https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* Page_001 ___K'arfe 7pm ne na daren ranar juma'a, tana zaune kan er kujerar dake gaban mudubin ta hannun ta rik'e da waya er k'arama wadda wasu ke kira da rakani kashi, sassanyan murmushi ke tashi daga kyakykyawar doguwar farar fuskar ta, tana nan zaune har zuwa lokacin da wata mata wadda kana ganin ta kasan mahaefiyar tace, saboda tsananin kama da suke yi, ta yaye labulen d'akin ta lek'o tana kallan ta "AYRAH wae har yanzu jiran Abban kike?" Murmushi ne ya sake wanzuwa akan fuskar wadda aka kira da Ayrahn wanda hakan ya bawa dimple d'in dake gefen kowanne kumatun ta lotsawa sosae sannan tace cikin muryar ta me dad'in saurare "Ehh Umma.." ta6e baki Umma tayi tace "Ae se kiyi ta jira.." daga haka ta saki labulen ta koma tsakar gida. Tana nan zaune bayan wajen minti 10 ta jiyo sallamar mahaefin nata daga tsakar gidan su, seta ajjiye wayar da sauri akan gadon sannan ta mik'e ta yaye labulen d'akin ta fito, hasken farin wata da kuma na k'wan fitilar da suka kunna ya sanya ni ganin kyakykyawar fuskar ta da har zan iya kwatanta muku ita, matsashiya ce er kimanin shekaru 19 doguwa ce fara sosae, me idanu manya manya da dogon siririn hanci, se d'an k'aramin red lips d'in ta, sanye take cikin doguwar riga bak'a babu d'an kwali a kanta dan haka ta yafa mayafin doguwar rigar akan ta "Abba sannu da zuwa.." ta fad'a tana neman waje ta zauna "Yawwah Ayrah" Abban ya fad'a yana neman waje ya zauna sannan da murmushi kan fuskar sa ya sake kallan Ayrahn bayan ya amsa sannu da zuwan da Umma ke masa "Toh in gyara zama dae in sha labarin karatun kin nan, dan da alama akwae magana a bakin ki" murmushi ta sake yi sannan tace "Abba ae tun d'azu kae nake jira nazo muku da wani babban albishir" Umma ta kalli Abba tace "Ahh toh, tun d'azu tak'i fad'a min abinda yake ta sanya ta murmushi tace seka dawo.." Abba ya maeda duban sa kan Ayrah yace "Toh muna jin ki, Allah yasa alkhaeri ne" gyara zama tayi daga inda take zaune sannan ta fara magana har lokacin murmushi yak'i barin kyakykyawar fuskar ta "Abba na had'u da RAJ.." ta fad'a da mad'aukakin murmushi akan fuskar ta, cikin rashin fahimta dukkan su suka kalle ta, seta d'an tsaya itama tana kallan su kafin tace "Raj fa nake nufi, Umma Raj d'ina fa, kun tuna?" ta fad'a tana d'an murmushi dan ita in dae akan Raj ne bata da wata kunya, kallan juna Umma da Abba suka yi kafin Abba ya runtse idanun sa sannan ya fara k'ok'arin magana "Umma cewa yayi ma na fad'a tun wuri Abbun sa zasu zo wajen Abba" Ayrah ta fad'a kafin Abban ya fara magana, Umma dake lura da yanayin Abba ta furta a hankali tana kallan sa sosae "Abban su lafiya dae koh?" jinjina kae yayi kafin cikin er dakiya ya furta "Kina nufin Raj d'an gidan Kabeeru..?" seta jinjina kae cikin jin dad'in yadda Abban ya gane maganar ta ta tace "Ehh Abba, bama mu ta6a tunanin.." d'aga mata hannun da Abba yayi ne ya sanya ta dakatawa daga fad'in maganar da take k'ok'arin fad'a, ta cigaba da kallan yadda lokaci guda k'wayar idanun sa ta sauya, haka zalika Umma ma tak'i kallan ta, seda Abban ya sake runtse idanun sa sannan ya bud'e ya fara fad'in "Kar ki sake min maganar sa ko maganar wanda ya shafi ahalin su gaba d'aya.." Abba ya k'arasa maganar idanun sa na sake yin jawur, cikin rashin fahimta take kallan Abban nasu, ta kuma kalli Umma sannan tace a d'an rud'e "Abba ko dae ka bayar dani ne ga wani bansani ba? Abba cewa nayi fa Raj ke so azo a nemar masa aure na.." "Ayrah..ki tashi ki bar wajen nan idan baso kike zuciya ta ta buga ba" Fararen idanun ta dake d'auke da bak'a sid'ik d'in k'wayar idanu ta d'aga ta sake duban mahaefin nata, take wasu k'walla suka tarar mata tana jin yadda k'irjin ta ke bugawa da k'arfin gaske, "me yake faruwa ne?" ta tambayi kanta "Abba Raj ne fa, Abba Raj dae wanda ka sani fa, akan sa nake magana.." Abba ya runtse idanun sa yana jin wani irin zafi a cikin ransa cikin 6acin rae ya furta "Ki saka a ranki in dae ina raye, har abada ba zaki ta6a auren Suraj ba" da wani irin razana ta d'aga ido ta kalli mahaefin nata, tana jin yadda kalaman nasa ke sauka a cikin kunnuwan ta kamar saukar mashi, kafin takae ga cewa komae ta sake jiyo Abban nata yana fad'in "Ki kawo koma waye a fad'in garin nan gaba d'aya amma dae_dae da minti d'aya kada ki sake ki yaudari kanki kiyi tunanin zan aura miki Raj, bama Raj ba duk wani daya dangance su bazan ta6a aura miki shi ba" kuka ne ya k'wace mata babu k'ak'k'autawa tana jin wani iri a rae da zuciya har ma da gangar jikin ta, a hankali taja k'afafun ta da rarrafe ta k'arasa gaban mahaefin nata ta rik'o k'afafun sa sannan ta fara magana cikin kuka, kyakykyawar fuskar nan ta ta tayi jajir "Abba..ka tausaya min, Abba ka taemakawa zuciya ta, Abba ko da wannan ce zata zama alfarma ta k'arshe da zaka iya yi min a rayuwa Abba kayi min ita don Allah" ta k'arasa fad'a tana sake fashewa da wani sabon kuka, a hankali Abba ya zame k'afafun sa bugun zuciyar sa na k'aruwa ko ba'a gwada shi ba tabbas yasan ciwon sa na dab da tashi, ya d'an runtse idanun sa kad'an sannan ya fara k'ok'arin tafiya, ta sake rik'o k'afafun nasa tana kuka kamar wadda ranta ze fita "Abba ina k'aunar Raj, zuciya ta zata iya bugawa idan kace zaka rabani da shi, Abba kace wani abu don Allah" juyowa Abba yayi yana kallan ta kana a fusace yace "Ko mutuwa zaki yi ba zaki ta6a auren Raj ba.." daga haka ya wuce d'akin sa, mik'ewar da Umma tayi ne ya sanya ta d'ago fuskar ta da tayi jajir tace "Umma ya zaki tafi ki barni cikin duhu, Umma me Raj ya muku da Abba zece bazan aure shi ba, Umma Raj fa ko har yanzu baku gane wanda nake magana akansa ba.. Umma kiyi wa Abba bayani don Allah" ta k'arasa maganar sanda wani kukan yaci k'arfin ta, ko kallan inda take Umma ba tayi ba ta wuce cikin d'akin da Abba ya shiga.. A hankali ta cigaba da rera kukan ta, seda tayi me isarta sannan taja k'afafun ta zuwa cikin d'akin ta har lokacin hawaye yak'i dena sintiri akan kuncin ta, wayar ta dake ajje ta d'akko ta danno wata number ta kira... ... A hankali ya sako k'afafun sa farare tass dake cikin takalmin wanka, seda ya cire su daga k'ofar toilet d'in sannan ya sako kansa zuwa cikin kyakykyawan bedroom d'in, k'arasawa yayi bakin k'aton mudubin sa ya sanya hannu ya d'auki comb ya fara taje sumar kansa data sha gyara sosae, banda ruwan daya ta6a ta a gyara take tsaf se tashin k'amshi me dad'i da take yi, yanayin yadda yake d'auke da towel ne ya sanya ni ganin yadda k'ak'k'arfan jikin sa yake, dogo ne me k'ak'k'arfan jiki, fari ne sosae wanda hakan ya sanya bak'ar sumar dake kan k'irjin sa ta bayyana kan ta sosae kan farar fatar sa wadda ke kwance luff luff kamar wadda ake kwantar da ita da Comb, yana da dogon hanci me tsayi, fuskar sa d'auke da bak'in sajen daya zagaye bakin sa, ringing d'in da yaji wayar sa nayi ne ya sanya shi sakin wani k'ayataccen murmushi ya ajje comb d'in kan stool d'in sannan ya mik'e ya k'arasa inda wayar ke ajje ya d'auka kana ya zauna ya jinjina da pillown dake kan tank'amemen gadon sa kana ya kara wayar a kunne bayan ya d'aga, da kukan ta ya fara cin karo cikin wayar, seya mik'e zaune yana bud'e manyan idanun sa yace "Subhanallahi..Ayrah meya saki kuka?" ya fad'a cikin kulawa, cigaba da kukan tayi kamar ranta ze fita, daga inda yake zaune kuwa yana jin kamar ana watsa masa dalma ne, mik'ewa tsaye yayi ya murza goshin sa da d'ayan hannun sa yana lumshe idanun sa har lokacin bata bar kukan ba, ya kuma yin k'asa da muryar sa yace "Ya isa haka don Allah, ya isa haka, pls kiyi shiru ki fad'a min why are u crying.." ya sake fad'a cikin rarrashi "Raj.." ta fad'a cikin kukan, ya lumshe idanu yana jin muryar ta ta har cikin gangar jikin sa "Na'am.. Ayrah, pls menene Uhmm?" daga inda take zaune ta d'an lumshe idanu tana sassauta kukan ta koma sheshshek'a se can ta fara magana tana yi tana d'an aje ajiyar zuciya "Abba ne.." "Me Abban yayi?" ya fad'a yana jin yadda ya k'agu yaji abinda ya sanya ta kuka haka "Abba yace bazan aure ka ba.. Raj meka yiwa Abba?" cikin rashin fahimta ya sake bud'e manyan idanun sa kana yace "Ni kuma?" kamar tana gaban sa ta jinjina kae, kafin yace komae kuma ta sake cewa "Na yarda da kae Raj, kawae ka fad'awa Abbun ku yazo wajen Abba, ina tunanin be gane Raj d'in da nake nufi ba.." neman waje yayi ya zauna kafin yace "Ohk..In Sha Allah, yanzu dae ki dena kukan kinji? In Sha Allah ni naki ne kema kuma tawa ce kinji?" jinjina kae tayi ba tare da tace komae ba, se kuma can tace "Ehh.." "Oh yah Smile.." ya fad'a daga inda yake yana d'an murmushi, goge fuskar ta tayi sannan ta d'an yi murmushin me d'an sauti wanda tasan hakan ze faran ta masa "Awwnnn That's my girl..yanzu dae ki aje waya kiyi bacci zan je na samu Abbu da wannan maganar.. I luv u.." ya k'arasa fad'a idanun sa a lumshe, itama nata idanun ta lumshe kamin tace "Tohm.." Tashi yayi ya k'arasa shiryawa cikin wata bluen shadda dan babu k'arya yayi missing manyan kaya, ba tare da ya d'ora hula akan sumar kansa ba ya d'auki wayar sa har lokacin be dena mamakin dalilin da yasa Abban nata yace haka ba. Kae tsaye parlourn k'asa ya sauko cikin nutsuwar data zame masa jiki, dae_dae lokacin da wata farar mata wadda ak'alla zatayi shekaru 45 zuwa 50, kyakykyawa ce kamar yadda d'an nata yake, tana sanye cikin wata atamfa me kyau d'inkin riga da skirt, jera warmers d'in data fito dasu daga kitchen akan dinning take, ta kalle shi da murmushi kan fuskar ta sannan tace "Ka k'araso ka fara cin abinci koh?, semu zauna mu samu muyi hira.." d'an murmushi ya saki kad'an kamin ya shafa sumar kansa yace "Tohm Ummee.. Amma inaso ne muyi wata magana me muhimmaci.." ya fad'a yana d'an lumshe manyan idanun sa kad'an, dae_dae lokacin Ummee ta gama jera kayan data fito dasu seta k'araso inda yake tsaye tace tana murmushi "Shikenan Raj, ni dama daga yadda na ganka nasan akwae magana a bakin ka" shima murmushin ya maeda mata sannan dukkan su suka wuce zuwa cikin k'aton parlourn daya k'awatu da had'ad'd'un kujeru, suna zama Alhaji Kabeer ya shigo cikin d'akin da sallama sanye cikin manyan kaya da babbar riga, dukan su suka amsa masa ya k'araso yana kallan su su duka kuma a lokaci guda yana amsa sannu da zuwan da suke masa, akan kujera ya zauna, yayin da Raj ya sauko daga kan kujerar yana shirin zama a k'asa Alhaji Kabeer yace "A'ah kayi komawar ka ka zauna, yau ae hira zamuyi.." murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa seya koma ya zauna yana kallan Alhaji Kabeer yace "Barka da dawowa Abbu.." "Barka kadae Raj" "Ko dae a kawo maka abincin nan ne?" Ummee ta fad'a tana kallan Abbun, girgiza kae yayi kafin yace "A'ah fara kawo min dae juice na sha.." mik'ewa Ummee tayi ta wuce inda ze sadata da dinning area, yayin da Abbu ya dawo da duban sa kan Raj yace "Ya hanyar dae? Kuma ya karatun?" "Alhamdulillah Abbu..ina tafe da wani albishir fa.." ya fad'a da murmushi kan fuskar sa, dae_dae lokacin da Ummee ta k'araso hannun ta d'auke da juice d'in ta ajjiye sannan ta fara k'ok'arin zubawa a cikin tambulan "Toh ko zamu bari mu fara cin abinci?" Abbu ya fad'a yana kar6ar juice d'in da Ummee ta mik'a masa kana ta nemi waje ta zauna, hannun sa ya kae kan sumar kansa ya d'an shafa sannan yace "A'ah Abbu.. Na k'agu na sanar daku ne.." Ummee ta kalli Abbu tana murmushi tace "Ae kawae ka k'yale shi ya fad'a dan tun d'azu ya kasa komae har abincin ma shima beci ba.." "Ohk ina jin ka.." Abbu ya fad'a yana kae juice d'in bakin sa "Abbu na samu matar aure.." dukkan su suka kalle shi cike da mamaki da kuma farin ciki duka a lokaci guda, mutumin da suka san kwata kwata baya kula wasu mata amma yau shine ke fad'in ya samu matar aure? Toh ta yaya? "Wacece wannan Raj?" Ummee tayi k'arfin halin fad'in haka, wani k'ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace bayan ya lumshe idanun sa ya bud'e "Ayrah.." "Wacece Ayrah?" Ummee ta fad'a tana kafe shi da idanun ta "Ayrah dae wadda kika sani Ummee, kada kice min har kin manta ta, Ayrah dae tawa wadda kika sani.." k'warewar da Abba yayi ne ya sanya su duka suka kalle shi, babu k'ak'k'autawa ya shiga yin tari sosae, da sauri Raj ya mik'e ya isa fridge ya d'akko ruwa ya kawowa Abbun, da k'yar ya iya kar6a yasha ruwan, ya shiga sauke ajiyar zuciya kamar wanda yayi gudu "Sannu Abbu..sannu.." shine abinda Ummee keta maemaetawa amma Abbun bebi ta kanta ba ya kalli Raj yace "Ya..akayi ka had'u da ita?" yayi maganar a rarrabe yana kallan Raj, sosae Raj ke binsa da kallo yana so ya gano abinda ya sanya shi lokaci d'aya ya zama wani iri "Abbu.." "Ya akayi ka had'u da ita? Ko dama kuna tare tsawon lokacin nan?" Abbu ya katse masa maganar da yayi niyyar yi, girgiza kae Raj yayi har lokacin idanun sa nakan Abbu "Tun wuri ka rabu da ita Raj, ka rabu da ita dan auren ku baze ta6a yiwuwa ba, tun wuri ma ka cire ta a ranka zefi maka.." Abbu ya fad'a yana mik'ewa yayi hanyar d'akin sa, da kallo yabi Abbun sannan ya maeda duban sa kan Ummee yana jin yanda k'irjin sa ke bugawa "Ummee.." ya fad'a yana kallan ta, seta mik'e kawae tabi bayan Abbun a ranta tana sak'a yadda zasu 6illowa al'amarin, lallae idan ba suyi wasa ba suna cikin matsala.. Runtse idanun sa yayi har lokacin yana jin yadda bugun zuciyar sa ke k'aruwa, me yake faruwa ne? Yakae wajen minti 5 zaune a wajen yana sak'awa da warwarewa sannan ya d'auki wayar sa ya lalubo number ta ya danna kira. A 6angaren ta kuwa har lokacin tana kwance kan madaedaecin gadon d'akin, kanta d'ore akan pillow hawayen da suka k'i tsayawa se zuba suke akan pillown, kanta babu d'an kwali hakan ya bawa sumar kanta damar bajewa akan pillown, dae_dae lokacin da kiran wayar tasa ya shigo wayar ta yayi dae_dae da lokacin da Umma ta yaye labulen d'akin ta shigo, ringing d'in da taji ya sanya ta kallan wayar, Ayrah ta tashi zaune tana kallan Umman lokaci guda tana maeda duban ta kan wayar "Mik'omin wayar.." Umma ta fad'a tana mik'a hannun ta, lumshe manyan idanun ta tayi wasu hawaye masu d'umi suna zubowa akan kuncin ta, ganin bata da niyyar mik'o mata wayar ne yasa Umman ta k'arasa da kanta ta d'auki wayar ta kashe ta gaba d'ayan ta sannan ta kalli Ayrah data fashe da wani irin kuka tace "Kiyi shiru ki dena kuka, ki tsaya ki saurare ni, base kin tada hankalin mu muma mun tayar da naki ba.." kafin Umman ta kae k'arshen zancen ta Ayrah tace cikin kuka tana girgiza kae "Umma meyasa haka? Shin baku san wanene Raj ba? Baku san halin sa ba? Ko kuwa iyayen sane baku sani ba.." K'arasawa Umma tayi ta zauna akan gadon kana ta kamo Ayrahn cikin jikin ta, bata fara magana ba seda taji ta fara sauke ajiyar zuciya, sannan ta kama dogon gashin Ayrahn ta d'aure a tsakiyar kanta kana ta fara magana a nutse tana jin zuciyar ta na mata wani irin zafi... B'angaren sa kuwa runtse idanun sa yayi bayan ya sake kiran layin Ayrah yaji shi a kashe, yaja wani dogon numfashi sannan ya mik'e akan k'afafun sa yana daedaeta nutsuwar sa a ransa yana jin ya zama dole yasan aenahin abinda yake faruwa kafin k'wak'walwar sa ta tarwatse, dan kuwa tabbas akwae rina a kaba, me yake faruwa haka?..... _*TUSHEN LABARI*_ ZARAH AUTA (Mhiz Innocent) ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page_002 ____kyakykyawa ce fara sol me manyan idanuwa, haka zalika kuma me k'aramin jiki da dogon hanci, a kallan farko zaka iya k'iyasta shekarun ta, san haka baza ta wuce shekaru 4 ba, tana sanye cikin Uniform dake a goge fes fes dasu, hannun ta d'auke da basket d'in ta dake d'auke da flask d'in abinci na yara en makaranta da kuma rubber ruwa, da d'an gudun ta take fitowa daga cikin d'akin daya kasance mallakin ta, fuskar ta d'auke da murmushi, seda tazo dab da Abban nata sannan tace cikin muryar ta da bata gama fita sosae ba "Abba na shirya.." "Yawwah..Ayrah" Abba ya fad'a yana jan kumatun ta kafin ya d'ora da fad'in "Ina yayan naki?" d'an k'aramin bakin ta ta tura gaba kad'an kana tace "Abba Yah Sadeeq fa be shirya ba" kafin Abban ya sake cewa komae sega Sadeeq d'in ya fito, fari ne se dae ba can ba, amma kamar su d'aya da Ayrahn, wanda hakan ze alamta maka da cewar yayan tane, shima yana sanye cikin Uniform d'in kamar nata, sedae akwae d'an banbanci a Uniform d'in nasu wanda hakan ke nuni da ita a primary take yayin da shi kuma yake a secondary, shima nasan a wanke suke tass kuma a goge hannun sa rik'e da jaka yana k'ok'arin goyawa a bayan sa yace sanda yazo kusa da Abba bayan ya watsawa Ayrah harara "Abba ka ganni fa a shirye nake.." mik'ewa Abba yayi yana rik'e da hannun Ayrah dae_dae lokacin da Umma ta fito daga kitchen tana kallan Sadeeq tace "Ba zakayi break bane?" kallan Umman yayi kafin ya saci kallan Abba "Wato so kake ka janyowa kan ka wata cutar koh?" sosa kansa yayi kana yace har lokacin kan nasa a k'asa "A'ah fa Abba, ae ina siyar wani abun a school.." "Toh yayi kyau, amma ko tea ne ka dinga sha ko ka samu hanjin ka ya warware" "Toh Abba.." ya amsa a hankali "Toh Allah ya tsare, ya bada sa'a.." Umma ta fad'a tana binsu da kallo su duka, suka amsa da "Ameen" sannan suka fice daga d'akin... Kae tsaye fire service suka wuce inda Abban ke ajiye motar sa k'irar Civic Honda, suka jira shi a bakin wajen, ya shiga ya d'auko sannan suka shiga ya wuce dasu zuwa makarantar kamar koda yaushe, a bakin makarantar ya ajiye su bayan ya sallami kowannen su sannan shi kuma ya wuce wata makarantar government da yake koyarwa a cikin garin nasu.. Hannun Ayrah cikin na Yah Sadeeq har suka k'arasa bakin ajin su Ayrahn, sannan ya sakar mata hannun yace yana kallan ta "Ayi karatu sosae, banda k'iriniya" "Toh" ta fad'a kawae tana yin cikin ajin nasu, seda yaga ta shiga sannan ya wuce nasu ajin.. Wajen k'arfe 10 aka fito break, kamar koda yaushe ita da k'awayen ta kan fito harabar makarantar suyi wasa bayan sun gama cin abincin, yau ma hakan ce ta kasance, dan kuwa suna gama cin abincin suka fito wajen suka fara wasan su irin na yara.. A hankali idanun ta suka sauka akan sa kamar koda yaushe yana zaune akan wani d'an dandamalin dake k'ofar wani aji, yayi shiru wani lokacin yana d'an kallan abinda ke faruwa a cikin makarantar, wani lokacin kuma idanun sa na kallan k'asa ko wani wajen, cigaba tayi da wasan ta sedae lokaci zuwa lokaci takan juya ta kalle shi har zuwa lokacin da aka koma break d'in suka koma aji bayan sunyi butu butu da Uniform d'in nasu. Suna zaune cikin ajin wani malami na musu karatu, seta d'an saci kallan tagar su da take kallan k'ofar ajin, kamar yadda ta tsammata kuwa seta hange shi d'an nesa kad'an yana lek'owa cikin ajin yana kallan malamin, cigaba tayi da kallan sa ba tare da ta cigaba da saurarar malamin ba "Ayrah!!" taji malamin ya ambata, seta juyo da sauri tana gyara zaman ta, idanun ta da suka yi rau rau akan malamin, maeda duban sa yayi kan inda take kalla, ganin haka ya sanya yaron saurin yin k'asa da kansa dan kar a gansa, hakan yasa malamin bega komae ba, da mamaki ya tako zuwa inda take yace yana kallan ta "Me kike kalla acan?" kamar zata fashe da kuka tace "Ba komae.." ta fad'a d'an k'aramin bakin ta a gaba, sake kallan wajen malamin yayi sannan ya dawo da duban sa kanta yace "Ohk toh me muke cewa?" ita sam bama ta gane tambayar da yake mata ba dan haka kawae ta bishi da kallo, ya girgiza kae kawae sannan ya koma ya cigaba da abinda yake yi, bata sake kallan wajen ba ta bada hankalin ta wajen karatun da ake musu, dan kullum ne idan ta koma gida se Yah Sadeeq ya sanya ta a gaba ta masa bitar abinda aka koya musu.. K'arfe 2 da en mintuna Abba yazo ya d'auke su a motar sa kamar koda yaushe, tunda suka shiga motar Ayrah keta basu labarin abinda ya faru a makaranta, Abba nata biye mata, yayin da wani lokacin Yah Sadeeq ya amsa mata wani lokacin yayi shiru har zuwa sanda suka isa gida, Abba ya sauke su a inda ya saba sauke su sannan ya wuce da motar tasa zuwa inda ya saba ajiye ta.. Sun riga shi shiga gida, da gudu Ayrah ta shige gidan tana k'walawa Umma kira, Umma dake kitchen ta fito tana kallan su tace "Sannun ku da zuwa yaran kirki" Yah Sadeeq ne ya amsa da "Yawwah Umma" yana cire jakar bayan sa, kallan sa Umma tayi sannan tace "Zaka fara cin abinci ne ko seka yi wanka?" "A'ah Umma bari nayi wankan, ina so ne nayi muraja'a kafin muje Islamiyya" "Ohk tohm" ta fad'a tana maeda duban ta kan Ayrah dake rik'e da hannayen ta "Umma kinsan me?" ta fad'a tana ware manyan idanun ta, murmushi Umma tayi sannan tace "A'ah sekin fad'a.." seta ta6e baki kamar wata babba sannan tace "Umma wani yaro a makarantar mu kullum sena ganshi idan Uncle ya shigo yana lek'e ta window" "Shi ba d'an makarantar bane?" Umma ta fad'a tana kallan sa "Ehh Umma" Ayrahn ta fad'a kawae ba dan tana da tabbacin abinda ta fad'a ba "Ke banda sharri.." Yah Sadeeq dake shirin mik'ewa ya fad'a "Allah kuwa da wasa nake.." ta fad'a dan ita a hausar ta idan tace da wasa take toh tana nufin da gaske take, idan kuma tace da gaske take toh tana nufin da wasa take, ta fad'a tana d'an rufe idanun ta hannun ta a saetin bakin ta "Lallae.." Yah Sadeeq ya fad'a yana mik'ewa da dariya akan fuskar sa na wannan hausar ta Ayrah "Toh yanzu dae muje na shirya ki ku wuce makaranta.." Umma ta fad'a dan tasan shirmen Ayrahn, Umman da kanta ta mata wanka ta sanya mata kayan Islamiyyar sannan suka fito suka ci abinci kana suka wuce Islamiyyar.. Washe gari ma hakan ce ta kasance koda suka je makarantar seda taga wannan yaron yana lek'e ta taga har zuwa sanda Abba yazo ya d'auke su, tunda suka shiga motar Yah Sadeeq ya fahimci akwae matsala dangane da mahaefin nasu saboda gaba d'aya yanayin sa ya chanja, amma ita kuwa Ayrah yarinta besa ta fahimci hakan ba ta cigaba da hirar data saba musu, inda Abban ke iya k'ok'arin sa wajen biye mata.. Tunda suka shiga gidan ya kasa mik'ewa ya tafi d'aki yayi wanka, dan haka sallah kawae yayi ya cigaba da zama cikin d'akin har zuwa sanda Abban ya shigo da sallama zuwa cikin d'akin, shi da Umma suka amsa sallamar tasa suna binsa da kallo, haka kawae k'irjin Umma ya buga da ganin yanayin Abban da bata saba gani a tattare dashi ba, amma se ba tace komae ba ta barshi ya zauna tace a hankali "Sannu da zuwa Abban su.." "Yawwah" ya fad'a ba tare daya kalle ta ba "Abba sannu da zuwa" Yah Sadeeq ya fad'a yana kallan Abban, mik'ewa Umma tayi da niyyar samo masa ko d'an ruwa ne wanda ze sanyaya masa zuciya, amma se taji yace "Dawo ki zauna kiji abinda ya same mu kuma.." babu musu ta dawo ta zauna tana jin k'irjin ta na cigaba bugawa, ganin kamar zaman nasa beyi bane ya sanya shi mik'ewa tunda duk alama ta nuna iyayen nasa magana zasuyi "Sadeeq dawo ka zauna.." Abba ya fad'a yana kallan Yah Sadeeq, komawa yayi daga niyyar tashin da yake yi, Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Wato ina chanjin dana fad'a miki anyi na principles da sauran manyan masu muk'ami?" Umma ta lumshe idanun ta sannan tace "Ehh.." "Toh tsautsayi ya biyo ta kanmu, an sallame mu..wae zasu kawo wasu sababbi.." Abba ya fad'a yana jin ciwon hakan har cikin ransa "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun.." Umma ta fad'a tana jin wani iri, lokaci guda kuma tana kallan Abban cike da tausayawa "Abba me kuka yi musu?" Yah Sadeeq ya fad'a fuskar sa cike da alhini, d'an murmushi Abban ya saki me cin rae kafin yace "Kada ka damu Sadeeq In Sha Allah ae Allah ba azzalimin bawan sa bane, da sannu duk wani me mugunta a fad'in duniyar nan ze girbe abinda ya shuka.." Abba ya fad'a kafin ya maeda duban sa kan Umma da har lokacin ta kasa furta komae bayan salatin da tayi "Ina ganin lokacin hak'ura da aekin gwamnati yayi, tunda nayi har sau 2 Allah beyi zan d'ore ba.." da sauri Umma ta d'ago ta kalle shi tace "Toh Abban su idan ka hak'ura ya za'ayi kenan?" murmushi me ciwo yayi sannan yace "Kinga dae aekin Bank d'in nan seda na sakankance suka zo suka dakatar damu, yanzu ga wannan ma, bana so na sake neman wani shima na sakankance kuma azo a samu matsala, yaran nan karatu suke yi, muma akwae buk'atun mu na yau da kullum, saboda haka.." seya d'an dakata kad'an kafin ya d'ora da fad'in "Ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, maganar wannan shagon In Sha Allah zan maeda hankali a kanta, Allah ya saka mana" Abba ya fad'a yana mik'ewa, dukkan su suka bi Abban da kallo cike da tausayawa, dan Abban wani mutum ne wanda kafin ka ganshi cikin 6acin rae se an dad'e, se an matuk'ar kaeshi bango sannan hakan kan bayyana akan fuskar sa, Umma ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "In Sha Allah se Allah ya sakawa me gaskiya.." ta fad'a itama tana tashi, Yah Sadeeq ya amsa da "Ameen Umma.." dae_dae lokacin da Ayrah ta fito daga d'aki kamar koda yaushe da d'an gudun ta "Umma ba'a min wankan ba fa" ta fad'a tana ta6e baki, Umma tace bayan ta d'an yi murmushi "Gani nan, dama yanzu can zance muje.." ta fad'a tana kama hannun Ayrahn zuwa d'aki.. .... Duk da abin nan daya faru hakan be hana Abba d'aukar 'ya'yan nasa yakae makaranta ba, sedae har lokacin bashi da walwala dan gaba d'aya hankalin sa na kan abinda ze cigaba dayi dan cigaba da kula da harkokin iyalin sa, ga rashin bacci daya samu a jiyan hakan ya k'arawa yanayin nasa rashin armashi, bayan ya sallame su suka masa a dawo lafiya sannan ya tashi motar sa, Yah Sadeeq ya kalli Abban nasu dan shi kanshi jiya kafin ya kwanta da Abban nasu ya kwana, duk da k'ananun shekaru irin nasa wanda ba zasu wuce 12 ba yana da hankali da nutsuwa, shiyasa wani lokacin Abban ke d'aukar sa kamar d'an shekara 20 dan ko shawara zeyi da Umma yana barin Yah Sadeeq d'in ya zauna a wajen suyi shawarar tare "Abba Allah ya bada sa'a, ya tsare, Allah ya kiyaye hanya.." ya fad'a kamar yadda suka sabawa Abban addu'a idan ze fita, murmushi Abba yayi kana yace "Ameen Sadeeq, Allah ya baku sa'a kaji, ka cigaba da taya ni da addu'a.." "Toh Abba.." Yah Sadeeq d'in ya fad'a yana wucewa... ... Sanda aka fito break bayan sun gama cin abincin kamar yadda suka saba, se suka fito zuwa harabar makarantar, ta kalli inda ta saba ganin sa kamar koda yaushe yana zaune yanzun idanun sa kan wata takadda yana kalla, a hankali ta fara takawa zuwa inda yake zaunen idanun ta a kansa "Ayrah..er carafke fa muma yau zamu yi" wata k'awar ta da itama ba zata wuce sa'ar ta ba ta fad'a da maganar ta me cike da tsamin baki, bata ma jita ba dan gaba d'aya hankalin ta yayi kansa, har zuwa sanda wata a cikin k'awayen nata ta dafa ta tana fad'in "A'ah ki taho enter zamu yi" ta fad'a tana dariya, hannu Ayrah ta saka ta zame hannun k'awar ta ta dake kan kafad'ar ta sannan tace "Ke ni ba zanyi ba.." daga haka tayi gaba, su kuma yaran duk basu bi ta kanta ba suka cigaba da wasan su, seda ta isa inda yake d'in sannan ta tsaya tana cigaba da kallan sa da kuma kayan dake jikin sa, a k'alla zeyi shekaru 12 ne, fari ne sosae kyakykyawa ajin farko, me manyan idanu da dogon hanci, ga wata bak'ar suma dake kwance akansa sedae daga gani kasan bata samun yadda take so dan haka ta d'an cukurkud'e kad'an, kayan jikin sa ma haka kana ganin su kasan sunji jiki amma da alama shi duk wad'annan basu dame shi ba dan kuwa har lokacin idanun sa na kan takaddar hannun sa ne "Kae!!" Ayrah ta fad'a tana kallan sa, da sauri ya d'aga manyan idanun sa ya sauke su akan Ayrahn, bece komae ba seya maeda kansa kan takaddar sa "Kae!!" ta sake fad'a a karo na, d'an lumshe idanun sa yayi sannan ya ninke takaddar a hannun sa ya mik'e, yana k'ok'arin barin wajen Ayrah tace "Kawo na koya maka.." seya d'an dakata kad'an kafin ya juyo yana kallan ta, hannu ta mik'a ta kar6i takaddar hannun sa tana kallan abinda ke ciki, ta karanta da karatun data iya sannan ta kalle shi yadda shima ita d'in yake kalla, seta saka dariya kawae hadda toshe baki kamar wata babba, dama fuskar tasa babu annuri yanzu kuma da yaga tana masa dariya seya sake tsuke ta ya sanya hannu ya kar6i takaddar hannun ta ya juya da nufin barin wajen, hannun ta ta saka ta rik'o nasa hannun, manyan idanun ta sun cika da k'walla tace "Yi hak'uri, gani nayi kae babba ne fa.." ta fad'a abinda take ganin shine ya dace ta fad'a "Allah kuwa idan kana so zan fad'awa Yah Sadeeq ya dinga kowa maka karatu.." seya juyo gaba d'ayan sa yana kallan ta lokaci d'aya murmushi na su6ucewa akan fuskar sa yace "Da gaske?" karo na farko kenan da yayi magana, seta jinjina kae kawae tana d'an murmushi... Ku sani wannan book d'in ina yin sa ne based on experience, zan iya cewa wani abun ma true ne wlh nake had'a muku dashi duk dan labarin ya k'ara armashi kuma ku fahimci sak'on da nake son isarwa, Allah yasa mu dace.. *ZARAH BINT YUSUF (Mhiz Innocent)*✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page_003 ___"Ke Ayrah!!" Yah Sadeeq ya fad'a yana k'arasowa wajen, dukkan su suka d'aga kae suka kalli inda yake, bata motsa daga inda take ba sedae ta cigaba da kallan sa har ya k'araso wajen, ya kalli inda yaron nan ke tsaye na tsawon sakanni sannan ya maeda kan Ayrah, kama hannun ta yayi ba tare da yace komae ba suka bar wajen, yayin da shi kuma ya bisu da ido har suka bar wajen, seda suka isa bakin ajin su sannan ya tsaya ya kalle ta fuskar sa a had'e yace "Meya kae ki can?" rau rau tayi da idanun ta, tana ta6e d'an k'aramin bakin ta kamar zata yi kuka "Ba nace miki ba'a wasa da maza ba?" jinjina kae kawae tayi, yace "Bari na sake ganin ki da wani!" ya fad'a yana sake had'e rae dan ta fahimci da gasken yake "Ya hak'uri Yah Sadeeq.." ta fad'a tana share k'wallar idanun ta, seya d'an yi murmushi kana yace "Yawwah..toh maza ki koma aji.." daga haka ta shige class d'in su shima ya tafi nasu ajin. .. Washe gari ma haka ta sake ganin yaron nan yana lek'e ta window, koda aka fita break seta ajjiye basket d'in ta a cikin ajin sannan ta fita zuwa inda ta ganshi a bayan ajin nasu yau sa6anin da da yake zama a gaban ajin nasu, yana zaune yau ma kamar jiyan yana karanta wata takadda dake hannun sa, seta k'arasa ta zauna tace "Wae kae ba'a saka a makaranta ba?" tayi maganar cike da sakarci, da sauri ya juyo yana kallan ta dan besan da zuwan ta wajen ba maganar ta kawae yaji, ganin ta ya sanya shi sakin ajiyar zuciya sannan ya jinjina kae "Kawo na koya maka toh" ta fad'a tana kallan sa, seya lumshe manyan idanun sa sannan ya mik'a mata takaddar hannun nasa, ta kalla abinda ke cikin takaddar, abinda aka koya musu yau ne seta dinga fad'a masa yadda ta fahimci aekin, shi kuma yana biye mata yana jin abinda take koya masan, kasancewar k'wak'walwar tasu ba d'aya bace kuma karatun su Ayrahn na yara ne yasa cikin k'ank'anin lokaci tana masa yake ganewa, tunda ta fara bece komae ba yayi shiru yana saurarar ta yana kallan ta yadda take maganar duk da ba wani iya magana tayi ba amma yana ganewa, wani abun ne dae sedae idan ta fad'a ya gyara da kanshi, idan ya fahimci bata san yadda zata fad'a ya gane ba, tana ji an kad'a k'ararrawa alamar an koma break seta yarda takaddar hannun ta ta mik'e tana waro idanun ta "Na tafi.." ta fad'a tana shirin wucewa yace "Nagode..ya sunan ki?" seta juyo ta zuba masa manyan idanun ta sannan tace bayan tayi murmushi "Ayrah.." ta fad'a tana juyawa, kamar wadda ta tuno wani abun seta juyo da sauri tace "Kae fa?" murmushi ne ya su6uce a kyakykyawar fuskar sa sannan yace "Suraj..." "Suraj!!" ta maemaeta sunan a la66an ta sannan ta wuce ba tare da ta sake cewa komae ba ta koma ajin su. ... Abba na sauke su a inda ya saba sauke su se suka tafi gida, kamar kullum da sallama suka shiga gidan nasu, Umma na zaune kan dadduma da alama sallah ta idar, tayi musu sannu da zuwa tana rik'e Ayrah data rungume ta "Tashi ki kae basket d'in kitchen.." Umma ta fad'a tana kallan Ayrah "Umma akwae abinci a ciki fa" da mamaki Umma ta kalle ta kana tace "Baki cinye ba?" girgiza kae Ayrah tayi tace "A'ah banci ba fa" mik'ewa Umma tayi rik'e da Ayrahn a hannun ta tace bayan ta zauna "Baki da lafiya ne ko a k'oshe kike?" "Ehh" Ayrahn ta fad'a tana cire hannun ta daga cikin na Umma ta wuce d'aki, Umma ta bita da kallo tana girgiza kae sannan ta dawo dashi ga Sadeeq dake tsaye tace "Meya hana ta cin abincin?" girgiza kae Yah Sadeeq yayi sannan yace "Wallahi Umma bansani ba, kuma amma banga alamar rashin lafiya a tattare da ita ba ballantana ace koh?" "Ehh hakane, may be ko yau a k'oshe take, ko kuma kana so ka koya mata halin ka" Umma ta fad'a tana kallan sa, murmushi Sadeeq yayi yana wucewa d'aki.. ... Suna zaune a parlourn suna cin abinci, ita a d'an k'aramin plate d'in data saba cin abinci a ciki wanda indae ba'a ciki aka zuba mata ba bata ta6a cin abincin, yayin da Yah Sadeeq ke zaune kan kujera shi kuma yana rubutu a littafi, ita kuma Umma tana zaune kusa da Ayrahn itama tana cin nata abincin a plate, kallo suke a er madaedaeciyar Tvn su, tashar MBC bollywood suke kalla inda suke nuna film d'in Mujhse Dosti Karoge, sosae Ayrah ke kallan duk da ba wani fahimta take ba, daga film d'in hausan har na Indian kawae tana zama ne idanun ta duka akan Tvn amma in za'a tsare ta a tambaye ta ba ganewa take ba "Raj.." taji an fad'a a cikin film d'in, seta sake kallan cikin Tvn sosae, shiru tayi tana tuna sunan wannan d'in nan daya fad'a mata "Suraj.. Raj.." ta fad'a a fili tana saka hannun ta a kumatun ta kamar me tunani "Ayrah.." Umma ta fad'a tana kallan ta, seta kalli Umman kafin Umman ta sake cewa komae tace "Umma irin sunan wani d'an ajin mu.." "Wanne?" Umma ta fad'a tana kallan ta "Raj.." "Anya kuwa?" Umma ta fad'a tana kallan ta, jinjina kae tayi kana tace "Allah kuwa Umma, shima sunan sa Raj" "Toh yayi, k'arasa cin abincin ki" babu musu ta cigaba da cin abincin ta tana yi tana kallan Tvn. ... "Monitor jeka taho min da yaron can.." Uncle Abdoul ya fad'a yana kallan Monitorn ajin su Ayrah, tashi yayi ya fita daga ajin, ya zagaya inda Uncle d'in yake nuna masa, yana zaune gaba d'aya ya gama muzanta haka kuma ya tsorata, yana ganin shikenan daga yau korar sa za'ayi a hana shi shigowa makarantar gaba d'aya, be ta6a tunanin za'a iya ganin sa ba dan yadda yake takatsantsan akan kar wanda ya ganshi, se gashi yau malami da kansa ya ganshi, ya d'an runtse idanu kad'an yana jin kwata kwata babu dad'i "Wae kazo inji Uncle" maganar data sanya shi saurin bud'e idanun sa kenan yana kallan yaron da yazo kiran sa, k'irjin sa na bugawa haka ya mik'e yana jin kamar ya gudu amma beyi hakan ba yabi bayan sa har zuwa cikin ajin, a k'ofar ajin ya tsaya ya kasa yin gaba ko baya har zuwa sanda monitorn ya wuce wajen zaman sa ya zauna "K'araso ciki" Uncle d'in ya fad'a yana kallan Suraj, ya kasa d'aga ido gaba d'aya ya kalli cikin ajin dan yasan idanun kowa na kansa ne "Me yake kawo ka nan?" Uncle Abdoul ya tambaya, kasa cewa komae yayi dan baya jin ze iya fad'in wani abun "Wani abun kake siyarwa?" k'arya bata daga cikin halayen sa amma yau yana ganin gwara yayi tan, dan haka kawae ya jinjina kae "Toh kada ka sake zuwa nan wajen siyar da abu saboda kana d'aukewa wasu hankali, ka tafi can harabar makaranta ka dinga siyarwa.. Ina kayan siyarwar taka?" "Toh.. Suna waje.." ya fad'a a hankali "Tashi kaje toh.." Uncle ya fad'a, da sauri ya mik'e cike da sassarfa ya fice daga ajin, binsa tayi da kallo dan tunda ya shigo take kallan sa har zuwa sanda ya fita d'in.. Ana fita break kuwa ta zagaya inda ya saba zama, yana zaune se dae sa6anin yadda take ganin sa da takadda a hannun sa yanzu ya d'ora kansa akan cinyar sa ne, ta k'arasa ta zauna sannan tace a hankali "Raj.." maganar da yaji ya sanya shi d'aga idanun sa ya kalle ta, seya maeda kansa kawae yayi shiru "Toh na dena kula ka" ta fad'a tana tura d'an k'aramin bakin ta gaba kuma tana shirin mik'ewa, da sauri ya juyo yana kallan ta se tace "Toh me aka maka?" ta fad'a har ranta tana jin ba dad'i na yanayin data ganshi, seya sake d'agowa ya kalli idanun ta da suka yi rau rau kamar za tayi kuka, da sauri ya girgiza kae kafin yace a nutse "Ance kar na sake lek'awa cikin ajin.." "Ya hak'uri" ta fad'a kamar me shirin yin kuka, bece komae ba illah kallan ta kawae da yake yi, ta rufe idanun ta sannan ta bud'e tace "Kawae ka dena lek'awa zan dinga koya maka komae kaga ni babba ce" ta fad'a tana murmushi, shima murmushin yayi sannan yace "Tohm nagode.." "Ae ni babba ce koh?" ta fad'a tana kallan sa, ya sake yin murmushi sannan yace "Ehh sosae ma" "Yeah" ta fad'a tana dariya har da rufe fuskar ta. Tun daga ranar ya kasance kullum taje makaranta idan aka fita break bata cin komae sedae ta tafi wajen Raj ta zauna ta koya masa duk abinda aka koya musu, kuma In Sha Allah kullum ta koma gida se tayi wa Umma zancen Raj, babu ranar banza da za'a tashi a kwanta Umma ba taji maganar Raj a bakin Ayrah ba. Yau ma kamar kullum yana zaune yana jiran ta dan yanzu yama dena lek'e ya hak'ura gaba d'aya, yafi ganewa idan tazo d'in kawae ta koya masa "Raj.." yaji ta fad'a daga inda yake zaune, se yayi murmushi ya juya yana kallan ta dan ba tun yau ba yake fad'a mata sunan sa Suraj ba Raj ba amma ita ta kasa chanjawa kullum da Raj take kiran sa, dan haka yanzun har ya hak'ura ya dena tuna mata idan ta kira shi da Raj d'in kawae amsawa yake yi, tazo ta zauna da littafin ta a hannu, d'ayan hannun nata d'auke da mangoro guda d'aya irin babban nan, ta shiga koya masa abinda aka koya musun, tana yi tana shan mangoron ta cikin nishad'i, yana lura da yadda take sha wani lokacin har da lumshe ido amma yarinta besa ko bismilllah tayi masa ba "Kina san mangoro ne?" yayi maganar yana kallan ta, da sauri ta d'aga kae ta kalle shi sannan ta jinjina kae tana murmushi, shima murmushin yayi sannan yace "Zan dinga tsinko miki a wata bishiya" "Don Allah?" ta fad'a tana kallan sa "Ehh" yace, sannan suka cigaba da karatun su.. ... "Wae Ayrah me yake damun ki ne? Kullum kika fita da abinci sedae ki dawo dashi babu abinda aka ta6a a cikin sa?" Umma ta fad'a tana tsare Ayrah da idanun ta, ba tace komae ba se tura bakin ta da tayi hawaye na taruwa a manyan k'wayar idanun ta "Umma shi fa baya zuwa makaranta, shine nake koya masa" tayi maganar tana kallan Umma "Waye?" Umma ta fad'a da mamaki "Raj!" Ayrah ta fad'a kae tsaye "Oh god" Umma tace tana dafe goshin ta, wae wanene Raj d'in nan ne? Kullum garin Allah se Ayrahn tayi zancen sa "Kikace d'an ajin ku ne kuma?" girgiza kae Ayrah tayi sannan tace "Allah kuwa Umma da gaske nake" murmushi Umma tayi kad'an sannan tace "Toh me yake kawo shi makarantar?" Shiru tayi da alama bata fahimci tambayar Umman ba, sema cewa da tayi "Umma shi nake koyawa karatu fa in an fita break" da mamaki Umma ke kallan Ayrahn, tace har lokacin tana kallan ta "Yaro ne?" girgiza kae tayi tana ta6e baki kana tace "A'ah babba ne." ta fad'a tana kae hannun ta sama kamar me auna tsayin wani "Babba kamar wa?" Umma ta fad'a "Kamar Yah Sadeeq" d'an sauke ajiyar zuciya Umma tayi dae_dae lokacin da Abba yayi sallama cikin d'akin, da gudu Ayrah ta tafi ta rungume Abban tana fad'in "Abba sannu da zuwa" hannu ya saka ya d'aga ta sama sannan yace "Yawwah an baby" ya fad'a yana sauke ta sannan yaja hannun ta zuwa cikin d'akin suka zauna "Sannu da zuwa Abban su" Umma ta fad'a tana kallan Abba, kallan ta Abba yayi yana karantar yanayin ta cikin kulawa yace "Wani abu ya faru ne?" girgiza kae tayi sannan tace "A'ah kawae dae Ayrah ce.." "Me Ayrahn tayi?" Abba ya fad'a yana gyara zaman sa, ajiyar zuciya Umma ta sauke tana bin Ayrah da kallo wadda tayi cikin d'aki da gudu "Kamar kasan sunan Raj a bakin Ayrah koh?" d'an shiru Abba yayi sannan yace "Ehh k'warae, kamar d'an ajin su koh?" girgiza kae Umma tayi sannan tace "Bana tunanin d'an ajin su ne, a yadda take bani labari kuma na fahimta, kamar ba'a makarantar yake ba, ina nufin baya zuwa makaranta, kuma yana son karatu shiyasa yake zuwa yana lek'e a ajin su.." "Lek'e kuma?" "Wallahi kuwa Abban su, nima abin ya bani mamaki" "Ikon Allah.." Abba ya fad'a yana jinjina kae "Shikenan In Sha Allah zan binciki al'amarin, idan da akwae halin taemakawa sena taemaka masa" murmushi Umma tayi kana tace "Allah ya saka da alkhaeri Abban su, ya k'ara bud'i.." ire iren halayen Abban dake sake birgeta kenan, duk da shima ba wani k'arfin hali yake dashi ba amma yana iya k'ok'arin sa wajen ganin ya taemakawa wanda ke k'asan sa kuma mabuk'aci, shima murmushin Abba yayi sannan yace "Albishirin ki.." "Goro.." Umma ta fad'a tana gyara zama "Alhaji mato ya yadda ze bani hayar shagon nan, idan yaso a hankali sena dinga biyan sa.." "Kae Masha Allah, Alhamdulillah Allah mun gode maka" Umma ta fad'a fuskar ta d'auke da mad'aukakin murmushi "Toh amma ina tunanin Sadeeq yayi k'ank'anta da wanda ze dinga taemaka min, koma ba haka ba inaso dukkan su su samu karatu me zurfi.." Abba ya fad'a yana zurfafa tunani cikin k'wak'walwar sa, murmushi Umma tayi sannan tace "Ae Abban su wannan me sauk'i ne In Allah ya yadda, tunda aka samu wannan" "Hakane kuma.." Abba ya fad'a yana kallan Yah Sadeeq daya fito daga cikin d'aki sanye cikin Uniform d'in Islamiyya, ya k'araso ya zauna yana kallan Abban yace "Abba sannu da zuwa" "Yawwah Sadeeq..za'a tafi makarantar ne?" "Ehh Abba" "Toh Allah ya kiyaye" Abba ya fad'a, Sadeeq ya amsa da "Ameen, Umma na tafi.." ya kae k'arshen maganar yana kallan Umma, itama addu'ar ta masa sannan ya fara k'ok'arin fita, yana dab da fita d'in Abba yace "Afff, Sadeeq..!" juyowa yayi yana amsa kiran Abban sannan ya dawo, Abba yace "Gobe idan kaje makaranta akwae wani yaro... Kikace sunan sa?" ya k'arasa maganar yana kallan Umma "Raj.. Haka dae tace min sunan sa" "Ikon Allah.." Abba ya fad'a yana maeda duban sa kan Yah Sadeeq yace "Kaji sunan sa Raj, anan makarantar ku yake, ita Ayrah ta sanshi, seta nuna maka shi kazo min dashi idan an tashi" "Toh Abba.." Yah Sadeeq ya fad'a yana ficewa daga d'akin, a ransa yana tuna sunan, kusan kullum se Ayrah tayi maganar me sunan amma be ta6a bawa zancen muhimmaci ba se kuma gashi Abba da kansa yace a kira masa shi... *Zarah Bint Yusuf (Mhiz Innocent)*✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* Page_004_005 ____Tun kafin ta k'arasa ta hango shi zaune yana kallan inda ta saba 6illowa ta wajen sassanyan murmurshi kwance akan fuskar sa, itama murmurshin ta maeda masa sannan ta k'araso ta zauna, ya sake yin wani murmurshin sannan yace yana mik'a mata wata leda "Gashi.." d'an bud'e manyan idanun ta tayi kamar wata babba sannan ta kar6a, tun kafin ta bud'e tasan menene dan haka ta rik'o hannun sa ta rungume tana jin dad'i tace "Wae siyowa kayi?" girgiza kae kawae yayi yana ta6e baki, bata kuma bi takan zancen ba suka cigaba da abinda ya kawo su wajen, suna yi tana shan mangoron ta, shi kuma yana kallan ta hakan na masa dad'i ko ba komae shima yau yayi mata wani abun da taji dad'i.. Seda aka tashi daga school d'in sannan Yah Sadeeq ya kama hannun Ayrah dake jiran sa a k'ofar ajin su "Muje ki kae ni wajen Raj" ya fad'a har lokacin suna tafiya, babu musu ta gyad'a kae tana cigaba da wasan ta hannun ta cikin nasa a haka har suka k'arasa inda tasan zasu same shi, cikin sa'a kuwa se suka tadda shi a tsaye da alama shima ya gama abinda zeyi zeyi gaba ne, juyawar da zeyi se suka had'a ido da Yah Sadeeq, sosae k'irjin sa ya buga sanda yagan su suna cigaba da tahowa inda yake, kawae se ya tsaya ya kasa gaba ya kasa baya, sam idanun sa be sauka akan Ayrah da keta yi masa murmurshi ba, a hankali ya lumshe manyan idanun sa dae_dae lokacin da suka ida isowa dab dashi, Yah Sadeeq yace yana kallan sa "Sannu.." d'aga ido yayi ya kalle shi se dae ya gaza cewa komae dan be san da wanne shi kuma yazo ba, se dae ga mamakin sa se yaji yace "Abban mu na son ganin ka idan babu damuwa" idan babu damuwar daya ambata shi ya sanya ya d'an ji sanyi dan da farko har ya fara tunanin ko za'a raba shi ne da Ayrah, amma abinda be gane ba shine meye had'in sa da Abban nasu? Ko dae abinda zuciyar tasa ke harsashe ne kawae dae yayi amfani da kalmomi biyun nan dan kada ya saka masa shakku akan maganar? "Zamu iya tafiya?" ya tsinto maganar Yah Sadeeq d'in "Toh" ya furta cikin rashin sanin mafita "Yau a gidan mu zaka kwana Raj?" Ayrah ta fad'a tana cigaba da tsalle tsallen ta, suna gaba yayin da Raj ke bayan su har suka k'arasa bakin Gate d'in ya cigaba da binsu zuwa wani waje ke6antacce kuma rufaffe wanda anan ne suka saba zama su jira Abban, Yah Sadeeq ya nemi waje ya zauna yayin da shi kuma ya tsaya a gefe tunani fall cikin ransa, Yah Sadeeq na zama Ayrah ta zame hannun ta zuwa wajen Raj ta fara masa surutu yayin da yau gaba d'aya yake jin sa a takure musamman da yake kusa da wata bak'uwar fuska, dan haka amsar sa ta zama bata wuce murmurshi da gyad'a kae, shi kam Yah Sadeeq bin su kawae yake da kallo yana mamakin yadda Ayrahn ta saba da shi cikin k'ank'anin lokaci, basu dad'e da zama ba Abba ya iso, ita ta fara yin gaba da gudu sanda ta hango Abban, Yah Sadeeq yabi bayan ta, seda ya kusa isa inda motar Abban take sannan ya tuna da Raj, ya juyo ya kalle shi yace "Ka taho ga Abban namu nan yazo" binsa yayi a baya suka k'arasa har inda Abban yake, Yah Sadeeq ya bud'e front seat ya shiga yayin da Ayrah ta shiga baya, Abba yabi Raj da kallo dake tsaye a waje kafin ya maeda duban sa ga Yah Sadeeq yace "Shine wannan?" jinjina kae yayi kafin yace "Ehh Abba" "Koma baya shi kuma ya shigo nan" Abba ya fad'a yana sake Kallan Raj, fitar yayi ya kalli Raj da Ayrah ke kalla tana fad'in "Ka taho mu tafi" ya kalle ta yayi murmurshi sannan ya maeda duban sa kan Yah Sadeeq daya fito daga motar "Ka shiga Abban na ciki" "Tohm" ya amsa da hakan yana k'arasawa ya shiga gaban dake a bud'e ya zauna "Barka da wannan lokaci" ya fad'a kansa a k'asa, cigaba da kallan kyakykyawan yaron Abba yayi wanda yake sa'an d'an sa Sadeeq, tun kafin ya kaega cewa yaron komae yaji wata nutsuwa tattare dashi amma duk seya watsar yace "Barka dae..yaya sunan ka?" Abba ya fad'a yana gyara zaman sa a inda yake zaune, har lokacin be d'ago ba ya furta "Suraj.." "Kaee Raj dae.." Ayrah dake baya ta fad'a tana waro idanun ta, dukkan su murmurshi suka yi kafin Abba ya sake cewa "Mahaefin ka fa?" "Kabeeru" jinjina kae Abba yayi sannan yace "Baka zuwa makaranta ne?" se a lokacin ya d'ago kae ya kalli Abban sannan ya maeda kan nasa k'asa yace "Ehh" d'an shiru Abba yayi yana tunanin tambayar da zata fito daga bakin sa haka dae ya cije yace "Suraj meyasa baka zuwa makaranta?" "Abba Raj ne fa" Ayrah ta sake fad'a, girgiza kae Abba yayi da d'an murmurshi akan fuskar sa kafin yace "Toh shikenan Raj" Yah Sadeeq dake gefen ta shima murmurshin yayi yana girgiza kae "Abbu bashi da kud'in saka ni.." "Shikenan kawae, idan nace zan saka ka zaka ji dad'i?" da sauri ya d'ago kae ya sake kallan Abban, ya lumshe idanun sa yana jin dad'i har besan sanda ya jinjina kae ba murmurshi na wanzuwa a kyakykyawar fuskar sa ba, Abba ma yayi murmurshi yace "Ka fad'a wa Abban naka idan yana da lokaci ya same ni a gida akwae maganar da zamu yi.." amsawa yayi da "Toh angode, Allah ya saka da alkhaeri" "Ameen" Abba ya fad'a yana sake yabawa da hankalin yaron, be bar cikin motar ba seda Abban ya bashi number sa yace ya kaewa Abban nasa ya kira shi.. (_A gurguje zanyi wajen nan pls, saboda idan nace zan ja nan d'in da nisa gaskiya zamu dad'e ne bamu matsa gaba ba, so shys nayi deciding kawae nayi briefing wajen amma yadda zaku fahimta_) ... Sanda Raj ya jewa da Iyayen sa maganar Abban sosae suka yi mamaki, dan da farko ma daya fad'awa Ummeen sa cewar mutumin yace ze sanya shi a makaranta bata yarda ba k'aryatawa tayi kuma ta rufe shi da fad'a dan lokacin ma tun safe babu abinda suka ci kuma har zuwa lokacin Abbun nasa be dawo ba, dama shine me fafutuka ya fita yayi er buga buga ya samo musu abinda zasu ci amma takamaemae bashi da tsayayyiyar sana'a, shiyasa idan ya fita ma ya samo wani abun gaba d'aya suna amfani dashi ne wajen samun abinda zasu ci "Toh hayaniyar me nake ji kuma da rana tsakar nan" maganar da taji daga tsakar gidan ne ya sanya ta dakatawa daga fad'an da take wa Raj, Malam Kabeeru ya k'araso hannun sa d'auke da wata leda, seta k'arasa ta kar6a tana fad'in "Sannu da zuwa Abbu" "Yawwah sannun ka dae" ya fad'a yana kallan Raj dake fad'in "Abbu sannu da zuwa" amsa sannu da zuwan yayi kafin yaja kujera er tsuguno ya zauna a tsakar gidan yana sauke numfashi "Meya faru ne kike ta fad'a tun daga soro nake jiyo muryar ki?" "Gashi nan yaron nan yazo min da wani zance wae wani mutumi yace ze sanya shi makaranta wae kuma ya bashi number sa ka ganta ma yace wae kaema kaje yana neman ka" ta fad'a tana mik'a masa wata takadda dake d'auke da number Abban, kallan su su duka Abbu yayi cikin mamaki, se kuma ya tsaeda idanun sa akan Raj yace "A'ina ya san ka?" d'an shiru kad'an yayi sannan yace bayan ya d'auke kae "A makarantar da nake zuwa" jinjina kae Abbu yayi yana mamakin yadda d'an nasa kullum burin sa shine yayi karatu amma shi kam ya rasa yadda zeyi ya cika masa wannan burin nasa, shi kansa sa yana sa kud'i zeyi k'ok'ari wajen cikawa d'an nasa buri ne ta hanyar kae shi wata k'asar ma ba Nigeria ba yayi karatu "Kuma ka tabbatar da gaske kake?" Abbu yayi k'arfin halin fad'in hakan duk da shi shaida ne akan d'an nasa duk da k'arancin shekaru irin nasa amma da wuya yayi k'arya a cikin lamarin sa "Ehh Abba Allah kuwa da gaske nake" "Ikon Allah" Abbu ya fad'a yana jinjina kae, Ummee tace "Toh zaka je d'in?" kallan ta Abbu yayi kana yace "Me ze hana, kika sani ko alkhaeri ke kiran mu?" "Toh Allah yasa, bari na tashi na d'ora mana shinkafar can mu samu mu ci" Ummee ta fad'a tana mik'ewa. Washe gari da wuri Abbu ya shirya tare shi da Raj, ya kira Abba da er k'aramar wayar sa yayi masa kwatancen gidan nasa sannan suka tafi gidan, daga gidan nasu akwae d'an nisa sosae dan haka suka d'an rage tafiyar a k'asa kafin suka tari adaedaeta ta k'arasa dasu da ragowar chanjin daya ragewa Abbu, a k'ofar gidan suka tsaya Abbu yayi wa Abba flashing a wayar sa saboda kud'in wayar sa daya k'are, ganin kiran nasa ya sanya Abba kawae ya fito dan ya fahimci yazo ne, suka gaesa cikin mutuntawa sannan kowannen su ya gabatar da kansa ga d'an uwan sa, tun a lokacin Abba yaji Abbun ya kwanta masa dan kana ganin sa kaga mutumin kirki gashi ko had'a idanu da Abban ya kasa yi, magana ta k'arshe data wakana a tsakanin su shine Abba yace bayan yaji yadda rayuwar su ke kasancewa, se yayi buga buga yake samu suci abinci, wani lokacin idan be samu komae ba haka zasu wuni da yunwa, shi gashi ba karatu yayi ba dududu iya secondary school ya tsaya, sana'a kuma ta k'i shi, shiyasa ma har lokaci be saka Raj a makaranta ba, saboda komae suka samu cikin su ne, kuma gashi Raj d'in ya tashi da k'aunar makaranta a ransa shi kuma be san yadda zeyi ya saka shi ba, dan idan yace ze saka shin zasu matuk'ar takura ne "Allah sarki, kar ka damu In Sha Allah kamar an saka Suraj a makaranta ne an gama, maganar sana'a kuma dama inaso na bud'e wani shago ne a cikin satin nan, toh idan zaka iya seka dinga zuwa muna zama tare ina sallamar ka" daga inda Abbu ke zaune kan wata kujera ya zamo kamar ze tsugunna yace muryar sa na rawa "Nagode sosae Alhaji, Allah ya saka da alkhaeri, ya biya buk'ata, yasa ka gama da duniya lafiya, nagode nagode sosae Alhaji" "Ya isa haka, babu komae Allah ya taemake mu.." Abba ya fad'a yana rik'o Abban, seya mik'e ya koma ya zauna dae_dae lokacin da Abba ke fad'in "In Sha Allah zuwa gobe se kazo mu fara shirye shirye.." "Toh Alhaji babu damuwa" ya fad'a yana cigaba da kwararowa Abban addu'a cikin matuk'ar farin ciki da jin dad'i. Sanda ya koma gida ya fad'awa matar sa zancen tayi matuk'ar farin ciki, haka suka had'u suka dinga yiwa Abba addu'o'i kala kala. Shima Abban daya jewa Umma da maganar taji dad'i sosae ta kuma yi addu'ar Allah ya taemaka. Washe gari kuwa kamar yadda Abban ya fad'awa Abbu se gashi da wurwuri a gidan, daga nan babu 6ata lokaci suka tafi kasuwar zuwa shagon da aka bawa Abba hayar sa, dama ba tun yanzu yake da burin bud'e shago ba amma be bawa abin muhimmaci ba seda wannan abin ya faru dan haka kayan da yake d'an siya yana ajjewa su yayi amfani dasu ya zuba a cikin shagon, sannan yayi amfani da ragowar kud'in da yake dashi ya k'aro wasu kayan ya zuba zuwa lokacin da Allah ze hore ya zuba wasu masu yawa, duk da shagon yafi k'arfin kayan daya zuba a ciki amma haka yake jin sa cikin farin ciki mara misaltuwa, haka suka isa shagon Abba ya bud'e bayan sunyi addu'o'i sosae, tare suka zauna cikin shagon shi da Abbu, Abbu ke kula da harkokin kayan siyarwar yayin da Abba ke kula da harkar kud'i, cikin ikon Allah a ranar kawae sunyi ciniki sosae musamman daya kasance ranar farko ce se Abba yayi discount akan duk wani abu da mutum ze siya, hakan yasa mutane da dama suka dinga zuwa suna siyar kayayyakin, basu suka tashi ba se dab da maghrib sannan suka tashi, Abba ya d'auki kud'i masu d'an dama a cikin cinikin da suka yi ya bawa Abbu, Abbu yayi ta godiya ya tafi gida cikin farin ciki, yau beyi wahala ya nemo kud'in da zasu samu suci abinci ba yana zaune kawae cikin shago babu rana kuma gashi an bashi abinda ko buga bugar yayi baze samu ba, hakan yasa farin cikin nasa ya sake ri6anyuwa. Tun daga wannan ranar ya kasance kullum Abba da Abbu zasu fita kasuwa da safe basa tashi se dab da maghrib, sosae Abba ya sanya idanu akan Abbu da al'amarin sa, cikin k'ank'anin lokaci Abba ya fahimci Abbu mutum ne me rik'on amana da kirki, babu 6ata lokaci ya shiga gwada shi lokacin da harkar ta bud'e dan yana so ne ya d'an dinga sakar masa abubuwa ba tare da wani tunani ba, sau da dama yasha gwada shi seya same shi da rik'on amana lamarin sa babu ha'inci a ciki, cikin ikon Allah da yaddar Allah sana'ar tasa ta samu kar6uwa a wajen mutane, sosae ake zuwa a siyi kayan da yake siyarwa saboda haka a hankali ya d'an fara sakarwa da Abba wasu abubuwa da dama saboda shima ya d'an samu sassauci. A 6angare guda kuwa ya sanya Raj a makarantar su Ayrah, an saka shi a Junior class saboda yanayin shekarun sa, ba laefi sun d'an fara sabo shi da Yah Sadeeq amma ba wani sosae ba, yayin da a tsakanin sa da Ayrah kuwa kullum wata sabuwar shak'uwa ke k'ara ninkuwa a tare dasu kamar wad'anda suka yi shekara da shekaru a tare, kamar kuma wad'anda suka fito ciki d'aya haka suke al'amuran su, kowanne najin d'an uwan sa a cikin ransa, a tsakanin su babu wanda ke son ganin d'aya yana cikin 6acin rae, sau da dama Umma kanyi mamaki na shak'uwar ta su amma idan ta tuna komae daga Allah ne seta dena mamakin, daga k'arshe ma gaba d'aya Raj ya dawo gidan su Ayrah da zama, idan Abba ya d'auko su daga makaranta seya wuce dasu dukkan su har Raj d'in gida, su tafi Islamiyya sannan idan suka dawo suci abinci kana Raj ya tafi gida, wata ran da k'yar yake tafiya d'in idan Ayrah ta saka rigimar seta bishi, da k'yar take hak'ura idan Umman dashi kansa Raj d'in suka rarrashe ta kana take hak'ura amma fa ta dinga nunk'ufurci kenan kamar wata babba, tayi ta bin kujera tana kwanciya kamar zata yi kuka, idan kuwa da rana ne ko a makaranta in dae basa cikin aji toh zaka same su ne kullum tare da juna, wata iriyar shak'uwa suka yi mara misaltuwa ko iyayen Raj d'in ma abin har mamaki yake basu, sunan Raj kuwa seda Ayrah ta lak'abawa kowa, daga zarar kace masa Suraj za tace ba Suraj ba Raj, kuma in zaka kwana kana fad'ar Suraj itama zata kwana tana gyara maka, dan haka yanzu en gidan su ma kwata kwata Raj d'in suke ce masa, Iyayen sa ne dae suke k'ok'arin ce masa Raj d'in ko dan Ayrahn musamman idan a gaban tane, shi kansa yanzun yafi jin dad'in