🪄...JUYIN KWAƊO...🪄 _Daga ruwa zuwa ruwan zafi_ From the writer of: YADDA ƘADDARA TA SO LABARINSU HASKE ƘADDARA CE ArewaBooks @SalmaAhmadIsah Wattpad @SalmaAhmadIsah *Gabaki ɗaya labarin JUYIN KWAƊO, da littafin kansa. Na sadaukar shi zuwa ga ZAHRA ROYAL STAR and NAINARH KD NKD'S. Your love and acceptance mean everything to me. Thank you for being my safe space and my forever friends.* بسم الله الرحمن الر حيم           *Page-01* *MK Fencing Academy,19th Floor, The Binary by Omniyat, Business Bay, Dubai, UAE.* ARMAN IƘBAL. Babu abin da yake tashi a ko ina sai hayaniya da iface-iface, sai kuma sautin sara da sukan takkuba. Kuma ko ina jini ne ke zuba... A tsakiyar wannan hatsaniyar yaƙin yake tsaye, can ya hango wani mayaƙi ya taho da gudu ya iyo kansa, hannunsa riƙe da wani takobi me tsananin kaifi, ya kawo masa sara da ita... Tahowar sukan takobin cikin tunaninsa ya yi dai-dai da tahowar sukan takobin abokin karawarsa a tsakiyar filin hall ɗin koyon wasan takobi na MK fencing academy. Cikin zafin nama ya buɗe idonsa, sannan ya yi azamar kaucewa sukar takobin wasan. Cike da ƙwarewa kuma ya yi amfani da nasa takobin ya kaiwa abokin nasa farmaki, farmakin da ya yi nasarar kai shi ƙasa, hakan yasa ya zamo zakaran wasan, domin shi ne ya lashe!. Malamai da ɗaliban wasan na takobi suka shiga tafa masa, hakan yasa ya juya kansa ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a hankali yake fitar da numfashi, domin wannan mafarkin da ya saba yi ido biyu yau ma ya raɓe shi, ya rasa mece ce alaƙarsa da wannan yaƙin da yake yawan yin mafarkinsa ido biyu ko cikin bacci. Ba ya jin ya taɓa tsallake sati ɗaya ba tare da ya yi mafarkin wannan yaƙin me firgitar da ɗan adam ba. Shi dai ya san ba a haifeshi a ƙarnin da aka yi yaƙin ba, amma kuma ya rasa dalilin da yasa a ko da yaushe yaƙin yake raɓar rayuwarsa. Hannu ya kai ya taɓa farin glasses ɗin da ba ya taɓa rabuwa da su duk rintsi, kasancewar yana fama da lalurar rashin gani, wadda aka haife shi da ita. Da ace kuɗi yana samar da lafiya ya tabbatar da mahaifinsa Sayid Iƙbal Alhadi zai ƙarar da duk dukiyar da ya mallaka domin sama masa lafiyar ido. Amma tun yana ƙarami ake fafutukar naima masa maganin da zai warkar da idon har zuwa yanzu da yake da shekaru talatin da ɗaya a duniya ba'a dace ba. Hakan tasa aka haƙura aka ƙyale maganin, ya ci gaba da amfani da glasses ɗin da da taimakonsu kaɗai yake iya ganin abin da Allah ya yassare masa ya gani. “Muna tayaka murnar lashe wannan gasa Arman! Fatan nasara!” Faɗin ɗaya daga cikin malaman dake koyar da su wasan takobi cikin harshen larabci. Yayin da yake miƙa masa award ɗin da aka tanada domin zakaran da ya lashe wannan gasa da aka saka a tsakanin ɗaliban makarantar. Hannu bibbiyu yasa ya karɓi award, sannan ya yi murmushi me kyau, tare da furta. “Na gode” Ya juya ya kalli abokansa da yake koyar wasan tare da su, ya ɗaga musu award ɗin, suka saka tafi har da masu ihu, shi dai murmushi kawai yake, har ya sauƙa daga kan stage ɗin wasan. Ya nufi ɗakin sauya kaya dake cikin hall ɗin, a nan ɗakin da ya shiga ya sauya kayan fencing ɗin da suke jikinsa, ya mayar da kayan da ya zo da su. Wato black plain hoodie, wadda ya ɗorawa red bomber jacket a sama, da blue jeans sai baƙaƙen canvas ɗinsa. Sannan ya nufi backpack ɗinsa ya buɗeta ya saka award ɗin da aka ba shi, kafin ya ɗauki wayarsa dake ciki, ya buɗe da fatan ganin missed call ɗin abokinsa ADAM, amma babu alamar ma ya kira, dan haka ya ja tsaki, ya buɗe wayar ya nemo lambarsa ya sake aika masa kira, a karo na barkatai a ranar, dan tun kafin ya shiga fencing class ɗin yake ta kiran wayarsa. *House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.* ADAM ALI ABBAS. “Adam! Adam! Adamm! Wai ba za ka buɗe ƙofar nan ba!?” Wata bahaushiyar mata ke faɗi, cikin harshen hausa, yayin da take tsaye a jikin ƙofar ɗakin da take a kulle, yanayin shigar dake jikinta kaɗai zai sanar maka da ƙabila da kuma ƙasar da take. Duk da su mazauna ƙasar ta Dubai ne bai sa ta daina saka kayan al'adarta ba, a matsayinta na ainahin 'yar ƙasar Nigeria, kuma bahaushiyar arewacin ƙasar. Daga cikin ɗakin da take buga ƙofarsa kuwa, wani matashi ne tsugunne a ƙasan desk, ya lulluɓa da blanket har kansa, yanayin tsoro shi ne kwance a kan fuskarsa, ban da rawar ɗari ba abin da yake, kamar wanda ya kwana a cikin fridge. Ɗakin bai cika girma ba, amma yana ɗauke da kaya masu kyau da sauƙin kuɗi, kallo ɗaya za ka yi wa ɗakin ka san cewa na mai ɗaukan hoto ne. Dan ko wace kusurwa ta ɗakin na ɗauke da hotunan mabanbanta abubuwa, da kuma hotunan cameras da ma cameras ɗin na zahiri, tarkacen da ɗakin ya cika zai sa ka san cewa ɗakin matashi ne. Daga wajen ɗakin, matar nan ta ɗazu da take ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta girgiza kanta cike da takaicin halin ɗan nata. “Allah ya raba bawa da wahala!” Ta faɗa kawai, sannan ta juya ta dawo ɗan ƙaramin falonsu dake ƙasan gidan, wanda ke ɗauke da kyawawan furnitures masu kyau. Tana shirin wucewa kitchen ɗin dake haɗe da falon wayar Adam ɗin dake a falon ta yi ringing kamar ɗazu. Dan yawan kiran wayar da ake run ɗazu ne yasa ta gane cewa Adam ɗin bai fita ba, shi ne ta je domin duba shi, amma sai ya ƙi buɗe ƙofar ɗakin. Wata shawara ce ta faɗo mata a rai, hakan yasa ta nufi wayar tasa ta ɗauka ‘Bin Iƙbal’ shi ne abin da aka rubuta a matsayin sunan wanda yake kiran, kuma ta gane cewa abokinsa Arman ne, dan haka ta ɗaga wayar, ta sanarwa Arman ɗin halin da Adam ɗin ke ciki. Daga ɗayan ɓangaren, Arman ya sauƙe wayarsa ƙirar iPhone 'yar yayi yana dariya a nutse, ba sai Maaman Adam ta yi dogon bayanin abin da yasa ya shiga ɗakinsa ya kulle kansa ba. Dan ya san dalilin ba zai wuce ya kalli wani horror ko Zombie movie ba, ya san abokinsa da tsoro kamar farar kura. Kuma ga shi da naci, dan duk yadda ya kai ga tsoron horror film ɗin sai ya kalla daga zarar sabo ya fito, Allah yasa yanzu haka bai kwanta zazzaɓi ba. Kansa ya sake girgizawa yana ɗaukan backpack ɗinsa, ya goyata a bayansa yana kama hanyar barin Business Bay, sai da ya fita daga building ɗin sannan ya fara dialing numbern ɗaya ƙawar tasu wato IVANA!. *Repton school Dubai, Nad Al Sheba 3, Abu Dabhi, United Arab Emirates.* IVANA SAGAR. Zaune take a kan maroon bowl chair, sanye take cikin farar hoodie da baƙin distressed jeans, ƙafafunta cikin farin canvas, baƙin dogon gashin kanta kwance a gadon bayanta, yayin da hannayenta ke kaɗa guitar ɗin dake kan cinyarta. Farar balarabiya ce, kyakkyawar gaske, me manyan idanuwa da dogon hanci da madaidaicin baki me ɗauke da farar fata me haske. Murmushi ne kwance a kan fuskarta, yayin da take kallon ɗalibanta da take koyawa kiɗan guitar zaune a gabanta. Dukansu sun nutsu suna sauraron daddaɗan kiɗan guitar ɗin da take... Wayarta dake aje a gefenta ce ta kaste musu darasin, ta hanyar ringing ɗin da ta fara. Hakan yasa ta dakata da kaɗa guita ɗin, ta kalli wayarta dake ruri, alamun shigowar kira ‘Rafiƙi’ (Abokina) shi ne rubuce tare da heart emoji a gaban sunan, kuma kaf duniya mutum ɗaya ne ta yi saving numbernsa da hakan. “A'aziruni lahza! (Excuse me please)” Ta faɗi cikin harshen larabci tana duban yaran ɗabilan nata. Sannan ta juya ta ɗauki wayarta, ta ɗaga kiran Arman dake shigowa. “Shu wainak halla? (Yanzu kana ina?)” Ta tambaya ba tare da ta bari ya yi magana ba, dan ta san sun yi da shi a kan yau yana da gasa tsakaninsa da abokan koyon wasan fencing ɗinsa. “Ai dai kya bari mu gaisa ko?” Arman ya faɗa daga ɗayan ɓangaren, sai ta yi murmushi, tana cire handle ɗin guitar ɗin daga wuyanta, sai da suka gaisa, sannan ya sanar mata da dalilin kiranta. “Na kira Adam Maama ta ɗaga, ta sanar min da tun jiya ya kulle kansa a ɗaki, ya ƙi fitowa. Da alama ya kalli wani horror film ɗin ne” Ivana ta kwashe da dariya tana rufe bakinta, dan ita ma ta sa halin abokin nasu. “Yanzu kana ina?” “Na baro business bay a motata” “Mashi (Okay) ka biyo ta nan sai ka ɗaukeni” “Ɗayib (Okay)” Ya amsa, sannan ya aje wayar. * Arman ya kwashe da dariya yana kallon Adam da yay tsuru-tsuru da shi, saboda yanda yake a tsorace. Ivana ta ɗan yi guntun tsaki tana dafa kafaɗun Adam dake basu labarin film ɗin ban tsoron da ya kalla daren jiya, wanda ya hana shi sukuni har zuwa yau ɗin nan. “Shifti? Huwa am yadhak alaiyyi” (Kin ga ba? Dariya mayake min) Adam ya faɗi yanayinsa na nuna damuwar da yake ciki, dan har yanzu a firguce yake. “Armaan la ad tadhak!” (Armaan kada ka sake dariya) Ivana ta gargaɗe shi, sai ya ɗora hannunsa a kan bakinsa, yana son toshe dariyar dake cinsa, amma ya kasa. Ivana ta girgiza kanta, sanan ta tura Adam suka fara tafiya tana kwantar masa da hankali. Arman ya biyosu yana ci gaba da ƙyaƙyatawa Adam dariyar mugunta. Da haka har suka shiga Cavo Espresso Bar dake kusa da inda suke, har suka zauna Arman bai daina dariya ba, ko ya so ya danne daga sun haɗa ido da Adam zai ji dariyar da taso masa. “Ivana kalli yaskut! Wa illa rah irja'a ala bait” (Ivana ki saka shi ya yi shiru, idan ba haka ba zan koma gida). Ya faɗa yana kallon Ivana. Ivana ta ɗakawa Armaan duka a baya tana faɗin. “Da ƙyar muka saka shi ya fito daga gida, yanzu kuma idan ka ci gaba da masa dariya ko zai koma gida ba zan yi ƙoƙarin hana shi ba” “Asif (Ku yi haƙuri)” Faɗin Arman yana toshe bakinsa. Ivana ta sake dafa kafaɗar Adam da har yanzu yake a dame. “Laik Adam! Shabah mu haƙiƙi! Killu mazah! Wa ma bi kaffu!” (Ka ga Adam, fatalwa ba gaskiya ba ce, duka shiri ne, kuma ba su da ban tsoro). “Me ya sa za ki faɗi haka? Bayan ni na ganta da idona, wata doguwa, me dogayen farata, idonta ja... Wayyo Maama” Ya ƙarashe yana rufe fuskarsa, saboda fuskar fatalwar da ya hango. Ivana ta sake dafa shi. “Ihda! Halla rah jiblak shai. Biddak shai mu?” (Ka nutsu, yanzu zan kawo maka shayi, kana son shayi ko?) Ya jinjina mata kai yana kallon Arman dake ta ƙoƙarin danne dariyar da ke ciyo shi. Ivana ta gyaɗa kai, sannan ta miƙe ta zagaya ta nufi wurin da zata yi order. Cup uku na shayin ta karɓa, sai dai a yayin da take shirin juyawa ta yi karo da wani mutum da shi ma yake ƙoƙarin zuwa wurin. Farko kofunan shayin dake jere a kan tray ta fara kalla, da ta ga ba su zube ba sai ta kalli mutumin da ta yi karo da shi. Wani kyakkyawan matashin balarabe ne, wanda ke sanye da baƙar suit, kalar farar fatar jikinsa me ɗaukar hankali ce, haka ma kammaninsa, dogo ne, kuma me matsakaicin jiki, yana da faffaɗan ƙirji, sannan sumar kansa na cikin asken high pade. Yana da buɗaɗɗen ido, wanda yake ɗauke da shuɗiyar ƙwaya, sannan hancinsa dogo ne sosai, ga bakinsa dai-dai wa dai-dai, yana da saje da kuma gemu, wanda suka ƙara masa kyau. “Ana ba'atazir! Ma intabahat!” (Ki yi haƙuri ban lura da ke ba ne). Ta ji muryasa me daɗi ta furta, sai kawai ta jinjina kanta, alamun ba komai, sannan ta raɓa shi ta wuce, har ta koma table ɗin da su Armaan suke bai daina kallonta ba. “Rifaƙ (Guys) ko kun san cewa yau Chris Brown zai yi live performance a Coca-cola Arena?” Faɗin Arman yana nuna musu takardar sanarwa a cikin wayarsa. Adam da Ivana suka dubi juna. “Wai yau?” Adam ya tambaya yana aje cup ɗin dake hannunsa. “Eh yau, duba ka gani” Ya miƙa masa wayar , Adam da Ivana suka haɗa kai suna karantawa. “Za mu je ne?” Cewar Ivana. “Akid! (Of course)” Arman ya bata amsa. Domin duk inda za su je ko za su fita shi ne ke biyan duk kuɗin da za'a kashe, ko cinema za su je shi zai sai musu ticket. Saboda kaf cikin su ukun babu wanda ya kai mahaifinsa kuɗi. Dan mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, wanda yake da kamfanunuwa masa masu zaman kansu. Shi Adam photographer ne, yana aiki tare da wani kanfanin magazine, ita kuma Ivana musician ce, tana koyar da kiɗan guitar a Repton school Dubai. Sannan tana aikin kiɗa a waƙoƙi idan har an buƙata, duk cikinsu shi Arman ɗin ne ba shi da aikin yi, ba wai dan ba'a naima masa a gidansu ba. Sai dan shi a rayuwarsa ya tsani duk wata harka da ta shafi kasuwanci. Duk da ya taso a gidan da ake kasuwanci, kuma hakan ya samu asali ne daga nakasar gani da yake fama da ita tun lokacin yarinta. Tun a tasowarsa kawunsa, yayan mahaifinsa ya saka masa ƙin harkar kasuwanci, dan a ko da yaushe abin da yake faɗa masashi ne. “Harkar jagorancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ba na makafi ba ne” Ya sha faɗa masa hakan tun ba shi da wayo har ya taso ya yi wayo, tun ba ya gane abin da kalaman ke nufi har ya zo ya gane abin da kalaman ke nufi. Sannan tsangwamar da ake yi wa mahaifiyarsa a halinsu ya ƙara cusa masa ƙiyayyar kasancewa ɗaya daga cikin ahalin Alhadi a ransa. Kuma suna nunawa mahaifiyarsu wariyar launin fata saboda ita 'yar Pakistan ce, su kuma ahalin mahaifinsa larabawan Qatar ne. Shi da ƙanwarsa Gulzar kaɗai iyayensu suka haifa, kuma bayan shi babu wani wanda zai iya gadon kasuwancin mahaifinsa sai Faisal!. Ɗan yayan mahaifinsa da shi ma ya bada tasa gudummawar wurin cusa ƙiyayyar son karɓar jagorancin Majmu'at Shirkat Alhadi (Alhadi Group of Companies). Zama shugaban Alhadi Group of Companies shi ne babban burin Iƙbal, wato mahaifin Arman. Kuma saboda yana yawan takura masa a kan batun kasuwancin yasa suka fara raba gari. Dan a yanzu Arman ba ya jin yana da maƙiyi sama da kujerar jagorancin gammayar kamfanunuwan Alhadi. Alaƙarsu da su Adam ta samo asali ne tun daga makaranta, abin da ya sa tafiyarsa da su ta yi nisa shi ne su ba su tsangwamarsa dan yana da ƙarancin lafiyar ido. Kuma sam ba sa ɗaukan cewa bai kai ba, dan yana saka glasses ɗin da za su taimaka masa wajen gani, saɓanin yanda ya taso ana nuna masa cewar tun da ba ya gani shi makaho ne. “Na ga kamar sauran awa ɗaya a fara wansa fa!” Adam da ya ci gaba da karanta takardar sanarwar ya faɗa, sai duk su ukun suka dabi juna, kamar wanda suka haɗa baki, haka kowa ya finciki jakarsa suka ruga da gudu zuwa waje, Ivana na faɗin. “Gara mu yi sauri kafin tikitin ya ƙare!” Ai a ɗari suka shige motar Armaan ƙirar Ferrari venon, Adam ya figi motar zuwa Coca-cola Arena, kamar yanda suka yi zato ticket ɗin ya kusa ƙarewa. Dan duk da haka sai da suka bi layin siyan tikitin. Yayin da suke bin layin siyan tikitin, Adam ya shiga bawa Adam labarin film ɗib da ya kala jiya. Shi kuma Arman sai kwasar dariya yake, kamar daga sama ya ji an kira shi da sunan da ya fi masa na mutuwa ɗaci a kunne. “Marhaba makaho! (Hello makaho)” Idonsa ya rintse, dan ko ba'a faɗa ba ya san wa ya mallaki muryar, dan haka ya buɗe idonsa yana gyara glasses ɗinsa, wanna ita ce ɗabi'ar da ya fi yawan yi, ba ya haura minti goma ba tare da ya gyara zamansa glasses ɗinsa ba, ko da ko bai zame ba. Ya juyo yana kallon Faisal tare da wata budurwa tsaye, dariyar da ya ga Faisal ɗin na yi ita ta fi baƙanta masa rai. “Ashe kuma makafi ana ganinku a wurare irin wannan?... Na ɗauka makafi ba sa zuwa kallon live performance!” Ya ƙarashe yana sheƙewa da dariya, budurwa dake tare da shi tana taya shi. “Ka ga malam! Babu wada ya buƙaci jin ra'ayinka a nan, dan haka bama son tada zaune tsaye.” Ivana ta dakatar da shi, dan ko kaɗan Arman ba ya iya tanka masa ko ƙanwarsa Sakina idan suna aibanta shi, idan suka taɓa Gulzar ko mahaifiyarsu ne dai ba ya shiru. “Yi haƙuri malama, ba da ke muke ba, da wannan makahon muke...” Ya yi fasali yana yin taku uku zuwa gaban Arman, sannan ya yi kamar zai rungume shi, ya kai bakinsa saitin kunnensa yana murmushi, sannan ya furta. “Jin daɗi da sharholiya irin wannan ba ta kamaceka ba, ka fi dacewa da yin bara a gefen hanya!” Ya ja baya yana dariya, Ivana ta riƙi kwalar rigarsa a fusace za ta mayar masa da martani, Armaan ya jata baya yana girgiza mata kai. Haka Faisal da budurwasa suka wuce suka barsu a wurin suna dariya. “Da ka bari na mayar masa da martanin da zai hana shi ba ci daren yau. Amma ka hana” Arman ya girgiza mata kai. “Maganganu irin wannan na saba jinsu tun tasowata, ba shi ne mutum na farko da ya fara faɗin hakan ba, dan haka ki share kawai” Ya ƙarshe yana ɗauke kai, cike da damuwa Ivana ta kalli Adam da bai ce komai ba, dan ba zai ce ɗin ba, tsoro ba zai bari yace komai ba, ko shi ya je ya takalo faɗa Ivana da Arman ne ke tare masa, amma ba ya iya taɓuka komai. *House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai.* Motar Armaan ta faka a gaban ƙaramin gidan da bai cika girma ba, amma duk da haka ko daga waje ma yana da kyau. Ivana dake gidan baya na motar ta buɗe ta fita, sannan ta goya jakar guitar ɗinta a baya, ta rufe motar tana kalon Adam da Arman dake gidan gaba. “Me kuka shirya mana zuwa gobe?” Arman da Adam suka dubi juna, sannan Adam ya sake subanta yana girgiza kai. “Babu wani abu, sai dai idan mun haɗu zuwa goben” Ta ɗaga hannunta suka yi fits bump, sannan ta ɗaga musu hannu ta nufi gidansu. Ƙofar shiga gidan ta buɗe, ta shiga, sannan ta rufe ƙofar tana cire takalman dake ƙafarta, ta saka wasu dake aje a bakin ƙofar, sannan ta nufi falon gidan dake a farkon gidan. “Assalamu alaiki ya Yumma!” Ta yi wa mahaifiyarta dake zaune a falo tanq cin fruit sallama, fuskarta ɗauke da murmushi, ita ma tsohuwar matar na ganinta ta fara murmushi, Ivana ta risina ta sumbaci kan mahaifiyarta, sannan ta zauna kusa da ita tana cire jakar guitar ɗin dake bayanta, tare da ajeta a gefe, ta gyara gashin kanta tana faɗin. “Shu yalli ɗabaktil yaum ya Yumma” (Yumma yau me kika dafa?) Mahaifiyar Ivana me suna Khadija, wadda Ivana da yayarta Hala ke kiranta da Yumma tace. “Shish taouk” “Ba na jin yunwa sosai, dan mun tsaya a Al Fayrooz lounge mun ci abinci tare da su Arman, dan haka ki zuba min kaɗan” “To” Cewar Yumma, sannan ta miƙe ta nufi kitchen ɗinsu dake haɗe da falon, dan wata gajerar katanga ce kawai ta raba kitchen ɗin da falon, komai dake cikin falon ba shi da tsada, kuma kayane irin na da, dan a cikin gidan aka haifi Ivana da yayarta Hala, wadda a halin yazu ta yi aure, har da yaronta guda ɗaya. Mahaifinsu ya rasu tun da ƙarancin shekarunsu, hakan ya sa suka taso ba su san shi ba sai Yumma, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, kuma ba su ɗauki rayuwa da zafi ba. Ivana ta miƙa hannu ta ɗauki apple ɗin dake cikin wani bowl a kan center table, tana shirin fara cin apple ɗin idonta ya kai kan wata magazine dake aje a kan center table ɗin. Sai ta aje apple ɗin ta ɗauki magazine ɗin da hannunta na dama, yayin da take saƙala gashinta a bayan kunnenta da hanunta na hagu. Ba komai ya ja hankalinta zuwa kan magazine ɗin ba face hoton dake jikin bangon magazine ɗin. Gani take kamar ta san mutumin cikin hoton, shiru ta ɗan yi tana son tuno inda ta taɓa ganin mutumin. Fuskarsa a yammacin yau ta da ta ganshi ta haska a cikin kanta. Ƙwarai kuwa, shi ne mutumin da ta haɗu da shi a Cavo Espresso Bar, sai ta shiga karanta bangon magazine ɗin. 'Business week' shi ne babban maudu'in abin da magazine ɗin ta ƙunsa. Sai ta zarce zuwa kan sunansa dake gefe guda, Sayyid UWAIS FAZIL... Ta sake kallon fuskarsa tana furta sunan a kan leɓenta. “UWAIS!” Ta furta sunan ba tare da ta ji komai a ranta ba, saboda ɗan adam ba shi da ikon hango abin da ke tunkararsa a gaba, ba shi da masaniyar abubuwan da za su faru da shi, sai na wanda suka riga suka faru da shi. “Ki ci Shish taouk ɗinki” Yumma ta faɗa tana aje mata Shish taouk da ta zuba a cikin plate, Ivana ta aje magazine ɗin tana murmushi, sannan ta kalli Yumma tana ɗaukan plate ɗin, ta soma cin abincin tana bata labarin yadda live performance ɗin da suka je suka kalla yau ya kasance. Bayan ta gama cin abinci ta nufi upstairs, dan gaba ɗaya ta gaji bacci take ji, ƙofar ƙaramin ɗakinta ta buɗe, ta shiga ciki tana kallonsa kamar baƙonta. Ɗakin sam ba shi da girma, amma ya ɗauki duka kayanta da take ajewa a ɗakin, akwai gadonta ɗan siriri na kwanciyar mutum ɗaya. Wanda ke ɗauke da baby pink duvet, sannan akwai pillows manya da ƙanana, sannan akwai wardrobe da ba ta cika faɗi ba, akwai kuma desk ɗinta, sannan dressing mirror. Mafiya yawan abubuwan dake ɗakin pink cokor ne, hatta da stikern dake jikin bango pink ne. Miƙa ta yi tana rataya jakar guitar ɗinta a sama, inda ta saba ajeta, sannan ta nufi bathroom, ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin, wardrobe ɗinta ta buɗe, ta ɗauki mayafi a ciki, ta yafa a kanta, sannan ta tada sallah a kan center carpet. Sai da ta gabatar da sallahr isha, sannan ta yi wanka ta sauya kaya zuwa night wear. Tana hamma ta bi lafiyar gado ta kwanta, tana rayawa ranta cewa me ake da rayuwar da babu gadon bacci, ita a duniyarta babu abin da ya fi birgeta sama da lallausan gado, dan ko a kan sofa ba ta iya bacci. _________________ _Ehem! Ehem! Ehem!_ _Salmanians! Ga wata sabuwar tafiya! Me ɗauke da abubuwan ban al'ajabi._ _Tafiyar ba me sauƙi ba ce kamar yanda za ku ɗauka!. Dan haka sai ku shirya da kyau._ _JUYIN KWAƊO zai zo a Book 1 and 2. Book 1 shi ne free, book 2 ne zai kasance paid a kan ₦400_ _Kuma za ku iya samunsa a ArewaBooks, domin akwai complete book 1 a can_ _Sai ku shirya, ku gyara zama, domin jin yanda rayuwa za ta yi juyi da waɗannan abokai uku, kuma juyin ma irin na kwaɗo, daga ruwa zuwa ruwan zafi._ #Bahaɗejia #Candy #SalmaAhmadIsah #JuyinKwaɗo °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-2 *House No. 106, Street 14, Jumeirah Bay Island, Abu Dabhi, Dubai.* Gidan na ɗaya daga cikin manya manyan gidajen dake hamshaƙiyar unguwar ta Jumeirah. Dan ko a yanayin gininsa za ka san an kashe kuɗi, ballantana ace ka samu damar kutsa kai ciki. Motar Armaan da ta ɗauko hanya tun daga unguwarsu Adam da ya aje a gida ta faka a gaban gidan. Ya kashe motar, sanna ya cire seat belt ya fito yana jan jakarsa dake a wurin me zaman banza, ya goya jakar a bayansa, sannan ya juya ya fuskanci hamshaƙin gidan. Glasses ɗinsa ya gyarawa zama ta hanyar saka ɗan yatsansa manuniya ya tura bridge ɗin glasses ɗin, sannan ya nufi kyakkyawar ƙaramar ƙofar shiga gidan. Dan gidan ba shi da wani compound, wanna ƙofar ita ce da ka buɗeta za ta sadaka da gidan, hatta da garejin aje motocinsu na daga gefen ƙofar shiga gidan. Hannunsa ya kai kan inda madannan sirrin buɗe ƙofar gidan suke manne a jikin ƙofar, daga gefe kuma door bell ne, wanda aka yi shi domin baƙi, dan idan har ɗan gidan ne babu buƙatar ya danna door bell, tun da duk sun san kalaman sirrin da suke buɗe ƙofar. Lambobin ya saka, nan take ƙofar ta buɗe, ya shiga yana kallon masu aikin gidan dake kaikawo, sanye cikin uniform iri ɗaya. “Haidar!” Ya yafito ɗaya daga cikin masu aikin, Haidar ɗin ya nufo shi yana amsa masa cike da ladabi, Arman ya miƙa masa mukullin motarsa, sannan yace. “Motata tana waje, ka saka min ita a gareji, idan ka saka key ɗin kuma ka aje shi a nan” Ya nuna masa wani abu me kama da basket dake aje kan wani cupboard dake farkon gidan, wanda ya ƙunshi tarin makullan motocin da mutanen gidan ke hawaya. Kuma daga jikin cupboard ɗin ma za ka iya hangen manya manyan motocin dake garejin, dan akwai ɗan glass dake wurin da zai baka damar hakan. Haidar ya karɓi key ɗin, sannan ya nufi ƙofar fita, yayin da shi kuma ya kutsa kai cikin kyakkyawan gidan, bayan wani ɗan gajeren corridorn dake bakin ƙofar shigowa, za ka iske hanyoyi uku, ɗaya ita ce wadda zata sadaka da upstairs, kuma duka ɗakunan kwanan gidan suna sama. Ɗaya kuma ita ce wadda za ta sadaka da living room, wanda yake ƙunshe da sitting areas guda biyu, tare da dinning area, sannan akwai kitchen ta kusa da dinning area. Kuma ta cikin falon za ka fita harabar garden ɗin gidan, dake ƙunshe da swimming pool. A kusa da swimming pool ɗin kuma akwai kujerun zama, wanda aka saka su a ƙasa, kamar dai zurfin swimming pool ɗin, kuma tsakanin wurin da suke da swimming pool ɗin glass ne kawai ya raba, ta yanda kana iya ganin ruwan cikinsa idan kana zaune a wurin. Da farko hanyar da za ta sada shi da upstairs ya nufa, amma sai ya juyo ya fasa bi ta nan, dan ta cikin living room ɗin ma akwai wani stairs ɗin da zai kaika sama. Ya bi ɗayar hanyar da za ta kai shi living room, komai dake cikin living room ɗin gray color ne, daga can dinning area ya hangi mahaifinsa Iƙbal Alhadi, tare da mahaifiyarsa Zahra Ali, zaune suna dinner. Wurin ya nufa yana kallon Imminsu, wadda ita ma ta ankara da shi, yana isa inda take ya sunkuya ya sumbaci kanta, sannan ya kama hannayenta ya sumbata. “Masa'ul khair ya Immi (Barka da yammaci Immi)” Zahra ta yi murmushi tana kallon ɗanta, ta shafa kansa tana amsawa. “Shu wa aina Gulzar?” (Ina Gulzar ne?) Ya tambaya ganin bai ganta tana dinner tare da su ba, Immi ta amsa masa da. “Ab us ne khaana khtm krte dekha aur kamre mein waaps chla gaya” (Yanzu ta gama cin abincinta ta koma ɗaki) “Ɗayib ana rayih (Okay ni ma na tafi)” ya bata amsa cikin harshen larabci, saɓanin ita da ta masa magana da harshen Urdu, ba wai dan bai iya mayar da amsa cikin yaren ba, sai dan ya san ita ma Immin tana jin larabcin. A wasu lokutan ma idan za su yi magana tsakanin su uku sai su dinga haɗa larabci da Urdu, saboda Urdu shi ne harshen Zahra. Ba tare da ya yi wa Abby magana ba ya shiga ƙoƙarin barin wurin, sai dai tun da ya tsaya a wurin shi Abbyn ke binsa da kallo, ya lura da yanzu sam Arman ba ya son masa magana, saboda daga ya masa magana zai tado masa da zancen zama shugaban kamfanin Alhadi. Kuma ya lura da ɗansa ba ya son maganar kamfanin ko abin da ya shafe shi, idan zai iya tunawa ma rabon Arman da kamfaninsu tun shekaru biyar da suka wuce, lokacin da suka yi murnar cikar kamfanin shekaru 30 da kafuwa. A yanzu babban burinsa bai wuce Arman ya zama shugaban Alhadi Group of Companies ba. Domin ba ya so ya mutu ya bar gadon kujerar shugabancin kafanin a hannun ɗan ɗan uwansa Faisal. A cikin halayen arziƙi Faisal ba shi da guda uku ƙwarara, kuma sam bai yi kama da wanda zai zama shugaba na gari ga ma'aikatan kamfanin ba, sannan a ƙa'ida, idan har Arman ya ƙi amincewa da karɓar shugabancin kamfanin to Faisal shi ne wanda zai karɓi kujerar. Ƙoƙarin karkato da hankalin Arman shi ne abin da yake ta son yi tun kafin lokaci ya ƙure musu, amma shi Arman ya kasa ganewa. A ko da yaushe yana ɗaukan kansa a ba jowa ba, ya bar zuciyarsa ta mutu, saboda an ce masa dan yana da matsalar gani ba zai iya zama jagoran kamfanin Alhadi ba. Kuma saboda yanda ake aibata lalurar tasa yasa ya tsani duk wata harka ta kamfanin. “Armaan ina zaka je ba ka gaishe da Abby ba?” Immi ta dakatar da shi, hakan ya sa ya juyo, ya kalli Abby da shi ma ke kallonsa. “Masa'ul khair Abby” Ya faɗa daga nan inda yake, dan a yanzu ko kusantar Abby ba ya so, daga ya kusance shi zai ji kamar yana kusantar kamfanin Alhadi ne. Abby ya sauƙe numfashi yana kallon ɗansa, sannan a hankali ya jinjina kansa yana amsawa, Arman na jin ya amsa ya juya ya nufi sama. Dan sam ba ya ma son zamansa da Abby ya yi tsayi, dan daga sun ɗan jima a wuri zai fara masa maganar da ta mutuwarsa ta fita daɗin sauraro a kunnensa. Yana shiga corridorn ɗakunansu ya hangi Gulzar na nufowa downstairs da alama wani abin za ta yi a ƙasa. Farar matashiyar da za ka iya kira da balarabiya sanye take da baƙin wide black jeans, da farar blouse top, ƙafafunta cikin fluffy sliders farare, dogon gashin kanta kuwa sai reto yake a bayanta. Ita sam ba ta kama da indiyawa, saɓanin Armaan da kammaninsa suka sirka da na Immi, ita Gulzar sak Abby ce, wayarta ce riƙe a hannunta tana latsawa, da alama ma ba ta lura da shi ba. Arman ya yi murmushi yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya