sukayi Hafeez yace "wannan kawai fa za'a danyi yabe ne Baffa, abun da bai wuce koni in nuna musu ba, har sai an zana a takarda, kaga Zaharadden je ku gama kwaso sauran kayan, kuma kunsan yadda zakuyi, ciki da parlo zaku fitar ku dan yayyaba, tsofaffi ne, suyi maneji, "Gidanku Hafeez, su tsofaffi basu san abu me kyau ba, muma munsan mai kyau dan haka sai an zana min, "Muntari tun muna mu biyu kaje ka fara zanen nan, "wai Baffa wa ma yace maka ina zane, to ni abu biyu kawai na iya zanawa a rayuwata, *full house* nd *complete face that only me can relate* .. kusa da maginin yaje yana dariya yace "zaku iya fitar da 2 bedroom ko, gyada kai Zaraddeen alamar eh, "Yauwa to sai kayi 2 toilets, karka matse su komai kayi shi enough saboda tsofaffine kamar yadda kaji yayana ya fada, Juyawa gurin Baffa yayi yace "shikenan kiran ko? "Shikenan tunda bazaka zana ba, ina son ginin zamani amma hali bazai sa in samu ba, bakomai, ya fadi da fuskar tausayi, Gaba daya gurin suka dauki dariya harda maginan, Duk wannan hidimar da akeyi Goggo bata nan, babu wanda yasan inda ta tafi, Wayar Hilal ce ta soma kara alamar kira na shigowa yayi saurin cewa Baffa sai anjima ginin sai yafi na zamani kyau, hannu ya dagawa su Jamal yana Murmushi sannan ya fita, A lokacin wayar ta katse, saida ya shiga cikin mota ya kira... Assalamu alaikum, Hilal ya fadi cikin girmamawa, daga daya bangaren aka amsa mishi sallama hade da fara magana cikin harcen turanci, "Hilal... Sheik yana yabawa kokarin ka, sannan yana kara yi maka godiya, domin kuwa a halin yanzu babu construction building companyn da yakai namu a cikin gari da wajen Turkey, muna godiya sosai, Sannan akwai wani business da zamuyi dakai,  akwai wasu estates guda hudu da zamu gina, each ana son 400 building,  different houses guda hudu a each estate, "Dat means in each estate ana son 100 houses iri daya har 400 ko? Exactly my boy... mutumin ya fadi yana murmushin hakanshi ya kusa cimma ruwa, ya cigaba da cewa dat will make it 16 different houses, kuma duplex sukeso, yanzu maganar kudi nakeso muyi dakai, yadda oga yake yaba ayyukanka nake son muyi deal da kai, bari in baka ďan oga kuyi magana, shi ya kawo business din, gyara zama Hilal yayi yana sauraronsu, "Hey xup, sunana *Irfan Ateek Deen* kamar yadda manager yayi maka bayani ni na samo business din, to yanzu so mukeyi ka rubuto adadin kudin da za'a biya ka, ni zan fada maka yadda zaka rubuta da adadin kudin, bayan payment sai ka cire actual price din da ake biyanka, ka bani sauran, karka damu da yawan amount din da zan fada maka, i'm very sure Dad will never refuse u, saboda ur hand work mks him loose control, baya iya rike farin ciki lokacin da yaji ana yaba irin aikinshi, so pls wannan aikim taimakon juna ne, *DAD* Hilal ya maimaita a zuciyarshi, katse mishi guntun tunanin da ya fara Irfan yayi yace "ka fahimceni, "yes na fahimta, karku damu, Yanzu bana nan but zan dawo on wed or Thursday daga na dawo zanzo sai mu kara tattaunawa, "Yessssssss Irfan yace  zuciyarshi wasai dan ya hango irin kudin da zai samu, sam mahaifinshi bai bashi kudi saboda halayyarshi na yaran masu kudi na shaye shaye, zinace zinace, da mugun yawo, Baiki dan almubazzaranci kullum yabi jirgi ya fita wasu kasashen ba, babu kamar ma in ana champions league, a lokacin ko baida kudi haukacewa yakeyi ya sato su gurin umminshi, ko kuma cikin sarkokin kanwarshi dake nema ba dare ba rana, Yanzu ma fake business ya kirkira saboda ya samu kudi, yana son zuwa kallon *Zee cine award* a london shi da budurwarshi masoyiyar india, yasan Hilal ne kadai wanda zai rubuta kudi a bashi nan take, Daga nan sai ya bar Hilal cikin matsala, shidai bukatarshi ta biya baiji kunyar *Ailah* ba, Sallama Irfan yayi wa Hilal, saboda tsabar farin ciki ya manta bai kashe wayar ba, nan suka shiga hira da managern suna fadin yadda zasu kasafta kudin da yadda zasuyi denying basu suka sa Hilal ba, dama managern na matukar jin haushin Hilal, saboda a da kaninshi ke musu zane kafin zuwan Hilal ya doke su, Saida ya gama jinsu tsaf har Irfan ya tafi sannan ya katse wayar yana tunanin rashin imani irin na mutane, wai ciki harda dan da ka haifa, kai duniya ina zaki damu ne, shikenan san kudi yasa mun manta komai na duniya, mun manta duties dinmu, zumuncinmu, matsayinmu, da kuma addininmu, Ya Allah ka sanyawa zukatanmu kyankyamin daudar duniya, *(Irfan Ateek bai san da wanda yake son ya fara harka ba)......* Mrs Tijjani Shattimah....... [27/03 8:43 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣7⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Zaune take cikin duhu da waya a hannunta, zuciyarta kamar zata fashe saboda bakin ciki, Tuno sanda suka taso daga makaranta tayi, tabi bayan motar malam Ali dan ya maida ita gida yace "Daddy yayi mishi kashedin kar ya daukata, kwafa tayi ta sake duba agogo karfe takwas da rabi, har lokacin Goggo bata dawo ba, plate din da taci chips da dankalin da ta siyo tayi wurgi dashi waje, tana jiyo masu ginin gidan na mata sallama tayi banza dasu dan bataga abun da zata musu ba, Muryoyi ta jiyo suna shewa suna fadin "lallai masu ginin nan sun iya fitar da foundation, sosai ginin ya burge Baffa domin irin ginin da yake so ne, Fitowa tayi da sauri dan tana ganin rokon Baffa ne kadai mafita, shi zai je ya samu Daddy ya bashi hakuri, inda suke taje ta fashe da kuka, Papy da ya tsani kuka musamman na mace yayi saurin cewa "lafiya?, meya sameki?, "kyaleta shagwaba ce, yanzu haka wani abun takeso, Baffa ya fadi yana kauda wani katon dutse, "Baffa dan Allah ka maidani gida, ka bawa Daddy hakuri, wallahi bazan kara ba, kusa da ita Baffa ya dawo dan baida masaniyar dalilin dawowarta gidan, "lafiya, me kikayi mishi? Share hawaye tayi tace "fada mukayi da Nadeeyah, kuma itace ta fara tsokanata, shine yace in zo nan gidan inyi wata daya, kuma Goggo bata bani abinci, tun safe banci komai ba, da na dawo makaranta ma haka, kuma har yanzu bata dawo ba, ga duhu gashi sauro sai cizona sukeyi, Papy duk yaji babu dadi, duk tunaninshi Daddy ne ya haifi Badariyya, girman Daddy ya kara gani idonshi, saboda yar da ba taka ba kace yarka ta bar gidanka, bazai yiwu ba, shima dole ya taka rawar gani a matsayinshi na uba ya mayar da ita, "share hawayenki, ki shirya mu tafi in maida ki, ai ba'a shiga fadan yara, maza shirya mu tafi, nasan yana gida yanzu, Murmushin jin dadi Baffa yayi yace "aiko ka kyauta, nasan zai hakura dan bai taba yin irin wannan fushin ba, kace ina gaisheshi, zaiji in shaa Allah, bari insa Jamal ya fitar da mota kafin nan ta fito, Fada sosai Baffa yayi mata na ta iya maraicinta, "Kina gani yanzu Muntari har ya fara cewa ki bar mishi gida, ina ga nan gaba in kika kaishi bango, wallahi ki maida hankalinki, Gyada kai tayi kamar taji abinda yace, bai san so takeyi ta koma tun kusancin Nadeeyah da Musaddiq baiyi nisa ba, tun yanzu ma kenan ta fara sa hularshi, gaba sai hada jiki da sunan soyayya.... ta karashe hade da runtse ido tana fadin Allah ya kauda idon Musaddiq akan Nadeeyah...... Saboda kunyar idon Papy, Daddy baiyi wata jayayya ba ya ce ta shiga gida, godiya Papy yayi mishi, nan suka shiga hira, ya fada mishi shirin da yayi na auren Baffa da Anni, Ba karamin farin ciki Daddy yayi ba, dan ya hango tsantsar tsoron Allah da ilimi a tattare da Anni, Yana da yakinin yanzu zumuncin zuri'ar matarshi da ta 'yayanshi zai gyaru ta sanadiyar Papy da Anni, Zama Mummy tayi bayan ta gama jin zancen auren, A zuciyarta bata ji dadi ba dan abun kunya ne a gurinta tace babanta zaiyi aure, me kawayenta zasu dauke shi, A fili kuwa saboda yadda taga Daddy na farin ciki kamar shi zaiyi auren, ta nuna itama ta amince, ta cigaba da cewa "gara a sakawa Anni ta wannan hanyar, dan tayi mana abun da bazamu taba mantawa ba, samun mutane irinta sai an tona.... Sai kusan goma Papy ya fara shirin tafiya, Dakatar dashi Daddy yayi, ya dauko Sarkar Atika yace "wannan Sarkar mahaifiyarku ce wacce mukayi tunanin su Hafeez ne magadan ta, to yanzu kai ne ke da gadonta domin Baffa yace ya bar musu, Dariya Papy yayi ya karbi sarkar dan jin dumin mahaifiyarshi yace "nima na bar musu, domin duk 'yayanmu ne, ka ajiyeta a gurinka, kaine uba a garesu, mun gode sosai da yadda kake kula dasu, karbar Sarkar Daddy yayi yace "to Madallah, zan cigaba da ajiye musu har lokacin da zasu bukace ta, Allah yayi wa zuri'armu albarka, Ameen.... Papy ya fada hade da mikewa yayi sallama da Mummy, Har gurin mota Daddy ya rakashi, nan ma suka dan taba hira sannan suka wuce cike da shaukin shakuwa kamar sun shekara tare...... Har kwana hudu babu Goggo babu dalilinta, Hankalin Baffa ba karamin tashi yayi ba dan ba inda bai nemeta ba, wayarta a kashe take, duk inda yasan tana zuwa yaje ya duba shuru, Allah kadai yasan inda ta shiga, Itama Mummy ba karamin tashin hankali ta shiga ba, saidai tasan bazata bata ba, ta yiwu tana can tana kulle kullenta, shiyasa ma ta kwantar ma Baffa da hankali... A ranar da Mummy tazo gidan, ginin da akeyi har yakai linta, aiki maginan sukeyi ba dare ba rana dan Papy baya son ginin ya wuce wata daya, Tasha mamaki da takaici, har ta dan yadawa Baffa habaici tace "bari a gamawa amarya nima insa ayi ma Goggo irinshi, karaff kalamanta cikin kunnen Papy da ya doso kai zai shigo, nunawa yayi baiji ba, suka gaisa ya gama duba ginin, yaga komai yayi mishi yadda yakeso, yana matukar son ganin Anni cikin jindadi shiyasa zai wadata ta da komai na bukata a cikin gidan, ko gishiri baya fatan ta neme shi koda na second daya ne...... Bayan tafiyar Mummy Papy yace ma Baffa "ko za'a fitar da kayan dakin Goggo sai ayi mata renovating in yaso itama sai a sake mata sababbi, nan take Baffa ya saki murmushi, guilt din da Mummy ta tafi ta barshi a ciki ya sakeshi, Albarka ya shiga sawa Papy kamar zai ari baki, farin cikin da yake ciki a wannan lokacin ba mai misaltuwa bane, ashe akwai ranar da zaiga danshi namiji har ya dauke mishi nauyin abu mai girma haka, alhamdulillah ya dinga jerowa babu adadi... Washe gari ko Mummy Baffa bai fadawa za'ayi aikin dakin Goggo ba, da kanshi ya cire kayan da yasan masu muhimmaci ne sauran yasa aka fitar dasu zuwa bola, duk wani takarcenta da take yawan ce mishi maganin basir, hawayan jini da na neman budi, duk ya zubar dasu, Gadonta mai runfa ya kira yan gwangwan suka tafi dashi, abubuwan da suka fado daga saman gadon Allah yayi yawa dasu, ba tare da ya kula dasu ba yasa Garzali da sauran samarin suka tattaresu suka konesu tass, harda dan akushin Goggo da ya fado kayan ciki suka far fashe..... *(shin ina Goggo take ake yi mata wannan ta'asar,)* abeg ummu iman nd Siyama help me luk fr her... ku hada kudi kubawa Meelah ta nemo ta... Yagar naman farfesun kazar dake gabanshi yayi da sauri hade da kara wayarshi a kunnenshi, "yes Mum, daga daya bangaren Anty Reemah tace "Hilal har yanzu baka wuce Abuja ba? "on my way mum, meyasa kika damu, 6pm ne fa jirgin zai tashi, "dis is madness Hilal, hanyar taka ce, pass 3 yanzu kana da assurance din kaiwa Abuja 5:30 or 40, ka maida hankalinka dani wallahi, wannan ai iskanci ne, "ohhhh calm down sweet heart, tare da little kaninki zamu tafi, ni zanyi driving, sai su dawo gobe da Malam Ali, "cikin sarkewar murya tace "ban yarda ba, karka soma yin wannan mahaukacin tukin naka, maza ka bani Malam Ali! "ummmm am nt a kid anymore haba mana, ki bari pls kar kisa a raina ni, in shaa Allah your Mukhtar will come home safe nd sound, kiyi min addu'a, yana kaiwa nan ya kashe wayar gaba daya dan yasan bazata fasa kiranshi ba, sai ta jishi a jirgi zata hakura... A gaggauce yayi sallama da Mummy suka fito daga parlon lokacin da sukaji horn din Malam Ali, Husnah na hangoshi ta rugo da gudu ta karbi jakar hannunshi ta turo baki, "yanzu zaka tafi? haba my PP, shikenan da bamu dawo ba bazaka jiramu ba, Bakin yaja yace "oya kara turoshi shi gaba, dariya tayi sosai tace "Allah da gaske da ka tafi baka jirani ba ko waya ka kirani bazan dauka ba, Gurin motar suka karasa yace "dama nayi niyyar baki wata kyauta, na fasa.. leda ya mikawa Nadeeyah dake tsaye tana murmushi, "amshi wannan ke, Husnah ta lashe, Tura daya ledar cikin motar yayi yana dariya, bude motar tayi da sauri tana fadin "sorry my pp, dauko ledar tayi cike da kosawa ta fito da abun dake ciki, waya ce sabuwa dal mai tsadar gaske, wani irin ihu ta saki tana fadin "thank u yaya Hilal, u are the best, Da kafada Musaddiq ya zunguri Nadeeyah dake tsaye kamar statue, murna ta hanata magana, kallonshi tayi zatayi magana, yace "ke bazakiyi godiyar bane, oya say it out kema, *Yaya Hilal u are the best*, yadda yayi da murya kamar mace yasata sakin dariya sosai harda rike ciki, shima dariyar yakeyi, Duk wannan abun da sukeyi a kan idon Badar da ta shige ciki tun shigowarsu gidan, dakyar ta iya danne tukukin da ya yaso mata, ta saki labulen windon da karfi, Shi kuwa Hilal tsintar kanshi yayi cikin nishadin ganin dariyarta mai kayatar dashi, wani masifar sonta ke ratsashi kamar dama a cikin jininshi akayi halittar son, ya shagala sosai cikin farin ciki shiyasa baiji muryarta tana mishi godiya ba, tabo shi Husnah tayi tace "Ana maka magana, kallonta yayi ya saki dan murmushin da ba kowa ke ganinshi ba yace "never mind, ki godewa Allah, nd ki kula da karatunki, murmushi tayi tace "inshaa Allah, Allah ya kiyaye hanya ka gaida min da kowa da kowa, gyada kai yayi suka shiga mota yaja suka wuce, saida suka fita a gate din sannan ya iya maida hankali kan tukin da yakeyi, gaba daya jikinshi yayi sanyi, gani yakeyi kamar wannan rabuwar da zaiyi da Nadeeyah itace rabuwarsu ta karshe, "ko dai mutuwa zanyi, saurin taka burki yayi saboda yadda tunanin yazo mishi, kashe motar yayi yace "malam Ali dawo ka tuka, ya bude baya ya shiga malam Ali yaja suka wuce, Har suka isa Abuja ya rasa asalin abin da ke taba zuciyarshi akan Nadeeyah, Addu'a kawai yayi na Allah kar ya kawo sanadin da wani zai zo ya kwace mishi ita, badan yanada abubuwan yi ba da ya dawo nigeria har ta gama secondary school ya sama mata university a cyprus, cikin damuwar da ya rasa dalilinta yace " in shaa Allah tana gama school nan da 5month zai dawo da ita cyprus, gara tana gabanshi, hakan kadai zai hutar da zuciyarshi, zai cigaba da tunasar da ita muhimmacin karatu har ta gama secondary... Text ya tura cikin layin da ya sai mata.. *Kyawun alkawari cikawa, Dan Allah ki kula, ki maida hankali kan karatun waec, nd ur line ya zama personal, kar ki bawa ko wani namiji ko macce numberki sai wanda ya zamto shakikinki, take care*.... Husnah na miko mata wayar bayan ta gama setting dinta, text din ya shigo da sunan *Arc Kangiwa* karanta text din tayi hade da murmushi, saboda sabo da rike wayar Husnah yasa ta iya wasu abubuwan, reply tayi mishi *In shaa Allah will keep my words, Allah ya saka da alkhairi thanks for caring* Yana gama karanta reply dinta ya ajiye wayar, inama zai iya ce mata *I love you* Yana matukar son ganin reply din da zai hana mishi sukuni ya sanya shi yawo cikin sararin samaniya kamar yadda jirginsu zai lula, saidai kashh.. bazai iya ba, domin tanadin da yayi wa soyayyarsu ba na yanzu bane, sai ta mallaki dukkan hankalin kanta, sai ta koyi duk wasu nau'ika na soyayya, yana son yin soyayyar da a tarihi ba'a taba samun kamarta ba, cije lebe yayi domin hango yadda zai maida ita sarauniyar shi, kuma sarauniyar matan duniya.... *(A bari ya huce)*..... 🤪😜😝 *MAFARI* ...... *(kauna)* *Shin so samu ne* Nidai rubutuwa nakeyi, mijin Nadeeyah na cikin ukun nan, Allah ya riga ya zaba... muje zuwa a Mafari.... *Team Hilal* *Team Diku nah* *Team Taheer* Mrs Tijjani Shattima...... [01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣6⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Ajiye motarshi yayi a gurin da aka tanada dan ajiyar motoci, saida ya kusan minti biyar yana tattara duk wasu abubuwa masu muhimmanci a cikin motar, sannan ya fito ya rufe hade da mikawa wani yaron gidan mai musu hidima kayan ya wuce ciki, jikinshi sam babu kuzari da walwala, Kauracewa abinda kake so dan farin cikinsa, ba karamin jarumta bane wanda samun masu yinsa sai an tona.... Koda ya shiga bayi domin watsa ruwa kasa tabuka komai yayi, yana tsaye a tsakiyar shower ruwa na ratsa dukkan sassan jikinshi, a maimakon yaji sanyin ruwan a zuciyarshi sai yaji wani irin zafin da ke kona duk wata kwayar halitta da aka halicceta domin soyayya a cikin ma'adanar ta, alwala ya dauro ya fito jikinshi sam ba karfi, karfe goma da rabi lokacin, brown jallabiya yasaka ya shimfida sallaya dan yin sallahr walaha (Duha).. Yafi minti talatin yana kai kukansa gurin rabbil izzati akan ya mallaka mishi Nadeeyah kuma ya sanyata farin ciki har karshen rayuwarta, "Tee lafiya ka dawo gida?, Momma da ta shigo dakin bayan ta fita taga motarshi a parke ta fadi hade da zama a kujerar dake fuskantarshi, Shafa addu'a yayi yace "Lafiya lau momma, dama yanzu nake shirin zuwa gurinki, Mikewa yayi ya nade daddumar ya dawo kusa da ita ya zauna, "Ina son komawa school Momma, munyi magana da Uncle Mus'ab nace su shirya min visa, ina son yin phd dina tun yanzu Momma, rike makaranta irin legacy sai da Phd, daga nan ma sai in kara gaba in shaa Allahu, ina son mu samu rassar makarantar a ko ina a cikin Nigeria, kinga dole in gogu cikin il--- "Ba gaskiya bane Taheer ta katseshi cikin sauri dan kar yayi zurfi cikin karyarsa, "Kalleni Tee, ni na haifeka, na raineka har kawo wannan lokacin, a kan murmushin fuskarka ina iya hangen damuwarka, "jiya ka gama cemin ka samu yarinyar da kake so da aure, yau kuma sai kazo min da zancen tafiya har Canada kuma ba wai kwana daya ba har shekaru, sannan kake tunanin in yarda baka da damuwa, "Fada min matsalarka maza maza, ka sani babu abin da yake cikin duniyar nan wanda bazan iya magance maka shi ba, koma me kake so ka fada min yanzun nan kaga aiki da cikawa, Hannunta ya rike a hankali yace "nasan zaki iya magance min komai Momma, amma ban da soyayyar Nadeeyah, bana son in a matsa mata ta zauna dani, nafi son ta zauna dani domin kanta, nafi son ta soni da kanta ba tare da an tursasata ba, nasan Allah swt zai kawo mana wannan ranar, Addu'a kawai zamu cigaba dayi, in shaa Allah zamu dace, Zan tafi ne dan in bata damar yin karatunta cikin kwanciyar hankali, in shaa Allahu lokacin da ta kammala karatunta nasan zata karbi bukatata, "Jiranta zakayi Taheer? Yadda tayi maganar cikin damuwa yasashi jin wani iri a jikinshi, yayi karfin halin cewa "kamar yau ne Momma, kuma kinga karatu zan tafi nima, lokaci gudu yakeyi, sai kiga kamar yau ne ta kammala, Shafa fuskarshi tayi tace "lokaci sakarai ne Taheer, wucewa yakeyi da abin da muke so, amma tunda ka bukaci haka kuma kana ganin itace wacce zuciyarka ta gamsu da ita shikenan, zan tayaka addu'ar samunta indai alkhairi ce a garemu, Sannan visar biyu za'ayi, me zan zauna inyi babu jigon gidana, murmushi yayi yace "nine gidan ma gaba daya, "ofcourse, yaushe zan zauna ni kadai a gida, ai sai zuciyata ta buga, School kuma zan barshi gurin Kamal da  Mr Kabeer, nasan zasu cigaba da rike mana Amana, cike da gamsuwa yace kwarai kuwa, ai ko yanzu ma su suke wasu abubuwan, zan koma school din anjima daga can sai in wuce office din *Captain Mus'ab*....... Dariya Hilal yayi ya kalli Baffa yace "me zan zana anan?, saidai in a rushe filin gidan kaf in zana full house a fara aiki malam, nan me za'a gina? Akurki! "Daidai ruwa daidai tsaki, Baffa ya fadi yana dariya hade da cewa nan din nakeso ka zana musu, kaga masu ginin suna son fara aiki, kallon Hafeez yayi yace "zo kayi mishi bayani dan Allah,   naga kamar akwai rikicin tsufa akanshi, Dariya Hafeez da Jamal sukayi Hafeez yace "wannan kawai fa za'a danyi yabe ne Baffa, abun da bai wuce koni in nuna musu ba, har sai an zana a takarda, kaga Zaharadden je ku gama kwaso sauran kayan, kuma kunsan yadda zakuyi, ciki da parlo zaku fitar ku dan yayyaba, tsofaffi ne, suyi maneji, "Gidanku Hafeez, su tsofaffi basu san abu me kyau ba, muma munsan mai kyau dan haka sai an zana min, "Muntari tun muna mu biyu kaje ka fara zanen nan, "wai Baffa wa ma yace maka ina zane, to ni abu biyu kawai na iya zanawa a rayuwata, *full house* nd *complete face that only me can relate* .. kusa da maginin yaje yana dariya yace "zaku iya fitar da 2 bedroom ko, gyada kai Zaraddeen alamar eh, "Yauwa to sai kayi 2 toilets, karka matse su komai kayi shi enough saboda tsofaffine kamar yadda kaji yayana ya fada, Juyawa gurin Baffa yayi yace "shikenan kiran ko? "Shikenan tunda bazaka zana ba, ina son ginin zamani amma hali bazai sa in samu ba, bakomai, ya fadi da fuskar tausayi, Gaba daya gurin suka dauki dariya harda maginan, Duk wannan hidimar da akeyi Goggo bata nan, babu wanda yasan inda ta tafi, Wayar Hilal ce ta soma kara alamar kira na shigowa yayi saurin cewa Baffa sai anjima ginin sai yafi na zamani kyau, hannu ya dagawa su Jamal yana Murmushi sannan ya fita, A lokacin wayar ta katse, saida ya shiga cikin mota ya kira... Assalamu alaikum, Hilal ya fadi cikin girmamawa, daga daya bangaren aka amsa mishi sallama hade da fara magana cikin harcen turanci, "Hilal... Sheik yana yabawa kokarin ka, sannan yana kara yi maka godiya, domin kuwa a halin yanzu babu construction building companyn da yakai namu a cikin gari da wajen Turkey, muna godiya sosai, Sannan akwai wani business da zamuyi dakai,  akwai wasu estates guda hudu da zamu gina, each ana son 400 building,  different houses guda hudu a each estate, "Dat means in each estate ana son 100 houses iri daya har 400 ko? Exactly my boy... mutumin ya fadi yana murmushin hakanshi ya kusa cimma ruwa, ya cigaba da cewa dat will make it 16 different houses, kuma duplex sukeso, yanzu maganar kudi nakeso muyi dakai, yadda oga yake yaba ayyukanka nake son muyi deal da kai, bari in baka ďan oga kuyi magana, shi ya kawo business din, gyara zama Hilal yayi yana sauraronsu, "Hey xup, sunana *Irfan Ateek Deen* kamar yadda manager yayi maka bayani ni na samo business din, to yanzu so mukeyi ka rubuto adadin kudin da za'a biya ka, ni zan fada maka yadda zaka rubuta da adadin kudin, bayan payment sai ka cire actual price din da ake biyanka, ka bani sauran, karka damu da yawan amount din da zan fada maka, i'm very sure Dad will never refuse u, saboda ur hand work mks him loose control, baya iya rike farin ciki lokacin da yaji ana yaba irin aikinshi, so pls wannan aikim taimakon juna ne, *DAD* Hilal ya maimaita a zuciyarshi, katse mishi guntun tunanin da ya fara Irfan yayi yace "ka fahimceni, "yes na fahimta, karku damu, Yanzu bana nan but zan dawo on wed or Thursday daga na dawo zanzo sai mu kara tattaunawa, "Yessssssss Irfan yace  zuciyarshi wasai dan ya hango irin kudin da zai samu, sam mahaifinshi bai bashi kudi saboda halayyarshi na yaran masu kudi na shaye shaye, zinace zinace, da mugun yawo, Baiki dan almubazzaranci kullum yabi jirgi ya fita wasu kasashen ba, babu kamar ma in ana champions league, a lokacin ko baida kudi haukacewa yakeyi ya sato su gurin umminshi, ko kuma cikin sarkokin kanwarshi dake nema ba dare ba rana, Yanzu ma fake business ya kirkira saboda ya samu kudi, yana son zuwa kallon *Zee cine award* a london shi da budurwarshi masoyiyar india, yasan Hilal ne kadai wanda zai rubuta kudi a bashi nan take, Daga nan sai ya bar Hilal cikin matsala, shidai bukatarshi ta biya baiji kunyar *Ailah* ba, Sallama Irfan yayi wa Hilal, saboda tsabar farin ciki ya manta bai kashe wayar ba, nan suka shiga hira da managern suna fadin yadda zasu kasafta kudin da yadda zasuyi denying basu suka sa Hilal ba, dama managern na matukar jin haushin Hilal, saboda a da kaninshi ke musu zane kafin zuwan Hilal ya doke su, Saida ya gama jinsu tsaf har Irfan ya tafi sannan ya katse wayar yana tunanin rashin imani irin na mutane, wai ciki harda dan da ka haifa, kai duniya ina zaki damu ne, shikenan san kudi yasa mun manta komai na duniya, mun manta duties dinmu, zumuncinmu, matsayinmu, da kuma addininmu, Ya Allah ka sanyawa zukatanmu kyankyamin daudar duniya, *(Irfan Ateek bai san da wanda yake son ya fara harka ba)......* Mrs Tijjani Shattimah....... [01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣7⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Zaune take cikin duhu da waya a hannunta, zuciyarta kamar zata fashe saboda bakin ciki, Tuno sanda suka taso daga makaranta tayi, tabi bayan motar malam Ali dan ya maida ita gida yace "Daddy yayi mishi kashedin kar ya daukata, kwafa tayi ta sake duba agogo karfe takwas da rabi, har lokacin Goggo bata dawo ba, plate din da taci chips da dankalin da ta siyo tayi wurgi dashi waje, tana jiyo masu ginin gidan na mata sallama tayi banza dasu dan bataga abun da zata musu ba, Muryoyi ta jiyo suna shewa suna fadin "lallai masu ginin nan sun iya fitar da foundation, sosai ginin ya burge Baffa domin irin ginin da yake so ne, Fitowa tayi da sauri dan tana ganin rokon Baffa ne kadai mafita, shi zai je ya samu Daddy ya bashi hakuri, inda suke taje ta fashe da kuka, Papy da ya tsani kuka musamman na mace yayi saurin cewa "lafiya?, meya sameki?, "kyaleta shagwaba ce, yanzu haka wani abun takeso, Baffa ya fadi yana kauda wani katon dutse, "Baffa dan Allah ka maidani gida, ka bawa Daddy hakuri, wallahi bazan kara ba, kusa da ita Baffa ya dawo dan baida masaniyar dalilin dawowarta gidan, "lafiya, me kikayi mishi? Share hawaye tayi tace "fada mukayi da Nadeeyah, kuma itace ta fara tsokanata, shine yace in zo nan gidan inyi wata daya, kuma Goggo bata bani abinci, tun safe banci komai ba, da na dawo makaranta ma haka, kuma har yanzu bata dawo ba, ga duhu gashi sauro sai cizona sukeyi, Papy duk yaji babu dadi, duk tunaninshi Daddy ne ya haifi Badariyya, girman Daddy ya kara gani idonshi, saboda yar da ba taka ba kace yarka ta bar gidanka, bazai yiwu ba, shima dole ya taka rawar gani a matsayinshi na uba ya mayar da ita, "share hawayenki, ki shirya mu tafi in maida ki, ai ba'a shiga fadan yara, maza shirya mu tafi, nasan yana gida yanzu, Murmushin jin dadi Baffa yayi yace "aiko ka kyauta, nasan zai hakura dan bai taba yin irin wannan fushin ba, kace ina gaisheshi, zaiji in shaa Allah, bari insa Jamal ya fitar da mota kafin nan ta fito, Fada sosai Baffa yayi mata na ta iya maraicinta, "Kina gani yanzu Muntari har ya fara cewa ki bar mishi gida, ina ga nan gaba in kika kaishi bango, wallahi ki maida hankalinki, Gyada kai tayi kamar taji abinda yace, bai san so takeyi ta koma tun kusancin Nadeeyah da Musaddiq baiyi nisa ba, tun yanzu ma kenan ta fara sa hularshi, gaba sai hada jiki da sunan soyayya.... ta karashe hade da runtse ido tana fadin Allah ya kauda idon Musaddiq akan Nadeeyah...... Saboda kunyar idon Papy, Daddy baiyi wata jayayya ba ya ce ta shiga gida, godiya Papy yayi mishi, nan suka shiga hira, ya fada mishi shirin da yayi na auren Baffa da Anni, Ba karamin farin ciki Daddy yayi ba, dan ya hango tsantsar tsoron Allah da ilimi a tattare da Anni, Yana da yakinin yanzu zumuncin zuri'ar matarshi da ta 'yayanshi zai gyaru ta sanadiyar Papy da Anni, Zama Mummy tayi bayan ta gama jin zancen auren, A zuciyarta bata ji dadi ba dan abun kunya ne a gurinta tace babanta zaiyi aure, me kawayenta zasu dauke shi, A fili kuwa saboda yadda taga Daddy na farin ciki kamar shi zaiyi auren, ta nuna itama ta amince, ta cigaba da cewa "gara a sakawa Anni ta wannan hanyar, dan tayi mana abun da bazamu taba mantawa ba, samun mutane irinta sai an tona.... Sai kusan goma Papy ya fara shirin tafiya, Dakatar dashi Daddy yayi, ya dauko Sarkar Atika yace "wannan Sarkar mahaifiyarku ce wacce mukayi tunanin su Hafeez ne magadan ta, to yanzu kai ne ke da gadonta domin Baffa yace ya bar musu, Dariya Papy yayi ya karbi sarkar dan jin dumin mahaifiyarshi yace "nima na bar musu, domin duk 'yayanmu ne, ka ajiyeta a gurinka, kaine uba a garesu, mun gode sosai da yadda kake kula dasu, karbar Sarkar Daddy yayi yace "to Madallah, zan cigaba da ajiye musu har lokacin da zasu bukace ta, Allah yayi wa zuri'armu albarka, Ameen.... Papy ya fada hade da mikewa yayi sallama da Mummy, Har gurin mota Daddy ya rakashi, nan ma suka dan taba hira sannan suka wuce cike da shaukin shakuwa kamar sun shekara tare...... Har kwana hudu babu Goggo babu dalilinta, Hankalin Baffa ba karamin tashi yayi ba dan ba inda bai nemeta ba, wayarta a kashe take, duk inda yasan tana zuwa yaje ya duba shuru, Allah kadai yasan inda ta shiga, Itama Mummy ba karamin tashin hankali ta shiga ba, saidai tasan bazata bata ba, ta yiwu tana can tana kulle kullenta, shiyasa ma ta kwantar ma Baffa da hankali... A ranar da Mummy tazo gidan, ginin da akeyi har yakai linta, aiki maginan sukeyi ba dare ba rana dan Papy baya son ginin ya wuce wata daya, Tasha mamaki da takaici, har ta dan yadawa Baffa habaici tace "bari a gamawa amarya nima insa ayi ma Goggo irinshi, karaff kalamanta cikin kunnen Papy da ya doso kai zai shigo, nunawa yayi baiji ba, suka gaisa ya gama duba ginin, yaga komai yayi mishi yadda yakeso, yana matukar son ganin Anni cikin jindadi shiyasa zai wadata ta da komai na bukata a cikin gidan, ko gishiri baya fatan ta neme shi koda na second daya ne...... Bayan tafiyar Mummy Papy yace ma Baffa "ko za'a fitar da kayan dakin Goggo sai ayi mata renovating in yaso itama sai a sake mata sababbi, nan take Baffa ya saki murmushi, guilt din da Mummy ta tafi ta barshi a ciki ya sakeshi, Albarka ya shiga sawa Papy kamar zai ari baki, farin cikin da yake ciki a wannan lokacin ba mai misaltuwa bane, ashe akwai ranar da zaiga danshi namiji har ya dauke mishi nauyin abu mai girma haka, alhamdulillah ya dinga jerowa babu adadi... Washe gari ko Mummy Baffa bai fadawa za'ayi aikin dakin Goggo ba, da kanshi ya cire kayan da yasan masu muhimmaci ne sauran yasa aka fitar dasu zuwa bola, duk wani takarcenta da take yawan ce mishi maganin basir, hawayan jini da na neman budi, duk ya zubar dasu, Gadonta mai runfa ya kira yan gwangwan suka tafi dashi, abubuwan da suka fado daga saman gadon Allah yayi yawa dasu, ba tare da ya kula dasu ba yasa Garzali da sauran samarin suka tattaresu suka konesu tass, harda dan akushin Goggo da ya fado kayan ciki suka far fashe..... *(shin ina Goggo take ake yi mata wannan ta'asar,)* abeg ummu iman nd Siyama help me luk fr her... ku hada kudi kubawa Meelah ta nemo ta... Yagar naman farfesun kazar dake gabanshi yayi da sauri hade da kara wayarshi a kunnenshi, "yes Mum, daga daya bangaren Anty Reemah tace "Hilal har yanzu baka wuce Abuja ba? "on my way mum, meyasa kika damu, 6pm ne fa jirgin zai tashi, "dis is madness Hilal, hanyar taka ce, pass 3 yanzu kana da assurance din kaiwa Abuja 5:30 or 40, ka maida hankalinka dani wallahi, wannan ai iskanci ne, "ohhhh calm down sweet heart, tare da little kaninki zamu tafi, ni zanyi driving, sai su dawo gobe da Malam Ali, "cikin sarkewar murya tace "ban yarda ba, karka soma yin wannan mahaukacin tukin naka, maza ka bani Malam Ali! "ummmm am nt a kid anymore haba mana, ki bari pls kar kisa a raina ni, in shaa Allah your Mukhtar will come home safe nd sound, kiyi min addu'a, yana kaiwa nan ya kashe wayar gaba daya dan yasan bazata fasa kiranshi ba, sai ta jishi a jirgi zata hakura... A gaggauce yayi sallama da Mummy suka fito daga parlon lokacin da sukaji horn din Malam Ali, Husnah na hangoshi ta rugo da gudu ta karbi jakar hannunshi ta turo baki, "yanzu zaka tafi? haba my PP, shikenan da bamu dawo ba bazaka jiramu ba, Bakin yaja yace "oya kara turoshi shi gaba, dariya tayi sosai tace "Allah da gaske da ka tafi baka jirani ba ko waya ka kirani bazan dauka ba, Gurin motar suka karasa yace "dama nayi niyyar baki wata kyauta, na fasa.. leda ya mikawa Nadeeyah dake tsaye tana murmushi, "amshi wannan ke, Husnah ta lashe, Tura daya ledar cikin motar yayi yana dariya, bude motar tayi da sauri tana fadin "sorry my pp, dauko ledar tayi cike da kosawa ta fito da abun dake ciki, waya ce sabuwa dal mai tsadar gaske, wani irin ihu ta saki tana fadin "thank u yaya Hilal, u are the best, Da kafada Musaddiq ya zunguri Nadeeyah dake tsaye kamar statue, murna ta hanata magana, kallonshi tayi zatayi magana, yace "ke bazakiyi godiyar bane, oya say it out kema, *Yaya Hilal u are the best*, yadda yayi da murya kamar mace yasata sakin dariya sosai harda rike ciki, shima dariyar yakeyi, Duk wannan abun da sukeyi a kan idon Badar da ta shige ciki tun shigowarsu gidan, dakyar ta iya danne tukukin da ya yaso mata, ta saki labulen windon da karfi, Shi kuwa Hilal tsintar kanshi yayi cikin nishadin ganin dariyarta mai kayatar dashi, wani masifar sonta ke ratsashi kamar dama a cikin jininshi akayi halittar son, ya shagala sosai cikin farin ciki shiyasa baiji muryarta tana mishi godiya ba, tabo shi Husnah tayi tace "Ana maka magana, kallonta yayi ya saki dan murmushin da ba kowa ke ganinshi ba yace "never mind, ki godewa Allah, nd ki kula da karatunki, murmushi tayi tace "inshaa Allah, Allah ya kiyaye hanya ka gaida min da kowa da kowa, gyada kai yayi suka shiga mota yaja suka wuce, saida suka fita a gate din sannan ya iya maida hankali kan tukin da yakeyi, gaba daya jikinshi yayi sanyi, gani yakeyi kamar wannan rabuwar da zaiyi da Nadeeyah itace rabuwarsu ta karshe, "ko dai mutuwa zanyi, saurin taka burki yayi saboda yadda tunanin yazo mishi, kashe motar yayi yace "malam Ali dawo ka tuka, ya bude baya ya shiga malam Ali yaja suka wuce, Har suka isa Abuja ya rasa asalin abin da ke taba zuciyarshi akan Nadeeyah, Addu'a kawai yayi na Allah kar ya kawo sanadin da wani zai zo ya kwace mishi ita, badan yanada abubuwan yi ba da ya dawo nigeria har ta gama secondary school ya sama mata university a cyprus, cikin damuwar da ya rasa dalilinta yace " in shaa Allah tana gama school nan da 5month zai dawo da ita cyprus, gara tana gabanshi, hakan kadai zai hutar da zuciyarshi, zai cigaba da tunasar da ita muhimmacin karatu har ta gama secondary... Text ya tura cikin layin da ya sai mata.. *Kyawun alkawari cikawa, Dan Allah ki kula, ki maida hankali kan karatun waec, nd ur line ya zama personal, kar ki bawa ko wani namiji ko macce numberki sai wanda ya zamto shakikinki, take care*.... Husnah na miko mata wayar bayan ta gama setting dinta, text din ya shigo da sunan *Arc Kangiwa* karanta text din tayi hade da murmushi, saboda sabo da rike wayar Husnah yasa ta iya wasu abubuwan, reply tayi mishi *In shaa Allah will keep my words, Allah ya saka da alkhairi thanks for caring* Yana gama karanta reply dinta ya ajiye wayar, inama zai iya ce mata *I love you* Yana matukar son ganin reply din da zai hana mishi sukuni ya sanya shi yawo cikin sararin samaniya kamar yadda jirginsu zai lula, saidai kashh.. bazai iya ba, domin tanadin da yayi wa soyayyarsu ba na yanzu bane, sai ta mallaki dukkan hankalin kanta, sai ta koyi duk wasu nau'ika na soyayya, yana son yin soyayyar da a tarihi ba'a taba samun kamarta ba, cije lebe yayi domin hango yadda zai maida ita sarauniyar shi, kuma sarauniyar matan duniya.... *(A bari ya huce)*..... 🤪😜😝 *MAFARI* ...... *(kauna)* *Shin so samu ne* Nidai rubutuwa nakeyi, mijin Nadeeyah na cikin ukun nan, Allah ya riga ya zaba... muje zuwa a Mafari.... *Team Hilal* *Team Diku nah* *Team Taheer* Mrs Tijjani Shattima...... [01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣9⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *MOROCCO* Kuka sosai Shareefa keyi tana kwala kiran Doctor, Doctor.... kokarin cire oxygen din Ummu Ayyu takeyi hawaye na tsiyaya ta gefen idonta, hannunta Sarki Tidjani ya rike yayi saurin maida mata oxygen din, girgiza kai ta shiga yi hawaye na tsare da dan uwanshi, Allah kadai azabar da mai rai yakesha yayi da yazo gangara, dago idanuwanta da suke lumshewa tayi tana musu alama da akwai abin da takeson fada musu, zuwan doctor ne ya sa suka matsa gurin suna kuka dukkansu babu mai ba wani hakuri, ganin Doctorn na girgiza yana cire oxygen din ya sanya Shareefah matsowa a gigice tana tambayarshi, bai ce mata komai ba ya zagaya ya cire drip din da ke taimaka mata ta samu karfi a jikinta, bin bayanshi Shareefah zatayi taji hannun Ummu Ayyu ya riketa, damke hannun tayi cikin kuka tace "Kiyi hakuri ummu na, nasan zai canza miki magani ne, bari in tambayeshi, tari ummu ta fara yi da karfi tana fadin "a'a, ki tsaya a nan in cika a gabanki, shima likitan yasan rayuwata yanzu bata da wani sauran amfani, amfaninta a gareni da Allah bai dauki raina ba ya barni in sanar miki da sirrin da ya dade a rufe, gyara zama Shareefah tayi tana sauraron mahaifiyarta, Shareefah..... ta fadi a wahalce saboda fitar maganar ma wahala ce a gareta, "na aikata abubuwan da ban taba tunani akansu ba, na aikata abubuwan da rana irin ta yau bata taba zuwa min a kwalkwata ba, *YAREEMA*.... *YAREEMA A....DA....* nan ta shiga tari sosai har tana jirkitowa daga kan gadon, kuka mai karfi Shareefah ta fashe dashi tana kallon Doctor dake tsaye yana monitoring heart beat din Ummu, doctor help me, kayi wani abu dan Allah, girgiza kai yayi yace "babu abinda zaiyi amfani a wannan ranar Shareefah, not even power, just listen to her before its late, "may be what she is going to tell u will be a relief to her, hannun Tidjani ummu ta kamo tace " *HAJJA*, *RUGAR HALDON SASSOUNBOROUN* ku nemi Hajja yar Riga, zata fada muku komai game da *YAREEMA... AD...* kasa karasawa tayi saboda yadda tayi wani tarin da ya hado da gudan jini, nan ta shiga fisge fisge suna danneta suna kuka sosai, murya can kasa take cewa *da na sani, da na sani, na cuci ka....ina* kalmar da dunga fada kenan har ta cika da ihun da ya ratsa ko ina a cikin katafaren asibitin..... *(Shin masu zalunci basa tuna wannan ranar, ranar da babu wani wanda zai iya taimakonsu, ranar da babu wani sauki sai saukin Allah da na abun alkhairin da ka shuka, shin in ka shuka tsiya baka tunanin wannan tsiyar ta zame maka kaya mai nauyi ranar da rayuwarka zata zamo ba taka ba, shin menene kazantar duniya da zata sanyamu mu dinga kauce hanya har mu dauki nauyin hakkin wasu muyi dakonshi, rayuwa kalilan ce, wallahi tsakanin mutuwa da rayuwa kamar kiftawar ido ne, yanzun nan komai na iya canzawa, dan Allah yan uwa ko me zamuyi mu tuno da wannan ranar, ranar da take tafe ga dukkan wanda yake numfashi a doron kasa, ba'a dauketa ga kowa ba dukkanmu zamu tafi, Allah kasa mu cika da kyau da imani)*........ ******** Orange rigar da ta saba bacci da ita ta dauko ta saka ta sanya bakar hula, minti minti ta duba wayar da ta barta a gida ta dawo ta tarar babu missed call da text ko daya daga gurinshi, abin da bai taba faruwa ba tun da ya bata wayar, dauko wayar tayi ta hau kan katifar da aka siyo dominta ta fara dannata, tunanin tura mishi text takeyi taji ko lafiya, lallai sabo turken wawa, tayi matukar sabawa da ganin sunan *Arc kangiwa* a cikin inbox dinta, har ta rubuta text din, ta kasa turawa tanata juye juye da wayar a hannunta, karar wayar yasata bude ido da sauri dan ta dauka shi ne, ajiye wayar tayi kirjinta na duka saboda dadin da taji na daukar shi ya kirata, saida wayar ta kusa tsinkewa lokacin ta saisaita kanta tayi saurin ďauka "Kin kwanta ne? "Ummm ta fadi kamar da gaske baccin takeyi, "shikenan ya fadi kamar abin tausayi, dariya tayi tace "idona biyu kana san wani abu ne? "Nidai na gaji.. zan bar gidannan, shikenan ku dan kunci abinci baku damu da nawa cikin ba, ki kwanta kawai ya karashe hade da kashe wayar, yaye abun rufarta tayi ta kalli Husna dake dariya da waya a hannu tace "muje kitchen pls, bata kalleta ba tace "muyi me? irin kallon da Badariyya ke mata yasa ta kasa bawa Husna amsa dan kar ta ambaci sunan Musaddiq ta fada mata bakar da zata hanata bacci, ficewa tayi a dakin ta wuce kitchen, tuwo ta gani guda biyu a cooler Daddy, har ta fara zuba mishi ta tuno baya san tuwo, gas ta kunna ta dafa mishi indomie da fish source din dake fridge, tana gawa ta soya mishi kwai ta kai mishi kan dining, dakinshi ta wuce ta fada mishi abinci na kan dining, da sauri ya tsayar da ita ya dauko coke mai sanyi a fridge dinshi, Zama yace tayi ta tayashi hira, bata mishi musu ba ta zauna, kallonshi takeyi yana cin abin kamar wanda yunwa ta gama cinyeshi, dago ido yayi suka hada ido tayi dariya hade da sunkuyar da kanta kasa, shima dariyar yayi yace "kallona kikeyi ki gama kwashe rahoton yadda nake cin abinci ko, zaki sani, dariya sosai tayi tace "wa zan fadawa in na kwashe, saidai in barshi a cikina duk ranar da na hadu da matar da zaka aura, labarin cikinka zan fara bata, dan in bata kula dashi ba akwai matsala, dariyar shima yayi yace "ai basai kin fada mata ba, day 1 zan fada mata, tayi wasa da komai banda cikina, har saima na jira wani ya fada mata, dariya ta sakeyi, kafin tayi magana taji ya dauki waya shima yana dariyar, "Main man, how far, hope ka kwashe, nasanka da kwashewa, tsaki Hilal yayi yace "Duniya ba gaskiya Musaddiq, kasan na baka labarin Irfan da yake san cutar mahaifinshi, to yau throughout muna tare, saboda naki amincewa da bukatarshi, kuma na rubuta letter zuwa company akan wannan business din fake ne, yau saida guy dinnan ya kusa kasheni, Allah ya taimakeni da Meerah muka tafi, ita ta kira police suka tafi dashi, but alhamdullilah.. anyi bailing shi dan kar Babanshi ya sani amma i promise not to work der again, bana son abun da zai kara hadani da Irfan, nd sai na nemi mahaifinshi na fada mishi irin cutar da suke mishi a companynshi, Ajiye cokali Musaddiq yayi yace "gaskiya gara kabar aiki a gurin, kar yazo da tsautsayi wata rana, dan ma kai ya samu, da su mune ai sai dai mu kusa kashe shi, "gerraut Hilal ya fadi yana dariyar da tunda ya dawo baiyi ta ba, dariya Musaddiq yayi yace "ka fa raina ni, irin girman uban nan ma baka bani, bakomai yaran zamani, sai da safe, sosai Hilal yayi dariya harda kyakyatawa ya kashe wayar dan kar Musaddiq yasa cikinshi ya murda, shiyasa in ya shiga damuwa mutum na farko da yake fara kira Musaddiq ne, dan yakan mantar dashi damuwa, haka shima Musaddiq Hilal yana solving ko wani irin problem dinshi, saidai in bai fada mishi ba, yana gama cin abinci ya kalli Nadeeyah dake kokarin tashi yace "ina zuwa? "Bacci nakeji ta fadi kamar zatayi kuka, "ni kadai zaki bari a parlor, ya fadi yana kwaikwayonta, Murmushi tayi tace "dan Allah kaje ka kwanta kaima, "To miss problem solving, thank u, dariya kawai tayi ta wuce daki, Daddy dake tsaye yana kallonsu daga sama ya wuce daki zuciyarshi cike fal da farin ciki da tunanin Allah yasanya abinda zuciyarshi ta kitsa mishi ya tabbata, hango futurn danshi yayi a tattare da Nadeeyah, ita kadai ce macen da ta dace da yanayin rayuwar dan da ya tashi cikin taron mata cike da rauni kuma a sangarce, badan Hilal dake sanyashi a hanya ba, yasan da Musaddiq ko sanin menene kalmar Namiji bazaiyi ba, Addu'a sosai Daddy yayi na Allah ya tabbatar da tunaninshi kuma ya sanya ta zamo alkhairi a gurin danshi..... Kasar Nigeria, kasar who u knw ba what u knw ba, washe gari tun safe Daddy ya kira abokinshi GMD din NNPC towers dake Abuja, bayan sun gaisa suka dan taba hira, kafin Daddy ya gabatar da bukatarshi Dr Barau ya rigashi da cewa "Musaddiq har yanzu bai gama servn ba? "saura watanni in shaa Allah Daddy ya bashi amsa yana dariya, "okk to ba matsala gobe akwai yara 6 da za'ayi ma interview a *EXXONMOBIL* ka turomin shi sai su hadu su 7, in ya karbi nysc cert dinshi sai a hada a cikin takardunshi, cike da farin ciki Daddy yace "ina ne Exxonmobil kuma? Dariya sosai Dr Barau yayi yace "Nigerian EXXONMOBIL, Oil nd gas company ne, American multinational oil nd gas cooperation, yanzu ake daukar yara, so gara yaran mu su samu tun yanzu, kaga nan gaba sun dade a ciki, lokacin da karfin mu zai tafi sukuma lokacin zasu mike, Fadin irin farin cikin da Daddy ke ciki ba kadan bane, dama kiran da yayi mishi kenan, matakin farko da zai fara sanya Musaddiq zama cikakken mutum shine aiki, in yaga ya fara samun kudinshi na kanshi zai nutsu sosai ya nemo girma ya daura ma kanshi, godiya sosai yayi Dr Barau sannan ya kashe wayar, Mummy dake tsaye da flask a hannu ya fada ma, ita ma cike da farin ciki ta sauka kasa ta kira dukkan yan uwanshi ta fada musu, Raudha dake lagos tasan in ne Exxonmobil, dan haka ta fara koda gurin tana sanyawa Mummy shirin fara nemo mishi mata yar masu kudi ko sarauta, dariyar farin ciki Mummy tayi tace "ba sai kin fada ba, Matar Little dina zata zamo yar gata gaba da baya, yar da iyayenta basa kyashin kashe mata dukkan dukiyarsu, yar da zata ayi aman kudi daga ko wani bangare, biki ne wanda nake shiryashi tun kafin yau, biki ne na garari....... Mrs Tijjani Shattimah...... [01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣8⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *Kaduna, Niger, Abuja, Nasarawa, direct,* wani dan saurayi ke tsaye jikin zungureriyar mota yana busa taba yana fadin sunan garuruwan da zasu, nan aka fara tururuwar shiga motar kowa na fadin inda zashi, cike da hanzari ta karaso gurin motar tana fadin kaduna, kallon motar saurayin yayi yace "Baba motar ta cika saidai Ko zaki hau baya kan kaya,  "karfe nawa wata motar zata zo to,  ta fadi cikin gatsali "keeee yane... kike min magana kamar wani danki, in zaki jira motar karfe shida na yamma ki jira in baki iya jira wareee, Cike da mamakin rashin ganin tsufanta tace "kai da uwarka baku da tsofaffi a gidanku ne, yaran yanzu sun fitsare kafarsu, basa ganin girman na gaba dasu, gaskiya anyi asarar haihuwa wallahi, ta karashe tana kokarin jan jakar gana most go dinta, "tare ta yayi da sauri ya busa ma fuskarta hayaki hade da cewa, wallahi bazan duba tsufanki ba zan yaga miki chuna, zigidir zan miki anan gurin kika sake sako sunan gyatuma ta, A fusace tace "nace kaci uwar ubanka, kaji min dan iskan yaro, ni nan da ka ganni bani da mutunci, zan iya yi maka mummuna illa in baka maida hankalinka ba, "ehhhhh yeeeeeeee, ya saki ihu hade da chukumar jakar Goggo yayi wurgi da ita, nan jakar ta yage  kayan ciki suka firfito, wata katuwar kwalba wacce take nade a zani ta tarwatse ruwan cikin ya bata sauran kullin dake cikin wasu takardu, ďaga hannu yayi zai kai mata mari drivern motar yayi saurin rikeshi, "kyaleta GARO, barta ta shiga bayan boot din ta zauna, kallon Goggo yayi wacce ta tsurawa kayan da ta kwana tara a hanya tana nemansu, wani irin tukuki taji a zuciyarta tayi kukan kura ta kama wuyan Garo, Dagewa yayi iya karfinshi yayi wurgi da ita gefe hade da zaro zarbebiyar wuka mai kyalli, nan take Goggo ta maida hankalinta ta mike tana kukan wayancewa hade da cewa mutanen dake rike Garo "yanzu dan Allah in ba sauyin zamani ba wannan yaron banyi jika na uku dashi ba, "Na sha tara kikayi dani dan mai cin----- toshe mishi baki drivern yayi yace "yi hakuri Garo, nasan laifinta ne, ka barta ta shiga mota mu tafi, maida wukar yayi yana ta muzurai hade da hararar Goggo, sum sum ta wuce tana kallon jakar da ta sha wahala ta kashe makudan kudi dan samo su, "tuno kashedin da bokan yayi mata na ta kula da kayan domin a shekara sau daya ake samun sa'ar samunsu, wasu zafafan hawaye ta share zuciyarta a dagule ta nufi bayan motar inda kayan mutane suke, "tana zama taji kukan talotalo a cikin wani kwali a bayanta, Tagumi ta zuba saboda shiga wani yanayi da tayi, yanzu ya zatayi ta sake samun wannan sa'ar, bazata ta taba bari tayi wata daya da Anni da papy ba tare da ta illata su ba, so takeyi taga bayansu dukkansu, so takeyi ta mallaki zuciyar Baffa da gidanshi baki daya ita kadai kamar yadda tayi a baya, daga ita sai yarta da jikokinta, Tana cikin wannan tunanin mai cike da takaici drivern yace ta bashi kudi, "nawa ne? , jaka goma sha biyu, "jaka har goma sha biyu, abin na sat----- ganin Garo a bayanshi yasata saurin sauya maganar zuwa "abin har yayi sauki haka, fito da lalitarta tayi ta bashi kudin ciff, irin kallon da Garo ke mata yasata saurin sunkuyar da kanta, shaff ta manta da yar posan kudinta a gefe, tana jin motar ta fara tafiya, ta dago kanta, tunane tunane ta shiga yi marasa dadi har bacci yayi gaba da da ita.... Mikakkiyar tafiya sukayi ta tsawon awa 8 saboda ana yi ana tsayawa Sallah  da cin abinci, Suna daidai *kawo* suka fara shelar kowa ya hada kan kayanshi domin yanzu yan kaduna zasu sauka, Goggo da bacci yayi gaba da ita sam bata san sunayi ba, haka drivern baisan kaduna tace ba, da yake yan kadunan basu da yawa ko minti biyar basuyi ba suka daga zuwa garin gaba da zasu, saboda tsabar baccin gajiya ko kuma ince hakki, saida suka kai bus stop din tafiyarsu da Goggo, Nan drivern ya tasheta a gajiye dan bacci yakeji matuka, a firgice ta tashi tana laluben poss dinta tana fadin har munzo Kawo? Wani kawon? drivern ya tambayeta cike da kosawa, "Kawo ta kaduna ďan nan, tsaki yaja yace "dan Allah Baba fito kar in miki rashin kunya, fitowa tayi cikin rashin fahimta tace "ban gane ba, ina ne nan, rufe boot din yayi yace "je ki tambayi wadancan, ya nuna wasu gungun mashaya a gurin ya wuce yana mika hade da wakar dan kwairo ta "mai dakin gabas, Zaman dirshan Goggo tayi a garin da bata san ko ina ne ba, saboda baccin da ta tika idonta ya soye sam bata jin shi, ga muguwar yunwa tana ji, ga bakin cikin satan da akayi mata, Tashar cike take da mashayan da basu da aiki sai na shaye shaye duk minti, mayafinta ta cire tayi matashi dashi, ta rasa yadda zata fassara irin hau din da hauta a wannan rana, saboda tsabar takaici har sambatun bacin rai takeyi, ga tsabar ciwon kai da ya sata a gaba,  Wani mai butar shayi ne ya gifta tayi saurin kwala mishi kira, dawowa yayi da sauri dan a tunaninshi siya zatayi, "sannu ďan albarka, nan wani gari ne dan Allah? "Tashar Akwanga! bakisan a Nasarawa kike ba, wani kululu Goggo taji ya taso mata, nan take hawaye ya wanke fuskarta, da yaron yaga ba siya zatayi ba yayi saurin mikewa ya nufi gurin wadanda suka kirashi, kuka mai hade da majina Goggo tayi shi a daren ranar, maimakon ta saduda tasan hakki ne ya fara dawainiya da ita sai ta kara kullatar bayin Allahn da zata sake ninka zunubbansu akanta.... Motar dake tashi da asuba zuwa kaduna tabi tanata roko su sata ko a sama ne, tana cikin wannan magiyar taji muryar da ko a mafarki taji ta zata ganeta, "Rilwanu ta fadi bakinta kamar gonar auduga, daga ina kake? Nuna mahaifinshi yayi yace daga Benue muke zamu wuce kaduna, wannan Mahaifina ne, kamar yadda na fada miki zan dawo dashi kaduna in nema mishi magani, da yake a cikin duhun subahi ne sai basu samu damar ganin fuskar juna ba, nan dai Goggo ta shiga aljihun kaskastaccen bawan gidanta Rilwanu...... Firgai firgai ta shigo gidan yunwa kamar zata kasheta, a lokacin har masu ginin sunzo, da masu gyara mata daki da masu karasa ginin da ake buga kwano, goge idanuwanta tayi dakyau ta fara dubawa ko ba gidanta ta shigo ba, dakin waje shi ya tabbatar mata da gidan ta shigo, zagaye dakunan tayi hade da fadawa dakinta, wani irin ja baya tayi cikin firgicin rashin ganin ko tsinke a dakinta sai ma hake haken kasa da akeyi ana sa tiles masu kyalli, nan take yunwar da takeji tayi murabus a cikinta ta fara fadin, "uban waya saku fasa min daki, ina kuka kai min kayan daki? Tabdijam, wallahi hukuma ce kadai zata rabani daku, ashariyya ta fara kundumo musu babu kakkautawa, Muryar Papy tajiyo daga tsakar gidan yana sallama, fitowa tayi da sauri har tana tuntunbe, tana fitowa Baffa ya murda kofa ya fito yana amsa sallama, baki ta saki tana kallon yadda muhammadunta ya canza a cikin yan satittikan da ta tafi ta barshi, gaba daya an aske farin gashin dake gemunshi da kanshi, tsufanshi ya boye sai wani annurin kyau da yake fitarwa, Bugaggiyar shadda blue ce a jikinshi sai hula da takalmi masu matukar kyau, ga wani uban kamshin turare da yake fitarwa, duk su biyun ta kalla taga kayan nasu iri daya har dinkin ma, bata kara shan mamaki ba sai da jiyo sallamar Daddy, kallon hanyar shigowar tayi taga ya shigo da danyar gezna ash, bayanshi Musaddiq, Hafeez da Jamal ne suma sunyi kyau sosai, *Zuri'ar Atika* ta fadi a hankali, wata juya ta fara ji wacce ta sanyata yin zaman dirshan, Papy ne ya fara isa gareta yana fadin "subhannallah, Inna lafiya? ina kika tafi har wannan lokacin kika barmu da jimami, bata iya yin magana ba sai kukan takaicin da ya kufce mata, taruwa sukayi akanta harda Baffa suna mata sannu, dan yanayinta na marasa lafiya ne, dakin waje suka shiga da ita Baffa ya tsaya a kanta yana mata tambayoyin inda ta shiga, kureshi da ido tayi alamar tuhuma, ga mamakinta murmushi yayi kamar yaro karami, haibarshi ta lokacin samartaka ta tariyo kanta, shi ma ita din yake kallo amma fa a tsorace yake dan yana tsoron abun da zai canza ra'ayinshi akan auren nan, dan kwanakin da ya jera yana haduwa da Anni yaji tayi matukar kwanta mishi a rai, yana fatan suyi zaman tare har mai rabawa ta raba, "Biki akeyi na ganka da sababbin kaya? yadda ta jefo tambayar sai ta bawa mai kallonta tausayi, "Gyada kai yayi yace "eh bikin Muhammadu da Hanne, agogon bango ya kalla yace "goma daidai za'a daura, yanzu tara da rabi, bari muyi saurin zuwa gurin, akwai kayan abinci a cikin drawer can kiyi kokari kici kafin mu dawo, sai ki fada min inda kika je kuma da izinin wa, *IZINI* Goggo ta maimaita kamar me koyon magana, yana gab da fita tayi karfi da jikinta ta damki babbar rigarshi hade da fadin "wallahi babu inda zaka, kai baka isa ka wulakanta ni ba Muhammadu, ko kunya bakaji, banda jika har tattaba kunni gareka amma dan budurwar zuciya irin taka harda yin anko kai a dole zaka angance, to wallhi saidai in ka kasheni ka ka fita, saboda rashin kuzarin da take ciki yasa shi kwace rigar yace "Raya sunnar ne abin kunya, bazan kasheki ba, kuma aure babu fashi mutuwa ka raba, yana kaiwa nan yasa kai ya fice, "aiko zaku mutu, wallahi tallahi kaji rantsuwar da bata da kaff------ ido cikin idon da sukayi da Daddy ne ya hanata karasa mummunan furucinta, ciki ta juya hawayen ido suka kafe sai na zuci da suka dinga kara kaini, kasa zaune tayi tanata safa da marwa tana tunanin ta inda ta kuskuro har wadannan abubuwan suka cakude mata haka, ga kayan dakinta duk an fitar dasu bare ta samo wasu cikin surkullenta tayi amfani dashi, dakyar ta zauna tana maida numfashi kamar zata mutu...... Foiling naman walima Nadeeyah da Husnah sukeyi a cikin tray suna hira, Mummy na bayansu tana hada coleslaw na dole dan ba yadda zatayi Daddy ya dauki nauyin walimar a gidanshi, suna gamawa suka jere komai a inda ya dace, rissinawa Nadeeyah tayi tace "Mummy akwai wani abun ne? gyada tayi kawai alamar a'a kamar me ciwon baki, Daki suka wuce dan yin wanka, kaya kala daya Papy ya dinka musu harda su Anty Raly, lace ne dark purple mai ratsin manyan pattern pink flower, dinkin riga da skirt mai matukar kyau, ko ina an sanya farin stones wanda ya kara kayata lace din, *Bismid cream* Husna ta dauko tana shafawa tana dariya, wayaga Baffa ango, wallahi ni abun kunya ma yake bani, su Daddy kuma harda wani daurewa karya ...... wai harda walima, dariya Nadeeyah tayi hade da jan zip din rigarta tace "ni kaina abun jinshi nake wani iri, saidai ba yadda za'ayi da hukuncin Allah, Badar sarkin nukufurci tana kwance cikin bargo tana latsa waya bata ma san suna shiri ba, light make up sukayi wanda ya dace da fatarsu, sunyi kyau sosai saboda lace din kalar farare ne, dauri sukayi mai matukar kyau iri daya suka feshe jikinsu da turaruka masu kamshi da saukin karfi, kara wayar Nadeeyah tayi alamar shigowar sako, da sauri ta dauka dan tasan wanda yayi text din, "baya kiranta a waya, amma text duk minti biyar yinsa yakeyi, ko ya rasa abin cewa sai ya nemo write up na yaudarar maza, ko yadda zata kula da kanta, ko adduoi ya tura mata, reply dinta koda kalma daya ce means the world to him, *Yunwaaaaaaaa, plss ku kawo min abinci kar in mutu*..... Dariya sosai tayi dan ganin mai sakon, ta mikawa Husna wayar, itama dariyar tayi tace acici, kinsan yau ya tashi da wuri to fa kowa ya bani a gidannan, flat shoe suka saka suka wuce kitchen, flask Nadeeyah ta dauka da hot chocolate da ta san yafi san karyawa dashi, ita kuma Husnah ta dibi naman kaza cikin pepper din da sukayi foiling, wani sakon ne ya sake shigowa.. *Nadeeyah so kikeyi in mutu ko, ba komai... ya sanyo alamar kuka*  Reply tayi mishi tana murmushi tace *Sorry, kana ina ne* Yana ganin reply din yayi saurin kiranta "ina BQ, yanzu muka dawo, plss kiyi sauri cikina na ta kiran sunanki, yasan ke kadai zaki taimaka, kashe wayar tayi tana dariya suka wuce BQ din, Murda kofar Husna tayi saboda ita ke da rangwamen kaya a hannu, karo tayi da mutum shima ya sako kai zai fito, subhanallah ta fadi hade ja baya tana kallon tray din da ya fadi kasa, kallon shi tayi taga shaddarshi ta baci da source "Ya salam.. Ya Hafeez dan Allah kayi hakuri, wallhy bansan zaka fito ba, Murmushi yayi yace "haba karki damu, da kinsani bazaki shigo ba nasani, ke da gaisuwa ma sai na roka, yaushe zakiso kiyi karo dani, dariya tayi sosai tace "kiji sharri Nadeeyah, bari in duba maka kayan Ya Musaddiq ka canza, "inyi yawo dai a ciki ya fadi yana goge jikinshi hade da kallon Musaddiq da yayi fuskar tausayi, dariya yayi ya kalli Nadeeyah yace "saura kiris a zare ran fa, maza kije ki bashi break fast.. Da sauri ta zare takalmin kafarta ta shiga da sallama tana fadin "sorry pls, rike cikin yayi ya kara bata fuska yace "naki sorryn na koshi, bude flask din tayi ta zuba ruwan zafi ta hada mishi tace "gashi kayi hakuri dan Allah kar a zare ran, in aka zare bamu san inda zamu sa kanmu ba, "Dadi zakuji mana ku huta da acici, sosai sukayi dariya Nadeeyah ta gimtse tata dariyar tace "ai ci dole ne yayana, kowa ma acici ne, gashi kaji, plssssss, ta fadi tana karkace kai gefe, "badan ni zansha ba sai dan tausayin hanjin cikina, Saboda dariya saida Nadeeyah ta durkushe a gurin, "dan Allah karka kashe ni, bari in kawo maka wani abinci me nauyi, kallon Husnah yayi dake kara jaddaddawa Hafeez suje ta bashi kayan shi ya saka, "in kinje ki bashi riga kadai ta isheshi, kinga sai kuji dadin zagin halitta ta, ya karashe yana kai kofin bakinshi, dariyar ma kin fitowa Husnah tayi suka fita tare da Nadeeyah, Dariya Hafeez yayi yace "manta da ita kaji, gida zan koma in canza kaya, bari in kira Jamal ya kawo min mota, ciro key Musaddiq yayi yace "ga tawa kaje ka dawo kafin a fara walimar, karbar keyn yayi yace "ka dai ajiye min nawa abincin kar ka cinye kai kadai, "Haaahaha... zan daina cin abinci kwata kwata a idon mutane, gara in rage wannan kibar, da zan iya ma harda tsawo zan rage, "dariyar Shirmen Musaddiq Hafeez yayi ya fita yana jin dadin yadda al'amura suke kasancewa kamar yadda Mamma take so, Allah sarki Mamma, ina ma ana mutuwa a dawo kiga yadda wuya take neman rikide mana ta zamto dadi, kiga yadda dan uwan da baki sani ba yake gatata mu kamar shi ya tsuguna ya haifemu, Allah yayi miki Rahama ya fadi ya shiga motar zuciyarshi a dagule saboda tuno iyayenshi da yayi....... Ana idar da sallar isha'i su Nadeeyah suka fara shirin barin gurin su Anni, hankalin Nadeeyah a kwance ta gama shiri dan tasan yanzu su Anty Radiya sun bar gidan, "kallon banza da habaicin talauci hade da rashin asali da suke mata yana sosa ranta matuka, kalmar da Anty Raudah ta fadi na "anyi clean fata ta murje da abinci akan kari sai kace wata yar shugaban kasa, a dai dinga tuno asali dan kar garin iyawa a wuce gona da iri!! Wadannan kalamai sun matukar tsaya mata, dan ma Musaddiq dake bayanta wanda dan shi Anty Raudah tayi mata habaicin yace "Haba Anty, sai kace sa'arki, dani take magana bada ke ba, ku ke jawa kanku raini wallahi, yayi tsaki a hankali hade da cewa Nadeeyah ta kira Husnah su tafi... Hannu ya kyasta mata a kusa da idonta, a firgice ta dawo daga tunanin abubuwan da suka gifta dazu a gidan, rage Murya yayi yace "Tunanin su Anty ko? Abin da ya kamata ki saba dashi ne tunda saidai in basu zo gidan ba, in kika kula mutum a kullum burin shi ya bata miki rai to sai kiyi fatali da duk abin da yace, domin shi kadai zaiyi dakon bacin ransa, "Zuciya is very special my sister, fill it with love, karki bari bacin rai ya samu kofar shiga cikinta, dan bacin rai na destroying duk abin da aka tanadarwa zuciya, dan haka bana san ganin tunani ko bacin rai nan a tare dake, kinji ko? gyada kai tayi hade da murmushinta mai kyau, "Thats my lovely sis, oya kira mana Husnah mu tafi, kafin ta kai ga amsawa suka hango Husnah sun fito tare da Hafeez da Ruwaidah a tsakiya, gefe kuma Jamal ne sanye da kayan bacci shima yana dosar inda suke,  "Badai bacci zakayi ba, Musaddiq ya tambayeshi yana mishi kallon mamaki, jingina jikin motar yayi yace "in banyi bacci ba ai sai in kasa moruwa, yau ko tamola bata kaini garuwa ba, wahalar da Baffa ya bani yau ba kadan bace, "duk wani abokinshi da yazo gurin daurin aure wanda baida mota saida na maidashi gida, just imagine kaine, hmmm thank Goodness akwai ruwan zafi, da yau sai na tashi aiki, ya karashe yana danna bayanshi, "Lazy youth!! Ruwaidah ta fadi tana boyewa a bayan Hafeez, dariya ta basu dukkansu Nadeeyah tace "duk kokarin nan da yayi ki kirashi lazy, murya cakwai tace "Allah Adda he is very lazy and he can exaggerate, yanzu haka gida uku yaje, haka Mami ke fama dashi baya san a moreshi, Rai a bace Jamal yayi inda take yana fadin "ni sa'anki, wani irin ihu ta saki hade da rugawa ciki, bayanta yabi da gudu dan yaci alwashin ko a gaban Papy ne sai ya gurji bakinta, Dariya Hafeez yayi yace ku shiga mota ku tafi dare nayi, indai su Jamal ne kullum sai sunyi sau ba adadi, ya kasa gane dadin tsokanarshi takeyi, saboda bata da abokin wasa shiyasa ta maidashi abokin wasanta, shi kuma san girma yasa baya wasa da ita, " haushin hakan yasa ta rainashi sosai, motar suka bude suka shiga suna dariyar Ruwaidah da Jamal, Sallama sukayi ma Hafeez da kunya ta hanashi katabus saboda irin kallon da Husnah take mishi,  dalilin da yasa ya sanya Ruwaida a tsakaninsu kenan da ya fito yi musu rakiya, ko a da lokacin da yayi wauta da rudin kudi mata ke kawo kansu, ita kuwa Husnah ganin irin gidan da ta fito ya sanyashi jin kunyarta da taka tsantsan, dan yasan tafi karfinshi, shi da bashi da cikakken asali kamar yadda Goggo ke yawan fada, wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, gara ya nemi saffa saffa dai dai shi.... Mrs Tijjani Shattimah...... [01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣0⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Kasa tabuka komai Nadeeyah tayi ta dauki wayarta ta latsa number Hilal, sai tayi kamar zata shiga sai tayi saurin kashewà, tun daren jiya take abu daya, tasan yadda ya saba da yi mata text haka nan bazai ki turowa ba sai da dalili, Abin da bata sani ba shine, duk latsin da zatayi ma numbershi tana shiga kadan sai ta katse, da haka ya fahimci ta damu da rashin tura mata sakon wanda yayi shi domin fahimtar wani abu daga gareta, Yana gama shiryawa ya dauki wayar ya latso ta, ajiye kwan da take kadawa tayi da sauri ta dauka ringing na farko, "ajiyar Zuciya yayi a hankali, ita din ma hakan tayi amma nata ya dan fito kadan, shuru ne ya ratsa wayar na yan sakwanni, shi ya fara katse shurun ta hanyar cewa "ina kwana Anty, saura kiris wayar ta fado a hannunta tayi saurin riketa tace "kayi Hakuri, ina kwana, "a'a ai ni ya kamata in fara gaisuwar, kina nan lafiya? bata amsa ba ta sake cewa "ina kwana, yasu Anty? dariya yayi mara sauti yace "kowa lafiya, "harda k--- shuru tayi ta kasa karasawa, "Harda ni Nadeeyah, lafiyata kalau, alhamdulillah ta fadi a zuciyarta, a fili kuma tace "to Masha Allah, gyara tsayuwarshi yayi yace "jiya kuma bakiga sakona ba, ke kuma baki damu ki turo ba, shikenan da mutuwa nayi haka zaki manta dani bare har in sa ran addu'a, cikin rawar Muryar da take nuni da alamun tayi matukar missing sakonnin shi tace "Dan Allah kayi hakuri, na rubuta sai na kasa turowa, "ehen me kika rubuta? fada min da baki, toshe bakin tayi da hannu taki sakinshi dan bata san abun da zata ce mishi ba, tana jiyo Muryar Hinad na cewa "Papa na kiranka, muryarshi taji bayan fitar Hinad yace "ina jiran ganin sakon irin na jiya sakk, zan gane rubutun na jiya da na yau, sai na jiki ya karashe hade da kashe wayar ya sauka kasa gurin Papa.... ******* Karfe goma na dare Mummy ta shigo dakin su Nadeeyah bayan ta gama kashe kayan kallon parlon, kallon Nadeeyah tayi wacce ke zaune da blue riga da wando na bacci, tasan Nadeeyah ce kadai a gidan zata iya yi mata aikin tashin asuba, "Nadeeyah, dan Allah da asuba ki tashi Musaddiq, ki hada mishi break fast dan jirgin 6 zai bi zuwa abuja, Yaye bargo Badariyyah tayi da sauri tace "zan tasheshi Mummy, "a'a Badar kar kisa ya makara, 9 ake son ganinsu, "Allah Mummy zan sa alarm ta fadi tana hararar Nadeeyah, to shikenan Allah ya kaimu, dan Allah kar ki bari ya makara, "karki damu Mummy ta fadi hade da dauko wayarta ta sanya alarm karfe biyar da rabi dan tsabar kwancewar noti, yaushe har ya tashi yayi wanka ya ci abinci, al'amuran Musaddiq lokaci suke bukata, mutumin da sai afi awa ana tashinshi a bacci, Badar kuwa cike da murnar zata kasance da abin kaunarta ta ja bargo ta rufe kanta.... Karfe hudu saura Nadeeyah ta tashi, kallon yadda Badariyya ke bacci ba tare da motsi ba tayi, a zuciyarta tana tsoron tashinta kar ta jama kanta zagi, "dakyar ta fara tashinta tana fada mata lokaci yayi, inaaaa Badar bacci yaci karfinta ta juya ta cigaba da baccinta, Hudu da yan mintuna Nadeeyah ta fita dan tasan in dai aka biyewa Badar tofa babu abin da zai hana Musaddiq kaiwa tara a gidannan, Murda kofar dakinshi tayi taji karar alarm a gefenshi amma ko gezau baiyi ba, karasawa tayi tana murmushi ta dauki wayar ta kara mishi karan a kunne, "ummmmmm kawai ya fàdi hade da toshe kunnenshi da pillow, ajiye wayar tayi a kan gadon ta yaye bargon jikinshi ta fara zare pillon, kara kankame pillon yayi yana sambatun dadin bacci, dan a wannan lokacin wani irin rarrashi shaidan yakeyi ma mutum mai sanya bacci dadi, babu lokacin da yakai karshen dare dadin bacci, dakyar ta iya fisge pillon wanda hakan yayi sanadiyar fadawanta jikinshi da karfi, cikin bacci ya kankameta ba tare da yasan yayi ba, kici kicin kwace kanta ta shiga yi wanda hakan yaki yuwuwa saboda girma da tsawon Musaddiq, gaba daya jinta tayi kamar wata babyn roba a jikinshi saboda tsabar kankantar da ta mishi, ganin ta kasa kwatar kanta ya sata sanya hannu a hancinshi ta toshe, tasan dole ya bude ido saboda babu hanyar numfashi, wani irin numfashi ya saki ta baki hade da bude idonshi ya sanya su cikin nata, kara runtsesu yayi dan ya dauka duk cikin mafarkin da yakeyi ne, yana kara rufesu ta kara rufe hancin, bude idon yayi gaba daya kamar zaiyi kuka yace "menene? dariya tayi maganarshi ta mantar da ita a inda take tace "ka tashi karfe shida har da rabi, ga Daddy can ya je dauko bulala, *Haka Mummy ke ce mishi in yaki tashi ya tafi makaranta*, Husnah ta bata labarin jiya kafin su kwanta, "uhmmm ni zan kara minti biyar ya fadi yana sake runtse idonshi, "Hello Daddy yaki tashi wai bazai je inter----- da sauri ya mike har yana bige mata hannu, dariya ta saki tace " kayi sauri kayi wanka, lokaci ya kusa, bari inyi saurin hada maka break fast, bayi ya fada yana lumshe ido kamar zaiyi kuka, daurewa yayi ya shiga shower ya wanke jikinshi tass, A bayin ya shafa mai bayan yayi alwala, saida ya idar da Sallah ya shirya cikin kananan kaya masu kyau cool colour, dakin ta kawo mishi kayan kari lokacin biyar da minti goma, "Bana karyawa da wuri, dan Allah ki maida, in naje can zanci abinci, "noo gara kaci tun yanzu in kaje can babu time, hada mishi tea tayi ta bashi bread guda biyu ta mika mishi plate din kwai, ka canza wadannan kayan, kai da zaka shiga cikin manyan mutane sai a ganka kamar area boy, "dauko min wasu kawai ya fadi yana mai jin kuncin tashi daga daddadan baccin da yakeyi, Drawershi ta bude tana dariya ta fito da golden brown shadda mai kyau da yauki, yana gama karyawa ta fita tabarshi, kayan jikinshi ya canza hade da feshe su da turare, milk takalmi yasaka sannan ya ratayo jakar takardunshi da laptop dinshi ya fito parlon, "ina hular fa? ta tambaya tana karasowa inda yake da leda a hannunta, shi yama manta da wata hula yace "ta dauko mishi, "gefen jakar hannunshi ta bude ta saka ledar hannunta, taba gurin yayi yace "meye wannan? "zaka gode min in kaje can, karka bude, zama yayi akan kujera yana jiran ta kawo mishi hular, Hular data dace da kayan ta dauko ta mika mishi, kanshi ya miko mata a cewarshi bashi da karfin daga hannu, gyara karin hular tayi ta sanya mishi ita akai, yayi kyau matuka kamar wani babban mutum mai cike da haiba da kwarjini, sakkowa Daddy yayi yana dariya yace "Saaaadiq ne yau da tashin asuba, baki ya turo gaba yace bakai kasa ta dameni ba, dariya Nadeeyah tayi ta tsuguna tace "ina kwana Daddy, "lafiya kalau yar albarka, kin samu ladan yayanki, Allah ya biyaki, murmushi tayi taja da baya ta barsu suna zantawa, kudi masu yawa Daddy ya bashi sannan yayi mishi fatan alkhairi, "har bakin mota Nadeeyah ta rakashi da addu'a sannan ta fada mishi in zai shiga ya karanta suratun Nasr kafa uku, Har Malam Ali ya tada motar tayi saurin cewa ka kira Mummy da Daddy lokacin da zaka shiga gurin, adduarsu mai karfi ce a gareka, gyada kai yayi yana murmushi ya daga mata hannu, itama hannun ta daga mishi tana fadin Allah ya bada sa'a, saida motar ta fita a gate din sannan ta koma ciki ta gyaro mishi dakinshi da kyau, lokacin biyar harda minti arbain, Dakinsu ta shiga ta ji karar alarm din Badar, tana hangenta tayi tsaki ta kashe wayar gaba daya, samm baccin asara yasata ta mance abin da kudiri niyyar yi, " bayi Nadeeyah ta shiga tayi wanka ta canza pad saboda tana hutun sallah, komawa tayi ta kwanta tana sauraron karatun qu'rani har bacci yayi gaba da ita, Badar bata tashi ba sai karfe tara da minti ashirin, da sauri ta duro a gado tana fadin "na shiga uku, kallon agogo tayi taga lokaci, jiki na rawa ta fito parlor taga ba kowa, dakin Musaddiq ta fada ta ganshi a gyare kamshi mai dadi hade da sanyi na tashi a ciki, tsaki taja mai nuni da tsanar irin lalurar baccin dake dawainiya da ita....... Karfe takwas na safiyar ranar Papy da iyalanshi sukayi shirin komawa Gombe, gidan Baffa suka wuce dan suyi Sallama dashi, A kofar gida suka tadda shi yana gaisawa da makota, fara'arshi ce ta karu da ya hangosu, Suna karasowa ya gabatar musu da danshi, jikokinshi, da amaryarshi, Gaisawa sukayi da su, Alh Jogana ya kalli Hafeez yace "wannan ba sai an fada min ba, dan marigayi Adamu buzu ne, kamanin sun nuna kansu, dariya Baffa yayi yace "kwarai kuwa babban danshi ne, Allah sarki... Alh Jogana ya fadi cike da tausayi, har yanzu dai ba'a samu labarin danginsa ba, mutumin kirki, ko yaushe na tambayeshi sai yace min daga Agadez yake, amma sunan garin da yake a agadez ya bace mishi, ba mamaki maraya ne, Allah yayi musu rahama, Ameen... dukka mutanen gurin suka ce sannan Baffa ya sallamesu ya shige gida, Wata sabuwar gaisuwa suka sake yi Baffa yace "Har kun shirya tafiya, "eh Papy yace hade da fito makudan kudi a aljihunshi ya bashi yace koda za'a bukaci wasu abubuwan, ya cigaba da cewa "na biya kudin furnitures a *landninterior* Raliya zata kawo matar tazo taga taga yanayin girman kayan da zasuyi, receipt din na gurinta, "dan Allah duk abin da ake bukata a kirani, in shaa Allah ana gama komai zansa ranar da zamu kawo Anni itama tazo tayi zamanta a gidan babana, ya karashe yana dariyar ganin fuskar Anni, Godiya sosai Baffa yayi mishi hade da sa albarka, "Ina Goggon take? Anni ta fadi tana mikewa dan taje su gaisa, rakata Baffa yayi yace "tana ciki babu lafiya, jiya saida wata nurse a makota tazo ta kara mata ruwa, mikewa sukayi gaba dayansu suka shiga dakin da Goggon take kwance tana kallon sama, koda suka shigo bata waigo ta kallesu ba saboda kar ta karawa kanta bakin ciki, har suka karaci yi mata sannu bata ce musu ta tafasa ba, dan tasan yadda takejin tashin kamshinsu in ta kallesu zuciyarta na iya fashewa, "Tana jiyo Baffa a tsakar gida yana fadin "zafin ciwo ne, haka takeyi in bata da lafiya, har bakin mota ya rakasu yana godiya hade da sa musu Albarka...... Cikin yaran shida uku yayan kusoshin gwamnati ne, uku kuma kannen matar GMD ne, interview din da za'a yi musu ma duk sun dauka camouflage ne, dan a ganinsu matsayin iyayensu ya wuce su tsaya yin wani interview, shiyasa basu damu ba sam, lift suka hau aka nuna musu hanyar office din