Compiled by Umar Dalha. ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Bismillahir Rahmanir Rahim *Page 1* Mallan Adamu haifafen garin Zaria neh, yana zaune a Unguwar Iya dake cikin zaria city, Yana zaune da matarsa Amina da y'arsu guda d'aya mai suna Jaleelah anma ana ce mata Ummy saboda sunan Mahaifiyar mallan Adamu ne... Jaleelah yarinya ce y'ar shekara goma sha takwas, tanada Ilimin addini daidai misali, Na boko ne bata samu ba dan a primary five ta tsaya kasancewar Mahaifinta baida hali, ga kuma chuta ta Makanta data sameshi lokaci guda.. Hakan ne yasa Ummy da Mama suka kasance cikin wani hali har takai Ummyn ta koma Suyan wara kofar gida dan su samu abin rufawa juna asiri. Ummy yarinya ce Mai tarbiya gata kyakyawa ga diri hakan ne yasa samari ke b'ulb'ulowa tako ina suna santa saida yawancin su da maganan banza suke zuwa hakan ne yasa bata kulasu. Saurayinta d'aya mak'ocin su Sunanshi Bilal, yana matuk'ar tausayama halinda su Ummy suke ciki duk da shima ba wani k'arfi gareshi ba, lebura neh so dayawa yakan sayo d'an kayan abinci daidai gwargwado ya kawo gidansu Ummy, hakan ba b'aramin d'adi yakema Mahaifanta bah. Yau tana shara a tsakar gida ta jiyo tarin Baba gashi Mama ta fita taje mak'ota barka, tsintsiya ta aje dasauri ta k'arkad'e hannunta a jikin k'od'adiyar zanin atamfan dake jikinta, kwance ta sameshi yana tari sosai, idanunshi sun jujuya, tsugunnawa tayu gabanshi ta fashe da kuka "Sannu Baba, Sannu Allah ya baka lapia" Tarin yake ba k'ak'autawa, Kuka take duk ta rud'e dama ita abu kad'an kesata kuka, fitowa daga d'akin tayi dasauri ta ja hijabinta dake igiya tayi waje, a xauren gidan ta had'u da Mama tana ganinta ta k'ara fashewa da sabon kuka "Mama jikin Baba ya tashi" Ai ba shiri Mama ta shiga gidan hankali tashe, d'akin ta shiga ta tarar dashi kwance sai aman jini yakeyi, nan da nan Mama ta fashe da kuka tana tsugunne gabanshi, Ummy ta shigo d'akin dasauri idanunta cikeda kwalla "Mama mu kaishi Asibiti" D'agowa Maman tayi hawaye na bin idanunta "Da wani kud'i zamu kaishi Asibiti Ummy?, kinsan bamuda kud'i" Fita tayi da gudu kamar tab'abba ta fita kofar gida tana waige waige, kuka takeyi sosai lokaci guda tana Addu'a, daky'ar ta samu me napep ta tareshi tace "Mahaifina ne baida lapia dan Allag badan niba ka taimaka min mu fito dashi" Bah musu ya fito daga napeep din suka shiga gidan, har lokacin Mama na zaune gaban Baba tana kuka, ganin Ummy ta shigo da wani yasa ta d'ago dasauri "Mama mu kamashi akaishi Asibiti" Bah musu suka kamashi suka fito dashi, komawa Ummyn tayi ta shiga d'akinta ta d'auko wani k'ullin bak'in leda a hankali ta kwance ledan, kud'i ne yan dari biyar ta rungume kud'in tareda fashewa da kuka, kuka take sosai tana cewa "Kayi hak'uri ya Bilal zanyi anfani da kud'inka" Ta maida kud'in ta kulle ta fito daga gidan dasauri, Asibitin Gambo sawaba suka nufa, suna lsa ta biya mai keke napeep nurses sukayi Emergency dashi, Suna nan tsatsaye wata nurse ta fito tana rik'e da wani paper a hannu "Ku kuka kawo wannan patient din koh" Mama ta matso "Eh mune" Papern ta mik'a mata tana cewa "Magunguna ne da zaku siya, sai kuma zaku biya kud'in gado" Dam! Gaban Mama ya fad'i dan ko sisi bata fido daashi bah, papern tasa hannu ta k'arba, Ummy ta karaso wajan ta karb'i papern a hannun Mama "Na magani neh" Gyada kai Mama tayi dan tama kasa magana "Barinje in amso" Tana juyawa Mama ta k'wala mata kira ta juyo dasauri tareda Amsawa, k'arasowa inda take Mama tayi tana kallan cikin idonta "Ummy ina kika samu kud'i da kike cewa zakije ki siyo" Inda inda ta soma idanunta cikeda kwalla, Mama ta daka mata tsawa "Bah dake nake magana bah" Fashewa da kuka Ummy tayi jikinta ya soma rawa "Wallahi Mama bah abinda kike tunani baneh, Wallahi Ya Bilal ne ya bani ajiyan kud'in" "Saboda kuma bakida hankali shine kika d'au kudin zakiyi anfani dashi" Kamin tayi Magana Sukajiyo Muryan Bilal din daga bayansu yana cewa "Mama yanzu nake zuwa gida Ilyasu mai faci yake cemin kuna asibiti" K'irk'iro murmushi tayi "Wallahi jikin Mallan d'in neh ya tashi" Tunda Ummy taji muryanshi kanta ke k'asa, kallanta yayi ya saki Murmushi, Baice mata komai bah ya janye papern dake hannunta yana dubawa Ya d'ago ya kalleta lokacin Mama ta bar wajan ta koma gefe "Hrt ya jikin Baban" K'anta a k'asa tace "Dasauk'i basu dai bari mun ganshi bah" Lalluba aljihunshi yayi fuskanshi da alamar damuwa, muje muji nawane kud'in maganin. A tare suka jera har zuwa pharmacyn, lissafi aka musu harda kud'in gado dubu goma sha biyar, wani miyau Ummy ta had'iye dakyar tana kallan mutumin, d'agowa tayi ta kalli Bilal din murya chan k'asa tace "Ya Bilal mu d'auki Baban kawai mu koma gida" Girgiza mata kai yayi dasauri yace "Aa Hrt, ko zamu koma gida ne kid'auko kud'in nan" A kunyace tace "Ga kud'in nan" Mik'amai tayi kanta a k'asa, amsa yayi ya irgo dubu goma sha biyar ya biya ya rage dubu biyu, suna dawowa suka samu ana chanza mai d'aki zuwa ward. A Tare suka shiga d'akin, Mama ta mai godiya sosai ganin an sayo maganin da duk abinda ake buk'ata, Itama Ummyn tamai godiya shidai baice komai bah sai Murmushi kawai dayake. Bilal kyakyawan saurayi ne d'an shekara Ashirin da biyar, Bak'i ne shi anma ba wulik ba, yana yanayi da Black americans, Yanada tsayi da fafad'ar kirji, idanunshi dara dara masu kyawun gaske. Mahaifinshi d'an Asalin Garin Yola neh, su biyu iyayenshi suka haifa shida k'aninshi Bahar, Mahaifinsu ya rasu tun yanada shekara Ashirin, Yanzu suna tareda Mahaifiyarsu ne. Mak'ota ne dasu Ummy tun tasowanta Allah ya d'aura mai santa da kuma tausayinta na halinda suke ciki, zan iya cewa shine kusan k'arfin gidansu Ummyn Wannan knan.. Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to my *Late Siblings* *Page 2* Satin Baba d'aya aka sallameshi, duk d'awainiyar su Bilal ya d'au nauyi har aka sallamesu suka dawo gida. Albarka kam Bilal yasha shi wajan Baba da Mama Ummy koh rasa bakin godiya tayi.. Bayan sun dawo Ummy ta koma bakin sana'arta na tuyan wara a k'ofar gida, sam Bilal baya san suyan datakeyi anma ba yanda zeyi haka ya hak'ura duk da zuciyarshi da ke misi suya kullum idan ya dawo aiki ya ganta k'ofar gida.. Yauma kamar kullun tana k'ofar gida tana suya, sam yau ba ciniki duk ta damu gashi yau basuda ko k'wayar hatsi a gidan kuma bataso Bilal ya sani dan d'awainiyar tasu tana ganin yayi yawa, Tana cikin tuya taji Muryan Bilal a bayanta cikin sanyayar Muryansa "Sannu da aiki Hrt" Da d'an murmushi ta juya ta kalleshi, sanye yake da wandan jeans duk ya fatattake daga guiwa, da bak'ar riga itama kod'adiya, fuskanshi da kayan jikinshi duk siminti duk yayi butu butu, da alama daga wajan aiki yake "Sannu da dawowa" "Yauwa sannu Hrt, ya kasuwa" Fuskanta d'auke da murmushi tace "Lapia lau" "Fad'amin damuwarki" Duk'ar da kai tayi tana y'ar fara'a "Babu wata damuwa" "Bai dace dakeba Hrt ki rink'a b'oyemin damuwarki, babu wanda zak'i fad'ama damuwarki duk duniya daga Baba da Mama sai ni. Duk inda nake ko me nake sai nayi tunaninki, ina sanki Ummy bazan iya rayuwa baki bah, a duk sanda kike cikin damuwa ina ganewa saboda tsananin damuwa da nakeyi dake" Hawaye ne suka cik'a mata ido, tabbas abinda Ya Bilal ya fad'a gaskiya ne akan irin sanda yake mata, anma dole ta rink'a b'oye mata damuwan da suke ciki saboda shima ya rink'a hutawa da d'awainiyarsu. Magananshi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi "Hrt fad'amin meke damunki?" Murmushi tayi tana kallanshi "Babu komai Ya Bilal" D'an dutsen dake kusada ita yaja ya zauna ya kafeta da idanunshi "Ashe har akwai ranan da zaki b'oyemin damuwanki Hrt, nayi tunanin a iya zaman mu da soyaiyar dake tsakanin mu da kuma shak'uwa ba abinda zamu b'oyema juna. Ina sanki Ummy kuma bazan fasa fad'a miki zan iya yin komai akan sanda nake miki bah" Kuka ke k'okarin kufce mata anma ta shanye ta dake tana cewa "Ya Bilal ba abinda zance maka saidai Allah ya saka da alheri ya baka lada, ya kuma saka a aljanna. Kayi mana komai nida Iyayena wanda y'an uwanmu basu mana bah. Bansan dame zan saka maka ba Ya Bilal, Ina so n.. " Saurin k'atseta yayi ta hanyar d'aga mata hannu "Ya isa Hrt, bana buk'atar godiyanki. Damuwarki kawai nake san ji" "Ya Bilal yanzu fa ka dawo daga aiki ko gida bakaje bah" Kallanta yayi tareda marairaice fuska "Hrt pls mana fad'amin, bana iya jure ganinki haka" K'arya tamai da cewa kanta ke ciwo, duk da bai yarda ba anma ya bita a hakan dan yaga bataso s fad'amai. Wani yaro ne yazo siyan awaran da kanshi ya iriga ya bashi Ummy nata kallanshi da murmushi, wani sanshi da tausayinshi ne ke k'ara shiga zuciyarta. Mik'ewa yayi yasa hannu a aljihu ya ciro d'ari biyar ya mik'a mata "Hrt ki rik'e wannan idan kuna buk'atar wani abu" Duk da suna da buk'atar kudin anma tayi saurin girgiza kai "Aa bama buk'atar komai" Hannunta ya rik'e ya chusa mata kud'in a tafin hannunta yana kallan fusanta "Hrt bana san musu pls, anjima zanzo muje chemist" Bai jira mai zatace ba yabar wajan ya shiga gida. Binshi tayi da kallo harya shiga gida sannan ta sauke ajiyan zuciya ta cigaba da suyanta. Cikin ikon Allah ta saida waran da wuri ta shiga da kayan gida. Mama ta samu tsakar gida tana hura wuta "Sannu da aiki Mama" "Yauwa sannu Ummy har kin gama?" "Eh Mama ya jikin Baba" "Dasauk'i kinga ma wuta zan hura na d'aura mai ruwan wanka" Kayan ta aje ta amshi aikin a hannun Maman, hura wutan tayi ta d'aura ruwan sannan ta lek'a ta gaida Baban. Albarka ya soma sa mata harda hawaye dan yana matuk'ar tausaya ma Iyalin nashi. Kud'inda Bilal ya bata ta nunama Baba yana gani ya fashe da kuka, Itama Ummyn kukan ta soma tana rarrashin Baban "Allah ya sakama yaron nan da Alheri" Mama dake bakin kofa ta amsa da Ameen. "Ku cigaba da hak'uri Ummy, komai yayi farko zaiyi k'arshe, jarabta ce haka Allah yaso, ku cigaba da min Addua" Mama itama ta fashe da kuka "Allah ya baka lapia Mallan, insha Allahu zaka warke ka cigaba da walwalanka yanda kake da" Ummy ta mik'e ta fita daga d'akin, hijabinta tasa ta fita tayo musu chefanen d'an abinda zasu ci abinci ta dawo gida. Tana shiga ta tarar da Ya Bilal zaune a tsakar gida shida Mama suna hira.. Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to my *Late Siblings* *Page 3* Tana shiga ta tarar da Ya Bilal zaune a tsakar gida shida Mama suna Hira, a suk'wane ta karaso tareda sallama, suka amsa mata ta gaidasu kanta a k'asa, Bilal sai binta da kallo yake, shige da fice ta soma dan d'aura musu abinda zasu ci, tana cikin jajjage taji Bilal na cewa "Mama ki tayani da Addu'a, Ogana ya kirani d'azu yake sheda min gobe zamuje wani aiki a binnin taraiya Abuja, Ginin gidan wani babban d'an siyasa kuma insha Allahu zamu samu alheri sosai" "Aa ina tayaka murna d'an albarka, Allah ya bada sa'a yasa aje lapia a dawo lapia" Ameen yace yana murmushi tareda maida dubanshi ga Ummy wacce tun sanda ya soma maganan ta saki tab'aryan dake hannunta gabanta na fad'uwa, had'a ido sukayi ta soma kuka mara sauti, dasauri tabar wajan dan kada Mama ta gani ta shige kicin tana kuka a hankali. Anya zata iya wuni guda batare da tasa Ya Bilal d'inta a ido bah, balle kuma wannan tafiya da take tunanin zai d'au lokaci, tanaji sukai sallama yabar gidan. A haka ta gama aikinta sukuku ta koma d'aki tayi sallan magrib, tana nan kan sallayan tayi tagumi Mama ta kwalla mata kira daga tsakar gida, dasauri ta fita ta samu Yaro a tsakar gidan "Wai ana sallama dake" Tad'an kalli yaron da mamaki "Wanene" "Wai Bilal" Mama tayi saurin cewa "Kace tana zuwa" Yaron na fita Mama tace "Kije kid'an murza hoda" Bah musu ta juya tashiga d'aki tad'an gogo hoda ta fito ta nufi wajan, tsaye ta sameshi ya jingina da bango yana game a y'ar k'aramar android d'inshi Turo baki tayi kamar zatayi kuka sanan tace "Sannu" Murmushi yayi mai sauti har lokacin idanunshi nakan candy crush d'in daya keyi "Hrt fushin menene" Ai kaman jira take tako fashe da kuka, ya sa wayan a aljihu yana kallanta da damuwa "Hrt kiyi hak'uri kinsan banasan damuwanki, nasan akan maganan tafiyata ne indai bakiso saina fasa" Share hawayenta tayi da bayan hannu tana girgixa mai kai "Aa karka fasa Ya Bilal, kawai dai xanyi kewanka neh, ka sabamin da ganinka kullum kuma gashi zakai nisa dani" Sosai yaji dad'in magananta har saida yayi murmushi "Hrt inaji a jikina wannan tafiyan da zanyi alheri ne, shi zai kawo sauyi a rayuwarmu insha Allahu, babban burina naga kinyi karatu Hrt mai zurfi keda Bahar, inaso naga na samu ayima Baba aiki a idanunsa ya rink'a gani.. Ki daina kuka ki rinka min addu'a kinji" Kai ta gyad'a wani sabon kuka tazo mata "Oh Hrt banasan kukanki, pls ki daina kinji bazan dad'eba just sati biyu zamuyi" Ganin kukanta nasan karya mai k'warin guiwa yasa tayi shiru sai ajiyan zuciya da takeyi "Allah tsareka ya sa kuje lafiya ku dawo lapia" Ameen yace yana murmushi, yasa hannu a aljihu ya ciro wasu kud'i ya mik'a mata "Kuyi managing wannan kafin na dawo kinji" Kallan kud'in take kuka na k'okarin kufce mata, dakyar tasa hannu ta karba tad'an duk'a kad'an tayi godiya. Kallanta kawai yake wani santa mai tsafta na kara shigan shi, ji yake zai iya yin koma menene akanta.. "Ki shiga ciki Hrt dare yayi and kuma akwai sanyi" Godiya ta kara mai sannan tamai addu'oi sosai ta juya zata shiga gida "Hrt" Ya kirata tad'an juyo tana kallanshi, hannu ya k'arasawa a aljuhun shi ya ciro wani zobe mai kyau na azurfa "Kawo hannunki" K'in mik'a hannunta tayi ta kafeshi da ido, yad'anyi murmushi "Oh Come on bani hannun" Bah musu ta mik'a mai hannunta yasa mata zoben yana kallan hannun tareda murmushi "Kyawun zoben yasa na siyeshi, dan nasan zaima Hrt d'ina kyau. Ki rik'emin amana pls, duk da nasan ke tawace, just 2weeks zanyi kinji" Kai ta gyad'a mai ya mata sallama ya shiga gidansu da sauri, tsaye Ummy tayi a kofar gidan tana kuka a hankali, tana san Ya Bilal tana kishinsa, batasan koda na kwana d'aya su rabu. Saida tayi mai isarta sannan ta shiga gida.. Kasancewar lokacin sanyi ne har Mama ta shiga d'aki saidai tana d'aga bak'in kofa tana jiran Ummyn, tana shigowa taji Mama daga d'aki tace "Ummy kece" A hankali tace "Eh Ni ce" "Yaudai kam kun dad'e" Batace komai ba ta shige d'akinta ta fad'a kan katifarta tana ajiyan zuciya. Kud'in dake hannunta ta duba, dubu biyu ne y'an dari biyar biyar guda hud'u. Ta tusa su k'arkashin Pillow ranta duk ba dad'i Tunanin rayuwar Ya Bilal ta soma, tun tasowan shi yake aikin k'arfi dan taimaka mai mahaifiyarshi da k'aninshi, ga kuma itada da iyayenta, duk da nauyin dake kanshi bai hanashi yin karatunshi bah, ynzu haka yanada degree saidai ita batama san maiya karanta bah. Tunani kala kala ta dunga yi har bacci ya d'auketa Da safe kamin ya tafi saida yashigo shida Bahar sukaima su Mama sallama, ya shiga sukayi sallama da Baba sannan suka fito Ummy na biye dasu, Bahar ya basu waje sukai sallama sai kuka takemai a haka suka rabu kowa zuciyarshi ba dad'i Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 11:34 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to my *Late Siblings* *Page 4* A haka suka rabu kowa zuciyarshi ba dad'i, yinin ranan sukuku Ummy ta yini, ko abinci tak'i ci saidai ta zauna tayi tagumi. Tun Mama na bata baki har ranta ya soma b'aci ta hau mata fad'a Haka suka cigaba da rayuwa a gida har na tsawon sati hud'u, tun Ummy na irga ranakun dawowan Bilal harta daina tasawa sarautar Allah ido, so dayawa takan shiga gidansu Bilal dan dai kawai taji ko ansamu labarinsa Anma shiru. Abubuwa sun taru sun mata yawa ga Rashin sanyin idaniyanta Bilal, ga talauci da suke fama dashi dan tuni sun cinye jarin waran, abinci ma yanzu dak'yar suke samu. Sosai abin ke damun Ummy duk ta rame tayi duhu kamar ba Ummyn dah bah.. Tana d'aki tana tunanin yanda rayuwarsu ta sauya lokaci guda, a hankali hawaye ya zubo mata murya chan k'asa tace "Allah sarki Baba Sanda kakeda idanu da lafiya ka watada mu, munji dadi Allah ya baka lafiya yasa kaci wannan jarabawan" Fashewa da kuka tayi mara sauti, saida tayi mai isarta sannan ta mik'e zaune tareda goge hawayen idanunta. Tunani ta soma na yanda rayuwarsu zai inganta nan gaba dole ta nemi mafita dan bazasu zauna su dogara ga Bilal ba shima akwai d'awainiyan gidansu a kanshi, dauriya kawai yake. Wasu hawaye ne suka zubo mata "Ya Bilal kana inane? Ka dawo dan Allah" Mik'ewa tayi a sanyaye ta janyo hijabinta tasa ta fito tsakar gidan, Mama ta gani tana kok'arin fitoda Baba tsakar gida yasha Iska. Dasauri ta k'arasa ta taimaka mata ta zaunar dashi kan tabarma "Sannu Baba" "Yauwa Sannu Ummy, ku cigaba da hak'uri kunji wata rana sai labari" Hawaye suka cika idanunta, ta shiga d'akinshi ta d'auko sandar shi ta tsugunna tace "Baba ga sandary ka" Lallube ya soma, ta kamo hannunshi ta saka mai sandar "Yauwa Ngd Ummy" Ta dubi Mama dake gefenshi tace "Mama barin shiga wajan Inna Yanzu zan dawo" (gidansu Bilal) "Tho a dawo lapia, karki dad'e" Tho tace ta mik'e ta fita, a zauren gidansu Bilal ta had'u da kaninshi Bahar, Gaidashi tayi ya amsa yana cewa "Ya kewar Yaya" D'an murmushi tayi kanta k'asa "Har yau bama samun wayansa, ina ga zanzo ne na bishi Abujan nan kawai dan jikina na bani ba lafiya" "Yanzu idan kaje Abujan ta ina zaka fara? Ance. Tanada girma sosai, mezai hana muje inda suke aiki ko zamu samu labarin shi wajan abokanan aikinsu dake nan" Gyad'a kai yayi "Hakane kin kawo shawara" "Barin shiga na gaida Inna sai na fito mu tafi" A tare suka shiga gidan, Inna na zaune tsakar gida tana bakace masara "Ummy ce da tsakar ranan nan" A kunyace ta tsugunna ta gaida Innan, "Ya Babanku da jiki?" "Dasauk'i" tace a hankali har lokacin kanta k'asa. Sallaman da akayi ne ya katse su, wata dilaliya ce dake anguwan ta shigo tana cigaba da rafka sallama, Ummy da Inna suka amsa mata ta k'araso ta nemi guri ta zauna, Ummy ce ta soma Gaidata sannan ta mik'e "Inna bari muje wajan aikinsu Ya Bilal yanzu zamu dawo" "Tho a dawo lapia" inna ta amsa mata, tana kok'arin fita daga gidan taji dilaliyan na cewa "Wallahi Ladidi wasu gidaje ne aka kawo min cigiyan masu aiki kuma za'a samu alheri dan ba gidajen k'ananan mutane baneh gashi har yanzu ban samu yarinya ba" Fita daga gidan tayi da sauri suka had'u da Bahar suka wuce wajan, mutanen dake wajan suka tambaya a nan suke shaida musu mummunan labari, d'ayansu ne yace "Ranar da suka tafi motarsu tai hatsari duka sun rasu babu wanda ya fita, dan achan aka musu sallah saboda yanda gawawakinsu sukayi" Ai bai k'arasa maganan ba Ummy ta fad'i wajan sumammiya.. Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 11:36 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ​Page 5​ Ai bai k'arasa Maganan ba Ummy ta fad'i wajan sumammiya. A gigice Bahar yayi kanta yana kuka, jama'ar dake wajan sun tausaya sosai. Masu aikin wajan suka tsare musu napep suka saka Ummy dake sume a cikin napep d'in suka nufi gida. Suna isa gida Mai napep da Bahar suka shi da Ummy cikin gida sai kuka yake, a nan yake sanar da Inna abinda ke faruwa, nan itama ta sume a wajan kamin kace me unguwan gaba d'aya ta d'auka ko wane lungu da sak'o sunji labarin rasuwar Bilal.. Sosai rasuwansa ya girgiza mutane saboda Bilal mutum ne mai Gaskiya da rik'on amana, ga addini da son jama'a. Ba abnda ke tashi daga gidan Inna sai koke koke, Baba da Mama suna daga cikin sukajiyo kuka daga gidan Inna, ta yafa mayafinta ta fito tun a kofar gida ta soma cin karo mutane sunata shiga, itama ba'a barta a baya ba tana shiga taji wannan mummunan labari. Kuka ta soma ta k'arasa inda ze zaune ta rungumeta tareda fashewa da kuka "Allah ya jik'anka Bilal yasa ka huta" Ta k'ara rushewa da wani sabon kuka, Ummy ko dogon suma tayi bata farka ba sai washe gari da safe, a hankali ta bud'e idonta ta suka k'ankance Mama ta gani kusada Ita itama fuskanta ba walwala, mik'ewan datake k'okarin yi yasa Mama tasan ta farka "Sannu Ummy, ina zakije" Fashewa da kuka tayi tana kallan Mama "Mama yanzu dagaske ne Ya Bilal ya rasu" Kanta Mama ta shafa tana lallashinta "Bilal lokaci yayi Ummy, yanzu addu'an mu yake nema ba kuka ba kinji. Kiyi hakuri ki fawala wa Allah" Girgiza kai take tana kuka da k'arfi "Aa Mama, Ya Bilal bai mutu ba ni nasani bazai tab'a mutuwa yabarni ba. Dan Allah Mama idan wasa yake kuce ya daina ya dawo" Hawaye suka gangaro ma Mama na tausayin y'ar nata, dama tasan dole za'ayi haka, kuka sosai Ummy keyi tana k'okarin sauka daga kan gadon "Mama d'an Allah ki sakeni zanje na nemo Ya Bilal ince ya dawo nida Inna muna kewarsa" Rik'eta Mama tayi "Haba Ummy kin tab'ajin anyi wasa da mutuwa?" Baba ne ya shigo d'akin yana jejefa sandarsa yana laluban waje, saida ya laluba waji tabarma sannan ya zauna, inda yake jiyo kukan Ummy ya maida fuskanci yace "Ummy Rayuwa da mutuwa duk ta Allah ce, Allah ya fimu sanshi shiyasa ya d'aukeshi. Kuma Allah baya barin wani dan wani yaji dad'i. Kiyi hak'uri ki mik'a lamuranki ga Allah, muma duk zaman jiranta muke, shida ya rigamu baiyi sauri ba mu kuma da muka rage bamuyi jinkiri ba, kiyi hak'uri uwata Allah yana tare damu." Duk'ar da kai kawai tayi tana kuka sosai, Haka suka cigaba da lallashinta anma sam Ummy tak'i daina kuka. Kullum sai ta shiga gidansu Bilal itada Mama, ba abinda take daga kuka sai kuka, Inna tayi tayi Ummy ta daina kuka anma ina. Cikin kwana biyu duk ta rame ta zafge kamar ba Ummy ba, sam ta daina cin abinci, Mama tayi fad'an harta gaji. Haka Inna itama tun tana binta da lallama harta soma fad'a anma Ummy taki. Haka aka gama zaman makoki kowa ya watse ya bar gidajen biyu cikin kewa da damuwa. Idan kaga Ummy saika tausaya mata yanda ta koma lokaci guda, sosai abin ke damun Mama musamman yanzu yanda ta daina magana saidai ta kur'ama abu idanu tayita kallanshi kamar tab'abb'a.. ​​Bayan Wata Shidda​​ Ummy tad'an sake kad'an bakaman da bah saidai yanzu ta koma shiru shiru batada yawan magana, har yanzu dai bata daina kukan Rashin Yayanta kuma masoyinta Bilal ba, Inna na tausayama Ummy sosai halinda take ciki. Yanzu Masa suka komayi da Safe da yanma kuma ba laifi suna d'an ciniki. Dashi suka dogara, duk riban da aka samu a rana dashi ake cin abinci a ranan. Bahar ko tuni ya koma yana a inda Ya Bilal yake aiki d'ah dan ya taimaki kanshi da Mahaifiyarshi.. Yau tun dare ciwon Baba ya tashi, Ummy nachan d'akinta tana bacci bayan ta gama kukanta wanda kullum sai tayishi kafin ta kwanta. A daddafe suka kai Asubah, Mama ce ta fara fitowa jin kiraye kirayen sallah, Kwankwasa kofan Ummy tayi itama ta fito "Sannu Mama" "Yauwa Sannu Ummy, jiya bamuyi bacci ba jikin Mallan" Idanun Ummy ne ya ciko da k'walla "Meya sameshi Mama?" "Ciwon nan ne dai nashi ya tashi" D'akin Ummy ta lek'a ta samu yana bacci, ajiyan zuciya ta sauke ta fito tayi alwala. Da gari yayi haske tana k'okarin fita da kayan sana'arta Jikin Baba yayi zafi sosai sai tari yake akai akai, d'akin ta shiga ta samu Mama kusa dashi tanamai sannu, Tari Mai K'arfi ya k'arayi saiga jini. Kuka Ummy ta saki ta d'aura hannayenta a kai "jini kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun mun shiga uku" Kamin kace me Baba ya fita hayyacin shi, Ummy da Mama ba abinda sukeyi sai kuka, da gudu Ummy ta fita ta samu mai napep suka d'au Baban suka sakashi sukai asibiti dashi.. Saida suka isa Mama tace "Ummy yanzu da muka d'auko Mallan muka kawoshi Asibiti da wani kud'in zamu biya" Hawaye ta share da bayan hannu "Insha Allahu Mama zamu samu abinda zamu abinda zamu biya, mu fara bada y'an kud'in dake wajanmu" An k'arbi Baba an bashi gado, kud'in hannunsu kwata kwata dubu d'aya ne da d'ari hud'u gashi sun kashe d'ari biyu wajan zuwa asibiti. Suna nan zaune aka likitan ya fito ya mik'ama Mama wata takarda "Muna buk'atar wad'an nan magungunan yanzu kuyi sauri" Kallan kallo suka tsaya yi da Ummy, jiki ba k'wari Ummy ta amsa takardan ta nufi pharmacy, Calculating aka musu kud'in dubu bakwai da d'ari biyar, ai nurse d'in bata gama fad'aba Ummy ta saki kuka mai k'arfi. Wata hajiya ce ta shigo wajan cikin takun k'asaita ta k'araso wajan tareda mik'a takardan dake hannunta, ganin Ummy a gefe rakub'e tana kuka yasa ta k'arasa wajanta ta tsaya tana k'are mata kallo Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 11:38 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ​Page 6​ Wata hajiyace ta shigo wajan cikin takun k'asaita ta k'araso wajan tareda mik'a takardan dake hannunta, ganin Ummy a gefe rakub'e tana kuka yasa ta k'arasa wajan ta tsaya tana k'are mata kallo "Y'an mata lapia dai wani naki ne ya rasu" D'agowa tayi idanunt cikeda hawaye "Aa Babana aka kwantar kuma bamuda kud'in da zamu biya na magani" Takardan Hannun Ummy ta amsa ta duba sannan ta mik'ama nurse d'in "Gashi ki basu magungunan, da kud'in gado na sati d'aya sai kiyi min total harda nawa" Ummy najin haka ta tsugunna guiwa biyu tana godiya sosai, hannu biyu hajiyan tasa ta d'agota tana share mata hawaye "Aa ki daina mini godiya, Allah ya bashi lapia" "Ameen" tace tana cigaba da godiya kanta k'asa, nurse d'in ta miko mata magungunan ta tafi tana waiwayen hajiyan har ta bar pharmacyn. Bata b'oyema Mama ba ta sanar da ita duk yanda sukayi da hajiyan, Itama tayi godiya tareda ma hajiyan addu'oi na fatan alheri. Cikin ikon Allah kwanan Baba shidda aka sallameshi, suka dawo gida bayan likita ya jajja musu kunne akan kula da maganin Baban da kula gudun abinda zai rink'a bata mai rai saboda ciwon zuciya dake damunshi.. Koda suka dawo gida d'aki Ummy ta shiga ta zauna tana tunanin ciwon Babanta, dole ta nemi kud'i dan cigaba da siyamai magani. Tana cikin tunanin Mama ta shigo d'akin da sallama, Ummy ta amsa tareda Gyara xama "Ummy nazo ne muyi wata shawara dake" "Shawaran meh kuma Mama" Saida Mama ta nisa sannan tace "Shekaranki Goma sha takwas yanzu ya kamata ache kin bar soye soye a k'ofar gida. Babban burina yanzu Ummy bai wuce ace kinyi aure bah anma nasan komai lokaci neh, fatana kawai Allah ya baki miji na gari" Duk'ar da kai Ummy tayi tana murmushi "Dama cewa nayi mai zai hana mu koma sana'a ta cikin gda" "Tho Mama wace sana'a kike ganin zamu koma yi na cikin gda? Ni wallahi babban tashin hankalina ma magungunan Baba inda zamu rink'a samun dubu uku na magani" Ajiyan zuciya Mama ta sauke "Dama ni cewa nayi naga gidajen bayanmu suna neman masu wankau ko shi zamu koma yi ana kawo mana munayi ana biyan mu" Jim Ummy tayi tana nazarin maganan Mama, sam batasan taga iyayenta sun wahala. Wankau aikine mai wahala tabbas kuma gashi Mama ta girma "Tho Ummy mai kikace" Maganan dilalliya ne ya fad'o mata a rai, wani lallausan murmushi ta sauke "Kwanaki chan na tab'ajin dilalliya na cigiyan y'an aiki wai wasu sun bata sautun a sama musu, shine nace mai zai hana naje idan har yanzu ana nema sai nayi kuma na tabbatar za'a samu alheri" Jim Mama tayi tana nazari "Anya kuwa Ummy aikatau kuma?" "Mama dan Allah karkice Aa, ki bari nayi wannan hanyan tamafi sauk'i kinga duk karshen wata mutun nada albashi" "Banak'i bane Ummy ina tunanin Mallan neh" Hannun Mama ta saka a nata "Indai kin amince Mama shiknan ni nasan na Baba abu mai sauk'i neh" "Shiknan Ummy Allah dai ya zab'a abinda yafi zama alheri, Allah kuma ya mana jagora" "Ameen Mama" A tare suka fito suka soma aiki gyaran gidan. Inna najin motsin su ta shiga ta k'ara gaida Baban dan dama taje ta gaidashi a asibiti. Bayan kwana biyu Ummy ta tari Baba da maganan aikin da takeso ta fara, da farko yak'i yarda dakyar ta shawo kanshi ya yarda dakyar. Nasiha ya mata sosai akan kare mutuncinta sannan ya bata izini taje gidan Dilalliyan ta tambayo, tana zuwa ko tace mata dama gida d'aya ya rage kuma har yanzu ba'asamu bah. Sosai Ummy taji dad'i sun aje akan washe gari zasuje ta kaita gidan. Da farinciki ta dawo ta sanar dasu Mama sun mata fatan Alheri sosai da haka ta soma shirinta na gobe dan zuwa gidan babban fatanta Allah yasa kud'in da xa'a biyata yakai dubu uku dan tasamu na sayama Babanta Magani.. ​This is just the Beginning​ Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 11:40 PM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ​Page 7​ Babban fatanta Allah yasa kud'in da za'a biyata yakai dubu uku dan ta rik'a samu tana sayama babanta magani. Washe gari da wuri ta tashi ta gama duk wani aikinta, tana shiryawa ta leka d'akin Baba tamai sallama ta fito, Addu'an nasara Mama ta mata sannan ta fita ta nufi gidan dilalliya. Tana zuwa suka d'au hanyan samaru, itadai Ummy sai rarraba idanu take tana kallan hanya, a wajan aviation suka sauka wani anguwa da ake cema hanyin mallan, nan suka k'ara hawa mashin suka d'au hanyan cikin anguwan, gine gine na zamani masu kyawun gaske suketa wucewa har suka kawo wani had'adden gida gate d'in gidan k'ato ne ga tsayi sai shek'i yake. Dilalliya ta biya masu mashin sannnan ta soma kwankwasa gidan, bin gate din da kallo kawai Ummy keyi da sha'awa, wani ne ya bud'e karamin k'ofan ya leko yana wani yatsine fuska "Lapia dai koh?" Dilalliya aka washe baki "Aa lapia lau, dan Allah iso za'a mana ace ma Hajiyar dilalliya ce" Baice komai ba ya rufe k'ofan, suna nan tsaye aka k'ara bud'ewa nan ya basu izinin shigowa, suna shiga Ummy ta bud'e baki tana kallan gidan, dank'ararren gida ne na gani na fad'a, Main building d'in na tsakiya sai kuma wasu parts guda hud'u, biyu gefen hagu, biyu a dama. Sosai gidan ya burge Ummy musamman Swimming pole d'inda ta hango a chan gefe d'aya, sai kuma wani d'an garden daga gefensa d'an cage ne a ciki akwai kaya na wasan yara iri iri, ganin tana k'okarin fad'uwa Dilalliya ta rik'eta tana b'ata rai "Wannan wanne irin kallo ne haka sai kinje kin fad'i kinjima kanki ciwo, keda a nan zaki cigaba da rayuwa" Itadai Ummy batace komai bah har suka k'arasa falon, nan ma Ummy tasha kallo dan tunda take bata tab'a ganin gida mai tsaruwa irin wannan ba. Hajiyar suka hango zaune a falon tasa Laptop a gaba tana daddanawa hannunta rik'e da wani paper. Dilalliya ta zauna kan carpet chan nesa da Hajiyar ta gaidata, batareda hajiyan ta kalleta ta amsa gaisuwan, Ummy itama ta gaidata har lokcin idanun Hajiyan nakan abinda takeyi. "Dilalliya maike tafe dake" Nan fa ta gyara zama ta soma magana cikin ladabi "Hajiya dama akan maganan y'araikin da kikamin kwanaki neh, tho gashi na samo miki" Kurrri tama Hajiyar tana jira taji mai zatace, saida tad'au minti Goma sannan ta d'ago tana duban Dilalliyar "Ai na riga na samu, danaji shiru sai naba wata cigiya" Ummy wacce kanta ke k'asa hawaye suka taru mata a ido ta d'ago da sauri tace "Hajiya d'an Allah ki taimakeni ki d'aukeni, ina buk'atar aikin nan dan Allah Hajiya" Ta k'are maganan da fashewa da kuka, Kallanta Hajiyan take bako kyaftawa "Menene Sunanki?" D'an dagowa tayi batareda ta kalli Hajiyar ba "Sunana Jaleelah anma Ummy ake ce min" "Ummy d'ago idanunki ki kalleni" Bah musu ta d'ago suka had'a ido da Hajiyar, sai a sannan ta shaidata Hajiyar data taimaketa a asibiti rannan kan tayi magana Hajiyar ta rigata "Ya jikin Mahaifinki?" "Dasauk'i Hajiya mun gode" Dilalliya sai kallansu take da mamaki "Ummy dama kunsan juna neh" Hajiyar tace "Babu damuwa zan d'aukeki aiki Ummy, tun randa na fara ganinki naji kin kwanta min arai, ina miki kallon kamar y'a a wajena" "Tho Tho Madallah Hajiya" cewar Dilalliya "Zakiyi hak'uri da abinda zan rinka baki dan ba yawa dubu goma ne" Ai a rud'e Ummy ta d'ago idanunta taf da hawaye "Nagode Hajiya Allah ya saka da Alheri ya k'ara bud'i" Ameen Hajiyar tace tana lumshe ido, Sosai taji dad'in addu'ar da Ummyn ta mata. "Abu na gaba shine a nan zaki rink'a zama saida sabda lalluran mahaifinki zan rink'a sawak'e miki kina zuwa gida duk ranar Sati ki dawo lahadi" Shiru Ummy tayi kanta k'asa "Ke nake saurare" cewar Hajiya "Amm da an bari sainayi shawara da iyayena tukun" "Tho babu damuwa zaki iya zuwa" Mik'ewa tayi ta haura sama chan ta sauko rik'e da wani envelop ta mik'ama Ummyn tana cewa "Gashi nan idan sun amince sai ki bar musu gobe ki fara zuwa aiki" Hannu biyu tasa ta karb'a tana godiya, Itama Dilalliyar an mata ihsani suka fito dukansu cikeda farinciki. Tana zuwa ta zaiyanema Iyayen nata duk yanda sukayi sosai sukaji dad'i kuma suka bata goyon baya, Mama ta mik'ama envelop d'in ta bud'e, kudi ne dubu goma sha biyar, Baba yasa albarka haka Mama. Kud'in ta amsa ta tafi kasuwa ta musu sayaiyan duk abinda suke buk'ata harda Inna tad'an mata siyaiya daga nan kuma ta saima Baba maganinsa ta dawo gida.. Albarka Su Mama suketa sa mata tanata murmushi cikeda jin dad'i, batasamu kaima Inna nata ba saida daddare a nan take fad'a mata aikin data samu itama tayi mata murna tareda Addu'a, a nan suka sha kukansu na tunawa da Bilal sannan Ummy ta dawo gida. Daren ranan kuka Ummy tayi sosai rungume da hannunta wanda ta sanya zoben da Bilal ya bata. Addu'an Naiman rahama ta dunga mai duk da ita har yau zuciyarta tak'i aminta da cewa Bilal ya rasu.. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:22 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ​Page 8​ Addu'an naiman Rahama ta dunga mai duk da ita har yau zuciyarya tak'i aminta da cewa Bilal ya Rasu. Washe gari da wuri ta gama ayyukanta, Mama da kanta ta had'a mata kayanta a ghana must go k'arama, Ummy ko sai kukan rabuwa da iyayen nata take dan tunda take bata tab'a matsawa daga kusada Iyayenta na kwana d'aya ba ma. Mama taita lallashinta har tayi shiru, d'akin Baba ta shiga da mai sallama, Lalluban kanta yayi ya d'aura hannunsa akai ya mata addu'a tareda nasiha, har lokacin kuka Ummyn keyi. Yana gamawa tayi mai sallama ta fito, suka k'ara sallama da Mama ta fito ta shiga gidan Inna itama sallaman tayi mata sannan ta fito ta tari adaidaita sahu ta hau. Kasancewar ranar Lahadi neh Hanyar duk yad'an chuse saboda masu zuwa church, cikin idon Allah suka isa kofar gidan, Mai gadi na ganinta ya shaidata saboda Hajiyan tamai bayaninta, Cikin gidan ta nufa kai tsaye a k'ofar falon ta soma knocking chan aka bud'e wata y'ar budurwa black beauty ce tsaye sanye da Legins bak'i daidai guiwa da farin top gashin kanta mai tsaye, d'an rusunawa Ummy tayi ta gaidata "Daga ina?" Cewar budurwar Ummy ta k'ara duk'ar dakai tace "Hajiya ce tace na dawo yau" Yatsine fuska tayi tana kallanta up and down "Kice y'an maula ne, tho Hajiyar na bacci" Kalmar da budurwar ta kirata dashi sosai ya b'atamata rai, batace komai ba ta k'ara d'ukar dakai. Tsaki taja ta bugo kofan, hawaye suka taru a idanunta a hankali ta juya ta soma tafiya, wata y'ar dattijuwa ce ta tareta tana tambayanta lapia, Bata b'oye mata komai bah, Tsohuwar tayi murmushin takaici. "Badai Hajiyar bace tace kizo" Kai Ummy ta gyad'a, Tsohuwar tace "Ki nemi waje ki zauna, anjima idan Hajiyar ta sauko zan mata magana" Godiya taima matar ta samu waje chan wajan gate ta zauna tana k'ara bin Gidan da kallo. Tana nan zaune wani ya shigo gidan shida wata daga gani likita ne sabda yarinya dake binshi a baya kayan nurses ne a jikinta ta rik'e wani folder. Suna shigowa kai tsaye cikin gidan suka shige. Binsu da kallo Ummy tayi tana tunanin kodai Hajiyarce bata lafiya shiyasa aka hanata ganinta. Takai kusan awa d'aya sannan taga fitowar likitan tareda Hajiya, mik'ewa tayi dasauri ta k'araso wajan daidai lokacin sun gama magana da likitan. "Ina kwana Hajiya" "Aa Ummy lapia lau, har nayi tunanin bazaki dawo bah" Kan Ummy a k'asa tace "Aa ai tun d'axu na shigo ance ne baki tashi bah" Hajiyar ta soma tafiya sannan tace "Biyoni" Falon suka shiga, wani d'aki dake nan k'asan Hajiya ta kaita tareda shaida mata nan ne d'akinta. D'akin ba k'aramin burge Ummy yayi ba duk da ba wani abubuwa bane a d'akin, Gado ne d'an k'arami sai wardrobe dukansu Pink, daga gefen hagu akwai wata k'ofa da alama Band'aki neh. Kayanta ta aje suka koma falo itada Hajiyar, Kan Carpet ta zauna ita kuma Hajiyar ta hakince a kujera "Inaso ki natsu kiji abinda zan fad'a miki" "Tho Hajiya" Hajiya ta gyara zama tace "A tsarina banasan Katsalandan ma'ana banasan mutum na shiga hurumin da ba nashi bah, Sannan ki tsaya a matsayinki na y'ar aiki ba ruwanki da shiga inda ban umarceki bah." Ummy ta k'ara duk'ar dakai tace "Tho Hajiya" Budurwan nan ne ta sauko tana wani juyi da alama wak'a takeji dan ta rufe kunnuwanta da katon earpiece, Tana ganin Ummy tayi saurin zame earpiece d'in daga kunnenta "Danace ki tafi wato baki tafi ba koh" Hajiya tayi saurin cewa "Haba Mabrooka, why kike koranmin mutane idan sunzo gurina" Ta turo baki tareda zama tana hararan Ummy Hajiya ta nuna Budurwar tana cewa "Ga y'ata sunanta Mabrooka sannan inada d'a namiji sunanshi Jamaludeen" Kai Ummy ta gyada har lokacin kanta a k'asa "Mami me tazoyi gidan nan" "Aiki tazoyi" Hajiya ta bata amsa Mabrooka ta gyara zama tana murmushi "Yauwa Mami kamar kinsan Wallahi banasan aikin wannan Baban bata iya gyaran d'aki ba" Murmushi Hajiya tayi "Babu damuwa" Ta maida dubanta ga Ummy "Aikinki a gidan nan shine gyarama Mabrooka d'akinta da nawa sai ki rink'a taimaka ma Baba da ayukan da takeyi" "Tho Hajiya" Hajiya ta k'ara da cewa "Karki manta da ki tsaya a matsayinki" Kai Ummy ta gyad'a Hajiya ta sallameta ta koma d'aki. Bayan azahar Mabrookah ta shigo d'akin tana yatsine fuska "Sai ki taso muje in nuna miki d'akin ki" Bah musu ta mik'e suka soma zagayawa, Sosai gidan ya burge Ummy tanata kallo harda sakin baki. Daddare bayan Alhajin gidan ya dawo Mami ta gabatar da Ummy wajanshi, yayi na'am da zuwanta nan Mabrookah ta shiga k'orafin ita hakanan taji yarinyan bata mata bah, Lallashinta Mami tayi dakyar ta amince da Ummyn. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 9 Washe gari Ummy na sallan asubah ta fito daga d'aki dan soma aikinta, tsayawa tayi a falon k'asa tana k'arema falon kallo dan batasan ta inda zata fara bah. Wata y'ar budurwa wacce bata wuce sa'arta bah ta shigo falon sanye da riga blue iya guiwa da bak'in wando, Ummy tayi mata murmushi tareda gaidata. Yarinyar ta amsa tana cewa "Jiya na ganki Aunty Mabrookah na zagayawa dake, kema aiki zaki fara?" Kai Ummy ta gyad'a tace "Eh jiya nazo, kema aiki kikeyi" "Eh ni ina b'angaren kicin neh, Sunana Laurat" Murmushi Ummy ta sakar mata tana cewa "Ni kuma sunana Jaleelah anma Ummy ake cemin, Hajiya tace zan rink'a gyara mata d'aki da kuma Mabrookah sai..." Toshe baki Laurat tayi ta waiga bayanta ta juyo tace tareda sassauta murya "Kada kija ma kanki dan Wallahi Aunty Mabrook batada mutunci. Wai dole sai an rink'a kiranta da Aunty" Da mamaki Ummy ta kalleta "Aunty kuma?" Laurat ta gyad'a kai tace "Umm barinje b'angarena zamu had'u anjima wajan amsar abinci" Bata jira mai Ummyn zatace ba tabar wajan dasauri, d'aki ta koma ta zauna dan tasan yanzu su Hajiyan basu tashi ba balle tayi aikinta. K'arfe bakwai da rabi ta fito, Hajiyar ta hango da Mabrookah kan dinning suna breakfast, dasauri ta k'arasa ta rusunna ta gaida Hajiyan, da fara'a ta amsa, ta juya ta gaida Mabrookah daketa cika tana b'atsewa kauda kai Mabrookah tayi bata amsa bah, Hajiya tad'anyi murmushi tace "Yau zaki fara aikinki, inaso ki kasance mai gaskiya sannan ki tsaya a matsayin ki. ina fata kin ganeh" Kai Ummy ta gyad'a tace "Insha Allahu Hajiya zan kiyaye" Mabrookah ta mik'e tad'au handbag dintah tana cewa "Mami zan tafi" ta juya ta kalli Ummy cikeda tsana tace "Make sure kin gyara min d'akina yanda nakeso dan idan bai gyaru ba na dawo sai kin sake" taja dogon tsaki tabar falon tana surutai, ga mamakin Ummy sai ganin Hajiyar tayi itama ta mike tad'au handbag dina da keyn mota ta fita. girgiza kai kawai tayi ta mik'e ta shiga store tad'au tsintsiya, mopper da parker ta haura sama zuwa d'akin Mabrookan. Batsa batsa ta sameshi kamar ba d'akin mace bah, wani dogon tsaki taja tana bin d'akin da kallo "Ji d'akin mace, sai shegen k'azanta" Kayan dake zube a k'asan d'akin ta soma kwashewa, sannan ta cire bedsheet d'in dan shima yayi dati sosai, Wardrobe ta duba ta ciro wani ta shimfid'a, dak'in ta gyara tsaf tayi shara tayi mopping tareda fesa room freshner, nan da nan d'akin yad'au kamshi, toilet ta shiga ta wankeshi tas ta kwashe kayan dake laundary basket ta fito dasu, tana saukowa k'asa ta had'u da wannan likitan data gani da nurse suna haurowa, gefe ta matsa ta gaidasu sannan ta sauko. Mamaki neh sosai ranta, tho ko meh wad'an nan mutanen ke zuwa yi gidan kullum? Da wannan tunanin ta zagaya chan bayan gidan ta soma wankin kayan, wani tsoho ne ya zo wajan rik'e da bokiti da wasu kaya, tsoho ne sosai dan a kalla zai kai shekara saba'in, gaidashi tayi ya amsa ya soma kici kicin fara wanki da alama kayanshi, k'arasawa tayi inda yake ta rik'e bokitin tace "Baba kawo na wanke maka" Ya d'ago dasauri yana kallanta da murmushi "Aa 'yar nan bashi kawai keda kike naki aikin" Tad'anyi Murmushi ta kwashe kayan tana cewa "Ba komai Baba ai zan iya kawo kaga" Albarka ya soma sa mata tareda tambayan sunanta, ta fad'amai yace shi yana aikin ba flower ruwa neh a gidan. Cikin y'an mintina ta gama wankin ta d'auraye ta shanya ta koma sama. D'akin Mami ta shiga, d'akin tsaf yake ba datti sai k'anshi dake tashi, bedsheet d'in taja da niyar karkad'ewa, bandle d'in dari biyar ne ya fad'o ta matsa dasauri da mamaki tana kallan kud'in, jim tayi sannan ta d'au kud'in ta aje saida ta gyara d'akin tsaf ta wanke toilet sannan ta d'au kud'in ta aje k'arkashin filo ta fito bayan ta rufe d'akin da key. Saukowa tayi ta nufi babban kicin d'in side d'in, ma'aikata ta gani sunata aiki duka sanye da irin kayan jikin Laurat, gaidasu tayi ta k'arasa inda Laurat d'in ke tsaye tana wanke wanken kayan da akayi breakfast dasu a sink. "Ummy har kin gama naki aikin?" Kai Ummy ta gyad'a tace "Na gama, nayi sauri koh?" "Sosai ma" Laurat tace K'aran bell sukaji Laurat ta wanke hannunta taja hannun Ummy tana cewa "Lokacin amsan Breakfast yayi muje" Binta Ummy tayi har zuwa wani runfa chan bayan gidan, nan Ummy ta baza ido ganin ma'aikata daban daban, dukansu sanye da uniform wasu da Blue riga da black wando, wasu Green riga, wasu pink. Sakin baki tayi ganin ma'aikatan gidan harda turawa su hud'u, maza uku mace d'aya, su kuma suna sanye da Arsh riga da bak'in wando. Tab'ata Laurat tayi tana nuna mata plate, a tare suka d'auka suka soma bin layin amsar abincin. Soyaiyar doyace da k'wai sai Slice d'in bread guda uku da Tea. Ma'aikatan sai kallan Ummy suke ganinta cikinsu kuma babu uniform, suna amsa itada Laurat suka shiga d'akin Ummy suka zauna suka soma karyawa. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 10 Bayan sun gama Laurat ta soma bin d'akin da kallo cikeda sha'awa "Keh kam kinji dad'inki, d'akinki daban" "Ku ya naku yake?" Ummy ta tambayeta "Tab aimu d'aki d'aya mutum biyar neh, ko ku nawa neh a b'angaren da kuke aiki to d'akinku d'aya" Gyad'a kai Ummy tayi sannan tace "Niko inaso na miki wani tambaya Laurat" Gyara zama tayi sannan tace "Ina jinki" Ummy ta cigaba da cewa "Naga Kunasa Uniform ma'aikatan kicin, Sauran dana gani ma'aikatan menene" Laurat tad'anyi murmushi tace "Ko wani b'angare da uniform d'insa, bakiga ko masu gadin gidan nan da uniform ba" Ummy ta gyad'a kai, Laurat tace "Wannan matsiyaciyar Mabrookan ce, da ba'asa Uniform itace ta kawo wannan tsurfan" "Na lura batada kirki ko kad'an" Laurat tayi dariya tace "Keda kikazo ma jiya knan har kin fahimta" "Tho wad'an nan turawan fa dana gani" Dasauri Laurat ta mik'e tana cewa "Ki bari zamuyi magana anjima, barin koma bakin aikina gwara ke har kin gama naki" Itama Ummyn ta mik'e "Barinzo muje na tayaki aikin" Kicin d'in suka nufa Laurat ta cigaba da wanke wankenta Ummy na mata d'auraya. Shanyanta ta kwaso ta nunke ta kai mata d'aki ta koma kicin inda Laurat take. Haka Ummy ta cigaba da aikinta a gidan, kullum sai taga kud'i a k'arkashin pillown Mami saidai ta aje gefe data gama ta mayar inda ta aje. Kullum tana gama aikinta zata tafi kicin su cigaba da aiki da Laurat. Hurama Mami wuta Mabrookah tayi dole akayi ma Ummy uniform dan itama asan cewa y'ar aiki ce a gidan, badan taso ba aka d'inka ma Ummyn Purple riga da bak'in wando wanda ita kad'aice mai irin Uniform d'in duk cikin masu aikin. Yau Sati, da wuri Ummy ta gama ayukanta wuraren k'arfe Sha biyu, Mami ta samu a falo tana rubuce rubuce a wani takarda, ta rusunna tace "Sannu da hutawa Hajiya" D'agowa Mamin tayi tace "Yauwa sannu Ummy" Jim tayi sannan tace "Hajiya na shirya zan tafi gida" "Ohh kinga ko na manta da maganan zuwa gida yin weekend" Handbag d'inta ta d'auko dake gefenta ta ciro dubu uku ta mika mata tana cewa "Gashi kiyi kud'in mota ki gaidasu" Godiya Ummy ta mata ta mik'e ta koma d'akinta, Uniform ta cire tasaka doguwar rigar atampha tasaka hijabinta har k'asa ta fito, Laurat tama sallama da sauran ma'aikatan gidan, tama Baba mai ba flower ruwa sallama ta fito. Saida ta biya kasuwa tayi sayaiyar kayan miya yarda kaza guda d'aya ta nufi gida. Mama da Baba sunyi farinciki sosai da ganinta, ranar ita ta musu girki sai sa mata albarka sukeyi, sai bayan isha sannan ta shiga gidansu Bilal, itama Umman Bilal tayi murna da ganinta, d'ari biyar ta bata tanata godiya sun d'an tab'a hira sannan tamata sallama ta dawo gida. Ranar sunday sai da yanma sannan ta koma gidan aikinta, Ranar tasha fad'a sosai wajan Mabrookah kan k'in komawanta da wuri. Sadda kai kawai tayi k'asa harta gama fad'anta tayi gaba sannan ta shiga d'akinta. Washe gari da safe kamar kullum Ummy ta fito dan gaida Hajiya da kuma Mabrookah, yau harda Alhaji ta gani suna breakfast d'in tare, Yau neh karo na biyu da ta tab'a ganin Alhajin gidan, daga gani ko ba'a fad'ama ba kasan babban mutum neh, Tsugunawa tayi har k'asa ta gaidasu duka suka amsa Alhaji yad'au Briefcase d'inshi ya musu sallama ya fita. Mabrookah ma ta mik'e tadau jakanta sai hararan Ummyn take tama Mami sallama ta fita. Har Ummy ta tashi Mami ta kira sunanta tareda nuna mata kujera nan kan dinning, ba musu ta zauna kanta k'asa Mami tace "Na gwada ki da dama Ummy kuma kinci jarabawar dana miki, Lallai kinada gaskiya da rik'on amana" Duk'ar dakai Ummyn tayi tana murza zoben dake hannunta, Hajiya ta cigaba da cewa "Inaso na k'ara miki wani aiki guda d'aya, duk da nasan wannan ba tsarin mai aiki baneh. Anma yanayin aikina neh banida lokaci. Inaso ki rink'a gyara ma Alhaji d'aki duk safiya" Ummy tad'an d'ago da mamaki tana kallanta, lallaima Matar nan ita ina ta tab'a ganin wata ta gyara ma mutum d'akin miji. "Kina jina" cewar Hajiya tana kallanta "Eh Hajiya" Keyn d'akin ta mik'a mata tana cewa "Ga keyn d'akin ya zamana yana hannunki. Karnaji ko naga ba daidai ba ina fatar kin ganeh" Ummy ta gyad'a kai "Insha Allahu Hajiya zan kiyaye" Batace komai ba ta Haura sama ta d'auko Handbag d'inta ta fita. Kallan Keyn Ummy ketayi tana jujuyashi a hannunta, a haka ta shiga kicin inda su Laurat suke, zaune ta sameta tana yanka kankana ta zauna kusada ita "Kinsan menene?" Cewar Ummy tana kallan Laurat "Aa saikin fad'a" Ajiyar zuciya Ummy ta sauke ta ciro keyn da Hajiya ta bata ta nunama Laurat tace "Wai keyn d'akin Alhaji Hajiya ta bani na rink'a gyara masa" Magana sukaji daga bayansu ana cewa "Lallai kam kina cikin tsaka mai muya" A tare suka juya sukaga wata y'ar dattijuwa wacce zatayi sa'ar Hajiyan saidai Ita Uniform d'inta Green neh, ta k'araso ta dafa Ummyn tace "Baki ganeni ba koh" Kai Ummy ta girgiza alamar eh, Matar tayi murmushi tace "Ni ce wacce na ganki Ranar da kika fara zuwa har Mabrookah ta hanaki shiga" Sai a sannan Ummy ta shedata tad'anyi murmushi tace "Na tuna" Dattijuwar tace "Sunana talatu, tun ranar dana ganki naji kin kwanta min a rai ganin sauk'in kanki da kuma tarbiyarki. Lallai kin chanchanci aikin da aka saki" Laurat tace "Mama Talatu anma Hajiyar nan batada hankali ina aka tab'a ba yar aiki gyaran d'akin miji" "Kull 'yar nan, kinsan dai irin gidan da kike. Ki kama bakinki kisa masa lunzami" Turo baki Laurat tayi ta cigaba da aikinta, Mama talatu ta kalli Ummy tace "Wannan wani aiki neh babba Ummy, ki kula ki tsare gaskiya. Kinsan zuciya batada k'ashi, kiyi taka tsantsan da duk wani abu da kika gani, kada ki zama mai yawan bincike. Ki tsaya a matsayinki inda aka ajeki, banda shishigi akan alamuran gidan nan kinaji" Kai Ummy ta gyad'a tace "Nagode Mama Talatu Insha Allahu zan kiyaye" Mama talatu tace "Sannan duk abinda baki ganeh ba ki tambayeni, ni ina b'angaren masu share share neh kinji" Ummy ta k'ara gyad'a kai, Mama talatu ta masu sallama tabar wajan. Laurat ta aje wuk'art hannunta tace "Aike Ummy kakarki ta yanke sak'a, kinsan su masu kud'in nan wani lokacin mantawa suke da kud'i idan suka aje" Ta juya ta kalli gabas da yanma ta waigo tana kallan Ummyn "Karki dai manta dani, idan kin samu ina nan" Dariya Ummy tayi ta mik'e tace "Laurat kenan kinada matsala, barin dawo zamuyi magana" Sama ta haura b'angaren d'akinsu Hajiya, d'akuna ne wajan guda shidda, biyun farko na Hajiya ne da Mabrookah, k'ugu ta rik'e tana kallan d'akunan, na kusada na Hajiyan ta hannun hagu ta saka keyn, murd'awa taitayi yakiyi ta zare tareda murd'a kofan d'akin, take ya bud'e tad'an tab'e baki ta tura ta shiga. Wani sanyi neh da k'anshi ya dakan mata hanci, a hankali ta shiga tana b'in d'akin da kallo, sosai d'akin ya burgeta komai na d'akin blue hatta labulen d'akin blue neh, d'aga ido da zatayi ta hango mutum zaune kan wheell chair yana facing windown d'akin. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:23 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 11 A rud'e tabar dak'in jikinta na rawa, bak'in k'ofan ta tsaya tana kallan cikin d'akin, har lokacin yana kallan windown bai juyo bah. Jim tayi wani zufa ya karyo mata, sad'af sad'af ta k'ara shiga d'akin jikinta na cigaba da rawa, ta zagaya gabanshi tana kallan fuskarsa. Kyakyyawan saurayi ne wanda a k'alla zaikai shekara ashirin da biyar ko fi, fari ne daidai misali dan baya sahun bak'ake, kuma baza'a kirashi wankan tarwad'a bah dan yanada haske. Gashin kansa nada yawa mai tsayi yayi curl sai shek'i yake. Saje ne kwance kan kyakyawar fuskrsa wanda ya k'ara masa kyau da kwarjini. Idanunsa yan madaidaita masu kyawun gaske, hancinsa ma ba dogo baneh sosai saidai yayi daidai cikin 'yar fuskarsa mai d'an tsayi. Bakinsa irin light red d'in nan neh madaidaici cikin fuskar tasa. Lumshe ido Ummy tayi ta bud'e tana cigaba da kallanshi, har lokacin idanunshi na kallan windown ko kyaftawa baiyi ba balle yasan da mutum a wajan. Hannu tasa tad'anyi motsi wajan idanunsa anma ko gezau beyi bah, kurrri tamai gabanta na cigaba da fad'uwa anya wannan mutum nada rai kuwa. Jim tad'anyi na wani lokaci sannan ta fita daga d'akin tana waiwayonsa. Sosai alamarinsa yabata mamaki, a sanyaye ta bibi duka sauran d'akunan tasa keyn anma beyi bah, k'asa ta koma ta samu Laurat tana aikace aikacenta, zama tayi duk jikinta a mace, Laurat ta matso tana kallanta "Yadai Ummy meh aka samo mana neh" Maganan Laurat dariya ya bata tad'anyi murmushi tace "Laurat knan, maganarki yana bani mamaki, rik'on amana na d'aya daga cikin abinda ke sa a k'ara yarda da kuma san mutum." Ta mik'e tana murmushi tareda dafa Laurat "Banida ra'ayin abinda kike fad'i, burina na kasance mai kiyaye duk wani doka da aka shimfid'a min, banasan wuce gona da iri akan lamuran dabai shafeni bah" Laurat tayi jim tana gyad'a kai "Gaskiya kika fad'a Ummy" Taja hannunta suka zauna ta kalli Ummy tace "Ni y'ar garin kaduna ce a anguwar tudunwada, na taso bansan iyayena bah ina hannun kakata wacce itama ta tsufa. Na tashi cikin talauci da matsin rayuwa saboda itama kakar tawa batada k'arfi, Iyayena y'an garin kano neh so d'aya ta tab'a kaini wajansu, suma basuda k'arfin da zamu iya rik'eni. Hawaye ne suka gangaro mata tasa bayan hannu ta share tace "Wanchan shekaran kakar tawa ta rasu, nan na koma hannun wata dilalliya dake nan mak'otan mu saboda banida kowa, shine ta d'auko ni ta kawoni nan, yanxu kimanin watana takwas knan a nan" Ummy ta tausaya mata sosai, tasa hannu tana share mata hawaye "Ki daina kuka Allah yana tare dake, insha Allahu rayuwarki zan inganta nan gaba" Gyad'a kai Laurat tayi ta mik'e ta cigaba da aikinta, Ummy tace "Banfa gyara d'akin bah" "Meyasa?" Laurat ta tambayeta Ummy ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni duk d'akunan dake sama ba wanda ban sa keyn ba baiyi bah, kinma san wani abu kuwa?" "Aa meya faru?" Laurat ta tambaya, Ummy tace "Wani d'aki na shiga naga wani mutum zaune a kujeran guragu gashin nan dai kamar baida rai" Murmushi Laurat tayi tace "Sau d'aya na tab'a ganinshi tunda nazo gidan nan, nima yanda kika ganshi haka na ganshi" Da damuwa Ummy tace "Tho shi wanene?" Laurat tace "Ance d'an su Hajiya neh" Kai Ummy ta gyad'a ta kauda maganan. Hajiya bata dawo gidan ba sai bayan magriba, bayan ta huta Ummy ta sameta a falo ta gaidata tareda shida mata bata gane d'akin bah. Murmushi Hajiya tayi tace "Ummy kenan, ba a nan b'angaren d'akin Alhaji yake bah, b'angaren dake kusada nan nan neh b'angarensa, bakiga makullin falo baneh" Sai a sannan Ummy ta duba tagani, Hajiya tace "Gobe in Allah ya kaimu ki tabbatar kin gyara" "Tho" Ummy tace ta mik'e ta mata saida safe ta tafi d'akinta. Washe gari kamar kullum tana gama gyara d'akin Hajiya dana Mabrookah ta wuce b'angaren Alhaji, Sakin baki tayi ganin Aljannar duniya, nesa ba kusaba b'angaren Alhaji yafi nasu Hajiya kyau duk da suma nasu ba baya yake ba. Gyara tayi sosai dan b'angaren yayi datti dayawa. Haka kullum take aikinta, ta gyara d'akin Hajiya dana Mabrooka ta kuma gyara na Alhaji, tun daga ranar bata k'ara ganin mara lafiyan nan ba duk da kullum idan ta hau sama gyara saita kalli d'akin, yanzu ta gane abinda likitocin nan keyi kullum a gidan. Yau wankin Inner wears d'in Mabrookahn ta kwaso dan ta mayarda ita kamar jaka. wankin kayanta itace duk da akwai washing machine dake gidan, Guga, da duk wasu sauran ayuka duk ita take mata. K'asa ta sauka zuwa bayan gidan inda ta saba wankin itada Laurat suna hira, Tsohon nan maiba flower ruwa ne ya k'araso wajan yazo cire tiyo daga jikin famfo, Gaidashi Ummy tayi ya amsa da fara'a dan yanzu sun saba dashi sosai, so dayawa idan tazo wanki sukan had'u wani lokacin suyita hira dashi. Itama Laurat ta gaidashi ya amsa yana cewa " 'yata wanki akeyi neh" "Eh Baba, ya aiki" Ya amsa da lapia lau, har zai wuce Ummy tai saurin cewa "Baba dama inaso nai maka wani tambaya" Ya dawo tareda zama kan benchn dake gefensu yace "Allah yasa na sani 'yata" Ta nisa tace "Baba ranan na tab'a ganin wani mara lapia a gidan nan, a wani d'aki yana zaune akan keken guragu. Wai shi wanene" Nan da nan fara'ar dake fuskan Baba ya kau, ya d'ago yana kallansu yace "Sunanshi JAMALUDEEN, shine babban d'a ga Alhaji Surajo, nakai shekara goma a gidan nan ina aiki tareda Alhaji, lokacin danazo nasamu Jamaludeen yanada shekara goma sha shidda, Alhaji Surajo mutun ne mai san mutane da kuma tausayin talakawa" Ummy da Laurat suka zubamai ido suna kallanshi ya cigaba da cewa "Bakuga ma'aikatan dake gidan nan ba, saboda tausayi dayake dashi yasa yaketa d'aukan marasa k'arfi da marayu suna aiki yana biyansu. Jamaludeen yaro neh mai hazak'a da tarbiya gasan mutanen..... Ku biyoni a page na gaba dan jin cigaban labarin JAMALUDEEN UmmyAbduol✍🏻 [3/12, 8:24 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Indo Magulmaciya(Aisha Abduolqadeer)* wannan shafin naki neh kyauta Page 12 "Jamaludeen yaro ne mai hazak'a da tarbiya ga son mutane, ya samu tarbiya mai kyau daga Iyayensa, da wuya kaga Jamaludeen yayi zagi ko wani abu daya sab'a k'aida." Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "Yayi karatunsa a nan k'asa nigeria, yayi saukar alkurani tun yana aji hud'u a sakandari, daga bisani mahaifinsa ya turasa k'asar misira ya k'arashe sauran karatunsa..." Hawaye suka gangaro ma Baba yasa hannu ya share yace "Ban tab'a ganin abokin fad'an Jamaludeen bah, yaro ne mai ladabi da biyaiya, yana matuk'ar san Iyayensa kamar yanda suma suke sanshi sosai. Ya d'au kowa d'aya a gidan nan, baya nuna banbanci dan mu masu aiki neh.." Laurat tayi saurin k'atseshi da cewa "To Baba wai meya samesa neh?" Ummy ta zungureta tana hararanta "Keh kin cika garaje" Baba ya kallesu yana murmushi "Da gaskiyarta Ummy gwara data tambaya, dan idan na tsaya baku labarin kyawawan hali irin na Jamaludeen zamu kwana neh a nan mu yini bamu gama bah" "Yauwa Baba ashe ka fahimta" cewar Laurat tana hararan Ummy "Shekara uku kenan da fara rashin lafiyarsa, bayan kamalla makarantarsa da shekara d'aya ya had'u da wannan tsautsayin a hanyarsa ta zuwa kaduna yayi hatsari." "Hatsari??" Ummy ta maimaita tana kallan Baba gabanta na dukan uku uku "Kwarai y'ar nan, hatsari ya samu akan hanyarsa ta zuwa kaduna, lokacin da aka kawosa duk an d'auka baida rai sai daga baya likitoci suka tabbatar da yanada rai" Ummy ta sauke ajiyar zuciya tace "Wannan wane irin ciwo neh haka? Baba wallahi idan ka ganshi zakayi zatan gawane dan ko kyafta ido bayayi" Murmushin takaici Baba yayi yace "A hakan ya samu lapia kenan, dan baki gansa baneh da. Ba k'asar da ba'a kaishi ba anma ba wani cigaba, a nan na yarda da maganan nan da akecewa ba komai dukiya ke siya bah" "Lallai wannan bawan Allah yaga jarabawar rayuwa" Cewar Ummy tana rik'e hab'anta Baba yace "Kwarai da gaske Ummy, yanzu ina gatan yake? Ina dukiyar da mahaifinsa ya tara? Ina ilimin dayake dashi? Duk kinga basu masa anfani bah" Laurat ta gyara zama tace "Anma kuma Baba sai naga kamar Iyayensa basu damu dashi ba yanzu" D'an dariya yayi yace "Ina! aiko shi Iyayensa suka damu dashi, har yau har gobe yana cikin gata kamar yanda yake dah. Kunga dai duk dukiya da matsayi irin na mahaifinsa hakan bai hanashi kullum da safe shi da kanshi yake zuwa yanama d'an nasa wanka ya shirya shi, bai yarda wani ya masa wannan bah. Ko turawan nan da kuka gani anfaninsu kawai kula da lokacin shan maganinsa dakuma abincinsa" "Allah sarki yabani tausayi, Allah ya bashi lapia" cewar Ummy tana girgiza kai cikeda alhini Baba da Laurat suka amsa da Ameen. Godiya suka masa ya mik'e ya koma bakin aikinsa jiki a sanyaye Suma kicin suka nufa suka cigaba da ayukansu. Da daddare tunanin Jamaludeen neh ya cikama Ummy zuciya, sosai labarinsa ya bata tausayi har take tunanin bashi nata gudun mawar a rayuwarsa ko Allah zaisa a dace. (Kujimin k'arfin hali) Tunani ta soma kan yanda zata b'ulowa alamarin a haka bacci ya d'auketa. Washe gari da safe kasancewar ranar juma'a ce da wuri Ummy ta tashi, yau ana public holiday dan haka Hajiya da Mabrookah suna gida, sai wuraren sha d'aya na rana suka fito daga d'akunan su, saman ta haura bayan ta gaishe su ta soma aikinta, d'akin Hajiya ta gyara farko sannan ta zarce na Mabrookah shima ta gyara tsaf. Fitowa tayi ta juya tana kallan k'ofar d'akin da Jamaludeen d'in ke ciki, wata zuciyar na ingizata akan ta shiga wata zuciyar na hanata. Hajiya ce ta hauro ta tarar da ita a haka, sunanta ta kira tayi firgigit ta juya tana kallanta tareda rusunawa "Meh kikeyi a nan a tsaye?" Gabanta ya fad'i ta dake tace "Fitowa na kenan daga d'akin Aunty Mabrookah na gama gyaran" Hajiya tad'anyi jim sannan tace "Yau kibar gyaran b'angaren Alhaji tunda yana nan" Ta kalli Uniform d'in jikin Ummyn tace "Kije ki sauya kaya kizo ina jiranki a d'akina" To tace ta sauka dasauri ta shiga d'akinta, atamfarta ta sallan bara ta ciro daga k'asan ghana must go d'inta ta saka tad'an murza farar hodan dake cikin kayanta, gaban madubi ta tsaya tana kallan kanta, wasu hawaye ne suka gangaro mata, lokaci guda ta fashe da kuka tareda jingina kanta a jikin Mirror tana cigaba da kuka "Ka tafi ka barni Ya Bilal a lokacin da nafi buk'atarka" Zoben hannunta ta soma murzawa tana cigaba da hawaye "Kayimin abubuwa da dama a rayuwa nida Iyayena wanda bazan tab'a mantawa dashi ba, ciki kuwa harda sutura" Tad'anja rigar dake jikinta tana kallan fuskanta a madubi tana hawaye, ta dad'e a haka sannan ta shiga toilet ta wanke fuskanta ta fito ta nufi d'akin Hajiyar, a corridor tayi kicibus da wad'an nan turawan maza sun gunguro Jamaludeen suna k'okarin sauka dashi. Binsu da ido tayi tad'an matsa gefe suka wuce, Hajiyar ta samu nan d'akinta, a nan Hajiyar ke sanarda ita cewa zasu fita ne takeso suje taro. Murmushi tayi tace "Tho" Kallan kayan jikinta Hajiyar tayi tad'an yatsine fuska ta juyar dakai, d'akinta ta koma ta d'auko hijab tasa ta fito daidai nan Hajiyar itama ta sauko. Mabrookah wacce shigowanta knan gidan ta kalli Hajiya tace "Mami naga Jamal a waje ina za'a kaisa?" Hajiya tace "I want to spend this day with my son" Ta k'are maganan tana murmushi, girgiza kai Mabrookahn tayi tareda yatsine fuska "I'm hungry dana biku" "Aa kiyi zamanki ga Ummy zata rakani" Ta nuna Ummyn dake tsaye gefensu tana muzurai "What?, yanzu Mami da wannan k'azamar zaki salan ta shafa masa wani cutan dama gashi muna fama" Hajiya ta had'e rai "Banasan Haka Mabrookah behave ur self whats all dis" Zumb'ura baki tayi ta haura sama tana gungunai, ita harga Allah batasan Yarinyan nan she dnt knw why. Hajiya ta juya ta kalli Ummy tace "Kiyi hak'uri ki kyaleta wata rana zata daina" Kai Ummy ta d'aga suka fita, already sun tarar har an sakashi a motan Hajiyar, Mercedes benz E350 sai d'ayan kuma Camrey wanda Turawa masu aikin Jamal d'in ke ciki. Cikin ABU suka shiga suka d'an zazaga sannan suka fito suka tafi wani park. Ummy sai raba ido take dan sunan tana zaria neh kawai anma tunda take bata tab'a shiga cikin ABU bah. Bayan sunyi parking motocinsu Hajiya ta fito tareda shimfid'a k'aton carpet a k'asa, turawan suka kamoshi aka d'aurashi kan wheel chair d'insa. Kusa dashi Hajiya ta zauna tana kallanshi idanunta cikeda kwalla "Allah ya baka lapia Jamal, Ina kewarka sosai, Allah ya tashi..." Kasa k'arasa maganan tayi ta tushe da kuka, Ummy hawaye ya cika mata ido ta rarrafo kusada Hajiyar tana cewa "Kiyi hak'uri Hajiya, Addu'a yakamata ki rink'a masa ba kuka bah" Hajiya ta juyo ta kalleta tareda share hawayen fuskanta, wani malalacin Murmushi tayi tace "Bakisan yanda nakeji ba Ummy, Inasan Jamal fiyeda komai a duniya, da kud'i zaisa Jamal ya warke da tuni ya warke, banida wani buri yanzu daya wuce naga koda murmushin Jamal koda bazai bud'i baki yayi magana bah" Hawaye suka gangaro ma Ummy tace "Kiyi hak'uri Hajiya, kid'au hakan jarabawa ce a gareku gaba d'aya. Kiyi ta masa addu'a insha Allahu zai warke ya dawo yanda yake dah" Wani kukan Hajiya ta fashe dashi "Na cire wannan tsamanin Ummy, shekaran Jamal Uku a zaune a wannan kujeran, baya magana, baya motsi" Hijab d'in jikinta tasa tana sharema Hajiyan hawaye. "Duk mumini baya cire rai daga rahamar Allah, kiyi hak'uri wata rana sai labari. Insha Allahu wata rana sai kin gaji idan ya fara miki surutu" Sosai maganan Ummy yaba Hajiya dariya, tad'anyi murmushi tana duban Jamal d'in dake zaune kamar gunki kan keke. Kayan ciye ciye Hajiya ta siya musu sukaci suka sha, dama shi Jamal yana sanye da NG tube ta hancinsa dan baya iya tauna abinci saidai a d'ura masa abu mai ruwa ruwa ta hancinsa. Maltina Hajiya taba d'aya daga cikin masu kula dashi ta bashi, ta syringe ta soma zuk'a tana d'ura masa ta tube d'in, ganin yanda ake basa abincin tausayi yasa Ummy fashewa da kuka mara sauti ta kauda kanta gefe. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:25 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 13 Tausayi yasa Ummy fashewa da kuka mara sauti ta kauda kanta gefe. Ji tayi duk kayan ciye ciyen sun isheta ta turasu gefe ta d'ago idanunta tana kallan Jamal d'in. Hajiya ta nisa tace "Ina jin dad'in zama dake Ummy, kinda Hankali da tarbiya ga natsuwa" Murmushi Ummyn tayi ta duk'ar da kanta k'asa "Inaso ki d'aukeni a matsayin Uwa a gareki, kada kiji tsoro ko shakkan sanar dani damuwarki kinji?" Gyad'a kai tayi sannan tace cikin sanyin Murya "Nagode Hajiya" Murmushi Hajiya tayi tace "Ki rink'a kirana da Mami kamar yanda Mabrookah take kirana. Ke da ita duk d'aya na d'aukeku" Godiya Ummy ta mata sosai, sun jima sannan suka d'au hanyan gida. A wani boutique suka tsaya Mami tace Ummy ta biyota ciki, kaya Mami keta d'auka na maza ga dukan alamu na Jamal neh, sai kuma wasu data d'auka na mata itadai Ummy sai binta take a baya, juyowa tayi suka had'a ido tace "Ki d'auka duk abinda kikeso" Ware ido Ummy tayi tana kallan Hajiyar, kasa d'aukan komai tayi ganin tak'i d'auka yasa Mami ta d'aukan mata dogaren riguna da ready made atamfofi wanda zasu mata. Sun biya Ummy ta d'au ledojin suka nufi mota suka wuce gida. Saida takaima Hajiyar kayan d'aki sannan ta sauko ta koma d'akinta ta sauya kayan jikinta zuwa uniform ta nufi kicin wajan Laurat, koda taje ta sameta ta cika tayi fam saura kad'an ta fashe. Kallo d'aya Ummy ta mata ta kyalkyalle da dariya "Hajiya Laurat, yadai meya faru?" Laurat ta k'ara turo baki ta kauda kai, dariya Ummy ta k'arayi tace "Ahaf karkiyi maganan, ai gobe ina gida abuna maga da wanda zakiyi" Jin haka yasa ta juyo dasauri tana yatsine fuska "Ai kece kin cika abin haushi, ba inda ban nemeki ba a gidan nan ban ganki bah" "Tho maida wuk'ar, mun fita ne da Hajiya d'azu" Da mamaki Laurat tace "Dah Hajiya?" Ummy ta gyad'a kai tareda zama kusada ita ta soma bata labarin fitar nasu. Hannunta Laurat ta kama tana murmushin farinciki "Ummy kin shigo gidan nan da k'afar dama, lallai kinada sa'a" Ummy tai dariya kawai batace komai bah. Washe gari misalin k'arfe goma Ummy ta fito daga kicin dan tasan a wannan lokacin ya isa ace su Hajiyan sun tashi, sama ta haura tayi knocking d'akin Hajiya, izini Hajiyan ta bata ta shiga da sallama, zaune ta sameta kan stool tana shafa cleanzer a fuskanta, har k'asa ta tsugunna ta gaidata ta amsa tana kallanta da murmushi "Barin baki guri kiyi aikinki" Tashi Hajiyan tayi har takai bakin k'ofa sai kuma ta dawo tace "Jiya shine kika ajemin kayan nan a d'akina? Ai na saya miki neh ki d'auka ki cigaba da anfani dasu." Ta nuna mata k'aton ledan dake kusada bedside tana cewa "Gashi chan ki d'auka" Godiya Ummy ta shiga mata tai saurin girgiza mata kai tana cewa "Ba godiya a tsakanin mu Ummy, kin wuce haka a wurina" Bata jira mai zatace ba tabar d'akin, aikinta ta shiga yi ta gyara ko ina tasa turaren wuta mai k'anshi ta fito bayan ta d'au ledan kayan. K'asa ta sauka ta kai ledan d'aki sannan ta dawo ta shiga d'akin Mabrookah, saida ta gama mata wulak'anci da zagi sannan ta fito ta bata waje. Dama kuka baima Ummy wuya, saida tayi mai isarta sannan ta gyara d'akin ta fito. Yau ko k'ofar d'akin Jamal bata kalla ba ta sauko k'asa ta koma d'akinta. Kayan da Mami tasai mata ta bud'e ta duduba, kaya ne masu kyan gaske da tsada, set biyu wanda tasan zaima Mamanta ta d'auka tasa a leda sannan ta sauya kaya cikin wanda Mamin tasai mata, dogon riga neh pink swait mai stones a k'irji, sosai kayan suka amsheta tayi kyau sosai, dama Ummyn ba banza ba akwai diri. Farin hijab tasa ta fito zuwa falo, Mami tama sallama wannan karon driver akasa ya kaita gida. Iyayenta sunyi farinciki da zuwanta, ranar kusan raba dare sukayi suna hira, a nan Ummy ke fad'a musu matsalan Jamal, sunyi alhini tareda mai addu'an samun Lapia. Washe gari saida ta musu girki da duk wani abu da suke buk'ata sannan ta taho, wannan karan bata shiga gidansu Bilal bah dan wannan satin a kuraren lokaci tazo. D'akinta ta shiga ta sauya kayanta sannan ta haura sama zuwa d'akin Mami ta shaida mata dawowanta, kicin ta shiga ta samu mutuniyar nata na gyaran alaiyahu, ta gaida sauran mutanen kicin d'in sanan ta zauna kusada Laurat tace "Sannu da aiki" "Yauwa, anma fah yau kin dad'e baki dawoba" Ummy ta saki murmushi tana hararanta da wasa "Keko ina tsakiyar Baba da Mama mai zai kaini dawowa yanzu" Murmushin k'arfin hali Laurat tayi, idanunta suka ciko da kwalla tunawa da Kakarta dan ita batasan dad'in Iyayeba saboda tana k'arama suka rasu. Ummy tai saurin kauda zancen da cewa "Mama na gaishe ki, har y'ar tsaraba ta bani na kawo miki" Da fara'a Laurat ta d'ago tace "Kai dan Allah dagaske?" Ummy ta gyad'a mata kai "Allah sarki Mama ya take? Ya jikin Baba" "Dasauki" Ummy ta bata amsa. A tare suka gama gyaran alaiyahun, sannan suka wuce d'akin Ummy, tsaraban ta ciro mata na kayan ciye ciye da Mama ta bata ta kawo mata, su goruba da tsamiyar biri dadai sauransu, sosai Laurat taji dad'i tayi godiya sosai. Sannan tace "Kinsan meke faruwa a gidan nan kuwa?" Ummy ta girgiza kai alamar A'a, Laurat tace "Nima d'azu muna hira da Mama Talatu take cemin wad'an nan turawan masu kula da Jamaludeen zasu koma k'asarsu gobe da safe" Ummy ta zaro ido dasauri "Kai dan Allah dagaske?" Laurat ta gyad'a kai "Wallahi kuwa, wai an kirasu a k'asarau, dama ma'aikatan asibiti neh" Jikin Ummy neh yayi sanyi tace "Tho yanzu wazai cigaba da kula dashi?" "K'ila zasu samo wasu neh ina ganin" Shiru Ummy tayi duk saitaji hiran ta gunduretah. Haka ta yini jugum ranta bai mata dad'i, tausayin Jamal ne ya cikata. Da safe bayan ta idar da sallan asubah tana zaune kan sallayabtaba lazumi aka banko k'ofan d'akin, Mabrookah ta gani tsaye tana yatsine yatsine tana bin d'akin da kallo "Ki fito Mami da Abba na kiranki a falo" Ta sake banko k'ofan ta fita daga d'akin. Girgiza kai Ummy tayi cikeda takaici, saida ta gyara hijabin jikinta sannan ta fito zuwa falon, bataga kowa ba dan haka ta haura zuwa falon sama, hangosu tayi zaune jugum jugum ta shiga da sallama ta samu guri k'asan carpet chan nesa dasu ta zauna, d'aya bayan d'aya ta gaishe su, Abba ya kalli Mami yace "Itace yarinyar" Mami tace "Itace, kuma nasan zata iya" Gaban Ummy ya yanke ya fad'i, tad'an d'ago kai tana kallan Mami, Abba yace "Ki kwantar da hankalinki, ba wani abu baneh. Nasan kinsan d'ana Jamaludeen" Ummy tace "Eh" Abba ya cigaba da cewa "Kuma nasan kinsan lalurar dayake tattare dashi" Nan ma ta sake gyad'a kai "Akwai turawa wad'anda suke lura dashi dangane ga abincinsa da kuma maganinsa dadai sauran yan abubuwa da suka shafe shi, tho yanzu wa'adin da suka d'iba ya cika kuma sunce bazasu k'ara kwanaki bah. Dan haka shine nake neman wanda zai cigaba da aikinsu" Ya nuna Mami yace "Shine Hajiya tacemin zaki iya" Shiru tayi kanta a k'asa. Hajiya tace "Bakice komai ba Ummy" Abba yace "Karki damu indai maganan albashi neh zan ninka miki akan abinda ake biyanki, zan rink'a biyanki dubu d'ari duk wata" Da mamaki Ummy ta d'ago ta kalleshi, ya gyad'a mata kai tace "Zan Iya Alhaji, saidai kud'in yayi yawa" Mami tayi murmushi tace "Karki damu buk'atarmu dai ki yarda, sanin halinki da k'wazon ki yasa na amince dake akan aikin" Shiru ta sakeyi anya kuwa zata iya wannan aikin? Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:26 AM] ‪+234 806 215 4020‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 14 Shiru ta sakeyi anya kuwa zata iya wannan aikin "Ke muke jira har yanzu bakice komai bah" Mabrookah ta tab'e baki tace "Mami dama kun kyaleta, wannan ba iyawa zatayi bah" Mami ta galla mata harara, ta kauda kai gefe tana turo baki. Ummy tad'an d'ago tace "Zan iya saidai ban iya bashi abinci bah" "Indai wannan neh karki damu, za'a nuna miki komai" cewar Hajiya Abba yace "Tho Alhamdulillah tunda kin amince, sannan aikin bawai zaki dauwama dayi baneh, nad'an wani lokaci ne zuwa sanda za'a samo wad'anda zasu cigaba" Ummy ta gyad'a kai, Mami ta sallameta ta tashi ta koma d'akinta tana tunani. Ranar Mami bataje aiki ba saboda tafiyan turawan nan, an musu sha tara ta arziki (abunku da gidan mai naira) har airport aka kaisu suka hau jirgin lagos dan tachan zasu tashi. A ranar Mami ta koya ma Ummy yanda ake feeding d'insa, da kuma nuna mata rosters abincinsa da magugunansa. Sosai ta fahimta kuma a ranar Mami tace zata fara aikin, Saidai abinda Mamin bata sani bah shine Ummyn bata iya karatu ba dan bata iya karanta abinda ke jikin rostern abincin Jamal d'in. Wureren k'arfe sha biyu ta shiga kitchen ta samu Laurat tana yankan albasa, murmushi ta mata bayan ta k'araso wajanta "Taimako zakimin Laurat" Laurat ta d'ago tana kallanta "Taimakon meh fah" Nan ta fad'a mata aikin da Mami ta bata na kula da Jamal, da mamaki Laurat tace "Anya kuwa zaki iya Ummy?" Hararan wasa Ummy tai mata tana cewa "Mai zai hana, wannan ai wani dama ce na samu na samun lada, kinsan kula da mara lafiya akwai lada sosai" Laurat ta gyad'a kai "Tho Allah ya bada sa'a" "Ameen, ni kinsan ma menene Laurat" Laurat ta girgiza kai "Wallahi ni rubutun kayan abincin nasa neh bana ganeh wa, dan Allah ko zaki karanta min" Papern ta mik'a ma Laurat ta duba tareda zaiyane mata duk abinda ke cikin takardan. Godiya ta mata ta amsa tana cewa "Oh Ikon Allah kenan, jidai duk dukiya irin na mahaifinsa anma ya koma shan kunun gero da dawa" Cikeda alhini Laurat tace "Allah kai mana rowan ciwo dai" Ummy ta amsa da Ameen. Sallama tama Laurat ta haura sama zuwa d'akin Jamal d'in dan lokacin bashi abincin rana yayi, kunun tamba dake flask ta d'iba tasa madara da sugar kad'an sannan tad'au syringe ta soma zuk'a tana d'uramai ta bakin NG tube d'in dake hancinsa. Tana gamawa ta dama maganinsa shima ta basa. Zama tayi kusada shi tana kallanshi fuskanta d'auke da Murmushi, duk da hali dayake ciki na rashin lapia, ko kad'an baida rama a jikinsa koh alamar wahala sai ma wani k'ara haske dayakeyi. Idanunshi kamar kullum yana nan kyam a wuri d'aya baya kyaftawa. A haka Ummy ta cigaba da aikinta a gidan har batada lokacin kanta, kullum da sassafe take tashi ta soma gyara d'akinta sannan ta haura nasu Mami ta gyara da side d'in Alhaji. Kula kuwa da Jamal ba'a magana, ta d'aukema masu gyara masa d'akin da wankin kayansa, kullum ita take masa a washing machine dan Mami ta hanata wankin hannu tasa an koya mata yanda ake anfani da machine d'in kuma ta iya, duk weekend tana zuwa wajan iyayenta. Wani lokaci ta shiga gidansu Bilal wata rana kuma bata samun shiga. Kimanin wata Ummy biyu kenan a gidan, Mami da Abba najin dad'in yanda take kula musu da d'an nasu, kyautatawa na abubuwa da dama tana samu daga wajan Mami da Abba, Mabrookah kuwa har yau ba abinda ya chanza daga halaiyarda take nunawa Ummy. Yau bayan ta gama duk ayukanta, feeding d'in Jamal take tana kallan kyakyyawar fuskarsa harta gama sannan ta basa maganinsa. Zama tayi kusa dashi kamar kullum tana kallansa, wani dabara ce ta fad'o mata ta mik'e dasauri ta sakamai belt d'in dake wajan hannuwansa, ta saka masa na k'afa ta gunguroshi ta fito dashi daga d'akin. Dakyar ta sauko dashi k'asa ta fita dashi waje zuwa chan garden d'in dake bayan gidan, ma'aikata sai kallanta sukeyi dan yawancin su basusan ita ke kula dashi bah. Garden d'in ta kaisa ta ajeshi, kneel down tai a gabansa ta sa hannunta ta d'ago fuskanshi tana murmushi "Yau kaima ka fito kasha iska kaga haske" Dariya tayi hawaye cike a idonta tana kok'arin yin kuka "Jamal! Yaushe zakayi magana? Insan jin maganarka. Inasan naga ka warke" Laurat ta shigo Garden d'in dasauri dan ta hangosu ta windown kitchen sanda take wucewa dashi. Ummy na ganinta tayi saurin share hawayen fuskanta "Ummy lafiyarki kuwa? Kin tab'a ganin an fito dashi idan ba fita za'ayi dashi bah" Ummy ta d'ago tana murmushin takaici "Bantab'a gani bah, anma kuma yanda ake masa baya min dad'i. Bai kamata ace kullum yana guri d'aya bah, yakamata a rink'a fitowa dashi yana chan iska" "Nidai da zakiji ta nawa da kin maidashi Ummy, karki jama kanki" Yatsine fuska Ummyn tayi tana cewa "Nifah bazan koma dashi ba sai mun gama shan iska" Laurat ta girgiza kai "Nidai ba ruwana" Bata jira mai Ummy zatace ba tabar wajan dasauri. Tsaki tayi ta zauna gabansa ta tankwashe k'afarta tana kallansa Labarin dariya da tatsuniya taita bashi, tanata magana ita kadai ita a dole suna hira, idan ta bada labarin dariya saidai ita tai dariyan, Wani lokaci kuma ta fashe da kuka. haka suka k'arashi zamansu ta gungurashi ta maidashi d'akinsa. Kamar kullum yauma tana gyara d'akinsa bayan ta gama nasu Mami, wardrobe d'inshi ta bud'e ta soma gyara masa kayansa dake ciki, wani riga ta d'aga wasu hotuna suka zubo daga k'arkashin rigan, hotunan ta d'auka ta soma dubawa, Jamal ne tun yana d'an yaronsa da kuma wani wanda yana ya fara tasowa har zuwa wanda ya d'addauka sanda yake makaranta a egypt, shagala tayi da kallan hotunan, Allah sarki rayuwa kamar ba'ayi bah. Wasu hawaye suka gangaro mata ta juya tana kallanshi cikeda tausayawa. A sanyaye ta k'arasa gyaran ta dawo kusada shi ta zauna, kurani ta d'auka a kan bedside ta dawo gabansa ta zauna ta soma karantawa cikin zazzak'ar muryarta. Suratul Yasin ta bud'e tana karantawa a hankali kanta k'asa, tayi shafin farko tana a nabiyu bata ankara ba taga Jamal ya fad'i tim a gabanta. Tho Fah! Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:33 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* OMG gaba d'aya littafin nawa ni kad'ai, Babu abinda zance sai nagode Allah saka da Khairan ya barmu tare my Swt *Ummu Farheen* Allah yasa yanda kika fara wannan littafi *K'alubalen rayuwa* lapia, Allah yasa ki gama lapia. Ameen Page 15 Tayi shafin farko tana a na biyu bata ankara ba taga Jamal ya fad'i tim a gabanta. A tsorace ta aje kur'anin ta zaro ido cikeda tsoro, dasauri ta k'asara ta juyoshi dakyar tana kallanshi cike tsoro, ga mamakinta ganin idanunshi tayi a rufe, ba shiri ta fashe da kuka ta soma jijigashi a tsorace "Jamal, Jamal" Dagudu ta fito daga d'akin tana kuka wui wui, haraban gidan ta nufa, ko Mabrookah dake gyara parking motanta batayi ba ta nufi wasu maza dake wanke mota da sauran ayukan gida tana cigaba da kuka, rok'onsu tayi su taimaka mata a d'aga shi. Mabrookah sukazo suka wuce har lokacin tana tsaye bakin motanta, ganin sunyi ciki itama ta bisu dasauri, Ummy ce ta musu jagora har zuwa saman tana cigaba da kuka. A tsorace suma mazan suka karasa inda take kwance suka d'agoshi, har lokacin yana k'asa idanunshi a rufe, kan wheel chair d'in suka d'aurashi. Daidai nan Mabrookah ta shigo rai b'ace tana binsu da ido, wani razananen k'ara ta saki ganin idaunshi a rufe fuskanshi yayi ja sosai, mazan summ summ suka bar d'akin dan sunsan halinta batada mutunci. Ummy bata ankara ba taji saukan mari a kuncinta, a gigice ta d'ago idanunta da suka rune zuwa ja tana kallan Mabrookah "Kin kasheshi kin huta, me ya miki da zaki kasheshi" Jin maganan Mabrookah yasa Ummy sakin wani sabon kuka mai k'arfi ta fad'i k'asa tana kallanta "Wallahi ban kasheshi bah, hakanan naga ya fad'i, dan Allah ki yarda dan..." "Shut ur dirty mouth" Mabrookah ta fashe da kuka ta fit daga d'akin tana laluban Mami a waya. Kuka sosai Ummy keyi ta rarrafo ta dawo gabanshi ta tsugunna tana kallansa. "Dan Allah karka mutu, ka rufamin asiri, nikad'ai ce wajan Iyayena, Allah ne gatanmu ni ce gatanmu" Ta sake rushewa da kuka ta rik'e wandonshi tana girgiza shi a hankali kanta k'asa. Labari ne ya cika gidan na cewa Jamal ya mutu, duka ma'aikatan gidan sun taru a haraban gidan kowa fuskarsa d'auke da damuwa. Horn akayi masu gadi suka bud'e gidan, Motan Abba da Mami a tare suka shigo, ba wanda yayi k'wakwaran parking Mami sai kuka take suka shiga cikin gidan dasauri. Mabrookah najin motsinsu ta fito daga d'akinta tana kuka, duk a tare suka shiga d'akin, har lokacin Ummy na tsugunne gabanshi tana kuka. Saurin d'agowa tayi tana kallansu tana girgiza kai "Wallahi ba abinda na masa Mami ki yarda dani" Ga mamakinsu ganin shi sukayi zaune yanda yake kamar da, idanun nan nasa a kafe. Wani nauyayyan ajiyar zuciya Abba ya sauke ta sunkuya ya tab'a kirjinsa, jin yana numfashi yasa ya juya yana kallan Mami "Yanada rai ba abinda ya samesa" Tsagaita kukanta tayi tana kallan Ummy rai b'ace "Meh kika masa Ummy" Cikin kuka tace "Ki yarda dani Mami ba abinda na masa hakanan ya fad'i" "Karya kikeyi, hakanan ba abinda kika masa zai fad'i?" Mabrookah ta fad'a tana nuna Ummy da yatsa Abba yayi saurin katsesu yace "Ya isa, tsautsayi neh nasan" Ya juya ya kalli Ummy yace "Sai a kiyaye gaba" Fuuu Mabrookah tabar d'akin, Mami da Abba suka bar d'akin a sanyaye, Mami ce ta fad'ama masu aikin bai mutuba, nan kowa hankalinsa ya kwanta suka koma bakin aikinsu. Duk da haka hankalin Mami bai kwanta ba saida ta kira likitansa yazo ya dubasa tareda tabbatar musu yanada rai sannan ba abinda ya samesa. Sosai Mami taja ma Ummy kunne akan kula dashi. zage dantse tayi wajan Feeding d'inshi akan lokaci da kuma bashi magungunansa. Haka kullum takan sauko dashi k'asa taita zagayawa dashi. Sam bata gajiya da d'awainiyar Jamal dan tausayinsa takeji sosai. Wannan watan kamar yanda Abba ya alkawarta, dubu d'ari ya biyata albashi, murna wajan Ummy ba'a magana har kuka saida tayi data amsa kud'in, dama ranar sati neh, dakyar Mami ta yarda ta barta taje gida weekend dan yanzu bata cika zuwa ba saboda hidimar Jamal, itama sam batasan barinsa saboda halinda yake ciki. Da murna isa gida, iyayen nata ta tarar a tsakar gida suna shan iska, da murna ta taresu, Mama ta soma fara'a tana "Lale lale, barka da zuwa" Ta k'arasa ta rungume Mama tana dariyar farinciki, Baba ma murnar yake yanata lallubenta da hannu, ta rik'o hannunshi ta d'aura a kanta tana dariya, ya shafa kanta yace "Allah ya miki albarka Jaleelah" Ameen Mama da Ummy sukace, ba b'ata lokaci ta ciro kud'in albashinta ta d'aurama Baba a hannu tana cewa "Baba ga albashina na wannan watan" Kud'in yake tattab'awa baki bud'e "Ummy ina kika samu wannan kud'in haka? Wannan daga ji yafi albashinki" Sai a sannan ta musu bayani, Iyayen nata sukaita murna tareda sa mata albarka. Ganin yanda suketa murna yasa ta fashe da kuka, Mama ta rungumeta tana lallashinta. Kasuwa ta shiga tayi siyaiyan kayan abinci sosai harda Umman Bilal, atamfofi kala shidda ta siya masu sauk'in kudi, tasai shadda d'aya da yadi biyu na Baba sannan tasai masa magungunansa da kuma sauran y'an abubuwan anfanin gida sannan ta dawo. Atampha uku taba Mama, yadi da shadda taba Baba yanata murna, da kanta takai musu d'inkin, ta biya kud'in. Bata samu shiga gidansu Bilal ba sai dare, ganin kayan abincin da Ummy ta kawo yasa Umman Bilal fashewa da kuka, lallashinta Ummy ta dungayi har Bahar k'anin Bilal ya shigo gidan yana cewa "Umma wannan shekaran ma na rasa, duk inda nake tunanin samun rancen kud'i naje ban..." Kasa k'arasa maganan dayake yayi ganin Ummy dan sai a lokacin ya lura da ita, duk da ya girme mata hakan bai hanashi gaisheta ba, dan murmushi tamai tana cewa "Ni yakamata na gaisheka bakai bah" Murmushi yayi ta gaida shi ya amsa, atampha ta mik'ama Umma shima ta mik'amai Yadi, nan sukaita zuba godiya kamar sun ari baki har saida tayi hawaye. Tambayanshi tayi ranchan kud'in me yake nema yace yasan ya rubuta jamb neh ya koma makaranta, batareda bata lokaci ba tace ya biyota gida ya amsa. Umma ta sake fashewa da kuka, Ummy itama ta saki kuka ta rungumo Umman tana cewa "Ki daina kuka Umma, duk abinda nake muku bazan tab'a biyan Ya Bilal abinda yamin ba a rayuwa" Sun dade suna kuka, Bahar ne yayita basu baki har sukayi shiru, Umma sai sa mata albarka take ta mata sallama Bahar ya biyota dan amsan kud'in. Bayan ta basa yayi godiya ta rok'eshi alfarman ya amso masu Mama d'inkinsu data bayar nan layin bayansu. Batareda b'ata lokaci ba ya amsa mata bayan ya k'ara mata godiya. Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:33 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Xaboorah Hapsert* Wannan shafi kacokan taki ce kyauta. Ina matuk'ar godiya Page 16 Batare da b'ata lokaci ba ya amsa mata bayan ya k'ara mata godiya. Koda ta dawo gida abinci Mama ta zuba mata, Tuwon shinkafa da miyar egusi sai k'anshi yake, nan kan tabarma suka zauna a waje suna shan iska kasancewar lokacin zafi neh. D'ibo tuwon Ummy tayi harta kai saitin bakinta Jamal ya fad'o mata a rai, tunani ta soma dan tasan yanzu lokacin cin abincinsa neh, Allah sarki ta fad'a a hankali, dakyar takai loman ta soma taunawa a hankali kamar tana cin magani. Mama dake gefenta tanaba Baba abinci ta kalleta "Ummy lapia, ko bakij dad'in abincin baneh?" Girgiza kai tayi ta kirkiro murmushi "Aa abincin yayi dad'i sosai, Jamal na tuna nasan ynzu lokacin bashi abinci neh" Baba yace "Allah sarki, Allah kenan shiyasa kullum nake k'ara godema Allah dayasa nake ji nake iya magana, kuma nake sauran Alamura na duk da bana gani" Tausayawa Mahaifin nata tayi tace "Insha Allahu Baba zak warke, zaka cigaba da gani kamar yanda kowa yake gani" Murmushin takaici yayi batare da yace komai bah. Labarin abinda ya faru da Jamal rannan ta basu, Mama tace "Anya kuwa ciwon yaran nan baida nasaba da mutanen b'oye" Baba ya gyad'a kai yace "Maganarki abin dubawa ce, saidai zai iya yuwuwa basu d'in baneh kawai dai ya fad'i neh" Itadai Ummy batace komai ba sai kallansu datake. Mama tace "Anma Mallan wannan alamace ai ta cewa akwai su a tare dashi, kasan su mutanen nan basu san suratul Yasin musamman idan sunyi k'amari" Baba ya gyad'a kai yace "Hakaneh maganarki, koma dai basu d'in bane kamata yayi asama masa na gargajiya inaga zaifi na bature" Ummy tayi murmushi tana kallan Iyayen nata yanda suke hira cikeda sha'awa. Washe gari wuraren azahar ta baro gida ta dawo bakin aikinta, kasancewar lahadi ce a falon k'asa ta had'u da Mami itada wasu bak'i, gaidasu tayi ta bar wajan ta shiga d'akinta. Saida tad'an huta sannan tasa uniform ta fito ta shiga kicin. Sun gaisa da mutanen kicin d'in, Laurat ta tareta da fara'a tana cewa "Oyoyo Nannyn Jamal" Duka ta d'akama Laurat d'in da wasa tana cewa "Bakida kirki wallahi" Dariya sukasa duka, Laurat tace "Kinbar Mami da aiki dan naga daga jiya zuwa yau ita ta chanje ki" Ummy tayi murmushi ta d'aga kai tana duba agogon kitchen d'in "Saura minti talatin lokacin feeding d'insa yayi, barinje zamu had'u anjima" Fita tayi ta haura sama zuwa d'akinsa, Yau kaftan ce a jikinsa, brown yadi mai tsadan gaske da santsi, d'inkin yayi fitting d'inshi kamar a jikinshi aka d'inka, sosai yama Ummy kyau sai kallansa take kyaftawa batayi. Muryan Mami ne ya dawo da ita tana cewa "Yauwa Ummy, gwara da kika dawo da wuri dan fita zanyi" Ummy tayi murmushi tace "Dama nayi tunanin wanda zai rik'e aikin kafin na dawo" Mami tace tana k'okarin fita "Babu kowa niketa d'awainiya, nima ga gajiyar aiki" Bata jira mai Ummyn zatace ba tabar d'akin. Coasterd ta dama ta barshi ya huce sannan tasa madara ta soma zuk'a a syringe tana d'ura masa. Haka tai tayi harta gama ta kwace kayan ta fita dasu, yau bata kaisa waje ba dan gudun magana wajan Mabrookah. Kula sosai Jamal ke samu daga wajan Ummy, har wata yar k'iba yayi, Abba da Mami na matuk'ar jin dad'in yanda Ummyn ke kula dashi. Yauma kamar kullum chan garden d'in gidan ta kaisa, tun bayan fitarsu Mami taganshi wani iri har yanayin idanunshi sun chanza kamar da abinda ke damunsa Jikinta ne yayi sanyi ta zuba masa narkakun idanunta tana kallansa, gashi batada waya balle ta kira Mami ko Mabrookah ta sanar dasu halin da ake ciki. Hannu tasa ta tab'a wuyanshi, zafi taji jikinshi yayi sosai, nan hankalinta ya tashi ta rasa yanda zatayi, kitchen ta shiga ta kira Laurat suka fito waje ta baya "Laurat kamar Jamal bashida lapia" "Bashida Lapia kuma? Shida baya magana ya akai kikan baida lapia" cewar Laurat tana kallan Ummyn Hannunta Ummy ta kama sukazo inda yake zaune a garden ta nuna mata shi tana cewa "Kinga yanda idanunsa suka sauya? Kuma jikinshi ma da zafi" Laurat tayi Jim sannan tace "Tho yanzu meye abinyi? Gashi su Hajiya basu nan kuma ni banga wani mai waya a cikin ma'aikatany gidan nan bah" Shiru sukayi gaba d'aya suna kallansa "Abu mafi sauk'i shine ki kyallesa kawai ko ki maidasa d'aki idan Aunty Mabrookah ta dawo sai ki sameta dan naga tana rigasu dawowa" Kai Ummy ta gyad'a Laurat ta koma kicin bakin aikinta. Rasa abinyi tayi ta sake tab'a jikinsa taji ya k'ara zafi fiyeda d'azu. Hankalinta ya tashi nan da nan hawaye suka cika mata ido. Kallanshi kawai takeyi tana chan kuma tace "Sannu! Sannu!! Allah bakay lapia" Ta k'arasa hannu ta tab'a goshinsa tana cewa "Kayi hak'uri kaga ba kowa da an kaika asibiti, Sannu" Tausayinta ne ya mamaye mata zuciya, saitin kunnensa tasa bakinta, Bismillah tayi sannan ta karanta fatiha ta da Qulhuwallahu, Falaq da Nas. Ta tofa masa a jikinsa gaba d'aya. Wani zufa ne ya soma karyo masa, tasa d'an kwalin riganta tana share masa a hankali, Suratul mulk ta soma rerowa a hankali cikin zazzak'ar muryanta tana cigaba da goge masa zufan dake goshinsa. Wangale gate d'in gidan akayi wata had'adiyar red doddge ta shigo ciki tayi parking a haraban gidan. Kyakyyawan saurayi ne bak'i ya fito daga cikin motar sanye da blue gezina sai hek'i take da d'aukar ido. Direct side d'insu Mami ya shiga sallama ya dinga dokawa a falon k'asa, d'aya daga cikin ma'aikatan gidan ce ta fito ta tsugunna ta gaidasa, Mami ya tambaya tace taje aiki, baice komai ba ya haura sama zuwa d'akin Jamal. Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:33 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* _*Shekara shidda kenan da rasuwan d'aya daga cikin yanina, Ina baran Adduar ku Allah ya masa rahama yasa Aljanna ce makoma a gareshi. Ameen*_ Page 17 Baice komai ba ya haura sama zuwa d'akin Jamal, wayam yaga d'akin ya fito dasauri ya nufi sashin masu aiki yana tambayansu inda Jamal d'in yake, Laurat ce masa jagora har zuwa garden din. Tun daga nesa ya hangosu tana share masa zufa tana cigaba da rera masa karatun alkur'ani, dakatar da Laurat saurayin yayi suka tsaya nan wajan sai binsu da ido yake. Suratul Baqrah tayi bismillah ta fara, tana kan aya ta ashirin bata ankara ba taji an mak'ure mata wuya, idanunta ta fifito dasu ta d'ago dasauri Jamal ta gani idanunshi sun rune sun koma ja haka fuskan nasa, tari ta soma had'e da kakari tasa hannayenta tana k'okarin cire hannunsa akan wuyanta. Dasauri saurayin nan ya k'araso wajan ya soma janta dakyar ya samu ya fincike hannunsa daga wuyan Ummyn, chan gefe ta fad'i tana rik'e da wuyanta tana tari had'e da kuka kamar ranta zai fita. Laurat ta k'arasa wajanta dasauri, shi kuma saurayin ya tsaya gabanshi yayi bismillahi ya cigaba da karatun daga inda ta tsaya fuskarshi d'auke da damuwa. Wani irin zabura Jamal d'in keyi yana wani irin ihu, belt d'in wheel chairn ya tsitsinka yana ihu yana k'okarin mik'ewa, kan kace meh ma'aikatan gidan sun taru a wajan suna ba idanunsu abinci, itako Ummy nachan gefe idanu sunyi luhu luhu sabda shak'an da yamata. Karatun saurayin ya cigaba yama wasu maza cikin masu aikin nuni akan su rik'eshi, su wajan biyar suka rik'eshi da kyar yanata k'okarin kwacewa. Wajan da Ummy take Saurayin ya k'arasa ya duk'a yace "Sannu tashi ki k'arasa ladanki" Kallanshi ta tsaya yi ya gyad'a mata kai ta mik'e tana rik'e da wuyan nata suka cigaba da rairo karatun alkur'ani a tare, chan gefe saurayin ya matsa ya soma neman Layin Abba, bayani ya masa sannan ya kashe ya kira Mami. Wani kukan kura Jamal yayi ya doke samarin dake rik'e dashi yayi kan Ummy, bata ankara ba taji ya d'auketa chak yayi wurgi da ita, wani razananen ihu ta saka a hankali ta sulale ta sume. Daddaneshi samarin suka k'arayi, duk hankalin saurayin nan baya jikinshi, kota kan Ummyn beyi ba sai safa da marwa dayake tayi a wajan, k'aran mota sukaji kan kace me masu aikin dake cike a wajan kowa yayi hanyarsa dasauri, Hankali tashe Abba ya shigo garden din shida wani dattijo, ganin halinda yake ciki yasa Abba ya karasa dasauri yana kokarin kama Jamal d'in, Dattijon ya dakatar dashi dasauri yamai nuni daya matsa, hawaye suka soma gangaro ma Abba ya matsa yana kallan d'an nasa. Ruwa dattijon yasa aka kawo mishi a wani bowl, addu'a yayi ya tofa yace samarin su sakeshi, suna sakeshi ya yunk'ura zai tashi Dattijon ya watsa masa ruwan a fuskansa da kirji, wani Ihu ya saki ya koma ya zauna har lokacin idanunshi a jujuye. Dattijon ya tsugunna gabansa yace "Wanene kuma me kake nema a jikinsa" Shiru yayi chan kuma ya soma wani irin ihu kamar na doki, Dattijon yayi murmushi yace "Kunaso ku nuna taurin kai koh? Idan bakuyi magana ba zan la'anta ku zan d'aidaita ku" Nan ma dai baiyi magana ba sai zare zaren ido dayake, Ana cikin haka Mami ta karaso wajan hankali tashe, ganin halinda d'an nata yake ciki yasa ta sulale ta zauna ta fashe da kuka. Dattijon nan kuwa ganin sunk'i magana yasa yayi gyaran murya ya soma karatu cikin k'ira'a mai dad'i, Nan ya soma ihu yana fizge fizge tareda Birgima a k'asa. Sun d'au lokaci a haka sannan yayi wani irin ihu yace "Ku tsaya zamuyi magana" Dattijon yace "Meyasa ka shiga jikinshi" Jamal yace cikin wani irin k'aton murya "Turomu akai dan mu kulle alak'ar sa, mu muka daki motarsa shekara uku da suka wuce mukayi anfani da wannan daman" Dattijon yace "Ka fita daga jikinshi sannan kaji tsoron mahalucin ka" Wani dariya Jamal d'ina yayi yace "Harkai ka isa kasa mu fita" Dattijon baice komai ba ya cigaba da karatun alkur'anin, Ihu ya cigaba ganin ba sarki sai Allah yace "Ka tsaya tsoho, ka daina k'onamu zamu fita" Dattijon yace "Maza ku fita sannan ku fita ta hanci" Atishawa Jamal d'in yayi sau uku sannan ya sulale baci mai nauyi ya d'aukeshi. Hamdala Abba ketayi ya k'araso ya tsugunna ya d'ago kan d'an nasa yana murmushin farinciki, "Allah na gode maka, Allah abin godiya" Dattijon yace "Alhamdulillah, sun fita sai a kiyaye" Ya kalli Abba yace "Zan turo akawo magani da zai cigaba da anfani dashi insha Allahu komai zai warware" Mami ta d'ago dasauri tana kallan Malamin "Yanzu Mallan lapia lau zai tashi ba wata matsala" Kai Mallamin ya gyad'a mata, ta fashe da kuka takai goshi k'asa taima Allah godiya. Godiya kam Mallamin nan yasha wajan Abba, kud'i masu yawa Abba ya basa yak'i karba yace yayi sadaka neh, nan suka k'ara masa godiya Abba yasa driver ya kaishi gida. Da taimakon Saurayin nan Abba ya d'au Jamal d'in suka d'aurasa kan Wheel chairn, sai a sannan idanunsu ya sauka kan Ummy dake kwace achan gefen Garden d'in kanta na fitarda jini. Abba hankali tashe ya nufeta shida Mami yana cewa "Ramadan garin yaya haka ta faru" Bai iya cewa komai ba ya d'auketa chak yana cewa "Tana bleeding akai, ka kira doctor Abba" Cikin gida yayi da ita, Mami ta gunguro Jamal ta shiga ciki tashi Abba kuma ya soma neman layin doctorn. Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:30 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* ``` Ina kuke JAMALUDEEN FANS group Wannan shafin naku neh. Kuna bani farinciki sosai, ina godiya buhu buhu ``` Page 18 Cikin gida yayi da ita, Mami ta gunguro Jamal ta shiga ciki dashi, Abba kuma ya soma neman layin doctor. Mami tama Ramadan nuni da d'akin Ummyn, ya shiga ya shimfid'eta kan gado yana kallanta, sosai kanta ke fitar da jini, yasa wani zaninta dake kan gadon ya tare jinin gabanshi na fad'uwa. Bayan kamar minti goma sha biyar likitan ya k'araso gidan, bashi guri yace Ramadan yayi shi kuma ya shiga dubata. Mami da Abba suna bakin k'ofan chirko chirko cikeda zullumi, a haka Mabrookah ta shigo gidan ta samesu, tambayan abinda ya faru tayi Mami ta mata bayani cikeda damuwa. Likitan ya d'au lokaci kamin ya fito ya samu Abba nan bakin k'ofan, Mami ce tai saurin k'arasowa itada Ramadhan, likitan ya kalli Abba yace "Da sauki Alhamdulillah, saidai ta bugu sosai a kanta sannan ta samu karaya a hannunta na hagu" Mami ta saki sallati tana duban likitan "To yanzu wani hali take ciki doctor?" Cewar Ramadan Likitan ya cigaba da cewa "Na mata allurar bacci saboda yanayin da take ciki, but idan so samu ne da an kaita asibiti idan ta farka saboda ai mata xray ko akwai wata matsala" Ramadan ya mik'a masa hannu sukayi musabaha yana cewa "Mungode sosai, and idan ta tashi zamu kawota insha Allah" Mabrookah na daga gefe tana b'ata fuska cikeda takaici. Abba ya k'arasa falon k'asa ya zauna su Mami suka bishi suma suka zazzauna yace "Munga ikon Allah koh? Mukaita magani ashe cuta bata asibiti baneh" Ya kalli Ramadan yana cewa "Babu abinda zance maka Ramadan sai Allah ya saka da alkhairi, lallai kai aboki ne na gari" Murmushi Ramadan d'in yayi yana d'an girgiza kai "Abba bani yakamata ka gode mawa ba sai yarinyan nan, ita yafi chanchanta da'a godema wah dan ni k'arashe nayi kawai" Mami ta gyad'a kai tana cewa "Allah saki Ummy, yarinyan nan mutum ce, ban tab'a samun mai aiki wacce takeda gaskiya da rik'on amana kamarta bah, Lallai ta chanchanci yabo" Abba ya sauke nannauyan ajiyan zuciya yace "Gaskiya neh, shiyasa nad'au wani alkawari a raina. Insha Allahu zan kyautatama yarinyan nan, zan inganta rayuwarta insha Allahu" Mabrookah ta saki d'an guntun tsaki tana cewa "Duk ba wannan yakamata ayi magana akai bah, Ya Jamal yakamata a san abinyi dan ba'asan menene ma'anar baccin dayake bah" Mami ta zafga mata harara, Ramadan ya mik'e ya haura d'akin Jamal d'in. Bacci yake sosai Lafiyar Allah, wani murmushi Ramadan din yayi yana kallansa dan tunda ya fara rashin lafiyan nan bai tab'a ganin yayi bacci irin nayau bah. Zama yayi d'akin yana gadinsa har dare, Jamal d'in bai farka ba sai k'arfe takwas da rabi, tashinshi yayi daidai da tashin Ummy. Kansa ya rik'e idanunsa a rufe, a hankali ya bud'e ido, ganin d'akin yayi yana juya masa yayi saurin rufe idon yana cigaba da rik'e kansa. Ramadan ya mik'e ya k'araso bakin gadon yana kallansa da farinciki "Jamal! Jamal kana jina" Jin muryan Aminin nasa yasa ya sake bud'e ido ya zubasu kan abokin nasa "Say something Jamal, yi magana ko zanj dad'i" Mami da Abba a tare suka shigo d'akin Mabrookah na binsu a baya Abba ya karaso bakin gadon yana cewa "Ramadan yaya?" Saurin bud'e ido Jamal d'in yayi ya zubasu kan Abbansa yana kallansa da d'an murmushi, daga Abban har Mami da Mabrookah mutuwar tsaye sukayi suna kallansa, kok'arin mik'ewa zaune yake yana yatsine fuska, Ramadan yayi saurin rik'eshi yana cewa "You have to rest, i knw jikinki ba dad'i yanzu" Girgiza kai yayi cikin sanyaiyar murya yace "No I'm alryt" Da taimakon Ramadan d'in ya zauna, Mabrookah tako a hankali ta zauna gefen gadon ta fashe da kuka tareda rik'e hannunsa. D'ago kanshi yayi yana kallan Iyayen nasa da tuhuma ganin suna hawayen neh ke fita daga idanunsu "Mami, Abba Lapia? Meya faru kuke kuka?" Ya juya yana kallan Ramadan da tuhuma "Ramadan meya faru? I tot ina kaduna wajanka, mekuma nadawo yi yau?" Mami ta k'arasa gabanshi tana shafa suman kanshi "Its a long story, have some rest zamuyi magana anjima" Maganan Mami ba k'aramin d'aure masa kai yayi bah. Zama yayi hankalinsa duk yana kan labarin da Mami tace zata bashi, hira Ramadan keta masa yana bashi amsa jefi jefi. A bangaren Ummy kuwa, koda ta bud'e ido wani irin mugun sarawa taji kanta ya mata, ta saki k'ara kad'an tasa hannunta na dama dafe kan, ga kuma hannunta na hagu dake mata zafi sosai. Laurat ce ta shigo d'akin dan tun dazu hankalinta ke kanta dan sanin halinda take ciki, bakin gadon ta k'arasa tana cewa "Sannu Ummy kin tashi" Batace mata komai ba sai runtsa ido datake tayi hawaye na gangara a idanunta. Fita daga d'akin Laurat d'in tayi dan kiran Mama talatu, Mami ta had'u da ita ta fito daga d'akin tace "Yaya ta farka ne" Ta bata amsa da eh, dakin ta shiga gainta tayi duk ta fita haiyacinta, a rud'e ta haura sama zuwa d'akin Jamal, tana shiga tace a rud'e "Ramadan taso mukai Ummy asibiti ta farka kuma... Ganin ya mik'e yasa ta fasa k'arasa maganan ta fita yana binta baya, Jamal ya bisu da ido kanshi a d'aure. Wai meke faruwa a gidan nan neh? Wacece kuma Ummy? Dakyar ya sauke k'afafunsa k'asa, jin jikinshi yake duk ya masa tsami, mik'ewa yayi tsaye ya koma ya zauna tareda sakan k'ara kad'an. Tsayuwa ne ya gagaresa, dakyar ya sake mik'ewa yana ririntse ido tareda yatsine fuska saboda yanda k'afar ke masa zafi. Bango ya soma dafawa yana takawa a hankali har ya sauko k'asa, daidai nan Ramadan ya fito daga d'akin Ummyn dauke da ita a hannunsa idanunta a lumshe tana numfashi d'ai d'ai. Ya bisu da ido da mamaki har suka bar falon sukayi waje, dakyar ya k'arasa saukowa ko kamin ya fito har Ramadan ya sakata a mota sun fice daga gidan shida Mami. _Zakuyi hak'uri da yanayin typing d'ina nayau, ina busy neh kuma banda chargi_ Ummy Abduol✍🏻 [3/11, 8:30 PM] Alion Bagari: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 19 Da kyar ya k'arasa saukowa ko kamin ya fito har Ramadan ya sakata a mota sun fice daga gidan shida Mami. Ya koma ciki yana takawa a Hankali har ya isa falon k'asa ya zauna yana cigaba da mamaki. Abba ya sauko da d'an saurinsa yana k'okarin fita, sam bai lura da Jamal d'in ba yaji ya kira sunansa a hankali, ya juya tareda k'arasawa inda Jamal d'in ke zaune ya zauna yana kallansa da murmushi Cikin sanyayar muryarsa yace "Abba wai meke faruwa ne a gidan nan? Jiya na fita natafi kaduna yau kuma na ganni a gida, gashi kuma naga an d'au wata za'a kaita asibiti" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya d'ago yana kallanshi yace "Labari ne mai tsawo Jamal, bt tunda ka matsa zan fad'ama anma ka bari naje na samu su Ramadhan a asibiti na dawo" Jamal yayi saurin girgiza fuska ba walwala "Pls Dad ka sanar dani" Jim Abban Yayi sannan yayi gyaran murya ya soma bashi labarin duk abinda ya faru shekara uku da suka wuce. Da mamaki yake kallan Abban baki bud'e, Abba ya cigaba da cewa "Tunda muka dawo daka gida ba wani cigaba sai lokacinda Yarinyan nan tazo" Hawaye suka cika idanun Jamal ya mik'e dakyar yana cewa "Abba muje asibitin tare i want to see her" Abba ya girgiza masa kai tareda rik'esa yana cewa "No ka bari idan ka k'ara jin k'wari sai kaje" Ya girgiza kai yana cewa "No Abba muje yanzu pls naga halinda take ciki tunda am responsible for her Sickness" Abba ya zaunar dashi ya haura sama ya d'auko masa wheel chair ya d'aurasa yana cewa "Muje" Wani switch Jamal d'in ya danna a jikin Wheel chairn ya fara tafiya da kansa, a bakin mota ya tsaya ya mik'e dakyar ya shiga cikin motan Abba ya saka Wheel chairn a booth. Ma'aikatan gidan sai bin Jamal suke da kallo da mamaki, yawancin su hamdala suke ganinshi ya samu lafiya. Shika suka nufa dan Mami ta fad'a masa chan suka kaita, kallo d'aya zakama Jamal ka gane hankalinshi a tashe yake musamman jin shine silan rashin lafiyan nata. Suna isa sukama Ramadan waya ya musu Jagora zuwa d'akinda take, a bakin k'ofa suka had'u da Mami take sanar dasu ana dubata neh. Nan suka tsaya sukayi chirko chirko, Ihunta sukaita ji daga d'akin tana kiran sunan Mama da Baba, Jamal ya runtse ido da k'arfi ya bud'e yana kallan Ramadhan "Why is she crying" Mami tace "Ana gyara mata hannu ne dan ta samu karaya" Gabansa ya fad'i, yayi shiru cikeda tunani, sun d'au lokaci a wajan kafin likitocin da nurses su fito. D'aya daga cikin likitocin yace "Bazaku samu daman shiga ba saboda tana buk'atar hutu" Ya mik'ama Abba wani takarda yana cewa "Za'a mata Xray a kanta dan a duba ko fashewan da kan nata yayi ya mata illah" Abba da Ramadan suka masa godiya ya wuce tareda sauran likitocin. Ramadan ya amsa takadan a hannun Abba yaje Ya biya ya dawo ya mik'ama Mami receipt d'in. Sun d'au lokaci a haka ba wanda yace komai kowa da abinda yake sak'awa a ransa, daga bisani wata Nurse ta basu daman shiga. Jamal ne ya soma shiga d'akin, kwace take kan gadon marasa lafiya, kanta nan nad'e da bandage sai d'an kumbura da gefen kan yayi, haka idanunta a kukumbure, hannunta na hagu shima a nad'e. Tausayinta ne ya kamashi ya k'arasa har bakin gadon yana cigaba da kallan fuskanta gabanshi na fad'uwa, Abba yace "Yakamata a sanar ma Iyayenta dan susan halin da take ciki" Mami ta kalli Ummyn cikeda tausayawa tace "Hakane, saidai ina tsoron sanar dasu dan mahaifinta yanada ciwon zuciya kuma ga makanta" Jamal ya juya dasauri yana kallan Mamin. Ramadan yayi folding hannuwansa yace "Dole a sanar dasu Mami coz wannan fa ba k'aramin ciwo bane da za'ace za'a boye musu" Abba yace "Gaskiya ne Ramadhan" Shidai Jamal baice komai bah haka kuma bai daina kallan fuskanta bah, Dare ne ya tsala sosai Abba ya d'au Jamal da Ramadan suka tafi gida ita kuma Mami ta kwana da ita. A chan gida kuwa Bacci ne ya gagari Laurat ta zauna shiru a kitchen ko b'angarensu bata tafi ba, tunanin Ummy ne ya sata gaba so kawai take tasan halinda k'awar nata take ciki. Tana nan zaune a kitchen wuraren karfe biyu na dare su Abba suka dawo, bata san sanda ta fito dagudu ba ta fito falon, ganin Abba dasu Ramadhan yasa taja burki tareda duk'ar dakai "Yaya dai me kikeyi har yanzu baki tafi b'angaren ku bah" Cewar Ramadhan yana kallanta Ta duk'ar dakai hawaye cike da idanunta tace "Ina jiran dawowan Ummy neh" Dama kan Jamal na k'asa jin ta ambaci Ummy yasa ya d'ago yace "An kwantar da ita a asibiti, go and have some rest gobe inasan ganinki da safe" A sanyaye ta juya ta tafi tana kuka a hankali, kan wheel chair d'in ya sauka ya kama kafad'ar Ramadan yana cewa "Na gaji da wheel chair d'in nan" A tare suka haura sama harda Abba ya musu saida safe ya shiga d'akinsa, suma suka shiga na Jamal. Ruwan wanka Ramadan ya had'a masa mai d'an zafi ya shiga ya gasa jikinsa ya fito. Bai cema Ramadhan d'in komai ba ya hau kan gadon ya juya fuska dan duk hankalinsa nakan Ummy. Washe gari da wuri suka shirya, hau Alhamdulillah k'afar tasa tad'anyi kwari, a falon sama suka had'u da Abba, A tare sukayi breakfast sannan suka sauko k'asa. Laurat suka samu zaune kan carpet tana jiransu, Jamal ya k'arasa ya zauna ta gaidashi sannan ta gaida Abba da Ramadhan, Jamal ya kalleta yace "Wacece Ummy a wajanki" Dan shiru tayi sannan tace "A nan gidan muka had'u da ita, k'awata ce kawai" Baice komai ba ya gyad'a kai ya mik'e tareda sa hannayenshi a aljihu yace "Ok zamuje dake sai ki zauna da ita a asibiti" Ta gyad'a kai tace "Tho" Abba yace "haka yakamata kam" Mabrookah ce ta sauko daga sama tana yatsine fuska tana kallan Jamal "Ya Jamal ina Mami" Wata uwar harara ya wurga mata fuskarsa ba walwala "Ke a rayuwarki bazaki tab'a Iya gaisuwa ba koh?" Ta turo baki tareda kauda kai sannan tace "Ina kwana Abba, Ina kwana Ya Ramadhan" Tad'an dubi Jamal d'in tace "Ina kwana Ya Jamal" Baice mata komai ba saima tsaki dayayi yabar falon. A motar Abba sukaje asibitin, Ramadhan na driving, Abba na gefensa sai Jamal dake baya shida Laurat. Suna isa suka samu an gungurota a gado za'a maida ita d'akin da take, Mami na biye dasu. D'akin suka shiga, nan Mami ke sanar dasu cewa anje anyi Xray d'in neh. Laurat ta tsugunna ta gaida Mami sannan ta aje basket d'in kayan breakfast. Abba yace "Ya jikin nata?" "Dasauk'i saidai har yanzu bata farka bah" Ramadhan da Jamal suka gaisheta ta amsa tareda tambayan jikin Jamal d'in, yace dasauki. Abba ne yayi dropping Mami a gida shi kuma ya wuce aiki, nan Jamal da Ramadhan suka wuni a d'akin, Laurat nachan gefe zaune duk a takure ranta ba dad'i ganin halinda k'awar nata ke ciki. Sun dawo la'asar lokacin Laurat na toilet Ummy ta farka, a hankali ta bud'e ido tana bin d'akin da kallo, Jamal ne yayi saurin mik'ewa ya tako zuwa inda take yana kallanta. Had'a ido sukayi ba shiri ta mik'e zaune dasauri lokacit guda ta saki razananen Ihu ta rik'e Hannunta wanda ta karye tana cigaba da kallany Jamal d'in a tsorace. Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 20 Had'a ido sukayi ba shiri ta mik'e zaune dasauri lokaci guda ta saki razananen Ihu ta rik'e Hannunta wanda ta karye tana cigaba da kallany Jamal d'in a tsorace. Kuka ta fashe dashi ta runtse idonta gam tana k'okarin sauka daga kan gadon, Laurat ta fito daga toilet ta k'araso ta rik'e "Lapia Ummy menene" A k'irjin Laurat ta b'oye fuskanta tana nuna mata Jamal da Hannu, Ramadhan ya rik'e kafad'ar Jamal yace "I think tsoronka takeji, muje waje tukun" ya k'are maganan da rik'o hannun Jamal d'in, har sun kai bakin k'ofa Jamal ya sake juyowa ya kalleta, sai kuka take tana cigaba da b'oye fuskanta. Laurat ta d'agata dakyar tana share mata hawaye "Bud'e idonki baya nan, bud'e kiga" Dakyar ta samu ta bud'e ta zubasu akan Laurat din har lokacin kuka take "Ki daina kukan, fad'amin menene" Nuni ta cigaba da mata da hannu tana cewa "Laurat Jamal, yana min fatalwa" Laurat batasan sanda ta kyalkyalle da dariya bah, Ummy ta d'aga kai tana kallanta da mamaki "Kai! Anma dai Ummy kin cika shirme" Ta sake kyalkyallewa da dariya ta zauna bakin gadon tana cewa "Bah fatalwa baneh, Jamal ne da kika sani. Allah ya bashi lapia" Ummy ta zaro ido da mamaki "Dan Allah dagaske" "Ehmana, ashe mutanen b'oye ne a jikinsa ba'a sani ..." Ramadhan ne ya shigo d'akin da sallama, duk'ar dakai tayi kunya ya kamata "Lapia dai Ummy" Laurat tayi dariya tace "Ta d'auka fatalwa yake mata bata san ya warke bah" Ramadhan yayi murmushi yace "Oh Allah sarki, ya jikin naki" A kunyace tace "Dasauk'i Alhamdulillah" Bai kuma cewa komai ba ya fita, chan sai gashi da Jamal d'in sun shigo. Kallo d'aya ya mata ya saki lallausan murmushi, itako sai sunar dakai take cikeda kunya. Kan kujera ya zauna yace "Sannu, ya jikin?" Murya chan ciki kamar mai koyon magana tace "Da...D..Dasauk'i" Murmushi ya sake yi ya juya ya kalli Ramadhan yace "Ram yaushe na zama fatalwa ban sani bah" Dariya Ramadhan yayi shida Laurat, shi kuma gogan murmushi kawai yayi yana cigaba da kallan Ummyn. Ramadhan yace "Ka mata uzuri bata sami baneh, kuma kaga tasamu buguwa akai kila ta samu matsala neh" Maganan Ramadhan ya sosa mata zuciya, wato kenan ya d'auketa mahaukaciya ma kenan, idanunta cikeda kwalla ta d'ago tana kallan Jamal "Ni ba mahaukaciya bace da hankalina" Ta fashe da kuka tace "Kuma ai bansan ka warke baneh shiyasa ka bani tsoro. Ta sake d'agowa tana kallan Jamal wanda shima ita ya zubama ido "Ni ban kiraka da wannan sunanba sai ku ne zaku kirani da mahaukaciya" "No bah haka baneh baki fahimceni baneh, I'm sorry ba haka nake nufi ba believe me" Cewar Ramadhan cikin tattausan murya. "Nagode Laurat, har dake aka had'u ana zagina bakomai" Ta kwanta kan gadon ta janyo blanket ta rufe jikinta har kai tana cigaba da kuka. Tab'o Jamal Ramadhan yayi "Say something mana" Guntun tsaki yaja ya mik'e ya kama hannun Ramadhan d'in suka fito daga d'akin. Jamal ya saki Hannunshi yana cewa "Kaifa Matsalata dakai kenan bakin ka baida control" "Eh naji bakina ba control, kai kuma idonka da shegen gulma, tun dazu kaketa kallan musu 'ya" Dukan wasa Jamal ya kaimai yana dariya "Kai kaidai Ram ta shiga uku" Laurat ta fito daga d'akin Ramadhan ya tab'o Jamal suka juyo suna kallanta "Dama inaso ne naje gida na d'auko mata kayan da zata chanza" Ramadhan yace "Taci abinci neh" ta girgiza kai alamar A'a "Tak'i taci tayi fushi sai kuka take" Shiru ne ya biyo baya, Ramadhan yace "Yanzu muje ki d'auko kayan mu dawo" Gaba tayi Ramadhan ya tab'o Jamal yana y'ar dariya "Na barka da ita ka lallasheta kasan kai na mata neh" Bai jira mai Jamal d'in zaice ba yabar wajan dasauri yana masa dariya. Jim yayi yana tunanin yanda zai shiga d'akin dan shifa bai iya magana da mace ba dan shi a rayuwarsa ko budurwa bashida. Handle d'in ya murd'a ya shiga da sallama ciki ciki, zaune ya saketa ta jingina da pillow idanunta a lumshe, kan kujeran gabanta ya zauna yayi shiru yana kallanta a hankali yace "Ummy" Batace komai bah kuma bata bud'e idon ba saima turo baki datayi ta juya kai gefe, murmushi yayi mai sauti yana shafa sajen fuskansa "Kiyi hak'uri da abinda Ram ya fad'a dazu, ba ya fad'a baneh dan ranki ya b'aci" Shiru ne ya biyo baya na y'an mintina ya cigaba da cewa "And kiyi hak'uri akan abinda ya faru jiya, i wasnt my self har naji miki wannan raunin. And ina godiya da lokacinki da k'arfinki da kikayi wasting wajan lura dani" A hankali ta bud'e ido tace "Bana buk'atar godiyanka" Ya saki murmushi mai sauti yace "Ok! Ok!! But kiyi hak'uri pls akan abinda ya faru" "Na hak'ura" ta bashi amsa a takaice. Shiru ya sakeyi har lokacin idanunshi na kanta, kujeransa ya matso dashi kusada ita sosai yace "Dan Allah na miki wata tambaya mana" "Ina jinka" Ya shafa suman kanshi yace "Anma dai lokacin da banda lapia baki tab'a min wanka ba koh" Kuji min Jamal d'in nan fah Fans...Haha Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:20 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 21 "Anma dai lokacin da banda Lapia baki tab'a min wanka ba koh" Maganansa sosai ya bata d'ariya, dakyar tayi k'okarin dakewa tana kallansa k'asa k'asa "Wanka na nawa kuma" Ta tab'e baki tace "K'arshen magana ma jiya ni na maka wanka" Mutuwar zaune yayi yana kallanta fuska a had'e, anma dai an gama cutar shi wallahi. Dogon tsaki yaja ya mik'e yana hararanta rai b'ace yana nuna kanshi, har ya bud'e baki zaiyi magana Mami ta turo k'ofa ta shigo, ya juyo dasauri yana kallanta har lokacin fuskanshi a had'e "Mami yanzu abinda akamin an kyauta knan?" Da mamaki Mami ta kalleshi ta juya ga Ummy tana kallanta "Me kuma aka maka?" "A rasa mai min wanka sanda banda lapia sai wannan?" Ya nuna Ummy fuskan nan nasa a had'e Mami da Ummy suka kyalkyale da dariya a tare "Ai Ummy tayi d'awainiya dakai sosai, wankan ka, wankin ka, kai hatta toilet idan kayi ita..." "Haba Mami! Habaaaaa" A fusace yabar d'akin yayi waje, Mami ta sake kyalkyalewa da dariya, "Allah ya shiryeka Jamal" Itama Ummyn dariya tayi, Mami ta mata sannu tana cewa "Nace ma dr ya sallameki ki koma gida sai a rink'a zuwa ana dubaki achan" Godiya tama Mamin, su Ramadhan suka shigo shida Laurat "Mami meh akaima Jamal ne naganshi yanata kumbure kumbure a waje" cewar Ramadhan. Mami ce ta fad'amai abinda ya faru, yayi dariya yana kallan Ummy "Oh kin rama knan" Harara ta wurga mai ta kauda kai gefe. Likitan da kansa ya kawo musu takadar sallama bayan ya k'ara dubata tareda rubuta mata magunguna. Laurat da Ramadhan suka kwaso kayan da aka kakkawo, Mami ta rik'o Ummy suka fito. A haraban asibitin suka had'u da Jamal sai cika yake yana batsewa, kallo d'aya Ummy tamai tayi dariya, harara ya zafga mata tareda kauda kai. Suna isa ya d'au wayan Ramadhan ya kira Layin Abba, saida ya tambayesa ya fad'a masa gaskiya sannan hankalinshi ya kwanta. Kiran ya kashe tareda sauke ajiyar zuciya "Lallai ma Yarinyan nan" Yayi k'wafa yace "Kinci bashi" K'in saukowa yayi k'asa shi a dole yayi fushi, yayi zamanshi a d'aki abinshi yanata bacci. Washe gari da safe Ramadhan ya koma Kaduna, hakan baima Jamal dad'i bah dan shi ke d'ebe masa kewa sbda har yanzu Abba yak'i yarda ya fita zuwa wani guri shi kad'ai. Ummy na zaune a d'akinta, duk hankalinta nakan Iyayenta gashi har weekend yazo ya wuce bataje ba kuma tasan suna chan hankalinsu tashe dan idan har zata jima takan fad'a musu. Laurat dake gefenta ta d'ibo abinci a plate, shinkafa da miyan naman rago sai salad, d'iba tayi takaima Ummyn baki dan bata iya cin abincin da kanta, ta kauda kai gefe idanunta cikeda kwalla "Ummy ci mana, tun safe fa Bakici abincin kirki bah" "Bazan iya ci bah, bansan halinda Iyayena ke ciki bah yanzu nasan hankalinsu nachan a tashe" "Haba ki kwantar da hankalinki, ai Mami tace yau ko gobe za'a kwance d'aurin kanki. Kinga hannu ma bazai jima ha knan" Gigiza kai kawai Ummyn tayi, dakyar Laurat ta lallab'ata tad'anci kad'an sannan ta koma bakin aikinta ta barta ta huta. Harta kwanta aka turo k'ofan d'akin, bata d'agoba dan a tunaninta Laurat ce. Kujera akaja aka zauna har lokacin ba'ayi magana bah. Jin shirun yayi yawa yasa ta d'ago suka had'a ido da Jamal, ya harareta yana cewa "Ke baki Iya gaisuwa bah" Fuska ta yatsine ta kauda kai gefe tace "Ina wuni" "Dah ban wuni ba zaki ganni" "Oho kai za'a tambaya" Buge mata baki yayi tasa hannuta na dama ta rik'e bakin tareda fashewa da kuka "Allah ya..." Rank'washin ta yayi a kai ta saki kuka tana sosa inda ya rank'washetan. Fuskansa ya matso dashi kusada nata yana kallan k'wayar idonta "I'm a free guy, kowa nawa neh, but banasan rashin kunya" Yayi murmushi yasa hannu ya shafa gefen fuskanta "Na lura bakida kunya, kuma gashi ni bansan rashin kunya" Ya saki murmushi mai sauti "From now on ke friend d'ita ce and my Maid, uh must obey my rules" Kallashi kawai Ummyn keyi dan ba abinda ta fahimta a maganarsa Kwalla ta matse ta kauda kai gefe murya k'asa k'asa tace "Kai kasan abinda kace, Mugu kawai" Yayi murmushi tareda mik'ewa "Mugaye dai, wayasan me kikaita min sanda banda lapia" Batace mai komai ba ta zunguro baki ta koma ta kwanta. Mabrookah na shigowa falon taji kamar maganan Jamal a d'akin, ji tayi anyi shiru ta girgiza kai, har ta gota d'akin zata wuce ta k'ara jin magananshi. Ba shiri ta tura k'ofar d'akin ta shiga, tsaye ta sameshi ya bada baya yana rik'e k'ugu sai kallan Ummy yake "Ya Jamal" Ya juyo suka had'a ido, ta k'araso kusada shi da mamaki "Meh kakeyi a nan?" "Meyasa bakiyi sallama ba da zaki shigo" Ta b'ata rai "So nawa zance kiyi sallama Mabrookah" Ta tsuke fuska ta juya fuu tabar d'akin tana danasanin shiganta gashi ya dizgata a gaban yarinyan daya tsana. Kallan Ummy yayi yaga ta rufe ido yayi murmushi, kwana biyu kenan da samun lafiyarsa har ya lura da rashin jituwar dake tsakanin Ummy da Mabrookah. D'akin ya bari ya haura sama dan cima Mabrookahn mutunci dan ya tsani yana ma mutum magana ya wuce ***** Sati biyu kenan da samun lafiyar Jamal, Alhamdulillah jikin Ummy yayi sauk'i sosai har an kwance d'aurin saidai ance ta daina yawan anfani dashi sosai kuma kada ta d'au abu mai nauyi. A sati biyun nan har saida zaman gidan ya gundureta saboda Jamal, kullum yana d'akin yayita sata surutu kuma bazai bar d'akin ba sai yaga tayi kuka sannan hankalinshi zai kwanta. Yau Sati kamar yanda ta saba shiri take da zuwa gida sai zumud'i take dan kimanin sati uku kenan bata je gida bah duk hankalinta nakan Iyayen nata. Kayanta set hud'u ta zuba a leda dan wannan karan kwana uku Mami ta bata. Cikeda farinciki da zumud'i take komai, Turo k'ofar d'akin da k'arfi, ko ba'a fad'a mata bah tasan Mabrookah ce dan ita kad'ai ke shigo mata d'akin haka. D'agowa tayi dasauri suka had'a ido "Zuwa nayi naja kunnenki, ki daina shiga harkan Ya Jamal, ki fita daga harkansa, kada na sake ganin ki kusa dashi. Kina jina" "Insha Allahu bazan k'ara bah" Dogon tsaki taja "Ku dama Talakawa haka kuke, shegen kwad'ayi a tara a kaima iyaye" Ummy ta d'ago ta kalleta dasauri, hawaye ya gangaro mata ta share. Wani tsakin ta sake ja tabar d'akin tareda bugo k'ofan. Rushewa da kuka Ummyn tayi, bah abinda ta tsana a rayuwanta kamar a zagan mata iyaye. Saida tayi mai isarta sannan ta tashi ta d'au ledan kayanta tasa hijab ta fito, Mami ta samu a falo ta mata sallama tasa driver ya kaita tayi godiya ta fito. A haraban gidan ta had'u da Jamal ya dawo sallan azahar, kallo d'aya ta masa ta kauda kai tana k'okarin shiga motan. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:29 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 22 A haraban gidan ta had'u da Jamal ya dawo sallan azahar, kallo d'aya ta masa ta kauda kai tana k'okarin shiga motan. Binta da ido yayi harta shiga cikin motan, tsayuwa yayi jim sannan ya k'araso ya amsa keyn motan a hannun drivern ya shiga, hankalinta sam bai kai wajansa ba dan duk a tunaninta drivern neh. Window taketa kallo kwalla na fita daga idonta, abubuwan da Mabrookah ke mata ya soma damunta, musamman yanzu data kirata da talaka kuma kwad'ayaiya. Hawayen idanunta ta share a hankali tace "Indai Jamal ne daga yau bazan k'ara masa magana bah" Taja dogon tsaki "Kema sai ki ja mai kunne ya daina shiga harkana" Burki taji anja da k'arfi ta juyo, ganin Jamal yasa ta bud'e baki zatayi ihu dan duk a tunainta Garba driver ne ke tuk'in. Ganin tana kokarin yi masa ihu yasa galla mata harara, k'ofan motan ta murd'a ta fita dasauri. "Ummy ina zaki" Batace mai komai ba tacigaba da tafiya, hakan yasa dole ya fito ya soma binta, tafiya ta cigaba dayi sauri sauri "Wai meye haka Ummy, tsaya mana" Dakyar ya sha gabanta, ta kauda kai gefe "Dan Allah Ya Jamal ka daina bina, ka koma gida" Had'e rai yayi dole ta natsu tana kallanshi, ledan kayanta ya amsa a hankali yana kallan fuskanta "Muje mota and banasan musu" Ba yanda zatayi hakanan ta soma binshi a baya har motan, gidan baya ya bud'e mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga. Kallanta yayi nad'an mintina fuskarsa d'auke da damuwa "Ummy fad'amin damuwarki, me aka miki" Batace komai saima kauda kai datayi gefe tana kallan Window "Fad'amin mana" Hawaye suka gangaro mata ta soma sheshek'a, lumshe ido yayi yana jin kukanta har ransa "Na lura kuka na miki dad'i" Hannu tasa ta share hawayenta ta d'ago tana kallan fuskansa "Wani alfarma nake nema dan Allah" "Ok ina jinki" "Inaso dan Allah daga yau ka daina zuwa inda nake, idan mun gaisa shi knan" Da mamaki yace "Saboda meh?" "Babu komai, dan Allah" Saida ya sauke ajiyar zuciya yace "Wa yasaki ki daina min magana" Ta d'an dago ta kalleshi da mamaki, gira ya d'aga mata "Tell me, ina jinki" Kuka takesan yi ta b'ata fuska hawaye cike da idonta "Dan Allah kai kaini gida, ko ka baro na hau adaidaita na tafi" "Zakije gida but sai kinmin alkawarin zako gad'amin" "Bazan iya fad'ama ba kayi hak'uri" Baice komai bah ya bud'e kofan ya fito "Ki dawo gaba" yace a takaice fuskarsa ba walwala Ba musu ta dawo gaba ta zauna, jan motan ya soma, tafiya kawai yake batareda yasan inda zai nufa bah, ganin suna shirin barin hanyan unguwansu yasa ta kauda kai gefe ta soma mai kwatance, murmushi yayi ya soma bin inda take kwatanta mai har suka kawo k'ofar gidan. Batace mai komai ba tad'au ledan kayanta zata fita, lock ya danna ta soma k'okarin bud'e kofan ta kasa "Ummy!" Ya kira sunnanta a hankali, bata juyo ba tace "Dan Allah ka bud'emin k'ofa na fita" "Banida aboki daya wuce Ramadhan, sai kuma keh" Ta juyo da mamaki tana kallansa, ya gyad'a mata kai "Kinada babban matsayi a gareni, dan ban d'aukeki a matsayin ma'aikaciya ba, kinada matsayi kamar yanda Mabrookah ke dashi" Shiru tayi bata daina kallonsa ba "Nasan zakice ina shiga rayuwarki" Yayi murmushi tareda danna lock d'in, tayi saurin murd'a kofan ta fita, ko waiwayowa batayi ba tayi shigewanta gida. Gabanta ne keta fad'uwa, saida ta tsaya bakin zaure ta daidaita kanta sannan ta shiga gidan da sallama, Mama ce ta fito dasauri jin muryan 'yar nata, rungume juna sukayi Ummy ta fashe da kuka "Ummy ina kika shiga tsawan sati uku bamu ganki bah" Ta sake rushewa da kuka, dakyar Mama ta samu ta lallasheta suka shiga wajan Baba, saida ta huta sannan take sanar dasu abinda ya faru. Sunyi Alhini sosai tareda farincikin samun Lapian Jamal d'in. Kwananta Biyu a gida ranar da daddare tana zaune a tsohon d'akinta tana cin abinci yaro ya shigo gidan da sallama, Mama dake tsakar gida ta amsa yace ana sallama da Ummy inji Jamaludeen. Gaban Ummy ne ya fad'i, Mama tace kace tana zuwa, Ummyn ta soma kwallama kira ta fito tana turo baki "Wani Jamaludeen neh" A shagwab'e tace "Wanda nake aiki gidansu" Daga d'aki Baba yace "Maza kije k'ila an aiko shi ne wajanki" Hijab ta shiga d'aki tasa ta fita tana turo baki, tsaye ta samesa tsaye jikin mota yana sanye da bak'in trouser da farar Tshirt mai mara kauri dan ana Iya Hango singlet d'in jikinshi saboda hasken bulb d'in dake wajan. Kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki ta k'araso wajan ta tsaya chan nesa dashi "Barka da fitowa" yace yana kallanta "Ina wuni" tace kamar ansata dole Murmushi yad'anyi ya amsa mata yana cigaba da kallanta "Nasan zakiyi mamakin zuwana, and nasan zakice na dameki" "Ya Jamal ka fahimceni, inaso na tsiratar da kaina da kuma iyayena daga wulak'anci" Ta d'ago ta kallesa tace "Kayi hak'uri ka daina bibiyata in har kanasan na cigaba da zama a gidanku" Ta nuna kanta tace "Ni nan daka ganni banda k'awa ko aboki, nikad'ai nake rayuwata tun bayan na rasa.... Yayi saurin d'aga mata hannu ranshi b'ace "Ki fad'amin waye ya hanaki huld'a dani? Tel me mana" "Kayi hak'uri bazan iya fad'ama bah" Baice mata komai ba ya zagaya ya shiga motarsa yabar k'ofar gidan a guje. Ummy ta dad'e tsaye a bakin kofan tana bin hanyan da kallo sannan ta shiga gida jiki a sanyaye. Kwanakin da aka bata na cika ta dawo bakin aikinta. Aikin da takeyi da ta cigaba dayi, wani abu daya bata mamaki shine tunda ta dawo gidan magana bai tab'a had'ata da Jamal ba, ko sau d'aya idan ta gaida shi baya amsawa. Hakan baima Ummy dad'i kwata kwata dan cikin wata d'ayan nan ta saba da hiranshi da damunta dayake yawan yi. har saida Laurat ta tambayeta tace bakomai. **** Kimanin wata biyu kenan, yau tana gyara d'akin Mabrookah da safe aka turo k'ofar d'akin, d'an juyowa tayi suka had'a ido da Jamal fuskan nan babu walwala. Aikinda takeyi ta cigaba ya zauna kan bedside dake kusada ita "Ummy abinda kikeyi ya dace kenan" Batace komai ba haka bata juyo ta kalleshi ba "We cant continue like dis, baxan iya jurewa bah. Munyi saba sosai" gyaran d'akin ta cigaba har ta gama yanata binta da kallo "Ummy magana nake kinyi banza dani" Ta juyo ta kalleshi tace "To me kakeso nacema Ya Jamal? Yanda kayi shine daidai" Ya mik'e tsaye ya soma takowa zuwa inda take, gabanta ya tsaya har numfashinta na sauka a goshinta "Nayi miki abinda kikeso saidai na gwada naga bazan iya bah" Kokarin barin wajan take yayi saurin rik'o hannunta, dai dai nan Mabrookah ta shigo d'akin dasauri dan tayi mantuwan littafinta akab gado. Mutuwar tsaye tayi yana kallansu d'aya bayan d'aya shiko gogan ko a jikinsa, kokarin kwacewa Ummy ketayi ta kasa dakyar ta samu ta kwace ta bar d'akin dasauri. Basarwa yayi yace "Sis lapia kika dawo" Dakyar ta iya cewa "Mantuwan littafi nayi" Ya gyad'a kai tareda saka hannunshi cikin pockets ya fita daga d'akin. Da kuka Mabrookah ta d'au waya ta soma neman layin Mami, tana d'auka ta soma fad'a mata tana kuka sosai. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:30 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Ina kuke Masoya Littafin JAMALUDEEN wannan shafi sadaukarwa ce gareku a ko ina kuke. Ina matuk'ar godiya da yanda kuke nuna min k'auna. Allah ya barmu tare Ameen* Page 23 Da kuka Mabrookah ta d'au waya ta soma neman layin Mami, tana d'auka ta soma fad'a mata tana kuka. Fasa zuwa makarantan tayi ta zauna a d'aki tanata kuka cikeda takaici. Da daddare bayan Abba ya dawo Mami ta sanar da Abba abinda Mabrookah ta fad'a mata, murmushi yayi yace "To menene Abin tada hankali Maimuna, karki manta Jamal kowa nasa neh, baida girman kai" "Anma Alhaji yakamata ace an masa magana, ka tuna fah akwai alkawari akansa tunda ya samu lapia sai ayi magana" Jim Abba yayi yana tunani, Mabrookah ta shigo falon fuska ba walwala ta zauna sannan ta gaida shi. Ya amsa yana kallanta da murmushi. Waya ya d'auka ya soma neman layin Jamal, yana d'auka ya sanar dashi yana san ganinshi. Cikin mintina kad'an ya iso falon da sallama ya samu guri ya zauna ya gaida su. Abba ne ya soma cewa "Tambayanka nakeso nayi kuma inaso ka fad'amin gaskiya" Jamal ya d'an d'ago sannan ya maida kai "Menene tsakanin ka da yarinyan nan Ummy" Dam! Gabanshi ya fad'i, ya d'ago suka had'a ido da Mami yayi saurin maida kai ganin yanda take kallanshi "Ba abinda ke tsakanina da ita, kawai mutunci neh" "To mutuncin shima na hana daga yau" cewar Mami tana kallansa rai b'ace "Haba Maimuna, wai meyasa kike haka neh? Menene to dan sunyi mutunci" Mami ta k'ara tsuke fuska tace "Nidai banaso Alhaji, kasan shi talaka bai iya samun guri bah." In banda hararan Mabrookah ba abinda Jamal yakeyi dan yasan ita kad'aice zata kai wannan gulman. "Wannan duk ba magana baneh Maimuna, menene to dan sunyi mutunci a tsakaninsu?" Abba ya girgiza kai ya maida dubansa ga Jamal daketa Hararan Mabrookah ranshi a b'ace "Jamal lokaci yayi daya kamata ka koma bakin aikinka, companyn nan na buk'atar jajirtace kamar kah dan haka har na gama magana monday mai zuwa zaka fara zuwa aikin" "Tho Abba insha Allahu Nagode" Mami ta hard'e hannayenta biyu tace "Tho Alhaji Maganan Alkawarin da akayi wanchan lokacin fah" Abba ya kalli Jamal da Mabrookah "Ku tashi kuje" A tare suka mik'e suka bar falon, Abba yace "Maimuna kina bani mamaki wani lokacin, bai kamata kina irin wad'an nan maganganun bah" "To Alhaji kayi hak'uri bazan sake bah" "Yauwa koke fah, sannan kaganan Alkawarin da kike ki bari sai nan gaba, komai ana binshi ne a hankali" Ta gyad'a kai suka cigaba da hira. Jamal na fita ya shak'e Mabrookah fuskan nan nashi a had'e "Ni kike kai k'ara koh?" "Dan Allah Ya Jamal kayi hak'uri ka sakeni bazan k'ara bah" Kanta ya buga da bango ta saki kuka, yayi saurin sa yatsanshi a lips d'inshi "Shhhh! Karki cika mana kunne, and idan har na k'arajin wani magana saina karya ki a gidan nan Stupid kawai" Ya saketa yabar wajan rai b'ace. Kuka ta fashe dashi mara sauti ta shige d'akinta ta fad'a kan gado. Washe gari Abba da Mabrookah na kan dinning suna breakfast, Mami ta sauko cikeda murna ta zauna kan dinning d'in tana cewa "Yanzu Fatima ta kirani tace suna nan zuwa yau d'in nan itada Zainab" Wani ihu Mabrookah ta saki cikeda murna "Dan Allah Mami dagaske?" Mami ta gyad'a kai, da gudu Mabrookah ta haura sama tana cewa "Ai yau ba kuma zuwa school sai next week" In banda murmushi ba abinda Abba yake, ya mik'e bayan ya gama yace "Na tafi su kuma Allah kawosu Lapia" Mami ta amsa da amin ya fita. Tana cikin breakfast Ummy ta fito daga d'akinta. Wajan da Mami ke zaune ta k'arasa ta tsugunna har k'asa ta gaidata, ba yabo ba falasa ta amsa tana dubanta "Yau munada bak'i suna nan isowa anjima, d'akunan dake sama zaki gyara guda biyu" Ummy ta amsa mata kanta k'asa "Kada ki sake ki shiga hurumin da banaki bah" Ta sake dubanta tace "Ba ruwanki da Jamal ko Mabrookah, ki tsaya a matsayinki. Banasan shiga sharo ba shannu" Banbara kwayi Ummy taji maganan, ta amsa da to a takaice sannan ta mik'e ta haura sama. Jikinta a sanyaye tayi ayukanta duka ta koma kicin ta had'u da Laurat, sai a sannan ta tuna yau Laurat d'in zataje ganin gida. Nan hankalinta ya sake tashi idanunta suka ciko da kwalla, da taimakon Ummyn Laurat ta had'a kayanta, Ummy ta rik'o mata kayanta suka fito haraban gida. Daidai lokacin da Jamal ya fito daga Falon, Laurat ya hango Ummy na biye da ita tana hawaye. D'aya daga cikin ma'aikatan yasa ya kira mai su, tsayuwa Ummyn tayi tak'i motsi da kyar Laurat taja hannunta suka k'arasa inda yake tsaye. Fuskan Ummyn yaketa kallo yana d'an murmushi ganin yanda ta had'e rai, Laurat ta d'an rusunna ta gaidashi ya amsa yana tambayanta inda zata, ba tareda b'ata lokaci ba ta amsa masa. Kud'i ya ciro a aljihunsa ya mik'a mata tayi godiya sosai, driver yasa ya kaita tasha. Haka Ummy tanaji tana gani Laurat ta shiga mota suka bar gidan tanata d'ago mata hannu. Wani kuka ne yazo mata ta fashe da kuka tayi hanyar Garden a guje. Kan Grass Carpet d'in dake malalle akan Garden d'in ta kwanta tana cigaba da kuka. A haka ya k'araso ya sameta, baice mata komai ba ya zauna kusada ita tareda tank'washe k'afarsa yana kallanta zuciyarsa na masa zafi. Sam bata lura dashi ba saida tayi mai isarta sannan ta mik'e zaune tana goge hawayen idanunta, ganinshi tayi zaune kusada ita har saida ta tsorata tad'an matsa kad'an tana kallansa da idanunta da suka kumbure saboda kuka. "Ummy meyasa kikesan kuka? Kiyi hak'uri ai zata dawo" Batace komai ba ta mik'e tana kakkab'e jikinta, harta juya zata bar wajan ya mik'e dasauri yace "Meyasa kike guduna Jaleelah" Da mamaki ta juyo suka had'a ido dan batayi tunanin yasan sunanta, damuwa ne sosai a fuskansa ya soma takowa zuwa inda take tsaye. "Baki bani amsa ba, meyasa kike guduna yanzu" Ya juya fuska idanunta cikeda kwalla tace "Kayi hak'uri ka daina bina, bansan na rasa aikina dan dashi muka dogara, idan na rasa aikina bansan yanda zanyi bah" Ta matse hawayen daya cika mata ido ta juyo tana kallansa ido cikin ido, abinda bata tab'a yi bah "Gaisuwa kawai ta wadatar a tsakanin mu, ka daina zuwa inda nake dan Allah" Ta had'e hannayenta biyu tana hawaye "I know Mami ce ko Mabrookah suka miki magana koh? ki kyalle maganan su Pls, Allah ne ya had'a mu kuma babu mai rabamu" Ya sauke ajiyar zuciya ya kama hannunta ya zaunar da ita shima ya zauna suna facing juna "Duk abinda Mabrookah ke miki ina sane, harda wanda ta miki baya, ki cigaba da hak'uri kinji" Tayi saurin janye hannunta daga nasa "Yakamata kaso abinda Mahaifiyarka da K'anwarka sukeso, ka rabu dani dan Allah, dan su suna tunanin ko soyaiya mukeyi kuma b..." Yayi saurin katseta yana girgiza kai rai b'ace "Mabrookah ba k'anwata bace..." Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:34 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 24 "Mabrookah ba k'anwata bace" Ummy ta d'ago ido da mamaki tana kallansa. Ya gyad'a mata kai "Bah k'anwata bace, Sistern Mami ce ta haifeta" Ummy ta jinjina kai cikeda Mamaki, yace "Ni kad'ai Mamina ta haifeni, banida yaya banida k'ani, shiyasa ta d'auko Mabrookah ta zauna tareda ita" Fuska yatsine tareda lumshe ido yana shafa sumar kanshi "Banasan zamanta a gidanan, i hate her" Itadai Ummy ido kawai ta zuba masa tana kallansa, ya d'ago suka had'a ido ta sakar mata murmushi, mik'ewa tayi shima ya mik'e dasauri "Ina zaki?" Baya ta juya masa ta soma tafiya tana cewa "Zanje ne na cigaba da aikina, ni zan chanji Laurat har sanda zata dawo" Bata jira mai zaice ba tabar wajan dasauri ta wuce kicin. Wanka Mabrookah ta sake d'auka ta sanyo wani Bak'in shadda dogon riga wanda yaji aiki Golden, saukowa tayi k'asa ta shiga kicin. Harda ita akayita shirye shiryen tarban bak'in, ranar Ma'aikatan kicin sunsha Masifa bama kamar Ummy har saida tayi kwalla. Cikin lokaci k'alilan aka gama komai aka zuwa a sababbin cooler aka kai dinning d'in sama. Ummy na ganin an gama ta koma d'akinta ta zauna, wuraren k'arfe biyu Mami ta dawo aiki itama ta soma nata shirye shiryen. Jamal na side d'in Abba yana bacci baisan wainar da ake toyawa ba a gidan. K'arfe Hud'u da rabi na yanma aka wangale gate d'in gidan, bak'ar mercedes ce ta shigo tayi parking a k'ofar side d'in Mami, Ummy dake jikin window sai bin motan take da kallo dan ba irin motan gidan baneh. Mabrookah ta fito a guje tana dariya cikeda farinciki. Wata 'yar dattijuwa ce ta fito daga gaban motan, kamansu d'aya da Mabrookahn, ta k'araso ta rungumeta tana dariya. "Oyoyo Mummy! Sannu da zuwa" 'Yan mata ne kyawawa suma suka fito daga bacl seat, kallo d'aya zaka musu ka gane 'yan biyu neh, suna sanye da Pink atampha d'inkin dogon riga, Mabrookah ta saki matar ta k'arasa ta rungumesu "Oyoyo Twins d'in Aunty" Suma suka rungumeta a tare suna mai farinciki, sakinsu tayi ta k'arasa ta rungume d'ayar matar da suke tare itama tana kama da Mami sosai. K'walawa Ummy kira Mabrookah ta fara bayan ta fito da Trolleys d'in dake booth d'in motan. Dasauri ta fito ta gaidasu, ta tura mata kayan tana hararanta "D'auka shi shiga dasu sama" Akwatuna hud'u neh, dakyar ta iya d'aukan Biyu ta haura dasu sama sannan ta dawo ta d'au biyu ta kai tanata haki dan kayan sunada nauyi sosai. Nan falon k'asa suka baje anata hira, sosai Mami da Mabrookah suka yi farincikin zuwansu. Mami ta sake kwallama Ummy kira ta fito dasauri ta k'araso falon, Abincin da aka kai Saman tasa ta sauko musu dashi dan sunce nan zasu zauna. Nan Ummyn ta soma zarya daga falon sama zuwa k'asa tana kwaso abincin. Tana gamawa d'aya daga cikin bak'in tace "Ina kika samo wannan yarinyan, ke haka ake bama mutane abinci bazaki zuba musu bah" Kanta k'asa ta tsugunna ta soma zuba musu d'aya bayan d'aya. Jamal ne ya shigo falon cikin takunsa na k'asaita, turus yayi yana binsu da kallo cikeda mamaki, dan baisan da zuwansu bah, twins d'in suka mik'e cikeda murna suka doso inda yake d'aya na cewa "Ya Jamal Sannu ya jiki" Murmushi ya musu ya kama hannuwansu suka k'arasa falon, mai kama da Mabrookah tace "Dole ka kallemu mana, tun d'azu muke gidan nan ka kasa zuwa ka gaishemu kuma bayan dan kai mukazo" Yayi murmushi ya zauna yana kallansu "Haba Aunty Faty bah haka baneh bansan da zuwanku ba wanda ya gayamin" Wacce aka kira da Aunty Faty tace "Ba wani nan kawai dai kace mulkin kane daka saba ya motsa" Murmushi kawai yayi ya maida dubansa ga d'ayar dake kusada Aunty Fatyn "Sannu Aunty Zainab kunzo lafiya" Tayi murmushi tace "Lapia lau ya jiki? Allah ya k'ara sauk'i" Ya amsa da lapia lau tareda maida dubansa ga Twins "Najma da Najwa kunyi girma fah, yaushe yaushe na ganku" Daidai lokacin Ummy ta gama serving d'insu tabar falon, binta da ido Jamal yayi har ta shige kwanan d'akinta, Aunty Faty sai kallanshi take da mamaki "Kaji Jamal da wani zance, shekaran su ashirin kenan, kaida kake zaune kan kujeran k'arfe har shekara uku ya za'ayi dama kasan wad'an nan" Twins dasu Mabrookah sukasa Dariya, nan suka cigaba da hiransu Aunty Faty sai tsokanan shi take yana bata amsa, itako Aunty Zainab ba ruwanta saidai idan anyi abin dariya tayi. Suna gamawa Mami ta sake kiran Ummy dan tazo ta kwashe kayan da'aka ci abinci. Mami tace "Mabrookah Mama tazo an wani mak'ale mata, ai zata tafi ne muna nan dake" Ummy ta d'ago dan taga wacece Maman Mabrookah, Aunty Fatyn nan tagani Mabrookan ta mak'ale mawa, ta sauke ido dasauri ganin sun had'a ido da ita ta soma kwashe kayan. D'aya daga cikin twins d'in ta mik'e ta soma tattara kayan tana cewa "Barin tayaki kwashewa, Umm mu mun saba dayin aikin gida" Tana tattarawa d'ayar itama ta mik'e ta soma tayata, Mami tace "Trainning d'in Zainab kenan, kedai har yanzu bakison mai aiki" Murmushi Aunty Zainab tayi ta gyara zama tace "Aa nikam ba ruwana da mai aiki, tunda chan ban santa balle yanzu gani da yara kaman su Najma ai sai suyi" Aunty Faty ta tab'e baki, Ummy ta shigo taga su twins sun d'auko kayan tayi maza ta rik'e tana cewa "Aa ku bari na kai ku huta" K'in yarda sukayi hakanan suka cigaba da kai kayan tare sannan Ummy ta koma d'akinta. Da daddare Ummy bata samu hutu bah, tana d'an zama Mami zata k'walla mata kira tayi wani aikin. Bata samu ta runtsa ba sai k'arfe sha biyu da rabi, sosai Jamal ya tausaya mata dan yana ganin duk abinda ke faruwa kasancewar a side d'in ya wuni. Da safe wuraren k'arfe bakwai da rabi Ummy ta fito kicin ta had'u da d'aya daga cikin twins d'in ta sauko, Murmushi tama Ummyn tace "Sannu da aiki, kina k'okari maine sunanki" "Jaleelah, anma Ummy ake kirana" Ta gyad'a kai tace "Ni kuma sunana Najma, and my twin sister Najwa. Kuma nice Hasana" Ummy ta gyad'a kai da murmushi "Allah sarki, sannu" "Keh Najma me kikeyi a nan wajan" A tare suka d'aga kai sukaga Aunty Faty ce tana k'okarin saukowa daga benen gidan Najma ta zumb'uro baki tana d'an bubbuga k'afa "Dake fa nake magana Najma kinyi banza dani" "Babu komai, kawai muna magana neh. I want her to be my friend" Aunty Faty ta zaro ido da mamaki ta k'araso inda suke tsaye "What! Kinsan meh kike fad'a kuwa?" Ta juya tana kallan Ummyn fuska ta yatsine "Ke kuma zaki b'acemin da gani ko saina b'alla ki" Ai a guje tabar wajan gabanta na fad'uwa. Fad'a sosai taima Najman dan tunda suka had'a ido da Ummyn taji yarinyan bata mata bah, ga kuma labarinta dataji wajan Mabrookah a daran jiya sai taji ta k'ara tsanan yarinyan. Ranar Ummy ta wahala sosai wajan Aunty Faty, duk bayan mintina sai tasa an kira mata ita tasata aiki, duk da ta gaji sosai anma bata nuna musu bah haka taketa daurewa tana aikin. Tana kwance a d'akinta wuraren la'asar aka turo k'ofar d'akin nata aka shigo, d'an d'agowa tayi sannan ta mik'e ta zauna ganin Najma da Najwa. "Ana kirana neh?" Ta tambayesu tana kallansu "Aa ba kiranki ake ba munzo tayaki hira neh" Ta d'anyi kasak'e tana kallansu da mamaki, d'aya daga cikinsu tace "Mene sunana?" "Najma" tace da murmushi Dariya suka fashe dashi, d'aya tace "Ni ce fah Najma" Ta nuna wacce tai ma Ummyn tambayan tace "Ita kuma Najwa" Ta kafesu da ido tana k'okarin banbance tsakaninsu, kan gadonta suka zauna suka soma mata hira. Sakin jiki tayi sunata hira, a nan take sannin cewa Aunty Faty yayar Mami ce, Aunty Zainab kuma itace mamansu kuma k'anwar Mamin ce. Sun dad'e suna hira kamin daga baya Mabrookah ta shigo ta korasu bayan ta zage Ummyn tas. ****** Ranar monday da safe Jamal ya shirya cikin suit Blue da farin shirt a ciki, k'afarsa sanye da Black cover shoes kanfanin versace, falon ya shigo bai tarar da kowa bah, d'akin Ummy yayi knocking a hankali yanayi yana kallan step, jin shiru yasa ya murd'a a hankali ya shiga. Kan sallaya ya sameta tana lazimi, ya k'arasa ya zauna kan gado yana kallanta, ganin ya zauna yasa tayi saurin shafa addu'an datake ta juyo tana kallansa "Ya Jamal me kakeyi a nan?" Ya mik'e ya k'araso inda take ya tsugunna yana kallanta da murmushi "Bah gaisuwa sai tambaya" "Ina kwana" tace dasauri a d'an tsorace tana kallan k'ofar d'akin "Karki damu basu tashi bah, i just came to see uh kuma kimin addu'a yau zan fara zuwa aiki" Ta sauke ajiyan zuciya ta d'an kalleshi tace "Allah ya tsare ya kareka daga sharrin mak'iya" Sosai yaji dad'in addu'arta ya amsa da amin tareda shafa gefen fuskanta yana murmushi "Matsoraciya kawai" Ya mik'e ya fita daga d'akin, kicibus yayi da Mami a falon, ya d'an zaro ido "Jamal zo nan" Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:38 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 25 n 26 Ya mik'e ya fita daga d'akin, kicibus yayi da Mami a falo, ya d'an zaro ido "Jamal zo nan" Sunne kai yayi ya k'araso ya zauna kan kujera yace "Ina kwana" "Yanzu dai Jamal ka daina jin magana ta" "Mai kuma nayi Mami tah" "Mai nacema akan maganan yarinyar nan" Ya sunnar dakai yana jujuya wayan dake hannunsa "Da kanajin magana ta anma yanzu ka daina, ka kiyayeni in ba haka ba ta kusa daina aiki a gidan nan" Ba shiri ya d'ago da mamaki yana kallanta "Kiyi hak'uri Mami bazan sake bah" "Menene tsakaninka da yarinyan nan neh wai" Ya sake duk'ar dakai baice komai bah, ba shiri ba mik'e tsaye dasauri "Noo! Karka cemin santa kake, dan bazan yarda bah, ya zakayi da Mabrookah daketa jiranka" Ya turbune fuska danshi harga Allah baisan Mabrookah, Aunty Faty ta sauko jin tashin muryan Mami "Lapia Maimuna kiketa d'aga murya haka" Nuna Jamal tayi tana cewa "Zo ki tayani jin abin kunyan da Jamal keso ya d'auko min" "Na meh?" Aunty Faty ta tambaya tana kallan Mami "Yaran nan ace duk jiran da Mabrookah ta masa yanzu ya samu lapia yake so ya watsa mana k'asa a ido" "Mami kiyi hak'uri ni fa ba san Ummy nake ba" Sai a sannan Aunty Faty ta gane inda Mami ta dosa "Jamaludeen me zakayi da mai aiki talaka, wacce ko boko batayi bah" Sosai maganan Aunty Faty ya b'atamai rai, Abba ne ya shigo falon da sallama, wayancewa sukayi Aunty Faty tace "Allah ya tsare ya bada sa'a Jamal" Wuf ya mik'e dan dama hanya yake nema, Abba ya gaishar ya musu sallama ya bar gidan zuciyarsa na masa suya. Nan Mami da Aunty Faty suka soma shawaran yanda zasu b'ulloma alamarin. Cikin satin Ummy tasha wuya wajan Aunty Faty kamar ba gobe, itadai Aunty Zainab Ummin su Twins batace wa komai sai ido data zuba musu, itama kanta batajin dad'in abinda akema Ummyn. Sosai Ummy ta shak'u dasu Twins, so dayawa suna tare a kicin suna aiki tare, ko idan tana gyaran d'aki su tayana, wani lokacin kuma suna d'akinta suna hira. Ba yanda Aunty Faty batayi ba akan ta hanasu anma sunk'i ji. Ranar Juma'a da safe akayi ma ma'aikatan albashi, bakin Ummy har kunne musamman dataga wannan karan shima dubu d'arin aka biyata. Dak'yar Mami ta yarda ta barta ta tafi gida weekend gida. Hankalin su twins sosai ya tashi ganin Ummyn zata tafi dan saboda ita gidan ke musu dad'i. Har bakin gate suka rakota suka koma cikin gida a sanyaye. Napep ta tara ta shiga, suna karyo kwanan layinsu ta hango gidan su da masu aikin gini kamar gyara yake a gidan. Da mamaki ta shiga tana bin ma'aikatan da kallo, dakunansu taga an had'e an fitar da two bedroom mai kyau, Mama ta fito daga Falor ganin Ummy yasa ta rungumota cikeda murna. "Mama wannan aikin fah" Hannunta Mama ta kama suka shiga cikin Palourn, nan Ummy ta saki baki tana kallan yanda gidan nasu ya koma, had'adden set d'in kujeru ta gani, ga tiles da aka malale falon dashi, sosai falon yayi kyau, tabi Plasman dake jikin bango har lokacin idanunta a warwaje "Mama wannan kayan daga ina" Baba ya fito daga d'aki yana dogara sandarsa yana murmushi "Muryan wa nakeji kamar na Ummyna" Dasauri ta k'arasa ta rungumeshi tana dariya "Baba ni ce" Ya shafa kanta yana cewa "Ba abinda zamuce ma yaron nan sai Allah ya mai albarka" "Baba Ya Bilal ya dawo neh? Dama nasan bai mutu ba zai dawo" Mama tace "Duk wannan abubuwan da kika gani, duk aikin Jamaludeen neh, kuma yace yayi dan Allah ne ba wani abu bah" Yatsine fuska Ummy tayi tace "To an gode" Ta shiga bedroom, nan ma taga an gyara shi tsaf harda sabon funitures, ta tab'e baki ta aje jakanta sannan ta fito. Albashinta ta mik'ama Baba kamar yanda ta saba, Albarka ya saka mata yace "Wannan karan ki adana kud'inki dan munada komai dangane ga kayan abinci" Ummy tayi murmushi tace "Tho Baba, anma yakamata mu sake komawa asibiti ka sake ganin likita" "Hakaneh" cewar Mama "Aa Ummy, nikam Alhamdulillah naji sauk'i, yanzu babban burina bai wuce naga kin daina bauta bah, kin koma makaranta ko kinyi aure" Mama tace "Komai Lokaci ne Mallan, Fatan mu ka samu lapia, komai yazo daga baya" Murmushin takaici kawai Baban yayi baice komai bah. Washe gari lahadi, masu aikin ginin basu zo ba suna hutu, yau D'anwake Ummyn tayi musu dan Baba nasan d'anwake sosai, bayan ta zuba musu nasu ta d'au nata ta fito tsakar gida kan tabarma tana ci. Ta saka loma kenan ta jiyo sallaman su Twins, dakyar ta iya had'iyewa suko mai zasuyi in ba dariya bah. Mik'ewa tayi dasauri ta rungumesu tana dariya "Sannunku da zuwa, ya akayi kukasan gidan mu" "Ya Jamal ne ya kawo mu yana waje" cewar Najma Ciki ta shiga dasu suka gaisa da Baba da Mama, sannan suka dawo waje dan ciki akwai zafi, d'an waken ta zubo musu suka soma ci suna santi, Ummy ko me zatayi inba dariya bah. Mama ta lek'o tareda rik'e hab'a "Oh ikon Allah, ashe ku nan zama kukayi kuka bar Yayan naku a waje" Sai a sannan suka tuna ashe da Jamal suke, Mama tace Ummy ta tashi tace mai ya shigo, turo baki tayi taja hijab a igiya ta fita, cikin mota ta sameshi yana waya, ta k'arasa ta juya fuska gefe tace "Ance ka shigo" Bata jira mai zaice ba ta koma ciki, shi dariya ma abin ya bashi Ummy sai kace mai Juju, wani lokaci ka gansu Lafiya suna shiri, watan kuma a yini ba'a masa magana bah. Da sallama ya shiga ciki, Najma da Najwa na zaune tsakar gidan suna cin abinci "Dama nan kukafi auki, Ci, Ci!" Najma ta b'ata fuska, Najwa ko Dariya tayi ta sake kai loma tana kallansa. Dariya yad'anyi ya girgiza kai ya shiga falon da sallama. Har k'asa ya tsugunna ya gaidasu, Ummy ta had'o mai d'anwaken. Ba ko kunya ya soma ci suna hira da Baba, Ummy sai binsu da kallon mamaki take ganin yanda suke hira kamar wad'anda sukayi shekara da sabo. Waje ta koma suka cigaba da hiransu da Twins, bayan sun gama Jamal yama su Mama sallama yace ma su twins suzo su wuce, Mama ta lek'o tace "Ummy ina ce kema yau zaki koma, kizo ki d'au kayanki mana ki bisu" Baki ta zungure tace "Mama ni sai anjima" Jamal yayi murmushi ya fita, har bakin mota ta rakosu tanata d'agama su Twins hannu, har yayi gaba ya dawo yayi parking ya fito "Wai Twins kad'ai kika gani neh" Ta galla masa harara "Ni su kad'ai na gani" "Koh" Ta kauda kai gefe "Zaki sani neh ai" "Zamu sani zakace" Yayi murmushi yana girgiza kai ya shiga yaja motan yabar anguwan. Sai bayan la'asar Ummy ta shirya tsaf dan komawa bakin aikinta, d'aki ta samu Baba dan masa sallama, ya rik'o hannunta yana cewa "Jamaludeen, Bahar da mahaifiyarsa duka ba abin yarwa baneh. Ki rik'esu Hannu bibiyu kinji" "Insha Allahu Baba" "Ki zama mai hak'uri a duk inda kike, ki kare mutuncin ki, ki zama mai biyaiyya da girmama nagaba dake, ki rik'e addininki, In kikayi haka insha Allahu bazaki tab'a tab'ewa bah. Kin faranta min Ummy, tunda na haifeki baki tab'a min abinda kika b'atamin bah, Allah ya miki albarka Ummy" "Amin Baba, Kai kuma Allah ya baka lafiya" "Ameen!" Ta fito sukayi sallama da Mama ta fita ta tari adaidaita ta hau ta koma gidan aikinta. Tana shiga dasu Twins tayi arba sunata murna, jakan hannunta suka amsa suka shigan mata dashi d'aki. Duk abinda sukeyi Aunty Faty na kallo, ranta sosai ya b'aci ta haura sama zuwa d'akinsu Tana mita. A ranar Aunty Zainab mahaifiyarsu Twins ta koma, su kuma zasu d'an yi hutu, Aunty Faty ko cewa tayi ba yanzu bah. Babban abinda ya d'aurema Ummy kai bai wuce rashin ganin Laurat bah, dan tun sanda zata tafi ta fad'a mata sati d'aya kawai zatayi gashi yau kusan kwana Shad'aya kenan. Da daddaren ranar Mami da Abba suna falon side dinshi, Mami tace "Alhaji magana nazo muyi" Yace "Ina jinki" D'an jim tayi tace "Alhaji har yanzu bakace komaiy kan alkawarin auren Jamal da Mabrookah bah" "Tho mai kikeso nace Maimuna" "Yakamata ace yanzu anyi auren nan, tunda ya samu Lafiya ga kuma aiki ya fara" Abba yad'anyi murmushi "Maimunatu kenan, abinda nakeso ki gane a nan shine, yanzu ba d'ah baneh, yanzu an daina wannan had'in. Gwara a bar yara su zab'i abinda sukeso" "Haba Alhaji yanzu ya za'ayi da alkawarin da aka d'aukan ma Yaya Faty, kuma itama Mabrookahn tana sanshi sosai, shima nasan yana santa" "Sanda kukayi alkawarin ai bana wajan, ba sai daga baya kike gayamin da alkawari bah" Fusata Mami ta fara ta juya fuska gefe "Mafita a nan shine, zan tarasu na tambayesu idan har duka suka amsa suna san juna shiknan" "Anma Alhaj...." "Aa Maimuna, wannan shine magana" Mik'ewa tayi tabar falon ta nufi side d'insu, Aunty Faty ta samu a falo ta sanar da ita yanda sukayi da Alhajin "Maimuna kina bani mamaki, yanzu ke bazak'i iya tank'wara d'anki bah" Shiru Mami tayi ta haura zuwa d'akin Jamal, bata ganshi ba ta sauko ta fita haraban gidan, nan ma ba kowa ta dawo, harta gota d'akin Ummy sai ta juyo muryan mutane a d'akin, a hankali ta dawo ta murd'a kofan. Jamal ta gani da Twins da Ummy sunata hira. Tsawa ta dakama Twins suka fito daga d'akin dasauri, ta hararai Jamal tace "Ka fito inasan ganinka" Tana tafe yana binta a baya har d'akinta, gefen gado ta zauna shi kuma yaja stool ya zauna "Jamal wannan shine zai zama magana ta k'arshe da zan maka akan yarinyan nan Ummy, wallahi ka fita idona na rufe" Ya duk'ar dakai k'asa "Wai mai kakeso ka zama ne Jamal, baso d'aya ba baso biyu ba na fad'ama banasan ganinka da yarinyan nan" "Mami kiyi hak'uri" "Duk ba wannan ba, ya maganan da mukayi dakai na Mabrookah" Dam! Gabansa ya fad'i "Mami pls kiyi hak'uri, wallahi i have no feelings for her" Da Mamaki tace "Me kake nufi knan" Ya sake duk'ar dakai "Yanzu Jamal bazaka iya cikama yayata burinta ba, yarta d'aya Mabrookah, batada burin daya wuce taga tayi aure." Ta turo baki yana jujuya kai "Alhaji zai kiraku ya tambayeku idan kunasan juna, inaso ka amsa kana santa. Hakan ne kad'ai xai sani farinciki" Ya gyad'a kai yace "To shikenan Mami" Tayi murmushi tace "Allah ya maka albarka" Ya mik'e yabar d'akin yana gungunai. Bacci ne ya gagari idon Jamal, shi gaskiya harga Allah bazai Iya auren Mabrookah ba dan baya santa. Wuraren sha biyu ya mik'e kamar wanda aka tsikara ya sauko k'asa, d'akin Ummy yayi knocking a hankali ya shiga, dan yau so yake ayita ta k'are. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:41 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 27 D'akin Ummy yayi knocking a hankali ya shiga, dan yau so yake ayita ta k'are. Tsaye ya sameta kan sallaya tana sallah, gefen gadon ya zauna yana kallan yanda take ganawa da ubangijinta cikin natsuwa. Ji yayi ta k'ara birgeshi, ya sauke ajiyar zuciya yana cigaba da kallanta. Tana idarwa ko addu'a bata tsaya yi ba ta juyo dasauri tana kallansa da mamaki "Lapia Ya Jamal meya kawoka d'akina da daran nan" "Nazo ne muyi wani magana" "Magana? Ka bari mana sai gobe yanzu dare yayi" Baice komai ba ya mik'e ya k'araso inda take zaune shima ya zauna yana cigaba da kallanta "Bazan iya hak'uri har sai gobe bah, maganar nada mahimmanci sosai" Ta gyara zama tana facing d'inshi "Ina jinka, saidai kayi sauri saboda dare kuma ina sallah neh" Ya sauke dogon ajiyar zuciya yana kallanta "Nayi tunanin na b'oye abinda ke raina game dake, wani abu yana neman yazo min wanda bana so" Kurrri Ummyn tayi tana kallanshi, dan sam bata san inda maganar tasa ta dosa bah. "Ina sanki Ummy, wallahi i so much love uh" Ba shiri ta mik'e a zabure tana kallansa da mamaki "Ki yarda ki aureni banasan Mabrookah, na miki alkawarin zan miki duk abinda kikeso pls" Hawaye suka soma gangaro mata a fuska tana girgiza kao tana kallanshi "So kuma? Haba Ya Jamal, dan Allah ka daina wannan wasan" Ya mik'e tsaye "Tun ranar dana fara ganinki naji ina sanki, ina sanki badan komai naki ba, komae.... "Ya isa! Ya isa!! Banaso inji" Hannayenta biyu tasa ta toshe kunnuwanta tana kuka sosai "Abinda yasa kenan kaje ka gyara mana gida, ka siyan mana kayan alatu dan ka siya iyayena...." "No! Ummy ki fahimceni, wallahi ko kad'an badan wani abu nayi haka...." Tayi saurin katseshi cikin muryan kuka "Ka makara, inada wanda nakeso, koda banida shi bazan tab'a sanka bah Ya Jamal. Tun bayan warkewanka nake cikin k'unci da hantara a gidan nan. Talauci bah hauka baneh, indai haka ake k'udi kada Allah ya bani" "No pls Ummy, ki tsaya ki saurareni" Cikin d'aga murya tace "Bazan ji bah, Ya Jamal ka fitar min daga d'aki banasan ji! Ka fita" Kallo ya bita dashi cikin tashin hankali ya fita ya haura zuwa d'akinsa. Ranar daga Ummy har Jamal babu wanda ya runtsa. Washe gari yana kan dinning yana breakfast tazo ta wuce idanunta a kukumbure, hakan ya tabbatar masa da cewa tayi kuka daran jiya. Wani tausayinta neh ya k'ara shiga ranshi, harga Allah yanasan Ummy, so na tsakani da Allah. Dan shi a shirye yake dayayi komai a kanta. Kamar wanda aka tsikara ya mik'e dasauri ya nufi side d'in Abba, saidai kash yana zuwa ya samu Mami a falon, k'eya ya sosa ya juya Abba yace "Yaya dai Jamal, akwai wani abu neh?" Yayi saurin cewa "Aa ba komai" Da sauri ya fita daga falon ya shiga motarshi yabar gidan. Saida Abba ya fita dan ranar zaiyi tafiya, sannan Mami ta fito daga side d'in ta dawo nata, Mabrookah ce ta soma saukowa tana murmushi "Mami dan Allah kiban kud'in, yau nakeso muje nida k'awayena mu fitar da ankon" Sosai maganan Mabrookah yaba Mami dariya, saida tayi mai isarta sannan tace "Mabrookah kenan! Ke kin tab'a ganin inda aka fitar da anko ba'a sa rana bah" Baki ta turo gaba "Mami ai ba sai ansaka rana bah, already Abba ya bashi ni, haka an bani shi. Kuma Mommy ce tace na fitar yanzu" Kai Mami ta girgiza zata haura ta d'auko handbag d'inta ta fita aiki. Ranar sukuku Ummy ta wuni, har lokacin maganan Jamal ne a ranta, harga Allah bazata iya san Ya Jamal ba dan har yanzu bata gasgata maganan rasuwan Bilal bah, har lokacin tana nan rik'e da alkawarin data masa na bazata tab'a auren kowa ba sa shi. ***** Wuraren k'arfe tara da rabi, Ummy na d'aki tana sallan isha'i dan tayi lattin sallan saboda aikin da Aunty Faty keta sata. Muryan Aunty Faty ta jiyo tana salati tana cewa "Maimuna! Maimunatu!! Ina kike an sace min sark'a" Mami dake falon k'asa itada Mabrookah sukayi saurin mik'ewa "Sark'a kuma? Wane irin sark'a" Cewar Mami "Sark'an nan dana siya mana danaje Dubai, Million d'aya da dubu d'ari shidda shi na nema ban gani bah" "Toooh!" Cewar Mabrookah tana rik'e da hab'a Mami tace "Aa bafa zai tab'a yuwuwa bah, dan gidan nan ba'a sata. Yaya Faty kidai k'ara dubawa" "Bafa inda ban duba ba, sark'an nan d'auka akayi" "Mudai je mu sake dubawa" Duka suka haura sama zuwa d'akin Aunty Fatyn, batsa batsa sukayi da d'akin suna nema anma bah sarka. Mabrookah ta rik'e k'ugu tana bin d'akin da kallo "Gaskiya abin nan da mamaki yake, kuma nasan dai masu aiki basa haurowa nan saman" Aunty Faty tai saurin cewa "Saidai Ummy ai ita ke shigowa tana gyare gyare, dan babu wanda zai d'au sark'an nan saboda ke Maimuna da Mabrookah kunfi k'arfin wannan" "Aa Yaya Faty, bana tunanin Ummy zata d'au sark'an nan. Dan duk abin yarinyan nan bata sata" "Maimuna! Lallai baki san talaka ba har yanzu, nidai gaskiya bazan yarda. Million d'aya harda dubu d'ari shidda ba k'aramin kud'i baneh. Gaskiya ban yarda ba sai anyi chaje kuma masu aikin nan za'a duba" Mabrookah tai saurin cewa "Gaskiya ne Mommy, dan tunda nazo gidan nan ba'a tab'a sata ba sai yau" Itadai Mami batace komai bah, Aunty Faty da Mabrookah suka sauko k'asa zuwa d'akin Ummy, ganin Haka yasa Mami ta biyosu a baya. Har lokacin Ummyn na zaune kan sallaya tana lazimi, yanda aka banko k'ofan ko ba'a fad'a ba tasan Mabrookah ce "Ke! Tashi" Ba musu ta mik'e ta koma baya tana kallansu, bincike suka soma ko ina, Mami dai na tsaye tana kallansu. Katifa Mabrookah ta d'aga sai ga sark'a kan katakon gado. Aunty Faty ta saki salati tareda d'auko sark'an tana nunama Mami "Tun ba'aje ko ina ba kin gani koh?, ai k'ila ba shi kenan bah" Kan kace me hawaye ya wanke fuskan Ummy sai kallansu take tana kuka sosai. "Wallahi Mami bani na d'auka ba, bansan yanda akayi yazo nan d'akin ba" Aunty Faty ta sake d'aga katakon gadon sai ga k'aramar b'akin jaka na Abba. Wannan karan Mami ce ta saki salati "Meya kawo jakan Alhaji d'akin nan? Dollar ne a ciki kud'in mutane" Nan ta sake rushewa da kuka ta matso inda Mamin take tana duba jakar "Wallahi tallahi Mami bani na d'au...." Kyawawan Mari guda biyu masu rai da lafiya Mami ta d'auke Ummyn dashi "Allah wadaran ki Ummy, ashe haka kike? Lallai gaskiyar mutane ne da sukace talaka bai iya samun guri bah. Tho wallahi yau zaki bar gidan nan" Ba shiri ta sake fashewa da kuka "Dan Allah kiyi hak'uri Mami, wallahi..." Wani Marin Mabrookah ta d'auketa dashi "Dole kibar gidan nan, dan ba gidan ubanki baneh" Mami tace "Dama ance idan kaga halin yaro to ka duba ta iyayensa, Uwa ko Uba an saba da sata. Kinsan ko dole itama ta koya" Ran Ummy ya sake b'aci ta d'ago tace "Mama na da Babana basa sata, haka nima ban tab'a sa..." Mami ta sake wanketa da mari, duka Mabrookah ta rufeta dashi, ko kad'an Ummy batayi niyan ramawa bah. Koran kare Mami da Aunty Faty suka mata ta fito daga gidan tana kuka sosai, ga dare yayi kusan k'arfe Goma da rabi. Jamal na karyo kwanan layin ya hango Ummy tafe tana kuka, ba shiri yaja birki ya fito dasauri. Ta ganashi ta bi ta wuce yanata kwalla mata kira ko waiwayowa batayi ba sai kuka datake yi. Binta ya soma yi hankalin shi a tashe yana kiran sunanta tareda tambayan abinda ya faru, juyowa tayi a fusace fuskanta ya gani yayi ja abinka da farar fata, gefen kumatun ta duk sun kumbura da shaidar yatsu. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 8:51 PM] ‪+234 703 981 8283‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Banida bakin godiya a gareku Masoyana, kun min komae. Ina alfahari daku kamar yanda kuke alfahari dani, ina matuk'ar sanku kamar yanda kuma kuke sona.* _Wannan shafin tukwuici ce gareku_ ```Sumaiyah Isah (k'awar arzik'i) Aysha Yusuf Aisha zagi Halimatu sa'adiya Meenah shuwa Canan Kabir (My swthrt) Mairo! Maryam sani Nafisah Jibril Yahanasu Bello (Your highness) Abdulhakam Idris Sultan Abba babaye``` _Da sauran wad'anda ban fad'a bah. Duk kuna raina ina sanku sosai.._ Page 28 to 30 Juyowa tayi a fusace fuskanta ya gani yayi ja abinka da farar fata, gefen kumatun ta duk sun kumbura da shaidar yatsu. "Ka rabu dani, bana san ganinka, kun cutar dani, baxan tab'a yafewa bah" "Pls Ummy ki tsaya, fad'amin me aka miki?" Ya rik'o hannunta tana ta k'okarin k'wacewa, fuskanta ya soma dubawa hankalinshi a tashe "Waya mareki?, Tel me pls" Batace mai komai ba, ta fizge da k'arfi ta cigaba da tafiya tana kuka sosai, ba irin rok'on da bai mata ba ko sauraransa batayi ba ta cigaba da yafiya. Haka ya hak'ura ya kyalleta badan ransa yaso ba ya hau mota ya nufi gida. Tafiya tayi mai nisa dak'yar ta samu mai Napeep ya d'auketa zuwa gida. Koda ta isa gida har Mama ta rufe k'ofar gida, bugawa ta soma tana kuka a hankali, Mama ta fito tana tambayan waye, cikin muryan kuka ta amsa mata, jin Ummyn neh yasa ta bud'e kofan da mamaki tana kallan Ummyn "Ummy lafiya da wannan tsohon daren" Kuka ta sake fashewa dashi ta rungume Maman, janta tayi suka shiga cikin gida bayan ta maida k'ofan ta rufe, suna shiga falo Baba ya dogaro sandarsa ya fito "Waye ne yake buga k'ofa, Aa! Kukan wa nakeji" "Kaga Mallan Ummy ce da wannan tsohon daren, sai kuka take ga kuma shatin yatsu a fuskanta" "Mene!" Baba yace yana rarraba ido kamar mai gani Mama ta d'agota tana share mata hawaye "Wai menene kiyi mana bayani mana" Wani sabon kuka ta fashe dashi sannan ta soma basu labari tiryan tiryan, Baba ya saki sallati yace "Ina! Ni shaida ce akan 'yata, baki sata Ummy, kuma nasan tarbiyan dana baki." Sosai ran Mama ya b'aci tace "Share hawayenki, Allah zai saka miki." Shiru Baba yayi ranshi ba dad'i, musamman dayanji Mabrookah da duki Ummyn. Dakyar suka lallabata ta shiga ta kwanta, duk da ba baccin zatayi ba sai kuka datake tayi. A b'angaren Jamal kuwa, yana isa gida ko k'wakwaran parking beyi ba ya shiga cikin gidan, Mami, Mabrookah, Aunty Faty dasu Twins ya samu cirko cirko a falo, ga mamakinsa Twins ya gani suna kuka, ya k'araso falon ransa b'ace yana kallan Mabrookah da alamar tambaya "Meya faru a gidan nan naga Ummy ta fita tana kuka, kuma da shaidar Mari a fuskanta" Aunty Faty ta turbune fuska "Ko zaka rama mata neh? Ai sai ka tsaya kaji abinda ya faru koh kamin kazo ka hayaiyak'o mana" Mami ta aje masa Jakan da aka gani a gabansa bayan ta bud'e dollars d'in dake ciki, ta aje masa sark'an Aunty Faty tace "Abinda muka gani kenan a d'akinta, kai kanka kasan bazan iya zama da b'arauniya a gidana bah" Najma tai saurin cewa "Ya Jamal wallahi Ummy bazata Iya sata bah, ni nasan..." Aunty Faty ta bige mata baki "Tho me kike nufi? Mun mata sharri kenan koh, ke kinsan halin talaka kuwa? Talaka shege neh" Ran Jamal ya k'ara b'aci yace "Mami bai kamata ki d'au wannan hukuncin bah, batare da kinyi bincike bah." "Wani bincike zanyi bayan na gani da idona, mu fa muka ciro kayan nan a d'akin" "Haba Mami, Haba! Wallahi baku kyauta min bah, Meyasa zaku min haka? Yanzu da wani ido zan kalli Iyayen Yarinyan nan. Mami I Love her! Ina santa so na gaske and i want to marry her" Mari Mami ta d'aukeshi dashi, ya dafe wajan tareda zaro ido yana kallanta, sai a lokacin ya tuna abinda ma yace. Aunty Faty ko ba shiri tayi zaman 'yan bori tana kallan Jamal d'in "Jamal a gabana kake fad'an irin wad'an nan maganan? Lallai wuyanka ya isa yanka. Ni! Ni Maimunatu?" Mabrookah ta fashe da kuka itama ta zauna wajan tana tuturje k'afa "Koda yake ba laifinka bane, ni nasan asiri suka maka. Ai duk abinda kakeyi kallanka kawai nakeyi, duk abinda kake musu inajin labari" Ta nunashi da yatsa "Wallahi ka shiga taitayinka, kuma kasani kaida Ummy har abada. Indai ina raye bakada matar data wuce Mabrookah. Wuce ka bani guri" Wani mummunan kallo yabi Mabrookan dashi sannan ya haura sama, Twins suma suka bishi dukansu ransu ba dad'i. Yanda Jamal yaga rana haka yaga dare, burinshi kawai safiya tayi ya tafi gidansu Ummy yaga yanda zasu kwashe. Ana sallan Asubah ya shirya ya fita daga gidan batareda kowa ya sani bah, kaduna ya nufa direct wajan Ramadhan dan maganar bata waya bace. K'arfe bakwai na safe daidai yayi horn a k'ofar gate d'in gidansu Ramadhan, Mai gadi ne ya bud'e masa ya shiga ya samu guri yayi parking, Ramadhan d'in ya soma nema a waya, cikin muryan bacci ya d'auka Jamal yace "Dallah ka fito ina k'ofar side d'inka" Ba shiri Ramadhan d'in ya mik'e, daga shi sai boxers da singlet ya fito haraban gidan da mamaki "Anma a hanya ka kwana koh" Jamal ya harareshi "Kaifa matsala ce dakai, Aa ka manta tun wachan shekaran nake hanya" Ramadhan ya fashe da dariya yana girgiza kai, side d'in Ramadhan d'in suka Shiga, bayan sunyi breakfast Jamal ya zaiyane wa Ramadhan duk abinda ke faruwa, dan bayada abokin daya wuce shi. Saida Ramadhan ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Tho yanzu kai ya kakeso ayi?" "Bangane ba Ram, Wallahi inasan Ummy so mai tsanani, kai kasani banda wata budurwa balle kace ko yaudaranta zanyi. Ni yanzu abinda nakeso ayi shine muje dakai ko Allah zaisa ta saurareni sai na bata hak'uri" "But Jamal, a yanda na fahimta kamar yarinyan nan bata sanka, meyasa zaka shiga inda ba'a buk'atarka" "She need me Ram, yarinyan da parents d'inta suna buk'atar taimako, Hmm dan baka zauna da ita baneh, Wallahi tayi ta kowane fanni" Ramadhan ya saki dariya yana girgiza kai "Kaifa d'an iska ne Ram, ya ina maka magana kana maidani wani abin dariya" Wani dariyan ya kuma yi, yana cewa "Ai naga abin naka neh naso ya wuce guri, harda wani ta had'u ta kowani fanni" Jamal ya b'ata rai, ganin haka yasa Ramadhan mik'ewa yana cigaba da dariya ya shiga bedroom d'insa. Wanka yayi ya sauyo cikin manyan kaya yana kallan Jamal "Anma dai ba haka zaka gidan sarakan naka ba kawani ci uban zanzaro, ka tashi ka shiga bedroom d'ina akwai kaya kan gado" Saida ya harari Ramadhan d'in sannan ya mik'e ya shiga d'akin ya chanzo zuwa kaftan, sid'e d'in Iyayen Ramadhan d'in suka ya gaida su sannan suka sake d'aukan hanyan zaria. Jamal ne ke driving motan har k'ofar gidansu Ummyn. Shiru dukansu sukayi Jamal ya sauke ajiyar zuciya tareda maida dubansa ga Ramadhan "Ta ina zamu fara?" "Muje mu nemi yaro ya mana sallama da ita" Jamal ya saki malalacin murmushi yana girgiza kai. Ramadhan ya fita daga motan, wani almajiri ya samu ya aikashi ya mai kiranta sannan ya idan ya tambaye shi waye yace Jamal neh. Tana zaune a falo tana tunani Mama na gefenta tana mata fad'an k'in cin abinci datayi, Almajirin ya shigo da sallama ya tsugunna bakin k'ofan ya isar da sako, Ummy tai saurin cewa "Kaje kace bazata zo bah" "Haba Ummy, meyasa haka? Ai ba shi ya miki laifi bah. Kije kiji mai zaice" Ta zunguro baki ta mik'e tad'au hijabinta ta fito, a bakin k'ofar gidan ta toge fuskanta had'e. Kallo d'aya Jamal ya mata yaji gabanshi ya fad'i, jiki a sanyaye ya fito daga motan suka k'arasa shida Ramadhan, "Salamu alaikum" Ramadhan yace yana murmushi Bata amsa ba saima juya fuskanta datayi gefe d'aya "Haba Ummy ai laifin wani baya shafan wani. Ko ba komai yakamata ki amsa sallama nah" Ta sake kauda kai gefe sannan ta amsa "Naji duk abinda ya faru kuma banji dad'i bah. Saidai ina rok'onki karki sa abin a ranki. Kiyi hak'uri da duk abinda ya faru" Hawaye suka cika mata ido tana kallan Ramadhan "Idan kai akayi ma abinda aka min zakaji dad'i? Talauci ba hauka baneh. Tunda nake ban tab'a sata bah haka iyayena, anma aka kirani da iyayena b'arayi" Ta rushe da kuka tasa hijab d'inta ta rufe fuska tana cigaba da kuka. Shidai Jamal ba halin magana saima ransa dake suya "Nasani an miki laifi, anma kiyi hak'uri" Ta d'ago dasauri tana kallanshi "Hak'uri? Inyi hak'uri fa kace?" "Allah muna masa laifi ya yafe mana balle mu y'an adam, karki zama d'aya daga cikin masu bin kururuwan shaid'an. An miki laifi kuma ba'a kyauta miki bah, Anma kiyi hak'uri. Kada ki yanke zumuncin dake tsakanin ki da Jamal Pls" Shiru tayi batace komai ba sai hawaye datake gogewa. Jamal ya d'ago kai yace "Pls Ummy badan niba, nasan harda laifina a ciki, anma kiyi hak'uri." "Shikenan komai ya wuce" Bata jira mai zasu ce ba tayi shigewanta gida. Ramadhan ya mik'ama Jamal hannu sukayi musabaha "Shikenan na gama nawa koh" Kai Jamal d'in ya gyad'a yana murmushi. Ranar a gidan Ramadhan ya kwana washe gari yasa driver ya maida shi gida. A ranar Jamal ya d'au su twins ya kaisu gidan su Ummy, tayi murna sosai da ganinsu dan tasan ba laifinsu cikin abinda aka mata, suma sun bata hak'uri dasu Mama, sun d'an jima a gidan sannan Jamal ya dawo ya d'aukesu Ya maida su gida. Da fad'a Mabrookah ta tari su Twins tana tambayan daga ina suke, Jamal na jinta ko kallanta baiyi ba ya bar wajan zuwa side d'in Abba. Har suka shiga falo tana balbalesu da masifa, Aunty Faty ce ta soma tambayan mai ya faru, Mabrookah ta soma magana tana cewa "Tun d'azu nake neman su ashe sun fita neh da Jamal, kuma bayan na fad'a musu zamuje wani guri dasu" Aunty Faty ta had'e rai tace "Daga ina kuke?" Batare da wani d'ar ba Najma tace "Daga gidansu Ummy, muje bata hak'uri" Wayan Hannun Mabrookah ne ya fad'i ta saki baki tana kallansu "Daga gidansu Ummy? Uban wa ya kaiku" Najwa tace "Ya Jamal" Nan Aunty Faty ta soma masifa, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, Mabrookah ko side d'in Abba ta nufa a fusace, kishingid'e ta sameshi kan kujera idanunsa a lumshe, "Ya Jamal! Jamal!" Bai bud'e idonsa ba saima gyara kwanciya dayayi "Nasan dai kana jina, akan wani dalili zaka d'au Twins ka kaisu gidansu matsiyaciyar yariny...." Marin dataji a kuncinta ne ya hanata k'arasa maganan datayi niya, ya mik'e a fusace yana nunata da yatsa "Kinyi na farko kinyi na k'arshe, wallahi kika sake zagin Ummy sai na lahira ya fiki jin dad'i. Kar kiga kina abinda kika gadama ina saka miki ido, taraki nakeyi, kuma wallahi ko mutuwa zakiyi bazan aureki bah" Ta tushe da kuka tana nuna kanta "Akan wata banza zaka..." Wani marin ya sake d'auketa dashi "Fita! Kafin na la'anta ki" "Wallahi bazan fita ba koda kasheni zakayi, akan wannan yarinyan zata dukeni? Me ta fini dashi? Diri ko meh, ko dan ni bak'a ce. Wallahi saina aureka" Duka ya rufeta dashi dan dama yana ciki da ita, ihu ta dunga yi ba mai kwace ta, haka ya mata ligi ligi yabar side d'in. Saida tayi kuka mai isarta sannan ta koma side dinsu, Mami ta samu a falo itada Aunty Faty, ta shigo ta fad'a jikin Aunty faty tana kuka tareda labarta mata abinda ya faru. Ran Aunty Faty ya sake b'aci tace "Maimuna idan bazaki d'au wani mataki ba zan d'au 'yata nabar miki gidan, akan me d'anki zai kamata yayita jifga kamar ya samu jaka, ai ba shi kad'ai bane Namiji" "Ni Mommy ba inda zani, ina sanshi" Hak'uri Mami ta soma ba Aunty Fatyn dakyar ta samu ta shawo kanta, a ranar Jamal yaga b'acin rai wajan Mami anma hakan baisa yayi nadama akan abinda yayi bah. Bayan kwana biyu ya sake komawa gidansu Ummy, wannan karan ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwarsa, maganan ranan ya sake d'auko mata, nan tayi kicin kicin darai "Na fad'a maka bazan iya aurenka ba Ya Jamal, yakamata ka cire wannan maganan a ranka indai baso kake ka b'ata shirin dake tsakanin mu bah" Kurri ya mata yama kasa cewa komai, ya sauke ajiyar zuciya idanunsa cikeda kwalla "Shikenan Ummy, na bar maganan kuma insha Allahu bazan k'ara tadoshi bah. Saidai inaso ki sa a ranki ni mai k'aunar ki ne koda yaushe" Jikinta ne yayi sanyi ta zuba masa narkakun idanunta tana kallansa, mik'ewa yayi yamata sallama ya fito daga gidan dan dama a falo suke. Bai sake waiwayo wa ba har ya shiga motarsa ya tada yabar k'ofar gidan a guje. Bin motar nasa tayi da kallo hawaye na gangara a idonta, tanajin wani abu gameda Jamal tun ba yau ba sai dai bazata iya k'arya alk'awarin data d'aukar wa Bilal bah. Gida ta koma ta tarar da Mama a falo fuskanta a had'e "Yanzu abinda kikayi ya dace Ummy? Keda yakamata ki rufama kanki asiri ki aureshi tunda yana sanki. Shi Bilal d'in da kike mawa baya duniya, babban abinda zaki masa yanzu bai wuce Addu'a ba. Ki so Jamal bazaki tab'a danasani bah" Shiru Ummy tayi tana nazarin maganan Mama "Mama kiyi hak'uri, bazan iya auren Ya Jamal bah. Ko ba dan shi ba kinga Iyayensa da k'anwarsa basa sona." "To ai badasu zaki zauna bah. Ni nasan har yanzu Maganan Bilal ne a ranki kuma yakamata ki cire shi tunda baya raye. Yau da Bilal na raye Jamal yazo bazan tab'a yarda ki auri Jamal ba sai Bilal, to k'addara ta riga fata, kawai sai muce Allah ya sa haka shi yafi alheri" Kuka Ummyn ta fashe dashi ta shige d'akinta. *Bayan sati d'aya* Hurama Abba wuta Mami tayi dole aka saka ranar bikin Jamal da Mabrookah wata d'aya, ranar karka so kaga Jamal sai ya baka tausayi, abin duniya ya taru ya masa yawa, ga sa ranan sa da Mabrookah ga Abinda ya faru tsakaninsa da Ummy. Dan tun daga ranar bai sake taka k'afarsa gidan bah. Wanda hakan sosai ya damu Ummyn dan tasan fushi yayi. Ranar juma'a da daddare Jamal ya shirya cikin farar yadi sai baza k'anshi yake, keyn motarsa ya d'auka bai zame ko ina ba sai gidansu Ummy. Yana isa k'ofar gidan yaga Wasu matasa run fito daga gidan d'auke da Baba Ummy ba biye dasu tana kuka, a rud'e ya k'arasa yana tambayan abinda ya faru, Mama ce tayi k'arfin halin sanar dashi ciwon sa ne ya tashi. Da taimakon sa aka sakashi a motarsa, Ummy da Mama suka shiga dukansu suna kuka, direct shika yayi dashi, nan likitoci suka duk'ufa kansa, cikin y'an mintoci Baba Ya cika. Innalillahi wa inna ilaihi raijun! Karku so kuga Ummy a lokacin, rikid'ewa tayi kamar mai hauka, Mama ko suma tayi saboda tsananin firgita, shima Jamal kuka ne ya sub'uce masa na tausayin halinda Ummy da Mama suka shiga, Ambulance ya biya suka d'auko gawan Baba aka mai doshi gida. Washe gari da safe aka masa sallah, ciki harda Abba da Ramadhan da sauran 'yan uwa da abokan arziki. Ummy ta koma abin tausayi, tun tana kuka sautin na fitowa har muryanta ya dishe, fuskanta ya kumbura yayi sintim gwanin ban tausayi. Abba da kansa ya ingizo k'eyar Mami dasu Aunty Faty harda Twins da Mabrookah sukazo sukayi gaisuwa sunata yatsine yatsine, dan ranar da aka sanar dashi abinda ya faru na koran Ummy, ranar yayi fad'a sosai kamar ya ari baki, Ranar saida kowa na gidan ya gane kuransa saboda yanda ran Abban ya b'aci. Sadakan kayan Abinci Abba yasa aka kawo, tun daga kan Shinkafa, masara, taliya, wake da sauran kayan masarufi dan yaji dad'in zama da Ummy nad'an kad'an bah. Ranar Uku Yannin Baba su biyu sukazo daga k'auyen wudil, kallansu Ummy take cikeda takaici, tunda aka haifeta bata tab'a ganin sunzo gidansu ba saidai su Ummyn suje, anma yanzu daya rasu gashi sun d'auko k'afa suna kukan munafinci. Bayan anyi addu'an uku kowa ya watse, Baba Sallau ya shigo falo inda mata suke ya kalli Mama yace "Dije fito muna san magana dake" Bah musu ta mik'e ta fito tareda tsugunnawa "Dama akan maganan Ummy neh, yarinya gand'ediya kamar wannan ku tasata gaba kuna kallo" Baba Tanko yace "Da a k'auye take ai da yanzu tanada 'yaya shidda" Itadai Mama batace komai ba kanta k'asa, Baba Sallau yace "Ina yarinyar take, kira min ita nan dan na yanke hukuncin aura mata d'ana Iliya" Dam! Gaban Mama ya fad'i ta d'ago tad'an kallesu "Wai ina Ummyn take ne" Mama ta mik'e ta kirata, tazo itama ta tsugunna kamar yanda taga Mama tayi, "Munyi shawara nida Tanko mun yanke hukuncin aurar dake ga d'ana Iliya nan da kwana hud'u, ma'ana ranar bakwai ana gama addu'an bakwai za'a daura auren ku" Ba shiri Ummy ta saki kuka tana kallan Mama "Haba Yaya Sallau yakamata ku fara tambayan yarinyan nan kuji idan tanada wanda takeso" "Iyeh! Lallai Dije, ke har kin isa ki fad'a mana abinda zamu yanke muda 'yarmu" Nan Baba Sallau ya soma sababi, Mama bata sake cewa komai bah kanta k'asa, Ummy ko sai kuka take. Bayan sun k'ulle a d'aki Mama ta zauna kusada Ummy wacce har lokacin take kuka "Ummy kiyi hak'uri ki daina kukan nan, ki tsaya ki saurareni" Hawayen idanunta ta share tana kallan Mama "Mai zai hana kima Jamal magana, kice ya turo magabatansa kamin lokacin, kinga da ki auri Iliya wanda ko ilimin addini bashida shi gwara kin auri Jamal, wata rana inda rai Mamarsa zata soki" Ummy ta girgiza kai tana hawaye "Mama ki kyallesu kawai su aura min Iliyan" Ta sake rushewa da kuka "Ni kuma haka Allah yayi dani..." Mama tasa hannu ta rufe mata baki dasauri "Kul! Karna k'ara ji, kibi shawara ta k'ila a dace, dan ni ban isa in hanasu abinda sukayi niyya bah dan a yanzu sun fini iko dake" Shiru Ummy tayi batace komai bah, duk yanda Mami taso ta fad'akar da ita k'i tayi haka ta hak'ura ta kyalleta, duk da tausayin 'yar nata dake cike a ranta. Jamal bai samu dawowa washe gari ba sai ranan da akayi biyar, gidan ya shigo kamar yanda ya saba, Ummyn ya samu makure waje d'aya tana tunani, zama yayi kusada ita na kusan minti goma anma har lokacin batasan yazo ba. Saida yad'an tafa hannunsa sannan ta d'ago a razane tana kallansa "Dan Allah ki cire tunani a ranki Ummy, Addu'a yakamata kiyita masa ba wannan dogon tunanin bah" Ta rushe da kuka tana kallansa k'asa k'asa, hankalinsa ne ya tashi ya zuba mata ido yana kallanta da mamaki "Menene damuwarki? Fad'amin me aka miki?" Kai ta kawar gefe tana cigaba da kuka "Pls Ummy, bana iya jure ganin damuwarki" Dakyar ya shawo kanta ta sanar dashi abinda ke faruwa. Ba k'aramin tashi hankalinsa yayi bah, dakyar ya iya mata sallama ya nufi gida. Dakinshi ya shiga ya soma safa da marwa cikin tunani, sai zufa yake kamar wanda yake filin daga. Waya ya d'auka ya soma neman layin Ramadhan anma switch off. Yana nan d'aki har Abba ya dawo, direct side d'inshi ya nufa yayi sa'a ya sameshi shi kad'ai, zama yayi ya soma ma Abban bayani, bai b'oye masa san da yakema Ummyn bah. Sosai Abba yaji dad'i duk da shima hankalinshi ya tashi dajin maganan auren da akeso ama Ummyn. Washe gari da wuri Abba ya nemi aminan sa suka tafi gidansu Ummyn nema ma Jamal aurenta. Baba Sallau da Baba Tanko fafur suka k'i yarda, duk magiyan da suka musu suka ce sam, haka suka hak'ura suka dawo gida a sanyaye. Ummy batasan wainar da ake toyawa ba dan dama bata sanar da Jamal d'in abinda Mama tace ta fad'amai ba, kawai da ta fad'amai abinda su Baba Sallau d'in suka cene. Washe gari ranar bakwai, Ummy kuka take kamar mai hauka, Mama itama na tayata, Alumma ne cike a k'ofar gidan ana addu'an bakwai. Da gudu ya shigo cikin layin kamar zai tashi sama, yana parking a ya fito aka shafa fatihar k'arshe na d'aurin auren Ummyn. Hannu ya d'aura aka ya fad'i guyawu biyu a k'asa tareda fashewa da kuka. *Idan banga dogon comment ba, bazan cigaba ba ehe!* Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Oh! Fans duk saurin ungwazo ma ta bari dai a haihu koh! Naga comment d'inku, masu addu'a ina godiya, masu k'orafi ma na gode, masu zagi suma na gode dan bazance ban gode bah.* _Aysha Humaira (Aunty Nurse) ina tayaki murnar zagayo war ranar haihuwarki. Allah ubangiji ya k'aro shekaru masu albarka, ya nuna min aurenki mu kwaso shoki Lol_ Wannan shafin sadaukarwa ce gareki K'awar arzik'i Page 31 Hannu ya d'aura aka ya fad'i guyawu biyu a k'asa tareda fashewa da kuka. Ganin kukan nasa ba ci yasa ya mik'e ya shiga cikin gida kai tsaye, Inna dake tsakar gida tana shara ta d'ago dan taga mai shigo mata gida ba sallama, ba shiri tsintsiyar hannunta ya fad'i ta dafe k'irji tana sallati "Bi...Bilal! Kai nake gani ko gizo kakemin" Ya soma takowa a hankali yana share hawayen fuskansa, "Ni ne Innata" Ya mik'a mata hannunshi "Tab'ani kiji" Cikeda tsoro ta mik'a hannunta ta tab'a shi, ba shiri ta fashe da kuka, shima kukan ya soma ya jata suka zauna kan tabarman dake tsakar gidan "Bilal ina ka shiga duk lokacin nan, meyasa ka tafi ka barmu bayan kasan bamuda kowa daga Allah sai kuma kai" Kuka ya sake fashewa dashi kamar k'aramin yaro tareda rik'o hannun Innan, Bahar ne ya shigo gidan yana k'walawa Inna k'ira, ba shiri ya koma waje a guje yana Ihu, Inna ta soma magana tana cewa "Munyi ta jiranka ba wani labari, har tsawon sati uku, sannan Bahar da Ummy suka je nemanka inda kuke aiki, a nan muka samu labarin kunyi hatsari kun mutu" Ya sake kama hannun Innan yace "Tabbas munyi hatsari, saidai kafin motar ta kama da wuta Allah ya aiko mutane inda suka ciro ni ganin ina motsi, wani Alhaji ne ya d'auke ni ya tafi dani abuja, kasancewar ba mazaunin k'asan nan baneh yasa lokacin komawar sa nayi ya d'aukeni ya tafi dani Egypt, k'asar dayake kuma a lokacin bana cikin haiyaci na dan ban farfad'o bah" Ya sake sharb'e hawayen idonsa yace "Na d'au watani bansan inda kaina yake bah sai daga baya na dawo cikin hankalina. Alhajin da matarsa sunyi d'awainiya dani sosai har zuwa wani lokaci. Dawowan mu k'asar kenan shekaran jiya shine na taho gida. Inna ba abinda take sai sharb'ar hawaye "Allah sarki mutanen kirki" Duk abinda suke tattauna wa Bahar na jinsu wanda ke bakin zaure yana lek'ensu. Bayan yaji bayanin sa ya shigo ya zauna kusada yayan nasa tareda rungumeshi "Yaya munyi kewarka sosai, badan Ummy data fara aiki tana taimaka mana ba da bansan halin da zamu shiga ba" "Aiki!?" Bilal ya maimaita yana kallan Bahar, Inna tace "Kwarai kuwa" Nan ta soma basa labarin abinda tasani har zuwa yau da ake sadakar bakwai na Baba, kuma ranar da aka d'aura auren Ummyn. Hawaye ne suka gangaro masa na tausayin halin daya bar 'yan uwansa da kuma Ummyn. Baice musu komai ba saima mik'ewa dayayi ya fita, gidansu Ummyn ya shiga kai tsaye, mutane ya gani a ciki, bin gidan ya soma yi da kallo ganin yanda aka gyara shi tareda k'awata shi sosai. Falon ya shiga da sallama ya hango Mama zaune a k'asa gefen kujera, ta d'aura kan Ummy bisa cinyarta wacce da alama kuka take. Jiki a sanyaye ya k'araso ya tsugunna gabansu "Sannu Mama" Muryan da Ummy taji ne yasa ta d'ago a razane suka had'a ido da Bilal, ba shiri ta fashe da wani sabon kukan, Mama ko tsoro taji ta d'an matsa "Bilal! Kaine" "Ni ne Mama, ban mutu ba" Ummy ta mik'e dasauri tabar d'akin tana cigaba da kuka, zaure ta nufa yayi saurin fitowa ya kamo gefen hijabinta dasauri "Ina zaki Hrt, pls ki tsaya ki saurareni" Cikin kuka ta d'ago idanunta tana cewa "Ina katafi Ya Bilal, ina kaje ka barni, meyasa ka tafi baka waiwayo ni bah. Dama nasan baka mutu ba dan naji a jikina." Ta chakume shi tana wani irin kuka mai cin rai "Kai kad'ai nakeso Ya Bilal, kai nakeso na aura. Gashi kasa an aura min wanda banaso. Meyasa Ya Bilal" Shima hawayen ya soma "Nasan nayi kuskure Hrt, anma yakamata ki tsaya ki fahimceni kafin ki yanke hukunci" A hankali ta zame hannu wanta daga rik'on data masa tana kuka. Labarin abinda ya faru dashi ya soma bata tiryan tiryan, sassauta kukan datake tayi "Yannin babana sun aura min wani wanda banaso, wanda banma tab'a ganinsa bah" Gabansa ya fad'i, ya d'ago rinannun idanunsa yana kallanta, Baba Sallau ne ya shigo zauren, ganin Ummy tsaye da wani wanda bai sani ba yasa ya soma fad'a "Ke Ummy, yanzu saboda iskanci da rashin hankali a d'aura miki aure ki tsaya kina kula wani" Ya daka mata wata uwar tsawa "Maza bar nan!" A guje ta shiga cikin gida tana kuka, ya juyo ga Bilal dake tsaye kamar gunki "Kai kuma zaka bar nan ko sai na bugeka" Jiki a sanyaye ya bar zauren ya koma gida. D'akin Innansa ya shiga ya soma kuka wui wui, dan harga Allah bazai iya rayuwa ba Ummy bah. ****** Bayan an gama d'aurin aure Abba ya baro wajan ya dawo gida, Jamal ya tarar a falonsa kishingid'e kan kujera idanunsa a lumshe, har ya nemi guri ya zauna kusada shi bai sani bah. Gyaran murya Abban yayi anma shiru, kai ya girgiza ya d'an buga hannunsa, bud'e ido yayi ganin Abba yasa ya mik'e zaune dasauri yana kallanshi "Jamal tunanin me kake?" Yayi saurin girgiza kai tareda k'ago murmushi yace "Bakomai Abba, bacci nakeyi" Murmushi Abba yayi irin tasu ta manya, ya gyara zama tareda cire babban rigan dake jikinsa "Meya hanaka zuwa addu'an bakwai" Ya sosa k'eya yana kame kame "Ahan kai nake sauraro" "Ummm..mmm Dama Ramadhan nayi ta jira muje tare kuma baizo bah" Murmushi Abban ya sakeyi, "Bakomai ai tunda ni naje, na wakilce kah. Yanzu abinda nakeso dakai shine ka shirya dan nan da sati d'aya za'a kawo maka matarka" Da mamaki Jamal ya d'ago yana kallan Abban "Yadai naga kana kallona" "Abba mata kuma?" "Duk abinda kakeso nima ina sonshi my one and only son, tun sanda kace min kanasan Ummy na soma shige da ficen yanda zanyi ka mallaketa a matsayin matarka, munje dasu Alhaji Tahir anma kawun nan ta suka k'i. Shine Jiya da daddare na sake komawa na k'ara tambayan su. Nan sunk'i amincewa har saida na had'a da nuna dukiyata sannan suka aminta" Wani runguma Jamal yama Abba yana dariya "Thank uh! Thank uh!! Thank uh dad. Uh are the best dad ever" Peck yama Abba a kumatu yana mai nuna farincikinsa a fili, dariya Abba ketayi ganin yanda tilon D'an nasa keta murna da farinciki. "Saidai kar kabari su Mamin maka su sani har sai na kamalla wasu shirye shirye danakeyi" "To Abba insha Allahu" Kar kuso kuga yanda Jamal keta d'oki, waya ya d'auko ya soma neman layin Ramadhan cikeda farinciki kamar wanda akama bushara da aljanna. Da daddare Mami na side din Abba, ya mik'a mata cheaque yana cewa "So nake cikin gobe zuwa jibi ki had'o min kayan lefe masu kyau da kuma tsada, kamar set uku haka" Da fara'a Mami ta amsa tana dubawa, miliyan hud'u ta gani, ta washe baki "Ahh Lallai Alhaji kanaji da 'yar nan taka" Ya saki murmushi baice komai bah. Bayan ta koma side d'inta ta sanar da Aunty Faty yanda sukayi, Ihu Mabrookah tayi cikeda murna, haka Aunty Faty. Washe gari suka d'au hanyan lagos dan achan zasuyi siyaiyan. Kaya suka jifgo, har saida Mami ta kira Abba tace saiya k'ara kud'i, ba musu ya tura mata dubu d'ari biyar suka sake wata siyaiyar na kaya masu tsada. Kwanan su uku suka dawo gida. Sosai Abba ya yaba da kayan da suka siyo dan shima sun burgeshi sosai, a nan side d'inshi ya umarce su da su bar kayan, haka kuwa akayi suka bar kayan nan side d'in nashi. _kuyi managing wannan banda chargi_ Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* _*Alhaji Haruna Jumare Marad'in Zazzau's Family*_ Wannan shafin sadaukarwa ce gareku Page 32 n 33 A nan side d'inshi ya umarce su da su bar kayan, hakan kuwa akayi suka bar kayan nan side d'in shi. Da yanma Abba ya kira Jamal yazo dan yaga kayan, sosai ya yaba tareda godiya ma Abban. Har lokacin ya hana ya fad'a ma su Mamin abinda ke faruwa. Baba Sallau da Baba Tanko ne zaune a falon gidansu Ummyn, Mama da Ummy na gefen su zaune suna sauraran abinda su Baba Sallan zasu ce. "To saboda yanayi da sauyi da aka samu, an fasa d'aura auren da Iliya d'an wajena. Yanzu an d'aura da yaran da kuka turo" Ummy ta d'ago da mamaki tana kallan Baba Sallau "Wani yaro kuma?" Cewar Mama itama da mamaki "Ko Jamalu, ko mene" cewar Baba Sallau Baba Tanko yad'anyi dariya yace "Jamaludeeni sunansa" Gaban Ummy ya yanke ya fad'i, ta fashe da kuka. Itako Mama murmushi tayi cikeda farinciki tace "Babu komai Yaya, Allah ya saka da alheri, ya kuma sanya Alkhairi" Da kuka Ummyn ta mik'e ta shige d'akinta tana kuka. itama Mama ta mik'e tabi bayan Ummyn. Baba Sallau ya kyalkyace da dariya yana kallan Baba Tanko "Ai wannan abu yayi, da mun d'aura ma Iliya ba abinda zamu samu saima wahala dan mu zamu rink'a ciyar dasu" Baba Tanko yace "Gaskiya ne Sallau, yanzu ko kaga kowannen mu yanada Million d'aya nasa na kansa" Suka kwashe da dariya tareda mik'ewa suka bar Falon. Duk abinda suke tattaunawa Mama najin su, sai yanzu ta fahimci cin hanci Baban Jamaludeen d'in ya basu har suka yarda suka bada auren. Allah wadai tayi da halaiyar su Baba Sallau ta shiga d'akin Ummy a sanyaye. Kuka ta sameta tanayi kan gado bil hak'i da gaskiya, ta d'agota ta zaunar tana share mata hawaye "Haba uwata, kukan nan na menene? Ai wannan abin farinciki neh, yakamata ki maida komai ba komai bah. Kiyi hak'uri ki fauwala wa Allah. Ni inaji a jikina Jamaludeen Alheri ne a rayuwarki" "Mama Ya Bilal nakeso, dan Allah kice Ya Jamal yayi hak'uri." "Ummy kibi umarnin Yanin mahaifinki, ki zauna da Jamaludeen d'in tunda har an d'aura. Ba kuma abinda zamu iyayi. Kiyi biyaiya zakiji dad'in rayuwar aurenki" Ummy ta sake rushewa da kuka ta fita daga d'akin dasauri, gidansu Bilal ta shiga tana cigaba da kuka, Inna ta fito a rud'e tana tambayanta lafiya, Bilal ne ya fito daga d'akin Innan yana takawa da kyar da alama baida lafiya neh. Tsugunnawa tayi guyawu biyu a k'asa a gabansa tana kuka, "Ya Bilal karka bari a rabamu, bazan iya auren kowa ba sai kai. Dan Allah karka bari a rabamu" Baice komai ba saima sulalewa dayayi ya zauna a wajan saboda jikinshi da ba k'arfi. Inna ta d'ago Ummyn ta rungumota jikinta tana share mata hawaye "Ummy ki daina kuka, Allah ya riga ya rubuta Bilal ba mijinki bane. Ki d'au dangana, haka Allah ya k'addara" Ta sake rushewa da kuka ta zame ta zauna kusada Bilal d'in. Zama Inna tayi ta dunga musu nasiha sannan da kanta ta sab'a hijab ta raka Ummyn gida tareda yima Mama murnar auren Ummyn. Yau da wuri ango Jamal ya tashi daga wajan aiki, direct gida yayi ya fesa wanka ya sauya kaya zuwa manya, keyn motarsa ya d'auka ya nufi anguwarsu Ummy. Yana shiga anguwan aka fara kiraye kirayen sallan Magriba, parking yayi ya tsaya wani masallaci nan kusada gidan ya tsaya yayi sallan sannan ya k'araso. Yaro ya samu ya aika cikin gidan, chan ya dawo yace tana zuwa. Cikin zauren ya shiga ya tsaya, chan sai gata ta fito fuskan nan nata a d'aure. "Barka da fitowa Gimbiyata" Harara ta wurga mai tareda b'ata fuska "Haba Gimbiyata ba gaisuwa" K'eya ta juyamai, ya saki murmushi mai sauti tareda tura hannayensa cikin aljihu "I know tun ba yau ba baki sona, ban tab'a tunanin wata rana zaki zama mallakina bah, sai gashi. Ina sanki Ummy fiyeda yanda kike tunani. zan iya sadaukar da komai da nakeda shi matuk'ar zaki soni ki yarda ki zauna dani" Juyowa tayi tana kallanshi idanunta cikeda kwalla "Ka tabbata kana sona" Kai ya gyad'a mata yana cigaba da kallanta "Dan Allah dan san Annabi ka sakeni, idan kamin haka shine zan yarda da cewa kana sona. Wallahi Ya Jamal bana sanka ni Ya Bilal nakeso" Ji yayi kamar ta soka mai mashi a k'irji, ya d'ago muryar shi a sark'e yace "Wanene kuma Bilal" Kan tayi magana suka jiyo Muryan Bilal gaba bakin zauren yana cewa "Ni ne Bilal" Ya k'araso cikin zauren suna kallan Juna shida Jamal. Ran Jamal idan yayi dubu ya b'aci, baice komai ba har lokacin idanunsa nakan Bilal dake tsaye kusada Ummy "Tun bansan Wacece Ni bah Ya Bilal ke sona yake tausaya ma Rayuwar da muke ciki ni da Iyayena. Ina matuk'ar sanshi, haka shima yana sona. Dan Allah ka sawak'e min ka barni na auri wanda nakeso" Ta fashe da kuka ba shiri ta shiga cikin gida a guje. Bilal ya tako gaban Jamal wanda yayi mutuwar tsaye kamar gunki yana kallan Bilal "Mallan kayi k'okari ka kyale min budurwa tah. Dan zan iyayin komai a kanta matuk'ar ana neman a rabani da ita" Jamal yayi murmushin takaici yace "Kana santa ka bari har na aureta? Hakan ya nuna kai raggo ne akan soyaiya, bazaka iyayin komai dan ka mallaki abinda kakeso bah duk cika baki neh" "Haka kace!" Cewar Bilal a harzuk'e ransa b'ace Jamal ya sake sakin murmushi yace "Haka nace" Fuuuuuu Bilal yabar zauren. Sosai ran Jamal ya b'aci ya figi mota yabar anguwan cikeda takaici. ****** A b'angaren su Mami kuwa zagewa sukayi itada Aunty Faty sunata gyara 'yar tasu dan saura sati biyu biki, su Mabrookah kuwa sai b'arin d'uwawu take ita a dole amarya. Ana cikin haka Laurat ta dawo bakin aikinta, a bakin masu aikin kicin take jin labarin abinda ya faru, kuka sosai tayi gashi batasan gidansu Ummyn bah balle taje wajanta. Su Twins ta samu suka mata kwatance, washe gari kuwa ta saci hanya ta tafi. Ummy na zaune a tsakar gidansu tayi tagumi kamar a mafarki taji muryan sahibar tata. Mik'ewa tayi suka rungume juna a tare kuma suka fashe da kuka, saida sukayi mai isarsu sannan Ummy taja hannunta suka shiga Falo. Mama suka samu a falon, Laurat ta gaisheta tareda mata gaisuwa, Ummy ta gabatar da Laurat a wajan Mama sannan suka shiga d'akin Ummyn. Bayan Laurat taci tasha Ummy bata b'oye mata duk abinda ke faruwa bah, sosai Laurat ta tausaya mata, Ummy tace "Gaskiya Laurat ina cikin tashin hankali, Wallahi bana san aurena da Ya Jamal, Ya Bilal nakeso" Laurat ta gyara zama tace "Duk da ban tab'a ganin Bilal d'in nan bah, kuma bansan halaiyarsa bah. Nidai haka nan hankalina yafi kwanciya da Jamal" Ta dafa kafad'ar Ummyn tace "Wallahi kun dace keda Jamal sosai" Ummy tai saurin buge hannun Laurat d'in tace "Wannan irin magana kikeyi Laurat, kema kina sahun masu san rabani da Ya Bilal kenan" "Ba nufina kenan ba Ummy, abinda nakeso ki gane a nan shine. Babu abinda yazo zaki iyayi dangane ga maganar nan, karki manta. Yanzu haka kina a matsayin matar Jamal ne, tunda har an d'aura aure ba kuma abinda ya rage daya wuce kiyi hak'uri kima mijinki biyaiya" Shiru Ummy tayi ta sake rushewa da kuka. Lallashinta Laurat ta soma dakyar ta samu tayi shiru sannan ta mata sallama itada Mama tabar gidan. Tun daga ranan Innan Bilal ta soma gyaran 'yar nata kamar ba gobe, dan ita sam bata nuna kishi akan auran. Bilal ko abin duniya ne ya ishesa yau ciwo gobe Lafiya, haka Itama Ummyn. Ango Jamal kuwa tunda Haka ta faru tsakanin su da Bilal bai sake zuwa gidan ba duk da yanda zuciyarsa kesan ganin Gimbiyar tasa. Abba ne da Mami sai Mabrookah dake gefe da kuma Jamal harda Aunty Faty dasu twins. Gyaran murya Abba yayi sannan yace "Kamar yanda kuka sani, yau saura sati d'aya d'aurin auren Jamal da Mabrookah, saidai akwai abinda baku sani ba wanda yau nakeso na warware muku" Mami tace "Menene kuma Alhaji" Ya d'anyi murmushi yace "Sati uku da suka wuce aka d'aura auren Jamal da Ummy" Mami ta mik'e dasauri "Ummy fah kace Alhaji" "Kwarai da gaske ita" "Haba Alhaji, ya zakayi mana haka yanzu ita Mabrookahn fah" Nan da nan Mabrookah ta fashe da kuka, Jamal ko sai hararanta yake, ji yake kamar ya shak'eta ta mutu kowa ya huta. "Bance miki ai baza'a d'aura da Mabrookah bah. Itama idan Allah ya kaimu sati mai zuwa za'a daura nata. Sannan inaso ku sani banasan tashin hankali ko k'ananan maganganu" Mami ta zauna a sanyaye tana kallan Aunty Faty wacce keta hararan Mamin, ba'a gama magana ba Aunty Faty ta mik'e tabar falon tana huci. Abba ya cigaba da cewa "Kamar yanda kika zab'ar mai Mabrookah, haka nima na zab'a masa Ummy saboda na lura yarinya ce marainiya" Twins sai dariya suke k'asa k'asa cikeda farinciki. "Gobe a tara 'yan uwa da abokan arziki dan akai lefe gidansu Ummyn, kuma inaso ya zama rana d'aya za'ayi bikin dana Mabrookah" Mami dai ba amsa sai huci datake yi cikeda bak'in ciki, sallaman su Jamal d'in yayi, Mabrookah ta mik'e tana kuka mai had'e da ihu ta haura sama, Twins ma suka mik'e suka bi bayan Jamal sunata mai Congrat. "Fisabillahi yanzu Alhaji abinda kayi ya dace" "Ni ko nasan ya dace" "Gaskiya Alhaji bazai yuwu bah, a rasa wacce za'a daura ma Jamal sai b'arauniya" "Ya Isa Maimuna! Ki shiga taitayinki, ya ina magana kina magana. Tho bari kiji, ba gudu baja da baya aure dai an d'aura, kuma kamar yanda na fad'a miki gobe za'a kai lefe gidan su Ummy, sannan set biyu za'a kai mana. Idan kuma kika sake naji wani magana ya taso zamu sabu sab'ani dake sosai" Ya mik'e fuuuu yabar falon ranshi b'ace. Haurawa Mami tayi zuwa d'akin Jamal, batareda wani b'ata lokaci ba ta d'auke shi da mari "Ni! Ni Jamal kakeso ka wulak'anta?" Ta rushe da kuka "Ba laifinka baneh" Ta bar d'akin dasauri, kuka shima Jamal d'in ya fashe dashi, shi yanzu ina zaisa ranshi, ga Ummy bata sanshi, Ga Mami na fushi dashi, ga kuma auren Mabrookah da aka tilasta masa akai. Ranar Aunty Faty da Mami kacha kacha sukayi, washe gari kamar yanda Abba ya umarta, set biyu na akwati aka d'auka aka barma Mabrookah d'aya, gidan su Ummyn aka kai, Mama tace akai gidansu Innan Bilal, nan Inna tayi kiran Mak'ota aka amsa kayan cikeda farinciki. Tunda Ummy taji shigowan masu kawo lefen ta fashe da kuka, shikenan tasan aikin gama ya gama an rabata da Ya Bilal d'inta. A ranar Ramadhan ya diro Zaria, shi kad'ai yazo gidansu Ummyn ya kawo mata kud'in d'inki, dubu hamsin wanda Abba ya bada a kawo. Saida ya dinga had'ata da Allah sannan ta amsa tareda waya k'irar Samsung da Jamal d'in ya bada a kawo mata. Duk abinda sukeyi Bilal na hango su wanda yake bak'in k'ofar gida, ranshi ya b'aci sosai. Ramadhan d'in na tafiya ta juyo tayi hanyar gida, had'a ido tayi dashi gabanta ya fad'i, baice mata komai ba yayi shige wanshi gida. A sanyaye ta nufi gida, Mama ta nuna ma kud'in da wayan, tasa albarka sannan tace takaima Inna dan itace mai shirye shiryen. Bata samu ta kaiba sai washe gari, Nan take Inna ta d'au kaya kala goma ta saka a leda ita da kanta takai Ummyn wajan masu d'inki dan tasan idan tace ita kad'ai taje bazata bah. Tun daga ranar Ummy bata sake ganin Bilal bah, ko ta shiga gidan bata ganinsa. Bahar ta tambaya a nan yake fad'a mata ya tafi abuja wajan Alhajin daya zauna wajansa. Wani k'walla ne ya gangaro mata tasa bayan hannu ta share. Yau saura kwana hud'u biki, Laurat dakyar ta samu Mami ta barta ta tafi hutu kan cewa marik'iyrata batada lafiya. Tana tafiya tayo gidansu Ummy dan tayata shirye shirye. Sosai Ummy tayi Farinciki da zuwanta. Wayan da Ramadhan ya kawo mata ta nuna mata, Laurat ta kyalkyale da dariya tana cewa "Hala ma ko kunnata baki iya bah" Harara Ummy ta wurga mata "Ni ina ruwana ma da wayar" Dariya Laurat tayi ta kunna mata wayan, text ne ya shigo ta bud'e tana cewa "Ashe ma akwai Sim a ciki, har an turo miki message" "Ni ina na iya wani karatu balle na karanta" ta k'are maganan tareda turo baki "To bari na karanta miki" Ta gyara zama tana kallan Laurat "Salam! Ina fata gimbiyar tawa tana cikin k'oshin lafiya. Duk da nasan Gimbiyar tawa bana gabanta, anma inaso tasan wani abu guda d'aya..." Ummy ta ja dogon tsaki "Dallah ki bari banason ji" "Haba Ummy bakyau wulak'anta d'an adam, ai sai ki tsaya ki gama sauraran abinda ya rubuto koh" Ta sake turo baki tace "Ina jinki" "Ina sanki Fiyeda yanda nake san kaina, Ina matuk'ar k'aunar ki. Dan Allah ki bani dama na shigo rayuwarki dan na jiyar dake farinciki da annashuwa na rayuwa. ke Alheri ce a rayuwata Ummy! Ke Alheri ce a tare dani. Ina san mu kasance tare koda kuwa zaki rink'a..." "Kai! Nifa na gaji da sauraran ki" Ta mik'e tana cewa "Muje wajan Inna dan tace na dawo d'an anjima" Laurat ta saki Murmushi ta mik'e suka tafi gidan Innan. Ana saura kwana uku 'yan Uwan Baba dana Mama suka sake dawowa biki, kan kace me gidan ya cika sosai da mutanen k'auye. Dole Ummy da Laurat suka tattara inasu inasu suka dawo gidan Inna. _dan jin yanda bikin Jamaludeen da Jaleelah da kuma Mabrookah zai kasance sai ku bini a page na gaba_ ```Zaku min afuwan jina shiru kwana biyu, hakan ya faru bisa rashin Lafiyan danake D'an fama dashi. Sai ku sakani a addu'a``` Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* _Naga sak'on Addu'an ku da dama, ina godiya Allah ya saka da Alkhairi_ ```Maman Ahmad, Ayoush Gidos, Maman Abba, Tintima Shuwa and all My Fans Grp``` Ina godiya Page 34 Dole Ummy da Laurat suka tattara inasu inasu suka dawo gidan Inna. Bahar na zaune a cikin gida yana waya suka shigo, Inna dake tsakar gida tace "Maraba da Amarya" Ummy ta turo baki tana gungunai, ta nemi guri kusada Innan ta zauna "Ni fa bah amarya bace" "Ke ko kike amarya Ummy, ni abinda ma ke damuna wannan Raman da kikayi a haka za'ayi bikin" Laurat tace "Nima dai haka nace" Dai dai lokacin Bahar ya gama wayan da yake yana cewa "Innan mu Ya Bilal ne yace na gaishe ki" "Aa to madallah ina amsa wah" Idanun Ummy suka cika da hawaye, Bahar dake gefe yace "Amarya kinsha k'anshi, d'azu nake ganin katin Programs d'in bikin hannun wani abokina. Allah ya sanya alkhairi" Batace mai komai ba sai ma kauda kai datayi gefe. Bahar ya mik'e ya fita, tana ganin haka ta mik'e dasauri tabi bayanshi "Bahar dan Allah numbern Ya Bilal zaka bani" Ba musu ya bata numbern ta dawo gida cikeda farinciki. Da yanma suna zaune itada Laurat wayan da Ramadhan ya bata ya hau ruri, Laurat ta d'au wayan tana cewa number ce. "Tho ni ai ko d'aukan kiran ban iya bah" Dariya Laurat ta mata ta nuna mata yanda ake d'auka, karawa a kunne tayi Muryan Jamal ya daki dodon kunnenta "Salam Amarya tah" Sunan da ya kirata dashi sosai taji dad'in shi ta d'anyi murmushi tabace komai bah "I know kina jina kodai saina sayi muryan neh" Nan ma shirun ta sakeyi, ya d'an sassauta murya yace "Kiyi hak'uri muna k'ofar gida nida Abokai na, pls badan niba ki fito" Ta yanke kiran tana kallan Laurat tana turo baki "Wai Ya Jamal ne da abokansa a k'ofar gida" Laurat ta mik'e dasauri tana gyara gyalen kanta, tashi to muje Myb zasu mana magana ne akan abinda zamuyi. Ummy tayi turus alamar bazata mik'e bah, Inna dake tsakar gida tace "Wai Ummy baji nayi kince Jamalu na k'ofar gida bah" Turo baki ta sakeyi ta mik'e tasa hijab suka fito tana turo baki, su Biyar ne jingine jikin motar. Kallo d'aya ta musu ta d'ukar dakai, ji tayi tana jin nauyinsu. Laurat ta d'an tab'ata murya chan k'asa tace "Dan Allah kar dai ki dizga shi a gabansu" Hannun Laurat ta rik'e suka k'araso wajan, kunyan su Ummyn keji sosai ta b'oye bayan Laurat tana Murmushi. Laurat tace "Sannunku da zuwa ina yinin ku" Karaf Ramadhan yace "Lah! Abin kunya, ki ma daina jin kunyan wad'an nan" Ya nuna sauran abokanan yana cewa "Wad'an nan da kike gani duk shaki yayi neh" D'aya daga cikinsu mai suna Mifzal yace "Lallai Ram kaci abinci, anma ba komai zamu rama" Suka sake kwashewa da dariya, shidai Jamal na gefe sai kallan Gimbiyar tasa yake yana murmushi. Dakyar Ummy ta iya cewa "Ina yinin ku" d'aya daga cikinsu yace "Oh ashe ba haka nan kawai baneh take mana rowan muryan nata" "Kai wai ya haka, kuyi abinda ya kawo ku dallah mu tafi" cewar Jamal yana hararansu Mifzal yace "Ni ban tab'a ganin Ango ma mara kunya irinka bah, waya cema ango na biyo abokai wajan k'awaye" Harara Jamal ya sake wurga mai, Laurat da Ummy dariya suke musu k'asa k'asa Taseem yace "Ni fah tarko na ne ma ya kama kurciya a nan wajan Wallahi" Ram ya had'e rai yace "Kai lets be serious" Mifzal yace "Saidai bamu san sunan Malaman bah" Laura tace "Sunana Laurat" "Woaw nice name" cewar Taseem yana gyad'a kai Ram yace "Dame dame kuke buk'ata wajan hidimar bikin naku" "Kawai walima zamuyi shikenan" Taseem yace "Tho kamar nawa kuke b'ukata" Laurat ta sake cewa "Duk abinda Allah ya hore muku babu matsala" Take Taseem yasa hannu a aljihu ya ciro bandir d'in yan d'ari biyar ya mik'a mata. Ansa tayi ta musu godiya, itadai Ummy har lokacin tana bayan Laurat dan kasa had'a ido tayi dasu. Takowa Jamal ya soma yi har zuwa bayan Laurat, ya kamo hannun Ummy batareda yace komai ba ya kalli su Mifzal yace "Idan kun gama ku fad'a mana" Ganin tana k'okarin turje masa yasa ya d'auketa chak ya sakata a seat d'in bayan motan Ram shima ya shiga suka kulle ya kulle k'ofan. Baki bud'e su Ram suka bisu da ido. Taseem ya dawo kusada Laurat ya tsaya suna hira. Ram ya sake had'e rai ya matsa chan gefe yana waya fuska a had'e. Ummy ko ido ta zaro tana kallansa "Dan Allah ka bud'emin na fita" Ya janyota jikinshi yana y'ar murmushi "Wai mena miki ne Yasa baki sona" Ta turo baki tana tureshi daga jikinta. D'an dariya yayi k'asa k'asa yana kallanta "Why are uh pretending, ni nasani kina sona. C'ommon ki daina, I love uh so much and i know uh love me too" Ta turesa da k'arfi tana kokarin bud'e kofan, hannunta yayi saurin rik'ewa ya d'aura mata katuna a hannu yace "Ga katu nan ki da zaki raba" Ya d'auko wani k'atan leda ya d'aura kan cinyanta tace "Gobe akwai Dinner, inaso kisa d'aya daga cikinsu. Jibi kuma akwai Kamu. Zamu zo nida abokaina mu d'auke ki" Batace komai ba sai bin ledan datake da kallo. Kwankwasa windown motan aka soma, Ya rik'o hannunta tareda yin kissing d'inshi a hankali, zame hannunta tayi dasauri tana turo baki "I love uh my pearl" Saurin bud'e kofan tayi ta fito rik'e da ledan da katunan, dakyar ta iya sallama da abokan nasa suka shige gidan Inna. Ram ko kamar ya fashe saboda b'acin rai. _manage it_ Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 9:44 PM] ‪+234 903 823 4806‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 35 Ram ko kamar ya fashe saboda b'acin rai. Harara yaketa wurga ma Taseem har suka bar wajan. Ummy na shiga zauren gidansu Inna ta mik'a ma Laurat kedan tana cewa "Wai kayan dinner da ko menene oho" Amsa Laurat d'in tayi suka k'arasa cikin gidan, Inna ta mik'ama kayan sannan suka bud'e, Gowns ne guda biyu, d'aya Red mai touch d'in yellow, sai Head Bak'i, d'inkin sosai yayi kyau Laurat sai yaba kayan take. Da zumud'i ta d'aga d'ayan gown d'in, shi kuma bak'i neh da Farin Head, sai rafan y'an dubu guda biyu daya fad'o. Inna ta d'auka baki bud'e "Wannan kud'in fah!" "Ina tunanin na manni neh" cewar Laurat Itadai Ummy ko uhumm batace bah saima kauda kai gefe datayi tana kallan kayan ta gefen ido, dan itama sun burgeta sosai. A chan b'angaren Amarya Mabrookah kuwa, shirye shirye ake duk da dukansu babu wanda ransa ke cikin dad'i na maganan Auran Ummy. Bak'i ne cike a gidan daga b'angaren Mami da kuma Abba, itama Aunty Fatyn nata tawagar duk a nan suka yada zango. Su Aunty Zainab duk sun iso, itadai sam batajin dad'in zaman da Aunty Fatyn keyi a gidan Mami, tadaiyi shiru ne dan tasan idan tayi magana zasu iya rabuwa baran baran dan ba hak'uri Aunty Fatyn keda shi bah. Da daddaran ranar Najma da Najwa suka samu Aunty Zainab Umminsu a d'aki, zama sukayi Najma ta soma rok'onta akan ta barsu suje Gidansu Ummy suyi nasu shagalin. Da mamaji Aunty Zainab tace "In banda shashanci irin naku, yaushe ake barin sha'anin gida a tafi na bare" Najwa tace "Ummi kinga fah mu itace k'awarmu, kuma Aunty Mabrookah ba kulamu takeyi bah" Nan suka kwashe duk abinda ya faru lokacin da ta tafi suka sanar da ita. Sosai ta tausaya ma Ummyn "Idan na barku kuka tafi zan jama kaina surutu neh, kuyi hak'uri kawai ku zauna nan" Ga mamakinta sai gani tayi sun fashe da kuka, binsu da ido take tayi da mamaki. Ajiyan zuciya ta sauke sannan tace "Shikenan kuje, anma dan Allah ku kiyaye" Rungumeta sukayi a tare har saida suka fad'a kan gadon datake zaune, duka ta d'aka musu "Tho ku k'arsani ku huta" Suka mik'e suna dariya suka nufi d'akinsu, kaya suka loda suka fito tareda ma Ummin nasu sallama. Ram suka samu ya kaisu lokacin anata kiraye kirayen sallan Magriba, dan dama shima Abba ya aikeshi gidan wajan kawun nan Ummy. A mota Ram ke cewa "D'azu muka dawo daga gidan, sun ce wallima kawai zasuyi" Najma tace "To Ya Ramadhan nawa kuka basu" "50k" yace a takaice "Haba Ya Ramadhan, 50k mai zeyi wallahi yayi kad'an." Murmushi yayi yasa hannu a aljihu ya ciro wani rafan yan d'ari biyar ya mik'a musu "Wannan fah" Najwa tace "Eh to za'ayi managi" Da mamaki ya d'an kuyo ya kalleta "Lallai ma yaran nan" Suka kwashe da dariya daidai lokacin da suka k'arasa gidan. Dasauri suka fito suka shige cikin gidansu Ummyn, a cike suka samu gidan, dakyar suka iya lalubo Mama, bayan sun gaisa take fad'a musu tana chan mak'ota. Rige rigen shiga suka soma yi gidan Inna, Ummy dake zaune tsakar gidan kan kujeran tsuguno zatayi alwala ta mik'e cikeda farinciki ta rungumosu tana dariya. Laurat da Inna suka fito suka musu sannu da zuwa. Sosai Ummy taji dad'i da suka fad'a mata nan zasu zauna ayi biki. Inna ma tayi farincikin zuwansu musamman data lura yaran wayaiyu ne kuma sunada tarbiya. Dakyar suka matsa ma Ummy a daran suka kakkai ma k'awayenta dake layin kati, da kuma maza wad'anda suke abin arziki lokacin da take saida Awara. Laurat ta d'iba taba Bahar dan ya rabama nasa abokanan da kuma 'yan uwa da abokan arziki. Ranar da daddare Ummy ta k'uduri niyan kiran Bilal dan suyi shawaran abinda za'ayi, dan yace mata kada ta k'ara nuna ma kowa bata san auren. Bayan kowa yayi bacci ta lalubo numbern Bilal d'in ta danna kamar yanda Laurat ta koya mata. Ringing biyu ya d'auka, sallama ta masa ya amsa a dak'ile "Ina yini Ya Bilal" "Lafiya lau ya shirye shiryen biki" Ta d'anyi Jim batace komai bah "Na lura duk fad'in sanda kike min k'arya neh. Har yana kawo miki kati kuna rabawa." "Wallahi ba haka baneh Ya Bilal ni..." Yayi saurin katseta da cewa "Ba abinda zaki fad'amin Ummy! Nagode da yaurada ta da kikayi" "Dan Allah ya Bilal kayi hak'uri, wallahi ina sanka karka min haka" "Inda kina sona da baki kai har yau da auransa a kanki bah. Nayi dana sanin baki amanar zuciyata Hrt, ashe bazaki iya amanar da kika d'aukan min bah" Kuka ta fashe dashi ta k'ara rik'e wayan sosai a kunnenta. Shima kukan yake a hankali "Bazan tab'a rayuwa bake bah. Sai na nuna ma Jamaludeen kuskurensa na san abinda nakeso" Kan tayi magana ya kashe kiran. Da kuka ta sake kira anma taji switch off. Kuka ta fashe dashi ta kwanta tana kuka sosai. Haka ta tashi washe gari da kumburaren fuska, Kallo d'aya Inna ta mata ta gane kuka tayi. Fad'a sosai ta mata dan tasan bai wuce akan maganan Bilal. Wuraren k'arfe takwas na safe suka bar gidan, Gyallesu suka nufa gidan Lalle, an rangad'a mata lalle kyan gaske da gyaran jiki, suma k'awayen amaryan an musu mai kyau duk sun fito tsaf abinsu. Twins ne suka biya cikin kud'in da Ram ya basu jiya. Sannan suka zarce Kanuri beauty saloon, nan ma aka gyara musu gashin su, su twins sai santin yawan gashin Ummyn sukeyi. Basu bar wajan Saloon d'in ba sai k'arfe biyu da rabi na rana, dan ma Dinnern k'arfe shidda ne. Kasuwa suka shiga suka sai abubuwan da zasuyi anfani dasu na walimar su sannan suka dawo gida a gajiye. Reedah makeover su twins suka gaiyato ta rangad'a musu kwaliya mai kyan gaske, black gown amarya ta saka, aka d'aura mata White head. Kar kuso kuga Ummy ni kaina sai dana yaba abinka da farar fata sai Gowm d'in ya fito da ita sosai. Su Twins dama sun musu d'inki su da Laurat, suma sunyi kyau cikin Milk Gown da Red head. Kan kace me gidan ya cika da k'awayen Ummy dukan su cikin shirin zuwa dinner. A chan gida kuwa rigima ce ya b'alle tsakanin Jamal da Amaryar tasa Mabrookah. Ummy Abduol✍🏻 [3/12, 9:45 PM] ‪+234 903 823 4806‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 36 A Chan gida kuwa rigima ce ta b'alle tsakanin Jamal da Amaryar tasa Mabrookah, lokacin da taji cewa shi da abokansa ne zamu je d'aukan Ummy Itama kwaliya taci cikin Brown Gown mai tsadar gaske da milk head, tayi kyau itama sosai, k'awayenta kuma suna sanye da red gown suma duk sunyi kyau. Ana gama shiryata ta shiga side d'in Abba dan a nan Jamal d'in yake, ko kallon abokanan angon dake nan falo batayi ba ta shiga bedroom d'insa. Tsaye ta samesa yana sanya agogo, shima yayi matuk'ar kyau, yana sanye da Arsh d'in shadda sai zuba k'amshi yake. "Haba Jamal! Ya za'ayi kace ni Mifzal ne zai d'aukemu ita kuma kai da kanka zaka je ka d'auketa" Juyowa yayi ya watsa mata mummunan kallo "Saboda ita Matata ce, hakk'inta tun sati hud'u da suka wuce ya dawo wuyana" "Wannan ai ba adalci bah, kamar yanda take matarka haka nima nake matarka" Ya tako zuwa gabanta yana cigaba da kallanta "Har yau ke ba matata bace, saboda ba'a daura bah. Idan kuma na k'arajin wani magana sai na fasa auren muga tsiya" Ya nuna mata k'ofa "Fitar min daga d'aki" Fuuuuu tabar d'akin rai b'ace kamar ta fashe da kuka. Wayansa dake kan bedside ne ya soma ruri, ganin numbern Najma yasa ya saki murmushi ya fito ya samu abokan nasa. Shi da Ram ne suka nufi gidansu Ummy, da kuma wasu daga cikin abokansa dan d'aukan sauran k'awayen Ummyn. Mifzal kuma dasu Taseem zasu d'au Mabrookah da k'awayenta. Daidai k'ofar gidan Inna sukayi Parking, numbern Najma ya soma kira ta d'auka tana cewa "Haba Ya Jamal tun fa d'azu muke jiranku" Saida yayi dariya sannan yace ku fito muna k'ofar gida. Najma ta gyara ma Ummy head d'in kanta tareda rik'o hannunta "To ku muje suna k'ofar gida." Ummy tad'an zaro ido tana kallan Laurat tana yatsine fuska "Ni fa wallahi wannan dogon takalmin ya isheni" "Haba karki badamu mana" Cewar Najwa. Najma na rik'e da hannunta har suka fito daga gidan, sauran k'awayen na take musu baya. Ram ya fito dasauri ya bud'e mata baya inda Jamal ke ciki, ba musu ta shiga ta sadda kanta k'asa ganin Jamal a cikin motan. Laurat ce ta shiga gaba, su Najma kuma suka shiga sauran motocin suka d'au hanyan Hall d'in da za'ayi dinnern. Tunda Ummy ta shiga ba abinda Jamal keyi sai aikin kallanta yana murmushi, kunya ne ya lullub'eta ta k'ara sadda kai k'asa tana wasa da clutch d'in hannunta. Hannunta ya kamo ya had'a da nashi ya d'an matse kad'an, kokarin k'wacewa ta soma yi. Yasa d'ayan Hannunshi ya d'ago fuskanta. Dasauri ta runtse ido saboda kunyarshi da taji tana ji sosai, motsowa ya sake yi har suna gugan juna, yakai bakinsa saitin kunnenta ya rad'a mata "Kinyi kyau sosai Pearl" Ta saki d'an murmushi har lokacin idanunta a lumshe. D'agowan da zaiyi suka had'a ido da Ram dake kallansu ta mirrown gaban motan "Ka kalli gabanka dai banasan gulma" Dariya Ram kawai yayi ya cigaba da driving suna hira da Laurat. Wayan Jamal ne yayi k'ara yasa hannu ya ciro, ganin Mifzal ne yasa ya d'auka ya kara a kunne "Mifzal ya akayi" Daga chan b'angaren yace "Wai kuna ina neh, muna fa nan k'ofar hall d'in tun d'azu muna jira, ga kuma Amaryar ka nan sai masifa take dan Allah kuyi sauri" Tsaki yaja sannan yace "Ba sai taita yi bah, ko so take muyi tsintsu muzo" Ya kashe wayan tareda sassauta rik'on dayama Ummyn, tana ganin haka ta zame dasauri ta matsa gefe. Su Aunty Faty dasu Mami da Aunty Zainab da sauran 'yan uwa da abokan arziki duk suna cikin Hall d'in da za'ayi Dinnern. Jin har lokacin Jamal bai tso ba yasa Aunty Faty ta had'e rai kamar zatayi bindiga, Mami ma ranta ya b'aci sosai da jin Jamal d'in ne da kansa yaje d'auko Ummyn. Basu iso wajan ba sai k'arfe bakwai da rabi lokacin har Mabrookah dake cikin mota ta gaji da jira. Ram na parking ya fito, Laurat ma ta fito. Najma ce ta bud'e side d'in da Jamal d'in ke ciki, Taseem kuma ya bud'e na amarya. A tare suka fito, Ummy kanta a k'asa kunya sosai ya rufeta musamman ganin Flash lights d'in cameras daban daban dake ta d'aukan su hoto. Laurat tayi saurin rik'e mata hannu ta jata zuwa inda Jamal d'in ke tsaye, Mabrookah ma ta fito itada k'awayenta, A tare suka soma jerawa Ummy na'a gefen damansa, shi yana tsakiya Mabrookah na gefen hagunsa. A bayansu K'awayen Mabrookah ne da abokan Ango sai su Najwa da Laurat. Nan da nan wajan ya d'au tafi, wajan zamansu da aka tanada dominsu suka zauna. Sosai Couples d'in sukayi kyau su duka, bama kamar Jamal da Ummy duk wanda ya kallesu sai ya k'ara kallansu. 