fara taku a hankali yana nufarta, sai da ya je dab da ita sannan yace. “Me dogon gashi!” Ya faɗa da ƙarfin da ya razana Gulzar, har wayarta na suɓucewa a hannunta, ta kalli wayarta da ta faɗi ƙasa sannan ta dube shi tana haɗe girar sama da ta ƙasa, ta kai masa duka a ciki tana faɗin. “Duk ka bi ka tsorata ni!” Arman ya dafe wurin da ta daka a cikinsa yana dariya, sannan ya sunkuya ya ɗauko mata wayarta, ya miƙa mata, ta warce wayar tana harararsa. “Idan ka sake min irin wannan sai na faɗawa Immi ta min maganinka” Ta faɗa tana nuna masa ɗan yatsa, Armaan na dariya ya dafata tare da juyata suka nufi ɗakinsa. “Ina am imzah! Bas, mu aksar (Wasa fa kawai nake miki ba komai ba)” Gul ta mintsini cikinsa tana faɗin. “Kada ka sake min irin wannan wasan” Armaan ya saketa yana dafe inda ta mintsi ne shi. “Yarinyar nan kin iya mugunta” Gul ta matsa daga jikinsa, dan ta san halinsa, yanzu zai ce zai riƙe mata gashinta da ta fi so, dan ko sau ɗaya ba ta jin ta taɓa rage tsayinsa. “La wain rayiha? (Ina kuma za ki je?)” Ya tambaya yana kallonta, ta ruga da gudu, shi ma ya bi bayanta zuwa ɗakinsa. Gul na shiga ɗakinsa ta faɗa kan gadonsa tana dariya. Shi kuma yana shigowa ɗakin ya yi tsaye yana kallonta a kan gadonsa. Kansa kawai ya girgiza, ya nufi wurin da ya saba aje awards ɗin da yake samu a wasan fencing da yake yi. Ɗakin nasa na da girma, komai na ɗakin brown da fari ne, gadonsa na daga bangon yamma na ɗakin, yayin da balconyn dake cikin ɗakin yake ta bangon gabas, ta yanda daga hasken rana ya fito zai sauƙa kan gadon, dan slide glass door ce a wurin. Akwai dressing mirror da 'yan wasu tarkacensa a ɗakin, yayin da closet ɗinsa ke cikin banɗaki. Babu tarkace da yawa a ɗakin, amma komai ka ga a ɗakin sunan kuɗinsa yake furtawa, dan kallo ɗaya za ka masa ka fara ƙissima tsadarsa. Daga kusa da chest drawern da ya saba jera awards ɗinsa kuwa, hotunansa, da wanda suka ɗauka shi da su Gulzar da Immi, da nasa shi da su Ivana ne manne a ko ina. “Ni fa kallon mara aikin yi nake maka aki! Ni ban ga dalilin da zai sa ina koyon wasan takobi ba. Bayan ni ba a 18th century nake rayuwa ba. Yanzu kai ya waye, babu wanda yake faɗa da takobi, da ma koyon harbi kake da sai na ce dama-dama!” Ya juya ya kalli Gulzar dake zaune a tsakiyar gadonsa tana danna wayarta. Lokaci guda kuma wannan yaƙin da ya saba yin mafarkinsa ya kutso cikin tunaninsa. Shi kansa ba ya ce ga dalilin da yabsa yake son koyon wasan takobi ba, amma haka kawai iya sarrafa takobi ke burge shi. “Ba ni na zaɓi fencing ba Gul! Fencing ne ya zaɓeni” Ya bata amsar yana cilla mata backpack ɗinsa, ta cafe jakar tana kallonsa sanda ya shiga bathroom. Wayarta ta aje a gefe, sanna ta buɗe jakar, ta soma fitar da wasiƙun dake ciki, wanda yawancinsu 'yan matan dake sonsa ne ke turowa. “Aki waɗannan fa? Ko tsofi ne?” Ta tambaya da ɗan ƙarfi, dan ta ji ya kunna ruwa, alamun wanka zai yi. “Satin da ya wuce aka aiko da su!” Shi ma ya bata amsa daga cikin bayin, Gulzar ta buɗe ɗaya daga ciki, sannan ta fara karantawa a bayya ne. “Zuwa ga kyakkyawan tauraron wasan fencing da babu kamarsa a MK fencing acadamy. Haƙiƙa ka iya sarrafa takobi cikin ƙwarewa, kana bawa takobi umarni cikin iko da burgewa, ka haɗu sosai Arman!...” Gulzar ta zaro ido tana rufe bakinta. “Aki ai wanna 'yar makarantarku ce” Tana jiyowa dariyarsa a cikin bayin, kafin taji ya bata amsa da. “Ba ɗaliba ba ce, malama ce!” Ita ma Gulzar ɗin kwashewa ta yi da dariya, sannan ta aje wadda ke hannunta ta ɗauko wata ta shiga karantawa, har Armaan ya fito daga bathroom ɗin sanye cikin blue polo shirt da baƙin cargo trouser. Ya tsaya a jikin dressing mirror yana busar da sumarsa da ya jiƙa yayin wankan da ya yi. “Ke dan Allah ki aje wannan wasiƙun da ba ƙarewa suke ba” Gulzar ta kalle shi ta cikin madubin da yake tsaye a gabansa, sannan ta aje wasiƙun agefe, ta saka hannunta a cikin jakar, ta fito da tikitin Coca-cola Arena da suka siya ɗazu. Ta karanta tikitin, sannan ta kalli Arman tana faɗin. “Wai yau Chris Brown ya yi live performance kuma ka je amma ba ka faɗa min ba?” Ta tambaya tana sauƙa daga kan gadonsa, Arman ya aje dryer dake hannunsa, sannan ya juyo ya kalleta. “To ai abin ne ya zo a ƙurace!” Gulzar ta iyo kansa da gudu tana faɗin. “Ai ka iya ɗaukan abokanka zuwa wurin! Ni kuma ka barni a nan” Shi ma gudun ya saka ya fice daga ɗakin, tana biye da shi har zuwa saman gidan, dake ɗauke da sitting areas, daku ma runfunan shaƙatawa. Masu aikin gidan kuma ma aikin tsaftace wurin, Arman ya zauna a kan kujera yana kallonta. “Ki yi hakuri mana me gashi” Gulzar da take a fusace, ta sa hannu ta mayar da gashinta da ya suƙo mata kan fuska zuwa baya tana huci, sannan ta zauna kusa da shi tana ture shi. “Ni dai ka cuceni” Ta faɗa tana sake ture shi, hakan ya sa glasses ɗin dake idonsa ya faɗi ƙasa, duhu ya mamaye sashin ganinsa, dan daga zarar ya rabu da glasses ɗin babu abin da yake gani face duhu. Cak ya tsaya yana motsa idonsa da babu abin da yake gani da shi, hannunsa ya miƙa kan inda yake zaune, yana laluben glasses ɗin nasa, dan ko tafin hannunsa ba ya iya gani, ita ma Gulzar ɗin sai a lokacin ta lura da shi. “Ya Ilahi ana asfe aki” (Wayyo Allahana ka yi haƙuri Yayana) Ta faɗa tana ɗaukan glasses ɗin nasa da ya faɗi ƙasa, ta goge shi a jikin rigarta, sannan ta saka masa shi. Glasses ɗin na hawa kan fuskarsa ya fara gani, sai ya raintse idonsa, sannan ya buɗe. “Mein bahut off-sori hoon bhradaar, mein iss ka matlab nahin tha...” (Ka yi haƙuri Yayana, ba da niyya na maka hakan ba) Ta faɗi cikin harshen Urdu tana dafa kafaɗunsa, sai ya riƙe hannunta yana girgiza mata kai. “Ma fi shi, insi halla (Ba komai fa, ki manta kawai)” Gulzar ta jinjina kanta, sannan ta miƙa hannu ta ɗauki Hummus daga cikin kayan maƙulashen dake kan teburin kusa da su, ta miƙa masa. “Za ka ci?” Ya ɗan yi murmushi yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya karɓa daga hannunta, ita ma ta ɗauki wani bowl ɗin suka fara ci tare. “Yau mun haɗu da Faisal a Coca-cola Arena” Arman ya faɗa yana kallonta, ita ma sai ta kalle shi tana gyara zama. “Ya faɗa maka wani abin ko?... Kuma me ka masa?” Ta jero masa tambayoyin, sai ya yi dariya yana shafa sumarsa dake cikin askin curly top, dan har sauƙowa take kan goshinsa. “Ban masa komai ba, kuma ban ce masa komai ba, Ivana ma da ta yi ƙoƙarin ce masa wani abin hanata na yi” Gulzar ta harare shi. “Shi ya sa gaba ɗaya ya bi ya rainaka, ba finka ya yi a haife ba amma kullum gainka yake kamar ƙaninsa. Ni ba za ka burgeni ba sai ka yarda ka karɓi shugabancin Alhadi. Ba ma ni kaɗai ba daga lokacin za ka bawa kowa na ahalin nan mamaki” Arman ya ɗaga kansa sama yana kallon taurarin dake ko ina a sararin samaniya. “Shugabancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ya fi ƙarfin makaho kamar Arman, bara a gefen hanya ita ce tafi dacewa da shi!” Gul ta ja tsaki tana aje bowl ɗin hannunta. “Wannan ra'yin wasu mutane ne da ban, kuma idan har ka ci gaba da faɗin haka kana nufin shugabancin ya fi dacewa da shashashan mutum kamar Faisal?” Armaan ya kalleta yana ɗage kafaɗunsa. “Ban sani ba!” Gulzar ta ɗauke ka tana juya idonta, kuma idon nata bai sauƙa a ko ina ba sai a kan saman gidan su Faisal dake ɗan gaba da nasu. Daga nan inda suke tana iya hango Faisal da ƙanwarsa Sakina zaune a saman nasu gidan, masu aikin gidan zaune a wurinsu suna musu hidima. “Kalli can” Arman ya kalli inda take kallo. “Yanda Sakina take ji da kanta kai kace ita matar sarkin Dubai ce. Ko a makaranta ba ta da ƙawaye sai 'ya'yan masu kuɗi. Kullum jin kanta take kamar wata sarauniya, tana kashe kuɗi ta yi yanda ranta yake so. Shi kuma Faisal, lalataccen ɗan da babu uban da zai yi alfahari da shi, a ƙalla 'yan matansa sun kai sha bakwai, babu hotel ɗin da bai taɓa zuwa ba a Dubhai, har ɗaki yake da shi a Burj Khalifa, yanda yake wadaƙa da kuɗi za ka ɗauka cewa babansa ne a kan kujerar shugabancin Majmu'at Shirkat Alhadi, daga an taɓasu za su ce su ne Faisak (FAISAL AND SAKINA)! Humm! Abin haushi” Ta ƙarashe tana mayar da gashinta dake kan kafaɗunta zuwa bayanta, Arman ya yi dariya. “Komai lokaci ne Gul, ki ƙara haƙuri” Ta masa wani irin kallo, sannan ta ɗauke kai. “Lokacin ba zai ƙare ba har sai ka karɓi shugabancin Alhadi.” “Wannan lokacin ba zai taɓa zuwa ba” Arman ya bata amsa zuciyarsa ɗaya. Da Gulzar ta ga takaicin ɗan uwan nata na neman kasheta sai ta miƙe ta bar shi a wurin. “Gobe laraba, ka shirya zan rakaka wurin Doctor Ƙuraishi” Ta faɗa tana barin wurin, Armaan ya yi dariya, Dr Kuraishi shi ne likitan idon da yake duba shi tun yana ƙarami. *House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.* ADAM POV. A razane ya kalli tvn da Maama ta ƙure Volume ɗinta, razannaniyyar ƙarar da ta fito daga cikin tvn ce take naiman sawa ya saki fitsari yana zane. “Maama dan Allah ki rage Volume ɗin nan” Ya faɗa yana marairaicewa, kuma cikin harshen hausa, dan a gida sam ba ya larabci ko wani yaren da ba hausa ba, sai idan ya shiga cikin abokansa ne yake magana da wani harshen, tun da su larabawa ne, saɓanin shi da ya kasance ɗan bahaushe. Maama ta yi tsaki, sannan ta kashe kayan kallon gaba ɗaya, ta dawo ta zauna kusa da shi kan sofa, inda yake zaune a tsorace yana cin abinci, Maama ta dungure kansa tana faɗin. “Kai dai ka ji jiki. Na rasa a ina ka kwaso wannan shegen tsoron, kai ba mace ba, amma tsoro kamar farar kura, na rasa yaushe za ka daina wannan tsoron, ni dai ina jiye maka ranar da tsoron nan naka zai kasheka kana tsaye.” Ya ƙifƙifta idonsa yana haɗiyar abincin dake bakinsa. “Ya kamata gobe ka je wurin aiki, tun da yau ba ka je ba” Ya jinjina kansa, dan har yanzu a dame yake. “Akwai sauran wani aiki da shugabanmu ya bani. Ina so na ƙarasa kafin gobe” Maama ta ɗauki wayarta, sannan ta miƙe tana faɗin. “Ya kamata dai, kuma saura ka sake kallon wani film ɗin ban tsoron, wallahi ko ta kanka ba zan bi ba” Sai ya ɗan yi murmushi yana kallonta, har ta bar shi nan zane a falon, a ƙalla yanzu kimanin shekaru biyar ke nan da rasuwar mahaifinsa. Kuma tun bayan lokacin ya rage daga shi sai Maama ne kaɗai suke rayuwa a gidansu. Mahaifinsa yana aiki a wata asibiti dake nan Dubai, kuma aikin shi ne abin da ya rabo shi da mahaifarsa wato Zamfara Nigeria. Dan shi kansa Adam ɗin ma a nan Dubai aka haife shi, kuma har bayan rasuwar Mahaifinsa ba su koma Nigeria ba, saboda shi ma yana aiki a nan. Salma Ahmad Isah ✍️ _Har yanzu somin taɓi ne, domin muna duba da rayuwar jaruman namu ne, kafin mu tsunduma cikin labarin... Ku fai kada ku gajiya, ku biyoni domin jin yanda za ta kaya..._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-3 *Moorfields Eye Hospital, 20 street Al Razi Building 64, Block E, floor 3, Dubai.* ARMAN POV. “Buɗe idon a hankali” Dr Ƙuraishi ya bawa Arman umarnin yayin da ya gama duba masa idonsa. Arman ya buɗe idonsa a cikin hasken da Dr Ƙuraishi yake haska idonsa. Amma babu abin da yake gani face duhun da ya saba gani, saboda shi bai san banbancin da yake tsakanin idonsa na a rufe ko a buɗe ba, tun da duka biyun abu ɗaya yake gani. “Kana iya ganin wannan hasken?” Dr Ƙuraishi ya tambaya. “Ba na ganin komai Dr babu komai sai duhu” Dr Ƙuraishi ya kashe fitilar da ya haska idon nasa, sannan ya ɗauki glasses ɗinsa dake aje a gefe, ya mayar masa shi idonsa yana faɗin. “Za ka iya sauƙowa” Arman ya gyara zaman glashin, sannan ya sauƙe ƙafafunsa ƙasa, ya ɗauki canvas ɗinsa dake aje a ƙasa, ya saka a ƙafarsa, sannan ya dawo cikin main office ɗin Dr Ƙuraishi, inda Gulazar ke zaune tana jiransu. “Babu wani ci gaba!” Dr Ƙuraishi ya faɗa yana miƙawa Gulzar takardun lafiyar idon Arman ɗin. Gulzar ta karɓa, sannan ta kalli ɗan uwanta da shi ma yake kallonta. “Za mu iya tafiya?” Ya tambaya yana murmushi, shi sam bai ga wani abin shiga damuwa ba, dan ya san sam babu ci gaba a lafiyar idon nasa, ba dan Gulzar ɗin ta takura masa ba ma da ba zai zo ba, dan tun daren jiya ta yi booking appointment. Gulzar da gaba ɗaya take a dame ta miƙe, sannan ta ɗauki bag ɗinta ta rataya a kafaɗarta, ta bi bayansa suka bar office ɗin. Suna tafiya a hanya ya dafa kafaɗarta yana bata haƙuri, kamar ita ce marar lafiyar ba shi ba. Har suka shiga mota suka nufi hanyar gida Gulzar ba ta sauƙo ba. Sai da suka kusa kaiwa unguwarsu kiran PAn Abby ya shigo wayar Gulzar. “Alo Falak ya kike?” Ta faɗa bayan ta ɗaga kiran, daga ɗayan ɓangaren Falak ta amsa, sannan ta faɗi dalilin kiran nata. “Agha (Honorable person) Iƙlab ne yake son ganinki yanzu a kamfani” Ta tattare girarta tana ɗagawa Arman hannu alamun ya dakata, ya dakatar da motar yana kallonta. “Lafiya yake naimana?” “Eh yace yana son ganinki ne” “Ɗayib jaye! (Okay gani nan zuwa)” Ta sauƙe wayar tana kallon Arman. “Abby yana son ganina a kamfani, dan Allah ka kaini can” Ba tare da yace komai ba ya jinjina kansa yana gyara zaman glashin dake idonsa, sannan ya ja mota ya juya akalar tuƙin nasa zuwa Alhadi Group of Companies. Duk kuwa da ya jima rabon da ya je kamfanin, amma tun da ta buƙata ba zai ƙi kaita ba. *Majmu'at Shirkat Alhadi, Al Saaha street, Lobby C, Downtown Burj Khalifa, Abu Dhabi, Dubai.* “Jininka ya hau da yawa Sayid Iƙbal (Mr Iƙbal). Ya kamata ka riƙa sauƙaƙawa kanka” Faɗin likitan Sayid Iƙbal, yayin da yake tattare blood pressure monitor ɗin da ta yi amfani da shi wurin duba hawan jinin nasa, saboda haka kawai ɗazu ya yanke jiki ya faɗi ba gaira ba dalili. Zaune yake a kan wata boudoir chair, yayin da suit ɗin da ya cire daga jikinsa ke rataye a jikin chair ɗin. Ya lumshe idonsa yana shafa damtsen hannunsa da aka cire abin blood pressure monitor ɗin a jiki. PAnsa na tsaye a gefe, haka ma babban abokinsa Sayid Nusayr (Mr Nusayr), duka sauna cikin karafaren office ɗinsa dake ma'aikatar ne. “Ni zan wuce” Cewar Dr, yayin da ya gama haɗa kayan gwajinsa, sai a lokacin Sayid Iƙbal ya buɗe idonsa, sannan da ido ya yi wa Falak alama da ta raka Dr, ta jinjina kanta tana nunawa Dr hanya. “Mu je na rakaka Dr” Daga haka suka fice daga office ɗin. Suna fita Sayid Nusayr ya zauna kusa da Abby yana masa sannu. “Bai kamata ka riƙa saka damuwa a ranka ba Iƙbal” Abby ya kalle shi yana sakin hannun dress shirt ɗin dake ƙasan suit ɗin da ya cire, dan bayan suit ɗin akwai waist coat a ƙasa. Zamansa ya gyara yana shafa sumar kansa da ta fara sirkawa da fari, alamun tsufa ya fara masa sallama. “Dole na shiga damuwa Nusayr! Sam Arman ya kasa fahimtar abin da nake son nusar da shi, ba na so na faɗi na mutu na bar shugabancin kasuwancin da na sha wahala kafin na kafa shi a hannun da ba na gari ba. Da ace Akhi Anwar da kansa ne yake son shugabantar kamfanin na bayan raina ba zan ji komai ba, amma Faisal yake so ya danƙawa shugabancin nan, ya nuna shi ba shi da sha'awar ci gaba da kasuwanci. Arman ba ya son karɓan abin da yake nasa, Gulzar mace ce, kuma har yanzu tana da ƙarancin shekaru, sam ba za ta iya shugabantar babban kafani kamar wannan ba... Na rasa abin da zan yi!” Nusayr ya girgiza kai cike da tausayin abokinsa. “Ka yi haƙuri Iƙbal, ka ci gaba da addu'a, da yardar Allah ba za ka mutu ba har sai ka ga Armaan a kan waccan kujerar!...” Ya ɗan yi fasali yana nuna hamshaƙiyar kujerar dake office ɗin, sannan ya ci gaba da faɗin. “A matsayin shugaban kamfanunuwan Alhadi..” Abby ya yi murmushi me sauti. “Wannan shi ne mafarkin da na daɗe ina yi, kuma da dukkan fatan duniya nake roƙon Allah ya sa ya zama gaskiya kafin na bar duniya” Kafin Nusayr ya kai ga faɗin wani abu Gul ta buɗe ƙofar office ɗin ta shigo a dugunzume. Tana ganin Abby zaune ta fara hawaye, ta nufe shi da gudu ta faɗa kansa ta rungume shi tana kuka. “Abby!?” Abby ya shafa dogon gashin kanta dake cikin style ɗin long wavy. Yana murmushi, a da Arman ne yake masa haka, saboda a baya Arman ya fi kusanci da shi fiye da kowa. Amma a yanzu Arman ya fi gudunsa fiye da kowa, kuma ba komai ya ja hakan ba face maganar gadon kamfani da yake yawan yi masa. “Abby me ya sameka?” Abby ya sake yin murmushi yana shafa gashin kanta. “Lafiyata ƙalau, kawai na ɗan ji jiri ne, sai na yi kamar zan faɗi, amma babu abin da yake damuna” Ta kwanta a jikinsa tana kallon Sayyid Nusayar dake murmushi. “Ammu Nusayr wai haka ne?” Sayid Nusayr ya jinjina mata kai. “Abby ka dinga kula dan Allah.” Ta ƙarashe tana kallon Abby, Abby ya share ƙwallar da ta zubo mata yana gyaɗa kai, sannan ya sumbaci kanta yana kwantar da kanta a kafaɗarsa. “Ina ɗan uwanki? Imminku ta faɗa min cewa tare kuka fita da shi” Nan da nan ta ɓata fuska. “Yana reception, wai zai jirani a can” Abby ya girgiza kansa, dan ya sam dalili, wato shi ba ma zai shigo ba, ballantana ya ga office ɗin da bathroom ɗinsa ma ya fi shi muhimmanci a wurinsa. “Ki yi haƙuri, Akuki (Ɗan uwanki) zai daina duk wannan abin da yake” Ran Gulzar a ɓace tace. “Ai sai dai idan zamanin baya yaje ya dawo, sannan ne zai sauya ra'ayinsa, taurin kai ne da shi kamar mutumin wancan zamanin!” Abby ya dungure mata kai. “Kin taɓa ganin wanda yaje zamanin baya ya dawo?...” Ta turo baki tana tura gashinta baya, sannan ta kwanta a jikinsa tana zuba masa shagwaɓarsu ta autanni. * “Asirul laimun wu bass (Juice ɗin orange ma ya isa)” Ya bawa ma'aikacin kamfanin da ya tambaye shi abin da yake son sha amsa. Ma'aikacin ya amsa da to, sannan ya bar wurin, Arman ya ɗaga idonsa yana kallon katafaren reception ɗin kamfanin dake ƙasan ma'aikatar. Gaba ɗaya jinsa yake kamar zaune a kan ƙaya, dan ko kaɗan ba ya son abin da zai haɗa hanyarsa da ta kamfanin nan, kamar yanda Faisal ya saba yi wa rayuwarsa karan tsaye, haka ma yau ya masa. “Makaho!?” Idonsa ya rintse yana gyara zaman glasses ɗinsa, kafin ya buɗe idon nasa ya ɗaga kai ya kalle shi, sai dai yau ba shi kaɗai ba ne, akwai Sakina tare da Anwar mahaifinsu. Kansa ya kawar daga barin kallonsu, dan haka kawai ya ji zuciyarsa na hassala da dariyar da suke masa. “Kaya ka kawo kamfanin ne?. Dan na san ko cikin ma'aikatan dake wurin nan babu makaho irinka” Cewar Sayyid Anwar yana dariya. Arman ya dunƙule hannunsa yana haɗiyar yawu da ƙyar, dan yau ji yake kamar ba zai iya ɗaukan cin zarafin da suke masa ba. “Ai ko a cikin masu shara babu makaho Abbu, ballantana a cikin masu kawowa kaya” Sakina ta faɗa tana tata dariyar. Arman bai tanka musu ba, kansa kawai ya sake sunkuyarwa, saboda yanda mutanen dake kusa da su suka fara kallonsa. “Allah sarki makaho! Su fa da ma makafi ba su da wani aiki da ya wuce bara a gefen hanya... A taimaka min da sadaka! A taimaka” Faɗin Faisal yana kwatanta yanda mabarata ke bara. Arman ya miƙe da sauri zai mayar musu da martani muryar Abby ta kaste shi. “Arman!” Ya tsaya cak da shirin dukan da yake son kaiwa Faisal yana huci, ya dunƙule hannunsa da mugun ƙarfi yana jin kamar ya daki bango ko zai huce. Abby da Gulzar da suka sauƙo ƙasa tare suka tsaya a wurin suna kallonsu. “Me yake faruwa?” Abby ya tambaya yana dafa kafaɗar Arman. Amma sai Arman ɗin ya kauce, ya kalli Gulzar. “Idan kin gama ina mota” Yana gama faɗin hakan ya juya zai bar Building ɗin kamfanin. Har ma'aikacin da ya tafi kawo masa ruwan laimo na binsa da shi yana faɗin ga ruwan laimon nan ya kawo masa, amma bai tsaya ba ballantana ya karɓa. Tun da Gulzar ta ga haka ta san cewa wata baƙar maganar Faisak (FAISAL AND SAKINA) suka faɗawa ɗan uwanta da har ta sa ya shiga wannan halin. “Me kuka gayawa ɗan uwana?” Ta tambaya tana raba idonta a kan su ukun. Amma babu wanda ya amsa mata, sai murmushin da suke suna duban juna. “Wai ko kunya ba ku ji?... Sakarkaru kawai!” Ta faɗa rai a ɓace, sannan ita ma ta juya ta bi inda ɗan uwanta ya bi ba tare da ta yi wa Abby sallama ba. Daga Anwar har FAISAK ba su ji haushin abin da Gulzar ta yi ba, dan sun san su ne a gaba. “Na ji an ce ka faɗi da fatan ba wata matsalar ba ce?” Sayyid Anwar ya tambaya yana duban Abby da murmushi, Abby dake cikin jin rashin daɗin halin da yaransa ke ciki ya girgiza kansa. “Na ji sauƙi” “To sai a kula nan gaba, dan wata ƙila idan an faɗi ba lalle a tashi ba!” Faɗin Sayyid Anwar yana murmushi, tare da taɓa kafaɗar Abby, sannan ya ja yaransa suka bar Abby cike da zullumi. *FACT MAGAZINE, Building 8, Dubai Media City, Abu Dhabi, United Arab Emirates.* ADAM POV. Sanye yake cikin baƙin dress trouser, da farar sweat shirt, kafaɗarsa rataye da briefcase ɗinsa, ƙafafunsa cikin moccasin dockside. Sumar kansa me ƙarfi irin ta Africans na cikin askin crew cut. A ɗarare ya ƙarasa seat ɗinsa dake cikin na tarin ma'aikatan kamfaninsu ya zauna yana raba ido. A hankali ya aje briefcase ɗinsa a kan table, sannan ya buɗe system ɗinsa dake kan table ɗin, ya ciki gaba da aikin da bai ƙarasa ba. Adam baƙi ne a kalar fata, kuma dogo ne, sannan yana da kyau dai-dai gwargwado, dan a fuskarsa ba ka ce ga abin kushe ba. Yana tsaka da aikin da yake wani cikin abokansa na wurin ya lallaɓo ta bayansa, ya shammace shi yace. “Booom!” Da ƙarfi, hakan yasa Adam ya zabura har yana ɗaukewa ƙafafunsa daga ƙasa, zuciyarsa kuwa kamar ta fasa ƙirjinsa ta fito tsabar tsoro. Sai jujjuya ido yake yana haki, abokin nasa da ya tsorata shi ya kwashe da dariya yana tafa hannu. Haka sauran abokan aikinsa da teburan aikinsu ke kusa da nasa suka taya shi dariyar. “Matsoraci!... Ka gama aikin da shugaba ya baka?” Abokin nasa ya tambaya yana duba system ɗinsa, Adam ya masa banza yana sauƙe ƙafafunsa da ya ɗora a kan kujera zuwa ƙasa, tare da dafe ƙirjinsa dake barazanar ɓallewa. “Haisam bana son irin wannan, kuma ka sani” Ya faɗa cikin son nuna ɓacin ransa a kan abin da Haisam ɗin ya masa, Haisam na dariya ya dafa kafaɗarsa yana faɗin. “Ka yi haƙuri abokina, a duk sanda na ganka cikin tsoro nishaɗi kake bani” Adam ya galla masa harara yana ɗauke kai. Har Haisam ya ƙaraci surutansa bai ce da shi uffan ba. Har ya ƙyale shi dan dole, ya ci gaba da aikin dake gabansa, kafin landline phone ɗin dake kan teburinsa ta shiga ruri. Shi ma ringing ɗin wayar sai da ya kusa tsorata shi, da ƙyar ya saita kansa ya ɗaga wayar. “Sabahul Khair Ustaz (Barka da safiya shugaba)” Ya faɗa bayan ya ɗaga wayar, dan kira ne daga wayar ogansu. “Barka da safiya, da fatan ka gama aikin da na baka?” Ya jinjina kai yana faɗin. “Eh Ustaz na kammala shi” “Ina son ganinka yanzu a office ɗina” “Hadir Ustaz (To Shugaba)” Daga haka ya aje wayar, ya ɗauki system ɗinsa ya miƙe ya nufi office ɗin ogan dake can wata kusurwa ta ma'aikatar. Sai da ya ƙwanƙwasa ƙofar gilashin dake ofishin, dan ko daga nan inda yake yana iya ganin ogan nasu zaune a kan kujerarsa yana cin shawarama, sai da Ustaz ya ba shi izinin sannan ya shiga da sallama. Shugaban ya amsa sallamar da ya yi yayin da yake zama a kan kujerar ofishin nasa. A ladabce ya buɗe system ɗinsa, sannan ya miƙawa Ustaz. Ustaz ya karɓa, ya shiga duba ayyukan yana jinjina kai, alamun sun burge shi. “Hotuna sun yi kyau Adam. Kuma na ji daɗin ganinsu a haka... Lalle na jinjinawa ƙoƙarinka” Adam ya yi murmushi me sauti yana faɗin. “Haza wajibi Ustaz (My pleasure shugaba)” Ustaz ya jinjina kai shi ma yana murmushi, sannan ya aje guntun shawarman da bai ƙarasa cinyewa ba, ya kalli Adam, kana ya furta masa dalilin ƙaddarar da za ta zama silar juyin rayuwarsa. “Nan da wattani biyu masu zuwa gwamnatin Dubai na shirin bamu kyautar karramawa, a wannan bikin da za'ayi ina so mu gabatar da hotuna masu kyau da jan hakali. Hotuna irin wanda ba'a saba ganinsu ba, kuma ina so ya zama kai ne wanda zai zo da hotunan... Da fatan za ka zo min da abin da zan yaba” *Dubai Miracle Garden, Street 3, Al Barsha South, Dubai.* IVANA POV. “Na gode” Ta yi wa mutumin da ta sai juice a wurinsa godiya, sannan ta juya da nufin barin wurin, domin zuwa wurin ɗan 'yar uwarta Imran da suka zo Miracle Garden ɗin tare, dan shi ne ma ta zo wurin. Hannayenta duka biyu na riƙe da cups ɗin juice ta nufi wurin da wani jirgin wasa yake, wanda aka haɗa shi da ganyayyaki, a jikinsa kuma akwai rubutun 'Emirates'. Kasancewar a kusa da wurin ta bar Imran na wasa da wasu yara. “Marhaba (Hello)” Ta ji muryar a bayanta, hakan yasa ta juya domin ganin me maganar, duk da ta ji kamar ta san muryar. Wannan matashin ɗan kasuwar da suka haɗu a Cavo Espresso Bar ne tsaye a bayanta yana murmushi, sanye yake da farin plain jogger sets. Hannayensa zube cikin aljihun hoodie ɗin kayan, yana kallonta yana murmushi a lokaci guda. “Ahalain (Hi)” Ta amsa da ɗan guntun murmushi, sai ta ga ya faɗaɗa murmushinsa yana nufota, sannan ya tsaya a gefenta. “Mu je” Ta jinjina kanta, sanna suka jera suka fara tafiya, kanta a ƙasa tana kallon interlocks ɗin dake ƙasan hanyar da suke bi. “Ke kaɗai kika zo nan?” Ta ji ya tambaya bayan wani lokaci, sai ta ɗaga kai ta kalle shi, amma shi ba ita yake kallo ba, ita ma kuma sai ta ɗauke kai tana faɗin. “A'a tare da yaron 'yar uwata na zo” Tana jin sautin murmushinsa, kafin yace. “Shi ne wancan?” Ya nuna mata Imran dake wasa tare da wasu yara. Ta kalli yaron da ya nuna, sanna ta jinjina masa kai. “Eh shi ne, ka san shi ne,? Ya girgiza kansa. “Ban sa shi ba, amma na ga sanda kuka shigo nan tare” Ta ɗan yi murmushi kaɗan, a lokacin da suka isa jikin wani bench, suka zauna ta kiran Imran. Imran ɗin da ta kira ya zo da gudu ya karɓi juice ɗin da ta siyo masa, sai da suka gaisa da Uwais, sannan ya juya ya koma suka ci gaba da wasa. “Asir?” (Lemo?) Ta faɗa tana miƙa masa cup ɗin da ya rage a hannunta, ya girgiza mata kai yana shafa sumarsa me kyau da ƙyalli a ido. Ita kuma sai ta jinjina kanta, sannan ta ɗan sha lemon kaɗan, kana ta aje shi a gefenta tana saƙala ganshinta a bayan kunnenta, sakamakon iskar da ake ta sa yana tashi a iska, dan yana cikin style ɗin flat iron waves ne “Wani aiki kike?” Ya sake tambayarta, wannan karon ma kafin ta amsa masa sai da ta kalle shi. “Ina aikin koyar da kiɗan guitar ne a Repton school Dubai...” Ya jinjina kansa. “Aiki me kyau... Ni ma na iya kaɗa guitar, ta kan bani nutsuwa a lokuta da dama, shi yasa ban cika kaɗawa ba sai ina cikin nishaɗi, domin ta ƙara daɗaɗa yanayin da nake ciki” Ivana ta yi murmushi. “Kai fa, menene aikinka?” Wannan karon ma kafin ya bata amsa sai da ya shafa sumar kansa. “Kasuwanci, mahaifina shi ne shugaban rukunin kamfanunuwan Al Aida, ni kuma ni ne magajinsa” Ta dube shi, dan ta san Al Aida babban kamfani ne, da suke sarrafa abubuwa da dama. Shiru ya ratsa wurin na wasu mintuna, kafin ya miƙe tsaye yana faɗin. “Ni zan tafi” Ita ma sai ta miƙe tana kallonsa. “Sai mun sake haɗuwa” Ya miƙa mata hannunsa alamun su gaisa, tare da faɗin. “Sunana Uwais Faizal” Ta kalli hannun nasa, sannan ta miƙa nata hannun suka gaisa. “Ivana Sagar” A lokacin da ya jinjina hannunsa tare wani abu kamar wucewar iska ya gifta a cikin kanta. Haka kawai take jin kamar ta taɓa haɗuwa da wani kamar haka a can baya, kamar akwai wani me kammani irin nasa da suka taɓa gaisawa irin haka, amma ba'a Dubai Miracle Garden ba, a wani unknown wuri da ba ta isa tace ga shi ba. “Na ji daɗin haɗuwa da ke Ivana” Faɗin Uwais yana murmushi, ita ma sai ta jinjina kanta. “Ni ma haka” *Salma Ahmad Isah ✍️* °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-4 *House No. 106, Street 14, Jumeirah Bay Island, Abu Dabhi, Dubai.