GMD, Hira sukeyi sosai saboda sanayyarsu da juna, shidai Musaddiq Addu'a yayi tayi kamar yadda Nadeeyah ta fada mishi, suna gab da shiga office din wata mace ta dakatar dasu, basu samu ganin GMD din ba saboda yana cikin meeting, yadai bari ayi musu interview din, Abin da yaran basu sani ba shine ba yan Nigeria bane zasuyi musu interview din, samun aiki a irin gurin ba sanayya bane, dace ne da kuma kwazo, Da ďan kanwar matar GMD *Zubair Ribeh* aka fara, yana shiga gabanshi ya fadi saboda irin mutanen da ya gani a gurin, takardunshi suka bukaci ya miko musu, nan ya mika musu a mutunce, dubawa sukayi sam basu damu da ganin takarddun Nysc dinshi ba, second class lower gareshi a *Bsc Chemistry* , tunda daga nan suka rufe takardunshi suka tambayeshi abubuwan da ya kamata, yayi iya kokarinshi ya basu amsa har jikinshi ya jike sharkaff, sallamarshi sukayi hade da tafa mishi dan yayi iya kokarin yake da dashi, haka ce ta kasance da sauran yaran, mai first class din cikinsu da suke da hope akanshi shima ya kasa amsa wasu abubuwan, sarewa sukayi har suka fara tunanin daukar *Zubair* dan shi kam result dinshi ya nuna kwakwalwarshi ce ta bashi, sauran kuwa duk siyan musu akayi, shigowar Musaddiq ne ya katse musu tattaunawarsu, da fari sun ki yi mishi dan ganin mutane shida kadai suka nema, babban cikinsu ne yace abashi chance may be su sameshi da abubuwan da sukeso, takardunshi suka bukaci gani, yayi saurin fitowa dashi, ledar da Nadeeyah ta bashi ce ta fado kasa, da sauri ya dauketa hade da mika musu takardun cike da girmamawa, Juya ledar yayi yana murmushi shi kadai, nan take kalamanta suka shiga yi mishi yawo a kai, baiyi wata wata ba ya fito da wayarshi, kasa kasa ya sa wayar ya tura ma Mummy da Daddy text din su tayashi addu'a yana cikin gurin, har zai mayar da wayar aljihu yaji karar shigowar text, dubawa yayi hade da murmushin ganin sakon Nadeeyah, kamar tasan yana bukatar irin wannan adduar a wannan lokacin, maida wayar aljihu yayi ya dago kai ya kallesu, Saida ya kusa kaiwa kasa saboda yadda suka zuba mishi ido, "am very sorry pls, ya fadi dan yasan laifinshi, cike da bacin ran rainuwar yan nigeria wata mata tace "nan gurin wasan yara ne, in ba aiki kazo nema ba, chatting kazo yi ka fita dan babu wanda ya zai matsa maka,, kartawa cikinshi yayi ya fara basu hakuri cikin harshen turanci yace "ina bukatar addu'ar iyayena, domin addu'a ita kadai ce zata samar min wannan aikin, shiyasa na tura musu sakwanni saboda su tayani addu'ar samun aikin, jikinsu ne ya mutu duk sukayi sanyi suka maida fushin da suke da niyyar sauke mishi, tambayoyi suka shiga yi mishi akan yadda ya kamata a sarrafa gas da karafan gas, da yake I.T din da yayi a cyprus a companyn gas yayi shi, nan ya basu gamsashiyar amsa mai cike da ilimi, Saboda tsabar burgesu da yayi basu san suna jefo mishi wasu tambayayoyin ba, kaca kaca suka fada da lamarin Musaddiq, ko amsa zai basu saiya russuna, duk inda bature yake yana matukar san girmamawa, nan take suka mike suna tafa mishi hade da jinjina mishi, wata takarda mace tayi signing tace "congratulations my dear, ta mika mishi takardar, har kasa ya tsuguna ya karba hade da sujjadar godiya ga ubangiji, sunan *Zubair* suka kira shima ya shigo da saurin shi, takardar shima suka mika mishi ya hau musu godiya hade da kukan murna, rasa inda zai kai murnar da yake ciki yayi dan yasan yau mahaifiyarshi bazatayi bacci ba saboda murna, Allah ya taimakeshi, yanzu zai tallafi yan uwanshi da mahaifinshi..... Sauran yaran basu damu ba saboda dama aikin ba damunsu yayi ba, iyayen keson gina su saboda gaba, Sosai Dr Barau yayi murnar ganin Zubair yaci, sam matarshi bata da masaniyar ya amshi takardun yaron, kannenta wadanda suke ciki daya ta bada takardunsu ta zame na Zubair, da yake Allah shine ke taimakon bawa, gashi Allah ya bashi sauran kannenta basu samu ba, Allah kenan mai kyauta a gurin wanda yaso a lokacin da yaso, Hotel ya kamawa Musaddiq bayan ya gama ture turen takardun su ta computer zuwa lagos, kwanciya yayi yana mika saboda gajiya, ga yunwar da ta addabeshi, wanka ya shiga dakyar saboda tsabar gajiya, bai taba irin yawon da yayi yau ba, duk block din cikin Towers saida suka kewaye shi, da ruwan zafi sosai yayi wanka hade da alwala, yana idar da sallah ya janyo jakarshi, ledar da Nadeeyah ta bashi ya fara karo dashi, da sauri ya bude, naman da suka soya na walima wanda aka basu suka ajiye cikin microwave shi ta dumama mishi tayi foiling tasa a leda, zafi har yasa naman ya fara nakewa, zai fara ci kenan yaji an buga kofar dakin shi, abinci ne aka kawo mishi wanda ya tabbatar zaiyi wuya ya iya cin shi, karba yayi hade da mishi godiya, ajiyewa yayi ya fara juya salad din, da sauri ya ajiye cokalin ya dauki juice din dake kai, Naman kadai yaci ya hada tea, yana idar da Sallar isha'i ya janyo wayarshi da ya soka ta a charge, 23missed calls ya gani ya fara dubawa, na Daddy da Mummy ne a sama sai Hilal, Badar, Nadeeyah da Husnah, Daddy ya fara kira sukayi murnarsu sosai sannan ya mikawa Mummy wayar itama tayi murna sosai hade da yi mishi adduo,i, cike da murna sukayi Sallama ya kira Hilal, Sunfi minti goma suna hira yana mishi fada akan ya dauki aikinshi serious, "banda baccin asara dan nasanka, baka cika daukar abu serious ba, dariya Musaddiq yayi yace "yau ma dakyar na tashi, saida Nadeeyah toshe min kunne ta kusa kasheni, yarinyar nan bata jin magana, but ta kyauta fa, gashi Allah yasa nazo akan lokaci kuma na samu nasara, saida Hilal ya danji abun a ranshi, kauda mugun tunanin da shaidan ya kawata mishi yayi saurin yi hade da cigaba da hirarsu.... Game yakeyi yana juyi akan gado bacci na dan fisgarshi kadan kadan, karar wayarshi ce ta sa ya watstsake ya dauka, "congrat yayana, Husnah ta fadi da karfi har saida ya cire wayar a kunne, "Thanks sis, baku kwanta ba?, "10 fa yaya, har ka fara bacci ne? Juyi yayi yace "ummm na fara, to ga Nadeeyah ku gaisa ta mika mata wayar da sauri, "Congratulations, Allah yasa ka fara sa'a, ya kaika matakai masu daraja a cikin aikinka, Sosai yaji dadin da ya rasa ko na meye, dadin jin muryarta da yayi ko kuma na adduoin da ta jero mishi, Ameenn My PS, ya fadi ya lumshe ido, Dariya tayi tace shi PS din meye shi? "Problem solver, nayi missing dinki sosai, furta kalmar yayi cikin gushewar hankalin mai bacci, bude idonshi yayi yace "naman da kika san min ya taimakeni, wani abinci suka bani kamar tsutsa, na kasa ci, Murmushi tayi mai sauti tace "haka nan zaka koya, aiki fa zaka fara, dole ka koyi cin abincin waje tunda ba'a gida bane, da haka zaka saba, Shuru yayi yana jin muryarta na ratsa ko ina na jikinshi, saboda tsabar dadin murayarta da yakeji har bacci mai cike da mafarkai ya daukeshi ba tare da ya sani ba...... Washe gari Dr Barau yace su shirya tafiya lagos, badan yana so ba haka ya daure suka tafi, A can ya sai kayyaki dan sun ma fada mishi tafiyar kwana bakwai ce, wahala iya wahala babu irin wace Musaddiq bai sha ba, nuna musu abubuwa akeyi ana koya musu yadda zasuyi ayyukansu, kwanansu takwas cirr suka dawo gida dauke da takardunsu na offer da komai nasu na accomodatio, wardrobe money da sauransu, tun a jirgi Musaddiq ke kiran wayar kowa a gidan bata shiga, dakyar ya samu number Malam Ali yace ya fada musu yana hanyar dawowa sannan yazo airport ya daukeshi....... Wurgar da komai nashi yayi a parlor ya nufi kitchen saboda muguwar yunwar da yake ji, a tsaye ya tadda ita tana goge gas tana bitar haddar da zata bayar, a hankali ya karaso inda take ya sanya yatsunshi daya cikin kunnenta, wani irin ihu ta saki wanda ya sanyashi toshe mata baki yana kyakyata dariya, rankwafowa yayi daidai kunnenta saboda gajertan da tayi a gabanshi yace "matsoraciya, irin wannan ihun ai sai ki firgita mutane, me kika dafa min? "Ayya bansan zaka dawo ba ai, kayi hakuri bari in tuka maka tuwo, kaje ka huta awa biyu ya isa, "In na kara minti talatin a duniya ki godewa Allah, kawai kice kaje ka kashe kanka, dan Allah ki daina wasa, Dariya sosai tayi ta fitar mishi da cooler shinkafa da miya da salad, kamar mayuwancin zaki ya fara cin abincin da ya dade baici irinshi ba, saida yaci yayi katt sannan ya fara dawowa cikin hayyacinshi, Dakinshi da ya shiga ne ya sake sanya nutsuwa a tattare dashi saboda irin gyaran da Nadeeyah tayi mishi, da takalmin kafarshi ya mike a gadon ya fara kwasar bacci hankali Kwance..... *TUN RAN GINI* Mrs Tijjani Shattimah...... [01/04 9:50 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣1⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *EMIR PALACE SASSOUN BOROUM* Sarkin sassoun boroum ne tsugune a gaban sarki "TIDJANI YALLO" yana mika gaisuwa kamar yadda sarakuna keyi wa na gaba dasu, bayan sun gama gaisawa aka cika kayayyakin abinci da sha a gabansu saboda girmamawa, babu abinda Sarki Tidjani da Shareefah suka kalla, bare har su kai ga cin shi, cikin nutsuwa da kasaita suka gabatar da dalilin zuwansu, nan da nan aka wakilta dogarai dan suje can rugar Haldo su nemo Hajja yar Ruga su taho da ita, da yake rugar bata da nisa da gidan sarki sai gasu sun dawo, cikin girmamawa suka ce bata da lafiyar da zata iya zuwa, daka musu tsawa sarkin sassoun burum yayi yace "maza su koma su dauko ta, dakatar dasu Shareefah tayi hade da mikewa tace "su barta kawai, su zasu isa zuwa gidanta, Duk yadda sarkin sassoun burum yaso nuna musu kaskancin zuwa rugar Haldo hakan bai hanasu zuwa ba, a cewarsu su suke nema a gurin ta, ya zame musu dole su ganta yau kota halin kaka..... Wani irin wari dakin Hajja ke fitarwa, warin ma marar misaltuwa, tana kwance a kan tabarmar da takai rabi saboda cinyewa, dakyar aka iya dagota ta jingina da wani sudadden pillow, "wani dan kara tayi saboda wani ciwo da yayi mata rami a mazaunanta, yaron dake kula da ita ne ya sa mata wani pillow a gurin ciwon, saboda tausayin halin da Hajja ke ciki ya sanya Shareefah sharar kwalla, Dakyar muryar Hajja ta iya fita tace "sannunku da zuwa, da kai suka amsa hade da gyara zama akan daddumar da dogarai suka shimfida musu, saboda son jin abun da ya kawosu ko kyankyamin dakin basu ji ba, "Daga ina ranka ya dade? Hajja ta fadi baki na rawa, Shareefah ce ta fada mata sunanta da dalilin da yasa suka zo gurinta, bude ido Hajja tayi sosai ta kure shareefa da ido, *SHAREEFAH YALLO* kece? murmushi Shareefah tayi tace "nice, ashe ma kin sanni, kuka Hajja ta fashe dashi tace "farin sani, ni na raineki tun kina tsumma, nafi shekara ashirin a gidanku tun kafin a haifeki, ashe zan sake ganinki, rabona da ke inaga in banyi karya ba yakai shekara arbain, dan tun kina shekara goma sha biyu na bar agadez, ashe ina da rabon sake ganinki ta karashe da kuka hade da tari, Cike da kosawa sarki Tidjani yace "sai hakuri Baba, dama haka rayuwa take, kuma duniya fadi gareta, wata rana in da rai dole a hadu, yanzu gashi sanadiyar mutuwar UMMU AYYU Allah ya kawo mu gurinki, yanzu bamu da isashen lokaci zuwa mukayi ki fada mana labarin da Ummu tace ke kadai ce kika san dashi, labarin YARIMA, wani kukan ne ya kufcewa Hajja a zuciyarta tace "yau labarin da yayi shekara da shekaru a kunshe, hali yasa zata bayyana shi, labarin da ya zame mata tamkar kwai a cikin zuciyarta saboda riritarshi, ajiyar zuciya tayi tace "babu mamaki fitar labarin nan ya zama silar samun warakarta, Nuni tayi ma yaron dake kula da ita wani gurin dake cike da kaya, mikewa yayi ya dauko wata jakar saka ya mika mata, hannu na rawa ta karbi jakar ta dauko wani ginin mutum mutumi wanda yake kewaye da kawunan mutane babu adadi, Saboda tsananin tsorata saida shareefah ta rungumi kafardar mijinta, abun ba karamin tsoro ya bata ba kuma ya daga tsigar jikinta matuka, yadda aka yanyame shi da wasu abubuwa kamar kwari yasanya har sarki jin tsoro amma kadan, wani guri ta daga a gefenta, inda take ajiyar abubuwa, nan ta mike dayar ruwa nabin bayanta ta fita tsakar gidan ta daki wani dakali dake kofar dakinta, nan take gurin yayi rami, hannu tasa ta ciro layu masu tarin yawa, daga can kasa ta hango kurciyar da suka binne shekara da shekaru kwance babu rai ga layu kewaye da ita, a gigice ta ciro kurciyar da duk wata sai ta bata ruwa ta mayar ta rufe, tun da ta kwanta ciwo kusan watanni takwas bata kara bi takanta ba domin itama ba lafiyar gareta ba, girgiza kurciyar tayi tana kuka tana fadin *YARIMA ADAMU* wayyo Allah Kunzo a kurarren lokaci, nasan duk inda Yareema yake a yanzu to kasa ta rufe idonshi, wannan kurciyar rayuwar Yareema ce, Allah na tuba, wayyo ni Allah, haka ta dinga fadi hankali tashe, Da karfi ta saki mutum mutumin hanunta ya tarwatse a tsakar gidan, nan tabi kowane kai ta cire dabaibaiyin da aka mishi, runtse ido Sarki Tidjani yayi saboda juyawa da yaji kanshi nayi, dakyar Shareefah ta tallabe shi ya zauna a kasa ba tare da duban dattin gurin ba, itama hakan ce ta kasance da ita, saidai ita ta kasa fahimtar komai, sabanin Sarki Tidjani da komai ya shiga yawo a kanshi, yadda abubuwa suka faru ya dinga tunowa kamar yanzu ake yinsu, kusa dasu Hajja taje dan itama wani karfi taji a jikinta, burinta ta sanar dasu komai da suka sani da wanda basu da masaniya... "Nasan yanzu wasu abubuwan sun fara dawowa a kanku da kuma daukacin mutanen da suka san Yareema a Agadez, to saidai abin da baku sani ba shine dalilin da yasa ya kaurace muku ya tafi can wani guri inda babu wanda zai ganshi bare har yasa shi waiwayen gida, "Adamu Yallo... sarki ya dinga maimaitawa a bakinshi, fuskarshi yake kallo kamar yanzu suka rabu cikin lambun *Shehrah Agadez*, ina dan uwanshi ya tafi har tsawon wannan lokacin, yana kallon fitarshi daga lambun lokacin bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa kiranshi bare har ya tambayeshi inda zashi, sai yau yaji tunanin ya dawo sabo dal game dashi, Da sauri ya maida idonshi kan Hajja yace "ina Adamu? Me ya sami Adamu? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me ya shiga kaina har na manta da dan uwa kuma aminina, Ya salam ya fadi hade da dafe kai.. "Ba laifinka bane Yallabai, Laifin namu ne, bakai ba ma kowa a garin Agadez a yau sai ya tambayin dalilin da yasa ya manta da Yareeman da suke matukar so fiye da sarkin Kanshi... har ke ma Shareefah, a karancin shekarunki zaki iya tunawa da *Yeeman ki* , *Yeeman Pappalinto* nan take mafarkinta ya dawo mata sabo, sunan Yeema take yawan fadi cikin mafarkinta, wani irin kuka ne ya kufce ma Shareefah ta dinga nanata sunan a ranta, tabbas ta tuno kuruciyarsu saboda mafarkinta bai rage mata komai ba, cikin kuka tace "Bani labarin Yeema nah! Bani labarin dalilin da yasa yayi nesa dani..... *TUNA BAYA.......* ********** Ranki ya dade kici abinci dan Allah, rashin cin abinci zai iya zame miki illa, kuma kin sani sarki bazai fasa abun da yayi niyya ba, cikin Kuka Fulani Ayyu tace "Hajjara yanzu anyi min adalci, ace sarki ya rasa da wacce zai hadani sai da *Kuyanga Rosalin* , kuyangar da na bawa yarda tasan sirrina fiye da kowa, tayaya zan iya kallon mutanen gari, wannan ai cin mutunci ne a gareni da masarauta baki daya, Gabanta Jakadiyya Hajjara ta dawo tace "ki kwantar da hankalinki, ki barshi yayi auren, zamu san yadda zamuyi da ita, da kalamai masu dadi Hajjara ta kwantar mata hankali har taci abinci.... Wata hudu bayan auren *sarki Abdallah Yallo* da Kuyangarshi mai kula da komai na alamuranshi *Rosalin Mujdaha* mahaifinta shine mai bawa sarki kariya, bayan rasuwar mahaifiyarta mahaifinta ya bawa sarki ita domin ta zama mai aikinsu ta jikinsu wacce zata kula dasu, garin binciken shi na rashin haihuwa Rosalin ta fado ciki har malaminshi ya fada mishi alherin da ke tattare da aurenta, bai damu da kalubalen da ya fuskanta daga yan uwa da matarshi ba aka sanya rana, har Allah yasa ta zamo matarshi, kyakykyawar gaske ce doguwa sambal, ga biyayya da hakuri, hakan yasa yake matukar kaunarta, babu irin asirin da Fulani Ayyu batayi ba dan taga bayanta amma Allah cikin ikonsa duk ta tsallake, saboda tsoron Fulani da Rosalin keyi hakan yasa bata fita ko nan da can, duk abin da zai hadasu tana neman hanyar kaucewa saboda bata san tashin hankali, mugun hakuri gareta ga kawaici da sanin ya kamata, Babu wanda keda masaniyar tana dauke da ciki domin tsakaninta da bayinta yar kallon fuska ce, ko mikewa a gabansu batayi, A ranar da cikinta ya cika wata tara ranar akayi haihuwa a gidan, wazirin sarki wanda ya zamo kani ga sarki, a gurin barka ne kowa ya fahimci ciki gareta, ranar Fulani mutuwa ne kadai batayi ba, gaba daya kansu ya kulle ita da Hajjara suka rasa ta inda zata bullowa al'amarin.. Ranar suna Yaro yaci sunan *TIDJANI*, A daren ranar sunan Rosalin ta tashi da nakuda, sarki da kanshi ya sa aka kira unguwar zoman gidan ta karbi haihuwar, yana daga bakin kofa yaji kukan jinjiri, wani irin kuka ya fashe dashi na murna wanda yaki dauke mishi har saida yaji dumin danshi a jikinshi, nan gaba daya gari ya dauka Sarki Abdallah Yallo ya samu magaji....., kwana goma akayi ana buduri a garin, gidan kuwa zama yayi kamar gidan gala, domin cike yake tun safe har washe gari, babu abin da akeyi sai ciye ciye da raye raye, ko ina ka zaga cikin garin farin ciki ke dauke a fuskar kowa saboda sarki ya zamo mai kyautatawa a garesu.... Shekarar Yareemah Adamu bakwai rikonshi ya koma gurin Fulani Ayyu da tayi sanadiyyar mutuwar Rosalin da karamin ciki bayan barin da ta dinga yi, sarki yayi kuka yayi bakin cikin mutuwar Rosalin mace mai matukar nuna kula a gareshi.... Duk yadda Ayyu takai ga son kuntatawa Yareemah Adamu hakan yaki yiwuwa saboda sarki yana sanya ido sosai akanshi, sai kuma matar waziri mahaifiyar Tidjani wacce yake yini a gurinta bacci kadai ke maidashi gida gurin mahaifinshi, Albarkacin Adamu Allah ya azurta Fulani da samun ciki a lokacin da ta fidda rai, saidai kashh tayi matukar bakin cikin ganin ya mace ta haifa, haka nan tayi ta dakon kiyayyar Adamu a ranta, shi kuma Allah ya daura mishi kaunar yarta Shareefah haka itama Shareefan, ko ina zasu tare suke zuwa... Yana shekara goma sha shida sarki ya fara barin mishi kujera yana ganin yadda yake gudanar da al'amuran sarauta, Adalin sarki Abdallah, ashe a lokacinshi bai kwatanta adalci kamar yadda Adamu ke kwatantawa yanzu ba, Izza ta mulki da kasaita gaba daya sun tabbata a jikin Adamu, wani irin farin jini Allah yayi mishi wanda ya sanya ko ina a garin ake maganarshi da yabonshi, A rana in baiyi abun alkhairi sau goma ba to zaiyi fin goman, gaba daya kowa a garin ya tabbata cikin walwala saboda zuwan Yareemah Adamu.... *Mummunan Kaddara* Ranar da ya cika shekara Ashirin ciff, ranar kaddara mummuna ta afka mishi, a ranar al'amura marasa dadi suka faru a cikin garin agadez.... *Yadda Abun ya faru* Cikin farin ciki Sarki ke sanarwa da fulani Ayyu ya game shirin komai na hutawa ya barwa Yareemah kujerarshi, sannan ya fada mata an kawo mishi yaran sarakunan da zai aura mishi saboda cikar kamalar sarki, nan ta nuna mishi farin cikinta sosai harda cewa zata tayashi zabe a cikin matan.. Tana barin gurinshi zuciyarta kamar zata buga ta kira Hajjara, nan suka kulla duk shirinsu na kawar da Abdallah domin a cewarta in ta kuskura ta yarda aka nadashi sarki kuma yayi aure wasu familyn zasu zama iyalan sarki su kuma su zama yan kallo.. Makudan Silalla ta bawa Hajjara ta shirya tafiya can kauyensu Sassoun burum, cikin sa'a, da kuma lokacin akwai wani boyayyen al'amari wanda Allah ya boye a rayuwar Adamu Hajja ta samu bokan da yayi nasarar yin aikin, ya kuma bukaci auren Hajja, a take ta yarje mishi domin dama tana bukatar yin auren, bayan sun kammala aikin ta koma agadez ta karbo sha tara ta arziki daga gurin fulani Ayyu.... Cikin Kuka Hajja tace "kudi ne wadanda basu rufe shekara ba suka kare suka barmu da wahala, saboda muhimmacin Amana naki yarda in watsa asirin, amma fa duk wata tana bibiyar asirin kamar yadda mijinta ya koya mata.... Shuru gurin yayi bayan Hajja tayi shuru, sai kuka dake tashi a gurin, Murya a dashe Sarki yace "Bazan manta ranar karshe da na ganshi ba, ranar muna tsaye a lambu muna hirar sarautar da za'a bashi, yana tsinko ma shareefah yalon lambu, a kasa ya zubar da yalon ya nufi kofar fita, yana kurewa ganina na bishi na hango Haroun da abokanshi, suna Kallon Adamu ya gifta gefensu babu wanda ya gaisheshi bare ya tambayi inda zashi shi daya... Ashe abubuwan da akayi mishi ba kanshi kadai ya tsaya ba har dukkan mutanen agadez, koda na koma gida babu wanda ya tambayeni shi kowa harkarshi yakeyi har sarki bai damu da tambayar inda yake ba domin babin yareemah shafewa yayi a cikin garin agadez, Ya Allahu ina zanga Adamu, ina zan ganshi.... Ganin kukan bazaiyi musu ba suka fita a gidan Hajja domin babu wani hukunci da zasuyi ma musaka irin ta, hukuncin Allah ma ya isheta, Motocin sarkin sassounburum suka shiga suka je gidanshi suka sallemashi sannan suka wuce airport din katsina domin hawa jirgi zuwa agadez, saboda sassounburum tafi kusa da garin daura.... Shawara suka yanke na baza malamai ayi adduar da Allah zai kawo sanadin haduwarsu in har yana da rai, domin basu yarda da maganar Hajja na ya mutu ba.... *Bawan Allah Adamu tun a cikin garin Agadez ya fara watangaliliya, duk inda ya wuce babu wanda ke ganeshi bare har ya bashi girman dan sarkin da suke matukar so, har ya samu motar da zataje zinder, a can ma saida yayi shekara biyu yana wahala, irin masu shigowa daga kawo kaya daga kano zuwa zinder su yabi zuwa nigeria, A kano ma saida ya shekara daya da watanni har Allah ya hadashi da Alh jogana, nan ya kaishi gidanshi dake kaduna dan yi mishi gadi, anan ne ya bude shago har kaddara ta hadashi da Suwaiba, barin agadez, zuwanshi kaduna, haduwarshi da Suwaiba, rabo ne na ya'ya, wanda Allah swt ya boye wasu al'amura a garesu, Tabbas haihuwar da namijin da suwaiba tayi a farko rubutaccen al'amari ne, mulki na Allah ne, shine yake bada aronshi ga wanda yaso koda kuwa almajiri ne.......* *A gurguje na takaita muku labarin Adamu saboda mu kai inda muke san zuwa a kan lokaci* _Akwai shagalin biki a page fifty...... ku cinka_ Mrs Tijjani Shattima.... [01/04 9:50 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣1⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *EMIR PALACE SASSOUN BOROUM* Sarkin sassoun boroum ne tsugune a gaban sarki "TIDJANI YALLO" yana mika gaisuwa kamar yadda sarakuna keyi wa na gaba dasu, bayan sun gama gaisawa aka cika kayayyakin abinci da sha a gabansu saboda girmamawa, babu abinda Sarki Tidjani da Shareefah suka kalla, bare har su kai ga cin shi, cikin nutsuwa da kasaita suka gabatar da dalilin zuwansu, nan da nan aka wakilta dogarai dan suje can rugar Haldo su nemo Hajja yar Ruga su taho da ita, da yake rugar bata da nisa da gidan sarki sai gasu sun dawo, cikin girmamawa suka ce bata da lafiyar da zata iya zuwa, daka musu tsawa sarkin sassoun burum yayi yace "maza su koma su dauko ta, dakatar dasu Shareefah tayi hade da mikewa tace "su barta kawai, su zasu isa zuwa gidanta, Duk yadda sarkin sassoun burum yaso nuna musu kaskancin zuwa rugar Haldo hakan bai hanasu zuwa ba, a cewarsu su suke nema a gurin ta, ya zame musu dole su ganta yau kota halin kaka..... Wani irin wari dakin Hajja ke fitarwa, warin ma marar misaltuwa, tana kwance a kan tabarmar da takai rabi saboda cinyewa, dakyar aka iya dagota ta jingina da wani sudadden pillow, "wani dan kara tayi saboda wani ciwo da yayi mata rami a mazaunanta, yaron dake kula da ita ne ya sa mata wani pillow a gurin ciwon, saboda tausayin halin da Hajja ke ciki ya sanya Shareefah sharar kwalla, Dakyar muryar Hajja ta iya fita tace "sannunku da zuwa, da kai suka amsa hade da gyara zama akan daddumar da dogarai suka shimfida musu, saboda son jin abun da ya kawosu ko kyankyamin dakin basu ji ba, "Daga ina ranka ya dade? Hajja ta fadi baki na rawa, Shareefah ce ta fada mata sunanta da dalilin da yasa suka zo gurinta, bude ido Hajja tayi sosai ta kure shareefa da ido, *SHAREEFAH YALLO* kece? murmushi Shareefah tayi tace "nice, ashe ma kin sanni, kuka Hajja ta fashe dashi tace "farin sani, ni na raineki tun kina tsumma, nafi shekara ashirin a gidanku tun kafin a haifeki, ashe zan sake ganinki, rabona da ke inaga in banyi karya ba yakai shekara arbain, dan tun kina shekara goma sha biyu na bar agadez, ashe ina da rabon sake ganinki ta karashe da kuka hade da tari, Cike da kosawa sarki Tidjani yace "sai hakuri Baba, dama haka rayuwa take, kuma duniya fadi gareta, wata rana in da rai dole a hadu, yanzu gashi sanadiyar mutuwar UMMU AYYU Allah ya kawo mu gurinki, yanzu bamu da isashen lokaci zuwa mukayi ki fada mana labarin da Ummu tace ke kadai ce kika san dashi, labarin YARIMA, wani kukan ne ya kufcewa Hajja a zuciyarta tace "yau labarin da yayi shekara da shekaru a kunshe, hali yasa zata bayyana shi, labarin da ya zame mata tamkar kwai a cikin zuciyarta saboda riritarshi, ajiyar zuciya tayi tace "babu mamaki fitar labarin nan ya zama silar samun warakarta, Nuni tayi ma yaron dake kula da ita wani gurin dake cike da kaya, mikewa yayi ya dauko wata jakar saka ya mika mata, hannu na rawa ta karbi jakar ta dauko wani ginin mutum mutumi wanda yake kewaye da kawunan mutane babu adadi, Saboda tsananin tsorata saida shareefah ta rungumi kafardar mijinta, abun ba karamin tsoro ya bata ba kuma ya daga tsigar jikinta matuka, yadda aka yanyame shi da wasu abubuwa kamar kwari yasanya har sarki jin tsoro amma kadan, wani guri ta daga a gefenta, inda take ajiyar abubuwa, nan ta mike dayar ruwa nabin bayanta ta fita tsakar gidan ta daki wani dakali dake kofar dakinta, nan take gurin yayi rami, hannu tasa ta ciro layu masu tarin yawa, daga can kasa ta hango kurciyar da suka binne shekara da shekaru kwance babu rai ga layu kewaye da ita, a gigice ta ciro kurciyar da duk wata sai ta bata ruwa ta mayar ta rufe, tun da ta kwanta ciwo kusan watanni takwas bata kara bi takanta ba domin itama ba lafiyar gareta ba, girgiza kurciyar tayi tana kuka tana fadin *YARIMA ADAMU* wayyo Allah Kunzo a kurarren lokaci, nasan duk inda Yareema yake a yanzu to kasa ta rufe idonshi, wannan kurciyar rayuwar Yareema ce, Allah na tuba, wayyo ni Allah, haka ta dinga fadi hankali tashe, Da karfi ta saki mutum mutumin hanunta ya tarwatse a tsakar gidan, nan tabi kowane kai ta cire dabaibaiyin da aka mishi, runtse ido Sarki Tidjani yayi saboda juyawa da yaji kanshi nayi, dakyar Shareefah ta tallabe shi ya zauna a kasa ba tare da duban dattin gurin ba, itama hakan ce ta kasance da ita, saidai ita ta kasa fahimtar komai, sabanin Sarki Tidjani da komai ya shiga yawo a kanshi, yadda abubuwa suka faru ya dinga tunowa kamar yanzu ake yinsu, kusa dasu Hajja taje dan itama wani karfi taji a jikinta, burinta ta sanar dasu komai da suka sani da wanda basu da masaniya... "Nasan yanzu wasu abubuwan sun fara dawowa a kanku da kuma daukacin mutanen da suka san Yareema a Agadez, to saidai abin da baku sani ba shine dalilin da yasa ya kaurace muku ya tafi can wani guri inda babu wanda zai ganshi bare har yasa shi waiwayen gida, "Adamu Yallo... sarki ya dinga maimaitawa a bakinshi, fuskarshi yake kallo kamar yanzu suka rabu cikin lambun *Shehrah Agadez*, ina dan uwanshi ya tafi har tsawon wannan lokacin, yana kallon fitarshi daga lambun lokacin bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa kiranshi bare har ya tambayeshi inda zashi, sai yau yaji tunanin ya dawo sabo dal game dashi, Da sauri ya maida idonshi kan Hajja yace "ina Adamu? Me ya sami Adamu? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me ya shiga kaina har na manta da dan uwa kuma aminina, Ya salam ya fadi hade da dafe kai.. "Ba laifinka bane Yallabai, Laifin namu ne, bakai ba ma kowa a garin Agadez a yau sai ya tambayin dalilin da yasa ya manta da Yareeman da suke matukar so fiye da sarkin Kanshi... har ke ma Shareefah, a karancin shekarunki zaki iya tunawa da *Yeeman ki* , *Yeeman Pappalinto* nan take mafarkinta ya dawo mata sabo, sunan Yeema take yawan fadi cikin mafarkinta, wani irin kuka ne ya kufce ma Shareefah ta dinga nanata sunan a ranta, tabbas ta tuno kuruciyarsu saboda mafarkinta bai rage mata komai ba, cikin kuka tace "Bani labarin Yeema nah! Bani labarin dalilin da yasa yayi nesa dani..... *TUNA BAYA.......* ********** Ranki ya dade kici abinci dan Allah, rashin cin abinci zai iya zame miki illa, kuma kin sani sarki bazai fasa abun da yayi niyya ba, cikin Kuka Fulani Ayyu tace "Hajjara yanzu anyi min adalci, ace sarki ya rasa da wacce zai hadani sai da *Kuyanga Rosalin* , kuyangar da na bawa yarda tasan sirrina fiye da kowa, tayaya zan iya kallon mutanen gari, wannan ai cin mutunci ne a gareni da masarauta baki daya, Gabanta Jakadiyya Hajjara ta dawo tace "ki kwantar da hankalinki, ki barshi yayi auren, zamu san yadda zamuyi da ita, da kalamai masu dadi Hajjara ta kwantar mata hankali har taci abinci.... Wata hudu bayan auren *sarki Abdallah Yallo* da Kuyangarshi mai kula da komai na alamuranshi *Rosalin Mujdaha* mahaifinta shine mai bawa sarki kariya, bayan rasuwar mahaifiyarta mahaifinta ya bawa sarki ita domin ta zama mai aikinsu ta jikinsu wacce zata kula dasu, garin binciken shi na rashin haihuwa Rosalin ta fado ciki har malaminshi ya fada mishi alherin da ke tattare da aurenta, bai damu da kalubalen da ya fuskanta daga yan uwa da matarshi ba aka sanya rana, har Allah yasa ta zamo matarshi, kyakykyawar gaske ce doguwa sambal, ga biyayya da hakuri, hakan yasa yake matukar kaunarta, babu irin asirin da Fulani Ayyu batayi ba dan taga bayanta amma Allah cikin ikonsa duk ta tsallake, saboda tsoron Fulani da Rosalin keyi hakan yasa bata fita ko nan da can, duk abin da zai hadasu tana neman hanyar kaucewa saboda bata san tashin hankali, mugun hakuri gareta ga kawaici da sanin ya kamata, Babu wanda keda masaniyar tana dauke da ciki domin tsakaninta da bayinta yar kallon fuska ce, ko mikewa a gabansu batayi, A ranar da cikinta ya cika wata tara ranar akayi haihuwa a gidan, wazirin sarki wanda ya zamo kani ga sarki, a gurin barka ne kowa ya fahimci ciki gareta, ranar Fulani mutuwa ne kadai batayi ba, gaba daya kansu ya kulle ita da Hajjara suka rasa ta inda zata bullowa al'amarin.. Ranar suna Yaro yaci sunan *TIDJANI*, A daren ranar sunan Rosalin ta tashi da nakuda, sarki da kanshi ya sa aka kira unguwar zoman gidan ta karbi haihuwar, yana daga bakin kofa yaji kukan jinjiri, wani irin kuka ya fashe dashi na murna wanda yaki dauke mishi har saida yaji dumin danshi a jikinshi, nan gaba daya gari ya dauka Sarki Abdallah Yallo ya samu magaji....., kwana goma akayi ana buduri a garin, gidan kuwa zama yayi kamar gidan gala, domin cike yake tun safe har washe gari, babu abin da akeyi sai ciye ciye da raye raye, ko ina ka zaga cikin garin farin ciki ke dauke a fuskar kowa saboda sarki ya zamo mai kyautatawa a garesu.... Shekarar Yareemah Adamu bakwai rikonshi ya koma gurin Fulani Ayyu da tayi sanadiyyar mutuwar Rosalin da karamin ciki bayan barin da ta dinga yi, sarki yayi kuka yayi bakin cikin mutuwar Rosalin mace mai matukar nuna kula a gareshi.... Duk yadda Ayyu takai ga son kuntatawa Yareemah Adamu hakan yaki yiwuwa saboda sarki yana sanya ido sosai akanshi, sai kuma matar waziri mahaifiyar Tidjani wacce yake yini a gurinta bacci kadai ke maidashi gida gurin mahaifinshi, Albarkacin Adamu Allah ya azurta Fulani da samun ciki a lokacin da ta fidda rai, saidai kashh tayi matukar bakin cikin ganin ya mace ta haifa, haka nan tayi ta dakon kiyayyar Adamu a ranta, shi kuma Allah ya daura mishi kaunar yarta Shareefah haka itama Shareefan, ko ina zasu tare suke zuwa... Yana shekara goma sha shida sarki ya fara barin mishi kujera yana ganin yadda yake gudanar da al'amuran sarauta, Adalin sarki Abdallah, ashe a lokacinshi bai kwatanta adalci kamar yadda Adamu ke kwatantawa yanzu ba, Izza ta mulki da kasaita gaba daya sun tabbata a jikin Adamu, wani irin farin jini Allah yayi mishi wanda ya sanya ko ina a garin ake maganarshi da yabonshi, A rana in baiyi abun alkhairi sau goma ba to zaiyi fin goman, gaba daya kowa a garin ya tabbata cikin walwala saboda zuwan Yareemah Adamu.... *Mummunan Kaddara* Ranar da ya cika shekara Ashirin ciff, ranar kaddara mummuna ta afka mishi, a ranar al'amura marasa dadi suka faru a cikin garin agadez.... *Yadda Abun ya faru* Cikin farin ciki Sarki ke sanarwa da fulani Ayyu ya game shirin komai na hutawa ya barwa Yareemah kujerarshi, sannan ya fada mata an kawo mishi yaran sarakunan da zai aura mishi saboda cikar kamalar sarki, nan ta nuna mishi farin cikinta sosai harda cewa zata tayashi zabe a cikin matan.. Tana barin gurinshi zuciyarta kamar zata buga ta kira Hajjara, nan suka kulla duk shirinsu na kawar da Abdallah domin a cewarta in ta kuskura ta yarda aka nadashi sarki kuma yayi aure wasu familyn zasu zama iyalan sarki su kuma su zama yan kallo.. Makudan Silalla ta bawa Hajjara ta shirya tafiya can kauyensu Sassoun burum, cikin sa'a, da kuma lokacin akwai wani boyayyen al'amari wanda Allah ya boye a rayuwar Adamu Hajja ta samu bokan da yayi nasarar yin aikin, ya kuma bukaci auren Hajja, a take ta yarje mishi domin dama tana bukatar yin auren, bayan sun kammala aikin ta koma agadez ta karbo sha tara ta arziki daga gurin fulani Ayyu.... Cikin Kuka Hajja tace "kudi ne wadanda basu rufe shekara ba suka kare suka barmu da wahala, saboda muhimmacin Amana naki yarda in watsa asirin, amma fa duk wata tana bibiyar asirin kamar yadda mijinta ya koya mata.... Shuru gurin yayi bayan Hajja tayi shuru, sai kuka dake tashi a gurin, Murya a dashe Sarki yace "Bazan manta ranar karshe da na ganshi ba, ranar muna tsaye a lambu muna hirar sarautar da za'a bashi, yana tsinko ma shareefah yalon lambu, a kasa ya zubar da yalon ya nufi kofar fita, yana kurewa ganina na bishi na hango Haroun da abokanshi, suna Kallon Adamu ya gifta gefensu babu wanda ya gaisheshi bare ya tambayi inda zashi shi daya... Ashe abubuwan da akayi mishi ba kanshi kadai ya tsaya ba har dukkan mutanen agadez, koda na koma gida babu wanda ya tambayeni shi kowa harkarshi yakeyi har sarki bai damu da tambayar inda yake ba domin babin yareemah shafewa yayi a cikin garin agadez, Ya Allahu ina zanga Adamu, ina zan ganshi.... Ganin kukan bazaiyi musu ba suka fita a gidan Hajja domin babu wani hukunci da zasuyi ma musaka irin ta, hukuncin Allah ma ya isheta, Motocin sarkin sassounburum suka shiga suka je gidanshi suka sallemashi sannan suka wuce airport din katsina domin hawa jirgi zuwa agadez, saboda sassounburum tafi kusa da garin daura.... Shawara suka yanke na baza malamai ayi adduar da Allah zai kawo sanadin haduwarsu in har yana da rai, domin basu yarda da maganar Hajja na ya mutu ba.... *Bawan Allah Adamu tun a cikin garin Agadez ya fara watangaliliya, duk inda ya wuce babu wanda ke ganeshi bare har ya bashi girman dan sarkin da suke matukar so, har ya samu motar da zataje zinder, a can ma saida yayi shekara biyu yana wahala, irin masu shigowa daga kawo kaya daga kano zuwa zinder su yabi zuwa nigeria, A kano ma saida ya shekara daya da watanni har Allah ya hadashi da Alh jogana, nan ya kaishi gidanshi dake kaduna dan yi mishi gadi, anan ne ya bude shago har kaddara ta hadashi da Suwaiba, barin agadez, zuwanshi kaduna, haduwarshi da Suwaiba, rabo ne na ya'ya, wanda Allah swt ya boye wasu al'amura a garesu, Tabbas haihuwar da namijin da suwaiba tayi a farko rubutaccen al'amari ne, mulki na Allah ne, shine yake bada aronshi ga wanda yaso koda kuwa almajiri ne.......* *A gurguje na takaita muku labarin Adamu saboda mu kai inda muke san zuwa a kan lokaci* _Akwai shagalin biki a page fifty...... ku cinka_ Mrs Tijjani Shattima.... [02/04 11:39 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣2⃣ By *Aysha Ya'u kurah* A gajiye likis suka nufo motar Musaddiq, sanye suke da white top kowacce da sunanta a jiki, sai bakin skirt mai tsagu da takalma masu mugun tsini suma bakake, saman kayan sun daura graduation gown da hularta gashinsu ya kwanta a gadon bayansu, bude gaba Husnah tayi ta shiga tana maida numfashin gajiyar rawar da suka tika, ita kuwa Nadeeyah kwanciya tayi a baya hade sakin ajiyar zuciya, dariya yayi yace "ina Badariyya? Ko ta wuce gida, "Tana ciki zasuyi class party dinsu yanzu, yaya dan Allah muje gida, kamar zan mutu ta karashe fadi tana kwantar da kanta, tada motar ya fara kokarin yi suka ji an kwala kiran sunan Nadeeyah, da gudu sabrinah ta karaso tana haki ta mika mata waya, "uncle Taheer ne, wai in kawo miki, kallon Musaddiq tayi wanda ya kure ta da ido, tana ganin ya maida idonshi gaba tayi saurin karbar wayar, "Assalamu alaikum ta fadi a hankali, "wa alaiki salam my omri ya amsa hade da lumshe ido, congratulations, kin kammala matakin farko na karatunki, in shaa Allah kin fara takasu kenan har karshen rayuwarki, hope kina kula da kanki sosa? "umm kawai tace tana wasa da hannun kofa, "Good, take care kinji, naji dadi sosai da naji muryar da na dade banji ba, Ina fatan ganinki soon in shaa Allah... love yhu bye, Bata bashi ba ta kashe wayar hade da mika ma sabrinah, karba tayi ta wuce ba tare da ta kawo komai a ranta ba... "Kin gama? ya fadi yana murda key, "ta gama mana yaya, muje plss, tada motar yayi ya figeta da wani irin mahaukacin gudu, ya rasa dalilin da ya sanya wani abu yayi mishi karan tsaye a cikin kahon zuciyarshi, menene yake shirin faruwa dashi, tun tafiyarshi lagos kome yakeyi ita ke fado mishi, har sabawa yayi da tashin da take mishi da asuba, komi nisan baccin da ya tafi in yaji karar wayarshi yasan ita ce, dan ita kadai ke kula da tashin shi, in ko yaje cin abinci babu wanda yake a gani a gabanshi in ba ita da daddan girkinta ba, yana matukar kaunar ganin yanayinta a duk lokacin da ya tsokaneta, wannan dawowar da yayi week end domin ta yayi shi saboda a matukar takure yake, kewarta na addabar shi, Tufka ya dingayi da warwara akan abun dake shirin faruwa dashi game da Nadeeyah, har ya isa gida bai tufka komai ba bare ya warware... Bakin motoci ya gani a harabar gidan shiyasa yayi parking daga can baya, da sauri duk su biyun suka karasa ciki saboda lalurar dake tare dasu, wasu lafiyayyun mutane suka gani su uku, manyan mata biyu sai wata tsaleliyar budurwa black beauty, hannunta rike da katuwar waya mai fadi tana ta latsata tana taunar cingam, gaishesu sukayi matan suka amsa da murmushi, yafito Husnah Mummy tayi da hannu tace "zo ki gaida Anty Aliya, takalmi ta cire ta karaso kusa dasu ta gaida su, shafa kanta Anty Aliya tayi tana murmushi tace "Husnah ta girma, waccen fa ban gane ta ba? daidai lokacin Musaddiq ya shigo parlon, "Yar step sis dina ce wacce ta rasu, Ayya, yar me kyau da ita, Allah ya jikanta, Ameen Mummy tace hade dayi ma Nadeeyah nuni da ido da ta wuce daki, juyawa tayi ta murda kofar dakin nasu ta shiga, kan gado ta kwanta tana mikar gajiya, karar shigowar sakon da taji a wayarta shi ya sanyata sakin wani irin Murmushi hade da daukar wayar, a yanzu shakuwar da tayi da Hilal ta wuce misali, har ta kanyi mamakin yadda ta saki jiki dashi sosai haka, saboda dadin da sakon yayi mata har saida hakoranta suka bayyana... *Congrats to my young Barrister, bigger yhu i pray, i'm very Happy, more grads are coming in shaa Allah....* Kiranta barrister da yayi shi yafi komai yi mata dadi cikin sakon, tunda ta fada mishi abun da take son karanta shikenan kullum sakonsu ya koma akan lawyers, _Thank you yayana, Allah ya biya maka bukatunka duniya da lahira, yhu are an angel......_ Wani irin juyi yayi a kan makeken gadonshi, "will be ur life soon Nadeeyah, ya Allah, i can't resist it, i have to tell her, wani irin faduwar gaba yaji da sauri sauri, Soyayyar Nadeeyah kullum kamar kara hurata akeyi a cikin qalbinshi, baya tunanin akwai abin da zaizo ya rabashi da ita sai dai ko mutuwa, a kasalance hannunshi ya rubuta. *Akwai wani sakon da zan baki zuwa anjima, kiyi ma sakon tanadi, domin yanada matukar tsada da kuma muhimmanci, take ur time daga yanzu zuwa dare dan sakon yana bukatar nutsuwa, domin a nutse za'a isar dashi, 10pm dot...* Kokawa ya fara yi da zuciyarshi, wannan tana ka tura wancan tana karka saba alkawarin da ka dauka na saita gama makaranta zaka isar mata, wata tana fadin karka bari ya huce domin zai iya kawo rabon wani, tunanin shi na karshe ne ya sanyashi saurin turawa, kashe wayar yayi gaba daya dan gani yakeyi kamar in a kunne take zata iya ganinshi, wani irin nishadi ya yake ji, ya tashi ya fita parlor gurin su zainab, wasan da bai saba yi dasu ba ya shiga yi har Anty Reemah na tsokarshi.. Ita kuwa juya wayarta ta dinga yi ta rasa wani irin sako ne wannan dake bukatar nutsuwa, ita dinma zuciyar sai bugawa take da sauri sauri, abu daya ta kawo a ranta kuma tayi saurin kawar dashi dan tasan ba mai yiwuwa bane, Hilal yayi mata zarra ta kowani bangare, nan take ta kauda tunaninta ta ajiye wayar ta shiga bayi, wanka tayi ta fito ta sanya wani plain material lemon green da jar flower a jiki, ta sanya jar hula a kanta ta gyara dakin ta fita dan zuwa yi ma Musaddiq abinci, karo sukayi da Husnah a kofar dakin tana kokarin shigewa ciki, "Har kinyi wanka, kaii kin huta, ni su Mummy sun hanani katabus, bari inyi wanka zan sameki a kitchen, dariya Nadeeyah tayi na ganin yadda jikin Husnah ke rawa ta karasa fitowa a parlon, wannan karon ba kowa a parlon sai Musaddiq da budurwar, hada ido sukayi tayi mishi Murmushin da ya sanyashi sukurkurcewa ya bita da ido, saida ya daina ganinta sannan ya dawo da hankalinshi gurin wacce ta kira kanta da *FAIDA*, "kana jina ko, ta fadi tana kallon cikin idonshi, "Eh yauwa, inaji, kikace wani level ma? "200l ta fadi tana murmushi, ta cigaba da cewa "dama Mum tace min i will like u, gashi daga farkon haduwarmu i like everything about u, i love you!, wani irin murmushi yayi ya shafo sajenshi hade da jan hancinshi yace "dats nice, i like u too, saidai anya zaki iya kuwa? liability ne ni, komai yi min akeyi, komai fa, infact ko toilet zani sai an rakani, dariya yayi wacce bai san ta fito ba yace "Kuma gash--- wata dariya yaji wacce ta sanyashi kasa karasawa, bata kalleshi ba ta bude drawer gurin dining ta dauki abun da tazo dauka, shima dariyar ya cigaba dayi yace "yauwa Nadeeyah zo, matse dariyarta tayi ta karaso inda suke, "Gani, "zauna ki bata labari na, zama tayi tace "Karki ce dan yana yayana ko dan yana zaune anan, gaskiyar kawai zan fada miki, "yaya Musaddiq a cikin dubu kafin ki samu daya irinshi sai kin tona, he is very nice, bashi da fushi sam, baima iya shi ba, yanada kyautawa fiye da tunani, sannan yana son a kula dashi da kuma cikinshi, gaskiya kinyi dacen samun yayana, yhu are very lucky... Tana kaiwa nan ta mike hade da kallon yadda ya kureta da ido, dariyar tsokana tayi mishi ta wuce kitchen, Dan tabashi yaji anyi nan ya dawo cikin hayyacinshi, ya salam ya fadi a zuciyarshi, abubuwan nan dake faruwa dashi game da Nadeeyah ba lafiya bane, ya kasa tantance menene shi, "Ko a ya kake kayi min! muryarta ta sake maidoshi cikin tunanin da zuciyarshi ta tafi, hankalinshi kacokan ya dawo dashi kanta yace "Menene So? Ya akayi kikaji kina sona daga ganin farko? Menene kikaji game dani har kika gane kina sona, Nan Faida ta gyara zama domin kwararrace a wannan fanin, bata san adadin samarin da tayi a rayuwarta ba, yadda ta maida kudi take watsarwa ko ina haka ta maida namiji *SO* Gamon jini ne, so wata halittace wace take kwance a cikin zuciya, Halittar na iya daukar mutane da yawa, saidai kowa da muhallinshi, Soyayyar iyaye tanada gurinta, soyayyar yan uwa, aboki da sauransu suma akwai muhallinshi, sai kuma main the main, soyayyar Abokin rayuwa, wannan soyayya ce wacce ke faruwa a lokacin da mutum bai shirya ba, Tausayi siga ce ta soyayya, duk wanda kake tausayinshi to tabbas soyayya ce ta jawo haka, damuwa, yawan damuwa da mutum wannan ma alama ce ta soyayya, Tsayuwa cikin rai, mutum ya zauna a ranka babu dare babu rana ko yaushe tunaninshi kakeyi wannan shine kankat, domin ko shakka babu soyayya ce mai karfi ta shigo lamarin, kamar yadda yanzu ina sanyaka a idona naji my heart beats for u, ban taba jin wani abu game da wani da namiji ba sai akanka, Surutanta take tayi shi kuwa ya tafi can wata duniyar, murmushi kawai kake gani a kan bakar kyakyawar fuskarsa mai cike da annuri, komai na Nadeeyah ke mishi yawo akanshi, "I'm in love ya furta a hankali, kallonshi Faida tayi hade da mikewa tace wawww, alhamdulillah, sama tayi da gudu dan kaiwa maman ta albishir, bai ma san tanayi ba ya shafa kanshi har lokacin yana furta kalmar "I'm in love, bayanshi ya jingina jikin kujera yana fitar da murmushi mai sauti, wasu irin numfarfashi yake fitarwa wanda duk fitarsu suke tafe da zazzafan kaunar Nadeeyah, muryarta keta yin amsa kuwwa cikin kunnenshi, "Yhu are very lucky, kasa ya koma ya mike kafarshi yace "yhu are the lucky one Nadeeyah, and I'm the luckiest, Muryarsu ya jiyo a kitchen yayi saurin zuwa kofar kitchen din ya nade hannuwanshi yana kallon duk wani taku da tayi a kitchen din, da ido Husnah ta nuna mata shi, saida ta shanye dariyarta ta juyo tace "mun kusa gamawa, angon mu, muma dai mun kusa hutawa, amma dan Allah a bari mu dawo daga Gombe ko Husnah, ta karashe tana taba kafadar Husnah, kusa dashi Husnah ta dawo tayi mishi rada a kunne tace "Yaya nidai bata min ba, bata da class, kaji wani ihun da tayi da sunan wayewa, samm batayi kama da matar yayana ba, bai dauke idonshi a kan Nadeeyah ba yace "Tunda ba tayi miki ba sai mu canza wata auta, yana kaiwa nan ya bar kofar kitchen din, bazai iya kara kwana daya ba tare da ya sauke wannan nauyin son a zuciyarshi ba, dakinshi ya shiga ya kwanta a gado hade da dauko wayarshi, Hilal ne kadai zai tayashi sauke wannan nauyin, daga bakinshi kadai zataji ta saki jikinta dashi ta kuma amince mishi, layin Hilal din ya kira, da farko yaki shiga sai da yayi sau uku, ana ukun ne yayi sa'ar ya kunna wayar, cike da Annashuwa Hilal ya dauki wayar da bashi da masinayar itace yankewar farin cikinshi na lokaci mai tsaho..... "A kasalance Musaddiq ya furta kalmar "I'm in love main man, cikin shauki Hilal ya jingina jikinshi a karfen balcony ya sauyawa wayar hannunshi mazauni zuwa kunnen dama yace "Wowww, is this a dream or? REALITY Musaddiq ya katseshi hade da lumshe manyan idanuwanshi, sajen fuskarshi ya fara shafawa yana fadin "i don't knw how Hilal, na tsinci kaina a tarkon kauna, ganinta kadai yana tsaida duk wani magudanar jinin jikina, idan najiyo muryarta nakan rasa nutsuwata in daburce na shiga rudani Hilal, Na rasa yadda zanyi in tunkareta da kalmar soyayyata, walhy sonta yayi min mugu kamu ba tare da na farga ba, ya karashe fadi yana mai taba gefen da zuciya ke adane a cikin kirji, Daddadar iskar da ta kada Hilal ya shaka jikinshi ya mutu tubus saboda haroro yanayin da suka shiga shi da dan uwanshi daya, har yana ganin ma yanayin nashi yafi na Musaddiq, saboda wani irin sonta da yake ji a dukkan sassan jikinshi ba zuciya kadai ba, A kagauce ya kauda tunanin yace "who is the lucky one my Guy, "call me lucky a ranar da zan iya tattaro kalaman so in fada mata, "Wait wait Kyari, u mean baka fada mata ba? gyada kanshi yayi fuska a dame yace "na kasa Hilal, wallahi i can't, dariya Hilal yayi yace "lallai baka shirya soyayya ba, a shagwabe musaddiq yace "kai zaka tayani fada mata, i knw zaka ce baka son raini, plss u have to help me out dan na gaji da wannan ciwon takurar, " it's well Hilal yace yana dariya sosai, fada min wacece , sannan ka turo min numberta Asap in tsara maka ita, cike da fargabar kar ya fada mishi sunanta yace bazai iya ba saboda baisan raini ko kuma wani abun daban yace "promise me in na fada maka bazaka ki fada ba? "Haba ai kaima kasan ko wuta take zan bita in fada mata for u, bare a cikin gari take kuma mutum ce kamar mu, kai dai kawai fada min everything about her,, *NADEEYAH...* *Hilal i'm in love with Nadeeyah....,* Tartsssssssssaas.... wayar hannun Hilal ta subuce ta fadi a kasa........... Mrs Tijjani Shattimah....... [04/04 10:04 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣3⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Sulalewa Hilal yai a hankali yayi zaman dirshan a gurin, kallon wayarshi yayi wacce yake jiyo muryar Musaddiq yana fadin "kana jina? Hello Hilal are u der?, girgiza kai Hilal ya shiga yi yana fadin "nooo dis is nt true, da sauri ya mutstsike idonshi ya bude dan ganin ko mafarki yakeyi, k'ara wayar da glass dinta ya tarwatse ta sakeyi, hannu na rawa ya mika shi ya janyota, dannata yayi ya sanya speaker, nan take muryar Musaddiq ta sake gauraye gurin "Pls Mana, kai kadai kake understanding feelings dina, kai kadai ne zaka taimakeni, wallahi i love her.... Toshe kunnuwa Hilal yayi kalmar *wallahi I love her* ta dinga amsawa cikin kunnenshi, runtse idanuwanshi da suka zama kamar gauta yayi kirjinshi na duka kamar ana daka, duk yadda yaso yayi kuka hakan yaki yiwuwa a gareshi dan ba sabawa yayi ba, kuka... sam bazai iya tuna ranar da yayi shi da girmanshi ba, A hankali yake maimaita "Why Nadeeyah, why nt order gal, ya Allah... ya karashe hade da dafe kanshi, daina jiyo muryar da yayi ne ya sashi saurin daukar wayar, juyata ya dinga yi a hanunshi yana jin haushin dalilin da yasa ya mallaketa tun farko, screen guard din daya fashe ya zare.. nan hoton da ke daure kan screen din nata da Musaddiq ya fito baroro, maida wayar yayi da sauri saboda wani abu da yaji ya taso mishi, Dakyar ya iya mikewa ya shiga dakin, rub da ciki yayi yana hango wa kanshi halin da zai shiga, yaso Nadeeyah kamar rayuwarshi, daidai da second daya bata taba fita a ranshi ba, sai gashi yau Musaddiq da bayan iyayenshi bashi da kamarshi shi yake son abun da yakeso, juyi ya dingayi a gado ya rasa abun da zaiyi yaji sanyi cikin ranshi, komai ya daina aiki a jikinshi, Zainab ce ta fado dakin da gudu, drawershi ta bude ta shiga tana fadin "boyeni yaya, Anty zata dukeni, yadda ta rufe kofar da karfi ya sa takardun saman drawer zubowa kasa, jiki ba kwari ya mike ya tattarosu ya zubasu a kan gado, nan take zuciyarshi ta raunana da yayi tozali da zanen da ya gama satin da ya wuce, tsugunawa yayi ya janyoshi ya zuba mishi ido, dariyar dake matukar burgeshi yayi nisa cikin kallo ba tare da sanin halin da idanuwanshi ke ciki ba... hannu yaji kan kuncinshi ana share mishi hawayen da baida masaniyar zubarsu, dago kai yayi ya kalleta itama nata idon ya ciko da kwalla, da sauri ya hada jikinshi da nata ya saki wani irin kuka mai tsayawa a zuciya, ita kuwa da karfi ta saki nata wanda ya janyo hankalin su Anty Reemah da Papa da shigowarshi gidan kenan, Da sauri ya turata waje ya sama dakinshi key, Hinad dake lekenshi tayi saurin komawa itama kukan ta saki dan abin da bata taba gani bane tun tasowarta kuka a idon Hilal, takardun ya tattaro yayi musu runguma kamar zai maidasu ciki, a lokacin kukan da yakeyi ya ci karfinshi dan har sheshshekarshi su Anty Reemah sunaji, babu irin bugun da basuyi ma kofar ba yaki budewa, da yaga sun matsa sai ya tattara duka takardun, ya zaga baya ya sanya musu wuta, ganin hayakin dake fita ta kasan dakinshi ya sanya Anty Reemah sakin Kuka sosai tana fadin "dan san annabi Muhammadu Hilal ka bude kofar nan, Papa kuwa ranshi ya gama baci ya dinga dukan kofar, ko gezau batayi ba dan mugun karfi gareta, murya a kausashe yace "Muktar bude kofar nan, wallahi kaji na rantse in baka bude ba zanyi maka mummunan furu--- bude kofar yayi ya tsaya a gurin, har lokacin idonshi bai bar zubar ruwa ba, da sauri Anty Reemah ta karasa tana share mishi hawayen, itama masu zafi na fita a idanuwanta, Rungumeshi tayi tana tambayar dalilin zubar hawayenshi, kamar ta sake kunno wutar cikin zuciyarshi haka ya kwantar da kanshi a jikinta yana kuka kamar karamin yaro, Papa bai bi ta kanshi ba duk da shima ya shiga tashin hankalin ganin hawayen dan nashi, bayan dakin yaje yaga komai ya kone sai toka, dawowa yayi da sauri rai a bace yaja hannun Hilal, "meye wannan? Yanzu in abun nan da kayi yazo da tsautsayi fa? dan iskanci ka rasa inda zaka sa wuta ka kona takardu sai a nan, karkatar da kai kawai Hilal yayi baya ma gane fadan da Papa ke mishi, abubuwa da dama ke mishi yawo a kai, "Papa please, Anty Reemah ta fadi cikin sigar tausayawa, bai kalleta ba yaja tsaki ya fita shima zuciyar ta shi a karye take, baisan me ya sanya Hilal kuka ba, amma yasan koma meye ba karamin abu bane... Anty Reemah kuwa zaunar dashi tayi tana rarrashinshi tana tambayarshi abun dake damunshi har ya sanyashi zubar hawaye, kwanciya yayi a jikinta wanda har ya manta rabon da ya kwanta a jikinta haka, Mugun tausayin kanshi yakeyi dan ya rasa makomar zuciyarshi, "Tell me Babana, menene? Cikin muryar kuka yace "Mum pls don't ask again, ki zauna anan karki tafi ki barni, hannu tasa ta share hawayenta ta fara shafa mishi kai, Hinad ce ta shigo dakin ido jajur hannunta da plate din farfesun kifi ta tsuguna a gabanshi tace "yaya ka tashi kaga nayi maka abun da kakeso, "harda zobo mai dadi, Zainab ta fadi itama har lokacin bata bar kukan ba, runtse idonshi yayi hawayen dake kwance ciki suka jika gashin idon, Cikin muryar Kuka Hinad tace "Yaaayaaa plss ka daina kuka dan Allah, ka fada mana abun dake damunka, Muryar Papa sukaji da karfi yana kiran Anty Reemah, amsawa tayi tace tana zuwa, "ki ce mishi ya fito mu tafi Masallaci, tadashi Anty Reemah tayi tace "Tashi kuje kuyi Sallah kaji, in ka dawo sai ka fadamin damuwarka koma meye in shaa Allahu zanyi maka maganinta.... A tare suke jerowa kai kace wa da kani ne, har Hilal ya dan dara Papa tsaho, bai tambayeshi abun dake damunshi ba dan baisan ji saboda kar nashi hankakin ya tashi, nasihohi ya dinga mishi akan yadda rayuwa take "dama dole a duniya mutum bazai samu abinda yake so daidai ba, dole yau zuma gobe madaci, Ganin hawaye a idonka ya fara tabbatar min da yanzu ka fara sanin me duniya take ciki Hilal, wacece ita?? Wani irin kallo yayi ma Papa ya dauke kanshi dan baisan sake zubda wani hawayen, lallai mahaifi daban yake, yasan abun da zai raunata Hilal har haka bai taba wuce soyayya, "Papa mu bar maganar, she is dead, "subhanallah Papa ya fadi cikin tausayawa, hannun Hilal ya rike cike da rarrashi ya shiga bashi hakuri dan tsaff ya yarda ta mutun ne... Dakyar Hilal ya ci wani abu sannan ya tashi ya wuce daki, da ido iyayenshi suka bishi suna tausaya mishi dan sunsan mecece soyayya, basu san tashi har gara ace mutuwar tayi da abun dake shirin rabasu ba, Five missed calls ya samu a wayarshi na Musaddiq, yana kokarin kira Musaddiq din ya sake kiranshi, bai bari yayi magana yace "ka fada mata? Gyaran murya Hilal yayi yace "karka damu, Nadeeyah is all urs in shaa Allah, godiya ya shiga yi mishi wanda ya sanya Hilal ajiye wayar a kan gado, wani irin tagumi ya zuba zuciyarshi na kukan rashin abin da ta dade tana dakon so, yafi awa biyu zaune a haka... Da wuri ta gama komai ta ciro wayarta a charge ta kwanta tana game, bini bini ta duba lokaci, ta kosa taji wani irin sakone wannan da har yake da lokacin badashi, ganin da tayi goma ta gifta harda minti goma yasata fara rubuta mishi sako, kafin tagama taji karar shigowar sako, da sauri ta goge ta bude sakon... *A rayuwa kowa yana tafe da kaddararsa, duk wanda Allah ya rubuta kaddararka ta zama tare dashi ne, to baka da dabara sai ka zauna dashi, naso kiyi zurfin karatu ta yadda zaki kere wasu matan kema a sanyaki cikin jerin masu ilimi sannan kiyi aure... amma hakan bazai yiwu ba saboda kaddararki batazo a haka ba, _I love Nadeeyah_ .... wannan itace kalmar da dan uwana yace in isar miki, Musaddiq na matukar kaunarki Nadeeyah, da fatan zaki amshi soyayyarshi, domin kun dace matuka, kuma nasan bazai barki ki zubda da hawaye ba, Allah ya barku tare kanwata take care.....* Tana kaiwa karshe taji wani irin jirin da Allah ya taimaketa a zaune take, dan ta fadi, Ya Musaddiq ke sonta, "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ya zama dole gobe tayi shirin tafiya Gombe kuma ta zauna a can, ina zata iya da bala'in Badar, su Anty Raudha, uwa uba Mummy da ta dau burin duniya tasa a kan shi, inaaa samm bazama ta taba nuna taga text dinnan ba, da sauri ta kashe wayarta ta dukunkune cikin bargo.... *MAFARKI* _Hannu tasa ta cire akan farar fuskarshi da ta koma jaaa saboda kukan da yaci, "rau rau idonta yayi murya ta fara rawa tace "Yaa Hilal, me ya sameka, wanene? Hannunta kawai ya rike dan kukan yaci karfinshi ya kasa magana, hawayen dake makale cikin idonta ya fara zuba kamar fanfo, a shagwabe tace "Dan Allah ka fada min, menene? Zaiyi magana kenan ya hango wani farin haske dan karami ya doso inda suke, hannun Nadeeyah ya rike yana janta yana fadin ta kyaleshi tazo su tafi, mikewa tayi duk da kankantar haske haka ya rinjayeta ta dinga binshi tana waigen Hilal da ya sunkuyar da kanshi kasa sautin kukanshi ne kadai ke tashi a gurin.... A firgice ta tashi zufaa duk ta jikata, janyo wayarta tayi da sauri ta kunnata, bata bari ta gama settling ba ta latsa number Hilal, lokacin karfe 1 a nigeria, tasan dakyar yanzu in bai yi bacci ba, saida ta kira sau uku bai daga ba, kwanciya tayi taji duk babu dadi dan so takeyi taji ko lafiyarshi kalau, yana idar da Sallah ya bi bayan kiran da tayi mishi, hannu na rawa ta dauka tace "ina wuni? "Kwana dai Nadeeyah ya fadi murya a dashe, "umm haka ne, ba kayi bacci ba? dama bacci ne ya daukeni kuma bani da charge shiyasa na kiraka saboda tunin sakon.. "yasani sarai ta gani, danne zuciyarshi yayi yace "mantawa nayi kanwata kuma surukata, bari in fada miki da baki amaryar Small uncle, yadda ya fadi murya na rawa ya sanyata kashe wayar da sauri, dana sani ta dinga yi dan yanzu ya tabbatar mata a kunnenta, Allah ya sani bata kin Musaddiq amma koda wasa bazata taba iya aurenshi ba, komawa tayi ta kwanta tunane tunane marasa dadi suka dinga zuwan mata har wani baccin ya dauketa.... A parlor ta zauna da asuba tana jiran ganin Daddy ya dawo daga Salla, ga mamakinta tare suka shigo da Musaddiq, dama ita ke tashinshi Sallar asuba to yau taki zuwa, tasan Daddy ne ya tasheshi, Har kasa ta tsuguna ta gaida Daddy, amsawa yayi hade da cewa baki koma bacci ba, "gyada kai tayi tace "eh Daddy dama ina son in tambayeka ne, cikin palon ya shiga ya zauna yace "zo zauna inji, kusa dashi taje ta durkusa tace "Daddy mun gama jarabawa, dan Allah ina son inje Gombe, tare zamu tafi da Husna, fadada Murmushinshi yayi yace "jiya muka gama magana da mamanku, ku shirya jibi Malam Ali zai kaiku, godiya sosai tayi mishi ta mike ta shiga kitchen, shima sama ya wuce dan bacci zai koma saboda lahadi ce babu aiki.. Saida yaji Daddy ya rufe kofar dakinshi sannan yayi saurin zuwa kitchen din, tsaye ya sameta a kofar shiga kitchen din tana jiran su shiga daki itama ta fito ta shige daki, Tana ganinshi tayi saurin juyawa zata koma ciki, shan gabanta yayi da sauri tsayinshi yayi mata rumfa babu abin da take gani a gabanta sai shi, jan hijab dinta tayi ta rufe bakinta tace "zanyi aiki ne, "nima shi zanyi ya fadi yana kwaikwayonta.. Gefenshi tabi zata wuce taga yasa hannu ya tare gurin, marairaicewa tayi tace "dan Allah ka matsa, ko baka san Daddy ya karya da wuri? nade hannuwanshi yayi yana murmushi yace "sai kin yarda muyi tare, gyada mishi kai tayi alamar amincewa, yauwa ya fadi hade da jan hannun jallabiyar shi, dankali ta debo ta dauko abin ferewa guda 2 ta mika mishi daya, karba yayi yana dariya yace "Allah sa dai kar in yanke, "in ka yanke zaka hakura ai ta fadi itama tana dariyar, "har so kikeyi in yanke ko? "Kai ka fada nidai bance ba! "Kin ce mana, ya fadi a shagwabe kamar karamin yaro, dariya tayi hade da tattara dankalin ta juya mishi baya ta cigaba da aikinta, "An fada miki sakona?? Wani irin faduwar Gaba taji da ya jefo mata tambayar, bata samu bakin amsashi ba ta cigaba da aikinta hannunta na rawa, Gabanta ya dawo yasa hannu ya dago fuskarta, da sauri ta runtse idonta tace "wani sako? In abinci ne kasan yanzu zan gama, "uhm ga acici ko? To wannan sakon yafi cikina muhimmaci, Hilal bai fada miki komai ba? Ya karashe tambayar cike da kasalar da soyayyarta ta sakar mishi, turo baki tayi hade da ture hannunshi tace "ni bai fada min komai ba, hannu yasa a aljihu ya dauko waya ya fara latsata, da sauri ta daura hannunta kan wayar tace "Dan Allah yaya Musaddiq ka bar wannan maganar, yin soyayya ni da kai ba abu bane mai yiwuwa, "dalili?? Ya tambaya fuskarshi ta nuna alamun damuwa, rasa abun ce mishi tayi kawai tace "saboda inada wanda nake so, zoben dake makale a hannunta ta nuna mishi tace wannan zoben alkawari ne, kuma kasan babu kyau karya alkawari, Hannunta ya rike a hankali yana shafa zoben zuciyarshi kamar zata soye saboda azabar radadin da take yi, iya karfinshi yasa ya fincike zoben a hannunta, tana kallonshi ya sa hakori ya karyashi yayi wurgi dashi ta window, kallonta yayi da wani irin yanayin da bata taba gani a tare dashi ba yace "koma waye saidai yayi hakuri dan ba samunki zaiyi ba, ke tawa ce ni kadai, kin gane ko? Kasa tayi da kanta hawaye ya fara zubo mata tace "kayi hakuri, ina sonshi sos---- *Nadeeeyah....* ya fadi da karfi rai a bace kamar namijin gaske, sautin kukanta da yaji ne ya sa jikinshi mutuwa, hannu na rawa ya dago fuskarta ya fara share mata hawayen, "kiyi hakuri ki daina kuka, bazan iya jin bakinki ya furta san wani bayan ni ba, bazan jure ba, rage murya yayi yace "dan Allah ki soni ni kadai, kamar dada ingizo kukanta yayi saboda bata son ya matsa su shiga cikin matsala tare, ganin yayi mata tsawo sosai ya sanyashi rage tsawonshi daidai fuskarta, "Nadeeyah---- "dan Allah kayi hakuri ta katseshi cikin kuka, "wai dame zan hakura ne? ya za'ayi in hakura da abun da nake so, kin san bazai yiwuwu ba, ya karashe yana daura hannunshi a saman idonta, "ki daina min kuka, bana so, in ba so kikeyi inyi ba nima, kiyi hakuri kinji? ki manta dashi ga dan uwanki, kinsan nafi sonki, kuma kema kina sona, zaki fi kula dani, abinci na, komai na, "Ni bana sanka ta fadi tana goge fuska da hannunta, saboda shaukin so dake dibarshi baisan sanda ya hada jikinshi da nata ba ya kankameta hade cewa "zaki soni sosai, Fiye ma da kanki Ma... Fiye da komai a duniya... lumshe idanuwanshi yayi ya cigaba da fadin *I love yhu Nadeeyah, more than life it self......* Innalillahi wa inna ilaihir rajiun..... maimata Kalmar Mummy tayi sau uku tana tafa hannun cike da mamaki da takaici....... Mrs Tijjani Shattimah...... [05/04 10:42 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣4⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Na shiga uku ni Zainab! yau me zan gani a cikin gidana, Da sauri Musaddiq ya mike har takalminshi daya na fita a kafarshi yace "me kika gani Mummy? "Ubanka na gani ta fadi a harzuke, abin da kukeyi kenan Musaddiq? yau ni na shiga uku na lalace, Oooh wato shiyasa kullum kike hanyar dakinshi da nufin tashinshi a bacci, ashe zuwa kikeyi ki koya mishi yadda mace da namiji suke jiyewa kansu dadi, yanzu Nadeeyah har kinyi girman da zaki koyawa namiji yadda zai dinga yi miki kiji dadi, *DANKARI!* lallai wannan abun babba ne, "Wai Mummy me ya faru ne? babu abin da mukayi fa, kawai ina taya---- zan ci maka mutunci in ka sake yi min magana, wallahi kana cewa takk zan kwada maka mari, sakarai wanda bai san inda yake mishi ciwo ba, maza ka biyoni.... kallon Nadeeyah dake tsaye tana share hawaye tayi tace "To munafuka maza ki wuce daki ki jirayi hukuncin da zan miki, yar iska mara mutunci, Rai a bace Musaddiq yace "ki daina zaginta Mummy, me tayi miki da zafi har haka kike kiranta da munanan kalamai, haba.... "Bance karka sake samin baki ba, zo ka fita ka wuce sama gani nan zuwa, Saida ya bari Nadeeyah ta fita sannan shima ya fita ya haye sama yana kunkuni dan shi samm baiga abin da sukayi ba..... "Ashe yarannan Iskancinsu sukeyi, wallahi da wani ne yazo ya bani labarin cewa yaga Musaddiq da mace a yadda na gansu wallahi bazan yarda ba, dan rashin kunya a cikin gida, ita kuma dan ta gama zama yar iska harda kankame wuyanshi.... *Zainab....