Raj d'in kuma babban dalili daya kasance Ayrah ce ta saka masa sunan. A cikin shekarar da taemakon Allah komae ya cigaba da bud'ewa Abba, seya kasance ma yanzun ya zuba atamfofi ne kala kala kuma masu yawa, sosae Abbu ke taemaka masa ta hanyoyi da dama, dan yanzun ya gama sakar masa komae, ko menene in dae shi da kansa ze iya yi toh fa ze iya d'ora Abbu akae saboda yadda yayi na'am dashi, haka suka cigaba da tafiyar da shagon su 2, sosae abubuwa da dama na Abban suka chanja ciki kuwa hadda cimar gidan sa da suturun da shi kansa da iyalan sa kan saka da kuma sauran abubuwa makaman tan wannan, shi kansa Abbu ba'a barshi a baya ba dan kuwa yanzun rayuwa suke cikin kwanciyar hankali babu yunwa babu komae, dan a lokacin ma seda ya nemi Abba ya sakar masa harkar makarantar Raj amma Abba yace a'ah tunda ya fara shi ze k'arasa In Sha Allah, beyi musu ba se k'ara godiya da yayi, godiyar da kusan kullum se yayi ta baya gajiya da ita. _*MAFARI*_ ... Da sallama Abba ya shigo gidan kamar koda yaushe hannun sa d'auke da ledar daya saba shigo da ita kusan kullum wanda hakan ma ya riga ya zame masa jiki, in dae ze dawo gidan toh In Sha Allah ze siyo wani abun ya tahowa da iyalin nasa shi, da gudu ta sauko daga kan kujerar ta k'arasa ta rungume Abban tana fad'in "Abba Sannu da zuwa" "Yawwah an baby.." "Abba meka siyo min?" ta fad'a tana murmurshi, shima murmurshin yayi sannan yace "Kar6i maza ki kaewa Umman ku, ina take?" seda ta sanya hannu ta kar6a sannan tace "Tana kitchen" daga haka tayi hanyar kitchen d'in tana kiran sunan Umma, Raj dake zaune kan kujera ya sakko a hankali ya furta "Abba sannu da zuwa" "Yawwah sannun kadae" Abban ya fad'a yana wucewa d'akin sa... Seda ya samu yaci abinci a cikin parlourn sannan Umma ta gabatar masa da ruwa ya sha kana yace "Dama akwae maganar dana ke so muyi" gyara zama Umma tayi kana ta kalli Ayrah dake shirin fita daga d'akin saboda Raj daya shigo yanzun kuma ya fita "Ina kuma zaki je?" Umman ta fad'a, turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Umma Raj zan bi" "Ina ze je?" "Wajen Yah Sadeeq.." ta fad'a tana kallan Umman, Abba ne yanzu kuma yace "Toh shikenan, amma banda shiga ball ta maza ce" jinjina kae tayi tana murmurshi ta fice daga d'akin, Umma ta juyo da kanta wajen Abba tace "Abban su ina jin ka" seda Abban ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Wato Alhaji Mato ne yazo min da wata shawara..toh yanzu dae so nake nayi shawarar dake inji me kikace, wato ba wani abu bane ya bani shawara ne wadda In Sha Allah akwae cigaba a cikin ta, cemin yayi meze hana tunda Allah yasa min albarka a wannan harkar na koma cikin kano ko da zama ko da sana'a, kin san kano cibiyar kasuwanci ce.." d'an shiru Umma tayi tana nazarin maganar Abban se kuma can tace "Hakan ma yayi Abban su, me son cigaban ka ae me k'aunar ka ne, ni ina ganin kawae ka amince da shawarar tasa.." "Toh shikenan amma batun zama fa? Acan d'in zamu zauna ko kuma dae in fara maganar ni kad'ae na tafi can sena dinga zuwa?" Abba ya fad'a yana Kallan Umma, murmurshi Umma tayi kana tace "Abban su ni bana tunanin wannan mafita ce, ni a gani na gwara ka tsayar da hankalin ka kan abu guda d'aya, ba kae kana can mu muna nan ba hankalin ka ze rabu gida biyu, ni a gani na kawae muma mu tafi tare da kae.." "Shikenan toh Allah ya taemake mu" Abba ya fad'a yana murmurshi. Be hak'ura haka ba seda ya nemi Abbu yayi shawara dashi, cikin ikon Allah kuma shima ya bashi goyon baya d'ari bisa d'ari, dan haka Abba ya sake jin nutsuwa a lamarin, saboda haka babu 6ata lokaci ya fara shirye shiryen tafiya kanon, ita kanta Umma ma ba'a barta a baya ba, shiri take yi na tafiyar ta su, dan haka babu 6ata lokaci Abban ya kusa gama komae, da yake Alhaji Mato yafi zama a kano ya saka shi ya nemar masa gida a cikin garin na Kano d'an madaedaeci haka me kyau, beyi k'asa a gwuiwa ba wajen tambayar Abbu yadda za'ayi, ze bishi can garin kanon ne ko kuwa anan ze zauna se Abban ya dinga yi masa aeke, girgiza kae yayi a lokacin da Abban ke masa maganar yace "Ayyah Abban Sadeeq, ya za'ayi in zauna anan kae kana can wani gari? In Sha Allah zan bika can d'in idan yaso sena dinga dawowa nan d'in wajen iyali na" Take Abba yayi na'am da maganar Abbun, dan haka yace "Toh shikenan, Allah ya taemake mu" "Ameen Ameen" Abbu ya fad'a.. Rana ku suka cigaba da tafiya babu tsayawa, har zuwa sanda Abba ya k'arasa abinda be gama ba, yanzu haka ya siyar da kayayyakin da yake siyarwa anan d'in ya had'e kud'ad'en nasa waje guda, be sanya su a banki ba saboda matsalar da account d'in sa ya samu, hakan ne yasa ya had'a su cikin wata jaka daban wadda yake ajje muhimman takardun sa masu matuk'ar amfani, duk wani abu da yasan yana da amfani a wajen sa ya had'e su duka cikin wannan jakar sannan ya had'a ragowar kayan sa cikin wata, haka zalika Umma ma tayi sallama da mak'ota en uwa da abokan arzik'i, ranar da zasu koma zuwa garin kano tazo... Tun safe Umma ta gama shiryawa tsaff cikin atamfa riga da zani da hijab dogo, ta shirya Ayrah cikin doguwar rigar en kanti da baby hijab suka fito parlour, tun d'azu Ayrahn ke ta 6ata rae da alama k'iris take jira ta fashe da kuka dan haka Umman na kallan ta tak'i kula ta ballantana ma ta sakar mata kukan shagwa6ar ta ta, tana zaune kan kujerar ta kwantar da kanta akan wata leda dake d'auke da kaya, Yah Sadeeq ne ya shigo cikin d'akin idanun sa akan ta ya fara sauka, shima yana ganin ta yasan yau da rigima ta tashi "Auta meya faru?" ya fad'a yana kallan ta, manyan idanun ta ta d'aga ta kalle shi amma ba tace komae ba, Umma dake kallan su tace k'asa k'asa "Ka rabu da ita don Allah, kar kasa ta mana kuka kuma" yaji abinda Umman ta fad'a dan haka kawae seya koma kusa da Ayrahn ya zauna, seta maeda kanta ta kwantar akan cinyar sa tana cigaba da kallan k'ofa.. Basufi mintuna 2 da zama ba sega sallama daga k'ofar d'akin, Umma da Yah Sadeeq suka amsa sallamar, yana sanye cikin riga da wando na wani yadi me kyau kasancewar sa me tsafta ya sanya kayan nasa a goge suke tsaff tsaff yayi matuk'ar kyau, da gudu ta mik'e ta k'arasa bakin k'ofar da suke k'ok'arin shigowa ta rungume shi tana sakin dariya kamar ba itace yanzu zaune kamar zata yi kuka ba, shima dariyar yayi yana fad'in "Oyoyo Ayrah" ta sake yin dariya kana tace "Ina ta jiran ka, shine ba kazo ba" dukka en d'akin binsu suke da kallo, ya rik'o mata hannu zuwa cikin d'akin yace "Gani fa nazo" "Zo kaji" ta fad'a tana janyo shi k'asa, seya d'an yo k'asan, ta sake jan shi ya tsuguna a k'asan sannan ta kae bakin ta kunnen sa tace k'asa k'asa "Jiya wata tace suna da mangoro a gidan su, zaka ciro min?" bud'e idanu yayi yana sake kallan en d'akin sannan ya mik'e ya sake kama hannun ta zuwa cikin d'akin, ita kuma ta tura d'an k'aramin bakin ta gaba, seda suka k'arasa ya zauna sannan ya gaeda Umma da suke gaesawa da Ummee sannan ya kalli Ayrah dake zaune dab dashi ta rik'o hannun sa kamar wanda ze gudu yace "Toh zan raka ki yi murmurshi" se a lokacin ta saki fuskar ta tana jin dad'i har cikin ranta. Basu dad'e da zama ba Yah Sadeeq daya fita d'azun yazo yace Umma su fito, har lokacin hannun ta na cikin na Raj sanda suka fito d'in, Ummee ta kalli Abba tace "Toh Alhaji mun gode Allah ya saka da alkhaeri, ya tsare ya bada sa'a" "Ameen Ameen" Abba ya fad'a yana shirin d'aukar jakar da Yah Sadeeq ya fito da ita a hannun sa, Abbu yayi murmurshi yana kallan Abba yace "Haba haba Alhaji ina wajen sannan zaka d'auki kaya?" shima Abban murmurshi yayi sannan yace "A'ah toh ka bar Sadeeq ya d'auka.." "Babu komae muje kawae" ya fad'a yana rik'e wata akwati kuma a hannun sa, Abba be sake cewa komae ba se kallan Ayrah da yayi wadda ta kwantar da kanta a hannun Raj yace "Toh taho koh?" mak'ale kafad'a tayi tana sake cuno baki gami da sake rik'e hannun Raj, Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace cikin rarrashi bayan ya matsa dab da ita ya kamo d'ayan hannun ta "Ki taho mu tafi kinji, zamu dawo ae" "A'ah" ta sake fad'a tana kuma mak'ale kafad'a, Umma dake gefe ta d'an lumshe idanun ta kad'an ta bud'e kana ta matsa kusa da Ayrahn tace "Taho kinji, ae zaki dinga zuwa Uhmm?" girgiza kae ta shiga yi sosae k'wallar data dad'e a idanun ta ta shiga sakkowa babu k'ak'k'autawa, shi kam Raj gaba d'aya ma ya kasa kallan ta dan zuciyar sa ta riga ta dad'e da gama karyewa, Yah Sadeeq ne ya k'araso a hankali ya rik'o hannun Ayrahn dake cigaba da girgiza kae yace cikin rarrashi "Ki taho mana kinji" ya fad'a yana janyo ta, a hankali hannun nata dake rik'e da nasa ya shiga zamowa daga sama zuwa k'asa har zuwa sanda ya zama tafin hannun su ne kawae cikin na juna, Raj ya rik'e hannun nata sosae yana kallan k'wayar idanun ta dake cigaba da zubar da hawaye, Yah Sadeeq be kalle su ba ya jata ya d'auke ta kawae a hannun sa, abinda ya sanya hannun su rabuwa dana juna kenan kuma dae_dae lokacin da Ayrah ta saki kuka me k'arfin gaske cikin kukan tana fad'in "Yah Sadeeq Raj, Yah Sadeeq Raj" be bi ta kanta ba se kwantar da kan nata da yayi a kan kafad'ar sa amma tak'i kwanciya ta cigaba da kukan ta kamar ranta ze fita, a haka yayi gaba. Lumshe idanun sa yayi sanda Ummeen sa ta d'ora hannun ta akan kafad'ar sa, yana jin wasu k'walla na tarar masa a cikin idanun sa, Ummee tace "Kada kayi kuka fa" kamar ma zuga shi tayi se kuwa hawayen suka cigaba da zuba yana saka hannu yana goge su, Umma data mik'e tace "Toh bari mu tafi" "Allah ya tsare Hajiya.." Inji Ummee "Ameen" Umma ta fad'a tana yin gaba... Tunda suke tafiya kukan take yi tana cigaba da ambatar sunan Raj, se rarrashin ta Yah Sadeeq keyi amma tayi kamar bata san yana yi ba, ta cigaba da rera kukan ta tana yi tana sauke ajiyar zuciya, seda suka kusa isa tasha sannan bacci yayi awon gaba da ita a kafad'ar Yah Sadeeq... Motar da zata kaesu Kano direct ita suka samu tana shirin tashi mutane 2 kawae ake jira ta tashi, ganin su Abba ya sanya su dakatawa kwandasta ya kalli Abba yana tambayar inda zeje, Abban ya fad'a masa sannan ya bud'e musu motar, Umma ce ta fara shiga sannan Yah Sadeeq daya zauna a maleji, kana Abba ya kalli wajen da yayi ragowa sannan ya kalli Abbu dake tsaye rik'e da kayan Abban yace bayan ya kalli kwandastan "Ae mu 2 ne kuma naga saura wajen mutum 1" kwandastan ya kalli Abba kana yace "Shawara idan zaka d'auka ku raba motar, idan yaso wasu su tafi yanzu wasu kuma idan wata za taje kanon seta d'auke su" Take Abba yayi na'am da shawarar ya kalli Abbu yace "Ko mu barsu su tafi, mu kuma ma taho?" Abbu yace "Alhaji kar a samu matsala tunda kaga basu ta6a zuwa kano ba se wannan karon.." "Hakane kuma" Abba ya fad'a yana tunanin mafita "Meze hana kuyi gaba ni sena taho daga baya?" Abbu ya katsewa Abban tunanin da yake, Abba ya d'aga kae ya kalle shi kana yace "Babu matsala?" "A'ah babu matsala" Abbu ya fad'a yana murmurshi, mik'a hannu Abba yayi da niyyar kar6ar kayan hannun Abbu, kwandastan yace "Yalla6ae cikin wajen nan wallahi babu wajen da zaka ajiye jakar nan, ko a jikin ka zaka rik'e zaka takura ne kuma ka takurawa mutane" Abba baya son dogon zance dan haka yace "Bud'e min bayan motar na saka to" "Ae da mutane a ciki" sauke numfashi Abba yayi yana tunanin meya kamata yayi yanzun, seya tsinto muryar Abbu na fad'in "Toh Alhaji kona taho maka dasu?" kallan Abbun Abba yayi sannan yayi murmurshi yace "Toh shikenan, yanzu zaka jira zuwan wata ne?" "Ehh In Sha Allah Alhaji, Allah ya tsare.." Abbu ya fad'a "Ameen Ameen, Allah ya tsare dukkan mu" "Alhaji lokaci fa na tafiya" kwandastan ya fad'a yana kallan Abba, kallan Abbu Abba ya sake yi sannan yayi murmurshi ya koma ya shiga cikin motar sannan kwandastan ma ya shiga, Abbu ya sake yi musu addu'a sanda drivern motar ke k'ok'arin tashin ta, be bar inda yake tsaye ba seda motar tasu ta tashi. Tafiyar awanni suka yi suka isa garin na Kano zuwa lokacin Ayrah ta tashi daga bacci ta cigaba da kukan ta, tayi kukan harta gaji ta hak'ura se ajiyar zuciya da take ta saukewa daga k'arshe wani baccin ya sake d'auke ta a jikin Yah Sadeeq dan shi kad'ae ne ze iya rik'e ta saboda yadda su Umman suke a matse a inda suke zaune, se a lokacin Abba yayi dana sanin k'in tahowa da motar sa, daya sani ya kae ta gyara saboda matsalolin da take bashi a kwanakin nan, ganin tafiyar tasu me nisa ce ya sanya be taho da ita ba ko dan gudun matsala.... Sanda suka isa Kanon kae tsaye gidan da Alhaji Maton ya nemar musu suka isa, su Umma ne suka fara shigewa cikin gidan ita da Yah Sadeeq yayin da Abba ya tsaya ya lalubo wayar sa dan tuntu6ar Abbu yaji ko shima ya taho d'in dan yana ganin kamar wannan d'in nauyin sa, yana so kuma ya sanar dashi idan be samu motar ba ya bari se gobe kada yamma tayi masa a hanya, kiran farko da yayi ta shiga ta soma ringing, se dae har kiran ya katse ba'a d'auka ba, hakan ne yasa Abban ya sake kiran layin se dae ga mamakin sa se suke fad'a masa wayar tana a kashe ne, ya riga ya yaddarwa zuciyar sa matsalar network ne tunda a yanzu yayi kira na farko ta shiga yanzu kuma a kashe dan haka ya sake trying number sedae abinda yanzu kuma take fad'a masa shine kwata kwata ma ba zata shiga ba....... *Zarah Bint Yusuf (Mhiz Innocent)* https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page_006 ___Sosae tsoro ya kama Abba, a ransa yana fatan ba wani abin ne ya faru ba "Lafiya kuwa Abban su?" Umma da fitowar ta kenan ta fad'a tana kallan Abban da damuwa ta gama bayyana akan fuskar sa, kallan ta yayi sannan yace "Na kira layin Kabeeru ne da farko ta shiga yanzu kuma ta dena shiga" Abban ya fad'a "Ae Ina tunanin yanzu yana cikin mota ne, babu mamaki ko shiyasa kaji wayar a kashe" d'an murmushi kad'an Abba yayi sannan yace "Babu shakka ma haka ne" itama murmushin ta maeda masa sannan tace "Ya kamata muje ciki koh?" Babu musu yabi bayan Umman da tayi gaba zuwa cikin gidan daya kasance madaedaeci, gida ne haka me k'ofa da d'aku na 4 a cikin sa, 1 parlour wanda ya kasance shine na Umma sannan d'akin gado shi kuma shine na Abba, sannan ragowar d'aku nan da suka kasance madaedaeta su kuma Yah Sadeeq da Ayrah kowannen su ya d'auki d'aya, se kitchen da ban d'aki, babu laefi gidan yayi kyau duk da ba wani girma gare shi ba amma an masa k'yale k'yale wanda suka k'awata shi. Kae tsaye cikin d'akin Abban suka nufa wanda shima yake d'auke da d'an madaedaecin ban d'aki a cikin sa, Umma ce ta taemaka masa yayi wanka kafin ya fito su d'an zazzagaya gidan, kukan Ayrah data jiyo daga parlourn nata ne ya sanya ta fad'in "Ya ilahy" "Toh rigimatu ta farka kenan" Abba ya fad'a yana murmushi, mik'ewa Umma tayi ta fita daga d'akin dae_dae lokacin da Yah Sadeeq shima yake shirin shiga d'akin, ganin Umma ya sanya shi fad'in "Alhamdulillah, Umma gwara ki rarrashi abar ki" ya fad'a yana juyawa yayin da Umma ta shige cikin d'akin, k'arasawa Umma tayi ta zauna inda Ayrah ke zaune ta kamo ta cikin jikin ta tace "Kiyi hak'uri kiyi shiru kinji Auta" "Umma Raj" Ayrahn ta fad'a tana kallan Umma da jajayen idanun ta, lumshe idanu Umma tayi a ranta tana cigaba da mamakin irin wannan shak'uwa tace "Shikenan za'a kira Abban sa ya kawo miki shi kinji?" seta cigaba da kallon Umman kamar me nazari se kuma tace "Umma ze zo?" murmurshi Umma tayi kana tace "Ehh ze zo" "Kuma in be zo ba na dena kula shi" ta fad'a cike da sakarci tana ta6e baki, girgiza kae Umma tayi "Toh shikenan, kukan ya isa haka Uhmm?" ta fad'a tana kuma shafa bayan ta, cigaba tayi da sheshshek'ar ta har zuwa sanda ta gaji tayi shiru a jikin Umman... Wajen k'arfe 7pm na daren ranar Umma ta shiga d'akin Abba, seta tarar dashi zaune kan gadon, a hankali ta k'arasa ta zauna tana kallan sa tace cikin nutsuwa "Abban su lafiya kuwa?" d'an gyara zama yayi sannan yace "Haka nan kawae nake jin kamar ba lafiya ba, ina tunanin zan koma in bincika dan har yanzu layin sa baya shiga, kuma yaci ace yanzun dae ya iso cikin garin nan" cikin kwantar da murya kuma dan ta k'ara bawa Abban k'warin gwuiwa ya sanya ta fad'in "In Sha Allah yana lafiya, lafiyar ce kuma ta 6oye shi.." "Allah yasa" Abba ya fad'a. Tun Abba na kiran layin Abbu har ya gaji ya hak'ura ya cigaba da addu'ar Allah yasa Abbun yana lafiya, duk kuma yabi ya takurawa kansa yana ganin kamar duk abinda ya samu Abbun shine sila, haka dae Umma ta dinga bashi baki akan ya kwantar da hankalin sa amma har zuwa dare babu kiran Abbu.. Washe gari Abba ya kasa sukuni dan haka tunda yayi sallahr Asuba ya shirya cikin wani yadi me kyau ya kalli Umma dake kallan sa "Har yanzu hankali na ya kasa kwanciya Ruk'ayya, gwara naje na duba da kae na" jinjina kae Umma tayi dan itama yanzun ta fara d'an shiga cikin tsoro gwara Abban ya duba ko lafiyar ce ta 6oye Abbu, amma dan ta sake kwantar masa da hankali tunda tafiya zeyi ya sanya ta fad'in "Hakan ma yayi Abban su, Allah ya tsare hanya..amma yadda nake ta tunani dae babu mamaki motar da zata zo zuwa Kano ne be samu ba shiyasa ya bari se yau ina ga" murmurshi Abba yayi kafin yace "Toh banda abun Kabeeru ae ya kira ni ya fad'a min ko dan kada hankalin mu ya tashi dukan mu" "Hakane Abban su, In Sha Allah lafiyar ce ma" "I hope so" Abba ya fad'a sanda yake d'aura agogon hannun sa. Sanda ya fito daga d'akin yayi dae dae da lokacin da Ayrah ke fad'in daga toilet d'in tsakar gida "Umma na gama" k'arasawa Umma tayi zuwa cikin toilet d'in ta yiwa Ayrahn tsarkin fitsarin da tayi sannan suka fito tare, da gudu ta isa wajen Abba tace hannun ta rik'e da nashi "Abba don Allah zan bi ka" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Tohm shikenan bari naje na dawo zan taho miki da tsaraba" d'aga idanun ta tayi ta kalli Abban tana murmurshi tace "Abba ni kad'ae ni da Raj zaka siyowa banda Yah Sadeeq koh?" shima murmurshin yayi sannan yace "Ehh.." seta saki Abban tana shirin shiga d'aki tace "Abba ada lafiya" kallan Umma yayi bayan ya amsa addu'ar Ayrahn yace "Ina tunanin zan d'akko Raj in had'a su da Sadeeq su cigaba da karatun su anan ko ya kika gani?" jinjina kae Umma tayi cikin na'am da zancen Abban sannan tace tana murmurshi "Hakan yayi Abban su, Allah ya k'ara taemaka maka, in dae hakan yayi maka nima ya min" "Toh gaskiya hakan ya min, ina tunanin zamu dawo ne tare da Raj yau d'in nan" "Toh Allah ya tsare" Umma ta fad'a.... K'arfe 2 Abba ya sauka a unguwar su Raj bayan ya sake trying number Abbu a kashe, ya sauka daga adaedaetar data kawo shi dan be kae ga d'akko motar sa ba, da k'afar sa ya k'arasa cikin layin cikin nutsuwa, tun daga nesa yake hango gidan kamar da kwad'o a jiki, amma be gasgata hakan ba seda ya k'arasa bakin gidan ya tsaya, kwad'on ne kuwa a jiki, mamaki ya sake kamashi kawae ya tsaya cikin rashin sanin abinyi, ya kae wajen minti 5 tsaye a wajen lokacin ya sake gwada kiran number Abbu har kusan sau 5, sega wani mak'ocin su Abbun yazo wucewa, ya kalli Abba dake kallan wayar sa yace "Salamu Alaekum" ya fad'a yana mik'awa Abba hannu, d'agowa Abba yayi yana kallan mutumin seya mik'a masa hannu suka yi musabaha sannan mutumin yace "Malam Kabeeru kake nema ne?" murmurshi Abba yayi yana jin In Sha Allah mutumin yasan inda yake sannan yace "Wallahi kuwa, tun jiya nake gwada kiran layin sa amma ban same shi ba, gashi kuma nazo gidan a kulle" "Ikon Allah" mutumin ya fad'a yana jinjina kae, jin abinda ya fad'a ne ya sanya Abba sake kallan sa sanda yake fad'in "Aekuwa da alama kunyi sa6ani dan kuwa jiya jiyan nan kafin azahar nazo na same shi suna had'a kaya shi da matar tasa a cikin wata mota, har nake tambayar sa dalilin tafiyar tasa haka babu sanarwa shine yake shaeda min tafiyar gaggawa ce ta kama shi da iyalan nasa shiyasa basu sanarwa da kowa ba amma muyi hak'uri zasu bar garin ne gaba d'aya" da sauri Abba ya sake kallan mutumin yana mamakin jin abinda ke fitowa daga bakin mutumin, cikin watsi da kuma kokawa da abinda ya fara zuwar masa k'wak'walwa da zuciya yace "Anya kuwa? Magana nake fa akan Kabeeru.." "Shi dae Malam Kabeeru baban Suraj, ni kae na nayi mamakin tafiyar tasu kamar wad'anda ake kora, babu wanda suka yi sallama da su se wad'anda suka gansu sanda suke k'ok'arin barin layin nan, kuma har yanzu maganar da nake maka bamu san takamaemae dalilin barin su garin nan ba" "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" shine kawae abinda Abba ke maemaetawa a cikin zuciyar sa, yayin da mutumin ya kalle shi cikin mamakin ganin yadda Abban yayi shiru bece komae ba amma gaba d'aya yanayin sa ya nuna yana cikin tashin hankali, d'an baya kad'an Abban yayi zuciyar sa na wani irin bugawa da k'arfin gaske "Subhanallahi" mutumin ya fad'a yana rik'o Abban, da sauri Abba ya nemi waje ya zauna dan yadda yaji kansa na wani irin juya masa ga wani jiri da lokaci d'aya ya nemi ya kayar dashi "Lafiya dae koh?" mutumin ya fad'a yana nazarin yanayin Abban, cikin k'arfin hali Abba ya furta "Lafiya k'alau, Nagode" "Babu damuwa" mutumin ya fad'a yana yin gaba. Seda Abba ya k'ara wajen minti 20 a wajen sannan ya mik'e zuciyar sa a cunkushe, yama rasa meya kamata yayi tunani, anya kuwa da gaske Kabeerun guduwa yayi masa da kud'i da takaddun sa masu muhimmaci? Anya kuwa ya kamata ya yadda da wannan maganar? Yana so ta k'aryata hakan se dae kuma duk wasu alamu dake nuna Abbun guduwa yayi sun bayyana "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" ya sake maemaetawa sanda ya ida fitowa titi, sam bashi da k'arfin gwuiwar yin tuk'i dan haka bebi takan fire service da yake ajje motar sa ba ya tari mota wadda zata kae shi tasha ya hau motar Kano.. Ko a cikin motar ma gaba d'aya zuciya da k'wak'walwar sa sun kasa sukuni, so yake ya gane cewa mafarki ya yi ba gaskiya bane ace Kabeeru wae ya gudar masa da dukiyar daya dad'e yana tarawa wata da watanni, takaddun karatun sa daya dad'e yana yi shekara da shekaru, anya kuwa ba'a chanja Kabeerun ba, Kabeeru mutum me kirki mutunci da kawaeci, rik'on amanar da shine ya zamo abinda ya birge Abban har ya koma yana masa kallan d'an uwa, kamar d'an uwan da suka fito ciki d'aya, yana ganin kamar ya samu wanda ze iya kular masa da dukiya koda baya wajen, wanda ze rik'e masa amana ko da a bayan idanun sa ne, se dae kashh ashe be sani ba duk wannan a banza ne, ashe Abbun ya yaudare shi ne da halayen bogi, yayi amfani da yaddar daya bashi ya yanke shi son ransa, ashe tun farko akwae k'udurin da yake son cikawa shiyasa ya kwantar da kae, ya nuna kamar shi na Allah ne "Meyasa zaka min haka Kabeeru?" Abba ya fad'a a fili yana dafe da k'irjin sa da har lokacin yake jin ya masa wani irin nauyi. ... Bin Abban tayi da kallo sanda ya shigo cikin gidan, a hankali ta bud'e baki ta amsa sallamar sa da taji yayi ta a hankali, seta mik'e tana goge hannayen ta daga cikin ruwan d'aurayar wanke wanke ta k'araso tana kallan sa tace "Sannu da zuwa Abban su" "Yawwah.." ya fad'a yana yin gaba, haka nan kawae taji zuciyar ta ta buga, seta lumshe idanun ta a ranta tana fatan Allah yasa ba wani mummunan abun ne ya faru ba, a hankali ta yaye labulen d'akin ta shiga da sallama seta nemi gefen gadon ta zauna tana cigaba da kallan sa tace "Ko na had'a maka ruwan wanka ne?" girgiza kae Abba yayi kafin yace "A'ah" cike da damuwa ta furta "Abban su lafiya dae koh?" Abba ya runtse idanun sa yana jin zafin abinda ze fito daga bakin sa "Kabeeru.." tun kafin Umma taji k'arshen maganar ta dafe k'irjin ta dan ita ta d'auka ko wani abun ne ya samu Kabeerun, se dae sa6anin abinda tayi tsammani se taji Abban yace "Kabeeru yaci amana ta, ya tattara kayan sa ya gudu da kud'ad'en nan da kuma takaddu na.." runtse idanun ta Umma tayi a ranta tana fatan ta bud'e idanu taga ba gaskiya bane abinda take ji a kunnuwan ta ko kuma ya kasance mafarki ne take yi, se dae har zuwa sanda ta bud'e idanun ta se taga Abban a yadda ta barshi "Anya kuwa Abban su?" ta fad'a cikin k'arfin gwuiwa, murmurshin takaeci Abba yayi wanda ake cewa yafi kuka ciwo kana yace "Tabbas haka ne, ban dawo gidan nan ba seda na bincika, har unguwar su naje aka tabbatar min a jiyan shima ya bar garin shi da iyalin sa" "Inna lillahi wa inna ilaehi rajiun" Umma ta shiga nanatawa tana kallan Abban tana jin da wani ne ya fad'a mata wannan zancen har abada ba zata ta6a yarda ba "Abban su.. Abbun Raj fa kake magana, mutumin da kullum zancen sa a bakin ka baya wuce na alkhaeri kirkin sa da kuma rik'on amanar sa, koda sau d'aya ban ta6a jin ka fad'i aebun sa ba, se dae gashi yau ina jin wata magana mara dad'i akansa tana fitowa daga bakin ka, Abban su kana nufin duka kud'ad'en nan ya gudu dasu don Allah.." "Toh ina suke Ruk'ayya? ae yanzu kinga irin sakayyar da yayi min na d'aukar amana ta da nayi na bashi koh?" wani numfashi me zafi Umma taja ta fesar sannan ta sake yin salati, daga nan kuma tayi shiru ta kasa cewa komae, dan kwata kwata ma bata san me za tace ba, mamakin ta d'aya yadda Abban da kansa yake fad'in Abbu ya gudu da kud'in sa, abin kamar almara, gaba d'aya k'wak'walwar ta ta tafi can tana mata bitar alak'ar Abban da kuma Abbu.... Sanda Yah Sadeeq yaji zancen nan seda yayi kuka sosae cikin tausayin Abban nasa, yana tuna irin gwagwarmayar da Abban yasha kafin ya samu wannan damar amma lokaci d'aya wani yazo yayi masa awon gaba da komae nasa, ya kuma yi alawadae da hali irin na Abbu, ya kalli Umma dake zaune ta jinginar da kanta kan kujera kamar me tunani "Umma bansan meyasa ba ni gaba d'aya daga shi Raj d'in har mahaefin sa ba suyi min ba Umma, Umma mutumin nan ya cuci Abba ya cuce mu, Allah ya isar mana wallahi" kallan sa Umma tayi, bata jin komae idan ta tattauna magana da Yah Sadeeq d'in dan k'ananun shekarun sa basu hana shi hankali ba, idan yayi wani abun kamar wani babban mutum tace "Bama seka fad'a ba Sadeeq, sakayya kam se Allah yayi mana ita, shi kuma yaje ya gani idan haram wata abace" dae_dae lokacin da Ayrah ta shigo d'akin ta k'arasa ta kwanta akan cinyar Umma kamar zata fashe da kuka ta furta "Umma Raj.." Yah Sadeeq dake zaune kujerar kusa da Umma ne ya janyo ta da k'arfi cikin fad'a yace "Wallahi idan kika sake mana maganar Raj a cikin gidan nan sena miki duka kinji na fad'a miki" ya fad'a yana d'aga hannu kamar ze mare ta, kuka ta fashe dashi kamar wadda ya ida dukan nata, Umma ta kae hannu ta rik'o ta ta d'auke ta zuwa kan cinyar ta ta kwantar sannan ta kalli Yah Sadeeq tace "Ita me ta sani? Wannan fad'an babu abinda ze janyo se rigimar ta kasan hali dae" "Umma ba duk itace ta janyo ba, da bata san Raj d'in bama ta yaya Abba ze had'u da baban sa ballantana har ya cuce shi" Umma na cigaba da rarrashin Ayrah tace a nutse "Ya zamu yi da k'addara Sadeeq?" ... Sau wajen 3 Umman na farkawa daga baccin da babu dad'i cikin sa se tarin damuwa da tunanun nuka tana ganin Abban zaune babu alamar zeyi bacci, se daga k'arshe dae ta kasa shiru tace "Kayi hak'uri Abban su don Allah kayi bacci, kada damuwa ta maka yawa.." Abba ya lumshe idanun sa, baya tunanin ko awa nawa zeyi zae iya yin wani bacci, amma dan ya kwantar mata da hankali ya sanya shi fad'in yana gyara zaman sa "Toh shikenan, yanzu zan kwanta kiyi baccin ki.." ... Wasa wasa wajen kwana 3 kenan Abban baya samun yin bacci, shi kansa besan dalili ba dan ko yayi niyyar yin baccin baya samu yazo masa, se dae kawae ya kwanta yayi ta tunani, zuwa lokacin tunani ya zama kamar wani mahad'in rayuwar sa ne dan kuwa in dae ze zauna toh fa zeyi tunanin nan ne, har kuma zuwa lokacin mamaki yak'i sakar shi, ga Kabeerun da kullum da shi yake kwana yake tashi, duk da guduwa da kud'in da Abbu yayi ya masa zafi amma be kae zafin yadda ya d'auki duk wata yadda tasa ya dank'awa Abbun ba amma daga k'arshe yaci amanar sa, ya yaudare shi, gefe guda kuma tunanin halin da zasu shiga a yanzun yake, yana ganin kamar rayuwa na gab da juya musu baya, babu sana'a, babu takaddar da ze iya zuwa ya nemi aeki, ga kud'in da Alhaji mato yake bin sa, duka tunanin sa yafi karkata nan 6arin ne "Allah ka bani ikon cinye wad'annan jarabobin" Abban ya fad'a akan la66an sa, yana jin wani irin rauni a tattare dashi.... https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 007_008 ___Washe gari wajen k'arfe 8 na safe Abba na zaune cikin parlourn yana yin iya bakin k'ok'arin sa dan kada iyalan nasa su fahimci damuwar da yake ciki se ga kiran Alhaji Mato a wayar sa, ya kalli wayar na tsawon sakanni sannan ya d'aga ya kara ta a kunnen sa, daga can 6angaren Alhaji Mato yace "Haji Ibraheem na jika shiru kwana 2 yasa nace bari na ta6o ka" d'an numfashi kad'an Abba ya sauke sannan yace "Wallahi kuwa, nima ina ta k'ok'arin kiran ka se kuma na sha'afa, dama zuwa anjima nake so nazo wajen naka, ina so ka sake min kwantance" "Toh toh Madallah.." Alhaji Maton ya fad'a yana d'orawa da yiwa Abban kwatance, Umma ta kalle shi sanda ya gama wayar tace a nutse "Yanzu ya za'ayi da shi kenan?" seda Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Zan fad'a masa gaskiya ne, idan ya yadda da k'addara shikenan idan kuma be amince ba yace sena biya shi kud'in sa se nasan yadda za'ayi.." "Toh Allah Ubangiji yasa ma shima ya kar6i wannan k'addarar" "Ameen" Abba ya fad'a ba dan yana da tabbacin hakan ba, dan shi sheda ne akan son kud'i irin na Alhaji Maton. .. Shiru Alhaji Maton yayi har Abba ya gama masa bayanin abinda ya faru, se yayi murmushi yana girgiza kae kana ya d'aga kae ya kalli Abba yace "Haji Khaleel ni fa gani nake ko menene ya faru kae ka jawa kanka, ba sau d'aya ba ba sau biyu ba na fad'a maka na kuma baka shawara ka rabu da matar ka, farar k'afa gare ta, an kore ka daga banki, kazo ka fara teaching an dakatar da kae ka fara kasuwanci wani ya gudu da kud'in wannan kad'ae be ishe ka ka gane.." "Malam ya ishe ni haka!" Abba ya fad'a yana d'aga masa hannu idanun sa akan sa cike da zallahr 6acin rae "Aou aou toh hakane abin, wato har yanzu kae ka kasa gane Annabi ya faku koh?, toh cigaba da zama da ita, ina ga ba zaka fahimci abinda nake fad'a maka ba se ranar da kayan sakawa ma ya gagare ka sakawa.." Abba ya runtse idanun sa zafin zuciyar da yanzun ya zame masa jiki se k'aruwa yake yi, a nutse ya mik'e tsaye sannan cikin kaurin murya ya furta "Kana buk'atar kud'in ka ne ko kuwa?" "A'ah se kuma in k'i buk'ata, ina jiran kud'i na a cikin satin nan kawae" Alhaji Mato ya fad'a shima yana mik'ewa ya bar wajen, da kallo Abba ya bishi yana mamakin wannan banzan hali irin na Alhaji Maton, shikenan kuma a matsayin ka na bawa musulmi Allah baze jarabce ka ba? Da wannan tunanin ya koma gida yana sak'a da warwarar yadda ze biya Alhaji Maton kud'in sa. Sanda ya koma gidan bayan yaci abinci Umma ta tambaye shi yadda suka yi da Alhaji Maton, duk se yaji tausayin ta ya kama shi yadda wani ke ik'rarin duk dalilin tane abubuwa ke faruwa dashi, abinda shi kuma baze ta6a yadda ba kenan, dan kuwa shi musulmi ne daya yadda da k'addara me kyau da kuma mara kyau, gyara zama yayi yana kallan ta "Kada ki damu, zan san yadda zanyi in biya shi kud'in sa.." cike da mamaki Umma tace "Aou yace se an biya shi?" "K'warae kuwa" Abba ya fad'a "Ikon Allah.." Umma ta fad'a tana girgiza kae... Abba beyi k'asa a gwuiwa ba wajen d'akko motar sa ya siyar da ita ba, saboda matsalolin da take dasu yasa ba tayi wani daraja ba gata kuma dama ba babbar mota bace, seya d'auki kud'in Alhaji Mato ya bashi sannan ya rik'e ragowar a hannun sa dan amfanin yau da gobe, abinda ya tsaya masa a rae yanzun kawae shine yadda zeyi ya samu sana'a ko dan ya sanya 'ya'yan nasa a makaranta, abinda ya k'ara masa k'aemi ma akan saka su a makarantar shine.. Rannan suna zaune a cikin parlourn dukan su suna kallan Al jazeera inda Abba ke kallan labarae, Ayrah na zaune gefen Abban itama tana kallan T.Vn kamar me fuskantar abinda ake nunawa a ciki, daga k'arshe a cikin labaran aka nuno wasu d'alibae da Uniform d'in su, se kuwa tayi zumbur ta tashi zaune tana kallan Abba tace "Abba mun dena zuwa makaranta?" kallan ta Abba yayi cikin mamakin jin furucin ta, se yayi murmushi sannan yace yana shafa doguwar sumar kanta dake a bud'e "A'ah za'a sanya ku mana" "Abba yaushe?" ta sake tambayar sa, seya d'an yi shiru kana yace "Nan bada dad'ewa ba Uhmm?" "Hadda Raj koh?" ta fad'a tana murmurshi, zancen kenan dan kullum idan ba tayi maganar Raj ba toh ba Ayrahn bace "Ehh" Abba ya fad'a yana maeda duban sa kan T.V. .... Sosae Umma ta takurawa Abba akan zuwa asibiti saboda rashin baccin da yake samu, shima kansa rashin baccin na damun sa dan haka a wannan karon da tazo masa da k'orafi be musa mata ba ya shirya ya tafi asibitin, gwajin hawan jini aka fara masa, kuma tashin farko su kaga yanda jinin sa ya hau, sosae suka bashi shawarwari akan hakan da kuma magunguna, hakan ba k'aramin kuma tayar masa da hankali yayi ba, amma gudun kada hankalin Umma ya tashi yasa be sanar da ita ba, kawae yace mata an gwada shi amma basu fad'a masa aenahin abinda ke damun sa ba se result d'in ya fito, haka ta yadda da abinda ya fad'a mata d'in, yayin da shi kuma ya cigaba da shan magungunan sa ba tare daya bari Umman ta sani ba. A lokacin ne ya cigaba da fama da rashin bacci da kuma tunanin daya zame masa jiki, se kuma bugun zuciya da shima baya rabo dashi, haka wataran ze kwana a zaune, se dae da yake baya bari lokacin ya tafi masa a banza se hakan yake sakawa baya wani damuwa sosae, dan kuwa k'arin lokacin karatun Qur'an ya samu, idan dae ya fahimci bacci baze zo masa ba seya fito tsakar gidan nasu ya shimfid'a dadduma yayi ta karatu har zuwa asuba, ranar da kuma ya samu baccin se yayi baccin sosae, sau da dama Umma kan farka ta same shi yana karatu, dalilin kenan daya sanya bata damu da rashin baccin nasa ba, saboda ta riga data saba da ganin sa cikin dare yana tashi karatu, se dae tasan ya k'ara lokacin karatun, amma duk da haka bata kawo rashin samun bacci ne ya sanya shi k'ara lokacin karatun ba, tafi ta'allak'a hakan da yanayin rayuwa kawae.. Sanda Umman ta gano ciwon dake tattare da Abban ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba, dan har kuka seda tayi, Abba ya fesar da iska daga bakin sa yana kallan ta yace "Kiyi hak'uri kiyi shiru, kada kisa nima nawa hankalin ya tashi mana" "Amma Abban su meyasa ka 6oye min?" "Toh yanzu ba gashi kin sani ba?" ya fad'a yana kallan ta, seta share hawayen fuskar ta sannan tace "Duk da kullum cikin yi maka addu'a nake, amma ko ba komae zan dage da maka addu'a akan ciwon koh?" "Toh shikenan nayi laefi amin afuwa" ya fad'a yana kallan ta da tattausan murmushi akan fuskar sa, itama murmurshin tayi duk da yadda can k'asan zuciyar ta ke cunkushe da tausayin Abban. .. Sosae Abba ya dage wajen neman sana'ar da zata rufa musu asiri, se dae har zuwa lokacin be samu ba, gaba d'aya yanzu burin sa be wuce na yadda ze samu ya sanya Yah Sadeeq da Ayrah a makaranta ba dan haka idan ya tashi tun safe ya fita baya dawowa se dare amma har zuwa lokacin be samu ba. .. "Abba wae ana sallama da kae" Yah Sadeeq ya fad'a yana Kallan Abba dake zaune "Inji wa?" Abban ya fad'a yana kallan sa, girgiza kae Yah Sadeeq yayi sannan yace "Abba bansan shi ba.." "Toh Ikon Allah" Abba ya fad'a yana mik'ewa, ya kalli Umma da itama kallan sa take yace "Bari naje.." "A dawo lafiya" ta fad'a sanda yake barin tsakar gidan zuwa waje.. Murmushi yayi sanda yaga mak'ocin sane wanda suke yawan had'uwa a masallaci, seya mik'a masa hannu suka gaesa sannan mutumin yace "Wato dama magana ce akan wani aeki, yasa nace bari na maka magana idan zaka iya toh seka fara ko ranar litinin ne.." sosae annurin fuskar Abba ya k'aru yace "Ina jin ka wane irin aeki ne?" "Aekin Company ne haka amma ba wani aekin wahala bane sosae, idan ka amince zaka iya se muje ka gani" sosae Abba yaji dad'in wannan abu dan haka cikin farin ciki yace "Toh nagode nagode sosae, Allah ya saka da alkhaeri.." "Ameen Ameen" mutumin ya fad'a. Abba na komawa gida ya sanar da Umma abin alkhaerin daya same su, sosae Umman ma taji dad'i dan haka babu 6ata lokaci Abba ya gabatar da isthikara, kafin ya fara zuwa aekin kuwa sosae yaji ya kwanta masa, har ya k'agu ma ya fara aekin.. Ranar litinin kuwa Abba ya fara aekin, kuma a ranar aka fad'a masa albashin sa, duk da kud'in basu taka kara sun karya ba amma shi a wajen sa da iyalin sa sosae suka ji dad'i, suka kuma godewa Allah.. Babu 6ata lokaci k'arshen wata nayi Abba ya sanya su Ayrah a makarantar gwamnati d'an nesa da gidan su, yayi amfani da kud'in ya siya musu duk wasu kaya na buk'ata da yasan zasu buk'ace su, farin ciki a wajen Ayrah kamar zata yi mene, dan sosae tayi missing School, yadda suka samu background me kyau ya sanya yanzun abin bezo musu da wahala ba, duk da yanayi na chanji da yake tsakanin government school da private school, dan haka suka cigaba da karatun su.. Kud'in Abban gaba d'aya yake k'arewa a wajen hidimar makaranta, kud'in mota da kuma kud'in cefane dan haka akwae wani mutum da yake siyar da kayan abinci a wajen sa yake kar6ar bashin abinci duk k'arshen wata, wani watan kuma seya bashi kud'in sa ya sake kar6ar wasu, haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa. Tun daga wancan lokacin Abba be sake bi takan Alhaji Mato ba dan ya riga yasan babu abinda ze saka ya sake bashi wani abun ko kuma jari, dan haka kwata kwata ma bebi ta kansa ba, ya fita harkar sa kamar yadda shima ya fita tasa. A 6angaren Ayrah kuwa zuwa lokacin tun tana zancen Raj har ta gaji ta dena yi, dan tun iyayen na biye mata har suka zo suka dena kula ta idan tayi zancen nasa, basu san me zasu ce mata akan Raj d'in ba dan kuwa a lokacin shekarun ta sunyi kad'an ta fahimci irin abinda Abbun yayi wa Abba. .. Kwanaki nata tafiya, haka watanni ma suna ta shud'ewa suka had'u suka bada shekaru, izuwa lokacin sosae hidimomi suka taru suka k'ara yiwa Abba yawa, ga kuma kullum yadda tsadar abubuwa ke k'aruwa amma kuma albashin sa kamar na da ne, ba'a k'ara musu ba ballantana su samu sauk'in yadda abubuwa ke ta tashi, k'arshen wata ne a lokacin sanda aka musu albashi, dama kuma kafin zuwan albashin ya riga ya kashe su da bashi, kae tsaye seda ya fara zuwa kasuwa ya siyowa su Ayrah sabbin Uniform, a yadda yaso ma har da jaka da takalma ze siya musu saboda yadda nasun suka tsufa amma kuma yasan idan yayi hakan zasu takura ne matuk'a, dan haka kawae daga Uniform d'in ya baro kasuwar, daga nan ya wuce ya biya wad'anda ke binsa bashi wanda bashi da yawa, ya zama na saura kud'in daya san na cefane ne kawae dana kud'in motar su Ayrahn. Wajen da yaje na k'arshe shine wajen wanda yake kar6ar kayan abinci a wajen sa, ya k'arasa da sallama yana neman waje ya zauna, amsa masa sallamar mutumin yayi sannan Abba ya d'an yi shiru yana tunanin ta inda ze fara, seya sanya hannu cikin aljihu ya d'akko kud'in daya ware wanda ze bashi, ya mik'a masa yace "Gashi.." kar6a mutumin yayi yana karkad'e hannun sa da fulawa ta 6ata, ya k'irga sannan ya kalli Abba "Wani abun za'a baka da kud'in ne?" girgiza kae Abba yayi cikin sarewa da yadda yaga mutumin kamar wanda ze bashi kayan kyauta yace "A'ah kayi hak'uri don Allah, kasan lamarin ne se a hankali, ka rik'e wannan, a bani kayan kamar yadda aka saba bani idan yaso se a d'ora akan wad'ancan" tun kafin ya kae k'arshen maganar mutumin ya fara girgiza kae, yana gamawa yace "A'ah wallahi bazan iya ba, kae ma kayi hak'uri, duk lokacin daka gama biyan bashin se kazo mu san yadda za'ayi, shine kawae alfarmar da zan iya maka" Abba ya runtse idanun sa yana jin gaba d'aya jikin sa babu dad'i, dama daga yadda yaga yanayin mutumin yasan ba lallae ya yadda da abinda yazo masa dashi d'in ba, dan haka ya mik'e yace a hankali "Toh nagode, zan kawo maka cikon kud'in In Allah ya yadda.." Abba ya fad'a yana yin gaba, mutumin ya bishi da kallo yace bayan yaja tsaki "Ayi mutum kullum cikin neman alfarma yake, na tsani irin haka wallahi" ya fad'a yana d'aura wani mae a cikin leda.. ... Da sallama Abba ya shiga gidan, Ayrah ta k'arasa ta rungume Abban tana fad'in "Abba sannu da zuwa" "Yawwah sannu Auta" ya fad'a yana sakar mata ledar hannun sa daya shigo da ita, tana shirin juyawa yace "Ina d'an kwalin kuma?" "Abba tsifa Umma ke min, yanzun na cire shi" ta fad'a tana d'an murmushi gami da shafa kanta "Toh ayi maza a gama tsifar a rufe kan" Abba ya fad'a sanda yake kallan Umma dake masa sannu da zuwa, Ayrah ta k'araso ta ajje ledar hannun ta, sannan ta tafi da d'ayar kitchen dan ko Abban be fad'a ba tasan tsarabar tace, er madaedaeciyar roba ta d'akko ta zuba mangoron nata a ciki sannan taje ta wanke shi kana ta dawo cikin parlourn dae_dae lokacin da Abba ke fad'in "Lafiya kuwa Sadeeq ke bacci da yamman nan?" "Wallahi kuwa Abban su kamar zazza6i ne a jikin sa d'azun" "Toh Subhanallahi Allah ya sawwak'e... Ga rama can ki kwad'a mana ita muci yanzun, kafin dare kuma mu san yadda za'ayi.." babu musu Umma ta mik'e ta fita daga d'akin zuwa kitchen ta gyara ramar tass ta kwad'a ta sannan ta kawowa Abba tasa kana ta zubo musu ita da Ayrah har ma da Yah Sadeeq, kallan Ayrah dake ta shan mangoron ta hankali kwance tayi ta girgiza kae tana murmushi tace "Tashi Sadeeq ya tashi haka nan yaci abinci.." da "toh" ta amsa sannan ta mik'e ta fita bayan ta wanke hannun ta ta dawo cikin d'akin, hannun ta ta saka a hankali tace "Yah Sadeeq, Yah Sadeeq.." a hankali ya shiga bud'e idanun sa da suka masa nauyi saboda wani azababben ciwon kae daya rik'e masa kae, kallan sa su duka suka yi sanda yake k'ok'arin tashi zaune kan kujerar, Yah Sadeeq ba gwanin raki bane dan haka kana ganin sa kasan da gaske rashin lafiya ce ta kama shi "Yah Sadeeq baka da lafiya?" Ayrah ta fad'a tana kallan sa da idanun ta da suka yi rau rau, seya jinjina kae kawae yana lumshe idanun sa "Kayi wanka se kazo kaci abinci ko zaka ji d'adin jikin ka" Umma ta fad'a tana kallan Yah Sadeeq, seya mik'e a hankali ya fita daga d'akin hannun sa dafe da k'irjin sa ya wuce toilet d'in yayi wanka sannan ya fito.. Tare suka ci ramar cikin kwano d'aya, yana ci Umma na lura da yadda yake ta 6ata rae alamar kawae ci yake babu taste a bakin sa, wani iri da yaji a k'irjin sa ya sanya shi d'aukar ruwan da Ayrah ta kawo yanzu ta ajiye ya kafa bakin sa ya fara sha, se dae kafin ya ida shan ruwan wani irin amae ya taso masa, dan haka babu 6ata lokaci kuma cikin hanzari ya jefar da cup d'in yayi waje, aekuwa ya dinga kwara aman kamar ransa ze fita, dukkan su biyo shi suka yi wajen cike da tausayawa babu ma Ayrah data fara matse k'walla saboda tausayin d'an uwan nata "Sannu" suka dinga jefa masa sanda Umma ta taemaka masa ya tashi ta k'arasa dashi zuwa parlourn nata, Abba ya kalle ta yace "Ina ga ki shirya kawae mu wuce asibiti.." Yah Sadeeq dafe da k'irjin sa yace yana d'an girgiza kansa dan shi kad'ae yasan yadda yake ji a cikin jikin sa "Abba bacci nake ji, a bari na tashi tukunna se muje don Allah" "Abba don Allah a barshi yayi bacci" Ayrah dake rik'e da hannun Yah Sadeeq ta fad'a, jinjina kae Abba yayi kana yace "Shikenan, kayi baccin.." babu musu Yah Sadeeq ya koma ya kwanta yana lumshe idanun sa k'irjin sa na bugawa da k'arfin gaske, cikin en mintuna kad'an wani nannauyan bacci yayi awon gaba dashi, duk da kuma baccin daya d'auke shi hakan be sanya ya d'auke hannun sa dake kan k'irjin sa ba, ita kuma Ayrah na zaune gefen sa har lokacin hannun sa cikin nata tana jin tausayin d'an uwan nata rabin jikin ta......... Mhiz Innocent.... ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 009_010 ___Sosae jikin Yah Sadeeq yayi tsanani a daren ta yadda dole seda suka mik'a shi asibiti, da kud'ad'en da suka ragewa Abba a hannu dasu yayi amfani wajen bada kud'in gwaje gwaje da sauran abubuwan da ba za'a rasa ba, tashin farko aka tabbatar da Yah Sadeeq d'in na d'auke da chronic ulcer ne, ga kuma matsananincin zazza6in daya sake rufe shi a ranar, dan haka asibitin suka rik'e shi ya kwana acan d'in, magunguna sosae aka had'a masa wad'anda suka janyo k'arewar kud'in daya rage a hannun Abba tass, sosae Yah Sadeeq d'in yaji jiki ya rame dama ba wani jiki gare shi ba, kamar wanda ya shekara a kwance, seda yayi sati 1 sannan aka sallame shi, zuwa lokacin kam tuni Abba ya fara tunanin mafitar daze samar musu wadda zasu dinga samun abincin da zasu dinga ci da sauran kayan amfani na yau da kullum. Sanda suka dawo gidan ma seya zama na basu da komae na dangane da abinci, dan haka Abba beyi k'asa a gwuiwa ba ya nemi bashi a wajen ogan su na company kuma cikin ikon Allah ya bashi, da wannan kud'in suka yi amfani har zuwa k'arshen wata, sedae fa a cikin watan dama Ayrah ce kad'ae ke zuwa makaranta saboda Yah Sadeeq har lokacin be gama warkewa ba, itama kuma babu kud'in da za'a dinga bata na mota dan haka Abba da kansa ke raka Ayrahn har makaranta a k'afa sannan ya wuce company shi kuma. A cikin wannan d'an tsukun ne Ayrah tayi k'awa Zaenab a makarantar bokon nasu, wadda take cikin unguwar su d'an nesa kad'an da gidan su, sosae suka k'ulla k'awance wanda har hakan ya janyo Abba yasan mahaefin ta ya zamana suna gaesawa sosae kamar abokae, sanda Baban Zaenab d'in ya fahimci yadda Ayrahn ke zuwa makaranta a k'afa se be cewa Abba komae ba washe gari kawae yazo k'ofar gidan su Ayrahn ya d'auke ta da yake yana da babur wanda a shi yake d'aukar Zaenab ya kae ta makaranta, sosae Abba yaji dad'in hakan ya yiwa Baban Zaenab d'in godiya. Tun daga ranar ya kasance kullum Baban Zaenab d'in ke zuwa ya d'auki Ayrah su wuce makaranta tare.. Sanda Yah Sadeeq ya warke bayan doguwar rashin lafiyar da yayi Abba da kansa yaje wajen Baban Zaenab d'in ya sake masa godiya sannan ya fad'a masa zancen warkewar Yah Sadeeq d'in kuma shine ze cigaba da tafiya da Ayrah makaranta, dan zuwa lokacin abubuwa sun d'an yiwa Abba kyau ba kamar da ba, da farko Baban Zaenab d'in ya nuna k'in amincewar sa akan hakan, ya nuna ze cigaba da kae Ayrah tare da Zaenab makaranta, se da Abba ya ganar dashi sosae kafin ya hak'ura... Haka rayuwar tasu ta cigaba da kasancewa wataran su samu suci abinci wataran kuma se dae suyi hak'uri, ko kuma su samu suci abincin sau 2 a rana, harkokin yau da kullum kuma wasu se dae ayi hak'uri, idan kuma abu ya zama dole toh Abba kanyi iya k'ok'arin sa wajen samar da abun... _BAYAN WASU SHEKARU_ __A cikin shekarun da suka shud'e sosae abubuwa suka cigaba da faruwa, ta 6angaren su Ayrah dae babu wani chanji dan kuwa har zuwa lokacin Abba aekin Companyn nan yake yi, yayin da Yah Sadeeq ya gama Secondary School har da shekara 3 da wani abun ma amma saboda yanayin rayuwa yasa har lokacin be cigaba ba, se dae wani lokacin ya kan bi Abba Company ya d'an taemaka masa da wasu auyukan.. .. Shigowar ta gidan kenan da sallama sanye cikin Uniform riga da wando blue da kuma hijab me d'an girma fari, k'afar ta tana saye cikin wani takalmi sau ciki bak'i me d'an madaedaecin kyau, matashiyar budurwa er kimanin shekaru 15, fara k'all da ita, zuwa lokacin data fara zama budurwa sosae kyawun ta ya k'ara fitowa sosae, haka zalika hasken fatar ta ya k'aru, Umma dake zaune cikin d'aki tana cigaba da sak'ar wata hula da yanzun take yi tana d'an samun kud'i, ta amsa sallamar Ayrahn, k'arasawa Ayrah tayi zuwa cikin d'akin sannan ta zube akan ledar tsakar d'akin hannun ta kan k'afar ta tana k'ok'arin cire takalmin k'afar ta tace bayan ta d'an tura k'aramin bakin ta gaba "Washh Allah na" ta fad'a tana cigaba da cire takalmin ta, Umma da take kallan ta ta girgiza kae tace "Sannu malalaciya" dae_dae lokacin data gama cire takalmin ta juyo tana kallan Umma seta sake maraeraece fuska tana fad'in "Allah kuwa Umma na gaji da gaske" ta fad'a tana d'ora kanta akan cinyar Umman, ajjiye sak'ar hannun ta Umma tayi sannan tace bayan ta d'ora hannun ta akan Ayrah "Qualifying d'in ta fito?" seta tashi da sauri wani murmushi na k'wacewa akan kyakykyawar fuskar ta, ta saka hannu ta janyo jakar ta data ajje a gefe sannan ta bud'e ta d'akko wata farar takadda ta mik'awa Umma har lokacin murmurshi be bar kan fuskar ta ba "Umma naci.." ta fad'a dae_dae lokacin da Umman ta kar6i takaddar, ta karanta sannan ta d'ago tana kallan Ayrahn itama da murmushi kan fuskar ta tana jin wani irin dad'i mara misaltuwa "Alhamdulillah, Alhamdulillah" shine abinda Umman ke fad'a har cikin ranta tana jin dad'i "Umma nayi k'ok'ari koh? Abba ya dawo yaji abin farin ciki, dama Yah Sadeeq yace ze siya min waya idan naci" murmushi Umma tayi tana kallan Ayrahn sannan tace "Sosae ma kuwa Auta, kinyi k'ok'ari, Allah ya k'ara miki baseerah" "Ameen Umma na" ta fad'a tana maeda kan ta ta d'ora akan cinyar Umman "Toh a tashi ayi Sallah koh?" seta jinjina kae tana tashi zaune ta cire Hijab d'in jikin ta sannan ta zame k'aramin d'an kwalin da yake kanta wanda hakan ya bawa dogon bak'in kwantaccen gashin ta damar zubowa akan kafad'ar ta kasancewar ko Ribbon bata saka ta d'aure shi ba, duk da bata saka komae a kan ta wanda ya danganci relaxer hakan be hana gashin ta kwanciya kamar ta saka masa wani abun ba "Je kiyi wanka kizo na miki kitso.." Umma ta fad'a tana kallan ta, seta 6ata fuska kamar me shirin yin kuka, k'uruciyar ta na bayyana sosae tace "Don Allah Umma bana so.." ta fad'a tana maeda d'an kwalin kanta ta d'aure, seya kasance gashin nata ya d'an lek'o ta baya, mik'ewa tayi hannun ta d'auke da takalmin ta data cire dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ya shigo cikin gidan da sallama, dukkan su suka amsa masa sallamar sanda ya k'araso cikin tsakar gidan, matashi ne kyakykyawa shima kamar er uwar sa, sedae bashi da wani jiki dan zamu iya kiran sa da siriri, da sauri Ayrah ta koma cikin d'akin ta d'akko takaddar nan sannan ta kalli Yah Sadeeq daya ida shigowa cikin d'akin tace tun kafin ya kae ga zama "Yah Sadeeq albishirin ka?" seya kalle ta yana murmushi kana yace "Goro fari tass" seta maedo da hannun ta data 6oye a bayan ta tace "Naci qualifying" ta fad'a tana mik'a masa takaddar, cikin farin ciki ya sanya hannun sa ya kar6a seda ya karanta sannan ya maeda duban sa kanta har lokacin yana murmushi yace "Dat's my lily, kinyi k'ok'ari sosae" ya fad'a yana dan jan kumatun ta, murmushi tayi kana tace "Yah Sadeeq alk'awarin mu.." "Ohh kinga har na manta kuwa" ya fad'a yana fiddo ido, seta d'an tura bakin ta kad'an sannan tace "Kae Yah Sadeeq.." dariya yayi yana d'an satar kallan Umma kana ya maeda duban sa kanta yace "Kada ki damu, ina d'aukar albashi zan siya miki Uhmm?" (shima yanzu ya samu aeki a wani company inda yake zuwa yayi aekin a biya shi k'arshen wata) er k'ara kad'an ta saki tana rungume Yah Sadeeq d'in cikin farin ciki tace "Nagode sosae Yah Sadeeq.." Umma dake gefen su tace tana kallan su "Gwara ma ka chanja wani abun ba dae waya ba, du du du ma yaushe ta dena shashanci balle kuma a d'auki waya a bata?" d'agowa tayi tana kallan Umma idanun ta sun cika taff da hawaye tace "Allah kuwa Umma na girma fa" "Toh in gani a k'asa" Umman ta fad'a tana mik'ewa ta fice daga d'akin, seta sanya hannu tana goge hawayen idanun ta, Yah Sadeeq yayi murmushi yana kallan ta yace "Kiyi shiru zan taushi Umma ta bari na siya miki er k'aramar waya ki dinga yin game, amma fa se kin min alk'awari.." "Ehh wallahi na yadda nayi" ta fad'a tana d'aga yatsan ta d'aya, dariya ta bashi dan haka seda yayi dariyar kana yace "Ohk toh yanzu yaushe zaku fara Neco?" "Aou na manta" ta fad'a tana dafe bakin ta kana ta ta6e bakin se kuma tace tana kallan Umma data dawo cikin d'akin "Umma wae kuma kinji se mun biya wani kud'in kafin mu fara Necon" da mamaki dukkan su suke kallan ta, Yah Sadeeq yace "Wane kud'in kenan?" seta k'ara ta6e baki kafin tace "Nima bansani ba" "Yanzu kuma naga kin ci exam d'in ae.." Umma ta fad'a tana kallan ta "Ehh Umma haka dae suka ce" "Toh Allah ya kyauta" Umma ta fad'a tana jinjina kae... Lokacin da Abba ya dawo yaji labarin Ayrahn taci exam d'in sosae yayi farin ciki, duk da kud'in da akace zasu bayar a makarantar hakan be wani dame shi ba, tunda dae gwamnati ta biya kud'i masu yawan da dama yake tunanin idan Ayrahn bata ci ba ya zeyi ya same su, se gashi cikin ikon Allah ma taci exam d'in.. ... Littafi ne a hannun ta na English tana duba wani aeki da yanzun malamin dake koyar dasu ya gama musu aekin ya fita, seta d'auki littafin tana d'an dubawa ko akwae abinda bata gane a ciki ba, k'awar ta Zaenab wadda suke kiran ta da zee ce ta ta6o ta tana fad'in "Kefa er raenin hankali ce, hala baki ji abinda ake fad'a ba" seta d'aga kae tana kallan ta kana tace bayan ta d'an 6ata fuska "Karatu fa nake, Allah kuwa banji abinda akace ba" "Toh cewa akayi wad'anda suka ci Qualifying suje PC na neman su" "PC kuma?" ta fad'a tana fiddo da manyan fararen idanun ta waje, sosae ta bawa Zee dariya dan haka tayi dariyar tana fad'in "Matsoraciyar banza, toh meze mana?" seta sake maraeraece fuska sannan tace "Allah kuwa ni dae tsoro nake ji" "Toh ae dad'in ta bake kad'ae bace ba koh? Ki tashi mu tafi kina gani duk wad'anda suka ci d'in sun fita" Zaenab ta fad'a tana mik'ewa, itama Ayrahn mik'ewa tayi ta ajje littafin hannun ta kan bench d'in su sannan suka fito daga ajin zuwa office d'in Principal d'in su, suna tafiya jefi jefi suna d'an ta6a hira kasancewar akwae sabo me k'arfi a tsakanin su, dan kuwa unguwar su d'aya su biyun, kuma Islamiyya ma d'aya suke zuwa "Ace yace dukkan mu mu wanke toilets" Zee ta fad'a tana satar kallan Ayrah, seta 6ata fuska gami da shagwa6e face tace "Don Allah ki bari" ta fad'a tana ta6e baki.. Akan ta idanun sa suka fara sauka sanda yake sakkowa daga cikin wata bak'ar hamshak'iyar mota, bak'i ne sosae sannan kuma me jiki babu laefi, sanye cikin wata Ash d'in shadda wadda ta sake fiddo da bak'in sa sosae, hannun sa d'auke da irin wannan sandar girman yana sanya ta duk inda k'afar sa zata taka, a kallan farko zaka iya bashi shekaru 40 zuwa 45 amma idan ka masa kallo irin na sosae zaka fahimci kud'in daya gama wadatar sane ya 6oye aenahin shekarun sa dan kuwa ak'alla ze kae shekara 55, seya lumshe idanu yana jin wani irin maganad'iso na fuzgar sa zuwa ga yarinyar, yanayin yadda take magana a shagwa6e hakan ba k'aramin burge shi yayi ba, seya bita da idanu kamar wani maye sanda suke k'ok'arin shiga Office d'in principal, nan ma seda suka tsaya suka d'an yi magana kafin suka tu6e takalman su duka suka shige ciki, wani numfashi ya fesar me k'arfin gaske lokaci guda kuma yana saeta numfashin sa da yanayin fitar sa ya sauya cikin k'ank'anin lokaci "Wacece wannan yarinyar?" ya fad'a sanda wani malami a cikin makarantar ya k'araso yana gaeda shi, amma shi sam be lura ba hankalin sa na kan Ayrah ne, da mamaki malamin ya kalli inda ya nuna da hannun sa yace yana kallan Alhajin "Wa kenan yalla6ae?" "Wata farar yarinya data shiga Office d'in nan yanzu ita da wata.." "Ohk wae Ayrah Ibraheem Khaleel?" "Ayrah!" ya ambata a fili, "kamar yadda sunan ke da dad'i haka mamallakiyar sunan ke da kyau" ya ayyana a ransa kafin a fili yace "K'warae wacece ita?" "D'aliba ce a makarantar nan.." malamin ya fad'a yana mamakin jin tambayoyin dake fitowa daga bakin Alhajin "K'arin bayani.." Alhajin ya fad'a yana kafe Malamin nan da jajayen idanun sa da suka kasance na halitta, seda yaja numfashi kad'an sannan ya furta "Hadda ita dae a cikin wad'anda suka ci qualifying, so yanzu akwae wani important issue ne yasa principal kiran su" ganin dae baze samu wani cikkaken information daga wajen sa ba ya sanya shi fad'in "Ohk ya yanayin k'wakwalwar ta yake?" seda ya d'an yi shiru sannan yace yana murmushi "Gifted, a cikin ajin su ita ke d'aukar first position koda yaushe" "Thank u" Alhajin ya fad'a yana mik'awa Malamin hannu suka gaesa