* “Ban san da wani yare zan yi wa Arman magana da shi domin ya gane abin da nake nufi ba... A ko da yaushe ɗana na nisantata saboda wannan dalilin guda ɗaya!” Faɗin Abby, yayin da suke hira da Immi a cikin katafaren ɗakinsa, da aka ƙawata da kayan adon ɗaki na zamani, kuma masu kuɗin gaske. Immi ta aje cup ɗin shayin dake hannunta, sannan ta shiga wasa da yatsunta tana faɗin. “Tun tasowarsa yayanka da wasu daga cikin 'yan uwanka ke nuna masa cewa kasancewarsa makaho ba shi da wani fata a rayuwa. Buri da mafarkin cimma shi na masu lafiya ne, shi da ya kasance nakasasshe ba shi da ikon son cimma wani buri nasa a rayuwa. Tun ɗana yana ƙarami aka nakasta min zuciyarsa, domin kalaman tozarci da na aibantawa su ne suka sa ya tsani duk wata harkar kamfani ko kasuwanci” Abby ya kai hannu aje nasa cup ɗin da yake riƙe da shi, sannan ya lumshe idonsa yana shafa kyakkyawar sumar kansa. “Abin da kika faɗa haka ne Zahra, amma a halin yanzu ba ni da ikon canzawa Arman ra'ayi, batun nakasa kuma ke kanki shaida ce, da ace ina da hali, da na bayar duk abin da na mallaka, domin sama masa lafiya...” Ya buɗe idonsa yana jin zuciyarsa na masa zafi. “Ina da wata shawara” Abby ya kalli Immi da ta yi wannan batu. “Shida ga watan nan da muke ciki ranar haihuwarsa za ta zagayo. Dan haka me zai hana mu haɗa shagalin taya shi murnar zagayowar ranar da aka haife shi. Ko da ba babban party ba, ɗan ƙarami, wanda za mu gayyaci ahali da abokai, yayin da ake cikin shagalin bikin, za ka gabatar masa da takardun kamfani, a gaban kowa, ka umarce shi da ya sa hannu, na tabbatar ba zai ƙi ba, kuma ka ga mu ma sai mu huta, dan daga zarar ya sa hannu magana ta ƙare, babu shi babu sake cewa ba ya son shugabanci!...” Abby ya yi shiru na wani lokaci yana shafa sajensa. “Arman yana da taurin kai, zai iya ƙin amincewa” Immi ta girgiza kai. “Duk taurin kansa ba zai so ya bamu kunya a idon duniya ba” Abby ya yi murmushi. “Na gode da wannan shawarar taki Azizati” Ya ƙarashe yana kamo hannunta na dama, tare da sumbatarsa. Immi ta yi murmushi tana kallon mijinta. “Bari na je na duba yaran nan, wata ƙila sun yi bacci” Ta miƙe tana tura gashin kanta baya. “Sai kin dawo” Cewar Abby yana ɗaukan cup ɗin teans. Immi na fita ta fara da ɗakin Gulzar, kuma kamar yanda ta yi zato ne, sanda ta isa ɗakin nata samunta ta yi tana bacci. Dan haka ta shiga ɗakin cikin kulawa, ba tare da ta bari ta yi making sound ɗin da zai sa ta farka ba. Sunkuyawa ta yi ta sumbaci kanta, sannan ta juya ta bar ɗakin. Daga nan kuma ɗakin Arman ta wuce, shi kam bai yi bacci ba, dan zaune ta same shi a kan gadonsa yana kallo a system. Tana shiga ɗakin ya tsayar da kallon, sannan ya rufe system ɗin yana binta da kallo, har ta zauna a kan gadon nasa. “Tu abhi tak kyun nahin soya?” (Me yasa ba ka yi bacci ba har yanzu?) Ta tambaya cikin harshen Urdu tana kallon kayan dake jikinsa, dan yana sanye da khaki trouser da shirt ne, sumar kansa duka ta sauƙo kan goshinsa, sannan glasses ɗin da suke tamkar rayuwarsa na maƙale a fuskarsa. Sai ya kwanta a kan gadon, sannan ya ɗora kansa a kan cinyarta. “Main neend mehsoos nahi kar raha, isi liye Immi” (Bana jin baccin ne, shi yasa Immi) Shi ma ya amsa mata da Urdu ɗin. Ta shafa sumar kansa da take a nannaɗe, saboda style ɗin curl ɗin da aka mata, dan babu wani aski da yakewa sumar tasa bayan top curly, kuma iyaka tsakiyar kan ne yake tara gashi, gefe da gefen da kuma ta baya aske shi ake. “Laish manak na'asan?” (Me yasa ba ka jin bacci?) Wannan karon da larabci ta tambaye shi. Dan duka yaren biyu babu wanda ba sa ji shi da Gulzar, kasancewar Urdu shi ne yaran ƙasarta Pakistan, duk da yana kamanceceniya da Hindi. Amma asalin yarenta Urdu ne, larabci kuma shi ne yaren mahaifinsu, hakan yasa duka yarikan biyu sun iyasu. “Bas haik Immi” (Haka kawai Immi) Ya bata amsa da larabcin shi ma. “Arman!” Ta kira sunansa tare da sumbatar sumar kansa, sai ya lumshe idonsa yana amsawa. “Umm” “Me yasa ba ka son faranta mana ta hanyar yin abin da muke so ni da Abby?” Tambayar tata tasa ya buɗe idonsa. “Immi ba zan iya yin shugabanci ba. Saboda ina da nakasa...” “Shiiiiii!” Immi ta yi saurin dakatar da shi, sannan ta sa hannu ta tura sumar kanta bata. “Na san cewa kana da halayen da kai kanka ba lalle ace ka san kana da su ba... A ƙalla ma'aikata ashirin ne ke aiki a gidan nan. Amma cikin mutum ashirin ɗin nan ba na jin akwai guda ɗaya da ka taɓa tozartawa, kuma ban taɓa gani ko jin sanda ka saka wani cikinsu aikin da ba za su iya ba. A wasu lokutan ma kana yin ayyukan da ya kamata ace su ne suke yi, kuma kana ɗaukansu a matsayin abokai. Duk da a ƙasanka suke aiki, ko ni da Gulzar sukan koka damu a wasu lokutan, amma ban da kai Arman. Hakan yasa na gane cewa ɗana shugaba ne, shugaba ne da zai iya jan ragamar masarauta ba iyaka Majmu'at Shirkat Alhadi kaɗai ba. (Alhadi Group of Companies)...” Kamar yanda ya saba shiru a kan maganar da ba shi da amsarta haka yau ma ya yi shiru, dan ba ya jin zai iya ce mata wani abin kuma... *House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai* IVANA POV. Zaune take a kan kujerar falo, ta lanƙwashe ƙafarta ɗaya a kan kujerar da take zaune, ɗayar ƙafar tata kuma na ƙasa, sanye take da casual palazzo trouser, me ɗauke da zanen dogayen layin baƙi da kore, sai baƙar tube top. Gashin kanta na cikin style ɗin halp up- halp down. Idonta a kan Tv, tana kallon wani show da ake haskawa a Wanash tv. Yayarta Hala mahaifiyar Imran na zaune a gefenta suna kallon shirin tare. “Ivana waye saurayin da Imran yace min kuna tare da shi a Miracle garden?.” Ta ji tambayar a bazata, dan sam ba ta yi zaton tambayar ba, kanta ta juyo ta kalli Hala, sannan ta ɗage kafaɗunta tana barbaza gashin kanta dake kwance a gadon bayanta. “Uwais Fazil! Haka yace min sunansa” Hala ta gwalalo ido tana kallonta. “Kada ki ce min jinin masu kamfanin Al Aida ne?” Ivana ta tattare naman goshinta cikin mamakin saiyawar yanayin Hala lokaci guda. “Eh shi ne. Mi ye wani abu na musamman a kasancewarsa jinin ahalin?” Ta tambaya. Hala ta yi dariya. “To idan ba ki sani ba na sanar da ke. Kin ga girman kamfanin baban abokinki Arman? To da kaɗan zai faɗawa Al Aida girma. Kuma idan har kamfanin Iƙbal Alhadi zai zama na farko cikin jerin manya-manyan kamfanunuwa a Dubai to Al Aida zai zamo na biyu!” “Waye bai san wannan ba to?... Ni ban ga wani abin birgewa a nan ba!” Ba ta kai ga rufe bakinta ba wayarta ta shiga ruri. Da ta duba kuma sai ta ga lambace babu suna, ta ɗauka da niyyar ba za ta ɗaga ba. “Ya kamata ki ɗaga, dan ba ki san wani alkairi ne yake shirin faruwa da ke sanadiyyar kiran ba” Cewar Hala, kuma a lokacin Yumma da ta tafi sama wankewa Imran rigarsa da ya ɓata suka sauƙo ƙasa tare da Imran ɗin. Dan haka Ivana ta ɗauki wayar ta yi sama, har Yumma da Ivanan ta raɓa ta wuce na binta da kallo, saboda saurin da take. Tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar, sannan ta kalli screen ɗin wayar, lokacin da kiran yake shigowa a karo na biyu. Sai da ta tsaya nazari na wasu sakanni, kafin ta ɗaga kiran. “Marhaba (Hello)” Ta faɗa tana lasar lips ɗinta, a lokaci guda kuma ta ɗora hannunta a kan ƙugunta. “Ahalain (Hii)” Tun da ta ji muryar ta gane waye. Amma abin mamakin shi ne, a ina ya samu lambarta?. Wa ya ba shi? Me yasa ya kirata. “Uwais Fazil ke magana” Ya sake faɗa daga ɗayan ɓangaren, jin ta yi shiru, Ivana ta zauna a bakin gadonta tana faɗin. “Na gane ai” “Good to ya kike?” “Ina lafiya, da fatan kai ma haka” “Ni ma ina cikin ƙoshin lafiya da amincin rai da zuciya!” Amsar da ya bata ta sa ta yi murmushi. “Na kiraki ne mu gaisa... Saboda tun bayan waccan ranar da muka rabu nake ta tunani da burin sake haɗuwa dake” “Wani abu ne na musamman haka da ya faru a haɗuwarmu ta farko da har zai sa ka yi marmarin sake haɗuwa da ni?” Ta tambaya. “Ke kanki ta musamman ce, ballantana kuma aje ga kalamanki na nutsuwa, yanayin yanda kike magana, yanayin da kike tafiya, da duk wani abu da ya shafeki na musamman ne” A wannan karon murmushi ta yi me faɗi, har haƙwaranta na bayyana. “Kin yarda ke nan? Tun ga shi har kina murmushi” Sai ta rufe bakinta, tana mamakin yanda aka yi ya san ta yi murmushi, tun da murmushin ba me sauti ta yi ba. “Zan sauƙa daga kan layi. Ina fatan sake haɗuwa da ke” “Sai anjima” “Na gode da lokacinki” Uwais ya sauƙe wayar, a lokacin da mahaifiyarsa ta shigo katafaren falon gidansu. Murmushi ta yi tana kallon ɗanta, tana zama kusa da shi ya kama hannunta ya sumbata. Ita kuma ta shafa kansa tana sanya masa albarka. “Da wa kake waya? Ko yarinyar da zata zama sirikata ce?” Ya faɗaɗa murmushinsa yana kallon mahaifinsa da shi ma ya shigo falon. “Ai da gani ba sai an faɗa ba. Tun da kika ga yana yin irin wannan murmushin.” Mahaifinsa Inayat Fazil ya faɗa yana nasa murmushin. Ƙudsiyya mahaifiyarsa tace. “Wace ce?” “Wata ce” Ya basu gajeriyar amsar yana kwasar wayoyinsa, sannan ya bar living arean yana murmushi me kama da dariya. *House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.* ADAM POV. Tsaki ya ja yana ci gaba da danna system ɗinsa, sakamakon binciken wurin da ya kamata ace ya je ya ɗauki hotunan da aka saka shi da yake. Amma ya shafe sama da awa uku bai samu wurin da ya kwanta masa ba. Arman dake zaune a gefensa yana cin tuwon da Maama ta ba shi ya ce. “To wai duk wannan tsakin da kake wa mutane na miye?” Adam ya juyo ya kalle shi, sai lomar tuwon shikafa miyar kuka yake, kamar wani bahaushe, ko irin ya saba da cin abincin nan. Kuma dan tsabar yana son tuwon yasa a wasu lokutan yake tattaki ya zo gidansu Adam, dan kawai Maama ta ba shi tuwo, yace a cikin abincin hausawa tuwo ya fi komai daɗi. “Ya zalame (Man) na rasa wurin da ya kamata ace na je na ɗauki hotunan da za su ja hankalin mutane, irin hotunan da ba'a saba gani ba ka gane?” Armaan ya gyara zaman glasses ɗinsa, sannan yace. “Ka je ka ɗauko hotunan Creek harbor, ko Dubai Fountain show, ko Museum of the future...” “Ina maganar abin da ba'a saba gani ba kana lissafo min wuraren da babu wanda bai sansu ba a Dubai. Duka waɗannan wuraren da ka lissafo ɗaiɗaikun mutanen garin nan ne kaɗai ba su taɓa zuwa ba, in ma ba su je ba sun san wurin. Kuma me zan nunawa mutane a wurin da suka riga suka sani?” Adam ya katse shi. Arman ya gyara zama yana aje bowl ɗin hannunsa a kan center table. “To ka je Bastakia, Deira, ko ka ɗauko gaba ɗaya Palm Jumeirah...” “Dakata Arman, hotunan wuraren nan tuntuni an riga an ɗauke su, imfact ba na son ɗaukan hoton wani abu a Dubai, na fi son na fita wajen Dubai dan na zo musu da sabon abu.” “Ina za ka je to?” Ya tambaya yana gyara zaman glasses ɗinsa. Adam ya yi shiru kawai, dan har yanzu ya kasa tsayar da shawarar inda ya kamata ace yaje. “Me zai hana ka je Nigeria, ka ɗauki hotunan masarautun gargajiya da al'adun Hausawa?” Maama dake tsaye a kitchen, tana sauraron duka hirarrakinsu ta bada shawarar. Kusan a tare suka juya suka kalleta. “Kyakkyawar shawara... Idan za ka je zan rakaka, dan ban taɓa zuwa ƙasarku ba, ko ba komai ka ga ni ma zan buɗe ido” Adam ya yi murmushi. “Zan duba na gani” Arman ya kai masa dukan da a ɗan ƙanƙanin lokaci ya sa ya razana. Dan sam bai zaci dukan Arman ɗin a wannan lokacin ba. “Miye ne?” Ya tambaya yana zaro ido. “Me za ka duba ka ga?. Ai tun da Maama ta riga ta bada shawarar nan ta karɓu, ko kai ba ka karɓa ba ni na karɓa maka, dan haka ni zan ɗauki nauyin tafiyarmu Nigeria. Dan a private jet ɗin Alhadi za mu tafi” Adam ya yi dariya. “To ya kamata mu sanar da Ivana, dan ita ma ba za ta kasa zuwa ba” “Zan faɗa mata” Arman ya faɗa yana ɗaukan wayarsa dake ruri, alamun shigowar kira, ganin lambar kakarsa ‘Jadda Nahila’ (Kaka Nahila) yasa ya ɗaga kansa yana girgizawa. Dan tun da har ya ga kiranta ya san wani abin aka ce mata ya aikata. “Shu sar (Me ya faru?)” Adam dake rufe system ɗinsa ya tambaya. “Jadda ce ke kirana” Ya faɗa yana nuna masa wayar. “To ka ɗaga mana” Sai ya girgiza kansa yana miƙewa. “Babu amfanin sai na ɗaga, na san cewa za ta yi duk inda nake, duk abin da nake na bari na tafi gidanta” Adam ya yi dariya yana kallon Arman ɗin da ya nufi kitchen, ya wanke hannunsa, sannan ya dawo falon ya ɗauki Denim jacket ɗinsa ya saka. Sannan ya ɗauki keyn motar da ya fito da ita. “Na tafi... Maama na tafi” Ya musu sallama yana nufar ƙofar fita daga gidan, wadda ta kasance ita ce ƙofar falo. “To Arman ka gaida Imminka” “Za ta ji” Daga haka suka fita tare da Adam. Motarsa silver color ƙirar RR (Rolls-Royce) sweptail. Na fake a ƙofar gidan. Kallon motar kawai idan ka yi za ta baka labarin kuɗinta. Dan sam motar ba ta yi kama da ta ƙananun masu kuɗi ba. Shi kansa Arman ba ya hawa mota ɗaya, idan yau ya hau Bugatti La Voiture Noire, gobe za ka ganshi da Lamborghini Venone Roadster. “Idan na dawo daga gidanta zan kiraka a kan maganar tafiya Nigeria ɗin nan” Arman ya faɗa yana buɗe ƙofar motarsa. Adam ya amsa masa da to, suka yi sallama, sannan Arman ya ja motar zuwa gidan kakarsa, wadda ta haifi mahaifinsa, dan duka 'yan uwan mahaifiyarsa suna can Lahore, Pakistan. Salma Ahmad Isah ✍️ _______________ _Shin a ganinku me Arman zai yi ifan jar ya san abin da iyayensa ke shiryawa?._ _Wata alaƙa kuke hasasowa tsakanin Uwais da Ivana?._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-5 A ƙofar gidan ya faka motarsa, sannan ya fito yana kallon kyakkyawan gidan da tsohuwar ke ciki, dan kakansu ya daɗe da rasuwa, ita Jaddan ce kaɗai ta rage, sai jikokinta da kan zo tayata zama jifa-jifa. Dan bayan mahaifinsa da Anwar Jadda na da 'ya'ya mata huɗu, waɗan da suka kasance ƙannen mahaifinsa. Ba tare da knocking ko danna door bell ba ya buɗe ƙofar gidan ya shiga, a ɗan hall ɗin dake bakin ƙofa ya tsaya ya cire takalmansa, ya saka wasu da ya ga a wurin, sannan ya shiga falo yana dube-dube. Bai ga kowa ba bayan wata kyakkyawar budurwa da ta fito daga ƙofar da ya san cewa kitchen ne. Hannunta riƙe da tray, wanda kallon kyanta bai sa ya san miye a ciki ba. Da alama ta ji buɗe ƙofar tasa ne shi yasa ta fito dan ganin wanda ya zo. “Marhaba” Ta faɗa tana kallonsa da murmushi, dan ita ta san shi, shi ne dai alamu suka nuna cewa bai santa ba. Kansa ya jinjina kawai yana ƙare mata kallo, ba zai yi ƙarya ba, yarinyar tana da kyau. “Aina Jadda” (Ina Jadda) “Bi gurfatah, kallini nadilah. (Tana ɗakinta, bari na kirata)” Ta amsa da muryarta me daɗin saurare. A living room ya zauna yana ci gaba da kallon matashiyar, har ta nufi corridor ɗin da zai sadata da upstairs. Sai a lokacin ya ɗauke idonsa a kanta, yana zaune a wurin har ta dawo, ta sanar masa ga Jaddan na sauƙowa, sannan ta koma kitchen ɗin. Tun da Jadda ta fito take wurga masa harara, har ta iso living room ɗin, ta zauna a gefe da shi tana kallonsa a kaikaice. Kuma duk da ya lura da hakan bai sa ya fasa dariya ba. “Masa'ul khair ya Jadda. (Barka da yamma Jadda)” Jadda ta masa banza ta ɗauke kai tana girgiza ƙafa. “Ƙira nawa na maka?” Ta tambaya bayan wani lokaci. “A ƙalla goma” Arman ya amsa. “To me yasa ba ka ɗaga ba?” “Saboda na san maganar da za ki faɗa, shi yasa na zo tun kafin ki ce na zo” Jadda ta kuma yin shiru. “Arman zo nan” Ya dubeta, sai ya miƙe ya koma gefenta ya zauna. “Magana nake so mu yi...” Ya jinjina mata kai, yana kallon yarinyar nan da ta dawo falon ɗauke da kayan taɓawa, ta aje a kan center table, sannan ta juya ta koma kitchen. “Jadda wace ce wannan?” Ya tambaya. Jadda ta harare shi, dan ta lura tun da ta shigo falon yake kallonta har ta koma inda ta fito. “Gufran sunanta, ita ce yarinyar gwaggonka Bilƙisa, wadda ke Qatar.” “Ohh na gane. To ina jinki” Ya amsa yana jinjina mata kai. “Da Anwar da Iƙbal duka 'ya'yana ne. Da kai da Faisal jikokina ne, haka Gulzar da Sakina. Amma Wallahi har cikin raina na fi son ka zamto magajin Alhadi fiye da Faisal Arman...” Arman ya yi murmushi, dan ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. “Jadda me yasa kowa yake son na zama shugaban Alhadi?” Ya matambaya. “Saboda kai kafi cancantar zama shugaba... Alhadi kamfanin mahaifinka ne, Anwar hannun jari kawai yake da shi!” Jadda ta ba shi amsa, ya girgiza kansa yana murmushi. “Jadda bani da suffofin shugabanci, saboda inada nakasar gani, ba zan iya shugabanci ba” “Arman! Ka ga wannan kujerar dake cikin office ɗin Iƙbal? Ka ɗauketa tamkar kujerar wata babbar masarauta a zamanin baya. Wadda ake yaƙi da zubar da jini duk domin a mallaketa, wannan kujerar na dai-dai da kujerar katafariyar fada a zamanin baya!” “To wai duk me ya kawo wannan zancen?” Jadda ta yi murmushi. “Saboda ba ma so ka bamu kunya. Nan da kwana uku zagayowar ranar da aka haifeka. Iyayenka na shirya maka babban shagalin taya murna. Kuma a wurin shagalin mahaifinka ya ɗauki niyyar baka takardun shugabancin gamayyar kamfanunuwan Alhadi, domin ka sa hannu a matsayinka na shugaba na gaba. Kuma ba na fatan ka bamu kunya Arman!.” *Maison De Curry, Souk Al Bahar, Sheikh Mohammed bin Rashid Blvd, Downtown Dubai, United Arab Emirates.* *10:52 na dare.* THE ADVENTURERS. “Wai me ya faru ne?” Ivana ta tambayi Arman da ya tarasu a restaurant ɗin, kuma ya zauna ya yi shiru ba tare da yace komai ba. Arman ya juya kansa ya kalli Fountain show dake nan kusa da restaurant ɗin, kuma ta tsakanin Fountain ɗin yana iya ganin dogon ginin Burj Khalifa. “Yau saura kwana biyu zagayowar ranar da aka haifeni. Abby da Immi suna shirya shagalin zagayowar ranar” Ivana da Adam suka dubi juna. Sannan suka kwashe da dariya suna tafawa, hakan ya sa Arman ya kallesu da mamaki. “To ai duk mu ma mun san wannan. Dan mu ma muna shirya namu shagalin... Mi ye na damuwa a ciki” Arman ya saka hannu ya shafa ganshi kansa dake a nannaɗe, sannan yace. “Ba wai batun shagalin ne abin da yasa ma taraku a nan ba. Abby yana shirin danƙa min takardun shugabancin Alhadi... Kuma kun san cewa wannan shi ne abin da bana so” Cak Adam da Ivana suka dakata da dariyar da suke, sannan suka dubi juna. Kafin Adam ya kalle shi. “Man! Ni fa da za ka ji shawarata da ka karɓi shugabancin kamfanin nan. Kasancewarka shugaba shi ne burin mahaifinka na ƙarshe. Bayan duk abubuwan da ya mallaka maka a rayuwa kuma sai ka kasa cika masa wannan burin?... Burin da a ƙarshe kai ne wanda za ka amfana da shi” Ya gyara glasses ɗinsa, sannan yace. “Adam ina so na cika burin Abby, saboda ban taɓa neman komai a wurin Abby na rasa ba. Duk abin da na naima cikin gaggawa Abby ke mallaka min shi, dalilina na ƙin shugabanci shi ne, duk wani abu da zai sa a na min kallon nakasasshe ba na sonsa. Duk wani abu da zai zama silar da za a muzantani gudunsa nake, bana so ana aibanta ni Adam. Kuma ku duka kun san cewa ta dalilin wannan kamfanin Ammu Anwar da Faisal da kuma Sakina ke aibantani a ko ina... Shi ya sa nake gudun Alhadi” Shiru ya ratsa tsakaninsu, dan duk abin da ya faɗa gaskiya ne. “Arman” Faɗin Ivana tana kama hannunsa. “A ganina maganar mutane bai kamata tasa ka sare da rayuwa ba. Allah shi ne me bada lafiya, kuma idan ya so a yanzu zai iya baka lafiya. Kuma tun da kana iya gani da taimakon glasses me zai hana ba za ka jarraba bin abinda iyayenka ke so ba” Ya girgiza kansa, Ivana da Adam suka sake duban juna. Sun san abokinsu da taurin kai, tun da yace a'a to fa ba zai sauya ra'ayinsa ba. “Yanzu mi ye shirinka?” Adam ya tambaya. Ya kallesu su duka biyu. “Kamar yanda suke zato. Sam ba zan taɓa basu kunya ba, domin da ace ban san da batun shagalin nan ba da zan amince na je wurin shagalin, kuma idan ya bani takardar a gaban kowa zan saka hannu. Amma tun da har na sani ba zan je wurin shagalin ba” “Me kake nufi?” Ivana ta tambaya a mamakance. “Zan bar Dubai a ranar da suka shirya shagalin, yayin da suke shirya shagali a nan ni kuma zan yi nawa shagalin a wata ƙasar” Adam ya girgiza kai. “Hakan bai kamata ba Arman. Da wannan abin da za ka yi sai ka fi basu kunya, fiye da ƙin amincewa ka sa hannu a gaban jama'a.” “Adam ya zan yi?... Sam ba na son abin da suke so, na kasa fahimtar da su, ya suke so na yi?” Suka yi shiru, tausayin abokinsu na kama su. “Shikenan. Mun yarda da shirinka, amma ba za mu barka ka tafi kai kaɗai ba, duk inda za ka je za mu kasance tare da kai” Faɗin Ivana tana kallon Adam, shi ma Adam kansa ya jinjina, alamun ya amince. Arman ya yi murmushi yana kallon abokansa biyu. “Amma ina kuke ganin za mu tafi?” “Tun da ni zan je ɗaukan hoto me zai hana mu tafi Nigeria?” Adam ya tambaya. Arman ya girgiza kai, a lokacin da idonsa ya kai kan allon da zai sauya akalar labarin gaba ɗaya, kuma allon dake ɗauke da zanen ƙaddararsu. Wadda za ta yi juyi irin na kwaɗo, daga ruwa zuwa ruwan zafi. Lokacin da ya gama karanta sunan wurin a jikin allon, fatar bakinsa ta furta sunan dajin a hankali. “Bayericher wald (Bavarian forest)!” “Germany ke nan?” Cewar Adam, Arman ya gyaɗa kansa. “Dajin yana da kyau sosai. Sannan za mu shaƙata a cikinsa, kai kuma za ka samu abubuwan da za ka ɗauka a cikin dajin... Kamar dai wancan hoton!” Ya ƙarashe yana nuna musu wani allo dake ɗauke da hoton Bavarian forest ɗin. Suka waiga suka kalli board ɗin a tare, allon dake ɗauke da zanen sauya labarin kowanne a cikinsu. *House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai* IVANA POV. Sanye take da yellow maxi skirt, da farar shirt, wadda a samanta ta saka denim jacket. Tana zaune a kan gadonta, yayin da take goge guitar ɗinta da hanki, Yumma kuma na shirya mata kayanta a cikin jaka, dan ta riga da ta sanar mata da cewar za su yi tafiya tare da su Arman. “Ivana” Yumma ta kirata tana saka wasu takalmanta a cikin jakar da take shirya mata kayan. “Na'am Yumma” Ta amsa tana ɗaga kanta, tare da kallon Yumman. “Me ya sa Arman ba ya son ya karɓi abin da yake nasa?” Ivana ta girgiza kanta tana murmushi, ta saka hannu ta ta saƙala gashinta a bayan kunnenta, sannan tace. “Tun yana yaro kawunsa da wasu daga cikin 'yan uwansa suka raunata masa zuciya. Bayan nakasar ido da yake da ita sun ƙara masa da nakasar zuciya Yumma. Abokina yana da zuciyar zinare, yana son taimakon wanda ba shi da shi, duk da tarin dukiya da Allah ya yi wa mahaifinsa sam ba ya dubawa, domin ba ya nuna banbanci tsakanin mu da shi. Amma wannan raunin da suka yi a zuciyarsa yasa sam ba ya son zama shugaban Alhadi...” Ta ƙarashe tana ɗaga kafaɗunta tare da taɓe bakinta. “Da ace Arman zai karɓi shugabancin nan Yumma da an yi shugaban da ba'a taɓa yin irinsa ba” Yumma ta girgiza kanta. “Allah ya karkato da zuciyarsa kan kamfanin, su kuma Allah ya musu abin da suka masa” “Amin” Ta amsa dai-dai lokacin da wayarta dake chaji a kan side drawer ta fara ringing, hannu ta miƙa ta ɗauki wayar, ganin lambar Uwais Fazil ya sa ta ɗaga wayar, tare da karawa a kunnenta. “Marhaba” Muryarsa me sanyi ta faɗa daga ɗayan ɓangaren. “Alo” Ta faɗa tana murmushi. “Shin zan iya ganinki?” Sai ta kalli Yumma da ke shirya mata kaya, da alama sam ba ta lura da wayar da take ba. Sai ta sauƙa daga kan gadon tana saka toe wrap shoes ɗinta dake kusa da gadon, sannan ta fita daga ɗakin. Sai a sanda take sauƙa downstairs sannan ta amsa. “Zan so hakan, domin ina sa ran zan yi tafiya nan da gobe...” “Yanzu haka ina ƙofar gida me lamba 27, titi na 45, a tsakiyar unguwar Mirdif.” Ido ta zaro tana rufe baki, sannan cikin sanɗa ta isa jikin windown dake kusa da ƙofa, ta ture curtain ɗin dake jikin windown ta leƙa. Daga nan inda take ta samu damar ganinsa, jingine a jikin motar da ya zo da ita. Yana sanye da baƙin sweat blazer trouser, me ratsin ja a gefe, da farar crew-neck sweater, wadda ya saka baƙar shirt a ƙasanta. Ƙafafunsa cikin garin sneakers. Gashin kansa na cikin askin high pade, sannan wayarsa kare a kunnensa, kuma suna haɗa ido ya ɗaga mata hannu, sai ta yi saurin sakin curtain ɗin tana dariya ƙasa-ƙasa. “Ina jiranki” Ba tare da tace komai ba ta sauƙe wayar, sannan ta koma sama da gudu. Har Yumma na tambayarta shin lafiya, ta amsa mata da tana zuwa. Guitar ɗinta kawai ta saka a cikin jakarta, sannan ta ɗauki canvas ɗinta ta saka a ƙafarta, ta tsaya a jikin mirror ta gyara gashin kanta. Sannan ta goya jakar guitar ɗin a bayanta, ta fita ba tare da mayafi ba, dan ta saba yin hakan kullum. Ba ma ita kaɗai ba, a muslman 'yan matan larabawa ba kowacce ce ke saka mayafi lokacin da za ya fita ba. Mafiya yawan waɗan da za ka ga da mayafi a waje to matan aure ne, dan 'yan matan ba su cika yin hakan ba, shi ya sa idan aka gansu a waje za a ɗauka cewa ba musulmai ba ne, dan duk wasu ɗabi'u na turawa sun ɗauka sun yafa a jikinsu. “Ina ya kamata mu je?” Uwais ya tambaya yana duban Ivana dake zaune a kujerar gefensa. Yayin da yake tuƙa motarsa cikin nutsuwa, kuma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana kan bakinsa. Ivana ta kalli hanya tana murmushi. “Duk inda kake ganin zai yi kyau da zama a lokaci irin wannan” Ya sake dubanta, sannan ya ɗauke kai yana dariya, bluewaters island shi ne wurin da ya fara zuwa ransa. Dan haka ya nufi wurin, a gefe ya samu wuri ya faka motarsa, sannan suka fito daga motar, yana riƙe da bag ɗin guitar ɗinta. Yayin da suka jera suna tafiya a cikin yammacin. Daddaɗar iskar da ruwan wurin ke badawa tana busawa a ko ina, akwai kaikawon mutane a wurin, kowa yana harkar da ta kawo shi. Da haka suka samu wani bench suka zauna. Kafin Uwais yace bari ya siyo musu abin sha, tana zaune a wurin har ya siyo ya dawo, ya bata drink ɗin, ta masa godiya tana kallonsa yayin da yake zama, a lokaci guda ta saƙala gashinta a bayan kunnenta, sakamakon iskar wurin dake kaɗa gashin nata. “Ina za ki je?” Uwais ya tambaya. Sai ta kalle shi tana shan drink ɗin da ya bata, sannan ta jinjina kanta. “Akwai abokina da zamu taya murnar ƙarin shekara. Dan haka muka shirya tafiya zuwa Germany” Ta ba shi amsa tana kallon wheel ɗin dake wurin. Uwais ya jinjina kansa. “Kamar kwana nawa kike ganin za ki yi?” Ta ɗan juya idonta, sannan ta tura gashinta baya tana faɗin. “A ƙalla sati ɗaya... Da wani abu ne?” Sai ya girgiza kansa yana kallon bottle ɗin drink ɗin dake riƙe a hannunsa, sannan ya sake dubanta. “Idan kin dawo akwai wani abu da nake so na sanar dake” Ivana ta yi murmushi me faɗi. “Me ya sa ba yanzu ba?” “Saboda ba na so wani abu ya katse ƙudirina a kanki, na fi so sai kin je kin dawo...” Ta yi shiru kawai, dan ba ta san me za ta sake cewa ba kuma. “Ina son kiɗan guitar, ko za ki kaɗa min?” Ya katse shirun yana ɗaukan bag ɗin guitar ɗinta. “Akid (of course)” Ta aje bottle ɗin hannunta a tsakiyarsu, sannan ta karɓi guitar ɗin, ta cireta daga cikin jakar, ta ɗorata a kan cinyarta, sannan ta riƙe neck ɗin guitar ɗin tare da ɗora hannunta a kan frets dake jikin neck ɗin. Ɗayan hannun nata kuma na kan body ɗin guitar ɗin, yayin da yatsun hannun ke kan sound hole na guitar ɗin, sai da ta dube shi, sannan cike da ƙwarewa ta soma kaɗa guitar ɗin. Cikin wani irin sauti me daɗin gaske, me sanyayawa tare da kwantar da hankalin mai sauraronsa. Ko daga nesa ka jiyo kiɗan dole ya ɗauki hankalinka. Dan ba ta daɗe da farawa ba masu wucewa suka fara tsayawa kallonta, har da wasu yara da suka tsaya a gabanta suna rawa, ba ita kaɗai ba, hatta Uwais abin ya ba shi nishaɗi. Salma Ahmad Isah ✍️ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-6 *MK Fencing Academy,19th Floor, The Binary by Omniyat, Business Bay, Dubai, UAE.