* Daddy ya daka mata tsawa da karfi dan yaga tana neman wuce gona da iri, shuru tayi tana hucin bacin ran kalaman da ta jiyo danta da ta gama shirin kece raini dashi yana fadawa Nadeeyah, Nadeeyar Adamu mai gadi! da sauri ta runtse idonta dan wallahi tuno abun ma mugun taba zuciyarta yakeyi, kallon Musaddiq Daddy yayi fuska babu alamun wasa yace "ka fada min gaskiya, menene tsakaninka da Nadeeyah? Nasan ko kai zaka iya rungumar mace Nadeeyah bazata taba kusantar namiji ba saboda i have full faith in Suwaiba's upbringing, Shin me mahaifiyarka ta gani wanda ya sanyata yin wannan tunanin, kamar jira yakeyi mahaifinshi ya kai aya yace "Daddy dan Allah ka aura min Nadeeyah, wallahi ina santa sosai, "Bakin cikin kiran Sunan Suwaiba da Daddy yayi da kuma na kalaman Musaddiq su suka hadu suka dugunzuma zuciyar Mummy ta sakar mishi wata irin kazamtaciyar ashariya, kallo daya Daddy yayi mata tayi saurin dauke kai idanuwanta sunyi jaa saboda bacin rai, Maida hankalinshi gurin danshi yayi Zuciyarshi fess saboda dama abin da yake ma danshi addu'a kenan, "ka nemi soyayyarta? Daddy ya tambayeshi cikin sakin fuska, "Eh Daddy, ita ma tana sona, "Karya kakeyi wallahi, inaji tana cewa bata sanka, Yadda Mummy tayi maganar ya sanya Daddy dauke kai dan dariya ta kusa kufce mishi, jiya bata barshi ya runtsa ba saboda labarin Faida yar gidan *Hon Danjuma Diriss*, ta matukar cin burin bikin, shi kuwa a gurinshi sam bayasan danshi yayi auren *MATAUL HAYAT*, irin su Nadeeya ya dade yana fata, sai gashi Allah ya kawo mishi cikin sauki, waya ya daga ya kira number Husnah yace suzo tare da Nadeeyah, Mummy najin haka ta dauko wayarta ta tura text din gargadi zuwa ga Nadeeyah, A lokacin da ta tura text din a lokacin Nadeeyah da Husnah sun kusa taka step din karshe..... Cikin hikima Daddy yayi musu Nasiha ya nuna musu muhimmancin aure at early age, sannan ya kalli Nadeeyah yace "Nadeeyah kina da wanda kike so? Aure zan muku ke da Husnah... A kunyace taja hijab dinta ta kasa hada ido dashi, ya za'ayi ta iya furta bata san danshi na cikinshi, Daddy, Hilal, Anty Reemah, Musaddiq, Anty Raly, uwa uba Husnah da bata banbanta kanta da ita, duk a cikin zuriar mutumin dake gabanta yana tambayarta ko tana san danshi, ta ina zata iya butulce mishi, a cikin jerin da ta lissafo babu wanda bai taka rawar gani cikin rayuwarta ba, kuma Daddy ne ya samar dasu, dago kai tayi suka hada ido da Mummy ta harareta hade girgiza mata kai, dauke kanta tayi da sauri ta kalli Daddy dake sake jefo mata tambayar, gyada kanta tayi a hankali alamar eh, wanene shi? Dan Musaddiq yazo min da zancenki, in wani kike so shikenan sai sawun giwa ya taka na rakumi, wani irin girma ya kara a idonta ta kasa bashi amsa, "Ko Musaddiq din kike so? Hannun Husnah ta rike sosai ta kasa dago ido ta kalleshi bare ta bashi amsa, sau uku yana tambayarta tana yin shuru, dariya yayi yace su tashi tafi, Nadeeyah har tana tuntube da kofa tayi saurin fita, Maida kallonshi gurin Musaddiq yayi yace "To Malam ka shirya ma aure? nawa ka tara daga albashinka, nidai kasan ba ruwana nima da kaina na auri matata ya karashe cikin zolayar dukkansu biyun, Ganin ya saki fuska yasa Mummy zama a kasan kafarshi, "Dan Allah Daddy ka rufa min asiri, bai kalleta ba yace "Allah ne mai rufawa Zainabu, me ya faru? Hawayen bakin ciki ta fara yi tace "Yanzu kai farin cikinka ne danka guda daya tiloo ya kare anan, tsakani da Allah duk yadda manyan abokanka ke miko ya'yansu mata gurinka domin shi, sai kuma suga ya kare a gurin yar Mai gadi, yadda ta fadi abun ya soki Daddy Matuka, nan da nan fuskarshi ta sauya yace "akan Nadeeyah zan iya bata miki rai wallahi, idan kika sake kiranta da yar mai gadi a matsayinta na jininki wallahi hukuncin da zan miki ba mai dadi bane, cikin bacin rai ta mike tace "ba jinina bace, uwarta ce kadai jinina, kai kasan asalinsu ne, wa yasani ma ko ubanta barawo ne ya shigo cikinmu aka bashi aure, wallahi bazan yarda in hada jini da marasa asali in samu bara gurbi cikin zuri'ata da zanyi tunkaho da ita ba, "wallahi bazata sabu ba, ai nima ina da hakki akan shi, saboda haka wallahi indai ni na haifeshi bai isa ya auri Nadeeyah ba, Sam Daddy bashi da saurin hannu amma tabbas a lokacin yayi niyyar dauke fuskar Mummy da mari, a hankali yace "ke kika haifeshi, ke kuma nike iko dake, wallahi tallahi in har kikayi abun da auren nan yaki yiwuwa sai kin bar min gidana, kinga sai kowa ya nuna ikonshi, Asali kuma Nadeeyah bata da wanda ya fini, a yanzu na zama asalin Nadeeyah, ni ne ubanta, ni ne danginta da komai nata, sai ki je maiduguri ki binciki Asalin Alh Garba kyari mai fata, kallon Musaddiq yayi yace ka tashi kaje ka fara shiri daga bangarenka, ni a bangarena bani da matsala... jiki a sanyaye Musaddiq ya mike ya fita daga dakin, bai taba tunanin zai samu wannan matsalar ba, gashi kuma har ga Allah yana son Nadeeyah bazai iya rabuwa da ita ba, ga kuma Mummy zata yi mishi karan tsaye cikin rayuwarshi, tunane tunane ya dinga yi ya rasa mafita ya dauki wayarshi dan kiran Hilal, a kashe wayar take dan haka ya kwanta yanata sakar da bata da karshe.... Mummy kuwa tana fita dakinta ta wuce cike da bakin ciki ta daga waya ta kira Radiya da Raudha da ta dawo gida weekend tace su kira Raliya suzo su sameta a gidan Goggo, jin yadda muryarta ke rawa suka san ba lafiya ba, ko wacce hankali tashe ta shirya tafiya gidan Goggo... "Radiya ina zaki da sassafe?, ko abun karyawa bakiyi ma su Umma ba kuma kinsan ba ita kadai bace, shekeke ta kalleshi tace "ni ma uwata ke nema na, ko bani da ikon amsa kiran, su tashi su daura da kansu tunda dai suna da hannu, shikenan ni bani da sukuni saboda umma tazo, a'a wallahi bazai yiwu ba, Raees babban danta ne ya shigo yace "Mama wai inji Umma tace ki kawo mata ruwan zafi zata sha magani, wani dogon tsaki taja tace "maza jeka gurin Gyatum kace ta kai mata, hijab ta dauko tasa tana kunkunin da tun zuwansu gidan takeyinshi, Mikewa mijinta yayi ya kira kanwarshi Haleesah yace "tazo tayi ma Su umma abinci, sam baya jin dadin abin da Radiya kema yan uwanshi dashi kanshi, hakuri kawai yakeyi saboda darajar mahaifinta, yana shiga kitchen ya tarar da wata yar budurwa wacce shekarunta bai wuce sha tara ba. tana tsaye tana taya gyatum aiki, Da sauri gyatum ta gaisheshi ya amsa yana kallon yarinyar, itama tsugunawa tayi har kasa ta gaisheshi, kamanninta da gyatum shi ya tabbatar mishi yarta ce, saidai wannan din bak'inta mai kyau ne, da dara daran ido farare tass ga kyawun diri, har zai fita yace "Gyatum wannan yarki ce? Murmushi tayi tace "eh Alhj, auta ta ce, a gurin kanwata take a jos, a can take karatu, yanzu ma tazo hutu ne tazo tayani aiki, gyada kanshi yayi yace "Dan Allah ku taimakeni ku hada ma su Umma abun karyawa, in san samu ne ma su samu tuwon laushi, da sauri gyatum ta mike tace "har sai ka roka, Bar wanke wanken nan Fatima ki fara hada kayan karyawa, Cike da jin dadi ya fita dan ko abincin baiyi dadi ba yasan zai fita kunyar mahaifiyarshi da kannenta... Cikin kwarewa Fatima tayi miyar kukar da taji daddawa da dagargajajjen naman kaza, sannan ta tafasa kifi kadan ta sa citta da karumfani da tafarnuwa ta dakesu tsaf ta juye a cikin miyar, nan gida ya kaure da kamshi, tana gamawa suka shirya komai cikin cooler gyatum ta dama musu kunun gyada ta fito da garin kosai ta kwaba tasa kwai da albasa ta soyashi gunin dadi, manyan Coolers gyatum ta zuba abincin aka kai musu sannan ta zuba a kananan coolers ta ajiye wa mai gidan a dining, saboda farin cikin ganin tuwon malmala biyu Umma ta cinye, cike da jin dadi Haleesa ta kalleta tace "yau Umma taci abinda take so, san samu kullum da safe da dare a dunga miki tuwo, to hakan bazai yiwu ba, hidimar Maman Raees tafi karfinta, harara Indo kanwar Umma ta jefawa Haleesa tace "yau da tayi kasheta aikin yayi, Dariya Haleesa tayi tace "waya fada miki ita tayi, ita bata gidan ma, mai aikin gidan ce tayi, a daidai lokacin fatima ta shigo kwashe kayan abincin, albarka suka shiga sa mata har ta gama ta fita, umma dai da ido ta bita, a kullum tana ma danta adduar samun mace ta gari ba mai kyale kyale irin Radiya ba, yanzu din ma bazata fasa ba, ganin da tayi wa Fatima na farko taji ta shiga ranta, saidai bazata tilasta shi ya nemeta ba, za dai ta cigaba da addua, dan tabbas danta bashi da mace a gidanshi...... *Wai ina Hajiya Goggo Ma'u ne* Bangaren Goggo kuwa tunda Anni ta tare kullum cikin kunan zuci take, tayi asirin, tayi tsafin duk a banza saboda yin auren Baffa ma kadai karyewar alkadari ne, ga yawan abinci sadaka da Anni keyi kusan kullum domin nema musu tsira ranar Gobe kiyama, Tunda Goggo taga asirin nata yaki aiki saidai suyi ta cin kudinta sai ta hakura ta fara kunno wutar tashin hankali da masifa a gidan, idan Allah yasa ranar a dakin Anni Baffa zai kwana tofa babu bacci, dan ta dinga dukan kofar da muciya kenan, abun ba karamin damun Baffa yakeyi ba, Anni ke hanashi magana ta nusar dashi yanzu tsufa yazo, ba lokacin sa'insa bane, lokacin da zamu koma ga Allah ne, haka zasu mike suyi ta Sallah har ta gaji ta koma daki tana zage zage kamar wata yarinya, Yau ma kamar Kullum Anni na tsakar gida ita da mai aikinta suna girkin sadaka , Shinkafa ce da wake sai lettuce da su tumatur, suna gamawa aka fara zubashi a farantai ana fita dasu waje almajirai na rige rigen karba, makota masu karamin karfi suma suka shigo da robobinsu aka zuba musu, sunyi nisa sosai gurin rabo Goggo ta fito da bokitin fenti karami, fitsari ne a ciki ya kai rabi, nan ta doshi katuwar tukunyar ta antaya fitsarin a ciki, Da kyar Anni ta iya danne bacin ranta dan ta harzuka matuka, rufe tukunyar tayi tace "Harira, ki kira almajirai su kwashe abincin nan su kai ma dabbobi yau ranar tasu ce, tana kaiwa nan tayi hanyar dakinta, gabanta Goggo tasha ta dinga dura mata zagi, ita dai Anni dariya kawai takeyi tana fadin nagode, "ni yanzu ai bana fada, fada na yara ne da kuma wanda bai samu abinda yake so ba, ni kuwa me zance ma Allah, ai sai godiya, in nayi fada ai na butulce mishi, inaaa ni ba butulu bace, Allah ya gamai min komai, Hannu Goggo ta daga yana rawa zata kwadama Anni, da sauri Baffa ya rike hannun ya maida nashi kan fuskarta, Rike hannunshi Anni tayi tace "Haba dan Allah, ba girmanka bane, yanzu kaga ni bata mareni ba, ka mareta, da ka kyaleta wallahi bazai min tabo ba, Dan Allah mijina kar ka sake daga hannu a kan mace koda kuwa yarinya ce, kasan daraja garemu, sake matse hannun tayi tace muje kaci abinci ka fita nemo mana halal, Duk abin nan da akeyi akan idon Mummy da su Radiya ake yinshi, nan ran Mummy ya kara baci, a harzuke ta iso kusa da Baffa tace "Baffa duka? Dukan mahaifiyata Baffa, dama irin ukubar da take ciki kenan, habawa kamar an bude famfo Goggo ta fara kuka mai sauti, riketa Radiya tayi tana harara Baffa da Anni, Murmushi Anni tayi tace "cikin jin dadi take wannan ma tsauts----- rufe min baki, Mummy ta katseta cikin tsawa, "wacece ke da zaki samin baki a cikin magana ta, da wanda ya haifeni nake ba da ke ba, ki tsaya a matsayinki kin gane ko? Murmushin dake kan fuskarta bai gushe ba ta sake damke hannun Baffa dan taga yana yunkurin kwacewa yayi wata aika aikar tace "muje mijina, kar yunwa tayi maka lahani, Bayanta yabi suka bar su da sakkaken baki, Goggo kuwa kuka takeyi bilhakki da gaskiya wanda ya zame mata dan kullum, wannan kukan da Baffa ke sata tasan bashi ne, duk ranar da ya dawo hannunta sai ya kwashi kashinshi a hannu, dan walhi bazata barshi ba, bari dai asirin da Anni tayi mishi ya sakeshi, ita kuma ta daura nata, "a tunaninta asiri Anni tayi mishi dan yadda ya zama sauna akanta tasan ba lafiya ba, bata san kyautatawa da kissa yafi asiri tasiri a gurin namiji ba... Wata ashar Raudha da Radiya suka saki da Mummy ta labarta musu shirin da Daddy yayi na auren Musaddiq, Raudha ta daga murya tace "Wallahi bazai yiwu ba, wannan uwar daular da Musaddiq ya shiga ni kadai na santa, sannan yadda muka ci burin aura mishi Faida mahaifinta yasa a kara mishi girma nan take shine Daddy yake mana bakin ciki, wallahi bazata taba sabuwa ba, wallahi da ya auri Nadeeyah gara ya mutu ba Aure, haka nan ga inda ake harkar arziki mu kare a dangin tsiya, dangin marasa asali, wallahi da kaina zanyi maganin abun, karma kisa kanki Mummy, ki bani kwana Hudu zakiji labarin ya wargaje, badai ni ke zaune dashi a lagos din ba, zanyi brain washing dinshi, ki barni dashi kawai, ki nunawa Daddy kin amince sai mu cigaba da shirya musu kulli ta bayan kasa... Assalamu Alaikum, Anni ta fadi hade da shigowa dakin ta ajiye musu cooler, "ga abin kari da fatan ban shiga cikin maganarku ba, tsaki Mummy taja ta juya baya dan bata kaunar ganin fuskar Anni, dariya tayi tace "na barku lafiya, A kofar fita ne tayi karo da Raliya, da sauri Anty Raly taja baya ta tsuguna ta gaida ta, mika hannu Anni tayi ta karbi Fadeel tace "Maigidan da babu cefane, muje daki na baka abincin tunda dai ni baka bani ba, dariya kawai Anty Raly tayi tace "Baffa na ciki, "yana wanka Anni ta bata amsa cike da kulawa, Daki ta wuce da Fadeel tana tunanin kalaman Rauda, ta rasa irin wannan kiyayyar da ake ma Suwaiba da 'yayanta, amma in shaa Allahu zata nuna musu itama tanada rawar takawa cikin rayuwar su Nadeeyah... waya ta dauka ta kira Papy tace "duk abin da yakeyi ya barshi yazo yau, da yake bashi da wani aiki ran monday sosai sai ya fara shirin tahowa..... Ita kuwa Raliya hankalinta ba karamin tashi yayi ba dan bata san ko kadan Nadeeyah ta kasance cikin danginsu, tasan zata sha wahala matuka, ta riga ta gama auno mata zamanta gurin Taheer wanda take da tabbacin zata ji dadi a gurinshi, a take ta kalli Mummy tace "gaskiya Mummy zanje in samu Daddy, dan Nadeeyah na bukatar wasu familyn bamu ba, nasan in ta auri little, ba karamin wahala zata sha ba, nan take Mummy ta gimtse farin cikinta dan duk tunaninta Raliya ta dawo hanya ne, ashe ita wani tunanin takeyi daban, nan suka shiga zaginta sosai har ta hassala ta tashi ta fita ta wuce gidan su..... Tana shiga gidan ta wuce dakin Musaddiq, a tsaye ta sameshi yana taje gashin kanshi yana yar waka, Ajiye Fadeel tayi a kasa tace "Zo ka zauna Diku ina son magana dakai, ajiye brush din hannunshi yayi ya dawo kusa da ita ya dauki fadeel suka zauna tare, kallonshi tayi sosai tace "baka isa aure ba kanina, in kana so ma zan iya tsuguna maka, Dan Allah ka hakura da Nadeeyah, she deserve better life, kasan halin da zaka sata in ka aureta mahaifiyarka bata so, ka hakura da ita, in har kana santa zaka so ganin ta cikin farin ciki, Dan Allah Diku kayi hakuri, ka barta tayi aure cikin wani familyn ba namu ba, kaga akwai wani makocinmu Taheer, inaga ma zaka ganeshi, wanda yazo nan suka samu matsala da Hilal, wallahi yana mutuwar kaunarta, kuma inada assurance akanshi, dan na dade da sanin shi da mahaifiyarshi, mu hadu ni da kai mu samar mata farin ciki mai daurewa kaji kanina... "Ajiye Fadeel yayi ya kamo hannunta yace "Anty Raly bakya sona ko? Kin fi son bare a kaina, yanzu har in furta ina son Nadeeyah kuce in hakura, ke da nayi tunanin zaki mara min baya ki taimakeni in samu abin da nake so, sai gashi kece kike iya cewa ni bazan bata farin ciki ba, kin fi son wani ya sameta bani ba ko? wallahi ban taba tunanin matar da zan aura zata shiga cikin bakin ciki ta sanadiya ta ba ko ta yan uwana, bare Nadeeyah da ta kasance jinina, wallahi alkawari ne bazan taba bari Nadeeyah ta wulakanta ba, Dan Allah ki goyamin baya plsss, "share kwallar idonta tayi dan ita tana hango mishi abinda bai hango ba, tasan in ya auri Nadeeyah ya gayyatar wa kanshi da Nadeeyah rashin kwanciyar hankali kenan har su koma ga mahaliccinsu, ita kuma Sam bata san duk su biyun su kasance cikin kunci, A hankali tace "To Little, in Nadeeyah mafi alkhairi ce a gareka Allah ya baka ita, Allah ya baka juriya da jajircewa, Hannun Fadeel ta kama hade mikewa tace "Bari in tafi gida, Babanshi na hanya, mikewa shima yayi ya bi bayanta har suka isa parlon, Dakin su Husnah ta shiga dan yin magana da Nadeeyah, bai bita ciki ba ya nemi guri ya zauna a parlon yana nazarin maganganunta....... Mrs Tijjani Shattimah....... [06/04 9:42 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣5⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *Matar Mutum kabarinsa* Kwance ta samesu a kasa su biyun Husnah na rarrashin Nadeeyah da har lokacin idonta bai bar zubar hawaye ba, kan Nadeeyah Fadeel ya fada yana tsallen murnan ganinta, cikin kukan ta fara mishi wasa tana dariya mai kama da yake, Tausayi sosai ta bawa Anty Raly, gefen gado ta zauna inda Badar ke bacci ba ta san wainar da ake toyawa ba, kallon Nadeeyah tayi tace "Ashe haka kuma abu ya faru, to Allah ya sanya alkhairi, kanina ya kasa Taheer, ko da yake so so ne, amma son kai yafi, ga Musaddiq dole Taheer ya hakura, Tashi muje ku rakani gida ku tayani aiki sai mu fara tsara yadda zamu shirya bikin, Mikewa Nadeeyah tayi da sauri dan sam bata san abun da zai zaunar da ita a gidan yau har su hadu da Mummy, muje Anty, kinyi wanka ne? Anty Raly ta tambaya tana kallonta.. "In naje can zanyi, bari in dauki kaya, to kuyi sauri ina jiranku, ko minti biyu basuyi ba suka fito da maka makan hijabansu har kasa kamar wadanda akayi ma mutuwa, kallo Musaddiq ya bi ta dashi yana ta kokarin hada ido da kumburarrun idanuwanta taki yarda dan kanta a sunkuye yake, Mikewa yayi ya sa hannu zai karbi fadeel, noke wuya yayi ya kwanta a kafadun Nadeeyah, "iyye to sauka zakayi yaro kar sa min ita ciwo, maza sauko, "kaga kyale min yaro ya rungumi abar kaunarshi kafin ka dauke mishi ita ka kai can wata uwa duniya, gara yaji duminta da kyau, dariya sosai Musaddiq yayi yaje saitin kunnen Husnah yace "Amaryar tawa tayi miki, murmushi tayi ta janyo kunnenshi tace "sosai ma, amma ina jin tsoro, girgiza kai yayi yace "karki ji tsoro, babu abin zai faru, "i pray soo ta fadi tana rugawa da gudu dan ta isko su, shima saurin yayi ya fito, lokacin har sun shiga mota, Gefen da take zaune ya zagaya ya kira sunanta cikin wani irin siga, kife kanta tayi a bayan Fadeel saboda kunyar Anty Raly da taji, murmushi yayi ya sunkuyo daidai kunnenta a shagwabe yace "Zaki fita bance I love yhu ba, u knw dat i love yhu ko? "take care of urself for mee alone, tada motar Anty Raly tayi tace "mijina zai dawo karka sa in makara, hannu ya daga musu yace "zanzo in dauke su anjima, Husna ki kular min da ita, *I LOVE YOU* ya fadi da karfi yana dariya dan yasan ya hana mata sukuni...... Ta window Badar ta leko dan ganin wacce Musaddiq dinta ke cewa i love u, babu kowa a gurin sai Musaddiq dake tsaye cikin Nishadi, sai kuma gate da taga an rufe... nan ta shiga tunanin su waye suka fita daga gidan kuma wacece yake cewa I love you cike da annashuwa, Bayi ta shiga tayi brush ta fito parlon ko zata ganshi, tana fitowa taji tashin motarshi, wani irin zazzafan kishi taji ya taso ya tokareta, da kyar ta samu nutsuwa ta dan tsakuri abin kari kadan...... Karfe biyar da yan mintina Papy da Hafeez suka iso gidan Baffa, Saida suka ci abinci suka huta sosai sannan Anni ta koro mishi dalilin da yasa tayi kiranshi, "Nasan zakayi mamakin dalilin da yasa nace kazo, to dalilin mai karfi ne, nan ta labarta mishi abun da taji daga bakin su Mummy da Rauda sannan ta daura da cewa, a yau ba gobe ba ina son kaje gidan Alhj Muntari domin maganar auren Musaddiq da Nadeeyah, Alh Muntari ya cancanci ayi mishi fiye da haka domin ďan halas ne, mutumin kirki ne, zuciyarshi kamar auduga haka take, tunda har ya nuna ya son abun nan, dan Allah mu nuna mishi mun fishi so saboda mu saka alkhairi da mafificin alkhairi, Cike da jin dadi papy ya gamsu da maganar Anni kuma yayi alkawarin a yau zaije ya sameshi su tsaida maganar auren, bazai jinkirta ba dan kar shaidan yasa shi jin kunya..... Tare sukayi Sallar Isha'i a masallacin kofar gidan Daddy, Cike da murnar sake ganin shi Daddy yaja shi zuwa cikin gidan dan suyi dinner tare... Suna gama cin abinci suka hau hira Daddy yace "Yata tana shirin zuwa sai gaka kazo, dariya Papy yayi yace "Nima zuwan ďana nayi, neman auren yarka nazo yi, Allah yasa ba'a riga mu ba? Dariyar rashin fahimta Daddy yayi yace wacce yar a ciki?? Nadeeyarka nazo nemawa ďana Musaddiq, Ajiyar Zuciya Daddy yayi dan gaba daya tunaninshi ya tafi can gurin ďan Papy Jamal, fadada Murmushinshi yayi yace wannan dan naka sai a hankali, gaskiya kace ya nemi wata, ni 'yata sai Governor, Wata irin dariyar manya Papy yayi yace "kasan in da rabo shima zai taka wannan matsayin, mun kawo kokon baranmu, Allah yasa a cika mana shi, Duk wanda yaga fuskar Daddy a lokacin yasan yana cikin farin ciki matuka, "Na baka ita Alhj Abdallah, au Proff Saifullah, Nadeeyah ta Musaddiq ce, in shaa Allah, yanzu sadaki kawai zan yanke muku ku kawo, sai a sa ranar daurin aure, kunsan yar tawa mai tsada ce, ku kawo miliyan goma, Mikewa Papy yayi yana dariya yace "zamu kawo fiye da haka, mun gode kwarai Allah yasa ayi auren nan a sa'a, Ameeen ya Allah... Daddy ya fadi hade da mikewa, rakiya yayi mishi suna hira har suka karaso gurin motar, Motar Musaddiq ce ta kunno kai cikin gidan, yana yin parking suka fito suka karaso gurin su Daddy, cike da girmamawa Musaddiq ya gaida Papy, dagoshi yayi ya amsa hade da cewa "kana lafiya Ango, sunkui da kai Musaddiq yayi yana sosa keya, dariya Papy yayi yace "Allah ya tabbatar mana da alkhairi, Ameen Papy... Musaddiq yace ya ja baya ya tsaya, kallon Nadeeyah da Husna Papy yayi yace "baku tambayi mutuniyar taku ba, da sauri Husnah tace "Ay gobe zamu je Gombe in shaa Allah, "aaa to masha Allah sai ku shirya goben sai mu tafi tare karfe sha biyu, da Murnarsu suka amsa da "To zamu shirya da wuri, Gurin Hafeez suka zaga suka cikashi da Hira, saida suka fi 30mints a gurin sannan duk suka shiga cikin motar, Hafeez na kokarin tada motar Husnah tayi saurin dakatar dashi, number wayarshi ta bukata nan take ya karanto mata sannan yayi musu sallama suka wuce....... Tashin Husna Nadeeya ta dinga yi akan taje ta tada Musaddiq kar ya makara dan jirgin 6 zaibi zuwa lagos, mikewa tayi tana turo baki tace "kije ki tasheshi mana, ni bazan iya ba, hakuri ta shiga bata har ta samu ta yarda ta wuce dakinshi, kamshin turarenshi da taji ne ya bata tabbacin ya tashi, a tsaye ta sameshi yana gyara links din hannun rigarshi, "ashe ka tashi?, alhamdulillah na huta, dariya yayi yace aikin Mummy ne, tun dazu ta tasheni, ina matata? Hamma Husnah tayi tace "tana daki ita ta matsa min inzo in tasheka karka makara, sosai yaji dadi har cikin ranshi yace "muje in ganta kafin in wuce, A kofar shigowa suka kusa karo da Mummy rike da plate din indomie da kwai, Cup din hot choco kadai ya karba ya yi hanyar dakin su Nadeeyah, "Ina zaka je? Mummy ta fadi tana bin bayanshi, "amm zan je.... zan ---- dawo nan ka zauna kaci abinci, ko jirgin na ubanka ne in lokaci yayi bazasu jiraka ba, "Mummy, Nadeeyah bata da lafiya ne zai duba ta.... wani mugun kallo tabi Husnah dashi wanda yasa ta saurin murda kofa, "zo nan sakarya wacce bata san ciwon kanta ba, sum sum Husnah ta dawo inda Mummy take, kunnenta ta kama tace "wallahi kinji na rantse, wannan rawar kafar da kikeyi akan Nadeeyah in baki daina ba sai na ci miki mutunci, kuma in sake jin maganar tafiya Gombe a bakinki sai na tattaka ki, marar mutunci kawai.. ta karashe hade da dungure mata kai, kafa Husnah ta fara bugawa a kasa tana fadin "ni wallahi sai naje, hanyar dakin Daddy tayi Mummy tayi saurin tareta dan karansu na daren jiya baiyi mata dadi ba, yanzu in ta bari Husnah ta kai kararta tofah tasan bazai mata da kyau ba, "Ina matsayin mahaifiyarki kike kokarin bijire min har kike yunkurin kaini kara, ni zakuyi ma tawaye? Babu komai kuyi abin da kuka ga dama ta karashe tana matso kwalla, kewayeta sukayi suka shiga rarrashinta, dakyar ta hakura ta tasa keyar Musaddiq har mota sannan ne ta samu kwanciyar hankali..... Dubu dari biyu Papy ya bada kudin sadakin Nadeeyah, sai dubu dari na gaisuwa... cike da farin ciki Daddy da abokinshi Alh Abubakar suka karbi kudin, nan Daddy yasa biki wata biyu dan yana so ya samar musu gida a can lagos dan suyi nesa da duk wani tashin hankalin gida..... *(Shaff ya manta Raudha na lagos kuma duk tafi kowa matsala cikin 'yayan nashi,)...* ******* Woww mashaa Allah my little brother ya girma, yaushe aka sa bikin Daddy? "June amma bamu cire date ba, Maganar shirye shirye na kira inyi miki, inaga zan turo miki kudi ku shiga Dubai kuyi mishi siyayya, sannan zan bawa su Raliya su siyo wasu anan dan mahaifiyarku tace babu hannunta, dariya Anty Reemah tayi tace "ko sisinka karka kashe Daddy, zamu hadu mu hada mishi lefe na gani na fada, "wallhy naji dadin wannan hadin dan dama bana son Nadeeyah ta kufce mana, kullum cikin tunaninta nake.. "Ajiye kofin zobon dake hannunshi yayi ya dafe kanshi da ke sara mishi, "shikenan ya rasa Nadeeyah, tunda har akasa ranar auren ya fidda ranshi da tunanin ko Allah zai taimakeshi ta zamo tashi, maida kwallar da ke kokarin fito mishi yayi da sauri yace "wish u all the best Nadeeyah, Allah ya dawwamar dake cikin farin ciki... yasan Musaddiq na can yana nemanshi, haka itama Nadeeyar, bashi da karfin kunna waya yayi magana da ko daya daga cikinsu, dan raunin da yake ciki bazai barshi ya danne zuciyarshi ba, dole ya koka musu har su gane yana cikin damuwa, Yana cikin wannan tunanin yaji Anty Reemah ta dafashi tace "shine baka fadamin wannan abun dadin ba, yanzu sai mu fara shiri daga bangarenmu, dan bazan bar kowa yayi mishi kayan lefe ba, kai kuma sai ka shir---- Mum kinsan ina Msc, kuma mun kusa fara exams, dakyar zan samu zuwa, "cike da Mamaki tace "Hilal... Musaddiq ne fa, kada kanshi yayi cike da damuwa yace "Mum bance bazani ba, amma for nw banda karfin shirye shirye, plsss ku barni inyi karatu... Mikewa tayi cike da tausayin danta tace "take ur time dear, Allah ya bada sa'a... tana kaiwa nan ta wuce kitchen ranta duk a dagule..... Gaba daya Nadeeyah ta mance damuwarta tunda tazo garin gombe, gidan karamci, wani irin ji dasu Mami takeyi kamar ita ta tsuguna ta haifesu, Yawo kuwa babu gurin da basu je ba a cikin Gombe, ga wani shiri na musamman da Mami tasa akewa Nadeeyah wanda ya kara fitar da kyawunta ta ciko tayi bulbul, fatar jikinta sai sheki takeyi ga santsi kamar tarwada... Husnah da Hafeez kuwa wata shakuwa mai kama da soyayya ce ta musamman ta shiga tsakaninsu, tun Hafeez na dari dari har ya saki jikinshi sosai da ita, raba dare sukeyi suna tsaftattaciyar hirarsu mai ban sha'awa, da Papy ya lura da hakan ya kirasu duk su biyun ya tambayesu, Husna ce ta fara amsawa da tana sonshi, sannan ne Hafeez ya samu karfin gwiwar bada tashi amsar, farin ciki marar misaltuwa Papy ya shiga.. sallamarsu yayi hade da kiran Daddy ya labarta mishi, Daddy cike da jindadi yace to ai bazamu jira ba, gara a hade bikin ayi shi rana daya, nan suka gama tsara yadda zasuyi sannan sukayi sallama cike da jindadi.... Kwanciya Daddy yayi yana kabbara da girmama hukuncin ubangiji, wato ubangiji ya hanashi auren Suwaiba saboda wannan ranar da auratayya zata bullo a tsakanin jinin da suka yi tsaftattaciyar soyayya ta tsakani da Allah, lallai *kaddara* itace jigon rayuwar dan Adam, domin da ita yake yawo duk inda zashi.... ina ma Suwaiba zata dawo taga hukuncin ubangiji, taga yadda rayukan 'yayanta suka canza, wata yar kwallar murna ya share yayi adduoinshi hade da runtse idanuwanshi...... Hauka ne kadai Mummy bata yi ba da taji labarin hade auren harda na Husnah da suka gama maganarta da kawarta Hajiya Safara'u, babu irin masifar da batayi ba, shiko Daddy ko a jikinshi kudin kayan kitchen ma yayi mata transfer zuwa account dinta dan sauran da kanshi zaiyi su, Sa kai yayi ya fita ya bar gidan dan lagos ma zai tafi da daddare akan maganar gidan da aka samu... Kuka ta zauna a parlor tana yi sosai kamar an mata mutuwa, bakin cikin da take ciki yau har gwammaci dama bata taba sanin Daddy a rayuwarta ba, Badar ce ta fito tana hamma, duk wainar da ake toyawa a gidan bata da masaniyarsu dan ba zaman gidan takeyi ba, da sauri ta isa gurin Mummy tana tambayar abun da yasa ta kuka, Ganin da tayi wa Badariyya ya sa hankalinta dan kwanciya, dan wani abu da ya darsu a ranta, tasan Badariyya ce kadai zata iya yi mata maganin damuwarta... Hannunta ta rike ta sake rushewa da kuka tace "Badar na shiga uku, Musaddiq zai auri Nadeeyah, Hafeez kuma Husnah, kinji a inda zan kare a ya'yan da basu da asali, yayan mai gadi ni zainab..... Wani irin ihu Badar ta saki tace "Whattt? Nadeeyah zata auri Musaddiq dina.... ta fadi hannu na rawa tana dafe kirji....... Mrs Tijjani Shattimah........ [11/04 12:07 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣6⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Mikewa Mummy tayi zuciyarta ta fara sanyi na yadda taga Badar ta harzuko, tasan tabbas Badar bazata taba bari auren nan ya tabbata ba koda kuwa zai zama ajalin Nadeeyah... Hannunta ta kamo tace "Musaddiq dinki Badar, mun gama magana da wani malamina akan halascin aurenku, da murnata nazo na fadawa Daddy, shine yake cemin wai ai Papy Saif yazo mishi da maganar yanason hadin auren Nadeeyah da Musaddiq, shi kuma nan take ya amsa mishi saboda kinsan yadda Daddynku yake da s-any-in haaa--li, ni yanzu bansan yadda zanyi da raina ba, ta karashe da kuka sosai wanda yake nuni da tabbas tana bukatar taimakon Badar... Furzar da huci Badar tayi murya a kausashe tace "Wallahi bazai yiwu ba, na dauki alwashin saidai Musaddiq ya zauna babu aure in har ban halasta a gareshi ba a baya lokacin da kika ce ba aure a tsakanin mu,, bare kuma yanzu da na tabbatar na halasta a gareshi zan yarda ya auri wata, watar ma Nadeeyah, wallahi Mummy saidai ayi auren nan babu raina, bazan ma mutu ba, sai dai ita ta mutu, hannu ta daura kan kafadun Mummy tace "ki kwantar da hankalinki, kima daina kuka, kisa ma ranki salama yau zuwa gobe zakiji sabon labari, zaunar da ita Mummy tayi cikin tsorota da yanayin kalamanta tace "Badai kauce hanya zakiyi ba? Dariya Badar tayi tace "karki damu nace, badai kin yarda da batun aurena da Yaya Musaddiq ba? Gyada kai Mummy tayi tace "eh, a zuciyarta kuwa tana jin tsoron karyar da tayi ma Badariyya, tasan sarai in auren nan ya lalace wata rigimar ce zata sake bullowa, kauda zancen tayi a zuciyarta, dan tasan yadda zata tafiyar da Badar bayan maganar auren Nadeeyah ta lalace...... *KUNGAMAR GARZAR* Washhhhh...., na taka qaya, duba min kigani Lawisa Lawal, hannunta Lawisa ta kama tace "sauri fa zamuyi Badar, kina ganin har la'asar tayi bamu karasa ba, dajin nan is very dangerous, nima Anty Laurah ta taba kawo ni, ban taba tunanin ma zan gane ba, dan Allah ki dago kafa, "dingisawa Badar tayi ta sake yin ihu hade da tsugunawa ta cizge kayar, bata damu da jinin da ke bin kafarta ba tabi Lawisa suka dinga sauri cikin dajin, minti talatin suka kara suka isa gaban wata katuwar bukkar fulani, almajirai ne kewaye da ita suna kara kaini da alluna, sai gungun kyawawan yaran fulani daga can nesa suna wasan kasa, matan na yar gala gala... Suna shiga gidan suka bangaji wata yar budurwa da ta arto a guje tana ihun kuka, wata katuwar farar mace fuska duk kalangu na biye da ita da bulala a hannu tana zaginta da fulatanci, ramawa budurwar takeyi tana fadin "Allah ya isa muguwa, azzaluma, bazan yi wanke wanken ba, in kinga dama ki kashe ni, ganin su Badar ya sanya matar yar da bulala tana fadin "marabanku, ku shigo daga ciki, a darare Badar ta kalli matar sannan ta kalli Lawisa dake kokarin janta zuwa ciki, zatayi magana kenan Lawisa tayi mata alama da tayi shuru su shiga daga ciki, a tsorace ta fara bin Lawisa da matar har suka isa wata lafiyayyar bukka dake kawace da adon fulawoyi, "babu abin da ke fitowa a bukkar sai hayaki mai karfin kamshi wanda ka iya buga kan mutum in ya shakeshi na tsawon minti goma, da sauri Badar taja gyalenta ta rufe hancinta gabanta na tsananta faduwa, a zuciyarta tana dana sanin biyo Lawisa gurin nan da tayi.. " *Lawisa ta dade tana bata shawara akan tazo suje inda zata karkato da hankalin Musaddiq da Mummy su yarda da aurensu koda kuwa bai halasta ba Badar taki, saboda a ganinta zata iya shawo kan komai saboda irin soyayyar da Mummy ke mata, jin batun auren Nadeeyah da Musaddiq shi ya harzukota ta nemi Lawisa suka taho ba bata lokaci, bata san azal ke kiranta ba* katse mata tunani Lawisa tayi tace "ance mu shiga Badar, firgigit Badar tayi ta cire takalmanta suka fada cikin bukkar, Suna suka saka kafarsu a ciki hankalinsu ya gushe suka manta inda suke, sai ganin kansu sukayi a cikin wani kayataccen parlon da duk iya maitar mutum bazai san ta inda yabi ya shigeshi ba, jiki na rawa Badar ta damki hannun Lawisa suka zauna a gaban wanda Badar tafi zaton shine bokan, gefenshi kuma saurayi ne dan shekarun da basu fi talatin da biyar ba yana zaune shima da kayan tsubbun a gabanshi, dago kai saurayin yayi ya kallesu yace "Badariyya da Lawisa barkanku da zuwa, nan cikin Badar ya duri ruwa saboda tsabar tsoron da taji, a ina yasan sunan su? Tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan, "Nasanki tun ranar da kika duro duniya Badariyya, babu motsinki da ban sani ba, har wannan zuwan da kikayi na sani, dan ni na shiryashi, gefen da Lawisa take ta kalla nan da nan ta saki hannunta saboda wata iriyar dariyar da takeyi mata mai cike da ban tsoro, mikewa lawisa tayi tana dariyar da ta ke amsawa a cikin dakin, sannan ta Kalli Badar tace "ke matar dan sarkin mu ce, wannan shine *Sarkin bokaye Shahalu* sai danshi *Yareemah Suhailu* karki damu Badariyya, ni kawarki ce kamar yadda kika dauka, amma ki sani na zo gareki ne saboda wannan ranar da zan cikawa Sarkin mu burinshi, "ni ba mutum bace, amma sarki da yareemah mutane ne kamar ke, kyakykyawar mu'amalar dake tsakaninmu dasu ita ta janyo har na taimakeshi, ki kwantar da hankalinki yau kinzo inda kaddararki take, zaki ji dadin zama dashi da yan uwanshi, bissalam kawata Badariyya.... ta karashe tana daga mata hannu tana dariya har ta bacewa ganinta, wani irin ihuu Badar ta saki tana bin gurin da lawisa tabi, "wayyo Allah Mummy ki taimakeni, wayyo Allah Daddy, na shiga uku na lalace, wayyyyyo Allah na, keeeeeeee!!! Wata irin tsawa taji daga bayanta wacce ta sanyata dunkulewa guri daya, murya a kausashe Sarkin bokaye yace "Karki sake yi min ihu anan, kin san Allah dama? In kika sake kiramin sunan Allah anan zan cire idon ganinki, na rantse da abun bautarmu *GARGAZ*, Kee... *Kande* ya kwala kiran katuwar matar da ta shigo dasu, Da sauri ta karaso ta tsuguna a gabanshi tace "Ranka ya dade gani, "Maza ki dauketa ki kaita cikin gida dakin da *Halyo* ya gyara jiya, an sa gado da katifa dama, jiran zuwanta kawai akeyi, sannan ki jawa *Gimbiya Sailuba* kunne, babu ruwanta da kishi da ita, domin wannan itace matar Suhailu ta farko, tun kafin tazo duniya Mahaifiyarta ta bashi, sai yau *Garzar* ya bamu ikon dawo da ita gurin mijinta, cike da girmamawa Kande tace "to ranka ya dade, an gama, nan ta damki hannun Badariyya tana janta a hankali Badar na turjewa tana ihun neman dauki a inda babu mai jinta sai Sarkin sarakunan da biyayyarshi bata dameta ba, sarkin da a sati baifi ta gaisheshi sau daya ba, sarkin da ya hore mata lafiya da kuma abun da lafiyar zata ji dadi... *ALLAH AZZA WA JALLAH* shi kadai zai fidda Badar daga kangin da take ciki...... *SHIN INA BADAR TA FADO* _(fadan da yafi karfin ka ya kai dan uwa, bar wa Allah yayi maka shi, domin shine mai dukkan karfi.......)_ Tun Mummy na jiran Badariyya a daki, har ta koma leke ta window da kofa, karfe 11 agogon parlon ya buga, a tsorace ta sake kiran Badar karo na ba adadi, har lokacin wayar a kashe take, zama tayi akan kujera ta Shiga jero salati, "Ina Badariyya ta Shiga har wannan lokacin, ya ilahi kasa ba wani abun bane ya same ta, tagumi tayi tanata sambatu dan hankalinta Sam yaki kwanciya, Har karfe 1 na dare babu labarin Badar, sai a sannan ne ta fara kiraye kiraye waya tana kuka Dan gaba daya ta gama tsurewa, duk wanda ta kira wayarshi a kashe, wayar Daddy ce kadai ta shiga, shi kuma bai dauka ba saboda gajiya da yayi, yar da wayar tayi ta fashe da kuka tana dana sanin barin Badar ta fita, gaba daya idonta ya rufe burinta kawai a fasa auren Nadeeyah da Musaddiq, Sam bata hango matsala a fitar da Badar tayi ba, sai gurin hudu bacci barawo yayi gaba da ita, ana idar da sallar asuba Daddy ya kira ta saboda ganin misd calls dinta da yayi, firgigit... ta farka tana fadin Badariyya, "Hello Badariyya kina ina?, gyaran murya Daddy yayi yace "ina Badariyyar ta tafi? Wani irin kuka Mummy ta fashe dashi tace "Badariyya bata kwana a gida ba, na rasa inda ta tafi, na kira wayarta har naji ba dadi na kasa samunta, cikin halin ko in kula Daddy yace "kinsan duk inda take zata dawo, ki kwantar da hankalinki, ai ba yarinya bace, big girl ce.. na turo miki kudin kayan kitchen, zuwa anjima kuje ku siyo, bana son muyi abubuwa cikin kurarren lokaci, yana kaiwa nan ya kashe wayar, Ajiye wayar tayi ta cigaba da rero kuka, "da wani baki zata fada musu cewa tana da masaniyar inda Badar taje, wa zata fadama ya fahimceta har ya taimaketa, Goggo ce ta fado mata a rai tayi saurin kiranta, saida wayar ta kusa katsewa sannan ta daga dakyar, yanayin muryarsu daya ko wannensu cikin kunci yake, Mummy ce ta fara fada mata damuwarta, nan take Goggo tace "rabu da ita zata dawo da kafarta, kin manta haka uwarta ma tayi, kina zaune zata dawo, ke dai kije kisan yadda zakiyi wadannan matsiyatan kar su shigo cikin zuriarki, dan babu alkhairi a duk inda suka sa kafa.. da kalaman Goggo hankalin Mummy ya kwanta ta mike tayi wanka tayi sallah sannan ta zauna tana tunanin ta inda zata bullo, kawarta Hajiya Martai ce ta fado mata, nan ta kirata ta kora mata matsalolinta, minti talatin Hajiya Martai ta bata tace ta sake kiranta zata sa wani malami yayi bincike akai, ko minti daya bata kara akan minti talatin din ba ta kirata, a sanyaye Hajiya Martai tace "Hajiya zainab wannan auren babu abinda zai hana shi sai mutuwa, akwai rabo mai karfi a tsakani, kuma akwai wani babban al'amari da zai taso marar dadi wanda Allah ne kadai ya barwa kansa sani, saboda haka shawara ce zan baki, in dai ba so kikeyi ki mutu ayi ba, to ki kwantar da hankalinki ayi kina da rai, bayan an daura sai ki shigeta kuyi mata illa har su rabu, amma tabbas akwai aure a tsakaninsu, Ajiyar zuciya mummy tayi hade da share kwallar takaicin da ta ziraro mata tace "to Hajiya martai nagode kwarai, in shaa Allahu naji shawararki, kuma zanyi amfani dasu... shawarwari ta dinga bata marasa amfani na yadda zata kori Nadeeyah cikin kankanin lokaci, sunfi minti talatin suna waya sannan sukayi sallama, sai a lokacin Mummy taji wasai ta mike da karfinta ta shirya zuwa kasuwa...... Shirye shiryen biki sukeyi ta ko wani bangare, Mummy da ahalinta sun danne bakin nufinsu sunata kankajere suna hidima da jikinsu da kudinsu, kowa ya manta da lamarin Badariyya saboda Mummy tayi musu karyar ta tafi cotonou makaranta, amma a zuciyarta kullum sai tayi tunanin inda Badar take da har wannan lokacin bata ziyarci gida ba, in ta tuno kalaman Goggo sai ta kwantar da hankalinta ta cigaba da cigaba da zuba idon ganin dawowarta... Anni itace ta dauki nauyin su cincin da dublan da sauran tarkacen garar amare, ita kuwa Goggo ba baki dan mugun tsoron Anni yanzu Allah ya daura mata, ta kan ce "ina zata iya da wannan matsafiyar, saboda duk asirin da ta dunkulo sai dai ya koma mata ko ya wargaje, ita a ganinta tsafin Anni ne yafi nata, bata san dogaro da Allah yafi tsafi karfi ba.... Tun ana saura kwana uku daurin aure Anty Reemah da Papy suka iso, babu yadda basuyi da Hilal ya biyo su ba, yace sai daren daurin auren zai shigo, hakanan suka kyaleshi sukayi gaba abinsu... Duk yadda suka so suyi bidi'a Mummy ta hana a cewarta Daddy yace bayason komai sai daurin aure, kawayenta ma babu wanda ta gayyata sai makota na kusa da ita, Bikin ya kasance na yan family kawai sai kawayen su Anty Raliya da yan Gombe da yan maiduguri dangin Daddy... Ranar jumm'a ake kamun amare, a cikin gidan akayi decoration wanda ya kawatu da kore da kumbo, Blue kayan kanuri suka sa dukkansu, fuskar nan tasu ta dau kwalliya gwanin kyau da sha'awa, kawayen Husna da yan tsirarrun na Nadeeyah sunyi ankonsu wanda ya dace da kayan amaren, sai su Anty Reemah suma sunyi nasu lafaya mai kyau da tsadar gaske, babu abin da ke tashi a gidan sai kidan piano da wani kwararren mawaki keyi, kida ne taushi mai ratsa zuciya, Ruwaidah da Zainab ne kadai a cikin tsakiyar filin suna rawarsu ta yaran da basu da wata matsala a rayuwarsu, sai gefe yaran makota suma suna rayawa dan kar a barsu a baya, Muryar inna Surayya (M.C Surry k mata) ce ta karade gidan da barkwancinta, nan manya da yara suka hau dariyar labarin da take bayarwa, Hinad... Anty Reemah ta kwala kiranta da karfi.. da dan gudu ta karaso gurinta bayan ta amsa tace "Mum gani, wata leda ta mika mata tace "maza ki kaima Uncle links dinshi, nasan yana can bai gama shiryawa ba, cire dankwalin kanta tayi ta karbi links din ta wuce dakin Musaddiq... A zaune ta sameshi ya tasa kaya a gaba yana tsaki, ya rasa taka mai mai kayan da zaisa cikin sabbin kayan da ya dinka, gashi sai kiran wayar Nadeeyah yake taki dauka, rabonshi da ya sata a ido tun ranar da ya koma lagos, sai jiya da suka iso daga Gombe, shima daga nesa ya hango ta, gaba daya ta toshe duk wata kafar da zata hada da shi, a waya ma saidai in ya kira Hafeez sannan ne zata amsa, shima bawani maganar kirki, zata kashe... "Uncle baka shirya ba? tsaki ya sake yi yace "Hinad ban shirya ba, zo ki zabar min kaya, banason inyi shigar da zata banbanta da ta matata, "Ummm ta fadi tana dariya hade da janyo wata danyar blue shadda taji aikin dark blue, tace "wannan is okay uncle, tun dazu uncle Hafeez ya shirya kai kana zaune, plss hurry up, kayan ya kwasa yace "i hate Hilal, shi ya kamata yayi min wannan ya wani ki zuwa, "kunfi kusa ta fadi hade da ajiye links dinshi a kan kayan ta fita waje..... Laaaaa Ya Hi---- toshe mata baki yayi hade da rungumeta yace "nasan yayi fushi, karkiyi magana yaji, jeki kawai, sakinshi tayi ta wuce tana dariya.. Makale lnks din yakeyi yana tsaki hade da mita, shi kanshi in ka matseshi baisan me yake fadi ba, yadai san rabin mitar akan Hilal da Nadeeyah ne da suka barshi all alone... karin hular dake ajiye akan gado Hilal ya gyara hade da matsowa cikin sanda ya daura mishi a kanshi... *Kyari is nw Complete* ya fadi hade da saita fuskarsu ta kalli mudubin, wani irin farin ciki Musaddiq yaji wanda a iya rayuwarshi bai taba jin irinshi ba a ganin Hilal sai yau, Da sauri ya rungumeshi yana fadin "idiotic being, sai yau kaga daman zuwa, komai ni kadai nayi, from lagos to kaduna haka na dinga wahala sai Zubair dake dan tayani, i hate you banza kawai, ya karashe yana dukan kirjin Hilal, dariyar yake Hilal yayi yace "da haka zaka zama jajirtacce mr Soft, maza da wahala aka sansu, kaga yanzu zaka shiga sahun cikakkun maza, dole komai kayi ma kanka, "amma akwai support ko? Musaddiq ya fadi yana hararar Hilal, dukan kafadunshi Hilal yayi yace "nd here i am, kasan bazan taba barinka kayi komai kai kadai ba, "na nawa kuma,, muje kasa kayanka gasu can a drawer, Musaddiq ya fadi yana jan hannun Hilal, Hannunshi Hilal ya rike sosai ya tako har inda yake ya kalli cikin idonshi yace "Musaddiq promise me one thing, alkawari daya kawai zakayi min, "nayi maka alkawari dan uwana, fada min menene, nan idon Hilal ya fara kokarin canza kala yayi saurin cewa "kayi min alkawarin duk runtsi duk wuya bazaka rabu da Nadeeyah ba, bazaka sata kuka ba, kuma ba--- malam biyu ka fadi ga na uku na shirin biyowa baya, Musaddiq ya katse shi yana dariya, bari in sa maka su a one word, "Nayi maka alkawarin bazan taba cutar da Nadeeyah ba, bare har abubuwan da ka ambata su faru, are u happy? Ajiyar zuciya Hilal yayi yace "sosai, muje insa kaya, shaddar shima yasaka milk tasha cofee aiki sannan ya daura coffe hula mai ratsin milk, sunyi kyau sosai kamar dukkansu ne zasu angwance, wani bakin glass Hilal ya kwama a idonshi saboda gudun bacin rana...... Mrs Tijjani Shattimah....... [12/04 7:01 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣7⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Ganin ba kowa a parlon sai tsirarrun mutane ya sanya Musaddiq kama Hilal suka nufi dakin su Nadeeyah.. Zaune suke... kowacce an rufe mata kai da mayafi suna jiran azo a kirasu, kawayensu na gefe suna daukar hotuna hade shewar murnan first kawance a rayuwarsu, *Amal Mus'ab* na ganin sun shigo tayi saurin isa gurinsu tana murmushi, kallon Musaddiq tayi ta miko mishi hannu tace "oya sako first step kafin muje second step, cikin rashin fahimta yayi dariya yace "ban gane ba, hannu Hilal yasa a aljihu ya ciro bandir din yan 200nts ya daura a kan hannun Amal, "Uhmmm nt bad ta fadi tana juya kudin, lallai ka iya zuwa ghana, guys bazamu sha wahala gurin abokan ango ba, but next time mr man a kara hannu ta karashe cikin zolaya.. Dariya yayi yace "next step? Haifa ce ta matso tace "a cikin su biyun nan ango ya dauki matarshi sai su fita kafin dayan angon ya karaso, nan dakin ya gauraye da ihun yanmata masu zallar kuruciya wadanda suke kan ganiyar shaukin soyayya, kallon duk su biyun Musaddiq yayi ya rasa kafar da zata sada shi da Nadeeyah, domin ko ina nasu a rufe yake, hatta yatsun kafarsu a rufe yake da takalmi, gefen da yake tsaye yabi dan ya gama sadakarwa itace a zaune a gurin saboda yadda gashi yayi tulluku a tsakiyar mayafin, Hannunshi Hilal ya janyo yace "kar kayi abun kunya Mr soft, ga matarka can ya nuna inda dayar take dariya Musaddiq yayi yace "har yaushe zaka iya tantance abun da bakayi ma kallo fin goma ko ashirin ba a zahiri, look Hilal, nasan komai game da Nadeeyah, everything saboda na ganta har ganin nata ya sanya ni na zamo cikin shaukin sonta, ganeta a haka bazai taba min wuya ba saboda tana makale a cikin zuciyata... dariya Hilal yayi a zuciyarshi yace "cikin jinina, a mafarkina, in my every breath kamanin ta kawai nake gani, Allah ya tsare akwai bakin glass a idonshi, da idanuwanshi sun nuna ma ma'abocin kallonshi irin tarin son dake dawainiya dashi, Karasawa kusa da ita yayi ya zauna hade da yi mata rada a kunne "My Young Barr--- bai karashe ba tayi saurin bude fuskarta, idanuwanta da suka tsaru da make up suka fara tara ruwa, saurin girgiza mata kai yayi hade da sakar mata murmushin karfin hali, wannan bakin glashin makafin ba karamin taimakonshi yayi ba dan da babu abinda zai hanasu ganin sirrin dake cikin kwayar idamuwanshi... "Ashe kina da kyau har haka kanwata?, ya fadi a hankali yana kokarin gyara mata mayafin kanta, "Nayi maka laifi ko? Yadda tayi tambayar ba tare da ta dauke ido akanshi ba ya sa shi saurin mikewa dan gab yake da rasa control din raunanannar zuciyarshi, da dariya Musaddiq ya karaso yace "na gama jin kunya, ace na kasa gane muradin raina, lallai ya kamata aci tarata.. Waje Hilal ya fita ko zai samu zuciyarshi ta dan mishi dama daman nauyin da tayi, Bq ya nufa inda su Hafeez suka Hinad na biye dashi a baya tana tambayarshi kudin liki, "kunnenta ya kama yace "baki damu da ki bani abinci ko wani abu ba, ke kawai kudin liki, ina Zee? "yaya sakar min kunne plss, Mum ce tace tasan zaka ci abinci fa, shiyasa ban samo maka ba, kuma Zee nima tunda na dawo saloon ban ganta ba, sakin kunnenta yayi ya ciro kudi a aljihunshi ya raba gida biyu ya bata, "yasan zasu bukaci kudin shiyasa yasa Galadanci yayi mishi canji tun kafin ya iso, Godiya tayi mishi tace bari ta kawo mishi ko nama ne, parlon ya shiga ya tarar da Hafeez a kimtse yana zaune yana jiran azo kiranshi, cike da zolaya ya dan naushi cikin Jamal dake kishingide yana game, mikewa yayi yana dariya yace "har ka iso, "wallahi kuwa.. ban dade da shigowa ba, mun sameku lafiya? lafiya lau Hafeez yace yana kallon idon Hilal, "yaushe ďana ya zama makaho? Ya tambaya yana dariya, shima Hilal dariyar yayi yace "fashion ne kawu karami, dariya mai sauti dukkansu sukayi suka hau wata hirar ta daban.... Inaa Amaryar take!!!! Hajiya Aliya ta tambaya hade da bankado kofar dakin su Husnah, lokacin Musaddiq na manne da ita kamar zai maida ita jikinshi, samm baiji kunyar kawayensu dake gurin ba, shigowar su Hajiya Aliya ne ya sanyashi matsawa kadan hade da gaishesu, amma har lokacin hannunshi na cikin nata.. Harara Hajiya Aliya ta watsa mishi sannan ta bude fuskar Nadeeyah da iya karfinta, "auuu kece amaryar, iko sai Allah, ashe Hajiya Zainab munafurtarmu tayi Hajja Asiya, "ashe dama tasan auren zumunci zasuyi ma dansu shine ta daura ma diyata dakon son da yake neman zamewa zuciyarta illa, waigowa tayi ta kalli Mummy da tayi tsamo tsamo saboda kunya da takaici tace "Wallahi tallahi Zainabun Muntari bashi kika ci, na rantse da wanda raina ke hannunshi ni Aliya bazan kyaleku ba, sai na sa kun muzanta a idon duniya, yanda kikayi wasa da rayuwar 'yata kema sai nayi da ta naki yayan, mu zuba mu gani, wuce muje Hajja Asiya ta karashe hade da buga kofar dakin tana huci, Kuka sosai Mummy ta fashe dashi hade da ficewa daga dakin itama, a rude Musaddiq ya saki hannun Nadeeyah ya bi bayanta hankali a tashe, itama Nadeeyar mikewa tayi tana share hawayen da ya ziraro mata tana kokarin bin bayan Mummy Anty Raly ta dakatar da ita, zaunar da ita tayi ta rarrasheta da kalamai masu dadi da kwantar da hankali, jakarta ta ajiye kusa da ita tace "ki kular min da jakar nan, yanzu zan dawo... Sau uku wayar dake cikin jakar na ringing Nadeeyah na kin dauka, saboda bata san bude ajiyar da aka bata, a na biyar ne ta bude ta fito da Wayar, *Tahir Legacy* ta gani a rubuce, da sauri ta ajiye wayar saboda wani irin mugun faduwar gaba da taji, "uncle Taheer ta fadi a cikin ranta, gaba daya ta manta dashi a cikin rayuwarta, gashi yanzu zata sake yi mishi mantuwar din din din, bai fasa kira ba har saida ta gaji ta dauki wayar zata kaima Anty Raly sai a sannan taga wani suna daban, *Aunt S 2* a gaggauce ta dauka tace "Assalamu Alaikum bari in kai mata... yadda yayi haddar sanyin muryarta dake yawan yawo cikin kanshi ya tabbatar mishi da itace, "My omri is going lv me, dagaske ne? Chakkk ta tsaya da tafiyar da ta farayi, cire wayar tayi a kunnenta ta sake kallonta dan ta tabbatar da ko dai sunan gizo yayi mata, maida wayar kunnenta tayi zatayi magana yayi saurin cewa "tell me plss, zama ta koma tayi tace "ina wuni, "Nadeeyah plss answr me, "ummm dagaske ne, ta bashi amsa a hankali... ji yayi gaba daya ya kusa zubewa a kasa, dama lokacin da yagani a status din sabrinah saida yayi jinyar magudanar jininshi na dan lokaci, hawayen da ya ziraro mishi ya share, yace "but why Nadeeyah, why?? Cikin rawar Murya tace "Kaddara ta ce haka, kayi min addu'a Allah yasa auren ya zame min alkhairi, kayi hakuri uncle, Allah ya baka wacce ta fini a komai da kake so, bata jira jin amsarshi ba ta kashe wayar ta dunkule kanta guri daya, dama dakin babu kowa dan Husna sun fita da Hafeez da kawayensu..... Kaga abun da ka janyo min ko Musaddiq, kaga irin cin mutuncin da ka janyo min gurin aminai na, yanzu gaba daya kawayena zasuyi Allah wadai dani, saida na fada maka Nadeeyah ba alkhairi bace a gareni ka nace saboda kaga jar fata da kyawun dan maciji wanda zai diga maka dafin sa ya tafi ya barka da ciwo, Wallahi Musaddiq ka cuceni kuma ka cuci kanka.... Anty Reemah ce ta zauna kusa da ita tace haba Mummy, matar mutum fa kabarinsa, kuma babu wanda yasan alkhairin dake tattare da auren Nadeeyah sai ubangijin halittu, yanzu ita wacce kike so din me tafi Nadeeyah dashi, "Gata da hanyoyin alkhairi, Mummy ta bata amsa tana harararta, "Hanyoyin alkhairi ai na ubangiji ne, shi ke budeshi ga wanda yaso, sai kiga auren Nadee--- a harzuke ta katseta da cewa "in kika kara magana zan balain saba miki, mahaukaciyar banza sakaryar hofi, tashi ki fita ki bani guri, shashasha kawai... Rai a bace Anty Reemah ta tashi ta fita daga dakin, Matsowa Musaddiq yayi ya share mata hawaye hade da kwantar mata da hankalin cewa ta kwantar da hankalinta, babu abun da zai faru, domin shi zai gyara komai, Hannunshi Mummy ta kama tace "Little ka taimakeni, bayan auren da kake so kayi wanda nake so, ka auri Faida, shi kadai ne zai sanya hankalina ya kwanta, in kuma aminta da Nadeeya a matsayin matarka, shuru yayi na dan lokacin zuciyarshi na harbawa da karfi, tunanin mafita ya shiga yi, Dakyar ya sama wa kanshi mafitar amincewa, dan a samu zaman lafiya, amma ko yayi hauka bazai auri Faida ba, daga ya tafi da Nadeeyarsa lagos bazai kara waiwayosu ba sai yayi shekaru, ganin ya amince zai auri Faida yasa Mummy farin ciki sosai har ta kira aminanta ta fada musu..... Sai bayan Magriba akayi kamun amare, "Mami da Anni su suka kama Husna, sai Anty Reemah da sauran yan uwanta sukayi ma Nadeeyah, Mummy ma in ka ganta zaka dauka albishir akayi mata da gidan aljanna saboda murna, Rawa kam kawayen Amare da yan uwa suyi ta sosai har saida suka kure mawakin, sai kusan goma makadin ya tattara kayanshi yayi gaba da tarin alkhairai masu yawa, su kuwa kawayen suka koma dakin kwanansu suka cigaba da hirarsu ta yammata, rabin hirar tasu ma akan Badar ta kare saboda sun so tana nan akayi bikin..... Rana bata karya.... A ran 23 ga watan yuli.. ranar sati da safe dubban jama'a suka shaida daurin auren *Musaddiq Mukhtar Kyari* da *Nadeeyah Adam* da kuma auren *Hafeez Adam* da *Husnah Mukhtar Kyari*... Marokin gurin na gama sanarwa Jamal yayi dariya sosai yace "vice versa, gyara bakin madubi Hilal yayi yace "ai fa, abin ya burgeni, Allah ya basu zaman lafiya.. saura mu, matsowa Jamal yayi yace "ai ni nama gama samu, saidai fatan dacewa, jira kawai nakeyi komai ya lafa in aika sakon zuciyata, bazan tsaya kallon ruwa kwado yayi min kafa ba.... "Kamar yadda Nayi Hilal ya fadi a cikin zuciyarshi.. amma a fili cewa yayi "woww kace anjima akwai gist, "Sosai ma In law... au My son ya karashe yana dukan bakinshi.. Mikewa Hilal yayi yana kyakyata dariya yace "ka tona kanka malam, muje gurin walima kafin mutumin ya fara kumburi..... Wannan kukan da kikeyi bazai taimakeki ba Amarya, dama kinci abinci, da kin samu sauki, "Kinsan adadin matan da suka shigo gidannan ta haka kuwa? to ki sani bake bace ta farko kuma bana tunanin zaki zamo ta karshe, da yawa irin ku son duniyan iyayenku ke ja muku, saboda son abun duniya sai idonsu ya rufe suyi kyautar da zata damesu nan gaba, ta shi kici abincin, kingani harda Farfesun Zomo, ga tuwon lapshi miyar yauki gaskiya ke yar gata ce, dan abin bauta Garzar ki rage min, ta karashe tana turo langar tuwon gabanta, Kafa Badariyya tasa ta ture langar tuwon, nan naman ya zube a kasa, komai ya bayyanar mata, kan zomo ne da kayan cikinshi, sai tsirarrun nama, da sauri kande da ta durkusa tafara kwashe naman tana suďe hannu kamar mayya wacce tayi sabon kamu, Idon da ya soye da bakin ciki Badariyya ta bita dashi tana hawayen zuci, "wannan wace iriyar jarabawa ta fado, kalmar na shiga uku har lokacin bata bar fita daga bakin Badar ba, tana kallo kande ta sude gurin tass kamar an goge sannan ta russuna tace "Ranki ya dade, ko bakya jin yunwa bai kamata ki wulakanta abinci ba, wannan naman yanzu da zan fita dashi tsakar gida sai an kusa kaini kasa saboda wawason shi, ki daure kici ko kadan ne saboda kar yareemah yayi fada, tsakii mai karfi Badariyya taja hade da sake yin tagumi tana tunanin way out.. Shigowar Yareemah ne yasanya kande fita da sauri bayan ta gaisheshi... Zama yayi a gefen Badar hade da dauko langar farfesun... "Sauka ki zauna a kasa ki cinyeshi tass domin ki samu karfin jikinki, a fusace Badar ta mike tace "wannan kazantar ce zata sa in samu karfi a jikina, wallahi kaji na rantse bazan zauna a gidannan ba, kukan bakin ciki ta fasa mishi tace "wallahi in na fita a gurin nan sunanku sorry, domin sai na gayyato muku sojoji sun tada wannan tsinannan kau---- "keeee... ya katseta cike da tsawa, nan take fuskarshi ta sauya yace "Zauna maza ki cinye abin dake cikin kwanukan nan, "Bazan ci ba! Nace bazan ci ba ka kashe n---- wani farin haske ne ya wuce ta makogoronta ya hanata Magana, sai ma bin umarnin shi da ta fara yi... tare suka zauna ya bata abincin a baki ta cinye tass cikin ficawar hayyaci, tana gama shan ruwa ya umurceta da ta fitar da kwanukan waje, ba musu ta kwashesu ta fitar dasu ta dawo dakin ta zauna a nutse, mikewa yayi ya dawo inda take hade da kamo hannuwanta, "ki kwantar da hankalinki, nima mutum ne kamar ki, saidai mu Allah yayi mana baiwar sanin wasu abubuwa, Tun kafin nayi auren farko lokacin ina yaro mahaifiyarki ta bani ke saboda jin dadi wani aiki da mahaifina yayi mata, tun daga ranar muke kula da duk wani motsinta, a ranar da aka haifeki mahaifina yayi murna domin a tunaninshi namiji zata haifa, tun daga wannan lokacin muke bibiyar dukkan sawunki, kina shekara tara a lokacin naga zuciyarki ta fara darsa wani abu game da dan uwanki, a sannan ne muka turo lawisa ta shiga rayuwarki, in kin lura a duk tarin kawayenku babu mai shiri da Lawisa sai ke, abun da yasa kuwa shine ba dan su tazo ba, domin ki tazo, a duk lokacin da ta kawo min batunki da Musaddiq, nakan ji kamar in kashe shi saboda kishi, mahaifina kan bani hakuri akan duk rintsi ke din tawa ce, yanzu gashi na sameki bayan shekaru 18 na jira... share hawayen dake gudu a idonta tayi a zuciyarta tana maijin tsanar fitowa daga kasan mahaifiyarta, a hankali tace "ka taimakeni ka maidani gida in aiwatar da abu daya, zan dawo daga zarar na gama aiwatarwa, Dariya yayi yace "Hana auren masoyinki? Da sauri ta gyada mishi kai, wani guri ya buga a gefen dakinshi nan take Hoton Musaddiq da Nadeeyah ya bayyana, zaune suke ta sanya rantsatsen leshi ja mai ratsin green, sai gyale green da ta rufe kanta dashi, gefenta Musaddiq ne shima yayi kyau har gaji yana yi mata mayataccen kallon kauna, Daddy da papy ke zaune bisa kujera suna musu Nasihar zaman aure saboda za'a tafi kaita gidan mijinta.... Kin ganshi, aikin gama ya gama, auren nasu ya tabbata, sai ki kwantar da hankalinki muyi zaman aurenmu, zaki ji dadi in kinso kiji, in kuwa kinso akasin haka duk zaki samesu a gidan nan... yana kaiwa nan ya mike hade da umurtarta da ta cire kayan jikinta........ Mrs Tijjani Shattimah....... [14/04 8:11 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣8⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Sake duba agogo yayi karo na ba adadi yaga karfe goma da rabi, Rai a bace ya mike ya fara rufe kofofin gidan hade da wutar globe, kitchen ya nufa dan duba ko an kashe kayan wuta, wutar corridor din kitchen ya kashe hade da faďawa ciki, Tozali yayi da Fatima tsaye tana fere dankalin da za'aci da breakfast, gyaran murya yayi wanda yasata juyowa a dan firgice, hada ido sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta hade da tsuguwa kasa ta gaisheshi, "Tashi Fadima, aikin ne kikeyi har yanzu?? bakya jin jikinki, murmushi tayi tace "naga gobe da wuri su Ummah zasu tafi shiyasa zan rage aikin da asuba sai in karasa, gyada kanshi yayi hade da fita parlon cike da tunani iri iri, A parlon ya zauna zuciyarshi na ta kitsa mishi abubuwa da dama, motsin fitowa yaji daga dakin dasu Ummah suke, Kanwar Umman ce ta fito da kofi a hannunta, ganinshi a zaune yasata zama kusa dashi itama tana dan janshi da hira, "Bakiyi bacci ba Inna? "ruwa zansha Shamsu, kaima baka kwanta ba, ga yar lelenka bata dawo ba, dariya yayi yace "kinsan biki, inaga a can zata kwana, "auu kana gani ne ma? Lallai kana da aiki shamsu, watanmu biyu a gidannan yarinyar nan bata taba zama ta kula damu ko na second daya ba, wallahi in zaka hankalta ka nemi macen mutunci ka nemeta ka aura, wacce zata zame maka macen gida ba ta titi ba, tana kaiwa nan ta fara kokarin mikewa, ganin Fatima ta fito yasa ta zama tace "yar albarka, zo ki bani ruwa, da sauri ta karbi kofin ta wuce kitchen ta dauko ruwa a gora ta kawo mata hade da yi musu sai da safe, Kallo suka bita dashi har ta kurewa ganinsu, Inna Indo ce ta fara dauke idonta tace "badan son duniya irin na 'yayan zamani masu son 'yayan masu kudi ba, da sai ince wannan yarinyar itace tayi daidai da tsarin macen aure mai mutunci da kamala, to saidai ita ba yar kowa bace, face yar mai aiki, Allah ya saka musu hidimar da sukayi mana ya kuma bata miji nagari, mikewa tayi tace "sai da safe, "Allah ya tashemu lafiya.. ya fadi yana cigaba da nazarin kalamanta, kafin safiya ya gama sawa ranshi zai auri Fatima badan yana sonta ba, sai dan su sami nutsuwa shi da 'yayanshi da yan uwanshi....... Washe gari kafin su Ummah su tafi ya fada musu abin da ya yanke a zuciyarshi, babu wanda a cikinsu bai nuna farin cikinsa ba, Inna indo da kanta ta samu Gyatum ta yi mata magana, sai da aka kai ruwa rana da ita saboda tsananin tsoron Radiya daya cikata, har saida shi kanshi Shamsun yayi mata magana sannan ta yarda, Fasa tafiyar Ummah tayi, tasa yan uwanta sukaje nema ma danta auren Fatima, so takeyi ayi auren kafin Radiya ta dawo.. Shima hakan yakeso saboda tsabar bacin ran da ta haifar mishi na cewa bazata dawo gida ba zasu wuce lagos da safe, in ba dan ta rainashi ba bazata iya dawowa gida ta yi mishi sallama ba sai ta waya saboda ta isa, shima zai nuna mata tashi isar........ "Uhumm, su Nadeeyah anyi kaura da talauci, irin wannan mansion haka, to Allah yasa a san yadda za'a tafiyar da gidan, "ai tare zamu tafiyar da gidan Anty Radiya, Raudha ta karbe cike da isgili, yaushe zan barta ta bata gidan da zatayi zaman wucin gadi a cikin sa, inaa sam bazai yiwu ba, kullum ina nan, zan nemi Badariyya a waya daga sun samu hutun makaranta ta dawo nan tayi hutu tunda kusa ne, barin irin su Nadeeyah su kadai a gidan nan ai hatsari ne, sai su la'anta shi, dole insa ido kafin mai guri tazo ta naďe kayanta... Mikewa Hinad tayi dan ta fara kosawa da maganganun da sukeyi a kunnenta, kuma dan cin fuska a gaban Nadeeya dake zaune kai a rufe, barin dakin tayi tana kun kuni ta fita harabar dan madaidaicin duplex din dake cikin lekki, babu abin da ke kadawa a gidan sai flowers wadanda suke huro da ni'imtaccen sanyi mai dadi, Hilal kawai take son gani ta bashi labarin abubuwan da ta jiyo tun daga kaduna har zuwa lagos, duk irin kullin da suke da shirin yi ma Nadeeyah ta nadeshi tsaff, bata son fadama Mamanta kar ta haddasa musu tashin hankali, amma dole ta fadi ma Hilal, tasan zai iya yin wani abu, Hango Jamal tayi da su Zainab a can wani lungun gidan kan wasu kujeru, nufarsu tayi cike da murna dan tasan tare suke yawo da Hilal, "Sannu ko, Zee ina Ya Hilal? "Ya tafi koyo sallama, Jamal ya bata amsa yana kallon cikin idonta, zama tayi tana dariya tace "lallai yayi kokari, bari ya dawo ya koya min, "Nafi shi iyawa, in na koya miki zaki fi dauka, "kuma fa hakane, to mu fara bita, ta fadi tana ajiye wayar hannunta, sake sanya idonshi cikin nata yayi yace "Allah dai yasa kan naja, dan i hate in koya ma mutum abu sau biyu, k'in dauke idonta tayi cikin nashi itama saboda wayewar turai tace "ban taba cin second ba Malam, fara koya min kagani may be ma in karasa in ka bani hint, cike da shauki yayi dariya yace "Anya ba burga bace? "Ka tambayi yaya Hilal, ni ai bana karya, nan fa hira sosai ta barke a tsakaninsu gunin ban sha'awa har sukayi exchanging numbr, saboda dadin hirar har Hilal ya iso gurin ta manta da abun da ta guntso ta fada mishi..... Ka kula da yarinyar Dan Allah, nasan harce da hakori suna sabawa, amma in sun saba suna kokarin sasantawa,, mu mata sai hakuri, nasan Nadeeyah ma zatayi avoiding duk wani abun da zai bata maka, kuma kaima i trust u, baka da fushi, da dai ďanka ne to dama tare zamu zauna saboda halinshi, Yadda ta fadi maganar tana kallon Hilal ya sanya shi mikewa yana dariya, itama dariyar tayi a ranta tana farin cikin sauyin da take gani a halin ďanta, cigaba dayi ma Musaddiq Nasiha tayi tana kara nusar dashi zaman aure, sunfi awa suna zantawa har lokacin tafiyarsu yayi.... Hilal ma ya kara jaddada mishi ya kula sosai ko ba dan komai ba ya kula da maraicinta, "Yanzu bata da kowa sai kai, dan Allah ka kula da ita, in ta bata maka rai, kafin ka yanke hukunci, ka tuna maraicinta sai ka yanke mata hukuncin daidai da ita, zaman aure hakuri akeyi, kadai ji kowa ya fada maka, sai school, dan Allah ka nema mata admission as soon as possible, kafadunshi Musaddiq ya dafa yace "worry not Daddy, in shaa Allah tare zamuyi kuka kuma tare zamuyi dariya, "Dariyan dai Hilal ya fadi yana dariya.. har gurin mota suka kai suna hirarsu cike da barkwanci, sam bayason ganin Nadeeyah shiyasa ma bai nemi yi mata sallama ba, yanaso yayi moving on, bayason sake tunanin ma ya taba son ta a rayuwarshi, saboda yanzu ta haramta a gareshi gaba daya..... Kowa ya watse a gidan sai Anty Rauda da Anty Radiya da batasan wainar da ake toyawa a gidan ta ba, Zaune suke a parlor sun bararraje suna hira suna cin dublan, ko tunanin mikewa suyi sallar isha'i basuyi ba, wayar Raudha ce ta fara ringing tayi saurin dauka hade da cewa "Hello Abbati kayi hakuri, har yanzu bamu gama jeren bane, Tsaki.. kawai yayi ya kashe wayar ya dauki *Hanna* da *Hisham* yayi daki dasu, Ajiye wayar tayi tana dariya tace "ai fa yanzu ba zama sai dai yayi hakuri, sai naga little ya rabu yarinyar nan sannan ne zan samu nutsuwa, karbewa Radiya tayi tace "ai nima zan fi sati biyu anan, gara mu hada karfi da karfe, wallahi badan imani da kuma zumunci ba da sai nayi abun da zai batar da Nadeeyah a doron kasa, duk Baffa ne ya cucemu da ya shigo mana da dangin tsiya cikin zuri'armu, nan fa suka hakikance suna aibata Nadeeyah da iyayenta, in ka gansu zaka rantse wasu bare suke aibatawa ba yan uwansu na jini ba.... Ajiyar zuciya yayi hade da ajiye ledojin da ya shigo dasu yace "Har yanzu baku wuce ba? "Au korarmu ma kakeyi, to ai da sai ka ce har yanzu ban wuce ba, dan Anty Radiya a nan zata kwana, "Kwana kuma? Ya tambaya haďe da zama akan kujerar dake fuskantarsu, "eh kwana little, ko gidan kanwata kakeso inje in kwana, tun yanzu zaka fara mana iyakw da gidanka, Radiya ta fadi tana rike hab'a, mikewa yayi yana dariya yace "nan ma gida ne, bari inje sama, duk abun da babu a dakin kasa sai ki kirani a waya, Salati Radiya ta saki wanda yasa shi saurin sakin ledojin da ya fara diba, "little ni zaka ajiye a dakin baki, ni bakuwace a gidan ka Diku, tabdijam, lallai duk inda muke tunanin abun ya wuce nan Raudha, "Hmmm ai ni abun yafi karfi na Anty, tashi kawai mu tafi gidana, dukda da kunya kina babba ki kwana a gidana, kusa dasu ya karaso a tsorace yace "haba baku fahimceni bane, dan Allah kiyi hakuri Anty, muje saman ki zabi wanda kike so a ciki, kanne mata ido Raudha tayi sukayi murmushi hade da tashi su nufi saman.... Dakin da Nadeeyah ke ciki suka nufa saboda nan yafi ko ina tsaruwa, nan ne sukaji Anty Reemah na kira da turaka, bata cikin dakin hakan ya basu tabbacin tana toilet, Ajiye ledar Musaddiq yayi a kan gadon ya tsaya kallonsu, yadda suka nufi bayin gadan gadan ya sashi tunanin ko lalura ce ta kaisu, Da karfi Raudha ta murda bayin ba tare da bugawa ba, dan dama shammatarta suka so yi, Saboda tsabar kaduwa Nadeeyah bata san ta zaune a gurin ba, Tsaki.. suka jaa a tare Radiya tace "dan Allah ji rashin kunya, in banda rashin ta ido yarinyar nan tasan sarai muna gidan nan kuma ta shiga bayi a haka saboda tasa yaron nan fitsare kafarshi a gabanmu, Allah ya kyauta matan zamani, mu a da ai sai muyi wata bamu shiga wanka ba sai ance muje, Kofar bayin Musaddiq ya ja yace "menene laifi dan tayi wanka, ai kowa nasan tsafta, dan Allah muje ki kwanta, ke kuma kije gida gurin su Hisham, "Anan zata kwanta, Raudha ta fadi alamar da ta fara hassala da kalamanshi, kafadunshi ya daga yace "ok fine, bari ta shirya sai muje can dakin, ai duk daya ne, bai tsaya kallon reactn dinsu ba ya bude drawer ya ga ba kayanta a ciki sai nashi, wata rigar baccinshi ya dauko wacce yasan inya sa mata zata wuce mata gwiwa ba tare da wando ba, ya wuce bayin ya barsu da mamakin anya kuwa zasu iya rabasu cikin sati biyun da suke tunani, basu kara shan mamaki ba bakunansu dake kuskus suka tsaya a haka na ganin yadda ya daukota cakk cikin faffadan kirjinshi, bai direta ko ina ba sa dakin dake dan nesa da inda suke, komawa dakin yayi dan dauko mata abin da ya siyo mata ya tarar dasu suna tafa hannu, kwaso ledojin yayi ya mika ma Anty Radiya daya, "Diku ko kunyarmu baka ji ba, "kunyar me? ya tambaya yana murmushi, "a gaban idonmu ka dauki matarka har kana kankameta cikin kirjinka, "Diku waye ya 'bata ka haka? Dariya yayi yace "Nadeeyah ko ba matata bace kanwata ce, zan iya daukarta in lalura ta sameta, to ya zanyi in barta a bayi tunda ku ba fita zakuyi ba itama kuma tace bazata fito ba, shiyasa kawai na raba gardama, "Hmmm yara kanana da makirci ni jikar Ma'u, to bari kaji in fada maka, wannan rawar jikin da kakeyi ka rageshi, ita mace in taga ana sonta sosai  nan ne take bude kafar iskanci, ka hankalta ka dinga jan ajinka, ka zamana kai mai gidan ne gaske, yawan sake fuska da hira duk suna sanya mace ta raina namiji, Barshi Raudha "zo ki zauna muci naman nan zan mishi course anjima, dan bana jin bacci... Shi mamaki ma suka bashi, kowa yana ce mishi matarka itace komai naka, itace abokiyar wasanka kuma sirrinka, su kuma ga irin tasu lakcar, murda kofar yayi yace "sai da safenku, "a'a karkayi bacci, zamu--- "Aiko zanyi bacci ya katseta hade da rufe kofar yana dariya, shi ya rasa me ke damunsu, bayan Mummy kawai suke bi, Wanda duk yaso Faida ya bar Nadeeyah a gurinshi baisan me yakeyi ba, a iya gane ganen yan matanshi bai taba ganin macen da ta hada komai irin matarshi ba, wayarshi dake kara ya dauka ya kara a kunne hade da cewa, "Mahmood har kun isa, daga daya bangaren Mahmood yace "yess yanzu na shigo gida, na manta, akwai wasu kaya da Mama ta bani in ba Nadeeyah, suna nan boot din *Zubair,* na kirashi zai kawo maka gobe, "ohk Besty ba matsala, thank u soo much, "most welcome Kyari, a kular mana da kanwa, nyt, "in shaa Allah, Allah ya tada mu lafiya...... Knock knock knock... Little ka kwanta ne, tsaki ya ja hade da nade daddumar da suka idar da Sallah akai, bude kofar yayi yace "lafiya Anty? dan tsaki tayi tace "wallahi na kasa bacci ne, ga gidan yayi min girma in kwana ni kadai a daki, turo min Nadeeyah mu kwanta tare, "Nima gidan yayi min girma, kinsanni da tsoro, har gara ke, ya fadi on a serious nt, "to sai mu kwana mu uku, in a nan ne in shigo in can ne kuma ku dawo, "Da kai kawai ya amsa mata hade da rufo kofar, Juyowa yayi yaga Nadeeyah a bayanshi, "ina zaki? zanje can dakin, tunda tana jin tsoro bai kamata mu barta ita kadai ba.. Hannunta ya riko haďe da janyota gab dashi, a dan shagwabe yace "nima tsoro nakeji, kokarin kwace hannunta tayi tace "ai tace muje mu uku mu kwana, dan Allah zo muje kar ranta ya baci... Hade jikinshi yayi da nata yana shinshinar daddan kamshin kanta hade da lumshe yace "ni dai tare da matata zan kwana, plss ki rabu da ita, kwana nawa rabona dake, kinsan irin wahalar da kika ba zuciyata, "Tsugunawa yayi dan saita tsayinsu haďe da sake narke mata, "pls, pls, pls, wata yar dariya tayi wacce ta sashi sake rikice mata, "dariya kike min ko? "Dan Allah maida bakin, ta fadi tana tura bakin da hannu. yadda ya sake turo bakin yasata sakin dariya mai dan sauti, abun da yake so kenan dama, nan yayi mata wata irin runguma mai dauke da shaukin so, wasu rikirkitattun sakonni ya shiga aika mata masu wuyar fassaruwa wanda ya sanya jikinta kyarma matuka, "kuka sosai ta sanya mishi na rashin sabo tana tureshi, shi din ma kanin kukan yakeyi wanda ya sanyashi daukarta ya ajiyeta a tsakiyan gado, Daga shi har ita basu taba shiga cikin yanayin da suke a yanzu ba, ba kamar Musaddiq da yake namiji mai jini a jiki wanda yake tashe da kuruciya da kudi, ga madarar kyau, amma Allah ya tsare shi da mu'amala da ko wace irin mace, Nadeeyar dai kadai yake gani mace a duk matan da yayi arangama dasu, bai taba sanin feelings din kasantuwa da mace haka yake ba shiyasa yayi matukar gigita fiye da tunani, babu abin da yake iya saurare a wannan lokacin sai kukan Nadeeyah da ya kasance abin so a gurinshi, duk irin bugun da Anty Radiya kewa kofar baiji ba saboda a inda Musaddiq yake guri ne wanda bayajin kira komin karfin kiran kuwa..... Mrs Tijjani Shattimah...... [14/04 8:11 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣8⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Sake duba agogo yayi karo na ba adadi yaga karfe goma da rabi, Rai a bace ya mike ya fara rufe kofofin gidan hade da wutar globe, kitchen ya nufa dan duba ko an kashe kayan wuta, wutar corridor din kitchen ya kashe hade da faďawa ciki, Tozali yayi da Fatima tsaye tana fere dankalin da za'aci da breakfast, gyaran murya yayi wanda yasata juyowa a dan firgice, hada ido sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta hade da tsuguwa kasa ta gaisheshi, "Tashi Fadima, aikin ne kikeyi har yanzu?? bakya jin jikinki, murmushi tayi tace "naga gobe da wuri su Ummah zasu tafi shiyasa zan rage aikin da asuba sai in karasa, gyada kanshi yayi hade da fita parlon cike da tunani iri iri, A parlon ya zauna zuciyarshi na ta kitsa mishi abubuwa da dama, motsin fitowa yaji daga dakin dasu Ummah suke, Kanwar Umman ce ta fito da kofi a hannunta, ganinshi a zaune yasata zama kusa dashi itama tana dan janshi da hira, "Bakiyi bacci ba Inna? "ruwa zansha Shamsu, kaima baka kwanta ba, ga yar lelenka bata dawo ba, dariya yayi yace "kinsan biki, inaga a can zata kwana, "auu kana gani ne ma? Lallai kana da aiki shamsu, watanmu biyu a gidannan yarinyar nan bata taba zama ta kula damu ko na second daya ba, wallahi in zaka hankalta ka nemi macen mutunci ka nemeta ka aura, wacce zata zame maka macen gida ba ta titi ba, tana kaiwa nan ta fara kokarin mikewa, ganin Fatima ta fito yasa ta zama tace "yar albarka, zo ki bani ruwa, da sauri ta karbi kofin ta wuce kitchen ta dauko ruwa a gora ta kawo mata hade da yi musu sai da safe, Kallo suka bita dashi har ta kurewa ganinsu, Inna Indo ce ta fara dauke idonta tace "badan son duniya irin na 'yayan zamani masu son 'yayan masu kudi ba, da sai ince wannan yarinyar itace tayi daidai da tsarin macen aure mai mutunci da kamala, to saidai ita ba yar kowa bace, face yar mai aiki, Allah ya saka musu hidimar da sukayi mana ya kuma bata miji nagari, mikewa tayi tace "sai da safe, "Allah ya tashemu lafiya.. ya fadi yana cigaba da nazarin kalamanta, kafin safiya ya gama sawa ranshi zai auri Fatima badan yana sonta ba, sai dan su sami nutsuwa shi da 'yayanshi da yan uwanshi....... Washe gari kafin su Ummah su tafi ya fada musu abin da ya yanke a zuciyarshi, babu wanda a cikinsu bai nuna farin cikinsa ba, Inna indo da kanta ta samu Gyatum ta yi mata magana, sai da aka kai ruwa rana da ita saboda tsananin tsoron Radiya daya cikata, har saida shi kanshi Shamsun yayi mata magana sannan ta yarda, Fasa tafiyar Ummah tayi, tasa yan uwanta sukaje nema ma danta auren Fatima, so takeyi ayi auren kafin Radiya ta dawo.. Shima hakan yakeso saboda tsabar bacin ran da ta haifar mishi na cewa bazata dawo gida ba zasu wuce lagos da safe, in ba dan ta rainashi ba bazata iya dawowa gida ta yi mishi sallama ba sai ta waya saboda ta isa, shima zai nuna mata tashi isar........ "Uhumm, su Nadeeyah anyi kaura da talauci, irin wannan mansion haka, to Allah yasa a san yadda za'a tafiyar da gidan, "ai tare zamu tafiyar da gidan Anty Radiya, Raudha ta karbe cike da isgili, yaushe zan barta ta bata gidan da zatayi zaman wucin gadi a cikin sa, inaa sam bazai yiwu ba, kullum ina nan, zan nemi Badariyya a waya daga sun samu hutun makaranta ta dawo nan tayi hutu tunda kusa ne, barin irin su Nadeeyah su kadai a gidan nan ai hatsari ne, sai su la'anta shi, dole insa ido kafin mai guri tazo ta naďe kayanta... Mikewa Hinad tayi dan ta fara kosawa da maganganun da sukeyi a kunnenta, kuma dan cin fuska a gaban Nadeeya dake zaune kai a rufe, barin dakin tayi tana kun kuni ta fita harabar dan madaidaicin duplex din dake cikin lekki, babu abin da ke kadawa a gidan sai flowers wadanda suke huro da ni'imtaccen sanyi mai dadi, Hilal kawai take son gani ta bashi labarin abubuwan da ta jiyo tun daga kaduna har zuwa lagos, duk irin kullin da suke da shirin yi ma Nadeeyah ta nadeshi tsaff, bata son fadama Mamanta kar ta haddasa musu tashin hankali, amma dole ta fadi ma Hilal, tasan zai iya yin wani abu, Hango Jamal tayi da su Zainab a can wani lungun gidan kan wasu kujeru, nufarsu tayi cike da murna dan tasan tare suke yawo da Hilal, "Sannu ko, Zee ina Ya Hilal? "Ya tafi koyo sallama, Jamal ya bata amsa yana kallon cikin idonta, zama tayi tana dariya tace "lallai yayi kokari, bari ya dawo ya koya min, "Nafi shi iyawa, in na koya miki zaki fi dauka, "kuma fa hakane, to mu fara bita, ta fadi tana ajiye wayar hannunta, sake sanya idonshi cikin nata yayi yace "Allah dai yasa kan naja, dan i hate in koya ma mutum abu sau biyu, k'in dauke idonta tayi cikin nashi itama saboda wayewar turai tace "ban taba cin second ba Malam, fara koya min kagani may be ma in karasa in ka bani hint, cike da shauki yayi dariya yace "Anya ba burga bace? "Ka tambayi yaya Hilal, ni ai bana karya, nan fa hira sosai ta barke a tsakaninsu gunin ban sha'awa har sukayi exchanging numbr, saboda dadin hirar har Hilal ya iso gurin ta manta da abun da ta guntso ta fada mishi..... Ka kula da yarinyar Dan Allah, nasan harce da hakori suna sabawa, amma in sun saba suna kokarin sasantawa,, mu mata sai hakuri, nasan Nadeeyah ma zatayi avoiding duk wani abun da zai bata maka, kuma kaima i trust u, baka da fushi, da dai ďanka ne to dama tare zamu zauna saboda halinshi, Yadda ta fadi maganar tana kallon Hilal ya sanya shi mikewa yana dariya, itama dariyar tayi a ranta tana farin cikin sauyin da take gani a halin ďanta, cigaba dayi ma Musaddiq Nasiha tayi tana kara nusar dashi zaman aure, sunfi awa suna zantawa har lokacin tafiyarsu yayi.... Hilal ma ya kara jaddada mishi ya kula sosai ko ba dan komai ba ya kula da maraicinta, "Yanzu bata da kowa sai kai, dan Allah ka kula da ita, in ta bata maka rai, kafin ka yanke hukunci, ka tuna maraicinta sai ka yanke mata hukuncin daidai da ita, zaman aure hakuri akeyi, kadai ji kowa ya fada maka, sai school, dan Allah ka nema mata admission as soon as possible, kafadunshi Musaddiq ya dafa yace "worry not Daddy, in shaa Allah tare zamuyi kuka kuma tare zamuyi dariya, "Dariyan dai Hilal ya fadi yana dariya.. har gurin mota suka kai suna hirarsu cike da barkwanci, sam bayason ganin Nadeeyah shiyasa ma bai nemi yi mata sallama ba, yanaso yayi moving on, bayason sake tunanin ma ya taba son ta a rayuwarshi, saboda yanzu ta haramta a gareshi gaba daya..... Kowa ya watse a gidan sai Anty Rauda da Anty Radiya da batasan wainar da ake toyawa a gidan ta ba, Zaune suke a parlor sun bararraje suna hira suna cin dublan, ko tunanin mikewa suyi sallar isha'i basuyi ba, wayar Raudha ce ta fara ringing tayi saurin dauka hade da cewa "Hello Abbati kayi hakuri, har yanzu bamu gama jeren bane, Tsaki.. kawai yayi ya kashe wayar ya dauki *Hanna* da *Hisham* yayi daki dasu, Ajiye wayar tayi tana dariya tace "ai fa yanzu ba zama sai dai yayi hakuri, sai naga little ya rabu yarinyar nan sannan ne zan samu nutsuwa, karbewa Radiya tayi tace "ai nima zan fi sati biyu anan, gara mu hada karfi da karfe, wallahi badan imani da kuma zumunci ba da sai nayi abun da zai batar da Nadeeyah a doron kasa, duk Baffa ne ya cucemu da ya shigo mana da dangin tsiya cikin zuri'armu, nan fa suka hakikance suna aibata Nadeeyah da iyayenta, in ka gansu zaka rantse wasu bare suke aibatawa ba yan uwansu na jini ba.... Ajiyar zuciya yayi hade da ajiye ledojin da ya shigo dasu yace "Har yanzu baku wuce ba? "Au korarmu ma kakeyi, to ai da sai ka ce har yanzu ban wuce ba, dan Anty Radiya a nan zata kwana, "Kwana kuma? Ya tambaya haďe da zama akan kujerar dake fuskantarsu, "eh kwana little, ko gidan kanwata kakeso inje in kwana, tun yanzu zaka fara mana iyakw da gidanka, Radiya ta fadi tana rike hab'a, mikewa yayi yana dariya yace "nan ma gida ne, bari inje sama, duk abun da babu a dakin kasa sai ki kirani a waya, Salati Radiya ta saki wanda yasa shi saurin sakin ledojin da ya fara diba, "little ni zaka ajiye a dakin baki, ni bakuwace a gidan ka Diku, tabdijam, lallai duk inda muke tunanin abun ya wuce nan Raudha, "Hmmm ai ni abun yafi karfi na Anty, tashi kawai mu tafi gidana, dukda da kunya kina babba ki kwana a gidana, kusa dasu ya karaso a tsorace yace "haba baku fahimceni bane, dan Allah kiyi hakuri Anty, muje saman ki zabi wanda kike so a ciki, kanne mata ido Raudha tayi sukayi murmushi hade da tashi su nufi saman.... Dakin da Nadeeyah ke ciki suka nufa saboda nan yafi ko ina tsaruwa, nan ne sukaji Anty Reemah na kira da turaka, bata cikin dakin hakan ya basu tabbacin tana toilet, Ajiye ledar Musaddiq yayi a kan gadon ya tsaya kallonsu, yadda suka nufi bayin gadan gadan ya sashi tunanin ko lalura ce ta kaisu, Da karfi Raudha ta murda bayin ba tare da bugawa ba, dan dama shammatarta suka so yi, Saboda tsabar kaduwa Nadeeyah bata san ta zaune a gurin ba, Tsaki.. suka jaa a tare Radiya tace "dan Allah ji rashin kunya, in banda rashin ta ido yarinyar nan tasan sarai muna gidan nan kuma ta shiga bayi a haka saboda tasa yaron nan fitsare kafarshi a gabanmu, Allah ya kyauta matan zamani, mu a da ai sai muyi wata bamu shiga wanka ba sai ance muje, Kofar bayin Musaddiq ya ja yace "menene laifi dan tayi wanka, ai kowa nasan tsafta, dan Allah muje ki kwanta, ke kuma kije gida gurin su Hisham, "Anan zata kwanta, Raudha ta fadi alamar da ta fara hassala da kalamanshi, kafadunshi ya daga yace "ok fine, bari ta shirya sai muje can dakin, ai duk daya ne, bai tsaya kallon reactn dinsu ba ya bude drawer ya ga ba kayanta a ciki sai nashi, wata rigar baccinshi ya dauko wacce yasan inya sa mata zata wuce mata gwiwa ba tare da wando ba, ya wuce bayin ya barsu da mamakin anya kuwa zasu iya rabasu cikin sati biyun da suke tunani, basu kara shan mamaki ba bakunansu dake kuskus suka tsaya a haka na ganin yadda ya daukota cakk cikin faffadan kirjinshi, bai direta ko ina ba sa dakin dake dan nesa da inda suke, komawa dakin yayi dan dauko mata abin da ya siyo mata ya tarar dasu suna tafa hannu, kwaso ledojin yayi ya mika ma Anty Radiya daya, "Diku ko kunyarmu baka ji ba, "kunyar me? ya tambaya yana murmushi, "a gaban idonmu ka dauki matarka har kana kankameta cikin kirjinka, "Diku waye ya 'bata ka haka? Dariya yayi yace "Nadeeyah ko ba matata bace kanwata ce, zan iya daukarta in lalura ta sameta, to ya zanyi in barta a bayi tunda ku ba fita zakuyi ba itama kuma tace bazata fito ba, shiyasa kawai na raba gardama, "Hmmm yara kanana da makirci ni jikar Ma'u, to bari kaji in fada maka, wannan rawar jikin da kakeyi ka rageshi, ita mace in taga ana sonta sosai  nan ne take bude kafar iskanci, ka hankalta ka dinga jan ajinka, ka zamana kai mai gidan ne gaske, yawan sake fuska da hira duk suna sanya mace ta raina namiji, Barshi Raudha "zo ki zauna muci naman nan zan mishi course anjima, dan bana jin bacci... Shi mamaki ma suka bashi, kowa yana ce mishi matarka itace komai naka, itace abokiyar wasanka kuma sirrinka, su kuma ga irin tasu lakcar, murda kofar yayi yace "sai da safenku, "a'a karkayi bacci, zamu--- "Aiko zanyi bacci ya katseta hade da rufe kofar yana dariya, shi ya rasa me ke damunsu, bayan Mummy kawai suke bi, Wanda duk yaso Faida ya bar Nadeeyah a gurinshi baisan me yakeyi ba, a iya gane ganen yan matanshi bai taba ganin macen da ta hada komai irin matarshi ba, wayarshi dake kara ya dauka ya kara a kunne hade da cewa, "Mahmood har kun isa, daga daya bangaren Mahmood yace "yess yanzu na shigo gida, na manta, akwai wasu kaya da Mama ta bani in ba Nadeeyah, suna nan boot din *Zubair,* na kirashi zai kawo maka gobe, "ohk Besty ba matsala, thank u soo much, "most welcome Kyari, a kular mana da kanwa, nyt, "in shaa Allah, Allah ya tada mu lafiya...... Knock knock knock... Little ka kwanta ne, tsaki ya ja hade da nade daddumar da suka idar da Sallah akai, bude kofar yayi yace "lafiya Anty? dan tsaki tayi tace "wallahi na kasa bacci ne, ga gidan yayi min girma in kwana ni kadai a daki, turo min Nadeeyah mu kwanta tare, "Nima gidan yayi min girma, kinsanni da tsoro, har gara ke, ya fadi on a serious nt, "to sai mu kwana mu uku, in a nan ne in shigo in can ne kuma ku dawo, "Da kai kawai ya amsa mata hade da rufo kofar, Juyowa yayi yaga Nadeeyah a bayanshi, "ina zaki? zanje can dakin, tunda tana jin tsoro bai kamata mu barta ita kadai ba.. Hannunta ya riko haďe da janyota gab dashi, a dan shagwabe yace "nima tsoro nakeji, kokarin kwace hannunta tayi tace "ai tace muje mu uku mu kwana, dan Allah zo muje kar ranta ya baci... Hade jikinshi yayi da nata yana shinshinar daddan kamshin kanta hade da lumshe yace "ni dai tare da matata zan kwana, plss ki rabu da ita, kwana nawa rabona dake, kinsan irin wahalar da kika ba zuciyata, "Tsugunawa yayi dan saita tsayinsu haďe da sake narke mata, "pls, pls, pls, wata yar dariya tayi wacce ta sashi sake rikice mata, "dariya kike min ko? "Dan Allah maida bakin, ta fadi tana tura bakin da hannu. yadda ya sake turo bakin yasata sakin dariya mai dan sauti, abun da yake so kenan dama, nan yayi mata wata irin runguma mai dauke da shaukin so, wasu rikirkitattun sakonni ya shiga aika mata masu wuyar fassaruwa wanda ya sanya jikinta kyarma matuka, "kuka sosai ta sanya mishi na rashin sabo tana tureshi, shi din ma kanin kukan yakeyi wanda ya sanyashi daukarta ya ajiyeta a tsakiyan gado, Daga shi har ita basu taba shiga cikin yanayin da suke a yanzu ba, ba kamar Musaddiq da yake namiji mai jini a jiki wanda yake tashe da kuruciya da kudi, ga madarar kyau, amma Allah ya tsare shi da mu'amala da ko wace irin mace, Nadeeyar dai kadai yake gani mace a duk matan da yayi arangama dasu, bai taba sanin feelings din kasantuwa da mace haka yake ba shiyasa yayi matukar gigita fiye da tunani, babu abin da yake iya saurare a wannan lokacin sai kukan Nadeeyah da ya kasance abin so a gurinshi, duk irin bugun da Anty Radiya kewa kofar baiji ba saboda a inda Musaddiq yake guri ne wanda bayajin kira komin karfin kiran kuwa..... Mrs Tijjani Shattimah...... [17/04 8:22 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣9⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Anty ya akayi? Raudha ta faďi bayan ta ďaga wayar Radiya rai a bace, "ba karamin faďa sukayi da Abbati ba akan dadewar da tayi, kuma ya tabbatar mata da yasan an gama jeren Nadeeyah tun kwana uku da suka wuce, bayan ya gama kwance mata kwandon masifarshi ya bugo mata kofa yaje ya kwanta cikin 'yayanshi, daga ďaya bangaren Radiya ta zauna akan gado tace "Hmmmm Raudha, ai ni yau naga jaraba, wallahi yaron nan ya haike mata, samm baya ko jin bugun da nakewa kofarshi, dan wani kayan takaicin ma muryarshi ce ta karaďe ko'ina a gidan babu ko kunyar ina gidan, wannan aikin yafi karfi na, gobe zanbi first flight in koma gidana, "Ki kwanta Anty, da safe zanzo sai musan abun yi, nima yanzu haka raina a bace yake, Abbati ya gama bata min rai, wallahi sai yayi paying for ci min mutunci da yayi, Allah ya kaimu gobe zan san abun yi, Raudha ta karashe hade da kashe wayar... Kwanciya Radiya tayi zuciyarta na tukuki tana dana sanin tsayawarta a gidan, tunanin yadda zata fara haďa ido dashi takeyi, tasan yasan taji komai da ya wakana a tsakaninsu da Nadeeyah, wannan kayan kunyar bada ita ba, domin Musaddiq kaninta ne sosai bawai immediate ba, da tunane tunane marasa dadi hade da kara jin tsanar Nadeeyah a cikin ranta bacci mai cike da mafarkai yayi gaba da ita..... Cikin sanďa Marakisiyya ta lallabo cikin dakin tana taku a hankali dan kar a farga da shigowarta, "Nasan da zuwanki hatsabibiya, ta jiyo muryarshi kamar daga sama, makewa tayi tana waige waige dan ganin ta inda yake mata maganar, Badariyya da baccinta baiyi nisa ba tayi saurin mikewa hade da lalube saboda duhun dake cikin ďakin, "wacece, "wacece a nan gurin, dan Allah kizo ki taimakeni, jin da Marakisiyya tayi ba wata muryar dake sake fitowa daga bayanta ya sanya ta karasawa kusa da Badar hade da toshe mata baki, ihu marar fita Badariyya takeyi tana mutsu mutsun neman kwatar kanta, "shhhhh, taimakonki zanyi, zauna ki kuma yi shuru, ni mutum ce yar uwarki, kamar yadda aka kawoki nan, nima haka aka kawo ni, shekarata ta biyu kenan a gidan nan, haihuwata ďaya talll, sunana Marakisiyya, a garin katsina nake, zanso jin labarinki sannan mu haďu mu nema wa kanmu mafita, gobe da safe kizo bayan Bukkar yara zanyi zaman jiranki.. tana kaiwa nan ta saki bakin Badar ta mike ta fita da sauri, tayi mamakin da taji muryarshi kuma bata ga bayyanarshi ba, har ta karasa bukkarta tana addu'ar Allah yasa bai jita ba.. Gimbiya Sailuba.. ita ta dauke hankalinshi daga isa gurin su Marakisiyya, yadai san dalilin zuwanta bai wuce dan neman mafita ba, wata dariya yayi haďe da maida kanshi jikin Sailuba, "yaro bai san wuta ba sai ya taka.... Badar kuwa tun zuwanta gidan bata taba jin abin da ya faranta ranta kamar maganar Marakisiyya ba, juyawa tayi ta tsinci kanta da murmushin jin dadin ta kusa barin gidan ta koma ta samu Masoyinta, abin kaunarta Musaddiq, tunanowa da tayi Nadeeyah na cikin rayuwarshi ya sanya zuciyarta tafasa haďe da sake saken muggan abubuwan da zatayi mata bayan ta kubuta a gurin..... (wasa farin girki) Jakar kayanta ta janyo ta sauko parlon haďe da sake kiran Raudha karo na uku, daukar wayar Raudha tayi haďe da latsa hon, "Gani a gate, kashe wayar Radiya tayi ta mike ta nufi kofar fita daga parlon, Da sauri Raudha ta kashe motarta ta fito ta nufi inda Radiya ke tsaye, "Anty dan Allah mu koma, wallahi bazaki tafi yau ba, sai kinyi wannan sati biyun da muka ce, wallahi sai mun cika burin mu, in kika tafi ma ai dadi zata ji ta samu damar juyashi san ranta, nayi waya da Mummy tun asuba na shirya mata maganganu, tace zata turo Faida gobe ko jibi, sannan tace zata nemi Badariyya tasa ta dawo daga makaranta, gara duk mu hadu mu kauda wadannan dangin tsiyan cikin zuri'armu, Ita kuma Husna mu zuba mata ido, tunda ita taji ta gani babu wanda zai tursasa ta, in taji wuya ta nemawa kanta mafita, bata bar Radiya tayi magana ba ta dauki jakarta ta bude kofar ta jata suka koma ciki, kafaďunta Radiya ta dafa tace "Raudha, bakiji abinda naji bane, wallahi yanzu haka kunyar ganin Little nake, nidai bazan iya ba, in zauna gidan yaro kullum yana zuba rawar kafa akan yarinya karama, ni kuma su barni da saurare, kuyi keda su Badariyyan kawai, ni kam na girma da wannan,,, "Ohhhh Anty, kunya ai shi zai jita, ke kam zama zakiyi a cikin gidan dan ki dinga lura da movements dinsu, ni kuma zanyi duk wasu kullin da suka dace, sannan Faida da Badariyyah sune zasuyi completing aikin in shaa Allah, zaunar da ita tayi ta gama tsarata tayi convincing dinta har ta yarda zata kara sati ďaya a gidan, cike da farin ciki Raudha tace "ko kefa, ai mu ya kamata mu maidashi hanya, in muka barshi ya cigaba da haukar kuruciyya ai sai ya bata rayuwarshi kan wannan yarinyar marar asali, cire hijab dinta tayi ta nufi sama tace "ina zuwa Anty, ita dai Radiya bata ce komai ba sai gyaďa kai kawai da tayi.... Bugu da Murda kofar da Raudha tayi yayi daidai da fitowar su daga bayi, sake gyara towel din da ya naďota yayi ya sake rungumeta cikin kirjinshi haďe da cewa "ina kwana Anty, plss come nd help me sai kuka takeyi, yadda yayi maganar shima kamar zaiyi kukan ya sanya Raudha yi mishi wani irin mugun kallo, "Me na faďa maka jiya? yanzu dan rashin kunya little bazaka iya jiran Anty ta bar gidan nan ba, bansan ranar da ka lalace har haka ba wallahi, kai da kayi barnar sai ka gyara da kanka, sakarai kawai... tana kaiwa nan ta fita daga dakin haďe da buga kofar da karfin gaske, kwantar da ita yayi yana share mata hawayen da yayi kaca kaca a fuskarta, "sorry plss, bari insa miki kaya muje asibiti, hannunshi ta kama haďe da girgiza kanta tace "ka barshi, ba sai naje asibiti ba zan sami sauki, rike hannunta yayi sosai yace "Noo ki bari muje, banasan wannan kukan da kikeyi plss, kanta ta juyar gefe tace "um um, ka bari kawai, ďago kan yayi ya zauna haďe maidota jikinshi yace "dan Allah ki tashi mu tafi, kinga jikinki yayi zafi, "Ni bazani ba, in naje kace musu meke damuna? hawayen da ya gangaro bayan ta gama maganar ya share mata ya rasa yadda zaiyi, murya a raunane shima kukan yake shirin farawa yace "To me kike so inyi miki ki daina kuka, "ka kyaleni, zan taimaki kaina, wayarshi ya mika hannu ya dauko ya latsa number Anty Reemah, "Little ango, an tashi lafiya?, "lafiya kalau Anty, yadda taji muryarshi yasata mikama Zainab plate din arish tace "maza kije ki karya kafin su Adeel su fito.. "Lafiya Diku? ya naji muryarka haka? Cikin Muryar shagwaba yayi mata bayanin komai, dariya tayi tace "To ni me zanyi, kai kayi barnarka ni kuma sai in maka magani, "Ni dan Allah Anty ki faďa min, bata tsaida dariyarta ba tace "bani Nadeeyah, da sauri ya kara mata a kunne yana cewa "kiyi magana, Anty Reemah ce, A kunyace ta gaisheta, cike da zolaya Anty Reemah tace "Allah yasa na samu ďa, kuma jika, rufe ido Nadeeyah tayi kamar tana gabanta, "ki kama jikinki Nadeeyah, ki sa ruwan zafi da gishiri ki zauna a ciki, sannan kisha tea mai zafi ki hada da paracetamol, kina yin hakan zakiji sauki, Allah ya kara lafiya, karki raga mishi ki bashi wahala kamar yadda ya baki kinji ko, Murmushin karfin hali Nadeeyah tayi tace "nagode Anty, ki gaida min su Hinad, "zasuji my sister, ki kula sosai da mijinki da kanki, yanzu ku biyun nan kune sirrin juna, ku kare ma kanku mutunci, in abu ya dameki ki sameshi ki fada mishi, ku tattala rayuwarku ke da shi, Allah ya baku zaman lafiya, "Ameen Anty nagode sosai, "bakomai dear, a tashi a kama jiki, sai na jiki, bata jira amsarta ba ta kashe wayar, ta cigaba da ayyukan gida.... Taimaka mata yayi ta koma bayin sannan ya fito ya sanya jallabiya ya fita da sauri dan nemo magunguna da abun karyawa, ko kallon inda su Raudha suke baiyi ba, hakan ba karamin dugunzumasu yayi ba suka mike suka nufi dakin da Nadeeyar take.. Jin karan ruwa ya sa su bude bayin a isgilance, yadda ruwan ke shiganta yasata lumshe ido tana jin wani dadi na ratsata, jin muryar Raudha da tayi babu zato shi ya sanyata bude kumburarrun idanuwanta, kallon da suke mata ne ya sa cikinta kartawa ta fara rawar baki tana fadin "ina kwananku, "Lafiya kalau karuwar karshen zamani, yadda maganar ta fito babu control ya sanya Nadeeyah jin wani irin bakin cikin da bata taba ji a kalamansu ba, sunsha zaginta da kalamai marasa daďi amma wannan shine zagi mafi muni da taba cin karo dashi daga garesu, maida kwallar idonta tayi ta dauke kanta a kansu, Nan fa suka cigaba da zaginta suna aibata ta kamar wadanda sukeyi da sa'arsu, kalamansu na batanci yana matukar sosa mata rai, amma haka nan ta danne ta maida hawayenta haďe da fitowa ta dauki towel ta nade jikinta dashi saboda girmanshi, bata sake kallon inda suke ba tayi hanyar fita daga bayin a dan hanzarce duk da tana jin zafin jikinta, ta kama kofar kenan zata murda Raudha ta janyota haďe da dauke fuskarta da mari, "Dan ubanki mu zaki mayar mahaukata, mu zaki bawa banza ajiya, ke har kin isa muna miki magana ki sanya kafarki kiyi waje saboda tsabar raini, cike da masifa Radiya ta karbe da cewa "kinga laifin yar matsiyata marasa asali, Allah kadai yasan daga inda ubanta ya fito har muka haďa jibi da matsiyata irin su masu siffar munafukai, wallahi tallahi in bakiyi dalilin da little ya sakeki ba sai mun sanya bakin ciki ya zama ajalinki, ki fara counting days dinki, dan zuwan Badar da Faida bazai taba zama abu mai dadi a gareki ba, shegiya yar iska, mai sakin jiki gurin namiji a daren farko, "kukan da Nadeeyah takeyi a wannan lokacin mai sauti ne, dan kalamansu yafi mari ciwo a gareta, kalmar rashin asali da ake yawan fadinta a garesu yana matukar taba mata zuciya, gaba daya ji tayi ta tsani zaman duniyan ma, da Allah zai dauki ranta a lokacin da kowa ya huta da kwasarma kanshi zunubi akanta, har suka gama zagi da aibata ta bata dago kai ta dubesu ba kuma bata fasa kukan da takeyi ba, da suka gaji sai suka dungure mata kai da karfi haďe furta wani mugun zagi ga matattun iyayenta, nan kofar bayin ta durkushe tana kuka mai sosa rai... A gigice ya ajiye kayan da ya shigo dasu ya nufi bayin a hanzarce, da sauri ya ďago ta kamar yar baby ya nufi cikin dakin da ita, duk tunaninshi ciwon ne ke damunta, ajiyeta yayi duk ya ruďe yace "bari in dauko miki riga muje asibiti, bazan iya jure ganin kukan nan ba, girgiza mishi kai tayi murya a dashe tace "Naji sauki, bana jin ciwon komai, "to meyasa ki kuka?, ya tambaya cike da damuwa haďe da kwantar da kanshi kan hannunta da ya dau zafi sosai, "Dan Allah yaya Musaddiq ka sakeni!!! Yadda yaji maganar kamar an soka mishi mashi ya sanyashi ďagowa ya kalli cikin idonta da yayi jawur, a hankali ya mike ya zauna sosai kusa da ita haďe da dagota itama ta zauna, "Kiyi hakuri, nasan na miki laifi sosai, na wahalar dake kuma na saki kuka, bazan kara yi miki komai ba in shaa Allah, "dan Allah karki kara yin maganar rabuwar mu, plsss... ya karashe yana mai shafo gefen fuskarta, tausayi sosai ya bata tayi saurin kauda kanta gefe, bata da karfin gwiwar fada mishi dalilinta na san rabuwarsu, yan uwanshi da mahaifiyarshi basa kaunar auren nan, da zaiji ta tata da sun rabu ko hankulansu zai kwanta, hannu yasa ya share mata hawaye ndake gangaro mata yace "komai zaiyi daidai kinji, bari in baki breakfast sai ki sha magani kiyi bacci....... Ajiyar zuciya Marakisiyya tayi bayan ta gama sauraron labarin Badar, ta tausaya mata matuka na ganin ta rabu da abin da take so lokaci kalilan kuma shi yana can yana jin dadinshi da wata, nan ta tambayi Badar tana son ta taimaketa ne ta koma gida, ko kuwa so takeyi ta zauna anan ta koya mata sihirin da ta koya a gurinsu wanda zai sanyata tayi gaggawar rabasu, zuciya marar kashi, Badariyya bata dubi halin da take ciki ba tayi saurin cewa tana son koyon sihirin, dariya Marakisiyya tayi a ranta tace "dama so nakeyi ki koya mu hadu mu biyu mu tada Rugar gaba dayanta sannan mu nemi hanyar garuruwanmu, a fili kuma ce mata tayi "an gama, wasu guraye ta fiddo daga jikinta ta mikawa Badar tace ta rufe idonta, tana rufe idonta ta fara ganin kanta cikin wani sururin guri mai tsananin ban tsoro, nan fa ta dada runtseshi haďe da kankame Marakisiyya tana ihu sosai, bakinta Marakisiyya ta toshe dan sam bata so asan abun da takeyi, sai da sukayi kusan minti 30 a haka sannan Marakisiyya ta kwace gurayen, Wuri wuri Badar tayi da idanuwanta saboda tsananin tsoro, "Kin tsorata ko? Gyaďa kai kawai tayi tana fitar da numfashin wahala, Wata dariyar Marakisiyya ta sake yi tace "Lokacin jin tsoro ya wuce, nan ta kwance wata leda ta cigaba da cewa "dafi kasar nan ki ayyana abu a ranki, zaki ga duk abinda kike yana dawo miki kamar a mafarki, (tayi mata haka ne dan ta kara zura jiki da ita ta).. *HUSNA* ce ta faďo mata a rai wanda a sonta rayuwar su Musaddiq taso fara gani, tana runtse idanuwanta komai na Husnah ya fara yi mata yawo kamar a film, "Zaune ta gansu a kayataccen parlonsu Husnah na zuba ma Hafeez shagwaba yana rarrashinta, komai na gidan su madaidaici gunin sha'awa, babu abin da yafi girgizata ya sanyata cikin bakin kishi kamar ganin yadda fuskar Hafeez ke mata kwarjini da kuma girma kamar wani sarki mai daraja, Saboda sabon shiga ce cikin sihirin shi ya hanata gano muhimmin abun dake tattare da Hafeez, amma tabbas taga alamu na sarauta mai girma a tare dashi.... Saida ta gama duba lafiyar kowa taga duk suna harkarsu ba tare da sun damu da bacewarta ba, Sai ta koma kan wanda take mammako da tsoron duba nasu, aiko tayi mugun gamo, domin kuwa yadda ta gansu a manne da juna ya 'ballo magani yana bata cike da rarrashi haďe da kwantar da ita a jikinshi ba karamin kai ganinta kasa yayi ba, kankancewa idanuwanta sukayi haďe da yin jawur kamar gauta, nan tayi saurin cire hannunta a kasar sihirin da Marakisiyya ta bata, mikewa tayi tana safa da marwah haďe da cin alwashin rabasu kuma ta kashe Nadeeyar gaba daya, Wannan shiga gonarta da Nadeeyah tayi wallahi sai tayi paying da rayuwarta, Cikin kwarewa Marakisiyya ta koya mata duk wasu nau'i na tsafi haďe da bata wasu abubuwan da zata sha tayi wanka dasu, "Hatsabibanci Marakisiyya ya sata koyon duk abubuwan a gidan, ko ina kewayawa takeyi tana koyo haďe da haďa su da kanta, duk yadda aka kai ga tsoron manyan gidan Marakisiyya bata wannan domin ga da ga zata zagesu tass, shiyasa aka koma sa mata bulala a jiki, ta zame musu karfen kafa, basa iyawa da ita, Tun ranar da taga Badariyya ta shin shino barinta gidan da taimakon Badariyya, shiyasa tayi saurin shigar mata da bukatarta kafin ma a samu wata a gidan ta shige mata.... Mrs Tijjani Shattimah.... [20/04 4:18 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣0⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Cikin shashshekar kuka take tambayar doctorn abin da ke damun ďanta, yanayin ruďewar da take ciki ya sanya doctorn dawowa kujerar kusa da ita, "Calm down Ma'am, "ba wani serious abu bane, kawai damuwa ce da rashin cin abinci ya sanya shi zama weak, but with time zai samu sauki in ya kiyaye, ko da baya san cin abinci atleast ya dinga ci ko kadan ne at the right time, sannan ya daina damuwa ko yaya take, thank Goodness bai taba zuciyarshi ba, but yaso yayi affecting dinta, plss ya kiyaye sosai cos life is very precious... Wasu zafafan hawaye ne suka biyo ta gefen idonshi bayan ya gama sauraron abin da doctorn ya faďi "Life is nothing without Nadeeyah, ya Allah ka sassauta min.. Hannu Anty Saude tasa ta share mishi hawayen itama ta share nata sannan tayi ma doctorn godiya ta kuma yi mishi alkawarin kiyaye duk abinda yace mata, har bakin kofa ta rakashi sannan ta wuce kitchen rai a bace, Wani maganin kwari mai karfin gaske ta dauko haďe da juice ta dawo kusa da Taheer ta zauna, yana kallonta ta ďure maganin a ciki, a hankali ya mike yana tambayarta abun da zatayi dashi, ko kallon inda yake batayi ba ta daga juice din zata kaishi bakinta, Wani irin karfi yaji a jikinshi haďe kabe juice din a hannunta, baki na rawa yace "Are u out of ur senses, poison ne fa, so kikeyi ki kashe kanki? "Gara in kashe kaina da irin kisar da kake shirin yi min Taheer, gara in mutu kafin ka kashe kanka kasa min mutuwar ko'ina na jikina, bani da wani muhimmanci a cikin rayuwarka, akan mace kake so ka kashe kanka har kake kiran rayuwa ba komai bace in babu ita, gara ka barni in fara mutuwa sai ka biyoni, bazan iya jurar ganin gawarka ba Tee... . bazan iya ba.... ta karashe tana kuka sosaiiii.... Kanshi ya daga sama da niyyar haďiye kukan da ya tokare makokwaronshi, inaa sam ya kasa, wanda yake kokarin haďiyewa ya fito da karfinshi, Zaman dirshan yayi a gurin yana kuka sosai kamar karamin yaro, bata hanashi ba dan itama kukan takeyi, wallahi da zatayi arangama da yarinyar da tayi wa ďanta haka sai ta shake wuyanta ta kusa kaita lahira, ita duk tunaninta cin amanar ďanta tayi, domin ita tace ya jirata, sai kuma yaji labarin aurenta, duk da bata san wacece Nadeeyah ba taji a duniya bata ko san karo da mai sunan a rayuwarta, Saida sukayi kukansu ma'ishi sannan Taheer ya rarrasheta ya kuma yi mata alkawarin daina tunani akan wacce ta zamto matar wani, sannan ya roketa da Allah kar ta yi mishi maganar aure nan kusa har sai yayi niyya dan kanshi, Badan taso ba ta yarda da kudurinshi, tasa ma ranta nemo mishi yarinyar da zata maye mishi gurbin cin amanar da akayi mishi...... Lafiyayyen abinci ta shirya mishi ta dinga mishi hira, "auu kaga damuwa ta dauke min hankali, jiya *Mus'ab* ya kirani, wai su *Aman* sun samu gurbin karatu anan university of Toronto, ina ganin gobe ma suna hanya, bakaji daďi da naji ba, dan zasu rage min kaďaici in ka tafi makaranta, nuna mata jin dadinshi yayi yace "mantawa nayi ban faďa miki ba, ni na nema musu admission din, Anty Nuwairah duk ta damu wai sunyi nisa, saida taji a gida zasu zauna shine hankalinta ya kwanta, naman karshe Anty Saude tasa a bakinshi tace "Haka tace min, ai naji dadi sosai, Allah ya kawo su lafiya, "Ameen ya faďi haďe da mikewa yace "bari in watsa ruwa, inaga gobe zani lagos, Kudin Abba na companyn coffee ya fito, sunce in je inyi signing..... cike da jin dadi tace "Kaii mashaa Allah, Allah ya kaimu goben...... ********** Tagumi tayi akan dadduma bayan ta idar da Nafila tana jiran a kira sallar asuba ta tashi tayi, tunanin irin rayuwar da takeyi a gidan aurenta takeyi, tunda tazo gidan ta auri zaman ďaki, bata san kalar kitchen dinta ba domin yadda su Radiya suka kanainaye komai, babu inda take fita kullum daga bayi sai ďaki, bata da matsala sam da Musaddiq domin yana kula da ita sosai, abinci ma in ya siyo da kanshi zai bata kuma ya kwashe kayan da kanshi dan shima tsoron tashin hankali yakeyi, a da bata jin son Musaddiq a matsayin abokin rayuwarta, amma kwanaki shidan nan da sukayi tare, halayyarshi ta samar mishi matsayi mai girma a zuciyarta, Mutum ne mai gudun zuciya, yadda bazai bata maka ba, kaima karka bata mishi, samm baya kwana da wani a ranshi, sanyin halinshi shine abu mafi soyuwa a gareta, tun ranar da ya kusanceta yaga irin kukan da tayi, bai sake koda kwatantawa ba, duk ko da tsabar dannewar da yakeyi, samm bayasan abin da zai sata cikin damuwa, ya gwammaci matsuwar ta dameshi akan yasata cikin damuwa... kiran assalatu ne ya katse mata tunanin da takeyi ta mike dan ta tashe shi ta kuma sabunta alwawarta, Bargon da ya dukunkune ta yaye a hankali, zufar da ta gani a fuskarshi ce ta sanyata zaunawa kusa dashi da sauri haďe sa hannu a goshinshi ta fara share mishi, hawayen da ya jika saman idonshi shi yafi komai daga mata hankali, a rude ta fara kokarin ďago kanshi ta kasa saboda har lokacin cikin bacci yakeyi, gefen kunnenta ta kwantar a saitin kirjinshi taji yadda zuciyarshi ke bugawa da sauri da sauri, ajiyar zuciya ya saki haďe da shashesheka ya sanya hannu ya rungumeta sosai a jikinshi, "plss don't lv me, i can't lv without u.... yadda yake maganar ido a rufe ya bata tabbacin mafarki yakeyi, duk wata kunyarta ta nema ta rasa ta rungumo kanshi haďe da share mishi hawayen da yakeyi tace "bazamu rabu ba, in shaa Allahu babu abinda zai rabamu, Allah ne ya haďamu, shine kadai zai iya rabamu in yaso, "bazan barka ba! Jin kalaman da yake a zahiri ba'a mafarki ba yasa shi buďe idonshi haďe da kwantar da ita sosai a jikinshi yace "promise? gyaďa kanta tayi haďe da cewa "Ummm, "umm me? Ya fadi yana daďa narke mata, turo bakinta tayi a shagwabe tace "um um, dariya yayi yace "kinsan nafiki iya shagwaba, in na fara nawa gari zai waye mana ba muyi sallah ba, kinji an tada kabbara, tashi muyi sallah mu roki Allah kar ya tabbatar mana da mafarkin da nayi, juyo fuskarta yayi ya daura hancinshi kan nata numfashinsu ya gauraya da na juna yace "i don't want to loose you, hannunta tasa ta toshe mishi baki cikin zolaya tace "hmmm... muje kayi brush, "bakina wari ko, "ni dai ban faďa ba! "laifin ki ne, baki sani nayi rinsing baki na ba, nidai ba ruwana, kaji anyi sallama ko, dan Allah muje muyi sallah, "zakiyi bayani bari mu idar da Sallah, ya faďi yana dariya haďe da nufar bayin...... Wai Mummy Faida bazata zo bane, babu wani improvement fa, kullum daďa like ma yarinyar nan yake, can u believe that ko gaisheni bata fitowa tayi, ni kam in bazaki turo Faida ba zan shirya in koma gurin 'yayana, Daddyn Ra'ees ko daga wayata baya yi, wannan bai dameni ba, dan nasan ina komawa gida zai huce, burina inga munyi winning yarinyar nan ta bar rayuwar little, Radiya na dire aya Mummy tace "Karki damu, Faida na nan tafe anjima, mun gama magana da Hajiya Aliya, in shaa Allahu komai ya kusa zuwa karshe, kudai ku cigaba da taka tsan tsan kar Daddynku ya gano kina can, dan wallahi in ya gane ba zamuji daďi ba, gyara zama Radiya tayi tace "bazai ji ba in shaa Allah, ai kwana kaďan ya rage, "To Allah ya nuna mana, "Ameen Mummy, sai anjima.... Ki shirya zamu fita bayan la'asar, maida pillow mazauninshi tayi tace "To Allah ya kaimu, "Ameen Habeebty.... Karfe huďu da yan mintina suka fito a shirye tsaff gunin sha'awa, Allah ya taimaka su Raudha sun tafi sama yin Sallah, shiyasa taji dadin fita daga parlon... Banana island suka fara zuwa gidan oganshi wanda suka saba sosai da matarshi, dan yawancin duk wasu muhimman aike Musaddiq ke zuwa, Tarba mai kyau suka samu daga gurin Hajiya Zubaida, mace mai mutunci da fara'a, ga sanin ya kamata, wayayyar mace ce yar birnin kebbi, yaranta uku duka maza, babban cikinsu bai wuce shekara 18 ba, Sai wanda take kira auta dan shekara 9, Bayan sun gama dan taba kayan da ta kawo musu suka dan yi hira kadan sai Musaddiq ya bukaci da su tafi, hana su tafiya tayi tace "ku jira shi, yanzun nan zai dawo, tana rufe baki suka ji an murda kofar, Alhaji Kamal Gumel ne ya shigo tare da ďanshi na biyu, faďaďa murmushinshi yayi yace "Ango kasha kamshi, tare muke da Zubairu, yanzu ya tafi siyomin kifi, ai da nasan kana ciki da na tsaida shi, cike da girmamawa suka tsuguna suka gaida shi, amsawa yayi ta sigar mayar musu da girman haďe da zama yace "masha Allah, gaskiya Musaddiq ka iya zabe, Allah ya baku zaman lafiya, nan hirar aiki ta kacame musu, "ba karamin wahala suke sha ba na hutun da Musaddiq ya dauka, dan in yana nan aiki bai musu yawa haka, akwaishi da azamar aikin office, samm bashi da kasala a nan, saboda yanda mahaifinshi ya nuna mishi muhimmancin aikin da kuma inda suke fatan ya kaishi nan gaba, Da Hajiya Zubaida ta gaji da hirar aikin tace ma Nadeeyah ta tashi suje karamin parlon, ba musu ta mike tabi bayanta, "Wannan hirar tasu ba mai karewa bace, gara muyi tamu anan wacce zata amfane mu, tambayoyi Hajiya Zubaida ta fara yi ma Nadeeyah, kasa bata amsar su Nadeeyah tayi domin wasu bata san yadda zata sa mata ba, dariyar manya Hajiya Zubaida tayi ta fara bata shawarwari kama daga kitchen har kwanciyar aure, da irin ladan da mace ke samu a gidan aurenta, sosai shawarwarin suka shiga Nadeeyah saboda haďawa da tayi da ayoyin Allah da kuma tarihan magabata, Saida suka kara kusan minti 30 sannan suka fara shirin tafiya, Sha tara ta arziki Nadeeyah ta fita dashi daga gidan, sunyi matukar farin cikin haďuwa da juna...... Sai bayan isha'i suka koma gida, fitar tayi ma Nadeeyah daďi dan dama zama guri daya ya isheta, Tun daga waje suke jiyo shewar su Raudha kamar wadanda akayi ma albishir da gidan aljanna, A darare Nadeeyah tabi bayan Musaddiq dake rike da ledojin da suka dawo dasu, "oyoyo my dear broo, Faida ta faďi haďe da nufo inda Musaddiq yake, Sakin fuskarshi yayi yace "Manyan baki ne a gidan, welcome, ya kike? Ledojin hannunshi ta amsa tace "am fine, bari in rage maka nauyi, Wani miyau mai ďaci Nadeeyah ta haďiye wanda bata san daga inda ya taru zuwa bakinta ba, Tana kallon yadda Faida keyi ma Musaddiq fari da idanuwa tans kwarkwasa jikinta, Hanyar sama ta nufa a hankali kamar mai koyon tafiya, ďaga Murya Faida tayi tace "Ina wuni Amarya... cakk.. Nadeeyah tayi a gurin ta kasa juyowa ta bata amsa, Cike da kirsa Radiya tace "uhmm, kaji inda ake girmama na gaba, a duk zaman da nayi a gidan nan Nadeeyah bata taba yunkurin gaida ni ba, "Hmmmm naga deal Anty, gashi yanzu ma ta wuce ba tare da kallon inda muke ba, ai ko ba komai mu yan uwanta ne na jini, amshewa Radiya tayi da cewa "nifa ban ga laifinta ba, dan taga little na rawar jiki akanta ne, shiyasa bata damu dayi ma yan uwanshi biyayya ba, yo ko Mummy ma bata gaisar wa bare ni, jiya Mummy 10missed call tayi mata bata dauka ba, amma ina jiyo muryarta da Hafeezu suna waya... "Kinga laifinta, Raudha ta faďi tana hararar Musaddiq, Zaiyi magana Faida ta rigashi da cewa "Haba Aunties, kuyi hakuri plss, may be amaryarmu kunya takeji, dan Allah kuyi mata uzuri, Daďi Musaddiq yaji har cikin zuciyarshi, duk tunaninshi Faida shigarwa Nadeeyah tayi, baisan duk part of der plan bane, "Thank u my sister, plss ki fahimtar dasu, "Karka damu dear, zasu fahimta, amma kaima ka ďan fahimtar da ita, kasan baka da kamar yan uwa da mahaifiyarka, "auchh Faida ta faďi cikin siririyar murya, na barka a tsaye kuma dawowarka kenan, muje in rakaka ďaki da kayan sai ku fito kuyi dinner da Amarya, Da sauri Nadeeyah ta haye sama ta murda kofar ďakin ta shige, mamakin yadda akayi wa ďakin gyara na musamman ta tsaya yi hawayen dake shirin sauko mata suka kafe, zanin gadon da aka canza ma abun kallo ne, "Did u like it? Waigowa tayi ta kalli Faida da ta shigo haďe da jefo tambayar, Wani irin kallon zaki sani ta gani cikin idanunta wanda yasata saurin kauda idonta ta wuce cikin bayi, tana jiyo muryarsu da Musaddiq a cikin ďakin suna dariya yana yabawa kokarinta, Shi bai dauki hakan da yakeyi komai ba saboda yasan matsayin da ya ajiye Faida, yana dai biye mata ne dan bakonka annabinka, baya son yin abun da zata ga yayi mata wulakanci, Hular kanshi ta cire haďe da shige mishi sosai, cikin wata iriyar murya tace "zan iya taimaka maka kayi wanka, hannunta ya cire kan button din rigarshi yace "noo never mind, in na shirya zamu fito, gefen fuskarshi ta shafo tace "okk dear, sai ka fito, gyaďa kai kawai yayi cike da kosawa, tana fita ya saki ajiyar zuciya ya wuce bayin, Kukan da ya tsani ganinta tanayi shi takeyi bilhakki, bayanta ya rungumo yace "Sorry baby doll, su Anty basu san wacece ke ba, nasan bazaki ķi gaishar dasu ba, kiyi hakuri kinji? Fisge jikinta tayi da karfi ta cigaba da kukan da takeyi, daukarta yayi ya fito da ita daga bayin ya direta akan gado, yadda take kukan yana matukar taba mishi zuciya, zaunar da ita yayi haďe da rungumeta sosai a cikin kirjinshi yana rarrashinta, Saida yaji ta fara ajiyar zuciya alamar tsayawar kukan sannan ya ďago fuskarta ya share mata hawayen, "wannan kukan na shagwaba ne ko na jin daďi, faďa min, ya karashe cikin tsokana.. "Nima ban sani ba, ta fadi tana turo bakinta gaba.. Bakinshi ya daura a kan nata yayi mata light kiss yace "kin sani mana, da bakiyi shuru ba ko, daukarki zanyi in kaiki gurin su Anty sai sun baki hakuri da kansu, Zaro ido tayi cike da tsoro tana niyyar yin magana ya rigata, "kiyi hakuri, plss ko yaya ne ki dinga gaishe su, nd Mummy ko bata kiraki ba ki kirata, ko ba komai mahaifiyarki ce, Danne kuncin da ya taso mata tayi na yadda suka juya maganar, "Babu ranar da zata tashi bata kira Mummy da Mami ba, saidai Mami ta dauka Mummy kuwa sam bata dauka, sannan su kuma mugun tsoronsu ke hanata fitowa inda suke, bata san meye kirsa ba saboda tayi yarinya ta sani, amma a cikin shawarwarin Hajiya Zubaida ta sama wa kanta mafita... Kwantar da kanta tayi a kirjinshi tace "kayi hakuri yayana, in shaa Allahu zan gyara, Lumshe idonshi yayi ya sake kankameta yace "shiyasa nake sonki, sosai sosai, rikita ta ya dinga yi da kalamai masu daďin sauraro, Bata gama tabbatar da tana sonshi ba sai da taga yadda Faida take mishi, ya zame mata dole ta dage in ba haka ba tana ji tana gani Faida zatayi sanadiyyar raba su.... Murďa kofar tayi haďe da shigowa ba tare da sallama ba, aiko tayi gamo, dan yadda ta samesu saida tayi dana sanin shigowa dakin, wani irin kishi ne ya taso ya tokare mata zuciya, ji takeyi kamar ta shako Nadeeyah ta kasheta kowa ya huta, Dakyar kafarta ta iya daukarta ta fita waje tana sharar kwalla, ganin haka yasa su Anty Radiya zagayeta suna tambayarta ko lafiya, girgiza kanta tayi tace "aikin nan da kamar wuya, munyi kaďan mu raba wannan auren, wannan aikin mutum ďaya ce zata iya shi, *uwa*, mahaifiya ce kaďai keda wannan karfin, in har son rabasu da gaske kukeyi sai kusa mahaifiyarku tazo, ni bazan iya ganin takaici ba, tana kaiwa nan ta wuce daki kirjinta kamar zai faďo kasa.... Assalamu Alaikum... "Ameen wa alaika salam, Shamsuddeen ne yau a office dina, Har kasa ya tsuguna ya gaida Daddy, "tashi tashi, ga guri ka zauna, kuna nan lafiya, sosa keya shamsu yayi yace "lafiya kalau Daddy, "To Madallah, ai haka muke son ji, Cike da kunya shamsu yace "dama nazo kawo maka katin bikina ne, jibi in shaa Allah za'a daura, Duk da abun ya sosa ran Daddy sai ya danne yace "Mashaa Allahu, aiko banji ba, kaii na tayaka murna, Allah ya kaimu, yasa ayi damu, Dabaibayi shamsu ya shiga yace "kayi hakuri Daddy, wallahi banda option ne, nan ya bashi labarin duk abin da Radiya take mishi, sannan ya daura da cewa har yanzu tana lagos gidan Musaddiq bata dawo ba, a gigice Daddy yace "Whattt! Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Tabdijam, nagode sosai shamsu, dubu dari biyu Daddy ya ciro a drawer yace "Dan Allah kayi accepting wannan a matsayin sadaki... Sosai Shamsu ya tausaya mishi kuma ya kara ninka girmanshi da yake gani..... Wacece ma me wannan Sunan? Daddy ya tambaya yana zana takardar dake gabanshi, Hajiya Martai kawata ta Maiduguri, wacce take zuwa duk wani sha'ani nawa ta kwana, "uhmmn sai akayi yaya? Dama mijinta ne ya mutu a sokoto, gobe da wuri za'ayi jana'izarshi, "Ayya, to Allah yayi mishi rahama, sai kin dawo, Cike da murna Mummy tace "nagode kwarai, ka fitar dani kunya, da ido kawai ya bita har ta shige ďaki, ticket din jirgin da Malam Ali ya kawo mata ya juya, bazai taba hanata ba, so yake yaga gudun ruwanta, A gurin yabar ticket din ya mike ya fita waje yana mamakin irin halayyar 'yayanshi, Raliya ya kira a waya ta tabbatar mishi da ita tana gida yanzu ma zata zo gidan, kashe wayar yayi ya kira Reemah, Cike da mamaki tace "Wallahi Daddy bani da Masaniya, yanzu Radiya tana gidan Diku, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Kwantar mishi da hankali tayi ta kuma tabbatar mishi yanzu zata kirata ta sata ta koma gida, "Karki damu Reemah, mahaifiyarku ma ta shirya tafiya, ki barsu kawai, so nake in ga gudun ruwansu, A sanyaye Anty Reemah ta kashe wayar ta faďa ma Papa abinda ke faruwa, duk abinda da akeyi a kunnen Hilal dake gaban system dinshi, Ajiye assignment Hinad tayi ta dawo kusa da Anty Reemah ta bata duk labarin da ta kunso daga gurinsu, ta kuma ce sunce ko sati biyu bazata yi a gidan ba, wallahi mantawa nayi ban faďa ma Yaya Hilal ba, i'm very sure Nadeeyah na cikin matsala, "ya kamata a taimaka mata ASAP mum... Rufe system dinshi yayi ya mike ya nufi sama, number Musaddiq ya nema, saida ya kira sau uku sannan ya ďauka, yadda yaji muryarshi ya tabbatar mishi da abun da yaji, dan a lokacin sun gama zagin Nadeeyah kenan saboda ta shiga kitchen zatayi abinci, Hilal baiyi wata wata ba ya kashe wayar, Number Nadeeyah ya kira, tana tsaka da kuka lokacin, duk tunaninta Zainab ce dan ita ke kiranta kullum da wayar Hilal, Cikin Muryar kuka tace "Zainab kuna nan lafiya, zakiji muryata haka, mura nakeyi sosai, ki gaida su Anty, tana kaiwa nan ta kashe wayar... Wani abu yaji ya taso mishi, tuni ya cire Nadeeyah a ranshi a matsayin macen da yake so, amma tana nan makale cikin ranshi a matsayin jininshi wacce ke yawo a dukkan sassa na jikinshi, waya yayi dan neman visa.. Wurgi yayi da wayar saboda tsabar bacin rai, dan sunce sai nan da 3days saboda jirage na hutu, Safa da Marwa ya dingayi a cikin dakin ya dinga jin kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a nigeria........ Mrs Tijjani Shattima.......! [20/04 7:01 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣1⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Yana hangota ya nufo inda take da sauri cike da murnar ganinta, Yasan zuwanta zai sanya su Anty Radiya su bar mishi gida ya samu sakewa da matarshi, baisan komai daga gurinta yake fitowa ba, "I missed u alot Mummy nah, "Missd u more little, nace bari inzo inji ko nayi ma Nadeeyah laifi da har yanzu bata daukar wayata, nan take wani abu ya ďarsu a cikin ranshi, "kodai da gaske ne dasu Anty Raudha ke cewa saboda yana tsananin sonta ne yasa bata girmama mahaifiyarshi da yan uwanshi, hango yadda Faidah take yi musu biyayya yayi a zuciyarshi yace "ina ma abar sonshi ce haka da yan uwanshi, Kauda abun yayi a ranshi yace "Sorry Mummy, wayarta nada matsala ne, kullum sai ta ce in gaishe ki, "Au to Madallah, Muje inga gidan ďana, gaskiya little nayi matukar farin cikin auren nan da kayi, kaga yadda ka canza, Tsaki yayi yace "Dan Allah mummy kice ma Anty Radiya ta koma gida, Cikin dabara tace "dama Radiya bata tafi ba, karka damu tun da nazo tare zamu tafi mu barka ka huta da amaryarka, Cike da jin dadi ya buďe mata motar ya shiga ya tada ta, cike da shauki yake hango su Anty Radiya sun barshi shi kadai a gidan shi da matarshi, so yakeyi ya bata kula ta musamman wanda zai mantar da ita duk bacin ran da ta shiga a farkon amarcinsu, Wani irin sonta yakeji har cikin bargonshi, baisan dalilin da yasa kullum kamar ana dada hura wutar soyayyarta cikin jininshi ba, in ko yana tare da ita jinshi yakeyi a sama kamar su biyun kadai aka halitta a duniyar, Murmushi yayi haďe da karawa motar gudu...... Yana Parking tace "Washh yunwa, da fatan anyi min abinci?.. "Baki da matsala Mummy, Nadeeyah tayi miki abincinta mai daďi, nuna mishi jin daďinta tayi tace "yayi kyau ďan albarka..... Gaurayewa gidan yayi da ihun su, suna kiran sunan Mummy, Kallon gidan tayi cike da jin dadi tace Mashaa Allah, gida yayi kyau little, Allah ya kawo min jikoki suyi ta yawo a gidan sai ya zama complete.. Dariya yayi sosai yana duban ta inda zaiga rabin rayuwarshi, hangota yayi cikin dogon hijab tana sakkowa daga sama fuskar nan dauke da murmushinta mai kyau, Gaban Mummy tazo ta tsuguna ta gaida ta, dagota tayi cike da kissa ta rungumeta tace "mun sameku lafiya?, "lafiya lau Mummy, ya hanya? "Hanya ba daďi, muje in huta sai inci abinci, "Ki fara cin abincin Mummy, Faidah ta faďi tana rike mata hannu, kyafta mata Anty Radiya tayi wanda hakan yasa ta nufi gurin dining din ta zauna, Zama Musaddiq yayi a gefenta ranshi wasai dan yasan Mummy zata ji daďin girkin matarshi wanda saida aka kai ruwa rana kafin su barta ta shiga tayi, Kamshin da ya karaďe gurin ya sanya Mummy faďin "Mmmm Masha Allah, nayi missing abincinki Nadeeyah, Murmushin jin dadin kalaman Mummy tayi, duk wani bacin rai taji ya gushe cikin zuciyarta, "Shinkafa zakici ko tuwo? Faida ta tambaya tana bude warmers din, "Saka min tuwon, Malmala biyu ta zuba mata sannan ta bude miyar ta fara karto kasan da serving spoon tana zubawa, Kallon kallo Radiya da Raudha sukayi wa juna, Kafin suyi magana Mummy tace "samin naman mana, "Babu a cikin nan, saidai ko a stew, bude stew din Faidah tayi ta fara zakulowa nan ma ba nama, Hankalin Nadeeyah ba karamin tashi yayi ba, dan tasan tayi miya da naman saniya, ganda da na kaza, Wata siririyar ganda Faida ta dauko cikin stew din tace "luckily an samu bpomo... Jan kujerar Mummy tayi ta mike haďe da cewa "Nagode, yunwar ma bata dameni ba, Faidah zo ki siyo min Nama a waje, tana kaiwa nan tace "ina ne dakin da zan kwana? Ko akwai BQ, in akwai a kaini can in yaso da safe sai in nemi hotel kar in takura ma little da Amaryarshi... ta karashe dauke da murmushi a kan fuskarta, "Wallahi ke da gidan danki babu abinda zaisa ki kama hotel, Raudha ta faďi tana hararar Nadeeyah da Musaddiq, "In ba rashin sanin darajar na gaba ba, ki dauko tafiya tun daga kaduna har nan amma ki tarar da abinci lami, tsiyar ýaýan talakawa kenan, basu san inda suke nuna makonsu da tattalinsu ba, Allah ya kyauta, Hannun Mummy Radiya ta kama tace "yi hakuri Mummy, muje sama ki huta, yanzu zan miki farfesu, "a'a karku damu, kuyi mata uzuri, inaga ko taga naman ba yawa ne, Gaban Nadeeyah taje wacce tuni hawaye ya jika gaban hijab dinta tace "daina kuka yar albarka, in banci nama yau ba gobe zanci, Sake sunkuyar da kai Nadeeyah tayi tana jin wani irin zafi a cikin ranta kamar zata mutu, tana jin su sunata maganganu har suka haura sama.. Kallon Musaddiq tayi wanda shi din ma ita yake kallo idanuwanshi jajur, ya rasa inda zaisa abun da idonshi ya gane mishi yau, ya jira ta kare kanta amma baiji ko kalma ďaya daga gareta ba, Ashe haka kike? Shine tambayar da zuciyarshi takewa tata, Bai taba tunanin rashin girmama mahaifiyarshi har ya kai haka a gurinta ba, ganin irin kallon tuhumar da yake mata ne ya sanyata takowa inda yake, tsananta kukanta tayi wanda a lokacin ya ke ganinshi kamar na raini, dan tasan baya son yaga hawayenta, "ka yar----- "Plss Nadeeyah ya katseta haďe da ďaga mata hannu, juyawa tayi ta ruga daki da gudu tana kuka mai sauti sosai, tana ganin sanda suka arta ciki a guje suna dariya... Waiii... lallai Faidah akwai kaifin tunani, dama tace ke kadai ce zaiga an taba ya hassala, Shhhhh.... Faida tace haďe da rage murya, "bazamu taba kuskuren maida maganar nan ba sai ranar da aiki ya cika, mistake kadan na iya watsa efforts din mu, Bakinsu suka kama sukayi gumm suka cigaba da zaman tagumi suna jiran shigowar Musaddiq.... Sosai suka ingiza zuciyarshi, Mummy na tausarsu tana hawayen munafurci tace "Ni ban san me nayi ma Nadeeyah ba, iya kauna na nuna mata, kowa yasan ajizancin dan adam ai, da sai tazo ta bani hakuri.... Naman da ya siyo ya ajiye mata ya tashi ya fita rai a bace najin har lokacin bata je ta bawa Mummy hakuri ba... Koda ya shiga dakin kasa yi mata magana yayi ya faďa bayi dan watsa ruwa, Kukan ta da yake ji har cikin bayin shi ya sake dungunzuma zuciyarshi, "ita dadi ne ma yayi mata yawa, ita ce tayi laifi kuma itace ta ke kuka, yana fitowa ya sanya kaya ya dauki pillow ya kwanta akan kujera haďe da toshe kunnuwanshi, Tafi awa tana kuka bai kulata ba, shima yin na zuci yake, Ita kadai ce a duk duniya zatayi mishi abin da tayi ya kyaleta, duk rashin fushinshi yakan yi action akan mahaifiyarshi dan yana matukar kaunarta kamar yadda take kaunarshi,, Da yaji kukan yaki karewa ya mike ya dawo inda take, "Ko zaki je daga waje kiyi kukan? kinsan in dadi yayi maka yawa babu abinda bazakayi ba! Kalamanshi sun sosa mata rai sosai tace "Ka sakeni sai in tafi can wani guri inyi kuka na, Kanshi ya juyar gefe zuciyar mai hakuri ta baci matuka, murya a kausashe yace "Sau biyu kenan kina furta min wannan kalmar, dan kinga ina sonki, kuma kina ganin bazan iya rabuwa dake ba shiyasa kike threatnn dina da ita ko? Cikin kuka sosai tace "Ni dai bazan iya ba, gara kawai mu rabu ko---- Wani mugun mari ya ďauketa dashi haďe da shake wuyanta, "Gara in kashe ki nima in mutu da kalmar da kike son kasheni da ita, samm baya ko ganin yadda ta rike hannunshi tana kakari saboda yadda idonshi ya rufe da bacin rai da hawaye, Saida yaji tana wani irin kuka kamar mage tasha damka sannan ne jikinshi yayi sanyi ya saketa ya zauna a gurin yana rusa kuka, "why did u want to lv me, why? Meyasa kike son gasgata mafarkina? Duk da wuyanta na mata makaki hakan bai hanata sakkowa inda yake ba, Tasan bata kyauta ba, duk dan halak hakan zaiyi in yaga abun da ya faru yau, wani ma zaiyi fin hakan, Cikin jikinshi ta shige kamar mage ta kwanta haďe da rungumo wuyanshi tace "am so sorry, dan Allah ka yafe min, Wata irin runguma yayi mata kamar zai maida ita cikinshi yace "Dan Allah karki rabu dani, no matter how hard tins are plss my love, bata bashi amsa ba tayi kokarin sanya bakinta cikin nashi dan ta kwantar mishi da hankali... A wannan daren da su Mummy ke kwance cikin farin cikin fara samun nasara, a wannan daren su kuma ma'auratan suka sake samun shakuwa mai karfi a tsakaninsu, wanda suke ganin in har wani abu yayi sanadiyyar rabuwarsu to fa zasu iya rasa rayuwarsu....... Washe gari tun shida na asuba Nadeeyah ta shirya ma Mummy breakfast mai rai da lafiya haďe da farfesun kaza, A kofar kitchen din ya tsaya yana kallonta cike da shauki, sai a lokacin ya sake tabbatar da jiya matsala aka samu, Haďe komai tayi cikin warmers, tana wanke hannunta taji ya kwanto ta bayanta, murmushi tayi tace "yauwa plss ka siyo kunun tsamiya sai a dama ma Mummy, kasan tana son karyawa dashi, Lumshe idanuwanshi yayi yace "nooo muje ki huta, gobe sai kiyi mata kunun, gyaďa kanta tayi tace "ko dai kaima yunwar kake ji? daukarta yayi yace "sosai ma, amma kinsan bana karyawa da wuri, "Daukata baya maka wuya, abinci zan fara ci inyi adding weight in ka daukeni kayi ta nishi, dan Allah ka saukeni kar wani ya fito ya ganmu, tafiya ya fara yi yace "in an ganmu ai da matata aka ganni, ni bacci nakeji, muje ki tayani, Sun kusa step din karshe Mummy ta fito daga ďakin da ta kwana, kokarin sauka Nadeeyah tayi ya sake riketa yana dariya, "Wai kunyar ki take ji! runtse ido Nadeeyah tayi tace "Dan Allah ka saukeni, a hankali ya sauketa yace "Good morning maa, Cike da danniyar maida danta bawa da taga Nadeeyah tayi tace "morning my dear, "Ina kwana Mummy, Nadeeyah ta faďi bayan ta tsuguna kasa, "lafiya kalau Nadeeyah, ya gajiyarki, "babu gajiya Mummy, ga breakfast can ko nan zan hawo miki dashi, "a'a barshi a can, zan fi jin dadin karin a can, Gefe suka matsa dan bata guri, ta wuce tana tunanin ta inda zata sake bullo musu, ya zame mata dole tayi abun da zatayi yau zuwa gobe dan jibi zata wuce...... Ranar throughout Nadeeyah bata basu wata kofar da zasuyi complain ba, kome zatayi a tsantsane take yinshi saboda bata san abin da zai kara sanya mijinta cikin bacin rai, duk yadda Faida taso provoking dinta taki yarda ta kulata dan bata da lokacinta, Cikin dare suka tashi suka shirya kulle kullensu, sannan daga can wani bangaren da basu masaniya ana taimaka wa aikinsu..... *(Kana Bacci ana maka nasari)* Mrs Tijjani Shattima..... [22/04 8:08 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣2⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Kamar kullum yau ma tun uku saura ta farka dan yin sallar Nafila, wata iriyar kasala ce ta sauko mata wacce ta hanata barin kan gadon, zaune tayi tana gyangyadi har huďu ta gota, da ta gaji da gyangyaďin sai ta ja pillow ta kwanta riris, bacci mai nauyi yayi gaba da ita... A kunnenta aka sallame sallah a masallacin kusa dasu, mikewa tayi jiki ba kwari ta nufi bayi dan yin alwala, sai da tayi minti goma akan toilet tana bacci sannan ta buďe ido da kyar tayi tsarki ta mike ta kunna pampo tayi alwala kamar me tsoron taba ruwan, koda ta fito daga bayin zama tayi a kan kujera tana tuno mafarkin da tayi wanda ya kashe mata jiki matuka, mafarkin ya taba ta sosai dan a iya saninta mafarkin dariya bai taba zama alkhairi ga mai yinshi, bare ita da taga dukkan wadanda suke nuna mata kiyayya kewaye da ita suna kuka ita kuma tana tsakiya tana kyakyata musu dariya mai sauti harda kaiwa kasa, gefe kuma Musaddiq na zaune shima dariyar yakeyi yana kurbar juice, dariyar da sukayi a cikin mafarkin kamar wadanda aka saukar musu da wahayin yinta, haka kukan da su Mummy keyi kamar wadanda suka rasa wani sashi na jikinsu, Anty Reemah, Hilal, Hafeez da Husnah kuwa suna tsaye rai a bace suna masifa kamar zasu ari baki, shigowar Daddy da Papy shi ya farkar da ita... Tunda ya farka ya lura da yanayinta, bai kulata ba ya nufi bayi yayi alwala dan yaga garin har ya fara haske, a yadda ya barta haka ya sameta, wannan karan idonta a rufe yake wani baccin take son sake yi, gyara hannun jallabiyarshi yayi ya zauna a gefenta haďe da taba kanta, a hankali ta buďe ido ta kalleshi, "Har ka idar da sallah? Kwantar da kanta yayi kan kafaďunshi yace "yanzu zanyi, shine baki tashe ni ba ko? Cikin magagi tace "Nima banyi sallah ba, bacci ya hana ni, zaunar da ita yayi sosai yace "whatt, ba dai bacci ba, sai dai shaiďan, tashi maza muyi sallah, Mikewa tayi jiki ba kwari tabi bayanshi sukayi Sallar, suna idar da sallar taji duk wani baccin da takeji ya tafi, sai dai kasalar da ta kasa barinta, Bayan ta gaisheshi ta fita dan zuwa kitchen haďa ma Mummy break fast, karar tv da taji shi ya bata tabbacin akwai mutane a parlon, a nutse ta karasa saukowa ta nufi parlon dan duk tunaninta Mummy ce ko Anty Radiya, turuss... tayi tana kallon Faidah wacce ke kwance daga ita sai mini skirt da wata yar riga wacce iyakarta cibi, kwanciyar da tayi bai boye komai na surar jikinta ba, kirjinta kuwa ya bulluko kamar zai faso rigar kayan kirjin su fito, Saman ta kalla taga ko Musaddiq ya biyota, ganin baya gurin yasata saurin karasawa gurin Faidah rai a bace, gaba daya tsoron da takeji nata ta nemeshi ta rasa, "Baiwar Allah, gidan nan ba na mata bane zallah akwai maza, dan Allah ki tashi ki canzo kaya, Mikewa Faidah tayi tana murmushi tace "Ba matsala bane dan ya ganni a haka, musulunci ma ya yarda in kana neman auren mace ta bayyana maka surar jikinta kafin ka aureta, karki damu dani je kiyi cookun ki, Ran Nadeeyah in yayi dubu to duka sun baci, baki yin kanshi yakeyi, bata san lokacin da bakinta ya furta cewar "Ke bakiyi kama da tsarin matan mijina zai ruďe akan surarsu ba, bance shi nawa bane ni kadai, amma fa ki sani ko zaiyi wani auren sai dai ya nemo wacce ta fini ba wai ya koma baya ya dauko wacce bata kaini ba... "Ahayyyyyeee..... Faidah ta faďi tana tafa hannu, wacce ta fiki me? kyau? Kudi? Asali ko me? Ko dayake banda lokacinki, nasan a cikin abun da kike takama dashi nafiki su 99%, Asali shi kadai zaka fini ka cuceni, Faďa min menene asalinki? Waye mahaifinki wanda ya kamata ya zamto ado a gareki? Waya sani ma ko irin yan fashin shanun nan ne aka buďe musu wuta suka arto nigeria neman maf--- Zazzafan Mari Nadeeyah ta sauke a fuskar Faidah wanda saida ta dauki lokaci mai tsawo tana tattaro confidence dinta kafin ta iya aiwatar dashi, sauke marin yayi daidai da sakkowar Mummy daga sama... "Kaii kaii, me nake gani haka? Mari fa? Mummy ta faďi tana karasowa har tana missing steps kafarta na gurďewa, ko kallonta Nadeeyah batayi ba dan a lokacin ji takeyi kamar ana hura wuta a cikin zuciyarta, Kuka Faida ta fashe dashi ta rungume Mummy wacce ta rufe mata jiki da hijab din da ta sakko dashi, "Subhanallahi.. Nadeeyah me yayi zafi haka harda mari, in baki dubi cewa ba sa'arki bace ai kya duba cewa ita bakuwarki ce, "Bakuwarku dai Nadeeyah ta faďi cikin ficewar hayyaci, ranta yayi matukar baci, ba'a taba aibata mahaifinta har haka ba, abun ya haďe mata biyu ne, ga kishi ga tabo iyaye, mai hankali ne kadai yasan halin da zuciyarta ke ciki a wannan lokacin, Sakin baki Mummy tayi tace "Ni kike fadama bakar magana, gefenta tabi ta haye sama ba tare da ta kulata ba zuciyarta na tafasa, ta gaji da zaman nan na kaskanci da takeyi, badan tana jin soyayyar Musaddiq har cikin jininta ba wallahi da babu abinda zai hana ta tattara kayanta ta gudu ta bar musu gidan, to bazata iya rabuwa dashi ko na second ba dan tayi matukar sabawa dashi, ta dai ďauki alwashin kwatar ma kanta yanci gurin duk masu neman muzanta ta, dakinsu ta shiga ta sameshi yana baccinshi hankali kwance, key tasawa ďakin ta karaso kusa dashi ta cire hijab dinta ta shige cikin jikinshi taja musu bargon, rungumeta yayi sosai yace "Har kin gama? a shagwabe tace "um um, bacci nakeji, in na tashi zanyi, bai damu ba dan yasan yadda yaganta da ta tashi, yadda jikinshi yayi mata rumfa yasata manta duk wani bacin ran da ta kwaso daga kasa tayi luppp har bacci yayi gaba da ita.... Karar waya ce ta tashi Musaddiq daga nannauyan baccin da sukeyi, hannu ya mik'a ya lalubota a gefen gadon.. kokarin zare jikinshi yakeyi a hankali dan kar ya tasheta yaji ta kara kankameshi haďe da sake gyara kanta a kirjinshi, hannunshi ya tura cikin gashinta yana squeezing dinshi a hankali, kallon wayar yayi yaga sha ďaya saura sannan ya duba kiran da ya zama missed call, bin bayan kiran yayi asap, "Yallabai hw far "Ango kasha kamshi, daga ďaya bangaren Zubair ya amsa cikin zolaya,, "Hutu dai ya kare, ga kuma wani hutun zaizo, tafiya Singapore 3month course kuma oga yasa sunanka, kaga sai kayi honeymoon dinka hankali kwance, "Woww Musaddiq ya faďi da karfi har Nadeeyah na farkawa a ďan firgice, murmushi yayi a hankali yace "sorry baby, "yaushe ne tafiyan Zubair? Dariya sosai Zubair yayi yace "Kaji shi, dama aikin ya isheka ko, to next week ne, "Mashaa Allah, bari mu fara shiri, gobe zan zo aiki tun 8 in shaa Allah, "To Allah ya kaimu ango, a gaida min amarya, "Gata nan tana amsawa, tace bakazo kaci abincin amarya ba, Dariya Zubair yayi yace "kace mata har sai ta gaji da gwauro, in na fara mata sintiri sai ta rufe min kofa... Dariya sukayi dukkansu sannan suka koma wata hirar daban... Daga Nadeeyah har Musaddiq basu san kalubalen dake cikin aure ba, har gara Nadeeyah tasan Hakuri da juriya sune ginshiki a zaman aure, shiko Musaddiq da ya tashi cikin gatan da babu fatawar komai sai ta sakarci duk daukarshi aure kawai jindadi ne da mace, ka bata abinci, ta kula dakai tayi maka duk wasu bukatu, bai san ainihin tushen aure shine Hakuri da jajircewa ba, bai taba hasaso wani tashin hankalin da zai sauya rayuwarshi na nan tafe cikin kankanin lokaci ba.... Jiyar da juna daďi sukayi a wannan safiyar saboda murnar zasu kadaitu da juna na tsawon lokaci ba tare da tashin hankalin yan uwa ba, abun da basu taba yi tare ba shi sukayi ranar wanka, Nadeeyah har mamakin yadda ta saki jiki dashi cikin kankanin lokaci take, kwata kwata duk wata kunya tata ta rasa inda tayi balaguro, sosai take son jinta like a jikinshi a koda yaushe, Kananan kaya ya saka wadanda suka fitar da ainihin kyawunsa.. Hannunshi Nadeeyah ta kamo ta zaunar dashi akan madubi tayi brushing gashin kanshi da kwantaccen sajen gefen fuskarshi.. "Kayi kyau sosai sosai, kewayeta yayi da hannunshi ya daura kanshi kan ruwan cikinta haďe da lumshe ido yace " *I can't quantify my love for you, it's more than the sand under the sea. Like a snail cannot live nor survive without its shell, I cannot live without you cos with you, there is life....* Bata san sanda ta sanya hannu ta rungume kanshi tana shafawa ba saboda daďin da kalaman sukayi mata, "I can't live without u either, Zaunar da ita yayi akan cinyarshi cikin raďa yace "Sure? Gyaďa kanta tayi haďe da kwanciya a jikinshi, Oya muje muyi breakfast, to 12 yanzu, munyi latti, Buďe bakinta tayi a firgice dan shaff ta manta bata yi ma Mummy abinda ya kaita kasa dazu ba, abubuwan da suka faru ta shiga tariyowa cikin kwakwalwarta, "Na shiga uku! ta faďi a hankali dan tuno yadda tayi ma Mummy dazu wanda sai yanzu taga rashin kyautuwarsa, Ganin idonta na shirin tara ruwa Musaddiq yayi saurin mikewa haďe da cewa "Hey calm down, ai ba yin kanki bane, Mummy will understand, nasan sun karya ma by nw, Jiki babu kwari dan bata san abun da zata tarar ba in ta fita parlon tace "To muje in haďa maka breakfast, sai inyi saurin daura lunch, "Kindai kusa hutawa, in mukayi tafiya ko cup bazaki dauke ba, so nakeyi kafin mu dawo ki zama big madam, "kaga nima sai in dinga daukarka a wuya na, ta faďi tana dariya haďe da bude kofa, dariyar shima yayi ya biyota yana cewa "impossible, ko hannuna bazaki iya ďagawa shi kaďai ba, Ringing din da wayarshi keyi shi ya hanata bashi amsa ta sauka kasa tana dariya, ganin ba kowa a parlon ya sa tayi tunanin ko suna daki ne, kitchen ta wuce taga komai tsaff kamar yadda ta barshi da daddare, bata kawo komai a ranta ba ta fara dafa mishi indomie dan itace mai sauki, tana yanka albasa taji muryarshi a bayanta, "Amm dazu da kika fito da safe wani abu ya faru ne? Gabanta ne yayi mugun faďuwa ta cigaba da yanka albasa tace "wani abu akace maka ya faru? Wukar hannunta ya karba ya juyo da ita yace "I trust u Nadeeyah, daga bakinki kawai nakeson jin gaskiyar magana, banason ki boye min komai, Kasa ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara sintiri a idonta, "Uhmm tell me! "Ni bansan yadda zan faďi maka ba, duk yadda suka faďa maka daidai ne, Zai sake magana yaji wayar ta sake ringing, da yake suna gab da juna taji duk abun da Anty Radiya tace a wayar, "Ka fito ne ko har yanzu kana like gurin wacce ta zagi mahaifiyarka har ta koreta a gidan danta? Kashe wayar yayi jikinshi ya fara rawa yace "Plss tell me Nadeeyah, tafiya ta fara yi dan kukan da takeyi na neman cin karfinta, "Kaje dan Allah, duk abinda aka ce maka nayi nayi ne, Ranshi ya fara baci da kalamanta ya juyota da karfi yace "A bakinki nake son ji, a harzuke ta ture hannunshi tace "Ka tambayi zuciyarka in ta yarda zan iya aikata abun da aka faďa maka fine, sai ka dau mataki a kaina, Rage murya yayi yace "Yaushe kika canja Nadeeyah, are u ok? "very okk, ban canja ba, saidai in kai ne ka kasa ganin abun da wasu da yawa ke gani a gurina, "Wallahi Allah na gaji, kullum cikin sharri, da nasan hakan ce zata kasance dani wallahi da bazan taba yarda da aur--------- Mari masu zafi har biyu ya sauke mata a fuska haďe da kaita jikin bango da karfin gaske, "Aaaaaa...... ta faďi tana rike kanta dan ta bugu sosai, Yanayinshi gaba ďaya ya sauya kamar zaki, babu abinda da yake iya furtawa sai wasu numfarfashi da yake fitarwa, komai zai iya sauraronshi daga gareta banda batun rabuwa sai kuma yanzu da ta nuna favours tayi mishi da ta aureshi, bacin ran da yake ciki a yanzu yafi na kullum, murya a kausashe kamar wanda ake ingizawa yace "Wacece ke? Wacece ke da kike ganin kamar kin taimakeni ne da kika aureni, badan zuciya me rore rore ba ke kin isa ki zamo matata, kalleni da kyau, kinsan nafi karfinki ta ko ina, babu abinda ban kere miki ba a rayuwa, Wallahi badan tausayinki da ya rikiďe ya zame min soyayya ba da babu abinda zanyi da marar asa---- Cikin kuka ta katseshi a hankali dan kalamanshi sun kashe mata jiki matuka, "Akwai wadanda suke so na, wadanda basu damu da sanin asalina ba, me yasa baka barsu sun aureni ba? meyasa baka bar wanda zai rikeni ya yarda da asalina ya aureni ba? sai yanzu da ka koyamin sonka zaka bullo da cin mutunci a gareni, why Yaya Musaddiq? Hawaye ne ya zubo a idonshi amma zuciyarshi sam bata karaya ba yace "I will free u, kije ki auri wanda kike ganin zai fini baki kwanciyar hankali, Toshe mishi baki tayi da hannunta haďe da shigewa jikinshi tana kuka sosai.. "Dan Allah kayi hakuri, don't separate urself from me, plss.... Su Mummy dake tsaye a bayanta tun jin kararta na farko suka dawo cikin gidan ta fashe da kukan munafurci, Shigowa kitchen tayi ta kashe gas din da ruwan ya kusa kafewa tace "Bana san rabuwarku, bansan me yasa kika tsaneni ba Nadeeyah, har kika kai ga zagi da cin mutuncina, har kina nuna min cewa ke ba son ďana kikeyi ba a idona, wace uwa ce zata juri wannan, waye yake zuga ki? Waye shi inje inji dalili, Dama harzuka Musaddiq din tazo yi aiko ya harzuka, nan ya fara zagin Nadeeyah, zagi na cin mutunci wanda a iya saninshi bai taba yinshi ga wani ba, da taga ya tabo inda bazata iya jurewa ba ta share hawayenta ta fara maida mishi, nan kitchen din ya gauraye da tashin hankali, su Raudha da Radiya suka shigo suka haďu akan Nadeeyah, Ganin har lokacin Musaddiq yaki furta kalmar saki ya sanya Mummy rike hannun Nadeeyah tace "A idona kike cin mutuncina da 'yayana, "a idonki 'yayanki ke cin mutuncin iyayena, kin hana su?, Rashin kunya sosai ta zubawa Mummy wanda dama shiryayye ne sun san dashi, kafin ta rufe baki Musaddiq ya daka mata tsawa haďe da furta kalmar saki cikin rashin sani da tsananin bacin rai, Yana furtawa Anty Raudah ta jashi waje dan ma kar kukanta ya karya mishi zuciya, cikin mota ta tura shi tace ma Faida taja shi su tafi...... Tafawa sukayi haďe da sakin tsalle, "zo "zo "zo Badariyya, akwai sauran rina a kaba, kalli ki gani... Hoton Faida ta nuno mata suna zaune cikin mota tana rarrashinshi cikin kwarkwasa, Kallon marakisiyya tayi cikin tashin hankali tace "Ya zamuyi da wannan?, "Ina zuwa Marakisiyya ta faďi haďe da mikewa, da dan gudu tayi dakinta ta dauko wata allura da naďin laya, duk abun nan da sukeyi a idon Yareemah Suhail, jiransu yakeyi su gama ya tarwatsa aikin sannan ya kwace duk wani sihiri da Marakisiyya ta mallaka, Shiryayyen shiri sukayi ma Faida wanda zaisa gaba ďaya taji Musaddiq ya fita a ranta kuma ta faďa mishi duk irin shirin da sukayi dan rabashi da Nadeeyah, ma'anar hakan shine Badariyyah naso in ta koma ya zamana ita kaďai ce wacce zata dinga kula da shi, dan tasan zai tsani Mummy da tayi mata zagon kasa da sauran yan uwanshi, sun fi awa hudu suna aikin kafin su iya samun nasarar aikawa gurin Faida da har lokacin suke tare da Musaddiq, Wani abu ne taji ya soketa wanda ya sanyata dauke hannunta daga kan kafaďunshi, a lokacin shi kuma wasu zafafan hawaye suka shiga fitowa da cikin idonshi, tausayinshi ne ya ratsata taji bata kyauta ba da ta raba shi da matarshi sabon aure, tasan yadda yakeji saboda tana ganin yadda masoya sukeyi a film, sannan ta tuna da rabuwarta da masoyinta Zubair wanda iyayenta suka hanata aurenshi saboda bashi da kudi, "Kayi hakuri Musaddiq, kwantar da kanshi yayi kan sit ya fara kuka mai sauti, "kamar wacce aka tsikara ta fara faďa mishi abubuwan da suka shirya tun kafin aurenshi da Nadeeyah, har zuwa na yau bata rage mishi komai ba, har marin da Nadeeyar tayi mata sannan ta karashe da cewa is not late Musaddiq, Kaje ka dawo da matarka, dan bazan boye maka ba, zaiyi wuya ka samu mace irinta mai kawaici da hakurin shanye abubuwa... Tunda ta fara magana yake mata wani irin kallo na mamaki, tana kaiwa aya ya dubi agogon hannunshi, biyar saura ya gani, bai tsaya bata lokaci ba saboda bashi da ishashshen lokaci yayi saurin cewa "Muje gida plsss, tada motar da sauri, Revrse tayi ta ja motar da gudu kamar zata tashi sama, burinta ta isa akan lokacin domin shirinsu na su koreta ne sai suce ita ta tafi da kanta bayan ta zazzagesu, wayarshi ya dauka ya dinga kiran Nadeeyah yaji wayar a kashe, dangwarar da wayar yayi haďe da dafe kanshi yana ta hango wautarshi, magiyar da ta dinga mishi ya ke tunonowa., runtse idonshi yayi sosai hawaye na artabu a cikin kwayar idonshi, "Me ya sameni,? ya furta a hankali kamar me koyon magana, Faidah da itama ta rasa abinda yake mata dadi cikin ranta tace "Babu, influence din mu, plss forgive me, am going outta ur life yau dinnan.... Suna isa kofar gidan ya buďe kofar tun kafin ta tsayar da motar, wani irin turi yayi ma gate din ya bude dukkanshi, gudu gudu yayi ya shiga ciki, Tun a harabar gidan yake jiyo shewar su Anty Raudha, bai bi takai ba dan shi burinshi daga ya shiga yayi tozali da Nadeeyah, suna jin an turo kofar sukayi gumm suka koma gurin Mummy suna danna kafaďunta suna bata hakuri, Taku uku yayi ya hau sama ya murďa kofar ďakin da karfi, jin karan ruwa a bayi yasa shi sakin ajiyar zuciya haďe da maida numfashi, matakin da ya shirya dauka akan yan uwanshi da mahaifiyarshi mai karfi ne, dan kiriss ya rage su rabashi da abunda yake jin so a yanzu fiye da komai a rayuwarshi, bayin ya nufa da sauri ya murďa haďe da sakin fuskarshi, ganin bata cikin bayin yasashi fara dube dube yana kiran sunanta, kayanta dake cikin dakin ya duba yaga wayam ba komai sai kamshinta dake manne a gurin, da sauri ya koma daya dakin dan duba ko tana can tana kwashe sauran kayanta, nan ma babu ita sai tsirarrun kayanta, faďin irin tashin hankalin da Musaddiq ya shiga a wannan lokacin bata baki ne dan kuwa babu inda a jikinshi baya rawa yana dube duben inda zai ganta, Kasa ya sauko da sauri yana kwala kiran sunanta, matsowa kusa dashi Anty Radiya tayi tace "Ka bar neman wacce ta mari mahai----- Don't u dare... ya faďi da karfi wanda ya tsorata dukkaninsu, wani irin yanayi suka gani akan fuskarshi wanda basu taba sanin akwaishi tattare da kaninsu ba, bai dauke idonshi a kanta ba yace "Ina Nadeeyah? ja da baya Radiya tayi dan ga dukkan alamu Musaddiq na iya dukanta domin yadda idanuwanshi suka canza launi jijiyoyi suka mimmike akanshi, "Ta tafi Musaddiq, nasan batayi nisa da gida ba, zo muje mu nemota kafin lokaci ya kure... kallon mamaki su Radiya suka bi Faida dashi, basu iya furta komai ba har suka bar parlon.. Duk inda ya kamata su duba sun duba basu ga Nadeeyah, gaba ďaya hawaye ma Musaddiq nemanshi yayi ya rasa saboda tashin hankali, gidan Hajiya Zubaida nan suka je a karshe bata can, duk tashoshin kusa saida suka duba basu ganta ba, ko wayarshi dake ta ringing bai duba ba bare yasan wanda ke kiranshi... Sake kiranshi Hilal yayi a karo na goma sha hudu har lokacin Musaddiq bai dauka ba, Zubair ya kira a waya yace "yazo ya daukeshi a airport bazai gane gidan ba, ya kuma rokeshi da yayi sauri dan tun jiya hankalinshi yaki kwanciya, Minti talatin ce ta kaishi airport din saboda gudun da yayi, gaisawa sukayi Hilal ya faďa motar suka nufi hanyar gidan Musaddiq.... Wani lungu Nadeeyah ta zauna a nesa da layinsu kusa da 3stars luxury Hotel taci kukanta ma'ishi, wanda har ya saukar mata da zazzabi, wayarta da zata kira Papy ma sun kwace mata, haka suka tasota a gaba ba ko sisi tare da sharadin kar ta nemi Daddy tunda ba ubanta bane shi, akwatinta ta dauka lokacin gari yayi duhu ta fara tafiya tana neman abun hawan da zai taimaketa ya kaita tashar da zata samu a kaita Gombe.... "Kusan fifty seven million Momma, but zasu cire 5m na workers sai 5m a each shareholders na gwamnati, yanzu ina driving ne kuma is late gobe da safe zanje bank inyi transferring zuwa acc dina, hope kina kula da kanki?, gyara kwanciyarta tayi cike da jindadi tace "sosai ma, ga kuma wasu kudin sun shigo na sake kula da kaina da kai, Allah dai ya jikan Abbanka, "Ameen Momma, na kusa karasawa masauki in shaa Allah, su Aman ma sun shigo lagos gobe zamu taho tare, "To Mashaa Allah, sai kun zo Allah yayi maka albarka, take care, "In shaa Allah bye.. Ajiye wayar yayi ya cigaba da tuki hankali kwance, yana karya sharp bend din da zai sadashi da hotel din ya fara latsa hon saboda ganin mace na tafiya a saitin inda yake bata waige bare taga abunda ke bayanta, Duk irin kokarin da yayi brake din ya taku ya kasa dan ya kure da yawa, sai da yayi mata mummunan buguwa ya daki ginin gabanta kaďan sannan motar ta tsaya, kwantar da kanshi kan sitiyari yayi yana maida numfashi sannan ne hankalinshi ya dawo inda mutane ke ihu suna tururuwa, buďe motar yayi ya fito a gigice ya nufi inda ya buge matar, dakyar ya iya kutsawa yana faďin ku taimakeni in kaita asibiti dan Allah, sam bai kula da fuskar ba shidai ya kinkimeta iya karfinshi ya nufi motar da wani mutum ya bude da niyyar taimakawa..... Subhanallah.... me ya faru a can gurin? Hilal ya faďi haďe da lekowa ta window, wani saurayi ya tambaya abinda ke faruwa, "Wallahi wani ne ya yayi accident har ya buge wata yarinya, kaii abun ba kyau yarinyar ta bugu, dakyar in zata rayu, "Ayya, Hilal ya faďi haďe da maida kanshi cikin motar, Allah ya kyauta gaba, muje Zubair, jan motar Zubair yayi suna addu'ar Allah ya tsare dukkan musulmin duniya.... Mrs Tijjani Shattima.... [25/04 9:12 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣3⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Ohhh Musaddiq... pick my call, Abbati ya faďi haďe da buga hannunshi jikin siyitiyari... Wayar Raudha dake cikin motarshi ya gani bayan ya idar da Sallar magriba, abubuwan da ya gani a wayar su suka razana shi matuka, "How can some1 be so selfish, meye laifin Nadeeyah da suke shirin tarwatsa rayuwarta haka, dama tun jiya da daddare yaga take takenta, in aka kirata a waya sai tace text me, duk iya hangenshi bai hango abinda suke kullawa har ya kai haka ba, in har Raudha zata iya kulla irin wannan abun ga ďan uwanta da matarshi wacce itama ta zamto yar uwa a gareta, to wa zatayi sparing, wani irin kyamarta yake ji a cikin zuciyarshi, bazai taba son 'yayanshi su kasance tare da ita da wannan mugun halin nata ba, da yaga Musaddiq baida niyyar daukar wayarshi sai ya kira wani abokinshi akan su ajiye mishi ticket din zuwa katsina, gara ya dauke 'yayanshi ya maida su gurin iyayenshi, ita kuma Raudha ya riga ya gama yanke hukuncin da zai zartar akanta, duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba to tasa ko huruwa bazata yi ba, kafin Musaddiq ya saki Nadeeyah shi zai rigashi sakinta, may be ta shiga hankalinta, Shi laifin Daddy ma yake gani, ya za'ayi ya bar 'yaya haka sakaka babu kwaba ba komai, har mahaiifiyarsu nada ikon zuwa a haďu a bata rayuwar wata da ita, "tirrr.. ya zama dole ya rabu da 'yar mace domin dama mugun hakuri yakeyi da ita.... Tada motarshi yayi ya nufi gidan Musaddiq dan ya sameshi ya fita hakkinshi akan abun da ya sani kafin hak'an su ya cimma ruwa.... *its too late....