sannan yayi gaba, drivern Alhajin ne ya matso kusa dashi kansa a k'asa yace "Yalla6ae kana buk'atar wani abu ne?" "A'ah.." ya fad'a yana kallan wanda ya fito daga cikin motar yana maeda waya cikin aljihu, da alama waya ya gama yi a cikin motar, shima kamar Alhajin zasu yi shekaru kusan d'aya se dae banbancin kamanni, dae_dae lokacin da Ayrah ke fitowa daga cikin Office d'in se dae wannan karon ita kad'ae ce, Alhajin ya kalli abokin sa Alhaji Baba yace "Wannan yarinyar ta min" bin Ayrah Alhaji Baba yayi da kallo kana ya dawo da duban sa kan Alhaji yace "Wannan abar?" jinjina kae yayi yana cigaba da binta da kallo harta 6acewa ganin sa "Wannan ae se dae ka raene ta yalla6ae.." Alhaji Baba ya fad'a yana kallan sa "Babu damuwa zan raene tan, daga yanzu zuwa sanda zata gama Secondary School, zan kashe ko nawa ne a kanta nasan ka gane abinda nake nufi.." murmushi Alhaji Baba yayi kana yace "Kana tunanin wannan yarinyar zata aure ka?" "Meze hana? Ina da wani aebun da 'ya mace zata guje ni ne? Musamman ma irin wannan da take zuwa makarantar talakawa irin wannan?" Alhajin ya fad'a yana kallan Alhaji Baba "Iyayen ta fa?" "Me kud'i suke yi? Ina tunanin ka manta nace zan kashe ko nawa ne a kanta koh?" Alhaji ya katse shi da fad'in hakan "A nemo min wace ce ita, su waye iyayen ta, menene burin su na rayuwa, dukka zan cika musu shi komae girman sa.." ya fad'a yana kallan drivern sa.... *_Doctor RK is coming...._*😌🌚 Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 011_012 ___"Sir mun binciko maka wacece ita" cewar wani d'an matashi daya shigo cikin wani hamshak'in parlour daya gaji da had'uwa, murmushi Alhajin yayi yana kallan sa sannan yace "Good job Muttala, wacece ita? Menene burin nasu? Yaya iyayen ta suke?" gyara zama matashin saurayin da aka kira da Muttala yayi kana yace "Kamar yadda muka tsammata talakawa ne futuk yalla6ae, kuma idan iyayen nata nada buri toh be wuce na d'iyar tasu tayi karatu ba" "Sure? Kuma kana nufin ka bincika da kyau?" Alhajin ya fad'a "Sosae kuwa ranka ya dad'e, idan da k'ari dae toh se dae ko a bawa baban nata jari, dan wallahi ranka ya dad'e da gani yana shan kebula" ya fad'a yana wani maraeraece fuska kamar wanda yaga wani abun mara dad'i, se kuma ya sake gyara zama yace "Amma wani hanzari ba gudu ba yalla6ae, ina ga da zan iya bada shawara da nace kar ka fara tarar abin daka haka, a fara da ita yarinyar saboda gudun matsala" jinjina kae Alhajin yayi cike da gamsuwa da maganar Muttalan yace "Hakane, yanzu abinda nake so, ayi duk abinda ya dace akan karatun yarinyar, kome take buk'ata zan samar mata shi, kada ayi sanya akan wannan al'amari kuma bana so a samu matsala" "Babu damuwa Alhaji..". Muttala na fita daga d'akin kae tsaye makarantar su Ayrah ya wuce direct ya tafi wajen Principal ya sanar dashi sak'on Alhaji, sosae shi kansa Principal yayi mamakin jin wannan lamari amma tunda abin na manya ne seya dena ganin laefin sa, ya maeda hankali wajen sanar dasu abinda Ayrahn ke buk'ata daya danganci makaranta.. Da sallama ya shigo cikin gidan, duka suka amsa masa sanda yake k'arasowa cikin tsakar gidan da suke zaune, Ayrah dake kwance kan cinyar Umma tana kalmashe mata dogon gashin kan ta me santsi, Umman ta mik'e ta k'arasa wajen Abba kafin ya gama shigowa, ta masa sannu da zuwa sannan suka k'araso suka zauna a tsakar gidan "Matso ina zaune na k'arasa miki kalbar.." Umma ta fad'a tana kallan Ayrah data d'auki mayafi ta yafa a kanta, seta kwa6e bakin ta sannan tace kamar za tayi kuka "Don Allah Umma a bari haka nan" harara Umma ta jefa mata, Abba dake kallan su yayi murmushi sannan yace "A'ah abar Auta ta huta haka nan, kinga ma nazo miki da wani albishir.." ya fad'a yana sanya hannun sa cikin aljihu ya d'auko kud'i sannan ya mik'a mata yace "Ga kud'in nan sun samu" ya fad'a yana murmushi, hannu biyu Ayrah ta saka ta kar6a sannan tana murmushi ta kalli Umma kana ta maeda duban ta kan Abba tace "Abba Albishirin ka.." Seya kalle su su duka kafin yace "Albishir kuma? Ikon Allah... Toh goro.." yayi maganar duka a lokaci d'aya, Ayrahn ta cigaba da fad'in "Abba PC da kansa yasa aka kira ni ya fad'a min wae an biya min kud'in ma saboda k'ok'ari na" ta k'arasa fad'a da k'ayataccen murmushi akan fuskar ta, shiru na wasu en sakanni kafin Abba yace "Ikon Allah, toh Masha Allah Auta, Allah ya k'ara miki k'ok'ari Uhmm?" "Ameen Abba" ta fad'a tana mik'a masa kud'in hannun ta, seya sanya hannu ya maeda kud'in cikin hannun ta sannan yace "Ki rik'e su a wajen ki bana so na kashe, in case koda wata matsalar zata taso, duk da bama fata ma" seta mik'awa Umma kud'in tace tana Kallan Abba "Allah ya k'ara arzik'i Abba.." ..... A cikin en tsukun su Ayrah suka zana NECO, sun shafe satittika suna gabatarwa, sosae Ayrah ta dage wajen yin karatu ko dan ta cika burin iyayen nata na son tayi karatu, a kwanakin sau da dama takan hana kanta bacci dan dae tayi karatun, har wani lokacin se Umma ta saka ta tayi bacci sannan take hak'ura da karatun tayi baccin.. .. Tun d'azu bacci ke ta barazanar d'aukar ta amma take ta basarwa dan jira take Abba ya dawo saboda tun d'azu ya fita a dalilin rasuwa da akayi a cikin layin nasu, bata k'ara minti 5 a zaune ba kuwa ta jiyo sallamar sa daga tsakar gida, seta tashi zaune tana janyo d'an kwalin ta daya sa6ule daga kanta ta yafa shi ta zubo dashi gaba sannan ta fito tsakar gidan "Abba sannu da zuwa.." ta fad'a bayan ta nemi waje ta zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gida "Yawwah Ayrah.." Abba ya fad'a yana kallan ta, seta cigaba da zama har zuwa sanda Umma ta fito daga kitchen d'auke da plate a hannun ta wanda ta yiwa Abba kwad'on salad a cikin sa "Sannu" ya fad'a yana kallan ta da murmushi kan fuskar sa, Ayrah tace "Abba.." yace "Na'am" ya fad'a yana kallan ta yadda take lumshe manyan fararen idanun ta da alama bacci take ji "Abba dama zuwa nayi na fad'a maka.." seya cigaba da kallan ta sannan yace jin tayi shiru "Ina jin ki" "Wae gobe idan Allah ya kaemu ance muje da wani d'an gidan mu za'a min registration na Jamb" sosae Abban ya cigaba da kallan Ayrah, I zuwa yanzu haka kawae yaji rashin yadda ya d'arsu a ransa, dan haka dole yayi wani abun "Shima cewa suka yi zasu biya miki?" seta jinjina kae kawae "K'arfe nawa?" "Wae kafin k'arfe 2 dae.." seya jinjina kae shima kafin yace yana janyo plate d'in gaban sa "Toh shikenan, Allah ya kaemu gobe inaso naje wajen principal d'in ku" "Toh Abba seda safe.." ta fad'a tana mik'ewa, Umma ta bita da kallo sanda take shigewa d'akin ta bayan ta mata seda safe, seta dawo da kanta wajen Abba tace "Amma gaskiya makarantar nan idan hakane suna da kirki, kuma hakan ba k'aramin k'arawa d'alibae k'warin gwuiwa zeyi ba" "Sosae kuwa" Abba ya fad'a a ransa dae yana tunani ne. Washe_gari Abba tare suka fita da Ayrah zuwa makarantar tasu, sanda suka shigo cikin makarantar da k'afar su suke takawa zuwa ciki, jefi jefi Abba kan d'an yi mata tambaya ita kuma ta amsa masa, har zuwa sanda suka k'arasa inda office d'in principal yake, a dae_dae lokacin da Alhaji ke fitowa daga cikin office d'in principal d'in nasu yayi dae_dae da lokacin da wayar Abba ta fara ringing, seya zaro ta daga cikin aljihu yana barin wajen zuwa baya dan amsa wayar saboda hayaniya, yana juyawar shi kuma Alhajin ya ida fitowa, a take idanun sa suka yi tozali da kyakykyawar fuskar ta sanda take tsaye a wajen tana jiran Abba ya dawo su shiga Office d'in tare, seya bita da wani mayattacen kallo da idanun nasa yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa saboda k'aunar yarinyar "Yalla6ae.." wani dake gefen sa ya fad'a, se ya d'an yi firgigit ya juya yana kallan mutumin sannan ya rufe idanun sa ya bud'e kana ya saki murmushi yace a hankali "Idan na ganta wallahi ina loosing control d'ina ne.." yayi maganar sanda suke barin wajen zuwa inda motocin su ke ajjiye, suna wucewar Abba kuma ya ida wayar sa ya k'araso yana kallan Ayrah yace "Muje..".... Da sallama suka shiga Office d'in, principal dake zaune ya kalle su sannan yayi murmushi ganin Abba fad'i yake "A'ah sannun ku da zuwa" ya fad'a kamar wanda yaga wani hamshak'in mutumin, shi kansa Abba seda abin ya d'an so bashi mamaki amma ya fuske ya nemi waje ya zauna yayin da Ayrah ta zauna a k'asa, seda suka gaesa sannan Abba yace "Dama magana ce akan yarinyar nan" yayi maganar yana nuna Ayrah da kanta ke k'asa, sannan ya cigaba da fad'in "Abubuwa da dama sun faru se dae ban samu damar zuwa wajen ku ba, toh shiyasa a wannan karon nace bari nazo naji daga bakin ku.. Naji yau ma ance wae za'a biya mata kud'in registration na Jamb?" murmushi Principal yayi kana yace bayan ya had'e hannayen sa cikin juna "Ae wato Alhaji Ibraheem ka godewa Allah, Allah ya baka yarinya me hazak'a, saboda haka dan mun d'auki nauyin ta wannan ba komae bane, In Sha Allah ma zamu d'auki nauyin ta ne har ta gama karatu.." dukkan su se suka kalle shi suna jin wani irin farin ciki na ratsa ilahirin jikkunan su "Toh Alhamdulillah, Masha Allah, muna godiya sosae Principal, Allah ya k'ara arzik'i" Inji Abba "Ameen_Ameen.." .... A kwanakin da suka biyo ne Ayrah suka zana jarabawar Jamb d'in, babu wani dad'ewa kuma result d'in ya fito, cikin ikon Allah kuma ta doko point dae_dae da course d'in data ke so dama kuma a Neco ma ta fito da 9 credit, dan haka komae yazo cikin sauk'i, wani malamin su ne ya shige mata gaba bayan fitowar result d'in nasu wanda shima Alhaji ne ya sanya shi yin hakan, sosae suka yi fafutuka wajen sama mata admission har Allah yasa ta samu Medicine a A.B.U Zaria. Ba k'aramin farin ciki Abba, Umma, Yah Sadeeq har ma ita kanta Ayrahn suka yi ba sanda suka ji an sama mata Admission d'in ta hanyar wannan malamin nasu, amma sanda duk suka ji a inda ta samu Admission d'in se duk jikin su yayi sanyi. Umma dake zaune kan tabarma ta kalli Abba dake fad'in "Duk da naji dad'in wannan Admission d'in da aka samu, amma bana tunanin zan yadda Ayrah ta tafi har Zaria karatu, ina tunanin kawae a bashshi.." Yah Sadeeq da shima yake kusa da Abba yace "Abba ni ina ganin kawae a batta d'in ta tafi, tunda duk da k'arancin shekarun Ayrah tana da hankali.." ya k'arasa maganar yana kallan Ayrah gami da sakar mata murmushi, itama murmushin ta saki tana jin dad'in wannan yabon na Yah Sadeeq duk da dae ita kanta ji take kamar ta hak'ura da makarantar, dan bata masan yadda rayuwar ta zata kasance acan wani waje babu Umman ta, ba Abban ta sannan kuma ba Yah Sadeeq d'in ta ba, Umma taja doguwar ajiyar zuciya sannan tace "Abban su barin wannan Admission d'in kamar mun saka k'afa ne munyi fatali da damar mu, ina ganin meze hana tunda mun yadda da d'iyar mu, mu barta taje d'in idan yaso mu dinga binta da addu'a kuma mu dinga kae mata ziyara..?" shiru Abba yayi na wasu en dak'ik'u kana yace "Zan sake tunani.." daga haka be sake cewa komae ba.. A cikin satin Abba ya amince da zuwa makarantar Ayrahn, dan haka daga shi har Yah Sadeeq suka tashi tsaye sosae wajen fara siya mata abubuwan da zata tafi dasu, duk da ba wasu kaya ne na azo a gani ba amma dae sun samu sun siya mata abubuwan da suka san zata buk'ata.. Cikin d'an k'ank'anin lokaci aka gama komae, duk wasu abubuwa da suka kamata aka gama su daga 6angaren Abban har daga can 6angaren Alhaji.. ..... Zubewa yayi a k'asan carpet kansa a k'asa yana jira Alhajin ya gama wayar da yake yi, seda ya shafe wajen rabin awa yana wayar da duk da ganin wani ya shigo besa ya katse ta ba "Muttala ina jin ka" yayi maganar sanda yake aje wayar akan kujerar gefen sa "Yalla6ae jibi ne tafiyar tasu fa" murmushi yayi kana yace "Toh madallah, yanzu abinda za'ayi.. ga kud'i nan kaje duk inda ya dace ka siyo duk wani abu da kasan yarinya budurwa nada buk'ata idan zata je makarantar kwana.." ya fad'a yana ajje masa wasu uban kud'i a gaban sa "Toh shikenan, amma bana tunanin a had'a da kayan lokacin da zasu tafi can makarantar, inaga gwara daga baya kayan su bita.." jinjina kae Alhajin yayi sannan yace "Hakan ma yayi.." ya d'an dakata kana ya d'ora da "Kana ganin idan naje wajen mahaefin ta a yanzu banyi gaggawa ba?" girgiza kae Muttala ya shiga yi ya d'an yi murmushi kana yace "A'ah ranka ya dad'e ka bari tukunna, kada su fahimci dalilin hidimar ka tun yanzu, zefi kyau mubi komae daki_daki.." "Gaskiya a haka ma nayi k'ok'ari wallahi, bari dae zan bar ta ta gabatar da first semester kawae zuwa lokacin zan je wajen baban nata" ya fad'a yana girgiza kae shima "Toh hakan ma babu laefi" Inji Muttala.. .... Tana sanye cikin doguwar rigar atamfa da hijab kasancewar sa favourite nata, sosae kyakykyawar fuskar ta tayi fayau kamar mara lafiya, fararen manyan idanun ta sunyi ja, hannun ta cikin na Umma tana kallan ta da idanun nata da suka sake yin rau rau, Umma tayi murmushi dan tana so ne ta kwantar mata da hankali tace "Ya isa haka shalele, kada ki 6ata fuskar nan taki yanzun nan mana Uhmm?" Umma ta fad'a tana sanya hannu ta d'auke k'wallar dake zuba akan kuncin ta "Umma ta zanyi kewar ki" ta fad'a tana kwantawa a jikin Umman, hannu Umma ta saka ta rik'o ta bayan tayi murmushi tace "Banda abin ki Ayrah ae ba dad'ewa zaki dinga yi ba, ko kin manta zaki dinga dawo mana hutu?" seta jinjina kae kawae "Toh idan kin gama kukan seki taho mu tafi" Yah Sadeeq daya shigo ya fad'a, seta d'aga kae tana kallan sa gami da murgud'a mitsitsin bakin ta "Iyeee.. Lallae ne yarinyar nan" Yah Sadeeq ya fad'a yana rik'e ha6a. Har k'ofar gida Umma ta rako su inda motar da zata kaesu Zarian take, seda taga tashin motar tasu sannan ta koma cikin gidan tana matse k'walla, dan kuwa tun tasowar Ayrahn baza tace ga ranar da suka ta6a rabuwa ba, dan tun tana yarinyar ta mayyar Umman ce, ko yadda da mutane ba wani sosae take ba ballantana ace taje ta kwana. ... "Ki maeda hankali kiyi karatu, sati d'ayan nan da aka wuce ki ki samu wata ta koya miki, banda yin k'awar da zaki zauna kina fad'a mata cikin ki duk da dae nasan halin ki amma dae gwara na tisa miki" Yah Sadeeq ya fad'a sanda suke tsaye a wani ke6antaccen waje, seta jinjina kae kawae dan bata tunanin zata iya magana, idan kuwa tace zatayi maganar toh tabbas kuka zata saka, Abba daya fahimci haka se yayi murmushi dan shi kansa har ya fara kewar Autar tasa, ya matsa kusa da ita yace "Ayi karatu sosae koh?" nan ma dae seta jinjina kan tana kae hannun ta idanun ta ta goge hawayen daya sauko akan fuskar ta, hannu Yah Sadeeq ya sanya cikin aljihun sa ya zaro wata k'aramar waya yace yana kallan k'anwar tasa "Yau dae ga alk'awarin mu.." seta kalli hannun nasa sannan ta kalle shi, bata san sanda murmushi ya su6uce a kyakykyawar fuskar ta ba, ta saka hannu ta kar6a cike da farin ciki kana ta d'an jujjuya ta sannan tace lokacin da wasu kyawawan hawaye suka samu damar zubowa akan kuncin ta "Amma nagode sosae Yah Sadeeq, Allah ya k'ara arzik'i" "Ameen" dukan su suka amsa da hakan cikin jin dad'in yadda ta d'an saki jiki.. seda suka d'an dad'e suna sallamar zuwa lokacin ta saki jiki suna ta d'an hira, se kuma daga baya tayi kukan ta ta godewa Allah, sannan su Abban suka tafi bayan sun kwantar mata da hankali... ... A hankali ta tura k'ofar d'akin hannun ta jaye da er trolley d'in ta da aka kar6o mata a wajen k'anwar Umma da itama zama ya dawo dasu cikin kano, dukkan su suka d'aga kae suka kalle ta sanda tayi sallama da kyakykyawar siririyar muryar ta data sake sirancewa saboda kukan da tayi, su 3 ne zaune a cikin d'akin, d'aya na daga gefe tana danna waya yayin da biyun ke zaune kusa da juna suna hira "Wa'alaeki Assalam" suka amsa dukan su suna bin bak'uwar fuskar da suka gani da kallo "Wow, tubarkallah Masha Allah" d'aya daga cikin su ta fad'a a ranta lokaci d'aya kuma tana mik'ewa tsaye ta k'arasa inda Ayrah take tace tana d'an yin murmushi "Anan d'akin kike?" tayi maganar tana kallan idanun ta da suka yi ja alamar kuka tayi, seta k'ak'alo murmushi ta wanzar akan fuskar ta wanda kana gani kasan beje ko'ina ba tana jinjina kae "U're highly welcome.." ta fad'a tana d'aukar bagcon data gani a gefen Ayrah tayi gaba, babu musu Ayrahn tabi bayan ta a hankali "Ruks ki tashi me waje tazo fa" wadda ta kar6i jakar Ayrahn ta fad'a tana kallan wadda ke zaune kan gado tana danna waya, wadda aka kira da Ruks d'in ce ta mik'e tana kallan Ayrah itama tayi murmushi tace "Barka da zuwa bak'uwa" "Umhum" Ayrah ta fad'a kawae tana jefa mata kalar murmurshin data yiwa Jidda, seta k'arasa ta zauna akan gadon tana jin ta gaba d'aya a wani irin takure, musamman yadda taga su duk lokaci d'aya suna neman sakin jiki da ita, seda Jidda ta ajje mata kayan ta gefe guda sannan ta dawo ta zauna kusa dasu Ruks ta zauna, Bahijja da tun d'azun ba tace komae ba se kallan Ayrah da take tace "Bak'uwa ya sunan ki?" a hankali ta bud'e bakin ta daya mata nauyi tace "Ayrah.." "Awwwn, sunan en gayu, suna me dad'i.." kusan a tare suka fad'i hakan, har seda hakan ya sanya ta tayi murmushi "Toh barkan ki da zuwa" Bahijja ta fad'a... Suna nan zaune d'akin har bayan isha'i suna hirar su, hirar da kusan duk akan abu d'aya suke yin ta, ita dae tana zaune a gefe guda se dae ta bisu da ido kawae, so take ta ke6e ita kad'ae tayi kukan ta ko zata ji sauk'in kewar gida data fara damun ta tun yanzun. "Ruks ki tashi ki d'ora mana ko Indomie ce pls, kinga bak'uwa ma ba taci komae ba" Jidda ta fad'a, Ruks ta kalli Ayrah tace "Ayrah kina jin yunwa ne?" seta girgiza kae kawae tana yabawa da kulawar mutanen da bata ta6a ganin su ba se yau "A'ah a k'oshe nake" ta fad'a tana kallan Ruks d'in "Toh dae kin ji, mu duk bama jin yunwa muma, a bar shi kawae pls" "Shikenan ae" Jidda ta fad'a "Kuuu, kun san k'arfe nawa kuwa?" Bahijja ta fad'a tana d'an waro eyes d'in ta "Wani abun ya faru?" Ruks da Jidda suka tambaya lokaci d'aya "Ni kam seda safen ku wallahi, kwanciya zanyi ko dan na tashi da wuri, gobe fa Doctor RK ne a farko, ko kun manta abinda yayi last Monday?" ta k'arasa maganar tana hayewa kan gadon ta "Nima kam seda safen ku" Ruks ta fad'a tana mik'ewa, harara Jidda ta jefa mata sannan tace "Toh ni me zan zauna jira hajiya? Ayrah seda safe" tayi maganar itama tana hayewa gadon ta.. Bin su tayi da kallo su duka lokacin da d'akin yayi shiru, se taji tsoro ya fara shigar ta, dan haka taja jikin ta ta maeda shi kan gadon ta kwanta, ta lullu6e kafatanin jikin ta da hijab d'in ta wani sanyi na ratsa ta, a hankali ta lumshe idanun ta wasu hawaye masu d'umi na sakkowa akan fuskar ta, wayar data tuna da ita ta janyo ta nemo number Yah Sadeeq ta danna kira, bugu 1_2 ya d'aga dan lokacin be kae ga yin bacci ba "Yah Sadeeq.." tayi maganar tana fashewa da wani marayan kuka a hankali, daga can 6angaren Yah Sadeeq ya girgiza kae yana murmushi dan yasan wannan kukan nata bana komae bane sena shagwa6ar data zame mata jiki "Auta rigima" ya fad'a yana murmushi, dae_dae sannan wayar Jidda tayi k'ara, taja tsaki daga inda take kwance tana amsa wayar ba tare da tasan me kiran ba, daga can 6angaren akace "Jidda don Allah kimin snapping aekin nan zanyi copying kafin gobe.." "Don Allah kiyi hak'uri Abeedah, ki koma kije kiyi bacci ko dan gobe ki samu shiga class d'in" banji me akace daga can 6angaren ba amma naji Jidda tayi dariya tace "Doctor RK fa.." daga inda Ayrah ke kwance ta d'an lumshe idanun ta tana jin yadda ta gaji da jin sunan da suke ta ambata tun d'azu, sunan da kusan duk hirar da suke tun d'azu a kansa ne suke yin ta, seta gyara kwanciyar ta ta kawae duk da tasan yau dae ba zata iya baccin ba... _*Yanzu wasan ze soma*_🥲 Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 013_014 ___Washe_gari tun asuba ta tashi tayi wanka ta gabatar da sallah sannan ta cigaba da zama kan carpet d'in da tayi Sallahr akae tana addu'a, bata dad'e da zama ba su Jidda ma suka farka kusan a tare, Jidda ce ta fara shigewa toilet yayin da Ruks da Bahijja suka tsaya a bakin toilet d'in kowacce na jira Jidda ta fito itama ta shiga. Tana nan zaune haka suka dinga sauri suna shiryawa kafin wajen k'arfe 7:30 dukkan su suka gama shiryawa kusan duk cikin dogayen riguna da k'ananan mayafae, Bahijja dake saka boot a k'afar ta tace "Kin gama shiryawa ne, ko har yanzu addu'ar ce ba'a gama ba?" tayi maganar tana kallan Ayrah, seta girgiza kae kafin tace "A'ah ku jira ni yanzu zan shirya" "Ayrah mun yi gaba, kiyi sauri ki shirya ki taho kafin 8 tayi" Ruks ta fad'a sanda take d'aukar jakar ta, jinjina kae kawae tayi ba tare da ta sake cewa komae ba, ta bisu da kallo sanda suke ficewa daga d'akin. A hankali ta mik'e ta sake fad'awa toilet ta wanko fuskar ta sannan ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfa kana ta saka hijab, ta d'auki sabuwar jakar da Yah Sadeeq ya siya mata wadda ta zuba littafan ta a ciki ta fito daga d'akin. A hankali take takawa a cikin filin makarantar cikin nutsuwar ta, duk da babu abinda ta shafa akan fuskar ta amma tayi kyau sosae, bayan ta d'auke da jakar goyo yayin da ta rungume wasu text books guda 2 wanda suma duk Yah Sadeeq ne ya siya mata saboda ta samu sauk'in karatu. Tun kafin ta k'arasa inda ze sada ta da ajin nasu taji shiru kamar babu mutane cikin ajin, har seda ta fara tantamar anya kuwa ba tayi 6atan kae ba?, dab da zata isa wajen ajin sassanya kuma daddad'ar muryar sa ce ta fara dakar mata kunnen ta, ba'a iya jiyo abinda yake fad'a d'in amma tana iya jiyo sautin yadda nutsatstsiyar muryar tasa ke fita, haka kurum taji k'irjin ta ya buga da wani irin k'arfi har seda ta dakata daga inda take tafe na wasu en mintuna kafin ta lumshe manyan idanun ta kana ta bud'e su tana mamakin yadda bugun zuciyar ta ya sauya cikin k'ank'anin lokaci. Da sallama akan la66an ta ta sanya k'afa cikin ajin nasu ba tare data kalli kowa ba, dan bata jin zata iya kallan kafatanin en ajin dan tasan duk idanun su na kanta ne "Hey!" nutsatstsiya, sanyayyiya kuma daddad'ar muryar sa me dad'in saurara ta daki dodon kunnen ta, a take kuma a lokaci guda k'afar ta ta d'auki rawa wanda har yanzun ta kasa gane dalilin wannan rawar da jikin nata ke yi "Ko dae da ita ake?" ta tambayi kan ta, gudun kada taje tayi laefi ya sanya ta dakatawa daga inda take, a hankali kuma ta shiga juyowa zuwa inda yake tsaye sannan ta d'aga raunannun idanun ta ta aza su inda ta tabbatar yana tsaye, ba ita yake kalla ba idanun sa na kan wani littafi dake gaban sa ne, kyakykyawa ajin farko, fari me kyakykyawan jiki kuma cikin kyakykyawar shiga, sanye yake cikin wasu riga da wando da suka dace da k'irar jikin sa, a saman kayan kuma suit ce itama me kyau, kansa babu komae se kwantacciyar bak'ar suma da tasha gyara na musamman, kamar yadda take a gyare haka kyakykyawan bak'in sajen sa ma yake a gyare kuma a kwance wanda hakan ba k'aramin k'arawa kyakykyawar fuskar sa kyau yayi ba, ganin da tayi ba ita yake kalla ba dan ita kanta bata ganin fuskar sa se gefen fuskar ta sa, seta d'an lumshe idanun ta kafin a hankali ta fara k'ok'arin juyawa "Hey, go out!" ya sake fad'a har lokacin be kalle ta ba, kawae se tayi shahada ta tabbatar da ita yake, har lokacin bata kalli kowa ba taja k'afafun ta ta fice daga ajin. Kae tsaye hostel ta koma har lokacin tana tuna sautin muryar sa a cikin kwanyar ta sannan kuma tana hana k'wallar data tarar mata a idanu zubowa, tana shiga ta ajjiye jakar ta ta haye kan gadon ta jinginar da kanta a jikin gado, iska ta fesar daga cikin bakin ta tana d'an jan numfashi kafin ta sanya hannu ta goge hawayen da suka fara sakkowa akan fuskar ta, a hankali ta cigaba da jan sheshshek'a tana jin wani irin zafi wanda da farko bata ji shi ba se yanzun, ta tsani yarfi, ta tsani dizgi, se gashi her first day in University wani yayi embarrassing na ta a baenar nasi, d'an mitsitsin bakin ta ta murgud'a kamar wani na kallan ta sannan tace akan la66an ta "Bashi da kirki". Tafi awa 1 a cikin hostel d'in seda ta kitanci lokacin da tasan ya fita sannan ta mik'e ta fita zuwa ajin nasu, cikin sa'a kuwa babu kowa cikin ajin a lokacin, se students kawae da kowa ke harkar gaban sa, koda ta shiga cikin ajin duk seta ji ta a takure musamman da taji a jikin ta idanun mutane da dama na yawo ne a kan ta, se take ganin kamar kowa kallan ta yake da wadda aka kora d'azu, duk se ta ji tana neman sark'ewa a tafiyar da take, gaba d'aya ma ta rasa inda za taje ta zauna, tsintsiyar hannun ta taji an kama se ta juya da sauri ta d'aga idanun ta ta kalli wadda ta rik'e mata hannun, Jidda ce, seta sauke ajiyar zuciya hadda lumshe idanun ta tana bud'ewa lokaci guda "Muje ki zauna" Jiddan ta fad'a tana cigaba da jan ta zuwa cikin ajin, babu musu kuwa kamar wata doluwa ta bita cike da sassarfa, wani dake zaune kan wani bench yace yana kallan Jidda "Hajiya Jidda an samu wata kenan?" seta juya ta watsa masa harara sannan tace "Shishshigi ba kwarjini" dariya yayi hadda dukan bench yace bayan ta wuce wajen "Yoh shishshigi kuma ya kae wanda kika yi?" ita dae bama taji shi ba suka k'arasa inda suke zaune sannan tace tana Kallan Ayrah "Yawwah ki zauna, nan ne kusan permanent seat namu dan tunda muka zo anan muke zama" murmushin yak'e Ayrah tayi dan har ga Allah wajen be mata ba, dan kuwa a baya ne bench d'in nasu yake, se dae ta nemi waje ta zauna kawae. Basu suka koma hostel ba a ranar se wajen k'arfe 6, dan haka suna komawa Ayrah ce ta fara fad'awa toilet tayi wanka dan sosae ta gaji tana fitowa ta zira doguwar riga mara nauyi ta maeda hijab d'in ta tayi sallah kana ta nemi waje ta zauna still dae da hijab d'in , dan haka kawae tunda tazo d'in tafi jin ta comfortable idan ta saka hijab d'in. "Toh mu dae kinga had'a girkin mu muke, kawae kowaccen mu zata kawo abincin tane duk abinda muke so se mu dafa muci, kema ayi hakan dake?" Ruks ce me maganar tana kallan Ayrah, seda ta d'an yi jimm, saboda haka kawae taji basu wani kwanta mata can ba musamman daya kasance hirar su gaba d'aya rabin ta ta samari ce, tun jiyan kuma da tazo ba taji wata a cikin su tayi maganar karatu ba, amma kuma suna da kirki yadda suka tarbetan kawae ma ya mata dad'i dan haka se tace "Tohm.." "Ohk guys..me zamu dafa?" Ruks ta fad'a tana kallan su su duka, ta6e baki Jidda tayi kana tace "Kawae mu dafa indomie, dan ni yunwa nake ji" "Nima dae kam" Bahijja ta fad'a itama, mik'ewa Ruks tayi ta nufi inda kayan abincin nasu ke ajiye cikin d'an k'ank'anin lokaci ta d'ora musu Indomien, sanda take zuba Maggi a ciki ne ta jiyo muryar Jidda na fad'in "Ke ni tun d'azu nake so mu tattauna akan shigar Doctor RK ta yau, amma wannan Abeedar ta mana k'erere, don Allah befi wancan satin kyau ba?" ajiye maggin hannun ta Ruks tayi sannan ta juyo tana rik'e ha6a kana tace tana murmushi "Umhum wallahi ke kam ki bari kawae.., shi fa kowacce shiga yayi naga alama kyau take masa, wallahi guy d'in ya had'u iya had'uwa" ta fad'a tana jan baki kamar wadda taci abu me yaji, daga nan fa hirar tasu ta soma, maganar tasan nan dae da kullum ita suke yau ma dae ta san suke, da alama basa gajiya da hirar tasa kamar wani abinci "Wae Bahijja meye haka naji kinyi shiru?" Jidda ta fad'a tana jefa mata harara, seta yamutse fuska kana tace "Ke kam ki bari kawae, kae na ke ciwo" itama tayi maganar tana yamutse ta ta fuskar "Toh Allah ya sawwak'e.. Ayrah ki sauko muci abinci" Ruks ta fad'a tana kallan Ayrah dake kwance kamar me bacci, se a lokacin ta tashi dan daga inda take zaune tun d'azu ji take kamar ta tashi ta musu duka, tana jin kamar tace musu sun ishe ta da maganar wannan mugun mutumin, haka dae ta mik'e ta sauko suka ci abincin. ...... Washe_gari k'arfe 7:40 dukan su suka gama shiryawa har da Ayrah, yau ma cikin hijab d'in dae ta shirya kamar jiyan, suka fito tare suna tafiya su Jidda na hira yayin da ita dae tayi shiru kawae, a dae_dae inda ze sada su da ajin nasu dukkan su suka ji wata murya na fad'in "Ayrah Ibraheem Khaleel.." kusan a tare dukan su suka juya, se duk suka tsaya suna kallan mutumin daya kira sunan nata kafin suka kalli Ayrah, itama da kallan rashin sani take bin sa dan tunda take bata ta6a ganin fuskar ba "Sak'o aka bani na kawo miki.." yayi maganar yana kallan ta "Sak'o kuma? Ni ban sanka ba" ta fad'a cike da sakarcin nan nata, se yayi murmushi kana yace "Ehh Hajiya, dama nasan baki sanni ba ae amma daga makarantar ku ne aka turo ni" seta d'an samu relief amma duk da haka tace "Toh mene?" "K'awa ta zo mu tafi 8 ta kusa, kuma kin san yau yana da first period a farko" Ruks ta fad'a tana jan hannun Ayrah, seta d'an maraeraece fuska sannan tace "Uhmm daga makaranta ne fa.." "Kinsan yadda za'ayi? Mu bari muyi gaba ke kuma kiyi sauri kiji abinda ze fad'a, but u should make sure dat kin shigo class before 8" seta jinjina kae tana bin su da kallo sanda suke wucewa ajin kana ita kuma ta dawo da duban ta inda mutumin yake, kafin tace komae yace "Kayan abinci ne dana sakawa Hajiya akace mu kawo miki daga makaranta" seta tsaya ta cigaba da kallan sa kamar me tunani se kuma tace "Kaya kuma?" yace "Ehh.." "A'ah Abba ya siya min" ta fad'a tana girgiza kae, seya sake yin murmushi kafin yace "Ehh wannan ae daban yake Hajiya, kuma kinga daga makaranta ne" seta d'an yi jimm kafin tace "Toh zan kira Yah Sadeeq na fad'a masa tukunna" mutumin ya sauke ajiyar zuciya yana mamakin wannan yarinya haka amma gudun kada ya takura ta shinshino wani abun ya sanya shi fad'in "Toh kira shi" "Ae ba yanzu ba.." tayi maganar cikin turo baki duk da bata san tayi hakan ba "Meyasa?" "Sauri nake" ta fad'a tana gyara tsayuwar ta, seya fesar da iska daga bakin sa kafin yace "Toh shikenan, bari na jira ki" ba tace komae ba ta juya zuwa ajin nasu, dae_dae lokacin da wani d'alibi yayi sauri ya shige cikin ajin, seta ji dad'i hakan na nufin 8 ba tayi ba kenan, dan haka da confidence d'in ta ta sanya k'afa cikin ajin, tayi wajen taku 5 a cikin ajin tana jin dad'in yadda yau ta samu class d'in, se dae ga mamakin ta seta jiyo kamilalliyar muryar sa na fad'in "Go out.." seta ta6e baki a ranta tana sak'a may be tana shigowa k'arfe 8 d'in ta cika, gashi nan har ze kori wata ko wani, dan haka ta cigaba da tafiya har zuwa sanda ta samu waje ta zauna tana lumshe idanun ta kana ta bud'e, abinda ya bata mamaki yadda taga kusan idon kowa na cikin ajin akan ta yake, seta sake kallan wani 6angaren taga still dae ita suke kalla, a hankali tabi jikin ta da kallo zuciyar ta na bugawa tana fatan ba wani abun ne ta manta bata saka ba, ta kalli jikin ta hijab d'in ta gashi nan har kusan k'asa, ita kanta kawae dae ta duba d'in ne amma tasan da akwae abinda beyi ba a jikin ta su Jidda zasu fad'a mata, inda taga kuma sun maeda hankali suna kalla itama ta d'aga raunannun idanun ta da suka cika taff da k'walla saboda wannan kallan da suke mata duk ya rikita ta, a hankali idanun ta suka sauka akan kamilalliya kuma nutsatsiyar fuskar sa me cike da wani irin zati, da kwarjini na musamman har bata san sanda ta d'auke idanun ta da sauri ba tana dafe k'irjin ta daya wani irin buga a lokaci guda "Kurma ce?" yayi maganar kamar baya so kuma ba tare daya kalli en ajin ba "Dake fa yake.. Ki tashi ki fita kin makara.." wata dake kusa da ita ta ankarar da ita, seta d'aga kae cikin rashin fahimta ta kalle shi dae_dae sanda shima ya d'ago nasa firgitattun idanun da suka ida rikita ta, ta sake jin zuciyar ta ta buga da k'arfin da yafi na d'azu, a hankali ya janye nasa idanun fuskar sa ba yabo ba fallasa ya sake fad'in "Fita!" yanzun kam ta tabbatar da ita yake, dan haka jiki a matuk'ar sanyaye taja k'afafun ta ta fice daga cikin ajin, tana jin yadda idanun en ajin suka mata chaaa aka wanda har hakan ya jawo tafiyar ta ta sake chanjawa tana tafiya tana wani rangaji kamar er maye, tun kafin ta ida fitowa daga cikin ajin wani kuka ya k'wace mata, dan haka ita tama manta da wannan mutumin dake jiran ta kawae ta wuce Hostel, akan gadon ta ta zube tana fashewa da kuka, ta san mutumin be santa ba bata san shi ba ba dan haka ba se tace tsanar ta yayi shiyasa yake korar ta kullum, ban da haka meyasa wani ya shiga kafin ita be kore shi ba se ita, wayar ta data ajiye akan gadon dama bata tafi da ita class ba ce ta fara ringing seta janyo wayar ta d'aga tana k'ok'arin tsayar da kukan "Subhanallahi Auta meya faru? Har yanzu baki dena kukan ba?" Yah Sadeeq ya fad'a, seta sake hasaso fuskar Rk cikin idanun ta kana ta harari iska tana murgud'a baki sannan tace "Toh ba wani malami bane, Yah Sadeeq wallahi mugu ne kuma.." "Kae Subhanallahi, Ayrah bakya so karatun naki yayi albarka?" "Toh Yah Sadeeq sau biyu fa yana hana ni shiga aji wae na makara" murmushi Yah Sadeeq yayi daga inda yake kafin yace "Toh kiyi hak'uri, kuma kada na sake ji kince bashi da kirki, daga yanzu ki dinga shiryawa da wuri kina tafiya class kin ji?" seta d'aga kae kamar yana kallan ta sannan tace "Ehh" "Dats my sister.." ya fad'a yana murmushi, seda Yah Sadeeq ya ajje wayar sannan tace bayan ta sake tuna fuskar Rk "Mugu kawae.." K'arfe 3 suka fito daga lectures d'in, Jidda, Ruks Bahijja har ma da Ayrah suka fito daga class d'in dan komawa Hostel, suna cikin tafiya kafin su k'arasa Hostel d'in Bahijja ta kalle su tace "Ku wuce pls yanzu zanje na dawo" "Ina zaki je?" Ruks ta fad'a tana kallan ta, seta d'an yamutse fuska kafin tace "Yanzun zan dawo pls, akwae sak'on da zan kar6a wajen wata cousin sister d'i ta data fara zuwa school d'in nan" "Ohk" suka fad'a kusan a tare, suka cigaba da tafiya yayin da ita kuma Bahijja ta juya.. A hankali take takawa zuwa wajen, seta kalli gefe da gefe ganin babu idon wad'anda ke kanta yasa ta wuce wajen, seta dakata a bakin k'ofar office d'in nasa sannan ta kalli wani wanda ke tsaye a wajen tace "Pls Doctor na ciki?" "Yeah.." ya fad'a yana kallan ta "Pls taemaka kamin iso mana" ta fad'a tana maraeraece fuska, seya d'aga kafad'a yana wucewa ciki, wajen minti 2 se gashi ya fito yace "Ki shiga.." murmushi Bahijja tayi cikin jin dad'i kana tace "Nagode sosae.." ta fad'a tana zame takalmin k'afar ta ta shige cikin office d'in, dae_dae lokacin Rk yana tsaye gefen kujerar office d'in, da sallama ta shiga ba tare daya kalle ta ba yace "Come in" seta lumshe idanu tana jin yadda muryar tasa ke k'ara dad'i, ta k'arasa ta zube a k'asa tana fad'in "Sir barka da rana.." kamar be ji ba seda ya nemi waje ya zauna ya bud'e wani littafi sannan yace "Barka..how can i help u?" yayi maganar a had'e "Sir.. Pls zuwa nayi na rok'i alfarma" "Umhum.." yayi maganar har lokacin yana kallan littafin hannun sa, sosae taji dad'in yadda ya amsa matan, dan haka seta gyara zama tace "Sir dama Mama na ce tace a cikin malamae na samu wanda ze d'an dinga taemaka min da abinda bangane ba, shine.. Shine nace bari nazo na kar6i koda contact naka ne, idan ina da buk'atar taemako sena kira ka.." a hankali ya ajje littafin dake hannun sa ya d'aga kyawawan idanun sa ya zube su kan Bahijja, be san sanda ya basu fuska da har irin wannan raenin ze shiga tsakanin su ba, seya kwantar da kansa akan kujera hannayen sa duka biyun ya sark'e su cikin juna kana ya sanya su a ha6ar sa yana d'an juya kujerar daya ke kae, jin shiru ya sanya ta fad'in ba tare data d'ago ta kalle shi ba, dan tasan idan tace zata kalle shin wannan kwarjinin nasa da idanun nan nasa zasu sanya ta kasa fad'ar abinda tayi niyyar fad'a, koma gaba d'aya ta manta abinda zata fad'a d'in "Shine dama abinda ya.." "U shut up bloody fool.." ya fad'a cikin er d'aga murya yana sake watsa mata idanun sa, tuni ta rikice ta d'ago kamar zata yi kuka dan gaba d'aya ya gama rikita ta da wannan razananniyar muryar tasa, bata jira ya sake cewa komae ba ta mik'e jiki na rawa ta fice daga Office d'in, dogon tsaki yaja yana jin wani irin 6acin rae na taso masa, a hankali ya lumshe idanun sa yana sake kwantar da kansa kan kujerar.. Seda ta tsaya ta saeta kan ta sannan ta tura k'ofar d'akin nasu, dukan su suka kalle ta cikin mamakin ganin ta kamar a birkice kuma a firgice "Bahijja lafiya?" Ruks ta fad'a tana kallan ta, se tayi wani yak'e kafin ta nemi waje ta zauna tace "Lafiya mana me kika gani?" "A'ah babu komae" Ruks ta fad'a tana d'an ta6e baki "Dama ke muke jira muna tattaunawa ne akan yadda zamu tunkari Doctor Rk da k'udirin mu, idan yaso seya za6i d'aya duk wadda ya za6a kuma ragowar se suyi hak'uri.." a hankali ta zuro k'afafun ta daga kan gadon da take kae ta kalle su su duka sannan tace "Sam banga amfanin mutum mara kirki ba, wanda be san darajar d'an adam ba, ku kamar ma bakwa ganin abinda yake min" Ayrah ta fad'a dan yau sun gama kae ta bango, kullum cikin zancen sa suke amma sau 2 yana mata d'iban albarka basu ta6a nuna sun gani ba ko sun sani, dukkan su suka kalle ta yadda tayi maganar da alama abin na mata ciwo a rae, Jidda ta dafa cinyar Ayrah tace "K'awa ta mutumin nan fa in dae kabi k'a'idar sa toh zaka zauna lafiya, though dae he is not friendly but he is nice wallahi, baya son hayaniya kamar yadda bashi da hayaniya, daga zarar kin san halin sa fa shikenan babu wata matsala da zata sake faruwa tsakanin ku" ta6e baki Ayrah tayi dan ita dae ba taga inda za'a yabi mutumin ba, kuma ma meye had'in ta dashi da har zata tsaya sanin halin sa? Banda ma dae ita za tayi missing da wallahi ba zata sake zuwa ajin nasa ba in dae tasan shine ze d'auke su, kawae seta mik'e ta shige toilet, Jidda ta dawo da duban ta kan su Ruks tace "Yawwah ya kuke ganin za'ayi?" Bahijja ta ta6e baki "Nifa bana tunanin ze za6i wata a cikin mu wallahi, ina ganin kawae mu hak'ura mu bar abin a ran mu" tayi maganar tana fatan duk su hak'ura d'in su bar ta ita tayi yak'in ta ita kad'ae, shek'ek'e duka suka kalle ta kafin Ruks tayi k'arfin halin fad'in "Kee.. Akwae mummuna ne a cikin mu? Ko kuma dae ke kin sare, idan kin sare ne just tell us kinga yanzu yak'in ya rage tsakani na da Jidda" Bahijja ta ta6e baki kawae ba tare da tace komae ba, Jidda tace "Idan baki janye ba toh zamu ware rana ne muje duk cikin dabara mu isar da sirrin dake zuciyoyin mu" da sauri Bahijja ta kalle su, kallan nan irin na baku da hankali wanda bata san tayi musu shi d'in ba seda taga suna bin ta da kallan tuhuma sannan tayi k'ok'arin saeta kan ta..... Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 015_016 ___"Bahijja!" Ruks ta fad'a tana sake kallan ta sosae, seta gyara zaman ta sannan tace bayan ta saki wani murmurshin yak'e "Na'am, ehh haka ya kamata muyi kam.." daga haka basu sake cewa komae ba suka yi shiru se dae kowa da abinda yake sak'awa a cikin ransa. A hankali ta k'arasa bakin gadon ta chanja hijab d'in jikin ta da wani sannan ta kalle su su duka tace har lokacin fuskar ta ba yabo ba fallasa "Zan d'an je na dawo" ta fad'a tana shirin ficewa daga d'akin, mik'ewa Jidda tayi tace bayan ta d'auki mayafin ta "Muje na raka ki.." kamar tace ta barshi se kuma taga kamar hakan be dace ba dan haka seta dakata ta jira Jiddan har ta k'araso inda take suka fita tare. Ba laefi yanzu suna tafiyar suna d'an ta6a hira, hirar da se Jidda ta d'auko ta sannan Ayrah kan amsa mata har zuwa sanda Jiddan tace "Ina zamu je wae?" "Mango zan siyo.." harara Jidda ta jefa mata sannan tace "Amma shine baki fad'a min ba, toh ae mun wuce wajen masu siyarwar" "Aou mantawa nayi" ta fad'a tana dariya gami da sanya hannun ta akan bakin ta, daga haka suka juya Jidda ta kae su wajen da masu saeda fruits suke sosae, kae tsaye wajen me mango d'in suka je, Ayrah ta fad'a masa adadin data ke so, shi kuma ya fara zuba mata cikin leda. A hankali wata bak'ar had'ad'd'iyar mota ta gangara ta tsaya kusa da me siyar da mangon, su biyu ne cikin motar Rk zaune a wajen me zaman banza yana danna waya, yayin da Yaseer ke driving, kallan sa yayi sanda yaga yayi parking motar a wani waje daban, da mamaki yace "A'ah meye haka?" Yaseer yace "Fruit zan d'an siya, sun min kyau gaskiya.." "Oh god, ji wani kuma" Rk ya fad'a yana watsa masa harara, Yaseer yace "5 min pls.." ya fad'a sanda yake bud'e motar yana kuma d'aga hannun sa, Rk bece komae ba se d'aga kafad'a da yayi gami da ta6e baki lokaci d'aya yana maeda kansa kan wayar sa, wajen minti 2 da fitar Yaseer d'in, a hankali ya d'aga manyan idanun sa ya kalli wajen, acan ya hango shi tsaye wajen me siyar da mango yana ta zuba shi da me mangoron, seya samu kansa da jan tsaki gami da furta "Yaseer!!" ya fad'a yana shirin d'auke kansa idanun sa suka sauka akan fuskar ta sanda wani sassanya kuma kyakykyawan murmushi yake tashi akan fuskar ta wanda ya matuk'ar k'awata kuma ya sake fito da aenahin kyawun ta, cikin en sekonnin da basu wuce 2 ba yaji yanayin bugun zuciyar sa ya sauya wanda har be san sanda ya rintse idanun sa ba yana sanya hannun sa saetin zuciyar sa, seya maeda kansa jikin kujera yana sake lumshe idanun sa kafin a hankali ya fesar da wata iska daga bakin sa "What happen to me?" he asked him self still dae idanun sa suna a lumshe haka zalika hannun sa dafe da k'irjin sa, yafi minti 2 a haka kafin bugun numfashin sa ya fara komawa dae_dae, dae_dae lokacin kuma da Yaseer ya bud'e murfin motar ya shigo, da mamaki ya kalli Rk da har lokacin be bud'e idanun sa ba yace "Rk.. Lafiya?" se a lokacin ya shiga bud'e idanun sa dake d'auke da dogayen bak'in gashin idanu masu matuk'ar kyau sannan ya sauke su kan Yaseer yace muryar sa a d'an ciki "Babu komae.." "Sure?" seya jinjina masa kae kawae yana sake lumshe ido, shi kansa ba zece ga dalilin da yasa yaji bugun zuciyar sa ya chanja tafarar d'aya ba "Ohk.." Yaseer ya fad'a yana kunna motar ya fara driving, seda suka yi nisa da fara tafiyar sannan Yaseer ya kalli Rk kana ya maeda duban sa kan titi yace "Ina tunanin gobe zan koma Kano fa.." "Saboda?" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalle shi "Madam ta matsa wallahi, ni kuma bansan 6acin ran ta, so dole na koma a goben gaskiya" murmushi Rk yayi wanda ya sake fito da aenahin kyansa kana yace bayan yaja k'aramin tsaki "Idan ba kayi haka ba ae bazan gane kae ne ba" "Me kuma nayi?" Yaseer ya fad'a yana dariya, shiru Rk ya masa dan yasan dama da biyu yayi maganar "Mutumi na kae ma ka daure kayi auren nan wallahi.." kafin ya kae ga k'arasawa Rk yace "Bismilllahi.., pls wae kae baka gajiya da zancen nan ne? Ka dae san bazan k'ara shekarun da nayi a baya ba tare da nayi aure ba koh?" "Yawwah mutumi na yanzu kace dae na fara shiri kenan?" Yaseer ya fad'a duk da yayi mamakin jin zancen Rk d'in "Kamar haka kake so na fad'a koh? Toh ae gashi nan na fad'a maka" Rk yayi maganar cikin basarwa, tsaki Yaseer ya ja yana fad'in k'asa_k'asa "Ae seka yi ta zama" duk da ya ji shi amma bece masa komae ba ya cigaba da danna wayar sa.. .... Da sallama ya shiga cikin parlourn, Mummy dake zaune kan kujera ta taso tana fad'in "Sannu da zuwa likita, ka dawo lafiya?" murmushi yayi kana yace "Lafiya k'alau Mummy, Daddy fa?" "Be shigo ba tukunnah" seya jinjina kae kawae, can ya jiyo Mummyn na fad'in "Ka dad'e da shigowa ne?" d'an ta6e baki yayi kana yace bayan ya girgiza kae "Nop, ban wuce 1 hour ba.." "Ohk bari Muneerat ta kawo maka abinci yanzun nan" seya d'an yi shiru kad'an, baya son Mummyn ta dinga had'a harkar sa da yarinyar ballantana har suyi tunanin wani abun, se dae 'ya 'ya ce, ko yaya ya nuna baya son hakan yasan ba zata ji dad'i ba, so ko dan kulawar Mummyn a gare shi ya sanya ya dinga d'auke kae akan wasu abubuwan, dan haka bece komae ba ya wuce dinning area, ya ja kujera ya zauna bayan ya ciro wayar sa daga cikin aljihu ya fara dannawa. Wajen mintuna 10 da zaman nasa, wata madaedaeciyar budurwa er kimanin shekaru 22 ta fito daga cikin kitchen sanye cikin riga da skirt na atamfa wanda suka yi cif cif a jikin ta, se dae kasancewar haka take a tsaye yasa kayan basu wani mata kyau ba sun dae yi mata cas cas kamar a jikin ta aka d'inka, daga fuska babu laefi tana da nata kyan dae_dae misali, bak'a ce se dae ba can ba, amma saboda man da take shafawa yasa fuskar ta ta ta fito tayi haske sosae kuma take wani irin shek'i, sannan kuma doguwa ce babu laefi, kan ta babu d'an kwali se wata hula data saka ta zame ta har wajen rabin kan ta, wanda ya fito da kusan rabin kitson attach d'in dake kan ta, a hankali ta k'arasa ta ajje cooler data d'auko sannan ta koma ta kwaso ragowar kana ta dawo taja kujera ta zauna tana kallan sa cike da matsananciyar k'aunar sa tace "Sannu da zuwa Yaya na" se a lokacin ma shi yasan da wanzuwar ta a wajen, ya d'an d'aga kan sa ya kalle ta da kyawawan manyan idanun sa sannan ya d'auke, seta lumshe idanun ta tana jin idanun nasa kamar wani abu ne a cikin su wanda ya sanya bata iya jure kallan cikin k'wayar idanun sa, sosae taji dad'in yadda ya kalle tan, kafin ta dawo daga wannan kuma taji yace "Yawwah barka.." seta sake yin murmushi tana janyo plate ta fara serving nasa, Mummy da fitowar ta kenan daga d'aki ta kalli Muneerat dake zuba masa abinci cikin plate da gasken gaske, seta girgiza kae a ranta tana raya "Lallae soyayya me chanja mutum" dan kuwa tasan halin k'wuiwa irin na d'iyar ta ta, bata aekin komae cikin gida, koda abinci ne kuwa se dae a kawo mata idan an kawo kuma a zuba mata, ina ganin da da dama ma cewa zata yi a bata a baki. Plate d'in ta tura gaban sa sanda ta gama zuba komae a muhallin sa sannan ta koma kan kujerar tana fad'in "Bismilllah Yaya na" seya ajje wayar sa a gefen sa, sannan yaja plate d'in a hankali yace "Thank u" wani irin farr tayi da idanu tana jin dad'i mara misaltuwa, ko ba komae tasan tayi abin kirki tunda gashi wanda tayi dan shi d'in har godiya ya mata, zata so ace kuma wannan kwalliyar ma ya kalla yace tayi kyau da tafi kowa farin ciki, se dae tasan kafin ma ya kalle tan abu ne me wuya ballantana yace tayi kyau, wayar sa daya ajje tabi da kallo sanda ta kawo wani haske, tana jin kamar ta janyo wayar ta duba wani abu amma se dae ba zata iya ba musamman daya kasance idanun sa na wajen, se kawae ta cigaba da kallan had'ad'd'iyar wallpaper wayar tasa dake d'auke da tambarin "A" wanda ita har yanzu tayi tunanin ta fad'ad'a k'wak'walwar ta amma ta gaza gane abinda yake nufi da hakan "Uhmm Yaya na ya d'alibae?" tayi k'arfin halin fad'in hakan dan katse shirun daya wanzu a wajen na wasu mintuna dan tasan ko da zata shekara ba tace komae ba, shi shirun baze dame shi ba balle yace wani abun, d'an ta6e baki yayi gami da yamutsa fuska ta d'auka ma ba zece komae ba se kuma taji yace "Alhamdulillah, baza kiyi karatu bane?" yayi maganar sanda ya ajje spoon cikin plate d'in, bata bawa maganar daya fad'a muhimmaci ba seta kalli abincin daya keci da kallo sannan ta kalle shi sanda yake k'ok'arin mik'ewa tace "Wae har ka gama?" ta fad'a itama bayan ta mik'e tsaye cikin maraeraece fuska, sake yamutsa fuska yayi kana yace "Ehh, dama ba yunwa nake ji ba, kije kiyi karatun ki" ya fad'a yana d'aukar wayar sa, seta bishi da kallo sanda yake wucewa har ya fice daga d'akin, komawa tayi ta zauna tana jin yadda wasu k'walla suka tarar mata a ido, dae_dae lokacin Mummy ta k'araso taja kujera ta zauna tana kallan ta tace "Muneerah meya faru?" seta d'ago idanun ta ta kalli Mummyn sannan tace "Mummy kinga fa abinda yaci, kamar dan ina wajen ne fa yak'i ci da yawa fa" "Ke waye ya fad'a miki haka Muneerah?" Mummy ta fad'a tana kallan ta, seta sake maraeraece fuska sannan tace kamar zata sanya kuka "Toh Mummy se yaushe ne zamu saba, har yanzu kullum jiya i yau" ajiyar zuciya Mummy ta sauke sannan tace "Uhmm Muneerah gajen hak'uri ne dake, idan ma kun saba idan ma baku saba ba aure ne dae kin san za'a yi shi koh? Ko kuwa kin ta6a ganin Daddyn ki yayi magana 2? Sun riga sun gama magana saboda haka ki kwantar da hankalin ki, ko ba yanzu ba zaku saba nan gaba" hannu Muneerah ta saka ta sake share k'wallar idanun ta sannan tace "Da gaske Mummy?" ta fad'a kamar zata yi kuka, murmushi Mummy tayi tana jan Muneerah jikin ta tace "K'warae kuwa Munee.." se a lokacin Muneerahn tayi murmushi tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na mamaye ta, ji take kamar taje tace wa Daddyn nata idan za'a saka musu rana kada a saka da yawa, kae ita da zata iya ma da kanta za taje wajen Abban Rk d'in tayi masa maganar kar a saka ranar da yawa. ... Yana fitowa compound d'in gidan motar Daddy ta shigo gidan, seya k'arasa zuwa parking space d'in zuwa wajen motar, ya sanya hannu ya bud'e murfin motar inda Daddy ke zaune, Daddy ya fito yana murmushi yace "Ka dawo kenan Doctor?" murmushi Rk yayi kana yace "Ehh Daddy, barka da dawowa" "Yawwah" ya fad'a sanda yake mik'a masa brief case d'in hannun sa, hannu 2 Rk ya saka ya kar6a kana suka fara takawa zuwa d'akin Daddyn "Ya karatu ya kuma d'alibae?" Daddyn ya fad'a har lokacin suna tafiya "Alhamdulillah Daddy" Rk ya fad'a "Toh Allah ya taemaka" "Ameen" ya fad'a sannan suka cigaba da tafiya, seda suka shiga parlour sannan Rk ya ajje brief case d'in hannun sa kan kujera kana ya sake fad'in "Sannu da dawowa Daddy" "Yawwah.." Daddy ya fad'a yana sake jin k'aunar Rk d'in a ransa, d'aya daga cikin halayen daya sanya yake son aura masa Muneerah shine tarbiyyar sa, sosae hakan ke k'ara masa k'aemi wajen son cika wannan burin nasu shi da d'an uwan sa "Bari na wuce.." Rk ya fad'a "Tohm shikenan, idan da akwae wata matsalar seka sanar dani" Daddy ya fad'a yana bin Rk da kallo sanda yake ficewa daga cikin d'akin. .. Fitowar su kenan daga Capteria, su 3 ne a wannan karon, rana ta farko kenan data fara bin su Capteria saboda k'aryar su data musu yawa, ita kuwa ba er kowan kowa ba idan tace zata biye musu d'an kud'in da take dashi seta k'arar dashi a kwanaki k'alilan, dan haka take kama kan ta sosae, daga ita se Jidda se Ruks ne yanzun, tana sanye cikin abaya maroon colour da mayafin ta data yafa shi bayan ta saka wata kyakykyawar hula saboda kada sumar ta ta fito. Sun zo zasu gifta ta wajen wasu jerin reading chairs Jidda tace "Ko mu d'an zauna mu huta ne?" da sauri Ayrah ta girgiza kae sannan tace "A'ah ni kam na gaji" dan har ga Allah ta gaji so take ta zauna ta huta, idan da dama ma ta kwanta "Haka dae, Allah kuwa Ayrah kin fiya lalaci" Jidda ta fad'a tana kallan ta bayan ta jefa mata harara, murgud'a d'an k'aramin bakin ta tayi ba tare da tace komae ba, Ruks tace "Gaskiya dae kam, ya kamata mu huta" ganin su dae hutawar zasu yi ya sanya ta ta6e baki sannan tace "Ni dae na tafi.." ta fad'a tana yin gaba, suka bita da kallo sannan suka nemi waje suka zauna. A hankali take tafiya zuciyar ta fall cike da tunanin Umman ta, sosae take jin kewar ta musamman a kwanakin nan duk da kullum se sunyi waya, amma ta k'agu ta gan ta "Raj!!" taji an ambata daga bayan ta, wanda kiran sunan ya gama fita ne da bugun zuciyar ta, take a lokaci guda taji bugun zuciyar ta ya sauya, suna ne da zata iya kiran sa da extra ordinary one, sannan kuma tun daga wancan lokacin bata sake jin me irin sunan ba ballantana tayi tsammanin ko suna ne yazo d'aya, "ko dae shine?" ta tambayi kan ta, wannan tambayar data yiwa kanta ya sanya har bata san lokacin data juya da wani irin sauri ba tana wuwwulga kyawawan idanun ta cikin harabar makarantar, dae_dae lokacin data hango wani ya k'arasa shigewa cikin wata hamshak'iyar mota, cikin sakannin da basu wuce 5 ba motar ta bar wajen, ji tayi kamar sun tafi da duk wani kuzari da numfashin ta, ta lumshe idanun ta tana jan numfashin ta a nutse ko zata samu ya dawo dae_dae "Raj!" yanda aka fad'i sunan ya sake dawo mata cikin kwanyar ta, seta sake bud'e idanun ta tana fatan ace taga Raj d'in ta a gaban ta, toh koma dae kunnen ta ne ke mata gizo?..... Mhiz Innocent....... ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 017_018 ___A hankali ta sauke numfashi tana sake lumshe idanun ta, ganin da tayi ta tsaya ne akan hanya ya sanya ta jan k'afafun ta ta fara takawa zuwa Hostel, da k'yar ta iya k'arasawa cikin d'akin saboda yadda jikin ta yayi wani irin mugun sanyi haka zalika k'irjin ta ya mata wani irin nauyi. Ajiye littafin hannun ta tayi sannan ta haye kan gadon ta taja pillow ta kwanta tana lumshe idanun ta "Raj!" ta sake fad'a akan la66an ta, cikin lokaci k'ank'ani rayuwar su ta baya ta fara dawo mata cikin kwanya kamar wadda ake haskawa, wata irin kewa ta musamman ta shiga ratsa ta, tana jin ina ma ace ta gan shi, ina ma ta sake ganin shi a rayuwar ta ko da sau d'aya ne, ko ina ya shiga? Ina yake? Meyasa bata sakr ganin sa tun wancan lokacin ba? Se yanzu ta tsaya tayi wa kan ta wad'annan tambayoyin wanda ada k'uruciya bata bar ta tayi ba, tabbas Raj d'in wani mutum ne na musamman a rayuwar ta wanda bata tunanin har abada zata ta6a mantawa da shi, koda kuwa bata sake ganin sa ba a kafatanin rayuwar ta, ko idan ta gan shi zata gane shi? Tana zaune a haka kamar me shirya film duk wani abu daya faru a rayuwar su tana k'ok'arin tuna su, duk da wasu abubuwan da dama ta manta saboda yanayin shekarun ta a wancan lokacin har zuwa sanda Bahijja ta shigo cikin d'akin, ta kalle ta yadda take juyi daga wannan 6angaren gadon zuwa wani 6angaren "Lafiya kuwa Ayrah?" seta bud'e ido da sauri yadda ta tsorata dan sam bata san da shigowar Bahijjan ba kawae maganar ta taji, ganin ta ya sanya ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Ehh.. Yanzu kika shigo?" "Ehh yanzun nan" Bahijja ta fad'a tana zame mayafin jikin ta, Ayrah ta koma ta kwanta dan sosae take jin dad'in tunanin da take yi. *** *** *** .. Littafin ta ta d'auka ta sake karantawa sannan ta rufe, Ruks dake kusa da ita tace "Wae Ayrah gaba d'aya littafin kike k'ok'arin karancewa ne? Test ce fa ba exam ba" ta fad'a dan tun jiya data farka cikin dare taga Ayrahn na ta karatu, shiru Ayrahn ta mata har seda ta gama zuba littafan ta cikin jaka sannan tace kamar bata son yin maganar "Ae dae na gama" jinjina kae Ruks tayi sannan tace "Gaskiyane, sannu da k'ok'ari, ni kam dae ina kusa da ke" "Toh" Ayrah ta furta dan ita sam bata da k'yashi a rayuwar ta, bata k'i duk abinda ta karanta kema ta baki ki rubuta ba, se dae abin nata har da rashin wayo da ga6un ta, dan kuwa zata iya bud'e miki paper ta kiyi copying ba abinda ya dame ta, Bahijja dake saka takalmi tace "Wallahi dama ni topic d'in daya gama mana last week kawae na karanta, couz ina da tabbacin a cikin sa zeyi tambaya" dariya Jidda tayi sanda take k'ok'arin ficewa daga d'akin tace "Ashe duk gwara ni ma, cha66.." tayi maganar tana ficewa daga d'akin, suma duk se suka rankaya suka fice daga cikin d'akin zuwa class. Sanda suka je 8 ba tayi ba dan haka sun riga shi zuwa, seda suka je da wajen mintuna 5 sannan yazo, tunda suka shiga ajin ta d'auko littafin ta ta cigaba da dubawa, Ruks da Bahijja sune a gefe da gefen ta yayin da Jidda ke kusa da Ruks, tun ranar data fahimci su zaman baya kamar a jikin su yake seta k'yale su kawae ita take zaman ta a gaba, se dae wani lokacin ne se suma su zauna a gaban, musamman kuma idan za'ayi test se duk su dawo gaban ko dan ta taemaka musu saboda yadda suka fahimci yanda kwanyar ta ke ja. Cikin takun nutsuwa yayi parking motar sa a bakin ajin, a hankali ya saka hannu ya zare bluetooth d'in dake kunnen sa ya ajje shi kan d'aya kujerar sannan ya cigaba da danna wayar sa, seda 8:00 ta buga sannan ya bud'e k'ofar ya fito bayan ya d'auki wasu books dake a back seat, sanye cikin k'ananan kaya kamar koda yaushe, kayan dake matuk'ar yi masa kyau, su sake fito da zalla kuma aenahin kyan sa, cikin nutsuwa ya cigaba da takawa zuwa ajin, kafin ya shiga wad'anda zuwan su kenan suka yi wani irin sauri suka shige ajin dan kada ya riga su shiga, yana shiga kuwa gaba d'aya en ajin suka nutsu "Wow! Kamar ko yaushe dae" taji Ruks dake gefen ta ta fad'a, shiru tayi dan tasan da wanda take, ita kuwa haka kawae take gujewa kallan inda yake, saboda yadda kallan nasa ke yawan haefar mata da fad'uwar gaban data rasa dalilin sa, ita har yanzu dukan su mamaki suke bata idan ta kalli yadda dukkan su suke crushing akan abu d'aya, kuma a gaban juna zasu zauna suna kod'a shi kowacce ta kawo nata point d'in, seta ta6e baki kawae a ranta tana ayyana "Meya shafeni ni?" kafin a fara test d'in abinda be yiwa su Bahijja dad'i ba shine yadda ya tarwatsa kan en ajin ta hanyar bawa monitorn su umarni, cikin lokaci k'ank'ani kowannen su aka tarwatsa shi zuwa wani wajen, sannan ya bada minti 20 kawae kowa yayi submitting test d'in sa duk da uban tambayar da yayi musu, duk da tambayar guda 2 ce amma idan baka nutsu ka fahimce ta ba yanzun nan zaka yi kwa6a, saboda haka daga wajen mutane da dama basu wani tsaya sunyi nazari ba kawae suka shiga amsa ta, se kuma wani 6angaren da suka tsaya suka yi nazari sosae akae, cikin su ne hadda Ayrah a ciki wadda seda ta shafe wajen minti 5 tana nazarin questions d'in kafin tayi bismilllah ta fara rubutu cikin k'warewa "Time taken" ya furta a nutse bayan cika mintuna 20 d'in daya bayar, mik'ewa Monitorn nasu yayi yabi kowa ya kar6a paper sa, wasu duk suka baada yayin da wasu k'alilan basu bayar ba saboda basu gama ba, Monitorn bebi ta kansu ba ya had'a paper hannun sa yabi bayan Rk daya fice daga cikin ajin har zuwa motar sa, ya bud'e ya shige motar sannan Monitorn ya ajje masa papers d'in a front seat, dae_dae sanda yake tada motar su 3 suka fito, Ayrah se wata er ajin tasu Fateema, sannan wani su kad'ae ne basu bayar ba, Monitor ya kalle su sannan ya kalli Rk yace a hankali "Sir.. Pls wad'anda basu bayar ba!" da mamaki Rk ya kalle shi kamar ba zece komae ba se kuma yace "Saboda raeni?" da sauri ya girgiza kae lokaci d'aya yana furta "No sir, ina sauri ne ban kar6i ta sun ba saboda kada dukan mu mu rasa, Sorry sir" "Leave them, next tym zasu yi saurin baka.." yayi maganar sanda yake maeda kan sa kan driving d'in daze soma "Pls Sir, ayi musu hak'uri ba dan halin su ba" yayi d'an shiru sannan yace bayan ya fesar da iska daga bakin sa "Su wakilta mutum d'aya a kae min office" ya fad'a yana yin gaba "Thank u so much Sir" Monitorn ya fad'a yana mik'ewa tsaye zuwa bakin class d'in, daga inda take ta runtse idanun ta tana ganin kamar tun yanzu tayi failing course d'in tunda gashi ta rasa C.A, tana shirin komawa cikin ajin hannun ta akan fuskar ta tana ji kamar ta fashe da kuka ta jiyo muryar Monitorn nasu na fad'in "Ayrah.." seta dakata lokaci d'aya tana juyowa, ya kalli yanda fararen idanun ta suka sauya kala sannan yace bayan yayi murmurshi "Doctor yace a cikin wad'anda ba kuyi submitting Paper ku ba ku wakilta mutum d'aya ya kae masa" lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin dad'i na ratsa ta, seta kalli Fatima dake gefen ta itama rik'e da tata Paper a hannun ta tace tana kallan namijin da shima be bada ba, bata san sunan sa ba dan ita harkar matan ajin nasu ma bata kowa take shiga ba ballantana ta mazan ajin nasu "Gashi zaka kae masa?" ta k'are maganar tana kallan sa, Monitor ya kalle ta yace "kin san yadda za'ayi? Ki kar6i Paper su ki had'a ki kae masa" da mamaki ta kalle shi jin furucin sa kafin tace komae ya sake jinjina kae, da sauri ta girgiza kae sannan tace da sauri tun kafin ma ya sake cewa komae "A'ah ba zan iya ba.." tayi maganar da dukkan gaskiyar ta, dan a yadda take ji koda za'a ce sun rasa exam ne ba C.A ba ba zata iya zuwa wajen mutumin ba, cikin maraeraecewa Fateema tace "Don Allah Ayrah kije ki kae kin ji?" "Toh ke waya hana ki zuwa?" ta fad'i abinda take sak'awa cikin ran ta, kafin duk suce komae ta sake fad'in "Babu inda zan je ni" tayi maganar kamar zata saka kuka, hannu Monitor ya saka ya kar6i takaddun hannun su duka har ta Ayrah sannan yace "Zo muje mu kae masa" tunda taga ya kar6a se kawae ta bishi a baya kamar wata doluwa, a haka har suka k'arasa Office d'in Rk, seya kalle ta bayan sun dakata daga tafiyar yace "Kinga abinda yasa nace ki kae masa da kan ki, su Fateema sun fiya kaud'i, kuma kin san halin doctor.. kada suzo su janyo muku shiyasa nace ke kije, yanzu dae kije ki kae kada lokaci ya k'ure yace baze kar6a ba" hannu ta sanya ta kar6a fuskar ta a cunkushe, sannan ta runtse idanu tana karanto addu'ar da duk tazo bakin ta kana ta fara takawa zuwa bakin Office d'in, da sallama d'auke akan la66an ta ta shiga cikin Office d'in, ba tare data kalli kowa ba ta zube akan k'afafun ta, wani irin sassanyan k'amshi ke tashi cikin Office d'in, wanda ya had'e da k'amshin turaren sa da kuma shi kan sa na Office d'in ga kuma sanyin A.C hakan ba k'aramin k'arawa yanayin Office d'in dad'in shak'a yayi ba. Da mamaki Muneerah dake zaune kan kujera ta kalle ta, seta saka hannu ta zame k'aramin glass d'in dake fuskar ta ta cigaba da kallan ta "Malama menene zaki shigowa mutane waje without even taking excuse?" taji maganar daga gefen ta, idan kujerar da Muneerahn ke kae ta d'ago ta kalle ta toh Ayrah ma ta kalle ta, seta d'aga kae a hankali ta kalli inda yake zaune kan kujera yayi shiru hannayen sa rik'e da ha6ar sa kamar me tunani "Sir.." karo na farko kenan data ta6a yi masa magana, ita bata so ma hakan ta faru ba, so tayi har ta gama makarantar wata magana ba zata ta6a had'a ta da shi ba, idanun sa masu kaefi ya d'aga ya kalli Muneerah dake sake fad'in cikin kufula "Kamar dake nake koh?" lumshe idanun ta Ayrah tayi ba tare data juya ta kalli Muneerah ba tace "Sir test d'in mu na kawo.." tayi maganar tana mik'ewa daga zaunen da take ta ajje masa kan bench d'in dake gaban sa, jin bece komae bane ya sanya ta mik'ewa tana jin k'irjin ta na bugawa lokaci d'aya kuma tana fatan Allah yasa kada yace wani abun, ya kar6a kenan "Don't ever try dis mistake again.." ta jiyo daddad'ar muryar sa yana fad'in hakan kuma a hankali kamar wanda akawa dole, ba tare data kalle shi ba ballantana bugun zuciyar ta ya k'aru tace "In Sha Allah" tana shirin fita ta jiyo muryar Muneerah na fad'in "Kin ci sa'a yau an miki uzuri, saboda haka se ki kiyaye" ta fad'a ita a lallae dole se an gane wata ce ita a wajen Rk d'in, kallan ta kawae Ayrah tayi tana jin wani irin takaeci da haushi na musamman na zuwa suka tirnik'e ta, dan haka yanzu ma ba tace komae ba se sake d'auke kan ta da tayi, daga haka ta sanya k'afa ta fice daga Office d'in, galala Muneerah ta bita da kallo sanda ta gama ficewa daga Office d'in sannan ta dawo da duban ta kan Rk tace "Baby wannan d'alibar ka ce?" kallan Muneerah yayi kallo irin na cikin ido wanda ya sanya ta kauda kan ta gefe se dae har lokacin bata ji yace komae ba dan haka ta sake furta "Baka tunanin shirun da ka mata bayan abinda tamin kamar ze janyo min raeni ne" "Meye had'in ki da ita?" yayi maganar cikin basarwa, se tayi shiru kawae tana mamakin wannan mutumin, yaja Papers d'in data kawo ya had'a su da ragowar sannan ya mik'e yana zura wayar sa cikin aljihu yace "Zan fita" "Da wuri haka Baby? Ina zaka je?" yamutsa fuska yayi ba tare da ya bawa tambayar ta ta muhimmaci ba yace "Zaki tafi ne?" a shagwa6e ta furta "Haba haba kae kuwa Yaya na, ni fa hira nazo na taya ka" kansa ya d'an dafe dan shi yana jin kamar ciwon kae take k'ok'arin saka masa, a yayin da ita a 6angaren ta tana yin komae ne dan saboda ta burge shi, jin da tayi bece komae bane ya sanya ta fad'in "Ohk muje na raka ka" ta fad'a tana murmushi "No babu buk'ata" ya fad'a yana d'aukar key d'in motar sa yayi gaba ita kuma ta rufa masa baya zuwa wajen, ya shiga motar sa yayin da ita kuma ta shiga ta ta kowanne ya tada tasa. A hankali take takawa fuskar nan ta ta kamar wadda aka yiwa duka, se cika take tana batsewa, wayar ta ce tayi k'ara ta zaro ta daga cikin hijab d'in jikin ta sannan ta d'aga tana karawa a kunnen ta, daga can 6angaren Yah Sadeeq yace "Ayrah.." "Na'am Yah Sadeeq" ta fad'a tana d'an tura bakin ta gaba kad'an, daga can 6angaren yayi murmushi kana yace "Yau kuma waya ta6a min k'anwa ta? Ko dae wannan likitan ne?" daga inda take ta d'an yi murmushi jin yadda Yah Sadeeq d'in ya gano hakan da wuri, ko da yake hakan ba abin mamaki bane dan kusan koda yaushe k'orafin ta baya wuce akan Rk "Shi ne" ta fad'a tana sake kwa6e fuska kamar tana gaban sa "Wae ni kam meyasa doctorn nan ya takurawa k'anwa ta ne?" "Oho masa" kafin Yah Sadeeq d'in yace komae ta sake fad'in "Yah Sadeeq ina Umma?" "Umma na gida, idan na koma zan kira ki In Allah ya yadda se ku gaesa" bata san sanda wani murmushi ya su6uce mata ba, haka suka cigaba da hira da yayan nata cike da k'aunar juna. ... Ita da Jidda ne cikin Cafe d'in, mutumin ya kalle su sanda Ayrah ke fad'in "Pls kayi mana kaaji" seya jinjina kae sannan yace "Ohk, amma zan je na samo mae idan zaku jira ni" "Babu matsala.." Ayrah ta fad'a tana neman waje ta zauna, dae_dae lokacin da mutumin ke shirin fita daga wajen yayi dae_dae da lokacin daya shigo cikin madaedaecin Cafe d'in, yana sanye cikin wata kyakykyawar riga da bluen jeans wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, kamar koda yaushe yanzu ma kan sa babu komae se kwantacciyar sumar kan sa da koda yaushe kamar ana k'ara mata shek'i ne da kyau, dakatawa mutumin yayi da murmushi kan fuskar sa yana fad'in "Doctor.. doctor barka da zuwa" yayi maganar yana mik'a masa hannu, Rk ya mik'a masa hannu suka gaesa shima da wani tsadadden murmushi akan fuskar sa, Jidda data ga shigowar sa sanda ta mik'e tace "Barka da wannan lokaci Sir" "Barka" yayi maganar har lokacin hannun su na cikin na juna shi da mutumin "Bari naje pls Ayrah, me zan siyo miki?" murmushi tayi kana tace "Mango" dariya Jidda tayi k'asa k'asa sannan tace "Nima bansan meyasa na tambaya ba bayan na san ina tare da mayyar mangoro Ayrah!!" ba saurarar su yake ba kuma be damu da kallan wadda ta gaeshe shi ba amma tabbas wannan maganar ta sauka cikin kunnen sa har be san sanda yayi sauri ya d'aga kae ya kalli Jiddan ba, ita kuwa sosae hakan ya mata dad'i har da chanja tafiya ko da ta janyo hankalin sa, se dae abinda bata sani ba sam bema kalli fuskar ta ba balle akae ga kallan tafiyar ta, bega wadda take bayan ta ba saboda ita Jidda ta taso zata fita ne, kafin kuma ya maeda duban sa wajen seya jiyo mutumin nan na fad'in "Raj pls bari na d'an je na samo mae zan yi wani aeki ne, idan babu damuwa a jira ni pls" yayi maganar yana murmushi, se kawae ya d'aga masa kae yana lumshe manyan idanun sa, shi kuma yace "Toh nagode" yayi maganar yana bin bayan Jidda data fita, tunda taji sunan da mutumin nan ya ambata ta d'aga dara daran idanun ta ta kalli wanda aka kira da Raj d'in, bata san sanda ta mik'e ba har handout d'in dake kan cinyar ta ta zame, shima ita yake kalla yana so ya bar k'wak'walwar sa tayi aekin daya dace, cikin en sakannin da basu wuce 2 ba idanun su suka sark'e cikin na juna, a lokaci guda zuciyoyin su suka buga wanda har seda Rk ya d'an lumshe manyan kyawawan idanun sa, yanayi ne da be ta6a jin sa akan kowacce d'iya mace ba, wani sabon al'amari ne daya dad'e yana bashi mamaki, dukkan su se suka kaasa d'auke idanun su daga cikin na juna duk da yadda hakan ke azalzalar zuciyoyin kowannen su, sun kae tsawon minti 1 a haka kafin Ayrah tayi watsi da duk wani tsoro, wasu wasi tare da taraddadi ta watsa su gefe sannan ta tattaro jarumta kana ta d'aga yatsan ta dake rawa kamar me, ta nuna shi sannan ta bud'e bakin ta daya mata wani irin nauyi bayan ta lumshe idanun ta sanda wasu kyawawan hawaye suka zuba akan fuskar ta ta furta.... Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 019_020 "Raj!?" ta k'arashe maganar da sigar tambaya, lumshe nasa idanun yayi daga cikin nata yana jin yadda zuciyar sa ke azalzalar sa na k'ara k'aemi, cigaba tayi da kallan sa har lokacin bugun zuciyar ta be koma dae_dae ba jira take kawae ta tabbatar, taji daga bakin sa cewar da gaske shine Raj, a hankali ya jinjina kan sa sannan da muryar sa wadda ta d'an shak'e shima saboda tsananin mamaki yace k'asa k'asa, wanda idan ba dan babu hayaniya a wajen ba da ko ita da take a cikin wajen ba zata ji ba "Ayrah!!?" seta shiga jinjina kae da sauri wasu hawaye na cigaba da ambaliya akan kuncin ta sannan lokaci guda kuma ta saki wani murmushi duk da har lokacin bata dena kukan ba, ta kaasa daurewa, ta kaasa cijewa, har izuwa lokacin wani irin azalzala zuciyar ta ke yi tana wani irin zillo dan haka cikin k'ank'anin lokaci da kuma sauri ta k'arasa ta rungume shi lokaci guda tana runtse idanun ta ko zata ji sauk'i daga abinda take ji a cikin zuciyar ta, k'irjin ta ya cigaba da bugawa da sauri da sauri kamar wadda tayi gudu, kamar wani soko ya tsaya kawae bayan sauke wata doguwar ajiyar zuciya, yana jin yadda ta rik'e shi sosae da alama tsananin farin ciki ne ya sanya ta hakan, wani sassanyan murmurshi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa sannan akan la66an sa ya furta "Har yanzu dae bata chanja ba" hannun sa ya saka ya zame ta daga jikin sa sanda take kuka me d'an sauti, a hankali ya k'arasa ya zaunar da ita kan kujerar wajen sannan ya saki hannun ta a ransa yana furta "Astagfirullah" a kunnen ta abinda ya fad'a d'in ya sauka duk kuma se taji wata matsananciyar kunya ta kama ta, ta kaasa controlling kan ta a lokacin, ta rasa abinda za tayi taji sauk'i, farin ciki da kuma mamaki gami da son tabbatar da abinda ta gani ne ya sanya ta rungume shi ba tare da wani tunani ba, yana tsugunne akan k'afafun sa daga k'asan inda take yana cigaba da kallan kyakykyawar fuskar ta, shi kan sa har ya zuwa lokacin ya kasa dena mamakin shin da gaske Ayrah ce? wannan d'in Ayrahn sa ce? Dae_dae lokacin ta d'ago jajayen idanun ta ta sauke su a kan sa farar fuskar nan tayi jawur haka zalika a d'an shagwa6e ta kalle shi, be san sanda wani murmushi ya su6uce masa ba, babu shakka ita d'in ce, kuma har yanzu halayen ta na nan "Da gaske Raj d'ina ne kae?" ta sake tambaya dan har lokacin tana tantama ne, musamman yadda tasan Raj d'in ta basu da hali, amma wannan tana ganin sa ne mutum me kud'i, a yadda ma taji ana kiran sa kamar likita ne in dae ba tayi mistake ba, idanun sa ya kashe mata wanda hakan ya sanya ta saurin kauda nata idon tana jin wani irin bak'on al'amari da tunda take bata ta6a jin sa akan kowanne d'a namiji ba, yanayin da take ji a yanzun wanda ke tafiya da dukkan wani bugun numfashin ta "Raj Kabeer" yayi maganar yana mik'ewa ya zauna gefen ta dan ya sake tabbatar mata da shi d'in ne ba wani ba, a hankali ta sake lumshe idanun ta tana jin wani irin dad'i na cigaba da ratsa ta, ita kam yau wace irin rana ce me muhimmaci a wajen ta? Wace irin ranar farin ciki ce a gare ta wadda a cikin ta taga Raj, yau gata ga Raj d'in ta bayan tsawon wasu shekaru? "Meyasa baku sake zuwa gidan mu ba?" tayi maganar tana langa6ar da kae gami da kallan sa, se dae a wannan karon bata kalli k'wayar idanun sa ba, kafin ya kae ga cewa komae me Cafe d'in yayi sallama ya shigo wajen, da mamaki ya kalli Rk dake zaune kujera d'aya da wata 'ya mace, abin ya matuk'ar bashi mamaki har hakan seda ya bayyana akan fuskar sa amma ya maaze yace "Doctor!!" dukan su suka kalle shi dan sam basu san da shigowar sa ba saboda yadda suka shagala da son jin abubuwa da dama daga kowannen su "Pls jira ni a waje!!" Rk ya fad'a bayan ya d'an kalli Mutumin, cike da mamakin dae ya furta "Ohk.." sannan yayi waje ya nemi waje ya zauna har lokacin yana cigaba da mamakin Rk d'in, kamar bashi ba.. "Bansani ba, nima bansan dalili ba" yayi maganar a ransa yana zurfafa tunani ko ze gano dalilin da yasa basu je gidan su Ayrahn ba amma ya kaasa, ita tunda ta gano shine Raj duk wannan tsoron nasa da take ji se taji kamar ya tafi, gaba d'aya ma ta manta shi a matsayin Rk kawae tana masa kallan Raj ne "Kullum ina tunanin ka, amma baka ta6a zuwa waje na ba" tayi maganar kamar zata saka kuka, d'an shiru yayi yana cigaba da kallan ta sannan yace bayan ya lumshe idanun sa "Ban san a ina zan same ki ba Ayrah, ki min uzuri pls.." yana gama maganar aka shiga kiran sallah a masallaci, dan haka dukan su suka yi shiru har zuwa sanda aka idar da kiran Sallahr sannan suka mik'e kusan a tare, Rk ya kalle ta sannan ya mik'a mata wayar sa daya fito da ita daga cikin aljihu yace "Samun contact naki" babu musu ta kar6i tsaleliyar tsadaddiyar wayar tasa ta sanya number ta a ciki sannan ta mik'a masa a ranta tana jin farin ciki mara misaltuwa, daga yanayin yadda ta fahimta abubuwa da dama sun chanjawa Raj d'in nata, kamar bashi ne Raj d'in da ba, kamar an chanja shi ne da wani sabo, ko da yake ba abin mamaki bane komae ikon Allah ne, da farko sune a sama yanzu kuma Raj d'in se dae ma shi ya taemaki wasu ba dae a taemaka masa ba, babu abinda Allah baya iya yi, yadda tayi shiru kamar me tunani ya bashi damar cigaba da k'arewa kyakykyawar fuskar ta kallo yana cigaba da karanto abubuwa da dama "Muje koh?" yayi maganar a hankali kamar me rad'a, seta d'aga kae ta kalle shi kana ta lumshe idanun ta a lokaci guda tana bud'e su, itace ta fara yin gaba sannan yabi bayan ta har suka fito, me Cafe d'in nan ya mik'e yana kallan sa yace "Doctor zaka wuce ne?" "Yeah" ya fad'a a gajarce "Tohm shikenan, Allah ya tsare" ya fad'a yana d'an satar kallan Ayrah yana so yaga wace me sa'ar ce wannan da Doctor d'in da kan sa yake kula ta "Ameen" ya fad'a yana wucewa zuwa wajen motar sa Ayrah na binsa har zuwa sanda ya bud'e murfin gaba sannan ya juyo ya kalle ta, se yaga a yanzu da suka fito haske sosae ma kamar tafi kyau, d'an guntun murmushi ya wanzu a gefen bakin sa sannan yace "I will call u Uhmm?" ya k'arashe maganar yana rufe idanun sa kad'an sannan ya bud'e, jinjina kae tayi ba tare da tace komae ba, haka kawae take jin babu dad'i har cikin ran ta, ji take ina ma su kasance a haka har abada, gefe guda kuma tana ganin kamar idan ya tafi d'in za'a sake maemaeta wancan karon, wato baze sake dawowa ba se bayan wasu shekaru, ko kuma yana matsawa daga wajen zata farka ne daga bacci taga duk abinda ya faru d'in mafarki ne ba gaske ba, haka dae ta kawar da duk wad'annan kawae ta jinjina masa kae sanda yake shigewa cikin motar, ta cigaba da tsayuwa har zuwa sanda yaja motar ya bar wajen yana cigaba da kallan ta, itama shi d'in take kalla. A hankali ta sauke wata ajiyar zuciya sanda ya 6acewa ganin ta, seta shiga jan k'afar ta data mata wani nauyi ta shiga takawa tana cigaba da tunanin Raj d'in, tana tuna Raj d'in da daga farko take masa kallan mutum mara kirki, mugu kuma mara tausayi, mutumin da mazan ajin su kaff ba taga wanda baya tsoron sa ba ballantana kuma akae ga mata, matan dake rububin sa kamar me, se gashi a rana d'aya a kuma lokaci d'aya hakan ya juye zuwa wani sabon al'amari, daga yadda zuciyar ta ke cigaba da harbawa tana tunanin Rk d'in ta fahimci akwae wani gagarumin abu, se dae ta gaza gane menene shi?. Cikin farin cikin daya gaza 6oyuwa akan fuskar ta ta shiga d'akin nasu, dukkan su suka bita da kallo, sabon abu ne da ba kasafae suka saba ganin sa akan fuskar ta ba, abu ne ma da zasu iya cewa in dae ba da Yah Sadeeq, Umman ta ko Abban ta take waya ba basa ganin irin wannan annurin akan fuskar ta, se dae na yau ma ya shallake wad'ancan d'in, dan kuwa tana shigowa ta jefar da Handout d'in hannun ta sannan ta kwanta akan gado tana sakin wani k'awataccen murmushi gami da lumshe idanu, da mamaki Jidda da Ruks suka kalli junan su, se kuma cikin k'arfin hali Ruks ta furta "Ayrah lafiya kuwa?" da sauri ta bud'e idanun ta dan gaba d'aya ma ta manta ba ita kad'ae ce cikin d'akin ba "Eh. Ehh" ta fad'a tana mik'ewa zuwa toilet, suka sake bin ta da kallo sanda ta shige toilet d'in "Ikon Allah" suka had'a baki wajen fad'ar hakan, babu dad'ewa ta fito, Jidda ta dube ta tace "Ga mangoron ki nan cikin leda" "Bash shi kawae, zuwa da safe zan sha" tayi maganar tana janyo hijab dan gabatar da Sallah "Toh lallae akwae damuwa" Jidda ta fad'a tana bin ta da kallo sanda take k'ok'arin tada Sallahr.. Wajen k'arfe 9pm ne na daren ranar tana kwance kan gadon ta, tun d'azu take expecting kiran sa amma kuma tana fatan kafin ya kira ace su Jidda sunyi bacci, se dae ba taga alama ba dan kuwa hirar su suke kamar yadda suka saba kullum se sunyi ta kamar farilla, se juyi take kawae akan gadon tana tuna kyakykyawar fuskar sa, ada sanda yake a Doctor Rk bata ta6a tsayawa ta k'are masa kallo ba ballantana har ta gano wannan kyan na musamman da matan ajin nasu kan kod'a shi akan sa ba, se yau ta kalle shi ta tabbatar da hakan, ta kuma ga zalla kuma aenahin kyau daga Raj d'in. .. Sanda ya koma gida kae tsaye d'akin sa ya wuce yau ko sashen Mummy be je ba, dan so yake kawae ya gama abinda yake ya kira ta yaji abubuwa da dama daga wajen ta, toilet ya fad'a ya watsa ruwa a jikin sa sannan ya fito ya shirya cikin wata brown d'in had'ad'd'iyar jallabiyya, ya zauna yayi karatun qur'an kamar yadda ya saba sannan yayi addu'o'i ya mik'e daga kan abin sallah, yana shirin ninkewa yaji ana knocking k'afar d'akin, d'an tsaki yaja sam be san wani ya kula da shigowar sa cikin gidan ba, kamar ba zeje ya bud'e ba se kuma ya ajje daddumar kan gado sannan ya fito parlourn ya k'arasa ya bud'e k'ofar, kawae seta sanya kae cikin d'akin ta shigo hannun ta d'auke da warmers d'in abinci guda 2 ta ajje a tsakiyar parlourn, sanye take cikin doguwar rigar shadda wadda tasha aeki ta fito tayi kyau da ita, fuskar nan kamar koda yaushe ta k'ara fari, tsaki ne ya su6uce masa akan bakin sa yana lumshe ido, ya akae tasan ya shigo gidan? "Baby yau baka shigo kaci abinci ba, yasa nace bari na kawo maka d'aki, ina fatan ban yi laefi ba?" tayi maganar tana matsowa kusa dashi, bece komae ba ya k'arasa ya zauna kan kujera sannan yace har lokacin be kalle ta ba "Sannun ki" seta saki murmushi tana dawowa itama ta zauna kan kujera tana shak'ar k'amshin turaren jikin sa daya cakud'e dana sassanyan k'amshin sabulun sa, ko second 5 ba tayi kan kujerar ba ta zame zuwa k'asa tana fad'in "Bari nayi serving naka" shi bema jita ba dan gaba d'aya hankalin sa ya tafi kan Ayrah ne, tunda ya baro makarantar ya kasa dena tuno kyakykyawar fuskar ta, gaba d'aya ta chanja, duk da dama tun tana yarinya kyakykyawa ce amma yanzu ta k'ara wani shahararren kyau kamar ita tayi kan ta, se dae har yanzu halin ta na nan, ga6untar nan da shagwa6ar nan har yanzu babu abinda ya ragu, tilas abinda ya tuna d'in ya sanya shi sakin sassanyan murmushi yana gyara zaman sa kan kujerar da yake, Muneerah data d'aga kae ta kalle shi taga murmushin da yayi, abinda yake da tsada a wajen sa, se gashi yau kusan zata iya cewa babu dalili yayi shi, seta samu kan ta da gyara zaman ta tana murmushi dan ita ta d'auka da ita yake "Yaya Daddy ya maka magana kuwa?" ta katse masa tunanin tana fatan Daddyn ya masa magana kuma ya kar6i zancen hannu bibbiyu, da mamaki ya d'an kalle ta sannan ya d'auke kae "Magana? Anya kuwa!" ya fad'a cikin er basarwa, seta yamutsa fuska sannan tace "Ohk toh ka sauko kaci abincin mana" ta fad'a tana cigaba da satar kallan sa ganin da tayi yanzu babu wannan murmushin akan fuskar ta sa, iska ya furzar daga bakin sa dan shi kam kwata kwata baya jin wata yunwa, toh wata ma yunwa zeji bayan gaba d'aya hankalin sa da tunanin sa na wajen Ayrah ne "Ban jin yunwa fa" ya fad'a yana zuba mata idanun sa, cikin er rawar murya ta furta "Haba mana Baby, pls kaci kada ka kwana da yunwa!" ta fad'a cike da kulawa kamar itace zata kwana da yunwar bashi ba, baya son dogon zance kuma ya k'agu ta fita dan yana jin idan har ta k'ara wasu mintuna bata fita ba toh ze tashi ne ya bar mata d'akin ita d'aya, dan haka ya furta "Ohk.. zaki iya tafiya, se da safe.." kallan sa ta cigaba dayi dan ita kam sam bata gajiya da kallan sa, jin shiru ya sanya shi sake fad'in "Ko na bar miki d'akin ne?" yayi maganar in a serious tune, da sauri ta mik'e sannan tace "Ohk bye luv, kayi bacci lafiya.." ta fad'a tana cigaba da kallan sa, ba tare daya kalle ta ba ya furta "Ohk" ya k'arasa maganar yana janyo wayar sa dake gefen sa, babu yadda ta iya haka ta fice daga d'akin zuciyar ta a cunkushe, ita ta k'agu kawae ayi auren nan kowa ma ya huta. Number ta ta ya lalubo ya danna kira, a 6angaren ta tana kwance kan gadon ta hannun ta rik'e da wayar ta ta tana jiran kiran sa tun d'azun, ganin kira da wata sabuwar number ya sanya ta tashi zaune da sauri tana kallan jerin gwanon numbobin dake shimfid'e reras akan wayar ta ta, kamar yadda yake special haka number sa ma take special, haka kawae taji a jikin ta shi d'in ne dan haka ta sake kallan gadon su Jidda taga duk bacci suke sannan ta d'aga tana karawa a kunnen ta, kafin yace komae tace bayan ta tura bakin ta daga inda take "Se yanzu ma zaka kira?" murmushi yayi daga inda yake yana kishingid'a a inda yake kwance sannan yace "Am sorry.." "Naqi ni dae, Allah kuwa tun d'azu fa nake jira ka kira" wani murmushin ya sake yi mara sauti yana karanto zallahr k'uruciyar dake tattare cikin maganar ta, da alama ko soyayya za'ayi da ita ba zata zama cikin mak'aryata ba, cikin k'asa da murya ya furta "Amin afuwa Uhmm? Raj ne fa" ya fad'a da er tsokana a maganar sa, se tayi murmushi kawae "Ina Umma? ina Abba? Ina Yah Sadeeq?" yayi maganar kamar ba Rk ba, seta sake gyara zama sannan tace "Alhamdulillah kowa lafiya k'alau, ina Abbun ku" "Abbu yana lafiya.." "Raj!" ta fad'a dan ta k'agu ta masa tambayar data tsaya mata arae sosae "Na'am" ya fad'a a nutse "Kae likita ne?" murmushi yayi daga inda yake sannan yace bayan ya d'an lumshe idanun sa kad'an "Yeah! likita ne, ki gyara zama na baki labarin rayuwa ta tun bayan rabuwar mu" kamar tana kusa dashi ta shiga gyara zama, dae_dae lokacin da Bahijja ta farka daga bacci saboda wani fitsari daya matso ta, ta kalli Ayrah dake zaune kan gadon ta sannan ta furta "Ayrah" cike da mamakin ganin ta, da sauri Ayrahn ta juyo tana kallan ta, se dae ba tace komae ba har Bahijjan ta shige toilet d'in, babu dad'ewa ta fito memakon ta nemi waje ta kwanta seta zauna tana cigaba da kallan Ayrah, haushi ya kama Ayrah ta had'e face d'in ta tsaff, sannan cikin had'e ran dae ta furta "Gobe zamu yi wayar" bata jira yace komae ba ta katse wayar sannan ta juya ta kwanta tana jin kamar ta tashi ta rufe Bahijja ta duka, cigaba da zama Bahijjan tayi dan so take ta gane da wanda take waya saboda abu ne da basu ta6a gani ba a wajen Ayrahn tunda tazo ba, kamar wadda aka tsikara ta janyo wayar data wulla gefe ta lalubo number Yah Sadeeq ta danna kira, se dae har ta tsinke be d'aga ba, ta sake kira nan ma dae be d'aga ba, a ranta kawae ta bada cewar may be ko bacci yake shiyasa be d'aga ba, duk da dae ta saba kiran sa a irin wannan lokacin kuma ya d'aga amma jiki da jini, k'ilan yau yayi wani aekin ne me wuya yasa yayi bacci da wuri, haka ta koma ta shiga lalubo number Abba.. se wata zuciyar ta zuga ta akan labarin baze musu armashi ta waya ba, kawae seta ajiye wayar tana murmushi a ranta tana sak'a gwara ta bari idan ta koma gida gata gasu Abban ta fad'a musu wannan babban albishir na cewar taga Raj, tasan suma za suyi farin ciki matuk'a k'ilan ma su fita farin cikin ko dan sanin da tayi iyayen nata na son farin cikin ta fiye da nasu.... Mhiz Innocent......✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 021_022 ___Bata dad'e da kwanciyar ba taji wani bacci na sakad'ar ta, se dae har lokacin bata hak'ura ba ta sake juyawa ta kalli inda Bahijja ke zaune tun d'azun, ga mamakin ta a wannan karon ma seta sake ganin ta zaunen dae tana danna waya, bata san sanda wani tsaki ya su6uce mata ba, se kawae ta hak'ura ta lumshe idanun ta amma mamaki ya cika zuciyar ta na Bahijjan, babu 6ata lokaci kuwa wani daddad'an barci me cike mafarkan Rk ya kwashe ta, ba ita ta farka ba se asuba. Yau ma kamar kullum da wuri suka gama shiryawa kasancewar ranar Monday ce, Monday d'in data kasance daga ita seta exam d'in da zasu fara, haka kawae taji tana jin haushin Bahijja amma kuma data tuna za tayi tozali ne da Rk se wani murmushi ya su6uce mata, a wannan karon Jidda ce kawae ta lura da murmushin wanda tun jiya ta lura da sauyawar Ayrahn, ta kasa hak'uri seda ta kalle ta tace "Ayrah wae meya faru naga daga jiya zuwa yau yanayin ki ya chanja?" d'an kallan ta tayi sanda take saka wani littafi cikin jaka sannan ta d'an ta6e baki kamar wadda ta gaji kana tace "Ni fa ba komae nace" "Haka kike ta fad'a tun jiya, Allah yasa haka ne" Jidda ta fad'a tana cigaba da nazarin ta, ba tace komae ba se d'an tura bakin ta da tayi tana k'arasa shirya kayan jakar ta, a ran ta se k'una k'uni take akan takura mata da suka yi tun jiyan. .. Tunda suka zauna jin su kawae take suna hira amma bama ta jin abinda suke cewa ballantana ta fahimta, gaba d'aya hankalin ta ya karkata ne ga son ganin ya shigo cikin ajin, ba'a k'ara minti 1 ba kuwa se gashi ya shigo cikin ajin dae_dae lokacin da ilahirin ajin ya d'auki shiru, lumshe idanun ta tayi tana shak'ar k'amshin sassanyan turaren sa me dad'in gaske sannan ta bud'e tana maeda duban ta kan fuskar sa da taga ta k'ara kyau fiye da jiya, se kawae ta shagala da kallan sa, yau d'in duka ya juye mata ya sake komawa Doctor Rk d'in sa babu fara'a yana yin komae ne cikin tsare gida, yau karon farko taji yanayin da yake d'in ya burge ta, ta san da yana sakin fuska kuma matan da za suce suna son sa se sun fi na yanzu yawa, tana jin sa ya fara magana cikin nutsuwa k'warewa da kuma takatsantsan amma sam bata fahimtar abinda yake fad'a d'in, kawae dae ta san magana yake amma ita bin sa kawae take da kallo kamar wata doluwa tana jin kamar ta had'iye shi amma duk bata san dalili ba, wayar ta dake rik'e a hannun ta ce tayi vibrate daga hannun ta, ta d'an dakata tana jin kamar ta share wayar se kuma tayi k'asa da kan ta ta duba wayar, d'an k'aramin sak'o ya bayyana akan wayar, seta shiga da sauri ta shiga karantawa ganin daga number da yake "Kallan fa?" shine abinda ke rubuce cikin message d'in daga number Rk, a'ah mamaki ne ya kamata har bata san sanda ta d'aga kae ta kalle shi ba, gashi dae anan lecturing d'in sa yake hankali kwance, toh kenan yaushe ya turo mata da message d'in? Toh yaushe ma ya gan ta tana kallan nasa, dan dae tunda ta zauna ba taga idanun sa akan kowa ba ballantana tace ya gan ta, a hankali ta sake maemaeta message d'in, se ta kae hannun ta ta rufe fuskar ta tana murmushi tuna duk kallan data masa ashe yana ganin ta? Lallae shi d'in na musamman ne "Ke meye haka wae?" Bahijja da tun d'azu take lura da duk wani motsin Ayrahn ta fad'a k'asa k'asa, da sauri Ayrah ta kalle ta ba tare da tace komae ba ta d'auke kae "Anya kuwa wannan yarinyar?" Bahijja ta fad'a a k'asan ran ta cike da mamaki, ita dae Ayrah bata sake bi ta kanta ba ta koma maeda hankali kan karatun da yake koya musu, amma duk iya k'ok'arin ta na ganin ta fahimta d'in ta kaasa, se kace wadda aka sanyawa hannu, a haka dae har ya gama lectures d'in baza tace ga abinda ta d'auka ba. ... Sanda suka koma Hostel bata lura da message d'in sa ba har seda ta zauna sannan taga message d'in nasa, da sauri ta shiga message d'in tana jin zuciyar ta na wani d'an bugawa a hankali kamar me jin tsoro "Nan gaba da face mask zan dinga shiga class, idan ba haka ba wataran za'a neme ni a rasa kin cinyewa su Abbu ni" komawa tayi ta kwanta kan gadon ta tana sakin wata dariya gami da rufe fuskar ta, ashe dae duk yana sane da ita duk kallan da take bin sa da shi yana gani, ita kan ta ta rasa gane abinda ya shiga kan ta ta kasa d'auke idanun ta daga kan sa, tana ji kuma kamar idan ta dena kallan sa zata bud'e ido taga baya nan, mik'ewa tayi ta fita daga cikin d'akin dan lokacin duk su Jidda suna ciki, suka bita da kallo kowacce da abinda take sak'awa a ran ta, amma abinda yafi damun kowaccen su shine chanjawar ta ta cikin lokaci k'ank'ani. .. Gyara zaman sa yayi kan kujerar da yake zaune kana a hankali ya furta "Kin wuni lafiya?" seta lumshe idanun ta sannan tace "Ehh.." murmushi yayi bayan ya d'an yi jimm kad'an yace "Ina fatan bakya fita daga cikin makarantar nan?" seta d'an bud'e manyan idanun ta kamar tana gaban sa, sosae yadda ta bud'e idanun yayi mata kyau, sannan ta rufe bakin ta tace a hankali "Ta66, ae na yiwa Yah Sadeeq alk'awarin bazan ta6a fita ba" ta fad'a a sakarce, yayi murmushi yana sake gyara zama muryar ta na masa wani irin dad'i yace "Dats my Ayrah" itama murmushin tayi sannan ta dakata sanda yake furta "Next week exam Uhmm?" kamar tana gaban sa ta jinjina kae kawae, shi kuma kamar yaga abinda tayi d'in yace "Idan anyi hutu In Sha Allah zan zo, may be ma har da su Abbu" yayi maganar a nutse, hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba tana murmushi tace "Buhh baka bani labarin ba" ta fad'a tana tura bakin ta gaba, iska ya d'an fesar daga bakin sa sannan yace "Ohh am sorry.." yayi maganar yana d'an dakatawa, yana tunanin tsayin maganar da zeyi, ya san tabbas ze dad'e yana yin ta abinda ya tsana kenan, dan haka ya janyo rubber water ya tsiyaya cikin tambulan ya sha, ya d'an sauke numfashi a nutse sannan ya d'ora da "Tun bayan rabuwar mu, Allah ya bud'ewa Abbu sosae, harkokin da yake yi sosae suka samu kar6uwa a wajen mutane, ban san meyasa tun bayan rabuwar mu daga mu har ku babu wanda ya sake waewayar wani ba, bansani ba, abinda kawae na sani na sha tambayar su Abbu ku amma bana samun cikakkiyar amsa wadda zan kama daga wajen sa, tun ina tambayar sa har nazo na dena tambayar sa, se dae har lokacin kina nan manne a rae na, ina jin ki ne acan cikin zuciya ta wanda hakan ne yasa na kasa manta ki a duk tsayin shekarun nan, a cikin wannan lokacin ne na gama secondary school kullum arzik'in Abbu yana yin gaba, dan haka dana tashi yin University ba'a nan nayi ta ba, sena tafi can Cyprus na karanci Medicine, yanzu haka ni cikakken likita ne, muna zaune anan cikin garin Kano saboda harkokin Abbu da suka cigaba, yanzu haka ina da asibiti na kae na wanda shima Abbun ne ya bud'e min, abinda ya kawo ni garin nan kuwa, sanadin k'anin mahaefi na ne da nazo sanda ze bud'e wani Company, tunda nazo kuma Abbu yace kar na zauna haka nan shi ya nemar min wannan lecturing d'in cikin makarantar nan duk da ni ba za6i na bane, da son raena ne aekin da nake kawae ya ishe ni, toh dae dan farin cikin Abbun yasa na fara lecturing d'in, se dae yanzu maganar da nake miki tuni Daddy (k'anin Abbu) ya gama bud'e Companyn komae ya kammala, dan haka ina saka ran ni kam daga wannan semester na gama koyarwa a makarantar nan... And.. ina me tabbatar miki In Sha Allah duk sanda muka had'u zan baki labarin a nutse" ya k'arasa maganar yana sauke wani gauron numfashi lokaci guda kuma yana 6alle murfin gorar ruwan daya ajje ya shanye tass sannan ya ajje ta yana sauke numfashi, dariya ya bata daga inda take zaune jin yadda yake sauke numfashi kamar wanda yayi wani aekin wahala, se dae kuma a ran ta tana cigaba da mamakin rayuwar Rk d'in, lallae Allah abin godiya ne da kuma d'aukaka, dan kuwa shine me yin yadda yaso a kuma lokacin daya ga dama "Uhmm, fad'a min kad'an daga naki kafin mu had'u" sauke numfashi Ayrah tayi sannan a hankali ta shiga sanar dashi makarantar da tayi da er gwagwarmayar da tasha har zuwa yanzun, duk da ba wasu shekaru ne da ita na azo a gani ba, ga kuma ga6un ta dake damun ta, amma duk yadda take ganin Raj d'in take kuma jin sa a jikin ta bata sanar dashi abubuwa da dama daga rayuwar su ba wanda take ganin kamar sirrin su ne wannan da ba kowa ya kamata ya sani ba, shiru Rk yayi yana nazarin maganganun Ayrah a ran sa yana sake tsarkake sunan Allah "Ikon Allah" kuwa ya maemaeta yafi sau nawa "Akwae wata magana dana ke so muyi, amma kafin nan ina so ki gama exam kafin ki koma gida.." "Wace maganar toh?" ta fad'a kamar za tayi kuka, murmushi me sauti yayi sannan yace "Ae nace se kin gama exam tukunnah" shiru tayi tana tuna yanayin Rk d'in a cikin aji da kuma yanzun kamar bashi bane, kamar mutum biyu ne masu kama d'aya wanda wancan da yake shigar musu aji daban shi kuma wannan da suke waya daban "Promise?" ta fad'a tana d'aga yatsan hannun ta kamar yana gaban ta "Yeah.." "Ohk". Wayar sa da tayi k'ara bayan ajiye wayar Ayrah yabi da kallo, ji yayi kamar kar ya d'aga dan a yanzun yana so ne ya dinga samun lokacin daze zauna kawae ya dinga hasaso kyakykyawar fuskar ta, kallan wayar yayi dan ganin me kiran nasa, seya kae hannu ya d'auki wayar ganin Daddy ne ke kiran, ya kae kunnen sa da sallama d'auke a bakin sa "Likita kana ina ne?" "Ina d'aki" yayi maganar cikin girmamawa "Ohk ka same ni a d'aki na idan babu abinda kake" babu musu ya amsa da "toh" sannan ya mik'e bayan ya jefa wayar a aljihun sa ya zura takalmi ya fito daga d'akin nasa cikin nutsuwa. Kae tsaye parlourn Daddyn ya wuce, a hankali ya zura kan sa ciki yanzun ma da sallama a bakin sa cikin nutsatsiyar muryar sa, amsawa Daddy yayi yana kallan sa lokacin da yake k'ok'arin zama a k'asa "Tashi ka zauna akan kujera magana nake so muyi ae" seya d'an yi murmushin nan nasa me tsada wanda ke sake fito da aenahin tsagwaron kyawun sa ya zame akan kyakykyawan Carpet d'in dake shimfid'e a k'asan d'akin yace "Daddy nan ma ya isa" murmushi Daddy yayi a ransa yana sake jaddadawa kan sa lallae abinda suka yanke ba suyi laefi ba "Amm yaushe zaku yi hutu ne?" seda ya d'an yi shiru sannan yace "Ina tunanin baza mu wuce 1 month ba" "Toh Allah ya taemaka, me kake shirya mana zuwa lokacin?" yamutse fuska yayi dan shi sam bema fahimci maganar Daddyn ba dan haka ya furta abinda ke ran sa "Daddy ina ganin zan ajiye lecturing d'in nan gaskiya am tired" ya fad'a dan da gasken ya gaji da lecturing d'in musamman daya kasance dama ba za6in sa bane, ga kuma muhimmiyar maganar da yake so daya koma yayi wa Abbun magana akae, wadda yake had'e da albishir d'in daze fad'a musu su duka cewar bayan tsawon shekarun nan ya had'u da Ayrah, wanda hakan na nufin Abbu ze had'u da Abba, may be ma abotar su ta da ta dawo sabuwa duk da be san abinda yasa kowa yayi watsi da d'an uwan sa ba "Haba haba dae Raj ka gaji kuma?" jinjina kae yayi ba tare daya kalli Daddy ba "Toh ya za kayi da Abbun ka kuma?" Daddy ya tambaya yana kallan sa "Zan same shi da maganar In Sha Allah" "Toh hakan ma yayi, seka maeda hankalin ka waje guda kenan, Allah ya taemaka.. Ameen" shiru ne ya biyo baya Daddy na tunanin ta inda ze farawa Rk maganar se can dae yayi k'arfin halin fad'in "Kana jina koh?" "Ehh.." Rk ya fad'a, kafin Daddy ya kae ga cewa komae wayar sa ta shiga ruri, seya janyo wayar yana kallan me kiran, da sauri ya kalli Rk yace "Raj je ka, za muyi maganar In Sha Allah, zan yi waya ne yanzun" jinjina kae kawae yayi ba tare da yace komae ba ya mik'e ya fice daga d'akin. ... A d'aya 6angaren kuwa Umma ce ta fito daga d'akin ta, dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ke tsaye bakin k'ofar d'akin sa hannun sa dafe da k'ofar d'akin yana sauke numfashi kamar wanda yayi tsere, da sauri Umma ta k'arasa tana kallan sa "Sadeeq lafiya kuwa?" tayi maganar tana rik'o shi "Haki kake?" ta fad'a sanda ta gama d'ago shi tana kallan fuskar sa, da sauri ya k'ak'alo murmushi ya wanzar a fuskar sa dan bega sanda ta fito ba se maganar ta kawae yaji, sannan yace bayan ya ida mik'ewa tsaye "A'ah Umma me kika gani? Kawae gajiya ce" ya fad'a cikin k'arfin hali, seta saki ajiyar zuciya sannan tace "Toh jeka kwanta ka huta haka nan Uhmm?" jinjina kae yayi kawae yana juyawa ya koma cikin d'akin a hankali, ya baje kan gado yana jin yadda k'irjin sa ke masa wani irin zafi kamar ze rabu da jikin sa. Komawa Umma tayi ta zauna tana d'ora hannun ta akan kuncin ta, lamarin duniyar nan sosae yake bata tsoro musamman a en kwanakin nan da abinda zasu ci yake gagarar su, dae_dae lokacin da Abba yayi sallama cikin gidan, Umma ta mik'e cikin son kawar da damuwar dake shimfid'e kan fuskar ta tace "Sannu da zuwa" "Yawwah sannu ka dae" ya fad'a yana son karantar yanayin ta, seta riga shi yin gaba dan bata so ya karanto raunin dake tattare da ita ballantana har shima yaji ya sake karaya "Wallahi ban samu komae ba" Abba ya fad'a muryar sa a raunane gwanin ban tausayi bayan ya zauna, ajiyar zuciya Umma tayi sannan tace "Babu komae, Allah ze kawo ko zuwa gobe ne In Sha Allah" seya jinjina kae kana yace "Ina wannan yaron? Allah yasa yaci wani abun ko dan rashin lafiyar sa" kallan d'akin da Yah Sadeeq ke ciki Umma tayi sannan tace "Ehh toh yaci zance, amma kasan halin sa ba son cin abincin nan yake ba, yanzu haka ma yayi bacci" "Bacci kuma? Lafiya dae koh?" Abba yayi tambayar cike da fatan lafiyar ce, ba tare da tunanin komae ba Umma tace "Ehh lafiya k'alau" "Toh madallah, bari na kira mana Ayrah" Abba ya fad'a yana fiddo wayar sa daga aljihu, da sauri Umma ta kalle shi tace "A'ah Abban su kada ka kira ta, bana so ta fahimci ko da akwae wata matsala daga nan wajen mu, kasan halin yarinyar nan" shiru Abba yayi cikin na'am da zancen nata kafin yace "Toh shikenan.." daga haka yayi shiru yana cigaba da tunanin rayuwar su ta baya data yanzu, shida yake ajiye abincin wata a gidan sa tafi tafi ya koma siya kad'an kad'an, yanzu kuma da yanayin rayuwar ya sake juyawa se gashi wataran a cikin gidan sa an tashi babu ma abincin da za'a ci, ya riga yayi na'am da k'addara, ya yadda da ita kuma yasan Allah ne ya k'addaro masa ita amma ta sanadin Abbu, Abbu yayi musu wani gi6i a rayuwar su da baza su ta6a mantawa ba, ta dalilin sa abubuwa da dama sun faru kuma suna kan faruwa ma, baya tunanin ze iya yafewa Abbu abinda ya masa koda kuwa basu sake had'uwa a duniyar nan ba, yana jin koda yace zeyi hakan ma toh kuwa wani 6angaren nashi baze ta6a yafewa kan sa ba, abinda ma baya tunanin ze faru kenan, wanda shi a gare shi ma baya fatan sake had'uwa da koda me irin halin Abbu ne ballantana kuma shi kan sa Abbun...... Mhiz Innocent...... ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 025_026 ___Kae tsaye Hostel suka wuce su biyun har lokacin suna tattauna maganar da tak'i k'arewa, dukan su mamaki yak'i sakin su, a haka har suka k'arasa d'akin su Jidda, ko sallama babu wadda ta iya a cikin su saboda yadda suka k'agu su isar da labarin nan, Jidda dake facing k'ofar d'akin tace "Kae jama'a lafiya kuwa?" bud'a hanci Abeeda ta shiga yi ita a dole ta kawo musu abu me muhimmaci "Jarida na kawo muku me tsada!" tayi maganar sanda take neman waje ta zauna, sakkowa Ruks tayi daga kan gadon ta sannan ta k'araso tana kallan Abeeda tace "Kinga kawae ki fad'a mana meya faru?" "A'ah wallahi nawa zaku siya?" Abeeda ta fad'a tana sake gyara zaman ta, k'aramin tsaki Bahijja ta saki kafin tace "Don girman Allah ki fad'a mana, haba mana" dariya Abeeda tayi kana ta sakko da jakar ta dake mak'ale a kafad'ar ta ta sanya hannu ta d'akko wayar ta tace lokaci guda kuma tana danna wayar "Ke kam Bahijja Allah ya shirye ki da son gulma wallahi" "Oho dae, mu dae fad'a mana kawae" "A'ah an shiga 3" Abeeda ta fad'a tana d'an bud'e ido ganin da tayi wayar ta ta sam tak'i dannuwa, ga dae ta ta kawo amma kwata kwata tak'i dannuwa "Kashhh! Shegiyar waya seda ta kwafsa min wallahi" ta fad'a tana dafe kan ta, Bahijja ce ta d'auki wayar itama ta ta6a, ganin da tayi babu abinda ke motsi a wayar ya sanya ta fad'in "Kinga fad'a mana da baki kawae pls" Khadeejah da ta gama k'uluwa dan takaeci da haushi tace bayan ta ja k'aramin tsaki sannan ta maeda duban ta kan su Bahijja "Doctor Rk" sunan sa suka ji ta ambata ne ya sanya dukan su kallan ta, Abeeda ta d'ago ba tare da ta kalli Khadeejah ba tace, dan gaba d'aya ita kan ta seda taji ta muzanta da abinda wayar ta mata bayan cika bakin da ta gama yi "Ina Ayrah ta cikin d'akin kun nan? Toh soyayya suke da Doctor.." dukan su suka cigaba da kallan ta kowannen su na ganin kamar zarewa tayi yasa take wannan maganar, Jidda tayi k'arfin halin fad'in "Wait mana hajiya! Wane Doctorn kike magana kuma wace Ayrahn kike magana akae?" tayi maganar cikin tsare ta da idanu, murmushi Abeeda ta saki sannan tace "Dama nasan ba yadda za kuyi ba shiyasa na d'auko muku hoto, amma kada ku damu zan kae a duba min wayar, idan ta gyaru zan dawo na nuna muku hoton dana d'auka na shi shi da ita yau da suka fita.." daga haka ta mik'e ta fice Khadeejah tabi bayan ta, kusan a tare suka bita da kallo kamar wasu dolaye, ta bar su da tunani kala kala, sun kae wajen minti 1 a hakan sannan Bahijja tayi k'arfin halin fad'in bayan ta kalle su "Kada fa ace da gaske Abeeda take" wani murmushi Ruks tayi sannan tace "Haba Bahijja kada ki zama shashasha mana, Doctor Rk fa take magana wae yana soyayya da wannan yarinyar? Dududu ma nawa take?" shiru Bahijja tayi na d'an wani lokaci kafin can tace "Ke wallahi ba tun yau nake zargin yarinyar nan ba, dama na dad'e ina tsoron kada kyawun ta ya rinjaye shi mu shiga 3" se a lokacin Jidda tace "Hmmm, kuna tunanin kyawu ze rud'i kyakykyawa ne? Bana tunanin haka gaskiya" tayi maganar tana d'an k'ank'ance idanun ta kamar me tunani "Toh koma dae menene akwae wata a k'asa" Bahijja ta fad'a, kafin wata a cikin su tace komae sallamar Ayrah ta ratso cikin d'akin, babu wanda ya iya amsa mata se bin ta da suka yi da kallo dukan su, kallo irin na tuhuma, ganin irin kallan da suke mata ne ya sanya ta sake had'e kyakykyawar fuskar ta ta k'araso cikin d'akin "Daga ina kike?" Bahijja tayi k'arfin halin fad'in hakan, kallan ta Ayrah tayi da mamakin jin furucin ta, kafin Bahijja ta gama fahimtar irin kallan da Ayrahn ke mata ta jiyo k'aramar muryar ta tana fad'in "Toh ina ruwan ki?" ta fad'a tana hararar gefe gami da murgud'a baki sannan tayi wucewar ta kan gadon ta, dukan su suka bita da kallo kafin Ruks ta jinjina kae tana ta6e baki cike da mamakin halin Ayrahn "Cha66 d'i jam!" Jidda ta fad'a tana cigaba da kallan Ayrah. Ta 6angaren Ayrah kuwa ba ta bi ta kan kowa ba ta zura hijab ta shige toilet, kamar wasu sokaye suka sake bin ta da kallo, yarinyar ta chanja musu sosae, duk da dama tun can sun fahimci miskila ce ta k'in k'arawa, amma yanzu abin yayi gaba sosae, dole su jira Abeeda dan su tabbatar da abinda ta fad'a musu, duk da abin ne akwae wuyar yadda. ... Babu nisa su Ayrah suka yi last paper d'in su ya zamana se komawa gida kenan. A 6angaren Abba kuwa se Allah ya taemake shi lokacin da ze je d'auko Ayrahn ya kar6i albashin sa, dan haka ba k'aramin dad'i yaji ba. Ranar daze tafi ya gama shiryawa cikin manyan kaya na wani yadi, daga d'aki ya fito lokacin Umma na d'akin Yah Sadeeq ta kae masa abinci, ta kalle shi tana murmushi tace "An fito kenan?" shima murmushin ya maeda mata sannan yace "Wallahi kuwa zamu wuce" yayi maganar yana d'ora hular sa samfurin zanna bukar akan sa "Toh Allah ya tsare.." "Ameen Ameen.. amma kafin nan zan biya nayi wa Baban Zaenab ya me jiki, saboda jinjirar da aka haefa masa da aka sallamo su daga asibiti" "Toh ayi mata sannu, gobe idan Allah ya kaemu se mu shiga mu duba ta" "Toh madallah" Abba ya fad'a yana yin gaba, seda ya shiga d'akin Yah Sadeeq dake zaune akan gadon sa yana danna er k'aramar wayar sa, Abba yace "Sadeeq!" "Na'am Abba zaka wuce ne?" "Ehh ba kaci abincin ba" d'an murmushi kad'an yayi sannan yace "A'ah yanzun dae zan ci, Allah ya dawo daku lafiya Abba" "Ameen_Ameen" Abban ya fad'a yana mik'ewa ya fice daga d'akin. Kae tsaye seda ya fara zuwa ya gaeda mara lafiyar sannan ya dawo ta hanyar gidan sa dan wucewa titi ya nemi abin hawa, a k'ofar gidan nasu yaga wata mota me kyau, tunda suka gan shi suka sauke glass d'in motar, wani malamin su Ayrah ya sauko ya k'arasa da murmushi kan fuskar sa yace "Barka da wannan lokacin Alhaji" yayi maganar yana mik'awa Abba hannu, shima Abban mik'a masa hannu yayi suka gaesa yana amsawa da "Barka dae, ashe kae ne?" "Wallahi kuwa, ina zuwa haka ne?" Abba yace "Zan je d'auko Ayrah ne kasan da yake sun gama exam" murmushi malamin nasu yayi sannan yace "Ahh toh ae dama daga makarantar ne aka aeko mu muzo mu d'auke ka a motar nan mu wuce can makarantar" "Toh Ikon Allah" Abba ya fad'a yana bin motar da kallo, dan sosae abin ya cigaba da bashi mamaki, tabbas makarantar tasu Ayrah mutane ne masu karamci da sanin ya kamata "Allah ya saka da alkhaeri" Abba ya fad'a "Ameen Ameen.. Muje koh?" ya fad'a yana yin gaba sannan Abba ya rufa masa baya zuwa wajen motar, shi malamin ya shiga gaba yayin da Abba ya shiga baya, a haka driver ya soma driving babu dad'ewa suka d'auki hanyar Zaria. ... Ayrah ta gama had'a komae nata ta kammale shi inda ya kamata, wani irin d'oki ne keta d'awaeniya da ita, ji take kamar tayi tsuntsuwa ta gan ta a Kano taga Abban ta, Umman ta da uwa uba kuma Yah Sadeeq d'in ta, gaba d'aya ta kasa sukuni tun d'azun wayar ta ke hannun ta tana jiran kiran Yah Sadeeq ko Abba, Jidda ce kawae a d'akin tun d'azu su Bahijja suka fita ko sallama ba suyi ba, bata k'ara minti 5 ba kuwa sega kiran Abba a wayar ta ta, zumbur ta mik'e dan dama k'iris take jira ta d'aga wayar tana karawa a kunnen ta "Abba kunzo?" ta fad'a tun kafin Abban yace komae, murmushi Abba yayi kana yace "Qwarae kuwa ke muke jira yanzu haka" jin da tayi yace suke ya sanya ta tunanin tabbas shi da Yah Sadeeq suka zo dan haka da sauri ta kalli Jidda tace "Mu dae mun tafi" ta fad'a tana Allah Allah Jidda ta amsa ta fice daga d'akin "Ba zaki tsaya kiyi sallama dasu Ruks ba?" 6ata fuska tayi sannan tace bayan ta girgiza kae "A'ah ki fad'a musu na tafi ni dae, se an dawo hutu bye.." ta fad'a tana ficewa daga d'akin "Toh Allah ya kaemu" shine abinda Jidda ta fad'a tana bin Ayrah da kallo sanda ta fice daga d'akin cikin d'oki kae seka rantse tafi shekara ba taga Abban ba. Sosae taji dad'in ganin Abban dan murna gaba d'aya ta kasa dena murmushi se dae tayi mamakin rashin ganin Yah Sadeeq tare da Abban, dan haka ta kasa shiru seda tace "Abba Yah Sadeeq fa?" "Yah Sadeeq na gida, kin san yanayin aekin su hutu yake shiyasa.." se tayi murmushi, a yanzu da taga Abba se d'okin nata kuma ya koma na son ganin Yah Sadeeq da Umma, suna tafiya a hanya suna hira sosae cike da farin ciki da kewar juna, Abban ya zage yana jan d'iyar ta sa da hira, se dae da yake basu kad'ae ne a cikin motar ba ya sanya yawanci hirar tasu bata wuce akan karatu. ... Da wani sauri Bahijja ta turo k'ofar d'akin hannun ta d'auke da wayar Abeeda, Abeeda da Ruks suka biyo bayan ta, idanun ta a warwaje ta furta "Ina Ayrah take?" tayi maganar cikin d'aga murya, da mamaki Jidda ke kallan ta yadda take a wani birkice kamar mahaukaciya tace "Meya faru?" "Ke dae ina take kawae?" "Yanzun nan aka zo aka d'auke ta" Jidda ta fad'a sannan ta d'ora da "Pls meya faru?" komawa Bahijja tayi ta zauna, tana tuna yau da taga Ayrah a cikin d'akin nan babu abinda ze hana ta shak'e ta ko zata ji sauk'in abinda take ji a cikin zuciyar ta, kar6ar wayar hannun ta Ruks tayi sannan ta mik'awa Jidda tace "Kalla ki gani" hannu Jidda ta saka ta kar6i wayar sannan ta shiga kallan hoton sannu a hankali, tana kae hannun ta tana zooming, ta kae wajen minti 1 tana kallan hoton sannan ta d'ago ta kalle su cike da mamaki akan fuskar ta "Kenan abinda Abeeda ta fad'a gaskiya ne?" tayi tambayar tana kallan su su duka, kamar wata k'adangaruwa Bahijja ta shiga girgiza kae tana jin kamar ta rusa ihu "Shegiyar yarinya ta cuce mu, dama seda nayi tunanin kyawun ta ze iya rud'ar shi, ashe mu bamu sani ba ma sun dad'e suna soyayyar su amma shegiyar yarinya seta dinga nuna kamar ma tsanar sa tayi, bamu sani ba ashe wawaye sakarkaru ta maeda mu, k'aramar yarinya tayi wasa da tunanin mu kenan?" ajiyar zuciya Jidda ta sauke kana tace "Lallae kam, ni kae na abin ya bani mamaki wallahi, yaushe muna zaune har hakan ta faru bamu sani ba? Ya akayi hakan?" tayi maganar cike da mamakin dae, girgiza kae Ruks tayi kafin tace "Wallahi ku bari kawae, ni dan mamaki ma na rasa wane tunani ya kamata nayi" Abeeda tace "Ahh toh, ni kae na nasan amanar ku akaci shiyasa naga bazan k'yale ba gwara na sanar daku" "Aekuwa wallahi za taci uwar ta yarinyar nan" Bahijja ta fad'a dan tana ganin kamar duk tafi su takaeci da abinda Ayrahn ta aekata musu, ta shammace su, tayi wasa da hankalin su, ta kuma nuna musu yawan shekaru ba shine wayo ba. .. Da sallama ya shiga d'akin yana sanye cikin wasu k'ananan kaya masu kyau da taushi, kan sa d'auke da facing cap data matuk'ar k'awata shigar sa ya fito yayi kyau abin sa, cikin sa'a seya samu Mummy har ma da Daddy a d'akin, ba k'aramin dad'in ganin hakan yayi ba, dan haka ya k'arasa ya zauna k'asan Carpet yace "Barkan ku da warhaka" "Barka kadae" suka had'a baki wajen fad'in hakan "Daddy dama inaso ne na shaeda maka yau zan koma Kano" "Kano kuma Likita? Wani abu ne ya faru?" seya girgiza kae kawae yana d'an lumshe idanun sa kad'an bece komae ba har zuwa sanda Mummy tace "Haba kae kuwa Raj, gaggawar ta me ce?" "A'ah Mummy.." shine abinda kawae ya fad'a, Daddy yace "Ko dae akwae abinda zaka yi ne acan d'in?" tambayar Daddyn ta matuk'ar yi masa dad'i dan haka da sauri ya furta "Ehh Daddy, akwae wani abu me muhimmanci da zan gabatar acan d'in.." "Toh shikenan babu damuwa, akwae maganar ma dama da zaku yi da Abbun naka.." be bawa zancen muhimmanci ba dan haka kawae abinda yace shine "Tohm" "Allah yayi maka albarka kaji Doctor, Allah kuma ya sanya albarka" shine abinda Mummy tace "Ameen" kawae yace duk da ita kan ta be gane akan maganar da take magana ba, ya dae fi tunanin itama taji labarin ajiye aekin da zeyi ne yasa take magana fatan alkhaeri, seya mik'e hannun sa d'aya cikin aljihun sa yace bayan yayi murmushi "Daddy bari naje na sake shiryawa" "Toh Raj, seka fito" daga haka ya fice daga d'akin. .. Ko jakar ta bata iya d'auka ba ta fad'a cikin gidan nasu da gudu tana kwad'a sallama da siririyar muryar ta, wani sanyi Umma taji ya ratsa ta jin muryar shalelen er tata, kafin ma ta kae ga k'arasowa Umman ta fito daga cikin d'akin ta, aekuwa tana shigowa ba tayi wata wata ba ta fad'a jikin Umman tana sakin dariya lokaci d'aya tana furta "Nayi kewar ki sosae Umma ta" murmushi Umma tayi ita kan ta tasan tayi kewar d'iyar ta ta sosae, dan haka itana ta rungume ta tana fad'in "Yanzu ae gani gaki koh?" seta jinjina kae har lokacin tana jikin Umma, sun kae wajen minti 1 a haka sannan Ayrah ta saki Umma tana fad'in "Umma ina Yah Sadeeq?" "Yana d'aki bacci yake" Umma ta fad'a tana kallan d'iyar ta ta "Umma wallahi yanzu Yah Sadeeq ya zama malalaci, kullum cikin bacci" ta fad'a lokacin data shiga d'akin nasa, seta hange shi kwance kan gadon idanun sa a rufe ya lullu6e rabin jikin sa da bargo, se tayi murmushi tana jin dad'in ganin sa sannan ta k'arasa ciki tana fad'in "Yah Sadeeq ka tashi, na dawo" kamar daga sama ya jiyo muryar lilin ta sa, dan haka a hankali ya bud'e idanun sa se kuwa ya sauke su a kan ta, murmushi suka sakarwa junan su sannan Yah Sadeeq yace "Yanzu kuka shigo?" "Ehh Yah Sadeeq nayi kewar ka wallahi" ta fad'a tana 6ata fuska, dariya yayi yana jin dad'in ganin k'anwar ta sa dan shi kan sa yayi kewar ta irin sosae d'in nan "Nayi kewar rigimar nan taki Auta" ya fad'a har lokacin yana murmushi "Kae Yah Sadeeq rigima kuma?" ta fad'a har lokacin dae tana 6ata fuska gami da tura baki "Toh shikenan dae ya hanya?" ya fad'a yana k'ok'arin tashi zaune, shi kan sa baya so ta gane karaya ce a k'afar sa dan ya riga yasan halin ta yanzun nan zata fishi shiga damuwa, se akayi sa'a ma tace "Yah Sadeeq kayi baccin toh, idan ka tashi se muyi hirar" ta fad'a tana kallan sa, seya koma ya kwanta ba dan yana tunanin ze iya baccin ba sannan yace "Toh shikenan Auta.." "Yawwah Yah Sadeeq" ta fad'a tana ficewa daga d'akin tana fad'in "Umma kin ga lalacin Yah Sadeeq d'in koh? Ya sake komawa baccin" ta fad'a tana k'arasawa tsakar gidan, dae_dae lokacin da Umma take fad'in "Za dae a tantance malalacin" turo d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Kae Umma" dariya Umma tayi tana fad'in "Toh shikenan, ina Abban?" "Aou" ta fad'a bayan ta kae hannun ta kan bakin ta sannan tace "Allah sarki Umma k'anwar Zaenab ce ta rasu shine ya tafi za'a kae ta" "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun, ashe ta rasu? Toh Allah ya ji k'an ta, ashe ba mazauniya bace" Umma ta fad'a tana tuna yarinyar data rasun wadda ba tafi wata 5 da haehuwa ba, k'arasowa Ayrah tayi ta zauna kan tabarmar da Umma ta shimfid'a, seda Umma ta zauna sannan ta d'ora kan ta akan cinyar Umman tace "Umma nazo muku da wani albishir, amma bazan fad'a ba se Abba ya dawo" "Wane albishir ne wannan?" "A'ah Umma se Abba da ya dawo" Ayrahn ta fad'a tana sake gyara kwanciyar ta kan cinyar Umma "Toh shikenan, ya exam ya karatun?" "Umma komae Alhamdulillah fa" ta fad'a tana murmushi, daga haka suka cigaba da hira, Umma nata jin labaran da Ayrahn ke ta bata, wani tayi dariya wani ta girgiza kae cike da ganin wautar Ayrahn, se dae lokaci lokaci ta kan yi shiru ta saki murmushi me k'ayatarwa idan ta tuna Rk, Umman na lura da ita amma har lokacin tak'i fad'awa Umma komae game da albishir d'in da tace zata yi musu, dan haka itama ta mata shiru kawae tana cigaba da saurarar hirar da take mata. ... A 6angaren Rk kuwa dab da maghrib ya isa gidan nasu cikin motar sa, k'atuwar harabar gida dake d'auke da manya manyan motoci a gefe guda, shuke shuke da sauran abubuwa na burgewa, kae tsaye parking lot d'in ya wuce da motar sa yayi parking nata dae_dae lokacin da wani ya k'araso da sauri yana fad'in "Barka da dawowa yalla6ae" ya fad'a yana duk'awa "Barka, a shigar min da kaya ciki" shine abinda Rk ya fad'a yana wucewa cikin tafiyar nan tasa ta nutsuwa hannun sa d'aya cikin aljihun sa, tafiya me tsayi ce yayi kafin ta sada shi da aenahin inda d'aku nan masu gidan yake, yayi murmushi sanda ya ganshi a k'ofar Parlourn Ummeen sa, babu 6ata lokaci ya sanya k'afar sa cikin k'aton hamshak'in Parlourn da sallama, Ummee na zaune kan kujera hannun ta d'auke da remote tana shirin chanja channel yayi sallama, seta ajje remote d'in akan kujera tana kallan sa sanda wani k'awataccen murmushi ya su6uce a fuskar ta tace tana k'arasawa inda yake "Oyoyo Oyoyo.." k'arasawa yayi inda take yayi hugging nata sannan ya zauna a k'asan kujerar yace cikin girmamawa "Ummee barka da wannan lokacin" "Barka dae ya hanya?" "Hanya Alhamdulillah" ya fad'a dae_dae sanda aka k'walla kiran Sallah a masallacin su dake jikin gidan nasu, se yayi saurin mik'ewa yana fad'in "Ummee bari naje" "Toh Raj seka dawo" ta fad'a tana bin sa da kallo har lokacin da murmushi kan fuskar ta. A harabar gidan suka yi kaci6us da Abbu dake sanye cikin wata dakakkiyar bluen shadda d'inkin babbar riga data matuk'ar yi masa kwarjini "Welcome my Son" Abbu ya fad'a yana bud'a hannun sa, Rk ya k'arasa yayi hugging mahaefin nasa sannan yace "Barka da wannan lokacin Abbu" "Barka dae Raj, ka dawo ashe? Mu wuce masallaci dae tukunna" babu 6ata lokaci suka wuce masallacin dake jikin gidan su, ana Sallahr Isha'i Rk ya koma gida saboda yadda yake so ya watsa ruwa a jikin sa yayin da ya bar Abbun a masallaci. Cigaban nan wajen yana page 1, yanzu haka mun ji TUSHEN LABARIN MU dan haka zamu d'ora ne da CIGABAN LABARI.... ... "Shin yanzu kin san wanene Raj d'in da kike magana a kan sa? Waye mahaefin sa? Meya aekatawa rayuwar ku? Mahaefin ku ya amince masa ya bashi amanar da be ta6a bawa wani ba amma daga k'arshe ya wulak'antashi ya tozarta shi yayi wancakali da duk wannan amanar, mahaefin ki ya d'auko shi daga rana ya sanya shi a inuwa amma daya tashi dame ya saka mishi? Seya d'auki mahaefin ki ya jefa shi cikin ranar shi kuma ya cigaba da rayuwar sa ba tare da tunanin halin da zamu iya shiga mu dukan mu ba, Yanzu haka Sadeeq na kwance ne a d'aki sakamakon karayar daya samu ana buk'atar a masa aeki amma babu kud'in aekin, mahaefin Raj ya cuci Abban ku, ya raba shi da dukiyar sa, takaddun sa masu muhimmanci, uwa uba kuma shine silar shigar mu cikin kowanne hali, silar abinda ya aekatawa mahaefin ku ne ya janyo masa hawan jini, ya cuce mu mu kan mu akan son zuciyar sa, ta yaya zan miki wannan bayanin a wancan lokacin ki fahimta? Ina k'wak'walwar ki take ta k'arfin fahimtar wannan zancen?" Umma ta k'arashe maganar tana kallan Ayrah da tunda ta fara maganar ba tace komae ba, idanun ta gaba d'aya Umma suke kalla har lokacin tana cigaba da tuno maganar Umman cikin kunnuwan ta wanda take jin su kamar amsa kuwwa suke mata a kunnen ta, dan kuwa duk da Umman tayi shiru hakan be hana ta cigaba da jiyo sautin muryar Umman a kunnen ta ba, kunnen nata ya mata wani duumm kamar wadda ta kurumce banda sautin muryar Umman babu abinda take ji har yanzun, bata ma sani ba ko Umman ta cigaba da fad'a mata magana ko tayi shiru ne ita dae bata sani ba, abinda kawae ta sani maganganun nan da suka sanya ta cikin sani irin shock da kuma hutun da k'wak'walwar ta ta tafi na wucin gadi su kad'ae keta dawo mata, jikin ta wani irin rawa yake yi kamar me jin sanyi, duk da idanun ta ba'a rufe suke ba amma se take so ta sake bud'e su tarr ko dan ta cigaba da kallan Umman da yanzun take ganin ta dishi dishi, gaba d'aya ta kasa koda bud'e bakin ta ne ballantana ta furta wani abun, koda yake idan ta bud'e d'in ma menene za tace?? Mhiz Innocent......✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 027_028 ___Ganin da Umma tayi har lokacin Ayrah ta gaza furta komae ya sanya ta sanya hannu ta share idanun ta itama da k'wallar ta gama tarar mata, kawae seta juya a hankali ta fice daga d'akin dan ta bar Ayrahn ta dawo daga shock d'in data shiga, ta san dole abin ya ta6a ta aenun, bata ta6a zata ba ba kuma ta ta6a tsammani ba se gashi rana tsaka taji dalilin rabuwar Abba da Abbun Raj. Ko d'aga ido ta kalli Umman ta kasa yi sanda Umman ta fice daga d'akin, ita bama ta lura ta fita ba dan kuwa har zuwa lokacin ta kasa gasgata duk maganganun nan da Umma take fad'a ba mafarki bane "Abbun Raj fa" shine abinda ta dinga maemaetawa a cikin ran ta tana so ta hasaso fuskar sa amma ta kasa dan shekarun nada yawa, ga kuma yanayin shekarun ta a lokacin, amma tabbas idan har bata manta ba mutumin ya zo wa Abban ta a matsayin mutumin kirki, bata san menene ya had'a su ba se gashi yau Umma ta bankad'a mata komae taji dalilin Abba na cewa ba zata auri Raj ba, tabbas in dae kuwa haka ne dalilin Abban yana da gaskiya, a hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya tana jin wani irin zafi a cikin zuciyar ta, sosae zuciyar ta ke zafi wanda har ta numfashin ta seda ya koma fita da zafi, se a lokacin taji wani kuka ya taho mata, bata hana fitowar kukan ba se kawae ta jefar da jikin ta kan gadon ta fashe da wani irin kuka, a hankali take dukan kan ta akan pillown kan gadon tana jin wata iriyar nadama da danasani na lullu6e ta, kunyar abinda ta fad'awa Abba d'azu na sake k'arawa yanayin da take ciki k'aemi, wani irin kuka take wanda ke fitowa daga can k'asan ran ta, kukan nadama, kukan danasani, kukan rashin sanin mafita, a yau d'aya taji tayi danasanin sanin Rk a rayuwar ta, meyasa ma ta san shi? Meyasa tayi silar zuwan sa wajen Abba? Meyasa ta zamo silar da Abba ya janyo mahaefin sa cikin jikin sa? Yanzu kenan itace silar komae? Itace ta janyo komae? Meyasa tayi hakan? Gani take kamar komae ya faru itace me laefi tunda ita ta kawo Rk d'in "Nice silar komae!" ta fad'a sanda take sake sakin wani kukan me cin rae "Tabbas nice sila, dan da ban san Raj ba Abba baze ta6a sanin Abbun sa ba, ni na janyo Abba ya jawo Abbu a jikin sa har me faruwa ta faru, nayi danasanin sanin ka a rayuwa ta Raj!" ta k'arashe maganar tana cigaba da kukan da har muryar ta ta fara dashewa, yau mamaki na neman kashe ta, wae Abbu ne ya cuci Abba, Abbu ne sanadiyyar tarwatsewar farin cikin su, Abbu ne sanadiyyar saka damuwa a zukatan iyayen ta, Abbu ne sanadiyyar abubuwa da dama da suka faru a rayuwar su, shi kam yanzu menene zece musu su yafe masa? A hankali ta sake komawa ta kwanta har lokacin ta kasa tsaeda kukan da take, haka zalika zafin da zuciyar ta yake yak'i raguwa sema k'aruwa da yake yi, ta rasa yadda za tayi, ji take dama zata iya janyo abinda ya faru ada ta goge komae akan alak'ar ta da Rk, da kuma ana iya tariyo baya data hana kan ta had'uwa da Rk, Yah Sadeeq ne ya fad'o mata, se taji wata sabuwar k'walla ta zubo mata, ta sanya hannu ta d'auke ta lokaci d'aya tana lumshe idanun ta, bata da k'arfin da zata iya tashi yanzu haka taje ta duba jikin sa, amma ita kad'ae tasan abinda take ji a cikin jiki rae da kuma zuciyar ta. ... "Don Allah Alhaji kayi hak'uri ka bari ko zuwa gobe ne, kaga ko hutawa ba kayi ba" Muttala ya fad'a yana kallan Alhajin daya fito daga d'akin sa cikin wata bugaggiyar shadda d'inkin babbar riga, juyawa yayi ya kalli Muttala sannan yace har lokacin be tsaya ba "Wallahi bazan iya hak'ura se gobe ba, gwara ma ka k'yale ni kawae" yayi maganar sanda ya isa motar sa, ya bud'e ya shiga sannan ya kalli Muttala yace "Zaka raka ni ne ko kuma in nemi wani?" seya girgiza kae sannan ya k'arasa ya bud'e wajen me zaman banza ya shiga ya kalle shi cike da girmamawa yace "Yalla6ae daka bari dae ko zuwa goben ne kada su fahimci wani abun!" wani kallo Alhajin ya jefa masa se kuma yayi murmushi wanda ya sake k'ank'antar da jajayen idanun sa "Tunda kaga zan yi driving da kae na kasan abu ne me muhimmanci, na kasa jurewa gwara naje ko nan sati 1 ne a d'aura mana aure idan yaso seta cigaba da karatun a cikin gida na" jin maganar da Alhajin ya fad'a ne ya sanya Muttala jinjina kae kawae, bece komae ba har zuwa sanda Alhajin ya tayar da motar sa suka fice daga gidan. A k'ofar gidan yayi parking motar ta sa, sannan ya kashe ta ya kalli Muttala da tunda suka fara tafiya har yanzu be sake cewa komae ba yace "Yi mana sallama da shi pls" seya kalli Alhajin sannan yace bayan ya girgiza kae "A'ah fa Yalla6ae kada ka manta sirikin ka ne, ina ganin gwara ka fito ko kan dakalin can ne seka zauna" Muttala ya fad'a yana nuna wani dakali dake a k'ofar gidan dake kusa da nasu Ayrah, shiru Alhajin yayi kamar ba zece komae ba se kuma can yace "Toh yanzu kae dae je ka" yayi maganar yana sanya hannun sa ya bud'e k'ofar, kusan a tare suka fito, Alhajin ya kalli wajen yana yamutsa fuska sannan ya zauna yayin da Muttala ya tsaya k'ofar gidan ya k'wala sallama, daga can cikin gidan Abba ya amsa yana mik'ewa ya zura takalmin sa ya fito daga d'akin nasa, k'arasowa yayi yana kallan Muttala ganin da yayi be shaida fuskar ba, se dae ya mik'a masa hannu suka gaesa sannan yace da d'an murmushi kan fuskar sa duk da yanayin da yake ciki a yau d'in na damuwa "Se dae ban shaeda fuskar ba" murmushi shima Muttalan yayi sannan yace "Ehh dama baka sanni ba gaskiya, ga can wanda yazo wajen ka akan wata magana me muhimmanci" yayi maganar yana nuna Alhajin dake zaune kan dakalin yana kallan wani wajen, saboda k'arancin hasken dake a wajen ya sanya Abba be iya hangar fuskar sa ba, seya dawo da duban sa ga Muttala yace "Toh ikon Allah" ya fad'a yana yin gaba zuwa wajen da Alhajin ke zaune, dae_dae lokacin da Abban ke dab da k'arasawa wajen Alhajin haske ya kawo a wani k'wan lantarki dake k'ofar gidan dake kallan nasu, hakan ne ya bawa Abba damar ganin fuskar mutumin da akace shi ke son magana dashi, cikin son sake tabbatarwa ya sake bud'e idanun sa dan ganin da gaske fuskar da yake gani ita d'in ce ko kuwa dae? Shi kan sa Alhajin kallan Abba yake with shock all over his face, se yaji gaba d'aya jikin sa ya d'auki wani mahaukacin rawa, ya had'iyi wani yawu da k'yar sannan yace bayan ya mik'a masa hannu "Kae ne mahaefin Ayrah?" Alhajin ya fad'a yana kallan Abba, a ran sa yana tuna cikakken sunan Ayrahn, tabbas da gaske shine mahaefin ta, amma dae gwara ya tabbatar ta hanyar ji daga bakin Abban, da mamaki Abba ke kallan sa jin maganar da yayi, meya kawo zancen Ayrah a tsakanin su kuma? "Meya kawo ka k'ofar gida na?" Abba ya fad'a yana kallan sa fuskar sa a d'inke tsaff, jikin sa ya sake wani sanyi wata zufa na karyo masa yace bayan yayi k'asa da muryar sa "Kayi hak'uri mu zauna sena maka bayani, wallahi ba tashin hankali ne ya kawo ni wajen ka ba" "Alhaji Mato!" Abba ya fad'a cikin er d'aga murya, a ran sa Abba na sak'a lallae duk abinda Alhaji Maton yazo da shi me girma ne "Bani da lokacin 6atawa, idan ba kada abin fad'a na shige gida" Wani yawun Alhaji Mato ya sake had'iyewa shi kan sa yana tunanin ta ina ma ze fara sanarwa da Abban son er sa yake? So na aure, ganin dae da gaske Abban yake idan bece wani abu ba ze iya tafiya ya k'yale shi ya sanya shi fad'in "Wallahi abin alkhaeri ne ya kawo ni, d'iyar ka na gani kuma ina son ta da aure shine kawae abinda ya kawo ni, kuma kada ka damu wancan lokacin akasi aka samu na fad'i magana saboda 6acin rae amma zan dawo maka da kud'in daka biya ni, kuma zan baka sana'ar da zaka dinga yi kana.... " "Dakata Alhaji Mato" Abba ya fad'a bayan ya d'aga masa hannu, zuciyar sa na wani irin zafi da jin kalaman Alhaji Maton na son zuciya "Kada na sake ganin k'afar ka a k'ofar gidan nan, kud'i kuma har abada na riga na biya ka kuma bazan ta6a kar6a ba, saboda haka kada ka sake tunanin zan d'auki 'ya ta in baka ita bayan na san wanene kae, ka cire wannan ma a cikin ran ka" daga haka Abba ya juya yana jin wani jiri jiri na d'ibar sa kamar ze fad'i, da kallo Alhaji Mato ya bishi zuciyar sa na wani irin tafasa, lallae yau ya kuma yadda Abban matsiyaci ne, be san me ake kira da arzik'i ba, har yanzu dae yana zaune cikin duhun kae, har abada ma baya tunanin Abban nada rabon arzik'i a rayuwar sa, tunda gashi yanzu arzik'in ya biyo shi har gida amma ya saka k'afa yayi fatali dashi saboda wani banzan ra'ayin sa na rik'au. Seda Abba ya shiga gida sannan Muttala ya kalli Alhaji Mato cikin mamaki yace "Yalla6ae wae dama ka san shi ne?" "Bar shashasha me k'ashin tsiya, arzik'i na kiran sa yana guduwa, wani k'aramin abu ne ya ta6a shiga tsakanin mu amma da yake zuciya ce dashi irin ta kafirae ya kasa mantawa, toh se yayi tayi ae, ba dae er sa bace na gani ina so kuma sena aure ta, dan kuwa ban ta6a ganin abu inaso ban same shi ba, kuma baza a fara akan ta er talakawa ma da ita ba, ko da amincewar sa ko babu wallahi sena aure ta.. Wuce muje.." ya fad'a yana huci sanda ya k'arasa ya bud'e motar sa ya shige, Muttala ma ya shiga, Alhaji Mato yaja motar da wani irin gudu kamar ze tashi sama. .. Akan la66an sa kawae Abba yayi sallamar dan baya jin ze iya d'aga murya sosae saboda yadda yake jin jikin sa, da kallo Umma ta bishi dashi sanda yake shigowa cikin d'akin, seta mik'e da sauri cikin mamakin yadda taga yanayin nasa ya sake chanjawa fiye da d'azun "Abban su" shine abinda ta iya furtawa tana cigaba da kallan sa, Abba ya nemi waje ya zauna amma har lokacin bece komae ba, fita Umma tayi ta d'ebo ruwa me sanyi cikin randa sannan ta koma d'akin ta mik'a masa a nutse tace "Gashi" babu musu Abban ya kar6a kofin ya sha ruwan sosae sannan ya ajiye shi yana sauke ajiyar zuciya "Don Allah ka dena d'aga hankalin ka haka nan, in dae akan wannan maganar ne nayi mata bayanin dalilin ka na hana ta auren sa" girgiza kae Abba yayi sannan yace bayan yayi murmushi me ciwo "Ba wannan kad'ae ba, yanzu fitar da nayi wae neman auren Ayrah akazo yi" "Ikon Allah.. Amma shine ka shiga damuwa haka?" Umma ta fad'a tana sake kallan Abban "Kin san wanene yazo neman auren nata?" Abba ya fad'a yana sake tuna fuskar Alhaji Maton, girgiza kae kawae Umma tayi sannan Abba yace "Alhaji Mato!" da mamaki Umma ta cigaba da kallan Abba har wajen second 30 ba tace komae ba se kuma can tace "Alhaji Mato kuma? D'an sa ko kuma shi kan sa?" "Shi dae kae.." Inji Abba "Wae Alhaji Maton dana sani Abban su?" "Ko shakka babu" Abba ya fad'a a gajarce, jinjina kae Umma ta shiga yi tana sake tuna waye Alhaji Mato, neman auren Ayrah yazo yi? Toh a'ina ma ya san ta? "Lallae mutanen duniya babu kunya" "Wallahi kuwa, ya d'auka wani banzan kud'in sa ze rud'e ni ne, in manta wane ne shi, Mutumin da be san k'addara ba, toh na d'auki 'yata kuma na bashi duk abinda ya same shi ae cewa zeyi itace" Abba ya fad'a yana sake jin takaecin Alhaji Maton "Allah ma ya kyauta Abban su" Umma ta fad'a tana sake jinjina wannan al'amari "Kamar fa har yanzu bata daena kuka ba, kije ki rarrashe ta mana" Abba ya fad'a bayan ya sake jiyo sheshshek'ar Ayrah daga cikin d'akin ta, Umma ta girgiza kae kana tace "Bar ta Abban su, bar ta tayi kukan, dole ne dama tayi, babu amfanin rarrashin yanzu dan koma nayi ba denawa za tayi ba, tun d'azun ta kasa furta komae tun bayan dana gama fad'a mata abinda Baban Raj ya aekata mana" "Allah ya kyauta" shine kawae abinda Abba ya fad'a kawae. ... A 6angaren Rk kuwa koda ya mik'e kae tsaye d'akin Abbu ya wuce yana jin yadda kan sa ya masa wani irin nauyi, haka zalika manyan k'wayar idanun nan nasa ta d'an lumshe kamar me jin bacci, ko sallama be iya yi ba ya fad'a cikin d'akin, dukan su suka kalle shi se dae babu wanda ya tanka masa har ya k'araso ya nemi waje ya zauna yana kallan su su duka, ganin basu da niyyar cewa komae ne ya sanya shi d'aga idanun sa da suka d'an lumshe yace "Abbu ko zan iya sanin dalilin ku na cewa bazan auri Ayrah ba?" yayi maganar yana jin zafin ta har cikin ran sa, dan ko maganar ma baya son furta ta dan kawae ya zama dole ne yayi ta dan sanin aenahin abinda ke faruwa, Abbu be kalle shi ba dan haka kawae yake jin kamar idan ya bari suka had'a idanu da Rk d'in nan take ze fahimto rashin gaskiyar dake tattare cikin idanun sa, Ummee tace cikin zafi "Ka tashi ka bamu waje Malam, idan kuma kana so a fad'a maka abinda ya faru ne mutuncin Baban Ayrahn ya zube a wajen ka toh se kayi magana" ta k'arashe maganar tana d'auke kan ta daga kallan sa, da sauri Abbu ya d'aga ido ya kalle ta cikin mamakin jin furucin ta, ita kam tak'i yadda ta kalli kowa dan bata so k'warin gwuiwar data tattaro su tashi a banza, da mamakin dae ya maeda idanun sa kan Ummee sannan murya a cunkushe yace "Mutunci kuma Ummee?" "Ehh mana, toh kasan abinda ya aekatawa mahaefin ka kuwa? Ina tunanin ae baka manta sanda mahaefin ka ke k'ark'ashin mahaefin Ayrah ba koh?" ta fad'a tana tsare shi da idanun ta, be iya cewa komae ba kawae ya cigaba da kallan Ummeen da lumsassun idanun sa, Ummee ta gyara zama tace "Toh duk uban aekin da mahaefin ka keyi masa cewa yake yi ze biya shi k'arshen shekara, amma da yake Abbun ka me hak'uri ne be ta6a nuna gajiyar sa ba koda kuwa a fuska ne, haka mahaefin ka ya duk'ufa yana masa aeki tuk'uru har zuwa sanda k'arshen shekarar tayi, amma kasan me mahaefin nata ya masa daga k'arshe? Guduwa yayi ba tare daya sallami Abbun kud'in aekin wahalar daya dinga masa kwana da kwanaki wata da watanni ba, ina ganin ko dan wannan abun ae yaci ace ka k'auracewa er mutumin daya yaudare ku koh?" Abba ya d'aga kae da sauri ya kalli Ummee da wani irin kallo irin kallan nan na "Meyasa zaki aekata haka?" se ita kuma ta d'auke kae bayan ta jinjina kae har lokacin fuskar ta a had'e, cigaba da kallan ta Rk yayi yana rarrabe maganar data fad'a d'in, shi sam yama kasa gane alk'iblar wannan magana "Amma kaga da yake Allah ba azzalimin bawan sa bane ae gashi nan yanzu mahaefin ka yayi arzik'in da ba'a so yayi" Ummee ta sake fad'a tana kallan Rk, lumshe idanun sa yayi yana cigaba da sauraron bugun zuciyar sa da yanayin fitar sa ya sauya cikin k'ank'anin lokaci, se a lokacin Abbu ya iya bud'e baki dan yin magana, dan shima ya tabbatar idan ba hakan suka yiwa d'an nasu ba baze ta6a hak'ura ya bar zancen ba, kuma yana ganin lokaci yayi da zasu sake yiwa tufkar hanci dan haka yace "Saboda haka ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, ni na riga na yafewa Abban Sadeeq amma fa bazan iya had'a alak'a dashi ba.." Abbu ya fad'a yana jin maganar tasa wani banbarakwae da ita, ganin har I zuwa lokacin Rk be bud'e idanun sa ba ya sanya shi fad'in "Dan haka ina me farin cikin sanar da kae na nema maka auren er uwar ka Muneerah.. kuma an baka, yanzu abinda ya rage kawae shine tsaeda lokacin d'aurin aure!" idanun sa ya bud'e da wani irin sauri, wanda saboda jimawar da suka yi a rufe ya sanya suka sake lumshewa suka kuma chanja colour daga aenahin colour d'in su zuwa ja, wani irin kallo yake bin Abbun dashi ido cikin ido wanda shi kan sa Abbun ze iya cewa tunda yake be ta6a ganin Rk d'in ya masa irin wannan kallon ba, saboda ya sani Rk d'in yaro ne me tarbiyya da sanin ya kamata amma yau shine ke kallan sa ido cikin ido duk kuma da Abbun ma shima kallan sa yake amma hakan be sanya shi ya janye k'wayar idanun sa ba, cikin murya me kauri kuma a d'an fusace ya furta bayan ya sake k'ank'ance idanun sa "Muneerah!!?" Hhh jama'a ina tunanin kamar yanzu wasan ze soma fa, nasan kan ku ya kulle sosae 🤧🥱 toh babu damuwa ku dae kawae ku cigaba da kasancewa da alk'alami na zaku ji yanda komae ze tafi..🌚😌 Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* *CHAPTER ONE* ✨ *TITAN'S OF TALENT* ✨ Page 029_030 ___Kallan sa Abbu har ma da Ummeen suka yi jin yadda yayi maganar kamar ba shi ba haka zalika idanun sa sunyi jawur fuskar sa babu annuri ko kad'an "Raj!" Abbu ya kira sunan sa ganin har lokacin idanun sa na kan su ne, se a lokacin ya lumshe idanun sa zuciyar sa na wani irin tafasa, haka jijiyoyin kan sa sun firfito saboda tsananin 6acin rae, a hankali ya bud'e idanun nasa da suka sake lumshewa sannan cikin k'arfin hali ya furta "Abbu Muneerah fa kace" "Ehh ko nayi sa6o ne bansani ba?" Abbu ya fad'a yana kafe shi da idanun sa, be sake bi takan kowa ba dan a yadda yake jin ran sa na suya komae ze iya faruwa ya mik'e duk da yadda yake jin d'an jiri jiri na d'ibar sa amma haka ya fice daga d'akin, bin sa da kallo dukan su suka yi har ya fice d'in sannan Ummee ta maeda duban ta kan Abbu tace "Kaga kuwa yanayin yaron nan?" ajiyar zuciya Abbu ya sauke sannan yace "Nagani mana, 6acin ran sa ko wani abun ba shi ne ze sa mu fasa abinda muka yi niyya ba, ina ganin gwara ma ya kwantar da hankalin sa ya kar6e ta hannu biyu a matsayin mata, dan kuwa babu abinda ze hana mu d'aura musu aure idan ranar da zamu tsayar tazo" jinjina kae Ummee ta shiga yi cike da na'am da zancen Abbun sannan tace "K'warae kuwa, kuma ina ganin wannan ce kad'ae hanyar da zamu bi dan ya manta da batun waccan yarinyar" "Ni abinda ke bani mamaki ashe har yanzu Abban Sadeeq na cikin Kano amma bamu ta6a had'uwa ba?" Abbu ya fad'a cike da mamaki, murmushi Ummee tayi kana tace "Allah yana son ka ae shiyasa hakan bata ta6a kasancewa ba" .. Kae tsaye d'akin sa ya koma har lokacin zuciyar sa na masa wani irin zafi, ya kwanta kan gadon sa ringingine yana sauke wani zazzafan numfashi daga bakin sa, hannun sa ya d'ora a kan sa tunani barkatae sunk'i barin k'wak'walwar sa, abubuwa na neman cakud'e masa, ya Abbu yake so yayi da rayuwar sa? Tun farkon rayuwar sa be san wani abu wae shi bijirewa umarnin iyaye ba, se dae gashi yau sun zo masa da wani abu da yake ganin ze iya bijire musu a kan sa, Muneerahn da idanun ta ke a bud'e, wayayyiya wadda wayewar ta tayi yawa, gefe guda kuma ga Ayrah, Ayrahn da yake mutuwar so, son da be san iya adadin sa ba, se dae ga wata k'addara na neman giftawa cikin alak'ar su, meyasa Abban ta zece baze aure ta bayan shine yayiwa mahaefin sa laefi? Meyasa ze yanke wannan d'anyen hukuncin? Duk inda d'iyar sa take yasan tana can zuciyar ta a cunkushe da hukuncin da mahaefin ta ya yankewa rayuwar su, seya mik'e zaune yana mantawa da rayuwar wata Muneerah dan kuwa yasan abu ne me matuk'ar wuya auren su ya yiwu dan baya tunanin ko da bashi da wadda yake so ze iya auran Muneerah duk da kasancewar ta er uwar sa ballantana kuma yana da ita. Wayar sa ya d'auka ya sake kiran number Ayrah se dae kamar d'azun yanzun ma abinda take fad'a masa shine wayar a kashe take, jefar da wayar yayi yana runtse idanun sa lokaci guda kuma yana sanya hannayen sa duka biyu ya cusa su cikin sumar kan sa, meya kamata ya aekata yanzun? Tabbas ba dan dare yayi sosae ba babu abinda ze hana shi tashi ya tafi gidan su Ayrahn dan yasan tabbas Abban ta ne ya k'wace mata wayar dan kada tayi magana dashi, gaba d'aya zuciyar sa ta kasa sukuni ta kasa hutawa ko dae_dae da second d'aya ne a cikin daren nan, bacci kuwa beyi ko da gangancin d'aukar sa ba balle kuma ya d'auke san. ... Tun d'azu yake sintiri cikin d'akin ya kasa zama, ran sa a matuk'ar 6ace yake so yake kawae ya tuna mafita akan wannan al'amari, be ta6a tunanin yarinyar nan da yake so er gidan Ibraheem bace, Muttala dake gefen sa shi kan sa ya kasa cewa komae, kawae yayi shiru ne yana kallan Alhaji Mato, ya kae wajen minti 5 a haka sannan ya d'aga kae yana kallan Muttala fuskar sa d'auke da wani shu'umin murmushi yace "Muttala!" "Na'am yalla6ae" Muttala ya fad'a yana d'aga kae ya kalle shi, Alhaji Mato ya nemi waje ya zauna kan kujera sannan ya fara magana "Ayi yadda za'ayi a d'akko min yarinyar nan daga daren yau zuwa safiyar gobe bana son 6ata lokaci.." kallan sa Muttala yayi sannan yace "Ranka ya dad'e satowa kuma?" shima kallan sa Alhaji Maton yayi kana yace "K'warae kuwa, zan tafi da ita wani k'auye dana ta6a zuwa aeki, acan zan samu wanda ze d'aura mana aure" jinjina kae Muttala yayi kana yace "An gama ranka ya dad'e, In Sha Allah zaka ji ni daga yau d'in zuwa gobe" jinjina kae Alhaji Mato yayi yana murmushi a ran sa yana ayyana yadda Ayrahn zata zama mallakin sa. ... Washe gari da safe wajen k'arfe 7 yana sanye cikin k'ananan kaya da suka matuk'ar amshe shi, se dae fuskar sa a cunkushe take kamar wanda akama mutuwa, haka zalika idan ka lura ma da kyau zaka ga har wani 6urmawa idanun sa suka yi, se dae da yake shi d'in na musamman ne hakan ma k'ara masa kyau yayi, wayar sa ya sake d'auka ya sake danna kiran ta a karo na barkatae, daga wannan kiran baya tunanin ze sake kira se dae kawae a tsince shi a k'ofar gidan nasu, cikin sa'a se yaji wayar na ringing, babu shiri ya mik'e tsaye zuciyar sa na cigaba da bugawa tare da sautin yadda ringing d'in ke fita. A 6angaren ta kuwa ita kan ta bata samu ta rintsa ba tun jiyan, data gama kukan ta kawae seta kwanta tayi shiru abin ta tana tunanin halin d'an adam, koda Asuba ma kafin kowa ya fito ita ta riga kowa fitowa tayi alwala tayi Sallah ta koma ta kwanta har lokacin idanun ta suna nan a yadda suke sun yi jawur haka zalika sun kumbura. Tana nan zaunen ta janyo wayar ta ta kunna ta sannan ta shiga contact a hankali ta lalubo number sa zuciyar ta na cigaba da harbawa da k'arfin gaske, tana so tayi fatali da duk wani abu daya ke so ya kawo mata cikas dan haka ta d'an runtse idanun ta sannan ta bud'e ta sake d'ora idanun ta kan jerarriyar special number sa, tana shirin yin blocking number tasa sega kiran sa ya shigo, seta tsaya tana sake k'arewa number kallo kamar me son karanto wani abun, tabbas ya kamata ta isar da abinda ke ran ta, ta fad'a masa babu ita babu shi koda hakan zesa ya rabu da ita kada ya sake gigin koda kiran ta ne, dab da zata tsinke ta d'aga wayar, daga 6angaren sa ya sauke wata 6oyayyiyar ajiyar zuciya sannan yace a hankali kuma a tausashe yana son kawar da duk wani 6acin ran dake d'awaeniya dashi "Ayrah!" da sauri ta runtse idanun ta tana jin yadda zuciyar ta ke bugawa ta kae wajen second 30 a haka sannan ta bud'e, dan shi har ya fara tunanin ko Abban ne ya d'aga da kan sa seya ji ta tana fad'in "Kada ka sake kira na, ka manta ka ta6a sanin wata me suna na ko me kama ta ballantana ni, kayi k'ok'ari ka goge duk wani lokaci da muka ta6a kasancewa tare, ka manta da babin rayuwa ta, kada ka sake kira na a waya dan kuwa har abada bazan ta6a auran mutum irin ka ba" daga haka ta katse wayar bata jira yace komae ba ta jefar da wayar a gefen ta tana fashewa da kuka lokaci guda kuma tana tuna yadda ta kawowa Abba Rk a farko amma daga k'arshe su suka koma cikin arzik'in yayin da suka tura su su kuma suka koma cikin k'uncin rayuwa. Tsayawa yayi kamar wani sak'ago, ya sauke wayar daga kunnen sa yana sake k'arewa wayar kallo, anya kuwa ita d'in ce? Anya kuwa Ayrahn sa ce? Menene haka ya faru wanda ya chanja mata ra'ayi haka daga daren jiya zuwa yau d'in? Me akace mata yayi da zata jefe shi da wad'annan kalmomin? Tabbas da tasan yadda kalmomin nata suka jefa shi cikin wani irin yanayi da bata fad'a masa ba, meya same ta haka? Shin ba shine ya kamata ya fad'i hakan ba tunda iyayen tane suka yiwa nasa iyayen laefi ba? Amma beyi hakan ba se ita? Kodae dama bata son sa ne tuntuni? Ko kuwa dae akwae wani 6oyayyen al'amari wanda dukan su basu sani ba? Lallae ya zama dole yasan gaskiyar al'amarin nan, yasan dalilin Ayrahn na jifan sa da wad'annan muggan kalaman, zuciyar sa dake masa wani irin zafi tana kuma harbawa da k'arfi ya danne da hannayen sa yana runtse idanun sa, ya kae wajen minti d'aya a hakan sannan ya bud'e idanun sa yana fesar da iska me zafi daga cikin bakin sa sannan kae tsaye ya fice daga d'akin bayan ya d'auki mukullin motar sa. Da sassarfa ya k'arasa inda motar tasa take ya shiga ya tashe ta da sauri duk da shi d'in ba ma'abocin gudu bane, Abbu da fitowar sa kenan daga parlourn sa yaga tashin motar Rk d'in, mamaki ne ya kama shi sosae dan shi kam yayi tunanin tun yau Rk d'in ze koma asibiti bakin aeki, dan shi indae ta 6angaren sa ne babu lokacin 6atawa, kowanne lokaci baya barin sa ya tafi a banza seya nemo abinda zeyi a cikin lokacin wanda ze saka ya samu kud'i, shiyasa ko lokacin da Rk d'in yaje Zaria yaga baze iya barin sa haka nan babu wani abun daze samu kud'i ba, dan haka shi in dae ta shine tunda jiya ya dawo toh yau ma ya d'ora kan aekin babu wani 6ata lokaci "Toh ina ze je haka?" Abbu ya tambayi kan sa, ganin dae babu wanda ze amsa masa tambayar ne ya sanya shi cigaba da tafiya a ran sa yana cigaba da tunanin inda Rk d'in zeje. ... Driving yake yi amma har lokacin tunani yak'i barin ruhi da k'wak'walwar sa, shi likita ne yasan illar da tunani kan iya haefarwa dan ya kan sha bawa mutane shawara akan hakan, amma a wannan karon shi kan sa ya kasa hana kan sa, se yanzu ya fahimci ashe idan k'wak'walwa na son yin tunani ba mutum ke tsarawa kan sa yin tunanin ba ita da kan ta take yin tunanin kuma babu yadda ka isa kayi da ita. A haka dae har ya k'arasa unguwar ta su yana tuna kwatancen data masa, a d'an nesa kad'an ya tsaya da gidan yana kallan cikin layin da babu kowa kasancewar safiya ce dan kuwa har lokacin ko 8 ba tayi ba, seya d'aga lumsassun idanun sa dake d'auke da bacci ya dubi gidan a ran sa yana sak'a tabbas nan d'in ne in dae yabi kwatancen data masa dae_dae, wayar sa ya janyo da take ajje kan kujerar kusa dashi ya danno number ta cike da fatan ta d'aga wayar, se dae addu'ar sa bata kar6u ba dan kuwa har ta gama ringing d'in bata d'auka ba tana kuma jin wayar na ringing ta san me kiran shiyasa tak'i kula wayar, wani kiran ne ya sake shigowa seta mik'e daga kwanciyar da take tana ganin blocking d'in da tayi niyyar yi tun d'azun shine kawae mafitar da tasan idan tayi ze dena kiran ta, kafin takae ga aekata abinda tayi niyya Umma ta d'aga labulen d'akin ta lek'o "Ayrah ki fito ki samu wani abun ki ci" se ta d'aga kae da sauri sannan ta furta "Toh.." kawae, itama Umman bata takura ba dan tana so ne ta bari ta gama kukan ta sannan ta rarrashe ta, idan ba haka ba tasan yanzu tunzura ta kawae zata yi, Umman na fita Ayrah ta maeda kallan ta kan wayar dae_dae lokacin da wani sak'o ya shigo cikin wayar, seta dakata ta shiga cikin sak'on, gajeren sak'o ne daga number Rk a hankali ta shiga karantawa "Don Allah ki fito ina k'ofar gidan ku, inaso naji tabbacin maganar dake fitowa daga cikin bakin ki, ina so na tabbatar da abinda kunnuwa na suke ji" fuskar ta a matuk'ar tamke haka zalika ran ta ya sake 6aci, tana ga lokaci yayi da zata kira shi da sunan dake ta yawo a cikin k'wak'walwar ta koda hakan zesa ya fahimci ta gane wanene shi da mahaefin sa, ko kuwa ya d'auka saboda son da take masa zata iya fatali da umarnin iyayen ta? Ko kuwa me yake nufi da ita? "Butulu" shine sunan dake ta yawo a k'wak'walwar ta, wayar ta ta ta d'auka ta danna number sa a blocking sannan ta jefar da ita gefe ta mik'e tana sanye cikin doguwar rigar atamfa ta zari hijab ta saka sannan ta lek'o tsakar gidan tana hange, babu kowa a tsakar gidan taji dad'in hakan dan bata so ta sake 6atawa Abba ko Umma rae daga dawowar ta jiya bayan 6acin ran data saka musu a jiyan, a hankali ta shiga takawa cikin tsakar gidan har zuwa sanda ta fice daga cikin gidan... ... Wanda ke driving d'in ya kalli Muttala yace "Nifa na gaji wallahi, tun jiya muke a wajen nan amma har yanzu banga alamar zata fito ba" tsaki Muttala yaja kana yace "Gaggawar ta menene? Wallahi idan ta nine bank'i mu sake kwana cikin motar nan ba tunda dae babu wanda ya ganmu har yanzun" Muttala ya fad'a har lokacin idanun sa na kan k'ofar gidan su Ayrah.. A dae_dae lokacin ne Ayrah ta fito daga cikin gidan, a hankali ta shiga bud'e manyan idanun ta dan hango inda motar sa take. A lokacin ne shi kuma kiran Abbu ya shigo wayar sa, seya d'auki wayar yana karawa a kunnen sa idanun sa a lumshe dan yanzu kuma be san da wanne Abbun yazo ba gashi kuma rok'on da yayi wa Ayrah baya tunanin taji ta kar6a zata fito, se abin ya sake masa yawa, daga can 6angaren Abbu yace "Ka shiga asibitin ne?" shiru yayi na d'an wani lokaci kafin a hankali ya bud'e bakin sa bayan ya kae hannu ya shafa kwantaccen sajen dake kwance luff luff akan fuskar sa "Abbu ban shiga ba tukunna" shiru Abbu yayi yana sake karanto yanayin Rk d'in daga cikin muryar sa, yace a hankali "Ko dae akan maganar dana maka jiya ce?" shiru yayi dan ko ya bud'e bakin sama be san abinda zece ba, Abbu yace "Toh ka bud'e kunnen ka da kyau kaji, in dae akan maganar nan ce ka kwantar da hankalin ka kamar an riga an d'aura muku aure ne da Muneerah, dan haka ina ganin ka ajje komae a gefe ka koma bakin aekin ka" kafin yace komae Abbun ya katse wayar, seya jefar da wayar yana sake jin yadda yanayin nasa yake sake ta'azzara, abubuwa na neman yiwa zuciya da k'wak'walwar sa yawa. A hankali ta cigaba da takawa har lokacin fuskar ta babu walwala manyan fararen idanun nan nata sun yi zuru zuru kamar mara lafiya, da sauri wanda ke driving cikin motar ya bud'e k'ofa ya fita yayin da Muttala ya koma mazaunin driver, seda ya kalli cikin layin ya tabbatar babu kowa sannan ya k'arasa inda Ayrah take, ita sam hankalin ta be kae kan sa ba yana kan motar Rk da take kalla dan tabbatar da tasan ce, beyi wata wata ba ya matsa bayan ta ya shak'a mata wani abu dake jikin handkerchief d'in hannun sa, lumshe idanun ta tayi tana jin wani irin yanayi cikin kan ta kafin a hankali ta kae hannun ta tana shirin dafe kan ta, take wani jiri ya d'ebe ta cikin sakannin da basu wuce 10 ba ta fice a hayyacin ta se kawae tayi baya zata fad'i mutumin ya saka hannun sa ya tare ta ya jata zuwa cikin motar har lokacin yana d'an juyawa bayan sa dan tabbatar da babu wanda ya gan shi, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin k'arasa shigewa da ita cikin motar Rk ya bud'e idanun sa daga lumshe sun da yayi tun d'azun, kamar ance ya kalli wajen se kawae ya hange ta jikin wani mutum yana cusa ta cikin mota, seya sake rufe idon ya bud'e dan tabbatar da abinda ya gani d'in gaskiya ne ko kuwa idanun sa ke masa gizo, cikin wani irin zafin nama ya tura k'ofar side d'in da yake yana shirin fita zuciyar sa na wani irin zafi tana cigaba da harbawa kamar zata faso k'irjin sa, Muttala yaja motar da k'arfin gaske tun kafin ma mutumin ya gama saka Ayrahn cikin motar, seya koma da sauri zuciyar sa na bugawa yama kasa tunanin komae kawae ya figi motar da wani irin gudun da tunda yake ze iya cewa be ta6a yin irin sa ba, sosae su Muttala suke gudu kamar zasu tashi sama yayin da shima ya cigaba da bin su, kawae burin sa ya san inda zasu je, ina zasu kae ta? Me zasu mata? Meyasa suka d'auke ta? Kwata kwata tunanin sa be kae ya kira police ya sanar dasu ba kawae shi dae burin sa ya cim masu. Sosae suka cigaba da tafiya kuma inda Allah ya taemake su kwata kwata basu samu traffic jam ba, mamaki ya sake kama shi ganin se tafiya suke yi kamar baza su dena ba, har lokacin kuma bugun da zuciyar sa take be ragu ba, haka ya cigaba da bin su zuwa lokacin da yaga sun fara barin gari suna shiga cikin wani waje daya fi masa kama da k'auye, mamaki ya sake kama shi amma da yake baya so su gane akwae wanda ke bin su seya dakata har zuwa sanda suka masa nisa sannan ya cigaba da bin su a nutse yana yi yana lumshe idanun sa saboda yadda yake jin jikin sa ya masa wani iri ga yadda bugun zuciyar sa ke ta k'aruwa. Dae-dae wani madaedaecin gida ya hango su sun yi parking d'in motar su, ze iya cewa tunda suka shigo k'auyen bega gida me kyan sa ba dan kuwa duk gidajen k'asa ne yayin da wannan d'in ya kasance ginin bulo ne, Muttala ya fita ya bud'e k'ofar gidan da mukullin hannun sa sannan ya dawo ya tashi motar zuwa cikin gidan kana ya saka mukulli jikin gate d'in sannan ya sauke ajiyar zuciya "Da alama mun tsira fa" ya fad'a yana fesar da iska daga bakin sa, mutumin da shima ya fito daga cikin motar yace "Wallahi kuwa, kayi maza ka kira mana Alhaji ka sanar dashi mun gama aekin mu" murmushi Muttala yayi kana ya fito da wayar sa ya lalubo number Alhaji Mato, tun kafin Alhaji Mato yace komae Muttala yace "Yalla6ae albishirin ka?" daga inda Alhaji Mato yake ya saki wani murmushin jin dad'i yana shafa tumbin sa, ko Muttalan be fad'a ba yasan sun yi nasara, amma saboda ya sake tabbatar wa ya sanya shi fad'in "Goro.." "Mun gama aekin mu, yanzu haka gamu a cikin gidan yalla6ae" "Weldone, ku jira ni yanzu zan taho.." Alhaji Mato ya fad'a yana jin wani irin dad'i na ratsa shi, yasan tabbas yau d'in Ayrah zata kwana ne a matsayin matar sa, baya shakkar wannan tunda dae an riga da an samo masa ita. .... A 6angaren Ummee kuwa ganin har bayan wajen awa d'aya Ayrahn bata fito ba seta mik'e ta sake komawa d'akin nata, gwara ta rarrashe tan kawae ko zata samu ta saki ran ta ta cigaba da harkokin ta, a hankali ta yaye labulen d'akin idanun ta kan gadon data san akae zata sami Ayrahn, se dae ga mamakin ta babu kowa kan gadon babu ma alamar akwae mutum cikin d'akin, sauke labulen tayi a ran ta tana ayyana babu mamaki tana cikin toilet, se kuma kwanyar ta ta tuna mata ae yanzun ta fito daga ban d'akin, dan saboda ta tabbatar da gasken bata cikin band'akin ya sanya ta k'arasa toilet d'in, k'ofar sa a bud'e take amma duk da haka seda ta shiga ta duba bata ga kowa ba, k'irjin ta ya buga tana tuna yadda suka rabu da Ayrahn jiya, kada dae halin en yau zata nuna musu? Kada dae ace d'iyar ta ta ta chanja hali bata sani ba? Kada dae ace d'iyar ta ta ta za6i d'a namiji akan su? Tsara hakan cikin ran ta yasa ta sake jin jikin ta yayi mugun sanyi, a hankali taja k'afafun ta zuwa d'akin Abba, Abba ya kalle ta da mamaki ganin yanayin ta yace a hankali "Lafiya kuwa Ruk'ayyah?" "Bana tunanin haka" Umma ta fad'a tana jin wasu zafafan k'walla na zubo mata "Subhanallahi, meya faru?" Umma bata tabbatar ba dan haka a ran ta taji gwara ta bari ta sake tabbatarwa ko fita tayi ta siyo wani abun dan haka seta furta "Babu komae" "Ya zaki ce babu komae kuma? Bayan kin fita lafiya, yanzu kuma kin dawo kina kuka?" "Babu komae" ta sake fad'a tana cigaba da share k'wallar dake ta zubar mata. Wasa_wasa se gashi Ayrah har wajen azahar babu ita babu labarin ta zuwa lokacin tuni Umma ta gama na'am da abinda take zargi "Ina yarinyar nan ne? Ko har yanzu baccin take?" Abba ya fad'a yana kallan Umma, kawae seta fashe da kuka tana jin wani iri a cikin zuciyar ta, a yau d'aya tana jin kamar tayi danasanin haehuwar Ayrah amma ta kasa, amma duk da haka yarinyar ta shammace ta, ta shammace ta aenun, bata ta6a tunanin hakan daga gare ta ba "Abban su yarinyar nan ina tunanin ta gudu da wancan yaron, ashe shiyasa ta kasa ce min komae tunda taji abinda ya faru, ashe tace kya yi kya gama bazan rabu da shi ba, Abban su yarinyar nan ta bani mamaki" dafe saetin zuciyar sa Abba yayi yadda yaji ya wani irin buga, seya shiga tari, saboda tsananin tashin hankali babu wanda ya iya kula shi, seda Yah Sadeeq ya dawo daga shocking d'in da maganar Umman ta shigar dashi sannan ya d'auki ruwan gaban sa ya mik'awa Abba, kar6a Abba yayi ya sha kana ya koma sauke ajiyar zuciya, kafin ya d'ago ya kalli Umma da har lokacin take share hawaye a fuskar ta "Waye ya fad'a miki hakan?" "Tun d'azu na neme ta na rasa cikin gidan nan Abban su, ko ka ta6a ganin Ayrah ta fita babu izinin wani a cikin mu? Abban su yau nayi nadama.." "Ya isa haka Ruk'ayyah" Abba ya fad'a yana d'aga mata hannu "Bar ta taje, in dae bijirewa umarnin iyaye ne taje gata ga duniyar, kada muyi mata baki saboda ni uba ne ke kuma uwa ce kada ya kama ta, amma ni kae na yau Ayrah ta wulak'antani a rayuwa.." kallan su kawae Yah Sadeeq yake yi ya kasa cewa komae, ya kasa koda bud'e bakin sa ne ya furta wani abu, dan maganar ta shige shi, bashi da bakin da ze iya k'arya ta wannan maganar ko kuma ya musa, toh idan ya musa d'in mene hujjar sa ta yin hakan? Meze kawo a matsayin hujjar sa? Amma meyasa Ayrah zata yi haka? Meyasa zata za6i d'a namiji akan iyayen su? Iyayen da suka d'auke ta tun ciki har tazo duniya suna d'awaeniya da ita har kawo yanzun basu gaji ba? Duk wani tunanin su akan ta ne, duk wani burin su akan ta, meyasa zata saka musu ta hanyar za6ar wanda ta had'u dashi rana tsaka a rayuwar ta? Ta fifita d'a namiji akan su??. ... Yana cikin motar har lokacin idanun sa na kan gidan yana tunanin yadda zeyi ya shiga cikin gidan, idan ya tuna maza ne har biyu suka d'auki Ayrahn suka shigar da ita cikin gida se yaji wani sabon tuk'uk'i da kuma wani zafi na cigaba da azalzalar sa cikin zuciya, seya bud'e murfin motar a hankali ya zuro k'afar sa dake cikin wani had'ad'd'en takalmi hannun sa akan goshin sa yana d'an murzawa, daga ganin mutanen da suka d'auke ta kasan sanya su akayi, kuma gidan da suka kawo ta babu alamar akwae mutum a ciki, kenan idan haka ne ogan nasu ze zo kuma ze nemi a bud'e masa k'ofar dan shiga gidan "Exactly" ya fad'a yana sake bud'e idanun sa, seda ya fesar da wata zazzafar iska daga bakin sa sannan ya cigaba da zama cikin motar har lokacin gaba d'aya hankalin sa na kan gidan gefe guda kuma yana jiran yaga ta inda wani ze 6ullo. ... Zubewa yayi a gaban me garin yana d'aga hannun sa alamar girmamawa "Allah ya taemake ka yalla6ae" wani matashi da zeyi 25 years ya fad'a kan sa a k'asa, me garin bece komae ba ya cigaba da kallan Mubarak yana jiran jin abinda ze fad'a "Yalla6ae acan gidan Alhaji Mato naga wasu bak'in fuska sun shiga gidan, ban ta6a ganin su ba kuma naga kamar basu da gaskiya" Mubarak ya fad'a har lokacin kan sa na a k'asa, seda me gari ya d'an numfasa sannan yace "Gidan Alhaji Mato?" Me gari ya fad'a, Mubarak ya sake jinjina kae kana yace "K'warae kuwa yalla6ae nima nayi mamaki" d'an shiru Me garin yayi sannan yace "Aje a zo min dasu" ya fad'a a nutse "An gama ranka ya dad'e" Mubarak ya fad'a yana mik'ewa ya bar wajen. ... Suna zaune a tsakar gidan Muttala ya kalli wanda suke tare yace "Kodae mu fito da ita, kada zafi ya mata illah" "A'ah mu k'yale ta, mu dae ba aekin da aka saka mu ba kenan? Ina ruwan mu? Gwara kawae mu jira yazo shi yasan yadda za'ayi da ita" jinjina kae Muttala yayi kana yace "Hakane kuma" babu wanda ya k'ara cewa komae a cikin su har zuwa sanda suka ji ana knocking k'ofar, da mamaki dukan su suka yi shiru suna saurarar knocking d'in sa ake dan tabbatarwa "Wallahi da gaske k'wank'wasawa akeyi, waye kenan?" "Ko dae Alhajin ne ya iso?" mutumin ya tambaya yana kallan Muttala, girgiza kae Muttala yayi kafin yace "No bana tunanin haka gaskiya, idan shine ae akwae mukulli a hannun sa" Muttala yayi maganar yana mik'ewa a hankali ya k'arasa dab da gate d'in sannan yace "Wanene?" Mubarak ne yace "Daga gidan Me gari ne, me gidan yana nan?" se Muttala ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "A'ah be iso ba tukun" "Toh Me gari na neman ku" Mubarak ya sake fad'a, kallan juna Muttala suka yi shida mutumin nan sannan Muttala ya d'aga kafad'a kafin a hankali ya furta "Babu wata matsala fa" jin abinda ya fad'a ne ya sanya mutumin k'arasawa ya bud'e gate d'in sannan suka fara k'ok'arin fitowa daga cikin gidan "Ku kad'ae ne a cikin gidan?" Mubarak ya sake tambaya, mutumin nan na shirin cewa "Ehh" Muttala ya girgiza kae da sauri kana yace "A'ah akwae matar Oga amma bacci take" "A taso ta itama ta fito, Me gari ke neman ku ku duka" had'iye yawu Muttala yayi kana ya koma cikin gidan ya k'arasa ya bud'e motar cikin tunanin yadda za'ayi ta farka saboda abinda suka shak'a mata, cikin sa'a seya hango wani ruwa wanda d'azun ya sha ya ajje ragowar, da sauri ya janyo kana ya bud'e ya fara zuba mata a fuska, seda ya kusa juye mata ruwan sannan ta fara bud'e dara daran idanun ta da suka sake komawa ciki saboda wahala, a hankali ta dinga bud'e su har ta gama ware su tarr cikin motar, idanun ta suka sauka akan Muttala, da sauri ta mik'e ta fara komawa baya tana shirin sakin k'ara Muttala ya girgiza mata kae da sauri yana d'ora hannun sa akan bakin sa sannan yace a hankali ganin yadda ta gama rikicewa gaba d'aya "Kada kice komae, kiyi shiru taemakon ki zan yi" yayi maganar har lokacin yana kallan ta, cigaba da girgiza kae tayi hannun ta d'ore akan bakin ta hawaye se sintiri suke akan fuskar ta "Ki dena kukan taemakon ki zan yi fa" ya sake fad'a ganin kamar bata ji abinda ya fad'a da farko ba "Kiyi shiru kada ki nuna a tsorace kike kin ji, ko me kuma za'a ce miki kada kice komae, komae kika ji an fad'a ke dae ki bisu a haka" ya fad'a a nutse dan gudun kada ta tona musu asiri a gaban jama'a, haka kawae taji tayi na'am da zancen mutumin dan haka seta jinjina kae sannan yace "Fito muje" babu musu ta sanya k'afa ta fito se dae har lokacin k'irjin ta be bar bugawa ba haka zalika tana mamakin ko nan d'in ina ne? Waye ya kawo ta? Yaushe suka zo? Ya akayi suka zo nan d'in? Su waye su? Meyasa suka kawo ta nan d'in? Amma koma dae menene tunda wannan mutumin ze taemaka mata bari ta zubawa sarautar Allah ido, seta sake bud'e idanun ta tana kallan gidan sanda Muttala ke fad'in "Yawwah ga ta" Mubarak ya kalle ta sannan yace "Toh ku wuce muje" babu musu duka suka fito daga gidan sannan suka kulle, tafiya take a hankali kamar wata mara laka tana cigaba da kallan garin da be mata kama da birni ba, ji take kamar ta saka kuka amma idan ta tuna abinda mutumin ya fad'a seta d'an lumshe idanun ta ta had'iye hawayen. Tunda suka fito idanun sa ke kan su, seya saki wata k'atuwar ajiyar sanda ya hange ta ta fito daga cikin gidan tana tafiya cikin k'oshin lafiya "Thank god" ya fad'a yana fitowa daga cikin motar gaba d'aya, seda suka kusa zuwa gidan Me garin yana hango su sannan yabi bayan su cike da tunanin inda zasu je d'in. A inda Me gari ya saba zama suka isa sannan dukkan su suka tsaya, Mubarak ya kalle su yace "Ku zauna dukan ku" Ayrah ta d'aga kae a hankali ta kalli Muttala seya jinjina mata kae irin kamar nufin sa babu wanda ya gan shi, bata iya zama ba seda taga shi kan sa Muttalan ya zauna sannan ta raku6e waje d'aya kamar munafuka tana matse k'walla, zubewa Mubarak yayi a wajen sannan yace kan sa a k'asa "Yalla6ae gasu nan" kallan su Me gari yayi su duka, ita kuwa Ayrah gaba d'aya jikin ta rawa kawae yake yi har yanzu ta kasa gane mak'asudin zuwan ta wajen, dan kuwa sam ta kasa tuna yadda akayi tazo nan wajen, gyaran murya Me gari yayi sannan ya fara magana a nutse "Meya kawo ku gidan nan? Ina Alhaji Mato?" dae_dae lokacin wayar Muttala ta fara ringing, seya fiddo ta daga cikin aljihun sa, ganin me kiran ya sanya shi d'aga kae a hankali ya saci kallan Me gari sannan ya maeda kan sa kan wayar kawae ya d'aga, ban ji me akace daga can 6angaren ba na dae ji Muttalan yace "Muna wajen Me gari dukan mu" se kuma yayi shiru can kuma yace "Toh seka k'araso" Muttala ya fad'a yana katse wayar sannan ya kalli Me gari yace "Yalla6ae yanzu ma Alhaji Maton ze zo da kan sa" "Ahh toh Masha Allah" Me gari ya fad'a yana gyara zaman sa. Shiru ne ya wanzu a wajen na tsawon mintuna har zuwa lokacin da Alhaji Mato ya k'araso wajen da sallama cikin shadda kamar ko da yaushe me babbar riga, tumbin nan nasa kullum kamar k'ara ha6aka yake yi ya samu waje ya zauna abin sa, haka jajayen idanun sa ma sun k'ara wani ja kamar me ciwon ido, ya zube gaban Me gari da fara'a akan fuskar sa "Barka da wannan lokaci Ranka ya dad'e yalla6ae" ya fad'a yana d'aga hannun sa alamar girmamawa "Barka dae Alaji Mato, ashe ma kana kan hanya, kasan mutane ba abin yadda bane shiyasa na saka amin bincike, amma tunda ga ka kazo seka d'auki bak'in ka ku koma" gyara zama Alhaji Mato yayi yana satar kallan sahibar tasa da yaga ta k'ara masa kyau yace "Wato yalla6ae dama wajen ka nazo gaskiya" "Toh Ikon Allah, Allah yasa dae lafiya" Me gari ya fad'a shima yana gyara zaman sa, seda Alhaji Mato yaja numfashi sannan ya sake gyara zaman sa yana tunanin ta inda ze fara "Yalla6ae wannan da kake gani mata ta ce, tsautsayi yasa na sake ta kuma ban maeda ta ba har ta gama idda, shine nake so a maeda mana auren mu yalla6ae dan nasan aekin ka ne wannan d'in" d'aga kae Me gari yayi ya kalli Ayrah dake zaune tana jin maganar da Alhaji Mato yake yi ba dan tana fahimtar sa ba, ko kuma ta fahimci akan ta ake magana ba "Ikon Allah" shine abinda Me gari ya fad'a kawae sannan ya sake yin gyaran murya yace "yanzu a take kake nufi?" da sauri Alhaji Mato ya sake yin wani murmushin kafin yace "Ehh Ranka ya dad'e yalla6ae" "Allah ya gafarta malam ni ne nake neman auren ta yanzu, kuma muna son junan mu" dukkan su suka d'aga kae suna kallan me maganar cike da mamaki, da wani irin sauri ta d'aga kae ta kalli me maganar dan ta tabbatar wa da kan ta abinda take tunani, ita gaba d'aya kan ta ya kulle, har tana so ta dena gane komae, magana ake tayi gashi dae a gaban ta amma bata ganewa, bata fahimta, bata fuskan ta, ji take kamar dukan su wani yare suke yi, shin akan wa suke magana? Akan wata mace suke magana? Cigaba tayi da kallan sa sanda yake neman waje ya zauna yana lumshe idanun sa saboda gudun da bugun zuciyar sa keyi wanda ya wuce misali, ba k'in biyan kud'in shekara ba baya tunanin ko da abinda yafi hakane ya shiga tsakanin Abbu da Abba ze iya bari Ayrah ta auri wanin sa, wanin ma a gaban sa, Abba yace baze auri er sa ba se gashi wani ya d'auko ta wata uwa duniya dan a d'aura musu aure, toh meyasa baze yiwa kan sa wannan fad'an har yayi winning ba? Ko me zeyi se yayi yadda yayi aka d'aura musu aure a garin nan ba da wannan k'aton mutumin ba dashi za'a d'aura, tun da yasan ko d'aukar ta yayi ya maeda ta gidan su daga nashi iyayen har nasa ba amincewa zasu yi da auren junan su ba, dan haka ze zage damtse yasan yadda zasu yi suyi auren sirri in dae hakan ce mafita, ya ceci zuciyar sa sannan ya ceci Ayrah daga hannun wannan mugun mutumin "Malam daga ina kae kuma?" Me gari ta fad'a yana kallan Rk, ajiye numfashi Rk yayi sannan yace har lokacin be kalli kowa ba "Soyayya muke yi da ita, kuma bazan iya bar wa wani ita ba" yayi maganar a nutse kae ba zaka ta6a cewa tsara zancen yayi ba, bin sa da kallo Alhaji Mato yake yi dae_dae lokacin da Rk ya d'aga kan sa ya watsa masa wani banzan kallo me nuni da abubuwa da dama, da sauri Alhaji Mato ya d'auke kan sa yana jin tabbas idan yace wani abun asirin sa ka iya tonuwa mutuncin sa ya zube a banza, dole yayi tunanin mafita, d'aga kae Me gari yayi ya kalli Ayrah dake zaune kamar wadda aka kafe ta yace "Toh ke kin ji? Shin kina da ta cewa?" se a lokacin Ayrah ta d'aga kae ta kalli Me gari tana jin zuciyar ta kamar zata tarwatse, kwata kwata ta kasa bud'e bakin ta ballantana tace wani abu, toh ta bud'e d'in ma tace mene? Gaba d'aya ta kasa fahimtar wannan wasan kwaekwayon da suke gabatarwa a gaban ta, a hankali ta shiga tuna maganar Muttala se kawae ta shiga girgiza kae kamar wata kad'angaruwa, sauke numfashi Me gari yayi sannan ya kalli Alhaji Mato da kuma Rk yace "Ina ganin dukan ku ku tashi ku tafi, zan rik'e ta a hannu na zuwa gobe kafin a kira magabatan ta, gobe bayan an sakko daga masallaci ni da kae na zan d'aura mata aure da wanda ta za6a a matsayin wanda take so!" dukan su kallan Me garin suke yi, Alhaji Mato yana ji kamar ya tashi ya rufe Rk da duka, idanun nan nasa suka k'ara yin jawur, ta 6angaren Rk kuwa gaba d'aya tunanin sa ya tafi yadda zeyi ya shawo kan Ayrahn ta amince da auren sa cikin garin nan. Kamar wata kurma doluwa kuma bebiya haka take bin wadda akace ta mata jagora zuwa cikin gidan Me garin, har lokacin ta kasa amincewa ba wasan kwaekwayo akeyi ba, a haka har suka k'arasa cikin wani madaedaecin d'aki seda ta zauna sannan wadda ta kawo tan ta fice daga d'akin. ... A zaune take kamar wata munafuka cure waje d'aya, kuka kawae take yi cikin rashin sanin abin yi, wannan mutumin kawae take jira yazo ya mayar da ita gida amma har yanzun shiru, ta rasa gane dalilin ta na zuwa k'auyen nan, abinda ya sake jefa ta cikin wani mad'aukakin mamaki shine ganin Rk da tayi, shin ko dae mafarki take yi ne bata sani ba? Tabbas ma babu mamaki mafarkin take yi dan kuwa wannan dae yafi kama da mafarkin. Tana nan zaune bata umm bata umm umm tunda kuma ta zauna ta kasa koda kae ruwa bakin ta ne ballantana akae ga cin abincin da aka dinga dire mata, ita bata ta su take yi ba, abinda kawae take buk'ata yanzu shine ta samu waya ta kira Abban ta ko Yah Sadeeq amma har yanzu bata ga wanda zata iya samun waya a wajen sa ba "Ki zo ana neman ki" wata mata ta fad'a tana kallan ta, da mamaki ta d'aga kae ta kalle ta sannan cikin k'arfin hali ta furta "Don Allah zan iya samun waya a wajen ki?" da mamaki matar ta kalle ta cike da mamakin yadda taji tayi magana dan kuwa ta d'auka bebiya ce, se kawae ta girgiza kae tana cigaba da kallan kyawun Ayrahn da duk da yadda take a firgice hakan be hana shi fitowa ba "Muje koh?" matar ta fad'a tana cigaba da kallan ta, se kawae ta mik'e cikin rashin sanin abinyi tabi bayan matar kamar rak'umi da akala, a soron gidan suka tsaya sannan matar ta kalli Rk dake tsaye jikin bangon soron idanun sa a lumshe kamar me bacci "Don Allah kada ku dad'e, kaga dae da yadda akayi na barka ka shigo gidan nan, da Baba ma ya sani baze bari ba wallahi" "Nagode" ya fad'a yana bin ta da kallo sanda ta koma cikin gidan, wanda Ayrah ta gani ne ya sanya tayi kicin kicin da fuskar ta tana shirin komawa ciki yace a nutse "Batu ne akan auren ki da za'a gabatar gobe" kamar wadda aka tsaeda ta seta dakata tana jin bugun zuciyar ta na k'aruwa, murmushi yayi ganin yaci nasara tunda gashi har ta tsaya, kafin yace komae ta juyo tana kallan sa murya a raunane tace "Bana buk'atar taemakon ka, ban ce ka maeda ni gida ba dan bana buk'atar hakan daga gare ka, abinda nake so kawae shine ka bani aron wayar ka zan kira Abba na na sanar dashi inda nake zezo ya d'auke ni" kallan ta ya cigaba dayi yana jin muryar ta ta dake fita a raunane har cikin kwanyar sa, wani irin tausayin ta mara misaltuwa na ratsa shi amma yasan abinda zeyi, ya furta "Kada kiyi wannan kuskuren, kada ki sake ki kira Abban ki, dan kuwa babu wanda ze yadda dake akan ba guduwa kika yi da kan ki