* ARMAN POV. Tun yana cikin hall ɗin horar da wasan takobin Gulzar ke kiran wayarsa, amma bai ɗaga ba, har sai da ya je office ɗin shugaban wurin, ya ɗauki izinin hutu na sati ɗaya, dan sati ɗaya shi ne tsawon lokacin da suka tsara za su yi a tafiyar tasu, ba tare da sanin abin da zai biyo baya ba. Sai da aka lamince masa, sannan ya yi godiya ya fito daga office ɗin yana jan tsaki, saboda wani kiran Gulzar ɗin dake shigowa wayarsa. Tafiya ya fara a cikin business Bay, yana gyara zaman glasses ɗinsa. Sanye yake da plain hoodie ash color, da kuma baƙar denim jacket da ya ɗora a saman hoodie ɗin. Sai ligh blue baggy jeans, ƙafafunsa na cikin farin huaraches, ya saka baƙar p-cap a kansa, wadda ta taimaka wurin rufe sumar kansa da a kullum take cikin curly top, amma duk da haka sai da gashin ya fito ta jikin hular, kasancewar ya juya rumfar hular ƙeyarsa. Sai da ya shiga motarsa sannan ya ɗaga kiran Gulzar. “A ƙalla na maka kira ya kai ashirin! Amma sai yanzu ka ga damar ɗagawa?” Ta soma da ƙorafi, Arman ya rufe motarsa ƙirar Rimac C_two, jar kala, dan yau da ita ya fito. “Ina class ne, ni ba na son ƙorafi, faɗi me zan miki?” “Shopping za ka zo ka kaini” Ta amsa daga cikin wayar, Arman ya saki baki. “Duk direbobin gidan nan a rasa wanda zai kaiki shopping sai Arman?” Ya tambaya yana nuna ƙirjinsa da keyn motar dake hannunsa. “Eh kai nake so ka zo ka kaini, saboda akwai wasu kaya da zan sai maka kaima” Sai ya yi dariya. “Gani nan zuwa” Ya katse kiran, tare da aje wayar, sannan ya yi wa motar key yana kunna wata waƙar Sa'ad Lamjarred da Elissa me taken Min Awal daƙiƙa. Da haka ya koma gida, ya je ya ɗauko 'yar rigimar tasa, sannan ya nufi Dubai Mall. Sai a lokacin ya lura da shigar da Gulzar ɗin ta yi. Wasu pink Chickankari (Pakistan) ne a jikinta. Rigar kayan da ta kusa taro wandon tsayi na ɗauke da ratsin sea green daga ƙasa, hakan yasa mayafin kayan ma ya kasance net sea green, wanda ta yafa shi a kanta, ammma duk da haka bai hana dogon gashinta bayyana ba. “Gul” Ya kira yana duban hanya, ta ɗago daga barin kallon wayarta ta dube shi. “Umm” “Su kuma waɗannan kayan fa?” Ta dubi jikinta. “Mi ye laifinsu?” Ta tambaya, ba tare da ta hangi makusar kayan nata ba. “Amma Aii (Mahaifiyar Immi dake Pakistan) ce ta aiko miki da su?” Gul ta ƙanƙace ido tana kawar da gashin da ya kwanta mata a gefen fuska. “Wato ni ba zan iya siyan Chickankari da kaina ba sai Aii ta aiko min ko?” Arman ya yi dariya, dan da ma abin da yake so ke nan. Ita ma da ta gane cewa kunnata yake son yi sai ta ɗauke kai tana duban wurin da suke nufa. “Akhi ni fa Mall of the Emirates zan je ba. Dubai Mall ba” Ya dubeta. “Shi Dubai Mall ɗin mi ye laifinsa. Na ga ko Immi a nan take siyayya” “La (No) ni ba zan je can ba, yau Mall of the Emirates nake son zuwa” Arman ya girgiza kansa. Sannan ya juya kan motar zuwa wata hanyar da za ta fi saurin sadasu da Dubai Mall ɗin da take son zuwa. Siyayya ta yi kamar ba ta masu hankali ba, dan kaya ta yi ta jibgowa kamar da za'ayi bikin aure ba na ƙarin shekara ba. Shi dai Arman bai isa yace ƙala ba, tun da Abby ne ya ɗaure mata gindi, don hatta da kuɗin siyayyar ma shi ya biya, yau da safe tace za ta je siyayya, dan haka ya bata ɗaya daga cikin ATM cards ɗinsa. Yayin da kowa na ahalin Alhadi da sauran 'yan uwan mahaifiyar Arman da suka samu zuwa tun daga Pakistan ke shirya masa kyakkyawar liyafa ta taya shi murnar ƙarin shekara. Shi da su Adam kuwa na can suna shirya tafiyarsu zuwa Germany. Shi da kansa yay musu booking flight, daga Dubai zuwa Germany, wanda zai tashi a daren da zai cika shekaru 32 a duniya. Kuma a ɓoye yaje ya yi siyayyar wasu kaya da zai buƙata a tafiyar tasa ba tare da ya bar kowa na ahalinsa ya sani ba. Hannu ya sa ya buɗe wata drawer dake kusa da dressing mirror ɗin ɗakinsa. Ban da glasses iri-iri babu komai a ciki. Gaba ɗaya glasses ɗin cikin drawern irinsu ɗaya, domin duka farare ne, masu ɗauke da square frame, banbancinsu kawai shi ne rims ɗin da suka zagaye frame ɗin glasses ɗin. Dan kaloli ne birjit, kuma ko wace kala akwai kayan da yake sakawa da shi, shi yasa adadin glasses ɗinsa suka wuce ɗaya, amma kuma ya fi saka mai farin rims da kuma mai baƙi. Glasses biyu kawai ya ɗauka, dan ba ya jin za su yi wata daɗewa a can da har zai ɗaibi sama da uku, har wanda yake tare da shi a yanzu. Wani kit ya ɗauka ya saka glasses ɗin duka biyu a ciki, sannan ya dawo kan gadonsa, inda jakar kayan da yake haɗawa take, ya saka kit ɗin a ciki. Kuma yana saka shi ya zuge jakar, domin ya gama saka duk wani abin buƙatarsa a ciki. Sauƙewa jakar ya yi daga kan gado, ya jata zuwa ƙofar bathroom ɗinsa, da nufin idan an jima kaɗan zai saka ɗaya daga cikin masu aikin gidan ya fitar masa da ita waje. “Aki Wainak? (Yayana kana ina)” Da sauri ya fito daga wurin, jin Gulzar na ƙwala masa kira, tsaye ta yi tana kallonsa. Dan alamu sun nuna cewa wani abu yake ɓoyewa. “Mi ye?” Ya tambaya cikin son waskewa tambayoyinta. Ita da yake akwai abin da ya kawota sai ta manta da wannan batun, tace. “Su Rahma ne suka zo...” Cikin rashin fahimta ya kalleta. “Wace ce Rahma?” “Mts ƙawata da take Riyadh, ta zo ne domin tayaka murna” Sai ya dage girarsa duka yana kaida kai. “Ohh na gane” “Me kake ne?” Ta tambaya tana kallon dressing table ɗinsa da yake a hargitse, domin gujewa zargi sai ya ɗauki hair dryer ya shiga busar da gashin kansa da babu ruwa yana faɗin. “Gyaran kai nake, ke yaushe za ki je a rage miki tsayin wannan gashin naki” Gulzar ta kalle shi tana taɓa dogon gashinta. “Ai ba zan taɓa yanke wannan gashin ba” Ya taɓe baki yana aje dryer, sannan ya ɗauki comb ya shiga taje sumar da take sama, kafin ya juyo ya kalleta. “Su waye suka zo kuma bayan ƙawarki? Na ji hayaniya ta ƙara yawa a ƙasa” Ta ɗage kafaɗunta. “Ban sani ba, amma mu je mu gani” Ta ƙarashe maganar tana juyawa, ya aje comb ɗin da ya ɗauka ya bi bayanta. Ko da suka sauƙa ƙasan ba kowa suka ga ba face 'yan uwan Abby na Qatar da suka samu isowa. Duk dangi sun zo, kai kace bikin aure za'a yi ba na ƙarin shekara ba. Duk waji abu da suke Arman kallonsu kawai yake, dan gani yake kamar ihu suke bayan hari, a ganinsu bai san abin da suka shirya ba, shi ya sa wasu daga cikinsu ke farin cikin zai zama shugaba ba tare da sun furta ba. Amma shi ya san farin cikin na miye, kuma zai musu albishir na wannan burin nasu ba zai taɓa cika a yanzu ba... Tunanin nasa na tafiya kafaɗa da kafaɗa da ƙaddararsa, domin kamar yanda yake ganin cewa ba zai karɓi shugabancin Alhadi yanzu ba yabbas ba zai karɓa ɗin ba, kuma hakan zai faru ne sakamakon ƙaddarar dake jiransu a Bavarian forest. Wadda za ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwarsu, daga ruwa zuwa ruwan zafi. *House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.* ADAM POV. Tsaye yake a gaban Maama wadda ke masa addu'ar Allah ya tsare shi, hannunsa riƙe da jakarsa ta kaya, yayin da yake murmushi yana dubanta. “Zan yi kewarki Maama” Ya samu bakinsa da furta hakan. Domin a ganinsa kamar sati ɗaya ya yi kaɗan da zai sa ya riƙa jin kewarta a ransa irin haka, Maama ta yi dariya. “A sati ɗayan? Na ga ka sha yin tafiyar da ta fi wannan tsayi, kuma kana daɗewa, sai wannan ta sati ɗayan ne zai sa ka yi kewata?” Ya aje jakar hannunsa, sannan ya rungumeta yana jin kamar ya fasa tafiyar, shi dai ba ya ce ga dalilin da ya sa yake jin cewa zai yi nisan gaske da ita ba. “Sakeni haka mana, sai ka karya min ƙashin tsufa” Faɗin Maama, sai ya saketa yana murmushi. “Allah ya tsareku, ya dawo da kai lafiya” “Amin Maama” Ya amsa yana ɗaukan jakar da ya aje. Sannan ya ɗaga mata hannu, ya juya zai fita, cikin raha Maama tace. “Kett!” Ya tsorata yana juyowa tare da kallonta. Maama ta kwashe da dariya, shi ma da ya gane cewa zolayarsa take sai ya yi dariya. “Ai zan daɗe ba na nan, sai na ga wanda za ki zolaya kuma” Ya faɗa yana fita daga gidan. A bayan motarsa ya saka jakarsa, domin sun yi da Ivana da kuma Arman kan a motarsa za su tafi airport. Domin shi Arman ba ya so kowa ya san cewa ba ya gida a lokacin da suke gudanar da shagalin ƙarin shekararsa. Shi ya sa ba zai ɗauki ɗaya daga cikin motocinsa ba. Kai tsaye gidansu Ivana ya nufa, da yaje gidansu ma ya daɗe, domin Ivana dake sallama da Yumma da kuma 'yar uwarta Hala. Kamar wata wadda za ta bar duniya haka ta fara hawayen bankwana da su Yumma. Sai da ban banki sannan ya samu ya ɗauketa suka tafi gidan Iƙbal Alhadi, a bayan gidan ya tsayar da motarsa, sannan ya kira Arman... ARMAN POV. Tsaye yake a balcony ɗin ɗakinsa, hannayenssa zube cikin aljihu, yana kallon masu aikin decoration na decorating garden ɗin gidan, dan daga nan inda yake yana iya ganin duk abin da ke wakana a garden da kuma wurin swimming pool ɗin gidan. Haka kawai yake jin kamar bankwana yake da kowa da komai, kamar wannan hukuncin da ya yanke ya yi tsauri da yawa, kamar idan ya aikatawa ahalinsa hakan sam ba za su ji daɗi ba, daga can ƙasan zuciyarsa kuma akwai wani abu da yake marmari da son tafi Bavarian forest, ba zai ce ga dalili ba, domin bai taɓa zuwa dajin ba, hasali ma sau ɗaya ya taɓa zuwa Germany... “Wai har yanzu ba ka shirya ba Arman?” Ya jiyo muryar Immi na faɗin hakan a bayansa, hakan ya sa ya juya ya kalleta, hannayensa zube cikin aljihu. Tsaye take a tsakiyar ɗakin nasa, hannunta riƙe da wani box me faɗi, wanda ya san cewa tufafi ne sabbi a ciki. Ta sha adonta cikin wani maroon chickankari, me ɗauke da ratsin golden. Wuyanta kunnenta da hannayenta duka ta saka jewelry masu tsada, fuskarta ta sha kwalliya, wadda ke ɓoye yawan shekarunta. “Shu? Ka'annak mu farhan ibini?” (Miye? Kamar ba ka farin ciki ɗana?). Ta tambaya ganin yanayinsa, ya girgiza kai yana nufota. Yana zuwa kusa da ita ya kama hannunta. “Kin yi kyau fiye da kullum Immi. Kamar yayata ba mahaifiyata ba” Immi ta aje box ɗin da ta shigo da shi, ta daki kafaɗarsa, ya yi dariya yana kallonta. “Sai ga shi kuma ni mahaifiyarka ce ba kakarka ba.” Ya kalleta yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya dafa kafaɗarta. “Da gaske kin yi kyau” Immi ta yi murmushin jin daɗi, Arman ya dawo gefenta yana dafa kafaɗarta ɗaya, tare da zaro wayarsa a aljihu yana faɗin. “Bari na ɗauki hoto” Ya ɗaukesu a hoton, sannan ya nuna mata. “Ya yi kyau. Ga su nan, kaya ne da na saka aka maka tun daga kamfani, ka yi maza ka shirya ka fito, masu kawowa cake sun kusa zuwa.” Ya kalli box ɗin yana jinjina kai, sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa da kiran Adam ke shigowa. Bai ɗaga kiran ba, ya jefa wayar a aljihunsa, ya samu ya lallaɓa Immi ta fice daga ɗakin, paper da pen ya ɗauka, ya yi rubutu a kai, sannan ya aje papern a kan box ɗin kayan da Immin ta kawo masa. Sannan ya ɗauki wayarsa ya kira mai aikin gidan da ya bawa ajiyar jakarsa, yace masa ya kai motar Adam, tana bayan gida. Daga haka kuma shi ma ya saɗaɗa ya fice daga gidan, ba tare da ya bari kowa ya ankara da shi ba. *11:40 na wannan daren.* Ko ina ka kalla a garden ɗin gidan Iƙbal Alhadi mutane za ka gani, cikin shigar da za ta sanar da kai tsadar kuɗin kayan da suka saka. Kuma ko ina na garden ɗin an ƙawata shi da kayan decoration wanda suka sa daren ya ƙara armashi. Daga can wajen kan wani table kuwa, cakes ne kala-kala, manya da ƙanana, ban da wasu nau'ikan drinks da snacks. Immi da Abby da kuma Gulzar ne tsaye a kusa da wurin, kowa ka kalla a cikinsu za ka ga yana cikin farin ciki. Kuma haka wasu daga cikin 'yan uwan Abby ma. Amma wasu daga cikin waɗan da suka san shirin da Abby ke yi na miƙawa ɗansa ragamar kamfanunuwan Alhadi akasin farin cikin suke. Musamman Anwar da yaransa, kai da ka kallesu ka san dole aka musu na zuwa wurin shagalin, dan Jadda ce ta kafawa kowa tsatssauran warning kan kada wanda ya kuskura wannan shagalin ya wuce shi, shi ya sa suka zo ba dan suna so ba, sai dan an musu dole. Ganin sha biyu saura ya sa Abby ya kira Gulzar gefe. “Ina ɗan uwanki ne? Tun ɗazu ban ga gilmawarsa ba. Kuma ko ɗaya daga cikin abokansa ban gani ba, duk da na turawa kowa katin gayyata, kuma shi ma na san ba zai kasa sanar da su ba” ”Yana ɗakinsa fa Abby, kuma wata ƙila su ma su Adam ɗin na tare da shi a can, bari na je na kira shi” Cewar Gulzar. “Ki yi maza ki kirashi ya sauƙo, dan sha biyu ta kusa cika” “To Abby” Ta amsa, sannan ta nufi hanyar falo, da ƙyar ta samu ya hau sama, sannan ta shiga ɗakin Arman. Tris ta ja ta tsaya a ƙofar ɗakin, ganin babu kowa a ciki. “Akhi! Akhi?” Ta kira tana leƙa kanta, jin shiru yasa ta ƙarasa shiga ɗakin, ta tsaya dube-dube, kafin ta nufi bathroom ta ƙwanƙwasa, amma shiru, babu alamar ma akwai mutun ciki, sai ta buɗe ƙofar bayin ta leƙa tana kiransa. Ganin baya cikin bayin yasa hankalinta ya fara tashi. Dan haka ta dawo ɗakin da gudu, tana shirin barin ɗakin ta yi arba da box ɗin dake kan hadonsa, kuma ta lura da wata paper dake kai, dan haka ta dawo jiki a sanyaye ta ɗauki takardar ta shiga karantawa. Ai ba ta gama karantawa ba ta fashe da kuka, sannan ta fita daga ɗakin da gudu, ta koma garden. Tun da Abby ya hangeta daga nesa ya gane cewar ba lau ba, dan haka ya yi saurin isa gareta yana tambayar abin da ya faru, kuka kawai ta sake fashewa da shi ta faɗa jikinsa tana rufe bakinta, kukan da take da tambayarta da Abby ke yi na me ya faru ya janyo hankalin baƙi da 'yan uwa. “Ke Gul mi ye haka?” Immi ta tambaya tana nufo wurin da suke tsaye ita da Abby, amma sai ta kasa amsata, ta shiga girgiza kai kawai. “Gul! Gul! Ina yayanki?” Jadda ta tambaya tana ɗagota daga jikin Abby, yanzu ma bata yi magana ba, sai takardar dake hannunta da ta miƙawa Abby, Abby ya karɓa hannunsa na rawa, dan sam zuciyarsa ta kasa gaya masa abu me daɗi a kan Arman a halin da ya ga Gul ta dawo bayan ta tafi kiran shi. _“Ina da tabbacin a lokacin da za ku riski wannan takardar jirginmu ya tashi. Dan haka kada ku sha wahala wurin naiman inda nake. Na daɗe da sanin shirin da kake a kaina Abby, kuma kamar yanda ka yi hasashe, ba zan taɓa baka kunya ba, babu wanda ya san gaibu, amma ina me tabbatar maka da cewa da ban san da wannan maganar ba da na saka hannu a takardun da za ka bani yau a wurin shagalin ƙara shekarata. Amma kuma tun da na riga na sani ba zan bar hakan ta faru ba Abby, na rasa ta wace hanya ya kamata ace na fahimtar da ku abin da nake son ku gane, na rasa da wani yare zan muku magana dan ku fahimta. Na zaɓi barin ƙasar Dubai ne ba dan komai ba sai dan nisanta kaina daga duk wani abu da ya shafi Majmu'at Shirkat Alhadi. Kuma ina me muku albishir da zan dawo bayan sati ɗaya. Abby kada ka shiga damuwa, Immi kada ki yi kuka, ki min addu'a, Gul kada ki zagi yayanki a kan abin da ya yi na ɗauki wannan hukuncin ne bayan dogon nazari.... Arman Iƙbal Alhadi!”_ Abby na kaiwa ƙarshen karatan takardar ya dunƙuleta a hannunsa, idonsa na sauya kala nan take. “Kai Iƙbal me ya faru?” Jadda ta tambaya tana riƙe shi. Cikin wani hali me kama da abin da ya fi tashin hankali ya kalleta. “Jadda me yasa kika faɗa masa abin da muke ɓoyewa?” Tun da ta ji wannan tambayar ta tabbatar da abin da take zargi. Shi kuma Abby ya san babu wanda zai sanar da shi face Jadda, ko Anwar ko ɗaya daga cikin 'Yayansa. Jadda ta sunkuyar da kanta. “Ban yi hakan da wata manufa ba Iƙbal, sai dan na gargaɗe shi kan kada ya bijire mana” Abby ya kasa magana, ya dafe kansa da ya fara juyawa, ita kuma Immi da ta kasa gane inda zancen ya dosa ta yi saurin ɓanɓare takardar daga hannun Abby domin ta karanta. A lokacin da ta gama karantawa sakin takardar ta yi, jikinta ya shiga rawa, haka idonta ya soma zubar da ƙwalla. “Iƙbal ɗana ya gudu!” Shi ne kaɗai abin da ta faɗa tana shirin faɗuwa. Abby da Gulzar suka yi azamar riƙota, suka tsayar da ita, Gul na bata haƙuri. Jin batun guduwar Arman ba ƙaramin faranta ran Faisak da mahaifnsu ya yi ba. Kuma duk da ya ga halin da mahaifiyarsa, ƙaninsa, matar ƙaninsa da kuma 'yar ɗan uwansa suka shiga bai sa ya fasa faɗar baƙar magana ba. “Da ma me kuke tsammani daga wurin nakasasshe kamar wannan?... Nakasasshen ma wanda ya fito daga jinin Indiyawa” Wata daga cikin 'yan uwan Immi ta nufo shi a zafafe, dan ta gane cewa magana ya yada musu. “Mu ba Indiyawa ba ne. Dan haka kada ka sake cewa mu indiyawa ne” “To yanzu da kika iyo kaina dukana za ki yi? Na ce dukana za ki yi?” Nan fa cecekuce ya kaure a tsakanin dangin Abby da na Immi. “Ya isheku haka!” Faɗin Immi cikin ƙaraji. Hakan ya sa wurin ya yi tsit. “Ku barmu mu ji da ɓatan ɗanmu mana. Bayan wannan abin da ya faru da mu kuma me yasa kuke son ƙara mana wata damuwa?” Ta ƙarashe tana kwantar da kanta a kafaɗar mijinta da ta jingina da shi, sannan ta fashe da wani sabon kukan. “Ko kana ina yanzu haka ɗana?” °•°•°•°•°•°•°•°•°•°•° A hankali Arman ya leƙa windown dake a ta gefensa, ya kalli gajimare dake ƙasan jirginsu da ya tashi sama, kafin ya juyo ya kalli Ivana da Adam dake kusa da shi, dan tikitin kujeru ukun dake kusa da juna suka siye, kasancewar jirgin da suka hau babba ne. Ita Ivana kallo take a system, yayin da Adam ke cin abinci hankali kwance, amma shi sam ji yake hankalinsa ya ƙi kwanciya, da ko wani ƙarin daƙiƙa da jirginsu ke nufar birnin Regen dake ƙasar Germany, wanda ya kasanci gari mafi kusa da Bavarian forest ji yake kamar yana ƙaura daga duniyarsa zuwa wata duniyar da bai sani ba. Idonsa ne ya kai kan agogon dake tsintsinyar hannunsa, a hankali ya furzar da iska daga bakinsa, sannan ya gyara glasses ɗinsa tare da tura sumar dake kan goshinsa baya. Ya lusmhe makafin idonsa yana jin wani abu na rashin daɗi na masa yawo a zuciya. “Arman? Shu fi (Me ya faru)” Adam da ya lura da shi ya tambaya. Amma sai ya buɗe idonsa yana girgiza kai. Sannan ya ɗauke kansa ya jingina da kujera yana kallon window, kasancewar shi ne a window seat. Adam ya kira ɗaya daga cikin flight attendant. Jim kaɗan ta iso seat ɗinsu tana murmushi, kamar yanda aka saba ganinsu, cike da girmamawa ta risina tana faɗin. “Me kake buƙata yallaɓai?” “Ruwa me sanyi” Adam ya amsa. “An gama yallaɓai” “Sannan ki tafi da wannan, na kammala” Ta sake amsawa, sannan ta ɗauke trayn da ya gama cin abinci da shi, ta juya ta tafi, sai da ta kawo ruwan, sannan ya bawa Arman. “Ka sha” Arman ya kalli ruwan, sannan ya kalle shi, ya sa hannu ya karɓa, ya sha sosai, sannan ya aje yana sake ɗauke kai ba tare da yace komai ba. Hankalinsa gaba ɗaya yana kan agogon hannunsa, dan jira kawai yake 12 ta cika. Kuma a dai-dai lokacin da ta cika, ya lusmhe idonsa, a hankali ya furta. “Eid Milad sa'id ya Arman (Happy birthday Arman)!”. Salma Ahmad Isah ✍️ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-7 *Furstlich zeil Hotel, Lower Town, 168, Regen, Germany.* *11:04 na rana.* IVANA POV. A karo na uku ta sake ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Arman, sannan ta janye hannunta tana jiran ya buɗe. Jiya bayan jirginsu ya sauƙa a birnin Regen kamfanin da Arman ya ɗauka musu domin su kaisu duk wasu wuraren buɗe ido ne suka aiko wakilinsu ya ɗaukesu a airport. Kuma shi ne ya kawosu wannan hotel ɗin, inda suka kama musu ɗakuna uku, kowa da ɗakinsa. Tun a daren jiya ita da Adam suka tsara cewa za su je siyayya, dan haka ne ma yanzu suka shirya domin fita, kuma wakilin kamfanin da kan zaga da masu yawon buɗe idon na tare da su, dan shi ne wanda zai zaga da su a cikin gari, kafin zuwa gobe kuma su nufi Bavarian forest, inda kaddararsu ke jiransu a cikinsa. Kallon Arman ta yi, wanda ya buɗe ƙofar a kasalance, sanye yake da sweate shirt eggplant color, da farin chinos trouser, idonsa saye cikin glasses ɗinsa, wanda rims ɗinsa ya kasance white color. Babu ko takalmi a ƙafarsa, hatta da gashin kansa a hargitse yake, alamar bai ga gyara ba. Shi ma kallonsu ya tsaya yi su duka ukun, sannan ya bar ƙofar ɗakin a buɗe, ya juya cikin ɗakin. Ivana da Adam suka shiga ɗakin, yayin da ɗan rakiyarsu me suna Hans ya tsaya a waje. Ivana da Adam kallonsa kawai suke, har ya zauna kan sofa yana ɗauke kai, ba tare da ya bari sun haɗa ido ba. Ivana da Adam suka dubi juna, dan sun gane cewa kamar abokinsu na cikin damuwa. “Za mu je siyayya ne, idan kana da ra'ayin zuwa” Cewar Adam. Kansa ya girgiza yana shafa sumar kansa, tare da ƙifta idonsa a hankali, kuma bai bari ya kallesu ba. “Arman” Ivana ta kira tana zauna a gefensa. Dubanta kawai ya yi yana aje wayarsa dake riƙe a hannunsa, dan ba amfanin komai yake da ita ba, hasalima a kashe take, domin ba ya so wani na gida ya kirashi. “Kamar akwai abin da yake damunka?” Ta tambaya tana son su haɗa ido, amma ya ƙi bata damar hakan. Tun jiya da suka baro Dubai har zuwa yau ɗin nan ba ya jin daɗi sam, duk tsayin awa shidan da suka kwashe a jirgi kafin su iso Regen sam bai ji daɗinsu ba, hatta yanzu haka da yake zaune ba ya jin daɗi. Kuma jinyar ba a jikinsa take ba, a zuciyarsa take. “Ka ga Arman! Idan har kana jin hukuncin da ka yanke bai maka ba muna tare da kai. Idan kana jin cewa ka yi nadamar abin da ka aikata za mu kasance tare da kai, wannan rayuwarka ce, kuma lokacinka ne, ka yi abin da ya dace a lokacin da ya dace, ka yi tunani me zurfi a kan wannan hukuncin, duk abin da ka yanke za mu amince da shi. Ko da kuwa kana so mu koma Dubai a ranar yau ne za mu koma, mu dai burinmu shi ne ka yi farin ciki!” Cewar Adam yana dafa shi, ya ɗaga kai ya kalli Adam, sannan ya kalli Ivana dake jinjina masa kai, alamun abin da Adam ya faɗa haka ne. Ya sauƙe ajiyar zuciya me nauyi, sannan ya shafa kansa yana rinte ido. “Mu za mu tafi siyayya. Ka tabbatar ka yanke hukunci kafin mu dawo” Cewar Ivana tana miƙewa, tare da ɗaukan bag ɗinta, ta bubbuga kafaɗarsa sau biyu, sannan tace da Adam su tafi, suka tafi suka bar shi cikin tunani me zurfi. Ivana da Adam sun zaga sosai a cikin garin Regen, kuma tun a cikin garin ma Adam ya samu ya ɗauki wasu hotuna. Sun shiga manyan kantuna da gidajen abinci, domin sun ɗauki alƙawarin shiryawa abokinsu babban bikin ƙarin shekara. Ta hanyar siya masa kyautuka da dama. Yayin da suke siyayya a cikin wani shagon da ake saida kayan tarihi irin na da can. Adam ya yi arba da wata sarƙa a cikin wani kit, zaren sarƙar baƙi ne, pendant ɗinta kuma wani abu ne me kama da key, kuma daga ganinsa an ƙera shi ne da gold. Tsabar muhimmanci da darajar sarƙar a keɓe take a cikin shagon, an sanyata cikin wani glass me ɗaukar ido. “Wannan ta kai kimanin nawa?” Ya tambaya yana ɗaukan glass ɗin da aka sakata a ciki, me kantin ya yanko maƙudan kuɗaɗe ya faɗa, duk da sarƙar ta yi tsada hakan bai sa Adam ya fasa siyawa Arman ita ba, domin ko da zai ƙarar da kuɗin da yake da shi zai yi domin faranta ran Arman. Ita kuma Ivana sabon takobin fencing ta sai masa, da wasu ƙanun kyautuka da ta san za su burgeshi. *Dubai...* “Ina zuwa!” Faɗin Maama dake wanke hannu a sink, yayin da take kallon ƙofar gidan da ake ƙwanƙwasawa. Hannunta ta goge, sannan ta nufi ƙofar ta buɗe, mamaki ya kamata, ganin Sayyid Iƙbal Alhadi da matarsa Zahra, da kuma 'yarsu Gulzar. “Barkanku da zuwa... Ku shigo ciki mana” Ta faɗa tana murmushi, tare da buɗe ƙofar gaba ɗaya, Abby ya ɗan yi murmushin yaƙe yana mata sallama, ta amsa yayin da yake shiga falon, ita kam Immi babu wata alamar walwala tare da ita, ta yi sallamar kamar da aka mata dole, sannan ta shiga falon ita ma, Gulzar kuwa bayan ta yi sallamar sai da ta gaida Maama sannan ta shiga. Su duka ukun a falo suka zauna, yayin da Maama ta koma flat kitchen ɗinta ta ɗauko abin sha, ta aje musu a center table suna sake gaisawa. “Shin Adam yana nan?” Abby ya tambaya, mamaki ya sa Maama ta kallesu, kafin cikin kokwanto tace. “Adam? Ai jiya suka tafi Regen, Germany, kuma yace min tare da Arman za su tafi, ko dai Arman ɗin bai samu zuwa ba?” Abby ya dafe kansa. Yayin da hawaye ya zubowa Immi. “Arman guduwa ya yi ya bar gida ba tare da saninmu ba, yanzu haka ba dan kin faɗa ba da ba mu san inda yake ba” Maama ta yi shiru, ta san irin haka sam ba daɗi. Da ace ita ce a matsayinsu da yanzu ita ma nata hankalin a tashe yake. “Sayyid Iƙbal ka yi haƙuri, haƙiƙa abu irin wannan babu daɗi, amma su yaran yanzu idan har suka yanke hukunci babu wanda ya isa ya tablnƙwarasu, dan za su iya aikata abin da suke so a ɓoye ba tare da sun sanar da kai ba, ku yi haƙuri ku ci gaba da masa addu'a” Abby ya dubi Maama, sannan ya yi murmushi kawai. Dan shi tun da har ya san inda yake matsala ta kau, Arman ba ƙaramin yaro ba ne da zai ɓata, ya sha yin tafiye-tafiye irin wannan, kuma shi kaɗai, dan haka yanzu hankalinsa ya kwanta, domin ko ba komai idan ya gama kwanakin nasa a Regen dole zai dawo gida!... “Allah ya kareka shugaba!” Shi ne kawai abin da ya furta. Dan ba ya jin yana da wani abin cewar bayan wannan. *Regen, Germany.* Adam ya ja tsaki a karo na barkatai, yayin da suke duban ƙofar hotel ɗin da suka kwana ciki, tsaye suke shi da Ivana da kuma Arman, a jikin motar da suka yo hayarta yau, domin yau ne za su shiga Bavarian forest. Ga shi rana ta kusa faɗuwa, amma har yanzu Hans bai zo ba. Ivana na sanye cikin purple crop top, me ɗauke da ratsin baƙi-baƙi, da kuma wideleg bleach jeans, takalminta farin orthopedic sneakers ne. Gashinta ya sha gyara cikin style ɗin side braid pony tail, ta saka wani purple hair clip a karshen side braid ɗin. Yayin da ta ɗora baƙar wide brim hat a kanta, wadda za ya sauƙaƙa mata zafin ranar da ake, idonta manne da shade. Adam kuma na sanye da maroon chinos trouser, da farar shirt, wadda ya ɗora mata ash hoodie a sama. Shi ma ya saka shade, saboda duk da rana ta kusa faɗuwa akwai zafinta har yanzu. Ƙafafunsa kuma na cikin farin huaraches. Yayin da Arman ke sanye da gray khaki trouser, da farar shirt, wadda ya ɗorawa black bomber jacket a sama. Saɓanin sauran da suka saka shade shi glasses ɗinsa na kullum ne a idonsa. Ƙafafunsa na cikin farin canvas. Shi ma tsakin ya ja yana shafa sumar kansa, sannan ya dubi su Adam. “Ya kamata mu tafi fa, dan da alama wannan ba shi da niyyar zuwa.” “To da kake cewa mu tafi mun san hanyar ne?” Cewar Adam, ya musu banza ya buɗe driver seat na motar ya shiga, har ya tada motar Ivana da Adam na kallonsa. Ganin ba su da niyyar shigowa motar yasa ya kallesu. “Dare ne yake shirin yi, da dare ya mana a hanya mu ɓata, gara daren ya mana a cikin dajin. Matambayi ba ya ɓata, kuma Bavarian forest sannanne ne a ko ina, ba za mu rasa wani ɗan rakiyar ba a hanya... Dan haka ku zo mu tafi kawai” Ivana da Adam suka haɗa ido, kamar kar su bi shawararsa su bari sai Hans ya zo, amma da yake tsautsayi ba ya wuce rana sai suka amince, suka shiga mota suka ɗauki hanyar Bavarian forest. Da ko wani taƙi da suke wucewa domin nufar dajin ƙaddararsu suke tunkara ba tare da sun sani ba. Domin da ace sun san abin da suke tunkara da sun yi tariyar zamanin baya, sun cire ranar da suka yanke shawarar zuwa Bavarian forest a cikin kwanakinsu na duniya. Kasancewar ba su san hanya ba ya sa suke tambaya, har Allah ya sa suka samu damar kutsawa cikin dajin sosai, dan ma suna tsayawa jiran Adam ya ɗauki hoton abubuwan birgewa dake dajin, da haka suka iso inda hanya ta rabu biyu. Kokwanto ya sa Arman ya tsayar da motar, dan a cikin hanyoyin biyu bai san ta ina zai bi ba, ga shi kuma babu kowa a wurin bare su yi tambaya. “Ina ya kamata mu bi?” Ya tambayi Adam dake zaune a gefensa, Adam ya ɗaga kansa ya kalli hanyoyin biyu. Kuma a lokacin abin ya faru, a lokacin ƙofofin ƙaddarorinsu suka buɗe. Domin zuciya ɗaya Adam ya ɗaga hannunsa ya nuna hanyar da ta yi dama. “Wannan hanyar ta maka kama da ana binta? Ji yanda ciyayi suka rufe hanyar fa, kuma sam babu alamar ana bin hanyar a yanzu” Cewar Ivana dake baya. Arman da Adam suka dubeta. “Ai dole hanyar ba za ta yi kama da ana bi ba, saboda an fi shigowa dajin a mota, so ba lalle ta nuna wata alama ba... Kuma ni jikina ya na bani cewar wannan ita ce hanyar” “Arman kar ka saurare shi, saboda ni dai na ce waccan ita ce hanyar.” “Ivana bari mu fara bi ta nan ɗin, idan ba ita ba ce sai mu dawo” Cewar Arman da shi ma tasa zuciyar ta raya masa cewar hanyar da Adam ya nuna ita ce wadda za su bi. Ya tada motar, sannan ya juya kan motar zuwa hanyar da za ta sauya rayuwarsu. Har motarsu ta shige hanyar, a cikinsu babu wanda ya lura da allon sanarwar dake gefen hanya, wanda aka rubuta ‘CHEETAHS AHEAD. KEEP DISTANCE!’