* Da..dd..y......, ya faďi cikin shashshekar kuka haďe da zuwan wani kukan mai karfin gaske... Gaban Daddy ne ya faďi ya mike daga kan daddumar da yake haďe da fita a masallacin gaba daya, "Me ya faru Saaaadiq, Musaddiq bai bashi amsa ba sai kukan da yake tayi karamar yaron goye, kuka ne mai cin zuciya wanda ya karya zuciyar Daddy ya sanya shi neman guri a dakalin masallacin ya zauna, saida ya barshi yayi kukan sosai ba tare da ya katseshi ba sannan yace "Bana san sakarcin banza, ya isheni haka, i have heard enough, faďa min abin da yake damunka? "Nadeeyah... sun raba ni da Nadeeyah.. Mummy da su Anty Radiya sun rabamu Daddy, na saketa da bakina Daddy, dan Allah Daddy ka dawo min da ita, i can't live... i can't... ya karashe cikin kuka mai tsanani... "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai Daddy yake faďi cikin zuciyarshi, ko a mafarki bai taba kawo abun da zai kai Mummy lagos kenan ba, duk tunaninshi bai kai nan ba, tunaninshi kawai taje ta zuga danta ya auri wacce take so ne, ya barta tayi kidanta ne in maganar tazo gurinshi tunda shine wakili ya barta ta taka rawarta, Ajiyar zuciya yayi yace "Kar ka bar Nadeeyah ta je ko ina, ku shirya gobe tun safe taho gida, nasan matakin da zan dauka... "Sun koreta Daddy, ban san inda zan ganta ba, na duba ko ina ban ganta ba.. Duk da Daddy bai iya fushi da Musaddiq, a wannan lokacin saida yayi mishi gigitacciyar tsawa haďe da mishi kashedin lallai duk inda take ya nemota, in ba haka ba wallahi sai yayi mummunan saba mishi, kalmar da Daddy ya faďa mishi a karshe ita ta sake assasasa hawayen idonshi, "YOU A LOOSER, U DOS'NT DESERVE A SPECIAL SOUL LIKE NADEEYAH.... Yana jiyo kalaman da Daddy ke faďa mishi wanda yasan shima ba'a cikin hayyacinshi yake faďinsu, bai iya furta mishi komai ba dan yasan ya tafka babban kuskuren da ya cancanci fin wannan zagin... Kasa tashi a gurin Daddy yayi har aka gama wa'azin bayan sallar isha'i wanda suke saurara a kullum, mutanen dake fitowa a cikin masallacin ma daidai yake kallonsu, yana ganin kamar duk matsalolin duniya a gidanshi aka tarasu, bai san lokacin da hawaye ke bin idonshi ba, "Yaso Suwaiba saboda komai nata ya zamo abun so ga kowani da namiji, yana ganin rashinta shine mafarin shigar rayuwarshi cikin kowani irin kalubale... Ya nemawa danshi auren yar da yake jin sonta fiye da 'yayan da ya haifa a cikinsa, saboda danshi ya samu zuri'a daga gareta kuma rayuwarshi ta inganta, sun rabashi da ita, same mutanen da dalilinsu ya hanashi samun abun da yakeso a baya sune dai har yanzu dalilinsu zai kuma hana danshi abun da yake so, *Tarihi ya maimaita kanshi*... Hukuncin da zuciyarshi ta gamsu dashi shi ya yanke ba tare da duba tsufa da tarin yaran da suka tara dashi ba, dakyar ya iya mikewa ya nufi gida zuciyarshi kamar ana soyata saboda gashin kumar da yakeji a cikinta...... Kashe motar Zubair yayi yace "Muje dai tunda ka matsa, dama amarya tamin gorin ban taba cin abincinta ba.. Dariya Hilal yayi ya saba jakarshi a baya suka wuce cikin gidan, Tun kafin su karasa suke jiyo muryoyi ana maida magana kamar karnuka, kalmar da ta da ta doki kunnen Hilal ita ta sashi yar da jakar hannunshi haďe da murďa kofar parlon... *Da ya saketa ai ku kuka koreta, ku kuka ce zaku koreta kuma kuka ce mata kar ta sake shigowa cikin rayuwarku, saboda haka ku zaku nemota ko in tona muku asiri wallahi...* Cikin rashin sani yake kallon wacce tayi maganar dan bai santa ba, shakar da Raudha ta kai mata ita tasata sakin ihu sosai tana neman ceto, dukkansu basu san Hilal da Zubair sun shigo parlon ba.. "Dan ubanki saboda wa mukayi? Saboda ki aureshi muka sanyashi ya saketa kuma muka koreta a gidan, Fisgewa Faida tayi tace "Saboda kwaďayi dai, kwadayin abin duniya da kuma kuna ganin Nadeeyah babu wani nata zai zame muku gata, ni kuma kunsan waye mahaifina, in banda son abun duniya waye zai ki Nadeeyah ya daukeni, ta fini komai na dan adam, ciki harda halin kwarai, ranar da muka kwashe naman miya muka boye batayi yunkurin kare kanta ba saboda girmamawa kuma tasan ku kuka dauke dan ta ganshi daga baya, hakan baisa tayi yunkurin tonaku ba, ku kukayi ma kanku dan ni ko Musaddiq kadai ya rage namiji a duniya bazan aureshi ba, banason zama da mijin da baya sona, gara in nemi wanda zai soni in soshi... "Dan bakya son Musaddiq yanzu shine zaki faďa mishi duk abun da mukayi dan ki haďa ni da ďana? Mummy ce tayi maganar cikin kunan rai da nadama, "Gara in faďa mishi yasan lallai fa uwar da ta haifeshi bata kaunar farin cikinsa, domin da kina kaunarsa bazaki rabashi da matar da ko sati biyu batayi a gidanshi ba, kuma kinsan irin son da yake mata, uhmm ni am out of this trash ku karata can, gida zan wuce, tana kaiwa nan tayi gaba abinta, Bin bayanta Radiya tayi ta janyota haďe da ďaga hannu zata kwaďa mata mari, kammm... taji hannunta alamun an rikeshi, waigawa tayi dan ganin wanda ya rike hannun tayi tozali da Hilal wanda idanuwanshi suka zama kamar jini saboda tsabar jaa da sukayi, wurgi yayi da hannunta wanda ya sanyata yin baya tagaga zata faďi, Buďe fuska Faida tayi saboda rashin jin saukar marin a fuskarta, ganin Hilal ya nufota yasata yin baya da sauri, kamo hannunta yayi da karfi har ta kusa missing step zata faďi, parlon ya dawo da ita ya zaunar da ita dabass kamar wanda yayi wurgi da kaya, nan idanuwanta suka firfito waje tayi saurin cewa "Waye kai? In kaji min ciwo fa? Akan me zak---- Shut up.... ya faďi da karfi har saida kirjin Mummy ya buga, Zama yayi yana facing dinta haďe da daukar waya dan kiran Musaddiq yaji inda yake, karar wayar yaji a parlor haďe da sakkowarshi daga sama a hankali kamar wanda aka zarewa laka... Maida kallonshi gurin Faida yayi yace "Bance ki rage min ko kalma daya ba, bance ki mance komai ba dan in kin mance u will be in for it, komai da ya faru nakeson ji nd lastly... ina Nadeeyah? Kamar jira takeyi ya rufe baki tace "cikin sauki ya kamata ka tambayeni ba sai ka kusa yi min lahani ba, in dai wannan ne zan baka labarinshi, harda shirin gaba da mukayi.... "Ba kai ba, uwarka ma bata isa ta shigo gidannan a yanzu tasan abun da ke faruwa ba, Musaddiq ďana ne, ni ke da ikon zaba mishi abin da nasan zai fi dacewa da rayuwarshi, kai waye da kake tunanin zaka iya interfering cikin rayuwarshi a koda yaushe... Runste ido Hilal yayi dan bashi da wani kuzarin da zai iya amsata, sake duban Faida yayi zaiyi magana yaji sautin Muryar Musaddiq "Ni ba danki bane, karki sake taba ni, babu uwar da zatayi ma ďanta haka, a da ina ganin babu wata mace da ta kaiki son 'ya'yanta, ashe ke din mace ce mai son zuciya, i hate you, i hate u.. hakan yayi ta maimaitawa haďe da durkushe a gurin.... Share hawayen da ya ďigo mata tayi tace "Taimakonka nayi, bazaka gane hakan ba sai nan gaba, yanzu nasan fushi ne da kuma shaukin dafin son da ta ďiga maka, da sannu zata fita a ranka ka gane gatan da nayi maka, kai kanka ka faďi "bata da asali, kasan kenan bata dace da mai cikakken asali irinka ba... Hannayenshi duk biyun ya daura akanshi yana girgiza kanshi hawaye na bin idonshi, kalmar *bata da asali* ita ta dinga yawo akanshi, rarrafawa yayi ya isa kusa da Musaddiq, "Nadeeyah bata da asali Musaddiq? Kai da bakinka ka fadi cewa bata da asali? To ina take? Ina Nadeeyah take.... ya faďi da karfi haďe da shake wuyan Musaddiq.. Da sauri Zubair da tunda ya shigo yake tsaye cike da mamaki ya fara kokarin banbare Musaddiq daga hannun Hilal, dukkansu hawaye ne ke zuba a idonsu, ture zubair yayi da karfi yace "He promised to take care of her, ina ya korata? Ina ya tura marainiyar Allah, just 9days of their marriage, Meyasa bai kyaleta ba tunda yasan bazai iya ba? meyasa ya zabi ruguza rayuwarta at this early age? he shud have lv her for me in yasan shi bazai iya ba, shi kaďai ne wanda zan iya sadaukarwa da abinda na dade ina dakon so, why did u do dis to her, Why Musaddiq? Ya karashe cikin ficewar hankali haďe da kwantar da kanshi a gurin.... Nan kallo ya koma gurin Hilal wanda ke kuka mai ban tausayi, Share hawaye Musaddiq yayi jikinshi na rawa ya durkusa gaban Hilal yace "Hilal---- Don't ask me anything Musaddiq, u are very useless, baka da amfani a rayuwarka bare ka amfani wani, you are a Coward... Irresponsible human bei--- Toshe mishi baki Zubair yayi da sauri yace "wannan abun da kukeyi bazai taimaka ba, gara mu fita mu nemo ta kafin ta shiga wani hali... Babu inda ďana zashi Mummy ta faďi tana rike hannun Musaddiq, A hankali ya zame hannunshi yace "Sau biyu kenan zan maimaita, ni ba danki bane, kin daina amsa sunan Mahaifiyata, yana kaiwa nan yabi bayan su Zubair zuciyarshi cike da tunanin maganganun Hilal, A kofar da zasu fita sukaci karo da Abbati, da sauri ya nufesu yace "yauwa Musaddiq tun dazu nake kiranka, fito da wayar Raudha yayi ya nuna mishi text din da sukayi tayi da Radiya a daren jiya, sannan ya kare da cewa kar kayi gangancin yarda da duk da zasu ce maka... Is too late Musaddiq ya faďi yana mai share hawayen da yaki tsayawa a idonshi, yana hango Hilal na matsama Zubair ya tada motar yayi saurin cewa "Kayi hakuri zamuyi waya, yanzu zamu je nemo Nadeeyah ne.. bayanshi Abbati yabi da kallo cike da tausayawa yace "Allah sarki, Allah ya haďaka da matarka, Cikin parlon ya karasa kanshi tsaye haďe da sallama dan ba mutunci bane ya kawo shi....... Kamar yadda su Musaddiq sukayi yawon dubata haka su Hilal sukayi, ganin babu alamunta yasa Zubair bada shawarar kai wa gurin police,, dan su zasu fisu iya binciken, Hilal da ya shiga cikin tunani yayi saurin cewa "Muje gurin hotel din nan da akayi accident, Baya Zubair ya juyar da motar yayi hanyar 3stars luxury hotel, tun kafin su karasa gaban su ke dukan uku uku, ganin babu kowa a gurin sai wani mai shagon provosion ya sa su tsayawa gurinshi, Balle motar Hilal yayi ya fito ya isa gurin mai shagon, a tsorace mai shagon ya arta shagonshi dan duk tunaninshi irin area boys dinnan ne masu mishi fashi, ya fara zuge shagon kenan su Musaddiq suka karaso, Hannunshi Hilal ya kama yace "Akwai hatsarin da akayi anan, an ce mace ce? Dan Allah macen yar budurwa ce ko babba? sannan ko kasan asibitin da aka kaita, ajiyar zuciya mutumin yayi cikin yaren yarbanci yace "Na gode ma Allah, cike da tausayawa yace "yar budurwa ce, bazata wuce 18yrs ba, ga ragowar kayanta can da wasu suka fara sacewa, sannan ban san asib----- kallo ya bisu dashi suna rige rigen buďe dauko kayan, Wani irin ihu Musaddiq ya saki haďe da rungumar akwatin sosai a jikinshi, "Wallahi itace, itace, Nadeeyah ce, Rike Hilal Zubair yayi dan kiriss ya rage ya faďa cikin wata katuwar kwata saboda firgici.. "Wani ne ya buge wata yarinya, kaii ta bugu, dakyar in zata rayu... wadannan kalaman su suka shiga yawo a kunnen Hilal, "Nadee----- Ihun bayereben ne ya sanya su isa gurin da Musaddiq ya yanke jiki ya, labarin irin hatsarin da akayi ya bashi wanda yayi sanadiyyar tsayuwar zuciyarshi na wucin gadi, duk wani haushinshi da Hilal yake ji nan take ya kau ya dinga kuka yana girgiza shi, kamashi sukayi suka sa a mota suka nufi asibiti dashi, shi kanshi Zubair kuka yakeyi dan a rayuwarshi ya tsani ganin crisis din soyayya, tunda ya gama university rabonshi da sake soyayya, tashin hankali ya hanashi kallon Faida duk da yayi mamakin ganinta har lokacin ba aure..... Mrs Tijjani Shattimah...... [25/04 10:21 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣4⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Gado nurses suka fito dashi da gudu saboda yadda Hilal ya cika musu guri da ihu, bayansu yabi yana faďin "Dan Allah karka mutu ka barni, am not angry with u anymore, plss wake up Musaddiq, Zuciyar Hilal gaba daya ta karye, abubuwa biyu a lokaci daya, wanne zai dauka? kuka sosai ya durkushe a kofar dakin da aka shige da Musaddiq ya keyi, tsugunawa Zubair yayi yana bashi hakuri haďe da share nashi hawayen... "She is no more Doctor, we tried our best but we cudnt save her, ya Salam Doctorn ya faďi haďe da dafe kanshi, "ina wanda ya kawo ta? "Ya gudu saboda ance ya kira police, accident case ne kasan, 2 accident cases duka mata kuma duk sun rasu, "Astagfirullah.... "dayan yaki yarda ta mutu, he took her to another hospital, i knw by nw ya yarda, "ya bani tausayi sosai cos shima yadda yake ba cikakken lafiya ce dashi ba, girgiza kai Doctorn yayi zaiyi magana Hilal yayi saurin rike hannunshi yace "Dan Allah ka nuna min gawar wacce tayi accident din, wani irin kallo yayi mishi haďe da cewa "Who are u? Cikin kuka Hilal yace "Matar uncle dina ta bata, we found out that tayi accident nd bamu san inda take ba, cike da tausayawa doctorn yace "Muje may be ka ganeta a jiki ko kafa, dan fuskarta tayi damage, bayanshi suka bi da sauri suna fargabar Allah yasa ba Nadeeyah bace, dakyar Hilal ya iya kallon matar wacce ta ďan manyata.. ajiyar zuciya yayi yace "Alhamdulillah ba ita bace, Suna gab da fita daga dakin ya hango hijab din da ko a mafarki ya ganshi zai ganeshi, hijab din da Nadeeyah ke yawan sawa a koda yaushe musamman in yana gidan saboda tsabar girmamashi da takeyi, rarumo hijabin wanda ya jike da jini yayi ya rungumeshi a jikinshi, "Doctor ina me hijabin nan, ina take? Nurse din dake biye dasu tace "itama ta mutu, wanda ya kawota ya dauketa yace bai yarda da aikin mu ba, zai canza mata wani asibitin, i told him komai nata ya daina aiki, yaki yarda, nasan yanzu ya yarda, Runtse ido Hilal yayi yana kuka haďe da yin dana sani kala kala marar amfani, "Dana san haka rayuwarki zata kare so quick da ban bari son Musaddiq ya rinjayi naki a cikin zuciyata ba, da nayi iya kokarin da zanyi in maidaki tawa, da na girmama bukatuna akan nashi da har yanzu kina nan da ranki, wayyo Allah na, Allah yayi miki rahama Nadeeyah..., Allah yayi haďaki da manzon rahama... Zubair me rarrashi shima kukan ya zauna yana yi sosai, Doctorn ne ya koma rarrashinsu haďe da basu shawarar su kira gida su faďi... Wayar shi ya ciro a aljihu ya kira Anty Reemah, ringing biyu yayi tayi saurin ďauka, "Tun dazu nake jiran kiranka, ya aikin ka kammala? bai bata amsa ba sai sheshshakar kukanshi da taji, Zaune tayi a gefen gado haďe da wurgar da rigar da ta dauko zata sa, "Me ya faru? "Mum Nadeeyah ta mutu, sun kashe Nadeeyah, sun kasheta... "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ajiye wayar tayi tana ta maimaitawa tana kuka tana dadawa, Hinad da ta jiyo ta tayi saurin katse wayar da takeyi da Jamal ta rugo dakinta da gudu, "Allah ya jikanki Nadeeyah, "Mum wacce Nadeeyar? Hinad ta tambaya haďe da kwalolo ido waje, Nadeeyah dai Hinad, Nadeeyarmu, nan fa dakin ya gauraye da kuka babu mai ba wani hakuri, Allah ya taimaka Zainab na bacci da abun sai yafi haka... *Aboki Kangiwa* ka shigo nigeria kenan, Daddy ya tambaya cike da dakiya dan kar Hilal ya gane halin da yake ciki, "Daddy Nadeeyah is no more, Musaddiq ya saketa, su Mummy sun koreta, mota ta bigeta ta mutu.. Rike kirji Daddy yayi yace "Karya ne Mukhtar, dan Allah ka karyata kanka, Nadeeyah na nan da ranta, na faďa ma Musaddiq ya nemo min ita, kuma wallahi rayayya zai kawo min yadda na bashi, ba matacciya ba, karka sake kirana har sai Musaddiq ya nemo min abin da na bashi, cikin koshin lafiya na bashi ita, hakan nake son ya dawo min da ita, "Shima yana tsakanin rayuwa da mutuwa Daddy, dan Allah kazo, wallahi Nadeeyah ta mutu.. kashe wayar Daddy yayi ya kifa kirjinshi akan pillow saboda raďadi da yake mishi, kuka kawai yake son yi amma yaki zuwar mishi, haka ya kwana da sake saken yadda zaiyi ya sanarwa da Papy abinda ke faruwa.... Da asuba ya daure ya kira Anni dan ita kadai ce wacce zata iya saita abun, Anni ta girgiza matuka dan har hawaye sai da ya fito a idonta, dakyar ta iya faďawa Baffa wanda ya rikice yana kuka haďe da sambatu sosai.... Papy kuwa tunda ya gama waya da Anni hankalinshi ya kasa kwanciya, kiran Hafeez yayi yace "ya shirya zasu tafi lagos ance Musaddiq ba lafiya, rai a hannun Allah, Sosai Husna ta marairaice tana kuka saidai su tafi tare, hakan kuwa akayi a safiyar suka yanki ticket dukkansu harda Mami, kowa cike da fargabar abunda zai je ya tarar.... A airport din su Daddy suka jira zuwan su Papy dan su karasa tare, Yanayin da Papy yaga Daddy ya ďaga mishi hankali matuka, kusa dashi ya matso yace "Kayi hakuri Alh Mukhtar, cuta ba mutuwa bace, in shaa Allah zai tashi, kukan da Daddy baiyi ba jiya shi ya saki mai karfi haďe da rungume Papy, share hawaye Anni tayi tace "Mu karasa can asibitin dan Allah, ba sai mun tsaya munyi magana anan ba... jiki a sanyaye Papy ya kama hannun Daddy yana bashi hakuri har suka isa gurin motocin da abokin Daddy ya turo musu... A kofar dakin da aka sa Musaddiq sukaga Hilal rungume da Hijab har lokacin idonshi na fitar da ruwa, daga shi har Zubair babu wanda ya runtsa, yana ganinsu ya mike da sauri ya rungume Daddy yace "Wallahi Daddy sun kasheta, Nadeeyah ta mutu, muje kaji daga bakin doctor... A ruďe Mami tace "Wace Nadeeyar, sai a lokacin Hilal ya lura dasu, nan wani sabon kukan ya kwace mishi ya shiga basu labarin abun da yaji da kunnenshi, Abbati da ya kira Daddy yace su haďu a asibiti shima ya daura daga inda ya sani, nan fa guri ya kaure da kuka, sun ma manta a asibiti suke, Jan Daddy gefe Abbati yayi yace "Ni yau zan koma india, yara kuma sun wuce katsina, na faďa ma Raudha in ta samu miji tayi aure, kayi hakuri dan Allah, Allah ya haďa mu da alkhairi, Murmushin yake Daddy yayi yace "Allah ya albarkaci rayuwarka Yusuf, ai kayi kokari, nagode sosai, Duk da Papy na cikin tashin hankali hakan bai hanashi mikewa da niyyar yi ma Abbati magana ba, rikeshi Daddy yayo yace "Ya cika dan halak, kowa hakan zaiyi in yaji abin da suka aikata, "Dan Allah ka yafe min proff, da sauri Papy yace "Haba, mu su waye da zamu tsallake hukuncin ubangiji, itama lokacin da ta dauko kenan, rayuwarsu ta jin daďi na gidan lahira in shaa Allah, yadda ya karashe maganar cikin rauni ya sanya su sake wani sabon kukan, Duk papy yadda yakai ga matsewa ya kasa saboda shima a karye yake, nan ya zauna ya rufe fuskarshi yana kuka sosai, a duk faďin gurin nan babu wanda yakeda karfin bawa wani hakuri..... Reemah... ki kira danki kice mishi ya dawo min da ďana, tun daren jiya da ya daukeshi ya fita dashi har yanzu basu dawo ba, ki kirashi ya dawo min dashi, tunda shima yana san Nadeeyar in ta gama idda sai ya aureta kuje can ku karata, tunda ke baki san ciwon kanki ba, ki haifi ďa ya dinga juyaki... Mummy na kaiwa aya Anty Reemah tace "Ina airport, danki yana asibiti, ďana bai kai ga yi mishi illa ba, ita kuma wacce kika tsana din da zata dawo gidan duniya da babu abinda zai hana ban aura mata Hilal ba, ai da nasan yasota tun farko da saidai Musaddiq ya hakura tunda shi matsayin uba yake a gurinshi, saidai kashh... yayi nauyin bakin da ya jefa rayuwar Nadeeyah cikin garari, yanzu tunda kunyi sanadiyyar da ta zama gawa, sai ku fara murna ku nema ma Musaddiq hurril aini, tana kaiwa ta katse wayar cike da ďacin rai, bata taba yi ma mahaifiyarta musu ba, amma a yau ta kai bango sosai wanda har ya sata fadin maganganu cikin ficewar hayyaci.... A gigice Mummy ta nemi guri ta zauna tace "Nadeeyah ta rasu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Raudha dake kiran wayar Abbati tana kuka tace "Whatt... ta rasu? "Wallahi ta rasu, yanzu Reemah ke faďa min, itama tana hanyar zuwa.. Daukar trolley Radiya tayi da sauri tace "Nidai ba ruwana, yanzu nan zan tafi gida gurin 'yayana, Allah ya taimakeni Shamsu bai san labarin nan ba, kallon Raudha tayi tace "Allah ya daidaita ku, Mummy, na tafi kaduna sai kun karaso, tana kaiwa nan ta ruga da gudu da jakarta tana mai dana sanin biye ma zuciya.... A tsure Mummy ta mike ta kira wayar Mahmoud tace ya tambayar mata Zubair wani asibiti suke, Mahmoud ya rude sosai ya kira Zubair dan jin abinda ya faru, sunan asibitin kadai ya iya faďa mishi ya kashe wayar saboda tashin hankalin da suke ciki na cewa Musaddiq ya shiga Coma, Kiran Mummy yayi ya faďa mata sunan asibitin, bata jira abinda zaice ba ta mike ta sanya gyalenta suka wuce tare da Raudha, burinta Allah yasa ba'a faďa ma Daddy abinda ke faruwa ba, tasan yadda zata lauya zancen har ya gamsu da ita.. Kuka ta kakalo ta dinga yinshi cikin motar da zata kaisu asibitin... Da Hafeez ta fara karo yana zaune a bakin gate din asibitin yana kuka sosai, Husna dake tsaye a bayanshi ta dafa kafadunshi a tsorace itama kukan takeyi, kukan rashin Nadeeyah da kuma kukan hali irin na Mahaifiyarta, Mummy na ganinsu ta fito daga cikin mota ta nufosu tana kuka, da sauri Husna tace "Dan Allah karki iso nan da dramarki Mummy, kun kasheta, hankalinku ya kwanta, sai kuyi celebrating ai ba kuka ba, Cike da mamaki ta kalli Husna tace "Auta ni kike faďawa haka, har kin yarda zan iya kashe Nadeeyah da nake so kamar raina, "So indeed, yaushe kika fara sonta? So bayan rai ko, wallahi alhakin Nadeeyah bazai barku sukuni ba, i ha---- toshe mata baki Hafeez yayi yace "Don't say anymore, uwa uwa ce, rungumeshi tayi tana kuka sosai haďe da bashi hakuri.. bayanta ya shiga shafawa yana kwantar mata hankali, yasan irin kaunar dake tsakaninsu, abin da mahaifiyarta tayi bazai taba shafar zamansu ba saboda Zuciyar Husna kamar gold take saboda kyalli.... Bayan sun tsagaita kukan Doctor ya basu shawarar da su bi manyan asibitoci su duba gawarta a samu a sallaceta cikin gaggawa, Suna cikin yanke shawarar yadda zasuyi Mummy ta faďo gurin da suke tana ihu mai haďe da kuka, babu wanda a cikinsu ya kalleta bare har yasan abun da takeyi, Ganin tana neman cika ma yan asibitin kunne yasa wasu Nurses cewa tayi hakuri ta fita daga waje, tana damun patients dinsu, "Sirikata ta mutu sannan ďana na kwance rai a hannun Allah zaku ce inyi shuru, bazanyi shurun ba, ya Allah ka sassauta min, wayyo Allah na shiga uku, Gadan gadan Daddy ya nufota dan ta kure duk wata dauriya tashi, tana ganinshi gab da ita tayi saurin mikewa tana share hawayenta, cike da kissa ta faďo jikinshi tace "Ance Nadeeyah ta mutu, daga sokoto na biyo jirgi na iso nan direct, me ya samu Nadeeyah, me ya sameta?... ta karashe tana kuka sosai, Ran Hilal ya baci matuka na rainin wayon da tazo dashi yayi saurin mikewa zaiyi magana Jamal ya rikeshi, danne hannunshi yayi yace "Karkayi magana, duk lalacewa ita ta haifi mahaifiyarka, dafe kai Hilal yayi yace "shine abun da nake jin haushi matuka, ina ma ace bare ce, wallahi hukuncin da zan mata ba mai sauki bane.. Raba jikinshi yayi da ita haďe da kama hannunta ya fara janta har suka fita waje, bayansu Papy yabi yana cewa "Kayi hakuri Alh Mukhtar, ka kyaleta sai mun koma gida, yanzu fatan mu Allah ya bawa Musaddiq lafiya, kuma Allah ya bayyana mana gawar Nadeeyah cikin gaggawa, Bai saurare shi ba ya hankaďata ta tafi tagaga zata faďi, riketa Raudha tayi jikinta na rawa itama na tsoron yadda taga fuskar Daddy... "Sanda zakiyi tafiya na hanaki? Girgiza kai Mummy tayi cike da tsoro tace "A'a, "Da kika isa inda zaki har kika aikata abun da kike so na hanaki? Nan ma ta kuma girgiza kai hawayen gaske na bin idanunta, "To kinga yanzu ina da ikon yin abun da nakeso babu wanda ya isa ya hana ni, ko akwai? Durkushewa tayi tana kuka tace "Dan Allah kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne, bansan meye ya ingiza ni har na aikata hakan ba, Dariyar takaici Daddy yayi yace "To nima bari in ďan aikata aikin shaidan kadan, dan baya kyautawa, kullum ya dinga zabarki yana bari na, gara ya haďamu dukka, "Kije Na Sake ki!! Kalmar akwai daďi ko? Ya tambayi Raudha dake kuka mai sauti... girgiza kanta tayi tace "ko kadan bata da dadi Daddy, dan Allah kayi hakuri, "Hakane kuma, bata da dadi in ku za'a furtawa, Amma in ku kuka sa a furta tafi komai dadin sauraro a gareku, ko da yake ďaya ce na faďeta dole kiji rashin dadinta, "Na sakeki Zainab... ya sake maimatawa yana mai kallon cikin idonta, A wannan lokacin daskarewa Mummy tayi ta kasa motsi saboda tsabar firgici, ita kuwa Raudha magiya ta shiga yi mishi, ko biyun har yanzu baku ji dadin furta shi ba? Da sauri Papy ya sanya karfinshi ya janyeshi haďe da cewa "Ba girmanka bane, kayi na ďaya na daukeshi a matsayin gargaďi, ya isa haka, Dan Allah kayi hakuri ka maida uwar 'yayanka, "Wani irin kallo Daddy yayi mishi yace "Ko za'a haďe sama da kasa bazan dawo da Zainab ba, yadda Nadeeyah ta bar duniya haka Zainab ta bar rayuwata har gaban abada, Sannan ke kuma Raudha, ki nemi gidan wani uban bani ba, dan bani da masaukin zawarawa a gidana, ita kuma Radiya kuyi mata kyakykyawan albishir kafin ta isa gida, mijinta ya angwance da yar Mutunci ba irin nawa 'yayan ba, yana kaiwa nan ya wuce ciki Zuciyarshi na kuna na haďa zuri'a da Mummy.... Kukan da Mummy takeyi na munafurci da na gaske duk ya kafe, burinta taga Musaddiq da saboda inganta rayuwarshi ta rasa mijinta abun kaunarta, duk yadda taso ganinshi bai yiwun mata ba saboda yadda Daddy yayi rantsuwar in ta shigo ciki bayan wani sakin sai ya bita da duka, Baffa ma yace "tana shigowa zai tsine mata albarka, duk yadda Anni taso basu hakuri abin yaci tura... Haka nan ta juya ta tafi Raudha na binta a baya tana kuka wiwi, Atm suka tsaya dan cire kudi, Mummy na tura atm dinta taga an sa mata invalid, jiki a sanyaye tace ma Raudha "bari inyi miki transfer mu samu kudin jirgi mu wuce kaduna, karki damu komai zaiyi daidai, share hawaye Raudha tayi ta bata acc no, sau uku tana yin transfer ana ce mata "Your account is restricted, Managern Bankin ta kira dan jin dalilin restricting acc dinta, nan yace mata Alh ne ya basu umarnin yin hakan tun da safe, faďa sosai ta fara mishi wanda ya sashi bata hakuri haďe da kashe wayar dan bazai iya budewa ba, da ya batawa Alhj rai gara nata in sun kai dubu su baci, Dubu hamsin din cikin account din Raudha dashi sukayi amfani da zummar in sunje gida Mummy zata bata dan tana da kudi a cikin drawer, kwantar mata da hankali ta dinga yi tace "Ai naci zaman gidanshi, a ciki zan zauna saidai shi ya bar min gidan, in kuma bai iya barin min saidai ya maida ni dakinshi, da tsufana bazan koma gida zawarci ba wallahi, yadda take maganar kowa ya ganta yasan bata cikin hayyacinta dan cikin kankanin lokaci komai nasu ya canza... *Allah kenan mai canza komai cikin kiftawar ido......* Mrs Tijjani Shattimah [26/04 7:28 AM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣5⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Dukkan manyan asibitocin dake garin lagos babu wanda basu zagaya ba, haka mutuary, duk inda sukaje da kwatancenta sai su nuna basu ganeta ba, A Oxford hospital dake Banana island ne kadai wata Doctor tace "Accident case daya muka karba daren jiya, mata da miji ne sukayi accident din, ita ta bugu da yawa dan har anyi tunanin ta mutu, shi kuma a kai kawai yaji ciwo, yayi collapse saboda tashin hankali, suna Vip Amenity, naji ana shirin fitar dasu Canada, Juyawa Papy yayi yace basu bane, wannan ita kaďai ce, dafe kai Daddy yayi hawaye na zuba a idonshi yace "Ya Allah ka bayyana mana Nadeeyah a mace ko a raye, Hafeez da jikinshi ke bashi duk inda Nadeeyah take tana kusa dashi yace "da munje mun duba saman Daddy, ta yiwu ita ce, ba suyi mishi musu ba suka fara taka steps din hawa saman... Da gudu wata Nurse ta ke sakkowa daga sama tana faďin "Doctor Marly... she is alive, ta farfaďo, and the most surprising thing is that her baby is perfectly fine and healthy, Single Fetus... "Wow Mashaa Allah.. Doctor Marliyya ta faďi cike da farin ciki, a gwajin jinin da sukayi mata sun gano tana dauke da karamin ciki shiyasa ma basu tsaurara yi mata allurai ba.... Kallon Hafeez Papy yayi yace "kaji wannan ciki gareta, Nad---- wayar Daddy ce ta katseshi daga karashe maganar... dagawa yayi da sauri saboda ganin sunan Hilal, "Ya farfaďo Daddy, kuzo da sauri, Ajiye wayar Daddy yayi yace "Musaddiq ya farfaďo... Alhamdulillah... Papy ya faďi haďe da sakkowa kasa yace "mu tafi gurinshi, in da rabon ganin gawarta zamu gani, in kuma tana raye Allah zai sa mu ganta, sai mu tsananta addu'a domin bata faďuwa kasa banza, tunda har bamu ga gawarta ba, na tabbatar tana raye, domin jikina bai bani Nadeeyah ta mutu ba, wannan kalmar itace mafi soyuwa da Daddy yaji tun da yaji labarin sakin Nadeeyah, Allahumma Ameen ya faďi haďe da damke hannun Papy, shidai Hafeez kallon saman kawai yakeyi hankalinshi yaki kwanciya har suka fita daga reception din, shima yasan yar uwarshi na nan da ranta bata mutu ba, share hawayenshi yayi yace ""Ya Allah ka tsare min Nadeeyah, ka haďata da alkhairai gabas da yamma kudu da arewa, Ya Allah ka zama gatanta dan bata da gatan da ya wuce kai.... ***** ******* Hannu Husna tasa tana share hawayen dake tseren fitowa a ta gefen idonshi, kallonsu yakeyi daya bayan daya yana adduar Allah yasa kallon da zaima na karshe ya zamto Nadeeyah ce tsaye tana mishi murmushinta mai matukar kyau... yana sauke idonshi kan Hilal ya runtse idonshi, Hilal ya cika masoyi, Hilal is a real definition of a brother, friend nd a guardian.., ya akayi bai fahimci son da Hilal yakewa Nadeeyah ba, lallai ya cika babban sakarai wanda bai iya fahimtar abu.. Hannunshi Hilal ya rike haďe da kwanciya a jikinshi dan ya fahimci tunanin da yakeyi.. murya na rawa yace "Bakayi min komai ba Musaddiq, u will always be my no 1, i will always love u, babu abinda zai canza soyayyata agareka, u are very nice, matsalata ďaya ce wacce nake son canza ta a gareka, u are very soft, a wannan duniyar ana daukar advantage din irinku, change!!, u have to change Kyari.. ya karashe yana kuka sosai saboda baisan yadda zai dauki mutuwar Nadeeyah in an faďa mishi ba.. kukan da sukeyi tare ya sanya dukka mutanen gurin zubda hawaye, an rasa mai rarrashi a cikinsu, Hannun Musaddiq Ruwaidah ta kama tana kuka tace "Ance my sister is no more, ina ka kaita,? ba kai muka tafi muka barma ita ba? Janyota Jamal yayi ya buge bakinta haďe yi mata tsawa, Shuru Musaddiq yayi yana kallon Hilal wanda ya kasa haďa ido dashi, Murya Na rawa yace "Na--aad-- bai karashe ba ya hango hijab dinta a hannun Husna, Durowa yayi akan gadon haďe da fisgo hijab din, jinin da ya gani a jikin hijab din ne ya sanyashi sakin wata razananniyar kara ya zube a gurin, wannan karan faďuwar da yayi tafi ta jiya dan babu inda yake motsi a jikinshi, Da gudu su Hilal suka fita suna kwala kiran doctor, nan dakin ya dauki sabon kuka har su Daddy da suka shigo a lokacin, Faďa sosai doctors din sukeyi suna faďin "Munce ku barshi ya huta, kunki, gashi yanzu kun janyo mishi faďuwar da tafi ta da, Allah ya tsareshi daga tabuwar zuciya ko stroke... Dukan Ruwaida Mami ta fara yi tace "Shegen bakinta yasata fada mishi Nadeeyah ta mutu, Anni ce ta shiga tsakani cike da faďa tace "baki san yarinta ba, duka nawa take? "Da haka kuke dada maida ita baya, Jamal ya faďi rai a bace haďe da fita waje, Su dai su Papy suna can suna leken halin da Musaddiq yake ciki.. Oxygen suka ga an taho dashi da gudu za'a sawa Musaddiq, Zaman dirshan Daddy yayi a tantagaryar kasa yace "Shikenan, Allah ya jikanka Musaddiq, Allah ya amshi bakuncinka, na yafe maka duniya da lahira, na yafe maka... "Haba Alhj Mukhtar, ciwo ya taba zama mutuwa ne, dan Allah karka karya mana zuciya, Cike da zarewa Daddy yace "Life Support, Musaddiq da life Support, numfashi ma sai da oxygen, wa aka taba sawa kaga ya mike, "Suna nan da yawa Daddy, babu abinda zai sameshi, wallahi Musaddiq bazai mutu ba, in kuwa kaga ya mutu to saidai ko mu mutu tare, yadda Hilal ke maganar ya sanya Daddy fashewa da kuka sosai haďe da rungumeshi.... Likitoci sunfi awa ďaya akan Musaddiq kafin su samu Allah ya basu sa'ar ceto ranshi, stroke ne ya kusa kama shi, ga hawan jini da yayi mugun hawa wanda yayi ma shekarunshi yawa, Cikin ikon Allah bai taba zuciyarshi ba amma fa dakyar yake numfashi shiyasa suka haďa mishi da oxygen... sosai sukayi ma Daddy kashedi akan kar su sake su faďi abun da zai ďaga mishi hankali dan condition dinshi is very critical, Shawara sukayi kowa ya tafi a barshi da Daddy da Hilal kawai, nan Jamal ya bukaci tsayawa saboda ya dinga taimaka musu.... Koke koke babu irin wanda ba'ayi a gidan Musaddiq ba, isowar su Anty Reemah da Raliya ya kara ďaga hankulan yan gidan dan sunyi kuka har sunji ba daďi... Dakin da aka maida Musaddiq guri ne da daga doctors sai mutum ukun dake jinyarshi kaďai ake bari su shiga.. A gidanshi sauran mutanen suka zauna suna jajanta lamarin haďe da yi mishi adduo'i na neman sauki da kuma na bayyanar Nadeeyah.... Dubu biyun da ta rage musu ita suka dauko drop suka iso gida, A garkame suka samu gidan da kwaďo ga kuma police guda biyu zaune akan kujeru suna gadin gidan, *(Shirin da Daddy yayi a waya kenan tunda yaga sun tafi, yasan gidanshi zata wuce shiyasa ya kira abokinshi commissioner dan ya tura a rufe mishi gida ayi gadi, kuma kar su bar kowa ya shiga)* jiki a sanyaye Mummy ta karasa haďe da gaida Police din, amsa mata sukayi gami da kallonta, "Ina zaki?, "Gida na ne, ina son zan shiga ne, juyar da kai sukayi sukace order aka basu na kar su bar kowa ya shiga gidan, ganin babu alamar rahama a fuskarsu ya sanyasu juyawa cike da tashin hankali, "Ta inda ya bullo kenan? kaya kala uku kadai gareta, gashi bata da kudi a hannunta, ba mota, babu komai na jin dadin rayuwa, Gidan Goggo suka nufa dan nan ne ya zame musu dole..... Mummyyyy oyoyo....., Raees ya faďi haďe da rugowa da gudu ya rungumeta, ajiyar zuciya tayi tana faďin "Alhamdulillah, aurena is safe, yanzu zan gyara zamana da mijina da yan uwanshi kar Allah yayi min mugun kamu.. wucewa ciki tayi tana godewa Allah da irin son da yakeyi mata.. Yaranta kanana biyu take son gani dan ta jiyo dariyarsu a parlor.. Turusss.. taja ta tsaya ganin Shamsu goye da Adeel ita kuma Fatima goye da Amma suna rarrafe suna zagayen parlon suna bangazar juna.. Wani tsawa ta dakawa Fatima wanda yasata saurin sauke Amma a bayanta, "Sannu da dawowa Anty, "Gyatummm.. gyatummm.. Radiya ta shiga kwala kiran ta da karfin gaske, "Mama bata nan, ta koma gida... Fatima ta amsata cikin ladabi "Sai ta barki kina min aiki kina wasa da mijina? Mijinta ne itama.. mai sukuni, Inna indo ta faďi tana dariya, "Whatt? Mijinta? "Kwarai kuwa, mijinta nake, ko kinada matsala da wannan me? Wani irin sarawa taji kanta nayi tayi saurin zama akan kujera, "Ni zaka ciwa Amana Shamsu? "Auren ne cin amana? Inna indo ta tambaya tana zama a gefen Radiya, "Ke dallah can rufe min baki, ina magana ne da mijina ba dake gayyar na aiya gayyar tsiya ba.. "Aheeee yayanki ma gayyar tsiyace tunda abun da yayi ni hi yayi su, "Shamsu kayi warning matar nan, kasani sarai bani da mutunci, "Rashin mutuncinki ya tsaya akanki, kinga na samu nutsuwa a gidana, karki zo ki nemi tarwatsa min, Fatima shiga da yara ciki, ki sirka min ruwan wanka kuma ki jirani a bayin.. A fusace Raudha ta mike ta fisgo hannun Adeel haďe da kwada ma Fatima mari, nuna ta da yatsa tayi tace "in baki fita a cikin gidannan yanzu ba, wallahi sai na kasheki, zo ki wuce, munafukai maciya amana, Marin da tayi mata shamsu ya mayar kan fuskarta yace "saidai ke ki fita, in har bazaki yarda da fatima a matsayin matata ba saidai ki fita ki barmin gida, "Wallahi shamsu kai baka isa ka haďa ni kishi da wannan kucakar ba, wallahi kayi kaďan, Rungumo Fatima yayi sosai yace "wannan kucakar ta shayar dani kaunar da wayayya ta kasa shayar dani, ta kula da mahaifiyata cikin kankanin lokaci, mai rabani da ita saidai mutuwa... "To ko saidai ka zaba koni ko ita... Radiya ta faďi tana huci.. "A bayyane yake Radiya, na zabi Fatima, saboda ta haďa abubuwa da dama, wayewa ce bata da ita, zan siyo mata a kanti tunda akwai su da dama kantin wayayyu, zan maida ita first class lady wacce zakiyi mamakinta, ban ce zan sake ki ba, amma in kina bukata ina iyawa, "Aiko dole ka sakeni, me zanci da kai, kaje can ka karata da yar talakawa yar mai min hidima, kazami kawai.. "Nagode mai tsafta ya fadi yana dariya, "Kije na sakeki, amma duk ranar da kikaji kina muradina kafin ki gama idda ina iya maida ki saboda darajar 'yayanki da mahaifinki, yana kaiwa nan yaja Fatima suka wuce daki.. Yana jiyo ihunta tana zaginshi da mahaifiyarshi, babu wanda a cikinsu ya tanka ta dan anyi mata mai kankat.... Dakinta ta shiga ta tattare kayanta da gwalagwalanta ta fice ta bar mishi gidanshi.... ********* Saida Musaddiq ya kwana uku a asibiti, lokacin ya farfaďo yana gane duk wanda ke kanshi, babu abinda yakeyi daga kallon su Daddy sai bacci in allurai sun ratsashi, tunda ya farfaďo kamar an tafi da hawayen da yakeyi, magana ba ya yinta ko kadan sai dai in sunyi ya bisu da ido, Da support yake zuwa yayi alwala da wanka saboda jikinshi samm babu kwari, a wannan lokacin ne aka yarda kowa yazo ya ganshi dan jikinshi yayi kyau matuka, abinci da ya zamo aminin Musaddiq yanzu ya maidashi babban makiyinshi domin sai anyi bacin rai kafin ya yarda yayi cokali daya, kowa burinshi ya farantawa Musaddiq dan dai kawai su samu ya saki jikinshi ya cigaba da Mu'amala kamar yadda ya saba, Zainab da Ruwaida ne samm ba'a yarda suje inda yake ba saboda har yanzu bakinsu bai bar tambayar inda Nadeeyah take ba... A cikin kwanan shi na bakwai aka sallameshi, har wannan lokacin babu wanda yayi mishi maganar inda Nadeeyah take, shidai yafi bada an binneta shiyasa ma baiyi yunkurin tambaya ba, dan kar ya sake tayar wa da hankalin su Daddy, Suma kuma har lokacin basu bar neman Nadeeyah ba, dan har police station suka kai, tunda Allah baiyi sunga gawarta ba sunsan tabbas tana raye, in da rai wata rana dole su haďu in shaa Allah.... **** "Karka damu Daddy, i will take care of myself, Kallon Zubair Daddy yayi yace "Dan Allah ka kula dashi, karka barshi ya dinga tunani, ka---- "Nace i will take care of myself, i'm nt a kid, yadda yayi maganar da tsawa ya sanya Anty Reemah matsowa kusa dashi, Dafa kafaďunshi tayi tace "Laifi ne dan ance a kula dakai, tafiyar nan ance ka hakura da yinta, baka da lafiya, ka dage sai kayi ta, dole a nemi mai kula da kai.. Hannunta ya cire a kafadunshi ya dauki brief case haďe da kallon Daddy yace "kayi min addu'a in shaa Allah babu abinda zai sameni, tunani shi ke yin kanshi, with ur Du'a komai zai daidaita, Murmushi Daddy yayi yace "In shaa Allah son, Allah ya tsare ku ya bada sa'ar abinda aka je nema... Gurin da Hilal ya ke tsaye Musaddiq ya kalla, suna haďa ido ya karaso inda yake ya rungumeshi, rashin walwalar Musaddiq na matukar damunshi, babu abinda yake sanya shi farin ciki, dariya kanta ya manta yadda akeyinta, domin wani sashi na yin dariyarshi ya mutu a ranar da ya rasa Nadeeyah, "Take care kaji, in na gama project zanzo Singapore inyi keeping dinka company, gyaďa kai kawai Musaddiq yayi suka fita, dukkansu yan parlon kowa na mishi fatan alkhairi haďe da adduar Allah ya kara sanya farin ciki a cikin zuciyarshi...... Mutum kamar Musaddiq wanda baisan menene bacin rai ko fushi ba a ganshi a haka dole hankalin makusantanshi ya tashi dan sun san ba karamin abu bane yake sanya Musaddiq fushi, Daddy yaso yayi quiting aikin da yakeyi amma Musaddiq sam yaki, saboda shi kadai ne yake ganin zai dabe mishi kewa, badan Daddy yaso ba haka nan ya yarda dan yaso ya zauna tare dashi har ya samu sassauci a zuciyarshi... Duk wani shiri na barin gidan su Badariyya sunyi domin abun kawai da ya rage musu shine su tarwatsa kuttun tsafin Bokan gaba daya, layar dake bakinsu suka matsa dan bacewa suka ji su har lokacin a gurin, cike da tashin hankali suka kalli juna haďe da sake latsata, hankalinsu bai kara tashi ba sai da sukaji damka a bayansu, waigowa sukayi dan ganin mai ganinsu a wannan lokacin da suka san sunyi komai dan bacewa ganin mutanen gidan, Yareemah Suhail suka gani gefenshi kuma duk wasu kulli da sukayi ne wanda ya warwaresu ya sanya musu wuta, Dariya sosai yayi yace "kun taba jin labarin wanda ya shigo gidannan ya fita shi kadai, shafa kanshi yayi ya cigaba da cewa "Badariyya nasan da hatsabibancinki kika zo, sai kuma kika kara da na Marakisiyya, da nice ke zanyi biyayya domin cikin biyayyar wata rana in da rabo ina iya kaiki gida ki ga yan uwanki har kiyi musu sati in kinaso, amma tunda kin biyewa wannan hatsabibiyar sai kuyi ta zama da taurin kanku, duk ranar da kuka ga kun amince da zaman gidan nan sai kuyi biyayya, in kuna da rabo sai kuga na kaiku gida dan ziyara, yana kaiwa nan yayi wurgi dasu cikin wani dakin da basu san da zamanshi a gidan ba.. Kukan jini ne kadai Badariyya batayi ba dan ta ga koshi ya rikide ya zame mata kwanan yunwa, tayi shirin komawa ta shiga Musaddiq sosai har ta kai ga aurenshi hankali kwance ba tare da kowa ya zargeta ba... Taci kuka sosai har saida faďa mai karfi ya kacame musu ita da Marakisiyya, faďan da ya sanya zubewar hakoran Badariyya na gaba, dan Sosai Marakisiyya tafi karfinta..... *6months later...* ******* Radiya.. bani dubu biyu zan baki gobe in Reemah ta turo min, Buďe baki Radiya tayi tace "ina na gansu Mummy, nawa nake binki? kusan 30k fa, ina zanga dubu biyu yanzu, Raudha dake kwance akan kujera tace "Ki bata mana, jiya fa kika siyar da zobenki, meye a ciki dan kin bata, kika san abunda zatayi dashi... To munafuka, da na siyar da zoben baki faďa mata abun da nayi dashi ba, saida zoben kaďai kika iya faďa mata, ni fa na gaji da wannan rayuwar, duk wani abu nawa ya kare, kullum ni kenan cikin bada kudi sai kace wata banki, na gaji wallahi ta mike fuuuu tayi cikin daki.... Share zufa Mummy tayi haďe ficewa daga dakin tana mamakin hali irin na Radiya, kwallar da ta fito a idanunta ta share haďe da yin tagumi tana tunanin a wani hali Musaddiq yake yanzu, rabon ta da ta sashi a ido tun daren da suka fita nemo Nadeeyah, ko sau ďaya bai taba tunanin nemanta ba, ta sani ta bata mishi matuka, a yanzu dana sani takeyi sosai na biye wa san zuciyarta da tayi, kawayenta da a da suke like mata kaff dinsu sun guje ta saboda halin da take ciki, Nairah dari yanzu mugun sha'awa take bata, ga Baffa ya dauke Anni ya maida ita gidan da Papy ya siya saboda ya dinga sauka in yazo, ko ganinshi basa yi a gidan saboda a cewarshi basa girmama matarshi, Daddy kuwa ko ta kirashi bata samu dan ya sanyata a black list, samm bata samunshi, koda text tayi mishi saidai ya dawo mata dan ko kusa baya isa gurinshi... Shigowar Rilwanu da kayan abinci shi ya katse mata tunanin da takeyi, da murnarta ta mike tace "Wadannan kayan daga ina? "Alhj karami ne ya zo shi ya sauke su, yana waje nasan yanzu zai shigo, Hijab ta dauko da sauri jiki na rawa ta fita tarbo Papy... Kuka wiwi ta dinga mishi tana neman gafararshi, rike mata hannu yayi yace "Haba, wallahi ban taba rike ki ba, we are all humans, we make mistakes, ni waye da bazan yafe miki ba, komai ya wuce wallahi, ina Goggo? Hmmm ta tafi kauye tun shekaran jiya, "Nace ya labarin Musaddiq, kana ji daga gareshi kuwa? Bai zo bane? Papy ya tambaya cike mamaki haďe da fito wayarshi, kuka Mummy ta fashe dashi tace "Rabona da Musaddiq wata shida kenan da kwanaki.. "Ya salam, ai ban sani ba, jiya da ya kirani nake tambayarshi yazo gida yake cemin yazo duk kuna nan lafiya, Hawaye Mummy ta share tace "Nasan nayi deserving more than this, tunda har Daddy yace in har aka sake mishi maganata zai cike ukun, shiyasa nake lallabawa ina hakuri har lokacin da Allah zai yanke min wannan punishment din... Cike da tausayin dan uwa Papy yace "karki damu, wata rana zai sakko, yanzu ya hau dokin zuciya ne, Gashi ya auri zaman lagos, gaba daya yayi ma kaduna kaura, in shaa Allahu komai zai wuce, ke dai kici gaba da addu'a da kyakykyawar niyya, zakiga kamar ba'ayi ba... Hira sosai sukayi ya bata dubu ashirin, sannan ya tashi ya nufi gidan su Anni..... *Memories are always special, sometimes we laugh by remembering the day we cried, nd sometimes we cry by remembering the day we laughed That's life*... "Na dade da manta yadda ake dariya, rabin rayuwata ya mutu ranar da kika tafi kika barni, " Kin manta alkawarin da kikayi min? we promise to live together duk rintsi duk wuya, Why did u live ur other half.. Why, Why did u go nd live me alone, Why Nadeeyah, Why.. hakan ya dinga maimaitawa yana yayyaga hotunanta haďe yin wurgi da laptop din da ya manna hotonta kan screen din, Da sauri Daddy ya hawo sama ya sameshi yana tattaka laptop din yana huci kamar mayuwancin zaki, Rikeshi Daddy yayi hade da janye shi da kyar daga kan laptop din, Idonshi da yayi jawur Daddy ya kalla yace "Meyasa kake yima rayuwarka haka, kafi Allah sanin abun da ya dace da kai ne, tunda kaga ya ďauketa yasan dalilinshi na yin hakan, Allah nasan masu tawakkali, "Tawakkali wanne kuke son inyi? Ya tambaya a harzuke, Ka taba ganin nayi kuka, ko na tambayeku inda take? Nasan ta tafi kuma bazata dawo ba, shiyasa nakeson yadda ta tafi ba tare tunanin halin da zan shiga ba, nima ta fita a raina.. I want to cry her love out of my life, i want to hate her so much, Nasan nayi mata laifi, amma laifina bai kai tayi min irin wannan hukuncin ba, ya zata tafi ta barni bayan tayi min alkawarin bazata rabu dani ba, in ta tafi dan bata sona meyasa zata bar min nata son a cikin zuciyata, da sai ta tafi dashi gaba ďaya, Plss Daddy help me, ka faďa min yadda zanyi ta fita a raina, bata bari na sukuni, komai nakeyi ita ke yawo cikin kaina da jinin jikina, dan Allah ka taimakeni ka cire min ita a cikin raina, plsss.... Rungumeshi Daddy yayi yana kuka sosai haďe da cewa "Cry Musaddiq, kayi kuka may be ka samu sassauci, *So* Allah ke sanya shi, baka isa ka cireshi ba, u have to move on, in Allah yasa zakayi wani farin cikin nan gaba to zaizo ba tare da shawara ba, sai kaga Allah ya baka wacce tafi Nadeeyah... Sakin Daddy yayi yace "Samun mace irin Nadeeyah abu ne mai wahala, Cikin hikima Daddy yace "Allah, har tafi Antynka Reemah? "Ita ba wacce za'a kwatanta da kowa bace, she is very nice.. Yadda ya bawa Daddy amsa cikin sakin jiki ya sanyashi zaunar dashi yana tambayarshi labarai akan Nadeeyah, labarinta ya shiga bashi wanda ya sanya mishi kaunarta marar adadi cikin kwana taran da sukayi tare, "Nadeeyah is so special Daddy, she is so sweet.. ya karashe haďe da yin wata yar dariya wacce bata kai ko'ina ba....... Mrs Tijjani Shattimah...... [30/04 4:57 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣6⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *A square Turkey constructing company*.... Ya rasulullah... dattijon ya faďi haďe da dafe kanshi, coffee din dake gabanshi ya ture gefe yana mai sake duba cikin system dinsa, ya dade bai duba ayyukan gidajen shi ba saboda yadda ya yarda da ingancin masu yi mishi aiki musamman mai mishi zane da engineern dake tsaye gurin ganin an tsara ginin yadda ya kamata, "kusan watanni shida kenan da gama aikin wasu gini amma har yanzu mutane biyar kaďai suka siya wasu bangare daga gidan, tun yana Egypt yake damuwa da outcome din business dinshi dake turkey, yau dai ya shirya zuwa dan ganin dalilin da ya sanya companynshi ya fara zama koma baya wurin ciniki a kasar instanbul, ganin yanayin tsarin ginin da ya kashe makudai kudi yayi su ya sanya hankalinshi tashi matuka, sam zubin tsarin baiyi ba, komai anyi shi a gaggauce, kama daga zanen har ginin, sam bai iya bacin rai ba domin shi mutum ne wanda ya yarda da kaddara mai kyau da marar kyau, asarar da yayi bata kananan kudade bace, haka ya bar gurin yana istigfari haďe da adduar Allah ya sanya asarar da yake shirin yi ta zame mishi alkhairi.... Yana komawa office ya bukaci sanin a inda matsalar take, engineern ya fara kira, nan ya gabatar mishi da zanen da aka bashi domin yin aikin sannan ya ďora da cewa "kanin manager ne yayi zanen, wanda ya saba yin zanen ya bar aiki damu kamar yadda manager ya faďa min.. Sheik na ganin zanen ya gane a inda matsalar take, bai bukaci jin wani karin bayani ba yayi zaune hankali duk a tashe yana hango dakushewar kasuwancinshi kwana kusa, Rufe system din yayi ya mike ya danna wata kararrawa dan yin taro na gaggawa da ma'aikatanshi, nan fa suka shiga tururuwar shigowa cike da ladabi suka tsaytsaya a muhallinsu..... Bayan ya gama musu bayanai na abun da ya tarasu sannan ya dora da irin barazanar da companynshi yake fuskanta ya kuma yi umurni da kar a sake baiwa wanda yayi zanen gidajen da sukayi musu bandaro aiki, Bayan nan ya bukaci duk wani wanda yasan mai zane wanda ya kware a zane ya je ya kawo shi ya kuma sashi ya taho da aikin da yayi, rabin yan gurin wadanda suka san Hilal suka fara ihun sunan *M H K*... wasunsu kuma suka fita domin kiran makusantansu suzo ga aiki ya samu, Cikin awanni uku aka haďa masu zane kusan su 15, nan duk suka gabatar da ayyukansu wanda ko rabin na Hilal basu kamo ba, cike da kosawa ya kalli zanen na karshen haďe da mikawa engineern, "Call for another meeting plss, ina son sanin dalilin da yasa Hilal ya bar aiki anan gurin.. cike da girmamawa engineern ya amsa shi ya fita da sauri ya sake kiran wani meeting din.. "Da harcen turancin dattijon da bai wuce shekaru hamsin da doriya ba yake magana, "Nasan akwai masu zanen gidaje da yawa, amma companyn nan kowa yasan "Hilal Kangiwa" ne yake zanen gidajen da muke ginawa masu daukar hankalin jama'a, duk wadannan masu zanen da kuka tara min dan Allah ku basu hakuri, a je a nemo min Hilal muyi eye to eye dashi inji nawa yake son a kara mishi, Cikin girmamawa manajan kamfanin yace "Ba kudin bane sukayi mishi kadan, matsala suka samu da IRFAN, shine yace ya bar aiki, Ya salam... dattijon ya fadi yana mai dafe kanshi, wato Irfan sai ya kori duk wani wanda suke kasuwanci tare, a kausashe yace "bani number wayarshi zan kirashi yanzu yazo office ya sameni... ****** "Duk tashoshin cartoon din yau basu yi zee, kin gani? ta tsaida kan Mbc 1, tana yunkurin canzawa wayarta ta dau kara, mikewa tayi da sauri ta zare wayar a charge, daki ta wuce tana waya da Jamal cike da so da qauna, Lamoo Zainab tayi cikin lallausar kujerar parlon tana kallo haďe da lumshe ido alamun bacci nason yin gaba da ita,  bata dauke idonta a kan tvn ba dan tasan in suka gama tallan drama's dinsu zasu sako cartoon, hannu tasa a baki tana sha a boye dan kar Hilal ya kamata, yadda ta naďe hannun da hula zaka rantse wani abun take sha daban, Kamar cikin mafarki ta tsinkayi kukan yar budurwa cikin wani tallan arabic drama, sanye take cikin jallabiya baka kanta yane da ďankwali, Mikewa zainab tayi ta isa gaban tvn dan kalolin hotunan budurwar ake nunowa, daga wanda take kuka sai wanda take dariya, *Adda* ta furta a hankali tana shafa fuskarta a screen.... " *Hey everyone i'm _MALEEKA SAHEEB SAIF_.... SAHEEBUL QALBEE will be in cinema's on the 3rd may in shaa Allah, don't miss the unconditional love story of NAINAH AND SAMIR, dos in Egypt will see ya on the 5th, nd Istanbul on the dday, love yhu oll my fans.. muahhhh..* Ya Hilal... Ya Hilal... A ruďe ya rufe laptop dinshi ya buďe kofa saboda irin kiran da Zainab take mishi, duk tunaninshi wani abun ne ya sameta, haki ya ga tana yi tana nuna mishi tv, "Adda na gani a cikin tv, wallahi itace, ajiyar zuciya Hilal yayi ya kwace naďin da tayi ma hannunta da hula yace "wannan abun da kikayi shi ya sanya tayi miki gizo, amma muje in ga ko itace, bin bayanshi tayi suka zauna a parlon lokacin an wuce tallan har an fara cartoon, a hankali tace "an gama, amma ka zauna a sake yin talla zaka ganta, janyota jikinshi yayi yace "Bacci kikeji my baby, kwanta kinji, anjima in kin tashi sai mu fita yawo, rufe idonta tayi tana hango fuskar Maleekah wacce tayi ma lakabi da Nadeeyah, babu abinda ya banbanta su sai tsayi da wayewa, Maleeka ta ďan dara Nadeeyah tsayi sannan wayewarsu da gogewarsu ma sam ba daya bace, amma kamannin fuska babu inda suka banbanta, da tunanin bacci yayi gaba da Zainab, kwantar da ita yayi a gurin ya mike dan karasa research din da yakeyi akan aikin da gwamnati ke son bayarwa, yana son Applying aikin amma yasan yafi karfin Papa ma bashi ba... Cike da confidence yayi Applying haďe da ayyukan da yayi a baya, tunanin yadda zaiyi ya haďu da mai *A square TCC* ya keyi, yasan zaiyi aikin domin kuwa karuwarsa ce da shi baki daya, dan in ya yarda sukayi aikin nan ba karamin kuďi zasu samu ba, Wayarshi ya dauko da niyyar kiran manajan companyn, tunawa da halinshi da yayi ya sanyashi ajiye wayar ya cigaba da tunanin yadda zaiyi ya hadu da CEO din cikin sauki,, har ya mike zai  shiga bayi yaji karar waya, da kamar kar ya dauka dan yaga bakuwar number, wani sashi na zuciyarshi ya bashi umarnin dagawa yaji ko alheri ne, Aiko Hilal yayi farin ciki matuka da jin mai kiran nashi dan abun da ya dade yana nema kenan, nan yayi alwala yayi sallah haďe da yin addu'ar Allah ya bashi karfin gwiwar fada mishi abun da ke ranshi, ya kuma sanya haduwar tasu ta zamto alkhairi..... "Shiryawa yayi tsaff cikin kaftan riga da wando ash, ya dade yana son haduwa da Ceo din companyn da yake wa zane  *SHEIK ATIKU SAHEEB SAIFUDDEEN* Saboda wadannan  ayyukan zanen gwannati da yake son nuna mishi, kuma yana son yi mishi gargadi akan macutan dake gudanar da ayyukansu a companyn shi... Sanyin A.c. hade da kamshi mai dadi ke tashi a cikin office din, Makeken Hoton jikin bangon idonshi ya sauka a kai gabanshi yayi mugun faduwa, su hudu ne a jikin Hoton, Irfan kadai ya gane saboda yayi mishi sanayya marar dadi, Hoton yar budurwar da mahaifinta su suka fi tayar da hankalinshi, bai gama shiga dimuwa ba sai da yaji muryar mutumin ya fito yana mishi MARHABAN ya Hilal, suman tsaye yayi da suka hada ido saboda tsabar firgici, tabbas yasan mama suwaiba bata da wani dan uwa namiji, to wannan mutumin me irin fuskarta daga ina ya fito... Hasbunallahu wa ni'imal wakeel ya fadi jiki na rawa, a zatonshi gamo yayi da aljani..... Karasowa kusa da Hilal yayi ya miko mishi hannu dan su gaisa, kasa daurewa Hilal yayi yayi saurin tsugunawa dan yi mishi irin gaisuwarmu ta hausawa, nan fa Sheik ya sake jin kaunar Hilal na yawo a cikin jininshi, dagoshi yayi ya haďe jikinshi da nashi haďe da sumbutar kumatunshi irin dai yadda larabawa ke gaisuwarsu, hoton dake kan makeken table dinshi kuwa saida ya kusa tsaida numfashin Hilal, Hotone kato black nd white, fuskar nan bata da maraba da ta su Mama Suwaiba, Sheik, Nadeeyah da yar budurwar dake cikin hoto, bai kara samun kanshi cikin ruďani ba sai da idonshi yayi tozali da sarkar wuyar tsohon hoton, wannan karan Hilal ya riga ya gama fita hayyacinshi, kar dai son da yakewa Nadeeyah ne ke neman kaishi wata duniyar daban, hannun dattijon da yaji cikin nashi ne yasa shi saurin matsawa baya, da karfi yake furta kalmar "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, cikin rashin fahimta dattijon ya nufoshi yace "Lafiya? Menene yake faruwa? "Dan Allah karka cutar dani, Innalillahi, "wa inna ilaihir rajiun sheik ya karasa cike da zullumi haďe da cewa "Subhanallah, jin ya ambaci sunan Allah ne ya sanya Hilal nutsuwa haďe da nemo duk wata jarumtakarshi, ganin ya samu nutsuwa ya sanyashi cewa "su shiga cikin parlon office din, bayanshi Hilal yabi yana ambaton sunan Allah... Kallon Hilal Sheik yayi yana tambayarshi damuwarshi, Murmushi kawai Hilal yayi yace "Babu komai kawai yayi mishi kama da wasu relatives dinshi ne nd they are no more, hoto ya kuma gani a kan centre table din cikin parlon an haďa pixmix da na Maleekah, dauka Hilal yayi ya fito da wayarshi yayi scrolling hoton Nadeeyah ya nuna ma sheik, second goma yayi yana kallon fuskar Nadeeyah, tabbas wannan tayi kama da yayarshi wacce ya rasa tun da kananun shekaru, katse mishi tunani Hilal yayi dan a lokacin tsoro ya fita a ranshi, yana da tabbacin wannan dan uwan Mama suwaiba ne bangaren uwa, "Wannan sarkar ya nuna sarkar wuyar tsohon hoton, da sauri Sheik yace "Ehem kasan sarkar ne, gyaďa kai Hilal yayi yace "Sosai, tana gurin grandfather dina, gaba ďaya sun manta zaman da suka zo yi, ko wannensu ya shiga shaukin son jin labarin juna, "A ina ya samu sarkar, yadda muryarshi ke rawa ya sanya Hilal dafashi, "calm down sir, farin cikin da nake ciki bazai barni in baka amsa ba, sunanta kaďai zanji ya sanya ni fita gurin nan cikin gaggawa dan bayyanawa yan uwana abun farin cikin da ke tunkaro mu, a gaggauce Sheik yace *At---* *ATIKA* Hilal ya karashe cike da kaguwa domin ya kasa jiranshi ya karasa, "Yesss, she is my sister Atika, my only sister, my everything ya karashe cikin matsanancin kuka haďe da rungumar hotonta wanda ya zame mishi kullum... "Ya Allah... Hilal ya faďi yana zubar hawaye, Nadeeyah were are uuu, Asalinki ya fara bayyana, ya ilahi, tsatso mai kyau, i knew it, nan gaba abubuwan shahara zasu bayyana gareku, Ina kika shige Nadeeyah, kuka sosai sukeyi, shi Sheik yana yi ne dan duk a tunaninshi zai sake sanya yar uwarshi a ido, shi kuma Hilal kukan biyu ya haďe mishi, na farin ciki da kuma na bakin ciki domin duk wanda ya kamata ya ga wannan farin cikin baya tare dasu, " *Is this a scene or reality?* Zazzakar muryarta ta karaďe dakin, a tare suka kalleta tana tsaye sanye da bakin dogon wando wanda kasanshi yake a buďe sosai sai milk riga mai dogon hannu, kanta yane da da bakin gyale wanda ya bayyana gashinta har gadon bayanta, karasowa tayi hankali a tashe tana faďin *ohh Abbu?* wurgi tayi da jakarta kan doguwar kujera ta zauna kusa dashi, hawayen ta fara share mishi tana magana da larabci, tasan Irfan ne kadai kesa mahaifinta hawaye haka, hoton da ya rike a kirjinshi ta karba ta zuba mishi ido, ajiyeshi tayi a mazauninshi ta dafa kafaďunshi, "Bazan hanaka zubar da hawaye ba dan nasan a wannan lokacin babu abinda zaisa su tsaya sai dai domin kansu, tunda nazo duniya nake ganin hawayen nan, plss Abbu kayi hakuri, kayi tawakkali, in kanada rabon ganinta zaku haďu cikin sauki in shaa Allah, Fuskarta ya tallabo haďe da sakin murmushi a bayan kukan yace "Allah ya kawo min lokacin my love, yanzu na samu labarinta daga gurin Hilal, kallon inda ya nuna mata tayi, shigowarta tabbas ta ganshi, amma ganin halin da Abbunta yake ciki ya mantar da ita akwai mutum a gurin, cikin ido ta kalleshi dan shima ita yake kallo tun shigowarta, mamaki ya hanashi furta komai dan ya tsorata da hukuncin ubangiji, irin wannan kamanni har haka, ya salam, tabbas badan gogewa da wayewarsu ba daya bace da babu abinda zai hanashi kiranta da Nadeeyah, Takalmin kafarta mai tsini ta cire ta mike rai a haďe ta isa gurin Hilal, ta riga ta gama hararo abun da ya kawo shi, tasan sarai yazo da niyyar cutar mahaifinta ne, shekara sama da hamsin da batar ta sai yau zaizo yayi taking advantage din son da mahaifinta kema yayarshi yace ya san inda take, in shi yasan inda take meyasa baizo da ita ba, "Heyyy, ta faďi haďe da buga hannunta a saitin idonshi, firgigit Hilal yayi ya dan matsa dan baisan ta karaso inda yake ba, kusa dashi ta zauna sosai tana fuskantar mahaifinta tana dariya dan kar ya gane manufarta, "Wa ya aiko ka? Ta tambaya ba tare da ta kalli inda yake ba, cikin rashin fahimta ya share hawayen dake makale a idonshi yace "Ban gane ba? "Zaka gane, hannu tasa cikin nashi tace "Muje ciki akwai tambayoyin da zan maka, mikewa yayi dan ta fara jan hannun tana tafiya, da larabci tace mahaifinta tana zuwa... Sosai ran Hilal ya baci da ta gama jero accusations dinta cike da faďa kamar zata mareshi, maganarta ta karshe ce ta sashi daka mata wata tsawar da ta daidaita ta, "Yesss nasan Irfan, sani sosai, "Ehen i knew it, nasan Irfan ne yasaka wannan aikin dan ku samu kudin banza ku je kuyi iskancinku, ku ko kunya bakwa ji, at ur age baku san yadda zaku dinga samun daily income ba sai kunyi cuta, to this deal is cancelled sai ku nemu wani, nuna shi tayi da ďan yatsa tace "Wallahi in na sake ganinka gurin Abbu na sai nasa anyi maka daurin rai da rai, babu inda ba'a sanni ba world wide duk inda na nemi alfarmar a kam----- Gerraut Hilal ya faďi haďe da buge hannun kasa, duk sanyin da ya shigeshi na rashin Nadeeyah ya fice gaba daya, "Count me out, ban sanki ba, ban taba ganinki ba, sannan Irfan a companyn nan na sanshi, u most be stupid in har kikayi tunanin nazo nan ne dan kudin mahaifinki, he called me himself, go and ask him, i'm his company architect, ban taba ganinshi ba sai yau, nd wat i saw ya sani faďi saboda ur aunt is my relative, hannu na rawa ya dauko wayarshi ya nuna mata hoton Nadeeyah, ganin jikinta ya fara sanyi ta kuma tsumu da mamaki ya sanya shi kwace wayar yace "I have my own self respect, nasan i'm nothing like ur father but i'm contented with the little i have, am not needed here, kuje ku nemi  real yan uwanku tunda ni fake na kawo, yana kaiwa nan yayi hanyar waje haďe da buga tsaki, Da gudu tasha gabanshi haďe da rike mishi hannu, "Sorry sorry sorry, plssss... ta kara faďi haďe da tsugunawa a kasa, kwace hannunshi yayi zaiyi magana yaji muryar Sheik a bayanshi, "Kayi hakuri Hilal, she is always like that, akwaita da tambayar da zata kai mutum bango, zo ka zauna na yarda da kai 100%, juyawa Hilal yayi ya koma kan kujera ya zauna fuskar nan a murtuke, wannan babu abun da ta haďa na hali da Nadeeyah, kalamanta na cin mutunci sun mishi zafi matuka, dannewa kawai yayi ya zauna dan sauke wannan nauyin badan ita ba sai dan Nadeeyah da su Hafeez, tambayoyi sheik ya fara mishi, babu abinda ya iya faďa mishi sai dai kawai ta Haifi twins... Yadda yaga ya ruďe da murna ya kasa sanar dashi ta mutu, a ranar maida Hilal ciki ne kadai sheik baiyi ba, tafiya ya shirya musu da private jet din abokinshi dan baya son wani delay a zuwa ganin yar uwarshi da zuri'ata, Murna tasashi ya yafe mata rashin nemanshi da batayi ba, tasan irin ukubar da ta tafi ta barshi a hannun Ummul da 'yayanta, share hawayenshi yayi bayan ya tuno gararanbar da yayi a baya wanda ya zame mishi tarihi... Har Hilal ya bar office din bai kalli inda Maleeka take ba, ita kuwa sai kai kawo takeyi da kayan kwadayi tana dire mishi, tasan bata kyauta mishi ba, idonta ya rufe ya hanata hango kamalar fuskar Hilal, Sukuku ta yini ranar har ta koma gida, duk abinda takeyi Hilal kawai take gani, masifarshi da komai nashi burgeta yakeyi, samm bai bata fuskar da zata amshi number shi ba, tayi yawon duniya sosai, ta haďu da maza haďaddu wadanda suke macewa akanta, bata karo da wanda zuciyarta tayi na'am dashi ba tun bayan Mutuwar Na'em sai Hilal, *Saheebul qalbee* ta furta a hankali tana mai hango soyayyarsu ta cikin film din.. "Kwatanta soyayyar da mai zafin zuciya irin Hilal zai fi armashi..  murmushin dake kan fuskarta samm yaki daukewa, tana hango Abbunta da Ummi na sakkowa daga sama cikin jallabiya tayi saurin nutsuwa ta isa gurinsu dan tambayar inda zasu a daren nan... Amsar da ya bata ya sanyata yin murmushi mai kyau haďe da cewa su jirata dan Allah zata rakasu, "Jira fa Malee? Ummi ta faďi da harcensu na larabci tana rike haba.. Kwantar da kanta tayi a kafaďun Abbu tace "Abbu kaga ummi ko? "Zan jiraki, komai dake zanyi, ke zata fara gani tunda sunanta gareki, rungumeshi tayi ta haye sama da gudu dan shiryawa.... 40mins Ya Habeebi, kasan jiran Maleekah... bata gama rufe baki suka hangota cikin purple jallabiya mai walkiya, kan nan ta yaneshi ta fito a balarabiyar asali, light makeup tayi wanda ya fito da kyawunta na musamman, kamshinta kuwa dadinshi kansa mai saurare yayi baccin da bai shirya ba, *ATIKA ATEEK SAHEEB SAIFUDDEN* kenan ta haďu matuka, tun tana karama take sha'awar drama, Shiyasa samm taki maida hankali a karatu, gata da kokari sosai, ganin hakan yasa Abbunta yi mata jumping, tanada 14yrs aka kaita university inda ta karanci theartre art, da yake field dinta ne sai ta dage sosai dan kullum cikin drama suke, hakan yasa ta kware sosai, a yanzu duk kasashen larabawa babu inda ba'a santa ba, haka tsirarrun yan wasu kasar irin nigeria masu kallon arabic dramas suma duk sun santa, shekarunta basu wuce 21 ba amma wayewarta ta zarce dan 30...   "Kinyi kyau my love, kiss ta mishi a kumatu tace "Thank u Abbu, nasan anyi complain? Dariya yayi yace "as usual, kin santa, gaba ummi tayi tana dariya tace "kwaji dashi..... Basu sha wahala gurin zuwa gidan ba dan estate dinsu sananne ne sosai, Da fara'a Hilal ya taresu tun daga kasa, dama ya gama shirya ma zuwansu, ya faďa ma Anty Reemah zaiyi baki amma bai faďa mata ko su waye ba... Zainab na zaune tana home work tana zana sunan da yake bace mata a kai, Maleekah sahy, Maleekah Sa'eed, Maleekah sahab haka ta dinga rubutawa a bayan littafinta, ko da taji an murda kofar duk su Anty Reemah sunje suna musu maraba bata dago ta kallesu ba, Na--deeyah... Hinad ta faďi a hankali tana nuna Maleekah, dago kai Zainab tayi ta mike da sauri ta isa gurinsu, kallonsu ta shiga yi daya bayan daya, tasan ba Nadeeyah bace, dan in itace abun da zatayi mata ya wuce ta tsaya tana kallonta, "Maleekah sahab ko? Dariya Maleekah tayi ta tsuguna kusa da Zainab tace "Saheeb dai my young fan, ko dai brothernki ne ya faďa miki sunana, ta karashe tana kallon Hilal, shuru Zainab tayi dan turancin na Maleeka yafi karfinta, Anty Reemah ce ta katse shurun ta hanyar nuna musu gurin zama, bayan sun gaggaisa Anty Reemah ta kalli Sheik cike da al'ajabi zatayi magana Hilal ya rigata dan baya son yasan mutuwar yar uwarshi samm sai yaje ga mijinta, "Mum wannan kanin maman su mama suwaiba ne, labarin yadda haďuwarsu ta kaya ya basu wanda ya cikata da mamaki, "lallai komai da sanadinsa, sanadin aiki ya sa ka samo wannan muhimmin abun, kaii masha Allah wallahi naji dadi sosai, introducing dinsu Hilal yayi, yana zuwa kan Zainab da Sheik ya kasa daina kallonta yace "Ur grand daughter sir, she is urs! hawayen farin ciki ne ya fito mishi dan yajita sosai a jininshi, mikewa yayi ya dauketa sosai a jikinshi, ya kosa a wayi garin gobe yaje yaga zuri'arshi, shakikanshi, wadanda yake da rashinsu tun kuruciya, a gidan Papa ya samesu shima yayi farin ciki sosai sukayi hirar kasuwanci da na iyalai, Sheik jin kanshi yakeyi kamar a yaune aka haifeshi dan ya fara jin kamshin yan uwanshi danginshi na uwa... Assalamu alaikum..... maida hankalinsu kan mai sallamar sukayi dukkansu, Sauka jikin Abbu Zainab tayi ta ruga gurin Meerah, "Anty Mee zo kiga Maleekah da nake baki labari dazu, hankalinta sam bai kan zainab tana can kallon yadda Maleeka tasa kafa tana shafo ta Hilal yana matsarwa, tray din hannunta ta damke dan kiriss ya rage ya faďi kasa, "Muje zee, Har kasa ta tsuguna ta gaida su Abbu sannan ta mike ta nufi kujerar da su Hilal suke, kan hannun kujerar ta zauna, ganin duk manyan suna can suna hirarsu yasata yi mishi raďa a kunne, Dariya sosai yayi dan ya gama gane inda ta dosa, mikewa yayi ya nufi dakinshi.. bin bayanshi tayi rai a bace dan ta gama kulewa, dangwarar da tray din snacks din da tayo mishi tayi a kan madubi, "Meerah plss, kar muyi creating scene a gidan nan kinga munada baki, "Eh naga baki, su bakin da suka san inda sukazo ai na samesu suna hira, kai fa, ko kunyar idon iyaye bakaji ba ka zauna kusa da mace tana shafa maka kafa kana jin dadi, Wannan karan dariya yayi mai sauti wanda ya kular da Meerah ya sata sakin kuka mai karfi, "La'ila, ke rufa min asiri plss, haba meerah, yarinyar nan kema kinsan tafi karfina daga yanayinta in kika kalla, "Me zanyi da yanayinta ni, abun da idona ya gane min shi na lura dashi, na gama fargabar wata yanzu kuma ga wata zata shi---- Meera.. ya katseta haďe da tsugunowa gabanta, Na faďa miki soyayya yanzu na rufeta a shafin rayuwata, bana tunanin zan sake faďawa cikinta so quick, na faďa miki kiyi hakuri, wallahi in nace miki zan yarda ki jirani nasan cutarki kawai zanyi, bazan iya sake yin wata soyayya ba, u are my best friend tun muna yara, dan Allah mu tafi a haka, Allah zai baki wanda yafini alkhairi, Share hawayenta tayi ta mike tace "Nagode Hilal, zanyi hakuri dakai dan dama nasan ba sona kakeyi ba, "Nooo Meerah... ya faďi haďe da matsowa kusa da ita, hawayen da ya makale a idonta ya share mata yace "kinsan Allah ina sonki, amma bazan iya zaman aure dake ba, who will be the husband? Yadda yayi tambayar cike da zolaya yasata yin dariya, tasan irin matan da yakeso, yara kanana wadanda zai yi musu yadda yake so, bayason a juyashi sam, ita kuwa Meerah kusan mates ne in ma bata girme mishi ba, "All the best besty ta faďi tana murmushi, Allah ya sake baka wata soyayyar wacce tafi ta da, "U will always be my best Meera, Allah ya baki farin ciki kema.... "Uhmmm wonderful.., Maleekah ta faďi tana karasowa haďe da tafa hannu, a tsakiyansu ta tsaya cike da tsiwa, hannun Meerah Hilal yaja yace da hausa dan yasan bata ji. "Muje in rakaki, ba kunya gare yarinyar nan ba, kallo ta bisu dashi ta rasa menene ainihin abin da yasa ta biyosu, kwafa tayi ta kama hannun Zainab suka koma parlor, lokacin har su Abbu sun mike da niyyar tafiya, wayarta ta dauka sukayi hotuna kala kala da Zainab da Hinad, Har kasa su Anty Reemah suka rakosu, tana ganin Hilal ya nufo inda suke tayi saurin sanya Abbu cikin mota, gefen driver ta shiga ta sashi ya koma mazauninta, Saida taga yazo dab da motar ta tadata haďe da bata wuta da karfi, tana kallon yadda ya tsaya cike da mamaki ta fito da hannunta waje haďe da yi mishi wani irin sign wanda bai gane ba, tana gama juyar da motar ta leko tayi mishi gwalooo sosai haďe da kaďa kai da ido, Tsintar kanshi yayi da dariya sosai yana faďin "naughty girl, matsalar yan drama kenan, komai sai sun maida shi wasan kwaikwayo, Har ya karasa cikin dakinshi bai bar hango yadda tayi mishi da fuska ba, duk abin da yakeyi in ya tuna sai ya keche da dariya shi kadai........ Mrs Tijjani Shattima..... [09/06 11:14 AM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣9⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *Kaduna garin gwamna...* Share gumin dake tsatstsafo mata akai tayi ta sake gyara zaman jakarta da ke kunshe da dubu uku kachal, samm bata san hawa adaidaita dan kar ta taba kudin da suka rage mata gaba da baya, auna tafiyar tayi taga cikin mintina talatin zai kaita gida... karya wata kwana ke da wuya taji an hankaďeta haďe da fisge jakar da tayi ma kyakykyawan riko, wani irin ihu ta saki haďe da bin yaron da gudu, inaaa gudun ba ďaya ba dan kafin kiftawar ido ta nemi yaron ta rasa, tsayawa tayi a bakin titi tana haki tana kokarin maida hawayen dake neman fitowa daga idonta, hijab din jikinta tasa ta share hawayenta haďe da juyawa zata cigaba da tafiya cike da tunanin halin da zata shiga na rashin kudin da take cancanawa.. "Mummy...., juyowa tayi da sauri dan kamar cikin mafarki ta jiyo muryar, *Ra'eess...* ta furta a hankali wanda ya sanya idonta bijire mata har saida hawaye suka zubo, balle motar yayi suka fito shi da kannenshi suka rungumeta, Uwa uwa ce, koda kuwa magajiya ce ta karuwai,, nan fa Radiya ta fashe da kuka haďe da daga autarta ta kankameta kamar zata maida ita ciki, Kafar Fatima ta hango cikin wani tsadajjen takalmi flat mai matukar kyau wanda ya dace da kafar da tasha jan lalle, dagowa tayi ta kalleta tana takowa cikin doguwar rigar atamfar bubu taji stone work tana nufo inda suke, fuskar nan tayi dau tayi kyau sosai, hannunta rike da ďaya daga cikin yan biyun da ta haifa cikin showel, "Ina wuni Anty, firgigit Radiya tayi dan bata san ta karaso inda take ba, "Lafiya lau.. kawai tace haďe da cigaba da hira da 'yayanta zuciyarta fal kishin Fatima.. "Teemah na zo mu tafi Hussain ya fara kuka, sai a lokacin ta kalli Shamsu dake tsaye jikin motar yayi fresh sosai shima rike da dayan jinjirin, Saurin kauda kanta tayi dan kar ya gano halin da take ciki, "Ammi in nuna ma Mummy, Ra'ees ya tambayi Fatima cike da girmamawa, "Yess my boy, bari in koma mota akwai rana, Anty sai anjima... bin bayanta kananan sukayi suna ďagawa uwarsu hannun... Mummy kingani abokin Abba ne ya bamu kudi da yawa, kina so? kallon motar tayi taga duk sun shige sun ďage tint glass tace "Kawo in boye maka, ina na kannenka?, "yana cikin mota, ya bawa Ammi da yawa itama, in ce ta baki? "A'a barshi, wannan ma boye maka zanyi karka faďa musu, hope kuna karatu ko? Kafin ya bata amsa Shamsu ya danna mishi horn, da gudu ya koma motar yana ďaga mata hannu, ta window suka turo kai suna mata bye bye, Duk yadda taso rike hawayenta yaki rikuwa neman dakali tayi ta zauna taci kuka ma'ishi ta kuma yi dana sani marar iyaka..... Yau ma teba Mummy? Ko kallon inda take bata yi ba karasa kwashe tebar cikin cooler, miyar ganyen da sukayi wacce bata samu arzikin nama ko kifi lando ba ta mayar kan gawayin da ta sauke tebar, na Goggo ta ďauka ta wuce mata dashi ďaki, Tari ta fara yi sosai cike da faďa tace "Wai har yanzu bazaki dawo hanya ba Goggo, kullum Allah na nuna miki abubuwan da kikeyi ba masu kyau bane ya cire hannunshi akanki sai cigaba kikeyi, da tsufanki kullum sai mugun abu kikeyi yana dada dawo mana, kai gaskiya da ana canza uwa da tuni na dade da canzaki wallahi, Ko ni da na faďa cikin wannan jarabawar nasani sarai hakki ne, hakkin Suwaiba da zuri'arta, na dade da mikawa Allah lamarina, nasan wata rana zaizo rescue dina, Maganin Goggo ta kuma zubawa cikin wutar tace "Tun kina karama nake shan bakar wahala dake, badan a gida na haifeki ba da zance daga tsatson Harďejo kika fito su suka canza min ke, in ke sakara ce to ni bazai yiwu in zama sakarai ba, ku uku ne a gidan nan dukkanku sakakku, mazajenku basu ko waiwayarku sannan kice in nemi guri in zauna, bana tunanin zan mutu nan kusa, nasani sai naga mutuwar zuri'ar Atika da tun shigowarta rayuwata ta tagayyara komai nawa... *MUSADDIQ...