ba, shawara d'aya ni kae na ba dan wani abun zan taemake ki ba se dan kasancewar ki er uwa ta musulma" ya d'an tsagaeta yana jin wani irin ciwo a cikin zuciyar sa wanda har hakan seda ya bayyana a cikin muryar sa da kuma kan fuskar sa sannan ya cigaba da fad'in "Taemako d'aya zan miki shine zan kar6i auren ki a matsayin wadda muke soyayya, sannan a bani ke na tafi da ke zuwa Kano, tun kafin ma mu shiga cikin Kanon zan sawwak'e miki seki tafi gidan ku, kin ga babu wanda ze ji labarin auren idan bake kika fad'a ba.." "Ya ishe ni haka malam, babu ruwan ka da rayuwa ta, na fad'a maka ka fita a rayuwa ta ni da iyaye na, ka bar ni zan auri koma wanene tunda ba zaka bani wayar ta ka bana buk'atar wani taemakon" ta fad'a sanda wasu kyawawan hawaye suka shiga zarya akan kuncin ta, runtse idanun sa yayi daga inda yake tsaye, baya tunanin kome zata yi a yanzu kam ze bata wayar sa tayi kira da ita, bama shi ba koda wani yaga ze bata wayar tayi kira toh ze san yadda zeyi ya hana wannan abin faruwa, kenan a 6ata masa budget? Kae ina hakan baze ta6a faruwa ba "Kina tunanin mutumin daze aure kin ze sake ki kafin ya maeda ki gida? Yana son ki fa, idan da baya son ki baze kawo ki wata uwa duniya a d'aura muku aure ba, ni kuwa fa? Yanzu babu ko d'igon son ki a cikin zuciya ta, dan haka kawae zan aure ki ne dan na taemaka miki ki fita daga hannun wannan mutumin, muna barin k'auyen nan kuma zan rubuta miki takaddar ki da sharad'in ba zaki sake neman inda nake ba" ya k'arasa maganar yana kafe ta da idanun sa masu kyau da kwarjini "Waye ze ne me ka? Tirrr!" ta fad'a tana sake tuna halin mahaefin sa, so take ta tambaye shi toh shi meya kawo shi nan d'in? Amma tasan idan tayi tambayar ze iya tunanin wani abun dan haka tayi shiru tana cigaba da kallan wani wajen, jin da yayi bata sake cewa komae akan zancen sa ba hakan ya alamta masa zata iya amincewa kenan da maganar tasa, lallae ya sake yadda Ayrahn har yanzu yarinya ce, seya saki wani shu'umin murmushi yana shafa bak'in sumar dake shimfid'e akan farar fatar sa da hannun sa kana yace cikin sake karantar yanayin kyakykyawar ta sa "Idan kin amince zamu iya yin hakan a rubuce saboda ki tabbatar da abinda na fad'a gaskiya ne, wato dae ina nufin zamu yi auren yarjejeniyar yini d'aya ne!!" ya fad'a dan cikin ran sa ya shiryawa kowanne irin k'alubale daze biyo bayan auren ta da yayi, baya jin ko d'arr akan abinda ya aekata d'in ko da zasu dawwama ne cikin auren sirri hakan ba damuwar sa bace, dan kuwa daya rasa ta gwara ya jurewa kowanne kalar abu daze tunkaro shi komae zafin sa kuwa... End of ZAZZAFAR KAUNA (CHAPTER ONE) In Sha Allah zamu d'ora da ZAZZAFAR KAUNA (CHAPTER TWO) nan da kwana 2 idan na huta, shima FREE ne duk dan jin dad'in ku 🤗😍 Dan neman qarin bayani se a tuntu6e ni ta 08124818273 https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 031 ___Manyan fararen idanun ta da colour d'in su ya sauya ta d'aga ta zube su a kan sa sanda yake maganar, ta cigaba da saurarar sa tana nazarin kowacce kalma da yake fad'a, sosae k'irjin ta ke mata wani irin suya yana zafi, seta shiga jera ajiyar zuciya kafin ta durk'ushe a wajen tana sakin wani marayan kuka na rashin sanin abinyi, a hankali kukan da take yake fita idanun ta a lumshe haka zalika zuciyar ta na cigaba da zafi, daga inda yake ya runtse idanun sa yana jin kukan nata har cikin jikin sa, seya sauke wata ajiyar zuciya yana d'auke kae daga inda take durk'ushe, ya zama dole ya koyi wofantar da al'amuran ta ko dan saboda wannan kasadar da yake neman aekatawa, idan ba haka ba tabbas ze koma shine me laefin ba wasu ba, duk da yadda kukan nata ke ratsa shi hakan be hana shi sake kicin kicin da fuskar sa ba, ba zaka ta6a gane menene a cikin zuciyar sa ba yadda kyakykyawar fuskar sa take babu annuri se ka d'auka haka ne a cikin ran sa ma, hannayen sa ya d'auka duka ya sak'ale su a k'irjin sa kafin ya d'an lumshe idanun sa kana ya bud'e su yace a hankali "Kuka bashi da amfani, ina ga gwara ki mik'e mu ida wannan aekin" ya d'an yi shiru bayan ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da fad'in "Wannan mutumin ya d'auko ki ne dan a d'aura muku aure dashi na dindindin, shiyasa ni kuma zan k'wace ki daga tarkon sa da kike k'ok'arin fad'awa..." da ya kae k'arshen maganar seya sake dakatawa yana cigaba da nazarin ta, sanda ta dena kukan se sheshshek'a da take yi kan ta har lokacin na kan gwuiwar ta, se a lokacin ta saka hannun ta ta share hawayen da suka k'i tsayawa da zuba a fuskar ta tace cikin raunanniyar murya "Idan da gaske taemako na zaka yi toh ka kira min Abba na, ko kuma ka maeda ni gidan mu saboda bana son ganin ka" tsayawa yayi ya cigaba da kallan ta yanda take maganar bilhak'k'i da gaskiyar ta, shi har yanzu idan tana wani abun mamaki take bashi, meyasa ta fishi d'aukar zafi haka? Meyasa duk da abinda Abban ta yayi wa Abbun sa besa ya guje ta ba se ita? Meyasa take abu kamar da mak'iyin ta take tare? Meyasa ta chanja lokaci d'aya? Lumshe idanun sa yayi yana hana yanda ran sa ke neman 6aci tasiri, sosae zuciyar sa ke masa zafi na maganganun ta amma ya daure ya sake runtse idanun sa na tsawon sakanni sannan ya bud'e su a kan ta sanda suka yi wani ja kamar wanda abu ya zubar wa cikin ido, seya maeda kallan sa kan ta sannan yace sanda bugun zuciyar sa ke cigaba da k'aruwa "Wannan shine abinda kike so na miki? Ki sani ba zaki ta6a barin garin nan babu aure akan ki ba, ko dae ki bari ki auri wancan mutumin ko kuma ki amince da aure na na Contract, The choice is yours.." yayi maganar yana lumshe idanun sa kafin ya d'ora da fad'in "Idan kuma kina tunanin abinda kike tunani shine mafita.. well.. se kije ki samu wad'anda suka sato ki dan a d'aura miki aure da d'aya daga cikin su kice su baki waya ki kira Abban ki..." ya k'are maganar da wani irin murmushin takaeci daya fice daga gefen bakin sa, daga haka ya juya yana shirin ficewa daga soron, bata san sanda ta mik'e da wani irin sauri ba se kawae tsintar hannun sa yayi cikin nata, ya dakata lokaci d'aya yana lumshe idanun sa lokaci d'aya kuma yana jin yanda jikin sa ya amsa, se kuma ta sake shi kafin kamar zata fashe da kuka ta furta "Na amince!!" ta fad'a dae_dae lokacin da wani kuka me sauti ya k'wace mata, seda ya sake runtse idanun sa kafin ya juyo inda take, ya sanya hannun sa cikin aljihu ya fiddo da wata takadda da biro sannan ya mik'a mata ba tare daya dubi kukan da take yi kamar ran ta ze fita ba "Ki saka hannu!" ya fad'a yana mik'a mata, kamar ba zata d'ago ba se kuma a hankali ta fara rage sautin kukan nata sannan ta sanya hannu ta kar6a, sosae bugun zuciyar ta ke k'aruwa ta kar6i takaddar daya mik'a mata, tsayawa tayi kawae tana kallan takaddar kamar me karatu ko me nazarin abinda ke cikin takaddar, hawayen da yak'i tsayawa a idanun ta se sauka yake akan takaddar, wajen minti 1 tayi a hakan da dae ta fahimci bata da wata mafita se kawae ta d'aga biron ta d'ora shi kan takaddar, duk da yadda hannun ta ke rawa hakan be sata dakatawa ba se da tayi signature sannan ta jefar da takaddar daga hannun ta tana runtse idanun ta, bata jira ta sake jin komae daga bakin sa ba ta mik'e ta fara takawa a hankali saboda jirin dake d'ibar ta, hakan ne ya sanya ta yin layi kamar wadda tayi maye, bin bayan ta yayi da kallo sanda ta 6acewa ganin sa daga inda yake yana jiyo sheshshek'ar kukan ta, ya kae minti d'aya a hakan kamar wanda aka sassak'a sannan ya lumshe idanun sa ya saka hannu ya d'auki takaddar kana ya fice daga soron. Kae tsaye cikin motar sa ya koma ya jinginar da kan sa akan kujerar daya kwantar da ita, idanun sa a lumshe zuciyar sa na harbawa da k'arfin gaske, hannun sa dake d'auke da takaddar ya rufe ta a cikin hannun nasa kamar wanda ze yaga takaddar, se kuma ya bud'e hannun yana sauke numfashi a hankali, wayar sa dake ajje kan kujera ce tayi ringing, se a lokacin ya bud'e lumsassun idanun sa ya d'ora akan wayar "Abbu" ya bayyana akan screen d'in, seya maeda idanun sa kawae ya rufe yana cigaba da sauke numfashi akae akae, be d'aga wayar ba har ta gaji dan kan ta ta dena ringing d'in sannan ya janyo ta ya kashe ta gaba d'aya, gaba d'aya zuciyar sa a dame take yanzu haka, ya rasa ma meya kamata yayi, baya tunanin koya d'aga wayar ma ze iya cewa wani abun, dan haka k'in d'agawar kawae shine mafita. ... B'angaren Ayrah kuwa a tsakar d'akin ta zube tana sakin wani gigitaccen kuka me tsuma zuciyar me sauraro, zuciyar ta gaba d'aya a cunkushe take, ta rasa abinda zatayi, ta rasa tunanin daya kamata tayi, abinda ta sani kawae shine yanda zuciyar ta ke bugawa kamar zata faso k'irjin ta ta fito, ta kae fiye da minti 30 tana kukan sannan ta fara sauke ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma tana neman kan wani d'an madaedaecin gado dake cikin d'akin ta d'ora kan ta akae cikin rashin sanin abinyi. ... "Yalla6ae kayi hak'uri ka zauna mu samo mafita" Muttala ya fad'a yana kallan Alhaji Mato daya kasa zama, idanun nan nasa sun sake ja kamar garwashi, haka zalika bak'ar fuskar sa ta sake had'ewa cikin rashin walwala "Waye shi? Wanene uban shi? Me yake tak'ama dashi? Ya akayi yasan da plan d'in mu? Ya akayi ya biyo mu cikin garin nan?" shine abinda Alhaji Maton ya fad'a a zafafe "Ka kwantar da hankalin ka Yalla6ae, zuwa gobe zan bincika maka waye shi" wani banzan kallo Alhaji Mato ya watsawa Muttala kafin yace "Muna da wannan lokacin? Tambayar ka nake muna dashi?" ya k'are maganar yana kallan sa, shiru Muttala yayi yana sake tunanin wata mafitar, hakan ya sake bawa Alhaji Mato damar yin shiru shima yana nazarin abinda ya kamata yayi kafin goben "Ya shiga gona ta, bazan k'yale shi ba wallahi, yana so yayi wasa dani, ba zeji da dad'i ba, Muttala asan yadda za'ayi a gama mun dashi kafin goben, shi kad'ae ne matsala ta a yanzun.." Alhaji Mato ya k'are maganar yana kallan Muttala "An gama ranka ya dad'e" .... Washe_gari da safe wajen k'arfe 8 tana zaune kan dadduma kamar maraeniyar data rasa uwa da uba, manyan idanun nan nata sun sake yin zuru zuru, ga yunwar da take ji amma saboda tashin hankalin da take ji ta kasa kae koda ruwa ne cikin bakin ta, haka nan kawae take zaune, ita ba Azumi ba ita ba cin abinci ba, idan ka gan ta seta baka tausayi musamman yadda har lokacin hawaye be bar zuba akan kuncin ta ba duk da yadda ta dena kukan amma hakan be hana hawayen zuba ba, ita kad'ae tasan yadda take ji a cikin zuciya, k'wak'walwa da gangar jikin ta, tana nan zaune gaba d'aya bata a hayyacin ta kamar wadda ta zare, ta tsaya ta k'urawa waje d'aya idanu se kuma hawayen dake sauka akan fuskar ta. Babu dad'ewa aka turo k'ofar d'akin, bata damu dame shigowar ba dan ita wannan sam ba damuwar ta bace, wadda ta shigo ta k'arasa ta ajiye abincin data shigo dashi, duk da ganin abincin data kawo jiya duk suna ajiye bata ce komae ba ta fice daga d'akin tunda dae ta gama aekin ta. .... Wajen k'arfe 1pm aka sake shigowa d'akin, har lokacin dae tana zaune a wajen yanzu kam ko hawayen ma sun gaji da zuba, tayi shiru kawae tana jiran taga yadda Allah zeyi da ita, yanzu wata matar ce ta shigo daban ta kalle ta sannan tace "Baba na kira!" sam bata ji ta ba dan kuwa bata tare da ita, hankalin ta da tunanin ta gaba d'aya suna ta wani wajen ne, ganin da matar tayi kamar bata tare da ita ne ya sanya ta k'arasawa gaban Ayrah ta tsuguna sannan tace "Baba na kiran ki" firgigit ta lumshe idanun ta sannan ta bud'e da sauri lokaci d'aya kuma k'irjin ta na bugawa, seta kalli matar dan har lokacin bata san aenahin abinda ta fad'a d'in ba, seda ta sake maemaetawa sannan kawae ta mik'e tana gyara zaman hijab d'in ta kan doguwar rigar da aka bata ta saka wadda take over size dan kuwa yawo take a cikin ta, lumshe idanun ta tayi bayan ta mik'e d'in sanda taji wani irin jiri na neman kada ta, a hankali ta kama kan ta tana sake rufe idanun ta, a haka dae suka cigaba da tafiya ba dan tana gane inda suke zuwa d'in ba. Cikin wani d'aki me madaedaecin kyau, ehh zamu iya kiran sa madaedaeci musamman idan muka yi duba da gidajen cikin k'auyen, dan kuwa wannan d'in shimfid'e yake da manyan tabarmi masu kyau, da kuma wata k'aramar kujera wadda Me gari ke zaune a kae, sam bata san wad'anda ke cikin d'akin ba dan idanun ta da kan su suke lumshewa ga kan ta daya cigaba da sarawa, Me gari yayi gyaran murya sannan ya fara magana a nutse "Kin yanke hukuncin wanda kika za6a a matsayin mijin ki?" ya jefawa Ayrah tambayar, seda matar nan ta d'an ta6a ta dae_dae lokacin da kan ta ya sake sarawa, a hankali ta sanya k'aramin red lips d'in ta na k'asa cikin bakin ta ta cija tana jin yadda ya bushe musamman saboda ruwan daya dad'e be shiga cikin bakin ba, d'aga ido Alhaji Mato yayi ya kalli inda Ayrah ke zaune, be ta6a tunanin tun yanzu Me gari ze kira su yayi tambayar k'arshe ba, gashi yayi sake saurayin na nan be kae gayi masa komae ba, meya kamata yayi a yanzu? "Ranka ya dad'e ina ganin kawae a bani ita zan maeda ta gidan su!" Alhaji Mato ya fad'a yana kallan Me gari, d'aga kyawawan idanun sa Rk yayi ya sauke su kan Alhaji Mato, kafin a hankali ya saki wani miskilin murmushi, dama seda yayi tunanin hakan zata kasance, shiyasa ya maza yayi wa tufkar hanci, girgiza kae Me gari yayi yana tuna maganar da suka yi da Rk, lallae shima yayi wannan tunanin, ze iya yiwuwa Alhaji Maton be yadda da wannan hukuncin ba ya d'auki Ayrah su tafi wani wajen a d'aura musu aure "Kace kuma ba anan garin iyayen ta suke ba?" cikin in'ina Alhaji Mato yace cike da danasanin abinda ya fad'a d'in "Ehh.. Ehh.. Ranka ya dad'e" jinjina kae Me gari yayi kana yace a nutse "Yanzu ba matar ka bace, shima ba matar sa bace saboda haka baze yiwu a had'a ku ku tafi a haka ba, dan haka kamar yanda muka saba, zan d'aura mata aure da wanda ta za6a, shi seya d'auke ta su koma gidan... Kae sake gwada layin nan muji" Me gari ya k'arasa maganar yana kallan wani dake gefen sa, seya fiddo da waya daga cikin aljihun sa ya sake danna wata number ya kira, kira wajen 3 number daya kira bata shiga ba, ya kalli Me gari yace "Yalla6ae kamar jiyan dae yau ma bata shiga" ya fad'a cike da ladabi, gyaran murya Me gari yayi sannan yace "Babu matsala, zamu yi abinda ya dace.. Cikin su biyun wa kika za6a?" Me gari ya k'are maganar yana kallan Ayrah "Raj!" ta furta ba tare data kalli kowa ba, ba kuma tare data bud'e idanun ta ba, har kuma lokacin hannun ta na dafe da kan ta ne daya cigaba da sara mata, daga inda yake ya lumshe idanun sa yana cigaba da kallan inda take kan ta a k'asa haka zalika idanun ta a rufe "Toh madallah, idan an idar da Sallahr azahar ni da kae na zan d'aura auren nan, Allah yasa albarka" Me gari ya fad'a, huci Alhaji Mato ke fitarwa daga bakin sa zuciyar sa na cigaba da tafarfasa, shi kad'ae yasan abinda ze yiwa Rk, dan ya riga yaci alwashin baze ta6a barin sa yaci bulus ba, baze ta6a k'yale shi ba, baze ta6a rangwanta masa ba. Matar nan ce dae ta kamata ta mata jagora zuwa cikin gidan, a lokacin kawae zubewa tayi akan gadon, daga kukan har hawayen yanzu babu ko d'aya dake fita, kawae ta cigaba da kwanciyar ne cikin rashin sanin abinyi, kuma cikin rashin sanin mafita, se a lokacin ta tsaya tayi tunani, shin wanene wannan mutumin? Meyasa ya sato ta daga gidan su? Meyasa yake son auren ta bayan ita ko sanin sa bata yi ba? Meyasa ya rabo ta da gidan su? Meyasa beje ya nemi auren ta wajen Abban ta ba kamar yanda Addini ya tanadar? Meyasa yake son neman auren ta ta wannan sigar? So take ta tabbatarwa da kan ta amincewa auren Rk da tayi ba kuskure bane amma hakan ya citira, kawae ji take kamar ta tafka wani babban kuskure ne auren sa data amince zata yi, nan take kuma wani tunanin ya fad'o mata "Auren kwangila ne ae, kwangilar ma ta yini d'aya, daga zarar ya sawwak'e miki babu wanda ze san kin aure shi, taemakon ki yayi ba komae ba..." abinda zuciyar ta keta sak'a mata kenan amma har yanzu ta kasa yafewa kan ta, musamman idan ta tuna Abban ta, ta tuna irin amincewar da yayi wa su Raj amma suka ci amanar sa, ta tuna yanda yace ba zata auri Rk d'in ba amma yanzu idan suka ji labarin ta aure shi na yini d'aya fa? "In har kin so baza suji labarin ba" abinda ta sake sak'awa kenan a cikin ran ta, se kawae ta lumshe idanun ta tana sake dafe kan ta da dukkan hannayen ta. ... Har aka idar da Sallah yana cikin masallaci, ya kasa motsawa ko nan da can ne, idanun sa a lumshe suke tunani barkatae na yawo cikin k'wak'walwar sa, tun jiyan nan daya kashe wayar sa be sake kunnawa ba dan baya son a kira shi ko kad'an. K'arfe 2:25 mutanen dake cikin masallacin suka shaeda d'aurin auren RAJ KABEER da AYRAH IBRAHEEM KHALEEL akan sadaki mafi k'ank'anta wato mafi alkhaeri.. Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 032 ___Wani irin sanyi ne ya shiga ratsa ilahirin jikin sa lokacin da yaji zancen d'aurin auren, a hankali ya lumshe idanun sa, se dae ga mamakin sa sosae bugun zuciyar sa ya k'aru, seya dakata yana tuna kasadar da yayi da kuma k'alubalen da yasan dole seya tunkaro shi, amma tunda dae ya gama da wannan koma wanne k'alubale ne yana ganin me sauk'i ne, a hankali kuma se yaji wani rauni na son shigar sa, cikin sakannin da basu gaza 2 ba ya bud'e manyan idanun sa da hakan yasa zaka iya fahimtar yadda yanayin fuskar sa take, sosae annuri ke fita daga kyakykyawar fuskar sa, seya fesar da iska daga bakin sa sannan ya cigaba da kar6ar hannun mutane dake mik'a masa suna gaesawa, wasu da gasken dan taya murna ne suke mik'a masa hannun su gaesa yayin da wasu suna so ne kawae su gaesa da shi d'in saboda yadda yake, d'an birni, had'ad'd'e kuma kyakykyawa, kwata kwata baya lura da yanayin mutum kawae ze mik'a tattausan hannun sa ne su gaesa duk da ba kallan fuskar mutanen yake ba. ... Ayrah na cikin gida sam bata san abinda ke faruwa ba, ita gaba d'aya tana jin komae ne kamar a mafarki ko kuma wani wasan film, dan haka ta gaza amincewa kan ta wannan abinda yake faruwa gaskiya ne, a yanda tafi d'auka wani mummunan mafarki ne take yi wanda yake nuni da tana neman bijirewa maganar Abban ta, dan haka take fatan tayi maza ta farka daga baccin, se dae me? Har yanzun tak'i farkawa, tun tana cigaba da yadda mafarkin ne har tazo ta fara tunanin shin ko gasken ne? Duk abinda ke faruwa a yanzun da gaske ne? Ba ita ta tashi daga kwancen da take ba seda taji ana kiran sallah, a hankali ta fara k'ok'arin mik'ewa se dae jirin daya kwashe ta ta sanya ta saurin komawa ta kwanta tana sakin wani kuka, ita kad'ae tasan abinda take ji a jikin ta, ita kad'ae tasan yanda take jin kan ta da gangar jikin ta, gaba d'aya jin kan ta take yi ya mata wani gingirin kamar ba'a jikin ta yake ba, ga jikin ta da gaba d'aya ta rasa gane a wane yanayi ma zata saka shi, ta kae wajen minti 1 a kwancen seda jirin ya d'an yi sauk'i sannan ta mik'e duk da yanda take kallan abinci da ruwa a ajiye hakan be sanya tabi ta kan su ba, kae tsaye ta fice daga cikin d'akin zuwa ban d'akin dake kusa da d'akin da take ciki, alwala kawae tayi ta dawo cikin d'akin ta tada sallah. ... "Toh kae Allah ya baku zaman lafiya, Alhaji Mato kuma Allah ya baka hak'uri, dama kasan ance ba komae ne idan aka rasa ake kuma samun sa ba, Allah ya musanya maka da wadda ta fi ta" Me gari ya fad'a yana kallan su su duka "Ameen ranka ya dad'e, Allah ya k'ara girma" Rk ya fad'a ba tare daya d'aga ido ya kalli Alhaji Mato dake jifan sa da wani kallo na gargad'i da kallan nan irin na zaka sani, Alhaji Mato be iya cewa komae ba saboda yasan idan ya bud'e baki komae ka iya fitowa daga bakin sa, k'ila ma yayi maganar da zata iya tona masa asiri a cikin k'auyen, dan haka yaga shirun nasa yafi masa alkhaeri "Ayi mata magana ta fito se ku tafi koh?" Me gari ya fad'a yana kallan Rk, jinjina kae Rk yayi lokaci d'aya yana lumshe idanun sa se kuma ya bud'e bakin sa a nutse ya furta "Ehh" babu 6ata lokaci Me gari ya aeka wani daga cikin yaran sa zuwa cikin gidan cewar a fito da Ayrah. ... Lokacin da matar nan ta sake shigowa cikin d'akin da k'yar take iya bud'e narkakkun idanun ta da suke wani lumshewa da kan su kamar er maye, sanyi sosae take ji a jikin ta wanda hakan ya sanya ta takurewa cikin hijab d'in ta tana jin kamar k'asusuwan ta zasu tsage, ciwon da kan ta yake yi kuwa se abinda yayi gaba, gaba d'aya jikin ta yayi wani irin tsami "Ki taso zaku tafi" maganar da taji matar tayi ya sanya tilas ta bud'e lumsassun idanun ta ta jefa su kan matar da take gani biyu biyu, ta d'auka ma ba taji abinda tace ba dan haka ta sake maemaetawa a karo na biyu, a hankali ta zura k'afar ta daga kan gadon da take, tilas ta sake runtse idanun ta saboda yadda taji kamar ginin gidan gaba d'aya ze fad'o a kan ta, bata so ma wasu su fahimci bata da lafiyar ballantana ace za'a d'aga tafiyar tasu, burin ta d'aya kawae ta bud'e idanun ta ta gan ta cikin gidan su, gata ga Umman ta, ga Abban ta ga kuma Yah Sadeeq d'in ta, seda matar tayi gaba sannan ta mik'e tabi bayan ta a nutse tana tafiya tana dafa bango saboda kada ta fad'i, sosae tayi da gaske dan kada ta zube kafin ta isa wajen, cike da k'arfin hali ta cigaba da takawa har zuwa wajen Me garin. Bin ta yayi da kallo sanda ta zube a k'asa idanun ta a lumshe, daga yanayin yadda ta zauna d'in kawae zaka fahimci ba'a lafiyar ta take ba "Toh yanzu dae zamu damk'aki hannun mijin ki, Allah ya bada zaman lafiya" shine abinda ta tsinto Me garin na fad'a, ta sake lumshe idanun ta a karo na barkatae tana jin wani irin yanayi, kenan da gaske an d'aura mata aure da Raj? da Me gari yasan tashin hankalin da take ciki tabbas da baze ambaci Rk a matsayin mijin ta ba, daga lokacin da aka fad'i hakan tana sake jin kan ta ne dumu_dumu a mae laefi, wadda ta bijirewa umarnin iyayen ta, se dae tasan wannan d'in bame yiwuwa bane, kwangila ce suka k'ulla tsakanin ta da Rk d'in kuma nan da anjima zata k'are, dan haka wannan d'in kamar wani wasan kwaekwayo ne aka gabatar dashi cikin k'auyen. Sosae Rk yayi wa Me gari godiya sannan ya mik'e yana kallan er rigimar tasa, be san yanda zasu k'arke ba, be san kuma meze faru anan gaba ba "A'ah ba dae tafiya ba?" Me gari ya fad'a yana kallan Alhaji Mato daya mik'e shima, dan so yake ya fara yin gaba kafin Rk ya riga shi, dan kuwa tun kafin ya isa gida yake so ya gama dashi, se dae da alama Me garin na son jik'a masa aeki "Ehh.. A'ah.." Alhajin Maton ya fad'a cikin inda inda yana komawa ya zauna "Yawwah koda naji, ae ka zauna muyi hira koh?" bece komae ba dan a yadda yake ji ze iya sussurfawa Me garin zagi ne "Allah ya tsare" Me gari ya sake bin Rk da addu'ar sanda ya k'arasa dab da ita, ya rasa yanda zeyi ya mata magana, mik'ewar da tayi ne ya sanya shi d'an lumshe idanun sa sannan yayi gaba yayinda ta bishi a baya hannun ta rik'e da kan ta da har lokacin be bar sara mata ba, hannu ya saka ya bud'e mata k'ofar wajen me zaman banza, zata iya cewa ta fishi k'aguwa su bar k'auyen nan ko dan a warware wannan auren wasan sannan ta tafi gidan su, uwa uba kuma ga yadda take ji a yanzun koda wane lokaci zata iya zubewa idan bata nemi wajen zama ba, dan haka babu musu ta shige cikin motar ta kwantar da kan ta tana sakin wata ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma kan ta na sake juya mata ta fara ganin ko ina na juya mata, sam be lura da yanayin da take ciki ba ya koma mazaunin driver yana sauke ajiyar zuciya, seda ya kalli inda take zaune sannan ya sake lumshe idanun sa kana ya d'auke kae yana jan motar ya fara tafiya.. .... A d'aya 6angaren kuwa a ranar da Ayrahn ta bar gidan gaba d'aya cikin su babu wanda ya rintsa, Yah Sadeeq zuciyar sa sosae take masa zafi idan ya tuna halin kafiya irin na k'anwar tasa data kasa barin d'a namiji duk da yadda Abba yace ba zata aure shi ba, ta 6angaren Umma kuwa kwana tayi tana kuka a ranar, ta kasa sakewa, koda tayi k'ok'arin tunanin ba hakan ne dalilin rashin ganin d'iyar ta ta ba se kuma ta kasa samun hujjar da zata rik'a akan hakan, koda tayi tunanin d'iyar ta ta bata da bud'ewar ido ko wayon da zata bi saurayi ta gudu se kuma ta tsaya ta tuna tasirin soyayya, musamman yadda Ayrahn ke k'aunar Raj d'in, da yadda taga rikicewar ta a jiya da Abba ke fad'a mata ba zata aure shi ba seta sake jin jikin ta yayi wani mugun sanyi, dan haka tayi kukan ta ta godewa Allah sannan tayi shiru, 6angaren Abba kuwa ranar da bugun zuciya ya kwana, wanda hakan ke alamta masa tashin ciwon sa, haka dae ya dinga daurewa baya so 6acin rae ya sanya yayi wa d'iyar tasa fata mara kyau. ... Washe_gari da safe Umma ta fito ta shiga kitchen dan ta samu ta sarrafa musu wani abun da zasu ci a matsayin abun karin, ta dad'e a kitchen d'in tana nazari se kuma ta fito kae tsaye ta wuce d'akin Abba, tana shirin shiga Abban ya fito seta dakata lokacin da shima ya dakata yana kallan yadda idanun ta suka yi ja da alama jiya kwana tayi tana kuka "Har yanzu kukan kike yi?" Abba ya tambaya yana cigaba da kallan ta, hannu Umma ta kae fuskar ta ta d'auke hawayen daya zuba, tun jiya take k'ok'arin cire damuwar daga cikin ran ta amma ta kasa, ta kasa mantawa, ko dae_dae da minti d'aya zuciyar ta ta kasa sukuni da wannan al'amari "Aou cigaba kuma zaki yi?" seta girgiza kae sannan tace bayan ta runtse idanun ta ta bud'e "Abban su bansan ina yin kukan ba, ko da nayi k'ok'arin mantawa hakan yana gagara ne a cikin zuciya ta, Abban su har yanzu na kasa amincewa ba mafarki nake yi ba" jinjina kae Abba ya shiga yi cike da gamsuwa da maganar Umman, shi kan sa jiya be rintsa ba ya zauna ne kawae se sak'e sak'e yake yi "Kiyi hak'uri ki dena kukan haka nan kin ji?" ya fad'a yana kallan ta "In Sha Allah, zan yi k'ok'ari naga hakan ta kasance.." Umma ta fad'a tana sake goge idanun ta. ... Driving yake a nutse kamar koda yaushe, jefi jefi yana juyawa yana duban inda take a takure cikin hijab ko k'wak'wk'waran motsi ba tayi, bece mata komae ba dan baya so ya tado da rigima tun yanzun dan haka ya mata shiru a ran sa yana tunanin mafita. Tafiya me tsayi suka yi kafin suka fara shiga garin Kano, zuwa lokacin kam mamaki take bashi ganin har lokacin bata motsa ba, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa sannan yaja motar ya gangara gefen titi ya kashe ta ya d'an jinginar da kan sa akan steering na tsawon sakanni kana ya d'ago kan nasa ya dubi inda take, seda ya lumshe idanun sa kafin a hankali yace "Ayrah!!" beji ta amsa masa ba ko kuma ta d'ago har bayan wajen minti 1 sannan a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in nata ya d'an yi tapping nata, nan ma dae ba tayi motsi ba, seya ware manyan idanun sa akan ta sannan ya kae hannun sa a nutse gaba d'aya ya rik'o ta, se kuwa tayo baya zuwa jikin sa, k'irjin sa ya wani irin buga lokaci guda yana mamakin yadda yaji jikin ta yayi wani irin zafi daya wuce na k'a'ida, idanun sa akan kyakykyawar fuskar ta da tayi fayau kamar wadda tayi wata da watanni tana rashin lafiya, idanun ta a rufe suke, dogayen zara zaran eye lashes d'in ta sun kwanta sunyi luff akan idanun ta, a hankali ya sake bud'e bakin sa se dae yanzu a cunkushe ya furta "Ayrah!!" nan ma dae ba tace komae ba, runtse idanun sa yayi yana jin wani abu me kama da tsoro na shigar sa "Meya same ta?" ya tambayi kan sa, seya kae kunnen sa saetin dogon hancin ta da yayi ja kamar me mura, cikin lokaci k'ank'ani hucin numfashin da take fitarwa me zafi da kuma hucin zafin dake jikin ta ya sauka akan fuskar sa, seya sake lumshe idanun sa yana d'an tsayar da numfashin sa har lokacin cike da tsoro, cikin ikon Allah yaji numfashi kad'an na fita, be san sanda ya saki wata ajiyar zuciya ba sannan ya maeda ta kan kujerar ya kwantar kana ya tashi motar da gudun gaske ya wuce asibiti, sam gaba d'aya ma ya manta, haka zalika beyi tunanin komae ba ya wuce asibitin sa. Parking d'in motar sa yayi har lokacin bugun zuciyar sa be koma dae_dae ba, ya fito daga cikin motar cike da sassarfa wanda komae abin ka baka isa ka gane a yanayin da yake ciki ba, dan kuwa fuskar nan haka take babu yabo babu fallasa amma cikin zuciyar sa shi kad'ae yasan abinda yake ji, bud'e inda take kwance yayi beyi wata wata ba ya d'auke ta gaba d'ayan ta a hannun sa, sam be lura da kallan da en cikin asibitin ke bin sa dashi ba, yama manta abinda ya aekata haka ya wuce da ita cikin Office d'in sa, duk wad'anda ke kallan sa mamaki ne ya kamasu yadda suka ga Doctor Rk d'in da kan sa ya d'akko wata mace a hannun sa, nan take aka fara gulmammaki cikin asibitin, seda ya tsaya ya kar6i spare key d'in Office d'in sa dake ajje sannan ya wuce ya bud'e ya shiga har lokacin tana rik'e a hannun sa ya kwantar da ita kan gado. .. Hannun ta har rawa yake yi ta d'auki wayar ta ta nemo number Abbu ta kira, babu jimawa Abbu ya amsa wayar "Yalla6ae Doctor Rk ya shigo yanzun nan" daga inda Abbu yake ya saki ajiyar zuciya yana jin dad'i har cikin ran sa dan kuwa tun d'azun yake kiran layin Rk d'in amma se ace masa a kashe yake "Ohk ina nan zuwa nan da 10 minutes" shine kawae abinda Abbu ya fad'a yana katse wayar sannan ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa asibitin. .. Kamar wanda aka jefo haka Abbu ya fad'o cikin asibitin, dae_dae lokacin da Rk ya fito daga cikin Office d'in sa, Abbu ya sake sauke ajiyar zuciya ganin d'an nasa, seya k'arasa kafin yace "Raj!" muryar wanda yaji ne ta sanya k'irjin sa ya d'an buga sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Abbun dake k'arasowa inda yake "Ina ka shiga ne haka? Kasa hankalin mu duka ya tashi?" d'an yatsine fuska yayi lokaci guda kuma yana kae hannun sa kan sa sannan yace "Amm... Abbu ina so ne nayi settling abubuwa da dama, bana buk'atar takura ne yasa na kashe waya ta, ina fatan dae ban yi laefi ba?" ya k'arasa maganar yana kallan Abbun "Ohk tohm muje cikin Office d'in akwae maganar gaggawa da nake so muyi" be san sanda yayi gaba ba yana tarewa Abbu k'ofar shiga Office d'in ba sannan yayi wani murmushin yak'e yace "Abbu pls.." "Shikenan, kayi k'ok'arin gamawa, koma dae baka gama ba ka tabbatar ka dawo gida dan akwae muhimmiyar maganar da zamu yi bamu da ishashshen lokaci" Abbu ya fad'a yana d'an nazarin d'an nasa, ganin yanda idanun sa suka d'an tasa kamar wanda baya samun bacci, se kuma daya tuna yanzu yake fad'a masa aeki ne ya rik'e shi sannan ya d'an ji dama dama "In Sha Allah" shine abinda Rk ya fad'a yana d'an kaucewa kallan da Abbun ke masa, dan gani yake kamar yana kallan k'wayar idanun sa ze karanto rashin gaskiyar dake tattare da shi "Allah ya yadda" Abbu ya fad'a yana juyawa daga wajen, se a lokacin Rk ya saki ajiyar zuciya yana lumshe idanun sa, se yanzu ya gane shirmen daya aekata na zuwa da ita asibitin nan, me ya shiga kan sa ya kawo ta nan d'in? Hannu ya saka ya bud'e Office d'in ya shiga sannan ya kulle, idanun sa akan ta lokacin da idanun ta ke a rufe tana sauke numfashi a wahalce, daga yanayin yanda ta 6ata rae kawae zaka fahimci ba dad'in baccin take ji ba, ga kuma yanda ta d'an tura red lips d'in ta gaba kamar me shirin yin kuka, seya samu kan sa da lumshe idanu na tsawon second 10 sannan ya bud'e ya k'arasa bakin gadon bayan yaja wata kujera ya zauna, duk da yanda take sake had'e jikin ta waje d'aya hakan be hana gumi tsatstsafowa daga fuskar ta ba, ya sake sauke idanun sa kan fuskar ta sannan ya maeda kan jikin ta da har lokacin ke d'auke da hijab, a hankali ya kae hannun sa kan hijab d'in, kamar me tunanin wani abun ya dakata da hannun sa a sak'ale, ya kae wajen second 30 a hakan sannan ya k'arasar da hannun nasa zuwa kan hijab d'in nata ya fara janye shi sama, be sake shi seda yazo dab da fuskar ta, se a lokacin kuma ya fara tunanin yanda ze cire shi daga wajen fuskar ta dan baya so ya tashe ta dan kuwa be shiryawa abinda ze fad'a mata ba, be kuma shiryawa rigimar ta ba, a hankali ya d'an mik'e tsaye sannan ya rank'wafa ya kae hannun sa k'asan kan ta da nufin d'ago kan nata, dae_dae lokacin data bud'e idanun ta da suka mata nauyi, se rumfar mutum kawae ta gani a kan ta, duk da yanda kan ta ke cigaba da mata ciwo hakan be hana ta sake ware idanun ta ba, duk da bata fahimci menene ba amma ta tsorata matuk'a dan haka bata san sanda ta mik'e zaune ba tana sakin k'ara, lumshe idanun sa yayi yana jin k'arar ta ta har cikin jikin sa, sanda ya ida bud'e idanun sa se nata idanun suka sauka cikin nasa, cikin wata rud'ewar ta saki k'ara tana yin baya gami da sake jan hijab d'in ta ta lullu6e kafatanin jikin ta tana sakin kuka kamar wadda aka daka, lokaci d'aya kuma jikin ta na cigaba da rawa, runtse idanun sa yayi saboda yadda yaji kan sa ya sara da k'arar da tayi har sau biyu, ya d'an dafe kan sa sannan ya bud'e idanun sa ya sauke su a kan ta lokacin da take cigaba da mak'urewa a jikin bango hannun ta rik'e da hijab d'in ta kamar zata maeda shi cikin ta, cikin karyayyiyar murya me had'e da kuka ta furta "Ina takadda ta? Meyasa baka maeda ni gidan mu ba?" tayi maganar sanda wasu hawaye masu d'umi suka samu damar zubowa akan kuncin ta, idanun sa yayi saurin janyewa daga cikin nata narkakkun idanun dake zubar da hawaye kamar an kunna famfo haka kuma sun cika taff da hawaye duk da wad'anda ke zuba, baya so tun yanzu raunin ta yaci galaba a kan sa dan haka ya d'an runtse idanun sa sannan ya bud'e su, ya d'auke su ya aza su a kan ta sanda ta cigaba da mutsu mutsu akan gadon tana cigaba da kukan ta "Me kike ci na baka na zuba Madam? Ae har yanzu yinin be k'are ba!" ya fad'a yana sakin wani miskilin murmushi.. Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 033 ___Ganin da yayi tana cigaba da bin sa da kallan tuhuma lokaci guda kuma tana sake kwa6e fuskar alamar koda yaushe zata iya sakin kuka ya sanya shi sake lumshe idanun sa sannan a hankali ya d'aga hannun sa dake d'auke da wani had'ad'd'en agogo ya juya mata dashi dan ta gani, bin hannun tayi da kallo dan fahimtar abinda yake nufi da hakan "Duba lokaci" ya fad'a har lokacin be d'auke hannun nasa ba, se ta sake bin hannun nasa da kallo sannan ta d'an runtse idanun ta dan har lokacin ganin ta be koma dae_dae ba, k'uri ta yiwa agogon kamar me k'irga sakannin da suke wucewa, ganin da yayi ta janye idanun ta daga kallan agogon ya tabbatar masa data gani, be sake cewa komae ba ya fice daga Office d'in, seda ya kulle k'ofar sannan ya tafi, bin sa tayi da kallo sanda ya fice d'in sannan ta dawo da kan ta kan gadon da sake kwantawa, ta k'agu ta koma gida, bata san nan d'in ina ne ba da babu shakka da kan ta zata koma gida. Wajen mintuna 20 se gashi ya turo k'ofar Office d'in ya shigo hannun sa d'auke da leda, se tayi sauri ta tashi dan tasan yanzu kam may be ya shigo mata da takaddar tane ta wuce gidan su, ganin yadda take shirin sakkowa daga kan gadon ne ya sanya shi fad'in "Kici abinci ki sha magani, sannan ki koma gidan" ya fad'a yana ajje ledar akan gadon ba tare daya kalle ta ba haka zalika fuskar sa a had'e, ji tayi kamar ta fasa ihu, ita gaba d'aya bata ta wani abinci bare akae ga magani, dan haka ta d'auke kae kamar ba taji ba, d'an d'aga kae yayi ya saci kallan ta yadda take ta wani cic cin magani ita a lallae dole bata ji shi ba ya sanya wani murmushin gefen baki ya su6uce masa se kuma ya sake had'e fuskar sa sannan yace "Well, se kiyi ta zama anan d'in, ni kinga tafiya ta" ya fad'a yana ta6e baki gami da soma tafiya kamar ze bar Office d'in, se kuwa ta fashe da kukan tana sakkowa daga kan gadon gaba d'aya cikin kukan ta furta "Don girman Allah kayi hak'uri, bazan iya cin abinci ba, ka maeda ni gidan mu ko ka bani kud'in mota na tafi.." tayi maganar tana saka hannun ta kan fuskar ta tana goge hawayen dake ta sintiri akan kuncin ta, dakatawa yayi daga inda yake ba tare daya juyo ba har wajen second 20, seda kukan nata ya fara raguwa sannan ya juyo a nutse ta fara takawa zuwa cikin d'akin, har ga Allah ya gaji da jin kukan nan nata, d'aga masa hankali yake yi, kuma babu damar rarrashi kada yaje ta koma zargin sa ko ta hasaso wani abun nan gaba, dan haka yanzu ma be kalle ta ba yaja wata kujera sannan ya janyo abincin ya d'ora akan kujerar kana yace "Ba zaki koma gida a haka ba, dan haka ki tsaya kici abincin kawae" yayi maganar lokacin daya ida bud'e abincin, ya ajje cokali a gefe sannan yaja gefe ya tsaya yana fiddo da wayar sa daga aljihu ya shiga dannawa, seda ta gama sheshshek'ar ta ran ta na cigaba da suya, tasan taemakon ta yayi amma kuma ita bata buk'atar wani abinci dan gaba d'aya hankalin ta da nutsuwar ta sun tafi gida ne, amma kuma daga yadda yayi maganar tasan idan ba taci abincin ba ba mayar da ita zeyi ba dan haka ta k'arasa ta zauna kan gadon kana taja kujerar, ruwa ta fara d'auka ta 6alle murfin robar ta kae bakin ta, se yanzu ta tuna rabon ta da shan ruwa har ta man ta, wata irin k'ishirwa ta taso mata dan haka bata sauke robar ba seda ta shanye shi tass, sannan ta ajje tana sauke ajiyar zuciya lokaci d'aya kuma jikin ta na d'aukar rawa, lumshe idanu tayi dan gaba d'aya bakin ta babu taste amma yaza tayi? Janyo abincin tayi a hankali ta fara kaewa bakin ta tana 6ata rae, spoon na farko data fara kaewa sega hawaye sharr akan fuskar ta, haka dae ta cigaba da ci lokaci d'aya tana kae d'ayan hannun ta tana d'auke hawayen, daga inda yake yake d'an satar kallan ta gaba d'aya wani tausayin ta yazo ya lullu6e shi, seya maeda wayar cikin aljihu sannan ya k'arasa cikin Office d'in ya fara wani abun, ita sam bata lura dashi ba seda yazo dab da ita hannun sa d'auke da allura, beyi tunanin ta lura da ita ba seda yaga tayi sauri ta koma kan gadon manyan idanun ta da suka yi ja sun sake cika taff da hawaye "Idan kana k'aunar Allah kada kamin allura, naci abincin fa, ka k'yale ni don Allah" ta k'arasa fad'a tana sakin kukan gaba d'aya, lumshe idanu yayi na tsawon sakanni kafin ya bud'e su still dae a kan ta, a hankali ya shiga takawa zuwa bakin gadon, ita kuma tana cigaba da komawa baya tana girgiza kae gami dayin kukan ta kamar wadda aka riga aka yiwa allurar "Oh god" ya furta sanda ya dakata yana d'an murza goshin sa "Wannan wace irin yarinya ce?" ya furta a k'asan ran sa kafin ya sake maeda duban sa kan ta har lokacin dae ba tayi shirun ba "Ina yi miki allurar zan maeda ki gida bayan na baki takaddar ki" yayi maganar a nutse kuma cikin lallashi, ita sam ba fahimtar sa take ba wannan allurar kad'ae data gani ta gama rikita ta dan kuwa zata iya cewa tunda take da girman ta ba'a ta6a mata allura ba, ganin da yayi zata cigaba da 6ata masa lokaci ne ya sanya shi tamke fuskar sa sannan ya hau kan gadon ya zauna kana ya sanya tattausan hannun sa yana k'ok'arin rik'o ta, wani sabon kukan ta sake fashewa dashi tana cigaba da komawa baya, hannu biyu ya saka ya janyo ta gaba d'ayan ta cikin jikin sa, duk da yanda take cigaba da k'ok'arin k'wacewa tana kukan ta hakan be hana shi zagaye ta da d'ayan hannun sa ba sannan ya fara k'ok'arin zame hijab d'in jikin ta, lokaci d'aya bugun zuciyar sa ya k'aru, wani irin kasala na saukar masa, d'an lumshe idanun sa yayi kafin ya bud'e har lokacin yana jin yanda take cigaba da kici kicin k'wace kan ta, be bi ta kan ta ba kawae ya saka hannun nasa ya zame hijab d'in zuwa kan kafad'ar ta, sannan babu 6ata lokaci yayi mata allurar, k'ara ta saka sanda taji tsinin allurar ya shige ta bata san sanda ta ruk'unk'ume shi ba lokaci d'aya gaba d'aya jikin ta ya wani saki, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya saki sanda ta ruk'unk'ume shin, idanun sa a lumshe ya sake rik'e ta gam yana sauke taggwan ajiyar zuciya, sun kae wajen minti 1 a hakan har lokacin tana kuka a hankali, se a lokacin ta fara tuna a'ina take kuma a jikin wa take, da sauri ta saka hannun ta ta ture shi sannan ta tashi da sauri k'irjin ta na bugawa, se a lokacin ya bud'e idanun sa da suka sake lumshewa ba tare daya kalle ta ba ya mik'e ya k'arasa ya jefar da allurar cikin dustbin sannan ya juyo ya d'an kalle ta k'asa k'asa "Tashi mu tafi" tun d'azun bata kalle shi ba se yanzu da taji yayi maganar nan da saurin da bata san tana dashi ba ta diro daga kan gadon duk da har yanzun tana d'an jin jiri amma tama manta da hakan, murmushin da tun kafin tasan wanene Abbun Raj rabon ta dayi ya su6uce akan fuskar ta lokaci d'aya kuma tana sake goge fuskar ta, wannan d'an murmushin da tayi seda yasa ya d'an ji sanyi har cikin ran sa, ganin tana k'ok'arin riga shi fita ma ya sanya shi fad'in "Je ki wanke fuskar ki" yayi maganar yana tattara abinda ze fita dasu daga cikin asibitin dan so yake ya chanja mata asibiti idan bata samu sauk'i ba, kamar zata yi musu se kuma kawae ta juya ta fad'a inda taga yayi mata kama da toilet, babu jimawa ta fito tana sake sharce ruwan dake kan fuskar ta, ba tace komae ba haka zalika shima bece komae ba yayi gaba ita kuma tabi bayan sa, seda ya kulle Office d'in sannan ya cigaba da tafiya a nutse, ita kuma tana bin bayan sa, duk haka kurum take jin ta a wani irin takure, d'an jiri jirin da take ji ya sanya tafiyar ta ta ta sake zama very slow, se kuma idan taga ya mata nisa sannan ta saka iya k'arfin ta ta kusa cimmasa, yadda ake d'an satar kallan su ne ya sanya shi sake tattaro girar sama data k'asa ya had'e su waje d'aya, dan haka yawanci mutane se suka shiga hayyacin su, seda ya tsaya a pharmacy ya kar6ar mata magunguna har lokacin tana bayan sa kamar wata munafuka se bin wajen take yi da kallo har zuwa sanda suka fita harabar asibitin, yana shirin bud'e mata k'ofar wajen me zaman banza kamar wanda aka tsikara kuma seya fasa, ya sake kicin kicin da rae dan abinda yake k'ok'arin aekatawa yanzun yasan wata rigimar ce ze kuma 6allowa, seya zagaya ya shiga driver seat ya zauna, ganin da tayi bece da ita komae ba ya sanya itama ta sake had'e ta ta fuskar kana ta bud'e ta shiga, babu 6ata lokaci yaja motar ya fice daga asibitin, sanda suka hau titin seta samu kan ta da juyawa tana k'arewa titin kallo, in dae har ba tayi mistake ba nan titin Kano ne, bata san sanda ta saki wani murmushi me sauti ba tana ji kamar ta tashi ta taka rawa, duk da yadda yaji tayi murmushin hakan be sanya shi kallan ta ba sema sake tsuke face da yayi, haka ya cigaba da tafiya tana cigaba da bin titin da kallo, ita dae ba taga yayi hanyar unguwar su ba, tun tana k'ok'arin yin shiru taga iya gudun ruwan sa har taji zuciyar ta na son karaya ta kalle shi yadda yake driving a nutse sannan ta d'auke kae tana 6ata fuska itama "Bafa nan ne unguwar mu ba mu" tayi maganar murya a cunkushe, yadda tayi maganar ne ya sanya shi yin murmushin dabe shirya ba, gudun kada ta gan shi ya sanya shi saurin sake had'e fuska, kamar ba zece komae ba se kuma can bayan ya gama jan ajin sa yace "A haka zaki koma musu gidan kamar korarriya? So kike hankalin su ya sake tashi fiye da da? Zamu je kiyi wanka ne ki chanja kaya sannan na maeda ki gidan" yayi maganar cikin tsare gida shima tasa muryar a cunkushe "Toh ina ruwan ka?" ta fad'a bayan ta jefa masa harara, daga inda take tana ji kamar ta tashi ta rufe shi da duka, yace taemakon ta zeyi, ya taemake tan to kuma ina ruwan sa da yadda zata koma gida? Meye nasa a ciki? D'aga kafad'a yayi yana ta6e baki sannan yace "Babu ruwa na, amma ni dae bazan kae ki gida a haka ba" kallan jikin ta ta shiga yi, dan ita dae bata ga abinda tayi ba da yake nema ya fad'a mata magana ba dan haka ta sake kufula tace "Toh ka ajje ni in tafi da kae na mana, bana buk'atar taemakon ka a karo na biyu" ta fad'a tana jin yanda zuciyar ta ke mata zafi, be kula ta ba haka kuma be kalle ta ba hakan ya sake fusata ta, se kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya tana runtse idanu, yasan yanzu zata soma kukan nan nata da bata gajiya dashi dan haka yana karya kwanar wani layi yace a nutse "Shikenan muje na rubuta takaddar ki tafi" jin abinda ya fad'a d'in ne ya sanya ta kalli inda suka shigo sannan taja doguwar ajiyar zuciya tana hana kukan daya taho mata fitowa, a k'ofar wani gida ya tsaya da motar tasa sannan ya dakata ya d'auki wayar sa ya danno number Yaseer ya kira, bata dad'e tana ringing ba Yaseer ya d'aga "Kana gida ne?" Rk ya fad'a "Ehh.. Na dawo" Yaseer ya fad'a daga inda yake zaune kusa da matar sa Hameeda "Toh gani k'ofar gidan ka" dariya Yaseer yayi gami da fad'in "Haba mana Mr man, ae ba seka zolaye ni ba, nasan ba ta6a zuwa zaka yi ba" d'an murmushi kad'an Rk yayi sannan yace "Toh ka fito ka tabbatar mana, hope dae Madam na nan?" da mamaki Yaseer ya kalli Hameeda sannan yace "Yeah, amma dae fari dae bari na fito dan tabbatarwa" ya fad'a yana mik'ewa sannan ya kalli Hameeda yace "Yanzu Rk ze shigo, yace min yana waje" "Ikon Allah! Amma kuma babu sanarwa irin wannan babban bak'o haka?" "Ke dae bari naje na fara tabbatar da zuwan nasa" Yaseer ya fad'a yana ficewa daga d'akin. Kallan sa ta cigaba dayi da manyan idanun ta da suka yi rau rau sanda yake wayar, har zuwa sanda taga yana shirin ajje wayar, yana sane da kallan da take masa dan haka ya sake rik'e wayar sannan yace "Ka taho min da takadda da biro" se a lokacin ta d'auke kan ta daga kallan sa tana sauke ajiyar zuciya, "gaba d'aya yau lokaci baya sauri" ta ayyana a ran ta. Suna nan zaune babu wanda ke cewa da d'an uwan sa uffan, se ga Yaseer ya bud'e gate d'in gidan ya fito, da murmushi ya k'araso bakin motar Rk d'in yana fad'in "Ohh Rk ashe da gaske kake? Ban ta6a tunani ba wallahi" ya fad'a dae_dae sanda idanun sa suka sauka akan Ayrah dake zaune tana jira a mik'o mata takaddar ta ta wuce gidan su (lol), murmushi Rk yayi kana ya bud'e murfin motar ya fita ya kama hannun Yaseer suka gaesa "Wacece wannan?" Yaseer ya fad'a yana kallan cikin motar sannan ya dawo da duban sa kan Rk, iska Rk ya fesar daga bakin sa sannan yace "Muje ciki zan maka bayani" sosae kan Yaseer ya kulle, shi dae yasan Rk d'in bashi da wata budurwa balle yace budurwar sa ce, kae abinda ma ya sani a yadda yasan Rk d'in baze ta6a d'aukar budurwar sa yaje da ita wani gidan ba, amma jin abinda ya fad'a ya sanya shi fad'in "Ohk, let's get in" Yaseer ya fad'a yana yin gaba, komawa Rk yayi ya lek'a ta window d'in side d'in sa sannan yace yana kallan ta yadda idanun ta suka sake cika taff da hawaye, baya so yayi wani abun da zesa ta sake yin kukan dan haka ya karyar da murya yace a tsanake "Kiyi hak'uri Madam, ya manta be fito da takaddar ba, kizo muje ciki in rubuta acan" "Ka aeko a kawo min" ta fad'a tana d'auke kae "Shikenan tunda baki shirya kar6a ba" ya fad'a yana mik'ewa ya fara takawa, babu shiri ta bud'e murfin motar ta fito tana sauke numfashi a jere a jere, murmushi ya saki lokaci d'aya yana kae hannun sa kan kwantacciyar sumar kan sa ya shafa, tana ganin ya shige cikin gidan itama ta saka k'afar ta "Barka dae Madam" Yaseer ya fad'a yana kallan ta, kamar baza tace komae ba se kuma ta d'an saci kallan sa tace ciki ciki "Ina wuni?" shi bema ji ta ba dan haka ya sake jerawa da Rk suka cigaba da tafiya se dae babu wanda ke cewa komae, ita kuma tana bayan su tana bin Rk d'in cike da sassarfa, a haka har suka k'arasa cikin parlourn "Bismilllah The great Rk" Yaseer ya fad'a yana murmushi dan sosae yaji dad'in ganin Rk d'in, shima murmushin ya maeda masa sannan ya k'arasa cikin parlourn ya zauna kan had'ad'd'iyar kujerar dake cikin parlourn, tsayawa tayi kawae tana cigaba da kallan sa, so take kawae taga ya d'auki takadda amma bata gani ba dan haka ta cigaba da tsayuwar ta "Madam ki shigo mana!" Yaseer ya fad'a yana kallan Ayrah "Rabu da ita, bata buk'atar komawa gida ne" Rk ya fad'a yana d'an kallan ta ta gefen ido, a hankali ta cigaba ta takowa zuwa cikin d'akin har lokacin idanun ta na cike da k'wallar nan, seta nemi gefen wata kujera ta zauna tana cigaba da k'ik'k'ifta idanu, murmushi Yaseer yayi dan ya fahimci kuka take 6oyewa, toh wacece ita? Ya k'agu yaji menene had'in ta da Rk d'in, dae_dae lokacin Hameeda ta fito daga d'aki sanye cikin doguwar rigar atamfa da mayafi madaedaeci, ta k'araso cikin d'akin fuskar ta d'auke da murmushi tace "Barkan ku da zuwa" ta fad'a tana neman kusa da Ayrah da bata ma kalle ta ba ta zauna "Yawwah barka dae Madam, mun same ku lafiya?" Rk ya fad'a shima da d'an murmushin dake k'ara masa kyau akan fuskar sa "Lafiya k'alau Alhamdulillah, da alama dae wannan ce sirikar tamu?" ta fad'a tana kallan Ayrahn, da kallan farko ta mata ta hango zallar kyan da take dashi, wani kallo Ayrah ta d'aga narkakkun idanun ta ta watsawa Hameeda, ita kan ta Hameedan seta gaza gane wane irin kallo ne wannan? Murmushin yak'e yayi dan baya so su sake 6allo masa wani aekin yace yana mik'ewa "Amm Madam.. Pls ga sister nan zata d'an yi wanka ta shirya pls, zuwa anjima zan zo na d'auke ta" duka kallan sa suke yi cike da mamaki, Yaseer yayi k'arfin halin fad'in "Bangane ba?" lumshe idanun sa yayi yana fesar da iska daga bakin sa sannan ya bud'e idanun nasa yana kallan Yaseer yace "Plsss idan na dawo zamu yi maganar, Abbu na jira na" ya fad'a yana fara yin gaba, mik'ewa tayi itama dae_dae lokacin da hawayen da suka dad'e cikin idanun ta suka samu damar zubowa akan fuskar ta, lura da hakan ya sanya shi d'an dakatawa kana yace a hankali yana kallan ta "Ki shirya, ina dawowa se mu wuce.." ya fad'a cikin taushi, ita dae ba tace komae ba se sake share hawayen da tayi yayin da shi kuma ya fice daga d'akin cike da fatan kada ta tubure masa, Yaseer da Hameeda suka kalli junan su cike da mamakin wannan abu, sauke numfashi Yaseer yayi kana yabi bayan Rk daya fita "Malam nifa bangane abinda kake nufi ba, ya zaka tafi kuma ka barmu cikin duhu? Ka fara warware mana wacece waccan d'in kafin ka bar gidan nan" numfashi ya sake fesarwa daga bakin sa sannan yace "Sorry Friend, zance ne me tsayi amma ina gamawa da Abbu nan zan dawo pls" yayi maganar sanda ya bud'e murfin driver seat "Shikenan karka d'au lokaci pls" "In Sha Allah" Rk ya fad'a yana shigewa cikin motar "Ammm pls kada a barta taje ko'ina kamin na dawo" Rk ya fad'a yana kallan Yaseer, yanzu kam kan Yaseer ya sake kullewa da al'amarin abokin nasa, dan haka bece komae ba ya bishi da kallo kawae, shi kuma Rk tunda yasan Yaseer d'in yaji abinda ya fad'a d'in ya sanya shi jan motar, bin sa da kallo Yaseer ya sake yi har ya fice daga cikin layin sannan ya sauke ajiyar zuciya yana komawa cikin gidan, "lallae akwae wani abun" ya fad'a a k'asan ran sa. ... Kae tsaye gida ya wuce zuciyar sa cike da sak'e_sak'e kala_kala, ya k'arasa yayi parking motar sa sannan ya fita ya shige cikin gidan, parlourn Abbu ya wuce da sallama d'auke a bakin sa ya shiga, Abbun na zaune akan kujera yana shan lemo gefe guda kuma yana kallo cikin k'atuwar T.Vn dake manne a jikin bango, seda ya d'auki remote ya rage volume d'in T.Vn sannan ya amsa sallamar Rk daya k'arasa shigowa cikin d'akin, murmushi ne ya su6uce akan fuskar Abbu sanda Rk yace "Barka da wannan lokacin Abbu" "Barka dae likita ya kamata ka samu bacci haka nan" jinjina kae Rk yayi yana yin d'an murmushin kana yace "In Sha Allah Abbu" gyara zama Abbu yayi daga inda yake zaune sannan yace bayan yayi gyaran murya "Wato maganar da nake so nayi da kae ita kan ta tana buk'atar nutsuwa, dan haka da zarar ka gama samun baccin da baka samu ba seka fara shirye_shirye saboda rashin ishashshen lokaci" Abbu ya fad'a yana d'an dakatawa, duk da Rk be fahimci maganar Abbun ba amma hakan be sanya shi cewa komae ba, yayi shiru yana cigaba da saurarar Abbun dan yasan ze warware masa komae ne "Dama magana ce akan auren ka da Muneerah da za'a gabatar dashi nan da sati d'aya" Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 034 ___Seda ya d'au wajen minti 1 bece komae ba yana ta kokawa da zuciyar sa akan zafin da take masa kada kuma 6acin rae yasa ya furta abinda be dace ba sannan a hankali ya d'aga idanun sa da suka sauya kala ya kalli Abbu "Abbu aure ka nemar min hadda tsaeda rana ba tare da sani na ba?" ya fad'a ba tare dama yana sanin abinda ke fita daga bakin sa ba saboda tsananin 6acin rae, da mamaki Abbu ya kalle shi na tsawon sakanni, sosae yayi mamakin jin abinda ke fitowa daga bakin Rk d'in amma seya sake gyara zama sannan yace har lokacin yana kallan sa "Toh ko ban isa bane?" se a lokacin Rk ya tuna abinda ya fad'a d'in a hankali ya d'an lumshe idanun sa sannan ya bud'e a nutse kuma a hankali ya furta "Abbu ka isa.." daga haka ya mik'e cike da sassarfa ya fice daga d'akin, bin sa da kallo Abbu yayi har zuwa lokacin daya gama ficewa daga d'akin sannan ya dawo da duban sa cikin d'akin yana jinjina kae. ... A hankali ya nemi waje ya zauna akan gadon sa idanun sa a lumshe, a karo na barkatae ya sake fidda iska daga bakin sa, hannu ya kae ya dafe kan sa daya cigaba da sara masa, ya kae wajen minti 5 a hakan yana sauke numfashi a jere a jere saboda yanda zuciyar sa ke cigaba da tafasa sannan ya mik'e kamar me tunanin wani abun se kuma ya koma ya zauna, tabbas Abbu na neman sakawa zuciyar sa ta buga, ta yaya ze iya kallan wata matar a matsayin matar sa bayan Ayrah? Be san ta yaya hakan ze kasance ba, son da yakewa Ayrah yana da yawa baya tunanin ko da ya auri wata ze iya adalci a tsakanin ku, toh ta yaya ma ze auri wata? Koda be auri Ayrah ba baya tunanin ze iya auren wata matar ballantana kuma yanzun daya same ta, se dae ga Abbu na neman saka shi auren wata bayan ita, baya so kuma ya d'auki zunubi akan hakan, amma ta yaya ze kalli Abbun ya fad'a masa baya son Muneerah saboda yana da wata matar daya aura ba tare da sanin su ba? Hannun sa ya kae ya cusa cikin kwantacciyar sumar kan sa nan take kuwa ta hargitse seya koma ya kwanta kawae cikin rashin sanin abinyi. ... A 6angaren Ayrah kuwa sanda Rk ya fita daga cikin d'akin seta cigaba kawae da kallan k'ofar kamar me tunani "Muje na kae ki d'akin koh?" Hameedah ta fad'a tana murmushi, kamar ta mata banza se kuma taga gwara kawae ayi komae a yanzu a gama a wuce wajen, dan haka se kawae tayi gaba ta fara tafiya a hankali, Hameedahn seta wuce ta ta k'arasa zuwa bakin wani d'aki tace tana kallan ta "Ki shiga kiyi wankan zan kawo miki kaya seki saka" se a lokacin ta iya bud'e baki tace "Toh" sannan ta shige cikin d'akin, madaedaecin d'aki ne me d'auke da gado, wardrobe da kuma toilet, bata tsaya tabi ta kan d'akin ba kawae ta fad'a toilet d'in, anan d'in ma ba wani dad'ewa tayi ba dan haka ko minti 15 ba tayi ba ta fito sanye da hijab d'in, se a lokacin ta tsaya tana k'arewa d'akin kallo kafin ta d'auke kan ta ta maeda shi zuwa k'ofar d'akin da aka turo, Hameedah ce ta shigo yanzu hannun ta d'auke da riga har da sabon hijab ta k'araso tana bin ta da murmushin dae, seda ta ajje kan gadon sannan tace "Bari na kawo miki abinci" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa "Na k'oshi ni" tayi maganar a cunkushe, kallan ta Hameedah tayi ganin yanda ta wani d'auke kae ya sanya ta girgiza kae kawae ta fice daga d'akin, seda ta fita sannan Ayrah ta d'auki doguwar rigar abayar ta zura kana ta d'ora hijab d'in akae sannan tayi sallah ta mik'e ta cigaba da tsayuwa tana jiran dawowar sa, tun tana tsayen har ta gaji da tsayawar seta nemi gefen gadon ta d'an zauna tana share k'walla, yanzu kam idan har ya k'ara awa 1 bezo ba zata tashi ta tafi gidan su ne, ita kuma takaddar ya rik'e ta karya bayar, se yayi ta zama da auren shi kad'ae, ita ba abinda ya dame ta. ... A kujerun da suke ajje a compound d'in gidan suke zaune kowanne kan kujera d'aya, kallan sa Yaseer yake sosae yana nazarin yanayin sa, daga d'azu zuwa yanzu se yake ganin kamar ya sake chanjawa "Wae me yake faruwa ne Rk?" d'an murmushin yak'e Rk yayi sannan yace bayan ya yatsina fuskar sa "Yaseer, ina cikin matsala fa" "Matsala kuma? Wace iriyar matsala? Ko