. *Da misalin 10:22 na dare.* Tantina (tent) uku ne kafe a tsakiyar wani fili, domin wurin da babu yawan dogayen bishiyu suka samu suka kafa tent. Yayin da motarsu ke fake kusa da tents ɗin, sun aje wasu gingimen bishiya guda uku wanda suke zaune a kai, yayin da wutar da suka hura domin ƙarawa daren nasu armashi ke a ci. “Akwai sanyi sosai a wurin nan” Faɗin Ivana tana ƙara nannaɗe hannunta cikin zip hoodie ɗin dake jikinta. Arman ya yi dariya yana shan drink ɗin dake hannunsa, yayin da Adam ke duba hotunan da ya ɗauka jiya a cikin garin Regen. “Adam!” Ivana ta kira tana dubansa, shi ma ya kalleta cikin alamun ya aka yi?. Da ido ta masa alama, take ya gane abin da take nufi, dan haka suka miƙe a tare kowa ya shiga tent ɗinsa, yayin da Arman ke binsu da kallo yana tambayar abin da ya faru. Cikinsu babu wanda ya amsa masa, dan haka ya miƙe yana kallon tents ɗin nasu, har suka fito, kowa a cikinsu hannunsa riƙe da gift box. “Barka da ƙarin shekara abokina, ina tayaka murna” Faɗin Ivana tana miƙa masa box ɗin kyautukan da ta sai masa, Arman ya yi dariya yana kallonsu, sannan ya saka hannu ya karɓa yana mata godiya, shi ma Adam ya miƙa masa nasa box ɗin guda ɗaya, wanda silar ƙaddararsu ke ciki, Arman ya aje wanda Ivana ta ba shi kusa da inda yake zaune da, sannan ya karɓi na Adam, ya masa godiya yana rungume shi. “Na gode sosai abokina...” Ya kalli Ivana dake kallonsu, sannan ya mata alama da hannu tare da faɗin. “Taho mana” Ta yi dariya sannan ta shiga space ɗin da suka yi creating ma ita, su duka abokan suka rungume junansu, a lokacin kuma kunnen Adam ya jiyo wani sauti me kama da kukan damisa. Hakan ya sa ya firgita ya janye jikinsa yana waige-waige. “Hey lafiya?” Ya kasa amsawa Arman, sai bin zagayen wurin da suke yake da kallo. “Adam” Ivana ta faɗa tana dafa shi, banda bugu babu abin da ƙirjinsa ke yi, kamar mace. “Me ya faru?” “Kamar... Kamar kukan damisa” Ya amsa a tsorace. “Damisa kuma? A nan ɗin?” Arman ya tambaya, sannan ya kunna wata touch light ɗinsu me haske, ya shiga haska dajin, amma shi bai ga komai ba. “Kai babu komai fa a nan” Adam ya haɗiyi yawu yana girgiza kansa, in dai baiwar ji to Allah ya hore masa kamar maciji. Dan haka ba ya jin cewa kunnensa ne ke haihuwa, yana da tabbacin ya ji kukan damisa. Amma da su Ivana suka ƙaryata shi sai ya haƙura ya zauna yana baza ido kamar ɓera a tarko. Yayin da Ivana ta ɗauki guitar ɗinta ta soma kaɗawa, saboda Arman da ya buƙaci hakan. Duka kyautukan da suka ba shi sai da ya buɗe su a lokacin, amma duk ciki babu wanda ya fi burge shi sama da makullin ƙaddararsu, wato sarƙar da Adam ya ba shi, dan sam kasa jurewa ya yi sai da ya saka sarƙar a wuyansa yana ta jin daɗi. Sun ɗau lokaci sosai a wurin suna hira tare da cin abinci, kafin suka yanke shawarar kowa ya shiga ya kwanta, kasancewar Adam a tsorace yake yasa yace dan Allah Arman ya yarda su kwana a tent ɗaya, amma fir Arman ɗin yaƙi. “To wai kai yanzu da kake haka ta ya za ka zama jarumi? Shi fa namiji da jarumta aka san shi, kalli Ivana, ita ma ita kaɗai za ta kwanta, mi ye zai cinyeta? Da har kai da kake namiji za ka ji tsoron kwana kai kaɗai” Da wannan batu dai ya ƙwararawa kansa gwiwa ya shiga tent ɗinsa yana karanto duk addu'ar da ta gifto cikin tunaninsa, dan a tsorace yake matuƙa. A lokacin da kowannensu ya shiga tent ɗinsa, Cheetah ɗin dake laɓe a cikin daji ta juya zuwa wata hanyar!... 😳 Salma Ahmad Isah ✍️ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-8 *Bavarian forest, Germany.* Yayin da hasken rana ya mamaye duniya, matasan uku suka shirya tsaf, domin zaga dajin da suka kwana ciki. Tun bayan da suka yi karin kumallo suka nannaɗe tents ɗinsu. Suka haɗa kaf kayansu cikin wasu dogayen backpack irin na matafiya. Arman na sanye cikin wani 3qtr milk color, da farar hoodie mara nauyi, wadda ya ɗorawa black denim jacket a samanta. ƙafafunsa cikin takalmin timberland. Adam kuma na sanye da blue jeans da baƙar shirt, ya ɗora casual Oxford shirt a saman rigar, sai bakar p-cap da ya saka. Yayin da Ivana ke sanye da Orange T-shirt, sai jeans overall (corpenta) da ta saka, gashin kanta kuma na cikin French braid. Kowanne a cikinsu na goye da jakar kayansa, yayin da suka kutsa cikin dajin cike da farin ciki da annashuwa, duk da har yanzu shi Adam a ɗarare yake, dan a tsorace yake ɗaukan hotunan wasu wuraren da suke da ban sha'awa. Duk da sam inda suke kutsawa a dajin bai yi kama da mutane na yawan bi ba bai sa sun fasa shiga ciki ba. Har suka iske wani kyakkyawan dausayi dake tsakiyar dajin, akwai nau'ikan bishiyoyi da tsirrai a wurin gwanin ban sha'awa, sannan akwai kogi dake a ta gefe, a gefe guda kuma akwai wani babban dutse da yake bayar da ruwa, wurin ya haɗu matuƙa. “Wow wow wow! Amma wurin akwai ban sha'awa” Faɗin Ivana tana ɗaga kanta tare da ƙarewa wurin kallo, yayin da shi kuma Arman ke gefe ta wurin kogin yana kallon yanda ruwan wurin ke gudana, shi kuma Adam ya riga ya fara ɗaukan wurin a hoto da camera ɗinsa. “Ivana gyara na ɗaukeki hoto” Ya faɗa yana saita camera ɗin a kanta, Ivana ta gyara tana murmushi, ya ɗauki hoton yana dariya, shi ma Arman ya matso yana faɗin a ɗauki hoton da shi, ya dafa Ivana Adam ya ɗaukesu tare. Suka sauya style suna jiran Adam ya ɗaukesu hoto, a cikin camerar Adam ya hango mutuwa. Dan haka ya sanƙare yana wangale duka idanuwansa, jiki a saɓule ya sauƙe camerar yana rawar jiki kamar an jona masa lantarki. “Ka ɗauke mu mana, ka wani tsaya a nan kamar saƙago” Faɗin Arman yana gyara glasses ɗinsa, Adam ya soma ja da baya, sannan cikin karkarwar hannu ya ɗaga ɗan yatsansa, ya yi nuni da bayansu, hakan ya sa cike da mamaki Ivana da Arman suka dubi juna, kafin Ivana ta juya tana faɗin. “Wai me ka gani da ka...” Haɗiyewa sauran kalaman ta yi, tare da binsu da yawun bakinta tana zaro ido, kamar yanda ta yi kyakkyawan gani haka shi ma Arman ya yi, dan yana juyawa suka yi ido huɗu da Cheetah ɗin dake saman dutsen da yake zubar da ruwa. Ba su tsaya ɓata lokaci ba suka ce ƙafa me na ci ban baki ba? Kowa a cikinsu ya ranta a na kare, gudu suke Cheetah ɗin na binsu, Adam ya fi koea ruɗewa, dan a gudun ma shi ne a kan gaba, dan tun da ya zo duniya bai san wani abu da ya firgita shi sama da wannan ba, sanin cewa Ivana me rauni ce ya sa Arman ya ruƙo hannunta yake janta suna gudu tun ƙarfinsu. A yunƙurin ceton rayukansu suka faɗa cikin wani kogo dake bayan dutsen da Cheetah ɗin take, kuma suna shiga cikin kogon ba su tsaya wata-wata ba wurin naiman maɓoya, Arman ne ya fara ganin wata tsohuwar ƙofar katako dake cikin kogon, dan haka ya yi azamar saka duka hannayensa biyu, tare da ƙarfin da Allah ya wadata shi da shi ya buɗe ƙofar. “Ku zo ku shiga” Ya faɗa ba tare da ya tsaya duba abin da yake a bayan ƙofar ba, ya janyo hannun Ivana ya turata, an ce idan ka ga mutuwa idonka rufewa yake, tabbas idanuwansu sun rufe, domin har suka gama shigewa ƙofar sam ba su lura da ina suke shiga ba. Abin da zai biyo bayan shigarsu wannan ƙofar sai ya fiye musu su tsaya wannan Cheetah ɗin da ta biyosu ta cinye naman jikkunansu ɗanye. Domin masifa da bala'in da zai biyo baya babu hankali ko tunanin da zai iya hasaso shi... Yanzu ne labarin zai soma, sai a yanzu ne za mu kama ainahin hanyar da labarin yabi, yanzu ne muka saƙo zaren labarin, domin gane warwararsa, sai kun ji abin da ya biyo bayan shigewarsu cikin wannan ƙofa... *Wani Zamani...* Wani zamani na nufin zamanin da ya shuɗe kafin samuwarmu, ko kuma wanda zai zo bayan wanzuwarmu, zamani na zuwa ya wuce kamar wucewar damina da rani... Sannan zamani ya kan shuɗe, har a manta shi a duniya, matsawar babu masu bada labarin wannan zamanin... Sunan zamani na wakiltar shekaru 100 da suka suɗe a baya, ko waɗan da za su zo a gaba... A kan iya gane bambancin zamani ta hanyar tufafinsu, abincisu, gine-ginensu da kuma kalar yarensu... * Wani kyakkyawan daji ne, ko ina ka kalla koren ganye ne ke kaɗawa a cikin iskar Allah, dogayen bishiyu da ciyayin da suka ƙawata ƙasa su ne a ko ina. Kuma duk girman dajin babu komai cikinsa sai ginin wata bukka ƙwara ɗaya tal, wadda aka yi ta da busasshiyar ciyawa. (Budu) Daga bayan bukkar, wani farin dattijo ne durƙushe, yana tsinkar 'ya'yan itaciyar da suka nuna har suna faɗowa daga jikin bishiryarsu. Wasu kayan saƙi ne sanye a jikinsa, wanda za su shaida maka daga zamanin da yake, gashin kansa dogo ne, domin har ya sauƙa gadon bayansa, duk da rawanin da ya yi a kansa. Wata iska me matuƙar ƙarfi ce ta fara kaɗawa a dajin, hakan ya sa dattijon ya miƙe tsaye yana kallon dogayen bishiyun dake wurin, waɗan da ke kaɗawa da ƙarfi, sakamakon ƙarfin iskar da ake. Kansa ya juya ta ɓarin damansa kaɗan, nan ya ga wani jan kyalle dake ɗaure a saman bukkarsa na shirin sulmiyewa ya faɗo. Hakan ya sa ya firfito da idonsa cike da abin da ya zarce a kira shi da mamaki. Bakinsa na rawa ya juya ya shiga bin dajin da kallo, amma bayan iskar dake ƙara ƙarfi babu kowa babu komai. Mamaki bai ƙara kama shi ba sai da ya ga jan ƙyallen ya kunce ya faɗi ƙasa... A nan ne ya tabbatar da wani abu guda, lalle ranar da ya daɗe yana jiran isowarta ta zo, ranar da ya shafe sama da shekaru ashirin na rayuwarsa yana rayuwa a wannan dajin domin ta zo, ranar da za a yi wasu baƙin matasa uku, daga wani zamanin zuwa nasu... “Tabbas! Baƙin matasa uku sun samu shigowa duniyarmu. Domin zama silar kawo ƙarshen mulkin zalunci. Sun zo domin tada gagarumin yaƙi da yake dai-dai da yaƙin duniya... Ƙaddara ba ta da siffa, ta kan juya rayuwar ɗan adam ta ko wace siga, sannan ta kan iya maida sama ta dawo ƙasa cikin abin da bai fi ƙiftawar ido ba. Lalle ƙaddara ita ce ta zamto silar wanzuwar waɗannan matasa a wannan duniya tamu... Wannan ƙaddara ita ce ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwar waɗannan matasa, daga zamaninsu zuwa namu...” Kwandon kayan marmarin dake hannunsa ne ya suɓuce ya faɗi, yayin da ya ga haske ya fara mamaye dajin, saurin durƙushewa ya yi a ƙasa yana me godiya da mai duka... * Yashe suke a kan ciyayin dake kusa da wata ƙatuwar bishiya, idan ka musu kallo ɗaya sai ka ce a mace suke, amma kuma ba a macen suke ba, wani dogon bacci suke me kama da suma. Arman ne ya fara motsawa, kafin ya buɗe idonsa yana dafe kansa da ya sara lokaci guda. Idonsa ya rufe ya sake buɗewa, amma saboda glasses ɗinsa a fashe suke ya sa ba ya gani da kyau, a daddafe ya miƙe zaune yana yarfe hannu, saboda Adam da ya danne masa hannun nasa, glasses ɗin ya cire, ya kamo ƙasan rigarsa ya goge shi, sannan ya mayar idonsa, a nan ne ya gane cewa glasses ɗin ne ya fashe. Tsaki ya ja, dubansa na kaiwa kan Adam dake kwance, ya sake jan wani tsakin tare da saka hannunsa ya ɗaka masa duka. “Mun mutu... Damisa ta cinyemu!” Ya farka da wannan batu a tsorace, amma ganin Damisar ba ta cinyesu ba ya sa ya fara son kwantar da hankalinsa, kusan a tare suka dubi Ivana dake can nesa da su, hakan ya sa Arman ya miƙe ya nufi inda take, ita ma ya tasheta. “Wai a ina muke ne?” Adam ya tambaya yana miƙewa tsaye, yayin da Arman ya cillar da tsohon glasses ɗinsa da ya fashe, Ivana kuma ta ba shi wani domin ya saka, sai da ya saka glasses ɗin sannan shi ma ya tsaya ƙarewa wurin kallo, daji ne fetal, ba gida gaba ba gida baya. “Kai! Ina ƙofar da muka shigo?” Cewar Ivana tana waige-waige, amma sam babu alamar ta a wurin, shi ko Arman shiru ya yi yana wani lissafi a cikin kansa, idan zai iya tunawa bayan wannan Cheetah ɗin ta biyosu sun buɗe wata ƙofa sun shiga, bayan da suka shiga ƙofar kuma ba su iya ganin komai ciki sai haske, sai wani abu me kama da iska da suka ji ya kwashesu, to daga nan ne ba su sake sanin me ke wakana a duniya ba sai yanzu... “Arman a ina muke ne?” Adam ya tambaya yana riƙo Arman, shi kansa Arman ba shi da wannan amsar, domin bai san a ina suke ba, bai san ya aka yi suka zo nan ba. A hankali ya ɗan matsa bayan bishiryar da suke kusa da ita, nan ya hangi wata bukka guda ɗaya tal. “Ga wani ɗaki can, mu je mu duba” Ya faɗa yana ɗaukan jakarsa, tare da goyata a bayansa. Suma nasu kayan suka ɗauka, sannan suka bi shi, shi dai Adam ya san cewa ɗakin bukka ce, su kuma sauran ba su san wani abu me kama da hakan ba. Shi ya sa tun kafin su ƙarasa kusa da bukkar suka fara taradaddin a duniyar da suke. Ko da suka iske bukkar sai aka tsaya kallon-kallo, dan ba su san me za su iske a ciki ba. Arman ne ya fara ƙundun balar nufar ƙofar, yana taku a hankali, hannunsa ya sa ya ɗaga wani abu me kama da labule da ya saya ƙofar, hakan ya ba shi damar ganin cikin ɗakin. Babu komai a ciki face tarin littattafai irin na da, da kuma wasu takardu da aka yi su da fatar dabbobi, sai wani gadon ciyawa dake a gefe, sannan wani gajeren teburi, wanda a kusa da shi wani farin dattijo ne zaune. “Barka da zuwa JAGORA” Su ne kawai kalaman da dattijon ya furta yana ɗora ido a kan Arman. Shi kuma Arman tsaye ya yi yana kallon tufafi da kayan ɗakin mutumin, ko kusa ko alama bai yi kama da wanda yake rayuwa a zamaninsu ba, mutumin ya fi kama da irin mutanen da suka rayu a baya. Shiru suka yi su ukun, yayin da suke zaune gaban dattijo, banda kallonsa ba abin da suke, suna jiran ya amsa musu tambayoyin da suka soma masa, shi kuma sai murmushi yake musu, kamar wanda ya san da zuwansu. “Ina ne nan?” Arman ya sake nanatawa datijjon tambayar da Ivana ta fara masa tun ɗazu. Kuma sai yanzu ya samu damar ba shi amsa. “Hayy al- Umda!” Arman Ivana da Adam suka dubi juna cike da kokwanton da ya zarce na da, su har yanzu sun kasa gane abin da yake faruwa, amma Arman ya fara fuskantar wani abu guda... “Ban taɓa jin sunan dajin nan ba, kuma mu a Bavarian forest muke ba Hayy al- Umda ba” Cewar Ivana. Dattijo ya yi murmushi, sannan cikin larabcinsa me matuƙar daɗi da bawa ko wani harafi hakkinsa yace. “A halin yanzu kun bar zamaninku matasa, a yanzu kuna zamaninmu ne, a ƙalla shekaru 1000 baya!” Wani abu ne ya bada sautin tau a ƙirjin Adam, dan zai iya cewa ya riga kowa sauraron shekaru dubu ɗayan da aka furta. Ita kuma Ivana sai ta ji kamar ba ta fahimci abin da yake faɗa ba, saboda kalar larabcin da yake ya sha banban da nasu, nasa kyakkyawan larabci ne irin wanda ke cikin Alkur'ani me girma. Su kuma ba da shi suke magana ba, dan haka kalaman nasa suka mata wuryar ganewa, duk da taso ta gane, amma da ta ɗora maganar a mizanin hankali sai ta ƙi yarda da gaskiyar. Shi ko Arman idonsa ya lumshe kawai, domin tun da ya kalli mutumin ƙwaƙwalwarsa ta fara raya masa hakan, amma ta ya ya ke nan? Ta ya mutumin da yake rayuwa a 21st century zai dawo 11th century?... Taya hakan za ta kansace?... “Na san cewa ba lalle wannan maganar ta zauna a kanku ba, domin kuna ganin kamar hakan ba me iyuwa ba ne... To yau ya iyu a kanku, kuma wata ƙila ku zamto ababen misali, domin gagarumin abin da za ku tunkara a gaba!” Dattijo ya sake faɗi. Arman ya buɗe idonsa, sannan ya kalli tsohon. “Ya za'ayi mu koma gida!?” Ita ce kawai tambayar da ta zo ransa, dan bayan ita kuma ba ya jin yana da abin faɗe. Tun da ya furta tambayar Ivana ta gaskata abin da datijjon ya faɗa ɗazu, amma ta yaya su da suke rayuwa a zamanin da dogayen gine-gine suka yawaita a ko ina, da wayoyin hannu, da kafafen sada zumunta, da ababen hawan zamani, da ci gaban technology za su dawo rayuwa a zamanin da babu skyscrapers, babu wayoyin hannu, babu ababen hawan zamani, babu... Babu... Babu, babu komai sai yaƙi da rigima a kan mulki!. Shi ko Adam ko motsi bai kuma ba, ya ƙame ne ƙam yana kallon mutumin, saboda shi yana iya jin kyakkyawan larabcin da dattijon ke yi. “Dogon labari ne, amma zan yi ƙoƙarin gajarce shi, kafin ku koma gida yana da kyau ku san manya manyan masarautu ukun dake mulkin wannan duniya a wannan zamanin!...” Ta farko MAMLAKATUL MAJDAL, Babbar masarauta ce, wadda a zamanin nan sam babu kamarta, masarautar na da girma da yawan al'umma na ban mamaki. Mutanen masarautar na rayuwa cike da farin ciki da kuma samun ci gaba a ko wani lokaci, domin sun yi sa'a da samun adalin sarki da ya dace da mulkarsu. Masarautar na da tattalin arziƙin noma, kiwo da kuma ma'adanan ƙarƙashin ƙasa, kana gari ne da ya zamto cibiyar kasuwanci. MAMLAKATUL MAJDAL tana a ta yammacin saharar Majma, ginin masarautar ya sha banban da sauran masarautu, domin a zamanin za'a iya kiran masarautar da ta zamani. Masarautar na kewaye da ganuwa, wadda aka ginata da duwatsu da kuma taɓo. A batun yaƙi kuwa sun zarce tsara, domin a ƙalla masarautar na da kimanin mayaƙa dubu goma, waɗan da suke a shirya ga mutuwa, ga kuma kayan yaƙi masu firgita abokin gaba. Rayuwa a MAMLAKATUL MAJDAL tana da sauƙi... Masarauta ta biyu ita ce MAMLAKATUL AFSAH, Babbar masarautar Aljannu dake a cikin gajimare, Masarautar tana da kyau da tsarin gine-gine masu ban sha'awa irin nasu na waɗan da suke ba bil adama ba. A fagen yaƙi su ma ba'a barsu a baya ba, domin suna da dakaru da kuma kayan yaƙin tunkarar duk wani abokin gaba idan yaƙi ya taso. Masarauta ta uku kuma ta ƙarshe ita ce MAMLAKATUL JIYAD. Babbar masarautar da a masarautun bil adama ta kasance ta biyu. Masarautar da na kyau da kuma albarkatun ƙasa, sai dai kuma sun yi rashin sa'ar shugaba, domin Allah ya hallata musu mugu kuma azzalumin sarki. Babban sarki me daraja ta farko, wanda bayan shi a iko ƙasaita izza da mulki babu wani a cikin sarakunan wannan zamani, shi ne Malik WASIMUDDEN BIN ABDUL ADAL. Kyakkyawan matashi kuma jarumin yaƙi, sadaukin sarkin da babu me taka shi ya wuce... Shi ne yake mulkin MAMLAKATUL MAJDAL. A ƙalla shekarunsa talatin da biyar a duniya, ya gaji mulki ne a hannun mahaifinsa, Malik Abdul Adal Abu Wasim, wanda shi ma ya gada daga wurin nasa mahaifin. Ya fara gudanar da mulkinsa tun yana da shekaru asibirin da biyar, hakan ya faru sakamakon mutuwar mahaifinsa a wannan lokacin. Malik Wasimudeen ba shi ne kaɗai ɗan Malik Abdul Adal ba, domin bayan mahaifiyar Wasimudeen Malik Abdul Adal yana da wata matar, wadda ita ma take da ɗanta na miji guda ɗaya Amir Ehan Ibn Abul Adal. Malik Wasimudeen adalin sarki ne, wanda yake gudanar da mulkinsa cikin adalci da tausayinsa ga talakawansa, sannan kuma shi dodo ne ga maƙiyansa, ba shi da imani wurin hukunta mai laifi, kusancin dake tsakaninsa da kai ba zai sa ya ɗaga maka ƙafa ba idan har aka kamaka da laifi. A halin yanzu yana da aure, sunan matarsa DANEEN SANAH (Princess Sanah)... Tarihin yanda wannan aure ya kasance kaɗai abin mamaki ne, domin Daneen Sanah ta kasance 'ya ga abokin gabar MAMLAKATUL MAJDAL, tun zamanin mahaifin Malik Wasimudeen ƙiyayya da mahaifin Sanah ta samo asali. Kuma har zuwa zamanin yanzu da Wasimudeen ke shugabantar masarautar ƙiyayyar ba ta ƙare ba, duk da ya auri 'yarsa kuwa. Ta wani ɓangaren ma wannan auren shi ya ƙara rura wutar ƙiyayyar, domin Malik Wasimudeen ya auri Sanah ba da son ran mahaifinta ba, amma kuma ita da Wasimudeen suna son juna. Sarki me daraja ta biyu kuma shi ne MALIK SAFRAZ BIN ANSER, wanda yake mulkin MAMLAKATUL AFSAH. A tashin farko ba za'a kirashi da adalin sarki ba, kuma shi ba mugu ba ne, amma za'a aje shi a sahun masu yin mulkin taka haye. Wanda bai gaji mulki ba, sannan bai iya gudanar da shi ba. Asalin sarautar ba tasa ba ce, ba kuma ta mahaifinsa ba ce, sarautar ta kasance ta MALIK DHAAKIR BIN AQEED. Babban sarkin aljannu da ba'a taɓa kamarsa ba. Kaf duniyar nan Malik Dhaakir ɗansa ɗaya, wanda matarsa ta haifa masa shi. UWAIS BIN DHAAKIR, Feroza mahaifiyar Uwais ta kasance bil adama, yayin da Dhaakir ya kasance daga jinsin jinnu, hakan ya sa Uwais ya mallaki ƙudurat guda biyu. Ya kan iya yin duk abin da bil adama za su yi, sannan ya kan iya yin wasu abubuwan na aljannu, amma kuma jinsinsa ya fi ƙarfi a bil'adama, domin hatta suffarsa ta bil'adama ce. A ƙa'ida Uwais shi ke da gadon wannan kujera ta mulki. Amma sai Safraz da mahaifinsa Anser suka shirya maƙarƙashiya, domin ƙwace mulki a hannun Malik Dhaakir. Sun shirya kashe shi yayin da suke tsaka da wani yaƙi. Kuma shirin nasu ya tafi yanda suke so. Domin sarki Dhaakir ya mutu a wannan yaƙi, bayan mutuwarsa kuma suka shiga aiki kan shirinsu na biyu, wato yanda za'a yi mulki ya dawo hannunsu. Lokacin da 'yan majalissar sarki suka zauna suna tsara wanda ya kamata ace ya zama sarki bayan rasuwar Malik Dhaakir Safraz da mahaifinsa Anser suka bijiro da wata magana. Ta cewa a shekarun Uwais a wannan lokacin bai kamata ace ya zama sarki ba, domin a lokacin bai fi Shekarau 9 ba, kuma suka ƙara da cewar sam bai kamata bil'adama ya mulki aljannu ba, ai hakan ma zai zama kamar cin fuska ne ga jinsinsu, sannan hakan zubar da ƙima ne. Haka suka hurewa aminttatun sarki kunne, waɗan da suka ƙi kuma suka basu cin hancin dukiya, har sai da aka amince da sarki na gaba shi ne Safraz. Lokacin da wannan labari ya iske Feroza sai ta ɗauki ɗanta ta gudu ta bar Masarautar. A lokacin babu wanda ya damu da tafiyarta, sai a ranar da za'a tabbatar da Safraz a matsayin sarki aka zo naiman takobin sarki na mulki aka rasa. Domin Feroza ta ɗauke shi ta gudu, Kasancewar tun kafin Malik Dhaakir ya rasu ya mallakawa ɗanta Uwais shi. Hakan ya sa aka naɗa Safraz mulkin, amma kuma har yanzu bai zama cikakken sarki ba, domin sai ya mallakai wannan takobin ne zai zama cikakken sarkin MAMLAKATUL AFSAH. Hakan ya sa har zuwa yau hankalinsa ya kasa kwanciya, domin bai huta ba ya ci gaba da naiman Feroza a duniya ruwa a jallo, domin ya ƙwace wannan takobin da ta gudu da shi. Sarki me daraja ta uku shi ne MALIK CANGAZ, wato mahaifin Daneen Sanah, matar sarki Wasimudeen, kuma shi ne yake mulkin MAMLAKATUL JIYAD. Babban burin Malik Cangaz a duniya bai wuce kada ya tsufa ba, ko kaɗan sarkin ba ya son ya tsufa, duk da a shekaru a ƙalla ya kai sittin da ɗori. Hakan ya sa idonsa ya rufe ya shiga naiman bokaye da nalaman tsubbu, domin naima masa maganin tsufa a duniya. Duk da magungunan da ake ba shi na sakawa ya dawo yaro ba hakan ke hana jikinsa nuna tsufa ba a wasu lokutan. Domin idan yau ka ganshi yaro, gobe sai ka ga ya rikiɗa ya dawo tsoho. Kuma sam shi hakan bai masa ba, shi yasa ya ci gaba da naiman maganin tsufa a duk inda yake, da haka har ya samo wata ƙofa, wadda aka sanar masa da cewa daga zarar ya buɗe ƙofar nan ya shiga, da zarar ya fito babu shi babu komawa tsoho har zuwa lokacin mutuwarsa. Sai dai wannan ƙofar a kulle take, kuma babu wanda ya san inda makullin ƙofar yake. Babu wanda ya taɓa buɗeta, ballantana har a san abin da ke cikinta. Sai dai duk da haka Malik Cangaz bai sare ba, ya sa an kawo masa ƙofar, ya ajeta a cikin masarautarsa, yana naima tare da binciken inda mukullin ƙofar yake, amma har zuwa yau bai samu ba. Malik Cangaz azzalumi ne na gaban kwatance, domin ko kaɗan ba shi da imani. Bai san tausayin takala da na ƙasa da shi ba, ba shi da wata suffa ta shugaba na gari. Tsabar zalunci irin na sarkin haka kawai sai ya bushi iska yasa dakarunsa su je su tashi wasu ƙauyinka da ba'a yankinsa suke ba, domin kawai a samo masa bayi, ko a samo masa albarkatun ƙasa. Yana da dakaru na ban mamaki, waɗan da ya shayar da su ruwan zalunci, domin kamar yanda yake haka ya horesu. Uwa uba kuma kuma ga ƙarfin tsafi da yake amfani da shi wurin yaƙar duk wani wanda ya gagare shi. Tsabar son duniya da son mulki irin na Malik Changaz ya sa ya kashe matarsa a ranar da ta haifa masa yaransa mata 'yan uku, domin bokansa ya sanar masa da cewa yana buƙatar jininta domin haɗa masa wani tsafin da zai dawo da shi matashi. Hakan ya sa har wa yau ba shi da mata, sai yaransa mata 'yan uku. Ta farko ita ce Daneen SANAH, wadda soyayya ta ƙullu tsakaninta da Malik Wasimudeen har ta kaisu ga aure, sai kuma Daneen ASRA. Wadda son zuciya irin na Malik Changaz ya sa ya tsafaceta, ya sauya mata tunani da kuma alƙibila. Ya mayar da ita karen farautarsa, domin ko yaƙi zai je tare da ita yake tafiya. A cewar bokansa idan har ta ci gaba da zama a matsayin me ba shi kariya babu wani mahaluƙin da ya isa ganin bayansa. Duk da ita sam Daneen Asran ba ta so, domin yana juya mata tunani da hankali ne kawai. Ya mayar da ita jaruma, domin kaf cikin su ukun babu wanda ya kaita iya sanin salon yaƙi da kuma faɗa, Daneen Sanah ita ce kawai za ta iya kaita a wurin sanin makamar yaƙi, domin ita ma jaruma ce ta gaske. Ta ƙarshen kuma ita ce Daneen IQRAH, wadda ita ce ta kasance zinariya a 'ya'yansa, domin ita ko faɗa da koyon yaƙi bai bari an koya mata ba, a cikinsu ita ce shalele, ita ce wadda aka shagwaɓa da gata da kuma riritawa irin ta 'ya'yan Sarauta, hakan ya sa ta zamto gimbiyar ta gaske. Duka yaran Malik Changaz babu wadda bai tsaface ba, su duka ukun suna da ƙarfin tsafi a jikinsu, musanman ma Asra, domin ita nata ya fi na kowa, ita kuma Iqra ba ta da shi sosai, domin ba ta cika amfani da shi ba. Yayin da na Sanah ya zame mata alaƙaƙai, domin a halin yanzu so take ta rabu da shi, amma ta kasa, saboda ta hanyarsa Changaz yake aiko mata da jinya iri-iri. A cewarsa yana hukuntata ne a kan laifin da ta aikata na bijire masa... “...Waɗannan su ne masarautu da kuma sarakunan da suke mulkin wannan duniyar a wannan lokacin” A lokacin da ya kai ƙarshen dogon tambihin nasa Adam ya fashe da kuka yana dafe kansa, dan tun da ya fara jin labarin ya san cewa shikenan kuma, shi tasa ta ƙare, domin ba makawa sai ya mutu a cikin wannan duniyar. Ita ko Ivana hawaye ne suka soma zubo mata, na tunawa da Yumma, Hana da Imran, da kuma Uwais, dan ta fara tunanin shikenan ta yi bankwana da su. Arman ne ya daure ya sake tambayar tsohon. “Ya za'ayi mu koma gida?” Ya sake nanata tambayar da ya yi ɗazu. Tsohon ya nisa, sannan yace. “Na san abin da zan faɗa yanzu zai firgita ku fiye da zato... Wannan ƙofar dake cikin masarautar Malik Changaz ita ce ƙofar da za ta mayar da ku gida!” Arman ya rintse idonsa, domin da ma shi ne abin da yake hasashe. “Ta ya za'ayi mu buɗe ƙofar da ba'a taɓa buɗeta ba?” Ya sake yin ƙarfin halin yin tambayar, a wannan karon dattijon murmushi ya yi, sannan ya nuna Arman da ɗan yatsa. “Wannan sarƙar da ke wuyanka, ita ce makullin ƙofar!” Ivana da Adam dake kuka suka dube shi baki buɗe, shi kansa sai da ya yi mamaki, sannan ya kai hannu ya taɓa mukullin dake jikin sarƙar. “Kana nufin wannan?” Adam ya tambaya yana nuna sarƙar, datijjon ya jinjina musu kai. Cike da ƙarfin hali Arman ya miƙe tsaye. “Zan je, kuma zan fuskanci Malik Changaz, zan tabbatar da na buɗe wannan ƙofar, domin mu koma gida.” “Ka yi hauka ne Arman? Saboda kai sirikinsa ne sai ka je ka ce masa ya buɗe maka ƙofar kai da abokanka za ku koma gida, ai ku matafiya ne, kun ɓata a hanya, saboda shi kuma shashashan afirilu ne sai ya matsa ya baka ƙofar cike da girmamawa?...” Faɗin Adam yana miƙewa, sannan ya nuna shi da ɗan yatsa. “Yanzu fa ba a 21st century muke ba, mun dawo zamanin baya ne, zamanin da ake kisan wulaƙanci a kan mulki! Zamanin da uba zai kashe ɗansa a kan mulki. Mutumin da bai ƙyale 'ya'yansa na cikinsa ba shi ne zai ƙyale mu saboda mu ba daga zamaninsa muke ba? Ka yi tunani mana!” Arman ya yi shiru kawai, a idonsa yake hango wahala tare da tarin ƙalubalen da za su fuskanta kafin cimmawa komawa gida. Ya kalli Ivana. “Ivana shin kin yarda da ni? Ivana na goge hawayenta ta gyaɗa kanta har sau biyu, ya juya ya kalli Adam. “Adam ka yarda da ni?” “Na yarda da kai amm...” Ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu. “Eh ko a'a?” Adam ya jinjina kai. “Na ɗauki alƙawarin tunkarar Malik Changaz, ko da kuwa zai kasheni, ruwa, iska sanyi ko guguwa ba za su dakatar da ni ba wurin cimma hakan. Tabbas zamu fuskance shi, idan ta kama zan yaƙe shi, domin mayarda ku gida, zan sadaukar da raina domin ku rayu, na ɗauki wannan alƙawarin, kuma babu abin da zai dakatar da ni wurin cika shi....” _The game starts now!🔥_ Salma Ahmad Isah ✍️ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-9 “Wannan shi ne kaɗai abin da zan iya taimaka muku da shi” Cewar datijjo me ban al'ajabi yana miƙawa Arman wata takarda dake naɗe, wadda aka yi ta da fatar akuya. Kansa ya juya ya kalli Adam da Ivana dake tsaye a gefe, kowannensu goye da jakarsa, dan sun ɗauki ɗamarar tafiya yanzu ba sai anjima ba. Hannu ya sa ya karɓi takardar, kafin ya buɗe takardar tsoho ya soma faɗin. “Wannan ita ce taswirar da za ta nuna muku hanya...” Adam da Ivana suka matso suna kallon taswirar da Arman a buɗe. “Duk wata hanya ko daji da kuka ga a kan takardar nan sai kun bi shi, za ku tsallake abubuwa masu tarin yawa a hanya, ban ce babu ƙalubale ba, ban kuma ce akwai zallar wahala ba, ban ce babu farin ciki ba, kuma ban ce akwai baƙin ciki ba... Abu ɗayaa na sani, hi ne kafin ku kai ga gaci za ku sha baƙar wahala!” Su duka uku suka dubi juna, kafin Adam yace. “Mu da za mu nufi Masarautar Jiyad me ya haɗa hanyar mu da Masarautar Majdal?...” Ya tambaya domin ya ga zanen sunan masarautar a cikin taswirar cikin harshen larabci. Dattijo ya yi murmushi. “Har Mamlakatul Afsah sai kun je, babu buƙatar na faɗa muku ta yaya kuma yaushe ne hakan zai faru, wata ƙila hakan zai rage muku armashin tafiyar, na tabbatar nan da wani lokaci ku da kanku za ku bani labarin abin da ya faru daku idan Allah ya nufi saduwarmu da ku a nan gaba, sannan akwai wani abu gudu...” Ya ɗan yi fasali yana shafa farin dogon gemunsa, sannan ya ci gaba da faɗin. “Ƙauyen Askar shi ne ƙauye na farko da za ku fara shiga bayan kun bar nan, tafiyar dake tsakanin nan da garin a ƙalla ta kai kwana uku a ƙafa, idan kuma a doki ne kwana ɗaya da yini ɗaya... Abu mafi muhimmanci shi ne mutumin da za ku haɗu da shi a can. A farkon garin akwai wani ɗan ƙaramin gidan ƙasa, nan za ku fara shiga, idan har kun shiga za ku iske wata tsohuwar mata, sai ku bata wannan taswirar, daga zarar ta ga taswirar ita za ta sadaku da abokin tafiya!” Suka yi shiru, domin duk cikinsu babu me abin faɗi kuma, tun da har rayuwa ta yi JUYIN KWAƊO da su sun riga sun karɓi hakan a matsayin ƙaddara. Tsoho ya ɗauko wata jaka ya miƙawa Adam, Adam ya sa hannu ya karɓa cike da naiman ƙarin bayani. “Akwai dabino da busasshen nama da kuma kubuz a ciki, zai isheku ku ci har na tsawon kwana uku da za ku yi kuna tafiya. Idan har kun isa Askar kuma naiman abinci ya ƙare, domin abokin tafiyar da za ku haɗu da shi a can shi ne zai ci gaba da kula da cikinku da ma lafiyarku!” Adam ya rataya jakar a kafaɗarsa, lokacin da tsoho yake bawa Arman wani takobi dake cikin gidansa. “Za ku buƙaci wannan a hanyarku, na san kai kaifi dacewa da iya sarrafata, ka kula JAGORA!” Ya ƙara kiransa da sunan da ya kira shi da shi ɗazu, tun da Arman ya kalli takobin abu ɗaya ne ya faɗo ransa, wata rana, wata magana da ta taɓa shiga tsakaninsa da Gulzar. _“Daga an yi magana sai ka ce kana zuwa fencing class, bayan ko takobin gaske ba ka taɓa riƙewa ba!...”_ _“Wata rana zan riƙe”_ Ita ce amsar da ya bata a lokacin, yanzu kuma ga ranar ta zo, cike da martabawa ya sa hannu biyu ya karɓi takobin, wani abu mafarkinsa, wani abu burinsa, wani abu da yake matuƙar son ya cimma a rayuwa, wato mallakar takobin da ba na fencing ba. Ya ɗan ɗaga takobin sama kaɗan, sannan ya zaroshi daga cikin gidansa, ƙyallin takobin ya haska a cikin rana, hakan ya sa ya dalle masa ido da har sai da ya rintsesu, a hankali ya sauƙe takobin yana ƙare masa kallo... Wani mafarki da ya saba yi na yaƙin nan da yake na tariyowa kansa a cikin tunaninsa, wato dai wannan mafarkin da ya daɗe yana yi yana da nasaba da wannnan JUYIN KWAƊON da rayuwa ta yi da su?. Daga ruwa zuwa ruwan zafi, takobin ya mayar gidansa, sannan ya kalli datijjo dake ta fara'a. “Mun gode sosai” Ya girgiza kansa. “Ni ya kamata ace na gode muku, domin zuwanku yau ya sa na sauƙe nauyin dake kaina, fatan nasara” Ya ƙarashe yana dafa kafaɗar Arman guda ɗaya, Arman ya gyara zaman glashinsa, sannan yace. “Mene ne sunanka?” A wannan karon kuma dariya ya yi. “Babu buƙatar sanin sunana yanzu, domin akwai yiyiwar sake haɗuwarmu a nan gaba, ku je, Allah ya bada sa'a.” Daga haka suka juya suka fara tafiya a kan hanyar da ya nuna musu, kowa a cikinsu jikinsa a sanyaye yake, ban da Arman, wanda ya sa fata da yaƙinin cewa ko ba yau ba tabbas za su koma gida, kuma zai tabbatar da hakan!. Sai da suka yi nisa sosai, sannan datijjon nan ya soma ja da baya, ya tsaya a gaban bukkarsa, ya lusmhe idonsa yana taɓa jikin bukkar, nan da nan bukkar ta ɓace, kamar ba'a taɓa hallitar wata bukka a wurin ba. Ya buɗe idonsa yana murmushi, sannan ya daka tsalle, kafin ya dire ya bi iska ya ɓace. Sun ɗauka cewa tafiyar mai sauƙi ce, dan tun da suka kama hanya ba su tsayawa sai idan sun lura da lokacin sallah ya yi, kuma daga sun tsaya sun gabatar da sallahr za su ci gaba da tafiya, duk da jikin kowanne a cikinsu a sanyaye yake, Arman ne kaɗai ke ƙokarin ƙarfafa musu gwiwa. Ba su tsaya yada zango ba sai da dare ya yi, shi ma a cikin dokar daji suka kafa tantinsu guda uku. Amma ba su shiga sun kwanta ba, suka zauna a waje suna jin ɗumin wutar da suka hura. Sai a lokacin Adam ya buɗe jakar abincin da tsoho me abin al'ajabi ya basu, ya shiga fitar da kayan ciki. “Ni dai ba na jin zan iya cin wannan abincin” Faɗin Adam yana nunawa Arman, Arman da ya nutsa duniyar tunanin 'yan uwansa ya dube shi. “Za ka ci idan har abincin da muke da su suka ƙare” Adam ya yi shiru kawai... Ita kuma Ivana na gefe tana duba service ɗin wayarta babu ko ɗaya, chajin wayar ma ya kusa ƙarewa. “Ba service, ba wutar nepa, babu abincin da muka saba ci, babu komai na more rayuwa!” Cewarta tana aje wayar, dan ta ga babu amfanin da za ta mata. “Ba ki da chaji ne?” Adam ya tambayeta, ta jinjina masa kai. “Ina da solar, gobe sai ki yi chajin” Ta sake jinjina kai tana shan tea ɗin da suka dafa. “Ban taɓa tunanin cewa zan wayi gari na yi rayuwar da babu abubuwan ci gaban zamani ba, wai ashe akwai lokacin da rayuwa za ta juya mana mu kasance a halin da ba mu isa mun yi communicating with wani ba?” Faɗin Adam yana rufe system ɗinsa. “Duk abin da zai faru damu a gaba ba mu da masaniyarsa, ba mu da ikon canza komai” Arman ya ba shi amsa. “Kuma ka san ina ga kamar wannan babbar dama ce na samu da zan ɗauki hotunan abubuwan da babu photographer ɗin da ya taɓa gabatar da su, masarautun mutanen da, al'adu da shigarsu da ma abincinsu!” “Ƙwarai, kuma ina ga kamar wata dama ce da za ta sauya tunanin Arman a kan Alhadi!...” Adam da Arman suka dubi Ivana da ta yi wannan furuci cikin mamaki... “Ke! A wannan duniyar fa ba su san masana'anta ba ballantana babban kamfani kamar Alhadi, ta ya za'a samu wani kamfani da zai sa Arman ya sauya ra'ayinsa kafin mu koma gida?” “Masarautun zamanin nan suna kama da kamfanunuwan zamaninmu!” Ta basu amsa, suka sake duban juna, amma shi dai Arman bai ce komai ba. Har suka gama zaman hirar suka koma cikin tent ɗinsu suka kwanta, cike da fatan wayar gari lafiya. MAMLAKATUL JIYAD. Cike da ƙasaita, izza da isa wani basaraken matashi ke tafiya, kamar wanda ba ya son taka ƙasa, hannayensa goye a baya, yayin da masu gadinsa ke take masa baya. Wasu irin kayan sarakunan da ne a jikinsa, wanda kai daga ganinsu ka san sun amsa sunansu kayan alfarma. Sai da suka kai ƙarshen dogon falon dake ƙarshen sashen sarki, sannan ya dakata, hakan ya sa su ma dakarun dake take masa baya suka dakata, cike da izza ya daga hannayensa, ba sa jira ko buƙatar ya furta musu abin da yake buƙata, cikin hanzari mutum biyu dake cikinsu, suka ƙara matsawa kusa da shi, sannan suka kama rigar sarautar dake saman kayan nasa da za'a iya kira da alkyabba. Suka sauƙeta daga kan kafaɗunsa, sannan suka ja da baya a tare suna riƙe da rigar tasa, sai da suka ja da baya, sannan mutum biyun dake jikin wata ƙofa da aka ƙera da zallar baƙin ƙarfe suka buɗeta, hakan ya bayyanar da doguwar matakalar da ta yi ƙasa zuwa harabar fadar. Kuma daga ƙarshen matattakalar akwai wani keken doki da matuƙinsa, wanda ke jiran fitowar sarki. Cikin wannan takun nasa na izza ya soma tafiya, har ya kai ƙarshen matattakalar, matuƙin keken dokin ne ya sauƙa daga wurin da aka tanada dominsa, ya buɗe gidan baya na keken, inda aka tanada domin zaman mai martaba, sai da ya shiga ciki ya zauna, sannan matuƙin ya rufe ƙofar keken dokin. Kana ya koma wurin zamansa, ya fara sarrafa dokuna biyun dake jan keken, suka bar ginin fadar, suka hau wata hanya ɗoɗar, wadda za ta sadasu da hanyar barin gari, da yake kowa ya san keken dokin sarki masu yasa gadi ba su yi ƙoƙarin dakatar da su ba, suka yi saurin wangale maƙareriyar ƙofar ganuwar masarautar. Ko da suka bar fadar dajin dake kusa da masarautar suka kutsa, dokunan na gudu a cikin dajin, yayin da Sarki Cangaz dake keken dokin ya matsu da su kai ga ƙarasawa fadar bokansa. Domin a daren jiya ya samu saƙo daga wurin bokan nasa, kan yana son ganinsa a safiyar yau, hakan ya sa ya yi sammakon tashi. A lokacin da ya ji dokunan tare da keken sun tsaya cak, matsuwa tare da zaƙuwarsa na son ganin bokan ta ninku, ta yanda bai jira matuƙin ya buɗe masa ƙofar ba, da kansa ya buɗe ya fita, duk wata izza da isa da yake nunawa a masarauta a cikin dajin bai yi ta ba. Hasalima sauri ya yi ya faɗa wani gida dake jikin bishiya a cikin ƙungurmin dajin. Yana buɗe ƙofar ya kutsa kai cikin gidan, babban boka Jalis dake durƙushe a gaban wani maƙareren allo ya ɗaga kai ya kalli Cangaz kammaninsa suke a na matashi, domin akwai wani sabon tsafi da boka Jalis ɗin ya haɗa masa a kwana nan, wanda yake sawa kamanin matashin kan yi tsawon kwanaki a jikinsa har na kimanin mako biyu, durƙushewa ya yi a gaban bokan, yayin da Boka Jalis ke ƙare masa kallo, fuskarsa ɗauke da murmushi. “Ka yi kira na amsa Jalis, da fatan da wani labari me daɗi ka zo min” Muryarsa me ɗauke da izza da ƙasaita ta furta suna duban juna shi da Boka Jalis. “Ƙwarai kuwa shugaban talakawa. Mafarkin da ka daɗe kana yi na tsawon kwanaki ne ya zama gaskiya...” “Ka yi saurin sanar da ni abin da yake faruwa” Ya yi saurin katse shi, dan sam ba ya son wani tambihi, boka Jalis ya girgiza kai yana murmushi, sannan a hankali ya juyawa Malik Cangaz fuskar allon dake aje a gabansa, Malik Cangaz ya kalli allon dake ɗauke da hoton wasu matasa uku, waɗan da sam kammaninsu da kuma shigarsu ba ta yi kama da ta mutanen duniyarsu ba, cike da kokwanto ya kalli boka. “Baƙi aka yi daga wata duniyar?” Boka Jalis ya girgiza kai. “Ba za mu iya kiransu da baƙi daga wata duniyar ba kai tsaye, amma za mu iya kiransu da baƙin sa'a, masu tafe da cikar mafarkinka... Kalli ka ga” Ya ƙarashe yana nunawa Malik sarƙar wuyan Arman. “Wannan shi ne makullin ƙofar da muke ta naiman mabuɗinta... Wannan makullin shi ne ƙarshen abin da zai sa ka ci gaba da zama a matashi har duniya ta naɗe” Lokaci guda Malik Cangaz ya saki wani ƙassaitaccen murmushi, suka haɗa ido da Boka Jalis. “Shin a ina waɗannan matasan suke? Domin ba na so na ƙara ko da sa'a guda ba tare da na buɗe ƙofar nan ba” “Ai ba'a nan gizo yake saƙar ba Shugabana, waɗannan matasan uku da kake gani, sam ba mutanen wannan zamanin namu ba ne, ƙaddara ce ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwarsu zuwa wannan zamanin namu. Kuma a halin da ake ciki su ma suna fafutukar yanda za'a yi su koma zamaninsu. Sannan an sanar da su cewa wannan ƙofar taka ita ce ƙofar da za ta mayar da su zamaninsu, dan haka su ma kansu suna tunkararka ne, ba kai ne kaɗai kake naimansu ba...” Malik Cangaz ya miƙe tsaye, ya yi taku uku tare da juyawa boka Jalis baya. “Ai ko ba za su taɓa komawa zamaninsu ba, domin ba zan taɓa bari su kai ga ganin ƙofar nan ba, ballantana har ta kai ga sun samu damar shiga cikinta... Zan sa a naimo min su duk inda suke a duniyar nan, domin a karɓo min makullin da suke tare da shi, saboda na buɗe ƙofar nan na cika burina!...” Ya ƙarashe yana bushewa da dariya, shi dai Boka Jalis bakinsa ya ja ya yi shiru, dan ba zai sake cewa komai ba, shi ya san abin da ya gani kawai, domin Malik Cangaz farkon yaƙin ya sani kawai, bai san ya ƙarshen yaƙin zai kasance ba, kuma shi ɗin ma da ya sani ba zai faɗa masa ba domin tsira da rayuwarsa... Malik Cangaz ya juyo tare da duban Boka Jalis. “Haƙiƙa yau ka sanar da ni labarin da ya fi ko wanne daɗi a duniyar nan, dan haka dole na maka gagarumar kyauta, sannan ina gayyatarka zuwa wurin ganawa da yariman masarautar Azad, wanda zai zo tare da mahaifinsa a kan maganar auren Gimbiya Iqrah, da fatan za ka zo?” Boka ya jinjina kai yana murmushin ɓoye sirrin zuciyarsa. “Ƙwarai kuwa shugabana, zan kasance a wurin a lokacin da ake buƙata!” DANEEN IQRAH. Yalwataccen hasken rana da ya fara ratsowa cikin masarautar ne ya samu damar shiga ɗakinta ta hanyar ƙatuwar tagar dake saman ɗakin. Hasken ranar ya samu nasarar sauƙa a kan wata kyakkyawar hallita dake kwance a kan katafaren gadon dake tsakiyar ɗakin. Kyakkyawan dogon gashin idonta na sama ne ya ɗaga zuwa sama, farin idonta dake ɗauke da ƙwaya kalar (brown) ya bayyana, sake rufe idon nata ta yi, sannan ta sake buɗe shi a karo na biyu, ta saka dogayen fararen yatsun hannunta, ta murza idonta, sannan a hankali ta saka hannunta ta yaye mayafin da ta lulluɓa da shi, ta tashi zaune, yayin da gashin kanta me tsayi ya lulluɓe kafaɗunta da kuma gadon bayanta. Lokacin da ta yi miƙa tare da hamma kuyangu da bayin da suka saba mata hidima a kullum rana suka fara shigowa ɗakin ɗaya bayan ɗaya, kowanne ya shigo ɗakin sai ya miƙa mata gaisuwa, sannan zai fara aikinsa na kullum. Yayin da ita kuma ta nufi bayin dake cikin ɗakin, wasu kuyangu biyu suka rakata zuwa bayin, domin tayata tsaftace jikinta. Lokacin da suka dawo ɗakin har an gama tsaftace ko mai da ko ina, a kan wata kujera ta zauna, kuyangun da aikinsu shi ne shirya gimbiya suka kewayeta, kowa da aikin da yake, wasu na gyara mata gashi, wasu na aikin gyara mata fata, yayin da wasu na taimakawa wurin saka mata tufafi. Sai da suka ƙawata sarauniyar da ado irin wanda ya dace da duk wata 'yar sarki me jin isa da iko a wannan zamanin, sannan suka koma gefe, masu aikin kawowa sarauniya shayinta na safe suka matso, aka bata shayin ta sha, sannan ta tashi domin zuwa ɗakin karin kummalo da kowa ya saba halarta domin cin abinci. Sai da ta yi taku uku, sai kuma ta dakata, hakan ya sa su ma bayin da suka shirya domin take mata baya suka dakata. Cikin iko isa da izza ta kalle su da gefen ido. “Ku bani wuri, akwai abin da zan gabatar cikin sirri” Ta furta cikin muryarta me sanyi da zaƙin sauraro. Dukan ma'aikatan nata suka risina mata, alamun sun amsa saƙon nata, sannan suka soma barin ɗakin ɗaya bayan ɗaya. Sai da suka fita daga ɗakin gaba ɗayansu, ya rage sai amintacciyar hadimarta kaɗai a ɗakin, ta kalli hadimar da kanta yake a ƙasa. “EID ya aiko da wani saƙo?” Hadimar ta jinjina kanta dake ƙasa. “Ƙwarai gimbiyar kyawawa...” Daga haka ta nufi tagar ɗakin dake a bangon gabas, ta saka hannayenta ta buɗe ƙofar, hakan ya bawa mujiyar (owl) dake waje damar shigowa ciki, ta shiga kaɗa fuka-fukanta har ta isa kafaɗar gimbiya. Wani kyakkyawan murmushi ta yi tana kallon mujiyar, sannan ta saka hannunta ta ciro takardar dake riƙe a cikin ƙafafun mujiyar. Ta buɗe takardar ta soma karanta wasiƙar soyayyar da masoyinta SA'EID ya aiko kamar kullum. Kan wata kujera ta koma ta zauna tana murmushi kamar wadda ta samu taɓin hankali, haka kalaman soyayyarsa ke ratsa mata zuciya, sai da ta gama karanta wasiƙar, sannan ta ɗauki wata takardar da alƙalami, ta rubuta nata kalaman, sannan ta saka a cikin ƙafar mujiyar, ta buɗe mata ƙofa ta turata zuwa waje ta tagar tana murmushi. “Ina da wata magana idan har ba za ta ɓata miki rai ba ya shugabata!” Gimbiya Iqra ta dubeta hadimarta Champa, murmushin dake kan fuskarta na samun kalaman masoyinta SA'EID ALI bai gushe ba ta furta. “Ina jinki Champa” “Ɗazu jakadan fada yake sanar da ni wani batu da nake da tabbacin ba ki san da shi ba...” Murmushin fuskarta na shirin ɓacewa ta furta. “Wani batu ne wannan?” “A yau yarima Wajid ɗan sarkin Mamlakatul Azad zai zo tare da mahaifinsa a kan batun naiman aurenki?...” Ɓat murmushin kan fuskarta ya ɓace a iska, wani abu me kama da ƙwai ya faɗo ya fashe a ƙirjinta. Sannan ta saki baki da hanci tana kallon Champa. Duk bayan tsawon lokacin da suka shafe suna soyayya da Eid masoyinta a rasa a gaɓar da za'a rabasu sai yanzu da soyayyarsu ta ɗauko daɗi?... Zuwan wani da ban fadar a kan maganar aurenta ba Eid ba na nufin za'a aura mata waninsa. Kuma sam ita ba za ta lamunci hakan ba, ko da za ta gudu daga fadar ne za ta yi, domin tseratar da soyayyarta. Ta san ko da ta gabatar da Eid a gaban Malik Cangaz a matsayin mijin da take so ya aura mata ba zai amince ba, domin Eid ba shi da mulki, sannan ba shi da kuɗi ko wata dukiya da za ta siya masa mutunci a idon mahaifinta ballantana ta kai ga ya aura mata shi. Salma Ahmad Isah ✍️ A zo a fara biyan kuɗin book, saboda book one ya ɗauko hanyar ƙarewa. If you wanna be part of the journey, pay ₦400 for nomarl group, and ₦800 for VIP group. 5487270431 Salma Isah Monie point Sai a tura shaidar biya ta 08130172702. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-10 ARMAN. A rana ta gaba ma haka suka ci gaba da tafiya a cikin dajin, kasancewar suna duba taswirar da tsoho ya basu yasa ba su ɓata hanya ba ko sau ɗaya. Har rana ta biyu a tafiyar tasu ta ƙare babu wata matsala da ta samesu, ko wani baƙon abu da ya ziyarce su, sai a rana ta uku, ranar da suke hasashen iske ƙauyen Askar wani baƙon lamari ya riskesu a hanya. Tun cikin daren ranar ake iska me ƙarfi, wadda take tafe da ƙura da kuma sanyi me shiga jiki, kuma tun a safiyar ranar iska ta ɗauke tentunan da suka kafa, lokacin da suka tafi naiman ruwan wanke jikunansu, sanda suka dawo suka iske babu tentin iska ta ɗauke. Sa'arsu ɗaya, jakukkunansu ba su cikin tent ɗin lokacin da iska ta yi gaba da su, cike da salallamin rashin tent ɗin suka haɗa kayansu suka ci gaba da tafiya, dan yanzu abin ma ya fara zame musu jiki, har sun fara sabawa da yanayin tafiyar. Suna tsaka da tafiya a tsakanin wasu bishiyoyi suka fara jin kuwwar wasu mutane, Adam ne ya fara jiyo kuwwar, hakan yasa ya ankarar da sauran, sai suka tsaya suna duba kewayen da suke, wai ko za su ga ta inda masu kuwwar za su ɓullo. Amma har bayan shuɗewar daƙiƙu biyu babu alamar komai. Sai da suka sakankance sannan suka ji faɗowar abu daga sama tim!. Hakan ya sa suka ƙara razana, Arman ya turasu bayansa domin basu kariya, yayin da yake kallon ta inda abin ya faɗo, girman idonsa ya rage yana kallon mutumin dake tsaye a gabansu, alamun dai shi ne ya faɗo daga saman. Tun daga kan kwarjallen dake ƙugunsa zuwa rigar dake sanye a jikinsa duka na fata ne, kuma fuskarsa a rufe take, shi yasa ba su iya banbance kamarsa. Kafin su yi wani yunƙuri wasu mutum uku dake sanye da kaya irin nasa suka sake dirowa daga saman bishiya, Arman ya sake kare Ivana da Adam da suke a matuƙar tsorace, shi ma kansa a tsorace yake, amma dole ya ɓoye tsoronsa domin kare abokansa. Kallon-kallo aka tsaya yi, su suna karantar kama da kuma nau'in tufafin dake jikin mutanen huɗu, yayin da su ma suke kallonsu, dan za su iya cewa tun da suke fashi a hanyar, tsawon shekaru tara, ba su taɓa ganin mutane masu kama da waɗannan ba, bawai dan sun banbanta da mutane ba ne, a'a su ma kamar mutane suke, amma kalar tufafin jikinsu shi ne abin mamaki... Sai dai mamakin son sanin su wasu nau'in mutane ne ba shi zai hana su ƙwace duk wani abu da suke tafe da shi ba, dan haka wanda ya kasance shugansu ya miƙa musu hannunsa, cikin larabcinsa me kyau yace. “Ku bamu kayanku!” “Kaya?” Adam ya maimata. “Ku bamu kaya ko kuɗi, idan ba haka ba ku yi ta ranku!” Dariya ta so kama Adam, dan shi ne ya fara fahimtar wasu irin mutane ne. Camera ɗinsa ya fitar ya shiga ɗaukansu a hoto. Yayin da su kuma suka shiga kare fuskokinsu saboda hasken flasher da Adam ke haskasu da ita. “Adam me suke buƙata ne?” Ivana ta tambaya tana kallonsa lokacin da ya gama ɗaukansu a hoto yana dariya. “Wai 'yan fashi ne” Ita kanta sai da abin ya so bata dariya. Ganin suna dariya ya harzuƙa 'yan fashin, ai rainin hankali ne ma, ya za'ayi su tambayesu kudi ko kayan kuɗi su zauna suna musu dariya. Hakan yasa suka fitar da makamansu masu firgita bil adama, suka yi kansu da shi. Amma Arman bai bari sun kai ga cutar da su ba, dan cikin azama shi ma ya fitar da nasa takobin ya nunasu da shi. “Kada ku sake ko da taku ɗaya zuwa garemu, duk wanda ya sake kuma zan raba kansa da gangar jikinsa” Ya faɗi a dake yana dubansu, juna suka kalla, dan ba sosai suka gane abin da yace ba. Ɗaya daga cikinsu ya sake yin wani takun zuwa gaba. Cikin ƙwarewa da iya sarrafa takobi, Arman ya juya takobin a hannunsa, sannan shi ma ya nufe shi, yana zuwa dab da shi ya kare farmakin da ɗan fashin ya kawo masa, sannan ya jujjuya takobin da hannunsa ɗaya, ya kai masa suka a gefen ciki, shi kansa bai ɗauka cewa zai iya samun wurin da ya hara ba. Domin bai taɓa amfani da takobin gaskiya ba, amma sai ga shi ya samu gefen cikin ɗan fashin. Ya ƙwalla ƙara yana naiman ɗauki a wurin 'yan uwansa, su kuma kallon Arman kawai suka tsaya yi baki sake, dan a fashin da suka kwashi tsawon shekaru sun yi ba su taɓa haɗuwa da wanda ya mayar musu da martani ba sai yau. Arman ya zare takobin da ya sokawa ɗan fashin, sannan ya tura shi wurin 'yan uwansa. Da sauri suka ɗauki ɗan uwansu suka ruga cikin dajin da gudu. “Hooooo! Abokina wai da ma haka ka iya sarrafa takobi!?” Cewar Adam baki buɗe, dan bai taɓa ganin Arman ɗin na wasan takobi ba sai yau. Ita kuma Ivana takan je ta ga wasan nasa idan suna yi a Fencing Academy ɗinsu, amma duk da haka abin ya bata mamaki. Shi kansa Arman mamakin abin yake ji, takobin dake ɗigar jini ya ɗaga yana kallo, kafin ya mayar da shi cikin gidansa. “Ya kamata mu yi saurin barin wurin nan, kafin wasu mugayen mutanen su zo” Da wannan maganar tasa suka ci gaba da tafiya, kuma ba su yada zango ba har sai da suka fara hango gidan da tsoho yace musu shi za su fara gani kafin su kai ga shiga ƙauyen Askar. Duk da haka Arman bai tabbatar ba sai da ya buɗe taswirar da tsoho ya ba su, sannan ya ga waɗannan hasken ukun suna tsaye a kan ƙauyen Askar da aka masa alama, kansa ya ɗaga ya dubi su Adam. “Wancan shi ne gidan da tsoho yace za mu fara gani kafin mu shiga ƙauyen Askar...” Suka sake kallon gidan. “To mu je mana” Cewar Adam shi ne kan gaba, su ma bayansa suka bi zuwa gidan da aka gidan da ƙasa. Kasancewarsu 'ya'yan musulmai yasa sai da suka gabatar da sallama, kafin su kutsa kai gidan. Su ukun duka suka jeru a tsakar gidan. Suna kallon kallo da matar dake tsakar gidan. Farar dattijuwa ce, wadda a ƙiyasin shekaru za ta kai hamsin da ɗori, sanye take da wasu tufafin da aka saƙa da zaren audiga, wanda aka rina shi zuwa kalar shuɗi. Ƙafafunta na cikin takalman fata irin na zamaninsu, hannunta riƙe da wata ƙwarya. Kamar yanda su ma suke kallonta, haka ita ma take kallonsu. Dan sam ba su mata kama da mutanen da ta sani ba. “Barka! Mu baƙi ne a nan, akwai wani tsoho da ya ba mu wannan yace mu baki” Cewar Arman yana nuna mata taswirar dake hannunsa. Nan take tsohuwar ta saki fuska, sannan ta musu alama da su shiga cikin ɗakinta. “Anya za mu iya yarda da wannan tsohuwar me kamar yamusasshen ganye?” Cewar Adam murya ƙasa yana duban abokansa. Arman ya bugi cikinsa da bayan hannunsa. “Ka mana shiru, a wannan halin da muke ciki ba mu da ikon zargin kowa, mu dai kawai abin yin mu shi ne kare kai a lokacin da aka kawo mana farmaki” Cewar Arman. “Haka ne Adam, tun da har muka yarda da tsohon can ita ma babu dalilin da zai sa mu ƙi yarda da ita” Cewar Ivana. “Ku shiga mana” Tsohuwar ta sake faɗa tana nuna musu ɗakinta da shi ma aka gina shi da ƙasa. Sai da suka gama ƙarewa gidan kallo, sannan suka shiga ɗakin nata da babu komai ciki sai wani gadon katako. Sai wasu jakukkunan fata dake gefe guda. A kan gadon dake ɗakin suka jeru su uku, Adam har da fitar da camera ya fara ɗaukan ɗakin a hoto. A lokacin kuma matar ta shigo ɗakin, hannunta tiƙe da wani abu me kamar kofi, ta aje musu tana faɗin su sha abin ciki, dai suka girgiza mata kai a tare, alamun ba sa sha. Suna ganin sanda matar ta yi murmushi, sannan ta juya kanta tana kallon ƙofar ɗakin, cikin muryarta ta tsufa ta ƙwala ƙiran. “UWAIS!” Cikin abin da ya zarce mamaki Arman, Adam da Ivana suka dubi juna, sannan suka kalli farar dattijuwar, idan dai har ɗan rakiyar da za su tafi da shi ya kasance UWAIS ke nan wannan matar ita ce gimbiya FEROZA, wato mahaifiyar Amir UWAIS BIN DHAAKIR?. _____•••____ UWAIS. A hankali daddaɗar iskar dake busawa a dajin take kaɗa ganyayyakin bishiyun da suka ƙawata shi. Yayin da wani daddaɗan busar sarewa ke tashi a cikin dajin, da daɗin da yake naiman zarce na iskar da ake. Daga can kan reshen wata doguwar bishirya yake zaune, ya harɗe ƙafafunsa, yayin da iskar wurin ke ɗaga dogon gashin kansa, idanuwansa kuma a lumshe, domin shi kansa yana jin daɗin busar. Sanye yake da Sirwal, wani nau'in tufafi irin na wancan zamanin, wanda ake yinsa da zare lilin. Takalman ƙafarsa na fata ne, wanda suke da zaren ɗauri, akwai ɗan siririn rawani a kansa, wanda bai ɓoye dogon gashin kansa ba. Wasu kyawawan tsuntsaye dake kan bishirya da yake zaune ne ke ta kukansu me daɗin saurare, waɗan da suka ƙarawa busar tasa ta yau armashi. Cak busar sarewar ta tsaya, sannan a hankali ya buɗe kyawawan idanuwansa masu ɗauke da shuɗiyar ƙwaya. Ya motsa kunnensa na ɓarin hagu, domin jiyo abin da yake dajin dake gaban wanda yake ciki. Gurnanin damusa haɗi da kukan barewa ya jiyo lokaci guda. Hakan tasa ya yi saurin miƙewa a kan reshen bishirya, sannan ya sofare zarewar hannunsa a cikin ma'ajiyarta dake saƙale a ƙugunsa. Tsalle ya daka ya iyo ƙasa, sai dai kafin ya kai ƙasa ya buɗe fukafukansa da ba su bayyana sai idan har shi ya bayyanar da su ya tashi sama. Cikin abin da bai fi ƙiftawar ido ba ya isa dajin dake kusa da wanda ya baro. A kusa da inda yake jin gurnanin damusar ya sauƙa, kuma yana sauƙa ya sake ɓoye fukafukansa guda biyu, ya tsaya yana kallon wata baƙar damisa da take shirin farmakar wata barewa. A hankali ya miƙe tsaye, sannan ya zaro sarewarsa dake maƙale a ƙugunsa, ya juyata a hannunsa, nan take ta rikiɗa zuwa bakar da aka ƙera da ɗanyar azurfa, sannan a hankali ya riƙeta da hannunsa na hagu, ya ɗagata sama, tare da saitata a kan damisar, yatsun hannunsa na dama ya motsa, wata farar siririyar kibiya ta faɗo hannun nasa, a hankali ya saita kibiyar a jikin bakar, sannan ya sakata cikin yatsun hannunsa biyu. Ya kanne idonsa tare da karkatar da kansa gefe, sai da ya saita damisar sosai, sannan ya saki kibiyar, babu kuskure ko kauce hanya kai tsaye kibiyar ta soki damisar a gefen cikinta, kukan da damisar ta saka ya sa barewar da take hari da farko ta razana ta falla cikin dajin da gudu. Murmushi ya yi kawai, sannan ya juya bakar ta rikiɗe zuwa sarewa, ya sake saƙalata a cikin ma'ajiyarta me kama da gidan takobi, sannan ya yi wurin da damisar ta faɗi tana numfashi da ƙyar, tsuggunawa ya yi a kanta, ya kalli wurin da ya harbeta na ta zubar jini. “Idan aka ce ku koma cin ciyawa ba iyawa za ku yi ba, kuma idan aka ce kada ku cutar da dabbobin da ba su ji ba ba su gani ba ƙi kuke, ya za mu yi da ku ne?” Ya tambaya yana ɗora hannunsa a kan kibiyar, sannan a hankali ya zareta daga cikinta, ya shafa wurin da ya harbeta, sannan ya miƙe yana kallonta. “Allah ya baki lafiya” Yana gama faɗar hakan ya buɗe fukafukansa ya tashi sama. Yana shawagi a iska kiran mahaifiyarsa ya riske shi, hakan yasa bai sauƙa a ko ina ba sai a cikin gidansu. IQRAH. Ƙuri ta yi da ido tana bin yariman da aka ce shi ne wanda za'a aura mata da kallo, fuskar nan a haɗe, dan sam babu alamar fara'a a tattare da ita, ta cika ta yi fam, jira take a tsikareta ta fashe tau!. Ba sai an yi wani tone-tone ba, sam ita matashin bai mata ba. Ba wai dan ba shi da kyau ba, ba kuma dan ba shi da nasaba me kyau ba, sai dan kawai Eid shi ne a zuciyarta. “... Yanzu amincewar Gimbiya kawai muke buƙata, daga zarar tace eh sai a saka ranar aure!’ Mahaifin yariman ya faɗa, Iqrah ta kalle shi, sannan ta kalli mahaifinta Malik Cangaz da shi ma ke zaune a ɗakin cin abincin. Amma shi sai ya ƙi ya kalleta, ya yi murmushi me kyau, sannan yace. “Babu buƙatar sai mun ji daga gareta, dan haka yanzu ma za mu iya saka ranar da za'a yi auren” Maganarsa ta tarwatsa duk wani fata da Iqrah ke da shi, kuma dalilin maganarsa yasa ta ƙudiri aikata abin da ba zai musu daɗi ba daga ita har shi. Ta kalli yariman tana jin kamar ta shaƙo wuyansa ta maƙure shi a bango har sai ya daina numfashi, sannan ta kalli mahaifinta, sai dai ba ta da ikon cewa uffan. Har suka gama yanke abin da za su yanke, aka sallameta. Champa da sauran hadimanta suka mata rakiya zuwa ɗakinta. Sai da suka sadata da ɗakinta, sannan ta sallami sauran hadiman, ta dakatar da Champa kawai. Sannan ta dubeta tana faɗin. “Gobe ki tabbatar kin zo min da kayan da kika saba kawo min na saka a duk lokacin da nake son na yi shigar ɓadda kama na fita, kada ki bari kowa ya san cewa gobe zan fita domin ganawa da Eid!” Kan Champa a ƙasa ta jinjina shi. “An gama gimbiyar kyawawa” Daga haka ta mata lamunim fita daga ɗakin. Tana shirin zama a bakin gadonta ASRA ta shigo ɗakin, kamar kullum, sanye ce kin shigar yaƙi, domin a ko da yaushe ita tana cikin shirinta na yaƙi. Kallon juna suka yi, kafin Iqrah ta ɗauke kai ta zauna a kan gadon cike da damuwa. Asra ta ƙarasa cikin ɗakin, sannan ta zauna kusa da 'yar uwarta me matuƙar kama da ita. “Ina kika tafi tsawon kwana uku bana ganinki?” Iqrah ta gefo mata tambayar bayan wani lokaci. Asra ta yi murmushi. “Malik ne ya tura mu yaƙar wani ƙauye dake cikin dajin Urf al-tawul... Tafiyar ta taso a bazata, shi yasa ban sanar miki ba kafin mu tafi!” Iqrah ta kalli 'yar uwarta, ita ke nan rayuwarta ba hutu, a ko da yaushe sarki na bata ayyukan da suka girmi hankali, har suna ganin kamar ya manta a mace aka haifeta ba namiji ba. Domin ya mayar da ita tamkar namiji, hatta da muryarta ta fi ta mata girma, yanayin tafiyarta da kuma shigarta ya banbantata ta mata, duk da ta kasance mace. “Darvesh (Holy man) yace min ya zaɓa miki mijin aure, hasali ma nan da mako guda za'a yi aurenki... Faɗa min kina farin ciki?” Asra ta tambaya, Iqrah ya juya idonta. “Bana farin ciki Asra, saboda bana son zaɓin Abbu, ni ina da wanda nake so, amma na san ko da na sanar masa da hakan ba zai goyi bayana ba” Asra ta dafa kafaɗar ƙanwarta. “Haka ƙaddarorinmu suke Iqrah, daga ni har ke ba za mu iya sauyasu ba, dole ne mu bi abin da Malik yake so, ko da kuwa mu ba ma ra'ayin hakan!” Iqrah ta miƙe tsaye. “Na daɗe ina bin duk wasu dokoki da zai kafa min, amma ba zan bi wannan ba...” “Me za ki yi ke nan?” Asra ta kasteta tana miƙewa ita ma. ”Zan gudu tare da wanda nake so!...” Ba ta rufe bakinta ba Asra ta sharara mata marin da ya yi sannadiyar fitar jini daga bakinta, sannan cikin zallar ɓacin rai ta nunata da yatsa. “Ki yi komai ba komai, amma yin kuskure irin wanda Sana ta tafka ba zan bari ki aikata shi ba...” Iqrah ta dafe wurin da ta mareta hawaye na bin kuncinta tace. “Tun da ke kin bari ya gurgunta miki rayuwarki sai ni ma na bari ya ruguje min rayuwa ta hanyar rabani da Eid? Duk abin da zai min sai dai ya min, amma ba zan taɓa rabuwa da Eid na auri wani ba...!” Asra ta sake ɗaga hannunta za ta sake marinta, amma sai ta fasa. “Mutuwa ce kaɗai za ta shiga tsakanin da dakatar da ke kan abinda kike son aikatawa... Zan yi komai domin ganin ban barki kin aikata irin abin da Sana ta yi ba, na gwammaci ace ni na kasheki da hannayena da na bari Malik ya saka miki ciwo irin wanda ya sakawa Sana...” Tana gama faɗin hakan ta fita daga sashin Iqra rai a ɓace. Yayin da Iqra ta kwanta a saman gadonta tana kuka. Salma Ahmad Isah ✍️ _______________ _Book one ya ɗauki hanyar ƙarewa, dan bai fi pages 5 ne suka rage a gaba ba._ _Idan kun shirya bibiyar wannan tafiyar sai ku biya ₦400 regular group. Akwai V.I.P ₦800._ _Za ku tura kuɗinku ta wannan account ɗin._ 5487270431 Salma Isah Monie point Sai ku tura shaidar biyanku ta wannan lambar 08130172702. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-11 ƘAUYEN ASKAR. Mamaki ne yasa Ivana ta sandare a tsaye, sakamakon ganin wani mutum me kama da Uwais Fazil wanda ta sani a Dubai, kuma a zamaninsu, yanzu sai ga shi suna ganinsa a matsayin wani Uwais ɗin, amma Uwais bin Dhaakir. Banbancin wancan Uwais ɗin da wannan da take gani kawai shi ne dogon gashin dake kan wannan, sai kuma yanayin shigarsu. Amma za ta iya rantsewa da Allah kan wannan Uwais ɗin da ta sani a Dubai ne. “...Ivana!” Adam ya kira sunanta yana taɓata, a ƙokarinsa na dawo da ita zahiri, dan ya ga kamar ta lula duniyar tunani, firgigit ta yi ta kalle shi tana amsawa. “Me ya sameki?...” Ta kalli Adam, sannan ta juya ta kalli Arman, ta sake tsayar da dubanta a kan yarima Uwais dake tsaye a gabansu, shigar jikinsa ta ƙara kalla, sannan ta sake duban fuskarsa. Shi ma sai kallonta yake kamar ya santa a wani wurin, wata ƙila kuma shigar jikinta yake kallo... “Ku ci abinci” Cewar Tsohuwa Feroza tana aje musu wani tray dake ɗauke da Mujaddara, wani nau'in abinci na wancan ƙarnin, wanda ake yinsa da shinka, kayan lambu da kuma nama. Kasancewar suna jin yunwa yasa ba su musa cin abincin ba a wannan lokacin. Suka fara cin abincin a ɗarare, kamar suna cin dutse, dan sam abincin ba shi da ɗanɗano mai daɗi a baki, na kamar wanda suka sana ci ba. Shi dai Adam a ransa mamaki yake na yanda aka yi mutanen da suka rayu cikin farin ciki. Har suka ƙare cin abincin Ivana na satar kallon Uwais, kuma daga zarar ta kalle shi za ta ga shi ma kallonta yake. Har Arman ya fara lura da hakan. Amma bai mata magana a lokacin ba har suka kammala cin abincin, suka samu damar yin wanka, sannan suka sauya tufafi. Lokacin da suka gama shiryawa suka dawo 'yar farfajiyar gidan Feroza, inda suke tsaye ita da Uwais. Shi ma da jakarsa a tare da shi, alamun dai ya gama shiryawa za su ci gaba da tafiya. Tsaye suka yi suna kallon uwar da ɗanta suna sallama, da alama duk tsawon shekarun da suke rayuwa tare ba su taɓa rabuwa da juna ba sai a sannan karo. “Ka tabbatar sun isa inda suke son zuwa cikin aminci!” Faɗin Feroza tana danƙawa ɗanta taswirar da su Arman suka bata, Uwais ya karɓa yana murmushi, sannan ya sakata cikin jakar kayansa, kana ya rungumi mahaifiyarsa. “Ki min addu'a ya Umma” Ya faɗa suna sakin juna, Feroza ta shafa kansa. “Addu'ata za ta kansace tare da kai a duk inda ka sa ƙafa yarimana” Ya yi murmushi me kyau, sannan ya ɗauki jakarsa. “Sai Allah ya mana dawowa Umma” Feroza ta share ƙwallar da ta zubo mata, tana kallonsu har suka fita daga gidan, ta cikin ɗan ƙaramin ƙauyen suka bi, mutanen ƙauyen suka yi ta binsu da kallo, sakamakon yanayin shigarsu Arman, dan ba su yi kama da mutanensu ba. Shi ko Adam hotunan ginin ƙauyen da kuma na mutanen ƙauyen ya shiga ɗauka, yayin da Ivana da Uwais suka ci gaba da satar kallon juna. Har suka fita daga ƙauyen suka nausa cikin daji, sun yi tafiya me matuƙar tsayi, kafin suka samu yada zango a cikin dajin, suka zauna suna hutawa, yayin da Uwais ya tafi naima musu abin da za su ci, sai a lokacin Arman ya fasu ya tambayi Ivana abin da ke ransa. “Ivana kin san Uwais a wani wuri kafin nan?” Duk da tambayar ta zo mata a bazata sai da ta yi murmushi, yayin da take karkaɗe jakar guitar ɗinta. “A ina za ta san shi? Ita da mai tafiya a tsakanin zamani ba?” Adam ya rigata bawa Arman amsa, amma sai ta girgiza kansa. “Ko kaɗan, mun taɓa haɗuwa da wani Uwais ɗin da ban a Dubai!” Adam ya zaro ido yana kallonta. “Kun taɓa haɗuwa? Ke nan har a zamaninmu yana raye bai mutu ba? Da ma fa aljannu suna da taurin rai, shi yasa nake kaffa-kaffa da shi, dan Wallahi tsoronsa nake ji” Ivana ta yi dariya. “Ba lalle ace shi ba ne, amma wancan zai iya kasancewa me kamarsa ne” Arman ya gyara zaman glasses ɗinsa yana jinjina kai. “komai zai iya kasancewa, kuma shi ma sai kallonki yake ta yi, kamar ya sanki” Ivana ta sake darawa. “Ban sani ba” “Ga shi can ya dawo” Cewar Adam yana nuna Uwais da ya nufo wurin da suke. “Barkanku da hutawa” Cewar Uwais yana aje jakar da ya zo da ita. Su dai kallonsa suke, an ce musu rabinsa mutum ne kuma rabinsa aljani, amma su dai mutum suke gani. “'Ya 'yan itaciya ne na samu, da fatan za ku iya ci” Ya ƙarashe yana duban Ivana, Ivana ta ɗan yi gajeren murmushi tana kallonsa ita ma. “Me zai hana mu iya ci” Arman ya ja jakar yana faɗa, Uwais ya zauna a gefe yana nasa murmushin, suka fitar da kayan dake ciki, har suka fara ci amma shi Uwais sarewarsa ma yake gogewa. “Kai ba za ka ci ba?” Cewar Arman yana dubansa, sai ya kalle shi. “Ba na jin yunwa yanzu, daga zarar na ji yunwar zan naimi abinci” “A ƙalla kana iya kwana nawa ba tare da ka ci abinci ba?” Adam ya tamabaya. “Mako guda” “Mako guda sati ɗaya ke nan?” Adam ya zaro idanuwansa cike da mamaki. “Wannan fa, mi ye a hannunka?” A wannan karon Ivana ce ta yi tambayar, sai ya kalleta. “Sarewa, takobi kuma baka!” “Sarewa, takobi kuma baka duka lokaci guda?” Faɗin Arman. “Eh, na kan iya yin busa da ita a lokacin da nake bukata, na kan iya juyata ta koma baka idan ina son kare kaina, amma kuma ainahinta ta kasance takobin mahaifina!” “Ke nan wannan ita ce takobin sarautar da sarki Safraz yake naimanta?” Cewar Adam. “Ƙwarai, ita ce, kuma na san yanzu haka zai samu labarin bayyanar takobin, sannan zai iya yunkurin ƙwaceta daga hannuna ta ko wace hanya” Matasan uku suka dubi junansa, a lokacin da tunani ɗaya ya ziyarci ƙwaƙwalansu. Sun fuskanci cewa haɗuwarsu da Uwais ba sauƙi zai kawowa lamarinsu ba face ƙarin wasu ƙalubale da kuma matsaloli. Da ace Malik Cangaz kaɗai za su yaƙa abin zai iya zama da sauƙi, tun da shi bil adama ne, amma faɗa da aljani ai abin ya girmi tunanin me hankali!. MAMLAKATUL AFSAH. Fadar masarautar cike take da 'yan majalissar sarki, yayin da sarki ke zaune a kan karagarsa, ana ta gudanar da sha'anin mulki. Sarkin na bayar da wani jawabi a kan wata matsala da ta kunno kai a masarautar. Cak ya tsaya da jawabin da yake, lokacin da ɗaya daga cikin masu gadin babbar ƙofar shigowa fadar ya shigo fadar da sauri, ya zube a gaban sarki ya kwashi gaisuwa. “Sarki ya amsa bafade, faɗi abin da ke tafe da kai kanka tsaye!” Cewar waziri, Ba fade ya risinar da kai, sannan ya furta. “Ya shugabana yanzu muke samun masaniya daga dakarun ɓoye dake bibiyar lamarin takobin mulki da kuka aika... Cewar suna jin alamun an fito da takobin daga maɓoyarsa” Babu shiri sarki ya miƙe tsaye a kan ƙafafunsa, domin haƙiƙa batun ya girgiza tunaninsa, ba ma shi kaɗai ba, hatta da sauran fadawansa sai da batun ya saka suke miƙe tsaye. A ƙalla yanzu an kwashi shekaru sama da ashirin, babu wani batu daga masu biciken takobin sai yau... “Ina wakilan ɓoye suke? Duk inda suke a tabbatar an naimo min su, an kawosu nan” Hadimin ya miƙe a kan ƙafafunsa yana risinar da kansa a gaban shugabansa tare da faɗin. “An gama adalin sarki!” Har hadimin ya fita daga fadar idon sarki na kan ƙofar shigowa fadar, yana saƙa mabanbantan abubuwa a ransa, shin me zai sa Feroza ta fito daga maɓoyarta bayan wasu shekaru masu tsayi? Imma dai ya kasance takobin ya bayyana ne ba tare da saninta ba, ko kuma ta bayyanar da shi da gayya, domin akwai wani abu da ta taka. Ko ma dai mene ne, shi ba zai sauka a daga kan ƙudirinsa na son ganin ƙwatar takobin daga gareta ko ɗanta. IQRAH. Tun a safiyar yau ta shirya tsaf a ɗakinta, tana jiran zuwan Champa domin ta kawo mata tufafin da ta saba sakawa a duk sanda take son ta yi fitar ɓadda kama ba tare da sanin kowa a fada ba. Lokacin da Champa ta kawo mata kayan yi ta yi kamar za ta sumbaceta dan farin ciki, cikin hanzari ta saka baƙaƙen tufafin a jikinta. Sannan ta rufe fuskarta, ta jawa Champa kunne kan kada ta kuskura ta fita daga ɗakinta, kuma duk wanda ya zo ganinta ta sanar da shi ita tace ba ta buƙatar ganin kowa. Da haka ta samu ta silale ta fita daga ɗakin, ta yi ta ratsawa ta faluka da wuraren hutawa dake cikin fadar. Har ta samu ta fita harabar fadar babu wanda ya ganeta, dan kanta a ƙasa take tafiya, yayin da ta sauya salaon takunta. Duk yawan masu gadin fadar da hadimai dake kai kawo babu wanda ya iya ganeta, da haka ta kutsa cikin gari, kyakkyawan birnin Jiyad na da kyawawan gine-gine irin na waccan lokacin. Sanda ta shiga cikin gari aka fara kiran sallah a babban masallacin garin, hakan yasa kaikawon mutane ya ƙaru, kowa na shirin tafiya masallaci. Kuma hakan kyakkyawar dama ce a gareta, wadda za ta yi amfani da ita wurin isa ga abin da take burin cimmawa. Can ƙarshen ganuwar garin ta bangaren yamma ta yi, har sai da ta fara nisa da gidaje, sannan ne ta fara hango shi a jikin wata bishiya ya jingina. Matashin saurayin SA'EID ALI, na sanye cikin tufafin Dishdasha, wasu nau'in kayan larabawa na wancan ƙarnin, wanda ake saƙa shi da zaren lilin, kayan ba masu tsada ba ne, hakan ya sa kowa kan iya saka shi a rayuwar yau da kullum. Rigar Dishdasha doguwa ce, haka ma wandon rigar. Kansa babu rawani, hakan yasa kyakkywan gashin kansa kalar (brown) bayyana. Mujiyarsa da ya yi wa laƙabi da Aafa na a kan kafaɗarsa ta dama. Tun da ya hangota ya fara murmushi, ya gyara tsaiwarsa har ta iso gabansa, suka tsaya kallon juna, duk da shi kwarmin idanunta kawai yake gani, dan gaba ɗaya ta rufe fuskarta, bayan idanuwanta ba ka ganin komai. Hannunta na dama ta saka ta buɗe fuskarta, hakan ya bayyanar da kyakkyawar hallitar fuskarta gare shi. “Tsawon lokacin da na ɗauka ba tare da na ganki ba ya sanya na ji kamar duniyar nan ba ta juyawa sarauniyar kyawawa, da fatan kina cikin ƙoshin lafiya” Cewar Eid cikin muryarsa me sanyi. Murmushi Iqrah ta yi, sannan ta jinjina kanta, domin ba ta ji tana da amsar maganar tasa ba, dan haka kai tsaye ta tafi kan maganar da ta haɗasu a wurin. “Ban sani ba ko labarin auren da Abbu yake son haɗawa tsakanina da yarima ɗan sarkin Mamlakatul Azad ya riskeka!” Lokacin da ta kai ga ƙarshen maganar tata fuskar Eid ta sauya launi, daga farin cikin ganin abar begen zuciyarsa zuwa baƙin ciki mabayyani. “Gimbiyata me ya sa za ki bari su fara ƙoƙarin rabani da ke?” Ya tambaya a dugunzume, Iqrah ta girgiza kanta, sannan ya yi taku biyu zuwa gareshi, sannan ta saka hannunta ta kamo hannayensa. “Ko da numfashina zai rabu da gangar jikina ba zan taɓa bari wani ya rabani da kai ba Eid, domin kai nake so, ba na son wani bayan kai, kuma kai kaɗai nake so a matsayin ABOKIN RAYUWA!” (Anty Candy's new book, lolz). Eid ya girgiza kansa, tare da ƙwace hannayensa da ta riƙe, ya juya bayansa yana kallon birnin Jiyad, murya ɗauke da damuwa ya furta. “Ba haka ba ne Mehbuba. Ƙoƙarin haɗa aurenki da wani bayan ni na nufin zan rasaki har abada, kuma rasaki a rayuwata na nufin zuwan ƙarshen numfashina!” Iqrah ta sake girgiza kanta, sannan ta zagayo ta sake tsayawa a gabansa. “Da ace ka mutu kai kaɗai gara ace tare muka mutu, mu mutu ba tare da mun mallaki juna ba na nufin ba mu cimma burin soyayyarmu ba, dan haka ni na yanke shawarar mu guda kawai mu je domin a ɗaura mana aure!” Eid ya mata wani irin kallo, sannan ya girgiza kansa. “Ba na so Malik ya cutar dake Mehbuba ba zan iya zuba ido ina kallo a cutar min da ke ba” “A'a Eid, zan iya yin komai a kan soyayyarmu, dan haka na yanke shawarar za mu gudu tare da kai a ranar da za'a ɗaura mana aure da wancan yariman, kuma a wannan ranar nake so a ɗaura mana aure ni da kai masoyina” Eid ya tsaida dubansa a kanta. “Kin tabbata abar sona?” Ta gyaɗa kai. Daga haka suka shiga tsara yanda shirinsu na guduwa daga birnin Jiyad zai kansace. Ba tare da sanin abin da hakan ka iya jawowa ba. Sai da suka gama tsara shirin nasu, sannan ta masa sallama ta tafi. Sai da ta ɓace masa da gani, sannan Eid ya sheƙe da dariya, har da hawaye, kafin lokaci guda ya haɗe rai. Ya saka ɗan yatsansa ya ɗauke hawayen da ya zubo masa. “Dole ne Malik Cangaz ya biya bashin da ya ci... Kuma wannan kyakkyawar dama ce da zan yi amfani da ita wurin rama abin da ka min!” Lokaci guda kalar zaluncin da Malik Cangaz ya aikata masa ya shiga dawo masa, amma sai ya yi saurin ture komai, ya sauƙo da mujiyarsa dake kan kafaɗarsa, bayanta kawai ya shafa, ta rikiɗa ta zama ƙatuwa. Ya kama bayanta ya ɗale, sannan ta buɗe fukafukanta ta tashi sama da shi. Salma Ahmad Isah ✍️. _____________ _Ta ko ina littafin nan ya kama da wuta, dan ƙiri ya rage papers ɗin book ɗin su ƙone!🤣._ _Na ce muku tafiyar bana ta sha bamban da sauran_ _Dan haka sai ku sake shiryawa, domin jarumanmu na cikin tuƙeƙiyar matsala._ _Sannan kar a manta da biyan kuɗin book, regular group ₦400, VIP ₦800._ _Ku tura kuɗinku ta account details ɗin da zan rubuta a ƙasa_ 5487270431 Salma Isah Monie point A tura shaidar biya ta 08130172702. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-12 ADVENTURERS. Tafiyarsu ta miƙa a cikin dajika da tsaunika, sun yi tafiya irin wadda ba su taɓa yi ba a rayuwarsu, hatta shi kansa Uwais bai taɓa yin doguwar tafiya irin wannan ba, dan ko shi kansa ba sanin hanyoyin ya yi ba, ta hanyar wannan taswirar da suke ɗauke da ita ne kaɗai suke iya gane hanyoyi. Batun abinci kuwa tun kafin su ji yunwa Uwais yake kawo musu abin da za su ci, tun abincin ba ya musu daɗi har ya zamto sun fara sabawa da abincin. Ranar da suka cika kwanaki biyar da barin ƙauyen Askar cif, suka shiga wani daji me yawan dogayen duwatsu. Su huɗun cif suna tafe a tare, Arman da Adam na kan gaba, yayin da camera ɗin Adam ke rataye a wuyansa, dan ba ya rabo da ita, daga zarar ya ga abin ɗauka zai ɗauke shi a hoto. Ivana da Uwais kuma na daga baya suna hirar da suka saba yi a lokuta irin wannan. “Me yasa kake yawan kallona?” Ivana ta jefa masa tambayar, dan za ta iya cewa daga zarar tana wuri Uwais ba shi da abin kallon da ya wuce ita. “Saboda irin shigar da kike, da farko na ɗauka cewa ke ba musulma ba ce, sai da na ga yanda kike suturta jikinki lokacin da za ki yi sallah, amma kuma bayan kin idar sai ki yaye ki koma shigarki mai nuna tsaraici!... Sai na cewa kaina, idan har za'a suturta jiki yayin yin ibadar Allah, me zai hana a ci gaba da suturta jiki ko ba lokacin da za'a bauta masa ba, domin zamanki da irin wannan shigar na cikin saɓa masa!” Hatta Adam da Arman sai da suka tsaya suna dubansa, saboda ya yi magana ta hankali. Ganin suna kallonsa yasa yace. “Ku yi haƙuri fa, na fuskanci kamar hakan ba komai ha ne a zamaninku... Amma ni gani na yi ya kamata ace na faɗa mata gaskiya” Ivana ta dubi shigar dake jikinta ta slacks trouser peach color, da farar blouse, wandon sam bai kai idon sawunta ba, har gwanda ma rigar na da ɗan tsayi, kuma duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, domin ita kanta ta san cewa abin da suka yarda da shi a matsayin wayewa kauce hanya ne... “Ki yi haƙuri idan maganata ta sa kin ji ba daɗi!” Uwais ya sake faɗa yayin da suka ci gaba da tafiya, ta girgiza masa kai tana murmushi, alamun ba komai, sannan ta gyara zaman jakar guitar ɗinta dake goye a bayanta, dan yanzu Arman ne yake ɗauka mata kaya. “Mi ye sunan abin da yake cikin jakar nan, na ga kina yawan kulawa da shi” Uwais ya tambaya. Ivana ta kalle shi, amma kamar yanda wancan Uwais ɗin yake mata magaba ba tare da ya kalleta ba shi ma wannan haka. “Guitar sunanta, kuma ana yin kiɗa da ita, kamar dai sarewarka!” Ya jinjina kansa. “Ina son kiɗa sosai” Ya faɗa, kamar yanda wancan Uwais ɗin ya taɓa faɗa mata cewar yana son kiɗan guitar. “Ka iya busa sarewa?” “Sosai, ko kina so ki ji?” Ta gyaɗa kai, sai ya saka hannunsa ya zaro sarewar tasa dake saƙale a ƙugunsa, sannan ya kafata a bakinsa, ya soma busa sarewar cikin sauti me daɗin saurare, wanda ya cakuɗe da yanayin sanyin dajin da suke ciki. Hatta su Adam kansa busar sarewar tasa na musu daɗi. Hakan yasa tafiyar tasu ta ƙara armashi, suna tafe yana musu busa me kwantar da hankali, a lokacin kuma suka yi kiciɓis da tawagar wasu mutane, sanye cikin shigar jajayen kaya. Hakan ya sa suka tsaya suna kallon yawan jama'ar, kafin su yi wani yinƙuri har mutanen sun musu ƙawanya... Kuma sam ba su da kataɓus, dan sarkin yawa, ya fi sarkin ƙarfi. ASRA. Tsaye take a cikin dakarun da take da alhakin koyar da su salon yaƙi na masarautar Jiyad, yayin da suke a wani babban fili da aka tanada domin koyar da faɗa a cikin masarautar, wani lallausan yashi ne zube a ƙasan wurin, yayin da muggan makamai na koyon salon yaƙi ke aje a ko wace kusurwa na wurin. Ta harɗe hannayenta, yayin da take kallon yanda ɗaliban nata ke nuna mata abin da ta koyar da su. Tun daga nesa suka fara jin takun sawun masu gadin Malik Cangaz, hakan yasa ta dakatar da ɗaliban nata tun kafin ƙarasowar sarki wurin. A kan idonsu aka buɗe ƙofar filin, Malik Cangaz tare da masu tsaronsa suka shigo cikin filin. Hakan yasa Asra da ɗalibanta duka suka durƙusa domin kwasar gaisuwa. Sai da sarki ya amshi gaisuwar tasu, sannan kowa ya miƙe kan ƙafafunsa, hakan ya bawa Asra damar matsawa kusa da Malik, domin jin abin da ke tafe da shi. Yau ma kammaninsa sak na matasa, ba za ka ce shi ne mahaifin gimbiyoyin uku ba, kai kace wani yayansu ne. “Horarwa na tafiya yanda ake so Asra!” Cewar Malik cike da izza, Asra ta yi murmushi tana duban mahaifinta, sannan ta jinjina kanta a ladabce. “Sosai ma kuwa Darvesh (Holy man)” “Ko za mu iya ganawa na wasu daƙiƙu?” Faɗin Malik Cangaz, Asra ta gyaɗa kai, a tare suka taka zuwa wata kusurwa dake cikin filin, wadda ta fitar da su (balcony) dake can saman fadar, daga wurin ma za ka iya hango gine-ginen gidaje masallatai da kuma kasuwar masarautar kaf. “Zuwa yanzu kwanaki uku kacal suka rage a ɗaura auren Iqrah da yariman Azad... Duk wasu shirye-shirye mun kammalasu, ɓangaren tsaro ne ba mu yi komai ba, dan haka ina so a tabbatar da tsaro a masarautar nan, domin akwai tarin baƙin da za su zo daga baƙin masarautun da suke maƙotantaka da mu... Ba na son a samu wani kuskure!” Asra ta jinjina kai tana saƙala gashin kanta a bayan kunnenta. “Zan tabbatar da hakan Darvesh...” “Zuwa gobe zan je kaiwa abokina sarkin Mamlakatul Dahi goron gayyata, domin ba na so na aika Manzo! Na fi so na je da kaina domin isar da saƙon... Dan haka ki shirya, ina so ki min rakiya!” Asra ta risina cikin girmamawa. “An gama Darvesh...” “Na sallameki” Da haka ta juya ta barshi tsaye a wurin yana kallon girman masarautarsa. Kafin kuma amintaccen hadiminsa ya shigo wurin a hanzarce. “An kamo matasan da ake zargi da cin amanar ƙasarmu ta hanyar fitar da bayanan kasuwancinmu na sirri ya shugabana!” Cewar hadimin, bayan ya kwashi gaisuwa. Malik ya dube shi cike da isa, sannan ya furta. “A kai min su kurkukun cikin ƙasa, a gana musu azaba ta mako guda, kafin na kai ga zartar da hukuncin da ya dace a kansu, kafin su mutu ina so su ɗanɗana azabar da za ta bawa duk wani me sha'awar aikata laifi irin nasu tsoro!” Hadimin ya risina cikin alamar dake nuna ya karɓi saƙon shugaban nasa. “An gama ya kai wannan adalin sarki!” Daga haka shi ma ya fita daga wurin ya barshi, tsaye cikin sallalamin jiran ranar da boka Jalis zai sake naimansa. Domin tun bayan ranar da suka haɗu a kan maganar gano matasan nan uku bai sake naimansa ba, kuma hakan na nuna cewa har yanzu boka bai gano inda suke ba. A tsarinsa shi kuma ba ya zuwa wurin bokan ba tare da bokan ya naime shi ba... Amma a wannan karon dole ya karya ƙa'idar, dole ya je ya ji yanda aka yi aka haihu a ragaya. MAMLAKATUL AFSAH. Cike da zaƙuwa Malik Safraz ya ɗaga kai ga tawagar ɓoyen da yakan aika domin bincike, ya ƙagu su sanar da shi inda takobin mulkinsa yake. “Ya shuganmu, haƙiƙa takobinka ya bayyana a ban ƙasa, sai dai samunsa shi ne abu mai matuƙar wuya a gareka!” Muryar ɗaya daga cikinsu ta furta, ba tare da ya bayyana ba, domin ko shi kansa ba ya iya ganinsu sai idan sun so hakan. Ya ɗaga kansa ya kalli saitin inda maganar ke tashi, sannan ya furta. “Shin har akwai wani abu da zai gagareni samu a faɗin wannan duniyar?” “Ƙwarai kuwa ya shugabanmu, kuma wannan takobi na ɗaya daga ciki!” “Me nene dalilinku na faɗin hakan?” “Wanda yake tare da takobin shi ne abin ji, domin ko da yankar naman jikinsa za'ayi a kan takobin nan sai dai a yi, amma ba zai taɓa bari a raba shi da wannan takobi ba...” “Waye shi?” Malik Safraz ya tambaya ransa na ɓaci. “UWAIS!” Muryoyi uku suka ba shi amsa take, a nan ne fa hantar cikinsa ta fara motsi, domin in har Uwais ko Feroza na raye a ban ƙasa mulkinsa na cikin haɗari!... Ke nan me ya kamata ya yi a wannan gaɓar!?... Tambayar ta tuno masa da wata hatsabibiya ɗaya da zai iya sawa wannan aikin hankali kwance. Lokaci guda ya yi murmushi, sai kuma ya haɗa da dariya yana jinjina kai, sannan laɓɓansa suka furta sunanta. “NATILA!” GARIN QUDWA, YANKIN GABASHIN SAHARAR SUBAH. Hayaniyar jama'ar dake kaikawo a cikin 'yar ƙaramar kasuwar garin ce ta cika ko ina. Komai na kayan siye da siyarwa daga ƙasashen duniya akan kawosu kasuwar wannan gari na Qudwa. Domin garin ya kasance cibiyar kasuwanci, duk da garin bai cika girma ba. Ko wani mutum dake cikin kasuwar za ka same shi sanye da shiga irin ta garinsu ko yankinsu, ko kuma masarautarsu. Yayin da ake hada-hadar cinnikayya a cikin kasuwar. Wata iska me ƙarfi ta taso daga cikin sahararar dake gabas da kasuwar, hakan yasa ƙura ta shiga bule mutanen cikin kasuwar. Kafin wata guguwa ta shigo cikin kasuwar, sannan ba ta sauƙa a ko ina ba sai kan rufin wani shago. Kaɗan-kaɗan iskar ta fara raguwa, har ta ɗauke gaba ɗaya. Yayin da wannan guguwar ta rikiɗa zuwa wata doguwar budurwa. Sanye cikin baƙaƙen kaya, ta yi kitso guda biyu a kanta, tsayin jelar kitson har cinyoyinta. Fuskanta kuma a rufe yake, a hankali ta yi tsugunnon mage a kan rufin shagon, sannan ta shiga baza idonta a kan mutanen dake kai kawo... Dan iskar da ta taso ba ta sa kasuwancin da ake gudanarwa ya dakata ba, sautin murmushin da ta yi ya fito tare da motswar ƙyallen da ta rufe fuskarta da shi, domin ta hango abin harinta, ci gaba ta yi da bin sawunsa, har ta ga sanda ya shiga wani loko da take da tabbacin babu kowa ciki. Take ta ɓace daga saman shagon, kuma ba ta bayyana a ko ina ba sai a cikin lokon, sannan a gaban mutumin da take bibiya. Shi kansa mutumin da ya ganta sai da ya razana, hakan ya sa kayan dake hannunsa suka zube a ƙasa, ya ɗaga hannayensa sama kamar me laifi. A wannan karon budurwar dariya ta yi, sannan ta buɗe fuskarta, kyakkyawar fuskarta ta bayyana gare shi, haƙika tana da kyau, amma kyawun ɗan maciji. Lokacin da ya ganeta bai san sanda ya saki fitsari a wando ba, jikinsa ya soma kyarma, domin ganin NATILA na dai-dai da ganin mutuwar mutum. “Sannunmu da sake haɗuwa, Malam Ayyaz!” Jikin Ayyaz na rawa ya shiga ja da baya yana son bata haƙuri, cikin wani irin sauri da ya ɗararma hankali ta isa gabansa, sannan ta saka hannayenta ta riƙe wuyansa. “Dole na kasheka, sannan na ciro zuciyarka na kaiwa shugabana, na masa alƙawarin sadaukar masa da zuciyarka a daren yau!...” Ta ƙarashe maganar wasu zaƙa-zaƙan fiƙoƙi na fitowa daga haƙwaranta na sama. Sannan ta kafasu a wuyansa, nan take Ayyaz ya fara shure-shure, amma Natila ba ta saki wuyansa ba sai da ta zuƙe fiye da rabin jinin jikinsa. Duk da haka ba ta ƙyale shi ba, da ta saki wuyan nasa ta ɗaga hannunta me yalwar dogayen farata, ta caka a ƙirjinsa, sannan ta ciro zuciyarsa, kana ta saki gangar jikinsa ta faɗi ƙasa. Zuciyar dake riƙe a hannunta ta kalla, bakinta duk ya ɓaci da jinin jikinsa, ta sa bayan hannunta goge bakin nata, sannan ta sake rufe fuskarta, ta tsallake gawarsa ta ɓace a iska. Salma Ahmad Isah ✍️ ___________ _😳 Akwai matsala!