* jin Raudha tayi ihun sunan gudan jininta da ta shekara har da doriya bata sashi a ido ba yasata fasa bawa Goggo amsar da tayi niyya, da gudu ta fito waje har tana bugewa da kauren ďakin, tana shirin karasowa ta rungumeshi yayi saurin ja baya wanda hakan yayi daidai da shigowar su Baffa da Sheik, Share hawayen da zubo mata tayi ta wuce daki ta dauko hijab, ďakin Anni da ta bari Baffa ya shiga dasu, sam baiyi niyyar shigowa da Sheik gidan ba, dan dai Papy ya matsa ne, Shigowa Mummy tayi da sallama hannunta dauke da tray din pure water, Papy, Papa da Sheik ne kaďai suka amsa sallamarta, da ido Papy yabi Musaddiq yana ta kokarin su haďa ido, kamar ance ya ďago suka haďa ya sakar mishi lafiyayyar harara, Kauda kanshi yayi ya sake tamke fuska ciki ciki yace "Ina wuni, kallon shi kadai tayi ta maida dubanta gurin Sheik wanda tsufa bai hanata ganin Atika cikin fuskarshi ba, "Ateek right? Cike da murna Papy yace "shine, ashe kin sanshi, hawayen daya zubo mata ta share tace "Na fi kowa mu'amala da yayarshi, lokacin inada karancin shekaru dan zan girme mishi da shekara biyu ko uku, kullum sai ta ambaci sunanshi fin sau goma a rana, duk wanda ya santa a cikin yaran gidan Harďejo yasan Ateek, dan labari nashi take bayarwa Maryam din Harďejo ko mai babban suna su dinga yi mana fassara, Kuka sosai ta fashe dashi na tuno ukubar da mahaifiyarta ta bawa Atika wanda bata da bakin faďawa wani.. Share hawaye Papy yayi yana matukar jin kewar rashin ganinta bawai dan ya rasa uwa a gurin Anni ba, shima Sheik kukan ya keyi bayan an fassara mishi abun da tace.... Dakyar Goggo ta iya shigowa dakin, a tsay tsaye ta gaisa dasu ta fita saboda rashin son ganin fuskar Sheik, duk ta kalleshi sai gabanta ya faďi... Hira sosai sukayi da Mummy, Papy da Sheik, Papy yaso Daddy ya shigo yaga sauyin da matarshi tayi, haka nan yaji ya kasa tsanarta duk ko irin abun da akace tayi, bayan fitarta ne ya kewa Musaddiq faďa sosai akan Muhimmancinta duk ko irin laifin da tayi mishi, ko gezau Musaddiq baiyi ba dan zuciyarshi ta kangare sosai bayajin akwai abinda zai sauya shi daga dawo ma mahaifiyarshi yanda yake da... Zubo teban Raudha tayi ta zauna a bakin kofa tana ci saboda tsabar yunwar da takeji, Hilal da ya shigo gidan bayan ya gama order abincin da zasu ci da kuma masaukin da Sheik zai sauka ya kureta da ido, Karyewa Zuciyarshi tayi yaji abun na yawo a cikin jininshi, blood is thicker than water, lallai bature yayi gaskiya, Bai bari ta ganshi ba ya fita ya je wani store dake kusa dasu ya lodo kayan abinci masu yawa har saida kuďin dake hannunshi suka kare, yana zuwa kofar gidan yaga Rilwanu, kiranshi yayi yasashi ya shiga da kayan yace ya faďa musu inji Daddy, Basu bama har Papy saida yayi murna sosai ya kuma sake zage damtsen yin addu'a har sai Allah ya daidaita su, Ita kuwa Goggo cewa tayi hayakin da tayi ne, ta dinga fankama nan da sati zaizo ya maida Mummy dakinta.... Gidan Anni suka yada zango nan suka ci suka sha sannan suka bararraje anata hira har bayan la'asar, Anni hana matan tafiya tayi tace saida mazan su tafi, haka kuwa akayi su Mami suka zauna a gidan suka raba dare suna hira ana fassarawa Anni da ummi.... Kuďi masu yawa Anty Reemah taba Mummy sannan ta je gidan Raliya tayi mata faďa sosai akan rashin taimakama su Mummy, a sannan ne Raliya take faďa mata Daddy ne ya hanata yace in tayi sai ya saba mata, dafe kai Reemah tayi tace "Daddy yayi fushi da yawa, wallahi ko maganar Mummy baya son ayi mishi, "Addu'a kawai zamu cigaba dayi danni ita kadai ke bani tausayi ba su Anty ba, dey deserve it... Raliya ta faďi rai a bace... sun dade suna hira suna nemawa mahaifiyarsu mafita.... Kwanansu Sheik Uku suka shirya komawa gida da yan uwa dan suje suga inda yake, kyautar ban girma yayi ma su Mummy wacce zata mantar dasu talauci na wucin gadi, tayi murna sosai da wannan kyauta dan saida tayi kamar zata mishi sujjada, har suka tafi baisan cewa Mummy matar Daddy bace, ya dauka kawai a gidan take zaune, ya dai san yayar su Papy ce.... *Cyprus...* Da yake mansion din Sheik yana da matukar girma hakan yasa ya kwashe dukkansu, harda Husna da suka taho da ita dan ta haihu, dadin duniya babu wanda bai jiyar dasu ba, duk companies dinshi saida ya nuna musu harda na wasu kasashen, Saboda murna ya cire wani babban companynshi dake Holland ya mallakawa Papy a matsayin gadon mahaifiyarshi, sannan ya bawa Hafeez wani abun shima, gaba ďaya ya kasa controlling kanshi akan zuri'ar yayarshi.... Kwanansu biyar a garin akayi ma Husna tiyata aka ciro mata baby girl saboda haihuwar tazo da Matsala, lokacin su Daddy sun koma Nigeria, murna a gurinsu ba'a magana saboda dama cikin na yawan bata wahala, Papy da kanshi ya shiryawa Mummy tafiya dan taje gurin yarta taga jikarta, Ita dai a kullum haushin kanta takeji na biyewa zuciya tayi wa Suwaiba abubuwa marasa dadi kafin mutuwarta, gashi yanzu danshin su take raba taji dadi, lallai da ta hana auren Hafeez da Husna da sai takaici ya kusa ajalinta, kullum bata da addu'ar da ta wuce Allah ya dawo da Nadeeya cikin koshin lafiya dan danta ya samu farin cikin rayuwa, a yanzu ko ita bata samu farin ciki ba 'yayanta su samu, ta fahimci farin cikinsu shine nata, ďan zaman da tayi da su Radiya ta fahimci cewa ba kowani ďa bane ke sadaukar da farin cikin sa akan iyayenshi, a nan ta koyi basu farin ciki, in ta gansu cikinsa tasan itama zata kasance a ciki... Ranar Suna Daddy ya sanya wa yar suna Suwaiba, sosai dangi suka nunawa yar gata dan ta samu kaya na gani na faďa, Mummy ta sake tsorata da ikon Allah da tazo taga daular duniyar da dangin Atika ke ciki, inama Suwaiba na raye tazo ta dandani arziki, wayyo, ita nata dadin a lahira ta ďeboshi..... Na fa lura da wani abu Anty, Raliya ta faďi tana sanyawa Nour ďiyar Husna pampers, "Me fa? Anty Reemah ta tambaya haďe da gyara zama, "Na kusa yin siriki, Raliya ta faďi tana murmushi.. "Wa kenan?? "Dadina dake ganewa Anty Raly, Husna ta faďi tana ajiye kofin shayi, ni ai tun tuni na sani, Jamal ya hanani faďi, "Kaii nifa ban gane ba, wai me kuke nufi? Anty Reemah ta tambaya cike da mamaki, "Y'ata ta wajenki tayi kasuwa, soyayya sukeyi da Jamal, Mikewa Anty Reemah tayi tace "to ai ba sai kun faďa min ba, kuma iyaye ne, in akwai alheri Allah ya tabbatar... Dariya sukayi haďe da tafawa suka ce Ameen Ameen, ashe zamu sha biki... Hinad da ta doso dakin ta juya da sauri ta nufi waje cike da murna, tasan tunda Anty Raly tasa baki Allah ya kusa cika mata burinta, soyayyar Jamal ta zame mata tamkar jini da hanta, bata jin akwai abin da zai cire mata sonshi cikin ranta, kamar shima yadda Jamal din keji game da ita saboda kyawawan dabi'unta, zuwanshi kasar yasake sanya shakuwa mai karfi a tsakaninsu, wacce har ta sa aka fara diga ayar tambaya akansu..... Zaune suke a katafaren parlon sama suna duba ayyukan da gwamnati tayi approving, Zanen da Hilal yayi wannan karan na musamman ne, cike da yabawa sheik ya kalli zanen karshe yace "Bravoo alaika ya Hilal, Allah ya albarkaci hannunka, yanzu kaga sai dai kawai mu fidda kudi a hau aiki, Murmushi Hilal yayi zaiyi magana Irfan ya faďo parlon babu ko sallama, kusa da Sheik yaje ya zauna haďe da faďin "Masa'ul khair Aby, kallonshi yayi sama da kasa yace "uhummm, kudin naka sun kare kenan, sosa keya yayi yana hararar Hilal yace "Eh, akwai wani business da nasa kudi na, inaso inyi clearing ne bani da cikon kudin, 20mill ne kawai, "I struggle to get 5 thousands aday nd u are calling 20mil only, it's well dear, zanyi maka addu'a Allah ya baka, Lokacin da na kiraka ina farin cikin ganin yan uwana kaima kazo su ganka kazo? Kayi ignoring dina so yanzu ni bani da abun yi maka, yana kaiwa nan ya kalli Hilal yace "My dear gobe ka sameni a office sai mu fara shirye shirye ko? Cike da girmamawa Hilal yace "Okay sir, Allah ya kaimu... A tare suka mike Sheik ya raka Hilal har kasa sannan ya wuce dakin da Husna take dan duba lafiyarsu... Rike gaban rigarshi yayi saboda jin shakun da akayi mishi ta baya, yana da tabbacin Irfan ne dan irin kamshin turarenshi ne ya cika gurin, ganin yana daďa tamke shakan yasa Hilal yanka rigarshi ta gaba saboda ta kama wuyanshi sosai, iya karfinshi ya sanya ya cire hannun Irfan haďe da hankaďa shi baya. Taba wuyanshi yayi yana tari kaďan, saurin rike hannunshi yayi dan kare kanshi murya a kausashe yace "Wai menene? Fisge hannun Irfan yayi ya nuna shi da yatsa.. warning mai karfi ya karta mishi na kar ya sake taka kafarshi cikin gidannan in ba haka ba wallahi sai yayi ajalinsa, Dariya Hilal yayi yana gyara singlet dinshi zaiyi magana yaji muryar Maleekah a bayanshi, "Hey akan ka yake? In yazo gidan nan gurinka yazo? Kayi aikin gabanka ka bar kowa yayi nashi tunda gidan ba naka bane kai kaďai! Cikin zafin nama ya shako wuyanta dama yana da cikinta na yadda yake ganin an barta tana facaka da kuďi ba tare da an sa mata ido ba, sakin keyn motarta tayi saboda azaba tasa hannu tana kakari, Hannu Hilal yasa ya banbareshi a jikinta haďe da shake mishi nashi wuyan da karfi, naushi mai karfi Irfan ya sakarwa Hilal a ciki da gwiwar hannunshi, da sauri ya sakeshi ya durkushe rike da cikin saboda azaba, gaba daya jikinshi ya dau rawa dan jin ciwon yake har tsakiyar kanshi, ihuu Maleekah ta saki tayo kanshi ta hankaďe Irfan dake kara tattaka cikin Hilal, girman gidan baisa kowa yaji ihun ba sai maigadi, lokacin da ya iso har Hilal ya gama fita hayyacinshi, cikin kuka tace ma mai gadin ya kira Abbu, a ruďe ya nufi cikin gidan, a parlon kasa ya samu Abbu ya fito daga ďakin da Husna take, yana ganinshi yasan ba lafiya, Nufar gurinshi yayi a tsorace yana tambayarshi abun da ya faru, bai jira ya gama faďa mishi ba ya fita tsakar gidan da sauri, daga can gate ya hango motar Irfan sai horn yakeyi yana shirin fita, inda yake jiyo kukan Maleekah ya nufa, ganin Hilal a kwance yasashi yin gudu gudu dan ganin abinda ke faruwa, cikin kuka Maleekah tace "Abbu Hilal zai mutu, plss help him, daukarshi Sheik yayi cikin tashin hankali yana tambayarta abinda ya faru, bata iya bashi amsa ba ta bude mishi motarta ya sa Hilal a ciki shima ya shiga, rufe motar tayi ta shiga mazaunin driver ta figeta da gudun gaske... Asibiti mafi kusa suka je, lokacin da suka isa Hilal na fitar da numfashi dakyar, Saboda gigita Sheik baisan takalmin kafarshi ya fita ba, suna shigar dashi nurses suka shigar dashi emergency, da sauri likita ya iso gurinshi da taimakon gaggawa, Allurar pain relief sukayi mishi kafin su gano abun da ya sameshi... Rungumeta yayi a jikinshi yana rarrashinta, labarin abinda ya faru take bashi cikin kuka tana zagin Irfan, Cike da tashin hankali ya zaro wayarshi ya latsa number Irfan, a kashe yaji ta yayi kwafa haďe da saka abubuwan da zai mishi in Hilal yaji sauki.... Allah ya taimaka babu abin da ya samu Hilal, zafin buguwar ce ta sanyashi fita hayyacinshi, Hamdalah Sheik yayi suka nufi ciki gurin Hilal, bacci suka sameshi yana yi hankali kwance, Zama kusa dashi Maleekah tayi ta kama hannunshi tana murzawa a hankali, sai a lokacin sukayi tunanin kiran su Papa faďa musu.... Hakuri sosai sheik ya bawa su Papa ya kuma yi musu alkawarin hukunta Irfan hukunci mai tsanani, "Ah haba, yarinta ne, dan Allah ka kyaleshi, wata rana bazai yi ba, Allah ya rubuta sai yayi ciwo, Irfan sanadi ne kawai, mu dai cigaba da addu'a Allah ya shirya mana su, Papa ya karashe fuskarshi dauke da murmushi... Jin shi kawai sheik yayi dan ya riga ya kuduri niyyar hukunta Irfan, yadda yake jin Hilal a cikin ranshi baya san wani abun da zai taba shi....... Karfe uku na dare Hilal ya farka daga baccin da ya samu, Hinad dake zaune a gefenshi ta sakar mishi murmushi haďe da kamo hannunshi, "Sannu Yaya, ya jikinka, gyada kanshi yayi ya kalli Anty Reemah dake kokarin ďagashi zaune, Karfi yayi da jikinshi dan kar ta wahala ya mike zaune haďe da jingina da pillow, "Me zaka ci in kawo maka? "Bana jin yunwa Mum, ya bata amsa yana yamutsa fuska, "Ai ba dan yunwa zaka sha ba, haďa mishi tea, papa ya faďi yana miko mata flask... Tea mai kauri ta haďa ta mika mishi ya fara sipping a hankali, Buďe kofar su Sheik sukayi, hannun Maleekah rike da wata leda, "Alhamdulillah, Sheik ya faďi yana nufar inda Hilal yake, "Are u okk My son? Murmushi Hilal yayi yace "yess sir, karka damu, da kun tafi gida dare yayi... "Nooo dole mu zauna muga yanayin jikinka, kayi hakuri Hilal, in shaa Allah sai na dau mataki akan Irf--- Plss sir, Hilal ya katseshi haďe da rike hannunshi "wallahi na yafe duniya da lahira, kaddara ce, tana kan kowa, haushina yake ji yanzu, with time komai zai zama normal.. Cike da so da kauna Sheik ya dinga yi ma Hilal godiya da fatan samun lafiya dawwamamma... Kofin dake hannunshi yake kokarin ajiyewa saboda yadda Maleekah ta kureshi da ido, kallon Anty Reemah yayi yace "Kuje gida i will be fine here, karku damu, ina zee dina? "Tana gidan Mimi Turaki, can na sauketa dan kar ta haukace mana, Meerah ma sai kira takeyi kasan dazu ta tafi Malaysia.. Anty Reemah ta bashi amsa tana gyara zaman hijab dinta.. "Yess ta faďa min, Allah ya maidota lafiya, plss kuje gida, Maida dubanshi gurin Sheik yayi shima ya rokeshi da su tafi kar su matsawa kansu, haka duk suka shirya tafiya dan sunga lafiya ta samu a gareshi... Chips da chicken salad Maleekah ta buďe ta ajiye a gabanshi ba tare da tace komai ba, bin bayan Sheik tayi dan tasa shi ya jirata, tana ganin motar su Anty Reemah ta bacewa ganinta ta fito cikin motar tace mishi tana zuwa, da yake su larabawa babu ruwansu da bin diddigin 'yayansu in suka yarda dasu sai ya kwantar da sit cikin rashin damuwa ya lumshe idonshi.... A rufe ta samu chips din ta sake budeshi har lokacin da zafinshi, gefen gadon da yake zaune ta zauna ta buďe tana kallonshi, ita yadda yake rufe ido ma dariya yake bata, shi a dole bai san haďa ido da ita, "Ya Hilal, ta faďi a saitin kunnenshi, da sauri ya buďe idonshi dan muryar Nadeeyah yaji, bashi da dabarar dauke idonshi cikin nata domin kallon da yake mata na daban ne, yadda ruwa ya kwanta a cikin idanun suka sake kayata kyawun idanun su suka tsuma Maleekah ta ajiye chips din ta kamo hannunshi, wannan wace irin masifa ce, a yanzu gaba daya zuciyarta da gangar jikinta sun gama na'am da cewar tana son Hilal kuma tana son karasa rayuwarta tare dashi, " *I LOVE YOU* cikin narkakkiyar murya kalmar ta fito ba tare da shiri ba, Runtse idonshi yayi hawayen dake kwance cikin idanuwanshi suka bayyana kan yalwataccen gashin idonshi.. zuciyoyinshi ne suka shiga kara kainin bashi shawara, wannan tace "Allah ne ya dawo maka da Nadeeyah ta wata siga, wannan yace "Duk wanda yaso Nadeeyah to ko bazai ki Maleekah ba, haka nan sukayi ta rikirkitashi... Bai ankara ba yaji kwanciyar fuskarta kan tafukan hannunshi, hawayen da ya ďigo a kansu shi ya sanyashi buďe ido da sauri haďe da ďago fuskarta, Share mata hawayen ya shiga yi zaiyi magana tayi saurin shigewa cikin jikinshi, "Plss don't say a word Hilal, plss.... daureshi tayi da jijiyoyinshi kamar tasan abinda yake shirin faďa, har ga Allah baya kin Maleekah domin wani sashi na zuciyarshi yayi na'am da ita, saidai sashin da ya mutu da wata soyayyar daban yaki aminta ya farfaďo, baya tunanin har ya mutu zai iya son wata 'ya Mace kamar yadda yaso Nadeeyah, ya zame mishi dole ya amincewa Maleekah domin ya daina jin abinda a kullum yake yunkurin mantawa dashi, Hawayen dake cikin idonshi ya ďigo a kan fuskarta yace "I love you too Maleekah...... Mrs Tijjani Shattimah..... [09/06 11:14 AM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣0⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Eidukum mubaarak wa aiyyamakum Sa'eedah taqabbalallaahu minnaa wa minkum,wa kullu aamin wa antum bi khair. Eid-el Fitr Mubarak. Allah ya maimaita mana Ameen..... Sake kankameshi tayi cike da jindadi tace "nt too, i want u to love mee more nd more, Murmushi yayi haďe da dago fuskarta yace "Will u teach me how to love u more more more? Hannayenta ta makalkale a wuyanshi  tace "we will love each oda more than life itself, ďaura kanshi yayi kan goshinta yace "Dare yayi, go home hoping to see yhu first thing in the morning.. narke mishi tayi tace "Yaci abinci ko itama taki ci in ta koma gida, hannu yasa ya ďauko chips din yace suci tare.. gyara zama tayi a kan gadon ya dinga bata a baki itama tana bashi, duk wani nauyin da Hilal yake ji a cikin zuciyarshi ya ragu, jinshi yakeyi kamar sabon mutum... Saida suka gama ci sannan tayi mishi sallama haďe yi mishi alkawarin zuwa da sassafe..... Cikin wata ďaya soyayya mai karfi ta shiga tsakanin Maleekah da Hilal, tun yana jin sonta kaďan kaďan har Allah ya jarbceshi da muguwar soyayyarta, domin ita ďin gwana ce gurin sace zuciya, Wannan soyayyar da sukeyi Sheik jinta yake duniya Allah ya gama mishi komai da ya bawa yarshi mutum irin Hilal, jira kawai yake yaji ta bakinsu ya shirya komai cikin kankanin lokaci dan bazaiso yajashi ba saboda masu kawo mata hari kar su hure mata kunne, shi ko yanzu ne yake jin dadi saboda zai samu surukin da zai iya barwa ragamar dukiyarshi ba tare da tunanin komai ba, Su Papa kuwa gani sukayi tafi karfinshi saboda Sheik ba karamin mutum bane, sai da Sheik ya nuna musu bacin ranshi sosai saboda banbanta kansu dashi da sukeyi.... A ranar da Maleekah taje mishi da maganar yayi matukar farin ciki, nan take ya kira Daddy da Papy ya sanar dasu sannan yace basai kowa yazo neman aure ba domin Hilal nashi ne, sati biyu ya sanya bikin saboda bashi da wani shirin da yake dashi, jin haka Jamal ya sanar da Papy wacce yake so domin a haďe auren gaba ďaya, Farin ciki a gurin Anty Reemah ba'a cewa komai domin Allah ya gama mata komai, ta samu nagartattun surukai wadanda zatayi alfahari dasu... *(wannan shine result of kyakykyawar zuciya)* ******** Tun ana saura sati ďaya biki Maleekah da kawayenta suka fara shagalin biki, abinka da yar drama, babu inda labarin aurenta bai zaga ba, daga mai kushe Hilal saboda bai kamo kafar samarinta a haďuwa ba, sai mai yabawa zarrarshi na samun Maleeka da maza kewa rububi, babu wanda yasan abinda Allah ya ganar dasu ya sanyasu suke kaunar junansu sai su biyun da kuma wanda yasan waye *Hilal Kangiwa....* ******* "Ya kira wayarta yafi a kirga bata ďaga ba, tun yana kira cikin marmari har ranshi ya baci ya ajiye wayar a gefe, duk yaji ringing sai ya dauka itace yayi saurin daukar wayar, in yaga ba ita bace sai ya ajiye wayar ya saki tsaki, rabon da ya sata a idonshi tun shekaranjiya da suka tafi Egypt yin wani bikin a can.. bai san fushi takeyi na kin binta da yayi, taso su tafi bikin tare yaki, dan ya fi son yayi zamanshi yayi hidimarshi cikin yan uwanshi... Karfe Sha ďaya ya kira layinta na Egypt yaji shi a kashe, hakan ya tabbatar mishi da yanzu ta shigo tunda jibi ne daurin auren, Shiryawa yayi cikin kananan kayan sanyi masu taushin gaske, yana matukar missing dinta dan ta koyar dashi soyayyarta mai sanyi, gashi bai iya soyayya ba dan in yana yinta gaba daya zuciyarshi yake sallamarwa wanda yake so... Saida ya biya ta wani gift shop ya siyo mata wani abu dan yaji dadin bata hakuri... A kofar gida ya sameta tare da kawayenta tana musu sallama, cikin shigar da yake matukar so ya sameta, jallabiya har kasa da gyalenta, Cikin gidan ya shigar da motarshi ya fito ya tsaya haďe da harďe hannu yana jiran dawowarta, Minti biyu kaďai ta kara tazo tana shirin wucewa ciki, kallo ya bita dashi har ta kusa yi mishi nisa, "A wife is angry wit her Hubbi!!, ya faďi cikin wata irin muryar da baisan yana da ita ba, Duk da taji sanyin jin muryarshi da kuma sunan da ya kirata dashi hakan bai sa ta tsaya ba, “Getting angry doesn’t solve problems, "Ana Aseef  “ya Radhi’a” plss don't be mad at me...  Ajiyar zuciya tayi haďe da tsayawa zuciyarta na maimaita kalmar *Radhi'a* duk wani bacin rai da ta kunsa na tunanin Hilal baya sonta kamar yadda take sonshi ta kaudashi, Sanyin dake kadawa a garin ya haďu da wanda ke kaďuwa cikin zuciyarta ya sanyata cikin wani irin yanayin da takeji tamkar su biyu kadai Allah ya halitta a duniya, "plss my love, ya faďi cikin raďa a saitin kunnenta, Lumshe idanuwansu sukayi a tare saboda qamshin da kowannensu ya shaka na juna, a hankali ta juyo ta fuskance shi haďe da shagwabe fuska, yadda ta turo baki yasan magana ce zata biyo baya, Cikin sauri ya fiddo wata red flower dake makale a bayan wandonshi, Saitin hancinta ya sata haďe da furta mata wasu rikitattun kalmomin da baisan ranar da ya iya su ba, Shidai yasan ya horu matuka da rashin jin muryar dake kwantar mishi da hankali, sannan idanuwanshi sunyi matukar kewarta, tayi matukar sabar mishi da kaunarta mai sanyin dadi, a halin da yake ciki yanzu baya jin zai iya koda yini ne ba tare da ganinta ba, "Ikon Allah kenan, shi yakan sanya so a lokacin da yaso, Ko a cikin mafarkinshi bai taba tunanin zai iya samarwa wata mace gurbi a zuciyarshi ba, bayan wacce ya kira da mamallakiyar Qalbinshi, *Zuciyar gaba daya*.. Sai gashi cikin kankanin lokaci soyayyar Maleekah na neman shafe babin dake adane da boyayyar soyayyar da tun yarinta yake dakonta, Wasu lokutan in ya zauna yana tunani sai ya alakanta abun da cewar saboda ita din jinin Nadeeyah ce, sai yanzu ne da ta hora shi na ďan kwanaki ya tabbatar wa kanshi irin kaunar da yake mata... "Fushin masoya hutu, cikin kankanin lokaci Maleekah ta manta komai ta saki jiki suka sha soyayyarsu wacce armashinta yafi na baya saboda amintar dukkan zuciyoyin biyu.. Sai da dare ya tsala sosai sannan Hilal ya rakata har cikin parlo ya juya ya tafi cike da kewarta.... Maleekah is very nice, halayyarta da kyakykyawar zuciya irin ta Mahaifinta shi ya kara mata matsayi a zuciyar Hilal... Har ya kai gida bai bar tunaninta ba, koda yayi parking mota saida ya dan jima cikin motar sannan ya fito fuskar nan cike da annashuwa, ta steps yabi zuwa sama, duk inda yazo wucewa sai an mishi congrat harda masu bashi gift din aure, "Al'adar larabawa da yan Nigerian dake cikin estate din kenan, musulmi da arne in abun farin ciki ko bakin ciki ya sameka to fa tare za'a raba jajen da farin cikin, wayewarsu tasa suka dauki juna tamkar jini ďaya... Yana karasawa kofar flat dinsu ya soma jiyo hira da shewa cikin parlon kasa, hakan ne ya bashi tabbacin yan uwa sunzo, farin cikin da yake ciki ya mantar dashi miskilin halinshi, nan ya murda kofar da sauri yagansu cike da parlon yan kangiwa da su Mummy, Cike da farin ciki ya karaso ya dauki Fadeel ya jefa shi sama, Sannunku da zuwa, kun sha hanya, gefen da Goggo ke zaune tana karkaďa kafa ya kalla yace "Harda su Goggo, Lallai yau muna da manyan baki, bata kalli inda yake ba ta cigaba da kaďa kafa tana sakucen hakori, "Tunda ta shigo gidan taga hoton Maleekah shikenan farin cikin da ta guntso ya tafi, da fari ta fara masifa akan duk matan duniya ya rasa wacce zai auro sai mai zubin karuwai, saida Mummy tayi tsaye akanta sannan ta maida hankalinta ta zauna a gefe tana cika tana batsewa.. "Ina Anty Rally, ya tambaya yana duban mahaifiyarshi, "Suna sama da su Raudha, wani aiki suke ma Hinad, Musaddiq na ďaki tun dazu yake jiranka, Hanyar saman ya nufa da sauri cike da farin ciki, yasan zaman su Mummy a parlon ne ya hanashi zama ayi hira dashi... "Hey Mr Soft, kana ina ne?  Kafin Musaddiq ya bashi amsa ya karaso balcony din inda Musaddiq ke tsaye yana duban sararin samaniya, Jingina yayi jikin karfen yanda zasu fuskanci juna, "how r u Kyari? Gyaďa kai Musaddiq yayi fuskarshi dauke da Murmushin da yafi kama da na ciwo, ganin Hilal ne ya sanya zuciyarshi karyewa har murmushin ya fito, A ko da yaushe in ya kasance shi kaďai yana jin sam rayuwarshi bata da amfani, Ya kasa daukar hakurin mantawa da ita, ita din mace ce da take da wuyar mantawa, rayuwa yinta kawai saboda mahaifinshi da kuma Hilal, amma yasan tabbas zuciyarshi na gab da bugawa dan ya kasa yin rayuwa mai dadi babu ita... Gyara tsayuwa Hilal yayi cike da damuwar yanayin da yake mishi ciwo a duk lokacin da suka haďu da Musaddiq, kafaďunshi ya dafa can cikin zuciyarshi yace "Nasan yadda kake ji, naji makamancin hakan, saidai nawa mai sauki ne dan nesa nesa nayi da ita, shakuwar mu bata kai ta ma'auratan da sukayi wa juna dandani haukaci ba... Amma a fili zancen Maleekah yayi mishi dan ya mantar dashi damuwa, labarinta ya dinga bashi ya kuma bashi labarin irin karamcin mahaifinta, "Inaa kayan mu, zamu kafa tarihi, dan nasan sai munyi faďa da Maleekah akan kayan da zan sa, dazu take faďa min tayi ordern kayan da zamu sa, muje inga yanayin dinki... Dakin suka koma Musaddiq na yaba tsarin dinkin da akayi musu,   Hilal yayi matukar farin cikin ganin kayan dan daga shaddar har dinki sunci kudinsu, ga wasu huluna masu matukar kyau kalar aikin kayan, baje kayan sukayi suka cigaba da hira cike da debewa juna kewa..... A katafaren masallacin gidan sheik aka daura auren, farin cikin da wannan zuri'a take ciki a wannan ranar ba mai misaltuwa bane, musamman Papa da Anty Reemah wacce saida tayi kukan farin ciki, 'yayanta Allah ya aurar mata dasu rana ďaya kuma cikin irin wannan zuri'a, ita kuwa me zata cema Allah banda godiya, yanzu Zainab ce kaďai a gabanta wacce take da burin faranta mata ta jiyar da ita dadin duniya.... Biki ne akayi shi mai kayatarwa dan an ci an sha kamar baza'a mutu ba, sai kusan uku suka shirya tafiya reception, yadda Hilal yayi zaton Maleekah sai ta bashi mamaki dan itama wani lace tasa wanda Anty Reemah tasa aka dinko mata, riga da skirt ne Ash yasha duwatsu, sunyi matukar kyau, hakan da sukayi yazo da sabon salo, hotunansu suka dinga yawo a kafafen sadarwa na kasa da duniya baki ďaya, wanda ma basu taba tunani ba yaga hoton, domin babu inda hotunansu bai zaga ba, Balarabiya da bahaushe cikin shiga ta hausawa, A wannan daren boyayyen ruhi na nesa yayi kukan farin ciki da kuma na kewar makusanta, hoton zamewa yayi tamkar wani kwai domin ya sanya ma'abocin kallonshi cikin shaukin son kasancewa da yan uwa.......... *6 years later* *Cambridge Montessori Elementary School.* The final round is here, *Expression words* we have only three players left, 1 *Naurah Josephine* 2 *Mukhtar Hilal M Kyari* 3 *Victoria vertran* Nan fa filin ya sake barkewa da ihu, kowa na kiran sunan dan uwanshi.... Naurah ce farko, tayi matukar kokarinta sai a wasu guraren ta kakare, Sai Mukhtar, kafin ya fara saida ya kalli inda wani mai irin kayanshi yake, kyakyawan mutum wanda hutu ya ratsa shi sosai, Nuni yayi mishi da addu'a da hannu sannan ya sumbaci hannun ya hura mishi iska, Lumshe ido Junior yayi ya rungume hannunshi haďe da jero adduoin da ya iya wanda ake koyar dashi a gida duk dare, *Suratul nasr* ya karanta karshe dan ya riga ya saba duk in zai zauna a aji sai ya karanta ta, Bayan gaisuwar da ya gabatar cikin kwarewa sannan ya rufe da godiya haďe da kambama makarantarsu, sannan ya rufe da wata siga ta marasa jin magana haďe da buga kwallon da ta gangaro gurin kafarshi, bayan ya gama ya rufe da wata godiyar ya jero sunayenshi kamar haka.. Yours most lovely one *HABIBI MUKHTAR HILAL MUSADDIQ KYARI* A.K.A *MHK TAHEER*..... ya karashe yana juya rigarshi baya dan kowa ga sunan karshe, Da sauri Taheer ya iso inda yake ya dagashi sama, duk wanda ya gansu yasan uba da ďa ne saboda ba kaya ba hatta glass din su irin daya ne....... tafin hannu da ihu kadai ke tashi a gurin..... Nan dayan yaron yazo ya gabatar da nashi shima, bayan sun gama aka basu kyaututtuka sosai dukkansu su ukun, kowa cikinsu cikin farin ciki yake domin anyi making day dinsu...... yara na san irin ranar nan musamman a makaranta...... ***** *Queens University, Faculty of Law Ontario* Yan mata ne biyu a tsaye cikin shiga mafi kyau da tsari wacce sai mai tsananin kamun kai ke yinta cikin university din.. Farar ciki sosai sanye take da koriyar riga wacce takai mata har kasa, kasan rigar ta baya a tsage yake saboda ta dan tsuke, jan sandals din kafarta mai tsini sosai ya kara mata tsayi wanda ya sake kayata dirin jikinta da hutu ya ratsa ko ina, daga sama kuma ta yane kanta da jan mayafi ďan karami wanda ya fitar da kwantaccen gashinta har gadon baya, gucci glass din dake makale a kan fuskarta shi ya sake fitar da natural kyan fuskarta wanda sam babu kwalliya a kanta, gyara rigar Barristers din dake hannunta tayi ta duba bakin agogon hannunta, Budurwar dake tsaye a gefenta wacce itama irin shigarta ce saidai colour da ya banbanta sannan ita babu rigar a hannunta tace "It's late, Aman is useless wallahi, batayi magana ba sai juyar da kanta gefe da tayi domin hango M.I Saleem da tayi, Muje Amal, mu koma office, dariya Amal tayi tace "Kinsan dai ko office din VC kika je sai ya biki, gara kawai ki tsaya, tsaki taja haďe da sake kiran Aman a karo na babu adadi, jin wayar ta shiga ya sata murna ta fara tafiyarta mai daukar hankali, "Haba Uncle Aman, ya zakayi mana haka? Mik'a yayi haďe da hamma cikin muryar bacci yace "Anty Mamma wallahi bacci nakeyi ma, banajin dadi, Uncle T ya tafi dauko Junior yace in bari zai biyo ya daukeku.. "Subhallah, sorry Uncle, kasha magani? "Eh shiyasa ma na samu na kwanta, ya faďi yana mikewa.. "Allah ya baka lafiya, ta mayar mishi cikin tausawa "Ameen sai kun dawo!!!.. Assalam Nadeeyah.. "Wa alaika salam M.I ya kake? Gyara tsayuwa yayi cike da jin dadi yace "Lafiya kalau, yanzu nabar office din director, vector yace min kina waje, Fisabilillah kin kyauta kenan, wayarki sam bata shiga, gashi bansan inda kuke ba, jiya na dawo daga Nigeria, "Ayya sorry Muhammad Ishaq, wayar ta ce ta lalece, ya ka baro Nigeria? Amal ta tambayeshi tana karasowa gurin... Lfy kalau Amal, amma da sai ta kirani, kin san yadda na damu kuwa, dakyar na iya kaiwa wannan lokacin, na kusa mutuwa fa, "Thank Goodness baka mutu ba, Nadeeyah ta faďi tana dariya, kuma gashi har wata yar kiba kayi Barr.. M.I, "kasan na-------   karar wusir din da ta ji ne ya katseta, da sauri ta waigo ta kai idonta gurin, tsaye ta hangoshi ta saman motar kanshi dauke da hular sport, farin glashin da ya mayarda tamkar dashi aka haifeshi yana makale a idonshi, Shekarunshi bakwai da doriya amma saboda girman jiki zaka rantse ya shekara tara zuwa goma, bakar chocolate fatarshi da a kullum in ana mishi wanka yake magiyar a wanke mishi ita saboda dukkan wadanda yake kewaye dasu farare ne tass sai kyalli takeyi saboda ranar da suka kwaso, Motar na tsayawa dab dasu ya kara sautin wusir din, *Anty Mammaa* *Your MHK will always win, we won Mamma*, Da sauri ta fara sakkowa daga matakalar dake kofar faculty din ta nufi inda suke, kafin ta karaso ya bude motar haďe da dakko wani cup da aka bashi a school ya nufeta da gudu ya dane jikinta, baya tayi zasu faďi saboda tsabar nauyin da yayi mata, rikeshi tayi da karfi dan kar su faďi tare tace "Kasan fa ka fini nauyi, kana son ka kai Mamma kasa ne? Sauka yayi da sauri yana dariya, "kinga award cup dina, sauran gifts dina cikin motar Daddy, Sai a lokacin ta kalli motar, haďa ido sukayi tayi saurin saukar da idonta kasa, sport wear ne a jikinshi shima irin na jikin Junior, babu wanda zai musa cewa ba mahaifinshi bane, saboda komai nasu iri daya ne, glass din idon ma kadai ya isa baka shedar duk tare suke ciwon, in ba su da suka sani ba kowa ya dauka medicated ke idon junior, basu san tsabar fitinar sai yayi abin da Taheer yayi bane, sai kuma  kamanni da ya banbanta su, duk wanda yasan Musaddiq in yaga Junior yasan ďanshi ne domin babu abinda ya rabasu, zuciyarsu ce kaďai ta banbanta, Junior Allah yayi mishi zafi sabanin Musaddiq da yafi ruwa sanyi... "Nadeeyah zan wuce anata kirana, bani phone number din zamuyi waya, Ba Nadeeyah kaďai ba har Amal dake tsaye rike da cup din Junior saida hantar cikinta ta kaďa, a tare suka kalli gurin da Taheer ke tsaye yana kaďa mukullin mota, Cikin sauri Amal tace "M.I bata da waya, bari in baka tawa in ta s------ "Amal... Taheer ya katseta cikin kausassar murya, haďiye miyan da ya taru a bakinta tayi ta nufo inda yake, lokacin Nadeeyah har tayi ma kanta mazauni a baya, "9100619" wayar Mamma na bata lalace ba, Anty Amal wasa take maka, Junior ya faďi da karfi yana kallon M.i dake tsaye galala, Turashi cikin motar Amal tayi ta zagaya baya ta zauna kusa da Nadeeyah.... Karasawa gurin da M.i ke tsaye Taheer yayi, duk cikinsu babu wanda yaji abinda yace mishi, har Junior dake ta kokarin buďe kofa suna hanashi, ga mamakinsu sai hango Taheer da Muhammad sukayi suna dariya haďe da tafawa, sunfi minti biyar a tsaye sannan sukayi sallama..... Daddy kaga Mamma ta dukeni a kai na ko?, cikin harcen hausa ya faďi wacce bai iyata sosai ba, tada motar Taheer yayi yace "Sorry big boy, Mamma tayi sabon aboki, yanzu batayi damu, karka damu kaji kai ma zan nema maka new Mamma, wacce bazata dukar min kai ba... Mikewa Junior yayi ya hau kan kujerar ya tura kanshi baya, Gwalo yayi ma Nadeeyah yace "New Mamma is coming, ba ruwan mu dake, Daddy harda Anty Amal ko? Itama ta ja min hannu, "Rabu da ita sweetheart munafuka ce, ita Aman ne zaiyi mana maganinta, "Allah uncle ba ruwana, ta faďi a shagwabe tana turo baki, "Laa Daddy ta turo maka baki, "Rama min Juju! Ya faďi yana gimtse dariyarshi, yanayin da ya hango fuskar Nadeeyah yasan tabbas hankalinta a tashe yake, wani irin shauki yake ciki tunda yaji kalaman M.i akanta, yasan tabbas bata da lokacin kula wasu dan da tana yi bazata fito da sakamako mai kyau a makaranta ba, "Aaaaaaaaaaaa.... Burki ya taka da karfi saboda ihun da junior ya saki, "Subhanallah lafy?, Amal da ta rufe idonta tana baccin karya ya nuna da yatsunshi... "Ya salam, Amaaaal... "Na'am Uncle ta faďi tana mutstsika ido, "har mun kawo gida ne? Dariya mara shiri Taheer ya saki yace "Wallahi zan bata miki rai, zaki sauka ki karasa gida a kafa dan jakarki ma kwace ta zanyi, "Kawai kace in muku bankwana dan ko nan da pizza hut bazan iya zuwa a kafa ba, saidai gawa ta, Tsaki yayi ya tada motar haďe da nutsar da junior a gaba ta hanya siya mishi candy ice cream.., babu wanda ya sake magana a motar sai zuciyoyi dake ta zance isu isu....... Ayi hakuri baifi 5 pages suka rage ba in shaa Allah...... Masu faďin maganganu san ransu karku damu, in shaa Allah  tafiyarmu ta kusa karewa, dan Allah kuyi hakuri maganganunku na sanya gwiwata karyewa, suna sanya typing fita a raina, ku kara hakuri... in sauri kuke so bazan yi shi yadda nakeso ba thou wasu guraren takaita su nayi, Nagode sosai..... Mrs Tijjani Shattima........ [10/06 9:33 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣6⃣ By *Aysha Ya'u kurah* *A square Turkey constructing company*.... Ya rasulullah... dattijon ya faďi haďe da dafe kanshi, coffee din dake gabanshi ya ture gefe yana mai sake duba cikin system dinsa, ya dade bai duba ayyukan gidajen shi ba saboda yadda ya yarda da ingancin masu yi mishi aiki musamman mai mishi zane da engineern dake tsaye gurin ganin an tsara ginin yadda ya kamata, "kusan watanni shida kenan da gama aikin wasu gini amma har yanzu mutane biyar kaďai suka siya wasu bangare daga gidan, tun yana Egypt yake damuwa da outcome din business dinshi dake turkey, yau dai ya shirya zuwa dan ganin dalilin da ya sanya companynshi ya fara zama koma baya wurin ciniki a kasar instanbul, ganin yanayin tsarin ginin da ya kashe makudai kudi yayi su ya sanya hankalinshi tashi matuka, sam zubin tsarin baiyi ba, komai anyi shi a gaggauce, kama daga zanen har ginin, sam bai iya bacin rai ba domin shi mutum ne wanda ya yarda da kaddara mai kyau da marar kyau, asarar da yayi bata kananan kudade bace, haka ya bar gurin yana istigfari haďe da adduar Allah ya sanya asarar da yake shirin yi ta zame mishi alkhairi.... Yana komawa office ya bukaci sanin a inda matsalar take, engineern ya fara kira, nan ya gabatar mishi da zanen da aka bashi domin yin aikin sannan ya ďora da cewa "kanin manager ne yayi zanen, wanda ya saba yin zanen ya bar aiki damu kamar yadda manager ya faďa min.. Sheik na ganin zanen ya gane a inda matsalar take, bai bukaci jin wani karin bayani ba yayi zaune hankali duk a tashe yana hango dakushewar kasuwancinshi kwana kusa, Rufe system din yayi ya mike ya danna wata kararrawa dan yin taro na gaggawa da ma'aikatanshi, nan fa suka shiga tururuwar shigowa cike da ladabi suka tsaytsaya a muhallinsu..... Bayan ya gama musu bayanai na abun da ya tarasu sannan ya dora da irin barazanar da companynshi yake fuskanta ya kuma yi umurni da kar a sake baiwa wanda yayi zanen gidajen da sukayi musu bandaro aiki, Bayan nan ya bukaci duk wani wanda yasan mai zane wanda ya kware a zane ya je ya kawo shi ya kuma sashi ya taho da aikin da yayi, rabin yan gurin wadanda suka san Hilal suka fara ihun sunan *M H K*... wasunsu kuma suka fita domin kiran makusantansu suzo ga aiki ya samu, Cikin awanni uku aka haďa masu zane kusan su 15, nan duk suka gabatar da ayyukansu wanda ko rabin na Hilal basu kamo ba, cike da kosawa ya kalli zanen na karshen haďe da mikawa engineern, "Call for another meeting plss, ina son sanin dalilin da yasa Hilal ya bar aiki anan gurin.. cike da girmamawa engineern ya amsa shi ya fita da sauri ya sake kiran wani meeting din.. "Da harcen turancin dattijon da bai wuce shekaru hamsin da doriya ba yake magana, "Nasan akwai masu zanen gidaje da yawa, amma companyn nan kowa yasan "Hilal Kangiwa" ne yake zanen gidajen da muke ginawa masu daukar hankalin jama'a, duk wadannan masu zanen da kuka tara min dan Allah ku basu hakuri, a je a nemo min Hilal muyi eye to eye dashi inji nawa yake son a kara mishi, Cikin girmamawa manajan kamfanin yace "Ba kudin bane sukayi mishi kadan, matsala suka samu da IRFAN, shine yace ya bar aiki, Ya salam... dattijon ya fadi yana mai dafe kanshi, wato Irfan sai ya kori duk wani wanda suke kasuwanci tare, a kausashe yace "bani number wayarshi zan kirashi yanzu yazo office ya sameni... ****** "Duk tashoshin cartoon din yau basu yi zee, kin gani? ta tsaida kan Mbc 1, tana yunkurin canzawa wayarta ta dau kara, mikewa tayi da sauri ta zare wayar a charge, daki ta wuce tana waya da Jamal cike da so da qauna, Lamoo Zainab tayi cikin lallausar kujerar parlon tana kallo haďe da lumshe ido alamun bacci nason yin gaba da ita,  bata dauke idonta a kan tvn ba dan tasan in suka gama tallan drama's dinsu zasu sako cartoon, hannu tasa a baki tana sha a boye dan kar Hilal ya kamata, yadda ta naďe hannun da hula zaka rantse wani abun take sha daban, Kamar cikin mafarki ta tsinkayi kukan yar budurwa cikin wani tallan arabic drama, sanye take cikin jallabiya baka kanta yane da ďankwali, Mikewa zainab tayi ta isa gaban tvn dan kalolin hotunan budurwar ake nunowa, daga wanda take kuka sai wanda take dariya, *Adda* ta furta a hankali tana shafa fuskarta a screen.... " *Hey everyone i'm _MALEEKA SAHEEB SAIF_.... SAHEEBUL QALBEE will be in cinema's on the 3rd may in shaa Allah, don't miss the unconditional love story of NAINAH AND SAMIR, dos in Egypt will see ya on the 5th, nd Istanbul on the dday, love yhu oll my fans.. muahhhh..* Ya Hilal... Ya Hilal... A ruďe ya rufe laptop dinshi ya buďe kofa saboda irin kiran da Zainab take mishi, duk tunaninshi wani abun ne ya sameta, haki ya ga tana yi tana nuna mishi tv, "Adda na gani a cikin tv, wallahi itace, ajiyar zuciya Hilal yayi ya kwace naďin da tayi ma hannunta da hula yace "wannan abun da kikayi shi ya sanya tayi miki gizo, amma muje in ga ko itace, bin bayanshi tayi suka zauna a parlon lokacin an wuce tallan har an fara cartoon, a hankali tace "an gama, amma ka zauna a sake yin talla zaka ganta, janyota jikinshi yayi yace "Bacci kikeji my baby, kwanta kinji, anjima in kin tashi sai mu fita yawo, rufe idonta tayi tana hango fuskar Maleekah wacce tayi ma lakabi da Nadeeyah, babu abinda ya banbanta su sai tsayi da wayewa, Maleeka ta ďan dara Nadeeyah tsayi sannan wayewarsu da gogewarsu ma sam ba daya bace, amma kamannin fuska babu inda suka banbanta, da tunanin bacci yayi gaba da Zainab, kwantar da ita yayi a gurin ya mike dan karasa research din da yakeyi akan aikin da gwamnati ke son bayarwa, yana son Applying aikin amma yasan yafi karfin Papa ma bashi ba... Cike da confidence yayi Applying haďe da ayyukan da yayi a baya, tunanin yadda zaiyi ya haďu da mai *A square TCC* ya keyi, yasan zaiyi aikin domin kuwa karuwarsa ce da shi baki daya, dan in ya yarda sukayi aikin nan ba karamin kuďi zasu samu ba, Wayarshi ya dauko da niyyar kiran manajan companyn, tunawa da halinshi da yayi ya sanyashi ajiye wayar ya cigaba da tunanin yadda zaiyi ya hadu da CEO din cikin sauki,, har ya mike zai  shiga bayi yaji karar waya, da kamar kar ya dauka dan yaga bakuwar number, wani sashi na zuciyarshi ya bashi umarnin dagawa yaji ko alheri ne, Aiko Hilal yayi farin ciki matuka da jin mai kiran nashi dan abun da ya dade yana nema kenan, nan yayi alwala yayi sallah haďe da yin addu'ar Allah ya bashi karfin gwiwar fada mishi abun da ke ranshi, ya kuma sanya haduwar tasu ta zamto alkhairi..... "Shiryawa yayi tsaff cikin kaftan riga da wando ash, ya dade yana son haduwa da Ceo din companyn da yake wa zane  *SHEIK ATIKU SAHEEB SAIFUDDEEN* Saboda wadannan  ayyukan zanen gwannati da yake son nuna mishi, kuma yana son yi mishi gargadi akan macutan dake gudanar da ayyukansu a companyn shi... Sanyin A.c. hade da kamshi mai dadi ke tashi a cikin office din, Makeken Hoton jikin bangon idonshi ya sauka a kai gabanshi yayi mugun faduwa, su hudu ne a jikin Hoton, Irfan kadai ya gane saboda yayi mishi sanayya marar dadi, Hoton yar budurwar da mahaifinta su suka fi tayar da hankalinshi, bai gama shiga dimuwa ba sai da yaji muryar mutumin ya fito yana mishi MARHABAN ya Hilal, suman tsaye yayi da suka hada ido saboda tsabar firgici, tabbas yasan mama suwaiba bata da wani dan uwa namiji, to wannan mutumin me irin fuskarta daga ina ya fito... Hasbunallahu wa ni'imal wakeel ya fadi jiki na rawa, a zatonshi gamo yayi da aljani..... Karasowa kusa da Hilal yayi ya miko mishi hannu dan su gaisa, kasa daurewa Hilal yayi yayi saurin tsugunawa dan yi mishi irin gaisuwarmu ta hausawa, nan fa Sheik ya sake jin kaunar Hilal na yawo a cikin jininshi, dagoshi yayi ya haďe jikinshi da nashi haďe da sumbutar kumatunshi irin dai yadda larabawa ke gaisuwarsu, hoton dake kan makeken table dinshi kuwa saida ya kusa tsaida numfashin Hilal, Hotone kato black nd white, fuskar nan bata da maraba da ta su Mama Suwaiba, Sheik, Nadeeyah da yar budurwar dake cikin hoto, bai kara samun kanshi cikin ruďani ba sai da idonshi yayi tozali da sarkar wuyar tsohon hoton, wannan karan Hilal ya riga ya gama fita hayyacinshi, kar dai son da yakewa Nadeeyah ne ke neman kaishi wata duniyar daban, hannun dattijon da yaji cikin nashi ne yasa shi saurin matsawa baya, da karfi yake furta kalmar "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, cikin rashin fahimta dattijon ya nufoshi yace "Lafiya? Menene yake faruwa? "Dan Allah karka cutar dani, Innalillahi, "wa inna ilaihir rajiun sheik ya karasa cike da zullumi haďe da cewa "Subhanallah, jin ya ambaci sunan Allah ne ya sanya Hilal nutsuwa haďe da nemo duk wata jarumtakarshi, ganin ya samu nutsuwa ya sanyashi cewa "su shiga cikin parlon office din, bayanshi Hilal yabi yana ambaton sunan Allah... Kallon Hilal Sheik yayi yana tambayarshi damuwarshi, Murmushi kawai Hilal yayi yace "Babu komai kawai yayi mishi kama da wasu relatives dinshi ne nd they are no more, hoto ya kuma gani a kan centre table din cikin parlon an haďa pixmix da na Maleekah, dauka Hilal yayi ya fito da wayarshi yayi scrolling hoton Nadeeyah ya nuna ma sheik, second goma yayi yana kallon fuskar Nadeeyah, tabbas wannan tayi kama da yayarshi wacce ya rasa tun da kananun shekaru, katse mishi tunani Hilal yayi dan a lokacin tsoro ya fita a ranshi, yana da tabbacin wannan dan uwan Mama suwaiba ne bangaren uwa, "Wannan sarkar ya nuna sarkar wuyar tsohon hoton, da sauri Sheik yace "Ehem kasan sarkar ne, gyaďa kai Hilal yayi yace "Sosai, tana gurin grandfather dina, gaba ďaya sun manta zaman da suka zo yi, ko wannensu ya shiga shaukin son jin labarin juna, "A ina ya samu sarkar, yadda muryarshi ke rawa ya sanya Hilal dafashi, "calm down sir, farin cikin da nake ciki bazai barni in baka amsa ba, sunanta kaďai zanji ya sanya ni fita gurin nan cikin gaggawa dan bayyanawa yan uwana abun farin cikin da ke tunkaro mu, a gaggauce Sheik yace *At---* *ATIKA* Hilal ya karashe cike da kaguwa domin ya kasa jiranshi ya karasa, "Yesss, she is my sister Atika, my only sister, my everything ya karashe cikin matsanancin kuka haďe da rungumar hotonta wanda ya zame mishi kullum... "Ya Allah... Hilal ya faďi yana zubar hawaye, Nadeeyah were are uuu, Asalinki ya fara bayyana, ya ilahi, tsatso mai kyau, i knew it, nan gaba abubuwan shahara zasu bayyana gareku, Ina kika shige Nadeeyah, kuka sosai sukeyi, shi Sheik yana yi ne dan duk a tunaninshi zai sake sanya yar uwarshi a ido, shi kuma Hilal kukan biyu ya haďe mishi, na farin ciki da kuma na bakin ciki domin duk wanda ya kamata ya ga wannan farin cikin baya tare dasu, " *Is this a scene or reality?* Zazzakar muryarta ta karaďe dakin, a tare suka kalleta tana tsaye sanye da bakin dogon wando wanda kasanshi yake a buďe sosai sai milk riga mai dogon hannu, kanta yane da da bakin gyale wanda ya bayyana gashinta har gadon bayanta, karasowa tayi hankali a tashe tana faďin *ohh Abbu?* wurgi tayi da jakarta kan doguwar kujera ta zauna kusa dashi, hawayen ta fara share mishi tana magana da larabci, tasan Irfan ne kadai kesa mahaifinta hawaye haka, hoton da ya rike a kirjinshi ta karba ta zuba mishi ido, ajiyeshi tayi a mazauninshi ta dafa kafaďunshi, "Bazan hanaka zubar da hawaye ba dan nasan a wannan lokacin babu abinda zaisa su tsaya sai dai domin kansu, tunda nazo duniya nake ganin hawayen nan, plss Abbu kayi hakuri, kayi tawakkali, in kanada rabon ganinta zaku haďu cikin sauki in shaa Allah, Fuskarta ya tallabo haďe da sakin murmushi a bayan kukan yace "Allah ya kawo min lokacin my love, yanzu na samu labarinta daga gurin Hilal, kallon inda ya nuna mata tayi, shigowarta tabbas ta ganshi, amma ganin halin da Abbunta yake ciki ya mantar da ita akwai mutum a gurin, cikin ido ta kalleshi dan shima ita yake kallo tun shigowarta, mamaki ya hanashi furta komai dan ya tsorata da hukuncin ubangiji, irin wannan kamanni har haka, ya salam, tabbas badan gogewa da wayewarsu ba daya bace da babu abinda zai hanashi kiranta da Nadeeyah, Takalmin kafarta mai tsini ta cire ta mike rai a haďe ta isa gurin Hilal, ta riga ta gama hararo abun da ya kawo shi, tasan sarai yazo da niyyar cutar mahaifinta ne, shekara sama da hamsin da batar ta sai yau zaizo yayi taking advantage din son da mahaifinta kema yayarshi yace ya san inda take, in shi yasan inda take meyasa baizo da ita ba, "Heyyy, ta faďi haďe da buga hannunta a saitin idonshi, firgigit Hilal yayi ya dan matsa dan baisan ta karaso inda yake ba, kusa dashi ta zauna sosai tana fuskantar mahaifinta tana dariya dan kar ya gane manufarta, "Wa ya aiko ka? Ta tambaya ba tare da ta kalli inda yake ba, cikin rashin fahimta ya share hawayen dake makale a idonshi yace "Ban gane ba? "Zaka gane, hannu tasa cikin nashi tace "Muje ciki akwai tambayoyin da zan maka, mikewa yayi dan ta fara jan hannun tana tafiya, da larabci tace mahaifinta tana zuwa... Sosai ran Hilal ya baci da ta gama jero accusations dinta cike da faďa kamar zata mareshi, maganarta ta karshe ce ta sashi daka mata wata tsawar da ta daidaita ta, "Yesss nasan Irfan, sani sosai, "Ehen i knew it, nasan Irfan ne yasaka wannan aikin dan ku samu kudin banza ku je kuyi iskancinku, ku ko kunya bakwa ji, at ur age baku san yadda zaku dinga samun daily income ba sai kunyi cuta, to this deal is cancelled sai ku nemu wani, nuna shi tayi da ďan yatsa tace "Wallahi in na sake ganinka gurin Abbu na sai nasa anyi maka daurin rai da rai, babu inda ba'a sanni ba world wide duk inda na nemi alfarmar a kam----- Gerraut Hilal ya faďi haďe da buge hannun kasa, duk sanyin da ya shigeshi na rashin Nadeeyah ya fice gaba daya, "Count me out, ban sanki ba, ban taba ganinki ba, sannan Irfan a companyn nan na sanshi, u most be stupid in har kikayi tunanin nazo nan ne dan kudin mahaifinki, he called me himself, go and ask him, i'm his company architect, ban taba ganinshi ba sai yau, nd wat i saw ya sani faďi saboda ur aunt is my relative, hannu na rawa ya dauko wayarshi ya nuna mata hoton Nadeeyah, ganin jikinta ya fara sanyi ta kuma tsumu da mamaki ya sanya shi kwace wayar yace "I have my own self respect, nasan i'm nothing like ur father but i'm contented with the little i have, am not needed here, kuje ku nemi  real yan uwanku tunda ni fake na kawo, yana kaiwa nan yayi hanyar waje haďe da buga tsaki, Da gudu tasha gabanshi haďe da rike mishi hannu, "Sorry sorry sorry, plssss... ta kara faďi haďe da tsugunawa a kasa, kwace hannunshi yayi zaiyi magana yaji muryar Sheik a bayanshi, "Kayi hakuri Hilal, she is always like that, akwaita da tambayar da zata kai mutum bango, zo ka zauna na yarda da kai 100%, juyawa Hilal yayi ya koma kan kujera ya zauna fuskar nan a murtuke, wannan babu abun da ta haďa na hali da Nadeeyah, kalamanta na cin mutunci sun mishi zafi matuka, dannewa kawai yayi ya zauna dan sauke wannan nauyin badan ita ba sai dan Nadeeyah da su Hafeez, tambayoyi sheik ya fara mishi, babu abinda ya iya faďa mishi sai dai kawai ta Haifi twins... Yadda yaga ya ruďe da murna ya kasa sanar dashi ta mutu, a ranar maida Hilal ciki ne kadai sheik baiyi ba, tafiya ya shirya musu da private jet din abokinshi dan baya son wani delay a zuwa ganin yar uwarshi da zuri'ata, Murna tasashi ya yafe mata rashin nemanshi da batayi ba, tasan irin ukubar da ta tafi ta barshi a hannun Ummul da 'yayanta, share hawayenshi yayi bayan ya tuno gararanbar da yayi a baya wanda ya zame mishi tarihi... Har Hilal ya bar office din bai kalli inda Maleeka take ba, ita kuwa sai kai kawo takeyi da kayan kwadayi tana dire mishi, tasan bata kyauta mishi ba, idonta ya rufe ya hanata hango kamalar fuskar Hilal, Sukuku ta yini ranar har ta koma gida, duk abinda takeyi Hilal kawai take gani, masifarshi da komai nashi burgeta yakeyi, samm bai bata fuskar da zata amshi number shi ba, tayi yawon duniya sosai, ta haďu da maza haďaddu wadanda suke macewa akanta, bata karo da wanda zuciyarta tayi na'am dashi ba tun bayan Mutuwar Na'em sai Hilal, *Saheebul qalbee* ta furta a hankali tana mai hango soyayyarsu ta cikin film din.. "Kwatanta soyayyar da mai zafin zuciya irin Hilal zai fi armashi..  murmushin dake kan fuskarta samm yaki daukewa, tana hango Abbunta da Ummi na sakkowa daga sama cikin jallabiya tayi saurin nutsuwa ta isa gurinsu dan tambayar inda zasu a daren nan... Amsar da ya bata ya sanyata yin murmushi mai kyau haďe da cewa su jirata dan Allah zata rakasu, "Jira fa Malee? Ummi ta faďi da harcensu na larabci tana rike haba.. Kwantar da kanta tayi a kafaďun Abbu tace "Abbu kaga ummi ko? "Zan jiraki, komai dake zanyi, ke zata fara gani tunda sunanta gareki, rungumeshi tayi ta haye sama da gudu dan shiryawa.... 40mins Ya Habeebi, kasan jiran Maleekah... bata gama rufe baki suka hangota cikin purple jallabiya mai walkiya, kan nan ta yaneshi ta fito a balarabiyar asali, light makeup tayi wanda ya fito da kyawunta na musamman, kamshinta kuwa dadinshi kansa mai saurare yayi baccin da bai shirya ba, *ATIKA ATEEK SAHEEB SAIFUDDEN* kenan ta haďu matuka, tun tana karama take sha'awar drama, Shiyasa samm taki maida hankali a karatu, gata da kokari sosai, ganin hakan yasa Abbunta yi mata jumping, tanada 14yrs aka kaita university inda ta karanci theartre art, da yake field dinta ne sai ta dage sosai dan kullum cikin drama suke, hakan yasa ta kware sosai, a yanzu duk kasashen larabawa babu inda ba'a santa ba, haka tsirarrun yan wasu kasar irin nigeria masu kallon arabic dramas suma duk sun santa, shekarunta basu wuce 21 ba amma wayewarta ta zarce dan 30...   "Kinyi kyau my love, kiss ta mishi a kumatu tace "Thank u Abbu, nasan anyi complain? Dariya yayi yace "as usual, kin santa, gaba ummi tayi tana dariya tace "kwaji dashi..... Basu sha wahala gurin zuwa gidan ba dan estate dinsu sananne ne sosai, Da fara'a Hilal ya taresu tun daga kasa, dama ya gama shirya ma zuwansu, ya faďa ma Anty Reemah zaiyi baki amma bai faďa mata ko su waye ba... Zainab na zaune tana home work tana zana sunan da yake bace mata a kai, Maleekah sahy, Maleekah Sa'eed, Maleekah sahab haka ta dinga rubutawa a bayan littafinta, ko da taji an murda kofar duk su Anty Reemah sunje suna musu maraba bata dago ta kallesu ba, Na--deeyah... Hinad ta faďi a hankali tana nuna Maleekah, dago kai Zainab tayi ta mike da sauri ta isa gurinsu, kallonsu ta shiga yi daya bayan daya, tasan ba Nadeeyah bace, dan in itace abun da zatayi mata ya wuce ta tsaya tana kallonta, "Maleekah sahab ko? Dariya Maleekah tayi ta tsuguna kusa da Zainab tace "Saheeb dai my young fan, ko dai brothernki ne ya faďa miki sunana, ta karashe tana kallon Hilal, shuru Zainab tayi dan turancin na Maleeka yafi karfinta, Anty Reemah ce ta katse shurun ta hanyar nuna musu gurin zama, bayan sun gaggaisa Anty Reemah ta kalli Sheik cike da al'ajabi zatayi magana Hilal ya rigata dan baya son yasan mutuwar yar uwarshi samm sai yaje ga mijinta, "Mum wannan kanin maman su mama suwaiba ne, labarin yadda haďuwarsu ta kaya ya basu wanda ya cikata da mamaki, "lallai komai da sanadinsa, sanadin aiki ya sa ka samo wannan muhimmin abun, kaii masha Allah wallahi naji dadi sosai, introducing dinsu Hilal yayi, yana zuwa kan Zainab da Sheik ya kasa daina kallonta yace "Ur grand daughter sir, she is urs! hawayen farin ciki ne ya fito mishi dan yajita sosai a jininshi, mikewa yayi ya dauketa sosai a jikinshi, ya kosa a wayi garin gobe yaje yaga zuri'arshi, shakikanshi, wadanda yake da rashinsu tun kuruciya, a gidan Papa ya samesu shima yayi farin ciki sosai sukayi hirar kasuwanci da na iyalai, Sheik jin kanshi yakeyi kamar a yaune aka haifeshi dan ya fara jin kamshin yan uwanshi danginshi na uwa... Assalamu alaikum..... maida hankalinsu kan mai sallamar sukayi dukkansu, Sauka jikin Abbu Zainab tayi ta ruga gurin Meerah, "Anty Mee zo kiga Maleekah da nake baki labari dazu, hankalinta sam bai kan zainab tana can kallon yadda Maleeka tasa kafa tana shafo ta Hilal yana matsarwa, tray din hannunta ta damke dan kiriss ya rage ya faďi kasa, "Muje zee, Har kasa ta tsuguna ta gaida su Abbu sannan ta mike ta nufi kujerar da su Hilal suke, kan hannun kujerar ta zauna, ganin duk manyan suna can suna hirarsu yasata yi mishi raďa a kunne, Dariya sosai yayi dan ya gama gane inda ta dosa, mikewa yayi ya nufi dakinshi.. bin bayanshi tayi rai a bace dan ta gama kulewa, dangwarar da tray din snacks din da tayo mishi tayi a kan madubi, "Meerah plss, kar muyi creating scene a gidan nan kinga munada baki, "Eh naga baki, su bakin da suka san inda sukazo ai na samesu suna hira, kai fa, ko kunyar idon iyaye bakaji ba ka zauna kusa da mace tana shafa maka kafa kana jin dadi, Wannan karan dariya yayi mai sauti wanda ya kular da Meerah ya sata sakin kuka mai karfi, "La'ila, ke rufa min asiri plss, haba meerah, yarinyar nan kema kinsan tafi karfina daga yanayinta in kika kalla, "Me zanyi da yanayinta ni, abun da idona ya gane min shi na lura dashi, na gama fargabar wata yanzu kuma ga wata zata shi---- Meera.. ya katseta haďe da tsugunowa gabanta, Na faďa miki soyayya yanzu na rufeta a shafin rayuwata, bana tunanin zan sake faďawa cikinta so quick, na faďa miki kiyi hakuri, wallahi in nace miki zan yarda ki jirani nasan cutarki kawai zanyi, bazan iya sake yin wata soyayya ba, u are my best friend tun muna yara, dan Allah mu tafi a haka, Allah zai baki wanda yafini alkhairi, Share hawayenta tayi ta mike tace "Nagode Hilal, zanyi hakuri dakai dan dama nasan ba sona kakeyi ba, "Nooo Meerah... ya faďi haďe da matsowa kusa da ita, hawayen da ya makale a idonta ya share mata yace "kinsan Allah ina sonki, amma bazan iya zaman aure dake ba, who will be the husband? Yadda yayi tambayar cike da zolaya yasata yin dariya, tasan irin matan da yakeso, yara kanana wadanda zai yi musu yadda yake so, bayason a juyashi sam, ita kuwa Meerah kusan mates ne in ma bata girme mishi ba, "All the best besty ta faďi tana murmushi, Allah ya sake baka wata soyayyar wacce tafi ta da, "U will always be my best Meera, Allah ya baki farin ciki kema.... "Uhmmm wonderful.., Maleekah ta faďi tana karasowa haďe da tafa hannu, a tsakiyansu ta tsaya cike da tsiwa, hannun Meerah Hilal yaja yace da hausa dan yasan bata ji. "Muje in rakaki, ba kunya gare yarinyar nan ba, kallo ta bisu dashi ta rasa menene ainihin abin da yasa ta biyosu, kwafa tayi ta kama hannun Zainab suka koma parlor, lokacin har su Abbu sun mike da niyyar tafiya, wayarta ta dauka sukayi hotuna kala kala da Zainab da Hinad, Har kasa su Anty Reemah suka rakosu, tana ganin Hilal ya nufo inda suke tayi saurin sanya Abbu cikin mota, gefen driver ta shiga ta sashi ya koma mazauninta, Saida taga yazo dab da motar ta tadata haďe da bata wuta da karfi, tana kallon yadda ya tsaya cike da mamaki ta fito da hannunta waje haďe da yi mishi wani irin sign wanda bai gane ba, tana gama juyar da motar ta leko tayi mishi gwalooo sosai haďe da kaďa kai da ido, Tsintar kanshi yayi da dariya sosai yana faďin "naughty girl, matsalar yan drama kenan, komai sai sun maida shi wasan kwaikwayo, Har ya karasa cikin dakinshi bai bar hango yadda tayi mishi da fuska ba, duk abin da yakeyi in ya tuna sai ya keche da dariya shi kadai........ Mrs Tijjani Shattima..... [10/06 9:33 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣7⃣ By *Aysha Ya'u kurah* New story from *Atika Saheeb* "Yaushe rabo,, Jamal ya faďi haďe da budewa, Tallanta na film din *Saheebul qalbee* ya gani wanda ya gani a wall din Samir dazu yayi saving, a da yana son films dinta saboda haďuwarta da barkwancinta da tsantsar iya soyayyarta, amma yanzu abun ya haďe mishi, yana matukar sonta saboda kamanni da takeyi da yar uwarshi Nadeeyah, bai gama wannan tunanin ba ya hango fuskar da ya yi ma sani sosai, fuskar Masoyiyarshi Hinad da yar uwarshi Zainab, sai ita kanta Maleekar, rawa hannunshi ya fara yi ya kara ma wayarshi full light, sune tabbas, Cike da mamaki yake karanta post din, *My hidden fam, love yah muahhh....* ta sanya alamun kiss, kwancewa kan Jamal yayi ya rasa ta inda zai kamo tunaninshi, da kyar ya tattaro nutsuwarshi yayi screenshot din hoton ya turawa Hinad haďe da tambayar wacece wannan? Hinad na bude hoton taga Maleekah, alamar dariya kawai ta tura mishi ta kashe wayarta gaba daya dan ance karta faďa ma kowa suna son ya zama surprise...... Su shidda ne cikin jirgin, Abbu, Ummi, papa, da Anty Reemah, sai Hilal da Maleekah, inda Hilal yake zaune nan Maleekah taje ta zauna da sharaďin kar ya soma yi mata magana, dauke kanshi yayi dan gidan ta tarar, Chocolates ta fito dashi da su ice cream tana sha tana bin wakar Nancy Agram, toshe kunne Hilal yayi ya jingina jikin kujerar haďe da rufe ido, duk ledar chocolate din da tasha sai ta wurga kan jikinshi, da taga yaki kulata har ya rufe ido tayi saurin bude wani ice cream mai hade da chocolate ta kai saitin bakinshi, Tura mishi tayi iya karfinta har sai da ya shige bakinshi, wata dariya ta saki ganin yadda bakinshi yayi dama dama, A harzuke ya ja gashin kanta da karfi wanda ya sanyata sakin kara, "Hilal wani irin iskanci ne wannan, Anty Reemah da karan yasa ta buďe ido ta fadi cike da masifa, Gyalen wuyanta yaja ya goge bakinshi dashi ya mike  zaiyi magana Ummi tace "Ba laifinshi bane, ina kallonta tun dazu, dawo nan kusa da Abbu kaji, Matse gurin Maleekah tayi tace saidai ita ta koma gurin Abbu, "To dawo ki zauna, ni sai in zauna a inda yake, "Noo bazai zauna kusa dake ba, saidai ya zauna shi kadai, "Maleekah..., Ummi ta faďi cikin tsawa dan iskancinta ya isheta, ga yadda take ganin fuskar Hilal zai iya maketa saboda bacin rai, Tabe baki tayi tana shirin yin kuka Abbu ya taso da kanshi ya kamo hannunta ya maida ita kusa dashi, badan taso ba haka ta zauna tana turo baki gaba, kwantar da kanta sheik yayi cikin sigar lallashi dan koda wasa baya son abin da zai bata ran diyar da yake matukar kauna, soyayyar yayarshi ya sanya shi sanya ma 'yayanshi biyar mata sunan suna wabi, bai fasa sawa ba dan yace ko zai haifi goma su mutu sai ya sanya sunan wacce ya sani a matsayin mahaifiyarshi, cikin ikon Allah Maleekah ta zauna duk da har yanzu da girmanta basu bar dar dar ba, tun daga kanta haihuwa ta tsaya musu, ba haka sheik yaso ba dan shi mutum ne mai son tara 'ya'ya domin ya huce haushin tashin da yayi a maraya babu uwa babu wani dan uwa da zai kira nashi, wannan yasa ya dauki son duniya ya daurawa Irfan da Maleekah, sam babu no a agendar shi ta 'yayanshi, hakan yasa Irfan ya zama sangartacce, ita kuma Maleekah sai Allah ya sanya ta zamo mai hankali da sanin ya kamata, shagwaba kaďai ta iya zubawa kamar baza'a mutu ba, amma in abu na serious yazo tafi kowa zama serious, son da sukewa juna da mahaifinta yasa basa yarda ran wani ya baci koda kuwa anyi mishi abun bacin ran....   Lumshe ido Maleekah tayi tana son yin bacci, gagararta baccin yayi saboda wani irin yanayi da takeji game da Hilal wanda mutum bai isa ya sanyashi ba saidai Allah, mikewa zaune tayi kamar an tsikareta ta dauko madubi cikin jakarta ta saitashi daidai inda zata ga Hilal, karaff idanuwansu suka sarke cikin na juna domin shima ita yake kallo tun zamanta, saurin daga kanshi sama yayi yana mai jin haushin kanshi, murmushi tayi wanda yake bayyana duk wata kyawun surar fuskarta, komawa jikin Abbu tayi ta lumshe ido tana mai mamakin yadda akayi zuciyarta mai mugun tsantseni tayi na'am da Hilal, tafi minti goma tana tunani har bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba da ita...... Sauri sauri yayi rounding aikin dake gabanshi dan yaje airport taro mutanen da a koda yaushe burinsu ya kasance cikin farin ciki, Zubair ne ya shigo cikin office din da wasu files haďe da zube mishi, harara Musaddiq ya bishi dashi yace "Wallahi bazanyi ba, kaga dan na daga maka kafa ka angwance shine zaka wani lalace ka haďani da aikinka, to saidai in kwana zakayi a office amma sai ka gama su, keyn mota ya dauka ya cigaba da faďin "Dama gida kaje Faidah ta tayaka, dan naga yar karanbani ce, bye ni na tafi... Dariya Zubair yayi yace "Gobe nan zaka dawo ka tarar dasu, in ka bude zakaga ko menene.. Musaddiq bai saurare shi ba ya wuce ya danna lift, yana buďuwa ya shige ciki da sauri ya danna basement.. Lafiyyar motarshi ya shiga ya tadata yayi hanyar airport.... Mintina kadan suka kaishi airport din, parking yayi a inda yasan bai tare kowa ba, koda ya isa gurin ya tarar jirgin  bai sauka ba, guda biyu ne kadai ya sauka, na USA, tambaya yayi aka tabbatar mishi da nan da minti talatin na Turkey zasu sauka, guri mai kyau ya nema ya zauna kusa da wani saurayi rike da jinjiri wanda bai wuce wata uku ba yana baccinshi cikin showel hankali kwance, Shima saurayin bacci ne ya fara daukarshi dan saukarsu kenan daga jirgi, Musaddiq na lura da yadda saurayin ke gyangyaďi ya kura mishi ido dan kar yayi sanadiyyar faduwar yaron, gyangyaďi mai karfi ne ya kama saurayin har yayi sanadiyyar subucewar wayarshi da yaron, Cike da azama Musaddiq ya taro yaron da har lokacin bai farka daga baccin da yakeyi ba, rawa jikin saurayin ya fara yi cike da tsoro dan da yaron ya faďi ba karamin buguwa zaiyi ba, waya ma kenan da take bata da karfi ta tarwatse inaga rai, Kallon Musaddiq yayi wanda ya zubawa yaron ido suna kallon juna dan yana zuwa hannun Musaddiq ya buďe idonshi tangaran, dariya jinjirin yayi wa Musaddiq wanda ya sanya duka kumatunshi lotsawa, cike da kasala Musaddiq ya maida mishi dariyar haďe da taba kumatunshi, haka nan yaji son yaron na yawo cikin jininshi, matsowa saurayin yayi yana ma Musaddiq godiya haďe da sa hannu ya karbi jinjirin, kuka sosai jinjirin ya fashe dashi wanda a iya saninsu bai taba yin irinshi ba tun haihuwarshi, a ruďe saurayin ya fara jijjigashi yana hangen wani guri alamar neman mahaifiyar yaron, kuka sosai jinjirin yakeyi har yana shakewa, hawaye shabe shabe a rufaffen idonshi, har cikin rai Musaddiq ke jin kukan jinjirin, ganin yadda saurayin ke jijjigashi cikin rashin iyawa yasashi matsowa kusa ya mika hannu ya karbeshi, sanyashi yayi a kafaďa nan take gurin yayi tsitt sai alamar shakuwa da ajiyar zuciyar jinjirin, cike da mamaki dan saurayin yace "Lallai junior, wato nayi maka yaro da raino ko? Dariya Musaddiq yayi yace "Abun mamaki, ban sanshi ba amma ganin farko ya shiga raina, ya sunanshi? *Mukhtar amma Hi*-------  "Amaaan.. da sauri ya katse maganar ya amshi junior yace "Sorry.. uncle dina na kirana, inaga zamu wuce ne, thanks alot, bin bayansu Musaddiq yayi dan keyn motarshi ya makale jikin showel din, tsayawa Aman yayi cike da mamaki yace "Any problem? Nuna mishi keyn yayi lokacin ya cireshi haďe da jan kumatun junior, "Bye Daddy, ka daina rigima kaji ko? yadda ya kaďa mishi keyn yasanya yaron sake yin dariyar da ta tsaya a ran Musaddiq, saida suka kurewa ganinshi sannan ne yayi ajiyar zuciya haďe da kokarin cire tunanin yaron a cikin zuciyarshi... Faďuwar da gabanshi yayi ne ya sanyashi faďin "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun... kamar an sake hura faďuwar gaban domin kuwa da sauri da sauri take harbawa kamar ana lugude, runtse idonshi yayi haďe da dafe kirjinshi, tunanin da yake kwana yi shi ya dawo mishi sabo fil kamar yau aka halitta shi a cikin zuciyarshi, Karar wucewar takalma ta bayanshi ya sanyashi buďe idon a hankali, kafin ya juyar da fuskarshi duk sun bi ta kofar sun shige sai Aman da shima ya bi bayansu, kamshin turarukansu da ya biye gurin shi ya sanya Musaddiq sake jingina da kujerar yana mai tsintar kanshi cikin shaukin da ya daďe bai shiga irinshi ba.... Saida jirgin yakai 45mins sannan ya sauka a wani kebabben guri saboda dama private ne, A gajiye likiss suka sauko kowa yana mika saboda zaman guri daya, Anty Reemah Musaddiq ya fara gani yayi saurin karasawa kusa da ita yana mata sannu da zuwa, Sakkowar Sheik ba karamin gigita Musaddiq tayi ba, bai dawo daga wannan shock din ba ya shiga wacce ta fishi, Maleekah ya hango kanta dauke da hular Hilal wacce ta cire suna gab da fitowa, "Kaga Nadeeyarka ko? Kunci ya kare, Papa ya faďi yana murmushi... Hmmm ya faďi cike da mamaki, "Mai kama da ita dai, Nadeeyah ba haka take ba, amma a ina kuka samo mai kama da ita, in ma kunyi haka ne dan hankalina ya kwanta in sake wani auren to ku sani ni da aure sai dai a lahira, yadda Nadeeyah ta gama aure ta tafi ta barni nima hakan zan je in sameta yadda ta barni.. Hannun Papa Anty Reemah ta kama haďe da girgiza mishi kai suka tsaya a gefe, cike da murna Hilal ya sauko ya rungume Musaddiq haďe da tambayarshi bayan rabuwa, Murmushin da dole uwar naki ta koya mishi shi ya sakar mishi haďe da tambayarshi su waye wadannan masu kama da su Mamma? "Hello broo, Ayyam Atika Ateek, a.k.a Maleekah, tsaki Hilal yayi haďe da cire hular kanta yayi gaba, "Salamu alaikum, nyc meeting u Atika, i am Musaddiq Kyari, Maida hannunta baya tayi dan yadda ya amsa mata sallamar ya burgeta, har kasa ya tsuguna ya gaida su Sheik, dagoshi Sheik yayi ya rungumeshi haďe da amsa gaisuwar, saida suka gaisa sosai sannan suka fita suka isa motar Musaddiq da wata da aka basu a airport din dan zurga zurga, har suka isa gida Musaddiq bai bar tambayarsu daga ina suka nemo dangin Mama suwaiba ba.... Cike da al'ajabi Daddy ya ke duban Sheik, "Ikon Allah kenan, to meyasa babu wanda ya nemeta? Murmushi sheik yayi yace "Kaddarar Zuri'a, a lokacin da labarin yazo mana ina da shekara shida a duniya, amma nakan tuna wasu abubuwan, Lokacin da labarin mutuwarta ya riski ummul bata tsaya tayi binciken komai ba, kamar jira takeyi ta tattara 'yayanta suka fita daga gidan da niyyar in ta koma tace harda ni aka kashe, wani yaron da muke wasa dashi *Husaimin* shi ya shigo ya tasheni yace "inyi sauri gashi can za'a gudu a barni, a lokacin ne yake faďa min cewa an kashe Habeebullah da yayata, da gudu nabi bayansu lokacin har sun hau amalanke sun fara tafiya, takalmina da ya cire na waiga zan dauko Husaimin yajani da tayar hannunshi mukayi gudu muka kamo su, dakyar na iya hawa saboda tsayin abun, ina hawa ummul ta fara yi min masifar borin kunya tana tambayata inda naje, ban bata amsa ba na tsugunar da kaina inata kukan rashin gatan da zan tarar, har muka isa inda zamu tsallaka ruwa ban daina kuka ba, muna zuwa muka samu wadanda zasu tsallaka zuwa Egypt, nan aka loda mu ciki muka fara tafiyar da ta kaimu washe gari cikin ruwa... Karya da gaskiya Ummul ta fadawa mahaifina har ta ce mishi an sallaceta a gabanta domin tasan bazai yarda da ita ba sai yasa an je an dubo ta, saboda tsabar bakin cikin rashin Atika mahaifina ya kamu da mummunan ciwon stroke wanda ya daukeshi shekara biyu yana yi kafin Allah ya dauki ranshi, gaba daya dukiyarshi ummul ta tattareta ita da yayanta ta maidani dan aikinsu, son zuciya yasa ta manta matsayina a gurinta, ta mance cewa inda mahaifiyarmu ta tafi itama zata je komi daren dadewa, gidan Sheik Al' Mannar abokin babana nan nake zuwa daukar karatu, ganin hazakata yasashi ya sanya ni a makarantar boko, daga can sai in wuce gurin da suke aikin gini in dinga koya ina samun na abinci, gaba daya kwanan gidanmu ya gagareni domin kwana nakeyi aiki bani da wani hutu, abinci ma ummul sai taga dama take bani a cewarta itama ba kudi gareta ba, duk wasu kadarori na mahaifinmu ta haďe ta siyar sun cinye kudin da 'yayanta... Muna da shekara sha takwass 'yaranta biyu sukayi wa wata yarinya fyaďe wanda hakan yayi sanadiyyar yi musu hukuncin da yayi ajalinsu, a lokacin ummul hauka ne kawai batayi ba domin saida tayi wata biyu a asibiti, ni nayi jinyarta saboda dayan yaronta an nemeshi an rasa ya gudu da ragowar kudin da ta ajiye, ashe shima smuggling din kwaya yakeyi, ranar da dubunshi ta cika aka kamashi ita ma a ranar rayuwarta tazo karshe saboda shock din fille mishi kai da akayi... Gaba daya ummul ta manta cewa akwai mutuwa a bayan rayuwa, damar da Allah ya bata ta butulce mishi tayi wasa da ita, lokacin aji na biyu a jami'a, da taimakon Allah da taimakon Sheik na samu na kammala makaranta, Dan kudin da gwamnati ke bamu na scholarship da kudin aikin ginin da nakeyi yasa ni na fara dan karamin business dina, cikin ikon Allah kafin shekara abun ya bunkasa dan har na sai fili nawa na kaina, a lokacin ne kuma Allah ya azurtani da samun mace ta gari Zeenat yar gidan Sheik, Shekararmu biyu da aure muka samu Irfan, daga nan ne kuma duk shekara sai ta haihu wasu suzo babu rai, wasu kuma suyi watanni su mutu, daga kan Maleekah ne kuma haihuwar ta tsaya mana duk da ba haka naso ba, amma zabin Allah shine zabin komai..... ya karashe yana share hawaye haďe da yin murmushin takaicin fitar da irin kunar ukubar da yasha yana yaro..... Babu wanda bai zubda kwalla ba a dakin, lallai mutanen zamanin yanzu banda rikon sakainar kashi da sukayi wa zumunci, harda illata rayuwar juna ma sun kware akanta.... Babu wanda yake da kwarin gwiwar faďin mutuwar Atika domin basu san katse mishi shaukin da yake ciki... Wayar Papy Daddy ya kira domin jin ko sun kusa isowa, kashe wayar yayi yace wa Musaddiq "har sun iso bakaje ka daukosu ba, "Zubair zai dauko su, Musaddiq ya faďi cikin girmamawa.. "Okk to, Allah ya kawosu lafiya, Daddy ya faďi haďe da sake jan sheik da hira.... Motar da Zubair ya sai mata farar matrix sabuwa dall ita ta tuko tazo gidan tare da kayan abincin da ta hadawa bakin, koda ta isa gidan kiran Musaddiq tayi a waya dan ya fito ya tayata shiga da kayan, Fitowa sukayi shi da Hilal suka kwaso kayan abincin, tsokanar Musaddiq Faidah takeyi wanda ya sanyashi yin murmushi haďe da matsowa amsan tray din hannunta, Garammmmm.... sukaji an saki kofar gidan da karfin gaske...... Mrs Tijjani Shatimah..... [11/06 8:34 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣2⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Anty.... Nadeeyah ta faďi cikin dashewar murya, juyowa Raliya tayi ta sake kankame junior a kirjinta, "Na'am Nadeeyah, wayar dake hannunta da take kokarin kira Nadeeyah ta karba ta ajiye a gefe, "Dan Allah kiyi min alfarma ďaya! Dan Allah karki sanar da kowa dawowata, inada dalilai masu karfi da in na faďa miki zaki fahimceni, dan Allah Anty ki dubi maraicina kiyi min wannan taimakon! Cikin sanyin jiki Raliya tace "Nadeeyah nayi miki alkawarin in har dalilanki masu karfi ne zan taimakeki har sai kin cika burinki, faďa min kanwata.... Anty bani da gatan da wuce Allah, bamu da asali ni da yan uwana kamar yadda ake