da yake da farko dae ya kamata koma wacece waccan yarinyar ka maeda ta gida tunda kaga dare na sake yi" kallan sa Rk yayi sannan ya d'auke kan sa bayan ya sauke ajiyar zuciya yace a nutse kamar babu abinda ke damunsa "Mata ta ce!" cigaba da kallan sa Yaseer yayi yana so ya gano ko dae abokin nasa ya fara shan k'waya ne? A iya sanin sa abokin nasa baya shaye shaye amma se gashi yau yayi magana irin ta en shaye shaye, se kuma ya saka wata dariya kana yayi shiru yana cigaba da kallan sa "Tsaya mana pls, ni fa wallahi ba maganar raenin hankali nake maka ba" murmushi Rk yayi yana kallan Yaseer dake magana da iya gaskiyar sa, seda ya d'an lumshe idanun sa kad'an sannan ya bud'e a lokaci guda kana yace "Am serious fah, mata ta ce ta sunnah" yayi maganar yanzu ma a nutse "Look Friend, don Allah joke apart.." yayi saurin katse shi, dan kuwa ya gaji da jin wannan tatsuniyar tasa, gyara zama Rk yayi sannan ya fara da "Nima ba wasa nake ba Yaseer, auren ne ya kasance kamar shirin film, ni kuma nayi kasada nayi aure ba tare da izinin su Abbu ba" daga nan ya shiga labartawa Yaseer d'in yadda auren nasu ya kasance, har ya k'are labarin Yaseer bece dashi uffan ba kawae kallan sa yake cike da mamaki, shima kansa daya gama bada labarin be d'aga ido ya kalli Yaseer d'in ba, sun kae wajen minti 2 a haka kafin Yaseer ya sauke ajiyar zuciya yace "Lallae Rk, aure ba tare da izinin su Abbu ba? Baka tunanin wannan wani babban kuskure ne ka aekata?" "Ya zanyi Yaseer? Ina kallo wani ya aure ta a gaba na? Ko kuma na maeda ta gida su aura mata wani bani ba?" ya fad'a yana kallan Yaseer da har lokacin mamaki yak'i barin sa, cike da mamaki Yaseer yace "A'ah na kasa gane duk wannan abin, meyasa iyayen ta zasu ce baza ka aure ta ba? Idan ma akwae wani dalilin ina ganin kamar Abbu ne zece baza ka aure ta ba saboda wannan dalilin koh?" ya k'are maganar da sigar tambaya, ta6e baki Rk yayi, shi kan sa a wannan wajen be san abinda zece ba, be san dalilin hakan ba, da farko kamar Ayrahn na bayan sa duk da yadda iyayen su kace baze aure ta ba, se kuma daga k'arshe gaba d'aya ta juya masa baya "Amma meyasa ba zaka tambaye ta dalilin ta na juya maka baya ba?" Yaseer ya katse masa tunanin da yake yi kamar yasan abinda yake sak'awa a ransa, ajiye numfashi yayi kafin yace "Tak'i bani wannan damar Yaseer, tun farko abinda naso inji kenan a lokacin ne kuma ta birkice min, yanzu kuma bani da k'warin gwuiwar tambayar ta dalilin hakan tunda ga abinda ya faru" jinjina kae Yaseer ya shiga yi cike da gamsuwa da maganar Rk d'in amma duk da haka yace "Amma yaushe zaka sanar dasu Abbun?" seda ya d'aga ido ya kalli Yaseer d'in sannan yace bayan ya girgiza kae "Ba yanzu ba Yaseer, maganar da nake maka aure na da Muneerah rana ita yau ne, me kake tunanin ze faru idan na fad'awa Abbu maganar nan?" ya k'are maganar yana d'an ajje numfashi, shima Yaseer sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace "Hakane kuma" ya fad'a yana jinjina kae cike da tunani a zuciyar sa ko ze samowa Abokin nasa mafita. ... Tana zaune cikin d'akin a ranta tana k'iyasta adadin lokacin da take jira ya cika ta tashi ta fita daga d'akin, wani irin bacci me dad'i ke ta sakad'ar ta tun d'azun, se yakice shi take yi ta k'arfi da yaji amma se dad'a lumshe idanu take yi kamar wadda tasha kayan maye, ko cikakken minti 1 bata k'ara ba ta 6ingire kan gadon se bacci. Sosae Rk yaji dad'i lokacin da Hameedah ke sanar dashi Ayrahn bacci take yi, dan haka ya d'an samu relief, hatta maganin ta ma bebi takan a tashe ta tasha a daren ba, a cewar sa goben seta sha tunda dae yanzu ta samu bacci, ko ba komae ze d'an samu nutsuwar zuciya kafin goben daya san me raba shi da ita se Allah. A hankali ta shiga bud'e narkakkun idanun ta da suka mata nauyi, har ta gama bud'e su tarr cikin d'akin, da sauri ta mik'e zaune tana cigaba da kallan d'akin, kallan agogon dake manne a jikin bangon d'akin wanda ya harba k'arfe 6:00 tayi, seta sake kallan agogon kamar me k'aryata abinda ta gani, se dae ga mamakin ta hakan dae ya sake nuna mata, wannan wane irin bacci ne? Bata san sanda hawaye ya soma sintiri akan kuncin ta ba, ta mik'e da wani irin sauri ta dirga daga kan gadon, sabon brush d'in data gani akan gadon ta d'auka ta fad'a toilet d'in tayi alwala tayi brush sannan ta fito tayi sallah tana istigfari cikin ran ta, bata san wane irin nannauyan bacci ne haka ya d'auke ta cikin k'ank'anin lokaci irin wannan ba, seda ta idar da Sallahr sannan ta sake fad'awa toilet d'in tayi wanka kana ta shirya yanzu ma cikin abayar data gani akan gadon ta maeda hijab d'in jikin ta ba tare data shafa komae akan fuskar ta ba ko ta shafa wani abu me kama da mae ba ta k'arasa ta ta6a k'ofar d'akin, cikin sa'a kuwa se taji ta a bud'e, sauke ajiyar zuciya tayi sannan ta k'arasa fitowa daga cikin d'akin, ba tare data kalli ko'ina ba kawae tayi hanyar fita daga cikin d'akin, daga inda yake zaune kan dinning shi da Yaseer ya mik'e da sauri dan tunda ta fito yake ankare da ita, bece da ita komae ba kawae ya k'arasa a nutse zuwa gaban ta, dakatawa tayi da sauri ganin yanda ya tsaya d'in dab da ita, Yaseer dake zaune shima ya mik'e ya bar parlourn gaba d'aya, se a lokacin ya d'aga hannayen sa ya sak'ale su a k'irjin sa sannan ya zuba mata idanun sa gaba d'aya, k'ok'arin komawa gefe ta soma yi ba tare data kalle shi ba har lokacin fuskar ta a had'e "Ina zaki je?" ya fad'a a nutse har lokacin idanun sa na kan ta, bata dae kalle shin ba se d'aga kae da tayi kawae ta kalli gefen sa sannan ta sake had'e fuska tace k'irjin ta na d'an bugawa saboda yadda ya tsare ta da idanun sa "Gidan mu zan tafi!" ta fad'a lokacin da wasu ruwan hawaye suka taru a cikin idanun ta, cike da fatan kada ya kawo wata maganar dake nuni da k'in zuwan ta "Gidan ku kuma?" ya tambaya yana d'an d'age girar sa guda d'aya yana cigaba da bin ta da wani irin kallo saboda yadda yaga ta masa wani shahararren kyau kamar ba cikin tashin hankali take ba, ba tace komae ba tunda tasan ae yaji abinda ta fad'a d'in dan haka ta sake k'ok'arin tafiya "Toh ya zakiyi da aure na kuma da yake kan ki?" "Zan fad'awa Abba na abinda ya faru, nasan zasu warware auren gaba d'aya.." ta fad'a har lokacin fuskar ta a had'e, murmushi ya saki daga inda yake tsaye sannan ya d'an lumshe idanun sa kad'an kana yace "Ohk je ki.." bata sake cewa komae ba ta sauke ajiyar zuciya sannan tabi gefen sa ta fice daga d'akin, bin ta yayi da kallo yana mamakin ta, sosae yake mamakin ta musamman idan ya tuna yanda suka fara soyayyar su hankali kwance amma rana d'aya ta sauya kamar ba ita ba, be ta6a tunanin zata ta6a juya masa baya ba, ya d'auka zata taya shi fafutuka ne da kuma nemo hanyar da zesa iyayen su su amince da auren su, se yanzu yaji inama kafin ta fita ya tambaye ta dalilin sauyawar ta? Koda yake yana da 80% sure cewar maganar iyayen ta kawae tabi yasa ta chanja masa, yasan tana k'aunar sa fiye da zaton sa, amma kuma soyayyar iyayen ta ta danne tashi, amma meyasa tun farko bata chanja ba se daga baya? Meyasa haka? Shi kad'ae yake tunanin sa kuma yasan babu me amsa masa dan haka kawae ya sauke hannayen sa sannan ya fita daga cikin d'akin, yana hango ta sanda ta fita zuwa k'ofar gidan, seda ta fita d'in sannan ya k'arasa ya hau motar sa ya jata shima ya fice daga gidan, a nutse kuma cike da takatsantsan yake bin ta a baya, baya so ta fahimci bin ta yake dan haka yake bin ta a hankali, itama a hankali take tafiya kamar wadda k'wae ya fashewa a ciki, se dae hakan na da nasaba ne da jikin ta da har lokacin take ji be koma mata dae_dae ba, a haka har ta fita titi ta tsaya tana kallan motocin da suke wucewa, se a lokacin ta tuna babu ko sisi a tare da ita, amma koma menene gwara taje gidan idan yaso seta kar6a ta bawa me Napep d'in, dan haka babu 6ata lokaci ta shiga tsare adaedaeta, daga cikin layin ya dakata da motar tasa yana ganin ta har zuwa sanda wata k'atuwar mota me kyau ta dawo da baya tayi parking a gaban Ayrah, d'an runtse idanun sa yayi yana jiran ganin abinda ze faru next, dae_dae lokacin da mutumin cikin motar ke k'ok'arin fitowa ita kuma ta gama fad'awa me Napep d'in data tara inda zata je, babu 6ata lokaci ta fad'a ciki dae_dae lokacin da mutumin ya gama fitowa daga cikin motar, wani banzan kallo Rk yabi shi da shi yana jin yanda zuciyar sa ta fara tafasa lokaci d'aya, tana shiga kuma me Napep d'in yaja, mutumin na shirin yin magana yaga yaja adaedaetar sa "Kashhh!" ya furta yana bin adaedaetar da kallo sanda suka wuce shi, se a lokacin Rk yaja motar sa ya fito daga cikin layin har lokacin yana d'an kallan mutumin yaga ko zeyi wani abun bayan nan, se dae yaga beyi ko k'ok'arin bin su ba, se a lokacin ya d'an ji sanyi sannan ya cigaba da bin ta, yana cikin driving d'in wayar sa ta soma ringing, kamar baze kalli me kiran ba se kuma ya kalla "Muneerah" shine abinda ya bayyana akan screen d'in wayar, runtse idanun sa yayi zuciyar sa na cigaba da wani irin zafi, kawae seya kae hannun sa ya kashe wayar gaba d'aya sannan ya jefa ta kan kujerar me zaman banza ya cigaba da driving d'in sa yana jin yadda ran sa ke kuma 6aci. Har cikin layin su ya shigar da ita seda suka kusa kaewa k'ofar gidan su sannan tace "Ya isa" babu 6ata lokaci ya tsaya ta sauka, se kuma ta d'an yi shiru tana tunanin yadda zata shaeda masa seta shiga gida ta kar6o kud'i, a ranta tana fatan Allah yasa me mutunci ne, ganin dae babu wata mafita ya sanya ta fad'in "Bari na kar6o kud'in don Allah.." kallan ta yayi sannan yace "Toh shikenan amma kiyi sauri don Allah" sauke ajiyar zuciya tayi kana a hankali ta juya, a hankali ta sauke idanun ta akan gidan nasu, se ta shiga kallan sa kamar yau ta fara ganin sa, a hankali ta lumshe idanun ta sannan ta taka k'afar ta cikin soron gidan nasu tana jin yadda bugun zuciyar ta ya k'aru lokaci guda.. Mhiz Innocent..... ✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 035 ___A hankali ta cigaba da takawa zuwa cikin gidan har zuwa sanda ta k'arasa cikin tsakar gidan, Abba da Yah Sadeeq suna zaune a tsakar gidan, yayin da Umma ke fitowa daga cikin kitchen hannun ta d'auke da tea flask ta k'araso ta ajje a gaban su Abba "Sannu da k'ok'ari" Abba ya fad'a, seta d'an yi murmurshi sannan ta fara k'ok'arin mik'ewa, dae_dae lokacin data d'ago d'in yayi dae_dae da lokacin da Ayrah ta shigo cikin gidan kuma idanun ta suka fara sauka akan Umma, da gudu ta k'arasa bata yi wata wata ba ta rungume ta tana fashewa da wani kuka me tsuma zuciyar me sauraro, lumshe idanu Umma tayi sanda Ayrahn ta rungume ta, lokaci d'aya taji zuciyar ta ta wani irin karyewa, babu 6ata lokaci itama ta rungume d'iyar ta ta, tana hana kan ta yin kuka kada su had'u su zama su biyu, Abba da Yah Sadeeq kallan su kawae suke yi babu wanda ya iya cewa komae har zuwa sanda Ayrah ta gaji da kukan ta soma durk'ushewa akan k'afafun ta, rik'o ta Umma tayi kafin ta kae k'asan se suka k'arasa zubewa a k'asan, a hankali taja sheshshek'ar kuka sannan tace "Umma!!" kallan ta Umma tayi kamar me son gano gaskiyar al'amari daga cikin idanun Ayrahn, idan ta tuna yanda Ayrahn ta fice daga gidan ba tare da izinin su ba se taji kamar ta sake ta ta tashi tayi tafiyar ta, amma kuma ta rasa dalilin da yasa ta kasa aekata hakan, bata amsa kiran da Ayrahn ta mata ba har zuwa sanda Ayrahn ta kalli Abba da har lokacin kallan ta yake tace "Abba na!" "Daga ina kike?" shine abinda ya fara fitowa daga bakin Abba yana tsare ta da idanu, seda ta d'an lumshe idanu nan take k'irjin ta ya soma bugawa idan ta tuna abinda ze fito daga bakin na ta, ba tare da tunanin komae ba ba kuma tare da tsayawa dogon nazari ba ta furta "Abba ban san daga inda zan fara ba Umma wani cukurkudad'd'en al'amari ne Umma" ta k'arasa maganar tana kallan Umma, dukkan su zuba mata ido suka yi suna kallan ta musamman Yah Sadeeq dake karanto zallar gaskiya a tattare da k'anwar ta sa amma duk da haka bece komae ba, ganin da tayi duk suna kallan ta ya sanya ta cigaba da fad'in "Umma yanzu haka an d'aura mana aure da Raj fa!" ta k'arasa fad'a tana jin wani zafi da ciwo a cikin zuciyar ta musamman yanzu data tuna a gaban Abba ne kuma laefin da aka yiwa Abba ne ya sanya yace ba zata aure shi ba, da wani irin sauri Umma ta saki Ayrah dake jikin ta sannan ta soma matsawa gefe har lokacin idanun ta akan Ayrahn k'irjin ta kuma still yana bugawa da k'arfin daya wuce na d'azu, Abba da Yah Sadeeq suma duka kallan ta suke yi kafin Abba ya girgiza kae yana d'auke kae wani murmushin takaeci me ciwo na su6uce masa, shi kan sa ji yake daze iya kuka da yayi koda abinda yake ji cikin zuciyar sa ze ragu, ya d'auki sakanni masu yawa a hakan sannan ya juyo yana cigaba da kallan Ayrahn dake share hawayen fuskar ta "Ashe zargin da muke gaskiya ne Ayrah? Bama iya za6ar namiji ki kayi akan mu ba? Kin je kin auri abinda zuciyar ki ke so acan wani wajen? Bama iya guduwa kika yi ba Ayrah? Hadda aure ku kayi? Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" Abba ya fad'a yana sauke numfashi saboda yadda k'irjin sa ya masa wani irin nauyi sannan a hankali ya zame a wajen ya kwanta ko zeji sauk'in abinda yake ji, se a lokacin hawayen da suka taru a cikin idanun Umma suka zubo cike da takaeci ta furta "Ayrah kin cuce mu kin cuci kan ki, kin wulak'anta mu kin wulak'anta kan ki, kin tozarta mu kin tozarta kan ki tunda har kika iya d'aukar jiki kika bi saurayi kuka tafi wani wajen aka d'aura muku aure saboda iyayen ki sun ce basa son shi, meyasa kika yi haka Ayrah?" Umma ta k'arasa fad'a wasu zafafan hawaye suna zuba akan fuskar ta, Yah Sadeeq dake gefe kawae kallan su yake yi su duka musamman Ayrah da yaga ta rikice daga kallan daya mata tun farkon lokacin da Abba ya fara magana, a hankali ta shiga girgiza kae k'irjin ta na wani irin bugawa idanun ta da suka cika taff da hawaye har wani dishi_dishi suke gani, cikin kuka ta kalli Umma tana girgiza kae tace "Umma ku yafe min don Allah, Umma nayi nadamar zuwa na duniya, ni banza ce kuma shashasha Umma, Umma ku tsaya inyi muku bayanin abinda ya faru don Allah.. wallahi.." d'aga mata hannu Abba yayi daga inda yake kwance dafe da saetin zuciyar sa yace "Ki tashi ki fita a gidan nan, bana son na sake ganin ki cikin gidan nan, kin za6i d'a namiji akan mu saboda haka kije duniya ce ae.." sake fashewa da kuka tayi a cikin ranta tana maemaeta kalmar "Innalillahi wa inna ilaehi rajiun" shin me yake shirin faruwa ne? A cikin su babu wanda ze tsaya ya saurare ta tayi musu cikakken bayani "Umma bani da laefi" ta fad'a cikin kuka, ba tare da Umma ta kalle ta ba tana jin wani iri cikin ranta, tana jin danasanin haehuwar 'ya irin ta, data san idan tazo duniya zata bijirewa umarnin su ta aekata wannan mummunan abun da har su mutu ba za'a bar yin gulmar su da hakan ba da tun farko tayi addu'ar Allah yasa cikin ya zube "Ki tashi ki fita a gidan nan bana son sake ganin ki, idan kuma na sake ganin k'afar ki cikin gidan nan sena tsine miki.." Umman ta k'arasa fad'a tana gyarawa Abba kwanciya lokaci guda kuma tana goge hawayen da suka k'i tsayawa da zuba akan fuskar ta, runtse idanun ta tayi hawaye sunk'i dena zuba daga idanun ta "Allah ka d'au raena na huta da wannan bala'in.." ta fad'a tana jin yadda ilahirin jikin ta ke rawa kamar mazari, kallan ta Umma ta sake yi tana shirin cewa wani abun seta mik'e da sauri, bata so Umman ta sake furta wata kalma mara dad'i a kan ta dan haka ta mik'e duk da yanda take jin jiri na d'ibar ta amma haka ta tashi bata ko ganin gaban ta ta fito daga cikin gidan..Tafiya kawae take yi ba tare da tana sanin inda take jefa k'afafun ta ba, hawaye ne ke ta sintiri akan kuncin ta, Raj ya cuce ta, ya cuci rayuwar ta, ya yaudare ta da kalaman bakin sa daga k'arshe ya raba ta da iyayen ta, ya sanya bata da wani 'yanci ta koma k'ark'ashin sa akan wani son zuciya nasa, meyasa dangin su duka suka kasance masu son zuciya? Meyasa Raj zeyi mata haka? tunda take bata ta6a tunanin soyayya na komawa k'iyayya ba, sedae yau gata dumu dumu cikin matsananciyar k'iyayyar Raj wadda bata san adadin ta ba, wadda ke ruruwa yanzun a cikin zuciyar ta saboda abinda ya aekata mata, bata jin a yanzu a fad'in duniyar nan akwae wanda ta tsana kamar shi, dan kuwa duk mutumin daze raba ta da iyayen ta mak'iyin ta ne, kamar daga sama ta jiyo muryar sa daga gefen ta "Muje ki huta da kae na zan zo na musu bayani" ya fad'a a nutse, wani banzan kallo ta d'aga fusatattun idanun ta ta watsa masa tana jin yadda zuciyar ta ke cigaba da mata zafi, bata jin a yanzu zata iya masa magana, ko da kuma ta bud'e baki da niyyar yin magana to tasan kalaman da zasu fita daga bakin ta masu zafi ne zuwa ga wanda za'a fad'awa, dan haka ta cigaba da tafiya ba tare data d'auki wani mataki akan hawayen dake ta zuba daga idanun ta ba, ya san yanzu ran ta a 6ace yake kuma ko ze mutu baza ta kula shi ba ballantana ta shiga motar sa, dan haka ya kalli gefe da gefe sannan ya k'arasa a nutse zuwa inda take babu 6ata lokaci ya sanya hannun sa ya d'auke ta dukan ta, duka k'arfin ta ta saka tana k'ok'arin k'wace jikin ta dan ta sauka daga jikin sa amma ina yak'i bata damar hakan, sema k'arasawa da yayi ya bud'e front seat ya jefa ta ya kulle sannan ya koma mazaunin driver ya shiga shima ya kulle side d'in sa, hannun ta ta saka dan bud'e murfin k'ofar amma ta ji shi a rufe dan haka ta sanya hannun ta ta fara turawa nan ma ta kasa, kawae seta koma jikin kujerar tana fashewa da wani marayan kuka, daga inda yake ya d'an runtse idanun sa kukan nata na ratsa shi, amma a yadda yaga k'wayar idanun ta cike suke da fusatattun abubuwa ya sanya shi yi mata shiru ta cigaba da rera kukan ta kamar ran ta ze fita. ... Wajen minti 1 bayan ta fita babu wanda ya sake cewa komae, Yah Sadeeq ya lumshe idanun sa sannan ya fara magana a nutse "Abba, Umma kada 6acin rae yasa ku man ta wacece Ayrah, Abba kada 6acin rae yasa ku aebata d'iyar da kuka haefa, Abba ina ji a jiki na akwae wani 6oyayyen al'amari dake faruwa wanda da zamu bawa Ayrah dama zata fad'e shi, amma Abba bamu bata ba, mun k'i bata wannan damar data nema, Abba Ayrah bata da wayo ko bud'ewar idon da zesa ta bi saurayi!" tashi zaune Abba yayi har lokacin hannun sa na d'ore akan k'irjin sa yace bayan ya girgiza kae "Shin baka ji abinda ta fad'a bane Sadeeq? Tun ina k'ok'arin k'arya ta abinda muke zargi yau Ayrah da kan ta tazo ta tabbatar mana harda k'arin wani abun ma" Abban ya k'arasa fad'a yana kallan Yah Sadeeq "Umma, Abba Ayrah ce fa, Umma Ayrah ce fa, kuna tunanin zata iya zuwa can wani waje tayi aure da wanda bakwa so? Ayrahn da kullum cikin son farin cikin ku take Umma?" shiru dukan su suka yi cikin nazarin abinda Yah Sadeeq d'in ya fad'a, kamar babu wanda ze tanka a cikin su se kuma Umma tace "Ya akayi hakan ta faru kenan Sadeeq? Me kake so ka ce mana? Dukan mu ba'a son ran mu muke zargin Ayrah ba Sadeeq, babu yadda zamu yi ne, mu iyaye ne ta yaya zamu aebata d'iyar mu? Abinda take fad'a yanzu ya zama dole mu shiga rud'ani, ta bar gida bayan maganar hana ta auren yaron nan, yanzu kuma ta dawo tace tana d'auke da auren sa, Sadeeq ya kake so muyi?" seda yaja ajiyar zuciya sannan yace "Umma, Abba don Allah mu bari naje na kira Ayrah tazo ta mana bayani, inaji a jiki na akwae wani abun.." ya fad'a har cikin ran sa yana jin abinda ya fad'a d'in, shiru na wajen minti 2 ya wanzu a wajen kowanne da abinda yake sak'awa a ran sa, se dae dukan su sun gamsu da zancen d'an nasu, a gefe guda kuma dukan su sun so su fahimci kamar sun yi laefi, k'in tsayawa suji abinda ze fito daga bakin Ayrahn, yanke mata hukunci tun kafin su san aenahin abinda ya faru, koma menene ya faru 6acin rae ne "Je ka kira min d'iya ta!" Umma ta fad'a tana kallan Yah Sadeeq lokaci guda kuma tana jin yadda wani nauyi dake k'irjin ta ya d'an ragu, seta saka hannu ta goge hawayen fuskar ta dae_dae lokacin da Yah Sadeeq ya saki murmushi kana ya mik'e yana kallan Abba yace a hankali "Abba in kira ta?" seda Abba ya runtse idanun sa sannan ya bud'e kawae ya jinjina kae, cike da farin ciki ya sanya k'afa ya fice daga cikin gidan yana d'an d'ingishi dan har lokacin k'afar ta sa bata ida warkewa ba. ... Dae_dae lokacin daya fito titi yayi dae_dae da lokacin daya hango Ayrahn cikin motar Rk, yana k'ok'arin k'arasawa wajen motar Rk ya tashi motar ya bar wajen, se yayi sauri ya tsaeda Napep ya sanar dashi yabi masa motar Rk d'in, babu musu me Napep d'in ya bi shi, dae_dae wani waje motar Rk d'in ta dakata wanda yafi kama da Hotel, Yah Sadeeq ya sauka ya biya me Napep d'in kud'in sa sannan ya cigaba da tafiya zuwa wajen motar. Saukowa Rk yayi daga driver seat ya zagaya zuwa wajen me zaman banza ya bud'e k'ofar yana kallan yanda take a cure waje d'aya, yanzu ta dena kukan se dae ita kad'ae tasan abinda take sak'awa a cikin zuciyar ta "Don Allah ki fito!" ya fad'a cikin rarrashi, idan motar da take ciki ta d'aga kae ta kalle shi toh itama ta kalle shi "Ayrah!" Yah Sadeeq ya fad'a sanda ya k'araso dab da motar, da wani irin sauri ta d'aga kan ta ba tare data shirya ba, nan take idanun ta suka sauka akan Yah Sadeeq, seda ta d'an lumshe idanun ta sannan ta bud'e dan tabbatar da Yah Sadeeq d'in ne ba gizo yake mata ba sannan ta sauko daga cikin motar a million ta k'arasa ta fad'a jikin Yah Sadeeq d'in tana sakin wani irin kuka, a hanzarce ya d'aga kan sa ya kalli wanda ta rungume d'in, ko wani be masa bayani ba ya fahimci wanene shi, amma me kuma ya kawo shi nan d'in? Shima Yah Sadeeq d'in rungume ta yayi yana jin yanda take kuka sosae, tana shirin fara magana duk dae cikin kukan yace "Ya isa! Ki bari mu zauna, ina buk'atar jin gaskiyar al'amari, bana son k'arya Ayrah.." kamar wata k'adangaruwa ta shiga jinjina kae har lokacin tak'i sakin sa, d'aga idanun sa yayi ya kalli Rk da har lokacin yake tsaye se dae basu yake kalla ba yace "Raj?" se a lokacin ya juyo ya kalle shi cike da mamakin yadda ya kama sunan sa, seya jinjina kae yana lumshe idanun sa, d'an murmushi kad'an Yah Sadeeq yayi kana ya furta "Sad..." "Sadeeq!" Rk ya k'arasa sunan yana nuna Yah Sadeeq "Ehh" shine abinda Yah Sadeeq ya furta sannan ya d'ago Ayrah dake jikin sa ya rik'e hannayen ta kana yace "Ina son magana da kae idan babu damuwa" "Why not?" Rk ga fad'a bayan ya d'aga kafad'a "Mu k'arasa can.." Rk ya fad'a yana nuna wani d'an madaedaecin waje dake d'auke da wasu kujeru masu kyau, babu wanda ya sake cewa komae cikin su Rk na gaba yayin da Yah Sadeeq ke a bayan sa suka cigaba da tafiya zuwa wajen, ita dae Ayrah babu abinda tace ta cigaba da rik'e hannun yayan ta dan tana ji kamar idan ta sake shi zata bud'e ido taga baya nan, a haka suka k'arasa wajen, Rk ne ya fara neman waje ya zauna sannan Yah Sadeeq ya zauna, ita dae Ayrah ko zaman ma kasawa tayi seda Yah Sadeeq ya kalle ta yace a hankali "Ki zauna kin ji?" kamar bata san da wata halittar a wajen ba taja kujera ta zauna har lokacin idanun ta na kan Yah Sadeeq, shiru Rk yayi kawae yana jiran jin abinda Yah Sadeeq d'in zece, kamar ya sani kuwa seya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta "Menene gaskiyar barin Ayrah gida don Allah? Menene gaskiyar auren ka da tace tana d'auke da shi a kan ta?" shiru ya d'an yi yana nazarin tambayar Yah Sadeeq d'in, kamar ba zece komae ba se kuma ya d'an lumshe manyan idanun sa sannan ya bud'e yana tunanin tsayin adadin maganar da zeyi, amma ya zama dole yayi ko dan hakan ze wanke Ayrah daga wajen iyayen ta, sannan kuma su yafe mata koda ze samu kan ta ta dawo asalin Ayrahn sa, a hankali ya shiga labartawa Yah Sadeeq abinda ya faru, duk wani abu daya sani seda ya fad'a masa, yana kaewa k'arshe yayi shiru yana d'an aje numfashi kad'an, shiru Yah Sadeeq yayi tun lokacin da Rk d'in ya fara bashi labari, mamaki, tsoro gami da al'ajabin wannan al'amari yak'i barin sa, ya rasa ma me zece kwata kwata, ya rasa ma wane tunani ya kamata yayi, abin ya bashi tsoro da mamaki aenun, a hankali ya dubi inda Ayrah take zaune duk tayi wani iri da ita kamar ba Ayrah ta asali ba, se yaji wani matsananincin tausayin ta ya mamaye shi, Allah sarki baewar Allah, ashe dae Ayrahn er halak ce, ta haefu cikin Umma da Abba, tana k'aunar farin cikin Abban ta dana Umman ta haka zalika kuma tana k'in abinda basa so, tunda gashi nan duk irin yawan k'aunar da take wa Raj daga ji iyayen ta basa son shi itama ta sauya masa "Amma pls ko zan iya sanin dalilin Abba na cewa bazan auri Ayrah ba?" tambayar data katsewa Yah Sadeeq tunani kenan, seya d'aga ido ya kalli Rk sannan ya girgiza kae yana kallan sa har lokacin yace "Kada ka nuna kamar wani baka sani ba mana!" iska Rk ya fesar daga bakin sa sannan yace "Wallahi ban sani ba!" ya fad'a dan ya cire duk wani kokwanto dake tattare da Yah Sadeeq d'in, shiru Yah Sadeeq yayi na en wasu sakanni, sam bega amfanin 6oyewar ba gwara ma ya fad'a masa ya sani d'in kada ya zaci haka kurum za'a hana shi auren ta ne bayan tana son shi yana son ta "Mahaefin ka.." Yah Sadeeq ya fad'a masa duk abinda ya faru kamar yadda ya sani, tun daga lokacin da suka zo hawa mota da kuma sanda suka dawo Kano, daskarewa Rk yayi akan kujerar da yake zaune yana cigaba da kallan Yah Sadeeq kamar wani sak'ago ko kuma wani mara wayo, anya kuwa Yah Sadeeq d'in yasan abinda ke fitowa daga cikin bakin sa? Shin me yake k'ok'arin cewa Abbun sa ya aekata? Anya kuwa ba ya fad'i hakan bane dan ya kawar dashi daga kan k'anwar tasa ba? A hankali ya shiga tariyo abinda Abbu ya fad'a masa da kuma wannan maganar da Yah Sadeeq d'in ke fad'a masa, seya shiga had'a su waje d'aya yaga ko iri d'aya ce, shin zasu zauna a mizani d'aya? Se dae ina, kwata kwata ba iri d'aya bace, sam babu ma ta inda suka had'u ko kad'an, toh kenan me yake faruwa?? Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 036 ___Ya d'auki wajen mintina 2 a haka, zuciyar sa a matuk'ar cunkushe, gaba d'aya ya rasa meke masa dad'i, duka tunanin sa ya tafi ne wajen tunanin menene gaskiyar abinda yake fitowa daga bakin Yah Sadeeq, shin me ya kamata ya amince da shi? Maganar Abbun sa ko kuma maganar Yah Sadeeq d'in? Iska me zafi ya fesar daga cikin bakin sa lokaci d'aya yana lumshe idanun sa, har lokacin kuma yana jin yanda zuciyar sa ke ta azalzalar sa "Yah Sadeeq ka tashi muje wajen su Abba" shine abinda Ayrah ta fad'a tana d'an jan hannun Yah Sadeeq d'in, kallan ta yayi sannan yace a nutse "Ina zuwa, yanzun zamu tafi.." ya k'are maganar yana maeda duban sa kan Rk da har lokacin ya gaza furta ko kalma d'aya, shi dae Yah Sadeeq abinda be fahimta ba shine..tsananin mamakin abinda Abbun nasa ya aekata ne ya sanya shi kasa furta komae ko kuma maganar ce tazo masa a bazata "Are u ohk?" Yah Sadeeq ya tambaya yana kallan yanda har lokacin idanun sa ke a lumshe, se a lokacin ya shiga bud'e manyan idanun sa a nutse wad'anda lokaci d'aya colour d'in su ya chanja, akan Yah Sadeeq d'in ya sauke su se dae har lokacin bece ko uffan ba in ban da jinjina kae kawae da yayi "Can i just go with her pls?" Yah Sadeeq ya fad'a har lokacin yana kallan Rk, a nutse ya d'aga kan sa ya kalli Ayrah dake zaune gefen Yah Sadeeq kamar bata san da zaman sa a wajen ba, dan kuwa har cikin ran ta tana ji in dae har Abba da Umma basu yafe mata ba ba zata ta6a yafewa Rk ba "Yeah" ya furta a hankali kamar wanda akawa dole, daga haka ya mik'e ba tare daya sake cewa komae ba ya fara barin wajen zuwa wajen motar sa, bin sa da kallo Yah Sadeeq yayi sanda yake barin wajen, gaba d'aya yanayin sa ya chanja cikin k'ank'anin lokaci wanda har hakan seda ya bawa Yah Sadeeq d'in mamaki, se dae hakan kad'ae ya isa ya nuna masa halin su ze iya kasancewa mabanbanta ne da shi da mahaefin sa. "Auta.." Yah Sadeeq ya fad'a yana kallan ta da murmushi saman fuskar sa, dan so yake ya d'an kawar mata da wata damuwar kamin su k'arasa gida, aekuwa yaci nasara dan kuwa seda tayi murmushin itama kafin ta sanya hannun ta akan fuskar ta ta goge hawayen fuskar ta still dae tana cigaba da murmushin "Tashi mu tafi.." ya fad'a bayan ya mik'e, babu musu ta mik'e suka bar wajen zuwa titi, suka samu abin hawa. A 6angaren Rk kuwa a nutse ya k'arasa wajen motar sa ya bud'e ya fad'a ciki, babu 6ata lokaci ya tayar da motar, sam gudu ba d'abi'ar sa bace amma yau seya tsinci kan sa da yin gudun sosae dan so yake ya samu nutsuwar da ze zauna yayi tunani akan wannan maganar, a haka har ya k'arasa gida. A compound d'in gidan yayi parking motar ta sa, ya sauka ya soma takawa zuwa part d'in sa, dae_dae lokacin da yake k'ok'arin sanya mukulli dan bud'ewa ya jiyo muryar Ummee na fad'in "Yanzu kake dawowa ne?" seya d'an dakata kad'an sannan ya d'aga idanun sa ya kalli Ummeen kana yace "Ehh.." kawae dan a yadda yake jin sa baya jin ze iya doguwar magana haka nan, kallan sa Ummee ta cigaba da yi tana nazarin yanayin sa "Kana lafiya kuwa?" Ummeen ta tambaya, nan ma da "Ehh" kawae ya amsa yana k'arasa saka key d'in ya bud'e ya tura kan sa cikin d'akin, bin sa da kallo Ummee tayi, se kuma ta juya itama da nufin shiga cikin d'akin nasa se kuma ta dakata ta girgiza kae kamin ta wuce part d'in ta. .. A hankali ya kwanta kan kujerar d'akin, sannan ya d'auki hannun sa d'aya ya d'ora a kan sa dake cigaba da masa ciwo, idanun sa a lumshe suke yana sake tuna maganganun Yah Sadeeq, be san dalilin da yasa ya kasa k'arya ta Yah Sadeeq d'in ba a lokacin da yake fad'a masa ga abinda mahaefin sa yayi, ya rasa dalilin hakan, haka kawae yake ganin babu abinda ze sa Yah Sadeeq d'in ya zauna ya d'irka k'arya akan mahaefin sa kuma yazo yana fad'a masa, abu ne me kamar wuya hakan ya faru, amma kuma ta yaya zeyi gaggawar amincewa ba tare da wata hujja ba? Duk da yana buk'atar bincike ko da akan takaddun Abba ne da Yah Sadeeq d'in yace Abbu ya tafi har dasu, amma kuma akwae abubuwa da dama da ke ta masa dirar mikiya cikin k'wak'walwar sa, tunda Abbu ya fita da niyyar raka Abba Kano, dawowar sa gida cikin gaggawa suka bar garin, tun daga lokacin be sake ganin Ayrah ko wani daga cikin dangin su ba, ko kuma wani abu daya shafe su ba, kenan me hakan ke nufi? Lokaci guda bugun numfashin sa ya k'aru, baya fatan ace haka d'in ne dan idan hakan ya tabbata gaskiya ne be san da wane ido ze kalli Ayrah da shi kan sa Abba ba, mutum me hallaci a gare shi, mutum me kirki da dattako, wanda tun a lokacin ba wani k'arfi gare shi ba amma saboda wadatar zuci da kuma tausayi irin na sa ya taemaka masa, be tsaya iya nan ba ya taemakawa Abbun sa amma ace abinda Abbun sa yayi kenan? Ya zama dole ya bincika. .. Babu wanda yace uffan a cikin su sanda Yah Sadeeq d'in ya gama bada labarin, Ayrah na taya shi har lokacin tana share k'walla a idanun ta, Abba gaba d'aya bashi da abin cewa shiyasa ma yayi shiru yayin da Umma kuma mamaki gami da takaeci sune suka taru suka mata yawa yasa ta kasa cewa komae, a hankali ta shiga goge hawayen dake ta saukowa daga kan fuskar ta tana girgiza kae, se yanzu ta sake gane kuskuren da suka aekata na yankewa Ayrahn hukunci ba tare da sun yi bincike ba, hannu Umma ta mik'awa Ayrah bayan ta d'aga fuskar ta ta kalle ta, sannan ta mata alama da ta taho da kan ta, babu 6ata lokaci Ayrah ta k'arasa da sauri ta fad'a jikin Umman tana sakin wani irin kuka, itama Umma bata hana kan ta kukan ba ta rungume d'iyar ta ta sosae tana jin yadda ilahirin jikin Ayrahn ke rawa "Kiyi hak'uri Ayrah, don Allah ki yafe min, nice na fara d'arsawa Abban ku zargin guduwa kikayi daga gidan nan bayan tabbatar da ba zamu aura miki Raj ba, kiyi min afuwa Ayrah!" ta k'arasa fad'a tana sake jin wani irin takaeci, se da Ayrah ta sauke sheshshek'a sannan tace "Umma ni ba abinda kuka min, wannan dalilin ne ma yasa nake ta sauri in dawo gida dan nasan za'a iya tunanin hakan, Umma ba kuyi laefi ba dan kun yi tunanin hakan musamman daya kasance a washe garin ranar da kuka hanani auren sa ne kuka neme ni kuka rasa.. Umma ni baku min komae ba, nice ma zan baku hak'uri.." "Kuull..ki bar fad'in mu miki hak'uri Auta, babu abinda kika mana mu ma" Umma ta fad'a tana sakin Ayrahn, bata sake cewa komae ba se k'arasawa da tayi inda Abba ke zaune har lokacin, tsugunawa tayi tana kallan sa, dae_dae lokacin daya d'auke kae yana jin zuciyar sa na karyewa "Abba..!" ta fad'a har lokacin tana kallan sa "Ayrah je ki huta bazan iya cewa komae ba, kiyi hak'uri kawae.." Abban ya fad'a, wani irin sanyi taji yana ratsa kafatanin jikin ta, ko ba komae yau d'in gata ga iyayen ta kuma da alama sun yafe mata, gashi ma har neman yafiyar ta suke yi "Abba ni zan nemi yafiyar ku don Allah.." Abba be iya cewa komae ba se girgiza kae kawae da yake yana ajje numfashi a hankali, Yah Sadeeq kuwa da yake gefe murmushi ne kawae ke fita daga kan fuskar sa, tana shirin mik'ewa dan komawa d'aki Abba ya juyo kamar wanda ya tuna wani abu "Ayrah!" seta juyo a hankali tace "Na'am Abba.." "Kin san mutumin daya saka aka d'auke ki?" tsayawa tayi tayi shiru tana hasaso fuskar Alhaji Mato, kwata kwata ba zata iya cewa ga fuskar sa ba dan haka ta girgiza kae kamin tace "A'ah Abba bansan shi ba.." "Idan kika gan shi zaki gane shi?" shiru tayi tana nazari, ko da ta san shi ma bata tunanin zata iya gane shi ballantana bata san shi ba dan haka a nutse ta furta "A'ah Abba.." "Tashi kije Allah yayi miki albarka" lumshe idanu tayi kamin ta mik'e tare suka wuce cikin d'akin ta ita da Umma, shiru Abba yayi bayan barin su wajen yana nazari, ya zama dole ya gano mutumin daya d'auke masa yarinya ya kae ta wani waje dan a d'aura musu aure, idan kuma ya tuna da maganar auren Raj dake kan er tasa se ya sake jin jikin sa yayi sanyi, a yanzu be san wanene Raj d'in ba be san ko halin su d'aya da mahaefin sa ba, be san yadda za'ayi su kasance sirikae tsakanin sa da Kabeeru ba, abinda be ta6a tunanin ze kasance a rayuwar su ba, abinda ya guda tun farko, se dae gashi Allah yayi ikon sa akan su ta hanyar da basu ta6a zata ba, seya koma ya jingina bayan sa da jikin bango yana cigaba da sak'a da warwara. ... Da sallama ya shigo cikin d'akin hannun sa d'auke da envelope, Mummy dake zaune kan kujera ta mik'e tana fad'in "Alhaji sannu da zuwa" "Yawwah sannu kadae, ina Muneerahn? Na gan ki ke d'aya?" murmushi Umma tayi sannan tace "Toh Alhaji ae dole ka ganni ni d'aya a kwanakin nan, kasan sha'anin amarya fa yanzu haka tana wajen gyaran jiki" "Toh madallah, ga kati dae ya iso" ya fad'a yana mik'a mata envelope d'in hannun sa, da sauri ta sanya hannu ta kar6a da murmushi kan fuskar ta take fad'in "Kae toh Masha Allah.." ta fad'a tana k'arasawa ta zauna kan kujera ta fara fito da katinan masu kyau da k'ayatarwa, girgiza kae Daddy yayi yana murmushi ganin yadda Mummyn ta shagala da kallan kati, ko bi ta kansa ba tayi ba hakan ne ya sanya shi jan k'afafun sa ya bar d'akin. Be dad'e da fita ba Muneerah ta shigo cikin d'akin cikin hijab har k'asa hannun ta d'auke da jaka da had'ad'd'iyar wayar ta, k'arasawa tayi da sauri kan kujerar tana kallan Mummy kamin ta saka hannu ta tu6e hijab d'in jikin ta, nan take shigar dake jikin ta ta bayyana, gajeran wando tiet ne a jikin ta da vest irin me bin jikin nan hakan ne ya bayyana yanda ta cika daga sama ba kamar da ba wanda ke nuni da siyo shi ba natural bane, haka zalika hips d'in ta ma sun k'aru ba kamar da ba dake kamar 1, kan ta babu d'an kwali se dae kamar ko yaushe a kitse yake da kitson attachment daya zuba a gadon bayan ta, ta k'ara wani irin mahaukacin fari bauu, fatar nan ta sake d'ashewa, da alama ba mae ta shafa ba se dae ko k'waya ko kuma allura "Kin dawo?" "Ehh Mummy, na gaji wallahi" "Toh sannun ki, gashi nan kati ya iso" farr tayi da idanun ta kafin ta kalli katinan, seta saka hannu ta d'auki guda d'aya ta kalla ta shiga karantawa, sunan ta ne gashi nan ya fito 6aro 6aro dana Rk, wani murmushi ya k'wace mata tana jin ita kam burin ta ya gama cika daga lokacin data auri Rk d'in, ajiye katin tayi seta d'auki wayar data ajje a gefen ta kamar koda yaushe ta danno number sa, amsar d'aya ce dae kamar kullum baya kusa, bata gaji ba ta sake kira amma har ta katse be d'aga ba, a karo na 3 ta sake gwada kiran na sa cikin sa'a kuwa ya d'aga wayar se dae bece komae ba, daga inda take ta maraeraece fuska kamar za tayi kuka "Haba Baby, ina ta kiran ka amma kak'i d'agawa, na maka magana ta whatsApp kak'i kula ni, ya kake so nayi? Auren mu saura kwanaki amma kak'i tsayawa muyi magana ko da akan shirye_shiryen bikin ne" tsaki ya saki akan la66an sa, ya kasa gane wannan dalilin na had'a auren sa da Muneerah, idan so suke zumuncin su ya d'ore ae ba dole seta hakan zasu biyo ba, shi abinda ma yake tsoro kada ace zumuncin su ya rabu saboda auren nan, dan a yadda yake ji har abada baze iya zama da wata a matsayin matar sa ba in dae ba Ayrah ba, toh ina ze kae ta? "Yaya na!" ta katse masa tunani da fad'in hakan "Wannan ne dama dalilin kiran?" ba tare data kawo komae ba tace tana murmushi "Ehh shine kawae.." "Ohk" ya fad'a yana katse wayar sannan ya jefar da ita gefe "Hello" ta furta bayan jin kamar kiran ya katse, seta sauke wayar daga kunnen ta tana kalla cike da takaecin katse wayar ba tare da sun k'are maganar ba, seta cigaba da kallan wayar kamar me nazari ko kuma me kallan wani abun a cikin wayar "Ke lafiya?" Mummy ta fad'a tana kallan ta "Mummy, Yah Suraj ne mana, Mummy har yanzun fa baya d'aga waya na ya yake so zuciya ta tayi?" ta k'are maganar kamar zata fasa ihu, tsaki Mummy taja sannan tace "Dallah rabu da shi, kwana nawa ya rage ya shigo hannun ki? Ke dae kawae ki maeda hankalin ki wajen gyaran jikin nan, dukkan magungunan nan ki tabbatar kina shan su kamar yadda suke a tsare, baki ga har kin fara chanjawa ba kina ta cika tako ina? ina me tabbatar miki a hannun ki zaki kama shi, dan kuwa da kan shi ze dinga bibiyar ki ba dae ke ki bi shi ba.." _*Ina fatan yanzu kun fahimci abinda nake k'ok'arin nuna muku, kowanne abu idan kaga writer tayi akwae dalilin yin sa, akwae dalilin rubuta shi, babu yadda za'ayi kayi abu babu dalili, nayi hakan ne dan janyo hankalin wasu iyayen masu saurin yankewa 'ya'yan su hukunci ba tare da sun yi dogon bincike b duk kuwa sa irin yaddar da kayi musu, su kan su ae gashi nan yanzu sun yi nadamar hakan da suka yi, dama kuma shi novel ya gaji haka, na san dukan ku baku yi tsammanin Umma ko Abba wani a cikin su ze d'auka Ayrahn da kan ta guduwa tayi ba, dukan ku nasan kun ta'allaqa ne akan zasu zata sace ta akayi, wannan dalilin ne yasa na juya muku kwanya, babu yadda za'ayi abinda readers ke tunani kae kuma kayi shi a wani lokacin, dan kuwa littafin ze zama lami ne, ze zamana kowa da kowa yasan abinda ze faru a gaba kenan, wannan ba shine kyakykyawan novel ba wanda tun farkon fara karantawa kasan abinda ze faru a gaba. Ina fatan za'a dena tambaya ta dalilin da yasa nayi hakan.*_ Kuyi manage da wannan pls.. https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 037 ___"Allah ko Mummy na?" Muneerah ta fad'a tana murmushi cike da jin dad'in zancen Mummy, murmushin itama Mummy ta maeda mata dashi kana tace "Kada ki saka kokwanto a ran ki, kamar yadda na fad'a haka ne ze kasance" farr tayi da idanun ta dake d'auke da lashes na kanti, wanda da tasan yanda ya sake shigar da k'ananun idanun ta da bata saka ba, amma ita gani take haka zalika ji take baya ita, mik'ewa tayi tana kallan Mummy tace "Yunwa nake ji Mummy kin gama abinci ne?" yamutsa fuska Mummy tayi sannan tace "Se dae idan yunwar kike ji ki dafa ko indomie ce ki ci" bata sake cewa komae ba se hanyar kitchen data wuce kawae. ... Sanye yake cikin k'ananan kaya, fuskar sa ta sake yin wani shahararren kyau kamar wanda ake k'arawa kyau, haka zalika kwantacciyar sumar kan sa ta sake yin bak'i da sake kwanciya, jikin sa babu abinda ke tashi se k'amshin sassanyan turaren sa me dad'in shak'a, a nutse yake takawa zuwa part d'in Abbu cike da fata a cikin ran sa, cikin sa'a kuwa k'ofar parlourn nasa a kulle take, lumshe idanun sa yayi sannan ya bud'e ya d'an kalli gefe da gefe sannan ya sanya spare key d'in daya d'auko daga d'akin Ummee ya bud'e k'ofar, a hankali ya tura kan sa cikin d'akin, kamar wanda ya fara ganin d'akin yau haka ya soma wuwwulga idanun sa ko ina na cikin d'akin, cikin sauri ya shige bedroom d'in Abbun sannan babu 6ata lokaci ya soma bincika inda yasan Abbun na ajiye abubuwa masu amfani a cikin wajen, ya kae wajen minti 30 yana binciken be samu abinda yake nema ba, har cikin ran sa ya d'an ji sanyi kad'an akan zargin daya soma yiwa Abbun nasa, se kuma ya dakata abu na k'arshe dabe duba ba shine saman wardrobe, cikin sauri yanzun ma ya soma bincikawa har zuwa sanda ya d'akko wata leda, be bud'e ba seda ya sakko da ita k'asa, cikin k'ank'anin lokaci ya shiga fito da abinda ke cikin ta, bayan ledar akwae wata ledar a ciki sannan wata jaka, seya tsaya ya bud'e madaedaeciyar jakar dae_dae lokacin da wani envelope ya bayyana, haka nan kawae yaji jikin sa yayi wani mugun sanyi duk da har zuwa lokacin be san menene a ciki ba, a nutse ya shiga zaro takaddun dake ciki, be tsaya ba seda ya fiddo su duka kana ya saka hannu ya d'ago su cikin hannun sa ya shiga karantawa, a hankali yake karantawa kamar me tsoron karantawa ko kuma me koyon karatu, abinda dae yake guda d'in shine ya faru, wato sunan Abban su Ayrah daya fito 6alo_6alo a jikin takaddar, runtse idanun sa yayi na tsawon minti 1 yana jin 6acin rae, zafi gami da wani irin takaeci mara misaltuwa, meyasa Abbun sa yayi haka? Meyasa Abbun sa ya zamo cikin mutanen da za'a kiran su da butulu? "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine abinda ya shiga maemaetawa a cikin bakin sa har lokacin kuma bugun da zuciyar sa ke yi be saitu ba, ya kae wajen minti 2 a hakan sannan ya mik'e dan tuna a inda yake, beyi k'asa a gwuiwa ba wajen d'aukar ledar ya maeda ta saman wardrobe sannan ya d'auki envelope d'in ya fito dashi, karo suka kusa yi da Ummee dake shirin shigowa cikin d'akin, da mamaki take kallan sa "A'ah Raj! dama kana nan? Abbun naku ya dawo ne?" seda ya d'aga idanun sa da suka yi d'an ja saboda 6acin rae sannan yace "A'ah.." ya fad'a yana shirin wucewa "Kae lafiyar ka kuwa a kwana biyun nan?" baya a mood d'in yin magana sosae, musamman kuma a yadda yake jin 6acin rae na taso masa haka nan ya sanya shi saurin girgiza kae sannan yace "Lafiya ta k'alau.." daga nan yayi gaba yana cigaba da kare envelope d'in hannun sa "A'ah wannan envelope d'in fa?" seya dakata da sauri kamar baze juyo ba se kuma ya d'an lumshe idanun sa sannan yace har lokacin be juya ba "Takaddu ne akan asibiti, nazo d'auka ne saboda naga baya nan" jinjina kae Ummee tayi ba tare data kawo komae a ran ta ba kawae ta k'arasa cikin bedroom d'in yayin da shi kuma ya cigaba da tafiya, yana shirin fita daga d'akin Abbu ya shigo cikin d'akin sanye cikin farar dakakkiyar shadda, kallan sa yayi da mamaki yace "A'ah Raj!.." "Wajen Ummee nazo, tana bedroom.." shine abinda ya furta kawae ba tare daya kalli Abbun ba kuma be jira cewar sa ba ya fice daga d'akin, da kallo kawae Abbu yabi shi dashi sannan ya dawo da duban sa cikin d'akin yana girgiza kae. Kae tsaye d'akin sa ya wuce, babu 6ata lokaci ya jefar da envelope d'in hannun sa sannan ya nemi kan side drawer ya zauna, gaba d'aya kan sa ya matuk'ar kulle, ashe maganar Yah Sadeeq gaskiya ce? Ashe iyayen Ayrah basu yi laefi ba da suka hana shi auren ta? Tabbas Abbu ya shammace su ya yaudare su sannan ya saka k'afa yayi fatali da yaddar da Abba yayi masa bayan irin tarin hallacin da Abban yayi musu su duka, meyasa Abbun yayi haka? Abba mutum ne me kirki wanda ya d'akko su daga rana zuwa inuwa, amma Abbun daya tashi se ya d'auki Abban ya maeda shi cikin ranar shi kuma ya koma cikin inuwar "Yah Allah! Why Abbu? Why?" ya fad'a a hankali yana cusa hannayen sa duka cikin sumar kan sa, gaba d'aya ji yake inama ace wannan abun ba gaskiya bane ba? Inama ace mafarki ne kawae yake yi, idan kuwa gaske ne ya zama dole ya nemowa kan sa da kuma shi kan sa Abbun mafita kamin lokaci ya k'ure musu, ranar gaba d'aya sukuku ya wuni, ko bacci be iya yi ba saboda wannan al'amari daya hargitsa masa kwanya. .... A d'aya 6angaren kuwa kwanakin da suka biyo baya seya zamana wata kulawa ta musamman iyayen ke bawa Ayrah, kamar ma k'ara musu soyayyar ta akayi dan hatta kulawar data ke samu a yanzun tafi ta da, ita kam farin ciki take ji kamar tayi mene, tana kuma iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta faranta musu ran su ba tare data 6ata musu ba. .. Suna zaune su duka a tsakar gidan suna hira cikin farin ciki da k'aunar junan su, Ayrah na daga gefen Umman ta cikin doguwar rigar wani yadi me matsakaecin kyau fuskar ta yanzun babu laefi ta d'an samu albarkacin kwalli data saka, dan haka ya 6oye kaso da yawa daga yanda tayi zuru zuru, tayi kyau sosae duk da bayan kwallin babu wani abu data k'ara a fuskar ta, se kuma mayafi data yafa shi a kan ta ta zubo dashi kan kafad'ar ta, kallan Yah Sadeeq daya d'an rik'e k'afar sa tayi kana tace "Yah Sadeeq k'afar ce?" murmushi yayi sannan ya girgiza kae kana yace "A'ah Auta, ba k'afar bace ba.." "Ayrah.. Je ki d'auko masa maganin nan ya shafa, kin san halin sa dae.." babu musu ta mik'e zuwa cikin d'akin dan d'akko masa maganin, dae_dae lokacin da wani yaro yayi sallama cikin gidan, dukan su suka amsa masa sallamar "Wae a waje wani yace ayi masa iso.." Abba ya kalli yaron kana yace "Waye?" "Yace wae Raj sunan sa.." tana shirin fitowa taji sunan da aka ambata, seta dakata da sauri tana jin yanda bugun zuciyar ta ya k'aru, ko taku d'aya ta kasa k'arawa daga inda take kamar me tunani. Kallan Umma Abba yayi sannan ya maeda kan yaron yace "Fad'a masa ya shigo" fita yaron yayi, ita kuma Umma ta koma d'akin ta ta d'auko babban mayafin ta ta yafa sannan ta fito ta nemi waje ta zauna, tunda taji Ayrahn shiru tak'i fitowa tasan taji wanda akace ze shigo, Ayrahn har mamaki take bata a kwanakin nan, duk irin yadda take k'aunar Raj d'in amma tun dawowar ta gida bata sake maganar sa ba, bata sake koda maganar abinda ya shafe shi ba, kuma duk Umman tasan hakan ya ta'allak'a ne da tun farko data fahimci basa k'aunar sa, toh amma yanzu kam yaya zasuyi tunda har igiyar aure ta ratsa tsakanin su?. Da sallama ya shigo cikin gidan sanye cikin bluen shadda jamfa da wando wad'anda suka matuk'ar yi masa kyau, se dae yanzu ma babu hula a kansa, kusan tare suka amsa masa sallamar sanda yake k'arasowa cikin gidan, a nutse ya tsuguna daga gefen tabarmar da Yah Sadeeq ke kae kan sa a k'asa ya furta "Barkan ku da wannan lokaci.." cigaba da kallan sa Umma tayi, da alama har yanzu nutsuwar sa tun ta yarinta tana nan, haka zalika kamannin sa suna nan se dae kamar ma yanzun an k'ara masa kyau ne "Barka dae.." Abba ya fad'a "Ka zauna mana" Yah Sadeeq ya fad'a ganin har lokacin be zauna ba, shiru ya d'an yi yana jiran jin ta bakin wani daga cikin Abba ko Umma, kamar sun san me yake nufi kuwa se Umma tace "Ka zauna mana" se a lokacin ya zame takalmin k'afar sa sannan ya zauna har kuma lokacin be kalle su ba, ya ajje envelope d'in dake hannun sa a gefen sa, seda ya d'an numfasa sannan ya fara magana a nutse "Abba.. Zuwa nayi in rok'i alfarmar ka don Allah.. Sannan kuma in baka hak'uri akan abinda ya faru.. bazan 6oye maka ba Abba a lokacin da naga wani na na neman auren Ayrah hankali na ya matuk'ar tashi, nasan abinda ya kamata inyi shine in d'auko ta in dawo muku da ita, toh amma bani da tabbacin idan na dawo da ita zaku aura min ita, ko kuma ita ta amince da aure na saboda yadda ta nuna a lokacin kwata kwata itama ba zata ta6a aure na ba, kuma a lokacin bansan dalilin ta na hakan ba Abba yasa kawae na yanke shawarar neman auren ta acan d'in idan yaso idan muka dawo na shirya kar6ar koma wane irin hukunci ne, duk da banyi la'akari da ku yaya zaku d'auki al'amarin ba, amma don Allah kuyi hak'uri Abba, ku min afuwa don Allah.." ya k'are maganar yana sauke numfashi kamar baze d'ora ba se kuma ya janyo envelope d'in gefen sa ya cigaba da fad'in "A yanzu na gano dalilin da yasa kuka hanani auren Ayrah Abba, ku dubi girman Allah ku yafe mana mu masu laefi ne, kuma yanzu haka gashi na dawo maka da takaddun ka badan mu biya ka abinda muka yi maka ba, a'ah inaso ne na fara warware wannan matsalar kamin inje gata gaba.." kallan envelope d'in Abba yayi sannan ya girgiza kae yana murmushi "Shi Kabeerun ne ya aeko ka?" seda ya d'an yi shiru sannan ya girgiza kae cike da takaeci kana yace "A'ah Abba.." sake girgiza kae Abba yayi dama yasan za'a rina "Ka d'auki takaddun ka maeda su inda ka gan su, duk lokacin da Kabeeru ya gane yayi laefi kuma yana neman yafiya ta seya d'auko yazo ya bani, kada ka sake saka kan ka cikin wannan maganar.. Zancen aure kuma dani da mahaefiyar ta duk bamu so ba, ba kuma mu ta6a tunanin hakan ze kasance ba saboda abinda mahaefin ka yayi, se dae ya zamuyi? Allah ya riga ya rubuta ita matar ka ce, ko da ba ta hakan ba in dae Allah ya nufa se anyi auren nan se kaga dukan mu ma mun mutu kuma a d'aura muku auren, dan haka ni na yafe maka daga kae har Ayrahn in dae akan auren nan ne, na san iyayen ka ma basu sani ba saboda haka wannan ya rage naka kaje kayi musu bayani da kan ka, ku sasanta da kan ku.." a hankali ya lumshe idanun sa yana jin wani nauyi na raguwa daga cikin k'irjin sa, ko babu komae ya samu matsala d'aya ta kau, yanzu se yaji da d'ayar data rage masa "Nagode sosae Abba.. Allah ya saka da alkhaeri.. Umma nagode" ya fad'a yana mik'ewa "Allah ya tsare" Umma ta furta da murmushi kan fuskar ta dan seta ke ji kamar little Raj ne wanda ta sani tun shekarun baya, d'aukar envelope d'in yayi a ran sa yana sak'a lallae akwae aeki a gaban sa, Yah Sadeeq ne ya mik'e ya taka masa zuwa k'ofar gidan, be baro wajen ba seda Rk d'in ya hau motar sa sannan ya juya, ya kasa hak'urin rashin ganin ta tun shigowar sa dan haka ya furta "Amm pls Yah Sadeeq bata nan ne?" juyowa Yah Sadeeq yayi kana ya d'an yi murmushi sannan yace "A'ah tana d'aki, ko a kira maka ita ne?" da sauri ya girgiza kae yana d'an lumshe idanun sa, duk da yanda idanun sa ke k'ishirwar ganin ta amma gwara ya hak'ura dan haka ya furta "A'ah barshi kawae nagode.." daga haka yaja motar sa ya bar layin yayin da shi kuma Yah Sadeeq ya koma cikin gida. Kallan Abba Umma tayi bayan fitar Rk d'in "Abban su yaya wannan auren ze kasance kenan?" d'an shiru Abba yayi sannan yace "Wannan ya rage nasa Ruk'ayya.." "Ina ganin kafin ta koma ko kae zakawa Baban nasa bayanin yanda auren ya kasance?" da sauri Abba ya kalli Umma cike da mamakin jin kalaman ta "Ruk'ayya kin san me kike cewa kuwa? Ashe har Kabeeru yayi arzik'in da zan je wajen sa yi masa bayanin wani abu? Bakya tunanin wani abu ze d'arsu a cikin ran sa?" ya k'are maganar yana girgiza kae sannan ya d'ora da "Bana fatan wannan ranar tazo.." se kuma a lokacin itama Umman ta fahimci hakan dan haka ta furta "Toh Allah ya kyauta, zamu iya bashi ita?" "K'warae babu damuwa.." Abba ya fad'a. A hankali Umma ta yaye labulen d'akin ta shiga, tana kwance akan gadon ta kamar me bacci, k'arasawa Umma tayi kan gadon tana fad'in "Ayrah wae bacci kike yi ne?" da zata iya shiru zata yi dan haka kawae take jin kunyar Umman tun zuwan Rk "A'ah Umma" ta fad'a har lokacin tana kwance "Toh tashi zamu yi magana.." Umma ta fad'a bayan ta nemi waje ta zauna, tashi zaune Ayrahn tayi tana had'e jikin ta kamar me jin sanyi "Meyasa kika k'i fitowa ko gaesawa kuyi?" tura d'an k'aramin bakin ta tayi sannan tace "Ummaaa.." taja k'arshen sunan, murmushi Umma tayi tana girgiza kae sannan tace "Ki bar damun kan ki, In Sha Allah in dae mu ne mun amince da auren ku, dan haka ki bar damun kan ki haka nan, Allah ya tabbatar da alkhaerin sa" hannun ta ta d'auka ta rufe fuskar ta tana murmushi, duk da har lokacin akwae d'an haushin sa kad'an da take ji amma yanzu da Umman tayi magana taji matuk'ar dad'i, seta d'ora kan ta akan cinyar Umman kawae ba tare da tace komae ba "Ayrah.." Umma ta fad'a tana murmushi.. ... Kwanakin da suka biyo baya amarya Muneerah ta cigaba da shirye_shiryen aure, yayin da 6angaren ango Raj yama manta da maganar auren musamman ma daya kasance shi kan sa Abbun ya fita a harkar sa saboda yadda ya lura sam auren baya gaban sa, dan haka hatta lefe Ummee ce ta saka aka had'a aka kae, be tashi sanin suna nan kan bakar su ba duk da yanda aka bashi katin d'aurin aure wanda tunda ya ajje su be sake bi ta kan su ba ballantana ko gayyata ce yayi, se ana i gobe d'aurin aure ya sake tabbatarwa sanda yaga gidan nasu ya fara cika da jama'a, haka zalika har lokacin be huta da sak'onni da kuma kiran wayar Muneerah ba, wanda gaba d'aya baya kulawa ita kuma kamar tsohuwar mayya bata hak'ura duk da yadda Mummyn ta tace tayi watsi da shi ze neme ta da kan shi amma ita ta kasa hak'uri, shi gaba d'aya hankalin sa da tunanin sa ya ta'allak'a ne akan yanda ze sami Abbu suyi magana akan zancen Abba amma be san ta inda ze soma ba shi kan sa. .... Washe_gari, fitowar sa kenan daga wanka wayar sa dake ajje kan gado tayi k'ara, seya k'arasa da mamakin me kiran nasa ganin asuba ce "Abbu" ya bayyana akan screen d'in, seda ya sake kallan agogon wayar dan sake tabbatar da lokacin da gaske ne ko dae shine yayi mistake, haka d'in ne dae dan haka kawae ya d'aga wayar yana karawa a kunnen sa "Raj!" "Na'am" ya fad'a muryar sa a d'an cunkushe "Ina fatan kana sane da d'aurin auren ka yau d'in nan koh?" Abbu ya fad'a shima ran sa a 6ace kuma babu fara'a dan yadda ya fahimci Rk d'in akwae rashin daraja a al'amarin sa kwana biyun, shiru na wajen second 30 sannan yace "Ehh.." daga haka Abbu ya katse wayar sa, gefen gadon ya nema ya zauna hannun sa dafe da kan sa yana jin yanda yake cigaba da sara masa, ga kuma bugu da k'irjin sa ke tayi kamar wanda yayi gudu, shi har yanzu ya rasa gane matsalar Abbu, Ummee, Daddy da kuma ita kan ta Muneerahn, shin ita bata da zuciya ne a k'irjin ta? Ya fad'a mata baya son ta baya son ta amma tak'i hak'ura, ya share ta ya share ta duk da haka tak'i hak'ura, toh ya suke so yayi da ran sa ne shi kam? Me zeyi da wata Muneerah a matsayin mata? Sam bata a gaban sa, kwata kwata yana ganin kamar za'a k'ware shi ne kuma itama a k'ware ta, amma tunda sun nace kuma sun dage bari ya bar su suyi auren duk abinda ya biyo baya kuma suyi kuka da kan su ba dae shi ba, tunda shi kam ya riga ya nuna musu baya ra'ayin ta ko kad'an. .. A cikin garin Kano aka d'aura auren Raj Kabeer da kuma Muneerah Abubakar, wanda saboda Abbu shine waliyyin amarya shi ya nemi da akawo auren Kano, shi kuma mahaefin ta bek'i hakan ba ya kawo shi nan d'in, daga lokacin da aka d'aura aure aka nemi ango aka rasa dama kuma da k'yar yazo wajen, seda Abbu ya masa tass sannan yazo wajen dan da farko cewa yayi ba zeje ba. Kae tsaye gida ya wuce ya sauya jamfa da wandon dake jikin sa da k'ananan kaya, fuskar nan kamar wanda akawa albishir da mutuwa, ya had'e ta tsaff kamar ze rufe wanda ya masa magana da duka, babu 6ata lokaci ya hau motar sa yaja be tsaya ko ina ba se gidan su Ayrah, dan yanzun ita kad'ae yake son gani ko ze samu sassaucin abinda yake ji a cikin zuciyar sa, a k'ofar gidan ya dakata ya lalubo number Yah Sadeeq sa suka yi exchanging ya kira, bugu 1_2 ya d'aga, a dak'ile ya furta "Pls.. Idan tana nan, ina waje zamu d'an gaesa ne.." "Ohk" Yah Sadeeq ya amsa yana ajje wayar, sannan ya k'arasa cikin d'akin Ayrah dake zaune ita da Umma yace "Umma Raj na k'ofar gida, wae zasu gaesa da Ayrah.." da sauri Ayrah ta d'aga kae ta kalli Yah Sadeeq se kuma ta sadda kan ta k'asa cike da kunya "Tohm shikenan" Umma ta fad'a tana kallan Autar ta ta dake ta sussunne kae "Toh tashi ki shirya ki je.." "Kae Umma!" ta fad'a bayan ta d'ago kan ta ta kalli Umman, girgiza kae Umma tayi tana murmushi sannan ta mik'e tana fad'in "Idan kin gama jin kunyar seki tashi ki je" daga haka ta fice daga d'akin, bin Umman tayi da kallo har ta gama ficewa daga d'akin sannan ta dawo da duban ta jikin mudubin d'akin nata ta kalli fuskar ta, babu komae akan fuskar ta ta, kuma itama bata buk'atar wani abun, se kwae ta mik'e ta ciro wani gogaggen hijab d'in ta a cikin wardrobe ta zura sannan ta fito tana kallan tsakar gidan nasu, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu kowa sannan ta fice daga cikin gidan. Tunda ya hango ta yaji wani irin sanyi na ratsa shi, wannan bak'in cikin da yazo dashi ya shiga kwaranyewa yana yin nasa waje, be san sanda ya saki murmushi ba lokacin data dakata daga inda take tsaye ba, bud'e murfin motar yayi ya fita sannan ya k'arasa ya bud'e wajen me zaman banza kana yace yana kallan ta "Bismillah gimbiya.." wata kunyar ce ta sake lullu6e ta dan haka da er sassarfa ta k'arasa ta shiga cikin motar, se da ta shiga sannan ya zagaya ya koma mazaunin driver har lokacin yana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa musamman daya tsinci murmushi akan kyakykyawar fuskar ta daya dad'e be gani ba, koda ya shiga motar ma juyowa yayi gaba d'aya yana kallan ta kamar ze cinye ta, hannu ta kae taja hijab d'in jikin ta tana rufe fuska da shi sannan tace "Kae don Allah!" wani k'ayataccen murmushi ne ya su6uce masa sannan yace "A'ah ki bar ni na kalla ni kam, kin san kuwa yanda na zak'u da ganin fuskar ki, nayi missing naki irin sosae d'in nan" ya fad'a yana ji kamar ya janyo ta ya rungume ta, se dae yasan halin abarsa dan haka ya d'an lumshe idanun sa dae_dae lokacin data d'ago kan ta "Ina fatan an yafe min abinda na aekata, kae na bisa wuya na" ya fad'a yana d'an rank'wafar da kan sa, bin sa tayi da kallo sanda ya rank'wafar da kan nasa, dae_dae lokacin da idanun ta suka sauka kan wasu jerin gwanon invitation card dake ajje a waje guda, haka kawae taji sun d'auki hankalin ta saboda yanda taga kamar idanun ta sun hangi sunan da take da tabbacin babu me irin shi a yankin su, dan haka babu 6ata lokaci ta d'auki katin sannan ta sauke manyan kyawawan idanun ta kan katin ta shiga karantawa, katin gayyatar d'aurin auren Raj Kabeer ne da kuma Muneerah Abubakar, idan har bata manta ba ko kuma kamar yanda ta sani sunan sa ne wannan, take kuma a lokaci guda k'afafun ta suka fara rawa kamar wad'anda ake kad'asu, tun kuma lokacin data karanta sunan wata mace tare da sunan Rk taji kamar wani abu ya gifta ta wajen idanun ta ne dan haka bata sake ganin wani abu dake a cikin katin ba, k'irjin ta ya shiga bugawa da k'arfin gasken gaske hannun ta kuma dake d'auke da katin ya shiga rawa shima dan haka cikin k'ank'anin lokaci katin yayi nasa wajen saboda yanda hannun ta ya gaza rik'e shi, gaba d'aya kan ta ya kulle, k'wak'walwar ta ta toshe haka zalika idanun ta sun makance kunnuwan ta kuma sun kurumce, babu abinda take iya tunani da hangowa se sunan sa dake jikin katin tare da sunan wata mace... Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 038 ___Jin da yayi shiru har lokacin ba tace komae ba ko tayi wani abun da zesa ya fahimci tana wajen ba ya sanya shi d'ago da kan sa a nutse ya sauke su a kan ta lokacin da jajayen idanun ta da k'walla ta gama cika su taff ke kan sa, abu kad'an ne ze sanya su zubowa, kallan sa kawae take yi kamar me son gano gaskiyar abinda ta gani a cikin katin nan daga cikin fuskar sa, da mamaki yake kallan ta ganin tana masa wani kallan tuhuma ga kuma kyawawan narkakkun idanun ta da suke cigaba da bin sa da kallo, a hankali ya kae hannun sa yana shirin rik'o ta lokaci guda kuma yake fad'i a nutse "Meya faru?" ya fad'a cikin damuwa, dae_dae kuma lokacin daya ida kae hannun sa jikin ta, se a lokacin ta soma dawowa hayyacin ta, ta kautar da jikin ta daga k'ok'arin rik'o ta daya ke yi, sannan cikin sake k'arya ta zuciyar ta da abinda ta gani tace "Aure kayi?" ta k'are maganar lokacin da hawayen da suka taru a cikin idanun ta suka samu damar zubowa akan fuskar ta, runtse idanun sa yayi lokaci d'aya k'irjin sa ya d'an buga "Ya akayi ta sani?" tambayar data fara zuwa masa a cikin kae kenan, kamar ta san me yake tunani seta saka hannu ta d'auko katin daya fad'i daga hannun ta d'azun duk da har lokacin jikin ta be bar rawa ba "Wannan katin auren waye?" iska ya fesar daga bakin sa sannan ya dafe kan sa daya sara masa, a hankali ya sake d'aga idanun sa ya zuba su a kan ta sannan yace "Ayrah pls ki tsaya zan miki bayani kin san.." "Na auren waye?" ta sake katse masa maganar daya fara yi, dan haka kawae taji jikin ta ya sake yin sanyi, seda ya sake lumshe idanun sa sannan yace "Nawa ne amma.." kukan data keta rik'ewa ne ya k'wace mata gaba d'aya, bata da k'arfin da zata iya ficewa ta shige gida tayi kukan ta dan haka ta d'ora kan ta akan cinyar ta ta shiga rera shi tana jin yanda wani irin takaeci, bak'in ciki da kuma k'unar zuci ke addabar ta "Yah ilahee.." ya ambata akan la66an sa, shi kam yau yaga ta kan sa, hannun sa duka biyun ya saka ya janyo ta cikin jikin sa har zuwa lokacin kuma kukan take har da sheshshek'a, fuzge jikin ta ta shiga yi amma ya k'arasa shigar da ita sannan ya zagaye ta da duka hannayen nasa yana lumshe idanun sa, har lokacin bata hak'ura ba ta cigaba da k'ok'arin tashi lokaci d'aya kuma tana furta "Ni ka sake ni, bana son ka, bana son ka" be san sanda murmushi ya k'wace masa ba yana girgiza kae, ban da abin Ayrah idan bata son shi mene na kishin sa haka? Sake rungume ta yayi tsam cikin jikin sa kamar ze maeda ta cikin sa, sannan ya d'ora kan sa akan ta dake kan k'irjin sa, da dae ta gaji da k'ok'arin tashin se kawae ta sake fashewa da wani kukan tana komawa jikin nasa gaba d'aya, hakan ne ya sake bashi damar rik'e ta sosae, be hana ta kukan ba dan yasan dole ne se tayi kukan musamman wannan abu data gan shi kawae daga sama, ta d'auki wajen minti 2 tana cigaba da rera kukan se kuma daga baya ta koma tayi lak'was tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya cike da jin haushin sa, se kuma a lokacin ta cigaba da kicin_kicin tashi, a wannan karon be hana ta tashin ba ya sake ta a hankali, kae tsaye ta ta6a k'ofar fita se ta ji ta a rufe, dan haka ba tare data kalle shi ba ta furta "Ka bud'e min na fita" shiru yayi yana bin ta da kallo duk da baya iya hangen fuskar ta "Don Allah ki tsaya ki saurare ni" kamar jira take seta juyo tana kallan sa, kafin ta fara magana fuskar nan ta ta tayi jajur haka zalika sassanyar muryar ta ta sake rusuna "Babu abinda zaka fad'a min Raj, ka bud'e min na koma gidan mu, kaje kayi rayuwa da wadda kake so nima yanzu bana son ka.." ta fad'a tana jin wani irin zafi da bata ta6a jin sa ba cikin zuciyar ta, zazzafar iska ya fesar daga bakin sa kana ya d'an lumshe idanun sa yace "Ayrah, wallahi Abbu ne ya aura min ita, akwae maganar auren dama tun kafin sake had'uwar mu, don Allah kiyi shiru ki dena wannan kukan wallahi yana nakasta min zuciya" hannu ta saka ta toshe kunnuwan ta, tana ji a ran ta kamar wad'annan d'in kalaman yaudara ne kawae yake fad'a mata, meyasa zeyi mata haka? Meyasa ta yadda dashi shi kuma yaci amanar ta? Meyasa ze had'a ta da wata bayan ita tunda take bata ta6a had'a shi da wani ba, tana cigaba da tare sabon kukan daya taho mata ta furta "Ni ka bud'e min k'ofa na fita.." yanzu kam babu musu ya bud'e mata k'ofar, da sauri ta saka hannu ta bud'e murfin motar sannan ta fad'a cikin gidan nasu, a tsakar gida ta taradda Umma babu 6ata lokaci ta fad'a jikin Umman tana sake sakin wani sabon kukan "Subhanallahi Ayrah.. Meya faru?" Umma ta fad'a tana rik'o Ayrahn dake cigaba da kuka kamar wadda akama mutuwa, bata iya cewa komae ba saboda yanda zuciyar ta ke cigaba da tafasa, haushi da kuma takaeci suna sake cika ta, seda ta gama kukan tsaf sannan ta d'ago tana kallan Umma da zuwa lokacin ta gama rud'ewa da yanda taga d'iyar ta ta na kuka haka "Umma wae aure yaje yayi! Umma ya yaudare ni bansan yadda zanyi ba zuciya ta na dab da bugawa" ta fad'a tama manta Umman ta take fad'awa maganar, da mamaki Umma take kallan Ayrahn kafin cikin k'arfin hali ta furta "Ay..." sallamar da Abba yayi cikin gidan itace ta katsewa Umma maganar da take k'ok'arin fad'a, seta d'aga kae ta kalli Abban, ga mamakin ta seta gan shi sun shigo tare da Rk, maganar sa da Ayrah ta jiyo ne ya sanya ta shirin mik'ewa a fusace tana shirin shigewa cikin d'aki Umma ta rik'o ta "Ki tsaya tukunnah" ba dan taso ba haka ta zauna d'in har lokacin kan ta na kan cinyar Umma kuma har zuwa lokacin zafin da zuciyar ta ke mata be ragu ba, haka zalika ji take kamar tayi ta kukan kar ta dena, sam bata san kuma meya shigo dashi cikin gidan ba, me yake nufin zece mata ta yadda dashi? "Ina jin ka Allah yasa lafiya" Abba ya fad'a bayan ya zauna akan tabarmar dake shimfid'e a tsakar gidan, seda ya d'an yi shiru kad'an kana ya saci kallan inda Ayrah ke zaune sannan yace "Abba dama akan maganar aure ne da nayi yau d'in nan, naso na yiwa Ayrah bayani se dae tak'i fahimta ta, Abbu be san da maganar aure na da ita ba shiyasa, kuma dama tun farko yana da burin aura min ita kasancewar er k'anin sa ce, se kuma yanzu Allah yayi za'a yi auren amma sam bani da laefi Abba" ya k'are maganar a maraeraece dan yana da tabbacin Ayrahn na jin sa, ajiye numfashi Abba yayi sannan yace "Ikon Allah, dama namiji ba dan mace d'aya akayi shi ba, kuma hakan ya sake nuna min kae d'in yaro ne me biyayya, dan haka ka tashi kaje Allah yayi maka albarka.. Ke kuma Ayrah ki tashi ki bi mijin ki dan banga amfanin zaman naki cikin gida bayan da auren ki ba" ya k'are maganar yana kallan Ayrah, da sauri ta d'aga narkakkun idanun ta ta sauke su kan Abban da yayi magana, ita kan ta Umma tayi mamakin maganar Abban, amma shi kam da yayi maganar da alama ko a jikin sa "Abban su.." Umma ta fad'a tana cigaba da kallan sa "Babu damuwa, ta tashi ta bishi d'in" shine abinda Abban ya sake fad'a, ajiyar zuciya Umma ta sauke sannan ta kalli Ayrah dake girgiza kae kamar k'adangaruwa cikin kuka tace "Abba don Allah ka bar ni a gidan nan kaaji" dama saboda hakan Abban yace tabi mijin ta, dan kuwa yasan idan ba yanzun ba nan gaba ma se gwagwarmayar tafi hakan dan haka ya kalle ta yace "Babu komae kinji, ki tashi kije.. Zamu yi komae daga baya" ita sam ba fahimtar Abban take yi ba dan kuwa kishi ya riga ya gama rufe mata ido, duk kuwa da irin bayanin da yayi ita har yanzun bata gamsu ba, kawae ji take yi kamar yaudarar ta yayi. Umma ce ta mik'e ta fad'a cikin d'aki ta shiga had'awa Autar ta ta kayan da tasan zata yi amfani dasu ko kuma ta buk'ata kafin komae ya daedaeta sannan ta fito har ran ta tana jin babu dad'i, a yadda ta bar ta a tsakar gidan a haka ta same ta, zaune ta d'ora kan ta akan k'afar ta tana sheshshek'ar kuka, seda ta fito d'in sannan Abba ya kalli Rk "Ku tashi kuje Allah yayi muku albarka, In Sha Allah zan neme ka ko ta layin Sadeeq ne" sosae yaji dad'in abinda Abban yayi dan haka yace "Nagode sosae Abba, Allah ya k'ara girma" "Ameen" d'ago da fuskar Ayrah Umma tayi tana kallan yanda fuskar ta tayi kace_kace da hawaye, seta girgiza kae tana jin tun yanzu har kewa ta fara kama ta "Kukan ya isa haka Ayrah, ki tashi kije zamu yi waya Uhmm?" Umma ta fad'a cikin rarrashi, tausayin Ayrahn na kamata yanda take yarinya da ita amma yanzu haka tana da kishiya wadda za'a kira da Amaryar mijin ta, d'aga ido tayi ta kalli Umma, tana shirin fara magana Umma ta girgiza kae tana murmushin yak'e "Ya isa haka ki tashi ki je kin ji?" sam bata so wani 6acin ran ya sake shiga tsakanin ta da iyayen nata dan haka ta mik'e tana jin jiri na d'ibar ta "Allah ya tsare Auta" shine abinda Abba ya fad'a sanda take shirin gifta inda yake zaune, bata iya amsawa ba dan ita kad'ae tasan yadda take ji a cikin zuciyar ta, shine ya d'auki kayan sannan yayi gaba ita kuma ta rufa masa baya, suna fita kuwa Umma ta mik'e da sauri ta shige cikin d'aki saboda kukan da taji ya taho mata, bin ta da kallo Abba yayi sannan ya dawo da kallan sa tsakar gidan da murmushi kan fuskar sa gami da girgiza kae. A hankali take takawa kamar mara laka zuwa wajen motar tasa, shi ya saka hannu ya bud'e mata, yanzu kam babu musu ta shiga sannan ya zagaya driver seat ya shiga ya zauna, kallan ta yayi yanda yaga tana ta curewa waje d'aya kamar me jin sanyi lokaci d'aya kuma tana matsar k'walla, lumshe idanun sa yayi a ran sa yana sak'a gwara ya bar ta tayi kukan dan yasan kuka dole ne musamman gare ta data shak'u da iyayen ta haka, bugu da k'ari kuma ga wannan maganar da itama ta sake tada mata da hankali. ... A cikin wani k'ayataccen Hotel yayi parking, a nutse ya juya ya kalli inda take kwance kan kujerar tayi shiru kamar me tunani, haka kawae yaji wani tausayin ta ya lullu6e shi, ya lumshe idanu lokaci d'aya wani haushi na taso masa tunawar da yayi yanzu haka akwae auran wata a kan sa "Ayrah!" ya fad'a a nutse kuma cikin tausashshiyar murya, a hankali ta bud'e lumsassun idanun ta ta watsa su a kan sa wanda har seda hakan ya sanya shi lumshe idanun sa, se kuma data ga hakan sannan tayi maza ya janye nata idanun tana iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta dena ganin laefin sa albarkacin maganar daya fad'awa Abba cewar bashi ita akayi amma har zuwa lokacin ta kasa, ta kuma k'i dena ganin laefin sa, se dae an samu ragin kaso me d'an yawa daga laefin sa data fara gani a farko. "Ki goge idanun ki pls, zamu sauka.." ya fad'a yana mik'a mata handkerchief d'in hannun sa, kamar ba zata kar6a ba se kuma a hankali ta saka hannun ta ta kar6a kana ta goge hawayen da ba dan kan ta suke fitowa ba da kan su kawae suke fitowa. Seda suka k'ara wajen minti 2 a haka sannan ya fita ya bud'e mata k'ofa ta fito kana ya koma ya d'auki kayan ta sannan suka wuce, yana gaba tana bin sa a baya kamar wata mara laka saboda yanda tafiyar ta ta ta k'ara sanyi, be damu da hakan ba ya cigaba da tafiya har zuwa sanda ya gama komae ya kar6i mukulli sannan suka wuce cikin d'akin. Madaedaecin bedroom ne me d'auke da babban gado, wardrobe da kuma mirror da sauran abubuwa dae da aka san bedroom na d'auke da, a hankali ya saci kallan yanda ta tsaya daga k'ofar wajen kamar me tsoron wani abun, bece mata komae ba ya k'arasa ya ajje jakar hannun sa sannan ya dawo cikin d'akin, tana nan dae inda ya bar ta, ya kalle ta bayan ya karyar da kae yace "Don Allah ki shigo ki zauna" ba tace komae ba kuma bata motsa daga inda take ba, a hankali ya sanya hannun sa d'aya saman goshin sa ya murza kana ya juya, wayar sa ya ajje kan k'aramar kujerar d'akin sannan ya soma takawa da niyyar juyawa, kamar jira wayar take ya ajiye ta ta soma ringing, kamar wadda aka tsikara ko kuma ake ja ta sauke idanun ta akan wayar "Muneerah!" taga ya bayyana akan wayar, dama kukan be ishe ta ba dan haka nan take idanun ta suka sake tara k'walla, dawowa yayi da baya dae_dae lokacin da kiran ya katse, ya k'araso ya d'auki wayar yana kallan kiran waye? Ganin me kiran ya sanya shi d'aga kae ya kalli Ayrah dake tsaye yanayin ta ya sake chanjawa daga d'azun, bata iya kallan fuskar sa ba se cigaba da rik'e kukan daya taho mata take yi, idan har bata man ta ba waccan d'in da aka d'aura musu aure ae sunan ta Muneerah, d'an runtse idanun sa yayi kafin ya ajje wayar inda ya d'auka sannan ya k'araso inda take beyi wata wata ba ya saka hannu ya d'aga ta gaba d'ayan ta ya d'auke ta kamar Baby, da sauri ta fara hantsilawa da niyyar sauka amma be sauke ta ba har seda ya k'arasa kan gado ya zauna sannan ya jata zuwa cikin jikin sa, kamar jira take yi kuwa ta saki kukan data kasa rik'ewa "Oh god" ya fad'a yana lumshe idanun sa, meyasa ita kuka baya mata kad'an ne? Yana jin ta sanda take cigaba da kukan, shiru yayi yana cigaba da saurarar ta ko zata yi shiru, da yaga dae bata da niyyar yin shirun seya d'auki hannayen sa duka biyun ya d'ago kan ta dake kwance male_male akan k'irjin sa, ya gaji da jin kukan nan na ta, d'an mitsitsin bakin ta red colour kamar wanda aka sakawa jan baki yabi da kallo yanda take motsa shi, ya d'an sake lumshe idanun sa sannan babu 6ata lokaci ya kama bakin nata cikin bakin sa, lokaci d'aya kukan nata ya tsaya saboda yanda taji bak'on al'amarin da tunda take bata ta6a ji ba, cikin sauri ta bud'e idanun ta a razane k'irjin ta na bugawa jin kukan nata yak'i cigaba da fita, fahimtar abinda ke faruwa ya sanya ta soma janye bakin ta da k'arfi lokaci d'aya kuma tana k'ok'arin tashi daga jikin sa cike da tsoro, sam be kula ta ba sema sake rik'o ta da yayi gam cikin jikin sa ya shiga kissing nata a hankali cike da matsananciyar k'aunar ta, idanun sa a lumshe haka zalika yana sake cigaba da shigar da ita cikin jikin sa, kuma yana cigaba da kokawa da numfashin sa daya soma chanjawa, ya d'auki wajen minti 1 yana kissing nata zuwa lokacin jikin sa ya gama yin sanyi, wani bak'on al'amari ya soma ziyartar gangar jikin sa, yanda ya d'an sassauta rik'e bakin nata ne yasa tayi amfani da wannan damar ta k'wace lips d'in ta tana jin yadda k'irjin ta ya cigaba da bugawa, ajiyar zuciya ya sauke sanda ta cire bakin nata daga cikin nasa har lokacin idanun sa na a lumshe ne, hannu ta saka ta dafe bakin ta da kuma iya k'arfin ta ta soma k'ok'arin mik'ewa tana ajje numfashin dake alamta kuka take mara sauti, se kawae ya sake saka hannu ya jata cikin jikin sa ya mata wata kyakykyawar runguma, hannu ya saka ya soma zame hijab d'in jikin ta har lokacin kuma be sake ta ba kuma yak'i bata damar tashi, girgiza kae ta shiga yi kamin cikin k'arfin hali tace cikin raunatacciyar muryar ta "Ni ka k'yale ni" ta fad'a kamar zata fashe da kuka, be kula ta ba kawae ya k'arasa zame hijab d'in gaba d'aya ya jefar gefe sannan a hankali ya shiga shafa bayan ta kamar yarinyar goye, shi kad'ae yasan yadda bugun zuciyar sa ya k'aru, kawae k'arfin hali yake yi yana jan numfashi a hankali, ga mamakin ta se taji kukan na neman tafiya inda ya fito, se dae bata ji zata iya d'aga ido ta kalle shi ba saboda kunyar abinda ya mata yanzun, shi ko kunya ma baya ji? Seta sake kae hannun ta bakin ta data ke ji kamar yanzu ne yake kissing d'in nata, dan haka ta d'an zabura kad'an kamar wadda aka daka tana shirin mik'ewa k'irjin ta na cigaba da bugawa cike da tsoro, gyara mata kwanciyar daya dake yi shine ya tabbatar mata da ba yanzu ne yake kissing d'in nata ba, duk jikin ta a matuk'ar sanyaye ta hak'ura da k'ok'arin tashin ta koma kawae tayi shiru se dae har lokacin akwae ragowar k'walla manne cikin manyan idanun ta. A hankali kuma taji wani irin bacci na sakad'ar ta, so take ya cika ta ta mik'e amma yak'i sakin ta dan haka kawae ta hak'ura ta bada kae bori ya hau, babu dad'ewa bacci me dad'i ya d'auke ta, seta shiga sauke ajiyar zuciya a nutse, se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya kamin a hankali ya furta "Rigimammiyar mata ta.." k'arar da wayar sa tayi ne ya sanya shi kallan inda take, be san me kiran nasa ba, kamar ze share se kuma ya kalli Ayrahn dake baccin ta hankali kwance kamar bata da damuwa, ya lumshe idanun sa wata matsananciyar k'aunar ta na sake ratsa shi, cikin dabara yanda ba zata farka ba ya shiga zame ta daga jikin sa har zuwa sanda ya k'arasa zame ta gaba d'aya, ya kwantar da ita kan gadon sannan ya lullu6a mata blanket kana ya sake kallan ta, ji yake kamar ya sake kissing nata se dae baya so ya 6allowa kan sa ruwa dan haka kawae ya k'arasa inda wayar tasa take dae_dae lokacin da ta sake yin ringing "Muneerah!" shine dae sunan daya sake bayyana akan screen d'in, tsaki yaja akan la66an sa dan har ga Allah ya manta da wata Muneerah musamman a yanzu da yake tare da Ayrah "Itama matar ka ce, at least yaci ace ka san a wane hali take" shine abinda zuciyar sa ta raya masa, ya sake jan wani gajeran tsakin yana maeda duban sa kan er rigimar tasa, yanzu taya ze fita ya bar ta cikin d'akin nan ita kad'ae? Idan kuma ya fita kafin ta tashi in ta tashi taga baya nan fa meze faru? Mhiz Innocent.....✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 039 ___A hankali ya maeda duban sa kan gadon yana kallan ta duk da fuskar ta ce kad'ae ake iya gani gaba d'aya jikin ta na lullu6e ne da blanket, ajiye wayar yayi kan kujerar kafin ya k'arasa a nutse zuwa wajen gadon, hannu ya saka ya janyo side drawer dake gefe ya matso da ita dab da gadon sannan ya zauna akae, murmushi ne ya su6uce a kyakykyawar fuskar sa sanda yaga tayi juyi seya kasance ta koma kallan inda ya zauna d'in, a hankali ya d'an lumshe idanun sa sannan ya kafe kyakykyawar fuskar ta da kallo, sosae kyawun ta ya sake bayyana da tana baccin, dogayen lashes d'in ta sun kwanta luff luff akan idanun ta, ya shafe wajen minti 3 a haka yana kallan nata sannan ya sake lumshe idanun sa kana ya kwantar da kan sa a gefen gadon. A hankali ya k'arasa kan gadon sannan ya d'an rank'wafa kad'an kana ya shiga hura mata sassanyar iska daga cikin bakin sa akan fuskar ta, dan baya so yayi wani abun daze zama takura a gare ta, a nutse ta shiga bud'e manyan idanun ta sanda taji iskar akan fuskar ta, seda ta gama bud'e idanun nata dae_dae lokacin da ta sauke idanun na ta akan sa, da sauri ta tashi zaune ganin yadda fuskar sa take a dab da ta ta, seda ta tashin sannan ya matsa daga kan gadon, ita kuma taja bargon da take ciki ta sake rufe jikin ta gaba d'aya, murmushin gefen baki ya saki lokaci d'aya yana kae hannun sa kan kwantacciyar sumar kan sa ya shafa, ya lumshe idanun sa yana taune gefen lips d'in sa na k'asa "La'asar tayi.." ya fad'a a hankali bayan ya maeda duban sa kan ta "D'an mik'o min hijab d'ina" ta fad'a ba tare data kalle shi ba tana d'an tura baki, bin inda hijab d'in nata yake yayi da kallo, seya saka hannun sa a hankali ya d'auka sannan ya jefa shi kan kujerar daya ajje wayar sa, itama hijab d'in tabi da kallo kafin ta dawo da kallan ta kan sa idanun ta sunyi rau rau "Don Allah ka bani" ta fad'a har lokacin bata sakko daga kan gadon ba kuma bata cika blanket d'in data rik'e ba, seda ya lumshe ido sannan ya sake zuba mata idanun sa kana yace "Ko inzo in sauko dake ne?" yayi maganar calmly, harara ta jefa masa kamar idanun ta zasu fad'o har seda hakan ya sanya shi yin murmushi me k'ayatarwa, kamar zata yi kuka tace "Ni dae Allah ka bani hijab d'ina sallah fa zan yi" seda ya soma takawa kamar ze hau kan gadon sannan yace "Bari kiga abinda za'ayi.." ya fad'a kamar ze d'aga ta, babu shiri ta saki bargon da sauri ta dirga ta d'ayan 6angaren ta fad'a toilet bayan ta sake murgud'a baki, lumshe idanun sa yayi bayan ta shige band'akin, seya samu kan sa da tuna yadda yaga rigar jikin ta tabi jikin ta ta kwanta sosae ta matuk'ar yi mata kyau, bud'e idanun sa yayi kamin ya fesar da iska daga bakin sa kana ya fice daga d'akin. Be dad'e ba ya dawo dan yana idar da sallah ya taho, sanda ya dawo yayi dae_dae da lokacin da take k'ok'arin fitowa daga cikin toilet d'in, akan sa idanun ta ya fara sauka, da sauri tayi maza taja k'ofar ta koma ciki tana ji kamar ta fasa ihu, kallan inda hijab d'in ta ke ajiye yayi da alama bata d'auka ba, yayi wani murmushi kana ya d'auki hijab d'in ya k'arasa bakin toilet d'in, bece komae ba yayi shiru yana jiran jin ko za tace wani abu, kamar kuwa tasan jira yake se yaji tace cikin er k'aramar muryar ta "D'an ban hijab d'in nan don girman Allah" ta fad'a a shagwa6e tana kwa6e fuska "Gashi" ya fad'a bayan ya matsa jikin k'ofar sosae, seda ta d'an yi jimm kad'an kafin a hankali ta saka hannun ta kan hannun k'ofar ta d'an bud'e ta kad'an, shi kuma ya mik'a mata hijab d'in, seda ta sauke ajiyar zuciya sannan ta saka hannu ta kar6a, kafin ta gama kar6ar ya saka hannun sa d'aya ya tura k'ofar se ganin shi tayi cikin toilet d'in, k'ara ta saki lokaci d'aya tana wara manyan idanun ta, ganin sa da tayi cikin toilet d'in, cikin rashin sanin abin yi kawae ta rungume shi gudun kada ya ganta a yadda take d'aure da d'an k'aramin towel tana fashewa da kuka kawae, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke sanda ta fad'a jikin sa d'in, seda ya tafi hutun tak'aetaccen lokaci sannan ya fizgo numfashin sa kana ya sake lumshe idanun sa, a hankali ya fesar da iska daga bakin sa yana shak'ar daddadan k'amshin dake tashi daga jikin ta wanda ya had'u da k'amshin sabulu suka had'u suke bada wani sassanyan k'amshi me dad'in shak'a, hannun sa ya d'aga da nufin d'orawa akan farin gadon bayan ta dan bata damar sake kwanciya cikin jikin sa bayan uwar rungumar data masa, seya jiyo muryar ta cikin rauni tana furta "Ka fita don Allah, ka fita don Allah.." abinda take fad'a kenan ilahirin jikin ta na rawa, bugun da zuciyar ta keyi yana iya jiyo shi saboda yadda jikin ta ke manne da na shi, ba k'aramin gudu yake yi ba, wanda ya had'u da nasa bugun zuciyar da ya chanja tun lokacin da ta rungume shi, sheshshek'ar data cigaba dayi har kuma lokacin tak'i sakin sa kamar ma sake shigewa cikin jikin nasa take yi duk dan kada ya gan ta shine ya sanya shi sakin ajiyar zuciya sannan yace cikin wata shak'ak'k'iyar murya kamar ba tasa ba "Zan fita.." ya fad'a yana k'ok'arin kae hannun sa kan ta, se kuma ya dakata saboda yanda yaji jikin sa ya sake yin wani mugun sanyi, se kawae yace cikin d'an k'arfin hali "Toh cika ni Madam" se a lokacin ta d'an rage kaefin rungumar data masa, amma duk da haka bata sake shi ba "Is ohk, na kulle ido na, bazan kalle ki ba shikenan?" "Tsakanin ka dawa?" ta fad'a cike da sakarci, duk da yanda rungumar data masa ta shige shi sosae har ta sanyaya duk wata ga6a ta jikin sa hakan be hana shi yin murmushi ba sannan ya furta "Da Allah" ya fad'a yana kulle idanun nasa da gaske, se a lokacin ta sake shi a hankali sannan ta mik'e tana kallan fuskar sa, da gasken idanun sa a rufe yake hakan ne ya sanya ta saurin saka hijab d'in ta har lokacin jikin ta na wani irin rawa dae_dae lokacin da shi kuma ya fice daga band'akin, bin sa tayi da harara kamin tace kamar zata yi kuka "Wannan ae iskanci ne" ta fad'a tana murgud'a baki gami da sake harara kamar yana gaban ta. Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya fito daga toilet d'in ya nemi waje ya zauna idanun sa a kulle har lokacin jikin sa a sanyaye, yana nan zaune ta fito kamar wata munafuka se sussunne kae take, seda ta saci kallan sa sannan ta k'arasa wajen kayan ta ta fidda wata riga kana ta koma toilet d'in ta saka sannan ta fito, babu 6ata lokaci ta tayar da sallah, har lokacin data idar idanun sa na a rufe ne, seta sake kallan sa kafin ta d'auke kae kawae. .. Wajen k'arfe 9pm ne, yana zaune kan kujerar d'akin yayin da take zaune akan gado tayi shiru kamar me tunanin wani abu, so yake ya kawar da wannan bak'untar data shiga tsakanin sa da Ayrahn amma kuma yanzu yana cikin wata matsalar ne yasan ba lallae ta saki jikin ta a yanzu ba kam, amma duk da haka ya gaji da ganin ta shiru haka nan, ba kuma yaso ya tuna mata da maganar da zata 6ata mata rae amma yanzu kuma ya zama dole ya mata d'in in dae yana son zaman lafiya, gwara ya fara gamawa da wannan matsalar kafin yazo yaji da waccan d'in. A hankali ya mik'e ya k'arasa kan gadon gefen ta, ya d'aga kae ya saci kallan ta yadda take zaune kan ta akan gwuiwar ta tayi shiru, hannu ya mik'a a nutse ya kamo tattausan hannun ta cikin nasa, janyewa ta soma yi, shi kuma ya sake rik'e hannun gam lokaci d'aya yana girgiza mata kae fuskar sa a narke, kallan sa tayi kafin ta d'auke kan ta tana jin kamar tayi kuka idan ta tuna wani abun "Ayrah don Allah kiyi hak'uri kin ji? Ki dena fushi da ni haka nan, yana ta6a zuciya ta, kin san yadda nake k'aunar ki, bana son ganin ki cikin damuwa, bansan da wane baki zan yi amfani wajen baki hak'uri ba, amma ni dae don Allah ki yafe min ki dena fushi da ni, ina so ne ki koma asalin Ayrahn ki, me so na, me yawan fara'a a gare ni, wadda bata son gani na cikin damuwa.." ya k'arasa maganar yana lumshe idanu, d'aga narkakkun idanun ta tayi ta kalle shi k'irjin ta na d'an bugawa, se taji tausayin sa ya kamata, ita kan ta zata so ta koma waccan Ayrahn amma bata san yanda zata yi hakan ba "Na dad'e banga murmushin ki ba, pls ki min ko da hakan ze faranta min.." yayi maganar har lokacin muryar sa a k'asa yana d'an murza hannun ta dake cikin nasa, bata san sanda tayi murmushin ba wanda ya taho da wani hawaye, seta saka hannu ta d'auke hawayen tana jan ajiyar zuciya, k'awataccen murmushi ne ya wanzu akan kyakykyawar fuskar sa kana yace "Dats my beauty.." seda ya d'an yi shiru yana tunanin ta inda ze fara mata magana, baya so ya sake 6ata mata mood amma wannan lokacin ne ya dace yayi maganar dan haka yace "Babe kina so ranar lahira na tashi da 6ari d'aya a shanye?" cikin rashin fahimta ta d'aga dara_daran idanun ta ta kalle shi, seda ya lumshe idanun sa saboda yanda yaji kallan nata har cikin jikin sa kana yace bayan ya jinjina kan sa "Kiyi hak'uri inaso naje wajen Muneerah in duba halin da take ciki" ya fad'a yana kallan cikin idanun ta, duk da yanda idanun nasu ke cikin na juna hakan be sanya ta janye nata ba "Muneerah!" ta maemaeta akan la66an ta cike da rashin fahimta "Ya ilahee kasa kada ta d'auka da zafi" ya fad'a cikin zuciyar sa har lokacin yana kallan ta "Matar da aka aura min yau nake nufi" cikin sauri ta fizge hannun ta daga cikin nasa wata k'walla na taruwa cikin manyan fararan idanun ta, ba ita taso kukan ya fito ba kawae seta fara kuka wani irin zafi cikin k'irjin ta, runtse idanun sa yayi yana jin babu dad'i har cikin ran sa, a hankali ya saka hannu ya jata cikin jikin sa, babu musu yanzu kam ta cigaba da rera kukan ta a hankali, seda tayi me isar ta sannan ta koma sauke ajiyar zuciya, se a lokacin ya cigaba da magana "Kiyi hak'uri..." ya fad'a, shiru tayi tana sauraron bugun zuciyar su daya had'u waje d'aya, ita wani lokacin har mamaki yake bata musamman yadda kalmar hak'uri bata masa wahala a bakin sa kamar ba Rk ba, cikin raunanniyar murya tace "Ka tafi toh" ta fad'a bayan ta tashi daga jikin nasa, shiru yayi yana bin ta da kallo cike da tausayawa "Kin amince naje?" seta jinjina kae tana saka hannu ta d'auke hawayen da suka k'i tsaya mata "I love u.." ya fad'a a nutse da tattausar muryar sa, bata iya cewa komae ba se bugun zuciyar ta daya k'aru, shikenan itama waccan d'in k'ila haka zeje ya fad'a mata yana son ta, wani kukan taji ya sake taho mata, se tayi saurin jan ajiyar zuciya dan bata so kukan ya fito, cigaba yayi da bin ta da kallo kamar me son gano wani abu, yana son watsa ruwa a jikin sa amma baya son ta zargi wani abun a ran ta dan haka kawae ya mik'e ya d'auki wayar sa ya fice daga cikin d'akin jikin sa a matuk'ar sanyaye lokaci d'aya kuma 6acin rae na taso masa daya tuna wannan k'ak'ababben aure da aka lak'aba masa. Bin sa tayi da kallo sanda ya fice daga d'akin zuciyar ta na sake karyewa, bata ta6a tunanin zata ta6a raba Raj ita da wata ba, se gashi k'addara tasa hakan ta faru, a hankali ta lumshe idanun ta tana bawa kukan daya taho mata damar fitowa ko zata samu sassaucin abinda take ji a cikin zuciyar ta. ... Kae tsaye gidan nasa ya wuce har lokacin fuskar sa a cunkushe, sosae yake jin takaecin zuwa gidan da zeyi wajen wata matar, amma haka dae ya cije kawae ya tafi gidan. Gida ne me girma wanda ke d'auke da part 2, nashi da kuma nata, gidan ya ginu ya had'u kuma iya had'uwa, yana parking motar ya sauka, baya son 6ata lokaci dan haka ya d'auki ledar daya shigo da ita kae tsaye ya wuce part d'in da yasan anan ze same ta. Bin parlourn yayi da kallo wanda shima an zuba kaya kamar babu gobe, be bi takan komae ba ya k'arasa bedroom, knocking ya fara yi bayan ya dakata, tana zaune kan gado sanye cikin lifaya, tun d'azu dama ta k'agu yazo hak'uri kawae take yi, dan haka tana da tabbacin shine "A bud'e take" ta fad'a bayan ta bud'e fuskar ta dake rufe, wadda itace ta fara rufe ta se taga ba zata iya ba kawae ta bud'e ta, kallan sa tayi sanda ya shigo cikin d'akin tana jin wani irin farin ciki musamman idan ta tuna yau d'in ta mallake shi bayan duk wannan gwagwarmayar da ta sha. A nutse ya k'araso cikin d'akin har lokacin be kalli inda take ba, seda ya ajje ledar sannan ya nemi gefen k'aramar kujerar dake cikin d'akin, wajen minti 1 bece komae ba, ita kuma ji take kamar ta tashi ta rungume shi dan dae ta tuna fad'an da tasha a wajen Aunties d'in ta ne da babu abinda ze hanata aekata hakan, shiyasa yanzun ma kamar yadda suka umarce ta tayi shiru tana saurarar sa "Kina lafiya?" ya fad'a bayan ya daddanne zuciyar sa, murmushi ta saki jin tambayar tasa me nuni da kulawa ga wanda ake tambaya, hakan ne ya sanya ta karyar da kae sannan tace "Lafiya k'alau Baby, se dae gajiyar biki kuma!" "Ga abinci nan idan kina buk'ata, akwae komae a kitchen shima in kina buk'ata, bayan nan akwae wani abun da kike buk'ata?" ba tare da tunanin komae ba tace "A'ah Baby.." "Ohk" ya fad'a yana mik'ewa a nutse ya fice daga d'akin. Bin sa tayi da kallo sannan ta kalli ledar daya shigo da ita, wani murmushi ya su6uce mata data tuna yau d'in ita da Rk zasu zama abu d'aya. Tana zaune kan gadon ta cigaba da jiran shigowar sa, har wajen minti 30, awa 1, bata sare ba har lokacin, se dae gajiyar zaman da tayi, da kuma wannan shegiyar lifayar dake jikin ta, dan haka kawae ta sauko daga kan gadon ta ware lifayar gaba d'aya ta jefa ta gefe sannan ta koma ta zauna tana cigaba da jiran sa, tun tana cigaba da saka ran shigowar sa har ta sare, a lokacin ne kuma ta fara tunanin ko dae ta bishi d'akin na sa? Maganar Aunties d'in nata suka sake dawo da ita hayyacin ta seta koma tayi zaman da6aro kan gadon tana jin kamar ta rusa ihu, ita kam da sun bar ta da yanzun bin sa d'akin nasa za tayi ita babu abinda ya dame ta, basu san halin Rk bane, ita data san shi ita ta san shi, tun tana kokawa da baccin da ke ta kawo mata hari har ta bada kae bori ya hau kawae ta shiga sharara baccin ta. .. Shi kuwa 6angaren sa yana komawa d'aki wanka kawae yayi ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya sannan yabi lafiyar gado, gaba d'aya tunanin sa da hankalin sa na kan Ayrah ne daya baro ita kad'ae cikin d'akin, dan ma dae daga waje ya kulle ta ne in case, saboda akwae komae na buk'ata a cikin d'akin, a hankali ya lumshe idanun sa zuciyar sa fall da tunanin Ayrahn barkatae. Muneerah kuwa ba ita ta farka ba se wajen k'arfe 8 na safe, da sauri ta mik'e mamaki ya sake kamata ganin har lokacin babu shi cikin d'akin, kae tsaye wanka ta fad'a tayi sannan ta fito tayi Sallahr asuba, dan dama tun a gida ta riga ta saba bata tashi Sallahr asuba se 8 wani lokacin ma har fin 8 d'in ma, duk da kasancewar safiya ce hakan be hana ta d'aukar nighties ta saka ba, wata shu'umar riga ce irin me net d'in nan kuma me bin jiki, gaba d'aya undies d'in ta ana ganin su saboda yanda rigar take me raga raga kamar gidan sauro kuma dududu da kad'an ta wuce gwuiwa, seda ta sake gyara fuskar ta sannan ta fito daga d'akin zuwa part d'in sa. Tura k'ofar tayi cikin sa'a ta jita a bud'e seta k'arasa fuskar ta d'auke da murmushi ta tura kan ta cikin d'akin, wani sassanyan k'amshi ne ya ziyarci hancin ta wanda ya tilasta mata lumshe k'ananun idanun ta kana ta cigaba da tafiya bayan ta chanja tafiya ta d'an soma jijjiga jikin ta da yanzun babu laefi akwae su saboda uban magungunan data dinga d'irkawa cikin ta. Fitowar sa kenan daga wanka d'aure da madaedaecin towel, hannun sa rik'e da comb yana taje sumar kan sa ta tura k'ofar d'akin, idanun ta suka sauka akan bayan sa da take iya hange, wata k'atuwar ajiyar zuciya ta sauke saboda yanda taji gaba d'aya jikin ta ya amsa da ganin sa da tayi a haka, dan kuwa tunda take bata ta6a ganin sa a haka ba, da sauri ya juyo dan be ta6a tunanin rashin kunyar ta ta zata bar ta ta shigo d'akin sa washe garin ranar da aka kawo ta ba, amma ga mamakin sa se yaga ita d'in ce, ajje comb d'in hannun sa yayi bayan ya d'auke idanun sa daga kan ta sanda ta sakar masa wani tattausan murmushi, sosae k'irar jikin sa ta tafi da imanin ta, a yau da take ganin faffad'an k'irjin sa a bud'e dake d'auke da wasu kwantattun bak'ak'en gashi masu kyawun gani, kawae seta k'arasa ba tayi wata wata ba ta rungume shi ta baya tana sakin ajiyar zuciya, tsaki ya saki cikin ran sa wani 6acin ran na taso masa, se yayi k'ok'arin danne shi kada 6acin rae yasa yayi abinda be kamata ba "Baby meyasa jiya daga fitar ka baka dawo ba? Nayi kewar ka Baby sosae, na d'auka za muyi spending night d'in mu ne cikin farin ciki, at least dae ka taya ni farin cikin wannan ranar dana dad'e ina jira" iska ya fesar daga bakin sa kafin ya d'an kautar da kan sa ya shak'i iska dan abinda ke tashi daga jikin ta sam be masa ba, dan in dae ba hancin sa ke masa k'arya ba wani d'an k'arni k'arni yaji tana yi, abinda dae be sani ba shine itace keyi ko kuma turare ta saka me k'arni haka? Me tayar da zuciya!? hakan ba mamaki bane dan kuwa bleaching d'in da take yi shahararre ne, tayi d'au da ita, kae seka rantse dama can farar ce ba bak'a ba, hannu d'aya ya saka duk da yadda yaji tsigar jikin sa na wani irin tashi ya janye ta daga jikin sa kana ya matsa gefe ya d'auki wata tattausar brown d'in jallabiyya ya d'ora akan towel d'in sannan ya zame shi ta k'asa, seta kalle shi duk da yadda ta d'an ji babu dad'i amma hakan be hanata furta "Haba Baby ka bari mana inji d'umin jikin ka don Allah" da sauri ya d'aga idanun sa ya kalle ta cike da mamakin kalaman bakin ta, se kuma ya d'auke yana neman kan gadon ya zauna ya d'an kishingid'a da pillown dake kan gadon sannan ya furta har lokacin idanun sa a lumshe "Ina kwana?" bak'in bakin ta ta tura gaba sannan tace "Kae Baby, toh lafiya k'alau.." ta fad'a tana k'arasawa kan gadon, a hankali ta haye kae ba tayi wata wata ba ta fad'a jikin sa tana rik'o shi sosae kamar zata koma cikin sa tana sake shigar da jikin ta cikin jikin sa, da wani irin sauri ya bud'e idanun sa sanda yaji ta kane_kane cikin jikin sa, hannun sa duka biyun ya saka ya janye ta daga jikin sa kafin ya mik'e yana kallan yanda take wani sake gaggantsarewa tana kuma narke fuska ita a lallae dole shagwa6a take yi, shi sam bema lura da abinda take yi ba, dan idanun sa na kan fuskar ta ne yace fuskar sa a tamke "Ke wae er kunyar nan irin ta mata baki da ita ne?" ya fad'a ran sa a matuk'ar 6ace cike da haushin wannan banzan halin na ta.... Mhiz Innocent......✍️ https://chat.whatsapp.com/DH0EIIWNPnSICxsGgh2DSd *CHAPTER TWO* *♡☆ZAZZAFAR KAUNA☆♡* *FREE BOOK* Page 040 ___Yanayin ta sam be nuna ta damu ko taji haushi ko zafin maganar daya fad'a mata ba, se dae ta kama kan ta bata sake gigin ta6a jikin sa ba, seda ta sauko daga kan gadon sannan ta sake basar da maganar daya fad'a mata kana tace "Amma dae ko ba komae ka fad'a min dalilin daya hana ka dawowa a jiyan koh?" k'aramin tsaki yaja har lokacin be kalle ta ba, baya jin ze k'ara koda rabin awa ne a cikin gidan nan da wannan matar, dan tabbas idan ta cigaba da wad'annan halayen na ta zuciya na iya tunzura shi ya fad'a mata maganar da ba zata ta6a mantawa da ita ba har abada "Zaki iya fita in shirya ko kuma na bar miki d'akin?" yayi maganar yana fiddo da wasu kayan daga cikin wardrobe, seda ta d'an sake gantsaro jikin ta kafin ta matso gaban sa tace "Bari na fita Baby, amma don Allah ka dawo da wuri.." shiru yayi na en wasu sakanni kafin yace sanda ya juya ya ajje kayan hannun sa kan gado "Sorry.. Ba'a nan zan kwana ba.." da mamaki take kallan kyakykyawar fuskar sa da kullum take gani take kamar ana k'ara masa kyau ne "Ba'a nan zaka kwana ba kuma Baby?" ta tambaya tana jin wani irin haushi ganin har lokacin yama k'i kallan koda shigar jikin ta ne ballantana hakan ya tabbatar mata da ze iya jan hankalin sa, jinjina kae kawae yayi "Amma meyasa? Amarya ce ni fa.." tayi maganar tana ji kamar ta rusa ihu, shiru yayi na en wasu sakanni kafin yace a nutse lokacin daya zubawa fuskar ta kyawawan idanun sa "Ohk in zauna kada in yi abinda ke gaba na koh?" ya tambaye ta cikin tsare gida, seda ta zame nata idanun da yanzun ma suke d'auke da lashes na kanti kafin tace "A'ah.. Ba haka nake nufi ba fa.." ta fad'a da er rikicewa da kallan da yake bin ta dashi, gefe guda kuma tana jin dad'i dan tasan yanzu kam tabbas yaga shigar jikin ta, abu d'aya take jira shine yayi wani abun daze nuna shigar ta ta ta tafi dashi, jin da tayi shiru har na wajen minti 1 ya sanya ta gyara tsayuwar ta tana d'an sake kad'a jikin ta kana tace "Bari na baka waje Baby, ina jiran ka da safe kenan? Amma ina fatan ya kasance daga yau kuma ba zaka sake fita ba se mun gama cin amarcin mu" ta fad'a tana jin kamar ta sake rungume shi dan dae kawae ta tuna maganar sa ne ta d'azu kamar be ji dad'i ba hakan ne ya sanya ta fasa yi d'in se kamo hannun sa da tayi cikin d'arr d'arr ta zuba masa wani kiss da har seda ya bada wani sauti "Muaahh" wato tayi shi cike da salo na jan hankali, se dae abinda bata sani ba shi kam ko a jikin sa, ya k'yale ta ne ma yanzun kawae dan kada ya zama mara adalci, amma daga shigar ta ta har abubuwan da take yi babu abinda ya ji shi cikin jikin sa, kwata kwata banda ma takaeci dake mak'ale a cikin ran sa. Cikin wani irin salo take takawa sanda zata fice daga d'akin tana wani karaeraya kamar zata 6alle, shi kam gogan naku bema san tana yi ba dan gaba d'aya hankalin sa yayi gaba wajen Ayrah ne. ... A 6angaren ta kuwa tunda ya fita da daren nan bayan ta gama kukan ta ta godewa Allah seta koma ta zauna tayi shiru zuciyar ta fall cike da tunani, seda ta d'an jima cikin d'akin sannan kuma ta fara jin wani irin tsoro na ratsa ta, a hankali take duban k'ofar d'akin se taga kamar wata inuwa ta gifta, da sauri ta runtse idanun ta tana jin yadda ilahirin jikin ta ke rawa, tunda take zata iya cewa bata ta6a kwana a waje ita d'aya ba, ta saba da jin motsin mutane kafin tayi bacci, se dae yau kwata kwata bata jin motsin komae shiru ne kawae ya ratsa ko'ina, haka kawae tayi ta tsarguwa, da dae ta gaji gaba d'aya se kawae ta koma kan gadon ta shige cikin blanket gaba d'ayan ta, tayi lamo tana jin wata k'walla na sakko mata, har lokacin bugun zuciyar ta be koma normal ba haka zalika tsoron be ragu ba, dae_dae kuma lokacin da er k'aramar wayar ta tayi k'ara, k'arar data sake rikita ta, take jikin ta ya cigaba da rawa kamar mazari zuciyar ta na cigaba da harbawa, seda ta soma nutsuwa sannan ta fahimci ringing d'in wayar ta ne, ta d'an lumshe idanun ta a hankali kana ta mik'a hannun ta har lokacin tana cikin bargon ta d'auka, ba tare data duba me kiran ba kawae ta d'aga wayar ba tace komae ba se sauke numfashi da take akae_akae kamar wadda tayi tsere "Auta!" ta jiyo muryar Yah Sadeeq, wata sassanyar ajiyar zuciya ta saki sannan ta kwa6e baki da murya tace "Yah Sadeeq.." duk da yanda yaji muryar ta amma be kawo komae ba saboda ya riga ya san halin Ayrah ciki da bae "Shine kika tafi babu ko sallama koh?" "Kae Yah Sadeeq, Abba ne fa yace wae mu tafi.." murmushi yayi kana yace "Toh shikenan Allah yayi miki albarka Auta, ya baku zaman lafiya, duk sanda na samu lokaci zan shigo mu gaesa dan har na fara missing naki" zuciyar ta ce ta sake karyewa amma dan gudun kada ta tayarwa da Yah Sadeeq d'in hankali ya sanya ta fad'in "Nima haka fa.." tayi maganar a sanyaye, babu laefi sun d'an jima suna hira a wayar, wadda ta kwashe kaso da yawa cikin damuwa da kuma tsoron da take ji kafin daga bisani suka yi sallama, zuwa lokacin dama ta fara jin bacci, dan haka cikin sauri ta k'ank'ame idanun ta ta rufe su ruff tana jiran d'aukar baccin. Barcin daya d'auke ta dududu befi na awanni 2 ba, data fara baccin seta firgita ta tashi, dan haka tun kafin asuba ta mik'e zaune, zuwa lokacin tsoron nata ya d'an soma raguwa kawae seta fad'a toilet tayi wanka sannan ta fito ta tayar da sallah, bata tashi daga kan daddumar ba se wajen k'arfe 8 kana ta mik'e ta koma kan gadon zuciyar ta a matuk'ar karye, idanun ta sun cika taff da hawaye.. Wajen k'arfe 10 ya isa Hotel d'in yayi parking motar sa sannan ya sauka kae tsaye ya wuce d'akin, a nutse ya saka mukullin hannun sa ya bud'e sannan ya tura k'ofar d'akin kana ya tura jikin sa cikin d'akin, acan tsakiyar gadon ya hango ta ta lullu6e jikin ta da bargo kan ta akan gwuiwar ta tayi shiru idanun ta akan k'ofar, ganin sa da tayi ya sanya zuciyar ta saurin karyewa bata san sanda wasu hawaye masu d'umi suka fara sintiri akan kuncin ta ba lokaci d'aya kuma tana cusa kan ta cikin k'afafun ta, runtse idanun sa yayi yana jin wani irin tausayin ta na ratsa shi, cike da sassarfa ya k'arasa cikin d'akin, kae tsaye ya haye kan gadon beyi wata wata ba ya jata cikin jikin sa yayi mata wata kyakykyawar runguma, dae_dae lokacin data fashe da kuka kenan me cin rae tana sake jin wani irin rauni a tare da ita, sake rungume ta yayi yana jin yadda bugun zuciyar ta ke fita da sauri da sauri, a hankali ya d'ora kan sa akan ta dake kan k'irjin sa sannan ya shiga shafa bayan ta a hankali lokaci d'aya wani tausayin ta na sake lullu6e shi, sosae take yin kuka wanda ke fita tun daga k'asan zuciyar ta, shi kuma be hana ta ba se dae har lokacin be dena shafa bayan nata ba, a hankali cikin rarrashi ya furta sanda ya kae bakin sa cikin kunnen ta "Kukan ya isa haka plsss.." ya k'arasa yana jan k'arshen maganar tare da hura mata iska a cikin kunnen na ta lokaci d'aya kuma yana sake shigar da ita cikin jikin sa, a hankali ta shiga rage sautin kukan na ta, har zuwa sanda ta koma sauke ajiyar zuciya, se a lokacin ya saki k'atuwar ajiyar zuciya sannan yace a hankali "Am sorry, am deeply sorry pls.." ba tace komae ba har lokacin kuma be sake ta ba dan sosae yake jin nutsuwa da take cikin jikin na sa "Plss Babe.." ya sake fad'a nan ma dae a hankali kamar me rad'a, kamar jira take suma kuma hawayen kamar jira suke se suka zubo kan fuskar ta sannan ta fara maganar cikin raunanniyar murya "Don Allah kada ka sake tafiya ka bar ni anan kaaji?" tausayin ta ne ya sake kama shi, shi kan sa baya son barin ta amma babu yadda zeyi dole se dae ya raba kwanan ko da d'ad'd'aya ne, yau idan ya kwana anan gobe ya kwana acan "Toh In Sha Allah" ya fad'a sannan ya d'ora da "Nan d'in ne bakya so?" "Tsoro nake ji ni dae, bana son nan gaba d'aya" tayi maganar tana k'ok'arin tashi daga jikin na sa, kamar kada ya sake ta amma seya sake ta d'in a hankali, se kuma a lokacin ya fahimci yanda ilahirin jikin sa yayi wani mugun sanyi, wata iriyar kasala ta gama rufe shi kamar kada ya motsa daga inda yake "Shikenan.. Zan fita na samo gidan da zamu zauna kafin komae ya daedaeta.." da sauri ta d'aga narkakkun idanun ta ta kalle shi jin da tayi yayi zancen fita, ya fahimci abinda ya sanya ta kallan na sa ba tare da ta shirya ba dan haka ya d'an yi murmushi kana yace "Kar ki damu da rana zan fita, dama Abbu na nema na, sena biya ta wajen su Abba ma mu gaesa" "Don Allah zan bi ka.." ta fad'a da sauri bayan ta rik'o hannun sa, hannun nasu yabi da kallo saboda yanda ya sake jin tsigar jikin sa ta tashi, ganin inda yake kalla ya sanya itama ta kalla, da sauri ta saki hannun nasa tana tura k'aramin cute lips d'in ta, nan ma seya sake bin bakin nata da kallo lokaci d'aya yana lumshe lumsassun idanun sa, ya kae wajen second 30 a haka sannan ya bud'e yana kokawa da zuciyar sa yace "Muje kici abinci" "Na ci kafin ka shigo!" ta fad'a ba tare da ta kalle shi ba "Kin ci?" ya fad'a yana kallan ta sosae, seta jinjina kae kawae tana sake kaucewa kallan daya ke bin ta da shi, jin bece komae ba ya sanya ta sake fad'in "Allah kuwa kuma ka duba ka gani idan ban ci ba" ta fad'a tana nuna masa abincin da ke ajje, seda yabi wajen da kallo sannan ya dawo da duban sa kan ta yace "Matso kiyi bacci kafin na dawo.." yayi maganar yana kishingid'a akan gadon lokaci d'aya yana mik'a mata hannun sa d'aya, tura bakin ta gaba tayi kafin tace "A'ah.." ta fad'a tana d'ora kan ta akan kafad'ar ta, tilas abinda tayi d'in ya sanya shi lumshe idanun sa yana sakin murmushi, hannun sa ya kae kawae ya janyo ta se gata cikin jikin sa, ya gyara kwanciyar sa sannan itama ya gyara mata ta ta kwanciyar cikin jikin sa duk da yanda take ta neman k'wacewa daga jikin nasa, wanda hakan ya bawa ma6allan rigar jikin sa na sama damar 6allewa, hakan ne ya bawa kyakykyawar farar fatar sa me d'auke da bak'a sid'ik d'in gargasa bayyana, ba tare daya lura ba ya sake manna ta da k'irjin sa, hakan ne ya bawa kan ta damar kwanciya akan zallahr fatar sa dake ta tashin wani sassanyan k'amshi, k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke sanda hakan ya faru, ya lumshe idanun sa bugun zuciyar sa na k'aruwa "Kiyi bacci" yayi k'ok'arin lalubo kalmomin biyu ya had'a ya fad'e su, ita kan ta sosae zuciyar ta ke bugawa musamman ma jikin ta dake ta rawa kamar mazari, amma duk da haka be sake ta ba, ganin bashi da alamar sakin ta ne ya sanya ta hak'ura ta runtse idanun ta tana jiran zuwan bacci, cikin ikon Allah kuma babu dad'ewa baccin ya d'auke ta seta koma tana sauke numfashi akan k'irjin sa, wanda hakan ya sanya shi saurin lumshe idanu gami da janye ta daga jikin sa a hankali yana jin yanda bugun zuciyar sa ke cigaba da k'aruwa fiye da d'azun, ba zeso wani abun ya shiga tsakanin sa da Ayrahn a Hotel ba, ba dan haka ba yau yadda yake jin sa babu abinda ze hana shi bin abinda zuciyar sa ke raya masa duk da yadda ita kan ta Ayrahn har yanzu bata koma asalin Ayrahn ta ba. Seda ya shiga toilet ya watsa ruwa sannan ya fito har lokacin tana baccin ta a nutse babu hayaniya, da alama dama baccin jiyan be wani wadace ta ba, hakan ne ya sanya shi saurin shiryawa ya fice yana fatan har ya dawo bata farka daga baccin ba, kafin nan ya samo musu mafita. ... Sanda ya isa gidan kae tsaye parlourn Abbu ya wuce dan yana da tabbacin yana nan, da sallama ya shiga d'akin, Abbu dake zaune kan kujera hannun sa d'auke da laptop yana aeki ya amsa sallamar har lokacin be d'auke idanun sa daga kan laptop d'in ba, a nutse ya k'arasa cikin parlourn ya zauna a k'asan had'ad'd'en carpet d'in dake malale a tsakiyar d'akin "Barka da safiya.." ya fad'a yana kallan Abbun, se a lokacin Abbu ya sauke ajiyar zuciya sannan ya rufe laptop d'in ya ajje ta gefe kana yace "Barka dae doctor ya Muneerahn?" "Alhamdulillah.." ya fad'a a nutse "Ya kamata ka koma bakin aekin ka haka nan likita.. Kasan bana son zama haka nan, ko kuma dae kada wannan satin ya cinye baka koma ba.." "In Sha Allah" Rk ya fad'a, a ran sa yana sak'a ta yadda ze fara yiwa Abbu zancen Abba, sam be san ta inda ze fara ba, ko ya sak'a ga ta inda ze fara d'in se yaga beyi ba seya bar shi, ya kuma tsarawa yaga beyi ba ya kuma barin sa. Wayar Abbu ce tayi k'ara, ya kalli me kiran nasa sannan yace sanda wayar ke hannun sa yana shirin amsawa "Bari na amsa kira.." yayi maganar yana kara wayar a kunnen sa, be san me suke tattaunawa cikin wayar ba se dae kawae yana jin Abbun na magana da alama akan kud'i ne suke magana, magana ta k'arshe da Abbun yayi itace taja hankalin sa "What? Me kake nufi? Wallahi baze ta6a yiwuwa ba, idan ma makirci kake k'ok'arin shiryawa ka fasa yi, dan kuwa ni ba shashasha bane, 50 millions wasa ne?" yayi maganar cikin d'aga murya kuma cikin 6acin rae, lokaci d'aya kuma yana jefar da wayar gefe sannan ya koma ya zauna kan kujerar da6ass zuciyar sa na bugawa "Abbu lafiya kuwa?" shine abinda ya iya furtawa yana kallan Abbun da gumi ke tsatstsafowa akan fuskar sa duk da yadda sanyin A.C ke ratsa gaba d'aya parlourn, kamar jira yake yi ae kuwa ya soma fad'in "Ni Mukhtar ze yiwa shashanci? Tunda nake ban ta6a yadda da kowa ba bayan kae da d'an uwa na, ta yaya ma zan yadda da wani inje yaci amana ta, ban san kuma wane tsautsayin ne ya sanya na bawa Mukhtar har 50 millions ba, se gashi mutumin banzan nan na fad'a min wae an masa kutse cikin Account d'in an kwashe duka kud'in, shin wannan maganar kamawa ce? Ni ze mayar mutumin banza? Toh wallahi seya fito dasu, k'arya yake yi so yake ya cuce ni Allah ya kama shi, nayi dana sanin shigar da bare cikin harkar kud'i na, toh wallahi se yayi kashin kud'in nan ko zeyi mene, millions 50 fa?" Abbu ya k'arashe maganar yana mik'ewa har lokacin yana jin zafi cikin k'irjin sa, sam ya kasa zama se safa da marwa yake cikin d'akin daga k'arshe ma seya haye sama kawae ya bar Rk da tunda ya fara magana bece masa uffan ba a zaune. Bin sa yayi da kallo sanda ya ida hayewa saman kana ya dawo da duban sa cikin parlourn, lumshe idanun sa yayi cike da takaecin halin mahaefin nasa, be so haka halin sa yake ba, amma duk da haka zeyi k'ok'arin chanja shi, se dae wannan kad'ae ya isa ya nuna maka Abbun na tsoron kada a aekata masa abinda yayi wa Abba shiyasa tun farko yak'i yadda ya shigar da bare cikin harkokin kud'in sa, se dae yau gashi ya shigar kuma an samu akasi, amma da yake shi ga abinda ya aekata sanda aka yadda dashi se yake ganin kowa ma haka ne, cutar sa akayi aka ci amanar sa ba tsautsayi bane. Sosae zuciyar Rk ke zafi, daze iya da yau d'in ze sanar da Abbu yasan komae game da zancen su shi da Abba, da irin abinda ya aekata masa, daze iya daya tsaya gaban Abbun ya fad'a masa abubuwan dake ta yawo a cikin kan sa, se dae baze iya ba, har lokacin Abbun na matsayin uban sa ne shiyasa yake neman hanya mafi sauk'i daze isar da sak'on sa wajen Abbun, koda hakan ze saka Abbun yayi nadama ya nemi yafiyar Abba akan abinda yayi masa shi da iyalin sa, ya tarwatsa musu farin ciki da rayuwar jin dad'i zuwa ta k'unci, baya so ya bar Abbun se ranar al_k'iyama sa had'e da Abba, sam baya fata hakan ya kasance. Mik'ewa yayi a hankali dae_dae lokacin da yake lumshe idanun sa lokaci d'aya ya fesar da huci daga bakin sa, be san me ze cewa Abbun ba koya shiga cikin d'akin, be san da wane baki ze yiwa Abbun magana ba, dan ze ga kamar idan yayi maganar zata zama kamar magana ce a fakaece yake fad'awa Abbun, hakan ne ya sanya shi jan k'afafun sa ya bar d'akin.. .... Da mamaki Abba ke kallan Alhaji Mato dake tsaye k'ofar gidan nasa jikin wata hamshak'iyar mota er uban su, lokaci d'aya annurin fuskar sa ya gushe, kamar ya juya ya koma se kuma ya kalle shi yace a nutse "Me ya kawo ka k'ofar gida na?" wani murmushin gefen baki Alhaji Mato ya saki kana ya sanya hannu ya gyara zaman babbar rigar jikin sa, hannu ya mik'awa Abba bayan ya matsa kusa dashi sosae yace "Ae ka bari mu gaesa koh?" ya fad'a da murmushin da Abba ya kasa gane manufar yin sa "Kaaga zaka fad'i abinda ya kawo ka ko kuma nayi tafiya ta?" "A'ah ae bata kae ga nan ba Alhaji Kabeeru.." ya k'are maganar yana sakin wata dariya kafin ya d'ora da "Wannan zuwan ae ba nawa bane naka ne" ya k'arasa maganar yana nuna Abban, da mamaki Abba ya cigaba da kallan sa dan yau d'in gaba d'aya Alhaji Maton ya chanja kamar bashi ba yana wasu abubuwa a juye wad'anda ya kasa gane su, jin Abban bece komae ba ya sanya shi fad'in "Zuwa nayi a bani kud'in da nayi asara akan d'iyar ka, dubban kud'ad'en dana kashe akan karatun ta, dubban kud'ad'en dana kashe dan naga ta zama wata amma saboda bak'in ciki irin naka wanda har d'iyar ka ma bakya k'yale ba ka saka k'afa kayi fatali dani d'in dae dazan rufa muku asiri.. Saboda haka yanzu base gobe ba ka shiga gida ka fito min da kud'i na gaba d'aya kada ko naira 5 tayi ciwo, dan kuwa babu inda zan je se kud'i na sun fito.." Alhaji Mato ya fad'a yana cigaba da kallan yanayin Abban daya chanja lokaci guda.. Mhiz Innocent....✍️