'Yan jarida da masu hoto sai d'aukansu suke, hakan ba k'aramin bak'anta ran Mabrookah yayi bah. Bayan anci ansha aka umarci Amare da ango su taso su d'an taka. Wuf Mabrookah ta mik'e Ummy ko kasa tashi, Jamal ya rik'o hannunta ya d'agata, kanta ta sauke k'asa duk jinta take a takure a wajan. Hannunta ya kama sannan ya juya ya fizgo na Mabrookah suka sauko daga step d'in dake wajan. Wak'an su Psquare bank alert ke tashi, Mabrookah ta zage sai rama take, itako Ummy tsaye ta tsaya dan ita bata iya rawa bah koma ta iya bazata iyayi a gaban mutane bah. Jamal na yana d'an rausaya wa a hankali yana bin wakan dan yana san wakan sosai. Hannun Ummy ya kamo ya matso da ita sosai kusada shi, hannayenshi biyu yasa a k'ugunta ya zagaye yana cigaba bin wak'an yana murmushi. Ba k'aramin burge mutane sukayi bah, kan kace me wajan ya cika da 'yan lik'i sai ruwan nerori ake musu. Ran Mabrookah idan yayi dubu ya b'aci, dakyar Ummyn ta iya sa hannu ta ciro kud'in daya basa ta masa lik'i saboda kunya. Sanda akazo yanka cake ma saida Mabrookah tasha haushi. Anci ansha tareda raba kyaututuka masu yawa sannan kowa ya kama gabansa. Kamar wanchan lokacin Jamal da Ram ne suka maida Ummy gida da k'awayenta. Ita kuma Mabrookah Taseem ya maida ta gida. Washe gari kuma kamu, shima Anyi shagali kamar ba gobe, anyi taro lafiya an tashi lafiya duk da su Aunty Faty ransu a b'ace yake da ganin rashin kunyan da Jamal keyi k'iri k'iri yana nuna banbanci tsakanin Ummy da Mabrookah. Bayan an dawo Kamu su Ummy suka koma gidansu dan washe gari za'a kaita. Sai a lokacin Ummyn kejin Abba yace ya d'auke musu yi mata kayan d'aki shi zai yi mata komai. Tun a ranar ta soma kukan rabuwa da Mamanta da kuma Sahibinta Bilal. A ranar sati duban jama'a suka shaida d'aurin auren Jamaludeen Surajo da Amaryar sa Mabrookah Ismail a bisa sadaki dubu d'ari. Ango yayi kyau cikin farar shadda d'an daidai shi, rigan iya guiwa dan yace shi baya isa saka babban riga. Fuskan shi ba yabo ba fallasa, sai dai ta wani b'angaren yana farinciki mara misaltuwa idan ya tuna da Ummyn shi. Bayan an d'aura aure akayi k'asaitaciyar walima a nan harabar gidan. Sannan kowa ya kama gabansa. Bayan Magriba ana shirye shiryen d'auko Amarya Ummy Abba ya kira Jamal d'akinsa. "Jamaludeen!" Ya d'ago ya kalli Abba tareda amsa wah "Yanzu ka shiga wani rayuwa na daban, ka zama babban mutum, inaso ka kasance mutum mai adalci tsakanin Iyalinka. Karka zama mai yawan sa ido, sannan kada ka fifita d'aya ka bar d'aya" Kan Jamal k'asa yace "Insha Allahu" Key Abba ya mik'a mai da takardu yace "Wannan keyn gidan ka ne na baka halak malak, saidai inaso ku fara zama a nan gidan saboda naga kamin ludayin zaman naku" Godiya sosai Jamal yayi masa kansa k'asa. Abba ya nisa yace "Akwai wani sirri dayake cikin zuciyata wanda nake son sanar dakai tun ba yau bah, nasan...." Mami ta shigo falon a fusace tama cewa "Wallahi abinda kakemin Alhaji banajin dad'in shi" Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Miss Eshaa* na baki wannan shafin kyautah Page 37 n 38 "Wallahi abinda kakemin Alhaji banajin dad'in shi" Abba da Jamal suka d'ago suna kallanta, kusada Abba ta zauna ta cigaba da cewa "Haba Alhaji, meyasa kake zartar da hukunci ba tareda ka tambayi ta bakina bah, kamar yanda kake da iko da Yaran nan naka nima tunda ni ce uwarsa" "To me kuma akayi Maimuna" "Meyasa zakace bazasu zauna a sabon gidasu bah sai a nan" Abba yayi murmushi yace "Uwargida sarautar Mata, to maida wuk'ar, ai ba wani abu nace bah. Inaso ne naga kamun ludayin zaman nasu sannan sai su koma nasu gidan" Shiru tayi tana turo baki Jamal ya mik'a mata takardun gidan da Abba ya basa harda makulle yana cewa "Mamina ki tayani farinciki, Abba ya bani gida" Nan da nan b'acin ran Mami ya kau ta soma murna tana "Ah! Lallai Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i" Takardan ta amsa tana dubawa tana farinciki. Abba ya kalli Jamal dake durk'ushe har lokacin yace "B'angaren chan na k'arshe a nan zaku zauna, komai na buk'ata akwai. Sannan ita Ummy tana sama tunda itace Uwargida, ita kuma Mabrookah tana k'asa" Kanshi k'asa ya amsa tareda godiya. Mami ta mik'a masa takardun ya mik'e ya fita. Wayanshi ya ciro a aljihu dan yana silent, nan yaga missed calls d'insu Ram dayawa. Murmushi yayi ya fita haraban gidan, nan fa suka masa cha, shidai baice komai bah saima Taseem daya kalla yana cewa "Yanzu dan iskanci ace har k'arfe takwas baku je d'auko min amarya ta bah" "Kuji mana wannan guy d'in, tun d'azu fah muke jiranka a nan ka bamu go ahead" cewar Mifzal. "To shikenan kuje, Anma Ram nasan kai ba hankali ka cika bah, ka d'auko min matana a hankali banasan tafiyar ganganci" Tunda ya fara magana Ram ya saki baki yana kallansa har ya gama. K'wafa yayi ya shiga motarsa, sauran ma duk suka shishiga suka d'au hanyan gidansu Ummy. Tun bayan la'asar Ummyn ta dawo gidansu tana kukan rabuwa da Mamanta. Wani sabon kuka ta saki lokacin da aka kaita gaban Maman nata dan ta mata fad'a. Kuka ne ke k'okarin kufce ma Maman, dakyar ta daure ta mata nasiha mai ratsa jiki, gidansu Bilal aka kaita, Itama Inna ta mata nasiha sosai sannan aka fito da ita. Suna shiga cikin gida su Ram suka iso k'ofar gidan. Wani sabon kuka Ummy ta kece dashi tana kokarin turjewa daga rik'on da Inna ta mata, da k'arfi ka kwace ta shiga ta rungume Mama tana kuka sosai "Mama idan na tafi wa zai kula dake, dan Allah kar ki bari a tafi dani" Duk dauriya irin ta Mama saida tayi k'walla tana shafan k'an 'yar nata "Allah na tare dani Ummy. Darajar Mace gidan mijinta, ki tafi gidanki. Ina miki fatan Alheri Ummy" Ummyn ta sake rushewa da kuka, dakyar aka samu aka b'anb'areta daga jikin Mama tanata kuka, Inna da kanta ta sakata a mota itama ta shiga dan Mama ta bata amanar 'yar nata tun bayan rasuwan Baba. Su Twins da Laurat duk motan Abdulhakam abokin Jamal suka bi da kuma sauran 'yan uwa da abokan arziki. A jere motocin suka shigo cikin gidan, wani malalacin murmushi Ram ya saki sanda ya hango Jamal tsaye chan wajan garden ya kasa ya tsare. A k'ofar side d'in Mami Ram yayi parking, Inna da kanta ta fito rik'e da hannun Ummy bayan ta gyara mata lulub'in dake kanta. Jagora Aunty Zainab ta musu har zuwa d'akin Mami. Bayan an gaisa Inna ta damk'a amanar Ummy a hannun Mamin, ba yabo ba falasa Mamin ta amshe su tareda adduan Allah basu zaman Lafiya. Suna fitowa aka musu jagora zuwa side d'in da zasu zauna, koda suka shiga sun samu mutane a ciki da alama an kai Mabrookah neh. Aunty Zainab ta musu jagora zuwa sama har d'akin Ummyn. 'yan kai amarya sai santin gidan suke dan Abba ya kashe kud'i sosai wajan k'awata musu b'angaren nasu da funitures masu kyau. Tareda kayan kicin masu tsada da kyan gaske. Da kuka Ummy ta rabu da Inna bayan ta k'ara mata nasiha sosai. Ya rage daga ita sai su Twins dan tunda aka kawo Ummyn Laurat ta sulale ta koma bakin aikinta. Hira Twins keta Jan Ummyn dashi anma hankalinta baya wajansu sai neman wayan Bilal take switch off. Takai awa d'aya tana kira baya zuwa, wani kuka ne ya kufce mata ta kife kan makeken gadonta tana kuka sosai. Najma ta soma lallashinta anma kamar k'ara zugata take. Suna cikin haka aka turo k'ofar d'akin, Najma da Najwa suka d'ago suna kallan k'ofan. Wasu 'yan mata ne suka shigo su uku suna bin d'akin da kallo tareda yatsine fuska, Najma uwar rashin hak'uri tace "Lapia malamai kuka shigo mana d'aki bah sallama" Ba wacce ta tanka ta sai zagayen d'akin da sukeyi suna cigaba da yatsine fuska, Ummy ta d'ago tana binsu da kallo har lokacin k'walla na gangara a idonta. "Warning mukazo mu baki, karki sake ki shiga harkan Mabroo dan ba sa'arki baneh" cewar d'aya daga cikinsu "Dalla malamai ku fitan mana daga d'aki, kun shigo sai warin gardi kuke ga wani shegen attachment sai d'oyi" Cewar Najma A harzuk'e d'aya daga cikinsu ta nufota tareda chakume mata gaban riga, ganin haka yasa Ummy sake rak'ubewa tana zubar da kwalla Ta cigaba da cewa "Ke kinsan mu waye da kike gaya mana magana" Najwa itama ta mik'e rai b'ace tace "Karuwai mana dan bakuda banbanci dasu, wallahi kiyi maza ki sakar min 'yar uwa idan ba haka ba nayi maganinki" D'aya daga cikinsu ta janye hannunta daga gaban rigan Najma tana cewa "Karki biyema wad'an nan yaran kuzo muje kawai" Ta kama hannunta da d'ayar suka bar d'akin rai b'ace. Najma tace "Lallai Wallahi Ummy sai kin dage" "Ni Wallahi tausayi ma ta soma bani" cewar Najwa tana kallan Ummy daketa zubar da k'walla. Suna nan zaune har wuraren k'arfe goma, da wayo suka sulale suka bar Ummyn tana sharb'ar Hawaye. A bangaren Ango Jamal kuwa yana falon side d'in Abba shida abokansa, lokaci lokaci yakan kalli Rolex d'in hannunsa yana d'an tsaki a hankali, duk abinda yake Abduolhakam abokinsa na lura dashi, shi ya fara mik'ewa yace "Kai ku tashi mukai angon nan dan naga alamun idan bamu kaisa ba za kai kansa neh" Ram yad'an b'ata fuska yace "Wajan wa za'a kaisa tho" Karaf Jamal yace "Wajan Baeby na mana, kasan itace uwargida tunda ita na fara aure" Dukansu suka saki baki suna kallansa da mamaki "Ya da kallo" Ya mik'e yad'au ledan dake kusada Mifzal yace "Dallah ku taso muje" Shine a gaba suna binsa a baya sai tsiya suke masa shi dai baice komai ba sai murmushin da yake. A hankali ya tura k'ofan d'akin ya shiga da sallama, wani sanyaiyar k'anshi ne ya musu sallama, Ya matsa dasauri Taseem ya soma shiga sannan Mifzal sai Jamal d'in da kuma sauran abokanan nasa. Tana kwance tana aikin kuka taji sallamansu, dasauri ta mik'e ta gyara zama tareda gyara zaman gyalenta. Ram na shiga ya baje k'asan tiles d'in d'akin "Wash! Nidai na kama gurin kwana" "Aina!" Jamal ya zaro ido daidai lokacin daya zauna kusada Ummyn "A nan mana" Harara ya wurga mai, Mifzal yace "Sannu amarya bah magana" Shiru batace komai ba sai sheshek'an kuka da yake a hankali "Taya amarya zata maka magana ba'a sayi baki bah" cewar Taseem yana kallansa. Mifzal yace "Au haka neh fah" Yasa hannu a aljihu ya ciro rafan y'an d'ari biyu ya aje mata a kan gadon. Duk da haka dai bata iya cewa komai ba har lokacin kuka take a hankali wanda Jamal d'in kawai ke jiyota. Shakiyancin sukayi tayi sannan suka musu sallama suka tafi. Har bakin motocin su Jamal ya rakasu sannan ya dawo. Harya haura sama ya dawo yana tab'e baki ya nufi d'akin Mabrookah. Kan gadonta ya sameta tana sanye da wasu fitinanun night wears. Gabansa na ya fad'i ya kauda kai tareda k'arasawa bakin gadon "Haba Mijina tun d'aku fa nake jiran shigowanka naji shiru kuma bayan naji hayaniyarku" Ta matso kusada shi tana san manna jikinta da nasa, dasauri ya janye jikinsa yana yatsine fuska "Nazo ne naga lafiyarki, sannan na shaida miki yau a d'akin Ummy zan kwana tunda ita ce babba, ita..." "Haba Ya Jamal wanne irin magana kakeyi, ni fa matarka ce kamar yanda take matarka" "Anma kinsan dai saida aka fara d'aura aurenmu sannan aka d'aura naki koh" Turo baki tayi tana bubuga hannuwanta akan gadon alamar shagwab'a. A hankali yace "Saida safe koh" Ya mik'e tai saurin rik'e gefen rigansa tana magana cikin shagwab'a "Ina wai zaka ni fa wallahi tsoro nakeji" Janye rigansa yayi ya hasale yana kallanta "Da dakike kwana ke kad'ai meya kamaki" Yad'anja guntun tsaki ya bar d'akin dasauri. Sama ya haura zuwa d'akin Ummy, yanda ya barta haka ya dawo ya sameta saidai yanzu ba kuka take ba sai ajiyar zuciya datake saukewa lokaci zuwa lokaci. Kan gadon ya zauna ya matso kusada ita tareda sa hannu ya janye mayafin dake kanta. Kawar da fuska tayi dasauri, yayi murmushi tareda d'ago fuskanta da hannunsa. Ta lumshe ido dasauri hawaye suka gangaro daga idanunta "Oh God! Ya zanyi dake Baeby, dan Allah ki daina kukan nan. Bud'e idanunki ki kalleni" Bud'e idon tayi a hankali ta sauke su k'asa ta fashe da kuka. Batareda b'ata lokaci bah ya rungumota jikinsa yana shafa bayanta a hankali, turesa ta soma yi tana kuka mai sauti "Meye haka ka sakeni banaso" Janye jikinshi yayi daga nata yana kallanta da narkakun idanunsa "Ni mai sanki neh, i so much love uh Baeby, pls karki ce baki sona dan zan iya shiga damuwa mai tsanani. Ina sanki sosai" Ta d'ago jajayen idanunta tana kallansa da kuka "Idan nayi haka na karya alkawari, Ya Bilal ya sadaukar da abubuwa da dama dan rayuwata dana iyayena su inganta, ya..." "Pls wannan maganan ya wuce, i know nafi shi sanki" Ta d'ago jajayen idanunta ta zubasu kan nashi "Babu namijin dake sona kamar Ya Bilal, shine wan..." Saurin katseta yayi tareda saukowa daga kan gadon "Ki aje a ranki ni mai sanki neh, kisa a ranki ni mai baki farinciki neh. Bandamu da ko ki soni bah, sanda nake miki ya ishemu. And pls ki daina min maganan Bilal hakan na k'ona raina" Bai jira mai zatace ba ya bar d'akin zuwa nashi dake nan saman. Ummy Abduol✍🏻 [3/22, 5:21 AM] 0mmer Farouk: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 39 Bai jira mai zatace ba ya bar d'akin zuwa nashi dake nan saman. Kuka Ummyn ta fashe dashi tana dukan gadon da duk iya k'arfinta, tana cikin kukan bacci mai nauyi ya d'auketa nan kan gadon. Jamal ko bacci ne yayi k'aura daga idonsa, sosai hankalinshi ke tashi a duk lokacin da Ummy ta ambaci sunan Bilal. Kukansa ya soma kaiwa wajan ubangiji sai gefen asuba sannan ya samu bacci ya d'aukeshi a kan sallayan. Da safe da wuri Ummy tayi wanka ta gyara d'akinta tsaf da toilet dan tasan a aladar hausa washe garin da aka kawo amarya anayin bud'an kai. Hakan ce ko ta kasance, 'yan uwanta da abokan arziki duk sunzo da kayan lefenta sai gara da Baba sallau da Baba Tanko suka mata wanda bai taka kara ya karya bah. Ango Jamal bai farka ba sai k'arfe shad'aya ta kwata na safe, shima hayaniyar jama'a ce tasa ya farkan. "Subhanallahi!" Ya fad'a ya mik'e dasauri ya fad'a toilet, wanka yayi tareda d'auro alwala ya fito ya tada sallah. Yana idarwa ya shirya cikin bak'in yadi mai sharashara, d'inkin rigan daidai guiwa, sosai kayan suka fito da kyansa saidai kalli d'aya zakama fuskansa ka gane yana cikin damuwa. Had'adiyar Lace Ummyn tasa cikin na kayan lefenta, Najwa ce tayi mata makeup tayi kyau sosai, Itama Amarya Mabrookah ta had'e cikin atampa lemon green d'inkin dogon riga, fuskan nan nata yasha heavy makeup har tayi wani iri kamar aljana. Anyi bud'an kai lafiya tareda walima, ango na side d'in Abba shida abokansa suna hira, wayansa ne yayi k'ara alamar sak'o, bak'uwar number ya gani ya bud'e ya soma karantawa kamar haka _Kada ka tab'a tunanin dan an d'aura maka aure da Ummy hakan na nufin ka sameta, Ni Bilal indai ina raye baka isa ka mallaki Ummy ba saboda tawa ce! Kana wahalar da kanka a inda ba'a sonka ba'a muradinka. Kayi gaggawan rabuwa min da matata dan babu mahaluk'in daya isa ya rabani da ita sai Allah_ Wani guntun murmushi Jamal ya saki duk da cikin zuciyarsa yana fargaban abinda zaije yazo. Haka ya zauna sukuku kamar mara lafiya har yanma. Bayan kowa ya watse da daddare bayan isha'i ya shiga ya gaida Abba dasu Mami sannnan ya nufi side d'inshi, kamar jiya yauma d'akin Mabrookah ya soma shiga, zaune take kan gado cikin wasu arnayen kayan bacci, kallo d'aya ya mata ya kauda kai. Baisan meyasa ba Sam Mabrookah bata burgeshi, shishige mai ta soma ya mik'e a fusace yana hararanta ya bar dakin. Kamar zai shiga na Ummy sai kuma ya fasa ya shiga d'akinshi. Itako Ummy tana chan d'aki zaune shiru abin duniya ya isheta. Dakyar ta mik'e ta shiga toilet tayi wanka ta sauya zuwa na bacci ta kwanta. Washe gari monday da wuri yayi wanka ya fito cikin shirisa na fita aiki, d'akin Ummyn ya kalla sannan ya sauko k'asa Nan kan dinning d'in k'asa ya tarar da Mabrookah tana breakfast, a hankali ya k'arasa ya zauna. Ta kalleshi tareda tab'e baki tace "Ina kwana!" "Lapia" yace ta takaice yana bin abincin da takeci da kallo, ganin haka yasa tace "Mami ce ta aiko dashi, na zuba maka neh" Yad'anyi jim sannan yace "Ni ina azumi but ki zuba Ummy, koda yake kirata inasan magana daku" Fara'ar dake fuskanta ya kau ta had'e rai tana murgud'a baki "Haba Ya Jamal ni ne zan kirata" Wani mugun kallo ya bita dashi ta mik'e tana turo baki ta haura saman, kamar yanda ta saba shiga mata d'aki a wulak'ance haka yauma ta shiga, zaune ta sameta kan gado tayi tagumi "Keh ki fito mijina na kiranki" D'an d'agowa tayi tana kallanta, a sanyaye ta mik'e tabi bayanta har k'asan, kamar yanda Mabrookan ta barshi haka ta dawo ta sameshi zaune, kujera Mabrookah taja ta zauna, ganin haka itama Ummyn taja ta zauna kanta k'asa. Gyaran murya yayi yace "Banasan tashin hankali, inaso ku zauna lafiya." Ya juya ya kalli Mabrookah data turo d'ankwali gaba yace "Kece k'arama dan haka bansan rashin kunya ko..." "Tab! Haba Ya Jamal wannan ai cin fuska neh, Kasan dai nesa ba kusaba na girme tah" Harara ya watsa mata yace "Ai ko jiya aka haifeta matsawar saida aka d'aura aurena da ita kafin naki to itace babba" K'ara turo baki Mabrookan tayi dan maganarsa sosai ya b'ata mata rai. Itadai Ummy batace komai ba kanta k'asa tana wasa da zoben hannunta. "Banasan hayaniya, kowacce ta kama girmanta. Kada naji wani abun da ba daidai bah" Yanda yake maganan yana kallan Mabrookah yasa ta gane da ita yake "Duk maganan nan da kake nasan dani kake tunda ni kake kallo" cewar Mabrookah Jamal yayi murmushin takaici ya juya ga Ummy yace "Jaleelah!" D'ago ido tayi da mamaki tana kallansa, ba wasa a fuskanshi yace "Ina fata kinji abinda nace" Kai ta gyad'a alamar eh hawaye cike a idonta, wato shi yana ma nufin zata dauwama a gidan kenan. "Kamar yanda aka saba a aladance, tunda Ummy ce babba, ita zan farama kwana bakwai sannan na dawo d'akinki" Ya nuna Mabrookah fuska ba walwala "Anma dai kasan kaci kana biyu koh" "Nasani ai ba bansani bah." Ya fad'a rai b'ace "Sannan ina gama kwanakin da zanyi a d'aku nan ku za'a fara raban kwana" Dogon tsaki Mabrookah taja tad'au handbag d'inta ta fita dan dama da shirin tafiya makaranta take. Zaman kurame sukayi a kan dinning d'in har lokacin kanta k'asa, murya kamar mai rad'a yace "Serve me" Ta d'an d'ago suka had'a ido ta maida kai dasauri, sun kai minti biyar a haka gashi ya fara latti, ya sake d'agowa yace "Na fara latti kuma yunwa nakeji" Ta sake d'agowa ta kalleshi tana b'ata fuska "To mai zan maka" Ta fad'a tana turo baki a shagwab'e "Serve me" Ya sake cewa yana kallanta da narkakun idanunsa "Ni fa bajin abinda kake cewa nake bah, kamin da hausa" Sai a sannan ya tuna da rashin makarantar da batayi bah. Yad'an dafe goshi yace "Serve me yana nufin ki Ciyar dani ko ki zubamin abinci. Duk wanda kika d'auka a ciki" Ta gyad'a kai tana d'an murmushi dan a rayuwarta ba abinda takeso kamar yau taji tanayin turanci. Abincin ta zuba mai ta tura masa gabansa, ya kalli abincin ya d'ago ya kalleta "Wannan abincin da kika zubamin kamar mu goma zamuci" Turo baki tayi ta juya zata bar wajan yayi saurin rik'o hannunta yace "Ai baki isa bah, sai dai ki zauna muci tare dake" Ta soma kici kicin k'wacewa tana k'okarin kuka. Saurin janyota yayi jikinsa ya matseta yana kallan fuskanta "Na gaji da shiru shirunki Baeby, na gaji da kukanki, na gaji da rashin maganarki" Duka ta soma kai mai a k'irji tana kuka sosai "Ni ka sakeni, ka sakeni ko na maka ihu" "Ki natsu Baeby muyi magana" Turjewa ta cigaba dayi tana kuka "Pls ki daina kuka ki tsaya ki saurareni" Rik'on daya mata ya sassauta yana kallanta "Meyasa baki sona Jaleelah, meyasa baki son zama dani? Meyasa kike guduna? Mena miki" Batace mai komai ba sai duk'ar dakai datayi tana kuka "Bani amsa pls, ba kuka zakiyi bah." Murya na rawa tace "Ni kawai bana sanka neh" Gabansa ne ya fad'i, kwalla suka cika idonsa ya d'ago yace "Saboda me baki sona" Shiru tayi ba amsa sai kuka dake. Wani wawan rik'o ya mata har saida ta saki k'ara, gaba d'aya fuskarsa yayi ja saboda b'acin rai "Tel me meyasa baki sona" "Saboda nama Ya Bilal alk'awarin zan aureshi" Hawayen dake mak'ale a idonsa suka gangaro, ya sake matseta a jikinsa tareda d'ago fuskanta suna kallan juna ido cikin ido "Kar kimin haka Jaleelah, ina sanki kamar raina" Yakai hannunta kan k'irjinshi "Kinji yanda zuciyata take bugawa akan sanki, plssssss" Sosai ya bata tausayi ta tureshi da k'arfi tana cewa "Taya zan iya sanka bayan Mami bata sona, Mabrookah bata sona, dan Allah ka taimakeni ka sakeni wallahi bana san zama dakai" Ta fashe da kuka ta juya ta soma hawa sama, jin muryan Jamal tayi yana cewa "Saki kikeso Ummy?" Ta juyo ta kallesa ta gyad'a kai a hankali, wasu hawaye suka gangaro masa yasa bayan hannu ya share yace "Zan sakeki Ummyyy.... ```Zakuyi hak'uri da yanayin typing d'ina da kuma jinkirin posting. Abubuwa ne kwana biyu suka min yawa. Dafatan zaku karb'i uzuri nah``` Ummy Abduol✍🏻 [3/22, 5:21 AM] 0mmer Farouk: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 40 "Zan sakeki Ummy anma dan Allah kiyi hak'uri ki bani lokaci" D'ago ido tayi a razane tana kallasa gabanta ba fad'uwa. Bai sake kallanta ba ya share hawayen fuskansa ya d'au jakansa ya bar wajan. Ba shiri ta sulale a wajan ta fashe da matsanan cin kuka. Ta dad'e a wajan tana kuka Laurat ta shigo side d'in da sallama, ganin Ummyn zaune a wajan tana kuka yasa ta k'arasa dasauri ta d'agota tana tambayanta "Laurat Ya Jamal zai sakeni" "Mene?" Cewar Laurat tana zare ido Kasa magana tayi sai k'ara rushewa da kuk datayi ta mik'e ta haura sama zuwa d'akinta tana cigaba da kuka. A sanyaye Laurat ta mik'e tabi bayanta, kwance ta sameta tana kiran wani number ana ce mata a kashe anma bata fasa kira bah. Saida ta k'araso kusada ita sannan ta hango ashe Bilal take kira. A fusace ta fizge wayan tana kallanta rai b'ace "Haba Ummy meyasa kike haka? Yakamata ki cire Bilal a ranki tunda yanzu ke matar aurece. Ki d'au kaddara kibi mijinkin insha Allahu zakiji dad'i a rayuwarki nan gaba" Ummy ta d'ago hawaye chab'e chab'e a fuskanta tana kallanta "Alkawari fa na d'auka Laurat, karki manta da girman alk'awari" Haushi Ummyn ta soma bata, batasan sanda tace "Alkawarin banza, to ai shi ya fara karya alk'awarin bake bah. Da yana sanki da gaske bazai je ya zauna abinsa bai waiwayi inda kike bah. Kinsan girman zunubin da kike kwasa kuwa Ummy? Kina da miji anma kina tunanin wani" Shiru tayi tana nazarin maganar Laurat "Haba Ummy sai kace baki je bah, karfa ki manta hukuncin macen da tace mijinta ya saketa" Gabanta ya fad'i sam ita batayi tunanin wannan bah. Wani kukan ta sake rushewa dashi ta kama hannun Laurat tana kallanta "Ya kikeso nayi Laurat, ina cikin tsaka mai wuya. Bansan me zanyi bah, gaba d'aya komai ya tsaya min" "Kibi mijinki Ummy shine kawai, Wallahi na rantse kuma bazanyi kaffara bah, Alkhairi ne aurenki da Jamal a yanda na lura. Kiso mijinki, ki janyoshi a jiki, ki basa kyakyawar kulawar daya kamata. Karki bari Mabrookah ta miki tsakiyar da ba ruwa" Ta sake yin shiru tana tunani, tabbas maganar da Laurat ta fad'a mata gaskiya ce, saidai matsalar duk lokacin da tayi yunk'urin yin haka saita kasa. "Ya zanyi Laurat, Ya Jamal yayi fushi dani" "Duk abinda ya faru ke kika ja, kiyi k'okari ki gyara rayuwar aurenki" Ta mik'e dasauri tana gyara rigan jikinta "Barin koma bakin aikina, dan daman satan hanya nayi nazo" Ummy dai ba bakin magana, gaba d'aya hankalinta baya jikinta, tunanin yanada zata b'ullo ma alamarin take. Laurat ta dafata tana cewa "Kiyi tunani akan maganar da namiki, Wallahi harga Allah Jamal yafi sonki, wannan abin da Bilal yayi ma kad'ai ya isa shaidar nuna miki ba mai k'aunarki baneh, ke kad'ai ke wahalar ki" Ta sauke ajiyar zuciya ta soma tafiya tana cewa "Kiyi k'okari ki basa hak'uri, ku zauna lafiya tun lokaci bai k'uremiki bah." Bata jira mai Ummyn zatace ba tabar d'akin dasauri. Kogin tunani Ummy ta fad'a akan maganganun Laurat, tabbas abinda Laurat ta fad'a mata gaskiya neh, anma yanzu ita da wani ido zata kalli Jamal bayan rashin kunyar data gama tata masa. Tana nan zaune d'akin ta jiyo hayaniyar a tsakar gidan, ta window ta lek'a taga Aunty Faty ce da tawagar ta da sukazo biki zasu tafi duka harda ita. Wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ganin Aunty Fatyn zata tafi, saidai kuma idanunta da suka kan su Twins suma tafe kowacce janye da trolley d'inta. Nan da nan hankalinta ya tashi, ta sauko dasauri, a falon k'asa taci karo dasu, Najma tace "Ummy zamu tafi dan Next week zamu koma school" Ta fashe da kuka, ba shiri itama Najma ta fashe da kukan suka rungume juna suna kuka. Sun d'an jima a haka, saida Aunty Zainab tayi kiransu a waya sannan suka sake sallama cikeda kewar juna. Ranar haka Ummy ta wuni sukuku kamar mara lafiya, ko abinci ta kasa ci. Jamal bai shigo gidan ba sai k'arfe tara da rabi, kamar kullum d'akin Mabrookah ya fara shiga tunda itace a k'asa, ya mata saida safe sannan ya haura sama. Duk da yanda zuciyarsa ke zafi akan maganasu ta d'azu hakan bai hanasa shiga d'akin ba. Bacci ya samu tanayi kan sallaya, kanta na kan gado sauran jikinta na k'asa kan sallaya. A hankali ya k'arsa ya kafeta da ido, zufa sosai take dan hijab d'in jikinta babba ne da kauri, Ac ya kunna mata harya juya zai fita sai kuma ya sake waiwayowa ya kalleta na 'yan mintina sannan ya dawo gabanta. Ba tareda b'ata lokaci ba ya d'auketa chak ya d'aurata kan gado yasa hannu ya cire Hijab d'in jikinta yana kallan kyakyawar fuskarta. Wani santa ne ke k'ara shigarshi, a hankali ya lumshe ido ya bud'e ya zubasu akanta. Motsi tad'anyi tareda bud'e idanunta a hankali, ganinsa yasa ta mik'e dasauri, shima yayi saurin mik'ewa yana k'okarin barin d'akin. "Ya Jamal!" Ta kira sunansa a sanyaye kallansa, tsayawa yayi chak anma bai juyo bah. Ba tareda tunanin komai ba ta mik'e ta zagayo gabansa ta tsugunna kanta k'asa dan yanzu ta gane kuskurenta "Dan Allah kayi hak'uri akan abubuwan dana maka insha Allahu bazan sake bah" Sam bazai juri ganinta durk'ushe gabansa bah, ya d'agota dasauri ta hanyar rik'e kafad'unta. Hawaye ya gani suna gangara daga idonta yace "Baki min laifin komai bah, ni ne dai nayi laifi dana ki sakinki. Dan Allah kiyi min afuwa, ina sanki banasan rasa ki Pls" Ta fashe masa da kuka tana girgiza kai "Dan Allah kayi hak'uri karka sakeni, nayi alkawarin zama dakai har abada" Jin maganar yayi kamar a mafarki, ya d'ago idanunsa da suka cika da kwalla yana kallanta baki bud'e "Baeby kece kuwa kikayi maganan nan ko mafarki nake" Kai ta girgiza masa, baisan sanda ya d'auketa chak ya soma zagaye da ita a d'akin ba yana dariyar farinciki, ita kuwa kunya ce ta lullub'eta, ita kanta tasan Jamal mai santa ne saidai kawai matsalar Bilal dake ranta. Ya direta tareda janyota jikinshi yana mai farinciki mara misaltuwa "I love uh so much Ki fad'a me kikeso na miki a rayuwa a matsayin tukwuicin farincikin da kika sani yau" Kai ta girgiza alamar ba komai, ya had'a goshinsu waje guda yana kallanta da murmushi "Tel me and nayi alk'awarin zan miki koma menene matsawar bai fi k'arfina bah" Kuka Mabrookah ta fashe dashi mara sauti wacce ke tsaye bakin k'ofar d'akin tana lek'en su ta ramin makulli tana kallo da kuma jin duk abinda ke faruwa. *Manage this Pls* lokaci ne banda shi kwana biyu Ummy Abduol✍🏻 [3/22, 5:21 AM] 0mmer Farouk: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 42 "Oh Come on bansan kunyan nan, yana tauye ni. Ki saki jikinki pls. I promise to shower uh with my love" Murmushi tayi tana k'okarin kwace kanta daga jikinsa, k'ara rungumota yayi "Kin fara koh" "Dan Allah ka bari" Ya mik'e kafad'a yana turo baki "Aa ni dai bazan bari bah" Turesa tayi dasauri tana mai dariya. Ya rik'e kugu ya d'an had'e rai "Allah koh zaki sani Wife" Dariya ta sake mai ganin yanda yake turo baki a shagwab'e. Biyota yayi ta fito a guje, falon ta sukayi ta zagaye wa tana dariya haka shima. Daidai nan Mabrookah ta hauro zuwa falon dan yau a shiryenta take. Chak ta tsaya ganin abinda sukeyi, sam basu ma lura da ita ba saida Ummy ta banga jeta by mistake, wani lafiyaiyar Mari Mabrookah ta d'auketa dashi a fusace "Keh makauniya ce" Sosai Marin ya shigi Ummy ta soma hawaye tayi dakinta tana kuka, Jamal baiyi wata wata ba ya d'auketa da marin itama "Akan wani dalili zaki dakar min mata" Ya nunata da yatsa yana cewa "Abubuwan ki sun fara kaini bango" Ta chakumi kwallashi ta fashe da kuka "Wallahi baka isa ba Jamal, duk fa abinda kukeyi kallanku kawai nake. Ni dan baka sona shine ka maidani bare" Ransa b'ace yace "Ki sakar min riga" Ta sake rushewa da wani kukan "Bazan saki ba wallahi, kamin laifi ina magana kuma kana k'orafi" Ransa idan yayi dubu ya b'aci, ya sake cewa "Ki sakar min riga Mabrookah, karki bari na nuna miki koni waye" "Wallahi bazan saki ba saidai ka kashe ni" Fizge jikinsa ya soma ta k'ara k'ankameshi tana kuka tareda dukansa "Ni wallahi bazan yarda bah, nima ma matarka ce. Anma akan wannan jakar zak...." Wani marin ya sake d'auketa dashi har saida tayi taga taga zata fad'i, duk da haka batayi shiru bah. Zagi ta uwa ta uba ta dunga d'urama Ummy, nan ko gogan ya sake harzuk'a. Belt d'in jikinsa ya cire ya soma lafta mata kamar Allah ya aiko sa. Saida ya mata ligi ligi sannan ya yarda belt d'in ya shiga d'akin Ummy. Kwance ya sameta kan gadonta tana kuka a hankali, runtse ido yayi cikeda takaicin abinda Mabrookah ta masa, kan gadon ya zauna ya janyota jikinsa ranshi ba dad'i. K'wace jikinta ta soma tana kuka tana fizgewa "Ni ka sakeni!" Ya k'ara rik'eta gabansa na fad'uwa "Haba Wife I'm sorry, pls kiyi hak'uri kinji" Fizgewa ta cigaba tana kukan shagwab'a. "Haba Wife nine fah" Ganin tak'i hak'ura yasa ya d'ago kanta ya had'a bakinsu guri d'aya. Ido Ummy ta zaro kamar na (Hafsat Xaboorah) Lol. Kokarin kwacewa ta soma ya k'ara rik'eta yana kissing d'inta a hankali. Wayansa ne tad'anyi k'ara alamar sak'o, sassauta rik'on daya mata yayi ya ciro a aljihunsa ya duba, murmushi yayi bayan ya karanta, har yanzu ya saba da sak'on nin da Bilal yake turo masa kusan kullum fiyeda sau uku. Fizgewa tayi da k'arfi ta mik'e tana goge hawayen dake fuskanta tana turo baki. Murmushi ya mata ya shafa cikinsa "Yunwa nakeji sosai Wife" Ta turo baki tana kauda kai "Yana dinning" Ya mik'e yana k'okarin k'arasowa inda take, ta matsa dasauri tana masa dariya had'e da turo baki. K'wafa yayi ya shafa gefen fuskanta "Barinyi wanka ina zuwa" Ya fita zuwa d'akinsa dan yin wanka. Mabrookah kuwa dakyar ta tashi a wajan tana kuka sosai, side d'in Abba ta shiga dan tasan by now Mami na chan. A bakin k'ofa sukayi kicibus da Abba yana sauri zaije masallaci, k'asa ta zube gabansa ta fashe da kuka "Mabrookah mai kuma ya faru" Mami dake cikin falon ta fito dasauri tana tambayan lafiya "Ya Jamal ne ya dukeni kawai dan naje wajansa na samesa da Ummy" Ran Mami idan yayi dubu ya b'aci "Alhaji kaga abinda nake fad'a maka koh, gaba d'aya yarinyan nan tanaso ta d'auke mana hankalin Jamal, gashi tun ba'aje ko inaba har an fara duka" Saida yayi Jim sannan yace "Bari na dawo masallaci" Mami taja Hannun Mabrookah suka shiga ciki. Waya ta d'auka ta soma neman layinshi anma bai d'auka bah. Shiko gogan, wanka ya fesa ya saka bak'in singlet da 3quarter irin na sojoji, D'akin Ummy ya nufa sukayi kicibus a bakin k'ofa tana k'okarin fitowa, hannunta yaja har zuwa dinning d'in yaja kujera ya zaunar da ita sannan shima yaja ya zauna. Sunkuyar dakai tayi k'asa tana wasa da zoben hannunta "Banasan kunyan nan Wife, ki saki jikinki" Ta mik'e ta bud'e kullan ta d'au leda d'aya ta saka masa a plate sannan ta bud'e na miyan shima ta zuba. Tunda ta bud'e kulan tuwon ya turo baki gaba har ta jere masa komai a gabansa, ya shagwab'e fuska yace "Nidai gaskiya Wife banacin tuwo" "Saboda meh?" Ya sake tura baki yace "Ni banacin tuwo haka nake" Kurrri tamasa ko k'iftawa batayi, shiko ya tura mata abincin ya rungume hannu kamar k'aramin yaro "Kafa ce yunwa kakeji" Ya d'anyi murmushin mugunta yace "Saidai idan kin yarda zaki bani a baki, to zan daure naci" Ta zaro ido baki na rawa "Aaaa..A baki? Uhummm" "Oh bazaki bani bah" Tayi shiru ta gaza ce masa komai. Ya saci kallanta ya rik'e cikinsa "Ouch! Ni yunwa nakeji" "Pls ki bani naci" Yanda yayi maganan a shagwab'e sai ya bata tausayi, anma ita harga Allah bata tunanin zata iya basa abinci a baki. Shiru ba wanda ya sake magana ya mik'e yana rik'e da cikinsa zai bar wajan "Dan Allah kai hak'uri to zauna na baka" Har a ransa yaji dad'i anma yad'an basar yace "Nidai kawai ki bashi tunda bazaki bani bah" Ta langwabar dakai idonta cike da kwalla, sai a lokacin ya lura da fuskanta inda Mabrookah ta mareta har yad'an tashi. Wani takaici yaji a zuciyarshi, shi bada dan Mami ta matsa ba mai zai kaishi auran Mabrookah. Wajan ya shafa "I'm sorry nasan laifina neh, saboda ban gyara gidana bah har hakan ta faru" Ta girgiza masa kai a hankali, kan kujeran ya koma ya zauna. Nan suka shiga daru wajan cin abincin, dakyar ta yarda ta basa haka shima ya ciyar da ita gwanin sha'awa. A tare sukayi sallan isha'i, tambayoyi ya mata na karatun da Lesson teachern ta na d'azu ya koya mata ta basa amsa har yana mamaki. Bayan sun gama ya d'au basket d'inda Tasa Abincin Abba a ciki tana binshi a baya zuwa side d'in Abban. A nan falonsa ya had'u da Mami da Mabrookahn suna zaune, shi sai yanzu yama tuna abinda ya faru tsakaninsu d'azu. Mami ko sai galla ma Ummy harara take har suka k'araso suka zauna, cikin girmamawa Ummy ta gaida Mamin, ta kauda kai gefe tak'i amsawa. Ana cikin haka Abba ya shigo falon, Ummy da Jamal suka gaida shi cikin fara'a ya amsa tareda k'arasowa ya zauna. Basket d'in Jamal ya tura masa yace "Abba gashi inji Ummy" Da fara'a yace "Ah to madallah, Allah ya saka" "Haba Alhaji, kazo kayi shiru bakace komai bah. Duka fa Jamal ya mata akan wannan" Ta nuna Ummy dake zaune k'asa kamar marainiya "Ka kyauta Jamal, ai gwara daka nuna yanzu na gani tun kamin ku je naku gidan" "Komai binsa ake a hankali, shi yakamata ki tambaya kiji mai ya had'asu" "Ga Algunguman data had'asu nan. Wallahi kinyi kad'an ki wargaza min 'yayana" "Maimuna kimin shiru, banasan na k'ara jin bakinki a nan" Mami ta turo baki tareda kauda kai "Jamal meya faru tsakanin ka da Mabrookah" Nan ya kwace duk abinda ya faru ta fad'ama Abban, Abba ya juya ga Mabrookah yace "Haka akayi ko ba haka akayi bah" Baki ta zunguro gaba tace "Hakaneh" Nan Abba ya bata rashin gaskiya, had'asu duka su ukun yayi ya musu nasiha, Mami dake gefe tace "Fad'a Alhaji yakamata kama Jamal, dan Wallahi yana tauye yarinyan nan, kwata kwata baya shiga d'akinta, baya shiga harkanta. Duk kuma saboda Wannan muguwar yarinyar" Kuka Ummy keyi mara sauti, duk hankalin Jamal na kanta ganin tana kuka. Abba ya b'ata rai yace "Ku tashi kuje" Hannun Ummy ya kama ya jata suka bar falon dasauri, Mami ko fad'i take "Kagani ko Alhaji, ga 'yar uwarsa baiko kalleta ba ya kama waccan sun wuce. Gaskiya dole na tashi tsaye dan da alama shanye min shi akayi" Rai b'ace Abba ya kalli Mabrookah "Tashi ki koma d'akinki" Ba musu ta mik'e ta fita. Ya juyo zuwaga Mami kacha kacha ya mata ya mik'e ya haura d'akinsa dan ta soma kaisa bango. Ummy Abduol✍🏻 [3/22, 5:21 AM] 0mmer Farouk: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 41 Kuka Mabrookah ta fashe dashi mara sauti wacce ke tsaye bakin k'ofar d'akin tana lek'en su ta ramin makulli tana kallo da kuma sauraran abin da ke faruwa, Dasauri ta sauka k'asa zuwa d'akinta ta sake rushewa da kuka. Jamal kuwa rungumo Ummy ya sakeyi yana jin wani farinciki na ratsa sa, bakinsa yakai saitin kunnenta ya rad'a mata "Ke nake saurare wife, fad'amin me kikeso" Tayi saurin girgiza kai a kunyace saboda yanda ya rungumota har numfashin su na had'uwa. Batayi aune ba ya d'auketa chak ya direta kan fado yana murmushi, ganin haka yasa ta mik'e a tsorace tana zaro ido kamar tayi k'arya. Murmushi yayi ya hayo kan gadon yana kallanta, matsawa tayi dasauri tana cigaba da kwalalo ido. Ya kamo hannunta ya had'a da nashi yana murzawa a hankali "I love uh so much Wife, da ban aureki ba bansan ya zanyi bah" Ta rausayar da kai k'asa tana 'yar murmushi tareda lumshe idonta alamar bacci. "Ya Jamal baccciiii.." Ta fad'a a hankali da sanyaiyar muryanta, ya shafa gefen kumatun ta da murmushi "Na lura ke ragguwa ce, nida kwanan nan nakeso naga kin fara tafiya da k'yar" Ba shiri ta bud'e idanunta a tsorace tana kallansa, dariya ya soma mata ganin yanda ta tsorata lokaci guda "Ni dai dan Allah ka fita bacci nakeji" Yanda tayi maganar a shagwab'e sosai ya burgeshi ya d'an rungumota jikinsa ya rad'a mata "Wife bakya san mu kwana tare" Kai ta girgiza alamar eh idanunta lumshe sboda kunyarsa. Peck ya mata a kumatu da goshi tare furta mata "I love uh Wife!" Ya k'ara sakin murmushi ya mik'e ya fita cikeda farinciki. Binsa da kallo tayi wani abu na shiga zuciyarta wanda ta kasa gane menene shi. Ranar daga Ummy har Jamal bacci sukayi mai cike da nishad'i. K'arfe bakwai da kwata y sauko cikin shiri na fita office, Bak'in shirt ne a jikinsa da brown d'in wando, ya nad'e wuya da farin tie. Sai baza k'anshi yake. D'akin Ummyn ya lek'a ya sameta zaune kan mirrow taci kwalliya cikin atampha purple and black. Sosai tayi kyau duk da ba wani makeup tayi bah. Kici kicin d'aura sark'a take tayi ta kasa, ya k'arasa ya amsa a hankali ya soma saka mata. Ta Mirrown suka k'urama juna ido, ta d'anyi murmushi ganin kallon yayi yawa ta sadda kai k'asa. Bata ankara ba taji fuskarsa a wuyan nata yana sunsunata yana lumshe ido cikin salo, idanunta itama ta lumshe tana d'an murmushi "Kinyi kyau sosai Wife" Shiru tayi ba magana, ganin haka yasa ya juyo suna fuskanta juna, light kiss ya mata a lips d'inta tayi saurin mik'ewa a kunyace zata bar d'akin. Hannunta ya kamo ya janyota zuwa jikinshi "Ina zaki bayan bamu gama magana bah" Ta d'anyi murmushi tana k'okarin k'wacewa daga rik'on daya mata. Baki ta turo gaba a shagwab'e tace "Dan Allah ka sakeni kaga fa zakayi latti" Yakai fuskanshi wuyanta yana sunsunar k'anshinta cike da nishad'i "Ai na riga da nayi lattin, kuma duk laifinki neh" Ta d'ago tareda zaro ido tana kallansa "Ni ba ruwana kai neh" Ganin abin nasa naso ya wuce wuri yasa ta d'an turesa da k'arfi ta fito daga d'akin tana mai dariya. K'asa ta sauko sukayi kicibus da Mabrookah akan dinning tana breakfast. Bata kawo komai ba tace "Ina kwana" Dogon tsaki Mabrookan taja ta mik'e ta d'au handbag d'inta tabar falon cikeda bak'in ciki. Zama Ummyn tayi kan kujera tayi shiru. K'aran saukowan sa daga sama taji ta d'ago tana kallanshi, shi ko harara ya sakar mata yana d'an murmushi, kai ta duk'ar k'asa tana wasa da zoben hannunta. Jan kujeran dake kusada nata yayi ya zauna ya d'an b'ata rai yace "Serve me" Ba tareda b'ata lokaci ba ya mik'e ta had'a mai abincin ta tura masa gabansa, folk ya d'auka ya saka yace "Mu ci!" Yanda yayi maganan fuska a had'e yasa ta d'au folk d'in ta soma ci a hankali. Shiko zagewa yayi yaci yayi nak sannan ya mik'e yana cewa "D'auko gyalanki muje" Gabanta ne ya yanke ya fad'i, kardai ace sakinta yayi, maimaita wa yayi yana kallanta fuskansa ba yabo ba fasara. A sanyaye ta hau sama ta d'auko hijab tasa, hannunta ya rik'e suka fito daga side d'in, tsakar gidan take bi da kallo dan rabonta da fitowa yau kwana hud'u kenan. Side d'in Mami taga ya nufa har lokacin yana rik'e da hannunta, da sallama suka shiga falon, kan dinning suka hango Mami da Abba suna breakfast, kici kicin k'wace hannunta ta soma yi ta kasa, shiko k'ara damke hannun yayi tareda d'an juyo wa ya kalleta. Har dinning d'in suka k'arasa, a kunyace ta sulale k'asa ta gaida su, Abba ne ya amsa da fara'a itako Mami kicin kicin tayi da rai, Jamal yaja kujera ya zauna ya gaida su, nan Mami ta washe baki tana amsa gaisuwan nasa. Abba yace "Taso daga k'asan tiles d'in nan 'yata, hau kujera ki zauna" A kunyace kanta k'asa tace "Aa Abba nan ma yayi" Ba k'aramin burge shi Ummy tayi bah, ganin yanda take da kunya da sanin yakamata. Itako Mami mik'ewa tayi fuska ba walwala tayi musu sallama ta fita. Ido Abba ya bita dashi yana girgiza kai. Nasiha sosai ta musu akan zaman aure sannan shima ya mik'e ya fita. Jamal na ganin ya fita ya mik'e ya dawo kusada ita ya zauna yana k'okarin janyota jikinshi, matsawa tayi tana turo baki "Ni dai ka tashi ka tafi" Ta nuna masa agogo tace "K'arfe fa takwas da rabi" "Na fasa zuwa yau" Ido ta zaro tana kallansa da mamaki "Meyasa" "Saboda ina tare dake" Ta d'anyi murmushi tace "Aa nidai ka tafi dan Allah nasan mutane na nan suna jiranka" Matsowa yayi kusada ita sosai yana murmushi "Kinaso naje" Ta gyad'a masa kai, yace "Idan dai kinaso naje to sai kin min Kiss" Mik'ewa tayi dasauri tabar falon a guje tana masa dariya. Shima dariyan yad'anyi ya girgiza kansa ya hau motarsa ya fice. Hau jinsa yake cikin farinciki mara misaltuwa, koda yaje office kyaytar dubu dubu ya dunga ma ma'aikatan dake k'arkashinsa. Itama Ummy kasa b'oye farincikinta tayi, albarka ta dunga sama Laurat a zuciyarta, lallai Laurat k'awa ce ta gari. Saidai matsalar ta d'aya son da Mami da Mabrookah basa mata, duk sanda ta tuna sai gabanta ya fad'i. Wuraren k'arfe sha d'aya na rana akayi knocking k'ofar side d'in, k'asan ta sauko ta bud'e a d'an tsorace. Wani mutumi ta gani tsaye, gaida shi tayi ya amsa tareda gabatar mata da kansa a matsayin malamin lesson da zai rink'a koyar da ita karatun boko dana addini. Da farinciki ta haura sama zuwa d'akinta, wayanta ne taji tana ruri ta d'auka da sauri ta kara a kunnen ta "Hello wife" Lumshe idanunta tayi ta bud'e, tad'anyi murmushi mai sauti yace "Ba magana? Any way idan nadawo yau zansaki magana" Ya d'anyi dariya tareda sassauta murya yace "Maganganu mah" Baki ta turo gaba, ya sake cewa "Kinga bak'on dana turo" Tace "Eh" a hankali. Jim yayi yace "Kisa Hijab pls, sannan ba Hira and banasan kina dariyan nan naki mai tsada a gabansa" Ta saki murmushi tareda k'ara rik'e wayan sosai a hannunta. A shagawab'e yace "Kinji!" Yanda yayi maganan sosai ya bata dariya, daga cikin wayan ya dunga jiyo dariyar ta a hankali. Lumshe ido yayi ya bud'e yana shafa cikinsa yana turo baki "Ina jin yunwa sosai Wife, dazu baki bani abinci bah" "Lah! Ba gaskiya baneh, ba kaci bah" "Nidai pls ki dafamin wani abu mai dad'i kafin na dawo kinji" "Ummm..." Tace a hankali ya sake cewa "I love uh so much, zamuyi magana ltr" Ya kashe kiran yana bin wayan da kallo yana murmushi. Itama wayan tabi da kallo da murmushi, ta rasa meke damunta daga jiya zuwa yau. Tunani ta soma, chan ta mik'e dasauri tunawa da tayi tabar lesson teacher a waje. Jotern bikinta ta d'auka da biro bayan ta binjima k'atan Hijab ta fito. Nan varendern side d'in nasu ta samesa zaune kan farin kujera. Zama tayi bayan ta sake gaisheta sannan ya soma mata 'yan tambayoyi na boko dana addini. Sam baiyi tunanin tasan abubuwa sosai na boko bah, na addini kuwa ba k'aramin yaba mata yayi bah. Nan suka soma karatu har zuwa k'arfe d'aya. Bayan la'asar kicin d'inta dake nan saman ta shiga shiru ta tsaya tana bin kicin d'in da kallo dan ya burgeta sosai. Fridge ta bud'e taga shima shak'e yake da nama kala kala da kuma kayan miya. Cikin sa'a d'aya ta had'a had'adiyar miyar kub'ewa d'anya dayaji nama. Sannan ta mulka tuwon semonvita ta kukulla a leda tasa a kula. Harta fito ta tuna Abba nasan tuwo, ta koma ta bud'e sabon kula ta zuba masa da miya a saka a tray ta aje gefe. D'akinta ta koma sake wanka ta sauya kaya zuwa dogon rigar yadi robber mai taushi, kayan sun mata kyau sosai saboda duk shape d'inta saida ya fito cikin rigan. Tana nan zaune akayi magriba, ta shiga d'aki tayi sallah ta zauna har akayi isha'i. Bud'e kofan d'akinta akayi lokacin ta cire hijabin jikinta kenan, ta juyo suka had'a ido. Wani miyau Jamal ya had'iye dakyar yana binta da ido. Kanta k'asa tamai sannu da zuwa, bai amsa ba sai k'arasowa dayayi ta janyota jikinsa yana murmushi "Kinyi kyau sosai Wife" K'ara sunkuyar dakai tayi tana murmushi "Oh Come on bansan kunyan nan, yana tauye ni. Ki saki jikinki pls. I promise to shower uh with my love" Ummy Abduol✍🏻 [3/22, 5:23 AM] 0mmer Farouk: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 43 Ya juyo zuwaga Mami kacha kacha ya mata ya mik'e ya haura d'akinsa dan ta soma kaisa bango. Binsa da ido Mami tayi ranta b'ace, tai kwafa tana cewa "Ai wallahi bai isa ki rabani da d'ana bah Ummy, inkin san wata ai baki san wata bah" Taja dogon tsaki ta fita zuwa nata side d'in. Jamal kuwa d'akinsa yayi da Ummy daketa kuka tana k'okarin kwace kanta daga rikon daya mata. Bakin gadonsa ya ajeta ya tsugunna gabanta yana share mata hawaye. "Kiyi hak'uri Wife, karkiyi fushi da Mamina, i know wata rana zata daina kinji" Kan gadon ta fad'a ta fashe da kuka mai sauti, shima ya biyota kan gadon ya rungumota jikinsa yana lallashinta. Dakyar ya samu tayi shiru, ya tayar da ita zaune ya share mata hawaye "Wata rana sai labari, insha Allahu Mami zata soki zata k'aunace ki kinji" Kai ta gyad'a masa da wani k'wallan a idonta. Lightt kiss ya mata a lips d'inta ya shafa suman kanta yace yana zuwa. K'asa ya sauka zuwa d'akin Mabrookah dan sosai ta b'ata masa rai yau. Yana ya tarar da ita ta fito wanka, nunata yayi da yatsa ransa b'ace "Yaushe na fara wasa dake da har kike neman raina ni" Ta zunguro baki "To mai kuma na maka" "Wallahi idan kika k'ara zuwa kika had'ani da iyayena, ko kikayi gigin sake tab'a Ummy" yayi kwafa "Kana tauye ni kuma kace bazanyi magana bah" Ta fashe masa da kuka "Baka shigowa d'akina, baka kula da alamura nah" "Jaraban ki ce ta rufe miki ido har kika ga bana shiga d'akinki. So nawa ina fad'a miki sai Ummy ce uwargida and saina gama mata ranakunta tukun" Ta rushe da kuka ta fad'a kan gado "Bakayin adalci Ya Jamal" Tsaki yayi ya fita daga d'akin dan yasan ransa ne zai cigaba da b'aci a banza a hofi. Haka rayuwar gidan Jamaludeen ta cigaba da kasancewa kullum Ummy zatayi girki tasa ma Abba, Ran Mami ko ya k'ara b'aci. Har side d'insu Ummyn tazo ta mata kacha kacha, ta kuma mata kashedin karta sake sakama Abba abinci. Kullum lesson teachern ta saiya zo, tana jin dad'in karatun sosai. Haka idan Jamal ya dawo daga office zai zauna ya sake mata bita da kuma k'arin bayani. Shak'uwa kam tsakanin Jamal da Ummy ba'a magana. Saidai Abu d'aya da kullum ke damunta rashin k'aunar da Mami da Mabrookah ke mata. Haka ango Jamal ya gama kwanakin sa wajan uwargida ya dawo wajan amarya. Ranar da zai dawo karku so kuga Mabrookah baki har kunne, sai rawar k'afa ake da iyayi anama Ummy kallan banza. Ranar bataje school ba da kanta ta shiga kicin tamai girki sai k'anshi ke tashi a gidan. Bayan ya dawo daga office sama ya haura yayi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska. D'akin Ummy ya lek'a ya sameta kwance ta takure waje d'aya, ya k'arasa bakin gadon ya tab'a jikinta yaji ba zafi "Wife ya dai" Zaune ta tashi saiga hawaye shar, nan da nan ya rud'e "Lapia Wife me aka miki" Kuka ta fashe dashi, ya rungumota jikinsa yana lallshinta, duk yabi ya rud'e dan ko kad'an baisan kukan Wife d'in tasa. "Fad'amin me aka miki, waya tab'aki" A shagwab'e tace "Ni inaso naje gida naga Mama" Ya d'ago fuskanta yana share mata hawaye "Mama kikeson gani" Ta gyad'a masa kai, wani hawayen na gangara a idonta. "Dauko mayafinki muje" Ta d'ago kai dasauri tace "Dagaske" Kai yad'an gyad'a mata, ta rungumeshi tana dariya. Murmushin jin dad'i yayi, ya k'ara janyota jikinshi ya had'a bakinsu guri d'aya. Mutsu mutsu ta soma ya rik'eta sosai. Sun dad'e a haka sannan ya janye bakinsa ya dafe kansa da hannayenshi. Tayi saurin mik'ewa tana turo baki ta shige toilet, dakyar ya iya tashi ya koma d'akinsa. Wanka ya sakeyi ya sauya kaya zuwa kaftan fari k'ar. A falo suka had'u itama ta shirya cikin pink shadda dogon riga. Ya matso ya kama kugunta da hannayensa biyu yana mata murmushi "Kinyi kyau sosai Wife" "Nagode" tace a hankali. Bakinsa yakai wuyanta yad'anyi kissing, tayi saurin lumshe ido dan sak'on nasa ya shigeta sosai. Murya a sanyaye ya rad'a mata "Yaushe zaki bari na nuna miki san danake miki, I'm suffering alot i need uh" Ta janye jikinta dasauri tana murmushi, sauka tayi k'asa, yad'anyi jim tareda sauke ajiyar zuciya sannnan yabi bayanta. Tana saukowa ta samu Mabrookah a falonta, tayi gayu cikin Top fari mai kyau da wando iya guiwa, ya matseta sosai, fuskan nan yasha makeup. Tayi kyau sosai dan itama mai kyau ce. Kallo d'aya Ummy ta mata ta kauda kai ta fita, tsaki Mabrookahn taja chan saiga Jamal ya sauko. zumbur ta mik'e ta k'araso tana karairaya "Haba Honey ina kuma zaka bayan kasan kwana na neh yau" Yad'an yatsine fuska tareda matsawa gefe sbda kokarin datake na chafko rigansa. "Uzuri ne ya kama zamu fita, but idan nadawo ai shiknan" Bai jira mai zatace ba ya fice ya barta tsaye cikeda takaici. Har tayi hanyan k'ofa dan zuwa sanar da Mami sai kuma ta fasa tuna abinda ya fad'a mata rannan. Hakanan badan ranta yaso ba ta koma ta zauna ranta b'ace. Bakin motarsa Ummy taja ta tsaya harya k'araso, bud'e mata yayi ta shiga sannan shima ya shiga suka d'au hanya. Tsaraba ya tsaya yama Maman nad'an abinda ba'a rasa ba sannan suka k'arasa. Dagudu ta shiga cikin gidan ta fad'a jikin Mama dake falo tana lazumi, a tsorace Mama ta janye jikinta dan bata ga fuskan waye bah, ganin Ummy ce yasa itama ta rungumeta tana tambayanta gida. Kuka Ummy ta fashe dashi tunawa da kullum idan ta dawo gidan aikinta, Bayan ta gaida Mama wayan Baba take zuwa su sha fira abinsu. Nan ta sake rushewa da kuka, Mama ta soma lallashinta, itama ta kasa daurewa sukayita kukan tare. Dakyar sukayi shiru, Mama ta tambayeta 'yan gidan nasu ta amsa da lafiya kawai. Jamal jin shiru shiru ba Ummy yasa yad'au ledan tsaraban ya shiga da sallama, jin sallaman shi yasa Mama gyara hijabin jikinta, ai sai kice min da mijinki kuke. Kai Ummy ta duk'ar ya shigo ya samu guri ya zauna tareda gaida Maman. Ledan ya mik'ama Ummy ta mik'ama Mama, godiya Mama tayi tana cewa "Badai ka gajiya" Yayi murmushi baice komai bah, Mama tace "D'an leka ki gaida Innan Bilal" Had'a ido sukayi da Jamal taga yayi kini kini darai, ya mik'e yana ma Mama sallama yace yana waje. A tare suka fito da ita, a cikin zaure ya kamo hannunta yana cewa "Badan Mama tace kije ba da bazan yarda bah" "Babu fa komai Ya Jamal, Innansa ce zan gaishar idan kuma baka gamsu ba muje tare" Ga mamakinta sai ji tayi yace "To muje" Dariya suka sa duka, saida ya tsaya zauren Innan ta shiga ta fad'a mata sannan ya shiga, sun gaida sosai ta musu nasiha mai ratsa jiki, Sannan suka fito bayan ta dire mata bandir d'in yan d'ari biyu ta amsa dakyar. Shi mamaki yake yanda Innan Bilal take ba ruwanta da kuma san mutane, cikin gida Ummy ta koma shi kuma Jamal ya koma mota ya zauna, message d'in Bilal ne ya shigo wanda ya zama ka'ida kullum saiya turo masa, bud'ewa yayi ya karanta kamar haka _Bazan fasa fad'ama baka isa ka mallaki abinda nakeso na kuma dad'e ina muradi bah. Ina gaf dana kwace muradina daga hannunka, na kuma maka tabon da har ka mutu bazaka manta bah. Saboda kaso abinda nakeso_ Murmushi yayi bayan ya gama karantawa, shi messages d'in Bilal dariya ma suke bashi. Ummy dakyar ta banbaro daga jikin Mama ta fito suka tafi badan ranta yaso bah. Koda sukaje gida har lokacin Mabrookah na falon ta cika tayi fam. Wuceta Ummy ta sakeyi ta haura sama, chan saiga shi shima ya shigo "Sannu da zuwa" tace fuska ba walwala "Yauwa sannu" ya haura sama abinsa. Wanka ya sakeyi ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya saida ya fara shiga d'akin Ummy ya mata sallama sai turo baki take kamar zatayi kuka. Shi kansa baisan rabuwa da Baebyn saidai ba yanda ya iya, lallashinta yayi har bacci ya d'auketa sannan ya sauko k'asa. Kan dinning ya zauna, ya taho tana karairaya ta d'an dafa kafad'arsa "Honey mai za'a zubama" "Koma menene" yace atakaice. Fried rice ta zuba masa da farfesun kaza ta tura masa gabansa tareda janyo kujera ta zauna kusa dashi "Ko nabaka a baki neh Honey" Ya girgiza mata kai alamar Aa, spoon ya d'auka ya d'ibo tareda bismillah ya kai bakinsa, taunawa ya soma yi yana yatsine fuska. Dakyar ya iya had'iyewa ya juyo yace "Waya girka abincin nan" Ta langwab'ar dakai tace "Ni ce, ko beyi dad'i baneh" Cike da takaici yace "Yayi sosai" Tayi murmushi ta sakala hannunta a wuyansa. Spoon uku ya k'ara dakyar ya ture yace ya k'oshi. Sama ya haura ta koma d'akinta ta sauya zuwa wani fitinanen night gown ta haura saman zuwa d'akinsa. Koda ta shiga dind'in ta samu d'akin ya kashe fitila da alama ya kwanta neh. A hankali ta k'arasa ta kwanta a bayanshi, shiko takaici ne ya cika shi, ta dunga matsowa har ta cin masa, ta rungumesa tana shagwaba "Honey shine ka juya min baya" Yi yayi kamar bai jita bah, k'ara mak'ale shi tayi tana mai waiwayi a k'irji. Saurin rik'e hannunta yayi a harzuk'e yace "Wai meye haka Mabrookah ki kyaleni bacci nakeji" "Haba Ya Jamal ni fa wallahi...." Kasa k'arasa maganan tayi jin ya turata gefen. Ba shiri ta fashe masa da kuka. Dogon tsaki yaja ya mik'e yad'au filo ya koma falo. (Wayyo Jamalu baka kyauta bah) Haka sukayi ta rigima har kwana bakwai, har mamakin rashin kunyan Mabrookah yake yanda ta nuna masa k'irki k'iri sex takeso, abinda shi ko a labari bai tab'aji ba ga Amarya bah. A ranar daya cika sati d'aya a d'akinta ya raba musu kwana. Sannan yace kowa ta rink'a girkinta dan yasan matuk'ar za'ace duk wacce takeda girki ita zata rink'a yi to za'a fuskanci tashin hankali musamman wajan Mabrookah. Ummy Abduol✍🏻 [3/29, 8:36 AM] ‪+234 701 141 1639‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 44 A ranar daya cika sati d'aya a d'akinta ya raba musu kwana. Sannan yace kowa ta rink'a girkinta dan yasan matuk'ar za'ace duk wacce takeda girki ita zata rink'a yi to za'a fuskanci tashin hankali musamman wajan Mabrookah. ***** *Bayan wata biyu* Abubuwa dayawa sun faru, ciki harda fara karatun Ummy a demostration dake cikin ABU, dan tana k'okari sosai. Dakyar malaman suka yarda aka sakata a SS1 kuma ba laifi tana fahimta. Yanzu tana iya karatu saidai idan kalma babba ce bata iya karantawa. Duk da saida aka kai ruwa rana tsakanin Mami da Jamal, dakyar suka samu ta amince. Tayi farinciki sosai da fara zuwanta makaranta. Yanzu sam batada lokaci, tana dawowa k'arfe biyu zatayi sallah ta jira lesson teachernta. Yau saturday ba aiki, tun safe Jamal ke d'akinsa yana bacci. K'arfe sha d'aya da rabi Ummy ta shiga d'akin, kan gado ta hangoshi yana sharan bacci abinsa hankali kwance. A hankali sad'af sad'af ta k'arasa ta zauna kusa dashi ta soma mai tafiyar tsuntsu a k'irji. Tunda ta shigo ya farka, lamo yayi yana sauraran abinda zatayi, salon datazo masa dashi yasa yad'anyi tsam duk da bai bud'e ido ba balle ya motsa. Ita kuwa cigaba tayi tana 'yar murmushi ita a dole tana masa mugunta. Tun yana daurewa har ya hankalinsa ya soma tashi, bata ankara ba taji ya janyota ta fad'a kan gadon, yayi saurin danneta ya mata runfa da jikinshi "Wife ke koh" Baki ta chuno gaba, "To ba kai baneh tun d'azu ina jiranka" Ya d'an sauke lallausan murmushi "Zaki bani sugarn ki neh?" Jin haka yasa ta soma kici kicin zamewa, ya saki 'yar dariya "Ai baki isa ba yarinya, tunda har kika zo sai na sha zuman nan" Ido ta runtse dasauri jin maganan dayake, mamaki ne a ranta yanda yau yake gaya mata maganan bako kunya. Shafata ya soma tayi saurin rik'e hannusa "Yaaa Jamal dan Allah ka bari" Bakinsa yakai saitin kunnenta ya rad'a mata "Ina wahala sosai Wife, ki bari nasamu natsuwa. Ba wani wahala zan baki ba indai zaki saki jikinki" Ta sake matse jikinta hawaye na gangara a idonta "Haba Wife ni neh fah" Bai jira mai zatace ba ya cusa bakinsa cikin nata. Wasa da ita ya soma, ina juyawa na hango 'yan Jamaludeen Fans grp sunata lek'e ta window. Zahra, Hafcycy, Xaboorah, Aunty Nurse, Zeenart, Maman sadeek sune 'yan gaba gaba. Lol Sun d'au mintina a haka, Ummy ba abinda take sai kuka, shiko baima san tanayi bah. Saida ya jagwal gwalata sannan ya fad'a gefe yana mayar da numfashi dakyar. Tana ganin haka tayi saurin mayar da zip d'in riganta ta fita daga d'akin dasauri tana cigaba da hawaye. Ya dad'e a haka sannan ya mik'e dakyar ya shiga toilet. Wanka yayi ya sa kaya, Top Blue da Brown trouser. Sosai yayi kyau sai baza k'anshi yake. Kasancewar ranar girkin Ummy ne d'akinta ya shiga, kan gado ya sameta kwance tayi samo. Murmushi yayi mai sauti ya k'arasa ya zauna kan gadon kusada ita, a tsorace ta mik'e ta zauna tareda duk'ar dakanta. "Yaya dai Wife, ko karatun mu na d'azu bai isheki baneh a cigaba" Ba shiri ta mik'e tana turo baki tareda girgiza kai "Ni dai banasan wannan karatun" 'Kai Wife! Fad'a gaskiya. Bayan gashi har kinyi wanka kin chanza kaya bayan kuma nasan d'azu kinyi" Kunya ne ya kamata kamar ta nutse k'asa haka takeji. "Ni dai tashi muje kiyi serving d'ina, yunwa nakeji inyaso idan muka dawo sai mu cigaba da karatun tunda naga kinfi fahimtarsa sosai" Kafa ta soma bubugawa a k'asa tana kukan shagawb'a "Ni dai wallahi banaso" Hannunta ya kama yana 'yar dariya suka fito falonta, da kansa yaja mata kujera ta zauna tana cigaba da turo baki. Shi da kansa yayi serving dinsu dan yasan bataci komai ba tana jiransa. Kamar yanda suka saba 'yan watanin nan shi da kansa yake bata a baki har ta k'oshi. Yauma hakan neh, duk abinda sukeyi Mabrookah na hangensu ta wajan staircase tana kallansu. Wani kululun bakin ciki ne ya tsaya mata a wuya, lokaci guda kuma ta fashe da kuka ta sauka k'asa ta koma d'akinta. Bayan sun gama cin abincin, Ummy ta tattara kayan takai kitchen ta wanke ta dawo, A falo ta hangoshi zaune yana kallo, k'arasawa yayi ta zauna tana cewa "Yau bamu je mun gaida Abba bah" "Ai yau a wajansa zan yini harda gobe" Ummy ta jinjina kai ta maida dubanta ga Tv. Wayansa dake hannunsa tayi k'ara ganin suna Abba ne yasa ya d'auka dasauri tareda karawa a kunne "Barka da safiya Abba, to gani nan zuwa" Ya kashe ya maida dubansa ga Ummy "Barinje Abba na kirana" Ta mik'e tana cewa "Yau fa bamuje mun gaida su bah" Ya tako a hankali ya k'araso inda take, k'ugunta ya rik'e da d'an murmushi yace "Nagode da yanda kike nuna damuwarki akan iyayena. I love uh so much" Murmushi ta masa, ya kai bakinsa kusada nata, tayi saurin kuccewa tana dariya "Allah zaki sai Wife" Gwalo ta masa yayo kanta ta gudu zuwa d'aki tana dariya. Kwafa yayi ya sauka k'asa, dakin Mabrookah ya leka ya sameta kwance kan gado tana kuka a hankali, har ya juya sai kuma ya dawo ya k'arasa kan gadon ya zauna tareda d'agota ya had'ata da k'irjinsa "Kukan menene kuma?" Sake rushewa tayi da kuka ta k'ara mak'aleshi sosai "Ya Jamal ina sanka sosai, banasan naga wata na rab'anka. Hakan na damuna. Dan Allah ka soni Wallahi ina sanka" Ya d'ago fuskanta yana share mata hawaye "Haba k'anwata, bar kukan ai duk abinda ke faruwa ke kikaja. Meyasa bakya jin magana nah" Ta turo baki, hancinta ya lakata 'yar murmushi "Its Ok ya isa haka, barin dawo sai muyi magana kinji" Ta gyad'a masa kai ya mik'e ya fita. Ihu ta saki ta fad'a kan gado tana murna, ko ba komai yau ya rungumeta. Waya ta d'auka ta soma kiran layin Aunty Faty, bugu d'aya ta d'auka ta saki k'ara "Shiyasa nake sanki Ummata, wallahi yau har rungumeni yayi" Daga chan b'angaren Aunty Faty tace "Ai bakiga komai bah, indai Jamal ne kin kusa samunsa har abada. Akwai wani magani dana amso wajan wani malami. Kina saka masa a abinci angama" "To Mommy yaushe zaki kawo min" "Ina nan zuwa musamman na kawo miki. Kedai kawai a yanzu ki cigaba da bin shawarata" "Tho Mommy" Hira suka cigaba, Aunty Faty nata kitsa mata abubuwa iri iri na yanda zata janyo hankalin Oga Jamal. *** Da sallama ya shiga d'akin Abban, zaune ya samesa kan gado ya d'aura system a cinyarsa yana wasu ayuka. Kusada shi ya zauna ya gaida shi ya amsa yana kallansa "Abbana gani" Suman kanshi Abba ya shafa yana murmushi "Ina jin dad'in yanda kake tafiyar da aiki a companyn nan, Allah ya maka Albarka" Da Murmushi a fuskansa yace "Ameen Abbana" Abba ya aje System d'in dake cinyarsa ya cire medicated glass d'in fuskansa yace "Na kiraka ne dan muyi wata muhimmiyar magana dakai" Ummy Abduol✍🏻 [3/29, 8:36 AM] ‪+234 701 141 1639‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 45 n 46 "Na kiraka ne dan muyi wata muhimmiyar magana dakai" Gyara zama Jamal yayi yace "To Abba" Abba ya cigaba da cewa "Har yau bazan fasa fad'a maka kayi adalci a tsakanin Matanka bah. Rik'on mata biyu abu ne mai wahalar gaske, saboda kok'arin sauke hak'i. Nasani Mabrookah ba zab'inka baneh, hakan kuma kada ya tab'a saka ka wulak'anta tah." Ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk wuya duk rintsi karka rabu da Mabrookah, sannan kayi k'okari ka rik'esu Amana. Karka manta dukansu Marayu ne, babu mai mahaifi a cikinsu" Jamal ya gyad'a kai ya sake sunkuyar da kai k'asa. "Jaleelah yarinya ce ta gari, bani fatan naga abinda zai wulak'antata a rayuwa, saboda 'yar halak ce. Ka rik'eta amana Jamal" "To Abba insha Allahu" Wani Jaka mai kama dana system Abba ya d'auko ya aje a gabanshi yana cewa "Inasan ka ajiye min wannan jakan a wajanka, akwai abubuwa muhimmai a ciki. Dan ina ganin kwanan nan zanyi wani tafiya" Kallan jakan Jamal ketayi ko k'iftawa bayayi "Amana ce tsakanina dakai. Idan Allah ya dawo dani daga tafiyar zan amsa sannan na maka k'arin bayani" "To Abba, anma ina zaka haka" Saida Yayi murmushi sannan yace "Chan wani guri zani, idan lokacin yayi zakaji" Jamal ya jinjina kai tareda jawo jakan gabansa ya ajiye. "Tashi kaje Allah ya maka albarka" Ba musu ya mik'e yama Abba sallama ya koma side d'inshi. D'akinsa yakai jakar ya aje cikin wardrobe ya saka key ya kulle. Yinin ranar Abba da Jamal suna tare, hatta abinci tare suka ci na rana dana dare. Washe gari ma haka, tare sukaje asubah, tare sukayi breakfast. Sosai Jamal yayi enjoying moments d'in, dan Nasihohi sosai ya dunga masa da nunaswa through out the day. Uwargida Ummy tana fito wanka kenan da bayan isha'i Jamal ya shigo d'akin bayan sun dawo sallan Isha'i da Abba, sam bata lura dashi ba sboda towel d'in dake fuskanta tana goge kanta dashi. Karo taji tayi da mutum, ba shiri ta matsa gefe a tsorace. Janyota yayi jikinsa yana k'are mata kallo. Cikin sanyin murya yace "Wife kina horani dayawa. Bakya tausayina koh" Baki ta turo tana kok'arin kwacewa "Dan Allah ka bari" Ya sake janyota jikinsa yana shin shina wuyanta "I badly need uh Wife, Plsss" Bai jira mai zatace ba ya soma kissing d'inta a hankali, biye masa tayi dan tana enjoying duk sanda yake kissing nata. Ganin haka yasa ya janyota suka fad'a kan gado, har lokacin bakinshi na had'e da nata. Hannu yasa yana kok'arin janye towel d'in jikinta tayi saurin rik'e towel d'in tana girgiza masa kai "Plsss...Wife..." Yayi saurin janye towel d'in ta runtse ido hawaye ya gangaro mata, nan da nan ya rud'e ya soma wasa da ita son ranshi. Ba abinda Ummy keyi sai hawaye. K'aran buga k'ofan d'akin neh ya dakatar dashi daga abinda yake. A harzuk'e yace "Wai Waye" Muryan Mabrookah yaji tana cewa "Ya Jamal Mami na kira, gatanan a falo" Ji dayayi Mami ce yasa ya janye jikinsa daga nata, tayi saurin jan Bedsheet ta rufe jikinta tana cigaba da kuka. Gefen fuskanta ya shafa yana murmushi "Ki jirayeni anjima" Ya mik'e dakyar ya fita yana rik'e da gefen maranshi. Mami ya hango a falon a tsaye, Mabrookah na gefenta zaune tana juye juye, a fusace Mamin ta juyo jin tafiyarsa a bayanta "To shanyaye, k'arfe takwas har ka shige d'aki, Jiba nan" Ta nuna masa Mabrookah dake gefenta tanata murd'a murd'e rik'e da cikinta tana kuka "Yarinya tun d'azu tana d'aki tana murd'e murd'e kana chan tareda wannan maiyar" Harara yaketa wurga ma Mabrookah batareda yace komai bah. "Ina magana kayi banza dani, maza dauko makullin mota kazo ka kaita asibiti" Juyawa yayi har lokacin baiyi magana bah, dakinsa ya shiga ya d'au makulin mota ya fito. "Sai kazo ka kamata ku sauka k'asan" Ransa a b'ace ya k'araso inda Mabrookan ke zaune, saida ya take mata k'afa da gangan itako zafin dataji yasa ta saki ihu tareda matsar da k'afarta. Fizgota yayi ya d'agota suna tafe Mami na binsu a baya har suka sauka k'asa. Saida taga ya sakata mota sun fita sannan ta koma side d'inta tana dariya. Sunyi tafiya mai nisa sannan yayi parkinga a gefen titi ya d'au wayansa ya turama Wife d'insa text akan tayi hak'uri ya fita. Mabrookah ko sai cigaba da murd'e murd'e take. Zuciya tazo masa wuya ya fincikota tareda shak'e mata wuya "Ni zaki ma k'arya, wallahi idan baki daina murd'e murd'en nan ba saina b'abbalaki a wajan nan" Tari ta soma tana neman k'wacewa anma ta kasa, huci yake ransa b'ace "Abubuwanki sun fara isana Mabrookah, wallahi ki shiga taitayinki ina gab da datse igiyar auren dake tsakaninan dake" Kuka ta soma ta sa hannu yana k'okarin janye hannun daya shak'eta dashi "Wa..wayyo Zak..ka kasheniiii" Sakinta yayi ya jurata baya ta bige da murfin k'ofan. Kuka tasa tana sosa wajan data bige "Duk abinda kakemin ban tab'a cewa komai ba sai kai, yau watan mu uku anma baka tab'a kusantata bah, baka kulawa dani, baka damu da harkata bah" A harzuk'e ya juyo yana zazzare ido "Anya Mabrookah baki tab'a sanin namiji ba kuwa" Ihu ta saki tana kuka "Karuwa kake so ka cemin kenan, baka kira Ummy karuwa ba sai..." Marin dataji a fuskanta ne ya hanata k'arasa maganan datayi niya. Nunata yayi da yatsa, wannan karan takai k'ololuwa wajan b'ata masa rai "Matuk'ar a furucinki bazaki daina sako Ummy bah, haka nima bazan daina d'aura hannuna akanki bah" Kuka ta sake fashewa dashi tana dukan ko ina ta samu a cikin motan, harzuk'a yayi ya fito ya fizgota waje ya zagaya ya shiga ya tada motan yabar wajan. Kuka Mabrookah ta sake fashewa dashi, gashi bata fito da wayanta ba balle ta kira Mami, kuma hanyar motoci sai jefi jefi suke wucewa. Kuka take kamar ranta zai fita tanata bubuga k'afa a k'asa. Har yayi nisa sai kuma yaga rashin kyautawar sa na barinta a wajan, ko ba komai matarsa ce akwai igiyan aurensa a kanta. Dogon tsaki yaja ya juya ya koma, inda ya barta nan ya dawo ya sameta tanata kuka, bud'e kofan gaban motan yayi batare da yace komai bah. Dagudu ta shiga yaba motar wuta kamar zai tashi sama. Ikon Allah ne kawai ya kawosu gida, Fita tayi dasauri ta nufi part d'insu ta fad'a dakinta. Shima rai b'ace ya fito ya shiga, dakinsa ya nufa kai tsaye. Tunda aka bud'e gate d'in gidan Mami tazo bakin window tana kallansu, sosai ranta ya b'aci da abinda ta gani ta koma ta kwanta a fusace. Ummy najin motsin su tun sanda suka dawo, sam batayi gigin zuwa d'akinsa ba dan yanzu wani irin tsoronsa takeji. Dare ya tsala sosai wuraren k'arfe biyu da kwata, Jamal na kan katafaren gadonsa yaji Tim! Kamar k'aran dirowan abu. Tashi yayi zaune dasauri ya mik'e ya tsaya bakin window ya d'an d'aga labule yana hange. Wasu ya hango suna zagaye gidan dukansu sanye da bak'aken kaya fuskokin su duk a rufe, ga wasu manya manyan bindigogi dake hannunsu. A tsorace yakai dubansa wurin gate, masu gadi ya hango kan kujera an d'auresu da igiya bayan an rufe musu baki. A rud'e ya d'au wayansa ya soma neman layin Abba, bugu d'aya ya d'auka yana cewa "Jamal lafiya cikin wannan daran" A rud'e yace "Abbana 'yan fashi ne gasu nan sun zagaye gidan" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine kalmar da Abba ya fad'a yace "Ku natsu karku bud'e musu k'ofa" "Tho!" Jamal yace ya kashe kiran. D'akin Ummy Jamal ya nufa, bacci ya sameta take hankalinta kwance, Sunnanta ya kira a hankali duk da hankalinshi a tashe yake, motsawa tayi bayan ta bud'e ido "Wife tashi B'arayi ne a gidan namu yau" Ba shiri ta mik'e tana k'okarin kwalla ihu, saurin rufe mata baki yayi da hannunsa, kuka ta fashe dashi tana yarfe hannu. Shi kanshi baya cikin natsuwa, hannunta ya kama suka zauko k'asa zuwa d'akin Mabrookah, Jamal ne ya tasheta itama ta tashi a tsorace. Tsakiya suka sakashi suna kuka sosai dukansu cike da tsoro. Sam hankalinsa baya jikinsa yana chan wajan Iyayensa. A chan kuwa b'angaren Abba, Mami ya tayar ya fad'a mata, ba shiri ta mik'e dasauri tana muzurai cikeda tsoro, kan kace me sunyi anfani da wani secret key sun bud'e kofan side d'in. Nan Mami ta sake tsorata, Abba kuwa ba abinda ke fita daga bakinsa sai addua, duk wanda yazo masa yi yake kawai. Wajan su Shidda suka shigo d'akin, bindiga suka nunama Abba da Mami suka tasosu gama zuwa Main falon dake k'asa. Jamal dasu Ummy nachan hankalinsu tashe, bud'e kofan side d'insu suma akayi, Mabrookah ta saki Ihu zata gudu, d'aya daga cikinsu yace "Kina guduwa saina harbeki" Chak ta tsaya, Suka shishigo, Ummy ta makale Jamal tana cigaba da kuka, d'aya daga cikinsu yace "Hands Up" Dukansu suka d'aga hannu, tasasu suma sukayi har zuwa side d'in Abba, sai a nan suka lura ashe ba k'aramin yawa garesu bah, sun zagaye gidan kaf har side d'in masu aiki. Abba da Mami suka samu a Falon an sakasu sunyi kneeldown, an d'ad'aura musu bindiga akai. Suka su Jamal aka sakasu sukayi irin nasu Abba, Ogan ciki dake hakince kan kujera rik'e da AK47 ya kalli Ummy Yace "Woaw! Anma kinada kyan diri" Sai a lokacin Jamal ya kalli kayan dake jikin Ummyn, Riga da wando ne iya guiwa mai santsi ya matseta duk ya mammane mata a jiki. Hakan ne ya k'ara fito da suranta a fili, Ran Jamal ya b'aci, Ogan ya cigaba da cewa "Lallai Alhaji Surajo, Ashe haka kakeda zuk'a zuk'an 'yan mata. Lallai zan kwashi ganima kafin natafi" Abba yayi saurin cewa "Dan Allah ku fad'i abinda kukeso mu baki, Naira, Dollars ko Cheque" Wani dariya Ogan ya saki ta sosa gefen fuskansa da bindigar dake hannunsa "Ni duk ba wannan ya kawoni bah" "To me ya kawo ku" cewar Jamal yana huci Oga ya maida dubansa ga Jamal yace "Ran d'aya daga cikinku mukazo d'auka" Nan fa Abba da Jamal sukayi tsuru tsuru, Ummy da Mabrookah da Mami kuma suka fashe da kuka. Oga ya nuna Ummy yace "Ke tashi, Bari na fara morewa tukun sai nayi abinda ya kawoni" Ummy ta fashe da kuka tana kallan Jamal tareda langwab'ar dakai. A zuciye ya mik'e yace "Wallahi kada ka sake ka tab'amin matata" D'aya daga cikinsu ya d'aga Ummyn tsaye tana kuka sosai, a zuciye Jamal yayi kansu bai ankara ba yaji saukan abu a kansa, ba shiri ya fad'i wajan tare da dafe kansa ya saki k'ara sosai. Abba yace "Dan Allah karku kashe min Iyalina, ku fad'amin me kukeso na baku" Mami kuwa sai Jamal take dake tsugunne a wajan dake da kansa dake jini, kuka take tana kallansa ba halin taimaka masa. Ummy har lokacin tana hannun d'aya daga cikinsu tana kuka tana fifizgewa. Wani daga cikin b'arayin ya shigo yama Ogan magana a kunne ya fita, chan ya d'aga kai ya dubi agogo sannan ya tako har inda Abban yake tsugunne yace "Kamar yanda na fad'a maka a baya, bama buk'atar kud'inka. Ranka kawai mukazo d'auka" Abba ya zaro ido, Haka Mami dake kusa dashi "Dan Allah kuyi hak'uri kar ku kashe min mijina na rok'e ku" Rarrafowa tayi ta kama k'afan Ogan, yayi kicking nata gefe, Ba Tausayi bare tsoron Allah ya saita Bindigar Hannunshi ya harbi Abban Har sau biyu a ciki. Wani ihu Jamal yayi ya mik'e yana ganin jiri yayi wajan Abban yana kuka sosai, Ummy kuwa luuuuu tayi ta fad'i sumamiya a Wajan. Da gudu b'arayin suka bar gidan suka shishiga motocin su suka gudu. Duk da yanda kan Jamal d'in ke jini ga kuma Jiri dake d'ibansa bai hanasa rungumo Abban ba zuwa jikinsa yana kuka yana girgiza sah. Dakyar Abban Ya iya bud'e idonsa yace "Ka...ka..k..ka Gafar...ce ni d'ana" Ummy Abduol✍🏻 [3/29, 8:36 AM] ‪+234 701 141 1639‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Wannan Page tukuici ce gareku Jamaludeen Fans a ko ina kuke a fad'in duniya* Gaskiya ina matuk'ar jin dadin yanda kuke so na kuma kuke san novel d'ina. Allah yabar zumunci Ameen Page 47 to 49 Dakyar Abban Ya iya bud'e idonsa yace "Ka...ka..k..ka Gafar...ce ni d'ana" Idanun sa suka rufe lufff, wani razananen Ihu Mami ta saki ta k'arasa tareda fashewa da kuka. Tuni Jamal ya fad'i jikin Abban shima ya some Mami duk tabi ta rud'e, Abba da Jamal kawai take jijigawa tana kuka da k'arfin gaske. Kan kace gidan ya cika dank'am da mutane, lokaci guda 'yan sanda suka cika layin. Abulance d'in ABUTH ne sukazo suka d'au Abba da Jamal da kuma Ummy, Mabrookah da Mami suka bisu sai kuka suke dukansu. Masu Aikin gidan babu wanda bai zubar da kwalla bah ganin yanda aka fita da Abba da Jamal. Cikin mintina kad'an suka iso asibitin, direct Emergency akayi dasu, nan likitoci suka duk'ufa akan Abba saidai Ina Rai ya ruga yayi halinsa. Shima Jamal sunyi treating d'insa, tareda suturing wajan saboda kan nasa ba k'aramin fashewa yayi bah. Mami da Mabrookah da kuma sauran mak'ota. Suna bakin k'ofar d'akin cirko cirko, Mami da Mabrookah sun rungume juna sai kuka suke, wasu daga cikinsu na lallashinsu. Jamal aka soma fitowa dashi, kansa nan nad'e da bandeji, Mami tayi kanshi tana tambayan Nurses d'in. Daya daga cikinsu ne ta juyo tace "Yana lafiya lau da ransa" Wani d'aki suka kaisa, sannan suka dawo suka fito da Ummy itama suka kaita d'akin. D'aya daga cikin likitocin ya fito yana cire gloves d'in hannunsa "Doctor yaya mijina, wani hali yake ciki yanzu" Ajiyar zuciya ya sauke ya d'an girgiza kai yace "I'm sorry to say..." Wani chafka Mami ta kaima kwalarsa "No Doctor kar kace min ya mutu" Bai iya cewa komai bah sai kura mata ido dayayi, ta sake fashewa da kuka, Mabrookah ta rungumeta tana kuka sosai, dakyar ta zama hannayenta daga rigan likitan ta fashe da kuka "Allah ya isa tsakanin mu daku, bazan tab'a yafe muku kashe min mijina da kukayi bah" Duk wanda yake wajan sai daya tausaya ma Mami, haka Mak'ota da sukazo tare suka d'au gawan Abba aka maida shi gida. Nan da nan gida ya d'auka da koke koke, Mami duk tabi ta zauce kamar ba ita bah. A cikin daren aka masa wanka. Washe gari kan kace meh gida ya d'auka, daga wurare daban daban sai bulbulowa ake janaiza. Jamal kuwa yana chan kwance har lokacin bai farfad'o bah, haka itama Ummyn. Nurses ne ke tare dasu suna kula dasu. K'arfe Tara na safe Ummy ta farfad'o da kuka, Nurse d'in dake tare dasu ta soma lallashinta, Jamal ta kalla dake kusada gadonta ta sake fashewa da kuka tana kallansa "Ya Jamal! Ya Jamal!!" Jin shiru yasa ta sake fashewa da kuka. Wajan nurse din ta juya "Ina Abba yake?" Saida Nurse d'in tad'anyi Jim sannan tace "Allah ya masa rasuwa" Karaf akan kunnen Jamal lokacin daya farka daga dogon suman dayayi. Ba shiri ya mik'e idanunsa cike da kwalla "Ina Abbana? Ina yake" Ummy ta rungumesa tana kuka "Abba ya rasu" Tureta yayi yace "Nooo!" Ya fad'i wajan guyawu biyu ya fashe da kuka. Daidai lokacin Ramadhan ya shigo d'akin wujiga wujiga, Jamal na ganinsa ya sake fashewa da kuka "Sun kashe min Abbana Ram, sun kashe shi" Duk yanda Ram yaso ga daurewa kasawa yayi ya fashe shima da kuka ta tsugunna kusada Jamal d'in, had'a goshi sukayi suna kuka mai ban tausayi. Ummy dake chan gefe itaba ba abinda take sai kukan. Dakyar Nurse d'in ta lallashe su ta fita dan ta kira likita. Jamal idanunsa na zubar da kwalla yace "An kaisa neh" Ram yace "Aa sai sha d'aya" Agogon d'akin ya kalla yaga goma da kwata, mikewa yayi dasauri ta tumb'uke Drip d'in dake hannunsa "Muje Ram, muje naga Abbana kafin a tafi dashi" Tausayin sa ne ke ratsa Ummy, duk hankalinta na kansa, ba musu Ram ya mik'e ya rik'e hannun Jamal d'in suka fito d'akin Ummy na binsu a baya. Suna shiga layin suka soma hango dandazon mutane, dakyar suka samu aka mamatsa musu suka shiga da motar cikin gida saboda kayan dake jikin Ummyn. Ganin cikin gidan dank'am da mutane yasa Jamal k'ara fashewa da kuka. Dasauri ya fito daga cikin motan, mutanen dake haraban gidan sai kallansa suke, direct side d'in Abban ya nufa yana kuka kamar ransa. A Falon sama ya hango gawansa, Mami da sauran 'yan uwa a gabansa suna kuka wasu na masa addu'a. Wani jiri ne ya d'ebesa yayi baya zai fad'i, Ram dake bayanshi yayi saurin rik'eshi. Har gaban gawan Abban ya kaisa ya zaunar dashi. Kuka kam Jamal yayi shi kamar ba gobe a gaban Abban, mutanen dake wajan ne keta basa baki, dakyar ya iya tsagaitawa ya d'aga hannu biyu yana masa Addu'a hawaye na cigaba da kwaranya daga idonsa. Ya dade yana masa addu'an, ya sake kallansa murya chan k'asa yace "Tafiyan dakace zakayi kenan Abba! Meyasa ka zab'i ka tafi ka barni" Mami ta fashe da kuka jin maganar da Jamal keyi. Dakyar aka d'agasa aka fita dashi daga falon, Ram ya d'iban masa ruwan Alwala ya tasa shi a gaba, kasa yi yayi, Ram da kansa ya masa alwalan ya d'agasa suka koma waje wajan jama'a. Ummy na chan side d'insu tana kuka bayan ta sauya kayan jikinta zuwa dogon rigan atampha. Kuka kam itama tayi har ta gode Allah na tausayin Rayuwarta da kuma na mijinta. Saida tayi mai isarta sannan tasa hijab ta fito zuwa side d'in Abban. Daga chan nesa da gawan ta tsugunna tana kuka tana masa Addu'a. Sai a lokacin ta lura da har su Twins dasu Aunty Faty da Zainab sun iso. Kamar yanda aka fad'a, karfe sha d'aya aka fito da gawan Abba, Aka masa sallah, Sannan aka tafi dashi zuwa gidansa na gaskiya. ``` A daidai nan gab'ar inaso naja hankulan mu 'yan uwa. Mu sani duniya ba matabbata bace, Kullu nafsin zaikatul maut. Kowace rai dole sai ta d'an d'ani zafin mutuwa, ko ka shirya ko baka shirya ba dole idan lokaci yayi zaka tafi. Mu cire dogon buri a zuciyarmu, mu cire hassada, mu cire k'yashi. Duniya ba matabbata bace,dan bakasan a halin da zatazo ta d'aukeka bah. Mutuwa lokaci d'aya takan zo. Mu yawaita ayukan Alkhairi, sadaka, biyaiya ga Iyaye, Barin abinda Allah ya hanemu, yin abinda Annabin mu ya koyar damu. Yawaita istigfari. Sallah akan lokaci, bin umarnin miji, Dadai sauran su``` _Allah ya yafe mana kurakuren mu, wanda muka sani da wanda bamu sani bah. Allah ka yafe ma magabatan mu da suka riga mu, mukuma idan tamu tazo kasa mu cika da kyau da imani Ameen_ Har aka kaisa aka dawo Jamal bai daina kuka bah, dan shi kad'ai yasan abinda yakeji. Nan k'ofar gida aka sanya canopy na amsar gaisuwa. Manya manyan mutane daga wuri daban daban suka soma tururuwa zuwa gaisuwa. Innan Bilal ce ta shiga gidansu Ummy da sallama hankali tashe take sanar da Mama abinda ya faru dan itama lokacin take ji a rediyo. Hankalin Mama ba k'aramin tashi yayi ba jin abinda ya faru. Ranar da aka kaisan Mama da Innan Bilal harda Bahar suka zo gidan gaisuwa, duk da yanda hankalin Ummyn yake ba'a kwance bah hakan bai hanata nuna farincikin zuwansu bah. Ita ta musu jagora har inda Mami ke amsar gaisuwa. Bayan sun gaisa Najma dake wajan ta gabatar dasu a matsayin Iyayen Ummy. Nan da nan Aunty Faty ta had'e rai, itako Mami amsa gaisuwan su tayi a mutunce. Sun d'an jima kad'an sannan suka musu sallama suka tafi. Yinin ranar zazzab'i ne sosai ya rufe Jamal, ba yanda Ram beyi dashi akan yasha magani ba anma yak'i. Ko abinci yak'i ci ga yanda jikinsa yayi zafi sosai. Da daddare bayan 'yan zaman makoki sun tafi, d'akin Abba ya shige ya hau kan gadon ya k'udundune cikin barko yana kuka yana kiran sunan Abban a hankali. A haka bacci ya d'aukesa cike da kewan Abban nasa. Tun daga ranar Jamal ya k'ulla abota da tunani, Ram da sauran 'yan uwa sunyi lallashin har sun gaji. (Hmm mutuwa kenan, Allah bai tab'a barin wani dan wani yaji dad'i) Tun da akayi rasuwan Ummy bata k'ara saka Jamal a idonta ba sai ranar da akayi uku da safe, lokacin ta fito daga side d'in su zata na Mami, ta had'u dasu shida Ram sun fito daga side d'in Abba. Jikinta ne yayi sanyi ganin yanda ya rame cikin kwana uku. Wasu hawaye ne suka gangaro mata, har sun gota ta, Jamal ya tsaya ya juyo suka had'a ido. Kai ta langwab'ar ya tako zuwa gabanta ya tsaya yana kallan cikin idonta "I hope ba inda ke miki ciwo yanzu" Kuka ta fashe dashi dan sosai ya bata tausayi, lumshe ido yayi ya bud'e ya zubasu akanta "Kukan menene? Ko akwai inda ke miki ciwo neh" Kai ta girgiza alamar Aa, sake lumshe ido yayi ya bud'e, ji yayi kamar ya rungumota cikinsa "Pls ki daina, ko kinaso nima nayi neh" Batace mai komai ba ta sake fashewa kuka ta bar wajan dasauri. Har ga Allah tausayin halin da yake ciki takeji, da kuma nata, sabda mai tare mata fad'an da wulak'ancin da ake mata yanzu baya nan. Ram ya k'araso yaja hannunshi suka bar wajan dan mutane ne a wajan dank'am suna jiransu dan yin addu'an uku. Bayan anyi addu'an an gama, Ummy na zaune a falo kusada su Najma wayanta ya soma ruri, bak'uwar number ta gani ta d'auka da sallama, Muryan Ram taji yana cewa "Hello Ummy kina jina" "Eh ina jinka" tace a hankali "Tun shekaran jiya rabon da Jamal yaci abinci, pls prepare something for him." "To" tace ya kashe kiran Tashi tayi ta koma side d'insu, rasa abinda zata dafa masa tayi, chan ta d'au dankali ta fere, ta d'ibo kayan miya tayi blending. Aikin take cikin natsuwa, cikin d'an lokaci ta had'a masa faten dankali daya ji kayan lambu sai k'anshi yake. Bayan ta gama ta kira Ram ta fad'a masa ta gama. Dakyar yaja Jamal zuwa side d'in. Duk yanda yayi yaci abincin k'i yayi. Haka ya hak'ura ya mik'e ya fita daga side d'in ya kira Ummy "Dan Allah kiyi k'okari kiga yaci abincin nan, baici komai ba tun sanda akayi rasuwan nan." To tace ta shiga side din a sanyaye. Kan dinning ta samesa zaune ya k'ura ma abincin ido. Tausayinsa ne ya ratsa ta, ta k'arsa taja kujera ta zauna kusa dashi tareda rik'o hannunsa. Ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya kalleta "Ya Jamal meyasa kaki cin abinci, zaka cutar da kanka neh. Dan Allah ka daure kaci" Girgiza mata kai yayi alamar Aa "Addu'a yakamata ka rink'a masa ba tunani bah. Rashin cin abincin ka bashi zaisa ya dawo bah" Rungumota yayi jikinsa ya fashe da kuka kamar yaro, kukan itama ta soma a hankali tana shafa sumar kanshi. Sun dad'e a haka, dakyar ta tsagaita da kukan ta soma lallashin sa. Abincin ta soma bashi a baki yana taunawa dakyar kansa a k'asa. Ba laifi ya d'anci dayawa. Ta tattara takai kayan kitchen ta dawo, d'akinsa ta shiga ta had'a masa ruwan wanka ta fito taja hannunsa zuwa d'akin. Binta kawai yake da ido har ta kaisa d'akin "Ga ruwa a toilet kayi k'okari kayi wanka" Ya nufi toilet d'in a sanyaye, ita kuma ta bud'e Wardrobe d'inshi ta ciro masa kayan da zaisa. Bayan ya fito ya shirya ya sake fita wajansu Ram da sauran abokansa da suke amsar gaisuwan tare. A ranar Ram ya koma kaduna sai kuma Ranar Bakwai zai dawo. Sauran 'yan uwa da abokan arziki duk ranar suka kokoma sai kuma ranar bakwai. Jamal bai shigo gidan ba sai bayan isha'i, side d'insu ya nufa ya haura sama zuwa d'akinsa da wani zazzab'i ne ke neman rufesa. Ummy na falonta taga ya hauro ya shiga d'akinsa sam bai lura da ita a falon bah. Ita kuma tsoro ne ya cikata, dan tunda akayi rasuwan kullum cikin tsoro take da daddare, su Najma ne ke kokarin tayata kwana. To yau suma suka koma saboda makaranta. Jim tayi a nan falon tanata muzurai, tunawa tayi da abincin da ta masa, hakan yasa ta mik'e dasauri tana waiwayan bayanta saboda tsoro. D'akin ta shiga da sallama, kan gado ta hangosa kwance ya k'udundune cikin bargo sai rawar sanyi yake. Dasauri ta k'arasa bakin gadon ta zauna tana kallansa hankali tashe "Ya Jamal bakada lafiya neh" Goshinsa ta tab'a taji zafi sosai, ta mik'e a rud'e "Barin je na fad'ama Mami azo a kaika asibiti" Kallo d'aya zaka mata ka gane hankalinta a tashe yake, dakyar ya iya cewa "No barki kirasu, i will be fine" Idanunta suka ciko da kwalla "Kaga fa jikinka da zafi sosai" D'agowa yayi dakyar yace "Zo kiga abinda zaki min" Ba musu ta matso gabab gadon tana kallansa, janyota yayi ta fad'a kan gadon ya rungumota sosai jikinsa. Idanu Ummy ta zare ta soma mutsu mutsu "Pls ki tsaya, inaso naji d'umin jikinki neh, sanyi nakeji sosai Wife" Yanda yayi maganan sosai ya bata tausayi, ta daina mutsu mutsun, rungumeshi tayi sosai ta d'aura kanta akan suman kanshi, d'ayan hannunta kuma tana wasa da suman. Sun dade a haka har bacci ya d'auketa. Cikin bacci taji kamar ana shafata, a razane ta bud'e ido taga wutan d'akin a kashe, rungumota yayi sosai a jikinsa ya had'e bakinsu waje guda. Nan ta biye masa sunata kissing juna, salan karatun nasa ne taji ya soma chanzawa jin hannunsa akan k'irjinshi. Mutsu mutsu ta soma tana k'okarin kwacewa anma ta kasa saboda rik'on daya mata. Lokaci k'ank'ani ya rabata da kayan jikinta. Ba shiri ta fashe masa da kuka tana girgiza masa kai tareda rad'a masa "Dan Allah Ya Jamal kayi hak'uri wallahi bazan iya bah" Kasa ce mata komai yayi sai wasa dayake da duk ilahirin jikinta yana wani irin numfashi. Wani kuka ta saki jin hannunsa a k'asanta. Gaba d'aya ya rud'e ya fita daga haiyacinsa. Ba irin rok'on da Ummy bata masa ba a daren ranar anma baiji bah. Bata k'ara rud'ewa ba saida taji yana addu'ar saduwa da iyali, wani wahalalen kuka ta saki ta k'ankameshi tana girgiza masa kai. Cikin kuka yace "Pls Wife" Sake k'ankamesa tayi, chan kuma ta saki wani razananen ihu. Ina ganin haka naja hannun k'awar arziki Sumaiya Eesah mukayo waje. Ummy Abduol✍🏻 [3/29, 9:23 AM] ‪+234 809 545 5143‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 50 n 51 Sake k'ankamesa tayi, chan kuma ta saki wani razananen ihu. Ina ganin haka naja hannun k'awar arziki Sumaiya Eesah mukayo waje. K'arfe Sha biyu da kusan rabi ya sarara mata, lokacin ko hannunta bata iya d'agawa. Gefenta ya fad'a yana maida numfashi da kyar, a hankali wasu sabin hawaye suka soma sauko masa, ya juya ya gefensa inda take kwace duk da baya hangota sosai saboda duhun dake d'akin. Tattaro k'arfinsa yayi ya janyota jikinsa dakyar yana maida numfashi. Wani wahalalen kuka ta saki a hankali, so take ta turesa daga jikinta anma ta kasa saboda yanda jikinta ya mata tsami. Bakinsa yakai saitin kunnenta ya rad'a mata "Its Ok Pls ki daina min asaran hawayenki" Tsoro tareda haushin sa ne suka cikata, tattaro sauran k'arfinta tayi tad'an tureshi ta sakw fashe masa da kuka. "Oh God!" Ya fad'a tare da dafa goshinsa. Mik'ewa yayi da kyar ya shiga toilet. Wanka yayi sannan ya tara mata ruwa mai d'umi. D'akin ya koma ya kunna wuta, jan bedsheet tayi ta rufe jikinta dashi tana cigaba da kuka. Bai ce mata komai ba ya k'arasa bakin gadon ya d'auketa ya kaita toilet. Yana sakata cikin ruwan ta saki k'ara a wahale da muryanta daya dishe, Tausayinta ne ya cikasa. Dakyar ya samu ya gasata tareda mata wanka dana tsarki. Duka da kukan shagwab'a kam yasha shi. A toilet ya nad'o ta ya ajeta kan bedside ya cire bedsheet d'in. Kuka ta sake fashewa dashi, ya dawo da ita kan gadon ya zaunar da ita shi kuma ya tsugunna gabanta "I'm sorry Wife, i dnt mean to hurt uh" Ta kauda kai gefe tana kuka tareda turo baki "Ni wallahi bazan yarda bah, kuma saina had'aka da Mama." Dariya yad'anyi yana shafa suman kanta dake d'igan ruwa "Bansan abinda zance dake ba Wife, uh really make my day. Allah ya miki albarka, ya barmu tare. I love uh so much" "Ni dai ka fita, kuma karka k'ara min magana" Yanda take maganan cikin shagwab'a ne ya burgesa, ya sa hannu yana k'okarin jan Towel d'in jikinta. "Wayyo ni ka bari" Ta sake fashe masa da kuka, dariya yayi ya zauna kusada ita tareda rungumota jikinsa "Kai Wife, haka zamu fara? Ni fah mabuk'aci ne, inasan kullum na rinka jin d'umin jikinki" Ta turesa tana k'okarin mik'ewa "Ahh!" Ta saki k'ara ta koma ta zauna tana kuka, fuskarsa d'auke da damuwa yace "Sorry! Ni neh koh" Ta juya kai gefe tana share hawaye, mik'ewa yayi ya d'auko vasline da kansa ya shafa mata tana ta nok'ewa. Nyt wears marasa nauyi ya d'auko mata a d'akinta ya saka mata yanata dariya ganin yanda ta chuno baki gaba tana b'ata fuska. "Kada dai bakin yakai gate" Duka ta d'aka mai ta sake fashe masa da kuka. Yayi saurin rungumota yaja musu bargo yana cewa "Oh God! Yaudai na shiga uku, bakya gajiya da kuka neh Wife" "Ni gobe gidan mu zan tafi bazan zauna bah, tunda mugunta kake min" Dariya yayi mara sauti, yana jinjina rigima irin na Wife d'insa. Lallashinta ya soma yi a haka bacci mai nauyi ya d'auketa a jikinsa. Murmushi yayi yana jin saukar numfashinta a k'irjinsa. Wani santa da tausayinta ne ke k'ara shigansa. Hawaye suka gangaro masa na tunawa da halin da suke ciki, gaba d'ayansu yanzu sun zama marayu. Tunane tunane ya soma har bacci ya d'aukesa. Wuraren biyar da kwata na asubah kukanta ya tashesa, d'an bud'e ido yayi ya hangota chan gefensa ta juya baya tana kuka, ba shiri ya mik'e zaune ya matsa kusada ita, janyota yayi jikinsa yaji jikinta da zafi sosai. Lumshe ido yayi ya bud'e Ya mik'e dasauri "Im so sorry Wife" K'ara narkewa tayi a jikinsa tana cigaba da kuka. Lallashinta ya soma ya mik'e dakyar dan shima zazzab'in yaji yana neman rufesa. Magani ya d'auko a drawer ya fita zuwa kitchen ya d'auko ruwa. Dakyar ta yarda ya bata maganin suka koma suka kwanta. Makara sukayi ranar, basu suka farka ba sai k'arfe goma na safe. Shi ya fara tashi yana sallati ganin gari yayi haske. Janyeta yayi daga jikinsa ya gyara mata kwanciya ya shiga toilet. Wanka yayi tareda alwala ya fito, zaune ya sameta kan gado tana turo baki, murmushi yayi ya k'arasa bakin gadon ya shafa gefen fuskanta "Morning Wife" Ta sake turo baki ta kauda kai, k'ugu ya rik'e ya tsaya gabanta "Idan baki daina turo min baki bah zan sake" Nan da nan kwalla ya cika idonta "Ayyah fah! Ayyah fah!! Ba kyau" Dariya yayi ya shimfid'a sallaya ya tada sallah. Dak'yar ta mik'e ta shiga toilet ta sake gasa jikinta sannan tayi wanka tareda alwala ta fito. Ta gabansa ta wuce tana tafiya a hankali tana cije leb'e, tausayinta ne ya kamasa ya mik'e ya d'auko mata hijab d'in da kansa ya saka mata ya kaita kan sallaya. Ranar da kansa ya musu breakfast sai tattalinta yake. Bashi ya shiga side d'in Mami ba sai bayan sallan Azahar. Zaune ta samesu a falo itada Aunty Faty da Mabrookah sai sauran masu amsar gaisuwa. Har k'asa ya tsugunna ya gaida su, Aunty Faty ta yatsine fuska tace "Sai yanzu ta sakeka kenan" Haushin Aunty Faty yakeji yanzu sosai, yace "Eh Bata da lafiya neh" Aunty Faty da Mabrookah suka kalli juna a tsorace. Mami ya kalla yace "Mami kuyi hak'uri Yau Wife bazata samu shigowa ba, batada Lafiya" Ya mik'e yace "Barinje waje wajan mutane" Baki bud'e Aunty Faty ke kallansa harya fita. Ita kuwa Ummy tana chan tana sharan baccinta dan yace bayasan taje ko ina ta zauna a d'akinta. Har yakai bakin gate wayansa ta hau ruri, numbern Bilal ne ya fito ya d'auka tareda karawa a kunne. Wani Dariya Bilal ya kwashe dashi kana yace "Jamaludeen Surajo! Har yanzu kana bani mamaki, lallai bakasan Bilal bah. Kamar yanda na fad'a maka a baya, akan abinda nakeso ina iya yin komai" Jikin Jamal ne ya soma rawa, ya katse kiran dasauri hankalinshi a tashe. Numbern Mifzal ya soma kira dan d'an sanda neh, ringing d'aya biyu ya d'auka. "Mifzal na samu wanda ya turo wad'an nan 'yan fashin, kuma yanzu ta tabbatar min da haka" Daga chan b'angaren Mifzal yace "Are you sure" Murya na rawa yace "I'm very sure." "To shikenan ka kwantar da hankalinka, ina nan zuwa yanzu" Bai jira mai Jamal d'in zaice ba ya kashe kiran. Waje ya fita hankalinsa tashe yana jiran k'arasowar Mifzal, cikin 'yan mintina ya iso k'ofar gidan. Bayanin duk abinda ke faruwa Jamal ya masa tareda nuna masa texts d'in daya ke turo masa. Da kuma wayan da sukayi yanzu dan yasa a record. Mifzal yace "Lallai bashida imani, anma inaso ka bani had'in kai. Dan a hankali nakeso abi komai, sannan ko kad'an kada ka nunama Ummy ko su Mami abinda ke faruwa" Kai kawai Jamal ya iya d'agawa. Numbern Bilal d'in yaba Mifzal sukayi musabaha ya tafi tareda alk'awarta masa komai zaizo k'arshe kwanan nan. Haka Ango Jamal ya cigaba da tattalin Wife d'insa har zuwa ranar da Abba ya cika kwana bakwai. Ranar sunga jama'a daban daban, har 'yan ajinsu Ummy sunzo mata gaisuwa da sauran 'yan uwa da abokan arziki. Aunty Faty kam zama daram dan tace nan zata zauna ta taya 'yar uwarta takaba. Ran Jamal idan yayi dubu ya b'aci dajin zaman Aunty Faty a gidan. Bayan bakwai Jamal ya koma bakin aikinsa, a ranar Ummy ce da girki, taci gayunta cikin Atampa riga da skirt, wanda ya amsa jikinta sosai. Kitchen ta shiga ta fito da kulolin abinci ta d'aura kan dinning da komai datake buk'ata. Har ta bud'e k'ofar d'akinta ta jiyo k'aran motansa, dasauri ta shiga ta sake fesa turare mai dad'in k'anshi ta fito. Kamar kullum d'akin Mabrookah ya shiga, itada Aunty Faty ya samesu suna k'us k'us, baice musu komai ba ya haura sama. Tun a stirecase k'amshi ya soma masa sallama. Wani lallausan murmushi ya saki ya k'arasa hawa saman. D'aki ta fito tana takawa a hankali tana masa murmushi "Sannu da dawowa" Tasa hannu zata karb'a jakan hannunsa, janyo hannun nata yayi ta fad'o jikinsa ya matseta sosai "Zaki kasheni da salon gayunki Wife. Kinyi kyau sosai" "Nagode" tace tana 'yar murmushi. Ya shagwab'e fuska yace "No Wife, ni dai ba haka nakeso kina min sannu da zuwa bah" Ya sake janyota jikinsa yace "Ko kiga yanda akeyi" Had'a bakinsu yayi waje guda, ya sureta yayi d'akinshi da ita sai wuntsile wuntsile take "Ni dai dan Allah ka saukeni" Duk abinda sukeyi Mabrookah na tsaye ta wajan stirecase tana kallansu zuciyarta na tafarfasa. Daga chan k'asa Aunty Faty tace "Maza jeki barbad'a kafin su fito" Ta goge kwallan daya taru mata a ido ta k'arasa dinning d'in. _Manage this pls_ bana d'an jin dad'i neh Ummy Abduol✍🏻 [3/29, 9:23 AM] ‪+234 809 545 5143‬: ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Assalamu Alaikum. A gaskiya bani da bakin da zan gode muku Fans d'ina, naga sak'o da dama naga kira da dama, ina godiya Allah ya barmu tare Ameen. Alhamdulillah na soma samun sauk'i, saidai zaku cigaba da min afuwa na jina ba akan lokaci bah. But uh guys are always on my heart* Wannan shafin naku ne Masoya *Ummy Abduol* Ina alfahari daku. My Facebook Fans kuma ina godiy ba iyaka Musamman Ahmad Yusuf Muhammad. Thank Uh so much. _ga masu san novels d'ina dana rubuta a baya, suna iya ziyartan Page d'ina na facebook UMMY ABDUOL NOVELS domin samun littafaina_ Page 52 n 53 Ta goge kwallan daya taru mata a ido ta k'arasa dinning d'in. Yana shiga d'akin bai ajeta ko ina ba sai kan gado, hawa yayi ta soma turo baki tana matsawa "Ba kyau fah Ya Jamal, ba kyau" D'an murmushi yayi ya sauka daga kan gadon tareda yin k'wafa, ya juya ya fita dan yabar jakan daya dawo dashi a falo. Har Mabrookah ta bud'e kulan zata barbad'a ta juyo k'aran kamar za'a bud'e kofa, dasauri ta mayar ta rufe ta shige labule ta b'oye dan yanada kauri sai ka k'ura ido zaka ganta. Fitowa yayi yad'anyi jim yanabin falon da kallo dan yad'anji motsi, Jakan ya d'auka ya juya Ummy ta fito daga d'akin tana turo baki "Keh koh!" Ta k'arasa dinning d'in ta zauna, "Ni yunwa nakeji, tun dazu nake jiranka" Baice mata komai ba saima k'arasawa dayayi kusada ita, tashi tayi k'okarin yi yasa hannu ya maidata zaune yana murmushi ya rad'a mata "Ni kuma ke nake buk'ata sosai Wife" Tayi saurin tureshi a hankali. yayi murmushi ya zauna kan kujeran dinning d'in ya k'ura ma k'irjinta ido. Serving d'inshi tayi sannan itama ta zuba nata kad'an ta koma ta zauna. D'aukan nata yayi ya had'a da nasa, ta turo baki tana kallansa. Mabrookah dake cikin labule sai zufa take tana kallansu, ga wani hawaye dake gangaro mata. Ji take kamar taje ta shak'e Ummy ta kasheta. A baki Jamal ya soma ba Ummy tana ci a hankali tana cigaba da turo baki, Yayi murmushi tareda shafa bakin yace "Wife rigima" Kamar ance ta d'aga kai ta hango Mabrookah tsaye cikin labule tana kallansu, sosai ranta ya b'ace Jamal yace "Yadai Wife naga fuskanki wani iri" Murmushin yak'e ta masa "Babu komai" Ta d'au spoon ta deba abincin takai mai baki tana shagwab'a "Ni dai inaso naje gida naga Mama" "Kai Wife! Yaushe yaushe kikaga Maman" Ta mik'e tana turo baki tareda bubuga k'afa a k'asa tana kukan shagwab'a "Nidai..Nidai zanje naga Mamana" Baki bud'e ya kalleta, ta cigaba masa da kuka tana turo baki, janyota yayi ta fad'a jikinsa tareda zagaye wuyansa da hannunta tana murmushi, wanda ita kad'ai tasan dalilinsa "Wife rigimanki tayi yawa, kinsan meh?" Ta girgiza masa kai alamar Aa Bakinsa yakai saitin kunnenta ya rad'a mata "I miss uh so much, pls yau dai ki tausaya min" Kokarin mik'ewa take ya rik'eta ya had'a bakinsu waje d'aya. Mabrookah dake cikin labule kamar ta sume haka takeji, kuka kawai take a hankali tana cigaba da kallansu. Biye masa Ummy tayi sunata kissing juna a falon, dakyar ta janye jikinta ta mik'e tareda jan gaban rigansa cikin salo "Baby tashi muje, dan akwai 'yan sa ido" Sam bai cikin haiyacinsa dan network d'insa ya riga ya d'auke. Haka ya bita har zuwa d'akinsa. Mabrookah na ganin sun shige ta fito tana hawaye hannunta aka tana kuka. Bata ko bi takai maganin ba ta sauka zuwa d'akinta. Aunty Faty ta samu a d'akin ta fad'a kan gado tana kuka "Ni wallahi na gaji, ni ya sawak'e min na huta" Buge mata baki Aunty Faty tayi rai b'ace "Anma ban tab'a sanin ke akuya bace Mabrookah sai yau. Ya sawak'e miki?" Ta maimaitana tana kallan Mabrookahn dake ta sharb'an kuka. "Umma Jamal baya sona, ko abinci na baya san ci. Bai damu dani ba sai Ummy" Dogon tsaki Aunty Fatyn taja "Ke wawiya ce, a gabar da ake ciki yanzu ko da d'ibar namanki zai rink'a yi yana ci karki sake ki rabu dashi. Gidan kud'i fa kike, Allah kad'ai yasan mak'udan kud'in da zai gada" "Ni dai Umma ina sanshi ban damu da kud'insa bah" Duka Aunty Faty ta d'aka mata tana huci "Wallahi ki shiga taitayinki, Albasa dai batayi halin ruwa ba Mabrookah" Ta mik'e a fusace tana cewa "Ki zauna nan soyaiya ta rufe miki ido, idan bakiyi anfani da maganin nan ba kina nan Ummyn da kika raina zata k'wace gidan gaba d'aya" Fuuuu tabar d'akin a fusace. Mabrookah ta sake fashewa da kuka tana ganin abubuwan da suka faru d'azu tsakanin Ummy da Jamal take gani a idonta. Suna shiga d'akin Ummy ta sakeshi ta shiga toilet ta had'a masa ruwan wanka ta fito. Kwance ta samesa kan gado fuskansa na kallan ceilng idanunsa a lumshe ta k'arasa bakin gadon "Ruwan wanka na jiranka" Yi yayi kamar baiji bah, ta turo baki ta matsa sosai kusa dashi. Yayi saurin janyota ta fad'a kan k'irjinshi, tashi take kokarin yi ya rik'eta sosai a jikinsa "Dan Allah Ya Jamal ka daina wallahi banaso" Yanda tayi maganan a shagwab'e yasa shima ya shagwab'e fuska yace "In ni kuma inaso fah" Ta mak'e kafad'a dakyar ta janye jikinta, ya mik'e yana cije leb'e ya shiga toilet d'in. Falo ta koma ta tarar Mabrookah tabar wajan, ta rik'e k'ugu tana murmushin mugunta. D'akinta ta koma ta sake wanka tayi sallan isha'i sannan ta chanza zuwa night wears ta kwanta. Har bacci ya soma d'aukanta taji kamar ana shafata, a razane ta mik'e zaune taga Jamal ne duk yabi ya susuce, kamar zatayi kuka tace "Dan Allah ka bari" "Pls Ki tausaya min wife, a matse nake plssss" Bai jira mai zatace ba ya soma shafata. (Asuba ta gari Angon Jaleelah) Kukan shagwab'a Ummy keyi tana kai masa duka a k'irji, murmushi ya mata ya d'auketa ya kaita toilet. Wanka ya mata ya dawo da ita sai kukan shagwab'a take masa. Dakyar ta yarda ya shiryata cikin dogon riga bak'i mai pink flowers a jiki. Har ya gama bata daina turo baki bah. Murmushi yayi ya d'ago hab'arta ta lumshe ido dasauri. Cikin sanyin murya yace "Allah ya miki albarka Wife, bansan da kalmar da zanyi anfani dashi ba wajan gode miki. I love uh so much" Hannunta ya kama ya saka mata keyn mota ya dunkule hannun "Tukuicin faranta min da kikayi First night, Thank uh so much" Tunda ya saka mata keyn a hannu take bin hannun da kallo idaunta waje. Kwantar da ita yayi yaja mata bargo "Kisha baccin ki dan jiya ban bari kinyi bacci bah" Cikeda kunyansa tace "Nago..." Yatsansa yasa a lips d'inta "Shhhhhh... Babu godiya tsakanina dake Wife, just sleep" Tayi saurin lumshe idonta tana murmushi. Farinciki yau yakeji fiye da ko yaushe, dakin ya sauka ya shiga na Mabrookah. Zaune ya sameta kan gado tana shirin zuwa makaranta, kallo d'aya ta masa ta kauda kai, ya zauna kusa da iya da d'an murmushi "Amarya tah!" Ta kauda kai gefe tana saka handout a cikin jakanta "Amarya yau ba magana" Batace komai bah ta d'au jakanta ta fita tana gungunai, murmushin takaici yayi ya mik'e ya fita. Sama ya hau yayi wanka ya shirya, d'akin Ummyn ya lek'a ya samu tana bacci, peck ya mata a goshi ya fita. Direct side d'in Mami ya nufa, bai tarar da kowa a falo ba ya haura sama zuwa d'akinta, zaune ya sameta tana latsa waya. Ya zauna k'asa kusada iya ya gaidata. Amsawa tayi tareda aje wayan a gefenta "Yanzu dai Ummy sai tagadama take zuwa tana gaida ni" Yad'an sosa k'eya tareda duk'ar dakai "Batada lafiya ne kwana biyu shiyasa" Gyad'a kai kawai tayi sannan tace "Naga sabon mercedes a haraban gida na wanene" Gabansa ne ya fad'i ya d'an dago suka had'a ido yace "Na Ummy neh" "Mene!" Mami ta furta a fusace "Na Ummy fah kace, waya bata mota?" Murya a d'an sark'e yace "Ni na siya mata" Ran Mami idan yayi dubu ya b'aci tace "Ita kuma Mabrookah fah" Jim yayi chan wayansa ya soma ruri, cirowa yayi daga aljihun shi yafa Mifzal ne yad'an kalli Mami dake ta hararansa "Tun ba'aje ko inaba kenan ka fara nuna rashin adalci Jamal, yau sati biyu da rasuwan mahaifinka har ka fara b'arna da kud'i" Shiru dai yayi baice komai bah kansa k'asa "Ina magana kayi banza dani" "Dan Allah kiyi hak'uri, kinga fa Mami kwata kwata Mabrookah bata daraja ni taya zanji dad'i har na mata ky..." "Rufemin baki shanyayen banza, to bari in gaya maka dole itama Mabrookah sai ka saya mata mota itama" "Anma Mami..." Ta d'aga masa hannu tana huci "Na gama magana, ka tashi ka bani guri" Mik'ewa yayi a sanyaye ya fita daga d'akin, a corridor ya had'u da Aunty Faty, saida ya juya k'eya sannan ya gaidata, harara ta zafga masa bata amsa ba ta bar wajan. Motansa ya shiga yabar gidan ransa ba dad'i, yana cikin driving Mifzal ta sake kiransa. Gefen titi yayi parking sannan ya kirasa, daga chan b'angaren Mifzal yace "Idan baka komai kazo Office akwai wasu mahimman abubuwa danakeso na fad'a maka akan Case d'in nan" Toh kawai Jamal yace ya kashe kiran ya tada motan ya nufi office d'in Mifzal. Bayan sun gaisa Mifzal ya gyara zama yace "Kasan hausawa na cewa idan baka iya kama b'arawo ba sai b'arawo ya kamaka" Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 54 n 55 "Kasan hausawa na cewa idan baka iya kama b'arawo ba sai b'arawo ya kamaka" Jamal ya gyara zama yana sauraronsa "Bazai yuwu hakanan muje mu kamasa ba duk da akwai hujjoji masu kyau a hannun mu" Jamal ya b'ata fuska "To yanzu me kace zaka fad'amin mai mahimmanci" Mifzal ya cigaba sa cewa "Munyi bincike a kansa sosai mun gano yana zaune ne a gidan wani hamshak'in mai kud'i mai suna Alhaji Ameenu, sai dai mutanen unguwar babu wanda yasan menene sana'ar mutumin. Kuma kwanan nan suka dawo k'asar dan da ba anan yake bah" Jimm Jamal yayi yana tunani, Mifzal yace "Yanzu haka sun bar k'asar shida Alhajin, anma iyalensa na nan. Dole yanzu zamu jira dawowan su dan mu cigaba da bibiyarsa, saboda mu gane shi Alhajin Ameenun wanene, kasan kama babban mutum a k'asar nan nada hatsari. Musamman shi da bamusan meya taka bah" Mik'ama Mifzal d'in hannu yayi sukayi musabaha "Nagode sosai Friend, Allah ya saka da Alheri" Da murmushi ya amsa da "Ameen. Ka kwantar da hankalinka, insha Allahu zamuyi iya yinmu dan mu kama mai hannu cikin wannan kisan" Ya lumshe ido ya bud'e a hankali tareda mik'ewa ya masa sallama ya tafi. Office ya nufa yana tunanin abinda Mami tasa shi dole yayi, bawai baida kud'in baneh Aa. Tunaninsa kawai yanda zai b'annatar da kud'insa wajan wacce bata darajasa, da biyaiya ko na second d'aya. Dogon tsaki yaja yasaka hannu cikin suman kanshi yana ya mutsawa yana b'ata fuska. Waya yayi dan a kawo masa motan, cikin awa da baifi d'aya ba aka kawo masa, sak irin na Ummy ce, saidai na Mabrookah Bak'i neh, ita kuma na Ummy Arsh ce. Gida yasa suka kai masa motan, shi kuma bayan ya tashi aiki ta biya kasuwa ya sayi kayan masarufi ya nufi gidansu Ummy. Sosai Mama taji dad'in zuwansa, hira sukayi sosai kamar ba suruki bah, sai bayan Magriba sannan ya mata sallama ya tafi tanata saka masa Albarka. A masallacin k'ofar gidan ya tsaya yayi sallahn Isha'i sannan ya shiga gidan, yanasa k'afa a k'ofar Falon side d'insu gabansa ya fad'i tunawa da yayi yau Girkin Mabrookah neh. Itakuwa Hajiya Mabrookah yau a shirye take, saboda wani Pills da k'awarta ta bata a makaranta datakai mata complain d'in baya kusantar ta. Ko takan Maganin Aunty Faty batayi ba tunaninta kawai yanda zata zuba masa k'wayar a drink har tasamu yasha. A sanyaye ya shigo ciki da sallama ya soma takawa a hankali yana bin Falon Mabrookah da kallo, rungumesa yaji anyi ta baya ko ba'a fad'a masa ba yasan Mabrookah ce. Sabda baisan rigima a daran yasa ya birkito ta yana mata murmushi "Sannu da zuwa Honey tun dazu nake jiranka" Fuskanta dayasha makeup ya shafa yana cigaba da murmush, peck ta kai masa a kumatu kana wani shu'umin murmushi "Nasan ka gaji, shiyasa ta had'a maka ruwan wanka tun d'azu" Har lokacin ya kasa magana sai binda da ido yake kamar ranar ya soma ganinta, hannunsa taja har sama, Ummy suka samu a falon ta takure waje d'aya da alama tsoro takeji, kallo d'aya ta musu ta kauda kai, janshi Mabrookahn ta cigaba dayi har d'akinsa, ta aje briefcase d'insa akan bedside ta k'arasa inda yake tsaye yana cire agogon hannunsa, mab'allin gaban rigansa ta soma cirewa, sai hanata ba har ta cire ya rage farin singlet, hannu tasa ta cire belt d'in wandonsa, ganin baice komai ba yasa ta samu k'warin guiwa tasa hannu zata cire mab'alli Wandonsa, saurin rik'e hannunta yayi fuskarsa a d'aure "Meye kuma haka Mabrookah, ki bari mana ko nace miki ne bazan iya cirewa bah" Ta shagwab'e fuska ta sake matsowa kusada shi tana d'an murmushi "Kai Yaya, anfa ce yana da kyau mace ta rink'a taimakon jikinta" Guntun tsaki yaja ya matsar da ita gefe ya shiga toilet d'in ya danna key yanata mita cikin ransa. Tana ganin ya shiga ta doka tsalle tana dariya ta fita daga d'akin dasauri, har lokacin Ummy na falon a takure wannan karan hawaye ne ke fita daga idonta. Kallanta Mabrookah tayi ta kwashe da dariya, karairaya ta soma har ta k'arasa inda Ummyn zaune, ta rik'e k'ugu tace "Ke k'aramar 'yar bariki ce. Yau zan nuna miki ke ba komai bace, ki toshe kunnenki da runtse idanunki dan yau zaki sha mamaki" Cike da takaici Ummyn ke kallanta, wani k'ollolon bak'in ciki ya tokare mata mak'oshi, kasa ce mata komai tayi. Mabrookah ta sake kwashewa da dariya ta bar wajan tana rawa tana wak'a a hankali. Sauka tayi ta kwaso abincin data masa ta shiga dashi d'akin. Har lokacin bai fito bah, ta juya ta kalli k'ofar toilet d'in sannan ta ciro tablet d'in da k'awarta ta bata ta bud'e 5alive d'in data kawo ta saka guda uku ta jijiga ta rufe. Ta sake kallan k'ofan sannan ta mik'e dasauri ta fita ta mayar. Koda ta dawo bata tarar da Ummy a falon bah, tayi dariyar mugunta tareda k'wafa "Ke k'aramar mara kunya ce" Taja dogon tsaki ta shiga d'akinsa, zaune ta samesa kan gado daga shi sai towel a waist d'inshi da kuma wani a hannunsa yana tsane ruwan kansa. Cikin tafiyar jan hankali ta k'arasa ta amsa Towel d'in dake hannunsa tana cigaba da tsane masa. Ko uffan baice bah, gaba d'aya hankalinsa na wajan Wife d'insa dan yasan batayi bacci yanzu. K'okarin mik'ewa yake tayi saurin kama hannunsa cikin shagwab'a "Ina zaka kuma Honey gafa abinci na kawo maka" Kallan kulolin yayi tad'an yatsine fuska yace "Am Ok! Nayi attending wani walima kafin nazo" Tad'an turo baki ta d'au cup ta tsiyaya masa 5alive d'in ta mik'a masa "To ga wannan kasha tunda ka k'oshi" Bai mata musu ba ya amsa ya kai bakinsa, saida yasha kusan rabin cup d'in sannan ya aje. Murmushin mugunta tayi ta d'au trayn da fita tana tafe tana dariya k'asa k'asa. Harya mik'e zai shiga zaije wajan Wife d'insa dan itace a ransa. Wani jiri ne ya kamasa ya koma ya zauna dasauri tareda dafe kansa. Mabrookah ce ta shigo cikin wasu fitinanun kaya tana karairaya, kam cinyansa ta zauna tana shagwab'a duk da yanda gabanta ke fad'uwa "Honey yadai" D'agowa yayi ya kalleta har saida ta tsorata ganin yanda idanunsa sukayi ja, rungumota yayi jikinsa ya kwantar da ita kan gadon ya soma aika mata sak'oni masu wuyan fassara, duk abinda yakeyi da zafi zafi yakeyi saboda yanda ya kamu sosai. Mabrookah ba baka ba har kunne, an samu abinda akeso, nidai ina ganin haka nayo waje na basu guri. Ummy tsoro ne ya cikata, ga wani kishi daya dabaibayeta, k'udundune wa tayi cikin bargo ta rufe har kanta. Tsoro ne ya k'ara cikata dan duk sanda ta rufe idanunta b'arayin nan take gani sanda suka harbi Abba. A guje ta fito tana kallan bayanta, kuka ta soma mara sauti ta fito falonta ta kunna switch na wuta tahau kan kujera ta kwanta tana cigaba da kuka tana waiwayen bayanta. Kan 1seater ta koma ta kwanta tasake k'udundunewa tana kuka. A hankali a hankali ta soma jiyo ihun Mabrookah daga d'akin Jamal, wani kukan ta saki mai sauti ta soma wurgi da pillows d'in dake kan kujerun. Ranar batayi bacci bah har saida aka kira sallahn Asubah, dakyar ta mik'e a wajan ta shiga d'akinta ta fad'a toilet tayo alwala. Dakyar ta iya yin sujjada sbda yanda idanunta suka kukumbura. A b'angaren Jamal da Amarya Mabrookah kuwa, wuraren k'arfe uku ya sarara mata, ya fad'a gefenta yana maida numfashi, sam baiyi tunanin zai samu Mabrookahn a budurwa ba sai gashi ya sameta fil a leda. Albarka ya soma saka mata itako sai kukan shagwab'a take masa da k'ara narkewa a jikinsa. Da kansa ya mata wanka ya shiryata tanata masa shagwab'a, shima ya shiga wankan, ya fito ya tada sallah, nafilfili ya soma har aka kira sallan asubah ya sake alwala ya fita masallaci. Bai shigo gidan ba sai k'arfe bakwai da rabi, duk hankalinsa na wajan Wife d'insa, sauri yake yaje gareta tunawa da yayi bai dubata ba daran jiya. A stirecase sukayi kicibus da ita cikin shirin makaranta, fuskanta ya kumbura yayi ja abinda da farar fata. Ta gefensa zata rab'a ta wuce yayi saurin rik'o hannunta "Wife meya sameki a fuska" Kwace hannunta ta soma yi idanunta taf da hawaye "Ka sakeni na wuce, ka kyalleni" Kalmar datake ta fad'a kenan, da mamaki yaketa kallanta, ta fashe masa da kuka "Ni ka sakeni, ka kyalleni" Rungumota yayi jikinsa ta soma kici kicin k'wacewa tana dukansa a k'irji "Pls wife kiyi hak'uri, nasan nayi laifi. I donno what came over me har na dawo ban dubaki bah" Harzuk'a tayi dajin maganansa, wato ita zai rainama wayo, turesa tayi da duk iya k'arfinta ta fashe da kuka ta fita daga side d'in da gudu. Binta yayi yaga tayi side d'in Mami, slow yayi ya sauke ajiyar zuciya ya tsaya daga bakin side d'insa. A bakin k'ofan Side d'in Mamin ta tsaya saida tayi kuka mai isarta sannan ta goge hawayenta ta tura k'ofan ta shiga da sallama. A falon k'asa ta had'u da Mamin, suna had'a ido da Aunty Faty gabanta ya fad'i. A hankali ta k'arasa ta zauna k'asa chan nesa dasu tace "Ina kwana Mami" Wani dogon tsaki Mamin taja sannan tace "Sai yau kikasan zakizo ki gaisheni?" Aunty Faty tace "Ai ta rik'a, kinsan itace mai gidan" Kan Ummy a k'asa tana hawaye, Mami tace "Baki isa ki rabani da d'ana ba wallahi, kuma kuruwana da d'ana kur, naman mu d'aci garesa" Ta nunata da yatsa ta cigaba da cewa "Ni nan da kika gani, asiri ya buga dani ya barni, asiri baya cina daga ni har d'ana. Baki isa ki chanza min alk'iblan gidana bah" Aunty Faty ta tab'e baki tana karkad'a kafa "Kuma kina dawowa ki kawo min makullin motan da ya baki, dan baki isa kina hawa mota, 'yata na hawa bah" cewar Mami. Aunty Faty tace "Fita kiba mutane waje" Dasauri ta fita tana hawaye, har lokacin Jamal na tsaye yana ciranta, ganin ta fito tana hawaye yasa ya runtse ido cike da bak'in ciki. Mota shiga driver yajata suka bar gidan har lokacin bata daina kuka bah. _Thank Uh so much My Fans_ I'm now better Alhamdulillah Ummy Abduol✍🏻 ♠♠♠♠♠♠♠♠ ♠♠♠♠ *JAMALUDEEN* ♠♠♠♠ ♠♠♠♠♠♠♠♠ By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* Page 56 n 57 Mota ta shiga driver yajata suka bar gidan har lokacin bata daina kuka bah. Ransa duk ba dad'i ya koma side d'insa, dakin Ummyn ya nufa yana murd'awa k'anshin room freshner had'e dana turaren wuta suka masa sallama, a hankali ya shiga ya soma bin d'akin da kallo, komai tsaf tsaf ba datti sai k'amshi had'e da sanyin Ac ke tashi. Toilet d'inta ya shiga yayo wanka ya fito sannan ya koma nasa d'akin dan babu kayansa a nata. Zaune ya samu Mabrookah sai turo baki take a shagwab'e, yad'anyi murmushi ya k'arasa kan gadon "Morning Sis" Baki ta sake turowa idanunta taf da hawaye "Ayyah Sis kuma, bayan ita Wife kake cemata" Yanda tayi maganan sosai ta basa dariya, gefen fuskanta ya shafa ya sakar mata murmushi ya mik'e ya soma shiryawa dan yayi latti. Duk abinda yake tana nan ta k'uresa da ido har ya gama shiryawa. Sosai yake mamakin irin rashin kunyan Mabrookah, ko gezau batayi ba sanda ya warware towel d'in jikinsa zai saka kaya. Yana gamawa ya juyo da murmushi "Sai na dawo" "A dawo Lafiya" tace tana cigaba da turo baki. Yana fita ya nufi side d'in Mami gabansa na fad'uwa, gaidata yayi itada Aunty Faty, ba yabo ba fallasa Aunty Faty ta amsa masa gaisuwan. Mami ko da fara'a tace "Naga mota Allah ya saka da alheri" Shaf shi yama manta da maganar mota, Ameen kawai yace ya mik'e ya musu sallama ya tafi. Bayan tafiyarsa Mabrookah ta mik'e dakyar ta koma d'akinta, wanka ta sakeyi ta sauya zuwa riga da skirt na material. Da d'angyashi ta shiga side d'in Mami Kan dinning ta samesu suna breakfast, tunda ta shigo Mami ke binta da ido har taja kujera ta zauna tareda "Washh" ta yatsine fuska kamar zatayi kuka "Yaya dai Lafiya?" Cewar Aunty Faty tana kallanta Ta sake shagwab'e fuska "Ba Ya Jamal baneh" Mami ta girgiza kai kawai dan ta fahimci inda maganan nata ta dosa, Aunty Faty tayi kini kini darai "Me ya miki Jamal d'in" "Ba shi baneh ya...." Mami tayi saurin katseta da cewa "Wannan ai tsakanin su ne na mata da miji, mu ba ruwanmu a ciki" Kurrrri Aunty Faty tayi ma Mabrookahn tana kallanta. Chan kuma ta girgiza kai ta janyo plate ta zuba mata breakfast d'in ta tura mata gabanta. Ranar a side d'in Mami ta wuni sai shagwab'a take suna biye mata, bama kamar Aunty Faty har cewa take ta natsu dan k'ila ta samu ciki kada yazo ya b'are suyi asara. Dariya ko Mami tayi har cikinta ya kusa yin ciwo. A b'angaren Ummy kuwa kuka ta dunga yi a mota, saida taga driver yayi parking a k'ofar makarantan sannan tayi shiru ta goge hawayenta ta fito. Gaba d'aya babu abinda ta fahimta a karatun ranar sai dai tad'anji dama dama tunda tabar kurkukun gidan nan. K'arfe uku driver ya dawo ya d'auketa ya maidata gida, d'akinta ta wuce kai tsaye ta cire uniform d'in jikinta ta d'aura towel ta shiga wanka. Tana fitowa ta saka bak'in jallabiya ta shimfid'a sallaya ta tada sallah dan la'asar tayi. Kicin ta shiga ta dafa indomie guda d'aya dan bama ta tunanin zata iya ci, ta fito ta dawo d'akinta. Kad'an taci ta ture gefe ta kwanta, kan kace me bacci ya d'auketa dan dama batayi bacci ba jiya. Tun k'arfe uku yaketa neman layin Wife d'insa anma a kashe, tunaninta ne ya hanasa sukuni, musamman abinda ya faru tsakaninsu d'azu. A daddafe ya gama aikinsa, lokacin ana kiraye kirayen sallahn Magrib. Saida ya tsaya masallacin k'ofar gida yayi sallah sannan ya shigo gidan. Side d'inshi ya nufa kai tsaye, Mabrookah ya samu a falonta taci gayu cikin wani farin top mai hannu d'aya tsawonsa bai kai cibiya bah, sai wani mini skirt na jeans mai kyau. Da d'an sauri ta k'arasa ta rungumesa tareda shiga jikinsa "Oyoyo Honey na" Tab'e baki yayi yad'an rab'ata da jikinsa "Ya kike" Ta turo baki "Bayan ka barni cikin pain da safe kayi tafiyarka" D'an murmushi ya mata, "Ina zuwa" Ya haura sama dasauri, d'akinsa ya shiga ya sami gadon kacha kacha kamar yanda ya bashi da safe, ransa ne ya b'aci yaja dogon tsaki ya aje briefcase d'in hannunsa. Wanka ya soma yi yana mai takaicin hali irin na Mabrookah, a girme dai ta girme ma Wife d'insa naisa ba kusa ba, Anma sam batada hankali da kuma sanin yakamata. Three quater yasa light brown da Bak'in top ya fito. D'akin Ummyn ya murd'a ya shiga da sallama, k'asa ya sameta kwance kan sallaya tana bacci. K'arasawa yayi wajan ya kwanta kusada ita ya janyota jikinsa sosai sannan ya soma shafa albarkatun k'irjinta a hankali. Cikin bacci taji ana shafata, ta bud'e ido dakyar dan bacci ne sosai a idota, ganin Jamal yasa ta k'ara bud'e ido ta soma turasa da k'arfi "Ni ka daina tab'ani, ka fita ka bani waje" Ta k'arashe maganan cikin kuka kanta k'asa. Bai damu da abinda zata masa ba ya sake rungumota jikinsa, kuka ta soma yi mai sauti tana dukansa "Ni ka kyalleni, ka koma wajanta. Shine kukayi tayi dan naji koh, ni bazan zauna ba gid..." Saurin had'a bakinsu yayi waje d'aya, sai yanzu ya gane fushin datake, sosai abin ya basa mamaki ganin yanda kishisa ya rufe mata ido. Ta wani b'angaren kuma yaji dad'i sosai, ko ba komai yanzu ya k'ara yarda tana sansa. Mutsu mutsu ta cigaba a jikinta tana k'okarin k'wacewa anma ta kasa. Saida ya tsotsi bakinta san ranshi sannan ya saki bakin, idanunta a lumshe hawaye na cigaba da gangara daga idanunta, a hankali ya rad'a mata "I'm so sorry!" Ta bud'e idanunta da sukayi ja tana kallansa, "Mabrookah matata ce, dole na sauke duk wani nauyi nata daya rataya a kanta. Pls ki daina fushi dani kinji, i so much love uh" Duk abinda ya fad'a gaskiya ne, sai dai har lokacin haushin sa takeji turesa tayi daga jikinta ta mik'e ta shiga toilet ta saka key. Binta da ido yayi tareda sauke ajiyar zuciya, shi baisan yanda zaiyi ba, sam baya san fushin wife d'insa. Mik'ewa yayi ya fita daga d'akin. D'akinsa ya koma ya cire bedsheet d'in dake kan gadon ya sala cikin washing machine, wani ya d'auko ya shimfid'a ya kwanta cikeda kewa da tunanin Wife d'insa. Mabrookah shiru shiru bata gansa bah, taja tsaki ta rufe ko ina ta haura saman. A hankali ta bud'e k'ofan d'akin, kwance ta samesa idanunsa a rufe, duk a tunaninta bacci yayi, ta kashe wutan d'akin ta k'arasa ta kwanta kusa dashi tana k'okarin shiga jikinsa, cike da takaici yace "Pls Live me alone I'm not in the mood" Ta b'ata fuska "Kai Yaya dan Allah" Tashi yayi ta d'au pillow ya fita daga d'akin ganin tana san b'ata masa rai. Dogon tsaki taja ta kwanta cike da takaici. D'akin Ummy ya murd'a yajishi a rufe, a sanyaye ya hau kan kujeran falon ya kwanta ransa ba dadi. Kiran sallahn farko ya tadasa, ya mik'e ya shiga toilet d'in dake falon yayi alwala ya tafi masallaci. Kamar kullun yauma sai k'arfe bakwai da kwata ya fito daga masallacin, wasu mutane su biyu ya samu a k'ofar gidan tsaye da mai gadi, d'aya sanye da suit bak'i, d'aya kuma magidanci sanye da blue babban riga. D'aya daga cikin masu gadin yace "Yauwa ga Oga nan" Jamal ya k'araso wajan rik'e da chasbaha a hannunsa ya mik'a musu hannu suka gaisa. Mai sanye da suit yace "Sunana Barrister Najib Abubakar, daga Federal High court" Ya nuna dattijon yace "Wannan sunansa Alhaji Tijjani D'an asabe, abokin business ne na Alhaji Surajo. Munzo ne akan bashi dake tsakaninsu kusan shekara uku da suka wuce" Gyad'a kai Jamal yayi yace "Ku mu shiga daga ciki, wannan maganan bana tsaye bane ku shigo daga ciki" Ba musu suka bisa har side d'in Mami, saida suka zauna sannan ya shiga yayo kiran Mami suka fito tare. Bayan sun zauna aka k'ara gaisawa. Barristern ya mik'ama Jamal wani takarda yana cewa "Alhaji Tijjani d'an Asabe na bin Alhaji Surajo kud'i kimanin naira million d'ari da ashirin" Mami ta zaro ido da mamaki tana kallan Barristern "Naira Million d'ari da ashirin fa kace" Sai lokacin Alhaji Tijjani yace "Kwarai da gaske, dan ma ka duba takardan zaka gani a rubuce, harda sa hannunsa dana shaidu" Kurrrri Jamal yayi yana kallan takardar, tabbas ga sa hannun Abba, saidai sauran shaidun ne baisan su waye su bah. Ya mik'ama Mami takardar ta duba tace "Tabbas wannan sa hannun Alhaji ne" Jamal yace "A gaskiya Alhaji, duk shige da fice na mahaifina babu wanda ban sani bah. Duk abinda zaiyi yakan fad'amin, ni bansan da wannan ranchan fa, sannan wad'an nan sunayen na shaidu bansan su bah" Mami tace "Haka neh" Alhaji yace a fusace "Idan kai baka sani ba ai shi Alhajin ya sani, maganan kuma rashin sannin naka ai lokacin kana rashin lafiya." Yanayin yanda Alhajin ke magana yasa ran Jamal ya b'aci, ya mik'e tareda mik'ama Barristern takardar yana cewa "Banida masaniya akan wannan, sannan idan har kunaso mu tabbatar sai ku kawoo shaidun da akayi dasu" Ran Alhaji idan yayi dubu ya b'aci, shima ya mik'e a fusace "Wallahi baku isa bah, ni da hakkina nazo amsa ku cimin mutunci" Uffan Jamal bai sake fad'a ba ya bar falon a fusace. Mami da Aunty Faty ne suka soma basa hak'uri, anma ina sai masifa Alhajin yake har yana cewa zai kai kotu a k'watar masa 'yancin sa. Jamal na shige side d'insa sukayi kicibus da Ummy a bakin k'ofa, kauda fusaka tayi tareda turo baki gaba. Kallanta ya tsaya yi yana murmushi "In kikayi wasa wata rana bakin nan sai yakai kaduna" Duk da yanda take fushi anma hakan bai hanata murmushi ba, ja janyota jikinsa yana murmushi "Pls wife I'm sorry kinji" Yanda yayi magana yasa taji zuciyarta ta sanyaya, taja hancinsa da k'arfi har saida yayi k'ara "Ashhh!" Ta kyalkyale da dariya ta gyara jakan makarantan ta gudu tana dariya. Yau ma kamar jiya side d'in Mami ta shiga, yau ma saida suka zageta tas tareda mata habaici. Makullin motan ta mik'ama Mami, Aunty Faty tayi saurin fisgewa. Haka yau ma ta fito tana hawaye ta shiga mota tabar gidan. D'akinsa ya koma ya shirya ko takan breakfast d'in da Mabrookah ta masa baiyi ba ya fita, side d'in Mami ya shiga, fad'a ta masa sosai akan yanda yama Alhajin nan. Baice komai ba har ta gama ya mik'e ya musu sallama ya fita. A hanya ya dunga neman wayan Lawyern Abba dan yasan shi kad'ai ne zai tabbatar masa da maganan bashin nan da yaga sign d'insa a cikin shaidu. Ajiyar zuciya ya sauke tareda shafa suman kanshi, yanzu ma duk maganan nan da ake, baisan komai game da dukiyar Abban nasa ba sai gidan da suke da kuma Company d'in dayake aiki. Wayan ya soma kira switch off, sosai abin ya basa mamaki dan Lawyers ba kasafai suke chanza number bah. Har yakai wajan aiki bai daina kira ba anma a kashe. Ummy kuwa tun da ta isa makaranta wani zazzab'i ya rufe ta, tasan ba komai ya hadasa mata wannan ba sai rashin baccin da batasamu ba kwana biyu. A daddafe tayi karatu har aka tashi, tana fitowa taga motar Jamal a k'ofar makarantar yana jingine jiki ya hard'e k'afa yana latse latse a wayansa. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Wannan shafin sadaukarwa ce ga * Professor Ibrahim Aliyu Malumfashi Family* Allah ubangiji ya sanya albarka a aurenki ```Swt Meenarh Prof``` Ameen. Page 58 n 59 A daddafe tayi karatun har aka tashi, tana fitowa taga motar Jamal a k'ofar makarantar yana jingine jiki ya hard'e k'afa yana latse latse a wayansa. Da murmushi ta k'arasa inda yake tsaye, kurrri ya mata yana kallanta, ji yayi kamar ya rungumota anma ba hali saboda student d'in dake ta shige da fice a k'ofar gate d'in makarantar. K'arasawa yayi ya amsa jakan hannunta wanda dama ya mata nauyi, gaban motan ya bud'e mata ta shiga yaja suka bar haraban makarantar. Titi take ta kallo tana yatsine fuska sboda yanda takae jin jikinta. Yana driving lokaci lokaci yakan juya ya kalleta, ganin yanda b'ata fuska yasa yace "Yadai Wife, ko bakiyi murnan ganina baneh?" Sake turo baki tayi bata kallesa bah, d'an dariya yayi mara sauti, yau rigima kenan take jin yi. Har suka iso gida bata daina kallan windown tana b'ata fuska bah, yana parking ya fito ya zagaya ya bud'e mata ta fito ta wuce side d'insu. Da kallo ya bita har ta shige ya girgiza kai ya d'auko jakanta dake seat d'in baya yabi bayanta. Mabrookah ya samu zaune a falonta itada wata k'awarta suna hira, k'awar nata na ganinsa ta gaida sa ya amsa yana murmushi "Amarya sannu da gida" Jakan hannunsa take ta kallo tana yatsine fuska, baisake ce mata komai ba ya haura sama abunsa, d'akin Ummy ya nufa ya bud'e a hankali da sallama, kwance ya sameta kan gado ko uniform bata cire ba, ta k'uddun dune waje d'aya idanunta a lumshe sai hawaye dake gangara daga idonta. Da saurinsa ya k'arasa ya hau gadon tareda rungumota jikinsa. sosai yaji jikinta yayi zafi, a rud'e ya d'agota "Wife meya sameki? temperature d'inki its so high" Kasa ce masa komae tayi har lokacin idanunta a lumshe. suranta yayi ya shiga toilet da ita ya mata wanka ya gasa mata jikinta. da kansa ya shiryata har lokacin hankalinsa ba'a kwance yake bah. dogon riga ya saka mata mara nauyi, sosai taji dad'in wankan dan har tad'anji dama dama. Rungumota jikinsa yayi ya rad'a mata "Sannu Wife, taso muje asibiti" Ta turo baki ta kauda kai, a shagwab'e tace "Nidai bazanje asibiti bah, na warke" K'ara matseta yayi a jikinsa "No pls, kinga har yanzu jikinki da zafi." Ya soma shafa suman kanta a hankali "I love uh so very much, Banasan ganinki a damuwa" Ta rungumesa sosai tana turo baki, bayanta ya soma shafa mata a hankali. Cikin mintina kad'an bacci ya d'auketa. Kwantar da ita yayi kan gadon yana mamakin baccin datayi dan yasan ita ba ma'abociyar baccin rana bace. Fita yayi ya koma d'akinsa shima yayi wanka ya fito. Wayan Mifzal ya kira bugu d'aya ya d'auka, bayan sun gaisa ya sanar dashi halin da ake ciki na maganar Alhaji Tijjani. Daga chan b'angaren Mifzal yace "Abu na farko shine ka fara neman Lawyern Abba first, kaje abujan office d'inshi ka duba shi. dan wannan ba k'aramin magana baneh" Ajiyar zuciya Jamal ya sauke sannan yace "Duk fa maganan nan da ake ni da Mami bamuda masaniya akan komai na dukiyar Abban" "Dole shi lawyern sa zaisan komae dangane da dukiyar nasa. abinda nakeso dakai shine kayi k'okari ka tafi abujan zuwa gobe ko jibi, sannan ka samu lawyer kaima dazai tsaya maka" Shiru Jamal yayi yana tunani, Ramadhan ne ya fad'o masa a rai, dan Barrister ne shima mai zaman kansa. Ya sauke nannauyan ajiyan zuciya yace "Zanma Ram magana, nasan komae zaiyi daidai" Sukayi sallama ya kashe kiran, hawaye ne ya gangaro masa. Shikenan yanzu ya zama maraya ba Abbah. Kuka ya soma kaman k'aramin yaro saida yayi mai isarsa sannan bacci mai nauyi ya d'aukesa a wajan. K'arfe hud'u da rabi ya farka saboda yunwar data addabeshi, yau kwanan Wife d'inshi ne gashi batada lafiya. Tashi yayi yayo alwala ya fito ya tada sallahn la'asar. Daidai lokacin itama ta farkah, toilet ta shiga ta sake yin wanka da alwala ta fito. tana idar da sallah ta mik'e ta cire hijab d'in jikinta ta fito dan tasan Jamal baici komai bah.Tana fitowa sukayi kicibus dashi shima ya fito daga d'akinsa. ware mata hannu yayi alamar ta taho gareshi, dagudu taje ta rungumesa tana murmushi. Janye jikinta tayi dasauri tana b'ata fuska. ya sake rungumota "Ya jikin Wife" Zuciyar ta ne ya soma tashi, ta k'ara turesa tana yatsine fuska "Kai Wife dan Allah, why bakiso ina zuwa kusa dake." Ya shagwab'e fuska kamar yanda takeyi, k'ara matsawa tayi "Ni banasan k'anshin turarenka neh" Da mamaki ya kalleta, ta turesa dasauri tabar wajan. Ajiyan zuciya ya sauke ya bita har kitchen din, indomie ta dafa yana tayata har suka gama. da kansa ya bata a baki, chokali biyu ta amsa ta kauda kai gefe "Na lura kwana biyun nan baki san cin abinci" Baki ta turo gaba "Na k'oshi" Kwaikwayan yanda tayi maganan yayi, dariya tayi tana hararansa. gaba d'aya k'amshin abincin ne ya addabeta, ta mike tana runtse ido, ya bita da kallo har ta shige d'akinta. Saida yaci ya k'oshi sannan ya shiga d'akinsa. kiraye kirayen sallahn magribah aka soma yayo alwala ya fita zuwa masallaci.Yana chan har akayi sallah isha'i, wayan Ram ya kira ya masa bayanin abubuwan dake faruwa, ba tare da wani dogon tunani bah yace su had'u ranar friday a kaduna sai su tafi abujan tare. Yana shiga gida side d'in Mami ya nufa dan rabansu da b'angaren tun da safe, Bai samu kowa a falon k'asan ba ya haura sama zuwa d'akin Mamin. Kan sallaya ya sameta tana lazimi, ya zauna kusada ita har ta gama tayi addu'a ta shafa. da murmushi yace "Sannu da hutawa Mamina" Murmushi ta masa sai kuma kuka ya kufce mata, da rarrafe ya k'araso inda take hawaye cike a idonsa ya rungumeta shima ya soma kukan, muryanta na rawa tace "Allah ya jik'an Alhaji" "Amin" yace a hankali yana rungume da ita har lokacin suna kuka a tare. Bayansa ta soma bugawa a hankali tana cewa "Your Dad was a very good Man. naji dad'in zama dashi" Kuka ne ya k'ara kufce mata dakyar ta iya cewa "Try to b like ur father Jamal. inaso nayi alfahari dakai a matsayin d'ana, kamar yanda nayi alfahari da mahaifinka. Mutun neh na gari mai gaskiya" Cikin muryan kuka tace "Mai tausayin talakawa, mai taimako. Har ya mutu yana rik'e da addini sosai" D'ago fuskanta yayi yana share mata hawayen dake gangara daga idonta. "Its ok Mamina, stop crying. Insha Allah zakiyi alfahari da kasancewa na d'anki" Hawayen fuskansa itama ta soma sharewa tana murmushi, ta sake rungumesa wasu hawayen na gangara daga idonta. "Allah ya isan mana wanda suka kashe mana shi, sun cucemu" Sake d'agota yayi daga jikinsa yana sake share mata hawayen "Insha Allahu komau ya kusa zuwa k'arshe Mamina" Kwantar mata da hankali ya dunga yi har zuciyarta yad'an sanyaya, sannan ya sanar da ita maganan tafiyarsu neman Lawyer. Addu'an samun nasara ta masa yayi godiya tare da mata saida safe ya fita. Wulgawan mutum ya gani a k'ofar d'akin, kamar an lab'e anji abinda sukace, bayansa ya juya baiga kowa ba ya yatsine fuska tareda d'aga kafad'a ya wuce. Aunty Faty ce ta fito daga inda ta b'oye tana tab'e baki tana bin hanyar dayabi da harara. Motansa ya shiga ya fita yayo musu take away harda Mabrookah ya dawo. Kasancewar ba ranar girkin Mabrookah baneh yasa ya lek'a d'akin da sallama rik'e da ledanta. Tana kwance ruf da ciki akan gadonta daya chukur kud'e ba gyara. Girgiza kai yayi cike da takaici ya aje mata ledan kusa da ita "Ga naki. Sai da safe" Bai jira mai zatace ba yabar d'akin, dakinsa ya shiga yayi wanka ya sauya kayansa sannan yad'au ledan ya nufi d'akin Ummy. Da sallama ya bud'e kofan, kakarin amai ya soma ji daga toilet d'inta, dasauri ya shiga ya aje ledan ya k'arasa toilet d'in dasauri. Tsugunne ya sameta tana amai dafe da k'irjinta saboda yanda yake amsawa. Gabanta ya tsugunna tausayinta na ratsa sa ya d'agota yana mata sannu, tana ganinsa ta sake fashe wa da kuka, ya d'ibo ruwa ya wanke mata baki ya kaita kan gado yana cigaba da mata sannu. Toilet d'in ya koma ya gyara ya fito, kud'undune ya sameta cikin bargo tana kuka tana maida numfashi. Hankalinsa duk a tashe ta zauna kan gadon kusada ita ya yaye bargon ya d'agota tare da mannata jikinsa. Rawar sanyi kawai take tana kuka tana k'ara shiga jikinsa. Rasa bakin magana yayi tausayinta da santa ke k'ara shigarsa. Harya bud'e baki zaiyi magana ta tursa ta mik'e dasauri ta koma bayin ta durk'ushe tana wani aman kamar zata shid'e, ya biyota bayin ya dafata yana mata sannu. Wani kukan ta fashe dashi tana k'ara shiga jikinshi tana kuka. Wanka ya mata sannan ya fito da ita, idanunta a lumshe duk jikinta yayi yaushi ko hannunta bata iya d'agawa. Rigan bacci ya saka mata mara nauyi yanata mata sannu. Yana gama shiryata ya kwantar da ita ta koma chan gefe ta k'udundune waje d'aya. Wutan d'akin ya kashe ya cire jallabiyan jikinsa ya haura kan gadon, janyota yayi jikinsa tako lefe. K'anshin turaren jikinsa ne ya daki hancinta tad'an turesa a hankali ta matsa gefe "Sannu Wife!" Shiru batace komai ba sai sheshek'an kukanta dayake ta jiyowa daga gefensa "I'm so sorry, gobe sai muje Hospital da safe koh" Wani amai ne ya sake taso mata ta mik'e dasauri tana ganin jiri, side lamp ya kunna ya mik'e yabi bayanta, bakin k'ofan bayin ta durk'ushe tana ta amai wanda yake zallan ruwa dan ba komai cikinta. Gaba d'aya jikinta rawa yake tana aman tana kuka, tsugunnawa yayi bayanta ya rik'eta shima yana hawaye harta gama. Haka suka kwana babu wanda ya runtsa cikinsu. Tausayinta ne ya cika Jamal, ji yayi dama ciwon ya dawo jikinsa ta huta. Ana fitowa sallahn asubah ya dawo, lokacin tasamu bacci yad'an d'auketa. Bai tasheta ba ya zauna kusada ita yana kallan kyakkyawan fuskanta, daga nan shima baccin ya d'aukesa daga zaune. Kakarin amanta ne ya tashesa, a rud'e ya mik'e ya shiga bayin ya sameta durk'ushe tana kuka. D'aukanta yayi ya k'arasa da ita cikin bayin ya mata wanka ya fito da ita. Kaya ya chanza mata ya saka mata hijab ya sake d'aukota suka sauko k'asa. Lafewa tayi a jikinsa dan bata jin k'arfi ko kad'an. A falon Mabrookah suka had'u da Aunty Faty da itama Mabrookahn, ko kallansu baiyi ba balle susa ran zai ce musu wani abu. Shi gaba d'aya hankalinshi nakan Wife d'insa, mota ya sakata ya tada suka bar gidan. ABUTH ya nufa kai tsaye, suna zuwa aka amsheta tare da bata taimakon gaggawa. Yana nan tsaye bakin k'ofan d'akin sai safa da marwa yake, chan likitan ya fito, Jamal yayi saurin taransa yana tambayansa halin datake ciki. Kafad'ansa likitan yad'an bubbuga, "She wl be alryt, dont uh worry" Ya mik'a masa wani takarda "Tests d'in da za'a mata yanzu ne" Amsa yayi ya masa godiya, likitan yace zai iya shiga ya ganta. Da saurinsa ya shiga ya sameta kwance kan gadon marasa lafiya, da drip a hannunta. Kurri ya mata ko k'iftawa bayayi, tsakanin Jiya zuwa yau har tayi rama sai wani fari data k'ara da k'irjinta da suka ciciko. Ajiyar zuciya ya sauke ya k'arasa ya mata kiss ya mata a goshi ya d'ago yana kallan fuskanta "Speedy recovery Swthrt" Kud'in test d'in yaje ya biya ya dawo, da kansu sukazo suka d'iba jininta suka kuma basa wani roba idan ta tashi tayi fitsari a ciki. Amsa yayi suka fita. Bata wani dad'e dayin baccin ba ta farka, sai lokacin ya tuna ko breakfast basuyi bah, Mifzal ya kira dan baiso Mami ta sani hankalinta ya tashi, ba dad'ewa sai gashi da kayan tea da sauran abubuwan da za'ayi anfani dasu. Yana gaisheta ya koma dan yanada wani case dayake handling.. Taimaka mata yayi ta shiga toilet tayi fitsari a roban, tea ya had'a mata mai kauri tayi saurin kauda kai tana yatsine fuska "Pls Swthrt kisha, i know kina jin yunwa" Sake kauda kai tayi tana yatsine fuska "Banaso!! Amai zanyi" "No bazakiyi bah, daure kisha kinji Wife" Dakyar ya lallamata tasha kad'an ta kauda fuska. Nan da nan Amai ya taso mata ya tara mata abu tayi tanata maida numfashi yana mata sannu. Sai wajan rana sannan result ya fito, Dr Amina ce ta musu Albishir da cewa tana d'auke da juna biyu na wata biyu. Murna wajan Jamal ba'a magana, ji yayi kamar ya maida Ummyn ciki saboda farinciki. Zama yayi kusada ita ya d'ago kanta tareda rik'e hannuwanta yana murmushi "Kin biyani Wife, kinmin komai a rayuwa. I love uh so much" Kuka ya fashe dashi ta d'ago dasauri tana kallansa "I wish Dad was here, da shi zan fara fad'ama wah" Ya rungumota jikinsa yana cigaba da kukan, hannu tasa cikin suman kanshi tana yamutsawa cikin salo. Saida yayi mai isarsa sannan bacci ya d'aukesa a jikinta. Kallansa take cike da tausaya wa, har mamakin irin shak'uwan dake tsakaninsa da Abban take. A ranar aka sallamesu da yanma bayan an rubuta mata magungunan da zata rink'a sha. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* IWA (Onward Together) Dedicated to My *Late Siblings* Page 60 n 61 A ranar aka sallamesu da yanma bayan an rubuta mata magungunan da zata rink'a sha. A haraban gidan yayi parking ya fito dasauri ya bud'e mata k'ofa ta fito. Hannunta ya rik'e "Ko na d'aukeki neh Wife" Ta girgiza kai alamar A'a, tana turo baki. Hannunta ya kama suka shiga ciki har zuwa d'akinsa. Kan gado ya kwantar da ita yana mata sannu ya fita ya moma ya kwaso kayan da suka dawo dasu ya shigo. Har tsawon kwana biyun kwanan ta kula yake bata na musamman, har lokacin bata daina Aman bah. Sosai take galabaita idan tayi aman, tun Mabrookah bata gane ba har ta gane. Ranar da kuka ta shiga side d'in Mami ta fad'a jikin Aunty Faty tana cigaba da kuka "Mummy Ummy ciki gareta" Mami dake gefe ta dafe k'irji tace "Ciki!" Fargaba ne sosai a fuskan Aunty Faty, ta d'ago Mabrookah tana zare idanu "Ke Mabrookah bansan wasa, kin tabbatar da abinda kike fad'a?" Cikin kuka tace "Ciki ne kullum batada lafiya kuma tana amai, hanzu kuma na gama jin yana waya da doctor" Hankalin Aunty Faty da Mami ya tashi sosai, Mami tace "Harga Allah banasan d'ana ya samu zuri'a da yarinyan nan. Bana santa ko kad'an a raina" Shiru Aunty Faty tayi tana sak'e sak'e a ranta, Mabrookah ko kuka ta cigaba kamar Aunty Fatyn ce ta mutu. Bayan sallan Magrib, Jamal na rungume da Ummy yana mata sannu bayan ta gama amai, kuka take sosai tana jujuya fuska a k'irjinshi. Sannu ya cigaba da mata hankalinsa a tashe. "Sannu Wife, fad'amin meh kikeso na miki kiji dad'i" Idanunsa taf da hawaye na tausayinta, cikin shagwab'a tace "Ni ka kaini gida wajan Mama" Jim yayi sannan ya d'agata da kansa ya shiryata, ya saka mata hijab tareda rik'o hannunta suka fito. Side d'in Mami suka shiga, a falo suka sameta zaune itada Aunty Faty, duk da yanda yake jin jikinta hakan bai hanata durk'usawa har k'asa ta gaidasu bah. Mami ce kawai ta amsa itama d'in a dak'ile. Jamal dake kan kujera d'are d'are yace "Mami zamu d'an fita neh, anma ba dad'ewa zamuyi bah" Hararansa tayi sannan tace "Adawo lafiya" Bako kunya ya mik'e ya rik'e hannun Ummy tana ta k'okarin k'wacewa yak'i har suka bar falon. Bud'e mata gaban mota yayi ta shiga sannan shima ya shiga suka bar gidan. Pz ya tsaya yayi siyaiyan Fruits dayawa ya dawo motan suka d'au hanya. A k'ofar gidan yayi parking ta fito dasauri ta shiga ciki. Ya bita da ido yana murmushi tare da girgiza kai. Fruits d'in ya d'auka ya bita cikin gidan. Ko sallama batayi ba ta shiga cikin falon tareda fad'awa jikin Mama ta fashe da kuka. A rud'e ta d'agota "Lapia Ummy, meya faru?" Sallaman Jamal ne ya katse ta ya shigo ya nemi guri k'asa ya zauna tareda gaida Maman. Da fara'a ta amsa masa tana tambayansa mutan gidan, ya amsa da lafiya. "Ke Ummy har yau bazaki girma bako" Turo baki tayi tace "Dan Allah Mama kice ya barni a nan mu zauna tare" Buge mata baki Mama tayi ta b'ata fuska "Hankali k'aranci Ummy, ke wa kika tab'a ganin ya dawo gida da aurensa indai ba mutuwa auren yayi bah" Jamal yayi murmushi "Mama barinyi sallah" Godiya ta masa ya mik'e yad'an saci kallan Ummyn sannan ya fita. Mama ta mik'e "Matsamin ki gani karki k'arasani." Ta shiga kitchen ta zubo mata fatan wake daya sha alaiyahu da kifi. "Yau abinda na fada kenan" Ummy tayi saurin rufe hanci tana b'ata fuska "Dan Allah Mama ki d'auke banasan k'anshin" Baki bud'e Mama ke kallanta, kantace komai ta fita daga d'akin dasauri ta durk'ushe ta soma amai jinkinta na rawa. Mama na tsaye bakin k'ofa tana kallanta tana 'yar murmushi. Tad'au buta takai mata "Gashi ki d'auraye bakinki" Ta amsa butan ta d'aura ye bakin, harta d'au tsintsiya zata share wajan Mama ta amsa "Aa bashi jeki huta abinki" Ba musu ta aje ta shiga d'aki tana cigaba da b'ata fuska. Wanke wajan tsaf Mama tayi sannan ta koma falon ta tarar da ita kwance kan 3seater idanunta a lumshe. Binta da kallo tayi daga sama har k'asa, tad'anyi murmushi batace komai bah. Sun d'an tab'a hira a nan take jin Inna zasu tashi daga gidan zasu koma abuja, sosai tayi mamaki saidai bata nunama Maman bah. Suna cikin hira Jamal ya kirata a waya, turo baki tayi sannan ta d'auka yace ta fito su tafi. Ba hakan taso bah, ta k'ara lafewa a kujera saida Mama ta mata fad'a sannan ta mik'e ta mata sallama tana turo baki. Haka Ummy ta cigaba da laulayi har na tsawon sati biyu sannan tad'anji dama dama. Ganin ta samu sauk'i yasa Jamal ya kira Ram akan maganarsu. Ranar Juma'a da safe yabar zaria zuwa kaduna cike da kewan Wife d'insa, wacce ya bari gida tana kukan rabuwa dashi. Saida ya tsaya yayi sallahn Juma'a a Sheikh Ja'afar dake unguwan dosa sannan ya k'arasa gidansu Ram d'in. A ranar suka d'au Hanyan Abuja. Bayan sun sauka a hotel Jamal ya kira wife d'insa, shagwab'a take ta masa ya dunga biye mata harda d'an kukanta na rashin son tafiyarsa. Hira sukayi sosai sannan ya kashe kiran. Ram dake gefensa yace "Yau dare yayi saidai mu bari gobe sai muje office d'insa" Kai Jamal ya gyad'a, Ram ya mik'e yana cewa "Ni fah kasanni banasan zaman waje d'aya, bani key dallah nad'an zaga gari" Jamal ya hararesa "Muje dai tare" Wayan Jamal ne yad'au ruri, ganin Numbern Mifzal yasa ya d'auka tareda sallama. Daga chan b'angaren Mifzal yace "Nasu Labarin Bilal da mai gidansa sun dawo Nigeria yau" Jamal yad'an zaro ido yace "Yanzu ya za'ayi" Mifzal yace "Na turo reports d'in nan abuja, gobe insha Allahu nima zan shigo sai mu cigaba da bincike" Sosai Jamal yaji dad'in labarin ya masa godiya sannan ya katse kiran. Ram yaba labarin yanda sukayi da Mifzal, yayi addu'an samun nasara suka fita zuwa yawonsu. A Zaria kuwa, bayan fitan Jamal da kusan awa biyu tajiyo hayaniya a farfajiyan Gidan, tashi tayi ta lek'a window Ma'aikata ta hango tsaitsaye a wajan sunata surutu. Aunty Faty ce ta fito ta tsaya gabansu "Zakuyi hak'uri yau kowa za'a sallamesa dan kusan ba'a tab'a dukiyar mamaci wuri" Nan fa ma'aikatan suka soma cece kuce, wasu na k'orafi wasu na fad'in albarkacin bakinsu. Mamaki ne ya cika Ummy, da tausayi ta dunga bin ma'aikatan da kallo hawaye cike a idonta. Mami ta hango ta fito sanye da hijab wasu mata na biye a bayanta. *Ayi hak'uri da wannan inada uzuri ne* Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/? Page 62 n 63 Mami ta hango ta fito sanye da hijab wasu mata na biye a bayanta rik'e da wasu buhuhuna. Wurin yayi tsit ganin Mami, d'aya daga cikin tsofafin masu aiki yace "Hajiya idan wani laifi mukayi ayi hak'uri, munyi Alka'awari Insha Allahu bazamu k'ara bah" Kan Mami tayi magana Aunty Faty tayi saurin cewa "Babu abinda kukayi bayanin dana muku farko shine dai" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Kuyi hak'uri, nasan yawancin ku da wannan aikin kuka dogara, muma ba munyi hakan baneh dan cin zarafin ku. Kunsan halin da dai ake ciki na rasuwar mai gidan, mu gaskiya bazamu iya d'aukan d'awainiyarku bah" Nan fa wuri ya sake kaurewa da hayaniya, Mami ta d'aga hannu tace "Ku saurareni" Nan wajan yayi tsit "Duk da haka bazan barku haka bah, duk da jiya akayi albashi, zan k'ara a kowannen ku naira dubu biyar biyar, mata na basu atampa super kowacce, maza kuma na basu shadda gezina." Badan ran ma'aikatan yaso ba suka bi layi, d'aya bayan d'aya Mami ke basu dubu biyar biyar, Aunty Faty na mik'a musu Atamfan, maza kuma shadda. Kuka Ummy ta saki sanda ta hango Laurat a kan layi. Sosai ta tausaya ma masu aikin. A ranar dukkansu suka tattara inasu inasu suka bar gidan. A sace Laurat ta shigo side d'insu Ummy. Rungume juna sukayi suna kukan rabuwa. Ummy ta haura sama dasauri ta d'auko paper da biro "Tunda baki da waya ki rubuta min addreshin ki insha Allahu wata rana zaki gani" Laurat ta amsa takardan tana hawaye ta rubuta mata address d'in ta mik'a mata. Suka sake rungume juna, cikin kuka Laurat tace "Allah yasa mu gana Ummy" Ta janye jikinta dasauri yana kuka tabar side d'in. Kuka kam Ummy tasha harta gode Allah, gaba d'aya ma'aikatan sun tafi sai masu gadi biyu da kuma wasu mata su biyu wanda batasan aikin me suke bah. Dadddare da Jamal ya kirata bata fad'a masa maganan tafiyan yan aikin ba dan a tunaninta da saninsa akayi. Hira suka sha sosai har zuwa sha biyu sannab sukayi sallama ta kwantah. Washe gari tana sallan asubah ta koma ta kwanta, bata farka ba sai k'arfe goma da kwata. A kasalance ta mik'e saboda yanda takejin jikinta, wanka tayi sannan ta shiga kicin ta had'a ruwan lipton ta fito dan shi kad'ai yanzu take iya kaiwa cikinta, shima wata ran amanshi takeyi. Dinning ta zauna harta kai kofin bakinta Mabrookah ta shigo falon tana yatsine yatsinen Fuska "Uwar kinibibi idan kin gama Mami nasan ganinki" Ta juya tabar falon tana wani botsaro baya, da ido Ummy ta bita har ta sauka, a gurguje tasha tean ta shiga d'aki ta d'au Hijab, wayanta ne ya soma ruri kamin ta k'arasa har ya tsinke, missed calls d'in Jamal ta gani har guda goma, bata d'au wayan ba ta juya ta fita sannan yasa hijabin ta nufi side d'in Mamin. Da sallama ta shiga falon, kamar kullum yauma hakane saida gabanta ya fad'i da suka had'a ido da Aunty Faty, ta nemi guri chan nesa dasu ta zauna tareda gaida su. "Wai na tambayeki" cewar Aunty Faty "A gidanku haka kikeyi har sai rana ya fito sannan zaki gaida uwarki" Gaban Ummy ya fad'i ta duk'ar dakai k'asa idanunta cike da kwalla. Mami ta tab'e baki tace "Ai kinsan tarbiya daga gida yake farawa, idan uwa babu ta yara zasu samu" Mabrookah ta amshe da cewa "Ragowar Soyesoye, Allah dai yasa cikin nan nasa neh" Aunty Faty tace "Aikuwa kinsan irinsu da bin mazan tsiya, wayasan nawa aka zubar kafin a samu wannan" Ummy ta fashe da kuka tace "Dan Allah kuyi hak'uri, zan dunga zuwa da wuri ina gaish..." "Dallah rufe mana baki" cewar Aunty Faty, itako Mami tsabar takaici ne ya hanata magana sai bin Ummyn take da kallo cike da tsana. "Ai tuntuni ke kikayi sakaci Maimunatu har kika bari ta zauna a gidan nan bayan warkewan sa" Mami ta tab'e baki "To ya zanyi, Alhaji ne yace bazata ko ina bah, kuma kinsan duk abinda ya fad'a ta zauna babu wanda ya isa ya tsallake" Aunty Faty taja dogon tsaki batace komai bah. Chan kuma tace "Ai ko wallahi kafin Jamal d'in ya dawo sai kinci ubanki a gidan nan" Ta maida dubanta ga Mami "Tunda yanzu babu masu aiki, ai ga wata mun samu" Mabrookah ta fashe da dariyan k'eta tace "Wallahi kuwa Mummy, ni kawai girki zata dunga min" Ummy ta d'ago ta kalli Mabrookah, aiko suka had'a ido "Bar kallona, shegiya Maiya. Kindai san Ya Jamal baya nan, wallahi sai na miki shegen duka naga uban da zai k'waceki" Nan Ummy tasha jinin jikinta, in akwai abinda take gudu bai wuce a tab'a lafiyar jikinta. Mami tace "Aikin gidan nan ya koma hannunki daga yau, shara, mopping, gyaran d'akunan mu da girki." Wani shu'umin murmushi Aunty Faty tayi tana kallan Ummyn sannan tace "Ai yau zata fara aikin nata tunda dai babu masu yi" Tana hawaye ya mik'e ta shiga store inda ake aje tsintsiya da sauran abubuwa. Mami ta kalli Aunty Faty tace "Babban bak'inciki na bai wuce cikin dake jikin yarinyan nan bah, harga Allah banasan had'a zuri'a da wannan yarinyar" Aunty Faty ta fashe da dariya mai sauti sosai "Kwantar da hankalinki Maimunatu, wannan ai abu ne mai matuk'ar sauk'i" Mabrookah ta sauke ajiyar zuciya dan itama sosai ta tsani cikin Ummyn. *** Da wuri Jamal da Ram suka shirya suka fita zuwa Office d'in lawyern dake zone 2, saidai abin takaici basu samesa ba sai PA d'insa nan yake shaida musu baya k'asar yaje wani confrence meeting a Cairo anma zai dawo zuwa tuesday. Ba haka ransu yaso ba haka suka koma hotel d'in da suka sauka. Sun yanke shawaran tsayawa a abujan har zuwa sanda zai dawo. Jamal ya d'auko wayansa ya cigaba da neman layin Ummyn bata d'auka bah. Hankalinsa ne ya tashi sosai na rashin d'aukan wayansa da batayi ba. Tunani ya soma ko jikin nata ne ya tashi, da lafiya lau yasan da yanzu ta d'auka. K'ara kira yayi har ya katse ba amsa, yayi wurgi da wayan tareda jan tsaki "Anya Ram bazamu koma zaria ba kuwa" Ram dake kan gado yana chating ya juyo da mamaki "Saboda meh?" "Tun safe nake kiran Wife bata d'auka, inaji a jikina something is wrong dan ko laifi na mata bata k'in daukan wayana" Ram ya mik'e zaune yace "To ka kira Mabrookah mana ko Mami" Jim yayi na 'yan mintina sannan ya soma neman layin Mami, bugu d'aya ta d'auka da sallama, bayan sun gaisa yace "Mami tun safe nake kiran Ummy bata d'auka bah, i donno ko jikin ne dan na barta bata jin dad'i" Tad'an juya ta kalli Aunty Faty dake zaune kusada ita sannan tace "Lafiya lau take kam, dan ko d'azu da safe tashigo ta gaishe ni" Nannauyan Ajiyan zuciya ya sauke har saida Mami ta jiyosa, ta tab'e baki tace "To ita Mabrookan ka kirata" Saida yad'anyi Jim sannan yace "Itama bata d'auka bah" Tambayansa abinda sukaje yi tayi yake shaida mata basu samesa ba sai ran tuesday. Tamai addu'a sosai sannan sukayi sallama. A b'angaren Ummy kuwa ta wahala sosai ranar, ga jikinta da ba wani k'wari, duk bayan 'yan mintina sai tayi amai, tana kuka tana aikin har ta gama, ba ita ta koma side d'insu ba sai bayan sallahn Magriba, dakyar ta iya k'arasawa d'akinta tayi wanka ta kwanta, nan da nan zazzab'i mai zafi ya rufeta. Cikin bacci taji wayanta na ringing kan bedside ta mik'a hannu dakyar ya dauka tare da karawa a kunne "Haba Wife yanzu abinda kikamin kin kyauta kenan" Kuka ta soma mara sauti "Ya salam! Meya faru? Ko jikin neh" Duk yabi ya rud'e hankalinsa a tashe, kasa fad'a masa tayi dakyar ta iya cewa "Bai kaine kak'i dawowa bah" Ya sauke ajiyar zuciya tare da k'ara kara wayan a kunnensa "Tun safe nake neman wayanki baki d'auka ba Wife, hankalina ya tashi sosai na d'auka jikin neh" Hawaye suka k'ara gangaro mata, cikin sanyin murya tace "Banga wayan baneh kuma yana silent, sai d'azu na duba k'arkashin gado ashe nan ya fad'a" "Pls ki daina sa wayanki a silent kinji" "To" tace a hankali, sun d'an tab'a hira sannan sukayi sallama. Kuka ta sake fashewa dashi na tausayin kanta kafin Jamal ya dawo. A daran ranar Mifzal ya iso abujan, nan hotel d'in dasu Jamal suka sauka nan shima ya sauka. Washe gari dasafe dukansu suka shirya suka fita. Saida Mifzal ya fara reporting a Station d'in dayakai case d'in sannan suka wuce Wuse 2 dan a nan suka samu labarin Bilal d'in yake. Daga bakin layin sukayi parking, Mifzal da Ram suka fito suka shiga cikin layin sosai suna takawa suna bin gidajen layin da kallo. Wani mai shago suka samu nan suka zauna kan benchn sa tare da masa sallama. Bayan ya amsa Ram ya mik'a masa dubu d'aya "Bamu Fayrous guda biyu" Jiki na rawa mai shagon ya mik'o musu dan yau kusan kwana biyu kenan babu ciniki, ya irgo chanji ya mik'a masa. Mifzal yayi saurin cewa "Ka bashi, dan Allah mallam in tambayeka mana" Jiki na rawa yace "Allah yasa na sani" "Dan Allah wani nake nema sunansa Bilal, abokina ne sosai saidai lambarsa ta b'ace a wayata. Kuma gashi tun daga Kano nazo nemasa" Mutumin ya rik'e baki da Mamaki "Wai! Kace kasha tafiya, sai dai ni bansan wani mai suna Bilal ba anan layin" Mifzal ya d'au wayansa ya zak'ulo hoton Bilal d'in dake jikin Dp d'insa na whatsapp ya nuna masa "Ka ganshi nan" Baki mutumin ya bud'e "Aa indai wannan ne ai na sanshi, yakanzo nan wayena yasayi sigari" Ram da Mifzal suka kalli juna da mamaki. Ram ya wayance yace "Tabbas kuwa shine, dan Allah bakasan gidan dayake bah" Wani dank'ararren gidan chan gefensa ya nuna musu da hannu "Ga gidan chan, saidai...." Yayi saurin yin shiru ya matse bakinsa da hannu, Mifzal ya kallesa yace "Fad'a abinda kakeso ka fad'a babu komae" Ram ya ciro dubu uku ya aje masa ga wannan ka tab'a, aiko d'an fulani ya gyara zama "Akwai abinda mu 'yan unguwan nan bamu gane masa bah" "Na meh fah" cewar Ram "Alhajin nan bashi fita sai da daddare, sannan kuma kullum sai kaga wasu murd'a murd'an mutane a k'ofar gidansa wanda mu bamu yarda dasu bah" Mifzal ya jinjina kai, "Kamar da wani lokaci sukafi zuwa?" "Kaman tara haka zuwa goma na dare idan dai kazo nan zaka samesu" Mifzal ya mik'e dasauri ya mik'a ma d'an fulanin hannu "Mungode sosai" Shima Ram ya mik'a masa hannun, d'an fulani ko sai godiya yake. A mota suka samu Jamal jingine da seat ya lumshe ido, jin motsinsu yasa ya bud'e ido ahankali. Basu ce masa komai ba shima haka, suka shiga ya tada suka bar anguwan. Saida sukayi nisa sannan Mifzal ya soma masa bayanin yanda sukayi da Mai shago, mamaki ne a fuskansa sanda yaji Bilal nashan taba. Police station suka koma suka kai report d'in da kuma record d'in maganan su da d'an fulani. Ummy kuwa irin jiya ce ta faru, aiki tayi tuk'uru duk ta galabaice ga wani ciwon ciki dake damunta. Yauma saida tayi aikin tas sannan ta wuce side d'insu tana tafiya da k'yar. Yauma kamar jiya saida suka d'anyi daru itada Jamal akan k'in d'aukan wayansa da batayi bah. Washe gari ko zazzab'i ne da ciwon jiki ya rufeta. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 64 n 65 Washe gari ko zazzab'i ne da ciwon jiki ya rufeta, sosai, har k'arfe sha d'aya na safe bata tashi bah. Ran Aunty Faty idan yayi dubu ya b'aci. Da kanta ta shigo side d'in dan Mabrookah ta tafi makarantah. K'ofan d'akin ta banko ta shigo, k'udundune ta sameta kan gado tana rawar sanyi sosai. Duk da yanda take kad'uwa hakan bai hana Aunty Faty d'aka mata duka a k'afa ba. Ba shiri ta mik'e zaune dakyar, idanunta na wani lumshewa "Uban me yau ya hanaki zuwa aiki" Ta fad'a tana huci. Cikin Kuka Ummyn tace "Dan Allah kiyi hak'uri Wallahi banajin dad'i neh bazam iya aikin bah" Wani duka Aunty Faty takai mata a baki har saida bakin ya fashe, ta dafe wajan tana kuka sosai "Saboda bakida kunya, kin rik'a harni kike cema bazaki iya aikin bah. To wallahi nabaki nan da minti biyar in ganki a falon chan" Fuuuu ta juya tabar d'akin tana sababi, wani marayan kuka Ummyn ta fashe dashi, ga wani irin sarawa da kanta keyi, dakyar ta iya mik'ewa ta fito ta nufi side d'in tana tafiya a hankali. Aunty Faty na isa ta labarta ma Mami abinda ke faruwa sannan tace "Bari tazo na bata ruwan nan, sai nace tasha magani dashi, indai tasha an gama. Haihuwa saidai taji anayi" Karaf a kunnen Ummyn, tad'anyi jim a k'ofar falon sannan ta shiga da sallama, kini kini darai Mami tayi, ta tsugunna ta gaidata. Anma bata amsa bah. Haurawa sama tasoma yi a hankali dan ta fara aikinta, Aunty Faty ta kwalla mata kira ta sauko da d'an sauri. Bottle water ta mik'a mata da wani capsule tace tasha, saida tad'anyi jim sannan tace "Ban karya bah" "To idan kin karya sai kisha" Cewar Aunty Fatyn, ajiyar zuciya tayi ta haura sama da maganin, zubar dashi tayi a toilet, ta saka maganin a WC tayi flushing. Tana aikin jiri na d'ibanta, so uku tana fad'uwa saboda jiri. Haka tayi aikin dakyar tana kuka. A wahale ta dawo side d'insu ta fad'a kan gado tana kuka tare da kiran sunan Jamal. A b'angaren su Jamal kuwa washe gari da daddare suka koma layin tare da rakiyar wasu daga cikin 'yan sanda anma bada uniform bah. Nan sukaga wad'an nan murd'a murd'an bak'akken mutanen da D'an fulani yayi maganansu. Suna nan b'obb'oye sukaga Alhajin da Bilal sun fito sun shiga motoci suma mutanen sun shiga suka bar anguwan a guje. Binsu su Jamal suka somayi anma kamin kace me har sun b'ace musu. Haka suka koma hotel d'in da suka sauka kowa da abinda yake sak'awa a ransa. Washe gari Tuesday, basu samu ganin Lawyern Abba ba sai da yanma, nan yake nuna alhininsa na rasuwar Abba dan baya k'asar tun lokacin. Jamal ne ya tambayesa dangane da bashin da Alh Tijjani yake bin Abba, ba tare da b'ata lokaci ba Lawyern ya basa tabbacin akwai bashin. Haka Jamal ya dawo jiki a sanyaye, Ram dake gefensa zaune yace "Yanzu Jamal ya xa'ayi maganan Bashin nan" Wani ajiyan zuciya ya sauke yace "Nima kaina bansani bah Ram, i knw nothing akan dukiyar Abba. Kuma kaji shima Lawyern yace baisan komai bah" Mifzal ya gyara zama yace "To why not ka koma gida ka binciki D'akinsa, Myb ka samu wani abu da zaiyi guiding d'inka zuwa inda abubuwan nasa suke" Jamal ya gyad'a kai alamar gamsuwa. Wuta ya hura yak'i bari su kwana, a ranar suka d'au hanyan Zaria saidai sun bar Mifzal anchan dan bai gama bincikensa bah. Saida ya sauke Ram a kaduna sannan ya d'au hanyan zaria. Karfe goma da rabi ya isa gidan. Bai shiga side d'in Mami ba dan yasan sunyi Bacci, side d'insu ya wuce yasa keyn d'insa ya bud'e ya shiga. D'akinsa ya wuce kai tsaye yayi wanka ya sauya kayansa sannan ya shiga na Ummy. Kwance ya sameta kud'undune cikin bargo tana rawar sanyi sai yamutsa fuska take. Ya hau kan gadon ya rungumota jikinsa a haka sukayi baccin. Da asubah sosai tayi mamakin ganinsa, ya shafa gefen fuskanta yana binta da kallo "Wife kinga yanda kika rame? Kin k'arayin ciwo neh" Girgiza masa kai tayi alamar Aa idanunta cike da kwalla. Da taimakonsa tayi wanka ya gasa mata jikinta sosai sai kuka take dan jikin mata yayi tsami. Da kanshi ya musu breakfast sukaci. Mabrookah na k'asa ta jiyo muryansa, da mamaki ta haura ta ganshi tsugunne a k'asa yana matsa mata k'afa sai dariya take masa. Ran Mabrookah in yayi dubu ya b'aci, rai b'ace ta shiga falonsu Mami, kan dinning ta xauna tana turo baki "Yaya dai" cewar Mami "Ya Jamal ne ya dawo yana chan yare da wannan maiyar yana matsa mata k'afa" "What!"cewar Mami "Har Jamal ya dawo ya kasa zuwa ya gaishe ni? Lallai na yarda Ummy ta shanye min d'a" Mabrookah ta sake zumb'ura baki tana kallan Aunty Faty "Ni babban abinda ke damuna ma, Mummy kince in tasha ruwan nan da akasa magani cikin zai zube anma har yanzu naji shiru" Aunty Faty ta gyara xama "Nima abin na bani mamaki" Sallaman Jamal da Ummy ne ya katse su, Mami ta sake had'a rai tare da amsa gaisuwan. Zama yayi kamar kullun sannan ya gaida su, Ummy ta tsugunna ta gaishe su, babu wanda ya amsa mata, hakan sam baima Jamal dad'i bah. Abin da yafara tambaya shine "Mami yau naji gidan shiru Ina Ma'aikatan neh bangansu bah" "Na sallamesu" cewar Mami Ya zaro ido da mamaki "Saboda me Mami" Ta sake b'ata fuska "Saboda bamu da abinda zamu cigaba da rik'esu" Bai sake cewa komai ba dan ransa ya b'aci sosai. "Ka dawo baka iya zuwa ka duba halin danake ciki ba anma ka tafi wajan matarka" Ya sassauta murya "Kiyi hak'uri Mami ban dawo da wuri bah cikin dare ne kuma nasan kinji bacci" Itadai Ummy kanta na k'asa. Aunty Faty ta daka mata tsawa "Ke! Akuya tashi kiba Uwa da d'a wuri suyi magana" Dasauri ta mik'e ta fita, Ja juya ransa b'ace wajan Aunty Fatyn "Matata ba Akuya bace, karki k'ara kiran matata da wannan sunan" Baki bud'e dukansu suke kallansa "Jamal yayar tawa kake gayama irin wannan maganan" "Mami kiyi hak'uri, duk abinda zaki kira matata zan jure anma banda ita" Ta mik'e fuuuu yabar falon ya barsu tsaye kamar an dasasu dukansu baki bud'e. Yana fita yabi Ummyn d'akinta, kan gado ya sameta kwance tana kuka a hankali. Janyota yayi jikinsa "I'm very sorry wife, ki k'ara hak'uri kinji. Wata rana sai labari" Kwacewa take k'okarin yi tana cigaba da kuka "Ni na gaji ka kaini gidanmu, bazan zauna bah" Dukansa ta somayi a k'irji, yayi saurin had'a bakinsu waje d'aya. Daina mutsu mutsun tayi cikin 'yan mintina ya rabata da kayan jikinta, ina ganin haka nayo waje na basu waje. Soyaiya sosai Jamal ya nunama Wife d'insa a ranar, ita kanta ta k'ara tabbatar da Jamal mai k'aunarta neh. Yinin ranar suna mak'ale da juna. Bai fita ba sai bayan la'asar. Suna ganin ya fita Aunty Faty ta shigo ta mata kacha kacha harda Mari. Kuka kam Ummy tayi har ta gode Allah. Koda ya dawo tambayan duniya babu wanda bai mata bah anma amsar d'aya cr bakomai. Ranar kwanan zazzab'i tayi sai kuka take jikinsa shiko yana aikin lallashi. Washe gari da wuri ta tashi dan zazzab'in ya saketa, breakfast ta had'a masa mai rai da lafiya sannan tayi wanka ta shirya cikin Uniform d'in makaranta. Tana gama shiri ya farka yana binta da kallo "Wife" Ya kira sunanta ahankali, ta juyo tana kallansa da murmushi. Bud'e mata hannu yayi alamar tazo gareshi, dagudu ta k'arasa ta fad'a jikinsa ya rungumeta sosai kamar za'a kwace masa ita "Wife keda bakida lafiya wani school zaki kuma" Baki ta turo gaba "Yau fa zamu fara exams kuma banasan nayi missing" Yakai mata light kiss a lips d'inta "Nidai da kin hak'ura kawai, banaso kije ki wahala ki kuma wahalar min da baby" Turo baki tayi gama ta tureshi ta mik'e dasauri ta fita, wanka yayi ya fito ya sameta kan dinning, kamar kullum tare sukayi breakfast ya bata taci sosai sannan ta mik'e tana duba agogon hannunta "Nayi latti" Ta sak'ala jakan makarantar ta "Pls Wife karkije, kinga fa baki da lafiya" Kukan shagwab'a ta soma tana doka k'afanta a k'asa, dasauri ya mik'e ya rik'eta "To naji a dawo lafiya kinji" Kiss tamasa a baki ta sauka dasauri tana dariya, da murmushi ya dunga binta da kallo harta fita. Side d'in Mami ta shiga dan ta gaishe su, yauma kamar kullun zageta tas Aunty Faty tayi ta fito a sanyaye ta shiga mota driver yaja suka bar gidan. Duk kewan Ummyn ne ya cika ransa, komawa d'akinsa yayi ya shirya ya fito, baiko lek'a side d'in Mami ba ya shiga motarsa ya fita. Tafiya yake yana keta layukan cikin anguwan, daga nesa ya hango taron jama'a an kashe hanyar fita unguwan, waje ya samu yayi parking ya k'arasawa wajan, ganin motan gidansu yasa gabanshi ya fad'i. Kukkutsawa yayi ya shiga cikin wajan sosai, driver ya gani kwance kansa na fitar da jini, ga Hijab d'in Ummy a k'asa da warin takalminta d'aya. Wani k'ara ya saki da k'arfi ya k'arasa inda Drivern ke kwance. Yana ganinsa cikin k'arfin Hali yace "Ummm.....Umm...Ummy su..sun d'auketa" *Ina Jiran Comment* Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 66 n 67 "Ummm.....Umm...Ummy su..sun d'auketa" Wani irin kuka ya saki, baisan sanda ya kamo kwalan Drivern ba yana jijigashi cikin kuka yace "Ina suka kai min Ummy, waye ya d'auketa" Sumewa Drivern yayi dan ba k'aramin jini ke fita daga kansa bah. Jiniyan 'yansanda ne ya cika wajan, mutanen dake zagaye da wajan suka bud'a hanya 'yan sandan suka k'arasa wajan motan. Har lokacin Jamal na durk'ushe a wajan yana kuka sosai kamar k'aramin yaro. Ambulance ne suka d'au driver, wasu daga cikin yan sandan suka dunga d'aukan motan hoto harda Jamal d'in. Dakyar aka samu ya tashi daga wajan ya shiga motan 'yansandan har lokacin yana kuka hannayensa biyu akai. ```Waiwaye``` Ummy na shiga mota driver yaja suka bar gidan, hawaye ta soma na tausayin rayuwarta a gidan aure. Sunyi tafiya mai nisa dan daga gidan zuwa bakin anguwan akwai tazara, basu ankara ba wata bak'ar jeep tasha gabansu, ba shiri driver yaja burki ya tsaya yana salati. Ummy ko k'walalo ido tayi tana kallan motan gabanta na fad'uwa, wasu mutane ne suka fito ciki, ba shiri ta saki k'ara dan ko tantama babu sune wad'anda suka kashe Abba. Numfashinta ne ya soma barazanar d'aukewa, suka bud'e motan wajan su hud'u dukansu da k'aton bindiga a hannunsu. Ba shiri ta fashe da kuka tana kallansu tare da girgiza kai, d'aya daga cikinsu ya daka ma driver tsawa "Kai! Fito daga motan nan" Ba musu ya fito ko ina na jikinsa na rawa ya d'aga hannu sama, d'aya ya bud'e k'ofan baya inda Ummyn ke ciki ta sake sakin k'ara tana kuka. Fincikota yayi daga cikin motan har saida Hijabinta ya cire, ta soma turjewa tana cigaba da kuka kamar ranta zai fita. Mutanen anguwa na lallab'e suna hango abinda ke faruwa saidai ba halin kawo d'auki saboda manya manyan bindigogin dake hannunsu. Ganin tana neman b'ata musu lokaci yasa suka saka mata wani hankercief a hanci, ba b'ata lokaci ta tafi luuuu xata fad'i daya daga cikinsu ya d'auketa ya sakata a motan. Driver ya d'aura hannu aka ya matso tareda rik'e rigan d'aya daga cikinsu "Ina zaku kaita, dan Allah k.." Saukan kan bindigan dayaji a kansa ne ya hanasa k'arasa maganan dayake, so biyu mutumin na buga masa kan bindigan sannan ya wurgar dashi ya shiga mota suka bar wajan da wani matsiyacin gudu. Tafiya kawai suke da gudu bako birki, har suka soma barin garin zaria. **** Har suka isa Police station Jamal bai daina kuka bah, saima k'ara sautin kukan dayake kamar ana zugashi. Duk yanda 'yan sandan sukaso ya musu k'arin bayani kasawa yayi sai neman guri dayayi ya zauna a k'asa. Haka suka kyallesa dan ya samu zuciyarsa ta sarara. Saida yayi mai isarsa sannan ya d'auko wayansa a aljihu ya soma neman layin Mifzal Bugu d'aya ya d'auka, cikin wani irin murya yace "Ya d'aukemin Ummyna, Ya d'aukemin ita" A razane Mifzal yace "Bangane ba, waya d'auketa." "Anyi kidnapping Ummy da safen nan, pls Mifzal ka taimakeni, ciki ne da ita and ba lafiya gareta bah. Karsu cutarmin da ita pls" Ya sake rushewa da wani kuka, "Kana ina neh" "Ina police station" Dakyar ya masa kwatancen police station d'in dayake. Ganin zaman wajan bazai fishe shi ba yasa ya mik'e dakyar ya fita ya tari adaidaita sahu yahau. A k'ofar gate ya sauka ya biya mai napeep d'in, kallo d'aya zaka masa ka gane hankalinsa a tashe yake matuk'a. Kai tsaye side d'in Mami ya shiga, a falon k'asa ya sameta itada Aunty Faty suna hira. Wani kuka ne ya kub'uce masa suka d'ago a firgice suna kallansa. Jikin Mami ya fad'a ya sake fashewa da kuka, Hankalinta ne ya tashi ta d'ago kansa a rude "Meke Faruwa Jamal! meya sameka" Itama Aunty Faty ta sauko duk hankalinsu a tashe, Mami ta girgizasa idanunta cike da kwalla "Jamal yimin magana mana, meke faruwa" Dakyar cikin kuka yace "Anyi kidnapping Ummy" "What!" Mami ta fad'a da k'arfi tana kallansa Aunty Faty tace "Ba d'azu tazo mana sallama zata makaranta bah" Kasa basu amsa yayi sai kuka yake da wani irin gunji, iya rud'ewa Mami da Aunty Faty sun rud'e dan ba k'aramin abu kesa Jamal kuka bah. Suna nan cirko cirko suka ji k'aran bud'e gate, ba dad'ewa Mifzal ya shigo gidan cikin kakinsa na 'yansanda tare da wasu 'yansandan. Jikinsa ne yayi sanyi ganin Jamal a wannan halin, durk'usawa yayi kusada Jamal ya d'ago kafad'arsa cike da tausayinsa "Its All right Jamal, ka daina wannan kukan pls" Jamal ya d'ago jajayen idanunsa ya zubasu kan Mifzal "Na daina kuka fa kace Mifzal, kasan yanda Ummy take a cikin raina?" Ya fashe da kuka ya cigaba da cewa "Shes My everything Mifzal, ina santa fiye da kaina" Ya kama hannun Mifzal d'in hawaye na gangara daga idonsa "Pls ku taimakeni kada wani abu ya samu Ummy, wallahi ba lafiya gareta bah, shes 3month pregnant, Plss" Duk da dauriya irin na Aunty Faty saida ta fashe da kuka na tausayin halin da Jamal d'in yake Ciki. Mifzal yace "Insha Allahu zanyi iya k'okarina akan wannan case d'in, Komai zaizo k'arshe" Ya mik'e zai bar falon, Jamal yayi saurin kamo hannunsa yana hawaye "Plssss try ur best Mifzal, banasan wani abu ya sameta Pls" Hawaye suka cika idanun Mifzal, cikin zuciyarsa ko mamakin irin san da abokin nasa kema Ummy yake. Murmushin k'arfin hali Mifzal d'in ya masa yace "Insha Allah" Ya bar falon suka d'au mota suka bar gidan a guje. Falon kuwa Mami kuka, Aunty Faty kuka ga kuma uban gaiya Jamal. Kan kace me zazzab'i mai zafi ya rufesa har lokacin kansa na cinyar Mami, nan ta sake rud'ewa, Aunty Faty ta kira doctor yazo dan ya dubasa. Magunguna aka rubuta masa, Aka aika mai gadi ya siyo. Ba yanda Mami da Aunty Faty basuyi akan Jamal yasha magani ba anma kememe yak'i saima k'udundunewa dayayi yana kukansa bil hak'i da gaskiya. *** Ummy bata farka daga nannauyan baccin da tayi ba sai k'arfe uku na yanma, dakyar ta bud'e idanunta da sukayi ja, ganinta a wani d'aki daba nata ba yasa ta bud'e idonta sosai ta yunk'ura ta mik'e dakyar tare da fashe wa da kuka tana bin d'akin da kallo. Kofan d'akin aka bud'e taja da baya dasauri tana kuka, mutanen nan ne dai da suka d'aukota sai dai wannan karan fuskokin su a bud'e yake. "Kyakkyawa har kin farka" Ya soma matsowa inda take tanaja baya, d'ariya yayi mai sauti yace "Ki bani had'in kai 'yanmata, tun wanchan zuwan danayi nake mugun sha'awarki" Jin haka yasa Ummy sake fashewa da wani kukan tana cigaba da ja da baya yana biyota "Dan Allah kuyi hak'uri, karku kasheni Wallahi ban muku komai bah" Dariya mutumin ya sakeyi yace "Ba'a bamu wannan izinin ba tukun, idan har aka bamu to sunanki gawa" Nan da nan jikinta ya soma rawa, maranta yayi wani irin juyawa har saida ta fad'i ta rik'e wajan ta sake rushewa da kuka. Umarni ya bayar da a d'aureta, ihu ta soma tana k'okarin mik'ewa suka maidata zaune, tanaji tana gani aka had'a kafafunta waje d'aya aka d'aure. Suka d'aure hannayenta ya bayanta. Har lokacin bata daina kuka bah tana kiran sunan Allah, wani kyakkyawan Mari mutumin ya d'auketa dashi har saida Bakinta da Hanci suka fashe "Kiyi min shiru, ba'a kiran sunan Allah a nan wajan" Ba shiri ta rufe bakinta taba cigaba da hawaye, kyalle yasa da kansa ya d'aure mata baki tamau ya mik'e ya fita. Wani marayan kuka ta saki ga maranta dake murd'a mata kamar zata mutu. A b'angaren Mifzal kuwa, a fusace yabar gidan, waya yayi abuja ba wani b'ata lokaci ya bada oder a kama masa Alhaji da Bilal da kuka yaransa. Saidai suna zuwa aka tabbatar musu da basa garin sunyi tafiya. Mifzal najin wannan labarin ya sake tabbatar da Bilal ne yayi wannan d'anyan aikin. 'Yan sanda aka baza a unguwan Iyayen Bilal d'in anma ba cikin kayan 'yan sanda bah. Ran Mifzal idan yayi dubu ya tashi musamman idan ya tuna halin da Jamal ke ciki. Waya yayi ma su Ram dasu Taseen ya fad'a musu abinda ke faruwa sannan ya dawo gida wajan Jamal d'in. Har lokacin yana nan kwance kan kujera gaba d'aya ya fita daga haiyacinsa saboda mugun zazzab'in dake jikinsa. Mabrookah na gefensa tana kuka itama cike da tausayin mijin nata. Mabrookah na ganinsa ta mik'e dasauri cikin kuka tace "An ganta?" Baice mata komai ba dan gaba d'aya hankalinsa na kan Jamal daketa rawar sanyi, Mami itama cikin kuka tace "Dan Allah Mifzal ku taimaka, kada Jamal ya shiga wani hali, shi kad'ai ya ragemin" Ta sake fashewa da kuka, inda Jamal d'in ke kwance ya k'araso ya zauna, wayan Jamal d'in ne ya soma ruri Mifzal ya d'auka ganin bak'uwar number ce yasa ya d'auka daga chan b'angaren akace "Jamaludeen Surajo" Dayake ana d'an jiyo magana yasa Jamal mik'ewa zaune ya amsa wajan dasauri ya kara a kunnensa, "Ina fata ina magana da Jamaludeen Surajo neh" Cikin rawar murya Jamal ya amsa masa, Mifzal ya danna speaker Mami da Aunty Faty suka matso kusa "Matarka abin k'aunarka tana tare damu yanzu haka" "Ina kuka kai min matata, ina take? Dan Allah Bilal karka cutarmin da matata, ka fad'i koma menene kakeso zan maka pls" Ya fashe da kuka, wani dariya mutumin ya saki sannan yace "Kai kasan wani Bilal, idan har kanasan matarka sai ka biyamu kud'in fansa Naira Million Hamsin, sannan cash mukeso" Jamal ya d'aga jajayen idanunsa yana kallan wayan "Ina zan samu Naira Million Hamsin Yanzu? Dan Allah kuyi hak'uri ku rage" Sautin kukan Ummy yaji ya k'ara kara wayan a kunnensa hawaye na gangara daga idonsa "Wife! Wife!! Yimin magana pls" Dakyar ta iya cewa "Wayyo Ya Jamal marana mutuwa zanyi" "Me suka miki, Wife talk to me, me suka miki" Amsar wayan sukayi daga hannunta "Jinkirin kawo kud'in shine dad'ewar matarka a wajanmu" "Dan Allah kuyi hak'uri karku cutarmin da ita, i promise you Yau zan baku kud'in" Ding! Suka kashe kiran, Jamal yabi wayan da kallo ya sake fashewa da kuka, Mifzal ne ya amsa wajan ya shiga record ya sake playing maganan Jamal da mutumin, sannan ya tura a wayansa ya d'au numbern. Mami dake chan gefe tana kuka tace "Yanzu ina zamu samu Million hamsin" Jamal ya mik'e dasauri, baya yayi zai fad'i saboda jiri Mifzal yayi saurin rik'oshi "Ina zaka? Ka zauna" "Bani da sauran zama har sai naga matata ta dawo gareni, pls ka kyalleni" Ba musu ya sakeshi ya fita daga falon yayi side d'in Abba. Yana shiga ya haura sama zuwa d'akin Abban, keyn d'akin dama yana attach da keyn motansa, ya ciro a aljihu ya bud'e ya shiga a hankali. Gaba d'aya d'akin yayi k'ura, ya durk'ushe ya sake fashewa da kuka tunawa da Abbansa. Dakyar ya mik'e ya soma bincike bincike anma baiga komai bah. Batsa batsa yayi da d'akin bai samu komai bah sai wani bandir d'in 'yan d'ari biyar guda hud'u. K'asa ya zauna ya sake fashewa da kuka "I'm so sorry Wife, kiyi hak'uri" Ya dad'e zaune a wajan yana kuka, sautin kukanta kawai yakeji a kunnuwansa. Ba shiri ya mik'e tunawa da Jakar da Abba ya tab'a bashi ajiya. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 68 Ba shiri ya mik'e tunawa da Jakar da Abba ya tab'a bashi ajiya. Yana tafe yana ganin jiri har ya k'arasa side d'insu, da kyar ya iya hawa saman har ya k'arasa d'akinsa. Direct wajan wardrobe d'in yayi ya bud'e ya ciro Jakan. Kan gado ya zauna ba b'ata lokaci yaja zip d'in ya bud'e, Tulin takardu ya gani ciki, ya soma fito da takardun yana ajewa gefe batare da ya duba bah. Wani k'aton diary ya gani a k'asan jakan, ya d'ago ya duba ya mayar ya aje. Idanunsa ne ya cika da kwalla ganin babu kud'i a cikin jakan. Ya dafe kansa da duka hannayensa yana kuka ahankali, ya dad'e a haka sannan ya mik'e a sanyaye. Chak ya tsaya ya juyo yana kallan diaryn dake cikin Jakan. Zuciyarsa ce ta dunga ingizasa ya duba diaryn, har lokacin yana tsaye bai daina kallon jakan bah. Ya koma ya zauna tare da d'aukan diaryn ya bud'e a hankali. Abinda ya fara cin karo dashi shine " *I'M SO SORRY JAMALUDEEN* " Gabansa yayi mummunan fad'uwa, ya sake bud'e page na gaba nan yaga dogon rubutu kamar haka. _Surajo Kadiri shine cikakken sunana, ni d'an asalin K'asar Niger ne. Na taso cikin matsi da wahalar rayuwa saboda mahaifana duk sun rasu, saboda hakan yasa na fara almajiranci har zuwa lokacin da wani Alhaji ya d'aukeni ya maidani gidansa ina masa aiki._ _Dad'i na rayuwa babu wanda banaji a gidan dan ya d'aukeni kamar d'ansa shida matarsa dan bai tab'a haihuwa bah. Nayi primary sannan na zarce secondry daga nan ya sakani a jami'a. Ina ajina na biyu a jami'a Allah ya masa rasuwa, bayan ya rasuwansa da wata biyu matarsa ta gaza rik'eni dole na bar gidan na koma sana'ar hannu dan taimakon kaina akan karatuna._ _Da wahala da matsi na rayuwa na samu na kammala karatuna. A nan Allah ya had'ani da matata Jamila, inda mukayi auren soyaiya muna zaune lafiya. Rashi yasa dole muka tattara muka komo Nigeria dan muyi cirani mu koma._ Hawaye suka gangaro daga idon Jamal jin irin wahalan da Abbansa yasha a rayuwa. Ya cigaba da karantawa kamar haka: *12 August 1990* _Ranar da muka iso Nigeria bamu sauka ko ina ba sai k'asar zaria. Inda mai motanmu ya saukemu bakin wani masallaci a cikin zaria city, a nan muka zauna har akayi sallahn Isha'i, Limamin masallacin ya nema mana taimako muka d'an samu 'yan kudi muka sayi abinci. Watan gaririya muka soma cikin anguwan da muke gashi dare nata yi bamu samu wajan saka hak'arkarin bah. Kwatsam......_ Wayan Jamal ne ya soma ruri ya d'auka ya duba dasauri, sunan Mifzal ya gani a screen d'in ya d'auka a sanyaye ya kara a kunnensa "Kana ina neh Jamal ka fito mun samu wani information" Ai ba shiri yayi wurgi da diaryn hannunsa ya fito dasauri, a haraban gidan ya samesu tsaitsaye, ya k'arasa inda Mifzal ke tsaye yana waya yace "Ya ake ciki pls fad'amin" Yanda yake maganan cikin k'osawa yasa Mifzal d'an bubbuga masa kafad'a "Come down Friend! Yanzu muka samu information d'in Alhaji Ameenu da Bilal suna cikin garin Zaria, saidai babban takaicin na shine bamu gane location d'in da akayi wayan nan ba d'azu" "I'm very sure indai yana Zaria to zaije gida wajan Family d'insa" cewar Jamal Mifzal yace "Yes u're Right, wanan shine hanya mafi sauk'i da zamu bi dan kamasa" A tare suka fita da rakiyar wasu 'yan sanda, suna cikin Tafiya aka k'ara kiran Jamal da wani numbern, baiyi wata wata ba ya d'auka tare da karawa a kunnensa "Na lura baka damu da Matar nan taka bah, To bari kaji mun baka daga nan zuwa gobe, idan baka turo mana k'udin nan ba, zamu maka kwatancen inda zaka zo ka d'auki gawar matarka" "No! Dan Allah kuyi hak'uri karku kashemin matata, Wallahi zan turo muku k....." Dif suka kashe wayan, ya jinginar da kansa a seat d'in motan yana hawaye a hankali, Mifzal dai baice komai ba dan yaji duk abinda sukace ma Jamal d'in. "Why!" "Why Bilal, meyasa kakesan tarwatsa rayuwata? Meyasa kakesan cutar min da matata. This Battle bana Ummy bane nida kai yakamata muyi" Ya sauke kansa k'asa ya fashe da kuka. Mifzal kasa cewa komai yayi, sai kallan titi dayake yana driving a hankali ransa a jagule. Police station d'inda case d'in yake suka koma, suka kwashi 'yansanda suka shiga cikin zaria city. Lab'ewa sukayi wurare daban daban, Jamal da Mifzal suna xaune cikin mota chan nesa da gidansu Bilal d'in har bayan Isha'i suna wajan ko zasu kanshi. Wuraren k'arfe tara har sun cire rai sukaga wani Jeep bak'i yayi parking a k'ofar gidan, Bilal ne ya fito ya zagaya ya bud'e ma Alhajin ya fito shima suka shiga cikin gidan. Mifzal yayi ma sauran 'yan sandan signal, suka zagaye gidan gaba d'aya, Sun d'an jima sannan suka fito, Ram Mifzal yama Bilal, daya daga cikin 'yan sandan ya kama Alhajin, Jamal na ganin Haka ya fito daga mota dasauri ta k'araso inda Bilal d'in yake tsaye ya chakume mai kwala "Ina kakai min Matata" Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 10:54 AM] Ayshaaaaaa: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 69 n 70 Mifzal ya kama Bilal, d'aya daga cikin 'yan sandan kuma ya kama Alhajin, Jamal na ganin haka ya fito daga mota dasauri ya k'araso inda Bilal d'in yake tsaye ya chakume mai kwala "Ina kakai min Matata" Duk da yanda Bilal d'in ya rud'e hakan bai hanasa kallan Jamal da raini "Ka bani ajiyanta neh?" Wani wawan naushi Jamal yakai mai har saida hancinsa ya fashe, idanunsa sunyi ja sosai ya sake kama kwalar shi "Ina kakai min matata nace, ka fito min da ita" Wasu 'yansanda sukayi saurin janye Jamal dakyar, cikin motan 'yansanda aka sakasu dakyar Mifzal yaja Jamal ya sakashi cikin mota suka bi bayan motan 'yansandan. Suna isa police station kamin Mifzal ya gyara parking Jamal ya fito hat saida ya kusan fad'uwa. Station d'in ya shiga bai ko kalli inda yansandan suke ba ya k'arasa bakin canther inda su Bilal ke zaune a k'asa ya sake chakume kwallarsa ya mik'ar dashi tsaye "Bilal were is my Wife? Ina kakai min Ummy? Meyasa ka kashe min Matata" Mifzal ya k'araso ya janye Jamal d'in "Come down friend" Gaba d'aya Jamal ya fita haiyacinsa idanunsa suna kad'a sunyi ja saboda b'acin rai. Alhaji Ameenu yace "Wannan wane iri abu neh haka? Kamar ni a kamani a kawo ni police station me na muku" Har Jamal ya bud'e baki zai mayar masa Mifzal ya janyesa dasauri ya fita dashi, mota ya turasa sai turjewa yake shima ya shiga yaja suka bar station d'in. Gida ya kaisa har gaban Mami ya tsaya ya kwantar musu da hankali ya tafi. Babu yanda Mami batayi da Jamal ba akan yaci abinci yak'i, sai kuka daya soma Mabrookah na tayashi. Ya mik'e dakyar ya koma side d'in Abba ya fad'a kan gado ya kwanta tare da runtse ido. Wayansa yayi k'ara yayi saurin d'auka, bak'uwar Number ya gani ya d'auka ya kara a kunnensa "Gobe k'arfe hud'u na yanma muke san kud'in nan sannan in cash mukeso" Hankalinsa tashe yace "Ina matata? Dan Allah ku bani ita zanyi magana da ita" Yayi wani dariya mai sauti yace "Matarka a nan cikin k'oshin lafiya a halin yanzu, idan har kanasan ran matarka sai ka kiyaye sharud'an da zamu gindaya maka" "Wani irin sharud'u nayi alkawari zan kiyaye matuk'ar zaku bani matata" Ya sake yin dariya yace "Ka kwantar da hankalinka, na d'aya bamaso ka saka 'yan sanda a wannan tafiyar, sannan kada ka sanar da kowa akan maganar daga mu sai kai. Kud'in da kuma zaka kawo kamar yanda na fad'a maka a baya in cash mukeso a cikin ghana must go. Gobe zamu kira mu fad'a maka inda zaka aje kud'in da kuma inda zaka d'auki matarka" Basu jira mai zaice ba suka kashe kiran, k'ara kira yayi jikinsa na rawa anma a kashe. Wani sabon kuka ya fashe dashi na tashin hankali musamman na tuna irin mak'udan kud'in da akeso wanda baida halinsu. Kuka ya dage yanayi bil hak'i da gaskiya ga wani irin yunwa dake cinsa. Ganin kukan bazai fishe shi ba yasa ya mik'e dakyar ya shiga toilet yayo alwala ya tada sallah. A police station kuwa, secret room aka kai Alhaji Ameenu, duk tambayan da Mifzal ya masa k'in amsawa yayi wai sai anzo da lawyernsa. Ganin zai b'ata musu lokaci yasa aka fita dashi aka kawo Bilal. Da wani kallan rainin wayo Bilal ke bin Mifzal yar ya zauna. Mifzal yayi folding hannuwansa yace "Bilal Tukur! Me ka sani game da kisan Alhaji Surajo" Bilal ya b'ata fuska yace "Waye kuma Alhaji Surajo" Kyakkyawan mari Mifzal ya d'aukesa dashi sannan ya chakume sa "Baka sanshi bah kuma ka aika yaranka suka kashe shi" "What the hell are you talking about" cewar Bilal ransa b'ace "Ranar Ashirin ga watan January da daddare an shiga gidan Alhaji Surajo an kashe sa, mai zakace game da wannan" Bilal ya sake had'e rai "Oho!" Mifzal ya saki murmushi mai sauti ya danna wani alarm sai ga wasu 'yan sanda guda biyu manya sun shigo, Mifzal ya sake kallan Bilal a karo na uku "Meyasa ka aika aka kashe Alhaji Surajo bayan bashi da masaniya akan Hatsaniyar dake tsakaninka da d'ansa" Yaja dogon tsaki rai b'ace "Ni bansan abinda kake magana akai bah" Tafi Mifzal yayi, 'yan sandan da suka shigo suka soma dukan Bilal da kulki iya k'arfinsu, Ihu da kururuwa babu wanda Bilal beyi bah, Mifzal ya dakatar dasu ya sake matsowa inda Bilal d'in ke zaune kan kujera, wayan da sukayi ranan bayan rasuwan Abba ya saka masa yaji yace "Me zakace game da sak'on nin da kake tura ma Jamal da kuwa wannan wayan da kukayi dashi ran nan" Cikin Kuka Bilal yace "Bani da wata masaniya akan kashe mahaifin Jamal" "Shi kuma wad'an nan sak'onnin da waya fah" Ya sake fashewa da kuka "Wallahi duk barazana ce kawai nake masa dan ya rabu da Ummy, tun fil azal ni nake san Ummy kuma munyi alk'awarin aure a tsakanin mu" Mifzal ya katseshi da cewa "Shine dakaga yak'i sakinta ka tura aka kashe mahaifinsa" "A'a Wallahi bani na tura aka kashe Mahaifinsa bah" Mifzal yayi murmushi ya sake bada oder aka cigaba da dukansa, sannan yace su tsaya. "Kana wahalar da kanka sannan muma kana wahalar damu, idan har kanasan kanka da arziki, ka tsaya kayi mana bayani" Iya rud'ewa Bilal ya rud'e duk jikinshi a farfashe sai share kwalla dayake "Iya gaskiyata na fad'a muku." Mifzal yace "Menene Alak'ar ka da Alhaji Ameenu" "Shekara d'aya da rabi da suka wuce ya tab'a tsinta na a hanya lokacin munyi hatsari, kasancewar ba mazaunin Nigeria baneh yasa ya tafi dani chan k'asar dayake da zama. A chan ya mini magani har na warke ina zaune a gidansa" Mifzal ya gyada kai yace "Good!" Ya kalli 'yan sandan dake tsaye yace "Lets all it a day, ku saka shi a Ceil, gobe ma cigaba daga inda muka tsaya" Ya fita daga d'akin ya koma inda Alhaji Ameenu ke tsare, "Alhaji Ameenu kasancewar ka babban mutum yasa bama san mu wahalar dakai sannan bama san duniya tasan halin dakake ciki" Rai b'ace Alhaji Ameenu yace "I told uh bazan tab'a yin magana dakai without my lawyer bah" Mifzal yayi murmushi ya bada umarni aka d'auko wayan Alhajin ya mik'a masa "Gashi ka kira Lawyern naka, muna jiransa gobe by 7:am" Ba tare da b'ata lokaci ba ya amsa wayan ya nemi layin Lawyern ya sanar dashi abinda ke faruwa. *** Kuka kam Ummy tasha har ta gode Allah, An kawo mata abinci ta kasa ci sai ma amai daya taso mata ta rasa yanda zatayi hakanan tayi a wajan rabi duk a jikinta. Tuni zazzab'i da matsanan cin ciwon kai ya rufeta har bata gani sosai, har lokacin tana nan a kulle kamar yanda take d'azu sai hawaye dake fita daga idonta. Wani matashi ne ya shigo d'akin datake ya aje mata abincin dare, sannan ya kwance mata baki da hannu ya tura mata abincin gabanta. Cikin kuka ta kalleshi "Dan Allah ku kaini gida, ban muku komai bah" Ogan ne ya shigo, saurayin ya mik'e ya fita dasauri, ya k'araso inda take yana murmushin mugunta "Gaskiya mijinki na sanki sosai, saidai idan har yayi yunk'urin b'ata mana budget ko yayi jinkirin kawo kud'in da mukace" Ya matso inda take zaune saitin fuskanta "Sunanki keda shi Gawa, dan an bamu umarnin mu kashe ku" Ta fashe da kuka tana girgiza masa kai dakyar "Dan Allah karku kashe shi, ni na yarda ku kashe ni a madadin sa dan Allah" Ta k'are maganan da matsanancin kuka. Ya saki wani irin dariya yace "Mu umarnin da aka bamu kenan mu kashe ku duka ke dashi koda an bada kud'in" Ya sake sakin dariya ya mik'e ya fita. Ta bisa da kallo tana kuka tare da kiran sunan Allah. •••••• Jamal ko ya dad'e yana kai kukansa wajan Ubangiji yana kuka yana rok'on Allah ya kawo masa d'auki akan abinda ke faruwa dashi har zuwa goshin asubah sannan ya mik'e dakyar dan shima kanshi ne ke wani irin sarawa ya fito daga side d'in ko tsoron dare bayayi. Side d'inshi ya shiga ya haura zuwa d'akinsa, Diary d'in nan yaci karo dashi a kan gado ya k'arasa ya d'auka ya bud'e page d'in daya tsaya ya cigaba da karantawa _Watan gaririya muka soma cikin anguwan da muke gashi dare nata yi bamu samu wajan saka hak'arkarin mu bah. Kwatsam munzo wucewa ta wani bola mukayi muka soma jiyo kukan Jariri a cikin bolan, cikin tsoro muka matsa, Jamila matata ya rik'o hannuna tace_ " _Gaske ne wanna kukan mutum neh_ " _Duk da ina cikin tsoro hakan bai hanani k'arasawa wajan bah, nan muka same KA cikin wani akwati kana ta tsaya ku....._ Cikin wani irin k'ara ya rufe diaryn ya fashe da kuka. *Toh Fah!* Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 10:54 AM] Ayshaaaaaa: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ _Salam Masoyana, kuyi min Afuwa jina shiru kwana biyu. Uzuri ne a gabana dts why, anma insha Allahu zan cigaba da posting kamar yanda nakeyi dah_ *Kusha Kurumin ku masu tambayan Labarin Jamaludeen, Insha Allahu yazo k'arshe nan da kwana kad'an zan gama* Page 72 n 73 Already dama ya sayi Ghana must go a hanya, zama yayi dirshan ya soma k'irga kud'in yana sakawa cikin Ghana must gon batare da wani tunanin bah, dan gaba d'aya hankalinsa nakan Wife d'insa. *A gurguje* Ram ya kali Mifzal fuskanshi ba walwala "Naji High court wajan lawyern dayazo da Wannan Alhaji Tijjanin, abin was terrible" Mifzal ya gyara zama yace "Kamar yah?" Ram ya sauke ajiyar zuciya yace "Anyi hayansa ne kawai yaje ya bada shaida akan bashin da akace Alhaji Tijjani na binsa" Sosai Mifzal yayi mamaki, yace "To yanzu menene abin yi?" Ram ya gyara zama ya matso kusada Mifzal yace "Kama Barr nan zakuyi ku tuhumesa, or a turashi state CID for investigation" Sosai Mifzal yaji dad'in shawaran Ram, ya mik'e yana cewa "Muje tare dan akwai tambayoyin da nakeso Alhaji Ameenu ya amsa min kuma inaso ya kasance a gabanka" A tare suka mik'e suka fito, already dama Mifzal yasa record a wayansa, inda Alhaji Ameenu yake suna nufa, Mifzal ya zauna kan kujera Ram kuma na tsaye gefensa "To Alhaji tunda ga lawyern ka a kusa dakai yanzu ina iya maka tambayoyi koh" Harara Alhaji Ameenu ya wurga masa, Mifzal yayi murmushi sannan yace "Inaso nasan ko kai wanene" Saida Alhaji Ameenu ya kalli Lawyernsa ya gyad'a masa kai sannan yace "Sunana Ameenu Jibril, ni d'an Kano neh, inada mata d'aya da kuma 'ya'ya biyu namiji da mace. Mafi yawan zama na a Egypt nake yinsa tare da iyalina" Mifzal ya jinjina kai sannan yace "Ko zan iya sanin sana'arka?" Barr. Ishaq ya karb'e da cewa "D'an kasuwa neh ku..." Saurin d'aya masa hannu Mifzal yayi ransa b'ace "Ina magana neh da Alhaji Ameenu Jibril bakai bah" Gum Barr. Ishaq yayi sai hararan Mifzal d'in yake a fakaice. Alhaji Ameenu yace "Kamar yanda lawyer na ya fad'a ni bussiness man neh, a da ne nayi siyasa" "Menene Alak'ar ka da Alhaji Surajo" "Mene kuwa tsakanin mu? Ni ko sunansa ban tab'a ji ba balle nasan shi" Sosai yanda Alhaji Ameenu ya daburce yaba Mifzal dariya "Come down Alhaji" Gaba d'aya Alhaji ya tsure sai muzurai yake yana zufa, Mifzal yace "An kashe Alhaji Surajo Ranar Ashirin ga watan January da daddare an shiga gidan Alhaji Surajo an kashe shi, ko zaka iya fad'amin ranar kana ina" Alhaji Ameenu ya k'ara tsurewa, muryansa na rawa yace "I...inna k..kuwa? Ina gidana dake Abuja mana" Barr. Ishaq yayi saurin cewa "Why all this questions? Ni Lawyern Alhaji Surajo kadiri neh, haka zalika ni Lawyern Alhaji Ameenu neh. Kuma inada tabbacin babu wanda yasan wani tsakanin su" Ran Mifzal in yayi dubu ya b'aci musamman yanda Barr. Ishaq ke d'aga murya yana magana a fad'ace. Yace "Kullum da daddare wuraren k'arfe tara zuwa goma kana fita daga gida ina kake zuwa?" Alhaji Ameenu ya juya ya kalli Barr sannan ya juyo ga Mifzal "Bana zuwa ko ina sai wajan kasuwanci nah" "Detective wannan tambayoyin ya isa haka, ba hannun Alhaji Ameenu a duk wad'an nan abubuwan. Kuyi gaggawan sakinsa ko na maka ku a kotu" Wani dariya Mifzal ya saki "Dako naji dad'i idan ka kaini kotu" A fusace ya mik'e yama Ram nuni ya biyosa, ba musu suka fita daga seil d'in. Barr ya kalli Alhaji Ameenu yace "Alhaji ka kwantar da hankalin ka komai zaizo k'arshe yau d'in nan" Mifzal na fita yasa wasu 'yan sanda su fito masa da Barr Ishaq, cikin sauri suka fito dashi aka kaishi Secret room sai fizge fizge yake yana fad'a. State CID aka kira sukazo suka tafi dashi dan a tuhumesa. Mifzal yace "Jamal na cikin wani hali na rashin Ummy, idan ka ganshi sai ya matuk'ar baka tausayi" Jikin Ram yayi sanyi yace "Kafin mu samu wani information akan Barr Ishaq mu duba Jamal d'in mu dawo. sai shima mu tambaya ko sun k'ara kira" Ba musu Mifzal ya zari key suka bar office d'in. A b'angaren Jamal kuwa, Cikin Awa d'aya zuwa da rabi ya gama had'a kud'in tsaf ya saka a ghana must go kamar yanda suka buk'ata. Zama yayi yana jiran kiransu dan su fad'a masa inda zai aje kud'in. Ba dad'ewa wayansa ya soma ringing, numbern Ummyn neh yayi appearing ya d'auka dasauri jikinsa na rawa ya kara a kunnensa "Hello Wife!" Muryan namijin nan neh ya sake ji, gabansa ya fad'i ya yayi saurin cewa "Ina matata? Ina take? Ga kud'in ku na had'a muku ina zan sameku" Daga chan b'angaren yace "Good Boy! Lallai kana san matar nan taka." "Dan Allah ka bani naji muryanta, dan Allah" Ba musu ya kara ma Ummyn a kunne, tana kuka tace "Ya Jamal ina kake? Dan Allah kazo ka tafi dani, ban..." Akayi saurin fizge wayan, hawaye ne suka soma zarya a fuskansa yace "Pls karku tab'ata, ku fad'amin inda zan aje muku kud'in na d'auki matata" Cikin wani irin dariya Mutumin yace "Ka aje kud'in a wajan bishiyoyin Bomo Village, daka iso wajan zamu ganka by 11:00am dot, kana wucewa zamu kasheta" Wani k'ara ya saki, kamin yayi magana aka kashe wayan, agogo ya duba yaga 10:15am. Ya fashe da kuka ya d'au ghana must go d'in dakyar ya fita, bai ko kalli Mabrookah dake masa magana tana k'okarin k'arasowa inda yake. Yayi saurin shiga motan ya tada ya bar gidan a guje. Fitanshi Express yayi daidai da k'arasowan su Mifzal bakin Layin, sam Jamal bai lura dasu bah ya k'arama motar wuta yayi gaba, da Mamaki Mifzal yabi motar da kallo "Kaga Jamal chan ina kuma zashi" Ram yace "Ji yanda yake driving da gudu, anya kamar ba lafiya bah mu bisa" Ba musu ya juya kan motan suka soma binsa da gudu suma. Hold up ya samu wajan ABU ya daki stiering motan wasu hawaye suka sake gangaro masa, agogo ya duba 10:40am, ya rushe da kuka yanata danna horn. Yakai Minti Biyar a wajan ya samu ya wuce ya cigaba da gudu su Mifzal na binshi, Bomo Village sukaga ya shiga suka suka sa kan motarsu ciki. Daga mirrown gaban motan ya Hango motar Mifzal d'in, ya sake dukan Stiering yayi saurin Parking ya fito yana kuka. Suma suna ganin Haka sukayi parking, ya k'araso inda suke tsaye "Dan Allah ku koma, ku kyalleni Pls karsu kashe min matana. Amsota zanje yi, dan Allahu ku koma" Gaba d'aya ya basu tausayi, Ram yace "Ka samu kud'in neh?" Ya duba Agogon Hannunsa 10:50am, wasu Hawaye suka sake zubo masa, cikin fad'a yace "Ku rabu dani! Ku tafi ku kyalleni" Ya sassauta murya cikin kuka yace "Zasu kashemin matata idan har bankai bah har 11:00am bah" Ha had'e hannayensa alamar bada hak'uri "Dan Allah ku koma, kuyi hak'uri" Hawaye Ram ya share na tausayin abokin nasa, ya duba agogon Hannusa 10:54am, Mifzal yace "Yi sauri tho" cewar Mifzal. Da gudu ya shiga mota ya figa a guje yabar wajan. Da wani matsiyacin gudu ya k'arasa inda sukace masa, Parking yayi ya bud'e booth ya ciro kud'in, a hankali yake tafiya har ya k'arasa wajan da akace ya ajiye. Gabas da yanma, kudu da arewa ya duba baiga kowa ba sannan ya aje gefen wani bishiya, ya juya ya koma wajan motansa, K'aran Harbin Bindiga yaji from no where. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 10:54 AM] Ayshaaaaaa: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Dis page goes to Sumaiya Eesah Aunty Nurse Precious Girl Xeeaction Team Bilal Team Jamal Maman Ahmad Ahmad yusuf And All Jamaludeen Fans Both Whtsapp and Facebook.💯❤ ILYSM Page 71 Cikin wani irin k'ara ya rufe diaryn ya fashe da kuka sosai "Wai meke shirin faruwa dani neh? Allah ka kawo min d'auki a wannan hali danake ciki" Ya sake fashewa da kuka, diaryn ya d'auka zaiyi gurgi dashi sai kuma ya tsaya yana kallanshi yana cigaba da kuka, dakyar ya sassauta gabansa na fad'uwa sosai ya sake bud'ewa ya cigaba da karantawa. _nan muka same KA cikin wani akwati kana ta tsala kuka, ni da matata mun matuk'ar tausaya maka. Matata tasa hannu cikin fargaba ta d'agaka, wasu daloli muka gani shak'e da akwatin da kuma wasu zinarai duk a ciki._ _Munyi matuk'ar mamaki tare dajin tsoro, haka muka d'aukeka da akwatin muka nufi wani runfar mai k'osai muka kwanta har lokacin muna cikin fargaba._ Wani kuka ya sake zuwa masa yana cigaba da karantawa _Washe gari da safe na duba cikin Jakan, inda na tsinci wata wasik'a a ciki wanda aka rubuta cewa kanada Iyaye Uwa da uba, sannan kai ba shege baneh. Da kuma wasu hotuna a ciki. Haka mukayi ta rainonka da kud'in da muka tsince ka dashi. Kud'i ne masu d'inbin yawa wanda na dunga chanza su a hankali na fara juyawa_ _Ina sanka fiye da yanda nake san kaina, haka matata ta d'auke ka kamar d'an data haifah. Na juya kud'in sosai kuma sun hab'aka fiye da tunanina. Ana haka Allah ya amshi matata Jamila ta sanadin Haihuwa inda bata ruga da ta haifi abinda ke cikinta ba ta rasu_ _Lokacin kanada shekara bakwai, nayi kuka haka kaima kayi kukan rashin Jamila. Ana haka Allah ya had'ani da Maimuna na aureta, sam na hanata sanar dakai cewa ba ita ta haifeka bah, sannan ko ita ban sanar ma ba Jamila ta haifeka bah. Wannan na rik'esa a matsayin sirrina da naka_ _Nayi matuk'ar kuskure da ban fad'a maka da wuri bah. Nayi tunanin barinsa a raina sai daga baya naga rashin dacewar hakan. Ka yafemin d'ana abin k'aunata, ka yafemin rashin fad'a maka ko kai waye....._ Page d'in gaba ya bud'e yana kuka yaga a daidai nan rubutun ya tsaya. Ya rungume Diaryn ya sake fashewa da kuka "Na yafe maka Abbana, Allah ya jikan ka kaida Mamana, nima ina sanku" Tsam ya rungume Diaryn a jikinsa yana cigaba da kuka, gyangyad'i ya soma hakan yasa ya kishingid'a jikin gadon har lokacin Diaryn na jikinsa. A haka bacci ya d'aukesa mai cike da mafarkai kala kala, kiran sallahn Asubah ne ya tayar dashi ya mik'e zaune yana mik'a a hankali, juyawa yayi gefensa yaga diaryn a fad'ai k'asa ya bud'e. Wani rubutu ya gani hakan yasa ya d'auka dasauri yana dubawa _Ajiyarka yana cikin system d'in dake had'e da wannan littafi_ Dasauri ya mik'e ya nufi inda Jakan yake, wani zip ya bud'e sai ga system k'irar toshiba ta baiyana. Dasauri ya ciro ya kunna yayi sa'a akwai chargi, Yana kunnawa yaga password, bai sha wahala ba dan yasan password d'in Abban na komai nasa. Bincike ya soma har Allah yasa ya samu wani information na wani b'oyayyen gidan Abban dake gyallesu, Harda inda keyn yake. Wani lallausan Murmushi Jamal d'in ya saki "Thank Uh dad! I love uh so much" Ya share guntun kwallar data gangaro masa. Toilet ya shiga yayo alwala ya fito. Koda ya isa masallacin har an tada sallah, yana idarwa ya fito dasauri ya shiga side d'in Abban. D'akinsa ya shiga ya duba inda yace Keyn gidan yake ya d'auka ya fito. Motarsa yama key yabar gidan dasauri duk da yanda garin yake duk'u duk'u dan garin bai soma haske bah. Cikin 'yan mintina ya isa gyallesu kwatancen ya soma bi har ya isa k'ofar wani madaidaicin gida. Keyn ya d'auka ya bud'e gidan ya shiga da k'afar dama. Ya bud'e gidan ya shiga yana haskawa da torch d'in wayansa. Gaba d'aya gidan yayi k'ura sosai, bedroom d'in daya gani ya shiga ya d'aga katifan kan gadon sai ga k'aton Akwati ya baiyana. Akwatin yajawo ya fito dashi ya bud'e. Ba shiri ya koma baya ganin mak'udan kud'i dollars da kuma naira a ciki, ware ido yayi da mamaki yana bin kud'in da kallo. Daga saman kud'in akwai wata farar takarda inda aka rubuta "Dukiyarka kenan d'ana Jamal, ka Gafarceni na rashin sanar dakai da wuri" Hawaye suka gangaro masa, ya duba k'asan takardan inda aka rubuta "Duk wani abu dakakeso ka sani game da kai kana iya duba cikin wardrobe" Ya aje takardan a hankali yana cigaba da hawaye, wardrobe d'in ya bud'e yaga wani akwati mai d'an girma duk ya kod'e. D'aukowa yayi ya fita dashi zuwa mota sannan ya dawo ya d'au na kud'in dakyar ya kai mota shima. A police station kuwa, kamar yanda Mifzal da Lawyern Alhaji Alameen sukayi, k'arfe bakwai tama Lawyern a police station d'in. Mifzal bai iso ba sai wuraren k'arfe Bakwai da rabi. A wajan canther ya samu Lawyern, Mifzal na ganinsa ya cire eye glasses d'in dake idonsa yana kallansa da Mamaki "Are uh not Barr Ishak Haruna Lawyern Alhaji Surajo" Yayi saurin gyad'a kai yace "Yes nine" Mifzal ya sauke ajiyar zuciya ya bashi dama suka shiga office d'inshi, bayan sun zauna Mifzal ya mik'a masa hannu sukayi musabaha "Sunanan detective Mifzal Ibrahim, muna zargin Alhaji Ameenu neh da laifi guda biyu, Murder da kuma kiddnapping" Da Mamaki Barristern yace "Anma kuwa wannan abin da mamaki yake, duka duka watan Alhaji Ameenu nawa da dawowa k'asar Nigeria da zama" Knocking akayi Mifzal ya bada umarnin a shigo, Ramadhan ne ya shigo da sallama yana sanye cikin Suit b'aki da wani breifcase a hannunsa. Sosai Mifzal yaji dad'in ganinsa ya nuna masa kujera ya zauna. Mifzal ya nuna Ram yace "Barrister Ramadhan Ahmad kenan Lawyern Jamaludeen Surajo" Sukayi musabaha, Ram sai kallan Barristern yake da harara. Barr. Ishak yace "Zan iya ganin Alhaji Ameenun" Mifzal yace "Why not" Waya ya d'auka ya kira, chan sai ga wani d'an sanda, ya bashi Umarnin yakai Barr. Inda Alhaji Ameenu yake tsare. Yana fita Ram ya kalli Mifzal yace "Akwai wani abu mai matuk'ar d'aure kai dake faruwa" Jamal bai zame ko ina ba sai gida, bai samu kowa a farfajiyan gidan bah, ya kinkimi Akwatin yakai d'akinsa, ya dawo yad'au d'ayan yakai. Already dama yasayi ghana must go a hanya, zama yayi dirshan ya soma irga kud'in yana sakawa cikin ghana must go d'in batare da wani tunani bah, dan gaba d'aya hankalinsa nakan Wife d'insa. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:16 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ _Salam Masoyana, kuyi min Afuwa jina shiru kwana biyu. Uzuri ne a gabana dts why, anma insha Allahu zan cigaba da posting kamar yanda nakeyi dah_ *Kusha Kurumin ku masu tambayan Labarin Jamaludeen, Insha Allahu yazo k'arshe nan da kwana kad'an zan gama* Page 72 n 73 Already dama ya sayi Ghana must go a hanya, zama yayi dirshan ya soma k'irga kud'in yana sakawa cikin Ghana must gon batare da wani tunanin bah, dan gaba d'aya hankalinsa nakan Wife d'insa. *A gurguje* Ram ya kali Mifzal fuskanshi ba walwala "Naji High court wajan lawyern dayazo da Wannan Alhaji Tijjanin, abin was terrible" Mifzal ya gyara zama yace "Kamar yah?" Ram ya sauke ajiyar zuciya yace "Anyi hayansa ne kawai yaje ya bada shaida akan bashin da akace Alhaji Tijjani na binsa" Sosai Mifzal yayi mamaki, yace "To yanzu menene abin yi?" Ram ya gyara zama ya matso kusada Mifzal yace "Kama Barr nan zakuyi ku tuhumesa, or a turashi state CID for investigation" Sosai Mifzal yaji dad'in shawaran Ram, ya mik'e yana cewa "Muje tare dan akwai tambayoyin da nakeso Alhaji Ameenu ya amsa min kuma inaso ya kasance a gabanka" A tare suka mik'e suka fito, already dama Mifzal yasa record a wayansa, inda Alhaji Ameenu yake suna nufa, Mifzal ya zauna kan kujera Ram kuma na tsaye gefensa "To Alhaji tunda ga lawyern ka a kusa dakai yanzu ina iya maka tambayoyi koh" Harara Alhaji Ameenu ya wurga masa, Mifzal yayi murmushi sannan yace "Inaso nasan ko kai wanene" Saida Alhaji Ameenu ya kalli Lawyernsa ya gyad'a masa kai sannan yace "Sunana Ameenu Jibril, ni d'an Kano neh, inada mata d'aya da kuma 'ya'ya biyu namiji da mace. Mafi yawan zama na a Egypt nake yinsa tare da iyalina" Mifzal ya jinjina kai sannan yace "Ko zan iya sanin sana'arka?" Barr. Ishaq ya karb'e da cewa "D'an kasuwa neh ku..." Saurin d'aya masa hannu Mifzal yayi ransa b'ace "Ina magana neh da Alhaji Ameenu Jibril bakai bah" Gum Barr. Ishaq yayi sai hararan Mifzal d'in yake a fakaice. Alhaji Ameenu yace "Kamar yanda lawyer na ya fad'a ni bussiness man neh, a da ne nayi siyasa" "Menene Alak'ar ka da Alhaji Surajo" "Mene kuwa tsakanin mu? Ni ko sunansa ban tab'a ji ba balle nasan shi" Sosai yanda Alhaji Ameenu ya daburce yaba Mifzal dariya "Come down Alhaji" Gaba d'aya Alhaji ya tsure sai muzurai yake yana zufa, Mifzal yace "An kashe Alhaji Surajo Ranar Ashirin ga watan January da daddare an shiga gidan Alhaji Surajo an kashe shi, ko zaka iya fad'amin ranar kana ina" Alhaji Ameenu ya k'ara tsurewa, muryansa na rawa yace "I...inna k..kuwa? Ina gidana dake Abuja mana" Barr. Ishaq yayi saurin cewa "Why all this questions? Ni Lawyern Alhaji Surajo kadiri neh, haka zalika ni Lawyern Alhaji Ameenu neh. Kuma inada tabbacin babu wanda yasan wani tsakanin su" Ran Mifzal in yayi dubu ya b'aci musamman yanda Barr. Ishaq ke d'aga murya yana magana a fad'ace. Yace "Kullum da daddare wuraren k'arfe tara zuwa goma kana fita daga gida ina kake zuwa?" Alhaji Ameenu ya juya ya kalli Barr sannan ya juyo ga Mifzal "Bana zuwa ko ina sai wajan kasuwanci nah" "Detective wannan tambayoyin ya isa haka, ba hannun Alhaji Ameenu a duk wad'an nan abubuwan. Kuyi gaggawan sakinsa ko na maka ku a kotu" Wani dariya Mifzal ya saki "Dako naji dad'i idan ka kaini kotu" A fusace ya mik'e yama Ram nuni ya biyosa, ba musu suka fita daga seil d'in. Barr ya kalli Alhaji Ameenu yace "Alhaji ka kwantar da hankalin ka komai zaizo k'arshe yau d'in nan" Mifzal na fita yasa wasu 'yan sanda su fito masa da Barr Ishaq, cikin sauri suka fito dashi aka kaishi Secret room sai fizge fizge yake yana fad'a. State CID aka kira sukazo suka tafi dashi dan a tuhumesa. Mifzal yace "Jamal na cikin wani hali na rashin Ummy, idan ka ganshi sai ya matuk'ar baka tausayi" Jikin Ram yayi sanyi yace "Kafin mu samu wani information akan Barr Ishaq mu duba Jamal d'in mu dawo. sai shima mu tambaya ko sun k'ara kira" Ba musu Mifzal ya zari key suka bar office d'in. A b'angaren Jamal kuwa, Cikin Awa d'aya zuwa da rabi ya gama had'a kud'in tsaf ya saka a ghana must go kamar yanda suka buk'ata. Zama yayi yana jiran kiransu dan su fad'a masa inda zai aje kud'in. Ba dad'ewa wayansa ya soma ringing, numbern Ummyn neh yayi appearing ya d'auka dasauri jikinsa na rawa ya kara a kunnensa "Hello Wife!" Muryan namijin nan neh ya sake ji, gabansa ya fad'i ya yayi saurin cewa "Ina matata? Ina take? Ga kud'in ku na had'a muku ina zan sameku" Daga chan b'angaren yace "Good Boy! Lallai kana san matar nan taka." "Dan Allah ka bani naji muryanta, dan Allah" Ba musu ya kara ma Ummyn a kunne, tana kuka tace "Ya Jamal ina kake? Dan Allah kazo ka tafi dani, ban..." Akayi saurin fizge wayan, hawaye ne suka soma zarya a fuskansa yace "Pls karku tab'ata, ku fad'amin inda zan aje muku kud'in na d'auki matata" Cikin wani irin dariya Mutumin yace "Ka aje kud'in a wajan bishiyoyin Bomo Village, daka iso wajan zamu ganka by 11:00am dot, kana wucewa zamu kasheta" Wani k'ara ya saki, kamin yayi magana aka kashe wayan, agogo ya duba yaga 10:15am. Ya fashe da kuka ya d'au ghana must go d'in dakyar ya fita, bai ko kalli Mabrookah dake masa magana tana k'okarin k'arasowa inda yake. Yayi saurin shiga motan ya tada ya bar gidan a guje. Fitanshi Express yayi daidai da k'arasowan su Mifzal bakin Layin, sam Jamal bai lura dasu bah ya k'arama motar wuta yayi gaba, da Mamaki Mifzal yabi motar da kallo "Kaga Jamal chan ina kuma zashi" Ram yace "Ji yanda yake driving da gudu, anya kamar ba lafiya bah mu bisa" Ba musu ya juya kan motan suka soma binsa da gudu suma. Hold up ya samu wajan ABU ya daki stiering motan wasu hawaye suka sake gangaro masa, agogo ya duba 10:40am, ya rushe da kuka yanata danna horn. Yakai Minti Biyar a wajan ya samu ya wuce ya cigaba da gudu su Mifzal na binshi, Bomo Village sukaga ya shiga suka suka sa kan motarsu ciki. Daga mirrown gaban motan ya Hango motar Mifzal d'in, ya sake dukan Stiering yayi saurin Parking ya fito yana kuka. Suma suna ganin Haka sukayi parking, ya k'araso inda suke tsaye "Dan Allah ku koma, ku kyalleni Pls karsu kashe min matana. Amsota zanje yi, dan Allahu ku koma" Gaba d'aya ya basu tausayi, Ram yace "Ka samu kud'in neh?" Ya duba Agogon Hannunsa 10:50am, wasu Hawaye suka sake zubo masa, cikin fad'a yace "Ku rabu dani! Ku tafi ku kyalleni" Ya sassauta murya cikin kuka yace "Zasu kashemin matata idan har bankai bah har 11:00am bah" Ha had'e hannayensa alamar bada hak'uri "Dan Allah ku koma, kuyi hak'uri" Hawaye Ram ya share na tausayin abokin nasa, ya duba agogon Hannusa 10:54am, Mifzal yace "Yi sauri tho" cewar Mifzal. Da gudu ya shiga mota ya figa a guje yabar wajan. Da wani matsiyacin gudu ya k'arasa inda sukace masa, Parking yayi ya bud'e booth ya ciro kud'in, a hankali yake tafiya har ya k'arasa wajan da akace ya ajiye. Gabas da yanma, kudu da arewa ya duba baiga kowa ba sannan ya aje gefen wani bishiya, ya juya ya koma wajan motansa, K'aran Harbin Bindiga yaji from no where. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:16 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 74 n 75 Gabas da yanma, kudu da arewa ya duba baiga kowa ba sannan ya aje gefen wani bishiya, ya juya ya koma wajan motarsa. K'aran Harbin bindiga yaji from no where. Wani tsale ya doka ya shiga mota dasauri yana haki duk yabi ya tsure, reverse yayi kamin ya juya wata bak'ar mota tasha gabansa. Dam! Gabansa ya fad'i ya soma karato duk addu'ar datazo bakinsa, mutanen nan ne dai masu bak'aken kaya suka tunkaro sa, kiran sunan Allah ya cigaba, d'aya daga cikinsu ya finciko sa daga motan tare da saka masa wani farin yadi a hanci. Luuuu yayi zai fad'i, daya daga cikinsu ya d'aukesa yayi motan dashi, daya ya dau jakan kud'in suka shiga motan suka tada. Mifzal da Ram na tsaye inda ya barsu, Mifzal ya soma kiran Office d'insu dan a turo mai 'yan sanda, bai gama wayan ba yaji k'aran harbin bindiga, ai a d'ari da tamanin suka shiga cikin motan suka bi bayan Jamal d'in. Daga Ram har Mifzal d'in a rud'e suke sai zazzare idanu suke, daga chan nesa suka hango motarsa murfin k'ofan a bud'e. Cikin tashin hankali Ram yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Sun tafi dashi" Baiyi kwakwaran Parking ba ya fito suka k'arasa wajan dukansu jikinsu na rawa. Kuka ne kawai dukansu basu yi bah, Mifzal ya daki Tyre motan Jamal d'in "Damn it!" Dai dai nan sauran 'yan sandan suka k'araso wajan, hotan Motan aka dadd'auka sannan Mifzal ya ciro wajan Jamal d'in dake cikin Motan yana duba last call d'insa duk hankalinsa a tashe. Bari mu koma Gidan Alhaji Surajo. Da safiyar ranar Mami da kanta ta shiga Kitchen ta had'a ma Jamal abin karyawa, koda ta isa side d'in Mabrookah ta samu tana k'okarin fitowa "Aa Mami kece da kanki" Da murmushi Mami tace "Ni ce, Ina Jamal d'in ga Breakfast na masa dan jiya ba abinda yaci" Mabrookah ta amsa Trayn Hannun Mamin tana tab'e baki "Tun Sassafe ya fita inata masa magana bai kulani bah" A rud'e Mami tace "Ya fita kuma? Allah dai yasa ba kiransa sukayi yaje ya samesu bah" Nan da nan Itama Mabrookah ta rud'e jikinta ya soma rawa, lokaci d'aya ta fashe da kuka "Wayyo Mami Allah ya kare Ya Jamal, banaso na rasa shi ina sonshi" Hankalin Mami idan yayi dubu ya tashi, fita tayi a guje ta koma side d'inta, Aunty Faty dake k'okarin saukowa tace "Lafiya dai Maimunatu kika shigo a hargitse haka" Batace mata komai ba ta d'au wayanta ta soma neman layin Jamal d'in, ta kira yafi sau goma bai d'aga bah. Bata ko kalli Aunty Faty ba ta haura sama ta d'auko Hijab da keyn mota ta sauko "Yaya Faty muje, wai meke faruwa?" Cikin k'osawa tace "Kedai Muje" Ba musu tabi bayanta dan akwai mayafi a hannunta. Sukaci karo da Mabrookah tanata musu magana basu tankata bah suka shiga mota suka bar gidan. **** Duk kiran da Mami takeyi wayan na hannun Mifzal kasa d'auka yayi dan baisan mai zaice mata bah. Station d'insu suka koma, ran Mifzal idan yayi dubu ya b'aci, inda Bilal ke kulle ya shiga da kulkinsa a hannu "Wannan shi zai zama warning na k'arshe kuma tambayar k'arshe da zan maka, ina kuka kai Ummy" Gaba d'aya Bilal ya rud'e ganin Kulkin dake hannun Mifzal, ya mik'e daga zaunan dayake dasauri "Wallahi Billahi lazi banga Ummy bah, rabon dana ganta tun kamin a kaita gidan mijinta" Duka Mifzal ya soma kai masa tako ina sai ihu yake yana magiya, Alhaji Ameenu dake Ceil d'in dake kusa dana Bilal gaba d'aya yasha jinin Jikinsa duk ya tsure. Ganin Bilal d'in zai b'ata masa lokaci yasa ya kyallesa ya fito rai b'ace. Ram ya kira suka nufi state CID dasauri. Inda aka aje Barr Ishaq aka kaisu tare da basu report d'in abubuwan daya fad'a musu. Iya rud'ewa Mifzal ya rude bayan ya karanta report d'in, tare da Ram suka shiga d'akin suka samesa zaune. "Barr. Ishaq ashe za'a iya had'a baki dakai ayi irin wannan ta'addancin" Cikin wani irin murya na nadama yace "Dan Allah kuyi hak'uri kumin rai banasan sunanan ya b'aci a idon duniya" Ram ya saki wani malalacin Murmushi "Sunanka ai ya riga ya gama b'aci Barr. Ishaq" Gaba d'aya jikin Barr. Rawa yake yana kallansu. Bud'e kofan d'akin akayi aka shigo da wani dattijo da wasu irin kod'addun kaya. (Saida na k'ura masa ido sannan na gane ashe Alhaji Tijjani neh) Dattijon ya soma kuka yana kama k'asan wandon Mifzal "Dan Allah kuyi min rai Wallahi sharin shed'an neh da kuma talauci. Rud'a na da kud'i sukayi" Takaici ne ya hana Ram da Mifzal magana sai binsu da ido suke. Wani dogon tsaki Mifzal yayi ya fita daga d'akin Ram yabi bayansa. Wayan Jamal d'in ya ciro yana k'ara duba kiran da aka masa k'arshe kafin na Mami, Wife ya gani a rubuce, dasauri ya ciro wayansa ya kira MTN office ya basu numbern dan su duba masa Location d'in wayan. •••• D'akin da Ummy take suka jefa Jamal, tana ganinsa ta sake fashewa da kuka duk da baya fita saboda dishewan da muryanta yayi da kuma tsuman dake rufe da bakinta. Dariya suka soma suna kallanta "Ga mijinki nan sai muga yanda za'ayi ku fita daga hannun mu" D'aya daga cikinsu yace "Ohhh Poor Girl, ji yanda take kuka gwanin ban sha'awa" Jan jiki ta soma har ta k'arasa inda Jamal d'in ke yashe tana cigaba da kuka tana kallansa. Fita sukayi suka barsu a wajan, chan kuma suka dawo shima suka d'auresa kamar yanda suka d'aureta. Jamal bai farka ba sai wuraren k'arfe hud'u na yanma, Sautin kukan Wife d'insa ya ne ya soma shiga kunnensa. Manage This Pls Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:17 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 76 n 77 Jamal bai farka ba sai wuraren k'arfe hud'u na yanma, Sautin kukan Wife d'insa ne ya soma shiga kunnensa. Ba shiri ya mik'e zaune yana kallanta, K'afansa ya kalla yaga an d'auresa haka hannuwansa da bakinsa, girgiza mata kai ya soma alamar ta daina kuka, ya ja jiki ya matsa kusa da ita yana cigaba da girgiza mata kai. Wani kukan ta sake fashewa dashi tana kallansa ganin yanda duk ya rame ya fita haiyacinsa haka itama. Kallan juna suka soma, wasu hawaye suka gangaro masa ganin irin wulak'ancin da akama matarsa ta sunnah. Suna nan manne da juna duk da a d'aure suke hakan bai hanasa lallashinta bah har yasamu tayi shiru. Wuraren k'arfe takwas da rabi na dare aka kawo musu abinci, gabansu ya tura abincin sannan ya fita, mutane biyu suka k'ara shigowa d'akin d'aya ya bud'e ma Jamal baki d'aya ya kwance ma Ummy sannan suka kwance musu hannu. Ogan da kansa ne ya shigo cikin takunsa na iza, Jamal yayi yunk'urin tashi a fusace Wad'an nan mutanen suka ririk'eshi. Ummy ko ta sake fashewa da kuka dan yanzu ya zamar mata kamar ibada. Cikin fad'a Jamal ya kalli Ogan "Me muka muku? Kud'i kukace kuma na kawo ku sake mu mutafi mana" Ogan ya saki wani irin dariya tare da matsowa inda aka ririk'e Jamal d'in, Fuskanshi yasa hannu ya d'ago, Jamal yayi saurin fizgewa yana kallansa rai b'ace. Shiko Ogan sake fashewa da dariya yayi "Ba'a bamu izinin sakin ku bah har yanzu" "Waye ya saku?" Jamal ya tambayeshi cikin fad'a Baice masa komai bah ya juya ya fita yana dariya, duka mutanen nan biyu sukama Jamal kamar ba gobe, Kuka da Ihu had'e da magiya babu wanda batayi bah. Saida suka masa lis sannan suka sake d'auresa suka fita. Da rarrafe ta matso inda yake dan ita basu d'aureta bah, kansa ta d'aura kan kafafuwanta ta fashe da kuka tana shafa sumar kanshi. Dakyar ya iya d'ago fuskanshi yana girgiza mata kai "Ban kasance miji nagari a gareki bah I'm s..." Tayi saurin rufe masa baki da hannunta, Rigan dake jikinta ta yaga k'asan ta soma goge masa bakinsa da hancinsa dake jini har lokacin bata bar kuka bah. Ya lumshe idanuwansa dan kukanta jinshi yake har cikin ransa. **** Duka sosai Mifzal yasa akama wannan dattijon da Barr. Ishaq dan ransa ba k'aramin b'aci yayi bah. MTN office ya koma suka sanar dashi sun kasa samun location d'in wayan dan a kashe take. Ransa ya k'ara b'aci ya bar wajan shida Ram suka nufi gidansu Jamal. Basu samu kowa ba sai Mabrookah, cikin mamaki Ram yace "Mabrookah ina Mami?" Ba tare da wani tunani ba tace "Basanan sunje neman Ya Jamal dan yau tun safe daya fita bai dawo bah" Ta fashe da kuka tace "Gashi har Magrib suma basu dawo bah" Mifzal ya jinjina kai baice komai bah, Ram ya kalli Mabrookahn dake ta share hawaye yace "Mabrookah inaso ki dubi girman Allah ki fad'amin abinda kika sani" Tsaida kukan datake tayi tana kallasu da mamaki "Ban gane me kake nufi bah" Mifzal ya sauke ajiyar zuciya yace "Me kika sani game da Kidnapping d'in Ummy da akayi" Ba shiri ta sake rushewa da kuka tana kallansu "Wallahi bansan komai akai bah, bani da wata masaniya" Ram ya gyad'a kai ya mik'e yafito daga d'akin, Wasu masu gadi ya nufa yad'an musu 'yan tambayoyi ya fita, daga nan farfajiyar gidan yama Mifzal waya ya fito suka tafi. Su Mami basu suka shigo gida ba sai k'arfe goma na dare, dukansu wujiga wujiga suka shigo, Mabrookah ta fad'a jikin Mami tana kuka "Mami baku gansa bah" Dakyar ta iya cewa "Duk inda kike tunani munje bamu samesa bah, mun kai report duk police station d'in da kika sani dake cikin Zaria" Aunty Faty ta karb'e da cewa "Wani police station da mukaje a nan mukaga motarsa ake shaida mana anga motar neh a wani k'auye anma baya ciki dan ana tunanin shima kidnapping d'inshi ak...." Mabrookah ta soma tsalle tana kuka sosai tare da yarfe hannu "Na shiga uku kada su kashe shi Wayyo Allah" Daga Mami har AuntyFaty babu wanda ya iya magana suka haura sama suka barta nan tana kuka kamar ranta zai fita. Su Jamal yanda sukaga Rana haka sukaga dare, Ummy na nan manne dashi tana mai kuka, dakyar ya lallasheta tayi shiru tana sauke jiyar zuciya. A zaune suka kwana wuraren k'arfe takwas na safe Oga ya shigo d'akin yana murmushi, Jamal ya d'aga kai sukayi ido biyu "Wahalar ku takusa zuwa k'arshe yau, yanzu ranku na tsakanin rayuwa da mutuwa" Ummy ta fashe da kuka ta sake k'ankame Jamal tare da chusa fuskanta a k'irjinsa. Hankalin Jamal ba k'aramin tashi yayi ba jin magana da Ogan yayi. Ogan yayi dariya ya fita daga d'akin. K'arfe Bakwai na safe a MTN office tama Ram da Mifzal. Sunyi sa'a an kunna wayan Ummyn, Nan suka soma bin location d'in a hankali, Bomo Village ya nuna musu, Nan akayi Hacking d'in wayan. Wani lungu chan ya nuna musu, Mifzal ya shafa suman kanshi yana kallan Computern "Ta yaya zamu iya gane wajan nan?" Shiru kowa yayi yana tunani, chan Ram yace "Yauwa Why not mu rink'a communicating dasu sai suna mana kwatance" Mifzal ya saki lallausan murmushi yace "Yes Good Idea" Dasauri suka bar wajan, mota hud'u suka d'auka na 'yan sanda, cikin 'yan mintina suka shiga cikin Bomo Village d'in. Communicating suka soma da mutanen Office d'in yawo sosai sukayi tayi cikin k'auyen basu gane wajan bah. Location d'in ya b'ace ta Office suka kira Mifzal suka sanar dashi. Ransa idan yayi dubu ya b'aci, cigaba sukayi da yawo suka kakkasu waje daban daban suna dudubawa. Jamal na rungume da Ummy aka sake turo k'ofar d'akin, Ogan ne ya sake shigowa da yaransa kusan su hud'u. Tsugunawa yayi inda suke ya cire kyallen dake bakin Jamal d'in, Sannan ya juyaga Ummy ya shafa gefen fuskanta tayi saurin fizge fuska "Karka sake ka k'ara tab'amin matata" Wani dariya Ogan yayi ya juya ya kalli yaran nasa suma suka kyalkkyale da dariya, ya juya ga Jamal d'in dake ta huci kamar zaki "Karna sake tab'a matarka kace?" K'okarin mik'ewa yakesan yi anma ya kasa saboda d'auresan da akayi hannu da k'afa. Ogan ya matso da fuskansa saitin na Jamal d'in yana murmushin mugunta. "Yanzun nan zakaga k'arshen tab'awa" Ta tallafo fuskan Jamal d'in suna kallan Juna "Zanyi Raping matarka a gabanka kuma baka isa kayi komai bah" Ummy ta saki kuka tana k'okarin mik'ewa. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:17 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 78 to 80 Ummy ta saki kuka tana k'okarin mik'ewa. Jamal ya saki wani irin k'ara yana k'okarin mik'ewa ya kasa. Yaran Ogan ne sukayi saurin rik'e Jamal d'in, sai k'okarin kuccewa yake yana huci "Karka sake ka tab'a min matata" Ogan ya saki dariya ya soma tafiya a hankali inda Ummyn ke zaune tana kuka, ja da baya ta soma yana binta yana mata murmushi "Ga mace har mace, ki bani had'in kai kawai dan yau babu wanda ya isa ya hana damo kaiwa ga harawa" Kuka take sosai tana matsawa baya yana cigaba da binta, kokarin kwacewa Jamal ketayi yana wani irin k'ara idanunsa na zubar da hawaye, su uku suka rik'esa duk yanda yayi ya kwace kasawa yayi. Cikin wani irin murya yace "Kada kayi haka dan Allah, ka fad'i duk abinda kakeso zan maka." Ya saki dariya yana shafa gefen fuskan Ummyn, "Bana buk'atar komai sai matarka, tun randa na fara ganinta na kwad'aitu da ita. Dan nasan zan huta da ita sosai" Jamal yayi saurin runtse ido yana cigaba da hawaye, Ogan ya tsugunna inda take makure a bango yana k'okarin kai hannunsa k'irjinta, tayi saurin goceta ta sake fashewa da kuka "Dan Allah kayi hak'uri kamin rai, ni matar aurece. Ka dubi girman Allah ka kyalleni" Ya saki dariya mai sauti yace "Idan kinga nabar d'akin nan sai naga na aikata abinda nakeso dake" Kokawa suka soma, Jamal nata ihu yana k'okarin k'wacewa had'e da rok'on ogan. Wani daga cikin yaransa ne ya shigo d'akin dasauri ya k'arasa inda Ogan ke tsugunne yamai magana a kunne. Mik'ewa yayi dasauri yama sauran yaransa dake rik'e da Jamal alama su sakeshi, ba musu suka sakesa ya fita dasauri suka bisa a baya. Ummy na ganin haka ta rarrafo ta dawo inda Jamal d'in ke tsugunne ta rungumesa, murya chan k'asa yace "Kwance ni Wife" A tsorace ta kalleshi ya gyad'a mata kai, batare da b'ata lokaci ba ta soma kwance sa, hannun ta kwance dakyar sannan ya kwance k'afan da kansa. Hannayensa ya bud'e mata yana kallanta, dasauri ta fad'a jikinsa tana kuka. Ya lumshe ido yana shafa suman kanta da duk ya b'aci da k'asa "I'm Sorry Wife" K'ofar d'akin aka banko, suka d'ago suna kallan k'ofan, ba shiri suka mik'e dukansu suna bin k'ofar da kallo. Cikin takun k'asaita ta k'araso cikin d'akin Oga da yaransa na mara mata baya, cikin tashin hankali Jamal yace "Au..Aunty Faty!" Dariya tayi mai sauti sannan ta juya tana kallan bakin k'ofan, Mami ya gani sanye da bak'in dogon riga tasha No respect a fuska tana taunar chewing gum. Suma neh kawai Jamal baiyi bah, idanunsa kuwa kamar zasu fad'o saboda firgici. Ta k'araso gabansa ta tsaya tana kallansa da murmushi "Kana Mamaki koh, sai dai ba abin mamaki baneh dan wannan kad'an kenan daga aikin da mutum kan iyayi" Kuka Jamal ya fashe dashi tana cigaba da kallanta "Meyasa kikayi Haka Mami? Mena miki? Me Abbana ya miki" Ta fashe da wani irin dariya tace "Ban tab'a san Mahaifinka bah, haka kai. Ni nan daka gani na auri Mahaifinka neh kawai dan dukiyarsa. Ganin sanda yake nuna maka yasa abin ya soma damuna shine nasa aka tura maka aljanu dan su hanaka jin dadi ko soyaiyar dake tsakanin ku zai ragu" Ummy sai rarraba ido take cike da mamaki haka jikinta sai rawa yake jin maganganun dake fita daga bakin Mamin. Aunty Faty ta karb'e da cewa "Mun dad'e muna san kawar dakai dan muci dukiyar Mahaifinka saidai kuma hakan bazai yuwu bah in ba mun fara kawar da mahaifin naka bah" Ba shiri Ummy ta sulale k'asa guiwayu biyu ta fashe da kuka jin maganar da Aunty Faty keyi, haka shima Jamal kukan yake daga tsaye yana kallansu da tsananin firgita. Rai b'ace Mami ta nuna Ummy dake tsugunne tana sharb'ar kuka "Tun danake a duniya ban taba tsanar wani kamar yanda na tsaneki bah, dan ke kika fara rusa min plan d'ina. Ban tab'a tunanin kawo ki zai shafi abinda nasa agaba bah." Wani zuciya ne ya ciyo Jamal yayi kan Aunty Faty dasauri Yaran Ogan suka rik'esa yanata k'okarin kwacewa yana kuka "Kun cuceni Mami bazan tab'a yafemuku kashemin mahaifi da kukayi ba da kuma cutar dani da matata da kukayi" Mami da Aunty Faty suka kyalkyalle da dariya, wasu documents ta d'auko cikin wani envelop tare da biro tana cewa "Gidaje guda uku a cikin garin Abuja wanda kowanne yakai darajar Million Ashirin da biyar, Filaye Guda biyar a garin kaduna da kuma gidan gona dake garin Shika. Hannu kawai nakeso kasamin a nan dan na mallaki ab..." Yayi saurin katseta da cewa "Bazan sa ba ko kasheni zakuyi bazan sa bah" Ummy ta sake fashewa da kuka tana kallansu, Mami ta kyalkyale da dariya tana mik'a masa takardan "Kasa min hannu tun muna shiri nida kai" Rai b'ace yace "Bazan sa bah" Ogan ta kalla, yama yaransa alama, duka suka soma kaima Jamal d'in tako ina yanata ihu. Ummy sai kuka take tana daga gefe dan wasu cikin yaran sun zagaye tah. Mami ta tsayar dasu sannan ta mik'a masa takardan "Jamaludeen kasa min hannu a takardan nan" Ya d'ago fuskanshi dake zubar da jini yana kallanta "Bazan sa bah" Aunty Faty tace "Bai horu baneh dakyau har yanzu" Sanda Mami ta d'auka dake gefenta ta matso inda Ummy ke zaune tana kallanta, Yaran suka d'agata tsaye tanata san kwacewa tana kuka. Duka Mamin takai Ma Ummy a ciki da k'arfi, wani k'ara ta saki ta sulale wayan. Jamal ya saki wani irin k'ara ya fizge daga rik'on da suka masa ya k'arasa wajan da Ummyn ke kwance yana kuka. Yawo Mifzal da sauran tawagar su suketayi a cikin k'auyen tare da yima mazauna k'auyan tambayoyi anma ba wani labari. Har sun cire rai zasu koma suka hango motar Mami ta wuce a guje. Dasauri Mifzal yayi reverse yama sauran 'yan sandan Alama akan su dakata, binta ya soma shida Ram a baya ta yanda bazasu san binsu ake bah. Tafiya sukayi sosai, tayi wata kwana wata babbar mota ta fito itama daga kwanar dole suka tsaya har saida motar ta wuce sannan suka suka shiga. Abin haushi basu ga motarta bah. Mifzal ya daki steiring motan yana tsaki. Parking yayi gefen Hanya Ram ya fito yana duduba wajan, shima Mifzal ya fito, shedan tayan motan Ram ya gani ya nunama Mifzal, dasauri suka soma bin shedan suna ta tafiya a hankali suna cigaba da bi. Sauran 'yan sandan yama waya tare da musu kwatancen inda suke suma suka biyo bayan motar Mifzal d'in. Mami ta saki Lallausan Murmushi tana cewa "Idan baka samin hannu bah, zan kashe Ummy na kashe abinda ke cikinta" Cikin wani irin kuka yace "Me na miki a rayuwa Mami? Kefa Uwace a gareni, kinyi min komai a rayuwa kin bani tarbiya, ban chanchanci haka daga gareki bah." Ta saki dariya tace "Ni ba Uwarka bace, ban tab'a sanka bah Jamal. Duk abinda kaga inayi yana cikin Plan d'ina neh. Da kuma ganin idon mahaifinka" Ta mik'a masa takardan "Karb'a kasa min hannu" Ya girgiza kai tare da maida dubansa ga Ummy dake kwance bata numfashi, kanta ya d'aga ya d'aura kan cinyarsa yana kuka sosai. Hannu ta mik'ama Oga ya saka mata bindiga, ta saita Ummyn dashi rai b'ace tace "Ko ka Sa min hannu ko na kashe Ummy" Yasake rushewa da kuka, he has no choice ya amsa takardan yana kuka ya soma signing hawaye na d'iga jikin Papern. Yana gamawa ya mik'a mata ta amsa ta duba sannan ta maida dubanta ga Oga. "Ya cika aikinsa sai kuma ku cika naku" Oga ya saki dariya ya amsa bindigan daga hannunta yana cewa "An gama ranki ya dad'e yau wasu zasuyi kwanan lahira" K'ofar d'akin aka banko a tsorace duka suke bin k'ofar da kallo, 'yan sanda ne sukayi ta shigowa kowannen su da bindiga a hannunsa, Mami ta saki salati haka Aunty Faty suna kallan juna. Mifzal da Ram suka shigo a tare "Drop ur Weapons" cewar Mifzal, ba musu duka yaran Ogan suka aje Bindigogin su. Ram ya k'arasa inda Jamal ke tsugunne yana dubansu da mamaki. Rai b'ace Mifzal yace "Mami kinji kunya" Ta had'e girar sama data k'asa, d'aya daga cikin 'yan sandan yace "Hands Up every Body" Dukansu suka d'aga hannu sama, cikin kuka Jamal yace "Ram Ummyna bata numfashi" Ram ya d'auketa chak, jini Jamal ya gani a inda aka d'agata ya saki k'ara shima ya fadi a wajan. Iya rud'ewa Ram da Mifzal sun rud'e, Dasauri Ram yakai Ummyn Mota sannan ya dawo shida wani d'an sanda suka d'au Jamal d'in. Mami ta fizge Bindiga daga hannun Oga ta saita Jamal d'in zata harbasa taji saukan harsashi a k'afarta. Ta saki Ihu ta fad'i wajan tana kuka dafe da k'afarta, handcop duka akasa musu aka ingiza k'eyarsu, ita kuma wasu 'yan sanda suka d'aukota aka sakata a bayan mota sai kuka take da ihu tana dafe k'afarta. Asibiti Ram da wani d'an sanda sukayi dasu Jamal, ba b'ata lokaci aka amshesu tare da basu taimakon gaggawa. Cikin awa da bai wuce d'aya ba Jamal ya farka tare da mik'ewa zaune. Ram dake kusa dashi yayi saurin rik'esa yana masa sannu "Ram ina Ummyna" Shine Farkon Abinda ya furta, cikin kwantar da hankali yace "Tana lafiya lau, ka kwanta ka huta" Ya fizge jikinsa yana k'okarin mik'ewa "I want to see her Pls" Ya sake maidasa zaune yana lallashinsa "Bazan iya zama batare da naga Wife d'ina bah. Dan Allah ka kaini na ganta hankalina ya kwanta" Hawaye suka cika masa ido, gaba d'aya yanzu tausayi Jamal keba Ram baice komai ba ya mik'e ya kira wata nurse ta cire masa drip d'in hannunsa. Da taimakon Ram d'in yasa takalmi suka fito Ram na rik'e dashi har d'akin da Ummyn take. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:18 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 81 n 82 Da taimakon Ram yasa takalmi suka fito Ram na rik'e dashi har d'akin da Ummyn ke take. Duk da yanda yake ganin jiri hakan bai hanasa sakin Ram ba ya murd'a kofan d'akin ya shiga. Kwance ya sameta kan gadon marasa lafiya tana bacci, hannunta sanye da canular ana mata k'arin jini. Ya k'arasa ya zauna bakin gadon yana kallanta hawaye cike a idonsa, sai yanzu abubuwan da suka faru suka dawo masa. Hawaye ya soma kansa k'asa har lokacin bai bar mamakin Mami da Aunty Faty bah. Yana nan zaune kusa da ita har bayan minti talatin, Ram da Mifzal suka shigo d'akin a tare. Hannu Mifzal ya mik'a masa sukayi musabaha sannan ya tambayesa ya jikinsa. "Dasauk'i. Nagode Mifzal" Ya juya ya kalli Ram yace "Nagode Ramadhan" Mifzal yayi murmushi yana d'an bubuga kafad'ar Jamal "Mu dakai ba godiya" D'an motsawa Ummyn tayi gaba d'aya hankalinsu ya koma kanta, ta b'ata fuska ta sake juya kwanciyanta. Duk idanunsu nakanta, juye juye ta soma tana rik'e da maranta tana kuka a hankali har lokacin idanunta a lumshe. A rud'e ya rik'o hannunta "Open ur eyes Wife, ni neh, Jamal ne" Kasa bud'e idon tayi har lokacin tana juye juye, Ram ya fita dasauri chan sai gashi shida Dr da wasu nurses. Rok'onsu Likitan yayi akan su bashi waje, dakyar Jamal ya saki hanunta suka fita daga d'akin har lokacin bai daina hawaye bah. Sun d'an dau mintina sannan suka fito, Jamal ya k'arasa inda likitan yake tsaye "Dr hw is she" Da murmushi yace "Komai Lafiya lau, munyi nasarar ba cikin jikinta kariya, yana lafiya ba wani abu. Jinnin data zubar da kuma buguwan data samu a maranta ne yake haddasa mata ciwo a maranta. But data farka zata dawo normal" Jamal ya mik'a masa hannu cike da murna, sukayi musabaha ya wuce. Ba yanda ba'ayi da Jamal ya koma d'akinsa bah dan shima yana under observation anma yaki, dole aka d'auko wani gadon aka sa a d'akin da Ummyn take suna karb'an medication tare. K'arfe takwas da rabi na dare lokacin Ram da Mifzal sun wuce bayan sun aje mai duk abinda yake buk'ata, tashi yayi daga kan gadonsa ya zauna kan kujeran dake kusada Gadon Ummy tare da d'aura kansa kan gadon. Nan da nan bacci mai nauyi da dad'i ya d'aukesa cike da mafarkai kala kala. A Police Station kuwa, Har aka kai Mami bata daina Ihu bah dan ji take kamar k'afar ya guntule ne gaba d'aya, tana kuka Aunty Faty nayi na danasani. Wani likita cikin 'yan sandan ne ya cire mata bullet d'in kafar nata tare da Treating wajan aka turasu a ceil itada Aunty Faty. Kan kace me dambe ya kaure tsakanin su wannan tace laifin wannan neh, wannan ma tace Laifin wannan neh. Babu wanda ya tankasu cikin 'yansandan, Mami ko taci duka wajan Aunty Faty dan ta kasa kwatan kanta saboda k'afarta dake mata zugi dan ko takawa bata iyawa. Iyalen Alhaji Ameenu ne suka zo garin Abuja dan labarin ya riskesu, Hankalinsu a tashe sukazo Police station d'in. Matarsa na ganinsa ta fashe da kuka "Alhaji haka ka koma? Garin yaya haka ta faru" Kasa magana Alhaji Ameenu yayi sboda tsananin b'acin rai, d'ansa kuwa ransa idan yayi dubu ya b'aci, kallo d'aya yama Abban nasa ya fita daga Station d'in. Duk yanda Matar Alhaji Ameenu taso a bada bailing mijinta da Bilal k'i sukayi kan cewa basu gama bincike akansu bah. Ba yanda ta iya hakanan ta hak'ura tabar Station d'in tana kuka. Wayan d'anta mai suna Areef ta soma kira har ya katse bai d'aga ba kuma ga motarda sukazo dashi a parke a k'ofar station d'in. Cikin motar ta zauna tana cigaba da hawaye na tausayin Mijin nata. Tana nan zaune ta hangosa ya sauka a Napeep shida wani sun shiga Station d'in. Ta fito ta bisa da sauri "Areef!" Ta kira sunansa, ya juyo tare da amsawa ransa a b'ace "Ina kaje inata nemanka" Ba tare da wani tunani ba yace "Naje Court ne nakai k'ara" Da mamaki ta kallesa "Kasan me kake fad'a kuwa" Kamar zaiyi kuka yace "Haba Ammi ki dubi abinda akama Abbana fah akan abinda baiji ba bai gani bah, nidai bazan tab'a yarda bah" Bai jira mai zatace ba ya shiga cikin station d'in. Mifzal na Office d'insa takardan sanmacin da Areef ya kawo ya samesa, bayan ya karanta ya saki lallausan Murmushi tare da duba date d'in da za'a shiga Kotun, ya sake yin murmushi "Allah ya kaimu! Ayita ta k'are" ••••••• Bud'e ido tayi a hankali tana bin d'akin da kallo cike da mamaki, tad'an juya gefenta na dama, Jamal ta gani ya d'aura kansa a gadon da take yana bacci bil hak'i da gaskiya. Tayi murmushi tare da cusa hannunta cikin suman kanshi tana d'an masa waiwayi, ya bud'e idonsa dakyar dan bacci ne fal a idonsa, murmushi ta masa ya bud'e ido dasauri tare da mik'ewa zaune. Hannu ta bud'e masa tana masa murmushi dan yanzu gaba d'aya tausayi yake bata, ba musu ta fad'a jikinta suka rungume juna sai hawaye na tausayin junansu, sun dad'e a haka sannan ya janye jikinsa yana kallan fuskanta hawaye na cigaba da gangara daga idonsa "Kiyi hak'uri Wife, nasan komai was my Fault, Laifi na neh ya sh..." Tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai, "Ba laifinka baneh My Prince haka Allah yaso" Sosai yaji dad'in sunan data kirasa dashi, ya langwabar dakai gwanin tausayi "Karki danne gaskiya Wife, laifina neh, nine na kasa baki kulawa data dace a matsayina na Mijinki. Ban kasance miji na gari a gareki bah" Ta b'ata fuska tare da juyawa tana kallan wani gefen, cikin shagwab'a tace "Nidai zamu b'ata idan kana wannan maganan. Kaddara ce haka Allah yaso" Ya sake rungumeta yana mai tsananin farinciki. Kula ya soma bata na musamman, shi da kansa yake jinyar abarsa, cikin kwana uku aka sallamesu Ram ya d'aukesu suka dawo gida. Direct Part d'insu sukayi yana d'auke da ita, Palour ya ajeta ya shiga d'akinta ya gyara tsaf sannan ya d'auketa ya kaita sai turo baki take wai ita ya barta tayi tafiya da kanta. Ya direta kan gado tana cigaba da turo baki "Zaki fara koh" Ta sake zumb'uro baki, bata ankara ba taji bakinsa cikin nata sam batayi yunk'urin hanasa ba dan ita kanta tayi missing d'insa alot. Sun dad'e a haka ganin yana neman wuce gona da iri yasa ta janye jikinta ta mike tana turo baki ta shiga toilet. Saida ta wanke toilet d'in sannan tayi wankan ta fito, kishingid'e ta samesa kan gado idanunsa a lumshe fuskarsa d'auke da murmushi. Itama murmushin tayi "Kaje kayi wanka sai ka huta" Yad'an bud'e idonsa ya zubasu akanta, ya mik'a mata hannu "Zo kiji na fad'a miki" Ba musu ta k'arasa inda yake ya janyota ta fad'a jikinsa, juyata yayi ta koma k'asa ya mata runfa da kafadarsa. Ba tare da b'ata lokaci ba yakai bakinsa kan nata, Soyaiya ya shiga nuna mata mai wuyar fassara kuma da alama tana karb'ar karatun nasa. Jin yanaso ya tsallaka yasa ta saki kuka tana turesa "Dan Allah ka daina" Ya d'ago idanunsa da suka rune "Pls Wife" Ta k'ara turasa tana cigaba da kuka shagwab'a "Nidai Aa" Baice mata komai bah ya cigaba da abinda yake, kuka ta cigaba da rera masa a wajan kunnensa, chan dabara ta fad'o mata ta turesa tana cewa "Dan Allah ka bari, kaje kayi wanka" Ya d'ago jajayen idanunsa tare da shinshina Armpit d'insa "Ina tsami koh?" Ta d'anyi murmushi tana turo baki "Bafa haka nace bah, ni dai kaje kayi ka dawo" Ba musu ya mik'e rik'e da maransa yana cije lab'e "Ki jira dawowana" Ya fita daga d'akin tana tafiya a hankali, tana ganin ya fita tayi saurin mik'ewa ta d'aura towel ta kulle d'akin da key tana dariyar k'eta. A falo ya tarar da Mabrookah wacce tun shigowan su ta shigo side d'in ta zauna tana jiranshi, duk tayi tsuru tsuru ta rame ko saboda meye oho. Sam baima lura da itaba, tana ganinsa ta tashi da gudu ta fad'a jikinsa tare da fashewa da kuka "Ya Jamal ina kuka shiga? Kun barni ni kad...." Tureta yayi dasauri ta d'ago tana kallansa da Mamaki. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:19 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 83 n 84 Tureta yayi dasauri ta d'ago tana kallansa da Mamaki "Karki kuskura ki k'ara tab'ani" Tsagaita kukan datake tana kallansa da mamaki. Ya nunata da yatsa "Kin bani mamaki Mabrookah, harda ke za'a had'a baki a cuceni" Ta fashe da kuka tana kallansa "Ni abinda kukamin banyi k'orafi ba saikai ne zakay..." Ya d'auketa da wani kyakyyawan mari, ta sake fashewa da kuka "Wallahi bazan yarda bah, kutafi ku barni a gida ni kad'ai sannan yanzu kazo kayita dukana" Ransa idan yayi dubu ya b'aci, d'akinsa ya nufa yana huci da alama ransa ya matuk'ar b'aci. Batsa batsa yaga d'akin kamar yanda yabarshi rannan. Ya k'arasa jiki a sanyaye ya soma tattara kayan wajan, tsaf ya gyara komai sannan ya shiga wanka. Ganin ya shige d'aki yasa Mabrookah fashewa da kuka ta sauka k'asa zuwa nata d'akin. Jamal bai fito ba sai dayaji ana kiraye kirayen sallahn Magrib, ya fita ya tafi masallaci, bai dawo ba saida akayi isha'i. Falon k'asa ya tarar da Mabrookah zaune taci kwalliya cikin atampha riga da skirt, kallo d'aya ya mata ya kauda kai. Idanunta ya ciko da kwalla ta mik'e dasauri tasha gabansa, rai b'ace yace "Matsa ki bani waje" Ta matso inda yake yyi saurin matsawa, ta sake matsowa ya k'ara had'e rai "Kinaso ki kaini bango Mabrookah, ki matsamin na wuce" Ta fashe da kuka ta tsugunna guiwa biyu a k'asa "Wallahi Ina sanka Ya Jamal, ban tab'a san wani a duniya ba inba kai bah, kaji tausayina" Ya d'aga mata hannu alamar dakatarwa "Kina sona kika bari aka had'a baki dake aka cutar dani? Menai muku a rayuwa Mabrookah" Ta sake fashewa da kuka "Ni ban gane abinda kake nufi bah, wallahi babu wanda na had'a baki dashi dan a maka wani abu. Ka yarda dani Ya Jamal" Kallanta ya tsaya yi na y'an mintina, batare da yace komai ba ya haura sama. Direct d'akin Ummy ya shiga, yana murd'awa yaji ya bud'e, mamaki ne ya kamasa dan d'azu yanaji sanda ta rufe da key. Kakarin Amanta yaji daga toilet ya k'arasa dasauri cikin toilet d'in ta rik'eta harta gama. Sannu ya dunga mata tana gyad'a masa kai tana hawaye. Laulayin Ummy ne ya dawo sabo, haka suka shafe kwana biyu kullum cikin amai da zazzab'i Cikin kwanakin sunyi zarya a asibiti, abubuwa ne suka taru suka masa yawa, ga Halinda Wife d'insa ke ciki, ga bak'in cikin abinda su Mami suka masa. Ga kuma Mabrookah wacce yanzu ya gama yarda batasan Plan d'in da su Mami sukayi bah, hasalima kullum saita tasashi a gaba tayi ta masa kuka na rashin Mami da Aunty Faty, daga shi har Ummy babu wanda ya iya fad'a masa abinda ya faru. Yau Sunday babu laifi Ummy tad'anji kwarin jikinta, da kanta ta tashi ta had'a musu breakfast, yana fitowa wanka wayansa ya soma ringing, ganin Numbern Ram yasa ya d'auka had'e da sallama, daga chan b'angaren Ram ya sanar dashi yana san ganinsa Shi da Ummy harda Mabrookah dan akwai tambayoyin dayakeso ya musu dan washe gari za'a shiga court. Jim Jamal yayi har Ram yayi tunanin baijishi bah, saida ya kira sunansa sannan ya sauke ajiyar zuciya yace "Ram Mabrookah batasan abinda ke faruwa bah, bansan ta yanda zan fad'a mata bah. And kuma akwai abinda nakeso ku sani" Ram yayi jim sannan yace "Ok to ka bari ina nan zuwa anjima sai muyi maganar gaba d'aya" "Tho" kawai yace ya kashe kiran. Cikin 'yan mintina ya gama shiryawa ya fito falo, dai dai lokacin Ummy ta fito daga kicin da Mugs a hannunta, amsa yayi dasauri "Haba Wife banace ki daina aiki bah, banaso ki wahalar min da baby nah" Tayi dariya tace "Banaso Daddyn Bbyn ya zauna da yunwa, kaga fah tun bayan faruwan abubuwan nan baka wani ci abincin kirki bah" Harya bud'e baki zaiyi magana, tasa yatsanta a lips d'insa "Shhhhh...!" Ta kama hannunsa har zuwa dinning d'in ta zaunar dashi kan kujera, babu surutu kayi breakfast kawai, har zata bud'e Warmern dake gabanta ta dakata tana kallansa "Na manta ban kira K'anwata bah" Yayi murmushi mai k'ara masa kyau "K'anwa!" Ya maimaita, ta hararesa da wasa "K'anwata mana ko ka manta nice ta farko" Dariya yad'anyi mai sauti sannan ya mik'e ya sauka zuwa d'akin Mabrookah, kan gadonta ya sameta ta kwanta ruf da ciki tana kuka a hankali, ya k'arasa dasauri ya d'agota dan yanzu tausayi take basa "Haba k'anwata kukan nan kuma na menene" Ta k'ankamesa ta sake fashewa da kuka "Kullum idan na kira wayan Mummy da Mami bana samu, hankalina yak'i kwanciya ji nake kamar wani abu ya faru dasu" Yad'anyi jim sannan ya d'ago kanta "Nasan inda suke" Da mamaki ta zaro idanunta da suka rune zuwa ja suka kumbura "Dan Allah dagaske ya Jamal" Ya gyad'a mata kai da d'an murmushi "Sosai mah, anma bazan fad'a miki ba sai kin hau sama munci abinci" Ta b'ata fuska a shagwab'e "Nidai banajin yunwa, dan Allah ka fad'amin kaji" Yanda ta langwab'ar dakai ta sake basa tausayi, ya d'agata zaune ya mik'e tare da kama hannunta "I promise uh indai kikaci abinci zan fad'a miki" Ba musu ta mik'e tana turo baki suka haura sama, kan dinning suka samu Ummyn tana jiransu, Mabrookah na ganinta ta sake mak'ale Jamal d'in sai wani zumb'ure zumb'ure take, yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna yana kallan Wife d'insa dake ta murmushi wanda ita kad'ai tasan dalilinsa "Wife serve us please" Ba musu ta mik'e tayi serving d'insu soyaiyar d'ankali da plantain da kuma kwai, shi ya had'a ma Mabrookahn tea. Itadai Ummy binsu kawai take da ido, Lipton kawai ta had'a dan shi kad'ai yanzu take iya sha. Mabrookah sai kaud'i take tana wani shagwab'a, Ummy sai kallanta take tana murmushi, tana gamawa ta mik'e tabar Falon ya bita da ido ganin yanda fuskanta ya sauya. Daru sukayi sosai shida Mabrookah dan k'in fad'a mata yayi wai sai anjima, nan ta tasashi a gaba tanata rera masa kuka. Ya dafe kansa cike da tashin hankali, ga Ummy daga gani Ranta ya b'aci, ga Mabrookah ta tasa shi gaba tana kuka. A ransa yace "Kai auren mata biyu beyi bah" A chan police station kuwa Ba'a sha wahala dasu Mami wajan tambaya bah, sun fad'i gaskiya kamar yanda aka buk'ata. Hakan yama Mifzal da Ram dad'i ganin bazasu wahalar da shara'a bah. Yanma lis Ram yazo gidan, a haraban gidan yayi parking ya aika masu gadi su Kira Jamal d'in dan wayansa na hannun 'yan sanda. A tare suka fito shida mai gadin, Jamal ya mik'a masa hannu suka gaisa sannan suka d'unguma zuwa ciki. Mabrookah ya kira sannan ya shiga d'aki ya kira Ummy suka fito tare. Suna zama Mifzal shima ya shigo, duka suka tattaru a falon su Biyar. Jamal ya mik'e ya shiga d'akinsa ya d'auko diaryn Abba ya fito dashi ya mik'ama Ram. Ummy Abduol✍🏻 [4/26, 8:20 AM] ‪+234 706 272 2689‬: 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 85 n 86 Jamal ya mik'e ya shiga d'akinsa ya d'auko diaryn Abba ya fito ya mik'ama Ram "Inaso ka karanta kowa yaji" Ya nuna Mabrookah da Ummy yace "Yakamata su sani a matsayinsu na iyalai na, sannan kuma ku sani dan bani da aminai kamar ku" Jikin Ram yayi sanyi dajin maganan abokin nasa, a hankali ya bud'e diaryn ya k'urama rubutun ido sannan ya soma karantawa a natse. Dukansu saida sukayi mamaki dajin Labarin dake k'unshe cikin diaryn, Ummy ko kuka ta dunga yi na tausayin mijin nata, lallai yanzu take k'ara godema Allah dan duk halin da ta shiga itada iyayenta bai kai wanda Jamal ya fuskanta bah. Mifzal ya dubi Jamal har lokacin fuskansa d'auke da alamar tambaya "Nayi mamaki sosai dajin wannan labarin, Abba da Mami dama basu suka haifeka bah" Ya gyad'a kai idanunsa cike da kwalla, yace "No Wonder ita da Yayarta suke san kasheka dan suci dukiyarka" Mabrookah ta kalli Mifzal da alamar tambaya "Bangane me kake nufi bah" Mifzal ya juya ya kalleta dakyau dan dama haushinta yakeji "Da uwarki da k'anwanta Mami suka had'a baki suka kashe Abba, sannan...." "What!" Ta mik'e dasauri ko ina na jikinta na rawa, ta fashe da kuka tare da juyawa tana kallan Jamal "Ya Jamal kanajin abinda yake fad'a? Tayaya Mummy na da Mami zasu kashe Abba me yayi musu" Ta kuma fashewa da kuka, Ram ya d'anyi gyaran murya yace "Abinda Mifzal ya fad'a gaskiya neh" Ta d'ago dasauri ta kallesa ya gyad'a mata kai "Yanzu haka suna police station a tsare kuma gobe za'a shiga court" Basu ankara ba ta sulale k'asa ta sume, Ummy ta rarrafa dasauri inda take tana kuka, Jamal ya k'araso wajan gaba d'aya hankalinsa a tashe. Ram yace "Ummy samo ruwa yi sauri" Ta mik'e ta shiga kicin dasauri ta d'auko ruwa, Tallafo ta Jamal yayi ya d'aurata a cinyarsa Ram ya yayyafa mata ruwa, ta sauke ajiyar zuciya a hankali, wani kukan ta kuma fashewa dashi tana girgiza kai "Mummy na da Mami bazasu tab'a iya kashe Abba bah" Ta bud'e ido a hankali ta rik'e hannun Jamal "Dan Allah Ya Jamal kace min Mafarki nake" Rungumeta yayi yana shafa kanta duk da shima hankalinsa a tashen yake "Its ok, ya isa kibar kukan." Ya mik'ar da ita tsaye ya kama hannunta tana kuka suka sauka k'asa, d'akinta ya kaita ya kwantar da ita tare da lallasheta. Bai fito d'akin ba saida tayi shiru anma zuciyarta cike yake da bak'in ciki da takaicin abinda taji daga bakin Mifzal. Koda ya koma Falon yanda ya barsu haka ya dawo ya samesu, sai Ummy dake gefe tanata jan majina tana sharan k'walla jefi jefi. Ya k'arasa ya xauna kusa da ita tare da rik'o hannunta yana murzawa a hankali. Ram yace "Menene Abinyi yanzu? Akwai abubuwa sosai a gabanmu, na d'aya Court d'in da zamu shiga gobe, na biyu neman Parent d'inka" Jamal yayi shiru baice komai bah, Mifzal yace "Gaskiya ne wannan, anma a bari sai an gama case d'in nan sannan sai mu soma binciken real parent d'inka" Cikin sanyin murya Ram yace "Kayi hak'uri Friend, kad'au duk abinda ya faru a matsayin Jarabawa, Haka Allah yaso, Haka yaso ka kasance. Allah ya baka ikon cin wannan Jarabawar" Ya amsa da Ameen Hawaye na gangara daga idonsa "Har gobe Inasan Mami banasan wani abu ya sameta, ko ba komai Uwace min dan bata rageni wajan Tarbiya da neman Ilimi bah" Mifzal yayi ajiyar zuciya yace "Hakaneh, babban tashin hankalina ma shine idan aka shiga court, Allah kad'ai yasan hukuncin da za'a yanke musu. Kasan sharri'a sab'anin hankali ce" Kuka Ummy keyi sosai daga zaunen datake, wani amai ya taso mata ta mik'e dasauri tayi d'akinta, Jamal ma ya mik'e zaibi bayanta, Mifzal na ganin haka ya mik'e yana gyara rigan jikinsa "Mu zamu wuce, Pls gobe k'arfe Tara na safe za'a shiga Court, make sure kin iso kamin lokacin" Kai kawai ya iya gyad'a musu ta bi bayanta dasauri. Amai sosai ya sameta tanayi, duk abinda tashi saida ya fito, kuka take sosai tana maida numfashi ya k'arasa ya rungumeta ta baya yana mata sannu. Saida ta gama sannan ya saketa ya d'auraye mata baki ya maidota d'aki. Ya d'aurata kan gado ya k'ara rungumeta tare da lumshe ido. Bashi da wani gata yanzu daya wuce Wife d'insa, duk sanda suke tare sai yaji damuwarsa ya yaye, Maraicinsa ya gushe. Ya k'ara mak'alkaleta itama ta rungumesa murya chan ciki ciki tace "Ya Jamal rayuwarka darasi ne da kuma ishara ga duk wanda ya jita, nasha wahala sosai a rayuwa ni da Iyayena tunda Mahaifina ya soma rashin lafiya, danaga Rayuwarka na kuma ji labarinka sai nake ganin namu ba komai baneh. Tabbas Rayuwar daka tsinta kanka a ciki Jarabawa ce daga ubangiji, kayi hak'uri sannan ka maida lamuranka ga Allah" Ta k'ara rungumesa tace "Kada ka k'ara tunanin bakada kowa, Am here for you, zan zame maka Uwa, uba dangin daka rasa" Ya fashe da kuka yana rungume da ita "Thank uh Jaleelah, Allah ya miki Albarka" Janye jikinta tayi daga nasa ta d'ago fuskanshi dake ta zubar da k'walla "Shhhh! Ka daina kuka dan Allah, ko kanaso nima nayi?" Ya girgiza mata kai yana kallan kwayan idanunta dake cike da k'walla Ta rik'o hannunsa tasa a maranta tana kallansa "Ni da Babyn mu muna tare dakai" Ta k'are maganan tana kuka a hankali, ya rungumeta tsam a jikinsa yana lallashinta. Ta shagwab'e fuska tace "Pls Ya Jamal inaso inje inga Mama, rabona dana ganta wata d'aya kenan kuma nasan itama tanasan ganina kawaici ne ya hanata zuwa" Ta k'are maganan tana zumb'ura baki, ya ja bakin ta saki k'ara k'adan. Murmushi yayi yace "Ba yanzu bah, ni nama manta jiya danaje tace na gaishe ki" Ta kallesa da mamaki, ya kashe mata ido d'aya ya mik'e ya fita, chan sai gashi da wani bak'in leda ya mik'a mata yace "Tace na baki" Jiki na rawa ta amsa ta bud'e, kayan k'amshi ta gani da sinadaran girki kala kala, sai wani leda kuma dake ciki shima ta bud'e, magunguna ta gani ko ba'a fad'a mata ba tasan na menene, tad'anyi murmushi tana cigaba da kallan cikin ledan. Karo sukayi ta d'ago tana kallansa tare da rufe ledan "Meye kake kallan min sirri" Ta murgud'a baki tana k'ara b'oye ledan a bayanta, yayi dariya ya k'ara matsowa "Idan abin ci ne to a raba aba kowa nasa dan bazan yarda bah" Hararan wasa ta masa "Bayan ka riga ka bud'e ka d'auka" Ya d'aga hannu dasauri kamar criminal "Babu ruwana, yanda ta bani haka na d'auko na aje, duk ke kika mantar dani jiya da nabaki da wuri" Ta sake turo baki "Dan Allah Ya Jamal ka kaini" Ya mak'e kafad'a yana kwaikwayan irin magananta "Aa nak'iya" Takai mai dukan wasa ya rik'e hannun ta saki kukan shagwab'a, kwantar da ita yayi kan gadon ya soma lallubenta, ina ganin haka na tattara nabar musu d'akin. K'arfe takwas da rabi na dare ya fito daga masallaci bayan yayi sallahn isha'i, side d'insu ya shiga dasauri dan so yake ya fita, Mabrookah ya samu a falonta tsaye duk tayi wani laushi, rana d'aya harta fad'a, ya k'arasa kusada ita dan yanzu tausayi take basa ya kama hannunta yad'an matse ta lumshe ido wasu sabin hawaye suka gangaro mata "Haba k'anwata, banace ki daina kukan nan bah" Ta bud'e idanunta a hankali tana kallansa "Bazan iya daina kuka na ya Jamal har sai naje naga Mummy da Mami, dan Allah ka kaini wajansu" Yad'anyi jim yana kallanta, shima chan d'in yakeso yaje kafin gobe a shiga court yaji yanda za'ayi, dan har a zuciyarsa baisan wani abu ya samesu, ko ba komai Mami tamkar mahaifiya take a garesa, sannan Aunty Faty surikarsa ce. Maganan datayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, ya d'ago yana mata murmushi, "Ki bari komai will be fine insha Allah" Ta girgiza masa kai tana cigaba da kuka "Aa pls, dan Allah Ya Jamal" Ya k'are maganan da matsanancin kuka, ya d'ago kanta yana share mata hawaye "Stop crying" "Dan Allah zanje na gansu" Ya sassauta rik'on daya maya mata yace "Jeki shirya" Dasauri ta shiga d'akinta ya bita da kallo tare da sauke ajiyar zuciya. Sama ya haura ya shiga d'akinsa ya sauya zuwa kaftan ya fito ya shiga d'akin Ummy, ta gama shiryawa kenan cikin doguwar rigar Atampha tana murza powder a fuska ya shigo, wajan mirrown ya k'arasa ya sak'ala hannunsa a wuyanta "Kinyi kyau sosai Wife" Tayi murmushi tana kallansa ta mirrown "Ya Jamal ina zaka?" Ya sunkuyo da fuskansa kusada nata yace "Ko kin fasa zuwa wajan Maman neh" Ai dasauri ta mik'e har tana kokarin turesa ta d'auko Hijab sai dariya yake mata, hannunta ya kama suka fito, a falon k'asa suka samu Mabrookah itama ta shirya, Tana ganinsu tare taja guntun tsaki tayi gaba suna binta a baya, tun daga k'ofar falonsu ya danna button d'in security motar ta k'arasa ta bud'e dasauri ta shige gaba. Sam Ummy bata nuna damuwa ba ta bud'e baya ta shiga yaja suka bar cikin gidan. Jefi jefi shida Ummyn suke hira har suka k'arasa kofar gidansu Ummyn, ta bud'e dasauri ta fita, ganin bai fitoba yasa ta juya tana kallansa "Ka shigo mana" Yad'an kalli Mabrookah dake gefensa tana cika tana batsewa yace "Zamu d'an fita ne idan zan biyo na d'aukeki sai na shiga mu gaisa" Batace masa komai ba ta juya ta shiga cikin gidan rai b'ace. Police station d'in suka nufa, sunyi sa'a sun samu Mifzal bai riga ya tafi bah. Jamal na masa bayani ba b'ata lokaci yasa wani daga cikin 'yan sandan ya fito dasu zuwa secret room. Mifzal da kansa ya musu jagora zuwa d'akin, Kallo d'aya Mabrookah ta musu ta fashe da kuka ta k'arasa inda suke zazzaune, Mami nakan wheel chair duk sun rame kamar basu bah. Ta tsugunna gabasu tana kuka tana kallansu "Mummy, Mami meyasa kukayi haka? Meyasa kuka bari shed'an yaci galaba akan ku" Barin musu wajan Mifzal yayi, Jamal na bakin k'ofa yana hawaye, kallan Mami yake tayi ganin yanda k'afanta ke nannad'e da bandage sai zuban ruwa yake yana wani irin k'arni. Daga Mami har Aunty Faty kasa magana sukayi sai bin Mabrookahn suke da kallo, A hankali Jamal ya soma takawa zuwa wajan, Mami da d'ago ad'an tsorace tana kallansa, ya tsugunna guiwa biyu gabanta ya kama k'afarta dabaida ciwo yana kallan fuskanta hawaye na zuba a idanunsa. Tayi saurin kauda fuska ta fashe da kuka, ya d'ago yace "Har gobe Mami ke uwace a gareni, har yanzu matsayinki a rayuwata yana nan bai chanza bah, duk abinda kikamin na yafe miki Mamina" Ta janye k'afanta daya rik'e tana cigaba da kuka "Rud'in duniya da bin zugan shaid'an su suka jamin na shiga wannan halin, ka gafarce ni D..." Yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai. Kasa magana Mabrookah tayi sai kuka datake kamar ranta zai fita. Mifzal ya shigo ya fad'a musu lokaci yayi, hakanan sunaji suna gani suka bar wajan suna kuka suna waiwayen su Mamin. Ransu duk ba dad'i suka shiga mota suka bar station d'in, saida ya tsaya ya d'au Ummy daketa cika tana batsewa sannan suka nufi gida. Daru suka sha daren ranar shida Ummyn dan sosai ranta ya b'aci na barinta dayayi suka wuce. Washe gari ranar da za'a shiga Court, da wuri ya tashi ya shirya saidai Yau Wife d'insa ta tashi da zazzab'i, dole saida ya tsaya ta shirya sannan suka sauko yana rik'e da ita dan jiri take gani, Mabrookah suka samu a falo ta shirya tana zaune tana jiransu lokacin k'arfe takwas da rabi. Shi da kansa ya bud'e ma Ummy mota ta shiga gaba, Mabrookah ta turo baki ta shiga baya suka d'au hanya. Tara daidai duka isa Court d'in, sun samu mutane duk sun hallara, bayan zazzauna aka soma gabatar da k'aran da Areef d'an Alhaji Ameenu ya kawo akan abi ma Mahaifinsa hak'insa, bada umarnin a kawo Alhaji Ameenun Alk'alin yayi, nan wani d'an sanda ya shigo da Alhajin da Bilal, Ummy dake rakub'e jikin Jamal saboda sanyin datake ji ta zaro ido tare da d'agowa tana kallan Bilal wanda duk ya rame kamar bashi bah. Gaban Jamal ya fad'i sanda ya d'ago ya kalli Alhaji Ameenu, Ummy ko Areef ta k'urama ido sannan ta juya ta kalli Jamal wanda har lokacin Alhaji Ameenu yake kallo. K'ara aka karanto sannan aka umarci Mifzal ya tashi yayi bayani, bayan ya gama Lawyern Alhaji Ameenu wanda d'ansa Areef ya samo masa yayi k'orafi tare da rok'on kotu tabi ma Alhaji Ameenu kadinsa na cin zarafi da aka masa. *A gurguje* Nan kotu tabada umarnin a saki Alhaji Ameenu da Bilal, Ummy dake gefe ta kalli Jamal murya chan k'asa saboda yanda take jin jikinta tace "Ya Jamal kaga wani mai kama dakai" Ya juyaga Areef yana kallansa shima da Mamaki har lokacin gabansa bai daina bugawa bah. Su Mami aka shigo dasu, Ram wanda shine Lawyern Jamal ya mik'e ya soma Jawabi, kasancewar su Mami basu da Lawyer sannan basuyi musu akan laifin da ake tuhumar su ba yasa shari'an baid'au dogon lokaci bah. Mabrookah dake gefe sai kuka take jin Abubuwan da su Mami suka aikata. An d'aga shari'a sai bayan kwana uku sannan a dawo dan Sauraran hukuncin da Za'a yanke ma su Mamin. Mabrookah ta fashe da kuka haka Ummy, Jamal ko hankalinsa ne ya tashi yabar Court d'in dasauri, Mifzal yabi dake k'okarin shiga mota "Mifzal ya duba dan Allah, kada a yanke ma su Mami hukunc...." Mifzal yayi saurin katseshi da cewa "Kana bani mamaki Jamal, matarda batada nufi na alheri a gareka anma kabi ka d'aga hankalinka akanta" Ran Jamal ya b'aci "Wanne irin magana kakeyi Mifzal, kasa...." Mifzal ya shiga mota yaja yabar Haraban Court d'in ransa shima a b'ace. Juyawa yayi a sanyaye ya nufi wajan motansa, yana danna security Mabrookah dake kuka ta bangaje Ummy ta shiga gaba ta zauna. Ummy ta bita da kallo cike da takaici. Har suka isa gida babu wanda yace k'ala, Yana Parking ya fito ya shiga side d'insu daga Ummy har Mabrookah binshi sukayi da kallo. D'akinsa ya shiga ya fad'a kan gado ta fashe da matsanancin kuka kamar k'aramin yaro. Koda Ummy ta haura sama kamar ta shiga d'akinsa sai kuma ta fasa tunawa da tayi itama fushi take. Ya dad'e yana kuka har tsawon wani lokaci, saida yayi mai isarsa sannan yayi shiru ya mik'e ya shiga toilet yayo alwala. Yana fitowa Ya kalli akwatin da ya d'auko ranar daga gidan, sai kallan Akwatin yake ko k'iftawa bayayi, nan ya tuna cewa shine akwatin da Abba ya rubuta masa cewa duk abinda yake san sani game dashi zai samu ciki. Batare da wani b'ata lokaci ba ya janyo jakan ya bud'e a hankali gabansa na fad'uwa. Showel yaci karo dashi da wani overall duk sunyi k'ura, ya d'agasu zai duba sauran abubuwan dake ciki, wasu hotuna nr suka zubo ya sunkuya ya d'auka yana kallo. "Innalillahi wa inna illaihi raj'iun" Shine kalmar daya fad'a yana zare ido duk ilahirin jikinsa na rawa. _Gaisuwa ta musamman ga Jamaludeen Maher_ Ina yinka irin sosai d'in nan. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Wannan shafin Tukuici ce ga *Real Jamaludeen* Ina godiya sosai da bani goyon baya dakake yi, Thank uh so Much Bro Page 87 "Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun" Shine kalmar daya fad'a yana zare ido duk ilahirin jikinsa na rawa. Wayansa ya d'auka cikin yanayi na tashin hankali ya soma neman layin Mifzal, saida ya kirasa kusan sau hud'u sannan ya d'auka, dan yayi tunanin zai kirasa ne akan maganan su Mami, cikin muryan kuka Jamal yace "Dan Allah kada ka bari Alhaji Ameenu ya tafi" "Saboda meh" cewar Jamal, Hankali tashe yace "Just do what i said, gani nan zuwa ka jirani a Station" Muryansa ya sake rauni, "Dan Allah karka bari su tafi" Mifzal baice masa komai ba ya kashe kiran sannan ya juya hancin motarsa ya koma Court, bai samesu ba sai 'yan tsurarun motane dake wajan da wasu 'yan sanda, tambayansu yayi a nan d'aya daga cikinsu yake shaida masa yaji suna cewa zasu je Hospital a duba lafiyarsu Alhajin. Jamal kuwa gaba d'aya ya rikice, kaya ya saka ya kinkimi akwatin daya ciro hotunan ya fito, Ummy dake falo ta bisa da kallo da mamaki, ko kallanta baiyi ba ya sauka k'asa yasa kayan cikin mota ya figa a guje yabar gidan. Mifzal ya sake kira ya shaida masa yana Court, direct chan yayi har lokacin hawaye bai daina zuwa daga idonsa bah. Yana isa yayi parking ya fito dasauri "Ka gansu?" Ya girgiza masa kai alamar Aa, Cikin wani irin yanayi Jamal yace "Dole muje Abuja ayau d'in nan Mifzal" Ya kallesa da mamaki, har zai tambayesa dalili sai kuma ya fasa yace "Suna cikin Zaria dan yanzu na tambaya aka shaida min anji suna cewa zasu Asibiti" Jamal najin haka yace "Wat are we waiting for? Mu tafi kawai" Mifzal ya zafga masa harara "Aina zamu fara nemansu" Dai dai nan Ram ya k'araso wajan dan tun d'azu yana cikin Court d'in, Mifzal ne ya masa bayani, Ram yace "Nemansu Abu ne mai sauk'i, na lura d'ansa yanada san asani da kuma nuna isa, Zai iya yuwuwa ABUTH sukaje" Mifzal yayi saurin cewa "Yes u're right" Duk a motar Jamal suka had'u suka d'unguma zuwa asibitin, cikin sa'a suna Parking suka hango su Alhajin sun fito daga asibitin harda Bilal, Jamal ya fita daga motan dasauri ya k'arasa inda suke, "Dan Allah ku tsaya" Dukansu suka juyo suna kallansa, Gaban Alhaji ne ya fad'i ya k'urama Jamal Ido, haka itama Matarsa sai kallansa take ko k'iftawa batayi ga gabanta daketa fad'uwa. Areef d'in Alhaji Ameenu ya juyo a fusace yana kallansa, "Waye kai?, me kakeso" Daidai lokacin Ram da Mifzal suka k'araso wajan, Nan da nan Alhaji Ameenu ya had'e rai haka d'ansa Areef, Areef yana kallansu Mifzal yace "Wai me kukeso damu neh? Inace shari'ar ta k'are? Ko kunzo ne wannan karan ku kamamu duka" Yana maganan yana tada jijiyoyin wuya ransa a b'ace "Na k'yalleku ne kawai saboda Abbana ya hanani d'aukaka k'ara, Ashe haka zama Nigeria yake" Ram ya katsesa da cewa "Babu abinda ya kawo mu, kuma dakake maganar zaman Nigeria, ai babu inda yakaita dad'i ma dan Asalin k'asar. Dan a nan ne kad'ai yake da 'yancin yayi duk abinda yakeso" Jamal yayi saurin d'agama Ram Hannu Alamar yayi shiru, Alhaji Ameenu yace "Ku fad'a mana abinda ke tafe daku dan sauri muke" Jamal ya tsugunna guiwa biyu a k'asa, gaba d'ayansu binshi sukayi da kallo bama kamar Bilal dake gefe yana muzurai, "Sunana Jamaludeen, ku...." Alhaji Ameenu yayi saurin nuna Jamal da yatsa yana cewa "Dama kaine Jamaludeen d"in da ake fad'a?" Ammi dake gefe tace "Shine yayi causing all this Problems" Har Areef ya bud'e baki zaiyi magana Alhaji yayi saurin d'aga masa hannu sannan ya maida dubansa ga Jamal yana cewa "Tunda nake ba'a tab'a cin mutuncina kamar yanda kasa akamin bah" Jamal ya fashe da kuka daga tsugunan dayake, Mifzal sai hararansa yake kamar ya mangaresa. "Abbana ka gafarceni, kayi hak'uri" "Waye Abban naka?" Cewar Areef a fusace Ya d'ago fuska yana kallan Ammi wacce itama tun d'azu shi take kallo "Ammi meyasa kuka kasa rik'eni, kuka zab'i yardani" Babu wanda bai razana a wajan bah, Lokaci d'aya Ammi ta fashe da kuka tana kallan Jamal d'in, Shi kansa Alhaju Ameenun Yanayin fuskansa ne ya sauya, anma ya dake yace l "Wani irin magana kakeyi neh?, me kake nufi" Ammi tayi saurin cewa "Areef kaine?" Areef ya zaro ido yana kallan Ammi da mamaki, Ram wanda ya gane inda maganar tasu ta dosa ya k'araso yana cewa "Wannan maganan ba'a nan yakamat ayita bah, ya kamata a natsa sai a zauna a tattauna" Ya mik'ar da Jamal tsaye, Mifzal yace "Alhaji ku shiga mota kubi bayanmu muje a tattauna a gida" Ba musu suka shishiga mota Jamal ya shiga nasa motan, Ram ne ke driving har zuwa gidansu Jamal. Suna isa Jamal ya musu Jagora zuwa side d'in Abba. Bayan an zazzauna ya koma cikin mota ya d'auko akwatin nan ya shigo dashi d'akin, Ammi na gani ta mik'e tsaye dasauri tana bin akwatin da kallo. Haka shima Alhaji zazzare ido yayi yana kallan akwatin, Areef da Bilal da kuma su Mifzal gaba d'aya bin su Abban suke da kallon Mamaki, Alhaji yayi k'arfin halin cewa "Ina ka samu akwatin nan" Jamal bai b'oye musu komai ba dangane ga abinda ya sani, Ammi ta fashe da kuka tana cewa "Na dad'e ina burin ganin wannan ranar gashi Allah ya kawoshi" Areef ya kalleta da Mamaki "Ammi kun sakani a duhu meke faruwa neh" Alhaji wanda shima k'walla ke zuba a idonsa yace yana nuna Jamal "Wannan yayanka neh, mu muka haifesa, sunansa kaci bayan mun rasa shi da muka haifeka muka maida maka da sunansa" Jamal dake gefe shima yana hawaye yace "Ammi meyasa kuka yar dani, baku damu da halin dazan shiga bah, baku damu da mai zai iya samu na a daran da kuka yardani bah" Ya fashe da kuka sannan ya cigaba da cewa "Ance tsakanin d'a da uwa akwai wata irin shak'uwa mai tsanani, meyasa Ammi kika yarda aka yardani, kuma baku k'ara waiwayan halinda zan shiga bah" Abba ya girgiza kai yana share hawayen dake gangaro masa "Ba laifin mu baneh Areef, ba laifin mu baneh" Haryanzu binsu da kallo Areef keyi cike da mamaki da kuma kokwanto, Alhaji ya soma magana cikin raunin murya "Sunana Alhaji Ameenu Jibril, ni haifafen Garin karaye ne dake Kano. Na taso cikin gata na iyaye kasancewar mahaifina hamshak'in attajiri ne a wanchan lokacin, nayi ilimin Addini dana boko sosai, ana haka iyayena suka rasu duka, hakan yasa na dawo garin kaduna da zama, inda na had'u da Hajiya zainab na aureta, cikin ikon Allah na fara sana'ar saida gwal da taimakon wani ubangidana danayi zuwana Kaduna" Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "Harkokin kasuwanci ya cigaba da bud'ewa, ina samun Alkahiri da dama haka ina samun cigaba a harkata, har nakaiga inacin gashin kaina nima inada yara, tunda sauran mutanen da muka fara sana'ar tare sukaga haka suka soma mini bak'in ciki, a haka na cigaba da sana'ata, na tara k'addara masu yawa, na gina gida na gani na fad'a. Ana haka matata ta haifeka inda muka saka maka suna Areef" Areef dake gefe ya zaro ido yana kallan Alhajin, Bilal ko k'uri ya musu shida Jamal tabbas ga kama nan da sukeyi da juna, haka kuma suna yanayi da Alhajin, ya cigaba da cewa "Ina sanka Areef fiyeda yanda nakesan kaina, dan kai ka zamo mini a matsayin 'yan uwana dana rasa, duk wani kula da jin dad'i nida matata munayi maka, ana haka wata rana da daddare wuraren k'arfe biyu na dare, mukajiyo shigowan b'arayi gidan, Sosai mukaji tsoro, Matata banda kuka babu abinda take, sunyi sunyi na bud'e k'ofa nak'i, a nan suke shaida min ba kud'i suke nema ba raina dana Matata dana d"ana suke nema, inajin mata jikina dana matata ya soma rawa, da kaina na sakaka a akwati na saka dukiya mai yawa a ciki, na mik'ama matata nace su gudu, ta k'ofar baya suka gudu ni kuma na sadak'ar nazo na bud'e musu k'ofan. Ganin ba iyalina yasa ransu ya b'aci suka sakar min harbi Allah ya taimakeni a Hannu neh, suna ganin na fad'i sukayi tafiyarsu" Ammi na kuka ta d'aura da cewa "Mun fita nayita gudu ina kuka, har Allah ya had'ani da wani mai mota inda ya sanar dani Zaria yayi, ba yanda na iya hakanan na bisa ya saukeni a wani anguwa nayi ta masa godiya dan bai amsa ko sisina bah, haka na kwana a wajan wani bola har washe gari da safe, na yini banci komai bah, da daddare yunwa ya addabeni dole na maidakai cikin akwatin dan bazan iya d'aukanka saboda jikina daba k'arfi, a nan na barka na tafi neman abinci, kafin na dawo an d'aukeka a wajan" Ta k'are maganan cikin kuka, Ram dake gefe yace "To ya akayi kuka had'u da mijinki" Ta share hawayen fuskanta tace "Nayi rayuwa a zaria na kusan shekara d'aya inayi ma wata mai abinci bauta, sannan daga baya na koma Kaduna wajan Iyayena inda anan na sake had'uwa da Mijina ashe yanada sauran kwana" Mifzal dake gefe ya tab'e dan gaba d'aya labarin akwai ganganci da rashin dabara a cikinsa. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 88 Mifzal dake gefe ya tab'e baki dan gaba d'aya labarin akwai ganganci da rashin dabara a cikinsa. Alhaji Ameenu ya zamo daga kan kujeran dayake ya xauna a k'asa yana kuka a hankali "Tun dawowar Zainab danaji labarin b'atanka daga wajanta, babu irin kukan da bamuyi bah da nemenka anma babu wani labari, Wallahi Areef dakai kullum nake kwana a raina har Yau, kullum ina addu'ar ganinka dan a kullum inaji a jikina kanada Rai" Ammi cikin kuka tace "Ka gafarce mu Areef sam bamu yarda kai bah" A hankali ya rarrafa shima yana kuka ya rungume Abba yana kuka a hankali "Ka daina kuka Abbana, bakumin komai bah." Ya juya zuwaga Ammi itama ya rungumeta ya saki wani kuka mai sauti tare da ajiyar zuciya, Babu wanda baiyi k'walla a wajan bah, Ya saki Ammi da Abba yayi sujada yana mai godiya ga Allah. Hannu ya bud'ema Areef k'arami ya k'arasa ya rungumesa ya saki kuka yana cewa "I'm so sorry Bro been so Rude" Jamal ya girgiza masa kai yana share masa hawaye "Its Ok" Mifzal yayi gyaran murya yace "To Alhamdulillah Allah muna godiya daka kawomu wannan rana" Ya kalli Jamal yace "Ina tayaka Farinciki da ganin wannan rana, ranar da kaga Iyayenka na asali." Jamal ya mik'e zumbur yace "Ina zuwa pls" Bai jira mai zasuce ba yabar Falon dasauri, side d'inshi ya shiga ya samu Mabrookah zaune ta zabga tagumi, ya k'arasa tare da kamo hannunta, firgigit tayi ta d'ago tana kallansa, murmushi ya mata itama ta mayar masa "D'auko Hijabinki ina zuwa" Ya haura dasauri zuwa sama, d'aki ya samu Ummy tana bacci wanda yanzu ya zaman mata k'aida kullum da rana sai tayishi, hura mata iska yayi a kunne tare da kai mata kiss a bakinta, tad'an bud'e ido a hankali tana kallansa "Baeby tashi kiji" Ta turo baki ta k'ara lumshe ido "Bacci fa nakeyi" Shima ya shagwab'e fuska yana tura baki "Yanada mahimmanci neh" Dakyar ya lallab'ata ta tashi ya d'auko mata hijab tasa suka fito, Mabrookah na nan falonta tana jiranshi, tana ganinsu tare taja tsaki yad'anyi murmushi daidai sanda suka k'arasa saukowa falon k'asan, Hannun Mabrookahn ya rik'e suka fito su duka. Bai sake hannayen nasu ba saida suka kai k'ofar falon Abba, ya shiga da sallama suma suka bi bayansa, Chak Ummy ta tsaya ganin Bilal a falon, Jamal ya janyo hannunta suka k'arasa cikin falon sosai, dukansu a k'asa kan Carpet suka zauna, Cike da girmamawa Ummy ta gaishe su, ganin haka yasa itama Mabrookah gaidasu tana yatsine fuska. Jamal ya nuna Abba da Ammi "Alhamdulillah ku tayani murna naga Parents d'ina" Ummy ta d'ago dasauri cike da fara'a "Dagaske?" Ya gyad'a mata kai yana nuna Abba "Wannan shine Abbana" Ya nuna Ammi sannan ya nuna Areef yana cewa "Wannan kuma k'anina Areef" Kallo d'aya zakama Ummy ka gane tana cikin farinciki, Mabrookah ko sai yatsine yatsine take daga gefe. Ya d'an duk'ar dakai yana sosa k'eya "Ummmm Abba wad'an nan Ummmm Ma..Matana neh" Ammi ta rik'e baki da mamaki "Duka matanka?" Ya sake duk'ar da kai yana murmushi, Albarka Abba ya saka musu sannan yace "Baka fad'a mana meya faru ba bayan rabuwan mu dakai" Nan ya gyara zama ya zaiyane musu komai har zuwa ranar, Ammi kuka take sosai na tausayin d'an nata, Jin gagarumar gudunmawar da Ummy taba d'an nata yasa taji ta shiga ranta sosai. Kallanta kawai take tana zubar da kwalla. Ganin yanda Ammin ke kuka sosai yasa Jamal ya rarrafa ya rungumeta yana shafa bayanta "Its ok Ammina, yau ranar farinciki ne garemu duka" Ta d'ago kanta tana mai zubar da kwalla tana shafa fuskansa "We are so sor..." Yayi saurin sa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai, sosai Suka burge duka mutanen dake falon. Areef dake gefe yayi murmushi yace "Abba Lil sis fah na gida" Abba yace "Hakane" Ya juya ga Jamal yace "Areef nada k'anwa sunanta Areefa" Jamal ya saki lallausan murmushi cike da faribciki yace "Woaw ashe inada k'anni dayawa" Duka falon sukasa dariya, waya Abba ya d'auka ya kira Areefan tana d'auka ta fashe da kuka tana shagwab'an barinta da akayi ita kad'ai, Abba ya soma lallashinta sannan yace gobe tasa driver ya kawota zaria idan suka iso sai ta kirasa. Cikin wani irin ihun murna ta amsa tare da kashe kiran. Har lokacin Ammi bata daina kallan Ummy bah wacce kanta ke k'asa tana ta murmushi, Ram yace "Bilal kayi hak'uri akan abinda ya faru, rashin sani neh" Bilal yayi saurin girgiza kai yana 'yar murmushi "Babu damuwa, rashin sani ne ai" Jamal ya sake bashi hak'uri, nan ma ya nuna babu damuwa. Sannan ya mik'e ya musu sallama dan zaije gida, driver Jamal yasa ya d'aukesa ya kaisa gidan bayan ya masa kyautar kud'i yaki karba. Gaba d'aya Jamal jinsa yake cikin wani irin farinciki, ji yake kamar an d'auke masa kaya. Mifzal da Ram suka musu sallama suma suka tafi, Jamal ya kalli Areef yace "Bro zo ka tayani wani aiki" Ba musu Areef ya mik'e yabi bayansa, Mabrookah na ganin sun fita ta mik'e tana wani cin magani tabar Falon, Ammi ta kalli Ummy tace "Tashi kije abinki Ummy Allah ya miki albarka" Cikin jin kunya ta amsa ta mik'e ta musu sallama cike da girmamawa. Ammi ta kalli Abba bayan Ummyn ta fita tace "Yau na fara ganin yarinyan nan, anma wallhi ta shiga raina sosai" Abba yace "Nima haka wallahi, kum daga gani tanada natsuwa da kamun kai" Ammi ta gyad'a kai tana murmushi. Mabrookah na fita taga Jamal da Areef sun shiga side d'in Mami, harta juya zata koma nasu side d'in sai kuma ta juyo tabi bayansu. Suna shiga Jamal yace "Wannan side d'in Mami ce itada wicked Sistern tah. Inaso ka tayani mu fitarda komai na ciki inaso Ammina ta dawo nan" Karaf a kunnen Mabrookah wacce take k'ofar falon tana kallansu fuska a had'e, ta k'araso ciki dasauri tana huci "Wallahi bazai yuwu ba Ya Jamal, me kake nufi a fitar da kayan Iyayena asa wani" Ya juyo ya kalleta rai b'ace "Saboda masu gidan wanda suke da iko da komai na gidan zasu dawo nan da zama" Areef ya haura sama abinsa yana tab'e baki dan kallo d'aya yama Mabrookah d'azu yaji sam bata masa bah, "Babu wanda ya isa ya fito min da kayan iyayena, kaje ka aro iyaye ka kawo to wallahi bazai yuwu bah, wad'an nan mutanen basu isa su..." Lafiyaiyan mari taji a fuskanta ta d'ago idanunta da sukayi ja tana kallansa da b'acin rai tana nuna kanta da hannu "Ya Jamal ni ka mara akan wad'an nan banz..." Wani marin ya sake d'auketa dashi ta fashe da kuka tana gagaya masa bak'aken maganganu, Areef ne ya sauko d'auke da Manyan Trolleys guda biyu yana jansu da kyar, ta k'arasa ta sauri ta rike akwatunan "Ina zaka kaisu, wallahi karka sake ka fita dasu" Jamal ya kira sunanta cikin kakkausan murya "Ki shiga taitayinki Mabrookah, ina raga miki ne kawai saboda Alk'awarin dana d'aukan ma Abba bazan rabu dake bah. Karki sake ki kaini bango" Areef iyayen k'eta ya d'anyi dariya ya fisge Akwatin yayi waje, ta k'arasa inda Jamal d'in ke tsaye tana kallansa hawaye na fita daga idanunta "Ka cika butulu Jamaludeen, kai butulu neh, ko me Mami da Mommy suka maka bai kamata ka sakamusu da haka bah, Kai butulu ne" "Karki k'ara kirana da butulu" "Na fad'a kai Butul..." Wani irin shak'a yakai mata dan gaba d'aya takaisa bango ta saki k'ara a wahalce idanunta gaba d'aya sun fito, Areef ya shigowa yaga abinda ke faruwa ya fita dasauri zuwa inda su Abba suke ya shaida musu, a tare suka taho dukansu da sauri. Har lokacin Jamal na shake da ita idanunta duk sun bulluk'o tana kakari kamar zata shid'e "Ban kira Mami da Aunty Faty butulu ba saini zaki kira da butulu, sun kashe min Abbana, sunyi k'okarin kashe min Matata dani kaina, duk wad'an nan ba butulci baneh, bariiii" Abba ya shigo falon tare da kiran sunan Jamal da k'arfi "Jamal! Ka saketa karka kashe musu 'ya" Ya sake mak'ureta idanunsa sai lumshewa take tana cigaba da kakari "Barin kasheki sai ki kirani da butulun da huja" Luuuu tayi zata fad'i Ammi ta k'arasa ta rik'e hannunsa tana hawaye "Ka saketa Jamaludeen, kar zuciya tasa kayi abinda zaka dawo kana danasani" K'in saketa yayi, Abba gaba d'aya ransa ya gama b'aci "Ashe Bamu isa mu hanaka abu ka hanu bako" Ya juya baya fuskansa ba walwala "Hakan ya nuna mana bamu da iko akanka" Sakinta yayi ta fad'i Luuu ta sume a wajan, baga d'aya fuskansa da idanunsa sun koma ja, Ammi ta rik'o hannunsa tana hawaye "Kome ta maka bai kamata kayi mata haka bah" Taja hannunsa ta zaunar dashi sai huci yake kamar zaki "Areef samo masa ruwa" Ruwa ya d'ibo a dispensern dake falon ya mik'a mata ta ba Jamal d'in, ba musu ya kafa baki ya shanye tas yana sauke ajiyar zuciya Abba ya k'arasa inda Mabrookah ke kwance ya yayyafa mata ruwa ta sauke ajiyar zuciya a wahalce tana kakari, dakyar ta mik'e tana rik'e da wuyanta ta fita daga side d'in dasauri. Ammi tace "Areef wai meya faru neh" Nan ya karkace ya labarta musu duk abinda ya faru, Abba yayi murmushi yace "Baka kyauta bah, haka itama bata kyauta bah. Muda ba zama zamuyi bah? Abuja zamu koma insha Allahu Jibi, Mun tsaya ne jiran Areefa tazo dan mu a gabanka tasan abinda ke faruwa" Ya d'ago idanunsa dake cike da kwalla "Pls Abba ku zauna dani, nayi maraicin ku for About 28yrs inaso mu kasance tare Pls" Abba ya girgiza kai "No Son, ai bai kamata muzo nan mu zauna bah" Ya rik'o hannun Ammi hawayen dake cike a idanunsa suka zubo "Pls Ammi kiba Abba hak'uri ku zauna tare dani Dan Allah" Areef ya karb'e da cewa "Ah! Nidai babu inda zani ina nan" Ya gyara zama tare da kishingid'a akan kujeran dayake, Jamal ya sake cewa "Pls Abba" Shiru Abban yayi sannan ya mik'e yana cewa "Zanyi tunani akai" Ya fita daga falon saboda kiraye kirayen Sallan da ake a masallacin gidan. Ammi ta rik'o hannunsa tace "What you did was wrong Jamaludeen, babu kyau namiji ya rink'a dukan matarsa, karna k'ara gani ko na k'araji kanajina" Ya gyad'a mata kai, ta shafa kansa tana murmushi "Allah ya maka albarka" Yace "Ameen" a hankali Suka mik'e shida Areef dan zuwa masallaci. Baiwar Allah Ummy sam batasan abinda ke faruwa ba tana chan side d'insu, yau cike take da farincikin ganin Iyayen mijinta, abinci mai rai da lafiya ta soma had'awa tana mai cikin nishad'i. K'arfe biyu na rana ta gama komai, Side d'in Jamal ya shigo shida Areef bai ko kalli D'akin Mabrookah ba ya haura sama Areef na binsa a baya, a falon sukayi kicibus da Ummy ta fito daga d'akinta taci kwalliya cikin wani dakakkiyar lace lemon green mai adon duwatsu Orange, sosai kayan ya amsheta, Murmushi ya sakar mata ta mayar masa, ya k'arasa inda take tsaye tana wasa da zoben hannunta, rungumota yayi jikinsa tad'an turesa ganin Areef na haurowa, k'ara matseta yayi yana shinshina wuyanta "Uh Look Cute Wife" Yad'an rad'a mata a kunne "I hope wannan ranan nawa neh" K'okarin turesa takeyi yana k'ara matseta, Areef dake tsaye a falon yayi saurin sa hannayensa biyu ya rufe fuskansa ganin yana k'okarin laluban bakinta, a hankali ta fisge tana tura baki "Juya bayanka ka gani" Ya juya a hankali suk had'a ido da Areef, Gyaran murya Areef d'in yayi yana Murmushin shakiyanci "Uhummm! Emmm Bro i tot fita kace zamuyi" _Fans bani da bakin baku hak'uri na rashin post kwana biyu, Ku cigaba da hak'uri da Ummyn ku komai ya kusa zuwa k'arshe insha Allah_ Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 89 "Uhummm! Emmm Bro i tot fita kace zamuyi" Jamal ya sosa k'eya "Ina zuwa" Yaja hannun Ummyn sukayi d'akinsa tanata k'okarin k'wacewa tana tura baki, kan gado ya direta ta mik'e tsaye dasauri "Kaga fah jiranka akeyi" Ya matso kusada ita ya rik'e kugunta yana murmushi tare da zira hannunsa a maranta "Ya babyna?" Ta sake turo baki, "Ni babu ruwana da babyn nan kullum sai yayi ta sa mutum rashin lafiya" Yayi dariya tare da kai bakinsa kusada nata, tayi saurin gocewa dasauri tana dariya "Bro d'inka na jiranka fah" Ya harareta yana d'aukan keyn mota kan bedside drawer "Allah ko Wife! Hmm zaki sani" A shagwab'e tace "Me nayi toh" "Bari naje mu nemo nida ke ne akan.." Ya nuna mata makeken gadon dake d'akin, hannu biyu tasa ta rufe fuskanta tana murmushi, shima murmushin yayi ya fita yana cewa "Sai na dawo" "Allah ya kiyaye hanya" Tace a hankali tana bin bayansa da kallo. K'eyar Areef ya kad'a dan ya lura baya jin magana suka fice. Saida taga fitarsu ta window sannan ta d'au hijab tasa ta fito, abincin data girka ta had'a akan Mayan trays guda biyu ta d'au d'aya ta nufi falon Abba. Da sallama ta shiga Ammi dake falon kan sallaya ta amsa mata tana murmushi, kan dinning ta aje sannan ta dawo ta tsugunna har k'asa ta gaida Ammin, cikin fara'a ta amsa mata ta mik'e ta d'auko d'ayan trayn wannan karan harda Abba ta gani a falon, shima ta tsugunna ta gaida sa ta k'arasa ta aje trayn, tsugunnawa tayi a falon cikin jin kunya ta gabatar musu da abincin. Sannu Ammi ta soma mata tare da sa mata albarka. Cikin nishad'i ta mik'e ta fito daga side d'in ta koma nasu, a falon k'asa ta had'u da Mabrookah tana zaune tana taunar cingum, kallo d'aya Ummyn ta mata ta kauda kai, Mabrookah ta saki dariya mai sauti tana cewa "Ayi dai mu gani idan tusa na hura wuta, uwar 'yan shishigi daga zuwan mutane an kama musu girki" Ta tab'e baki tare da kauda kai "Dangin miji dai ko kanka zaka yanka ka basu basa gani, a gama kankan ban a bari" Ummy ta saki murmushi ta haura sama tana girgiza kai, tana daga falon ta tana jin habaicin da Mabrookahn keyi. A Side d'in Abba kuwa, Ummy na fita Ammi ta mik'e tana cewa "Allah kuwa Alhaji Yarinyan ta shiga raina, kaga dai yau na fara ganinta Anma Wallahi ta kwanta min" Ta k'are maganan tana bud'e warmers d'in dake kan Dinnin d'in, k'amshi ne ya musu sallama, Ammi ta sake cewa "Alhaji ga abinci sai dai ba abincin ka akayi bah" Dinning d'in ya k'araso ta bubud'e sauran warmers d'in tana dubawa, ya zauna yana cewa "Sai dai ki zubamin Farfesun kawai naci" Ba musu ta zuba masa farfesun kajin a saucer ta mik'a masa ya saka cokali ya soma ci. K'aran bud'e gate sukaji chan sai ga Jamal da Areef sun shigo da sallama rik'e da ledoji, Chak Areef ya tsaya yana cewa "Ashe ma anyi abincin" Ammi ta juyo tana kallansu, Areef ya k'araso dasauri ganin Abba nacin nama, Ammi ta hararesa "To kura!" Yayi dariya "I love Meat Mum!" Dariya sosai yana Jamal ya k'araso wajan yana dariya, ledojin hannunsa ya aje yana kallan abinda suke ci "Ammi girki kikayi" Kai ta girgiza tana cewa "Aa sarakuwa ta ce ta kawo mana" Ko ba'a fad'a masa ba yasan Ummy ce, sallamanta sukaji daga bakin k'ofan falon, suka amsa Areef ya mik'e dasauri ya amsa trayn hannunta dake d'auke da bottle waters da drinks kala kala "Kawo na tayaki Aunty nah" Tayi saurin duk'ar dakai tana murmushi a kunyace, gaba d'aya kunya ce ta lullub'eta dan ko ba'a fad'a ba tasan Areef ya girme mata nesa ba kusa bah. Kallanta kawai Jamal yake cike da so da k'auna, Ammi tace "Sannu Jaleelah Allah ya miki albarka" A hankali tace Ameen ta d'an d'ago ta saci kallan Jamal, kashe mata ido yayi tad'an yi murmushi ta musu sallama ta juya zata fita, jin muryan Jamal tayi yana cewa "Abba bakacin abincin" Areef ya amshe da cewa "Ai Abba baya cin Shinkafa, yanada Diabetes" Bataji amsar da Jamal d'in ya basa ba ta fita daga side d'in. D'akinta ta koma ta d'au wayanta ta shiga internet, browsing ta soma yi sannan ta mik'e dasauri ta shiga kitchen. Miyar Egusi ta d'aura mai rai da lafiya, nan da nan gidan ya bud'e da k'anshi, Mabrookah dake falonta sai had'iyar yawu take tana Hararan Stirecase d'in falon. Tana nan zaune Jamal ya shigo kallo d'aya ya mata ya kauda kai gefe, Ledan Takeaway da sukayo ya aje mata nan falon ya haura sama, binsa da harara tayi tare dajan tsaki ta mik'e ta d'au ledan tana dubawa. K'amshi ne ya masa sallama yana haurawa Falon, jin motsinta a kitchen yasa ya k'arasa cikin sand'a, tuwon semo ya samu tana tuk'awa tana haki kamar wacce tayi gudu. Tausayinta ne ya kamasa ya k'arasa ya zagaye k'ugunta da hannunsa yana mata sannu, murmushi ta masa tana cigaba da aikinta. Tayata ya soma yi har suka gama, ta had'a komai a tray ta mik'a masa tana turo baki "Dan Allah kakai ma Abba, naji baici wani abinci bah" Farinciki ne ya lullub'esa mara lissaltuwa, ya amsa Trayn "Thank uh so..." Tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai, a sanyaye ya fito daga kitchen d'in ya koma side d'in Abban, Ammi na ganin Abincin ta soma hawayen farinciki "Son Allah ya maka Albarka, ka samu mace ta gari. Allah ya baku zuri'a ta gari" A hankali yace Ameen Sosai Abba yaci abincin dan ya masa dad'i sosai, Saida ya gama sannan ya wanke hannu, Hannu yasa a aljihun Rigansa ya ciro tsabar kud'i masu yawa ya mik'a ma Jamal d'in "Gashi kaba surukata, Allah ya mata albarkah" Ya amsa yana murmushi tare da godiya. Koda ya koma ya samu tayi wanka ta kwanta tana bacci, sosai yayi mamakin Saurin baccin Ummy kwana biyun nan. Gefenta ya kwanta ya shige jikinta shima nan da nan bacci ya d'aukesa. Ba ita ta farka ba sai bayan la'asar, salati tayi ta mik'e ta shiga toilet tayi wanka ta fito tare dayin sallah. Ranar gaba d'aya hidima tayi da sirrukanta, har Mamaki Abba da Ammi suke na irin karramasu da Ummyn keyi. Albarka ko tasha shi wajan Iyayen mijin nata dashi kansa Jamal d'in. Washe gari Areefah ta diro garin zaria itada da drivern su Abban, k'arfe sha d'aya na safe a gidan ta musu tare da taimakon Jamal dayayi tama Drivern kwatance. Sosai tayi murnan ganin iyayen nata, bayan ta huta Ammi ta umarceta data je side d'insu Ummy ta gaishe su, hakan ko akayi, a falon k'asa ta had'u da Mabrookah ta gaisheta, dakyar ta amsa tana yatsine fuska. Areefah ta tabe baki dan a rayuwarta babu abnda ta tsana kamar wulak'anci, Sama ta haura a falo ta had'u da Ummy itama kwance kan kujera Ummy najin sallamanta ta mik'e zaune tana mata murmushi, ta k'arasa ta zauna tare da gaisheta Da fara'a Ummyn ta amsa tana ta kallanta ganin tsantsar kamar da suke da Jamal kamar an tsaga kara harma tafi kama da Jamal fiye da Areef, Ummy ta mik'e tana cewa "Barin samo miki wani abu" Tayi saurin cewa "No Aunty Thank uh. I'm Ok" Ummy tayi kitchen tana cewa "Aa wallahi ai bazai yuwu kixo wajena bakici komai bah" Ya shiga kicin ta kawo mata drinks da 'yan kayan motsa baki. Yanda Ummyn ta tarbeta yasa ta saki jiki ta soma mata hira, Areefah akwai Barkwanci. Daga k'asa Mabrookah keta jin dariyansu, ranta ya k'ara b'aci lallai idan tayi wasa sai Ummy ta kwace mata mutane. Taja dogon tsaki ta shige d'akinta. Tare da Ummy sukayi Sallah, Da taimakon Areefahn ta had'a ma su Ammi abinci a Warmers Areefah ta taimaka mata suka kai. Ammi da Abba sai albarka suke saka mata. Bayan ta fita Areefah ta zauna kan dinning tace "Abba nan gidan wanene?" Ammi ta bud'e baki zatayi magana Jamal da Areef suka shigo falon da sallama, kurrrri tama Jamal tana kallansa, ganin yana kama da Areef, ya k'araso wajan ya tsugunna ya gaida iyayensa. Abba da Ammi suka amsa da fara'a, Itama ta gaidasa ya amsa cikin fara'a yana cewa "Uh welcome sister" Murmushin yak'e ta masa ta d'au spoon d'in gabanta ta saka cikin abincin tana kallansa k'asa k'asa. Ganin sun zauna kan dinning d'in shida Areef dake ta hararanta yasa tad'an kalli Ammi cikin rad'a tac "Ammi wanene wannan" "Just eat" Ammi tace mata. Kasa sakewa tayi sai kallan Jamal take dake ta hira dasu Ammi suna cin abinci. Bayan sun gama Abba ya mik'e ya koma falo, Areefah na ganin haka ta mik'e dasauri ta bisa, Kusa dashi ta zauna tana tura baki "Abba were are we? And hu is he" Ta nuna Jamal dake tahowa shida Areef, Murmushi kawai Abba yayi, saida duk suka zazzauna sannan Abba ya soma ba Areefah labarin duk abinda ya faru da kuma abinda ya faru sanda aka kamasa. Batayi wani mamaki bah ganin tsantsar kamar da yake da 'yan gidansu, Hamdala tayi da k'arfi har saida duka suka juya suna kallanta, ta d'aga Hannu sama tana cewa "Alhamdulillah Thank uh Allah for accepting my Prayers" Sosai ta basu mamaki, ta kalli Areef dake ta kallanta tace "Kullum ina Addu'a Allah bani wani Bro gashi ya bani" Ta nuna Areef fuska a had'e "Mugu to daga yau uh are no more my Bro" Gaba d'aya dariya sukayi banda Areef da ransa ya gama b'aci "Dama ke wake k'anwa dake, jibeki k'azama kawai" Ba shiri ta fashe da kuka "Abba kajishi koh" Ammi ta k'arbe da cewa "Kun had'u zaku fara koh, da baku tare kwana biyu har bakina yayi shiru" Abba yace "Karka sake cema Babyna k'azama, kaga nan k'azami" Jamal sai kallansu yake da sha'awa tare da farinciki. Yace "Zo kiji" Ba musu ta dawo kusa dashi ta zauna, ya goge mata hawayen fuskanta yana murmushi "I'm now ur Bro ki kyalle Areef babu ruwanmu dashi" Gwalo tama Areef ya mik'e "Allah kikayi wasa saina mangareki" "Iyeh!" Cewar Abba "Tho Mangaretan" Ya fita daga falon yana huci, Jamal yace "He's ur brother ki daina masa rashin kunya kinji" Ta tura baki tana shagwab'a "To bashi ke tsokanata bah" Yanda take shagwab'a ta tuna masa da Wife d'insa "How old are you?" "17yrs" tace Jamal yayi dariya "Woaw! Ashe big gal ce" Tayi dariya tana cewa "Bro su waye wanda na gani a wanchan side d'in" Murmushi yayi batare da ya bata amsa bah, Ammi tace "Matansa ne" Baki bud'e tace "Duka biyu" Ya sake sakin murmushi, tab'e baki tayi tace "Nidai Faran tafi kirki, b'akan batada kirki bab...." Ammi tayi saurin cewa "Kull! Karna sake ji" Ta tura baki, Jamal ya mik'e yana cewa "Abba barinje naga Mifzal coz gobe za'a koma court" Abba yace "Eh yakamata, muma ana fitowa daga Court d'in zamu koma" Gabansa ya fad'i baice komai bah ya fita daga falon. Bai samu shiga side d'inshi bah ya wuce station d'in. A office d'in ya had'u da Ram, bayan su gaisa Mifzal yace "Komai dai zaizo k'arshe gobe insha Allahu" Jamal yayi murmushi yace "Pls ko zan iya ganin su Mamin" Dogon tsaki Ram ya saki "Wani me matar nan ta maka neh kabi ka damu da ita haka?" "Ko ba komai ta raine ni ta rik'eni kamar d'anta" Mifzal yayi saurin cewa "Anma ba tsakani da Allah bah koh" Ram ya d'aura da cewa "Wadda ta iya sa a kashe mijinta, kai ko ba mijinta ba ma mutum fah" Ran Jamal idan yayi dubu ya b'aci, ya mik'e yace "Banasan cin fuska idan bazaku taimaka min ba ku bari" Fuuu zai bar office d'in Ram yayi saurin rik'osa yana cewa "Haba D'an Mami yi hak'uri mana, zauna kaji" Ya zaunar dashi shima ya zauna suna fuskantar juna "Suna prison yanzu haka baza'a bari ka gansu bah" Shiru yayi baice komai bah, Ram ya soma jansa da hira har ya samu ya ware sukayi ta hira, a nan yake basu labarin zuwan Areefah." A gida kuwa Areefah na sallah ta koma side d'insu Ummy, Kallo d'aya tama Mabrookah taja guntun tsaki ta haura sama wajan Ummy. Hira sukayi tayi gwanin ban sha'awa, tare sukayi abincin dare sunata hira kamar sun dade da sanin juna. Ran Mabrookah ya sosu sosai, ta mik'e ta shiga kicin ta soma kici kicin d'aura abinci. Tuwon shinkafa tayi da miyar Alaiyahu datasa Mai gadi tasayo mata. Cikin k'ankanin lokaci ta gama, wanka tayi ta sauya zuwa dogon rigan shadda. Ta had'a abincin a tray ta d'auka bayan anyi sallahn magriba, dai dai nan Areefah ta sauko da Tray itada Ummy, Kallansu Mabrookahn tayi ta watsar tayi gaba suna binta a baya, Areefah sai yatsine fuska take dan gaba d'aya Mabrookah bata burgeta, da Sallama Mabrookahn ta shiga Ammi ta amsa, kan dinning ta aje Trayn a tsaye k'erere ta gaida Ammin tana wani cika tana batsewa. Areefah ta k'arasa kan dinning d'in ta ture trayn Mabrookahn gefe ta aje na hannunta, Sannan ta amsa na Ummy a aje, Ammi na daga gefe tana ta musu sannu da godiya. Mabrookah tayi gaba, Itama Ummy ta mik'e ta musu saida safe ta fita, a falon k'asa tayi kicibus da Mabrookahn tana jiranta "Kwad'ayaiya, nasan dai duk abinda kikeyi nan na kwad'ayi ne dan kinga suna dashi, An saba da maula" Ran Ummy ya sosu ta wuce zata haura sama ta sake jiyota tana cewa "In ma so kike ki mallake su karyanki tasha k'arya, Uwa ta saba da bin bokaye dole 'ya ma tad'au hanya. Wayasan abinda aka kitsa miki da kikaje gidan ranan" Ran Ummy idan yayi dubu ya b'aci, ta sauko k'asan "Kullum kina zagina ban tab'a maida miki da martani bah, dan har yanzu ina miki kallan wadda ta girme mani, ko ba komai kin fini shekaru bazanyi musu dake bah. Anma yau kin kaini bango" Wani shewa Mabrookah ta saki tana cewa "In kinama Allah kada ki k'ara ganin girman nawa" Murmushin takaici Ummyn tayi tana cewa "Kiyi ta zagina daga nan har abada anma karki k'ara zagin iyayena dan basu miki komai bah" Bata ankara bah taji saukan Mari a kuncinta, ta dafe wajan dasauri tana kallan Mabrookahn "Kika mareni" Tana huci tace "An mareki ko zaki rama neh, shegiya 'yar masu bin bokaye" Mari Ummyn ta d'auke Mabrookahn dashi mai rai da lafiya, nan fa fad'a ya kaure tsakaninsu, kokawa suka shiga yi tsakaninsu dai dai lokacin Jamal ya shigo cikin gidan, kamar zai shiga side d'in Abba sai kuma ya nufi nasa, yana shiga Mabrookah ta rarumi Dogon speakern home theatern dake Falonta ta bugama Ummyn a...... Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 90 _*A Gurguje*_ Yana shiga Mabrookah ta rarumi Dogon speakern home theatern dake falonta ta bugama Ummyn akai, Wani k'ara ta saki take ta fad'i wajan a sume jini na fita a kanta. Jiki na rawa ya k'arasa falon gaba d'aya jikinsa rawa yake, tsugunawa yayi inda Ummy ke wance ya d'agota hawaye cike da idanunsa, d'agowa yayi yana wani irin huci yana kallan Mabrookah wace ya yarda Speakern itama jikinta na rawa tana kuka. A fusace ya mik'e ta juya zata gudu ya kamota ya soma had'ata da bango yana kuka, ihu take a wahale tana neman agaji, Ammi da Areefah ne sukaji yo ihun Ummy da farko, har Areefahn ta mik'e Ammi ta hanata, jin wani ihun yasa suka mik'e a tare sukayo side d'in. Suna shiga ya sake bugata da bango ta saki k'ara take itama kanta ya fashe. Ammi ta k'arasa dasauri inda suke tsaye ta rik'esa gaba d'aya ta rud'e "Jamaludeen karka kasheta, stop! Control your anger" Ya jefar da ita tare da nunta da yatsa "Na sakeki! Na sakeki!!" Harya bud'e baki da niyar furta wani abu Ammi ta d'aukesa da wani gigitacen Mari "A gabana Jamaludeen!" Baice komai ba sai hucin dayake, Areefah ko tunda ta shigo ta fashe da kuka ganin Ummy kwance cikin jini, inda take ta k'arasa ta tsugunna tana kuka. Jikinsa na rawa ya d'au Ummyn yayi waje da ita, ko takalmi babu a k'afan Areefah tabi bayansa, mota ya sakata ya ja da k'arfi bayan Areefah ta shiga suka bar gidan. Fitowansa yayi daidai da fitowan Abba da Areef daga masallaci, da ido sukabi motan ganin yanda yake gudu kamar wanda zai tashi sama. Suna shiga Ammi ta fito daga side d'in rik'e da Mabrookah wacce itama kanta ke jinin "Subhanallahi meya faru?" Cewar Abba yana k'arasawa wajan, Ammi bata b'oye masa komai akan abinda ta gani bah, sam Abbah baiji dad'in abinda ya faru bah. Areef yana daga gefe yana cin magani yanata ma Mabrookahn Allah ya k'ara a zuciya dan dama kwata kwata bata burgesa. Wani Private hospital mafi kusa Jamal yakaita, duk tabi ya rude in banda hawaye babu abinda yake haka Areefah dake gefensa sai kuka take itama, suna isa aka amsheta sukayi Emergency da ita, Wata nurse ta umarce shi daya je ya biya kud'in kati da sauransu, ba musu ya nufi receiption Areefah na biye dashi. Suna nan zaune wata nurse ta fito daga d'akin, Areefah tayi saurin mik'ewa tasha gabanta "Dan Allah ya jikin nata?" Nurse d'in ta mata murmushi "Dasauk'i karku damu" Bata jira cewar Areefan ba tabar wajan dasauri, suna nan tsaye likitan ya fito, Bayani yama Jamal d'in akan abin bai yi serious ba saidai su kiyaye nan gaba. Sannan ya basu umarnin shiga su ganta. Kwance suka sameta kan gado kanta nan nad'e da bandage tana bacci hankali kwance, wani nannauyan ajiyan zuciya Jamal ya sauke ya k'arasa bakin gadon, Areefah ta rik'e hannunta hawaye cike a idonta "Allah zai saka miki Aunty, kuwa wallahi..." Taji k'wafa ranta b'ace. Shidai Jamal bai iya cewa komai bah. Suna nan Abba ya kira wayan Jamal yana tambayansa mai jiki, halinda ake ciki ya fad'ama Abban sai a lokacin suma hankalinsu ya kwanta. A gida kuwa Ran Ammi ya b'aci sosai gaba d'aya ji tayi Mabrookah ta fitar mata a rai, babban damuwarta bai wuce cikin dataga alamar Ummyn nadashi bah. Buris tayi da Mabrookahn haka shima Areef ji yake kamar ya rufeta da duka. Dad'in ta d'aya ma dayaji Ammi tace Jamal ya saketa. Rashin sani gari yasa Abba had'a Mai gadi d'aya da Areef da ita Mabrookahn aka kaita wani Chemist nan kusa akayi mata treating kan. Koda Jamal ya fad'ama Abban halin da Ummyn ke ciki kasa sukuni Ammi tayi, kwatance tasa ya musu Areef ya d'aukesu itada Abba sukaje asibitin. Ammi har hawaye tayi ganin Ummy kwance a kan gado, Kwana biyun nan da sukayi sosai ta shiga ranta. Ta share hawayen fuskanta tana kallan Abba "A gaskiya Alhaji zaman Jaleelah da Yarinyan nan Mabrookah bazai yuwu bah" "Wani irin magana kike haka Hajiya, karki manta fah matarsa neh bamu isa mu rabasa ta itaba" Shidai Jamal baice komai saboda b'acin rai, ji yake kamar ya kashe Mabrookah ya huta, hannayensa ya saka a aljihu tare da sakin huci mai zafi. Areefah ta zumb'uro baki "Ai wallahi bazan yarda bah, wallahi ta k'ara maimaita makamancin haka dukan tsiya zan mata" Ran Abba ya b'aci, ya daka ma Areefah tsawa abinda bai tab'a yi bah "Karna k'ara ji" Ta sake shagwab'e fuska ta kauda kai. Suna nan har ta farka daga baccin, sunata mata sannu har abin ya bata kunya ganin harda Abba a wajan da kuma yanda gaba d'aya suka nuna damuwarsu a kanta. Ba kunya Jamal ya zauna kusa da ita ya d'an rab'ata da jikinsa sai k'okarin k'wacewa take ta kasa, shiko gogan ko a jikinsa. Ammi na ganin haka ta mik'e daga kan kujeran datake, "To bari muje gida mudai" Ummy najin haka ta tura baki tana kallan Jamal "Nifa ba inda kemin ciwo dan Allah a sallameni" Bai iya mata musu ba ya mik'e yace ma su Ammi yana zuwa, wajan likitan yaje ya rok'esa ya sallamesu, X-ray aka rubuta musu da kuwa wasu magunguna sannan yace su bari drip d'in dake jikinta ya k'are. Godiya yayi ya koma, yana zuwa ya samu su Ammi sun wuce sai Areefah dake d'akin tanata ma Ummyn hira itako sai dariya take cike da nishad'i, Yanda ta damu da Wife d'insa yasa ta sake samun gurbi a zuciyarsa, ya k'araso ya shaida musu yanda sukayi da likitan. A b'angaren Mabrookah kuwa tana ganin su Ammi sun fita ta fashe da wani matsanancin kuka, sai lokacin kalmar Jamal dayake anbata mata kalmar saki ya dawo mata k'wakwalwarta. Ta sake rushewa da kuka, chan kuma ta mik'e kamar wacce aka tsikara, ta goge hawayenta ta nufi bedroom d'inta dasauri. Drip d'in na k'arewa aka sallamesu suka dawo gida, Ammi dake falon tana jiransu tana jin shigowan motan ta fito dasauri ta rungume Ummyn tana mata sannu, Hannunta ta kama tana cewa "Banasan wani tashin tashina, zo muje d'akina" Jamal ya turo baki gama harda doka k'afa d'aya a k'asa sam ba haka yaso bah, Areefah dake kallansa ta kyalkkyale da dariya ya galla mata harara, ciki sukayi yana binsu a baya har lokacin bai maida bakin bah. Ganin sun haura sama yasa ya zauna a falo yana cika yana batsewa, Kan gado Ammi ta zaunar da ita tana cigaba da mata sannu "Kiyi Hak'uri Jaleelah kinji" Murmushi kawai tayi ta duk'ar dakai k'asa, Ammi ta shiga toilet ta had'a mata ruwa mai d'an zafi ta umarceta taje tayi wanka. Cikin daran nan nan nan da Ummyn Ammi ta dunga yi sai dataga tayi bacci hankalinta ya kwanta. Tana saukowa ta samu Jamal kwance kan 2seater bacci ya d'aukesa, murmushi tayi ta k'arasa ta tab'asa tana cewa "Jamaludeen a nan kake bacci, maza tashi kaje ka kwanta" Ya bud'e ido dakyar "Ammi ina Wife" Duka ta d'aka masa ya bud'e ido dakyau yana muzurai "Maza je ka kwanta, karna dawo na sameka a nan" Ta haura sama ta barshi nan. Da Asubah Abba ya sauko dan tashin Areef zuwa masallaci, a d'akin ya samu Jamal kwance kan Tiles yana bacci abinsa hankali kwance, Mamaki ne k'arara a fuskanshi ya k'arasa ya soma tashinsu, Areef ma yayi mamakin Ganin Jamal d'in a d'akin. Tare suka tafi masallacin su uku. K'arfe takwas na safe duk sun hallara a falon before ayi breakfast, Ummy na zaune k'asa kan carpet kusada k'afar Ammi itada Areefah, Haka Jamal shima zaune kusada Abba, Abba yayi gyaran murya ya soma da cewa "Wannan zaman yakamata ayishi da d'ayar matarka, saidai kafin tazo inaso nayi magana akan abinda ya faru Jiya" Jamal ya duk'ar dakai dan yasan dashi za'ayi, Abba ya juya garesa fusaka ba yabo ba fallasa yace "Da Mabrookah da Jaleelah duk matanka neh, duk sadaki ka biya ka aurosu koh?" Jamal dake gefe ya gyad'a kai kamar kad'angare kansa k'asa "Sam banji dad'in abinda ya faru bah jiya, idan rai ya b'aci bai kamata hankali ya gushe bah. Yakamata ka tsaya kayi alk'alanci kafin ka zartar da hukunci. Anma zartar da hukunci cikin fushi babu abinda yake haifarwa sai danasani" Ya numfasa yace "Baka kyauta ba sam Jamaludeen" Ammi dake gefe tace "Saki nawa ka mata?" Kansa k'asa yace "Biyu!" "What!" Cewar Abba ransa a b'ace "A haka kakesan mu zauna a nan gidan" Ya d'ago idanunsa cike da kwalla yace "Abba dan Allah kayi hak'uri!" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Areefah jeki kiramin Mabrookahn" Ta mik'e tana zunguro baki ta fita, Side din ta shiga ga mamakinta yanda falon yake jiya haka ta samesa, ta tab'e baki "Sai shegen k'azanta" Knocking ta soma a k'ofar bedroom d'in shiru ba amsa tafi minti goma a tsaye taja tsaki ta banko k'ofan ta shiga. Batsa batsa ta samu d'akin kayan wardrobe duk a k'asa da sauran tarkace. Ta taka tana yatsine fuska har Toilet d'in nan ma ta dunga bugawa ba amsa. Har zata fito idanunta suka sauka kan wani Farin takarda mai d'auke da rubutu da aka d'aurama Kwalbar humra. D'auka tayi ta soma karantawa _Kayi ma iyayena k'azafi hankalinka bai kwanta bah, ka..._ Tayi saurin dakatar da karatun ta fita dasauri zuwa d'ayan side d'in. Tana shiga tace "Abba ban ganta ba saidai naga wannan takardan" Ta mik'a masa ya duka na 'yan mintina sannan ya mik'ama Areef yace ya karanta kowa yaji _Kayi ma iyayena k'azafi Hankalinka bai kwanta bah, ka d'auko wasu mutane dan suci dukiyar Abba wai kai Iyayenka, to ka sani alhakin Iyayena bazai tab'a barinka bah. Sannan indai Ummy ce wallahi baku isa ku zauna lafiya bah, badai saboda ita ka sakeni bah? To wallahi baku ba samun Farinciki indai ina raye. Na tafi na bar muku waje ku shak'ata saidai ku jirayi dawowata.A_ Daga Matarka abar sonka Mabrookah. Areef na gama karantawa yaja dogon tsaki "Abba kagani koh? Ni dama wallahi tunda na ganta sam batamin bah" Kasa cewa komai Abba yayi Ammi tace "Areefa kuje keda Ummy sama kuyi breakfast sannan kuyi sauri dan 10 za'a shiga Court gashi 9 yanzu" Ta kama hannun Ummyn suka haura sama zuwa d'akin Ammin, suna shiga Ummy ta zauna bakin gado ta fashe da kuka, Areefah ta zauna kusada ita dasauri tare da dafa kafad'arta "Haba Aunty Ummy ki daina kuka, insha Allahu babu abinda Mabrookah ta isa ta miki wanda Allah bai miki bah" Ta saki murmushin takaici "Nasan Halin Mabrookah sarai akan abinda takeso tana iya komai Areefah" Areefah ta soma share mata hawaye "Oh! Stop crying Allah ya fita" Bata sake cewa komai ba sai kukan data cigaba, Breakfast d'insu Areefah ta d'auko musu, ba yanda batayi akan Ummyn taci ba taki, saima kwanciya datayi wani mugun zazzab'i ja neman rufeta. A falo kuwa su Areefah na haurawa Ammi tace "Gaskiya Alhaji inasan rayuwar d'ana dana matarsa. Banasan abinda zai tab'asu, cikin biyu gaskiya za'a zabi d'aya ko mu zauna dasu ko mu koma gaba d'aya abujan tare" Jamal ya karb'e da cewa "Abba Ammi dan Allah ku gafarceni ku yafemin abinda na muku". Abba yace "Babu komai anma kada hakan ta k'ara faruwa" Shiru ne ya biyo baya, Ammi ta sake cewa "Alhaji bakace komai bah har yanzu" "Ammi dama inso idan kun amince sai na saida gidan nan na sayi wani a chan Abujan" Sai a lokacin Abba yace "Gaskiya nayi matuk'ar mamakin kalaman yarinyan nan, yarinya k'arama kamar wannan da irin wad'an nan maganganun" "Ba abin mamaki baneh ai Alhaji, ka manta gado?" Ya sauke ajiyar zuciya yace "Na aminta da maganar taka bama saika saida gidan bah, chan is ok for us ai" Ammi ta saki lallausan murmushi "Allah ya k'ara rufa mana asiri ya kuma karemu daga sharin mak'iya" Duka suka amsa da Ameen. Nan Ammi tayi serving musu breakfast sannan ta haura sama wajansu Areefah. Ganin Ummy kwance yasa ta k'arasa dasauri bakin gadon "Ummy lafiya?" Ta d'agota taji jikinta da zafi, gaba d'aya Ammin ta rud'e ta soma neman magani. Dakyar ta samu tad'anci wani abu sannan ta bata magani, kan kace komai ta amayar dashi. Koda lokacin tafiya yayi Ammi tace su tafi ita zata zauna da Ummyn, hankalin Jamal gaba d'aya yana kan Wife d'insa hakanan badan ransa yaso ba suka tafi Court d'in dasu Abba harda Areefah. A chan suka samu su Ram da Mifzal, bayan alk'ali ya zauna aka gabatar dasu Mami, kallo d'aya zaka musu duk su baka tausayi sunbi sun rame sunyi bak'i kamar basu bah. Idanun Mami na kan Jamal tana hawaye tana kallansa. Bayan an karanto shar'ia aka yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai. Ba shiri Jamal ya fashe da kuka a Court d'in, Areef ya fito dashi waje yana lallashinsa. Mami sai kuka take itada Aunty Faty, haka aka fito dasu Aunty Faty na tafiya da k'afafunta while Mami na kan Wheel chair ana turata. Jamal na ganinsu ya fizge daga rik'on da Areef ya masa ya nufesu Mami ta fashe da kuka "Ka yafemin Jamaludeen, ka yafemin" Yana aniyan k'arasawa akayi saurin sakasu a mota aka tafi dasu. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 91 Yana aniyan k'arasawa akayi saurin sakasu a mota aka tafi dasu. Guiyawu biyu yasa a k'asa yana bin motan da kallo hawaye na cigaba da zuba daga idanunsa, Areef ne yayi saurin k'arasowa ya d'agosa daga k'asan tare da rungumesa yana hawayen tausayin yayan nasa. Mifzal wanda fitowansa kenan daga court d'in ya tab'e baki cike da takaici, sosai abin Jamal ke basa mamaki. Abba shima ya k'araso ya rik'e masa hannu yana lallashinsa, mota suka sakashi suka d'au hanyan gida. Maganganu Masu dad'i Abba ya dunga ma Jamal na kwantar da hankali har ya samu yad'an saki ransa kafin su isa gida. Uffan Areefah batace ba sai bin Jamal d'in datake da kallo. Koda suka isa gida bai shiga side d'in dasu Ammi suke bah, d'akinsa ya wuce ya kwanta yana sauke Ajiyar zuciya, gaba d'aya jinsa yake wani iri ga zuciyarsa dake masa suya. Areef ne yaba Ammi labarin hukuncin da aka yanke masu Mamin, hamdala tayi na godiya ga Allah, Areef tace "Ammi ina Aunty Ummy" "Ta samu bacci" cewar Ammin tana k'okarin shiga kitchen dan kawo musu abinci. Koda Ummyn ta farka Alhmdullh jikin nata da sauki sosai, sai zuciyarta dake cigaba da tashi anma Aman yak'i zuwa. Areefa ne ta had'a mata ruwa tayi wanka sanan ta gabatar mata da abincin da Ammi ta mata. Sosai taci dan ya mata dad'i ga kuma yunwa dake damunta. Kulla da gata Ummy tasha shi ranar, koda Jamal ya fito sallan Azahar a masallacin ya zauna bai shigo ba har akayi sallan La'asar. Ana idarwa Abba ya kama hannunsa suka shiga cikin gidan, kan dinning ya zaunar dashi yasa Areefah ta zuba masa abinci. Ya yatsine fuska yana kallan Abincin "Abba na k'oshi" Abban ya zauna kan kujeran dake kusa dashi yana kallansa cike da tausayawa "Nasan yanda kakeji a halin yanzu Jamaludeen, anma hak'uri da Addu'a shine abin abinda yafi dacewa. I knw its hard ka manta dasu, mutanen da suka rik'eka duk da ita bata maka rik'on daya dace bah" Hawayen daya gani sun gangaro ma Jamal d'in ne yasa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "Addu'ar neman gafara shi ne kad'ai soyaiyar da zaka nuna musu a halin yanzu" Ya daga kafad'arsa yana cewa "Kasa ranka a inuwa, bansan ganinka cikin damuwa" Jamal ya gyad'a kai tare da share hawayen idanunsa "Nagode Abbana" Abba yayi murmushi ya janyo plate d'in Abincin ya diba a spoon ya kai bakinsa "Eat my son" Yayi murmushi tare da bud'e bakin kad'an Abba ya saka masa yana cigaba da masa kalamai masu dadi. Daga Ammi har Areefa da Ummy wacce ta sauko yanzu sun matuk'ar burgesu bama kamar Ummy, hawaye suka taru mata a ido ta k'arasa kan kujera ta zauna, Tana matuk'ar kewar Mamanta, kawaici kawai take dan bataso ta damesa musamman ganin halin da ake ciki yanzu. Bayan ya gama ci Abba ya basa ruwa yasha, Sannan ya rik'o hannunsa suka dawo falon, Ummy tayi saurin zamewa daga kan kujeran ta gaida Abban ya amsa tare da tambayanta jikinta. Satan kallanta Jamal keta yi ta kauda kai gefe dan fushi take dashi. Abba yace "Wai ina Areef ne tunda muka dawo ban gansa bah" Ammi ta tab'e baki tace "Kasan Areef da d'an banzan yawo, ba ya soma sanin gari bah" Jamal yad'anyi murmushi yace "Abba inaso muje mu gaida Umman Ummy idan ba damuwa nida su Ammi" Ammi tayi saurin cewa "Wallahi kamar ka shiga raina, ina zuci zuci na maka magana ka rigani" Ummy ji tayi kamar an sakata a aljanna, badan su Ammi ba babu abinda zai hanata rungumansa dan farinciki, Abba yace "Hakan nada kyau, mezai hana kuje yau dan gobe insha Allahu zamu koma" Ya turo baki "Pls Abba ku bari kud'an kwana biyu sai mu tafi tare" Abba yayi murmushi yace "Nabar abubuwa da dama achan kuma rashina zai iya saka damuwa" Shiru Jamal yayi fitan da Abba keyi da dare kamar yanda suka gani rannan ya fad'o masa, baice komai bah na d'an lokaci, Ammi tace "Aa gobe insha Allahu zamu koma, kuma da 'yata zan tafi dan harga Allah ina tsoron Abinda zaije ya dawo musamman wannan yarinyar Mabrookah" Ya tura baki ya mik'e ya fita yana gungunai, Areefah ta doka tsale ta rungume Ummy tana farinciki, itako Jikinta ne yayi sanyi, tunani ta soma a haka ma bata samu taga Mahaifiyarta balle kuma idan ta k'ara nisa. Ammi ta dakama Areefah tsawa "Karki buge min 'ya dallah saketa" Ta tura baki ta matsa gefe, Ammi ta rik'o hannun Ummyn suka haura sama. K'arfe bakwai bayan Sallahn Magriba suka je gidan Mama, sosai tayi farinciki da zuwansu, bata wani yi mamaki ba dan Bilal ya bata labarin duk abinda ya faru. Murna wajan Ummy ba'a magana, Abinci Mama ta gabatar musu, babu wani k'yankyami Ammi da Areefah suka ci tare dayin santi dan Mama ba baya bace wajan iya girki. A nan Ammi ke shaida ma Maman tafiyar Ummy Abuja, Jikinta yayi sanyi anma ba yanda ta iya hakanan tad'anyi murmushi tare da musu fatan Alheri. Hira sosai Ammi da Mama sukayi kamar sun dad'e da sanin juna. Tare sukayi sallan Isha'i, suna nan Jamal da Areef suka shigo suka gaida Maman cike da girmamawa. Sun shiga gidansu Bilal, Umman Bilal tayi farinciki da ganinsu sosai tare da musu godiyan abinda sukayi ma Bilal d'in. Shima Bilal yayi farinciki sosai, A nan Areef ke shaida masa Abba yace ya shirya gobe su koma. Umman Bilal ta soma godiya kamar ta ari baki. Waya daleliya Jamal yaba Mama bayan ya saka mata sim da recharge card, tayi godiya haka Ammi da Ummyn, Ummy ne ta shiga nuna mata yanda ake anfani da wayan da kuma yanda akeyin kira. Sun jima a gidan Ummy kamar karta rabu da Mamanta, da hawaye suka fito gidan sai dai bata bari su Ammi sun gani bah. K'arfe Tara da rabi na dare suka shiga gida, Jamal ya wuce side d'insu ita su kuma suka wuce side d'in Abba. Har Ummyn ta kwanta kusa da Areefah bayan tayi wanka Ammi ta shigo d'akin da sallama "Jaleelah kinyi bacci neh?" Ta mik'e zaune "Aa Ammi idona biyu" Ammi ta zauna tana gefen gadon tana cewa "Tashi kije gun mijinki, kinga gobe zamu d'au hanya sai ki shirya daga nan" A kunyace ta mik'e ta d'aura hijab kan kayan baccin jikinta ta fita kanta k'asa. Koda ta shiga kofar a bud'e sameshi, a hankali ta haura sama zuwa d'akinta. Ga mamakinta d'akin ta samesa kwance yayi ruf da ciki da alama bacci yake. Tausayinsa ne ya kamata ta k'arasa a hankali kan gadon ta zauna kusa da kansa. Idanunsa a lumshe yana sauke numfashi a hankali, suman kanshi ta soma shafawa a hankali. Charap taji ya chafke hannun ta bud'e ido tana kallansa har lokacin idanunsa a rufe suke ta soma kici kicin kwacewa, bata ankara ba ya mik'e tare da birkitota yana kallan fuskanta "Thank uh very much Wife, kin daina sona koh" Ta girgiza masa kai a shagwab'e tana tura baki "Ba wani ki fad'amin gaskiya" Ya kai mata light kiss yana d'an murmushi "Ke da kika yarda akesan rabamu dake" Ya shagwab'e fuska "Kwana nawa kenan baki damu dani bah" Ta fashe masa da kuka mara sauti, lokaci guda ya rude ta kwantota jikinsa yana lallashinta "To I'm sorry, pls ki daina" Ya d'ago kanta ya had'a goshinsu waje d'aya "Menene fad'amin Pls, na miki laifi neh?" Ta girgiza masa kai alamar Aa "Ko na mari kaina?" Nan ma ta sake girgiza masa kai, "Na ciro kaina na baki" Dariya tad'anyi mai had'e da kuka, ya rungumeta sosai a jikinsa yana lallashinta "Kinga zaki wahalar min da babyna, fad'amin pls me kike so na miki da zaisa ki daina kuka" Cikin muryan kuka tace "Babu komai" Ya sake matseta a jikinsa yace "Kawai jin dad'in kukan kike" Ta turo baki, ya kwantar da ita kan gadon ya soma lallubanta yana cewa "To bari kiyi kukan mai dalili" K'okarin k'wacewa takeyi ya rik'eta sosai yana cigaba da abinda yake. Ina ganin haka na tattara 'yan matan k'afana tare da taso k'eyar *Khairat* Ummu Manal mukayo waje. Da Asubah da kansa ya had'a mata kaya tana daga kwance kan gado, zazzab'i taji na neman rufeta na kewar mijinta, saida ya gama tsaf sannan ya d'ago suka had'a ido yana cewa "Banaso kiyi nisa dani Wife, but Ammi ta matsa ba yanda zanyi" Ya k'araso bakin gadon ya rungumota jikinsa, hawaye suka zubo mata wanda yajisu akan kafad'arsa, d'agota yayi yasa hannunsa yana goge mata tare da girgiza mata kai a hankali fuskansa d'auke da damuwa "Its ok kinji, dana gama abinda nakeyi zanzo mu zauna tare har abada" Tad'anyi murmushi, rad'a ya mata tayi saurin gocewa tana dariya tana k'okarin mik'ewa "Kai dan Allah wife, bakya tausayina koh. Kinga zamu dad'e bamu had'u bah" Ta turo baki gaba "Ni..ni nagaji wallahi" Yayi saurin kamota ya had'e bakinsu waje d'aya. (Wannan karan Matan Jamaludeen Fans na koro daga d'akin mukayo waje). Lol K'arfe sha d'aya suka gama shiri tsaf, Tuburewa Areef yayi akan bazai bisu bah, Jamal yace su barshi sai su taho tare. Areef ya d'au akwatin Ummyn ya saka a mota yana cewa "My Aunty Mudai sai munzo" Tad'anyi murmushi tana daga bakin k'ofan side d'in, Abba ya shiga gaba gefen Driver, Ammi ta shiga Baya itada Areefah, har Ummy ta bud'e k'ofan zata shiga Jamal yayi saurin Jan Hannunta suka shiga daga Falon side d'in Abba, d'an zaro ido tayi tana kallansa "Suna jirana fah" Rungumeta yayi batare da yace komai bah, ta sauke ajiyar zuciya tare da k'ara k'ankamesa, ya d'ago fuskanta ya had'e bakinsu waje d'aya bata hanasa bah har yayi mai isarsa ya janye bakinsa a hankali. D'agowa yayi fuskansa kamar mai shirin kuka "Zanyi missing d'inki Wife" Yasa hannunsa cikin riganta yana shafa maranta a hankali "Take care of ur self and my Baby kinji" Ta gyad'a masa kai hawaye cike a idanunta, Knocking sukaji daga bakin k'ofan falon Areef yace "They are still waiting" Tayi saurin janye jikinta ta fita yana binta a baya, Areef ne ya bud'e mata motan ta shiga, kasa k'arasawa Jamal yayi wajan mota daga chan baya yana d'aga musu hannu. Kasa d'aga masa hannu tayi ta fashe da kuka mara sauti tana binsa da ido har suka bar gidan. Hijab d'in datasa taja gaba ta rufe fuskanta tana kuka a hankali, a haka bacci ya d'auketa cike da kewar mijinta. Ba ita ta farka ba sai da suka shigo cikin binnin taraiya, a hankali ta bud'e ido lokacin da suka iso k'ofar gidan. Gate ne k'ato mai kyawun gaske, masu gadi suka bud'e musu suka shiga ciki. Wajan adana motoci drivern yayi parking. Areefah tace "Kin tashi" Ta gyad'a kai tare da d'an murmushi, Drivern ya fita dasauri ya bud'e ma Abban, Ammi ta fito Suma suka fifito. Bin gidan da Kallo kawai Ummy keyi cike da sha'awa, duk da irin tsaruwan gidan da ta baro anma nesa ba kusa ba nasu Ammi ya fisa komai. Areefah ta d'auko Trolleyn Ummyn da nata tana cewa "Aunty Ummy muje" Ba musu ta soma binta abaya har suka shiga cikin falon gidan. Nan Ummy ta saki baki tana ganin Aljannar duniya, d'aki mai kyawun gaske Ammi ta zab'a mata Areefah takai mata trolleynta ciki. Bayan tayi wanka ta fito kiran Jamal ya shigo wayanta, d'auka tayi ta soma masa shagwab'a, cike da damuwa yace "Baby kin tafi kin barini da kewanki" Ta tura baki kamar yana kusa da ita "To ba kak'i ka biyomu bah" "Ina nan zuwa dana gama abubuwan danake zan zo kinji" Ta gyad'a kai tare da amsawa, sun dad'e suna hira yana mata kalamai masu dad'i sannan sukayi sallama. Mama ta kira suka gaisa ta shaida mata sun isa Abujan, Addu'a ta mata sosai tare da jadada mata ta zama mai biyaiya ga 'yan uwan mijinta. Areefah ce ta shigo da sallama tace ta fito suci abinci, ba musu ta fito dinning d'in dake Falon suka zauna itada Areefah sukaci abinci suna hira gwanin ban shawa'awa. Bayan sun gama Areefah ta zagaya da ita taga ciki da wajen gidan, sosai gidan ya burge Ummy dan nesa ba kusa ba yafi nasu Mami tsaruwa. Da daddare Bilal ya iso dan ya shaida ma Abba zai taho daga baya, d'akinsa na daga chan bq shi kad'ai. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Ummy najin dad'in zaman gidan sosai, kullum sai sunyi waya da Jamal fiye da sau biyar, yakan fad'a mata yanda yayi kewanta tare da jadada mata daya gama abinda yake zai taho. Cikin 'yan kwanaki Ummy ta ware ta zama 'yar gida sosai, idan ba ka sani ba bazaka tab'a cewa ba Ammi ta haifi Ummy ba ganin yanda take kula da ita kamar 'yarta. *Bayan Wata Biyu* Cikin Ummy ya shiga wata na hud'u, ya d'an fito ya mata kyau sosai, ta k'ara murjewa fatarta tayi kyau har d'an kiba tayi na hutu. Suna zaune a garden d'in gidan itada Areefah suna kallan wani indian Film a system d'in Areefah wayan Ummy yayi k'ara, ganin Jamal yasa ta d'auka cikin shagwab'a tace "Hello Kaki kazo koh? Kullum sai kace zakazo kak'i zuwa" Daga chan b'angaren Yace "Nafiki k'osawa nazo Baby kodan naji d'umin jikin matata na kuma gaisa da baby na" Ta d'anyi murmushi mai sauti yace "Kinsan meh" Ta girgiza kai sannan tace "Aa" Yace "Ki jira zuwana gobe insha Allah, and i will suprise uh tomorrow" Tad'an tura baki "Kullum ba haka kake cewa ba anma kaki zuwa" Ya d'anyi murmushi "Wallahi dagaske nake" Bata jira mai zaice ba ta kashe kiran cike da murna "Gobe Ya Jamal zaizo" Areefah tace "Dagaske" Ta gyad'a mata kai cike da farinciki. Gaba d'aya farinciki ya lullub'e Ummyn kasa kallan tayi haka suka tattara suka koma ciki. Da daddare Jamal ya kira Ammi ya shida mata zuwansa gobe, Farinciki wajan Ammi ba'a magana. Ranar kasa bacci Ummy tayi saboda farinciki, sai bacci b'arawo ya saceta. Washe gari ko da wuri Ammi ta tashesu dan su soma shirye shirye dan ya shaida masa da bak'i yake. Nan fa aka soma girki kala kala, a sauke wanchan a d'aura wanchan. K'arfe D'aya da rabi na rana aka wangale gate d'in gidan, daga d'akinta ta d'aga labule tana kallan motar data shigo, Areefah ta fita dasauri ta k'arasa wajan motan, Areef ya fito daga motan, sannan Jamal shima ya fito, batasan sanda ta sauke wani lallausan murmushi bah. K'ofar baya ya bud'e ta fito tana d'an murmushi, Ummy ta zaro ido kamar zasu fad'o tana kallan Windown. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 92 K'ofar baya ya bud'e ta fito tana d'an murmushi, Ummy ta zaro ido kamar zasu fad'o tana kallan Windown, K'ara mutsu tsuke idon tayi dan ta tabbatar da abinda take gani. Ganin Maman ce dai dagaske yasa ta ruga a guje ta fito daga d'akin, a k'ofar Falo sukayi kicibus ta fad'a jikinta tana dariyar farinciki. Mama ta soma tureta ganin su Ammi a wajan itako sai k'ara k'ankameta take tana cigaba da dariya. Dakyar ta samu ta saketa sai a lokacin ta lura da mutanen dake falon tad'an sadda kai k'asa, Ammi tayi dariya tana cewa "Iyeh Jaleelah anga Mama" Ta sake duk'ar dakai k'asa tana Murmushi, sannu da zuwa Ammi tama Maman suka wuce zuwa d'akinta. Gogan kuwa tunda ya shigo ya kafe Wife d'in nasa da ido ko k'iftawa bayayi, ta d'ago suka had'a ido tayi saurin barin wajan tana dariya. Ya bita dasauri tana shiga d'akin ya shigo shima, kallanta ya tsaya yi daga sama har k'asa dan sosai tamasa kyau ga cikinta daya d'an fito yayi d'as a jikinta. Ganin ya nufota yasa tayi hanyan toilet yayi saurin rik'o hannunta ya janyota ta fad'a jikinsa "Ina zakije, Wife kekoh? Bakiyi missing d'ina ba koh" Ta tura baki gaba taba d'an doka k'afa yayi saurin rik'ota "No tho I'm sorry karki wahalar min da kanki da babyna" Ya sake matseta ya zira hannunsa a riganta yana shafa cikinta a hankali, lumshe ido tayi tana d'an murmushi bata ankara ba taji ya had'e bakinsu waje d'aya. Dukan k'ofan da ake ne ya dakatar dashi daga abinda yakeyi ya juya yana kallan k'ofar da idanunsa da suka rine "Wanene?" Muryan Areefah sukaji tana cewa "Ammi tace ka fito kuci abinci" Yad'an sassauta rik'on dayama Ummy tare da sake kai maka peck a kumatu "I so much miss uh, sai mun had'u anjima" Ta tura baki yad'anyi dariya ya shafa bakin ya fita yana waiwayenta. A k'ofa ya samu Areefahn tayi masa jagora zuwa falon Abba, nan ya samu an baje masa abinci kala kala, Areefah tayi serving d'insu shida Areef Jama sai santi yake Areefah nata dariya. Abba ya tambaya take shaida masa yayi tafiya shida Bilal. Tarba mai kyau Mama ta samu daga wajan Ammi har tana mamakin irin kirkinsu. Kunya ne ya hana Ummy zuwa gaida Maman saida Ammi tazo da kanta tasa taje ta gaisheta. D'akin Ammi ta bar musu dan su gana, Ummy ta tsugunna ta gaida Maman ta amsa da fara'a tana kallanta da sha'awa. "Ya jikin naki" Ta amsa da sauk'i tana d'an duk'ar dakai. Mama tace "Ina mai farinciki sosai da Allah ya baki miji na gari Ummy, ya kuma baki iyayen miji masu sanki." Maman ta cigaba dacewa "Sai dai har yau bazan fasa fad'a miki kiyi musu biyaiya da kuma kyautata musu." "Insha Allahu Mama zanyi k'okarin haka" Ammi tayi knocking ta shigo tana cewa "Maman Jaleelah ko a k'aro miki abincin neh" Da fara'a Mama tace "Aa Hajiya Alhamdulillah na k'oshi wallahi gama wannan ban cinye bah" Ammi ta fita daga d'akin tana murmushi. Yinin ranan Mama na tare da Ummynta sunata hira na yaushe gamo. Ummy da Jamal basu samu daman keb'ewa ba shiko yana chan d'akinsa da aka basa yana zuba ido yaga ta inda Wife d'in nasa zata bullo. Da daddare Abbah ya dawo, Yayi farinciki sosai da ganin 'yayan nasa, bayan yaci abinci ya natsa Ammi ta rako Mama tazo ta gaishe shi, sunyi gaisuwa na mutunci Mama ta soma musu godiya akan d'awainiyar da sukeyi da ita da kuma kulan da suke bama Ummy. Ammi tace "Haba Maman Jaleelah babu godiya tsakaninmu ai, Wallahi muna jin dad'in zama da Ummy. Muna jinjina muku da irin tarbiyar da kuka bata. Mune da godiya" Mama ta sadda kai k'asa tana murmushi. Abba yace "Gobe in Allah ya kaimu Jamal zai kaiki sabon gidan daya siyan miki dan gwara ki zauna kusa dasu karkiyi nisa" Ido Mama ta ware tana kallan Ammi da mamaki, Ammi tayi dan murmushi, Mama ta soma godiya Ammi tace "D'anki ne ya siya miki bamu bah" Har hawaye Mama tayi na farinciki. Ammi ta rakata zuwa d'akin da aka sauketa nan suka baje sunata hira kamar wad'anda suka dad'e dayin sabo. K'arfe Tara da rabi Ummy ta fito wanka, kintsa kanta tayi da mayuka masu k'amshi da turaruka. Night wears masu kyau ta saka ta kwanta tare da rungume Pillow so take taje wajan Jamal anma kunyan sa dana su Ammi ya hanata. Kira ne ya shigo wayanta da d'auko tare da dubawa, ganin Jamal yasa ta d'auka ta kara a kunne "Wife bakya tausayina koh?" A shagwab'e tace "Menayi" "I need uh right now dan Allah kizo karna mutu" Yanda yayi maganan tausayinsa ya kamata tad'an sassauta murya tace "Nifa kunyarsu Ammi nakeji" "Plsss wife ina jira kinji" Bai jira mai zatace ba ya kashe kiran Shiru tayi tana tunanin yanda zataje ta samesa har ga Allah tausayinsa take sai dai kunyarsu Ammi bazai bari taje bah. Da haka bacci mai ya d'auketa. Cikin bacci tayi ana shafata ta mik'e dasauri a razane, duhu ta gani a d'akin, cikin wani irin murya yace "Shhhh! Ni neh, Pls Wife ki tausaya min" Yanda ya rik'eta yasa ta soma kokarin kwacewa "Ni kunyansu Ammi nakeji dan Allah ka tafi d'akinka kada tazo ta samemu" Bai ce mata komai bah ya kwantar da ita kan gadon tare da soma mata wasu salo wanda yasa hankalinta ya d'auke. (Asubah ta gari Amaryan Jamal" Kuka ta dunga masa gaf da asubah kan ya koma d'akinsa dakyar ya kyalleta ya fita ransa a d'an bace wanda ta lura da hakan. Washe gari bata fito da wuri ba sai k'arfe Tara na safe, da Ammi ta soma had'uwa ta durk'usa har k'asa ta gaidata, ta amsa da fara'a tana cewa "Kije Mama na d'akinta" To tace ta mik'e ta shiga d'akin, Itada Bilal ta da Jamal ta samesu suna hira, ta k'arasa a sanyaye ta zauna kusada Maman ta gaisheta sannan ta gaida Bilal kanta k'asa, ya amsa shima yana sunne kai dan gaba d'ayansu kunyan juna suke yanzu. Jamal ta gayar saida ya harareta sannan ya amsa tad'anyi murmushi kawai. A bakin Areefah take jin Maganan Gidan da Jamal yasai ma Mama, da farinciki ta shiga d'akinsa lokacin ya fito wanka yana saka kaya, saurin juya baya tayi tasa hannayenta ta rufe fuskanta tana dariya. Shima murmushi yayi sannan yad'an d'aure fuska "Kina buk'atan wani abu neh" Cikin sanyin murya tace "Mungode Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i, ya kuma rabaka da iyayenka Lafiya, ya kareka sa sharin mak'iya" Sosai yaji dad'in addu'anta ya amsa a hankali yanda bazataji bah sannan yace "Da akayi meh" Tad'an waiwaya ta kallesa tace "Gidan da aka saima Mama" K'ugu ya rik'e yana murgud'a mata baki, ta saki dariya "Ina ruwanki toh, ai mamana masai mawa ba naki bah" Ta ruga ta fad'a jikinsa tare da kaimai kiss a kumatunsa "Thank uh so much Noorul Qalb" Ya d'agota da mamaki "Repeat what u said Plsss Wife" Murmushi ta masa ta sake rungumesa tana dariya "I love uh so much Noorul Qalb" "I love uh more" yace a hankali yana k'ara rungumeta, ganin take takensa yasa ta kwace da k'arfi tayi hanyan k'ofa "Ni koh" Tamai gwallo "Eh d'in" Binta yayi ta fita da gudu, da Ammi tayi kicibus tayi saurin b'oyewa a bayanta. "Ammi kingansa koh" Ammi ta had'e fuska "Jamaludeen ka kiyayeni fah, kazo kenan zaka daman min 'ya. Baka ganin abinda take tare dashi" Ya sosa k'eya, Ummy ta masa gwalo yayi kwafa ya koma d'aki yana gungunai. Summ summ tabar wajan ta shiga kicin wajan Areefah. Bayan la'asar gari yayi sanyi sukaje ganin gidan Ammi, k'aton gida ne mai kyan gaske da tsaruwa, sosai Ummy tayi santin gidan. Suna fitowa suka shiga na kusa dana Ummyn, A nan yake shaida musu nan ne zasu zauna. Gidan shima yayi kyau matuk'a, bakin Ummy yak'i rufuwa saboda farinciki. Ammi da Areefah suka tayasu Mama yi masa godiya ya kauda kai gefe yana murmushi tare da girgiza kai. Da farinciki duka suka koma gida, ba yanda baiyi Ummy taje d'akinsa ba tak'i. Haka ya hak'ura ya kyalleta anma wannan karan yayi fushi sosai. Wuraren k'arfe Tara da rabi na dare ya dawo daga yawo yaga wad'an nan manyan mutanen masu sanye da bak'aken kaya a k'ofar gidan, parking yayi bai fitoba yana nan zaune cikin mota Abba ya fito shida Bilal suka shishiga motan suka fita da gudu daga layin sauran mutanen na mara masa baya a wata hilux. Ummy Abduol✍🏻 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤 *JAMALUDEEN* 🖤🖤🖤🖤 🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤 By *Ummy Abduol* Dedicated to My *Late Siblings* *Fcbuk Page* https://facebook.com/Ummy-Abduol-Novels-1033022590196192/ Page 93 🔚 Parking yayi bai fitoba yana nan zaune cikin mota Abba ya fito shida Bilal suka shishiga Motan suka fita da dugu daga layin sauran mutanen na mara masa naya a wata helux. Shiru yayi yana tunanin Abinda ke fita da Abba da daddare, ya kunna motan yayi horn mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga. Ammi ya samu a falo itada Mama dasu Ummy suna hira, a hankali ya k'arasa ya zauna tare da gaidasu suka amsa da fara'a. Su Ummy suka mai sannu da zuwa ya amsa yana satan kallan Ummyn. Ammi tace "Yauwa Jamaludeen dama Maman Jaleelah ce tace mai zai hana Umman Bilal ta dawo gidan da take su zauna tare" Mama tace "Gidan ne yamin k'ato kaga idan muna jin motsin juna yafi dad'i tunda itama ba miji gareta ba kuma Bilal d'in na nan" Ya d'ago fuskansa d'auke da murmushi yace "Babu damuwa Mama wannan shawaran yayi" Mama ta sake masa godiya ya mik'e ya shiga d'akinsa. Gaba d'aya jikinsa ne yayi sanyi ala ala yake su dawo dan yau ya k'uduri niyan tambayan Abban inda suke zuwa. Kwanciya yayi kan gado a rigingine yana kallan ceiling ya dad'e a haka yaji knocking a k'ofar d'akin, bada izini yayi a shigo, Da sallama Ummyn ta shigo hannunta d'auke da k'aton tray ta k'araso ta aje k'asa sai binta da ido yake. Tad'an kalleshi tace "Yau naganka wani iri lafiya kuwa" Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Lafiya lau kawai dai na gaji neh" Ta duk'a ta soma zuba masa abincin, tana cikin zubawa yace "Barshi haka" Ta d'an d'ago ta zuba masa narkakun idanunta "D'an kad'an fa na zuba ai bazai isheka bah" Ya gyad'a mata kai kawai batare da yace komai bah. Ganin yanayin sa yasa ta mik'e ta xauna kusa dashi tare da kamo hannunsa "Ya Jamal ko bakada Lafiya neh" Yad'anyi dariyan k'arfin hali "Lafiya na lau Wife kawai gajiya neh" Plate d'in ta d'auka ta diba a spoon takai bakinsa, ya kauda kai tare da yatsine fuska "Plsss Ya Jamal" Yanda tayi maganan a shagwab'e yasa ya juyo ya d'an bude baki tasa masa. Da kanta ta basa yanata mata shagwab'a tana dariya har yad'anci dayawa. Yana gamawa ta tattara kayan ta aje gefe ta shiga toilet ta had'a masa ruwan wanka. Nan ma saida sukasha daru dan tsayawa yayi kai da fata dole ita zatai masa. Guduwa tayi niyan yi yayi saurin janyota ta fad'a jikinsa ya sakar musu shower. Soyaiya mai tsafta ya nuna mata wajan wankan sai susune kai take kamar *Ummu Manal* har suka fito. Da kansa ya shafa mata mai tanata turjewa idanunta a lumshe. Wajan shafa man ne kid'a ya soma chanzawa ina ganin haka nayi waje abuna. Su Abba basu dawo gidan ba sai k'arfe shabiyu da rabi, lokacin gidan tsit da alama duk mutanen gidan sunyi bacci banda Jamal dake kwance rungume da Ummynsa dake bacci hankali kwance. Jin k'aran gate yasa ya zame daga jikinta ya d'an d'aga labule yana lek'awa. Bilal ne ya bud'e ma Abban mota ya fito sannan ya wuce side d'insa shi kuma Abban ya shigo cikin Falon gidan. Jiki na rawa yad'au jallabiya yasa ya fito daga d'akin, ga mamakinsa Ammi ya gani a falon tana karb'an babban rigan daya cire, Yana juyowa suka had'a ido da Abban, Ammi itama ta juyo suna kallan kallo, Kamar wanda k'wai ya fashewa a ciki ya k'arasa indasu Abban suke ya sadda kai yace "Sannu da zuwa Abba, Ab..." Yayi saurin d'aga masa hannu yace "Nasan me zaka tambayeni" Ya kama hannunsa suka zauna a falon, itama Ammi ta zauna. Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Kamar yanda na baka labarin abinda ya faru damu shekarun baya har hakan yayi sanadiyar b'atanka. A lokacin da Mahaifiyarka ta tafi dakai ni kuma suka b'alle k'ofan suka kamani sukamin duka a nan suke shaida min wani Alhaji Dauda ne ya aikosu su kasheni. Alhaji Dauda Abokin kasuwanci na neh, tare muka shiga harkan kasuwanci dashi, sanda muka fara Allah ya soma bud'amin sosai sai ya soma min zagon k'asa dajin haushina. Shima a lokacin yana samu saidai ba kamar ni bah.. Tun sanda na bud'e shagon zinari tsanar dayake min ya yawaita, har takaiga ko na gaishe shi baya amsawa." "Tun a wannan lokacin na gane ba masoyina baneh. Mutanen daya aiko suka harbeni na suma, sai sukayi tunanin na mutu ne suka tafi. Alumma annabi suka taimakeni aka kaini asibiti. Kwana hud'u da faruwan hakan mahaifiyarka ta dawo, babu wanda na fad'ama abinda suka shaida min sai matata. Ita ta cigaba da kula dani a asibiti saida na shafe wata hud'u sannan aka sallameni" "Kwana na Uku a gida a ranar na hud'u na fita kasuwa, abin mamaki duk shagunana wasu sabbin ma'aikata na samu nan na soma fad'a akan waya basu izinin shiga shagona, a nan sukama Alhaji Dauda waya sai gashi yazo yake shaida min Shaguna mallakinsa ne ba nawaba. Nayi mamaki sosai na dangana ga Office d'in 'yan sanda, bayan nakai k'ara aka umarci wasu 'yan sanda su taho dashi. Ina nan zaune suka zo dashi aka d'au statement d'inmu akace naje sai gobe na dawo. Washe gari dana koma abin mamaki 'yan sandan suka nuna basu sanni bah haka zalika basu san zancen bah har suna k'okarin kulleni" Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa "370million shine darajan kayan shagona, Ba takaicin rashin kud'in nake bah, takaici na d'aya yanda ya hak'ikance akan rashin gaskiya. A lokacin babu Ofishin 'yan sandan da banje bah anma duk magana d'aya ce. Haka na had'a sauran kud'in danake dashi muka haura k'asar Masar da Mahaifiyarka, a chan na cigaba da kasuwanci cikin ikon Allah abubuwa nata hab'aka" "Bayan dawowa na naji labarin ta dalilin dukiyata Alhaji Dauda ya zama babban d'an siyasa wanda a halin yanzu yake da babban matsayi a siyasar da muke ciki yanzu, shine nad'au alwashin saina d'au fansan abinda yayi min. Anma kash babu wani jami'in tsaron daya mara mani baya sai wani guda d'aya dake cikin garin kaduna, shi kuma bana samunshi sai dare lokacin ya dawo aiki. Duk sanda kaga nayi fitar dare Kaduna nake zuwa duba D'an sandan sannan kuma mu tattauna akan abinyi, ta bakinsa na samu labarin har yanzu Alhaji Dauda bai daddara ba yana cigaba da kwacen dukiyar mutane batare da ance uffan ba saboda d'aurin gindin dayake dashi a gwamnati" Jamal ya sauke ajiyar zuciya cike da gamsuwa da maganganun Abban nasa, yace "Abba mai zai hana nayi ma Mifzal magana, nasan insha Allahu za'a dace, kuma kaga IG k'anin Abbansa neh" Ammi tace "Jamaludeen kenan babu wani babban d'an sandan da ba'ayi masa magana bah" Abba yace "No ki barsa ya jaraba wata k'ila a dace" Ran Jamal ya sosu sosai da jin labarin da Abban ya bayar "Insha Allahu Ammi za'a dace, In Allah ya yarda K'arshen Alhaji Dauda yazo kuma wallahi bai isa yaci kud'in Abba bah sai ya amayo su" Abba ya mik'e yana bubbuga kafad'ar Jamal "Allah ya bada sa'a my Son, go and have some rest" Saida safe ya musu ya koma d'akinsa cike da tunani kala kala. Washe gari da asubah Ummy ta sulale ta koma d'akinta, Shima bai tashi da wuri bah sai k'arfe goma, Koda ya fito Ya samu su Ammi da Mama zasu Kasuwa siyaiyar kayan da Maman zata buk'ata a sabon gidan nata. Gaidasu yayi tare da musu sallama suka fita. A ranar ya nemi izinin Abba na zuwa Zaria don su gama da Mifzal, ba musu Abba ya amince masa da Bilal suka tafi, sun samesa sun masa bayani, ba tare da b'ata lokaci bah ya kira k'anin Abbansa ya masa bayanin abinda ke faruwa. Nan ya shaida musu su had'u a Abuja ranar Sati, sunmasa godiya sosai basu dawowa ba sai washe gari, a ranar suka d'auko Umman Bilal basu d'auko Bahar ba dan yana karatu a ABU kuma yana tsaka da karatu. Ranar da suka iso Mama da Umman suka tare a sabon gidansu, Godiya wajan Umma da Bilal ba'a magana dan sunyi matuk'ar farinciki sosai. Kwana biyu tsakani Mifzal ya iso a ranar suka samu ganawa da IG gaba d'ayansu harda Abba, ba'a dau lokaci ba aka fara Bincike kan maganan. Cikin satin Ummy ta tare a nata gidan Bakin Jamal har kunne. Soyayya Jamal ke nunama Ummy nasa kamar ba gobe, yana tattalin abinsa sam bayansan abinda zai tab'a matar tasa. Kyautatawa babu irin wanda Jamal bayama Sarakan masa. *Bayan Wata Biyar* Cikin Ummy yayi girma sosai yakai watan haihuwa, kulawa babu irin wanda bata samu daga wajan Mijinta da surukan nata harda su Mama. Dole Ammi tasa Jamal ya d'aukota ta dawo kusada Ita, cikin yayi nauyi sosai har anata tsammanin ko 'yan biyu ne anma duk scanning d'in da'akai d'aya yake nunawa. Hakan yasa kullum da yanma Jamal ke sata gaba sai sun fita road work duk bayan la'asar. Yauma kamar kullum sun fito suna tafiya a hankali sai sannu yake mata tanata tura baki, kamar daga sama taji an kira sunanta "Ummy!" Juyawa tayi dasauri wa zata gani in ba Laurat bah, da mamaki Ummy tace "Laurat kece" Da murmushi ta k'araso inda suke tace "Ni ce Ummy ashe da rabon zamu sake had'uwa" Ta gaida Jamal ya amsa fuska a sake dan ya ganeta, tace "Ina aiki ne a nan bayan layin, Allah sarki tun bayan barina Gidan Mami bamu sake had'uwa bah" Jamal yace "Yanzu ku muje mu k'arasa gida sai kuyi Hiran dakyau" Ba musu Laurat tabisu har gida, Ammi ta amsheta dakyau suka k'ulle a d'aki sunata hira. A nan Laurat ke shaida mata tasan duk abinda ke faruwa a gidan ta bakin wani Mai gadi dake unguwar d'an anguwansu ne dake chan kaduna. Ta sauke ajiyar zuciya tace "Gaskiya Mami batada imani, zataga K'arshenta insha Allahu" Ummy tayi murmushi dai batace komai bah, Laurat tace "Wai meya faru da Mabrookah dan kwanaki na ganta a wani guest house a nan garin, nifah yanda na ganta kamar karuwanci take" "Karuwanci?" Cewar Ummy tana zare ido "Wallahi kuwa, bakiga ma kayan jikinta bah" "Innalillahi wa inna ilaihi raj'iun" cewar Ummy tana dafe da goshinta, ta cigaba da cewa "Gaskiya Mabrookah ta b'ata wayonta, Allah ya kyauta" Laurat ta amsa da Ameen suka chanza hira, tad'an dad'e a gidan sannan ta tafi bayan tama Ummy kwatancen Gidan da take. Bayan kwanaki Akayi shar'iar Alhaji Dauda da Abba kuma Alhamdulillahi shari'a ta tafi yanda akeso dan su Abba sunyi nasara. Bayan fitowa daga shar'iar wanda Ram ya kasance Lawyern Abba, nan suka samu chinchirindon mutane masu son abi musu hak'insu wajan Alhajin Daudan, nan aka sanar dasu kowa za'a bashi hak'insa sukayi ta godiya. Kwana biyu tsakani Akama Mifzal k'arin girma tare da transfer ya koma Abuja, Ram shima ya samu wani contract da wani Company inda ya kasance Lawyern Companyn duk dai a nan Abujan. Ranar wata talata Ummy ta tashi da ciwon nak'uda, cikin ikon Allah ana isa asibiti ta sub'uto santalelen d'a namiji mai kamada Jamal sak. Murna wajan Jamal ba'a magana, su Abba sunyi Farinciki sosai Bakuna yak'i rufuwa. Ranar suna Yaro yaci sunan Abba Mijin Mami wato *Suraj* anma ana kiransa da *Alwaz* anyi bidiri sosai ranar suna harda su Laurat duk sun zo a nan Ram ya ganta ba wani b'ata lokaci ya nuna mata buk'atarsa bata tsaya wani jan aji ba ta amince masa. ```Bayan shekara D'aya abubuwan cigaba da alheri dayawa sun faru, Alwaz yayi wayo sosai har ya soma tafiya, Ummy tana shekarantanta na farko a Turkish Nile University, Ta k'ara murjewa tayi kyau kamar ba itaba. Kallo d'aya zaka mata ka gane tanada shigan ciki saboda yanda tayi fari da ta cicciko. A cikin watan Jamal ya samu aiki a k'asar Germany tare da sabon Companyn Versace. Murna wajan Ummy ba'a magana su Abba sunyi farinciki tare da sa Albarka.``` A cikin watan akasa Ranar Mifzal da Areefah wata Uku, Lokacin saura Wata biyu bikin Ramadhan da Laurat wanda za'ayi a tudun wadan kaduna. Tun a makaranta take ta jin kamar zazzab'i zai rufeta, dakyar ta iya attending lectures d'in ranar, tana fitowa ta kira Jamal a waya, ba'adau lokaci bah ya iso makarantar duk hankalinsa a tashe, hand bag d'inta ya amsa tare da rik'o hannunta ya sakata a motan yanata mata sannu. Sun d'au hanya suka hango chinchirindon jama'a a tsakiyar titi, parking yayi ya fito wani mutumi ya gani yana baro wajan, ya masa sallama tare da tambayansa abinda ke faruwa, mutumin yace "Wata 'yar shaye shaye ce ta shigo hanya mota ta bigeta wallahi, tama mutu. Kai irin wannan rayuwa ta 'yayan yanzu Allah ya sawake" Jamal ya masa godiya harya bud'e kofan mota ya hango ambulance d'in road safety sun k'araso wajan, nan aka mutane suka mamatsa aka basu waje, kamar a mafarki ya Hango Mabrookah kwance a wajan, sake mutsutsuke idanunsa yayi dan ya tabbatar da abinda ya gani, bai san sanda ya saki k'ofan motan ya k'arasa wajan bah, har an d'auketa an sakata a mota. Sai bin motan yake da kallo gabansa na fad'uwa. Yana nan tsaye aka wuce da gawanta, hawaye suka gangaro masa yayi maza yasa hannu ya share. Koda ya shiga motan bai fad'ama Ummyn wacece bah, yadai ce wata aka bige. Da damuwa suka isa gida har lokacin yana tausayawa Mabrookahn da tunanin Makomanta. Bayan wata d'aya Jamal yayi reporting a wajan aikinsa achan Germany, ba b'ata lokaci ya soma aiki dasu kuma yana jin dad'in aikin saidai abu d'aya dake damunsa rashin iyalinsa kusa dashi. Haka itama Ummy tun bayan tafiyarsa ta dawo gidan Ammi da zama saboda kewar mijinta, tare suke zuwa makaranta da Areefah, Alwaz shekaransa d'aya da wata d'aya yayi wayo sosai kamar d'an shekara d'aya da rabi. Lokaci guda yak'i nono ya yaye kansa, gashi bashi da k'iuya hakan yasa ya koma Wajan Ammi tana kula da jikan nata. _A nan sai ince Allah ya k'arama wannan Family zaman lafiya da san juna Ameen_ *ALHAMDULILLAH* A nan na kawo k'arshen Littafina mai suna _JAMALUDEEN_ Kurakuren danayi Allah ya yafeni, abinda na fad'a daidai Allah ya bamu ladan gaba d'aya. Darusan dake ciki Allah ya bamu ikon d'auka Ameen. ```Na yanke labarin neh saboda Zuwan watan Ramadhan, dan banaso mukai har bayan sallah bamu gama bah. Ina fatan zakumin Afuwa``` Ina godiya ga Masoyana gaba d'aya, Allah ya barmu tare. Ina sanku kamar yanda kuke sona. Sai kunjini a cigaban littafina mai suna *GA ZARAH GA WATA* bayan sallah insha Allah. Inayi ma kowa fatan alheri, Allah yasa muyi azumi Lafiya ya kuma bamu lada da falallan dake cikinta Ameen. RAMADHAN KAREEM In Advance Ummy Abduol✍🏻