faďi.. na taba ji a bakin wani malamin mu cewar Allah da ilimi sune gatan maraya, babu wanda zai zama maraya sai rago, sannan wannan ilimin shi zai sa ka samu yancinka a cikin al'umma, a yanzu in na zauna tare daku, Mummy da su Anty Raudha bazasu taba barina in yi rayuwar yanci ba, sannan bazan iya jurar ganin yaya Musaddiq da wa------ Shhhhhh... Anty Raliya ta katseta saboda ganin junior na kokarin yin bacci, sabashi tayi a kafaďa tace "ina jinki? Na dade da burin yin ilimi mai zurfi, dan Allah ki goyamin baya in samu abinda zan tsaya da kafafuwa na, banason mu kare a haka ni da zuri'ata, kinfi kowa sanin rayuwar rashin gatan da mukayi mu da iyayenmu, bana fatan mu kasance a cikinta ni da ďan da na haifa, nayi miki alkawarin zan kare mutuncin kaina, zan nemi kuďin halal inyi sponsoring kaina, su uncle Taheer sunyi min duk abinda ya kamata dan uwa yayi maka, yanzu zan fita in nema da kafata har Allah yasa na dace.... "Duniya nada faďi Nadeeyah, ta ina zaki fara? Gabas, yamma, kudu ko arewa? Inada dukkan karfin da zan dauki nauyin karatunki a duk inda kike so, bazanyi hakan bane sai da yardar wani naki, shiyasa na kawo ki nan saboda ita kadai na sani a cikin yan uwanki, in yarintarki na faďa miki cewa duniya kankanuwa ce to kinyi kuskure, domin ko a kaduna north kaďai aka barki an haďa ki da aiki dan bazaki taba sanin ta inda zaki fara ba, ki dogara da Allah sannan ki nemi zabinsa akan duk abinda zai zame miki alkhairi a rayuwarki, in karatun alkhairi ne ni zan dauki nayinshi har ki gama.. In kuma babu alkhairi to tabbas Allah zai nuna miki ta hanyar zama cikin yan uwanki... Gyara zama Anty Raliya tayi bayan Taheer ya disa aya, kallonshi tayi tace "Taheer zauna, zauna muyi magana, ka riga ka zama dan uwa, babu abin da zamu boyeshi a gareka... Bayan ya zauna ta kwantar da Junior ta dubi Nadeeyah, "Tabbas maganganun ki gaskiya ne Nadeeyah, nasani sarai a yanzu in har kika dawo cikin mu wasunmu bazasu bar rayuwarki da ta ďanki su inganta ba, zan jure duk wasu matsalolin da nake gani a cikin yan uwana, zan kauda tausayin nawa domin rayuwarki ta inganta, nayi miki alkawarin babu wanda zaiji inda kike daga gareni, yanzu inada wasu kuďaďe zasu kai 1.2m.. zan baka Taheer sai kayi amfani dashi ku koma can Canada da zama tunda Anty saude nacan, in yaso duk abinda ciko ya biyo baya ka sanar dani, sannan zan dinga turo da wasu yan kuďaden da zata dinga amfani dasu, nayi alkawarin inganta rayuwarki da ta Daddyna in shaa Allah... Hawayen dake zuba a kuncinta Nadeeyah ta share mata ta tsuguna tana mata godiya kamar zata bauta mata.. Kallonsu Taheer yayi cikin tausayawa da farin cikin cewar akwai mai kaunarta a cikin yan uwanta... "Anty Raliya, ba sai kin bani ko sisi ba, nima ki barni in samu ladan marainiya, babu mamaki sanadin hakan ya sanya na samu biyan bukata a gurin Allah sannan zanyi hakan sadakatul jariya Allah ya kai ladan kabarin mahaifina.... Murna sosai Anty Raliya tayi ta dinga mishi godiya da addu'ar samun abin da yake so cikin sauki ba tare da yasha wahala ba.. Bayan yaci abinci ya koma gidansu ya bar Nadeeyah da junior Anty Raliya nata musu hidima kamar kar su tafi.... Wannan shine mafarin zaman Nadeeyah da junior a gurin su Taheer.. Da farko da suka koma Anty Saude kin yarda tayi da zaman Nadeeyah a gidan, Duk da tana kaunar zaman junior haka ta rufe ido dan gudun kar ďanta ya koma gidan jiya, Saida ya tubure yace shima zai bar gidan sannan ne ta amince da sharaďin bazai taba zuwar mata da zancen soyayyar Nadeeyah ba... Ba tare da doguwar jayayya ba ya yarda dan a lokacin so yakeyi yaga ya taimaketa ya mayar da ita cikakkiyar mace..... Cikin sauki yasa Kamal ya turo da result dinta na waec sannan ya fara cuku cukun samar mata makaranta mafi kyau ta mata zalla a canada.... Ba tare da bata lokaci ba ya samar mata ta fara zuwa, da fari rainon junior yana dan bata wahala saboda yadda karatun yazo mata, saidai kuma cikin ikon Allah Anty saude ta hanata fita dashi ko nan da can a cewarta rana na matsa mishi... Soyayya da kauna babu irin wacce junior bai gani ba a gurinsu, shekararshi daya ta yayeshi a nono saboda wahalar da karatu ke bata, nan Taheer ya maida ita Hostel saboda ta samu nutsuwar yin karatu, hutu kadai ke dawo da ita gida... Hakan ya sanya hankalin Anty saude kwanciya dan taga sam hankalin danta baya gurin Nadeeyah... a yanzu bata da burin da ya wuce ta hadashi da Amal domin tana matukar kaunar yarinyar, koda ta sameshi da maganar nuna mata yayi ta jira Amal din ta gama karatu... a haka dai rayuwarsu ta cigaba da tafiya yau da dadi gobe babu saboda dama haka rayuwar duk dan Adam take... Ranar da ta kammala karatunta ta fito da sakamako mai kyau Taheer yayi farin ciki matuka domin dama hakan yake so, yana son daga ta gama ta fara practicing aikinta... A yanzu kuwa Nadeeyah ta zama wayayyar mace wacce tasan yancin kanta, in ka ganta shuru to a gaban Taheer ko Anty saude take, amma a school bakinta buďe yake, ko wani irin presentation da defense da ita, bakinta ya goge sosai da kwararren turanci wanda in tana yi zaka rantse baturiya ce... Bata kara girma ba saidai ta murje sosai kamar renon turawa..... Ajiyar zuciya yayi bayan ya gama tunano duk abubuwan da suka faru a baya, Sai a yanzu sharaďin mahaifiyarshi ya dameshi da ta fara tuna mishi maganar Amal, yaya zaiyi ya nusar da ita bazai iya zama da kowacce mace bayan Nadeeyah ba, ya zaiyi da soyayyar da ya dade yana danneta a cikin ranshi.. Juyi yayi ya rungumi pillow kamar karamin yaro, "Ya Allah karka kawo abinda zai rabani da Nadeeyah.. Abin da ya fadi kenan cikin nukurkusar soyayya, soyayyarta na cin can cikin ruhi da bargon jikinshi, daurewa kawai yakeyi saboda baya son ya furta mata taga ko domin haka ne ya taimaketa, karar agogo yaji alamar hudu tayi, mikewa yayi ya nufi bayi dan watsa ruwa... Zuciyarshi cike take da tunanin yadda zai fuskanci duk mutane biyun nan masu muhimmanci a rayuwarshi da sirrin zuciyarshi, Runtse idonshi yayi lokacin da ruwa ya fara ratsa tsakiyar kanshi, ajiyar zuciya ya dinga jerowa yana jin wani abu na tsargawa a jininshi.. Wannan abu babu mai fahimtarshi sai wanda ya taba tsintar kanshi cikin matsananciyar soyayya...... Cikin coffee jallabiya ya shirya yayi sallahr la'asar ya fito ya nufi dakin junior dan ganin ko yayi sallar... Shi kanshi yasan yazama tuzuru domin yanzu kiriss ya rage ya shiga arba'in, in har zaiyi ma Momma adalci yasan dole taso taga zuri'arshi, da wannan zancen zucin ya isa dakin Junior wanda yake kusa da na su Nadeeyah.. Daki ne na musamman Anty saude tayi mishi domin faranta ranshi, Da katuwar kwallo yayi karo a bakin kofa, can ciki kuma tulin kayanshi ne da ya zubosu daga cikin drawer, dayan gefen kuma takardu ne na sketch dinshi da katon Allon da ake koya mishi... Can cikin luntsumammiyar kujerar dake gaban tv ya hangoshi sanye da sky blue riga da jan gajeren wando hannunshi dauke da control din game yana bugawa... Ta jikin switch din ya kashe tvn ya karaso ya mika mishi hannu, "Tashi muje sallah, ajiye game din yayi ya kwantar da kanshi jikin kujera haďe da noke wuya, Zaro ido Taheer yayi yace "Sallah fa Junior, wasa kakeyi sweetheart tashi kaji, in ka idar da sallah sai muci abinci muje yawo, cire glass din idonshi yayi ya fara sosa idonshi yana shirin yin kuka, Hankali tashe Taheer ya zauna ya daukeshi a jikinshi, "waye ya taba min kai? Faďa min, "Mamma.. ya faďi a hankali kamar me raďa, "Me tayi maka? Faďa min, kayan dake kasa ya nuna mishi yace "wai sai na kwashe da kaina ko ta min bulala, Daddy zan iya kwashewa? Dariya Taheer yayi yace "Ina fa zaka iya, nasan dai ka iya zubarwa amma kwashewa sam bazaka iya ba, rabu da ita, zansa Amal ta kwashe, kuma in zaka sa kaya ka kirani inzo in dauko maka kaji? Gyaďa kai Junior yayi haďe da rungume Taheer yace I love u Dad... "love more dear, tashi muje..... ********* Sauri sauri ta wanke hannunta da liquid soap dan gudun kar wayarta tayi karni, kafin ta isa ta dauki wayar har ta kuma katsewa a karo na uku, bin bayan kiran tayi da sauri, Saida wayar ta kusa tsinkewa taji an ďaga, "Hello Aunt Rally!!, A kiďime ya cire wayar a kunnenshi ya sake duba number me kiran, *M J Canada* sake maida wayar kunnenshi yayi, Cikin harcen turanci wanda ko me take faďi saita haďa dashi tace "yhu der? Jingina yayi da ginin gurin dan yadda yaji kanshi ya fara juyawa, samm bazai iya tuna inda yasan muryar nan ba, amma ruhinshi ya tabbatar mishi yanada alaka da mai muryar, "will call back may be ba network... kittt.. yaji ta kashe, bai cire wayar a kunnenshi ba sai muryarta daketa mishi amsa kuwwa... Gabanta ne ya faďi da ta doso gurin da ta bar wayarta taga Musaddiq da ita a kunne, cikin dakiya ta zare wayar tace "Little kai ne yau a gari, kallo ya bita dashi da kyawawan fararen idanuwanshi, Karaso ka zauna mana, ko ka shiga force ne ban sani ba, ta karashe cikin zolaya, Babu laka a jikinshi ya karaso ya zauna, zamanshi yayi daidai da sake shigowar wayar, Dakewa tayi dan kar ya gane ta dauki wayar, kafin ta kaita kunnenta tace "Maraba da Dikuu, yau an tuno damu, Hello Maman junior ya kike? Ina Daddy na, da sauri Nadeeyah ta kashe wayar numfashinta ya shiga safa da Marwa.. Ita kuwa Raliya cigaba da wayarta tayi tana dariya kamar dayan bangaren ma ana magana, saida tayi minti daya sannan tace "Kiyi hakuri inada bako, kanina yazo gida after a long period of time, to sai na jiki ta ajiye wayar a gefenta.. Diku kaga yadda ka zama kuwa? kuďi sun zauna ka manta damu, yaushe ka dawo daga Malay? Ajiyar zuciya yayi ya fara kauda tunanin mamallakiyar muryar nan, Shekaran jiya, Ance Mummy bata da lafiya shiyasa nazo dubata, me akeyi a gidan ne naga ya cika? "Bikin Rilwanu almajirin Goggo, Baffa, ya bashi dakin waje yasa amaryarshi, walhy stress ne yake damun Mummy, Yaushe Daddy zai dawo daga Holland? ta tambaya cike da kosawa, dan taci alwashin in shaa Allahu wahalar mahaifiyarta tazo karshe tunda yanzu kam ta gane kuskurenta fiye da tunani... Kasumbar daya tara a fuskarshi ya shafa yace "Zan je in sameshi jibi, zamu wuce Canada gurin wani taro, In shaa Allahu next week ko upper zamu dawo tare, to Allah ya kaimu ta faďi tana mikewa dan kawo mishi abin ci da shi... Wai ya maganar aure ne Little, haba, ka zama tuzuru, komai ya zauna, ya kamata ace ka ajiye iyali sune cikar mutuncinka.. Zai bata amsa kenan wayarshi tayi kara, da sauri ya dauka annurin fuskarshi ya karu sosai, "Habibi! ta faďi cikin shagwaba.. Yess My Baby, hw r u? ya amsata cikin kulawa.. "Fine sweetheart.. "Yhu sure My life? Ya tambaya cike da kulawa.. "Yeah buh i wanna see yhu, yadda ta make murya kamar zatayi kuka yasa yayi saurin kashewa dan suyi video call, tab dinshi ya dauko ya kirata... Nan take kyakykyawar yarinya yar shekara hudu ta bayyana, gashin nan yasha gyara da jan ribon, rigar jikinta ma jace mai tsananin taushi, tana da yar kiba wanda ya kara ma fuskarta kyau... "Yeyyy Habibi, i love uu, "Like wise my angel.. muahhh.. Sai a lokacin hankalin Anty Raliya ya kwanta, "Nadeeyah ce?, juyota in ganta, yar banza in ba iyayenta da kai ba, bata yarda da kowa, juyo mata ita yayi yana dariya yace "Matsa mata kukeyi, ku kyalemin matata tayi abin da ranta yake so... Tana ganin Anty Raliya ta hada rai haďe da turo baki, dakuwa Anty Raliya tayi mata tace "Ubanki Hilal kikayi ma, daga nesa ta hango Hilal yana dariya a gefen gadon yace "Nagode Anty, na karba,, Wai Hilal bazaka zo gurin yan uwa yarinyar nan ta sanmu ta ganemu ba, wallahi zanzo in dauketa in dawo da ita nan saidai ta mutu da kuka... Karbar wayar yayi yana dariya yace "kinsan Allah da kin kyauta, fitinar yarinyar nan sai irinku, gara a ďan gyara mata zama, Musaddiq ya batata da yawa, nan fa suka cigaba da hira da Hilal har Maleeka ta shigo ta zauna akayi da ita....... Uncle... ta faďi murya can kasa, Rufe mujallar hannunshi yayi ya fuskanceta sosai, "Nadeeyah ya akayi? Kina san wani abu ne? Girgiza kai tayi tana murmushinta mai sanyi, takarda ta mika mishi tace "An gayyacemu wani taro ne a Hallmark.. shine na kawo maka, buďe takardar yayi ya duba sosai, ganin karuwarta ce yasa shi cewa Allah ya kaimu ya kuma bada nasara, godiya sosai tayi mishi ta mike ta koma cikin daki... Ajiye jaridar yayi ya luntsuma cikin tunani, lokaci yayi da ya kamata ya sanar ma Nadeeyah abinda ke ranshi, burinshi ya shawo kan mahaifiyarshi kafin ya gabatar mata da bukatar zuciyarshi... Momma.. ya faďi haďe da kwantar da kanshi a kan cinyarta, hannu tasa tana shafa kanshi haďe da cewa yau shagwabar ce ta tashi, hannunshi ya daura akan nata ya rike sosai, Momma Junior is lvin us soon, "Saboda me? Ina zashi? Ta faďi da alamun tashin hankali, ya za'ayi ta iya zama a gidannan ba tare da Mukhtar ba, inaa sam saidai in Nadeeyah ta siyar mata dashi amma ko sama da kasa zasu haďu bazata taba bata shi ba... maganar da takeyin ta a zuci ta fito fili, Wani irin sanyi Taheer yaji a cikin ranshi dan a yanzu shawo kanta bazai mishi wahala ba... "Momma dole ya barmu, yana da uba, kuma itama mahaifiyarshi dole zata barmu tayi aure, a wani dalili zata bar mana danta? "A wani dalilin zata daukeshi ta kaishi agolanci wani gidan, wallahi bata isa tace zatayi aure ta tafi dashi ba, yadda take haki ya sanyashi mikewa zaune... "Calm down Momma, babu abinda muka haďa da Nadeeyah, ina faďa miki ne dan na kusa maida ita gida, kuma kinga tunda babu abinda muka haďa bazata bar mana danta ba... Rau rau idon Anty Saude yayi tana shirin fara kuka, gaskiya ne Tee babu abin da muka haďa da ita, amma ai tasan rabani da Mukhtar abu ne mai wahala, zata wahala dani matuka, Allah ya daura min kaunarshi a cikin raina.. "Ki kaunaci mahaifiyarshi Momma, Nadeeyah ba muguwa bace, bari in baki labarinta, ta yiwu ki tausaya mata ki barni in aureta kodan mu taimaki maraicinta.. cikin nutsuwa ya bata labarin Nadeeyah wanda saida ya sanyata zubar hawaye, tausayin Nadeeyah da soyayyar junior ta sanya Anty saude ajiye dukk makamanta, ta yarda da batunshi sannan ta umurceshi da ya sanar da Nadeeyah domin ta kira can Nijar suje nema mishi aurenta.. Cikin jikinta ya shige ya fashe mata da kukan murna, jikinshi har rawa ya farayi saboda tsabar farin ciki, Addu'ar da ya kwana yi Allah ya amsa mishi... Alhamdulillah... ya dinga jerowa babu adadi..... Shigar bakar doguwar riga tayi wacce ta ďan kamata ta ko ina, can kasan shima a tsuke yake saidai a tsage yake dan jin dadin tafiya, ta yane yellow dankwali a kanta, dan karamin yellow dankunne ta maķala a kunnenta sai sandals mai tsini yellow wanda a yanzu sashi ya zama sabon ta.. Kamshin da take fitarwa abin dadi ne domin kamshi ne mai ratsa zuciya.. "Haba Anty Amal ba rakiya? Juyi Amal tayi a kan gado tace "Wallahi Anty Mamma project zan kai karfe tara, naso zuwa inga yadda zaki ruďa min su, dariya Nadeeyah tayi ta dauki jakarta tayi waje, Dakin Amaan ta nufa dan ta dauka shi zai kaita, a parlor ta hangosu su biyu a tsaye suna jiranta, Gezna shadda suka sa blue iri ďaya haďe da hula, sunyi matukar kyau a sanyin safiyar nan... Da murmushi ta karasa gurinsu, saidai duk ta tsargu da kallon da Taheer yake mata, samm yaki dauke idonshi a kanta, Wani irin sonta yakeji kamar ana ingizashi, "Ina kwana, Lafiya kalau Mamma! Ya amsa har lokacin bai daina binta da kallo ba, Sunkuyar da kanta kasa tayi ta kama hannun junior tace "Harda kai, zaka bar Momma cikin kewa ko? Koma gida, Noke wuya yayi ya kankame Taheer yace "Daddy ne yamin wanka dan mu fita, ni sai naje, agogon hannunta ta kalla tace "7:40 uncle, 8 zasu fara, wucewa gaba yayi yana faďin muje na manta ne, bin bayansu tayi suka shiga motar suka wuce...... Mrs Tijjani Shattimah..... [11/06 8:35 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣3⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Hall din ya cika makil da turawa da bakar fata domin taro ne na karawa juna sani a kasa da professor's suka shirya, duk wasu dalibai da suka gama makaranta a kowani course an gayyaci mutum daya a cikinsu domin ya wakilcesu, kaf universities din dake Ontario a law su biyu kadai aka turawa gayyatar, daga ita sai dan wani makaranta Godwin... Cikin kwararren turanci professors din suka fara gabatar da abunsu, bayan sun gama bayanansu aka shiga jefo tambayoyi ga masu professional courses domin asan yadda karatun nasu zai amfanesu, da doctors aka fara, sai engineers, tafi tafi har aka iso kan Barristers.... Tambayace akayi musu na yadda zasu gane mai laifi, kuma cikin kankanin lokaci su wanke marar laifi... Cikin zazzakar muryarta tace "Assalamu Alaikum, Nan fa guri ya dauki shiru har wadanda suke ba musulmai ba, Cikin kwarewa ta dinga jero yadda za'ayi a fidda mai laifi cikin kagen da aka mishi, in ta hau kan common law sai ta sakko zuwa islamic law kamar yadda aka koyar musu... Musaddiq dake cikin masauki yana jiyo komai da akeyi daga Hall din domin cikin Hotel din ne kuma kusa da dakinsu.. bai fara jiyo su daga farko ba dan yana waya da little Nadeeyah, tun yana daure jin muryar har ta kaishi ga mikewa ya sanya riga ya fita... Jiki a sanyaye ya bar cikin lodge din ya nufi kofar Hall din, yana isa gurin tana gamawa, kai tsaye yasa kanshi zai shiga gurin, security suka dakatar dashi da tambayar ticket dinshi, Runtse ido yayi saboda takaicin zasu hanashi gasgata zuciyarshi wacce tayi mishi ingiza mai kantu zuwa nan, yana hango inuwarta tana barin, "Plss let me in, its very important, plsss.. Ko kallonshi basuyi ba suka cigaba da karbar pass din wasu, Ganin bazasu bashi dama ba ya sashi komawa baya ya tsaya, gaba da toilet din dake kofar shiga hall din ya tsaya, "Heyy mista, u can have my ticket!! Ya fadi haďe da mika mishi ticket din, Musaddiq bai waigo ya kalleshi yace "Thanks.. kawai yasa kai zai wuce dan bijirewa umurnin zuciyarshi... Shan gabanshi Junior yayi cikin fushi dan tun kafin ya shiga fitsari yaga ana wulakanta shi, kuma alamu sun nuna shi musulmi ne tunda Shadda ce a jikinshi duk da baiga fuskarshi ba, cikin tsiwa yace "Hey stranger i offered u my ticket nicely, who are u to refuse m--- Makalewa maganar tayi a makoshin juniir saboda tsabar firgici, komai dake kan fuskarshi ya gani a ta mutumin, glass din idonshi ya cire ya zura mishi ido sosai, Durkusawa Musaddiq yayi cikin ruďani ya tallabo fuskar yaron, saman idonshi ya shafa wanda ya lumshesu ya sake budesu dan ganin ko gamo yayi, raba hannunshi yayi akan kuncin yaron ya shiga shafa ko ina nashi, zuwanshi yatsun hannun yaron yasanya duk ilahirin jikinshi saki, Duk kyankyamin mutane da junior keyi saboda rashin sabo ya kasa nuna shi ga Musaddiq, saima shafa kasumbar da tayi kwance a fuskarshi da yakeyi, "Who are yhu.... Suka faďi lokaci ďaya suna nuna juna, wata irin dariya Musaddiq ya saki wacce bai san sanda ta fito ba, ďaga kanshi sama yayi ya shaki iskar dake kadawa ya maido da dubanshi gurin yaron da ya gama naďe zuciyarshi, yatsunshi ya ďaura kan bakin yaron yace "What is ur name, Murmushi junior yayi wanda ya sake bayyana kamannin su, lotsawar da kumatunshi daya yayi shi kaďai ya banbanta su, "Ur Twinny, My name is Mukhtar, *MHK Taheer..* nd uu.. ya nuna kirjin Musaddiq, Rike hannunshi Musaddiq yayi cikin wani irin yanayi yace " *MMK*, Mus----- Juniorrr..., cikin gaggawa yace "Yess Tell me, My Dad is calling me, Kafin Musaddiq yayi magana wani security ya janye hannun Junior suka wuce, Yana gab da shiga cikin Hall din ya waigo suka haďa ido, ďaga mishi hannu yayi haďe da sumbatar hannun ya hura mishi iskaa, Lumshe ido Musaddiq yayi yana jin kaunar yaron da kamaninsu yazo ďaya har cikin qalbinshi...... *MMK* *MMK* sunan yayi ta maimatawa a cikin mota, tun yana faďi a hankali har ya furzoshi da ďan karfi dan mutumin ya makale a cikin ranshi.. "MMK, who is he Juju? Kallon Taheer yayi yace "A stranger Dad, he looks just like me, he is my twinny, "Really... Taheer ya faďi dan shi gani yakeyi shirmenshi ne, "Yeaahh baka ganshi bane, will try nd sketch him tonight.. Dariya Taheer yayi yace "Allah ya kaimu, Pizza Hut or restaurant? Pizza nd ice cream Dad, kwanar da zata sadasu da Pizza hut ya shiga suka karasa suna dan taba hira da junior, ita kuwa Nadeeyah dake zaune a baya gabanta sai faďuwa yakeyi tana Maimaita sunan, *MMK* *Musaddiq Mukhtar Kyari*... No no no, tayi saurin kauda hakan a ranta haďe da runtse idonta.... Duk da bai kware a zane ba yayi kokarin zana fuskar Musaddiq haďe da kasumbar da ta kawata kayunshi, saidai zanen samm bai fita ba dan yayi yarinta da yinshi... daga gefe ya rubuta katon *MMK Mus* Bayan ya gama ya zura mishi ido har bacci ya daukeshi a gurin.... Madarar da ta shigo mishi da ita ta ajiye akan madubi ta fara tsince kayan dake kasan dakinshi tana mitar yadda kullum yake bata daki, "Bai yar a kasa ba, zuciyarta ta yi mata tuni da hakan, murmushi tayi bayan ta tuno da Musaddiq a baya kafin soyayya ta shiga tsakaninsu har kaddarar rabuwa ta gifta.. Zanen da yayi ta daga ta ajiye a gefe, ta maidashi kan gadonshi ta tofeshi da addu'a haďe da rufe mishi jiki da bargo, warm ta maida a.cn dakin mai hade da room heater saboda sanyin garin, tana gamawa ta tattara takardun dan maidasu mazaunin su, tana dauko wanda ya zana tayi saurin wurgi dashi haďe da dafe kirji, Yaya..Musa...ddiq, ta faďi a hankali idonta ya ciko da kwalla, dago takardar tayi ta kare mata kallo, bata san lokacin da zuciyarta ta ingizata ta haďe hoton da kirjinta ta durkushe a kasa ta fara jero kuka mai taba zuciya, "Yhu forgt all the love, all the promises, Why did u lv me, dis is nt fair, why will yhu remind me of ur existnce, Whyyy.....??? Ta karashe cikin silent cry mai cin rai... saida tayi kukan ta ma'ishi sannan tayi ma takardar buya ta musamman inda junior bazai taba ganinta ba..... A sanyaye ta fito daga ďakin bayan ta kashe mishi wuta, hanyar dakinsu ta nufa dan babu abinda take son kasancewa dashi sai gado da pillow, tana gab da shiga dakin taji iska sosai tana kaďawa, dama tun yamma hadari ya haďu, ragowar kayan junior dake veranda tayi saurin fita dan ta kwaso, Tsaye ta samu Taheer ya na kwasosu, karasawa tayi kusa dashi ta fara tayashi kwashewa haďe da cewa "Ashe ka rigani, bani in kai su daki, "Bakiyi bacci ba? Eh yanzu zanyi in shaa Allah, ta bashi amsa tana cigaba kwashe kayan saboda yadda ruwan ya fara sakkowa da feshi, Jallabiyar da ta rage ta karshe ta daura hannunta zata cire shima ya daura kan nata cikin rashin sani saboda sauri, A firgice ta kalleshi ta fara kokarin cire hannunta, yanayin da ya shiga ya haneshi cire hannun saima sake damkeshi da yayi.. Cikin rawar murya tace "Uncle ruwa, duk irin karfin da ruwan yayi shi bai gani ba saboda yanayin da yake ciki, ya zame mishi dole yau ya sauke duk wani nauyin dake cikin ranshi ko zai samu sukuni, a hankali ya ďaga hannun haďe da rikoshi cikin nashi, cike da kasala ya matso dab da ita har yana iya jiyo numfashinta haďe da bugun zuciyarta, Runtse idonta tayi ruwan dake fesowa ya dinga gangara akan fuskarta zuwa jikinta, sajen ta da ruwa ya kwantar ya kalla wanda hakan yayi sanadiyyar tashin tsigar jikinshi yayi saurin kai bakinshi saitin kunnenta, "U promise to be with me years back, will u fulfill ur promise? everything is back Nadeeyah, ur love is back, i love yhu alot, Will u marry me? Plsss Nadeeyah.... Yadda yake maganar a wahale ya sanya jikinta mutuwa tubuss, ya zama dole tayi ma Taheer adalci, ya sota tun kafin ta gama sanin kanta, saboda ita ya kai matakin tuzuru babu aure, ya kula da ita da danta ba tare da bijiro mata da soyayya ba, ita kuwa me ya rage mata a yanzu banda ta yarda da nagartaccen miji irin Taheer wanda zata samu nutsuwa a tare dashi, "Uhmm answer me plss ya sake faďi kamar zaiyi kuka, kayan dake hannunta ta saki kasa cikin raunanniyar murya tace "Yess i will, am all yours Uncle... Ko babu shaidan a wannan lokacin dole zuciyar da ta daďe da tsumuwa da soyayya ta aikata ba daidai, kamar yadda bature yace (Everything is fair in love and war) Taheer baisan sanda ya haďa jikinshi da na Nadeeyah ba, "Thank yhu Nadeeyah, Thank u so much, itama lupp tayi cikin faffadan kirjinshi tana sakin ajiyar zuciya mai karfi... duk irin ruwan dake zuba yana jika su basu dubashi ba saboda dukkaninsu sun shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa.... Saida zuciyar Taheer ta samu nutsuwa sannan ne ya nemi tsari daga sharrin zuciya ya raba jikinshi da nata, da sauri ta wuce ciki tana maida numfashi da sauri sauri..... Cikin kwanaki uku soyayya mai karfi ta wanzu a cikin gidan wanda har saida duk mutanen gidan suka gane, Amal da ta sawa ranta auren Taheer tayi gaggawar cirewa dan tasan dama tuni Nadeeyah yake so, a take tayi wa kanta addu'ar samun duk abin da zai zamo mata alkhairi.... Ga mamakin Nadeeyah sosai Anty Saude ta sake mata ta dinga lallabata tana nuna mata kauna ta musamman.. Hakan ba karamin daďi yayi ma Taheer ba.. A daren ranar alhamis suna zaune dukkansu a parlor Taheer na yanke ma junior farce yana tsoma baki cikin hirar tasu.... Kallon shi Anty Saude tayi tace "Munyi magana dazu da kawu Tidjani, na faďa mishi maganar zuwa neman aurenka, na sanar dashi ina son ayi komai cikin sati ďaya dan banasan wata matsala ta biyo baya, Mikewa Nadeeyah tayi ta wuce ďaki da sauri, Dariya yayi yace "Sai su taho ranar sati dan mu haďu tunda gobe zamu tafi, ni zanso ma a ďaura auren a ranar Mommah tunda babu wani shirin da ya rage.. Buďe baki tayi cikin mamaki haďe da sakar mishi dakuwa, Dariya yayi sosai ya dauki Junior suka wuce dakin Nadeeyah...... ******* *Kaduna* Toshe hanci Raudha tayi kamar zatayi amai, hawayen idonta ta share tace "Ya Allah ka sassauta mana, mun wahala iya wahala, mun gina ramin mugunta mun auka ciki, wuyar da muka so wata tasha ita muka haďiya har na tsawon shekaru takwas... Audugar da ta share ruwan ciwon dake fita a jikin Goggo ta yar a bola.. mistakely ya sauka cikin waken da Radiya ke gyarawa, Wata ashar ta sakar mata haďe da mikewa tace "wallahi bazan dafa abincin ba, ni na gaji wallahi, duk ku kuka jamin, yanzu ga Shamsu ko waiwayata baya yi, yana can ya koma Italy da zama shi da yarinyar da tayi min aikatau, wannan wace irin masifa ce.. Mummy dai jinsu kawai takeyi tana kokarin daga Goggo ta daurata akan pour, Kafin ta daurata har ta saki kashin a gurin, a sittin su Raudha sukayi waje dan dama su ba aikin sukeyi ba, Shekara uku kenan Goggo na fama da ciwon da babu wanda yasan irinshi, asibiti sun gaji sun maido ta gida, wani katon rami mazaunanta yayi saboda zama, ga wasu ramuka da jikinta yayi yana fitar da ruwa mai matukar wari, Mummy ce kullum ke hidima da ita saboda a yanzu komai ya fice mata a rai, gara tayi wannan, ta yiwu Allah ya yafe mata sanadiyyar hakan, Dakyar ta iya wanke mata kashin ta canza mata gurin kwanciya, saida ta gyara dakin tsaff sannan ta fita dan shan iska.. Tana zama taji sallamar su Papy da ahalinshi da su Anni, nan fa ta mike ta dinga musu maraba, yadda ta fita hayyacinta sai wanda dama ya santa shi zai ganeta, duk da yanzu suna samun gata domin Raliya na taimakonsu sosai.. Bayan sun duba jikin Goggo suka koma dayan dakin suna ta hirar yaushe gamo, Awan su ďaya sai ga su Hafeez da 'yayanshi uku.. Suwaiba, Adam, da Autan wanda yake hannu mai sunan Papy, sai Husna da ta zama big madam, Dakin suka shiga suka gaida su Mummy sannan suma suka zauna akayi hirar dasu.... Daddy ka dawo ne? akwai abin da nake so mu tattauna.. Raliya ta faďi cikin girmamawa kamar yana gabanta, "Eh Raliya, muna kaduna, jibi zan koma lagos kina iya zuwa gida yanzu, Cike da jin daďi ta mike ta fara shirin zuwa gidan su Goggo dan ta taho dasu Mummy, dama tun last week ta gindaya ma Anty Reemah karyar Goggo ta shiga coma tazo su dubata.. Anty Reemah ta tabbatar mata yau suna nan tafe, saida ta kaiwa su Fadeel abinci makaranta sannan ta wuce gidan Goggo... Taji dadin ganin su Papy, nan take ta shirya plan din da yasa duk suka shirya tafiya gida.. Goggo kaďai aka bari a gida sai Rilwanu dake zaman jiran zuwan iyayenshi.... Suna isa gidan Mummy ta fara hawayen bakin ciki da dana sani, lallai in baka godewa Allah ba to tabbas zaka godewa azabarshi, A darare ta karasa cikin gidan saboda gudun wulakanci a gurin mamallakin gidan... A lokacin da yaji sallamar su yana parlor yana kallon news, da sauri ya mike ya taro Papy yana faďin maraba da proff, bismillah shigo, bai lura da mutanen bayanshi ba saboda yadda yayi kewar ganinshi shekara da shekaru, Saida suka nutsu cikin gaisuwa sannan ya kalli sauran mutanen parlon, yana sauke idonshi kan su Mummy mood dinshi ya canza gaba ďaya, Cike da masifa ya mike zaiyi magana yaji Sallamar su Anty Reemah, nan take fuskarshi ta sauya yace "A'a yau gida yayi albarka, Allah ya sanya alkhairi a wannan taron.. kafin a amsa da Ameen Muryar little Nadeeyah ta karaďe parlorn, *HABIBI*, *YAA OMRI*.. Ta sama Musaddiq ya leko dan jin muryarta kamar amsa kuwwar speaker.. ganin parlon a cike yasashi sakkowa da sauri.. Da ita ya fara tozali rike da kugu tana mishi wani irin kallo, karasowa yayi ya dagata sama ya dinga juyata tana kyalkyala dariya, Wani wawan duka Hilal ya kai mishi a baya sai a sannan ya dakata ya rungumeshi, haka nan ya tsinci kanshi cikin farin cikin da ya rasa na meye, Cikin parlon suka karasa suka gaiggaisa da mutane, Mummy ce kadai ya gimtse fuska kafin ya gaisheta, shi dinma dan yaga su papy ne a zaune da Anty Reemah dake yawan matsa mishi, hirar yaushe gamo palon ya karaďe dashi, Sudai su Mummy suna ra'be kamar Mamma Suwaiba lokacin da take da rai bata da galihu, *Allah kenan*, babu yadda bai iya ba..... Murďa kofar dakin sukaji anyi an shigo ba tare da sallama ba, Yara biyu farare cikin kayan fulani kafarsu tayi butu butu suka shigo suna ta ďari ďari da kafarsu dan kar su faďi, can bayansu kuma mace ce ta shigo naďe da zani akanta hannunta rike da kullin dankwali, sai wani namiji fari da riga budaddiya da layu a duk jikinshi har kunne, Babu wanda a cikinsu ya gane Badariyya, sai Mummy wacce ko a cikin dubu ne zata tsamo ta, "BADARIYYA! "Na'am Mummy ta amsa haďe da fashewa da kuka, karasowa inda take tayi ta rikota haďe da yin wurgi da kayan hannunta, kowa a cikin parlon da ido ya bita cike da mamaki, Zama yaran sukayi a gefe suka matse juna su a dole suna tsoron tiles, Shi kuwa Yareemah Suhail gani yakeyi duk ya fisu muhimmanci a parlon, Hafeez ne kaďai yayi mishi kwarjinin da zai iya tsuguna mishi, direct gaban Hafeez yaje ya tsuguna har kasa irin gaisuwar da akema sarki yace "Ina wuni ranka ya dade, Shi Hafeez abin ma tsoro ya bashi, da sauri ya maida kafarshi baya yace "Ga iyayenmu can su ya kamata ka fara gaisarwa, "Duk cikin runkar nan babu mutum mai muhimmanci, daga kai saini, ranka ya daďe, sauran duk mu ya kamata su gaisar... Kallon mahaukaci duk sukayi mishi suka maida dubansu kan Badariyya wacce take kuka tana neman gafara, Labarin abinda ya faru da ita ta fara basu, har yadda ta taimakawa su Mummy suka raba Nadeeyah da Musaddiq saida ta faďa musu sannan ta roki gafararsu domin ita yanzu rayuwarsu ba irin tata bace... Cike da takaici Daddy yayi daya sanin haďa zuri'a da jinin Ma'u, Wani irin huci ya furzar na bakin cikin irin halayyarsu, mugunta ma har ga kanka sai kayi ta domin biyan bukata, tirrr da dabiyar karnuka irin tasu Goggo ya faďi da kausassar murya... Ke Badariyya... ,tashi maza ki fitar min a gi---- Jiniyar da sukaji ne ya sanya shi yin shuru domin sauraron daga inda jiniyar ke fitowa.... A take Yareemah Suhail ya durkusawa Hafeez kamar zai bauta mishi, Allah yaja ran sarki mai jiran gado, Abubuwa masu Muhimmanci Allah ke yinsu, Mu aron mulki mukayi ta karfin tsiya, kai kuwa Allah ne ya baka shi daga fadar shi, wannan mulkin rubutacce ne a cikin allon Allah, Allah ya baka nasara... Buďe baki Hafeez yayi ya koma can baya, da sauri Husnah ta riko hannunshi suka koma daki dan a ganinsu wata cutar yarima suhail zaiyi mishi..... Mrs Tijjani Shattimah...... [12/06 7:23 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣1⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Cikin azama ta fara tattara langunan gabanta tana turasu cikin lokar katakon dake kofar dakin da aka bata, "Badariyya ina naman da kande tace mu raba? Kinga bana son tashin hankali, ki fito dashi kawai mu raba, wannan ma ai keta ce, Sharce zufar da ke goshinta tayi ta kalli Marakisiyya tace "Na cinye, na bawa Tanimu da jazuli suma sunci, kinga sunci kason uwarsu, ni nawa 'yayan ko kamshi basu ji ba, "Marakisiyya ina namanmu? gashi can su Hannafi suna ci suna mana gwalo, "Tanimu ďan Marakisiyya na farko ya faďi cike da dacin rai.. Maida kallonta gurin Badariyya tayi zuciyarta na k'una ta kasa yi mata magana sai nuni da tayi mata da hannu na "kina jin abin da Tanimu yake faďi? Tsaki mai karfi Badariyya taja ta wuce daki tana goge fuska da zaninta da yasha jiki, Tana sanya kafarta cikin dakin taji an shako wuyanta harda haďawa da labulen tsummar dake kofar dakin, Marakisiyya bata jirayi komai ba ta fara naushin bakin Badariyya tana faďin ina naman mu yake?wallahi in baki fito da naman nan ba sai na yagi na jikinki ya zame mana naman shekarar da bamu ci ba, "Ke ni fa a yanzu saidai a mutu a gidannan, dan wallahi kiriss ya rage in fara maita, in banda mugunta naman da kika san sai shekara muke cinshi shine kika haďa da nawa da naki kika cinye saboda haďama, Wallahi ko ki fito min da naman nan ko inyi fata fata da naman cinyarki, yin karar suya bazai min wahala ba ko Tanimu yayo... Yadda take maganar tana haki idanuwanta yayi jawur ya sanya Badariyya tsurewa, "Tabbas Marakisiyya ta fara maita, cikin muryar azaba jini faca faca da bakinta tace "Sakeni zan baki! Sake shake ta Marakisiyya tayi tace "Ai saidai muje tare, wallahi babu inda zaki ke daya, matsiyaciyya mai bakin hali, Kuka Badariyya ta fashe dashi ta fara tafiya har ta isa gurin da ta boye naman, tana sa hannunta taji an wafce langar harda hannunta sannan ta hankadata jikin katakon, kusar dake jiki ta caki tsakiyar goshin Badar, Wani irin ihu ta tsala wanda ya tattaro hankalin mutanen cikin yalwataciyyar bukkar sarkin, Kande ce ta isa gareta ta toshe mata gurin jinin sannan ta shige da ita daki, ita kuwa Marakisiyya ko a jikinta, namanta ta tusa a gaba suna yaga ita da 'yayanta..... ****** Nayi Nadama, Na tuba, wallahi na yarda zan zauna da kai, yanzu 'yayana biyu da kai, Hannafi, da Suwidi, ina zan tafi in barsu? dan Allah ka yenta ni kamar yadda ka yanta gimbiya Sailuba, na saduda zan zauna dakai, wahalar da nake sha a gidannan ta isheni, ka taimakeni ka kaini inga iyayena ko sau ďaya ne takk, nayi alkawarin bazan bujire maka ba duk abin da kake so shi zanyi---- ta karashe cikin matsanancin kuka.. garin maganin da aka sa mata a goshi ya murmuso mata a ido... Dariya yayi sosai yace "Wuya makarantar kare, To ai dama laifinki ne da kika biye wa mai son zuciya irin Marakisiyya, da a yadda aka kawoki gidannan kinyi min ladabi da babu abinda zai hanaki fin Sailuba fada a guri na, to sai kika nuna kinfi Marakisiyya rashin imani, shiyasa na nuna muku karfina a kanku, na sanya ku kuka zamto tamkar karnuka, tunda kin gane kanki yanzu to baki da matsala, zan kaiki kiga yan uwanki nan bada jimawa ba, amma sai naga kamun ludayin nadamarki, in har kika canza hali gaba daya to babu wanda zai kaiki jin dadi duk cikin matana domin na fi kaunar kasancewa dake.... Janyota jikinshi yayi cikin wani irin siga ta sha'awa, karfin turaren dake tashi a jikinshi ya kusa zautata saboda tsabar rashin dadi, wasu zafafan hawayen dana sani ne ya dinga kwaranya a cikin idanuwanta, dana sanin rashin kasantuwarta mutuniyar kirki har halayyarta da kaddararta ta sanya wannan masifar afkuwa da ita, tunano irin rashin mutuncin da ta dinga yi ma yan uwanta musamman Nadeeyah da Musaddiq tayi, da ace lokaci zai sake bata dama, da ta kaunaci har mai gadin gidansu, da ta nuna ma yan uwanta kauna domin tana tsananin kewar su... Ta sha wahalar da ko makiyinta bata fatan yasha, mace kamar ita ace bata da zanin kirki da take daurawa, dakin baccinta babu ko katifar da zata sanya hakarkarinta, ba'a ma maganar hasken lantarki domin bata taba ganinshi a gidan ba, duk yadda mai karatu ke auno kuncin rayuwar da Badariyya take ciki ya wuce haka domin kunci ne na mutane marasa galihu da 'yancin kai, 'ya'yanta da ta samesu ta hanyar tursasawa, tamkar almajirai saboda tsabar wahala da suke sha, tasan tabbas in akayi bincikenta abin da za'a fara cin karo dashi a tare da ita shine infection, sannan wasu ciwukan su biyo baya, Runtse idonta tayi saboda azabar da takesha na cakalkalata da yakeyi, saida yayi fin awa yana abu daya, bayan ya gama yayi mata albishir da indai tana san ganin yan uwanta to ta cigaba da kasancewa mai biyayya da dauriya a gareshi kamar yadda ta kasance mishi a yau...... *Canada* Ohhh.. ya Allah Mukhtar ai sai ka karyani, ajiye remote din hannunta tayi ta karbi cupin da ya bata, "Mashaa Allah, nasan jika na is the best, Allah ya albarkaci rayuwarka.. ta karashe haďe da sumbatarshi... "Barka da gida Aunty!! Nadeeyah ta faďi a ďan russune, "Barka dai ta amsa babu yabo babu fallasa, ta cigaba da yi ma junior wasa.. Ciki Nadeeyah ta wuce ba tare da ta damu da yadda Anty Saude ta amsa mata gaisuwarta ba, ko wacce uwa hakan zatayi in dai danta ya fuskanci abunda Taheer ya fuskanta, soyayyar da take nunawa Junior shi yake sanya zuciyarta sanyi a duk lokacin da ta ga irin halin ko in kulan da Anty sauden ke nuna mata, kula babu wacce bata yi mashi, ita ko me zata ce mata banda godiya, sannan tana rokon Allah ya kawo lokacin da zata saka musu da mafificin alkhairin da sukayi mata..... "Me zaka ci?, noodles ko peppersoup? Kallon Taheer Junior yayi yace Daddy me zamu ci? A'a my dear ba cin abinci yanzu sai anyi wanka, jeka Mamma tayi maka wanka kazo muci duk abinda kake so, "Kallon Anty Saude yayi cikin fuskar mamaki yace "Momma ba kince ni zan dinga yin shower da kaina ba, ni dai ba wanda zai min wanka, "Yess big boy jeka toilet dina kayi wankanka, amma fa kar kayi min barna, kuma ka wanke kanka da kyau kaji? Gyaďa kai yayi ya nufi bayin da gudu bayan ya watsar da dukka kayanshi a parlon..... "Momma... wai meyasa har yan---- look Tee, Dan Allah kar mu fara wannan zancen, go and get urself ready kazo kaci abinci, kayi abinda kake so na kyaleka,, ka barni inyi abinda nakeso... Mun fara magana dakai akan Amal, zan kira Mus'ab anjima in sha---- Bai karasa jin abinda zata ce ba ya mike yayi hanyar dakinshi... Taheer lokaci yayi da bazan zauna in zuba maka ido ba, wallahi tallahi cikin kwanakin nan zakayi aure.... Dariya sosai yayi saboda yadda ta daga murya, bai waigo ya kalleta ba ya shige dakinshi yana cigaba da dariyar da yasan zuwar mishi kawai tayi babu shiri, Gefen katafaran gadonshi ya zauna haďe da dafe kanshi, "Ta ina zai fara sanarwa da Momma abinda ke ranshi, yasani sarai ko za'a haďi sama da kasa bazata yarda ya auri Nadeeyah ba, da yaya ma ta yarda da zamanta a gidan, saida ta gindaya mishi tsauraran sharudda akan Nadeeyah kafin har ta yarda da zamanta, Haihuwar junior da tayi ita ta sake samarwa da mahaifiyarshi kwanciyar hankali domin Allah ya daura mata son yaron... kishingida yayi yana tunano baya lokacin da ya fidda rai da samun muradin ranshi, Sai gashi kaddara ta haďasu a lokacin da bai taba zato ba........ *Tuna baya....* Suna isa asibitin ya fito daga motar dakyar, Mutumin da ya sasu a mota ya taimaka mishi suka shiga da ita saboda yanayinshi na buguwa da kuma jini da daketa zuba a kanshi, da sauri nurses suka iso garesu suka sanyata akan gado, Dishidishi Taheer yake gani saboda karfinshi ya kusa karewa, bayan nurses din yabi har zuwa kofar dakin emergency, suna gab da shiga ganinshi ya sauka a kan Nadeeyah da gefen fuskarta ya baci da jini, a firgice ya karasa kusa da gadon ya fara kiran sunanta yana kuka sosai, Dakyar mutumin da ya rakosu ya rabashi da gadon ya zaunar dashi a kan kujera, karfafa jikinshi yayi ya dauko wayarshi ya shiga neman number Anty Raliya, dakyar ya iya ganin number dan hankalinshi ya fara gushewa, Ya kira wayar yafi sau goma bata daga ba, cikin neman mafita yayi kiran uncle Kamal, ringing biyu tayi ya dauka, Cikin wahalalliyar murya yace mishi yaje gidan Alh Mukhtar kyari ya sanar dashi hatsarin da sukayi, Rashin sa'a akayi Kamal yace mishi yana hanyar dawowa daga Abuja, amma gobe da sassafe zai safe zaije gidan ya sanar musu, sunan asibitin da suke ya faďa mishi sannan ya kashe wayar dan gaba ďaya jijiyoyin kanshi sun daina aiki, Ba karamin tashin hankali kamal ya shiga ba na jin muryar Taheer, yana kashe wayar ya nemi *Comr-David* ya sanar mishi da halin da Taheer yake ciki sannan yasashi zuwa asibitin dan ganin halin da yake ciki... Kafin zuwan David har Taheer ya faďi unconscious, cikin kankanin lokaci shima aka bashi gado... Washe gari Yadda David ya ga jikin na Taheer ya tabbatarwa da Kamal suna cikin mayuwacin hali, ya kamata ya sanarwa Anty Saude saboda gudun bacin rana, Hankali a tashe Kamal ya a jiye wayar ya sake kallon masu gadin kofar gidan da sukayi bake bake suka hanashi shiga, Rokonsu ya shiga yi akan suje su fadama me gidan hatsari yarshi tayi, cikin halin ko in kula suka daka mishi tsawa suka tabbatar mishi babu kowa a cikin gidan... Rasa abin yi yayi gashi Taheer bai san inda yake ba, motarshi ya shiga ya koma gida ya soma shirin tafiya Lagos...... Yana isa bai bata lokaci ba ya kira Anty Saude ya sanar da ita, rikitashi tayi da kukanta tace maza ya shirya su taho nan zaifi samun kula, bai mata musu ba ya koma dakin da Taheer yake... Doctorn da take kula dasu doctor Marliyya batayi jayayya da Kamal ba tayi yan rubuce rubucenta ta bashi sannan ta shawarceshi da ya bari su farfado saboda komai ya tafi mishi cikin sauki, ta dade tana faďa mishi irin Halin da Nadeeyah take ciki, sannan ta faďa mishi tana dauke da karamin ciki, barinta ta farfaďo yana da matukar muhimmaci, Na'am yayi da zancenta ya gaza furta mata ba tare da Nadeeyah zasu tafi ba saboda kar taga rashin hankali da kyautawarsu..... Nadeeyah... Nadeeyah... Na-dee-yaaàaa.... ya furta da ďan karfi, da hanzari Kamal da David suka shigo dakin, Kwanta Uncle T, baka da karfi a jikinka, Alhamdulillah tunda ka farfaďo, dama na riga na yanki ticket 8pm jirgin mu zai tashi, "Where is Nadeeyah Kamal? Ya tambaya dakyar yana dafe kanshi.. She will be alright Tee, lafiyarka itace abin bukatarmu, i went to der house ance babu kowa, in na kaika gurin Anty safely zan dawo in sake komawa gurin yan uwanta, i promise u i will neva lv her alone Taheer, trust mee, Runtse ido Taheer yayi hawayen dake boye a idonshi ya sauka a kumatunshi.. "Ba babanmu daya ba, iyayenta sun rasu shine Daddynmu ya daukota ya dawo da ita gidanmu... "Gara kai Uncle, kana ganin Mahaifiyarka, ni fa bani da dukka, maraici ya kangeni gaba da baya, bamu da kowaaaaa.... Mikewa yayi dakyar bayan ya gama tunano kadan da ya sani daga labarin Nadeeyah... Cannular dake hannunshi ya cire ya fara tafiya dakyar zuwa Dakin da Nadeeyah take Kamal da David na binshi a baya... Ganinta da oxygen ya sanyashi zaman dirshan a gaban gadonta, kuka ya shiga rerowa mai sosa zuciya wanda komin rashin imaninka sai ka tausaya mishi, Dan Allah karki mutu Nadeeyah, Karki mutu ki barni da guilt din kashe abinda zuciyata tafi kauna, Dan Allah ki tashi... "Zata tashi ranka ya daďe, wata nurse ta faďa mishi cike da tausayawa, "Yaushe? Yaushe zata tashi?, Dan Allah ku tasheta---- "Calm down Taheer, tunda suka ce zata tashi she will be fine, ka tashi mu tafi, cikin raďa Kamal ke maganar, Wata gigitacciyar tsawa Taheer ya dakawa Kamal wacce ta sanya kanshi juyawa ya tafi tagaga, Tsugunawa Kamal yayi ya rukoshi yace "Meyasa kakeson wasa da rayuwarka, why Tee? Plss Kamal kasan yadda zakayi mu tafi tare da Nadeeyah, i will call her Aunt, in taji sauki zan dawo da ita, nasan ba karamin abu bane ya fito da ita da daddare da akwatinta, plsss Kamal, Yadda yayi maganar yana ambaliyar hawaye ya karya zuciyar Kamal, "Karka damu in shaa Allah zamuje da David muyi mata duk abin da ya dace... Nurse din dake tsaye a kansu tace "ku samu Dr Marli, she will help alot da report dinta, ba shine mijinta ba? N--- Yess nine yayi saurin katse Kamal, fine biyoni muje, in shaa Allahu ko gobe zaku gama mata komai, Taimaka ma Taheer sukayi ya koma daki tayi mishi allurai sannan suka wuce office din Doctor....... A daren da zasu tafi a daren Nadeeyah ta farfado, ba karamin farin ciki Kamal yayi ba dan yanzu kam zasu san inda wani nata yake dan wayar Taheer tun daren ranar basu sake ganinta ba... Da matsanancin kuka ta farka amma ta gaza furta komai dan daga ta buďe idonta zata maida ta rufe, hawaye ne kaďai bai yanke mata, ga azabar ciwo da take ji a hakarkarinta da hannunta, babu irin tambayar da Kamal baiyi mata ba taki kulashi sai ma kallo kawai da take binshi dashi, Dr Marliyya ce ta hanashi matsa mata domin gudun kar wani abu ya sameta, badan yaso ba ya kyaleta har suka fara shirin tafiya airport a motar asibitin..... **** Satin Taheer ďaya ya warke sosai kamar bai taba ciwo ba, saidai ita Nadeeyah kamar lokacin ciwon ya sameta domin ta jikkata sosai a jikinta, Sau huďu Kamal na zuwa gidan Alh Mukhtar sai ya samu a rufe, karshe karya yayi ma Taheer yace mishi sun bar kasar kwata kwata, sannan Number Raliya sam basa samu, haka gidanta sau uku mai gadin gidansu na zuwa bai samunta.. Da haka Taheer ya hakura ya maida hankalinshi kan nemawa Nadeeyah lafiya, duk wadannan abubuwan da yakeyi yana yinsu ne kawai dan Allah da kuma wani abu da yake ji a cikin jininshi game da Nadeeyah, amma bawai dan ta dawo mishi ba, tunda yaji labarin tana da ciki yasan lallai Nadeeyah tayi mishi nisan da bazai taba kamo ta ba, yasan duk inda mijinta yake yana nan yana nemanta, ya dauki alwashin sai ta warke sarai sannan zai maida ta gidan mijinta domin shine silar ciwonta... Watanta uku ta fara tafiya kaďan kaďan da taimakon su Amal da Aman domin Taheer ko rabar kusa da ita bayayi, shidai burinshi ta warke sosai, a kullum in ya tambayeta number wanda zata kira sai dai ta fashe mishi da kuka, samm bata da number Hafeez da shi zata bayar domin tasan yana can cikin tashin hankali, number Hilal ma in tayi yunkurin kawota kanta sai ta manta domin gargadin da su Raudha sukayi mata na su ba danginta bane.. wahalar da take sha kashi biyu ce, ga ta rabuwa da Musaddiq wacce tayi mata kiki kaka a cikin zuciya, ga kuma ta azabar ciwo wanda take tunanin babu ranar warkewa.... Cikinta na wata takwas da kwanaki ta warke sarai har tana iya hawa da sauka, babu wanda baiyi farin ciki ba a cikinsu, Anty Saude kula sosai take bata domin bata san wacece ita ba a lokacin, duk tunaninta wata ce daban wacce danta ya bige da mota yake taimaka mata... *Nadeeyah....* Ajiye ice cream din da take sha tayi tace "Na'am uncle, kujerar da ke fuskantar gadon da take ita ya zauna yace "Ina son yau mu kai karshen komai, kinga lafiya ta gama samuwa a gareki, ki faďa min inda yan uwanki da mijinki suke dan in maida ki, nasan yanzu hankalinsu na nan a tashe, a yanzu na daukeki tamkar kanwata ta jini, babu zancen soyayya a tsakaninmu.. bazan so inga wani naki ya cutu saboda ni ba, Dan Allah ki faďa min inda suke domin mu samu mu maida ke hankalinsu ya kwanta muma namu ya kwanta... Tunda ya fara maganar take kuka, "Kuka bazaiyi mana magani ba, ki faďamin matsalarki, in zan iya inyi miki maganinta, nasan bani da hurumin sanin damuwarki, dan Allah ki faďa min ko zan samu sukuni.... "Ya sakeni, Mijina ya sakeni, sun ce kar in sake zuwa inda suke, sunce bani da asali uncle.. bani da number wayar yayana, yana zaune a gombe, nasan shi kaďai ne yake cikin damuwa, sai Papy, sai kanwata Zainab.... Rashin asali na bazai barni in zauna cikin masu asali ba, nasan mahaifina mutumin kirki ne, ba barawo bane kamar yadda su---ka fadaaa.... runtse idonta tayi saboda yadda taji wani irin ciwo a bayanta... Share hawaye Taheer yayi bayan ya dawo daga shock din labarin sakin da ta bashi.. Mikewa yayi saboda yadda yaga tana cije baki, Subhanallah, lafy? Ya faďi da karfi bayan ya isa gurinta, mararta ta rike tana kokarin mikewa ta kasa, "Momm---- gani nan Tee, gani nan, ina jinku, duk abinda kuke faďi inaji, ashe dama itace Nadeeyar da ta yaudareka? "Momma plss help her, in muka dawo gida zamuyi maganar nan, kinsan sunce kar mu bari tayi labour, c.s zasuyi mata, hararashi tayi ta kamo Nadeeyah domin tasan ciwon nakuda bazata taba barinta cikinshi ba, amma tabbas lokacin barinta gidanta yayi..... Suna isa asibitin babu bata lokaci suka karbeta sukayi aune aunensu, bayan sun gama suka yankata suka ciro santalellen yaro wanda ya shiga cikin zuciyar Anty saude a ganin farko, farin ciki a gurin Taheer da Amal ba'a cewa komai, tun daga nan yaro ya fara ganin gata ta musamman domin yini yakeyi a hannu... Ranar Suna yaro yaci suna Mukhtar.. Hilal, shima dakyar Nadeeyah ta faďi dan da cewa tayi su sa da kansu, duk yadda Anty Saude taso ta nuna ma Nadeeyah bata kaunarta Taheer ya hana domin ya nusar da ita cewar ba laifinta bane... Akwai wani dare da tace mishi "Kar dai so kakeyi ka koma gurin bazawarar yarinyar nan, to wallahy Taheer in har tunaninka kenan gara ka janye dan bazan taba yarda su kashe min kai ba, karka yarda kace zaka dawo da ita cikin rayuwarka in ba haka ba sai nayi mugun saba maka, Shidai kwantar mata da hankali yayi bai bata amsa ba.... Watanta biyu da haihuwa Taheer ya fara lallabata su tafi gida, cikin kankanin lokaci ta yarda cike farin cikin sake ganin Musaddiq, tasan in yaga gudan jininshi zai dawo da ita su cigaba da rayuwarsu cikin kaunar juna, Saboda tsabar sonshi da takeyi ta manta da irin wulakancin da yayi mata shi da su Anty Raudha, tayi musu uzuri na ajizancin dan adam... Ganin yadda take farin ciki ya sanya Taheer soma shirin tafiyarta, ranar da suka tafi tare dasu Amal saida Anty saude tayi kewa, tayi matukar sabawa da Junior, komai ita ke mishi, tsanar da tayi wa Nadeeyah sam bata shafi danta ba, domin sau daya takk a rayuwarta ta taba samun opportunity din raino, sai gashi Allah ya kawo mata wani wanda kaddarashi tazo da ta tsani mahaifiyarshi, Soyayyar Taheer ce kadai tasa ta yarda Nadeeyah ta zauna har wadannan kwanaki, sai kuma soyayyar dan mala'ikan Allah..... Lagos Nigeria.. Da murnarta ta sauko a cikin motar haďe da lumshe idonta, memories din baya ya shiga yi mata yawo, kofar gate din ta kama ta tura, Mummunan gamon da tayi shi ya sanyata sakin kofar Garammmmmm.... ta koma motar su Taheer da sauri tana sheshshekar kuka... "Lafiya Nadeeyah? Menene, "Muje kawai uncle, zanyi maka bayani, tada motar yayi yajata ya fita daga layin ya wuce hotel din da ya sauka kwanakin baya, daki biyu ya kama da parlor, saida suka gama kimtsawa sannan ne ya tambayi Nadeeyah da har lokacin bata bar kuka ba... "Babu amfanin komawa garesu Uncle, sun manta dani, Musaddiq ya riga yayi aure, ya auri Faida wacce tayi sanadiyyar rabuwarmu, Dan Allah uncle karka matsamin in koma gurinsu, domin rayuwata bazata taba inganta ba, bazasu taba barina na zama independent ba, kowa a cikinsu ya manta dani, bani da sauran gatan da ya wuce in nemi ilimi, ku tafi kawai, zan shiga duniya neman ilimi har Allah yasa in dace da tsayuwa da kafafuwata... Tissue ya mika mata yace ta share hawayenta, wayarshi ya dauka ya kira number mai gadin gidansu ya sashi ya duba ko Raliya na nan.. saida yayi kusan minti goma sannan ya kirashi yace bata nan amma ya samu number da take aiki dashi yanzu, cike da murna ya umurceshi da ya turo mishi, bayan ya turo mishi ya wuce daki dan kiranta, yana kira ta daga kamar dama tana jiran wayar, "Hello salamu alaikum, ameen wa alaiki salam mummyn Fadeel, ya gida? Cikin rashin sanin muryar tace "lafiya kalau ya harkoki, fine alhamdulillah ya faďi yana gyara zama, Taheer ne, in bazaki damu ba dan Allah ina son ganinki, Ayya Taheer ya su Anty saude, shikenan sai kuyi zamanku haka akeyi.. dariya yayi yace "Ba haka bane karatu ne ya rikeni, ina Fadeel? Gashi can yana wasa, yaushe zaka zo? Gobe da safe in shaa Allah, to Allah ya kaimu Taheer, sai kazo..... Washe gari suka hau jirgi zuwa kaduna, saida ya fara sauke su Amal a gida suka ci abinci suka huta sannan suka wuce gidan Anty Raliya... Basu sameta a gida ba saida suka jirata har na tsawon minti goma.. Ayi min afuwa Taheer, na kusa fara exams ne walhy, ban cika samun zam---- muryarta ta kakare saboda yin tozali da Nadeeyah da tayi, Mutsitstsika ido tayi haďe da sakin hannun Fadeel, Na---dee--yahh.... ta faďi cikin rawar murya, rau rau idon Nadeeyah yayi tace "Na'am Anty, kirji Raliya ta rike itama idanuwan nata suka kawo ruwa, "Nadeeyah, dama kina nan a raye? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina kika shiga? Kasa bata amsa tayi sai kuka mai karfi da ta fashe mata da shi, zama Anty Raliya tayi ta rungumo Nadeeya tana share hawayen farin cikin, Taheer ina ka nemo mana Nadeeyah, shekara ďaya da watanni kenan muna nemanta, an shiga matsaloli sosai na rashin ta, ashe tana nan da rai.. Alhamdulillah, Allah nagode maka da ka dawo mana da Nadeeyah cikin koshin lafiya, kankame Nadeeyah tayi tana shafa bayanta haďe da kukan farin ciki.... kushun kushun din yaro taji yana shirin fara kuka, hannun Taheer ta kalla taga ya daurashi a kafadarshi yana jijjigashi, kallon mamaki ta bishi dashi tace "Taheer kayi aure ne? Babynka ne? ina Mamanshi? Duk wadannan tambayoyin tayi su ne cike da zullumin kar yace mata Nadeeyah ya aura, tasan in hakan ne tabbas rayuwar kaninta na cikin hatsari.. Jin Babyn tayi a kusa da ita tayi saurin kallon Nadeeyah da ta fara kokarin bashi nono, dago kai tayi da sauri taga Taheer har ya fita daga dakin saboda ya bar Nadeeyah ta shayar da Babynta... Nadeeyah yaushe kukayi aure? Ya salam ta faďi haďe da dafe kai hawaye ya sauko a idonta... Daura mata babyn tayi a hannunta tace "Danki ne, jininki ne Anty, dan yaya Musaddiq---neeee.. ta karashe cikin kukan tunanin Musaddiq yayi mata nisa... Wata irin runguma Raliya tayi ma Junior ta dinga sumbatarshi tana zubar hawayen farin ciki, tabbas wannan jininta ne, komai nashi na mahaifinshi ne, wayyo Allah, wannan ita ake kira *Zazzafar Kaddara*, ina ma Musaddiq zai iya zuwa yanzu yaga gudan jininshi... kuka sosai ta dinga yi tana sambatu a fuskar Junior.... Mrs Tijjani Shattima..... [12/06 7:55 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣8⃣ By *Aysha Ya'u kurah* A tare suka waigo dan ganin wanda yayi wa kofar gidan haka kamar dama yanada haushin gidan, horn din da zubair yayi ne ya sanyasu manta batun kofar Hilal yaje ya bude mishi gate din.... Daya bayan daya sheik ya kalli su Papy da su Baffa, ganin har ya gama kallonshi bai dire idonshi kan yayarshi ba ya sanya shi tambayar inda take, Baffa da tun shigowarshi gurin ya ke kallon Sheik yana hasashen da ya tabbatar gaskiya ne, Daddy ne yayi karaff ya fara ma sheik nasiha da sigar tunatarwa sannan ya nuna Baffa yace wannan shine mijinta, wannan kuma danta ne, Allah yayi ma twin sis dinshi rasuwa, introducing kowa na gurin Daddy yayi mishi sannan ya karashe da cewa Nadeeyah is no were to be found, bamu samu gawarta ba shiyasa muka yarda da cewa she is alive, Baffa ne ya cigaba da magana bayan Daddy ya dire ya ba sheik labarin yadda rayuwar Atika ta kasance da yadda kullum bata da magana sai tashi, har ranar da zata koma ga mahallincinta saida ta ambaci sunanshi.... Kukan da sheik yakeyi mai sauti shi ya katse Baffa daga bashi labarin Atika, babu wanda ya hanashi zubda hawaye saima wadanda ke tayashi irin su Papy, Baffa da Maleekah, saida sukayi mai isarsu sannan suka fara tsagaitashi saboda nasihar da Daddy ya cigaba dayi, Labarin gararin rayuwar da Papy ya gani suka bashi wanda ya sake jefashi cikin mamaki da tsananin tsoron Allah, sosai Sheik yayi bakin cikin rashin sake ganin yayarshi, amma yayi murna matuka da ganin yadda zuri'ata ta yaďu gwanin ban sha'awa duk da baiga mutum biyu ciki ba, daya bayan daya ya shiga rungumarsu kamar zai maidasu ciki, farin cikin kasantuwa da yan uwa baya misaltuwa, a wannan rana sheik ya kira Hilal da alherin rayuwarshi, dan a sanadiyyarshi ne ya haďu da yan uwanshi na kusa, zuri'ar yar uwarshi da tasoshi matuka...... Masauki na musamman Daddy ya kamama Sheik da iyalanshi, a can ma saida suka raba dare suna hira kamar babu gobe.... Jamal da Ruwaida ne zaune kusa da Maleekah suna faďa mata yadda suka daďe suna kallon films dinta, cike da jindadi tayi musu alkawarin tafiya tare dasu domin kallon sabon film ďinta Saheebul qalbee, sun dade suna hira haďe da daukar hotuna, sai kusan 12 na dare suka fara shirin zuwa masaukinsu suma.. Har waje ta rakasu tana karewa kasar da bata taba zuwa ba kallo, Har motar su Papy ta bacewa ganinta bata koma ciki ba saima waje da ta fito tana zagayawa dan karewa arear kallo sannan ta jira ganin fitowar Hilal da ke can kasa yana ma Abbunta order irin coffeen da yakeso duk dare.... "Omoo see fine girl.. wani dan bayerabe ya faďi bakinshi kunshe da wiwi, dayan da gaba ďaya a buge yake yana kallonta dishi dishi yace "O boy i no see anything, kamo hannunshi yayi suka nufi inda take takunta day day hannunta rungume da kirjinta, rigar dake jikinta girmanta duka bai wuce gwiwa ba, sai dan karamin mayafi da ta ďaura shi akanta, Suna karasowa kusa da ita taji wani mugun warin da bata taba jin irinshi ba duk rayuwarta, da sauri ta matsa baya tana faďin "Ya subhanallah, sake matsota sukayi gadan gadan har suka samu sa'ar cafke hannunta, gaba daya yanayinsu kyama ya bata hakan yasa ta fara masifa cikin harcen larabci tana kokarin kwatar kanta, da taga sunfi karfinta kuma suna janta iya karfinsu ta saki wani ihu tana neman ceto, Shurun unguwar ya sa babu wani mataimaki a gurin sai Allah, kara karfin ihunta tayi lokacin da taga sun nufi wani lungu da ita, "Ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagithu.... hakan ta dinga faďi hawaye na fita sharrr daga cikin idonta... Full light aka saki wacce ta haska gurin da suke, basu saketa ba sai sa hannu da sukayi suna kare fuskarsu suna masifar dalilin haskasu, A haka Hilal ya bar motar ya fito da sauri ya nufi inda suke, ganin haka yasa dayan me makami sakinta ya zaro wuka a cikin aljihunshi ya tsaya a gaban Hilal, a ruďe Maleekah ke rokon Hilal da ya koma kar su kashe shi, bai ma san abun da ta ke cewa ba dan hankalinshi yafi tafiya gurin dayan dake luguiguitata, Tsugunawa kasa yayi da niyyar cire takalminshi yayi saurin jan kafar mai rike da wukar, sara ya kai mishi a hannu kafin ya ankara yajishi a kasa, sosai saran ya shiga hannun Hilal wanda baisan dashi ba saida ya danneshi ya kwace wukar haďe da tattakashi, shiko dayan na ganin haka dama ba cikin hayyacinshi yake ba yayi saurin ja da baya, kamoshi Hilal yayi ya nakaďa mishi mugun dukan da duk suka kasa motsi, wurgi yayi da wukar haďe da yin gaba yana mai dafe inda jinin ke zuba, A guje ta biyo bayanshi ta kwance dankwalin kanta tana kokarin kama hannunshi dashi, ture hannunta yayi da karfi har ta kusa faďuwa ya buďe motar ya shige, "Ta inda kika bi kikazo nan ki bi hanyar ki koma masauki.. yana kaiwa nan ya tada motar da karfi yana shirin janta, buďe kofar tayi da sauri tace "Heartless being, so zaka iya tafiya ka barni a nan a matsayina na bakuwarku? "Kokarin banbare rikon da tayi mishi yayi ya kasa saboda tayi mishi mugun riko, kallon cikin idonta da yayi jawur yayi yace "let go off me! Sake dukunkuneshi tayi haďe da noke wuya, yadda tayi da baki tana shirin fara kuka ya sanyashi kashe motar haďe juyar da kanshi gefe, ganin haka yasa ta sa hannu ta buďe bayan motar sai a sannan ta sakeshi tayi saurin shigewa ciki.. kuka sosai ta shiga rerowa kamar karamar yarinya, gaba daya ta tsorata da Nigeria gani takeyi kamar in ta sake kwana ďaya za'a iya kasheta bayan an lalata mata rayuwa, Jan motar Hilal yayi ya maida ita masaukinsu, sosai kukan da takeyi yake taba mishi zuciya, sakkowa yayi ya buďe bayan motar, "Its late, i want to go home, dago kanta tayi ba tare da ta kalleshi ba tayi saurin bin dayan gefen ta ruga ciki da gudu tana sake yin wani sabon kukan... Rufe motar yayi da niyyar bin bayanta sai wata zuciya ta haneshi da yin hakan, motar ya shiga ya tada ya canza wata hanyar da ya tabbatar zata kaishi gida domin gudun sharrin dare da na mutanen da suka samu matsala.. .. Washe gari tun asuba Maleekah ta shirya ta wuce dakinsu ummi... Bugu sosai tayi ma kofar wanda ya sanyasu mikewa a tare dan ganin mai dukan kofar haka, "Lafiya? Ummi ta tambaya haďe da janyota cikin dakin, Jakar dake hannunta ta ajiye ta karasa kusa da Abbu tace "Abbu ka shirya mu tafi yau plss, i hate Nigeria, yadda takeyi kamar zatayi kuka ya sanya shi zaunar da ita haďe da tambayarta abun da ya faru, labarin abun da samarin nan sukayi mata ta bashi sannan ta kare da cewa "Ta rantse bazata sake kwana a kasar nan ba! Jin haka Sheik ya bata hakuri akan ta bari ya gama yan uwanshi dan yayi niyyar tafiya dasu, "Noo Abbu, ka tsaya ka tafi tare dasu, we will go with Jamal nd Ruwaidah, gamsuwa yayi da maganarta bayan ya tabbatar da hakan ya gamsar da ita... Karfe goma na safe dukkan ahalin suka iso masaukin Sheik, bayan an gaggaisa duk suka haďu sukayi breakfast cike da kaunar juna sannan suka shiga hira sosai, Matan na bangarensu haka mazan ma, anan ne Sheik ke sanar dasu komawar Maleekah ya kuma ce tare zasu tafi dasu Jamal, cike da murna Papy ya amince dan dama cikin hutu suke, shi kuwa Jamal aiki ake nema mishi, "Na dauka sai tayi sati daya itama? Daddy ya tambaya yana dariya, Murmushi Abbu yayi yace "Akwai abinda zai maida ita, sannan she is not comfortable here, kaga ita kadai ce mace, "Sai in kaita gurin Husna, itama dan bazata iya zuwa bane shi yasa na barta a gida, Hafeez yayi karaff ya amshe saboda yana matukar jin dadin ganinta, ko ba komai tana ďebe mishi kewar mutane biyu a idonshi, Dariya sheik yayi yace "Bazata yarda ba ai, next time zatazo ta dade muku in shaa Allah, nan suka kauda zance suka shiga wani zancen daban na tsara inda zasu je ziyara ya ga yan uwa wadanda suka jibanci yayarshi ko sukayi zama tare, Kaduna... nan ne gurin da suka tsara tafiya washe in Allah ya yarda..... Karfe sha biyu na rana jirgin nasu zai tashi hakan yasa Jamal yin wasu yan siyayya near by dan bada shiri yazo ba, Hilal ke tuka motar yana sauraron duk murnar da su Jamal sukeyi na yin kallo cikin cinemas din turawa.... Ya rasa asalin abun da yake ji a cikin ranshi, duk tunanin da ya dauko sai yayi saurin kaudashi dan ba'a cikin muhallinshi yake ba, soyayyar da yayi a baya bayason sake yin makamanciyarta dan zata iya buga zuciyarshi, ya samu dakyar ya maida soyayyar Nadeeyah wani muhallin daban, baya kaunar sake tsintar kanshi cikin mawuyacin halin da ya shiga a baya, suna isa airport din yayi parking haďe da runtse idanuwanshi yana tuno abubuwa da dama, "Ur problem is lving! Buďe idonshi yayi yaganta tsaye jikin windon gefenshi, bai dago kanshi daga kwanciyar da yayi ba ya zuba mata manyan lumshashun idanuwanshi, ita din ma cikin idonshi take kallo babu ko kiftawa, maida idonshi yayi ya rufe dan a rayuwarshi ya tsani mace a tsaytsaye, abubuwa da dama kan sashi ya ragawa Maleekah, kofar ta buďe tasa hannu ta buďe idonshi duka biyun, nata idon ta gwalo ta turo fuskarta kusa da tashi, Ya Allah... ya fadi haďe da kauda fuskarta, "Maleekah kin tabbatar kina da lafiyar....... kanta ya nuna da hannunshi, haďe rai tayi kamar zatayi kuka tace "Dan ina kulaka shine zaka ce bani da hankali, laifi na ne, "Heyy tambaya ce, ya faďi da ďan sakin fuska.. bata tsaya sauraronshi ba taja hannun Ruwaidah suka wuce ciki, Murmushi yayi bayan yaga kurewarsu yaja motar yayi gaba..... Mrs Tijjani Shattimah........ [13/06 10:15 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣4⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Mamaki sam ya hana mutanen parlon yin magana sai Badariyya data dawo kusa da mijinta ta rokeshi da yayi shuru, in gaskiya ne zasu fahimci hakan da kansu... Jin da sukayi jiniyar taki tsayawa yasa Hilal da Daddy yin waje, Shi kuwa Musaddiq sama yayi da little Nadeeyah dan ya bata chocolates, samm bai tausayawa Badariyya ba domin ta sanyashi cikin ukubar da bata da magani... Suna fita sukayi karo da motoci takwas, huďu daga gidan sarkin Zaria, biyu daga gidan gwamnati sai biyu tasu Taheer, Dukkan motocin numfashi kawai sukeyi, saboda tsabar haďuwa babu wanda a unguwar bai bisu da kallo ba, Dogarai ne suka fito da sauri suka tattare kofafin fitowar kowacce mota, Sarki Tidjani ne ya fara fitowa shi da Shareefah, Sai ďayar motar Sarkin Sassounburom da mutanenshi, Cikin kasaita Anty Saude ta fito cikin wani kasaitaccen lace irin na jikin Shareefa, wuyoyinsu da hayyensu sai kyallin zinari yakeyi.. Samm idon Anty saude bai kai mata kan Daddy dake tsaye a kofar shiga parlon ba.. Motar karshe wacce Kamal ya tuko ita wani dogari ya buďe, Junior ne ya fara fitowa yana rawar wakar *Issa goal* da Kamal yasa mishi, Dariya Anty saude tayi tana kara jin kaunar yaron a cikin ranta... A hankali yake mata magana cike da kauna yana lallabata ta fito, karfin gwiwa ya bata akan babu abinda zai faru, ta fito su tafi, he will not lv her here, Dakyar ya samu ta ziro kyakykyawar kafarta wacce take cikin wani lafiyayyen jan flat shoe mai beza.. Numfashin Hilal neman daukewa yayi saboda ganin yatsun da ko cikin magagi ya tashi zai gane maishi... *NADEEYAH....* ya furta a hankali gabanshi na dukan uku uku.. Bayyana kanta tayi fatar nan sai kyalli takeyi, Ash jallabiya ce a jikinta wacce akayi ma ado da jajayen duwatsu, gyalen kanta bata samu nutsuwar yane shi ba sai nadashi da tayi akan jelar suka sakko a dukka kafadunta.. Rufe kofar Taheer yayi yace "Calm down Baby, babu abinda zai faru, ďaga idon da zatayi dan bashi amsa ta saukesu cikin na Hilal wanda ke tsaye kamar wanda aka dasa... Wani irin sanyi taji ya ratsata ta fara gudu a hankali dan isa gurinshi, "Ya Hilal.. ta faďi cikin muryar kuka, Kauda kanshi yayi dan baya so sam taga hawayen da ya taru a cikin idonshi.. Ganin hakan yasa ta shigewa cikin jikinshi ta fashe da matsanancin kuka, kukan da yake boyewa dole ya sakeshi ya rungumeta shima yana fadin "Kina nan da ranki all this while Nadeeyah, ina kika shiga? Alhamdulillah ya Allah... "Barrister Nadeeyah! ur Nadeeyah is now a Barrister Ya Hilal, i missed u alot... Dago fuskarta yayi yana dariya mai dauke da kuka, "Missed u more, dis is tears of joy, Alhamdulillah... "Nadeeyah... da sauri ta waigo ta kalli Daddy dake tsaye idonshi jajur, 'Kasa ta tsuguna yayi saurin dagota ya haďata da jikinshi... "Kin nuna min ban haifeki ba Nadeeyah, meyasa kikayi min haka? Daddy ya faďi yana mai jin zafi a cikin ranshi na rashin ta cikin wadannan shekarun.. "Kayi hakuri Daddy, kaddara ce, dan Allah kayi hakuri.. "Bana fushi dake Nadeeyah samm banyi fushi ba, Nadai gode ma Allah da yasa zan sake ganinki kafin na mutu.....   " *MG Kyari* cike da mamaki Daddy ya dago ya kalli me maganar... " *SAUDATU HALLIRU*... ya faďi yana zaro ido.... "Ikon Allah.... Anty Saude tace tana rike haba, ashe rai kan ga rai?, "Saudatu kina nan abinki, lallai duniya tanada faďi, shekara kusan nawa rabon da mu haďu, Kaii mashaa Allah Nourun ala nourun ya faďi cike da farin ciki.. Ga kawu na can ka barshi a tsaye... Cikin daburcewa Daddy ya karasa kusa dasu ya tsuguna har kasa ya kwashi gaisuwa sannan yace su shigo ciki... Cikin takun kasaita suka fara takawa har cikin parlon... Kashe wakar Kamal yayi Taheer ya kama hannun junior suka bi bayansu.. Hannu Hilal ya mika ma Taheer da fara'a dauke a fuskarshi, "Wow, matured mind, Taheer ya faďi cikin tsokana, yanzu ba faďa ko? Dariya Hilal yayi  yace we are Family, hannu Taheer ya mika mishi da sauri haďe da rungumeshi.... Durkusawa Hilal yayi ya kalli junior, a hankali ya zare glass din idonshi yace "Mashaa Allah Junior Kyari, Mr soft or Hard? ya tambayeshi yana nuna mishi hannu, da karfi junior ya dunkule hannu ya buga hannun Hilal yace "Mr Hard ofcourse!! Dariya sosai Hilal yayi yace "Name? *MHK TAHEER* amma *MUKTHAR HILAL MUSADDIQ KYARI* ake cemin a school.... Runtse ido Hilal yayi ya kankame Junior kamar zai maidashi ciki, my nmsake, ya Allah.., I love you boy... ya karashe haďe da sumbatar shi..... I love yhu too Junior ya faďi yana mai mayar mishi da sumba.. Hannunshi ya kama suka nufi mota dan su fita ya dan jiyar dashi dadi kafin ya zauna.... A cikin parlon kuwa kowa mamakin ganin Nadeeyah yayi banda Raliya daketa dariya da farin cikin ganin yadda Nadeeyah ta koma... Anty Reemah da Anni kuwa faďa suka rufeta dashi wanda ita kanta tasan na daďi ne.... Sun dade rungume da Anty Reema tana tambayar ina Zainab? Cikin kuka Anty Reemah tace "Tayi Fushi, kika manta da ita ma bare ita, tuni ta mance dake, tana can gida suna jarabawa ne shiyasa ban taho da ita ba... Dakyar Nadeeyah ta iya gane Mummy dasu Raudha, har kasa ta tsuguna ta gaida Mummy wacce fuskarta tayi faca faca da hawayen farin ciki, rungumae Nadeeyah tayi wani irin kamshin sanyi ya daki hancin dukkaninsu wanda tun zuwansu duniya har kawo yau basu taba jin irinshi ba... Dafa kafaďunta taji anyi ta raba jikinta da Mummy ta waigo tana murmushi tana kallon matar cikin rashin fahimta, "Nadeeyah, dan Allah ki yafe min, yadda ta haďe hannayenta biyu tana kuka sosai yasa Nadeeyah rike hannun tace "Me kikayi min, baiwar Allah? Wallahi na yafe miki duk da ban sank---- Badariyyah zanyi fitsari, Hannafi ya katse Nadeeyah yana matse cinya dan fitsarin ya fara zubar mishi, Zaro ido Nadeeyah tayi,, "Badar!! Ke---ce... ta faďi cikin rawar murya, nan take wani tsagoron tsoron Allah ya tsarga a zuciyar Nadeeyah, tana kallon Badariyya ta ďaga yaron da yayi faca faca da fitsari tayi famfon waje dashi... Jikin Papy Nadeeyah ta kwanta bayan ya gama mata faďa tana tambayarshi Ruwaidah... "Tana can gurin su Jamal, a can take makaranta... ya bata amsa yana mai jin dadin ganinta... Husnah da ta tura mijinta daki saboda mijin Badar, ta fito kamo hannun Nour da Abi taga parlon a nutse sai manyan mutane masu rawuna dake zaune kowa na kasa a nutse, Gefen da Papy yake ta kalla ta hango fuska kamar ta Nadeeyah, tasan dai ta baro Maleekah a cikin daki tana sallah, to wacece wannan? Karasawa tayi ta tsuguna ta gaida bak'in sannan ta kai dubanta kan Nadeeyah, "Nadeeyah... ta faďi da karfi har saida Hafeez ya jiyota.. Da sauri ya buďe kofar ya fito yana dube dube yana faďin "Me ya sameta?, duk tunaninshi Nadeeyar Hilal ce, Ganinsu kankame da juna yasa shi saurin matsawa kusa dasu dan ya gasgasta idonshi... "Yaya Hafeez.. ta faďi tana nufo inda yake, Share hawayen dake idonshi yayi ya juya zai koma inda ya fito, Da gudu ta bi bayanshi ta rungumeshi, "Am sorry, dan Allah kayi hakuri, rufe idonshi yayi hawaye na mishi ambaliya.. gabanshi ta dawo tace "Dan Allah yaya.. Share hawayen yayi yace "In kowa yayi deserving haka ni banyi ba Nadeeyah, in akwai wanda ya kamata yasan inda kike to nine, meyasa zaki bar min tabo a raina?, kullum ina ganin kamar gazawata ce tasa kika bace, samm na kasa rike zumuncinmu.. Meyasa zaki min haka? Sake kankameshi tayi tace "Nasan ban kyauta, haka kaddararmu take, Dan Allah kayi hakuri Yaya.... sunfi minti biyar suna tattaunawa kafin ya sauko ya fara share mata hawaye.... Tun fitowar Hafeez Sarki Tidjani ya mike fadawan shi suka fara yan yameshi, haka itama Shareefah da hirar Daddy da Anty Saude ta hanata jin komai ta mike cike da firgicin ganin Hafeez... "ADAMOU YALLO... sarki ya faďi cikin rawar murya, Adamou, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ashe kana nan da ranka Adamou? Ajiye sandar hannunshi yayi ya isa gurin Hafeez, sai a lokacin ya dawo hayyacinshi ya fahimci cewa shekarun da yawa Adamou bazai kasance haka ba, fuskar Hafeez ya shafa yace "Ina Adamou? Mikewa Papy da Daddy sukayi suka isa gurin cikin girmamawa, "Ranka ya dade, ba Adamu bane, wannan Hafeezu sunansa, "Eh na gane yanzu, ina Adamoun yake, nasan tunda naga gudan jininshi dole shima ya kasance a kusa.... Garammm.... gaban mutanen parlon ya faďi, Sai a lokacin yawancin su suka tuna cewa sunan buzu mai gadi marar asali da galihu *Adamu*, Daddy ne yayi saurin cewa "Kwarai Adamu shine mahaifin Hafeezu da Nadeeyah ne, Allah dai yasa lafiya, ya karashe cikin zullumi ko Adamun ya taba yi musu wani mummunan abu ne, "Lafiya kalau sai alheri, Shareefah ta faďi idonta cike da kwallar farin ciki, "Ina Yayana Adamou?? Dan Allah ku nuna min shi, ku nuna min shi ko zan samu salama a cikin zuciyata.... Kallon kallo aka fara yi a cikin parlon, Papy ne yayi karfin halin cewa Sarki ya zauna sai ayi maganar a nutse, Kamo hannun Hafeez yayi suka koma inda yake zaune, share kwallar da ta ziraro mishi yayi yace "Dan Allah ku kira min Adamou, ashe munada rabon sake ganin juna... Anya ba kuskure kukayi ba? Wannan buzu Adamu, mai gadi ne, bashi da wata alaka da sarauta, inajin kamanni ne kawai, kunsan babu yadda Allah bai iya yi cikin halittarshi... Baffa ne ke maganar cikin taka tsan tsan dan kar ya bata ran Sarkin... Murmushin takaici Shareefah tayi  ta nuna Hafeez da hannu tace "In dai wannan jinin Mai gadin ne, to tabbas jinina ne, idan yayana yayi nisa dan Allah ko zan iya samun hotonshi saboda in tabbatar da zancenku in karyata kaina... Cikin azama Daddy ya tashi zai nufi sama, kafin ya karasa Hafeez ya dakatar dashi ya ciro wallet a aljihunshi, kananan hotunan iyayenshi ne suka bayyana, da sauri ya mika mata... *Pappa.....