_ _Ko su waye suka kama ADVENTURERS ɗinmu?. Shin ya za a yi su kuɓuta?_ _Batun wannan Natilar! Ya kuke ganin haɗuwarta da ADVENTURERS ɗinmu za ta kasance?._ _Book 1 ya kusa ƙarewa, dan haka ya kamata a fara biyan kuɗin book 2 tun yanzu._ 5487270431 Salma Isah Monie point Shaidar biya kuma ta 08130172704. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-13 ADVENTURERS. Kukan Adam shi ne ya cika ɗan ƙaramin akurkin da aka cusasu ciki, dan duka su huɗun tare da wata mata da ba su santa ba na cikin wani abu me kamar keji, yayin da mutanen da suka kamosu ke zaune kusa da kejin, sun yi ayari suna gabatar da bautarsu zuwa ga wutar da suka hura, domin sun lura cewa mutanen wuta sukw bautawa. Kuma bayan hasken wutar babu komai a wurin sai na farin wata da ya samu zarafin ratsowa ta jikin ganyen bishiyoyin da suke a ko ina na dajin, sai kuma na fitilun wayoyinsu da suka kunna. Tun bayan da mutanen suka kama su ba su musu komai ba, kuma ba su ce da su komai ba, sai kallonsu da suke ta yi tun ɗazu, kamar za su cinyesu. “Mi shan Allah Adam skut! (Dan Allah Adam ka yi shiru!)” Cewar Ivana cikin rarrashi, Adam ya goge hawayen da yake, yana duban Arman dake wurga masa harara, shi kuma Uwais kallonsu kawai yake yana murmushi, dan kukan da Adam ɗin ke yi dariya yake son ba shi. “Ki bar ni na yi kuka, wata ƙila wannan shi ne kukana na ƙarshe, daga shi kuma ba zan sake ba!... Saboda waɗannan abubuwan yanka mu za su yi, ko su cinye, ko su bawa dabbobinsu!...” Ya ƙarashe yana jingina kansa da jikin itatuwan da suka kafa kejin. “Idan ba ka mana shiru ba sai na maka duka!” Cewar Arman a ƙufule. Sannan ya ƙara da. “Kalli Ivana, ko ita ba ta yi kuka ba sai kai, ƙaton banza kawai!” Adam ya kame jikinsa yana ƙifƙita ido. A karo na barkatai, Arman ya sake haske matar da suka tarar a cikin kejin da fitilar wayarsa, amma har yanzu tana a yanda suka shigo kejin suka sameta. Dunƙule take a wuri guda, ta haɗa kai da gwiwa, kuma duka jikinta a rufe yake. “Uwais ka tambaya mana wannan matar ko ta san abin da mutane nan suke so!...” Cewar Arman yana gyara zaman glasses ɗinsa. “Da ace za ta faɗa da ta faɗa tuntuni, tun yaushe nake mata magana? Amma ko tari ka ji ta yi?...” Uwais ya ƙarashe da tambaya. Arman ya girgiza kansa yana ci gaba da haska matar, sannan ya ƙura mata ido. A hankali ya fara takawa zuwa inda matar take, yana daf da durƙusawa a kusa da ita, mutumin da suke sa ran shi ne shugaban mutanen da suka kamasu ya furta. “Ku je ku fito da su yanzu mu sadaukar da su ga wutar bautarmu!” Hakan ya sa Arman ya fasa durƙusawa, ya juyo ya kalli abokansa cikin tashin hankali, Ivana ta dubi Uwais, sannan ta dubi Arman, yayin da Adam ya ƙara fashewa da wani sabon kukan yana faɗin sun mutu. Har zuwa lokacin da wasu mutum biyu suka buɗe ƙofar kejin da suke ciki ba su iya taɓuka komai ba, sai da aka gama fito da su daga cikin kejin, har da matar da a yanzu suka lura da cewa fuskarta a rufe take, aka jerasu a gaban wutar dake ciki. “Dan Allah Arman ka yi wani abin!” Cewar Adam cikin kuka. Arman ya lumshe idonsa, yayin da yake lalubo takobin da datijjo ya ba shi a cikin jakar dake bayansa. A lokacin da ya riƙo takobin ya buɗe idonsa, sannan cikin zafin nama ya miƙe tsaye, ya zare takobin yana nuni da shi ga mutanen da suke riƙe abokansa da wannan matar. “Kada ku cutar da su! Ku ƙyalesu!” Ya faɗa yana nuna musu takobin. “Me kuke jira wai? Ku danna min kawunansu a cikin wuta!” Shugaban mutanen ya basu umarni cike da isa, wanda yake riƙe da Adam ne ya riƙo gashin kansa, yana shirin danna kan Adam a cikin wutar Arman ya yi tsallen albarka, ya ɗaga takobin hannunsa ya datse hannun mutumin!. Ƙarar da ya ƙwalla ce ta janyo hankalin sauran mutanen wurin. Sannan kuma ita ta razana sauran da suka ga faruwar lamarin. Sai suka yi saurin ja baya daga jikinsu Ivana, yayin da shi ma Uwais ya yi amfani da wannan dama wurin juya sarewarsa zuwa baka, sannan ya motsa hannunsa ya fito da kibiya, tare da sakata a jikin bakar, shi ma ya nuna mutanen da ita. Adam da Ivana kuma suka yi saurin ɓuya a bayansu, su kuma suka musu garkuwa, amma wannan matar ta ɗazu har zuwa lokacin tana durƙushe a gaban wutar, ba ta motsa ba ballantana ta yi yunƙurin guduwa, kuma kanta a ƙasa, sannan fuskarta a rufe. “Lalle kun aikata babban kuskure, tun da har kuka iya illata ɗaya daga cikinmu, kuma a sansaninmu... Ina me muku albishir da ba za ku bar nan da rai ba... Dakaru! Ku tabbatar da kun gama min da su yanzu...!” Cewar shugaban dakarun, nan da suka yi kan Arman da Uwais, amma kuma sam ba su ba su damar cutar da ɗaya daga cikinsu ba, domin sun zage iya ƙarfinsu suna yaƙin kare kai. Ƙarshe ma shi Uwais fuka-fukansa ya buɗe ya tashi sama, daga saman yake harbin mutanen da kibiya, yayin da Arman ya bada himma wurin sarrafa takobi daga ƙasa. Amma kamar ƙara musu yawa ake. A nan ne fa Arman ya fara gajiya, saboda sam shi bai saba ba, hakan ya sa ƙarfinsa ya fara gazawa, har ta kai ga an samu wani a cikin dakarun ya buga masa wani madoki. Da ya yi nasarar kai shi ƙasa, hakan ya jawo glasses ɗinsa suka faɗi ƙasa, duhu ya mamaye ganinsa, sannan takobin hannunsa ma ya faɗi gefe guda. Dakaren da ya samu nasarar kai shi ƙasa ya tsaya a kansa yana dariyar cin nasara. Adam da Ivana kuwa na gefe suna ganin ikon me duka, duk yanda suke jin ana batun yaƙi a tarihi ne kawai, ashe akwai lokacin da za su tsinci kansu ana yaƙi a gabansu. Ita Ivana Uwais ma ya fi bata mamaki, dan su duka ba su taɓa sanin cewa yana da fuka-fuki ba. Lokacin da Arman ya faɗi suka ankara, dan haka ita da Adam suka yi wurin domin ceton abokinsu dake laluben glasses ɗinsa a ƙasa, domin ba ya ganin komai, yayin da shi kuma mayaƙin dake kansa ya ɗaga mashi yana shirin soka masa... “Kai!...” Cewar Ivana hankali tashe, yayin da ta nufi wurin Arman da gudu, Adam na binta a baya. Sai dai kafin su ƙarasa wurin, wani takobi da aka cillo daya can baya ya caki mayaƙin a ciki... Hakan ya sa suka taka birki suna kallon mayaƙin, yayin da yake silalewa zuwa ƙasa. Baki buɗe kuma dubansu ya zarce zuwa inda aka wullo takobin, ganin wannan matar ta ɗazu tsaye, kuma riƙe da takobi yasa suke san cewa ita ce wadda ta cillo takobin wannan takobin. Take mayaƙan da abin ya faru kan idonsu ita ma suka far mata, tsayuwarta ta gyara, tare da gyara riƙon takobinta, tana jiran isowarsu, kuma har zuwa lokacin fuskarta a rufe take. Ai suna isa wurin da take aka fara yaƙin gaske, dan yanda suka baibayeta sai kace za su cinye namanta ɗanye, amma ba ka jin komai sai ƙaran takobinta, daga ta kai suka wuri za ka ga gawa na faɗuwa ƙasa timm. Nan fa wurin ya yamutse, gawawwakin mutanen nan ne kawai suke zuba. A lokacin kuma Adam da Ivana suka samu isa wurin Arman dake yashe a ƙasa, suka samu suka ɗaga shi zaune, sannan Adam ya ɗaukar masa glasses ɗinsa da glass ɗin frame ɗaya ya fashe, amma duk da haka suka saka masa, domin ya samu ya ga wannan bidirin da ake a filin. “Sannu Arman” Cewar Adam yana miƙar da shi. Zaman glasses ɗin ya gyara, yayin da ya tsayar da dubansa a kan matar nan ta ɗazu dake ta'asa a filin wurin, hatta Uwais ɗan kallo ya koma... Domin yanda take sarrafa takobi a wurin ya matuƙar basu mamaki. * Arman ya sa hannu ya buɗe kit ɗin glasses ɗinsa, domin ɗaukar wanda ya rage masa, tun da wanda yake tare da shi ya fashe. Guntun glasses ɗin ya ɗauka, sannan ya sa hannu ya cire na idonsa, kana ya saka wanda ya ɗauka, ya maye wurin wanda ya ɗauka a cikin kit ɗin da wanda ya cire a idonsa. Ya kuma gyara zaman glasses ɗin a idonsa, sannan ya saka yatsun hannunsa a cikin sumarsa da ta yamutse, yana ɗaga kansa, tare da kallon Ivana dake zaune kan sleeping bag ɗinta, dan bayan sun rasa tent ɗinsu a kan sleeping bag ɗin suke kwana. Yanayin zamanta kaɗai zai sa ka gane cewa a gajiye take, domin sai da ta jingina da bishiyar dake kusa da ita, tana bincika wani abu a cikin backpack ɗinta, yayin da suke magana da Uwais. Ya juya kansa zuwa ɓarin damansa, inda Adam ke zaune a kan tasa sleeping bag ɗin, shi kuma lafiyar camera ɗinsa yake bincikawa saboda ɗazu ba a gama yaƙin nan ba sai da ya ɗaukeshi a hoto. Batun yaƙi da ya gifta a cikin kansa ya sa ya yi saurin kallon wannan budurwar ta ɗazu da ita kaɗai ɗinta ta ƙarar da mayaƙan ɗazu. Tana zaune daga kan wani itace, ta saka wani ƙyalle tana goge jinin da ya ɓata takobinta mai tsananin kaifi, wanda ta yi ta'asa da shi ɗazu. Hankalinta kwance, kamar ba ita ce ta yi kashe-kashen ba. Har zuwa yanzu da suke zaune a wurin ba ta yi magana ba, hakan yasa suka fara zaton ko kurma ce. Shi kuma Uwais yana daga gefen Ivana, yayin da take masa bayani a kan chocolate ɗin da ta ba shi. “Miye ma kika ce sunan shi?” Ya tambayeta yana juya ledar chocolate ɗin. Ivana ta yi murmushi a gajiye, ita ba ita ta yi yaƙin ba, amma haka take jinta a gajiye. Ko wannan tafiyar ƙafan da suke ma ai dole ta gaji, tun da abu ne da ba ta saba ba. “Shukulata, da turanci kuma Chocolate!” Ya jinjina kansa yana taɓe baki, sannan ya kaita baki zai ci da ba tare da ya cire laidar ba, ta yi saurin dakatar da shi. “A'a zai ka cire ledan fa” Ta karɓa daga hannun shi, sannan ta buɗe masa ledan, shi dai kallonta kawai yake, ta sake miƙa masa. “Mi ye shi ledan?” Ta yi dariya. “Ana sakawa ne domin ya bawa chocolate ɗin kariya daga datti ko cutuka kafin a ci, kuma yana ƙara tsayin daɗewar chocolate ɗin...” Ya sake jinjina kansa. “Kuma yana da daɗi?” Ta gyaɗa masa kai tana nannaɗe gashinta cikin top knot bun. Uwais ya saka chocolate ɗin a baki, sannan a hankali ya gutsira, ya fara taunawa yana juya idonsa. “Da akwai daɗi ba?” Ivana ta tambaya. “Akwai daɗi sosai” Ya bata amsa yana murmushi. A dai-dai lokacin kuma Arman ya tambayi wannan matar. “Wacece ke? Me ya sa waɗannan mutanen suka kama ki?” Tambayar da ya mata ta jawo hankulan sauran. Suka dubeta, cak ta tsaya da goge jinin da take, sannan ta kallesu da idonta. “SANA!” Kawai suka ji ta furta, sannan ta sa hannu ta yaye ƙyallen da ta rufe fuskarta da shi, cikin su ukun babu wanda ya santa, amma shi Uwais ya san fuskarta, ba ma ita kaɗai ba, har ma da sauran 'yan uwanta uku babu wanda bai san kamarsa ba, duk da bai taɓa ganinsu ido da ido ba. “DANEEN SANA BINT MALIK CANGAZ!?” Shi ne kaɗai abin da Uwais ya samu furtawa. IQRAH. Zaune take a wani wuri da aka keɓe a fadar domin shaƙatawa. Akwai wani (Fountain) dake tsakiyar wurin, yayin da (grass carpet) ke zube a ko ina na wurin, sannan akwai iska me daɗi dake busawa a ko ina. Hadimanta na zaune a ƙasa, yayin da suke bata labaran nishaɗi, ita kuma sai murmushi take. Domin duka wasu tsare-tsare da suke ita da Eid na guduwarsu a ranar da za'a ɗaura aurenta ya kamalla, hatta da ƙauyen da za'a ɗaura musu aure Eid ya zaɓa musu. Yanzu ranar ɗaurin auren kaɗai suke jira, domin sun yanke cewa ba za su gudu ba sai a ranar da za'a ɗaura auren. Buɗe ƙofar shiga sashen da aka yi ya sa hankulansu ya koma zuwa wurin, Asra tare da wasu bayi har uku ne suka shigo wurin. Ko wacce baiwa na ɗauke da wani (tray) da aka rufe da ƙyalle. Asra na sanye da wata Thawb kalar ruwan zuma, ta ɗora Muƙawar a kanta, wanda bai ɓoye dogon gashin kanta ba, tana tafiyarta irin ta jarumai, dan sam ba ta tafiya irin ta sauran mata. Da hannu ta yi wa hadiman Iqrah alama da su basu wuri, hakan ya sa duk suka fice daga wurin, Iqrah ta miƙe tsaye tana kallon 'yar uwarta. “Barka da zuwa Ukti!” Cewar Iqrah tana murmushi. Ita kuma Asra sai ta murtuke fuska tana binta da kallon tuhuma, dan haka kawai take jin ba ta yarda da ita ba. Da farko tace mata ba ta son wannan haɗin auren, ya za'ayi yanzu kuma ta zo tana murmushi?... Dole dai da akwai abin da take ƙullawa. “Sarƙoƙi ne Darvesh ya aikoni da su, yace a kawo miki ki zaɓi wanda kike so” Cewar Asra, tana yi wa bayin alama da su nunawa gimbiya kayan da suka zo da su. Iqrah ta nufi wurin bayin, ta ci gaba da duba sarƙoƙin, sai fara'a take abinta. “Wannan sun fi kyau” Ta nuna wadda ta fi burgeta. Hakan ya sa Asra ta duba wadda ta zaɓa, ba tare da ta furta komai ba ta sallami bayin, sai da suka fita sannan ta dubi 'yar uwarta da kyau. “Ina mai fatan Allah yasa ba wani abin kike shiryawa ba” Cewar Asra, Iqrah ta kuma yin murmushi. “Kada ki damu 'yar uwa, ba zan aikata abin da yake ba dai-dai ba!” “Ni ma haka nake fata” Cewar Asra tana jinjina kai, da haka ta fita ta bar Iqrah a wurin. Salma Ahmad Isah ✍️ _Pages ɗaya ya rage book 1 ya ƙare, idan regular group kike so za ki tura ₦400 through account details ɗin da zan rubuta a ƙasa. Idan kuma VIP ne sai a tura ₦800._ 5487270431 Salma Isah Monie point Shaidar biya kuma ta 08130172704. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-14 MAMLAKATUL AFSAH. Zaune a gaban Malik Safraz Natila ce, sanye cikin baƙaƙen kaya, amma yau fuskarta ba a rufe take ba. Ta nutsu tana sauraron buƙatar Malik da yake so ta biya masa. “Idan dan ta wannan ne kada ka damu Shugabana. Zan tattaro sauran yarana, za mu bisu har zuwa cikin dajin da suke, kuma zan tabbatar da na ƙwato maka takobinka!...” Malik Safraz ya yi murmushi, dan ya san aikin Natila, idan tace za ta yi to za ta aikata. Ya sha sakata ayyuka makamantan wannan, kuma cikin sa'a tana nasara. Miƙewa tsaye ya yi, yana goya hannayensa a baya, sannan ya ƙarewa katafaren falon da suke ciki kallo, kana ya juya bayansa yana faɗin. “Idan kuwa har kika kawo min wannan takobin, zan miki gagarumar kyautar da ban taɓa miki irinta ba!” Natila ta miƙe tsaye, sannan ta amsa da. “Zan kasance me cika alƙawari kan abin da na alƙauranta maka shugaba, ba zan taɓa baka kunya ba!” Malik Safraz ya sake murmusawa, sannan ya juyo ya dubeta. “Ki je domin ƙwato min takobina!” Ta risina alamun ta amsa. Kana ta ɗaga kai, kafin kace me har ta ɓace. A lokacin kuma Anser mahaifin Safraz ya iso falon shaƙatawar sarkin tare da masu take masa baya. Sai da ya isa falon sannan ya yi musu izini da su jira shi a waje, sai da suka fita sannan ya dubi ɗansa. “Wata magana nake ji haka Safraz?...” “Wata magana kuma?” Safraz ya mayar masa da tambayar. “Magana nake a kan ƙwatar takobi daga hannun Uwais!” “Shin laifi ne dan na karɓi abin da yake nawa?” Safraz ya tambaya cikin halin ko in kula. “Abin da nake so ka fahimta a nan shi ne, yanzu kai ne sarkin Afsah, wannan takobin ba zai kareka da komai ba, tun da ko a da rashinsa bai sa ka kasa zama sarki ba” Safraz ya girgiza kai. “Ba wai mallakar takobin ne kaɗai abin da ya tsaye min a rai ba. Kasancewar Uwais da Feroza a raye shi ne babban abin da yake damuna... Idan har Uwais ya ci gaba da kasancewa a raye ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba, domin mulkina zai kasance cikin haɗari, wanda ni kuma ba zan lamunci hakan ba!” Anser ya sake matsawa kusa da ɗansa, sannan ya dafa kafaɗunsa. “Rabuwarka da Uwais shi ne abu mafi alkairi, idan har ka ce za ka ci gaba da bibiyar rayuwarsa to fa ni da kai duka ba za mu ji daɗi ba. Dan haka a shawarce ka ƙyale shi zai fi!” Safraz ya ture hannayen mahafinsa dake kan kafaɗunsa, sannan ya tashi sama ya fara yawo a iska yana faɗin. “Ba zan ƙyale shi ba, dole cikin biyu a yi ɗaya, ko dai shi ya mutu, ko Feroza ta mutu!...” Yana gama faɗin hakan ya ratsa rufin falon ya fice ta wurin. MALIK CANGAZ. Kallon kallo aka shiga yi tsakaninsa da Boka Jalis dake sanar masa da wurin da matasan da yake naima suke. Can kuma sai ya kwashe da dariya yana cilla kansa baya. “Tabbas zan taƙaita musu kwanakin tafiyar dake gabansu!” Ya faɗa bayan ya gama ƙyaƙyata dariyar tasa. Cikin rashin fahimta boka Jalis yace. “Ban fahimceka ba shugabana!” “Tun a daren yau zan shirya dakaru, sannan na turasu suje su tarbesu kafin su samu isowa nan!” Malik Cangaz ya bawa Boka Jalis amsa. Shi dai boka bai cce ƙala ba, dan shi ya hango abin da ya hango. Har suka gama tattaunawa da bokan bai sanar da shi wani abu bayan nasara ba. Da wannan farin cikin ya koma fada, duk da akwai manyan baƙi dake zuwa domin halartar bikin gimbiya bai sa ya fasa sawa a shirya dakaru domin turasu ƙwatar mukullin dake hannun baƙin matasa uku ba. Sai da ya gama da wannan fannin, sannan ya dawo cikin fada ya fuskanci lamarin baƙinsa, a gefe guda kuma shirye-shiryen bikin gimbiya na ci gaba da wanzuwa a fadar, domin duk mutanen gari sun san cewa za'ayi biki a gidan sarki. EID. Hannu ya miƙa ya karɓi sabbin tufafin da ya siya a wurin wani mutum dake cikin kasuwar ƙauyen Aban, domin ƙauye aban shi ne ƙauyen da ya zaɓa domin gudanar da ɗaurin aurensa da gimbiya Iqrah. Auren da zai yi amfani da shi wurin tarwatsa zuciyar Iqrah, auren da zai yi amfani da shi wurin rama kwatankwacin abin da Malik Cangaz ya aikata masa. Sai dai kuma ta wata hanyar wannan auren ya taɓa rayuwarsa, tun farko shi ba son gaskiya yake yi wa Iqrah ba, hasali ma komai yake faruwa tsakaninta da shi duka shiri ne. Domin hatta da farkon haɗuwarsu shiri ce, shirin da ya taso shi tun daga nahiyarsu zuwa Mamlakatul Jiyad. Domin asalinsa ba ɗan garin ba ne, babu wani abu da ya haɗa alaƙarsa da ta daular Jiyad, cin burin ɗaukan fansa ya sa ya yi takekeniya ya bar nahiyarsu ya kutsa zuwa wannan gari. Lokacin da ya zo garin duka tsarukansa sun tafi dai-dai, ciki har da sawa Iqrah soyayyarsa a ranta. Kuma hakan ma ya tafi yanda yake so, sai dai kuma wa gari ya waya? Domin a ƙarshe shi aka bari da jinyar zuciya. Duk taka tsantsan ɗin da yake na gujewa soyayyar Iqrah an yi rashin sa'a shirinsa ta wannan fannin bai yi ba. Domin a halin yanzu shi kansa ya san cewa yana sonta, amma kuma ya yi rantsuwa kan ba zai bari soyayyarta ta hana shi ɗaukan fansarsa ba, ko da kuwa hakan zai sake raunata zuciyarsa ne a karo na biyu... “Eid!” Kamar kullum, kamar yanda ya saba tunaninta haka yau ma muryarta ta kutso cikin tunaninsa. A hankali ya zauna kan wata bishiya, yana kallon wasu yara dake wasa kusa da bishiryar. Hannu ya kai ya sauƙe Aafa dake kafaɗarsa, sannan ya ajeta a gefensa yana ci gaba da kallon yaran. Haka kawai murmushi ya suɓuce masa, domin ya tuna da nasa ahalin, da ace har yanzu matarsa Maryam na raye, da ita ma ta haife masa ɗan cikinta... Ɗansa, jin zuciyarsa na ɗacin tunowa da mutuwar Maryam xa ta mahaifinsa ya sa ya kawar da kai daga barin kallon yaran, gudun kada ya haɗiyi zuciya ya faɗi ya mutu ba tare da ya ɗauki fansa ba. “Daga gobe ba za ka sake kwanan farin ciki ba Cangaz! Zan tabbatar da na ƙuntata maka dai-dai da yanda ka ƙuntata zuciyata!” Ya furta yana haɗe haƙwaransa na sama da na ƙasa, zuciyarsa na tabbatar masa da cewar zai iya!. ADVENTURERS. Bayan shafe tafiyar awa uku a ƙafa, suka yanke shawarar zama su huta a wani daji. Yayin da suke hutawa Uwais yace zai je ya naimo musu abinci, amma sai Arman yace kada ya je, shi ma ya zauna ya huta, tun da shi ma zai gaji ne. “Ba lalle ba! Shi da mu akwai banbanci!” Cewar Sana da yanzu ita ma ta zama abokiyar tafiyarsu. Lokacin da suka gane cewa ita ce sun sha matuƙar mamakin ganin matar sarki 'yar saki a wuri irin wanda suka haɗu, bayan ta sanar da su cewa tafiya ce ta kamata har ta kai ga mutanen nan sun kamata, sai suka cire ko wani kokwanto, su ka ci gaba da tafiya da ita har zuwa yanzu. “Me ya sa na zama ba ɗaya da ku ba?” Uwais ya tambaya yana murmushi. “Saboda kai ka kasance ruwa biyu, aljani kuma mutum!” Sana ta amsa shi, har zuwa yau fuskarta na a rufe da mayafin da take rufe kanta da shi, domin ba ta cika buɗe fuskarta ba. “Uwais!” Adam dake yi wa Ivana tausa a ƙafa ya kira sunan. Hakan ya sa Uwais ya dube shi. “Ya ka ji lokacin da aka ƙwace mulkin mahaifinka, sannan ya kake ji idan ka tuna cewa abin da yake mallakinka na tare da wani da ba kai ba!?” Adam ya tambaya da biyu, dan lokacin da ya cilla masa tambayar sai da ya saci kallon Arman, kuma ya lura da tambayar ta sa shi cikin nazari. Ivana da ta fahimci inda ya dosa ta daki kafaɗarsa cikin gargaɗi, duk da yau a gajiye take liƙis, saboda ita ne ma suka yada zango ba dan dare ya yi ba, ga ƙafafunta dake mata mugun ciwo, shi ya sa ma ta saka Adam ya mata tausa. “Lokacin da aka sanar mana da cewa mahaifina ya mutu ji na yi kamar ni ma zan mutu na bi shi. Har ina jin kamar na samu Safraz da Ammi Anser (Kawuna Anser) na ce da su su kwashe komai da muke da shi, amma su bar min Abi. Na ji haushi sosai lokacin da na fuskanci cewar a kan kujerar mulki suka kashe min mahaifina. Bayan kuma sun fara shirin ƙwace abin da yake nawa sai na ji cewar na rasa komai, wannan kujerar ita ce kaɗai abin da nake ganin cewa Abi ya bar min... Lokacin da ya mutu ina ƙarami sosai, amma duk da haka ba na mancewa abubuwan da suka shefi shi, a ko da yaushe yana yawan cewa babu wanda ya dace da zama sarkin Mamlakatul Afsah bayan Uwais!...” Ya ɗan yi fasali yana murmushi me ciwo, ya shafa kansa sannan ya ci gaba da faɗin. “Ashe hakan ba zai zama gaskiya ba, ashe wani bayan ni ne zai zama sarkin! Ashe ba ni da rabon gadar mahaifina...” Lokacin da ya kai ƙarshe duk hankalin Adam da Ivana na kan Arman da jikinsa ya yi sanyi, ba komai yake tunowa ba face Abby. Ta wani ɓangaren zai iya cewa rayuwar Uwais na kamanceceniya da tasa rayuwar. Idan aka kwatanta Anser da Ammu Anwar, Safraz kuma da Faisal, Malik Dhaakir kuma da Abby, Uwais kuma a matsayin shi!... Ke nan son abin duniya zai iya sawa Ammu Anwar da Faisal su haɗa hannu wurin kashe Abby?... “Arman!” Kiran da Ivana ta masa ya katse masa tunani, sai ya kalleta, sannan ya gyara zaman glasses ɗinsa. “Lafiya?” Ta tambaya tana taɓa shi, ya girgiza mata kai, sannan ya miƙe ya nufi cikin daji, sai da ya yi nesa da su sosai, sannan ya jingina da jikin wata bishiya, kewar ahalinsa na mamaye masa ruhi. Wayarsa ya ɗauko, ya buɗe, sannan ya shiga gallery, ya dubo hoton da suka ɗauka shi da Immi ranar da zai gudu daga gida. Ƙwalla ya ji na taruwa a idonsa, hakan yasa ya kai hannu ya cire glasses ɗinsa, sannan ya goge idonsa, ya mayar da glasses ɗin, kana ya dubo hotonsu shi da Abby, wani tsohon hoto da aka daɗe da ɗaukansa... “In Allah ya sa ba ni da rabon dawowa gida ina fatan ka yafe min Abby, idan kuma har Allah ya nufi dawowata ina me baka tabbacin zan yi abin da kake so, zan karɓi shugabancin da ake fata da tuƙuburin na karɓa... Domin a yanzu na gane cewa kuskure ne bijire maka da na yi ta yi a baya, ka yafeni Abby!” Ya furta wani hawayen na zubo masa. A dai-dai lokacin kuma ya ji ihun Ivana, hakan tasa ya buɗe idonsa da sauri, sannan ya juya yana kallon bayansa, domin ta nan ya jiyo ihun. * “Kamar akwai abin da yake damunsa!” Cewar Uwais lokacin da Arman ya tashi daga wurin. Adam ya girgiza kansa. “Ta wani ɓangaren rayuwarka da tasa tana kamanceceniya. A zamaninmu mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, sannan yana da manyan kanfanunuwa, kuma shi mahaifin nasa yana da ɗan uwa, wanda yake da ɗa namiji, shi ma ɗan nasa yana da burin zama shugaban kamfanin. Kasancewar shi Arman na da nakasar gani ya sa kawun nasa ya yi amfani da wannan damar wurin cusa masa ƙiyayyar shugabancin kamfanin. A halin yanzu kuma mahaifinsa ya fara gazawa, tsufa ya fara masa sallama, yana buƙatar Arman ya maye gurbinsa, amma sam Arman ya ƙi aminta da hakan... Hatta da wannan tafiyar da muka yi ta samo asali ne daga gujewa karɓar shugabancin kamfanin!” “Abin tausayi!” Cewar Uwais. “Me ya sa yake saka wani abu a saman idonsa?” Sana ta tambaya. Adam da Ivana suka yi dariya. “Glasses ake kiransu, kuma su ne suke taimaka masa wurin gani, ba tare da su ba ba zai iya ganin ko da tafin hannunsa ba!” “Na gane!” Cewarta tana waigawa tare da kallon hanyar da ya bi. “Adam taimaka min na miƙe!” Cewar Ivana, Adam ya taimaka ya ɗagata. “Ina za ki je?” Ya tambaya ganin ta yi hanyar kogin dake gefe da su, Ivana na ɗingisa ƙafa tace. “Zan wanke fuskata ne” Da haka ta ƙarasa bakin kogin, ta tsugguna ta fara wanke fuskarta, sai da ta gama ta miƙe, tana shirin komawa inda su Uwais suke ta ga wani abu ya faɗo gabanta tim!. Razana ta yi ta ja baya tana ƙarewa budurwar da ta faɗo gabanta kallo. Kafin ta yi wani yunƙuri budurwar ta ruƙo wuyanta, sannan ta buɗe fuska-fukanta ta tashi sama da ita, hakan yasa ta ƙwala ihu domin naiman ɗaukin abokanta. Lokacin da Su Adam suka iso bakin kogin har budurwar ta yi nisa da ita a sama. “Ivana!” Cewar Adam cikin matsanancin tashin hankali. “Me ya samu Ivana?” Cewar Adam da ya ƙaraso wurin da gudu, shi ma kuma sai a lokacin ya lura da Ivana dake sama. “Wace ce waccan?” Arman ɗin ya tambaya yana kallon budurwar dake tare da Ivana. Kafin wani ya amsa masa Uwais ya buɗe nasa fukafukan zai tashi sama, Arman ya dakatar da shi. “Uwais! Zan tafi tare da kai!” “Zo mu je!” Kawai Uwais yace, sannan ya riƙe hannun Arman ɗaya, ya tashi sama da shi, suka bi bayan budurwar da ta ɗauke Ivana. ...End of book 1... ____________________ _Humm! Shin wacece wannan wadda ta sace Ivana?_ _Shin kuna ganin cewa Uwais da Arman za su iya cetonta?_ _Wata ƙiyayya ce tsakanin Eid da Malik Cangaz?_ _Wani abu ne ya samu matar Eid da ahalinsa da har ta kai ga yana son ɗaukar fansa!_ _Me Malik Safraz yake shiryawa?_ _Wani ƙudiri ne ya sa Sana matar Malik Wasimudeen shigowa cikin ADVENTURERS?_ _Shin kuna ganin dakarun Malik Cangaz za su iya riskar ADVENTURERS?_ _Mece ce makomar auren da Malik Cangaz yake shiryawa?_ _Yaushe ADVENTURERS ɗinmu za su riske ƙofar Malik Cangaz?. Shin za su iya samun nasarar buɗe ƙofar? Shin za su koma gida ko a'a?_ Domin ci gaba da karanta book 2 za ku biya ₦400 for regular group. ₦800 for VIP to. 5487270431 Salma Isah Monie point Shaidar biya kuma ta 08130172702. Sannan za ku samu complete book one and 2 on Arewabooks, kada ku manta ku yi following ɗina domin samun notification da zarar na yi update. Ina me tabbatar muku da book 2 is giving 🔥🔥🔥. A har kullum, godiya ta musamman zuwa ga masoyana a duk inda kuke. I ❤️ like WUJIGA-WUJIGA 💋. See you in book 2. Best regards Salma Ahmad Isah ✍️ A.k.a Candy🦋 A.k.a Bahaɗejia🐎 2024...