* Ta faďi cikin kuka dan fuskar mahaifinta ta gani a cikin ta dattijo Adamu, shi kuwa Hafeez fuskar Yareemah Adamou Sarki Tidjani ke gani a idonshi, Dan Allah ina yake, Ku faďa mana inda yake?? Sarki ya tambaya cikin ďaga murya... Da sauri fadawa suka shiga faďin Allah ya huci zuciyarka... Baya tare damu, dan uwanku ya rigamu gidan gaskiya, ya tafi inda duk zamu tafi komi daren dadewa, shin dama shi ďin dan gata ne kuka barshi cikin gararin rayuwa? Ya ilahi me muka maida *ZUMUNCINMU A YAU* ace yanzu sai in baka raye za'ayi Zumunci da kai, To Adamu yayi tafiyar da ganinshi yake da matukar wuya, Adamu yayi muku nisa, saidai 'ya'yanshi.... yadda Daddy yake maganar ya sanya Parlon yin shuru, sai tashin sheshshekar kuka.... Cikin matsanancin kuka Shareefah ta zaune a kan carpet tace "Yareemah shine Gata, kalmar Gata in aka zo kanshi an disa aya, Shine ďan Sarkin Agadez *Diya Muradun Abdallah Yallo* na farko, shine Yareeman Agadez.... Kaddararshi a nan take, kaddarar samun magaji a nan Nigeria take, hannayen Hafeez ta rike tana kuka sosai tace "Rubutun Allah baya goguwa, Allah bai nufeshi da zama Sarki ba wanda hakan shine muradin mahaifinmu da duk daukacin mutanen Agadez, lallai sarauta rigar ubangiji ce, ya baiwa mijina wanda yake ďan uwa ga mahaifinka, sannan ya hanamu haihuwa dan dama ya tanade ta ne domin ka.. Wallahi Allah dole ya zama abin tsoro da girmamawa cikin mu bayinsa, domin ya wuce duk yadda muke tsammani, ku duba kuga yadda ya maida dan sarki wanda ya kamata ya zama sarki bawa, mai gadi kaskantacce a gidan bayin da ya kamata su zasu bauta mishi, cikin kankanin lokaci ubangiji ke sauya alkalaminsa, ku dubi nisan Agadez da Nigeria, haka kudurar ubangiji ta ingizo shi nan da taimakon marasa imani da tsoron Allah, duk dan saboda me? saboda yasan akwai wanda ya tanadarwa aron rigar sarautarshi, Lallai zaren kaddara baki ne, ganinshi sai wanda ya halicci kaddarar kanta, haďuwar Taheer da Nadeeyah,, zuwan mu nan domin su biyun duk zaren ne ke janmu ba tare da mun ganshi ba, Allahu Ahad, Allahu Samad, buwayi gagara misali, mai dauke da rayukan da babu wanda yasan adadinsu sai shi kaďai... Naji dadi matuka da Allah bai dauki raina ba sai da naga gudan jinina, rungume Hafeez tayi ta yafito Nadeeyah ta haďesu tana kuka tace "Ina sauran 'yayana? Share hawayen farin ciki Papy yayi yace "ďaya ce ta rage, Zainab, tana can Cyprus tana karatu, ga wacce take rikonta can ya nuna Anty Reemah da hannu, Kiranta gabanta tayi itama ta rungumeta tana mata godiya haďe yin hamdala gurin ubangiji.... Na faďa muku, yanzu kun gasgata zancena? Yareemah Suhail ya faďi cike da kasaita, maida dubansu inda yake zaune shi da 'ya'yanshi sukayi, a harzuke Daddy ya mike yace "Kai ku tashi ku fice min a gida, mikewa Papy yayi ya dakatar dashi yace "Yau ranar farin ciki ce, ka bar shi alkhairin ne zai fitar dashi in shaa Allah..... Labarin irin gatan da Yareemah Adamou ya samu da kuruciyarshi suka shiga basu har kawo sanadiyyar barinshi gida... sannan Sarki ya faďa musu yadda suke da Adamoun ya kuma nuna Taheer yace "Wannan shine dan kanina, shima dan uwan Adamoun ne.... Kallon juna sukayi shi da Nadeeyah yayi murmushi haďe da kashe mata ido, da sauri ta kauda kanta cike da kunya, dadin da takeji a yau kamar an mata albishir da gidan aljanna... Ashe Taheer dan uwan Nadeeyah ne na jini, haba kaunar tayi yawa, Taheer baya taba likewa mace haka, ashe connection din mai karfi ne, Anty Saude ta faďi tana dariyar farin ciki.... Dariya akayi a parlon duk da zuciyar Daddy ta ďan sosu da jin maganar kauna daga bakin Anty Saude..... Baffa ne ya fara basu labarin irin wahalar da Adamun yasha da kuma haďuwarsu da Mamma Suwaiba har mutuwarsu... Cike da jin daďi hira ta barke a tsakaninsu... Har wannan lokacin su Daddy basu san da zaman junior ba dan basu ganshi ba..... Su Mummy bayin Allah suna can dai a rabe har lokacin, sunga karshen asali, kowacce a cikinsu tana cike da dana sanin rayuwa.. Raliya da Reemah ne kadai ke kai kawo a kitchen suna hada hadar haďa lunch, sai Husna, Maleekah da Nadeeyah dake tayasu, Maleekah da Nadeeyah hira sosai sukeyi kamar sun dade da sanin juna, gasu dukkansu wayayyu babu wacce ke jin kunyar yin magana... Bayan sun dan taba abinci duk suka nufi waje dan yin Sallah.. su kuma matan suka nufi daki dan yin tasu a can... Gyara parlon Husna da Nadeeyah sukeyi suna hirar yaushe gamo, labarin abubuwan da suka faru bayan bata nan take bata, ga mamakinta bata ji inda tace "Musaddiq yayi aure ba, sharewa tayi ta kauda tunaninshi a ranta domin yanzu tana son tayi moving forward... rashin ganinshi a cikinsu ya tabbatar mata yana can yana rayuwarshi cikin jin dadi.... Duk wannan budurin da akeyi Musaddiq na cikin daki ya kure volume suna game shi a dole bayason jin wani abu da ya shafi su Badariyya.... Ganin little Nadeeyah tayi bacci ne ya sashi gyara mata kwanciya ya shiga ya watsa ruwa, kananan kaya yasa wadanda suka fitar da kyawunshi sosai, yanzu girma ya sanya Musaddiq ya zama moderate, wannan kibar duk babu ita, sai tsawo sosai da dan murjajjen jiki, kwantacciyar kasumbarshi ya taje ta kwanta lup a fuskarshi, turaruka masu kamshi ya feshe jikinshi dasu sannan ya kashe wutar dakin, Sallah kawai zanyi in nemi abinci, abinda ya faďi kenan haďe da murďa kofar dakin ya fito.... Ta sama ya leko yaga ko an ragu a parlon, ganin bakowa ya sashi fara tafiya cikin kasaita dan isa gurin steps din,  kamar ance ya sake kallon gefen console, Tsaye ya hangota ta maida gashinta gefe tana kokarin cire dankunnenta a jikin rigarta, Hannayenshi biyu ya daura akan karafen da ke kewaye da saman yana kokarin ganin fuskarta ta mudubin... Haaaa... ta faďi bayan ta cire dan kunnen, maida gashin baya tayi ta naďe shi ta goge fuskarta da hannunta sannan ta fara kokarin nade gyalen, jin kamar wani abu yabi ta kunnenta yasata noke wuyan dayan dan kunnen ya sake makalewa, wannan karan ya shiga da karfi, ajiye gyalen tayi ta fara dambe dashi tana tsaki.... Tunda fuskarta bayyana a gareshi ya shiga rudani, da sauri ya mutstsika idonshi yaga ko gizon da ta saba yi mishi ne, ganin dai mutum ce a tsaye ya sashi sake dubawa da kyau ko Maleekah ce, yadda yaga tayi da baki kamar zatayi kuka yasa shi lumshe ido kirjinshi sai lugude yakeyi... "Husnaa... yaji ta faďi da muryar neman taimako, A hankali kafarshi ta fara janshi, shidai yaki gasgata idanuwanshi wadanda suka tara ruwa a lokacin.. Saura kaďan ya isa gareta yaji wani kamshi mai dadi acn gurin na bugo mishi, zuciyarshi ce ta ingiza hannunshi ya dagoshi da niyyar taimaka mata... Mamma... we am back.. Juyowa tayi da sauri ďan kunnen ya fita a kunnenta gaba ďaya, kyammm.. idanuwansu suka makale cikin na juna, nan fa zuciyoyin da suka daďe suna kewar juna suka fara zubar da hawaye a junansu,  daga Nadeeyah har Musaddiq babu wanda jikinshi baya rawa, babu kamar Musaddiq da a lokacin yake jinshi kamar mutum mutumi, Cikin karfin hali da dauriya Nadeeyah ke kokarin raba idonta da nashi amma sam zuciyar da ta daďe tana ďoki da marararin ganin mahaďinta taki bata haďin kai..... A tare Hilal da Musaddiq suka shigo parlon suna ďan taba hira, hirarsu makalewa tayi da sukayi arba da abinda ya sosa ran Taheer.. Hannun da Musaddiq ya ďaga yasa a gefen rigarta ya cire mata dan kunnen har lokacin bai dauke idonshi cikin nata ba... Badariyyah data fito daga kitchen ta tsaya kallonsu zuciyarta sai rawa takeyi hawaye ya shiga yi mata ambaliya.. a yanzu tasan mai gadi ma rayuwarshi tayi mata nisa bare Musaddiq.. Mamma.. Junior ya faďi yana girgiza mata riga, a firgice ta kalleshi cikin sanyin murya tace "Ummm, ina kaje?, "Munje yawo ni da namesake, yace shima sunan mu ďaya haka ne Mamma? Gyaďa mishi kai tayi ta karbi ledar hannunshi ta ajiye ta wuce kitchen da ďan gudu gudu tana maida numfashi..... Bayanta Junior ya fara kokarin bi Musaddiq ya rikoshi da sauri, dafashi yayi ya tsuguna kirjinshi na dukan uku uku yace "My Twinny, Zaro ido Junior yayi yace "Yayyy *MMK*  right? Yess... Musaddiq ya faďi jikinshi samm babu kuzari.. Kallon inda Taheer yake tsaye yayi ya taho da sauri yace "Daddy, zo kaga strangern da na gani a Hallmark, i told u he is just like me, har gaban Musaddiq ya janyo Taheer yace "Kaga idonshi irin nawa, i will not lv here sai nayi grabbing face dinshi, sketch din da nayi baiyi kyau ba.... *Daddy.....* Musaddiq ya dinga maimatawa a cikin ranshi, dakyar ya iya dago kanshi suka haďa ido da Taheer, nan take halittar nan marar dadin faďi a baki ta shiga motsi a zukatansu... Ganin haka Hilal ya karaso gurinsu da sauri yana murmushi, "Hey Kyari, ka ganeshi, Uncle din su Nadeeyah, ashe all this while Nadeeyah is with him.. sun kula da ita sosai da gudan jininka, Janyo Junior yayi kusa da Musaddiq ya haďe hannayensu guri ďaya yace "He is ur blood Kyari, ur flesh and blood.. "Tell him ur name, Hilal ya sake cewa ma Junior cike da doki, *MUKTHAR HILAL MUSADDIQ KYARI* a.k.a *MHK TAHEER* ya karashe haďe da damke hannun Taheer.... Runtse ido Musaddiq yayi yanajin dukkan nauo'in biyu a cikin zuciyarshi, farin ciki da akasin haka, a hankali ya buďe idonshi ya sake tsugunawa a gaban Junior, janyoshi yayi ya rungumeshi tsamm a jikinshi.. Wasu zafafan hawaye ne suka shige tsere tsakanin idanuwanshi zuwa kuncinshi, da sauri junior ya raba jikinshi da nashi saboda jin ruwan hawaye da yayi a kafaďunshi, "Hey twinny, ya faďi a dan tsorace yana ja da baya zai koma gurin Taheer, rike hannunshi Musaddiq yayi yana girgiza kanshi wasu hawayen na fitowa kamar ana ingizo su, "Daddy... Junior ya fara faďi yana kokawar kwace hannunshi cikin na Musaddiq, a tsorace yake matuka dan bai taba ganin zubar hawayen babba ba, Cikin sanyin jiki Hilal ya tsuguna a gaban junior, dayan hannunshi ya kamo yace "My dear he is ur Dad too, ur biological father, go to him, he is *MUSADDIQ KYARI* His name is connected with urs... Juyawa Taheer yayi wani makoko ya tokare kahon zuciyarshi, hawayen da yaketa matsesu suka zubo daga idonshi.. "Noo... Junior ya faďi haďe da fisge hannunshi daga dukkansu, da gudu ya koma gurin Taheer ya rungume kafafuwanshi ta baya, "Dis is my Dad, his name is also connected with mine, "Daddy plss tell them u are my biological father ya karashe bayan ya dawo gaban Taheer ya tsaya.. Daga kai Taheer yayi sama ya share hawayen da ya sake taruwa yana neman zubo mishi, dan kar Junior ya gani, ďagoshi yayi ya daurashi a kirjinshi yace "He is ur father Sweetheart, i'm ur father and ur name sake is ur father too, we are all ur Dad.. "Only one is my biological, who among the three? ya tambaya idonshi kyamm akan Taheer, Runtse ido Taheer yayi maganar da yake kokarin yi ya kakare mishi a makoshi... Share hawaye Anty Saude tayi ta karaso ciki da sauri ta karbi Junior, "Ina ka shiga My dear, ko abinci baka ci ba, and all ur so called fathers basu damu da su baka ba, duk kace bakayi dasu muje kaci abinci.. Kwantar dashi tayi akan kafadarta ta wuce cikin kitchen dashi, tayi hakan ne dan ya samu nutsuwar sanin ainihin mahaifinshi, duk nauyin Junior a wannan lokacin Anty Saude ji tayi yayi mata shafal, zaunar dashi tayi akan kujera ta kwalawa Nadeeyah da ta hangota acan baya kira.... A gaggauce Mummy tabi bayan Anty Saude itama idonta cike da kwalla, samm bata damu da ganin su Daddy tsaye curko curko bayan gama kallon abinda ya faru ba.. Tana shiga ta kankameshi tana kuka mai sauti haďe da sumbatar ko ina na jikinshi... Cike da kyankyami kamar zaiyi kuka yace "Momma, plss lts lv dis house... Mummy bata damu da kyankyaminta da yaji ba ta sabashi a jikinta ta durkushe gaban Nadeeyah tana kuka tana rokon gafararta, cikin kuka Nadeeyah ta tsuguna tace "Dan Allah Mummy ki bari, we are all humans, we are bound to mk mistakes, walhy ban rikeki a raina ba.. "Kuskurena yakai girman da za'ayi min koma meye, sakarcina ya hanani hango alkhairan dake tare dake Nadeeyah, yanzu wannan jikan nawa da kuskurena ya sanya fitarshi bazan taba yafewa kaina ba, dan Allah kuyi hakuri ta karashe cikin matsanancin kuka.... Su Anty Reemah da suka shigo gurin duk idonsu ya ciko da hawayen tausayi, Raudha da Radiya ma cike da Kuka suka tsuguna a gabansu suka shiga ba Nadeeyah hakuri... Hamdala Raliya tayi a cikin ranta sannan ta sake godewa Allah da yasa dukka yan uwanta da mahaifiyarta suka gane kuskurensu... To kukan ya isa a miko min jikana in bashi abinci, dariya Mummy tayi ta Saki Junior da yake a matse dama, da sauri ya koma gurin Anty Saude ya ďane jikinta haďe da kwanciya ya runtse idonshi.... Sai a hankali zai saba, kunsan yanzu ne ganinku dashi na farko, sai kunyi hakuri da koma meye... yadda Anty Saude ke maganar cikin fitar da tsammanin zamanta tare dashi ya sanya Nadeeyah barin kitchen din da sauri, ta riga ta gama yanke hukuncin zama da Taheer, babu wani dalili na tausayi ko wani abu da zai canza mata ra'ayinta, Halaccin da zatayi wa bayin Allahn nan kenan, ta kare rayuwarta tare dasu..... Gyaran murya Sarki Tidjani yayi yace "Hukumullahu laa Ajabun, hukuncin Allah ba'a mamaki akanshi, abin da ya kawo mu daban sai gashi Allah cikin ikonsa mun haďu da abinda muka shekara da shekaru muna nema..... Kamar dai yadda na faďa maka Alh Mukhtar, Taheer ďana ne, kanina ne ya haifeshi, mahaifinshi Allah yayi masa rasuwa shekarun baya da suka wuce, to yana zaune tare da mahaifiyarshi acan Canada, wannan zuwan da mukayi, alkhairi ne ya kawo mu, a yanzu da na fahimci wacece Nadeeyah sai nakejin kamar yau dinnan a kaddamar da komai a hutar da kowa, domin ita din 'ya ce ga kowanne a cikin mu, duk da na fi kowa karfi akanta a al'adarmu da kuma musuluncinmu, yanzu a gurina nine mutum marar karfi akanta dukkanku nan kun fini karfi, ku kuka san komai nata tun tasowarta, Saboda haka Alhaji Mukhtar nazo gareka ina nemawa ďana *Taheer auren ďiyarka Nadeeyah.... * yana disa aya fadawa suka yi mishi kirari haďe da miko mishi ruwa yasha domin yin magana mai tsayi... Ya ilahi... haskowa masu karatu halin da daukacin yan uwa da masoyan Musaddiq halin da suke ciki.. A kiďime Musaddiq ya mike da zaman da Papy ya tursasa masa yinsa, domin yaso bin bayan su Anty Saude da kuma Nadeeyar da ya tabbatar tana kitchen din... Cikin kaurarrar murya yace "whatt a jo---- da sauri Hilal ya toshe mishi baki haďe da kokarin maidashi ya zauna, iya karfinshi yasa ya hankaďa Hilal ya tafi tagaga zai faďi.. Daddy da a ganinshi yafi Musaddiq din shiga tashin hankali yayi saurin mikewa ya rike Musaddiq dake shirin sake magana, "Da aka fara magana kaji an kira sunanka? Ko irin tarbiyyar da ka samu kenan?, a gaban bakin mu wanda yake kamar Mahaifi ga Nadeeyah kake kokarin nuna musu irin rashin mutuncin da ka koya cikin kankanin lokaci ko?, to bismillah, in ka gama dasu sai ka dawo kaina..... 'Dago idonshi da ya zama kamar gauta yayi ya kalli gefen da Taheer yake, da sauri ya kauda kanshi haďe da fara takawa baya a hankali, cikin rashin sani yayi muguwar buguwa da bangon bayanshi.. Da gudu Hilal ya doso inda yake, kafin Hilal ya karaso ya juya ya haye sama da gudun da taku uku kaďai yayi ya isa ďakin da yake... Dafe kai Papy yayi cike da tausayi ya kalli Daddy da ya koma ya zauna yana magana cikin karfin hali.. "Mashaa Allah ranka ya daďe, na baku Nadeeyah, Allah ya sanya albarka a cikin auren, karku damu da sakarcin Musaddiq, yarinta ke damunshi.. Cike da jindadi Sarki yace "To madallah, sai a yanke mana sadaki domin muna da nisa, munfi son ayi komai cikin lokaci... Wannan karan duk wani kuzari na Daddy ya kare da kyar ya iya cewa "Da kai da kaya duk mallakan wuya ne, ranka ya daďe duk hukuncin da ka zartar daidai ne... Kuka sosai Anty Raliya ta fashe dashi na tausayin dan uwanta da kuma halin da taga mahaifinta, daki ta wuce da gudu Husna ta rufa mata baya itama kukan takeyi... Innalillahi wa inna ilaihir rajiun... shi kaďai take maimaitawa tana faďin duk laifi na ne, a tunanina in Nadeeyah ta dawo zata komawa Little, ashe wata kaddarar Allah ya shirya mana daban, Cikin kuka take bawa Husnah labarin komai da tayi wanda yake neman jefa dan uwanta cikin barazanar rayuwa.... Wani irin wawan mari Anty Reemah da ta biyo bayansu taji komai ta wanka mata.. cikin masifa ta fara zaginta tana kiranta da marar imani, tasan inda Nadeeyah take tabar kowa cikin zullumi musamman Mahaifiyarta dake fuskantar rayuwar ukuba saboda hakan, ta inda take shiga bata nan take fita ba.. Durkusawa Anty Raliya tayi cikin kuka ta bata hakuri da kuma amsar laifinta, ita tayi shi ne in a good faith dan Nadeeyah ta samu ingantacciyar rayuwa, ashee inganta rayuwarta zaiyi sanadiyyar shigar rayuwar Musaddiq cikin wani rudanin..... ta karashe cikin matsanancin kuka..... Zama sukayi su ukun suna cikin jimami suna zubarwa da dan uwansu hawaye... Minti goma kaďai su Sarki suka kara sukayi shirin tafiya, Kallon Hafeez Shareefah tayi tace anjima suzo shi da iyalanshi su sameta.. cikin ladabi ya amsa mata da "To, Adress ta karba gurin Taheer ta bashi cike da farin ciki..... Katse wayar dake shigowa cikin wayar Baffa yayi karo na biyar ya tashi ya tafi yin rakiyar su Sarki shima jikinshi ba kwari, kawai dai basu da bakin bijire musu ne dan suna da dukkan iko akan Nadeeyah, ga kuma taimaka mata da sukayi, ya zama dole suma su rama musu halaccin da sukayi mata... Kallonshi tayi cike da tausayi bayan ya gama nacin Junior yazo gurinshi yaki, A hankali tace "Bari mu tafi *KYARI* in shaa Allah gobe da safe zan kawo maka shi, baka bani phn numbernka ba, kai dai har yanzu kana nan da miskilancinka akan mace, to ni na tambaya a bani, Dariya yayi wacce da gani yake ce, ya fara faďa mata number, Shafa kan junior yayi yace "Takwarana sai gobe ko, ka zo da kaya da yawa dan rikeka zanyi.... Saida suka ga fitar motocin sannan suka koma ciki dukkansu babu mai karfin yiwa dan uwanshi magana... *DADDY* sunan da ya bayyana a jikin wayar haďe da special ringing tone, Dauka Husnah tayi ta nufi kitchen da wayar, can baya ta hangota zaune tana wasa da yatsun kafarta, dafata tayi haďe da zama a gefenta, Idonta da sukayi luhu luhu ta dago ta kalli Husnah haďe da kakaro dariya, zatayi magana kenan wayar ta sake kara, Ajiye mata wayar Husnah tayi akan cinyarta ta kauda kanta can gefe, ganin sunan ya tabbatar mata da junior ne da aikin nan dan tare suka siyo sim din Nigeria dashi,, Saida ta kusa katsewa ta dauka,, "Mamma.. ya faďi kamar karamin yaro.. "Uhmmm Uncle,, tafiya babu sallama ko? Kwantar da kanshi yayi a jikin kujerar yace "Na daga miki kafa ne, nasan yau baki da lokacin mu ni da junior, kinga yan uwa bayan dogon lokaci, just call to tell yhu "I love yhu alot.. Runtse idonta tayi tace "Uhum, "Uhummm, say it plss, ya faďi cikin kaguwa, "Same to yhu.. Dariya yayi yace "Muna nan zuwa anjima bayan isha'i, take care plss... "Ohk uncle, in shaa Allah bye.. tana kaiwa nan ta katse wayar... "Husnah kun dawo kaduna ne ko kunzo hutu ne? Hannayen Nadeeyah Husnah ta kama ta fashe mata da kuka, "Dan Allah Nadeeyah karki auri Uncle, dan Allah karkiyi sanadiyyar mutuwar Yaya Musaddiq, Sake dawo mata da ainihin labarin halin da ya shiga bayan tafiyarta tayi, sannan ta kara mata da irin halin rashin walwalar da ya ke ciki har yau dinnan da ya ganta.. Da sauri Nadeeyah ta share hawayenta tace "Walwala? wacce yakeyi da FAIDA matarshi fa? "Faida? Husna ta faďi cike da mamaki, Faidar da keda 'ya'ya uku? Faida ai tayi aure bayan rabuwarku da sati biyu, ta auri abokin yaya Musaddiq Zubair.. Cikin sanyin jiki Nadeeyah tace "Na gansu tare a gidanshi suna tsaye cikin annashuwa da jin dadi.. "Kwarai kuwa zaki gansu, basu da nisa, kinsan bayan rabuwarku Daddy ya saki Mummy, sai ya koma lagos da zama, duk wanda yaje gidan ita ke kawo mishi abinci, may be kin samesu ranar da baki a gidan ne..  Shuru Nadeeyah zuciyarta ta raunana matuka, tausayin dan uwanta Musaddiq ya ratsa dukkan sassa na jinin jikinta, saidai is too late... wata zuciyar ta faďi mata yayin da ta tuno da irin halaccin Taheer a gareta, Shanye kwallar da ta taso mata tayi tace "Husnah, Allah ya kaddara zamana da yaya Musaddiq na ďan lokaci ne, rabon da ya haďa mu gashi nan ya fito duniya, kinsan an ce Matar mutum kabarinsa, a yanzu bana tunanin zan iya zama da kowani namiji in ba Uncle ba, dan All--- da sauri Husnah ta bar gurin tana fitar da kuka mai sauti... Rufe fuska Nadeeyah tayi itama ta fashe da kukan da ya daďe da tokare makoshinta..... Tun Hilal na bugun kofar dakin Musaddiq har ya hakura da bugun ya koma ban baki.. "Look Kyari, don't harm urself, ka bude min kofar nan, everything will be alright, trust me.... Kamar da dutse yake magana, dan Musaddiq bai ma san abinda yake fada ba, tsaye yake gaban madubi hannayenshi dukka biyu ya daurasu kan table din yana fitar da numfarfashi kamar zakin da ya hangi nama, Kalmar "Daddy da yaji daga bakin gudan jininshi, da kuma kalamanshi, har kawo furucin sarki, sai amsa kuwwa sukeyi a kunnenshi, runtse idanunwanshi yayi saboda wani irin yanayi da yake ji a cikin jikinshi, kaunar Nadeeyah dake adane a majiya mai tsafta ta taso mishi gadan gadan kamar guguwa mai karfin gaske, da sauri ya buďe idanuwanshi wanda hakan yasa ya daki glass din mudubin dake dakin saboda yadda yaga idon kamar jini dan tsabar jaaa....   A firgice Little Nadeeyah ta farka da tsananin ihu tana waigen ta inda karan ya daki kunnenta, hango Musaddiq tayi yana sake bin glass din yana farfasa su da hannunshi da jini ke zuba.. a tsorace ta nufi kofar fita tana ihu tana kiran sunan Mahaifinta.. Muryar Hilal taji yana magana cikin ihu yana umurtata da buďe kofar, dakyar ta iya dabarar da ta murďa lock ta buďe da sauri ta faďa jikinshi tana ihun kuka,,, Mika ma Maleekah da karar glass ya tarkato su zuwa sama yayi ya nufi Musaddiq da gudun gaske, Hilal na ta'bashi yayi wurgi dashi ya cigaba yin wurgi da kayan gaban madubin yana faďin "i'm useless, Daddy is right i'm a fool nd a looser, bani da amfani a gurin kowa, gara in mutu kowa ya huta da mutum marar amfani iri na... Cikin kuka yan uwanshin ke kiran sunanshi suna hanashi ji ma kanshi ciwo, duk suna tsoron matsawa kusa ya illata su, Mummy kuwa da tasan duk itace silar hakan zama tayi a bakin kofa tana kuka ririsss, Cikin zafin nama Daddy ya karaso cikin ďakin ya isa gaban mudubin ya juyo dashi da karfi ya daukeshi da kyawawan mari har guda uku, yana shirin sake yin na hudu Baffa da Papy suka hanashi.. Cire hannun Papy Musaddiq yayi a jikin Daddy ya kai hannun fuskarshi ya cigaba da marin kanshi, "Slap me to death Daddy, Dan Allah ka mareni har sai mutuwa ta riskeni, i'm dead already, numfashin ne kadai ya rage, wallahi ko baka kasheni ba, ni zan kashe kaina.... Da karfi ya janyo gudan jininshi cikin kirjinshi ya rungumeshi tsamm yana kuka mai taba zuciya, Sai a lokacin zuciyar Musaddiq ta karye ya soma rero kuka mai cike da sambatu..... Mrs Tijjani Shattima....... [22/06 10:21 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣5⃣ By *Aysha Ya'u kurah* Jugummm jugummm.. sukayi a parlon kowa da abun da yake sak'awa a cikin ransa, fitowar likitan da Hilal ne ya sanya su nufarsu da sauri, "Doctor yaya? Hope all is well? Daddy ya tambaya cike da damuwa, Guri likitan ya samu ya zauna haďe da ajiye akwatin taimakon gaggawarshi, "Ka kwantar da hankalinka Alhaji, komai lafiya kalau, jinin da ya zubar ne kaďai ya sanyashi zama weak, amma ya farfaďo, saidai ya samu bacci, yana bukatar hutawa da kulawa sosai.. yana kaiwa nan ya kalli mutanen dake zaune a parlon, ganin rabinsu duk mata ne yasa shi mikewa yace "Alhaji anjima ka sameni a office, akwai abin da zamu tattauna, Allah ya bashi lafiya ya karashe yana dafa kafadun Daddy haďe da yin hanyar waje.... Kasa zama Daddy yayi ya bi bayanshi da sauri dan baijin zai iya kaiwa anjima baiji abinda yake son su tattauna ba wanda ya tabbatar akan ciwon ďanshi ne.... Hilal kuwa zama yayi a can gefe, hawayen dake zarya a idanuwanshi sun kafe saboda tsananin tashin hankali "Ta ina zai fara, wace hanya zai bi dan ganin ya samar wa Musaddiq abun da yakeso ba tare da hankalin kowa ya tashi ba, yafi karfin awa ďaya yana tufka da warwara amma bai samo mafita ba, runtse idonshi yayi saboda yadda yake jin nauyi a kan kirjinshi, dakyar ya iya mikewa da taimakon Maleekah suka koma can dakin da Musaddiq yake.... Cikin kalaman hikima irin na likita, Doctor Lawal yake wa Daddy magana, "Ya taba samun attack a yanda na lura, saboda halin da na riskeshi a yau ban taba tunanin zai rayu ba.. Alhaji Mukhtar, ďanka na cikin critical condition, zuciyarshi na iya bugawa at any time, dan Allah ku kula a daina sanyashi cikin damuwa sannan a taimaka a samo mishi abinda yake so, Cike da damuwa Daddy ya dubi Doc Lawal bayan ya gama mishi jawabi yace "Samun abin da yake so wannan na Allah ne, nidai zanyi kokarin ganin ya daina shiga damuwa da bacin rai... Shawarwari Dr Lawal ya bashi kafin suyi Sallama.... Parlon ya koma jiki a sanyaye yana tunanin kalaman Doctor, yadda ya barsu a parlon haka ya dawo ya samesu saidai wannan karan suna dan tattaunawa da su Papy... Bayan ya zauna ne  suka shiga kum kum wannan na cewa wannan tayi magana suna ki, a tare suka daure dan suna ganin hakan shine kaďai mafita ga rayuwar Musaddiq domin zaifi samun kula daga gurin uwa.. "Daddy dan Allah kayi ma Mummy afuwa, ta gane kuskurenta, dan Allah kayi hakuri ka sassauta mata... Kallon 'ya'yan nashi yayi fuskar nan babu walwala zaiyi magana muryar Baffa ta katseshi.... "Me ya faru Rilwanu? Me ya samu gidan nawa? To to to gamu nan zuwa yanzu da yardar Allah ya karashe haďe da mikewa, mikewa su Daddy sukayi suna tambayarshi ko lafiya? "To nima dai ban sani ba, Rilwanu yace inzo gida ba lafiya, a hanzarce suka fita dan zuwa gidan suga abinda ke faruwa.. Mummy dake can sama gurin Musaddiq itama tayi saurin mikewa ta biyo bayan Radiya da ta kawo mata rahoto... Da sauri Malam Mato mahaifin Rilwanu ya debo ruwa ya mikawa matarshi dake tsaye kan Goggo tana taimaka mata, wani irin ihu takeyi tana fisgar gashin jikinta haďe da firzar da ruwan da ake zuba mata a baki, "Gishiri, Gishiri, hakan ta dinga faďi tana zaro harcenta da yayi fari tass kamar mayya, Gishirin rilwanu ya debo a cikin buhu ya kawo musu dan a tunaninsu ciwukan jikinta zata sawa, yana kawo mata ta yafa kusan rabin kofin a bakinta, A firgice suka fara kokarin kwace kofin suka kasa saboda a wannan lokacin karfin ba ďaya bane, ko jariri ne wanda bashi da zunubin komai sai ya fuskanci barazanar wannan rana bare mutum irin Goggo wacce ta naďi kayayyakin bil adama marasa adadi... Sarketa gishirin yayi ta shiga tari kirjinta na ďagawa sama kamar zai rabu da jikinta, yaye zanin jikinta tayi saboda tsabar azaba ta mike ta fara zubar da kayan dakinta tana ihu sosai.. Halacci da iyayen Rilwanu suke ganin an yiwa dansu shi ya hanasu barin dakin duk ko da irin warin dake fita a jikin Goggo... Wasu gungun hotuna ta zubo har gaban malam mato, saura kiris glass din da ya fashe ya taba kafarshi, da sauri ya matsa baya ya tsuguna ya fara tattara hotunan ya umurci Rilwanu da matarshi da su riketa, yana gama tattara hotunan ya ajiyesu a kan table zai komo gurinta.. Tsayawa yayi cakk ya waigo da sauri ya sake duban hoton saman wanda bashi da kala samm, dauko hoton yayi jiki na rawa yace "Ma'un Ukari, *Nankwat Manasir* shigowar su Baffa ne yasashi mayar da hoton da bazai taba manta ranar da akayi shi ba, "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.. shi kawai yake maimaitawa cikin ranshi tare da tunanin inda mutanen nan masu matukar karamci suka san mace marar imani irin Ma'u... Mummy ce ta karaso ciki ta dauko zani dan rufe mata tsiraicin jikinta tana kuka sosai, Baffa kuwa hannunta ya rike yana faďin "Ma'u zauna kiyi ta salati, a yanzu ihu ba naki bane, da karfinta ta fisge tayi hanyar waje tana ihun da ko gida uku ne tsakaninku zakaji ta, da azama suka bita suka rikota suka maidata daki suka garkameshi dan yadda take jiyar da mutane ciwo.... Malam Mato kasa rike abun yayi a ranshi yace "Marar lafiyar nan itace Ma'u wacce naga hotonta da kananan yara biyu? Da sauri Baffa yace "Eh itace, ka santa ne? Juyayi Malam Mato ya shiga yana tunanin ta yanda zai fara sanar dasu abubuwan da ya sani shekaru da dama wanda babu wanda yasan dasu sai ubangijin talikai sai shi da ita kanta Ma'un, Nufar inda yake Baffa yayi zaiyi magana sukaji ihun Goggo tana faďin "Na shiga uku, ku kira min Bokan Ukari yazo ya tamaikeni, yagar naman jikina akeyi, wayyo, wayyo, ku kirashi yazo ya taimakeni, yayi min alkawarin bazan mutu  ba, yayi min alkawarin karashe rayuwata har kowa ya mutu ya barni.. "Mai kashewa shi ke tsoron mutuwa, shin akwai adalci a cikin wannan? Malam ya Mato yayi tambayar ba tare da jiran amsar kowa ba, da sauri ya nufi dakin ya buďeshi domin a yanzu samm ya daina tausaya mata... "Ai bai kamata wanda yake da karfin zuciyar sanadiyyar rayukan mu'imunai da dama tsoron mutuwa ba, *JUMMA'ATU BABBAN RANA* Ranar yin katako daga kauyen ukari zuwa Gembu, *Ma'u yar gidan Manasir*... Tunaninki zai iya tafiya shekaru hamsin da doriya suka wuce, in kin manta ni bazan manta ba, zan fara tuna miki in yaso sai ki karasa da bakinki.. Tunda ya fara maganar azababben jikin Goggo ya saki, maganarshi tafi ciwon azaba... "Harďejo, Musulman kauyen Gembu, suna Sallar Jumma'a... ko zaki iya tuna abun da faru a ranar, cikin dabara yace "Faďin ainihin abin da ya faru shine kadai zai taimaki rayuwarki ki dawo kamar yadda kike da, sannan babu zancen mutuwa har sai dan kanki kinji duniyar ta isheki... Saboda jahilci da kuma tsabar son duniya, Goggo ta fara faďin dukkan labaran da suka faru a baya, har kawo mutuwar Atika da yunkurin kashe Papy da kuma irin ukubar da ta bawa Mamma Suwaiba, har yadda tayi ta raba Daddy da Mamma suwaiba ta hanyar asiri, wannan confession din tayi shi ne cike da sa ran ciwon zai barta sannan bazata mutu ba, ta sa rai bayan ta rayu zata yi asirin da zai mantar dasu komai... *Goggo dai tazo duniya zama ne, tazo ne kawai ta karaci rayuwarta cikin asarar da lokacinta gurin yiwa wasu sihiri domin kawai gamsar da zuciyarta*.... Ajiyar Zuciya Malam Mato yayi ya kalli duk mutanen gurin da suka mutu a tsaye saboda jin rashin imanin Goggo, "Alhamdulillah da Allah ya taimakeni ta faďi da bakinta domin inata tunanin yadda zan gamsar daku, a lokacin da Ma'u ta sanar da yan ta'addan nan cewa akwai Musulmai a kauyen Gembu, bani da bakin magana domin na riga na ce musu ni ba musulmi bane, bayan mun shiga garin na saukesu sai na nufi can wani guri na samu maboya, ganin irin kisan gillar da sukayi ma musulman kauyen yasani barin garin Taraba gaba dayanta saboda tsabar tsoron wata rana wannan abun zai faru dani ko wani nawa, a kullum kwanan duniya cikin shekarun nan sai na tuno da wannan al'amarin, rashin sanin inda zanga mai aika aikar yasani barin wa cikina komai, da nasan a gidan nan take wallahi da kaina zan mikata ga hukuma su hukunta ta tun da sauran karfinta, amma yanzu ko an mikata ga hukuma babu amfani domin hukuncin ubangiji ya fara tun anan duniya kafin ta riskeshi a lahira.... Wani irin kuka Baffa ya durkushe a gurin ya fara yi cikin kunan rai, shekara da shekaru yana tare da wacce ta rabashi da ahalinshi, a harzuke bayan kukan ya lafa ya mike ya nufi inda take zaune tana yakushin jikinta ya kaiwa wuyanta shaka.. A gaggauce su Papy suka share hawayensu suka nufi gurin Baffa, dakyar suka iya rabashi da Goggo wacce take ihun ceton rai.. "Karka zama irinta Baffa, sai ka kwashe dukkan zunubbanta, ka barta da abunta ta girbe abun da ta shuka da hannunta.. Daddy ne ke magana cike da takaicin haďa iri da wannan zuri'a karo na ba adadi, dole ya dinga fuskantar kalubale kala kala a cikin tashi zuri'ar... Mummy samm ta kasa motsawa daga inda take, juya maganganun ta dingayi a cikin kwakwalawarta, rashin imanin mahaifiyarta har ya kai haka, tabbas dole ta dinga ganin jarabawa kala kala, Allah bai bata uwa ba, wannan wacce irin uwa ce wacce sam babu kwayar halittar imani a cikin zuciyarta... Zaburar da Goggo ta sakeyi ita ta dawo dasu daga duniyar sake saken da suka tafi, babu wanda yayi yunkurin bin ta sai Papy da Anni, kafin su kai inda take har ta kusa kofar gida.... Da gudu wani mai baro wanda ya lodo karafe da langar kwanon aluminum tsofaffi ya taho dan wucewa yana jin wakarshi, tsayawa yayi a gefen gidan su Baffa dan siyan rake ya parka baron a gurin, Fitowar Goggo keda wuya wata langa mai tsini ta kama yaďuwar fatar cikinta, da yake gurin gangare ne nan fa sukayi kasa ita da baron kaifin langar yayi fata fata naman cikin Goggo, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai mutanen gurin suka fara faďi haďe da yin kanta da gudu, Dakyar aka samu aka zare wasu parts din langar a jikinta, har lokacin tana da rai sai ihun azaba kawai takeyi cikin sarkewar murya, da sauri Papy da me baron suka dauketa suka yi gurin mota da ita, jinin dake zuba a jikinta ba jinin wasa bane, ga tsagu da cikinta ya samu can ciki ana iya hango wasu daga cikin kayan cikin, suna isa gurin motar Papy ya kalli Daddy da suka fito gaba dayansu yace "Bude motar Alhaji muje, Ďauke kai Daddy yayi yace "Ba'a mota ta ba, kallon Raliya yayi dan ita kadai ce tazo da mota yace "Kema in kika dauka ban yafe miki ba, yana kaiwa nan ya shiga motarshi yayi gaba ba tare da ya kalli kowa a cikinsu ba, samm babu digon tausayinta a ranshi bare har ya kai ga taimakonta, Papy ya rasa yadda zaiyi dan tashi motar na gurin Hafeez, motoci suka fara tsayarwa na haya, duk motar da ta tsaya in taga yanayin Goggo sai tayi gaba dan kar a bata musu mota, Cikin tsananin tashin hankali mai baron yace "Ko zamu dauketa cikin baro na, ni zanyi tukin sai ku biyomu a mota, da wannan shawarar aka dauki Goggo aka sata a cikin baron bayan an shimfida bargo aka rufe mata jiki, tausayin rai da matsawar Anni su suka sa Baffa bin bayansu, gudu sosai mai baron yakeyi dan yana tsoron mutuwarta a sanadiyarshi, go slown da suka tarar shi ya sanya shi yin yanke ta wani lungu dan su isa asibitin da wuri, Yana shiga kwanar yayi tuntunbe da katon dutse wanda hakan yayi sanadiyyar subucewar baron yayi wani kwaron kudiddifi da Goggo, ihuu ya saka yabi bayan su, yana isa yaga baron makale  jikin wani dutse ita kuma Goggo kwance kan wani katon dutse kanta yayi fata fata, cike da tsoro yaron yaja baronshi jiki na rawa ya bar gurin dan kar hakan yayi sanadiyyar shiganshi wani hali... Motar da suka hawo na biyowa lungun sukaga mutane sunyi dafifi a gurin kudiddifin, da sauri Papy ya dakatar da mai motar ya sauka yana tambayar abun da ke faruwa, labarta mishi wani yaro yayi sannan yace sunbi mai baron basu ga inda ya shiga ba.. Cikin tashin hankali Papy ya biya wasu yara majiya karfi yace su cirota, koda suka cirota har lokacin bata mutu ba saidai ta jikkata iya jikkatuwa, babu ta inda jini bai zuba a jikinta, fashewar da kanta yayi ya sauya halittar fuskarta, azabar da take sha a lokacin har gara ta gwammaci mutuwa da rayuwa, to saidai inda matsalar take bata san me zata tarar bayan mutuwar ba.. *(Allah a'alamu, shi kadai yasan hukuncin da zaiwa bayinsa masu mugun hali iri ko kuma kwatankwacin na Ma'u, Bawa bai isa ya yanke ba domin shi Allah mai gafara ne a lokacin da yaso, ta yiwu mutum ya sha iya wahalarshi a nan duniya a ranar da zai koma ga Allah, ta yiwu kuma sai anje can, wannan Allah buwayi gagara misali shi kadai yasan daidai.... Allah ka datar damu da aljanna firdausi, ka tsarkake zuciyarmu kasa mufi karfinta)* Kudi mai yawa Papy ya bawa mai motar sannan ya yarda zai dauki Goggo a boot, asibiti mafi kusa suka isa saboda jinin dake zuba a jikinta, kin karbarta sukayi dan acewarsu yafi karfinsu a wuce general hospital, Mummy dai kuka kawai takeyi tana fadin *Astagfirullah ya Allah*, mai motar da aka sake roka ya wuce dasu General hospital, koda suka isa emergencyn kanshi a cike yake da marasa, dakyar aka samu aka shiga da Goggo wacce babu abunda bakinta ke furtawa sai wayyo na shiga uku, Boka Garbuji kazo ka taimakeni, duk yadda likitoci suka kai da kokarin tsaida jinin abin yaci tura domin zuba yakeyi kamar ana kara wani a jikinta, allurar bacci sukayi mata dan ta samu tayi bacci suyi mata aiki, itama allurar sam taki aiki a jikinta, sai ihu kawai takeyi, a haka sukayi mata aikin azaba na karaďe dukkan sassa na jikinta, bayan sun gama suka barta a gurin suka bada alluran da za'a siyo ko zata samu bacci, Anyi mata allurai uku amma samm taki rissinawa bare tayi bacci, ga fusge fusgen azaba da takeyi tana kiran sunan bokayenta ko zata samu taimakonsu... *A wannan ranar Goggo bata san ko waye bazai tseratar da mutum daga abinda dake rubuce ba, domin in har ganyenka na zaman duniya ya bushe har ya kai ga faďuwa kasa to fa babu wani tsumi ko dabarar da zai hanaka faduwa kasan nan kaima*... Har karfe goma na dare Goggo na abu daya, ita bata rintsa ba ita bata bar na kusa da ita sun runtsa ba, duk yadda ahalinta suka so tayi salati abin yaci tura domin suna diga aya zata dura musu ashar tace basu san abun da take ji ba.. *Kwatan kwacin hakan bayin Allah da kika sa aka kashe suka ji, su da basu dauki zunubin kowa ba ma kenan kin wahalar dasu, bare ke da kika kwashi na mutane marasa adadi...* Karfe 2:40 na dare jikin Goggo ya kara tsamari, domin a yanzu samm ta kasa kwanciya, jikinta kuwa babu komai sai rigar da aka saka mata, ihuu kawai takeyi wanda yake ratsa ko ina na asibitin, Mummy da ta rage ita kadai ta dinga zubar da hawaye haďe da ambaton Allah.. Wata zabura da Goggo tayi babu wanda ya ankara sai ganinta akayi a can waje asibiti domin ita Mummy mai jinyarta ta tafi makewayi.. Ihuu kawai takeyi tana tsallen azaba tana kiran sunaye kala kala, dinkin da akayi mata a ciki nan take ya warware saboda rashin kwarin jikinta da kuma sabontakar dinkin, Warwarar dinkin tayi daidai da tahowar motar wasu gayu wadanda suka sha giya sukayi tatil, saboda yanayin duhun garin da kuma yanayin buguwarsu sai jin wani kara sukayi wanda yasasu taka birki, shurun da sukaji babu wanda yayi magana yasa drivern yin ihu haďe da sake kara volume din motar fiye da da ya takata suka wuce, securityn dake dutyn dare ne ya fito yana ihun neman taimako, ihun da yakeyi shi ya janyo hankalin Mummy da attendance din dare wadanda suke yawon nemanta a harabar asibitin, da gudu suka nufi gurin shi suna tambaya ko lafiya, ganin ya nufi wata katangar dake tsallaken asibitin yasasu binshi a baya suna daďa tambayar ko lafiya, suna isa gurin tambayarsu ta makale a makoshi domin Goggo suka gani hange jikin tsinin karfen katangar wanda ya burma cikinta har baya, Kuka sosai Mummy ta sanya tana kiran sunanta domin har lokacin da sauran ranta tana ta gumshekar azaba wacce tafi kama da ta mutuwa, Da kyar security's din ciki da suka fito suka zarota suka nufi ciki da ita, Karasawarsu ciki keda wuya ta damki cikin inda ciwukan suke haďe ciza harcenta da karfi har saida jini ya fito, ihun karshe da ta saki yayi daidai da daina motsa kafarta da kuma sakin dukkan jikinta, Ajiyar zuciya wata nurse tayi taja zani ta rufeta ta kalli Mummy tace "Saidai hakuri, ta mutu!! Bazan mutu ba Goggo ta faďi a wahalce haďe da yayewa ta damki hannun nurse din, irin jinin da ya zuba a jikin Goggo ya isa dukkan karfinta ya kare, A tsorace Nurse din ta fincike hannunta taja da baya da sauri, dan minti ďaya baya tabbas taga mutuwa a tare da Goggo.. Sunan Mummy ta fara kira a hankali saboda duhu ya fara ziyartar ganinta, daga nesa Mummy ta amsa dan tsabar tsoron irin rayuwar da Goggo ta ďibo, gaba ďaya yanayinta ya canza daga farar bafulatana wacce tsufa ya tattare fatanta zuwa wani irin yanayi na ban tsoro, jinin dake zuba a jikinta gaba ďaya ya kafe dan babu ragowarshi a jikinta, karfaffiyar zuciyarta wacce rashin imani ya kesashar ita kadai ke aiki a jikinta... Babu wanda a dakin bai bata mutuwa ba saboda irin ukubar da tasha kuma take kan sha, a lokacin nan mutane da dama sun sake tsorata da Allah domin shine ke da ikon yin wannan abun al'ajabi,, Sake kiran sunan Mummy Goggo tayi a karo na uku, a ďarare ta matso kusa da ita tace "Gani, "Yanzu duk wannan azabar da nake ciki bazaki iya zuwa ki kiramin wani bokan ya fidda ni ba, duk abubuwan da nayi a baya saboda ku nayi shi, amma ni yanzu abu ďaya da zaki min in fita daga wannan azabar bazaki iya ba....  babu wanda ya fahimci abinda Goggon ke faďa sai Mummy domin ita kadai ce a gefenta, Cike da damuwa Mummy tace "Shin har yanzu baki saduda kin san Allah daya bane? Har yanzu kina tunanin akwai wanda ya isa ya hanaka yin aure bare ya hanaka mutuwa, lallai kuwa in dai wannan azabar da kika sha ta tsayin watanni bata nunar miki hanyar Allah ba babu wata azaba da zata maidaki daidai, Mutuwarki itace alheri ga dukkan yan uwa musulmi, domin ke ďin anno----- wata damka Goggo ta kai mata wacce idonta bai nunar mata gefen da ta kaita ba saboda duhun da ya fara rufesu, a hanzarce Mummy ta mike haďe da fincikewa wanda hakan yayi sanadiyyar kai Goggo kasa, zafin faďuwar ya sanyata sakin ihun karshe wanda daga shi bata sake cewa komai ba sai fisga da jikinta yakeyi yana dukan gadon.. A wannan lokacin mai daukar rai ya ziyarci tsohuwa Goggo wacce tayi kisan ban mamaki kuma take tsoron mutuwar kanta, a lokacin Goggo ta dandanin azabar da matattun da suka mutu a sanadinta suka dandana, babu rayuwar da bata tunano ba kafin ganinta ya dauke baki ďaya.... *(Kullu nafsin za'ikatul maut,, Duk mai rai sai ya dandani mutuwa)*... *Anzo a banza an koma a wofi...* Furucin wata tsohuwa ne doki kunnen Mummy dake zaune tana kuka tana jiran azo daukar gawar Goggo, Wani sabon kukan ne yazo mata tanata adduar nemawa mahaifiyarta sassaucin ubangiji, *(Allah ghafuru raheem*).... Mutuwar Goggo ta taba makusantanta, domin ko babu komai rai daraja gareshi duk ko irin bakin halin wannan ran.. A ranar da akayi sadakar uku Baffa yasa aka kwashe kayan Goggo aka kaiwa tsofaffin mabaratan bakin titi, kayan kudinta ne kadai ya bawa Goggo domin itace magajiyarta shi kuwa a bangarenshi yace baya bukatar komai nata domin ta fita a sahun matarshi kafin rai yayi halinsa... *********** Har gurin mota Daddy ya raka su Anty Saude domin hirar da ta jashi da shi ba wacce zasu katseta bace, Cike da damuwa  ita ta katse hirar bayan ta ajiye jakarta a bayan mota, "Ya jikin Musaddiq? Hope da sauki, Hafeez ke faďa mana jiya ashe bai ji dadi ba kwana biyu, Cike da basarwa Daddy yace "Alhamdulillah, jiki kam da sauki sosai, dan har ya fita ma yau.. "To mashaa Allah Anty Saude tace cike da farin ciki, jikanka dai yana neman haddasa min fitina, daga yaga zamu fita zai fara kuka saidai a barshi a gida, yanzu dai na barsu da Taheer zasu zo zuwa anjima suyi muku gaisuwa sai yayi dabara ya barshi can gurin Nadeeyah, "Murmushin dattaku Daddy yayi wanda ya tuno mata da samartakarshi yace "Babu komai, nasan rashin sabo ne, wata rana ba zaiso ya bar gidana ba, "In shaa Allah Anty Saude ta faďi tana dariya, motar ta shiga tana faďin "Kyan alkawari dai Kyari, ina nan ina jiranka,, Baki da matsala, in shaa Allahu gobe zanzo ai ni na faďa.. ya faďi cike da jaddadawa... "To saika zo bari mu wuce Allah ya kara hakuri, Ameen Daddy ya faďi haďe da rufe kofar motar... A tare motar su shigo cikin katafaren gidan, sai da kowacce tayi parking a mazauninta sannan suka fito rike da kaya niki niki.. Cike da ladabi Kamal ya gaisheta bayan ta sakko daga cikin motar, Amsawa tayi hannunta nakan kayan tace "Har kun dawo? Allah yasa dai bakuyi shirme a list dinnan ba, Girgiza kai Taheer yayi cike da gajiya yace "komai muyi momma, muje ciki ki gani, My dear kawo ledar nan ya karashe yana duban Junior dake rike da leda yana ja, "Noo Daddy, muje kaima naka akwai nauyi, daya daga cikin mai musu aiki ne ya karaso ya karbi dukkan kayan harda na hannun junior, sai a lokacin suka saki ajiyar zuciya suka wuce ciki ko wanne na dauke da gajiyar kasuwa data zaban kaya.. Buďe kayayyakin Shareefah takeyi tana duban Anty Saude dake cire warwarayen hannunta tana kallon kanta a mudubi, "Kaya Machaa Allah Saude, yanzu abu kadan ya rage a gama, sai kuma su *plaķiù'oòl..* Nasa Raahilar masu gari ta siyo ta taho dasu, naso ayi bikin nan a can Agadez saboda a nuna su ga dangi kuma ayi biki kashi biyu, na Yareemah mai jiran gado da kuma daurin auren tunda abun duk phàmèè ne, to Taheer ya hana yace dole ayi shi anan, amma ki faďa mishi daga an daura zamu wuce can sai ayi biki domin bazai yiwu bikin yazo min a yar karo ba alhali dukkansu nawa ne, dole a buga tambura agadez ta dauki bikin jinina, shakikai na wadanda zan bugi kirji ince su din nawa ne...  Warwaron karshe Anty Saude ta zare ta dawo kusa da Shareefah, "Karki damu yar uwa, yin bikin a nan ya zama dole, bayan an daura sai kiyi yadda kike so babu wanda zai hana, kwana nawa ya rage, kedai kisa a fara shirye shirye a can kafin isowarmu.. Wannan ba matsala bane, biki kam za'ayi shi wanda ba'a taba yin irinshi ba a tarihi.. Shareefah ta faďi zuciyarta cike fal da murna... ********** Tsakurar indomien dake gabanta takeyi a hankali tana kaita baki, tunanin abubuwa da dama sun cika zuciyarta, ga tausayin halin da Musaddiq yake ciki ga kuma tausayin Taheer  wanda ya sallamar da dukkan hope dinshi a kanta, tsaki tayi a hankali ta ture indomien gefe dan dama cinta takeyi badan daďi ba sai dan yunwar dake neman yi mata illah... "Nadeeyah in kin gama Daddy yace kizo.. kafin ta juyo ta ba Husnah amsa har ta bacewa ganinta, ruwa kaďan ta kurba ta gyara gyalen dake daure a kanta ta nufi parlon kamar wacce kwai ya fashewa a ciki... Cikin dariyar karfin hali Daddy yace "Amarya taho nan ki zauna mana, Cike da karyewar zuciya ta tsuguna can nesa dashi tace "Ina kwana Daddy, " Lafiya kalau Nadeeyah, ke kuma haka akeyi, kullum ina son muyi magana sai kiyi bacci baki jirana in dawo, baki kyauta min ba, gashi yau saura kwana huďu kadai ki tafi, yanzu dai kije ki shirya kizo muje ki zabi abinda kike so.. Hawayen dake kwance cikin fararen idonta ne suka sauko kan kumatunta, "Daddy bana bukatar komai ta faďi cikin rawar murya.. Cike da zolaya yace "Nasani Nadeeyah, amma ai a matsayina na uba duk da ban kai matsayin kuďin su Taheer ba ai bana kai ki haka ba, sai a goranta mana, tashi maza ki shirya.. "Sautin kukanta ne ya fara karaďe cikin falon wanda ya dauki hankalin Hilal dake saukowa kasa.. "A'a Kuka kuma Nadeeyah, ki daina kuka dan Allah kar ki karya min zuciya, wasa nake miki, tashi kije ciki zamuje da Reemah.. "Dan Allah Daddy kuyi hakuri, wallahi na rasa yadda zanyi, ina cikin tsaka mai wuya..... ta karashe cikin tsananin kuka.. Tasowa Daddy yayi ya isa gareta, a hankali ya dagota ya shiga share mata hawaye, "Allah shi zai fidda ki, nasani baki da laifi dan baki isa ki ketare kaddararki ba, duk abinda Allah ya rubuta akanki babu wanda ya isa ya gogeshi, Musaddiq ko baki aureshi ba yana nan dai a matsayin jininki babu wanda ya isa ya raba, rabuwa da Taheer kuma samm babu adalci domin bazan fifita son ďana akan na wani ba, shima ďa ne, kuma yana da zuciya a kirjinshi, ki kwantar da hankalinki ki barwa Allah lamuranki shi ne mai saukakawa... Ajiyar zuciya tayi mai karfi zatayi magana muryar Junior ya katseta.. A tare suka waigo suka kalleshi Daddy ya saki murmushi haďe da cewa "Aboki, kaine a gidan da safe? Ina Daddynka? Jin ya ambaci sunan Daddy yasa shi waigawa dan tare suka tako har kofar parlon, "Daddy, Daddy.. ya fara kwala kiran sunan Taheer wanda ya riga yayi nisa, "Dama kawoshi yayi ya zauna a gidan dan ya saba dasu, sai kuma abinda kunnuwanshi suka jiye mishi abin da ya sanyashi cikin tsananin tausayi da kuma sake ganin girma da kimar Daddy.. Kuka sosai Junior ya farayi dan ya fito baiga motar Taheer ba, Hilal da ya gama sauraron su Daddy shi ya fito wajen yana lallabashi haďe da yi mishi alkawarin maidashi in yayi wanka, da kyar ya yarda amma har lokacin bai bar kuka ba... Cike da kuluwa Nadeeyah ta kama hannunshi ta nufi ďaki dashi tayi mishi tsawar da ya sake sanyashi cikin wani gigitaccen kuka, "Tsanar da kikayi wa ubanshi ce ke neman shafarshi, Husna ta faďi tana janyoshi jikinta, ga mamakinta sai ya turata baya ya koma jikin Nadeeyah ya kankameta yana cigaba da kukan, Kukanshi da kalaman Husnah su suka sake dugunzuma zuciyarta, nan take ta turashi gefe ta faďa bayi tana kuka mai sosa zuciya, tana jiyo ihun kukanshi yana faďin "bazai sake yin kuka ba Dan Allah ta buďe mishi kofa, duk yadda Husna taso kamashi kasawa tayi haka Anty Reemah da Maleekah, duk wanda ya tabashi sai ya turasu ya cigaba da ihun sunanta, Hilal ne kaďai ya iya calming dinshi ya daukeshi suka fita daga dakin, Sama suka nufa yana rarrashinshi haďe da yi mishi alkawura kala kala... Gaban mudubin da babu glass suka samu Musaddiq zaune da towel a jikinshi alamun yanzu ya fito wanka.. a kunne Hilal ya raďawa Junior cewa "Go nd say sorry to ur Twinny, kasan bashi da lafiya, he will feel better in dai yaji sorry daga bakinka.. Da sauri ya sauka ya isa kusa dashi yace "Sorry Twinny, hw is body? Hope u are feeln better? A hankali ya maida dubanshi gareshi ya tallabo fuskarshi yace "Yes twinny, hw are u? "Nt fine, Mamma shoutd at me nd she is crying.. ya faďi kamar zai sake yin wani kukan,,  Raunanniyar zuciyarshi wacce ake lallabawa ta fara mishi zugi, nan take idanuwanshi saka kawo ruwa, burinshi bai wuce ace in ya rufe idonshi ya farka ya ganshi a kabari ba, ya tsani rayuwar gaba ďayanta, Tunda ya taso a duniyar nan baisan mecece rayuwar duniya ba, shiyasa ya ke kiran Nadeeyah da rayuwarshi baki ďaya, itace duniyarshi, Daddy ya kasa fahimtarshi, kowa ya zuba ido yana ganin za'a rabashi da rayuwarshi.. hannun Hilal yaji a kafadarshi wanda ya sanya hawayen karasa saukowa kamar an ingizo su, "Hilal babu wanda zai iya taimaka min a cikinku, haka zaku zuba ido--- toshe mishi baki Hilal yayi yace "Bamu isa mu shiga hurumin ubangiji ba Kyari, ka fahimci hakan, dan Allah kayi tawakkali, kaddara babu yadda bata zuwarma bawa, Rungume junior yayi saboda jin hannunshi yana share mishi hawaye, "Please Hilal take care of my son bayan raina, wallahi bazan rayu ba, Dogon tsaki Hilal yaja haďe da raba junior da jikinshi yace "Sai ka kashe kanka tunda rayuwarka a hannunka take.. Muje kasa kaji takwara, ur twinny is crazy ya karashe haďe da jan hannun junior sukayi waje... Maida kai Musaddiq yayi ya kwanta yana rusa kukan da tunda aka haifeshi bai tunanin ya taba yinshi, duk yadda yaso yin karfi da zuciyarshi kamar yadda Daddy ya bukata ya kasa saboda zuciyar ta raunana matuka da kaunar Nadeeyah, Ya Allah Ka sàssauta min, haka ya dinga faďi yana juyi akan gadonshi.... ******* Alkawari dai Kyari, gashi har karfe biyar baka ba labarinka, Yadda take maganar ya sanya Shareefah kureta da ido domin ta dade bata ga yar uwarta cikin wannan yanayin ba, "Kiyi hakuri Saudatu, in shaa Allahu zanzo zuwa anjima, ina nan sane ban manta ba, Daddy ya bata amsa yana mai duban agogon hannunshi domin ganin lokaci... "To ina nan dai ina zuba ido, nasan dai baka saba alkawari bansani ba ko ka koya kasan shekarun da yawa, Dariya suka saki a tare saboda yasan tabbas tsokanarshi takeyi, "In ma na koya bazan so in gwada miki shi ba, domin an daďe ba'a hadu ba, ya kamata a barwa juna memories masu daďi bayan rabuwa, ina nan zuwa, just a second plss inada baki zan kiraki, bai jira jin amsarta ba ya kashe wayar ya cigaba da duba abubuwan da aka kawo mishi... *BAYAN RABUWA* Shi ta dinga maimaitawa a cikin ranta, yana tunanin rabuwa da ita kenan bayan shekarun da suka dauka basuga juna ba, har yanzu Mukhtar baya tunaninta kamar yadda tayi a baya da kuma yanzu da ganinshi ya tado mata matacciyar soyayyarshi.... *Flash back a gurguje* _Shekaru da dama da suka wuce Allah ya jarabci Anty Saude da Soyayyar abokin makocinsu kuma malaminta wanda yake mata lesson Uncle Abubakar, a duk lokacin da uncle Abu yazo yi mata lesson Kyari kan je gidansu yayi ta tsokanarta musamman in akazo kan mathematics, tun abun na bata haushi har ya rikiďe ya koma birgeta, in yana tsokanarta sai ta biye mishi suyi tayi har lokacin tashi lesson yayi ba'a tabuka mata wani abun arziki ba, in Kyari yayi tafiya babu zancen karatu ta dinga damun uncle Abu kenan tana tambayarshi ranar da zai dawo, kasancewarsu dukkansu 'yayan masu kudin lokacin sai ya zamana tasu tazo daya musamman ta bangaren Anty Saude, ita duk a tunaninta soyayya ce ke kawo Kyari (kamar yadda taji uncle Abu na cewa) gurinta, bata san shakuwar da sukayi da Abubakar tun suna makaranta ita ce ta sanya ďaya baya barin daya ba, a ranar da ta yanke shawarar faďa mishi abinda ke ranta a ranar taji mummunan labari daga gareshi na haďuwa da wata yar makaranta wacce ya kwallafawa ran aurenta, cikin sanyin jiki ta tattara takardunta tace ma Uncle Abu bata da lafiya, bata tsaya duba kulawar da Kyari ke kokarin nunawa a gareta ba ta wuce cikin gida idanuwanta na zubar da hawaye, tasan tabbas kyari ya faďa cikin tarkon so domin a yadda ta kula baya son kula mata gashi da yawan kushesu tasan wannan din da ya gani ta dabance, a daren ranar taci kuka har ta gode Allah sannan ta roki Allah da ya kawo mata wanda zai aureta cikin gaggawa ko ta samu ta mance *Mukhtar Garba Kyari*..._ Washe gari da safe da taje gaida Mahaifinta  Alhaji Halliru Ďan Magarya, bayan sun gaisa yake tambayarta yaushe zasu fara jarabawa, cike da damuwa ta amsa mishi da cewa "Jibi in shaa Allah, "Mashaa Allah Mamana, Allah yasa ku rubuta alkhairi, yasa ku fito da sakamako mai kyau, tunda an kusa zana jarabawar karshe sai maganar aure, shin kina da wanda kike so? nasan dai bazaki rasa ba kar inyi miki katsalandan, Kauda kanta gefe tayi dan bata so sam mahaifinta ya gane halin da take ciki tace "A'a Pappa, duk wanda ka zabar min ina maraba dashi, Cike da murna yace "Mashaa Allah, shiyasa nake daďa sonki a cikin raina, sai yanzu na fahimci dalilin da yasa Allah ya mallaka min ke kadai, saboda yasan ke ďin daya ce tamkar da dubu, Allah yayi miki albarka, ki shirya gobe, Haroun Yallo dan wazirin Agadez zaizo neman aurenki, satin da ya wuce da naje Agadez na bawa mahaifinshi ke, shi mazaunin nan ne, a nan yake kasuwancinshi, Allah ya sanyawa haďin albarka, Amsa mishi tayi da Ameen sannan ta tashi ta wuce ďaki tana kuka ririss.... Bayan tayi candy da sati biyu aka daura aurenta da Haroun, da fari ta dan samu matsalar zama dashi saboda tunanin kyari da takewa son da bai san tanayi ba, sai daga baya kyautatawar Haroun ta kashe boyayyar soyayyar cikin zuciyarta... Ashe dai soyayyar ba mutuwa tayi ba, ashe doguwar suma tayi, wanda a yanzu ruwan soyayyar Daddy ya farfaďo da ita... Ajiyar Zuciya tayi tace "Wannan karan bazan rasaka ba Kyari, koda zuciyarka bata sona zan koyar da ita yadda zatayi shi, a yanzu na haďu da kai bayan na cire rai da sake yin wata soyayya bare har inyi aure, haduwarmu dakai ta nuna min tabbas kai ďin nawa ne koda kuwa ba nawa bane ni kadai, rabuwa a tsakanin mu babu ita saidai mutuwa ka raba, tana kaiwa nan ta tashi ta nufi daki dan sakeyin wani wankan.... Da ido Shareefah ta bita tana mata adduar samun abinda take so, domin Allah ma yasan tayi hakurin rashin miji a gefenta, yadda ta damu da maganar Kyari ta tabbatar tana matukar sonshi, zata tayata da addu'a in alkhairi ne Allah ya tabbatar..... Bayan isha'i Daddy yazo gidan, tarba mai kyau ya samu daga dukkansu harda Taheer wanda a yanzu yake matukar jin kunyar haďa ido dashi, kimarshi ta karu sosai a idonshi.. Bayan sun gama gaisawa Anty Saude ta cika gabanshi da abinci da sha, zama tayi a gefenshi tana mishi hira yana cin abinci suna tuntsira dariyar tuna baya, sosai sukayi hirarsu har Daddy yakai karfe goma bai san ya kai ba, yayi matukar jin daďin hira da ita, zuciyarshi da tayi mishi nauyi ta rage saboda ta tuno mishi da memories ďin baya, lokacin yana kan ganiyarshi, bashi da wani bacin rai sai tarin farin ciki musamman lokacin haďuwarshi da Suwaiba.... Rike murfin motar tayi bayan ta gama jin tambayarshi na "Bayan biki zaki koma can canada ne? Kallonshi takeyi cikin ido dan jinta takeyi kamar yar budurwar da ta fara tsayawa da saurayi tace "In ka shirya komawa can me zai hana! Dariya Daddy yayi yace "Wato dai kin maidani joker, karfin ramawa ne bani dashi da kema kinsan bazaki sha ba, dare na daďa yi bari in wuce, Ina miki fatan alkhairi haďe da murnar samun suruka irin Nadeeyah, Allah ya basu zaman lafiya... "Ameen Anty Saude tace haďe da rufe mishi kofar cike da tausayawa halin da ďanshi yake ciki, ya zatayi ta iya yin wannan taimakon? Ya zatayi da zuciyar tata ďan in ya rasa Nadeeyah, Addu'a ita kadai ce mafita a garesu domin Allah shine kadai mai sassautawa.... Bayan tafiyarshi da awa ďaya ta tura mishi text din godiya da ban gajiya sannan tace "Akwai muhimmin abun da zan faďa maka, in shaa Allahu bayan biki komai zai ziyarci ji da ganinka, have a nice dream *Joker* ... Dariyar rashin shiri Daddy yayi ya kashe wutar dakin da Musaddiq yake ya fita daga dakin, saida yayi shirin kwanciya sannan ya tura mata cewa... *Same Sauden Himma, Amaryar gandiroba...* Dariya sosai tayi na tuno sunan Himma,, gandiroban da ya like mata lokacin yarintarta, ashe bai manta ba ta furta a hankali cike da nishaďi, *Soyayya ruwan zuma, ita soyayya babu ruwanta da tsufan mutum, in ta kama ka dole ta zautaka*..... Good morning bride, Maleekah ta faďi tana haďawa Little Nadeeyah tea, Rau Rau Nadeeyah tayi da idonta haďe da kwabe baki zatayi kuka, "Hey, ba ruwana fa, kiyi saving kukan nan zuwa anjima ki sakarwa Abbu shi, kinsan yau zasu zo bikin unknown jika... ta karashe cike da zolaya, kafaďunta Nadeeyah ta daka haďe da haďiye da kukan dake shirin zubo mata, Dariya Maleekah tayi tace "Let it flow beb, kinsan in daďi yayi maka yawa hawaye kansu dadin fita sukeji, My Inlaw da ciwo ke da kuka, nd for once baki taba tunanin zuwa dubashi ba, haba Nadeeyah, if nt for him sai kiyi for his child, kinsan duk inda kikaje that child will always connect u saboda ya riga ya haďaku... Share hawaye Nadeeyah tayi ta juya ma Maleekah baya, zancen zuci takeyi wasu hawayen na sake bulbulowa, rabon da tasa shi a idonta tun ranar mutuwar Goggo da ta shiga ďakin dan duba jikinshi lokacin yana bacci, bata san abun da zai sake sawa ya ganta domin bata san yi mishi fami akan abun da take da yakinin yana yunkurin mantawa dashi, kwana uku ya rage ta zama mallakin wani, runtse idonta tayi saboda hangota cikin wata sabuwar rayuwa, rayuwa ba tare da Mussadiq ba, wanda ya fara koyar da ita soyayya, wanda ya shayar da ita gubar soyayyar da ya illata ruhinta... "Go nd see him for the last tym Nadeeyah, atleast zai samu sukunin cewa kin damu dashi, kaddara ce zata rabaku, plsss Nadeeyah.. ta karashe haďe da hada hannayenta guri ďaya tana rokonta... duk wadannan maganganun cikin harcen turanci take yinsu... Share hawaye Nadeeyah tayi da Hijab dinta ta fara tafiya dan bin umarnin yar uwarta, tana zuwa kofar dakin taji kafarta ta fara rawa, dakyar ta iya murďa kofar tana addu'ar Allah yasa yana bacci, Ajiyar zuciya tayi bayan ta gansu kwance suna bacci shi da junior da fushi ya hanashi kwana a gurinta, shagala tayi cikin kallonsu tanajin wata irin nutsuwa na saukar mata a curarrar zuciyarta, ko ba komai hankalinta ya kwanta tunda Junior ya saki jiki da mahaifinshi, ko a yanzu tasan Musaddiq zai samu saukin kaso 50 cikin ďari... Cikin sanďa ta isa gurin gadon dan gyarawa Junior hannu dan gab yake da famawa Musaddiq ciwon dake hannunshi wanda hakan zaiyi sanadiyyar katsewar baccin da ta tabbatar yana jin dadinsa, da dabara ta gyara mishi taji ya rikota yana sambatun "Daddy am very angry with u, i will nt talk to u ever again, Dariya tayi haďe da sumbatar kumatunshi ta zame hannunta cikin nashi, bargon dake jikinsu ta gyara musu ta shafa kan Junior ta dago da niyyar yin hanyar waje, kamar gizo haka taga idon Musaddiq a buďe, sake juyowa tayi ta kalleshi tagansu a rufe, ajiyar zuciya tayi ta fara tafiya dan zuwa kofar da zata sadata da waje, "Nadeeyah... Taji ya furta a hankali wanda ya sanya hantar cikinta kadawa, tsayawa tayi cakk a gurin ba tare da ta amsa ko ta waigo ta kalleshi ba.. jin har minti uku baiyi magana ba yasata juyawa dan ganin halin da yake ciki, wannan karan a juye yake idanuwan nan a rufe wani sabon bacci ne ma yayi gaba dashi wanda daga gani kasan yana cikin mayen magani ne, da sauri ta murďa kofar ta fita saboda kwalla da taji ta taru a idonta, wannan wacce iriyar zazzafar jarabawa ce, ya Allah ka kawo mana mafita baki dayanmu dan alfarmar annabi Muhammad s.a.w..... Gidan Alhaji Mukhtar ya zama tamkar gidan zaman makoki, kamar babu wata hidima da za'ayi a cikinsa nan da kwana biyu, Anty Reemah dasu Raudha sune kadai ke hidimarsu bisa ga umurnin Daddy, sai kuma Mummy da a yanzu takan samu shigowa duba jikin Musaddiq, duk da bata samun koda gaisawa da Daddy hakan yayi mata daďi tunda ya yafe mata kuma ya yafewa 'yayanshi yana sakar musu yanzu, a yanzu bata da burin da ya wuce taga rayuwar Musaddiq ta inganta, ta rasa kalmar da zata roki Nadeeyah dashi ta yarda da auren ďanta wanda ta zama sila a rabuwarsu, gashi abun da tayi yayi sanadiyyar sanya shi cikin tsakiyar rayuwa da mutuwa... A yau ma kamar kullum bayan ta gama gyara ďakin Goggo inda take kwana ta shirya tsaff dan tafiya dubo Musaddiq sannan ta zauna ayi kamun Nadeeyah da ita, tana rufe kofa ta jiyo muryar Badariyya wacce a yanzu Yareemah Suhail ke fitowa da ita ya kawo ta har gida tun dawowar Nadeeyah,, kwancen kayan da su Husna suka bata shi ta sanya tayi kyau abunta, sannan su suwidi suma sunyi kyansu dan a yanzu suna samun sake da kuma abinci wanda duk tazo sai yan uwa sun sai mata, "A'a Badariyyah kece a gidan, to juya muje ki duba jikin Musaddiq daga nan ki jira ayi kamun Nadeeyah dake, cike da damuwa ta juya suka fita suna tattauna damuwar da Musaddiq din ke ciki a sanadinsu, Badariyya a cikin ranta ta dau alwashin kebewa da Nadeeyah ta faďa mata abubuwan da tayi wanda ya rabasu, babu mamaki taji tausayinshi in tasan baya cikin hayyacinsa sanda yayi sakin.... Bayan ta gama sauraron kalaman Badariyya wanda takeyinsu cike da nadama tace "Badariyya abun da kukayi bai isa ya raba mu ba, tunda kika ga mun rabu to tabbas Allah ya rubuta rabuwar tamu ne a lokacin, sannan a yanzu in na ki uncle Taheer shi munsan halin da zai shiga, dan Allah ku fahimceni, ni kadai nasan halin da nake ciki, ku tayani addu'a nasan komai zai daidaita da yardar Allah... Share hawaye Badariyya tayi tace "Zamu tayaki, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.... Karfe huďu da yan mintuna Nadeeyah ta shirya cikin wani lace mai kyau da tsada cikin kayan da Taheer ya dinka mata, Anty Raly ke tsaye a kanta tana gyara mata kwalliyarta haďe da yi mata ďauri, wata farar alkyabba mai adon yellow ta dauko ta daura mata a kanta wanda hakan ya sake fitar da kayatuwar da amaryar tayi, jan lallen da akayi mata ya rinu sosai ya koma dark maroon hakan ba karamin sake fitar da suffar yatsunta yayi ba, zaunar da ita Anty Raly tayi tana jiyo sautin maganganu yan biki daga waje,, Cike da masifa take shirya su Nour tana daka musu tsawar su tsaya ko ta zanesu, a hankali Nadeeyah ta janyo hannun Abee tace "Kawo in shiryashi Husna, "Barshi.. kadai ta faďi haďe da janyo hannunshi ta sa mishi irin kayan dake jikin Hafeez, oya a je ayi wasa, banda barna da bata jiki, mikewa tayi da niyyar shiga bayi Nadeeyah ta riko hannunta, "Husnah nasan ni mai laif--- Lokaci na kurewa Nadeeyah, baki da laifin komai kaddararmu ce tazo a haka, na kasa dai jin saukin zuciyata ne shiyasa har yanzun kika ganni haka, with time in shaa Allah komai zai daidaita, Husnah ta katseta fuskar nan murtuke tamkar wacce akayi ma mutuwa.. ganin Nadeeyah na kokarin sake magana yasata zame hannunta daga cikin nata ta faďa bayi, wani irin kuka ne yazo musu a tare mai cin rai, saida sukaci suka koshi sannan Husnah tayi wanka ta fito ta shirya da sauri sauri tayi waje.... Sai biyar da kusan rabi dangin Taheer suka zo sa lallen amarya, sai da suka biya kawayen amarya wacce Amal ce kaďai sai Raliya da ta shiga cikin zancen, turaruka masu kamshin gaske suka karar a jikinta sauran yan uwansu na Agadez wadanda suka ji dadin ganin Nadeeyah da Hafeez suna rangaďa guďa, kwaryar nono wacce suka kawo gidan kanta ta kai hamsin, banda sauran gararrakin arziki da suka kawo, sunci sun sha a gidan sosai dan komai nasu daban aka ware musu, sai bayan Isha'i motocin da suka kawosu suka maida su.... A daddafe Musaddiq ya amsa gaisuwar Taheer wanda ke tsaye rike da danshi cikin tsadajjiyar shadda iri ďaya, lallaba Junior ya shiga yi bayan ya fuskanci irin fushin da yakeyi dashi, sannan kuma dan ya daukewa kanshi damuwar da ke cinshi tun kwana uku baya, wani mugun tari yaji Musaddiq nayi wanda ya sanyashi sakin hannun Junior ya isa gareshi haďe da dauko ruwa yana faďin sannu, ga ruwa kasha, runtse ido Musaddiq yayi haďe da kauda fuskarshi gefe, ya riga ya gama yanke duk wani hukuncin da ya dace, yasani a yanzu ganin gobe a gareshi nada matukar wahala, a yanzu ya sadaukar da komai yasan Nadeeyah da ďanshi bazasu taba yin kunci ba tunda suna tare da nagartaccen mutum irin Taheer wanda a haďuwarka dashi ta farko zata tabbatar da hakan komin kinka dashi, dafe kanshi yayi da hannayenshi biyu saboda hawayen dake zubo mishi babu kakkautawa, Mikewa Taheer yayi dukkan lakar jikinshi a sake ya kama hannun Junior suka sauka kasa, a hanyar da zai sadasu da kofar fita ya haďu da Hilal da ya dawo daga rakiyar abokansu, shima duk ya fukace ya fita hayyacinshi kamar shine mai ciwon, "A'a yallabai har kun fito, ya faďi yana mika mishi hannu, "Eh dare nayi, Allah ya bashi lafiya, "Ameen Hilal ya amsa haďe cewa sai da safe mun gode, "Allah ya tashemu lafiya Taheer yace yana mai saka kafarshi a waje, A gurin motarshi suka tsaya ya kira number Nadeeyah wacce ke kan dadduma tana zubda kwallar da ta zame mata jiki, a hankali ta ďauka cikin nuna bata cikin damuwa tace "Uncle kun wuce ne? "No muna waje, muna san ganinki ne ya faďi wani ďaci na tokare makogaronshi, Kara sassauta murya tayi tace "Gobe ne fa, daga gobe bazan sake barin gefenka ba, har sai ka gaji da ganina, kayi hakuri plss, Lumshe idanuwanshi yayi haďe da kallon sama a zuciyarshi yana rokon ubangiji sassauci akan wannan jarabawar, *Tayi min tsauri da yawa* ya faďi ba tare da yasan ta fito ba, yana mai kwantar da kanshi kan murfin motar, "Gani nan zuwa Uncle, in dai rashin ganina yayi maka tsauri, bakayi deserving shan wahala akaina ba, bata jira amsarshi ba ta kashe wayar ta mike haďe da ninke dardumar tayi waje.... Duk abin nan da sukeyi a kunnen Raudha wacce ta fashe da kukan Nadama, gashi dukkaninsu na suffering daga mugun halinsu, babu wanda ya tsira, shiyasa akace Sharri dan aike ne, in ka aikashi dawowa yakeyi ya shafi wanda bai nan sanda kayi aiken, tayi nadama matuka a yanzu da itama bata ga tsuntsu, domin ko ďuriyar 'yayanta bata ji, har gara Radiya ta roki Shamsu ta waya yayi mata alkawarin yana dawowa italy zaizo su sasanta, ita fa, babu waya daga Abbati bare har tasan ko har yanzu yana nan da ragowar soyayyarta a cikin ranshi, Addu'a ta shiga yi ba kakkautawa tana faďawa Allah damuwarta haďe da neman afuwarshi..... Cike da kulawa ya kalleta yace "Kuka ko? Wa ya sa kanwata kuka har ya koďar min da idanuwanta? Rufe fuskarta tayi da hijab kukan da ke tokare a wuyanta ya fito da karfinshi, barinta yayi tayi ma'ishi sannan yace "Me kike so? Tell me ko me kike so zanyi miki in dai zai saki daina zubar hawaye kullum, Junior ya faďa min bakya cin abinci, bakya kula dashi, har ihu kike mishi, tell me ur problem, i promise to solve it for u komin wahalarshi... Hannunshi ta riko a hankali tace "With u my problems are always solved, bani da wata matsala Uncle, thanks for always being dere for me.... Sanya hannun yayi ya share mata hawayenta shima duk gabban jikinshi a karye suke a zuciyarshi yace "I will also solve this for u, sadaukarwa a soyayya wani abu ne, i will make sure u get wat u want, a fili kuma cewa yayi ta kwantar da hankalinta zai cigaba da solving ko wace irin matsala tata har ranar da kasa zata rufe idonshi.. kwantar da fuskarta tayi kan tafukan hannunshi wasu sabbin hawayen na zuba a kansu.. "Bari in tashi Junior yazo yaga shagwabar da baya yi Mamma nayi, abin kunya ya faďi cike da zolaya yana girgiza kai, Dariya tayi sosai tace "Kai ka koya min, leka cikin motar tayi ta hangoshi kwance ya mike yana bacci, "ya kamata ku tafi gida, plss uncle kuyi bacci gobe kasan zakasha wahala sosai, "Ai bakinki ne wahala, ke zanma wannan faďan, kuma ki tabbatar kinci abinci yanzu kafin ki kwanta, inason gobe in ganki kinyi kiba kamar Husnah kina jina ko, Buďe baki tayi tana dariya tace "sai dai in kamoka, ko kuma------ Ihun da suka jiyo a cikin gidan ne yasata katse maganar da tayi niyya, tabbas wannan muryar Hilal ce sai kuma ta Husna da ta biyo baya, da sauri ya rufe kofar suka ruga ciki da gudu.. Ganin daukacin yan gidan sun nufi dakin da Musaddiq yake yasasu nufar ďakin suma, a tare suka iso ciki da Daddy, abin da suka tarar ne tada hankalinsu, Hilal ne ke kokawar kwace kwalbar hannun Musaddiq ya kasa saboda wani irin karfi da ya karu wa Musaddiq, sannan kuma girman ba ďaya ba, duk sauran yan uwanshi dake gurin sunyi yunkurin karba ya hanasu, Tsaye Daddy yayi ya kasa tabuka komai saboda bashi da karfin yin wani abu domin yayi iya kokarinshi ya fahimtar da ďàn nashi ba komai kake so kake samu ba, bazai iya tunkararsa ba a yanzu ya riga ya sare da rayuwar danshi, yasan zaiyi matukar wahala ya rayu.. ganin Daddy ya kasa cewa komai yasa su Anty Reemah sake sakin wani kukan, ita kuwa Husnah kiran wayar Hafeez da Papy takeyi tana ihu tana kiran sunan Musaddiq, Da sauri Taheer yayi gurin suka haďu da Hilal suna kokawar tare, wani hauri ya kaiwa Hilal a ciki wanda sam baisan yayi ba ma, ya riga yaci alwashin aikatawa shiyasa yasa ďaya daga cikin abokansu siyo mishi ba tare da yasan abun da zaiyi dashi ba, sannan abun da idonshi ya gane mishi daga sama shi ya sake tunzura zuciyarshi ya tabbatarwa kanshi babu fashi sai ya aikata abun da yayi niyya... Rike ciki Hilal yayi ya kasa tashi aka bar shi da Taheer da ya matse hannunshi koda kuwa kwalbar zata tsaga dukkan hannunsu, ba tare da ankara ba Taheer yaji nashi ta bayan hannun, a gigice ya saki hannun wanda hakan ya bawa Musaddiq damar ďaga kwalbar da sauri, ihuu dakin ya dauka suna rokarshi da Allah da annabi, Juyawa Daddy yayi ya bar ďakin yana mai kuka cikin zuciyarsa na irin tarbiyar da kowanne cikin 'ya'yansa suka samu, ya sadakar ďan da yafi kowa kauna cikin yayanshi yau zai kauracewa ganinshi, ya barshi ya aikata abun da yake so domin kuwa ko ya hanashi sai ya aikata tunda tun tasowarshi bai nemi abu ya rasa ba sai wannan.. A hanzarce Nadeeyah ta haye gadon da zai sadata da daidai hannunshi ta sanya iya karfinta ta kabe hannun haďe da daukeshi da lafiyayyun mari har biyu sannan tayi mishi wata iriyar runguma wacce bin umurni ne daga zuciyarta, Tsittt dakin yayi kamar babu wani mahaluki da yake rayuwa a cikinsa, daddadar muryar Nadeeyah kaďai ake ji wacce take fitar da ita cikin raunannen kuka....... more on our website 👇👇👇 https://hausanovels001.com.ng Mrs Tijjani Shattimah........